Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

JALALUDEEN Soyayya Tsakanin Girman Kai da Kaddaraby AYUSHER MOHD

Author :  AYUSHER MOHD Category :  African Stories & Novels

Chapter   37 / 37

108K to 108.9K   out of 108.9K words

za'ai ko me?"
Jalal ya rungumeta yace " bakomai sai musai wani."
Ta mik'e tace naki wayan.


Washe gari kuwa sai da Jalal ya matsa aka sallameshi duk lokacin abinci ana aikowa daga gidan su Dad.

Ammar kam hotel ya koma kawai ya tare, su Dad basu sani ba ashe yayi booking d'in jirgi, washe gari da safe yazo ya sanar da Dad zai koma England amma ba dadewa zaiyi ba, ba musu Dad ya amince saboda yasan halin da Ammar din ke ciki.




Bayan Jalal ya warke da kanshi ya kaita gun Abdul, nan ya nemi yafiyarta tare da alkawarin canza halayensa, sunyi ziyara har garin iyayenta nan sukaje taga 'yan uwanta.


Jalal ya kama gida a Abuja inda suka zauna shida Seemah, kulawa kaunar dake tsakaninsu ta wuce duk yanda zan kwatanta muku, Yau yakama wata tara kenan da auren su, duk karshen mako yake tafiya kaduna Seemah ita ta tsara mai hakan saboda tana ganin yanda yake rashin damuwa da Zainab hakan bazai mata dadi ba, shikanshi yanzu yana daidai kokarin kwatanta adalci a tsakaninsu, sam Zainab bata jin haushin Seemah ita gani take ma auren da Jalal d'in yai shine sanadiyyar kulata da Jalal yake, Seema na d'auke da tsohon ciki, itakuma Zainab laulayi takeyi.


Jalal ya shigo gidan ganin yanata sallama ba'a amsa ba, a rude ya shigo gidan ya fara neman inda Seemah take, har daki ya shiga batanan, d'akinshi ya nufa, yana budewa yaga ta fesheshi da wani farin abu, baya yai yana mamaki, nan ta matsamai ya kalli d'akin, candle ne kanana an jera shi a kasa anyi kwalliyar Iā™”U dashi kwaliyar tayi kyau, ya kalleta cikin mamaki, kayan bacci ne a jikinta shara shara ya sakar mata wani sansanyar murmushi tareda karasowa ya rungumeta, murmushi itama tai tace " My Deen kardai a manta da babynmu."
Sassauta rikon yai sannan ya d'ago a hankali ya kai bakinshi cikin nata, wani irin salon kauna sukema junansu, jitai kafarta naneman kasa d'aukanta, Jalal ya riko kugunta nan suka cigaba da aikama juna sakwanni, a hankali Jalal ya jata kan gado sannan ya tare neck tie d'insa ya cigaba da sumbatarta, cikin salo a kuma hankali ya bakinshi na nata ya zare mata 'yar rigar dake jikinta, itama mab'allin rigarsa ta dinga cirewa har ta cire su duka, sumbatar kirjinsa ta fara nan fa suka shiga cikin wani yanayi wanda su kadai sukasan halin da suka shiga.


Sai da suka gama sannan ta kwanta akan kirjinsa, shikuma yana shafa kanta, yace " Meemah wannan gyaran fa? Decoration d'in yayi kyau, kara kwanciya tai a kirjinsa tace " a internet na dubo yanda akeyi."
Yai ajiyar zuciya yace " Meemah in miki wani alkawari?" Ta d'aga kai, tare da juya fuskarta saitinshi, yace " indai mace kika haifa sunan Mahaifiyarki zamusa mata Fatima, in kuma namiji ne to sunan Ammar ko Dad sai kizab'a a ciki."

Murmushi tai tace" nagode sosai Deen, amma ya maganar Ya Ammar?"
Yace " yace next week zai dawo."

Tai ajiyar zuciya tace " kaii nayi missing d'in yaya."

Mikewa yai ya sunkuceta sukai toilet, kafin suyi wanka sai daya wanke mata kai da kanshi, dan tace bata iya sunkuyawa, nan sukai wanka suka fito a tare, shi ya shafa mata mai sannan itama ta shafa mai tana shafamai tana tambayar yasu Ya Zainab?" Yace suna lafiya.......





Ammar ya zaune a cikin jirgi yana karanta jarida watace a zaune a kusa dashi ta zake sai bacci take, haushi ya kama Ammar ya juya kansa jikin window, tana gama baccin ta mik'e tare da yin mika, ta kalli Ammar tace " dan Allah awa nawa mukai?"
Kallanta yai yace " ke agoggonki tsayawa yai?"
Agoggon hannunta ta kalla ashe da agoggo a hannunta da sauri ta juya fuskarta, yai murmushi sannan ya juya, mai service ce ta karaso ta kallesu tace " mai kukeso a kawo muku? Tea ko coffee? "
A tare sukace " Coffee."
Kallan juna sukai sai sukai dariya, matar tai dariya itama tace " da alama ku couples ne kunyi matching sosai."
A tare suka kara cewa " a'a."
Tai sake dariya sannan ta tafi, tana tafiya Ammar ya kalleta kadan kyakyawa ce sosai, juyawa yai jiyai tace " A Abuja kake?"
Yace " eh kefa?"
Tace nima...........
Murmushi sukama juna a tare.





Zahra ma ankusa haihuwa, Dad da Abban Jalal aminta ta dawo sosai, yanzu Abban Jalal yananan yana kasuwancinsa a babban shagon da Jalal ya bud'e mai.

Zaid ma saura wata d'aya ya auri Zaheeda wacce ta warke sumul, har malami Jalal ya d'aukar mata yana koya mata karatu.

Abdul kuma an sakeshi yana zaune a dan karamin gidansa shida matar sa 'yar uwar Sagir, Ya canza kamar bashi ba.


Jalal da Seemah masha Allah kauna kam suna san junansu sosai........nace To Allah yasauketa lafiya


Nima nace mu had'u a wani littafin nawa in Allah ya yarda.......





*GODIYA TA MUSAMMAN GAREKU*
*Yan Group d'ina*
*THE QUEEN BEE*
*AYUSHER FAN CLUB*
Sannan ina godiya gareku 'yan
*NAGARTA*
BEELY BADARU GROUP
'YAN SAUYI NA KCK
EXCELLENT HAUSA WRITERS
MU SAN JUNA
TALENTED HAUSA WRITERS
MARYAM MAI DALA
HAUSA NOVEL
MY BLOG FANS
HAUSA NOVELLA
BE A LADY WITH FASHION
Da kuma ragowar group d'in da duk nake ciki ina godiya gareku.





Ina alfahari daku
*MY BEELY BADARU*
*SIS PHARTY*
ASY KHALEEL
MAMAN SHAHEEDA
MUNAY
SADNAS
AUNTY KYADY
FATTY



Ahh gaisuwa gareki babbar Aminiya *AISHA M.UMAR....*
*NI AYUSHER MUHD ke muku fatan alkairi*😘😘😘😘

37 / 37