Author : Mai Farin rubutu Category : African Stories & Novels
akai ma fyade kamar ta, ganin hakan yasa mutumen ya roki a dorasu akan babur, a fitar da su sauran da suke iya tafiya a kafa kuma a korasu a kasa. Wadanda aka kora a kasa suna tafe suna jin tsoro saboda daukin ba dadin da ake da babbar daba, daman can sun fi kowa dauka da zafi, karama daba kudin fansarsu ba su da tsada kuma ba da taurin kai kamar babbar daba, kasancewar karamar daba matasa ne masu tasowa wasu ma duk yara ne, babbar daba kuma manya ne wadanda suka dade a cikin harkar.
Su Aminatu sun riga isa kusan da bakin dajin saboda an dauke su a babur, sai dai zubesu akai a kasa suka zauna a gurin har sai da na kasan suka karaso sannan aka hadasu aka nuna musu hanya. Sauran wadanda sukai musu rakiya kuma suka juya suka koma ana kusan kiran sallah asuba suka fiton daga dajin, Aminatu na tafiya daker tana hawaye, idan ta gaji da tafiyar sai ta zauna a kasa ta yi rarrafe idan ta gaji sai ta unkura ta mike tsaye ta fara tafiya.. Da haka har suka iso bakin gari a inda motocin sojojin suke. Da farko sun tsorata duk kuwa da kasancewar an fada musu akwai sojoji a gaba, sai dai ganin a cikin barayin ma akwai masu uniform din sai ya saka wasu suka tsorata, sai dai kana ganin wadandan sojojin kasan zaratan sojoji ne ba kamar yan bindigar ba. Karasowa sukai suka dauki mutanen a mota, Aminatu kuma da ire irenta suka daukesu suka saka a motarsu, suka kama hanyar gari da su.
Ko da tara na safe ta yi, labarin nasarar da sojojin suka samu a kokarinsu na kwato mutanen da akai garkuwa da su ta kwarade ko'ina, labarin barin wutar da akai ya shiga lungu da sako na nigeria, ya leka gidan jaridu ya cika social media.
Masu lafiya aka tafi da su inda za a buka fuskarsu ayi ado da su a jaridu, marasa lafiyar kuma aka wuce da su asibiti a sirrance.
A tsakanin iskar dake dajin dana cikin gari zuwa na asibitin da aka wace da su Aminatu ko wane dabam, na dajin na tawaya ne da damuwa da bakinciki, shigowa garin kuma samun iskar yanci ne, sai dai shiga asibiti kuma na fata ne, wata kila ta rayu wata kila kuma rayuwar ta zaba mata mutuwa.
Mutanen da suka zo da gudu suka karbeta a hannun sojan daya dauko ta, sai su ka yi mata kama da wata halittar da taban kasancewar suna cikin farin uniform ne na aikinsu. Lumshe ido tai tana sauraren yadda aka dagata sama aka dorata saman gadon asibiti ana turata.
FARUQ POV.
A gurin mai shagon ya karbi wayarsa, ya saka line sa ya kira number Baturiya ya jita kashe. Hakan ya saka ya kira ta kanwarta sai da ta kusa tsinkewa sannan ta yi picking.
“Hello Raliya ya kike?”
“Lafiya Kalau Ya Faruq”
“Yayarki ta zo?”
“Aa, tana Kano fa”
“Kano?”
Ya maimaita cikin tsananin mamaki.
“Eh Napep ta hau shi ne...”
Ajiyar zuciya ya sauke bayan ya gama sauraren abun da Raliya ta fada masa, sannan ya sauke wayar yana jin babu dadi. Ya sani ba dan komai Baturiya take masa haka ba sai dan talauci, da yana da arziki da bata isa ya mata umarni ta saba ba, daman ai ta fada idan yana da kudi ba zata taba gujewa umarninsa ba, tabbas da yana da arziki da iyayenta sun nemi inda yake sun fada masa halin da matarsa take ciki, sai dai ba su yi hakan ba saboda ba kowa ba ne a idonsu, wannan dalilin ya saka a duk lokacin da ya kai kararta akan abun da take masa sai du bata gaskiya su goyi bayanta. Cire line yayi ya ya mika masa wayar ya juyo ya dawo cikin gida cikin yanayi na rashin dadi ya maida gidan ya rufe.
BATURIYA POV.
Washe gari mutanen gidan suka bata wani tsohon Hijab ta saka ta talkami, Bayan ta karya suka rakota har bakin titi suka tara mata Napep zuwa tashar mota. Su suka biya mata na napep din, tana ta musu godiya, idonta har yanzu be warware daga kukan da tasha ba, babu abun da take ji kamar wayarta, domin samun wata wayar a gareta yanzu abu ne mai matukar wahala a halin da suke ciki, har kara ma a gidansu wata kila mahaifiyarta zata iya taimaka mata da wani abu, yayanta ya cika mata sauran ta siye wata wayar, amman ba daga bangaren Faruq ba kam.
Tun daga yanayin hausarta suka gane yar zamfara, abun ka da kanawa sai dariya suke mata ita kam bata ma bi ta kansu ba gaba daya hankalinta yana kan wayarta data bata yadda zata samu wata wayar kawai take tunani, gashi hanyar samun kudinta ta facebook ne inda take yaudarar maza, yanzu kuma babu wayar yaudara ma.
“Kai Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un”
Ta furta wasu hawayen na cika mata ido.
‘Dan Allah aljanuna idan kuna jina ku taimaka min da wayata ku dauki kudin na bar muku’
Wannan karon a cikin zuciyarta tai maganar hawaye na sauko mata.
“Malama Lafiya dai?”
Wani matashin saurayi dake kusa da ita ya tambaya yana kallonta. Banza tai masa ta ta juya masa fuska, sai yai murmushi ya cigaba da danna wayarsa. Sai da motar ta cika sannan suka kama hanyar Zamfara suna tafe suna addu'a saboda yanayin hanyoyin nigeria kowa ya san yadda tafiya take a yanzu. Sai da tafiya tai nisa sannan aka kira saurayin a waya, Baturiya ta kashe kunne tana sauraren yadda yake amsa wayar a cikin har da amsar da yake fadawa cewar motar haya ya shigo saboda motarsa ta tsaya ya barta a nan Kano.
Baturiya na jin haka sai ta juya ta kalleshi sai a lokacin ma ta lura da shaddar jikinsa babbar shadda ce, haka zalika wayarsa ma.
Tun da suka kama hanyar direban be tsaya ba har suka iso Zamfara.
“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un”
Baturiya ta fada da muryar kasa kasa tana fashewa da sabon kuka. A nan ma kallonta yai ya tambayeta.
“Lafiya...?”
Kai ta girgiza ta share hawayenta ta fada masa abun da ya faru da ita, sai dai ta canja cewar tana da aure, sai ta fada masa cewar mahaifitarta ta aiketa.
“Subhanallahi, ki gode Allah ma be kai ki wata kasar ba”
“Haka yan gidanmu suka ce, ni daman Allah ya sani gidanmu bama hawan Napep duk inda zamu je a mota ake kai mu yanzu ma tsautsayi ne”
Ta fada kamar gaske, kallon lace din dake jikinta yai kamin ya kalli kyakkyawar fuskarta.
“Allah ya tsare gaba”
“Amin”
“Amman miyasa kike kuka?”
“Haba Malam dubi tufafin dake jikina fa? Ban taba kwana a irin gidan dana kwana ba sai jiya, yanzu kuma motar haya na biyo tun daga Kano har Zamfara abun da ban saba ba”
“Ba dadi gaskiya, ni ma ban saba hawan motar haya ba sai dolen dole”
“Ba dadi ai”
“Gaskiya”
Daga haka be sake cewa komai ba sai da suka isa cikin tasha. Bayan sun fito ta jero ita da shi suka fito titi, fitowarsa tai daidai da fakawar wata bakar mota mai kyau har wani sheki take tsabar sabuntaka.
“If ba wani matsala zan iya sauke ki a gida ai”
“Aiko da naji dadi Wallahi domin tsoron Napep nake yanzu.”
Murmushi yai ya bude mata baya ta shiga, shi kuma ta bude front seat ya shiga ya zauna.
“Ku gaisa da abokina”
Ya fada yana juyowa ya kalleta.
“Sannu ya aiki”
“Alhamdulillah ya hanya”
“Da godiya”
Ta amsa sai ta maida dubanta gefen titi tana kallon motocin dake kai kawo.
“Wace unguwa ma?”
“Gada biyu”
Ta amsa masa ba tare da ta kalleshi ba, ko kadan tsoro be kamata ba balle ta ji faduwar gaba, ta saba shiga motar maza duk kuwa da kasancewar tana da aure, sai dai bata barin wanda ya santa ya ganta, wannan karon ma bata haufin ganinta ne saboda ta san yayanta ya san labarin bata tan idan ya ganta da wani ba zai mata fada ba.
Har kofar gidan yayanta suka sauketa, kato gidan mai kyaun gaske, sai da tai musu godiya sannan ta bude motar zata fita.
“Ga katina maybe zamu iya gaisawa”
“Okay thank”
Ta fada tana karbar katin sannan ta fice ta maida motar ta rufe sannan ta tura gidan ta shiga.
“Ina ka hadu da wannan?”
“Ta sha kuma ta min”
Ya fada yana murmushi.
“Tana da kyau gaskiya”
Dukansu dariya sukai sannan abokin nasa yaja mota suka juya.
LEILA POV.
Tsaye take jikin windo tana kallon garden din dake cike da itatuwa, fuskarta dauke da hawaye, haka ma zuciyarta babu dadi ga rashin natsuwa da samun sukuni da take.
Hannu ta saka ta share hawayenta tana jin wani irin nadama da bakincikin abun da ta aikata.
“Why? Sometimes I'm very selfish”
Ya fada tana kai hannunta ta shafa wuyanta, bakinta ta cika ma iska ta busar sannan ta juyo ta baro jikin window ya nufi kofar fita har yanzu jin take babu dadi, tsaye tai tana kallon bakin kofar dakin a daidai inda Baaba ta tsaya sannan ta dauke kai ta fara tafiya, sai da ta leka dakin Momy ganin bata ciki yasa ta sauko kasa gaba daya sai ta same ta zaune akan sofa tana amsa waya. Wucewa tai dinning taja kujerarta ta zauna tana ta kallon abincin dake gabanta kamar mai wani nazarin.
“Leila...”
Momy ta kira sunanta bayan ta gama wayar, sai Leila ta juyo ta kalleta da idanuwanta dake nuna alamar bata samu bachi da yawa ba. Tasowa Momy tai tana karantar damuwar yarta, a take ta nemi bacin ran dake tare da ita ta rasa, hannu ta kai ta rika fuskar Leila.
“Dear ba ki bachi ba?”
“Wallahi Momy na kasa bachi kamar yadda na saba, Wallahi dana rufe ido matar nan nake gani”
Momy taja kujera ta matsa kusa da yarta sosai ta zauna.
“Leila ki kwantar da hankalinki babu abun da zai faru, babu wanda zai san wannan abun even if ma sun sani ba su isa su yi komai ba, they're poor ba su isa su ja da mu ba, kuma wannan abun ai kaddara ce, ki dauka haka Allah ya rubuta”
Ta gyada kai cike da gamsuwa. Sai Momy tai mata murmushi ta share mata hawayenta.
“Ko kadan bana son na ganku a damuwa, ku kenan uku Allah ya bani bana son kuna samun kanku a damuwa, wannan matsalar ma ta Talba zata wuce inshallah sai ya sauke duk girman kan nan”
“Anya Momy Talba zai ce?”
“Dole ya canja, sometime lamarinsa har daure min kai yake, yanzu maganar nan ta Baaba har ya kai ta gurin mahaifinki, simple abu Talba ya rika yinsa kamar wani mace ko karamin yaro, gashi na je Mahaifinku yace ba zai sake biyan mai aiki ba”
“Ba zai rika dafa abinci kenan?”
“Dole a aljihu zan rika biyansu, ai na yi magana da Hajiya Samira ta nemo min wasu yan aikin, a dole mu dauki wasu amman da ni zan biya su”
“Ban san miyasa Talba ya fita dabam a gidan nan ba, ni na rasa gane wane irin mutum ne”
“Shiyasa nake son ki kwantar da hankalinki, domin bana son ya fara zarginki, ni kam ba dan kin matsa kina son Talba ba....”
Kamin Momy ta karasa Leila tai saurin tare numfashinta tana rike hannunta.
“Wallahi Momy ina son Talba, ina mugun sonsa, Wallahi idan ba shi ba ba zan iya auren kowa ba”
“Shikenan ai ba zamu bari ya dauko mana bare ba, amman halin nan nasa ina ganin kamar zaki wahala idan akai auren nan”
“Momy ba zan aure shi ba sai ya canja, zan canja shi inshallah na san yana son mu yi aure ai zan yi amfani da wannan damar na canjan shi”
“Allah yasa yanzu dai sai ki karya”
Ta daga mata kai ta kai hannu zata fara bude kular akai knocking, kusan a tare ita da Momy suka kalli kofar falon sai dai ta riga Momy mikewa tsaye ta karasa gurin kofar ta bude.
“Madina...”
Suka sakarwa juna murmushi, sai kuma Madina ta juya tana kallon Talba dake kokarin shiga mota, kamin ta juyo ta kalli Leila.
“Fita zai yi?”
“I think”
“Kamar ya you think zai fita baki sani ba”
“Kina abu ke ma kamar baki san Talba ba”
“Ke ce ya kamata ki canja ba shi ba”
Madina ta fada tana sake juyawa ta kalli motarsa, ajiyar zuciya ta sauke a sirance sannan ta shiga cikin falon gabanta na mugun faduwa, irin faduwar gaban da take yawan samun kanta a ciki a duk lokacin da tai arba da Talba.
Alhamdulillah a nan na kawo karshen free page duk page din da zai biyo bayan wannan na kudi ne.
If you want to subscribe Pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660. Yan Nijar zaku biya ta wannan number +227 90 16 59 91.
An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT