AJIYA A DUHU BOOK 2 BY BILLYN ABDUL

Author :  Category :  African Stories & Novels

Chapter   13 / 80

36K to 39K   out of 237.4K words

na farko a rayuwarsa. Duk da ya jima da fahimtar halinta na munafunci dan ta sha haWashi da Daddy a baya bai taSa maida hankali ko damuwa da lamarinta ba. Amma a yau ji yake kamar ya maketa dan ba?in ciki. Shifa ya amshi auren Nazeefa ne kawai dan ya samu dai Mamma ta ha?ura ya auri Maanal. Amma shine munafukar matar nan zata kawo wannan ?auli da ba'adin. Kasa daurewa yayi cikin sanyin murya ya ce,  Ummi anawa tunanin ai ba komai bane. Idan ta dawo ?ar?ashina zama tafi samun kwanciyar hankalin da su likitocin ke bu?ata. Maanal na bu?atar hutu ne da kulawa. Kuma ina sha ALLAHU duk bazan gaza yin hakan akansu su duka ba .
? ? ? Ganin kamar zancen ya shigi baba yasa Ammie saurin tare numfashinsa.  Hakane Yazeed, amma dan ALLAH nima ina ro?onka da abi shawarar Hajiya. Saboda ya kamata aje neman auren Maanal wajen dangin mahaifinta. Ita kanta kuma sake samun nutsuwar zaisa komai ya tafi mana dai-dai yanda ya kamata. Idan akayi na Nazeefar kamar da wata biyar haka itama sai ayi natan. Kamar yau ne ai ka kwantar da hankalinka kaji Yazeed .
? ?? Ji Yazeed yay kamar ya fashe da ihu. Dan idanunsa har wani Wan tara ?walla sukayi. Baba Kalla ne ya ce,  To da gaskiyarsu kuma ta wani fanin idan muka kalla. Tabbas mai irin wannan ciwo mai haWari ya kamata abi dokar likitocin domin samar mata da nutsuwa. Sannan kamar yanda mahaifiyarta ta faWa yana da ?yau aje neman aurenta wa mahaifinta. Dan haka kayi ha?uri Yazeedu kamar yau ne in sha ALLAHU. Kaima idan akai haka zaifi baka nutsuwa da kwanciyar hankali. Ai rabon baima zoba ballantana ya wuce .
? ? ? Albarka duk suka saka da fatan ALLAH yasa haka shi yafi alkairi. Sai dai a Sangaren Yazeed zuciyarsa a matu?ar ?untace take. Haka shima Daddy sam wannan tsarin bai masa ba. Kawai dai dan anfi ?arfinsa ne. Amma ya ?ullaci Ammie da Hajiya Basariyya. Da haka dai taron ya watse.....

? ?? _________&

? ?? Bayan wucewar su Baba Ammie ta samu Daddy akan zataje gaishe da Nene tai mata godiya da ban gajiya. Amma sai yace bai yarda ba. Abin ya bata mamaki, saboda a fusace yay maganar. Zata ro?esa kuma ya Waga mata hannu da nuna mata ?ofa alamar ta fita. Tsantsar biyyarta garesa yasa bataja zancen ba ta fitan, dan ta fahimci a fusace yake da ita ne, sai dai bata san ainahin laifin nata ba ita kam. Koda ta kira Nene ta sanar mata ya hana, sai tace ta jirata gata nan zuwa ita....

?? ________&

? ? ? Hajiya Basariyya kam dariya ta dinga she?awa. Sai kuma tai kiran aminiyarta ta lambarta mata komai. Dariyar suka haWu sukayi tayi su duka. Sai da sukai mai isarsu cike da zolaya Hajiya Kamila daga can tace,  Aminiyata ke kwalba ce wlhy uwar sharri. Cikin ?an?anin lokaci kinsa dole anbi yanda kike so. Ho tawajena kina wuta fa .
? ? ? ??  To ni Win ta wasa ce aminiya ai idan sun san wata basu san wata ba. Idan har ina raye Asiya bata isa samun abinda ni ban samu ba. Ita kanta Hajiya Sadiyya da take ganin kamar na mata aiki ne ta saurari shirina akanta.
? ? ?  Kai ta wajena mi kike shirya mata ita kuma? .
??  hhhhh karki damu sai mun haWu zaki ji komai da komai. Ke dai yanzu kice da Malam Nagode. Zuwa gobe kuma zan turo miki Huznah ya mata dukkan abinda yace dan ina son shap-shap yaron nan ya kawo kasa tunda har na gumtsa musu zancen kada a fara Waukata ma?aryaciya .
? ??  An gama ai karki wani damu kanki .
??  To shike nan sai tazo.
Daga haka sukai sallama kowa ya yanke wayar. Hajiya Basariyya ta faWa saman gado tana mai jin kanta a sama can ?olokuwa da tabbatar ma da kanta yau sa'a tata ce........
'?



('ZAFAFAN DAI ('

1 ?ALBIM (Mamu gee)
2 ?IRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)


Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000

0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070

Kati MTN:- 09032345899

?an NIGER 1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu =?-?=?O?_*
*_Typing=???_*








*_=???AJIYA A DUHU....=???_*




*_Bilyn Abdull ce >??

*_(P3REP 'DDQNGP 'D1QN-RENpFP 'D1QN-PJE_*
_Da sinan Allah, Mai rahama, Mai jin ?ai._

*_My TikTok account =?G?_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram=?G?
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30


_Duk wanda bai fallowing Wina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama=??=??



.......Sosai ?annen Yazeed sukai farin cikin dawowar mahaifiyarsu gidan. Gaba Waya sun zagayeta anata cakai-cakai kowa na bata labarin abinda ya faru da bata nan. Itako sai murmushin jin daWi take yi musamman akan abinda suka dinga ma Ammie. Suna a hakan Aunty Sabuwa ta samesu. Tashi Hajiya Yaya tai suka shige ?uryar Waki suka rufe kansu. Dama itace tai kiranta tunWazun bayan wucewar su Babansu. Sai da Aunty Sabuwa tasha fresh milk Win data Wakko daga falo sosai sannan ta dire tana sauke ajiyar zuciya da faWin,  Kai nafa kwaso rana da yawa. Kin ganni nan daga tudun wada nake. Kin san munata shirye-shiryen bikin ?ar ?awata Sailuba. Ko sanda kika kirani muna tsaka da meeting ne ma dan tun sassafe na baro gida
? ? ??  Kai kar dai kice min bikin yarinyar nan har yazo? .
??  Wlhy kuwa yazo Yaya ai abin babu wuya...
? ?  Gaskiya ba wuya kam. Abin mamaki wai Sailuba da aurar da ?a .
??  Hhh kai yaya da abin dariya kike. Yo ALLAH na tuba komu badan yaran nan sun tsaya ruwan ido ba ai da tuni jikoki sun cika mana ko'ina.
? ??  Ai dan ubansu dole kam suzo su fito da mazajen aure dan na gaji da ganinsu Wirka-Wirka a gida sai yawo bikin wasu da taron birthday party. Ba maneman nan suka rasa ba amma narasa mi sukema hange-hangen .
? ??  A'a to yadai kamata wlhy Yaya. Yanzu abin sha'awa bakiga yarinyar nan yanda mijin ya haWo lefe na nunama sa'a da tsara ba. Jiya mukaje muka duba gida komai yaji gidansa kamar ka zauna kaita kallo. Kuma karki daWa karki raga yaron shagone wlhy. Amma komai babu raini .
? ? ? ?  To Sabuwa ai dama abin zuciya ce ba dukiya ba. Sai dai kuma kana gudun inda yaronka zai je ya ?as?anta ne. Ko ka saida akuya ta dawo tana ci maka danga.
? ?  Da wannan kuma dan wannan. Yanzu dai zakije min baici ko? .
??  A mizai hana, ranar yinin biki insha ALLAHU zan zo, ai Sailuba nada mutunci da girmamawa. Yarinyar nan ko sanda kike zaune a Kano indai tayo tanan anguwar dai ta shigo mun gaisa .
? ??  Sailuba ai bata da damuwa Yaya. Damma ALLAH ya bata shegen miji ne kawai. Wai shi uztazu. Ko akan bikin nan sai da muka bisa ta ?asa sannan fa ya amince da wannan shagulgulan amma da duk ya hana .
? ? ?  Oh kice dai kuna nan da halin bin malam nan ma?aryata ko Sabuwa? .
??  Ko Waya aunty kawai dai sai ta kama. Wani lokacin ne halin mazan nan sai ka haWa da dabaru. Yanzu ko ke abinda Yaya ke miki a gidan nan da zaki bari ai masa Waurin huhun goro ai da kin wuce wajen. Ko su su Basariyyan haka nan suka zauna ne kike gani. Ai wlhy ba banza ba yake wannan rawar jikin akansu har shi ma Yazeed Win .
? ??  Zan iya yadda dake wlhy Sabuwa, dan yau naga abu a gidan nan. Kai Basariyya makirar mata ce. Tabbas na tsani Asiya kuma bana sonta amma wani lokacin gara min ita sau dubu akan Basariyya..........
?? Tsaf Hajiya Yaya ta labartama Sabuwa yanda komai ya faru yau a zaman da akayi, har hukuncin da su Baba suka yanke. Sosai Aunty Sabuwa ta sauke ajiyar zuciya da har sai da Hajiya Yaya ta ce,  Lafiyarki kuwa irin wannan ajiyar zuciya haka? .
? ? ??  Wlhy ?alau Yaya. Naji kawai abubuwan duk sun zo da sau?i ne. Koba komai ai mu munafuncin Basariyyan yaman rana yau, dan in dai an rigada anyi na Nazeefar Asiya kuma sai dai ta nema ma ?arta wani mijin amma ba Yazeed ba .
? ??  Nima haka nace ai, shiyyasa ma na ?yalesu aje a hakan. Amma kuma kin san Basariyya maciji ce bata ramin kanta. Mi kika fahimta a wannan salon nata? .
? ?  Hassada ce kawai wlhy Yaya. Tasan auren Yazeed sai ya zama na nunama tsara a gidan nan shiyyasa take so ta cusa na ?arta ayi tare. Kuma tayi na banza dan babu abinda zamu fasa sai ma mu ?ara in sha ALLAHU. Ita waye ?ar nata zata aura ma shin? .
? ? ? ? ?  Yo waya sanan musu bata faWa ba. Ai kin santa ita komai nata ?unshe-?unshe saboda munafunci bata so a sani. Amma nidai tunda nake a gidan nan ban taSa ganin wani fitaccen ba?on mutunci da za'a kirashi mijin aure yazo wajen Huznah ba. Sai dai idan ba'anan gida ake taWin ba .
? ??  Eh ai munafuka ce zata iya tsara komai. Shiyyasa wlhy Yaya ki zagargari yaran nan suma su fiddo mazan aure, in ba hakaba zataita kutsawa ne dan taga ta gama aurar da nata yaran duk Wan abin arzi?in su wawashe a barsu su da saura. Kina dai gidan nan agololi biyu sukai aure Yaya ya dinga Sarin kuWi kamar babu gobe. Badan mun da?ile wannan ba ma dana uku kenan. To shi dama aurar da yara haka yake na farko-farkon nan sunfi morewa, dan anfi kashe musu dukiya .
? ? ? ? Sosai zancen Aunty Sabuwa ya shigi Hajiya Yaya. Cikin juyayi ta ce,  Oh dama haka abin yake Sabuwa? Amma shine baki fargar dani ba tuntuni .
? ??  Ba fargar dake ne banyi ba Yaya. Kin san auren agololin can munafuntarmu akai akaita komai kamar talakawa zasu aura shiyyasa bamu bama abin muhimmanci ba. Sai daga bayan nan muke ganin ashe lulluSin biri akai mana da fatar kura. Kuma ko rantsuwa nayi banyin kaffara Yaya ne ya samawa yaran nan mazansu. Shegu da yake suma burin su kenan gasu nan har da ?a?a bibbiyu .
? ? ??  Humm ai Daddyn Yazeed ya jima yana zaluntata a gidan nan ban farga ba. Kiga fa Asiya ta bayan bayana wai itace da waWan nan nasarorin. Babu komai zamu Wauki mataki .
? ?  Babban Waukar mataki ALLAH Yaya kuWi zaki fiddo ko ki shirya ma dake muje ayo miki aiki Wan gaske. Mufa ba bokaye muke bi ba. Malamai ne na zaure, kin ga ko kaje wajen malami ba bokaba ai babu batun rasa sallar da ake cewa ta kwana arba'in ko? .
? ? ?  Hakane kuma. Inaga dai wannan karon zanje Win .
? ?  Haba koke fa yaya .

? ? (Humm ALLAH ai ba'a masa wayo ko dabara Sabuwa. Idan abu ya dameka ka mi?a lamarinka ga UBANGIJI shi baya barci kuma baya mantuwa. Fafi yawan wasu abubuwan da muke Waukarsu damuwa a rayuwarmu hassada ke mana jagora akansu. Amma mu sani rabonkafa rabonka ne. Sannan wani baya canja maka ?addararka. Duniyar nan cike take da arzi?i, ka tsarkake zuciyarka ka nema naka kaima in dai nakan ne wani bai isa tare maka wannan samun ba ko ya ?arama kansa. Shima iya nasa kawai zai ci. Ya rabbi ka yafe mana kurakuranmu=?-?=?O? ka gafartama iyayenmu =?O?).

____________&

? ? ??  Tabbas da manufa kam ta ?arfafa maganar taki Asiya. Amma kada ki wani damu. Mu ALLAH yasa haka shine mafi alkairi. Dan nima ta bakinki zuwa yanzu auren Maanal da yaron nan ya fita a raina. Duk kuwa da shi Win mutumin kirki ne. Amma halin uwarsa da ?an uwansa bazai bar Maanal zama lafiya ba. Gata ita mai rauni. Ni yanzu abinda nake gani kawai mu lallaSa Maanalu ta bama yaron nan Rafeeq dama ya shigo sosai, shi kansa Yazeed Win ba lallai idan sun aura masa tasu ba su barshi haka ai .
? ?? Tabbas hakanne Nene, ni kaina wlhy yaron nan Rafeeq yamin. Yaron a haka dai kamar baida wata damuwa. Gashi kuma Wan uwan Majdiya uwa Waya uba Waya. Majdiya mutuniyar kirkice ga addini. Dan hatta yaranta tarbiyyarsu ta banbanta da sauran ?a?an gidansu. To dan dai yaran yanzu ne kai kana hango musu alkairi su suna wani hange daban. Amma dai yanzu zanyi duk yanda zanyi ta cigaba da zama can Abujan dan bana sha'awar dawowar Maanal gidan nan a yanzu kuma sam Nene wlhy .
? ? ?  Wannan ma tunani ne mai ?yau. Gara ta zauna a can Win kusa da ?ar uwarta. Tunda shima can yake Rafeeq Win sun ma fi samun sha?uwa. To amma shi maigidan naki bazaiga an masa ba daidai ba?. Kinga dai yanda yake matu?ar ?aunar yaran nan da musu hidima. Tunda kuka dawo hannunsa bai taSa bambanta al'amarin su dana ?a?ansa ba .
? ??  Tabbas hakane Nene. Nima idan na tuna hakan jikina yana sanyi. Dan ya musu abinda mahaifinsu da ?an uwansa suka gagara musu. To amma yaya zamuyi, matar nan wlhy ta wuce duk yanda kike tunani. Nata ma mai sau?i ne, dan babbar matsalarta itace ?anwar nan tata. Saboda mashawarta ne bata moreba kawai, amma duk masifarta ta wani fannin tafi Basariyya sau?i .
? ? ? ? ?  To mu cigaba da addu'a, ALLAH ai bai manta da kowa ba. In sha ALLAHU komai zai kasance da sau?i. Yanzu dai sai kisan dabarar da zaki masa akan zamanta Win can dan a rabu lafiya har su gama wannan bikin nasu. Saboda yanzu kam kema fa sai kinyi ha?uri, zakiga abubuwa da yawa wanda za'a dinga miki su da gayyane.
? ?  Hakane Nene. In sha ALLAHU babu damuwa. Dama dai matsalar tawa Maanal ce. Dan su wannan samarin babu ruwansu. Itace dai dama ina tsoron a jangwalo ciwon nan nata. Amma idan bata gidan koma mi suke shirin yi suyita yi .
? ? ? ? Nene ta gamsu sosai. Dan haka suka cigaba da tattauna batun Maanal Win dai. Nene bata bar gidan ba sai bayan magrib. Ammie ta rakota sukaci karo da Hajiya Yaya itama ta rako Sabuwa. Kallon banza suka dinga musu. Dan Nene ma na gaishesu amma ko kulata basuyi ba sai ma tsaki da Sabuwa taja musu mai ?arfi. Abin ya Satama Ammie rai amma sai ta danne. Itama Nenen duk da nata ran ya Saci sai ta danne dan bata son ?arama Ammien damuwa...

?? _________&

? ? ?? Damuwa da Sacin rai da tashin hankalin hukuncin da aka yanke yasa a ranar Yazeed ya koma Abuja batare da sanin kowa ba. Ita kanta Hajiya Yayan sai da dare ta aika Basira kiransa ta dawo ta sanar mata Wakinsa ma a kulle yake. Waya ta Waga tai kiransa. Batare da amsa sallamarsa da gaisuwarsa ba tace yazo tana nemansa. Ha?uri ya bata akan shi fa ya koma Abuja. Dan ya samu kira na gaggawa. Ranta ya matu?ar Saci amma sai ta danne bisa shawarar da Sabuwa ta bata na a dinga lallaSashi yanzu har ayi a gama lafiya. Cikin sau?a?a murya tace shike nan idan ya dawo sayi magana. ALLAH ya bada sa'a.
? ?? Ya amsa mata da Amin, dan ko yaya ya Wan ji sau?i a ransa na jin bata fushi da shi. Yazeed mutum ne mai kiyaye fushin iyaye, sannan yana da takatsantsan akan al'amarinsu. Ko wannan maganar Manaal Win da ace babu goyon bayan Daddy duk son da yake mata da tuni ya ha?ura saboda mutuntasu....

?? ________&

? ? ?? A Abuja dai kam RK ya ri?ema Maanal wuta. Dan kullum sai yazo gidan Shahidah sai ya fake da dubata yazo yi kasancewar dama sun sanar dasu hakan. Sai dai abinda basu sani ba duk tsarin RK ne dama akan batun zuwa gida dubatan kullum. Ya cigaba da kwaWaita mata zancen aiki. Tun tana dojewa harta sanarma Shahidah. A mamakinta sai Shahidah ta bata goyon bayan mizai hana ta amshi tayinsa. Ai abune mai ?yau neman nakanka musamman a wannan zamanin. Cikin damuwa Maanal ta ce,  Amma Didi kin san Ammie bazata yarda ba. Hakama Daddy zaiga kamar mun nuna gazawarsa ne musamman idan mukai dubi da duk yaransa mata babu wadda ya bari tayi aiki, ko ku sai da kukai aurene yace idan mazanku sun yarda kuyi aikinku. Idan ni kuma nazo masa da sabon tsari sai yaga kodan bai haifemu bane ba .
? ? ? ??  Hakane Maanal. Amma idan aka duba naki al'amarin ke ai yana bu?atar uziri. Bazamu yanke hukunci ba yanzu ki bari zan sanarma Ammie to. Itama Amal zanyi magana da ita. Amma ko nan Daddyn su Barru shi goyon baya ya bada Wari bisa Wari, ya kuma ce in dai dan Daddy ne shi a barsa zaiyi magana da shi. Kinga an samu sau?i kenan ai .
? ??  Shike nan ALLAH ya zaSa mana abinda yafi alkairi.
? ?  Amin ya rabbi, wannan dama itace addu'ar daya kamata kiyi tun farko. Sannan dan ALLAH idan yazo ki daina WaWWaure masa fuskar nan taki, hakama idan ya kiraki kina Wauka Auta. Wula?anci sam bashi da ?yau .
? ? ??  Didi ba wula?antasa nake ba nima. Bana son ya saki jiki akan abinda bazai samu bane kawai .
? ?  Hummm Maanal kenan. ALLAH dai ya zaSa mana abinda yafi alkairi .
? ? Maimakon ta amsa da Amin sai Maanal Win kawai ta koma ta kwanta dama tana a Wakinta ne tana karatun novel Win nata na fama Shahidahn ta sameta........
'?



('ZAFAFAN DAI ('

1 ?ALBIM (Mamu gee)
2 ?IRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)


Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000

0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070

Kati MTN:- 09032345899

?an NIGER 1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu =?-?=?O?_*
*_Typing=???_*








*_=???AJIYA A DUHU....=???_*




*_Bilyn Abdull ce >??

*_(P3REP 'DDQNGP 'D1QN-RENpFP 'D1QN-PJE_*
_Da sinan Allah, Mai rahama, Mai jin ?ai._

*_My TikTok account =?G?_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram=?G?
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My

13 / 80