Author : Category : Drama
shi ba a kansu. Zata iya yiwuwa sun shirya musu wani tuggu ko kisan mummuƙe bayan sun samu cikar burinsu. “Mtsoww!!” ya sake jan tsakin dai yana kallon agogo. Gulma yake son suyi dana kusa da shi, amma ba dama oga na kallonsu. Dole ya haƙura kamar kowa shima ya dake. A haka 4pm ta cika. Masu salla har sun gabatar.
4:23pm dai-dai kira ya shigo layin Imran. A tare Imran da Dada daya saje cikin yaran Imran ta yanda babu wanda ya gane shi ne suka kalla wayar. Sai kuma suka haɗa ido. Idanu Dadan ya lumshe masa alamar ya ɗaga, sai kuma ya gyara tsaiwa cikin basarwa ya koma kamar yanda yaran keta kai kawo. Sai dai duk abinda Imran ke saurare a cikin wayar shima yana ji, dan sun raba bluetooth ɗin ne kowa da ɗaya a kunnensa.
“Nan da mintuna talatin da bakwai kayanmu zasu iso. Zasu wuce zamu baku ita. Idan kukace zakuyi wani yunƙuri zakuga sakamakon hakanne a kanta. Daga yanzu ka fara ƙirga lokaci, sannan ga saƙo ka faɗama oganka, YA KULA DA KANSA. Idan ya shagala a kula da wannan ƘASAR, shine zai zama ƘASAR dan a maimakon kejin prison wannan karon CIKIN KABARI zai shiga”. Ƙittt. Wayar ta yanke kafin Imran ya iya cewa komai.
Kamar yanda Imran ya ji komai, shi ma Dada ya ji komai. Sai dai wannan ba shine lissafin sa ba a yanzu. Ta inda Nimrah kawai zata bayyana yake kallo.
4:40pm dai-dai baƙar mota mai duhun glass ta iso wajen, sai dai nesa da su kaɗan. Sannan ta ɗayan ɓangaren ba ɓangaren da suke ba. Gaba ɗaya hankalinsu akan motar yake, sai dai tunda ta tsaya babu wanda ya fita a ciki sai da ƙurar da suka tayar ta gama kwanciya kusan mintuna uku. 4:45 aka buɗe murfin motar, jibga-jibgan garada guda biyu majiya ƙarfi suka fito cikin shigar rufe jiki gaba ɗaya dan babu abinda ake gani nasu. Ɗaya ya buɗe baya Nimrah ta fito. Kayan dake jikinta ne dai na jiya, sai dai yanzu an rufe mata baki, hakama idanunta da baƙin ƙyalle. Ƙafarata babu takalmi. Sannan an ɗaure mata hannayenta da aka maida baya. Sun lulluɓa mata towel alamar akwai abinda suka rufe a jikinta. Dan Imran har ya motsa saukar idanunsa akan towel ɗin da suka rufa mata ɗin ne ya saka shi tsayawa cak. Shi fa jam'in soja ne, daya kwashe shekaru yana aiki tun ƙuruciya. Ta ya zai gagara gane kowanne makirci koda daga nesa ne.
Inda Dada yake ya kalla, sai ya ga shima Dada ya kallo shi. Da ido Imran ya masa magana, Dada ya mayar masa murtani alamar ya gane komai. Sake maida dubansu sukai kan Nimrah, a kuma dai-dai lokacin mutanen dake tare da ita suka yaye towel ɗin jikin nata. Bayyanar rigar bomb ta saka yaran sojojin zabura baya a firgice, shi kansa Imran da Dada sai da zukatansu suka buga duk da dama abinda sukai hasashen gani kenan.
Received at 7:46 PM
[11/02, 4:38 pm] Abue Saleh: “Da....d...dah!”.
Ta faɗa lips ɗin nata na rawa sosai fiye da da. Murmurshi mai nauyi ya sakar mata. Murmurshin da zata iya rantsuwar bata taɓa ganin irinsa akan fuskarsa ba. Sai kawai hawaye suka shiga silalo mata. Ta sake buɗe baki zata yi magana ya girgiza mata kansa. Tare da ciro dabino a aljihunsa ya sashi a bakinsa ya raba biyu ya cire rabin ya nufi bakinta da shi...
“Haah”.
Ya faɗa a hankali. Ai bama tasan ta buɗe lips ɗin nata ba a hankali ya saka mata. Sai kuma ya shafa lips ɗin nata da yatsa yana sakar mata wani murmushin. Ita dai kallonsa take kamar sakara, tama kasa tauna dabinon. Yanda ma ta shagala a kallonsa kamar wadda ta suma sai da ya fara share mata hawayen da suka gagara tsayawa sannan ta kawo nannauyan numfashi alamar dawowa hayyacinta..
Baiyi magana ba, bai kuma daina murmurshin ba, ya dai maida hankalinsa akan wayoyin bomb ɗin cike da nazari, bayan ya kalla lokacin daya rage musu 18-minutes.........✍️
[14/02, 9:15 am] Abue Saleh: Sai ta samawa kanta lafiya akan ai yau ma rana ce. Dan haka yau ɗin ma ta matsu su taho da wurin nan.
Har akai la'asar ƙawayen nata na nan. Sai da suka gama shaƙiyancinsu da ɗirka mata abubuwa sannan wajen 5 suka tafi. Da Ismat kawai aka barta, dan su Amimah basu biyosu ba. Itama Ismat ɗin Momy bata san ta biyosu ba, so take kuma daga nan ta gudu gidan Abbansu kawai.
Ismat ɗin ta tura yau ma gano mata ko yana nan, idan ma baya nan taje wai dan su Mammah su san ta dawo, ai tasan Mammah ɗin zata saka shi zuwa inda take ko bai niyya ba. Sai dai me, Ismat na zuwa ta dawo mata da labari mara daɗi. Cewar shi baima kwana a gidan ba. Su Mammah kuma duk suna asibiti Ruƙayya babu lafiya. Ga kuma Lailah ma ta faɗi an shiga da ita cs har yanzu ba'a fito da ita ba.
Maimakon hankalin Nabeeha ya tashi tace suje asibitin sai tayi shiru. Sai ita Ismat ɗin ce ta ce, “Aunty kodai asibitin zamuje muma. Dan na fahimci abin fa babbane, hankalin masu aikin nasu duk a tashe yake wlhy”.
“K rabani da wani asibiti Ismat babu inda zanje gaskiya. A gama zuba min wannan uban ƙamshin a jiki da gyara ni na kuma ƙare a asibiti. Ƙamshi nake son D. ya ji ba warin magunguna ba”.
“Amma Aunty.....”
“Kefa matsalata dake kenan. To ALLAH zan kora ki gida yanzu. Haba ki fahimceni mana. Ke bama ƙya ganin idan nace zan fita daga kawoni akwai ganganci a ciki. Karfa ki manta yanda D. Ya tsani yawo”.
“Hummmm”.
Ismat ta faɗa kawai. A ranta ko faɗi take (Baki san ya tsani yawon ba sai yanzu. Bayan tunda yabar gidan kema baki zauna ba Aunty. Kina tunanin kuma baza'a sanar masa ba. Ke matsalar ki baƙya son gaskiya da ɗaukar shawara. Kin bar Momy ta tasirantar da ƙiyayyar dangin mijinki kuma ƴan uwanmu ma ta wani fannin a zuciyarki. ALLAH yasa ki gane, dan inba haka ba wannan karon ma zaman nan naki bamai ɗorewa bane. Dan yanzu mutanen gidan nan bana da bane da suke miki kawaici, sun ɗanɗana zama da wasu surukan sun ji daɗi)...
<<••>><•••••><<••>>
“Dada zan MUTU ko? Zan mutu bazan sake ganin Mammah da Ruky ba, bazan sake ganin su Uncle's Ja'afar ba da su Mu'azz”.
Dada da hankalinsa gaba ɗaya ke kan aikinsa ya saki murmurshi kaɗan. Sai kuma ya ɗan taɓe baki da faɗin, “Bayan kin shiga labor room sau goma sha biyu, kin haifo magadan SOJA, jikokin Abdul-rasheed Shehu Kobi ko Kiddo?”.
Ita sam bata wani fahimcesa ba. Shima kuma yanda yay maganar a basarwarsa yana kuma aikinsa bama zakace shi ya faɗa ɗin ba. Ya sake kallon mintinan da suka rage. 9 kawai. Dai-dai nan Imran dake nufosu ya taka wani abu. Cak ya tsaya yana kallon ƙafarsa. Dan haka Faro dake kallonsa shima ya ce, “Yaya dai?”.
Ƙafarsa ya nuna masa sannan yay masa alamar bomb. Sai kuma yay masa nunin yay shiru kada Dada yaji. Ya ilahi wata muguwar bugawa zuciyar Faro tayi, a take jikinsa ya kama rawa. Ya kalla Imran ya kalla su Dada. Ya rasa ma ina zai kama. Suma sauran sojojin hankalinsu ya tashi matuƙa. A take suka fara zagaye wajen da na'urorin bincike bomb. Dan tunda ogansu ya taka hakan na nufin akwai wasu a wajen. Ai ko sai gasu cikin ikon ALLAH kusan bakwai a cikin ƙasa irin wanda Imran ɗin ya taka. Tuni masu ilimin akansa suka fara aikinsu. Sauran jami'an suka ja baya sosai. Sai dai Faro ya kasa yin hakan. Ya kafa ma su Dabo idanunsa kawai da sukayi jazur na tashin hankali...
“Dada ƙara min Dabino”.
Nimrah ta faɗa idanunta a rufe dan ta sadaƙar kawai lokaci yayi. Shi kansa uban gayyar hankalinsa ya gama kaiwa ƙarshen tashi. Dan saura minti huɗu ya rage musu. Gashi ya katse waya har biyu basu bane, saima ƙara na ƙidaya lokaci da suka saka bomb ɗin ya fara. Dabinon ya ciro ya saka mata a baki, batare daya bar abinda yake ba.
A dai-dai wannan lokacin kuma Faro ne ɗauke da wani ƙaton dutsi yana tafiya a hankali a hankali ta bayan Imran dake tsaye cak a wajen nan har yanzu idanunsa a rufe. Babu abinda yake maimaitawa sai kalmar shahada a zuciyarsa. Dan ya riga ya sadaukar ya kuma sadaƙar yau babu makawa ranar amsa kiran UBANGIJI ce. Babban fatansa Nimrah da Haysam su tsira a idanunsa kafin lokaci ya cika.....
Received at 10:47 AM
[14/02, 9:15 am] Abue Saleh: 6
.........Fitowar doctors ya sanya gaba ɗayansu zabura, Gwaggo Khadijah da Mammah ne kawai basu tashi ba. Doctor ta saki murmushi mai faɗi ganin duk sun zubo mata idanun cike da ƙaguwa. “Alhamdullahi congratulations. Mun samu nasarar ciro Baby girl cikin ƙoshin lafiya”.
Wasu irin nauyayan ajiyar zuciya suka shiga saukewa a tare. Yayinda Ma'aruff ya kai duƙe yay sujidar shukur. Dai-dai nan Nurse ɗin dake ɗauke da jaririyar ta fito daga bayan doctor. Hannu biyu Ammar dake kusa da ita ya saka ya amshi Babyn, fuskarsa washe da murmushi ya nufi Mammah. Amma saboda kawaici irin nata sai ta nuna masa Gwaggo Khadijah. Ƙaramar dariya yayi cikin jin kunyar abinda yay ɗin shima ya miƙama Gwaggo Khadijah ɗin...
Suna cikin farin cikin kallon Baby aka fito da Lailah da za'a miƙa ɗakin hutu. Ma'aruff ya kai duƙe gaban gadon yana mai kama hannunta. Itama kallonsa take dan idanunta biyu har akayi aka kammala Alhmdllh. Yanda shima ya zuba mata idanunsa da suka rine saboda tashin hankali ya sata sakar masa murmushi. Sai kuma ta ɗaga hannunta takai fuskarsa ta shafa. Hannun nata ya kamo, ya matso da shi a hankali kan lips ɗinsa ya sumbata. Kafin ƙasa-ƙasa ya furta, “ALLAH yay miki albarka Mar'atussaliha. ALLAH ya baki lafiya”.
Kai ta jinjina masa kawai cikin lumshe idanunta da sukai mata nauyi. Isowar su Mammah wajen yasa ta fara ƙoƙarin janye hannunta da har yanzu yake akan fuskarsa. Shi ko idanunsa akanta suke bai gansu ba, sai ya sake damƙeshi. Sai da Ja'afar ya zungure shi cike da shaƙiyanci. Ya ɗago da nufin harararsa sukai ido huɗu da Mammah da Gwaggo Khadijah. Ai da gudu yay ƙasa da kansa yana sakarma Lailah hannu. Su Bilal suka gimtse dariya. Ƙasa-ƙasa Ammar yay magana a kunnen Bilal. “Yaya Billa muma dai ALLAH ya aurar damu. Dan gaskiya an tafi da ni”.
Mintsini mai zafi Bilal ya sakar masa ya gefen ciki. Ya ce “Unch!”. Duk juyowa sukai suna kallonsa. Ruky ta saki dariya batare da tayi niyya ba. Juyawa yay inda take yana kai mata rankwashi. Da sauri ta maƙale jikin Gwaggon Alawiyya. Mammah dake harararsa ta ce, “Yanzu wadda ke gadon asibiti zaka daka Ammar?”.
“Mammah dariya fa tamin”.
“To wannan ihun da tsallen daka buga ba dole tai dariya ba, sai kace wanda kunama ta harba”.
Caraf Ruky ta ce, “Mammah mintsini ya sha wajen Uncle Billa, wai aure yake so dan ALLAH a gaggauta a masa kada ya.....”
Da bala'in sauri Ammar ya waro idanu waje jin harda sharri ta ƙara masa. Bilal ya kwashe da dariya. Dan gaba ɗaya yanda Ammar ɗin ya daburce har yana damƙo Ruky ya rufe mata baki dole abin ya ta baka dariya. Su kansu su Ja'afar daƙyar suka danne. Ruky nata mutsu-mutsun san ƙwacewa yaƙi sakinta sai da Mammah tace, “Malam sakar min yarinya kada ka cire mata haƙori. Badai aure ba, bari Muhammad yazo za'a maka”.
Bashi da zaɓin daya wuce sakin Ruky yabar wajen saboda kunya, ji yake kamar ƙasa ta tsage ya shige. A ransa kam ayyanawa yake sai yayi maganin bakin Ruky. Murmushi kawai su Ma'aruff sukai suna girgiza kawuna. Sai Mu'azz dake ma Ruky gwalo tana harrarsa da gyara hular kanta da Uncle Ammar ya zame tana maƙale da Mammah.
An shigar da Lailah dan haka suma suka koma ɗakin jiyyar Ruƙayya aka fara kiran ƴan uwa da abokan arziƙi kuma. Duk da hankalinsu a rarrabe yake akan al'amarin Nimrah, amma an fita daga wata matsalar Alhamdullah. Dan kasancewar jaririyar a hannunsu har yanzu har hirar da yanzu tana nan data hana kowa ɗauka akayi. Atake damuwarsu ta sake dawowa sabuwa. Kowa ya shiga jero addu'oin gareta. Mammah da batace komai ba kuwa layin Dada ta fara ƙoƙarin kira. Sai dai gashi tana ringing amma ba'a ɗaga ba. Bata damu ba dan tasan tunda har ta yanke bai ɗaga ɗin ba yana kan aiki ne........
×××××××××××××××
Vibration ɗin wayarsa dake jikinsa ne ya farko da shi daga ƙaramar sumar da yayi sakamakon azababbiyar bugun zuciyar data riski ƙirjinsa a lokacin da ƙarar fashewar bomb ɗin ta nema tarwatsa dodon kunnensa. A hankali ya buɗe idanunsa, ya zubama sauran baƙin hayaƙin dake yawo a samaniyar inda suken.
Received at 10:47 AM
Viewed 1 time
[14/02, 9:15 am] Abue Saleh: Sai kuma tarin sauran sojoji daya karaɗe wajen da ƙananun hayaniya...
“Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un
Imran...”
Kalma ta farko data sakashi tashi a razane. Bai damu da ƙasar data wanke jikinsa ba. Ya kai dubansa inda ake kiran Imran ɗin. Ganin Faro ya ɗago shi fuskarsa wanke da jini ya saka duniyarsa sake girgizawa. Baima san ya miƙe kan ƙafafunsa ya nufi inda suke ba. A lokacin su ma su Yusuf suka iso da gudu ɗauke da ɗan gadon bada taimakon gaggawa. Dada ji yake kamar kansa zai tarwatse. Dan yana isowa daga can wani soja cikin ƙaraji ya furta, “Bomb ɗin nan ya tashi da yarinyar nan f....”
Ai baima ƙarasa ba duhu ya mamaye idanun Dada. Kawai yaci tuntuɓe da Faro zai zube sai da aka riƙoshi. Dole Faro ya sakar musu Imran ya miƙe yana kama Dada. Zaunar da shi yayi, tare da amsar gorar ruwan da wani soja ya kawo ya ɓalle murfin ya saka masa a baki. Hannu yasa zai ture Faro yay saurin dakatar da shi...
“Dan ALLAH kasha ko kaɗan”.
Kurɓa ɗaya yayi ya kauda kansa. Faro zai sake magana wani soja ya katse hakan ta hanyar ƙwala kira, “Sirs!!!!!”.
Ai a tare suka zabura. Sojoji sukai wajen da gudu. Dole Faro ya miƙe shima. Sai kawai Dada ya miƙe cikin ƙoƙarin danne firgicinsa shima ya nufesu. Yayinda motar data ɗauki Imran tabar wajen dan nufar asibiti da shi...
“Bata mutu ba!”.
Furucin daya nema sakashi amayo zuciyarsa ta baki. Tuni ya fasa sojojin ya shiga. Caraf ta riƙe sojan dake ƙoƙarin kai hannu kan Nimrah dake kwance ƙasa ta buleta har ba'a ganinta da ƙyau. Sojan zai yi magana Faro ya ce, “Leave...”
Dole yaja jikinsa baya. Dada yakai duƙe wajen yana saka hannayesa ya zarota gaba ɗayanta, bai damu da ƙasar dake jikinta ba ya sakata a nashi jikin kawai ya rungume yana sauke wani irin bahagon wahallen jerarrun ajiyar zuciya. Ganin haka Faro yama sojojin umarnin barin wajen domin bincika ya akai haka. Dan bomb ɗin daya tashi dai na jikinta ne. Wanda Imran ya taka yayi nasarar danna masa dutsi a dai-dai lokacin da na jikin nata ke fashewa, shi kuma Imran ya ɗaga ƙafarsa saboda razanin tunanin wanda ya taka ne, shine sukai tsalle gefe kan Imran ya daki dutsin....
“Tabbas yarinyar nan nada wayo, dan sai dai idan cire rigar nan tai tayi jifa da ita Sir”.
Sosai Faro ke jin gamsuwa da abinda sojan ke faɗa. Haka ma sauran sojojin dan sun gama dube-duben su da aune-aune. Kuma gaba ɗaya alama ta nuna musu a sama Bomb ɗin ya tashi musamman yanda yay nesa da inda suke. Sannan itama aka cillata gefe ƙasa ta rufeta. Dada dake ƙoƙarin sake zubama Nimrah ruwa a fuska da Yusuf ke zuba masa a hannu duk yana saurarensu. Sai dai hankalinsa ba'a kansu yake ba. Zubawa ta uku babu alamar zata farfaɗo. Ga masu son bata taimakon gaggawa yaƙi basu dama. Ya zuba mata na huɗu yana ɗan bubbuga kumatunta wani ya yunƙuro zai yi maganar kodai a wuce da ita asibiti kawai saita wani irin banƙare, da sauri ya riƙota da ƙyau ya matse a jikinsa. Wata razananniyar ƙara ta saki mai firgitarwa tana fisga zata fita a jikin nashi gaba ɗaya. Da yake ƙarfin ba ɗaya ba dannawa ɗaya ya maida ita. Dole hankalin su Faro ya dawo wajen gaba ɗaya, cikin sauri aka kawo mota wajen, dan dole a wuce da ita asibiti da gaggawa....
©️©️©️©️©️©️©️©️©️©️©️
“Done Oga. Komai yazo hannu”.
Wani murmushin ƙasaita Oga Jush ya saki yana kallon Viper. Sai kuma ya miƙa masa hannu alamar yazo gareshi. Matsawa yay suka rungume juna.
“Proud of you darling”.
Oga Jush ya faɗa yana bubbuga bayan Viper. Matuƙar farin ciki Viper ya ƙara jinsa a ciki. Ya rissina cike da girmamawa shima ya ce, “Proud of you too Sir”.
Oga Jush yay murmushi mai faɗi yana jinjina masa kai da lumshe idanu. Kafin ya gyara zama da faɗin, “Yarinyar fa?”.
“Gaskiya tana da wayo, ta kuɓuta. Amma kaɗan ya rage a samu matsala”.
Received at 10:47 AM
[14/02, 9:15 am] Abue Saleh: “Hakan na nufin zatai mana abinda muke buƙata sosai ai”.
“Tabbas zata iya, sai dai Oga data mutu fa?”.
“Dama ɗayan biyu ne tsarin ai, kota mutu a wannan gaɓar ubanta ya ƙarasa aikin, shi kuma mu gigita duniyarsa da rashinta. Kota tsira tayi mana aikin. Kaga tunda ta tsira ƴar sa'a ce kenan.”
“Gaskiya