Author : Billyn Abdull Category : African Stories & Novels
haushi, sai sukaga tayi murmushi kawai da faɗin, “A to shike nan ai ba damuwa. Bari naje sai ta kira shin”. Tai maganar tana watsama Ummu kallon banza, ita bama tasan tanayi ba, dan tunda ta shigo ko kallonta ma batayi ba.
Tana fita su Aunty Ummi suka saka dariya. Aunty Mommy tace, “Kai Mammah kin iya bada amsa, ALLAH yau sai naga kamar bake ba. Dan na gama shirya zanyi rashin mutunci fa”.
Mammah ta harareta da faɗin, “Ku kuna son bala'i yay barci ne? Shiyyasa ga yaranku nan sun nuna sun fiku iyawa ai.” ta ƙare maganar da kallon su Ruky dake ta hidimarsa. Dariya manyan suka sanya, daga haka hirar ta koma kan su Nimrah ɗin ko tada zancen Hajiya Hasiba babu wanda ya sake yi. Sai bayan kusan mintina arba'in har Mammah ma ta manta da zuwanta sai ga Mu'azz ya shigo wai yaga ana shiga da kaya sashen. Mamaki ya kama kowa, su Aunty Ummi zasu fita Mammah ta hana su.
“Haba Mammah ya zaki ce a barsu, kenan fa ɓalla kofar sukayi?”.
Gwaggo Khadijah ce tai magana yanzu kam. “Suma ɓalla ginin, kar wanda yace musu komai. Itafa shari'a idan zakayi ta yana da ƙyau kayita da hujja. Kuda kuka tara mutane kuna hidima ina zaku biye ai tashin hankali da ku. Ai amsar da Maman Ma'aruff ta basu ya wadatar, abinda kuma suka aikata sai ku jira Haysam ɗin, ai sun san ba kanwar lasa bane ba. Dan wannan karon na roƙeku kada wanda ya shiga wannan maganar a gidan nan, Maman Ma'aruff kema dan ALLAH ki bar Haysam yayi yanda yake so”.
Murmurshi Mammah tayi. “In sha ALLAHU bazan tauye shi ba Addah Khadijah. Dama na saka a raina su ƙarata.”
Daɗi ne sosai ya kama su Mimi. Dan dama sun san Mammah ce matsalar Dada. Idan kuma ta cire hannunta komai zai tafi yanda suke so. Ai koda akace kada suyi magana wlhy sai sun gasama Nabeeha aya a tsakiyar tafin hannu. Suda suke da babban makami a hannu yanzu Nimrah. Ai zama zasuyi su zuge su Gwaggo Khadijah Nimrah ta tare itama idan son samu ne ma kafin su koma ɗin nan. Dama tunda Dada ya dawo suke wannan ƙulle-ƙullen. Yanzu haka ana gama sunan nan su Ja'afar zasu wuce kawo kaya daga nan zasu haɗo kayan Nimrah dana Biebah. Iya su suke ƙulle-ƙullen su sunƙi bari Mammah ta sani balle Dada ko uwar gayyar Nimrah da bata ma san da auren ba........✍️
78
.......★A ɓangaren Hajiya Hasiba tana komawa wajen su Nabeeha tai kiran wani yaronta mai yin ƙofifi. Babu jimawa kuwa yazo. Bata gayama su Nabeeha abinda ya faru ba. Ta kuma gargaɗi Amima. Yaron nata ne yay dabarar kwance injin key ɗin ƙofar gaba ɗaya, sai dai kuma ya kasa maidawa dan ya lalata shi. Bata damu ba tace ya ajiye musu, idan sunga zasu gyara sa gyara. Ko su cire ƙofar su canja.
Matuƙar haɗuwa fa sashen ya haɗu. Sai dai yanda tsarin ƙasa yake ya tabbatar da na zaman mace biyu ne, kasancewar ƙofofin duk a buɗe suke suka shiga ko'ina. 2 bedrooms ne, da falo ɗaya babba sosai, sai ƙarami, sai kicin, store. A kwai bayi a babban falon sannan akwai a bedrooms ɗin. Acan sama ma ƙaton falo ne guda ɗaya sai bedrooms biyu, sukam ma duk suna a kulle ne.
Cikin kuka Nabeeha ta ce, “Momy mi hakan ke nufi? Haysam na nufin harda waccan yarinyar.....?”.
“Haysam ko munafukar uwarsa da ƴan uwansa da wannan shegen Imran ɗin. Shi da baya nan sukai gini miye nashi”.
Nabeeha zata sake magana Ismat ta riƙe mata hannu. Ƙasa-ƙasa ta ce, “Aunty wlhy kada kima kanki ganganci, duk da baki san manufar Momy akan dawowar ki gidan nan ba koba komai kin tsira. Ya kamata ki sani fa yaƙin gidanki a hannunki yake, ke ya kamata kiyi. Kuma yanzu duk da bata faɗi abinda ya faru ba da taje can sashen yanda aka ɓalla ƙofar nan ya isa ki fahimci bada yardar mutanen gidan nan bane, sun hana keys ɗin kenan. Ina baki shawara kada kiyi abinda zaki rasa Dada gaba ɗaya a wannan karon, dan ba ƴan uwansa kawai ba har Mammah a wannan gaɓar ta shirya hakan”.
Sosai zantukan Ismat sun shigi Nabeeha. Dan kasa cewa komai tai sai bin Ismat ɗin da idanu. Hajiya Hasiba ta zaɓa sashen da za'aima Nabeeha jere da kanta, kamfani sukai gwaje-gwajen su, kasancewar dama sun riga sun zaɓi kayan da suke so.
Ƴan suna na shagalinsu ɓangaren Nabeeha ana zafga jere. Hajiya Hasiba da su Ismat na tsaye kan komai suna nuna inda za'a gyara, da kuma abinda za'a ƙara. Kowa na tunanin Dada na gab da dawowa gida kenan daga asibiti da aketa ƙishin ɗin yana jiyya ne. Sai dai yanda a ɓangaren masu gidan babu wanda yace komai babu kuma wanda ya nuna yama san mi su Hajiya Hasiba ɗin keyi yasa ƙananun maganar basuyi tasiri ba. Har suka kammala komai zuwa bayan azhar kamfanin da Hajiya Hasiba suka wuce, su kuma yaran suka hau shara da goge....
★••★•••★••★
A dai-dai wannan lokacin kuma Nimrah data tabbatar kowa ya gama shagala da bikin suna ta gama shirinta tsaf na silalewa domin ganawa da Dagger. Yayinda Sanda yay mugun saka mata ido kamar yanda ya saba a kwanakin nan.
Sai dai abinda bai fahimta ba Nimrah nada shegen wayo. ALLAH ya bata basirar iya tsara abubuwa duk da ƙarancin shekarunta. Hatta wannan fatin ita ta ƙirƙiresa ta sakama Ruky son ayi a zuciya dan kawai ta samu damar. Dan ta tabbatar koda hidima ta ɗauke hankalin su Mammah a kanta banda Ruky. Amma yin wannan fatin zata samu hankalin itama Rukyn ya koma can ɗin.
Lallai dabarar tata kuwa tayi, dan kamar yanda suka tsara anayin sallar azhar suka fita can bayan sashen Dada da babu yawan mutane da hayaniya suka fara shirya kujeru, wajen an gyara shi ne da green carpet da flowers masu ƙyau. Duk da ba zaman sashen ake ba sanda na ƙoƙarin tsaftacesa bisa umarnin su Ammar. Dan wani lokacin sukanje can suma su ɗan huta.....
Lokacin da suka fara aikin su kuma su Nabeeha hankalinsu nakan nasu aikin, shiyyasa babu wanda ya maida hankali akan wani, musamman daya kasance bata wannan bangon ɓangaren Nabeeha ɗin yake ba. Sun kammala suka koma sashen Mammah yin shiri, dan sabon ɗinkuna su Uncle Ja'afar suka musu har kala uku-uku na suna. Afrah na maƙale da Nimrah, dan haka ta fara shiryata ta mata wayon aikata wajen Mammah. Daga haka itama tahau shiri, su ma su Ruky nayin nasu. Sauri-sauri ta kammala nata shirin, ta idar da sallar la'asar sai ga wasu ƙawayen Bintu sun kira akan basu gane Street ɗin ba. Caraf Nimrah tace ta bata wayar tunda ita ta shirya zataje ta tarbosu. Basu kawo komai a ransu ba ta amshi wayar Bintu ta fito, dan suna da waya daga ita har Feedo.
Lokacin da Nimrah ke fita a gate Sanda na cikin bayi, sai baba maigadi kawai. Shi kuma bai kawo komai a ransa ba jin tana waya tana yin kwatance alamar wasu zata tarbo. Hakama securitys ɗin dake waje, yanda ta tsaya tana waige-waige ga waya tanayi yasa suma basu maida hankali ba, gashi ma abinci da aka kawo musu suke ƙoƙarin fara ci. A wannan lokacin da gaske Nimrah ta fito ne da niyyar tarar baƙin Bintu, amma daga nan tana son tayi waya da Dagger ta sanar masa da anyi magriba ya fito su haɗu. Amma sai mi ta ɗan bar gate ɗinsu kaɗan sai ga su Adeel da Yohan da yake gidansa zaune. Nimrah bata san shi ba, kai ko Yohan ɗin bata sani ba, dan haka ko kallo ma basu isheta ba ta cigaba da tafiyarta tana tunkaro su.
Cak Adeel ya tsaya kansa na wani irin tsuwwa da ganin Nimrah a bazata. Dan yau kwanansa biyu kenan da dawowa ƙasar amma ko mai kama da ita bai taɓa gani ba. Kai koda Ammar ma basu haɗu ba. Ganin kallon da yake mata Yohan ya fahimci akan ta ne kenan Adeel yazo anguwar ya tare, shi kansa yaran biyu suna birgeshi dan yana shan ganinsu idan za'a wuce dasu makaranta haka a mota. Ita dai Nimrah tazo ta gittasu a taƙaice tace musu “Good Afternoon”. kawai, dan gaishe da na gaba da su koda basu sanshi ba wannan tarbiyyarsu ce. Da ƙyar Adeel ya iya controling kansa baibi bayanta ba, sai dai yace da Yohan su dakata a ƙofar gate ɗin su kira Ammar idan yana nan, dan yau bazai iya haƙuri ba sai ya shiga gidan nan duk da yaga anata shiga da fita alamar wata hidima sukeyi.
Nimrah data gotasu kaɗan tana ƙoƙarin sake kiran su Teemerh dan har yanzu bataga wata alamarsu ba kuma ta fara gajiya gashi tayo nesa da gida kawai wata farar mota ta tsaya mata. Ganin motar ba wata babba bace sosai tayi tunanin su Teemerh ɗin ne, dan haka tabi ta da kallo tana ƙoƙarin kai wayar kunnenta kawai taji an fesa mata abu a fuska. A kiɗime ta ɗago numfashinta na fisga zatai magana kawai ta tafi gaba ɗaya, duhu ya mamaye mata cikin idanu, sautin motsin anguwar da ba wani mai yawa ba yay nesa da kunnenta. Daga haka bata sake sanin abinda ke faruwa ba...
Wani mai gadi dake ƙofar gate ɗin wani gida da yay facing inda Nimrah ta tsaya, sai dai motar tai blocking ɗinta dan har yana jin haushi saboda tunda Nimrah ta ɓullo suka zuba mata ido shi da abokin zamansa suna magana kawai sukaga motar tabar wajen a guje. Koda suka duba inda sukaga Nimrah kafin zuwan motar sai sukaga wayam babu komai.
“Anya lafiya kuwa Zailani? Kalli fa yanda motar can ta bar wajen kuma babu yarinyar fa”.
Wanda aka kira Zailani ya miƙe cikin mamaki yana faɗin, “Ai ni nazata ko wanda ta sani ne. Amma gaskiyarka fa wannan gudun marasa gaskiya ne”.
Da wannan surutun suka tsallako titin zuwa inda Nimrah ta tsaya, sai ko ga wayar Bintu yashe a ƙasa, harda abin hannunta da mayafi alamar fita sukai. Wayar su Zailani suka ɗauka, dai-dai nan kira ya shigo. Bintu ce ta kira da wayar Feedo jin Nimrah shiru bata koma ba. Zailani na amsa wayar kafin ma yayi magana daga can Bintu ta ce, “Ninah wai har yanzu baki gansu ba ne?”.
Zailani yaja numfashi ya fesar, sannan cikin son fahimtar da ita yace, “Ba ita bace ba.”
“Kai! Waye to? Ina mai wayar? Ya akai tazo hannunka?”.
Kai tsaye ya bata amsa da, “Akwai fa matsala. Yanzu wata mota ta ɗauki mai wayar suka gudu da ita, shine suka yadda wayar, sai kiyi ƙoƙarin faɗa a gida azo a amshi wayar da mayafinta kuma....”
Wani kalar razannanen ihu Bintu ta saka. Ihun daya dawo da hankalin kowa dake falon ɗakinsu Nimrah ɗin. Suma su Ruky dake ɗauri a gaban mirror tuni sunyi kan Bintu a hargitse. Dan sai kwarara ihu take tana faɗin, “Ninah! Ninah! Ninah”.
Ruƙayya ta fashe da kuka tana faɗin, “Ki gaya min miya samu Ninah ɗin dan ALLAH Bintu, wlhy zuciyata zata buga”. Itama ta fashe da kuka jikinta na rawa. Cikin ƙanƙanin lokaci ɗakin ya cika, kowa Bintu yake tambaya dan ita keta faɗin, sunan Nimrah. Sai da Ummu tai mata tsawa da faɗin ta nutsu tai musu bayani sannan ya faɗa abinda wanda suka kira ya faɗa.
Wayar Feedo aka amsa daga hannunta akai kiran layinta, kai tsaye nan ma Zailani ya amsa. Irin bayanin da yayma Bintu kuma yay musu. Hankali ya ƙara tashi, akace ya faɗi inda yake. Babu kwana-kwana ya sanar musu. Tsabar rikicewa wasu ma ko gyale babu akansu suka fito,........✍️
79
........Mammah ma sai da aka biyota da takalma. Securitys ɗin wajen gate najin abinda ya faru suka watsar da plates ɗin abinci. Su Adeel sun bar wajen dan sun kira Ammar yace musu baya nan, kuma a gaban securitys ɗin nan akayi, ɗan sanin da sukaima Yohan dakan fito daga gida kullum motsa jiki ko idan zai wuce wajen aiki sukan gaisa yasa basu kawo komai a ransu ba. Kafin kace mi gayyar mutane sun zagaye su Zailani. Kamar yanda sukai bayani a waya haka suka maimaita.
Jikin Mammah rawa yake sosai, dama tunda ta tashi yau gabanta ke faman faɗuwa. Sai ta barshi akan wannan taron ne maybe, da su Hajiya Hasiba sukazo kuma sai take ganin ko sunzo da wata fitina ne dan su ɓata mata taro, shiyyasa ta kwaɓi al'amarinsu cikin sauƙi tanata addu'a, ashe ga abinda ke shirin faruwa nan...
<<<<<。◕‿◕。>>>>>
A dai-dai wannan lokacin Imran da Dada na gidan Baffa ne. Tare da shi sukai sallar la'asar sukaci abincin rana. Sun sake dasa sabuwar hira da gaba ɗayanta akan al'amarin ƙasar ne sai ga Uncle Nasiru. Wannan ya ƙarama hirar armashi har lokacin la'asar da suka fita massalaci. Bayan sun dawo salla suna shirin daga nan suyi sallama da Hajjo da Baffah, sai dai da yake Baffa akwai son hira abinka da tsufa sai ya ƙara riƙesu da labarinsa. Da ƙyar ya sakesu suka fito suka barshi da Uncle Nasiru.
Kai tsaye gidan nan na sirri da suka sakama suna UNIT ZERO suka nufa. A yanzu gida ne bana kai tsaye ba. Komai a cikinsa da tsari da tsaro. Suma kansu sai sunbi tsarin suke shigarsa musamman security na ƙofa da baya buɗewa sai da password. Kuma su biyu kacal suka sani. Imran ya saka Password ɗin ƙofar ta shige. Sun shiga kenan sun zauna Imran na ƙoƙarin buɗe laptop da faɗin, “Dabo ya tura min saƙo yanzu nan, idan ka basu izinin zasu ƙaraso shi da Yusuf”.
Kafin Dada ya bashi amsa motsin da wayarsa tayi ƙirar Samsung a karo na kusan uku kenan yasa shi jan ɗan siririn tsaki. Ajiye haɗaɗɗen pen ɗin hannunsa daya ɗauka shima saman takardar da zai yi rubutu yayi, sannan ya ɗago yana mai ɗaukar wayar. Ganin sunan Mu'azz ga miss calls ya jera masa kuma ya cigaba da kira ya sashi ɗaga wayar ya kai kunnensa a nutse, kafin ya motsa lips ɗinsa cikin dakakkiyar muryarsa dake a buɗe irin ta ainahin jaruman maza ya furta, “Kai ka iya damun mutane suna aiki ko?”.
Cike da girmamawa daga can muryar Mu'azz na rawa ya furta, “Dada. Dama Ninah ce ta fita wai tarar ƙawayen Bintu a waje wai wata mota ya ɗauket.....” kuka ya sarƙe shi ya kasa ƙarasa faɗa.
Wani irin duka zuciyar Dada keyi a cikin ƙirji. Ya dai daure cike da dakiya ya ce, “Ita kaɗai ta fita a gidan?”.
“Eh ita kaɗaice sai wayar Bintu.......” nan ya bashi labarin duk yanda su Ruky sukai bayani akan fitar tata da abinda kuma masu gadin nan suka sanar musu.
Kasa cewa komai yay, sai ya katse kiran gaba ɗaya yana furzar da iska mai nauyi.
“Lafiya dai?”.
Imran daya maida hankali a kansa ya tambaya.
Sai da ya ajiye file ɗin hannun nasa kafin ya furta, “Muje gida akwai matsala.........” a taƙaice yay ma Imran bayani. Cikin ƙanƙanin lokaci Imran ya rikice. Tuni shima ya miƙe yana kashe laptop ɗin. Dada ma miƙewa yay yana sake kiran Mu'azz da saka wayar a hans free ya ajiyeta saman center table ɗin yana fara tattare takardun daya gama bazawa yanzu nan, sai dai kunnensa nakan wayar.
“Dada naji ka katse ne!”.
“Kai kaɗai ne a gida?”.
“Eh, amma an kira su Uncle Ja'afar suma gasu nan tafe. Kaima tun ɗazun su Mammah ke gwada kiranka yaƙi shiga, shiyyasa hankalinmu ya ƙara tashi sosai.”
“Gani nan zuwa gidan”.
Ya faɗa yana nufar ƙofar fita. Imran yabi bayansa. Hankalisa a natuƙar tashe ya kallesa, “Haysam kodai a sanarma jami'ai ne?”.
“Imran karka ruɗa kanka, ko su wanene suna da dalili....” Ya faɗa dai-dai yana ƙoƙarin ficewa, dan haka shima Imran ya zabura. Cikin ƙanƙanin lokaci suka iso gidan. Gaba ɗaya a compound suka same su, idan ka cire Mammah dake falo da su Ja'afar da suka ƙaraso. Amma sauran mutane da yawa ƴan suna duk suna compound, a hakama kasancewar yamma tayi mutane sun ragu sosai sai iya na jiki-jiki.
Yanda ya ɓalle murfin motar ya fito. Ya isa ya sanar maka lallai kam shi ɗin tsayayyen mutum ne kuma jarumin sadaukin gaske da ko'a cikin sojojin ya isa a kirashi BARDE. Ga dai shekaru sun ja amma da alama har yanzu jinin jikin da ƙarfinsa yake gudana. Dan yanda yake taku ma kawai ya isa ka shaida asalin ZAKI ne, kuma tabbas a ƙuruciya an baza capacity iya capacity na manyan BARADA. Daga shi har Imran ɗin nasa a tsayensu suke.
Badan da yawan wanda ke wajen sun san shi waye ba da sai suce kamar babu damuwa a tare da shi ma. Amma shi Imran yasan waye Zakinsa. Tarnaƙi baya bayyana kai a fuska sai a cikin zuciya da kwanji.
Suna isowa wajen cike da girmamawa aka fara gaishe su, Imran ne kawai ke amsawa. Shi kam hannu kawai ya ɗaga musu ya wuce hanyar falo Agogon hannunsa ƙirar Maawad Company ya kalla, ganin lokacin sallah na sake matsowa. Tura ƙofar da shigarsa ya saka duk wanda ke a falon juyowa, sai kuma duk suka miƙe a kusan tare, banda Mammah da Gwaggo Khadijah.
Kai tsaye Ja'afar da Ma'aruff suka nufosu suna musu sannu shi da Imran, shima idonsa a kansu dan haka ya jinjina musu kai. Ruƙayya dake jikin Mammah tana kuka ta taso da gudu ta shige jikinsa tana sake fashewa da kuka.