HATSABIBIN ALJANI Part 3 Littafin.txt

Author :  Category :  Romance

Chapter   2 / 2

3K to 3.3K   out of 3.3K words

wannan murgujejen dutsen ya fado Masa aka, nan take RA'UFUL KALLUS ya ragargaje ya zama tamkar an Nika hatsi.

Nan take Dutsen ya dauke kanshi da kanshi ya koma ainihin inda yake.
Bayan kamar Dakika arba'in Kasusuwa da fatar jikin RA'UFUL KALLUS suka hade, jikinsa ya koma kamar babu abinda ya same shi.

Kafin yayi wani yunkuri tuni wannan Katon Dutsen ya sake fado Masa, ya sake rugurgujewa.
Haka dai wannan dutsen ya rinka fado Masa Yana dagargajewa Kuma Yana sake tashi har sai da akayi haka sau dubu sannan ya dena.
Koda faruwar wannan Ala'mari sai RA'UFUL KALLUS yaje can Karshen dakin sannan yayi arba da wata takobin Zinari Mai tsananin haske a sakale a jikin bangon dakin.
Da zuwansa sai ya Mika hannu ya dauko takobin, Nan take kofar daki ta wanzu, Sannan ya kunna Kai a cikin kofar.

Da shigarsa sai ya tsinci Kansa a tsakiyar birnin Kuma, yaci karo da wadannan bishiyoyin guda hudu a wuri daya.
Nan take yaji wani Gagarumin Karfi ya shige shi ninka na daa sau goma.

Nan take batare da Bata wani lokaci na, yazo wajen bishiyoyin nan sannan ya cizgo ganyayen su ya Saka a cikin battarsa sannan ya debo Kasar birnin yayi gaba.

Sai da yayi tafiyar kwana biyu Sannan ya iso birni na shida.....

ME ZAI FARU A BIRNI NA SHIDA?

SHIN RA'UFUL KALLUS YANA SAMUN NASARAR TSALLAKE DUK HADARURRUKAN DAKE SAURAN BIRANEN?

INA LABARIN WADANNAN DODANNI DA KUMA SARAKUNAN DUNIYA?

SU WAYE ZASU SAMU NASARA A TSAKANINSU A WANNAN YAKIN?

SHIN BURIN RA'UFUL KALLUS ZAI CIKA KUWA?

MU HADU A HATSABIBIN ALJANI NA HUDU don Jin cigaban wannan Kasaitacce Kuma Kayataccen labari Mai dadi ✍️♥️
Ni Najibullah Muhammad nake cewa ku huta lafiya fatan kunji dadin wannan littafin✍️✍️🙏🙏❤️

2 / 2