Author : NAJIBIBULLAHI MUHAMMAD Category : Romance
**GASAR JARUMTAKA**
LITTAFI NA UKU ✍️✍️
PART A ✅✅
MARUBUCI: NAJIBULLAH MUHAMMAD 🧔
TYPING/POSTING NAJIBULLAH MUHAMMAD 🥷🥷
Whatsapp Number 08112778656
*************************
Lokacin da wannan jibgegen aljanin ya takarkare wajen kisan Jaruman Gasar, sai kawai yaji wani abu ya doke shi ta baya, saboda tsananin karfin dukan sai dai yayi tafiyar taku goma sannan ya samu dakyar ya turje.
Cikin tsananin mamaki, sai Aljanin ya waigo don ganin Wanda yayi wannan gagarumin aikin, ba wani bane ya gani a tsaye rike da takobi cikin gagarumar shigar yaki ya rike kugu Yana murmushi face SARKI ZURMATU.
Cikin tsananin mamaki Aljanin ya juyo ya Kalli Sarki Zurmatu yace, ya Kai wannan Sarki Ina Mai shawartarka da ka tattara sauran dakarunka ku koma gida domin bazaku iya kwatar jarumi margim a hannunmu ba.
Koda Jin wannan tambaya sai Sarki Zurmatu ya ce, na rantse da girman KARAGATA Koda BOKA GARGUS dakanshi yaxo Nan to sai na hallakashi da karfin tsiya Kuma na kwaci Jarumi Margim.
Koda Jin wannan batu sai ALJANIN ya bushe da mahaukaciyar dariya wadda ta sa gaba dayan Dajin ya hautsine da wata irin Kara tamkar ana ruwan kwarankwatsa a sama, sai da ya tsuke bakinsa sannan komai ya lafa, daga can ya dubi Sarki Zurmatu ya ce to ai sai an gwada akan San na kwarai muje zuwa ni da Kai a San Gwani.
Kafin wani daga cikinsu ya Kara cewa wani abu, tuni SARKI ZURMATU ya falfalo da azababben gudu tamkar Mai Shirin tashi sama, yayo Kan wannan Aljani Yana ihu da Karaji.
Shi kuwa Aljanin sai ya daga kafarsa guda da nufin ya talitse shi, cikin tsananin zafin nama na ban mamaki Sarki Zurmatu ya daka wani wawan tsalle ya hau Kan Saman tafin kafar Aljanin sannan ya rinka falfalawa da azababben gudu yana tsalle-tsalle a samansa tamkar Dan biri ya hau Katuwar bishiya.
Nan da nan Aljanin ya rinka kawo mahaukacin duka a jikinsa da nufin ya mako Sarki daga jikinsa, Amma duk Inda ya Kai duka sai Sarki Zurmatu ya daka tsalle ya cigaba da falfala gudunsa..
Haka yayi ta yi har ya iso Kan Kafadarsa cikin bakin zafin nama ya daga falleliyar takobinsa ya soka ta a jikin wuyan wannan ALJANIN, Nan take Takobin ta lume a cikin wuyan tamkar an luma wuka a cikin kabewa.
Kawai sai Sarki Zurmatu ya rike takobinsa Yana Lilo a sama, cikin hargowa da mamunga Aljanin ya cafko Sarki Zurmatu ya jayo shi tare da takobinsa sannan ya mangareshi da dayan hannun nasa, saboda karfin dukan sai da Sarki Zurmatu yayi katantawa a sama sannan ya mako a jikin wata Katuwar bishiyar Zaitun Mai tsawo da kauri har sai da jijiyoyin bishiyar suka tun6uko daga cikin Kasa sannan suka fado Kasa a tare da bishiyar.
A wannan lokacin tuni SARKI ZURMATU ya Suma saboda tsananin dokuwar da yayi a jikin bishiyar, ya baje a Kasa wanwar ko shurawar kirki baya yi, Amma duk da haka takobinsa na rike a hannunsa.
Koda su Boka RAKUL da su Sarki FALWAN da sauran Dakarun suka ga haka sai suka yo kanshi domin su ceto rayuwar shi.
Ba zato ba tsammani sai aka wannan NARKEKEN ALJANIN yana wani irin ruri mara dadin ji, ga jini na kwarara a jikin wuyansa, Nan da nan ya haukace ya rinka Kai duka da taku tako'ina a cikin Dajin.
Ya zamana cewa Yana Kai duka da hannuwansa, sannan Yana feshin wuta da bakinsa sannan Yana Kai mugun taku da kafufuwansa, cikin kankanin lokaci ya hautsina Dajin gaba Daya domin duk abinda hannuwansa suka buga Nan take abun yake ragargajewa tamkar mutum ya taka karmami, Nan da nan hargowa da yawace-yawacen da yake a cikin Dajin ya haifar da manyan ramummuka masu tsananin zurfi da fadi saboda mugayen takun da yake kawowa da Kafarsa, sannan Wuta ta kama bishiyoyi da Duwatsun Dajin, ya zamana cewa Dajin ya ya dume da wani irin mugun zafi Wanda ka iya Narkar da mutum saboda tsananin zafin Wutar.
Nan da nan Boka RAKUL yayi tsafi sai ga wata Katangar tsafi ta bayyana a tsakaninsu da wannan rafkeken Aljanin, ya zamana cewa duk wannan zafin Wutar da girgizar Kasar basa ji daga inda suke.
Bayan kamar faruwar hakan da kamar Dakika Dari biyu da sittin sai akaji Aljanin yayi shiru, sannan ya dena Kai duka da feshin wuta.
Kawai sai akaga Aljanin ya wangame bakinsa sai gani akayi jikinsa nata narkewa Yana fadowa Kasa, Bai gushe ba Yana yin hakan har sai da gaba dayan jikinsa ya narke ya zama ruwa, Nan da sai ya sake rikidewa ainihin siffarsu ta Dakarun Boka GARGUS, sai gashi sama da ALJANU Dari uku daga cikin sun mutu sakamakon soka mashi takobi a wuya da Sarki Zurmatu yayi.
Cikin tsananin bakin ciki Shugaban Aljanun yazo kusa da gawarwakin 'yan uwansa ya tsaya, yana zubar da hawayen bakin ciki da takaicin rashin su.
Sannan ya dubi su Boka RAKUL ya ce, yaku wadannan mutane kuyi sani cewa fiye da shekaru dubu uku baya ba a taba samun wata halitta data iya kashe Koda guda Daya daga cikinmu ba, Amma yau gashi sarkinku yayi sanadiyyar Asarar sama da guda Dari uku.
Don haka na rantse da gemun Sarkin Aljanu cewa dayanku bazai bar Dajin Nan a Raye ba, duk sai mun zare maku ruhin numfashi.
Yanzun Nan zamuyi maku mummunan kisan gillar da ba a taba yiwa wani irinsa ba.
Gama fadin hakan keda wuya sai gaba dayan ragowar Aljanun suka ruga izuwa kan su Boka RAKUL da sauran Dakarun dauke da muggan malamai don suyi masu mummunan kisan gilla, a lokacin lokacin gaba dayan adadinsu Bai wuce su Dari takwas ba.
Da zuwansu sai suka hau Sara da Sukar Jaruman su Sarki FALWAN Nan da Nan suka fille kawunan mutane suka rinka shawagi a sama tamkar ana ruwan sama.
Nan fa mutuwa ta baje kolin Kasuwarta a wurin, domin duk Wanda suka Sara da takobinsu sai dai kaga ya ragargaje daga karshe ya tarwatse yayi bindiga tamkar an cika balan-balan da iska.
Cikin kankanin lokaci suka kashe sama da Dakaru dubu uku.
A bangaren Boka RAKUL kuwa sai ya rinka Amfani da karfin tsafi wajen Kashe Aljanun, Amma bisa mamaki sai ga tsafin baya masu komai, walau wuta ko kibiyoyi ya watsa masu, Kai kome ya jefa masu, to da zarar yazo kusa da su sai abun ya narke ya fadi Kasa.
Ala'marin da yayi matukar bashi mamaki kenan, kawai ya rinka kokarin kare Kansa da karfin sihirin tsafi.
Abinda Bai sani ba shi ne duk abinda ke faruwa a filin wannan Yakin BOKA GARGUS na hangosu Kuma Yana bawa wadanda ALJANUN kariya ta musamman ta yadda babu tsafin da zai iya tasiri akansu.
A bangaren su Sarki FALWAN da YARIMA FAZAMAL kuwa, sai suka kutsa cikin Aljanun suka wanzu suna masu Kai masu Sara da suka Amma duk Aljanin da suka Sami nasarar Sara a wuya ko a wani wuri sai suji tamkar sun sari karfe, ko kadan makaminsu baya tasiri a jikinsu.
Ala'marin da yayi matukar Dugunzuma hankalinsu kenan ya zamana cewa har sun fara gajiya basa iya mayar da martani sai dai kokarin kare Kai kawai.
Ana cikin haka ne wani BARDE daga cikin ALJANUN ya shammaci YARIMA FAZAMAL ya lafta mashi Sara a kirji, Nan take Takobin ta lume ta haifar da wani katoton rauni.
Ba shiri jini yayi tsartuwa da feshi daga kirjin nasa, kawai sai Yarima ya kwarara uban ihu sannan ya sulale Kasa sumamme faruwar hakan keda wuya sai wannan barden ya daga takobinsa da nufin datse Kan Yarima gida biyu, Koda Sarki FALWAN yaga abinda ke Shirin faruwa sai dako wani wawan tsalle tamkar an cilloshi daga cikin baka, Yana zuwa sai ya dira a gaban wannan Barden cikin tsananin zafin nama na gaban kwatance yayi alkafira ta tsakanin Kafafunsa ya bullo ta bayansa, kawai sai ya sa takobinsa ya tsargeshi gida biyu, sai gashi kowane bangare ya fadi can gefe guda.
Nan take Sarki FALWAN ya Suri YARIMA FAZAMAL da hannu guda tamkar shaho ya Suri 'yan tsaki, ya Dora shi a Kan Kafadarsa sannan ya falfala da guda izuwa cikin Dakarunsa sannan ya cire wani Jan mayafi Dake daure a kugunsa ya daure Masa inda ke zubar da jinin, Sannan ya sunkuya ya dauki yarima ya Goya shi a bayansa ya daure shi tamau, sannan ya fuskanci Dakarun Aljanun yaci gaba da fafatawa.
A wannan lokaci ALJANUN sun kusan Karar da gaba dayan Dakarun Sarki FALWAN domin sun kasance sama da mutum dubu Tara da Dari bakwai, Wadanda suka rage Basu wuce Dari uku ba.
Kai! Komai rashin imanin mutum idan yaga yadda aka salwantar da gawarwakin mutane birjik a Kasa tamkar kanyar da ba a so, dole ne ya tausaya masu.
Domin duk Inda mutum ya duba gawarwakin Dakarun Sarki FALWAN ne fululu a kwance a mace, wasunsu kawuna aka fille masu, wasu Kuma an fafake masu ciki an fitar da gaba dayan kayan cikin, wasunsu kuwa an kashe su ne ta hanyar yi masu gutsin-gutsin tamkar ana daddatsa Albasa.
Kai! A wannan Rana Kasa Tasha Azaba saboda tsananin yakin da aka kafsa a samanta hatta bishiyoyin dajin da Duwatsun Dajin duk sai da suka ragargaje suka ratattake tamkar an tattaka busassun Kasusuwa.
A wannan lokacin akwai sauran JARUMAN GASAR sama da guda dubu Saba'in a can gefe sun zura Ido suna jiran Umarnin Sarki Zurmatu alhalin Kuma Sarki ya Suma Kuma gashi har an kusa Karar da Dakarun Sarki FALWAN Amma Bai FARFADO ba, Kuma tabbas sun San cewa muddin wadannan Aljanun suka kashe Dakarun gaba daya, to kansu zasu dawo.
To kenan ya matsayin kasancewarsu a cikin GASAR JARUMTAKA?
Suna cikin wannan tunani ne suka hango farfadowar Sarki Yana Mai caka takobinsa a Kasa sannan ya riketa ya dafa ya Mike tsaye.
Koda mikewarsa tsaya Kuma ya kyallara Ido yaga irin mummunar Barnar da wadannan ALJANUN sukayi sai ya takarkare ya kwarara uban ihu Mai tsananin razanarwa, Wanda yasa aka tsayar da yakin cak, kowa ya waigo wajen Mai ihun.
A wannan lokacin an kashe gaba dayan Dakarun Sarki FALWAN shi kadai ne yake fafatawa dashi sun Kasa samun nasara a Kansa, a gefe guda Kuma ga BOKA RAKUL can Yana ta Amfani da karfin sihirin tsafi wajen kokarin hallaka Aljanun Amma baya tasiri.
Koda SARKI ZURMATU ya gama ganin wannan mummuna kisan gillar da ALJANUN Nan suka yiwa mutane, sai ransa ya 6aci zuciyarsa ta kufulo, saboda tsananin fusata har fuskarsa ke yin gatsine, Nan take jikinsa ya kama yin karkarwa saboda tsananin fushi jijiyoyin jikinsa suka yi burdin-burdin, Kwanjinsa ya kukkumbura tamkar an hurashi da iska.
Bayan shudewar dakika Dari da saba'in sai aka ga SARKI ZURMATU ya falfalo azababben gudu saboda karfin gudun har wata karamar guguwa ke biye dashi, Koda ya zama tazarar shi da Aljanun Bata wuce taku goma ba, sai ya daka wani wawan tsalle yana Mai zare takobinsa, ai kuwa sai ya duro akan Daya daga cikin Aljanun Nan take Kaftawa Aljanin Sara a ka, take Takobin ta lume cikin Kan, ta faskarashi biyu sai gashi Aljanin ya sulale Kasa matacce ko shurawa Bai Kara Yi ba.
Nan fa Sarki Zurmatu ya wanzu a tsakanin Aljanun Yana Mai Kai masu mugun Sara da suka cikin tsananin zafin nama juriya da bajinta tamkar na tauraruwa Mai wutsiya.
Nan da nan Sarki Zurmatu ya wanzu Yana Mai Kai masu hari ta ko'ina cikin kankanin lokaci ya kashe sama da ALJANU Dari da Ashirin.
A wannan lokaci kowa ya zubawa SARKI ZURMATU Ido don tsananin mamakin irin Jarumtakarsa, tabbas Basu taba tunanin cewa JARUMTAKAR SARKI ZURMATU takai haka ba, lallai ya cancanci a jin-jina Masa.
A bangaren Shugaban Aljanun kuwa, Koda ya hango irin 6arnar da SARKI ZURMATU ke masu shi kadai sai ya fusata ainun.
Nan take ya daka tsawa kowa ya Dakata sannan ya Tako yazo daf da Sarki Zurmatu yace, tabbas ka cika sadauki na gaban kwatance, to Amma kayi sani komai Sadaukantakarka ni ne Nan zan zare maka ruhin numfashi domin na gagari duk Jaruman duniya da duk Sadaukan Duniya.
A gaban dayan nahiyar Aljanu ma sun rasa yadda zasuyi Dani ballantana ku bil'adama don haka tabbas a yau din zanyi maka mummunan kisan gilla ta hanyar ciccisge sassan jikinka Daya bayan Daya har kayi mutuwar wulakanci.
Koda Jin wannan batu sai Sarki Zurmatu ya bushe da dariya Yana Mai daka ma shugaban Aljanun tsawa sannan ya ce " Kai wannan takadarin Aljani Ina Mai gargadinka da ka kiyayi bil'adama domin mun wuce duk Inda ku ke tunani.
Na rantse da karfin mulkin KARAGATA komai jarumtakarka a yau sai na kawo karshenka.
Koda gama wannan Batu sai shugaban bakaken aljanun Nan ya bawa sauran Dakarun Aljanun Umarni akan cewa lallai su Afkawa wadancan Jaruman Gasar su tabbatar sun hallaka kowa a cikinsu.
Cikin zafin nama yayo Kan Sarki Zurmatu shi kadai, Nan take Shima Sarki Zurmatu ya tare shi cikin mugun nufi.
Suna haduwa sai suka ruguntsume da masifaffe azababben yaki mai matukar ban tsoro suka wanzu suna masu kaiwa junansu Sara da suka cikin juriya da bajinta Kai kace jikinsu ba na jini da tsoka bane.
Cikin kankanin lokaci suka tashi hankalin duk wata halitta Dake rayuwa a wajen.
Domin yakin yayi Tsamari ainun, ta yadda ko hangosu ba'a iya yi sakamakon Kura da ta turnuke su, ba abinda ake gani face gilmawar makamai yayin Kai Sara da suka.
Wohoho! Tabbas idan bala'i da masifa suka wanzu a wuri, to dole ne zaman lafiya ya tattara nasa'i nasa yayi kaura daga wurin.
Yayinda bala'i yayi bala'i sai dukkansu suka ja da baya suna haki kowannensu na tunanin dabarar da ya kamata yayi domin ya samu nasara akan Abokin gwaminsa.
Bayan shudewar wasu 'yan dakiku sai suka Kara yunkurowa da dukkan karfinsu da nufin ayita ta kare ko a mutu ko ayi Rai.
Cikin mugun nufi kowane daga cikin su ya daka tsalle sama tare da kawo mugun hari da nufin su hallaka juna.
Takobin Sarki Zurmatu ta nufi wuyan Shugaban Aljanun da nufin ya tsinke Masa Kai, cikin tsananin zafin nama na gaban kwatance ya kaucewa harin da dukkan karfinsa Amma duk da haka sai takobin ta Dan yankeshi a wuyansa.
Shima Kuma ya kaiwa Sarki Zurmatu mummunan Sara a ciki da nufin ya tsarge shi gida biyu, SARKI ZURMATU yayi Amfani da dukkan zafin namansa ya goce Amma duk da haka sai da takobin tayi Masa rauni a Saman cibiyarsa.
Ba shiri dukkansu suka rikito Kasa suna masu dafe inda suka yiwa junansu rauni.
Koda kowannensu ya dafa jikinsa yaga jini, sai ransa ya Baci zuciyarsu ta harzuka, Nan da Nan suka sake ruguntsume da wani sabon masifaffen yaki mai tsananin ban tsoro.
A bangaren Jaruman Gasar Sarki Zurmatu kuwa da sauran Dakarun Aljanun nan, bayan sun ruguntsume da masifaffen yaki, Nan da nan sai suka cakude suna masu kaiwa junansu Sara da suka, ya zamana kowa na Neman hallaka Abokin gwaminsa kota wane Hali.
Duk da cewar Dakarun Gasar sun lillinka Aljanun yawa, Amma sai suka Kasa kashe Koda Daya daga cikinsu, domin Aljanun sun fisu zafin nama nesa ba kusa ba, kafin Daya daga cikinsu ya kawo Sara sau Daya to su sun kawo sau biyar.
Kuma a duk sa'adda suka kawo Sara wani kare saran sai yaji tamkar an wurgo Masa wani Katon Dutse saboda tsananin karfin saran Aljanun, domin mutum har durkushe Kasa yake a yayin tare saran.
Wannan yasa cikin kankanin lokaci ALJANUN suka kuntata Dakarun Gasar har suka gano lagonsu suka fara kashe su.
Bayan kamar shudewar sa'a biyu cur sai gashi Aljanun sun kashe sama da DAKARUN GASAR guda dubu goma..
Wannan yasa Jaruman Gasar da Sarki FALWAN da Boka RAKUL suka hada karfi da karfe wuri Daya domin yakar Aljanun.
Boka RAKUL ya rufe idanunsa Yana Karanta wadansu dalasiman tsafi ya tofa a hannuwansa na hagu da dama, Nan take sai wata zabgegiyar Adda ta wanzu a hannunsa na hagu, irin Addar wadancan DAKARUN GASAR JARUMTAKA na birnin BALLUS, a dayan hannun Damansa kuwa sai wata majaujawar karfe Mai fitar da wuta ya wanzu.
SARKI FALWAN, BOKA RAKUL, DA SAURAN JARUMAN GASAR, suka hada karfi da karfe suka yiwa ragowar Aljanun Kawanya suna masu Yi masu kisan wulakanci.
Domin a wannan lokacin an masu Taron dangi ta yadda kota ina hari ake Kai masu, duk Aljanin da Boka RAKUL ya kwala ma wannan majaujawar karfen aka sai dai kaga Kan ya dagwargwaje tamkar an taka tumatur.
Cikin abinda Bai wuce sa'a Daya da rabi ba, suka samu nasarar kashe gaba dayan Dakarun Bakaken Aljanun, ya zamana cewa babu dayansu da yayi saura a tsaye face SHUGABANSU WANDA YAKE FAFATAWA DA SARKI ZURMATU.
Tabbas su Boka RAKUL da Sarki FALWAN sun taka babbar rawa a wajen kashe Dakarun Aljanun nan, duk da Sarki FALWAN na goye da Yarima FAZAMAL a bayansa, Amma hakan Bai hanashi yaki ba, domin yadda yake Sarrafa jikinsa tamkar ma babu kowa a jikinsa.
A bangaren su Sarki Zurmatu kuwa har yanzu suna nan suna ta fafatawa a tsakaninsu, duk da cewa Sarki Zurmatu yayi matukar gajiya ainun Amma hakan Bai hanashi yaki ba, sai da suka Kara shafe sa'a guda suna bakin Artabu Amma Basu samu nasarar juna ba, cikin bacin Rai da shammace Sarki Zurmatu ya yi tsalle sama ya kaiwa SHUGABAN Aljanun wani irin mummunan Sara aka da nufin ya tsargeshi gida biyu, kafin takobin takobin Sarki Zurmatu ta sauka akan shugaban Aljanun ba zato ba tsammani sai kawai akaga wani Jan haske Mai tsananin gudu ya taho daga sama ya Doki kirjin Sarki Zurmatu, saboda karfin dukan sai da Sarki Zurmatu yayi sama yaje ya gwaru a jikin wani Dutse, take hannunshi guda ya kare kawai sai ya fado Kasa sumamme.
Cikin tsananin mamaki sai SARKI FALWAN da Boka RAKUL da sauran jaruman Gasar suka rugo domin kawowa SARKI ZURMATU dauki..
Ba zato ba tsammani kawai sai suka ga BOKA GARGUS tare da wasu gungun bakaken aljanun wadanda adadinsu yakai dubu Dari, yana Mai kyalkyala wata irin dariyar mugunta..
Kafin wani daga cikinsu yayi wani yunkuri tuni ya nuna Sarki Zurmatu da hannun Hagu, faruwar hakan keda wuya sai akaga wata sarkar tsafi ta kanannade Sarki Zurmatu ta matse shi tamau, kawai sai ya Kara nuna dai-dai inda Sarki Zurmatu yake Nan take wani Kejin tsafi ya wanzu tare da Sarki Zurmatu a cikinsa.
Mu hadu a GASAR JARUMTAKA na 3 part B don Jin cigaban wannan Kayataccen labari Mai dadi, Wanda ni Najibullah Muhammad na rubuta Kuma nake kawo maku shi.
Anan nake cewa ku huta lafiya ✍️✍️✍️👌👌🤝🤝🤝
**GASAR JARUMTAKA**
LITTAFI NA UKU ✍️✍️
PART B ✅✅
MARUBUCI: NAJIBULLAH MUHAMMAD ✍️✍️
POSTING NAJIBULLAH MUHAMMAD 🥷🥷
Lokacin