Author : sumayya Abdulkadir Takori Category : Romance
SANADIN KENAN!
3
SUMAYYAH ABDULKADIR
takorikabara@gmail.com
babbangoro2015@yahoo.com
SADAUKARWA
Sadaukarwa ne ga duk makaranta littattafan TAKORI. Wadanda na sani da wadanda ban sani ba, Allah ya hada mu cikin alherin sa, har zuwa ranar da muka daina numfashi.
DON TUNAWA DA
Domin tunawa dake marigayiya Kakata kuma Goggo na HAJ. HAWWA ABUBAKAR WALI (Hajiya mai Mage).
GARGADI
Ban yarda a kwafi wannan littafi a kowacce kafa ta sadarwa ba ko karanta shi a rediyo ba tareda iznina ba, hakan zai kaimu ga tsayawa gaban hukuma, wadanda bansan inda kuke ba kuma zamu hadu a kotun Allah ranar da bawa bashi da abin biyan hakkin dan uwansa sai kyawawan ayyukan sa. Takori
JINJINA
Littafin SANADIN KENAN! 3&4 Dole Ya jinjina miki AUNTY ZULAIHA ZUBAIR (Mrs. Late Tafidan Kano Hakimin Kura) sabodagudummuwarki gareshi. Aunty Zulai Madallah Allah ya kara zumunci.
FATAN ALKHAIRI
Fatan alkahairi gareku makaranta nada jimirin bin littattafaina ina yi muku fatan alkhairi a duk inda kuke nagode madallah da yabawarku.
SANADIN KENAN! 3
A
n shake katafaren dining-table din da nau'ikan abinci da abin sha kala daban-daban. Ga wasu greeting-cardsmanya-manya an manna a kowacce kusurwa ta falon. Mutum biyu ne zaune a 'dining' din suna cin abinci, a jikin kowanne greeting-cardan rubuta 'Welcome to Government House ILYAS'.
Duk suka dago suka dube ta da murmushi, Ilya ne da Gwamna Ma'arouf Habibu Ji-kas. (Ilyan Goggo). Ta hada ido da Ilya, wanda idonsa ya ciko da hawaye, ga murmushi yana yi duk a lokaci daya, da gani babu tambaya hawayen farin ciki ne. Ya sha farar shadda kal 'yar ciki da babbar riga da hula da bata taba ganinsa da su ba, yayi fes kamar ba Ilya ba.
Ta kama baki da hannunta cikin mamaki tana kallonsu (extremely puzzled). Baban Ameena murmushi yake yi yana dubanta, saida ya tabbatar ta gama jikuwa cikin mamakin sannan cikin rashin damuwa yace.
“Karaso mana! Ilyas ne. Ko baki gane shi bane?”Ilya na kuka da dariya, ya ce,
"Dr. Amina!".
Amina ta ajiye mamakinta a gefe, ta gunguro keken Amina ta nufo su, ta ce, "Ilyan Goggo?"
Ya ce, "Na'am Amina, SANADIN ilminki, Sanadin ilminki yau ga ni gaJI-KAS! Ba zan iya kwatanta miki farin cikina ba. Sanadinki na hadu da wanda na fi kauna a rayuwa ta......". Sai kuka.
Amina ta karaso inda suke tana turo keken Ameena a hankali, ta zauna a wata lallausar kujera a gefen Ilya, little Ameena na cikin wheel dinta a gabanta.
Ta ce"To Ilya ai ni kun kashe ni da mamaki, ban fada masa ba, ban taba yi masa zancenka ba.........".
"Kada ki cika kwakkwafi mana......". In ji Baban Amina,ya fada yana murmushi hadi da mikewa tsaye alamar sun gama cin abincin.
"Kina zaton zan amince in damka amanar 'yata guda daya ga mutumin da ba ni da cikakken sani a kansa da asalinsa? Ba abinda bansaniba a kanki da kowa naki.Ba wajenki ya zo ba, ya tsaya neku gaisa, don an gaya masa kina ta nemansa kafin ki taho last week".
Ya fada yana goge hannayen sa da bakinsa datissue ya wuce su ba tareda ya sake duban inda take ba, ya kama hannun little Ameena ya sumbata ya saki ya wuce.
Amina jikinta har rawa yake ta kara matsawa kusa da Ilya.
"Ilya ya aka yi? Last week ya ce in gaishe ka, shine nake ta nemanka in gaya maka, in kuma tambayeka a ina ku ka hadu?Ina cikin rudu. Kai ka ba shi account number dina?"
Ilya ya goge idonsa yana dariya, "Wallahi Amina ni ne. Wannan kwamishinan malaminku ya zo har gida bidar account number din da kansa ba aike ba. Goggo ta ce in ba shi. Ya tambaye ni, ni ne Ilya? Na ce ni ne, sai kawai ya ce in biyo shi.
Da farko Goggo ta dan ji tsoro kada a ce laifi na yi, na ce mata ta kwantar da hankalinta shi ne wanda ya zabeki ki yi aikin ai. Haka ya dauko ni a mota, bai ajiye ni a ko'ina ba sai ofishin Gwamna, sai ga ni ga JI-QAS ido da ido.
Ya ba ni hannu mukayi musabaha, ya ba ni ruwa na sha. Kwamishina ya gaya masa ni Yayanki ne ba na ciki daya ba, kuma kin gaya masa yadda nake matukar kaunarsa tun kafin ki fara aikin nan, da yadda na ja ku ke da Goggo ku ka je ku ka jefa masa kuri'a. Ya ji dadi sosai, ya gode mini, ya kuma gayyace ni yau in zo mu ci abincin rana tare. Wadannan kayan na jikina shi ya aika mini ya ce nashi ne, in sanya in zan zo....".
Amina ta ce, "Ikon Allah!".
Ya ce, "Ke ce SANADI ai. Ya kuma dauke ni aiki a gidan nan nima, ni ne shugaban babban kichin.
Da fari ya tambaye ni ko na yi karatu? Na ce a'a sai na yaki da jahilci. Ban taba dana sanin rashin tsayawa in yi karatun zamani ba Amina sai yau. Don cewa ya yi, da nayi karatu daya ba ni mai bashi shawara kan harkokin matasa. Duk da haka bazai barni haka ba ya san abin da zai dace dani".
Amina ta yi dariya, "Har na hango Ilyan Goggo a office".
Suka sa dariya, ya ce, "Wannan din ma da hadadden ofis dina, duk abinda da za’a ci a gidannan nine mai bada umarni ga masu dafawa,cefanen gidan bakidaya yana hannuna, amma fa da kyar in zan karba, in na bar Goggo ya ya za ta yi da tata sana'ar tunda ni ne karfinta?"
Amina ta girgiza kai "Ka nada wani cikin yaranka masu tayaka wanda ya gane kan sha’anin sosai, amma kai namiji ne iyali za ka tara Ilya, dole ka tsaya da kafafunka.Goggo ma za ta fi son haka fiye da a ce saboda tata sana'ar kai ka kasa tsayawa ka gina kanka".
Ya mike yana sabe hannun babbar riga, "Ke kin faya tsari. Bari dai sai na yi shawara da Goggon. Ni na tafi".
Ka gaida gida, Goggo da Inna Zulai, Talatuna da tantabaruna".
"Za su ji! Wannan ce 'yar taki?" Ya fada yana dafa kan Ameena.
"Ita ce Ameena".
"Allah sarki! Yarinya kamar Babanta ya yi kaki. Allah ya ba ki lafiya Ameena".
Ameena karama ta ce a hankali, "Amin".
Suka yi sallama ya tafi, ta tura Ameena suka koma daki.
****
Haka Amina ta ci gaba da aiki a gidan Gwamnati har ga shi yau ta debi watanni goma tana kula da Ameena da iyakar iyawarta da iya zurfin ilmin da Allah ya hore mata, bata tsaya anan ba, tana cigaba da bincike akan wahalar ‘paralysis’, dare da rana yini da safiya tana kuma hadawa da addu’a, nafilfili, tsayuwar dare duk akan lafiyar Ameena Ma’arouf. Kullum kuma yarinya Ameena kara samun lafiya da kuzari ta ke.
Hannayenta hagu da dama duk suna motsi, kafar ce guda daya har yau Allah bai ba ta damar takawa ba, Amina ta soma yi mata amfani da karafuna biyu hagu da dama, tana taimaka mata tana koyon takawa da su.
A hankali sabo mai tsanani ya ci gaba da shiga tsakanin Gwamna Ji-kas da Amina, cikin dabara yake janta a jiki yana shiga al’amuran rayuwarta, hali shi ne babban abin da ke sanyawa a so mutum. Kuma Amina tanada hali, hali kuwa mai kyau abin yabo.
Kullum Ma'arouf Ji-kas cikin (observing) halayen Amina yake, na yau daban, na gobe daban masu yi masa kamanceceniya da na A’ISHA. A sannu soyayya mai girma ta cigaba da ginuwa a zuciyarsa ba tare da sanin shi kansa ba. Irin son nan mai shiga ahankali batareda sanin ma’acbocinsa ba.
Abinda ya nuna masa son Aminan ya dade da kama shishine; halin kewa da rashin sukunin da yake samun kansa a ciki a duk lokacin da ta je gida karshen mako, ga damuwa da al'amuranta. Ga son ganinta akai-akai, ga son jin sassanyar muryarta. Ya samu kansa da damuwa da Amina cikin duk abubuwan da yake gabatarwa, komai yake yi sai ta fado masa a rai da wani irin yanayi mai wuyar fassaruwa.
Goggo da Ilya, wanda yanzu ya zama na hannun daman Ma’arouf kuma babban (officer) na (catering) a gidan gwamnati sun dade da gane His Excellency son Amina yake yi, amma ita wawiyar har gobe ta sanya Baban Ameena a matsayin wani mutum mai son ci gabanta, mai kula da al'amuranta, mai darajja iyayenta da ‘yan uwanta. Mai son kowa nata.
Hatta Talatu da Zulai Jikas ya san da zamansu. Don haka itama a gare ta Ma'arouf Habibu Ji-kas, mutum ne mai daraja da kimada bata ajiye matsayin sa nan kusa a zuciyar ta ba, irin matsayin nan da kake baiwa babban Yayanka da kuke ciki daya.
A gefe ga kaunar da Hajiya ke mata kamar ta hadiye ta, kusan kullum sai sun yi waya. Kaji su suna hira rai-rai-rai kamar ‘ya da uwa. Amma bata cika zuwa ba. Hajiya na da wannan dadadden burin a zuciyarta na Allah ya hada zuciyoyin Ma'arouf da Amina, amma idan ta tuna tsarin da a kullum yake fadin ya yi wa rayuwarsa sai jikinta ya yi sanyi. Duk da haka tana addu'a idan Allah ya tashi sauya zuciyar Ma'arouf daga kan tsarinsa na auren mata daya kacal, Ya sanya Amina ce.
Ita ba za ta tilasta masa ya kara aure ba, ko ta tallata masa Amina ya zo ya ce a'ah ta zubar mata da martaba a banza a idanunsa.
A daya gefen zamansa da Laila na kara tabarbarewa. Kullum ba ta gida, in kuma tana nan za ka tadda falonta cike da kawaye da women leaders. Idonta ya bude sosai da harkar siyasa ta yadda har ba ta da lokacinsa. Ko tafiya ce ta kama shi ya nemi rakiyarta ba ya samu yanzu, za ta ce tana da biki, ko gayyatar taro ya je abinsa.
Tafiya ta yi tafiya aka gangara watanni goma sha daya. Ma'arouf Ji-kas ya soma ganewa, wato bayan ilmin likitancin tada mataccen kashi da Allah ya baiwa Amina, ita din fasiha ce, tana da sani a fannonin rayuwa daban-daban. A hankali zuciyarsa ta cigaba da afuwaga soyayyar Amina mai girman gaske.
A karshen wata na goma sha daya ne Amina ta duba asusunta. Kudin ciki sun ba ta tsoro, sai ta ga lokacin da ya dace ta cika burinta a kan Goggonta ya yi.
A wani yammaci ta kira Ilya kafin ya wuce gida, bayan ya tashi daga aiki. Suka zuna a wani hadadden dankaramin falo, ta gyara zama ta fuskanceshi, tace,
"Ilya, na kira ka ne don ka taimaka mani, na samu abin da zai ishe ni cika burina. So nake Goggo ta ji dadi a wannan siradin na rayuwarta. Ta daina wannan wahalalliyar sana'ar, shekarunta sun ja. Tana bukatar hutu.
Inaso Goggo nata daina shiga motar haya, ta je ta sauke farali. A rushe gidanmu a yi mata na zamani. Ga abinda nake da shi, gaba daya na damka wannan hidimar a hannunka.
Ina kuma rokonka kada ka gaya mata sai ka kammala komai. Aikin hajji kuwa, sai an sa musu ranar tashi za ka gaya mata".
Ilya ya dubi Amina, sai ya ga tana share hawaye.
"To kukan na mene ne kuma? Allah ya yi miki albarka Amina, Allah ya ba ki miji na gari da zuri'a mai albarka masu jin kan mahaifa. Hakika ni ma na yi wannan tunanin, lokaci ya yi da Goggo za ta huta haka a rayuwarta tunda dukkanmu ni da ke yanzu mun tsaya da kafafunmu, mun kawo karfi.".
Amina ta yi sharbe,
"Ba komai ya sa ni kuka ba Ilya, illa tuna Baba da na yi. How I wish shi ma yana raye? Ya shigo cikin inuwar ilmin da suka dora ni a kai? Suka tsaya min nayi? Allah ya yi masa rahama!".
"Daina kukan haka, ya isa. Ki ba ni wata guda, komai zai kammala a gabanta insha Allah. Amma maganar gini, ki ba ni wata biyu, ba nata za a rushe ba, sabo za a yi. In aka ce sai an rushe dole sai ta fito daga gidan, kuma sai ta tambayi ba'asi.
Sabon fili za a saya ayi sabon gini, a gaba kadan damu akwai wasu sababbin filaye da ake sayarwa kwanannan. Aikin hajj kuwa an kusa gama biyan na wannan shekarar, don haka zan hanzarta. Mota kuwa har Kwatano zani da kaina na auno mai kyau, ta zamani. Allah ya yi miki albarka".
Amina ta ce, "Ameen.Sai abu na biyu. So nake Goggo ta daina wannan sana'ar wahalar kwata-kwata daga lokacin da za ta tare a sabon gidanta, zan dinga raba albashina biyu duk wata ina bata rabi".
Ilya ya dan girgiza kai,
"Da kyar za ta yarda da wannan. Zan dai dauki ma'aikata a dinga biyansu su ci gaba da komai, nata ya zamo umarni".
*****
Gadan-gadan Ilya ya shiga aiwatar da aikin amanar da Amina ta damka masa. Sai da ya kammala komai, madaidaicin lodge dinGoggo mai brown rufi ya kammala, mota kirar (E-Class) ta iso. Matsala daya Ilya ya samu, wato dole Goggo ta je a yi mata fasfot da daukan hoto.
Daga baya dabara ta zo masa, ya je ya samu Goggo ya ce ta yi shiri su je wani waje za a yi musu takardar zama 'yan kasa, kuma dole sai an dauki hoto.
Goggo ba ta yi musu ba ta shirya suka jeimmigrationofficeaka yi mata fasfot ba da saninta ba. Aka dauke ta hoto, ba ta sa wa ranta komai ba, Ilya ya je ya biya kudin kujerar hajjin Goggo, aka yi mata visada komai aka sanya musu ranar tashi, sannan ne ya zo ya gaya wa Goggo komai ya damka mata fasfot dinta.
Goggo don dadi sai hawaye. Wai ita ce za ta je dakin Allah mai alfarma karkashin inuwar Amina. Lokacin Amina na government house, Goggo ta kira ta a waya.
"Sai kuma na ji wannan abin alheri haka? Aminan Goggo,Allah ya yi miki albarka, Ya baki miji nagari wanda zai tallafi maraicinki, ya rike ki da amana da kauna ta gaskiya".
Dadi ya rufe Amina, dama abinda take so kenan, (albarkar Goggo),cewa ta ke, "Amin-Amin Goggo, Goggo Allah Ya bar min ke!!!".
Ranar juma'a su Goggo suka tashi zuwa kasa mai tsarki. Don haka wannan satin Amina ta yi zamanta ba ta zo gida ba, ta ci gaba da kula da Ameena.
Idan Hajiya Hauwa tana dawafi a Ka’abah, ba abinda ta ke rokosai miji nagari ga Amina. Idan sujjadah ta yi a Maqama Ibrahima, addu'ar da ke kan halshenta kenan. Idan Safah da Marwah ta ke, roqon Allah ta ke ya fiddo wa Amina miji nagari cikin gaggawa. Yasa jinkirinta ya zame mata alkhairi. Ta yaya Allah zai juyar da wannan addu’ar ta UWA? Wannan shi ne kadai sauran burinta a rayuwa, sai neman cikawa da imani.
Goggo na can Makkah, Amina na dakinta na gidan gwamnati tare da patientdinta, wadda ke kwance kan cinyoyinta tana mata messaging a gabobinta. Sai kawai Ameena ta yunkura ta tashi zaune.
Dr. Amina ta ce, "Mene ne Amina?"
"Fitsari zan yi".
Kafin ta yi wani motsi na taimaka mata don mikewa, Ameenar ta mike da kanta a kan kafafunta (all of a sudden). Ta yi hanyar bayan gida.
Amina Mas'ud Shirah, ta rasa abinda za ta fara yi don farin ciki. Sai kawai ta sauko daga gadon ta yi lullubi ta gurfana goshinta gaban mahaliccinta ta yi sujjadah.
"Tsarki ya tabbata gare Ka sarkin mulkin da bai haifa ba, kuma ba a haife shi ba. Ba dabara ta ba ce, ba iyawa ta ba ce, ba gwanintata ba, iko da buwayarKa ne. Wanda in Ya ce, 'kasance' sai ya kasance. Tsarki ya tabbata gare Ka zuljalali wal ikrami". Abinda ta fada cikin sujjadar ta kenan.
Ta dago ta karanta fatiha ta shafa, ta mike ta bi bayan Ameena bayan gida.
Ameena ta yi fitsarinta, ta yi tsarki ta dubi Dr. Amina da ke tsaye bakin kofa, da murmushi ta ce,
"Aunty yau na yi tafiya da kaina babu karfe!".
Da sauri Amina ta share hawayen farin cikin dake kwarara