SANADIN KENAN! 3 SUMAYYAH ABDULKADIR takorikabara@gmail.com babbangoro2015@yahoo.com SADAUKARWA Sadaukarwa ne ga duk makaranta littattafan TAKORI. Wadanda na sani da wadanda ban sani ba, Allah ya hada mu cikin alherin sa, har zuwa ranar da muka daina numfashi. DON TUNAWA DA Domin tunawa dake marigayiya Kakata kuma Goggo na HAJ. HAWWA ABUBAKAR WALI (Hajiya mai Mage). GARGADI Ban yarda a kwafi wannan littafi a kowacce kafa ta sadarwa ba ko karanta shi a rediyo ba tareda iznina ba, hakan zai kaimu ga tsayawa gaban hukuma, wadanda bansan inda kuke ba kuma zamu hadu a kotun Allah ranar da bawa bashi da abin biyan hakkin dan uwansa sai kyawawan ayyukan sa. Takori JINJINA Littafin SANADIN KENAN! 3&4 Dole Ya jinjina miki AUNTY ZULAIHA ZUBAIR (Mrs. Late Tafidan Kano Hakimin Kura) sabodagudummuwarki gareshi. Aunty Zulai Madallah Allah ya kara zumunci. FATAN ALKHAIRI Fatan alkahairi gareku makaranta nada jimirin bin littattafaina ina yi muku fatan alkhairi a duk inda kuke nagode madallah da yabawarku. SANADIN KENAN! 3 A n shake katafaren dining-table din da nau'ikan abinci da abin sha kala daban-daban. Ga wasu greeting-cardsmanya-manya an manna a kowacce kusurwa ta falon. Mutum biyu ne zaune a 'dining' din suna cin abinci, a jikin kowanne greeting-cardan rubuta 'Welcome to Government House ILYAS'. Duk suka dago suka dube ta da murmushi, Ilya ne da Gwamna Ma'arouf Habibu Ji-kas. (Ilyan Goggo). Ta hada ido da Ilya, wanda idonsa ya ciko da hawaye, ga murmushi yana yi duk a lokaci daya, da gani babu tambaya hawayen farin ciki ne. Ya sha farar shadda kal 'yar ciki da babbar riga da hula da bata taba ganinsa da su ba, yayi fes kamar ba Ilya ba. Ta kama baki da hannunta cikin mamaki tana kallonsu (extremely puzzled). Baban Ameena murmushi yake yi yana dubanta, saida ya tabbatar ta gama jikuwa cikin mamakin sannan cikin rashin damuwa yace. “Karaso mana! Ilyas ne. Ko baki gane shi bane?”Ilya na kuka da dariya, ya ce, "Dr. Amina!". Amina ta ajiye mamakinta a gefe, ta gunguro keken Amina ta nufo su, ta ce, "Ilyan Goggo?" Ya ce, "Na'am Amina, SANADIN ilminki, Sanadin ilminki yau ga ni gaJI-KAS! Ba zan iya kwatanta miki farin cikina ba. Sanadinki na hadu da wanda na fi kauna a rayuwa ta......". Sai kuka. Amina ta karaso inda suke tana turo keken Ameena a hankali, ta zauna a wata lallausar kujera a gefen Ilya, little Ameena na cikin wheel dinta a gabanta. Ta ce"To Ilya ai ni kun kashe ni da mamaki, ban fada masa ba, ban taba yi masa zancenka ba.........". "Kada ki cika kwakkwafi mana......". In ji Baban Amina,ya fada yana murmushi hadi da mikewa tsaye alamar sun gama cin abincin. "Kina zaton zan amince in damka amanar 'yata guda daya ga mutumin da ba ni da cikakken sani a kansa da asalinsa? Ba abinda bansaniba a kanki da kowa naki.Ba wajenki ya zo ba, ya tsaya neku gaisa, don an gaya masa kina ta nemansa kafin ki taho last week". Ya fada yana goge hannayen sa da bakinsa datissue ya wuce su ba tareda ya sake duban inda take ba, ya kama hannun little Ameena ya sumbata ya saki ya wuce. Amina jikinta har rawa yake ta kara matsawa kusa da Ilya. "Ilya ya aka yi? Last week ya ce in gaishe ka, shine nake ta nemanka in gaya maka, in kuma tambayeka a ina ku ka hadu?Ina cikin rudu. Kai ka ba shi account number dina?" Ilya ya goge idonsa yana dariya, "Wallahi Amina ni ne. Wannan kwamishinan malaminku ya zo har gida bidar account number din da kansa ba aike ba. Goggo ta ce in ba shi. Ya tambaye ni, ni ne Ilya? Na ce ni ne, sai kawai ya ce in biyo shi. Da farko Goggo ta dan ji tsoro kada a ce laifi na yi, na ce mata ta kwantar da hankalinta shi ne wanda ya zabeki ki yi aikin ai. Haka ya dauko ni a mota, bai ajiye ni a ko'ina ba sai ofishin Gwamna, sai ga ni ga JI-QAS ido da ido. Ya ba ni hannu mukayi musabaha, ya ba ni ruwa na sha. Kwamishina ya gaya masa ni Yayanki ne ba na ciki daya ba, kuma kin gaya masa yadda nake matukar kaunarsa tun kafin ki fara aikin nan, da yadda na ja ku ke da Goggo ku ka je ku ka jefa masa kuri'a. Ya ji dadi sosai, ya gode mini, ya kuma gayyace ni yau in zo mu ci abincin rana tare. Wadannan kayan na jikina shi ya aika mini ya ce nashi ne, in sanya in zan zo....". Amina ta ce, "Ikon Allah!". Ya ce, "Ke ce SANADI ai. Ya kuma dauke ni aiki a gidan nan nima, ni ne shugaban babban kichin. Da fari ya tambaye ni ko na yi karatu? Na ce a'a sai na yaki da jahilci. Ban taba dana sanin rashin tsayawa in yi karatun zamani ba Amina sai yau. Don cewa ya yi, da nayi karatu daya ba ni mai bashi shawara kan harkokin matasa. Duk da haka bazai barni haka ba ya san abin da zai dace dani". Amina ta yi dariya, "Har na hango Ilyan Goggo a office". Suka sa dariya, ya ce, "Wannan din ma da hadadden ofis dina, duk abinda da za’a ci a gidannan nine mai bada umarni ga masu dafawa,cefanen gidan bakidaya yana hannuna, amma fa da kyar in zan karba, in na bar Goggo ya ya za ta yi da tata sana'ar tunda ni ne karfinta?" Amina ta girgiza kai "Ka nada wani cikin yaranka masu tayaka wanda ya gane kan sha’anin sosai, amma kai namiji ne iyali za ka tara Ilya, dole ka tsaya da kafafunka.Goggo ma za ta fi son haka fiye da a ce saboda tata sana'ar kai ka kasa tsayawa ka gina kanka". Ya mike yana sabe hannun babbar riga, "Ke kin faya tsari. Bari dai sai na yi shawara da Goggon. Ni na tafi". Ka gaida gida, Goggo da Inna Zulai, Talatuna da tantabaruna". "Za su ji! Wannan ce 'yar taki?" Ya fada yana dafa kan Ameena. "Ita ce Ameena". "Allah sarki! Yarinya kamar Babanta ya yi kaki. Allah ya ba ki lafiya Ameena". Ameena karama ta ce a hankali, "Amin". Suka yi sallama ya tafi, ta tura Ameena suka koma daki. **** Haka Amina ta ci gaba da aiki a gidan Gwamnati har ga shi yau ta debi watanni goma tana kula da Ameena da iyakar iyawarta da iya zurfin ilmin da Allah ya hore mata, bata tsaya anan ba, tana cigaba da bincike akan wahalar ‘paralysis’, dare da rana yini da safiya tana kuma hadawa da addu’a, nafilfili, tsayuwar dare duk akan lafiyar Ameena Ma’arouf. Kullum kuma yarinya Ameena kara samun lafiya da kuzari ta ke. Hannayenta hagu da dama duk suna motsi, kafar ce guda daya har yau Allah bai ba ta damar takawa ba, Amina ta soma yi mata amfani da karafuna biyu hagu da dama, tana taimaka mata tana koyon takawa da su. A hankali sabo mai tsanani ya ci gaba da shiga tsakanin Gwamna Ji-kas da Amina, cikin dabara yake janta a jiki yana shiga al’amuran rayuwarta, hali shi ne babban abin da ke sanyawa a so mutum. Kuma Amina tanada hali, hali kuwa mai kyau abin yabo. Kullum Ma'arouf Ji-kas cikin (observing) halayen Amina yake, na yau daban, na gobe daban masu yi masa kamanceceniya da na A’ISHA. A sannu soyayya mai girma ta cigaba da ginuwa a zuciyarsa ba tare da sanin shi kansa ba. Irin son nan mai shiga ahankali batareda sanin ma’acbocinsa ba. Abinda ya nuna masa son Aminan ya dade da kama shishine; halin kewa da rashin sukunin da yake samun kansa a ciki a duk lokacin da ta je gida karshen mako, ga damuwa da al'amuranta. Ga son ganinta akai-akai, ga son jin sassanyar muryarta. Ya samu kansa da damuwa da Amina cikin duk abubuwan da yake gabatarwa, komai yake yi sai ta fado masa a rai da wani irin yanayi mai wuyar fassaruwa. Goggo da Ilya, wanda yanzu ya zama na hannun daman Ma’arouf kuma babban (officer) na (catering) a gidan gwamnati sun dade da gane His Excellency son Amina yake yi, amma ita wawiyar har gobe ta sanya Baban Ameena a matsayin wani mutum mai son ci gabanta, mai kula da al'amuranta, mai darajja iyayenta da ‘yan uwanta. Mai son kowa nata. Hatta Talatu da Zulai Jikas ya san da zamansu. Don haka itama a gare ta Ma'arouf Habibu Ji-kas, mutum ne mai daraja da kimada bata ajiye matsayin sa nan kusa a zuciyar ta ba, irin matsayin nan da kake baiwa babban Yayanka da kuke ciki daya. A gefe ga kaunar da Hajiya ke mata kamar ta hadiye ta, kusan kullum sai sun yi waya. Kaji su suna hira rai-rai-rai kamar ‘ya da uwa. Amma bata cika zuwa ba. Hajiya na da wannan dadadden burin a zuciyarta na Allah ya hada zuciyoyin Ma'arouf da Amina, amma idan ta tuna tsarin da a kullum yake fadin ya yi wa rayuwarsa sai jikinta ya yi sanyi. Duk da haka tana addu'a idan Allah ya tashi sauya zuciyar Ma'arouf daga kan tsarinsa na auren mata daya kacal, Ya sanya Amina ce. Ita ba za ta tilasta masa ya kara aure ba, ko ta tallata masa Amina ya zo ya ce a'ah ta zubar mata da martaba a banza a idanunsa. A daya gefen zamansa da Laila na kara tabarbarewa. Kullum ba ta gida, in kuma tana nan za ka tadda falonta cike da kawaye da women leaders. Idonta ya bude sosai da harkar siyasa ta yadda har ba ta da lokacinsa. Ko tafiya ce ta kama shi ya nemi rakiyarta ba ya samu yanzu, za ta ce tana da biki, ko gayyatar taro ya je abinsa. Tafiya ta yi tafiya aka gangara watanni goma sha daya. Ma'arouf Ji-kas ya soma ganewa, wato bayan ilmin likitancin tada mataccen kashi da Allah ya baiwa Amina, ita din fasiha ce, tana da sani a fannonin rayuwa daban-daban. A hankali zuciyarsa ta cigaba da afuwaga soyayyar Amina mai girman gaske. A karshen wata na goma sha daya ne Amina ta duba asusunta. Kudin ciki sun ba ta tsoro, sai ta ga lokacin da ya dace ta cika burinta a kan Goggonta ya yi. A wani yammaci ta kira Ilya kafin ya wuce gida, bayan ya tashi daga aiki. Suka zuna a wani hadadden dankaramin falo, ta gyara zama ta fuskanceshi, tace, "Ilya, na kira ka ne don ka taimaka mani, na samu abin da zai ishe ni cika burina. So nake Goggo ta ji dadi a wannan siradin na rayuwarta. Ta daina wannan wahalalliyar sana'ar, shekarunta sun ja. Tana bukatar hutu. Inaso Goggo nata daina shiga motar haya, ta je ta sauke farali. A rushe gidanmu a yi mata na zamani. Ga abinda nake da shi, gaba daya na damka wannan hidimar a hannunka. Ina kuma rokonka kada ka gaya mata sai ka kammala komai. Aikin hajji kuwa, sai an sa musu ranar tashi za ka gaya mata". Ilya ya dubi Amina, sai ya ga tana share hawaye. "To kukan na mene ne kuma? Allah ya yi miki albarka Amina, Allah ya ba ki miji na gari da zuri'a mai albarka masu jin kan mahaifa. Hakika ni ma na yi wannan tunanin, lokaci ya yi da Goggo za ta huta haka a rayuwarta tunda dukkanmu ni da ke yanzu mun tsaya da kafafunmu, mun kawo karfi.". Amina ta yi sharbe, "Ba komai ya sa ni kuka ba Ilya, illa tuna Baba da na yi. How I wish shi ma yana raye? Ya shigo cikin inuwar ilmin da suka dora ni a kai? Suka tsaya min nayi? Allah ya yi masa rahama!". "Daina kukan haka, ya isa. Ki ba ni wata guda, komai zai kammala a gabanta insha Allah. Amma maganar gini, ki ba ni wata biyu, ba nata za a rushe ba, sabo za a yi. In aka ce sai an rushe dole sai ta fito daga gidan, kuma sai ta tambayi ba'asi. Sabon fili za a saya ayi sabon gini, a gaba kadan damu akwai wasu sababbin filaye da ake sayarwa kwanannan. Aikin hajj kuwa an kusa gama biyan na wannan shekarar, don haka zan hanzarta. Mota kuwa har Kwatano zani da kaina na auno mai kyau, ta zamani. Allah ya yi miki albarka". Amina ta ce, "Ameen.Sai abu na biyu. So nake Goggo ta daina wannan sana'ar wahalar kwata-kwata daga lokacin da za ta tare a sabon gidanta, zan dinga raba albashina biyu duk wata ina bata rabi". Ilya ya dan girgiza kai, "Da kyar za ta yarda da wannan. Zan dai dauki ma'aikata a dinga biyansu su ci gaba da komai, nata ya zamo umarni". ***** Gadan-gadan Ilya ya shiga aiwatar da aikin amanar da Amina ta damka masa. Sai da ya kammala komai, madaidaicin lodge dinGoggo mai brown rufi ya kammala, mota kirar (E-Class) ta iso. Matsala daya Ilya ya samu, wato dole Goggo ta je a yi mata fasfot da daukan hoto. Daga baya dabara ta zo masa, ya je ya samu Goggo ya ce ta yi shiri su je wani waje za a yi musu takardar zama 'yan kasa, kuma dole sai an dauki hoto. Goggo ba ta yi musu ba ta shirya suka jeimmigrationofficeaka yi mata fasfot ba da saninta ba. Aka dauke ta hoto, ba ta sa wa ranta komai ba, Ilya ya je ya biya kudin kujerar hajjin Goggo, aka yi mata visada komai aka sanya musu ranar tashi, sannan ne ya zo ya gaya wa Goggo komai ya damka mata fasfot dinta. Goggo don dadi sai hawaye. Wai ita ce za ta je dakin Allah mai alfarma karkashin inuwar Amina. Lokacin Amina na government house, Goggo ta kira ta a waya. "Sai kuma na ji wannan abin alheri haka? Aminan Goggo,Allah ya yi miki albarka, Ya baki miji nagari wanda zai tallafi maraicinki, ya rike ki da amana da kauna ta gaskiya". Dadi ya rufe Amina, dama abinda take so kenan, (albarkar Goggo),cewa ta ke, "Amin-Amin Goggo, Goggo Allah Ya bar min ke!!!". Ranar juma'a su Goggo suka tashi zuwa kasa mai tsarki. Don haka wannan satin Amina ta yi zamanta ba ta zo gida ba, ta ci gaba da kula da Ameena. Idan Hajiya Hauwa tana dawafi a Ka’abah, ba abinda ta ke rokosai miji nagari ga Amina. Idan sujjadah ta yi a Maqama Ibrahima, addu'ar da ke kan halshenta kenan. Idan Safah da Marwah ta ke, roqon Allah ta ke ya fiddo wa Amina miji nagari cikin gaggawa. Yasa jinkirinta ya zame mata alkhairi. Ta yaya Allah zai juyar da wannan addu’ar ta UWA? Wannan shi ne kadai sauran burinta a rayuwa, sai neman cikawa da imani. Goggo na can Makkah, Amina na dakinta na gidan gwamnati tare da patientdinta, wadda ke kwance kan cinyoyinta tana mata messaging a gabobinta. Sai kawai Ameena ta yunkura ta tashi zaune. Dr. Amina ta ce, "Mene ne Amina?" "Fitsari zan yi". Kafin ta yi wani motsi na taimaka mata don mikewa, Ameenar ta mike da kanta a kan kafafunta (all of a sudden). Ta yi hanyar bayan gida. Amina Mas'ud Shirah, ta rasa abinda za ta fara yi don farin ciki. Sai kawai ta sauko daga gadon ta yi lullubi ta gurfana goshinta gaban mahaliccinta ta yi sujjadah. "Tsarki ya tabbata gare Ka sarkin mulkin da bai haifa ba, kuma ba a haife shi ba. Ba dabara ta ba ce, ba iyawa ta ba ce, ba gwanintata ba, iko da buwayarKa ne. Wanda in Ya ce, 'kasance' sai ya kasance. Tsarki ya tabbata gare Ka zuljalali wal ikrami". Abinda ta fada cikin sujjadar ta kenan. Ta dago ta karanta fatiha ta shafa, ta mike ta bi bayan Ameena bayan gida. Ameena ta yi fitsarinta, ta yi tsarki ta dubi Dr. Amina da ke tsaye bakin kofa, da murmushi ta ce, "Aunty yau na yi tafiya da kaina babu karfe!". Da sauri Amina ta share hawayen farin cikin dake kwarara daga idanunta, ta karasa ta rungume ta na mintuna, sannan ta kamo hannunta suka fito. Karo na biyu a tsayin zamanta tare da su, da ta ga ya kamata ta kira Ma'aroufJi-kas a waya.Ma’arouf din da a baya take ganin bazata taba iya kira a waya ba. To komai dalili yakeyi, wannan dalilin yayi dalili. ***** Yana fadar shugaban kasa tare da sauran gwamnonin Najeriya gaba daya na Kudu, na yamma, na gabas da na Arewa, suna tattaunawa ne a kan yadda za a habaka harkar noma a Nigeria da yadda za’a magance hauhawar farashin man fetur nababugaira babu dalili da ake fama dashi. Kiran Amina ya shigo wayarsa da ke aljihu, wadda ya manta bai kashe ba kafin shiga dakin taron. "Ameena's Doc" ke yawo a kan fuskar wayar, in bai manta ba, tsayin watanni goma sha daya da suka yi tare wannan ne karo na biyu kacal da ta taba kiransa a waya. It must be important. Wani nishadina bazata ya ziyarci zuciyarsa da shi kansa ya ba shi mamaki. Murmushin fuskarsa ya fadada. Idan akwai mai kallon sa zai gane (Ma’arouf is in love). Soyayyar da shi kansa har yanzu bai gama yardarwa kansa ita ba.Tsam ya mike ya fito daga dakin taron zuwa harabarsa, ya amsa kiran da dukkan kulawar da ya mallaka. "Dr. Ameena, ya aka yi ne?" Ya fada cikin taushin murya, da kokarin boye eager din sa. Amina bakinta har rawa yake, ga in'ina ta kasa fadin takamaiman dalilin kiranta. Dadi da farin ciki da suna kisa, da yau sun kashe ta. Saidai Ma’arouf yazo ya tadda gawarta. "Um-um-um Ameenah ce......" "Me ya samu Ameenar???" Ya fada cikin jin faduwar gaba. "In ba’a nesa kake ba, nace umm-um idan bakayi nisa ba, ka zo ka gani da kanka zai fi. Amma fa alkhairi ne, mu wuni lafiya". Ta kashe wayarta. Ma'arouf Ji-kas ya dade rike da wayar a hannunsa, yana kallon ‘screen’ dinta har hasken ta ya mutu, ya kasa tantance yanayin da ke cikin sautinta, farin ciki ne ko tashin hankali? Ya ji 'yar damuwa ta ziyarce shi. A sanyaye ya juya ya koma dakin taron. Haka aka karasa taron da shi a daddafe ba tare da ya kara fahimtar abin da ake tattaunawa ba. Bai kwana ba kamar yadda ya tsara, a daren ya nemi jirgi ya taho Bauchi. Amina da Ameena, sun yi wankan barcinsu. Amina ta sanya wa 'yar tata kayan barci, ita kuma ta nemi doguwar rigar atamfa da kallabinta ta sanya suka bi gado suka kwanta, suka rufa da bargo bayan Amina ta gama ba ta magungunanta. Carbi ne a hannunta tana ja, idonta a lumshe. amma ba ta kai ga yin barcin ba. Knocking aka yi, ta tashi zaune ta yi lullubi, sannan ta bada izinin shigowa. Ya shigo cikin jamfa da wando na shadda 'Excelsior' ruwan makuba, babbar rigar da ya cire rataye a kafadunsa, kansa babu hula kamar koyaushe ya shigo gida cirewa yake yi, ba ya tara sumaa kansa sam, yanada yawan saisaye. Akwai 'yar damuwa a kan fuskarsa na rashin sanin me zai tarar, duk da tace alkhairi ne, amma ya yi kokari kwarai wajen boye ta. Daga bakin kofar ya tsaya, idonsa ya sauka cikin na Dr. Amina. "Me ya faru?" Ya tambaya cikin tsaka-tsakin yanayi. Babu fargaba kuma babu tashin hankali. Kawai sai Amina ta dan girgiza Ameena karama. Yarinyar ta bude ido nan da nan, dama barcin nata ba wani nisa ya yi ba. Ta nuna mata bakin kofa. "Je ki Daddy ya dawo". Ta kalli Babanta, sai ta tsallako daga gadon da gudu, ta nufe shi ta rungume. "Daddy yau ka ga ina takawa da kafata, babu karfe". Ma'arouf ya tsaya standstill, ya kasa ko da motsi. Domin bai amince idonsa biyu ba, ya fi gasgata mafarki yake yi, ire-iren mafarkansa a dan tsukin, Ameena rungume ta ke da kafafunshi tana ta ba shi labarai. Yawanci dai duk na abubuwan da Auntynta ta yi mata ne, wanda ke sa ta farin ciki, irin su danwake, wainar fulawa, kai ta bakin ruwa a wheel-chair da sauransu. Lokaci ya ja, in mafarki ne ya kamata zuwa yanzu a ce ya farka, amma shiru! Don haka ya sanya hannuwa a kan 'yar tasa yana shafawa a hankali. Daga bisani ya rage tsawo, ya zama daidai tsawonta ya rungume ta. Sunkuyar da kai ya yi ba tare da ya saki Ameena ba, sai kuma ga hawaye suna disa dis-dis a bayan Ameenar. Ya zarce da fuskantar alkibla ya yi sujjadah. Ameenah karama da ta ga ya dago daga sujjadar, sai ta kai 'yan kananan yatsunta tana share masa hawaye, tana tambayarsa. "Daddy me ye ka ke kuka? Daddy na warke fa". Ya tsane hawayensa da hankicinsada ya zaro daga aljihunsa, ya yi mata murmushi. Ya rike dukkan hannayenta biyu cikin nasa, "kukan farin ciki nake yi Ameena, ko ba ki ga kafafunki sun warke ba? Da taimakon Allah da na Dr. Amina?". Ameena ta dubi kafafun nata, "Ai kuwa, tun dazu na watsar da karafan Daddy, na ce Aunty ta yi maka waya ta gaya maka, ta ce za ka zo, Daddy na warke". "Ce ne alhamdulillahi Ameena, mun gode wa Allah, mun kuma gode wa Dr. Amina". **** Kwana uku bayan nan Dr. Amina ta soma harhada tarkacenta don barin gidan gwamna Ji-kas, bayan ta kara tabbatarwa a lafiyar Ameena karama babu sauran kalubale. Sai dai kuma abin da ya ba ta mamaki, duk yadda ta kai ga murnar komawa gaban Goggonta abin da ta fi so a rayuwarta, jikinta a matukar sanyaye yake. Ta fara samun kanta cikin wannan sanyin jikin bayan murnar warkewar Ameena, ga wata irin damuwa da zuciyarta ta shiga in ta tuna lokacin rabuwa ya zo da Ameena da BABAN TA. Baban Amina kuma??? Wata zuciyar ta tambaye ta, bata amsawa zuciyar ba, illa kawai ta san tayiwani mugun sabo da shi a tsayin shekara guda ba kadan da suka yi tare. Ma'arouf Ji-kas, ya samu wani irin muhalli a zuciyarta da ba za ta iya fasalta shi ba. Ta dade tana nazarin halaye irin nasa masu wuyar samu a wannan zamanin. Ga nagarta, ga tsare mutuncin kai dana duk wanda ke karkashinsa, da tsare nasa mutuncin a kan-kansa. Shugaba ne abin koyi, wanda kowane talaka ya bude baki a jihar Bauchi, alheri yake fada a kansa. Su da ke cikin gidansa ma, sun shaida hakan; Aadali ne. Ma'arouf ya tsaya a zuciya da ruhinta da matsayin da ba ta san wane iri ba ne. Ta dai san akwai shakuwa. Tana jin rabuwar nan har cikin bargonta ba zuciyarta kadai ba. A hankali ta ke ciro kayanta daya bayan daya daga wardrove tana ninkewa tana jefawa a 'trolley' dinta, Ameena na gefenta tana cin abinci da kanta, ta dube ta ta ce, "Aunty yau ba juma'ah ba ce, naga kina hada kaya, ina za ki je? Don Allah ki tafi da ni". Amina ta dube ta idonta cike taf! Da kwallah. Ta kasa ce mata komai, ta dau diyar Gwamna ta kai gidansu a wane dalili? Yaushe ta kai wannan matsayin? Amma ko da zai ba ta da ya yi mata babban adalci. Cikin ire-irenadalcinsa da basa karewa agareta. Da duk wannan damuwar kashi hamsin cikin dari ta kama gabanta. Tana tare da jinin Ji-kas, ai kamar Ji-kas ne suka ci gaba da rayuwa tare. Watakila watarana har ta ganshi a dalilin diyarsa. A'ah! Wai me ke damuna ne ni Amina Mas'ud?" Ta tambayi kanta, "Ma’arouf Ji-qas!”. Zuciyarta ta bata amsa. Ba tun yau ba sunan nan yake yi mata wani irin nauyi azuciya da kwakwalwar ta. Tun sanda ta fara jin sunan,ba ta iya fade a bisa dalilin da bata sani ba, saidai tafi danganta hakan da girmamawa. Amma a yau ta fahimci bayan girmamawa, akwai wani kebantaccen al'amari da zuciyarta ke lullube dashiakan wannan bawan Allah, mai girma da tasirin da ya bi ya mamaye zuciyarta, wanda yasa sunan nasa yi mata nauyi a harshe da zuciya. Wasu dumammun hawaye suka ziraro daga idanunta wanda ta tabbatar na kewa da sabo ne. Wanda tasan zasu cigaba da gudana har karshen rayuwarta. Ta daura hannu a kan Ameena tana shafawa a hankali. Daga bisani ta ture akwatin gefe ta rungume ta, kuka sosai ya kwace mata. An yi (knocking) har sau biyu Ameena da Ameena ba su ji ba, dukkanninsu kuka kawai suke yi. Ameena Ma'arouf ta gane Antinta barinta za ta yi, tunda ta warke, in tayi duba da yadda tayi parking komai nata, ita kuma ba za ta iya zama a gidannan babu Antinta ba. Cikin kuka ta ke fadin, “Aunty ni binki zan yi, wallahi ba zan zauna da Anty Laila ba!". Amina ta dago fuskarta jike da hawaye, ta soma yiwa yarinyar magana cikin lallashi. "Cool down Ameena, da Daddy za ki zauna ai ba da Anty Laila ba...". "Kullum ba ya nan, Aunty ni ma ba zan zauna ba.......". Sai kuka. Amina ta rasa abin da za ta ce mata, sai ta biye mata suka dunkule wuri guda suna ta rera abinsu. Sabo turken wawa!!! Alamu Dr. Amina ta ji na an zauna a gefensu. Ta yi saurin bude ido, ta juya inda ta ji alamun zaman mutum din da kamshin turarensa na koyaushe ya gaya mata MA'AROUF JI-KAS ne. Hadiye kukan ta yi baki dayansa ta saki Ameena ta ba shi baya. Bata so ya ga kukan ta ba, bata so ya ga hawaye a idonta ba kada ya yi zargin tana kuka ne don za ta bar Government House. "Kukan naku ya yi yawa...". Ya fada a hankali. Ba ta ce komai ba, ya koma kan diyarsa. "Kukan me ki ke yi haka Ameena?" Ta share hawayenta da tafukanta biyu, kafin cikin shessheka ta ce, "Aunty ce take hada kaya za ta koma gida yau, wai saboda na warke. Daddy ni ma ba zan zauna ba. Aunty zan bi Daddy......". Ya janyo ta jikinsa, ya aza ta gefen kafadarsa ta dama yana lallashinta, "Ameena makaranta zan sanya ki, wadda ake kwana acan. Dr. Amina ta gama aikinki za ta koma asibiti, tacigaba da taimakawa wasu marasa lafiyan, za ta yi aure ta haifa maki kanne. Ba kya son wadannan ci gaban ga Auntyn taki?" Ta yi sheshsheka. "Ina so Daddy. Amma ita zan bi, bana son makarantar kwanan......". Rigima sosai Ameena ta ke yi, ta birkice musu, hatta Dr. Amina ta tsorata da borin da yarinyar ke yi, ta juyo ta kamo ta tana nata lallashin. Amma Ameena ta fizge ta tubure. Ya kai hannu ya cire hular kansa da ya mayar ya ajiye a gefe, sai gumi yake duk da na'urar sanyaya daki da ke aiki babu kakkautawa. Idanunsa sun kada don ko fushin Ameena ba ya so balle kukanta, shi ma ya san zamanta da Laila ba zai yiwu ba, Ji-kas ne waje na farko da ya yi tunanin maida ita ta zauna wajen Hajiya. Amma lokacin shiga makarantarta ya yi har ya wuce, ya kamata a ce tana Primary 1 amma ko nursery ba ta fara ba, shekarunta shidda. Abin da ba ta sani ba shi ne; ya fi ta jin tafiyar Dr. Amina. Wata maceguda daya tal a duniya da ta shigo cikin rayuwarsa ta sauya ta. Rana daya ta yi fatali da bulullukan da ya gina rayuwarsa a kai na falsafar auren mace daya. Ya dade yana nazarin kansa akan Amina kafin wadannan bulullukan su ruguzo. Bai taba haduwa da mace mai kyawawan halayenta da nasibobinta ba, (he’s sorry to say) hatta A’ISHA. Amina Mas'ud Shira, ta dade da canza wannan tunanin, ta kawo sabo fil ta gina, kullum kwana yake ya tashi da tunanin ta, ta inda zai tunkareta kai tsaye ya kasa. Ba wai ba zai iya gaya mata ya yanke shawarar hada rayuwa da ita ba ne, a'ah! Azancin fadar hakan ne babu, tunda ya gama cika duniya da furucinsa na mace daya ta ishe shi rayuwa, a talabijin ne, a jaridu ne, a radiyo ne da sauransu. Shi ya sa ba a so mutum ya ce ya tsara wa kansa rayuwa, muna namu Allah na naSa, rayuwarmu tun haihuwarmu tana rubuce ne a allon lauhul mahfuz. Ya nisa a hankali ya dan saci kallon Dr. Aminah, wadda ke faman fyatar hanci, ta ci kuka har ta gode Allah. Itada little din baisan wadda tafi tikar kuka ba. "Ki daure ki kara kwana biyar, ban gama sallamarki ba ai, da bakina nace na sallameni ne iye da kike faman hada kaya?Kokari kike ki sallami kanki, albashin wannan watan bai shiga account dinki ba, tun jiya ban zauna ba balle inyi magana da Turaki, kaina yayi zafi ki barni in gama da abubuwan da ke gabana please". Ta sunkuyar da kai, cikin ladabi ta soma magana da murya mai tsananin taushi. "I’m sorry You’re Excellency, na riga na yi waya da Goggo, na fadi mata yau zan koma, alreadynace ina hanya......". Ya bude idanu sosai ya dube ta daga kankance su da yake yi a baya. "Da iznin wa kika yi hakan? Ok. Sai ki fadi yadda za a yi da Ameenah......". Da sauri ta dago ta dube shi, jin yadda yayi maganar fada-fada, bata ga laifi cikin abinda tayi ba, wannan wace irin tambaya ce? Shi ya kamata ya fadi wannan ai, ita ya za a yi ta sani, shi da 'yarsa? Ya karanci abin da idanunta suka fadi, ya kara janyo Ameena jikinsa suka hadu suka narke mata,kallon ta yake straight into her eyes, wani ‘chemistry’ na fita daga narkakkun kwayan idanunsasuna shiga nata. Ita ta fara dauke idonta. Ilahirin jikinta babu inda baiyi la’asar ba, da karbar wani sabon yanayi da bata taba tsintar kanta a ciki ba.Data sake dagowa ta dubesusai suka bata tausayi. Ba ta san lokacin da ta bude baki ta yi magana ba. "In za ka ba ni ina so, da ma Goggo ba ta da wadatar 'ya'ya. I'm sure za ta hada mu ta rike da amana". Murmushi ya yi, domin ya lura iya gaskiyarta ta yi furucinta,cike da wauta da gabunta irin na ‘yan fari zai ce ko auta?. "Ku kuma ‘physiotherapists’ haka ku ke zama gaban Goggonninku ba kwa ko tunanin yin aure? Al’adar ku ne yin hakan? Dube ki don Allah (close to 26)amma ko kunyar ambatar Goggo za ta rike kuba kya yi bayan ke ma kanki kin isa zama Goggon wasu irin su Ameenata. Amina Mas'ud Shira, in kin amince ki maye min gurbin Babar Ameena. Ina nufin, ina sonki, ina kaunarki ina ra’ayin aurenki ba don Ameena ba, I just love you, so do I since..... Amma fa idan har ban yi miki tsufa ba. Ina son dukkan halayenkiAmeena wadanda su suka ja ni ga kwadayin ki zamo cikin iyalina. Wannan sakona ne gare ki da Goggo, na ba ki kwana uku ki yi tunani dakyakkyawan nazari ki kuma yi shawara da Goggo. Ban yarda kiyi shawara da kowa ba sai ita. Kwana uku bai yi kadan ba? Dr. Amina ki ba ni amsa!". Amina wadda ta mutu a zaune, tun daga farkon furucinsa, 'In kin amince ki maye min gurbin Babar Ameena...' ta daskare ta kasa motsawa, sai dai abinda ya bata mamaki shi ne; jin can wani lungu na zuciyarta ya yi sanyi daga azabtar da yake yi na rabuwa da Ameena da Babanta, "........ Amma fa in har ban yi miki tsufa ba...”. Ta tuno jimlarsa ta gaba. A wannan karon sai ta yi murmushi. A shekarun nasakwarai zai yi wa 'yammatayara irin masu shekara 18 da yawa tsufa, to ita mai 26 ta ce me? Kada dai sake-saken zuciyar nan yana nufin tuni zuciyarta ta aminta da soyayya da kaunar Baban Ameena? Mutumin da duniya ke so, ba abin mamaki ba ne in itama ta so shi. Sai dai fa nata feelings din daban suke da na sauran al'umma irin su Yayanta Ilya, natanare extraordinary; ba na citizen ga leader dinsa bane, bata taba jin irinsu a kan kowa a duniya ba. Kamar da ma suna ajiye a wani sako na zuciyarta ne, jira suke a sanya kara a zunguro su. Kuma yanzun aka zunguro sun. Kamar tun da ma can an halicce su a cikin kirjinta ne. Ta yi nisa a duniyar sake-saken nan, ta sunkuyar da kai ta kasa dagowa. Ba ta san sanda ya mike ya nufi kofa ba. Sai da ya murda marikin kofar ya dan ba da karaAmina ta dawo daga duniyar tunaninta. A tsakiyar kanta ta tsinkayi sautinsa yana fadin. "In kin gama kintsawa Akilu na jiranki. Ameena za mu wuce Ji-kas da ita, ki gaida Ilyas!". Ya fice. Ta mike cikin sanyin jiki ta ci gaba da harhada yanata-yanata da kayan amfaninta. Ameena ta yi kuka ta gaji, ta bingire ta yi bacci a wajen. Wannan damar ta samu ta silale da akwatinta biyu. Duk kayan sanyawar da ta tarar a gidan ta yi amfani da su a nan ta barsu, ba ta dauki ko daya ba. **** A cikin mota suna tafe suna gaisawa da direba Akilu, ta ji shigowar sako a wayarta. Ta dauko ta duba, sakon shigowar kudi (Alert) ne daga Kwamishina Usman Turaki. Adadin kudin sun ba ta tsorofiye da na baya, sun tada hankalinta. Da hanzari ta dannawa malamin nata kira. Dr. Turaki ya san za a yi haka, kuma tuni ya shirya karbar kiranta, don haka tana kira ya yi murmushi ya dauka. "Dr. Amina ya aka yi?" Amina ta feso ajiyar zuciya. Ta tsane gumin daya tsatstsafo mata a goshi da hankicin ta. "Doctor wannan kudin sun fi karfina, me na sayar muku? Me na yi muku na wahala haka? Doctor na fi son iya cikon albashina, Goggo za ta yi zargi, wanda dama kullum cikinsa nake a gurinta". Ta jero maganganun a jere babu shan numfashi,amma cikin taushin murya mai nuna ladabi da damuwar da take ciki a fili. Dr. Turaki ya yi magana cikin muryar kwantar da hankali. “Take it easyAmina. Me na gaya miki sanda za ki fara aikin nan? In ban manta ba na ce da ke, 'Allah ya sa ta hannunki za ta samu lafiyar, ina addu'ar tukwicin hakan ya zamo naki ne'. Anyi haka ko ba’ayi ba? Kinyi kokari sosai a kan Ameena, ta samu lafiya a hannunki.Idan Ma'arouf ya mallaka miki rabin abinda ya mallaka ba zai ji komai ba fa. Sai bai yi hakan ba, ya yi daidai hankali da tunani don kada ya razana ki. Ina so ki sani, wane neGwamna kuma Engnr. Ma'arouf Ji-kas, wannan tukwicin da ya ba ki kwatantawa ne ba kankat ba a kan son da yake yi wa 'yarsa Ameena. Ki sanya a rankiilminki ne ya ba ki ba Ma’arouf ba. SANADIN KENAN! Ki yi wa mahaifiyarki bayani kada ta damu, ilmin da ta tsaya miki ki ka yi ne ya ba ki, babu matsayin da ilmi ba ya baiwa mutum a rayuwa. Sannan a wajen His Excellency wannan kamar an fitar da allura daga kogi ne (so relax please, say thanks to Almighty Allah, not Ji-kas)". Amina ta yi murmushi ta sauke wayar daga kunnen ta. Tunda ya kashe tasa alamar bai son (anymore word from her) karin wata kalma daga gare ta. A kalla ta samu peace of mindyanzun (kwanciyar hankali). Ta yarda da duk abi da ya fada. Ta shiga tunanin zama karamar attajira mai zaman kanta sanadin ilminta, ta samu zuciyar mutum irin Ma'arouf Habibou Ji-Kas SANADIN ILMINta. Dadin-dadawa ta samu (exposure) na rayuwa kala daban-daban a gidan gwamnati, wanda za su taimaka mata wajen tafiyar da zamantakewarta har karshen rayuwarta. Har Akilu ya yi fakin a kofar gidansu tana wadannan tunaninnikan. Sai da ta ji motar ta daina motsi ta farga. "Sai watarana Akilu, sai watarana! Daga yau an gama!!!". Murmushi ya yi, a ransa yace “yanzu aka fara dai”, a fili kuma ya ce, "Ranki ya dade mungode, Allah ya kyautata rayuwarki,yadda ki ka kawo karshen matsalar ubangidanmu Allah ya kawo karshen matsalolin rayuwarki.Allah ya kara wa Ameena lafiya". "Amin Baba Akilu, sai watarana!". Ta fadi tana 'waving' dinsa ta shige gida tana jan kafarta, sakamakon nauyin data yi mata, ga wasu tawagar hawayen sabo da suka shimfido mata, shi kansa Akilun kewarsa take, zuciyar ta na gaya mata ta rabu dasu fa kenan, ta bar gidan gwamnati har abada! Alfarmar ubangidan nasu ba mai yiwuwa ba ce agareta, ba shine irin mijin da ya dace da ita ba, ina ita ina kishi da Anty Laila? Aka ce yaro tsaya matsayin ka kada zancen ‘yan duniya ya rude ka! Kwarya ta bi kwarya in tabi akushi sai ta fashe. Jikas, (as a governor) mijin mata da yawa ne ba shine Mr. Right dinta ba. Tunaninta yafi karfi ga cewathe best is yet to come.....A ra’ayin ta data tsara a zuciyarta tun lokacin da ta soma mallakar hankalin kanta:Tanaso ta auri mijinta ita kadai don tanada tsananin kishi, yaro matashidaidai ita, wanda bai mallaki komai ba sai kwalin ilmin boko, wanda bai taba yin aure ba, akanta zai fara, wanda zasuyi fafutukar rayuwa tare su gudu tare su fadi tare su tashi tare, amma Jikas ai mijin mace hudu ne. A lokacin da ta tuna alkawarin data yiwa Goggo kafin ta barta ta fara aikinsai hankalinta yayi mugun tashi...... “Duk mijin da ya fara zuwa ko waye zata bar aikin tayi aure.....”. Akan haka suka tsaya itada Goggo, kafin ta amince mata zuwa gidan gwamnati. Ta tuno da maganganunnoble laureateZainab Alkali inda take cewa. “Dreamsare conceived, but not all dreams are born alive, some are aborted. Others are stillborn”. (Mafarkai kamar ‘ya’ya suke, ana yin cikin su, amma ba duka ake sa’ar haifesu a raye ba, wasu tun suna ciki ake zubar dasu, wasu kuwa a mace ma ake haifarsu). In hakane ba lallai ka samu duk abinda kake so ba a rayuwa kuma ka zauna lafiya??? Akilu direbadai sai bada kayanta ya yi aka shigo mata da su don ya lura kwata-kwata bata cikin hayyacinta har ta shige gida. Abin ya wuce ace kewa ce kadai ta sanya ta a wannan halin, ga dukkan alamu akwai wani muhimmin al’amarin a tare da ita kamar yadda suke hasashensa daga ubangidansu. Jikin sa ba laka ya ja motar ya tafi shima cikin kewar Amina.Yana addu’ar allah ya maido ta cikin rayuwarsu bada jimawa ba. Yarinya ce mai matukar kirki, girmama manya da shiga zuciya,wadda ba zuciyar Jikas kadai ta shige ba har ta wadanda ke zagaye dashi sabida halayenta ababen so. ***** Goggonta kadai ta samu a gida, suka yi murnarsu har suka gaji. Wannan karon ma ba ta gaya wa Goggo adadin kudin da ke cikin asusunta ba. Tasan Goggo tsorata zatayi ko ta darsawa ranta zargi, ta dai gaya mata ya biya ta albashinta cikakke, da kudin tantabarunta. Ta ce masa kyauta ta ba shi, ya ce in ba ta karba ba, zai maido mata kayanta. Goggo ta ce, "A'a ba a yi haka ba, ki karba". Ta yi murmushi, "Na karba Goggo". Sun yi sallar isha a daren ranar, bayan Amina ta idar da shafa'i da wutiri ta ji wayarta na kara. Ta dauka ta duba mai kiran 'HAJIYAN JI-KAS' Kamar yadda ta adana sunan, shi ke yawo a fuskar wayar. Ta juya ta kalli Goggo, sai ta ga lazimi ta ke, da cikakkiyar nutsuwa, da ladabi mai yawa ta amsa kamar yadda ta saba amsa wayar Hajiyan. "Assalamu alaikum Aminatu". "Amin wa'alaikumus-salam Hajiya, Ya ya Ameena?" Hajiya ta ce, "Kya bari mu gaisa ai, Uwa Mai Ameena, kwana uku baya ya kamata in bugo wayar tun sanda na ji Ameena ta mike a kan kafafunta. To garin in kira ki saboda zumudi da farin ciki hannun nawa karkarwa ya shiga yi na jefa wayar tawa a ruwa, sai yanzu da ya zo ya hada min wata (tana nufin Ma'arouf). Ubangiji shi Ya nufa, amma da kokarinki da sadaukarwarki. Mun gode, madalla Amina. Ba ni mahaifiyarki in tana kusa mu gaisa". Amina ta mika wa Goggo, "Hajiyan Ji-kas ce". Ba tun yau ba Goggo Hauwa ta san Hajiyan Ji-kas, Amina ta sha hada su su gaisa idan ta zo (weekend) Hajiyan ta kira ta. Don haka da sanayya suka gaisa Hajiya ta yi mata godiya a kan taimakon da Dr. Amina ta bawa jikarta. Goggo ta ce, "Babu godiya a tsakani, ai aikinta ne. Ko ba ta yi wa Ameena karama ba za ta yi wa sauran al'umma ko ba ko sisi balle Amina da ake biyanta". Ita dai Hajiya Saude godiya ta ke tana karawa har suka yi sallama. A ganinta basu da abinda zasu biya Amina duk tarin dukiyar su. **** Kwana daya, biyu, Amina ba ta da kuzari, ta rasa kwarin gwiwar isar da sakon Ma'arouf ga Goggo. Ta barwa zuciyarta wannan al'amari mai girma da ya tunkaro ta. Ta kasa aiwatar da abubuwan da ta saba yi yadda ya kamata saboda tunanin amsar da za ta bai wa His Excellency da kwarin gwiwar sanar da Goggo. Tuni dai zuciyarta ta riga ta gama nutso da ninkaya cikin maliyar So. So irin wanda ba za ta iya fassarawa ba. Tun tana ignoring fassarar abubuwan da take ji din da ganganakan Ma’arouf, da kalubalenta kala-kala marassa madafa, ba shine Mr. Right ba da sauransu, wannan da wancan,har ta yarda ta fassarasu da Son Ma’arouf ne. Idan akwai abinda yafi Mr.Right to Ma’arouf to Ma’arouf Ji-Kas ne. Ta yarda da Zainab Alkali. Wanda ba lokaci daya ya shiga zuciyarta ba, ya dade yana kassara ta, yana huda kasusuwa da bargonta a hankali a hankali (like a biological VIRUS). Bata bashi muhimmanci ba ne tun lokacin da ya soma samun muhallin, don sanin cewa abune da ba zai taba yiwuwa ba, zuciyarta yaudararta ta ke yi. Don ba ta taba ganin wata alama da ke nuna hakan daga Ma'arouf Ji-kas ba. Mutumin da ko cikakken kallo ba ta ishe shi ba a baya. A hankali suka soma shakuwa, shakuwa mai yawa akan siyasarsa, duk da haka babu wata alama makamanciyar wannan data gitta a tsakaninsu. Sannan kuma ta kan tuna matarsa 'yar kwalisa Anty Laila. Ina ita ina iya shiga kishi da wannan kasaitacciyar mace? Wadda bata ajiye kanta anan kusa ba? Yaushe ma ta kai wannan matsayin banda giggiwa irin na zuciya? Beside, tana jin kamar lokacin yin aure ya wuce mata, babu wanda zai kara cewa yana sonta daga shekaru ashirin da shida. Tunanin komawa karo ilmi ne a ranta da zarar ta bar gidan Gwamnati, don haka ta dauko gingimemen bulo da katon dutse ta danne gurbin da kedarsa soyayyar Ma'arouf a zuciyarta (A baya kenan). Amma daga kwana uku bayada ya furta neman soyayyarta da ra’ayin sa na son aurenta da kansa ba waya ba ba aike ba, gaba daya sai ta ji kamar an sauke wannan bulo da dutsen da ta adana tsofaffin ajiyarta suka fito suka yi yabanyakoriya sharr suka lullube zuciyarta. To amma da wane harshe za ta gaya wa Goggo? Ya ya Goggon za ta dauki al'amarin? Kada ta zarge ta da cewa tun can baya soyayya ta ke yi ba aikinta ba, duk da ta san Goggo ta yarda da ita dari-bisa-dari. Hasashen zuciyarta ne wannan kawai. Gaskiyar magana shi ne, kunyar Goggo ta ke ji. Bari ta yi shiru abinta kawai. A ina zai ganta har ya bukaci jin amsa daga bakinta? Ta san yawan ayyukan da ke kansa ba za su bari ya kara tunawa da wata Dr. Amina ba. Don haka ta like bakinta da (super glue) ta shiga sabgoginta da kula da tantabarunta. Lokaci-lokaci littleAmeena Ma'arouf na fado mata a rai, sai tace cikin ranta, ko an kaita makarantar kwanan? Ko ba’a kaita ba? Ko me take ciki? Amma in ta tuna tana hannun Hajiyan Ji-kas sai ta ji damuwarta a kan kewar yarinyar ya ragu. Tana da yakinin tana samun kauna da kulawa yadda ya kamata fiye da na Babanta. Ta lura shi kansa ba ya alakanta rayuwar diyarsa da matarsa Laila, ko me ye dalili? Oho! ***** MA’AROUF JI-KAS! A ofishinsa yake, bayan tafiyar Dr. Amina da kwana uku. Mutanen da ke son ganinsa sun fi dari. Ayyukan da ke gabansa wadanda suke bukatar ya sanya hannu (signing) sun fi guda hamsin. Amma me? Ya kasa yin ko daya, ya kasa (attending) ko mutum daya. Idan ya tuna in ya koma gida ba zai tarar da Dr. Amina da Ameena ba sai ya ji wani irin kadaici da damuwa sun taru sun lullube shi. Kamar shikadai ya ragea duniyar Subhana. Ya kasa aiwatar da komai wadanda ya saba yi a rayuwarsa. Hatta kiran waya damuwa yake jefa shi don jira yake ko Amina za ta turo masa sako, ko ta kira shi ta ba shi amsa kan bukatarsa, na zamowarsu abokan rayuwar juna na har abada, amma har aka cinye kwanaki ukun, babu 'text' ko wayar Dr. Amina. A karshe ya gane mafitar daya ce, ya bar komai ya ajiye komai dake gabansa, ya yi yakin mallakawa zuciyarsa abin da ta ke so da kauna, wannan preciousgem mai daraja wato AMINATU don ya zauna lafiya cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, wata da watanni yana dannewa, yana boye halin da zuciyarsa ke ciki. Amma yanzun an zo wani limit(geji) da ya fahimci cewa, ci gaba da dannewar nan ba abin da zai haifar a gare shi sai (psychological depression), mafitar kawai ita ce mallakarAMINA. Wadancan falsafofin na son rai wato nagudunauren mace fiye da daya, a yau ya sauke su a gefe, ya cinna musu ashana ya kone su kurmus! Dama bai taba rantsuwa a kai ba. Ya kan fada ne dai kawai a matsayin ra’ayin sa. Ya fahimci in ya tsaya ta jin amsa daga bakin Amina zai shekara bai ji ba, soyayyar da ke cin zuciyarsa ta zauta shi. Ya yarda ko Amina ba ta sonsa to ba ta kinsa. Ya amince zai aure ta ko da ba ta sonsa, in dai har zai mallake ta cikin gidansahe believed zai samu soyayyar a hankali, kai ko tana kinsa din ya amince ya aure ta a hakan, in dai za ta dawo cikin rayuwarsu shi da Amina, ta bar downstairs ta koma upstairs wannan shi ne babban burin zuciyarsa a yanzu, ya yanke shawarar sauke rawanin Gwamna ya nada na yakin neman soyayyar Amina da aurenta. Ya dauki wayarsa ya kira mataimakinsa Prof. Yusuf Bugaje, ya ce duk ayyukan nan da ke gabansa ya yi masa, ya ci gaba da handling komai, zai yi hutu na kwanaki uku. Farfesan ya amsa da girmamawa komai ya koma hannunsa. ***** Ilya ya shigo gidan da yammacin ranar da Amina ta yi kwanaki uku da dawowa. Goggo ta shiga makota barka. Ya ji dadin samun Amina ita kadai. Tana suyar awara ne da ta tashi da marmarinta tun azahar ta ke aikinta. Ta gama soyawa tana kwashe wa Ilya ya tsaya a kofar kicin din. "Anty Amina, ina nawa? Raina ya biya wallahi". Ta ce, "Dauki guda daya, shugaban kicin din gidan Gwamna da kwadayi, ban taba ji ba". Ya kyalkyale da dariya ya mika mata farar leda. "Ungo ga guzurin gidan Gwamnatin na yo miki ke ma, don na san kwana biyu kina kewarsu". Ta galla masa harara, "Wa ya ce da kai ina cin abincinsu? Wanda na saba ci shi nake dafawa da kaina". Ta dai karbi ledar ta leka, (shawarma fal, soyayyun kaji da samosa, springroll da wani dunkulallen cake). Ita da ta ke cewa ba ta ci, sai ga ta tana cika baki tana taunewa tana hadiyewaharda lumshe ido, kunnenta har motsi yake. Ilya ya dinga yi mata dariya, ya yi kyau ya yi kiba, ya yi tsaf farinsa na Fulani ya fito. Amina har mamaki ta ke yadda Ilya ya murje cikin 'yan watanni ya waye sosai, kamar ba shi ba. Ya ja kujera 'yar tsugunne ya zauna, "Ke muhimmiyar magana ta kawo ni, gidan Goggo ya kammala fa, har an yi fenti. yanzu kudaden abubuwan da za a zuba za ki tura ta account dina, ga takardar abubuwan cikin gidan su kujeru, air-conditions, kayangado, labulaye, cooker gass, carpet, kayan kicin da sauransu. Ga list din da kudin komai a rubuce a kasansa". Amina ta karba tana dubawa, ta yaba da komai, Ilya dan baiwa yana ba ta mamaki, ya san kaya na zamani masu tsada, amma da quality da nagarta, ban sha'awa da burgewa. Ta zabi kalolin da ta ke so wanda Goggo sune kalolin da ranta ke so, ruwan madara da brown, ta ce, "An jima zan sako (transfer) in na gama ciye-ciyen nan, yunwa nake ji yanzu, motar fa?" "Mota tuni ta iso tana rumfar adana motoci na gidan, kamfanin ‘Julius-Berger’ na hayo ta hanyar wani abokina a gidan gwamnasukayi ginin cikin sati biyu.Yanzu har ya fara bushewa. Nafi so sai ta je can ta same ta. Amma ya za mu yi mu daga Goggo da komai nata daga gidan nan ba tare da ta sani ba? Sai dai mu dauke ta mu kai ta har dakin barcinta?" Amina ta yi dan tunani, "Ta ce min za ta Shira jibi bikin 'yar Kawu Bilya, kuma tun safe har dare don haka ka yi kokari daga yau zuwa gobe a saka komai a muhallinsa. Washegarin dawowarta da safe zan ce mata ta raka ni asibiti duba matar Kwamishina Turaki ta haihu na san ba za ta ki ba, Astagfirullah na shirya karya". Ilya ya yi dariya, "A kan abin alkhairi ki ka yi karyar ai, Allah zai yafe miki. Gama ci maza ki turo min". Ta ce, "Saura kai Ilya. Gidan nan na ba ka shi halak malak. A rushe shi ko a yi furnishing dinsa da kyau ya zama na zamani ka nemi mace haka ka yi aure Ilya. Ni zan dauki nauyin ginin.Ni dai burina ka yi aure Goggo ta ji dadi, tunda nawa babu rana". Ilya ya tsura mata ido, kwalla suka cika idonsa. "Dr. Amina hidimar ba ta yi yawa ba? Na fa tsaya da kafafuna yanzu ina tari tunda na fara aikin nan". "Ba ruwana da aikinka Ilya. Burina in faranta wa wadanda suka tsaya min a rayuwa ta a lokacin da na rasa mahaifi. To Ilya kai ne mutum na biyu bayan Goggo da ku ka tsaya wa ilmina. Ba ni da abin da zan biya ka sai dai in kamanta ihsani. Baba Talatu zan turo maka kudi ka ba ta ta yi duk abin da ta ga dama da su, ta tallafi ilmin marayunta. Haka Inna Zulai. Za ka raka ni Shira kuma in na kara hutawa in ba su abin da ya rage min a account bana bukatar komai a rayuwa ta, I'm o.k, mota kawai zan saya saboda zuwa aiki". Shi dai Ilya ya kasa magana daga karshe ya yi ta sanya mata albarka kamar shi ya haife ta. ***** Duk shawarwarin da suka yi ita da Ilya haka suka aiwatar da su. Goggo ta budi ido ta ganta a wani dankareren gida mai hawa daya (flat house). Ga dalleliyar mota a rufe cikin tamfol an ce ta kai ta unguwa ce. Duk tarkacenta Amina ta bai wa Inna Zulai ta zuba mata sabo. An karo mata mai aiki sun zama biyu sunanta Rabi, suna ci gaba da yin sana'ar ta Goggo, ita kam nata umarni ne da taimakawa yanzu, ga samari maza uku masu (barrow) da suke aiki tare da Ilya tuntuni sun tsaya madadinsa. Goggo ba ta da bakin gardama Amina ta gama komai, ta cika burinta na kyautata rayuwar Goggonta a shekarun girmanta kamar yadda ta shanye shekarun kuruciyarta cikin aikin karfi da wahala wajen gina rayuwarta da inganta future dinta. Hajiya Hawwa tayi kuka sosai don farin cikin haihuwar 'ya irin Amina, daya tamkar da goma, mace da kamar maza. Ta sanya mata albarka har kamar harshenta zai bushe. Ta ce da Amina, "Burina daya ne yanzu a rayuwa, Allah ya nuna min mijinki kamin ya dau raina. Saboda kyautayinki ga iyaye Amina jikina yana ba ni Allah ba zai barki haka ba, zai ba ki miji na gari wanda kowa sai ya daga ido ya kalla, wanda zai rike ki da maraicinki da amana ko bayan raina". "Wai Goggo me ya sa ki ke kira ma kanki mutuwa ne? Tsufa ki ka yi? Life began at fourty? Insha Allahu sai kin dauki jikokina ba ma 'ya'yana kadai ba Goggo. Ki daina cewa bayan ranki, zuciya ta tana girgiza". Goggo ta ce, "Na bari Amina, Allah ya ci gaba da raya mu tare, rayuwa mai tsayi da albarka. Ya ji kan mahaifinki, Ya yi masa rahama, Ya ba shi aljannah albarkar faranta min da ki ke yi". Amina na dariya ta ce, "Amin-Amin Goggona". Goggo ta yi dan jim tana tunani, kafin ta tsare Amina da ido. "Ina ki ke samun wadannan makudankudi haka? Wannan ya fi karfin albashinki ko ninki goma ne, musamman ginin gidan nan, da motar nan". A wannan lokacin ne Amina ta yanke shawarar yi wa Goggo gaskiyar bayanin komai, har wayar da suka yi da Dr. Turaki, ta ci gaba da cewa, "Dr. Turaki ya taba gaya min cewa, da ma ya yi alkawari duk likitan da Ameena ta warke a hannunsa ta sanadinsa, zai ba shi tukwici wanda shi kansa bai sani ba, kuma ya ce a hakan ma ya rage ne kamar yadda shi kwamishina ya ba shi shawara kasancewa ta mace, kuma bukatuna da kudi kadan ne. Na nemi shi Turakin mu raba ya ce wallahi sam, kuma in daina damuwa, a cewarsa a wurin Ji-kas wannan kamar an fidda allura ne daga cikin kogi, sama da haka ma yana bai wa wanda Allah ya ci da shi ko ba su yi masa aikin komai ba". Goggo ta yi murmushi tana kallon Amina tana ta bayani tana mamakin wautarta watarana, kiri-kiri ga alamomi masu yawa da ke nuna Turaki yana sunsunarwa abokinsa takalmi, amma ba ta gane komai ba. Komai ya gaya mata sai ta hau kai ta yarda. Wannan kulawar da yake ba ta, Ubangidansa yake yi wa. Shi din ne dai ba ta da tabbas din hakan daga gare shi tunda ba ta taba ganinsa ba, sai dai ta tsinci abubuwan da ke gasgata mata tunaninta daga kalaman da Amina ke yi a kanshi kullum, kwashe rabin tantabaru a wane dalili? In tantabaru yake so ya je kasuwa ya saya mana, sai na gado? Jikinta ya ba ta akwai abin da yake son yi wa Amina da tantabarun nan don ta amfana, amma shi me zai yi da su? Ko kuma yana son bullo da alaqa kyakkyawa a tsakaninsu a lokacin shine dalilinsa na cewa lallai ta bashi abinda tafi so a rayuwarta. Ta nisa a hankali ta dubi Amina, "Na yarda da ke Amina". Amina ta ji dadin furucin Goggo, don ba ta so ta fahimci akwai wani abu binne a zuciyoyinsu ita da Ji-kas din. Tunda ta bangarenta hakan ba zai taba yiwuwa ba duba da hujjojinta masu karfi data fada a baya. Ta nashi bangaren ma watakila ya manta da ita, ya bar maganar, ganin har kwanakinta goma a gida babu wayarsa, text dinsa ko aikensa. Damuwa da tunanin kada hakan ta kasance na kassarata, na sagar mata da gwiwa, taji kamar an bubbuge gabban jikinta da murfin kwano, amma hakan ba ya hana ta jarumtar daukar kwagirita fatattaki damuwar da tunanin daga gabanta, ta cigaba da harkokinta. Sati biyu kenan da gama aikin Amina a gidan gwamnati, ba Ma'arouf ba wayarsa, babu ko dan aikensa. Ya rage saura sati biyu ta koma bakin aikinta a asibitin koyarwa na Abubakar Tafawa Balewa. Duk da tana fatattakar tunanin da damuwar da rashin jin nasa ya jaza mata, wani lokacin zuciyarta na ingiza ta da ta kira shi a waya ta ji ko lafiya? So ba karya ba ne...... Gashi ya faru da Amina. Kuma ba abu ne da ke wanzuwa a duk sanda mutum ya so ba, a’ah, abu ne dake faruwa a duk sanda ya so akan-kansa, ya gudanar da tunani ya sarrafa gangar jiki... To hakan ce ta faru da Amina da Engnr. Ma'arouf Ji-kas. Juriya da fin karfin zuciya su suka hana Amina kiran Ma'arouf amma ba zuciyarta ba. Ina Ma'arouf Ji-kas din??? **** Yana can cikin takunkumin abokinsa, amininsa kumakwamishinansa consultant Dr. Usman Turaki, wanda ya haramta masa tuntubar Amina ko zuwa inda ta ke ko yi mata aike har tsayin sati biyu. Ya je masa da bukatarsa ne na ya shige masa gaba su dumfari neman auren dalibarsa. Ya gane cewa shayi ruwa ne, ba zai iya rayuwa cikin sukuni ba tare da ya aure ta ba, Ameena ta dawo hannunta. Hakan ne kadai zai sa ya ji shi cikakkensa (complete) kamar sanda Aisha ke raye, amma yanzun he’s totallyincomplete, shattered! Turaki ya yi dariya a boye, ya yi farin ciki a fili da boye, amma bai bari ya gane ba. Ya yarda 'LOKACI' ba abinda ba ya canzawa a rayuwar dan adam, kuma babu wani yanayi da yake tabbatacce ga dan adam, in ji Dr. Usman Turaki. Yau ga lokaci ya canza Ma'arouf Ji-kas, wanda shi da ma ya tabbata watarana za’a yi haka. Watarana irin wannan na nan zuwa. Amina ba macen da za a zauna da ita na lokaci kalilan a bari ta wuce har abada ba ce, ba tare da an janyo ta ta dawo ba. Ba don kyawunta kadai ba, sai don dabi'u da halayya, wadanda in ya auna sai ya ga duk irin na Ma'arouf Ji-kas ne, kuma ita kadai ce ta dace da mutum na gari mai kyakkyawar zuciya irin sa. A dai cikin matan da ya sani a fadin duniya. Kasancewarsa likita fitacce, wanda ya yi alaka da mata kala-kala a wajen karatu ne, a wajen koyarwa, a wajen aiki ne, a wajen (counselling) da sauransu. Ga abin da ya ce da ubangidan nasa, a lokacin da ya zo masa da wannan bukatar tasa na ya shige masa gaba ya auri likita Amina. Turaki bai yi masa shakiyanci ba, ko tuna masa yadda suka yi a baya, ko don yanzu ubangidansa ne? Oho! Sabanin da kafin ya hau kujerar Gwamna sanda suke abokan makaranta. Ba irin shakiyancin da baya yi masa. Har ce masa yake shi ba namiji bane saboda yadda yake nuna halin ko’in kula ga ‘yammata.Da hannu bibbiyu ya karbi maganar, amma in ya tuna yadda suka yi da Ma'arouf a baya sai dariya ta shaqe shi, yayi abarsa shikadai ya more. "Zan taimaka, kuma zan shige gaba Yaa Maulaaya, to amma sai ka yi min alkawarin ba za ka kara tunkarar Amina ba, ta waya, ta ido da ido ko ta aike sai bayan kwana goma sha hudu". Ma'arouf ya zaro ido, "Idan kuma wani ya riga mu fa? Me ye hikima cikin hakan? Kai kamar ba ka tausayi na Turaki? Sati biyu? Yau kwana uku dubi yadda na koma ina ga sati biyu? To amma ban san me ye a zuciyarka ba, me ye hikimarka cikin hakan? Na san dai (your brain is sharp) fiye da ni ko a makaranta”. “Haka ya kamata ka tambaye ni, ba idan wani ya riga mu ba. Do you think a yanzu Amina za ta iya auren wani ba kai ba?" Ma'arouf ya dube shi idanu a russune na neman karin bayani. Ya yi murmushi, "Ita ma tana sonka Yaa Maulaaya, babban alamun so sune kunya da jin nauyi. Jin nauyinka da Amina ke yi yayi yawa. Za ka iya hada yadda ta ke mu'amala da ni da yadda ta ke yi da kai? Kwata-kwata daina tunanin wani zai riga mu, sai dai a riga mu a fatar baki, amma ba a riga mu a zuciya ba. Hikima ta a nan shi ne, a sati biyun nan ta huta, ba daga komawarta gida sai neman aure ba. Sannan a sati biyun nan za ta shiga cikin kewarka da damuwa da rashinka, za ta yi kyakkyawan tunani akai ba na hanzari ba. Zata tantancewa zuciyarta aya da tsakuwa na cewa son ka take ko ba son ka take ba? Idan mukayi hakan (I’m sure) da mun je za ta amshi bukatarmu ba tareda jan rai ba, don soyayyar da ke zuciyarta ta yi zafi har ta fara kona ta. Sai dai ina tabbatar maka ba za ta taba iya fadawa mahaifiyarta ba, a dai halinta na kawaici da alkunya da na karanta. Sai dai mu mu sanar da ita. Bayan sati biyun, ka san yadda ku ka hadu daga kai sai ita, ka kwantar da kai sosaika ji amsarta, ku tattauna,ku aminta da juna daga nan sai mu shiga neman aure da karfin mu". Dole kan ba yadda zai yi ya amince da shawarar Turaki, amma fa sati biyun nan ya gansu kamar shekaru goma sha hudu. Dararen cikinsu sun kasance masu matukartsayi a gareshi. Sai ya kirkirarwa kansa yin tafiye-tafiyen kauyuka duba 'projects' don rage tsayin nasu a idanu sa har zuwa sati biyu. ***** BAYAN SATI BIYU Ranar da sati biyun nan ta Ma’arouf ta cika Amina ta shirya za ta tafi Shira gaido Baffanninta, don ta tabbata in ta koma aiki ba za ta samu lokaci ba. Ilya ke janta a karamar motarta data siya (Kia Picanto) kasancewar hannun nata bai gama fadawa ba. Gida-gida ta bi ta gaishe su, kowa sai murnar zuwan Dr. Amina yake yi don an san ba ta zuwa hannu rabbana. Balle yanzu da labari ya iskesu ta zama attajira ta ginawa Goggonta dallelen gida da mota, ta kaita Hajji. Haka kuwa, ba wanda bai samu rabonsa daga Amina 'yar Mas'udu ba, Baffaninta kuwa jarita basu mai tsoka na makudan kudade ta ce, su kara a gona ko su bude tireda. Amina ta sha albarka har ta gode Allah wajen tsofaffinta. Da la'asar suka kamo hanyar dawowa. Goggo ta jaddada mata lallai ta je gidan Kawu Sule ma, don haka da suka shigo cikin gari ta gaya wa Ilya su je. Amina dai sai da tambaya suka gane gidan Kawu Sule saboda yadda ya bi ya bushe kyamas ba shuka ko daya, ya ratattake ya lalace ba maigadi ba motocin nan nasa na alfarma. Haka dai suka boye mamakinsu suka shiga. Ashe cikin gidan har ya fi wajen lalacewa. Kai! Komai na Duniya bashi da tabbas. Atika Babar Hafiz wadda ita ma duk ta canza wahalar rayuwa ya bayyana a jikinta ta yi musu iso dakin Baffan nata Sule. Yana kwance a kan wata tsohuwar kujera. Ta gaishe shi cikin ladabi ya amsa sai kuma nan da nan ya kama kuka yana rokonta gafara a kan yadda ya yi watsi da rayuwarta. Ya ce, “yanzu alhakin zumunci ya kama ni, dubi yadda karayar arziki ta rufto mini rana daya. Na hada duk abin da na mallaka nasa a wani sari na auno kaya jirgin ruwan da ya dauko su ya nutse". Ya ci gaba da sharar hawaye yana rokonta gafara, fadi yake, "Ban kyauta wa Yaya Masa’udu ba, ba abinda bai yimin ba a rayuwa, ‘yar kwaya daya na kasa rike masa a bayan ransa. Idan na mutu ba ki yafe min ba, ba ni da abin da zan iya yin uzuri da shi ga dan uwana, son zuciya kadai da rudin abin duniya". Ta tabbatar masa da cewa, da ma ita da Goggo ba su kullace shi ba. Ya ci gaba da gaya mata, "Ba don Hafiz ba, da abin da za mu sanya a bakin salatinmu ma babu. Ga shi shi kuma mace ta mallake shi, sai dan abin da ta ga dama ta ke sa wa ya ba mu. Ba kuma ya nan yanzu an canza masa wajen aiki zuwa Adamawa". Haka Amina ta baro gidan Kawu Sule bayan ta yi masa ihsani mai yawan gaske wanda zai dade bai manta ba. Suna tafe a mota suna tattauna al'amuran rayuwar duniya masu ban tsoro. Ta tausaya wa Kawu Sule, ta koka yadda al'umma muka yi watsi da martabar zumunci, kuma a haka wai muna burin shiga aljannah. Bayan duk martabar zumunci da darajja shi da Allah (S.W.T) ya yi, Ya yi mana umarni da mu kyautata shi, yana daga cikin manya-manyan hanyoyin shiga aljannah. Allah ya sa mu dace, amin. Ba su iso gida ba sai karfe takwas na dare. Wata mota ce 'yar karama mai duhun gilasai 'tint' a kofar gidan Goggo, ta dan fara tsufa duk ta karkarce kuma ba a shaida wadanda suke cikinta saboda bakaken gilassanta. A daidai sanda Ilya yake kokarin sanya motar a inda ake ajiye ta. Amina ta ce, "Hala Goggo ta yi baki ne?" Ya ce, "Ko kuma sabon saurayi ki ka yi ba?" Ta harare shi ta bude kofar bangarenta ta fita. Kanta tsaye ta shiga cikin gida, ta baro Ilya a waje. Ya juya kan motar ya nufi gidansu budurwarsa Sadiya. Sanya kanta falon Goggo ke da wuya ta ji wani sassanyan kamshi, ya gauraye da sanyin iya kwandishan, wanda a cikin kanta ta dade da saninsa, ta yi (marking) dinsa a matsayin kamshin mutum daya, domin bayan shi ba ta kara jin mai irinsa a ko'ina ba, kai ka ce kamfanin da ya yi shi mutum daya ya yi wa shi, ya kuma gargade shi da kada ya rabar da shi da sauran al'umma. Gaban Amina ya yi wani irin faduwa, saura kadan dunduniyar dogon takalminta ta kayas da ita garin cirewa. Ba don mutane ukun da ke falon sun dago sun dube ta ba da tabbas ta juya ta bar gidan. Mutum na farko da ba ta taba sanya wa a ranta za ta gani tsakiyar dakin Goggonta ba. Sanye da kaftan na shadda mai taushi, fara kal. An yi aikin zarenta da zare silver, hular kansa ma fara ce kal, a hannunsa na hagu agogon (swatch) ne mai farar fata. Ya saya kwayar idanunshi cikin farin gilashin ido siriri mai garai-garai wanda ya kara fiddo ilhama da cikar zatinsa. Dogon hancinnan ya tsaya kyam akan fuskarsa a tsakanin fararen idanunsa. His Excellency Ma'arouf Ji-kas ne. A kusa da shi kwamishina Dr. Usman Turaki ne. Shi kam ya sha suit ya tsuke abinsa, har da neck-tie. Da shi ta fara hada ido don shi ke fuskantar kofa. Ma'arouf din bayansa ke kallon kofa. Sai da ya juyo jin karar takun takalminta da ya kusa kayar da ita, sannan ta shaida fuskarsa. Goggo ta sha lullubi da katon mayafinta ta takure can gefe, Dr. Amina ta samu kanta cikin rikicewa, ta rasa me za ta yi? Shiga za ta yi ko fita za ta yi? Jikinta ya hau mazari. Sallamar da ta fara yi ma makalewa ta yi a makogaronta ta hadiye abarta. Ta kasa gasgata abin da ta ke gani; Ma'arouf Habibu Ji-kas shi ne ya tako kafafunsa har dakin Goggonta ya zo neman aurenta!. Dr. Turaki ya fahimci halin da ta ke ciki na razana da rashin sanin abin yi saboda ganinsu unexpected (ba zato). Ya dauko murmushin karfafa gwiwa da sanya (courage) irin na Malami ga dalibinsa mai hazaka da yake matukar so, ya shimfida a kan fuskarsa. "Shigo Dr. Amina, shigo mana, ai mu ba baki ba ne. Ko kuwa baki ne???" In ji Dr. Turaki. Ta girgiza kai, sannan cikin sanyin jiki ta cira kafa kamar wadda kwai ya fashewa a ciki rike da takalmanta ahannuta shiga falon. Ta tsugunna gaban Dr. Turaki ta gaishe shi, abin mamaki ta kasa isa inda Ma’arouf yake balle shima ta gaisheshi, sai ta wuce dakinta wanda ke kusa da dakin baccin Goggo mai ban sha’awa. Abinda ta kashe wa dakin baccin Goggo bai kai wanda ta kashe wa nata dakin ba. Wannan abu da Amina ta yi, ta gaida Turaki ba ta gaida Ji-kas ba ya fusata Goggo, har kunya sai da ta ji. Ya kuma tabbatar mata da abin da suka fada mata, wato akwai kauna da soyayya a tsakaninta da mai girma Gwamna, wanda ita da ma tuni ta sanya wa zuciyarta akwai din. Ta dauka Aminan ce ba ta sani ba, ko ba ta fahimta ba, ashe ita Amina ke wa kallon sakarai, Allah ya ba ta mijin da ta ke hana idonta bacci tana roka mata har a dakin Allah, ta tattara maganar ta zuba a kwandon shara yadda ta saba. Bayan alkawarin da ta yi mata kafin ta barta ta fara aikin nan, na cewa, duk wanda ya zo na farko za ta bar komai ta yi aure, yau me raba ta da Amina sai Allah. Sun dau tsawon lokaci tare da Goggo, har karfe goma na dare. Amina ba za ta ce ga abin da suke tattaunawa ba. Ta kwanta lamau ta yi rigingine a gadonta ta ja bargo mai laushi ta rufe jikinta, kirjinta in ban da dukan tara-tara ba abin da yake yi. Shi kenan ta faru ta kare, wai an yi wa mai dami daya sata, tunda zance ya zo kunnen Goggo, ta lissafa kanta cikin AMAREN BANA (in ji Aziza Idris Gombe). An zuba wa Goggo magani a kan ciwon da ya addabe ta. Ba ta san yaushe suka tafi ba, ta dai bude ido ta ga Goggo tsaye a kanta tana bubbuga ta sabida barci ne ya dauke ta ba da saninta ba, mai cike da mafarkai marasa kan-gado, wai Goggo na zane ta da wayar rediyo. Tana bude ido kuma ta ga Goggon tsaye a kanta tana huci. Da sauri ta mike zaune, ta koma bakin gadon ta takure ta sunkuyar da kai. "Sannu, sannunki likiciyar duniya". Amina ta yi shiru, kai a kasa. Goggo ta ce, "Alkawarin da muka yi da ke kenan? Yaushe ki ka koma boye min sirrikan rayuwarki Amina?" Amina ta soma hawaye, "Wallahi Goggo ba abin da na boye miki". "Daina rantsuwa, kin gaya min Baban Amina ya yi miki maganar aure? Kin gaya min ya ba ki kwanaki uku ki yi shawara da ni?" Amina ta yi shiru tana share hawaye. Goggo ta ce, "Ba da ke nake magana ba Amina?" Ta saki kukan gabadaya sosai, "Goggo na kasa ne, maganar ta yi min nauyi a baki, sannan ina gudun kada kice soyayya mukeyi tuntuni wallahi ba haka bane, bansan ya zanyi miki bayani ki fahimta ba, abin is mysterious(wanda ya gagara fahimta)". Goggo ta ji zuciyarta ta fara hucewa. Ta zauna gefen gadon itama, "Amma kin san burina ki yi aure ko Amina? Duka naki burikan na lamunce miki kin cika su, ni me ya sa ba za ki cika min nawa ba in samu cikon nawa farin cikin? Bayan na haihuwar 'ya ta gari da Allah Ya ba ni, idan na mutu ban ga aurenki ba alhalin Allah ya ba ki mijin auren, ke ce ki ka sa kafa kika shure, ba zan yafe miki ba Amina". Ita ma ta soma kuka, ta sanya fuska cikin mayafinta. Hankalin Amina ya yi kololuwar tashi, ba kankanin abu ke sanya Goggo kuka ba,ko sanda ta rasa mijinta bata ganta tana kuka ba, ta sauko da hanzari ta durkusa a gaban Goggo, ta dora hannu a kan cinyoyinta. Hawaye na zuba daga idonta. "Don Allah ki yi hakuri Goggo, wallahi ko gobe ki ka ce na yi aure zan yi. Na tuba na bi Allah na bi ki..." Sai da Goggo ta yi kukanta mai isarta, cikin dalilin kukanta har dana rashin marigayi mijinta, ta san da yana nan da ko kusa Amina bata kawo wannan lokacin ba a dakin aure ba,sannan ta kai hannu ta daga Amina daga durkuson da ta yi a gabanta tana neman gafara. "Na yafe miki duniya da lahira. Kin amince za ki iya auren Baban Amina saboda Allah ba don wani dalili ba, ko don 'yarsa Amina?" A hankali Amina ta daga kai ta kalli Goggo. "Goggo duk da ina jin nauyinki, amma a yau zan gaya miki, na dade ina son Baban Amina. Amma Goggo ba kya tunanin jama'a za su ce kwadayi ne ya kai mu ga aurensa, ko wani abu makamancin hakan? Ga kuma matarsa wata iriyar halitta mai mugun hali da in ba mutum mai tsananin hakuri da kauda kai ba ne kamar shi (Ji-kas) babu mai iya zama da ita". Goggo ta yi murmushi, "Amina in ki ka ce za ki daka ta mutane ko abin da za su ce a kanki, ba za ki taba kulla wa rayuwarki wani abin alheri ba. Ke dai komai za ki yi, to ki yi shi don Allah da neman yardarSa. Ki tsarkake niyya da zuciya. Ki yi don neman falalar Ubangiji, ki rabu da mutum wanda ko Ubangijinsa ba ya iya masa. Maganar matarsa, ki nemi da ya raba muku gida...". "Hakan ba zai yiwu ba Goggo, har sai ya sauka daga kujerarsa, ma'ana sai (tenure) dinsa ta cika, saboda tsaro". Goggo ta ce, "To ai ni ban san yaushe ki ka koyi tsoro ba. Aminata da na sani mai dabarun zamantakewa ce. Duk da halin nata da ki ke kokawa kin taba ko musayar yawu tare da ita?" Da sauri Amina ta girgiza kai, "Ko sau daya ban taba ba. Mafiya yawan lokuta ma ni dariya ta ke ba ni, saboda abubuwan da ta ke yi na marasa hankali da tsinkaye ne". "Madallah!" In ji goggo, "Ci gaba da zama da ita yadda ki ka zauna da ita tun farko. Na tabbatar miki ranar da ta gaji da kanta za ta neme ki da ku zauna lafiya". Amina ta ce a sanyaye, "Toh Goggo". Hajiya Hauwa ta kawo murmushin lallashi da karfafa gwiwakan fuskarta, tana magana kamar tana yi da karamin yaro. "To tunda mun yi shawarar da ya ba ki kwana uku mu yi, ba ki gaya min ba sai yau, bayan kwana goma sha hudu da ya gaya min da bakinsa. Mun kuma tsaida shawarar, kin amince wa auren bawan Allah irin Baban Ameena, sai ki kira shi ki gaya masa amincewarki, saboda yana cikin damuwa na rashin ji daga gare ki. Ki kuma yi masa gaisuwar da dazun ba ki yi masa ba ki ka wuce shi kai a sama......" Amina ta turo baki kamar kankanuwar yarinya, "Don Allah Goggo ki bari sai in shi ya kira, na yi miki alkawarin zan dauka. Ai sai ya ga kamar neman kai ki ke yi da ni". Goggo ta danna mata harara, "Da me nake yi ba neman kan da ke ba? Kin ga bana son iya shege, ta bakinki suke jira Ilya ya raka Turaki Shira, da wajen Sule. Cikin watanni uku suke so a gama komai ki tare a dakinki". Ta yi ficewarta ta bar Amina tana kakabi da sambatu ita kadai, "Wata ukku Goggo? Sai ka ce wata 'yar tsana???" ***** Sujjada ce kadai Ilya bai yi wa Amina saboda girmamawa da kauna lokacin da Goggo ta fayyace masa ko me kenan a washegarin ranar, Ji-kas nasa zai auri Amina. Ya shirya sati mai zuwa zai raka kwamishina Turaki da waliyyan Baban Ameena Shira wajen iyayenta maza a yanke maganar daurin aure. Allah ne ya yi ba zai hadu da su ba, don da ya sauke Amina bai shigo gidan ba ya kada kan motar ya tafi zance wajen budurwarsa Sadiya. Don bai taba kawowa a ransa sune suka zo a wannan kujajjiyar motar ba. A lokacin ya gaya wa Goggo shi ma yarinyar da yake nema an ba shi, kanwar babban abokinsa ce, an ce ya turo in ya shirya. Yana rokon a yi daurin aurensa rana daya da na Amina, don ya samu tubarrakin ta, ita din ta zamo yarinya mai sa’a mai albarka a rayuwarta. Gidan da ta rushe ta sake gine masa, an gama komai. Goggo ta ji dadi, Ilyanta ma zai zama magidanci, Amina da Ilya za su kawo mata jikoki kwanan nan...... Sai godiyar Allah. Amina a can dakinta bayan fitar Goggo, wayarta ta rike tana jujjuyawa, umarnin Goggo ya yi mata tsauri, ga shi Goggo ta ki karbar uzurinta, ta ce dole ita za ta kira Ma’arouf ta ce ta amince za ta aure shi. Shekarar ta guda tareda Ma’arouf Jikas amma sau biyu ta taba kiransa a waya, kuma duka dalili tayi. Tana son kira na uku ya zama wani dalilin ba wannan ba. "Goggo kin kasa ganewa, jan aji a wurin diya mace ai wani abu ne mai daraja. Haba Goggo ya ya za ki ba ni wannan umarnin mai zafi?" Abin da ta ke fadi a fili kenan ita kadai kamar zautacciya. "Maza masu wuyar samu a wannan zamanin irin Ma'arouf Habibou Ji-kas a ke ja wa ajin Dr. Amina? Anya ba zai tsitstsinke ba?" Wani sako na zuciyarta ya kawo wannan kalubalen. "Banda SANADIN ciwon 'yarsa kina tunanin haduwa da shi ma ko a hanya abu ne mai sauki? Balle har ya yi bad-da-kama ya tako gaban mahaifiyarki da kafafunsa? Zauna nan kina ta jan ajinki Anty Laila ta kwace abinta ya kira ki ya ce ya fasa.......". Ita da kanta sai da ta yi wa kanta dariya. "......Baban Ameena ya maida ni zautacciya saboda sonsa da kaunarsa...!". Abin mamaki sai ga kira ya shigo cikin wayar. Da ma kuma wayar na rike a hannunta, 'JI-QAS' kamar yadda ta yi 'saving' shi ke yawo a madubin wayar. Shidewa ta yi na wucin-gadi, daga bisani murmushi mai taushi ya bayyana a kan siraran labbanta. At last!Ya cece ta daga umarnin Goggo mai tsauri da hasashe daban-daban da zuciyarta ke kawowa akan hakan. Ta tabbata Ma'arouf na sonta, ya damu da ita, ya ajiye rawanin Gwamna ya nada na yakin neman aure da neman soyayya. Ita ta fara yin sallama bayan ta amsa, ta san halinsa shiru zai yi mata. "Kina sha'aninki, Allah ya ja da ranki". Murmushi ta yi, "Bana kowanne sha'ani, Allah ya ja da ran Baban Ameena". "Ina ki ka je har karfe takwas na dare?" Ya yi tambayar ne bada irin muryar da ya soma magana ba, wannan kai tsaye cike da tuhuma yayi maganar. Don haka itama ta kwantar da murya, cikin ladabi da girmamawa. "Mun je Shira ne ni da Ilya gaida Baffannina". A take ya sassauto, ya saki ransa. Ya koma magana da wacan muryar mai cike da kulawa da yayi amfani da ita da farko. Allah ya yi shi da son ka amsa laifi a take in ya tuhume ka. "Da ma ku 'yan Shira ne? Kin fi kama da mutanen gabas". Ya ba ta dariya sosai, "His Excellency kuma mutanen yamma ko?" "Ni kaina ban san ni dan wane gari ba ne. Amma ki bari wataran mu sa Hajiyan Ji-kas a tsakiya ta ba ni gari daya cikin tarin garuruwana". Amina ta tintsire da dariya, "Yanayin rayuwa babu inda ba ya kai mutum. Ka san kuwa Goggo 'yar Sierra Leone ce?" "Haba! Akwai alamun haka. Dr. Amina, ba ta yi kama da cikakkiyar Hausa/Fulani ba. Wannan tsayin... wannan dogon hancin... wadannan manyan idanun... I'm always assessing daga ina Amina ta samo su???" Ta kai hannu kamar yana ganinta ta rufe fuskarta tana dariya. Bai taba yi mata kallo uku a lokaci daya ba, amma ashe a kallo dayan yana gama kare mata kallo ne. Yadda ya saki jiki yake magana da ita a yau ya ba ta mamaki, ya kuma faranta ranta. Shi kansa har mamakin kansa yake yi. "Well, ina cikin wani irin nishadi da ban taba tsintar kaina a cikin irinsa ba Dr. Amina. Kullum zuciya ta a takure ta ke, a kuntace, tun rasuwar matata ta fari. Amma tun daga lokacin da ki ka shigo rayuwarmu ni da Ameena takurar da kuncin suke raguwa a hankali. Daga jiya zuwa yau kuwa da na yanke shawarar zuwa neman aurenki Goggo ta amsa mani ta bani babu ko kadan, na neme su na rasa a tare da ni. Jin kaina nake kamar ba ni ba, jina nake 'new Ma'arouf'. Wannan ya tabbatar min ke alkhairi ce a gare ni, wadda za ta tafiyar da dukkan bacin raina ta kawo min farin cikin da na rasa na lokaci mai tsawo. AMEENAH,I desperately need you in my life, in samu rayuwar aure nagartacce nima kamar kowa. Amma Amina har yau ban ji daga bakinki kin ce kin amince za ki aure ni don kina sona ba. Ga shi kuma ni din, wani irin mutum ne da ba ya tilasta wani don amfanin kansa.Zan so in samu amsa daga bakinki Amina, mai dadi ce ko mara dadi duk a sikelin adalci daya zan dora su. Kin amince za ki aure ni in fito neman aurenki?" Amina ta samu kanta cikin gigicewa, kunya da rashin tantance abin yi. Da za ta iya da ta ce da shi, "Na dade ina sonka Engnr. Ma'arouf Ji-kas, kawai ina tsayawa a matsayina ne". Amina ba ta san cewa kalaman da take fadi a zuciyarta a kunnen Ma'arouf din ta ke zuba su ba. Ya lumshe ido ya bude a hankali. A cikin zuciyarsa ya ce, "ALHAMDULILLAH!". A fili kuwa ya ce, "......Tsayawa a matsayi kamar ya ya Dr. Amina?" Amina ta ankara da sakin bakin da ta yi. Kunya ta kara lullube ta, ta tura kanta cikin pillow tana makale da wayar. "Ka yi hakuri Baban Amina, zance ne irin na zuciya da mamallakinta!". Dariya ta ba shi sosai, "Ai ni ne mamallakin zuciyar. Daure ki yi min fashin baki a kan kalaminki. Ina so in dora shi a sikeli ne in yi miki bayani a kansa, wanda zai kwantar da hankalinki". Amina ta nisa, "Your Excellency, ina nufin matsayinmu ba daya ba ne, ni ba 'yar kowa ba ce, ba jikar kowa ba. Kowa ya ji ka aure ni zai yi mamaki, zai fadi abin da ransa ke so.......". Murmushi ya yi, "Na fahimce ki Amina. Amma ko kin san a da ni malamin makaranta ne? Makarantar sakandire? Mahaifina ma haka, babu irin fafutukar rayuwar da ban yi ba. Irin wadda baki taba zato ba. To cut it short, babu wanda aka haifa da arziki, kowa a duniya yake samun rabonsa. Saboda haka kada ki kara yin wannan tunanin ko makamancinsa. Ina sonki, ina kaunarki, na yi wa Goggo alkawarin zan rike ki da soyayya da amana har karshen rayuwarmu!". Hawayen farin ciki suka zubo wa Amina, ta kai tafin hannunta ta share su. "Na amince Baban Ameena, ko gobe ka kawo sadaki a daura mana aure". Runtse idanunsa ya yi yana gode wa Allah cikin zuciyarsa. Bai yi zaton al’amarin zai zo masa haka da sauki ba, a yadda ya fahimta Amina bata san so ba, bata san komai da ya dangance shi ba,bata da hope akan shi, she’s naive,innocent, yayi zaton zai sha wahala kafin ya karkato da zuciyarta ya fahimtar da ita har kafin ta amince masa. A fili yace. “lefe kuma fa? Ko shima an yafe mini? Kamar yadda aka ce da Turaki an yafe mini Tantabaru?” Dariya ta subuce mata, ta kai tafin hannunta ta rufe fuskarta. Yana jiyo sautin dariyar data ke yin da ya jefa shi cikin wani matsanancin nishadi, zuciyarsa tayi kal itama tata zuciyar tayi fes! Duk damuwoyin dake cikin ranta sai ta nemesu ta rasa. Wani irin yanayi take ji a kirjinta mai dadin da bazai misaltu ba.Ta tambayi to kanta, to ko wannan shine ‘Son’ data ki amincewa da gangan shine saida ta samu zuciyar Jikas din? “Ke nake sauraro Amina, ko shima lefen baza’a karba ba sadaki kawai za’a karba?”. Matsananciyar kunya tayi mata lullubi, amma jin ita yake sauraro kuma yana son jin ta bakinta akan abinda yace din sai ta daure ta magantu. “If my humble consultant ya kawo ai bani da ikon mayarwa saboda karfin ikonsa a kaina. In yace bazan karba ba ma Dr. Turaki ya isa da ni”. “Naga alama, shiyasa nima yake juya ni yadda ransa yake so don ya san ya isa da ‘yar tasa. Well, yanzu ki bani labari, hira nake so mu yi, irin wadda bamu taba yi ba”. Murmushi tayi “Baban Ameena kenan. Akwai hirar da bamu taba yi bane tsayin shekara guda?” Hirar ai kala-kala ce kuma kowacce da lokacin ta. We always talked on politics, bamu taba yin hira irin ta zuciya da zuciya ba, ban taba gaya miki wacece ke a zuciyar Ma’arouf ba. Girman matsayinki, da yadda kikayi overwhelming ruhi da zuciyar sa ba. Ke ko dan ‘Ji-kas’ din da ake fada ma ba ki iya ba, you always call meBaban Ameena? This is not my name.It didn’t deserve you. Ki ba ni wani sunan ko ki kira ni da sunan da iyayena suka ba ni, zan fi son hakan, zan fi farin ciki da shi". Ajiyar zuciya tayi, in wani ya gaya mata MA’AROUF JI-KAS yana magana haka, yanada baki har haka zata karyata, kalaman sa na kullum a kayyade suke koyaushe masu tarin ma’ana da hikima musamman a media, zababbu kuma dai-daiku kafin ya furta, yau gashi yanata zuba kamar ‘ya’yan kanya. Yau ta yarda ta amince soyayya gaskiya ce kuma ba wanda yake iya iko da kansa akanta, ta tabbata da Ma’arouf bai so ta har haka ba. Murmushi tayi, wani irin tattausan murmushi da batasan daga ina ya fito ba tsakanin zuciya da ruhi. Ta san dai na tsananin jin dadin kalamansa ne. Duk da bata taba ko da gwada fadar sunan Ma’arouf Ji-kas ba, saboda nauyin da yake mata. A yau zuciyarta ta amince ta fada din,tunda ya ce fadar za ta sanya shi farin ciki. Ita kuma burinta kenan, ya kasance cikin farin ciki har karshen rayuwarsa. "Good night MA'AROUF". Ta fada da dan sauri, ta yi hanzarin kashe wayarta, ta tura kasan filo, ta bi ta karkashin filon ta tusa fuskarta suka buya tare. Kunyar Dr. Amina yawa ne da ita. Murmushi ya yi da ya fahimci ta kashe wayarta, zuciyarsa ta nutsu sosai, sai godiyar Allah ne fal a cikinta. Ya amince daga kwanaki casa’in masu zuwa zai fara wata irin rayuwar aure mai nagarta kamar kowanne dan Adam, irin tashi ta farko da wadda bazai taba mantawa ba koma fiyeda ita, ba irin wadda yake yi da Laila Ji-kas ba. Burin da yake dashi akan rayuwar da zaiyi da Ameena mai yawa ne saboda soyayyar ta ma mai yawa ce, mai tsayi da fadi. Wadda ta cike filin zuciyar taf! Babu wani gurbi da wata ‘ya mace zata sake samu he believed. **** Sati biyu da yin haka ya kara yin bad-da-kama ya zo don jin me Amina ta shirya wa aurensu? A babban falon Goggo suke, Amina ta cika shi da ababen sha masu sanyi, wadanda ta sarrafa da hannunta daga 'fruits'. Yana kan kujera tana zaune a kan kilishi. Yanzu kunyarshi da ta ke ji ta ragu sosai, tana iya bude baki ta yi magana a gabansa babu jin nauyi. Sabida yadda yake jan ta da hira sosai a waya, ya maida kansa matashi dan ashirin da shidda kamarta. Tun daga ranar da suka yi wayar farko, duk dare sai ya kirata sun sha hira mai dadi da kara fahimtar juna da sanya dankon soyayya a zukatan su. Amina ta muskuta ta gyara zamanta ta tattara hankalinta akan Ma’arouf din. "Shirye-shirye nasu ne, bana son a sanar da daurin aurenmu a kowacce kafar sadarwa, a dauro a Shira, zan yi walima a nan gidanmu don 'yan uwa, iyaye, abokan karatu, na aiki da duk wasu abokan arziki. These are my programme of events your Excellency, please don't say no!". Murmushi Ma'arouf Ji-kas ya yi, kwayar idanunsa a kanta da wani irin yanayi a cikinsu. Ita kuma sai ta sadda kanta cikin jin kunya. A tausashe ta tsinkayi furucinsa cikin kunnuwanta. Daga ji ba shi yake sarrafa kalaman bakinsa ba, suna sarrafa kansu ne tun daga karkashin zuciyarsa. "A kan me zan ce NO? Bayan kowa da irin yadda yake tafiyar da tsarin rayuwarsa? Wanda ya tafiyar da rayuwarsa da sauki,ya kuma dauketa da saukin,shi ya huta. Ina da irin ra'ayinki a wasu bangarorin Aminahhh, ina sonki, ina yinki, ana mugun tare!!!". Amina ta yi dariya, har fararen hakoranta suka bayyana, dariya sosai mai kyau da ban sha’awa, wadda ta nuna halin farin cikin da kalaman sa suka jefa zuciyarta.Shi ma ya taya ta. Sukayi abarsu mai isarsu. Goggo na daki tana jiyowa, da ma a kan sallayarta ta ke, ta idar da sallar lsha kenan, sai ta dungura ta yi wa Allah sujjadah, ta gode maSa da ya share mata hawayenta, Ya bai wa Aminanta irin mijin da kullum ta ke mata addu'ar samu, kafin Ya dau ranta. Tsarki ya tabbata ga Sarki Allah!!! **** Don haka Dr. Amina bata koma aikin asibiti ba, ta kara jingine aikin, don Ma’arouf ya gaya mata bazai yiwu ba matarsa sa da aikin asibiti. Yana da shirin da yake yi mata a ransa don bazai bar ilmin data sha wahala ta nema ya bi iska ba dole al’umma ta cigaba da amfana da shiin one way or the other. Shi dai ta kasance cikin yi masa biyayya akan ra’ayinsa shine burinsa kuma ta amince. Sun cigaba da fahimtar juna, bai fasa bad-da-kama yazo gidan Goggo ba, soyayya kamar a birnin Hindu, mai ma’ana kuma tsabtatacciya. A bar Goggo da kunshewa a daki. A daya bangaren,Amina da Goggo na cigaba da shirye shiryensu a hankali. Ma’arouf ma na nasa. Ance rana bata karya saidai uwar diya ta ji kunya. Irin kudin da Amina taga Goggo na zarowa tana mata saye-saye sun bata mamaki, ta kuma yarda ba’a raina sana’a,kaji tsoron koda mai sayarda allura wanda ya tsaya sosai akan sana’ar tasa. Kwana dai-dai har dari ba goma haka sukayi ta zuwa suna wucewa kamar kiftawar ido, suna kara kusanta Ma’arouf da Aminah, sun gama yarda they are meant for each other, an kuma halicce su ne don junansu, kuma Ameena karama itace SANADI, sanadin alkhairi a garesu bakidaya.Allah Ya kara mata lafiya. Ranar wata juma'a aka daura auren Engnr. Ma'arouf Habibu Ji-kas da Amina Mas'ud Shira. A kauyen Shira ta jihar Bauchi. Akan sadaki mafi albarka wato mafi kankanta. Naira dubu dari kacal. A can kauyen Jikas Hajiyan Ji-kas wato Hajiya Saude sai kukan farin ciki ta ke yi tana mika godiyarta ga Allah, da ya nuna mata wannan ranar da burin ta ya cika tana raye cikin koshin lafiya. Da yamma kuma bayan an sauko daga masallaci aka daura na Ilyas da Sa'adiyya. Washegari asabar da yamma aka gabatar da kasaitacciyar walimar kamar yadda Amina ta tsara, ba abinda ba’a ci ba, babu irin abincin da ba’a yi guzurinsa ba bayan an ci an koshi,anyi guzurinsa, kowa sai sanya wa auren albarka yake yi. Wasu kan tambayi junansu wane irin miji ne haka Amina ta aura? Su dai ba su taba zuwa walima mai wadatar abinci da abin sha irin wannan ba. An kayar da shanu an kayar da raguna har ba adadi, ba’a maganar kankanuwar halitta kaza. Akilu ya kawo akwatuna guda goma sha biya shake da kayan lefe na fita hankali, ya ce da Goggo Yallabai ne ya turo shi a baiwa Ilyas, sai mukullin motamatrix dalleliya duk na Ilyas ne. Ina ruwan dan gaban goshin Jikas! Abu naku maganin a kwabe ku. Goggo ta kawo tukwici mai yawa ta baiwa Malam Akilu ya tafi yana godiya. Har zuciyarsa shima cikin farin ciki yake da wannan al’amari, koda dai a matsayin sa na babba mai hankali da ke bibiyar mu’amalar likiciyar da ubangidanta, yasan bata tafi ba, zata dawo. Watarana irin wannan na nan zuwa(which will alter the dream to reality). Sanda yayi driving dinta na karshe take fadin wai sai watarana! Malam Akilu daga yau an gama! A zuciyarsa ya ce “yanzu aka fara!”. Gashi kuwa Allah Subhana Ya tabbatar da alkawarinsa wanda ba ya tashi. Ya kawo farin ciki cikin rayuwar Ogansu kamar yadda yake sanya su farin-ciki da nau’o’in alkhairansa garesu marassa yankewa. Ya kawo AMINA SANADIN AMINA don ta sauya duniyar mahakurcin bawansa. Suna addu’ar Allah ya sada shi dadukkan alkahairanta ya kareshi daga sharrinta in akwai. Da ango Ilya ya zo har da taka rawa don murna. Yana tsokanar Amina, wai Yallabai ya fi sonsa a kanta. Ita ko dankwali bai bata ba. Ga Sa’adiyyar sa ta sha akwatuna na garari. Bayan ya san Goggo ce ta roki Hajiyan Ji-kas kada a kawo komai, in ta tare ya bata. Ita ba ta son 'yan tsegumi su cika mata gida. Ita da jama'arta suka dauka suka kai gidan su matar Ilya. An sanya tarewar Amina kwana goma masu zuwa, don ta roki Hajiyan Ji-kas alfarmar a barta ta kimtsa a hankali ta yi sallama da danginta na Shira, ta raka Goggo kasarta ta haihuwa‘Sirrleone’ kamar yadda ta dade da burin sai ta aurar da Amina zata koma, za su yi kwana bakwai a can. Da fari hankalin angon na Amina ya tashi a kan tafiya Sirrleone din nan. Amma daga baya da Hajiya ta gaya masa shekaru talatin da doriya kenan rabon Goggon da kasarta ta haihuwa da iyaye da ‘yan uwanta, kuma Amina ba za ta iya barin Goggo ta tafi ita kadai ba, a cewarta don kada ta ki dawowa, sai ya amince. Ya yi musu booking jirgin ‘Arik’ zuwa kasar Sirrleone. ***** SIERRA-LEONE (West Africa) Asalin su daga Lardin Kenema suke, manyan biranensu kenan; Bo da Kenema, in ka cire babban birni Freetown. Kenema shine birni na biyu mafi girma da shahara. Kakan Haj. Hauwa Alhaji Ibraheem Sissey Babban Malami ne wanda yazo Sierra Leone daga Guinea-Conakry ya haifi ‘ya’ya goma anan maza da mata,suka yadu sosai cikin kasar. Yanzu sun fi dari, ‘ya’ya da jikoki. Goggo Hauwa itace babbar jika a family kuma dukkaninsu suna zama a Lardin Bo, Freetown da Kenema. Lardi yana nufin (province). Mutanen kasar nada tsayi da girman jiki hadi da kyawun sura. Allah ya albarkaci kasar SierraLeone da albarkatun kasa musamman (diamond). Basu fiya noma ba, don basu da kasar noma, sannan kasar su jar kasa ce wato laka, don haka yawanci daga kasashen ketare ake shigo musu da kayan abinci, hatta albasa daga kasar Holland ake shigo musu da ita, fara, mai kyau, mai sa abinci kamshi da dadin dandano, sun fi shuka kwakwa da plantain kuma suna da albarkar kifi. Yanayin kasar yana yanayi da kasashen mu na kudu (garuruwan inyamurai a Nigeria). Kasa ce da ba shahararriya wajen kyau da kyale-kyale ba, amma akwai kwanciyar hankali da bin doka da oda. Akwai kwakwa ko’ina a kasar da bishiyoyinta suna kiranta (jelly). Currency dinsu shine ‘Leone’. Kasar Sirrleone tanada dadin zama, da talaka da mai kudi duk cimarsu daya. Komai talaucin ka zaka ci abinci mai kyau kuma mai dadi. Miyar ganyen rogo da miyar ganyen dankali sune manyan abincinsu/miyoyinsu, ana ce musu ‘keren-keren’ dasu ake cin shinkafa ba sa cin tuwo, basu san tuwo ba. Kasa ce da turawa sukeso suka kuma nacewa, ko don albarkar ‘diamond’ da yanayi mai dadi da Allah Ya basu. Haka zaka ga manyan ‘trolls’ na karfe cike da ‘diamond’ a airport ana fitar dashi zuwa kasashen turai. Kada kaso kaga yadda manyan jirage ke tashi da sauka a kasar na manyan kasashen duniya abin gwanin ban mamaki. Ga manyan duwatsun ‘hills’ a ko’ina. Ginin gidajen su akan ‘hills’ sosai. Zaka ga gidaje kamar 100 akan hills (tsaunuka) saboda basu da fadin kasa, ruwa ne ya kewaye garin Freetown yayi masa kawanya wanda yake daga Atlantic Ocean. Babban yarensu shine ‘kiryo’ yana shige da ‘pidgin’. Fulan, wato (Fulani) da Mande da Timini da Soso sune manyan kabilu a kasar. Kabilar da Goggo Hawwa ta fito watoFulan, sune kan gaba, wato mafi kima da daraja a kasar. Mafi akasarin Fulan ba ‘yan kasar bane sunzo ne daga Guinea-Conakry wanda makotan kasar Sirrleone ne kamar Nigeria da Nijar. Turawan yamma sunyi tasiri a wannan kasa wajen tura musu akidunsu musamman matasansu, matan su yawanci sai sun girma suke sanya mayafi. Don haka inda duk Amina da Goggonta dake sanye da Hijab suka gifta sai suka zama abin kallo abin sha’awa. Hills da suke dasu ya sanya bazai yiwu ayi filin jirgi cikin birnin Freetown ba, sai aka je wani dan tsibiri nesa kadan da garin aka yi, ana cewa tsibirin Lungi. Idan jirgi ya sauka a Lungi za’ayi tafiya ta akalla mintuna 25-30 zuwa bakin ruwa, inda daga nan za’a shiga jirgin ruwa (sovereignferries) ya shiga da kai garin Freetown tafiyar mintuna 30. Idan (ferry) yana sauri zaku iya isa a mintuna 15. Lungi tsubiri ne kuma dan kauye, saboda haka kodayaushe (ferry) cike yake da (passengers) masu shiga ko fitowa daga garin Freetown. Wani abin sha’awa harda motocinku zaku iya shiga (ferry) ya tsallakar daku in a mota kuka zo.Bayan ‘ferry’ ana hawa ‘helicopter’ ko Babur din ruwa. FREETOWN Babban birnin kasar kenan. Kisi Road babbar unguwa ce a cikin gari kuma mahada ta hada-hadar kasuwanci tamkar kana cikin garin Lagos. Lumley, itace kamar GRA dinsu kuma unguwa data tara kusoshi da masu kudin kasar da sauran baki masu zuwa yawon bude ido kasar musamman turawa. Kuma anan ne dukkan ‘embassies’ da ‘high commissions’ na kasashen duniya suke da kuma Quaters na ma’aikatan su. Kusa da Lumley sai Aberdeen itama unguwa ce, a nan kuma ‘beach’ yake (Lumley Beach) da manyan ‘clubs’ da sai wanda ya isa yake zuwa. Daga Kisi Road zakiyi tafiya zuwa Grassfield, sai ki wuce zuwa Waterloo, to kin fita daga Municipal na Freetown kin fara shiga kauyuka. Shi Kisi Road itace babbar hanyar da zaki fita daga Freetown zuwa Bo,da kamar awa daya sai ki isa mahaifar Hajiya Hawwa wato Kenema.Nisan su daga babban birni Freetown kamar awa biyar zuwa shida ne. Turawa yamma na son kasar SierraLeone sosai don yanayin kasar na zaman lafiya ba don yaki da ya bata musu kasa ba. Kasar Sierra Leone tana cike da plantations na kwakwa, tanada kyau gwargwado, saidai babu shuwagabanni nagari da zasu ciyar da kasar gaba. **** Jirgin ‘Arik’ ya sauke Amina da mahaifiyarta Hajiya Hauwa a tsubirin Lungi(Lungi International Airport) wanda ya kasance Airport dinkasar Sierraleone, Amina sai rarraba ido ta ke tana kallon ababen mamaki, wato al'adu daal’ummatai da suka sha bamban da wadanda ta saba gani. Tsayin shekarun da Hajiya Hawwa ta yi a Nigeria bai sa ta manta yadda zata yi ta sadu da mahaifarta ba wato gidan iyayenta a Lardin Kenema. Goggo ta biya kudin ‘ferry’ nata dana Amina (Leone 20000) daidai da naira (1000) kudinmu na Nigeria. Sun shiga VIP ne saboda Amina na tsoron ruwa. Ferry baya sauri yau don haka saida suka shafe mintuna talatin sannan suka shigo garin Freetown. Daga Kisi Road suka hau mota mai tafiya Kenema, tafiyar awanni shidda cur sannan suka iso, Hajiya Hawwa bata sha wahalar gane gidan iyayenta da kakannin ta ba duk tsayin shekarun nan. Babban gidan gandu na Alhaji Ibraheem Sissey. Ta gode wa Allah da ya sada ta da iyaye da 'yan uwanta lafiya, ana ta murnar zuwansu kamar me amma murnar ta fi karkata ga ganin Amina. Wadda sai a hoto suka taba ganinta, hoton ma na tun tana karama, ta samu mahaifinta ya rasu, Allah bai yi zasu gana ba, wasu da yawa a bayanshi ma duk sun rasu. Amma mahifiyarta na raye. Wasu sun hayayyafa, 'ya'yan sun girma. Haka aka yi ta kai su suna zaga dangi dake cikin Kenema ita da Amina. Kwanansu uku a Kenema sun huta sosai sannan suka tafi Lardin Bo, inda danginsu na can suke, kannen mahaifinta uku suna can da iyalansu, suka kwana daya sannan suka wuce babban birni Freetown inda kannen Goggo guda uku suke aure; Zainaaba (Jal’an) Aisata (Aishatu) da Fatimata (Fadimatu). Jal’an na aure a Aberdeen, mijinta babban ma’aikaci ne na hukumar tsaro ta kasar, Fatimata na Lumly, mijinta jami’in custom ne, Aisata na Waterloo tana auren wani babban dan kasuwa. Kar kiso ki ga Amina a tsakiyar (aunties) dinta da kyawawan ‘ya’yansu masu kama da ita. Kowacce na nan-nan da ita, don ma basu iya hausa sosai ba, sau-tari sai Goggo ta shiga tsakani tayi musu tafinta, in ba haka ba rabin hirar da kwatance ake yin ta, gashi basa jin turanci sai yarensu ‘kiryo’. Lokacin da Hajiya Hawwa ta gayawa Aisata, Jal’an da Fatimata cewaAmina amarya ce tarewa zatayi da sun koma, tafiya Aisata tayi da ita gidanta ta soma yi mata shirin amare irin nasu.Jal’an da Fatimata ma ba’a barsu a baya ba kowacce ta kawo gudunmuwarta, suka gyare ‘yarsu tsaf ciki da bai dinta, hatta gashin kan Amina ya sanja launi, ya koma na mutanen Sierraleone. Amina ta canza kwata-kwata ta fito a cikakken asalinta (Sierraleonean). Amina ta ga ‘gata’ irin gatan nan na dangin uwa, wanda bata sameshi ba a tsayin rayuwar ta. Kuka take sosai tana rungume su Aisata daya bayan daya, a lokacin da suke sallama zasu koma Kenema,inda daga nan zasuyi shirin komowa gida Nigeria, Amina cike take da ganin beken Goggo, ashe tanada irin wannan gatan ta barsu sukayi ta ragaita? A Kenema, Mahaifiyarsu Goggo Kaka Maryaama, wadda ta tsufa ainun ta ce da Goggo cikin yarensu, "Ina fatan kin dawo gida kenan Hauwa'u? Tunda ba aure ki ke da shi ba, ki samu miji a nan ki yi aurenki yafi tunda ba wuce auren kikayi ba, kuma tunda kin ce kin aurar da Aminatu tarewa za ta yi". Ai kuwa Amina ta balle musu da kuka da aka fassara mata abinda kakarta tace, "Na roke ki kada ki kara fadin haka Kaka. Ki yi wa Allah ki bar min Goggona a kusa da ni. Ni kadai ta haifa ba ni da dan uwa ko abokin shawara sai ita. Ba ni da burin da ya wuce duk sanda nake son ganinta in ganta, ke kuwa kinada su Anty Jal’an da ‘ya’yansu. Kaka don Allah ki yi hakuri ki tausaya min,ina rokon ki ke ma ki bi mu, muna bukatar dayan ku cikinmu mu ci gaba da rayuwa tare, da yardar Allah bazamu kara yin dadewar da mukayi bamu zo ba, zamu dinga zuwa akai-akai". Kukan Amina ya yi yawa, sai da Kakarta ta dafa ta tana lallashi. "Na bar miki uwarki Aminatu, na amince zan biku mu koma tare in zauna tare da ita, nimain ke ganinta duk sanda nake so. Amma ku yi min alkawari ke da mijinki duk sanda mukeso zaku kawo mu gida nida mahaifiyarki". Duk da hausar tasu ba irin ta Nigeria ba ce, Amina tana ganewa. A take Dr. Amina ta kira His Excellency sukayi magana ta gaya masa ko me kenan da abinda Kaka Maryaama keso, yace ta bashi Kakarta, kasancewar tana jin hausa sosai, magana yayi mata da Amina bata san me suka ce ba, ta dai ga Kaka ta hau hada kayanta ta ce ta amince zata bisu Nigeria kuma tare dasu Jal’an bakidaya da kannen mahaifin Goggo za’a tafi, zasu raka ta dakinta sai su dawo, ita Kaka da Goggo su zauna tare har illa masha Allah. Kukan dadi Amina ta fashe dashi ta shige daki ta rufo kofa ta kira angon nata. A bakin ‘swimming pool’ din gidansa yake zaune bisa fararen kujeru, cikin gajerun rumfunan gargajiya (hut) wadanda aka fi sani da bukka, sanye yake da jallabiyya mai yankakken hannu ruwan madara, a gabansa tebir ne karami shake da kayan marmari. Yammaci ne mai lumshi da kadawar iska mai sanyi kasancewar damuna ta kawo kai, mujallu da jaridu ne fal a gabansa,wadanda duk shafukan su na farko(cover photo) kyakkyawar fuskarsa ce ta mamaye su, yana duba wadanda zai iya yana wucesauran, yana ganin yadda gwamnatinsa ke tafiya ne tareda ra’ayoyin talakawa a kanta, masu dadi da marassa dadi. Wayarsa daya tayi ruri da wani irin ‘tune’ mai taba zuciya da shikadai ya san wanda ya sanyawa shi. Murmushi yake yi sosai a lokacin da ya amsa kiran, kamar dama jiran kiran yake yi. “Sierraleoneans!”.Abinda yafara fada kenan cikin taushin murya. Murmushi tayi mai sauti. Bai bata damar ta amsa ba ya dora. “Tunda aka samu dangi kuma sai aka manta da miji, wannan wace irin Amina ce? Ni idan na kira baya shiga, ki kirga dakikun agogo, awanni nawa ne suka bada kwana shidda? To duk sun tafi ne tareda bugun zuciyata na rashin samun wayarki, ina fatan kun daure kaya? Jirgin ku zai taso daga Lungi karfe biyu na ranar gobe ne insha Allahu”. Ta sauke ajiyar zuciya. “In nace nagode yayi kadan fa! Ban san da kalmar da zan gode ba, ina rokon Ubangiji Ya fini godewa”. Murmushi yayi mai sauti, wai don ya kwaso mata danginta take wannan godiyar, bata sani ba, in duk kasar Sierraleone zai kwaso mata don tayi farin ciki zai yi hakan in yanada iko. Balle mutum goma. “Akwai hanyoyi da yawa na godewa mijiba da fatar baki ba. Akwai hanyoyin da za’a gode min din ai. By the way, in baki san su ba zan sanar dake a gadon baccin mu. Ina jiran ki Amina da bashin da ni kaina bansan yawansa ba. Kiyi barci mai dadi da mafarkin Ma’arouf a cikinsa. Na barki lafiya, ki gaida Goggo”. Cikin mutuwar jiki da rudewa Amina ta sauke wayar daga kunnenta, wata irin murya Baban Ameena ke magana da ita a yau da bata taba jinsa da irinta ba, batasan ya zata kwatanta tasirin muryar a dukkan gabban jikinta ba, ta san dai ta kurda kowanne sako da kowanne lungu na jikinta ta yi masa illah, ta saukar mai da wata irin kasala mai wuyar fassarawa. Washegari sun cika kwanansu bakwaicif, suka yi sallama da sauran 'yan uwan Goggo, wadanda suke (far-relation) wato wadanda ba na jiki bawadanda baza’a taho taredasu ba, ta Bo suka bi suka dauki kannen mahaifin goggo su uku da ‘ya’yan Yayar shi biyu, suka zarto Freetown suka tadda su Aunty Aisata sun gama shiri. Tuni Ma’arouf ya gama yi musu shirin tikiti da komai na jirgin Arik suka taho Nigeria. **** Mu karasa a littafi na 4, kuma na karshe Insha Allahu. -Takori Ina baku hakuri makaranta da littafin ya kai har 4 bayan nace iyakacin sa 3. Yanayin rubutu ne ya janyo hakan domin labari shi yake jan zarensa da kansa. Kada ku damu tare suke. Taku har abada TAKORI. DANDANO DAGA AUREN KWANGILA! (Littafin Takori mai zuwa) H awaye masu dumi suka biyo idanun Ambassada Hamza, bai damu da ya kai hannu ya share ba, haka ya barsu suka yi ta malala akan kundukukinsa, abokan nasa suka ci gaba da ba shi baki, ba su san kuka biyu yake yi ba; kukan rashin mahaifiyarsa da kukan nadama...!!! Rayuwa kenan. Hafsat bata san bidirin da Daddy ke yi da zuciya da kwakwalwar sa ba, ta sayo wa Mammah katin wayar da ta aike ta ta kamo hanyar dawowa. Tafiya take kanta a sunkuye don bazata iya daga ido ta dubi taron mazan nan dake zazzaune a kofar gida ba. Kamar ance da ita ‘dago kanki’ gab da zata shiga gida ta dan daga kai sabida jikinta ya bata ana kallonta sosai, ai kuwa karaf! Sai idanunta cikin na Daddy. Ta ganshi yana shatatar hawaye kamar karamin yaro, sukayi ido hudu dashi. Tuni ta gigice ta saki katin wayar da canjin kudin ta ci uban tuntube da wani katon dutse dake kofar shiga gidan an tare kofar dashi, ta fadi kiff! A kasa. Don tayi tsammanin a cikin mutanen nan balbaleta zaiyi da balbalin bala’in nasa. Ji tayi ansa hannu biyu an dago ta, ta ji zafin faduwar sosai da sosai, gwiwoyinta duk sun kukkuje leben ta ya fashe jini ya wanke bakin. Ta cira ido a sannu cikin dauriya ta dubi wanda ya daga ta; Hamza Atiku Dakata ne. “Wace irin tafiya kikeyi haka Addah? Ba kya kallon abinda ke gabanki, Addah in don ni kika rude haka don Allah kiyi hakuri, kar ki sake firgita in kin ganni, ba dodo bane ni, BABAN KI NE!!! Hafsat-Suhaana, ta runtse idanunta, mafarki ne kawai ire-iren mafarkan da ta saba yi akan Daddyn, saboda yadda tasa damuwa da lamarin sa a ranta. Ta ki bude idon don bata so ta farka daga wannan daddadan mafarki. Daddy yasa hannu ya dauko hankicinsa daga aljihunsa fari tas dashi ya shiga goge jinin da ke zuba daga bakinta. Mutane wajen bakwai suka taso suka isko su. Nan da nan labari ya isa ga Mammah, daga bakin dan Anty Mariya, wai Addah ta fadi a waje. Daddy ya sa an tafi da ita a mota a kaita asibiti. Sai taji maganar banbarakwai, ina ruwan Daddy da Suhaana har da zai ce a kaita wani waje a mota? Kar dai fa ya aika da ita GIDAN MARAYUN da yake ikirari? Tayi wata irin zabura ta mike, da gudunta tayi waje har zaninta na kwancewa ko mayafi babu a jikinta tayi hanyar soro, uban karo suka gabza da Daddyn yana kokarin shigowa saura kadan su fadi. Jikinta na bari, muryarta na karkarwa cikin son fashewa da kuka ta kama shi tana girgizawa. “Ina Hafsat? Ina Addah ta? Ina ka tura a kaita? Ina ‘ya ta ina ‘yar amana ta???”. AUREN KWANGILA! Littafin SUMAYYAH ABDULKADIR (Goron Sabuwar Shekara) Yana zuwa ba da jimawa ba insha Allahu.