MIJIN BUZUWA complete BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM MUNA GODIYA GA ALLAH DA YA BAMU DAMAN RUBUTAWA DA KARANTA WANAN LABARI UBAGIJI YADDA MUKA FARA LAFIYA MUKAI KARSHEN SHI LAFIYA . KISHI DA BUZUWA SAI KA KWANTAR DA HANKALI KA KAI AIKI DA HIKIMAR KA WAYEWA DA ILIMI BAI FITAR DAKAI A GARESU, , , , GODIYA GARE KUMA KARANTA NOVEL DINA DA KUKE KOKARIN DAUREWA DA HAKKURI WURIN KARANTA LABARAINA WANDA ABUBUWAN DAKE YAWAN FARUWA A NAHIYAR MUCE MUKE TABOWA DON HASKA KAN YAN UWA DAMA MU DUKA. NOVEL DINA NA KAUYAWA NE BABU YAWAN KARAYAN ARZIKI A CIKIN SHI SAI DAI ABINDA LABARIN YAZO DASHI BABU FAYYACE FITSA A FILI YADDA WASU KE SON IN SAUYA ZUWA HADI DA FITSARA NA KASANCEWAN MACE DA NA MIJI A GADO A HAKKAN KUMA NAKE DA DINBIN MASOYA MASU KARANTA SHI A HAKAN, GODIYA GARE KU HAR KULUN MASOYA DA MASU KAUNA NA. GAMA SU SON NOVEL DIN ZAKU IYA KIRA NA DA WANAN LAYIN DON NEMAN KARIN BAYANI DARI UKU NE GA MAI SON BIYA TA WANAN ACCOUNT DIN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK 09026931792 KO 08036959257 Hadari ne ya hade garin sosai baka ganin komai sai walkiya da kara kainan motoci a lokacin wanda suke haskawa don ganin gaban su. A daidai wanan lokacin ne motoci guda uku da suka karyo titin a jera wanda ke nuna wani mai akwaine tafe a lokacin yadda mutane suke ta kaucewa a titin suna basu wuri. Wasu daga bakin titi ke fadin yanzun haka ma ba maigidan bane tafe wanan fitsarariyar matan tashine haka da bata ganin kowa da mutunci a idon ta. Wani gida motocin suka shiga a lokacin gini ne na zamani motan ne suka dan tsaya da alama magana akeyi da wani a cikin gidan. Ba a dade ba suka wuce zuwa cikin gidan kai tsaye security ne suka fito don bude motar nan naga wata farar mata buzuwa ta fito tasha ado na fada da gani daga saman ta har kasanta kwaliya ne. Doguwa ce sosai ga fari sai dai idan ka kura mata ido zaka iya gano farin ne kawai ke aki yake rudin mutane don kyau akwai kyau inda bamu matan mu na Nigeria masu kyan asali da dire bayan farin da gashi da kuma tsayi babu abin da suka dara matan Nigeria dashi na fannin kyauwo. Tana wani tako ta shige ciki zuwa part din ta ta dan jima ciki ta fito tana kwala ma wata mata mai suna Labara kira da karfi . Da saurin matar ta iso gareta tana dukawa tare da fadin hajiya barka da zuwa an dawo lafiya yaya han, , , , Dakata tace wa matar yaya naga witan part din can a kunne ko mara zuciyar nan ta dawo ne kuma ? Matar ta dago kai a hankali tace wa hajiya babba kike nufi waye hajiya baba ina nufin fatima matar wancan shiyan ta fada a fusace jin an kira uwar gidan nata da hajiya babba taji haushi. Eh ta dawo laraba tace ai tun ranan da kuka wuce washe gari ta dawo kutawa tayi tare da juyawa da karfi ta shige part din ta a hasale. Anan tabar laraba da kallon mamaki ta nisa tana fadin ikon Allah mata da mijin ta kinzo kin hana zaman lafiya a tsakanin su haka ? Ita kuma a daki sai faman huce takeyi ita daya nan ta dauki waya ta kira mijin nasu da suka rabu yau ya tafi waje yin wani aiki. Duk da tasan dare ne a duk inda yake amma bai hanata kiran shi ba a wanan lokacin saboda tsananin kishin dake damun ta a lokacin. Kiran farko ya tsunke bata hakkura ba ta sake kira a karo na biyu bai daga ba sai wayan na gap da katsewa ya dauka da alaman barci yake a lokacin . Murya irin ta masu barci ya daga wayan tare da fadin Nafisa lafiya kira da dare haka yanzu fa kin san dare ne nan sosai a wanan lokacin. Bata jira ya gama magana ba tace watau munafuntana zakayi ashe kasan matar ka ta dawo shine baka fada min ba tun muna tare sai kawai in dawo in samu ta dawo gidan. Ajiyan zuciya ya sauke tare da fadin tadawo fa ni ban san ta dawo ba don basu fada min da cewa zata dawo ba ma kit ta kashe wayan. Ta wurga a gefen gadon ta tana fadi a fili duk sai nayi maganin shegun tsofin don sai auren nan ya mutu inga ta bakin naci irin nasu. A daidai lokacin ne kuma aka turo kofan side din nata wata matace cikin dogon riga ta dora hijjab a saman rigan nata. Fuska da murmshi tace mutanen Abuja ashe kuna tafe yanzu ne an sauka lafiya yaya hanya fuska a daure ta juyo tana fadin eh muna tafe ko idan zan dawo sai na sanar da wani akace ko ma ? Ke yanzu don baki da zuciya dawowa kikayi duk da maigidan ya nuna baiyi dake saboda rashin zuciya irin naki sai da kika dawo kamar ana zama dole ne. Matar tadan sake murmushin dabai kai ciki ba tace nake ganin ke nan haka amma ni nasan yana yi dani har gobe ke ce dai ganin ki ke rudin ki ga hakan don ko na bar gidan shi bamu rabuba don ga diya ga zumunci a tsakanin mu. Fati ke nan zakiko ga abinda ba daidai ba wallahi in dan kin nace sai kin zauna min da miji don sai na rami ya fiki shan iska a gidan nan tunda haka kika zaba wa kanki sannu sugar mai iyali ko tasbi sarkin zumunci shida bakajan da daya bai biyo ka ba . Murmshi tayi Allah na tare da mai gaskiya dama jin kin dawo ne yasa nazo taron ki da dawowa ba wani abu ya kawo ni ba a huta lafiya bata tsanmanin ta amsa mata ta fice daga dakin . Zuciyar ta yana ciki da mamakin fitsara irin na Nafisa wanda sam babu kunya a cikin shi ko kadan sai zallah cin fuska da fitsara filli. Daki ta nufa a daidai lokacin da ruwa ya gauce sosai a garin na kaduna kamar da bakin kwarya da sauri ta isa ta rufe mirrow da sauran abinda baison walkiya a dakin saboda tsaro wanda ba kowa ke wanan ba a wanan lokacin sai masu sani da hakan a baya suka saura rufe irin wa yan nan abubuwan a daki yayin da ruwan sama ke zubuwa daga samaniya don kariya daga fitinan walkiya. Falo ta dawo ta zauna tare da yaranta dake cin abinci a wanan lokacin ido ta tsurawa yaran biyu sai da ba wai don tana kallon su hankalin ta yana gare ta ba ne tunane takeyi a zuciyar ta na irin rayuwan da ta tsunci kanta a ciki yanzu. Tun shigowan Nafisa cikin su komai na rayuwan ta da mijin nata ya sauya sallo a lokaci daya ba yadda suka saba gudanar da rayuwan su ba suda yaran su da sauran yan uwa. Hatta yaran yanzu a matse suke da zama gidan mahaifin nasu sun fison zama a gidan kakanin su da zaman gidan nasu saboda matsin da suke ciki a yanzu. Ita dai tasan aure ne a tsakanin ta da mijin ta na soyayya tun tana karama soyayyan su ta samu asali don gidajen su basu da nisa da juna shi din abokin yayan ta ne. Kuma akwai zumunci na makwabtaka da ya koma kaman na jini daya a tsakanin gidajen su tun kakan su zumunci ya kulu a tsakanin gidajen biyu. Wanda yakai bako ba zai iya banbanta tsakanin su ba sai wanda yasan tushen abin koda ta girma bai daina kulata ba cikin yan uwa haka ya kai har aure ya kullu a tsakanin su. Tayi haihuwan farko lafiya ga cikin na biyune ya samu aiki kano suka koma can sun koma bada dadewa ba ya hadu da Nafisa yar mutan Niger da suka shigo Nigeria neman kudi da iyayyenta ta lake mai tun bai kula ta har ya soma kulata don suna sayar masu da abinci a bakin ma,iakatar su ne. Yaron ta ne dayazo inda take zaune tana tunane ya katse da da fadin mama daddyn mu bai dawo bane naga anty ta dawo. Shafa kan yaron tayi taja sauke ajiyan zuciya tace bai dawo ba Affan da kaga ya shigo nan ai anty ce ta dawo ita kadai. Yaushe daddy zai dawo mama yaron ya kara jefa mata tambaya kuma tace Affan ban sani ba idan ya dawo ai zaku ganshi. Bai barta ta huta ba ya sake jefo mata tambaya again yace mama ai anty ce bata bari mu ganshi ko munje wurin shi sai tace mu fito muna damun shi yana hutawa. Murmushi tayi tace kai Affan ba yana zuwa nan ida muke kuna ganin shi ba to may kuma kake so shiru yaron yayi kamar yana tunane a zuciyar shi. Sai kuma yace ni mama ban ma son ya dawo saboda may Affan uwar ta tambaye shi yace saboda idan ya dawo sai ki ta kuka mama su kuma suna dariya da anty kuma su fita tare. Affan ban son yawan surutu fa ka faye surutu ina jin tsoron wanan bakin naka kullu naji ka kara fadawa wani matsalan mu sai na yanke ma kunne daya. Shiru yaron yayi yana tunanen kada uwar ta yanke mai kune kamar yadda tace din kayan da sukaci abinci ta kawar ta gyara wurin suka shige dakin kwanan su. Da safe bata fito ba sai da ta gyara part din nata ta nufi kitchen don dafa ma yara abincin zuwa school sai ta samu kitchen din a rufe. Dakin kwanan laraba mai aiki ta nufa a nan ta samay ta tace yau laraba lafiya naga kitchen a rufe Labara tace aikin hajiya karama ne hakan. Nima na fito zan gyara tace na barshi taja kofa ta rufe nayi tunanen zaki fito don saboda abincin yara gashi kuma ta kulle kitchen din. Dan jimm tayi tana tunane a ranta wai may Nafisa take nufi da ita ne haka abinci dai na kowa ne a gidan amma haka take mata idan ta bushi iska sai tace wai ana barnan abinci da yawa gidan. Bayan abinci ma da take ita daya sai ta ba wasu balle yanzu da ya samu karin girma sosai a wurin aikin shi basu da talaucin komai a rayuwan su. Muryan Laraba ne ke fadin sai hakkuri hajiya idan mutum ya ci gaban ka sai dai bi wallahi gama tana ganin ta samu miji a hannu sai abinda tace a gidan. Ba komai Laraba na gode badin tura su can cikin gida wurin hajiya su karba haka ta juya ta wuce zuwa part din ta tabar Laranba a wurin tana jin tausayin ta. Daki ta koma ta shirya yaran ta fito dasu da kanta ta mika wa kanin mijin su dake zaune dasu a gidan ya kaisu cikin gida wurin hajiya a basu abinci. Yace yau kun makara ne tace eh salis koda na tashi har gari ya haska sosai wallahi kaga idan nace zan tsaya dafa masu yanzu sai su makara. Ta koma ciki ya kwashe yaran zuwa gidan su dasu don duk a unguwa daya suke zaune da iyayyen nasu gida uku ne a haka kuma Nafisa ke tsula tsiyar ta a gidan. Don tafi son zaman kaduna saboda anan kawayen ta suka fi yawa da yan yaren su na buza da suke kara zugata tana iya shegen. Salis na shiga gidan kafin ya isa part din mahaifiyar mijin nasu da yaran matan gidan suka fara magana a, a su Affan ne haka yau da safe nan. Salis yace eh maman su ta makara ne yau bata tashi da wuri tayi masu abin karyawa ba shine zasu zo nan su dauka. Murmushi hajiya kubura tayi tace Fatice zata makara da safe kawai dai yar bakin halin gidan su ta dawo jiya akwai da wata a kasa. Ba an mayar da Fati bata san tadawo ba shine ta dawo ta samay su bakin halin nata na banza ya tashi yanzu ta soma ke nan har sai ta kure ta ta tanka mata. Allah dai ya sauwa dayar matar gidan ta fada daga daki tace shi kuma da yazo sai ya biyewa iya shegen nata ba daga daki suke magana. Sun shiga gun kakan su tana ganin su tace ai na sani ba yar iskan yarinyar nan ance ta dawo jiya ba nan yanzu tsiya zai tashi a gidan wanan karo ko ba zan saurara mata ba wallahi. Salis yace cewa tayi makara tayi fa bata samu dafa masu abinci ba yau yaya maganan ku yazo daya da na mommy ne ? Hajiya bata iyayin magana ba sai jan yaran datayi zuwa cikin part din ta ta zuba masu abincin da tayiwa yan marayun jikokin ta da suke hannun ta. Bayan ta gama sallaman yaran ne ta dauki waya ta kira Fati din tace wai may ke faruwa ne yau a gidan naku cikin fara a ta fara gaida surukar nata da bata ko tsaya gaisawa da ita ba. Amsawa tayi sama sama dakyat tare da maimaita tambayan ta a gare ta tace hajiya makara nayi tace jinan fati na san komai walahi nasan abinda yar banzan yarinyarin nan zata iya. A sanyaye fati tace hajiya ba haka bane makara nayi yau din ban samu dafawa ba kashe wayan hajiya tayi badon ta yarda ba. Kashe wayan nata yayi daidai da shigowan hajiya kubura wurin ta tace sai gasu Affan na ga sun zo karban abinci kuma ? Bari hajiya Kubura duk da uwarsu ta boye min na san akwai wata a kasa wallahi bai yuyuwa haka kawai taki tanadarwa yara abin zuwa makaranta. Nan suka zauna suna maganan hajiya kubura tace idan ita fatin bata iya magana mu ba kyalewa zamuyi ba ai ana horo da yuwa ne kuma ? Kai hajiya ta dafe tace Allah ya kawo muna karshen wanan yarinyar a gidan nan hajiya kubura tace amin tana mikewa tare da fadin bari mu gani zuwa rana idan har sun dawo nan kin ga hasashen mu ya tabbata ke nan ta rufe kitchen din nasu ke nan. Ta fice ta bar hajiya a cikin bacin rai tana tausaya ma wanan rayuwa da yayan nasu suka tsunci kan su a ciki na bamin auren buzuwa da ya dorawa rayuwan shi yana zaune kalau da matar shi ya jajibo masu wahala haka. A gidan Fati kuma bata karya ba tun safe ba tunanen kanta takeyi ba a yanzu sai tunanen idan yaran sun dawo may zata basu idomie ne ya fado mata arai ta sayo ta dafa masu suci. Damay zaki dafa wani zuciya yace mata tsaki taja tana tausaya masu a ransu take tunanen da can baya lokacin tana ita kaida ya fado mata a rai. Abinci sai wanda ransu ke so zata dafa da ita da yaranta da maigidan ta har sai taba makwatab wani lokaci yau kuma gashi a sanadiyar kishi da buzuwa har horo yakai ga a rufe store da madafar abincin gidan baki daya. Babu wanda zata kara kai kara gareshi tunda baji mijin nasu keyi ba ko ta fada karshe ma ya dawo ya hauta da masifa gashi ita ba son masifa take ba a rayuwan ta. Haka ta taso da tsoro sam bata fada ko kadan saboda ruwan ciki irin na matan hausawa da ta taso a cikin shi wanda a cikin tarbiyan diyan hausa yake. Kamun kaina a diyan hausawa rasgin hayani da fada da mutane barkatai wanda akasarin matan hausawa hake ne ke cutar su a gidan mazaje su da gun kishiyoyin su yan bana bakwai. Tana tuna yadda Nafisa tazo gidan daga ita sai ghana most go din yan kayan ta a ciki amma yau ta koma kamar wata hamshikiya a gida. Auren ta da aka dauro ba tare da sanin iyayyen su ba can bariki suka dauro auren su da ita inda ta tare a gidan da yake a lokacin a kano. Sannu a hankali har ya samu iyayyen shi suka hakkura ta fara shiga cikin su inda take baiyana harin ta na zahiri a hankali. Da farko ta yaudari mutane inda taja yan uwan miji a jikinta duk suka yarda da ita ta gama jin sirin su kaf kafin daga baya data bunkasa ta fara fitar da kalan ta ga mutane. Inda yanzu kowa ya gama gane ta wasu masu zuciyar imani sun gujeta masu kwadai kuma har wanan lokacin suna tare da ita duk da abin hannun ta bai ban baruwa wasan dadi sai kayi mata bauta kafin kaci abu daga gare ta. Don haka take kallon kowa a wullakance sai uan uwanta dakan zo jefi jefi cin arziki wurin ta wanda ba a wuce wata daya basu zo gidan ba. Tazo da wata yarinya da take cewa wai kaunar tane sai da tafiya yai tafi aka gane cewa yar tace ta cikin ta yarinyar. Nafisa zata girmay ma Fati ga shekaru haka yasa tafi fati wayo sosai har take jin tsoron ga fin karfi ga sihiri don bata shigo haka kai tsaye ba sai da ta shirya ta shigo gidan . Shi kan shi maigidan ba a banza ta barshi ko yanzu kuma bawai ta fasa abinda takeyi din bane sai ma abinda yaci gaba a cikin halayen nata. ZAINAB IDRIS MAKAWA Ina isa na fara bude kofana na lokacin yarinyar ta iso da kayan da Yusuf ya bata tana mika min kallon kayan nayi sai na karba ta karasa min da sauran a cikin daki na. Godiya nayi mata tace babu komai ai ana tare bayan na aje kayan na fada saman katifa na wasu hawaye masu zafi ne suke silalo min a fuska na. Idan na tunana da maganganun da ya fada min masu zafi duk da nima din nayi karfin halin ramawa a lokacin sai nake ganin ya kwaraini da yawa. Na dade a wurin ina neman hanyan da zan rama abinda yayi mun din don yaji zafin da naji ban kai ga samun mafita ba wayana yayi kara a lokacin. Yusuf ne ya kirani sai da ta kusa tsukewa na dauka na kara a kunne na ina sauraron shi yace har yanzu kina fushi ne yar mama. Daurewa nayi nace ai ban fushi dakai don bakai min komai ba yaya na yace dakyau ina son ki saurare ni dakyau magana nake so muyi dake yanzu. Ina jinka nace mai. Khadija don Allah ina son ki bani hankalin ki ki fahinci abinda zan fada maki yanzu naji na kara furtawa. Don Allah ina son in rokeki wata alfarma wani aiki zaki nake son ki min a kan aboki na amma aikin yana da wahala sosai sai dai indan kin daure ba wani wahala a cikin sa. To ina jinka Allah yasa zan iya kuma Allah yasa dai aikin bai fi karfina ba, murmushi yayi yana fadin bai fi karfin ki ba ma insha Allahu don zaki iya. Nace fada min inji aikin idan ba zai shafe karatuna ba da rayuwa na zan iya insha Allahu yace good girl dama na dade ina neman mace irin ki mai gaskiya da zan saka. Ba wani abu zan saki ba sai taimako rayuwan abakina Samad nake son in danka a hannun ki don kice a yanzu kadai nake da ita da zatayi min wanan kokari. Nace ni kuma yayana yace kwarai kuwa ke khadija don ko zaki iya idan munyi laakari da irin halin ki na san zaki iya shiyasa na zabo ki. Tun ranan da muka shiga dakin hajiya mama na fara ganin ki da kuma abinda yafaru dake da Nafisa matar shi kika tsaya min a rai. Ban kuma gaskanta hakan ba sai da naga kin iya biyu su a motar su zuwa nan Abuja kuma komai bai faru ba yasa na kara yarda da abinda nake shirin yi din . Sai gashi kuma yanzu abubuwa suna wakana a yadda nake son su tafi a tsakanin ku cikin hukuncin Allah komai yana tafiya daidai. Khadija ko kin san ba macen da ta isa ta tsaya kusa da Samad tun lokacin da ya auri Nafisa buzuwar matar shi kuwa. Nasan kin san matar shi Fati da akai masu auren gida har suka haifi yaya biyu shigowan buzuwa gidan ya sa suka rabu da ita badon basu son junan su ba. Khadija kin san abinda ya daure min kai nace a a yace yadda Yusuf ya aminta dake a lokaci daya duk da nasan ba abu bane mai wuya a wurin Allah idan ya tashi yin ikon sa akan abu. Don haka nake son ki taimaka muna ki sake jiki da shi tayadda zai aminta dake idan haka ya samu gare mu na tabbatar da sheri buzuwa yana gap da karyewa. Da sauri nace ba zan iya ba gaskiya ku nemi wata wanan miskilin mara mutunci ai buzuwar ne daidai dashi yace khadija zaki iya zaki iya komai. Kyau dai Allah ya baki shi ilimin addini da na boko duk kina dasu a wadace to may zai saki ce bazaki iya ba ai ko ba don niba ko don hajiya mama da fati da yaran ta zaki iya. Nace yanzu may kaka son in yi wai yace shina ke son in fada maki da farko dai idan ki bi labari na zaki gane Samad bai iya ssoyayya ba shine matsalaan farko da aka samu gare shi. Murmushi nayi nace bai iya soyayya ba ta yaya ya auri matan shi har suka zauna Fati har ta haihu dashi biyu shima din murmushi naji ya dan yi yace. Bamu tare ke nan kin manta na fada maki ita fadi hadin iyayyene auren su ita kuma buzuwa abu biyu muke zaton shine silar auren su na farko dai ta rude shi da kyaun ta na biyu kuma ta hanyar sihiri da sauri nace sihiri kuma bada ni ba gaskiya. Yace da zata iya maki komai da tayi tuntuni ai shine ya bani daman sakaki wanan aiki a yanzu. Nace a takaice dai kana son in bata lokaci na a kan shi abinda ya kawo ni in barshi inje taimakon wani wanin ma wanda bai san darajan mutane ba. Aikin da zaki muna ke nan dama ki koya mashi zama da mutane da sauran abubuwan da ya watsar a baya ki dawo muna dashi Abdulsamad din shi na baya. Babban magana ke nan yayana yace ba wani babba bane a matsayin ki na mace zaki amfani da daman ki taimaka muna ki tai maki hajiya dake cikin halin bakin ciki a kashi. Shiru nayi ina tunane ko badon Yusuf ba ko don hajiya da yaran Fati zan iya kasadan yin wanan gwajin da suke sona dashi yanzu. Nace to shike nan naji zan yi matukar hakan ba zai shafi mutunci na ba dai yayi saurin cewa idan nasan zai zubar maki da kiman ki ba zan saka ki ba ai. Nace amma fa in ya nemi keta min mutunci ba zan kyale shi ba zan dauki mataki da kaina yace wanan ba halin shi bane don nasan halin shi tare muka taso tun muna yara dashi. Nace Allah bamu sa,a yace amin na godd da kika fahince ni yanzu zan samu lokaci in shigo inji mai kike bukata don kin san dole sai kin koma ke ma babban yarinya sosai. Kada ka damu zanyi amfani da wanda nake dashi yace kin wuce wanan yanzu khadija zaki zama budurwan mayan garin abuja ne fa. Yace ina son ki fara daga yau nace yau din nan ina zanganshi yace zai bugo maki waya ba yana da layin ki ba nace eh zaki kaga ya kiraki kan abinda yayi maki. Amma sai dai please ki bishi a hankali yana da izza da saurin fushi da zuciya bai son yawan magana idan ba yaso ba amma banda wanan baida komai da zaki damu. Ni kuwa nasan haka nida ya fada ma magana yau sun ranshi sai dai zan jure kamar yadda kuke so inyi din. Ajiyan zuciya naji ya sauke yace ban san irun godiyan da zanma maki ba ga wanan haracin da kikai muna wanda nasan insha Allahu zai zamo maki alheri ke ma nan gaba. To Allah yasa hakan alheri ne a gare ni dai fatana in ga ya koma da iyalin shi normal sai naji ya sauke ajiyan zuciya yace final shine dama bukatan mu . Mukai sallama ya barni ina tunanen yadda abin namu zai kaya tsakanina da miskilin mijin buzuwa ta ina zamu fara nace anya ban daukar wa kaina abinda ba zan iya ba kuwa. Gashi kuma Yusuf yace sirine ne tsakani na dashi sai Allah sai ko nan gaba da zai fada ma hajiya mama shirin shi. A raina nace zan iya insha Allahu indai iyalin shi zasu dawo gare shi sai dai ban taba zaton abin zai zo a kaina haka ba amma ba komai wahala bata kissa ai. Nan dai nayi ta tunanen ta yadda zan fara deal din akan shi amma dai Yusuf yace shi zai fara aiwatar da komai kamar yadda yake yi da farko. Safiyan lahadi wanki nayi sai wanan bakuwar yarinyar da ta shigo min da kaya don dai han san ta a gidan ba tazo min hira dakina ina gugan kayan da suka bushe min. Nan take fada min ai ita yar jos ne amma tana zaune ne da yayanta a nan cikin gari ta dawo hostel ne don ta samu yin karatu da kyau naji dasin haduwa na da ita ko banza zan rage zaman kadaici ni kadai da nakeyi ni kadai. Waya na yai kara na daga Yusuf ne bayan mun gaisa yace fito gamu kofan hostel din ku dam naji gaba ya bada na kalli maryam dake gefe na nace ina zuwa ta mike ita tace zata je ta gyara daki don gobe akwai classes. Ba wani dogon kwalliya nayi na dan yafa gyale na na fito tun fitowa idon su yana kaina har na iso inda suke a cikin motar su. Na gaida Yusuf din yace ga abokina ogana baki gaida shi ba na dan juya wurin shi a yatsune nace oh ashe tare kuke ina wuni. Haushi da takaici ya kama shi ya rasa ma zai yi sai da Yusuf yace khadija na gaishe ka fa cikin yanayi da alama na ko in kula yace lafiya kawai ya kawar da kanshi gefe. A ranshi yace i hate dis girl wallahi Yusuf ya katse shi da cewa oga gata nan ta fito fa ya fada cikin tsigar tsokana ya juyo da sauri yace wa wurin na tazo dama. Yace bakai kace muzo kabata hakkuri ba abinda kai mata jiya kasa ta kuka ya damay ka da sauri na tare Yusuf da cewa ai nice zan bashi hakuri nida na bata mashi rai jiya. Don fadin gaskiya ni kuma nasan gaskiya na fada duk cikkaken namiji da yasan ciwon kanshi ba zai tsaya mace na juya shi macen ma kuma buzuwa wai. Yusuf dama ka kawo ni nan ne don ta kara ci min mutunci ko may haushi ya ishe shi yarasa may zai ce min wallahi na tsani wanan yarinyar ya fada a hasale . Cikin ko in kula nace i hate you too dama abinda yasa kuka zo ke nan daga ganin ka nasan ba yin kanka bane buzuwa ta hasala ka ka koma ma matar ka kawai ta asali ko mutuncin ka zai dawo ga idon jamma, a. Yusuf yace kai oga fitina khadija ko rigima nace bai son gaskiya ne gadai mutum har mutum amma bai kai ga cikan kamala ba har yanzu ga idon jamma a. Oh stop it gara ku fito fili kununa ma duniya soyayyan ku da wanan sallon soyayyan naku da kuke yi kullun u don't need to pretend garama ku fara tun yau. Wai Yusuf may kake nufi dani akan wanan yarinyar ne da kullun kake kawo ni wurin ta taci min mutunci hakane. Ni dramar kuce take burgeni wallahi don naga idan na kawo ka wurin khadija tana saka magana kana rage damuwa ko yaushe kuma tana ma tuni da abinda ka manta. Gyara zama yayi a motar ya kwantar da kai tare da harde hanaye shi wuri daya yana kallon bakin hostel din mu yadda mutane ke ta shiga da fita ciki. Nima kallon Yusuf nayi nace yayana wani wuri zaku ne yace muna dan yawata wane muka zo duba ki kin san ke amanan hajiyan mu ce gare mu yajuya wurin shi yana fadin ko ba haka ba aboki na ? Tsaki yaja ya kara kawar da kanshi gefe nace sai dai tsiyan abin indan yayi fushi fushin bai mashi kyau sai ma ya kara mai muni sosai. Murmushin dole ya sake yace kai Yusuf muje don Allah wanan na gane zata iya haukatani in banyi da gaske ba. Kaiko daukanta zamuyi mutafi da ita adan sawo mata wani abin mana kaga sai ta kara hucewa ko tunda gashi har ta baka hakkuri yanzu ai komai ya wuce kenan. Kinga ba sai kin fada ma hajiya mama dukan bakin ki da yayi ba jiya ai yanzu kun zama friends kuma ko fada ya kare ke khadija ba yayaki hakkuri don Allah. Da sauri ya juyo inda nake sai na dan durkusa nace ya Samad kayi hakkuri don Allah idan na maka laifi. Oh baki san ma kin min laifi ba ke nan Yusuf yace shigo mota sai mu karasa magana a hanya yamma nayi kwarai. Banki ba tunda nasan plain ne na shiga motar a hankali ya harba titi ina harara dan iska a inda nake zaune Yusuf ne ya shiga aiwatar da nashi shirin a lokacin cikin motar yana dan muna nasiha. Yace kar kuji komai indan nine take a deep breath and confess your love to each other wani irin dogon nunfashi yaja tare da lumshe idanuwan shi. Da sauri nace yayana love kuma a ina kataba jin anyiwa mutum dole haka akan abinda yaki jini yace don't say dat again just say yes to each other don kuna bukatan hakan. Khadija ina son ki rike min oga na tsakani da Allah ko babu soyayya ku zama aminan juna muna son ki gyara tsakanin shi da hajiyan mu ta fahince shi ta bar hushi dashi. Sai lokacin ya kallo Yusuf ya sauke wani ajiyan zuciya don ya zaci Yusuf yana son hakane don gyara tsakanin shi da mahaifiyar shi. Nace yaya zanyi in gyara mashi laifin dashi yayi da kan shi har kake tunanen nice zan gyara hakan yace yes idan hajiya taji kuna tare nasan zata ji dadin yin hakan da kuka kin ga zata fitar ma abokina da zargin da suke mashi na buzuwa bata bari ya rabi wata mace sai ita. Sai yanzu na gane nufin ka abokina ya danyi gyaran murya sai kuma yayi shiru can yace da farko dai na gane manufan ka yanzu Yusuf . Yace zamu shirya dake idan har zakiyi min wanan taimakon iyayyena su fahince ni a hankali nace idan ka shirya yin hakan a shirye nake in taimaka ma in har zaka koma masu da zuciya daya. Maganan ta dan soshi ranshi amma haka ya dake yace na gode a hankali ai lokacin gode min baiyi ba nace mashi. Tsayar da motar yayi a bakin wani babban sai da kayan sawa irin na mata da maza ga motoci birjit a wurin an paka su a haraban wurin. Bissimilah yace muna kallon shi yayi yace wa wai ni kake nufi kowa yace daku duka nake magana ai yace may zanyi a wanan gurin yace kaunar mu zamu ma sayayya mana. No kuje kawai yace yana gyara zaman shi a yadda yake nace da ka barshi ma ban bukatan komai a yanzu yace tunda nayi niyar yin haka barin in fita induba zaku iya jira a mota yana bude motar zai fita yake wannan magana. Da sauri nace dashi barin fito mu shiga tare yace No ki zauna abinki yanzu zan fito ba dadewa zanyi a ciki ba. Yana wuce na koma na zauna bayan na bishi da kallo wayana na dauko ina dubawa shiru motar babu mai maga a cikin mu sai can naji yaja guntun tsuki wai da bai harka da kananan mata sai manya masu aji ko su sai a waje idan yafita duk da ba wai yana yawan hurda dasu bane yanzun ga Yusuf yana son ya dauko mashi wani aiki ga wanan yar karamar yarinyar dako sa,an kannen shi batakai ba sosai. Nima tsakin naja ina gyara zama cikin tunanen da nakeyi nashi. Ga dai mutum har mutum kudi kwaliya kwarjini duk Allah ya bashi sai dai yawan miskilanci da girman kai da jan aji din yayi yawa kamar ba mace ce ke juta shi ba a gida. Ke ni kike wa tsuki ko kowa ya juyo tare da zuba min kyawawan idanuwan shi a kaina na ma mance kana cikin motar nan murmushi mai kama da takaici yayi yaci gaba da zuba min kyawawan idanuwan shi can ya koma ya lumshe su tare da komawa saman kujera ya zauna. Ya sake cewa kina aji nawa ne yanzu ba tare da ya juyo ya kalle ni ba shiru nayi ina game da wayana batare da na nuna mai dani yake magana ba. Dake nake magana ko bakiji bane nace wa ni ai na dauka da kurma nake a motar a hankali ya kada kanshi ta dan sake murmushi yace ke dai ba zaki bar wanan halin naki ba ke nan. Nace ba halina bane hakan a ra nayi don in kare kai na daga masu raina ma tallaka hankali ya fido ido waje yace haka kika dauke ni ke nan . Hakan na gani kamar kana tsoron talaka a kusa da kai sai dai ba abun mamaki bane don ko a gida haka naga kanayi masu wanan daure fuskan. Kin san nayi ma aboki na alkawarin ban kara fada dake yanzu don haka ki kama min bakin ki tunkan in hasala da wa yan nan maganganun naki. Kai ashe kasan girman alkawari haka ne nakoji dadin jin hakan saidai kamar yadda kai mashi alkawari ka cika nima ada hakana naiwa kaina alkawarin ba zan tsaya da wani namiji ba sai gashi a sanidin taimako ina son karya alkawarin da na dauka ma kaina. Yaja numfashi tare da cewa wanan deal ne a tsakanin na dan wani lokaci banga abinda zai sa ki dauke shi kamar serious ba. Nayi dariya tare da cewa wasa mai kamar wahala ba indan buzuwa ta sanda hakan akwai matsala babba ashe sai na kwashe da wanni irin dariya mai ban haushi dake wa yayi bai ce komai ba cikin kuluwa. Yusuf ya fito da manyan jakkuna a hannun shi yana kokarin bude motar ta kofar baya ya saka jin dariya yasa shi cewa abin ya fara tafiya ke nan dai. Ya dai kusa na bashi amsa a takaice kai a fasa wanan deal din nace a fasa gaskiya zai fi don wanan ba zai kai ko ina ba. Zai kai mana yace yana rufe kofan motan ya zagaya ya shiga kallon Samad dake dafe da kan shi yayi muka kama hanya a lokacin hadari ya hadu sosai a garin ruwa na iya zuba a ko wani lokaci. Mun iso Yusuf ya tsayar da motar yace khadija mun gode sai mun kara haduwa yanzun ba time hadari ya hade gari ta ko ina nace nagode kwarai. Ka kula min da mijin buzuwa don Allah na bude motar zan fita yace ga kayan ki nan ki kwasa duka naki ne godiya na sake mai karo na biyu na fice daga motar. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABUYanayin damana yanayi mai cike da albarka yayin da ban gare guda yake burge alumma ko babu komai yanayin da daminar kan haddasa jamma,a sha,awan ta saboda ire iren abunda damanan kanzo wa jamma,a dashi musanman musan nan abuja da ba noma suke ba amma yanayi yana kawatar da jamman cikin ta yayin da damanan ta fara mikewa zaka ga tsirrai iri daban daban dake kara kawata garin. Wanan yanayin yakan saukar min da nishadi sosai musanman idan naga garin ya gaure da hadari kasan ba wuya ruwa ya sauko masu. Yau ma na fito daga aji ke nan naga yanayin garin ya sauya nasan bamu nisa da samun ruwan sama ke nan kusan kwana shida ke nan ana zuga muna ruwa a irin wanan lokacin. Tafe nake a hankali nake takawa daga cikin haraban makarantan zuwa hanyar da zai fitar dani daga cikin makarantan sai dai zuciyana cike yake da tunanen rashin kudin da ban samu fita zuwa turawa daddy ba har yau ko da zan fito hadari ko ruwa zai tare ni gashi ban son inyi missing din lecture da safe. Abu biyu ne yake damu na yanzu yunwa da tunanen daddyn mu saboda banci komai ba tunda safe da na fito don yau na makara ban tsaya na karya ba. Saboda nacin karatu da nake dashi a raina don koda dare haka nakan raba dare ina karatu ni kadai a daki sai na gaji zan dan taba barci asuban farko kuma in tashi in fara nafila ina kusanta kai na ga Allah idan na gama kuma karatu zan dan dasa a wurin sai zuwa haskawan gari zan tashi in wanka in karya in kama hanyan shiga cikin makaranta. Yau sai aka samu akasi na makata ban tashi da wuri ba har rana ya fito hakan ne ya hanani tsaya in karya wanan tsarin dana dauka yana matukar wahal dani . Amma ni ina aganin shine daidai don iyakacin abinda ya kawo ni kenan a garin indan ban yi ba may zanyi. Domin karatu na bar gidan mu na bar dangina da kowa nawa a gida nazo nan idan ban mai da hankali ba mai zanyi sai shiririta ke nan kamar yadda naga sauran dalibai suna yi. Don a ganina karatun shi yazama min dole dashi na dogara dashi nake saka ran samun ci gaban rayuwa na dana iyayyena nan gaba . Buri na ne burin iyayye na da yan uwa na ya ta,allaka ne akan karatun don haka babu dalilin da zai sa in zauna ina wasa dashi. Nikan zauna in dinga tunanen yadda nake ganin wasu dalibai suna wasa da daman su ta hanyar zibar da abin da ya kawo sai in rika mamakin su ina tausaya masu don nayi imani da cewa suna cutar da kansu ne sun kuma ha,inci iyayyen da suka turo su karatu . Ire iren su gasu nan da yawa sai yadda suke so sukeyi a cikin makaranta kwata kwata basu damu da karatun ba sai idan jerabawa yazo ne ido ya rena fata duk dadai wasun su ne suke damuwa da hakan. Wasu ko iyayyen su ko samarin su suna masu hanya su haye ire iren tunanen da nake yi ke nan ina tafiya saman dogon titin da zai sada ni da gidajen da muke ciki. Ido na zubawa wata dankareriyar motar jeep dake nufo inda nake a hankali ba ka gane wanda ke cikin motar dan glassen motar da ya kasance masu duhu baka gane na cikin motar balle ma wana sani ni anan. Ta gefen ido nake kallon motar har zuwa lokacin da motar tayi gaba kadan dani ta tsaya a gaba na ban dauki komai a raina ba don a gani na wani abin maishi ya tsaya yi. Nazo zan wuce motar ne naji muryan kamar wanda na sani yana cewa yar garin mu yanzu nake tunanen ki da hanya ya biyo dani ta wurin ku. Don sheda muryan maishi da nayi yasa ni sakin dan murmushi kadan nace kaine kuma yau a wurin namu yace wallahi aiki ya biyo dani tanan din kuma ashe da rabon ganin ki. Murmushi nayi na fara gaida shi ya amsa yana fadin ummm Khadija ko nace eh ashe baka manta da sunan yar garin naku ba dai. Murmushi yayi yace ina zan manta da yar mama baki tambaye ni mijin bazuwa ba yau murmushi na kara yi nace kace dai miskilin mijin buzuwa. Yace kin kara masa inkiya ke nan nace shine daidai dashi ai suna lafiya ko ya labarin gida koda yake muna waya dasu Binta ma nasan suna lafiya koda yake tace an ma mama rasuwa zariya ta tafi can tun jiya zata kwana uku a can. Yace kai haba bata ko fada muna ba wallahi wa ya rasu a can zariya din sai kuma yace kada in tsare ki a hanya don naga kamar bakin son hakan ke. Murmushi nayi nace idan hakan ya dauro yaya zanyi sai yace shigo mana in karasa dake idan ba damuwa nace lah ai ba wani nisa don na kusa karasawa ai. Sai dai don Allah ina zaka bi don ina son sauka a bakin, banki in tura kudi yace to shigo mana in sauke ki ai ke din kanwar mu ce na zagaya gefen ina fadin na gode. Mun dan fara tafiya wayar shi tayi tsuwa ya daga yaya akayi ne mijin buzuwa banji may yace ba don karan kira,an dake tashi a motar murya malam Ahmed sulaiman kano ne. Yace wallahi gani nan dawowa sai dai kuma uzuri ya tare ni din na hadu da yar garin mu a hanya na rage mata hanya zamu banki da ita. Wake nan ya tambaya a cikin wayan yace khadija wama surname din ki Adamu nace mai a takaice yace khadija a dabu kawar tafiyan ka na ranan. What Yusuf sai da ka kara nemo yarinyar nan don Allah yarinyar nan bata da kunya fa ganin Yusuf nata dariya yasa ni wafce wayan ina karawa a kunne na naji yana fadin wanan yarinyar matsalace wallahi sam bata ganin girman babba. Nace nakai matar kane rashin ganin girman dan adam kai har kana da bakin fadar haka yace baki da kunya ko nace aikai kana dashi kada ka kara kirana da mara kunya wallahi. Yusuf ne ya karbi wayan a hamnu na yana dariya yace kadai ji abinda tace kada ka kara kiran ta da mara kunya ehheh. Yusuf abin naka ya girmay sani na yanzu tunda har ka iya mika mata waya ta zage ni yace bata fa zage ka ba man ina jin yadda kukayi da ita sarai. Mun iso ya tsaya na fita ina mai godiya yace shiga ki fito ina nan ina jiran ki har ki gama kin ga akwai hadari a garin sosai komawa zai maki wuya kuma. Nagode nace dashi ina fita yace ara min wayan ki kafin ki dawo dan jimm nayi kamar ba zan bashi sai kuna mika mashi wayan na fice daga motar sai da na gama abinda nakeyi na tabbatar da kudin sun shiga na fito lokacin har an fara yayafi kadan kadan a gari yana zaune yana duban wayan shi na dawo na samay shi ina shiga yace har kin gama eh nace mai ina rufo kofar motar waya na ya miko min na karba ina fadin ka gama dubawa ne yace dama waazi neke dubawa a ciki murmushi na danyi kasan baki na. Lokacin aka fara ruwa mai yawa duk da ban ganin hanyan da kyau amma na gane ba hanyar da muka fito bane muka bi yanzu. Dan kallon shi nayi yace kada ki damu zan dauki mutumi ko ne ya gama mintin driver kuma wai yakai Nafisa Nasarawa bai dawo ba. Banji dadin jin hakan ba sai dai ba yadda ja iya kuma a wani ma, aikata muka shiga ya tsayar da motar da sauri ya fito ya shiga motar ni kuma na koma baya. Kamar ban cikin motar don banyi magana ba sai fada yakewa Yusuf wai ya dade baizo ya dauke shi ba yace kan wani aikin da kasa kanka can . Ya haba taimako ne fa nayi kasan ace a taimaki mata ai a duk sanda suke ga bukatan taimako cikin tsawa yace ya ishe ka hakana Yusuf enough ta fada da karfi yana dafe kan shi da hannun shi daya. Nan zan sauka nace a daidai lokacin da yake dafa kkan nashi da alama bai san dani a cikin motan ba ma sai a lokacin dan juyowa yayi yana kallo na da mamaki a fuskan shi ya sai kuma ya juya yana kallon Yusuf din. Na sake fadin a nan zan sauka nace fa nace ma Yusuf ya juyo yace acikin ruwan nan zaki sauka haka a ina zaki samu abin hawa nace kada ka damu ai zan samu idan na fita. Yace to bari in dan karasa dake inda zakiyi saurin samun abin hawa ya fadi shima fuska a dake da alama yaji haushin abinda yayi mashi a lokacin. Karasa da ita ka ajeta yace ba tare da ya kalli kowan mu ba yai magana dama ba sauke ta zanyi ba ai sai na kaita inda na dauko ta. Ba wanda ya sake magana a motan har bakin gidan ya tsaya da mota lokacin an dan rage ruwa sosai amma anadan yi kadan kadan yace ashe hajiya an mata rasuwa ne. Ina fita naji yana fada mai hakana na gode yaya Yusuf agai da gida da mutanen gidan Allah ya kara rufa asiri na fice daga cikin motan abina. Ban tsaya ba don ruwan sama bai bani lafiya idan ya buge ni sai dai ban tsira ina fita ruwan ya sake saukowa da karfi da gudu na karasa cikin . Sun kama hanya ya dubu Yusuf din yana fadin wata hajiya akaima rasuwa nace yace hajiya mama mana hajiya mama nawa kake nufi ita yanzu wanan yarinyar ke fada min . Shiru yayi bai sake magana ba sai zuwa can yace wata ce ma yarasu a zariya din kana son sani kake daure fuska haka tsuki yayi sai can yace barin kira hajiya din in ji. Har ya dauko wayan ya fara duba lanban mama din sai kuma ya dago kai yace kana da nomban wanan yarinyar kaba in kira ta. May zakayi da layin ta kuma yarinyar da bata da tarbiya yace malam idan zaka bani ka bani kawai ba dogon zance nake so ba kyale shi yayi kamar bada shi yake magana ba. Sai zuwa can yace ana son ai maka gata kana wani jiji dakai wanan jida kai din ba zai kaika ko ina ba a harzuke yace nomba nace kabani kada ka fada min wani magana da zai kara bata min rai bayan wanan. Har saida yakai shi hara ban gidan shi ya ajeshi zai fita ya miko mai wayan shi yana fadin ga nomban nan kamar ba zai karba ba sai kuma ya daure ya karbi wayan ya kwashe nomban. Ya mika mai wayan ya shige ko sai anjima baice dashi ba shiko murmushi yayi yadan bugi sitiyaein mota shi ya juya ya fice gidan. Nafisa buzuwa ce suke tafe da kawar ta nan cikin garin Abuja sun fito nasawa state ganin wani malamin su a can da tai ma mijin karya zasu duba wata aminiyar ta ne . Bai hanata zuwa duk inda take so shiyasa tale samun yin yadda take so a gidan don shi kwata kwata bai dauke ta da irin wanan halin ba na matan dake shige shige. A hankali suke magana yadda sani driver ba zai fance su ba shiko a idan yake tuki ya mayar da hankalin shi ga hannya ne amma kunnuwan shi yana gare su. Nafisa ke fadin kin san Allah wanan sakawa zanyi yai min aikin da ko uwar shi ba zai iya daga ido ya kalla ba balle wata mace don naga alaman wanan arnen yada aiki sosai. Don su malam kasan mu ko ka basu aiki irin wanan sai sun kawo maka Allah kusa kafin su duba maka kukan ka. Suwaiba kawar ta ya mutsa baki tace ke ma kikan so damun kanki nafisa mijin da ko a yanzu a hannun ki yake wanda kika sa ya kore uwar yayan shi kuma ka zauna lafiya may kuma yanzu zai wani daga maki hankali. Bai fa kallon mace sau biyu a yanzu hakan ba anan matsalan yake ba suwaiba wanan abokin nasa da suke kamar tagwayen sheri dan iska mara zuciya nayi kora da hali nayi na fili amma ya na lake kamar kaska dashi. Kina ganin ko baiyi niyar yi ba shi bai iya dauko ko mace ya kawo mai ke komai tsiyan su fa baki taba gane sirin su dashi dashi. To ai yanzu ba tashi zakiyi ba tunda shi kin riga da kin samay shi a hannu ko sai yadda keki so dashi yanzu akan wanan abokin nasa zaki koma ki san yadda kika raba su. Gaban Sani driver ne ya fadi har yana batun kauce hanya dama yana zargin gidan da yakai su din ga zargin shi ya zama gaskiya har ana batun raba ogan nasu da aminin shi. Wanda yasa in tayi nasaran yin hakan ta gama da ogon nasu ke nan gaba daya tunda shi kadai ne dama ya saura yana sashi a hanya yanzu. Muryan ta yaji ta daka mai tsawa ya kula da tukin da yake yi ya dubi hanya mana yace hajiya rami na kaucewa shi ya kawo hakan. Suwaiba tayi mata rada su bar maganan harsu sauka kada yaji abinda suke kullawa sai suka dauko wani sabon hira. Sai kuma tace malam sani ke nan dama ina son magana ta siri dakai sai dai maganace ta taimakon juna dani dakai. Yace hajiya wani taimako kike sona dashi tace siri ne kuma amana a tsakanin mu dakai amatsayi na matar ogan ka kuma wanda yasan wasu abubu nawa. Idan kuma kaga bazaka iya taimaka min ta wanan hanyan ba to zamu hada deal dakai in dinga biyan ka akan aikin ka. Dan juyowa yayi yadan kalle su zuciyar shi ya tabbatar mashi da cewa wani abu mai muhinmanci zata saka shi yai mata da ya shafe ogan nasa. A fili yace hajiya fadi bukatan ki a shirye nake da in aiwatar maki matukar bai fi karfin iyawa na ba murmushi tayi tace ai ba wani abu mai wuya bane zan saka ka yi. Ogan ka nake son ka sama ido don Allah duk wata mace da kaga yana hurda da ita a bayana har sun shaku a tsakanin su banda gaisu ka sanar dani ni kuma nayi maka alkawarin duk wata zan baka dubu biyar bayan wanda mai gida ke baka. Yai dan dariya yana shafar kanshi yace hajiya idon wanan ne kar kiji komai aran ki nayi maki alkawarin ko gaisawa da wata naga yayi wace bata gamshe ni ba zan fada maki. Suwaiba tace dakyau dan gari dama ai na fada maki babu abinda kudi bai bayar wa ke bude bakin jakkan ki ga aiki da cikawa kawai. Da sunan zuciyar Sani driver da basu furta komai a gaban shi ba don nasiha hajiya mama kullun suka je kaduna ya shiga gaida ita shine don Allah ga amanan yaro na baka Sani ko ba komai yanzu mun zama daya dakai tunda ana wuri daya. Duk da kasalan dake damu na a lokacin bai hanani tashi in girkawa kaina abinda zanci ba lokacin bayan na gama ne na fitar da kayan da nayi aiki na wanka na shiga bayi na watsa ruwa masu zafi don ruwan sama bai bani amana ajikina. Ina fitowa daga bayi ne mukai kicibis da zarah da ta shigo dakin nawa a lokacin wanda alama ya nuna yanzu ta dawo daga cikin gari sabada ledan da take dauke dashi a hannun ta. Nasan key din dakin ta tazo dauka tana saye da wasu kaya da ya matse mata jiki sosai kin dawo nace mata eh kin gani sai yanzu na dawo wallahi. Inda key din yake na nufa in dauko mata na mika mata leda daya ta aje min daga cikin ledejoji dake rike a hanun ta nace lah dakin dauka wallahi na fada maki ai ban son komai daga irin abinda kike dawowa dashi. Lumshe idon ta tayi cike da jin takaici na tace na sani amma wanan ba inda kike zato na samo shi ba sako ne da samu an kawo min daga gida naga idan na barshi ma a hannu na baci zai yi shiyasa nace bari kawai in mika maki. Ledan nabi da kallo a raina nace watau sakon da iyayyen ta suka aiko mata dashi bai da wani amfani a gare ta sai na mazan da take bi ke nan. Karban key din ta tayi ta fita dakin na bita da kallo tana saye da kayan da ya matse mata jiki sosai ga kitson kanta da ta sako su har kafadan ta. Tsuki nayi na shimfida anbin sallah na tayar da sallah na na idar na koma na jingina da katifa na ina jan casbi a hankali waya na dake gefe yayi kara a lokacin. Number ne ba suna na daga ina mamaki waye mai wanan special number yake kirana kuma kusan kiran zai katse na dauka. Da sallama a baki na sai naji shiru kara maimaita sallaman nayi wanan karon sai aka amsa min a gadarance kamar naso in sheda mai kiran amma na kasa canka. Shiru har lokacin na sake cewa hello naji ance ina jinki nace wai waye please ko wrong number aka kira ne yace ke kina magana da Abdulsamad Abdulrahim ne . Nace waye haka kuma bazaki sani ba don ba lallai ne ki sani din ba nace kai ta shafa wanan kuma banda lokacin irin ku haka kuke kiran mutane don bata masu lokaci kawai. Ke ban son rashin kuyan da kika iya ke har a wayan ma sai kin nunawa mutane halin ki ba wani abu yasa na kiraki yanzu sai don inji wayarasu hajiya ta tafi zariya. Au kace min miskilin mijin buzuwa ne nikan ina zan sani kaji ka da wani magana ni zaka tambaya wa hajiya ta rasa kuma ? A har zuke yace eh don a bakin ki mukaji ta tafi zariya shiyasa nake son jin wanda muka rasa din bawai na kiraki bane kimin rashin kunya. To ban sani ba kuma kada ka kara kiran layi na kaji na fada maka zan kashe nace wai ma a ina ka samu layina dan fitina ? Wanda kika ba ya bani layin ki mara kunyar yarinyar kawai zaki gane baki da wayau idan na kama ki don naga rashi kunya yana nema yakawo kaina. Kit na kashe wayan ban bari ya gama fadin abinda yake fadi ba don ba zan iya tsaya in saurare shi ba nace wanan wani iri fitina ne kuma? Ina ruwan shi dani da zai wani bugo min waya wai yana tambayana wa mahaifiyar shi ta rasa da ta tafi zariya gaisu dan rainin wayau shi ba danta bane baifini kusa da ita ba waini may hadina da wa yan nan mutanen ne haka da suke son su shiga min rayuwana ina zaune kallau. Shiko a ban garen shi ji yayi kamar ya samay ni ya fafala min mari ya sauke haushi yaya akayi ne na raina shi haka ne. Yaja tsuki ya fara laluben nomban mahaifiyar tashi dole ba don yaso ba yaji may yasa har abu na faruwa irin haka take nisan ta shi da ita duk da yasan fushin da hajiyan keyi dashi a kan Fati ne ba komai ba. Kamar bata dauka ta dauka tare da fadin sallamu alaikum ya karba mata a cikin ladabi sai ya fara gaida ita bayan gaisuwa ne yace cikin kwantar da murya hajiya naji ance anyi maki rasuwa a gida kin tafi ? Eh haka ne nayi rashi amma ni ya shafa ai rashin da nayi don jin ka baida wani amfani a gareni inda dai dangin ka na kauyen maradi ne da ka tafi ko tuntuni. Shiru yayi yana sauraren zafafan maganan da mahaifiyar shi take fada mai tace wai tunkuna ma wani dan karabanin ya fada ma nayi rashi a dangina har kaji duk da nasan ba kiran mutane yanzun kake yi ba buzuwan matar ka da dangin ta sun ishe ka. Hajiya kiyi hakkuri nima a wurin yariyar nan Yusuf ya jiyo muna shine nace ba a fada min ba tunda har zaki je zaria ki kwana biyu haka ba karamin rashi kika yi ba. Tace wace yarinya ke nan kake magana a kanta yace yarinyar da kika hadamu da ita kwanaki muka taho abuja sai dai yarinyar bata da kunya ban gane inda maganan ta ya dosa ba. Au khadija kake nufi ko wa yace ina ganin sunanta ke nan Yusuf ya hadu da ita take fada mai yaban layin ta na kirata tana karanta min shirmay . Tace Ladi ce matar kawun ka Allah ya karbi abinshi shine nazo ita khadijan kuma ta damu da nine shiyasa tasan damuwa na har taji. Yanzun kai bakaji kunya ba ace wai har khadija zata ji zance na kai bakaji ba haduwan ka da yarinyar gaba daya ya canza muna kai kana ko tuna makomar ka ga Allah. Bani ba ba mahaifinka ba duk kayi watsi da alamarin kowa kana ganin buzuwa da yan uwan ta sun isheka rayuwan duniya. Mu din dai da kake gudu din mune dai iyayyen naka har gobe zance guda ne abin nan da ka guje mu akan shi yana nan yana jiran ka . Sannan da kake kiran khadija mara kunya ita ma ka sa mata tsanar ne na babu gaira babu dalili saboda da tafi karfin matar son naka ko may . Zai yi magana ta kashe wayan ta ta kyale shi ranshi yaji ya baci sosai da maganan hajiya yasan akan Fati take wanan fushin haka dashi to shi may ye laifin shi a ciki. Hajiya suna gama waya binta ta kira tana tambayan ta ko sunyi waya da khadija tace mama ta kura tana tambaya na ke nace kin tafi zariya an maki rasuwa acan zaki kwana biyu. Tace oho yanzu yayan ku ya kira waya wai sin hadu da yusuf take fada mai a wurin ta suke jin an min rasuwa don baida kunya har khadija taji abu ya samay ni tana jajantawa amma shi bai ji ba. Sai kokarin son ya zagi yar mutane yake wai bata da kunya shi waya fishi rashin kunya yanzu shida ya nuna muna ba komai muke a gare shi ba. Sun gama da binta gulma ya ci binta sai ga kiranta ina shirin kwaciya ya shigo min. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: 🧠MIJIN BUZUWA🧠 2ï¸âƒ£ ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU NOVEL DIN NAN NA KUDI BIYA DARI UKU KO KATIN DARI UKU TA WANAN ACCOUNT DIN 2254380105 ZAINAN IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KI KIRA TA WANAN LAYIN 09026931792 KO 08036959257 ASHA KARATU LAFIYA Hayaniyar yaran da suka dawo daga makaranta ya dawo da ita ga tunen tace shike nan nawa ta samay ga Affan da dan banzan wayo kawai na shiryasu zuwa cikin gida wurin kakanin su tasan idan sunje can sa samu abinda sukaci a cikin su. Yaran suna shigowa suka fada mata a jiki suna fadin mama mun dawo yunwa nakeji sosai wallahi karamin ya fada take taji gabanta ya fadi don hakan halin su ne . Sai subar abinci a cooler makarantarsu su dawo dashi kuma suce yunwa suke ji halin yaro ke nan oya a cire uniform kuje cikin gida wurin su hajiya kwaci abinci a can banson yawan hayaniya yau. Acan cikin gida kuma dawowan yaran gidan makaranta yasa hajiya ta kasa kunne taji shigowan jikokin nata da take zaman jiran tsamanin su tunda safe. Ba afi min ashrin ba ta fara tsinkayo hayaniyar su daga kofan shigowa gidan tace a ranta nasan a rina dama tabbas hashe na ya tabbata ke nan wanan yarinyar har takai can. Yaran suka shigo dakin da murnan su don anan kawai suke samu su sake suyi yadda suke so batare da wani tsangwama ba. Suna shiga Affan ya cire rigan jikin shi ya rage daga shi sai singlet yana fadin hajiya maman mu tace muzo nan muci abinci a wurin ki wai yau bata son damuwa. Yar ta Aisha ta kwala wa kira tazo ta basu abinci sai gata ta fito daga daki tana saye da dogon riga a jikin ta tana ganin yaran tace a a su Affan ne yau da rana tsaka anan zakuci abincin rana ke nan ? Hajiya tace zuba masu Abinci don Allah ki kawo masu nan ta wuce kitchen cika umurnin mahaifiyar nata da sauri sai gata dauke da plate din abinci ta kawo masu. Hajiya na zaune gefe ta kurawa yaran ido tana kallon yadda suke cin abincin gwanin ban tausayi dasu tunane tayi aranta da yau babu ita fa kamar yadda babu ran kakarsu ta wajen uwa yaya Fatima zatayi da wanan ukuban haka ? Hajiya kubura da take matse ita tunda rana sai gata ta shigo wurin hajiyan da mamaki a fuskanta tana fadin yaya kin ga hasashen yana son ya tabbata a kan yarinyar nan ko sai ga hajiya karima uwargidan su tashigo a bayan su tace tabbas maganan mu ya zama gaskiya. Ya tabbata ke nan ta ki bari yarinyar nan ta girka abinda zasuci a gidan abin har ya tashi ga ta hana mai aiki yi masu girki suci ya koma ta hana masu abinci. Sallama ake daga kofan shigowa dayar yarinyar gidan ta leko daga kofan hajiya karima tana fadin sannu da zuwa yaya Suraj. Bai amsa mata gaisuwa ba sai tambaya yayi ba kowa a gidan ne ina sallama gidan shiru tace suna dakin hajiya mama ina gani can yanufa dakin don yasan idan sunyi irin wanan taron akwai abinda ke faruwa da ya shafi dayan su ne don don iyayyen nasu nada hadin kao sosai a gidan. In ka debe ko wanan ya kasance amaryan su Asiya bata gida ne a lokacin da su hudu zasu hade a dakin kofan ya nufa yana saye cikin uniform din shi na sojoji. Sallama yayi a bakin kofan daga ciki suka amsa mashi mahaifiyar shi hajiya karima tace kamar muryan suraj nake ji a kofa yace nine ummi. Dakin ya shiga kallo daya yayiwa iyayyen nashi alokaci guda ya gane akwai wani matsalan da suke fuskanta wanda ya shafi hajiya mama a gidan. Gaida su ya fara yi a cikin ladabi kamar ba soja ya samu wuri ya zauna bayan sun karba mai gaisuwa. Duban hajiya kubura yayi yace mommy akwai matsalane su Affan dake cin abincin su hankali kwance ta nuna mai tana fadin wanan fitinaniyar matar uban tasu ce kila ta rufe dakin girkin gidan ne yau ko da safe a nan suka dauki abincin zuwa makaranta. Yanzun kuma kaga uwarsu ta turo su nan su da sauri yace ita Fatin fa may zataci to ya tamnaya yana kallon fuskokin su gason jin amsan su. Mommy tace ai shi muke tunane a nan dafe kai yayi yace wanan mata ban san abinda take nufi ba a gidan nan tana son mayar muna da dan uwa binan. Kada kaga laifin ta ai shine mai babban laifi mama ta fadi a hasale sai mummy tace ba yin kanshi bane yaya bar irin shuuman matan nan wallahi. Suraj ya mike a hasale yana fadin yau sai naci mata mutunci idan haka gaskiya ne wallahi ko a gidan maza ana ma mutum horo da yunwa ne balle gidan brother za a ce anyiwa mutum haka. Ko maigadin gida ai yana iya kyauta da abinci tunda bai rasa ba balle diyan shi ummi ta kalle shi lokacin da yake shirin fita daga dakin tana fadin ina zaka ? Kai tsaye yace gidan zanje wallahi idan na samu gaskiya ne yau sai tabar gidan nan wallahi ummi tayi saurin cewa dashi kaifa mahaukaci ne na sani a dai karbe key din ka bude wurin shike nan. Kasan yadda dan uwanka ke son ta hakan zai iya kawo matsala a tsakanin ku yace wallahi sai dai ya kawo ummi wanan wani irin bakin haline haka ? Ai haka suke mommy tace mashi abinda ake mai gudu ke jan tun farko bai gane ba basu son kowa sai kan su da yan uwan su kawai wanan halin su ba wai ba. Mama dai ta rike goshin tada hannun ta sai wanda duk yai magana cikin su ta bishi da ido kawai shine nata yayin da zuciyar ta ke mata soya a ciki tana jin wani irin ba dadi a ranta. Yana tsaye daga kofa mommy tace bari muje tare dakai zaifi da sauri ummi tace haka zaifi kan don wanan kin san mahaukaci ne ya shawo Alluran shi ja sojoji kar yaje ya sauke wa yar mutane a kai. Ai da zai sauke din haka zai fi gani take duk ta gama da kowa a gidan babu wanda bata iya takawa shiyasa take abinda taga dama inji mama. Yanzun dai bari mu tafi idan munje ni zan fara shiga wuri ta inji ba asin yin hakan da tayi sai asan abinyi sukace yayi kyau hakan mikewa tayi zuwa dakin ta ta dauko hijjib din ta ta saka suka fice da suraj din a motar shi suka karasa gidan. Daidai lokacin Abba ya dawo shi da anty amarya daga asibiti da dan ta da bai da lafiya ganin motar suraj ya gilma ya nufi gidan dan uwan nashi yasa suke mamaki. Anty amarya ke fadin yau suraj ziyara zaikai gidan Abdul ne haka mahaifin nasu yace kila yazo ya samu Fati ta koma dakin ta ne zai dubuta. Sai da suka shiga gidan ne suke jin abinda ke faruwa karban key anty Amraya tayi bata shiga dakin taba ta bar yaron wirin uwar gidan nata ta mara masu baya. Sun samu kofar gidan a rufe wai taba maigadi sallahu cewa kada ya bari kowa ya shigo gidan ya damay ta don yanzu ta dawo da yarta daga makaranta zasu huta. Da kyat ya bude masu kofa sai da suraj yayi mashi jan ido wanan abin shiya kara harzuka suraj din rashi ya baci sosai kusan a tare suka shiga gidan da anty amarya don samun delay din shiga da sukayi. Bin gidan Suraj yayi da kallo daga sama har kasa kafin ya karasa fitowa daga motar shi cikin hasala mommy tace ashe kun dawo ke nan take cewa anty amarya tace mun dawo ina shiga ake fada min abinda ke faruwa nace barin biyo ku don ba mutunci ne da ita ba. Anty tasan ida take rashin mutunci ta ai nika yau idan tayi min wallahi balbalata zanyi in daki banza sai dai mu rufe da mijin ta ai mun saba. A tare suka shiga gida jin karan bude get din gida ta fito a fusace tana fadin maigadi wani dan bura, uba kabudewa, , , , , ganin su mommy yasa tayi shiru ta juya da saurin tana zaton basu ganta ba suko sun ganta. Kafin su iso ta wuce part din ta ko da sauri don tasan ba bakin ta bane na Fati ne don ita suke zuwa gidan su . Tunda ta sallamay sallah la,asar take zaune saman sallaya ta tun tana addua ta koma tunane ga tunanen ya bowayeta don yunwan da ke cin ta. Sun shiga da sallaman su aka gaisu tace mommy kune tafe ashe mune fati har kasa takai tana kara gaida su cikin mutunci suka amsa mata ta dago tana fadin yaya Suraj marmari daga nesa. Ke kin ci abinci yau ko baki ci tambayan da ya jefo mata ke nan a lokaci daya tayi murmushi tace kajika da wani magana kuma ba a gida ka samay ni ba zakai min wanan tambaya haka ? Mommy tace Fati ba tambaya muka zo yi ba don mun san abinda ke wakana a gidan ko yau dai bakici komai ba tunda garin Allah ya waye haka ne ko ba haka ba. Kai ta sadda kasa tace hakane mommy tace to akan may Fati zaki zauna ana maki horo da yunwa dake da diyan ko haka abincin nan akwaishi ba babuba kuma. Mommy yau fitina take ji tun jiya data dawo ta samu na dawo gidan ta fada min bakaken magana har tana ikirarin sai na rami ya fini shan iska a gidan nan. Shine yau da safe zan shiga kitchen na samu ta kulle komai tunda asuba wai kada a dora girki a gidan ta fadawa Laraba ni kuma ban koma ta kanta ba tunda nasan don ni tayi hakana. Haba Fati sai ki zauna da yunwa ai zaki kashe kanki ne idan kina haka yanzu bari muje mu samay ta muji may take nufi wai. Suraj bai bisu ba ya dan tsaya ganin Fati din yana kuma tambayan ta may zataci yaje ya sayo mata tace duk abinda ta samu yace kayan tea fa tace suna store acen muke ajewa fita ya yi ya mara masu baya. Sun shiga da sallama cikin isa ta karba masu sai suka tsaya gaisawa da ita tunda iyayye ne su bayan gama gaisuwan mommy tace munzo ne dama muji dalilin rufe kitchen da tsore din gidan da akayi wa mutanen gidan. Hajiya nan fa gida na ne ina da daman da zan rufe ko ina nake son don Abdul bai bar abinci da Fati a gidan nan ba tunda bai cata dawo ba ta dowo don haka sai ta jira idan ya dawo ya bata abinci ita da diyan ta suci. Karya kike yi munafukar Allah kuma baki isa ba wallahi muryan Suraj ne da batayi tsamani ba ya fado dakin yana zazzare mata ido a cikin hasala yake magana yana huci. Tare da daka mata tsayawa yana fadin ban makulin nan tun ban balbalaki yanzu a wurin nan in kuma sa sojoji suzo su kwashe ki sukaiki barikin mu su daure har ranan da miji ku ya dawo inji shiku idan shiya ai horo da yunwa haka. Kallo da tayi wa Suraj raga fuskan nan nashi ba imani a cikin sa zai iya aikata abinda yace a kanta tsoran ta Allah tsoran ta soja da sauri ta mike ta shige dakin ta yabi ta da harara. Yadawo da fuskan shi kan yar ta dake cin abincin da tayo masu take away a hanyan dawowanta gida ya watsa ma yarinyar harara da sauri ta noke kanta kasa ta kasa cin abincin da tun shigowan su dacin abincin ta take yi bata ko gaida su ba. Da sauri tafito daga dakin dauke da key din a hannun ta tana mika mashi cikin ladabi ya fisge a hannun ta har ya fara tafiya su mommy zasu bishi sai kuma ya juyo yana fadin. Ina ne kitchen din da tsore suke ki taso muje yau za a yi ta ta kare and idan bayan tafiya ko harara naji kin ma yar uwa wallahi yau ba ubanda zai hanani daureki a garin nan jiki na rawa ta bi bayan shi zuwa tsore din yace ta bude da kanta ta bude. Laraba da mai masu aikin gida namiji da ta dauko dan kabilar su can garin su wanda ya zama kamar CID din ta ga komi a gidan ko tana nan ko bata nan ya kira. Komai na tsore din aka fito dashi waje aka kasa uku yace Fati ta kwashi kashi biyu ita da diyan ta kashi daya ta dauka nata ne. Ga abin magana ba halin yi don tsoron soja da ke zuciyan ta tun da zasu shigo Nigeria sojoji suka latsu a hanya take tsoran soja inda duk ta ganshi. Yana tsaye a rike kunkurun shi da hannayen shi biyu yake tambayan fati akwai wani tsore da kitchen a gidan tace eh akwaishi a part din ta wanan nata ne ita fatin suke amfani dashi in generar. Kwashi naki kikai part din ki da sauri taja wani kwali da kyat tana fadin kasiye dauko mun sauran ta matsu tabar wiein wanan dan banzan soja mara hankali dake gabanta. Dama tun zuwan ta gida da ta fara ganin shi aka nuna mashi ita a matsayin sabuwar matar wan shi bai yi murna da ganin ta ba a fili ya nuna hakan kowa ya gani. Don shi kyamar irin su yake yi bai dauke su wasu cikakkun mutane ba a idon shi, yafi daukan mayaudara aduk inda ya gasu haka yake kallon su a yatsune. Shine dan uwan shi ja jini ya auro ya kawo ta cikin zurian su take juya mutane yadda ta ga dama a gidan da takaicin ta ya juya tafi bai shiga gidan nasu ba a lokacin mommy tare da anty Amarya suka koma gida bayan sun yiwa Fati nasiha kadan. Nan suka tafi suka bar Fati da tsoro a zuciyar ta fam sai dai abinda bata sani ba a halin yanzu Nafisa tafita shiga tashin hankali don tsoranta Allah tsoron ta Suraj soja. Wanda ta hango mugunta zalla cikin kwanyan idon shi abinda ya fadi tasan karamin aikin soja ne yayi shi ya aiwatar da abinda ya fada din dole ga magana nacin ta da zata fadawa Fati a yau sai dai babu halin yin hakan gare ta dole ta kawo ido ta saka mata a gidan tana jiran dawowan mijin nasu wanda zata sa ya ci fuskan Fati din a gidan. Ai idan sun san wata basu san wata da makirici zataci galaban su gaba daya don ta gane yan uwan mijin da iyayyen shi duk munafukai ne a kanta. Can gidan su hajiya sun koma kumshe da dariya a cikin su sai da suka shiga mota suka fara dariyan abinda suraj din yayi wa Nafisa . Yanzu sun gano takon ta Suraj ne zai dinga mata hukunci irin nasu na sojoji na rashin imani sun shiga gida nan suke bada labarin abinda ya wakana a gidan. Mama taji dadin har cikin ranta ko banza Suraj ya kwantarwa Fati incin ta yau wanda inba shi din ba, ba wanda ya isa yayi haka a zauna lafiya da ita tunda tayi niya. Maganan mommy ne ya dakatar da ita da taji abinda Nafisan ke fadi a lokacin shigan su gida da take fadin wai babu rabon su Fati da yayan ta ga abinda maigidan ya bari a gidan. Lalaima wanan matar tantiriya danta ya dauko mata ba kwai ba donge amma har take ikirarin cewa wai ba abincin su a gidan. Wani zafi na bakin ciki irin wanda iyayye ke ji a gamay da diyan su idan sun yi abu ba daidai a cikin alumma wanda sai uwa ko mahaifi suka san da irin zafin da mama taji a lokacin. Haka dai ta shige daki a dadafe bakin ciki da takaicin da matan dan nata ke kumsa mata a zuciyar ta yayi yawa kuma dan nata ya sani amma bai iya daukan wani mataki akan hakan. Wunin ranan haka suka kare shi da maganan Nafisa wanda hakan ba bakon abu bane agurin anyi sau tari da yawa sai dai na yau din ya banbanta da sauri don ta fito ta nuna masu karfin iko da izan da take dashi a cikin kan dan nasu . Wanda suka haifa suka tarbiyartar da hannun su kuma ya tashi da tarbiya suke saka ran samun farin ciki a wurin shi kamar yadda duk wasu iyayyen ke fata ga diyan su idan su samu Amma lokaci guda Nasifa ta shiga rayuwan dan nasu wanda ya watsar da duk wani rayuwan farin ciki da suke hasashen samu daga gare shi. Gashi a yanzu yana a cikin ganiyan samun duniyan shi wanda bai zauna ba tsaye yake wurin neman na kanshi a rayuwan wanda ba komai yakawo hakan ba sai addun mahaifa da yawaita ta sadaka akan diya yake bibiyan shi a yanzu. Don a baya in zata iya tunawa bata da aiki sai yawai ta sadaka fiye da kowa a gidan in anyi magana sai tace ba neman duniya nake wa kaina nemawa na baya nake madogara. Ga yawan taimakon na kasa da ita tundai idan ance yaro maraya ne sai mama tasan yadda takai alherin ta ga yaron ko ta saka yayan ta suyi mai alheri daga abinda suke dashi na jikin su mai kyau wanda zai farauta ran yaron da za a ba abin. Don Allah iyayye mata mu kula kada muyi sakaci da wanan dama akan marayu da muke gani zaki iya dafa kan yaro maraye zai ji dadin hakan da kikai mai har a cikin ranshi. Bawai duka maraye bane zai bukaci taimako wasa ma da dariya a gare su sadaka ce dan abinda zai farauta masu rai sadaka ne Allah ya bamu ikon yi ga maratun dake a kusa damu. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: 🧠MIJIN BUZUWA🧠 3ï¸âƒ£ ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU NOVEL DIN NAN NA KUDI NE BIYA DARI UKU KO KATIN DARI UKU TA WANAN ACCOUNT DIN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KI KIRA TA WANAN LAYIN 09026931792 KO 08036959257 ASHA KARATU LAFIYA YAN UWA. Tsaye take gaban mirrow tana gyara rigar da ta sa a jikin ta na tampha wanda akai mata dogon riga dashi mai wani launi kamar jikin damisa brown colour. Dinkin mai dan kwala sai da wuyan rigan V neck akayishi wanda yasa gaban ta ya fito dakyau daga cikin rigar kasan rigan ma an bude shi free yadda zata iya walla kafafuwan ta ba cikin matsuwa ba. Turare ta dauka ta feshe jikin ta dashi ta juya ta dauko gyalen ta dake saman godo gefe ta fesa mashi turare ta mayar a hand bag din ta dan kwali ta dauko ta dan daki lokaci tana daurawa take fuskanta ya fito tsonen a jikin mudubin. Duk wanan shirin da take yi ranta ba dadi don bata son zancen zuwa kaduna a zuciyar ta tafi son tayi rayuwan ta a gidan ubanta dake a cikin garin Minna. Inda gidan su yake a kwangila road asalin su su hausawa ne zamane na kakan ni ya kawo su garin minna har suka zama yan ainihin gari baza kace su bakin gari bane yanzu don kowa nasu anan aka haifeshi. Daga wajen gidan wanda irin ginan da can bayane na siminti wani murya ya kirata da fadin Khadija kina makara fa a cikin irin hausan mutane Niger shiba kananci kuma ba hausa pure ba do ya dan hade da surkin harshe. Muryan Khadija ne ke fadin mama shiri nakeyi gani fitowa yanzu da sauri ta karasa shirin ta jawo dan trolley din da ta sa tufafin ta a ciki tare da rataya handbag din ta a kafada ta fito waje. Kallon ta mama tayi wace zance a wurin ta khadija ta debo kyau da na saba kafin in ga mahaifin ta farar mace ce doguwa yar kabilan gwarin may kunkele dake a cikin minna din. Kallon yar nata tayi tace kin fi son ko yaushe kiyi tafiyan marance mama nina fison in shiga da yamma yafi ba wanda yasan zuwan ka sai dai a ganka. Maimakon tayi haraman tafiya sai ta ja kujera roban dake gefenta ta zauna kallon ta uwar tayi tare da fadin yaya haka kuma ? Banbara nake jira na aika a sayo dashi zan tafi bana son in mising din shine idan naje ke dai yanzu na gane baki son zuwa wurin yar uwan naki tunda kika girma kika fara karatun jamia . Ta dan ya motsa fuska mai kama da sallo ko yanga wanda ba haka bane kusan yanayin yan garin ne haka suke maganan su da kamar sallo da yanga tace ni nafison in yi hutu na a gida. Amma ita ya Amina kullun sai tace sai mutum tafi wurin ta hutu yanzu kuma ba da bane ban son ina missing din gida sosai murmushi kawai uwar tayi don tasan halin yar nata. Ba ajima ba mahaifinta ya shigo gidan yana ganin ta yace a Khadija an fito ke nan eh baba zan tafi hannu yasa ya fara laluban aljihun shi sai ya fito da dubu biyu ya cire guda ya miko mata. Kai ta girgiza mai tace baba ka barshi kawai kudin da anty ta turo min zai ishe ni na gadone a daidai lokacin yaron da ta aika ya sawo mata banbara ya iso da leda a hannun shi yana mika mata da canjin karike canjin tana bude ledan ta debo banbaran ta mika mai ta mike tana gyara jakkan ta yaron ya taima ya fita mata da kaya ida ta tare Napep zuwa Abdulsalam garej . Tana isa saura mutum daya ta biya suka shiga suka kama hanyan garin kaduna yamma lis suka shiga gari lokacin kuma akai hadarin marancen nan da Nafisa ta dawo ta samu Napep din da zai kaita unguwar da yar uwar nata ke aure wanda kusan rabin zaman ta a baya a nan tayi shi sai data girma ta koma gida karutun da take yi Abuja yanzu shine silar mayar da rayuwan Khadija gida Niger state. Tun ranan da khadija tazo kaduna bata fita ba tana daga daki sai falo indan ta fito ko kuma ta shiga kitchen tayi masu girki a gidan. Yau da yamma ya Amina ne ke kwala mata kira tana zaune tana cin banbara da tayi worming din shi kamar yanzu akayi shi bai kwana ba. Ya Amina gani ta fito tana fadi cikin ranshin kallon fuskanta don Allah zo ki shiga gidan su mommy ki karbo min sako tace yanzu in tura a karbo min. Fuska khadija ta ya motsa tace ni ban shiga ba tunda nazo banje na gaidasu ba Amina tace wai khadija may ke damun ki ne haka ? Ke a rayuwan ki sam baki son shiga jamma a ban san inda kike dauko wanan rayuwa naki ba haka cikin bacin rai ta juya dauko gyalen ta kayan da tazo dasu garin ta kara sakawa a jikin ta. Yaran anty nata biyu ta, ta kira su rakata gidan da aka aike ta din fitowan su bakin get din gidan yayi dai da zuwan wata mota a guje ta watso masu ruwan dake kwance a wani dan rami saman hanya. Cikin bacin rai Khadija ta dago kai tana fadin you are very stupeid bakya gani ne kika watso ma mutane ruwa haka. Horn kawai Nafisa tayi masu ba tare da ta tsaya khadija tabi motar da hararan takaici tana dan kakabe riganta da ruwan ya dan taba a lokacin. Raina yayi matukar baci haka muka doshi gidan mutane ina mita wani saurayi dake tafe a bayan mu naji yace yar iskan buzuwan nan ne haka take tuki kamar mahaukaciya wallahi. Dan juyawa nayi na kalli mai maganan nace sannu yace yawa bata dai zuba maku ruwan sosai ba ko nace kadan ya taba mu inayi har lokacin ina kakaban ruwa a jikina. Gidan muka shiga wanda har lokacin raina a bace yake da buzuwar da naji saurayin nan yace min da sallama muka shiga gidan. Wanda sai kawuce kofan falon gidan kabi wani dan siririn hanya da zai sadaka da cikin gidan da muka shiga wanda babban gida na ba yau bane farkon shigana gidan don duk zuwa nayi sai anty ta aike da gidan ina shiga akai akai yanzu tunda na girma bani shiga idan nazo sai da wani dalili. Sallama mukayi inda kofan uwargidan ne fara isa sai na mama daga can ciki sai kuma wasu biyu dake kallon nasu din na mommy dana anty Amarya ke facing din su. Hajiya ummi da yaranta nake jiyo hayaniyar su daga kofan part din ta na dan matsa daga kofan dakin ina gaida su dakyat aka amsa min ban tsaya ba na wuce. Lekowa akayi daga dakin ummi don ganin mai gaidasu din da bai shigo ba bata gane ni ba alokacin har nakai kofan mama shiyasa ban son shiga wanan gidan don yawan dake garesu kuma sai kabi kowa kagaida shi dole don hadin kai irin na matan gidan. Koda baka gaida mutum ba wanda kaje wurin shi zaice dakai ka ko gaida mutanen gidan sanin haka danayi yasa na fara binsu daga daga ina gaida su. Dakin mama ma a kofa naja na tsaya ina fadin ina kwana mama ta amsa min daga ciki tana fadin waye shigo mana ciki. Dole na shiga daga cikin dakin tare da kara gaida ita inda nakai gwiwana duka biyu a kasa irin gaisuwan mu na mutanen Niger. Daga kuryan dakin ta aka fadin muryan wa nake ji kamar khadija Adamu da sauri mai maganan ta fito falon ida nake wani irin ihu ta sake a lokaci daya tare da kwalawa binta kira tana fadin ga khadija Adamu ashe tana garin nan mukayi maganan ta jiya. Murmushi nayi ina dagowa daga gaida mama da nake nan suka shiritar dani nace anty ta aiko ni wurin mommy. Bayan nagaida amaryan su ne na wuce zuwa dakin mommy ta tareni da fara anta mun dade tana jana da hira wanda ni ban iya sake jiki dasu muyi hiran sosai saboda mutunci da girma da nake gani a idona. Sakon ta dauko min na fita mukai sallama dasu nan suka rakoni suna dan taka min in baki mantaba mai karatu na fada maki a nan kaduna nayi rabin rayuwa na. Kamar abin tsokana wanan motar dai ne na dazun ta dawo a guje ta kara yin facali da ruwa a take nace wanan wani irin iskanci ne wai haka ? Har motar ta wuce sai ta dawo baya a hankali zuwa gare mu a lokacin zainab ke fadin Nafisa ce fa ta dawo zai tai muna cin mutunci kila taji zagin da khadija tayi ne. Gab damu ta tsaya tare da sauke glass din motar wata farar mata nagani ciki tare da wata zaune a gefen mai zaman banza. Tace wace yar iska ce cikin ku take zagina shiru naji sunyi suna soke kai kasa nan san lokacin da nace mata kece dai yar iskan da baki san darajan mutane ba kika gudu da mota haka a wulkance cikin gari kamar yar koyo. Ke tafadi a zafafe tana kokarin bude kofan motan da sauri naji su Binta da zainab na fadin yi hakkuri anty bata san ke bace . Cikin zafin rai nace ke wacece da zaki watsa ma mutane ruwa kice kada ayi maki magana wallahi ko diyar shugaban kasa kike sai nayi maki magana . Karasa fitowa tayi daga motan tana fadin ke yar gidan uban waye a garin nan take raina ya kara baci nace kedin yar gidan uban waye da baki da tarbiya fada min naki in fada maki nawa. Fisgan hannu na Zainab keyi ni kuma ina turjewa don ban ga wani kimar ta da suke gani ba idons a lokacin don sam ban da tsoro akan gaskiya na. Ke yar waye da zaki tsaya kina fada min magana son ranki nace ni yar gidan ubane ke kuma cewa akai titin na gidan ubanki ne da zaki dinga gudu kina watsa ma mutane kura da ruwan titi. Yadda taga ina yi sai ta tsaya tana kallo na kafin ta mayar da fadan akan su Binta da zainab din tana fadin zamu hadu da kune wallahi don nasan da sanin ku take min hakan. Nace wai kun san wanan banzan ce da kuka tsaya tana fada maku maganan banza saman hanya haka ? A harzuke tace nice banza nace an fada maki idan ba banza kike ba may kike zaki tsaya kina ma mutane son raki ke gaki mai kudi ki takamu ki wuce lafiya kin taki banza ko ? Zaki gane kurenki wallahi wani kallon banza na watsa mata nace sai dai mu gane kuren mu amfada maki don kina da kudi zanji tsoron ki ne ko may kudin ki bai damay ni ba tunda ban taba zuwa wurin ki neman wani abu ba. Matar da take cikin mota ne taji abin yayi yawa kuma dukkan mu munki bari ta bude mota ta fito tana jan ta tana fadin haba Nafisa zaki tsaya kan wanan karamar mara kunya kuna raba hali a saman hanya ai sai ta ja maki raini ga jama, a. Kuta tayi ta watsa min harara na mayar mats ta shiga mota tana fadin zaki san kin shiga hurumi na nace inga alheri . Fisgan mota tayi sai da yayi wani irin kugi suka nufi hanyan cikin gari zainab tace wai Khadija kin san kowacece ita din ? Wacece kuwa banda kila matar wani ko wata kusan gwaunati shike nan don muna kasa sai ta rena mu Binta ce ta katse ni da fadin matar yayan mi ne kishiyar anty Fati. Inda motar yabi nabi da kallo nace yanzu wanan matar matar dan uwan ku ne wallahi na dauka irin matan bariki din nan ne masu zaman kasu nima ban san yaya akayi idona ya rufe haka ba naci mata mutunci. Nan nake fada masu abinda tayi muna da zamu shiga gidan su yanzu kuma ta sake maimaita muna shiyasa raina ya baci don naga kamar da gaiyya tayi hakan amma kuyi hakkuri don Allah. Binta tace ai mu yau kin muna daidai wallahi don ba karamin dadi naji ba da kikaci mata mutunci nan a gaban mu. Mun da jima a tsaye dasu karshe mukai sallama muka shige gidajen mu har lokacin ina da zafin matar nan a raina. Nafisa ko sai fada take kawar ta na bata hakkuri tana fadin ban son ki biye mata ba tunda kinga kannen mijin ki a wurin may yuyuwa tasan ki ke baki santa ba. Zanyi maganin ta wallahi sai ta rena kanta zata san ba a taba ni a zauna lafiya ko wacci tuwo dani miya ya sha na san dai ba yar gidan uban kowa bane ita. Su zainab na shiga gidan su suka fara bada labarin arangaman mu da matar yayan nasu nan mutanen gidan suka fito suna sauraren su. Mommy tace kai amma wanan yarinyar wallahi ta burge ni sosai yau da haka Fati ke daurewa ta mayar mata da martani da abin nata ya rage. Anty amarya tace ai ba zata iya ba ne don ta riga tasa mata tsoron ta a zuciya kuna ganin a banza ta bar mutane ne haka da kowa ke shayin ta. Ummi tace kwarai ai irin su ba a banza suke barin gida ba sai sun kama bakin kowa sun daure yadda ba mai iya motsawa a kan su. Sai lokacin mama tayi magana tace aini wanan yarinyar ta gama shereni wallahi tayi min daidai yanzu zata san in ta daure bakin wasu bata iya daure na wasu. Nikan da muka shiga gida ya Amina tana daki mika mata sakon nayi a cikin wani dan leda wanda ban san abinda ke ciki ba dakina nakoma na fara rage kayan jikina. Na mayar da dan riga mai karamin hannu da bujen body hook dana cire sai hula dana dora a kaina kitchen na nufa don dora abincin dare saboda yamma yayi. Kafin wani lokaci har na kammala na gyara wurin na mayar da kauan da nayi aiki a inda suke daki na kofa nayi wanka kafin a kira sallah na fito na canza kayan jikina. Kananan kaya na kara sawa a jikina don idan ina gida sune kayan sawa na wayata na jawo ina duba sakon dana samu daga abokaina da muke karatu dasu. Lokacin sallah yayi na mike na gabatar da sallah ban daga ba sai da na yi har isha,i na nike abin sallah na fito din in ba yaran anty na abinci. Anty ce ta fito daga dakin kwanan ta muryan ta naji daga baya na tana fadin har kin fito eh kawai nace mata ba tare da na juya ba ina zuba abincin a plate na mika ma yaran dake zaune suna jirana. Juyowa nayi inda nake tsanmanin take zaune nace in zuba mata abincin yanzu ne kallo na naga tanayi cikin mamaki tambayan da ta jefo min a lokacin ban zaci ji ba. Khadija may ya hada ki da buzuwa yau kin ko san waye buzu kin san ko matar waye don Allah ki rufa min asiri tunda nake unguwan nan ban taba fada da wani ko wata ba ina jin tsoron rashin tsoran nan naki wallahi. Kara daure fuska nayi nace ina ruwa da wata buzuwa ko baturiya take ba zan yarda ta wullakantani ba ga banza don tana takama tana da kudi tunda ba kudin ta nace ta bani ba. Don Allah dai ki bari ban son irin haka ni na dauka kin bar halin nan naki yanzu da kika girma ashe halin na nan baije ko ina ba. Mijin ta fa na iya sakawa a kore mu a unguwan nan wallahi don suke fada aji yanzu a garin don Allah dai ki bari. Kamar zan yi magana sai nayi shiru ranan banci abinci ba saboda haushin buzuwan nan dake ci min rai haka na kwana da tunane kala kala a raina. Hajiya mama haka ranan itama ta kwana tana tunane a ranta kan yadda zatayi da danta akan buzuwan da ta zama masu fitina da masifa a cikin zuri,an su. Dan ta ya zubar mata da mutunci da kimar da mutane ge gani nata duk a kan auren wanan matar da bata darajja mutane da halin ta. Da safe nafito na hada breakfast har na gama ya Amina bata fito ba tana daki na gyara ko ina na gidan sai na koma na shiga wanka na fito na shirya tare da hayewa gado in dan huta. Sai lokacin na fara jin hayaniyar su a falon gida alaman sun tashi ke nan daga barci hakan baisa na fito ba sai kara lafewa danayi saman gadon barci ne ke son dauka na a lokacin. Muryan ya Amina naji na bude idona a hankali ina kallan ta daga inda nake kwance nake mata ina kwana murshi tayi ta karaso gare ni tana fadin. Har kin gama kin kwanta yau barci ne ya dauke ni tana fadi tana kaiwa zaune a saman gadon da nake kwance jin banyi magana sai naji tayi murmushi . Tace khadija fushi kike yi akan maganan da nayi maki jiya akan buzuwan nan bata da mutunci ne khadija shiyasa kowa ke tsoron shiga tsabganta don mijin ta zai iya keta ma kowa a kanta yadda yake son ta. Dagowa nayi nace OK shike nan don mijin ta na da kudi ko mulki ba zanyi fada akan dama na na dan adam ba murmushi naji tasake yi tace khadija ina raba ki da shiga tsabgan irin mutanen nan. Kai na kawar gefe ina hade miyau takaici da yazo min a lokacin haka abin yai ta cina har na gaji na sake na manta da wata can a zuciya. Jin shiru da su Binta sukayi yasa su ranan biyo ni gida a falo suka samay mu dukkan mu nan muka zauna har anty muna hira suna min korafi wai kullun ina gida kumshe ban fita. Zainab tace kodai kina tsoron haduwan ki da Nafisa ce nace waye Nafisa kuma tace matar yayan mu mana da kuka kwasa ranan . Oh kuce mi buzuwa mana ai sai in gane ba Nafisa ashe sunan ta ke nan ni na fi gane ma buzuwa ai Binta tace ai bata son a kira da buzuwa shiya sunan ya mutu a bakin mu. Ranan da ra kai kara wajen yayan a gidan bakiga irin fadan da yai muna ba ni tun lokacin gidan ya fita raina wallahi. Ashe ya zama mijin buzuwa ke nan yar sani in fika wai agola da rabon gida ina kika san yar sani in fika ne ai sai kin ga yadda ta mayar da anty Fati a gidan. Ita da mijin ta yanzu ta koma yar kallo a gidan ko dan aikin gidan yafi ta daraja a gidan kwanan fa sai da ta fito aka maida ita kin san may ? Da ta koma bata gidan tana dawowa sai cewa tayi wai uban wa yace ta dawo gidan sai ta kama kitchen da komai tarufe na gidan ta hana ma anty Fati da yaranta. Sai lokacin anty dake gefe ta saka baki a hiran da mukeyi a falon tace amma samun wurin nata yayi yawa wallahi nace wai wace anty fati kuke magana haka ? Wanan da ta taba haihuwa har mukai fati daku a baya dan tunane nayi nace nagane ta itace mijin ta ya auri wanan matar wallahi itace inji Binta zainab dai sai dakilan wayanta takeyi tana charting. Anty ce tace yanzun yaya akayi akan abincin nan dai take fada muna yadda suka kwashe da suraj anty ce ke dariya ni banga abin dariya ba tunda ba dukan ta naji yayi ba. Sun kai wani lokaci suka ce zasu tafi na mike na dan taka masu har bakin get din gidan anty na na dawo ciki. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Bayan mun gama waya da ita naji raina ya baci sai a lokacin na gode ma Allah da ban goge number shi ba a wayana kira nayi har sau biyu bai daga ba sai na tura mashi sako masu zafi na kashe wayan. Don nasan zai gani da safe in ma kwanciya yayi a lokacin haka yasa na danji zafin da nake ji ya rage min da kyat barci ya dauke ni a ranan. Har na rufe ido sai nayi wayana yana kara na dauka a zatona shine yaga sakona ya kira wayan sai dai ba number daya kirani daya kira dashi bane. Nace ummhumm ina jin ka naji ance haka ake karba kiran wanda baka sani ba na sheda muryan Yusuf din nace yayana kaine a na dauka wani ne. Yace nice injin ruwa bai saki jin zazzabi ba dariya nayi nace ai na watsa ruwan zafi a jikina yace good dama na kiraki ne don mutumin ki ya karbi number ki a hannu na nasan zai iya kiranki kada ki biye ma halinshi don Allah don bansan abinda zai kiraki ya fada maki ba koda yake yace akan maganan hajiya mama zai kiraki yaji don Allah , , , Na katse shi da fadin ai ya kirani ko har munyi tsiyan shi ya dauka kowa nema yake a gare shi ko yaushe ni kuma na wanke shi tass. Da karfi naji yace haba don Allah nace wallahi na kwashe komai na fada mai har text din da na tura mai mai zafi yace amma baki kyauta ba wallahi. Nace saboda may zai mun hadi yace khadija kin san kuwa kece mukee son kizama weapon din mu wurin yakan buzuwa nan gaba. Don Allah ki dinga sausautar harshen ki gare shi nace wa ni ni ina ruwa da shi da zan zama muku makami a gare shi da buzuwan shi. Dariya yayi yace ke ko ke dashi khadija ke da komai da zaki yakar muna buzuwa don kin cancanci yin hakan. Ni din yayana yace kwarai kuwa kauna na sai dai idan mun hadu zan maki bayani yadda zaki gane nace to shike nan tunda haka ka fada yace bani na fada ba umurni nima aka bani kan hakan . Yace sai dai idan mun hadu din zan maki bayanin komai nace Allah ya kaimu ina saurarenka da haka muka yi sallama dashi ya barni da tulin tunane a zuciyana. Da safe zarah ce take buga min kofa jin bugun kofan na tashi na bude daki tana tsaye kofan dakin nawa ganin tana son shigowa na bata hanya ta shiga daga ciki. Tambaya na tayi ko da safe zan fita nace ai kemakin sani yanzu haka shiri nakeyi kada in makara take cewa dani zata fita amma wai za a kawo mata sako shine take son in karba. Nace zarah fitan kuma zakiyi yanzu tayi dan guntun tsaki tana fadin eh wani friend dina zaiyi tafiya nake son inje muyi sallama dashi. Zarah ba zaki wankan ki fada ki zauna ki abinda iyayyenn mu suka kawo mu yi ba wanan dabiar da kika dauko bai da amfani gare ki nan gaba. Ta dan yi murmushi ta nufi wurin da taga na aje plate din abin ci da tukunya tana bude bayan ta bude ta dago tana dariya tace an fada maki yadda bakin san wayen kai ba haka kowa yake yanzu da anganki kamar may wayayen kai . Nace in dai irin wanan wayen wane kada Allah ya nufe ni da yin shi ina neman tsarin Allah ga irin wanan dabian naku Allah kuma ya shirye ku ku gane gaskiya. Ta juya ta debi arish a plate ta zauna ta fara ci ni kuma ina ta shirina nace kiyi ki gama gada ki makarar dani anan don banson in makara. Tayi murmushi tana kai abinci a bakin ta sai da ta hade tace wanan halin naki na ina kika fito karatu ina zaki karatu sai ke khadija. Khady look at you me kika rasa ke kanki jarin kanki ne amma kin tsaya kina wahal da kanki haka har kina wani girki tunda safe kamar wata matar aure amma waike nacin karatu sai wahala kike haka. Wallahi da zaki yarda akwai wanda zan hada ki dashi cikin kwana biyu kiyi clean ke baki daukan misali a kwaina khady da haka nake ? Amma yanzu gani tunda hanya ya bude min mai na rasa na rayuwa atare da ni amma ke gaki da abin kawo kudi kina ta faman kumshe shi a jikin ki ta fada tana dariyan shakiyanci. Ni dai ina tsaye ina mata kallon mamaki da huduban shedan da take min har kuryan dakina ta dauka nasihan ta ya na shigana ne ganin yadda na tsaya ina kallon ta. Tace ina son ki fahimci wani abu tsarin rayuwa yanzu ya canza ki shigo kawai a dama dake yarinya. Nace cikin murmushi zarah baki fance ni batsarin rayuwa ta daban yake da naki ban sanya ma zuciyana kwadayi ko son jin dadi a ko wani irin yanayi ba don haka kada kiyi tsammanin guntun huduban ki zaiyi tasiri a raina . Ni da kika ganin nan ina da mutunci na kuma nasan ciwon kaina dana iyayyena kada kiyi tsammanin kananan kwarin da kike bi zasu iya rudana da wani abu. Shi jin dadi lokaci indan lokaci yayi sai inji amma ba ta hanyar wullakata kai yadda kukeyi din nan ba kema idan da zakiji sharata da kin watsar da wanan rayuwan ki rungumi abinda ya kawo ki Abuja. Su kansu mazan da kuke bi aida karatun suke amfana yanzu bance maki ban saurayi ko rayuwa ba sai dai in gajarce maki ni indan zanyi mai tsabta da sanin ciwon kai zanyi amma bana kwanan gida irin naku ba. Baki zarah ta tabe min tana dariya ta saba da nasihana kullun wanda ita a ganin ta ni har yanzu ban waye ba ban san ciwon kaina ba bansan ta kan duniya ba kuma. Nace keyi dariya amma ni idan zan faso gari ba irin wa yan nan kanana kwari masu gurbata rayuwa zan tsaya dububa ba sai wanda ya san kanshi da mutuncin kanshi. Ta mike bayan ta gama ci dama ina magana ina kallon agogona ne kada in makara tace ina son ki fahince ni a yanzu ba a samun irin wa yan nan mazan da kike hasashe kinga ko zaki shawa wuya wurin neman su. A naki ganin ke nan zarah amma muna nan dake zakice na fada maki watarana ta miko min key din ta nace kenan yauma till down zakiyi tace yo may za a fasa kuma. Ta fita na rufo kofana muka fito tare da ita a titi muka raba hanya tana neman lift ni kuma na nufi cikin makaranta ina mamakin wanan rayuwa da zarah ta daukan ma kanta. Itama yar minna ce kama na dalilin haduwan mu ke nan da ita don ko a minnan ba unguwa daya muke ba su suna zama a cancaga ne ni kuma muna tsakiyan gari. Kasancewar mu yan gari daya yasa muka zama kamar yan uwa da ita da farko halin ta mai kyaune kafin idon ta ya bude da bin mazan abuja. Sai lokacin muka raba hannu da ita amma hakan baisa mun daina kula junan mu ba kamar baya sai dai ban taba yarda naci abinda take samuwa ba daga wurin yawon banzanta ba. Tun abin na damun ta har yazo ya daina damun ta ta daina ba sai wanan da iyayyen ta suka kulla suka aiko mata yanzun tana ganin tafi karfin shi ita shine ta kawo min inyi amfani dashi. Tun asuba yake tayar da ita ta tashi tayi sallah amma tana kwance tana barcin ta har yagaji yatayar da ita da karfin tsiya ta zauna tana mustsukan ido alaman barcin bai isheta ba har lokacin yana ganin ta tashine yasa shi fita daga dakin azaton shi zata tashi tayi sallah. Ya fita zuwa dakin motsa jikin shi da yakeyi duk safe inda kuma yake aje wasu kayan amfanin shi jiya anan yabar wayan shi yana canji ya je ya kwanta yana tunanen rashin son ibadan da batayi. Ya gama komai na motsa jiki da yakanyi da safe ya wuce zuwa inda wayan shi yake jone ya dauko din ka idan shine sai takwas yake bude waya da safe. Budan wayan yasa sakon da suka taru mai shigowa ya gane su wanda farko budewa nawa ne ya shigo da farkon. Mamaki yayi don ba suna sai lamba ga dogon sako kuma da maishi ya turo mashi kamar kada ya karanta tunda baisan mai sakon ba sai kuma wata zuciya tace dashi karanta kaji mana abinda sakon ya kumsa kila mai amfani ne gare ka. Fara karanta sakon ne yaji ranshi ya baci don ya fahinci inda sakon ya fito don ganin farkon rubutun nawa kamar haka Mijin buzuwa a zaton ka zaka iya rabani da hajiya mamane ko ka zubar min da mutucina da take gani kayi kuskure wallahi kuma kayi karya don bakina da naka ban fada ma hajiya mama tana gida an mata rasuwa ba. Ga wanda yasan mutuncinta yasan darajan ta na fadawa shida ya tambaye ni ko ina da labarin su bakai da buzuwa wace bata da daraja da galihu tasa ka zubar da matan ka da yayan ka da kowa naka kana ganin tsohuwar buzuwa tana maka rudi da huduban shedan kullun. Kai bari ma kaji wallahi wanan buzuwar ta zubar ma da kima da komai naka a idon duniya tunda kiri kiri ta mai dakai mijin hajiya. Ga mutum har mutum amma baida ta cewa saboda mace macen kuma buzuwa wace bata san Allah how dear you kaida mace bata bari ka zauna dako matar sunnan ka har kake da bakin yi mun hadi a wurin mama, , , , Jikin shi har rawa yakeyi da yake karata text din kasa kai kashen rubutun daki ya nufa da sauri da zuman ya shiga yai wanka ya fita ya samu Yusuf shida yaja mashi rene da wullakanci wurin yar karamar yarinya harta iya turo mashi text din banza haka. Sai yayi magani na a garin sai yasa na raina kaina may nike dashi may nake takama dashi da zan iya yimai cin fuska haka ina aibanta shi shi da matar shi. Waya ya fada min maganan da sukayi da hajiyan su hajiyan ne zata fada min kowa komai dai may nene sai ya rena min wayo sai na gane banda wayo yau a garin nan duk inda na shige sai ya tononi a cikin garin nan yayi min wulkanci Sai dai yana shiga dakin su kuma sai bacin ran nashi ya karu ganin Nafisa kwance tana barcin ta hankali kwace rashi ne ya kara baci ya tuna abinda nace a text dina. Bai san lokacin da ya isa wurin ta yakai mata mugun maka a tsakar bayan ta ba ta mike firgigit tana fadin Samad may nayi maka ? Tsawa ya daka mata yace wanan abin zai hada ni dake ke sai yaushe ne zaki rike ibada a zuciyar ki ne yaja tsuki ya shige wanka. Da sauri ya watsa ya fito ranan ya fito bai wani dauki dogon lokaci ba ya shirya ya fita daga gidan koda ta fito ta samu baya gidan. Tun a mota ya kira Yusuf yana fadin kana inane yanzu? Gani gidana ya bashi amsa OK kajirani ganin zuwa yanzu gidan yace eh mamaki Yusuf yaji yana tunanen mai zai kawo Samad gidan shi wanan lokacin haka. Don ka idar shine sai takwas yake fitowa ko takwas da rabi ware hannu yayi alaman shi ya sani ya mike ya shiga wanka kada yai mashi girshi. Yana shiri ya sake bugo mai waya gashi kofa gidan shi ya fito ya karasa ya fito ya samay shi don ko driver bai fito dashi ba Yusuf din na gani haka ya rufo gidan nashi ya fito ya samay shi. Anan ya bude mai mota ya shiga yarufe sai ya dauki hanya batare da yasan inda zasu nufa ba sai yaga ya miki mashi wayan shi duban wayan yake da mamaki yake fadin na maye wanan kuma ? Ka duba mana cewa fuska a daure ya karbi wayan ya fara karantawa a hankali yana sake murmushi ya gaba yana mika mai wayan yace kai amma wanan yarinyar takai jaruma wallahi haduwan zai zama abin shaawa ga mai kallo. May ne kace yanzun kai baka ga abin jin haushi ba a nan yace ban gani ba sai ma wani abin da na hango na daban tsakanin ka da beauty din. Yau sai nanu namata ita ba kowa bane a garin nan sai na wullakanta ta a garin nan dariya yayi sosai yace da kaima kan ka wallahi da ka tozarta kan kuwa. Wai kaiko kaga yadda kukai balain dacewa da yarinyar nan kuwa wallahi ni abin naku burgeni yake yi idan kuna yi har wani dadi nake ji. May kake nufi ne wai yace abinda idona ya hango min mana a kai saidai fatan alheri amma zancen ka ci mata mutunci bai taso ba ko kaje ka tozartata duk ba wanan a tsakanin ku ko kamanta da hikimar hajiya na hada ka da wanan yarinyar ne ko kana nufin kai baka gane hakan ba. To bari kaji Khadija itace zata iya fitar dakai daga zargin da ake maka na cewa Nafisa ta gama dakai da cewan da ake saboda ita ka kasa zama da Fati. Akan wani dalili zata fitar dani ta yaya din zata fitar dani yace muje zuwa nan gaba zaka sani idan lokacin hakan yayi yanzo ina zamu ne kadauko ni tunda safe haka. Wurin ta zamu in gwada mata ita din ba kowa bace ya kwashe mai da dariya yace ta zama kowan ke nan tunda har zaka iya biye ma shirmay ta na mata. Bai kara magana ba sai juya kan motar yayi zuwa office din su ya shige bai tsaya jiran Yusuf din ba. Anan malam musa driver ya tsayar dashi yana fadin yana da magana dashi na siri da yake son suyi a tsakanin su yace da malam sani din wani abu ya faru ne yace eh to sai dai maganan nason siri gaskiya yace dashi babu damuwa kasa may ni a gida da yamma idan mun tashi. Ga haka suka bar zancen da malam sani din sai dai ya barshi da tunane a zuciyar shi ko akan may yake bukatan kebewa dashi bai sani ba ya san dai abune mai muhinmanci sosai. Shiko gogan acikin office maganan da sukayi da Yusuf ne yake ta mashi yawo arai wai zata zama mai garkuwa a kan matsalan shi da Fati da Nafisa ta yaya ma haka zai faru . Nan dai ya watsar da maganan ya ci gaba da aikin dake gaban shi sai dai yanayi yana tuna zancen a zuciyar shi. Kai tsaye da na fito kamar yadda na saba gidan da muke na nufa yau yawan ci basu da lectures sai karan gida ke tashi ko ina a cikin gida. Yunwa nake ji don ban tsaya nayi karin kwarai ba da safe sallah nayi sana fara hada tea na nasha sai da na dan huta a wurin na mike ina sauya kayan jikina. Na saka dan guntun rigan da nake zama a daki dashi gyaran dakin nayi na gyaro ko ina na dakin sai na dora girkin dare don shinkafa da miya nake son yi irin na yan makaranta. Bayan na gama miya na dora shinkafan na koma na zauna a bakin katifa ina tunane zarah ne ta fado min a rai yau in zan lissafa kwananta biyar bata dawo ba. Zarah tana daya daga cikin "ya"ya dake cin amanan iyayyen su don babu inda suka rageta don koba a fada ba zarah tafi gata don sati biyu bai shigewa iyayyen ta basu turo mata da sako ba. Amma duk ta watsar da wanan gatan nata tabi ra,ayin kwadan abin hannun samari wanda ya rufe mata ido a yanzu har yakai ga ta watsar da karatun ta. Ido na lumshe tare da girgiza kaina ina cewa ubangiji katsare mu ka karemu ya Allah kasa mufi karfin zuciyar mu don yanzu rayuwa abin tsorone . Sai gata washe gari ta dawo dakina ta nufa don karban key din ta koda ta shige ban sake mata fuska ba daga inda nake kwance ta tambayi key din ta na nuna mata da hannu kawai ta nufi wurin ta dauka. Harara na bita dashi tana ficewa daga dakin andan jima kadan sai gata ta dawo dakin daga ita sai wani dan guntun tawul da ta daura iya cinyan ta tana tambayana wai ban rage abinci ba in bata. Wani kallo nayi mata nace inda kika fito gantalin ki kwana da kwanaki baki kici abinci bane acan ? Tace kin san yanzu wata yayi nisa ba wani abin kirki ake samu ba sai maneji nace sai ki je gaba ki nema ni banyi abinci ba yau. Ta ce khady yaushe kika fara rowa haka ba halinki bane rowa nace ban dafa ba nace maki ashe karyan iskanci kike yi da zaki dawo kwana da kwanaki hannu empty. Ta dan tsaya jin ganin ban kulataba ina karatuna sai ta fice min daga dakin dagowa nayi nabita da kallon mai kama da harara har tafice daga dakin. Bayan ya gama saurare abinda malam sani ya gaya mashi jikin shi ne yayi sanyi karshe yayi mai godiya tare da jaddada mashi kan kada ya fada ma Nafisa komai ya dai saka ido ga alamarin ta kawai. Bayan fitan shi gidan nine na fado mashi a rai wayana ya kira mun gaisa dayake shi mai son wasa ne nan yajani da wasa wanda bai wuce hiran mijin buzuwa. Yace gobe dai weekend ne ba shiga aji ke nan nace eh sai dai ina son zan fita zuwa wurin wankin kai don ina son gyaran jiki gobe dai. Yace ashe shi gyaran ma sai anje wani guri yin shi dariya yaban don irin zolayar shi nace ana mace ba gyara ne yace kwarai kuwa har in ta san kanta. Karfe nawa zaki ya tambaya nace wuraren goma zan tafi nasan zuwa karfe sha biyu ko da rabi na gama yace da safe banda time da nazo na kaiki sai dai ki fada min sallin din da kike zuwa in duba ki idan na rarage abinda nake yi. Nace No kabarshi kawai ba wani nisa yake dashi da inda muke ba nagode yace aini nace ki fada min ko nace beauty hair drasses na fada mai layin da yake a saman babban titi. Munyi sallama ina mamikin halin shi da saurin sabo irin nashi na zauna na tsefe kaina a cikin daren nan don kada in makara in samu mutane a wurin. Washegari da safe na shirya na isa sallon din ba wasu mutane dayawa don haka nabi layi sai da akawanke min akai min drying din shi kafin su fara min kitso. Ranan nasha gyara sosai na jiki daidai zan fito sai ga wayan Yusuf shigo yana tambayana ina wurin ko wuce nace an kusa gamawa nan da minti talatin zanbar wurin . Nakashe wayan akaci gaba da min gyara sai yaba yawan gashina da tsayi suke yi nidai murmushi kawai nake masu ban wani dogon magana da kowa a wurin. Sun fito daga kubuwa duban fili da sukaje gani a hanyansu na komawa gida yaga Yusuf ya dauki hanya bai iya magana ba yana aiki a system din shi kan shi a duke yake. Sai dai yasan ba hanyan gida Yusuf ya nufa dasu ba aikin da yakeyi ya dauke mashi hankali a lokacin ganin ya tsaya a bakin wani gyaran jiki na mata yasa shi dago kai yana tambayan shi ina ne nan kuma ? Kafin ya bashi amsa yaji yana fadi a wayan shi fito gamu a kofa idan an gama maki nace gani tafe na fito tun fitowa na ya hango nice tafe kallon mamaki yake wa Yusuf din. Har na karaso bakin motar nasu sai a lokacin nasan tare suke dashi fadi yusuf ke yi da na karaso wai wanan haduwa haka fa kanwata . Kaike kara zuzuta yayi maganar kamar bashi ya fada ba yace ba dole ba in zuzuta kanwata yar gidan mama wanan ai kyasa ayi karo a hanya nidai murmushi kawai nayi mashi. Na fara gaida su yace shigo mu sauke ki mana ba hostel zaki koma ba nace a a nagode yayana ku tafi abinku kawai dakai dayane zan shiga amma dai ku tafi kawai. Yace au don wanan miin buzuwan da kika gani ai bashi ke jan motar ba ko shiga muje don ki kawai muka biyo nan fa. Jin haka yasa na bude motar na shiga batare da na sake wani magana ba shiko sai aikin shi yake yi kawai ana tafiya mun kai wurin wani babban shago yace don Allah ku bani minti biyu in dawo. Ya faka motar yafita sai mu biyu a cikin motar kowa da abinda yake yi a lokacin sai can naji yaja tsuki yana kallon shagon na dauka dani yake yi nace dakata malam bafa kai ka dauko ni ba da zaka ja min tsuki haka. Da mamaki ya dago kai yana kallo yace ke dani kike nace da wani nake haka kawai zaka kama jamin tsuki a mota da mamaki yake kallo na yace ke wata irin yarinya ce da bata da tarbiya. Kadai gyara maganan ka malam tarbiya ai ko makaho yasan akwaishi nan sai dai a lalaba a gani ai ba bace marasa tarbiya suke ba. Bai kai karshen magana ba cikin zafin nama da kunar zuciya ya juyo inda nake yace wa kike nufi baida tarbiya cikin muryan nan nashi mai dadin saurare da yake rowan ta. Tsoro naji ganin irin kallon da yake bina dashi mai kama da harara ko tsana sai nayi kasa da kaina na kasa furta komai don kwarjin da yai min a idona Ya nuno yatsan shi daidai saitin fuska na tare da tsure ni da idanuwan shi lumsarsu yana fadin ke in badan Yusuf da bai san ciwon kan shi ba har kucaka irin ki ta isa ta shiga min mota na a tare dani. Yace kallani nan ko a hanya nagan ki baki isheni kallo ba a cikin mata don banga abin gani a wurin irin ki ba cikin dakiya da dauriya nake kallan shi ina jin kalamin shi har cikin raina sai dai ina tara abinda zan mayar mashi ne a zuciya ta duk da naji tsoran yanayin shi. Yaci gaba da fadin idan baki hankali da ni ba watarana sai na balbala ki wallahi don ni mace bata kawo min raini nace dashi. Don Allah malam matsamin bakumayi mamaki jin haka don ba abin mamaki bane don ka fadi hakan tunda dama kai irin maza nan ne dake raina jinsin su sai kai ido ga mata ketere saboda zalama irin na rashin sanin ciwon kai. Don wanan matar taka abin kyama ga jamma a da kai ka mayar mutum har kake ganin tafi ko wace macen kasan nan dadin abin dai kaima macen kasan nan ta haife , , , , Fat naji yakai min bugu a baki don zafi sai da na dafe baki na ina dubawa ko jini yake min ban san lokacin da idona ya fara fitar da hawaye ba na yun kura zan fita daga motar yasa hannu ya danna lock mutar ta rufe kit yace kuma ki saurare ni. Duk kika sake ganina a mota kikayi gigin shigan shi sai ya jefar dake a waje mota ya take ki kin mutum in kashe ki in kashe bazan . Nace ni wallahi ba banzan bace sai dai in kaine yace bakin naki bai mutu bako yana kokarin kai hannun shi ya kamo baki na na noke kaina a kafana sai bai samu kama bakin nawa ba. A daidai lokacin Yusuf ya iso wurin da manyan ledoji a hannun shi yana bude motan zai sa ganin mu haka yasa shi ya sake murmushi. Ina jin shi nayi saurin dago kai nace mugu kawai azzalumi yace kai yaya haka may kai mata don Allah take kuka kuma ya waigo zai kara jamin baki na noke ina son fita a motan Yusuf ya tare ni yana fadin haba dai yaya zakaci zalun ta kuma haka ? May tayi maka haka wai kasa ta kuka ya juya yana cewa bakin nan mai rashin kunya na daka ido ya zaro yana cewa ka dake ta Abdul ? Kadan ma ke nan nayi mata ai fita nake son yi ba hanya don Yusuf dake wurin yayi rufe kofan ya zagaya ya shigo motar sai da muka fara tafiya yace ka bata hakkuri Abdul. Ina baya ina kuka naji ya fada mai hakan yace nace ka bata hakkuri yace wani zanba wanan yariyar hakuri ko wa yace bakai ka zalunce ta don may bazaka bata hakkuri ba ko kafin ka tafi da hakkin ta ne a kanka ? Baiyi magana ba sai aikin shi dayaci gaba dayi yace wai may ya hada kune haka da sauri nace zagina yayi na rama. Motar ya tsaya a kofa gidajen mu na fita da sauri ya biyo ni yana kirana ban tsaya ba wata yar gidan yaba kayan ta shigo min dasu suka tafi ban san yadda suka karata ba. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Bayan mun gama waya da ita naji raina ya baci sai a lokacin na gode ma Allah da ban goge number shi ba a wayana kira nayi har sau biyu bai daga ba sai na tura mashi sako masu zafi na kashe wayan. Don nasan zai gani da safe in ma kwanciya yayi a lokacin haka yasa na danji zafin da nake ji ya rage min da kyat barci ya dauke ni a ranan. Har na rufe ido sai nayi wayana yana kara na dauka a zatona shine yaga sakona ya kira wayan sai dai ba number daya kirani daya kira dashi bane. Nace ummhumm ina jin ka naji ance haka ake karba kiran wanda baka sani ba na sheda muryan Yusuf din nace yayana kaine a na dauka wani ne. Yace nice injin ruwa bai saki jin zazzabi ba dariya nayi nace ai na watsa ruwan zafi a jikina yace good dama na kiraki ne don mutumin ki ya karbi number ki a hannu na nasan zai iya kiranki kada ki biye ma halinshi don Allah don bansan abinda zai kiraki ya fada maki ba koda yake yace akan maganan hajiya mama zai kiraki yaji don Allah , , , Na katse shi da fadin ai ya kirani ko har munyi tsiyan shi ya dauka kowa nema yake a gare shi ko yaushe ni kuma na wanke shi tass. Da karfi naji yace haba don Allah nace wallahi na kwashe komai na fada mai har text din da na tura mai mai zafi yace amma baki kyauta ba wallahi. Nace saboda may zai mun hadi yace khadija kin san kuwa kece mukee son kizama weapon din mu wurin yakan buzuwa nan gaba. Don Allah ki dinga sausautar harshen ki gare shi nace wa ni ni ina ruwa da shi da zan zama muku makami a gare shi da buzuwan shi. Dariya yayi yace ke ko ke dashi khadija ke da komai da zaki yakar muna buzuwa don kin cancanci yin hakan. Ni din yayana yace kwarai kuwa kauna na sai dai idan mun hadu zan maki bayani yadda zaki gane nace to shike nan tunda haka ka fada yace bani na fada ba umurni nima aka bani kan hakan . Yace sai dai idan mun hadu din zan maki bayanin komai nace Allah ya kaimu ina saurarenka da haka muka yi sallama dashi ya barni da tulin tunane a zuciyana. Da safe zarah ce take buga min kofa jin bugun kofan na tashi na bude daki tana tsaye kofan dakin nawa ganin tana son shigowa na bata hanya ta shiga daga ciki. Tambaya na tayi ko da safe zan fita nace ai kemakin sani yanzu haka shiri nakeyi kada in makara take cewa dani zata fita amma wai za a kawo mata sako shine take son in karba. Nace zarah fitan kuma zakiyi yanzu tayi dan guntun tsaki tana fadin eh wani friend dina zaiyi tafiya nake son inje muyi sallama dashi. Zarah ba zaki wankan ki fada ki zauna ki abinda iyayyenn mu suka kawo mu yi ba wanan dabiar da kika dauko bai da amfani gare ki nan gaba. Ta dan yi murmushi ta nufi wurin da taga na aje plate din abin ci da tukunya tana bude bayan ta bude ta dago tana dariya tace an fada maki yadda bakin san wayen kai ba haka kowa yake yanzu da anganki kamar may wayayen kai . Nace in dai irin wanan wayen wane kada Allah ya nufe ni da yin shi ina neman tsarin Allah ga irin wanan dabian naku Allah kuma ya shirye ku ku gane gaskiya. Ta juya ta debi arish a plate ta zauna ta fara ci ni kuma ina ta shirina nace kiyi ki gama gada ki makarar dani anan don banson in makara. Tayi murmushi tana kai abinci a bakin ta sai da ta hade tace wanan halin naki na ina kika fito karatu ina zaki karatu sai ke khadija. Khady look at you me kika rasa ke kanki jarin kanki ne amma kin tsaya kina wahal da kanki haka har kina wani girki tunda safe kamar wata matar aure amma waike nacin karatu sai wahala kike haka. Wallahi da zaki yarda akwai wanda zan hada ki dashi cikin kwana biyu kiyi clean ke baki daukan misali a kwaina khady da haka nake ? Amma yanzu gani tunda hanya ya bude min mai na rasa na rayuwa atare da ni amma ke gaki da abin kawo kudi kina ta faman kumshe shi a jikin ki ta fada tana dariyan shakiyanci. Ni dai ina tsaye ina mata kallon mamaki da huduban shedan da take min har kuryan dakina ta dauka nasihan ta ya na shigana ne ganin yadda na tsaya ina kallon ta. Tace ina son ki fahimci wani abu tsarin rayuwa yanzu ya canza ki shigo kawai a dama dake yarinya. Nace cikin murmushi zarah baki fance ni batsarin rayuwa ta daban yake da naki ban sanya ma zuciyana kwadayi ko son jin dadi a ko wani irin yanayi ba don haka kada kiyi tsammanin guntun huduban ki zaiyi tasiri a raina . Ni da kika ganin nan ina da mutunci na kuma nasan ciwon kaina dana iyayyena kada kiyi tsammanin kananan kwarin da kike bi zasu iya rudana da wani abu. Shi jin dadi lokaci indan lokaci yayi sai inji amma ba ta hanyar wullakata kai yadda kukeyi din nan ba kema idan da zakiji sharata da kin watsar da wanan rayuwan ki rungumi abinda ya kawo ki Abuja. Su kansu mazan da kuke bi aida karatun suke amfana yanzu bance maki ban saurayi ko rayuwa ba sai dai in gajarce maki ni indan zanyi mai tsabta da sanin ciwon kai zanyi amma bana kwanan gida irin naku ba. Baki zarah ta tabe min tana dariya ta saba da nasihana kullun wanda ita a ganin ta ni har yanzu ban waye ba ban san ciwon kaina ba bansan ta kan duniya ba kuma. Nace keyi dariya amma ni idan zan faso gari ba irin wa yan nan kanana kwari masu gurbata rayuwa zan tsaya dububa ba sai wanda ya san kanshi da mutuncin kanshi. Ta mike bayan ta gama ci dama ina magana ina kallon agogona ne kada in makara tace ina son ki fahince ni a yanzu ba a samun irin wa yan nan mazan da kike hasashe kinga ko zaki shawa wuya wurin neman su. A naki ganin ke nan zarah amma muna nan dake zakice na fada maki watarana ta miko min key din ta nace kenan yauma till down zakiyi tace yo may za a fasa kuma. Ta fita na rufo kofana muka fito tare da ita a titi muka raba hanya tana neman lift ni kuma na nufi cikin makaranta ina mamakin wanan rayuwa da zarah ta daukan ma kanta. Itama yar minna ce kama na dalilin haduwan mu ke nan da ita don ko a minnan ba unguwa daya muke ba su suna zama a cancaga ne ni kuma muna tsakiyan gari. Kasancewar mu yan gari daya yasa muka zama kamar yan uwa da ita da farko halin ta mai kyaune kafin idon ta ya bude da bin mazan abuja. Sai lokacin muka raba hannu da ita amma hakan baisa mun daina kula junan mu ba kamar baya sai dai ban taba yarda naci abinda take samuwa ba daga wurin yawon banzanta ba. Tun abin na damun ta har yazo ya daina damun ta ta daina ba sai wanan da iyayyen ta suka kulla suka aiko mata yanzun tana ganin tafi karfin shi ita shine ta kawo min inyi amfani dashi. Tun asuba yake tayar da ita ta tashi tayi sallah amma tana kwance tana barcin ta har yagaji yatayar da ita da karfin tsiya ta zauna tana mustsukan ido alaman barcin bai isheta ba har lokacin yana ganin ta tashine yasa shi fita daga dakin azaton shi zata tashi tayi sallah. Ya fita zuwa dakin motsa jikin shi da yakeyi duk safe inda kuma yake aje wasu kayan amfanin shi jiya anan yabar wayan shi yana canji ya je ya kwanta yana tunanen rashin son ibadan da batayi. Ya gama komai na motsa jiki da yakanyi da safe ya wuce zuwa inda wayan shi yake jone ya dauko din ka idan shine sai takwas yake bude waya da safe. Budan wayan yasa sakon da suka taru mai shigowa ya gane su wanda farko budewa nawa ne ya shigo da farkon. Mamaki yayi don ba suna sai lamba ga dogon sako kuma da maishi ya turo mashi kamar kada ya karanta tunda baisan mai sakon ba sai kuma wata zuciya tace dashi karanta kaji mana abinda sakon ya kumsa kila mai amfani ne gare ka. Fara karanta sakon ne yaji ranshi ya baci don ya fahinci inda sakon ya fito don ganin farkon rubutun nawa kamar haka Mijin buzuwa a zaton ka zaka iya rabani da hajiya mamane ko ka zubar min da mutucina da take gani kayi kuskure wallahi kuma kayi karya don bakina da naka ban fada ma hajiya mama tana gida an mata rasuwa ba. Ga wanda yasan mutuncinta yasan darajan ta na fadawa shida ya tambaye ni ko ina da labarin su bakai da buzuwa wace bata da daraja da galihu tasa ka zubar da matan ka da yayan ka da kowa naka kana ganin tsohuwar buzuwa tana maka rudi da huduban shedan kullun. Kai bari ma kaji wallahi wanan buzuwar ta zubar ma da kima da komai naka a idon duniya tunda kiri kiri ta mai dakai mijin hajiya. Ga mutum har mutum amma baida ta cewa saboda mace macen kuma buzuwa wace bata san Allah how dear you kaida mace bata bari ka zauna dako matar sunnan ka har kake da bakin yi mun hadi a wurin mama, , , , Jikin shi har rawa yakeyi da yake karata text din kasa kai kashen rubutun daki ya nufa da sauri da zuman ya shiga yai wanka ya fita ya samu Yusuf shida yaja mashi rene da wullakanci wurin yar karamar yarinya harta iya turo mashi text din banza haka. Sai yayi magani na a garin sai yasa na raina kaina may nike dashi may nake takama dashi da zan iya yimai cin fuska haka ina aibanta shi shi da matar shi. Waya ya fada min maganan da sukayi da hajiyan su hajiyan ne zata fada min kowa komai dai may nene sai ya rena min wayo sai na gane banda wayo yau a garin nan duk inda na shige sai ya tononi a cikin garin nan yayi min wulkanci Sai dai yana shiga dakin su kuma sai bacin ran nashi ya karu ganin Nafisa kwance tana barcin ta hankali kwace rashi ne ya kara baci ya tuna abinda nace a text dina. Bai san lokacin da ya isa wurin ta yakai mata mugun maka a tsakar bayan ta ba ta mike firgigit tana fadin Samad may nayi maka ? Tsawa ya daka mata yace wanan abin zai hada ni dake ke sai yaushe ne zaki rike ibada a zuciyar ki ne yaja tsuki ya shige wanka. Da sauri ya watsa ya fito ranan ya fito bai wani dauki dogon lokaci ba ya shirya ya fita daga gidan koda ta fito ta samu baya gidan. Tun a mota ya kira Yusuf yana fadin kana inane yanzu? Gani gidana ya bashi amsa OK kajirani ganin zuwa yanzu gidan yace eh mamaki Yusuf yaji yana tunanen mai zai kawo Samad gidan shi wanan lokacin haka. Don ka idar shine sai takwas yake fitowa ko takwas da rabi ware hannu yayi alaman shi ya sani ya mike ya shiga wanka kada yai mashi girshi. Yana shiri ya sake bugo mai waya gashi kofa gidan shi ya fito ya karasa ya fito ya samay shi don ko driver bai fito dashi ba Yusuf din na gani haka ya rufo gidan nashi ya fito ya samay shi. Anan ya bude mai mota ya shiga yarufe sai ya dauki hanya batare da yasan inda zasu nufa ba sai yaga ya miki mashi wayan shi duban wayan yake da mamaki yake fadin na maye wanan kuma ? Ka duba mana cewa fuska a daure ya karbi wayan ya fara karantawa a hankali yana sake murmushi ya gaba yana mika mai wayan yace kai amma wanan yarinyar takai jaruma wallahi haduwan zai zama abin shaawa ga mai kallo. May ne kace yanzun kai baka ga abin jin haushi ba a nan yace ban gani ba sai ma wani abin da na hango na daban tsakanin ka da beauty din. Yau sai nanu namata ita ba kowa bane a garin nan sai na wullakanta ta a garin nan dariya yayi sosai yace da kaima kan ka wallahi da ka tozarta kan kuwa. Wai kaiko kaga yadda kukai balain dacewa da yarinyar nan kuwa wallahi ni abin naku burgeni yake yi idan kuna yi har wani dadi nake ji. May kake nufi ne wai yace abinda idona ya hango min mana a kai saidai fatan alheri amma zancen ka ci mata mutunci bai taso ba ko kaje ka tozartata duk ba wanan a tsakanin ku ko kamanta da hikimar hajiya na hada ka da wanan yarinyar ne ko kana nufin kai baka gane hakan ba. To bari kaji Khadija itace zata iya fitar dakai daga zargin da ake maka na cewa Nafisa ta gama dakai da cewan da ake saboda ita ka kasa zama da Fati. Akan wani dalili zata fitar dani ta yaya din zata fitar dani yace muje zuwa nan gaba zaka sani idan lokacin hakan yayi yanzo ina zamu ne kadauko ni tunda safe haka. Wurin ta zamu in gwada mata ita din ba kowa bace ya kwashe mai da dariya yace ta zama kowan ke nan tunda har zaka iya biye ma shirmay ta na mata. Bai kara magana ba sai juya kan motar yayi zuwa office din su ya shige bai tsaya jiran Yusuf din ba. Anan malam musa driver ya tsayar dashi yana fadin yana da magana dashi na siri da yake son suyi a tsakanin su yace da malam sani din wani abu ya faru ne yace eh to sai dai maganan nason siri gaskiya yace dashi babu damuwa kasa may ni a gida da yamma idan mun tashi. Ga haka suka bar zancen da malam sani din sai dai ya barshi da tunane a zuciyar shi ko akan may yake bukatan kebewa dashi bai sani ba ya san dai abune mai muhinmanci sosai. Shiko gogan acikin office maganan da sukayi da Yusuf ne yake ta mashi yawo arai wai zata zama mai garkuwa a kan matsalan shi da Fati da Nafisa ta yaya ma haka zai faru . Nan dai ya watsar da maganan ya ci gaba da aikin dake gaban shi sai dai yanayi yana tuna zancen a zuciyar shi. Kai tsaye da na fito kamar yadda na saba gidan da muke na nufa yau yawan ci basu da lectures sai karan gida ke tashi ko ina a cikin gida. Yunwa nake ji don ban tsaya nayi karin kwarai ba da safe sallah nayi sana fara hada tea na nasha sai da na dan huta a wurin na mike ina sauya kayan jikina. Na saka dan guntun rigan da nake zama a daki dashi gyaran dakin nayi na gyaro ko ina na dakin sai na dora girkin dare don shinkafa da miya nake son yi irin na yan makaranta. Bayan na gama miya na dora shinkafan na koma na zauna a bakin katifa ina tunane zarah ne ta fado min a rai yau in zan lissafa kwananta biyar bata dawo ba. Zarah tana daya daga cikin "ya"ya dake cin amanan iyayyen su don babu inda suka rageta don koba a fada ba zarah tafi gata don sati biyu bai shigewa iyayyen ta basu turo mata da sako ba. Amma duk ta watsar da wanan gatan nata tabi ra,ayin kwadan abin hannun samari wanda ya rufe mata ido a yanzu har yakai ga ta watsar da karatun ta. Ido na lumshe tare da girgiza kaina ina cewa ubangiji katsare mu ka karemu ya Allah kasa mufi karfin zuciyar mu don yanzu rayuwa abin tsorone . Sai gata washe gari ta dawo dakina ta nufa don karban key din ta koda ta shige ban sake mata fuska ba daga inda nake kwance ta tambayi key din ta na nuna mata da hannu kawai ta nufi wurin ta dauka. Harara na bita dashi tana ficewa daga dakin andan jima kadan sai gata ta dawo dakin daga ita sai wani dan guntun tawul da ta daura iya cinyan ta tana tambayana wai ban rage abinci ba in bata. Wani kallo nayi mata nace inda kika fito gantalin ki kwana da kwanaki baki kici abinci bane acan ? Tace kin san yanzu wata yayi nisa ba wani abin kirki ake samu ba sai maneji nace sai ki je gaba ki nema ni banyi abinci ba yau. Ta ce khady yaushe kika fara rowa haka ba halinki bane rowa nace ban dafa ba nace maki ashe karyan iskanci kike yi da zaki dawo kwana da kwanaki hannu empty. Ta dan tsaya jin ganin ban kulataba ina karatuna sai ta fice min daga dakin dagowa nayi nabita da kallon mai kama da harara har tafice daga dakin. Bayan ya gama saurare abinda malam sani ya gaya mashi jikin shi ne yayi sanyi karshe yayi mai godiya tare da jaddada mashi kan kada ya fada ma Nafisa komai ya dai saka ido ga alamarin ta kawai. Bayan fitan shi gidan nine na fado mashi a rai wayana ya kira mun gaisa dayake shi mai son wasa ne nan yajani da wasa wanda bai wuce hiran mijin buzuwa. Yace gobe dai weekend ne ba shiga aji ke nan nace eh sai dai ina son zan fita zuwa wurin wankin kai don ina son gyaran jiki gobe dai. Yace ashe shi gyaran ma sai anje wani guri yin shi dariya yaban don irin zolayar shi nace ana mace ba gyara ne yace kwarai kuwa har in ta san kanta. Karfe nawa zaki ya tambaya nace wuraren goma zan tafi nasan zuwa karfe sha biyu ko da rabi na gama yace da safe banda time da nazo na kaiki sai dai ki fada min sallin din da kike zuwa in duba ki idan na rarage abinda nake yi. Nace No kabarshi kawai ba wani nisa yake dashi da inda muke ba nagode yace aini nace ki fada min ko nace beauty hair drasses na fada mai layin da yake a saman babban titi. Munyi sallama ina mamikin halin shi da saurin sabo irin nashi na zauna na tsefe kaina a cikin daren nan don kada in makara in samu mutane a wurin. Washegari da safe na shirya na isa sallon din ba wasu mutane dayawa don haka nabi layi sai da akawanke min akai min drying din shi kafin su fara min kitso. Ranan nasha gyara sosai na jiki daidai zan fito sai ga wayan Yusuf shigo yana tambayana ina wurin ko wuce nace an kusa gamawa nan da minti talatin zanbar wurin . Nakashe wayan akaci gaba da min gyara sai yaba yawan gashina da tsayi suke yi nidai murmushi kawai nake masu ban wani dogon magana da kowa a wurin. Sun fito daga kubuwa duban fili da sukaje gani a hanyansu na komawa gida yaga Yusuf ya dauki hanya bai iya magana ba yana aiki a system din shi kan shi a duke yake. Sai dai yasan ba hanyan gida Yusuf ya nufa dasu ba aikin da yakeyi ya dauke mashi hankali a lokacin ganin ya tsaya a bakin wani gyaran jiki na mata yasa shi dago kai yana tambayan shi ina ne nan kuma ? Kafin ya bashi amsa yaji yana fadi a wayan shi fito gamu a kofa idan an gama maki nace gani tafe na fito tun fitowa na ya hango nice tafe kallon mamaki yake wa Yusuf din. Har na karaso bakin motar nasu sai a lokacin nasan tare suke dashi fadi yusuf ke yi da na karaso wai wanan haduwa haka fa kanwata . Kaike kara zuzuta yayi maganar kamar bashi ya fada ba yace ba dole ba in zuzuta kanwata yar gidan mama wanan ai kyasa ayi karo a hanya nidai murmushi kawai nayi mashi. Na fara gaida su yace shigo mu sauke ki mana ba hostel zaki koma ba nace a a nagode yayana ku tafi abinku kawai dakai dayane zan shiga amma dai ku tafi kawai. Yace au don wanan miin buzuwan da kika gani ai bashi ke jan motar ba ko shiga muje don ki kawai muka biyo nan fa. Jin haka yasa na bude motar na shiga batare da na sake wani magana ba shiko sai aikin shi yake yi kawai ana tafiya mun kai wurin wani babban shago yace don Allah ku bani minti biyu in dawo. Ya faka motar yafita sai mu biyu a cikin motar kowa da abinda yake yi a lokacin sai can naji yaja tsuki yana kallon shagon na dauka dani yake yi nace dakata malam bafa kai ka dauko ni ba da zaka ja min tsuki haka. Da mamaki ya dago kai yana kallo yace ke dani kike nace da wani nake haka kawai zaka kama jamin tsuki a mota da mamaki yake kallo na yace ke wata irin yarinya ce da bata da tarbiya. Kadai gyara maganan ka malam tarbiya ai ko makaho yasan akwaishi nan sai dai a lalaba a gani ai ba bace marasa tarbiya suke ba. Bai kai karshen magana ba cikin zafin nama da kunar zuciya ya juyo inda nake yace wa kike nufi baida tarbiya cikin muryan nan nashi mai dadin saurare da yake rowan ta. Tsoro naji ganin irin kallon da yake bina dashi mai kama da harara ko tsana sai nayi kasa da kaina na kasa furta komai don kwarjin da yai min a idona Ya nuno yatsan shi daidai saitin fuska na tare da tsure ni da idanuwan shi lumsarsu yana fadin ke in badan Yusuf da bai san ciwon kan shi ba har kucaka irin ki ta isa ta shiga min mota na a tare dani. Yace kallani nan ko a hanya nagan ki baki isheni kallo ba a cikin mata don banga abin gani a wurin irin ki ba cikin dakiya da dauriya nake kallan shi ina jin kalamin shi har cikin raina sai dai ina tara abinda zan mayar mashi ne a zuciya ta duk da naji tsoran yanayin shi. Yaci gaba da fadin idan baki hankali da ni ba watarana sai na balbala ki wallahi don ni mace bata kawo min raini nace dashi. Don Allah malam matsamin bakumayi mamaki jin haka don ba abin mamaki bane don ka fadi hakan tunda dama kai irin maza nan ne dake raina jinsin su sai kai ido ga mata ketere saboda zalama irin na rashin sanin ciwon kai. Don wanan matar taka abin kyama ga jamma a da kai ka mayar mutum har kake ganin tafi ko wace macen kasan nan dadin abin dai kaima macen kasan nan ta haife , , , , Fat naji yakai min bugu a baki don zafi sai da na dafe baki na ina dubawa ko jini yake min ban san lokacin da idona ya fara fitar da hawaye ba na yun kura zan fita daga motar yasa hannu ya danna lock mutar ta rufe kit yace kuma ki saurare ni. Duk kika sake ganina a mota kikayi gigin shigan shi sai ya jefar dake a waje mota ya take ki kin mutum in kashe ki in kashe bazan . Nace ni wallahi ba banzan bace sai dai in kaine yace bakin naki bai mutu bako yana kokarin kai hannun shi ya kamo baki na na noke kaina a kafana sai bai samu kama bakin nawa ba. A daidai lokacin Yusuf ya iso wurin da manyan ledoji a hannun shi yana bude motan zai sa ganin mu haka yasa shi ya sake murmushi. Ina jin shi nayi saurin dago kai nace mugu kawai azzalumi yace kai yaya haka may kai mata don Allah take kuka kuma ya waigo zai kara jamin baki na noke ina son fita a motan Yusuf ya tare ni yana fadin haba dai yaya zakaci zalun ta kuma haka ? May tayi maka haka wai kasa ta kuka ya juya yana cewa bakin nan mai rashin kunya na daka ido ya zaro yana cewa ka dake ta Abdul ? Kadan ma ke nan nayi mata ai fita nake son yi ba hanya don Yusuf dake wurin yayi rufe kofan ya zagaya ya shigo motar sai da muka fara tafiya yace ka bata hakkuri Abdul. Ina baya ina kuka naji ya fada mai hakan yace nace ka bata hakkuri yace wani zanba wanan yariyar hakuri ko wa yace bakai ka zalunce ta don may bazaka bata hakkuri ba ko kafin ka tafi da hakkin ta ne a kanka ? Baiyi magana ba sai aikin shi dayaci gaba dayi yace wai may ya hada kune haka da sauri nace zagina yayi na rama. Motar ya tsaya a kofa gidajen mu na fita da sauri ya biyo ni yana kirana ban tsaya ba wata yar gidan yaba kayan ta shigo min dasu suka tafi ban san yadda suka karata ba. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: A raina sai mamaki nake wai wanan matashin da nagani wanda bai wuce ace yanzu zaiyi auren farko ba ke da mata har biyu haka. Buzuwan nan dai da za a zauna a fadi gaskiya tana iya girmay mashi daga shi har matar shi sai idan ance yanayin jikin su kawai da ba a gane hakan. Ita kuma Fatin baka ce sai dai da zata zauna ta gyara jikin ta banga abinda buzuwan nan zata gwada mata ba sai dai kasshh yanayi irin namu na matan hausawa yana cin rayuwan ta da haka nake hango buzuwa ta kwace mata miji . Yau da gobe sai Allah dama sati uku zanyi don hutun ba yawa shiyasa ban so zuwa kaduna ba a wanan lokacin amma anty na ta dage sai nazo ita kadai ne a gida mijin ta yayi tafiya. Ashe kuma da rabon mu kwasa da matar mulki ne a garin ya kawoni don haka shiri nake inda ba komai nake shiryawa sai kayana don ban daukan provition da ga gida sai na tafi can nake saya. School zan wuce direct sai nakwana biyu zan shigo mina in masu weekend in kwashi abinda na samu in koma bayan kwana biyu don haka nake ta shirin komawa makaranta a lokacin. Kwatsan da safe muna karyawa saura kwana biyu tafiyana sai ga wayan mommy ta bugo ma anty wai Fati ta dawo gida yanzu haka tana nan gidan su naji anty na fadin o o Allah yanzu matan nan da karfi da yaji sai ta raba wanan auren take nufi. Banji may mommy ta fada mata ba nadaiji tana fadin gaskiya haka nane idan abu yaki sai ayi hakkuri kada zumunci ya baci idan abin ya sake shi inda rabon komawan ta gidan sai ta koma. Bayan ta kashe waya tace mummy tace ki shiga kafin ki wuce kada ki tafi baki sallamay su ba nace haba anty may yasa kika fada mata zan wuce ai sai yazama kamar roko idan naje sallaman su. Kai ta girgiza min tace ba haka halin su yake ba dauka na sukeyi kamar wata ta gida a gurin du duk zuwa kikayi kika wuce sai sunyi min korafin hakan. Shiru nayi sai tace o Allah sarki wanan buzuwan dai ta hana Fati zama gidan mijin wai yanzu kuma ta kara fitowa tace bazata koma ba. Dudufa baifi wata da ta koma gidan na yanzun kuma ta kara fitowa jiya wai sai dai na shiga inji may kuma ya hadasu fada yanzu. Takaici bai barni nayi magana ba sai dai a zuciyana nake bankawa mijin zagi da rana su binta suka shigo gidan mu anan muke jin labari wai tunda ya dawo buzuwa taki bari ya ke be da fati hakan bai isheta taja Fatin da fada har tana fadin sai ta kashe ta. Shiya ba Fati tsoro tace barin gidan yafi mata nace shike nan ta samu galabanta ai ta kashe ta din idan ta isa mana. Gaskiya matan nan ta samu wuri da yawa wallahi nace shiko sokon yayan naku fa may yayi a kai tace jiya baban mu ya kirashi sai cewa yayi shi yagaji da halin fati tana bata mashi suna. Ai wallahi idan da nice tace sai ta kashe ni da na nuna mata hauka ke matsorata ne fa iskancin abaki yake masu kawai Fatin dai ne wallahi she is to slow . Anty tace khadija baki san aure ba fa shi wanda ake abin a kansa bai nuna wani feeling din shi akan ta gara dai da ta hakkura ta basu wuri. Zata tafi nace barin bisu daganan in masu mommy sallama tun ranan da mukai fada da buzuwa ban sake shiga sai yau da zan tafi sallaman su da anty ta matsa min. Tsab na shirya na fito cikin wani dogon riga mai hannu shara shara shara da gyalen shi na yafa akaina sai turaren da na fesa a jikina. Mun shiga gida inda na fara zuwa dakin mama na gaida ita sai na fito naga anty amarya a waje anan na gaida ita har zan wuce tace khadija ashe haka kike ina ganin ki shuru shiru dake ashe ke ma jaruma ce ban sani ba. Dan guntun murmushi nayi nayi kasa da kaina kawai dakin mama na nufa ina jin suna maganan a waje da mai masu aiki na shige wurin mama in gaida ita. Tana zaune a falon ta tana waya haka yasa na samu wuri a kasa gefeta na zauna ta gama wayan ta dago kai cikin fara a tana fadin yau khadija ne gidan nace mama ina kwana. Ta amsa min fuska a sake nace mama nazo in sallamay ku gobe zan koma school tace a a har hutun ya kare wanan karon nace eh mama. Ta sake cewa gida zaki ko Abujan zaki wuce aa zan wuce school ne daga nan tace barin baki tsaraban yan makaranta ko nace mama da ki barshi ai ba zan dauki kaya daga nan ba sai naje can saya. Tace a a wanan kan zaki so dambu ne da akai ma yayan zai tafi dashi kin san yana son dambun nama sosai shine na aikai mashi shima gobe zasu tafi. Ta mike ta shiga daga ciki sai gata da roba dan madaidaici ta fito da kudi a hannun ta ta miko min nayi godiya namike zan fita ko ba a fada ba yanzu na sheda wanan kamshi ba kowa bane sai dan ta Abdulsamad mijin buzuwa. Zai shigo ni kuma zan fita ban yi tunanen in kauce mashi ba a lokacin dole suka jaye a hanyan na fita ashe da buzuwa suke tana bayan shi. Mama ce naji ta kwala min kira sai na dawo wanan karon sai da na bari sun gama shiga na shiga dakin nima na karasa wurin ta gwiwa na biyu a kasa na zube ina fadin mama gani. Buzuwa ke gaida ita ta tsaya amsawa ta dago tana cewa dan ta gobe ne zaku tafi din ko yace insha Allahu mama yanzu ma mun zo mu sallama ku ne don goben sakko muke son yi dan zan shiga office. Ta juya gare ni tana fadin gobe sai ki shirya su tafi dake indan zasu wuce gaba na ya ba da damm da sauri nace a a mama ba tafiyan safe zanyi ba ni. Khadija yayan ku ne fa ki shirya ki bishi yafi shiga motar kasuwa su wuce da ke shidai baiyi magana ba ya rike goshin shin da hannu guda . Sai buzuwa ne tace motar tamu ai a cike take dayan ni dashi ne sai driver dayan kuma na masu aiki mun ne su larba sai na security din mu . Naku zata shiga don ita din ba bare bace yar gida ne kaji na fada maka tau mama yace ta shirya da safe din kada ta makara sukuku na mike tare da fadin mama na gode. Fitana dakin mommy na tafi ina nuna mata abinda hajiya mama ta bani tace ai yaya tafi danan ban fada mata zancen bin mijin buzuwa da tace in yi ba a lokacin itama daki ta shiga sai gata ta fito min da wani bakin dogon riga da takalma cikin na sayarwanta tace ga wanan a samu na sakawa. Binta ce ta shigo dakin tana dariya mommy tace maynene kuma tace khady nakewa dariya mommy mama tace da yaya gobe su tafi da ita. Ga buzuwa can tana fada bayan fitar mama daki wai bata yarda ba bata san mama ta jita ba shine mama ta fito tana fadin har ta isa tace ga abinda take so tace ita bata yarda ba yaya ce shi baice ba zata bisu ba ai. Juyowa mommy tayi ta kalle ni nace nifa ban iya bin su gaskiya don idan tayi min wallahi nima yi mata zanyi gara ko kada in bisu din. Dariya take min mommy tace akan may kin samu sauki bazaki bisu ba ai shi Abdulsamad baida hakana tunda har yaya tayi mai magana da bai daukan ki tun a nan zaiyi magana balle yanzu da yasan yaya tana hake dashi ai ba zai so ya bata mata rai ba kuma. Daga cikin dakin mommy anty Fatine ta fito tana saye da wani hijjab har kasa fuskan ta duk ya kode alaman tasha kuka har ta gaji. Gaida ita nayi ta amsa kasa kasa ta zauna a daya daga cikin kujerun falon mommy tace kin tashi tace eh mommy tace ga mutanen ki can sun shigo sallaman mu zasu koma gobe wai. Shiru tayi batayi magana ba sai mommy ta kara cewa kin san yaya da son jan magana wai cewa tayi gobe su wuce da khadija da zata koma makaranta goben. Wai ai ba zata bari ba wallahi bata son kowa ya rabe shi balle wanan da take gani mace haka maikyau kuma gasu da wata a kasa daman. Aiko banyi niyan binsu ba da amma yanzu sai na bisu tunda abin haka inga yadda zatayi a motan dani idan na shiga. Murmshi mommy tayi tace ki shirya da wuri don shi da wuri yake tafiyan shi idan zai tafi tashi nayi nayiwa mommy sallama muka fita da binta ta rakani. Naje gida na nuna ma ya Amina tsaraban da suka bani don da zanfito anty amarya taji zan wuce ta dauko min wani set din turare mai kamshi ummi ce bata ban komai ba a cikin su. Sai can muna hira nace ya Amina kinsan wai mama cewa tayi in shirya gobe in bi mijin buzuwa da buzuwa idan zasu koma. Da sauri tace may ne ? Nace wallahi da banyi niyan binsu ba amma tunda ta nuna bata son haka zan bisu din inga yadda zatayi dani a hanya . Nidai wanan zuwan wai damay yazo muna haka ne da tarihin buzuwa ko damay yanzu ke binsu din zakiyi, ba zaki hakkura kibi motar kasuwa ba. Don mama ne kawai zan bisu kada in bata kunya tunda tana sin gwada masu ikon ta ne a kan su da kuma ita buzuwan zantafi. Da yamma sosai na fito zan shiga gari in karbo dinkina da nakai ina fitowa bakin get sai ga motan shi tundaga nisa na kawar da kaina don ban san wanda ke cikin motar ba sun kawo kusa dani na gane su ne na watsa mai harara na kawar dakai. Yusuf wacece wanan yarinyar wai da nake gani a gurin mama yarinyar bata da kunya ko yanzu baka ga wanj harara da ta watsa muna ba kullun shi take min fa har a falon mama da muke haduwa. Dariya Yusuf din yayi yace amma kuma tana da kyau gaskiya koda yake kai yanzu baka ganin kyaun mace gaka da buzuwa a gidan ka. Wai Yusuf may ya kawo wanan magana haka daga tambayan ka yarinya idan baka santaba kace kawai baka santa ba period. Dariya Yusuf din yayi yace kai ke nan da anga mace mai kyau kace kada ayi magana wallahi yarinyar ta hadu sosai shiya take da jan aji da yawa. Nafisa fa tayiwa rashin kunya a gida na ka sani kuma kake wanan magana yace a a suka dai yiwa juna ta zage ta ta rama don uba baifi uba ba. Matsalan Nafisa tace kowa zata juya don tana takama mijin ta na da kudi kaji dai abinda yarinyar tace mata ai batazo roko wurin ku ba zumunci ya kawo ta. So tayi ka kama mata kuyi wa yar mutane cin mutunci a banza. Yace ai don na ganta a wurin mama ne yasa na kyale ta amma da ba zan yarda ta shigo min gida tayi min tujara ba for what ? Matar ka ce yar cin mutunci ai ya furzo iska daga bakin shi yace matsalan ta ke nan wallahi cikin ina tsawata mata ta bari ke nan ma. Yanzu dai kun kori Fati kun huta tabar maku gidan yace ta dai kori kanta amma ni ban kore ta ba ai ban san irin Fati ba wallahi . Bandai san irin ka ba malam buzuwa ta hanaka ka ba Fati da yara hakkin su kai kuma ka biye mata ranan fa a gaban kowa ta banbare hannun Fati a jikin ka kuma ka yarda. Wallahi idan zakai ma kan ka fada kayi tun baka makara ba kana ganin su Affan idan suka girma sukaga kanawa uwar su haka zakaji dadin su ne. Kai wa kan ka fada wallahi akan buzuwan nan kada ka tashi ranan lahira da bari shayaye . Bugu yakai ma abokin nashi yace Allah man abinda akace yana samun masu karkata gin mace daya ke nan na fada ma tun farko ban yarda da ita ba yanzu kaji abinda hajiya ta fada muna ranan. Nisawa yayi yace ai Fati ta riga da ta hadani dasu har baba fushi yake dani a gidan da sauran yan uwa. Yusuf yace buzuwan ka kuma tana jin dadi ba ta kori yar masu gida an bar mata gida tana yadda take so ita kadai tayi hankali wallahi da iyayyen nan namu. Shiru yayi yana nazarin maganan abokin nashi baice komai ba san cen yace kasan hajiya don jan magana cewa tayi gobe da wanan yarinyar zamuyi tafiya. Ina Yusuf ya tambaya da sauri yace wai Abuja zamu tafi a can take tace nowarder idon ta yake a bude haka bata da tsoro da ganin ta ai. Na karbo dinki na dawo na shirya kaya na bayan na gama komai na zauna ina tunanen yadda tafiyan mu zai kaya a goben. Ya Amina ta ban abinda zata bani taja min kunne don Allah kada in kula buzuwa har mu isa nace ni ina ruwana da ita su dai kaini su sauke kawai. Da safe ya Amina ta tana dani da wuri na shirya jiran kawai nake ace in fito mu tafi ya Amina tace in dauki jakkana da sauran kayana inje dasu gidan su mommy nace ai wanan ya zama tonon asiri haka . Ni madai su wuce idan haka ne dole ta kyaleni don ba yadda zatayi dani na gama komai har da karyawa ya Amina ta sani yi da safe don tafiyan da zamuyi din. Can sai ga su Binta sun shigo wai in fito da kayana ga su buzuwa nan sun fito suna ciki suna sallaman su mama zasu biyo nan su dauke ni inji mama. Tashi nayi na fara fito da kaya na waje suna tayani fitarwa kofan gida sai ko ga motan su ya tsaya suna baya dashi da buzuwa gaba zan zauna dani da driver su. Ina jin ya Amina tana gaida su binta ta bude min na shiga duk da kamshin turen su amma nawa ya karade motar har na shiga na zauna ban yi masu magana ba ina daga wa su ya Amina hannu muka tafi. Tsayawa sukayi suna bin motar da kallo Binta tace yau akwai tafiya a wurin nan jifa yadda anty Nafisa ke cika tana batsewa kamar ta fashe. Zainab tace suna daidai da khady ai ta fita iskanci daidai zasuyi a motar niko saida aka fara tafiya na dan juyo nace dasu ina kwanan ku murya can ciki bai fita. Ina kokarin cire airpies dina na sa a kunnuwa na tare da sake kira, a a wayan na lumshe idanuwa a hankali ban kara bi ta kansu ba kuma. Tun ina bi sai dan barci ya dauke ni ina yi ina falkawa na gyara zama tare da dan satan kallon su ta karkashin idanuna na naga yadda suka zauna manne da junan su sai dai aiki yake a laptop din shi. Ita kuma tana gyangyadi daga zaune da yake lafiyayun motoci ne kafin wani lokacin har mun kusa isa Abuja driver yaiwa magana yatambaye ni ina za a sauke ni . Ya juyo idanuwa suna lumshe ya dan taba sit din na bude ido tare da cire airpies din dake a kunne na yace yallabai yace a ina za a sauke ki ne ? A hostel nake zaune na bashi amsa ya juya gun ogan nashi yana fadamai abinda nace mai bai kara magana ba har muka shiga gari. Ban ankara ba sai naga suna shiga jerin gidajen dake asorock a wani gida motar ta danna kai suka shiga katon gida ne mai wani babban get ginin gidan sai mutum yace a turai yake sai lokacin na cire airpies din kunne na naji buzuwa na fadin ita a ina za a sauke ta banji may mijin ya fada mata ba nidai ban fita motar ba su kuma sun shige ko godiya ban masu ba. Driver ya shiga masu da kaya ciki ni dai sai bin gidan nake da kallo a raina nace shiyasa yake abinda ya ga dama ashe yasan abinda ya taka, Ga wasu manyan motoci gudu uku a fake wata katuwar jeep ta dauke min hankali har ina satan kallon ta a wurin motar sai sheki take tana daukan ido da gabin ta sabuwace. Sai dai ga daular duniya matashi dashi amma ya kasa auren yar kasamu suci arziki a tare sai wata bare ce buzaye ne gidan naga suna fitowa daganin su kasan yan uwan buzuwa ce ba sai an fadi ba nace mijin hausa ke nan inwar giginya na nisa ka more ka. Driver ne ya fito tare da wani dan saurayi buzu a baya shi yana dauke da tire da drinks yace gashi mai gida yace a kawo maki No na gode na fada tare da juyawa da kaina gefe a can cikin gida kuwa fitina na tsakanin buzuwa da mijin ta. Wai sai dai in shiga motar haya akaini hostel bata yarda ya wuce su sauke ni ba dole yasa driver yakai ni sai ya dawo ya kai shi office daga baya. Mun kama hanya driver ke cewa kai matar oga akwai kishi yanzun haka ta rike shine ciki wai bata yarda ya fito atafi kai ki dashi ba. Murmushi nayi nace mahaukaciyar banza kawai itake nata haukan ni ko a jikina yace nayi mamakin yadda ta yarda aka dauki ai nasan shi take ma fushi har muka zo ba shiri a tsakanin su. Surutun nashi ya isheni don haka nakawar da kaina gefe kamar ina kallon titi don abokin gulma yake nema da alama ganin na kyale shi shima yaja bakin kishi yai shiru har muka isa gidan da nake ba a cikin hostel sai dai gidane na haya da yan makaranta ke kamawa. Driver shi ya taimaka min da kayana har zuwa bakin gidan namu ya shiga min dasu sai dai bai shiga ciki ba kudi ya miko min yace gashi oga yace idan na sauke ki in baki. Dan jimm nayi kamar bazan karba ba sai dai nasa hannu na karba tare da fadin kace nagode sai dai ban faye karban irin kyautar nan ba kallo na yayi ganin na fara jan trolley dina yasa shi wuce yana mamaki na a ran shi. Dakina na bude wanda mijin ya Amina ne ya kama min hanyan shi dakine ciki da falo da bandaki a cikin sa sai inda mutum zai danyi girki daga waje haka dakunan suka a jere har dari da wani abu. Dakin yayi kura dan sati biyar din da nayi ban ciki daga kofa na aje kayan da na dawo dashi na fara gyara dakin tukun sai da na sharo ko ina na dakin. Na mayar da komai yadda nake son shi na fito ba zan iya fita ba haka yasa na kwanta don in sauke gajiyan dake jiki na a lokacin. Ba wanda yasan na dawo do haka na rufe kofa na kwanta abina sai barci mai nauyi ya dauke ni a cikin barci sai gashi wai muyi mumunan fada da buzuwa mijin kuma na tsaye yana kallon mu baiyi magana ba. Falkawa nayi don kiran wayana da akeyi na lalubu wayan da kyat saboda barci da yaci idona ya Amina takirani. Ina dauka naji muryanta tana cewa ina kika shiga ne haka waya nata kara baki dauka ba cikin muryan mai barci nace wallahi barci nakeyi anty. Tace yaya kuka sauka shine koki kirani hankalina ya kwanta nace wallahi lafiya kalau muka sauka tace badai wani matsala ko ke da buzuwan ki ? Naja guntun tsaki nace suna can gidan su muka sauke su driver su ya kawo ni hostel ni komai bai hada mu ba a motan bayan gaisuwa. Tace to barin barki ki huta an jima zan kira son naga yanzu barci yaci karfin ki nace ai na tashi yunwa ma nake ji yanzu tace to ki samu abinda kikaci kin san kina da ulcer nace yanzu zan tashi. Baki sayo komai ba ma ke nan nace yau na gaji ne anty ba zan iya zuwa ko ina ba sai dai gobe idan na fito lecture. Allah yakai mu tace muka kashe waya ina jin dadin yar uwa ta sosai saboda kulawan da take bani na musanman shiyasa nima nake mata komai kamar ita ta haife ni. Mafalkin da nayi ne ya fado min a raina lokaci guda yake dawo min dan dariya nayi nace ikon Allah wanan buzuwar kamar manya ta tsaya min a rai haka ? Sai a lokacin kudin da driver nan ya bani ya fado min a rai na jawo jakka na daga kwance na kirga kudin ido na zaro ganin har dubu hamsi ya bani nace wanan yasan zafin kudi kuwa ? ZAINAB IDRIS MAKWA SEENABU 1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Ina shiga ruwa na saukowa daga sama da karfi dama hadarin da ya gama haduwa a lokacin kiris yake jira ya fara zuban ruwa. Ruwa ake sosai a lokacin na kuma san basu kai gidajen su ba duk da ba zan iya cewa ga nisan gidajen su ba a lokacin. Na fara cire kayan jikina aka turo kofan dakin nawa da na saya da sauri na juya don ganin wanda ya shigo min a wanan lokacin haka. Maryam yace sabuwar kawar da nayi a cikin hostel din namu tana rike da wani warmer dain abinci na silver mai marika tashigo tana dauke da murmushi a fuskanta nima murmushin na mayar mata a lokacin nace cikin ruwan nan kika fito. Tana aje kulan tace tun dazun nake dakon dawowar ki ai sai yanzu na ga wuta a dakin ki na san kin dawo gami da yi min sannu da dawowa na amsa ta. Na karasa cire kayan na daura zani a jikina tace abinci na kawo muci don yanzu na samu yar uwa na huta zaman kadaici hakana murmushi nayi ina zama a saman katifan nace fitan nan nawa har kikai girki haka ? Tace dama akwai miyan a fridge sai shinkafa ne kawai na girka muna yanzu nayi mamakin jin har da fridge a dakin ta don ban taba shiga ba sai ita ce mai zuwa dakin nawa. Ido na ta kai ga ledan da na shigo dasu dakin yanzu na dauko na fara budewa kayan mata ne a ciki irin doganyen rigunan nan har kala biyar sai takalma da jakka biyu. Sai dayan ledan mai dauke da kayan drinks da su packed din sweet irin mai tsadan nan tace woow duk wanda yayi sayayan nan yasa kansa wanan rigunan duk letes ne fa don anty na business din da take yi ke nan wanan dawowan da tayi daga dubai naga ta dawo dasu har nace taban guda daga ciki tace sai dai in saya. Nace uhmm kyautar maya ne haka maryam wasu yan yan gari mu ne da suka zo yanzu muka fita tare suka saya min su. Maryam tayi dariya tace manya ko ba nawa sa ba nerbough don wanan wawan kyautar sai da wata a kasa kin san ko ba karamin kudi aka kashe wurin nan ba. Nace kuma kin ga ba wani abu a tsakanin mu sun dai ce ne mudan fita in rakasu wani wuri ni ban ma shiga shagon ba Yusuf kadai ya shiga sai gashi da wa yan nan kayan haka ya fito. Tace haka abin yake ai don masu kudi basu jin zafin fitar da kudin su, ga abinda suke so don wanan kyauta ai ta maya ne daganin su duniya na damawa dasu Allah. Nace sam ban san yayi min wanan mahaukacin sayayya ba da na dakatar dashi wallahi ni na dauka ko irin dan drink's din nane da sweet fa. Maryam tace may ye na damuwan kan ki tunda bake kikace su saya maki ba sai dai gaskiya kyauta yana nuna alama ga abinda ake so ne. Nace so kuma ai sun san ban da lokacin wani so a yanzu kawai dai raayin su ne yin hakan sai dai zan dakatar dashi ga yi min haka nan gaba. Abinci ta fara zuba muna muna hira na kwashe kayan na kawar gefe guda ina ce mata kinga yanzu sai dai mu canza tsari ba wai kullun kita dafawa kina kawo min muna ci ba haka. Dariya tayi tace kin manta da rana naki mukaci shiyasa nima na dafa muna yanzu muci ai ko hakan kuma laifi ne nerbough ? Muna ci muna hiran makaranta da ita har mun kusa gamawa wayana dake gefe yayi kara da sauri na mika hannu na dauko don kada ya tsunke. Daddyn mune akan layin na dauka da sauri ina hadiye abincin da ke a bakina yace may kike ci haka khadja ko dadi kuke ci a makarantar mu muna nan gida muna hadiyan shikafa da mai ya fada cikin zolaya . Nace daddy Allah ya nuna muna mun samu kuma kuji dadin da iyayye ke ji ga diyan su watarana indai zakuyi farin ciki da hakan. Yace ko yanzun ma mun gode maku don muna cin moriyan ku a haka yaushe yaushe kika turo muna da kudin hannun ki wai mu kara nayi fada ai da yar uwarki nace ke da kike makaranta kin fimu bukata a yanzu ai. Burin mu daya shine muga kin tsayar da miji da wuri kiyi koyi da yar uwar ki kema kiyi aure basai kin yi dogon karatun nan dakike so ba. Dariya nayi nace kai daddy aure yanzu kuma nida nake son in zama babban lauya kafin in aure amma tunda naga raayin ka ke nan ba damuwa . Daddy da izzinin Allah zan cika maku burin ku daddy na karasa fadi cikin sanyin murya daddy yace da sauri . Dear kada ki sa wanan a rai yanzu buri na fada maki kawai shi aure ai dan lokaci ne indan lokacin yayi ko da shiri ko ba shiri zakiyi ne ai nafison in ganku cikin farin ciki a koda yaushe bana son bacin ranku kada magana na ya kara maki zuciyar ki akan karatun ki. Ya kara da fadin Allah dai yayi maku albarka dake da yan uwanki don baku taba bata muna rai ba da halin ku. A hankali na goge hawayen da ya zubo min a idona nace mukai sallama dashi bayan ya gama kwatar min da hankali na. Maryam ido ta tsura min ina aje wayan tace dani ina son nima inga ina haka da iyayyena wallahi sai dai hakan bai samu ba a gare ni don na taso ne ba tare da iyayyena a wuri daya ba. Mahaifiyar mu sun rabu da babban tun muna kanana sai dai idan naje inkai masu ziyara dukkan su tunda riko na yadawo hannun yayata. Nace Allah sarki lalai dole kiji sha, awan hakan gaskiya don iri haka babu daddy ni kinga iyayyena sun fi son suga nayi aure ko yaushe maganan su ke nan a kaina. Sai dai ko yaushe auren nawa zai zo ban sani ba tunda ko sauriyi tsayayye ban kai ga tsayarwa ba a yanzu haka. Tace to ina ga dai yazo din ne tunda ga wanan yanzu da ya fito ya fara nuna maki son shi dariya nayi nace maryam ke nan baki ganewa ne ke. Bandai fada mata komai ba mukaci gaba da hiran mu sai goma ta koma dakin ta nima na gama abinda nakeyi na kwata. Har na kawanta naji wayana na verviration a gefena nasa hannu na dauko wayar nace salamu alaikum. Yar mama kina lafiya yaya ruwa , ? Na sauke lafiyayyen murmushi nace lafiya kalau yaya Yusuf yace kina kara fasa min kai fa da yayan nan da kike kirana dashi nace kai ka saya a kira ka da sunan. Nace yaya kuka isa gida kuma yace lafiya kalau sai yanzu na kai mutumin ki gida yanzu haka ina hanyan gidana ne na kiraki mu gaisa. Yace bayan mun rabu dazu mun dade muna maganan ki da mutumi na nasan zai kiraki yau din na shiya na kira ki in fada maki don naga ya yarda sosai da shawarana. Nace anya kuwa zan iya cika maka alkawarin da na dauka don mutumin naka akwai zuciya sosai wallahi ni kuma ban iya daukan haka don nice zan taimake shi ba shi zai taimake ni ba. Dariya yayi yace a yadds kuke yi din nan shakuwa zaizo ya shiga tsakanin ku sosai zakice na fada maki watarana bagashi yanzu ya fara saukowa ba. Idan ba ta haka na fito mashi ba da wuya yayarda mu aiwatar da komai yadda muke so amma ki daure don Allah mubi abin sannu ni dai buri na shine ki san yadda kikayi kika kara ma wanan buzuwar kadarin ta a gurin jamma,a. Abin ne da kamar wuya yaya na sai dai zan yi kokari inga nayi yadda kuke so din yace good girl Allah ya taimaka ya bada sa,a nace amin. Shine kuma ka yi min dawainiya haka mai yawa don Allah nan gaba kada ka kara min irin haka don hakan zai yi maida ni cikin wani yanayi daba shi nazo yi a gatin ba. Dariya yayi yace Khadija kin san dai sutura shine mutum yanzu don haka farawa akayi don ina son ki goge sosai ki fito a cikin classes ladies ta yadda zamuji dadin aiwatar da komai a cikin sauki nace to na gode sai dai a rage don Allah. Kada kiji komai mana lokacin kine yayi kawai ki kwantar da hankaki kici arzikin ki a saukake wanan ba komai ba kada ki damu da hakan don har motan shiga ba dadewan nan ba zaki samu in komai ya tafi daidai. Zanyi magana ya katse ni da cewa na iso gida zan shi sai dai indan mun kara waya don yanzu zamu rage haduwa sosai kada a zargi wani abu a gare ni. Mun gama wayan ina mamakin su kudi kamar na sata haka nikan ban cika amincewa da irin haka ba azo ba a daidaita ba shirin mu ya watse abarni cikin wahala daga baya. A hankali ya shigo gidan babban falon su ya samu su hidaya da sauran yan su zaune suna shan bakin shayin su na buzaye. Gaisuwa sukayi bai tsaya ta kansu ba ya shige ciki bai jin dadin yadda suke cika mashi gida a ko wani lokaci haka. Duk da wani lokaci abin yana taba mashi zuciya ganin yanzu babu wani nashi da yake zuwa wurin shi kamar lokacin da suke zaune kano da fati . Yan uwan shi na yawan ziyarar su maza da mata amma tunda abin ya juye haka sai dai kulun idan ya dawo gidan ace mai akwai bakin da suka zo daga kauyen maradi. Dakin ya nufa ya tura kofa a hankali dakin na nan a yarda ya barshi da safe ba a gyara shi ba in zai iya tunawa yau kwana uku ke nan bai samu lokacin da zai tsaya ya gyara dakin ba. Don cikin yan kwana kin nan suna zirga zirgan filin da suke son saya a kubuwa ga kuma wanan shirin da Yusuf yake son yi a kan shi. Rigar shi ta sama ya jefar a saman gado ya kara bin dakin da kallo ya ja tsuki ya nufi yanyar bathroom din shi wani zarni ne ya daki hancin shi da sauri ya fito ya nufi hanya wajen dakin. Dakin Nafisa ya shiga don yana kyautata zoton tana ciki tunda bai ganta falo ba kuma bai ganta a nan dakin shi ba. Yana shiga nan ma wani tsami ya tare shi mai kama da karni karni yabi dakin da kallo ga kaya a ko ina watse a dakin tana kwance saman godon dake tule da kayan da bai san ko na maynene ba. Nafisa na ganin shi tace ka dawo ashe yanzu nake tunanen ka fa a raina nace ko ina ka shiga tunda ka fita da safe baku dawo ba. Haushine ya kamashi yadda take kwance ta mike kafa sai kadasu take yi tana magana kamar wata basaraka da ita. Kallon da yake mata ne yasa ta tsargu yace Nafisa wai ke dadin may kike ji ga kazantar nan naki ne haka don Allah dubi dakin da mutun ke rayuwa wai a cikin sa. Kina mace kice ba zaki iya gyaran muhalin ki ba sai wasu sunyi maki wai ma ina masu aikin da kikace kin dauka ban ga wani abinda suke a yi a gidan nan ba. Tace Samad yan uwana ne fa ko kuma yanzu kana bakin ciki da zaman su ne a gidan ko suyi aiki ko kada suyi zasu dai zauna anan tare dani ne ko ? Nasan wanan munufakin kila yaka su hadiye a falo ya zuga kwanan nan sai nayi maganin shi wallahi ni banga dalili da zai sa yayi ta shigo min gida ba haka ba gaira ba dalili yana sa muna ido. Ke na fada maki duk abinda zakiyi idon ki ya fita ga Yusuf don idan kikace zakiyi kokarin raba ni dashi kan ki zakiyi wa kin dai san halina and kuma ki tashi kije ki pulloshing din rubish din da kikayi min a bandaki tunda ba dakin ki bane. May nayi kuma kewayawa fa kawai nayi a ciki na fito yace zaki tashi ko sai na bata maki rai yanzu ya fadi yana dan zare mata idon shi. Mikewa tayi da kyar tazo ta wuce shi zuwa dakin ya bita da harara ya mara mata baya yana sa kai warin bayin ya ji har cikin dakin da sauri yafita zuwa dakin hutun shi tare da rufo kofan da key don bai son damuwa. Anan ya cire kayan shi ya yi wanka ya fito sallah ya gabatar ya dade zaune a wurin yana tunanen halin Nafisa ga gida da ta cika mai da yan uwanta babu halin ya zauna a tsararen falon shi ya sha iska a ciki. Tsuki yaja ya mike don ya kwanta nan yaga wayan shi da ya jefar saman gadon daya shigo dakin kafin ya kewaya dauko wayan yayi yana duba lokacin maganan Yusuf ya fado mashi a rai. Da yake ce mashi kabi yarinyar nan a sanun har mu cin ma manufar mu a kan hajiya ba wai nace kaso ta bane dole a a wanan wani dama ne da muka samu zamuyi amfani dashi. Nomba na ya bida a wayan da ya rubuta ma tsoturburn girl ya danna kira sai ko kiran ya shiga tunanen ya fara yi idan na dauka may zai ce min sai yaji na dauki wayan da sallama a bakina. Queen yar matsala yaya kika shiga gida yaya kuma ruwa i hope bai taba ki ba dai ? Murmushi nayi sai da yaji shi cikin zuciyar shi nace au mijin buzuwa ne a layi lallai kana son aikin nan da zan maka ke nan ? Yace to yaya na iya tunda Yusuf yace ke ce maganin matsalata yanzu indai har zaki min hakan ai ya zama dole in koyi zama dake da halin ki . Nace ashe shiyasa na samu queen din yan matsala yace idan akwai abinda yafi queen din su kinci a baki wanan muka min. Murmushi na sake yi nace nace nako gode da wanan sunan da aka rada min sai dai ina ganin bada ni sunan ya dace ba yanzu ai. Da sauri yace dawa ya dace nace kaida buzuwar matarka mana fara yar dagwas mai gashi har baya sai dai kassh kuma gashin sai naga kamar bai samun gyaran da ya dace dashi balle har kaji dadin shakan shi dakyau. Ke kada fa kiga na kiraki ki nemi tozarta min matata don kin san tafi komai da kike takama don wanan banzan dalilin na Yusuf da yakawo bashi ne zai sa ki samu daman fada min maganan banza ba. Wanan kuma fadi kayi mijin buzuwa don yanzun haka ma nasan tunanen yar asaline ya hana ka shakat sai da ka kirani kaji yaya nake sai dai kana tsoron buzuwar ka nasan ma yanzu haka wani wuri ka samu ka labe kake wanan waya dani. Idiout stupied girl kawai ya fada ya ja tsuki ya kashe wayan yana huci wai may yarinyar nan take takama dashi ne wai zuciyar shi tace kyau ilimi tsabta da fadin gaskiya. Idon shi ya lumshe yana tunane sai kuma ya sake guntun murmshi a yadda yake rigingine a kwace taba kofan da Nafisa keyi yasa shi bude idon yana jin ta har ta soma bugun kofan bai tashi ya bude mata ba sai gyara kwanciyar shi yayi dakyau ya fara adduan barci haka har barcin ya dauke shi yana tunane. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: A zoto na shika dai ne a cikin motar sai da na isa kusa ne naga sabanin haka ashe tare suke da dan baiwa yana zaune kamar kullun ya aza Laptop a cinyar shi yana dubawa. A sanyaye nake nace dasu sannu ku da zuwa yaya hanya yaya mutanen gida kun barsu lafiya ? Yusuf yace ke ce African ta gidi khadija tambaya haka a jere lokaci guda wani zamu fara amsa maki daga cikin wanda kika jero muna a lokaci daya ? Nace amsa daya ya wadata gareni wanda nake fatan alheri a cikin shi yace to duka amsan ki alheri ne don duk Alhamdullahi gaba daya kowa na lafiya kuma hanya lafiya. Murmushi nayi sai yace baki gaisa da oga na ba kuma aboki na dan satan kallon shi nayi nace ai bugu daya nayi maku gaba daya nashi gaisuwan daban ne kuma ? Yace oga ne fa khadija kema kin sani ai dole gaisuwan manya ya zama daban da na saura nace a wurin ka yake daban don kace shi din ogan ka ne amma ni a wuri na duk daya kuke gare ni. Eh to kya iya fadin haka yanzu amma dai nasan nan gaba bazaki fadi hakan ba dariya nayi nace saboda may kana ganin zanyi aiki a karkashin shi ne ko may , ? In wanan kake tunane may zai kai lawya aiki a FCDI kuma sai in dai bukatan haka yataso mu a bukace mu a wurin muyi aikin mu mu bar wurin. A a a ashe da babban lauya muke bamu sani ba haka nace cikin murmushi lawyer to be insha Allah ba ya juya gare shi yace kai kaji ashe da Barister muke bamu sani ba shike nan yanzu muyi abin mu ba kwabo muna da mai kare mu. Nace wa ni ai nice ma zan tsaya sai na kama masu cinye ma gwaunati kudin filayen ta in daure mutum inga tsiyan kwashe kudi ana tura ma yan Niger suna cinyewa dama yan Nigeria kuke ba sai in maku sausaci a kai. Sai lokacin ya dan sake murmushi yace ashe har kin fara hada evendece a kaina ban sani ba nace tun yaushe na fara hadawa zan tura babban kotun mu. Dariya sukayi sosai gaba dayan su yace dama karatun da kike yi ke nan ashe nace kwarai don kama manyan bariyin gwaunati ba. Yace ashe aiki ya ganki magana yake ba tare da ya dago kai ya kalle ni ba sai dakilan laptop da yake yi hankali kwance da gani abin ya zama mai jiki hakan. Yusuf yace wai kin san ban taba sanin abinda kike karantawa bs ke nan sai yanzu na dan natsu nace shi nake karantawa ai Allah ya bada saa yace nace amin nagode. Still bai dago kai ba yace wace zata kama ka kakewa addua haka kuma yace ai addua ya zama dole muyi mata shi fadi take yi kawai mutum ya taba kama kanshi da laifi ne. To wai ni fa kun barni a cikin duhu yakamata ace yanzu ina gida kun tsayar dani a nan aikin oga ne haka khadija bai son ki bar garin nan yanzu ne yasa ya tsayar dake. Kallon shi nayi sai faman aikin shi yake yi hankali a kwance bai dago ya kalle mu ba nace ni ai ba yar Niger bane da yake tarawa a gidan shi kamar almajirai. Dama titi yake bi yana ba mabukata alheri da zai fi samun lada ga Allah da wanan ciyar da mayaudaran dayake yi zai fi mai Alheri sosai. Rufe Laptop yayi tare da fadin wai ke maye matsalan ki da yan Niger ne cikin rashin sani nayi subul da baka nace kishi mana lokaci daya suka ce kishi nace wallahi. Murmushi naga yayi yana lumshe ido Yusuf ko sai kallo na yake yana dariya shi ya bude idon shi yace kishi yana jijiga kai nace na kasata ba . Sun zo suna kwashe muna dukiya suna raya kasan su da sunan aure nan ko barayi ne na zaune Yusuf yace a a kada ki gyara zancen kuma mana khadija yar mama. Nace a in ba kishin kasata ba kishin may zanyi kuma Yusuf yace gashi a gaban ki kishin dai kike yi amma kada ki gyara kice kuma wai kasan ki. Ikon Allah akan may zanyi kishin shi shi mijina ne ko wani nawa ba hadin kifi da kaska ai Yusuf yace waye kifin waye kasa yanzu. Yace itace kaskan mana nine kifin ba ita ta lake min ba kana gani kuwa ido na waro waje nace ni din yace Yes kamar zanyi magana sai kuma na kalle su tare da fadin sai anjiman ku. Ina juyawa da sauri Yusuf yake kirana ban tsaya ba ya fito daga motan ya sha gabana shiko yana ciki sai murmushi yake ba abinda ke mai yawo a rai sai kallaman kishin da nace. Ya samu na tsaya yace ke ko daga wasa zaki mai da abin wani magana nace ina nuna shi bakiji may ya fada min bane yanzu wai ina like mai. Yace ai wasa ne ko shima yasan baki like mai shiyasa ya juye maganan yace ke ce mai like mai yanzun bamu muka zo wuri ki ba wake nan kaskan a cikin mu ? Bude motar yayi ya fito yana mika tare da nufo inda muke tsaye yana fadin wai may kaskan nan take fadi ne haka ka tsaya wani bata magana can. Yusuf yace kin gani ba har ya kai ga fitowa a mota don ki yace ai ita ma ta fito don ni ko, kallon shi nayi na kauda kai na gefe daya. Ya karasa takowa zuwa inda nake yace wai yaushe ne zaki tafi in samu in huta da wanan matsalar taki. Nace nice yar matsalar yace gashi ko kina muns ko yanzu kai na girgiza kawai nace ba komai baka da laifi fito war maryam ya tsayar damu daga maganan . Ta fito tana gaishe tare da masu yaya hanya da mutanen gida yusuf yace suna gaida ku tace kuna nan da miss barister ne yace wallahi kuwa kauna a kwai rigima ai. Tace da kyat na shawo kan ta ta tsaya da yanzu tana gida baku samay ta ba Yusuf yace kin kyauta shi dai tunda ta fito bai mata magana ba ko gaisuwan da tayi bai karba ta ba sai ma daure fuska da ya kara yi yanzu. Yaushe ne zata wuce Yusuf ya tambayi maryam tace bataki ko yanzu wanan ta bar gari ba ta isa da dare da sauri shi yayi magana da fadin No bako a cikin daren nan ba kan gaskiya. Nace may ye a hanya da zaka ce ba da daren nan ba zan isa ko lafiya yace No sai gobe za a zo a kai ki har gida. Nace a a kada ku wahal da kan ku motar kasuwa nake shiga yanzun ma shi zan bi in Allah ya yarda bani kadai ba kowa dake wurin yayi mamakin maganan shi da yace. Ba zan yardan ba ki bi motar haya ke kadai idan wani abu yaje ya samay ki fa a hanya ki sani a wani hali don haka ki shirya gobe zan turo malam sani ya kaiki gida da safe. Ido gaba dayan mu muka tsura mashi da yake maganan kamar wani uba da yar shi ko miji da matar shi yadda ya hakikance yana fada a hasale dani. Zan yi magana Yusuf yace ya gama yanke hukunci akai Allah ya kai mu gobe din ai yau da gobe duk na Allah ne ko amma ki bi motar haya wani abu yaje ya samar mashi ke a hanya kuma ? Maryam ne tayi dariya nikan hararan shi nayi mai dani gida yace a dake Yusuf yace to bissimillah muje in sauke ka ko ya juya ya fara tafiya ba tare da yayi magana ba kuma. Sai Yusuf ne ya tsaya yana ce muna yar mama ni zan tafi ban sani ba ko zamu sake haduwa ga wanan ayi ma kanne tsara ba dashi ya mika ma maryam sai kuma ya sake ciro wasu yana miko min wai na karba. Kai na girgiza mai nace daka barshi don ni ina da kudin mota a hannu na tsaraba kuma ai kowa yasan makaran ta naje basu expecting din tsaraba a wuri na. Yace daga wanan time din sai ki fara masu tsaraba baki san tsaraba ko ga babba yana da muhinmanci ba ne mutuka kauna na. Dole ya mika min na karba tare da mashi godiya har dan Baiwa ya fara mashi horn a mota yace Allah sada mu da alherin sa nace amin yaya Yusuf ya juya ya tafi sai da suka shige muka koma ciki. Maryam bata shigo daki ba don haka ni kadai na shiga na adana kudin tare da cire rigar da nasaka a jikina. Can ta shigo ta hada muna abinda zamu ci ina kwance a wurin tunane ya addabe ni a raina har ta gama tace inzo muci don na idar da sallah a lokaci. Sai da muka zauna cin abincin ne muka fara hira da ita take tuna min maganan shi da yayi dazun tare da fadin guy din ya hadu wallahi Daure fuska nayi nace a naki ganin kike ganin haka amma ni mai zaisa in sawa raina abinda nasan ba mai yuyuwa bane gare ni ai ko a mafalki wallahi. Ko dai baki san ko shi waye bane yasa kike wanan magana haka shima dai Yusuf ai yanayi ne don wasa kawai amma ba gaskiya bane so kima daina wanan zancen don Allah. Wayana dake gefe ne yayi kara ban gani don wayan a silent take lokacin sai maryam ne ta gani take ce kamar kiran ki ake a waya fa sai nayi saurin juya don in duba. Tashi nayi na dauko wayan mai kiranane yaban mamaki tunda basu dade da barin wuri na ba, daukan wayan nayi na kara a kunne na da sallama yace fito gani waje. Da mamaki nabi wayan da kallo muryan shi naji yana fadin kin ji abinda nace nace eh maryam na kalla da ta tsareni da idanuwan ta nace a sanyaya wai shine a waje . Ta kwashe da wanin irin dariya bance da ita kala ba komai ba na zura rigana na fita zuwa jin may ya kawo shi kuma. Ina fita na hango motan shi dan nisa kadan damu na karasa wurin na samu ya fito da kafa daya a waje yana duba abu a cikin motar na iso wurin. Ina wuni ya dan juyo ya kalle ni yace zagaya ki shiga dan jin nayi bai zagaya ba kamar yadda ya umurce ni dayi ya sake dagowa bayan ya rufe cabinet din motar yana fadin baki ba ne dole na zagaya kamar yadda ya umurce ni din dayi. Bayan na shiga naga ya tayar da motar ya bar gurin down hostel din ya halba motan muka hau expresse ba wanda yayi magana a motan sai dai gaba na yana dan fadi don ban san ina muka nufa dashi ba. Mun dan yi nisa da gurin ya juyo ya kalle ni yana fadin maman ki ita kadai ne a gurin mahaifin ki ? Mamakin tambayan nashi nayi sai ban iya bashi amsa ba na kawar da kaina gefe yace ina magana kin kyale ni nace akan may zakai mun wanan tambayan haka. Yace don na isa na tambaya yasa na tambaye ki OK idan kana son sani sai kaje ka gani da idon ka ai. Kan nen ki nawane dariya tambayan ya bani sosai nace yau ni naga ikon Allah to kannen na biyar ne na bashi amsa tare da kawar da kaina. Ok kawai yace mukaci gaba da tafiya sai wani katon Plaza muka tsaya ya juyo yana fadin bissimillah fito mu shiga yace. Ban ki ba na fito muka shiga shagon sai faman gaida shi masu shagon keyi layin kayan sawa muka nufa yana gaba ina bayan shi. Abin ya ban mamaki yadda naga yana jidan kaya a wurin ya ban mamaki ya koma layin kayan yara sai lokacin ya juyo ya tambaye ni shekarun su nawa ne kallon shi nayi nace a kwai sha uku da sha daya sai takwas da shidda mutum biyu. Maza da mata ne ya kara tambaya nace maza uku mata biyu sai yaran yaya na biyu yan she kara takwas da shidda maza. Bayan mun gama wurin takalma muka nufa muka zaba sai layin zanuwa nan ya zaba da dama ya zaba sai ya duba kudi ya gani yake daukan mafi tsada a wurin. Ya sa yaron shagon ya tura yakai yace a samu trolley masu kyau a saka mai kayan a ciki muka bar shagon hanyar down hostel muka nufa sai lokacin hankalina ya kwanta. Bayan ya tsaya da motar nayi kokarin budewa naji ta a rufe gam na juyo na dan kalle shi naga shima ni yake kallo a lokacin sai na kawar da kaina gefe daga kallon shi. Ina son in maki godiya amma kin kasa tsaya ki bani daman yin hakan gare ki nace godiya akan may fa ? Au baki ma san abinda kikayi ba ke nan nace ban sani ba sai ka fada min iska ya dan furzu daga bakin shi yace OK you can go zamuyi waya idan kin isa ki gaida gida na gode kawai nace na fita. Banji yace dauki kayan ko wani abu ba nikan na shige abina ina fadin dan rainin wayo kawai dama sayayya zan rakashi shine yake min tambayan bazan a hanya. Har yasa gaba na faduwa ina zan kai wanan uban kayan danaga ya jida a shagon sai yanzu hankalina ya kwanta. Koda takwas na safe yayi mun gama shirya komai muna zaman jiran su sai na tafi maryam tace zata wuce itama takwas da wani abu ya bugo min yana fafin in fito da kayana ga mota a waje ana jirana. Fitowa nayi da kayan maryam ce mai karasa min su a wurin motar har aka gama na rufo kofana na saka key din a jakka ta mukai sallama tace za a zo yanzu a dauke ta ta buga waya gida itama. Driver ya bude min baya na shiga muka dauki hanyan minna shigan wuri zan ma minna wanan karon ba yadda na saba ba da dare nake shiga garin. Tunda muka kama hanya barci ya dauke don sanyin motar da lafiyar ta sai faman gudu driver ke shararawa dani ina barci na hankali kwance. Barci nayi sosai driver naji ya tsaya a wani gari na bude ido fita naga yayi zuwa gun masu sai da manja da doya a hanya ya saya aka loda mashi a motar muka kama hanya kuma. Tun ina duban waya sai na koma barci abina muryan driver ne ya tayar dani yana fadin hajiya wani unguwa zamu je na bude ido ina kallo har mun isa deport din mai zamu shiga cancaga . Nace a cikin gari kwagila road, zaka kaini yace ban san wurin ba don ni bakon garin ne nace OK mushiga sai in nuna maka. Miko min envelop yayi yace oga yace idan mun iso in baki wanan sako wai sai kin shiga gida ki bude nace OK Mun wuto ina mashi kwatance har kofan gidan mu motar ya tsaya duk da rana ne kowa na zirga zirgan gaban shi nai hana masu zama layin namu zama suna ganin motar ya tsaya kofan mu suka sako ido caa suga waye a motar yazo gidan mu. Driver ya fito ya bude min motar na fito can naji wani classmates dina na primary yana fadin yau Khadija ce a garin namu. Murmushi nayi mai nace Faisal mun samay ku lafiya ya karaso muna gaisawa dashi na shiga yace bari ya taimaka min da saka kaya a gida. Da sallama na shiga inda kanne na dake daki suka fito da gudu taro na suna ihu na rungumay su tsayawa nayi ina kallon kayan da su Fesal ke shigowa dashi gidan namu. Na kasa furta komai mama ma kallon kayan take da mamaki yaran suka fita sai gasu suna shigowa da ba adadi nace wai duk mu muka zo da wanan kayan haka wai ? Mama tace waya zo dashi in ba ke ba bagashi kin ga ana shigo dasu ba tare da kayan ki ko kina nufin baki san da su bane wai ? Wallahi mama ban sani ba sai yanzu nima nake ganin su anan kamar kowa yadda ya gansu mama ta katse nu da cewa motar wa kika shigo ne naji yara na fadin kin zo a mota mai kyau. Shiru nayi na dukar da kaina ba tare da magana ba har suka gama shigo da kayan mama tace ku dauki ruwa kusa a plate kukai ma mai motar kafin ya tafi. Yaran suka ruga da gudu suka dauki ruwan leda suka sa a plate suka fita dashi waje kamar yadda mama tace dasu ta wuce tabar ni tsaye a gurin. Dakina na nufa tare da dan hand bag dina dake rike a hannu na rai na babu dadi ko kadan a tare dani ina fadin yaya wanan mutumin zai min haka ya hadani fada da iyayyena su fara zargina. Anty khadija wai yace a fada maki zai wuce nace ya kice Allah ya kaishi lafiya nace a hasale yaron ya fita da gudu daga dakin zuwa fada mashi. Daddy ya shigo gida yana fadin ance baby na ta dawo sai kuma yaja ya tsaya yana kallon kayan da mamaki dake zube a tsakar gida. Mama tace kai nake jira dama kazo ka gani ko zata fada ma inda kaya ya fito haka don wai ita ma bata sani ba tace kuma su sukazo da kayan. A sanyayye na dago labule dakin na fito ina fadin daddy sannu da dawo wa mun samay ku lafiya ? Lafiya baby na sai dai wanan kayan kuma fa ina suka fito haka nace wallahi daddy ban san da su ba sai da muka iso na gansu. Kamar yaya bakin san dasu ba bake kika zo dasu ba sai nayi kasa da kaina ban yi magana ba kuma kayan yake bi da kallo tiryan tiryan yace ikon Allah. Shiga ciki ki huta zamuyi magana anji yanzu zan tafi inyi sallah ne ya wuce gurin da buta yake yana dauka ni kuma na sake labule na koma ciki jiki a sanyayye. Na fada saman gadon dakin duk da kuran da yake ciki don ba gyara ake ba a kai akai tunda ba kowa a cikin sa ina zaune kamal kanina ya dawo shiya fara shigo min da kaya yana min sannu da zuwa. A dadafe na amsa mai ina kallon akwatinan daya shigo min dasu akwatunan da muka sayo a daren jiya ne dashi inba idona ke min gizo ba. Watau kayan de na yan gidan mu ne kenan ba wasu ya saya wa ba mikewa nayi don in yo alwala ina shiga banda ki sai na samu ai period dina yazo min ba daman inyi sallah ke nan haka na fito jiki a sabule na aje butan. Sai mama ta aiko da abinci a kawo min ban kali abincin ba nace kaunata ta aje min a nan kawai ina jiran dawowan daddy daga wurin sallah. Envelop din da driver yaban na tuna dashi na dauko a cikin jakata na bude a hankali kudine a ciki sabbi ful din su anyi rubutu kamar haka a wrafer farko daddy sai na biyun mama. Na ukun ne bai rubuta komai ba na shiga uku nace tare da yin nadama da haduwa da shi karo na farko a rayuwana don ban san yadda daddy da mama zasu fahince ni ba. Nayi dana sanin tsaya jiran shi da yace inyi har na tsaya din sam ban kawo komai a raina ba irin haka don ban taba zaton hakan ba dayayi min. Muryan daddy daya shigo naji ana gaida shi yasa ni kaduwa bai min magana ba har yaci abincin shi ya fita haka na tashi na gyara dakin tsab na fita da na wankewa na wanke a ranan. Na dawo na sa kamshi a dakin tare da gyara komai a yadda nake bukatan shi a dakin na koma na zauna wayan maryam ne ya shigo tana tambayana yaya muka isa ? Nace wai kin san abinda mutumin nan yayi mun kuwa maryam nan dai na koro mata labarin abinda ya faru bayan isowar mu gida da driver. Tace ikon Allah sakayyan da yai maki ke nan ashe kai lallai mutumin nan yaci sunan sa dan Baiwa ne shi din. Nace ke maryam har kin samu bakin yabashi ko may may kike son in fada ma iyayyena yanzu don Allah wa zance yake gare ni da yai min wanan kyauta haka. Tace ki fada masu gaskiya taimakon shi kikayi ya saka maki da alheri haka nace ban sin su san ko shi waye tundai Ya Amina . Dariya tayi tace komai dadewa ai zata sani ne nace amma fa ba yanzu ba koda zata sani din don ban son ta fasara ni da wata manufa. Har dai dare banji daddy yayi min magana ba haka yasa na dan sake jiki naji shigowan daddy gidan sai na sha jini jikina a daki ban fito yadda na saba muyi hira ba dashi. Ina nan kwance wayana yayi kara na dauka kamar yadda na rubuta a sunan shi dan Baiwa shi ya baiyana a wayan. Kamar ba zan dauka ba dai na daga maimakon inyi magana sai na kama kuka nace may yasa zakai min haka don Allah ? May kake son in fada ma iyayyena yanzu a kan kayan nan yace daddy na gida nace yana nan yace dama shina ke son magana dashi na kira ki yanzu. Da sauri nace may zaka fada ma daddy din yace gaisawa nake son muyi dasu in masu bayanin kayan ba shike nan ba. Yasir na kira nace ya kaiwa daddy waya ana magana dashi ban san yadda sukayi ba a wayan har mama naji suna gaisawa da ita. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Bayan gama wayan mu dashi jikina ne yayi sanyi sosai a kan maganganun da yayi sai naji wani iri ba dadi a raina yadda mutum kamar Abdulsamad yake magana da ni haka acikin mutuunci da girmamawa. Karatun da ban sake komawa gare shi ba ke nan cikin sanyin jiki da tunane barkatai barci ya dauke ni a wurin maryam dai batace dani kala ba a ranan. Washegari bayan munyi sallah asuba zaune nake saman sallaya na nakasa motsawa abubuwa da yawa ne suke min yawo azuciya na. Na dauko kura,ani na fara karatu don ka,idane duk safe sai nayi kafin in fita dakina sai dai idan ina cikin lalura a ranan. Wayana yayi kara ban kula in duba mai kirana ba har sai da nakai karshe sanan na mayar da hankali da wayan da ke neman agaji kuma mai kiran bai fasa kira ba. Yusuf ne ke kirana akai akai haka mamaki naji don bai taba kirana da safe irin haka ba ga kuma kiran dana gani yayi yawa. Yasa nace lafiya wanan kiran haka da safe haka na tambayi kaina kiran ne ya kara shigowa again da sauri na dauka don kada ya kara katsewa a lokacin tare da fadin yaya Yusuf lafiya dai. Naji yace ina kika shiga haka waya nata ringing baki daga ba nace ina zaune karatun kur,ani nake a lokacin yace da kyau yar mama da alama dai ke din babban malama ce hakan na dakyau wallahi. Tambaya shi nayi lafiya kira yau da safe haka yace ina fa lafiya yar mama ta ruda min ogana kuma abokina nima umurni aka bani akan lallai in kiraki in fada maki don Allah kada ki tafi yau ko gobe ki bari mu shigo abuja gobe. Katse shi nayi da fadin yaya Yusuf may zan mashi duk abinda nayi kona fada mai da ya faru wanan haka Allah ya kaddara a kan shi. Sai mu godema Allah da yasa yayi saurin ganewa yasa kuma halin ya dore a gare shi haka kada yayi nadaman mazuru don jiya yakirana wai yana min godiya. Ni abinda na fahinta shine rashin mai fada mashi gaskiya a tare dashi yadda ya dace yasa buzuwar matar shi ta samu galaba a kan shi haka sosai. Yanzun kuma na tunar dashi Alhamdullahi tunda ya fahinci gaskiya har yayi niyar gyarawa da kanshi so ni yar barni don Allah ban son matsala ko wani abinda zai jawo ma karatuna matsala. Dariya naji yayi yace duk mun san da hakan amma ki dan daga muna kafa kijira har mu dawo din please maryam ne ta wafce wayan a hannu na tana fadin insha Allahu zata jira ku dawo yace maryam mun gode da hakan. Bayan ta kashe wayan na kalle ta nace akan may zan tsaya jiran su maryam ki tuna fa na gama abinda ya shigo dani abuja satin nan iyayyena kuma sun san da haka mai zaisa na kara kwana. Wanan ba komai bane mai yuyuwa shima so yake ya saka maki da makan mancin abinda kikai mashi idan ya dawo. Maryam bayi don ya saka min saboda Allah nayi haka tace dole ne tunda yana ganin kin cece shi daga halaka abinda wanan shi bai taba lurar dashi ba. Don Allah kiyi hakkuri har su dawo din gobe ne fa kawai ba wasu kwana masu tsawo zaki kara ba hakan shiru nayi ban nata amasa ba sai dai zuciyana cike yake da tunanen dalilin da yasa yake son in tsaya sai sun dawo garin zan tafi. Khadija godiya ya kamata kiyi ga abinda kikayi ya zama alheri gare shi wurin Allah nace nayi maryam kuma na gode ma Allah da haka ya kasance ta sanadina. Amma maye dalilin shi na son ya tsayar dani wai sai ya dawo zan tafi tunda yasan bashi ke da ikona ba, tace dole akwai dalilin dayasa yace ki dan dakance su din yau da gobe ne fa kawai insha Allahu. San nan kuma nasan dai dalili daya ne kawai don kin cancanci hakan a gare shi yanzu amma mu bari din har yazo muji. Kila kuma dai sai kuma ta kama dariya a hasale nace don Allah dai ki bari karki bata min in ce na fasa tsayawan. Shiru tayi do ganin yanayina daya sauya tasan zan iya abinda na fada din ita kuma bazata so ace na wuce ban jirashi ba. Haka kawai naji kaina yana sarawa raina yamin mugin baci haka yasa na mike daga wurin na koma saman katifa na, na kwanta ina ci gaba da tunane a raina. Wayan aminiyar ta takira cikin tashin hankali take mata bayani tana kuka wai samad din ta yana son juya mata baya a lokaci daya . Don ma idon ta naga ala,amarin shi ne yasa tayi saurin ganewa da wuri ta kare da cewa na shiga uku madam tawa ta samay ne wallahi idan Samad ya fara neman mata ni yaya zanyi. Tace haba ki kwantar da hankalin ki tunda akwai mafita zamu iya kaishi wurin mai rafanne yasan yadda ya lankwasa muna shi ko uwar shi indai mace ce ya dinga jin ko ganin ta kamar jaba. Ke dai kada ki nuna mai kin fahince shi lankwasa shi zamu a cikin ruwan sanyi batare da wani hayaniya ba. Wa ni tun yaushe nagama buda mai wuta wai fa satin nan har kaduna ya shiga ba tare da sani ba kinga ke nan abubuwan sun lalace don samad bai taba shawaran zuwa gida batare dani nabashi shawaran ya tafi ba ko shi sai idan ina da abinyi acan. Don haka nayi mai kaca kaca kafin yatafi wai ma kin san may wanan zuwan don ki san komai ya fara lalacewa har sayayya yayi masu da zai tafi abinda ban taba gani ba tun zuwa na gidan nan. Madam tace matsalan ki ke nan Nafisa baki da kwanciyan hankali idan abu yazo maki abishi a sannu sai kinyi hargowan nan naki da kika saba ko yaushe. Don haka yanzu ki kwanta kamar komai bai faru ba yadda muka saba ta haka zamu fito mashi mu kara kaifin aikin mu a kansa don ba zamuyi sanyi muna kallo Samad ya kubuce muna ba don muna samu a wurin shi sosai. Don haka ki kwantar da hankalin ki zan shigo gidan naki sai mu tsara yadda zamu shawo kan ala,amarin tace da ita Madam hankalina baya kwanci don natsani in bude ido inga samad yana mu,amula koda na aiki ko na yan uwantaka da wata mace a duniyan nan musan man matan hausawa yan uwanshi. Kada ki damu madam tace da ita zanzo gobe sai muyi magana a tsanake amma fa sai kin kwantar da hankalin ki . Ajiyan zuciya ta sauke tana fadin zanyi kokari hakan suna gama waya ta sake kiran wata wai hajiya Auta da ke mata shige shige a kaduna. Itama bayani tayi mata na halinda take ciki tace kada ta damu gobe zata je mata zaria wurin malamin da take zuwa tayi mashi bayanin halinda take ciki. Daga nan kuma gida Niger ta kira tayi ma yar ta wace ke mata shige shige acan bayanin halin da take fuskanta daga Abdulsamad din yanzu tace kada ta damu za,a yi komai yadda ya dace. Sai lokacin hankalinta ya kwanta don tana ganin kamar har anyi aikin mako don ta yi believe da aikin bokaya da malamanta sosai. Shawaran da madam ta bata take so ta fara aiwatarwa indan ya dawo daga kadunan inda take sa ran dawowan shi yau din don tasan ba zai wuce kwana daya ba can tunda ba tare suka tafi ba. Nikan nace Abdulsamad da sauran mazan dake cikin irin halin nan sun shiga uku ga matan su ruwan sha surukule abinci ma haka wurin kwanciya ma hakane Allah ya tsare ya kare ya shirya zukantan mu. Baidawo ba ranan kamar yadda tayi tsamani abinda ya kara tayar mata da hankali ke nan ta kwana a cikin tashin hankali da damuwa. Yana gurfane a gaban hajiya mama yana mata sallama zasu tafi inda take zaune akan kujera falon ta . Akwai wani nauyi da kawaici dake tsakanin shi da mahaifiyar tashi tun farko kansancewar shi dan fari a gurin ta ba wani sakewa ko shakuwa mai yawa a tsakanin su tun farko don kawaici. Ya dubeta sanan ya sunkuyar da kanshi tare da fadin hajiya mu zamu koma ke nan ta dan dubeshi ta kawar da kai gefe tace. Allah ya kai lafiya mun gode da hindiman da akaimu Allah ya karams dukiya albarka cikin sauri suke hada baki da Yusuf wurin cewa amin hajiya mungode. Sai dai kuma rufe bakin su yayi daidai da cewan ta yaya zancen iyali ka kuma har yanzu bamuji shawaran da ka yanke a kai ba kai suka dukar kasa gaba dayan su don basu zaci hajiya zata kawo wanan zancen ba a yanzu. Taci gaba da fadin babangida kayiwa yarinyar nan adalci da diyan ka don ko sune ne jigon ka watarana kana ganin wanan abinda ka dauko na tallaban wata wace ko haihuwa bakuyi da ita ba zai haifa maka da mai ido gobe. Yaran nan fa girma suke yi yanzu idan har suka san abinda kake yi ma uwar su kana ganin abin ba zai shafe ruwan ka ba wataran. Yusuf ne ya kawar da shirun dakin bayan hajiya ta gama magana yace hajiya a dan bamu lokaci kadan don Allah akwai shirin da muke yi komai zai zama daidai bada dadewa ba da yardan Allah. Sai dai a taya mu da addua da rokon Allah wanda shi muke bukata gare ku yanzu amma nan gaba kowa zai dara in Allah ya yarda. Allah ya yarda tace dashi bata kara magana ba suka mike suna fadin zasu tafi ta bisu da addua wanda yasa zuciyar shi jin kamar an gafarta mashi a lokacin. Abinda ya dade bai samu ba daga gare ta idan yazo da fada sukan rabu a gidan rayuka sukan baci sosai. Tunda suka kama hanya ba wanda ya iya magana a cikin su kowa da abinda yake tunane aranshi saida sukai nisa Yusuf yace wanan abin yayi min dadi matuka. Yau hajiya ta rakamu da addua tare da fatan alheri a gare mu abinda ta dade batai muna fatan alheri da sakin fuskan da muka samu gareta ba irin yau. Murmushi yayi tare da kwantar da kan shi saman widow motar yana lumshe idon shi cikin jin wani irin yanayi a jikin shi. Har suka iso Abuja kamar bai cikin motar gida ya wuce dashi direct inda ya samu gidan kamar yadda ya barshi Nafisa ce da yan uwanta suke yadda suke so su kadai a gidan babu kowa nashi a ciki. Bayan sun gaisa ne ya haura zuwa sama dakin shi ya fara rage kayan jikin shi don ya dan watsa ruwa ya kwanta ya dauki lokaci a bayin kafin ya fito ya fara saka wasu kaya masu sauki a jikin shi don ya sha iska. Yana saka kayan Nafisa ta shigo dakin bako sallama tana cewa kun dawo ashe yadan juyo ya kalleta ya mayar da hankali ga abinda yake yi din. Ba laifi yau ta sa kaya masu dan kyau a jikin ta da alama kila tafita ne ko zata fita din don idan ba fita zatayi ba ita kwalliya bai damay ta ba haka take zama a gida ga kaya nan kamar ya kashe ta kuma bata kyauta wasan dadi. Cike da sallo ta karaso gare shi ta amshi dan tawul din da yake tsane jiki dashi tana goge mai kai tare da fadin kaje gida hankalin ka ya kwanta ke nan ? Bai mata magana ba haka kuma bai saki fuskan shi ba har lokacin tace nayi mamakin zuwan ka gida a wanan lokacin bayan ba haka muka saba zuwa ba. Yace banda daman zuwa ganin mahaifana sai mun tsara dake ko may ba haka nake nufi ba gani nayi ya kamata ace nasan da zuwan ka tun wuri ai. Sai da ya soma tafiya yace yanzu na canza sallon tafiya ne ba dole bane sai naje dake indan zan tafi don kema idan zaki gida ba binki nakeyi ba ai. Cikin yanayi mamaki tasha gaban shi tace may kake nufi da fadin ka canza tsarin ka yanzu yace komai ma don na fahinci baki kaunar yan uwana yanzu da ci gabana. Na fahinci sakin fuskan da nake maki ne ya jawo min abubuwa da dama daga gare ki na koma nine mata kece miji a yanzu gidan nan. Don zan tafi wurin iyayyena har kike tayar da jijiyoyin wuya wai jayi masu sayayya ke nawa nake baki idan tafiya gida ya kama ki. Kuka ta sa mashi wai yayi mata gori kan abinda yake mata ita da iyayyen ta kallon ta kawai yayi ya fara kakabe gadon shi inda yake son ya kwanta cikin kuna rai. Ta dawo bakin gadon bayan ya gama kakabewa ya kwanta ta zauna a bakin gadon tashi gaba tana kukan munafunci. Sai da kukan ya ishe ne ya juyo gare ta yana fadin kukan ya isheni hakana in zaki gyara ki gyara dan gaba tace haba Samad may kake nufi da maganan da ka fada min. Kana nufin ina hanaka yiwa yan uwanka alheri ke nan yace baki hanawa kikayi bakin ciki ga abinda zan dan kai masu a gaban kowa. Tace kowa su wa baidai Yusuf bane gurin da sauran drivobin ka yace su ba mutane bane komai tace to kayi hakkuri haka ba zai sake faruwa ba insha Allahu. Nasan ban kyauta raina ne ya baci a lokacin bayin kaina bane ka sani son kane ya rufe min zuciya na. Yadan dubeta yace don kina sona sai ki hanani yima iyayyena da iyalina alheri ko may kai min afuwa ba zan sake ba tana fitar da hawaye gwanin ban tausayi. Nace naji ya wuce kuma kada ki sake yi min haka don ranki zai baci dani idan kin sake ina son in kwanta in huta ne haka yasa ta mike ta fita jiki a sabule da ita. Mamaki take a zuciyar ta yau ita Samad ke da bakin fada mata haka da bakin shi babu shayi ko tsoron da yake gwada mata. Tace zaka san koni waye idan na kulleka a wuri daya a karkshin ikona ba yan uwanka ba har iyayyenka da iyalin ka sai abinda nace maka a kan su. Kwantawa yayi don ya huta amma ya kasa samun sukuni a lokacin saboda damuwa dayayi mashi yawa ga tunanen zuwa ya duba khadija ya damay shi ga kuma Nafisa da ta fita tana kuka yanzu a dakin. Mun gama exam na dawo hostel tun jiya da na shigo ba fita ko kofan gida ba ina jin ya gidan nata parkin suna fita daya bayan daya a gidan. Kwaciya na gyara ina jan tsoki haka kawai an tsayar dani don wani bukatan da ban sani ba an bata min lokaci na ga banza. Da yanzu ina gida don tun da yamman jiya naso wucewa tunda ba wanj mugun nisa ke ga Abuja zuwa minna ba ko goma na dare zan iya tafiya gida idan na so. Wayana yayi tsuwa ban yi saurin dagawa ba sai da na lalabo na dauka naga ya Aminace take kirana a lokacin . Dauka nayi ina mata sallama bayan mun gaisa da ita ne take tambaya na kama hanya karya nayi mata nace ban gama ba sai gobe zan gama sai in tafi tace Allah ya kaimu. Na tambaye ta ina su boy yaron ta tace sun shiga wurin mommy ta aike su can. Nace ke dai da mommy sai Allah anty tace suna da kirkine mutanen akwaisu da so jamma,a sosai wallahi. Dan murmushi nayi kawai tace ah ai na manta in fada maki mutumin ki fa yazo gida ya kawo wa iyayyen shi da matar shi alheri da yan uwa kowa yana ta mamakin sauyi da aka gani a gare shi. Nace ah haba dai don Allah tace wallahi baki ga irin alherin da ya kawo masu bane khadija nima da na shiga gidan mommy take nuna min . Nace shidai ya sani ai kila buzuwan matar shi ta barshi ya kawo masu ne tace bai ma zo da ita ba ai shika dai yazo wanan karon. Nace kila shiyasa ya samu kawo masu alheri tace waya sani khadija Allah dai ya kyau ni ba kishiya nake gudu ba irin wa yan nan matan dake juye kan miji a lokaci daya ka rasa gane kan mijinka ne abin tsoro ai. Nace da sauri No no ya Amina don Allah kada ki hada yaya da wanan mutumin don ba halin su daya ba ma tace saboda may shima ba namiji bane irin sa nace na fada maki ba daya suke ba ya Amina. Tace Allah ya sauwaka nace amin tare da kawar da zancen nace idan naje gida may zance ma daddy tace nima ai zanzo kafin ku koma school idan anty hauwa ta haifu. Don ina ganin tun last month ake sa ran haihuwan ta gata ta wuce lokacin ta nace ashe cikin ya tsufa haka ne muna gida zata haihu ke nan tace insha Allahu. Mun gama waya mun kashe na ci gaba da tunanen hiran mu da ya Amina din murmushi nayi nace baki san komai ba yar uwa. Zaki sha mamaki idan kin san nice mai shirya wanan plain din haka murmushi na dan sake nace ashe nima shu,umar kaina ne ban sani ba. Kiran Yusuf ne ya shigo min yana tambayan ina ina nace hostel a takaice yace akwai mutane ne nace akwai su amma kadan yace gashi nan zuwa yanzu sai kazo nace dashi ya kashe wayan. Maryam ta dawo daga wurin gyaran kai ta samay ni akwace take fadin ai na dauka barci kike yi nace na fara ya Amina ta tayar dani ga waya. Nan nake bata labari hiran ya Amina dani tayi dariya tana bude tukuyan abincin mu tace bata san ke ce mai director ba yanzu na zuciyar shi. Da sauri nace zuciyar shi fa kikace tace uhumm wai ke baki sani ba idan baso a tsakanin ku kina nufin zai ko kalle ki ne ma. Shiru nayi ban bata amsa ba sai da ta zauna nace wai ke da tunanen ki ke nan akai mu tace bani ba kowa ma saboda kun dace dashi. Nace baki ji ba ke nan don babu ta ida muka dace dashi wallahi ni ina ni ina wanan miskilin mara dariya da fara,a. Zaiyi dariya wata rana sai kinyi mamaki zakice nace maki watarana amma fa idan kinyi nasaran canza shi din don kan ki ne zaki taimaka ba wani ba. Nace a a gyara maganan ki dai maryam don ba gaskiya zuciyar ki take fada maki ba tayi murmushi ta soma cin abincin ta. Yusuf ya kirani yace fito gani a waje ban bata lokaci ba na mike saboda na matsu inji abinda yasa suka tsayar dani garin har wanan lokaci. Dan simple makeup nayi na fito a can nesa da mu na hango motar su a fake na karasa inda yake da sallama na gareshi. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Agidan su kuma Nafisa ne ke waya da kawar ta da ta baro kaduna wace suke kira da madam a cikin su tantiriyace ta kwarai na fada. Da mijin ta sai dai kamar itace mijin ba mata ba don sai yadda tayi da mijin a gidan idan tace kada ya zauna bai isa ya zauna ba. Atakaice dai ya zama mijin tace ga madam ko kawayen nata zasu iya aiken shi ya tafi komai nisan wuri koda da kafane sai yatafi yadawo. Itace Nafisa ta kira tana son fada mata abinda ya faru da ita bayan barin su kaduna ta dauko wayan ta madam ta soma nema a wayan sai dai wayan nata ringing ba a daga wayan ba takaici ne ya kama Nafisa. Ta ja tsaki ta na fadin yar iskan ko gidan uban wa ta shiga waya nata ringing haka bata dauka ba har ya katse bata dauka ba kin sake kiran layin tayi a lokacin sai taci gaba da tunanen ta tanayi tana kada kafan ta daya dake har de. Babu abin da take tunawa sai irin shirmay da ta tafka jiya din akan bakin kishin dake damun zuciyar ta akan mijin ta wanda take mashi son daba taba yi ma wani abu ba sai dai kuma a kasan zuciyar ta ba so bane can na har abandan don da zai iya shiga wani halin jarabtan rayuwa a yanzu tsaba zata iya gudun shi ta koma wa mai maski. Wayan nata aka kira ya hanata karasa muna jin birnin zuciyar sai ta dan sake guntun murmushi tana daukan wayan nata tare da fadin Aloh ina kika shiga nake ta kiranki baki daga waya ba. Cikin muryan barci madam din tace tana hamma baki hangale bata fasa magana duk da tana hamman tace wallahi barci nakeyi tunda rana. Tsuki Nafisa taja tare da fadin barci sai kace wata mai ciki ko kasa ni don Allah watseke fuskan ki kiji ni magana nake son muyi dake ki ban shawara. Madam tace ina jin ki matar manya dadi Nafisa take ji idan su madam na fada mata wanan sunan madam din ne tace ke nake sauraro fa. Wallahi ke dai madam kin san ko sai da munafukar tsohonwan nan ta hadamu da yarinyar da nake fada maku tace mu rage mata hanya ? Don Allah ki bari madam ta fada itako tace sosai kuwa ai saida muka dauke ta a mota daya mukai tafiyan. Tace yaya kika bari haka ya faru don Allah kin ko san iein mijin ki neman su mata keyi ido a rufe nasha fada maki ki nisanta shi daga ko wace mace in ba muraharamin sa bace har kika yarda hakan yafaru dake. Ke dai bari madam nanu mashi rashin yarda na ga hakan amma ya rufe ido yace shi yace umurnin mahaifiyar shi ce dole ya bi. Madam tace yaya kukayi a motar injin baki basu daman sakewa da juna ba a motan ? Tace ai in fada maki ban yarda ko daga kai yayi ya kalle ta ba kuma nima ban sake ayi hakan ba sai dai mun kwashi rikici dashi sosai da muka iso gida wai zai tafi office a sauke shi sai a wuce da ita. Bude mashi wuta nayi sosai in fada maki sai da mukayi kaca kaca dashi na kuma hana shi fita sai da aka kaita a ka dawo san nan ya tafi. Da haushi da bakin ciki ya kamani duk na farfasa kayan falon nan gaba daya don in nuna mashi bacin raina don gobe kada ya kara min haka. Madam tace kash aike kinji matsalan ki ke da zaki bishi da lalama ki nuna mai ba wata mace sai ke a duniya daga baya sai mu sake shirya wa tace. Madam idona ya rufe a lokacin da kishin ganin wanan yarinyar a kusa dashi amma da ya fahintar dani shi irin su ba su gaban shi shi yanzu wace mace zai kalla ta bashi sha,awa sai naji hankalina ya dan kwanta a lokacin. Madam tace amma kin so ki bada mu wallahi kai kin ma dai kwafasa wallahi yanzu ke ko irin matan abujan nan ya lalubu maki har ki ta da hankalin ki haka mudake da wuka a hannun mu nama kawai muke jira. Kawai yanzu idan ya dawo kije ki bashi hakkuri akan abinda kikai mai din don kada ya zarge wani abu a gare ki. Kin ga zaki ji a bakin shi ko ita wanan yarinyar wacece a garesu kin dai san yadda zaki bugi cikin shi ai muji komai a saukake. Tace zanyi kamar yadda kika ce din amma ba yanzu ba zan dai saka ido in gani idan suna tare ko basu tare sai musan abinda zamuyi daga baya. Sun dauki lokaci suna maganan akaina ana ta kulla sheri da tugu akan mazajen su kafin suyi sallama madam tace zata kira zuwa gobe taji indan da wani matsala kuma. Na gama shiga da komai daki na da taimakon wata yar gidan namu da ta dawo tagan ni da kaya ta tsaya taimaka min. Kayan jikina na fara cirewa san nan na fara gyara kayan ina aje komai a inda nake bukatan shi na gama na zauna ina tunane a raina. Bakomai nake tunane ba sai mijin buzuwa da Allah ya jefo a rayuwana a dan lokaci ya taimaka min yau gani da kudi a hannu na wanda yakai dubu dari ta dalilin mijin buxuwa da iyayyen shi duk na samay su. Waya na dako a cikin handbag dina ina neman layin ya Amina don in fada mata abinda ya faru don komai ya faru dama nakan kirata in fada mata. Kira uku ta daga wayan ina ji bata kusa da wayan ne a lokacin mun gaisa nake tambayan yaranta tace suna lafiya sun tafi islamiya. Nace anty kin san wani abu da ya faru yau tace ina zan sani Khady nidake kaduna zaune kina abuja ke. Nace anty yau na hadu da mijin buzuwa danaje sayayya tace kun sake haduwa kuma again nace wallahi anty wai duk wanan uban kayan da na sawo nazo biya sai ake ce min ai ya biya bayan da suka sauke ni ranan ya ba driver dubu hamsim ya bani. Kai da gaske khadija nace wallahi anty kuma su suka kaini gida sai dai shi bai so su dauke ni ba sai abukin shi ne yace saboda mama ne suke min haka. Dariya tayi tace to Allah ya saka da alheri ki dai bi a hankali inda duk kuka hadu don buzuwan nan ba imani ke gare ta tana iya komai akan mijin ta. Ya Amina ni inama zan kara ganin shi kuma Allah dai ya tsaga rabona daga Aljihun shi wanan karon mutumin da ko yaushe take a cikin hade fuska banda gaisuwa may zai hada ni dashi kuma. Daga haka muka kawar da zancen shi muka dauko na iyayyen take fada min cewa sunyi waya da baba yana fada mata kudin su na ritaya ya kusa fitowa kwanan nan. Ihun jin dadi nayi don murnan iyayyen mu zasu fita acikin hali talaucin da suka shiga na ritayan da mahaifin namu yayi muke cikin halin kaka nakayi. Tace ai zan riga ki ji idan kudin sun sauka don haka sai abinda kika samu daga baya nace ai ni indai daddy zai samu bukata na ya biya ke nan. Yanzun ma shawara nakeyi inje banki gobe in tura mai kudin da mijin buzuwa ya bani don akwai kudaden da zasu isheni a hannu na tunda ina da abinci waddatace . Tace haka akeso mutum idan ya samu ya tuna da iyayyen shi dama dako kin kyauta wallahi dama sallaman ki ya hanani tura mashi kudi wanan watan. Haka dai mukai ta hira da ita daga karshe mukayi sallama na kashe wayan tare da mikewa na jona electric dina don in dafa dan abinda zanci da dare. Kira, a na saka a wayana ina aiki ina bin kira a don ni gwanace a wurin iya hadda tun ina yar shekara sha hudu na sauke alkurani mai girma na sake maimaitawa yakai kashi uku yanzu don duk wanda yasan yaran minna ya sansu da ibada da kamun kai ga girmama na gaba dasu a duk inda suke. Da wanan halin namu nake shiga ran mutane farat daya kowa tsakani na dashi gaisuwa ne na mutunci da sani girman wanda ya girmay mun. Na gama na zuba a plate na dauko ledan ruwa guda cikin wanda na sayo na aje a dakin na zauna don in fara cin abincin sai ga kiran waya ya shigo min. Binta ce ta kirani a lokacin na dauka kafin wayan ya tsunke hiran mukayi sosai ranan da ita har nake mamakin ko nawa ta sa awayan ta haka don da mun sake wanan hiran take dauko min wani. Har take fada min yadda akayi ranan da zamu wuto da buzuwar yayan su tace bazata shiga mota dani ba mama ta dage daya zo mata da maganan kan lalai sai sun tafi dani. Nace kin ko ga tunda muka kama hanya batai min magana ba nima ban masu ba daga ita har mijin ta. Tace wanan ai dama shi miskili ne magana kamar aiki yake ganin sa a gare shi zai iya zama da kai kuyi awa daya baice uffan ba haka kuma matar shi anty fati itama take shiru shiru bata magana. Nace aiyanzu sun samu mai magana a tsakanin su haka yasa ta samu daman musguna mata yadda take so ai. Tace ke kin ko san halin wanan matar shu,uma ce wallahi ta karshi da farko da tazo boye halin ta tayi kamar wata mutumiyar kwarai da ita. Sai daga bayane ta fitar da kalar ta kowa ya sani bata kaunan ko dan uwan yaya ta ganshi a gidan nan wallahi. Nace wuri ta samu wallahi ni kar nake kallon ta don banga abin tsoro ba anan ku dai na fahince ku kuna bata girma ne don mijin ta yana da hali a cikin ku. Tace ga tsiya nace eh mana haka din ne amma in bashi ba ta yaya zaku zauna wanan matar ta dinga raina maku hakali har tace wai idan tana wuri kada ayi dariya . Tace ina ma kika sani khadija ai sai wani lokaci da mukaje hutu wurin su a abuja ba girma muka dawo gida kwanan mu biyar ko sati bamu kai ba matsi yai muna yawa a gidan. Muka matsa ma yaya zamu dawo ga yan uwanta nan muna ganin yadda take ji dasu amma mu ko falo ta hana mu fito muka koma kamar wasu bare ba yan uwan maigidan ba. Dariya nake mata sosai tace Allah ko magana mai karfi wai ba ai mata a gida tace ba kallo ba komai sai zagi da hattara ga anty Fati damu da ita duk muka koma daya. Bayan mun dawo sai ga anty Fati ma ta dawo wai a kaduna zata zauna bata iya zama da buzuwa a abuja bata bari ko miji ta gani idan yana gida. Nace ke ki bari don Allah ashe ba karamar shuuma bace tace baki santa bane Khady wanan fa ko kashe mutu tana iyawa fa. Nace wanda Allah yabata ikon kashewa ba wani kan ai yafi karfin ta wallahi ba abinda zata iya wanda Allah bai tashi yi da bawan shi ba. Ni don Allah har kin ban haushi da wanan maganan naki don ba a gidan ku nake ba wallahi da taga tsiya a guri na nifa irin matan barikin nan haushi irin su nake ji. Zako kiji nata don bata da hali mai kyau ko kadan akan mijin ta zata iya yiwa mutum komai musan man ma ce ko waya tayi da wata ranan sai sunyi jidali sosai da ita ke ta zama mai kaya ko shi yanzu bai da yadda zaiyi da ita ne kawai wallahi. Nace ya dai ga dama ne Binta idan ka ganshi ga mutum har mutum amma baida kuzari gun mace tir yayan ku ya zama mijin hajiya wallahi. Haushin abinda na fadi taji da fada muka karasa wayan a rana na kashe ina mata dariyan shakiyanci na gama na wanke kayan na samu wuri na kwanta. Washe gari da wuri na fita don ban yarda in makara in ba wani dalili ya tsayar dani ba mai karfi shi kadai zai sani makara kawai. Ban da yawan kawaye sai mutum biyu yan department din mu kosu shirin mu dasu don sun ga nafisu kawo wuta sosai a class din shine likewan su dani. Banda wasa ga abinda ya kaini abujan daga school sai gidan mu sai ko idan wani dalili zai sa na fita a ranan zan fita. Yau ya dawo a gajiye don daga wurin aiki ya wuce wuri wasan polo da suke yi don dan wasan ni ne sosai wanda yana daya daga cikin abinda ke kawo mashi kudi a lokacin bai dogara ga aikin shi ba yana buga buga irin na maza gida da waje shike sa yana samun mahaukacin kudin da yake riko. Wanka yayi yana saka kaya a jikin shi ta shigo dakin dan juyawa yayi ya kalle ta ya kawar da kan shi yaci gaba da abinda yake yi. Karaso wa tayi gare shi tana wani rangaji na daukan hankalin shi ta sake abinda yake so ya sauko mata har mazaunan ta. Cike da sallo ta iso gare shi sai dai tsiyan shi da ita duk gayun ta bata damu da saka kamshi ba kuma har yanzu ba gwanewa tayi ba da iya kwalliya shine ma yake kokarin wurin gyara mata idan tayi wani kwaliyan zasu fita. Gata da son karya sai dai ko bokon kasar su bata samu ba kuma babu na Allah a tare da ita abin ya taru yai mata yawa amma hakan bai hana shi son abin shi ba. Rungumoshi tayi ta bayan shi ya sauke wani ajiyan zuciya yana dan murmushin jin dadin ganin ta tace yau ina ka shige haka ne ta dawo ta gaban shi suna fuskantar juna. Bai ce komai ba yadan jajeyeta ya dauko turare yana fesa ma jikin shi tace har da daren ma sai an feshe jiki da turare ko fita zakayi ne haka ? Sai lokacin yayi magana yace sai zan fita ne zan saka kamshi a jiki na ke baki son kamshine ashe yasa baki sakawa . Taji zafin maganan amma ta daure don in da sabo ta saba da gorin saka kamshin da yake mata din ko yaushe kuma hakan bai sa ta saba da sakawa ba. Tace muje kaci abinci yace na koshi ta dubeshi da sauri tace tare da fadin ban gane ba yace mun ci abinci da Yusuf kafin in dawo. Juyawa yayi ya nufi saman gadon su yana jawo laptop din shi tasan idan ya fara dakilan laptop sai ranta ya baci kafin ya gama. Idan tayi magana kuma yace business yake a ciki shi ko wani abin dariya tayi ya dago yana duban ta na lafiyan ki kalau kuwa ? Sai yaji tace maganan turaren da kayi ne dai yaban dariya har na tuna da yarinyar da mama ta saka mu dauko ranan. Bakaji wani irin kamshi tiraren da takeyi ba kamar tayi wanka dashi yace tasan kan ta ne yasa ta saka turaren haka don kada a raina ta. Tace shi saka turare kuma har wani sanin kai ne dashi wai ma may ye alakan ta da mama ne data nace sai mu dauko ta wai ? Yana bude laptop din yace sai yanzu kike son jin halakan su da mama da kishi ya rufe maki ido baki tsaya tambayan ta ba da farko. Tace kayi hakkuri cikin yanayin tausasa harshe tace nasan ban kyauta ba kishin ganin ka kusa da wata mace nakeyi tundai irin wanan yarinyar dake cikin ganuwan kurciyan ta ga kyau kuma da gani tana kuri da ilimin ta. Ina tsoron ka hango kyawon tane wallahi kazo kace zaka dauko min ita a gidan nan wata rana son ka nake har karshen zuciya ta ka sani. Ya tsaya yana mata wani irin kallo yace don kina kishina sai ki min hauka mata nawa nake gani a rana da ina raayin mata ne zaki san lokacin da zan nemay su ne. Har kina fada min cewa mahaifiya ta da biyu ta hadamu tafiya da yarinyar don in so ta kika haukace har kina fashe fashe a gida. Kwantowa tayi a jikin shi ta dan shafi kan shi tace kai min afuwa don Allah haka ba zai sake faruwa ba a tsakanin mu. Yaji hakkurin da ta bashi har cikin ranshi yace ki rage kishin nan nake don ni din mijin mace hudu ne watarana. Da sauri ta rufe mai baki tana fadin don Allah ka daina fadin haka don kana sa zuciya ta tana bugawa da wanan zancen kishiyar da kake min. Yace idan lokaci yayi ai yi zanyi sai dai ki tausasa zuciyar nan naki bakiga mahaifina matan shi hudu ba kin sani ko in gado shi nima ? Kuka ta soma mashi tana fitar da hawayen munafunci a idon ta dariya yayi mata yace akan kishiya kike wanan kukan haka fati fa ba kishiyar ki bace kin ga ai ko yanzu kina da ita ke nan. A bar maganan Fati tace don ni kaina ma kunya nakeji ace wai ita din kishiya ta ce balle kai ace matar ka ce Fati ta sunna. Ohh kin fison indan zai ne ma yanzu in nemo wace idon ta ya bude sosai don itace ta dace dani tace ba haka nake nufi ba don Allah mu bar zancen kishiyan nan haka na. Tambayan ka nayi cewa wacece wanan yarinyar ne sai ka dauko min wani dogon zance kuma akan kishiya ? Yace nima ban san ta ba a gurin mama wanan zuwan da nayi na fara gani ta koma waye dai ita nasan alakar ta da mama mai muhinmaci ne sosai. Shiru tayi tana nazarin maganan shi daga karshe dai data ga ya fara aikin shi ta kwanta tana ci gaba da tunane kala kala a zuciyar ta. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Maryam kamar jirana take in gama debe kayan a jikina ina zama tace amma friend zurinfin cikin ki yayi maki yawa wallahi. Ashe wanan guy din da ake nema ruwa a jallo dan uwan ki ne ban sani ba saurin kallon Maryam nayi nace ruwa a jallo ake nemas may yayi. Tace tsadan ganin gare shi mana gashi dai matashi ne amma Allah ya kai shi ga babban matsayi nace wani matsayi ne gare shi wanda kike zuzutawa haka wai ? Kai haba friend zakice baki san koshi waye ba kina tare dashi haka mutumin nan fa na hango tsatsan son ki a kwayar idon shi. Nace baki hango gaskiya ba idon ki bai hango maki gaskiyan alamarin ba kuma koda kin hango ma bai taba zama gaskiyan magana. Mutumin da gidan shi yafi karfin shi a karskashin mulkin ki mace yake wanda baida mutucin duban yan uwan shi tunda na fara magana ta kafe ni da idanuwan ta. Shiru nayi don na farga na fara sakin layi dariya tayi tace min kin dakata kuma mana nace barni da abin haushi don Allah kwantawa nayi rigingine ina tune a raina sai kuma na bushe da dariya ni kadai. Kallo na tayi tana mamakin abinda nakewa dariya haka ni kadai nace yau akwai bura uba a gida Samad tace akan may kuma nace ke dai bari. Buzuwar matarshi ta bugo waya tana tambayan shi na dauki wayan nace mata gashi nan wuri na baida lafiya. Ido ta zaro waje tace kika amsa kiran matar tashi khadija nace kwarai kuwa ina dariya nace zata gane shayi ruwa ne maryam. Ba gani take ta mallake shi ba ba macen da ta isa tazo kusa da shi hatta uwar shi ta raba shi dasu duk yan uwa ganin su take muggaine bata yarda dasu ba. Kirikiri ta hana matar shi zama a dakin ta dole yanzu saida ta koma gida take zaune ba ruwan shi da yaran da ya haifa da cikin shi. Tace khadija kina nufin wanan guy din yana da iyali haka dama idan ka ganshi sai ka dauka ko auren farko baiyi ba a rayuwan shi. Nace wa mai iyali ne da kike ganin shi wurin nan auren gata ya samu ga iyayyen su shine kuma bai iya riko ba saboda buzuwar matar shi. Nace Wasa farin girki yanzu muka fara wasan da ita sai na manna mata karamin hauka a zuciyar ta tunda tace bata son hurdan shi da ko wace mace. Haduwa goma zamuyi dashi sako goma zan tura mata muje zuwa indai nice ko wace mace da dabaranta ake haihuwan ta sai dai na wata yafi na wata kissan. Khadija kin ko san kisan macen buzuwa macen buzuwa fa duk inda take shu,uma ce bata bari miji ya zauna da matar shi lafiya sai ita. Nace maryam kin san ko matan minna ko waye su ba buzuwa ba ko tsakiyan matan maradi za a kaini na shirya mata indai akwai ayar Allah. Zan bi dare in bi rana sai na nuna mata muma matan Nigeria akwai shu,umai cikin mu ai banda matsala tunda na san lagonta ta . Allah ya bamu saa tace nace amin sai na girgiza kai nace bawai da manufar yaso ni har cikin ranshi nake wanan abin ba yi dai nake in nuna mata boka da malam karya ne. Tace yanzu yaya kuka kare dashi nace korata yayi daga motar shi kai tsaye dariya ta kwashe dashi tace ai ba zaki kara ganin shi ba ko. Nace gobe ma yayi nesa ki gan shi nan ai ni abin har mamaki nake ji wallahi tace don dai kince buzuwa ce matar shi amma da sai in ce wani namiji zai samay ki ya bari ki kufce mashi khadija. Kyau Allah ya baki tsayi da gashi ga ilimi addini dana boko kin tara ranan da naji kina karatu wallahi har rudewa nayi na raya a raina da naje gida komawa zanyi makaranta ni ma na samu in sauke. Tun ina karama fa na sauke maryam yanzun haka ban bar karatu ba don ina nan ne bana zuwa amma a gida ban wasa da karatu ko kadan kinga yayata malama ce sosai wallahi. Tace ai naga alama tun haduwa na dake idan kuna waya da ita zata tana makaranta ko gata tana shiri fita makaranta may yafi wanan dadi ga mace. Nace kinga mu zama yakawo kakannin mu zama garin minna amma aslin mu yan wani gari ne da ake kira ka,oje tun ana hade da sokoto da Niger yanzun haka mu bamu san gida ba mu filani ne na asali wallahi. Mahaifiyar mu ce kwarin minna amma saboda zama muka juye muka zama mutanen minna baki sanin mu baki ne idan ba mun fada ma ba. Haba nature din ki yayi kama sosai da na fulani ashe ma ke ruwan su ne nace ada ke nan ina so zuwa garin mu sosai inga yan uwana wallahi. Don ance har yanzu yan uwan mu suna garin don daddy din mu shi yasan gari har yakan je lokacin da bai tara iyali haka ba. Tace ya kamata ku nemi gida su san ku fa nace muna da burin haka nida ya Amina ai sai dai kin san abin sai an shirya ne . Dakin shi ya nufa ya fara cire kayan shi zuciyar shi yana mai soya yana jin kamar ya ganin a gaban shi ya shake ni don haushi da takaicina da yake ji. Nafisa ce tazo dakin har lokacin a hasale take daidai ya fito daga wanka ta yi mai wani mugun kallo tace yau sai ka fada min gurin wace kaje har ta dauki wayan ka ta kirani dashi. Baiyi magana ba sai kokarin saka jallabiyan da yake yi a jikin shi ta karaso tana ce mai wata yar iska yar kasada ke son shiga rayuwan ka Samad ? Ido kawai ya tsura mata yana kallon ta batare da yayi mata magana ba ta sake maimaita tambayan shi samad ka fada min wa cece kaje wurin ta har ta dauki wayan ka ? Ta karaso tana rike mai kwalar dogon rigan da ya a jikin shi yanzu kama hannuwan nata yayi ya murde ya wurgata saman goda ya nufi inda turaren shi suke ya dauko yana fesawa jikin shi. Ta kara juyowa ta nufo shi a hasale tana cewa kunji kun gama iskancin ku shine ka dawo gidana kana min wankan tsarki anan. Da mamaki yake kallon ta ya bude baki da kyar yace Nafisa yau ni kike wa zargin aikata zina da wata kace tace dole in maka samad may ye hadin ka da wata mace , ? Yace dani mazanaci da akan ki zan fara tunda dashi kika gabatar min da soyayyan ki farkon haduwan mu dake. Haushin maganan shi taji sai ko ta haushi da duka da yakusa tana ture shi tsayawa yayi yana kallon ta da mamaki. Jayeta ya kara yi ya hakadata gefe ya fice daga dakin ta biyo shi tana zagi ta uwa ta uba ya shige dayan dakin ya kyale ta. Yana shiga wayan shi na kara ya dauka Yusuf ne yake son fada mashi ya gama tsara masu tafiyan da zasuyi kaduna. Yace sai dai abinda zamu saya wa yaran nake son mu dauko khadija ta zaba muna abinda ya dace dasu tunda mu ba zaben kayan yara muka iya ba. Yusuf ya ambaci sunan shi a kasalance Yusuf din ya amsa mai yace don Allah ka rabani da wanan yarinyar dake batun tarwatsa min gida da rayuwa na. Cikin mamaki Yusuf din yace tayi ma wani abune kuma ban sani ba yace may ne ma batai min ba yanzun haka in ka saurara zaka iya jiyo hargowan Nafisa akan khadija. Da sauri Yusuf din yace dashi kai haba sun hadu ne komai ko ta samu labarin khadija din ne yace basu hadu ba sai dai yau kaddara ya hadasu a wayana. Nan ya koro mai abinda ya faru yau din dariya sosai Yusuf ya kwashe dashi lokaci guda yace kai khadija akwai jan magana da rashin tsoro. Yace ni yau taja min masifa da fushin Nafisa a gidan nan ban son wanan bakin kishin na Nafisa wallahi idan ya tashi bataji bata gani imagine wai har ni Nafisa ke ma zargin zina yau. Intrested ashe yau tasan zaka iya kara aure ko wani lokaci ke nan wow i am impress da jin wanan labarin Allah yasa haka yasa ta fara gyara halin ta. Rikici kake son jawo min Yusuf da ka hada ni wanan aljanan yarinyar mai shegen rigima wai dole sai itace zatai min wanan aikin ne ? Kana son mu canza wata ce ya tambaya shi a cikin gatse yace No da sauri yace ta faye matsala ne wallahi. Yace da matsalan nata za a gyara komai kai dai ka kara hakuri don Allah yace wallahi yarinyar ta fara shiga raina amma kuma ta faye matsala ne ai. Yanzu yaya zan iya shawo kan Nafisa a gidan nan gaba daya ta birkice min yau kan kishin wace ma bata sani ba har da duka na fa takeyi. Duka kuma subbahanallahi kai kuma sai kai tsaye tana dukan ka ko mai yace to may zan mata Yusuf kit Yusuf din ya kashe waya alaman yaji haushin maganan abokin nashi. Dariya ya soma yi bayan ya kashe ma Samad waya yace komai na zuwa yadda nake so da alama samad ya fara son khadija. Wayana ya kira bayan mun gaisa yake tambayana ashe yau mutumin yazo gurin ki shi kadai nace eh dan matsalan yazo min wai bashi da lafiya. Sai bayan na taimaka mai da magani yaji sauki ya soma karanta min haukan shi wai na fita mai a motar shi tunbai balbalani ba. Dariya yayi yace may ya hada ku har haka nace bakin rigima na yasani daukar mai wayan matarshi da take neman shi ganin kamar barci yake wayan nata ruri nikuma sai na dauka. Dariya yayi sosai a lokacin yace aiko nasan yau suna can suna tafka fitina a tsakanin su kin ja mashi aiki yau Nace shi ta sha matsoracin namiji kawai wanan ma ko ga maza yan uwan shi nasan matsoracine wallahi dariya Yusuf yayi sosai. Yace to yanzu na kiraki ne don Allah gobe indan kina free zaki taimaka muna da sayen kayan yaran samad don Friday zamu shiga kaduna insha Allahu. Nace idan dashi ne gaskiya ba zan tafi ba yace saboda may khadija kefa kika kawo wanan idea din zaki ce kuma bazaki tafi ba. Ki daure ki karasa ladan ki don Allah ai ba don shi zakiyi ba yaran fa kika dauki alkawarin taimakawa saboda Allah shiru nayi yace may kikace nace a hankali naji sai dai idan ya wuce gobe ba zan samu fita ba don ina da exam talata kuma zan wuce gida. Yace nagode khadija Allah ya biyaki da alherin sa yadda kike muna Allah ne kadai zai saka miki sai mun hadu goben zamuyi magana Allah ya kai mu nace dashi. Na kwanta cike da tunane a raina wai dama da gaske akwai mazan da suke irin wanan rayuwan a gidajen su don dai ni nasan mahaifin mu zaki ne a gidan shi akan iyalin shi. Wai duk gidajen masu kudi haka yake ne rayuwan su sai mata ke juya su yadda suka ga dama idan ka gansu awaje sai kai masu kallon isa da izza amma a gidajen su sai ka raina su. Yaya matashi kamar Samad zai zauna mace tana juya shi haka yadda take so wai kuma yana sunan miji a gidan shi gashi da ilimi daya dace yayi amfani dashi ako ina ya kama amma mace ta na juya shi son ranta. Kwafa nayi nace wallahi gobe zasu ga tsiya don sayayya zanyi masu kamar na hauka inta gani ta haukace da tushe. Washe gari nace ma maryam ta shirya zamu fita da su yaya Samad zasu zo mu muyi wa iyalin shi sayayya tace tau da murnan ta. Mun shirya tsab don Yusuf ya bugo min waya suna kan hanya zuwa wani dan abu ne ya tsayar dasu yanzu. Sun iso wayan Yusuf ya shigo min gasu a kofan mu nace gamu tafe yace keda wa khadija nace da kawata maryam zata tayani zaben kayan ne sai kun fito yace min. Mun fito daga gidan kwanan namu na dalibai muka hango su can nesa kadan inda suka aje motar su muka karaso wurin . Motar Yusuf ya fito ya bude muna muka shiga ya rufe sai da muka zauna muka fara gaida su wanda nidai kusan Yusuf kawai na gayar maryam ne tace da Samad yaya jikin shi yace cikin daga hannu da sauki. Sai looacin ciwon kan da yazo dashi jiya ya fado mashi a rai don fitinan da suka kwana sunayi da Nafisa yasa ya manta da komai nashi. Kawar ki bata magana ne Yusuf ya kawar dashirun da motar yayi a lokacin maryam ne ta bashi amsa da fadin ai itace dai magana ya zama aiki a gare ta nikan ko aku ya ganeni ya kauce min wurin zuba. Ashe kuna da aiki shi yasa abin yazo maku daidai naji mamakin da kika iya zama da wanan mai zubin yan ruwan dariya ta danyi tana cewa ashe kaima kyaunta na ruda ka haka. Haka take ruda maza a cikin makarantar dama wajen makarantar amma kunsan may wai duk wanan bata ga may mata ba har yanzu ga kyau yana tafiya a banza a gurin maza. Tsuki yaja tare da juyowa ya dan watsa mata harara lokacin da take fadin ni wallahi ina son ganin lucky man din zai iya sace zuciyar wanan yar kwalisan yarinyar. Zaki ko sha zaman jira don maza basu son zuben mace irin wanan da ko ina tabi surar ta na rawa sun fi son mace mai natsuwa da kamala. Yusuf yace har kin sa yau na fahinci wani abu da kika kawo wanan maganan haka nayi real sign ba karamin kyau ki ga khadija ba da har na kasa fahintar abinda yasa abokina yake yawan rudewa idan ya hadu da khadija ashe kyawon tane yake yawan tsorata shi yana mata kallo mai kama da tsoro but still yanzu da yai maganan nan sai na gane kyauta ne yake yawan ruda shi. Da na dan shiga rudanin wanan abin amma yanzu maganan nan da kikayi yasani a hanya watau a takaice aboki na yana rudewa idan yaga khadija sai take mashi zubin yan ruwa idan ya kalle ta. Tayi saurin fadin ya gano sirin da Allah ya boye ne anan ai khadija matar manya ce wallahi duk namijin da yai saa ta kalleshi da manyan idanun nan nata yakan shiga rudu ne ya rasa inda yake ina ga shiya take tsoron fita wallahi. Don Allah malam idan kun gama kaja mota kakai mu inda zamu ko ka mayar damu inda ka dauko mu zaifi ya fada batare da ya juyo gare shi ba Yi hakkuri malam abinda na gani na fada yasin khadija ta hadu ba karya a gurin nan kai mai dani inda ka dauko ni ya fada a dake. Nidai nayi kamar badani suke yi ba kaina yana duke ina danna wayana dake hannu na muna charting da zarah. Yusuf yace karkai fushi dani abokina gaskiya muka fada anan take a deep breath and confess khadija ta fi matan da kake gani haduwa. Bude baki yayi ya zaro ido yana kallon yusuf da mamaki kalaman shi dayaji na bazata yasan Yusuf ne kadai duk duniya yake iya fahintar shi lokaci daya. Yusuf ya sake kallo shi ya dan lagabe kai tare da girgiza mashi kai yace dont give me that look just say yes to your mind she is realy beautiful as you see. Take ya daure fuskan shi tamau tankar bai taba dariya ba yace Yusuf kayi kuskuren furtan hakan a gare ni don kafi kowa sanin banda lokacin yin hakan . Nace kunyi babban kuskure Yusuf da kuke son kamanta da wanan mutum matsoraci ko kuna zaton sakewan da nayi daku kun dauke shi da wani manufane ? Ba so ko wani abu makamancin haka cikin zuciyana don ban taba daukan haka ba a tsakanina dakai sai mutunci da niyar taimakon ka a zuciyata don rayuwan ka na bukatan taimako da agaji ga wanda yasan shi. Tsakanina daku kuma sai dangantarkar irin na zumunci na an fito wuri daya da biye min da kukeyi da kyautatawa . Da ka sani da baka dauki haka ba da zafi don zuciyar ka ta baka ba daidai ba me yasa zakayi zaton soyayye zai yuyu a tsakanin mu don kana kyakyawa mai kudi maiji da ilimi da wayewa ko may ? To ni duk wanan nasaban naka baya burge ni don ni ina fatan samun miji ne wanda yasan kanshi yake iya mulkata ba in mulkeshi ba ko wata tana mulkanshi. Barin fada maka ban taba jin son ka wallahi a raina don halinka bai mun ba bai kuma taba burgeni ba tausayi ne da fatan alheri ka shirya da iyayyen ka takowani hali . Don halinka da dabiar ka yanayin rayuwan da ka shiga da komai naka yana bukatan gyara a yanzu. Ya isa yace da karfi ya fada cikin kuna rai, yayin da maryam tunda na fara magana take rufe min baki waina bar maganan . Idon shi yayi mai jawur hankalin shi yana neman barin jikin shi zuciyar shi yana son tarwatse mai yace ba laifin ki ba ne. Yaja wani irin huci ya furzar a bakin shi yace Yusuf ka juya mu sauke su inda ka dauko su don Allah. Bana son inkara ganin fuskan yarinyar nan na tsane ta wallahi bana son kara haduwa da ita a rayuwa na . Shiko Yusuf a ranshi ya gigice da fadan mu sosai yana rayawa yaushe ne zai samu cin ma manufar shi a kan mu yaushe zasu bar wanan halin may yasa Samad ke biye mata suna haka kamar wasu yara kanana. Ya zama mai dole ya shiri mu tun yanzu tun kan mu rabu a hakan ba wani ci gaba gashi ya fara ganin hasken alamarin tun ba a je ko ina ba. Ya zama dole ya gyara wanan abin tun anan don ba zai yarda abokin nashi yaci gaba da zama haka ba yanzu in ya bari muka watse a hakan abin bayi ba wallahi. Naji Yusuf din yace Khadija ba nufin abokina ke nan ba baki fahince shi bane tun farko kin san tun jiya fa yana da haushin ki a ranshi don haka don Allah bashi hakkuri ya huce dake haka please. Yadan juyo yana kashe min ido sai na gane manufarshi da sauri sai da na hade wani bakin ciki na iya furta to kayi hakkuri don Allah ban fahince ka bane na fada a sanyaye. Da kyau Khadija matar na tuba ko bata laifi komai rintsi ya juya gurin shi yace kayi tsamanin jin hakan daga bakin ta yanzu a yadda tahau din nan. Wani iri yaji yace a ranshi may yasa na kasa fahintar wanan yarinyar ne wai me yasa na fadi wanan maganganun masu zafi gareta yanzu bayan nasan gaskiya Yusuf suka fada. Halinta daban ne da na sauran matan dake bina suna ribibin in so su kai tsaye zata iya fada ma gaskiya batare da tsoron komai ba kuma ya amfane ka. A sanyaye yace Yusuf ban san may yasa take son bata min rai ko da yaushe muka hadu ba zan bata dama taci gaba da min yadda take so ko yaushe. Motar ta tsaya a bakin wani plaza babba ba wanda yayi magana Yusuf ne yace bissimila mun iso mu shiga mu fito tukun. Fita mukayi a motan har lokacin jikina a sanyaye nake jin shi don abinda ya faru a motan Yusuf ne yazo daidai inda nake yace khadija na gode da kika fahince ni ba komai nace dashi cikin yake. Muna shiga shi yana bayan mu yana tako a cikin izza da kamala maryam tazo daidai kunne na tace dan dakata mai ku jera mana. Hara na aika mata nace sai dai ya mutu idan sai na jera dashi din ya dai ci albarkacin Yusuf da kuma na iyayye wallahi. Ban garen kayan yara muka nufa inda maryam ta fara duba kayan ina tayata har lokacin ban sake ba nan muka shiga jidan ma yaran kayan sawa da sauran abubwan yara. Mu koma bangaren takalma da dasu sauran abin bukatan yara harda su tawul da sabule da su kulan zuwa school muka hado dashi a hankali na taka wurin kayan mata na zaba ma anty fati kusan kala goma masu kyau da tsada. Su dai ido kawai suka saka min har lokacin da muka gama Yusuf yace mu zabi abinda muke so ni wani jakka da takalma kawai na dauka maryam kuma ta dauki wani dogon riga da jakka. Munje gun biya muka da ja baya naga ya ciro katin shi na bakin ya basu suka debe kudin su suka miko mai mun shiga motar mun zauna. Yace kina ganin mun sai komai da zasu buta nace insha Allahu har maman su ma da sauri ya juyo yadan kalle ni kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa yusuf yaja motan muka tafi. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Hutun sati uku kacal muka samu wanan karshen zangon don haka naji dadi sosai da bai kasance dogon hutu bane don zan samu zama a minna tare da iyayyena in yi hutu. Wanda rabo da in samu kasancewa dasu haka a wadace har na manta yanzun haka na fito daga zana jerabawan karshe na wanan zangon da mukayi da yazo min da rikicin haduwa da Abdulsamad da abokin shi Yusuf. Ba ranan zan tafi ba sai washe gari don haka maryam ta tsaya jirana don taso muje gidan yayar ta na nuna mata ban son zuwa can din. Komai na gama shiryawa a dakin sai kayan da zan saka ne da katifa ban samu daga wa sama ba don kwantawa da zanyi na yau kawai da safe in dage shi sama in tafi gida. Bayan mun rabu dasu yusuf ya kirani yana tanbaya na ya muka isa hostel din mu tare da kara yi min godiya . Bayan mun kashe wayan gidan Abdulsamad suka nufa sun kusa shiga gidan ne Abdulsamad din yace dashi idan sun tafi kada a sauke kaya da aka sayo a gidan shi abar kayan acikin mota kawai idan sun isa Yusuf yagane manufan shi na fadin haka. Sai dai bai ma abokin nashi magana ba gamay da abinda ya fahinta na son kada a sauke kayan dayace kada ayi har lokacin gidan ba dadi tsakanin su da Nafisa. Wanka ya fito yana goge ruwa akanshi ta shigo dakin har lokacin tana nan cikin fushinta da shi zuwa tayi tambayan shi kudin da tayi requesting wana zata yi tafiya zuwa gida. Tace Samad kwanaki na ta matsowa har yanzu bakai magana kan abinda na bukaci ka bani ba wanda zan je gida dashi indan zan tafi sai in wuce dashi. Yadda take magana bai sa ya daga kai ya kalle ta ba Samad dakai fa nake magana ya dan wuce ta zuwa bakin gado ya zauna . Ta juyo gareshi tace magana fa nakeyi maka kana ji kuma ta fadi a hasale sai lokacin ya dago yace kada ki kara yi min maganan nan. Don bashi ke gaba na ba gobe kaduna zan tafi in daba iyayye da iyali na wani irin gumzi tayi tayo kan shi tana fadin wallahi baka isa ba. Ba kuma inda zaka kaje na fada ma don baka fada min zancen tafiya ka ba don haka ban shirya ma tafiyan ka yanzu. Murmushi yayi yace kice ma mai shirya min tafiyan don kece zaki sallamay ke nan ko ? May kake nufi da wanan maganan haka ban ci na sani bane idan za kai tafiya yanzu koma ko da da kake fada min ni nake sa ka fada min . Yace shine kuskuren da na aikata a baya yanzun kuma a shirye nake da na gyara komai da ya faru ido ta zuba mai cikin firgici take. Ganin zata damay shi yasa ya fice ya bar mata dakin don da dakin yaso ya gyara kafin ya kwanta don ya kwana biyu ba samu tsayawa ya gyara ba. Don yanzu gyaran dakin kwanan nashi ya dawo kan shi saboda indan yan uwan nata sun mashi gyara sai abubuwan da dama suyi ta bacewa a dakin. Wanan yasa ya daina bari su shiga mai daki suyi mashi gyara sai shi ya ke gyaran dakin nashi da kanshi ya don yafi mai sauki idan bai gyara ba ita bata da lokacin gyaran . Haka kuma zata shigo ta kwanta a cikin dakin ba kunya ba tsoron Allah haka dai ake rayuwan a dunkule ba wani jin dadin irin na aure tsakanin mata da miji. Laptop din shi ya dauko ya na dubawa sai dai tunane ya hana shi yin wani aiki a ciki bakomai yake tunane ba sai irin maganan da nake fada mai, mai kama da shagube yana jin haushi na ashe gaskiya nake fada mashi. Yaushe rabon shi da yaran shi suzo kusa dashi su zauna a matsayin shi na mahaifin su suji dadi babu. Ya tanbatar da ya tafka babban kuskure da Allah zai iya kama shi da laifin da ba zai iya amsawa ba gobe kiyama. Khadija khadija ya furta a hankali kin taimake kin ceci rayuwana ta yadda ban taba zato ba wanan wace irin yarinya ce mai hikimà da basira. Ya dade a wurin zaune har ya kai kwance sai da wayan shi yayi ringing ya daga wani yaron shi na wurin aiki ke gaya mai an samu wasu filaye ns gwaunati a gwagwalada da wasu mutane ke son ci. Yace da yaron nashi ya bari sai next week za a duba case din idan Allah ya kaimu sun gama waya kiran Yusuf ya sake shigo mai inda yake fada mai gashi a kofan gidan shi sin dawo da motaci an gama duba su . Yace gaya nan fito mikewa yayi ya zura santala santalan kafan shi cikin wasu budaddun takalma ya sauko zuwa kasa inda ya samu falon cike da yan uwan Nafisa kamar suna shawara. Ganin yadda ya fito yasa ta dago kai tana kallon shi ya fito ya samu Yusuf din zaune a saman dan wani dakali yana jiran fitowan shi. Ya fito ya fara mai baiyanin komai basuyi aune ba sai ganin Nafisa sukayi a gaban su tana huci ba bata lokaci ta shiga dura ma Yusuf din zagi tana ai banta shi. Bai tanka ta ba sai faman kururuwa take masu a kai tana kiran da munafuki dan bakin ciki ko bai so sai ya gansu da Samad agidan shi. Dama tasan duk wani munafuncin da ga wurin shi yake fitowa daga shi har samad din sai ta dauki mataki a kansu. Amma dai karki manta bakece Allah ba ko don haka babu wani abin da zaki iya muna sai Allah don in da sabo ya saba da wanan halin na Nafisa. Sau da yawa idan sun kwaso rikici da mijin ta a kanshi take saukewa don tana ganin shine mai zuga shi sai taga ta kamo shi da kyau dan lokaci kadan kuma sai abin ya juye mata. Wanda take ganin Yusuf din ne ke mata zagon kasa a hakan sai dai bai nasaran rabata da Yusuf din da yake son yi ko yaushe. Da kyat yan uwanta suka samu takoma ciki bayan sun kare masu kallon banza suka shige da ita cikin gida tana ta haure hauren rashin mutunci. Washe gari tun da safe ya shirya Yusuf yazo zasu tafi kamar yadda ya saba motoci uku zasuyi tafiyan da shi sai dai wanan karon tafiyan ya canza masu sallo. Na farko su kadai ne ba tare da buzuwa ba na biyu kuma tare da a abin arzikin da bai saba tafiya dashi ba zasu dunfari gidan. Ana kara gyara kaya kamar daga sama sai ganin ta sukayi a wurin motacin tana ganin kayan ta shiga tonawa har ta gano abinda ke cikin buhuhunan da akayi siling din su din. Ranan sun ga masifa haka sukaja mota suka tafi ransu bace da halin da Nafisa ta nuna masu din sun isa a cikin lokaci gari bai je gidan ba sai da ya karasa gidan shi ya huta don sun iso kan shi yana mashi ciwo sosai saboda hayaniyar da baiso. Tunda Yusuf ya sauke shi yanufo gidan nasu da abinda suka zo inda sai gani motane keyi anata shiga da kaya a cikin gidan ana jibgeasu a kofan hajiya mama kamar yadda ya umurce shi da yi. Sun kasa boye mamakin su anty amarya ce ta fara tambaya anya wanan abin da Nafisa ko aka zo wanan karon dariya Yusuf yayi yace bada ita bace anty muka dai muka zo. Mommu tace abin kan da mamaki gaskiya Allah yasa babangida ya canza daga wanan karon dariya Yusuf yayi yace insha Allahu mommy kudai taya mu da addua. Ya shiga dakin hajiya mama don ya gai da ita ya samay ta da yan matan ta suna mamakin wanan sayyayan da suka gani haka wai daga gun Abdulsamad ya fito haka ? Ya shiga dakin sai da ya zube kasa ya fara gaida ita sai faman murmushi take yi har lokacin ta kasa boye mamakin ta bayan sun gama gaisawa dakin take tambayan shi wanan sauyin yanan Abdul din data gani. Yace hajiya adai taya mu da addua kusan kece sillar canzawan nan nashi lokacin fada maki komai baiyi ba amma nan gaba insha Allahu zan sanar dake komai so nake komai ya tafi haka yadda muke so dashi . Don yanzu insha Allahu akwai canji sosai wallahi nan dai suka dan taba hira yace Abdulsamad na tafe zamuyi bayananin komai idan ya shigo. Duk da zaman lafiyan da akeyi gidan bai hana a kebe gefe ba ana gulman wanan sabon yanayin da aka hango a gare shi. Sai dai kowa ya matsu yaga abinda ke cikin buhuhunan wanda ba wanda ya iya gane komau ye a cikin su su indan gaiyan aikin nasu ya shigo. Saida suka sauko sallah jumma a ya shiga gidan iyayyen nashi a falon Alhajin su ya fara shiga ya gaida shi da mashi yaya jiki ranan yaga sauyi sosai na sakin fuska a wurin mahaifin nashi wanda ya dade bai gani ba. Bayan sun gama da mahaifin nashi ne ya shiga ciki ya fara gaida ummi sai mommy sai anty amarya ya wuce dakin hajiya mama wanda dama kullun itace karshen shiga da yafito kuma sai ya bar gidan. Sun gaisa da ita acikin sakin fuska ya dubi Affan dake zaune gefenta yana cin abinci ya kira yaron saboda rashin sabon da basuyi ba dashi ya dago ya kalle shi kawai ya gaida shi. Sai baiji dadin yadda yaron yayi mashi ba shiru ya dan biyo dakin take tambayan shi iyali ya amsa da duk sina lafiya hajiya tace dole ita da yan uwanta zamu tambaye ka don sune yanzu iyalin naka. Babangida yanzu kana ganin abinda kakeyi kana aikata daidai a rayuwanka mutum ya watsar da iyalin shi ya rugumi wasu bare can. Shiru yayi ya dukar da kanshi tace kaima kanka fada kada ka mutu a cikin wanan halin kasan Allah na zai barka ba Yusuf ne yace ayi hakkuri hajiya komai zai zo daidai in Allah ya yarda adai tayamu da addua. Nan ya fara mata bayanin kayan da suka zo dashi inda ta fahinci komai yace saura kayan abinci muyi magana ko za a kawo zuwa yamma sai a raba yadda ya kamata. Yayi mamakin yadda yaji mahaifiyar tashi tana kwararo mashi addua yau da saka mashi albarka wanda ya dade baiji ba daga gare ta duk zuwan da yake yi da fada sukan kare ya fita rai a bace. Yau sai gashi sanadin yarinyar da yake gani mai matsala a gare shi yaja mai samun addua irin haka a gurin mahaifan shi bai fita gidan ba sai da yayi masu alheri yakuma mata alkawari zai je zaria yayi masu taaziyan rashin da akayi can. Taji dadin jin hakan sosai na ya fito ya barsu a cikin farin ciki ya koma gidan shi don yana bukatan hutu a lokacin bayan fitar shine hajiya ta kira su mommy tana masu bayani aka shiga bude kayan da ta nuna masu din. Kowa yayi mamakin ganin hakan don basu zaci haka ba yanzu a gare shi sai addua suke mashi da fatan gamawa lafiya kowa aka cire mai nasa cikin farin ciki da jin dadi. Tunda ya koma wake kwance a dakin shi na gidan ba abinda yake tunane sai irin yadda na fada mai magana mai amfani acikin gatse kuma yayi mai tasiri. Yani yace a ranshi lalai ya zama dole in san yadda zan gyara alamarina da yarinyar nan don ita din ba abin yar wa bace . Cikin dan lokacin kadan tayi min sanadin dawo min da farin ciki tsakani na da iyayyen har da yan uwa wanda wanan tunanen bai taba zuwa min ba ko wani ya tsayar dani ya fada min gaskiya yadda take fada min kai tsaye. Tayi namijin kokari wurin ganin ta tsaya ta fada min maganna irin haka kai tsaye bataji shakka ko nauyin fada min yadda kowa ke shayi na ba. Wayan shi aka kira ya daga Faiza ce take mai godiyan abinda aka kawo masu yace babu komai ta kashe kuma Lawisa yar wurin ummi ma ta kirashi tana mashi godiya haka suka dinga kiran shi sai da yagaji ya kashe wayan shi ranan. Wani irin farin ciki yake jin kanshi ciki mara misaltuwa da wanan kiran da yan uwan shi suke mai a lokacin don ba zai ce ga ranan da suka kirashi karshe ba. Ya zama dole gare shi ya san yadda ya gyara mu,amulan shi da duk wani dan uwa nashi da ya watsar da farko. Sai yaji yana sha, awan ya kira layin khadija a lokacin yayi mata godiya haka yasa ya jawo wayan shi ya kira layin ta. Ina fitowa cikin makaranta na samu guri na zauna ina jiran maryam tafito mu wuce cikin gidajen mu don an kara muna kwana daya yanzu. Kiran shine ya shigo min wanda tun bayan rabuwar mu ranan ban kara ji daga gare ba sai yanzun da ya kirani din na tuna dashi. A hasale na dauki wayan ba tare da nayi magana ba don na gane shine jin shiru ya danyi yawa banyan na dauki wayan sai nace A hasale nake fadin lafiya ka kirani ko ka kirane ka fada min ka tsane ni din da kake fada min ko yaushe ?. Murmushi naji yayi kasa kasa sai ya sake kiran suna full yace khadija a zuciye nace ina jinka ai yace ba wanan kiran nayi maki ba yanzu. Nace may ye ka kira malam ni kada ka bata min lokaci haushi ne ya ishe shi a lokacin yana rayawa a ranshi yaya zai yi dani ne wai ? Cikin sanyi murya yace min thanks khadija na gode kwarai da taimakon ki gare ni sai dai don Allah, , , , Dama abinda yasa ka kirani ke nan don ka samu wani sabon yaudara ka zageni kuma dashi na fahince ka don haka banda lokacin ka ni yanzu. Na fadi a cikin tsigar tsokana tare da saurin kashe wayan sai dai a zahiri jikina yayi sanyi da yadda naju yana maganan cikin wani yanayi. Shiko ina kashe wayan yabi wayan da kallo kamar nice wayar ya sauke wani irin ajiyan zuciya yana fadi a fili shi kadai a daki. Wanan yarinyar ni yaya zanyi da ita ne wai ta fahince ni yanzu ya girgiza kai yace kina da matsala khadija yarinya haka bata da kwaciyar hankalin fahinta. Why why khadija baki so na da kwanciyan hankali a tare dani yanzu ne mikewa yayi daga kwancen da yake ya nufi fridge ya dauko goran ruwa mai sanyi a ciki ya kwankwada tare da wurgi da goran ya fito falon shi. Mutane ya samu sunzo gaida shi inda ya bisu da alheri sai yamma lis ya samu suka rage nan ya nufi bathroom din shi don ya dan watsa ma jikin shi ruwa ko zai ji sanyi. Dan ruwan dumi ya hada saboda yanayin garin na kaduna ya shige jacuzzi ya dan dauki lokaci yana tunane kafin ya fito ya sa kaya a jikin shi ranan a maslcin uguwan su yayi sallah magariba tare da jamma, an unguwa da mahaifin shi aciki. Ba abinda yake tunane sai yadda zai samu mu shirya a tsakanin mu gashi dan lokaci kadan yarinyar ta shiga zuciyana ta samu wuri a ciki. Tunanin yadda zai shawo kaina amma ya kasa samun mafita har wanan lokacin shigowan suraj soja wurin shi yasa ya matan halin da yake ciki don sun dauki lokaci dashi suna fira kafin Yusuf ya shigo mai da abincin da mommy ta girka masu. A tare da Suraj da Yusuf din sukaci abincin suna hira a tsakanin su bayan fitan Suraj ne suka samu kebewa da Yusuf wanda tun bayan zuwan su basu samu zama a tare ba. Nan yake kara mai godiyan kokarin da yake mashi inda yake sanar dashi ya kira ni don yai min godiya amma naki fahintar shi Yusuf din yace ya sake kirana zan fahince a hankali. Ba laifi yace dashi sun dan dauki lokaci sukayi sallama akan da safe zai shigo su tafi zaria idan sun dawo yana son kuma ya dan je wurare masu muhinmanci a kaduna daya dade bai tafi ba. Yusuf na fita ya kira waya maryam ta dauka ta miko min bayan ta dana recieve na dauka da sallama na kara a kunne na. Bayan mun gaisa ne yake rokona da in karba wayan abokin shi inji may zai fada min dariya nayi tare da fadin abokin nan naka ne ai sai a solo baida mutunci. Yace kada kice haka Khadija baki fahince shi bane amma abokina mutumin kirki ne wallahi ki bashi dama ku fahinci juna yanzu zai bugo waya godiya yake son yi maki akan taimakon da kikai mashi na bashi shara kuma yabi yaji dadin shawaran ki shine zai maki godiya akai. Munyi sallama dashi ranan maryam tazo dakina wai a nan zata kwana saboda exam din da zatayi washegari yana da zafi ita kuma tana son tayi karatu a daren ranan. Muna tsaka ga karatu wayana yayi kara na daga tare da karawa a kunne na muryan shi naji yana tambayana har yanzu baki barci bane. Karatu mukeyi na bashi amsa yace OK dazun na kiraki in maki godiya kika kashe waya nace ina busy ne a lokacin. Khadija ya kira sunana amsawa nayi ciki ciki yace please ki bani dama in maki godiya akan abinda kikai min shiru nayi na kasa magana. Khadija kina jina nace ina jin ka mana sai naji tayi wani kasalalen murmushi yace in tambaye ke zaki ban amsa tsakani da Allah ? Nace sosai makuwa idan har na sani may zai sa in boye maka tunda ba rike min baki zakayi ba. Ajiyan zuciya naji ya sauke sai can yace may yasa kike son yawan bata min kina son ganin hasalana ni koda ban tashi hasala ba ? Kin tsane ni kin ki jini baki kaunar ki ganin a cikin farin ciki why khadija why kika zabi wanan rayuwan a tsakanin mu. Shiru nayi na kasa magana nauyin shi da kunyanshine suka kamani a lokaci daya na rasa may zance dashi don yadda yake magana bazakace shi din bane mai izza da jiji da kai. Nasan kin san bawai son soyayya ne a tsakanin mu ba amma kuma kika zabi yin haka a gare ni ki fada min may ke sakina tsana na haka da yawa. Dan murmushi nayi tare da fadin yaya Abdulsamad ke nan ni nasan babu dingo soyayya ma a tsakani mu tun farko sanan kuma ni ko in so ka ko da so ka ba abinda zai ragaka dashi duk dayane a wurin ka. Ni dama ba kai na tsana halin ka na tsana da matar ka da bata san mutucin yan uwanka ba har hali ku ya juye iri daya da ita. A yau in rayuka zai sauya kasan mutucin kan ka dana yan uwanka ka farga ka dawo yadda mahaifan ka suke son ganin ka da yan uwanka ka san darajan su da mutuncin su fiye da kowa. Amma ni may zai sa na tsane ka kana a matsayin yayana aiko don mama zan so ka zanyi muamula dakai kamar kowa. Don dama ba kinka nayi bani halin ka dai na tsana bani ba kowa ma zai so ya kulla halaka dakai ta yadda baka zata ba. Murmushin da naji yayi yasani shiru yace khadija idan nace maki ashiri nake da in caza yanzun zaki yarda koma in ce dake din na canza a sanadiya ki. Jin shi kawai nakeyi ta yaya ni zan iya canza mutum kamar Abdulsamad a lokaci daya haka. Muryan shi naji yana fadin kina mamaki abinda na fada ne yanzu yace yes ke khadija kin tunatar dani abinda na manta acikin abinda nake dauka shirmay kukeyi ke da Yusuf a lokacin. Nace ba abinda mukayi da har zai kawo sauyi gare ka haka da wuri sai dai idan dama Allah ya kaddara tamu din abin zai fito ma. Kuma ina mai farin ciki da jin haka idan ya kasance gaskiya ne maganar ka da sai nafi kowa farin cikin haka a duniya. Yace to ki fara farin ciki daga yau don ko kin sa iyayyena sun min abinda suka dade basu min ba a yau don haka khadija ban san ta yaya zan gode maki ba da tunatar dani da ki kayi ga abinda na manta hakki na ne yinsa a baya. Koda da wasa ko gatse kika fada min wanan magana to ki sani your words inspired me har nakai ga samun kalmar albarka a bakin iyayyena yau abinda na dade baji ba a gun su. Yau kin dawo min da farin cikin dana rasa da dadewa a tare dani kalman ki na ranan gare ni sun sa na dawo da natsuwana. Ya kuma fara dawo min da respect da power na ga idon mutane dana rasa a baya wa yanda ya kamata ace komai wuya komai dadi ina tare dasu. Ba zan iya kwantata maki dadin da naji ba yadda na kasance da yan uwana da abokai kai har ma da makwabta na ayau suna murna da zuwa gare su. Don haka yazama dole in gode maki please khadija kada kiki fada min gaskiya a duk lokacin da kika ga na kauce ma hanya. Murmushi nayi nace naji dadi kuma na tayaka murnan dawowa farin cikin ka gare ka don ko yau ranan kace ranan farin cikin ka. Ka kuma gode ma Allah da bai sa ranan ya kasance ranan nadamar ka bace ya fargar dakai da wuri haka. Allah ya kars shirya zukatan mu ni zan kashe karatu nakeyi ka tsayar dani don gobe zamu gama exam jibi gida zamu. Da sauri yace jibi wata rana nace talata inda Allah ya kaimu da safe zan tafi gida don yin hutu a can. Yace No kada ki tafi don Allah ranan ki jira in dawo akwai abinda nake son in shirya akan tafiyan ki nace Allah sarki dama ka hutar da kan ka don ni a shirye nake yanzun haka. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Zaman da maryam yana min dadi sosai don itama bata da wasa da karatun ta gashi musan mutuncin junar mu kamar mun dade da haduwa da ita. Ita ta tilasta min fara amfani da kayan da Yusuf ya saya min tace may ye amfanin ajesu da nakeyi gara dai a fara gani a jikina zai fi. Ban sake bi takan su Yusuf din ba na mayar da hankalina ga abinda ya kawo ni garin sosai sai dai muna waya da kowanin su har yanzu wanda wayana da Samad duk ya kira fada ne da zolayan junan mu har ai fada a kai ga kashe wayan. Munyi jerabawan karshen zango na farko inda muna gap da gamawa Yusuf ya kirani nake ce mai sati mai zuwa zan tafi minna don ba zan leka kaduna ba wanan hutun saboda hutun ba mai yawa bane . Nan yake ce min suna tafe gurina kafin in wuce gida don suma zasu shiga kaduna don Samad ya dade bai je gida yana kokari yaga ya shawo kan shi su tafi. Nace ka barni dashi in gwada in gani idan zamuyi sa, a da nawa dabaran yace ya gode muka kashe wayan suna zaune tare aiki suke a wani file. Yusuf yayi mamakin jin ya tambaye shi khadija yace tana nan lafiya kasan jerabawa suke yi kwanan nan wayan shi ne yai kara baiyi saurin dubawa sai da ya gama abinda yake ya dago wayan. Kallon Yusuf yayi da mamaki tare da fadin Yusuf yarinyar nan ko mutum ce jifa itace ke kirana yanzu muna maganan ta. Yusuf ya kalle shi yace mutum ce mana kamar kowa kaima kana ranta kamar yadda take a ranka ke nan . Ya dauka ciki daure fuska kafin in magana ya fara fadin lafiyan kirana ina aikina nace lafiyan ya kawo haka ai . Ya sake kiran suna na a zuce da karfi yace matsala na amsa mai da cewa may ye ne haka zaka fasa min kunne da kira haka kamar makaho. Kai na tsani wanan yarinya ya fada a hasale na amsa mai da nima haka wallahi cikin yanayin na bashi amsa. Nace dama abinda yasa na kiraka don in fada ma ya kamata kaje gida ka duba tsofin ka don gudun su da kakeyi ba shine mafita ba gare ka. Yace what da karfi don bai yi tsammanin jin wanan magana haka ba a baki na Duk wani da mai neman albarkan iyayyen shi yana tare da su a kullun suna saka mai albarka da fatan gamawa da duniya lafiya don samun haske a gare shi. Kai kana ganin kudi da girman kai da suke rudin ka zasu iya sama ma farin ciki haka ne a gare su, sunyi ciwo sun yi rashi amma bakai tunanen zuwa ka duba su ba har yau. Who dear you are da zaki fada min abinda zanyi akan iyayyena, nace ni bakowa bace sai mai neman albarka iyayyena don haka kai ma na tunar da kai akan hakan. Kuma kada ka manta da su Affan don sun fi kowa bukatan ka a wanan lokacin don nasan zaka iya zuwa masu hannu sake kai ba abin kunya bane a wurin ka. Don haka oga aje a duba su kada a shagala da yawa wataran sune masu duba mu you are stupid kece zaki tunatar dani komai kike nufi wai ke wacece wai waya baki wanan right din da zaki min wanan magana haka. Nace gani kamar kowa na tsoron fada maka gaskiya don suna ganin kana da kudi niko kudin ka ba damuna sukayi ba wallahi gaskiya komai dacin ta dole ne in fada ma mutum shi. Amma gani nayi buzuwan ka kamar kanta kawai ta sani sai yan uwanta ai don haka nima dan uwa na na sani a yanzu. Kit na kashe wayan ina dariyan keta shima Yusuf dake zaune yana jin yadda mukayi dashi sai murmushi yake yi yana huci yabi wayan da kallo. You see abinda nake fada maka kenan gashi yarinyar nan har ta hango tunda kaji ta fadi haka akwai abinda taji ya faru a gida may be. May yarinyar nan ta dauki kanta ne wai zanyi fa maganin ta a garin nan Yusuf da sauri Yusuf din yace kunfi kusa ai ni dan kallo ne a tsakanin ku sai dai ya kamata ka bincika idan ba wani taji bai da lafiya a gidan ba. Tsaki yaja yana rufe file din da suke aiki akai alaman rashi ya baci sosai ya dafe kai da hannun shi daya tunane ya shiga yi yaya akayi yayi sake rainin da bai taba shiga tsakanin shi da kowa ba har shiga tsakanin mu haka wai abinda nake mai zakace ko mu din cousin ne. Kan shi yana dafe da hannu shi daya Yusuf yace muci gaba mana yace kana iya tafiya yanzu makarasa next yanzu matsala ya shiga . Dariya yayi yana mikewa yace matsalan khadija ke nan ko hararan shi yayi da idanuwan shi da sukai mashi ja shidai ya fice bai yi magana ba. Ya dade zaune a gurin a karshe ya jawo wayan shi yana neman layin mommy don ita kadai ce zai tsaya yayi magana na fahinta da ita ya gane komay ke guda. Kira biyu ta dauki wayan da sallama a bakin ta ya amsa mata tare da fadin mommy kowa na lafiya ko kwana biyu ban kira waya ba. Tace lafiya kalau muke sai dai Alhaji ne jikin nasa ba dadi wallahi wanan matsalar tashi dai ta kwanaki ke damu shi kuma sai kuma Affan da suka kwanta asibiti amma dai yaji sauki sosai yanzu. Wanan yarinyar takai shu,uma wallahi mommu tace wace yarinyar ke nan kuma yace da sauri No magana mukeyi a nan bayan ya gama waya da mommy sai ya kira hajiya mama. Sun gaisa ta fara mai korafin rashin kula da kyautatawan da bai yi take mai fadan ga mahaifin shi nan ba lafiya yan uwan shi na kai da komo akan sa amma ace shi yayi biris dasu badon suraj da yazo ya kai shi asibiti ba may yake son mutane su fada a kan shi. Hakkuri ya fara bata yana fadin in Allah ya yarda jumma,an nan mai zuwa zai shigo ya tabayi jikin Affan sai bata bashi amsa ba. Bayan sun gama waya ya dade zaune a wurin kafin ya mike ya nufi hanyar fita office din ya rasa abinda ke yawan shagaltar dashi yanzu gamay da iyayyen shi haka. Zuciyar shi ne tayi mashi zafi don haka ya nufi gidan shi dan ya dan sarara batare da ya sanar da kowa ba ya fice a ma,aikatar nasu sai gida. Tun a kofa yake jin suruntun yana shiga Nafisa tana zaune a tsakiyan falon tana shan bakin shayi a dan karamin cup tana lumshe idanuwanta. Ganin shi a wanan lokacin tayi mamakin dawowan shi gida yanzu rigar da ya barta dashi na barci ne saye a jikin ta har wanan lokacin ga su hadiye na busa shisha duk falon ya gauraye ta ko ina kamar ba falon da ya narka ma makudan kudi ba haka. Batare da yabi ta kansu ba ya haye sama zuwa part din shi har ya kama hanyan da zai kaishi dakin shi sai kuma ya juys ya shige dakin hutun shi ya rufo kofan. Sai da ta gama shan attayen ta ta mike zuwa wurin mijin nata ba tare da damuwa da irin shigar dake jikin ta ba bata samay shi a dakin ba don haka tasan yana dayan dakin da yakan kebe kan shi wani lokaci. Can ta nufa duk da tasan ba lalle bane ta samu kofan a bude sai dai tayi mamakin da ta tura taji kofan a bude ta sa kai ta shiga yana kwance yayi rub da ciki a saman gado ta iso gare shi tana fadin. Samad yau lafiya ka dawo irin wanan lokacin tana kokarin hawa saman gadon ta zauna a kusa dashi juyowa yayi yana fuskantar ta wani irin karni da bashi kanta da jikin ta ke sakewa da kyat ya daure yace banjin dadi jikina ne tace oho ba sannu ba Allah sauwaka. Samad dama ina son in fada maka satin nan akwai bukin da zamu maradi sai kuma wayan nan kannen nawa maza da suka zo zasu koma gida. Gashi kuma ina son ka canza min mato don wanan naje dashi har sau biyu an sani dashi sai kuma su hadiye da nake son inyi wa sayayya kafin mu tafi dakuma, , , , Ke enough ya ishe ni don Allah duk wanan abin a cikin sati daya kike son inyishi ko kay wai may yasa ke baki da tunane ne wai ? Tsayawa tayi tana kallon shi galala tana mamaki yadda a dan lokaci yake son juya mata baya haka a lokaci guda tace Samad ni kake dakawa tsawa haka. Kallon ta yayi yace an daka maki ke baki da aiki sai na abaki dai a naki ai ma yan uwanki kaza ai masu kaza sam baki damu da na wa yan uwan ba da damuwar su. Tace amma kasan ina da yan uwa da ka aure ni ko yace wa kika fi yan uwa da bukatu ni nawa yan uwan basu son ai masu ne komay. Tace wanan kai ya shafa matsalar kace kuma ni dai nawa yan uwan na sani kuma dole kai masu don dani sula dagora. Mamaki da karfin halinta yaji yadda take fadin magana son ranta kai tsaye ta nuna mashi nata kawai ta sani shi yaji da nashi. Queen matsala kinyi gaskiya yace a ranshi ya ta tunar dani wani abu mai nauyi da na manta a rayuwana shiru yayi taci gaba da masifan ta akan shi bai iya furta komai ba a lokacin. Tashi yayi ya fada bathroom ya rufo kofan da karfi ruwa ya watsa a jikin shi yai wanka tare da yin alwala don yayi sallah la,asar don har lokaci ya dan gwauta da mintoci. Har ya fito tana zaune a wirin inda ya barta ya dauki room fresh ya fesa a dakin don bashin da dakin ya dauka ganin zai ta da sallah ya sa ta fita daga dakin ta barshi. Gyaran kai da jiki mukayi na zuwa gida don haka agajiye muka shigo hostel din mu maryam ta zauna dafa muna abinci ni wanka nashiga don zafi nake ji jikina ina ganin yayi min dauda. Tsab na fito nayi sallah a wirin na jawo ledan ice cream din da maryam ta sayo muna na fara sha a hankali maryam tace wallahi ji jake kamar kada ai hutun nan da za ayi. Da sauri na juyo ina ce mata saboda may maryam kika fadi haka tace ban son rabuwar mu wallahi yanzu ko ja koma gida banda wata abokiyar hira a kusa dani don anty na ba zama takeyi ba tana da yawan tafiye tafiye kullon don ita business woman ce . Nace ko dai ai koya nene kyayi kewan gida mana ni banki ba yanzun haka in bude ido in gani a cikin garin minna ma. Tace kin ji dadin ki wallahi khadija na yarda ba jin dadi bane farin ciki don ko dashi ne da bazan fadi haka ba farin ciki yana ga inda kake da sukunin aiwatar da komai. Kafin in magana wayana yayi kara na dauka kina ina nace maynene yace ki ban amsa kada ki min halin ku na yan African don Allah . Katambayi mutum ya mayar ma da tambaya shi kuma nace ina hostel mana yace ok kawai ya kashe wayan shi dip bin wayan nayi da kallo nace miskilin banza kawai. Maryam ta gama abinci wanda indomei da kwai ta dafa muna wanda yaji danyen attarudu mai yaji a ciki zubawa tayi a plate guda ta dauko muna lemon kwali a cikin fridge din ta wanda muke ajewa yanzu a ciki ida mun samu. Na fara cin abincin ke nan cibi biyu kawai nayi wayana yayi ringing na duba yaya Samad nagani a layin kamar kada in dauka dai na dauka kuma gani a kofan ku ya fada kawai. Kofan mu na maimaita da mamaki nace may kazo yi a nan kuma ban sani ba yace idan zaki fito ki fito sai ya kashe wayan kawai. Tsaki nayi na wurgar da wayan tare da fadin dan wahala kawai maryam dake zaune ta tsura min ido tana kallo na murmushi tayi tace. Uhm wani lucky guy din ne yazo haka ake ja mashi aji kuma abinda wasu ke nema ido rufe a zo gurin su anzo kike wanan masifa haka ? Nace sister kin faye bin kwakwafi wanan fa ba masoyi na bane zuwa kawai yayi ya bata min lokaci na ina zaune kalau. Don Allah ko may ya kawo shi kije ki saurare shi ba dadi mutum yazo wurin don ka ka wullakanta shi haka muje in zaba maki kayan da zaki saka in maki rakiya. Dole na mike muka tafi dakina ita da kanta ta zaba mi wani dogon riga mai ruwan ganye da dan karamin gyale shi sai da na shirya tsab a cikin rigan tabi jikina ta feshe da turararuka masu kamshi muka rufo kofan muka fito tare. Yana zaune a cikin motar shi riga da wandon shadace mai guntun hannu rigar ma iya ciya dinkin yake light green kayan su matukar karban jikin shi da dinkin . Wurin dirkekiyar motar shi da ke fake a kofan can dan nesa kadan damu muka nufa ko ganin maryam ya hana shi fada ban sani ba sai cewan da yayi. Ita ko maryam tunane take a ranta ina tasan fuskan nan nashi ne ya katse mu da cewa kin san ina waje zaki shanyani a wanan wurin naku mai kazantar tsiya haka ? Nayi dan dariya tare da cewa cikin wayance abinda yafa da nace ga kawata maryam tazo gaida kai don ma ita ta matsa min in fito yanzun haka. Anyway maryam ga yayan mu Abdulsamad Abdulrahim nan ku gaisa tace dama nace kamar nasan fuskan nan ai tace ina wuni yayan mu anzo lafiya yaya iyali. Yace lafiya kalau yaya karatu koda yake exam kukeyi yanzu ko yana wani kauda kai yana basarwa . Tace karatu Alhamdullahi mun kusa cin ma karshen shi da yardan Allah ai a huta gajiya dama nace barin zo mu gaisa ne kawai yace to na gode kwarai da alama kin fi kawar taki kirki sosai. Dariya tayi tace a a wallahi ai kirkin khadija na daban ne wallahi tana da kiki matuka shiyasa ma nake jin dadin zama da ita wallahi. Baki ya tabe ta juya ta tafi tana mashi a huta gajiya ta nufi hanyan shiga hostel din namu sai lokacin na sauke ajiyan zuciya bayan tafiyan ta. Katse ni yayi da fadin tsaye zaki min sai kace wanda tazo tadi da buduruwar shi haka bude kofan motar shi yayi na zagaya na shiga sai naji ya rufe motar. Shiru daga ni harshi ba wanda ya iya magana a lokacin sai ma gyara kwanciya yayi a motar bansan lokacin da nace dashi baka da lafiya ne Yaya Samad. Shiru yayi kamar baiji ni ba sai can yace may kika gani a tare da ni nace yau na ganka so weak ne ba miskilancin nan naka yasa na gane bakajin dadi ko baka cikin good mode. Wai ke aljana ce ko may dazun kin fada min magana akan ahalina ya zama gaskiya yanzu kuma waya fada maki banjin dadin jikina ? Nace yanayin ka ya nuna min haka sai ya dago da sauri ya na kallo na nima kallon shi nake yi sai dai ba zan iya jimirin kallon nashi ba a lokacin saboda kwarjin shi da ya cika min fuska a lokaci daya dukar da kaina nayi kasa ina wasa da yan tsun hannu na. Yau ina bakin naki ya shiga nace ko don Yusuf ne dama kike da bakin a gaban shi nace da sauri ko daya wallahi gani nayi yau kana bukatan kulawa don baka cikin hayacin ka sosai. Don jikina ya bani baka da lafiya sai naga ya koma ya kwanta kamar yadda yake da farko ya fadi a kasalance cewa kaina kamar zai rabe biyu nake jin shi khadija. Kasha magani na tambaye shi da sauri yace ban sha ba wani magani kake sha yace panadol extra nakan sha wani lokaci. Wayana na fara dannawa ina neman layin maryam ta dauka nace fito min da panadol extra din nan da goran ruwa don Allah yaya Samad bai jin dadin jikin shi tace to da sauri na kashe wayan. Motar shiru ba a dauki lokaci ba sai ga maryam ta iso da maganin ta kwankwasa glass din motar ya bude mata karba nayi ina mata godiya tace babu komai mana Allah ya bashi lafiya. Maida marfin motar nayi na rufe na fara kokarin bare mashi maganin tare da bude goran ruwan nace mai gashi ka sha. Ya dago kanshi da kyat ya kalleni ya kalli maganin da ruwan da nake mika mai sai naga ya bude min bakin shi alaman in bashi da kaina . Dan rankwafawa nayi ina saka mashi maganin a baki na kawo goran ruwan na bashi ya hadiye da kyat yana wani lumshe idonun shi yana bata fuska. Komawa yayi ya kwanta tare da fadin thanks nace Allah ya baka lafiya amin yace da kyat ni dai komawa nayi na zauna na zuba mai ido. Wasu irin jijiyoyi naga sun fito rada rada saman goshin nashi wanda ban taba kula ko yana dasu bane dama tsoro ne ya kamani kada wani abu yazo ya samay shi fa a nan wurina nawa ya samay ni kuma. Shiru daga ni har shi ba wanda yayi magana a cikin mu har mintina na shudewa a hakan suna batun zama awa daya muna nan a hakan dashi kamar mai barci. Abu daya ne yasa hankalina dan kwantawa ganin yana numfashin shi normal a lokacin yasa nayi shiru tare da zuba mashi ido kawai ina kallon ikon Allah. Wayan shi dake aje a motan ne ke ringing ganin anata kira bai dauka ba yasa na daga kiran don ba suna batare da na saurari mai magana ba nace mai wayan bai da lafiya please. Naji muryan mace tana fadin ke wacece da sauri ya dago ya kwace wayan a hannu na ya katse kiran yace akan may zaki daga min waya waya baki wanan damar da ikon daga min kira a wayana. Zanyi magana yace get out tunda ka samu lafiya yanzu zaka iya ci min mutunci sai dai ka sani ba zan ce ma komai a yanzu ba don yanayin da kake ciki na bukatan natsuwa. Get out i said na bude motar na fita ba tare da na juya na kalle shi ba naji ya tayar da motar ya jata da karfi yabar gurin nashige ciki abina. Dakina na shiga na wurgar da sauran maganin saman katifana na fara kokarin cire kaya a jikina sai ga maryam ta shigo tace ashe kin dawo. Eh ya tafi ya samu lafiya ai nace mata ina daura zanin a jikina na nike kayan na za saman jakkunan kayana dake gefe daya a dakin. Shiko tunda ya kama hanya yake jin wani bacin rai da bakin ciki a ranshi yana fadin wanan aljanan yarinyar sai ta kasheni wata rana. Yarinya yanzu ta sauke min bacin raina yanzu kuma ta kara sakani a wani anya ma mutnce kuwa dai , ? Yana shiga gidan a hargitse ya samay su duk kan su Nafisa ta haukace masu daga ita sai dan buje a jikin ta tana fadin yaushe samad ya fara cin amana na haka ? Yaushe samad ya canza ban sani ba nayi sakaci da yawa har na bari haka ya faru a yau da ban dauki mataki ba. Haka ya shigo ya samay ta tana wanan sambatun a cikin yan uwanta da suke ririke da ita kamar sabuwar mahaukaciya. Nan ya shigo baice da kowa kalaba cikin fushi ya shigo gidan don haka basu ga fuskan wani magana a gareshi ba. Tayo cikin shi da zagi tana fadin macuci mayaudari sai Allah ya isar min a gare ka har zaka dauki waya kabawa wata mace ta fada min wai baka da lafiya a wurin ta. Da karfi ya banbare hannun ta da ta rike mai wuyan rigar jikin shi ya fisge ya shige dakin shi a hasale. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Bai iya bata amsa ba sai kokatin wuceta da yake yi ya karasa cikin dakin rigar shi ta riko ta baya da mamaki ya juyo yana kallon ta. Shi da magana take mai wuya ina shi ina tsayawa fada irin haka da mace sau da yawa nafisa takan tunkare shi da irin wanan fita tana kokarin kama mai kaya ko ta sha mai kwala sai dai bai biye mata sai dai ya shige ya kyale ta tayi ta masifanta har ta gaji. Inda ita kuma a nata ban garen take ganin tafi karfin shi ne, dan bai da yadda zaiyi da ita dole ya zauna da ita take gani yau da ta cakuma rigar shi ta baya tana kokarin kaimai duka ya juyo da sauri yana fadin Nafisa ki na da hankali kuwa ? Cikin shi tayi tana banda hankali sai ka fada min wacce aka ganka da ita a asibiti dazun hannu yasa ya banbare hannun ta da karfi ya jefar da ita gefen kujera. Zafin kishi sosai ya rufe mata ido nan ta fara ja mai Allah ya isa ya ci amanan ta ya cuce ta sai taga bayan ko wacece ke son mata katsalandan a rayuwan ta. Yan uwanta suna tsaye cirko cirko suna kallon ikon Allah sai yare ne ke tashi suna magana rai a bace suna nuna goyon bayan yar uwan su. Harara ya watsa masu sai suka fara sulalewa daga falon kowa yana barin gurin don yanayin kallon da yayi masu din . Sama ya hau a hankali inda yake tafiya yana jin sautin kukan Nafisa yana isa inda yake. Tsaye yake yana balle bottom din rigar shi a hankali sai dai zuciyar shi cike yake da mamakin waya gan shi ya fada ma Nafisa cewa ya ganshi tare da wata mace a asibitin doctor Bisi.Doctor Bisi ne ya fada a ranshi sai kuma yace No it can't be doctor bisi is a man he can do such full to me. Beside, ma nine na hadasu da doctor bisi din anan don bata san kowa ba a Abuja sai zuwan da yayi da ita ne tasan kan garin. Bayan wucewan mijin nata ciki ne ta watsa ma yan matan uku da suga rage a falon harara tace a cikin yaren su na buzaye. Simi simi suka mike suka bar gurin itama mikewa tayi ta bishi ciki su karasa a can sai dai ta samay shi har ya shiga wanka ko. Zama tayi a bakin gadon cike da masifa tana jiran fitowan shi daga wanka su aza a inda suka tsaya. Zancen malaman ta ne ya fado mata a rai da kyat ta yaki zuciyar ta ta dan sasauta zafin da take ji nashi koda ya fito anan ya samay ta zaune cikin masifa bai kula ta ba ya fara gyaran jikin shi kamar yadda ya saba yi idan ya fito daga wanka. Kallo daya yayi mata fuska a daure ya kawar da kan shi gare ta ta mike ta tako gare shi tace samad ka daina ganin laifina. Ni kadai ce macen da ta dace kai a duniya da ina da iko ko macen kudi ba zan bari ta sauka a akan ka ba balle macen mutum. Ta hade wani miyaun fitina da yazo mata a makoshi tare da fadin nasha alwashin duk macen da tayi gigin shiga gonar ka sai naga bayan ta a duniyan nan. Kallonta yake da mamakin abinda ta fada yaga kuma gaskiyar maganan nata har cikin kwayan idon ta da gaskiya take maganan. Kuma ko wacece wanan macen sai na tono ta a garin nan na nuna mata ruwa ba sa, an kwando bane. Juyawa tayi ta fita daga dakin a fusace bayan taja wani uban tsuki tare da rufo kofan da karfi, binta yayi da kallo bayan ta fita ya girgiza kan shi ya tabe bakin shi gami da daga kafadan shi yace mahaukaciyar banza kawai. Karasa shirin shi yayi ya fara gyara gadon shi don yana bukatan ya huta don ya gaji yau sosai ga maganan Nafisa da ke ci mashi rai kishi kamar wace bata da hankali. Gadon ya hau ya kwanta bayan ya gama gyara yana sauke ajiyan zuciya a hankali may Nafisa take nufi da kalamin ta na sai taga bayan khadija. Yasan zata iya abinda ta fada mashi a yanzu karfa ya ja ma yarinyar mutane matsala a rayuwan ta don bai san abinda Nafisa zata aikata mata ba. Tunane yayi kada ya sare Nafisa ta samu daman da zats yi mai abinda taga dama a rayuwan shi don haka zuciyar shi ta bashi shawaran gwada Sa,an shi akan khadija ko zai yi nasara akai. Bai koma ta kanta ba yadda ya saba binta yana bata hakkuri har sai yaga ta hakkura yake samun saida a ranshi wanan karon sai yaji ba zai iya tunkaranta ya bata hakuri ba akan kuskuren da take tuhumar shi da aikawa ba. Kamar yadda Nafisa itama a dakin ta take zaune abin duniya duk ya damay ta ji take tankar tayi hauka don bacin rai wai yau samad din tane yakai wata mace asibiti ba ita ba. Wai wacece wanan da samad har ya iya tunkara da sunan so may take dashi may take tunkaho dashi a duniya wanda ake cewa tafi ta komai. Zubur ta mike ta fara zagaya dakin duk da dan cikin ta dake mata motsi a lokacin bai sa ta damu ta tuna da yadda take kaunar cikin nan ba. Kishi ne zalla a rayuwan ta kawai so take tasan wacece wanan yarinyar don tasan ta inda zata iya fito mata da shirin ta. Tana yi nata kallon lokaci don tasan dole yazo gare ta idan ta yi mai irin wanan boren nata sai dai a yan watanin nan tana ganin abubuwa suna son sauya mata sallo ga aikin ta. Shiko Abdul a dakin shi yana kwance barci yaki zuwa mai a lokacin tunane kala kala yayi shi a wurin Yusuf ya kirashi yana tambayan shi ko yaji yaya jikin nawa don ya kira wayana yana a kashe. Yace ban kirata ba don likita yace zatayi barci sosai a idan maganin ya fara mata aiki a jiki wata kila ta samu barci ne ta kashe wayan. Nan yake labarta mashi yadda suka kwashe da Nafisa da ya dawo gida hankalin Yusuf ya tashi yace sai nake zaton doctor ne ya fada mata tunda kace baku hadu da kowa ba a gurin. Yace idan shine ya fada mata kuwa yayi kuskure don cikin shi tayi don zan can za wani likita ke nan yanzu. Yusuf yace baka tunanen kada Nafisa ta gano a inda khadija take tayi mata wani abin yace haka ma ba zai faru ba zanyi tunane mafita akan hakan. Sukai sallama bayan sun gama tataunawa ga maganan ya kashe wayan yana gyara kwanciyar shi a hankali. Bai dade da gama wayan ba yaji an turo kofan an shigo dakin yasan ita ce don ita kadai ce mai shigo mashi daki. Ta karo gaban gadon ciki da mamakin ganin shi a kwance da tayi cikin rashin damuwa da ita har ta iso a gadon ta zauna tana fadin nasan ba barci kakeyi ba. Ya dago ido ya dan kalle ta yace banyi barci ba kuma hutu nake so a yanzu ta gyara zama tana kallon shi tace samad cikin sanyayar murya. Wai may na rage ka dashi a duniya may ye wanda ban maka har kake kokarin hadani da wata mace a duniya bayan kasan irin son da nake maka ba na wasa bane. Ta kamo hannun shi tana fadin gaba daya ka canza min a yan watannin nan ko dan ka gani da ciki ne ka dauko yimin hakan. Ka hana mu kwanciyar hankali gaba daya a gidan nan sai faman takura min kake yi ko yaushe. Sai ga hawayen da yaki zubu mata a daki yazubo mata a lokacin tace ko wacece sai na kashe ta a garin nan idan na gane ta. Cike da jin haushinta yace ashe ko ke ma za a kashe ki ke nan kinga matsalar ki ko meyasa ne har kullun ke baki tunane a rayuwan ki sai bakin kishi . Ni ina kokarin ganin ko yaushe inga lafiyan ki ke ko sai wani banzan kishi ke a gaban ki ban tsamaci haka daga gare ki ba na dauka kece mutum ta farko da zata shedi rayuwana a idon jamma,a. Yarinyace na kadai ta zan dawo gida in dubaki dole na dauke ta na kai asibiti doctor Bisi ya dubata ashe yariyar bata da lafiya shine ya taimaka mata. A rashin wayo na Nafisa sai cewa tayi ashe wanan likitan munafuki ne shine ta kirani yana fada min wai yaga ka kawo amaryan ka asibitin shi yanzu. Kawai may yake nufi don ya hada mu fada yayi min wanan maganan ko may yace da yake ke baki da tunane sai ki biyewa zancen shi ko ? Ace kulun mutum ba zai saka ma zuciyar shi salama ba koda yaushe sai bakin kishi ke baki hangen nesa akan ki fa duk yan uwana suke fushi dani. Hakan bai maki dadi ba sai kin tayar min da hankali kuuma har na tunzura na aikata abinda ban tashi yi ba. Tace da sauri don Allah samad kayi hakuri sherin shedan ne wallahi dana doctor Bisi sai da ta san yadda ta bashi hakkuri har ya hakura suka koma dai dai suka sulhunta kan su. Bai fita ba sai washegari bayan ya gama abinda yakeyi ya fice a gidan kiran Auta tayi ta fada mata ta koma kusfa ta fada ma malamin ta ya duba mata idan akwai matsala. Sai da ya duba wasu file ya dan huta tare da kiran layina maryam ce ta dauki wayan tana fada mashi ina bandaki amma naji sauki. Bai kai ga magana ba tace gani nan ma na fito tana mika min wayan tayi tana fadin yaya Abdulsamad ne a layin. Karba nayi tare da kara wayan a kunne nace hello cikin murya kasa kasa yace yaya jikin naki nace da sauki baki je class ba ke nan nace sai anjima zan shiga. Kin karya ko nace yanzu zan karya dai to idan kin karya kisha maganin ki zan shigo idan na rage aiki zuwa yamma in dubaki. Nagode na tsunci kaina da fadi Allah ya sauwaka ya fadi yana kashe wayan maryam tana gefe tana sauraren mu bayan ya kashe wayan na zauna saman katifa tare da kaiwa kwance. Tashi kisha tea din kada yayi sanyi gashinan na hada maki yamutsa fuska nayi nace miko min in sha bakinane bana jin dadin shi har yanzu. Daure dai kisha ko kadan ne sai kisha maganin ki gashi ta mike tana dauko min ledan maganin dake aje a gafen kayana. Tea din nasha tare da hade magani na koma na dan kwanta wayan daddy ne ya sake shigo min yana tambaya na ko lafiya jiya tanemi wayana yaji ta a kashe. Daddy iam sick yace may ke damun ki khadija murmushi nayi nace naji sauki ai period time dinane yake damu na amma kin je asibiti yace ? Naje daddy wanan mutumin ya kaini asibiti jiya yace good zan buga inyi mashi godiya don kwana biyu bai kirani ba yace nace bai kasan ne daddy ya kara da Allah ya sawaka ki kula da kanki ki abinda kika je yi khadija insha Allahu daddy na gode ka gaida mama. Madam ranan a gidan Nafisa ta wuni sun kule a dakinta suna jiran kiran Auta daga zaria suji abinda malam zai fada masu. Madam ta kawar da shirun da cewa wai shi wanan mijin naki wani irin mutum ne da baijin magani haka sai anyi kamar an samu kanshi sai abu ya zo daga baya ya can baki daya. Tace shike damu na madam dubi irin kudin da nake zubawa akan bawan Allah nan sai naga nasara daga baya sai komai ya lalace. Komai zan iya yi akan Samad din in dsi zan samu ya kawar da ido akan ko wace mace a dunuyan nan. Madam tace idan shiya kawar da idon shi a kan mata su matan kina tsamani zasu kawar da ido su ne akan shi dole suma dole da tasu shirin da suke don suga sun kamo shi. Don shegen kyau da daukan hankalina da wanan mijin naki ga abinda mata keso a tare dashi kudi da kyawo da hali. Hankalin Nafisa ne ya tashi sosai da maganan madam tace wallahi da ina da hali da boye shi zan dinga yi a gida. Dariya madam tayi tace idan kika boye shi kuce may ke da yan uwan ki Nafisa karki matanta shine hannu da kafar ku kaf zurian ku. Yanzun dai zan tafi Ondo ance akwai wani boka acan may aiki kamar yanka yuka wata kawatace ta gano hakan. Nikan ina can na dan samu karfin jikina shiryawa nayi zan leka cikin makaranta don kada a wuce ni da karatu da nazo yi. Daddy ya kira Abdul yana mashi godiyan kaini asibitin dayayi yace ba komai insha Allahu zai kula dani kamar yadda zai kula da kaunar shi. Bayan ya gama abinda yake ya kira Yusuf don su leka wurina kafin yaje gida Yusuf din yabar abinda yakeyi yazo suka tafi. Sun samu na dawo ke nan ya kirani a waya na fito na samay su a waje lokacin da na karaso wurin su na samu suna magana suna kallon laptop din dake a saman kafan Abdul din nasan wani abu suke duba a ciki. Karasowana suka bar abinda sukeyi din tare da maida hankalin su a gareni Yusuf ke fadin lalai jiki yayi sauki kauna na sai dai har kin dan fada kadan wallahi. Murmushi nayi na dan jingina jikina ga motar su nace naji sauki sosai yusuf yace barin in dan je can inga shagon yan makaranta indawo ina son duba wani abu a gurin. Nasan yayi haka ne don ya bamu wuri mu gana dashi wuce wanshi yace dan gyara zama yana fadin abin ya daina zuba ke nan ko ? Harara na aika mai tare da fadin ban sani ba sai ka fito ka duba ai tunda kana son sani ne sai yau naga dariyan shi yace kin dai ji abinda likita ya fada saukin abin ai. Banji ba kuma bana son naji tunda ba kai ke da lalurar ba au yanzu tunda kinji sauki kina da bakin magana ashe jiya fa nan kike ta murdemurde ina tausaya maki. Kawar da kainayi gefe guda ban bashi amsa ba na share shi yace na tambaye ki jiya ciwo ya hana ki ban amsa na. Nace may ka tambaye ni jiya din yace kwana nawa kike dauka kina off shiru nayi tare da bashi ba a raina ina fadin wai shi baisan ina matukar jin kunyanshi bane da yasan abin dake damu na. Gashi kuma ya tsare ni da tambaya irin haka da zai sani jin kunya da nauyin shi ai wanan kamar kamar yar iska ya dauke ni. Niko gidan mu in badon ciwon mara ba har zanyi in gama basu sani ba ji nayi yace may nene abin jin kuya kibani amsa na kawai don ya kama ne in sani. Nace don Allah yaya Abdul ka daina wanan zancen naji yace na daina tunda baki son zancen yanzu. Badai kina shan maganin ki ba akai akai nace ina sha na gode daddy ma ya bugo waya nake fada mai ka kaini asibiti yace zai kiraka yayi ma godiya. Yace ya kirani ai dazun sai danace mai kaina nayiwa aiki ba sai ya godd min ba nace ka fada ma daddy hakan ? Yes ya dace ne in fada mai don lokaci yayi da zai fahinci hakan daga inda Yusuf yake tsaye yake kallon mu yana jin farin ciki a ranshi. Hikimar yin haka da yayi ke nan a gusa daga wurin don mu samu daman sakewa da junan mu don idan yana wurin komai bazai wakana ba a tsakani karshe ma muna iya yin abinda muka saba fada ke nan. Ka samu zuwa duban su Affan kuwa na kawar da zancen da wanan tambayan murmushi yayi yace ban samu komawa ba sai dai na fara shirin komawa. Sai dai wanan karon ban san wani shiri kikai ma tafiyan nawa ba idan zan koma nace dama idan zaka nike shirya maka tafiyan. Yanzu shirin ya dawo kan ki don haka kece mai shirya komai ta wanan bangaren ya kamata ace na fara maki albashi a wanan bangaren don kin ci hakan a gare ni . So ki fara shirya min nan da two weeks zan tafi ina jira inji shirin da kai ma tafiyan nawa da abubuwan da zan yi a can. Yusuf ne ya iso gurin yana fadin mu tafi ko kada lokaci ya kure maka anan tunda munga lafiyan kaunar tawa sauki ya samu. Har kagama duba shagon nace mai yace ko dai in koma ne kada in takura maku kuna hiran ku na jin dadi zan katse ku kai haba yayana wani hira kuma a haka ? Ni dai daukar shi ku tafi kada yar buzaye tace ina shigewa mijin ta yanzu Abdul yace kina tsoron ta ke nan ? Nayi saurin fadin tsoro fa tsoron mace yar uwana kuma macen ma kuma buzuwa da kyau kauna ta haka nake son naji mace jaruma wallahi. Kai kaji ya juya wurin Abdul din yana fuskantar shi tare da fadin na fada ma kauna ta jaruma ce ba irin ka ba mai tsoron buzaye yan haure. Idan bata tsoro ai sai mu gani a kasa ba cika baki a nan ba nace ko agaban ta wallahi zan cika baki idan ya kama in cika akan may zanji tsoronta ne wai ? Mace ce fa yar uwata kowa sai ya gwada sa an shi yayi mai fishe shi duk abinda take takama dashi wallahi ni khadija ina dashi fari kyau da tsayi kagako ba zanji wani shakkata ba. Irin kallon da yake jifana dashi daga cikin motar yasa nayi shiru dole don kallone da ke dauke da fassara irin mai nuna feeling ga mutum din nan. Mun gama shan matan juna suka ja motar su suka tafi ni kuma na koma ciki tare da tunanen da yawa a raina na canjin yanayin da na hango a kwayar idon shi. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Alhamdullahi mun sauka lafiya inda na samu maryam ta dawo ko saboda kwanakin da na kara ta rigani shigowa na samu har ta gyara min daki ko. Anan driver ya zube mu ya wuce abinshi ko ba a fada min ba nasan anty ta biyoni ne don taga yanayin zaman da nake a Abuja inda tazo da sunan kwana daya sai gashi ta share biyu kuma muna tare da ita ban je ko ina ba. Washe gari da safe na rakasu tasha suka shiga motar kaduna suka tafi bayan yan nasihohin da taimin na in kula da kaina in maida hankali ga abinda ya kawo ni. Muka rakata garage ta shiga motan kaduna wanda ta dauka ita kadai sai yaranta har kaduna mun dawo hotel a gajiye don haka na kwanta barci don nadan ji dama jikina. Tun da na kwanta ban tashi ba sai bayan sallah la,asar na tashi nayi wanka na tare da gabatar da sallolina ban dade ba maryam ta shigo tana fadin kin tashi ? Nace wallahi tace ga abinci nan ki cikin kula idan kin tashi ci ni na koshi sauran kayan bukin da ya rage na zauna ina ci nace abinci sai da dare. Ina zaune kamar daga sama zara ta shigo dakin nace mutumiyar ashe ke ma kin dawo ke nan tace dazu fa na gama tunanen ki. Zarah tayi dariya tace ai ni na riga ku dawowa tun wancan satin daya wuce na dawo school da sauri nace ai lokacin ba ai resuming ba. Ta wallahi gajiya nayi da zaman gidan shine nace hutumu ya kare aka shiryani na dawo school kaina jinjina nace Allah ya kyauta da halinki zarah tunda har kin san ki aikata haka. Dariya ta sake min tana fadin gidan ne babu dadi yanzu da na saba da ruyuwan independent din kaina . Sai da taci abinci a dakin ta koshi tana bani labarin tafiya sukayi da saurayin ta ta raka shi kano shiyasa ban ganta ba maryam baya ta bamu tana diban takardun da take hadawa har zarah tabar dakin. Sai lokacin ta juyo take ce min irin wa yan nan bai kamata mutum yana hurda dasu ba ai kada su bata ma mutum suna a banza. Nace yaya zanyi mun fito gari guda da ita bazan iya kyale ta ba ai kin ji dai ina bata shawara ko zata daina halin nan da tasawa kanta. Allah ya kyauta tace muka canza hiran kada muci namanta bamu sake fita ba har gari ya waye muka shiga school. Wanan karon Nafisa bata yar da ba dakanta ta shirya tafiya zuwa kaduna bayan ta dawo Niger don an bata labarin wani sabon malami a Kusfa. Abdulsamad bai hanata zuwa ba don tace kaduna zata leka don ta kwana biyu da zuwa shiri sosai yayi mata don zuwa kadunan a ganin shi ai gida zata. Ranan da ta isa kaduna bata samu zuwa ko ina ba sai washegari suka tafi ita da Auta yar take ga su Abdul din sai dai halin kwadai irin nata zata iyayin komai akan kudi. Haka yasa suka kule sosai da Nafisa har aminci ya shiga tsakanin su tana mata shige shige dama Auta irin yan duniyan matan nan ne tunda ta fito gidan mijin ta bata sake aure ba tana zaman rayuwa kawai a gida. Su biyu sukai tafiyan sai driver daya kaisu bayan sun gama yi ma malamin bayanin komai ne malamin yayi dariya yace kamar yadda take zargi gaskiyan maganan ke nan ya fada tarkon son wata yarinya a yanzu sai dai abin bai wani yi nisa sosai ba. Idan kuma bata bi alamarin a hankali ba zafin kishin da take nunawa ne zai sa komai ya iya faruwa da ita. Hakalin ta ya tashi sosai wanan ne mutum na biyu daya fada mata haka malamin yace alamarin yarinyar yana da karfi sosai. Don asiri baya kamata kai tsaye da zaran zamcen yakai ga iyayyen shi komai zai iya faruwa a tsakanin su a yadda bata zata ba. Don haka sai kin natsu aiki zamuyi maki wanda zaki kama mijin ki a hannun ki indan shi ya kamu yadda muke so komai zai iya zo maki da sauki. Amma koda zakici nasara akan hakan sai kin bi a sannu don yarinyar tafiki komai da kike tunanen kina dashi abune wanda sai an aiwatar dashi a sannu saboda mijin ki yana mata mugun son da bai san yana mata ba. Nashiga uku tace malam tafini komai fa kace yace kwarai da gaske don gata nan a gaban mu kina gani ta shige maki gaba ko a wurin shi. Kuka ta fara tana fadin don Allah malam kai min rai ka taimake ni ko nawane zan iya baka indai zaka min aikin da za a raba su hayatan hayatan ya ji bai kaunar ta ko kadan. Gaba daya yanzu na daina gane kan shi ada komai yana min kai tsaye yanzu sai yaja min rai yake min abu da na dauka ko cikin dake gare ni ne yasa yake min hakan. Yace magana dai guda ce ga yarinyar nan kina gani taurarin ta na da matukar haske sosai duk abinda ta sama gaba takan cin ma nasara a kan shi lokaci daya. Yana nuna masu zanen da yayi a kasa wanda su basu fahintar abinda ya zana sai dai bayanin da yake masu wanda ke matukar tayar wa Nafisa da hankali. Yace saukin abin daya ne yarinyar mijin ki baya gabanta don wani dalili nata amma shi yana kokarin cusa kanshi ko yaushe a wurin ta ne. Tace da karfi shi samad din malam yace kwarai kuwa muddin muka ce zamuyi aiki na gagawa komai zai iya faruwa na fada maki. Idan baki yarda ba zaki iya zuwa gurin wani kiji nasan duk wanda zai fada maki tsakani da Allah ba zai fada maki sabanin abinda na fada maki ba. Tana share hawayen dake zubo mata take fadin malam yanzu may ye abin yi don ko yanzu da dabara na samu nazo nan din. Wanan ba wani matsala bane aiki zamuyi mashi wanda hankalin shi zai fita a kan wata mace baki daya sai mu cus mashi kaunar ki ke kadai. Ta gyara zama tana fadin in hakan zai samu malam shi nafi bukatan ai min a kan shi a raba shi da ko wace yar iska ce kison tayi min kutse a gidana. Ya zayyana masu aikin da zai masu din ta yarda ta amince zata biya makam din abinda ya bukata a wurin ta suka biya shi ba tare da taji komai ba sukai mashi sallama. Tun a mota take zazaga balai tana zaginshi da iyayyen shi Auta tana kara zugata da fadin wanan wata irin yarinyar ce da za a ce ta fiki komai har kyau ke nan malam yake nufi ko may. Don banda kyau babu wani abu da Nafisa ke kadagi dashi don ba arabi ba boko haka take dip dinta bakauya kuma. Koda ta dawo kaduna bata biya gidan su Abdul din ba bata mayi tunanen shiga gurin su ba don daukan su take a makiyan ta dama balle yanzu da sunan su ya fito ga zancen. Kwanata uku a kaduna bayan Auta ta koma ta koma ta karbo abinda zasuyi amfani dashi idan ta koma sauran sai ya hada yace zai kira Auta ta karban mata don sai ya nemi abin hadi. Haka ta shirya sai da zata wuce ne ta dan shiga tsatsaye ta gaida su hajiyan shi da sauran mutanen gidan ta juya suka tafi. Almarina kuwa tunda na dawo sau daya muka hadu dashi koshi a tsatsaye don ina sauri zan tafi class karatu don muna da test din da zamuyi washe gari. Yazo min da provition mai yawa kamar ba gobe har sai danace kayan suyi min yawa yace naci da kawayena. Sun tafi abisa alkawrin zamuyi waya amma har wani lokaci bai kirani ba Yusuf ma haka bai kira ba nikan haka yafi min nono fari. Don dama neman mafita nake dashi kuma na samu yanzu sun sarara min ranan muna hira da maryam take tambaya na su. Nace banji komai daga gare su ba na nuna mata ni basu gabana yanzu abinda ya kawo ni nakeyi. Tace kai amna abin mamaki ne khadija ace sun share ki haka ba labarin komai daga wurin su ko yusuf ai ya kamata ace ya kira musan halin da suke ciki. Ke kuma baki neme su ba halarci baice haka ba fa khadija shiru nayi mata don mu kawar da zancen su da ta dauko min ina zaune kalau. Sai bayan da na kwanta sai kuma maganan ya damay ni a rai gaskiya maryam ta fada min ya kamata ka kula mai kula ka koba komai zai san ka damu dashi ai. Ranan da kyat na samu nayi barci da tunanen su a raina sai dai ni ba zan iya kiran shi ba sai dai dan dama dama Yusuf din. Washe gari haka na tashi da jin bakin rai a zuciyata sai dai kawai na danne abin a raina don na kudurta a raina ba zan taba kiranshi ba indai nice zakira inji ko lafiya suke. Tunda dama ba wani soyayya ko wani abu ke tsakanin mu haka ba mai karfi kawai dai ya gaji danine shima ya hutar da kan shi. Na share kawai kada maryam ta fahince ni na shirya muka nufi cikin school don daukan lectures na watsar da maganan su a raina kada in sa wa kaina damuwa a banza. Alamarin gidan shi kuwa yanzu tun dawowan Nafisa daga kaduna sallon zaman su ya sauya don yana dan samun kulan daya kamata daga gareta duk da ba wani dadin yake ji ga hakan ba don baya samun sakewa har yanzu a gidan shi yadda yake so. Shima Abdulsamad din ina a ranshi yakan so ya kirani yaji lafiyata sai dai yanzu duk lokacin shi na aiki ne dana Nafisa a haka har yayi tafiya tare suka ketara da nafisa zuwa wanan tafiyan. Satin su biyu suka dawo Nigeria koda suka dawo abuja bai samu kafan kiran na ba don Nafisa ta mamaye komai a lokacin. Yau suna tare da Yusuf a office din shi Yusuf ma wanda yayi tafiya yake tambayan shi labarina ya yamutsa fuska yana fadin wallahi banda labarin ta itama bata neme ni ba. Yusuf yace haba kai ma kasan bazata nemay ka ai, amma hakan bai mun dadi ba wallahi dakace baka kirata ba waya ya dauko daga Aljihun shi ya fara neman layina a lokacin. Ban shiga school ba ranan don na tashi da ciwon mara ina kwance a dakin mu ko karyawa ban yi ba har lokacin don haka ina cikin barci mai nauyi daya dauke ni naji kira a wayana. Da kyat na lalubo wayan dake gefe na ina jan tsakin wanda ya tayar dani a wanan lokacin dana dan samu sa,ida na samu barci ya dauke ni. Koda na dauko har kiran ya katse sunan Yusuf na gani akan wayan ban kai ga tunane ba wani kiran ya sake shigowa again. Tunane nake a raina may kuma zai fada min yanzu mutanen da suka shareni kusan wata daya ke nan yanzu kuma zai kirani yace min may ? Kamar in share shi kiran ya katse sai dai na danna recieve inji abinda zai fada min a lokacin na amsa da sallama cikin muryan barci da yanayin ciwo a tare dani. Naji yace subbahanallahi khadija baki da lafiya ne may ya samay ki naji muryan ki a haka ? Da sauri ya dago kai yana kallon Yusuf dake magana a waya yaji yace ayya sorry sannu ko kin je asibiti ne nace nasha magani ai ba sai naje asibiti ba. Idon shi har lokacin yana akan Yusuf din yace may ke damun ta ne naji Yusuf din na fada mai wai banda lafiya ne a kwance nake ma. Taje asibiti Yusuf yace tace ba sai taje asibiti ba wai karban wayan yayi daga hannun Yusuf din naji muryan shi yana fadin ki shirya yanzu gani nan zuwa nakai ki asibiti ya fada kai tsaye. Nace naji sauki ba sai kazo ba na kashe wayan wayan ya kalla tare da mikewa tsaye yana rufe file din dake gaban shi ya fara tafiya. Yisuf dake zaune ya mike juyowa yayi yana fadin ka zauna ka karasa aikin barin je na ganta in dawo Yusuf yace amma kana ganin zata saurare ka idan kaje kai kadai. Wani kallo yayiwa Yusuf din kamar zaiyi magana sai kuma ya juya ya fita Yusuf ta girgiza kai yana murmushi halin abikin nashi na bashi mamaki ace mutum haka da girman kai. Nikan ina kashe wayan naja tsuki nace mayaudari kawai naja filo na gyara kwanciya na barcin da ban koma ba kenan idona a rufe nake tunane nace yanzu na tabbatar da karkashin mace yake. Wata kila matan shi tasamu labari ne ta hana shi kula kowa yanzu ya dawo zai yaudare ni kuma ya bata min lokacina a banza. Dama ban sa zancen ko kadan a raina ba balle ya damay ni in ma junin shi iya yaudaran mata ne ya bata masu lokaci Allah ba zai bashi saa ba anan naja tsuki na gyara kwanciyana. Na samu barci ya fara dauka na naji wayan shi ya shigo min na duba na bar wayan nata ruri har ya katse kira uku yai min ban daga ba . Ranshi ne ya baci sosai yana shirin juyawa sai ga maryam kamar daga sama ta dawo don hankalin ta bai kwanta a yadda ta barni ta dawo ta dubani. Sai ganin shi tayi yana shirin juyawa da sauri ta karsa wurin shi tana gaidashi tare da fadin wallahi tana ciki bata da lafiya ne tun jiya nima yanzu na dawo in dubatane. Yace shi yakawo ni yazu asibiti nake son zuwa da ita a ranta tace boye min khadija ke nan rayi ashe suna waya dashi shine take boye min. Taji yace nakira wayan ta taki ta ga bayan yanzu Yusuf ya gama waya da ita ta fada mai bata da lafiya tace barin shiga in fito maka da ita nasan fushi take daku. Fushi ya tambaya da mamaki dariya tayi tace ina zuwa don Allah ta wuce ya bita da kallo har tabace yana mamakin kalamin ta wai fushi take da ku fushi akan may ? Tana shiga dakina ta nufa ta samay ni a kwance zama tayi a gefe na tana min sannu tare da fadin ga mutumin ki nan a bakin get yana jiran ki wai kuje asibiti yanzu. Wani kallo mai kama da harara na watsa mata nace rabu da mayaudari nine zai kai asibiti akan may zai zo min a yanzu da bana son ganin shi. Haba khadija kin san uzurin da ya tsayar dasu basu nemay ki ba tunda har yanzu ya iya zuwa da jin baki da lafiya ai ya kamata ki saurare shi. Haba maryam abinda kika sani ne nafi jin dadin zaman da nake yanzu babu takuran kowa a kaina akan may kuma kike son in kara fadawa tarkon mayaudari irin wanan mutumin da matar shi tafi karfin shi kuma. Kada kice haka khadija ko ba komai ya nuna kulawan shi a kan ki yanzu ina laifin wanda ya nuna maka haka a lokacin da kake cikin halin ciwo. Don Allah ki tashi ki daure badon ni ba sai don Allah ki tafi ki ganshi ko ba komai zakiji abinda ya tsayar dasu kwanaki mai tsawo haka baki ji su ba. Allah da kika hadani dashi ne zai sa in tafi badon wani abu ba can nasa, don ina son inyi nisa da shuumancin su yanzu tace daure kiwa Allah da kika ce zato kike yanzu kila ma ba matar shi bace ta hana ya kulaki. Kalaman ta yayi tasiri sosai a raina koba komai ina son jin abinda ya hana injisu kwana biyu don ban sin jawa kaina wulakanci ko kadan. Ita ta taimaka min na shirya atamfa na daura don yanayin da nake ciki tare muka fito zuwa ida yake zaune a motar shi. Yana yi yana kallon agogon hannunshi can ya ga fitowan mu tare da maryam ina tafiya da kyat yanayin ina jin jikin nawa sosai. Har muka karaso bai dauke idon shi a kan mu ba yi hakkuri mun barka kana jira wallahi barci na samu tanayi yanzu na tayar da ita. Bai yi magana ba sai kallona yayi yana fadin shiga mota mu tafi nace basai naje asibiti ba na sha magani naji sauki ina magana da kyat cikin daure fuska. Shiga muje nace maki da sauri maryam ta riko min hannu ta nufi gefen mai zaman banza tana bude min motar tare da fadin sai kun dawo Allah ya sauwaka. Sai da na zauna da kyau ya tayar da motan muka hau dogon titin da zai kaimu cikin gari sai da mukai nisa kaina da duke na dafe goshina da hannu na daya naji yace. May damun ki ne haka ban bashi amsa ba sai gyara zama da nayi ina cije baki don dan motsawan da nayi maran yana min ciwo yanzu. May damun ki ya sake maimaitawa shiru nayi can nadan sauke nufashi nace da kyar banda lafiya ne kawai tare da dan dafe mara na. Au ko abin ne yazo maki na manta yanzu kike cikin time din period din ki ko hararan shi nayi tare da kawar da kai ina cewa a raina kaji min mutum da bin didigi haka ? Kwana nawa yakeyi halan sake dago kai nayi na kalle shi kamar bashi yake maganan ba nayi saurin kawar da kaina daga kallon shi. Yace bakiji bane kwana nawa kike dauka kina period din nace ya fada tare da dan kallo na nace ban sani ba kada ka wuce hurumin da ba naka ba mana na fada ina kwantar da kaina. Murmushi yayi yace haka kike ce ko nace na fada din ni banga dalilin tambayana haka ba kai ba likita ba wani sai nayi shiru. Yace go ahead you say your words out, shiru nayi tare da kawar da kaina gareshi gaba daya ya sake fadin you free to say komai zaki iya fada don ance fushi kike damu. Da sauri na jiyo ina kallon shi nace fushi fa akan may zanyi fushi daku in ba ina son sama kaina nauyin da bai hauni ba ? Murmushi yayi da sai ka saurara zakaji shi yace kwana biyu bamu kasan ne daga ni har Yusuf na fita da madam dina ne mun tafi check up ciki ke bata matsala. Don Allah malam ni ban tambaye ka ba in zaku iya ma ku tare a can ba damuwa na bane wanan ciki kuma Allah ya bata lafiya ya sauketa lafiya amma mi ya hadani da tafiyan ku kuma. Kwana yasha muka shiga wani clinic inda yasa na fito muka shiga guri ya sama min na zauna ya nufi gurin tankan kati ba mu dade ba duk da mun samu mutane a gurin yace in taso mushiga gurin likita. Mun shi likitan yare ne don turanci suke dashi sun gaisa naji likita na cewa kayi sabin aure ne ashe yace mashi eh yace madam ta kwana biyu bata shigo ciki ya zaunu ko yace eh a gadarance yake ma mashi magana yace ina son ka duba min ita tana fama da mesturalpain ne. Yace ayya sorry madam yakamata ace ya rage maki ciwo yanzu da kiyi aure ya kamata ace kin rage jinshi haka indan zakiyi period don agana kawai matsalan hakan. Nauyi kunya ya rufe ni a wurin na kasa daga kaina shima wayan shi yake dakila baibi ta kan likitan ba sai da likitan ya fara tambayana ina mashi bayanin ya dago yana kallo na. Tashi nayi zuwa inda likitan yace in kwanta ya dan dadana cikin nawa na dan sake kara daidai kasan mara na daya tausa da dan karfi yace in tashi ya dawo ya zauna yana rubutu a wani farin takarda ya mika mai lokacin na dawo na zauna dakyat dafe da marana dake min tsananin ciwo sosai. Bayan ya mika mai yayi mai bayanin anemi wanan maganin in sha zasuyi min allura kuma zan samu sauki da yardan Allah ya mika mai hannu tare da fada mai inda zamu kai takardan a duba ni. Sai da muka gama komai muka fito yana min sannu muka dauki hanya wani shago ya tsaya yace min yana zuwa ya shiga ciki yadan jima sai gashi ya fito yaron shagon na binshi a baya dauke da wasu manyan ledoji biyu a hannun shi. Ya saka bayan motar ya shiga muka tafi bayan ya mikawa yaron kudi yana mashi godiya kaina na duke yace sannu likita yace zaki samu sauki dan anjima kadan amma zaki barci sosai ki ci wani abu don kince baki karya ba. Bana jin shi do murdan da mara na keyi ina dan cije baki ina jijiga kafa na da matse hannaye na duk yadda na so in daure na kasa sai da na yi ya gani a bakin down hostel din mu ya tsaya da motar shi. Zaki kara kawar ki ta taimaka maki ne ko in taimaka maki ki fita duk da ciwon da nake ji sai dana harare shi na bude motan na fita ko godiya ban mashi ba. Ina fita yace turo min kawar ki ta daukan maki magani kai na iya dagawa na shige ciki na samu maryam na girki a dakina din bata da kiuyar girki ita tana gani na tace har kun dawo kaina gyada mata na fada saman katifa nace yana kiranki a waje. A saka hijab da sauri ta fita daga dakin zuwa wurin shi bata jima ba ta dawo dauke da ledojin nan da ya sayo tace yana maki sannu wai sai kunyi waya yace kici wani abu kafin ki kwanta. Itace ta zauna ta bude ledan kayan ciyeciye ne a cikin dana sha tarkace dai gasu nan sai dayan ledan dake dauke da pad din mata always kamar mai bude shago dashi ban san ranan da zai kare ba. Abinci ta debo min na dan ci kadan na kwanta sai barci mai nauyi ya dauke ni a gurin ban kara sanin inda nake ba kuma. Yana fita ya daga wayan shi six miscall ya gani na Nafisa da sauri ya danna wayan ya kirata yana fadin sorry ina wani abune yasa banga kiran ki ba. Tace Samad ina kaje wacece akace mi an ganku tare a asibitin doctor Bisi yanzu waka kai asibiti wata macs ce aka gan ku tare tare ta fada cikin tashin hankali. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Washe gari muka shirya zuwa beji duba wani kakan mu dake zaune acan kanin mahaifin maman mu ni da ya Amina da yaran su. Bayan Nkwa bamu iya wani gaisuwan kirki ba sai habalu da sauran kananin kalma irin na gwarawa da muka rike a bakin mu. Tsohon yaji dadin ganin mu yana ta murna da zuwan mu gidan duba su anan muka wuni tare da su sai yamma muke son mu dawo mu biya maikunkele gidan iyayyen mama din. Tsohon bagwaren yana waje zaune da bakon shi muka fito zamu wuce muna masu sallama bakon nashi ne yayi yare sai naga tsoho yayi dariya tare da fadin yaki nan amarya na. Nazo na duka a gaban shi yace bako na ne ke son ganin ki sai na gaida dattijo ya mika min hannu alaman in bashi nawa hannun. Ban ki ba nayi kamar yadda yace min sai da ya kalli tafin hannu na da kyau yayi murmushi yace Allahu akabar akwai tarin alheri ga wanan hannun naki sosai zan ba kaka ku wani abu ya baki gobe ba mai wuya bane abin inda zaku tsaya na awa daya zan iya hada maki ko anan ma. Don tsari juyawa nayi na kalli ya Amina tace ai zamu iya tsayawa mu karba nan saman tabarman muka zauna ya bude jakkar shi ya ciro wani dan farin abu a wani kwanko yayi ta abinda zaiyi a abin sai ya miko min hannu na mika mashi nawa. Ya fara murza min abin a tsakiyar tafin hannu na har saida abin ya bace bat a hannu na ya dan dade rike da hannu na yana min tofi har kaina sai daya dafa yayi min yadda yayi a hannun ya sake ni dama tsamin jikin shi duk ya isheni sosai. Ya Amina ma tace aiwa yaranta da ita ba irin wanda yayi min yayi mata ba zamu tafi na bude jakka na fido dubu daya na bashi ya girgiza kai. Yace idan ina da dari biyu in bashi kawai yaci goro dashi na duba naga wani sabon dari biyo na dauko na bashi nayi mai godiya muka tafi. Muna cikin mota ya Amina tace na rasa may sa tun kina karama idan mun fita ke kawai mutane ke taimakawa wanan karo na biyu ke nan da haka ya faru dake. Nace su suka san abinda idon su ke gani a kaina wanda mu bamu gani hakan dariya tayi tace kila ya hango maki buzuwan ku ne . Kai ya Amina may yasa kuke fadar haka ne karfa maganan nan yakai kunnen su mommy da yan gidan su fa. Tace indan ya kama suji ai ji zasuyi khadija lokacin jin su ne baiyi ba kawai amma duk wanda yaji mamaki zai yi wallahi. Sai dare muka isa gida don mun bata lokaci a maikunkele wurin yan uwa da abokan aarziki ko da muka dawo wanka kawai nayi na samu wuri na kwanta abina. Da safe muka tashi da labarin haihuwan antyn mu Anty Hauwa dake aure a pilamigo easther wanka mukayi muka nufi gidan ta acan muka wuni sai four muka baro gidan ta. Koda muka dawo gida mama tana dora girkin dare sakwara zatai muna da miyan egushi tubewa nayi na fara taya mama aikin dakan sakwara don doyan ya dahu ko. Ya Amina data fito dakin ta tsaya tana kallon yadda nake dakan sakwaran ta kwashe da dariya tace ashe kin iya idan nace muyi sai kice bakya son ci. Sallaman da muka jiyo a kofan shigowa gidan mu ya hana ni bata amsa naci gaba da dakan sakwarana. Anty Amina ce ta dan leka raga mai sallaman sukai kicibis da Yusuf a tsaye yana gyara rigar shi da ya dan takure ga zaman mota. Kamar daga sama ta san shi a gidan su mommy shine dai bai santa ba tace cikin mamaki Yusuf kune tafe haka da yamman nan ? Yayi mamakin sanin shi da tayi haka shi bai santa ba sai dai ya gane muna da kama da ita sosai sai dai tsayin da nafita da kuma hasken fata don ni daddy na fadin gidan mu na debo sosai ina da zubin fulanin su na ka,aje ne. Ta juya tana fadin barin sanar da Khadija gata can yau sakwara take daka muna a gidan yayi dariya ta wuce ciki ina ganin ta shigo tana dariya ina rike da tabarya mama na duke tana saka wanda na daka a leda tace khadija ga ki da baki fa a kofan gida. Da sauri nace da ita su waye ya Amina tace wa kike tsamani zai zo maki yanzu banda su Yusuf da abokin shi nace kai haba dai ya Amina may zai kawo su nan in ba gulma ba. Tace to gulman ko ya kawo su gasu can a waje dai nace wai da gaske tace ina wasan haka dake ne dama tabarya na aje ina fadin yau na shiga uku. May suka zo yi yanzu kuma don Allah tace kyaji idan kin fita ai ni wallahi sai naci masu mutunci don may kuma zasu biyo ni har gida haka ? Harara mama ta watsa min tace idan zaki natsu ki natsu kije ki gan su falo ya Amina ta shiga ta fara gyara wurin inda zasu zauna ko kafin in fita na samay su da daddy suna gaisawa a waje na juyo na dawo ciki abina. Har ciki daddy ya shigo dasu ina labe a dakin mu ina kallon su sai da suka shiga sun dade ciki da daddy da ya Amina kafin ta fito ta kwala min kira ban fito ba ta samay ni a dakin tana dariya. Ya Amina may wanan mutumin ke nufi da nine wai for god sake may ya kawo su har gidan mu ne don bata min suna. Kallona tayi da mamaki tace zuwa gidan ku shine barnan suna khadija ai gara da suka zo zai fi hankali mama ya kwanta. Ni kan na shige su wallahi tace don Allah ki natsu kije ku gaisa sunce hanya ne ya biyo dasu nan suka ratso su gan mu. Ina shiga na samu har da abinci aka aje masuz sai hira Yusuf keyi da daddyn mu shiko sarkin miskilanci ido kawai ya zuba ma kofan shigowa falo. Da sallama nashiga tare da samun wuri gefe na zube gwaiwa na a kasa ina gaida su Yusuf ne ya amsa min shiko ido kawai ya zuba min kamar yadda na samay shi zaune. Daddy ya fita falon yana cewa dasu yana zuwa ya fita daga falon bayan fitan daddy ban daga a yadda nake na dago ina kallon su nace may ya kawo ku may kuka zo yi gidan mu ? Baiyi magana ba sai bude kula abincin yayi yana kallon sakwaran tare da fadin ke kika yi wanan abincin wai ? Yaya akayi suka san haka nake tambaya kaina a zuciyana Yusuf ma budan abincin yake yana faadin yar mama ashe kin iya girki ne haka ? Yayana may kuka zo yi nan yace gashi kinga munayi kawai dai mun yi marmarin cin girkin gidan ku ne mukazo muci dan harara na aika masu. Abdulsamad din ne yace kina ganin zaki iya kashe min waya don kada na kiraki da sauri nace ni ba kashe ma waya nayi ba. May yasa baki kuna wayan naki ya tambaya cikin kura min idanuwan shi dake ban tsoro yanzu nace wayar ce bata da lafiya. Baiyi magana ba ya fara cin abincin ba ko kunya hankali a kwace nace baku da kunya ne zaku ci a binci a gidan mu ku wai wasu irin mutane wai ? Ruwan abincin gidan ku zaki muna ya fada nace ni naci na gidan ku ne to yace wayasan iyaka wallahi ban taba shan ko ruwan gidan ku ba ni. Yusuf yace saboda may yar mama yana kai lomar sakwara a bakin shi kunya su nake ji ban iya shan ko ruwa a gidan don nauyi. Ashe ko kin cuci kan ki don ni dai a sani na gidan mu bako bai shiga ba a tare shi da abin sha ko na ci ba daddy ya kwala min kira daga cikin gida na mike na fita da sauri ya daga kai ya bini baya na da kallo. Saurin kawar da kanshi yayi yana cin abincin da yaji dasin dan danon shi har cikin ranshi ina fita naga baba da leda ya sawo drinks. Yace in kai wa baki a falo a tire na saka nakai na dire masu a gaban su nace gashi kun sa baba kashin kudi bai shirya ba. Murmushi magana na yadan yi sun ci abincin sosai suka wanke hannu na fita da kayan bayan sun gama ne suka ce inyi masu iso su gaida mama zasu tafi. Fita nayi na kira ya Amina ina fada masu abinda suka ce man ita ta fada ma mama zasu shigo su gaida da ta nan mama ta gyagyara suka a kofan daki aka shimfida masu tabarma suka zauna. Bayan fitar sune na samay su a waje har sun shiga mota ina isowa Yusuf ya miko min waya kallon wayan nayi ina tambayan shi ta may yace ogana yace a baki tunda naki ta lalace kiyi maneji da wanan kafin ki dawo Abuja a sai maki wani. Amma don Allah kada ki kara kashe muna waya mu kira bamu samay ki ba ran mu baya dadi rashin jin ki da bama yi a koda yaushe. Kai na girgiza tare da fadin kubar wayan ku ni wayata lafiya take kashewa nayi kawai don, , , Ban karasa ba naji yace don kada kiji muryan mu ko may khadija nace kawai abubuwa ne sukai min yawa a nan bata waya nakeyi ba. Yaushe zaki dawo school don hutu ya kara nake gani nace sai anyi sunar yayan mu data haihu zan dawo uffer week may zaki zauna yi har uffer week Abdulsamad ya tambaya. Ba a gida nake ba tare da iyayyena na bashi amsa da hakan yace ranan tuesday zan turo a dauke ki yana fadin haka ya rufo kofan motar Yusuf yayi min sallama tare da kara mika min wayan suka tafi. Azato sun tafi ne sai ga yara suna shigo da drinks da wasu abubuwa a kwali wai i ji su ina daki ina kallon wayan daya ba babban wayace mai tsada fara kwal da ita. Ya Amina ne ta shigo dakin tana kallo na tare da fadin wai shi baya gajiya da wanan daiwaniyar da yake haka ne kuma kin ce ba soyayya kuke dashi ba. Wayan da ya bani ne na miko mata ta karba tana fadin ta maye wanan kuma nace shiya bani do kawai nace tawa ta samu matsala ne yasa basu samu na . Abin nayi ne ashe yanzu a ka fara wasan da ba ansan maci tuwo ba sai miya ta kare nace ba wani wasan da aka fara indai nice da na koma zan kakabe shi in huta da zancen su gaba daya. Tace ai wanan da alama kin samu kaska baya kakabuwa wasan dadi don ko ya fiki dabara yanzu gashi ya gama daure ki a gurin daddy da mama ko. No way to exscape daga tarkon shi a kwai game da na sani kan nan gaba din ba karamin aiki kika banbaro muna ba yarinya. Kai ke ya Amina ke kekara ma abin wuta wallahi ni may zanyi da mijin da wata ke juyawa a gidan shi kina so in shiga nima in koma yar bi ce kamar fati ? Ke zaki tsayane ki zauna kamar ita a wirin shi ta kai zaune tana fadin da farko ina tsoron abinda ke shirin faruwa tsakanin ku da shi. Amma yanzu zuwa na gida da daddy ya wayar min dakai sai hankali na ya kwanta da zance nake ganin kece haske da zai yaye duhun da Abdulsamad din ya shiga. Ya Amina ki bar wanan magana kimun fatan alheri a rayuwana ba irin wanan fatan ba na shiga wurin da fitina ta nuna kan ta a fili. Khadija kin taba ji ko ganin Abdulsamad ya taba bata lokacin shi ga wata mace irin haka amma sai gashi a kanki abubuwa na ta shirin faruwa a tsakanin ku. Na tabbatar da su hajiya mama zasuyi fari ciki da jin wanan labarin don wata kila adduan su ne ya fada kan ki. Shiru nayi ina sauraren ta tace abu daya zuwa biyu ne na farko gaba dayan mu sai mu dage da addua gaba dayan mu na biyu kuma kiyi kokari ki cusa mashi so da kaunar ki ta yadda buzuwa ba zata iya mashi gibi ba. Har muka gama magana ta fita ban iya cewa komai ba ta barni ina cike da tunane a raina na yadda abubuwa ke zo min a haka. Sai dare sosai suka shiga Abuja inda Yusuf ya aje shi gida ya nufi nashi gidan da motar shi da ya bari gidan don tafiya da ba shiri sukayi. Ko da yashigo gidan shiru yaji kamar yau mutanen gidan nashi basu ciki bai tsaya falon ba ya haura sama inda dakunan kwanan su yake. Ga kaya nan ko ina a warwatse ko ina agidan anyi amfani dasu an kasa kawar dasu don tsabagen kiuya da lalaci har ya kai kofan dakin ya tura a hankali ya shiga. Baiyi mamakin ganin ta a yanayin da ya samay ta ba don duk kwanankin nan a yamutse take a gidan ba wani gyara ko kwaliya da take samun yi . Tana zaune saman gado gashin kanta a wawatse ba gyara ta dago ido ta kalle shi tare da kallon agogon bangon dake dakin tace Samad ina kafito a wanan lokacin. Aikena kikayi da kike tambayana ya bata amsa tare da wuce wa wurin wardrobe din shi yana rage kayan jikin shi. Samad neman mata kafara ko mai yace idan na nemay su ba namiji nake ba wallahi baka isa ba ta fadi da karfi ya juyo gare ta yace ban isa ba fa ki ka ce Nafisa. Tace baka isa ba wallahi may na rage ka dashi a wanda ban baka da har zaka lakanci neman mata a yanzu daga sama. Ya ciro wani dogon jallabiya baka yana fadin waya san iyaka Nafisa baki san komai ba banda son kan ki da kashin kudi abaki kuma baki godiya. Kudi dole ne ka bani don kasan sune buri na kuma akwaisu bathroom ya shiga ya barta ta ta fadin bakaken maganganu gare shi har ya fito bata fasa magana ba. Gadon ya duba yace duba don Allah wai a inda mutum zai kwanta ke nan ya fara kakabe shimfidar da wani dan karamin towel daya fito dashi daga ban dakin. Yace mace sai tarin kazanta na fada maki bani son wanan kazantar taki amma ke abin sai gaba yake yi gare ki. Ai kasan a haka nake kuma ka aure ni na dauka idan kin shigo cikin daula zaki canza ne ashe ni ban san abin a jinin ki yake ba. Kazantar ne a jina na yake Samad yace in ba ajiin ki yake ba za a ce duk yawan ku baku iya gyaran wuri tace samad wa kake so in sa aiki a cikin gidan nan. Kafa san daga kanne na sai yayyena anan sai kuma kawu naina da gwago na yace may yasa kika boye min hakan da farko kin fada min yan aiki ne kika samo min kuma biyan su nake duk wata. Sai yanzu zaki ce min wai yan uwan ki ne na jini baki iya saka su aiki a gidan nan kin zo gidan nan kin samu masu aiki kika ce baki yarda dasu ba. Na baki go ahead da zaki kawo wanda kika yarda su suyi mana aiki ashe ke yaudarana kikayi ki kwaso yan uwanki kika cika min gida dasu. Samad ta fada da karfi kawo yan uwana danayi a gidan shi ne kake kira da yaudara yace yaudara ne mana mutum da gidan shi ba dama ya shigo ya huta a ciki yaji dadin ranshi. Samad yau ni kake fada ma haka don ka gani da ciki kake kokarin ka wulakantani yanzu ko may babu zancen wullakanci sai maganar gaskiya. Haukace mai tayi ranan tana fadin bai isa ya rabata da yan uwanta ba don tare ya gansu ya kuma yarda ya aureta a hakan. Haka ya kwana da tarin bakin ciki babu kunya washe gari kuma sai gata ta neman sulhu dashi don dai kawai ya biya mata bukatan ta don bata iya hakkuri dashi duk yadda ranta ya baci dashi ga wasu kudi da take son karba a wurin shi masu yawa don ai mata aiki a kan shi. Bata samu ko daya ba ranan don asubanci yayi ya fita wirin aiki da wuri koda yaje gurin aikin bai iya aiwatar da komai ba. Yusuf ya shigo ya samay shi a haka yake tambayan shi wai may ke faruwa dashi ne bai tsaya boye mashi ba ya sanar dashi halin da yake ciki da nafisa a gidan shi. Da yan uwanta da suka cika maigida da sunan yan aiki ta kwaso yana biyan su a wata ashe ba haka abin yake ba. Kai inji Yusuf lamarin Nafisa akwai daure kai wallahi Abdul yace nima bashi ba kazantar nan ke damuna Yusuf. Ka san dai halina da kyakyami wallahi komai na gidan nan yanzu kazantar shi nake ji in ba ruwan gora ba ban iya cin komai a gida na . Yusuf yaya zanyi da wanan masifa dana dauko ma kaina nasan ina son nafisa sosai why da ba zata gyara halin ta ba may ye ban ma Nafisa a rayuwan ta. Kamar karta samu cikin nan yanzu abin ya karkare jagule mata mace ba wanka ba saka sutura a jiki idan anyi magana sai tace wai lalurar cikine haka take cikin ta. Au dama ta taba ciki ke nan naga auren budurwa mukai mata wani kallo ya jefe shi dashi yace Nenan yar waye idan bata taba haihuwa ba nima daga bayan nan na fahinci yar tace ashe. Yanzun haka zan kare ga yawon restaurant ina cin abinci a garin nan kamar wani mara galihu dani. Kai innalillahi abin nakune akwai daure kai wallahi saukin abin khadija zata dawo next week zaka dan samu sauki a awurin ta. Saukin may zan samu a gurin ta ya tambayi Yusuf a yanayin rashin fahintar maganan shi Yusuf yace koba komai tunda ta iya girki naga ai zata dan dinga maka idan tana da time. No ban san in jefa rayuwan yarinyar ga halaka ko kadan nafi son ayi komai a kaidance yace kana nufin auren ta zakayi. Shiru yayi ya dafe kanshi bai sake magana ba ya fahinci bai son maganan don haka ya kyale shi tare da canza topic. Yusuf na fita ya jawo wayan shi ya kira layina muna gida ya Hauwa mai jego ya kira wayana ina wanke kayan miya a kitchen aka kawo min wayan. Sai da ya kusa katsewa na dauka tare da sallama yace ina kika shiga kika bar waya na ruri haka nace ina kitchen ina girki wa ya hauwa da ta haihu. Kuna gidan ta ke nan ya tambaya nace eh may kike girka mata nace miyar shuwaka zanyi mata da tuwon shikafa. Ke wa ya koya maki girki haka ne wai nace girkin ma har sai an koya ma mutum yin shi idai kana mace ai zaka iya girki ko wani iri dole. Aranshi yace ga macen da ta san kanta ba sai kuma yace ke wace irin yarinyace da baki iya kiran mutane kiji ko sun sauka lafiya ? Na aiku tafiyan dare ne ko ni na saka ku yin tafiyan da kuyi din yace OK haka zaki ce ma nace haka din ne ma ai. Sai naji ya kashe wayan dariya nayi nace zaka kaji ai ka daina in yar da magoro in huta da kuda har dare muna gidan sai tara muka dawo gida a gajiye . Ban kara bi ta kanshi ba har akai bukin suna aka watse lafiya drinks din da suka kawo muna yayi muna rana do shi mukai amfani dashi wurin taron sunan. Mun fara shiri don tare da yaAmina zamuyi tafiyan kamar yadda na fada mata yace zai turo mota hakan ne ya faru sai ga mota zuwa sha biyun rana ya tsaya a kofan gidan mu. Nan muka fito mukayi haraman tafiya nasha nashi ha a wurin mama da daddy kafin mu wuce muka dauki hanyar Abuja tare da ita don zata kwana a wurin mu. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU INA BUKATAN ADDUAN KU YAN UWA ALLAH YASA MU DACE 1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Kamar yadda yace nice mai tsara mashi tafiyan haka yasani a gaba dole sai dana tsara mashi zuwa gidan da zai yi da abinda zai kai gida. Da farko na dauka zolayane sai da naga abin nasa da gaske ne na tsaya na tsara da taimakon maryam nayi komai. Wanan karon bai sai kayan tsaraba ba kudi muka tsara zai bayar idan yaje sai abincin da zai sai ma iyayyen shi don rage ma mahaifin shi nauyi. Da yamma lis suka isa kaduna don haka ya wuce gidan shi bai shigo wurin su hajiya ba sai da safe bayan ya karya ya shiga gaida su. Sai da yagama gaida abokan zaman hajiya suka wuce nata part din dake daga can ciki yana fuskantar part din mommy. Sai dai tsakanin su akwai dan filin tsakar gida da shuke shuken filawoyi a gurin da wani babban icen ambrale dake basu innuwa a gidan. A kofa su kai sallama ta amsa masu daga ciki suka shigo ko ina na falon tsab yake sai kamshin turen wuta dake tashi a falon. Tana zaune tare da kannen shi Binta da zainab su uku a falon gaida shi kannen nasa keyi ya amsa masu a tsatsaye tare da zama saman center capet din falon shi da Yusuf. Gaida hajiyan sula farayi a cikin ladabi inda hajiyan ke nuna farin ciki da ganin su tare da fara,a a fuskanta. Tana man kamar yadda take a cikin gyaran ta ko yaushe atamphar super ne ja a jikin ta babu wani alamar tsufa ko girma a tare da ita hutu da jin dadin da mijin su ke basu ya kama ta. Cike da kula take amsa masu tare da tambayan da Nafisa suka zo ne Yusuf yace su kadai suka zo don Nafisa cikin ta ya fara girma yanzu. Tace cikin mamaki ciki ke ga Nafisan bamu sani ba mu tana kallon su cike da kulawa Yusuf yace wallahi hajiya ai cikin ma yanzu zai kai wata shida ko bakwai. Ikon Allah to Allah ya raba lafiya ashe da baka fada yanzu ba da sai dai muji haihuwa kawai. Yace ba akai ga haka ba ai hajiya zakuji ne don dai ba a tare ne Affan ne ya shigo falon bai mai da hankali shi wurin su ba sai fada ma hajiyan dayayi a jiki yana fadin wai yaji ciwo a waje. Tace baka ga Abban ku bane Affan daba gaida su ba yaron ya dan kara lafewa a jikin kakan nashi Yusuf yace malam Affan kuna lafiya ina daddy yake ? Hajiya ke fadin maza ka gaida Abban ka da baban ku daga jikin kakan yace ina wuni bazakaje kusa dasu ka gaida su ba in ji Binta dake dagawa daga inda take zaune zainab ko sai charting take a wayan ta. A dadare yaron ya isa gurin su yana kara gaida su Yusuf ya jawo yaron a jikinshi yana tambayan shi dan uwan shi yace yana gurin mommy su. Hajiya tace ai shi wanan dan lake ne tunda uwar tabar gidan ga ta koma gidan su kullun yana can like da ita. Da sauri Yusuf din yace hajiya Fati ta koma gida ne kuma tace to mu rike ta ne nan tunda abin yaki ci yaki karewa haka. Ai gara dai ta koma gida ko hankalinta zai kwanta a can anan taki ta sake sai rama da takeyi kullun Abdul ya mika hannu yana tambayan yaron labarin makaranta. Yayin da Yusuf da hajiya ke magana akan komawan fati din gidan su yace zamu lekata kagin mu koma abin ne sai an hada da hakkuri. Don Fati taki tayi hakkuri da yanayin Nafisa amma ai ita ta zabi ta zauna nan kaduna cewan ta hankalin ta yafi kwanciya da nan din. Wayan zainab dake gefe ne yayi kara ta dauka tana fadin Khadija Adamu wallahi nayi fushi dake ai tana mikewa ta shige dakin su. May wanan yarinyar ta bugo ta fada ma zainab yanzu ko dai komai da sanin su take aiwatar wa yace a zuciyar shi sai ga khadijan ta fito tana hajiya ga khadija na son gaida ke. Ta amshi wayan da faraa a fuskan ta muka fara gaiswa da ita ba wani dogon magana bane gaida ita kawai nayi tana sa min albarka. Ta mikama zainab wayan ta ta sake shigewa ciki shiru falon yayi sai hajiyan ne ke fadin yar albarka yariyar na da hankali sosai wallahi. Ta juya tana fadin yarinyar nan da nasa ku rage ma hanya wani lokaci da zaku koma abujane Yusuf yace oh khadija tana da kirki sosao wallahi. Ai nikan dan leka ta wani lokaci mu gaisa idan na samu lokaci tace ka kyauta haka ake son mutum ya zaba ma kanshi abu na gari. Yace hajiya babu komai a tsakanin na da ita wani dai ma yake raayin ta yanzu haka don yabawa da hankalin ta da yayi har lokacin hira yake da dan shi dabai sake jiki dashi ba. Ya dago kai yana fadin hajiya ko Abba ya fito yanzu mu gaisa dashi kafin ya fita tayi murmushi tace ai yanzu Alhaji ya rage fita kasuwa don yanayin girma da kuma jikin shi yana gida koda yaushe. Binta ta kwala wa kira tazo ta kira mata mommy a dakin ta don tai masu iso gurin Alhajin mommy ta shigo tare da Binta dataje kiran ta hajiya ke fadin dan ki zaki wa iso gurin Alhaji wai. Mommy tana murmushi tace kai hajiya sai kace wani bako a gidan Alhajin yana nan falo ya fito yanzu ma na baro wirin sa ta juya ta fita zuwa fada ma Alhajin zuwan su. Sai lokacin ya dubi hajiya yace wanan karon ban riko komai ba yana sa hannu a cikin aljihun shi yace ga dai kudi a kasa fa aba su mommy dubu daridari sai yaran nan a raba masu dari biyu ke kuma ki dauki sauran ya zube kudin a gefen mahaifiyar sai kuma abinci da anjima za a shigo dashi. Ta kasa boye farin cikin ta nan ta shiga saka mai albarka mommy ne ta dawo dakin tana fada masu su shiga yana jiran su har mommy ta juya hajiya tace . Mommu yara da alama adduan mu ya fara kana dan ki yanzu ga kudi ya kawo a raba ga kuma kayan abinci a tafe. Komawa mommy tayi dakin tana fadin kai madallah Allah mun gode maka da dan mu ya fara dawowa gare mu. Haka ake so wallahi amma da babangida kamar wanda baida kowa a duniya da gatan ka zaka bari shedan yana rudin ka. Ga dan uwaka nan Suraj sai shine ke bamu talafi bawai don bamu dashi ba don nemawa kansa albarkan mahaifa kawai don Allah aci gaba da kula da hakkin mahaifa dana. A da ya tsani mommy sosai don yana ganin nuna mashi kulawan da take kamar duk a munafunci ne sai yanzu yake fahintar halinta ne kawai a hakan ga yaran gida musanman na hajiyan su da takan nuna nata ne. Ita mommy Allah bai bata haihuwa da yawa a gidan ba daga Sadiq danta na fari sai salma kuma ba wasu manya bane sosai yanzu ma suke a secondary. Yace mommy in sha Allahu za a gyara kwanan nan ma zaki tafi abuja wurin mu don Nafisa ta kusa haihuwa ke nake son kije tare da iya na zaria ku zauna a gidan. Ba mommy ba har hajiya sai da tayi mamakin jin wai yau Abdul ne da kansa ke fadin wani nasa yaje gidan shi ya zauna don matar shi da zata haihu. Kirikiri a baya tace bai yarda kowa nasa yaje gidan shi ba don suna zuwa suna tayar kashi da hankali a gidan shi haka Nafisa ta fada mai a baya. Hajiyan su ce tace yar ikon naka tasan da haka kuwa yace haba hajiya sai ta san da hakan mahaifana da yan uwana zasu zo gidana. Idan na gama shiri zan aiko a dauke su yanzu idan na shiga gurin Abba zan sanar dashi bukatan hakan don ba zan so ta haihu babu wani dan uwana a kusa ba. Allah ya kaimu mommy tace da murnan ta fita daga dakin cikin farin cikin canjin da suka gani gareshi. Wayan shine yayi kara ya mike yana amsawa ya bar Yusuf a gurin hajiyan Yusuf yace hajiya muna bukatar adduan ki kamar kulun yanzu haka akwai yarinyar da Abdul ya fara so ina ganin zata iya zama da Nafisa. Duk wanan shiri nane don ba mace matsoraciya bane zata iya gwabzawa da halin nafisa ba don haka a tayamu da addua akan zancen in lokaci yayi nasan zakifi kowa farin ciki da zancen. Hajiya tace ashe ba batun mayar da Fati kuke yi ba ku wani tashin hankalin kuke shiri daukowa yace hajiya wanan shi kadai ne nake ganin mafita ga alamarin. Tace to shike nan addua dama kulun munayi Allah yasa hakan shine saukin abin amma dai wanan yarinyar ta cuta muna da yawa a rayuwan mu. Babu komai hajiya komai ya kusa zuwa karshe insha Allahu Allah yasa tace ya mike tana mashi godiya ya fita ya samu Abdul din a waje suka wuce wurin alhajin shi. Da sallama suka shiga dakin na Abba yana zaune saman kujera yana duba wayan shi ya dago kai yana amsa sallama tare da kallon su ta cikin farin glass din shi idon na medical. Kasa suka zube suna mika gaisuwa ga Abban girma da kuma ciwo ya ramar da Abban don mutum ne mai jiki a da yanzu ko girma da ciwo yasa duk ya zube. Sun gaisa sosai sabanin da da in yazo gaida Abban yake amsa mai a dadafe ba wani saki a fuskan shi. Ya aje wayan tare da mayar da hankalin shi gare su magana yake irin na dattako yana tambayan su yaya aiki da iyali suka amsa da lafiya kalau Abba Alhamdullahi. Kallon da yake masu ne yasa suka san da magana a bakin Abba din jikin Abdul yayi sanyi yana tunane a ran shi may kuma yayiwa Abba din yake mashi kallon tuhuma a yanzu. Yasan dai ba wuce maganar yar aminin shi ba da yake ganin yayi mata ba daidai ba shi dai Fati taja mashi kiyayya a gun mahaifan shi yanzu komai yake masu baya fari a gare su. Gyara zama yayi yana kallon Abba din don jin abinda zai fada masu Abba yace Yusuf zan iya cewa yanzu Alhamdullahi a yadda naga abokin ka yana waiwayan mu akai akai. Ko ba a fada ba alama ya nuna cewa yanzu ya fara samun kwanciyar hankali a tare dashi shidai Abdulsamad ya zuba ido yaji karasan magana shi. Abba yace ya na dade ina jiran wanan ranan tun ban mutu ba ranan da zaka gano gaskiya ka dawo a cikin hankalin ka irin haka. Wanda nasan ba yin kan ka bane don ba haka muka tarbiyarta da kai ba da farko don haka nake son ka kara natsu ka tsayar da ibadan ka duk wani abinda zakayi kada ka manta da yawan addua a tare da kai don shine jagoran rayuwa ko ba haka ba ya tambaye su. Lokaci guda suke kada ma Abban kai tare da fafin hakane Abba , murmushi Abban yayi masu yace to yanzu saura maganan iyalin ka zan so inga ka hada kan iyalin ka a wuri daya. Kamar yadda ka taso ka gani a gidan nan kasan hakan shine cikar kamalan ko wani magidanci aga yana ba ko wace mace hakkin ta daidai gwargwado. Suka ce hakane Abba, Abban ya dan tsura masu ido yayin da kanun su yake a kasa suna sauraren shi Abban yace kai kuma Yusuf na dawo gare ka mai kake jira har yanzu baka maye gurin matar ka da ta rasu ba shikenan kana nufin ba zaka sake aure ba a rayuwan ka ko may. Yusuf din ya dago da sauri yana fafin ba haka bane Abba zan sake insha Allahu da zaran an gama na Abdulsamad dake tafe. Au Abdul din aure zai karane kuma Abba ya tambaya sai Yusuf yayi kasa da kai yana fadin insha Allahu Abba basu gama daidaitawa bane da yarinyar shi yasa bamu gabatar maku ba tukun. To madalla ka nuna ka gado gida ke nan to yaya maganan Fati kuma fa may ake ciki game da alamarin ta ? Abba insha Allah zata koma daki ta ba da dadewan nan ba akwai abinda muke tsarawa a kai ne yanzu to Allah ya bada sa a sukace amin ya kara da fadin a kula da hakkin akai dai. Insha Allahu suka fadi suna mikewa ta ciro kudin da ya ware na Abba ya nufe shi yana aje mai a gefen kujeran da yake zaune a sama. Suna fita dakin Abba suka sallami mutanen gidan suka fice a gidan Abdul yace Yusuf yaya zakai min haka kace wa Abba wai aure zan kara kwanan nan ? Idan ba haka na fada mai ba kana ganin iya abinda zai fada muna ke nan a yadda yake kallon mu din nan shine kawai mafita ai kai kasan ba auren zaka kara yanzu. Bai yi magana ba ya bi bayan shi yana murmushi don yasan ya kulu dashi sosai da yamma motar kaya ya tsaya a kofan gidan Yusuf yasa akai ta shiga da kayan cikin gida. Kowa na gidan sai farin ciki duk da zaman kishi dole na ciki na ciki a ransu ganin sauyin da yayi hakan bai hana a kebe gefe ai gulma ba tsakanin ummi da anty Amarya. Nafisa da madam murnan tafiyan shi kaduna a satin sukayi don dama kafan zuwa ondo take nema don Abdulsamad ya hanata tafiya yanzu ko ina. Tafiya sukayi sosai tun suna na dadin rai har ta fara galabaita ga tafiya don dan karan nisan da garin ke da tsakanin shi da Abuja. Bata dauka nisan shi yakai haka ba sai da suka fara hanya duk wanan bakar wahalan bai sa ta janye kudirinta na zuwa wurin wanan bokan dataji ana yabon aikin sa ba. Ko da suka isa ondo da safe wani motar suka kara bi zuwa kauyen da bokan bayaeraben yake zaune sun isa a wahalce don har amai da zazzabi sai da tayi a hanya. Sun isa dajin mai kama da gari da baifi yan gidaje a kirga ba sai da suka huta kafin su samu ganin bokan don ranan suke son su koma Akure su shiga motan dare su koma abuja. Bayan ta gama fadin abinda take son yai mata nan boka ya fara surukule shi ya dago yana kallon ta na dan lokaci. Sai duk suka tsargu da irin kallon da yake masu wanda ke nuna akwai magana kai ya girgiza sanan yace aikin ta akwai dan wahala a cikin sa. Don yanzu haka mijin ta yana tare da wata yarinya sai dai bai hango soyayya tsakanin su ba amma akwai aure har da haihuwa a ciki. Kirjin ta ta doka tana fadin ta shiga uku ita samad zaiwa kishiya wacece zai aura har su haihu ? Sam ta mace da Fati ma mallakin mijin ta ne har da diya shi boka Allah bai bashi ikon tsafin shi ya hasko ni ba nan tasa ai mata aikin da za a raba tsakanin shi da ko wacece . Akuma fitar da ranshi ga ko wace mace a rayuwan shi sai ita kadai ya kara yin saddabarun shi na bokayen da suka gwane da tsafi yace ya ga wata mace sai dai baiga gaban ta sai bayan ta kamar tana son shiga rayuwar mijin ta amma dai bari ya mata aiki akan wace ta baiyana in yaso daga baya aikin da zaiyi zai gusar da waccan matar da yaga bayanta din. Tace tana son koda kashewa ne a kashe mata wace aka gani ko a haukatata gaba daya kowa ya huta. Yace an gama sai dai aikin ta na da tsada sosai tace kada yaji komai indai aikin zaiyi kyau nan ya shiga hada mata irin nashi surukulle da bayanun yadda zatai amfani dashi ba tare da kuskure ba. Yace ba mijin ta ba wata mace da zai duba a duniya muddin tayi abinda ya fada mata daidai suka kama hanya komawa gida bayan ta cika shi da kudi. Sam bata san Abdul kwana biyu zaiyi a kaduna ba lokacin da Abdul ya iso gida ya neme ta sai cewa sukayi ta tafi unguwane. Har ya shiga ya huta ya dan kwanta bata dawo ba ran shi ne ya baci sosai da ita yaji yana son fita don haka ya shirya ya fito dan yasan kafin ya dawo ta dawo gida a lokacin. Sai dai abinda ke bashi mamaki baifi ganin motocin shi duka dayayi ba a gidan yana tambayan kan shi da wace mota nafisa ta fita ? Yana fita batare da sanin inda zai tafi ba har ya yanke shawaran zuwa wurin Yusuf sai ya fasa don ya san yanzu shima hutawa yake a gidan shi kada yaje ya damay shi. Sai kawai ya yanke shawaran ya leka khadija don ya kwana biyu da ganin ta hanyar hostel din mu ya dauka sai da ya iso ya kira waya gashi abakin hostel. Nace da yamman nan yace na koma ne nace gani fitowa yaja iska ya kashe wayan na fito ina tako dadaya wanda ni ban san inayi ba ma. Na karaso wurin motar cikin yar murya na nace dashi sannu da zuwa baki maraba da zuwa na bane ko may ? Murmushi nayi tare da fadin naga baka fita a wanan lokacin ne kawai har ina da lokacin fitane na daban da ban sani ba yace shigo mota mana. Ina shiga sai kawai ya tayar da motar nace da sauri sata na zakayi ko may ? Bai bani amsa ba yaci gaba da kallon titi may zan sata anan, nace mutum, dariya yayi yace kan nan naki kuwa zaiyi kudi sosai nace ai kafin ka sai da nawa ka fara sayar da na buzuwar ka ita bakuwar haure, Kuff naji yake ma bakina dan bugu da sauri na dafe bakin nace saboda buzuwa ka dukar min baki ? Yace ban san hadinki da wanan buzuwar ba nace halinta halinta bai mun bane don tana da ji da kai da son wullakanta mutane. Ita abi kyama ba a kyamace ta ba sai itace zata kyamace mutane matar tawa ce abin kyama khadija ? Ba ita duk buzaye abin kyama ne gare mu yan Nigeria sai iri kune dake mai dasu mutane kawai baku kyaman su don su din ba abin yarda bane mazan su da matan su. Sai mutum ya yarda dasu daga baya su zo su yaudare shi yaudara a wurin su ba abin kunya bane don su din basu da kunya ko kadan. Shiru yayi yana tunane a ran shi bai bani amsan magana na ba nace kuma gasu da son raba mutum da yan uwan shi su cika gida da nasu yan uwan. Ga kazatar tsiya da son mamaye komai ya koma nasu su kadai koda kuwa sun samu wasu mata ne a gidan shiru nayi don na dauka bai saurare na a lokacin. Sai naji yace uhmm go on yaya kikai shiru ba labari kike bani ba nace au na dauka baka sauraro na ai gasu da dan banzan bin malamai da bokaye basu yarda da kowa ba sai kan su suna iya yiwa yan uwan su yankar baya su zauna da mijin yar uwar su. Zasu iya ketarowa da auren su suzo su auri wani anan alhalin duna da mazan da suka baro a gida sai lokaci lokaci suke lekasu. Kai bazaye muggan mutane ne sosai wallahi duk wayon ka zasu san yadda suka juya ka indai na miji ne ji nayi ya tsayar da motar da karfi yace bari inyi sallah please sai kici gaba da bani labarin ki. Fita yayi a motar ya nufi wani gu sai yanzu na duba naga ashe massalaci ne a wurin shiga yayi a ciki na mayar da kaina akan sit din motar ina kallon mutanen da ke gurin. Ya dan jima a ciki ya fito ya shiga motar ya kama hanya mun dan taba tafiya ba tare da nasan ida zamu nufa ba. Yace bissimila cigaba da labarin ki nace labarin yai ma dadi ke nan kwarai kuwa ina jin dadin labarin sosai nace toba zan kara fada ba. Don may ko don kar naji halin buzaye nace ba wanda baka sani ba a cikin wanan kai da ke da ita a gida may ya rage da baka sani ba. Ina ga saura bani kuddi baba ko a yaye ka kafa ka wayi gari ka samu ta ketara kasan su da dukiyar ka. Yace da taci rabon ta ashe idan ta iya ketara kasa da dukiyana duka eh tunda a banza kake samun kudin yace haka kike zato ashe ? Ni ba ragon namiji bane ko da yaushe ina tsaye da kafana wurin neman na kaina zaune a office din nace mai. Au haka kike dauka na ni ko a gidana nake ina neman na kai na nace gun buzuwa ke nan kai ya girgiza min. Koda yake dama abinda kuke nema a wurin su na daban ne da sauri ya juyo yace may muke nema a gun su nayi shiru tare da kawar da kai gefe. Fada min may muke name muka aure su nace su mana tunda irin su ne ku din jara, , , , shiru nayi karasa mana ina jin ki. Hannu yakai yana kamo min baki nayi saurin rike hannun nashi a karo na farko dana taba taba jikin shi da sauri na sake hannun nashi. Na kawar da kai na gefe hannun nashi ya duba a hankali sai naga ya sauke murmushi a fuskan shi yace how lucky you're ? Ke ce mace ta uku da na taba hada jiki da ita a duniya nace nima ina regreting din hakan da nayi wallahi. Shiru mukayi yaci gaba da tuki wani guri ya shiga da motar mai yawan ginene gine da sasa da yawa yace kin san wanan gurin tsoro ne ya kama ni dana kalli gurin sai na dauka ko hotel ne. Kai na girgiza alaman tsoro ya kamani sai naji yace nan ne ma,aikatar mu wanda daga MD din mu sai ni a gurin. Da sauri na kalle shi yace ko kina bukatan shiga kiga gurin da sauri na girgiza kaina nace a,a don Allah ka mayar dani hostel inda ka dauko ni. Ai bamu gama ba don baki ban amsata ba da sauri nace tamay yace irin mu da kika fara fadi baki karasa ba nace maganar yawuce ai. Yace a gunki ya wuce ni a wurina bai wuce ba sai naji karasan maganan ki ko mu kwana a nan da sauri na dago ina kallon shi don Allah dai kayi hakkuri ka mayar dani inda ka dauko. Maimakon yayi abinda na nace sai naga ya gyara set din motar ya kwantar dashi tare da sa hannayen shi yayi matashi dashi yakai kwance. Muna wurin shiru ba wanda yai magana a cikin mu sai tsukin da nake ja can yace a kasalance kada ki kara jamin tsuki a mota yanzu na fitar dake na wuce. Kayi hakkuri don Allah ka maidani hostel ina da exam next tomorrow ban son in fadi wani mutum ne ya dun faro inda muke yana haska toci a hannun shi. Ni dake zaune nake iya ganin mitumin dake tafe nace ga wani nan yana zuwa gurin nan fa bai damu da abinda nace ba yana kwance abinshi yadda yake. Har mutumin ya karaso ko ya sheda motar shine sai naga ya dan tsaya daga nesa damu yana fadin barka da dare yallabai an wuni lafiya cikin harshen turanci. Ya dago yana amsa mashi da lafiya kawai sai mutumin ya juya ya koma ciki ban san na firgice ba sai bayan wucewan mutumin yace lafiya kika shige min a jiki haka ? Ko kina son jin abinda buzuwa ke ji ne ajikina ta leke min da sauri nayi kokarin jaye jikina dana dan manna da nashi sai naji ya riko ni. Ta yadda har muke iyajin saukar numfashin junan mu a lokacin ka sake ni don Allah wai may kake nufi da nine haka wai ? Fada min amsan tambayana mubar aurin nan kada masu gadin nan su dauke ni dan iska nace sake ni in fada ma to yace sai kin fada jin irin rikon da yaimin yana kara manna ni a jikin shi nace jarabbabu irin su mana. Sake ni yayi ya daga bai ce komai ba ya tayar da motar muka bar gurin sai da naga mun hau titin da zai sada mu da hostel din mu hankalina ya kwanta dashi. Don yadda a lokaci daya naga canjin yanayi a gare shi ya firgitani ainun sai da muka dauki hanyar hostel din yace ki shirya shiga cikin jarababbun mutane daga yanzu. Ban iya magana ba bukata na shine inga kafata a kasa yanzu a wani shago ya tsaya ya shiga har ya dan dade sai gashi ya fito ina hangen shi tun daga nesa na raya a raina Allah yayi halitan namiji a nan . Baya ya bude aka saka mai kayan a ciki ya sallami yaron ya shiga muka tafi bakin hostel din mu ya tsaya bai bude motar ba niko a kage nake da in fita daga motar. Yace zan yi tafiya may yuyuwa baza mu hadu ba sai idan na dawo Allah ya tsare hanya nace dashi tare da kallon shi ya bude min motar. Kina level nawa yanzu a karatun ki nace two a takaice yace yayi nisa da yawa gaskiya nace ai ni ke yi ba wani ba ban ga amfanin karatun ba a guna amma ai naga su Binta da zainab sunayi suma ? Wanan matsalar su ne ni nawa matsalar na sani bata wani ba su ya shafa wanan bani ba amma kai mugu ne ko ? Zaki iya ba kan ki amsa idan kin so ko wani kalar nake ya bude min motar tare da miko min ledojin dake bayan motar ina karba na fice ina fadin mugu kawai da karfi. Girgiza kan shi yayi ya tayar da motar ya tafi sai da ya fara tafiyane tunanen Nafisa ya zo mashi a rai yana tunanen ko ina taje dazun ya dawo bai samay ta a gida ba. Ya iso gidan ya shiga a falo ya samu su Hadiye zaine suna hira suna ciye ciye gaishe suke da dawowa yace Nafisa ta dawo sukace bata dawo ba ya shige ya barsu a gurin zaune. Ya shiga ran shi a bace ya dubi lokaci yaga tara da wani abu na dare goma saura kadan wanka ya shiga yana tunanen Nafisa a ranshi har ya fito ya kwanta shiru ba Nafisa. Ni na fado mashi a rai jarababu irin ku murmushi ya danyi yana rufe idon shi kamshin turen oud dina yake tunowa daya shaka. Ya lumshe idon shi tare da gyara kwanciyar shi yana lumshe ido yaji dadin kasancewa mu a tare yau hiran da nake mai na buzaye ne ya dawo mashi a rai. Ba abinda na raga daga halin da yasan Nafisa dashi zai iya cewa kila wani ya fada min kadan daga cikin halinta daya fahinta. Sai dai abinda ya tuno inda nace suna barin mazan su a gida su zo duniya su auri wani mijin na daban sunayi suna zuwa ziyarar mazan nasu. May wanan maganan yake nufi kodai shiyasa Nafisa take yawan ziyaran gida akai akai bai sani ba da sauri ya kawar da wanan zancen kada zargi abinda bashi ba yashiga zuciyar shi. To wai ma ina Nafisa taje ne uban may tafitayi da tun safe har wanan lokacin bai ta dawo ba yaja tsuki yace zan gwada ma Nafisa matsayin ta na mace a gidan nan. Goma, sha daya shabiyu saura ya mike zubur hankali a tashe ya mike yana zura riga a jikin shi ya sauko zuwa kasa komai na falon a kashe yake . Su hadiye sun shige dakunan kwanan su kayan da sukaci abinci gurin babu kowa a wurin tsuki yaja ya fita waje ya nufi gurin maigadi yana tambayan shi ko yaushe nafisa tafita a gidan. Maigadi yace rabon shi da ita tun shekarajiya da kawar ta tazo suka fita komawa yayi ciki yana tunanen tun shekaran jiya da kenan Nafisa dama bata gidan tun lokacin da shima yayi tafiya ko may ? Kamar zai tayar dasu hadiye ya tambaye su sai kuma ya fasa ya koma ya kwanta suna barin mazan su a gida su je wani guri su kara aure suna yi suna ziyarar su. Abinda ya fado mashi a rai ke nan karfe daya agogon da ya kalla ya nuna mai da sauri ya mike zaune biyu saura na dare yaji ana buga gidan maigadi ya bude kofa motar ta shigo sai ganin nafisa yayi ta fito daga motar ta dan tsaya suna magana da ta cikin motan. Ta shigo gidan a gajiye take kafafuwan ta har sun dan kunbura saboda zaman motan da tayi mai tsawo dakin su hadiye ta fara zuwa. Ta samu suna barcin su hankali kwance ta ta da ita a cikin magagin barci tace kin dawo da yare tace na dawo bata gane komai a guta ba ta juya zata shige tace Alhaji ma ya dawo dazu da safe. Dam taji gaban ta ya fadi da sauri ta fita zuwa dakinta ta kayan sihirin da ta dawo take kokari boyewa a wardrobe din ta sai taga an kuna wutan dakin ta. A fusace ta juyo sai ganin Abdulsamad tayi tsaye yana kallon ta da sauri ta kara gare shi sai yayi saurin juyawa ya fice daga dakin . Boye kayan ta karasa yi ta rufa mai baya ta murda kofan dakin a rufe taji shi gam ta juya zuwa dakin ta ciki da fargaba da tsoro a ranta. Washe gari ta samay alokacin ya gama shiri zai fita yana daura agogo a hannun shi yana gani ta ya daure fuska tankar bai taba dariya ba a rayuwan shi. Rudewa tayi tama rasa may ta fada mashi can dai tace Samad kayi hakkuri na san ban kyauta ba na fita ba da sani ka ba. Jakar laptop din shi ya dauka zai wuce ta zube kasa gaban shi tana fadi ka yafe min gurin buki naje shine naka wanan lokacin ban dawo ba. Nasan nayi laifi fita in dade baka nan amma kayi hakkuri haka ba zai sake faruwa ba insha Allahu. Yace don gani saunar na miji ki fita gida na kwana da kwanaki yanzu kizo kice inyi hakkuri haka kai tsaye bayan kin gama yawon gantalin ki a can. Kin kwaso kafan ki kin dawo min gida ki koma inda kika fito zai fi maki sauki na baki minti awa daya ki fice a gidan nan da kowa naki. Samad kayi hakkuri ka yafe min ba zan sake ba yace rufa min baki munafuka wace bata san ciwon kan ta da darajan aure. Ya sure jakkar shi ya fice a dakin da kyat ta iya mikewa tsaye daidai lokacin ya dawo yana fadin fita min daga daki zan rufe abina ne . Ta bishi da kallon mamaki a kofan tana tsaye ya rufo dakin shi karo na farko a gidan abin ya mata zafi saidai cikin ranta tana fadin yi abin ka a hannu na zaka dawo kwanan nan. Ya fice ta bishi da kallo tare da juyawa ta wuce zuwa dakin ta tana mai jin haushin shi. Kutayani da addua yan uwa ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Washegari da safe ban tashi da wuri ba don fashin sallah da nakeyi sai da naji motsin daddy ya dawo na fito don in gaida su har lokacin a cikin damuwa nake. Daddy yana zaune a cikin dan karamin falon mu ga abin karyawa a gaban shi mama tana gefen shi ta motsa mashi kunun da ta aje mai a gaban shi sai kamshi kosai ke tashi a falon. Daga kofa na tsuguna ina gaida su daddy yace a a baby na shigo mana daga ciki na tashi na karasa shigowa cikin falo har lokacin na kasa sakin jiki dasu kamar kullun. Daddy yace ya karatu nace daddy Alhamdullah yace babu matsalan komai ko nace daddy ba matsalan komai na fada tare da sunkuyar da kaina kasa. Ina kokarin mai da hawayen da ya ke shirin silalowa a idona nace daddy sai dai wanan mutumin da ya hado ni da kayan nan wallahi ban san ya sakasu a mota ba sai da muka zo nan taimakon shi nayi shine ya saka min da haka. Ido duk kan su suka tsura min da nake masu bayanin daddy yana kallona yana yaba hankalina don yasan ba zan boye masu komai dake faruwa ba. Saboda karya ba halina bane kai tsaye nake fadin gaskiya ga mutum yace dakata khadija kin mashi alheri kin shirya shi da iyayyen shi. Shi kuma yaji dadin hakan ya saka maki da alheri ko kamar yadda yace na gyada kai nace hakane daddy. Mama tace ina kika hadu dashi haka khadija nace mama a wurin da aka tura mu aiki ne na hadu dashi ya samu matsala da iyayyen shi da yan uwanshi. Shine na basu shawara ya nemi shiri da yan uwanshi da mahaifar shi ta hanyar aikata masu alheri daya jaraba hakan sai suka shirya dashi. Shine yazo yace zai saka min da alheri akan abinda nayi mashi tace khadija shine ya kashe maki wanan uban kudin daga taimako kawai irin haka ? Nace mama wallahi ni ban san haka zai min ba daga ta Hussai yace ma mama kin san ni ya kamata in dauki zafi akan maganan nan fiye da kowa. Amma sanin halin ya ta danayi yasa na yarda da bayanin mutumin nan tunda ya rantse min da bata roke shi ba kuma ba da wani manufa yayi mata haka ba. Yai min bayanin da hankalina ya sa na yarda dashi da ita sai dai yanzu ba yadda muka iya tunda kayan nan sun riga sun shigo gidan nan. Kiga ba komawa zasu yi ba tunda dai ba rokon shi tayi ba sai dai khadija a gaskiya nayi mamaki da wanan abin don ba karamin kudi ya kashe ba ga kayan abincin nan. Da sauri nace daddy ba kayan abinci bane kawai har da na sakawa da kudi sune a cikin wanan akwatin da ga gani jiya. Ido maman mu ta fitar waje tace khadija anya ba dan yankan kai bane kika hadu dashi kada fa watarana ya gama zolayar ki da abinduniya mu nemiki mu rasa. Dariya maganan ta yaso bani sai na dake nace mama ba dan yankar kai bane don nasan kowa nasa na kuma san matar shi. Share kawai duk wanan tunanen nayi shi a daren jiya har nafila sai da nayi akai banga wani abin cuta ba daga gare shi sai tarin alheri da na hango ga wanan alamarin. Shiyasa kika ga ban wani damu ba da hakan sai da ita din ta kula da kanta da mutuncin ta da irin tarbiyar da mukai mata zan sake yin yau na gani don ni kaina abin ya daure min kai sosai. Mikewa nayi na dauko kudin da kayan na turo zuwa dakin nan na fara fitarwa ina masu bayani yadda kayan suke nima mamakin yawan kayan nake yi a cikin macewa jiki. Daddy yace aje kayan zamuyi sai na nemi yar uwarki a waya naji shawaranta akai da yadda za ayi da kayan. Zan dage da rokon Allah don ina jiba jikina kamar akwai alheri ga haduwan khadija da wanan mutumin sai dai mu bar ma Allah sanin shi. Koda yakira ya Amina yayi mata bayanin abinda na dawo dashi wanan karon tare da fadin ta sake binkice na tsakani na da wanan mutumin don a gono gaskiyar maganan. Ta kira ni lokacin ina kwance mara na yana damu na da ciwo na dauki wayan ina gaida ita bata tsaya amsawa ba sai cewa tayi Deeda make faruwa ne daddy ya kirani yana fada min wani magana da safen nan. Shiru nayi sai da ta kara maimaita maganan ta nace cikin kuka wallahi ya Amina ba halina da kuka sani da na canza yanzu. Nima ban san da kayan nan ba sai da muka shigo garin nan na gani nan dai na koro mata bayanin komai don ba zan iya boye mata ba ita. Tace khadija kina nufin dama Abdulsamad ne ya yi maki wanan alherin ban sani ba khadija baki jin tsoron buzuwa ta san wanan labarin ta yi maki illar nace ya Amina yaya zanyi ni ban roke shi ba shiya bani. Tace dama khadija kece kika saka yayi wanan alherin da yayiwa iyayyen shi ashe dama duk kece sanadi ni ba komai nake ji wa ba sai buzuwan matar nan tashi wallahi. Takira daddy tayi mai bayanin komai yace shi zancen buzuwan matar shi bai damay su ba tunda ta sheda ba mugu bane. Nema ne idan naga zan iya sai in yi dashi wanan ba komai bane Allah yasan abinda ya hada a tsakanin mu ya kawo hakan sai dai mu saka ido a kan yar mu don har yanzu khadija yarinyar ce karama. Ya Amina tace gaskiya ne daddy zan shigo kafin ta koma dayardan Allah anan suka rufe maganan tare da taya ni addua ga wanan lamari tunda daddy yace abarwa Allah sanin shi a tsakanin mu. Maryam ta kirani nake mata bayanin abinda ya faru dani maimakon ta tayani jimamay sai naji tana min dariyan shakiyancin da ta saba min tace shike nan ya nuna maki wayon manya ya gabatar da kan shi ke nan gare su. Nace wai ke maryam don Allah may yasa kike irin haka ne sai a na maganan gaskiya sai ki dauko wani zance daban tace shike nan yanzu mubar zancen a haka dai. Nace zai fi sauki muka dauko maganan karatu bayan mun gama wayan ne barci ya dauke ni a wurin wanda nasan barcin da ban samu bane a daren jiya. Nan dai na kwashi barci na sosai a ranan sai wani lokaci na tashi don mama taki sake min fuska yasa ban son fita a tsakar gidan sam. Wayana yayi kara na dauka Dan Baiwa nagani a rubuce wani haushin shine ya kamani a raina nayi banza da wayan nashi bandaga ba har kiran ya katse. Ya sake kirana da kyat na iya daga wayan don har yanzu ina fama da ciwon mara dake cina jin murya na da yayi yasa shi saurin fadin. May ya samay ki baki da lafiya ne may ke damun ki ne khadija haka yadda naga ya rude ne nace banda lafiya ne . Tun yaushe nace tunda safe daddy na gida naji ya tambaya nace yana waje turo min da layin shi may zakayi da layin shi nace dashi. Ban number shi nace maki ya fada a dake nace ban san number shi OK zan kira a bani number yar ki in karba a gurin ta yace da sauri nace a a din Allah ni dai kada ka kirata naji sauki. Dole na bashi layin daddy din don naga yana niyar kashe wayan bayan na bashine ya kashe wayan bai fi minti goma ba sai ga daddy ya shigo gidan yana fadin ina khadijan take ne wai ashe bata da lafiya bamu sani ba. Sai da wanan yaron ya kirani yanzu yake fada min khadija bata da lafiya a kaita asibiti wai zai turo da kudi kamar shine ya haife ta. Mama tace ni tunda jiya da ta dawo na ganta kwance ban san may ke damun ta ba, har dakina daddy ya shigo ya samay ni kwance sai dai ba barci nake yi ba. Zama yayi saman tsohowar kujeran dake falon yana fuskanta na yaga yar raman da nayi yace baby na may ke damun ki ne yanzu wanan mutumin ya kirani wai baki da lafiya. Sai dai ban san ida ma yasamo lambata ba ya kira nace niyace in bashi na tura mai yanzu amma ban san kiranka zai yi bz ai daddy yace zai turo da kudi wai kije asibiti nace ya barshi bayan kudin da ya turo muna zai kara dawainiya kuma. Daddy yayi murmushi yace kin san may yace dani na girgiza kai cewa yayi wai dawainiyar ki yanzu akan shi yake. Nace daddy kada ka yarda da maganan shi wallahi ni ba komai a tsakanin mu yace naji sai dai yadda yake ya nuna min da fuskan gaskiya yazo maki don bai bar abin a tsakanin ku ba ku biyu ya sakomu mu iyayyen ki a ciki bai boye muna ba. Yanzun dai yace a tura mashi da account number da zai turo kudi kije asibiti nace daddy nifa ba komai a tsakanin sai mutunci kawai yace yaji. Sai ga daddy ya shigo zuwa sha biyu yana fadin ya turo dubu hamsin in tafi asibiti nace nasha magani naji sauki daddy dama ciwon mara ne kawai ke damu na. Yanzu yaya kike son ayi da kudin da ya turo maki kasa kasa da murya nace kayi amfani dashi kawai daddy. Sai yamma ya kira yana tambaya ko naje asibitin nace eh yace sun baki magani nace eh nasha har naji sauki sosai yace ashe period kike yi kike wanan raki haka ? Shiru nayi banyi magana ba yace duk wata haka yake maki nace ban sani ba yace kan ki ga Yusuf ku gaisa. Kunya naji sosai jin har da Yusuf yasan ina period yanzu muka gaisa yayi min yaya jiki nace da sauki yace ki sha magani kin ji sauki ko nace eh yayana . Sai shiru ya biyo nace Yusuf batare da fadin yayan da na saba kiran shi dashi ba yayi makin jin hakan daga bakina sai ya dake yace yaya akayi yar mama ? Nace kayiwa mutumin nan fada mijin buzuwa akan abinda yayi min bai kyauta min ba don may yake son saka iyayyena su zarge ni. Yace zargi kuma khadija akan may nace yanzu haka tunda na dawo mama sai fushi take yi dani akan abin da ya saka a motar da naje gida dashi. Saboda shi take fushi dake nace wallahi ni na rasa may zanyi akai suna ganin kamar ban kama kaina bane a Abuja ina hurda da mazan banza ne a can. Sai daddy ne kawai daya fahinci komai da taimakon ya Amina na samu ya dan sausauta min bai fishi dani muryan shi naji yana fadin why mama zata yi fushi dake akan dan abinda na tura masu. Mama bata yarda da tarbiyan da sukai maki bane ko may in haka ne kuwa zan shigo da kaina in mata magana da zata fahince ni ita ma. Ban saka ba haka ka hadani dasu dazun daga na fada ma banda lafiya ka fadawa daddy yazo yana yi min fada balle maman mu da ta hau dani. Ba matsalan ki bane nasan abinda zance da ita idan nazo nayi saurin fadin bansaka ba dai ka barni da ita zamu shirya wataran. Bayan na kashe wayan na mike na shiga wanka na fito na canza kaya jikina zuwa dogon riga nayi kyau sosai a cikin rigar lokacin yamma yayi sosai nace zan je gidan su hafsat kawata da tai aure ta haihu bani gari. Kallon da mamaki min ne yasani tsarguwa sai daga baya na fahinci rigar da na saka ajikina ne yasa take min wani kallo da bashi ba. Sai na dawo tace min batare da ta kalle ni ba na fita jiki a sanyayye zuwa gidan hafsa din dake bayan minna minicipla coucil. Hafsa kawa ta ce tare muka taso da ita kasancewar unguwar mu ba nisa da karatuna ya dawo minna na hadu da ita muna zuwa girl day dake a bayan old airport tare kusa da tsohon makarantar wtc na mata. Bayan mun gama ta samu wani guy ta aura dan kabilar Nufe dake tashen kudi a lokacin . Na fito gida a hankali nake takawa iskan marance yana kadawa inda nake ganin fuskokin wa yan da na sani muna gaisawa jefi jefi dasu a hanyan. Har na isa gidan na samay ta tana girkin abincin dare tana gani na ta tare ni da murna muka gaisa ta nufi falon su dani ina biye a bayan ta. Sai bayan na zauna ne ta dauko min baby ta har yaron ya fara wayo sosai ta miko min shi sai bina take da kallo wai na sauya gaba daya na zama wata big girl dake nace kai haba dai hafsat har dake cikin fadin haka. Tace wallahi gaba daya kin sauya ma sani na ne khadija nace yanayi ne kawai wallahi yazo a haka ba wani abu may ye sunan yaron na tambaye shi. Muna hira tana duba girkin da takeyi har ta karasa takawo min nace wallahi hafsat a koshe nazo gidan nan watarana zanci. Mikewa nayi saboda magariba daya kawo jiki sosai na bata asai ma yaro takalma ina shirin fitane mijin ta ya shigo gidan. Allah ya gani jini na bai hadu da mijin ta ba tun farko asali ma nice ya fara cewa yana so sanin shi da nayi dan duniya mai wayan yan mata da kyale kyali yasa ban bashi fuska ba. Naje hutu kaduna kafin in dawo na samu sun dinke da hafsa har sukai aure yanzun ma da ya shigo gidan ya samay ni sai da ya daga min gira ba tare da sanin hafsa ba. Harara na watsa mai na fice gidan tare da yi mata sallama nadan yi nisa naji muryan shi a baya na yana fadin khadija ji mana. Juyowa nayi fuska a daure ina kallon shi nace lafiya dai ko ya washe baki yace don Allah sorry to distub you kin boye fa da yawa ban san kin zo garin ba ai dana kawo maki gaisuwa. Dan murmushi nayi nace ba komai ai gashi mun gaisa yanzu dama boye nazo gani na ganshi har yayi wayo. Yace in ba laifi ki bani layin ki akwai maganan da zamuyi kin san dai yanzu ba da bane zaki iya fahinta na har yanzu ba kin fita raina bane. Auren hafsa Allah ya nufa sai munyi da ita amma ni ke ce choice dina tun farko hafsa dai ta shishige min har na aure ta. Dakata Adam kada ka kara taro na da irin wanan maganan ko da hafsat bata gidan ka kai ba choice dina bane ka sani ban hurda da maza irin ku da kafan su bai tsayo a guri daya ba. Ke kizo kici arziki kibar arziki kawai don yanzu arzikin bana yaci uban na da zan iya daukan lalurar ki da komai naki wallahi. Wani kallo na watsa mai na up and down nace a haka din kake tunanen zan iya cin amanar kawata aminiya ta nace Allah ya tsare ni da masu irin halinka. Na wuce na barshi tsaye a gurin yana bina da kallon zalama irin ta yan iskan maza yana sosa kan shi baida mu da mutanen dake wuce ba a saman titin. Na shigo gida ana kiran sallah magariba dakina na nufa sai da mama ta gama alwala ta kwada min kira na fito inyi sallah lokacin sallah yayi. Nace mama kin manta bana sallah ne ta ce oho ta shige dakin ta sai bayan sallah isha,i daddy ya dawo gidan suka zauna a dan falon mu har kanne na ciki suna kallon NTA dake labaran marance. Daddy ya duba bai ga na shigo ba yake tambayan ina nake mama tace ina dakina kafin yace wani abu wayan shi ne yayi kara ya dauka bayan sun gaisa ne yayi mai magana yana son magana da mama ne daddy yasa handfree din wayan yadda zai ji abinda yake fadi. Sun gaisa yace mama don Allah a dan sasauta ma khadija da takurawa tace na saka kuna zargin ta da aikata ba daidai ba ni kuma nasan idan har kun yarda da tarbiyan da kukai mata ba abinda zaisa ta canza daga baya kuma. Mama kiyi hakkuri khadija na nan a yadda kika santa alheri kuma yanzu na fara maku kuda ita muddin ina raye sai abinda yafi karfina ne bazan maku ba. Alherin yar ku gare ni ne ya jawo maku hakan ba ina nufin Khadija da wata manufa bane sai alheri don ta cancanci haka a gare ni so kuyi hakkuri a sake mata fuska babu komai sai alheri ga haduwana da khadija. Bayan sun gama waya da mama ya gama daure ni a gaban su da ban gane manufar maganan shi ba daddy ya kwala min kira daga falon. Da sauri na shigo dakin har lokacin shigan da na fita gidan hafsat ne a jikina ban cire ba na samay su a zaune falon. Gaidasu na fara yi tare da samun wuri na zauna mama tace khadija yaushe ne kika canza haka wai ? Nace cikin dago kai da mata kallon mamaki nace mama wanin abin nayi kuma again tace yanzu bamu da shakat a gidan nan dan abu kadan sai ki kai karan mu ga saurayin ki. Da sauri nace mama wane saurayina kuma danakai karan ku gare shi tace wanda kika jajibo a Abuja mana wanda ya fimu sanin zafin ki a yanzu. Mama ni ba saurayina bane wallahi ba wani abinda ya taba shiga tsakanin mu na soyayya har yau tace in babu yaya kika kai karana wurin shi wai na saki gaba a gidan nan tunda kika dawo. Kai kai innalillahi haka yace maku mama fada nayi mai fa akan abinda yayi min nace kina zargina ga abinda kika gani ya bari ban so. Daddy sai dariya yake muna ni da mama don yasan duk iya binciken shi bai gano wani abu da nake aikatawa a bayan su. Tun daga wanan ranan mama bata kara daure min fuska ba muka koma daidai a gidan kamar yadda muke a baya. Wayana gaba daya na kashe sai zan kira nake kunna wa don ban son wani abinda zai haifar min da matsala kuma tsakani na da iyayyena a gida. Ya rage saura kwana biyar mu koma makaranta sai ga kamal mai bi mun ya shigo da kaya wai ya Amina ta shigo gari. Da gudu na kwasa nayi waje ina masu sannu da zuwa tana sallaman driver da ya kawo ta gida na rungumay ta na sake ta naja hannun yaran na rungume su a jikina. Ciki muka shiga gaba dayan mu bayan ya Amina ta huta taci abinci tana zaune a falo na shigo da karamin dan ta a hannu na tace dada hutu ya kusa karewa dai nace wallahi ya Amina. Nakai zaune kusa da ita tace dama ina son in zo gida in samay ki kafin ki koma ne nace tau wani abin nayi ya Amina ? May ye ma baki yi ba khadija ina ke ina Abdulsamad mijin buzuwa fati da mijin ta ta barshi dole don wanan buzuwa ke yanzu kike kokarin jefe kan ki ciki. Kai ya Amina kuna bani mamaki wallahi wai ya fada maku muna soyayya dashi ne halan na san dai shi ba zai fada ba. In kuma don wanan abinda yayi ne kuke zaton muna tare ne da bakin shi ya fada ma daddy gaskiya ba sona yake ba. Haka kike tsamani ke ko azaton ki duk wanan alaman da yake gwada maki ba so bane hakan wani namiji zai samay ki yace bai so ki. Kin fi buzuwa durin na ya mace sai dai fari da gashi zata gwada maki ko farin ma ba wani can ba don ke ma ba baya ba. Sai yanzu nake gane maganan baban boy da yake cewa ke din matar manya ce watarana ina ganin kamar fadi dai yake yi. Abin mamaki ne yadda har Abdulsamad ya fada tarkon ki abinda ba wanda ya taba tsammani zai iya sai gashi lokaci guda har kin fara canza shi da naki sallon soyayyan. Mama da ta shigo dakin dauke da kwanon da ta tuka muna tawaska ta aje tana cewa ke ma dai kya fada idan anyi magana tace an matsa mata ba soyayya suke da shi ba ko takai karan guri shi. Shi ko ba kunya gare shi ba ya kira mutane yana rokon su akan a daina matsa mata don Allah ni daddy ku har mamaki yake bani yarda ya yarda da mutumin nan a lokaci daya. Da ban san halin shi ba sai ince ko don kudin shine yake son shi ya Amina tayi sauri cewa a a mama ba halin daddy bane haka da yana bin kudi da ba zan auri Abban su boy ba. Mama tace nasani ai shine abin ke ban mamaki yanzu ai tace yarda ne kawai wallahi in badon buzuwar matar shi ba ai Abdulsamad mijin aure ne ga ko wace mace ta samay shi. Nan ya Amina ta fara ba mama labarin shi da rayuwan su har karshe nace wai ku may yasa kuka damu da wata buzuwa can ne. Kowa tashi tafishe shi amma ni bata cikin tsarina ni dai kawai bai min bane ina zan jefa kaina ga family man mai iyali da yawa haka. Wanan duk ba matsala bane tunda yana da abin kula da koda mata nawa yayi niyar yi abin damuwa shine kishi da wanan buzuwan da bata da imani ko kadan. Balle idan taji ba barin shi zatayi ya aure ki ba kuna tana iya yima rayuwan ki illar yada taiwa fati ko sunan ta baya son ji yanzu. Allah bai bata iko a kaina nace ke don Allah rufawa mutane baki ana baki kina roko may kika taka da kike fadan haka nace mama Allah. ZAINAB IDRIS MAKAWA 1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Mommy wayayir mace mai haba haba da jamma irin matan nan ne masu fara,a a fuskan su kuma ita har cikin zuciyar ta haka take da kowa sai dai bata daukan raini. Abin ta bai rufe mata ido ba tana da ilimi na boko wadattace don duk matan na Abban su Abdulsamad suna da ilimin su ya aure su in ka debe ummi wace iyakarta secondary kadai tayi har hajiya mama mahaifiyar Abdulsamad a gidan shi ta hada karatun ta na NCE wanda dama koyarwa take koda ya aure ta. Ita anty amarya ma da aikin ta ya auro ta wanda yanzu ta daina duk ya hana matan nasa aiki ya tsaya ga bukatun su kuma. Mommy ne zaune tare da Abban yana karyawa hajiya mama wadda yaranta ke kira da hajiyan mu ko hajiya mama ta shigo falon. Akan maganan tafiyan mommy da Abdul din ya bugo yana mata tuni a daren jiya don sun fara tatauna maganan sai Abban bai bada goyon baya akan haka ba. Yanzu shine ta shigo ayita akaare idan zai yarda shigowan mama yayi daidai da shigowan hajiya ummi da anty Amarya data kira kaffinta shigo. Sun sami wurin sun zauna tare da fuskantar shi yasa yasan da magana sukazo mai ummi ce ta fara maganan amma sai anty amarya ta dan saka larin kishi a ciki tace ni naga ai ba sai taje ba ya mayar da matar shi mana zaifi sauki. Ummi da wanan kkaron bata goyi bayan maganan anty amaryan ba tace a a Sadiya tunda har kika ji wanan yaron ya bukaci hakan ai sai mu gode ma Allah da har wanan tunanen yazo mashi a rai. Ko ba komai ya kamata ace sanin halin ita Nafisa ya kamata wani daga cikin mu yaje ya zauna kamar yadda ya bukata din don ace mai daki shiyasan ida ruwa ke yoyo a dakin. Nidai kunsan ba lafiya ke gareni ba ba zan iya zuwa ba ita dai suwaiba din ya dace ta tafi don ita dai zainab din ya dace taje ta zauna dasu ta saka ido tunda da iyan bawa zasuyi tafiyan. Murmushi Abban yayi yace ke nan dai kun gama magana kuna goyon bayan dan ku ko ummi tace ba hakana bane Alhaji. Ganin dai dacewan hakan mukayi yasa muka goya baya ga maganan shi da kan shi babangidan ya fara tuntubana da wanan zancen da yazo na bashi goyon baya akan haka. Sai anty amarya ta kalle ta ta rausaya da kanta gefe daya bata kara magana ba har lokacin da Abba ya gama ja ma mommy kunne akan zaman da zatayi a gidan dan nasu. Suka bar mommy dashi a falon kowa ya kama gaban shi tun wanan ranan mommy ta fara shirin tafiya Abuja gidan Abdulsamad wanda suke kira da babangida kasancewa sunan mahaifin maigidan su ke gare shi. Abdulsamad bai fada ma Nafisa zuwan mommy ba gidan sai cin karen su ba babbaka suke ita da yan uwanta a gidan banza ta fadi masu kasa gasasa dama haka aladansu yake yar su ta auri mai arziki dangi su kwaso a taru aci arzikin ta. Mommy bata boye ma Anty Fati zancen tafiyan ta ba inda ta kirata ta fada mata da bakin ta tare da cewa zatayi iya kokarin ta taga ta shirya tsakanin ta da mijin ta kafin ta bar Abuja din. Allah ya kiyaye hanya Fati tai mata tare da cewa mommy amma fa sai kin hada da hakkuri don kun san Nafisa bata kaunar taga kowa ya rabi yaya Abdulsamad. Abinda yakai ni shi zanyi idan tayi ba daidai ba dole ne in fada mata gaskiya koda kuwa bata so dariya tayi don sanin halin Nafisa da tayi kamar yunwar cikin ta. Tsaye yake tsakar falon inda yake umartan masu aikin da ya shigo dasu da su gyara part din Fati yana masu kwatance yadda yake son gyaran. Nafisa da ke barci a dakin ta Yanyala ta shiga mata da maganar cewa may ke faruwa ne taga ana gyaran dayan part din da tace na uwar gidan ta ne. Kamar ba cikine a jikin ta ba ta diro saman gadon ta fito inda masu aikin su nan ta hausu da fada wayasa su aiki a gidan ta ba a fada mata ba. Daga bayan ta ya bata amsa yana saukowa daga sama yace nine nan maigidan na basu aiki suyi in biya su wani irin kallo mai kama da kai asuwa ta aika mashi. Bai tsaya kulata ba sai kokarin shiga dakin da yake yi tasha gaban shi da sauri ta tsare shi may kake nufi ne samad da wanan gyaran da akeyi ? Yace abinda kika gani Nafisa shi nake nufi don gida nawa ne ba naki ba kamar yadda kika fadi yanzu. Nan hankalin ta ya tashi sai ta fara surutu ita may yake nufi da ita da zai mata haka yace don yaga zata haihu zai dawo da fati da yaranta gidan shi. Tace nasan dama kule kulen da ake shiryama ke nan kake yawan zuwa kaduna akai akai yanzu dama ba so na yan uwanka keyi dani ba . Shi dai bai mata magana ba don mazan dake gidan suna aiki ya fita batunta basu raba hali a gaban su ba. Hankali tashe ta kira madam tana fada mata abinda ke faruwa madam tace kika sani ko watace zai dauko ya saka a dakin ba Fati ba ? Nan hankalin ta ya kara tashi sosai tace Nafisa dam wanan tunanen baizo min ba sai da kika tunatar dani haka yanzu. Madam tace to zauna nan kina fada akan fati wata tazo ta shige dakin kina gani saboda sakaci irin naki in zaki mike ki mike tun yaushe muka gama da wata fati can. Wacce hudi daya mukai mata muka fitar da ita a gidan har diyan ta sai tarihin su yanzu har kike tunanen ita zai mayar dakin ta. Ke kasar ku fa zaki koma aiki kaifi sai Niger nan kusa kafin ma mu dawo aiki ya kankama ko mu huta da ko wacece ma ke son muna kutse haka cikin ruwan sanyi. Nafisa tace madam kin san ba zuwan ba kuma ba kudin nake jiwa ba don zan iya saida da duk wani kaddara da nake da akan wanan aikin tunda yanzu na rasa gane kan shi. Matsala daya ne shine mutumin nawa yanzu kin san matsi yake min tun wanan tafiyan da mukayi ondo ya kara burge min a gidan nan baya sake min har yanzu ga kuma lalurar cikin nan dake jikina yanzu. Madam tace ke dai kawai tawa ki nemi kudi in ma bai barki ba sai ni inje maki manene amfanin zaman mu tare da ba zan iya maki komai ba. Ai kawai ki daina damun kan ki mu za a gwadawa hanyar boka ko malam kuma ko latsandan ne gaba da lahira indai ana zuwa zamuje shi. Sai lokacin Nafisa tayi ajiyan zuciya taji dadi a ranta tana ganin aduniya bata da kamar su madam dake tsaye a kan ta yanzu. Tace uwar dakina Allah dai yaja muna nisan kwana tare ni nasan banda kamar ki a duniyan nan yanzu. Da wanan shawaran hankalin Nafisa ya kwanta nan ta shiga buga waya gida Niger ko an samu wani bakon boka ko malami mai tashe a kasan. Sai da ya ga komai ya kankama yadda yake so ya bar gidan bayan ya sallami mutanen da sukai mashi aiki duk da yawan samari yan uwan Nafisa a gidan ba wanda zaiyi bugun gaba dashi yayi mashi aiki alhalin biyansu yake duk wata dasunan aiki suke mai a gida. Bayan kwana biyu su mommy sun gama shirin su tsab ya tura Yusuf ya dauko su zuwa garin Abujan mommy a gutin hajiya mama ta bar yaran ta tazo ita kadai sai iyan Bawa da suka zo tare da wata yar mai masu shara budurwa don taimaka masu da wani abin. Mommy sunyi waya da Ya Amina tana sallaman ta tace zata gidan Abdulsamad wanda matar shi watan haihuwan ta ya kama zasu dan kwana biyu acan . Ya Amina sai sulbul da baka tayi tace mommy ashe zaku hadu da Khadija na ke nan mummy tace banda abinki khadija dake makaranta ina zan ganta ni ? Sai dai idan sawa zanyi a dauko min ita ko akaini in gano maki lafiyan ta idan na samu lokaci dariya kawai ta Amina tayi don ta san gidan su Abdulsamad basu san komai ba a tsakanin mu dashi. Tafiyan rana sukayi don haka sai da yamma lis suka shigo garin Abuja din direct gidan shi suka nufa yana gida a lokacin don yana dakon zuwan su. Nafisa wace ke falo tana shan iska ga yan uwanta a kewaye da ita kowa na shaanin gaban shi sai sallaman su mommy da su iyan bawa suka ji . Gaban tane ya fadi da ganin su mommy din gidan don bata taba zaton zuwan su ba don a wautan Nafisa ta gama da kowa nashi yanzu babu mai marmarin zuwa inda yake. Zuwan su mommy ba karamin faduwan gaba yasa ta ba sai take ganin ai zancen auren da take zato ko dawowan Fati gidan gaskiya ne. Shiya fito daga daki bayan sunyi waya da Yusuf ya sheda mai sun iso ya fito da yar fara, a a fuskan shi yayin da ko kallo su mommy basu ishi Nafisa da yan uwanta dake falon ba . Shi da kanshiyayi masu iso dakin da zasu sauka din bayan dun gaisa sun mashi yaya gida ya fito tare da Yusuf da ya shigo da kayan su ciki da taimakon wani saurayi. Falon ya dawo inda suka samu Nafisa da yan uwanta sun juye harshe cikin yaren su na buzanci suna maganan zuwan su. Fuska a daure ya kalle ta yace Nafisa baki san mommy bane da gwago na iyan bawa da baki tare su da zuwa ba ? Tace a yatsune na san su mana ba matar mahaifin ka bane ita yace OK cikin wani irin kallo har ya fara tafiya sai ya juyo yace tunda kin san ta kin san kuma matar mahaifina ne baki iya taron su ba nima haka ban son in fita yanzu in dawo in samu wa yan nan yan uwan naki a gidan nan yanzu. Yana fadar haka ya juya ya fara tafiya tace wallahi baka isa ba don zuwan su zakace yan uwana su bar maka gidan ka yanzu yace zaki san na isa idan yan sanda dun shigo sun fitar min dasu. Idan akwai abin da yan Niger sukaki jini shine dan kakin Nigeria don basu yi masu da wasa idan sun farmake su. Nan Yanyala ta fara magana tace haba Allaji ai bin baikai can ba daga dan wanan magana har zaikai ka kira muna polizawa kawai dai jira muke su huta mu mika masu gaisuwan mu. Ya fice zuwa nemo ma su mommy abinda zasu ci a gidan don yasan ba zasu iya taba cin abincin da suka dafa ba. Bai dauki lokaci ba ya dawo dauke da ledoji iri na restaurant dauke abinci dasu ruwa a ciki ya bayar aka shigo masu dashi har dakin. Mommy ta idar da sallah sai ga yaron shi isyaka yana shigo da kayan ciki tare da gaba tar masu da abincin. Sunka ce har da dawai niya zuwa sayo abinci kuma nan dai iyan bawa ta kasa hakkuri tace zainabu may kika fahinta ga wanan zaman ? Murmushi mommy tayi tace ke dai iyan bawa ai ayi shani kawai wai ancuci na kauye wanan matar bata da hali ko kadan. Kin dai fara ganin makasudin zuwan mu garin nan ke nan don fitar shi kunyan abokan shi nasan halin matar nan tashi dakilace na gani a fada. Ba zamu sakar mata fuskan da zata kawo muna raini ko wulakanci ba don nasan tun zuwan mu batayi farin ciki da ganin mu ba. Sunci abinci sun huta sai ga Nafisa ta shigo tayi wanka ta saka sutura a jikin ta yan uwan ta suna mara mata baya suka shigo dakin. A falo suka samay su nan ta ja ta tsaya bata zauna ba tana fadin kunzo lafiya ya hanya da mutanen gida ? Mommy tace lafiya duk suna gaida ku yaya nauyi Allah ya rabaku lafiya tace amin sauran suka shiga gaida su da yi masu ya hanya suka fice daga dakin ba wanda ya zauna. Shiko bayan ya mika sakon wuri na ya nufa kamar yadda ya saba zuwa man koda ya kirani muna tare da maryam da zarah a dakina kiranshi ya shigo min. Mutumin ki ne halan yazo maryam take tambayana nace cikin tabe baki shine ai kin san bai tashi zuwa min sai wanan lokaci. Maryam tace ai kuna daidai dashi in kin isa ki fadi a gaban shi yana da amsan baki indai wanan yaya in love din kine. Kai maryam kina da wuyan sha,ani wallahi na fada maki ba soyayya a tsakani na dashi sai amin taka kawai na damuwa. Zarah ta dago kai tace min wani guy kuke magana muje in gani idan ya min in saka shi a layi mu shiga sha,ani dashi. Zarah wai ke baki jin kunyan fadin fitsrane haka tace in banda abinki wake ta wani wasa da so yanzu khadija bari kiyi wasa da daman ki yanzu yan jami,an nan suyi maki wuf dashi. Idan banda abinki an fada maki kowane yan matan jamia ke iya wuf dashi kai daya zarah wanan ya wuce sanin ki wallahi. Dariya tayi tace muje inga guy din nan dai da kuke wani zuzutawa haka dai murmushi nayi kawai don ba zan so a ganni da ita ba. Duk da ba wani shiga na yi ba amma suna ta yaba kyau da nayi wai na hadu zarah na fadin ashe zaki zama yar hannu haka khadija. Tare muka fito dasu sun zo su gaida shi tunda muka tunkare shi zarah ta tsunke da ganin motar da yazo da ita tana fadin tun ban ga guy din ba wallahi nasan zai hadu ko don motar nan da nagani how lucky you are da kika iya canko wanan zukeken guy haka. Mun iso yana ta faman ansa call a wayan shi sai da zarah ta kare mai kallo ta dago bayan ya gama wayan suna gaida shi bai wani sake fuska ba ya amsa gaisuwan. Tare da kawar da kanshi gefe daya zarah tace dama na sani sai irin wanan guy din khadija wanan jan ajin naki yayi yawa wallahi har ta gama ta wuce bai yi magana ba suna shiga maryam ta nufi dakin ta. Maganar shi ta farko bayan wucewar su shine ina kika samo wanan kawar kuma ? Nace a inda ka gan mu yanzu yace No ba girman ki bane da mutuncin ki yawo da irin wayan nan nace kawatace fa tare mukazo karatu daga gida. Na fada maki bana son in kara ganin ki tare da ita please na juyo ina kallon shi ido cikin ido nace tana da aibu ne komay ? Au ke baki ga aibu ta ba wanan bata da kamun kai ba girman ki bane yawo da ita nace ka taba ganin mu a tare ne ko yanzu ma daurowa tayi ka gan mu da ita. Har ya bude baki zaiyi magana sai kuma yayi shiru nima shirun nayi ba wanda yayi magana daga cikin mu. Can naji yace idan na fada maki wani abu zaki yarda dani ? Zaki yarda gaskiya nake fadi. Murmushi nayi nace idan maganar ta kama gaskiya mai zai hana nayarda tunda nasan gaskiya ka fada. Kin yarda dani khadija ? Nace na yarda dakai mana yaya Abdul fati da mijin buzuwa ina fadi ina mashi dariyan shakiyanci cikin gatse. Shima murmishin ya dan yi wanda sai wanda ya sanshi zai iya fahintar hakan daga gare shi yace kin san kamun kan ki yasa muke tare da ke har wanan lokacin. Kasan ni ne da zaka wani ce ina da kamun kai bayan iyakar mu dan wanan haduwan da muke yi. Na tsinci muryan shi yana fadin niko na sanki khadija you are classic baby da na taba haduwa da ita a rayuwana. Katse shi nayi da fadin may ke faruwa daksi haka ne wai ke irin wanan magana yanzu a kai na ko last zuwa da kayi haka ka dinga min wanan maganganun. Ya girgiza min kai tare da fadin ba komai cikin lumshe idanuwa shi sai kuma ya bude su ya sani gaba yana kallo na. Shirun motar na kawar da fadin yau ba fita ke nan yace ina kike son muje nace inda ka saba zuwa mana mu zaga gari kawai kana barnan man motar ka. Haka kika dauki fitan namu dama nace hakane mana tunda ba wani guri muke zuwa ba. Ke ce baki fahinci muhinmancin fitar namu ba kila amma ni yana da ma,ana masu yawa a gare ni matuka khadija. Don kasan cewan mu a tare you have change me now na fahinci su abubuwa da dama da ban taba fuskantar su ba a baya. Maganan gaskiya yau kin dawo min da farin ciki rayuwana har iyayyena sun zo gida da sunan kwana biyu a wuri na. Da sauri nace cikin murna wai da gaske kake yi yace kwarai kuwa deeda don yanzu haka mommy da gwagona iyan bawa na gida maganan nan da muke yi dake. Taya kike ganin bazan maki godiya a wanan kangin da nake ganin kin fitar dani wanda a da nake dauka da shirmay irin naki na yara kike yi. Sun kuyar da kai nayi kasa ina tunane hankalina yayi nisa bani jin abinda yake fadi tsoro na daya ne kada mommy tasan ina tare dashi ta fasara haduwan mu a wata manufa. Ban sauri maganan shi ba na katse shi da fadin zan roke don Allah kada ka bari mommy tasan kana zuwa inda nake don bansan da wani ido zan kallesu ba har hajiyan ka. Ya lura da irin rudewan da na shiga sai dai baice min komai ba ganin bai yi magana ba yasa nace please yaya Abdulsamad ka boye wanan a matsayin siri a tsakanin mu don Allah. Kallo na yayi ya sauke murmushi yace saboda may kike son kada su san ina tare dake nace dashi wayyo Allah kana son su dauke ni yar cin amana ne ko may ? Cikin sanyi murya nace kasan su ba zasu gane mutunci ke tsakanin mu ba sai su dauka muna tare da wani manufan da bashi ba. Hakan kuma yana nufi na ci amanan su ke nan gama yadda suke son Fatin ka a gidan yanzu kuma sai su gan mu tare yaya kake ganin zasu dauki abin. Kai tsaye yace zasufi kowa farin cikin da hakan na sani tunda sun san ki sun san halin ki zasu yi farin ciki da hakan. Daga yau magana ya kare ba sauran wani abu a tsakanin mu tunda bukatar mu ya biya ka shirya tsakanin ka da yan uwan ka. Mamaki magana na ya bashi yace juyo yana kallo na sai can yace ai deal namu bai kare ba tukun ko kin manta baki karasa aikin ki ba akan fati ? Na amsa da fafin kwarai bamu kai nan ba cikin takaici nace wana kuma yanzu ya rage gare ka sai kasan yadda ka shirya da matarka. Ba wani sauran magana yanzu a tsakanin mu kuma na fada cikin tsiwa ya juyo da kyau ya kalle ni yace don mommy tazo duk kike fadan wanan magana ko may. No ba don tazo ba in ma don tazo din ne haka ne bana son su dauki abinda wani fassarane kawai. Ya zura min idon sa yana kallin yadda duk na rude yace a ranshi ashe karyan rashi kunya nakeyi a da gashi yanzu daga jin mommy tazo duk na bi na birkice lokaci daya. Motar tayi tsit kowa da abinda yake tunane a ran shi sai da ya shafa kan shi naji yace relax deeda wace dake mommy zata san da wanan maganan dake tsakani mu wai ? Wata zuciyane ta bashi shawaran ya min wayau kawai don yadda na rikece din nan daga jin mommy tazo zai iya sa komai ya faru idan ya biye min. Kawar da zancen yayi da fadin zuwa nayi ki ban shawara yaya zan yi da Nafisa don batai farin ciki da zuwan nasu ba yanzu haka. Da sauri na dago kai na kalle shi da idona da suka sauya kala nace baka fada mata zancen zuwan su bane dama , ? Kai ya girgiza min yace ban fada mata zasu zo ba tunda ba itace ta aje ni ba yan uwan ta dake zuwa ai ba fada min take yi ba itama. Kada kaga laifinta a yanzu don kai kai sake har haka ya kasance tun farko saboda tsoron ta da kake nuna kanayi da farko. Ba tsoran ta nake yi ba deeda kaunane kawai na tsakanin miji da mata wanda ita ta dauka tsoron tane yasa nake mata hakan. Sai yanzun kasan da wanan yana iya faruwa ka manta a lokacin da take saka abu kana mata shi koda kuwa baka son abin ? Ya gyara zama yana fadin shine babban kuskure dana tabka a farko wanda nake nadaman yi shi a yanzu haka. Duk abinda zakayi ko zatayi kada ka bari rainin matarka yakai ga iyayyen ka don ko zaka iya canza mata amma ba zamu iya canza iyayye ba. Wai ke wake koya maki wanan hikimar haka nr ya tambaya cikin son in bashi amsa nace baka son maganan ke nan. Yace No idan ban so ai ba zan fada maki zuciyana na ba a yanzu don da zuwan su abinda tayi masu yaci min rai sosai ba zan boye maki ba don yanzu ke ce abokiyar shawarata shiyasa nazo maki da zancen. Yaya zanyi khadija ina son in fita daga cikin dana shiga a bayane gida na yanzu bana son su mommy su fahinci sakaci na a gida na. Nace na yaushe kuma saidai kada a kara muma makwabta ku mun sanni balle su mommy dake gidan tare ku. Ina son mata na khadija shiyasa har haka ya faru da ni kallon shi nake cikin mamakin kalamin shi na wai yana son matan shi da yace. Shin shi wani iriin mutum ne wai nace nafisa dai kake so amma baka son fati kowa ma yasan da hakan ? Haka kuke tunane ya fadi cikin zafin zuciya amma ita ai tasan ina sonta halin ta ne kawai baizo daya da nawa ba shine matsalan mu. Kalon shi nake sororo kamar na samu tv da alama yarasa yaya zaiyi da damywar shi ne ya tsinci kanshi cikin fada min sirin zuciyar a matsayi shi na mutum mai shekaru kamar shi. Tausayi ya bani don na fuskanci bayan Yusuf da suke tare baida wani wanda zai fada ma zuciyan shi ya fahince shi shiyasa yazo gare ni. Nace wallahi rayuwan ka na cikin hadari ya kamata ka koma ga Allah kayi abinda Allah yace shine kawai mafita a gare ka. Lokaci ya duba yace zai tafi lokacin sallah ya gabato zai dawo gobe tunda ba school mu karasa tataunawa mukai sallama ya tafi ya barni cike da tausayi shi. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Tunda ya je office ya kasa aiwata komai a office din ga Yusuf bai shigo ba har lokacin ranshi ke kara baci idan ya tuna da kalaman nan daya dana fada shi yafi bata mashi rai ko yaushe. Shigowan Yusuf office din tun daga nesa ya karanta zuciyar abokin nashi ya karaso gaban tebur din shi yana fadin wani abu ya faru ne na ganka haka. Tsuki yaja tare da juya kujeran da yake zaune sama yace may ye ma bai faru ba Yusuf wai kasan matar nan bata gida tun ranan da muka tafi kaduna. Ba ita ta dawo ba sai karfe biyu da wani abu ta shigo gida jiya da sauri Yusuf yace ina taje haka ko da sanin ka ta tafi yace idan na sani abin zai damay ni haka ne ? Kai wai may yasa wasu matan samun wuri ke sa su wuce limit din su ne na mata akan may mace mai ciki zatayi irin wanan tafiya haka ba tare da sanin mijin ta ba. Bata tsoron wani abu yaje ya samay ta a can yace ma Yusuf ni ba wanan ne damuwa na ba damuwa na shine ina taje ? Jiya jiyan nan Khadija taban wani mugun labari wai buzaye sukan baro mazan su na gado su shigo nan suyi auren bugi don kudi ni wanan abin shi abinda ya tsaya min a rai na. Ita Khadija ta fada ma hakana sosai kuwa jiya muna tare da ita tana zayano min halin buzaye sai naga babu abinda ta rage daga cikin halin Nafisa har ma da wasu da ban sani ba takara min haske akai. Lalai Khadija jarumar gaske ce tunda har ta tsaya ta iya fahintar dakai wanan abin yace ka san hauka irin nata ita bata dauka maganan ai zaiyi tasiri a raina ba haka. Yanzu fa har na fara zargin yawan tafiyan Nafisa kasan su akai akai da takeyi tunda gashi har yakai ta fara satan tafiya haka. Da fa shi yayi yace kada ka zargeta da wanan don ta fadi haka ba lallai ne haka ya zamo gaskiya ba akan Nafisa din sai dai idan wasu sun su suna yin hakan bance a a ba don son kudin su yayi yawa. Kai ina bazan yar da ba Yusuf ko na yarda da komai ba zan yarda da wanan gantalin da Nafisa ta dauko yi ba dole ne in dauki mataki a kai. Tunda ta fara haka maganin abin kawai ya kamata kayi don tana ganin ita kadai ke gare ka yasa take abinda taga dama a gidan. Yanzu zabi biyu shine nake ganin mafita a gare ka na farko walau Fati ta dawo ko nabiyu ka kara aure don ganin da takeyi ita kadai ce yasa take wa yan nan abubuwa haka. Ido ta kura wa Yusuf dake magana sai da yayi shiru yace Fati ita ta kasa zama saboda rashin hakkurin ta. Kai ya girgiza mashi yace ka daina fadin Fati bata da hakkuri halin Nafisa dai ya kori Fati gidan ka wanda a lokacin baka ganin haka kai. Zaka iya bata wani daman a yanzu ko abin zai gyaru a tsakanin ku amma fa sai ka jajirce wa hakan kafin komai ya zama dai dai don Nafisa shuumace ta kwarai. Ba zata taba bari kuyi zaman lafiya da Fati kawai a gidan ka dole sai da wace mace a tsakani mai kwato mata nata hakkin idan kun cuta mata. Bai iya magana ba sai jawo file din gaban shi yayi ya fara aiki ba tare da ya san abinda yake yi ba. Fita yayi ya bar mashi office don yasan halin tunda yayi haka ba amsan maganan shi zai samu ba a lokacin. Ya kai wani lokaci yana aikin da zuciyar shi raki sakewa don haka ya rufe files din ya mike tare da nufar hanyar fita office din. Gida ya nufa kai tsaye lokacin sha biyu da wani abu na rana tun daga kofa yake jin tashin sautin wakan yan yaren su cikin harshen buzaci ya karade gidan. Bai ko kali gefen da suke zaune ba ya hau sama ya shige dakin shi tare da rufo kofan da karfi zuwa yanzu sun fara isan shi a gida. Mutane haka ba kimsi ko kadan sai bakin ci da ihu yau ma don samun wuri kidan suka sake mai haka a gida anya ma suna wani cikaken ibada kuwa tunanen da yake kenan Nafisa ta turo kofan dakin ta shigo. Sau daya ya kalle ta ya kawar da kanshi gare ta ta karaso kusa dashi da shi ra tsaya cikin murya da maida hankali gare shi tace lafiya yau kadawo a wanan lokacin haka ? Kallon ta yayi ya kawar da kan shi gefe daya ta sake cewa magana fa nake maka wai may ke damun ka ne haka ? Ya dago ido ya sake kallon ta da idanun shi da sukayi jawur yace ban son damuwa a wanan lokacin tace haba mai gida ai wanda duk ya ganka a wanan lokacin yasan akwai damuwa a tare da kai. Matsalar ki ce ta isheni Nafisa in ma ina da damuwa bai wuce halin ki ba tace halina na kamar yaya wani abin nayi maka ko may ? Au baki ma san abin da kikai min ba ke nan kike nufi tace don kawai na fita na dade shine zai zama matsala haka ? Fita nayi kuma gani na dawo lafiya sai may da zaka dauki wanan a babban matsala kuma ko nace ka barni in fita na san ba barina zakayi ba inje inyi lalurar gabana. Ina kika je har kwana biyu baki gidan nan tayi shiru tana tunanen karyan da zata yi mashi ya yarda da ita a lokacin. Ya sake tambayan ta sai tace na tafi bukin kawata ce da ta haihu a jos don ko na fada ma ba zaka yarda in tafi ba. Duban ta yayi cike da zargin ta sannan yace wata kawa kike da ita haka a jos da ban santa ba har zaki iya zuwa ki kwana biyu a bukin ta ? Ta dan zaro idanu tace dole ne sai ka san kawaye na duka wai yace da kyau Nafisa wanan halin da kika dauko a yanzu sam ba zan dauke su ba . Tunda har kika iya tafiya na kwanaki don kawai bukin wata kawa taki buki nawa akayi a gidan mu sau nawa kika taba zuwa? Sam yanzu zuciya ta ta soma zargin ki da aikata wani abu akaina da ba daidai ba sakamakin hurda da matan barikin da kike a yanzu. Zargina ka fara ne Samad akan may ba zan rage ki ba halayen ki gaba daya yanzu sun gundureni baki zama gida ba yar aiki ba ba wata yar kasuwa ba amma ke kenan kulun yawo fita. Gaba daya kin shiga rayuwana kin hana min farin ciki kin hana mata na ta zauna dakinta ke kuma ba kula nake samu a gurin ki ba. Au matar ka kace kace dama matar ka kake son ta dawo kawai kake wanan kamay kamay haka idan zata dawo zaki hana ne ko may ? , Ta dube shi a hasale to ta dawo din mu gani mana sai may yadda ta dawo haka zata koma da kafan ta. Yace haka kika ce tace na fada sai may ? Baya ya bata batare da ya kara juyawa kanta ba ta tsaya tana ta jidali wai ai dama ta sani zuwa kadunan da yakeyi yanzu saboda fati yake zuwa da yaran shi. Mamaki yayi sosai da ta iya karfin halin furta hakan lallai yasan ya cuci Fati da yawa ita da tazo daga baya ta iya fadan haka ? Ina ga Fatin da zaman gidan ya gagare ta da yaranta dole suka bar mata gidan har diyan shi ita ko tana zaune yan uwan ta da yarta a cikin salama. Lalai ya tabka babban kuskure a rayuwan shi dole kowa nashi ya tsane shi yanzu don sam shi bai taba hango wanan abin ba sai yanzu da taimakon Yusuf da khadija suka ganar dashi gaskiyar hakan. Ido ya rufe kamar yana barci don bai son hayaniya ko kadan gashi ya jawowa kanshi yar hayaniya a rayuwan shi bai taba nadamar auren nafisa ba sai wanan karo. Mikewa yayi ya shiga ban daki ya dauro alwala yazo ya tayar da sallah azahar ya gama ya dade zaune a gurin anan wayan Yusuf ya shigo mai yana tambayan shi yana ina ne ? Yace gida sai ya kashe wayan yasan damuwa ce taimai yawa yasa ya koma gida yasan ko a gidan ba wani sauki zai samu ba, don ko yasan Nafisa ba zata kyale shi ba. Sai dayayi sallah karfe hudu ya fito daga gidan kai tsaye ya yanke shawaran zuwa guri na don irin shammatan junan da mukeyi yana sashi nishadi a ranshi haka yasa ya nufi inda nake. Bai faye son zuwa wurina tare da Yusuf ba yanzu don idan sunje tare hiran kan koma tsakani na da Yusuf ne don bai iya sake jiki yayi komai a gaban Yusuf di yanda ya samu dama a zuwan karshe. Ya iso bakin hostel din sai da ya kare ma gurin kallon yadda mutane suke ta faman shige da fice ya daga waya ya kirani kamar kullun gani kofan hostel din ku yace ya kashe wayan. Muna zaune girki na gama muna muna ci kiran shi ya shigo min kalon maryam nayi nace wai may wanan mutumin ke nufi ne maryam jiya fa ce min yayi zai yi tafiya ba zamu sake haduwa sai ya dawo yanzun kuma may zo nema nan ? Dariya tayi tace ke mana don Allah tashi kije kada ki bata mai lokaci dan hararan ta nayi nace na kirashi ne ? Sai da na tsaya shirya nasa wasu material a jikina din kin buje da riga akai min wani zuwa kaduna da nayi maron colour dinkin yadan matse min jiki kadan don dan jikin dana kara yanzu. Sun kama min jiki tam sai kitson da mukayi satin nan na ghana wiving ya kara fito min da fuskana shar ga matsiyacin kamshin dake tashi a jikina wanda ke tafiya da imanin wanda ya shaka. Tun daga nisa ya zuba min ido yana karewa shiga na kallo har na karaso inda yake kofan motar ya bude min wai nashiga. Naki nace cikin girgiza mashi kaina yace common shigo don Allah mu tafi rakiya zaki min wani guri da sauri nace a hakan zan tafi wani gu. Ko banza kuma ba zan shiga motar ka ba again agogon hannun shi ya duba yace cikin dakewa kina bata min lokaci ki shiga mutafi. Tunda muka fara tafiya ba wanda yai magana a motar sai shi dake tuki a hankali cikin wani irin yana yi yana yi yana wani furzo iska daga bskin shi lokaci lokaci. Sai can ya juyo inda nake yace zakici wani abune kaina yana a waya na da sauri na dago kai nace wani sai kuma ja girgiza mashi kai nace ni a koshe nake. Ok rakani inci wani abu tun safe banci abinci ba da sauri na zaro ido nace azumi kayi ne ? Dashi nayi ma da zai fi min sauki yace ba tare da ya dube ni ba na mayar da kaina ga titi ina kallo sai kuma can kamar an tsunkule nace matar ka tayi tafiya ne ? Bai bani amsa ba sai karya kan motar shi da yayi zuwa wani restaurant din abinci mai kyau gurin da daukan ido ya parke a wurin . Mun shiga naga tsarin wurin yana da kyau sosai da alama yasan wurin da kyau don wani ke bebben wuri naga yana nufa a cikin wurin. Min zauna masu aiki gurin suka zo suna tambayan shi mai za a kawo muna ne yace ferfesu kawai zai sha bayan an mika mai dan takarda ya duba. Koda aka kawo mai bai wani sha da yawa ba naka ya aje cibin yana goge bakin shi tare da fadin tashi muje kawai nikan mike wa nayi nabi bayan shi. Sai da ya biya su kudin su muka fice muka bar gurin ina mamaki a raina nace yaya mutum kamar shi baici komai ba sai a wurin cin abinci zaici kuma bai tsaya yaci wani abin kirki ba. Kasa hakkuri nayi nace amma wanan ba girman ka bane cin abinci a waje alhali kana da iya li kuma a gari. Kamar bai jini ba yana tukin shi sai dai ban san ida muka nufa ba can naji yace dani yaya kike son inyi khadija in banci abinci a waje ba ? Kamar yaya kuma kana da mata a gida zaka ce haka yaya Abdul yace sunana Abdulsamad ko ke ma zaki bata min suna ne ? Yi hakkuri bani na kashe karen ba ratayan buzu ba zai zama nawa ba in bai zama naki ba wace ki dauki karen ? Naci yau kana da magana ke nan yace da yawa khadija iam not in good mood at all. Ayyah sorry Allah ya sauwa koma maye yayi maka mafita a kan shi yace amin na gode da adduan ki gare ni yaci gaba da tuki. Matsala a gun aiki ne ya taso maka yace matsala a gida na yake subbahanallahi nace dashi tare da dan kallon fuskan shi. Yace khadija dole in ci abinci a waje ko in zauna da yunwa ko zaki taimaka ki dinga bani abinci in dinga zuwa wurin ki ina ci idan na taso office. Kai don Allah ka daina zolaya abincin yan makaranta ne zakaci wanan ai sai mu da yazama muna dole muci shi. Badai ke kina ci ba nace sosai kuwa yace to ni mai zai hana inci tunda ke kika iyaci sai dai idan rowa zaki min kuma beside ke kika ce na daina cin abincin waje. Nace matar da ran ta da lafiyan ta zaka wai ni na dinga dafa ma abinci kamar wata wacce ka aje da zaman banza. Bai kara magana ba sai horn da yayi a bakin wani gida aka bude mai muka shiga dayan motar da suke zuwa wuri na da farko ne na gani a gidan. Maigidan na ciki ya tambayi mai gadi ya na gaishe shi bai amsa ba ya jefa mai tambayan shi sai maigadin yace yana nan bai dade da shigowa gidan ba. Fita yayi daga motan ya zagayo ya bude bangare da nake zaune jin ya tambayi mai gidan yasa banji wani tsoron shiga gidan ba. Sanyin A C ne ya tari fuskana da kamshin air freshner da falon ya dauka falon ya tsaru komai akwai a ciki ga wasu manyan kujeru da aka kawata falon dasu. Yana waya koda muke shiga gidan yana fadin kafito gamu a falon gidan ka yace a wayan baifi second ba naji ana bude kofan daga cikin gidan sai ganin Yusuf ya fito yana saye da kayan shan iska irin ta maza wando dogo tare da yar riga armless a jikin shi. Yana gani na ya bude baki da mamaki yace kace yau ina da babban bakuwa a gidana ina kafito da yar mama da yamman nan haka ? Ya nuna mun kujera da hannu yace bissimillah zauna mana khadija bamu hadu ba sai yau nace ina wuni ya amsa da lafiya kalau ya kike ? Ina nan lafiya yace Alhamdullahi yau sai gaki a gida na kwatsam na gan ki ba tsammani nace wallahi ga wanda ya dauko ni nan bai fada min ida zamu zo ba yace dai wani guri zan raka shi. Yayi maki wayan manya kenan don ya baki mamaki dan hararan gefen da yake nayi mikewa Yusuf yayi yana fadin barin kawo maku abinsha sai dai kiyi hakkuri kin san gidan gwauro kika zo. Da sauri na dago kai ina kallon shi da mamaki nace baka da aure ne dama yace eh baki sani bane yar mama ? Ashe mutumin bai fada maki komai game da ni ba yace ma Yusuf din an fada ma kowa irin ka ne mai zuba a lokaci guda. Yusuf yana dariya ya wuce inda fridge din shi yake ya dauko drink a ciki tare da kofuna ya kawo gaban mu ya aje nidai ido nake binsu dashi kawai. Ya aje tare da zama yana fadin bissimillah kusha lemon shi yasha nin ban sha ba gani nake kamar plain ne suke shirya min in fada ciki. Yayi yayi dani don insha nace wallahi na gode mai zai sa ka damu haka idan bata sha ba yace mai kasan bakuwa tace ita dole in damu idan tazo gida na bataci wani abu ba. Daukan cup nayi na tsiyayya kadan na dan kurba na aje cup din ina fadin na gode shima tunda ya kurba sau biyu ya koma ya jingina da kujera tare da dafe kanshi da hannun shi . Yaya dai Abdulsamad lafiya ko dan tsuki yaja tare da kara dafe kan nashi fuskan shi ya nuna alamun bacin rai da damuwa. Juyawa yayi guri na yana fadin may ke faruwa ne khadija nace nima haka naganshi wallahi ko maganan da nayi mai ne yasa shi bacin rai ban sani ba ? Ni kuma gaskiya na fada mai ba girman shi bane cin abinci a waje ban san ranshi zai baci da kalamina ba na fada mai haka. Dariya ya dan yi tare da fadin see you akan dan wanan maganan zan bata raina ai gaskiya kika fada bai dace ba nima na san da hakan. Watau khadija mutumin naki yana da matsala ne a gidan shi wallahi wana abin ya dade yana damun mu muma. Ace mutum kamar wanan ba abinda ya nema ya rasa a duniya amma cin abincin gidan shi ya gagare shi sai na waje ? Shiru nayi ina kallon shi yace ya zama dole mu samu mafita akan wanan matsala kada abin yazo yai yawa na yaushe kuma ? Ko sau daya aka ganka a waje kana magidanci kana cin abincin sayarwa ai girma ya fadi ko a wurin mutane sai dai a gyara don gaba. Yarinya kamar tsuhuwa wurin iya tsara magana haka ashe shiya take karatun lauya ya fada a ranshi. Khadija ni na rasa samun mafita ka wanan matsalar wallahi don ko nafisa ba gyarawa zatayi ba tunda in ita batayi ba bata bari kuma ya dauko yar aiki irin namu na nan wace ta iya saidai yan uwan ta zasuyi. Wanan kuma shi ya daukar mata don shi yaga zai iya zama a haka don may ba zai dawo da matar shi hala tsoron ta yake yi ? Sai lokacin ya cire hannun shi da ke saman kanshi yace tsoro tsoron wa nace ka alamu nan sun nuna kuwa buzuwa ta shiga gaban ka. Ke fa baki da kunya din kikan wuce limit din ki nayi saurin fadin wurin fadin gaskiya ba haka nan Ya Amina na ke fada min wai banda tsoron fadin magana ga kowa. Ni kuma naga idan gaskiya tazo a fadeta komai dacin ta kuwa dayake baki da kunya ba zaki iya fadin maganan da wani bai iya fadi ai . Ciki ciki nace a nan zaka zare idanu agida ko a zare maka idanu matsorancin banza kawai. Ban yi aune ba na gan shi a gaba na waye matsoraci yace cikin zare min idanu Yusuf nace ni gaskiya na fada ai Yusuf ne yace daga fadin gaskiya sai leifi ? Laifin ka ne mana kaima ka sani ai in ba tsoro ba ka dauki mataki mana a kan haka mugani nace aishi na gani walla, , , Hannu shi yake ya kamo bakina yana fafin wanan wanan baki sai nayi maganin shi wataran zai shiga hankalin shi. Don Allah ka bari bana son namiji yana taba min jiki wallahi kin dauke ni dan iska ke nan ashe nace bai da kyau yin haka ka sani. Yusuf yana dariya yace ina zuwa ya barmu a gurin zama yayi a kusa dani yana fadin bari ma yau in nuna maki dan iskan nake. Tsoro ne ya kamani yadda ya zauna a kusa dani din nace may ye haka malam ? Malama iskancin nake son nuna maki kalan tawa ki gani ya rankwafo inda fuskana yake har muna iya jin hucin numfashin juna a lokacin. Cikin sanyi murya nace ka dai san hakan bai dace ba a addinance ai kin san ban san addini ba ni yace wanan ba gaskiya bane don gidan ku kaf hazifai ne kuna karatun addini tun kuna kanana . Sai naga ya maida kanshi saman kujera yana zaune kamar yadda yake bai daga kusa dani ba yace khadija ina cikin matsala wallahi ina son in gyagyara wasu abubuwan da suka baci min a yanzu. But i don't know how to make things easy ? Tausayi ya bani nace ka yawai ta addua da sadaka ga dukan al,umurorin ka sai kaga Allah ya kawo maka mafita a ciki. Sai ya mike daga hannun kujeran yana fadi n muje in mayar dake yamma ya fara yanzu saurin mike wa nayi ya kira yusuf a waya yana fadin mun tafi. Yafito da sauri tare da fadin har kun gama hiran ta masoyana zaku tafi kai haba yayana firan masoya kuma a haka ? Har ya fara tafiya shi muka mara mai baya yusuf ya bani hakkuri akan bai bani komai ba gashi na kawo mai ziyara. Ba koma nace muka kama hanya na tsaye sai da yaga wucewar mune ya sauke murmushi tare da fadin ikon Allah komai yana da sanadin shi. Wanan karamar yarinya kuma Allah ya jefo a rayuwan Abdulsamad mutumin da magana da mace a wurin shi aiki ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Gidan ya nufa kai tsaye tare da sayayyan da yayiwa bakin shi na abubuwan bukatun su ya nufi part din fati dashi. Babu kowa a falon sai yake mamaki yau ina mutanen gidan su shiga haka duk da basu ciki hakan bai hana falon nashi jin tashin yanayin da jikin su ke dashi ba a falon. Hakana har ya isa gurin su mommy zuciyar shi cike da tambaya da tunane ya samay su a zaune suna hira yarinyar da suka zo da ita tana cin abinci. Sai da ya aje kayan a gaban mommy ya zauna lokacin ya fara gaida su suna kara mashi yaya sula samay su yace mummy lafiya sai hamdala. Nan dai ya zauna dasu suka dan taba hira har wani lokaci sai ga Nafisa ta biyu shi har dakin dags kofa ta tsaya ta kira sunan shi. Bayan ya amsa kamar ba zai tashi ba sai kuma ya mike ya tafi sude su mommy kala basu ce ba suna kallon ikon Allah kawai. Ya fito ya samay ta zaune falo tana ganin shi ta mike da kyat ta fara fadin muje sama ina da magana dakai ne ta juya ta fara tafiya yana biye da ita a bayan shi. Ko da suka hau sama bai tsaya bin ta nata ba don har ta juyo da nufin tayi mai abinda ta kulla a ranta sai hango shi tayi yana bude kofan dakin shi kai tsaye. Ido ta bishi dashi tana fadin samad maganar nakira ka muyi zaka shige kuma yace baki san dakina bane ko a kan hanya kike son maganan da ni ? Sai lokacin ta dan juya ta dubu wurin da suke tsaye din sai kuma tayi shiru don ita bata ga komai a nan ba don sunyi magana ai gidan su ne. Dakin ta samay shi tsaye yana rage kaya a jikin shi ta fado dakin babu ko sallama ya dan juyo ta kalle ta ya kawar da kanshi gefe yaci gaba da abinda yake yi. Bayan shi ta tsaya tana kama baya tare da fadin Samad wai may wanan mutane suka zo yi ne a gidan nan ? Yaushe zasu koma don ban son sa ido da takura a gida na sai da ya gama cire kayan ya rage daga shi sai boxes a jikin shi yace cikin duban ta ina fatan wa yan nan mutanen da nace su bar min gida na yau sun bari ? Tsaye tayi sororo tans kallon shi ta shige ban daki ya barta a wuri tsaye tana mamakin yau wai itace samad ke ba amsa haka daidai da nata tambayan. Da dane da yanzu ya fara matairaice mata yana bata hakkuri akan zuwan su mommy din itako tana cika tana batsewa tare da kafa mashi sharudda dole ya bi ya juye mata makudden kudi yana lalashin ta. Yanzu ko da yake kokarin kwato kanshi daga sherin ta sai take ganin wasu ne suke kokarin bata mata aikin ta ta baya. Tunda ya shiga bayin taja kafanta ta zuwa bakin gadon dakin ta zauna tare da tin tagumi don ta fahinci ba maganar da zatai sanyi bane dashi sai da yanzu cikas din ta shine cikin da ke jikin ta don bai bari tayi yadda take so sam. Da mamaki samun ta wurin yake kallon ta da ya fito daga ban dakin don yayi zaton tuni ta tafi dakin ta ta kwanta sai ganin ta yayi zaune cikin damuwa. Samad wai may kake nufi danine yanzu da ke tsiro da wasu halaiya na daban da ban san ka da su ba a da don may zakace sai na sallami yan uwa na gidan nan ? Yace saboda ba gidan yar uwasu bace su bari idan kin kaiga naki gidan sai su kwaso gaba dayan su su dawo inda kike ba dai nan gida na ba. Da bakin ka kake fada min haka Samad yaushe ka tashi ga samad din da na sani mai so na da tausayina da son duk wani abinda nake so a rayuwa na. Da ke nan Nafisa a lokacin da ban fahinci koke wacece ba amma yanzu da na fahinta yasa kike ganin sauyi daga gare ni haka . Ban taba yarda da halin ki ba sai yau Nafisa da har mahaifa na zasu zo gida na ki tsare ni kina tambaya na wai yaushe ne zasu koma ? Alhalin ke ga yan uwan ki nan a gidan sun hana ni shakat dani da gida na ba daman in huta in samu natsuwa a ciki ga dan banzan kazanta da kuka bata min gida dashi ya koma wani iri. Samad mune kazamai dani da yan uwana kake nufi ko may yanzu ne kasan da kazantan mu din ko may yace da na dauka idan idon ki ya bude zaki daina Nafisa ashe abin ba haka yake ba a gun ki. Komai ai zaka iya fada a kaina tunda kaga yanzu banda moriya a gareka yadda kake so a da, da kake yawan naci a kaina da banda komai. Wanan ne tunanen ki ashe kike min yadda kikaga dama bakin ce in dauki matakin da zan dauka ki gani ba ranan to matakin ne yanzu na fara daukar wa kaina. Su mommy kuma da kika gani nan sun zo gidan nan ke nan harsai kin haihu kinyi arbain zasu koma gida. Ido ta zaro waje tace ina zasu zauna din yace a inda kika gan su and bari kiji idan naji wani rashin mutunci ya fito daga gare ki zan baki mamaki sosai a gidan nan. Mamaki ne ko rudewa ya kamata a wanan daren na Abdulsamad wanda take gani karfin haline irin nashi daya iya fada mata wanan magana haka babu ko dar a idon shi. Bai kara kulata ba ya shiga gyaran jikin shi ya barta zaune a gurin cike da mamakin shi fita yayi ya duba ko an rufe gidan ya samu ko ba a rufe ba shi da kansa yaja kofa ya rufe yasa mashi key. Washegari mommy da wanan yarinyar da suka zo mai suna Aisha bayan sunyi sallah basu kara kwantawa ba suka fito falon gidan suka gyara tas ta saka turaren wuta dana tsunke a ko ina na gidan. Take gidan ya dauki kamshi da sanyin Ac kitchen suka koma sai da gaban mommy ya fadi ganin yadda kitchen din yake kamar ba mata ke amfani dashi ba. Nan kuma suka shiga aiki a kitchen din gyara can gyara nan take kitchen din ya koma na macen da tasan kan ta girki suka dora na abinda zasu ci a gidan. Sai da suka kusa gamawa ne matan dake gidan jin kamshin girki yasa suka fara fitowa daga dakunan kwanan su daya bayan daya. Suna lekawa kitchen din suna masu ina kwana don tsaron mutuncin su ga maigidan. Bayan sun gama girki mommy ta zuba masu nasu taba Aisha nasu ta shige masu dashi ciki tabar saura da mutanen dake gidan zasu ci. Yanyala ce ta shiga dakin Nafisa take kwarmata mata abinda ke faruwa a gidan da fushi Nafisa ta sauko kasa zuwa kitchen din don taga abinda ke wakana mata a gida. Komai na gidan neat yake yau ya samu gyaran da ya dace daga bakin su ta shiga kitchen din taga yadda suka gyara komai suka jera shi a inda ya dace. Fita tayi zuwa sama ta samu Abdulsamad ya gama shirin fita tsab ta fado dakin da fushi tana fadin ban san may kuke nufi ba kaida wa yanda kake fadi wai iyayyen ka ne ? Ya juyo yana fafin kamar ya fa tace don may zasu zo min gida suna min abinda suka ga dama a ciki suna matsayin baki a gare ni. May sukai maki ya tambaya cikin bata lokacin shi yana sauraren amsa daga bakin ta tace a hasale yanzu ya dace ace sun shiga kitchen sunyi abinda suke so haka ? Sai da ya dubeta dakyau yace kada ki manta gidan dan su suka zo suna da ikon yin komai da suke so a gidan nan. Dansu ko dan ta da sauri ya kalleta yace may kike nufi da wanan maganan naki tace dashi gani nayi itama arziki tazo ci kawai a gidan nan do ba itace ta haife ka ba. Au dama wanan ne tunanen ki ke nan dama raba daya biyu a gida to bari kiji mommy tankar hajiya mu take gare ni don matar mahaifina ne ita ma kamar hajiyan mu don haka nake daukan su daya. Yanzu ke baki jin kunya baki tashi kin tare su da abin karyawa ba sun tashi sunyiwa kansu har kike fadan akan haka don baki da kunya ? Tace ba zan yarda da wanan wuce wurin ba irin nata dama na dade da sanin halin ta tun shigowa na cikin ku do haka kayi saurin taka mata burki a hakan. You're very stupid ya fada da karfi sai data razana yace kada ki fara kice zaki saka masu ido a gidan nan ko bayan fitana ne don zan saba maki sosai kuwa. Fita yayi daga dakin ya barta cike da mamaki tana ganin wankin hula zai kai ta dare wai itace samad din ta keyi wa abubuwa haka yanzu. Lalai duniya na shirin juya mata baya idan batayi da gaske ba tin yanzu dakin ta ta koma ta jawo wayan ta cikin tashin hankali take fada wa madam abinda ke faru da ita. Sai da ta gama sauraron ta tace Nafisa sai kin hada da hakkuri fa yanzu don ni a gani na akwai ida aiki ki ya samu matsala ko kuma don cikin dake jikin ki ne asiri ya daina kama mijin ki yanzu. Ina cikin wani hali walahi haka na nufin yan uwan samad zasu dawo gare shi suyi yadda suke so gidan nan ke nan wanda ba zan taba yarda ba sai dai duk abinda zai faru sai dai ta faru. Madam tace Nafisa kibi sannu fa ba kullun ne ya zama dole mutum yayi nasara ga abinda yake so ba kowa kika gani sai yanayi yana hadawa da hakkuri da kuma kissa bawai ga magani kawai muka dogara ba. Madam ni abin ne yazo min a bazata wallahi tace yanzun dai ki kwantar da hankalin ki mubi komai a sannu. Tace na ji amma duk da haka zan nuna masu gidana suka zo ba zan bari suyi min abu gaba gadi ba haka tace kiyi a sannu dai na fada maki. Shiko yana fita tun a falo ya fara ganin sauyin da gidan nashi ya samu da zuwan su mommy din ga gida ya koma neat a lokaci daya a falo ya hango su hadiye suna kuskus a cikin yare suna ganin shi suka shiga gaida shi. Fuska a daure take amsa masu ya wuce part din su mommy din wanda anan fati da take zaune da yaran ta ganin haka yasa ya tuna da abubuwa da dama na rayuwan su a baya a gidan. Kagin zuwa yanzu da komai ya hargitse mashi haka wanda kan shi yanzu ya dorawa laifin kasancewar haka kamar yadda na fada mai. Ya samu su mommy sun yi wanka suna karyawa a cikin tsanaki ya shigo da sallama ya gaidasu tare da masu ya gajiyan hanya. Mommy tace gajiya ai yabi lafiya don mun zama yan gari yanzu ko yace mommy duk ku kukai wanan gyaran haka a gidan nan ? Tace ba dole ba babangida gida ya koma kamar ba mata a cikin sa kasan mu mun saba mijin mu baya son ganin kazanta ko kadan. Iya bawa tace mai ni ina mamaki gida da mata haka ace bai samun gyaran da yadace mace ta yi a gidan ta wanan matar taka akwai bakin son jiki ne da ita. Ciki ai bai hana ka gyara muhalin ka sai dai dama idan gyaran bai damay ka ba can amma yaushe ne mace kirki zata bar gidan ta haka ? Mommy tace ga abin kari can a kitchen idan ta fito sai ta raba maku ka karya kafin ka fita yace mommy zuba min zanci anan gurin ku don bata fito ba ko ina sauri ne. Anan ya zauna ya karya tare dasu yana mai jin dadi a ranshi yaushe rabon da ya karya a gidan shi haka cikin dadin rai. Bayan ya gama yayi masu sallama tare da tambayan ko akwai wani abinda suke bukata a gidan ya sayo masu idan ya fita. Mommy tace sai kayan kitchen din da taga sun soma lalacewa saboda rashin amfani dasu da ba a yi akai akai yanzu dole a sayo wasu yaje matar shi tai mashi lissafi don gudun su shiga mata hakkin ta. Bai koma takan Nafisa ba ya fice gidan inda ya samu Sani driver yana jiran shi a waje suka dauki hanyar zuwa office din su. Barci nake a dakina tun dawowana class wayan shi ne ya tayar dani daga barcin da nakeyi nayi mamakin kirana a wanan lokacin da yayi. Bayan na karba mun gaisa ne yake tambayana idan maryam tana nan don Allah zai aiko Sani driver shi mu taimaka mu sayo mai abin girki a gidan shi. Da sauri nace mai kaga malam bafa zaman ka nake a garin nan ba da zaka dora min nauyi irin haka a kaina ina matar ka kaje ka tura ta ta sayo ma mana . Don Allah kiyi hakkuri ku taimaka min for today only naji nace na kalli maryam dake barci nace yanzu yau friady muna hutawan mu ya dauko wahala ya dora muna kuma. Ban sake komawa barci ba motsina ya tayar da maryam nan nake fada mata abinda ya bukata da mu tace to may ye a hakan khadija ? Ai taimako ne kin san matar shi ba wani wayewan kaine da ita ba kuma kin san gata da ciki baki yanzu nace wanan ai ba excuse bane. Son dorawa mutane wahala kawai yake yi don kada a zauna lafiya muna zaune kalau zai dauko wahalan gidan shi ya dora muna. Kin san may khadija nace aa cikin kada kaina tace walahi sai nake ganin wanan Abduldin yana bukatan taimako a rayuwan shi. Bai samu macen da ta dace da irin halin shi bane har yanzu yasa komai yanzu yake bukatan taimakon ki ban san yaya zaiyi ba ranan da zaku rabu dashi tunda kince ba soyayya bane a tsakanin ku. Nace ai ke kin fi kowa sanin hakan shiya san yadda zaiyi don ni bashi ne a gabana ba karatuna ne ya damay ni inga na kammala Allah yaban sa,a in samu aiki da wuri. Duk da haka khadija akwai matsala ranan rabuwan ku kan inda ran mu zamu sha kallo nace in babu sai abaku labari ai. Tace labarin taimako ya juye ya zama soyayya haushi maganan ta yabani ban samu bata amsa ba naso ta biye min kada muje ko ina ya karata can da halin shi shiya sani. Karfe uku bayan an fito sallah jumma,a sai ga malam sani driver yazo daukan mu nan yaban kudin yace wai zamuyi waya dashi. Muna hanya ya bugo min yana fada min duk wani abinda muka sani ana amfani dashi a fannin girki har nama da kaji da sauran su mu sayo mommy ne ke bukata a gidan. Kai dama duk wanan abin ba a saya a gidan ka may kuke ci a gidan silly girl ya fada ya kashe wayan shi naja tsuki. Mun shiga kasuwa maryam tayi kaca kaca da kudin komai mun hada sai yamma lis muka baro cikin kasuwan inda ya fara sauke mu a hostel ya wuce bayan hilux din su acike muka bashi sauran kudin shi ya kai mashi canji. Wanka nayi tea kawai nasha da nai sallah muka samu wuri muka kwanta don gajiyan da muka debo a kasuwan bamai taimaka wa wani a cikin mu duk a aikin sa kai da mukayi. Barci yana batun dauka na wayan shi ya shigo min jin murya na yasa yace har kin fara barci ne ko may ? Nace ba dole ba yau an samu wahalan da ba namu ba lada ba zunubi sai tarin gajiya khadija ke wace irin yarinya ne wai da ba tsoron fadin magana a bakin ki ? Yanzu dai ba wanan ba don may kuka ba sani ragowan kudin da ya rage yakawo min kuma ya fada min komai baku sayo wa kan ku ba ku. Saboda ba hakkin mu bane yasa muka bashi yakai ma kudin ka don Allah barni na huta malam gara da kai kana da madafa. Murmushi naji yayi yace ina dashi tunda ina da matar da zan runguma inji sanyi ke ko sai dai ki kama filon ki ko ? Kaidai ka sani nace mai sai da safe yace ba zaki tsaya nayi maku godiya ba zaki kashe min waya ?nace ai ba don ka gode muna muka taimaka maka ba na kashe wayan gaba daya. A gidan shi ya iso da kayan akai ta shiga dasu ciki shi kanshi yayi mamakin yawan kayan da muka sayo din ya kira Nafisa kafin ta sauko ya kira mommy da kanshi kan tazo idan akwai abinda babu sai a sayo gobe. Nafisa na zuwa mommy tana fitowa tare dashi yake tambayan ta ta duba ta gani ranta a bace tace komai yayi sai mommy tace komai an sayo sayayya haka kamar na mace. Nafisa da ta juya zata tafine ta juyo da sauri ta kara kura ma kayan ido tana kallo kayan da bata kalla ba da farko saboda idon ta ya rufe da masifa a lokacin. Maganan mommy ne ya tsaya mata a rai da tace sayayya kamar mace tayi komai an saya yadda ya kamata ta kira hadiye da yanyala wai su kawar da kayan wurin tana daure fuska gata mai gida. A daki ta samay shi zaune lokacin muna waya tace gurin ka nazo ya aje wayan da na kashe yana kallon ta ta samu guri ta zauna da kyat. Tausayi ta yaji ya dirka mai a zuciya tace may kake nufi da baka shawarce ni ba ka sayo wanan kayan haka sai da kasayo abinka zaka kirani. Yace saboda baki damu da asaya din bane yasa na sa a sayo min tace wace yar iska ce ta sayo ma cikin kura mashi ido da son jin amsa daga gare shi. Wanan ba matsalsn ki ba ne ke dai kiji da kanki ya fada mata yana kokarin mikewa tsaye samad mai kake nufi dani ne wai ? Da akayi may kuma yanzu tace ban fa gane inda ka dosa ba gaskiya da irin wanan halin naka yace saboda baki son gaskiya ne yasa na canza nima. Kana nufi nice mai laifi yanzu aike ma kin sani idan kina son mu shirya dake to ki canzs ke ma yaushe rabon da na karya a gida na in ba yau ba da mommy tazo. Dama nasan abinda ya kawo su ke nan ai hadin fada a tsakanin mu in bashi ba may zai sa su kwaso kafan su suzo nan wai sai na haihu. Yace saboda ina dan su kuma ni na bukaci haka a gare su tunda ke baki san komai ba sai bakin yawo da lalaci kawai da kashin kudi. Nice mai kashin kudi murushi yai mata yace ko yanzu ma nasan amsan kudin ne ya kawo ki ai ba wani abu ba tunda baki damu da damuwa na ba. Kaine dai ai naga kamar kana gudana yanzu nan dai suka shirya ranan ace tsakani miji da mata sai Allah suka manta da komai a ransu. Washe gari mommy ta sake hada masu break fast mai rai da lafiya tasa Aisha ta gyara dining din aka jera kkmai a yadda ya dace ta aikawa su hadiye da nasu. Tare suka sauko suka karya a tare sai hadiyan abincin take ba kunya ko wani nauyi a tare da ita bayan sun gama ya fita zuwa wurin aiki. Sai lokacin Nafisa ta kalle gefen dakin da su mommy ke ciki ta kira hadiya ta rufe mata kofan kitchen da store din gidan gaba daya. Da rana mommy ta turo Aisha ta gyara mata kitchen din sai ta samu gurin a rufe ta koma ta fada ma mommy. Mamaki ne ya kama mommy ta kira hajiya mama tana fada mata abinda Nafisa tayi masu ita kuma mama ta kirashi inda take shiga ba nan take fita ba tace maza ya dawo dasu gida tunda yasan gidan shu ba a hannun shi yake ba ya dauke su. Hakkuri ya fara bata yace zai dauki mata hakan tace ya yake son yi idan Abban su ya samu wanan baki labarin dama abinda yake ma gudu ke nan ya hana su zuwa tu farko. Hakkuri ya dinga bata har ta saurara mai tace tana jiran taji matakin da ya dauka a gidan idan ba haka ba zata fada ma Abban su abinda ke faruwa kada yaji a gurin wasu. Yusuf yana zaune yana sauraren su yana kashe waya ya dago idon shi da suka kade sukai ja yace wai may Nafisa take nufi da nine ? Guri ta samu take wanan abin mana Yusuf ya bashi amsa yace in bashi ba rashin mutuncin nata har yakai ga su mommy kuma yanzu. Mommy ne zata rufewa dakin girki bata girka ta basu ba basu damu ba suna yi kowa kuma yaci har zata rufe kada suci su kwana da yunwa komay ? Tasan yadda Abba yake ji da iyalin shi kana zaton da ba mommy bace in anty amarya ce Abban zata kira da kan shi ta fada mai kasan ko yau ba zata kwana gidan ka ba. Wallahi idan zaka kara aure ka kara shine kawai mafita ga wanan shu,umar mace da ka dauko wai mata bazata taba ganin darajan ka ba idan ba ta bude ido tagan ka da wata mace ba a gidan. Idan tana zama ta zauna in bata zama kuma ta kara gaba dama ba akirata ba kutse ne da sa kai irin su ta kallamay kada dadin baki da komai ta aure ka. Kai yace tare da bugun tabur din gaban shi ya mike cikin fushi Yusuf yace ina zaka kuma yanzu ? Gida yace cikin wani irin murya kamar mau zazzabi shima mikewa yayi ya bishi a baya tare suka fita daga office din shiya jasu don Abdul din bai da karfin haka a yanzu. Suna tafiya yana dafe da kanshi ba tare da ya kalle shi ba Yusuf din yace ba irin ku masu sanyin hali ne ya kamata ya auri irin Nafisa ba. Sun fi daidai da irisu wa yanda zasu caja junan su a zauna lafiya amma ai dama ita haka suke so su samu wanda suke juyawa son ran su. Yanzu ai ta fara koya min iya magana ita da wanan yar matsalan khadijan din nasan idan an auna ni za a samu VP dina ya hau wallahi Yusuf damay Nafisa take son inji ne wai ? ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Yau take son ta gwada abubuwan da aikin boka dan Ondo wanda ya ja mata kunne da gujewa aikata kuskure tace zata tsare in sha Allahu. Ya shigo bai jima da dawowa ba ya fada wanka Nafisa ta shigo dakon kai tsaye tasamu yana ban dakin gurin wanka nan ta zauna a bakin gadon cike da jiran mijin nata. Ya fito daga ban dakin ta taso ta karbi duk wani abinda yake ma jikin shi tana mai gama daga goge jiki da shafan mai da saka turare da sauran su. Shidai ido kawai ya saka ma ta yaga iya gudunta don zuwa yanzu ya fara gano shirin ta sam bai yarda da wanan abinda take mashi ba . Ya gane sai tana son abu take mashi ladabin shegu a lokacin yake miji da zaran ta samu abinda take so shike nan ta koma ma halinta na I don't care da ta saba dashi. Zama yayi a bakin gado yana jiran yaji ta inda zata bullo mashi ta dan yi dariya tare da karasowa wurin shi ta zauna itama. Sai bayan ta zauna ne tace samad a ranshi yace nasan da wanan kan tace wai yaushe ne zamu tafi shopping ga ciki ya fara girma haka ? Yayi mata kyar da ido sai kuma ya sake guntun murmushi a fuskan shi yace ban san da wanan maganan ba ai. Ita ko tayine don tana ganin shi ne zai fi saka shi farin ciki har ta samu ta sake da ita ta aiwatar da nufinta gare shi sai kuma taji sabanin hakan a bakin shi. Sai ta dan tsuke fuska tare da fadin gaskiya ya kamata ace ka shirya wa tafiyan mu zuwa yanzu don kada nazo nayi nauyi da yawa kace ba zan fita ba. Abdulsamad ya tsura mata ido yana mamakin rigimar Nafisa yanzu bata aje kanta a kusa ba shi kayan bany ko a nan gida Nageria za a samau su ai. Ya cikin daure fuska kin fi kowa sani komai nake so zan iya odan shi a dan kan kanin lokaci ya iso gare ni ballanta na babu dan da aka haifa a gidan nan da na fita waje na sayo mashi kaya. Ranta ne taji ya baci don may zaya danganta sauran diyan shi da abinda ke cikin ta a yanzu da ta san tafi karfin kowa ma nashi. Shikan gado ya hau yana gyara kwanciyan shi don yasan ba tayin abinci zai samu a gurinta ba duk dako yana son saka wani a bakin shi yanzu. Nafisa kuma bataji dadin haka ba don tana gani idan ta kyale shi bazata samu yadda take son komai ya tafi ba har ya sadu da ita don ta riga ta shafa maganin da boka ya bata tayi amfani dashi. Tabo shi tayi tana kwantawa a jikin shi da sauri ya juyo gareta yana fadin barni banda lokacin aiwatar da wani abu yau a tsakanin mu. Tace aiko tunda ni ina da bukatan ka tare dani dole zaka daure ka biya min bukatana haka nan yasan ta da son ya kusance ta akai akai wanda a baya yakan biye mata. Kara kwanto mashi tayi ya kara daga ta ajikin shi karo na biyu yace ki barni please na fada maki ina bukatan kasancewa ni kadai ne duk iya nacin ta dole ta barshi tafita kamar zatayi hauka take jin kanta a lokacin. Ta jefeshi da harara ya karkace kai yana mamakin tace ba laifin ka bane tunda kai kana fita waje yanzu kana samun inda ke sauke nauyin ka acan. Sheri zaki min yau kuma Nafisa tace amma kasan baka kyauta mi ba nima idan kai min haka yau don ina bukace dakai a yanzu yace ki hakkuri nace yau ba zaki samu ba ya gyara kwanciya yana fadin hakan. A yadda ta rude sai ta bashi tausayi amma bai iya aiwatar da komai a yadda yake jin gabanshi yana faduwa mai. Jin fitan ta a fusace bayan ta gama mashi mita ta fice daga dakin ya girgiza kanshi ya gyara kwanciyan shi sai barci acikin barcin ne yayi mafalkin mara dadi da Nafisa wanda ya tayar mashi da hankali. Tunda ya falka bai koma barci ba tunanen mafalkin da yayi ne ya tsaya mashi a rai mikewa yayi ya dauro alwala ya gabatar da sallah tare da samun sauki alamura a gare shi kamar yadda mahaifan shi ke koyar dashi ko wani lokaci. Washe gari ta tashi gaban ta yana fitar da wani irin kaikayi dake damun ta sam bata kawo cewa aikin boka da ta sakane ya jawo mata hakan ba. Tunda ya watsa ruwa ya fito yana shiri zuciyar shi cike da tunanen abubuwan da suke faruwa dashi ya yanzu din. Sai da ya biya dakin ta ya dubata kamar yadda yayi mafalkin a haka ya samay ta tana ta faman da soshe soshe don kaikayin dake damun ta. Yace may ke damuwan ki haka ne kike wanan soshe soshen haka cikin bacin rai tace dama ai haka kake so dani tunda na bukace ka kashere ni. Banga dalilin da zaka daukoni karabo ni da kasata ba kazo yanzu kana nuna min gazawanka a kaina inda take shiga banan take fita baya ya ciki da irin kalaman da take fada mai. Hannu ya daga mata tare da fadin ya isheki haka na kada kine me ki fada min maganan banza an fada maki ni banda abinyi ne sai na kwanciya da mace kullun , ? Kallon shi take da mamaki don bata dauka zai fada mata wanan magana haka ba yace kinje kinyi biye biyen ki kin dauko wa kanki cuta kiike son aza min. Kuka ta saka mai tan , aza mai kururuwa bai kulata ba ya fice daga gidan kai tsaye kukan ta ne ya jawo hankalin yan uwanta gare ta suka shigo dakin. Har yaje office bai iya tsinana komai ba da yamma koda ya dawo ya samay ta a hargitse ya dawo har ya dade ta bishi dakin shi ta samu ya fito wanka yana daure da dan karamin tawul a jikin shi. Tunda ta shigo mai daki ya dago ido ya kalleta ya kawar da kan shi gefe daya yaci gaba da abinda yake yi din tazo gaban shi tace. Allah kuwa sai ka fada min abinda yasa ka tsiro yimin wullakanci haka ko dan kaga ina dauke da ciki ne a jikina yanzu yasa har kake guda na. Ya jefeta da wani muggun harara har sai da taji tsoro ta dan ja bays kadan yace look Nafisa idan dan dai kina son mu zauna lafiya dake sai kin aje kanki a matsayin da na dauko ki a gidan nan na mata. Macen kwarai itace wace ta san damuwar mijin ta da cin shi da shan shi da gyara mai makwacin sa da sauran su. Amma duk ke baki san yin wanan ba sai dai kici arziki ki wadatar da yan uwan ki ba tare dani kin dubi nawa da komai daya shafe ni ba. Don haka kodai ki gyara halin ki ko kuma in karo wata a gidan nan ku zauna tare wacce zata dinga kyautata min. Ya na kaiwa nan yaja dogon tsukiy ya dauki key din motar shi ya fice dakin ya barta tsaye tana kurma ihun bakin ciki. Wanan halin da Nafisa keyi wani lokaci kamar zautata sai daga baya kuma idan ta samu abinda take wa haukan ta dawo ta gyagije kamar ba ita ba. Iyanzu ya fahince ta idan tana bukatan abu bai mata shi ba babu sauran zaman lafiya a gidan tsakanin ta dashi shiyasa da zaran ta bijiro da bukatatun ta yake saurin biya mata akan lokacin. Wanda ita kuma take ganin aikin bokayen tane da mahaukacin son da yake mata yasa yake biya mata bukatanta a haukace kamar ba gobe. Wanda tayi believing da baka da malamai ta ne aikin su yake ci a gareshi da kuma kyau da zati wanda take gani dashi take rudan shi ba zai taba samun mace kamar ta a cikin matan hausawan Nigeria ba sai dai kalan matan mu na nan. Burin mazan Nigeria ne su malki mace mai kyau koda bata da hali na gari adai ce matar shi ta gwada wa tsara ne a gari. Bata san Nigeria akwai wanan akwai kuma la,akari da ilimi tare da wayen mace da tarbiya ga mazan da suka san kan su. Yau ma kamar jiya tashigo mai tana bukatan su kasance tare amma fir yaki amincewa ya biya mata bukatan ta kamar jiya haka ta wahala da wanan dan banzan kaikayin na gaba da tadamay ta. Yanzu kan ya gama sakankancewa a ranshi mafalkin shi gaskiya ne inda ya ganta dauke da wani mugun abu tana goga ma gabanta. Washe gari har ya shirya bata tashi ba daga barci tana ramuwar barcin da bata samu tayi ba a daren shiya tsaya ya tayar da ita cike da tsanar halin ta na rashin son yin ibada. Idonta da sauran magagin barci bai gama watsakewa ba tace har ka shirya fita ke nan yace idan ma ban fita ba wani abin zaki min ne tunda ba abin kari zaki hada min ba. Cikin bacin rai ga maganan shi tace ba muyi wanan alkawarin da kai ba na cewa nice zan dafa ma abincin da zakaci na dauko masu dafa ma kace basu iya ba don haka banda matsala ga wanan. Yace yana daukan jakar Laptop din shi tare da sabawa a kafadan shi Nafisa zakiyi nadaman wanan maganan da kike fada min don ya zama dole idan baki canza ba in dauko wace zata bani kulawan da nake so a gidana. Maganan shi Ya bata mamaki kwarai don bata zaton zai iya fadin wanan magana a gabanta ba kai tsaye sai gashi yau yana fada mata da bakin shi wai zai dauko mai kula dashi a gidan. Wai ina kudin da take narkawa malaman ta yake shiga ne haka gashi ta dalilin bin bokaye da malamai dasa gaba yanzu ta daina kai kudin da suke kaiwa gida duk wata ana amfani dashi. Ya bata mamaki kwarai ta samu ta danne zuciyar ta don ta san yanzu akwai sauyi a tare dashi ta dago ta kalleshi yana shirin fita daga dakin. Fuskan shi a daure yake har lokacin gabata ne ya kara faduwa sosai dole sai ta hada da kissa da kisisinan mata yanzu. Tace kayi hakkuri don naga yanzu magana kadan sai ka dauki zafi dani haka yace ai kece zan bawa hakkuri keda ban san na dauko ki kawai ne gidana don ki ji dadi ba. Ta sada kai kasa tace ba laifina bane ka sani don ba girki zan iya yi yadda kake so ba bai sake yin magana ba yaci gaba da shirin shi bayan ya gama ne ya dago ya kalle ta yana fadin ki tashi ki sallah don lokaci ya gama kure maki ko. Ya fice daga dakin bayan ya gama fadin haka bishin shi tayi da kallo har ya bacd ma ganin ta sai lokacin ta saukar da ajiyan zuciya. Tace lalai da sake ya zama dole ta canza halin ta idan ba haka ba wankin hula zai iya kai ta dare wanan wani irin mutum ne da magani bai saurin kamashi. Shin shi ba kamar sauran mazaje yake bane da take jin mata na hiran yadda suke samun kan maza je nasu suke juyasu ne ? Yazama dole duk wani abu da zatayi taga ta samu ya sauko kamar yadda malam yace ta bi komai a sannu kada alamarin ya juye mata gashi ko taga abubuwa na shirin juyewa da ita. Wai shin ko da gaskiya ne asiri baya kama mutum idan mace nada ciki ko ta haihu dole ne ta jirkinta har ta haihu ta bishi a yadda yake so ta nuna mashi ta kwanta yanzu. Alaadan shine idan ya fita office zai mata kira uku ko sama da haka amma sai take ganin sabanin haka yanzu tun yana mata kira daya har yakai yau ya bai kirata ba ki daya. Haka yasa ta fara zargin dama dalili yake nema da ita ai sunsha yin fiye da haka dashi amma bai sa ya daina kulata ba sai wanan kawai zai dauka da zafi haka. Har tayi wanka ta fito falo wurin yan uwanta da ta samu suna shayen shayin su bata daina tunanen halin da take ciki da mijin ta ba. Gaida ita suka farayi ciki harshen buzaci tana karba masu da kyat yanayin ta ya nuna ba ta cikin dadin rai. Yar dattijuwa daga cikin su ne tace yau ba zaki fita bake nan ta amsa tare da yamutse fuska tana fadin ba inda zanje yau suko sunfi sin tana fita a gidan don sun fi sake jiki suyi yadda ransu ke so idan bata gidan. Matar tace yanzu ya kamata ace kin fara natsuwa guri daya saboda cikin ki da ya fara girma don kina bukatan hutu. Ta dan lumshe ido tare da jan tsoki ta dafe kan ta tace wani irin hutu Yanyala, ni da abubuwa suke son rikewa a gidan nan yanzu. A lokaci daya suka zaro ido tare da mayar da hankalinsu gare ta suna sauraren ta tace ya zama dole dukkan ku ku gyara a gidan nan. Yace mun bata mashi gida bamu gyara ba ai mai girkin da na dauko ku da sunan masu aiki a gidan saboda haka nake son kowa ta dan fara aikin ta. Yanyala ta fidda idanuwa waje tana mamaki tace garin yaya har kika bari haka ya faru a tsakanin ku tace wallahi ke ma shedace ina iya kokarina don ganin haka bai faru ba amma hakan bai samu a gare ni. Yanyala tace gaskiya ya kamata ki fara tura kaya gida tun yanzu ko za a watse dai kin riga da kin debi rabin ki ko ke. Dama bazan Nigeria ai basu da tabbas ba kowane ke kamuwa yadda ake so ba don haka muke daukan su kamar wurin cin kasuwa a gare mu. Don ko da kasuwa zata watse dan koli yakasa ya kwashe rabon shi nan dai sukai ta shawaran abinda zasu yi akan sauyin da ta ke gani ga mijin nata yanzu. Idan da sabo na saba izuwa yanzu haka kawai zai zo ya dauke ni a mota sai dai mu zagaya gari ya dawo dani ya aje ya wuce makaranta. Yau ma da yai kwana biyu bai zo inda nake ba komai na tafiya a guri na normal sai dai zan iya cewa haduwa na dasu ya bude min wani sabon babi na rayuwane. Duk da nake yarinya kuma mace ban yarda na fara hurda dasu ba sai da na karanci rayuwan su nagane zama dasu ba yana nufin jefa ni a gurbataciyar rayuwa bane. Yauma ina daki kwance ni kadai ina nazarin wani littafi don sabon da nayi da yawan karatu sai dai ance sabo turken wawa ne don har na dan fara shiga damuwan rashin ji daga gare shi kwana biyu. Waya na da yai ringing na juya ina kallon mai kirana a lokacin ganin sunan shi a screen din wayan yasa na dan sake murmushi sai da naja mai aji na dauki wayan. Da sallama na fara magana ya amsa min yace kina hostel ko kina cikin makaranta ne nace ina hostel yanzu fito ina waje yace ya kashe wayan shi. Na shirya cikin wani dogon riga mai dan hannu shara shara riga yana dan matse kadan daga saman shi kasan shi a bude. Kai tsaye daga inda yake zaune a motar yana sana,an shi na hango shi cikin motar ya mayar da hankalin shi sosai ga abinda yake yi. Tun da ya dago kai ya hangoni tafe ya daina abinda yake yi ya tsura min idanuwan shi masu kashe min jiki da zuciya haka ya sake min su tankar wanda ya samu tv har na iso gare shi. Daga waje na gaida shi kamar wanda baiji ni ba yayi sai bude min motar yayi da alaman in shiga kai na daga na kalle shi carab muka hada ido dashi. Nan nace dashi karatu nake fa yallabai ka kirani yanzu yace shiga mu tafi na sani ai. Tambayan shi nayi da ina zamu tafi tare da kashe shi da idanuwana dasu ke rikitashi idan ya kalla. Sayar dake zanyi yace murmushi nayi nace ai dako kayi babban kamu yau galleliyar yarinya kamata ba karamin kudi zaka samu ba ko. Nace yanzu ya kamata ace kana wurin aiki ka ko gida kana hutawa dan murmushi ya sauke tare da fadin. Bazan iya zama gida ba ne yanzu. To ka koma office yanzu mana tunda lokacin aiki bai kare ba don nima karatu nake yi yace don Allah ki shigo mu tafi kona fito na daukeki in sa a mota. Nayi saurin nuna kaina nace ka dauke ni sai kace wata yar tsana ko matar ka can da zaka dauke ni. Don Allah shigo mu tafi kin sa mutane suna kallon mu na dan juya naga wasu yan mata dake gefen mu sun kura muna ido. Dole na bude motar na shiga ya tayar da motar muka bar gurin sai da mukai nisa ne naji yace may yasa duka mata wani lokaci halin ku daya ne wai ? Na bata fuska tare da dan kallon shi nace haba mijin buzuwa da alama yau baka cikin dadin rai kake hango matsalan gidan ka ga kowa. Kada ka danganta abinda ya hada ka da matar ka dani don bai shafeni ba ko kadan yanzu ma banga abinda nayi da zaka fadi haka ba. Yace nima ban san dalili kawai dai ina hango hakane gun ko wace mace kamar halinku duk dayane wani lokaci. Nace baka canka da kyau ba malam ai kaji ance mata suna suka tara . Ya kalle ni ya girgiza kai yace bazan iya tabbatar da haka ba sai na gwada don naga biyu halin su daya basu damu da damuwan mutum ba kansu kawai suka sani da son abinduniya. Wow i am impress dama haka ka dauki mata a ranka ashe ? Yes sai dai ban sani ba ko kamar yadda kika fada inke din ta daban ce don na dan ga alama haka. Shiru mukayi duka a motar sai can yace cikin langabar da kai please khadija kiyi hakkuri ki fahince ni don yanzu bani da zabi sai wanan tunanen. But sai dai ban san may yasa ba nake yawan son in kasance a tare dake muna irin wanan tafiya tare da shammatan junar mu. What na fada cikin mamaki da rashin fahintar maganan shi tare da fadin me ye maanar hakan a gare ka may yasa sai nice zaka ji dadin fada dani ranka yai maka dadi. Don haka kaje ka dauko ni a lokacin da nake a tsakiyan karatuna don kawai son fitina kace wai kana son muyi ta shammatan juna kana jin dadi. Murmushi yayi yana fadin bazaki gane ba ne khadija hakane kawai farin ciki na a yanzu a take na daure fuska tare da fadin maidani inda ka dauko ni don Allah. Haba mana khadija may kike fadi haka ke nan baki bukatan ganin farin ciki na ne komay yanzu fa kika gama fadin mata suna suka tara da bakin nan naki. Nace da ban dauka farin ciki kaka samu daga yin haka da nake maka ba ai na dauka bacin rai nake sakaka. Hummm yace sai ya juyo ya kalle ni yace to indai ina da wani matsayi a gare ki yanzu dai ki zauna mu tafi. Ba yadda na iya haka na koma na zauna tare da kawar da kaina gefe daya yace yanzu na fara sanin ashe suna kuka tara. Tunda gashi na roki alfarma a gurin ki kin yi min abu biyu ke nan na fahinta a gare ki yanzu zaman mu tare da ke. Nace wanan bata min lokaci na kawai kake son yi a banza bayan kasan ina da abinyi a gaba na yanzu. May yasa zan so bata maki lokacin ki haka bayan nafi kowa sanin amfanin abinda kike yi yanzu. Yanzun dai mubar wanan magana may kadauko ni yi a yanzu ne don Allah na tambaye shi tare da kura mai ido ina son jin amsa na. Wanan lokacin da wanan yanayin yafi min ko wani lokaci jin dadi a rayuwa na yanzu matukar ina tare da ke khadija. Kece mace ta farko da nafi jin natsuwa idan ina tare da ita khadija ya juyo ya kalle ni tare da fadin kin san may yasa nace haka ? Kai na girgiza mai cikin sanyin jiki alaman ban sani ba sai ya fada dai zan sani daga gare shi. Yayi murmushi ya kalleni yace kin san yadda zakisa zuciyar mutum ya sake ba tare da an rabu cikin bacin rai ba khadija. Ina jin dadin hakan da kike min ke ta daban ce da sauran matan zan iya yarda a yanzu saboda wasu dalili da na kafa akan ki. Wani dalili ne haka na tambaya da sauri tare da kallon shi yace baki taba rokona wani abuba khadija alhali nasan kina da bukatan abubuwa da dama tunda kin san ina da halin shi. Na nuna kaina nace ni in rokeka kuma akan may zan roke ka bayan nasan rabo ne idan rabona ya ratsa a kan ka zaka bani ko ban roka ba. Good girl tafiya zatai dadi a tare dake kuwa tunda kin san haka she nayi saurin fadin ashe kai marowaci ne ke nan ga mata ? Ya dan lumshe ido yace ko daya wallahi na dai fi son inyi abinda ba sai an roke ni bane sai dai ina haduwa da matan da basu da hakkuri ne khadija. Ban san lokacin da baki na ya bude ba nace kana nufin har da anty Fati haka take yaushe ma ta samu gurin roko a wurin ka kai ? Ya na tukin shi hankali kwance ya murmusa yace kin ga yanzu ma kin fada da bakin ki yaushe na kula ta balle ta samu tambaya na ? Haka kowa ke gani khadija shiyasa manya sukace tsakanin miji da mata sai Allah wanan abin na bar wa kaina sani kawai. Daga ya mayar da kanshi ga titi yana ta tuki a hankali tare da shakan isakan dake kadawa a lokacin may hade da kamshi kasa wanda ke nuna dama na son sauka a lokacin. Ba wani guri mukaje ba sai yawata garin da mukayi kawai ya dawo dani hostel ya aje ba tare da na tsaya ba na shige kai tsaye yaja motar shi ya tafi. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Suna shiga gidan su Nafisa ne zaune a falo da yan uwanta sai wata bukuwa da tazo mata a lokacin wace bai san ko wacece ba. Sun fara gaida shi sai dai ita bata dago kai ta dube su ba ganin su tare da Yusuf da taki jini da tayi don a cewan ta Yusuf ne ke kulla mashi duk wani shawara a gamay da ita. Shima Yusuf din bai tsaya ta kan su ba ya wuce dakin da su mommy suka sauka dauke da ledan take away da suka sayo masu a hanya. Nafisa may ne hujjan ki na rufe kitchen da kikayi yau tace saboda gida nane yasa na rufe don ina da ikon yin hakan ko ? Idan abinci yayi saurin karewa wa zaka tambaya yadda akayi dashi ai naga da kawo abincin sai da ka kirani ai in gani ko ba haka na bane ? Nafisa lalai wuyan ki ya yi kauri a gidan nan har da zaki iya rufe ma iyayyena wuri kada su dafa abinda zasu ci ko suyi amfani dashi. Amma ba laifin ki bane laifina ne da na sakar maki wan har kike ganin kin isa kike son wuce gona da iri a gidan nan da rayuwa na. Baki dafa kin basu ba sun dafa ma kansu kuma kinyi bakin ciki da haka da suke yi ko kin mata nan din gidan dasu ne halal malal suna da iko da komai yadda suke su. Ai ban sani ba sai yanzu da ka fada a gaban kowa nasan yan uwanka sun fini muhinmanci a gare ka yace da may kike daukan kanki ne. Tace ai sai su fito mu zuba dasu a gidan bansan ka kawo su nan bane don su kara dani tsawa ya daka mata cikin kiran sunan ta da karfi. Mikewa tayi da kyat itama tana fadin ban san sun isa da kai ba sai naga muna raba kwana a gidan nan dasu. Haka kike ce tace an fada din yace bada su zan raba maki kwana ba amma ki sani zan kawo wace ta dace in raba maku kwana gidan nan wace zakuyi daidai da fitsaran ki. Su wa yan nan iyayye nane yanzu na kawo amma mai zuwa in raba maku kwana tana tafe kwanan nan. Madam ne dake zaune ta mike tana fadin Nafisa kina da hankali kuwa kin san may kike shirin aikata ma kan ki yanzu ? Ta figi jakkanta dake aje gefen kujeran da ta zauna tana fadin ni na tafi tunda baki da wayo yace bata san bata da wayo ba yanzu ne zata sani. Waya ya ciro daga aljihun shi ya fara fadin hello inspector kana jina wasu froriners nake son kazo ka kwashe a gida na yanzu don Allah. Jin haka duk suka mike tsaye don da a zaune suke gefen guda sun zuba masu ido suna sauraren su madam ce ta fara bashi hakkuri da fadin. Assha Alhaji ai a bin bai kai haka ba basai ka kira hukuma a cikin zancen iyalin ka ba anan akayi sai a sasanta shi a nan Nafisa kin yi kuskure ki bashi hakkuri ke kuma. Bani taiwa laifi ba su da ta bari da yunwa tun safe ne za ta ba hakkuri tace ni ban masu komai ba balle in basu hakkuri. Yace da kyau mommy da suke daki da Yusuf suka ji hayaniya yai yawa a gidan yasa suka fito daga dakin gaba dayan su. Sun fito daidai lokacin da take fadin batai masu laifi ba bazata basu hakkuri ba mommy tace Nafisa kinyi kuskuren ki ba mijin ki hakkuri mu namu mai sauki ne. Don shi muka zo gidan nan kuma da bakin shi yasa muzo ba wai haka kawai muka kwaso kafan mu zuwa nan ba tunda mun san baki son wani nashi ya rabe shi yasa kowa ya sallama maki shi yanzu. Shigowan inspector din da wasu polisawa uku ne ya ruda Nafisa da da ta dauki abin da burgan maza yake mata sun gaisa ya nuna su Yanyala da su hadiye yace gasu nan . Yar uwar su na aure suka zo suka tare min a gida ban san dalilin su nayin haka ba sai ku tambaye su hankalin kowa a falon ya tashi ya juya gurin su mommy ya fara basu hakkuri. Mommy tace mu bakai muna komai ba don wurin ka mukazo dama ba wurin wani ba macen police din ne ta fara ingiza keyan su hadiye gaba. Samad kayi hakkuri don Allah ba sai ka wulakanta min yan uwa ba don ni suka zo gidan nan sai ka hada dani duka kace a kwashe mu. Bissimila yace idan haka yafi maki yan uwa na daine dole na a yanzu gidan nan na kuma gwada maki haka kina iya binsu ga hanya nan a bude ya juya gurin police din yace ku tafi dasu duka. Samad ni zakai wa haka ni zaka fada a kwashe mu a tafi damu babu ko nauyin haka a bakin ka kake fada. Ke uwata ce ko may ko ajeni kika yi a gidan mara mutunci kawai ya juya zai fara tafiya da sauri tasha gaban shi tana fadin kuskure ne nasan nayi ba daidai ba don Allah kayi hakkuri. Madam tace tun farko da haka kikayi da abin baikai haka ba ya nuna su mommy yace su zaki ba hakkuri bani ba ai. Mommy kiyi hakkuri kisa baki a maganan nan don Allah mommy tace naji zan bashi hakkuri amma haka ya zama ishara a gare ki gaba. Nan Abdul din ya dage sai idan ta basu hakkuri zai jaye maganan tace cikin dukawa mommy kuyi hakkuri nayi kuskure don Allah. Iyan bawa tace amma ke kan anyi mutumiyar banza a nan yanzu baki ji kunya ba don Allah ga yan uwan ki ko ina a gidan baki bakin ciki da cin su ba sai mu da mukazo zama daku na dan lokaci. Dan mune fa mai dukiyan da kike kadagi dashi din har kike ganin kowa ba kowa bane a gurin shi sai ke da yan uwan ki keda iko komai dashi. Nan suka kaita fada mata abinda suke so a cikin nasiha tace ayi hakkuri zata gyara yusuf ne ya sallami yan sanda suka wuce. Ranan dai anyi ta ba dadi a gidan tayi nadama tayi bakin ciki abinda Abdulsamad din yayi mata a gaban kowa ya nuna bata da wani power a gare shi yanzu ga madam ma tayi fushi da ita ta tafi tana fadin ta bashe su a idon duniya. Ta kula wanan ta kwance wancan haka na ta wuni da sake sake a ranta a kan sai ta rama abinda yayi mata akan su mommy din da suka zo gidan don ganin bayan ta. Ita sam bata dauka don dan su da taimakon ta suka zo ba har yanzu don idon ta ya rufe da son bata kaunar taga wani wanda ba nata ba ya rabe shi saboda tsananin kishi da take dashi irin na buzaye. Ta kira madam ta bata hakkuri har suka shirya take anan kuma suka fara sabon shirin da zasu aiwatar a kan kowa ma daga bangaren shi. Shiko a bangare shi ranan daki ya shige bai son yawan hayaniya da kowa don haka ya ke be kan shi a daki ba abinda yake sai tunanen hanyar da zai samu mafita ga alamarin Nafisa. Saboda yasan ba canza halin ta zatayi ba kwanto kawai tayi a yanzu tana nazarin ta idan zata biyo mashi ne. Allah ya gani yana son ya kara aure kamar yadda Yusuf yasha fada mai shine kawai mafita gare shi akan Nafisa to amma wa zai aure din da zasuyi daidai da Nafisa a zauna lafiya. Khadija ina khadija karama ne sosai ga Nafisa da halinta ba zai dauko yar mutane ya jefa a matsala ba ya cuta mata don yanzu yana jin yarinyar a wani bangare na rayuwan shi . Don haka ba zai cuta mata ba ta wanan hanya na hada aure a tsakanin su wani abu yazo ya samu yar mutane a hannun shi. Ga mahaifin ta ko yaushe sukai waya yana mashi godiya akan kyautatawan da yake ba yarsu wace kamar kauna take a gareshi. To amma kuma ga shakuwan da sukayi taya zai iya rabuwa da khadija a yanzu nan tunanen irin rayuwan da suke yi da khadija din ya fado mashi a rai abinda ya sa shi dan murmushi ke nan kadan ya gyara kwaciya yana lumshe idanuwan shi. Wayan shi ne ya yi tsuwa alaman kira na shigo mai ya dan juya ya daga wayan Queen of matsala ya gani da sauri ya daga kiran nawa. Tambayan shi nayi lafiya kake kuwa yau ? May kika gani ya bani amsa dashi sai na rasa abinda zan fada mashi karya na samu kaina da yi nace kawai dai sai nake tunanen hakan . Fada min kewa na kikayi ko may kika kirani a cikin wanan daren haka baki san ina da mata bane ni Family man ne idan kika hadani fada da mata na fa ? Wayan na kashe ina ci gaba da tunanen mafalkin da nayi dashi a yanzu daga dan barci ya dauke ni sai wanan mafalkin yazo min gaba daya na saka waya na a off na gyara kwanciya cike da zullumi ina tunanen mafalkin. Can dai barci ya dauke ni na manta da zancen mafalkin koda na tashi naci gaba da alamura na shima kuma bai kira ba don haka na kara share shi. Nafisa ko hankalinta bai kwanta ba gida Niger ta kira mai mata aike a can da kukan ta wiwi matar tace may ke faruwa Nafisa ko sakin ki mijin ki yayi ? Tace bai sake ni ba serah sai dai gaba daya ya canza min yanzu nan dai ta koro mata bayanin abinda ke faruwa cikin kuka. Serah tace share hawayen ki Nafy murde dan iska zamuyi ya koma sai yadda kika ce a gidan ki bai isa ba wallahi yanzu dai ki daure kibi yan iska yan da suke so daga yau zan shiga in fita zaki gannin nan da kwana uku kedai turo min da kudi kiga aiki da cikawa. Tace serah har kin kwantar min da hankali na wallahi don yanzu ni damuwa na bai wuce cikin nan dake jikina ba don cewa ake wai idan mace nada ciki ko jinin haihuwa wai komai nata baici. Serah ta katse ta da fadin da ke nan wanan zancen yanzu may ye kudi baiyi Nafy ina nan shigowa nan da kwana uku kada kiji komai. Bayan sun gama wayan ta zauna ta zabga ta gumi ta rasa ta ina zata fara da shi zata fara ko da iyayyen ko wanan mugun abokin nasa da ta tsana. Zaman gidan yanzu haka ake yin shi ba ruwan wani da wani sai gaisuwa a tsakanin su dasu mommy kowa na harkan gaban shi. Shiko yana tsananin basu mommy girma da kulawan da ya dace a gidan wanda hakan keyi wa Nafisa ciwo matuka ta rasa yadda zatayi dasu a gidan. Kunci cikin zuciyar ta ba a maganan shi har yakai bata iya boyewa hakan yasa ma ta daina yawan saukowa kasa inda zata gan su ko wani abinda sukeyi shiko sam bai kula da halin da ta jefa kanta a ciki ba yanzu. Kamar yadda serah tayi alkawari haka ya faru tazo da kule kule da sihiri kala kala tun a ranan suka fara aiwatar da komai kamar yadda suke so ya tafi. Nafisa sai gani take har aiki ya fara ci saboda yarda da tayi da maganin don irin labarin da Serah ta bata yadda ta shiga kungurumin dajin kasan su wurin samo mata wanan asirin mai amfani da ci da sauri ga wanda akaiwa. Haka kawai yake ji kwana biyu yana jin haushin kowa a gidan inbanda Nafisa da yanzu yake jin wani irin so da kaunar ta yana shigan shi. Mommy dake da kaifin basira ta fahinci abubuwa suna sauyawa a gidan don haka ta fara tuntubar Iyan bawa akan abinda da ta fara hangowa ga dan nasu don tun zuwan Serah mommy tasha jinin jikin ta da ita don tsarin ta da zubin ta yafi kama dana yan duniya ta irin mutanen su. Batai kasa a gwiwa ba ta sanar da mahaifiyar shi hasashen ta amma tace kada ta bari kowa ya fahinci abinda ta fada mata ta dai taimaka mashi da addua. Hajiya mama tayiwa mommy godiya bayan sun gama tataunawa akan zancen sukai wa juna sallama aka aje wayan. Sosai hankalin hajiya mama ya tashi da maganan mommy haka yasa ta kira yayan ta da suke uwa daya uba daya a zaria tana neman shawaran shi. Yace ta bari zai ga wani malamin shi a nan cikin garin zaria da zancen don rayuwar Abdulsamad da wanan matar tashi yana bukatan addua sosai. Haka suka bar zancen akan zai kira ta taji duk yadda sukayi da malamin nashi idan ya dawo daga wurin shi. Ban san mun shaku da shi ba sai wanan karon ga jerabawa ya na gaba to muna ga zancen zuci dake damuna haka ya dan sani rama kadan. Karshe nabawa kaina shawaran abinda ka fisheni na watsar da komai na rugumi karatu na gadangadan ina yi tare da share zancen su gaba daya a raina. Ranan muna zaune da Maryam a dakin ta tsifar kaina na ke da ya kitso ya tsufa min zan je in wanke kai na wayana yayi tsuwa na duba Yusuf ne a kan layin. Nayi mamaki kwarai da ganin kiran shi a wanan lokacin na dauka da sallama tare da gaida shi ya amsa yana fadin kanwa ta ina kika shige haka ? Kai yaya Yusuf ina nan inda nafi karfi mana na bashi amsa yace ko dai mutumin nawa ya boye muna ke ne ban sani ba ? Wa ke nan kake magana nima na tambayeshi yace abokina mana kuma ogana a wurin aiki nace wai mijin buzuwa kake magana ? Dariya ya kyalkyale dashi yace kai khadija baki da dama wallahi har yanzu dai mijin buzuwa aiko zaku kwasa dashi idan ya jiki. Nace ina ruwa na dashi balle balle ya jini . Yace ke ko keda ruwa dashi khadija yar mama amma dai baki da kirki Abdul din ne zaki ce yau ina ruwan ki dashi da bakin ki kike fadin haka . Tsuki naja na tabe baki kamar yana gani na a lokacin nace ni na fita batun shi yanzu banda lokacin shi. Yace subbahanallahi may yai zafi haka ne a tsakanin ku kuma keda mutumin naki khadija ? Mutumi na ko naka yaya na kai nifa ko wancan lokacin da nake kula shi albarkacin ku ya samu a gare ni har na biye mashi amma ba don shi ba. Kai haba yar mama bai dace ki fadi haka ba tsakanin ki dashi yanzu ai kunyi nisa sosai bai kamata aji wanan maganan ba a bakin ki. Taimako fa kikace zakiyi sai da abu ya kusa kai karshe zaki ce ba ruwan ki dashi yanzu ai ko kece mai ruwa har da tsaki akan shi yanzu. Mu dai bar wanan zancen nace dashi da sauri yace akan may zamu bari idan na tambaye ki zaki fada min gaskiya ? Nace akan may ke nan yace akan mutumin naki mana nace idan na sani may zai sa na boye maka kuma ? Yace Yaushe rabon da yazo gurin ki ko kuyi waya dashi when last kukayi koda waya ne please kada ki boye min komai just feel free with me khadija? Dan jin nayi sai can nace gaskiya mun kwana biyu dashi don ba zan iya tuna zuwan shi gurina ba na karshe ko wayan shi a yanzu. Yace abinda nake son ji ke nan daga bakin ki sai dai zan ari bakin aboki na inci mashi albasa Abdulsamad yayi tafiya two weeks ago amma dai yanzu ya dawo. Sai dai ko a yanzu da bukata nazo maki a kan shi don gaba daya khadija ba zan boye maki ba Abdulsamad ya canza ga komai cikin yan kwana kin nan. Gashi matar shi na shirin haihuwa watan ta ya tsaya tun last month sai dai har yanzu bata haihu ba yana gida ko wani lokaci tunda ya dawo like da ita. Katse shi nayi da fadin ni may ye nawa a cikin zancen nan kuma can su karata shi da ita tunda shi ba tsayayyen namiji bane ko yaushe. Namiji ne mana khadija ai shiyasa na kiraki don ki sheda mai cikin wanan wasan da kuke yi don ya farga ga abinda yake yi din. Ni tsoro na shine kada su mommy daya dauko gidan shi su fahinci susucewar shi a kan wanan shuumar matar tashi sugane gazawan shi a gaban kowa. Shiya sani mana tunda shi ke ji a jikin shi ba wani ba yayi saurin fadin a a khadija ba haka zamu yi ba daurewa zakiyi mu fitar dashi daga wanan kangin don Allah. Ni haba yaya Yusuf ni may zan mai kuma shiya sani don Allah khadija dakata ki saurare ni don Allah nace ina jin ka ai. Zaki iya hakkuri ki daure ki kirashi a waya ki fada mai magana daya wanda zai shi ya natsu ya dawo cikin hankalin shi yanzu don ke ce kawai mafitar da nake dashi bayan Allah. Ni kuma why sai nice mafita akan haka yace saboda ban taba ganin wani ko wata dake fada mai magana yadda kike fada ba azauna lafiya kuma yai amfani da abin da kika da mai a zauna lafiya. Dan jin nayi ina tunane yace kada ki karaya khadija don nasan zaki iya ki taimaka muna please wanan taimako ne indan kin yarda. Yaya Yusuf wanan ya zama na karshe da zan ma wani alfarma akan wanan mutumin don gaskiya baida niyar canza halin shi nake gani . Khadija ba laifin shi bane shu,umar mace ya hadu da ita take juya shi yadda take so nace har da halin shi a haka. Kin yarda zaki taimaka muna ke nan nace naji zan gwada don Allah don kai amma da ba haka ba babu abinda zai kara damuna da rayuwan shi. Nagode kwarai da hakan da zaki min don wanan ne kadai hope din da nake dashi yanzu akan wanan matar tashi. Ina aje wayan maryam dake zaune ta kura min ido tana sauraren maganan da muke yi din tace kai wasu maza suna haduwa da shu,uman mata wallahi. Koda yake ba abin mamaki bane ga wanda yasan mazajen da ke auren irin yan yaren buzaye zai san mazan ne a kasa matan suna sama. Sai abinda sukace komai su mamaye na miji yazama nasu su raba shi kuma da kowa nasa sai su da yan uwan su zasu dinga bushasha da shi da dukiyan shi. Sai dai kima sam basu son auren mazan yaren su don irin bakar wahalan da suke sha wurin su amma namu mazajen su ke kwadayin matan buzaye saboda bakar jaraban da suka iya. Yanzu dai kira shi muji yadda zaku kwashe a tsakanin ku don nasan akwai drama nace ni wanan daure ni suke son yi maryam. Ban san may yasa suke cewa wai sai nice zan iya masu haka ba bayan yana da kanne mata da yan uwa da zasu iya. Su iya may khadija ai abin sai da hikima ke fa ba yar uwan su bace kin ga yadda kuke moved dashi kamar saurayi da budurwa ne. Ke komai zaki iya fada mashi a zauna lafiya wani dan uwa idan yafa da sai inda karfin shi ya kare ke ko sai ki fada mai a wasa bai dauki abin da zafi ba. Wayan ta na karba ta hanyan yi mata karya wayana ba kudi a ciki tace ai bai san layi na ba don haka ba lale bane ya dauki kiran . Bari dai mu gwada mu gani idan bai dauka kiran har ya kusa karewa ya daga tare da fadin hello nace dole zama da yan haure ya kowa ma wani akidar banza. Wake magana please ya tambaya nace wata buzuwa ce ko kana son kari su zama biyu a gidan ka murmushi yayi yace khadija nace ba ita bace. Kina zaton muryan ki nan zai bace min ne nace marya na yana kama da na buzaye ne ? Yace ai kamar ma ta baci baki ganin zubin ku daya dasu sai dai yaren da baki ji nasu kai malam ni kiran ka nayi naji ko mommy ta koma ne? Don nasan ba lale bane buzuwan gidan ka ta barsu su dade a gidan yace idan kina son sani kije gidan ki duba mana. Ban tashi ba ne da zanje yace ya kike nace ina nan yarda ka sanin a baya ke ba a maganar girma da arziki dake ne ? Nace banson don ba gaisuwa na kira ka muyi ba ko tambayana yaya ni yace ai kogi ba ki dadi ba ko nace . Wani kogin ke nan dai wani ko wani ruwa ne ya shige shi in ba nasa bane amansa yake yi don haka ba gaisuwan ka nake nema ba. Yace becareful nace a nan ko sai kaga mutum har mutum amma a gidan shi sai ka rena mai wayo idan kaga abinda yake yi. Ta yaya bakin haure har zasu shigo su samu mutum a gidan shi in ba samun wuri ba suce sai abinda suke so zasu mai ni wallahi na dade da raina aya don tsakuwar ta. Yau hausa kike ji ke nan nace daurowa ne hakan adai ji tsoron Allah kada mutum ya zauna mace ta mayar dashi saniyar tatsan ta . Ba mai ci sai ita da yan uwan ta kadai yace kina son wani abu ke nan nayi saurin fadin haram wallahi adai ci lafiya. Ga yan ketare nan suna taya ka ci idan ka wawuro su kuma sai su cafke ranan na zuwa da zan maka irin ku kotu masu ba bakin haure makafa suyi yadda suke so da dukiyar kasan mu. Yace magana kike ji ke nan dai nace ba wani magana sai fadin gaskiyan da na saba kulun idan naga anyi ba daidai ba. Ya Abdul ace mutum baiwa kansa adalci kulun sai abinda mace ta dora shi a kai yake bi yace wai may kike nufine don na rasa gane ida maganar ki ya doso har yanzu. Mafalki nayi naga ka susuce kazama bawan mata sai goyon su kake yi a bayan ka ka manta da kowa na naka sai masu jajayen kunne kasa a gaba. Murmushi yayi yace ki fito fili kice kin yi kewa na kawai kin tsaya kina dora wa wani laifi kuma ko na kulata ba mata na na kula ba na kula matar wani ne ? Mata wai mata matar namu duka dai inji manya mata kan tana kaduna ka barota can wanan ai ta bugi ne . Khadija you are very stupid matar nawa kike aiban tawa a gaba na nace ko a idon ka sai na fada don gaskiya ake fadi. Namiji kamar mace baida say a gidan shi sai na mace macen ma abin kyamatar mu gaskiya ka gyara halin ka sai anjima nayi saurin kashe wayan batare da najira amsan da zai fada min ba. Wanan yarinyar ta ci uban rainin wayo wallahi yace Yusuf da ke zaune gefen shi yana murmushi yace khadija ce halan ? Wa kasan zai min wanan idan ba ita ba ban san mayeatsalar ta da Nafisa ba ko da yake su mata haka suke dama ko Nafisan da tasan da zancen khadijan Allah kadai yasan iya boren da zatai min. Kana zuwa gurin ta ke nan har yanzu ya danja tsuki yana fadin wallahi na dade ban ganta ba tunkan naje Lesvegan rabo da na ji daga gare ta. Yusuf yace ai gashi yau ta kiraka ita yace ta kirani taci min mutunci ba sai nayi maganin yarinyar nan wallahi ta raina ni da yawa I don't know why take min abinda taga dama haka ? Kun fi kusa ai bani shiga tsakanin ku yanzu ai wani kallo yaiwa Yusuf din yace tunda ka gama hadawa ba ai ka fadi haka yanzu ? Au ni ma hada ke nan ashe wa ya manna min wanan chewing gun din idan ba kai ba ina zaune kalau abina. Amma ai tayi muna rana ba kadan ba kasan da hakan dai ? Tsuki yaja yace ban san ya nakoma ba wallahi yar karamar yarinya ta shige min na kasa yin komai akan hakan ? Kun dai shige ma junan ku yanzun ne kuma kake neman maraba da ita ko why zaka so ka rabu da khadija bayan kasan tana da amfani a gare ka ? Amfani fa kace Yusuf yana kallon shi da idon shi da ya kafa mashi sai da Yusuf ya rausaya kai yace kafini sanin haka malam. Kada ka bari shedan ya rudeka kaiwa kan ka hasara zukekiyar yarinya kamar khadija may kake fadi ne wai Yusuf ? Kiran kawun shine ya katse masu magana da mamaki a fuskan shi ya furta kawu habu yau lafiya kawu ya kirani haka ? Ya dauka suka fara gaisawa da kawun nashi wan mahaifiyar shi cikin kunya da nauyin kawun nashi yake amsa mai gaisuwan. Don ya manta yaushe rabon shi daya kira shi ya gaida shi a matsayin shi na wan mahaifiyar shi da take ji dashi a cikin yan uwanta. Bayan sun gama gaisawa ne kawun nasa yace dama na kiraka ne idan da hali ina son ka shigo kaduna a cikin wanan satin . Da mamaki ya tambayi kawun nasa yace kawu lafiya ko yace a, a lafiya kalau sai alheri akwai abinda nake son kayi ne idan kazo amma fa idan ba takura. Haba kawu ba komai in sha Allahu satin nan zan shigo ranan jumma, a asabar zan karaso zaria in gan ka kawun nashi yace nagode Allah yayi maku albarka ya kara tsare muna ku. Ya amsa da amin kawu na gode ya aje wayan yana mamakin maganan da kawun nashi ke dashi akan shi Yusuf dake gefen shi ne ya tambaye shi ko lafiya. Yana mai da kan shi bayan kujeran da yake zaune sama yake fadin wallahi ban san abinda yasa yake nema na ba a yanzu. Zamu tafi karshen satin nan don haka sai ka shirya muna tafiyan yadda ya kama sai dai ban so tafiya yanzu ba a yadda Nafisa take haka haihuwa yau ko gobe. Zamu iya zuwa muyi kwana daya idan hakane sai mu juyo idan ka gama ganawa da kawun. Yace hakan za ayi Allah ya kaimu lafiya gaba daya har ya manta da zancen wata khadija ko don mantuwan da yake fama dashi a yanzu. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Yan uwa da abokan arziki ba laifi sun zo mashi karan suna sai dai taron ba wani dadi don mai jego ta tsare komai na gidan ta hana mutane suyi yadda suke so. Ganin haka ne tu sha biyu suka buga min waya suna tafe gurina don basu ga amfanin zama gidan da suke yi ba gara kawai su fita suga gari. Da waya har suka iso gidan da muke zama inda ake kira da up k na mata inda a nan nima nake da dakin na da aka kama min tun zuwa na Abuja. Ranan nayi mayan baki don karshen ta dole suka samu gaba wai mu zamu nuna masu gari shigan dai guda ne don ko yau wani abaya baki mai kyau ne ke saman lace din da nasa. Shigan yayi min kyau matuka don ya mayar dani kamar wata yar bukuwar haure dani munje wuse market mun dan leka gura re sai yamma lis muka bar SAHAD zuwa inda gidan yayan nasu yake inda suka zo suna. Don nace dasu ni ban sani ba can ko sai faman tambayan su ake don wata ta bar yar ta karama na barci a gidan ta biyo mu yarinyar ta tashi tana kuka sosai don haka ake tambayan ina suka je. Har shi kanshi maigidan da kukan yarinyar ya damay su yake tambaya akace mai suna gurina bai tsaya mamaki ba ya fara fadin may suka je yi wurin yarinyar dake makaranta. Mun shigo suna falo an gama rikici ke nan da buzuwa matar shi da Fauziya kanwar shi da su mommy don komai da ake shigowa dashi gidan buzuwa ta hana aba mutanen Abdulsamad sai idan kaje wurinta munafunci zata baka ko matan abokan shi haka bata ba abin sai taga dama. A daidai lokacin da suka gama rikici da Fauziya da tace sai an raba an basu nasu, ranan ta murje ido tayi ma buzuwa tas a gidan abinda a da suke tsoron mata. Shigowan mu ne gidan ya dawo da hankalin mutane a gare mu su tambaya ina suka shige haka ne ni da zainab ce da Binta sai maryam muka shigo daga karshe gidan ina tako dadaya duk kan mu kwaliyan mu ba laifi. Tsaye yake yana magana a cikin fada muka shigo da sallama falon sai da ya so rudewa a lokacin da mukai arba dashi nayi saurin kawar da kai na mommy da na hango zaune na nufi gurin ta har kasa na zube ina gaida mommy ta dafa ni tana fadin khadija kina garin nan nazo na dade a nan ban ganki ba. Yanzu ma nasan don su Binta ne kika zo gidan nan da bamu gan ki ba na san har mu koma Nafisa dake zaune ta cika ta batse sai huci takeyi tana kokarin son tuno a inda ta san fuska na amma ta kasa ban dade ba muka ce da su zamu koma ko dakin bamu shiga ba. Binta na fadin ba wani abu a basu mommy shi kuma maigidan ns fadin Fauziya tashi ki hada nasu snack din nan da aka yi da drink's lokacin har mun kai kofan fita daga katon falon nasu ko. Binta da zainab dake bin mu a baya ne ke fadin ku tsaya don Allah a kawo maku abin buki kutafi dashi na juyo nace da ita. No ku barshi kawai dama mommy muka zo gaidawa a a yan mata ashe kun samu shigowa bukin ku ma ? Muryan Yusuf ne dake fitowa daga cikin motar da ta parker a gaban mu yake fadin haka maryam ce ta bashi amsa da fadin wallahi fa. No ba buki ya kawo mu ba munzo mu gaida mommy ne tsaye Binta tayi tana kallon mu da mamaki tafiya na fara yi zan wuce wurin Binta tace don Allah ku tsaya ku karbi abin buki mana. Nace a barshi kaya zai muna yawa idan mun tsaya daukan wani abu kuma ke khadija wani kaya ke gare ki banda handa bag da kika rika nace shima ai kaya ne ko. Khadija ya kira suna na da karfi na juyo tsaya mana ku amshi kayan bukin maryam tace ya Yusuf muna sauri ne mu samu abin hawa kasan unguwar nan naku idan yamma yayi akwai matsalan abin hawa. You known each other ne dama ? Zainab ke tambaya cikin mamaki No ya dade da na san su ba irin familier din nan ba dai na fada ina yatsune fuskana. Barin sauke ku mana Yusuf yace da sauri nacevka barshi kawai zamu karasa ai na fadi ina ci gaba da tafiya na nufar get din zuwa waje. Da sauri ya shiga babban motar Abdul din yana fadin ku shigo in sauke ku nasu in ki amma Binta na ta kaudi motar yayan sune ai in shiga a kaimu hostel din . Zainab tace friend ku shiga don Allah bari muje tare a sauke ku sai yaya Yusuf ya dawo damu abubuwa ake fitowa dashi daga cikin gidan wai duk namu . Mommy ne ta fito waje lokacin da zamu shiga motan tana magana dani tace ga abin buki nan yayan su Binta yace a baku kuje dashi wai angode nace lokacin shima ya fito wajen. Yusuf ina zaka ne yace zan sauke su khadija ne hostel in dawo barin bi ka mu fita daga can zan tafi gidan MD dayani. Ga mommy tsaye ta kura muna ido dole na yarda muka shiga motar a tare dashi dasu Zainab da binta ya juyo yana fadin ku kuma ina zaku sukace zamu raka friend din mu ne yaya. Ba yanzu zamu dawo ba fa ku fita don Allah rike zainab nayi nace a tare zamu fita ke nan don saboda su nazo nan din da kuma mommy. Sun yi mamakin jin maganan da na iya fada ma yayan nasu wanda suke matukan tsoro da girmamawa su. Sun dauka zai yi wani abu sai sukaji yayi shiru bai sake magana ba sai tsawan da ya daka ma Yusuf akan ya tsaya mana su sauka kokarin sauka nike yi zainab tace ki bari gobe zan shigo wurin ki da safe ai. Ta fice daga motar da sauri ta rufo kofan da mu a ciki yusuf ya kama hanya ya tafi daga gidan ba wanda yayi magana a cikin motar. Ya Yusuf ka tsaya dan Allah in sauka ko sauraro na bai yi ba sai tukin mota yake a hankali kwance abinshi. Tsuki na naja daga inda nake zaune muryan shi ne naji yace kibi a hankali fa kada ki bata muna rai a nan sai kace wace aka ce za a sace ta. Nace ai in ma kunyi niya zaku iya hakan don iya yaudaran ku dariya sosai Yusuf yayi yace munyi kama da mayau dara ke nan khadija. Kasan ta iya shirme wani lokaci mu sace ki muyi may dake ai ba irin ki zamu sata ba har in muna satan yan mata. Yusuf yace nikan irin su zan sata don yanzu suna danyun su shar ai kaga daidai sata ke nan nace ai dama nasan zaku iya haka ba sai kun fada ba. Yace Yusuf ya tsaya a wani guri da ake sai da kaji ya mika mai kudi ya sayo muna da abinsha mai sanyi Yusuf ya fita ya barmu a motan tare dashi. Naji dadi da maryam ke cikin motar a lokacin ba a barmu mu biyu ba ko kallo gefen da yake ban yi ba maryam ne ta dan zugure ni wai in yi mai magana. Na kawar da kai kamar ban gane abinda take nufi ba tunane nake ta yadda zan fita motar nasu a lokacin Yusuf ne ya dawo dauke da ledoji a hannun shi ya shigo motan yana aje kayan a gefen shi ya ta da motar muka tafi. Ban akara ba sai gamu bakin hostel din mu da sauri nayi niyar fita daga motar amma motar tana rufe har lokacin ga sanyin A C motar daya damay ni. Suna zaune ba wanda yai magana a cikin su har dan wani lokaci can naji Yusuf yace daidai lokacin da nake fadin ka bude mu fita mana. Shikuma yana fadin gaskiya khadija ba a kyauta maki ba a kyauta maki ba da sauri ya dago kai yana kallon Yusuf din dake magana. Yusuf fitar masu da tsaraban sunan su su sauka don Allah zaka tsaya wani magana kuma yace ya zama dole mu bata hakkuri don bamu kyauta mata ba. Da akai mata may kuma ya tambayi Yusuf din cikin tsare shi da ido yace ai kaine mai lafin yaya zaka saka ta saba da kai daga baya kuma kazo ka share ta haka ba dadi wallahi irin haka kaima ka sani. Please ka fitar masu dashi mu tafi don ina da abinda nafito yi yanzu ba wanan ne a gabana ba zaiyi magana yace fito masu dashi nace please. Ai da ka barshi zuwa kawai mukayi in gaida mommy da su anty Fauziya da suka zo ya sake fafin don Allah ciro mata mu tafi ya sake maimaitawa. Fita Yusuf yayi daga motar ya bude bayan motar yana fitar da kayan da aka saka a bayan motar sai da nayi mamakin ganin yawan kayan da aka debo muna mu kadai. Haka na dake fuska daure na fita daga motan ban koyi masu godiya ba na fice fuuu a motar Yusuf ne ya tsayar dani yana fadin haba yar mama ki sasauta wanan fushin naki ku fahinci juna da mutumin ki. Dan Allah yaya Yusuf ka daina hadani da wanan mutumin don ba ajina bane shi mutumin da yake under control din mace macen ma yar haure ba jinsin nahiyar mu ba. To waima may kake son in kula shi aka in kula shi ya bata min lokaci ya hana mutanen arziki zuwa gurina ko may ? Subbahanalahi ina wanan maganan ya fito haka a bakin ki baki taba tunanen Abdulsamad son ki yake bane ko may ? Da sauri nace so so fa kace na girgiza kaina nace a,a dama kace kawai yana amfani dani ne wurin cin ma wani manufa nashi da zan yada da hakan amma ba wanan kalamin naka na so ba. Sam na sake girgiza kaina karo na biyu tare da fadin wanan wani sallon yaudarane kuma ka dauko yanzu. Yace to ko ki yarda ko kada ki yarda ni yau na fada maki son ki Abdulsamad keyi har cikin ranshi wallahi bai dai iya fitowa fili na ya fada maki ko ya nuna maki hakan. Wani irin kallo nayi mashi tare da girgiza kaina na juya na fara tafiya ina jin wani bacin rai a zuciya har na shige ba tare da na dauki komai nasu ba da suka aje muna. Kwanciya nayi ina tunane a raina maryam da wata suna shigo da kayan daki har suka gama ta debar masu ta basu daga ciki. Ta dawo ta zauna tana ta faman cicire kayan guda guda tace kai khadija akwai wanda ya samu abinda muka samu kuwa a wurin nan jifa wanan uban kayan da aka loda muna wai duk namu ne mu kadai ina zamu da wanan kayan haka ? Sai lokacin na dago kaina ina duban kayan data tara a gaban ta na maida kaina saman filo na kwanta magana Yusuf ne ke ta min yawo a zuciyana har wanan lokaci. Maryam ne naji tace wallahi khadija na yarda da Yusuf daya ce son ki Abdulsamad keyi har cikin ranshi ba karya ya fadi ba don ni na dade da sanin haka tun tuni. Ina jinta saidai ban yi mata magana ba har ta gama fadin abinda zata nace ke idan nace zan bata lokaci ga wanan mutumin ba zaki min fada ba maryam. May ke cikin gidan irin su Abdulsamad banda tarin rikici da tashin hankali kulun ni kwadayi bai kai idona ya rufe ga abin hannun shi ba wallahi. Salama nike nemawa rayuwana ko yaushe ba zan tsaya in yaudari kaina ga abin da nasan yafi karfi na tun yanzu akan matar shine fa ya daina kulani ke ma kin san da hakan. Tace da sauri Kin san uzurin shine da zaki yanke mai wanan hukucin haka khadaji idan yana son ki ko Allah ya kaddara akwai aure a tsakanin ku matar shi ta isa ta hana ne ko tayi kamar Allah ne. Sai dai in kece zaki bata kafan da zata hana din ta dauki kanta inda Allah bai kai ta ba kinatsu khadija ki san may son ki da zuciya daya. Ni na fahinci A,A irin mazan nan ne da furta kalman so ke wahala a bakin su sai dai suyi ta nuna ma mace alama amma basu iya furta mata da baki. Nace shine kike son in tsaya wahal da kaina gare shi ko may ni koda ya furta bai mun ba don ba zan so shi ba ma ban ra,ayin mijin tace a rayuwa na. Ban yarda ba wallahi ke ma kina son shi kishine dai ke damun ki ke ma kina ganin kamar ya mutu akan matar shi ya daina kulaki don ta. Haka zuciyar ki ta fada maki ashe nace mata bata ko fada maki daidai ba ke nan idan tace maki nima ina son shi. Tace idan baki son shi may yasa yanzu kika rage mashi tsiwa irin da don da dane da yanzu kunyi fada a motan nan yafi a kirga. Nace amma kin san wulakanci bai da kyau ko saboda haka ne na kyale shi badon komai ba yanzu dai ai kanku ake ji ku karaci gulman ku ku dawo hanya dai. Indai har kin san kina son shi ya kamata ku daina wanan shirmay tun wuri tun bazuwa bata kara kwace maki shi ba kuma. Ta kwace shi mana shi ya shafa bani ba nace mata cikin kunan rai tace dukkan ku dai ya shafa khadija bashi daya ba kin dai san so yanzu koda kike kirarin baki taba so ba a rayuwan ki. Washegari a wurina su Binta da zainab suka wuni don ba shiga school Friday ne yau sai sunday zasu koma kd. Don haka da yamma muka shiga gari dasu yawo sunyi mamakin sanin garin da nayi don sanin da sukayi min ba mai rigima bace ni. Munsha yawo sosai rana sai dare muka dawo hostel dasu bamu dade da dawowa ba wayan Binta yai kara ta dauko da sauri tana dubawa take fadin nashiga uku yayane fa ke kirana zainab. Zainab tace dauka mana kiji may yake kiran mu nasan dai sunga dare yayi ne bamu dawo ba suke neman mu ta dauka tana fadin hello yaya A,A yace kuna ina ne har wanan lokacin hankali mutane ya tashi. Tace gamu nan wurin khadija tun dazu ita ce zata rako mu mu dawo yanzu yace tana da motane tace a a yaya karatu fa take yi ina zata samu mota kuma ? Yace ganinan zuwa in dauke ku yanzu ku jirani in zo yace ya kashe wayan kallon ta mukayi nace yanzu ba zai bari ku kwana nan ba ke nan ? Tace tunda kika ga yakiramu ai haka yake nufi damu nace bari yazo ni zan fita nagan shi da sauri tace ke baki san halin shi bane bari kawai yazo din mu tafi gobe sai mu dawo muyi sallama ba shike nan ba. Zainab tace ni nafi sakewa a nan wallahi amma can gidan duk a tukure muke wallahi shegiyar matar nan tashi bata bari mutum ya wala a gidan. Dariya nayi mata sosai da take fadin haka ba a jima ba sai gashi ya kirats yana fadin su fito nace barin je in gashi tace bari dai mu tafi ban son fadan nan nasa wallahi. Maryam tace ku bari ta fita ta gan shi mana ai zai yarda ku kwana nan idan ta roke shi baku san ko waye bane yaya AA kawai. Mikewa nayi na fita batare da na kula da kayan dake jikina ba a lokacin yana zaune a cikin motar shi ya fitar da kafa daya waje yana shakan iskan dake kadawa a lokacin . Na iso gurin sallama nayi mai ya dago kai da sauri yayi min wani irin kallo ya kawar da kan shi kuma kallon da ada in yayi min nasan na bata mashi rai ke nan. Sai dai yau ban san may yake nufi da hakan ba da yayi min shi nace don Allah ka barsu su kwana guna tunda gobe ne kawai haduwan zasu koma gida jibi. Ya sake kallo na a karo na biyu yace su ke son kwana nan din sukace maki nace suke son hakan bani ba yace to shike nan indai zaki basu kulawan da ya dace may zai hana nace mai sai yadago ya dube nayi saurin kawar da kaina gefe daya nima. Nace na gode na juya zan tafi naji yace khadija nayi saurin juyowa sai naga ya kada kai kawai sai kuma yace may yasa kika fito waje haka da wanan kayan ? Don Allah ki bar fitowa haka na roke ki please kallon kayan dake jikin nawa nayi sai lokacin na ga kayan don na cire abayan da na dora sama da muka dawo daki. Ki kula daga yau ban son ganin mace a waje haka gara idan mace tana cikin gidan ta zata iya amfani dashi haka ko ga mijin ta. Kai na rausaya cikin wani irin jan aji da ban san nayi ba nace ga matar da bata da miji fa itama sai a hanatayin yadda take so ko may. Yayi tsuki yace na dai fada maki ban so ki kula daga yau kada in sake ganin ki haka a waje daga yau. Jikina ne yayi sanyi na kasa yin wani magana kuma ya kawar da kan shi gefe bai sake magana ba sai ya mayar da kafan shi daya dake waje tare da jan kofar motar yana fadin ni na tafi sai da safen ku. Kin dai ji abinda nace dake ki kiyaye duk abinda nace dake ban so ban so ne ya rufe motar yai mata key gurin nake tsaye kamar wace aka kafe har ya bace ma gani na naja kafata na koma ciki. Ina shiga na samay su har sun shirya suna jiran shigowa na dakin nace dasu yadda na gansu a takure yace ku fito bai yarda ba wai. Zainab tace ai dama na sani don kada kice mun hana ki ne do ba mu son kwana din amma ninasan ba zai yarda ba ta fada a sanyaye. Tare da fadin tashi muje Binta binta din taja wani tsuki tana shirin mikewa nace ya tafi fa tace don Allah ki bari nace wallahi ya tafi tun dazu na tsaya magana ne a waje. Wai da gaske kikeyi khadija nace wallahi ya tafi yace sai da safen ku tunda anan kuke son kwana indai kula daku naso ce mashi mudake nan wake kula damu ? Da sauri tace da kin muna tsiya wallahi nan dai muka sake muna ta hiran mu kayan bukin da muka dawo dashi a tare dasu mukai amfani dashi. Sai hiran buzuwa da Binta ke ta bamu a dakin wanda inda tasan yadda raina yake baci da ta daina bamu labarin abin haushi haka. Washe gari ma kusan tare dasu muka wuni a hostel din mu sai da yamma muka je gidan tare dasu yiwa sauran yan uwa sallama. Mommy tace khadija kice bakin naki ne dai wanan irin fresh da sukayo haka wurin ki dan kwana daya da rabi injin dai ba dan abincin naku suka cinye ba. Shine ya shigo nan ya gan mu kallo daya yai muna ya kawar da kanshi gare mu gaishe shi suke yi yace da alama kunji dadin zama a inda kukaje din ke nan. Mun dan jima tare dasu mukai masu sallama suka rako mu zamu tafi sai ga driver yace ance ida zamu koma a sauke mu . ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Tunda mukai waya da Ya Amina tace min bata da lafiya sosai sai naji hankalina bai kwanta min ba ina bukatan zuwa kaduna weekend in dubata. Kwatsam aka wayi gari inace wa maryam kaduna zan tafi yau in duba jikin Ya Amina da bata da lafiya tace shine baki fada min zaki tafi ba muje tare . Nace kada ki damu watarana mu tafi tunda muna tare ai har bakin titi ta rako ni na shiga mota ta koma ita. Da wuri na isa don sammakon da nayi na samu jikin nata da sauki sosai na fahinci ciki ne ta samu ashe yana bata matsala dama haka take ciki da wahala ita. Gidan da bai samun gyara saboda laulayin da takeyi yasa gidan yayi datti da yawa sai da nayi wa gidan tas na yi wanka na kwanta don in huta. Tunda ya fara shiri Nafisa take tsaye a kansa tana fada dashi akan may zaiyi tafiya yanzu bayan yasan halin da take ciki zata iya haihuwa ko yau ko gobe. Ya dago yana ce mata tafiyan ya kama shi ne dole don haka na fada maki gobe zan dawo insha Allahu may nene kuma na fada yanzu. Tace yanzun dai baka damu dani bane ban san may kake yawan zuwa yi gida ba akai akai haka ? Au ke da kike zuwa gida wani abu kike zuwa yi a can tace zaka hada kaina da kaine nifa kasan ba nan iyayyena suke ba ya zama dole in rika duba su a kai akai. Da kyat ya samu ta barshi zai tafi koshi don yace aikin shine zai sa ya tafi yasa Nafisan ta daga mai kafa. Da suka isa kaduna zaria suka wuce kai tsaye don ganawa da kawun nashi dake neman shi ida sukai saa sun samu kawon a gida wanda ya nuna jin dadin shi da amsa mai kiran da yake mai din. Bayan gaisuwa sun natsu ne kasun ke fadin ba wani abune yasa na kiraka ba sai yar wata magana da ta taso daga mahaifiyar ka a gamay da kai. Zama ya gyara don ya saurari may mahaufiyar nashi hajiya mama tazo ma kawun nashi dashi duk sunyi tsit suna sauraron kawun. Yace tazo nan ta samay hankali a tashe take fada min abinda ke faruwa dakai na rayuwa musanman da kai da iyalin ka. Dama yasan maganan ba zai wuce wanan ba ai yace cikin karfin hali kawu wani abin tace nayi kuma yanzu ? Yace eh to tace bata ce ba kasan dai tsakanin da da mahaifi akwai wani kulawa da damuwa na musanman shiyasa tazo min akai ya kamata a taimaka ma da addua da wani taimako. Shine na kwantar mata da hankali nace zan yi wani abu akai don kasan naka sai naka a yadda naga damuwa a tare da mahaifiyar taka. Yasa bayan mun rabu naje wurin wanj malami tsohone aminin mahaifin mu tun yana raye nakai mashi wanan matsalar taka. To Alhamdullahi ya karbi maganan namu sosai da muhinmanci ida ya ce in bashi sati hudu zaiyi istihara sai a san abinda za a yi bayan satin hudun dana koma sai yace dani yana bukatsn ganin ka sai kazo da kanka zakuyi magana dashi. Wanan ne yasa na kiraka don kazo ku samu ganawa dashi kaji may zai fada maka sai musan mafita ga zancen. Zama Abdulsamad din ya gyara acikin ranshi yana fafin ikon Allah ita kuma mama tanan ta bullo min kuma yanzu bayan tasan ban son irin abubuwan nan tun farko. Amma a fili cewa yayi to kawu ba matsala amma dai sai dai ina fata aikin shi ba na kaucewa Allah bane dai ? Murmushi kawun nashi yayi yace haram haram kana ganin munyi kama da masu kaucewa alamarin Allah ne ya kamata ka shedi mahaifiyar ka kasan halin ta. Yanzu haka ma bata san komai ba tukun a wanan zance nafi son muyi magana ta maza da maza kafin ta samu labarin komai. Yace hakan na dakyau kawu don nima ban isa can gurin su ba tukun nan muka fara zuwa yanzu sai mun koma zan isa gidan. Tashi sukayi zuwa gidan tsoho malam illu don su gana dashi sun samu yana ganawa da wani babban mutum don haka suka zau a motar su suna jiran fitowan mutumin. Bayan mutumin ya fito ne kawun nashi ya ce su taso su shiga daga ciki suka fito daga motar zuwa ciki amma sai Yusuf yace zai jira shi a waje. Ya juyo yana fadin haba haba Yusuf ya zakace haka kuma mushiga don Allah zai fi akwai abin da baka sani bane nawa. Kawun yace mu shiga mana ai ba komai bane wanan mushiga daga ciki kawai mugan shi. Cikin suka shiga tsohon yana kishingide saman farin buzu irin na dabbobi da malaman da ke zama a sama. Yana ganin su ya dan dago daga kwanciyan manya da yayi nan suka zube don girmamawa suka fara gaida tsohon yace salihu kune tafe yanzu ? Yace eh baba yaron da kace yazo ne dan wurin ita kanwar tawa hafsat yazo yau daga can abuja inda yake aiki don amsa kiran da kai mashi din. Tsohon ya daga kai yana kallon su Abdul din yana jijiga kai yace Allahu Akbar yanzu wanan jikan mahaifi ku ne Allah ya jikan malam shaibu suka amsa da amin . Ya dauko wani tasbaha ya rike a hannun shi ya dan murza ya mikawa Abdul din baya ya ce shine wanan din ko kawu salihu yace shine baba. Yace canki daya a nan yana mika mashi tasbahan dake a hannun shi Abdulsamad din ya mika ya zabi dayan dan tasbahan tsohon ta girgiza kai yana murmushi. Ya dago kai yace Abdul yake ko yace eh Abdulsamad yake sunnan kakan shi yaci na wurin mahaifin shi yace to kamar yadda na fada ma zanyi istihara akan jikan nawa Allah ya bani iko nayi. Sai dai naga abubuwa da dama da suke faruwa da jikan nawa wanda da farko zan iya cewa akwai sakaci aciki alamarin jikan nawa. Abdulsamad yaya akayi kabar gida haka kana dan musulmai jikan malamai kamar mu kabar abubuwa suka cabe haka a lokaci daya gare ka. Zama Abdul din ya gyara yana sauraron shi maganar da ta fara zuwa bakin tsohon shi ne na fitar da yayi zuwa kasan waje satin da ya wuce zuwa wasan da suke yi acan na milloners in world. Zufa ne ya tartso mashi a goshi yadda tsohon ke bashi labarin abinda ya faru acan har ya fadi a wasan ya dai san babu wanda yasan wanan abin don ko Yusuf baida labarin abinda ya faru can sai ga wanan tsohon na bashi labari tiryan tiryan. Bayan ya kare mai wanan bayanin ya dago ya kalli Abdul din wanda kanshi ke kasa yana tunane yace sai kuma maganan da ya shafi iyalin ka yanzu. Malam ya danyi shiru na wani lokaci ya sunkuyar da kan shi kasa kamar mai nazarin wani abu yana kada kafan shi jefe jefi yace. Yace gaskiya nayi istihara a kan ka sai dai abinda zan fada ma ba lale bane ka yarda zaka iya zuwa wurin wani yai maka ko kai kayi da kan ka don zaka iya istihara ba abu bane mai wuya idan mutum yasa kansa yi. Yusuf ne yace malam ba matsala ai zaka iya muna bayanin abinda ke nan yanzu don musan abinda ke nan. Malam yayi baiyananen murmushi ya na gyara zama yace bani hankalin ka nan ka saurare ni da sauri suka dago suna sauraren bayanin shi. Yace abinda nagani a satin farko shine kana tsare a karshin wata mace fara doguwa sai kayi kamar zaka kubce daga sherin ta sai ta sake sabon shiri a kan ka ta kara daure ka. Sai dai dana sake yi naga wata yarinya fara itama a cikin rayuwan ka ban sani ba ko kasan da ita ko baka sani ba tana nan dai yar matashiya ce haka da ita. Sai dai ina ganin itace kamar warakan matsalan ka watarana amma dai ban sani ba Allah masani. Sai wanda nayi a karshen nan ya nuna min cewa zaka kara aure wanda haduwan ka da yarinya alheri ne sosai sai dai akwai matsala daga wurin wanan matar taka . Zaka kara aure nan bada dadewa ba zai zams maka alheri dan yarinyar mai biyaya gare ka ta kawo karshen komai a gare ka don arzikin ku yazo daya da ita sosai. Duk zauren akai shiru ana sauraren tsohon sai Abdulsamad wanda ke shatan zufa daga goshi shi. Malam yaci gaba da fadin sai kayi da gaske ka zama namiji zaka samu mafita don yanzun haka matar da zaka aure ban debe tsamanin ba ayau ko gobe zaku iya haduwa da ita. Yace wanan ke nan bansan abinda yasa yaran yanzu kuke sakaci da ibada ba bayan kuna da sanin da Allah ya baku wanda idan mutum ya rike yanayin sa ba wani shedanin da zai iya tunkarasa. Ya dauko wani abu yace amshi rika nan ya mika hannu da sauri yana karban abinda yake miko mashi din yace yau nake son kayi amfani da wanan abin idan ka isa gida. Zaka shaye shi duka sai ka rage kadan ka wanke fuska da hannayen ka kamar dai yadda kake alwala zakayi dashi sai ka kwanta insha Allahu zaka kubta daga sherin su da yardan Allah. Yace har in kayi yadda nace kayi da yardan Allah ba wani sihirin da zai shige ka koda kuwa sun hada da jinnu da sauran su don kamar ka dafe wani kafa na jikin ka ne da wanan tsarin Allah ya tsare ya kare yace dasu. Yusuf ne ya ce da tsohon malam batun yarinyar da kace fa tana nan kusa tsohon yayi murmushi yace gaskiya tana nan kusa damu a yadda nagani yanzu. Kuma ina sa ran haduwan ku ko yau ko gobe idan Allah ya kaimu sai dai mu bar ma Allah sanin shi. Gaban Abdulsamad din ne ya fadi a ranshi yana tunanen don yana tunane wacece wanan yarinyar da zai hadu da ita yaji har yana so ta. Godiya sukai ma malamin suka kawo kudi suka bashi kai ya kada masu yace ba wanan a tsakanin mu aikai jika nane bazan karbi ko kwandala a gare ka ba. Sukai mashi godiya suka mike zasu tafi sai tsohon yace akwai tafiyan da zai taso maja gashi na gani a gabana kayi kokari kayi wanan tafiyan don zaka samu alheri mai yawa a cikin shi. Ya kara godiya suka fita sai da suka sauke kawu salihu suka kama hanyar kaduna a lokacin yamma yayi sosai. Ba mai magana a cikin su kowa da abinda zuciyar shi ke saka mashi a lokacin don shi da farko bai yarda wai nafisa tana mashi sihiri bane. Ya dauka so ne kawai yake mata na tsakani da Allah mutane ke ganin wai sihirce shi tayi baida ta cewa akan ta sai abinda taga dama takeyi. Amma yanzu sai gashi dan tsohon nan ya jefo zancen ta a cikin maganan shi shi bawai ya yarda bane to amma kuma abinda ya daure mashi kai shine zancen tafiyan da yayi tsohon ya sani. Zai gwada abinda yace don ba a kin ta maya koma maye zai gwada maganin ya gani zai kuma bi a hankali yaga maganan tsohon ko gaskiya ne. Muryan Yusuf ne yaji yana fadin wallahi na dauka khadija ce tsohon nan ya gani a tasbahan shi ashe ma watace. Sai dai wallahi naso ka auri khadija ashe abin ba haka bane muna namu Allah na nasa ne. A tunanen ka ke nan kai ni ban kawo komai ba har yanzu don ba wata mace a gaba na yanzun haka abinda ya damay ni ya damay ni. Koda suka isa dare yayi don haka suka bari sai da safe idan zasu wuce su shiga su gaisa da su hajiya mama. Barci nake bayan na gama mata komai sai na koma in huta can cikin barcin naji muryan Y Amina a kaina tana fadin khadija don Allah tashi ki shiga gidan su mommy ki karbo min lemun tsami. Na dago idona cike da barci nace haba ya Amina nifa ban son shiga gidan nan har in koma tunda ba dadewa zanyi ba. Khadija magani zan hada dashi don Allah daure ki shiga ki karbo min dole na daure na mike ta fita daga dakin ta koma falo ta zauna. Na fito sai take cewa dani wurin hajiya mama zaki karbo min don mommy bata nan tana Abuja gidan Abdulsamad takai wata can an dauka matar shi zata haihu a lokacin suka tafi gashi har yanzu bata haihu ba. A raina nace ai nafiki sani na fita ina ce mata sai na dawo a gidan sunyi mamakin ganina don basu san da zuwa na ba . Sai da nabi kowa na gidan na gaida su na nufi dakin hajiya mama nan falon ta na samay ta na zube kasa ina gaida ita take cewa hadija yaushe a garin ? Nace jiya da safe na shigo nazo duba Ya Amina ce da jiki tace ayyah ai amina taji jiki wallahi haka take cikin ta ita. Nayi murmushi nace tace in karbo mata lemun tsami a gurin ki ne tace to barin in tashi in duba maki ko akwai saura. Sallaman su ne ya katse muna magana ta amsawa tare da fadin yaushe kuka shigo garin nan kuma ba labari don da gani anan kuka kwana. Hajiya jiya muka shigo munje zaria ne gurin kawu salihu sai dare yai muna a can kafin mu dawo cikin fadada murmushi tace toh daga wurin yaya din kuke ashe. Wuri suka samu suka zauna suka fara gaisawa dasu kaina na duke a kasa na somay da gani du sai bayan sun gama gaisawa ne hajiya ta tuno dani tace Aff. Kinga khadija na manta dake wallahi zuwan wa yan nan na bazata da sukai muna da sauri suka kallo ni kowan su na mamakin ganina a dakin mahaifiyar tasu. Mikewa tayi tana fadin khadija ga yayan ku nan wanda ya taba rage maki hanya kwanaki ashe suna hanya suma da kin sani ai dasu kika biyo koda yake kin ce ke shigan safe kikayi. Ina wuni nace dasu cikin jin kunya ban ko saurari amsar su ba na kawar da kaina gefe ina wasa da yan yatsun hannu na. Fita tayi zuwa wurin fridge din ta dake waje fitan ta naji muryan Yusuf yana fadin khadija yaushe kika zo garin nan ne ? Nace don Allah malam ban saku ba ku bari in rabu lafiya da hajiya don kunyar ta nake ji sosai na fada ma wanan aljanna ce wallahi. Inba ba wanda ya saba dashi ba ba zai dauka shi yayi maganan ba alokacin ban basu amsa ba don na hango hajiya tafe da bakar leda a hannun ta. Miko min tayi tana zama tana fadin ki gaida min ita da jiki in na samu lokaci zan kara shigowa in duba ta. Nace to mama an gode na mike da sauri ina barin dakin naji tace yaushe ne zaki koma Abuja ke. Nace gobe zan koma mama tace ku yaushe ne zaku koma tana tambayan su suka amsa mata da yau insha Allahu. Ai na dauka sai goben zaku tafi sai ku rage mata hanya nidai na wuce na barsu nan ina sauri in fice gabana na faduwa da ganin su. Har nayi nisa naji muryan Yusuf a bayana yana fadin yar gidan mama gani fa na biyo bayan ki. Tsayawa nayi ina jiran karasowan shi inda nake ya iso yana fadin surprise to see you dama ashe kema zaki shigo kaduna baki fada muna ba ? Yaya tace bata da lafiya nazo duba ta yace gaskiya naji dadi da na ganki nan nace namay fa baka san ina zuwa nan bane dama ? Yace na sani amma banyi tunanen zuwan ki nan a wanan lokacin bane sai abin ya ban mamaki matuka. Nace zai shige sai mun hadu idan mun koma yace shike nan amma da wata mota kika zo ne nace motar haya mana ina wucewa nake bashi amsa. Naba da baya naji yana fadin zamu biyo mu gaida yayar tamu nace basai kun zo ba an gode na shige gidan ya tsaya yana kallon gidan da na shiga. Abdul ya fito ya samay shi waje yake fadin dama kasan zata zo garin nan ne ita ma ko ta san da zuwan mu ne ta biyo mu. Murmushi yayi mai yace haka dai Allah ya tsara abinsa nima yanzu na ganta wallahi. Ina shiga nace dana sani wallahi da ban shiga gidan nan ba yanzu wallahi ina mika mata ledan nake maganan tace saboda may? Nace wai fa mutanen nan nagani a gida da sauri tace suwa nace su Yusuf da Abdulsamad mana tayi murmushi ta fara bude ledan tace a haka da yawa aiko na gode. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Ido Ya Amina ta bini dashi kaawai na shige daki iya yanzu haushin su su duka nake ji shiru shiru basu zo ba yasa na saki jiki na koma normal life dina a gidan. Kwana hudu nayi a kaduna na juya na dawo Abuja ban tsaya na sallami kowa ba don dama banda gidan su mommy ban shiga ko ina ba . Tafiyan marance nayi don ban da kaya a tare dani ba zansha wahalan zuwa hostel ba daga inda na sauka. Maryam ta tare ni da murna tana fadin wallahi har hankalina ya tashi da naga yau ma har dare baki dawo ba nace na tsaya ne inga yadda jikin nata ya kara sauki. Ban mata hiran haduwan mu dasu ba itama din bata tambaye ni ba don batayi tsamanin zamu hadu dasu ba a can. Suna gaisawa da Abba shine Nafisa ta kira shi tana fadin bata jin dadin jikin ta yau tun da ta tashi yace subbahanallahi yanzu zamu taso. Sun iso sun samu taje asibiti ance haihuwa da sauran lokaci suka dawo gida duk wanan abin su mommy dake gidan basu san wainar da ake toyawa ba a gidan. Don dama sai taga dama take gaida su da kwana bayan nan zasu wuni basu ganta ba a gidan. Ga A,A sun ga sauyi a gare shi sosai tun bayan zuwan wanan matar a gidan komai da yake masu na kulawa ya rage a yanzu wani lokaci har fita yake bai gasa dasu ba. Ya dawo duk da yadda yake ji ya rage jin shi yau direct gurin su mommy ya fara zuwa ya gaisa dasu sukai mai sannu da zuwa tare da tambayan shi mutanen gida. Ya amsa da suna lafiya suna gaida su ya fito ya nufi part din su kwance ya samu Nafisa tana barci ya dan dade a tsaye kanta yana dubata ya juya zai fita ta falka. Shima juyowa yayi yana fadin kin tashi tare da zama a kusa da ita yana tambayan ta jikin ta tana wani yamutse fuska take fadin da sauki. Taje asibiti an dubata ance ba haihuwa bane da sauran lokaci Allah ya sauwaka yayi mata ya mike zai fita tace samad yanzu ya dace katafi kai zaman ka ka kyale ni. Haba Nafisa jiyane fa nayi tafiyan nan kwana daya nayi a can kawai shine kike fadin na tafi na kyale ki haka ? Nasan wurin wanan yar iskan matar taka fati kaje ka fake ga wai aiki ne zai kai ka can barin fada maka wallahi baka isa kace zaka wullakantani ba ka dawo da Fati a gidan ba. Kallon mamaki yake mata yace idan baki yarda Fati ta dawo ba ai zaki yarda wata ta shigo gidan nan ta zauna ko ya fadi a hasale. Ke baki damuwa da abinda ke gaban ki sai bakin kishi kawai dake cin ki haka har zaki ce wai saboda fati naje kaduna. Idan ma naje gurin ta ai ba laifi bane don fati matanane kowa yasan ina da hakki a kansu yana fadin haka ya juya ya fice daga dakin. Bin shi tayi da kallo mamakin shine ya rufe lokaci guda a lokaci daya ya juye mata haka har yana da corrage din bude baki yana fada mata magana son ranshi. Amma sai ta basar da zance da fadin kila gajiya ne a tare dashi ita kuma ta tare shi da zancen Fati da bai kaunan ayi mashi. Washe gari na idar da sallah ina zaune wayan Binta Abdulrahim kaunan Abdul samad ya shigo ga wayana. Na daga in fadin B,A ya kike tace wallahi khadija Adamu baki da kirki yanzu kizo kd ko neman mutane bakya yi in ba mama da ra fada muna yanzu muna maganan ki ba wai kin zo kin shigo har gida mu baki ne may mu ba Dariya nayi nace Binta Abdulrahim ke nan ni da na shigo gidan ko amsan abu kuma ban dade ba wanan miskilin yayan naku mai jin kai ya shigo na fita. Ashe kwana biyu kika yi kawai nace hudu dai don jiya na dawo Abuja da dare tace baki da kirki naji nace da ita. Zamu shigo Abuja idan matar yayan mu ta haihu zan nemay ki ai idan mun shigo kin san mommy na garin gurin shi ai. Nace Ya Amina ta fada min da nazo kd ai tace kin san yanzu mun dan fara samun kan shi yana dan kula mutane sai dai ba can ba. Nace da san nu zai kula ku ai watarana tace ai shi nace ma hajiyan mu da ta tayar da hankali kin san shegiyar matace buzuwan nan. Don su mommy sun je gidan kawai sai ta kule kitchen wai ba zasuyi mata girki a gida ba ki san muguwa wai da yunwa zata hore su kuma ? Don kawai su bar mata gida tunda bata kaunar ta bude ido taga yan uwan shi sun rabe shi ko kadan nace wanan yayan naku kamar soko yake ai mutum ya zauna haka mace tana juya shi. Khadija kin fa san buzayen nan yadda suke wurin mallake maza ai ke da gani kin san ba banza tabar shi ba idan munzo dai ai zamu sha kallo don nasan sai an kwasa da ita. Nace idan haka ne may zai kawo ku kuma ba sai ku zauna gida abinku ba tunda ba dole bane sai anzo din tace kindan haihuwar ta ke nan na farko a gidan shekara shidda da aure sai yanzu ta samu ciki dashi ana ta cin duniya. Wani abu da ban sani bane na ji ya tsaya min arai nace ku kuka sani ni dai idan kin samu lokaci don Allah ki shiga ki duba min jikin yar uwata don in san halin da take ciki. Tace insha Allahu zan shiga in duba maki ita nace halan ina Z,A take ko ta fita ne tace gata zaune tana jin mu wai fushi take da ke . Dariya nayi nace su zainab manya fushi akan may idan batai hankali ba sai na hada ta da buzuwa matar yayan ku ta latsa min ita da kyau. Tace ai kawar ki ce gaku kuma zaune a gari guda waya sani ma ko kun kulane da ita dariya ne ya kamani sai naji wayan ya mutu nasan kudin ta sun kare ne. Ita Binta bata jin ta kiraka ta dade kuna hira har sai kudin ta sun kare zata kyale mutum sai kuma tunanen buzuwa ya fado min a rai . Tsuki naja ina fadin lalle wanan takai shu,uma nan nake ba maryam labari muka zauna nan muka rage mata zunubin ta wurin cin naman ta. Bayan kwana hudu da dawo wan shi cikin dare ana ruwan sama sosai na kuda ya taso ma Nafisa gadan gadan da kyat ta iya saukowa falo hayaniyar su ne ya tayar da su mommy inda mijin duk ya rude saboda bai taba ganin mace tana labour haka ba sai wanan karon don anty fati haihuwan da tayi duk a gida take haihuwan ta bai nan. Ganin ga haihuwa yazo mata gadan gadan bata ko iya daga kafa yasa mommu tazo da sauri gurin tana fadin ta duka anan shiko duk ya rude sai fafin yake mommy ku kamata mu kaita mota muje asibiti. Tace bata iya tafiya Iyan bawa ne tace don Allah mazan su fice su barsu zasu kamata zuwa waje su Yanyala ko komai sun kasa iya sai yare suke sun rude . Da taimakon Iyan bawa da mommy ta samu ta haifi yarta a gurin kukan yarinyar da ya karade falon ya dawo da hankali wa yanda ke waje suna jiran a fito da ita. Sai da suka gama komai ne suka ce a shigo daga ciki mommy ta kamata zuwa sama dakin ta ta zaunar da ita a ciki tace tayi wanka sai suje asibiti a dubata. Shine ya shigo dakin yana gaida ita da yima mommy sannu da fama iyan bawa kuma tayiwa yar wanka bayan an yake ci bi. Ta fito wanka ya kara dawowa dubata tana zaune ta dubar yar ta da tasha kayan sanyi a jikin ta tana barci don ruwan zafin da iyan bawa ta gasa ta dashi . Da murmushi dauke a fuskan shi yake fadin baki kwanta kin huta ba har anyi sallah fa tace yanzu dai zan kwanta. Yace ki dan kwanta idan mommy ta dan huta gari yayi haske sai muje asibiti a duba ku tace ai ko bamuje da mommy ba ga Yanyala nan sai mu tafi da ita. Mommy dai zamu da ita itada tasan kan komai yanyala mai ta sani yanzu ai kinga ranan dauko su danayi suzo su zauna damu ko ? Tace ko basu zo ba ai haihuwa dai zanyi yau balle ni kadai na sha wahala na ai ba da wani ba yace yanzu zaki fadi haka amma da kike son taimako ai sunan ta kike kira ta taimaka maki. Fuska ta daure da alaman bata son magana ya mike yana fadin yanzu dai sai ki huta kafin gari ya kara wayewa mu tafi ya fice daga dakin. Ranta ne taji ya baci bata so su sa mata hannu ga alamarin ta ba sai gashi haihuwan ma a hannu su mommy tayi shi taja tsuki tana jin haushin yan uwan ta da suka kasa taimaka mata a wanan lokacin. Taja dogon tsuki tana kwanciya tare da tsurawa yar baby ta idanu tana son gano inda tayi kama da uban ta sai dai don kankantan yarinyar bata gane komai ba a gare ta illa yawan kaman da yarinyar keyi da ita na zubin buzaye. Shiko yana shiga ya fara kiran yan uwa da abokan arziki yana fada masu karuwan da ya samu . A ban gare na Binta ce ta fara kirana tana sheda min zancen haihuwan wanda yayi masu daidai don a karshen sati ta haihu don haka zasu samu daman shigowa wurin suna. Bayan mun gama waya da ita ne na shiga tunane a raina maryam na shigowa nake fada mata zancen haihuwan matar A,A din addua tayi ga yarinyar sai cewa tayi saura muje barka ko ? Da sauri nace wa ai ni nan da kika ganin ba abu kadan zai kaini gidan nan ba sai ya kama dole balle idan bai kira ya fada min ba ko barka ba zan mai ba, . Dariya ta dinga yi wai ko ina kishine zai sa ba zan tafi ba nace yanzu idan nace zan tafi gidan shi ke ba zaki min fada ba maryam. In dai ya samu nayi masa a waya ya gode a watse taro lafiya dai indai wanan yar barikin mata nashi ne in ba a watse da tsiya ba da yan uwan shi. Nan nake bata labarin da binta ta bani na hana ma su mommy dafa abinci a gidan da sauri tace abincin da muka sayo masu ke nan fa khadija ? Nace wa ya sanar mata mara mutuncin mata kawai wai kamar mommy zataiwa rashin mutunci irin haka saboda ta samu guri a wurin shi. Dariyan mumuke maryam take yi nace wanan dariyan fa haka kamar wace taga an cuci wani ? Ganin bata da niyar dainawa ne yasa nayi banza da ita har tayi ta gaji ita kadai sai bayan kwana biyu ne Yusuf ya kirani yana fada min wai an masu haihuwa. Nace nako taya ku murna Allah ya raya yasa dadin musulmi ne aka samu yace amin sai dai baki tambaye ni ko wa ya haihu ba koda yake bazaki rasa ji ba a wan gurin. Wa yasan na san ku da zai fada min an maku haihuwa ni yanzu nake ji a wurin ka Allah ya dada sa albarka ga abinda aka samu . Amin yace tare da godiya kamar shi akaiwa haihuwan ya tambaye ni jikin anty na nace da sauki na gode mukayi sallama ya kashe wayan. Wurin gi nayi da wayan gefe na naci gaba da karatun da nakeyi sai dai ban gane komai ba a cikin karatun yi dai nake yi kawai. Maryam ta shigo dawowan ta ke ban daga cikin makaranta gaida ita nayi ina fadi kin dawo ta amsa min da eh tana cire kayan jikin tace yanzu naga abin mamaki a waje zan shigo. May kika gani na tambaya ba tare da na dago na kalle ta ba tace zarah ki na gani yanzu ko kallo na batayi ba ta shige Napep. Zarah fa kika ce yaushe rabon da nasa ta a idona nima yanzu ina ganin ta watsar da zancen karatu ne tana abinda taga zai fishe ta. Maryam tace amma gaskiya tayiwa kanta tana ganin wanan rayuwan da ta zaba shi zai fida rayuwan ta watarana. Ba ace mutum kada yayi yadda yake so ba amma idan zakayi sai kayi yadda ya dace don kada gaba kazo kayi daka sani. Don maza mayaudara ne idan ka hadu da wanda baida tsoron Allah kin ga kamar wanan mutumin ki din yasan ciwon kan sa sosai haka nima MS yasan mutunci na amma kawai don kazo karatu sai ka biye wa maza suna bata ma lokaci bayan su sun gama gina tasu rayuwan a baya. Idan da basu tsaya sunyi karatun ba yaushe ne zasu zama haka har su samu kudin da take kwadiyi a wurin su. Wanan tunanen nake yi kika ga ina son rage hurda da kowa yanzu tace khadija Allah ya raba mu da wanan halin ita fa mace batayi sai da namiji haka namiji bai yi sai da mace. Abinda yasa nace maki haka don rayuwa ne na taimakawa juna a tsakanin mu dasu to amma idan zakayi kada kayi haramtaciya wanda Allah ya hanna yanzu rayuwan ne yazo da haka. Sai dai mutum kada ya shagala da ruden duniya ya biyewa shedanun maza sukai shi su baro tun farko a yadda na sanki da mutymin ki dan iska ne na tabbatar tafiyan ku ba zai yi nisa haka ba. Mu godewa Allah da ya dube mu ya hada mu da natsatsun mutane sai kuma muyi adduan Allah ya kara kauda shedan a tsakanin mu ko wani lokaci. Nikan har ta bar maganan amma abin ya tsaya min a rai sosai sai nake ganin may ma zai hana in watsar da kowa yanzu har sai na gama karatuna in fara dating. Yau tunda ya fita office ya rasa gane kan shi sai ta fara aiki yaji bai iya karasawa ya aje, a haka Yusuf ya shigo ya samay shi zaune ya tas files a gaba sai kallo yake yi. Kallon shi yake tun daga kofa har ya karaso tun bai kai zaune ba yake fadin lafiya dai ko naga yanayin ka ya canza a lokaci daya. Dan gyara zama yayi yana kama goshin shi yace wallahi haka kawai naji jikina ya mutu yaki fada mai gaskiyan maganan yadda yake jin gaban shi na yawan faduwa haka kawai. Kallon shi Yusuf yayi yace muje in sauke ka gida ka dan huta kila yawan jigila da baki ne ya jawo maka haka tunda baka saba ba. Shi ya sauke shi gidan shi don haka ba a san dawowan shi gidan ba babu kowa a falon sai tv dake aiki don haka ya wuce kai tsaye sama inda dakunan barcin su yake. Tun yana hawa yake jin hayaniya na tashi a saman sai ya dauka yan barka ne har saman suka hau a step din karshe ya fahinci dariyan wani abu suke sai yaji yana son zuwa ya duba baby shi kafin ya kwanta. Haba Nafisa kina bani mamaki namiji kamar mijin ki zai gagare ki kin kasa juya shi yadda kike so a hannnun ki. Itako Nafisa sai tace ba na kasa juya shi bane dama vikin nan dake jikina ne ya hanani aiwatar da sauran aiki na amma yanzu tunda na haihu lafiya may za a fasa sai in dora a inda na tsaya kawai. Sai na kama shi na mayar dashi marayan dole sai abinda nace kamar mahaifiyar shi zan koma duk wa yan nan dagin kala dake ganin dun samu kan shi har zasu zo gidan shi suyi yadda ran su ke so ba za su ga kafan sake gigin zuwa ba kuma. Don kafin su wuce sai na samu sherin da na kula masu gidan nan sun tafi ta baibai ai ni kowa yaci tuwo dani ya san miya kawai yasha. Da baya baya ya koma dakin shi ya koma ya bude a hankali ya shiga ya kwanta bai taba yarda Nafisa zata iya fadin magana ba haka duk da yasan halin ta amma bai dauka takai haka ba. Sai zuwa can ta raka madam ko may ta shigo dauka dakin taji shi a bude ta sa kai ta shiga kwance ta hango shi rigingine ya na tunane. Da sauri ta karasa wurin shi tana fadin lafiya kadawo a wanan lokaci yace ban jin dadin jikina ne na dawo in huta. Tace tun dazu ka dawo ke nan yace shigowa na ke nan kika shigo sai ta sauke ajiyan zuciya yana lura da ita. Zata zauna yace ki barni in huta please ko zan samu barci jikin nawa ya sake haka yasa ta mike ta fita daga dakin yabita da kallon mamaki yana fadin Allah ya kara kare shi daga kaidin ta. Ranan yayi tunane iri iri a ranshi barcin da yake son yi gaba daya ji yayi ya fice mashi a idon shi. Shiryawa yayi ya fice daga gidan ya rasa inda zai nufa yaji sanyi sai tunane na yazo mashi a da in yana cikin wanan yanayin guri na yake zuwa muka shi rikici dashi har yaji ya manta da komai a ranshi. Sai da yakusa kaiwa ne tunane yazo mai a rai yaushe rabon da yazo guri na ya dubani yanzu zai iya kai wata hudu fa tun cikin wancan hutu kafin muje gida. Gaskiya dole ya hakkura da zuwa sai kuma wata zuciya yace mai ya tafi kawai yasan abinda zai fada min uzurin rashin zuwan shi din. Waya ya dauka bayan ya iso ya kira ni ina ganin wayan shi gaba na sai da ya fadi nayi saurin kashe wa ya sake kira ba kashe don yasan naga kiran nashi kai ya girgiza ya kara danna kiran na sake kashewa. Tsaki yaja ya kira Yusuf yace kace ma wanan yarinyar ta dauki wayana na kirata ta kashe min waya Yusuf yace wata yarinya ke nan. Kai tsaye yace khadija a takaice Yusuf yace ko tana class ne yanzu bata don yanzu sun rufe ya kashe wayan nashi. Yusuf din ne ya kirani shima ban dauka ba har kiran ya katse ban daga ba karshe ma da naga zasu damay ni sai na kashe wayan gaba daya. Kiran shi tayi ya fada mai abinda ke faruwa yace bata dauki wayan nawa ba sai dai barin kira kawar ta maryam in ji. Maryam din ya kira yana tambayan ta ni ko ina ciki ne tace mai eh ina nan bari ta duba dakina ta gani sai zuwa can sai gata tace na duba bata dakin ashe tayi mai karya. Yace mata ya gode ya tayar da motar shi ya wuce badon ya yarda ba do yadda yaga maryam din ta da farko ranta a bace ta dai kare ni ne kawai kada ya dauki wani abu. Bakin cikin da yake ciki yaji ya karu mashi kai tsaye gidan Yusuf ya nufa yana aje mota ya fada ciki yana huci tare da fadin ni za a kawo wa iskan ci don ta samu na zubar da ajina ina kulata take daukan kanta wata mace can. Kaida waye kuma Yusuf dake zaune yana kallon shi yake fadin haka cikin kafa mashi idanun shi yana so ji ko shidawa ke fada. Sai cewa yayi duk haka suke dama irin daya mata basu da banbanci wurin karamin kwakwalwa wallahi ko wace taga kana kokari sata a inuwa sai tayi kokari kai ka rana kai. Wai may ke faruwa ne haka duk ka hargitsa kan ka haka yace Nida wanan yarinyar ne mana khadija don kawai yau na tuna da ita naje gurin ta shine har zata nemi ta wullakanra ni. Kai mutumi na cool down don Allah ka fa san khadija yarinya ce mai kaifin basira da aiki da hankalin ta kamar ba karamar yarinya ba. Ke nan ka goyi bayan wulakantani da nakai kaina tayi min ke nan ko may ? Dole in goyi bayan ta don itama mutun ce kamar kowa don may zata yarda ka bata mata lokacin ta a banza bayan ta gama fahintar ka ba don Allah kake tare da ita ba. Ba don Allah ba fa kace Yusuf Kwarai kuwa don hakane tunane ta a yanzu tsakani da Allah yau rabon ka da zuwa wurin yarinyar nan zaka iya tunawa ? Waye khadija da zan ta binta koda da yaushe don banda aikin yi ko may ko yaushe zan kama hanya gurin wata can daba matana ba ko wata nawa ? Yusuf yace ba wanan ba yanzu in tambaye ka may kaje yi gurin ta har tayi ma haka ? Wani kallo yayu mashi yace May naje yi kacs da ban kan lekata ne idan na tashi ko yanzu abinda ke kaini gurin ta ne ya kai ni ba wani abu . Kai mutumina kafito fili muyi magana kan yarinyar nan ni dai ba bako ka bane ko na khadija ka sani watau kaje ka ganta ka sata wani abin sai aka samu akasin hakan kake ganin laifinta don taki. Yace ko gani ta nayi ta ki daukan wayan mu na tura akira ta kuma wai ni zatace ace wa bata nan may ta dauki kanta ? Yace ita ce daidai da kai wallahi wace daga kai har Nafisa zakuyiwa ta tsaya ta kwatar wa kanta yan ci a gurin ku ba Fati bane ya dace tayi kishi da nafisa sai khadija ta dace da wanan. Kai duk mata a yau din nan daya na dauke su a guri na don may zanje gurin ta na debo baci rai a gida nazo gurin ta don inji sauki sai ita ta zuba min nata dafin. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Tun wanan ranan ban sake ji daga gare shi ba ban kuma koma ta kan su ba ina karatuna hankali kwance don komai ina dashi a tare da ni. Ashe suna da kwana biyu bayan tafiyan bakin shi tafiya ya kama shi nan Nafisa ta tubure akan may zaiyi tafiya yanzu bayan yan buki basu gama tafiya ba. Idan na zauna may zan maki a gidan ina kudi kika sani na kashe maki wanda ni kai na ban san iyakar shi ba. Yan uwana sun tafi da takaicin abinda kikai masu a gidan nan bayan sun san da komai nayawa kike kadagi a gidan nan amma kika rufe ido kika hana masu komai da na kawo gidan . Haka suka tafi da bacin rai a tare dasu don ma mommy mace ce mai tunane da sanin ya kamata ta sa na samo masu abinda zasu koma gida dashi. Don baki da kunya yanzu zakice ba zan tafi neman kudi ba idan ban fita ina samo kudin nan a zaune kudin da kike kashewa zasu samay mu ko may ? Tunda ya fara magana bata katse shi ba sai da yakai karshen maganan shi tace ina da sunana kasai abin bukin ? Baka ce da wasu yan uwa naka zamu raba shi ba idan bakayi ba wa kake son yayi min da ? Tafiya kuma kana nufin ni kadai zaka bari da wahalan dubar yar ka ko may tare muka samay ta don haka tare dakai zamu rene ta babu inda zaka a yanzu kaji na fada maka. Yace tunda ke kika ajeni sai ki hanani zuwa mugani idan zaman ki nake yi ba ke ke zama na ba a gidan nan Nafisa kin dauki kanki ki kai inda Allah bai kaiki ba fa. A da ana fadin ina ganin don ba a kaunar ki cikin mu ne yasa ake maki haka ashe halin ki ne hakan ban sani ba ina jiye maki ranan da reshen ki zai juye maki a gidan nan idan har baki nemi shiri da yan uwana ba. Tace wanan tunane kake a ranka dama akwai wani rana da zaizo min ba daidai ba gidan nan har in neme shiri da yan uwan ka to kasani babu wanan ranan a rayuwana da zan shirya da yan uwanka. Tunda tun farko sun iya nuna min rashin kaunar su gare ni yanzu may zai sa in dawo ina shiri da mutanen da basu so na ko kadan. Yace aike baki da kunyan fadin magana wani irin sone basu nuna maki ba da kika zo gidan nan musanman ma mommy amma kikai fatali da kowa don ke kan ki kawai kika sani . Ya ture ta gefe ya fita rai bace zuwa inda ake neman su dan bayanin tafiyan su ta tsaya tana kallon shi cikin mamaki. Don dai malamin ta yace da ita yanzu AA a tafin hannun ta yake saboda sun gama daure mata shi yadda take so kuma ba karamin kudi ta tura wurin yin wanan aikin ba. Shiko bayan ya fita daga gidan rai bace bai tsaya ko ina ba sai inda club din millonear in the world yake ya cika komai da zai cika na tafiyan shi kasan. Take a nan wurin suka maida mashi da amsa sakon shi ya karbu sai kudin da zaiyi tafiya da na komai suka turo mai yana barin haraban wurin ya wuce wurin Yusuf kai tsaye. Ya samu Yusuf wajen gidan yana shan iska taee da waya a hannun shi yana yi wuri ya samu ya zauna daga gefen shi ya tsiyaya lemon da yagani wajen yana sha. Yayi mamaki daya fahinci Yusuf da mace yake wayan yana kashe murya tare da zuba soyayya baki ya tabe ya kawar da kan shi gefe yana jiran ya gama wayan. Ya gama yana kallon shi fuskan shi dauke da murmushi yace ya dai ina ka fito yanzu haka sai da ya dauki cup din juice din ya kara korawa yake fada mai inda ya fito. Yace amma kasan may wai ni yar rainin wayon nan zata raina ma hankali wai bata yarda inyi tafiya yanzu ba. Nafisa ke nan Yusuf ya fada yace ai kaima ka sani wazaiyi wanan haukan idan ba ita ba yusuf yace wai may matar nan ta dauki kanta ne halan ? Komay ta dauka zan bata mamaki ai kwanannan kuwa don sai ta rena kanta wallahi yusuf yayi saurin fadin baka iyawa ne ai shiya sa take kawo maka raini haka. Haka kake gani ko kamar yadda kowa yake dauka na ban iya aiwatar da komai akan nafisa yanzu kaima hakan ka dauko ke nan ? Yusuf yace ai haka din ne yanzu fa don haihuwa kai mata wanan irin sayayan haka bayan wanda ka din ka mata wanda zata fita dashi ga kuma sayayya kamar na hauka da ka da mata daga baya. Wanan ba komai bane Yusuf har in zatai amfani dashi ni mutum ne mai son in ga iyalina suna shiga suna fita a gida don haka ban jin kyashin kashe ma iyalina na kudi ko nawa ne. Kasan wanan halin ne ya hadani da Fati bata sawa bata kuma gyarawa amma mutane basu ganewa ida matsalan mu yake da ita. Mutum ko yaushe baka gane dadin ran shi kullun ya zauna kamar an mashi wani abu babu marmari ko kadan. Ita nafisa tana maka yadda kake so ne halan da ita da fatin duk jirgi daya ya kwasosu a gidan banbanci dai kace ita nafisa tana sakewa da kai kawai ne. Yanzu badon yarinyar nan khadija da ta muka saya ma yara da ita fatin kaya ba a kwanaki ina ban dashi tunda suka tafi har yau bakai tunanen ka kara saya masu komai ba. Yarinya ta dauko saka ka a hanya tanayi hanyar alheri wanan bakar shu,umar ta shiga ta fita yanzu ta raba ka da ita nasan wurin shige shigenta can aka bata labarin khadija din ta sani. Khadija khadiji Yusuf ka fasan tafiyan mu ba zai zo daidai da wanan yarinyar da take daukan kanta wani tsiya ba. Yasuf yace yanzu ka gama fadi da bakin ka mace yar kwalisa da iya gyaran gida da jiki kake so a gidan ka. Daga cikin wanan wani khadija ta rasa a tare da ita ka fada min ya ja iska yace baka san wani abu ba wallahi ranan naje dauko su Binta da dare wurin ta. Kasan yarinyar nan sai da taso ta rikitani gaba daya Yusuf ya tambaya yace akan may kuma yace wallahi wani shegen shiga tayi tafito waje dashi sai da na kasa kallon ta. Ban san lokacin da nayi mata fadan haka na ba don wanan shigan sai ya rikita mutum a banza wallahi. Dariya sosai Yusuf yayi mashi har sai da yaji haushin shi yace malam na fada ma son yarinyar nan kake yi wallahi ka tsaya kana wani noke noke. Bari garin kallon ruwa wani ya rigaka jefa fatsan shi kana kallo dama ya samu ka fida zuciyar ka ka tsaya kana wani izza haka. Shiru yayi mai yace bazan bata lokaci na ba kan wanan da yanzu ma take zama mace bata gama mallakan hankalin ta ba. Zaka sha mamaki wallahi khadijan ne macen da bata san wani abu ba idan bata san komai ba yanzu akan may take fushi damu. Badon share tan da mukayi bane kwana biyu ta dauki wanan zafin haka kana tunanen ita ma bata fada tarkkn son ka bane ko may ? Kallon Yusuf din yake yi yace abinda take ma fushi ke nan dama yace don may baza tayi fushi ba kuwa ? Kwana biyu da yin maganan su ya shirya ya tafi club din su inda zai buga game a can . Banda labarin yayi tafiya sai dai ina murna a raina sun gaji sun barni ke nan tunda ban kara jin labarin su ba kuma. Sai dai tunanen su yana nan a zuciya na inda nayi wani sabon saurayi dan kabilar nufe koshi haduwan mu dashi a wani shago ne yana waya da yaren su na Nufe sai ya yar da dan wallet din shi kasa. Da yaren Nufanci da nake ji don zaman gari daya da nufawa da nakeyi nace dashi da yare kayar da wallet din ka fa. Ya juyo ya dauka yana min godiya a cikin yare yana fadin (Nufe wayyo ni )nace dashi a a ke yar ina ce ya tambaya a cikin yare nace ni yar Niger ce yace (kiyyo sunayo) nace dashi khadija. Sai yace Iam mamud by name yana aiki ne a CBN dake nan cikin garin Abuja shi mutumin garin Bidda ne dan murmushi nayi don kamar naga na gida ne da na ganshi. Nomber na ya tambaya na nuna bazan bashi ba ya matsa min sai na bashi da na sai turaren da nazo saye sai gashi mun hade wurin biya ya biya min nafito zan wuce sai gashi yace in zo ya sauke ni. Banyarda na bishi ba ashe ya biyo ni baya muna sauka shima ya tsaya yana dariya ya fito daga motar shi nan muka tsaya dashi yake fadi ashe karatu ya kawo ki, nan ke nan. Murmushi nayi nace may yasa ka biyo ni har nan kuma yace don in san zahirin ki tunda kin ki yarda in dauko ki ni kuma ba zan yarda ki bace min ba ina ganin nayi babban kamun yar garin mu haka. Tun daga wanan ranan muka hade dashi saboda nacin shi dole nasaba dashi don mutum ne mai saurin sabo da mutane ga baa da iya magana kamar shiyayi kan shi. Tun ranan da suka fara haduwa da maryam tace yanzu kan kin samu daidai dake khadija haduwa da mamud yasa na manta zacen wani AA can a rai na. Shiko yana can yayi nasaran tafiya don shi yazo na daya ga gasan da sukayi na wanan lokacin ya samo makuden daloli a wanan tafiyan. Tsaraba yayo wa iyalin daga ciki Allah ya ciyar dani ya sako min a wani jakka na daban tun daga can ya ware min nawa. Yusuf yazo gurina inda ya samu mamud yazo sai da ya jira ya wuce yana zaune cikin motar yana kallon yadda nake kwasan dariya daga inda nake tsaye. Yana mamaki a ranshi yaushe har na hadu da mamud har mukai nisa haka dashi muna irin wanan hira don yaga na sake jiki sosai da mamud din. Mamud ya wuce sai lokacin ya kirani yana fadin gashi nan tsaye bakin hostel din mu yana jirana waige na fara yi sai dai ban ganshi ya fara fada min irin kayan dake jikina da yadda nake tsaye ina waige waige. Har na gano shi na iso gare shi abinda ya fara tambaya na shine waye wancan danaga ya tafi yanzu khadija ? Mamaki nayi da tambayan shi nace wani abu ne halan sai yace a yanda naga kuna hira dashi yasa na sha jinin jikina khadija kada fa yayiwa abokina yankan baya. Kai na rausaya nace wani abikin ka kuma ke nan yayana yace haba khadija tun yanzu har kina nufin kin manta damu ne. Nace haba dai abokin ka ai ba saurayina bane kuma bai taba cewa yana so na ba asalima shiba irin mazan da nake so bane. What har akwai irin mazan da mace ke so ashe sai yau naji wanan a bakin ki nace kowa da abinda ke masa kasani . Yace kina Nufin bai maki ba shikenan ko ko sai wanan dan kyamazon ne yayi maki da sauri nace kada muyi haka dakai yayana. Yace Allah ganin shi nayi kamar dan tsurut a motar bai wani cika motar tashi ba sosai nace akwai dai kishi ga maganan ka ke nan , ? Dole muyi kishin ki khadija don kin cancanci hakan a gare mu saboda ke mace wance ko wani namiji yake fatan ya mallaka a gidan shi. Nayi dariya tare da fadin kazo da wata magana ta daban ke nan idan kai nayi ma ai shi abokin naka ban mashi ba. Ko ya taba cewa dakai son na yake da gaskiya kaga yayana mu bar wanan zancen muyi wanda ya kawo ka yanzu yace maganan tana cikin abinda ya kawo ni ai. Bashi ya kawo ka ba kadai zo ne don duba kanwar ka na sani kuma gani ka ganni ai na kuma gode kwarai da gaske. Khadija ya kira sunana wanda ya nuna maganan da zaiyi tana da muhinmaci sosai a lokacin gare ni amsawa nayi da naam yaya na. Yace don Allah ki natsu kiyi abinda ya kawo ki garin nan ki bar biyewa irin mutanen nan da suke zuwa da karya. Nace yayana ban yarda na tsaya da mamud ba sai da nasan ko shi waye da sauri yace dani shi waye din kika sani. Dariya nayi nace yanzu dai mu bar maganan don Allah don naga bazaka fahince ni ba a yanzu gaba mayi idan mun hadu. Yace to shike nan tunda kin hada ni da Allah yanzu ina maryam ina son ganin ta nace ayyah maryam yau taje gida da yamman nan gurin yayanta. Kasan ita anan garin take da zama yayan nata ne tayi tafiya ta dawo shine taje mata sannu da zuwa yace ashe idan Abdulsamad ya dawo zaku zo tarun shi ke nan ? Da sauri nace da zai tafi ya sallamay ni ne da zanje tarun shi yace kece baki bashi dama ba don kina fushi dashi yasa bai sallamay ki ba. Wanan maganan kane kana kokarin gyara shi a wuri na ne kawai wanda ba zai taba gyaruwa ba kuwa. Murmushi yayi yace zan gano ko waye wanan dake shirin hure maki kunne haka har kike son yin wa kanki zaben tumun dare. Haka dai mukai ta zubawa dashi har ya kaimu wani lokaci a wurin karshe dai yayi min sallama ya tafi. Maryam ta dawo daga gida tana fushi dani wai naki zuwa gidan su in gaida yayanta da dawowa nace ba haka na bane maryam kina dai gani ba fita nakeyi ba amma kullun Daddy fadan da yake min ke nan in natsu. Kada ki damu watarana zan tafi mu gaisa da ita har ma in kwana ba shike nan ba haka yasa ta sake jiki dani tana bani labarin yayan nata da abinda ta dawo dashi wanan tafiyan. Ta ciro wani dogon riga tabani tace yayan nata ne ta sayo muna ni da ita don yawan labarina da take bata ko yaushe. Nayi godiya tare da karban lanbata nace zan kirata inyi mata godiya tace mutumin ki baizo bane yau nace yayi tafiya ai da yanzu kin gashi nan.. Yusuf dai yazo bakya nan ya gan mu tare da mamud yake wani maganan robish a kan sa tace saboda Allah nace wallahi ko. Ai dama na fada maki ina jiye maki ranan da zasu san mamud ya shigo rayuwan ki gashi wanan mamud din da alama baizo ba kamar sai da ya shirya maki . Nace kin jjiki da wani magana kuma ba wani shirin da yai min sone kawai wallahi ni kuma ya kwanta min sosai a raina. Tunda bada wasa yazo min ba ke ma kin sani idan yau zan ba mamud baki ya fito a shirye yake da yafito din. Allah ya zaba muna abinda yafi zama Alheri a gare nace amin yama zaba min din Allah sa albarka ya rage kice. Kwana hudu da maganar mu na dawo daga class don yanzu karatun mu ya dau zafi sosai muyi nisa mun zama manya a cikin makarantan. Kwance nake ina hutawa ban cire kaysn da na dawo dasu ba wata ta shigo tana fadin wai ina da baki a wajen hostel nayi mamakin ko suwaye ? Sai lokacin na tuna wayana a kashe yake tunda zan shiga class na kashe wayan mikewa nayi daga kwancen ina gyara bujen jikina dakyau. Dinkin wasu material ne na india da mijin ya Amina ya sawo muna tsaraba nasa takalmana flats shoes na saka don ban faye sa takalma mai hill ba. Wani dan yalalon gyale na yafa akaina duk rabin jikina yana bude na fito don ganin wanda ke nema a wajen. Motar AA na hango can nesa kadan sun faka shi da Yusuf sai naji gaba na ya fadi ras don ban san may ya kawo su ba nasan kuma Yusuf ya fada mai zancen mamud yanzu haka ? In bashi ba may zai sa su zo gurin mutumin da bani a gabasa zai zo wurina yau kuma ? Haka na daure fuska na karasa inda motar tasu take aje cikin daure fuskana na isa inda suke sallama nayi masu irin na addinin musulunci. Tare da fadin sannun ku da zuwa Yusuf ne ya amsa min sallaman nawa don shi sai wani kallo yayi min ya kawar da kan shi gefe daya. Nima yi nayi kamar ban ganshi ba a wurin khadija ya kuke ya karatu nace Alhamdullahi kune tafe yanzu ashe yanzu ko na shigo hostel din ina cikin makaranta tunda safe. Aike ko alhudahuda ya kauce maki ga karatu yanzu kin zama ina zaki karatu, ina kika fito karatu . Dariya mukayi dukan mu dashi nace sunan da na samu ke nan kuma yanzu yace sunan ki ke nan ai bakiga mutumin ki ya dawo bane banji kin tare shi ba. Nace ai bansan yayi tafiya balle in gaida shi da dawowa yace a a fa kada muyi haka dake nace to an dawo lafiya ya hanya ya mutanen can ? Saida ya sauke wani irin sayayan ajiyan zuciya yace Lafiya kalau suna gaidaku ya karatu fa nace Alhamdullahi lafiya. Allah bada sa a nace amin yace ya naga kin ramay haka may ke damuwan ki kuma ko duk karatun ne haka ? Nace kila dai idon kane ke ma gizo amma ni ban ji na ramay ba Yusuf yace yaganine ya fada halan dan banufen ki bai fada maki kin ramay ba. Daidai lokacin Mamud din daya fito office ya biyo ta gurina ya faka motar shi gurin idon ni da Yusuf muka bi motar dashi. Bai fito ba nima banje gurin shi ba don wullakanci baida kyau Yusuf yace wanan mutumin ya zama maye ana maganan shi sai gashi. Rai bace ya juya yana kallon shi yace waye wanan din kuma ? Cikin dakiya na bashi amsa da fadin wanda zan aura ne in sha Allahu nan bada dadewa ba cikin wani yanayi yace What da mamaki nace barin kirashi ya gaida yayye na ai. Ban tsaya jiran abinda zasu fada ba na wuce wurin mamud nace mashi ga yayyena sun zo yazo ya gaida su da saurin shi ya fito daga motar yazo gurin su su gaisa. Sun dawo daga tafiya ne suka zo su duba ni ya mika masu hannu da kyat AA, ya bashi hannu suka gaisa dashi yana masu yaya hanya . Yace khadija zan tafi sai eight zan dawo tunda kina da baki yanzu ya juya tafi ya barmu nan dasu. Shiru gurin yayi na dan lokaci yusuf ne ya kawar da shirun da fadin khadija wai kina nufin da gaske wanan mutumin zaki aura ko may ? Kana mamaki ne da ba auren shi zan yi ba zan gabatar maku dashi ne a matsayin ku na yayyena a gaban ku. Yusuf don Allah ciro mata tsarabanta ka bata mu tafi kar mu bata lokacin mu anan nace ai da kun barshi ai ko ganin ka dawo lafiya yafi tsaraban da zaku kawo min . Don Allah ciro mata mu tafi don banda lokacin magana yanzu ban son damuwa akwai gajiya a tare dani ka sani. Fita Yusuf yayi ya bude bayan motar ya fito da wani jakka mai daukan ido yana miko min tare da fadin ga tsaraban ki nan aboki na ya kawo maki daga Italy. Nayi mamakin ganin wanan katon jakkan yadda ya dauko shi ba tare da matar shi ta gani ba godiya nayi bayan ya aje min jakka a gaba na. Ya koma mota ya tayar suka tafi na ja jakkan zuwa ciki ina mamaki a raina guri na samu na aje can kuryan dakina ina jiran shigowan maryam dakin. Sai da ta dawo tana shigowa da jakkan tayi arba tana fadin wanan kuma fa khadija ? Nace bari ke dai maryam wai tsaraba ne duk wanan kike gani su Yusuf ne suka zo min dashi A A ya dawo daga italy tace bakaji batun ba maye a ciki. Ban bude ba ina jiran ki dawo mu bude ne da sauri ta karasa wurin tare da jawo jakkan ta fara budewa tana ciro kayan dake ciki. Dogayen riguna ne a ciki har kala bakwai sai turare da su man shafi da jakka handa bag da sauran tarkacen mata a ciki . Zip din jakkan taja sai ga set din sarka da yan kune da awarwaro suma a ciki da sauri ta karasa fidowa waje. Sai da na gyara zama na alokaci don mamaki sai ta kara fida wani agogon hannu na mata mai ruwan gold mai daukan ido shima. Nauyi da kunyan kaina naji maryam ta dago kai tana kallona da mamaki fal a fuskan ta tace khadija kin ga wanan kayan kuwa ? Nagani maryam nace mata tare da lumshe idanuwana ni kadai nasan abinda nake ji a lokacin. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Tunda muka muka bar asibitin shiru nayi ban iya magana ba sai su ke dan hira jefi jefi a motan ajiyan zuciya na sauke ina fadin yanzu baku ganin kamar yawan ciwon kan nan wani abune ? Da sauri Yusuf ya juyo yana fadin wani abu kamar yaya sai nayi shiru kuma yace tambayan ki nake yi mana kin yi shiru kuma. Nace akwai ciyon kai irin wanan da yake na shihiri ne in kunyi diba ga irin matar nan nashi zai yuyu wani aike tayi mai wanda bai zauna a jikin shi ba sai ya iya haifar mai da hakan. Idan ba kasan da irin shi ba ba kowa ne yake gane hakan ba zaka mutum na fama da ciwon kai mai tsanani ayi ta magani kamar ba a yi. Nima gani nayi a makwabtar mu haka ya faru koma dai ba shi bane ya kamata ku hada da na gargajiya tunda likitoci sun ce basu ga komai ba su . Shiru yayi na wani lokaci ba tare da yayi magana ba abubuwa da dama yake tunane a ranshi sai can yace maganan ki na da kamar gaskiya khadija. Don dai a yadda yake rike kai yana kugi zakace zai iya mutuwa ne a lokacin kuma kan sai cikin dare kawai yake damun shi . Nace abinda ya ban mamaki ke nan nima ace ciwon kai kamar na sihiri sai dare kawai yake tashi cikin ne ma wani lokaci yake dan tashi da safe ko idan ya ci wani abu. Allah ya sauwaka nace maryam dashi suka amsa da amin lokaci daya maryam tace gashi har ya ci ayaba ya zauna mashi ciki lafiya abin ya ban mamaki ai. Nidai har muka shiga hostel ban yi magana ba sai dai ido da sauraren su da nake yi kawai. Kwance nake tun bayan dawowan mu da nayi sallah magariba da ishai na kwanta nan iya cin komai ba na kwanta zuciya na cike da damuwa. Washe gari tunda safe da na tashi ina shiri jikina ba karfi a tare dani sai tunane nake na yadda na ganshi kwance jiya yana jin jiki sosai wai a haka yaji sauki ke nan. Waya na nadauko ba tare da na tsaya tunane ko yana barci a wanan lokacin ba na dana mai kira wayan ya shiga yana ta ringing ba a daga ba. Sai kusan zai katse aka daga wayan muryan shi da alaman barci a tare dashi yace hello Deedar ya kike nace ina kwana ya amsa da lafiya nace ya jikin yace jiki da sauki nagode. Sai nayi shiru yace hello dayaji shirun yai yawa nace kaji sauki sosai ko yace mm a ji sauki Deedar ya kuka koma jiya nace lafiya a sanyaye. Can nace nagode Allah saka da alheri yace namay fa nace na tsaraban da ka kawo min ranan nagode kwarai Allah saka da alheri tsaraba haka da yawa. Yace ba komai nagode sai an jima na kashe wayan ajiyan zuciya na sauke ina aje wayan cikin hand bag dina tare da lumshe idona. Haka na shiga makaranta jiki ba karfi duk yinin ranan haka nayi shi a sukurkuce dani yau ma kamar jiya na dawo ban dade ba a cikin makaranta na dawo. Yusuf tunda ya aje mu hankalin shi ya koma kan maganan mu kawu salisu ya kira yana fada mai matsalan Abdulsamad din. Kawu yace zai je a ga malam yayi mashi bayani komai kai tsaye asibiti ya nufo inda ya samu Nafisa na fada da security a bakin get. Nan ya tsaya rai bace yake masu magana abin mamaki sai ta maida fadan wurin shi tana fadin sune ai munafukan da suka ja a wullakanta ta din sun dauko karuwa sun kawo ma samad har cikin asibiti tazo tana iskanci. Da mamaki yace karuwa may ya hada AA da karuwa kuma tace in ba karuwa bane may zai sa tazo tana bashi ayaba a baki ? Kai ya girgiza yana mamakin inda maganan ya fito mata yayiwa security din magana akan su kyalesu su wuce basai sun tura ta ba. Ciki ya shiga fuskan su kawai da ya kalla yasan akwai damuwa a tare dasu yace mommy ya akayi har Nafisa tazo nan da fitina haka ? Yusuf Nafisa tana fada ne bisa ka,ida zuwa tayi nan tana hauka nasan kawayen ta ne da suka zo dazun suka fada mata don dun samu yana cin ayaban da suka shigo. Ya girgiza kai yana murmushi yace mun dai auna arziki bata samu su khadija a nan ba da ba karamin tashin hankali zasu yi ba don ko ita khadija ba baya ba da alama wurin fitina. Khadija ce kaidai zata yi daidai da gidan Abdulsamad a halin yanzu mommy don itace kadai nake ganin zata iya da Nafisa a yanzu. Shi babangidan yace yana son ta ne ko ya nuna wani alama na ra,ayin tane da dai zanyi hakan gaskiya da yayi dace da kamilan mace a gidan shi don ni yarinyar tanayi min wallahi. Don akwaita da natsuwa da girmama na gaban ta ga ilimi addini da na boko ta samu a tare da ita kaga kowa ma zaiyi kwadayin wanan mace a gidan shi ai. Tun farko ina ma yaran gidan mu kwadayin ta sai dai kasan yaron yanzu ba ai masa haka gara inshi yagani da kanshi yace yana yi shine za a zauna lafiya. Duk da nasan khadija tana da masoya ko anan kaduna din amma haka bai hanani jin wani nawa ya so ta ba. Amma kai da kake fadin haka akwai wani abu makamancin so ne a tsaka su dama kodai dacewan haka kaima ka hango yasa kai magana ? Mommy gaskiya ba zan boye maki ba akwai sai dai dan nakine miskilanci da ji da kai da izza yahana shi tsaya su fuskanji juna shi da ita kin san kuma ba a son mutum da haka. Shi yana ganin idan yaje mata da zancen so kamar ya zubar da kiman shi a gare ta ita kuma khadijan kallon yan uwa take muna a yadda na fahinta ni. Sai dai dukkan su suna boye feeling din su ga juna ne amma indan so akwai so gaskiya miskilanci shi dai ne ya hana ya nuna mata haka din. Murmushi mommy tayi tana fadin dana ai ba a haka yanzu matan yanzu sai da so ake saye zuciyar su bawai da kudi ba kawai don ba ko wace mace bace kudi yake gaban ta ba. Mommy dan nan naki in kiyi duba gare shi bai fa san so ba shi don a yadda ya auri Fati da Nafisa ba wai an tsaya anyi wani soyayya bane dasu. Auren fati dai kin san komai akai hadine na iyayye tun farko ita kuma Nafisa abu biyu ne nake ganin ya kai su ga aure. Na farko kin san akwai shi da son fararen mata dogaye sai na biyu ita din batazo mashi abanza ba sai da ta asirce shi. Wani kallo yayi ma Yusuf din dake magana yana kwane ya harde hannayen shi sama kirjin shi kafafuwan shi a harde yana karkada su a hankali. Ni kake wa sheri haka Yusuf kuma a gabana Yusuf yace ba sheri bane abinda nagani nake fadi ni baka son khadija ne karya ne maka ? Ke nan ashe sun dade tare da ita mommy ta tambayi Yusuf din cikin son karin bayani gare shi. Don ni na dauka zuwan nan na su Binta ne kuka hadu da khadija din har kuka santa yace a,a mommy ba zuwan su bane muka santa don gaskiya dama muna tare da ita. Ikon Allah a mu kuka boyewa mawa dama amma yaran nan kun iya taku har karshe yanzu ashe kuna tare da yarinyar nan kuna nuna ba komai a tsakanin ku da farko ? Hakan na da kyau da kuka boye ba laifi bane haka yayi daidai nima zan kama baki na inja ga wanan maganan badon komai zamuyi haka ba sai don matan shi. Duba yadda Nafisa tazo nan tayi muna yanzu bata san da komai ba ke nan ina ga inta sani din sai idan abu ya kankama a tsakanin su lokacin da wani bai iya komai za a fitar da zancen ga kowa yaji. Don idan ba haka ba maganar sai yazo yabi ruwa azo ba ayi shi ba sai dai babangida ya kamata ka daina wanan halin naka don ba haka ake neman ba yanzu. Kamata yayi ka bata lokacin ka ka nuna mata so da kauna ta yadda zata saki jiki dakai har a cin ma abinda ake so. Mommy sheri Yusuf ne kawai yarinyar nan a yan uwa ta dauke mu har ta gabatar muna da wanda take so ta aura fa. Tayaya zaice kuma ni na kutsa kaina ga abinda ta riga tayi nisa ga wani gare shi da sauri Yusuf yace. Wanan magana ba gaskiya bane dakai da mamud din da tace wa yariga wa ta riga sani cikin ku biyun kai ta fara sani kasani ba wancen ta fara haduwa dashi ba kaine ta fara sani. Yusuf kabar wanan zancen don Allah yarinyar da kaji mommy ma ta fada tana da masu son ta akan may zan tsaya bata lokacin gun ta karamar yarinya ma da ita haka da tara maza ai babu komai sai wulkanci a gurin ta. Da sauri Yusuf yace ta taba yima wullakanci ne da zaka fadi haka san nan kuma kowa ai da karfin shi yake zuwa ya gwada tashi sa,an akan mace idan tai ruwa rijaya idan batayi ba masai. Banda wanan lokaci kai ka sani so don Allah kubar wanan zancen na Deedar please zan dai yi hakkuri ina zauna da wa yan nan da Allah ya hadani dasu. Munyi magana da Abba Fati zata dawo dakin ta karshen watan nan ya kuke son inyi da mata uku yanzu biyun ma yaya na iya dasu balle na kara ma kaina wani wahala can. Aure ne kawai mafita gare ka a yanzu saboda ta haka ne kawai zai kawo fitar da zargin da ake maka akan Nafisa ta mallake ka don ni nasan matsalan ku da Fati wanda ma kowa ya sani in ba wani aure kara yi aka gani ba, bazaka fita bakin mutane da zargi su a kan ba. Mommy ban damu da abinda mutane suke cewa a gare ni ba tunda nasan ina tsare kaina ga duk wani abin hani. Mommy tace babangida kada kace haka idan kasan kana son yarinyar nan kada ka bari wani yazo ya kwace ta daga gare ka. Shawaran da zanbaka shine ba,a kin shawara idan na kwarai ne ka gwada a gani ko hakan ne mafita a gare mu kaga sai a wuce wurin a manta da komai sai fatan samun zuri, a masu albarka. Murmushi Yusuf yayi Allah yakawo lahadi don litinin yai niss inji maza ranan nasan ni za,a kira da munafuki yafi a kirga gun Nafisa. Yanzun dai maganan mommy ne mubar wanan zancen a yadda yake a rufe sai munga komai ya kan kama za a ji. Mommy kaifin basira irin na khadija yasa nake mashi kwadayin ta a gidan shi don khadija yarinya ce mai tunane wallahi. Mommy ta tashi taje yin alwala lokacin ne Yusuf ke fada mashi gobe yana son ya je zaria da safe akan ciwon shi yaga malamin nan na gurin kawu salisu. Yace kana ganin zuwan ka wurin shi yana da wani alaka da ciwo nane ko may ko wani abin ne zai kaika wurin shi. Sai da ya mike tsaye don zuwa sallah ya bashi amsa da cewa akan ciwon ka nake son zuwa can don yanzu wanan shawaran yazo min . Bai mai magana ba sai mikewan da yayi shima don zuwa yin sallah magariba data gabato a lokacin. Da dare yana kwance na kira shi muka gaisa na ba maryam ita ma tayi mashi yaya jiki yace da sauki ya gode muka kashe wayan. Maryam ne tace ni har yanzu sai nake ganin kamar jikin nashi da sauki a yadda naji muryan shi a yanzu nace haka nima nake tsammani danaji. Daga haka ban kara cewa da ita komai ba ina kwance rigingine ta dauko waya tasa muna kira,a shine naji hankalina yana kwantawa a hankali naji damuwan da nake ciki wanda ban san dalilin shi ya fita a raina har barci ya dauke ni daga hakan. Washegari na tashi wasai dani wanka nayi na shirya na kama hanya zuwa cikin makaranta don ina da test a ranan gashi banyi wani karatu ba isashe. Ban fito ba sai yamma lis na fito daga cikin makarantan alokacin yunwa ne ya addabe sosai a sukwane na shigo dakin ina wurgar da handbag dina ina cire hijjab din dake kaina a lokacin. Maryam kuma bata dawo ba nake gani alokacin don haka na fara kokarin hada jeloup din taliya don ina ganin shine mafi saukin dahuwa a gare ni a wanan lokacin. Agurguje nake aikin daidai lokacin da na kusan gamawa ne wayana kira ya shigo min sai da na duba abincin sama sama na dauki wayan. Ban tsaya duba mai kiran nawa ba naji murya shi yana fadin yau ba akira anji jikin nawa ba dan banufen naki ya dauke maki hankali ko ? Murmushi nayi a baiyane ta yadda har yaji a cikin wayan mommy bata nan ne daka bugo min waya ? Kina tsoron taji ina waya dake ne a gaban ta komay ? Ina da kunya da girmama na gaba shiyasa amma ba don tsoro ko wani abuba kawai don kawaici ga manya ne . Gata zaune tana jin ki ko in bata wayan ku gaisa ne kana fara shi wanan ma ai fadi ne kawai nasan mommy tafita yasa ka kirani kamar yadda nake da kunya kai ma nasan zakaji kunyan waya a gaban ta ai. Muryan mommy ne take fadin khadija kun koma lafiya jiya ya karatun Allah ya tsare ya kare ban iya cewa komai ba sai daburcewan da nayi a lokacin. Hello khadija ba kya jine ina magana kin yi shiru nan ma ban iya magana ba shiru nayi mata a lokacin sai naji tayi murmushi. Wayan na kashe sai da na gama girkin sai kuma cin abincin ya gagare ni duk da yunwar da nake ji din da farko . Waya na dauko na tura mashi text kamar haka baka kyauta min ba ya zakai min haka ka san girman mommy a idona kuwa ai sai kasa ta zargi wani abu a zuciyar ta a gare mu. Na gama na tura mai maryam ta shigo dakin tana fadin wai yau na gaji wallahi zama tayi tana kallon yanayin da ta samay a ciki. May ya faru tace tana kallon fuska na cikin damuwa ga yadda ta ganni din sake tambayana tayi tana maida hankalin ta gare ni. Ga abinci can ki diba ina kika tsaya har yamma haka lis wallahi mugun malamin nan namu ya tsaida mu haka yau test din yayi wuta sosai tamike tana fadin har kin ci ne ke tana kallo na. Kaina girgiza mata tace kin ci wani abin ke nan ko naga ko karyawan kirki baki tsaya kinyi ba kika fita yau. Wallahi da yunwa na dawo sai da na gama kuma naji ban son cin komai ki sha wanu abu mai ruwa kila yunwa ne yai maki yawa ya hanaki cin abincin. Ta debo ta fara ci tayi nisa ga ci nake cewa da ita kin san may wanan mutumin yai min yau maryam. Da sauri ta dago kanta tana fadin wani mutumi mamud ko wa nace wani mamud kuma AA fa don ya maidani karamar yarinya wai a gaban mommy zai kirani yai waya dani. Maimakon inga damuwa itama a fuskan ta sai naga sabanin hakan a fuskanta dariya ta soma tana fadin lalai wanan dan barki ne . Ya daure tamau yanzu a gurin mommy ta gama sanin komai a tsakanin ku ke nan ? Komai kamar yaya ya dai daure ni wallahi tace ai maganin ki ke nan tunda bakya jin shawara ai gara da ya fito maki tanan. Haushin ta naji sosai a rai na don rashin nuna jin haushin hakan dayayi min da ta nuna rashin damuwan ta akaina. Bayan ta gama ta mike lokacin nayo alwala zanyi sallah itama ta shiga bayin ta dauro alwala muka gabatar da sallah mu. Zaune nake bayan na idar da sallah ban bar wurin ba sai da nayi isha,i na mike ina nade sallaya maryam ta mike ta dauki heater tare da dauko cup ta hada min shayi mai kauri saida ta gama ta miko min. Kamar ba zan karba sai dai na mika hannu ko ba komai nasan shan tea din zai taimaka min ga yunwa da ke ciki na. Tunda na kwanta ban sake bi ta kan komai ba har barci ya dauke ni a haka yadda nake cikin dare na falka na ga ta rufe min kofa itama tana kwance a kusa dani ranan a dakina ta kwana. Zaune take a falon madam datai ma tsuke tunda safe ta isa gidan madam din a yadda ta ganta sai take tambayan ta ko lafiya haka da safe. Madam gaskiya yanzu samad ya rikice min tunda na haihu din nan na rasa gane kan shi gaba daya. Jiya fa a gaban wanan kishiyar uwar tashi yake fada min wai aure zai kara saboda kawai nace sai ya fada min wace yarinya ne tazo gaida shi har take bare mai ayyaba tana bashi ? Ke a ina kika ji wanan labarin ne wai waya fada maki ne shiya daure min kai tace kai tsaye su hajiya karima ne da suka je gaida shi. Baki ga irin wullakancin da security din asibitin nan sukai min bane suka fitar dani waje yana kallo baiyi magana ba. Haba Nafisa kullun ina fada maki magani fa bai ci sai da siyasa da kissa da kisisina da kutungwila na mata. Ya zama dole yanzu ki bishi a sannu ko banza kin zubar da jinin haihuwa a gidan ki kiga komai da kikayi na asiri yanzu ya karye. Ai ba karamin hikima bane aka samo na haihuwa asibiti da mata ke yi yanzu bature ya taimaka ma mata da ya fito da wanan hikimar haka na haihuwa asibiti. Kinga ko da za a dawo da mace gidan ta an wanke komai a asibiti kinga wanan uwar tafiyan na haihuwa yafi komai karya asiri ga mutane ba matan ba ba mazan ba. Shiyasa iyayyen mu na da basu wasa dashi a gida zakiga da sauri ake fitar dashi gida asamu gefe a binne shi amma mu matan yanzu sakacin mu yayi yawa ga komai wallahi. Yanzu ya zama dole gare ki ki lalaba shi ki kara sabon shiri sosai a kanshi dan kada yazo ya bijire maki nan gaba. Zancen kuma aure ni nasan ba dagaske yakeyi ba don ba abinda kika rasa da ake so gun mace yana kuma son ki tsakani da Allah. Zancen kuma ita yar iskan yarinyar dake dmson maki kutse a gidan ki ta dauke maki hankalin mijin ki tambaya zamu muji da gaskiya ne hakane ? Idan da gaske ne sai mu san ta inda zamu fito da zancen nata ga wanan irin arziki da ya taso ma mijin ki haka ina zamu bari muba wata daman da zata shigo ciki muna kallo. Yar iska bamu san ko wace iri bace ita tazo tafimu iyawa dashi babu yadda zamuyi ko wacece zata shigo maki kin san itama ta shirya. Don kishi da buzuwa ba wasa bane duk matan nahiyar nan namu sun sani shiyasa suke tsoron ku buzaye don cire ice har sayen shi komai tsufan shi ba wasa bane gare ku. Madam duk da haka ya zama dole gare ni in tashi tsaye in hana gaba da bayan shi motsi a gare shi ko mace ba zai iya daga ido ya kalla da sunan tausayi ba balle so. Yanzu dai duk ba wanan ba sai fa kin kwantar da hankalin ki ko ta siyasa zaki iya gano gaskiyar maganan gare shi idan kin kwanta amma. Tace a sanyaye naji zan gwada yin abinda kika ce min din tai mata godiya tare da sallama ta nufi gida tana ba kanta hakkuri. A ranan ya samu sallama bayan dawowan Yusuf da bayanin abinda ya girgiza shi daga malam don yace a lemon da ta tare shi dashi yasha batare da yayi bissimillah ba. Yayi arziki akwai tsari sosai na Allah a jikin shi da ba karamin wahala zaiyi ba don ba maganin alheri akabata tabashi ba. Ya iso gida zuciyar shi ba dadi wanka ya shiga don ya tsabtace jikin shi don baijin zai iyacin abinci ga yadda yake jin kanshi a lokacin. Yana zaune bakin gado ta shigo dakin ta saba diyar ta a kafada tana rangaji tana zuwa ta azamai yarinyar saman jikin shi itama ta samu wuri ta zauna a gefen shi. Yadda taga bai sake fuskan shi ba yasata fadin har yanzu abinda ya faru ne kake ma fushi haka ko jikin naka ne har yanzu. Kallon ta yayi yace may ya faru kamar bai fahince ta ba tace akan maganan nan na asibiti da ya faru raina ne ya baci a lokacin nayi haka ba tare da nayi tunanen komai ba. Wanan matsalan ki ne sai dai ki sani duk abinda zaki karbo daga yau da sunan malakana a gidan nan kada ki sake karbo wanda zai cuta min haka don ki sani nasan abinda kika zuba min a lemon da kika bani ranan. Kuma shiya haifa min wanan ciwon danayi ban hanaki yin abinda kike ganin shine mafita a gare ki ba don dama haka yawancin mata kuke da wanan shigeshigen din sai dai ki sani ba zaki taba mallakana ke kaidai ba domin ni din mijin mace hudu. Yana fadin haka ya mika mata yar tare da mikewa ya bar mata dakin nan ya barta cike da mamaki tana wasi wasin ko dai wani ya fada mai a gidan. To ina ma wani ya ganni nida na zuba a cikin dakina amma yaya akayi wanan maganan ya koma kunnen shi haka. Watau ke nan abinda ta zuba mai ne ya jawo mashi haka ba maganin kwarai aka bata ba kena cutar ta akayi akan maganin da ta kashe makuden kudi akan shk a bazan zai tafi ba zaiyi aiki akan shi ba tunda had ya gane may ake ciki. Ko dai shima yana irin nata ne har yaje wani ya fada mai abinda tayi mai tace kai wanda ke kwance haka ba lafiya ina zai iya zuwa ? ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Kwance nake saman katifan dakina ina karanta handout dina maryam zaune a bakin katifan tana gyara kumbar kafan ta. Waka take wanda take damuna dashi sai ya hanani yin karatun tunanen mamud nakeyi wanda ya kai sati biyu yanzu bai lekoni ba kuma banji daga gareshi ba har wanan lokaci. Hijjab dina dake gefe na dauka na rufe jikina dashi tace sanyi kike ji ko may da zaki rufe jiki haka nace sanyi nake ji wallahi. Na kara jawo handout inci gaba da karatu tace wai ni ko dazun sai naji kina waya ina son in fito in tambaya wakiraki ko mutumin naki ne naga ya dade bai zo ba kuma banji yana kiranki ba. Maryam kin damay ni fa karatu nake kuma kin gani a, a wani karatu yanzu inga kina tunane ke kika ga wanan din na gyara kwanciya ina bata baya. Sai da ta gama abinda takeyi tace don Allah tace muje mini market mu sayo kayan miya nace ban zuwa tare da lumshe idona. Fada min a jiki naji tayi tana dariya tare da sake ihu daidai kunnuwa na a zabure na mike na biyo bayan ta da gudu zuwa waje. Dagani sai dan body hook da nake sakawa a ciki in dora abaya kaina ba dan kwali gashina dana daure ya fado min a baya don duk zuben filani na gajeshi wurin kakannin mahaifan daddy na. A daidai lokacin nz hango motar su tana fakin a daidai inda suke tsayawa da mota idan sunzo guri na ban dauka su bane sai da na duba da kyau don gurin na kowa da kowane masu zuwa wurin yan matan su. Itama maryam din ta gansu da sauri ta dawo inda nake tsaye tana fadin su yaya Yusuf ne can ko ? Ba yadda zanyi don sun gama gani na gashi ko dan kwali babu akaina da sauri na koma ciki ita ce ta tafi wurin su tana gaidasu. Yusuf ne ya tambaye ta gudun may muke haka kamar yara tace wallahi khadija ce ta biyo ni da gudu wai ina damun ta tana karatu. Na fito daga ciki na dora a baya saman kayan ina hararan khadija na iso inda suke tundaga nesa ya watso min harara yi nayi kamar banganshi ba na kawar da kaina ga kallon shi ina gaida su baki daya. Har muka gama gaisawa da Yusuf yana tambayana karatu da kwana biyu nace lafiya maryam taso ta bar gurin da dabara Yusuf yace ta tsaya ai . Munzo muyi maku sallama ne zamu tafi umura gobe idan Allah ya kaimu mukayi masu adduan adawo lafiya Allah yasa a karbi ibada. Daga ida yake zaune baiyi magana ba tun zuwa su yace ashe baki jin magana baki daina saka kaya irin wanan ki fito dasu waje ba ? Nace wasu kaya kuma ina duban kaina da shigan da nayi yace ai kema kin sani yaya kika fito waje dazun ? Haba yaushe zaka daina samin ido hakane aiko wanda zan aura yanzu bai isa ya zaba min kayan da zans saka ba a jikina sai idan naje gidan shi. Murmushi mai kama da yake ya sakar min yana fadin au haka ne fa kuma gaskiya na faye sa ido. Yusuf yace kajiki da wani magana kuma akwai wanda yafishi sanin ya kamata akan ki ne yanzu dole ya nuna bacin rai ga abinda yake da iko dashi. Dariya nayi sosai nace sai kace nice buzuwa ko anty Fati wanan dokan yanzu ai sai daddy na yakai can. A bari a rabu lafiya kin ga tafiya zai yi kada a rabu kuna halin naku kuma kinga zai tafi dake a zuciya kila ba zai maki addua ba idan yaje. Addua kan kulun ai mahaifa na suna min shi kuma yana tasiri gare ni wanan bakin naki kuwa anya wataran bazai mutu ba khadija ? Dariya nayi nace yau dai kun tuna mu ke nan aka kawo muna ziyara haka yace bakin ki zuwa gida ki kara gaida shi da jiki ba ai shi baiyi fushi ba gashi yazo. Dan satan kallon shi nayi naga hankalin shi baya gare mu nan dai mukayi sallama dasu suka tafi. Da yamma ina kwance sai ga kiran shi ya shigo min a wayana nayi makai dalilin kiran shi sai cewa yayi fito gani bakin hostel din ku kai tsaye kamar yadda ya saba ya katse kiran. Na shirya na fito shi kadai na sama kamar yadda nayi tsamani bayan na gaidashine yake fadin dawowa nayi don dazu muna barin wurin nan Abba ya kirani. Yana son mommy ta koma gida kafin in wuce don haka nake son ki rakani musai masu abinda ya dace diban lokaci nayi a wayana bakwai da rabi na dare don haka akwai lokaci. Ciki na koma na shirya sai da na zauna ya tayar da mota nace kana dai son ka ban wahala kai da sukai ma hidima dakai da matar ka ni may ye nawa a ciki yanzu. Na dauka yanzu ma ai da shigan dazu zaki fito tunda ban isa in baki umarni ba ban dai ga dama bai don ba mai iko dani a yanzu. Allah yakaimu in dawo lafiya zanyi maganin wanan fitsaran naki lokaci daya . Ka fara maganin fitsariyar matar ta gida mai fita rabi tsira wace bata damu da hijjab ba balle gyale kafin kazo kafa min dokan ka . Sallon yaudara kawai zaka wani gama kalle min jiki kawani ce kai baka son haka na bayan sai da ka kalle ni tsab. Dama badon akalle ki kika saka ba idan ni kadai zan kalla ba matsala bane a gare ni wasune kawai ban son suga abinda nagani din. Don kanawa a gare ni zaka hana wasu su kalle ni kada ka mata ni yanzu a kasuwa nake banda hakkin kowa ai kaina amma ga masu hakki baka tsa, , , Jinin hannun shi kawai nayi a jikina yana fadin barin fara gwadawa in gani ko tayi min tunda a kasuwa kike kinga idan yayi min basai kin tallata ma wasu mazan ba. Bugu nakai ma hannun nashi sosai da yakai ma jikina yana shafawa bai san ina yi ba sai kokarin gwaucewa nake yi ina buge hannun shi. Fuskan shi a daure bai fasa min abinda yakeyi ba wuri ya samu ya sauka daga titi. Da karfi nace bude min in fita ina kokarin bude kofar motar a gigice hannun shi naji yana cire min dan gyalen da na yafa saman dogon rigar da nasa. A take gashin kaina dana tufke daniyar in na samu lokaci inje gurin kitso ya bayana a fili hannu yasa yana wasa da gashin har zuwa inda ya tsaya. Take naji wani hawayen bakin ciki ya silalo min a fuska na haka bai sa ya daina abinda yake min ba sai ma ji danayi ta rungumay tsam a jikin shi yana sauke wani irin numfashi yana shafa na son ran shi. Kara sautin kuka na nayi a lokacin sai naji ya sake ni yana fadin are you crying bocouse of dis akasuwa fa kike yanzu. Hannun shi yakai saman fuskana yana wasa da hawayen dake zubo min din sai kuma naji ya rungumay ni zuwa jikin shi tsam na dan wani lokaci. Sai da ya gaji don karan kanshi naji ya sake ni ya koma saman kujeran motar ya kwanta yana maida numfashi a hankali. Kaina na dukar naci gaba da kukan abinda yai min din can kuma naji ya tada mota a hankali ya hau titi ba tare da yayi magana ba . Kofan bakin wani plaza mai girma ya tsaya ban taba sanin akwai wuri haka a abuja ya bude motar a hankali tare da fadin fito mu shiga ki zaba masu abinda ya dace dasu kuma ki share wanan hawayen kada ace satoki nayi. Sai lokacin na dago kaina na dubi wurin nace ka sani har kullun Allah ba zai taba baka sa a akaina ba mayaudari kawai. Dariya naji yayi yana bude motar yace banda wanda Allah ya bani yanzu a kanki kuma koko kina nufin karfin ki ne ya kwace ki a kaina . Kuma ki daina kira da mayaudari don da yardan ki muka fito nan ki sani banda niyar aikata komay yanzu a gare ki amma ki aje a ran ki time will soon come . Ko yanzu ke kikaja in maki haka da wanan bakin naki da bai taba mutuwa don ki san irin abinda zaki fada ma mutum. Fita yayi ya zaya ya bude min gefen da nake zaune na sauko motar a hankali na fito don girman jeep din nasa. Mun fara tafiya naji ya rada min a kunne anya kuwa ke ma ba buzuwan bace deedar wanan irin gashi da jiki mai dadin tabawa haka fa ? Hararan shi nayi idon shin kyam a kaina ya sake fadin nayi haka don ki san har gobe nafi wani banzan dake zuwa wurin ki komai. Banyi magana ba don mun kawo bakin shagon haka muka shiga a jera da juna sayaya nai wa mommy har da gaiya don har yaran ta na zabawa abu. Ya kalli kayan mai makon inji yayi korafin sunyi yawa sai ji nayi yace kina ganin wanan kayan sunyi ke nan idan kuma kin sai wa yaran mommy ita kadai su sauran yaran anty amarya fa ? Dole na koma na kara zaba muryan shi ne naji a bayana yana fadin ki zaba ma su ummi da su hajiyan mu kayan suma. Sosai ya kashe kudi bayan na mommy dana su iyan bawa gana su hajiya mama dana zaba masu super masu kyau su ma. Mun kai ya biya ko dar nanga yayi ba da akai mashi list din kayan aka saka ga wani katon buhu zuwa inda motar shi take tsaya nayi ban shiga ba sai da ya zauna ya leko yana fadin shigo mana mu tafi. Nace dashi katafi kawai zan bi taxis in koma ni da sauri naga ya bude kofan motan ban san lokacin da na bude na shiga ba muka bar wurin. Sai da mukayi nisa naji yace kina zaton abinda ya faru zai kara faruwa a tsakanin mu ne yanzu idan haka kike tunane kinyi kuskure. Don ni ko matana dake gida sai naga dama nake waiwayan mace do ba haka nake ba kowani lokaci. Sai dai nayi mamakin ganin yadda kika narke min a jiki kaman dama jira kike in taba ki haka ya nuna min ke nan dama a jirace kike da hakan ya faru. Ban san lokacin da nace mai mugu mayaudari kawai macuci ba wanda ya taba min haka a duniyan nan sai kai kai kasan wani mace ta narke ma ajiki dan, , , , Hannu yakai zai kara kamoni na gwace da zafin nama yayi murmushi yace gobe idan halin ki ne ki kara cika min baki haka. Ba sai ka kara ganina ba zakace in cika ma baki kaji dadin yaudaran da ka sabayi wa mata a kaina. Zaki bar Nigeria ne ko mutuwa zakiyi don wanan ne kadai abinda zai hana in ganki in kara kallon wanan suran da kike kasawa a kasuwa in riga kowa kwashewa. Haushi bai barni na sake magana dashi ba sai juya mashi baya danayi kawai shima bai sake magana ba sai da muka kusa tsayawa naji yace Wallahi shiyasa kike kara burge ni da wanan halin naki na dan juyo na harare shi yace yes i mean it da wata ce sai tayi nata sayayyan amma ke naga ko tsinke baki dauka a shagon ba naan kuma dole kin ga abinda zuciyar ki ke so a ciki . Kinga ke nan kin nuna min abin mutum baya gaban ki idan bai baki ba yana da kyau hakan keep on da wanan hali. Sai dai ai na biyaki ladan ki ko ina ganin ba sai an rubuta maki wani lada ba ko bani wanan lafiyan fresh body din da kika yin kin more ai ke ma. Ya tsaya da motar na bude najita a rufe na juyo na kalle shi nace bude min in fita hug me for d last time tunda kin ce baza mu sake haduwa irin haka ba. Malam ka bude min mota in fita ni ba yar iska bace ka sani wallahi ban sani ba zan dai sani nan gaba in Allah ya yarda ban fahinci abinda yake nufi ba bai kuma bude min motar ba yana jiran wai abinda yace. Na sake cewa da kai fa nake magana ka kyali ni yace even peck kiss yana lumshe ido kamar zan kai kiss din sai na cije shi a kumatunshi. Yana shafa wurin yana fadin wassh ko hakan ai na gode zan tunaki watarana na taba haduwa da wata manya yar Niger mai zubin half cas. Ya bude motar tare da fadin thanks ki kula da kan ki don Allah don kin bar min tarihi nace mugu kawai azzalumi mayaudari da sauri na fita do kada ya kara rufe kofan yana dariya yaja mota tare da min horn ya tafi . Ko da na shiga hostel na samu har martam ta kwanta ina shugowa tace kun dawo tare da duban time tana fadin ban dauka zaku dade haka ba ai. Zama nayi jagwal a wurin fuskana kawai zaka kalla kasan ina cikin bacin da sauri ta mike zaune tana fadin wani abu yayi maki ne. A takaice nace may ye bai mun ba yau maryam AA ya cuci ni ya shammace ni sosai wallahi da sauri naga ta fida ido waje. Nace ban taba sanin dan iska bane sai yau wai nifa AA ya ruguma maryam har da taba min kai kiji min dan iskan banza. Ajiyan zuciya naji ta sauke tare da fadin wallahi har kin saka gaba faduwa na fa dauka ko raping dinki yayi wallahi wani irin harara nayi mata nace ya ma isa. Tace cikin dariya yadda kikai maganan ai dole mutum ya tsorata yayi zaton hakan ne ya faru a tsakanin ku. Nace may ye marabin wanan da hakan don Allah bada hakan ake farawa ba har aje can daga magana kawai sai naji ya rungumay ni don kawai ya nuna min dan iska yake macuci kawai. Tace akan kayan dazu ko na kada mata kai nace ashe kin san abinda zai min kika bari nabishi ke nan tace kema kin faye baki wallahi . Ai gara da kika zabi law don kin iya bakin ki don Allah bani labari nikan in sha dariya don nasan yau ashe yasha zagi a gunki. Nace ban sani ba cikin hararan ta ina mike tace indai gulma kuka kai shi ke dashi kuna son juna kuna wani noke noke . May zanyi da wanan dan iskan ni bakiji ba ma wai shi ko matan shi sai yaga dama yake kara waiwayan mace idan yaga dama. Dariya mai karfi ta kwashe dashi tana fadin ashe akwai aiki kuwa kuma yake sha, awan kara mata fadi dai yayi wallahi. Toni ina ruwana da rashin kula matan shi ko ya kula ko kada ya kula duk uwar su daya a gun khadija don ba abinda ya shafe ni da hakan na fada mai. Nan nabarta tana min shakiyanci alwala na dauro ina son yin waka don kada ta zarge ni haka na fito na tayar da sallah na gama na kwanta banci komai ba ranan. Sai dai ba barci nayi ba don tunane ya hana ni shakat a zuciya na don da zaran na rufe ido abinda ya faru tsakanin mu ne yake zuwa min. Har dai barci yazo ya dauke ni ranan na makara da sauri na mike ina shiryawa sai ga wayan shi ya shigo min. Kamar ba zan daga ba kallon da maryam ke min yasa na daga wayan murmushi naji yayi tare da fadin nasan dai kamar yarda banyi barci ba kema hakan bazaki barci ba daren jiya. Akan may zan hana idona barci nace mai, yace akan dan gidan mommy mana kema kin sani , nace Allah dai ya sauwaka kana ganin kayi wani abun gwanewa kenan, mutumin da ko runguma bai iya ba sai ta hanyar karfi, zai sa na kasa barci na kashe wayan. Yayi kiran duniya naki daga wayan sai ga text din shi ya shigo min kamar haka. Saboda kin san kin zuba min dahin ki a jiki daren jiya yasa kika fara garani ko may ? Niba macijiya bace ai, balle in zuba ma dafi Na tura mashi, ba a jima ba sai ga amsa shi kamar haka , Kin fi macijiya dafi karfa ki manta ke mace ce, mace ko shu,umace ko wace iri ce ita tasan sallon sheri ga da namiji. Kai dai ka sani da kayan sherin ka in ma dafi ne kai kazubawa kan ka bani ba ya karanta yana dariya bai san shigowar Nafisa ba dakin. Sai jin muryan tana tambayan shi kaidawa ke waya haka kake dariya ? Dakewa yayi duk da kaduwan dayayi cikin ranshi amma a fili cewa yayi da ita nida Yusuf ne don yasan ba karatun boko ta iya ba balle ta amsa ta karanta. Ba don ta yarda ba ta kyaleshi kawai tana zargin shi a cikin ranta don yanzu ya fara bata tsoro gaba daya don ya daina sayin ta da yake yi a da can baya. Daga haka ya sauka kasa yana yana kiran yaran aikin gidan shi ya shigo mashi da buhun da ya dawo dasu jiya. Ya sa akai masu dakin da su mommy suke tare dasu iyan bawa a gidan daidai lokacin Nafisa ta sauko kasa tana fadin Sabel wanan kayan haka daga ina kuma ? Yaro gidan dan yaren su na buzaye yace maigida yace ya dauka yakai dakin dabakin shi suke ciki tabi buhun kayan da kallo nan ta so sanin abinda ke ciki. Don haka tabu shi a baya wai taje da sunan gaida mommy yau da kwana yana zaune saman kujeran dakin suna hira da iyan bawa ta shigo tana gaidasu idon ta akan buhun dake gaban shi nan ya fahinci buhun ta biyo a lokacin don ganin may ke ciki. Idon ta ya gano mata atamfan da ya fara fitarwa kasa yana son fitar da sauran sai gata ta daure fuska tamau idan da dane da ya shiga hankalin shi ga yadda ya ga ta daure fuskanta. Sai ci gaba da fitar da kayan yake yana bin sunaye su yadda na rubuta ajikin ko wani ledan kayan yana ajewa gaban mommy bai fara bayani ba ta juya ta bar dakin a fusace cikin bacin rai. Sai bayan fitan ta daga dakin ya fara yiwa mommy bayanin kayan tare da dora ma ko wani kudi a saman kayan yace suyi dinki sai Allah ya dawo dashi lafiya zai shigo yayi masu ban gajiya. Kallon shi mommy tayi da kyau bayan ta gama sauraro shi tace wanan hidimar yayi yawa haka babangida don haka kabar kudin nan abin kuma ya koma biya , ? Mu da mukazo aikin lada zaka saka muna da wanan irin alherin haka mai yawa gaskiya hakan bai muna dadi ba gaba baka son inzo zama da diya ta ke nan in Allah yayi abin. Murmushi yayi yace ko baku zo nan ba mommy zan iya maku fiye da hakan don haka wanan ba komai bane Abba yace a tura ku gida yau kafin in wuce. Nasan ya kiraki ya fada maki komai ai don haka idan da sauran wani abin sai ku fada min a sayo maku kafin ku wuce na kuma gode kwarai da kokarin ku a kaina. Sai dai ayi hakkuri da yanayi matar gidan don Nafisa sai hakkuri nima dai kun ga shinakeyi. Ka dauki kudin nan ko ka rage dawainiyar yayi yawa haka abin ya zama kamar biya mu kayi ke nan ya mike yana murmushi yana fadin ba komai iyan bawa ai yima kaine. Na shirya driver da zai sauke ku idan kun gama sai aimin waya zan dan leka office don tafiyan mu sai dare zamuyi shi akwai dan sauran lokaci zuwa yanzu. Godiya sosai sukai mai ya fita nan dai mommy suka fara shirin tafiya don ba a ketare maganan Abba a gidan. Yana fitowa bai koma ciki ba ya nufi hanyar fita daga gidan muryan Nafisa yaji a bayan shi tana fadin dama nasan abinda ya zaunar da su ke nan a gidan nan tun bayan suna basu tafi ba kamar yadda kowa ya wuce. Suwa ke nan kike nufi wanda kasai wa kaya bada sani ba yanzu Allah ya tona ma asiri na gani do baku so in gani ba. Wai nafisa kina da hankali kuwa iyayyen nawa ma bakin ciki kike dasu akan nayi masu alheri tace ai ba su kadai suka wahala a gidan ba har dasu Yanyala sun wahala . Don may ba zaka saya masu tare ba ka ware naka kadai watau sune ka sani ke nan kai ya girgiza cikin kunan rai yace ba laifin ki bane sai kawai yaga ta sha mai gaba ta inda zai wuce ta. Hayaniyar su ne ya fito dasu mommy waje ganin su mommy ba sa ta fasa ci mai mutunci ba mommy ce ta hana shi magana. Duk ta hade dasu mommy tana zagi tare da fadin tayi ma kowa nashi iyaka da gidan tun da ba zuwan arziki suke yi ba jifa samun wuri a gurin wanan matar ita ha gida taf da yan uwanta kullun sai kara yawan su takeyi a gidan. Kowa yazo da sunan ganin ta sai ya nemi wuri ya zauna ba maganan zuwa gida kuma gare su an shafe ke nan. Haka ya fita gidan ranshi bace ranan su mommy sun ga fitsara a gurin Nafisa inda tayi ta aiban ta su suna ji suna gani ba abinda zasu iya yi tana gani taci gaban su. Ranan haka dai ya wuni cikin bacin rai halin Nafisa ya jutayin irin zaman da suke na rashin jin dadi a gare shi kuma bai jin zai iya rabuwa da ita ko kadan. Bayan su mommy sun gama shiri suka kirashi yace gashi nan zuwa ya samay su a shirye don haka basu bata lokaci ba suka fito da kayan su Yusuf suka loda a mota sukai sallama dasu suka tafi suna kara bashi hakkuri. Da yamma ya fito cikin shirin shi ya samay ta a dakin ta tana zaune tana waya ganin shi bai sa ta katse wayan ba sai data gama yake fadin su zasu tafi. Wani sabon lalura ta kirkiro mashi aladole kudin da take hasashen ya kashe ma iyayyen nashi sai ya kashe mata su bayan ya riga da ya sallamay ta da safe ta lissafa mai abinda take so ya bata. Nafisa wai may zakiyi da kudin da kike karba ne haka ya tambaye ta wani kallo tayi mashi tace idan zaka bani ka bani ba sai ka tsaya ka tambaye ni ba kuma ina sin idan ka dawo zan tafi gida inyi gyaran gidan mu na can. Dole ya bata daga cikin kudin da zaiyi amfani dashi don kawai su rabu lafiya da ita. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Wanan magana ya tsaya min a rai sai dai gaskiya ban aminta da maganar maryam ba don ba zan iya bude baki na in roki namiji koda kwandala ba balle har mota. Ina zan kai mota idan ya bani a gida ince dasu ina nasamo mota kana wa yaban motan akan wani dalili zai min kyautar mota haka inma har zai bani din. Gaskiya maganar ta bai karbu ba a wuri na sam zandai gwada mata nima ba kyale bace zan mata abinda sai tarena kanta da kanta anan na aje maganan azuciyata. Sai dai ban fada ma maryam abinda na yanke a zuciyana ba nabar abin a raina don ita maryam ba abinda ya damay ta wanan nake ganin a gurin su ba komai bane hakan sai abin alfahari. Washe gari na mike kamar komai ba faru dani ba ajiya ganin yadda na sake yasa maryam dauka ko na dauki shawaranta ne. Ban damu da fita ba don yanzu karatuna shine a gabana ranan mun dawo maryam ke tambaya na wai har yanzu taji shiru mana ko ban buga ma AA waya bane akan batun motar. Banza nayi da ita kamar badani take magana ba sai da ta sake tambayana nace mata don Allah maryam ki bar wanan zancen . Don bashine a gabana ba yanzu abinda nazo yi nake fuskanta ban son abinda zai raba min hankali ko kadan. Amma dai khadija kin kwabsa wallahi don kawai kin tambayi AA abu shine kike ganin rage ajine a gurin ki wanan ai ba komai bane wallahi. Yan mata nawa samari ke sayawa mota kuma a zauna lafiya so maye bai sakawa a yi wanan ai kara ma kanki daraja ne ba wani abuba. Wani kallo nayi mata nace rokon shine karin daraja ga mace rokon ma irin na rashin hankali haka wai ma idan har ya bani motar ina kike son in kai mota yanzu. May yasa kike magana kamar wata bagidajiya ne khadija samu yafi iyawa aida samu din ai yadda zakiyi dashi ba abu bane mai wahala. To bazan roka din ba period sai kuma may a take ta bata ranta a wuri banza nayi da ita na mike ina dauko kayana da zan goge itama batayi min magana ba. Yana zaune a falon shi kiran Fati ya shigo mai a waya bayan sun gaisa dashi dan shiru ne ya biyo baya sai can ta kau da nata miskilancin tace naga dubu dari biyar ga account dina dazun. Shima cikin magana kamar yana gune dayin maganan ya bata amsa da cewa eh kudin da kika bukatane nace a tura maki har wanda zaki wanin abin. Angode tace mashi zata kashe wayan yace ke baki taba kiran mutum sai idan wani lalurar kudi ko wani abin ya taso maki zaki kira. Bazaki kira kiji halin da mutum yake ciki ba anan tace yanzun kiran nawa inyi godiya ya zama laifi ne kuma ? Tsuki yaja tare da kashe wayan ya lumshe idon shi yana jin takaicin wanan baki halin na fati a kulun ita bata taba wayewa tana nan a yadda ya san ta a baya. Karan takalma daji ne yasa shi bude idanuwan shi ya sauke a gare ta ba laifi idan zata fita tana kwalliya na kure a daka. Sai dai a gidane baka taba samun ta a cikin shiri yadda ya kamata gashi shi mutum ne mai son yaga mace ko yaushe a cikin kwalliya hakan nayi mashi dadi sosai. Karasowa tayi gare shi tana fadin zan fita don kasan yau saura yan kwanaki kadan bukin namu zan leka inga may ake shiryawa a gidan kareemay din. Yanzu wa kike fadawa da zaki fita kin nemi izzinina kan zaki fita din kallon shi tayi tana dariya tace wata sabuwa ke nan ? Yanzu fitan ma da zanyi nan cikin gari sai na nemi izinin ka ko may bafa gari zan bari ba wanan wani magana kake nema kuma ? No ba sai kin nemi izzini ba tunda haka kika daukar wa kanki amma ki sani komai daren dadewa watarana wace zata nemi izzini na a gidan nan tana tafe. Da sauri ta gimtse fuskan tace bako a gidan nan ba idan ma mafalki kake ka falka ba wata shegiyar mace da zata sake shiga rayuwan ka kuma muddin ina raye kai koma ban raye na fada maka haka. Kina zancen ki dai yanzu don kin ga ban tashi ba cikin daure fuska tace don Allah mu bar wanan zancen zan fita lafiya kana son bata min rai na. Ta juya ta fita ba tare da tayi mai sallama ba don ranta ya gama baci sosai dashi a lokacin nan ta fita ta barshi zaune a falon . Zaman falon yaji ya ishe shi daga inda yake zaune yake jin kukan yar shi na zuwa mashi haka yasa ya mike yabi inda kukan nata yake zuwa. A dakin Yanyala ne kukan ke fitowa ya tsaya daga kofa yana kwakwasawa ba a karba ba yasa kai dakin ya samu yarinyar ta tashi daga barci tana zaune tana kuka ita kadai a dakin. Dauko ta yayi zuwa sama yayi mata wanka ya bata abinci har ya shirya ta ya fito gidan ba wanda ya nemay ta cikin gari ya fita da ita yawo. Gidan Yusuf ya nufa ya samu zai fito sai suka fita tare da yusuf din Yusuf ne ya kalle shi yace ina mukayi yanzu ga yarinya ka dauko kuma ? Yace dashi kaini gun khadija please batare da ya kalle shi ba murmushi Yusuf din yayi yace yau ranka a bace yake halan ? May kagani kace haka yace naji kace in kai gun khadija abinda na dade banji ba a gare ka shiyasa nasan an bata maka rai ke nan. Ya furzo iska daga bakin shi tare da kara rungumay yarinyar a jikin shi yace ban san irin rayuwan Nafisa ba Yusuf yau da yake ranan hutu ga kowa daya kamata in zauna gida in huta da iyalina. Sai gashi ta kirkiro fita wanin unguwar da baida dalilin komai wai kawar kawarta ne zata buki shine suka fita gin shirye shiryen bukin. Aka bar wanan yarinyar tana kuka ita kadai a dakin da sauri Yusuf yace subbahanallahi ina masu kula da yarinyar suka tafi kuma ? Yaja tsaki yace itama ta iya fita tabarta don may zasu tsaya kula mata da ya suma sun tafi nasu mana. Kai Allah ya sauwaka da halin bariki wallahi ba don nasan ka tun farko ba Abdulsamad da sai ince auren bariki kukayi da nafisa. Yanzun dai ni kaga ina jin kunyan Khadija wallahi na dade ban kirata ba kuma ban nemay ta ba tasan kuma muna garin . Ranan yakai three weeks mun hadu da ita da Nafisa a shago nakaita taiwa Bannan sayayya sai gasu ita da maryam har dan rikincin kayan shafa yaso hada su a gurin. Kasan halin nafisa da rashin hakkuri nan dai suka rikece ya bashi labarin komai da ya faru a wurin a tsakanin mu. Dariya Yusuf yayi sosai yace dakyau khadija baki daukan ta kwana ko kadan AA yace shine matsala ta da ita wallahi. A bakin hostels din mu suka tsaya aikawa sukayi a kirani bayan an tabbatar masu da ina ciki wata Annah ce tazo ta fada min ina da baki a waje. Ban tsaya wani gyara ba nasa kai na fita ganin kowaye yake nemana din tun daga nesa na hangoshi yana ma yarinyar wasa a mota. Har na iso inda suke fuska daure bai dago kai ba hannkalin shi naga yarinyar muryana yaji ina gaida Yusuf. Ya dago ya dan kalle ni bance dashi komai ba lafiya dai na gan ku a wanan lokacin na tambayi Yusuf din cikin daure fuskana. Haba kaunata kin daure fuska haka kamar ba gobe ai kya gaida dayan yayan naki ko tunda kin gan mu tare dashi nace ai ba wuri na yazo ba. Ka taba ganin mai arziki mijin hamshakiya yazo wurin diyar matsiyata wace bata kai matsayin a tsaya da ita ba ? Haba khadija ina wanan maganan ya fito haka kuma nace gashi nan ai ka tambaye shi idan nakai matsayin yazo inda nake sai ya fada ma . Murmushi AA din yayi yace da zaki shigo daga ciki zaifi don wanan zafin ranan zai iya maki illa anan har lokacin bai daina wasa da yarinyar ba. Ido na waro waje nace mota ai sai ku da matan ku yar matsiyata da bata gaji shiga mota ba ina zan taba motar ku in sha maku talauci a ciki. Motan ku na gama shigar ta tun ranan na dogara ga yadda Allah yayi mu ni da mahaifa bamu kai kan mu inda Allah bai kai mu ba. Ido ya runtse yana jin maganan da nake fadi har cikin ranshi Yusuf yace dakata kauna na nasan abinda yasa kike wanan maganan yanzu ma shi yace muzo mu duba ki don tun ranan bai samu lokacin zuwa nan ba. Ga kuma yar ki nan ya kawo maki ita ki ganta mun san Nafisa bata kyauta a yadda kukayi din nan ina ganin shine dalilin ramshin zuwan shi gurin ki don yasan dama a jirace kike dashi gashi kuma ashe har yanzu baki huce ba ke ? Akan may zanyi fushi da abinda ta fada ai gaskiya ta fada ba karya ba ni yar tallakace bamu da ko keke a gidan mu ita kuma da ya mayar yar masu arziki ba rawa taiwa Allah ba ya bata shi. Sai dai ta sani daren baiyi ko balle gari ya waye tajira taga zuwan daren tukun kafin ta wullakanta mutum. Yarinyar ne tasa rikici don haka hankalin mu ya koma gare ta yana dan jijiganta ta kallon inda nake tsaye a side din Yusuf tana mika hannun ta. Yusuf yace kin ga Banan tana ba mamanta hakkuri on behave of her father murmushi nayi ina kallon yarinyar nace fine girl wanan bai shafe ki ba ko ? Daga inda nake na mika hannu sai yarinyar ta zillo zuwa gurina banyi gigin karban ta a wurin shi ba sai cewa nayi ku kaita gida mana. Taga kuna kama da uwar ta ne take dauka ko ita ne nace Allah dai ya tsare min kama da wanan matar yarinyar bata bar kukan ba haka yasa naji har cikin raina na mika hannu ya miko min ita in dauke ta. Da sauri ko tazo wurina karban yarinyar nayi ina dan jijiga ta a hankali tare da shafa mata bayan ta sai tai shiru tana ajiyan zuciya a jikina. Ikon Allah banan kin san ta ne Yusuf ke fadan haka yana dariya AA yace daga inda yake zaune dauka ta ko maman ta ne don ta ganta fara. Farin mu ba daya da ita na na fadi a tsiwace shi dai murmushi yayi kawai bai yi dogon magana ba sai Yusuf ne yace dani wai yanzu na fahinci gori motar nan ya bata maki rai sosai fa. Wallahi ko daya raina bai baci ba don nasan rashin ilimi ne yasa ta fadi haka ba wai tasan ni ko wacece bane don ita halinta ne wanan. Khadija kina son mota da sauri na dago kai ina kallon shi kamar bashi yayi maganan ba sai kuma na mayar da hankali na gurin yarinyar dake kokarin yayemin gyale dana yafa a kaina. Yusuf yace ana tambayan ki wai kina son mota ne kai na girgiza nace ina yar tallaka dani ina zanje da mota ita mota ya dama a yanzu har take fankama da hakan. Kiran sallah azahar aka fara yi Yusuf yace tau ashe har lokaci ya jane haka ban an kara ba zamu tafi da fatan kanwana ta huce ko ? Murmushi nayi don ban son jan zance ina son fara aiwatar da shiri na akan buzuwa yanzu ina kokarin mika yarinyar gare su tare da fadin . Sai ko yarinyar ta make a jikina taki zuwa karshe da na matsa da mikata sai tasa muna kuka tana lafewa a jikina. Yusuf ya juya ya kalle shi tare da fadin yaya ke nan za ayi yace mutafi kawai anjima zan dawo in dauke ta in mai da ita gida. Bazatai kuka na na tambaya da sauri yace ba gashi kin gani da idon ki ba taki zuwa wurin mu ku shiga da ita don ba gida zan tafi ba dama. Haka suka ja motar su suka tafi yarinyar kuma bata damu da tafiyan su ba din muka shiga ciki da ita maryam bata nan sai da ta dawo ta samu ina bata indomie dana dafa mata tana ci. Tambaya na tayi ina na samo yarinya haka diyar AA ne na bata amsa kai tsaye ido waje take kallona da mamaki a ina kika samota kuma ? Shiya kawo ta na bata amsa in bata wanan in bata wancan har barci ya dauki yarinyar . Ina da wasu set din ribon a jiye kana na a hankali na kama kan ta ina mata kitso tana barci . Har na gama bata tashi ba na daura mata ribon din a kowani tukuwa yarinyar ba tashi don yadda nake kama mata kan a hankali. Wayan shi ne Nafisa ta kira a gigice wai basu ga Banan ba a gida yace kamar ya ba a ganta ba may kike nufi. Nan ta rikece mashi tana koro mashi bayanin yadda yanyala ta kirata daga gidan buki tana fada mata basu ga yar su ba wai. Yace maganan banza ke nan duk inda suka kai min yarinya na su fito min da ita kafin in dawo gida ko rayuka ku su baci ya kashe wayan cikin hasala. Ranan dai nafisa ta kirashi a waya yafi a kirga bai dauka ba kuma bai koma gidan ba kamar yadda suke jiran shi ya dawo duk ta fita hayacin ta yar ta ta bata a gidan. Yanzu baiji kunyan idon ki ba khadija ya dauko yar shi ya kawo maki yar matar da tayi maki zagin wulakanci a saman hanya. Wallahi da nice ba zan ko kalli inda yarinyar nan take ba balle ya bar min ita da sunan lalashi duk wanan abin fa sallon ba da hakkuri ne irin na maza. Shi a dole matar shi ta saba maki ya wani dauko yarta ya kawo maki nan don ya nuna maki ya isa da gidan shi ko may ? Dariya nayi nace ke ma kin san in dai wanan mutumin ne ba zai taba bani hakkuri ba bakina da nashi ba kuma kawo min yarinyar yayi ba nan . Sun zo da itane tagani ta lakemin taki yarda su tafi da ita shine yabar ta har anjima zai zo wai ya dauke ta yace . Tace bakin ji ba may ye na kawo maki ya kina makaranta kina fama da karatun ki ni dai nasan akwai wani abu a bayan wanan abin. Tashin da yarinyar tayi ne tana kuka hankali na ya tashi na rarashe ta tea na hada mata tare da bata cup cake sai tayi shiru taci gaba da wasan ta. Sai bayan magariba ya dawo daukan yarinyar ya bugo layina yana fadin gashi ya dawo in fito da yarinyar ya mayar da ita gida. Tun daga nesa ya kura muna ido yana kallon mu cikin mamaki yadda yarinyar batai min kiuya ba har muka iso gurin tana ganin shi ta washe baki tana dariya. Sai dai yana tara hannu tazo ta make tare da lafewa saman kafaduna ban san lokacin da murmushi ya subce min ba yace Banan yau fushi kike damu ne a gidan haka ? Nace kasan yaro kamar kyanwa yake yana son a kyautata mashi ko da yaushe indai zai samu jiki gurin mutum . Wanan ne kuma bata samu a gurin mu daga ni har uwar ba mazauna gida bane dukkan mu nace kuna daukan alhakin ta gashi babu ruwan ta wallahi. Dan shafan ta da nakeyi daga tsaye yasa ta koma barci nace kaga tayi barci yanzu lalaba ka maida ita wurin uwar ta tun kan ta tashi tasa rikici. Banji yace komai ba haka yasa na dago ido ina kallon shi sai naga yana wani lumshe ido yana kallon mu. Da sauri na kawar da kai daga kallon shi kamar bangan shi ba muryan shi naji yana fadin . Kun dace da Banan kamar kece uwar ta kenan goyo zai maki kyau sosai fa nace don Allah kakai yarinyar nan gida tun bata tashi tasa rikici ba. Yace af koran mu kike yi don na fadi gaskiya gaskiya kuma da kama da ita kamar kece mahaifiyar ta fa. Nace kaidai ka sani da jan magana a bayan idon uwar ta zaka iya fadin komai yanzu . Tsoron idon uwarta nake ashe nace ai naga zahiri ne ranan don Allah ka karbe don hannuna ya fara tsami da daukan ta. Miko jikin shi yayi don ya dauki yarinyar numfashin mu ne ya hade a guri daya nayi saurin ja da baya jikina yana rawa rigumay ta yayi a jikin shi yana fadin Thanks for today Banan da baban ta sun gode. Yana kallon kan yarinyar da ya sha kitso fuskanta ya fito shar da goshin ta saboda kitson da akai mata din yace wayayi mata wanan kitso haka nace gun wa ka kawo ta. Matsala na dake kenan tambaya a cikin tambaya halin ku na yan Africa leda na miko mai ciki da kayan ciye ciye nace a rika mata wanan idan ta tashi yai min godiya muka rabu yana cikin farin ciki da ya kasa boye wa. Sai da ya wuce a zuciyana nace ko yaya akayi yazo da wanan yarinyar nan yanzu kuma may zai koma ya fada mata kai halin maza sai su wallahi maganan maryam ne ya dawo min a raina. Ya na isa gida suna waje bakin get cirko cirko dasu sai da ya gama seta kan sa ya fito da yarinyar a kafadan shi. Gaba daya suka nufo inda yake nafisa ta mika hannu zata karbi yarinyar ya gwauce ya wuce ta ba tare da yayi mata magana ba. Sai da ya kwantar da yarinyar dake barci a saman gado ya juyo zai wuce ta tace ashe kaine kafita da yarinyar nan baka fada muna ba. Ke ki fita min a ido banson maganan banza har kina da bakin tambaya na haka da kikasa kafa kikabar ta agidan tana kuka iidan wani abu ya samay ta fa. Wallahi kasan su Yanyala na barwa ita amma sai suka bugo min waya suna fada min wai basu ganta ba. Yace bari kiji akan yarinyar nan zan iya bata muku rai baki daya a gidan nan duk sanda kuka bari haka ya kara faruwa. Kitson dake kan yarinyar dake barci saman gado take kallo muryan ta ne take tambayan shi a wurin mace kakai ta ke nan wani kallo yayi mata sai lokacin ya tuna da zata iya tambayan shi haka. Kallon yarinyar yayi da take a kwance shar kamar zaiyi magana sai kuma yaja kafar shi ya wuce zuwa dakin shi. Zuciyar shi a cunkushe yana jin bacin rai wanka yayi ya fito ya shirya gado ya koma ya kwanta da niyar taba aiki a laptop din shi . Amma sai yasamu kan shi da jin kasala nan ya fara tunane abinda na fada masu yau tunane ya zurfafa dayi sosai har zuwa daukan yarinyar daje yi da yamman nan. Ido ya lumshe yana tuna irin yanayin dayaji lokacin da muke hada jiki wurin amsan yarinyar yace a fili khadija khadija yana girgiza kai a hankali. Bude idon shine yaga Nafisa tsaye tana mashi kallon tuhuma dakyat ta iya daga kafa zuwa wurin da yake kwance tace yaya naga yanayin ka gaba daya ya sauya ne ? Samad ina kakai min yarinya yau wuni guda ace batai kuka ba nifa wanan abin ya daure min kai. Gun wa kakai ta baka fada min ba yace muna gidan Yusuf da ita muna aiki shiyasa kika ga ban damu da kiran da kike min ba din tunda nasan yarinyar na wuri na. Wani irin ajiyan zuciya ta sauke tare da zama a bakin gadon tana fadin sai yanzu hankalina ya kwanta wallahi. Gobe da safe zan bar gidan nan zamu je gyara ma amarya gida juyowa yayi yana kallon ta tare da tambayan ta wai a wakike cikin wanan bukin ne don naga kin mayar dashi kamar bukin gidan ku . Ga buki can za a yi a kaduna amma banji kina shirin zuwa ba sai wanan bukin da baki da wani dalili dashi kike maganan shi haka. Tace bukin wa za ayi a kaduna din idan ma na sani bazan tafi ba wanan kai ya shafa don ni bai shafe ni ba yace haka kika ce tace kwarai kuwa. Gyara kwanciyan shi yayi ya bata baya tace don kawai za ai bukin kannen Fati zan kwashi kafana in je don ban san ciwon kaina ba ko may ? Mutanen da basu sona basu kauna na basuki su bude ido suji ance na mutu ba a yau din nan kake son in kusance su. Ban son Fati ban kaunan ta da duk wani nata don su, , , enough Nafisa ya ishe ki ya isa haka baki zuwa ya isa wanan kalamin ba da Fati kikeyi ba dani kike yi don nima zurian gidan ne ko kin manta ne da hakan ? A kusan tsatso daya muka fito da Fatin da kike aibantawa haka da yan uwan ta may Fati ta tare maki a duniyan nan da baki kaunar ta haka saboda wani bakin kishi naki can mara dalili. Matan nan tun shigowan ki gidan nan kika dauki tsanar duniya kika dagwara mata katse shi tayi da fadin muka dai dagwara mata don bani kadai takewa abinda takeyi ba. Yace matsalan ki daban nawa daban ko may Fati tayi min nimijin tane kuma uban diyan ta zan zauna da ita a ko wani irin hali. Samad ni kake fada ma kai mijin Fati ne kuma uban diyan ta kake ni kake fadawa haka a gaba yace an fada maki kiyi abinda zakiyi. Wani shuumi murmushi ta sauke tace dama maza haka kuke don kana takama da wanan dandanin da taima shine har kake ganin ta a mace take yanzu. Kutawa tayi tafita daga dakin rai a bace ita samad zai kawo wa wani maganan wata matar shi can wai fati wai may yasa shirin ta akoda yaushe yake lalacewa ne idan tayi. Tasan dai tanayi amma kuma maimakon yayi aiki yadda take so sai komai yazo ya lalace daga baya taki jinin fati da diyan ta a duniyan nan amma mace kamar kaska duk wanan abinda takeyi sai fatin ta dawo a rayuwan samad din. Tana ganin taje gida tayi aiki akan kowa nashi amma kuma yanzu ta lura asiri bai cika kama samad din ba idan tayi ko tayi bai wani dadewa yana tasiri a jikin shi sai abin ya kare. Kudi dai bata da matsalan shi ko nawane ta bukata tana samu a gurin samad din yanzu abinda tafi zargi shine mahaifiyar shi take lalata mata aikin ta don haka wanan karon da hajiya mama zata kara don na samad din mai sauki ne. Don ko yanzu a tafin hannun ta yake don dai sai abinda tace dashi a gidan bai musa mata inba wani lokaci da yakan dan turza mata ba wai shi a dole ga namiji. Tasha alwashin wanan karon sai taga bayan duk wani mai mata aiki ta bayan fage akan samad din zata raba shi da kowa nasa taga yarda uwan nashi zatayi. Da haka barci ya dauke ta tana rungumay da yar diyar ta mumunan mafalkin da tayine ya falkan da ita sai gumi take hadawa a dakin duk da sanyin ac dake dakin alokacin. Wacece wanan macen da tayi mafalki da ita samad din ta ya rike ma hannu yara na binsu a baya kodai don ta kwanta da zancen Fati ne a ranta tayi wana mafalkin haka. Mace tare da samad din ta kaita kada tana fadin wanan ba gaskiya bane koma may ne gobe zata je wurin malamin ta a duba mata agani. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Jikina yayi sanyi sosai da kayan da naga ya sayo min musu kya dagani kasan ai kashe kudi a wurin sarkan maryam ta daga tana fadin. Wanan kan kizo kiji kudin shi zai kai a kala dubu dari uku fa saurin kallon ta nayi nace kai haba wanan dai kila mafa fashion ne kawai. Khadija wallahi gold ne haba baki ganin shi ko agogon nan ban debe tsamanin shi ma fashion bane nace a wani dalili zai sayo min kaya haka masu tsada bayan yasan iyayyena talkawane idan naje gida dasu may zan fada masu akan wanan kayan haka ? Rigunan ta sake tabawa tana daga su tace wallahi ko kayan nan anan zasu kai dari biyu kila koma sufi zaune nakai ina fadin shi wani irin mutum ne da baijin wuyan kashe kudi haka ? Maryam dariya tayi tace khadija ke nan baki san ko waye shi ba yasa kike fadin haka bafa karamin mutum bane wallahi kudi na shigo mai ta kowani hanya. Zasu iya sai da fili daya a wuni su samu milayan dari riba bakomai bane wanan a gare su wallahi kwanaki da mijin yaya na zai sai wani fili AA akace sai ya gani ya sa mashi hannu zai iya samun filin. To mutum da ke samun kudi haka don ya sayo wanan ai kamar ki jefa allura ne a cikin teku gare shi gashi nan muna ganin shi a banza amma mijin yayana yakai wata uku yana neman ganin shi bai samu ganin shi ba. Da sauri nace shi din tace wallahi Allah khadija wanan AA din kuwa shine don na tambayi anty na nayi mata kwatancen shi tace shine kuwa wallahi ba karamin kudi yake dashi ba ai. Banda abinki duk wanda kika ga ya auri buzuwa gidan shi har ta zauna haka ai ya mallaki abinda ya mallakane. Dubi shadda da tasa ranan da gwalagwala a hannun ta da wuya ke ko shaddan nan da zaki ji kudin shi zaki sha mamaki wallahi. Ido na lunshe na koma na kwanta ina tunane a raina gaskiya ya zama dole in raba dasu kada suzo su batani haka da itin kayan nan in zo gaba abin ya damay ni na saba da saka mai kyau in sha in kuma ci maikyau. Ranan da banda mai bani irin wanan yaya zanyi ga iyayyena tallakawa ne lis muna neman abinda zamuci a gidan mu. Muryan maryam ne ya dawo dani daga tunanen da nakeyi tana fadin khadija zaki iya samun fiye ma da hakan gun samari don kyauki ne ya jawo maki haka . Don ke din baki da maraba da yan buzaye dole ne na miji ya ganki ya rude haka sai dai shi AA nashi sallon son yazo daban da na sauran maza ne. Yace dake sona yake yi da kike fadin haka kawai dai mutunci ne a tsakanin mu kune dai dake da Yusuf kuke ganin haka din amma ni ba wani abu makamancin so daya taba hada ni dashi. Balle yanzu nasan da wuya su kara dawowa inda nake don na fada masu mamud zan aura kuma har na gabatar dashi a garesu sun gaisa dashi dazun. Kikayi may khadija amma wallahi baki kyauta ma kanki ba wanan wani irin cin fuskane haka kikayi masu lalle kan da wuya su dawo gurin ki kuma sai dai da yake maza ne basu fushi da abinda suke so kai tsaye. Mun dauki lokaci muna maganan da ita har dai nagaji na kyake ta tanayi ita kadai na bata baya. Yau da wuri muka dawo dawo daga class bamu dade irin yadda mukan dade acikin makaranta ba maryam ta rigani dawowa har na samu ta gama abinci ko. Dafa dukan manja yaji atarudu ta hada muna sai naman datayi amfini dashi a ciki danye zaune nake ina cin don ita tace tasha tea da tadawo don maryam bata wasa da cikin ta ko kadan. Na kusan gama cine wata Ruth Samuel ta shigo dakin tana cewa ina da bako a waje yana jirana maryam ne ta kallo ni bayan Ruth tafita daga dakin tana fadin yanzun haka mamud ne dan kadafin tsiya ya biyo ki. Nace kada kiga laifin dan bawan Allah a banza don nagane ke son wanda baisan kinayi ba kike yi yasa kike ganin laifin mamud din. Hijjab dina karami na dauka ina sawa nake maganan na fita waje ban jira may zatace ba kada ta bata min rai. A zatona mamud din ne yazo amma ina fita sai banga motar shi ba a wurin fitowa Yusuf yayi daga cikin motar da yazo da ita yana min hannu. Zuwan Yusuf din ya bani mamaki matuka don banyi zaton zasu kara dawowa inda nake ba kuma . Na iso inda yake tare da sallama yanayin shi kawai ya nuna min bai cikin dadin rai a lokacin yace ya karatu nace Alhamdullahi. Shirune ya dan biyo baya sai ido daya kura min yace dama nazo ne neman alfarma a gurin ki idan zaki iya yi min . Da sauri nace in zan iya may zai hana in maka tunda har kataso kazo gare ni a wanan lokacin haka. Ajiyan zuciya ya sauke yace ina son ki shiga ki shirya yanzu ki fito in kai ki asibiti ki gaida Abdulsamad ne yau kwanan shi biyu kwance bai da lafiya ya dawo da ciwon ciki sosai tunda ya dawo. Subbahanallahi na fada mace ciwon ciki kuma kodai yaci wani abin ne baku sani ba yace ciki da kai yake fadin yana mai ciwo tun kwana biyu da dawowan shi waje. Ko ranan da muka zo wurin ki cikin karfin hali nasa shi muka zo ke kuma sai kika bata muna rai da dan banufen ki. Murmushi nayi nace kuka dai bata ranku ga banza amma ni ban bata maku raiba gaskiya yace kin ko san kishin maza yafi na mata khadija ? Kishi akan may zaiyi kishi kuma don dan wanan magana kawai yace wallahi ba don nasan Abdul tun farko baida lafiya ba da sai in ce har da maganar dan banufen nan ya sashi ciwo haka. Sai dai bai karamin magana ba tun wanan lokacin a kan ki yanzu ma ni naga dacewan haka nazo daukan ki muje ki duba shi don Allah. Nace gaskiya ba zan iya zuwa ba da sauri yace khadija kada muyi haka dake mana na dauka zan iya saki abu kiyi don ni koma badon niba ai yaci kije ki gaida Abdulsamad din tunda akwai mutunci. Kai na girgiza tare da fadin Allah dai ya bashi lafiya amma ni ba zan tafi ba idan ma naje matar shi ta ganni may kake son in fada mata kuma don komai tamun tana da gaskiyan ta. Balle ma bazaku hadu ba don ita tana gida bata faye zuwa ba sai sa a mommy ce dai a gurin nashi take jinyan shi. Ko zan tafi bani kadai zan tafi ba sai inda maryam na fada yace gaskiya ne hakan yana da kyau ai wallahi ni ma kin ga na rude ban ko kawo haka ga raina ba sai yanzu. Don Allah ki daure kizo muje khadija yin hakan yana da kyau sosai wallahi ciki na koma na fadama maryan zuwan Yusuf din tace muje don Allah ki duba shi gaisuwa ai ladane gare shi so sai. Mun shirya ba laifi don zakace ba asibiti zamu tafi ba don maryam ne ta saka in shirya haka don kada muje mu hadu da buzuwa a can ta raina muna wayo. Nace in sha Allahu ma baza mu hadu ba har mu dawo muka fito muka kama hanya ina gaba tare dashi maryam na zaune a baya. Yusuf ya kawar da shirun da motar yayi a lokacin yace nasan zaiyi mamakin ganin ku yau saidai don Allah ki tuna a wani hali yake yanzu. Nan dai ma banyi magana ba sai murmushin da na danyi kawai yace maryam khadija ta fada maki abinda tayi muna ranan ko ? Wallahi ta fada min bata kyauta ba ai nayi mata magana kasan tayi nisa yanzu ga son dan banufen nan bata jin kira sai ta kai. Da sauri yace ehyehh tayi nisa fa kikace har ya shiga gidane bamu sani ba komay ? Amma khadija idan kin muna haka baki kyauta muna ba wallahi yaya zaki yi da abokina kuma idan kika fitar da wanan mamud din ? Nace Allah kadai yasan wa zan aura yanzu da kuke wanan magana niko mamud din ina shakku a gare shi ne don ban faye son mutum mai mata ba a rayuwana . Murmusgi Yusuf yayi yana kada kanshi yace yanzu dai kikai magana dama nayi zaton don ki musguna na munane kikai hakan. Nace a a wallahi ni gaskiya na na fada maku har cikin raina bandai son mai mata ne a rayuwana yasa nike shakkan shi. Tsaya yayi ya sayo kayan dubiya asibiti ya dawo ya shiga motar muka tafi dan jefi jefi yake dan jan mu da magana har muka kai inda zamu. Motar ta shiga cikin Turkeys hospital ya samu wuri ya faka muka fito zuwa cikin dakin da aka kwantar dashi wurin tsit yake baka cewa akwai mutane saboda natsuwan da wurin ke dashi. Da sallama muka shiga dakin yana gaba muna bayan shi biye har zuwa cikin dakin yana kwance rai,rai ya doran hannun shi daya saman goshin mommy tana zaune gefe saman kujera tana duban wayan hannun ta. Sallaman mu yasa ta dago kan ta tana amsa muna tare da zuba muna idanu don bata sheda ko suwaye tafe don maryam ce ke bin Yusuf din. Sannun ku da zuwa tace muka amsa da sannu mommy muna gaida ita sai can tace khadija kune tafe kun san baida lafiya ne ashe , ? Yusuf ya karba da fadin wallahi sunji mommy yanzu na gansu shigowa nan din na karaso dasu ya mai jiki nace da mommy . Mai jiki gashi nan yaji sauki yau ai mun ga hankalin shi jiya kan da muka zo abin ai ba dama wallahi. Maida hannkali na nayi inda yake kwance yana saye da wandon three quarter fari sai yar riga irin na shan iskan maza din nan mara hannu amma rigar na da kauri blue colour. Ya jikin nace a cikin wani irin murya mai taushi da sanyin jiki tare da dan kura mai manyan idanuwa na a hankali ya sauke hannun shi saman kan shi yace da sauki. Shirune ya biyo dakin na dan wani lokaci Yusuf ne ya karaso zuwa bakin gadon suna magana dashi wanda ba lalai ne mu jisu ba. Ledan da muka shigo dashi ya mika wa mommy yana fadin mu muka zo dashi tace kai khadija ina laifin zuwan da kukayi ke da ke makaranta kikaje yin wani dawainiya kuma haka ? Tana nuna mashi daga inda yake kwance tare da fadin kako gane ta yarinyar nan ne kawar su Binta da suka kwana wurin ta kawar matan officer na layin mu. Murmushi yayi mata kawai ba tare da yace komai ba muna nan tsaye jin yace yace Deedar akwai ayaba ki bare min in ci kai na gyada mai ba tare da nasan ko akwaishi ba. Na bude ledan ina ciro ayaba daga ciki na fara barewa na miko mai tashi yayi zaine ya dan jingina jikin shi da filo ina mika mai a hankali yana karba dakin yayi tsit a lokacin. Kofan aka turo wasu mata ne suka shigo dakin hamshakai dasu idon su caraf a kaina a yadda nake tsaye wurin kan shi ina bare mai ayaban ina bashi yana ci ko mommy ido ta zuba muna tana kallon mu sai take gani kamar da can musan junane ko kuma namu daine yazo daya bata sani ba. Shigowan matan ya dauke mata hankali ga barin kallon mu ta maida hankalin ta gare su suna gaisawa dasu. Kun fara jerabawa ne ko da saura ya tambaye ni mutum ba zai iya fahintar abinda yake fadi ba saini dake kusa nake jin shi nima a hankali na mayar mashi da amsa da cewa next week zamu fara insha Allah. A yadda muke magana zaka dauka wani magana mai ma,ana mukeyi idon matan nan da suka shigo su uku ya dawo a kan mu suna kallon mu gashi jikina na kusa da nashi kamar dai mata da miji. Mommy ke fadin yaji sauki sosai yau gashi ma yana cin ayaba har mun ga idon shi ai jiya abin ba dama wallahi. Basu tsaya ba suka yi ma mommy sallama tare da fatan Allah ya kawo sauki suka fita muma bamu dade ba mukace zamu tafi Yusuf ya taso yana fadin barin je in sauke ku ko ? Sallama mukai masu muka baro asibitin Yusuf ya fito ya sauke mu tare da yi muna godiya nace ba komai ai Allah dai ya bashi lafiya. Fitan matan kenan daga daki suna shiga motar su dayan tace nikan yau naga abu wallahi wai waye wanan yarinyar danagani tare da mijin Nafisa. Dayan tace aini yau imani ya kashe ni anan anya Nafisa batai sakaci ba kuwa ta yaya zata zaune gida ta bada damar wata na mata jinyar mijin ta don tsaban son jiki da sakaci irin nata. Wanan may ta sani banda karyan arziki da nuna son miji a baki kawai waya ta daga ta kiranta tana labarta mata abinda suka gani. Bata jira ta gama bayani ba ta kashe wayan tare da fitowa waje a sukwane tana zunduma ashar tare da fadin su Yanyala su biyu ta. A hanya take fada masu abinda ke faruwa a asibiti da mijin ta da wata sai dai kafin su zo mommy tasha ita da Yusuf da mijun nata uwa uba yarinyar da bata san ko wacece ba . A fusace ta turo kofan mummy dake zaune tana lazimi ta dago kai tana kallon ta da shigowan ta tace ina yar iskan yarinyar da tazo tana bare ma Ayaba ina karuwan yarinyar ta tafi ? Wacece ita wa ya bata dama tazo kusa da miji na haka tana magana tana zaran ido ta kalli mummy ta kalli Abdul di dake kwance yana kamllon ta. Nafisa you're very stupid zaki shigo ma mutane daki ba sallama kizo kina fadin rubish haka wakika ba ajiyan yarinyar da kike tambaya ? Mommy tace wace yarinya wai take magana ne wani kallon wullakanci tayi ma mommy din tace ko wace yarinya ce ai kun sani ni za a munafunta kuma ? Dama na sani ai abinda ake kulla min ke nan ba yau ba wallahi anyi kadan aga baya na a gidan nan balle aje a dauko wata karuwa tazo tana bare ma ayaba tana baka a baki. Subbahanallahi wani munafuki ya fada maki haka mommy barta an bare min ayaban an bani a baki may zakiyi ? Au ashe ma kasan karuwan ka tazo har ta baka ke nan karuwa kema kin san nafi karfin karuwa don yar kwarai ce ba irin ki ba da tashigo duniya tabar iyayyen ta. Babangida kubar maganan nan don Allah tunda kai kasan gaskiya tace dole kice haka mommy tunda dake ake hada bakin yin haka. Samad akan karuwa kake zagi na har kake min gori na baro iyayyena gida nazo nan ni kadai. Ba karuwa bane yadda na aure ki haka itama zan aure ta in kawo gida ta zauna dani tafiki komai da kike tunanen kina dashi. Ido ta waro waje kafin tai magana security din asibitin suka shigo suna kokarin jan ta waje suna fadin ba ai masu hayaniya anan kuma ba lokacin zuwa duban marasa lafiya bane yanzu. Samad aure kake fada min da bakin ka zakayi aure fa kace suka tura ta waje tana masifa tana zagi mommy mamaki ne ya cika ta da jin kalamin da ya furta. Bayan fitar ta tace Babangida dama kuna tare da khadija ne ko dai ka fada mata hakane don ka bata mata rai. Mommy bar yar iskan matar nan da bata da hankali zanyi maganin ta nan bada dadewa ba. Lamarin Nafisa ne sai hakkuri kabar biye mata kuna sai da hali haka haka ba tarbiyan ka bane wallahi. Bai iya mata magana ba don ranshi a bace yake da abinda nafisa tazo tayi masu yanzu sai mommy tace wai ma a ina taji wanan abin ? Har take aibanta yarinyar mutane haka khadija ne take kira da karuwa wanan bata da tarbiya wallahi. Har ta kare bai mata magana ba tace Allah ya kyauta taja bakin ta tayi shiru zuciyar tab da sake sake a cikin shi. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Zaman da maryam yana min dadi sosai don itama bata da wasa da karatun ta gashi musan mutuncin junar mu kamar mun dade da haduwa da ita. Ita ta tilasta min fara amfani da kayan da Yusuf ya saya min tace may ye amfanin ajesu da nakeyi gara dai a fara gani a jikina zai fi. Ban sake bi takan su Yusuf din ba na mayar da hankalina ga abinda ya kawo ni garin sosai sai dai muna waya da kowanin su har yanzu wanda wayana da Samad duk ya kira fada ne da zolayan junan mu har ai fada a kai ga kashe wayan. Munyi jerabawan karshen zango na farko inda muna gap da gamawa Yusuf ya kirani nake ce mai sati mai zuwa zan tafi minna don ba zan leka kaduna ba wanan hutun saboda hutun ba mai yawa bane . Nan yake ce min suna tafe gurina kafin in wuce gida don suma zasu shiga kaduna don Samad ya dade bai je gida yana kokari yaga ya shawo kan shi su tafi. Nace ka barni dashi in gwada in gani idan zamuyi sa, a da nawa dabaran yace ya gode muka kashe wayan suna zaune tare aiki suke a wani file. Yusuf yayi mamakin jin ya tambaye shi khadija yace tana nan lafiya kasan jerabawa suke yi kwanan nan wayan shi ne yai kara baiyi saurin dubawa sai da ya gama abinda yake ya dago wayan. Kallon Yusuf yayi da mamaki tare da fadin Yusuf yarinyar nan ko mutum ce jifa itace ke kirana yanzu muna maganan ta. Yusuf ya kalle shi yace mutum ce mana kamar kowa kaima kana ranta kamar yadda take a ranka ke nan . Ya dauka ciki daure fuska kafin in magana ya fara fadin lafiyan kirana ina aikina nace lafiyan ya kawo haka ai . Ya sake kiran suna na a zuce da karfi yace matsala na amsa mai da cewa may ye ne haka zaka fasa min kunne da kira haka kamar makaho. Kai na tsani wanan yarinya ya fada a hasale na amsa mai da nima haka wallahi cikin yanayin na bashi amsa. Nace dama abinda yasa na kiraka don in fada ma ya kamata kaje gida ka duba tsofin ka don gudun su da kakeyi ba shine mafita ba gare ka. Yace what da karfi don bai yi tsammanin jin wanan magana haka ba a baki na Duk wani da mai neman albarkan iyayyen shi yana tare da su a kullun suna saka mai albarka da fatan gamawa da duniya lafiya don samun haske a gare shi. Kai kana ganin kudi da girman kai da suke rudin ka zasu iya sama ma farin ciki haka ne a gare su, sunyi ciwo sun yi rashi amma bakai tunanen zuwa ka duba su ba har yau. Who dear you are da zaki fada min abinda zanyi akan iyayyena, nace ni bakowa bace sai mai neman albarka iyayyena don haka kai ma na tunar da kai akan hakan. Kuma kada ka manta da su Affan don sun fi kowa bukatan ka a wanan lokacin don nasan zaka iya zuwa masu hannu sake kai ba abin kunya bane a wurin ka. Don haka oga aje a duba su kada a shagala da yawa wataran sune masu duba mu you are stupid kece zaki tunatar dani komai kike nufi wai ke wacece wai waya baki wanan right din da zaki min wanan magana haka. Nace gani kamar kowa na tsoron fada maka gaskiya don suna ganin kana da kudi niko kudin ka ba damuna sukayi ba wallahi gaskiya komai dacin ta dole ne in fada ma mutum shi. Amma gani nayi buzuwan ka kamar kanta kawai ta sani sai yan uwanta ai don haka nima dan uwa na na sani a yanzu. Kit na kashe wayan ina dariyan keta shima Yusuf dake zaune yana jin yadda mukayi dashi sai murmushi yake yi yana huci yabi wayan da kallo. You see abinda nake fada maka kenan gashi yarinyar nan har ta hango tunda kaji ta fadi haka akwai abinda taji ya faru a gida may be. May yarinyar nan ta dauki kanta ne wai zanyi fa maganin ta a garin nan Yusuf da sauri Yusuf din yace kunfi kusa ai ni dan kallo ne a tsakanin ku sai dai ya kamata ka bincika idan ba wani taji bai da lafiya a gidan ba. Tsaki yaja yana rufe file din da suke aiki akai alaman rashi ya baci sosai ya dafe kai da hannun shi daya tunane ya shiga yi yaya akayi yayi sake rainin da bai taba shiga tsakanin shi da kowa ba har shiga tsakanin mu haka wai abinda nake mai zakace ko mu din cousin ne. Kan shi yana dafe da hannu shi daya Yusuf yace muci gaba mana yace kana iya tafiya yanzu makarasa next yanzu matsala ya shiga . Dariya yayi yana mikewa yace matsalan khadija ke nan ko hararan shi yayi da idanuwan shi da sukai mashi ja shidai ya fice bai yi magana ba. Ya dade zaune a gurin a karshe ya jawo wayan shi yana neman layin mommy don ita kadai ce zai tsaya yayi magana na fahinta da ita ya gane komay ke guda. Kira biyu ta dauki wayan da sallama a bakin ta ya amsa mata tare da fadin mommy kowa na lafiya ko kwana biyu ban kira waya ba. Tace lafiya kalau muke sai dai Alhaji ne jikin nasa ba dadi wallahi wanan matsalar tashi dai ta kwanaki ke damu shi kuma sai kuma Affan da suka kwanta asibiti amma dai yaji sauki sosai yanzu. Wanan yarinyar takai shu,uma wallahi mommu tace wace yarinyar ke nan kuma yace da sauri No magana mukeyi a nan bayan ya gama waya da mommy sai ya kira hajiya mama. Sun gaisa ta fara mai korafin rashin kula da kyautatawan da bai yi take mai fadan ga mahaifin shi nan ba lafiya yan uwan shi na kai da komo akan sa amma ace shi yayi biris dasu badon suraj da yazo ya kai shi asibiti ba may yake son mutane su fada a kan shi. Hakkuri ya fara bata yana fadin in Allah ya yarda jumma,an nan mai zuwa zai shigo ya tabayi jikin Affan sai bata bashi amsa ba. Bayan sun gama waya ya dade zaune a wurin kafin ya mike ya nufi hanyar fita office din ya rasa abinda ke yawan shagaltar dashi yanzu gamay da iyayyen shi haka. Zuciyar shi ne tayi mashi zafi don haka ya nufi gidan shi dan ya dan sarara batare da ya sanar da kowa ba ya fice a ma,aikatar nasu sai gida. Tun a kofa yake jin suruntun yana shiga Nafisa tana zaune a tsakiyan falon tana shan bakin shayi a dan karamin cup tana lumshe idanuwanta. Ganin shi a wanan lokacin tayi mamakin dawowan shi gida yanzu rigar da ya barta dashi na barci ne saye a jikin ta har wanan lokacin ga su hadiye na busa shisha duk falon ya gauraye ta ko ina kamar ba falon da ya narka ma makudan kudi ba haka. Batare da yabi ta kansu ba ya haye sama zuwa part din shi har ya kama hanyan da zai kaishi dakin shi sai kuma ya juys ya shige dakin hutun shi ya rufo kofan. Sai da ta gama shan attayen ta ta mike zuwa wurin mijin nata ba tare da damuwa da irin shigar dake jikin ta ba bata samay shi a dakin ba don haka tasan yana dayan dakin da yakan kebe kan shi wani lokaci. Can ta nufa duk da tasan ba lalle bane ta samu kofan a bude sai dai tayi mamakin da ta tura taji kofan a bude ta sa kai ta shiga yana kwance yayi rub da ciki a saman gado ta iso gare shi tana fadin. Samad yau lafiya ka dawo irin wanan lokacin tana kokarin hawa saman gadon ta zauna a kusa dashi juyowa yayi yana fuskantar ta wani irin karni da bashi kanta da jikin ta ke sakewa da kyat ya daure yace banjin dadi jikina ne tace oho ba sannu ba Allah sauwaka. Samad dama ina son in fada maka satin nan akwai bukin da zamu maradi sai kuma wayan nan kannen nawa maza da suka zo zasu koma gida. Gashi kuma ina son ka canza min mato don wanan naje dashi har sau biyu an sani dashi sai kuma su hadiye da nake son inyi wa sayayya kafin mu tafi dakuma, , , , Ke enough ya ishe ni don Allah duk wanan abin a cikin sati daya kike son inyishi ko kay wai may yasa ke baki da tunane ne wai ? Tsayawa tayi tana kallon shi galala tana mamaki yadda a dan lokaci yake son juya mata baya haka a lokaci guda tace Samad ni kake dakawa tsawa haka. Kallon ta yayi yace an daka maki ke baki da aiki sai na abaki dai a naki ai ma yan uwanki kaza ai masu kaza sam baki damu da na wa yan uwan ba da damuwar su. Tace amma kasan ina da yan uwa da ka aure ni ko yace wa kika fi yan uwa da bukatu ni nawa yan uwan basu son ai masu ne komay. Tace wanan kai ya shafa matsalar kace kuma ni dai nawa yan uwan na sani kuma dole kai masu don dani sula dagora. Mamaki da karfin halinta yaji yadda take fadin magana son ranta kai tsaye ta nuna mashi nata kawai ta sani shi yaji da nashi. Queen matsala kinyi gaskiya yace a ranshi ya ta tunar dani wani abu mai nauyi da na manta a rayuwana shiru yayi taci gaba da masifan ta akan shi bai iya furta komai ba a lokacin. Tashi yayi ya fada bathroom ya rufo kofan da karfi ruwa ya watsa a jikin shi yai wanka tare da yin alwala don yayi sallah la,asar don har lokaci ya dan gwauta da mintoci. Har ya fito tana zaune a wirin inda ya barta ya dauki room fresh ya fesa a dakin don bashin da dakin ya dauka ganin zai ta da sallah ya sa ta fita daga dakin ta barshi. Gyaran kai da jiki mukayi na zuwa gida don haka agajiye muka shigo hostel din mu maryam ta zauna dafa muna abinci ni wanka nashiga don zafi nake ji jikina ina ganin yayi min dauda. Tsab na fito nayi sallah a wirin na jawo ledan ice cream din da maryam ta sayo muna na fara sha a hankali maryam tace wallahi ji jake kamar kada ai hutun nan da za ayi. Da sauri na juyo ina ce mata saboda may maryam kika fadi haka tace ban son rabuwar mu wallahi yanzu ko ja koma gida banda wata abokiyar hira a kusa dani don anty na ba zama takeyi ba tana da yawan tafiye tafiye kullon don ita business woman ce . Nace ko dai ai koya nene kyayi kewan gida mana ni banki ba yanzun haka in bude ido in gani a cikin garin minna ma. Tace kin ji dadin ki wallahi khadija na yarda ba jin dadi bane farin ciki don ko dashi ne da bazan fadi haka ba farin ciki yana ga inda kake da sukunin aiwatar da komai. Kafin in magana wayana yayi kara na dauka kina ina nace maynene yace ki ban amsa kada ki min halin ku na yan African don Allah . Katambayi mutum ya mayar ma da tambaya shi kuma nace ina hostel mana yace ok kawai ya kashe wayan shi dip bin wayan nayi da kallo nace miskilin banza kawai. Maryam ta gama abinci wanda indomei da kwai ta dafa muna wanda yaji danyen attarudu mai yaji a ciki zubawa tayi a plate guda ta dauko muna lemon kwali a cikin fridge din ta wanda muke ajewa yanzu a ciki ida mun samu. Na fara cin abincin ke nan cibi biyu kawai nayi wayana yayi ringing na duba yaya Samad nagani a layin kamar kada in dauka dai na dauka kuma gani a kofan ku ya fada kawai. Kofan mu na maimaita da mamaki nace may kazo yi a nan kuma ban sani ba yace idan zaki fito ki fito sai ya kashe wayan kawai. Tsaki nayi na wurgar da wayan tare da fadin dan wahala kawai maryam dake zaune ta tsura min ido tana kallo na murmushi tayi tace. Uhm wani lucky guy din ne yazo haka ake ja mashi aji kuma abinda wasu ke nema ido rufe a zo gurin su anzo kike wanan masifa haka ? Nace sister kin faye bin kwakwafi wanan fa ba masoyi na bane zuwa kawai yayi ya bata min lokaci na ina zaune kalau. Don Allah ko may ya kawo shi kije ki saurare shi ba dadi mutum yazo wurin don ka ka wullakanta shi haka muje in zaba maki kayan da zaki saka in maki rakiya. Dole na mike muka tafi dakina ita da kanta ta zaba mi wani dogon riga mai ruwan ganye da dan karamin gyale shi sai da na shirya tsab a cikin rigan tabi jikina ta feshe da turararuka masu kamshi muka rufo kofan muka fito tare. Yana zaune a cikin motar shi riga da wandon shadace mai guntun hannu rigar ma iya ciya dinkin yake light green kayan su matukar karban jikin shi da dinkin . Wurin dirkekiyar motar shi da ke fake a kofan can dan nesa kadan damu muka nufa ko ganin maryam ya hana shi fada ban sani ba sai cewan da yayi. Ita ko maryam tunane take a ranta ina tasan fuskan nan nashi ne ya katse mu da cewa kin san ina waje zaki shanyani a wanan wurin naku mai kazantar tsiya haka ? Nayi dan dariya tare da cewa cikin wayance abinda yafa da nace ga kawata maryam tazo gaida kai don ma ita ta matsa min in fito yanzun haka. Anyway maryam ga yayan mu Abdulsamad Abdulrahim nan ku gaisa tace dama nace kamar nasan fuskan nan ai tace ina wuni yayan mu anzo lafiya yaya iyali. Yace lafiya kalau yaya karatu koda yake exam kukeyi yanzu ko yana wani kauda kai yana basarwa . Tace karatu Alhamdullahi mun kusa cin ma karshen shi da yardan Allah ai a huta gajiya dama nace barin zo mu gaisa ne kawai yace to na gode kwarai da alama kin fi kawar taki kirki sosai. Dariya tayi tace a a wallahi ai kirkin khadija na daban ne wallahi tana da kiki matuka shiyasa ma nake jin dadin zama da ita wallahi. Baki ya tabe ta juya ta tafi tana mashi a huta gajiya ta nufi hanyan shiga hostel din namu sai lokacin na sauke ajiyan zuciya bayan tafiyan ta. Katse ni yayi da fadin tsaye zaki min sai kace wanda tazo tadi da buduruwar shi haka bude kofan motar shi yayi na zagaya na shiga sai naji ya rufe motar. Shiru daga ni harshi ba wanda ya iya magana a lokacin sai ma gyara kwanciya yayi a motar bansan lokacin da nace dashi baka da lafiya ne Yaya Samad. Shiru yayi kamar baiji ni ba sai can yace may kika gani a tare da ni nace yau na ganka so weak ne ba miskilancin nan naka yasa na gane bakajin dadi ko baka cikin good mode. Wai ke aljana ce ko may dazun kin fada min magana akan ahalina ya zama gaskiya yanzu kuma waya fada maki banjin dadin jikina ? Nace yanayin ka ya nuna min haka sai ya dago da sauri ya na kallo na nima kallon shi nake yi sai dai ba zan iya jimirin kallon nashi ba a lokacin saboda kwarjin shi da ya cika min fuska a lokaci daya dukar da kaina nayi kasa ina wasa da yan tsun hannu na. Yau ina bakin naki ya shiga nace ko don Yusuf ne dama kike da bakin a gaban shi nace da sauri ko daya wallahi gani nayi yau kana bukatan kulawa don baka cikin hayacin ka sosai. Don jikina ya bani baka da lafiya sai naga ya koma ya kwanta kamar yadda yake da farko ya fadi a kasalance cewa kaina kamar zai rabe biyu nake jin shi khadija. Kasha magani na tambaye shi da sauri yace ban sha ba wani magani kake sha yace panadol extra nakan sha wani lokaci. Wayana na fara dannawa ina neman layin maryam ta dauka nace fito min da panadol extra din nan da goran ruwa don Allah yaya Samad bai jin dadin jikin shi tace to da sauri na kashe wayan. Motar shiru ba a dauki lokaci ba sai ga maryam ta iso da maganin ta kwankwasa glass din motar ya bude mata karba nayi ina mata godiya tace babu komai mana Allah ya bashi lafiya. Maida marfin motar nayi na rufe na fara kokarin bare mashi maganin tare da bude goran ruwan nace mai gashi ka sha. Ya dago kanshi da kyat ya kalleni ya kalli maganin da ruwan da nake mika mai sai naga ya bude min bakin shi alaman in bashi da kaina . Dan rankwafawa nayi ina saka mashi maganin a baki na kawo goran ruwan na bashi ya hadiye da kyat yana wani lumshe idonun shi yana bata fuska. Komawa yayi ya kwanta tare da fadin thanks nace Allah ya baka lafiya amin yace da kyat ni dai komawa nayi na zauna na zuba mai ido. Wasu irin jijiyoyi naga sun fito rada rada saman goshin nashi wanda ban taba kula ko yana dasu bane dama tsoro ne ya kamani kada wani abu yazo ya samay shi fa a nan wurina nawa ya samay ni kuma. Shiru daga ni har shi ba wanda yayi magana a cikin mu har mintina na shudewa a hakan suna batun zama awa daya muna nan a hakan dashi kamar mai barci. Abu daya ne yasa hankalina dan kwantawa ganin yana numfashin shi normal a lokacin yasa nayi shiru tare da zuba mashi ido kawai ina kallon ikon Allah. Wayan shi dake aje a motan ne ke ringing ganin anata kira bai dauka ba yasa na daga kiran don ba suna batare da na saurari mai magana ba nace mai wayan bai da lafiya please. Naji muryan mace tana fadin ke wacece da sauri ya dago ya kwace wayan a hannu na ya katse kiran yace akan may zaki daga min waya waya baki wanan damar da ikon daga min kira a wayana. Zanyi magana yace get out tunda ka samu lafiya yanzu zaka iya ci min mutunci sai dai ka sani ba zan ce ma komai a yanzu ba don yanayin da kake ciki na bukatan natsuwa. Get out i said na bude motar na fita ba tare da na juya na kalle shi ba naji ya tayar da motar ya jata da karfi yabar gurin nashige ciki abina. Dakina na shiga na wurgar da sauran maganin saman katifana na fara kokarin cire kaya a jikina sai ga maryam ta shigo tace ashe kin dawo. Eh ya tafi ya samu lafiya ai nace mata ina daura zanin a jikina na nike kayan na za saman jakkunan kayana dake gefe daya a dakin. Shiko tunda ya kama hanya yake jin wani bacin rai da bakin ciki a ranshi yana fadin wanan aljanan yarinyar sai ta kasheni wata rana. Yarinya yanzu ta sauke min bacin raina yanzu kuma ta kara sakani a wani anya ma mutnce kuwa dai , ? Yana shiga gidan a hargitse ya samay su duk kan su Nafisa ta haukace masu daga ita sai dan buje a jikin ta tana fadin yaushe samad ya fara cin amana na haka ? Yaushe samad ya canza ban sani ba nayi sakaci da yawa har na bari haka ya faru a yau da ban dauki mataki ba. Haka ya shigo ya samay ta tana wanan sambatun a cikin yan uwanta da suke ririke da ita kamar sabuwar mahaukaciya. Nan ya shigo baice da kowa kalaba cikin fushi ya shigo gidan don haka basu ga fuskan wani magana a gareshi ba. Tayo cikin shi da zagi tana fadin macuci mayaudari sai Allah ya isar min a gare ka har zaka dauki waya kabawa wata mace ta fada min wai baka da lafiya a wurin ta. Da karfi ya banbare hannun ta da ta rike mai wuyan rigar jikin shi ya fisge ya shige dakin shi a hasale. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Ganin zamu dan huta har kwanaki yasa na yanke shawaran zuwa kaduna wurin Ya Amina in masu hutun dan break din da muka samu a can. Bayan mun fito daga lectures ne na shigo na fara shirin tafiya kaduna maryam ma da tasa rai a gidan su zamu yi dan break din sai ganin ina shiri takeyi ta tambaye ni nake cewa kaduna zan tafi in duba ya Amina kin san hutun nan ban samu zuwa can ba. Ranta ya baci amma na bata hakkuri akan wani lokaci ai zan tafi nayi Sa,a ina zuwa na samu mota ta cika saura mutum biyu. Bamu dade ba motar ta bar tashan motar na da gudu sosai sai dai muna wuce maraba mun dan ba kauyen dage gaba baya kadan motar tamu ta tsaya. Drivern yayi tsaki yana fitowa daga motar ya fita ya bude gaban motan ya dan taba ya dawo ya tayar taki tashi bude motar yayi yace mu fita daga waje mu sha iska zai duba motar. Abu wasa wasa muna wurin har hudu na yamma motar bata gyaru ba raina duk ya baci nayi tunane kala kala a wurin tsaye. Wasu motoci ne guda uku tafe a jere da gudu suka wulga a gaban mu, ina jin mutanen dake cikin motar suna fadin kai jama,a akwai dai motoci a duniyan nan hadadu wallahi duba motocin nan kamar su suka kera kan su don Allah. Kuran motan da suke magana akai nabi da kallo sai naga motan suna dawowa baya a hankali zuwa inda muke kawar da ido na nayi daga kallon su na mayar da hankali na ga waya. Muna charting da maryam ina fada mata abinda ya faru damu a hanyar jin muryan masu hiran nayi suna fadin wai Allah yaba wasu duniya duba mutanen cikin motar nan don Allah. Daidai nan na dago ido na in ga abinda suke magana akai Yusuf ne yake kokarin fitowa daga motar tare da AA a daidai inda sukai parking yana kallon mu. Yi nayi kamar ban gansu ba na dukar da kaina a kasa ina ba maryam amsa ya karaso yana gaida mutane tare da sallama suka amsa mai a mutunce suma don yadda yazo masu din. Bayan ya gaisa dasu ne yake tambayan driver motar ce ta samu matsala yace wallahi Alhaji lafiya kalau kuma na fito da ita halin karfe ne kawai. Wurina ya mayar da hankalinshi yana fadin khadija ina zaki haka a wanan lokacin bamu sani ba kuma ? Ko kaina ban daga na kalle shi ba nace KD a takaice wata mata da muke mota daya ta dan manyanta matar dama akwai zuba don bakin ta bai huta ba tunda muka tsaya din. Sai cewa tayi malam hala matar ka ce matar oga nane gashi can a cikin mota zaune tace haba. Tun shigowan mu nasan yarinyar nan diyar manya ne ko kuma matar wani babba dama ina mamakin abinda ya shigo da ita motar hanya yanayin ta kawai ya nuna min haka. Dago kai nayi ina kallon matar da mamaki karara a fuskana zan yi magana tace in kina ma Allah kiyi hakkuri kibi mijin ki yarinyar nan kila shiya sa motar tamu tsayawa haka nata tashi ba kin ko san girman tashi (yaji)ga diya mace wurin Allah. Aiko jin haka sauran mutanen suka sa muna baki a lokaci daya ga abin dariya abin kuma haushi har da drivern suna ta bani hakkuri. Drivern da kan shi ya dauko jakkata wanda dan karamin traveling bag ne na saka kaya na a ciki dama, driver ya dauka yakai wurin motar tasu. Hannu Yusuf yasa a aljihun shi yaciro kudi yaba duk mutanen dake wurin dubu bibiyu wai su shiga wani mota su tafi. Godiya sosai sukai mashi suna kara min nasiha akan hakkurin aure anan kan dariya saida ya subce min a fuska na. Bude min baya yayi wai in shi ga naja na tsaya a wuri daya bakin motar tare da fadin kada ka manta na fada ma bazan sake shiga motar ku ba again. Haba khadija ai ko don idon mutane nan da nayi wa karya ki daure ki shiga ji yadda matan nan ke hada ki da Allah tana fada maki yaji fa baida kyau ga mace . Wa nayiwa yaji din ai gara su san gaskiya tinda ban san inda zan kara haduwa dasu ba yanzu idan mun rabu don haka please sauke min kaya na in tare wani motar in tafi. Don gidan mu a motar haya muka saba tafiya tunda bamu da motar yace please kanwa na kada mu tsaya jayayya anan kiyi hakkuri don girman Allah mu tafi yamma keyi yanzu hanyan kuma babu kyau kin sani. Girman Allah da ya ambata ne yasa na shiga motar ba tare da nayi wani magana ba kuma sanyi da kamshin motar ne suka daki fuska na a lokaci daya. Kira, a ke tashi a cikin motar a hankali muna shiga sauran motocin suma suka tashi muka kama hanyar kaduna ga yamma yayi. Sai da muka danyi nisa da tafiya yace kin daiji abinda manyan mata suka fada maki fushi baida kyau khadija don ko wanan tafiyan ya ishe ki ki gane mu da alheri muke bin ki khadija. Sai yanzu AA yayi magana da cewa ke kina haukane ko rashin sanin ciwon kai ne yakai ki bin motar haya cikin wa yan nan mutane haka masu yawa. Idan wani abu yaje ya samay ki a cikin jejin nan fa kina son ki salwantar da rayuwan ki ne a banza ko may ? Tunda ya fara magana ban dago kai na kalle shi ba kaina yana a wayata sai da naji ya fadi hakane na dago kaina nace a tsiwace . In salwantar da kaina kamar yaya don kawai nabi motar haya zan salwantar da rayuwana yace a zurke yana kallona. May yakai ki shiga motar haya a wanan hanyar ? Nace ai kasan ubana tallakane ko banda motar da zan shiga inwa mutane tsiwa asan ina dashi, don banda motar ya wuce ta haya a yanzu don kowa yasan ubana ban kwadayin karaya ko abin wani a rayuwa. Wani kallo ya watso min daga inda yake zaune ya kada kai ya koma ya zauna yana maida numfashi. Yusuf ne yace kaunata kin san kowa ke din mai tsada ce a yanzu don Allah kibar wanan gangancin da rayuwan ki murmushi nayi nace ganganci kai nama rasa may zance dasu alokacin. Gudu suke shararawa da mu sai can ya juyo kamar mai maganar lalama yana fuskantana yace kina jina daga yau duk inda zaki ki buga ma Yusuf waya a turo maki mota bana son shiga irin wa yan nan motocin please I hope you understand me ? Malam bafa don na shiga motar ku bane yanzu zaisa ka dinga bani commad son ranka ina dai nike da rayuwana bawani ba. Ya ce haka kika ce nace kwarai kuwa don may zan ka so takura min kamar wani wanda ya ajeni can a gidan shi. Ya juyo ya kara fuskantana yace haka kike so kiga an adanaki a gida ko sanan zaki bi maganan da ake fada maki na kula da kan ki ? Nace haka din ne ai shiya na fada haka kawai ba matar aure nake ba zaka wani kafa min doka kamar wace ke karkashin wani. Yusuf yace kai kanwa ta ba kayau ne haka yasa kikaji ana maki magana kada ki dauki zancen da zafi mana. Yace barta ai ka santa da bakin tsiya wanan bakin naki ya kai karshen tsiwan sa daga yau zaki kula kisan abin fadawa mutum. Wai ma may zaki je kaduna a wanan lokacin haka kuna karatu ko kin fara wasa da karatun ki ne yanzu ? Nace kai wanan ya dama ni gurin yar uwata zanje in dubata karatu kuma nike da abina ba wani ba. Murmushi yayi yace yarinyar nan ina tausayawa ranan da bakin nan naki zai dinke ya koma shiru wallahi kaina na kawar wanan karon ban biye mashi ba ya koma ya jingina da kujara ya dafe kan shi da hannun shi daya. Sai Yusuf ne ke dan jana da hira jefi jefi ban bashi amsa sosai sunyi sayayya a hanya sai ba a wani dade ba sai gamu mun shigo garin kadauna garin gwauna. Lokacin duhun yamma ya fara a yi sosai nace ku sauke ni in karasa a motar haya wani irin kallo ya watso min daga inda yake zaune yace saboda kin saba shiga motar hanya baki mai dashi komai ba ko ? Koda muka shigo layin mu har an fara kira a wasu wurare na magariba daidai get din gidan Ya Amina Yusuf ya tsaya da motan da muke ciki na fito tare da fadin yayana na gode sai da safe. Ki gaida sister idan kin shiga kice muna mata yaya jikin kafin mu shigo gaida ita zataji kawai nace dasu na dauki jakata na nufi ciki. Sai dai may daga get din har ciki a rufe na gansu waya na ciro ina kiran ta har ya katse ba a dauka ba nan dai na sake kira karo na biyu yana gab da katsewa ne aka daga wayan nace. Ya Amina kina ina nazo gida ban samay ku ba gida a rufe khadija ce nace eh don ba muryan ta naji ba a wayan. Tace mommy ce Amina tana gidan mu sallah take yi nace ok ina wuni mommy tace lafiya kalau yaya hanya nace Alhamdullahi mommy. Na kashe wayan don ban son dogon magana da ita nasan dai tunda mommy tasan nazo kamar Ya Amina taji ne na zo din. Na dan jima a tsaye sai can na hangota da saurin ta tana fadin ke tafiya haka babu sanarwa ashe kina hanya ne ? Don Allah bude min gida ni fitsari ya damay ni tun a mota nake jin shi wallahi tace kika ki magana a tsaya maki kiyi haka fa na jawo matsala ga mata. Tsuki nayi lokacin da ta bude gidan na fada da sallama a bakina ban tsaya ba na aje jakka kawai na fada ban daki da sauri. Har da alwala na dauro kafin in fito na zo falo na tayar da sallah don bata cikin falon a lokacin ban daga gurin ba sai da na gabatar da ishai. Wayana ake kira na dauka maryam ne take tambaya na yaya hanya kuma mun isa kd din nace mun iso yanzu tace an gyara motar ne nace ina fa ke dai bari maryam. Muna wurin ana gyara motar ba sai ga dan fitinar ga ba mai shegen izzan tsiya tace wa nace wa kika sani ni wallahi da nasan yau zai shigo kaduna ne da ban zo ba wallahi. Wai kina nufin su AA wallahi maryam su muna tsaye a jejin nan da na fada maki sai kawai ganin su nayi daga sama kamar a mafalki a gurin. Fitowa yaya Amina daga dakine yasa nace ma maryam ta bari idan na huta zan kirata muyi magana, muryan Ya Amina ne naji tana tambayana mota ce ta baku wahala a hanya. Nace bari ya Amina banji dadin wanan tafiya ba yau don dai kawai na kwallafa son ganin ku ne nayi shi dana koma wallahi. Gashi ko abinci ban tsaya nayi ba na ranane na rage wa yara don mun shiga gidan su mommy kin san ana buki a gidan nace buki kuma ina suka samu buki ? Tace a, a kin san ai da gidan su da gidan su Fati matar Abdulsamad kamar Family daya ne kannen ita fati din ke aure ai. A raina nace no warder ashe shi yasa mutanen nan nan suka zo garin ashe buki suke yi gaskiya naga an shake mota da kaya haka ? May zakici yanzu in dafa maki ko in shiga aurin mommy in karbo maki abinci don ni naci ko acan tun dazu. Nace barshi ko tea ne zan sha idan na watsa ma jikina ruwa zan kwanta muna wurin zaune muna hira sai mukaji sallama. Binta ce da zainab da wasu kawayen su biyu da ban san su ba suna dauke da basket din abinci a hannun su. Da ihu Binta ta karaso inda nake ta rungumay ni tana fadin wallahi khadija Adamu nafi kowa farin cikin zuwan nan naki ko kema dama kin san da zancen bukin ne wai ? Nace cikin fara,a wallahi bansan da zancen wani buki ba zuwa nayi duban ya Amina na kawai don nayi kewan ta da yarana. Aiko wallahi kinzo a sa,a don akwai casu wallahi nace ke har yanzu baki daina maganan wani casu ba can tace ba dole ba mutumiyar fa za aiwa engament jibi . Da sauri nace wa kenan kuma ta nuna min zainab tana fadin gatanan a gaban ki kuwa wallahi wayo take son muna nidake. Kallo na mayar ga zainab din dake zaune tana faman taba wayan ta nace wai da gaske ne ko sherin Binta ne kawai dayar yarinyar tace da gaske ne wallahi. Dan ihu nayi nace amma zainab kin bani mamaki ashe da Allah bai kawo ni ba da saidai inji labari. Tace a wani yanayi ba haka bane khadija nima ban dauka a yanzu za, ayi abin ba na dauka ko da sauran time ne shiyasa ban fada ma kowa zancen ba. Ta fada cikin izza da yanga sai yau nake ganin mugun kamar su da yayan nata komai nasu iri dayana sosai sunfi dauka kamanni da mahaifinsu fiye da kowa a gidan. Nayi murna kwarai sai can na kallo ta nace wai waye wanan lucky guy din da ya iya sace zuciyar wanan yar kwalisan yarinyar haka a lokaci daya. Binta ne ta bani amsa da fadin ina guy fin nan abokin yayan mu da always Suna tare da yayan mu Abdulsamad mijin buzuwa din nan wanda ake ce Yusuf. Shine ya sace zuciyar wanan mai zurfin cikin tsiyan da kike gani nima da muke daki daya da ita ban taba sanin wanan labarin ba sai da abin yanuna ya fashe naji. Kin san matar shi ta rasune a wurin haihuwa shakara biyar da ya wuce shine bai yi wani aure har yanzu ashe rabon zainab ta shiga gidan shi ne ya kashe matar . Harara zainab din ta aika mata na ki kama kan ki dinan nace amma zainab kinyi dace da mutumin kirki dan arziki daya san mutuncin mutane. Binta tace kin san shi khadija da kike fadin haka wallahi kin canka daidai kuwa don har yau ban taba jin wani hali nashi na assha ba da aka fadi. Na dafa zainab din ina fadin yar uwa ina tayaki murna da wanan babban kamu da Allah yayi maki muma Allah ya kaimu ga danshin ki. Zainab tana murmushi tace baki dai so bane khadija da tuni wani yayi wuf dake wanan zubin naki sai kace wata halfcas dake wani namiji zai ganki ya kau da ido gurine kawai maza basu samu ba. Kiba da dama yanzu ki gani in bakiga layi a kofan gidan nan ba har ba iyaka na maza a kofan gidan nace ba zasu samu ba yanzu zainab baki ba dai in nan gaba na kammal karatuna na fara aiki ko shi sai kila. Ya Amina da tunda muka fara magana baita magana ba sai yanzu tace yarinya in tunanen ki ke nan ki canza don baba a jirace yake dake wallahi. Nace Ya Amina baba ai yafi kowa sanin matsalana karatune burina inga na zama babban lauya wata rana Binta tace wai da mun sha dauri wallahi. Nace kamar ko kin sani don da na gida zan fara sharia na kada ma kiji wai binta ki rike dakayau a ranki. Zainab tace kinga mun kama zuba kamar ba gobe ga abincin nan mommy tace mu kawo maki a gurin ta ma muke jin zuwan naki yanzu. Daga inda Ya Amina take zaune tace wai mommy dai bata gajiya yanzun fa muke maganan abincin nan kamar ta sani sai gashi ta aiko muna dashi. Mommy ai tafi danan wallahi inji dayar yarinyar ta fada kowa yace wallahi halin mommy ai yayi ne sosai. Basu jima ba sukai muna sallama akan gobe zamu hadu sai mu kara tatauna abinda za a yi nace dana san da wanan zance ai da tare muka zo da maryam. Binta tace Allah sarki ban tambaye ki maryam din ba nace tana can na barta tace gobe ita ma gida zata tunda na wuce na barta. Har bakin get na rako su suka tafi na dawo ciki a inda na bar ya Amina zaune a nan na samay ta nace wai ina yaran suka tafi ne tace suna can gidan kakannin su zasu kwana masu biyu. Ban san zaki zo ba aida ban kai su can ba don in samu yadda nake so ne yasa nakai su can inji dadin shiga mutane babu takura. Wanka na shiga na fito na saka wani dogon riga a jikina na shan iska mai dan karamin hannun yadin rigar baida kauri sosai falo na dawo na samu ya Amina tana kallo. Zama nayi ina jawo kulan abincin da mommy ta aiko min dashi nayi mamakin ganin abincin haka kamar na wata hamshakiya. Ban san lokacin da nace wai mommy irin wanan hadin haka wallahi ni har kunyar matar nake ji Allah kuwa. Dariya Ya Amina tayi min tace ko har kun fara sarakutane da ita ban sani ba nace wa zata bani cikin diyan ta haka dai kawai nake jin nauyin ta yanzu. Wai ni ina Abdulsamad ne ina zancen ku ya kwana dashi ne tun lokacin ban kara jin labarin ba ko da yake yanzu kin fi zama minna ai. Tsuki nayi ina zama kasa nace ina ruwa na da wanan miskilin mutum da bai san darajan mutane ba halin su au daya da matar shi shiyasa nasu yazo daya da ita. A,a wallahi baki ko fahince shi ba khadija Abdulsamad mutum ne wallahi mai mutunci da sanin ya kamata ke dai kice Allah ya hada shi da yar banza mata ne mara mutunci kwanaki fa har gari nan tazo taci ma iyayyen shi da matar shi mutunci. Don Allah ya Amina abinci zan ci kada ki fada min maganan haushin nan ai ita bata da laifi shine mai lefin don ni wallahi da nice Fati da tasha takaici a wurina. Don wallahi tsab zan zauna da ita don tun yanzu na karanci iya shegen ta balle fati da suka zauna tare tasan halin ta da komai nata may zata gwada mata. Ke dan Allah can kin san aure ne da kike wanan haukan haka auren fa akace maki khadija ba wani abu ba ita mace dama ta gaji ganin haka walau mai kyau walau akasin hakan. Abincina naci gaba daci ban taka mata ba ganin nayi shiru itama taja bakin ta tayi shiru tunda ta fahinci ban son zancen . Ina gamawa tace min a dakin ta zan kwana tunda ita kadai ne a gidan kuma ba a gyara dakin nawa ba don bata san ina tafe ba. Nace aiko dakin baiyi wani datti ba dan fes na ganshi har da ban dakin tace duk sati ina shiga ina gyarawa don gudun irin haka duk da haka ki bari sai gobe idan an gyara ki kwana a ciki. Bayan nagama don naci abincin sosai na kwashe kayan zuwa kitchen daki na koma nayi shirin kwanciya wayana kawai na dauka da hijabin da zanyi sallah da safe na fito xuwa dakin ya Aminan. Na samu ta shiga wanka haka yasa na kwanta abina don dakin ba bako na bane wayana kunna na bude data sakone ya dinga shigo min daga ciki biyu kawai na duba na farko sokon mamud ne yana tambayana karatu. Sai kuma karshe da yake ce min ya matsu in gama muyi aure in haifa mai yara masu kama dani yana yawo dasu a mota a gari. Tsuki naja ina fadin baka da hankali mamud nice zan shiga ma ta uku gida don na rako matan duniya komay ? Sai sakon maryam tana fadin hostel din ba dadi dana tafi don haka gobe gida zata tunda safe duk da tasan yayan ta basu gari da mijin ta. Zatai zamane na kadaici koda taje amma yafi mata zama a hostel bani amsa na bata nace niko kinga nazo na samu ana buki anan har da engement din zainab da Yusuf alama murna ta nuno min tace yaushe ne bukin nace mata sturday idan Allah ya kai mu. Gobe zaki ganni tace kai maryam da gaske tace insha Allah ko naje gida Anty basu kasan suna waje da mijin ta ai gara inzo inda kike muyi hutun tare. Mukai sallama ina murna har ya Amina ta fito ta samay ni hakana nake fada mata gobe maryam zata zo tace ashe ina da bakuwa gobe a gidan kin ga sai kin min list din abinda take ci a sayo maku kada tazo nan ta takura. Dariya nayi nace da kin hutar da kanki don maryam suna masu kudi ne kawai amma bata da matsalan komai wallahi komai da kika san muna ci tana son shi. Allah ya kawo ta lafiya nace amin daga haka had barci ya dauke ni nayi mafalkin ga mutane sun taru ina kuka haka yasa na kasa barci har safe nakai a hakan. Haka na tashi da safe a cikin damuwa ina tsoron in fadi wani abu mumuna ya faru dani da gari ya karasa wayewa nace da anty zan fita bakin titi in ba da sadaka. Bata tsaya tambaya na ba na fita zuwa titin in da nayi saa na hadu da wata mata mabukayi tana neman abinda zataci da yaran ta na bata dubu biyu tana min addua na juyo zuwa gida. Ban yi nisa ba ina karyo kwanan unguwar mu tun daga nesa na gane A A tafe a cikin kayan motsa jiki yana judging shi da su mutum biyu a bayan shi. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Hutun mu yana karewa na fara shirin komawa makaranta bayan na kara sati daya a sama agida ina tare da iyayyena da yan uwa na. Duk da ba so daukan kaya nake yi ba hakan bai hana mama ta dan tanadar min irin abubuwan da uwayen mu mata suke tanadarwa yaro idan zai koma karanta. Inda mahaifina ya bani kudin da zanyi sayayya na raba kudi biyu na mayar mai da rabi nace ina da kayan abinci da ban ci ba a daki na. Bayan na shirya ina shirin zuwa Abdulsalam garage da kayana inda zan shiga motar zuwa abuja na fito a cikin shiri na yan uwana suna a bayana zasuyi min rakiya bakin titi. Gaban daddy da mama nazo na durkusa har kasa ina fadin daddy zan tafi ya dago kai ya kalle ni tare da fadin khadija kin fito ke nan. Yace do Allah khadija ki kula da kanki kamar yadda kika saba a baya ki maida hankali ga karatun ki kinga lokaci na tafiya yanzu. Kaina na kasa nace in sha Allahu daddy na gode mama tace banda kai kai inda Allah bai kaika ba kawar da kanki ga komai sai kiga komai yazo maki a cikin sauki nace na gode mama na mike tsaye jiki a sanyaye. Ban dade ba na samu mota naba kanne na kudi su raba daga cikin wanda daddy ya bani in rika din muka tafi tare da kanina dake bin min. Na isa Abuja da wuri inda na samu maryam ta rigani dawowa lokacin ranan mun jima tare muna hira ko barci bamuyi da wuri ba dan shaukin juna da mukeyi duk da muna waya kusan kullun da ita. Dayake muna da abinci ga kuma wanda maryanm ta karo don haka ban damu da nashiga gari in sayo komai ba don akwai shi a dakin. Mun samu sabbi fuska a gidan namu don an dauki sabbin dalibai yanzu wasu sun tafi kuma koda zan dawo ban bari mamud ya sani ba . Idan ya tambayeni yaushe zaki koma nakan ce dashi ba yanzu ba idan na tashi zan sanar da kai lokacin da ya samu labarin na koma school ranshi ya baci sosai dani. Kirana yayi ga waya yana fada wai ya fahinci gaba daya yanzu ban damu dashi ba don may zan koma school ban sanar dashi ba saida yazo gidan mu ya samu labarin na tafi. Nace dashi na fada maka tun farko kada ka wahal da kanka gare ni don ba auren ka zanyi ba na riga na rufe babin nan ko a raina. Satina biyu da dawowa sai ga mamud din ya kawo min ziyara gaskiya banji dadin zuwan shi ba don na gane yana son da karfi da yaji ya shiga raina again. Yadan jima a guri na muna hira dashi wanda hiran duk a kan zaman mu dashi ne anan maryam da wata Aisha da yanzu muke tare da ita suka samay mu. Da zasu tafi ya basu alheri sukayi mai godiya yace ma maryam ta taya shi kanfen a guri na dariya tayi tace ban maka wanan alkawarin ba don abaya ka gujemu ba wani dalilin komai. Haba maryam banyi zaton jin haka a gare ki ba yace tace gaskiya na fada don yanzu tace karatun tane a gaban ta doon kaga muna gab da gamawa ba wasa a gare mu. Kaya masu yawa yazo min dashi irin na bukatan yan makaranta na nuna mashi hakan da yake yi ba daidai bane yace yace bai son irin kalamin nan da nake mashi. Bayan tafiyan shi ne muka bude kayan da yazo min dasu muna kallo Aisha tace amma ni kan sai naga kun dace dashi very handsome dashi wallahi. Nace Aisha ba handsome bane abin damuwa abinda ke cikin gidan mamud din ne ai maryam tace da ita ai khadija haka take samun handsome guys don baki ga AA bane har kike ganin mamud a matsayin handsome a gare ta. Nafitar da zancen wani mamud da AA a raina karatuna kawai nake fuskanta a yanzu da ya dau zafi gare mu banda lokacin kowa a tare dani ban kuma shiga gari ko yaushe ina cikin makaranta ko hostel din mu. Zaune yake a office din shi yana aiki a wani file aka turo kofan office din nashi aka shigo baidago ya kalli wanda ya shigo din ba don yasan daga Yusuf ne sai ko masinjan office din nashi. Muryan da yaji yana mashi sallama ne yasa ya dago a lokacin wani hamshakin Alhaji ne ya shigo office din tare da wata mata a bayan shi. Yana ganin su ya kara daure fuskan shi tare da amsa masu sallaman su wuri suka samu suka zauna tare da fara gaida shi hakan yasa ya aje aikin da yake a lokacin yana fuskatar su. Bayan sun gama gaisawa ne mutumin ya fara magana da cewa yau ma gamu mun dawo gare ka bayan wahalan da mukasha kafin mu iso gare ka. Cikin daga hannu ya dakatar da mutumin ga maganan da ya fara yace Alhaji na fada ma wanan business din ba zai yuyu ba tun farko. Ba haka muke sake fili ga mutanen da basu san darahan shi ba suna gina abinda suka ga dama a cikin gari. Mutumin yace ba zancen gina wancen company a yanzu gare mu ni buri na kawai a yanzu shi ne in mallaki filin nan isan yana a matsayin nawa ne. Zan baka ko nawa kake bukata muddin zaka yarda ka saka min hannu in malaki daga milayan daya har zuwa hamsin zan baka idan kana so don wallahi ina , , , , , Table di gaban shi ya buga tare da mikewa tsaye yace na fada maka tun farko ba haka nake aikina ba kada kayi tsamanin da cin hanci ire iren ku na dogara. Ina da abinda zanyi a wuni daya million dari ya shigo min a accout dina ba tare da nasha wani wahala ba nafison in ci halan dina da na tsaya amsan cin hancin ire iren mutane irin ku. Matar ne ra katse shi da cewa ba wai cin hanci muka kawo maka ba kanina ka sani gogi bai ki kari ba balle mutum mai lalura da jama, a irin ki ko yaushe. Ina son ki sani wani gogin ne ke son kari wani ko an zuba mai wani ruwan aman shi yake yi don ba wurin zaman shi yazo ba. Don haka na roke ki ku fita min office yanzu ina da abubuwan yi a gabana da yawa da zanyi kada ku bata min lokaci. Matar zatai magana don ranta ya gama baci a lokacin mutumin ya daga mata hannu yace barshi mu tafi Allah ya bashi hakkuri bata mai rai da muka. Ya mike yana fadin mun barka lafiya sai dai ka sanin haka ba zai sani fushi dakai ba don abinda nake so nake nema a gare ka. Kuma ka sani ni ma ba irin mutanen ne da kake zargin suna sayen filin gwanati su gina abinda bai dace ba dashi nima kamar yadda zuciyar ka yake fari a kan kasan ka haka nawa zuciyar yake fes ga komai. Do haka mun barka lafiya matar tace bai kamata kana saurin yanke hukunci haka ba akan abinda bakai bincike akan shi ba. Binsu yayi da kallo har suka fice a office din nashi wani iri tsuki yaja tare da dafe kan shi da hannu shi daya yana fadin wai may mutane yanzu suke daukan kan su ne ? Yana jan tsuki tare da bude file din gaban shi yana gyara zaman shi da kyau Yusuf ne ya turo kofan ya shigo da sallama ciki. Tun daga nesa yake kallon yanayi abokin nashi yace may kuma akayi naga yanzu yanzu ka sauya gaba daya mana ? Bai yi magana ba sai duban files din yaci gaba dayi wuri Yusuf din ya samu ya zauna yana fuskanta abokin nashi tare da kara maimaita tambayan shi gare shi. Yace wanan mutumin mai bakin nacin tsiya akan sai ta mallaki filin da yake so mu bashi ne ya sake zuwa yanzu tare da wata mace dake son karanto min hauka. Wai har ni zasuce zasu iya ba daga million daya zuwa dari don dun mai dani mubukaci ban san ciwon kaina ba ko may ? No ba haka bane wasu ne ke bata wasu ga alumma shiyasa suke daukan haka ga kowa idan da sun san ko kai waye da ba zai tunkare ka da wanan zancen ba. Kai din ne ka faye boyon kurwa ga jamma, a kaki fitar da kan ka fili mutane sunan kokai waye may zai hana irin mutanen bazasu dinga tunkaran ka da suna baka ci hanci ba ko yaushe. Murmushi ya sake a fuskan shi yace dole ne sai na fito na nuna ma duniya ko ni waye san nan zasu sani kana ganin ko a gidana da matsalar Nafisa kawai bai isheni ba yanzu. Ni ba wanan ba ma gida nake son ka sama mun mai dakuna da yawa inda zan sai wa yan uwata su koma nagaji da zaman da suke min a gida na wallahi. Mutum da gidan shi baida halin ya huta yaji dadin gidan nashi sai a hana shi shaka wanan abin yana damun raina sosai wallahi. Ya zakayi abinne sai hakkuri tunda yan uwar matakar ce kaga ko don yar uwasu zasu zo gidan da son ka ko ba da son ka ba. Iska ya furzo daga bakin shi tare da ci gaba da aikin shi yayin da Yusuf yake dan tunane a zaune a gaban shi. Can ya dago kai yace ina ganin fa hutun su khadija ya kare don haka nake ganin tana garin nan duk yadda akayi yanzu ta dawo school din. Ummm nima abinda nake tunane ke nan do hutun su ya kare ai ita ba zata iya neman mutane a ida take ba tana jira a nemay ta ko ? A, a kaiko yaya zata nemay ka kafa san halin mata da jan ajin su ko yaushe aji kawai take ja muna ita ma a matsayin ta na mace. Ashe ko zata tsunke idan nine ya fadi ba tare da ya dago kanshi ba ya kalli Yusuf din dariya Yusuf yayi yace idan bata tsunke ba kai ai zaka tsuke din. Nayi mamaki da tunda muka dawo ka daina maganan khadijan amma acan kusan kullun kana min zancen ta har ina jin dadin ta shiga ranka yanzu ashe abin ba haka yake ba a gurin ka ban sani ba ? Au so kake banda aikin yi sai na ta yanzu kai ni fa tunda yanzu muna lafiya da Nafisa wani batun karama kaina wahala ya kawu min a zuciya. Ban gane may kake nufi ba yace Yusuf amma dai kaga aiki nakeyi ko yana mikewa yake fadin nagani barin baka wuri ka taba aikin ka. Har ya mike yake fadin ina son ka turawa Fati kudin da ta bukata na bukin da suke dashi don jiya take fada min bukin ya gabato. Kallon shi Yusuf yayi yace baka fada min nawa zan tura mata ba and kuma ina ganin ya dace ka tura ma da wanda zasuyi suturan fita bukin dashi. Katura mata biyar dakomai da komai don saboda laluran yara idan zai ishesu dariya Yusuf yayi yace indai fati ne ko bai isa ba baka jin korafin ta akai shiya nake ganin zubin su daya da khadija wallahi a wani gu. Baiyi magana ba sai murmushin da yayi a baiyane tare da fadin yar matsala wai ita a dole fushi take ba a kulata ba. Mata idan suka samu guri sai so wuce limit din su akai ni dake da mata biyu wata mace zata tsaya jawa rai a waje yanzu ? Fita Yusuf yayi yana mashi dariya tare da fadin ni dai nasan yanzu akwai nadi a lauje muje zuwa dai a hakan . Kwance nake a dakina ina so in huta don yau a gajiye nake ga test ga pratical da muka fita da rana maryam ce ta shigo dakin tana fadin malama tashi zakiyi fa mu fita. Don har kayan miya nake son mu sayo kin ce kuma kina son kayan make-up ke ma da sauran abubuwan bukatan ki. Wani kallo nayi mata nace cabdi jam a yanzu yadda nake din nan don Allah ki tafi ki dawo yau na gaji wallahi sosai maryam. Ke ma kin san dole zaki tashi mu tafi don yau kadai kike free kara kwantawa nayi na fita batun ta tana ta shirin ta har na fara barci sai naji takai min doka a baya. A zabure na mike tana fadin don Allah tashi muje khadija kada ki bata muna lokaci mana nace maryam ba zaki barni in huta ba don Allah wallahi na gaji ne yau. Matsa min tayi dole na mike na fara shiri ba don naso ba dogon riga na saka kaman kullun don sune kayana ko atamfa zan dinka nafi inyi dogon riga dashi yanzu nafi sakewa a cikin shi. Mun fito maikon mu tsaye kusa sai da ta jamu zuwa ciki gari a shagon da take ganin zamu samu kaya da sauki a gurin. Raina na bata ina fadin ni ban iya wahalan ki wallahi shiyasa nace kizo ke daya don ban iya wanan wahala saboda son banza zaki jawo mu zuwa nan. Dariya take min tace kin dai riga da kin fito yanzu sai yadda nayi dake kuma ai shagon babbane so sai kaya iri iri ne a cikin sa . Binta nake a baya kamar dole banko iya magana don gajiyan da nake ji din ta sai wanan ta dauki wancan. Wani set din kaya make-up na gani mai kyau na mika hannu zan dauka naga hannun wata mace ta mika itama zata dauka. Duk tare da ita muka dauka a lokaci guda na juyo ina kallon ta Nafisa ce a baya na ta ke daukan set din ita ma nace cikin wani irin murya sake don na rigaki dauka. Nawa gare ki da zaki biya wanan make up din halan ta na shirin bangajeni ta dauka na riga ta rike kit diin nace don Allah ban wuri malama. Baki isa ba mara kunyar banza nace marasa kunya din ke wacece da zan dauki abu kice wai na bar maki kamshin turaren shine naji a hancina yana fadin may ke faruwa ne Nafisa ke da waye kuma ? Yana tsaye bayan ta rungumay da yarsu a kafadan shi tana barci tace dashi cikin zafin rai wanan mara kunyar mana tana ganin ina da raayi abu kuma zata sa wani kazamin hannun ta ta dauka. Bar mata mana tunda ta riga ta daukan wanan ba sai a kawo maki wani ba tunda baza su rashi ba anan din . Haba malam yaya zan ce ina son abu sai kace wai in bar mata ita wacece da zan bar mata murmushi nayi nace au shagon dama na gidan ku ne ashe. Maryam ne ta iso take tambaya ganin shi kuma sai duk ta daburce tana gaida shi tare da gaida nafisa wace ke ta kunduma ashar a bakin ta. Nace da maryam muje ko ban tsaya kulataba na raba su na wuce maryam ta biyo ni baya duk a tsure take bamu tsaya magana ba muka mika kayan wurin biya suma a lokacin suka iso gurin biyan kudi yace hada kudin da nasu ka cire a katina lokacin nafisa ta iso ta samay shi tace dani. Karya kike yarinya zanyi magananin ki a garin nan dani kike wasa wallahi nace kafin kiyi magani na ni zan fara yin naki a garin nan na watsa masu harara har mijin nata naja hannun maryam muka tafi. Bayan mun fito muna saman titi da maryam muna jiran abin hawa sai ga su sun fito daga cikin shagon suma suka shiga wata hadadiyar motar su a gaban mu ta leko glass din motar tana fadin matsiyaciya ko mota ashe baku da. Tsawa mukaji ya daga mata tare da fadin wai manene haka nafisa ya ja motar da karfi suka bar gurin tsuki naja gami da harara na raka su dashi. Maryam tace yau naji takacin barin mota na a gida wallahi da dashi muke wanan matar bata isa tayi muna haka ba. Nace au ke kin damune da maganan ta ita uban wa ya bata motar gidan su badai da namijin nata take barazana ba. Matar nan lallai bata da hankali khadija jifa yadda take abu kamar wata yar bariki can nace guri ta samu tayi abinta amma ni bata isa ta fada mi in kyale ta ba. A can kuma cikin motar su fadi Nafisa keyi wai ni ina ma nasan wanan fuskan ne na mance ida nasan wanan yarinyar wallahi ? Bai mata magana ba sai tukin motan shi yake yi shi kadai yasan abinda yake ji a ranshi a lokacin wai a haka zai hada wa yan nan yan zafin rai guri guda. Tace wai ashe ba yarinyar nan bace kuwa sai kuma tacce ba ita bace don waccan bata waye haka ba koma waye taci bashi wallahi in dai nice zamu hadu wata rana ai zata raina kan ta. Tana takama don tana da kyau da diri wa zata nunawa kyau da fari anan kai dake dani a gida tana ganin kyauta zai rude kane take wani far da idanuwan ta haka. Murmushi ya danyi cikin kunan rai tare da fadin ki san abinda zaki fadawa mutane don baki san ko ita din waye ba a garin nan kizo ki jawo wa kanki matsala wata rana. Maryam ke ta zuba a mota nace please maryam ki rabani da maganar wanan matar mara mutunci wallahi sai na gwada mata ita karamar yar iska ne daga yau . Ni fa laifin ki nake gani da kika bata wanan daman take ganin ita wata tsiyace da kin jaye hankalin mijin ta ai da zata gane bata da wayo. Nace cikin mata wani iri kallo wani mijin kike magana badai wanan mijin da baida ta cewa ba a gaban matar shi kike nufin in sace zuciyar shi in kai ina idan na sace ga mai iko da zuciyar shi kina gani. Jifa yadda yau ya nuna bai sanmu ba a gaban ta kwata kwata wallahi saboda tsoron mace da yakeyi. Ta kada kai tana fadin wallahi ba tsoro bane mutunta matar shi ce kawai yayi kuma ko wani namiji ne ma haka zai yi ai a gaban kowa. Don dai kawai a zauna lafiya amma da gidan shi kike yai haka shine zakice wani abu kyale ta nayi don ina ganin don ba ita akaiwa hakan ba yasa take fadin hakan. Har muka isa hostel din ba wanda yayi magana da dan uwa wanka nashiga na fito da alwalana na tayar da sallah ina gamawa na kwanta tare da bata baya . Muryan ta naji tana fadin bazaki ci komai ba ke na kike nufi zaki kwanta yanzu banjin cin komai murmushi tayi tare da fadin . Ai ba haka ya kamata ki bullo mata ba da fushi da abinci don ita ko shi basu ma san kina yi ba ai yanzu wallahi khadija lokaci yayi da zaki falka daga barcin da kike yi. Kamar yaya na katse ta tare da juyowa ina fuskantan ta nace may kike son in yi mata tace wallahi ki cusa kanki ga A A shine mafita a gareki. Kaina girgiza nace haba maryam wanan zubar da ajin kike son inyi komay kuma ni nasha fada maki ban ra, ayin wanan A A din sam. Tace ko baki son shi ki girgiza buzuwan nan don Allah tasan shayi ma ruwa ne ba ita kadai bace mace a duniya har duniya ta kare akwai mata kyawawa a duniya. Nasan wallahi kyau ki da zatin ki kadai ya ishe ta ballw uwa uba karatu da kike dashi wanda nasan ko bokon primary ita batayi ba kila acan . Dama na farko da zaki fara nuna mata kai tsaye shine gorin motar da taimaki kona kwana gudane kice mashi mota kike so anan zamu gane idan yana son ki sai muci gaba da aiwatar da shirin mu akanta sannu a hankali. Kallon ta nayi wani iri nace mota fa kika ce maryam ina zankai mota tace baki zaiyi kai tsaye akace maki balle ki damu. Fada mai hakan kawai zakiyi don mu gani kina da tasiri a gurin shi ko baki dashi ajiyan zuciya na sauke tare da fadin zan gwada in gani to. Har na kwanta kuma na juyo nace mata maryam idan ya bani motar fa ai na kashe kaina a gurin iyayyena wallahi. Kyautan mota wasa ne khadija ai ba baki zaiyi ba kai tsaye anan kin ga zamu san abin yi kuma nace to shike nan tunda haka kika ce tare da juya mata baya. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Tun bayan rabuwan mu dashi ban kara jin labatjn su ba haka yasa nasan sun tafi ke nan tun tafiyan su kuma ban sake ji daga gare su ba bakuma labarin mamud. Duk da son mamud da nake a zuciya na yanzu na fara fitar dashi a raina don na fahinci ba wani son gaskiya yake min ba . A cikin haka muka gama exam din mu na wanan zangon kaduna ya kamata in tafi amma don gudun haduwa da mommy a can yasa na kekeshe kasa nace ma Ya Amina ba zan tafi can ba gida nake son yin hutu dole ta kyale ni don tasan tunda nace haka ba zan zo ba. Tunda na dawo gida in ba islamiya ba ban fita ko ina don haka ba kowa ne yasan ina garin ba yau satina biyu da zuwa gida na shirya zuwa gidan anty mu dake aure a falamingo easthe. Tare da karamin kanina muka fito daga gida mun zo bakin titi inda zamu tare Napep din da zai kai mu unguwar nasu mun dan tsaya a gurin na hango wata mota daga can gefe tafe. Zuwa mai shi yayi roud ya dawo inda muke tsaye da kanina a hankali yazo inda muke tsaye ya tsaya ban daga kai na kalle shi ba wata taxis tazo tana tambayan inda zamu. Sai lokacin na cikin motar yace wai ba khadija bace wanan a hankali na dago ina kallon shi mamud ne ya kara yin fresh dashi har bakin shi na sheki. Ya samu wuri ya parka motar shi da kyau ya fito daga cikin motar zuwa inda muke tsaye tare da fadin hajiya khadija ke nan ashe kin shigo garin namu. Nadan yi murmushi nace mamud manya ashe kuna kasan na dauka baka kasan murmushi yayi yana fadin i am sorry wallahi na bar Abuja ban samu leka wuri ki ba sai yanzu gashi mun hadu. Mun gaisa duk da ban wani sake mai fuska ba sai kame kamay yakeyi yace ya labari nace kai za a tambaya kai dana ga sauyi a tare da kai. Yace sauyi gare ni ko a gare ki jifa yadda kika koma dan kwana biyun nan danayi ban ganki ba kin koma wata danya dake kamar wata diyan larabawa wai ma ko kina karatu kuwa ? Dariya nayi nace kai mamud bari bani dariya haka akan titi muke fa yace haka fa ina zaku naga kamar mota kuke jira nan. Filamingo easthe zamu na fada kai tsaye yace muje in sauke ku nace ka barshi kawai zamu samu taxi anan yanzu . A a khadija kada muyi dake please ai ko ba siyasa akwai daga hannu ko dariya nayi nace ashe dai hausa ya zauna a bakin ka haka ? Yana dariya muka taka zuwa bakin motar shi ya bude min gaba na shiga ya bude baya mansur ya shiga ya zagayo ya shiga mazaunin driver ya fara tuki. Mun dau hanya yace van san yaya zan fara maki bayani ba ma sai dai da farko na gode da kika fahince ni har baki nuna min komai ba haka. May kake son in nuna maka gudu da kayi daga wuri na ko may yace wallahi khadija ba laifi na bane ba naki bane. Laifin waye na tambaye shi cikin kallon fuskan shi yace ba zaki gane bane khadija amma tunda kina gari zanzo har gida in maki bayanin komai. Nace kasan gidan mu ne yace zandai sani yanzu daga bakin ki idan kin bani dama can kuma yace gaskiya khadija kin kara wani itin kyau da girma a lokaci daya. Nace kai mamud wanda ke karatun wahala kake fadan haka gareshi dan kallo na yayi yace kin ko ga yadda kika koma kuwa ? Ina dariya na kalle shi nace yaya na koma kuma ya dan bugi sitiyarin motar da hannun shi yace I don't know how to say. Amma ai kema kin san kin sake gaba daya wallahi nace dama ance ku Nufawa mayu ne to kurwa na kur kada ku cinye ni. Dariya yayi sosai yace amma kin kusa gama karatun naki ko yanzu dariya abin na mamud ke bani don na gane nufin shi sarai. Katse shi nayi da fadin ina madam din ka ya fadada murmushin shi yace yaya akayi ki san ina da aure yanzu ? Nace tambayan ka ai nayi suna lafiya yace lafiyan su kalau wallahi daidai lokacin muka shigo Filamingo din da kwatance har muka iso kofan su antyn nawa. Godiya nayi mashi ina bude kofan motar yace khadija na juyo ina kallon shi cikin jan aji yace wani time zaki koma gida inzo in dauke ku ? No ka barshi kawai mun gode da hakan sai anjima nafita daga motar Mansur kanina ya kira yasa hannu a aljihun shi ya ciro kudi ya ba yaron ya tafi bayan yayi min horn. Gidan Ya Hauwa muka shiga da sallama na bude labule falon su da danta babba na fara cin karo zai fito yana ganin mu ya saki ihu yana fadin ga mommy khadi . Murmushi nayi ina kamo shi nace Lawal kaine ka girma haka ina yan uwan ka yace suna ciki jin ihun yaron yasa Ya Hauwa ta fito daga kitchen din su tana fadin sai yau kika ga daman zuwa gidan mu ? Haba dai ya hauwa kema kin san ba halina bane haka na dawo da gajiyan karatu ne wanan karon na dan tsaya in huta. Mansur ne ya gaida ita tace a a mansur tare kuke tafe da antyn naka ashe nace ai kin san mutumi nane shi nan dai muka zauna a falon shi wanda ke bukatan gyara ba halin yin hakan gare su don yanayi. Ranan ni na girka masu abincin rana a gidan yaran suna ta murnan kasancewa tare da mu bayan na gama na gyara mata gida don haka take ba gwanan gyara bace ita amma idan ka ganta a waje sai ka dauka ko agidan ta haka take da tsabta. Ranan sai magariba muka koma koma gida na samu daddy yana fadan rashin dawowan mu da wuri gida. Muna shiga ya mayar da fadan da yake wa mama akan mu may yasa na bari nakai wanan lokacin ban dawo gida ba idan na fita kada in kara kai dare haka bamu dawo gida ba . Kaina yana sunkuye a kasa na amsa da toh daddy daga haka ya fita daga gidan rai bace buta na dauka naje na kewaya na dawo na daura alwala don har an sallamay sallah a lokacin. Sai da na idar da sallah na gaida mama da gida da take dakin ta zaune saman sallaya tana jan tasbaha. Tace khadija may yasa kuka kai wanan lokacin a waje haka kika bari har magariba yayi maku a waje haka baki san fita a wanan lokacin baida kyau ba. Mama kuyi hakkuri ba zan kara kai haka ba tsayawa nayi gyara ma ya hauwa gida shine yasa mukai wanan lokacin a can . Tsuki tayi tana kawar da kanta tare da fadin ita ke nan malalaciya bata iya gyaran gida kullun sai dai ai mata ina amfanin a ganta a waje fes amma a gidan ta baya kalluwa. Ban san inda ta dauko wanan hakin nata ba nidai nasan na koyar daku abinda ya dace koda kun kama dakin ku zaku iya kulawa dayi amma sai dai kayya bata dauki wanan tarbiyan dana baku ba ita. Wanka nashiga don inji dadin kwaciya saboda yau na aikatu a gidan yar uwar tawa bayan na fito na tayar da sallah isha,i mama ta turu yaro wai idan na gama inje in debi abinci nace a koshe nake munci abinci gidan ya hauwa kafin mu dawo gida. Wani yaro ne ya shigo yana sallama da bazan iya sheda muryan yaron ba yana fadin wai ana sallama da khadija a waje. Da mamaki daga cikin dakin da nake, nake tambayan yaron ko waye yace shima zai wuce ne ya aiko shi don haka bai san ko waye ba. Jekace dashi tayi barci yaron ya fita can sai gashi ya dawo yana fadi cikin daga murya wai yace kiyi hakkuri kizo minti biyu . Na fito daga dakin ina fadin bana ce kace dashi nayi barci bane yaron yace na fada mashi yace indawo in fada maki haka. Zan sake magana mama tace da yaron ya tafi ganin nan zuwa tace kije giga kowaye kin san damay yazo gurin ki wulakamci bai da kyau ina fada maku. Hijjab na dauko na aza saman rigar dake jikina na fita tun daga nisa na gane motar mamud ta dazun da ya dauke mu dashi. Mamakin abinda ya kawo shi nake yi da wanda ya nuna mashi gidan namu yazo yana ganina ya fito daga motar zuwa guri na. Bayan mun gaisa ne yace kin yi mamakin hani na yanzu ko nace kwarai kuwa yace to kibar mamaki don abin jiya na dawo maki dashi. Da sauri nace meke nan sai da yayi murmyshi yace khadija ke nan So mana da kaunar ki khadija don tun dazun dana ganki na kasa natsuwa tundazu na kasa control din kaina akan ki abin ya dawo min sabo yanzu a raina. Mamud ke nan abinda ya wuce ai ya riga da ya tafi don ni kuma sai naji yanzu sam baka kwanta min ba a raina. Da sauri yace saboda may khadija nace halinka bai mun a yanzu don ba zan kara yarda ka sa min miki a zuciya ba. Kasan ina son ka da farko mamud sai da ka bari na gama yarda dakai ka gudu ka barni babu bayanin komai daga gare ka Allah ya taimake ni, ni ba mai sa abu ga zuciyana bane . Khadija ba haka na bane wallahi don koda muke tare dake already ina da mata karawa nake son yi sai kuma naje ma iyayyena da maganan ki amma sukaki banin goyon bayan haka don basu son in auri wace ba yaren mu ba. Kin ga kuma bazanki maganan iyayye na ba sai naji kunyan komawa gare ki in maki bayanin halin da nake ciki . Katse shi nayi da fadin basu sona yanzu may kadawo yi wuri na kuma yace ina da daman yanzu in zabi wace nake so tunda ina da yaren mu mutum biyu . Kai na girgiza tare da fadin mamud kasan tun farko ban kika ba kai da kanka ka guje ni yanzun kuma baka da bakin cewa ka dawo gare ni. Ko banza na farko ba zan shiga inda ba a sona ba sai na biyu yanzu ni mai zai kaini wurin mai mata biyu in ba daukan magana ba. Dariya yayi a lokacin tare da fadin khadija ke nan watau kin mayar da laifin a gare ni ni daya to naji na dauka kuma ki kwantar da hankalin ki ba a gida daya zan ajeki dasu ba. Don haka ai min hakkuri muci gaba kamar yadda muke da don son ki yana son ya min illa a rayuwana. Mamud gaskiya sai dai kayi hakkuri don ba zan iya ba yanzu gidan ka yafi karfi na da sauri yace what ? Nace yes I mean it don bazan dauki wanan risk din ba da hankali na ina ji ina gani. Shiru yadan yi na dan wani lokaci kafin ya dago kai yace is ok naji amma zaki yarda ina kawo maki ziyara lokaci lokaci don ban sani ba koda rabo na ciki. Dadai kayi hakkurin kamar yadda nace dakai zafi kyau don ban son ka dinga wahal da kan ka yace ke kika dauke shi a wahala. Ni abinda nake so ne na damu dashi don haka ban hakkura ba ki sani nace wanan kuma matsalar kace ni dai na fada ma gaskiya. Bai dade ba mukayi sallama ya tafi na shigo gida alwala nayi na gabatar da shafa,i da wuturi na samu wuri na kwanta. Amma ranan sai barci ya gagari idona saboda tunanen dayayi min yawa a lokacin a raina nace ohh ni khadija haka rayuwa zai kasance kuma sai masu mata ne ke zuwa ne mana ni ban san ko may yakawo haka ba gare ni. Gashi ni kuma banda sha,awan auren namiji mai mata don ban son yawan fitina daga anayi a gidajen masu mata nasan da laifi nane kin kula samari amma yanzu ban san dalilin rashin samun su ba, da haka har barci ya dauke ni ban sani ba. Matafiya umurah sun sauka lafiya don haka yan uwa da abokan arziki suke shigowa gaida shi gidan shi wanda ba wasu mutane ke zuwa ba don sanin hslin matar gidan da sukayi sai wa yan da ya zama ma dole sai sun zo ke zuwa gaida shi. Bata san cewa Fati ta koma dakin ta ba sai a bakin wani abokin shi da yazo yana mashi sherin yaushe zai leka can kaduna yaji ance fati na gidan shi yanzu. Wani kallon mamaki ta aikawa AA din sai da yasha jinin jikin shi don yasan akwai rikici babba yau a tsakanin su dakewa yayi kamar bai ganta ba yaci gaba da hira da abokin shi. Sai dai hankalin shi yana gurin ta duk abinda yake yi din bayan tafiyan mutumin tun a falo ta fara tambayan shi Fati ta dawo gidan ka ne baka fada min ba. Yace ta dawo suna nan gida yanzu haka shewa tayi tare da mikewa tsaye tana fadin haukan banza ke nan yadda ta dawo haka zata koma inda ta fito. Wanan kuma maganan ki ne don dama ai ba wanda ya kore ta ita da kanta taga daman fita yanzu kuma ta dawo tace ashe ko zamu zuba daku mugani a gidan nan. Ke ban fa son haukan naki na bazan Fati bakuwa ce a gare ki ko yanzu ne na fara zama da ita zaman ki na nan Abuja ita kuma yanzu bayan shekaru ta zabi zama kaduna ita da diyan ta. Don haka ban son jaye jayen wani matsala kima da zai kawo muna tashin hankali ba gaira ba dalili haka, Yana fadin haka ya mike ya haura sama ya barta a falon cike da mamaki halin irin na Nafisa da bata iya boye kishin ta . Satin shi biyu abuja yana hutawa ya kama hanyan zuwa kaduna gida don ya hana kowa yazo daga can yace yana nan tafe. Nafisa bata yarda cewa iyayyen shi zai tafi gani ba ta shirya wai tare zasu tafi ba yadda ya iya dole a tare da ita yayi tafiyan. Tunda suka shiga garin ta hana komai a tsakanin shi da Fati din bayan gaisuwa bata yarda komai ya kara hada suba don ko abinci da Fati ta gama sai cewa nafisa tayi abincin yayi mai nauyi ba zai ci ba. Suna zaune da dare ta na kokarin hana shi shiga wurin Fati da kissa da iyayi wayan hajiya mama ya shigo mashi nasiha tayi mai sosai wanda ya kashe mai jiki inda take mai tuni da cewa ya tuna hakkin ko wace yana a kanshi do haka ya daure yana ba kowa hakkin ta. Bayan sun gama waya ne da mahafiyar shi bai wani dauki lokaci taga ya mike da sauri take tambayan shi ina zai tafi kuma. Kai tsaye yace mata gun Fati zan tafi bata iya boye bacin ranta ba ko kadan tace bai isa ba don tare suka zo fati ta bari idan bai zo da ita ba sai ta kwana dashi. Yace a garin ku haka akeyi wanan dokan hakan wai Nafisa may kika dauke ni kamar wace ta haife ni zaki dinga bani umurni kai tsaye. Ba sake kula ta ba ya shige sashen Fatin kamar yadda yayi tsamani hakan ya samay ta sunyi barci da yaranta a saman gadon dakin ta tana saye da kayan data wuni dashi a jikin ta tunda suka zo, Ya dade tsaye a kansu bata san ya shigo dakin ba sai da ya dan bubuga mata kafa ta falka ina zan kwanta yace da ita kai tsaye dan watsake idon ta takeyi daga nauyin barcin da ya fara kama idon ta din. Sai can tace dakin ka fa yace Nafisa na cikin dakin kin sani mikewa tayi tana gyara ma yaran kwanciya tare da gyara dan wurin da ta bar mashi ya kwanta. Kallon ta yayi daga inda yake tsaye yana tambayan ta wai dakin su fa da kika dawo da kwanan su nan kamar ba zata bashi amsa ba sai can tace ban san anan zaka kwana ba ai tare muke kwana tunda ba kowa a gidan. Tsuki yayi yana hawowa gadon ya takure kan shi a guri daya kamar may kyankyamin dakin amma kin san hakan ba daidai bane nasha fada maki haka kwana da yara a daki daya. Banza tayi dashi ba wai banzan bane ya sani halin ta daine nakasa da kyaluwa haka take kindis da ita ko yaushe fuska ba fara, a. Tunda ya samu barci ya dauke shi bai falka ba sai karfe hudu da rabi na asuba da bugun kofar nafisa ke masu ya tayar dashi a firgice. Tambaya yayi yana zura riga a jikin shi tace itace ya bude kofan ya bude da mamakon ta a fuskan shi yana tambaya lafiya take cewa dashi. Banan ce bata da lafiya basuyi barci ba kallon yarinyar dake sabale a kafadan ta yayi tare da fadin ta miko mashi ita. Sai da tayi mai wani kallo tace ka karasa fitowa daga dakin mana murmushiin gefen fuska ya sauke kafin ya fito din muryam Fatine take tambayan make damun yarinyar ne ? Kada ki soma ki taba min ya ta yanzu ranki ya baci a gidan nan tana fadi tare da watsa mata harara da saida taja jikin ta ta koma daga bayan shi. Karban yarinyar yayi ya nufi falon kasa da ita suna biye a bayan shi dukan su ruwa ya fara ba yarinyar tasha sosai tare da ajiyan zuciya ta lafe a jikin shi. Dakin da bai koma ba ke nan ya zauna nan falo da yarinyar data koma barci a jikin shi tana sauke ajiyan zuciya . Juyawa fati tayi ta koma dakin ta don ta san kadan ne daga cikin sherin Nafisa ko ba yarinya a tsakanin su haka take masu idan zai kwana a dakin Fati din tace bata da lafiya karshe a dakin ta zai kwana. Do haka ta juya abinta taje ta kwanta bata kara ganin shi ba har rana breakfast din da ta hada mai baci ba wani aka kawo masu daga gidan Auta amiyar Nafisa din. Haka fati tayi ta hadiyan bakin ciki da wanan zuwan nasu ita da ganin miji sai dare idan zai kwanta zai lalabo ya dawo dakin ya kwanta da safe ya fice kuma ranan nafisa tace itace zatai girki . Dole Fati ta kyaleta tayi yadda ranta ke so tunda har mijin ma ya biye mata ita yanzu burin ta shine ta zauna a cikin yaranta kawai su girma a tare da ita. Nafisa bata shiga gaida sarakkanta ba balle suga yar jikan tasu data haifa da dan su sau daya ta shiga gaidasu ana gobe zata koma bata ba kowa yar ta ba suma basu taya zasu dauka ba. Sai kuma abin ya bata mata rai don yadda ta shirya bata samu yi ba sai taji haushin basar da ita da sukayi takoma fadin wai yanzu har kiyayyan da suke mata ya shafi yar ta jikan su. Haka ya sa AA yaji haushin abinda sukai mata a ranshi har ya kira mommy yana fada mata abinda sukaiwa Nafisa da yar shi baiji dadin hakan ba. Don ba halin ya kira mahaifiyar shi ya fada mata yasan kwanan wasa yanzu za a jisu da ita idan ta fara mai fada yasa shi kiran mommy. Mommy tace dashi babangida kasan halin matar ka fa ta make yarta a jikin ta bata ba kowa ba mune zamu karba tai muna wullakanci amma munyi kuskure gaba zamu gyara insha Allahu. Bayan kwana hudu suka nada suka koma abuja tun da suka kama hanya ta washe ranta da ya rasa gane mata da suke a kadunan. Yanzu ko kamar ba ita ba sai hira take jan shi a motar tana faman dariya tana kuma wasa da yar dake zaune a cinyar baban ta din. Tunda ya dawo ta samu kansa da kyau sai dai abinda bata sani ba yanzu asiri bai faye tasiri ya dauki lokaci a jikin shi don maganin tsarin da malam na zaria ya bashi. Kuma abokin shi Yusuf bai zauna ba akan shi yana tsaye da alamarin shi haka ma mahaifan shi suna tsaye da mashi addua sosai yanzu. Yau tunda na dawo daga islamiya nake kwance ba wai don banda lafiya ba sai dai ina jin jikina ba dadi ne ko aikin gida da nake taya mama ban iya tayata yi ba. Barci nayi sosai a ranan can zuwa rana yaro ya shigo yana fadin ana sallama dani a waje mama ta shigo ta tadani tana fadin min wai ina da bako a waje. Mikewa nayi da kyar don barcin dake idona na ban tsaya gyara fuskana ba na fita daga gidan haka na mamud ne zaune a motar shi da yaran shi biyu. Na iso inda suke ina gaida shi bayan motan na bude inda yaran suke zauna kafa na suna waje ina gaidasu tare da tambaya su yaya makaranta. Kafin yaran su bani amsa ya jefo min tambaya yaya naga fuskan ki haka kuma ko baki da lafiya ne ya tambaya ? Nace daga barci na tashi yanzu ba tare dana kalle shi ba hannu na mika wa yar karamar yarinya dake saye a cikin uniform din shekk lemo sai yarinyar ta noke taki zuwa. Tambayar ta nayi yaya sunan ta yace sadika dayan kuma nasir ina taba kafar yarinyar nace zakici biscut ta daga min kai nace to sai kinzo wurina sai ta kara makewa. Ina zuwa nace dashi cikina koma na hado masu kayan kwalama na yara wanda na dawo dashi muna ci da kanne na nafito rike da leda a hannuna namikawa yaran. Da sauri suka karba nan dai muka taba dan hira yace zai maida yaran gida daga islamiya ya dauko su mukai sallama ya tafi. Bayan sun isa ma sai da ya kirani muka taba hira ya kashe wayan tare da fadin zai zo amsa gudane wurina nace na hutar dakai kada ka wahal da kan ka. Yace to zamuyi waya nace sai najika aiki gida na taya mama ta koma folo tana kallo sai dana gama zuwa dare na shiga daki na samu wayan mamud har six miscall ya kira ban dauka ba. Kiran layin shi nayi aka dauka ban tsaya sauraren ba nace ina waje ne ina aiki banga kiran ka ba. Ban karasa magana na ba naji muryan mace tana fadin ke wacece da zaki kira lamban mijina kin san ko waye mamud kuwa ? To bari kiji daga yau kada ki sake shiga harkan mijina in ba haka ba zan sa ayi maganin ki a garin nan shiru nayi ina sauraren ta sai da ta gama nace. Ke kuma wacecd a guri mamud din bari ki ji ki sani ba don ki ke kadai akayi shi ba daga yau ki gyara kalamin ki inzaki magana akan shi ki dinga cewa mijin mu. Ina fadin haka ban tsaya jin haukanta ba na kashe wayan ina dariya nace banza mahaukaciya ni mijin ki bai a gaba na yanzu da kin ga tsiya wallahi. Bai kirani ba nima ban kirashi ba sai bayan kwana biyu sai gashi ya aiko kirana wai ace mamud ne mace ace ban samun fitowa aiki nake yi. Mamace ta samin baki dole na fita naci karo da dan aiken ya dawo wai yace don Allah inyi hakkuri minti biyu kawai zanyi. Tare muka koma da dan sakon na samay shi zaune a cikin motar shi yana duban wayan shi karasowa na ya fito yana washe baki. Fuska na a daure na gaida shi magana yake na kyale shi sai ko umm ko ummumm nake bashi amsa dashi kaina a kasa ina dakilan wayana. Muryan shi naji yana fadin yau gimbiya may ya faru ne naga an fito min haka a daure nace wani abu ka gani halan ? Yadan motsa kafan shi kadan yana murmushi tare da harde hannayen shi guri daya yace ko gimbiyar tawa mulki take jine haka ? Sai da nayi mashi wani irin kallo shekeke nace mulki ai mulki yana gidan ka don ko wayan ka sai an baka izinin dauka kake dauka ko zuwa gurina yanzu waya sani ko santan hanya kayi kada matan ka su gani. A cikin rashin kuzariya dago kai yana kallona yace wanan wani irin magana ne haka khadija kikeyi kai tsaye ba tare da tunane ba. Nace irin wamda matar ka tayi min jiya daga kiran wayan ka ta dauka tana zagina a wayan ta daukar min waya fa kikace nace ka duba nan ga kirana a wayana kana gani katuna ina kaje jiya a daidai wanan lokacin ? Look mamud na fada ma soyayya dakai a yanzu akwai matsala ka nace akan sai munyi gashi tin ba a je ko ina ba an fara kirana ana zagina daga gidan ka har da yimin iyaka dakai. Ya kai duban shi gare ni tare da sake dan murmushi yace mai shi tayi nasara gare ki ke nan tunda gashi har kin karaya zaki bar mata ni. Haka muka kasance dashi muna musayan maganan karshe dai yaban hakkuri nace ya wuce amma ya daina zuwa wurina. Yace ba da sanin shi ba amaryan shi ce ta dauka daya shiga wanka kuma da ya fito bata nuna mashi akwai wani matsala ba. Nace wanan kai ta shafa ni dai na gama magana kuma. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Kawar da kaina nayi gefe kamar ban ganshi ba ko ban san shi ba karfin gudun ya rage ya dinga sarsarfa zuwa wurina yayin da ni kuma nake sauri in shige get din gidan Ya Amina din. Ke ji mana yace bai juyo ba sai saurin da nakeyi na kara harda dan gudu nashige ciki tsayawa yayi ya rike west din shi da hannun shi biyu yana dan murmushi. Yadda na shigo gidan kamar wacce aka koro yasa Ya Amina fadin ke lafiyan ki kuwa nace ina waigen kofan shigowa lafiya sauri nake na bar wayana daki. Ajiyan zuciya ta sauke ta kalli kofan sai ta juyo ta kalli inda na shiga ta tabe baki na dade a ciki zaune kafin in fito danaji shiru. Wanan kaaton da soja yaje daya fi mai yya more karfin shi a can nace ina dagawa wanka nayi na fito na shirya na fito falo. Na samu yaAmina bata falon sai gata ta fito daga uwar dakin ta tana fadin zan dan shiga gidan su mommy akwai aikin da zamuyi da safe nan kin san ance ka rama alheri ga mai maka. Dana haifi Na,ima mutanen nan baki ga irin alheri da sukai min ba wallahi banda abin basu in ba ta haka zan maryar masu da alherin su ba gare ni. Adawo lafiya nace mata ina lafewa saman kujera tare da danna wayana ta juyo tana fadin idan ban fito da wuri ba sai ki dora girkin abinda zamuci da rana kada bakuwan ki tazo ta samu ba abinci. A kwai komai a kitchen da zaki buka wanda babu ki buga min waya ko ki fita ki samu nan bakin layi sai kin dawo nace da ita tafice daga gidan. Ban dade ba barci mai nauyi ya dauke ni a guri firgigit na tashi daga zaune don mafalkin hajiya mama da nayi ta sani gaba tana min murmushi. Firgigita na falka daidai lokacin da ta mika hannu zata share min hawayen dake bin fuska na ina mamakin wanan mafalkin da nake yi tsakanin jiya da yau. Na dade zaune a gurin kafin in mike in shiga kitchen ban ankara ba ashe har shadayan rana ya gwauta ban sani ba a gurguje na dora muna girki ina yi ina duban time. Wayana naji yana ruri daga falon inda nasa chagi da sauri na nufi gurin maryam ne a layin na dauka ba ko sallama naji tana fadin wani unguwa zan ce a kawo ni nace GRA na fada mata sunan layin mu. Isowan ta yayi daidai da gama girki na na fito na tare ta a waje muka rungumay juna muna dariya tare da shigewa ciki sai bin gidan takeyi da kallo. Falo muka shiga na karbi jakkanta nakai dakina da na gyara na dawo falin ina dariya tambaya na tayi ina ya Amina nace humm kin san sune kan buki tun safe ta shiga wai aiki a family house din su AA. Nikan na matsu in san wanan uwar gidan nashi abin tausayi na kallo ta nace may abin tausayi a ciki an fada maki tana cikin wani hali ne ? Khadija labarin dasu Binta suka bamu nata ne ai matar abin tausayi ne wallahi malama kice dama gulma ya kawo ki ba taya zainab murna ba. Sannan ita fa Fatin nan halin tane haka shiyasa mutane suke mata kallon abin tausayi tana da sanyi hali da rashin nuna kulawa ga abu shiyasa mutane ke fadi haka. Amma ni ina ganin lafiya kalau take da mijin ta yanzu don ban kara jin wani maganan haushi ya faru ba koda yake idan ma ya faru ni ina zan sani. Mikewa nayi na shiga kitchen na fito mata da abinda zata ci mun dade muna hira har bayan azahar muka mike zuwa sallah. Ina idarwa wayana na karan kira ya shigo min na dauka da sauri Zainab ce a layin gaisawa mukayi take fadin khady har yanzu baki shigo ba mana bamu shirya komai ba fa ke ake jira. Nace gani nan da maryam ta iso dazun tana hutawa ne amma mai zai sa sai nazo kuyi duk abinda kuka ga ya dace mana zainab. Look indan ba zaki zo ba ni ganin nan zuwa dayani in gaida maryam da zuwa don binta sun fita sai kin zo din nace Allah ya gani yanzu kunyan shiga gidan su nakeyi. Ba a dauki lokaci mai tsawo ba sai gasu tare da Binta sun shigo da murna suna taron maryam din nace ga gandoki muje buki ta iso daga ina fata mata kawai tace gata nan zuwa ai. Wayan zainab ne yayi kara ta dauka da murmushi tana mikewa wurin da muke din Binta tace ango yayi kira ke nan dariya nayi nace au shine ake gudun muji yadda ake soyewan ta dan waigo tana fadin wallahi yayana ne ai ba wani soyewan da muke yi ke dai. Munafuncin banza sai ki fada masu su da basu sani ba nikan nasan komai ai yanzun tana dauka yake tambayan ta tana inane haka waya ke ta ringing bata dauka ba? Tace nazo wurin kawar mune Khadija da tazo nan makwabtan mu ba nisa damu murmushi yayi yace khadijan na kusa ne ki bata waya tace eh sai gata tazo tana miko min wayan. Yayana ashe kwanan nan zakayi wuf da kawata gaskiya munyi murna sosai Allah ya sa albarka ga alamarin. Ameen khadija Allah yasa ayi namu da naku a lokaci daya ya fadi da sauri nace dani dawa kuma ai ni ban ko tsayar da miji ba balle aje ga zancen aure . A yadda muke magana dashi yasa dukan su zuba min ido a cikin tuhuma sai kuma ga maryam tace kice ina gaida shi ina taya shi murna. Ga mayam tana tayaka murnan samun zukekiya kamar zainab na fada cikin zolaya yace haba yaushe tazo nace yau din nan ina fada mata jiya tace da ita za, ayi komai shine ta taso yau aba maryam din waya yace. A lokacin da nake mika wa maryam waya binta tace wai tsaya nifa ban gane ba ? Dama kun san shi ne ko may maryam ta karbi wayan tana fadin yaya Yusuf ashe wani abin arziki ya samu kuma munyi murana sosai wallahi. Yace ya gode ta mika wa zainab wayan ta zainab din ta juya tana make murya muka sa mata dariya wai tsaya don Allah dama kun san yaya Yusuf ne khadija ? Mun san shi mana farin sani kuwa kallon da tati min ne yasa na gyara zancen da fadin ai a sanadin ku ne muka san shi kin manta ne. Zainab ne ta juyo tana fadin wai yana waje yana jiran mu mu fito gaskiya something is fishing here don ina mamaki har da gidan ku yaya Yusuf wai ya sani. A yadda nasan yaya Yusuf bamai yawan magana ba ne da zai san ku haka farat daya dariyan da maryam keyi ne yasa ta mayar da hankalin ta gare ta. Mikewa mukayi zuwa wajen inda yace yake a waje bakin get muka samay shi ya fito daga motar shi gaidashi muka fara yi muna tayashi murna. Yace in Allah ya yarda khadija na fada maki da naku za ayi bukin mu nace don Allah yayana kabar zancen nan wai dawa zaka hada nine halan. Koma da waye kin fi kowa sani don yanzu lokaci yayi da kowa zai sani na gaji da wanan wasan boyar naku maryam tace ashe ka gane su yaya ? Maganan mu ya daure ma su Binta kai nace cikin daure fuska don Allah yayana abar zancen nan anan kada kasa in koma yau Abuja. Yace an gama ama watarana ai dole kowa zai sani nace wai asan may da kake ta fadin haka yace ai na bar zancen tunda baki son matana ta sani ko ? May kuka shirya zakuyi ne goben nayi saurin cewa ba wani bidia zamuyi mai yawa ba kawai dan get together zamu da kawayen mu su ma su sheda. A ina zakuyi ke nan binta tayi tsagal tace yaya a kama muna holl a gamji kawai muje can mu cashe da sauri nace a, a wallahi nan dai kusa zamu samu wani gida muyi event din mu wanan ai kya jira har aure yazo. Zainab tace ga gidan yayan mu nan ai ya ishe mu muyi komai don ko falon gidan kunga babba ne sai dai in ba zai bari ba kun san shi da rashin son hayaniya. Cabdi akan may zai hanamu shi da matar shi tayi buki na banza ma a ranan fa Yusuf yace to shike nan kunji madam ta gama maga dole ko zai yarda da hakan. Balle ma ai bazai hanaku yi ba a gidan sai ka fada mai da kanka Binta tace yace kedai ki bar zancen tunda kin ji khadija tayi magana ai an gama. Yayi muna sallama yace zai tafi idan munyi list din abinda muke so sai mu turo mai amma ga wanan ya ciro kudi a motar shi yana miko min wai mu fara amfani dashi. Kai na kada nace a a yayana kudin nan sunyi yawa wallahi bafa wani abu mai yawa zamuyi ba a wurin just friends din mune zamu hada su tayamu murna. Binta tayi saurin mika hannu tana karban kudin wai din may zance sunyi yawa inda wani ma a karo. Murmushi yayi yana fadin khadija dama nasan halin ki ba karba zakiyi ba amma ita kaunar nan nawa da tasan dadi kashin kudi kinga ta karbe da sauri ai. Duk muka sa dariya ya wuce ya barmu a gurin nan gardama ya kaure muna akan abinda zamuyi sai zainab tace ba fa wanan ba shi yayan mu yasan gidan shi zamuyi event din gobe ? Maryam tace ai mashi magana mana aji ko zai bari indan bai bari ai da wurin yi da yawa bashi kadai ke da gida ba khadija baki san halin yayan mu bane da masifa. Amma mu gwada kiran shi mu gani yanzu da sauri binta tace wa zaiyi magana idan mun kirashi din maryam tace a ba khadija tayi. Kira Binta tayi ta miko min wayan kafin in magana kamar ba zai dauka ba sai can aka daga yace wake magana ? Malam gidan ka muke son aro gobe zamu danyi get together ne da kawayen mu na engament din Zainab yace kuna da hankali kuwa ? May zakuyi wa wasa ko kun manta matar shi mutuwa tayi kada ko fara gigin yin wanan abin na fada maku wai ma wake magana ne ya tambaya. Nan sani ba nace na kashe wayan da sauri Binta tace ke zaki ja muna masifan shi ne baki san shi bane wallahi . Maryam tace yanzu yaya ke nan don maganan yaya AA gaskiya ne fa tunda mutuwa matar shi tayi binta tace humm ummm wallahi sai munyi shekara nawa da mutuwar matan shi yanzu. Zainab tace mommy zamu fadawa ita kadai ne zatace ayi ya yarda ayi don kun san hajiyan mu ba zatai magana ba don haka muje wurin ta kawai. Da sauri nace wa nikan sai kun dawo maji yadda kukayi amma nikan gaskiya ban iya zuwa wurin mommy kan wanan magana. A take Zainab ta nuna min bataji dadin haka ba don nine hope din ta yanzu kuma nace ban zuwa dole na yarda muje wurin mommy din . Mun koma ciki na dan gyara jikina muka fito muka tunkari gidan nasu a dakin mommy muka yada zango bayan mun gama gaisawa da mutanen gidan sai dai bamu je aurin hajiya mama ba sai mun fito. Ni da maryam a kasa muka zube muna gaida mommy cikin fara,a take amsa muna tare da tambayan mu munzo lafiya ? Ta kalli maryam tace wanan ne kuka zo asibiti ranan tare ko nace itace mommy tace yarinyar nada kirki wallahi ku yi hakkuri da junan ku kun ji nace to mommy mun gode. Binta ce ta fara mata bayanin abinda ke tafe damu mommy tace shiko dai abinda ba a gari daya ake ba may zai sa ya hanaku yin farin ciki ai wanan farin ciki ne ga kowa. Ya barku kawai kuyi abin ku tunda ba wani abu can zakuyi ba dan taruwa ne kawai mommy ayi addu,a binta ta fada wani addua kuma binta abinda za a tara yan mata. Kada ki kawo min wanan karyan naki yanzu dai ku bari zan ganshi in mashi magana kafin goben ya kyale ku kuyi abinku tunda shima yusuf din baiki ba. Zamu daga mi bar dakin mommy tace khadija an kusa gama karatun ko nace mommy da dan saura kadan insha Allahu. To ai mu mun matsu ki karasa ansan abinda ake ciki don na matsu in kai ga sarakuwa irin ki sai dai ki matsa da addu, a fa don Nafisa ba wasa. Mun fito wurin mommy dakin hajiya mama muka nufa muka gaida ita da fara,a take fadin ikon Allah ashe Allah ya nufa ayi dake sai gashi kin zo garin. Dan dariya nayi ciki ciki nace wallahi mama basu fada min ba zuwa kawai nayi duba ya Amina don na dade ban zo ba tace ina zakizo wanan karatun naku mai wuyan sha, ani Allah yasa dai a gama lafiya nace amin mama nagode. Muka shige dakin su Binta suna ta faman buga ma abokan su waya kan event din mu dai muna gefe muna jin su. Hajiya mama ne ta kwala ma binta kira tafita tadan jima sai gata ta dawo tana fadin ga su yaya AA nan sun shigo yanzu kuzo ku gaida su. Nace daga inda nake kwance ku tafi kawai ni ina nan ba inda zanje sai kun dawo su fita sai ga zainab wai mama tace muzo mu gaisa da yayan su. Dole na fito muka gaida su na tsaya can baya daga kofa maryam ne ta dan fita fili sosai yace kinzo lafiya maryam ? Ai ba ita daya tazo ba ga diyana nan a bayan ta ai ina kun san ta khadija itama jiya tazo daga Abujan kasan acen take karatun ta. Mama wanan diyar taki mara kunya ce baki ga inda ta tsaya tana gaida mutane ba daga nesa gaisuwan ma sai da kika roka mana tazo. A a ban yarda ba kai kadai naji ka fadi haka ga khadija amma khadija ai tana da tarbiya ko dan hararan shi nayi daga inda nake lokacin da yake maganan. Mommy ce tashigo dakin inda shigowanta baisa mama ta fasa maganan ta ba tace kai ai kowa ba daidai yake ba saboda murdaden halin ka. Mommy tace may kuma yayi yanzu da shigowan shi yaya tace haka kawai zai saka min diya a gaba daga gaida shi wai bata da kunya. Ina shi kunyan ne gare shi yaya ki barsu kawai don sun fi kusa idan kika shiga maganan nan kunya zakiyi . Au to haka zancen yake to Allah ya tabbatar muna da alheri da nafi kowa farin ciki da hakan kuwa da sauri nace mama ba haka zancen yake ba mugune shi kawai nama rasa may zance dasu a wurin. Dariya mommy sukayi tace na fada maki barsu kawai su gama boye boyen su kyaji may ke nan watarana. Mommy ai ba sai watarana ba gashi sun nuna a gaban ku ai yanzu kowa ya sani haka da kika gansu muke fama dasu wallahi ko maryam ? Yana tambayan maryam din tace mama kyale su haka suke ko yaushe ba a shiga tsakanin su don ko an shiga zasu dawo su shirya ba a sani ba. Ji nayi wurin bai dauka na da sauri na koma ciki ina jin wani bacin rai tare dani ban san yaya suka kwashe a falon ba na daiji binta ta shigo tana murna wai an mashi magana yace muyi. Suna murnan su nikan raina a bace yake da maryam da yusuf har da mommy data biye masu din. Sai da kyat na saita kaina na dan koma normal kada a fahince ni bamu bar gidan ba sai dare so sai muka koma gida tare da ya Amina da dawowan su ke nan daga gidan jere. Wanka nayi na kwanta don raina a bace yake da kowa nayi dana sanin zuwan danayi kadunan a yau da nake ganin ana son kula min sheri wurin matan da nake jin nauyin su. Shi kuma munafukin bai fada masu ba gaskiya bane dan ya kullamin sheri kawai a wurin su komay yake nufi oho zan gani idan ana kula abinda ba alaka ne a cikin sa. Da safe tun safe su zainab suna gidan mu ana sha,anin buki a cikin gida mu muna shirin namu event din. Unguwar yacika da baki nakusa dana nesa ko ina mutum ya duba motane na masu zuwa daurin aure a haka muka ratso tarun mazan har kafana yana hardewa. Kamar ance in daga kai can na hangoshi tsakiyan mutane daga nesa muka watsa ma juna harara mun shiga ciki zakace a gidan ne ake buki don jama, a da suka cika gidan. Nan na kara yarda ba karamin alaka ke tsakan gidajen biyu ba mun zauna ke nan massage ya shigo a wayana na dauka ina dubawa. Kina da hankali kuwa da zaki ratso wanan taron maza haka da dan gyale karami. Haushi naji har cikin raina na mayar mashi da amsa ina ruwan ka da ni ka fara tsare matan ka kafin ka fito sa ido waje. Yarinyar dani kike wasa ida na kara ganin ki haka a garin nan sai na bata maki rai . Kaji min mutum da sa idon tsiya kai waye da kake son saka min doka na rubata mashi. Ya sake rubuto min barin shigo ciki in nuna maki ko ni waye a gaban su mommu da hajiyan mu yanzu. Ban bashi amsa ba don tsoro ya kamani kada bakina yaja min jin kuya sai hira muke a falon hajiya mama ban yi aune ba sai ganin mutum nayi ya shigo falon. Da sauri na noke kaina kasa ina hajiyan mu ya tambaya cikin daure fuska take dakin yayi tsit kamar ba kowa a ciki lokacin. Sai zainab ne tace mai yanzu ta shiga dauko abu a ciki sai gata ta fito yace a hada muna abinci akwai bakin da suka zo daga Abuja yanzu. Kai babangida shine kaki fada da wuri a cire masu tun farko ai da ko matar ka sai kasa ta aje masu yace ni kaina wai bata aje min ba tace. Kai wanan irin abu naku damay yayi kama ace ana buki a gidan ku bazaka aje ma mijin ka abinda zaici ba sai ya tambaya mama ta fada cikin bacin rai. Nan ya fice daga falon na sauke ajiyan zuciya muna zaune kafin wani lokaci an hada masu aka kai ina jin mommy da mama suna ta fadan abinda banji dadin shi ba kan fatin. Mun dage bukin mu sai washe gari don hidimar bukin da yayi yawa a gidan dole muka dage namu din sai washe gari four na yamma zamuyi inda nasa rai ya wuce a lokacin don Sunday ne dole ya koma aiki na manta akwai hutu Monday da za ayi. Kamar yadda muka tsara zamuyi four mun gama shiri a cikin dogayen riguna bakake gaba dayan mu sai zainab ne tasaka fari kwal a cikin mu. Mun gyara wurin dakyau kawaye na zuwa guda guda har wurin ya dan cika mu mata zalla ne a gurin muna gidan Fati ta dawo daga gidan su daukan abu. Maryam ta zuba mata ido tana kallon ta ina gefe ni kuma ina kallon maryam din bata tsaya ba ta fice ta barmu a gidan . A falon su ne zamuyi event din so ba wasu maza a gurin sai wanda zai muna dj da aka dauko bayan yan bayane aka fara gudanar da event din gwanin ban shaawa. Mun sake sosai don mu kadai ne a gidan haka ya bamu daman sakewa yadda muke so a gidan kira ake guda guda mu fito mu taya zainab din murna a fili muna fitowa har akazo kaina na fito na fara takawa kamar ance in daga kai sama tsaye yake da waya a kunnen shi yana saukowa kasa. Da sauri na rage rawan na fita fiilin suka sa ihun basu yarda ba don time din da ake ba kowa baiyi ba na fita. Gyaran muryan da yayi daga bayan mu ne yasa kowa dake wurin ya natsu sai da ya fita muka koma abinda mukeyi din wayana naji yana kugi da sauri na ciro a jakkana ina dubawa fito nan waje yace dani. Sai na basar da sakon naki fita wani sakon ne ya kara shigo min again ki fito ko inzo wuei in samay ki cikin bacin rai na fito cike da rashin mutuncin wanan takuran haka da yake min. Ina fitowa na duba ban ganshi ba sai naji horn a gabana na gane yana cikin motar shi zaune wurin na nufa na samay shi zaune a motan. Shigo yace min nace bazan shiga ba nan yayi min nace dashi kai tsaye yace ki shigo tun ban fito ba wallahi ban shiga nace kai tsaye yana fitowa na fara ja da baya baya har nakai jikin wani mota na tsaya. Ashe karya rashin kunya kike yi may kika rubuto min jiya tsakanin mu bai wuce tako daya ba nace may ka gani ya tako kenan zuwa gare ni binta tafito daga ciki tana kwala min kira. Da sauri ya ja baya na sauke ajiyan zuciya kirana ta kara yi ya juya a fusace yana cewa da ita stupid wanan kira haka fa kamar makauniya. Ta juya simi simi zata wuce nace jirani muje Binta yace bace min da gani ta wuce ba ko waige ta shige ciki da sauri ya dawo da kallon shi gare ni da zuman nufo ni na zille da gudu na bar wurin. Sai gab da magariba muka gama muka kwashe kayan lokacin har ishai yayi kai tsaye gidan ya Amina muka nufa ni da maryam. Binta mamaki ne ya cika ta ta kasa sakin jikin ta na abinda ta gani yana aukuwa tsakanina da dan uwan nasu sai da sukaje gida ne take fada ma zainab abinda ta gani. Zainab tace nima naso in fahinci hakan tun ranan da taje waje tayi mai magana a hostel din su amma koma may ye zan binkici yaya yusuf inji ko akwai wani abu a tsakanin na su. Wai har khadija taban tausayi wallahi ina zata iya da Nafisa anty Fati da take babba yaya ta iya da ita balle khadija da take karama ? Zainab tace ai abin badaga nan yake ba in fada maki sai ko kiga khadija ta iya zama da ita tsab balle khadija da take da baki. Magana may naji kuna yi haka baku kwanta ba muryan hajiya mama ne a dakin nasu take tambayan su zainab tace a a magana mukeyi kawai. Binta tace mama wani abin mamaki na gani yau wallahi yayan mu tare da khadija nagani sun ban mamaki don akwai wani abu a tsakani su nake gani. Koma may ye a tsakanin su Allah ya tabbatar muna da alheri shi muke fata ga kowan ku yanzu ta fice ta bar masu dakin cikin sanyin jiki. Kodai dama hajiyan mu tasan da wani abu a tsakanin su ne ga yadda tayi magana yanzu kamar tana da masaniya akan abinda nagani. Kokarin rungumay khadijan fa naga yanayi sai dai ita khadijan kamar a tsorace take a lokacin kai Binta banda sheri fa. Au kin dauka karya nake yi ai koma may gobe zan tambayi khadija din don nasan ba zata boye muna komai ba inji Binta. Zainab tace yau zan tambayi yaya Yusuf idan ya kira ni inji don shi zai san komai akan haka ? Washegari Mun sha barcin gajiya don haka bamu tashi da wuri ba gashi ina son zuwa hidan kakanin yaran Ya Amina in duba yaran dake can. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Zaune nake a gaban ya Amina da maigidan ta sai maryam da muke zaune saman kujera daya mijin ya Amina ne ke magana bayan ta gama kora mashi halin da ake ciki dani da gidan su AA har nace zan koma gobe. Magana yake min ta fahinta yadda zan fahinci komai a tsanake ina sauraren shi sai dai hankali na yana kan maganan da mukayi da su binta da zainab a dakin mu dazun. Abinda naji ya fada ne ya dawo dani daga abunda nake tunane din yace a gaskiya khadija naso ace sai kin gama karatun ki zakiyi aure. Amma yanzu yadda wanan zancen ya fara bullowa nasan abune mai wuya ki samu ki gama karatun ki ba tare da aure ba. Yace mun sha waya da daddy yana min complain din kiyi aure haka na don yan uwan ki ba wanda ya yi karatun gaba da secondary acikin ku sai ke kadai. Hawaye ne ke fita min daga fuskana da ban san lokacin da suka silalo min ba yace abu ne mai wuya idan daddy yaji zancen nan ya barki har ki kare karatun ki babu aure. Don haka nake baki shawara ki lalaba wanan mutumin ya dakatar da maganan nan sai idan kin gama kin ga zuwa lokacin idan Allah ya kawo maki wani sai ku shirya kuyi auren ku dashi idan kuma wanan din ne to sai dai muce Allah yasa albarka don dai gaskiya Abdulsamad mijin aure ne ga ko wace mace. Da sauri nace yaya Adam don Allah ka bar zancen shi ni ba soyayya muke dashi ba wallahi kuma shima nasan ba sona yake ba har cikin ran shi. Kawai dai don yaga iyayyen shi sun nuna suna so ne ya nuna masu shima yana so na karasa da fadin ni may zanyi da mai mata har biyu a gida. Yace ba a auren mai mata ne ya tambaye ni yana dariya nace ga wanda ke so tanayi amma nikan harga Allah ban da wanan raayin a raina. Wanan ma ya Adam banda fitina mai ke akwai a cikin auren shi duk macen da ta shiga gidan shi ai tasan abinda ta takane. Ni dai don Allah ku basu hakkuri su bar wanan zancen please ya Adam yayi saurin fadin a, a khadija ai mi bamu shiga maganan aure ke dai ce da kan ki zaki nuna mashi hakan. Yanzu idan mun hana Allah yazo yayi auren ku da wani ido kike son mu kalle shi dashi ba fa zai manta da abinda muka fada mai ba. Nace ni wallahi zan iya yanzu ma ba sai anjima ba zan kirashi in fada mashi maganan da zai sa yaji haushi ya ce ya fasa . Ke dallah ja can halina dake rashin kunyan tsiya may zaki fada mai wanda zai sa yaji haushi banda rashin wayon ki can . Ya Amina ne take fadin haka rai bace dani nace wallahi ya Amina idan ba haka nayi mai ba tarko yake son ya dana min kawai ya cuce ni. Ki daibi sannu maryam dake gefena ta fada tace kin san mutumin da baya magana mugunta na nan tare dashi. Ya Adam dake zaune yana kallona ya harde hanayen shi saman chest din shi yace kada ki fada mai maganan da zai dawo ya damay ki daga baya don ni nasan ko waye AA don kusan a unguwa daya muka tashi dasu. Nace cikin bacin rai da damuwa ni to yaya zanyi dashi lalaba shi zakiyi ku rabu lafiya inji yaya adam din yace min . Kuka nake sosai yace ai ba abin kuka bane don aure dole ne kiyi shi sai dai yanzu idan zaki tsayar da wani ne daga cikin maneman ki sai dai yaji kawai kin tsayar da mijin aure. Shawaran da yaya Adam ya kawo yanzu yayi min sosai a haka muka tsayar da zancen ya dan dade yana min nasiha kafin ya shige dakin shi ya bar mu wurin da Ya Amina. Bayan ta wuce ne muna muka shige dakin kwanan mu nan na duba lokaci naga dare bai wani yi ba a lokacin don haka nakasa hakkuri na dauko wayana nakira shi. Kiran ya kusa katsewa ya daga kiran nawa da sallama na fara yi mai magana maryam na zaune daga gefe na tana sauraren mu don wayan a handfree na sashi. Ke baki san lokacin kiran mutum bane ya fada a gadarance nace kai kasan wanan a wurin ka ni bawani abu yasa na kiraka ba yanzu. Sai maganan da ke yawo a tsakanin mu wai kana so na yace wai ne ma ashe nace wai ne mana don kaima kasan ba haka bane zancen. Don Allah ina son ka fada ma su mama da bakin ka ba gaskiya bane wanan maganan da sukaji don su bar zancen. Yace ke baki da bakin fada masu ne ko an dinke maki baki ne wanan maganan ke ya shafa dasu da ke son hadawa. Na dan marairaice nace ina da baki kuma ba a dinke min ba sai dai ba zan iya fada masu bane su fahince ni yadda kai zasu fahince ka. Murmushi naji yayi yace ke nan kina umurtana da naje masu da rashin kunya ko ke dai da baki so sai ki fada masu su fahince ki. Na kara marairaicewa cikin muryan kuka nake fadin don Allah yaya Abdulsamad ka taimake ni please ina jin kunyan su mamane ba zan iya fada masu ba don naga sun dauki maganan kamar da gaskiya. Au ke a wasa kika dauki zancen ashe nace kaima kasan wasa ne wanan maganan yayana yusuf ne yace ke kin san may nace cikin girgiza kai kamar yana kallo na. Ki daina kira na akan wanan magana do ni baya gabana sam nace a hasale kamar yadda baka gabana nima har abada. Haka kika ce nace haka di ne dan kawai ina ma magana na fahinta don kaine babba zaka so fada min magana halan an fada ma nayi kwantai ne ko zan auri miji mai mata ba irin ka ba cus ragowan wasu matan da suka gama dakai. May zanyi da mijin tace wanda baida tacewa a gidan shi wanda duniya ke ma kallon sususun namiji may ke gidan ka banda wahala. Wayan Maryam ta fisge a hannu na tare kashewa tana fadin kina da hankali kuwa nace ke bakiji rainin wayon da yake son fada min bane . Tace ke shine zaki biye mashi kuyi sai da hali kin manta da abinda mijin ya Amina ya fada maki ne nace wallahi bai iya min komai sai Allah. Sai don ina wawiya ina zauna ya fada min maganan banza don ina tsoron shi ko may kai ta girgiza min tace kina da aiki wallahi. Sai da muka kara kwana biyu a garin muka koma makaran ta cike da kewan su ya Amina da yaran ta don su binta bamu kara haduwa dasu ba tun wanan lokacin da suka zo da dare gidan ya Amina. Kafin in wuce sai da mijin ya Amina ya zauna dani ya sake maimaita min da inyi gagawan tsayar da wani cikin manema na. Yace in iya sanin shi aure abune daya shafi fanin rayuwa n mutum saboda haka ina son ki kwantar da hankalin ki kwantar da hankalin ki ki zabi na kwarai ba zabin zuciyan ki ba. Ki zabi mutumin da zai iya baki kulawa keda iyayyen ki da duk wani naki nan gaba don kwanciyan hankalin ki. Ya Amina tana gefen shi tace ki fada muna sai mu sanar da daddy cikin maneman ki wa kika zaba kallon ta nayi nace ni wa zan zaba ya amina ? Sai dai idan mamud zan tsayar ko ismail don yanzu su biyun nan sufi zama serious akaina. Salati naji ya Amina ta saka min tana fadin wani mamud wanda kuna tare yaje ya kara aure ba ke kika ce baki son mai mata ba da farko. Nace nace tun farko kin san ismail nake so ku kuka hana tace ki tsinci mai wurin wanan dan karyan mai neman mata nace ni ina son ismail don mun dade tare dashi. Tace lallai ke yarinya ce har yanzu don Allah kada ki kara min maganan mutum biyun nan idan ina wurin nace ai kulun haka kuke fadi idan ana maganan shi. Shin wai may shi Abdulsamad din yayi maki da baki son shi da sauri nace don Allah ya amina ki bar min maganan shi don ni bai cikin lissafi na ina fadi na kawar da kaina gefe. Shiru mukayi falon dukan mu na dan wani lokaci sai can tace yanzu mamud din kika ga yafi maki ki aure nace yafi min gaskiya. Kallo daya nayiwa ya Amina naga yadda ta hade rai mijinta yace yanzu dai zamu baki lokaci kije ki kara tunane akai nace zan yi yace in bashi layin mamud zai kira shi. Na tashi na shiga dakin mu na dauko jakka na tare da fada ma maryam ta tashi muje kada rana yayi muna a hanya. Mun isa makaranta lafiya sannu a hankali na fara mantawa da abinda na baro a kaduna nan ma da muka dawo ban sake kulla komai ba sai karatuna. Fati dake zaune a falon su tana kallo zaune da balaraba mai aikin su wayan tane yayi kara ta dauka bata sheda mai layin da ya kira ta ba. Tana dauka tare da sallama taji ance ke Fati wai ke wata irin kaska ce mai bakin naci mara zuciya wawiya mara wayo dabaki san ciwon kan ki ba ? Ta sheda muryan nafisa don inda sabo ta saba don wanan ba shine karo na farko da takan kirata a waya ta zage ta ba tas akan mijin ta. Har yakai ta daina daukan layin ta idan ta kirata shine wanan karon ta canza layi saboda tasan bata daukan nata din bai ma shiga don ta sakata a black list. Idan kin gama haukan ki zan kashe Fati ta fada cikin bacin rai tace wallahi sai nayi ajalin ki idan kin ce bazaki fita hanyan samad ba baza karya kawai. Allah yabaki daidai dake ni banda lokacin ki don don ga Allah na dogara kece duniya take rudin ki har kike ganin anan zaki tabbata a cikin sa. Eyyeh ke har kinyi bakin da zan fadi ki fadi wallahi zaki san da wanda kike zance don kin sanni na san ki. Sanina na alheri ta ja tsuki ta kashe wayan tana tunanen wanan halin kishin hauka na nafisa da bata daukanta a mai hankali. Hajiya wanan matar tana da kai kuwa inji laraba take tambayan Fatin taja tsuki tace ita kuma nata kalar kishin ke nan na hauka. Laraba ban iya wanan haukan kishin na Nafisa shiyasa mutane ke ganin laifina akai tunda ko nace zan dauki mataki shi ba yarda zaiyi sai yace nice banda hakkuri. Hajiya kin sani ba aikin kan shi bane idan da abin na kai sake ne da yanzu ya isa ya gane halin ta amma matar da bata zauna ba kullun tana hanya bin bokaye da malamai da bokaye. Ranan ma fa da tazo ina jin tana tambayan su jummai da suka shigo wai akwai wani malamin dake tashen aiki a garin nan zataje akan maganan yar ta ne. Allah dai ya kyauta laraba ni nagaji wallahi ai abin yanzu ma da sauki tunda ba guri daya ake ba zaune hakan yafi min alheri ranan da ya tuna mu yazo shiya sani. Hajiya ki dai kara hakkuri don hakkuri bai faduwa kasa banza wata rana dadin ki yana tafe insha Allahu. Murmushi fati tayi tace kin ce Allah da sai in ce yaushe kuma ko sai lokacin da karfi na yakare zaizo din tace kin san fa buzayen nan haka su ke. Duk gidan da suka shiga wanan gidan sai ya girgiza ke makin yi arziki ta barki a cikin diyan ki kin zauna ai ta gidan Alhaji garbati ai duk ta watsa matan gidan baki dayan su da baki halin ta. Hajiya ai badon in fada maki wani abu ba hankalin ki ya tashi dana fada maki wallahi da sauri fati ta juyo tace may zai sa inta da hankalina laraba wani dare ne jemage bai gani ba. Tace ai shine na gani don ke abin ai kamar ma saukin ki ne laraba tace fati ta sake tambayan ta may kike son fada min ne laraba. Laraba ta gyara zama kamar mai son gulma tace wani magana najiyo a gurin anty Amarya dazun dana shiga. May kika jine wai tana kallon ta take tambaya tace abin ne da wuyar fadi ai amma ai dole ne kiji ko a wani gurin. Wai ji nayi suna magana da kawarta wai maigidan ku zai kara aure kwanan nan tace aure kuma laraba tace abinda naji suna fadi ke nan wallahi. Gaban tane ya fadi sai laraba taji tsoro tace niko a ganina hajiya wanan bai shafeki ba kamar sauki ne a gurin ki ai. Don yanzu akanta wanan buzuwan zata koma kinga ke kin samu hutu wani abin ke nan sai dai ki zama yar kallo a tsakanin su. Sai lokacin tayi ajiyan zuciya tace zata koma kanta amma laraba tunane na kowa cece zai aura din yanzu kuma oho ? Don itama kin san da nata sallo zata shigo kishiya fa kishiya ce ba ko yaushe ake samun ta Allah ba a wanan zamanin. Gaskiya ne hajiya Allah dai ya hauda ke kansu duka baki daya don zamanin nan sai a hankali. Shiru tayi tana tunane a ranta tanajin wani bakin kishi na taso mata a zuciyan ta ace kuma yanzu aure zai kara kenan ba batu su ma yakeyi ba ke nan. Can kuma wata zuciya tace mata ke maiye naki a cikin karin auren shi duk tsiya dai tana zaune a cikin su can kuma tace kai may zai sa in damu haka ai bani za a kawo wa kishiyan ba. Ita ma maynene bata gani ba akan nafisa a gidan nan don dai da rabon sai ta zauna a gidan ne take ciki har yanzu amma da ita da babu duk daya ne a gidan. Samad ban gane may kake nufi ba da zakaje kaduna ka kwashe har kwanaki hudu wurin wanan gajar matar taka da bata da wani amfani. Zaune yake a bakin gadon shi ya tasa laptop din shi a gaba yana aiki a ciki bai dago kai ya dube ta ba don tunda ya dawo fushi take dashi wanda shi bai san dalili ba. Yayi lalashi taki ta sauko jin abinda ta fadi ne yanzu yasa shi gane abinda take ma fushin dashi. Iska ya furzo yace da ita a gurin ki ne bata da amfani ni a wurina tana da amfani don uwar yayana ne kuma yar uwata ce ita. Yaya wasu yayan baidai wa yan nan masu kama da kama ba yayan nawa kike zagi haka babu nauyi ko kunya a idon ki nafisa. Yayana ne daba zan zagesu ba wani kallo yayi mata yace ok tace kuma kudi zaka ban do da bakanan nayi lalurar kudi a bayan ka. Yace idan na baki kudin za a zauna lafiya wani zaman lafiya idan baka daina bibiyan wanan matar taka ba mai busashen gaba ta kaduna. Dariya maganar ta bashi yace ashe sai in nemo wace take ajike ku dinga jikani a tare da sabuwar da zan dauko. Baka isa ba wallahi idan ma mafalki kake ka falka don babu zancen karin aure a gare ka don na shigo ke nan a gidan nan zaman lafiyan ka shine ka sallami fati shine zamu zauna lafiya don ni ka sani ban zama dako wace kishiya wallahi. May ka rasa a gurina may kake nema a gurin wata mace wanda ni banda shi ko zaka kewaye kasan nan naku kaf ba zaka taba samun mai zubina ba. Kaiko a Niger kaje a yanzu da wuya ka samo irina acan don haka kaba kan ka lafiya da zancen wata mace a duniyan nan. Kai ya girgiza mata kawai shi dai bukata shi shine subar wanan zaman doya da manjan da sukeyi a gidan shi da ita na kwanaki da suke yi. Kudin ta kara tambaya yace nawa ne tace dubu dari biyu ya mike zuwa wurin da yake aje kudi a gida ya kirgo ya mika mata ta fice daga dakin. Kai ya girgiza yana mamakin halin Nafisa din da kanta kawai ta sani banda wani agaban shi yanzu ta aibanta diyan shi daya haifa da cikin shi. Sai lokacin ya tuna da khadija yaja dogon nufashi ya sauke yar matsala ko tana ina yanzu waya sani. Ya tuna wayan mu na karshe dashi yayi dariya tare da fadin yarinya zanyi maganin ki ne kwanan nan don ba zan tsaya jin haukan ki ba. Sai dai matsala daya daya tsaya mai arai shine anya kuwa khadija zata iya zama da Nafisa jifa irin ikirarin da tayi yanzu akan shi. Kada fa ya jawa kanshi wani sabon tashin hankalin da ba zai iya magance shi a gidan shi gaskiyan nafisa ne bata rasa komai ba a tare da ita namace da ake so namijin ya samu. May kuma zai kai shi wani karin aure a yanzu ya ja wa kanshi matsala hajiya mamane ta fado mashi a rai yadda suka rabu da ita take ta nanata mai ya nemi son khadija a gurin ta don aure a tsakanin ba fashi saboda taga dacewan hakan a tare dasu. Yanzu yaya zaiyi yace a ranshi shi dai gaskiya ba zai iya tsayawa wani soyayya ba a yanzu kan wata mace dole ne ya nemi shawaran Yusuf don yafishi sanin irin wa yan nan abubuwan. Ina zaune dawowan mu daga lectures ke nan jikina ba dadi nake jin shi maryam bata dawo ba a lokacin sai four zata shigo. Wayana ne ya dauki ruri a lokacin na duba mamud ne a layin sai da na dan ja tsuki na dauki wayan don ni haushin su nake ji baki daya yanzu na tsani kowa. Bayan mun gaisa ne ya dinga min kamaykamay rashin zuwan shi gurina nace wanan kuma ai na saba idan da sabo mamud. Ya kira sunana khadija na amsa yace a gaskiya yau nayi farin ciki da jin wani dan uwan ki ya kirani akan maganan mu dake. Don haka yanzu zan daina wani daridarin da nakeyi akan ki in Allah ya yarda zantura magabata na suzo su gana da iyayyen ki akan maganan mu. Nace ka dakata mamud ba yanzu ba sai na gama karatuna za fara maganan aure yace a, a haba khadija nace shine ra,ayina . Yace to babu komai zan yi hakkuri ayi yadda kike so sai dai idan kin dawo zaki min iso mu dinga gaisawa da iyayyen ki don su san dani nace wanan ba matsala bane. Mukai sallama ya kashe wayan yana mai jin dadi don gani yake kamar har ya mallake ni ko yanzu. Nace wawa a fili kaje gaba ka nemi matar ka ba nan ba ina mai jan tsaki tare da gyara kwanciyana barci nake son yi a lokacin sai dai tunane ya hana ni. Nace kuyi gaba yaushe kuka gama da matan ku na gida balle ku dauko wani wahala kuma tunowa da AA nayi tunda mukai wayan nan ban kara ji daga gare su ba kuma. Kuma ban kara ganin ko daya daga cikin su ba don haka na dauka ya yi fushi da abinda na fada mashi ne ranan dama ya dauka ko ni kanwan lasa ce zai fada min magana son rashi in kyale shi don yana takama da kudi ko mukami. Abinda ban sani ba ashe Yusuf da AA duk sun bi kowa nawa sun nuna kansu garesu wurina ne kawai basu kula ba. Amma duk wani nawa sai da Yusuf yasa ya Amina ta kwatanta mashi suka sani sun nuna masu nine na bada bakin su nemay su. Sam nan san da hakan ba don ba wanda ya kirani ya fada min ya Aminace tace su kyale ni don ban son zancen aure yanzu. Su kuma suka dauki maganan ta suka zauna akai ba wanda ya taba nuna min hakan da sukayi sai da muka samu hutu da yake mai dan tsawo ne na yanke shawaran zuwa gida in dan kwana biyu sai inzo kadauna in karasa hutu na can. Sai da naje gidan su maryam na kwana biyu kamar yadda nayi mata alkawari na wuce zuwa minna tafiyan dare nayi na iso ba wanda ya sani sai da safe aka ganni a garin. Tunda na dawo ban fita ba ina ta ramuwar barci don karatun da mukasha na jerabawa ranan ina kwance dakina mama ta shigo dakin wurina. Kusa dani tazo ta zauna haka yasani dagowa daga kwancen da nake tace magana nazo muyi dake khadija. Da sauri na dago kai ina kallon ta yanayin ta ya nuna min magana ne mai muhinmanci tazo muyi a dakin da ita. Nace mama wani abune da baki kirani ba kika zo da kan ki tace nan din ma ai bai baci na gyara zama na dakyau ina sauraren ta. Tace shin khadija tunda kika dawo daddyn ku ya taba maki maganan mutumin dayazo neman auren ki ? Dago kaina nayi da sauri tare da fadin wani mutumi kuma mama na tambaye ta cikin kura mata ido da son jin wanda yazo bidan aure na ban sani ba. Tace wani mutum ne daga Abuja ko mutumin kaduna ne ban sani ba ya dai zo nan har can suke gurin kakanin ki ya zagaya. Da sauri nace mama ni ban turo kowa ba wallahi tace baki turosu ba yaya zasu zo gidan nan in ba ke kika basu baki ba ? Wallahi mama ban turo kowa ba da maganan aure tace to sunzo sun kuma gana da mahaifin ku akan maganar auren ki dashi. Lokaci daya zuciyana naji yai min nauyi waye wanan yazo zai mun sheri a gurin iyayyena nake tambayan kai. A take naji hawaye na fita a idona wani na bin wani nace mama wallahi ni ban turo kowa ba gare ku sheri dai maishi ke so yi min. Tace ba maganan sheri a cikin aure mudfin kina so shi ni abinda ban so kizo baki son shi ayi maki dole dashi. Nace wallahi mama ban san kowaye ba yanzu haka ki hawaye wani nabin wani yaki tsaya min a idona. Tace na fada maki ne don naga kin zo har kinyi kwana ki baki mana maganan ba kuma shi mahaifin ku bai tambayi kan maganan ba. Don naji tsoron irin abin arzikin da ya shigo muna gidan nan dashi da sunaan sunzo neman izini suna son a basu dama su nemay ki. Mama wallahi bani na turo su ba tace na sani kuma na fahince yanzu sai ki bari mahaifin ku ya dawo zan tayar da zancen muji shawaran da ya yanke akai tana kaiwa nan ta mike ta fita daga dakin. Nan ta barni zaune ciki da tunane a raina na wanda yazo gidan mu bada sani na ba koma waye zaiga rashin mutunci a wurina wallahi nace a fili. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Mun shirya tsab don zuwa gidan hajiyan mijin ya Amina idan yaran ta suke zan diba su kafin in koma Abuja ban fada ma anty gidan da zamu tafi ba sai da muka shirya mun fito nake sheda mata inda zamu tafi din. Taji dadin jin hakan dama tasan ina matukar son yaran nata sosai har cikin raina don ban yarda idan ina nan wani abu ya taba su. Muna fitowa bakin get din gida ya Amina muka samu motar da zai kai mu har unguwar su hajiyan baban su yasir din. Sai da muka fito maryam tana ba mai taxi din kudi Yusuf ya faka motar shi a gaban mu kallon mamaki nayi mai don bamu san lokacin da ya biyo bayan mu ba. Kina mamaki ne yace lokacin da ya karasa fitowa daga cikin motar shi sai alokacin na tuna da zancen dake cina a zuciya. Bayan mun gaisa ne nake cewa yayana dama ina son ganin ka wallahi yace wani abin ne kanwa ta nace i am sorry to say wallahi ban taba sanin matar ka rasuwa tayi ba sai yanzu dana ji. Fuska ya dan daure yace wallahi haka ne khadija Aisha ta rasu ta barni da kewan ta a wurin haihuwa Allah ya karbi ranta babban bakin cikina shine ban samu ganawa da Aisha ba tunda na kaita gida haihuwa sai labarin mutuwan ta da ya riske mu lokacin ina waje dani da AA bamu kasan. Allah yayi mata rahama ya gafarta mata Allah yasa ta huta yayi masu rahama maryam ma takarba da Allah ya jikanta da rahama mukace amin yace ya gode. Sai dan shiru yabiyo baya sai da ya hade wani miyaun bakin ciki yace dama nima ina son ganin ki shine na biyo ki nan yanzu. Nace gani ai yayana lafiya dai ko ya gyara tsayuwan shi tare da jingina bayan shi a motar shi yace well maryam ga khadija gaki ina son muyi magana ne na fahinta amma kuma naga kamar ku zo wani wuri ne ko ya tambaya ? Nace cikin hausa da yake gauraye shiba na gwari ba bana nufawa ba ba kuma hausan yan kaduna ba sai dai idan nayi zaka san may muke nufi don hausa daya ce sai dai daga kara harshe ko tausa shi. Ba matsala ai kana iya yin maganan ka gidan iyayyen mijin anty na nazo gaida su don yaran ta na nan dukan su a gidan kada na koma ban gansu ba. Yace ok aiko kin kyauta shiyasa nake son ki wallahi don kin san abinda ya kamata sosai nadan yi murmushin jin yabon da yayi min. Yace akan maganan ki ne da AA yau da safen nan hajiya mama da mommy sun kirani kan maganan sai dai ban san ra,ayinki ba ke don haka nace su ban lokaci zan ganki kafin in yake maku hukunci akai. Da sauri nace akwai wani abu a tsakanin mu ne dama daban sani ba murmushi ya dan sake a fuskan shi yace haba haba kanwa kada muyi haka mana dake ke ma kin san akwai shi ai. No,no kada muyi haka dakai ya Yusuf kai ma kasan babu komai a tsakanin mu sai mutunci don haka don Allah abar zancen nan gaskiya banji dadin, yadda sukai ma zancen wani fahinta ba na daban dan kai ma kasan ba wani abu a tsakani na dashi tun farko har zuwa yanzu sai mutunci. Kai naga ya girgiza min yace kada ki fadi haka khadija don kowa a nan yasan akwai soyayya a tsakanin ku da AA din daga ni har maryam da kuke tare don may kuma yanzu ana son akai karshen magana zaki fadi haka ? Ya Yusuf ka taba jin Ya AA ya furta kalman so a gare ni tunda muka hadu ba zanyi deceive din kai na ba ba abinda bashi bane gaskiya ka fada masu ba wanan a tsakani na dashi. Khadija ya fadin in serious voice na kalle shi yace ke ma kin san AA da shegen girman kan tsiya ba zai taba hurta ma mace wanan kalman ba gaskiya. Da sauri nace ban mace ya furta ba ya rike abinshi don nima bai min ba bani fatan in auri na miji irin wanan mutum da baisan darajan mace ba sam. Ya yusuf may yasa kake son in decieven din kaina na kada kaina ina fadin ban taba jin son shi ba wallahi a raina don haka ku daina maganan nan na fada tare da hade hannaye guri daya ina rokon shi. Kai ya girgiza yace amma idan kin ce haka baki kyauta muna ba khadija don ke ce hope din kowa a yanzu ga AA nace kunyi kuskuren fahintar hakan. Don ba wanan kun sani a tsakanin mu so ka fitar dasu daga abinda suke tunane na gode yayana a lokacin na fara tafiya bai tsayar dani ba sai cewa da yayi zaku dade anan din ne ko in jiraku na mayar daku gida. Haba dai katafi kawai abinka don bamu san lokacin da zamu fito ba na bashi amsa haka na ci gaba da tafiya nan na barsu da maryam a gurin tsaye. Sai dana jirata tazo muka shiga tare da ita ciki da kanin Abban su yasir muka fara haduwa yana ganin mu yace a, a, a yau yau baki muke dasu haka a gidan nan ? Nayi dan dariya tare da fadin uncle hamza ina kwana yana dariya ya amsa min tare da fadin dan dai yaran ki na gidan nan ne yasa muka ganki da sai ki wuce bamu san kinzo ba. Murmushi nayi nace kai uncle hamza kana dai son hada mu da hajiya ne amma ai tasan nakan zo gaida ita idan na shigo garin. Daidai muna zama a falon hajiyan ta fito daga ciki tana magana da nana yar karamar jinkanta yar wurin ya Amina din da ta yaye. Tana ganin mu tace lale marhabin yau khadija ce a gidan namu kunya ya kamani nace hajiya ai nakanzo wanan karon dai ne na dade ban shigo kaduna bane. Kin san hali karatun mu ban zuwa kaduna yanzu kamar da can baya ta kai zaune muna gaisawa da ita sai ga yaran sun fito suna gani na sukayo kaina da gudu da murnan su akan ganina. Maryam dai na zaune gefe tana kallon mu cikin sha, awan mu nan na manta da kowa a falon muna hira da yaran suna zuba min surutu su na yara. Abin sha irin na sauka ke ta kawo muna kunun aya da zobo mai sayi a ka aje a gaban mu mun dan taba na mike ina fadin barin gyara maki wuri hajiya kafin mu tafi dama nazo gaida kune. Nan dai maryam ma ta mike muka shiga gyara mata gida dama idan naje gidan haka nake mata don halin girma yanzu hajiyan bata samun gyara wuri yadda ya dace. Har abincin rana mun hada mata tuwo shikafa da miyar wake sai busashe kifi da mukai amfani dashi wurin hadawa. Hajiyan ta yaba kwarai da girkin namu tace idan an ganku wa zai dauka kun iya girki haka sai a dauka gayun kawai kuka iya kadai. Nace hajiya a gida idan naje hutu nike hada ma maman mu abinci har in dawo a gidan muka wuni sai yamma zamu koma after four nan yaran suka lake min zasu bini nima dama ina son zuwa dasu hajiya tace ai dama nasan haka zai faru. Tunda sun ganki bazasu zauna ba kuma nan dai ta shirya masu kayan su mukai mata sallama muka tafi. Kafin mu iso gida nana tayi barci a jikina a rugumay da ita na shigo gidan mun samu Abbasu yasir ya dawo ranan a hankali da sallama muka shigo gidan. Mun gaida shi na nufi kujera na shimfede nana akai fada ya Amina ta fara min wai may yasa na dawo da yaran ranan bata gama hutawa ba. Dariya daddy su yayi yace kema kin san ba zasu zauna ba can sun ga khadija wuri na samu sai da nakai zaune nace mata ai ba ke zaki kula su ba tunda ina nan. Tace har kwana nawa zakiyi dazaki ce haka ni wallahi dakin barsu a gurin hajiya da yafi min sauki ban yi magana ba sai kallon maryam da nayi nace akawo maki ruwa ne ki sha ? Yaya Adam mijin Ya Amina ya kalle ni yace lalle bazan gane khadija ba a hanya wanan irin canzawa a lokaci daya fa kin koma wani classic lady a lokaci daya haka ? Dan kallon shi nayi cikin zolaya nace Ya Adam har dakai cikin fadan haka don Allah abinda wasu ke fada min yau kaima ka fada min haka ? Yace wallahi khadija kin canza min ne gabadaya a lokaci daya yana min shakiyanci da zolaya na ya jima zaune muna hira dashi wanda hiran duk na karatun mu ne. Kafin yace zai shiga gari ya sayo abu yana fita ya Amina tabi bayan shi nida maryam muka kalli juna mukai dariya saboda yadda suke kula junan su gwanin ban sha, awa dasu. Nace shine kuke son hadani da wani mai tarin iyali haka mutum ko marmari babu wallahi ni bai taba burge ni ba Allah don namiji ba marmari haka ai ba mijin aure bane kema kin sani. Maryam tace min an fada maki har a gida haka yake da iyalin shi ba marmari waje daine yake haka a gimtse kulun. Amma ai namiji bai gimtsewa iyalin shi ko yau she ke dai sai dai idan baki son zama da kishiya nace ba kuma zan zauna da ita ba don uwata da yayyi na duk ba mai kishiya cikin su. Baki ta tabe min tace sai akace maki abin na gado ne kema bazaki zauna da ita ba ko ai suma dace sukayi baki san gaba mai zai faru dasu ba. Ya Amina na shigowa nace au fatan da kike masu ke nan ya Amina kin ji wai ya Adam zai kara mata wata rana da saurin maryam.tace kada ki mun sheri wurin anty fa. Nan ta koro mata kan maganan tayi dariya tana zama ta kalle ni tace dama ina son magana dake ai dazu bayan fitan ku har gidan nan mommy take akan zancen ki da Abdulsamad . Da sauri nace wani zance kuma nifa ins ganin gobe zan bar garin nan ma don ban son abinda zai kawo wani fitina a tsakanin ku ana zaune kalau. Ta sauke ajiyan zuciya tace nima abinda na fada ma mommy ke nan wallahi ga matar shi Fati muna mutunci da ita za a dauko wanan maganan kuma yanzu don Allah a bar zancen ga mutunci da kikace kawai. Ya Amina ni abin na ban mamaki fa mutumin dax bai taba cewa yana sona ba bakina da nashi shine za a kawo wanan zancen idan hakane ko mutuncin abari ma shiya fi. Kafin tayi magana wayan ta yai kara jin sunan mommy data ambata yasa ni kallon ta da sauri naji tana fadin eh ta dawo gamu zaune a tare ma. Naga ta duban waya ta aje batace dani komai ba nima ban tambaye ta may tace ba mukaci gaba da maganan mu maryam dai tana zaune tana sauraren mu. Bamu jima ba mukaji sallaman mummy a kofa ta shigowa duk na rude a lokaci daya ashe ba ita kadai bane tare suke da hajiya mama suka shigo da sallaman su muka karba masu. Mikewa nayi zan shige ciki bayan mun gama gaidasu tun kan su zauna ina kuma zaki dawo ki zaune ai gurin ki muka zo inji mommy. Simi simi na dawo na zauna a kasa wanan karon tare da dukar da kaina kasan ina sauraren su mommy taci gaba da magana . Khadija ta ambaci sunana hakan baisa na iya dago kai na kalle ta ba sai dan amsan wan danayi ciki ciki tace may ke faruwa ne tsakanin ki da yayan ku mukaji amsa sabanin wanda muke tsamani da farko ? Shiru nayi sai kara dukar da kaina kasa danayi tace khadija iddan wani abune kada kiji nauyi ko kunya ki fada muna ra,ayin ki tunda kikaga mun taso mun zo da kan mu kin san ba maganan wasa muka zo dashi ba nan . Kaina na kasa nauyi da kunya ya rufe ni a lokacin ban san yadda zan daga kaina basu amsa ba muryan hajiya mama naji tana fadin ki saki jiki kiyi magana ni a matsayin yar ciki na nake daukan ki khadija magana ce ta fahinta don shi mun kasa gane inda ya dosa ga maganar shi. Kakakarakaka ga wurin fadin magana sai dai babu hali a gare ni mommy tace shi ya nuna muna da muka tuntube shi kamar kun gama tsaida magana a tsakanin ku dashi wanda dama haka mu muke fatan muji. Yau yafito da kan shi ya nuna ga abinda yake so a ranshi kin san babangida mutum ne mai murdaden hali da ba a gane kan shi a lokaci daya idan bai ra,ayin abu bai ma abin kallon muhinmaci sai yaga dama. Muna farin ciki ga abinda muke ji sai ga Yusuf dazu yazo muna da wani magana wanda bamu fahinci may yake nufi da amsar ki ba don haka muke son ji daga bakin ki. Don idan kin tafi yanzu bamu san lokacin da zaki dawo nan ba maza don yanzu baki faye shigowa garin ba kai tsaye kamar a da da a nan kike yawan hutunki. A hankali na dago kai na sai na dukar nace mommy ni ba soyayya muke da yaya Abdulsamad ba don bai taba cewa yana sona ba nima haka ban taba jin son shi ba sune dai suke fahintar haka a tsakanin mu. Ashe khadija muryan hajiya mama ta katse ni tace soyayya kuma wanda yusuf ya fada muna a tsakanin ku idan yafi haka ai ya baci . Shi nashi kalan soyayyan ke nan a baude yake nuna maki halin babangida sai shi wallahi da farko danaji wanan zancen nafi kowa farin ciki da jin hakan. Amma kuma sai ga magana yazo muna ta karkace wai kin ce ba komai a tsakanin ku shiyasa na taso da mommy ku muzo muji wanan magana da kan mu. Khadija kamar yadda kika sani babangida yana bukatan taimako macen da tasan kanta don gyara halayan shi na wanda yake mai murdade ra,ayi wanda sai macen da yake zaune da ita jaruma ne zata kwato man shi daga tarkon wanan buzuwan da ya ke aure a gidan shi yanzu. Kin dai san komai khadija basai na fada ba yanzu anan kin san komai dake faruwa dashi tunda kusan a tare muke da ke da yar uwar ki a unguwan nan. Don haka don Allah khadija ina rokon alfarma a wurin ki da, , , da sauri na dago kaina alokacin har na fara hawaye a fuskana nace cikin karfin hali mama bazan iya don Allah ki yi hakkuri abinda kuke nufi bashi bane a tsakanin mu wallahi ko mama mommy ku fahince ni mana wallahi ba komai a tsakanina dashi. Mommy ta gyara zama tana fadin nafahince ki khadija abin da mu kuma muke rokon ki shine ki yarda da bukatan mu akan shi don girman Allah ki tausayawa mahaifiyar shi tunda ta tako gare ki. Yanzu kin san maganar ba karamin magana bace Ya Amina ce tasa muna baki don tunda aka fara maganan take jin wani iri a ranta ganin kamar suna son su tursasani abinda ban so ne abinka da dan uwa tace don Allah mama ku bar zancen nan a yanzu zan zauna da ita mu fahinci juna don yanzu bata a cikin hankalin ta zata iya rikice muna anan don khadija na da iska masu karfi yana iya tashi yanzu haka anan idan ranta ya baci. Jin haka yasa suka kalli juna da mama sukai murmushi mama tace hakan na da kyau ba sai mun tsaya wani dogon magana ba yanzun ai kun fahince mu. Ya Amina ta sake fadin mommy da anbar zancen nan don Allah ko don mutuncin dake tsakanina da Fati kada ta zargi wani abu akai. Hajiya mama ne tayi magana tace ai wanan abin har fatin taimakon kanta ne idan ta gane balle Fati ba mai matsala bane don haka ku kawar da zancen Fati yanzu don zamu fahintar da ita komai ta gane. In Allah yaso zanyi magana da ita zakuji in Allah ya yarda komai zai zo da sauki ta lalabasu don su tafi don ita ma kanta abin ya bata tsoro don bata dauka abin zai zo a haka ba. Mikewa nayi nabarsu a falon maryam ma ta rufa min baya zuwa dakin ta samay ni na kifa kai a filo ina kuka a hankali zama tayi kusa dani ta dafani tare da fadin may ye kuma na kuka khadija ina sai kina yi za a yi wa zai saki auren dole a yanzu idan baki so ai ba mai maki dole. For god sake maryam ya su mommy zasuyi min haka suzo su sani agaba mama tana rokona akan wanan miskilin dan nata yaya kike ganin zan iya musa mata bukatan ta a gareni. Gashi ni kuma wallahi ba zan iya auren wanan dan nata ba mai mata har biyu yaushe yake da wani lokacin mutum a haka. Yanzu dai ai ki barsu da yaya Amina don gata can falo suna maganan har yanzu gaskiya ni basu min adalci ba don may bazasu barni dashi ba sai su zo su saka bakin su a ciki kuma. Zan iya cewa mama ko mommy a a ne tace ai kin fada ko dan naga karfin halin ki sosai da kika iya yin magana a gaban su. Ba dole in magana ba tunda sun kasa fahinta na da gaskiyar maganan shikuma munafuki wai harda fada masu wai ni na yarda. Kin san fa alama ya nuna suna matse da yayi aure ko za a kawo karshen buzuwa a gidan nan nace ai Allah kadai ya isa da hakan a tunanen su ni zan iya mata wani abin ne ko may ? Dariya sosai maryam keyi tana kumshe baki kada su jiyo ta a falo tace wallahi don ansa baki da tsoro ne yasa suke son sakaki cikin maganan. Ban saki da yawan raki ba haka don naga yanzu kina son ki sare akan buzuwa kawar ki ko kishiyar ki zan ce ban sani ba. Ke dai kika sani suje can su karata badani ba shiga sharo ba shanu ba abinda ya shille ne da zancen gidan su shi da ya jajibo ta yaje can ya karata da ita su suka sani. Mama na shigowa falon ta ta zauna tare da jawo wayan ta tana dadannawa takira dan uwanta kawu salihu a waya. Kira biyu ya daga wayan yana karbawa yace salamu alaikum Aisha kun wuni lafiya ta amsa lafiya yaya dama akan maganan yaron ka ne na kiraka. Tabsa yarinyar da malam ya fada ta bayyana sai dai tazo da akasin da shi malam din ya fada za a samu sai dai muna bakin kokarin mu don ganin ta yarda da maganan . Aisha kin san dama malam ya fada muna za a samu jayayya akan haka don haka abunda nake so dake yanzu abi komai a hankali har mu cin ma manufar mu. Allah ya gani alheri muke hadawa ba wani abu ba akasin hakan mudin hakan zai muna kwanciyan hankalin mi zamubi ta ko ina muka wanan abin ya tabbata idan haka din ne mafita gare shi damu duka baki daya. Don haka yau da dare zan koma wurin malam in mashi bayanin komai ko akwai wani karin haske akan haka. Idan da hali sai yayi muna istihara agani ko itace zabin Allah akan shi idan da alheri sai muci gaba da rokon Allah a kanta. Tau yaya na gode tace Allah ya bar zumunci yace ba komai Allah dai yasa a dace Allah yasa muga bayan wanan abin tace amin sukai sallama ta kashe waya . A gidan ya Amina sai hada kayana nake ina fadin da safe zamu koma Abuja don gujewa wannan abin da ya kunno kai. Sallaman su Binta da zainan ne a falon ya Amina bayan su gaisa suke tambayana tace ina ciki ina shiri gobe zan koma Binta tace ba tace sati daya ko kwana goma zatayi ba yanzu kuma tace komawa zatayi. Ta mike tana fadin barin ganta zainab ma ta biyo ta zuwa cikin dakin inda muke maryam na zaune da earpiece a kunen ta tana sauraron waka nikuma ina tsaye ina nike kayan mu ina sakawa a jakka suka shigo dakin. Kallona Binta tayi tana fadin wai zaki koma gobe zainan ta samu guri ta zauna a kusa da maryam take zaune tana kallona. A raina nace shegeya mai kama da dan uwan ta wurin miskilanci nace da Binta gobe zan koma nan iya fitinan da su yusuf suka fito min dashi. Wai akan wanan magana kike son komawa ai ko kin koma baki tsira ba don gara ki tsaya ayi ta takare anan kowa yasan matsayin shi. Don nima wallahi ban goyi bayan wanan maganan ba gaskiya ina zaki iya da wanan yar iskan matar tashi mai bakin kishin tsiya kamar kafira. Ke Nafisa fa bata sallah sai taga dama ki fada min in akwai imani a gurin mutumin da bai cika sallah shi. Zainab tace ni inda take ban tsoro shine idan fa yaya zaizo weekend da sai ta biyo shi garin nan tazo kawai don ta takura ma anty fati da yaran ta. Tana daki da miji sai Fati ne zata girka masu abinda zasuci har ya koma wai kuma sunan anzo wurin ta ita dake nan zaune . Amma haka zai koma bata mijin ba sai dai ta hango su suna mu,amulan su a gidan da abokan sherin ta sai da su mama suka taka ma haka burki. Yasa yanzu ta daina biyo shi don mama tace idan sun zo anty fati ne kadai zasuyi girki har su koma haka yasa da taga da gaske mama keyi ta daina zuwa ki idan zamu zauna baki labarin nafisa da shu,umancin ta sai mun kai safe anan. Nace shine kuma su mommy ke son ni sakani a cikin bala,i sun san yadda take, Binta tace ni nama shina gani wallahi zainab ne ta katse ta da fadin ke Binta kin kai su hankaline da wayo ko haka kawai zasu ce suna son wanan abin. Maryam taceai shi na gani nifa banga wani abin jin tsoron a wurin wanan nafisan ba tunda kinga har suna ra,ayi a kan ki akwai abinda suka hanga a hakan ne. Kai na girgiza nace nidai badani ba wallahi kwatakwata ban ra,ayin auren mai mata a rayuwana shine kawai magana ta amma ni wata nafisa bata gabana yanzu. Nasan bata gaban ki ya kamata ki jaye wanan ra, ayin naki na baki son mai mata don ke nasan kuna daidai da ita. Ban iya magana ba don abinda nake ji a raina a lokacin nan binta taci gaba da fada muna halin nafisa ciki da bai. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Kuka zanyi ko ihun takaici zan sake a lokaci daya don tunane na ya karkata akan mamud ne yayi min hakan don a haukan shi na yarda zan aure shi yake zato. Jiran dawowan daddy gida nakeyi duk da nasan zai dauki lokaci bai shigo ba yana kasuwa wurin neman kudin shi. Ina son tashi in kira wayan maryam nauyin da jikina yayi ya hanani tashi zaune ko ya bari inyi wani abu sai zuciyana ne kawai ke aiki ajikina a lokacin. In kulla wancan in sance haka har yamma yayi na mike da kyar ta fito na samu ruwa na watsa ma jikina. Ban jima da fitowa ba ina zaune ina saka kaya naji shigowan dadddy gidan haka kawai naji gaba na na faduwa dashi sai dai na daure na fito ina mashi sannu da zuwa. Yace ah khadija ya gida ya kuka wuni na amsa da daddy lafiya fridge din gidan mu na nufa na daulo mai ledan pure water na sa a plate na kai mai. Sai da ya zuke ruwan ya sauke ajiyan zuciya yace dani Allah yayi maki albarka da fara,a a fuskana na amsa mai da amin daddy. Mikewa yayi ya nufi inda muke zama muyi alwala ya dauki buta ya fara alwala ina tsaye rakube a kofan dakin mu har ya gama ya dago yaba fadin khadija lafiya kike kuwa ? Daddy lafiya na kalau ina dai , , , ki bari yaje sallah kada ya makara kin san su basu tsayar da sallah da sun tayar suke haraman tada sallah. May ke faruwa ne ya tambaya cike da son jin abinda yake tambaya yana kallon fuska na nace daddy ba komai bane mama tace idan kadawo sai kuyi maganan yace yana da kyau hakan. Ya fice mama ta kalle ni tace kije kiyi sallah kafin ya dawo ta na fadin haka ta dauki buta zuwa ban daki ta kewa yawa. Bayan na idar da sallah na zauna a gurin ina addua tare da mika kuka na ga Allah akan ya kuburar dani daga sherin masu sheri da fatan cikawa da imanin a zuciyar mu. Sai da akai sallah isha,i daddy ya dawo gidan inda mama ta gabatar mai da abincin shi na dare gaban shi. Sai da na tabbatar da ya kare abinda yake na shiga wiri shi da sallama yana zaune a kasa saman jan carpet din dake shimfide a falon ga kayan abincin aje a gefen shi yana kallon labaran NTA minna da akeyi . Na samu gefe na zauna kasa nima na kara gaida daddy da wuni daidai nan mama ta shigo falon itama dauke da kayan abincin ta da zata ci. Sai data samu wuri ta zauna ta kalle ni tana cewa ga khadija nan dazun da rana na samay ta da maganan mutanen da suka zo neman ta take nuna min bata san da maganan ba. Sai lokavin daddy ya cire idon shi ga kallon da yake yi tare da fadin idan ita bata sanda maganan ba ai mu mun sani don itace ta fara kawo muna su a gidan nan. Da sauri na dago kaina ina fadin daddy ni ban kawo kowa a gidan nan ba daddy kaima kasani da zan kawo wani nice zan sanar dakai zuwan nasu ai. Khadija a gaskiya naso ace sai kingama karatun ki zamuyi wanan maganan amma kuma daga baya naga rashin dacewan hakan gare ki yanzu. A gaskiya bazan iya barin ki haka har ki gama karatun ki babu aure gare ki ba don ko yanzu hakkuri nayi aka kai hakan idan kinyi duba ga irin yadda tan uwan ki sukai aure da wuri a baya. Ke har kin samu kin dibi karatun jamia wanda mijin yar uwar ki ya sakaki yi a gurin su nauyin shi da kunya yasa har na barki kikai haka. Shiru mukayi falon babu mai magana a cikin mu muna sauraren daddy din dake magana don haka idan har kince bake kika turo mutumin nan ba yanzu sai ki turo muna wanda ke kike so a ranki ko waye zan aura maki shi insha Allahu. Mama ne tayi magana bayan daddy ya gama magana tace gaskiya batin auren nan yanzu ya kamata ka jaye shi tunda har ta kusa gama karatun ta. Da sauri daddy ya katse mama din da fadin haba Aisha ra,ayi zamu bi ko maganan Allah kada ki kawo wanan maganan yanzu. Khadija kiyi hakkuri kiyi yadda nake so ki fitar da miji kin san gidan mu gidan malamai ne hankali baya kwanci ganin ki a haka da nakeyi kullun kuna gwada sa,a da uwar ki a cikin gida ina ranan wanan abin . Yanzu ne kike a damarki na fida manemin kwarai daga cikin manemanki tun basu gudu daga baya ba ki koma kina neman su su watse su barki dana banza. To aini gani nayi yanzun karatun nata baifi saura shekara daya ba ko watanin ta gama dadduly yace ta karasa shiba gidan mijin ta yafi mutunci hakan. Don ba ido na zan saka mata ba tana abinda taga dama ke kuma kina biye mata tana abinda taga dama don haka ke nake saurare ki turo wanda kike so din yazo mu gana dashi. Daddy na gamawa namike nabar falon idona taf da hawaye da na kasa controling din su nafice daga falon zuwa dakina. Kuka nayi sosai dana koma dakina ina tunanen may yasa daddy ya sauya min acikin dan lokacin nan ya damu da maganan aure na bayan yasa abinda ke gabana yanzu. Zai bijiro min da wani zancen aure may yasa kowa ya maryar da hankalin shi yanzu a kaina haka ne wai ? Kaduna banji dadin abinda su Yusuf suka kula min ba nayi gudun zuwa can yanzu kuma na dawo gida na samu wanan matsalan a wurin daddy again. Mamace tashigo dakin zuwa dare lokacin goma na dare ya gwauta sosai tashigo ta samay ni kwance ina faman tunane dake ci na. Ki tashi kici abinci don kin san maganan daddyn ku idan ya fada ba fasawa zaiyi ba don haka yayi ma yan uwan ki a baya. Ke ma kinyi arziki har yadan barki kin taba karatu yan uwan ki ko kwatan kwacin hakan basu samu ba a gurin shi. Na dago fuskana dake tsiyayan hawaye nace mama bansan may nayi wa daddy yanzu ya tsane ni haka ba karatun nan fa in nayi shi karuwan mu ne duka bani kadai ba. Yasan hakan kin ji ai abinda ya fadi abin kunya ne a gurin su yarinya ta dade haka batai aure ba don haka kiyi shawara ki tsayar da daya daga cikin maneman ki ya turo sai a wuce wurin. Mama ni wa zan turo yanzu ban fa da wani tsayayen mutum a zuciya na su dukan basu kwanta min a rai ba zaune mama takai daga tsayen da take tace min. Ya zama dole a cikin maneman ki ki tsayar da mutum daya a matsayin wanda zaki aure san nan ki sani shi rayuwan aure abune wanda ya shafi rayuwan mutum. Saboda haka ki natsu kiyi zabin daya dace da rayuwan ki kada kiyi zabin tumun dare da za a dawo ana da an sani daga baya. Don daddy ku ba fasa abinda ya furta zaiyi ba yanzu shiru nayi nace mama ni ban son su dukan su gaskiya da dai za a dan daga min kafa abani lokaci sai in fitar da wani daga baya amma ba cikin wa yan nan ba. Mikewa tsaye tayi tace yanzu dubara ya saura naki ai, wai maye matsalan su masu neman naki ne da sauri nace mama suna da mata fa nan dai na bata labarin kowa a cikin su. Sai naga hankalin mama ya tashi sosai dajin abinda na fada mata sai da ta nisa tace min ni ina ganin wanan ba matsala bane don suna da mata. Gidan da ake tashin hankali ne kawai baida dadin shiga don gujewa matsala da saura su ki koma a wurin Allah nima zan taya ki addu,a , Allah yayi maki zabi na alheri. Nace mama ina yi dama kullun sai dai har yanzu ban kai ga matsaya ba tace Allah yayi muna zabi mafi alheri nace amin mama. Har ta juya zata tafi sai kuma ta juyo tana fadin sai dai ina ganin kamar mijin buzuwan nan ne yazo fa gidan nan da sauri na dago nace mama bar maganan shi inma shine yazo ni bai cikin lissafina gaba daya. Allah yayi muna zabi mafi alheri tace ta juya tafita daga dakin nabi ta da kallo ina takaicin AA a cikin raina. Wayana na jawo na kira nomban shi sai ya nuna min busy yake har dare sosai ina kiran shi wayan na nuna min busy nagane yayi blocking dina ne a wayan shi. Dasafe bayan nayi sallah ban sake fitowa ba ina daki har saida naji baba ya fita daga gidan na dan fito na samu abinda naci na koma na kwanta a dakina. Yusuf na nema kira biyu ya daga wayan tare da sallama ya dauka muka gaisa yake tambaya na lafiya na dana iyayayyena nace kowa lafiya yake. Yayana dama tambaya ka nake son yi don in san gaskiya don Allah kune kuka zo gidan mu wurin iyayyena ko wasu ne. Sai da yayi dan jim yace mune Khadija munzo ne neman izzinin a gurin su kuma mun ji dadin yadda baba ya karbe mu sosai wallahi. Do har lokaci ya bamu da zamu dawo nan bada dadewa ba katse shi nayi da fadin why yayana zakuyi min haka yace khadija kin ki tsayawa ku fahinci juna dake da AA akai ga matsayan maganan. Kashe wayan nayj saboda raina daya baci a lokacin gaba daya ma na kashe wayan don kada ya kara kirana again. Sai lokacin nake nadama da dana sanin sake masu fuskan danayi har suka shiga rayuwana ban tsaya wani tunane ba na fita wurin mama na samay ta mun dade muna magana daya da ita bamu kai ga mafita ba. Sai da kyat mama ta samu na sake na dan rage damuwa a raina har da yamma na fita zuwa gidan anty suwaiba na gaida ita na dade a gidan sai gab da magariba muka koma gida. Sai bayan kwana biyu na kunna wayana maryam na kira ina fada mata halin da nake ciki ssi bayan da tagama saurarena tace dama nasan AA ba kyale ki yayi ba akwai abinda yake shirya akan ki. Yanzun ke wani shawara ki ka yanke akai nace ban kai ga yanke shawara ba sai dai mama ta ban shawara kamar yadda su ya amina suka fada min in samu wani in tsayar a matsayin wanda zan aura tace shine daidai wallahi . Abinda ban sani ba shine kan su daya da su AA don haka muna gama waya ta labarta masu abinda na shirya wa zuciya na yanzu. Kwana biyu da maganan mu da maryam ina daki ina barci kamar daga sama naji muryan ya Amina a kaina da mamaki na bude idona ina kallon ta. Mikewa nayi daga kwance na yunkura na tashi ina fadin Ya Amina tafiya haka babu sanarwa tace wallahi daurowa ne yayi don nima ban san zan zo ba a wanan lokacin. Ni dai ban san dalilin zuwan ta don bata fada min ba amma tare muka tashi washe gari muka gyara ko ina na gidan mu da ita. Fita tayi zuwa gidan ya suwaiba tace zata je ta ganta ta dauki lokaci a can sai da yamma ta shigo gidan irin girkin da naga ana shigowa dashi gidan mu washe gari yasa na tambaya ko baki zamuyi a gidan. Ban samu wani kwararen amsa ba daga gare su don haka nima na share zancen misalan daya da wani abu motoci suka tsaya a kofan gidan mu kafin bakin su shigo aka fara shigo da akwatuna ciki . Ina dakina ban san may akeyi ba jin hayaniyan mutane da nake ji a tsakar gidan ya sani tashi in duba ko su waye suka shigo. Mommy ce na fara tozali da ita sai su fauziya su biyu kannen AA dake aure tare da wasu biyu daga cikin dangin su daban sani ba. Gabana ne ya fadi take naga wani duhu na neman rufe min ido da baya baya na koma saman gadon mu tare da dafe kaina. Sun shiga dan falo gidan mu inda ana aka saukw su tare da gabatar masu da abinsha dana ci gidan gaba daya ya kaure da gayaniya babu wanda ya koma ta kaina kuma. Barci ne ko tunane naje ban san yadda akayi ba ni dai na falka naga mama zaune a kusa dani tana fadin kin tashi khadija ido na bita dashi ba tare dana mata magana ba wai ashe suma nayi a dakin ban sani ba. Ki sha tea gashi nan na hada maki kada ya huce kuma ki natsu don sarakuwar zata shigo dubaki yanzu tana fadin haka ta fice daga dakin ta barni kwance ina binta da ido. Ya Suwaiba ta shigo dakin tana cewa khadija sannu akan wanan abin kike son daga hankakin ki haka wurin kayana ta nufa tana fadin wasu zan dauko maki ki saka don zasu shigo su dubaki kafin su tafi. Ya Suwaiba don Allah kada ku shigo min dasu ni yanzu ma gidan zan bari wallahi don bazasu ganni ba har su tafi kuma ku basu tarkacen su su koma dashi. A daidai lokacin mommy ta shigo dakin da sallaman ta saurin yunkurawa nayi don in tashi don daga ni sai wani dogon rigar danasa ne a jikina kaina babu kitso gashina ya zubo ya kwanta min a bayana wani kuma ya fado a goshina. Haba khadija ki kwantar da hankalin ki kina natsu akan wanan zancen zakibi ki tayar da hankalin ki haka idan kin halaka kanki fa badon Allah ya gyara ba. Mu bamasu cutar ki bane kin sani mu ba masu cutar ki bane masoyan ki ne mu don haka kika ga muna kokarin wanan abin ya yuyu. Nasan Babangida bai kyauta maki ba tunda bai nemi so daga gare ki ba yasa muka kwaso jiki zuwa nan ba tare da sanin ki ba don da kin sani baki yin hakan da kikayi. Ki natsu don Allah kada wanan zancen ya koma kunnen mutane don bamu bari sun fahinci halin da ake ciki ba don idan hajiya mama taji a yadda take son abin nan ranta ba zaiyi dadi ba wallahi. Fadawa nayi jikin mommy din ina fadin mommy ki taimake ni ya jaye wanan kudurin nashi a kaina don ba sona yake ba ya fada min shima yayi hakane kawai don ya kwatar maku da hankalin ku. Nasani tace tunda shi namiji ya iya daurewa yayi haka ke mace mai zai hanaki nuna ke mai tarbiya ce kema kibi maganan iyayyen ki ki masu biyayya. Mommy wallahi ba zan iya ba AA mugu ne babu komai gidan shi sai tarin fitina da bakin ciki kuma kun sani mommy may zai sa kusani a cikin wa yan nan hali bayan kun sani. Na sani khadija nasan komai da kike tunane akan babangida sai dai ina son ki sani wanan abin da kike tunane insha Allah ba zai faru a kan ki ba da yardan Allah. Don sanin ki da nayi jarumar mace wace zata iya tsayawa ta kwatar wa kanta yanci a gurin ko waye har nafisa dake tunanen ta mallake kowa dake kewaye da shi. Mommy wallahi bazan iya ba nidai ku rabani dashi ban son shi wallahi ni akwai wanda nake so tace naji yanzu tashi ki shirya sai ku gaisa da mutane daga baya zamuyi waya dake idan na koma gida. Da wannan magana na mommy naji karfi gwiwan tashi na kimtsa jikina cikin wani lace sabo dana dinka na dora abaya a saman kayan tare da daura gyalen abayan akaina. Da jagoracin ya Amina da anty suwaiba muka shiga falom inda suke zaune sun sake jiki kamar yan gida su ma ba wani takura a tare dasu. Ina shiga naji matar daya da ban sani ba tace masha Allah wana ita ma kamar buzuwan ne ai lalle na yarda da zaben dan nawa ya iya zaben tankar da dubu. Kaina na kasa na durkusa har kasa gefen kujera ina gaida su daya tace a a gaskiya da alama yanzu kan babangida yakai ga matan nunawa tsara ga kyau ga tarbiya ga natsuwa masha Allah. Allah yasa muce gwama da akayi anty Fauziya tace daga inda take zaune dako kai muyi hoto in nuna ma hajiyan mu zaben dan ta. Kaina na kara nokewa ina zagi a cikin raina nace matar shi nacan inda take badai ni ba kan. Nan dai sukai ta magana a kaina ina duke sai da mommy ta tasu ta daga ni tana fadin ku barta hakana don Allah kun san sarakuwan nawa alkunya ke gare ta kun damay ta. Jan hannu na tayi muka fice falon ina rungumay a jikin ta tana rada min kin gani kowa na farin ciki da shigan ki rayuwan babangida khadija . Sai da ta zaunar dani a dakin take fadin kwantar da hankalin ki babu komai sai alheri mun san abinda muke hangowa cikin wanan auren naki. Zamu dinga waya dake ina sanar dake komai da ya daure maki kai wanda baki gane bama zaki iya bugomin ki tambaye ni a shirye nake da in fitar dake a duhu. Ke dai ki rike addua don shine makamin mumini nace a sanyayye mommy na gode insha Allahu zan kira ki tace haka nake son ji diya ta Komai zai zo da sauki da yarda Allah sai hudu da rabi suka kama hanya komawa abuja suka barmu da tarin kaya da suka zo dashi wai sun gani suna so har kuma daddy ya saka masu ranan da zasu zo a tsayar da lokacin buki shi da yan uwan shi. Ban fita ba don haka ban an wani tarkace suka zo dashi ba sai dai ina jin mutane na shigowa yan uwa da abokan arziki suna fita suna yaba irin kamun da nayo. Wai nayi dace mijin na gwada ma tsara babu wanda yayi min tunanen irin halin da zan fada ciki don idon su ya rufe sai mahaifiya ta ce ke tayani jimamay. Ina mamaki a yadda nasan daddy bamai kwadai ba yadda yayi saurin yarda da AA din a lokaci guda sai nake ganin kamar bai bincika komai akan shi ba suke kokarin cusa ni a gidan shi. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Da sauri na kwace daga tabanin da yake son yi daga inda na makure saman gadon naji idona suna fitar da dan siririn hawaye. Ba zaki yi sallah bane ko a gidana kike son ki karfita sai dai ba zan so muyi haka dake yanzu ba nafi da son sai munfara koyi da sunnan ma,aikina SAW. Da sauri na kallo shi yace don haka ki tashi mu gode ma Allah a tare don falalan dake cikin wanan ranan mai albarka a gare mu. Ya juyo guri tare da kafeni da ido yana magana cikin tsigar lalashi tare da karashewa da please yau ba rana bace da ta wasa a gare ko ms may kike ji zaki iya boyoe shi har mu idar da wanan sallah. Kin dai san biyayya mata ga mijinta , saboda nasan gida an fada maki komai idan har da farko baki sani ba , Wani hararanshi na karayi sai kuma zancen iyayyena daya sako, ya fado min a rai don nasiha kan iya nasiha na sha kafin in bar gidan mu zuwa nan. Jikina yai sanyi kamar zanyi magana sai kuma na fasa sauka nayi daga gadon ina gyara zanin da na daura tare da shimfida salaya da kyau abinda ya ban mamaki sai yadda yake jan surorin alkur,ani mai girma a natse cikin taushin murya. Raka,a biyu mukayi sai dai duk dogayen sura yake ja abin ya bani mamaki don ban taba sanin yana da ilimin adini haka ga yadda nake ganin shi. Bayan mun idar da sallah ina batun mikewa ya juyo inda nake tare da dora hannayen shi a kaina ya dinga kwararo min addua idona suna rufe sai naji yan siraran hawaye suna fita min daga idona muryan shi ne naji yana fadin tashi kije ki kwanta. Ban ko bi ta nasa ba na mike nabar wurin da sauri zuwa saman gadona ban sake bin ta kan shi ba da tunane na kwanta don haka ban san lokacin da barci ya dauke ni a hakan da nake kwance. Tunda na kwanta ban falka ba sai da naji kamar ana buga wani abu na bude idona firgigit a inda na barshi nan na sake ganin shi zaune abin ya bani mamaki. Nace cikin raina ko ina ya kwana oho da sanda na shige ban dakin tare da duba jikina ko ina a bandakin kafin in dauro alwala in fito. Inda ya idar da sallah nan nima nazo na tayar da sallan daga bayan shi har na idar yana bin yadda nake sallahn a hakali da idon shi ta gefe har ya gane abinda yake son ganewa a gareni din . Ban idar da addu,a ba naga ya mike yafita daga dakin nawa inda ya fita ya barni a wurin na kwanta saman sallaya sai barci mai nauyi ya dauke ni ban falka ba sai wani lokaci mai tsawo na falka da sauri namike ina dube dube a dakin. Ganin kofan kamar yadda yake a rufe na mike zuwa bandaki daga nan na tsaya nayi wanka na fito na gyara jikina a cikin wani cotting lace dark blue mai duwastu kanana a jikin shi ko ina. Wani bakin abaya na dora a sama wanda bayan shi kawai keda kwaliya sai gaban hulan tare da dora gyalen abayan saman dan kwalin da na daura. Ga kumshin kafana da mama Tani ta matsa min sai da akai min yana ta sheki kamar yau aka zana min shi a hannu na da kafafuwana. Flat shoes na saka a kafafuwa na part din da su mommy suka sauka na nufa sai dai part din yana rufe na dauka basu tashi daga barci bane sai na nufi wanda nake tsamanin na Nafisa din ne. Tun daga kofa na jiyo musayan maganan da sukeyi kamar a cikin tashin hakankali ita da maigidan ina ta sallama ba a karba min ba. May kake nufi da zuwa dakin Amarya ka kwana tun mutane basu watse daga gidan ba kana nufin tun yanzu zaka fara wulakantani ko may har wani auren kayi wanda kakewa dauki haka ? Kana nufin ka auro wata mace don kaji dadi ne ko ta baka abinda ban dashi a tare dani ko haihuwa ka auro ta zo taimaka a gida maganan nake ji kamar fada shiyasa na daina sallaman ina sauraren su Nafisa tace to bari kaji lndan kaji dadi ka auro ta ka sani babu wani dadin da zataji a gidan nan wurin ka. Idan kuma an aura maka ita ne don tazo tai haihuwa maka a gidane kamar bera ko kaza don ni nazama juya to itama ba zata taba haihu a gidan nan ba muddin ina raye,. Kasani tsakanin ka da ita daga yau sai kallo nan naji muryan AA a dakin yana cewa ai baki kamar Allah ba Nafisa duk wanan maganan da kike yi a shirmay nake daukan shi da zafin kishi. Kuma bari kiji ninaga Khadija da idona nace ina son ta karki sake zargin wani dan uwa nawa don su abinda nake so ne suke tayani so ko may nene na dauko gare su kuwa zasu fini son abin nan indai alheri ne. Kuma diyar mutane tafi daga bakin ki don ba yadda zaki yi da ita don ta riga da ta shigo ko yanzu matsayin ku daya a wurina . Don ta riga tafi karfin ki tunda har ta shigo gidan nan ta ture zancen ki da kike fadin ba macen da ta isa ta shigo gidan muddin kina raye. To ita ta kauda wanan burin naki tun yanzu ta nuna maki ke ba kowa bace face baiwar Allah kamar kowa. Oh watau taga mai kudi ta shiga tafita sai da ta kutso kai ta shigo gona na ko ai zakace nace indai nice dani kuke zancen wallahi. Taga mai kudi ta biyo ka to ta sani ta biyo wahala a rayuwan ta don yadda ta shigo haka zata fita don ba gidan zaman ta bane gidan nan. Ke kudi ya dama Nafisa don ita kudi ko wani abina ba shine a gaban ta ba nata take kokarin nema ko yaushe don ita duk wanan bai gaban ta. Don haka ni naganta nace ina son abina don ita ba sona take ba ko wani abina keko ke kika ganin kiga abinda nake dashi kikace kina sona don shi. Don haka kinga akwai banbanci a tsakaninku don nike son ta don nasaban ta ke kuma ke ke sona don abina. Dadai naga basu da niyar barin musayan maganan da suke ma juna nayi sallama da karfi na shiga falon nata Gaba dayan su mamakin ganina ya kamasu na dan samu gefen kujera na zauna ina fadin ina kwana anty Nafisa , ? Ke ta nunani da hannu tare da waro idanuwanta gare ni tana fadin wai dama kece ko dai wani abin ya kawo ki kuma gare ni yanzu.? Gyara zama nayi nace eh nice ina kwana anty tace cikin hasala waye anty naki garama tun wuri ki canza salon ki ashe ke yar akuyace wallahi samad ka cuce ni karasa wace zaka dauko min sai wanan yarinyar mara mutunci ka cuce ni daka dauko min wanan a matsayin kishiya a gare ni. Bari kuji daga kai har ita nafi karfin ku nafi karfin wanda ma ya dauko ki gidan nan har ke kin isa kizo min har gidana ki kwana min da mijina a matsayin mijin ki ke ma. Bari kiji idan kina son kanki da lafiya tun wuri gara ki tatara naki ina ki kibar gidan nan ki barni da mijina tun duniya suna shedaki. Murmushi nayi tare da mikewa tsaye nace waki ke da suna ne buzuwa kike kowa ake kiran ki idan junin ki iya shege yanzu kin samu mai tayaki yi agidan nan. Idan kuma kurin ki kiran mijin taro da sunan mijin ki ke kadai to yanzu ki gyara zancen ki, bakin ki ya saba da kiran mijin mu, mu uku, Fati uwar gida sai buzuwa yar tsaka sai khadija amaryan tsakiya don bansan ko akwai wata zuwa bayana ba don haka bazan kira kaina amaryan gidanan ba. Na kara takawa zuwa gaban ta nace duk wani abin da kike takama dashi ko yanga da zakiyi ko kike yi yanzu ki shirya yin shi tare da wata a gidan nan don bake kadai bace mamalakiyar wanan gidan ba yanzu. Ki sani ni nan da kike gani ba fitina yashigo dani gidan nan ba don ni tsakani da Allah na auri mijin ku badon wani abinshi ba ko kudi ko kyau shi ko sabar shi, a, a na girgiza kaina nace Allah ne ya hadani da mijinki don haka ni dake mu zuba a gidan nan kamar yada kika furta yanzu. Ina fadin haka na hankade su na fice daga dakin na koma dakina ido na rufe da abinda ya faru yanzu tsakanin mu da Nafisa. Allah ya gani ba haka naso mu fara da ita a gidan ba sai mamakin kaina yadda na iya kallon su na fada mata magana son raina har dakinta nafito. Binta da zainab nake tunanen ina suka shiga haka banji duriyan su ba a gidan har wanan lokacin. Cikina ne ya fara neman agaji daga gare ni sai lokacin na tuna da abinci fita nayi zuwa kitchen don in ceci kaina zan halaka da yunwa kawai a gidan nan. Kitchen din na shiga sai na tsayawa ina karema kitchen din kallo yadda aka tsara komai a cikin sa gwanin ban shawa, a dashi sai da na gama duban kitchen din. Komai na aiki akwai acikin sa ga freze nan da sauran na,urorin kitchen a kune suna ta aiki a ciki fridge din na bude wani tururin sanyi ne ya daki fuskana. Ledan da nagani sama ne na bude naga kaji ne a ciki da sauran drinks a cikin kwalayen su ga kuma danye kajin da ba,a gyara ba nan zube acikin sunyi kankara. Ledan kajin na jawo na dauko daya na sa a oven ina gasa kazan hawaye ne ke zuba a idona saboda irin rayuwan da na riska tun yanzu a gidan. Sai da na kammala na dauka zuwa falo na na zauna ke nan zanci sai ga shi ya shigo part din nawa tunda na dago kai nayi mashi kallo daya na duka naci gaba da cin kaza na a hankali. Karasowa yayi a cikin dakin daga inda nake zaune nace dashi ina kwana a ranshi yaji dadin haka ya amsa min a sake da kin tashi lafiya ? Ni zan fita zuwa office yanzu don yau ina da aiki sosai a office sai dai wanan aikin da naga kinyi yanzu akwai masu aiki a gidan sai idan na dawo yau da yamma zan hadaku in sanar dake komai na gidan don ki sani na gaba . Tunda ya fara magana ban dago kai na kalle shi ba ya karaso inda nake zaune saman kujera na tasa kaza a gabana yana turiri ina ci. Wuri ya samu ya zauna a kusa dani yana fadin ina nawa kazan ko haka zaki bar angon naki yafita da yunwa don nasan ba haka akace ki min ba idan kin zo. Wanan matsalan kane kai haka akace kayiwa bakon gidan ka kabarshi da yunwa idan gari ya waye . Dariya yayi yana kai hannu ga kazan dake gabana yace ai ke yanzu kin wuce bakuwa a gidan nan tunda har kin gabatar da kanki ga matan gidan ko tasan ko wata kalane ke tun yanzu. Nace eh don a haka kuka ja in gabatar maku da kaina ko ni wacece a gare ku ya kara kai hannun shi ya dibi naman yana fadin. Ke may yakai ki shiyan ta a yanzu da sauri na dago kaina ina fadin kada ka dauka shishigi naje maku ni har ga Allah gaida ku da kwana naje yi amatsayi na karama a gare ta. Yace na sani kuma nasan manufar ki sai dai ki sani ba iri Nafisa akewa wanan shishigin ba don a yanzu duk abinda kikayi gani take da sheri kikazo mata don bata da yarda ko kadan. Shiru ne ya biyo a gurin dagani harshi babu mai magana shi ya kawar da shirun da fadin barin bar maki abinki kada kice na cinye maki. Nace kaci ni ya ishe ni su Binta nake jira su shigo mu shiga kitchen mu girka abinda zamuci yau a gidan. Hannu yake gogewa da tissue, ya kallo ni yace au ban fada maki sun tafi ba kina barci mommy tace abarki ki huta kada a tadake sai kunyi waya dasu . Wani iri naji ba dadi a raina har na kasa boyewa a fuskana ya mike yana fadin kar kiji haushin hakan don ba da wani manufa suka tafi basu sallamay ki ba. Sunyi hakane dan a zaton su kin kwana da angon ki daren jiya kina cikin gajiya da wani hali yasa mommy tace su kyaleki ki huta haka. Hararan shi nayi yana murmushi zai fice daga falon yace amarya mai rowa zan kira daddy in fada mai barci kikazo kina min a gida. Kai kadade baka fada mai ba tunda baka da kunya au da wasa kika dauka ke nan sai ya ciro waya a aljihun shi yana kiran daddy na. Kira daya gana biyu daddy ya dauka da sallama a bakin shi, shi yafara gaida daddy din tare da tambayan shi baki sun isa gida lafiya ? Banji amsan da daddy yabashi ba a lokacin sai dai naji yace ma daddy gani nan yana kokarin mika min wayan. Na karba ina gaida daddy din cikin sanyin murya mai ban tausayi don jin muryan daddy ya sakani a wani hali a lokacin gida ne ya dawo min sabo a raina. Da kyat nake iya bude bakina ina amsa ma daddy amin kan adduan dayake kwararo min a wayan wanda nake ji kamar in fashe da kuka a lokacin. Wayan na mika ma AA din ya amsa yaci gaba da magana da daddy cikin sakewa kamar sun dade da sabawa dashi tun farko. Suna gama magana dashi ya kashe wayan yana kallon yadda nake zubar da hawaye daga inda nake zaune. Takowa yayi a hankali zuwa inda nake zaune yana fadin kuka kike don kin ji muryan daddy a yanzu suma fa sun fi son zaman ki anan yanzu da zaman ki a wurin su. Dago kai nayi na kale shi nace rashin sanin zai sa su soni a inda ba a sona da sun san da wanda suka hadani dashi ba sona yake ba nasan da bazasu yarda su dauko ni su kawo ni inda rayuwana zai shiga tangariri ba. Ba,a son ki fa kikace da ba a son ki da baki shigo gidan da bakin ki ka fadi gidan mijin kine ba. Nace dashi ka dogara ashe yace dashi din kowa yasan kina zama gidan yanzu nan gida miji ki ne uban "ya"yan ki masu zuwa. Uban wasu dai a ina zan haifi diyan da uban su bai taba sona ba balle ya furta min wata kallama mai kama da hakan. Murmushi yayi a baiyane yace kalman so kike so a furta maki san nan ki yarda ana son ki na dago na kalle shi na kawar da kaina daga kallon shi. Gap dani ya matso kamar zai shige min jiki sai da na dan ja da baya na makure a gefen kujera ya ce koya min abinda zan fada maki yanzu a shirye nake in fada maki matukar zaki yarda dani idan na fada maki din. Sauran yaya kayi ka fada masu kana son su har ka zauna dasu a gidan ka zai yi magana mukaji sallama a kofan shigowa part din kafin mu amsa maishi har ta shigo falon ko. Ba sai an fada min cewa buzuwa bace itama don yanayin su dana gani a tare da ita ba gaisuwa ko wani abu sai cewa tayi Alaji yayan mu tace kafito yanzu tana magana dakai. Yace kice da ita gani nan tafe ya na shirin mikewa tsaye itama ta juya zata fice tana wani harare hararen da tsage ranci nace ke buzuwa. Daga yau idan zaki shigo wuri ki bari idan kinyi sallama sai an baki iso zaki shigo kada ki kara fado min a shiya haka kamar kafira. Ta juyo tana kallona kamar zatai magana sai kuma ta kalli fuskan shi yace kije nace ina zuwa yanzu . Ya juyo ya kalle ni na tsura mai idoina kallon yadda zai fita daga dakin ina ganin ya gane may nake nufi sai ha kalli agogon hannun shi yana fadin malamata kin sa na makara zuwa office yau gashi kuma ban dauki komai ga darasin ki ba har zan wuce. Harara na aika mai nace je kada kai laifi gun madam yanzu ta turaka waje ba shiri dariya yayi yana buga kafan shi kasa ya fice yana fadin zan kiraki idan naje office inji lafiyan amaryana, na bishi da harara ina jan tsuki nace a raina akwai aiki a gaba na ja kuwa. Mikewa nayi daga inda nake zaune na fara gyara falon duk da bai wani yi dattiba amma sai da na kara gyara shi na koma kuryan dakin dana gyara tun kan in fita da safe na kara gyarashi shima. Misalalin sha biyu namike nayo alwala nazo zanyi nafila wanda dabi,anane hakan tun a gida idan ba uzuri ya fitar dani waje ba zanyi sallah a wanan lokacin idan ina gida. Aka turo kofan dakin aka shigo wasu mata ne su uku ko wace daga cikin su taci ta koshi tana tafiya da kyat da ita na mike daga inda nake zaune ina masu sannu da zuwa don ban san ko su waye bane a lokacin. Gaida su nake suko sai kallo na suke suna kada kan su cikin gamsuwa da ganina Nafisa ce ta shigo dakin a karshe . Tana wani ya tsune kamar mai jin wari wani abu a part din nasan salon iya shegen tane haka yasa ban wani tsargu ba. Tace ashe har kun shigo ko taja tayi tsaye a bayan kujera daya daga cikin su ne take fadin eh lalai kuwa mun ga amarya itama gata da zubi irin naku na buzaye ai ba a raba ku da ita don kusan zubin ku daya da ita. Daga inda take tsaye tacevkin sani ko farin mai ne do yanzu akwai fari a shago sai yadda kake son ya tsaya maka zai tsaya. Nace ai kin san tun kafin ai farin shago akwai na asali wanan da kike gani daga Allah na samay shi ba saye nayi ba kamar wasu. Madam tace a, a Nafisa kardai kishi yasaki yin maganan nan amma ai wanan fari ke ma kin san na asaline jin haka da madam ta fada yasa tayi shiru tasan katse ta tayi daga yin katobara a gaba mu. Ina zuwa tace kasu ta fice daga dakin na gane mutanen tane don haka ban wani sake dasu ba a dakin. Nafisa na fita waje madam tace dama mun shigo mu gan ki ne kuma muyi maki nasiha ku zauna lafiya a tsakanin ku ki biyayya ga mijin ki da matar gidan da kika samu. Kada ki wuce matsayin ki garesu kamar in bude baki in ce mata akwai wani matsayi ne da ya wuce in shiga a gidan sai dai nayi shiru inji karshen maganan ta. Tunda ba sa,ar yina bace don dukkan su ukun sun manyata ga ido bazan iya masu rashin kunya ba a yadda suke. Taci gaba da fadin kada ki zaman to cikin irin matan nan masu shiga gida su tarwatsa zaman lafiya agida. Ki maza ke ma ki sama muna yan dugwidugwi ki cika muna yaya a gidan koda yake ancd ba son shi kikeyi ba ma aka aura maki shi. Sai lokacin nayi magana tunda ta fara nace cikin dariya ai hajiya zancen rashin so ya kare gareni yanzu tunda na shigo sai a fara damawa dani nima. Kallon juna naga sunyi dana fadi hakan ta gyara zama tana fadin yawa yad gari ai zancen so ya kare kan tunda an shigo ta sake kashe murya tace kin ga dai kishiyar taki ai. Don haka ki bita a sannu don muke tare da ita mu muka san halin ta ba son kishiya take ba don haka nake fada maki kibi a sannu kada ki shiga sha,anin da ba naki ba. Ki kwanta kikaga gudun ta kafin ki aitar da komai garesu don sai kasan kan gida kake kafa naka ikon nace ai gidan tane hajiya don tare na samay ta da mijin ta may zai sa in sa mata ido ga alamuranta bayan tare nazo na samay su. Ina kallon su suks kalli juna suka daga ma junan su gira cikin sytle suka mike suna fadin to amarya min gaida ke mu zamu tafi muna maku fatan alheri . Nagode halin ku na alheri gare ni ya rakaku suka kali juna suka fice a dakin naja tsuki suna fita sai dakin Nafisa suka shiga. Tana zaune tana jiran shigowan su taji yaya akayi madam na zama tace Nafisa wanan amaryan taki ido ta a bude yake wallahi naga kamar kar take kallon mu ta gane plain din mu fa. Hajjaju tace aini amsan da take bakine ma ya firgitani wallahi yarinya da an fadi magana sai ta bada amsa daidai da maganan mutum. Wallahi shegiya ni kyau tane ma ya rudani wallahi dole samad ya rikice muna haka a kan ta babu namijin da zai samu wanan ya bari ta kubce mashi. Yadda suke zuzutani a gaban ta yasa ranta ya kara baci taji wani irin kishi da hassadana ya kara shiga ranta a lokaci daya. Taji in akwai wanda ta tsana yanzu a duniya bai wuce ni din ba sai a lokacin take tunanen ina ta fara sani na don ita a zaton ta anan abuja ta sani. Gani sukayi ta mike zubur suka mai da hankalin su gare ta suna kallon ta tace tsaya hajjaju yarinyar nan kamar itace wace mahaifiyar samad ta taba hado mu da ita wani lokaci mu rage mata hanya daga kaduna. Nan dai ta koro masu yadda abin ya faru take madam tace duk yadda akayi da sanin mahaifiyar shi wanan abin ya faru. Sun dade suna magana akan zancen suna neman mafita yadda zasuyi su kawar dani a gidan cikin dan kankanin lokaci. Hajjajune tace ni anawa ganin dan bakan nan zata fara dana masu ya zamanto babu abin da ya wakana a tsakanin su don babu shegiyar da zata zauna haka tana kallon namiji kamar samad bai taba ta ba. Madam ta juya wurin ta tace ba mutumin nan na maiduguri ya bamu shi tace ai tun ranan da aka kawo ta na fito da shi yanzun haka akan shi na dogara in ga iya gudun su kafin in shiga masu Niger din kansu. Don nafi gane ma asirin mutanen kasar mu don na nan sai ya dauki lokaci kafin kaga fa,idan abu. Yinin ranan ya kirani har sau biyu ban daga waya ba sai ga na uku ne na dauka cikin basarwa nake amsa mashi maganan shi ba wani magana bane sai zolayan da yake min da fadin. Amarya na ya na barki kifa shirya idan na dawo darasin mu zaici gaba daga inda muka tsaya don kin san dalibin naki ba kan daukan magana yake dashi ba. Kaidai ka sani na bashi amsa a hasale tare da fadin wanan ne sallon yaudaran ka ashe idan ka saba yaudaran matanka da dadin baki anan kan kayi kuskuren yin haka. Dariya dake bani haushi ya soma na kashe wayan tare da jan tsuki na koma na kwanta naci gaba da tunane a raina ina tuna yadda zaman mu zai kwashe dasu a gidan shi. Gashi na fahinci gidan cike yake da yan uwan Nafisa da alaman rashin mutunci a tattare dasu kuma. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Iya kana dasu ido banda mama da yan uwan ta ban magana da kowa a gidan namu kosu don sun gwada min kulawan su a kaina ne kuma nasan su na sona. Har maryam da nasan ta zo nan don ni ne ban yarda da ita ba yanzu don bala,in haushen ta da nake ji a yanzu din ita ko bata damu ba sai aiwatar da sha,ani buki takeyi hankali kwance. Duk shirin da ake iya kata dasu ido ne ban san may suke shiryawa ba ina dakina kwance na sala airpiece a kunne na ina sauraren kira,an malam Ahmed sulaiman kano mama tani ta shigo dakin mu. Ganin ta yasa na cire airpiece din a kunne na ina kokarin tashi zaune tace daughter tashi ki shirya ki rakani unguwa ba nisa zamu tafi ba nan lapai zaki rakani. Ba musu na tashi na shirya ba wani dogon shiri nayi ba sosai nafito tsarkar gidan namu da har yau bai rabuwa da mata masu shirye shiryen buki. Ita da kawar tane a motar dan haka na shiga baya na zauna itake jan motar do mama tani wayayiyar mace ce nurser ce a IBB hospital minna nan take aiki. Tunda na zauna na kawar da kai gefe ina kallon hanyar ban kara bi ta kansu ba can naji kawar nata na fadin diyata ance kishiyar ki daya buzuwa ce ko ? Banji taba sai da mama tani tace khadija baki ji bane na waigo su da sauri ina sauke ajiyan zuciya maimaita maganan ta ta sake yi a hankali na amsa mata. Tace wai akwai aiki ja agaban ki wallahi don buzayen matan nan shegune wallahi akwai su da shiri na siri wanda su kadai suka san abinda suke ma maza kaga namiji ya mutu a kansu. Mama Tani tace shine abindake ban tsoro ai for god sake mijin yayana kamar wanda baiso yar shi kadauki diyar ka ka mika a irin wanan gidan. Wallahi mairo in ba don nasan halin shi ba sai in ce kudi yabi amma nasan ba haka bane dan shi mutum ne mai tsatsauran ra,ayi ga abinda yayi niya. Nurse Mairo tace kada ki yarda da ita ko kadan don itama ba yardan zatayi dake ba ki sa ido da kyau ga komai da kikeyi a gidan do ko ba gida daya za a aje ku ba sai tasan yadda tayi maki aike. Kuma ki rike ibadan ki muddin kin rike Allah insha Allahu abinda duk zatai maki zaizo da sauki and kina ji kada kiji tsoron ta ko kadan don zatai maki barazana da komai da kika sani tun yanzu ki nuna mata ke ba kanwar lasa bace Ehhe, . Don haka kadai ne zai kwace ki daga sherin ta da kaidin ta don akwaisu da iya hada tugu gasu duk gayen nan da kike gani sunayi a waje wallahi in kin zauna dasu sai kin raina masu . Don ko girki basu iya ba bazaki iya ci abincin su ba ko kadan sanan kuma gasu da jaraban tsiya namiji baya taba isan su shiyasa makike jin anace dasu sadaka yallah. Suna da aure suke bin wasu mazan a waje don bakin shaye shayen su na tsiya sanan kuma wanan bakin tea din dakikaga suna sha ba shayin banza bane hadine na abubuwa suke dirka ma cikin su. Mama Tani tace diyata ga Allah ta dogara shine zai kare muna ita a duk inda take hakane inji Anty Mairo tace amma ance idan kana da kyau ka kara da wanka ko Allah yace tashi in taimake ka. Mama Tani tace haka ne shiyasa kika gana dake muzo wurin babakin da ita kafin a kaita gidan mijin ta don a samu abinda aka bata. Kina ji daughter bance kiji tsoron ta ba ko kadan duk yadda kike jin tsoron ta kiyi kokari kibar tsoron a cikin ranki kada ki bari su gane hakan don da huda ki saudaya akaga wuka ya shiga shike nan baki da sauran shakat a gida. And don Allah kiyi amfani da ilimin ki kada kije ki biye mata kuyi kishin hauka irin su a cikin ruwan sanyi ake guma masu halin su da tayi maki send her back to sender. Zaki ga tayi saurin kariya dake tana fadin wai shige shige kike yi da sauran su ke har tsafi sai ace kina nayi da sauran su. Ke dai daure kiwa miji biyayya don Allah ki fara kamo kan mijin ki shine abuna farko samuwar zaman lafiyan ki a gidan. Sai kin jajir ce wurin tsabta da iya gyaran jiki kiyi kokari ki san irin kayan da yafi so su zaki dinga sawa idan baki da girki kina kwalliya mai daukan ido da hankalin namiji sai kiga namiji ya matsu ya dawo gare ki. Girki kafin ya bar gida ranan girkin ki kin hada mai abin karyawa haka kafin ya dawo kin hada mai abincin dare ko dan abin jika makoshi da zai taba. Kada ki yarda kamshi ya rabu da jikin ki ko yaushe dakin ki jikin ki shiyan ki zama kamahine a koda yaushe. Kalamai masu dadi su dinga zuwa suna dawowa a bakin ki da irin dan shagwaban nan na mata da sauran su sai kin mai da kan ki karuwan gida da kyau gada ki yarda ki nuna gajiyan ki ko kadan ga miji. Haka dai sukaci gaba da min huduba iri iri wasu ma ban san may suke nufi dasu ba a kofan wani gida motar su ya ja ya tsaya. Gidan irin ginan lakan nan ne na kauye mai kofofi fiye da uku ga rumbu a tsakiyan gidan na laka. Matan gidan suka shiga taron mu suna gaida mu a cikin harshen nufe Anty Mairo na amsa masu . Sai da muka dan huta kadan wurin matan gidan akai muna iso zuwa wani daki shima dai ginan lakane kamar sauran sai dai shi an mai bugun kwana sai dai kwanon ya tsufa. Wani dattijo ne baki mai farin gemu zaune saman wani buzu fari ga littatafai nan da yawa a gefen shi ga wani katon tasbaha yana ja a hannun shi sai kamshin turaren mutanen da ke tashi a dan dakin. Ga hoton iyas a ko ina an manna a dakin wuri muka samu mu ukun muka zauna sai daya gama adduan shi ya shafa san nan ya juyo gurin mu yana fadin sannun ku da zuwa. Sun gaisa sosai da Anty Mairo sai ta gyara zama tace baba ga yarinyar kawata zatai aure ita muka kawo wurin ka son akwai matsala zata ci gaba yace yana kallona dakata Mairo. Yace ai bata da wani matsala da kuke tunane tunda naga mijin da ta aura yana son ta sosai a zuciyar shi kuma zasu haihu dashi sosai ai kun ga matsala ya kare ko ? Da sauri na dago kai na kalli mama Tani muka hada ido tace malam don Allah ko akwai wani abinda za a taimaka mata dashi haka ko da addua, ne. Don gidan mutumin akwai matsala sosai don kishiryar ta daya ma buzuwa ce ka shige shige da nbin bokaye da malamai da sauran su. Haka ne na gani ai sai dai shawaran da zan baku shine ko nan gaba kada ku bata kudin ku ko lokacin ku zuwa wurin wani don yarinyar ku tana da tsarin Allah a jikin ta. Kuma Aljannun ta ma duk musulmai ne bazasu bar wani abin cutarwa ya cutar da ita haka kai tsaye ba don da taimakon Allah har aka kai ga yi auren su yanzu da ba don ita din bace kai ina wane buzun ta. Da yanzu an mata da labarin ta ai kun dade tare da mutumin ko yace yana mai tsura min idanun shi jajaye irin na nufawan gidi. Mama Tani ta kara fadin malam a dai dan tai maka mata don Allah da wani abin yace kai bazaku yarda bane amma tunda kun matsa batin bata wani abin. Sai da ya yunkura yana dauko jakkan shi daga gefen shi yake cewa sai dai don Allah ki dinga hakkuri ko yaushe don hakkuri shine a kan gaban ko wani alamari kin ji. Nace a sanyayye naji malam yace kada ki kuskura kiwa wani sheri haka kuma wanda yayi maki shima zai girbi abinsa don irin mabiyan da kike dasu. Wani dan kyale ya bude ya ciro garin magani daga ciki yana fadin ga wanan ki shaka idan kun koma gida yau da gobe sai wanan da zan rubuta maki ki shanye shi a nan gurin na kada kaina. Sai daya rubuta ya bani na shanye duk sun tsare da ido yace in shafa dan kwakwagin a fuskana na shafa yace Allah ya tsare ya kare a duk inda kike. Su mama tani suka fara yi mai godiya suka balle jakka suka fito mai da kudi da sauri ya girgiza kan shi yana fadin ina ba zan karbi ku sisin ku ba don Allah nayi mata. Anty Mairo ne ta bude jakkan ta tafito da kulin goro manyamanya ta aje mai a gaban shi yace to kin ga yar gida tasan abinda nake so fiye da kudi indan kin bani wanan kin gama min komai. Jikina duk babu karfi haka na fito na tsaya a bakin motar mama Mairo na jingina bayana ga motar ina tunanen duniya tare da bin garin da kallon mamaki kai duniya da fadi yake wallahi. Ban taba zuwa lapai ba sai wanan karon da dalilin auren ya kawo ni garin ko da muka iso minna la,sar yayi a lokacin. Haka na shigo na samu wuri a dakin mama na kwanta yayin da suka shigo ciki suma a gajiye suka samu wuri suka zauna. Ruwa da abinci mama ta kawo masu mikewa nayi don inje inyi alwala inyi sallah Anty mairo ne ta dubeni tace ke kuma fa bazaki zauna kici abincin ba ? Na koshi nace dasu can kasan makoshina tace gara kici abinci kada kije gidan angon ki ba karfi waima kun fara bata abin gyara jiki ko ? Ban samu zama ba yau dai nake son mu fita da dare zuwa gidan hajiya Bayi mu san abin yi baki na turo gaba na fice daga dakin. Bayan sun huta sun ma mama bayan nin komai sai lokacin naga hankalin ta ya dan kwanta taci gaba da dan walwala a fuskan ta. NAFISA Tunda ya haura sama bata kara bi ta kan shi ba ranan ko runtsawa batayi ba ta rasa may zatayi taji sanyi a ranta. Ta tsani Yusuf da iyayyen Samad dan tana ganin su saka shi wanan auren bawai yin kan shi bane a ganin ta. Maganan wata daga vikin kawar tane ya tsaya mata arai da take cewa wai yar minna wa yan nan gogaggun matane fa su ma ga iya tsafi don mayu ne. Gasu da kyau tsiya kamar su sukai kansu ga ilimi da jin kai sai kinyi aiki babba gaskiya amma sai wata kawar su tace mata ko yaya take dai ki san batai kamar nafisa ba dai ko ? Don haka karkiji komai a ranki karaf daya zaki ma shegiya wa ya aiko ta cikin mu ai ba sani ba ragowa ga kishiya yanzu. Ire iren magan ganun da take ta tunawa kenan har gari ya waye tunda safe tabar gidan bata ko tsaya bin ta kan maigidan ba don bata da lokacin shi yanzu kallon mataudari take mashi so take ta gama da karamar yarinyar da take son shige mata hanci kafin shi ta waiwayyo shi. Hanya suka dauka sai maiduguri su ukku sun sha tafiya a hanya kagin su isa maidugurin ta koro bayanin komai da wa yanda take so a illanta mata mutumi yace zai mata akan kudi masu yawa kuma ta yarda. Yabasu abinda zai basu suka kama hanya inda yai masu alkawarin khadija ba zata shiga gidan nan ba ko ta shiga ba zaman lafiya a tsakanin su. Suna hanya a gajiye madam tace aini dama na sani akwai abinda yarinyar nan ta taka muna kwance an muna nasari a inda bamu zata ba. Ji irin kudin da muke narkawa akan wanan mutumin amma wai ace yau shine yai muna abinda bamu zata ba haka. Nafisa taja tsaki tace kin san ba kullun ake kwana a gado ba suma nasan ba don sun iya asiri ba haka da wane su da Samad. Kin san fan Niger din nan akwaisu da maganin tsiya wallahi gasu da mugayen malamai da kudin ki kadan bukatan ki sai ya biya. Barsu kawai madam wasa suke dani wallahi basu san ko cikin buzayen suna suka tara ba yanzun dai in samu in karya asirin tukun in koma kan su da kyau babu yar iskan da ta isa ta aure min miji ina kallon ta. Ni kishiya kota lahira in ba dole ba bani son ta ai balle ta duniya bazan yarda ina kallo ba wata tazo shimfida da mijina ba ina kallo ta lasar min zuman miji. Wanan kayan nawa ne ni kadai ba wata yar iskan data isa takai wurin nan ko Fati a kullun shine bakin cikina da ita bakar manya kawai. Dariya madam yayi sosai tace Nafisa baki da kyau wallahi ke wanan ne kawai abinda kika tsana kar wata ta lasa zumar bindin ki tace bari madan ina bakin ciki da hakan wallahi yafi komai kona min rai da kishiya. AA Tunda ya falka daga barci baiji duri ya ta ba yasan fushi take dashi don haka bai nemay ta ba kuma bai fito daga dakin ba. Sai da Yusuf yakira shi yake sheda mashi gashi a waje ya fito ya fito ya samay shi a wajen bayan sun gaisa ne suka fara shawaran inda zasu gyara min . Yace kasan yanzu sama kusa da dakina Nafisa ta koma ita so sai dai idan kasan za a gyara mata ita khadijan . Wani kallo Yusuf ya jefa mashi yace kana iya adalci agidan ka kuwa may nene na rashin adalci anan yace dashi kai kaga yadace ace kuna sama kai da Nafisa ita kuma khadija na kasa kayi adalci ke nan ? May kake son yan uwan ka su dauki hakan da kayi tun yanzu ka nuna masu irin zaman da yar su zatayi a gidan. Yace kai mata problem ne wallahi yanzun may ye a cikin haka ba na bata daki zama ba ita a gidan yace look A A wallahi idan zaka gyara iri halaiyar nan da nafisa ta koya ma ka gyara tun wuri kasan dai khadija ba irin Fati bane da kuja samu kuna cuta mata bata magana. Yace don Allah ya isa yanzu yaya kake so yace ko gaba dayan su ka gyara masu dakin saman ko kuma su dukan su dawo kasa tinda akwai dakuna part din sunanan basu komai ba. Ok dama fiti Nafisan ne ya isheni nasan ko a wanan sai mun taba fitin don yan uwanta ne a dakin kai kai Yusuf yace. Yan uwanta a dakin ba yan uwan ta bane idan zasu zauna da ita su zauna idan taga tana iya zama dasu sama dai ne kan ya haramta mata har abada. Murmushi yayi yace ai kun fi kusa zaka ita da ita yace barin je in fada mata ta kwashe ta dawo kasa jerin dakunan su na da. A tare suka shiga gidan zuwa falon yace a kira mai Nafisa wace ya tura tace tun safe tafita gidan bata dawo ba. Kallon juna sukayi suna mamaki Yusuf da kanshi ya zaba min inda za a gyara min nan yabar AA yana tambayan su inda taje. Gyara sosai ake ma gidan har dare an kwashe tsofin kujerun gida da sauran abubuwa an shigo da wasu har dare mutanen suna aiki gidan duk da gwanaye ne amma sai da aikin yakai su dare kafin wani lokaci gidan ya sauya kamar ba shi ba an kawata ko ina na gidan. Sai biyu da wani abu na dare ta dawo gidan kai tsaye tayo ma falon tsunke tana kunna wuta indon ta ya sauka ga sauyin da gidan ya samu na dan lokaci kadan. Sai da ta gama bin ko ina da ido kafin ta ankara da maigidan tsaye saman steps yana kallon ta. Zata karaso yace ke dakata nan daga ina kike yanzu kamar bata ji shi ba tana kokarin haurowa sama yace cikin daka tsaya nace daga ina kike yanzu a wanan lokacin. Tace cikin tsiwa naje samun mafita ne akaina abinda zai fitar dani don ba zan zauna ka dauko ni ka kawo garin mutane kaso ka wullakan ta ni ba ko ina akwai mutanen arziki a duniya. Zaki fada min ida kika je ko sai ranki ya baci tace wani guri muka je kuma dare yai muna sai yanzun muka dawo ta fadi tana kokarin haurawa sama. Yace dakata dakin ki yanzu ya koma kasane dukkan ku a kasa zaku zauna ku bar min part dina dama nawa ne ni kadai na gina. Ranan yaga hauka da tonon asiri a wiein ta sai da ya nuna mata namiji ne shi ma ta kyale shi sai da safe yake fada mata ranan amaryan shi zata tare. Sai da madam tazo gidan ta ya samu ta natsu daga haukan da take fada sosai su madan sukai mata suna fadin zasu barta don tana son bada su a idon mutane su kuma basu nuna rakin kishiya a fili sanan ta natsu. Sai kai da koma Yusuf keyi a gidan yayin da yake shige da fice nafisa na daki da yan uwan ta da kawayen ta ana ta faman zugata a gidan. KHADIJA Tunda muka dawo lapai da su mama Tani ban kara lafiya ba haka nake zube har washe garin da za a kaini din dunga yadda nake bai sa daddy yayi hakkuri ba har in ji sauki. Duk wani wanda zai min nasiha akan aure a cikin yan uwa yazo yai min nasiha a dakin mu fada kan zaman aure da sabon yanayi da zan shiga yanzu. Daddy sai fada yake suyi su tafi kada dare yai masu a hanya motar data dauki kayan da zan tafi dashi daga gidan mu duk da Yusuf yace kada ai min wani tarkace komai zan samu acan amma bai hana iyayyena su saya min abinda ya dace dani ba. Wani siri da iyayye mata basu sani ba akai min mama ce ta wanke barin jikin ta na gefen dama aka bani ruwan in wanke jikina dashi tare da dauro alwalan barin gidan mu nazo nayi sallah raka,a biyu. Sannan su Anty Amina da mama Tani suka shirya ni cikin wani lafiyayyen cotting lace mai laushi da daukan ido aka kawo alkyaban aka dora min sama mai hula da gyale a jikin shi irin na matan kasar yamal. Suna rike da hannu na a guda mutane suka raka ni kofan dakin daddy don muyi sallama dashi ina kuka kamar zan shude mun samay shi shida mama a dakin suna magana muka shigo. Na tsunguna a gaban su tare da kifa kaina a jikin maman mu ina kuka Daddy ne yayi karfin halin magana a dakin yana fadin haba khadija ( kijjo) wai mainene a ciki harshen Nufan ci yace kukan ya isa haka mana. Khadija aure ba yana nufin kin rabu damu bane har abada a, a muna tare dake har abada ga Amina da suwaiba kina gani duk da sunyi aure amma ko yaushe muna tare. Khadija ni ne dai mahaifin ki na yafe maki duniya da lahira duk abinda zakiyi a gidan mijin ki ina son ki tuna da Allah ki sa Allah a gaba sai kiga komai yazo maki da sauki. Ki bi mijin ki sau da kafa don yanzu Aljannan ki ya koma karkashin mijin ki nayi bincike da dama khadija kafin in aura maki shi na gane mutumin kirki ne sosai ban ba dake haka ba sai da nayi kwakwaran bincike a kan shi. Allah yayi maki albarka yabaku zuria masu albarka da amfanin a duniya da lahira mutanen dake wurin suka ce Amin sai mama tani tace maman mu tayi min fada. Sai da ta fara magana sai ta kasa sai cewa tayi Allah yai maku albarka ya tsare mun ke da tsarin sa na alheri ya kare min ke ga abinki sai kuka ya kubce mata ta dora hannu a kaina tana dan bubuga min kaina a hankali. Duk wanda ke wuri kuka yake yi banda daddy dake murmushin yake na ciki na ciki mama tani ne ta dago ni tana fadin kin dai ga yadda mahaifiyar ki ke yi a gidan ku don haka ke ma kiyi koyi da halin ta. Daddy ne yace a fito yana fadin a tafi kada ayi rana a hanyan dare yayi nan aka firfito masu zuwa dama suna a shirye motoci biyar ne za su tafi yan rakiya na sai yan uwan ango daya da suka zo yau da sassafe. Ni da mama Tani da maryam ne a motar mu maryam na gaba muna baya zaune da mama sauran yan uwa da abokan arziki suna sauran motocin. Uku saura na rana muna cikin garin Abuja direct gidan muka nufa sai dai abin mamakin da muka fara karo dashi shine motar farko data tashi da kayana a ciki tana tsaye kofan gidan na AA a bakin get tun lokacin da suka iso wai an hanasu shiga ciki. Gwagona da wata yar maman mu sune suka biyo kayan suma gasu waje zaune cirko cirko a bakin get din gidan. Motocin mu na tsayawa sukayo gurin mu suna fadin kun iso ko wallahi tun dazun muka iso akwai matsala a gidan nan don wai uwargida tace ba za,a shiga da kayan khadija ciki ba. Kamar yaya baza a shiga da kayan ciki ba mama tani da kawayen ta suka tambaya gwago tace haka dai mai tsaron kofan yace muna da muka iso. Su mama suka taka har zuwa kofan gidan ta kwankwasa shiru ba a bude ba sai wata kawar aikin mama ta karaso ta fara dukan kofan da karfi kamar zata balla get din shiga gidan. Nan mata da aka zo suka shiga fadin albarkacin bakin su shiru ba wanda ya bude kofan maryam ne daga inda muke zaune ta daga waya ta kira Yusuf tana fada mai halin da ake ciki. Yace what kice a bari muzo yanzu ya kashe wayan nan maryam ke fada masu abinda suka ce mama tani tace lallai akwai magana a gidan nan. Wanan wata irin mace ce yar iska haka da ita sauran sukace yau ko zata ga tsiya don zamu gwada mata mun fita iskanci babu tsoro a gare mu ko kadan. Sai lokacin dariya ya subbuce min don su ma sunga abinda nakewa gudu yanzu da idon su zasu je su karas a gida idan sun koma. Maryam dake zaune gaban mota ta gama waya ta juyo tana ce min muguwa may kikewa dariya nace sun fara sheda abinda nake fada maku tun yanzu. Daga inda muke zaune muna kallon yadda ake rikici a kofan gidan yadda yan kawo ni ke faman halako da tada jijiyoyin wuya aka a budw masu kofa su shiga dani. Da suka fara dukan kofan iya karfin su gaba dayan su kamar zasu ta da unguwa a lokacin. Dole aka fito su madam ne suka fito daga ciki suna fadin wai waye zasu balla muna kofa haka ne suna fadi da karfi daga ciki ? ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Kawayen mama Tani da su Ya Amina sukace baki ne na alheri daga minna daga ciki su madam suka amsa nan ba gidan mutanen Niger bane kunyi bata. Mommy da motar su ya tsaya ta fito da sauri daga motar tana tambayan may ke faruwa ne haka nan matan ke fada mata abinda suka sama a gidan rai bace ta daga waya ta kira Abdulsamad din yazo ga abinda ke faruwa a gidan shi. Mommy ta kasa hakkuri taje kofan tace ku bude kofan nan amaryan Abdulsamad ne ta iso badai samad bakan don mata daya gare shi Nafisa. Kun makara don dan zaki ya girma inji wata daga cikin yan kawo ni yau komai tsiyan ku komai kishin ki sai amarya ta shiga gidan nan sai dai ku mutu da bakin ciki. Yan takife sun so abarsu su haura su bude mommy tace idan kun shiga baku san su nawa bane a ciki don haka kuyi hakkuri maigidan ya taho. Sai ga yusuf yazo yana zuwa ya shiga dukan kofan da karfin tsiya amma basu bude ba wani layi ya kira sai ga wani mutum ya iso ya balle kofan ta baya. Mu dai muna daga gefe muna kallon su anata hayaniya a gurin har aka bude kofan gidan matan dake ciki gasu tsaye cirko cirko daga ciki Yusuf ya wagale kofan gidan gaba dayan shi. Wata daga cikin yan uwa ta sakai gida ta debo ruwa daga cikin gidan a sabon butan da suka riko suka bita da kallo takawo inda nake tsaye tace in fito inyi alwala da shi. Nafisa ta fito da tana fadin malam ko kamanta nan din ba gidan ka bane da zaka sa a balle muna kofa haka ka barmu sake macucin banza mayaudari. Ina idar da alwalan motar AA tana isowa gurin ya sa kai ya shiga haraban gidan a hasale Yusuf ne dashi ganin mun tsaya cirko cirko suka zo suna ba yan uwa na hakkuri. Mama Tani tace ai gara su mai dani gida don tun yanzu sun gane kalar macen dake gidan shi bazasu iya wucewa su barni gidan ba. Ganin kamar mama da gaske take maganan ta yasa suka fara bata hakkuri mommy tace su mama suyi hakkuri haka auren da zaiyi albarka ya gada wani lokaci sai anyi rigima aure ke zama aure. Tacei ba komai alwala muka tsaya amaryan ka tayi yanzun zamu shigo da ita lokacin su mommy sun sa kai shiga cikin gidan duk kunya ya rufe su na abinda ya faru. Gwagona da mama Tani ne a gefe na sun riko min hannu muna tafe suna fada min abinda zan karanta gap da kofan shiga muka ja muka tsaya mama ta rada min in fara kallon barin dama in yi auzubillahi mina shaitanin rajin sau uku hakama barin hagu na. Sai in shiga gidan da sunayen Allah ko kulhuwallahu a bakina da yarda Allah duk wani abin ki zai kauce min alheri zai tare ni a ciki insha Allahu. Wanan abinda suke min yasa hankalin su Nafisa ya tashi sosai muna shiga muka samu sun kai su goma sha a cikin gidan . Gudan da yan uwana suka shigo dashine ya kara firgita Nafisa din ga bakin labarin da ake bata wai ba a shigo dani gidan ba sai da nayi alwala kuma ana tafiya ana tsayawa dani kenan mun san dai abinda muka taka mukazo mata dashi gidan. Gefen da aka bani anty Fauziya kaunan shi tayi muna iso zuwa can ina rike a hannun mama tani har wanan lokacin a daidai bakin kofan shiga part din suka tsayar dani a gurin addu,oin kariya da fatan samun alheri sukai ta karantawa duk wanda ke gidan zai iya jiyo muryan mai karatun. Wannan abin yayi matukar kara ta da hankalin Nafisa da mukarabanta sai fadin suke yi wani sabon sallo sai da wata mai dan sauran imani daga cikin hamshakan matan dake zaune tace sun fimu dubura duk suka kallo ta. Tace Allah da manzon sa suna son masu koyi da abinda Annabi ya kowa yar damu daga cikin addinin shi wanan karatun da suke da alwalan da aka ce tayi ku baku fahinci manufan su ba har yanzu sun mayar da hankali suna sauraren ta. Tace wallahi wallahi wanan abin da sukayi ko sarkin aljannu yau muka dauko muka aje a gidan nan yana muna tsafi komai da mukayi ya karye don dawuya duk abinda akayi yai tasiri akan yarinyar nan. Nufawan nan fa shegun mutune ne sun san addini kamar tsiya yanzu kin ga sun samu lincage din mu shi yasa suka shigo muna da shirin su suma. Ki dubi idon su duk a bude yake babu wace bata san abin da takeyi ba suma daga cikin su akwai aiki babba gare ku don dai ni na hango hakan. Kafin ta rufe baki suka shiga fadin magana kowa da abin da yake fadi dakin jikin nafisa yayi sanyi ta fara fadin Samad ya cuce ni wallahi da bai fada min tun farko in shirya ba. Tana son sake layi madam ta tare ta tana fadin babu komai wallahi koda Alhaji malam zasu kawo ta mun fisu sheri damu suke wasan ba zasu wuce su barta anan bane tare da mu suyi suga su tafi. Fasawa za,ayi kome yadda ta shigo haka zata koma don ba gidan zaman ta bane nan gidan Nafisa da mijin ta ne ita kadai. Ihu suka sa suna fadin sai madam mun sanki mun san sherin ki balle an taba maki yar lele ai sai inda karfin ki yakare yanzu kan mun bata sati biyu ayi waje road da yar iska kishiya ko kaya. Ana zaune kalau yaje ya jajibo muna wani wahala wai kishiya na tsani kalman kishiya balle kishiyan afili . Wata tace kwadayin namiji dai ne idan ya motsa may zata kai Nafisa dashi kyau ko fari ko tsayi ko gashi nasan babu ko daya wallahi don haka kodon kyau ki dole a daga maki kafa. Maganganu iri iri ke wanzuwa a cikin dakin tare da kara mata hudubun shegu da kara koya mata tugu da kisisina da kada ta daga min kafa ko na rana guda in samu wuri. KHADIJA Da fatiha na saka kai acikin dakin duk da idona yana a rufe bai hana in gane na shigo wani sabon rayuwa ba idona nakara lumshewa wasu hawayen bakin ciki suka ziyarci fuskana. Ina jin mata na yaba kyan part din da tsaruwan shi wanda ni bashi ne a gabana ba yanzu duk da dai haka kowa ke fatan samu a rayuwan shi amma ni wanan abin da suke fadi tankar guba nake jin shi a raina. Zaunar dani akayi a bakin gadon dakin mama Tani ce mai rada min komai a kunne sai yanzu na gane ma,anan abinda ake idan za, a kai amarya inga wata mace ta rike ta gap da gap ajikin ta ana magana kuskus da amaryan yau da yazo kaina na fahinci komai. Sallolin da ake bin mu aka fara gabatarwa a gagauce sai ga su Fauziya da sauran yan uwan su na shigo muna da kulolin abinci lafiyayyu a part din. Anci ansha aka shiga tsumi fadi akan Nafisa muna cikin uwar daki dani da maryam da wasu yan matan minna a saman gadon nidai sauraren hiran su nake ban magana komai da kowa abinda ya damay ni ya damay ni a raina. Don ban san ta ina zan fara ba a gidan nan da Nafisa zan fara koda maigidan da yai min yankan baya . Idan ina wanan tunanen sai huduban daddy na ya fado min a rai inji jikina yayi sanyi sosai don na shirya mashi rashin mutunci sosai a raina sai ga mahaifina ya aza min doka akan AA din. Ido kawai nasa da kunne ina tsintar maganan yan uwa da suka kawo ni gamay da zaman gidan kowa sai fadan albarkacin bakin shi yake yi. Part din da akace shine nawa ya ishe mu da yan uwa na sai bayan mun huta mun sauke gajiya ne mama Tani ta shigo tana fadin in shirya zasu kaini wurin uwar gida na mu gaisa a raina nace ashe akwaita kuma. Ina zaune saman sabon salayana banyi niyar tashi maryam ne tace da mama su bari a gyara mi jiki tsab na fito bayan sun gama min feshe feshen tura da sauran su daganin shigana ba sai an fada ma gogagiyar yar boko bace ni muka nufi part din Nafisa din. Tana tsakiyan aminanta suna ta tofin Allah tsine ga maigidan dani da yan uwan miji da nawa wata yar uwarta ne ta shigo da sauri tana fada masu gamunan tafe part din ta. Nafisa ta mike zubur tana haki tana fadin may zasu zo suyi min a shiya ko an fada masu ni sa,ar yarsu ce da zasu wani kawo min ita nan suje can su karata da wanda ya kwaso ta gidan. Su madam suka rike ta suna fadin haba haba Nafisa ki natsu mana ki kwantar da hankalin ki kiji damay suka zo wanan aladan haka akeyin shi ko ina akasan nan ba yau ne farau ba. Kada idanun ki su rufe mana akan kishi ki manta da matsiyaci yanzu ki kwanta kiga takon ta tukunna. Tana huci tana fadin dani zuwa zanyi in dakatar da yan iska da sauri sukace mata dako kin bada kan ki a wurin su may zai sa ki nuna kan ki gare su tun yanzu ai nuna masu kawai ke din ra kwarai ce. Ki daure ki natsu su shigo muji abinda ya kawo su daga nan mu ga kalar tsiyan da ya dauko maku gaki duk kin kasa controling din kan ki kamar bake bace. Ta dubi madan ta sauke ajiyan zuciya tana fadin nima ban san dalili ba wallahi sai dai ina mai tsananin jin kishin yarinyar da tsanar tane. Don Allah manta da kishin nan ki natsu wuri daya da sun shigo su gane kwaruru ba tsaran wake bane kada ki yarda ki nuna komai a gaban su. Ta zauna kamar mutumiyar kwarai taci jan shadda dinki su na yan Niger ga gwala gwalai a jikin ta suna sheki. Da sallama muka shiga suna hada baki wurin amsawa muka shigo aka fara samun wuri ana zaunawa inda mama ta zaunar dani a saman wani kujera dake fuskantar inda suke zaune ita da madam. Nan aka fara gaisuwa a tsakani sai madam tace ina kaunar tamu take ne daga ciki kawar mama tani ta nuna inda nake a kundundune tace a, a baza ki bude fuska muga fuskan kanwar tamu ba. Anty Mairo ta ce to uwargida ga yar mu mun kawo maku amana kafin Anty mairo ta rufe baki wata daga cikin su tace ai ba a karban amanan kishiya Nafisa tace tayani gani kedai sai dai kowa ya zauna da halin shi. Anty mairo tace asha ai zomu zauna zomu saba sai hakkuri da mun dauka kece babba a gidan don haka zatai maki biyayya a gidan amma tunda kince kowa halin sa yafida shi shike nan. Wata daga cikin su ta karbe da fadin ai biyayya yazama dole gare ta don mu ta samu a gidan don haka ita ta zama yar bi a yanzu. Gyara dai, maganan ki don kun riga da kun gama magana kowa tashi tafidda shi dama haka zaman gidan miji yake ai, Allah ya bamu alheri ta mike tare da cewa sauran ku tashi mu tafi. Kowa daga cikin mu ya mike don barin dakin mun kai kofa mukan har mun fice daga dakin sai wata daga cikin su tace ni fa banga mutum ba a nan . Sauran suka amsa da ai shine duk da tana rufe amma kamar ba wata mai fasali bace daga cikin mu wata ta amsa masu da fadin ahaka kuma mijin ku ya gani yace yana son ta. Nafisa zatai magana madam tayi saurin kwabarta da cewa zancen ya isa haka shi dai ya gani yace yana son abin shi ai. Mu dai Allah ya bada zaman hakkurin ki dai kau da kai kawai tayi hakane don kare Nafisa daga sakin layin da take son yi a gaban kowa. Don ko a cikin kawayen nasu akwai munafukai nan take Nafisa ta gano maganan madam din sai tayi shiru. Muna gama fita daga dakin wata ta sake cewa amma dai da kuke wanan maganan kamar kallon tsoro kukai wa amaryan nan ? Saboda may kika fadi haka tace humm ku baku lura da takon ta ba da tsayin ta kafarta mafa farine sol ji yadda ya sha lalai yana daukan ido anya ba boyon kama tai muna ba ? Koma dai may nene kinsan dai mun mata tazara ko sai dai bi don gidan nan sai Nafisa suka saka ihu gaba daya su dake wurin. Washe gari sai ga su fauziya sun shigo da kayan karyawan mu ruwan zafi ne da gwangwanaye madara milo suga da liptop da kuloli dake dauke da kwai da irish a ciki sai turiri suke yi. Nan aka shiga gaidasu da sa masu albarka ita ko matar gidan ko bude part din su basuyi ba sai bayan mun gama karyawa ne ta aiko muna da wani bussashen doya da bai soyu ba wai shine abin karyawan mu bayan makudan kudin da ta karba a wurin AA din tace za aiwa baki abincin dashi. Tace ai yan Niger basu da abincin da yafi doya shiyasa na ce a soya masu doya busakakai suji dashi yan kauyen bazan dasu. Ana shigowa dashi su mama Tani sukace a mayar mata sun koshi don sun karya ko sai da suka gama shiryawa ne suka fito dani zuwa dakin da su mommy suke ciki mun samay su, suna karyawa suma nan dai suka tare mu akai gaishe gashe a tsakani. Mommy ta tare mu da fara,an nan nata tana ba su mama hakkurin abubuwa da ya faru a gidan mama tace ba komai irin su Nafisa haka suke dama zafin kishi da zugin kawayene ke wahalshe su. Mama da ya Amina suka kara danka wa mommy amana don shiga cikin su yanzu danayi sai alokacin nasan su Binta da Zainab na gidan da suka shigo daga gidan da suka sauka suna aikin abincin taron bakin. Nan suka tasani gaba wai sai in bude fuskana su gani mama tace ai zaku ganta don ta zama naku yanzu mintsilar da Binta ke min yasa na jawota zuwa jikina muna maganan siri da ita. Ba wanda yasan da shirin da suka zo ashe har walima suka hada sai dai kawai ganin mata na taruwa a gidan don zuwa yin walima. Nafisa dake daki labari ya samay ta tafito da zuman fada don may mata zasu taru mata a gida bada sanin ta ba Fauziya tace malama gyara zancen ki dai gidan ki ko gidan dan uwan mu. Mommy ne tafito ta kara kwantar da fitinan ta koma daki da tarin bakin cikin da ke cin ta a ranta nan dai malam da aka gaiyato suka fara gabatar da waliman wanda wa,azi ne akan aure sai hakkin miji ga matansa da hakkin mata a gun mijin ta. Inda nasihan ya shiga mutanen dake wurin sosai anci an sha a wurin an raba calander dake dauke da ayatul qursiyu da suna na dana AA da ranan auren mu. Bayan an watse daga walima ne kannen ango suka sai baki sun bada abinda ya sawaka daga garesu gwagona da mukazo da itane ta yaye gyalen dake rufe da fuskana. Aka sa guda nan maza suka shigo abokan ango suka dinga zuba kudi Nafisa dake dakin ta kamar ta kama da wuta a gidan ta rasa yadda zatayi sai surfa ma AA zagi da yusuf da yan uwan shi take yi. Uku daidai yan uwana suka fara shirin tafiya zuwa gida ina ganin haka na shiga damuwa sai da suka ce zasu bar muna yan matan anan su kwana min biyu na sake da zasu tafi ne sukace bari suba da sako daga nan ne ban kara ganin su ba har maryam din duk sun tafi. Shiru ni kadai a dakin da zaman ya isheni ne na mike na shiga bandakin da niyar dauro alwala sai kuma na canza shawara na hada harda wanka nayi. Ina nan zaune ni kadai a dakin gurin da na sallamay sallah magariba sai naji an turo kofan Binta ne da Zainab suka shigo dakin a lokacin. Dauke da kayan abinci a hannun su kallo daya nai masu na kawar da kaina gefe Binta na dariya ta aje kayan tana fadin Amarya kina kamshi. Nace a, a ina wari yanzu ai nasan zama na daku wallahi wai kuna garin nan amma kuka share ni haka kamar baku damu dani ba. Ke nan kuna bayan dan uwanku kike nufi ko may dariya suke min suka samu wuri suka dan zauna zainab tace wallahi ba share ki mukayi ba khadija. Aiki ne yai muna yawa can aka kwashe mu aka kai gidan anty maimuna wai mu dinga ma bakin da suka rakoki abunci baki ga yadda muka ji haushi ba wallahi. Yanzu jiran mu akeyi wai muje gidan mu hado kayan su anty Fauziya yau anan zasu kwana tare dasu mommy tunda an rage yawa a gidan. Da sauri nace don Allah kada ku tafi dukan ku don wallahi tsoro nake ji zaman nan ni kadai ya ishe ni wallahi. Da sauri Binta tace haba khadija tsoron may kuma keda gidan mijin ki wallahi ki fitar da tsoron nan tun yanzu a ranki don wanan kishishiyar taki idan ta gane haka zaki sha wuya a wurin ta gara tun wuri ki nuna mata kefa ba kanwan lasa bace. Nace ni wanan bata a gaba na yanzu amma dai kin san abinda yayan ku yai min bai kyauta min ba wallahi. Haba khadija kada kice haka mana mijin ki ne fa yaya Abdulsamad yanzu komai yayi maki asai ki yafe mashi ko tunda kun zama daya ke dashi yanzu. Wani kallo nayi mata nace eh gaskiya ne zainab kin nuna min bayan dan uwan ki kike tun yanzu tace ba hakana bane wallahi gaskiya ne dole a fade ta. Nace gaskiya akan auren dole don dole yasa iyayyena sukai min a kan shi ba da sanina ba komai ya wakana shine zaki wani ce wai mun zama daya yanzu. Binta ta karbe ni da cewa dama na fada ma hajiyan mu ba da yardan ki yace wai kin yarda dashi ba har kun shirya mu har muna fushi dake akan kin boye muna komai dake tsakani ku dashi sai dai kawai muji aure daga sama. Binta wai may yasa ke baki da hankali ne don Allah maimakon ki bata hakkuri ki kwantar mata da hankali zaki kuma zo kina maganan abinda ya wuce. Binta ta turo baki tana fadin dama ai ke ko yaushe ne magana sai kice ban fadi ba daidai ba tana fadin haka ta mike tana fadin ida kin gama ki samay ni waje. Khadija sai mun dawo ko ince sai da safe mu hadu idan mun shigo kafin mu wuce makarasa maganan mu tana fadin haka ta fice daga dakin. Zainab ta juyo inda nike ta dibeni tana fadin don Allah khadija rabu da mahaukaciya nan Binta kin san girman ne kawai badon ta kai ba. Ban mata magana ba don ina ganin ba sona take ba dan uwanta kawai take so mikewa tayi tabar dakin . Mikewa nayi na ninke salayan da nake zaune akai na dauko wayana tare da kunna kira,a a ciki turare na dauko na feshe ko ina dashi kamshi ya gauraye dakin har falona na koma na kwanta batare da na bude kulan abincin da suka shigo min dashi ba. Kwance nake sai dai ba barci nakeyi ba ina bin kira,an a hankali idona suna a rufe luf nayi hakan ne don in kawar da damuwan dake damuna a lokacin. Duk da kamshin dake tashi a part din nawa ina shaka ina jin dadi a raina amma hakan bai hanani shako kamshin turaren AA dayafi amfani dashi ba ko wani lokaci. Banyi shakkan jin haka ba don a cikin gidan shi nake yanzu don haka ban bude idanuwa na ba har lokacin da nake jin kamshin na karuwa a hancina. Dan babban yatsan kafana na dama ya kama yaja a hankali zubur na bude idona tare da mikewa zaune AA nagani zaune a gefena. Cikin wasu fararen shada sai maiko su ke daukan ido da sauri na mike zaune ina jawo hulan da na saka akaina ya zamay na barshi saman filo. Murmushin shi mai tsada ya sake min tare da mikewa daga inda yake zaune yana fadin kinci abinci kuwa ? Shiru nayi ban bashi amsa ba sai sakon harara da na aika mashi daga inda nake zaune din ya sake cewa wallahi yunwa nake ji khadija tashi muci abincin nan. Tsam na mike na nufi falo na zauna nan tare da barin shi cikin dakin can ya fito falon ina zaune ya kalleni bai min magana ba yasa kai yafita daga dakin. Yana fita nabi bayan shi da kallo tare da jan tsuki sai kuma na dawo da kallona falon ina kallon yadda aka tsara komai gwanin ban sha,awa a raina nace dama ace da wanda nake so yake sona ne falona yake haka danafi kowa morewa a duniya. Can sai gashi ya dawo dakin wanan karon ya sauya kayan dake jikin shi zuwa na shan iskan maza na zaman gida. Kallon na yayi na sauya kayan jikina zuwa rigar barci saidai na dora zani a saman kayan ya rufe min daga sama zuwa cinya na. Kamar badani yake magana ba yace ki tashi ki dauro alwala kizo muyi sallah godiya ga ubangijin mu da ya nuna muna wanan ranan gare mu. Ai kasan ban sallah sai dai in a gidan ka zan koya yanzu dan dariya yayi a baiyane yace a iya sanina dai ba lokacin fashin sallah ki bane wanan lokacin . Au sa idon ka da shishigi har yakai ka ga sanin lokacin fashin sallah na ashe sai yanzu na kara sanin kokai waye . Yace ni waye cikin rankwafowa inda nake kwance ina kokarin zama zaune nace mugu mayaudari maciji wanda bai iya gina ramin kan sa. Wai duk ni daya ke da wanan sunan yau khadija nace sunan kama yafi haka a wurina indai kace shishigi ka iya. Kara matsowa yayi kusa dani ta yadda zamu iya jin numfashin junan mu tare da dora hannun shi saman kaina nayi saurin kaucewa daga tabanin da yake yi. ZAINAB IDRIS MAKAWA 1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Zaune yake ya harde hannayen shi saman kitjin shi yana sauraren bayanin da Yusuf yazo mashi dashi na tafiyan su mommy zuwa Minna gidan mu. Sai baysn ya gama bayanin ne ya sauke ajiyan zuciya tare da fadin ban tsamanin abin zai zo da sauki haka ba Yusuf ne ya dan kalle shi tare da fadin don baka san irin yadda mukai tsaye dani da mommy ba har haka ya faru ko ? Kallon Yusuf din yayi yana fadin kasan wanan auren da zanyi naku ne kaida su momcy din da mama so don kun wahala ai wanan ba komai bane ko ? Au mune ma keda auren ke nan ba kai ba yace Abdulsamad sai kuma ya kasa magana ya girgiza kan shi cikin takaicin shi tare da mikewa tsaye don ya bar office din. Juyowa yayi ya kalli Abdulsamad din yace ban ganin laifin Khadija har kullin don ta karanci ko kai waye kalamin ta bai min zafi a kan ka don halin ka ne take fadi ba sheri ciki . Kai ya rausaya wa Yusuf din tare da fadin zata ko sha wahala idan tazo min a haka ka sani dariya Yusuf yayi yace a naka tunanen ke nan amma ni banga wani wahalan da zata sha ba don tana da basira magance matsalan ka. Ya fada yana kallon shi ido cikin ido tare da dan buga tabur din shi da hannu har yakai kofa yace sai ka zauna a cikin shitin zama angon Khadija mijin buzuwa. Harara ya bishi dashi ya fice ya bar mashi office din a hankali ya sauke ajiyan zuciya ya kalli files din dake gaban shi ya ja tsuki. Tun fitan Yusuf wurin shi bai iya aiwatar da komai ba wunin ranan hudu daidai ya mike don barin gurin zuwa gidan shi ya huta. Shigan motar shi gidan yayi daidai da fitowan Nafisa zuwa unguwa kallon ya bita dashi yadda tasha gaye kamar mai zuwa gasan kyau. Sai da tazo inda yake yana fitowa cikin motar shi ta tsaya da motar ta da sai kidan yaren su ke tashi a ciki tana fadin lafiya ka dawo yanzu ? Lafiya ya bata amsa dashi tare da fadin ina zaki a wanan lokacin yana kallon agogon hannun shi fita zanyi zuwa gidan madam akwai abinda nake son yi a can ne. Tana fadin haka taja motar ta don barin gurin batare da ta saurin abinda zai fada mata ba ta sake mai horn din motar tayi gaba. Binta yayi da kallo kawai yana girgiza kan shi ya sa kai zuwa cikin gidan nashi a falo ya samu yan uwan ta zaune sun dora butan shayi a dan karamin abin da suke dafa shayin dashi sai kidan yan kasan su ke tashi a falon . Ta bayan kujerun falon yabi ya raba don takaicin da yake na ganin haka a gidan shi kuma bai iya yin wani abu akai don ba fasawa zasu yi ba. Sai da yakai sama ya tura kofan dakin ya shiga dakin na nan yarda ya barshi yau kwana uku ke nan yana son ya samu time ya gyara dakin bai samu ba duk dakin a hargitse yake mai. Zubewa yayi saman gadon shi don ya huta sai karan kira ya shigo mai a waya a kasalance ya mika hannu yana daukan wayan. Mommcy ya gani a wayan yasa shi dana received da sauri tare da sallama ta amsa mashi tana fadin sun sauka lafiya tun dazu. Yace Alhamdullahi tace tafiyan namu akwai nasara sosai a cikin shi don babu wani miskilan da muka samu sai dai ita khadija din da taso ta zautu lokacin da ta ganmu. Babangida yakama ace ka zama namiji wanda sai ya nemi so a wurin mace kafin wani abu ya wakana a tsakanin ku amma sai gashi munje ta nuna muna ita still bata san da zancen ka ba balle na zuwan mu. Da kyat na samu na shawo kanta don kada yan uwan tafiya na su fahinci hakan zancen ya kama yawo ga yan uwa har maganan ya koma kunnen matan ka duk da nasan cikin kin mu babu wace ba ta jinin ka bace. Mommy ita fa wanan yarinyar haka take da rikici ba zata taba kwantar da hankali tayi abin mutane ba a daidai sai takawo matsala a cikin abu. A a babangida ba haka ake neman aure ba kamar abin wasa ko wani abin saye can ina son kasan wanan auren ba fa tursasa ma zamuyi kayi shi ba don ra,ayin mu. Yarinyar nan tana ikirarin baka taba nuna mata so ba daga gare ka yanzu kuma na tabtar da hakan don kasan suma khadija tayi lokacin da ta tabbatar da zuwan mu akan maganan ku. Haka ya nuna min khadija ba kudi ko kyau ko nasaban ka ya damay ta ba illa soyayyan ka take nema a gare ka. Mommy suma tayi a kaina don ta gan ku ya tambaya cikin mamaki mommy tace wallahi shi nake son ka gane khadija ta daban ce. Da wata ce murna da farin ciki zatayi don abinda mukazo mata dashi hankalina ya tashi da kalaman yarinyar da take rokona akan na lalashe ka kajenye kudirin auren ta akan ka. Na lura mahaifan ta nason mata dole ne ga abinda bata so sai da muka zauna da uban na fahinci halarci yai muna na ba da ita don Amina da muke zaune da ita cikin salama anan . A yadda ya nuna muna yayi haka ne don dankon zumuncin dake tsakanin mu ya karu mutuncin hakan suka duba zasu ba da yar su gare ka don mun roki hakan gare su kuma sun yarda. Ba don iyayyen ta suna fada taji ba na tabbatar da khadija zata iya sa mu dawo da kayan mu a jiyan da muka kai gidan su a yadda ta nuna muna. Cikin ranshi yace zata iya fiye da hakan ai mommy baki santa bane da shegen girman kan tsiya kamar ba yar tallaka ba. Ashe ana samun masu irin wanan ra,ayin acikin yayan tallakawa a yanzu shi me take so dashi ne bai dai taba hurta ma wata mace kallaman so ba sai dai alama ya nuna sukai ga aure don may yanzu zata tsiro da wani surfan su na mata wai sai ya nuna yana son ta zata yarda son ta yake yi. Mommy ce ta katse shi da fadin kayi kokari ka nuna mata so kamar yadda take so ita kasan fa boko da wayewa yariga yayi karfi ga zuciyar yarinyar nan. Wayenwan kanta ya hango mata haka wanda kuma gaskiya ta hango ma kanta don may zata cusa kanta a inda ba son ta akeyi ba yaushe zatayi tasiri a zuciyar ka. Wanan shi take hangowa ta kasa tsayawa ta fahinci manufar mu wanan maganan ko yaya ba zan so taji shi ba don mu manufar auren mu gare ka ba munyi shi ba ne don gidan ka ya watse ko mu kara jefaka a cikin matsala a, a muna son auren nan ne a tsakanin ku don ganin dacewa ku da juna saboda kwadayin iri daga gare ta. Mommy na fahince ki kuma zanyi kamar yarda kika ce ya fada a takaice cikin gajiya da sauraron maganan ta. Sukai sallama yabi wayan da kallo tare da fadi a fili may deedar take nufi da somaywa akaina da tayi tana nufin har cikin ranta bata kauna ne ko may ? May take son in nuna mata bayan wanan da nake nuna mata wace mace na bata lokacina haka a kanta a wurin neman ta. So take na maida kaina karamin yaro in dinga binta ina fadin deedar ilove you such things like that ko may ? Tsuki yaja tare da mikewa yaji kwanciyan ya isheshi a lokacin wanka yayi ya sauya kayan jikin shi ya fice daga gidan ba tare da yasan inda zai dosa ba. Sai tafiya yake yana zaga garin kamar wani tababe sai da ya gaji ya samu wuri ya faka motar shi tare da fitowa yana shakan iskan da ke kadawa alokacin. Sai tara na dare ya shigo gidan nashi shigowan shi yayi daidai da dawowan nafisa gidan don ganinta da yayi zaune falo yaran ta sun rufa ta da sauran mutanen gidan. Bai tsaya ba kamar kullun don yawan mutanen dake gidan baida daman ya kebe da iyalin shi su gana saboda yawan yan uwan nafisa a gidan. Har ya gama abinda yake ya kwanta bata shigo inda yake ba barci ya fara daukan shi tazo tana taba shi firgigit ya mike tare da cafke hannun ta yana fadin deedar. Tsaye tayi tana mashi kallon mamaki don jin abinda ya furta mata kokari mikewa zaune yake yana tattaro natsuwan shi guri daya. Samad waye dida kuma take tambayan shi cikin kura mai ido tare da tuhuman shi gabanta sai wani irin mugun bugawa yake yi. Sai da ya zauna yace da ita ke bakiji abinda na fada bane da turanci a fili ta sauke ajiyan zuciyan ta tare da zama a bakin gadon tana fadin wallahi har nayi mutuwar wacingadi na dauka ko sunan watane didan da ka furta. Ance kije makaranta kin ki zuwa ki samu ilimi ke kenan kullun a cikin tuhumar mutum ya fadi yana komawa saman gadon ya kwanta rairai yana kallon rufin dakin. May zanyi da wani karatu yanzu banyi jaratin kasan mu ba zan zo nan in bata lokacina da karatun kasarku ni dake da samad inani ina wani karatu kuma ? Yace hakanane amma nasan nan gaba rashin karatun nan zai zo ya damay ki tace a kan may lokacin da take hawowa gadon da kyau ta kwanta. May ake so a duniya banda arziki kuma Allah ya hore ma mijina arzikin da zai dubeni ni da diyana da yan uwana don haka babu wani ilimin zaman duniya da zan nema. Kyau ne da diri Allah ya ban da mijina ke alfahari dashi wanda nasan ba wata macen da zata gilma a gaban ka ka dubeta da sunan so don kafin ka dubi mace da wanan yanin sai idan na daina numfashi kai ko na daina ba zaka kalla ba don tunawa da zube na. Murmushi yayi yana jin maganan wautan da take zuba mashi mai kama da almara a fili yace watau ke nan haka kike gani ke ? Haka din ne na sani na kuma san matan ku na Nigeria yadda suke kaima din kuma kwadayin kirana ne ya jaka gareni ba wani abu ba don haka ba zanji kunya fada komai a gaban ka tunda bani gishiri in baka manda muke ni da kai. Really tace yes ciki yin kwalkwal da idanuwanta kanana tana juya su wanda a da intayi haka abin na burgeshi sabanin yanzu da yake ganin ta mai kananan ido don yaga inda manyan ido madaidai ta suke ga mace. Yau kwana biyu daddy bai sani a ido ba shima bai damu da yanemay ni ba ina ji fitar shi gidan ya na sallama da maman mu ya dan dade da fita gidan na fito daga dakin zuwa dakin mama. Sallama nayi na shiga na samay ta zaune tana ninke kaya da aka wanke kai ta dago ta kalleni tare da mayar da hankali ga abinda takeyi. Mama ina kwana ta amsa min da lafiya ba tare da ta kalleni ba wuri na samu na zauna na dan yi shiru sai can nace da ita. Mama ke ma fushi kike danine yanzu na tambaya cikin kura mata ido ta dago kai ta kalle ni sau daya ta kawar da kanta tare da fadin. Khadija don may ba zanyi fushi dake ba kin kasa hakuri da kaddaran ubangiji a kan ki har yanzu fushi fa naga kinayi da mahaifin ki baki fitowa ki gaida shi kamar yadda kuka saba. So kike shi yaje ya gaida ke a dakin ki ko may mama ni ba fushi nake da ku ba wallahi kun dai kasa fahinta nane kusan may mutimin nan ke nufi dani. Wallahi mama AA ba sona yake tsakani da Allah ba so yake yayi amfani daku don ya cuta min da sauri mama tace Allah ba zai basu ikon cuta maki ba khadija. Nasan abinda kike ciki ba ban sani bane so nake kiyi biyayya kamar yadda shima yayi biyayya ga iyayyen shi. Allah kadai yasan may wanan auren naku ke nufi da ya hada ki da wanan mutumin fatana gareki koma manene ubamgiji ya kara mayar dashi alheri ga kowa. Hawaye ne ya zobo min a idona wanda na kasa controling din shi na barshi yana tsiyaya kamar yadda yake son zuba din shike nan yanzu itama mama ta yarda da wanan hafin ke nan. Tace khadija da farko na dauka don kudin shi mahaifin ki ke son maki haka amma da Amina ta zauna ta fahintar dani sai na gane taimakon su kawai mahaifin ki ke son yayi dake bawai do abin hannun shi ba. Ku diya mata Allah ya fara bamu a farkon haihuwan mu don haka na jajirce inga ke din kinyi karatu duk da mahaifin ku bai son hakan na samu da goyon bayan mijin Amina mukaci nasaran hakan. Sai yanzu ne nake fahintar ba diya mace ne kadai keda matsala da rauni ba harda namijin da mata da yawa suke fatan samu farkon haihuwan su suke da matsala. Wanda a zaman nin nan da namiji ya zama tankar innuwar giginya ne ga iyalin shi na nesa kasha innuwar shi ma,ana matan shi da wasu can daban zasu ci amfani shi ba iyayyen da suka reneshi suka gina shi ya zama wani abun ba. Khadija akwai aiki ja a gaban ki wanda aka taru aka dora nauyin shi a gare ki yanzu da addua kadai zamu biki don taimakon ahalin wanan bawan Allah. Cancantan kine ya ja maki haka bawai rashin son da kike tuhumar ba ai maki bane ko wani abin ko nine yau dana yake cikin wanan halin dole in nemi mafita a gare shi. Matukar naga abinda zai fitar dashi din ga halaka kada kiga laifin kowa ga wanan abin abinda Allah ya kaddarane a kanki ya tabbata ubangiji yasa haka shine daidai. Ki natsu ki san abinda kikeyi kada ki sakacin da za a gane tako ki da sauri ki fara aiwatar da shirin ki tun yanzu wanda ba komai bane wanan shirin sai komawa ga mahalincin ki Allah ki mika alamuranki a gare shi tunda bakin alkalami ya riga da ya bushe mahaifin ku ya riga da ya bada ke garesu. Kuka namike inayi nabar dakin da sauri zuwa dakin mu ban fito ba har tsawon wani lokaci sai da zanyi sallah azahar na fito na watsa ma jikina ruwa. Biyar na yamma daddy ya shigo gidan ina jin shi na fito ina mashi sannu da zuwa ya amsa min ba yabo ba fallasa a fuskan shi. Na juya zan wuce naji yace dama ina son magana dake sai na dawo na tsuguna a gaban shi tare da dukar da kaina kasa ina sauraren shi. Yace khadija da na zaci zaki fahinci manufana amma yanzu tunda kina ganin zamuyi maki dole ne na janye kudirina ga maganan mutumin kaduna a kan ki ki fada ma wanan mahmud din da kike so ya turo wanan satin don ba zan janye lokacin dana sa akan ki ba yana fadin haka ya juya ya shige bandaki da buta a hannun shi ya barni a wurin tsugun ne. Bayan kwana biyu sai ga mahmud ya amsa kiran daddy har falon daddy ya shigo nan daddy ya aika a kirani nida mama muka shigo falon. Banyi tsananin ganin mahmud afalon ba kallo daya nayi mai naga duk ya rama bakin shi ya kara fitowa fili tausayin mu ya kara kamani. Dan mun nasan muna cikin wani hali dani dashi a lokacin gefen kujera na samu na tsugun na bayan yan gaisuwan da akayine a tsakani daddy ya fara magana. Yace mahmud mun aika kazo ne don maganan da ke tsakanin ka da yarinyar waje na khadija wanda nace ta fada ma ka turo magabatan ka yau kwana biyu naji shiru. Don haka na kiraka gaka gata ga uwar ta lamari ne na aure ban son wani boye boye don lamarin aure ba wasa a cikin sa. Ina kallo sai da mamud ya goge zufa a goshin shi ya fara magana da fadin a gaskiya daddy ina son khadija tsakani da Allah. Sai dai matsalan da aka samu shine maganan yanzu yazo min a girshi banyi tsamani jin haka a yanzu don tun farko naso muyi aure a lokacin da nake bukatan karin aure sai ta nuna min sai ta gama karatun ta. Yanzun kuma nasan idan na kara tunkaran iyayyena da zancen karin aure a wanan lokacin abune mai wuya iyayyena su yarda a yanzun din. Zaici gaba da magana daddy yace dashi dakata haka mamud ya isa haka ma sai dai a gaskiya baka kyauta muna ba da kasan da hakan tun farko da ka bari son ka ya zurfafa a zuciyar diyar mu. Yace daddy ba haka bane wallahi na dauka sai ta kare karatun ta ne za a fara maganan auren ba yanzu ba zuwa lokacin na shawo kan iyayyena da maganan. Wallahi da gaskiya nazo ma khadija bada wasa ba don ina son khadija tsakani da Allah irin son da ban taba yiwa wata mace shi ba. Daddy ya amsa da fadin wanan magana ai ya wuce mamud don gaskiya ba zan dauki diyana in bayar inda iyayyen miji da yan uwa basu son ta ba. Don irin haka har jikokin da zata haifa masu sai kaga rashin kauna ya shigo tsakanin su da su don haka kayin hakkuri kabi umurnin iyayyen ka yadda suke so. Ita kuma Allah ua bata wani mai albarka ta aura daddy yana fadin haka na mike nayi waje da gudu zuwa dakin mu ina kuka. Ba wanda ya kara bi ta kaina har kwana biyu mama ta samay a dakina kwance ina faman tunane ta samu wuri ta zauna tana fuskanta na tace. Yanzu may ya rage kuma banda kiba kanki hakkuri agaban ki dai akai komai ba a bayan ki ba kinji da bakin shi ya fada matsalan daga iyayyen shi ne. Kina son ki fada gidan da ba a san muhinmancin ki bane da darajan ki abi yazo har ya shafi diyan da zaki haifa nan gaba kin fi kowa sanin halin nufawa ga abinda suke ki. Cikin kuka nace mama nidai naga kamar nice daddy baya so yanzu in bashi ba mai zai sa ya matsa sai nayi aure yanzu bayan yasan karatu nake yi. Daddy yasan ba wasu maza nake kulawa ba nafi ba karatuna muhinmanci a yanzu bisa ga komai da nakeyi amma zai bijiro da zancen wani aure yanzu a kaina da rana tsaka. Ke ki shiga hankalin ki ki natsu kisan abinda kikeyi aure ne kin san ba fashi kuma mahaifin ki ya baki daman ki kawo duk wanda kike so a yanzu ba sai wanan din daya fito ba. Nace cikin kuka mama daddy ya kara bani dama in fito da wani bayan wanan don ni gaskiya ba zan auri wanan AA din ba. Yanzu ai dabara ya saura gare ki tunda ke baki daukan shawara ki yarda da kaddara ta mike zata bar dakin nace mama don Allah kada ki fushi dani don ke kadai nake da ita wace ke tausayina a yanzu. Kamar zata wuce sai kuma taja ta tsaya tana cewa dole un fushi dake khadija idan kowa zai cuce ki banyi tsamanin ni da mahaifin ki zakiyi tsamanin zamu cuce ki ba. Sanan ki sani mahaifinki ya na nan ga bakan shi na aure zai maki bada dadewan nan ba sai dai ki karasa karatun ki a gidan mijin ki can . Mama duka duka nawa nake yanzu da daddy ya matsa da maganan aure a kaina kodon nayi saurin shiga makaranta kuma anyi fushing dina don kokarina kuke ganin na girma da yawa a waje. Tace sai ki tambayi mahaifin ku do shi keda amsan hakan bani ba daga haka ta fice dakin ta barni da tunane a raina. Kamar daga sama zuwa rana sai ga maryam gidan mu naji ana taron ta da sauri nafito waje don in gaskanta abinda nake ji ita dince tana tsugune gaban mama suna gaisawa. Da murna na isa wurin ta ina fadin ke kuma sai ki fadowa mutane haka ba sanarwa tace cikin jefo min harara ke tun yaushe ana neman ki a waya va a samu ki ba dole in biyo ki ba wana shiru haka. Bayan taci abinci muna zaune dakina muna hira nake koro mata abinda ke faruwa dani sai da ta gama saurare na tace min. Tace haba khadija kin so ki tayar da hankalin ki ne amma ni dama na sani duk cikin masu neman ki kun fi dacewa da AA don hadi ku daga Allah abin yake hankali na yafi kwantawa dashi gaskiya . Don shi yafi dacewa dake tsakani da Allah kece dai baki gane hakan saboda wani dalili naki can. To ai ke ma mace ce zaki iya auren shi tunda ya fi kwanta maki a rai don ba haram bane idan kin aure shi ai don naga halin ku kusan daya dashi don haka kunfi dacewa dashi. So don haka kada ki kara min maganan wani AA can don Allah don ni bashine a gaba na ba yanzu mafita nake nema na yadda zan shawo kan daddyn mu. Wani irin kallo take min can tace may yai zafi haka khadija daga fadan gaskiya sai ki fada min bakar magana kuma ke dai yagani yace yana so bani ba. To ba zan aure shi final sai yaje can ya samu daidai dashi bani khadija ba dariya take min bata kara bi ta kaina ba kuma ba mu fada yayi nisa don haka ba a dauki lokaci ba muka shirya da ita. Kwanan ta biyu da zuwa wanda naji dadin hakan don na manta da halin da muke ciki da iyayyena. Sai dai maryam takan zolaye da wasan ga amarya ba ango tsayayye nakan ce da ita ke ki ganta can. Zuwan Ya Amina yasa nasha jinin jikina don yanzu ina ganin zuwan ta ba alheri bane gare ni sai dai danaji tace tare da mijinta suke yazo wani aiki nan ne yasa hankalina ya kwanta. Sai dare ya shigo gidan suka gaisa da iyayyen mu sun dade suna magana da daddy a falon mu kafin ya fito ya bar gidan tare da matar shi nan tabar muna yara a wurina. Na dade ina barci da safe ban tashi ba ko da na tashi ina tambayan maryam mama tace min wai ta fita nayi mamaki wa ta sani a garin kuma ina taje wanka nayi don na samu mama ta gyara yaran ya Amina koda na tashi. An daura auren mu sha biyun rana a unguwar Daji unguwar da yan uwan daddy suke zaune wanda daurin auren ya samu halartan mutane da yawa daga yan uwa da abokan arziki. Tun da na tashi nake jin jikina ba dadi ga tunanen ina maryam ta shiga da nakeyi a raina sai sha daya dawani abu suka shigo gidan dasu ya Amina da wasu mata da yawan su. Bayan mun gaisa ne na koma dakin mu na samu maryam tana sauya kayan jikin ta nake tambayanta inda ta fito haka. Bata kai ga bani amsa ba naji wata daga cikin matan waje tana rangada guda cikin nufanci Allah yayi auren khadija yau. Zubur na tsaya ina sauraren abinda matar ke fadi ta juya da hausa tana kara maimaita abinda ta fadi da yaren nufancin again. Maryam na kalla naga tana dariya tare da fadin matar nan ta iya guda wallahi bata ankara ba sai gani tayi na fadi kasa . ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Kwance take tana barci har zuwa wanan lokacin bata tashi ba ga kira nata shigowa a wayan ta can cikin barci take jin kiran yayi yawa. Tsuki tayi tare da dago kiran tana zagin mai kiran nata ta dauka a hasale muryan madam taji a wayan tana fadin wai ina kika shiga ne ake ta kiran ki baki daga waya ba haka. Barci nake walkahi may kina da hankali Nafisa da har kika samu idon barci a cikin wanan fitinar da ya kunnu muna kai ? Da sauri tace may ke faruwa waya mutu kuma madam tace ai da mutuwane zai fi sauki don mun san may shi ya tafi ke nan . Muna kukan targade sai kuma ga kariya ya samu yanzun haka mijin ki yai muna wanan yankan kaunar a idon jamma,a ? Nafisa dake mamaki a ranta na abinda mijin ta yayi haka ya bata wa madam rai tace ai kin san samad miskiline bai da sabo sai ni nasan kan abina. Madam tace ke dan Allah abin kin may can ki gyara kalamin ki yanzu kice abin ku don aure zai kara yau din nan nasan baki sani ba da naji don jiya muna tare dake har dare banji kin min zancen ba. Nafisa da tai mutuwar tsohowa a zaune bataji sauran abinda madam din ke fadi ba a lokacin sai da madam ta kirata da karfi ta dawo a hankalin ta. Madam tace kina jina tace madam ko dai baki gane wanda ake fadi bane kika dauka mijina ne ? Kamar ya ban gane ba ni da akaturowa har kayin daurin aure ko bashi ma fam sec din FLAS ba na nan Abuja wani irin zufa ne ya keto ma nafisa duk da sanyin da dakin ya dauka na AC alokacin. Madam ko dai baki karanta da kyau ba madam tace ki bincika da kyau ki gani idan kin bincika kikirani anjima tana fadin haka ta kashe wayan ta. Madam na kashe waya nafisa ta rasa wani irin tunane zatayi yanzu ta dai san suna tare da Samad suna raya dare dashi sai sha biyu suka kwanta bata ga wani alama da ya nuna mata wani abu na faruwa dashi ba. Ta rasa wani irin tunane zata ba a lokacin cikin karfin hali ta mike zaune daga inda take kafarta taji baya daukan ta a lokacin ta nufi dakin maigidan wanda ta bar dakin tun asuba daya ta da ita tayi sallah asuba ta gudo ta dawo dakin ta ta kwanta. Ta tura dakin yana tsaye a bakin wardrove din shi yana ciro kayan da zai saka tun daga kofa take mashi kallon tuhuma. Kallon ta yayi ya kawar da kai yana fadin yaya nagan ki haka kamar mara lafiya ? Tace shine dalilin zuwa na yanzu don in tabbatar da lafiya na don amsan na wurin ka yace kamar ya tace yanzu madam ta kirani take fada min wani magana dan gane ba ? Yace may ta fada maki yana kokarin zura wando a jikin shi takai ma kayan kallo taga sabbine full din su shi kuma ba gwanin saka kayan hausawa bane. Ta karaso inda yake tana fadin cikin kura mashi ido wai aure za daura maka yau samad ? Cikin cijewa ya amsa mata ashe kin samu labari ke nan yanzu nake son fada maki dama sai gaki kin shigo dakin. Yanzu zamu tafi daurin auren minna ai bata bari yakai karshen maganan shi ba ta sake wani irin uban ihu tayo kan shi da duka duk abin da ta samu buga mai shi takeyi akai. Tun yana kaucewa har ya tsaya wuri daya yana mamakin ta daya ga abin ba mai karewa bane sai ya hade hannun ta wuri daya ya hankadata zuwa waje. Yana shiri yana tunanen wanan wani irin fitina ne haka gana Nafissa ga kuma na khadija da zai tara bai san yadda zasu kwashe da ita ba don ita ma bata sani akace. Don shi rabon shi da ita tun a kaduna da suka rabu bai karaji ko ganin ta ba yanzun dai yaga haukan nafisa saura na yar matsalan kuma ya fadi yana murmushi tare da fadi a fili kai mata dai kayyah wallahi. Yaci gaba da shirin da yake ranshi idan yayi dubu ya baci a lokacin dama yasan da wanan abin na zuwa gare su shi da ita idan taji da haka yagama shirin shi. Ihun Nafisa ne ya tayar da sauran mutanen gidan dake barcin safe suka firfito a razane daga na dukan nasu dake kasa. Suka fito a sukwane suna tambayan may ya faru sai dai ba amsa daga bakin ta a lokacin don ta haukace masu gaba daya. Yana gama shirin shi ya nufi kofa ya bude ya ji kofan a rufe haka yasa ya gane ta rufe shi daga bayane da wani makulli waya ya dauka ya kira Yusuf akan yazo ya bude shi. Yusuf yace taji ne yace kaima ka sani ai ajiyan zuciya Yusuf ya sake yana fadin haka yayi daidai yanzu ka daina jin shakkan fada mata. Don Allah malam kazo ka bude ni kaji ka tsaya min surutu haka dariya Yusuf yayi yace kai angon khadija mijin buzuwa uban gidan Fati. Tsuki ya kara ja Yusuf yace ganinan zuwa sai dai kasan nima ba barina zatayi ba yau nasan akwai tsiya tsakanin mu yace kadai zo din. Yusuf yazo gidan tun daga kofa a yadda ya samu mutanen gidan cirko cirko yasan akwai matsala a gidan haka yai kundunbalan fadawa gidan kai tsaye yana rike da master key ya shigo. A falo ya samay su zaune da yan uwan ta zuwan shi yayi daidai da shigowan madam gidan da yan uwan nafisa suka kirata hankali tashe. Tana ganin Yusuf tayo kanshi a sukwane da niyar bugamai flawer base din da ta raruma a hannun ta ta nufo shi gadan gadan dashi. Su madam suka rike ta suka kwace abin flawer da kyat a hannun ta ta kwace tayo kanshi da duka da cizo tana zagi. Mari ya kwashe ta dashi cak ta tsaya tana mamakin shi idon ta na tsiyar da hawaye take kallon shi wuce ta yayi ya nufi sama ta sake kukan kura ta bishi zuwa saman kafin ta iso yasa key ya bude kofan dashi. AA ya fito rai bace tayo kan su gaba daya tana fadin yau sai ta kashe su sai ta halakasu sai ta illanta su a duniyan nan. Madam na gefe sai faman buga ma abokan su na kut da kut waya take su zo gidan nafisa din ba lafiya. Bayan sun fito ne Yusuf yace ke wata irin mace ce ba ki da hankali ne idan kin mashi rauni fa kan ki aka kishiya kema ba wata kika shigo kika sama a gidan ba. Ganin zasu fita subar gidan ta sake yowa kansu ta fisge hannun su madam din suka sake riko ta suna bata hakkuri ta shiga surfa masu zagi har su madam din Yusuf ya kallota yace mahaukaciya. Nan suka fice suka barta da mutanen ta a gidan da suka fara taruwa ranan kawayen ta sun nuna mata bakin cikin su kwarai da gaske kowa da abinda yake fadi a bakin shi a ranan. Suna fita ya sauke ajiyan zuciya Yusuf ya kalleshi yayi yayi dariya yace somi ke nan amma komai zaizo karshe insha Allah sai ka zama namijin duniya sosai kafin ka samu mafita ga haukan matar ka. Sun samu har wasu sun kama hanya a bisa jagorancin kawu da mahaifinshi da yazo daga kaduna tare da wasu yan uwa nasu don daurin auren da daddy yasa cikin kwana uku daga zuwa magana daddy ya tsayar masu da ranan daura aure. KHADIJA Na falka naganin saman gadon dakin daddy kwance maryam da Ya Amina akaina suna min fitara. Nakai kallona garesu su ukune tsaye akaina Ya Amina maryam da wata kanwar maman mu kanwar maman mu na kalla don su a matsayin makiyana nake kallon su yanzu. Nace mama Tani da gaskiya aure aka daura min da mutumin da ban sani ba tace tana dafani yanzu ba lokacin magana bane khadija. Barin maki allura ki samu natsuwa tukun ta dauko allura tana aunawa zata dirka min kaina na girgiza mata nace mama ba sai ki min allura ba don Allah . Ido na rufe a hankali ina ji aka dirka min alluran dole sannu a hankali barci ya fara dauka na ban san inda nake ba kuma. Sun rufe dakin da nake ciki kwance bamai shiga sai su ukun ke zaraya a kaina hankalin su duk a tashe sai yanzu suke dana sanin goyan bayan da sukayi aka hada kai dasu aka daura min aure da ban so. Don sun dauka wasa ne ina son A A din barazane kawai nake masu na mata amma yanzu sin gane gaskiya nake har cikin raina. Hankalin yan uwana duk ya tashi amma banda daddyn mu don cewa yayi a ranan za a tafi dani sabanin yadda akace dafarko aure kawai za a daura daga baya sai in tare. Ina kwance ban san wainar da ake toyawa ba a gidan barci nake mai kamar wahala don ban iya cewa ga inda nake ba. Maryam tayi kokarin neman Yusuf a waya tana fada mai halin da ake ciki don haka yaja AA gefe yana sheda mai abinda daddyn mu yace. Kiran maryam sukayi su fito ita da anty Amina su damay su a waje sun iso inda suke Yusuf ke tambayan su halin da ake ciki. Taso ta boye mashi amma sai ya Amina tafada masu halin da ake ciki bata boye masu komai ba abindake faruwa harda maganan daddyn mu. Daga inda yake tsaye yake sauraren maganan su yaji idon shi ya rufe yana jin wani zafi a ranshi shine mace zata nuna ma wanan kiyayyan haka ? May ta taka may khadija ke ji dashi a cikin ranta may take takama dashi muryan yusuf yaji yana cewa anty zasu ga daddy su bashi hakkuri abar tarewan har wani sati lokacin sun shirya inda zasu aje ni. Sun sami ganin daddy inda daddy ya nuna masu bai yarda ba saida a tafi dani ranan idan mutuwa zanyi saidai in mutu akan aure bazan kwana mashi gida da igiyan aure a kaina ba . Suka bashi hakkuri akan basu gyara inda zan zauna bane tukun abasu sati daya yace sati yayi yawa ai mutane sai su zage shi a hakan. Sai da kyat ya yarda da kwana uku suka amince da haka sun bar wurin shi suka nemi maryam tai masu iso inda nake su ganni kafin su wuce. KHADIJA Koda na farka mama nagani zaune a kusa dani ta kuramin ido cikin tagumi tace dani khadija kin falka nace eh mama. Tace tashi ki ci wani abu ko tea mai zafi ki korama cikin ki tun safe baki kai komai a cikin ki nace banjin yunwa mama tace dani a,a khadija ban son gardama fa. Daure ko kadan ne kisha sai musan abinyi daga baya jin haka ban son gardama da mama kodon in kwantar mata da hankalin ta yasa na mike zaune ina kokarin tashi sai dai ban iyawa na koma na zauna a bakin gado. Kofan dakin akaturo gaba dayan mu muka dago muna kallon mai shigowa dakin maryam ne a gaba sai yusuf ke bin ta daga bayan su AA ne ya shigo a gadarance. Yusuf ne ya fara gaida mama sai shi ya juya wurina yace khadija yaya jikin naki ni bisu da ido tare da kawar da kaina gefe ina son kwantawa. Mama tace barin hada mata tea maryam biyo ni ki kawo mata tea din ta dan sha maryam ma tabi bayan ta. Kara tambayana jikin sukayi daga inda suke tsaye akaina ban basu amsa ba sai kukan dana sake a lokaci daya shiru sukayi dukan su suna kallo na. Ya Amina ne tare da maryam suka shigo dakin kukan nan bazai kare maki bane har yanzu kina son ki jawa kanki wani matsalane kuma ? Ya Amina ta juya wurin su tana fadin ashe kun samu ganin daddy din yanzu yake fadin sai nan da kwana uku za, a kaita suka ce Allah ya kai mu sautin kuka na kara sakewa a lokacin. Shi ya fara barin dakin don bai iya jimirin sauraren kukan da nakeyi wanda yake jinshi kamar ana diga mai garwashin wutane a zuciyar shi. Wai shine mace kewa kuka haka hartana neman halaka kanta saboda rashin kauna yanzu ya tabbatar da khadija ta wuce sanin shi. Sallama yusuf yayi mata akan zasu wuce yajuyo gurin da nake ta gurzan kuka yace khadija kiyi hakkuri ba munyi haka bane don mu saba maki hannu na dago mai daga inda nake yasa yayi shiru da bakin shi ya fita. AA Tunda suka kama hanya baiyi magana ba yana dafe da goshin shi da hannu daya Yusuf ne ya kalle shi yace dashi wai ya nagan ka haka ne kayi weak dakai. Ba a mijin mata biyu ko uku ko hudu haka fa wan halin mijin mai mata daya ne kakeyi ya kamata ka jajirce ma duk wani kalubalin da zaka gani daga matan ka yanzu don kasan mata da kishi suke. Zaka samu kalubali masu yawa har ta inda baka zata ba amma idan ka zama masu namijin duniya sai kaga komai ya lafa an zauna lafiya. Ajiyan zuciya ya sauke tare da lumshe idon shi yace ban jin komai a yanzu duk wani haukan da Nafisa ko Fati zasuyi ban dauke shi a komai ba illa mamakin da nake wai ni Abdulsamad yau mace ke nuna ma kiyayya haka ? Why khadija why ashe har abinya kai haka a zuciyar ta ban sani ba ina dauka halin su na mata ne take nuna min kai ina bazan zauna da macen da bata sona haka ba a gidana. Yusuf dake kallon shi yana murmushi yana gurgiza kanshi yace duk laifin na waye AA kai ka jawo abin nan yakai haka nina sani nafi kowa sani halin ka do haka nasan kana son khadija har cikin ranka. Sai dai girman kai da izza ya hana ka nuna mata son da kake mata din wanda ita kuma tai amfani da haka wurin daukan kaima ba son ta kake ba illa tilasta kan da iyayye sukayi ne a kanka ka yarda ka aure ta. For god sake ya kuke son in nuna mata so ne bayan wanda na nuna mata din for how long take son in nuna mata ina son ta ne kuma ta yaya. Yace just say to her a words of love shi irin wanan matan ke so ba tarin dukiya ko wani kyau da nasaban ka ba duk basu a gaban irin khadija akwai mata da yawa haka Allah ke yi su . Kamar yadda ko cikin mazan ma akwaisu zan iya cewa kana daya daga cikin su yanzu haka don baka san may ye so ba sai an nuna maka don haka dakai da ita jirgi daya ya dauko ke nan. Ya Sallam ya furta yana kara dafe goshin shi da hannun shi daya so so so may zance mata tasan ina son ta yace kalman nan da kuka kasa furta ma junan ku da dadewa shi zaka furta mata yanzu dubara ya rage naka. Bazan so khadija ta shiga gidan ka a haka ba har matan ka su gane abinda ke tsakanin kai da ita gara ka gyara maysalan tun wuri nima zan tayaka gyara in Allah ya yarda. Tunda ya dafe kai baiyi magana ba sai da suka tsaya a kofan gidan shi ya bude idanuwan shi da suka kada sukai mai jawur dasu ya dago kai yana kallon Yusuf din. Yace bissimillah kadai shiga da addu,a a bakin ka don nasan rikici na ciki yana jiran ka yau yace tare zamu shiga ma Yusuf yace tsoro kake kenan ? Tsoron may haukan nan nata ne ban iya dauka sai in mata illan daban tashi yi mata ba don fitinar Nafisa yayi yawa. Bude motar Yusuf yayi yana fadin bissimillah mu shiga kadai tina da addua na fada maka ba abinda zata iya insha Allahu. Suna shiga falon gidan sai da sukai mamakin iri hamshakan matan da suka samu a falon ko wace ka kalla tayi murtuk da fuska kamar suna zaman makoki a gidan. Suna gani shigowan su ko wace ta sako masu na mujiya don dama ba sani AA din sukayi ba sai faman jijiga kai sukeyi kowa da abinda take rayawa a zuciyar ta. Cikin karfin halin ya fara masu magana tare da fuskan ta su yana fadin lafiya nagan ku haka a wanan lokacin. Nafisa da tai wani wujiga wujiga da ita a tsakiyan su ce ta fara magana cikin bacin rai sai madam ta tare da da fadin haba Alhaji kai muna laifi mun taru kuma har kana tambayan mu ko lafiya ka gan mu a nan ? Wani kallo yayi mata da ga haka bai kara furta komai ba sai kokari ciro wayan shi da yake yi daga aljihun shi yana duba lamba. Hello IG Fam sec ne na FLAS ke magana ina son yanzu a turo min yan sanda gida nane zubar suka fara mikewa tsaye suna fadin ai abin bai kai can ba daga zuwa abin arziki abu zai zamo tsiya kuma. Kafin haka sun watse sai madam ta rage nafisa ko tana kan bakin ta tazage shi ta zagi Yusuf da iyayyen su zagi na fitan arziki take aika masu. Madam ne tai magana tana fadin suyi hakkuri ran Nafisa ne ya baci da ya fada mata tun farko ta san da maganan ta shirya da haka bai faru ba tunda tana da masaniya. Yusuf ya watsa mata kallo daga inda yake a ranshi yace kaga shegiyar kilaki maikai mata ga halaka watau a fada muku ku shiga ku fita ko kafin a farga zancen ya rushe . Sai dai a fili cewa yayi banda abin Nafisa may ye na tayar da hankali haka kan kishiya tunda ba a kanki zata zauna ba. Gidan ta daba naki daban maye na damuwar kan ki haka da fitina a hasale tai saurin fadin wallahi babu inda zaku kaita nan dai zamu zauna tare da ita. Ko wace shegiyace zata shigo ta samay ni anan in ga damay zata zo wani kallo ya watsa mata lokacin da take fadin haka na. Maganan da madam ke masu a cikin lalama yasa suka zauna don a sulhunta magana a tsakanin su ta nuna an mata laifi don ba,a fada mata ba don haka an munafuce ta. Yusuf ne yabata hakkuri yace nan kan anyi kuskure gaskiya kuma ko su daurin auren yazo masu a bazata ne ta sake cewa don may bai fada mata tun farko yana neman aure ba. Yusuf yace wanan kuma ba dole bane saboda kwanciyar hankalin ku yasa ya boye maki ne man tace dashi munafuki ai duk shirin shi don ai mata haka yace ya dauka shine ya hada auren. Zata fara hauka AA yai magana yace ke dakata idan abin da kuka zaunar damu ke nan kuyi muna bazan lamunci haka ke uwata ce ko ubana da dole sai na fada maki komai nawa aure na nakara idan zaki zauna ki zauna in baki zama kofa a bude yake maki ban tsare ki ba. Ke ba wata kika shigo kika sama a gidan ba ko nayi maki alkawari cewa bazan kara aure bane nan gaba tace eh lallai samad na yarda sun gama dakai. Tunda ka dubi idona yau kana fada min magana haka so ranka madam ne ta katse ta gada ta sake layi a gaban su yadda taga ta burkice komai tana iya fadi. Tace ya isa haka Nafisa ki kwantar da hankalin ki ai magana na fahinta a tsakanin ku in ba haka ba zan tafi in barki bazan iya ba gaskiya. Sai lokacin ta natsu don tasan da gaske madam keyi zata iya wucewa ta barta dasu kamar yadda tace din. Yisuf ne yace yanzu may kuke so ayi Nafisa tayi caraf ta sake fadin ban yarda a kaita wani gida ba can a nan zamu zauna da ko wacece a gidan nan . AA din yace haka yayi maki tace eh sai kuma motar da zaka can zamin ka kuma sake mi sarkoki na da sauran abubuwan bukata na. Dama yasani maganan ta da haukan ta ba zai wuce kudi ba yace bayan wanan fa tace idan kai haka sauran zai biyo baya. Haka dai sukai ta bugawa har ta yarda ta dan lafa haukan ta barsu a zauna lafiya yace madam itace sheda don idan sun tayar da wani fitina daga baya zai dauki mumunan mataki akan su. Bayan ya raka Yusuf ya tafi ya dawo dakin shi ya na rage kayan jikin shi tare da neman abinda zai kora ma bakin shi. A dakin Nafisa kuma madam ne tare sa ita dasu Yanyala madam ke fadin ke kina da hankali da zaki ce a kawo ta gidan nan tace madam nasan halin samad sarai don haka bazan yarda yakai ta wani gida ba tace da ita tunda ke kika zabi hakan shike nan ai. Amma ina ji maki tsoron abinda kaje ya dawo tace madam nine fa ban tsanmani akwai wata mace a kasan nan da yanzu zata girgizani ba kai ko a cikin jinsin mu na buzaye ta fito banji zata iya kai ni a gurin samad. Barni dasu daga shi har ita har wa yanda suka bada goyan bayan yin haka gare ni sai nayi maganin su daya bayan daya wallahi. Haka dai suka rabu da madam din tana kara karfafa mata abinda zata sun aje kan washegari zasu maiduguri suga malamin su idan sun dawo sai su shirya su ketara camaron inda sukaji labarin sabon malami mai tashe. Allah ka shirya shirya muna zukatan mu kasa mufi karfin zuciyar mu musan Allah keyi ba mutum ba ya bamu ikon dogara da shi. Nafisa ta raja,a da boka da malam suke yi suke iya sa aso ka ta ko wani hanya ansan asiri gaskiya ne amma kuskuren ne mace ta kauce da yawa irin haka ba abinda zata kai kukan ta ga Allah sai dai gurin wanin Allah din. Shima kuma wanin ga Allah subbahanahu wata,ala ya dogara don ko sihirin da sa,an ubangiji bokayen ke yin shi don may ke ba zaki zauna kiyi a cikin dakin ki ba sai kinje gurin wani . Yanzu wasan ya fara yan uwa ku biyo ni kuji zaman kishin da buzuwa da mijin buzuwa. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU. 1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Mun dauki lokaci da maryam a dakin muna magana guda kan zaman gidan AA din ida maryam ke fadin ni ke nike jiyarwa a gidan nan. Nace nima tunanen da nake kenan wallahi don abinda nagani jiya ya matukar ban tsoro wallahi. Shiyasa nake son mashi magana ko in koma hostel in zauna ko kuma ya sama min wani guri na daban da zan zauna kada yazo bai nan su sameni su illanta ni a banza. Dariya tayi tace kina haukane da zakice zaki koma hostel da zama da auren ki ko an gaya maki shi mahaukacine irin ki kidai zuba ido muga matakin da zai dauka akan su. Ai shi ba jahili bane sun mashi haka ina gake dole yai wanan tunanen nasani cikin ranshi nace wallahi maryam bari kiji indai ba zai dauki wani mataki ba akan haka da sukai mai ni zan daukarwa kaina don zaku neme ni ku rasa a gidan nan. Tace ina zaki nace nina sani ai don ba zan zauna wasu banzayen fulanin su illantani ba ga banza dariya ta kwashe dashi tana fadin. Wallahi sai kin zama jaruma a gidan nan tunda kinga sun fara haka don dai ba wai ba wata rana zai zo akanki ranan ko da mun sha dariya . Hararan ta nayi ina fadin Allah ba zai kawo ranan ba balle ku sha dariyan muguwa kawai kofan falon aka turo nasan shine don babu mai shigowa inda nake in ba shi ba. Maryam ta dan shiga kamay kamay tana gaida shi yace maryam yau kin leko mu ne gidan tace na yi kewar mutumiyar tawa ne nazo ganin ta. Dan murmushi yayi ya kalleni fuskana a daure yake tamau don haushin abinda ya faru jiya nake ji a rana har wanan lokacin . Kimun list din abinda kike buka za,a shiga kasuwa sayayya yau ya fada yana kallon cikin fuskana ban bukatan komai idan ma ina bukata ga maryam nan sai ta sayo min. Maryam kina kallon yadda nake fama dai da mutumiyar taki ko har yanzu ita bata dauke ni da wani matsayi ba. Dan dariya tayi tana cewa haba tama isa haka dai halin mutumiyar taka yake ai dama da sannu zata bar wanan halin ta juya wurina tana fadin ki fadawa mutane abinda kike bukata kin tsaya jawa mutane aji. Maryam idan ina bukatan wani abin sirina dole sai wani yaji abinda nake so saboda ban san ciwon kaina ba komay wani zai tafi sawo min abu. Au kin fi bukatan abaki kudin komai da zaki saya a hannun ki ke nan ya tambaya yana tsaye nace idan dai bakai zaka da kan kaba hakan yafi mun sauki. Murmushi kawai yayi ya sake gaida maryam din ya fita daga part din maryam ne ta kalle ni tana fadin wallahi ban taba zaton haka yake da saukin kai a gidan shi diba yanzu lokaci daya ya gano nufin ki. Kuma har ya yarda shi isa buzuwan nan take yadda take so a gidan nan kema gashi yanzu kin fara shimfida naki mulkin na gani. Don Allah khadija ki bi mijin ki asannu ki gama fahintar halin shi amma hankan da kike cikin garaje ba daidai ne ba. Nace maryam could you believe cewa itace yanzun haka mai bada sakon zan zaune kishiya irin wanan yar renin wayon ta sanan sirina watarana mafa ai sai tai min gori akan hakan. Gara tun wuri in kwatar wa kaina yancin haka yafi min alheri tace badai kina nufin har sun shirya ba ne ? Nace gashi kin gani a zahiri zai masu sayyan suci suji karfin kara dukan shi gobe idan yai masu ba daidai ba. Kai wanan abin akwai daure kai a cikin sa wallahi yana da saukin kai sosai wallahi nace na dole ba ba dolen shi yayi saukin kai ba tunda ya zama mijin tace. Inba shi ba zaizo ya tambaye ni wai may za a sayo mi nace dashi ina bukatan wani abin shine. Nauyin dake kan shi ne na hakan yake son saukewa khadija banda wani nauyi a kasa da zai sauke min tace tunda baki dandani zumar shi bako, kin san kuma abinda buzuwa kewa kishi ke nan. Nace kuma ba zan taba dandanawa ba in dai haka zamu zauna wai Khadija may ke damun ki ne ana gabas kina yamma. Wallahi ya kamata ki shiga karatun na natsu tun dare bai maki ba ki rungumi mijin ki ki jashi a jikin kin ki kinunawa diniya ke din diyace ta halas. Ta ko wani fanni ido aka saka maki aga takon rawan ki ko so kike ku koma daya ke da buzuwan da Fati ya rasa tundun dafawa a gidan shi duk ku ukun ku zama iri daya. Maganar ta ya fara shigana ta sake cewa so kike ki watsa ma iyayyen ki kasa a ido su da akai sha,awan hada iri dasu don ganin ya Aminan ki da sukayi. Ko so kike su da sukaji suka gani suji kunya dayin wanan hadin khadija kina da wayon ki kin san abinda ya kamata ba sai na tsaya fada maki komai ba. Daga irin nau,in magana da miji, kwalliya, iya girki taron bakin sa ki tararaye su yan uwan shi da iyayyen shi su zama tankar naki, ladabi da biyayya shine kawai banbancin ki da wanan buzuwan. Ta dago kai ta kalleni taga ina sauraren ta cikin sanyin jiki tace koke fa khadija wallahi dana shigo irin yadda muka fara dake yasani jin tsoro da farko. Yanzu maryam yaya kike son inyi don Allah wallahi ni har yanzu bai kwanta min a rai bane ban san may yasa ba na kasa yi mashi biyayya. Tace ki sa a ranki daga yau zai ga canji a gurin ki ki koma khadijan ki ta ainihi da kowa ya sani kiga yadda zaku kwashe dashi da buzuwa a gidan nan. Na sauke ajiyan zuciya tare da fadin ban san ta inda zan fara bane nima abin yana damuna don nasan hakan ba halina bane. Nan dai ta dinga bani shawaran da ya dace har bayan uku na rana mukai sallama akan zan roke shi idan ya yarda zata zo muje wurin gyaran kai da ita don kaina ya tsufa yana damuna yanzu. Bayan tafiyan maryam ban zauna ba don nasan nice da girki da yamma don haka na shiga kitchen na dora muna girkin abinda zamuci da dare semo na tuka sai miyar agushi da nayi wanda yayi kauri sosai banda fresh vegetables don haka nayi amfani da bussashen shuwakan da nazo dashi don akwai ni da son miyan shi. Daga nan na wuce part din shi na gyara mai ko ina na wanko bathroom tare da saka kamshi na sake mai zanin gadon dake saman gadon nashi dakin ya dauki kamshi da kyali. Nagama nazo na gyara part dina na saka mai kayan kamshi tare da kuna AC din falon wanka na shiga na gyara jikina na fito na shirya a cikin wani dogon riga na Afri Abaya dinkin rigar yai mutukar karban jikina sosai. Don fashin sallah da nakeyi yasa ina ganin magariba tayi na dauko tasbaha na ina ja daga inda nake zaune a falon. Tun fitan da yayi muna tare da maryam bai sake shigowa part din ba, don haka abin ya damay ni sosai a raina don ban san halin da yake ciki ba. Har wurin nine bai shigo ba don haka na yanke shawaran bin shi da abincin a part din shi sai dana gama jera abincin na nufi dakin in gani ko yana ciki. Turan kofan nayi a hankali bakina dauke da sallama kwance yake rairai saman gadon shi ya dora hannu daya saman fuskan shi. Ciki ciki ya amsa min sallaman na karaso inda yake kwance na karaso gaban shi tare da fadin mun wuni lafiya. Ya dan sauke hannun shi tare da fadin lafiya kalau ya kika wuni na amsa da lafiya sai na dan tsaya ina kallon yadda ya kara maida hannun shi saman fuskan shi. Zanyi maganan da ya kawoni naji ya rigani fadin yau ban jin dasin jikina tun dazun nake kwance fitana ke nan zuwa asibiti kika shigo kika gyara min dakina. Sannu nayi mashi sai naji ba zan iya fadin abinda ya kawo ni wurin shi ba a lokacin don ciwo ya kawar da komai. Allah ya sauwaka nayi mashi tare da fadin abinci yana falo na ajema yace ya gode na juya zan fita daga dakin mukaji karan fashewan abu da sauri ya daga yana kallon kofan nima wurin nake kallo. Karan muka kara ji kamar ana wurgi da kaya aka bankado kofan da karfi duk muka sake kallon kofan a razane nafisa ne ta shigo tana huci tare da fadin. Ke karamar yar iska may kike nufi da mijina ne wai kina nufin in saka maki ido da mijina kina yadda kike so to ki sani duk kwanakin da kuka je kukayi dashi a kaduna sai ya rama min shi a gidan nan. Watau ke mai wayo ko kin dauke shi kun tafi kaduna kun gama iskancin ku dashi yanzun kin dawo kin wani kwaso dan iskan abincin ki kin kawo mashi. To sai dai uwarki ta nemi wani kulan ta kawo maki ba dai wanan ba kuma bari kiji sai na rama kwanan ki da kuka yi a can tunda nasan ba zai kwana da fati yana kallon ki ba. Wai ku masu wayo kun gudu kunje can ku huta to in kun gudu nan ai baku guje ma sheri na ba abinda zai taba wakana a tsakanin ku har abada sai dai ku tabbata a hakan. Zata ci gaba yace ke Nafisa wai kina haukane komay kike haka ne yarinyar nan bata kula alamarin ki amma duk da hakan ke sai kin san yadda kika shiga alamarin ta. Ya ishe ki haka na tun baki kaini bango na maki abinda ban tashi yi ba a gidan nan kin isheni nafisa kin fara kaini bango ya fada da karfi . Daidai lokacin na bude dakin na fita tare da kallon kayan abincin nawa da ta watsar a karamin falon nashi inda yake cin abinci da hutawa. Wuce kayan nayi zuwa dakina zuciya na yana tafarfasa badon huduban maryam da nake son amfani dashi da ranan taga kalar nawa fitinan . Don sai nayi mata hasaran da yafi na kulan data nana min a kasa suka watse ina shiga dakina nayi mashi key ban kara bi ta kan su ba nagama abinda zanyi na kwanta. Sai da safe bayan na tashine nayi wankan tsarki na fito na fara tsefe kaina da nake son zuwa gyaran kai kofa naji ana murda min don haka na tashi na bude kofan. Yana tsaye saye da farar jallabiya kamar yadda yake fitowa da safe guri na bashi ya shigo daga ciki. Kallom fuskana yakeyi nace dashi ina kwana kafin ya amsa na sake cewa ya jikin yace da sauki tare da samun wuri ya zauna a falon. Bayan kujera naje na tsaye tare da rankeafowa ina wasa da yatsun hannu na dan shiru ne ya biyo bayan sai can yace. Deedar na fa gode abinda kikai min a daren jiya nace namay fa yace da baki biyewa wanan mahaukaciyar ba kukai min tashin hankali a gida. Yaci gaba da fadin sai dai baki kyauta min ba da kika rufe min kofan dakin ki kika hanani shigowa inda kike. Yau ina son fita gurin gyaran kai don kaina ya damay ni na sance ina son in je ai mun wani yace baki son zancen ke nan yasa kika kawar da maganan da zancen zuwa wurin gyaran kai. May zan ce tunda kaji abinda tace kaga a barta ta maida kwana kin da take so tunda ba wani abin zama dama don haka afaki gaba. Dago kai yayi ya kalle ni tare da idan naki ra,ayin ke nan haka a biye mata ni ba haka abin yake a wurina ba. Bazan dauki wanan dokar ba don nike auren ku ba ita ba da zata kawo min wanan jahilin a gida wanda ra,ayin ta ne kawai yin hakan. Wanan ni ba matsalana bane ku hakan ya shafa dakai da ita, don kun fi kusa kallona yayi ya dan harara ni tare da mikewa yana fadin idan kin shirya sai ki fada min in sa a kaiki. Ya mike ya fita nabi bayan shi da kallo har ya bace min da ganina na sauke ajiyan zuciya tare da fadin Allah ya sauwa ka. Maryam tazo bamu fita ba sai da ta karya a wurina muka shirya na kira shi ina sheda mai mun shirya yace drive na waje yana jirana. An wanke mun kai da kitso tare da gyara min kafa sukai min zanen da maryam ta matsa sai aimin . Ni kaina sai da gabana ya fadi yadda nagani na sauya a dan kankanin lokaci kamar bani bace bamu dawo gida ba direct sai da muka shiga wani plaza muka danyi sayayya wanda ni duk kayan kamshi ne na kwaso. Mun shigo gidan Nafisa da yan uwanta ne zaune a falon sai shewa suke ban san abinda yayi masu dadi ba suke wanan jin dadin haka. Mun yi sallama amma ban tsamanin wani daga cikin su ya karba muna muka shige su muka nufi part dina shirun da naji sunyi ne yasani gane mu suka bi da kallo. Muna shiga daki maryam tace dani kai khadija wai kina nufin wa yan nan garadan maza da matan duk gidan nan suke gaba dayan su. Murmushi nayi nace kema dai ke fada ni ma ban san iya adadin su ba don ban gama tantance su ba. Shawarman da muka sawo muka baje a falo muna ci bayan munyi sallah la,asar wata ce daga cikin su ta fado mun dakin babu ko sallama sai da na kalle ta da kyau na gane bata ranan bace ma yau. Kallon ta nayi cikin daka mata tsawa kafin ta fadi abinda ta shigo yi gurina din nace wai ku wasu irin mutane da baku iya sallama ku fado ma mutum daki kai tsaye babu sallah kamar kafirai. Zatai magana na sake fadin idan ba zaki mun sallaman musulunci ba ki fice ki bar min shiya na fadi cikin fusata sai da ta juya ta fara tafiya ta juyo tana fadin dama maigidan ne tace in fada maki kije ki kwashe kayan da kika bari a shiyan maigidan. Nace jeki ce ta barsu nan sai idan ta kara tsowo zan zo in kwashe amma yanzu tayi kadan. Maryam ta kallo tana fadin wasu kaya sai lokacin nake ba maryam labarin abinda ya faru a daren jiyan kallon mamaki take min tace khadija anya matar nan tana da hankali kuwa ? Nace in bata dashi ai zatayi bari muji may zatayi maryam tace khadija wallahi ban son tashin hankali a rayuwana. Banko muna kofa mukaji anyi nace wani dan iskan ne haka ba sallama ya turo min kofa ido waje take kallo na mikewa nayi tsaye don jin damay tazo min. Ke wa kike da suna don ni ban ko sa sunan ki a raina ba nace amma kin sani a ranki dai zaki iya kirana da kishiyar ki ko sunan bai maki ba na tambaya cikin kureta da ido. Nafiki iskan ci don ni banda wata kishiya a gidan nan nace gani ko kina gani inba kishiyar ki nake ba yaushe zaki barni na zauna a gidan. Banga kishiya ba don banga mutum a gidan ba nace nine nan mai shirin zama maki ciwon ido ki fadi abinda ya kawo ki, ki barmin shiya na don ba hurumin ki ba ne nan kuma saurara kiji iskancin ki ya tsaya iya mijin ki kada ya kawo kaina. Zagi da ashar babu wanda bata aika min ba ga maryam ta hanani magana Allah da ikonshi AA ya shigo gidan tun da ya doso falon yake jin hayaniyar nafisa da mamaki ya karaso part. Abinda ya fara zuwa mai a baki shine Nafisa may ya kawo kinan haukan naki har yakai ki shigo part din ta da fitinar ki. Kan shi ta juya da masifan tana fadin ya dauko karuwa tazo tana mata iya shege a cikin gida yace gidab ki ko nawa ni na dauko ta ko ke. Turata ya fara yi ganin da gaske idan ta tsaya zai iya jibganta yasa ta fice daga part din maryam ne ta kalleni tace gara da kika kyale ta yanzu kin ga ya gani da idon shi. Ban san yaya suka karata ba bayan tafiyan maryam ne na gyasra part dina na shiga nayi wanka na zauna na feshe jikina da turararuka dakin shi na nufa. Yana ciki zaune ga laptop ya tasa a gaban shi amma ya kasa aiwata komai a ciki shigowana yasa shi dago kai ya dan kalleni gaidashi na fara yi na samu wuri na zauna. Haka yasa ya dawo da hankalin shi gareni nace dama nazo ne in maka tunin monday in Allah ya kaimu nike son fara shiga school. Nan take ya bata ranshi tare da fadin kai nifa wanan karatun ba dole bane sai kinyi shi kuma ko kin gama ba aiki zan bari kiyi ba. Nace amma kasan ba haka kukayi da iyayyena ba tun farko ai kasan ina karatu ka auro ni a hakan ka kawo wanan gida naka na fitina. Sanan kuma a hostel zan zauna don yafi min sauki ko ka sama min wani gida na daban in zauna don ban iya fitinar wanan matar taka haka . Wanan shine ra,ayina don zama na anan ina takura maku kai da matar ka yace wanan kuma maganar kine don haka ba ra,ayina bane kinji na fada maki. Wasu hawayene suka zubo min a fuskana kamar zanyi magaba sai kuma na juya na fita daga dakin batare da nayi magana ba. Bina yayi da kallo har na fice daga dakin ban san may yagani ba sai gashi a dakin ya biyo ni, sai da yasamu wuri ya zauna ya fara magana. Khadija may yasa kike son kema ki daga min hankali ina kokari in ga na shawo kan nafisa a gidan nan abubuwa su koma daidai. Ke kuma zaki zo min da wanan magana yanzu ina sane da zancen karatun wanan nasan dashi amma zancen in canza maki gida bai taso ba. Nace fitinar matar kace bazan iya ba tun yanzu ta fara kawo min takakka a daki na ba don maryam dake gidan ba da yaya kake son in yi. Ni kadai kagana ganin zan iya sune ko sai sun min yadda sukai maka sanan zakaji dadi ance sarki yawa yafi sarkin karfi. Ki bani lokaci akwai abinda nake shiryawa komai zai zo da sauki da yardan Allah amma yanzu indan munyi haka ai kamar taci galaban ki ke nan kece fa ake fadin zaki iya da ita amma gashi tun yanzu kin fara sarewa da ita. Ba tsoron matar ka nake ji ba fitinar tane nake son kaucewa sai ta lafa yace aiba lafawa take bukata ba barin gidan take bukata gare ki. Wanan mai sauki ni idan nice ba sai tayi fitina dakai ba yace aina san da hakan ba sai kin fada ba a fili amma nayi mamakin saurin kariyan ki tun yanzu ko wasan ba,a fara ba. Nace ashe akwai sauran wasa a baya yace ai ba a ko fara ba don yanzu somin tabi ne tunda bataga kin fara rungumana ba kina goya ni. Hararab shi nayi baka so hakan ba don baka biyo ta hanyan da za ai hakan ba yace saboda ban maki may ba ? Ya kasheni da idanuwan shi da ba zan jure kallon shi ido cikin ido ba ya mike tare da fadin ki sawa kan ki hakkuri komai zai wuce da yardan Allah . Har yakai kofa ya juyo yana fadin wai yaushe ne zaki kare wanan abin naki nace wani abu cikin watsa mashi harara yace barin zo in gani don ina ganin kamar ya dauke ni kike kwara. Ya nufoni gadan gadan nai saurin mikewa na shige bayi tare da turo kofa ina saka key yace matsoraciyar banza kawai ai ba sai kin gudu ba. Jin ya fita daga dakin nafito na nufi falo na rufo kofana na dawo na kashe wutan dakin na kwanta tare da tunane a raina. AA mutum ne mai saukin kai a yadda na fahince shi sai dai matane bai samu ba ji yadda yazo yana min magana cikin tsigar lalashi. . ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Sai da ya gaji da ya mutsani don kan shi ya sakeni idanuwa na lumshe ina mai jin takaicin hakan a raina yana koma gefe ya mirgina yana mai da nunfashi a wahalce . Bakajin komai a dakin sai shiru sai ko karan na,uran dakin dake aiki a lokacin kasa kasa naji muryan shi yana fadin. I am sorry Deedar kada ki dauke hakan don haka nayi na bane hakkinane na fara bi a gurin ki daga inda nake kwance bai iya tabuka komai sai hawaye dake fitamin daga idona wanda da taimakon haka nake jin dan relief a zuciyana. Can ya mike zaune yana fadin ki tashi ki yi breakfast mushiga mu gaida su Abba a cikin gida don sun ji muna garin nan tun jiya da dare and ba aladana bane inzo ban shiga wurin su ba a duk lokacin dana iso. Kinga sai su dauka naki sallon ne haka na hana ni shiga in gaida su sai lokacin nayi karfin halin yin magana nace tunda ka iya keta zaka sa su dauke a hankan ai don ka bata min suna. Murmushi yayi ya mikewa tare da fadin ba ga laifin ki ba da kike karatun low don shine daidai da wanan bakin naki mai surutun tsiya. Yakai kofa nace mugu kawai wanda bai san tausayi ba ya juyo yadan kalle ni yana fadin ke aikin sani tunda kin iya. Bayan fitan shi dakin nan iya dagawa a yadda ya banni ba a gurin nake kwance yayin da wayana yayi kara na dauka Ya Amina ce take fada min gata nan zuwa. Nace ki bari sai anjima don yace wai cikin gidan su zamu shiga yanzu idan mun karya tace to shike nan hakan yana da kyau ai. Kirana yayi da waya in fito mu karya mu fita nafito falon zaune na samay su shi da Yusuf suna magana Yusuf din na dan rankwafa ina gayarwa ya amsa min da kanwata ya gajiyan hanya Alhamdullahi na bashi amsa kawai. Zagayawa nayi ban yarda na bi ta faman su ba na samu wuri dan nesa dasu na zauna fuskan shi na akaina sai dai na kasa daga ido in kalle shi ni. Labara ta fito ta nufi dining din gidan ta fara jera abinci a sama sai cewa yayi kawo muna nan zafi don baku gyara wurin nan mutum nacin abinci zuciyar shi na tashi. Sai lokacin na dago ido na kalle su gira ya daga min nayi saurin kawar da kaina gefe kamar ban gan shi ba zama sukayi kasa don su karya iba zaune ban motsa ba. Kefa yaya ne bazaki karya bane yace min ba yanzun zan karya ba sai an jima na bashi amsa koma da zan karya a tare da abokin shine zan zauna ina budan baki. Yana bude kula naji ya ja tsuki yana fadin idan zaka iya ci Yusuf kaci ni ruwan tea din kawai zan kora Yusuf yace kaci mana ko kadan ne yace wanan abin haka kokai nasan ba zaka ci ba. Mikewa nayi don barin falon lokacin da suka fara karyawan naga Yusuf ya gutsuri doyan ya mayar a cikin plate din daya diba. Ko ruwan tea din dana zo sha ba wani kamshi ko dandano a cikin sa sai kona baki yakeyi amma haka na daure na shanye duka na aje cup din. Sai gaya ya shigo yana fadin mutafi ko idan na gama na dankara gyara fuskana nafito har daki nabi anty Fati ina fada mata inda zamu tace mu dawo lafiya na fito muka dauki hanyan shiga cikin gidan su. A kofan gidan nasu Yusuf ya tsayar da motar sai da suka fara fita kafin ni in fito suna gaba ina bayan su muka shigo gidan wanan karon bai barni nayi yadda na saba ba idan na shiga gidan. Dole duk inda yasa kafa yacire in dora nawa nima tare da mika gaisuwa na gare su. Watau duk yadda akayi wanan kishin sai an samay shi a tsakani mata kaji ana cewa su wance kai gidan su lafiya lau wallahi . Akwai zaman lafiya da fahinta da yar uwar ta ko abokiyar yazaman ta idan kinji wanan zancen a gida ba sai kin tona ba. Daya ce ta kwanta daya a sama ko kuma daya ta iya hakkuri da duk wanin abinda za ai mata bata nunawa. Yanayin zaman sarakaina yasa nayi wanan magana don anty Amarya amaryan su mommy tana da wani hali mai wuyan fahinta don kokai waye ka shigo gidan su kana sallama zata karba amma idon ta yana kasan zanin ka ko a jikin ka ta karance yanayin shigan ka a lokaci daya. Yauma hakane ya faru damu da muka shigo part din ta don mu gaida ita ina sallama gaba daya idon ta a kaina yake baifi second ba ta kare min kallo. Sai naji banji dadin abinda tayi min ba na duka har kasa na gaida ita da gida tana tambayana yaya amarci kaina na noke kawai ina dan murmushi muna fita tabini da harara wanda ban san abinda nayi mata ba nayi kamar ban ganta ba. Ummi ma da muka shiga wurin ta ta tare mu ba yabo ba fallasa cikin mutunci da girmamawa muka gaida ita tana ta saka muna albarka har muka bar dakin sai dakin mommy daga nan zamu shiga na hajiya mama hajiyar su AA din. Mommy kasa boye farin cikin ta tayi da ganin mu tana ta faman yi muna sannu da zuwa tana washe baki don ta kasa boye farin cikin ta ita kuma haka Allah yayi rayuwan ta da rashin kyashin duk wani wanda ta sani har mutanen gidan sukan ji haushin ta wani lokaci. Mun dan gaisa da ita yake fadin bari muje mu gaisa da hajiya do a nan zan barta ta wuni maku zan tafi wani wuri ne daga nan tace gaskiya mun ji dadin wanan abin sosai wallahi. Surajo ma ya kawo muna yarinyar da zai aura shekaran jiya anan ta wuni muna sai wani lokaci ta wuce. Hajiya mama na zaune a falon ta muka shiga da sallaman mu bantaba ganin farin cikin ta ba irin yau din da muka shiga gaida ita. Akusa da kafanta na zauna suna gefe dashi da Yusuf zaune guri daya muka fara gaida ita sune suke gaisawa da ita amma hankalin mama na wuri na. Sai da suka gama gaida ita na fara gaida ita cikin ladabi tace naji dadin hakan dana ganku Khadija ki kwantar da hankalin ki kuyi zaman lafiya da mijin ki da abokan zaman ki aure shi zaman hakkuri ya gada. Zo mu zauna zo mu saba haka abin yake ba ko yaushe ake zama dadi da miji ba musanman ma idan mijin yana da mata da yawa kamar irin na mu dana ku yanayi. Sai an kai zuciya nesa ga komai da zaka gani kagani kaki gani Allah yayi albarka ya baku zuria masu albarka. Suka amsa mata da amin mama mun gode yace gata nan a nan zan barta zamu dan je wani wuri sai zuwa anjima zamu dawo in Allah ya yarda. Sai mun dawo zamu gaisa da Abba don ance yau yayi sammako ya fita zuwa unguwa bamu samu ganin shi ba koda muka shigo Tace Allah ya tsare ya kare Allah ya dawo daku lafiya suka mike zasu tafi ya juyo yana fadin bataci wanin abin kwarai ba tun zuwan mu garin nan. A a khadija baki ci komai ba har yanzu kina bakunta ne keda gidan mijin ki idan abinda a girka bai gamshe ki ba ai zaki iya shiga ki girka ko kisa a girka maki. Ki saki jikin ki nan gidan ki ne gidan auren ki ne kuma mu iyayyen ki ne kada kiji nauyi ko kunyan yin abinda kike so ke tankar diyan gidan nan kike yanzu dama kuma haka din ne ke yar mu ce. Sun fice sin bar mama na mun wanan nasihan tare da dan yi min nasihan rayuwan aure wanda duk abu dayane duk wani wanda zai mun nasiha akan biyayya ne akan aure zai mun shi. Suna fita sai ga mommy ta shigo dakin tana fadin gashi kuma su Binta suna school tun safe suka fita gidan nan. Hajiya Mama tace yanzun yake fada min wai bataci abinci ba tunda suka zo garin nan don haka nasan halin khadija da kunya kwasheta ku tafi can wuri ki ko zata sake dama kece uwar yara. Haba khadija kina amarya zaki zauna da yunwa a cikin ki haka tashi muje ki samu abinda kikaci don Allah kardai wai har yanzu baki sake a gidan ba kike nufi ? Nan ta kamo min hannu muka fice daga part din hajiya mama nabi mommy zuwa nata wurin nayi mamakin ganin Ya Amina a dakin mommy da muka shiga ban wani sake ba sai wuri da na samu na zauna a gefen ta. Khadija kece kika koma haka kallon kaina nayi ina mamakin abinda zata ce na koma nasan dai bai wuce tace na ramay ba inma raman nayi ai su suka kaini ga hakan. Hawaye na fara daga inda nake zaune hankalin Ya Amina ya tashi sosai tace haba khadija muna murnan ganin ki haka zaki saka muna kuka kuma. Mommy ne ta kawo min abinci ta aje min a gabana tana fadin bari taci abinci Amina kafin ki fara mata wani magana don mijin ta yace taki ta cin komai tunda suka zo. Mommy ba gaskiya bane ko yanzu na sha ruwan zafi kafin mu zo nan mommy tace taji amma don Allah in dan ci abincin kafin a gama na rana. Tabude kulan naga dafa dukan cus,cus da ganye ta zuba min da kanta nan suka tasa ni gaba sai da na dan tsakura. Bayan na gama ne Ya Amina ke fadin khadija ki natsu ki saure ni ban son ki boye muna komai dake faruwa dake a gidan nan don mu san ta inda zamu bullo ma zancen. Mommy ta karbe da fadin ki saki jikin ki khadija ko ba zaki iya fada min ba nasan zaki fada ma yar uwar ki Amina halin da kike ciki don hankalin ta ya kwanta. Don tun ranan da muka barki hankalin mu ba akwance yake ba da barin ki da mukayi a gidan nan da Nafisa da yawan yan uwanta ke ke dai. Wasu hawaye suka zubo min ban boye masu komai ba har zuwan mu kadunan da mukayi na fada masu kai kawai suke kadawa suna mamaki. Mommy tace babu komai ke dai ki kara sa Allah a gaba shi zai kare ki daga duk wani sherin da suke kullawa ga kowa a gidan nan. Saukin abin ma da tayi maki baki bata bashi hakan zai dan kawo shakkun ki a zuciyar ta harta dan rage abinda tayi niyya akan ki. Kin san dai yanzu akwai hakkin miji a kan ki kada ki yarda ki tauye mashi hakkin ki da Allah ya rataya maki akan ki. Sanan duk wani abinda kika san yana so ki dinga yin shi a kai kai abincin da yake so shi zaki dinga girka mashi kin san dai dressing na jan hankalin miji ga matar shi nasan baki da wasa a wurin kwaliya da sauran su. Kinga mijin ki maison jin dadin rayuwa ne shine babban matsalan da suke samu da Fati tun farko nayi nayi ta canza tsarin ta amma bata daukan shawara ko kadan. Zaki natsu sosai ki fahinci komai nasa ki dinga aiwatar da nufin ki a kan su sannu a hankali ba a cikin garaje ba yadda kika tilasta shi yakai yaran shi makaranta yau da safe hakan yana da kyau sosai wallahi. Nan suka zaunar dani suna min nasiha sosai akan rayuwan gidan aure har barci ya dauke ni a gurin suka zauna da ya Amina suna maganan abinda suka fahunta a cikin magana na. Mommy tace don kada ta tayar min da hankali ne bata sanar dani ba don kada hankalina ya tashi. Tace ba karamin magana bane wanan fa Amina ni abinda na fahinta shine kamar irin asirin da taiwa fati ne ta sake maimata wa Khadija yanzu kuma don Nafisa ba karamar shu,uma bace wallahi. Saukin abin ma ita khadija ba irin yaran yanzun bane ai da ta fahinci halin da suke ciki da mijin. Wace amarya za akai yanzu harta share wanan kwanakin miji bai neme taba a zauna lafiya kuma ko da bata son auren ai ba sin shine batayi ba a yadda na fahince su. AA Sun isa zaria suka fara zuwa wurin kawu salihu nayan sun gana dashi ya gama jin abin da ya kawo su bai tsaya ba yace suje wurin wanan tsohon malamin nasa. Sun isa gurin shi sunyi sa,a ba mutane a gurin shi bayan sun gaisa dashi kawu yace malam gamu mun sake dawowa da dana na wancan lokacin. Nan ya koro mashi matsalan dake addaban shi a yanzu wanda basu fahinci ko maynene ba dan murmushi malam yayi irin na manya yace ai nasan zaka dawo in ka tuna da istiharan da na baka kaje kayi zaka gane wanan matsalan ya fito a ciki amma kai baka gane hakan. Wani zobe fari ya zare daga hannun shi ya mika ma AA din yace kai zaifi maka amfani a yanzu sama dani. Yace don naga kana da rauni wurin ibada ta haka ake samun daman cuta maka ta inda baka zata ba . Ya kara dauko wani garin magani yana mika mashi yace wanan za kayi amfani dashi idan ka koma gida daidai lokacin da kake fara jin yanayin da kake ji. Don daure ka ake bazaka iya aiwatar da komai ba akan mace zakaji ka koma tankar mace a duk lokacin da bukatan kasancewa da matar ka ya taso maka. Ya dauko wani dan abu ya bashi yace ya binne a cikin gidan shi indan har ka saka wanan abin a gidan ka da yardan ubangiji duk wani sheri da za a aiko maka bazai yi tasiri a kan ka ba. Sukai ma malam godiya tare da bashi dan sadaka don bai karban wani abu a gurin su sosai suka juyo zuwa kaduna. Sun kamo hanya suna magana AA ke fadin wai wake binshi da wanan sheri hakane may ya tare wa mutane. Yusuf ya kalleshi yace maganar gaskiya shine a cikin iyalin ka wata ke wanan sheri idan ba su din ba wazai maka wanan sherin haka akan iyalan ka. Huci ya sake daga inda yake zaune yana cewa indan na gane may mani wanan sheri ba zan saurara ma mutum ba ko wanene. Khadija Shiru shiru basu dawo ba har nayi barcina na tashi dawowan su Binta na koma dakin hajiya mama sarakuwa na muka kebe a daki dasu muna hira. Duk yadda suka so su bugi cikina suji zaman mu a gidan na boye masu ban fada masu komai ba sai dai in masu dariya idan suna maganan su. Can zuwa hudu suka dawo part din Abban shi suka yada zango a wurin shi sun dade a zaune da Abban ya aika in zo in gaida mahaifin nashi don yace bai sanni ba. Nashigo falon na Abba suna zaune a saman kujera a cikin sakewa da mahaifin nashi na shigo bisa jagorancin mommy . Kasa na zube kaina yana kallon kasa na gaida shi da wuni yake cewa da mommy eh lallai naga sarakuwan nawa alama ma kawai yanuna min daga inda ta fito. Don kin san su mutanen Niger akwasu da tarbiya mayne ma sunan ta mommy tace ai uwan tace khadija take Abba yace suna mai kyawo da fatan zaki halin mai sunan da kika gado. Yadan muna nasiha a tare har lokacin ban dago kai na kalli Abban ba yace mutshi mu tafi Allah yayi muna albarka araina nace amin don irin su bakin su karba ake idan an dace. Zan fita naji AA na fadin ki fito mu tafi gida don ina son tafiya yanzu ban amsa shi ba nafita muna shiga mommy ta kara min nasiha ta rakani na sallami sauran mutanen gidan muka fito suna waje suna jirana a lokacin. Barin mu gidan nasu kafin mu karasa gidan su kira ya shigo a wayan shi ya dauka tare da sallama bata karba ba tace Samad idan baka dawo ba wallahi zanzo garin nan in samay ku. Watau kai ga mai amarya ka dauke ta kaje can kuji dadi da ita ni ka barni nan yace ke ban son wanan haukan naki ya kashe wayan shi . Nikan mota na tsayawa na bude nafice daga ciki ban tsaya jiran su ba tunda yanzu nasan hanya ba sai an nuna min ba. A falo na samu su Anty Fati da sallama nashigo ganin su yasa na tsaya ina gaida su da wuni tace kun dawo ya su hajiyan suna lafiya ? Lafiya suna gaida ke na wuce zuwa sama inda dakunan suke na bude na shiga dakin na nan a yarda na barshi tubewa nayi na fara gyara dakin sai dana gama na sauko kasa don shirun da yai min yawa. Basu falon motsin su naji a kitchen na nufi can bayan Anty Fati na fara hangowa na karaso ina fadin ashe kuna nan ne ? Eh ta fada tana juyowa gareni karasowa nayi cikin kitchen din ta dan kauce min na shiga daga ciki nace anty may za a dafa sai inyi mama laraba yau ta huta ita. Haba dai ki barta tayi ai aikin ta ne hajiya ki barshi zan iya ai laraba tace nace ba komai nagaji da zama guri daya ne ina son in dan motsa jikina. Anty Fati tace na rasa may za, a girka yanzu kin san shi dan matsalane wallahi azo ma ayi yace ba shi yake so ba. Nace ina ga kamar tunda dare ne ai zai fi kyau a girka tuwo tace dare baiyi ba nace idan akwai kayan aiki ai za a iya yi. Tace to shike nan ta juya ta fita daga kitchen din nan muka fara aiki da mama laraba wanda kusan aikin nice may yi tana miko min abinda nake bukata. Bayan magariba mun gama komai da muke bukata har mun fitar dashi a falo nan dai na shige daki inyi wanka naga period yazo min. Wanka nayi na gyara jikina na fito dama ina expecting din zuwan shi nazo da pad dina na shirya na feshe jikina da musk mai kan shi na samu wurina dan kwanta tare da bude datan wayana. A take sakonni suka fara shigo min wanda kusan yawanci yan makarantan mune suke tayani murnan aure tare da yi min korafin rashin fada masu suzo. Ina cikin basu amsa ne ya shigo dakin ya sauya kayan jikin shi kallo daya nayi mai na mayar da hankali na ga abinda nake yi din. Takowa yayi zuwa bakin gadon abinci fa madam na dago nace mai naci kafin in shigo taso muje falon yace min. Nace amma kasan haka baida kyau don itama tana son kebewa dakai yanzu tunda ita kazo yiwa weekend don may zan dinga takura maku haka. A binda mutum baiso kada yayiwa wani don shima in an mashi bazai ji dadi ba ashe malama na kawo gidan ban sani ba. Ba zancen malama sai gaskiya matar ka tana bukatan ka a kusa da ita banga dalilin da zan takura ma rayuwan ta ba ina da hankali fa. Fitan ki shi zai sa mu takura mu fasa abinda zamuyi yallabai ba zan fita ba gaskiya ka bar ni please ? Sunan da na samu kuma yau ke nan a gurin ki nace ai naga kamar kafi yallabai din mulki ne yanzu. Yace lalai kan tunda ina a gaban gimbiya ai na zama yallabai din kaidai ka sani kana dai gaban matan ka ni may ye nawa a cikin wanan. Ya juya yana fadin idan fa baki fito ba bazanci abincin ba nima yana fadin haka ya fita abinda ya fadi yasani tunanen kadafa su zarge ni idan banci abincin ba tunda nina girka. Don haka na mike na fita ina saukowa ya tsura min idon har na karaso wurin na samu wuri zauna yaran suna gefe suna cin nasu abincin. Affan kun dawo ya makarantar nace lokacin da nake zama na mayar da hankali a gun yaran daidai lokacin Anty Fati ta fito har wanan lokacin tana daure da zanin da ta wuni dashi a jikin ta ne. Ba tare da tayiwa kowa magana ba ta samu wuri ta zauna batai magana ba shima bai mata magana ba sai ni da yaran ke dan fira a falon. Karamin yace min yau anty yan school din mu sunga daddyn mu nace ashe kaji dadin hakan ya gyada kan shi dariya ya bani nace idan daddy na gida ashe shi zai dinga kaiku school ke nan kuna jin dadi. Ke fa nake jira ki ba ni abinci yace mata ta wani juyowa tace ga abincin nan ai an gama tun dazun mikewa nayi daga in da nake zaune na dauko plate uku na jera a gaban su na fara zubawa. Na aje mai yace min thanks na zuba mata nata na aje mata a gaban ta na dan zuba nawa kadan na koma gefe na zauna ina tsakura don ban jin ci. Ina gamawa na mike nabar wurin tare da kwashe kayan da mukaci abincin da na su Affan daga can na wuce zuwa daki na ban koma wurin su ba. Barci ya fara dauka na ban riga da na rufe dakin ba yashigo dakin da sauri na zabura na tashi ina tsoron ya aikata min abinda ya aikata min jiyan. May ye haka ba barci kike yi ba ne nace barci nake ji dai na mike zaune ya karaso har inda nake zaunen ya samu wuri ya zauna shima. Yace akan may zaki girki ba na hanaki wana aikin hakaba may ye amfanin masu yi din da aka dauko. Kallon shi nayi nace don girki kuma shine aiki nayine kawai don in dan motsa jikima ba don wani abuba. Yace au motsa jiki kike so ashe barin dan tayaki motsawa da saurina yun kura zan tashi ya rike ni na kasa tashi a inda naken. Kokuwa muka dan fara yi dashi ina kokarin kwatar kaina daga gare shi amma na kasa danne ni yayi tare da raba hannaye na biyu ya shige tsakiyana. Ban son haka don Allah ka sake ni please kasan haka baida kyau fa nake fada mai cikin wani murya yake cewa may nene baida kyau don miji ya rike matar shi ? Zanyi magana ya hada baki na da nashi ya fara tsotso ina kokarin kaucewa amma na kasa don yafi karfina. Jagwalgwala ni ya fara yi yadda yake so tare da cusa hannuwan shi cikin kirjina da karfi na zubura ina kokarin kwatar kaina. Har kasan mara na yakai yana jin ya tabo pad naji ya sakeni yana fadin na manta lokacin ki yayi fa naga ya mike yana gyara rigarsa daya takure wurin kokuwa dani. In kin fitar ubangiji yabi min hakkina a kan ku yar uwa don ba zan yafe hakkina ba ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Idan kin fitar min da novel waje ubangiji yabi min hakkina akan ki din na fada maku online novel ne na kudi da kuke cewa kun biya kuna da iko dashi kin san ai ba takarda kika saye ba. Ki karanta nan ki barshinan idan kuma bakiyiwa Allah da Annabinsa da na hada ku dashi wanan kuma sakkayan na hannun Allah Kada ki karanta min novel idan baki biya ba don ban yafe maki ba har ga Allah. Allah yagani ban ji dadin zuwa kadunan da zamuyi ba saidai banda yadda zanyi don yan zu a karkashin dokar wani nake. Wani abinda ya fara kula dashi shine sabon canjin yanayin jikin shi daya samu yanzu don tun randa ya gama min sati dayana a dadafe ya samu kwanakin suka cika mai. Shikan shi bai san dalilin dayasa ya kasa aiwatar da komai a kaina ba amma a ranan da Nafisa ta karbi girki lafiya kalau ya kwana babu wanan sanyin da yake ji idan dare yayi ko nauyin zuciya yaji shi ya koma tankar mace ba namiji ba. Amma saidai may da gari ya waye zan karbi girki tun da karfe bakwai yake jin yanayin yana ziyar tanshi. Hakan bai sa ya kawo komai a zuciyar shi ba sai dai abin ya dan damay shi a cikin ranshi haka ya kare min wuni na a dadafe. Haka yaci gaba da wakana a tsakanin mu saidai baiga damuwan hakan dake faruwa dashi a fuskana ba don haka ya dan rage damuwan shi. Don ni ko kadan abin bai damay ni ba ban kuma daukeshi wani abuba rawan kan da take tana wani hura hanci ita a dole ga mai miji haka zai wuni bai shigo part dina ba. Batasan ni mijin bai damay ni ba don da ina son shi a lokacin duk wani rawan kanta bai razana ni shiko idan ya dan samu ya shigo ya fara dan kame kame irin na mazan da basu da gaskiya. Ya samu Yusuf da ya dawo daga tafiya da zancen tun shigowan shi wurin AA di yana mashi ba,a yaga ya koma so silent wuri Yusuf din ya samu ya zauna. Yana tambayan shi may ke faruwa ne ko sun fara caza maka kaine a gidan gaka ka fada a lokaci guda. Dan murmushi yasake tare da girgiza kan shi yana fadin ba wanan ba Yusuf wani bakon yana ne ke ziyarta na kusan wanda nake ji a baya idan ina tare da Fati sai dai wanan akwai banbaci sosai dana bayan. Don da zaran ina dakin khadija akace bakwai na yamma yayi zan wuni lafiya kamar bani na amma da zaran bakwai yayi sai in fara shiga cikin wanan bakon yanayin nawa. Zan din gajin jikina yana sake min sai in koma tankar mace ga wani mugun sanyi da kaduwa da zan kwana dashi bani zan samu kaina sai gari ya waye watarana kai in gajarce maka a haka zan wuni da wanan yanayin a jikina. Kai kawai Yusuf ke iya kada mashi yana sauraren bayanin da yake mashi din sai da yakai karshen maganan shi Yusuf yace wanan magana fa kada ya zamo gaskiya. Da sauri AA yace wani magana ke nan kake nufi zai tabbata yace yanzu dai ba wanan ba neman mafita ne a gaban mu don wanan ba karamin magana ba da za,ayi wasa dashi. Ita khadijan ta fahinci hakan ne ko may yace ban dauka ta fahinta ba don kasan har yanzu ba wai ta sake bane irin haka. Zaka iya barin garin nan na wani dan lokaci tare da khadijan kamar yadda mukayi akan Fati ta daga daga garin nan ita ma. Kai ya girgiza ma Yusuf din yana fadin kasan haka ba zai samu agare ni ba yanzu naso sai zuwa next week ko upper week mu leka kaduna mu gaida su su gane ta taga yan uwa. Yace ya zama dole ku dan daga ma garin nan muga abinda hali zaiyi daga can mu shiga neman magani akan wanan matsala don zai yuyu abinda nake hasashe bashi bane ko shi din ne. Yanzun ba zamu iya gane hakan ba sai kun dan daga ma garin nan na wani lokaci zamu san abin yi akai. Ina kwance a falon dakina karatu nake barci ya dauke ni a gurin yadda ya samay ni shiya kara kidima shi yazo dap inda nake kwance yayi min kallon tsab yau ba inda bai kalla ba a jikina sai inda yake rufe a cikin rigana kallon shi ya tsaya cak akan kirji na da ya dan taso ya tsaya cak da sauri ya mayar da idon shi a fuskana. Da sauri ya juya zai bar falon nawa yaji na motsa ya juyo yana fadin na shigo na samu kina barci ki tashi ki shirya yau zamu shiga kaduna. Mamaki ne yakamani ba wani shiri ace wai tafiya da rana tsaka ba kai aure ma dai matsala ce wallahi don banda yadda zanyi dole in bi umurnin shi a hakan. Ya fara tafiya ya juyo yana fadin ba wasu kaya masu yawa zaki dauka ba don bai wuce muyi kwana uku ba mu juyo ban iya bashi amsa ba don raina ya baci. Kaya kala ukun dayace na dauka sai wanda na saka ajikina ya cika hudu koda muka fito Nafisa bata gidan don haka ko sallama ban samu yi da ita ba . Yusuf yana zaune a gaban motar da zamu shiga yana jiran fitowan mu har lokacin cin bacin rai nake fuskana ba wani walwala a tare dani gaida shi kawai nayi na shiga motar. Tunda muka fara tafiya su kadai ke firan su a motar hankalina yana a wayana da nake duba tafiya naga saurin shi don ba a dauki wani lokaci mai tsawo ba sai gamu garin kaduna. Lokacin magariba ya gabato sosai muna shiga layin su daidai get din gidan ya Amina ko kallon wurin basuyi ba suka nausa shiga cikin unguwar kai tsaye. Babu abinda ke raina sai irin tarban da zan samu gun anty Fati ga nauyi da kunyan ta da nake ji a raina na yadda zan hada ido da ita a matsayin kishiyar ta a yanzu. A hankali na furta da kun sauke ni gidan ya Amina in sauka a nan nace dasu ko kallona ba wanda yayi daga cikin su sai da Yusuf yake karya kwanan shiga get din gidan yace min yanzun ai kanwa ta ke da gidan antyn ki sai dai ziyara kuma. Wani iri naji a raina don ni gaskiya an dai takura ma rayuwa na don ban taba kawo haka a rayuwa na ba a yanzu. Bayan motar ta tsaya ban fito ba muryan AA naji yana fadin ki fito mana ko dadin motar ne bai isheki ba a baki key ki koma abuja a yau. Sai da Yusuf ya fita ya zagayo ya bude min gefen da nake zaune yana fadin kaga aboki na kada kai mata laifi kuma ka koma zolayan ta yanzu. AA yace nidakai wa yafi laifi a gare ta yanzu yanzun nan fa ta gama tambayan ka ka sauke ta gidan antyn ta kaki. Banyi magana ba sai fitar da kafa na daya da nayi waje bakina yana dauke da addua na dauko hand bag dina na fito daga cikin motar. Tsaya wa nayi daga gefen da nake ina kallon su Yusuf ne yace bissimillah mana khadija mu shiga welcome to yaur house ki saki jikin ki don gida kika zo. A hankali na fara takawa ina gyara mayafin kaina sai kuma na ja na tsaya guri daya sai da suka karaso driver dayan motan ya fara shiga da kayan cikin gidan na bisu a baya. Falon muka shiga babu kowa a cikin sa shiya hau sama inda dakunan kwanan su yake ya shige ya bar mu a gurin. Labara ne ta fito daga kitchen tana muna sannu da zuwa tana ganina tace ashe da amarya ake tafe sannun ku da zuwa ga wuri ki zauna. Taron da matar tayi min yasa na dan fara sakin zuciya na saura na matan gidan mu gani yadda zata tare ni can sai gata tana saukowa daga saman fuskan ta babu yabo ba fallasa a cikin sa. Itama sannu da zuwa take muna na dan duka ina gaida ita vikin mutunci a daidai lokacin ya sauko daga saman yana fadin ku basu ruwa mana. Cikin muryan ta mai kamar taka da basarwa tace laraba kawo masu ruwa don Allah ta kai zaune tana fadin ashe tare kuke tafe. Na dan dago kaina a kunyace nace eh anty mun samay ku lafiya ta wani ya motse fuska tana maida kanta bayan kujeran da ta zauna take fadin wallahi lafiya. Goran ruwan da laraba ta dire a gaban mu Yusuf ya dauki dayas ya balle ya kafa bakin shi ba tare daya zuba a cup ba. Yana gamawa yace zan tafi gida yanzu don su san nazo ya dago yana fadin kanwata ahuta gajiya ko ? Dan murmushi nayi daga inda nake zaune a tsawala AA ne ya mike yana fadin bude mata dakin dake kusa da nawa ta zauna ciki. Daga haka ya fice daga gidan laraba ta umurta da taje ta bude dakin ta nuna min dan kallon ta nayi ina fadin anty don Allah sallah nake son inyi. Ok zaki iya shiga dakina ki hau sama ai kin san dakin ko na dan gyada mata kai a hankali na tashi ina daukan hand bag dina dake aje saman kujeran.. Tace baki sha ruwan da aka kawo maki ba zansha nace na dauki gora daya na fara tafiya dashi na kai saman sai gata ta biyo ni tana fadin. Bari in dan gyaro ban dakin kafin ki shiga nace ba komai zanyi hakana a tare muka shiga dakin nata da ita. Na aje jakkana da gyale na na nufi bandakin ko dana tura saida tsikan jikina ya tashi gurin na dan gyara do naga abin gyara a je gefe daya na wanke nayi abinda zanyi na fito don akwaini da kyankyami. Na samu ta shifida min abin sallah na gabatar da sallah na zauna a gurin ina jiran a kira magariba ta sake shigowa dakin lokacin nace da ita su AFFAN fa anty. Sai lokacin naga ta danyi murmushi tace suna cikin gida sun je islamiya ne sai zunyi sallah zasu shigo. Kiran sallah da agogon dakin yayi yasa na mike na fara gabatar da sallah na a gurin sai da nayi ishai na dako wayana na kira ya Amina. Tana dauka ta fara fadin Amarya mai batun hankali yau na samu an kirani ne fushi ya rage ke nan nace su Nasir na nan gidane ? Sunanan wani abin ne nace ki turo akawo min shi don Allah da sauri naji tace ina da mamakin ta gani nan gidan Anty Fati dazun muka zo. Khadija kin zo garin nan shine baki sanar dani zuwan ku ba sai da na bata rai cikin gajiya nace nima ban san zamu zoba yau sai da ranan nan yake fadin in shirya. Tace gaskiya yanzu ba zan samu turo su ba dare yayi da safe zan shigo nace Allah ya kaimu na kashe wayan. Shine ya shigo dakin yana dadin ba,a gyara part din bane ta koma ciki tace ba sakin fuska an gyara sallah ta ke yi. Deedar idan kin huta zamu shiga mu gaida Abba ya fada kai tsaye to kawai nace don naga anty a tsaye dakin. Yana fita na mike tsaye tare da tambayan Anty Fati wani daki zan shiga tace muje in kaiki yana nan kusa ai tayi gaba nabi bayan ta zuwa dakin . Sauran dakunan duk a rufe suke sai wanda zan shiga ne ta tura kofan muka shiga tace wanan ne dakin nagode nace mata. Har ta juya zata fita ta juyo tace min idan kina bukatan wani abu sai ki min magana to nace tare da fadin nagode. Tana fita nabi dakin da kallo komai na dakin Fati akwai shi dakin sai da wanan bai tsufa ba don ba a zama cikin shi yana nan sabon shi fil. Sai dai dakin yayi kura sosai ba zan iya zama a cikin sa haka ba gyale na na cire tare da aje hand bag dina na fara gyara dakin. Kayana Laraba ta shigo dashi dakin tana fadin a, a baki huta ba da sai da safe nake son shigowa na gyara maki nace kada ki damu mama ai gyaran ba wuya don na gyara. Bayan fitan laraba ne na shiga wanka na dan dauki lokaci a bayin kafin in fito ina fitowa AA ne zaune a bakin gadon dakin ya tsurawa wayan shi ido. Gashi da daura gaba na fito bayin don ko tawul babu a dakin na rasa yadda zanyi shi kuma ya dago kai ya kafe ni da ido na rasa yadda zanyin in karaso gashi zaune a dakin. Dan komawa nayi kamar zan shiga bayin can kuma naja na tsaya wuri daya nace don Allah dan fita in gyara jikina kamar mai jira inyi magana ya mike daga zaunen da yake yace idan kin gama ina jiran ki a falo bazamu fita ba sai gobe don yanzun dare yayi. Cikin sauri na shirya jikina jin bazamu fita na saka dogon rigan da na dauko don shan iska tare da dora hijjabin sallah na akai. A falon na samay su zaune da anty Fati da yaran su lokacin yaran sun dawo daga babban gidan su wurin kakanin su. Karasowa nayi inda suke ina dan taba kan karamin daga ciki ina fadin kun dawo ba tare da ta dago kanta ba tace bazaku gaida anty da zuwa ba. Yaran suka dago suka kalleni sai kuma suka maida hankali wurin uwar su suna tambaya mama wace anty. Kyalesu ta yi nidai na samu wuri na zauna ba tare da nayi magana ba tace kai Affan jekace laraba ta fito da abinci. Yaron ya sheka da gudu zuwa kiran laraba din na sake mika hannun gun karamin nace bazaka zo ba mu gaisa a hankali ya tako zuwa wurina. Hannun shi na kama ina tambayan sunan shi gaba daya na mayar da hankalina ga yaron Affan na dawa ganin karamin a gurina shima yazo inda nake. Laraba tazo da abinci tana jerawa a kasan carpet gaban shi ta gama ta wuce yace ina wanan maganin da na bari nan tace kai Affan je daki ka dauko ma babban ku maganin sa a kwalba. Yace kai enough dawo ka zauna idan ke ba zaki tashi ba ki bari komai yaro ko wata zasu yi min ke bazaki iya motsa jikin ba ko kadan wanan son jikin naki baida amfani wallahi. Dan dago kai nayi na kalleshi sai naji nauyin abinda yai mata a gabana ta mike zuwa dauko maganin . Cikin harshen turanci nace da shi haka fa baida kyau kana mata tsawa a gaban diyan ta da ni don ko nice bazan ji dadi ba. Bai min magana sai zama da yayi kasa ya fara bude abincin da aka aje din tsuki yaja yace daidai tana kawo wa wurin amma dai kin san bancin shikafa da dare ko. Shina dafa tunda rana na dauko da wuri zaku iso rufe abincin yayi ya koma ya mayar da jikin shi ga makarin kujera tare da mai da hankalin shi ga tv. A dauka kenan bazaka ci ba yace bai ci tace amarya kefa nace zanci anty na gode sannu da aiki tace ba komai. Sauka nayi tare da yadon a hannuna na zauna a kasan ina fadin Affan zakuci abincin in zuba daku? Yaran sukace eh anty tare na zuba muna suka zauna muka fara ci a tunane na tunda yace bai ci zata shiga kitchen ta girka mai abinda yake so. Amma sai naga ta koma ta zauna tana sakatan hakoranta tare da mayar da fuskan ta ga tv tsakuran abincin nake don ba dadi amma haka nake kokarin turashi a cikina. Wayan shi ne yai kara yana kallo bai dauka ba har kiran ya katse ba a kai wani lokaci ba kiran ya kara shigo mashi ya dauka ba tare da sallama ba. Sai dai mun ji yana fadin zaki fara wanan haukan naki ko kina wurin yawo ki zan tsaya jiran sai kin dawo in fada maki zamuyi tafiya ko may , ? Ban ji abinda ta fadi ba mashi ba mun dai ji yace saboda ke kika aje ku ke kika haife ni ne Nafisa kina fa son wuce gona da iri nagani yana fadin haka ya kashe wayan shi. Aka kara kira sai da ya kallo inda muke kaina yana kasa naji yaja tsaki ya kashe wayan tare da jefata gefen shi. Baba gobe zaka kaimu makaranta da kanka kullun abokan mu babban su ke kaisu school kafin ya bada amsa nace zaikai ku mana tunda yana gari. Kuma, asan baban ku yazo ko ? Uwar tace kada ma ku sa rai don kun san ba kaiku zaiyi ba nace haba anty ki barsu su roke shi mana tunda gashi a zaune. Murmushi tayi kawai ta kawar da kanta gefe bata sake kallon su ba nace jeka gurin daddy ka rokesa ko zai kai ku yaron yana makewa na turashi dole yaje gaban uban sai ya kasa magana. Daga inda nake zaune nace dashi ana magana da kai ya juyo fuska a daure yana kallon yaron yace maynene ? Wai suna son ka kai su school gobe don Allah shine ya kasa magana ns bashi amsa yace Ke kuma da baki jin tsorona ko kunya kece mai iya fada ko ya tambaya yana kallon fuska na ? Shi zuwa school din ka kai diyan ka ne abin jin kunya kuma ko tsoro ina fadin haka naja bakina na daure fuskana ban kara magana ba kuma ban ci gaba da cin abincin ba. Kai ku tashi kuje ku kwanta dare yayi gobe ba kuna shiga school ba yace cikin daure fuska, yaran sukayi saurin mikewa tun bai rufe bakin shi ba don tsoron shi da suke ji. Mikewa nayi na fara kwashe kayan da mukaci abincin nakai kitchen ban zauna ba ina batun wucewa naji yace ke dawo ki zauna. Kallon shi nayi da mamaki sai naci gaba da tafiya ban tsaya ba ya sake fadin bakiji bane Deeadar nace ban san dani kake magana ba ai. Dawowa nayi na samu wuri na zauna dan wani lokaci baiyi magana ba sai can yace wanan itace first wife din Fati nasan kin santa tun baya. Ya ce ke kuma wanan itace khadija wace na aura kwanan nan a garin minna da fatan zaku zauna lafiya a tsakanin ku ban son inji wani fitina ya fito a gidan nan. Da fatan kun fahinci abinda nake nufi shiru ya biyo maganan shi yace ina kuna jina tace a gyatsire munji Allah ya bamu hakkurin zama. Nace Amin sai na dan yun kura nace zan iya tafiya yanzu yace is Ok ba tare da ya juyo inda nake ba haka yasa namike nabar masu falon na koma dakin da aka bani din. Ban tsaya yin wani abuba na samu guri na kwanta da niyar barcin da nake ji sai dai barcin yaki zuwa min a lokacin sai tunanen yanayin zaman shi da matar shi har diyan su nakeyi. Can barci ya fara dan fisga na naji an turo kofan dakin da nake kwance da sauri na bude idanuwa na na sauke su akan shi. Yana tsaye daga kofa ya rike hanayen shi saman kirjin shi yace bakiyi barci ba ashe wutan dakin nagani a kunne na shigo. Nace tsoro nake ji yasa ban kashe wutan ba tsoro ya tambaya cikin mamaki nace tsoron wanan gida mai girma haka nake ji na karasa fadi cikin kara rufe jikina da bargo. Yace kenan izo in tayaki kwana ke nan kada dodon gida ya kama ki a gidan nace Allah zai tsare ni ba sai ka zo ba. Allah da gaske nake gunda naga kina jin tsoro yana magana yake nufo inda nake kwancen da sauri na mike zaune nace rufa min asiri kada matar ka ta dauke ni macuciya. Da can kaike tayani kwana da nake jin tsoro ni haka nake idan zan kwana inda ban taba zuwa ba. Don na kwana wurin amarya na sai ta daukeki macuciya ai tasan abinda ke tsakanin amarya da angon ta ko ? May ke tsakanin amarya da ango na tambaye shi ina hararan shi yace a tambaye ki ai kaidai zata a tambaya don kai kasan wanan. Don Allah malam kafita don kada ta dauka wani abin ne ban son bata wa mutum rai a sanadina sai da safe. Dariya ya soma yi ya fita daga dakin yana tunane a ran shi karfa maganan Yusuf ya zama gaskiya don yau jin kan shi yake kamar bashi ba ga wani feeling da yake ji a kaina wanda bai taba jin shi ba tunda na shigo gidan. Deedar da yake so yake kauna a baya yanzu gata a gidan shi a matsayin matar sunnan shi ya kasa tabuka komai a ranshi yadda yake so . Wani akasi yazo ya muna hijjabi a tsakanin mu wanda bai san ko may nene ke damun shi ba a halin yanzu. Sai dai yanayi yau jin shi yake wasai ba faduwan gaba ko jin wani kasala da ke saka shi jin sanyin da yake ji yan kwana kin nan. Yanzun tun deedar bata fahinci halin da nake ciki ba da ita har tazo ta gane abindake faruwa dani ai sai ta dauke ni mayaudari . Ko ya zata fassara abin ya zama dole inyi nisa da ita har lokacin da abin zai zo mashi karshe. Da wanan tunane kala kala ya shiga dakin shi ya kwanta inda ba a dauki lokaci ba Fati tashigo dakin ta samay shi. Da safe ko dana tashi da zancen yaran dake so ya kaisu makaranta na tashi a raina sai dai bansan a halin da yake yanzu ba gashi kuma ina son tuna mashi. Na rasa yadda zanyi fitowa nayi falon na samu laraba na faman shirya yaran nace barin taimaka maki mama kije ki karasa hada masu abincin. Sun gama shiryawa na rasa yadda zanyi don haka na tura mai text har biyu a jere da juna laraba na fadin su fito su wuce kada su makara nace tadan dakata ta gyara ma karamin rigan sa don dai aja lokaci. Yana kwance cikin barci yaji text na shigo mashi har biyu jere ga juna a wayan shi hannu yasa ya laluba wayan tare da duba text din. Ka taimaka ka kai yaran ka makaranta tunda sun sa rai tun jiya muna falo muna jiran fitowan ka mamaki yayi sai ya ja tsuki ya koma barcin shi. Ko may ya tuna kuma sai ya mike tare da zura rigan shi ya sauko kasa zuwa kai yaran makaranta. Can ko sai gashi ya sauko da alaman daga barci ya tashi ina ganin shi na yi ajiyan zuciya ya sauko yana fadin idan kun shirya muje in sauke ko. Da murnan su suka fita gidan na koma dakina bayan sun wuce don in yi wanka in gyara jikina don na saba da wanka tunda safe idan gari ya waye. Na fito na zaina na shirya tsab dani don nasan da zancen shiga wurin iyayyen shi da zamu yi yau wanda yau shigan nawa wurin su a wani matsayi na daban ne. Ina son indan mun fito in roke shi ya sauke ni gidan ya Aminan mu dan zan fi sake jiki a can idan ina tare da ita. Kwance na koma nayi kwanciyar rigingine ina kallon rufin dakin sai aikin tunane nakeyi ban san barci ya daukeni ba a gurin sai wani lokaci naji ana taba min marana. Firgigit na tashi daga yadda nake shine tsaye a kaina yana kallona kokarin tashi nayi zaune yace wanan kwamciyan da kikayi wuyan ki bazai maki ciwo bane haka. Zaiyi na dan kwanta ne ashe barci ya dauke ni ban sani ba nace ina kwana ya amsa min da lafiya . Deedar kina son kawo min wani sabon tsari a gidan nan da sauri na dago kaina nace har yaushe na shigo gidan da zan fara tsara wani rayi na dabsn can. Don may zaki kwadai ta wa yaran nan abinda kika san ba zan iya yi masu shi ba nace zaka iya mana tunda kai ka haifi abin ka. Wanan shine wani sabon tsari na dauka wani abin ne can na daban don uba yakai diyan shi makaranta kai ba abin alfahari bane a ganka da diyan ka kun fita. Wani nacen yana nema Allah bai bashi ba kai ka samu kake sakaci da baiwan da Allah yayi ma saboda wani ra,agin ka na daban. Bakina ya cafke yana fadin idan ina magana kinayi zanyi maganin wanan bakin mai katsalandan watarana . Kokarin kaucewa nakeyi shikuma yana kokarin kama bakin nawa har ya hada jikin shi da nawa da sauri nake kokarin dago shi daga sama na amma na kasa. Cikin karfin hali nake fadin may kakeyi hakane wai don Allah kadagamin mana kada wani ya shigo yagan mu a haka ya zarge mu. Wanda ya shigo shi ya kawo kansa ai don ansan nan dakin ma,aurata ne nace wani aure masu aure dai suna inda suke yace barin gwada maki inda suke din. Banyi aune ba naji ya laluba bakina yana kokarin hadawa da nashi cikin karfin hali da wani yanayi dake ziyarta na nayi kokarin daga shi gareni. Sai naji na kasa sai faman motsu motsu nake ya kasa barin baki na can na samu na kwace bakina daga nashi ina gogewa yace baki natsuba ke nan. Sake kokarin kamoni yayi zuwa jikin shi na gwauce ina fadin don Allah ka bari kada wani ya shigo ya samay mu a hakan.? Idan suka samay ai tare da matata suka ganni ko ba zina nake aikatawa ba dai kayi hakkuri don Allah nace don nauyin shi akaina ya fara isata. ZAINAB IDIRIS MAKAWA SEENABU 1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Bai kara bi ta kaina ba tun wanan ranan da ya kusa kawai gareni ban san may ya tsayar dashi ba ni dai naga ya koma baya yana sauke numfashi da karfi. Bayan na gama sauke nawa numfashin ne na lalaba na gudu dakina na barshi nan sai da safe ya shigo min ido yayi mai zurun zurun kamar wanda yayi jinya kwana da kwanaki. Zaune naki a gaban mirrow ina shirin fita school ya samay ni dago kai nayi na kalleshi na sauke kaina kasa da saurin don kunyan abinda yai min jiya nake ji. Karasawa gaban mirrow din yayi ya dan jigina jikinshi saman mirrow din yana fuskanta na ina kwana nace dashi ina kokarin ci gaba da shafa mai a jikina. Kin tashi lafiya yace tare da kai hannun shi ga man ya lakato ya fara murzawa ga hannayen shi a hankali. Ban san may zaiyi da man ba sai da naga ya fara shafa min a bayana a hankali har zuwa mazauna na da sauri nace dashi nace ma ba zan iya bane ? Basai kin fada ba don nasan bazaki iya mulke wurin nan ba ina tsaye to kafita mana tunda mun gaisa sai in karasa. Fitana da rashin fitana baida wani amfani a gare ki yanzu don na gama ganin inda baki son in gani a jikin ki saura wuri daya yarage min in kai. Wanda kema kin san dashi yanzu magana yake kamar mai yin rada kada wani yaji shi a dakin baki na turo gaba ina fadin . Wanan ai shiga hakki ne yaya zaka kama kalle min jiki kamar wata yar , , , , , ji nayiya dagoni daga zaunen da nake yana kokarin mikar dani tsaye tare da fadin Deeder nima nasan ina shiga hakkin ki da yawa kuma kina hakkuri dani sosai a hakan. Sai dai ki sani ba laifi na bane yin haka don Allah ki kara hakkuri ki kuma tayani da addua a bisa hakan dake faruwa damu ko yaushe. Hakkuri hakkuri fa kace sai ya kashe ni da ido yana jiran jin abinda zan furta nace hakkuri akan may kuma bayan haka dama kake so kuma an kawo ni gidan naka kana yadda kaga dama dani. Ajiyan zuciya ya sauke do bai tsamani amsar da zan bashi ba ke nan sai yaji ina maganan shirmay kuma. Nan ma bai barni ba sai da ya hade goshin shi da nawa yana fadin yau zanyi tafiya zuwa waje nima tafiyan yazo min unexpected ne ban kwana da zancen tafiyan ba na tashi dashi. Ya sake ni yana fadin bansan yaya zamuyi da zuwa school din ki ba sai dai zanwa musa driver magana ya dinga kaiki ua dauko ki idan kin gama. Don Allah ki natsu Deedar ki kara kama min kanki duk da nasan kina iya kokarin ki but sai dai in ce ki kara don kada wani abu ya samay ki. Kaima kasan rawan kai ba aikina bane mursmushi yayi yace na san baki da matsala ga hakan saidai yanayin zaman gidan nan dake da wa yan nan mutanen nake ji mawa. Ka bari in koma hostel da zama har lokacin da zaku daidaita da matar kanace mai kai yana girgiza kai yake fadin haka wai kina haukane ke da wanan hostel din yanzu ai sai dai ziyara kawai. Ina fa da gidajen da zan iya kai ki ki zauna a cikin garin nan ban kaiki can ba sai wani hostel gidan kowa da kowa ko da yake naga maza basu shiga amma dai ai wurin ba safe. Ya juya ya nufi gadona ya dan kai kishingide yana fadin maryam zan wa magana tazo ku zauna da ita idan na dawo kuma sai ki sa a kawo maki wata wace zaku zauna a tare tana debe maki kyawa don gudun hakan don ni mutum ne mai yawan tafiye tafiye a rayuwa na. Wardrobe dina na bude na fito da wani buje da riga na atamfa tare da hijjab don suna fitar min da shape dina idan na saka su da gyale. Kallon kayan yayi sai ya tabe baki yana fadin sorry fa nikan manta da zancen hado lefen ki da hajiya mu ta tuna min . Dama ka bar abinka don ni banda bukatan su yace saboda may ko sai kin haihu zan hado maki gaba daya. Wani kallo na watsa mai idon shi na akaina nayi saurin kawar da idanuwa na shima shiru yayi yana tunanen da ban san may yakewa ba. Bandaki na shiga na shirya ganin ba zai fita min a dakin ba ina shiri ina tunane a raina har na gama na fito yana a yadda na barshi a wurin. Kallo na yayi tare da mikewa yana fadin idan kin gama muje in sauke ki zanga maryam in mata magana daga can. Na maryam mai sauki ne ai don ko ni nayi mata magana zata zo sai dai wa yan nan kardawan da zaka barni da sune abin dubawa don mazan ma tsoro shigan su ke bani. Dariya yayi yana mikewa tare da fadin ba mutane bane kamarki su da zasu baki tsoro ai baki da matsala da mazan sai matan da ke cikin gida tare da ke. Ko matan banda matsala dasu don ba a kaina suke zaune ba ba kuma ruwa na dasu don ba zaman su nake a gidan ba. Tare muka fito dashi na kulle wurin nawa yana gaba ina bayan shi muka fice a gidan lokacin babu kowa a falon suna cikin dakunan kwanan su. Tafiya yake kamar baiso har muka kai kusa da school din ya juyo yana fadin kira maryam kafin mu isa ta fito ta samay mu a waje. Banki ba na daga waya na kira maryam din tace gata nan fitowa tana hostel bata karaso ba tukun hostel din ya nufa muna isowa tana fitowa. Da fara,a afuskanta ta tare mu tana fadin Mr & Mrs AA sannun ku da zuwa yau yallabai da kanshi ya jawo motar wani abu sai amarya wallahi. Waye amaryan nace mata ina hararan ta tare da kokarin saukowa a motar yace zauna itama shiga zatayi in sauke ku baya ya bude mata ta shiga ya ta da motar. Ya dan hau titin da zai sada mu da cikin makaranta yake fadin maryam an tashi lafiya tace sorry ganin ku haka wallahi ya rudani sai nake ganin abin kamar a falki wallahi. Nace mafalki kike koma ki kwanta kan shi ya girgiza tare da murmusawa yace ke kowa baki bari ba ashe ? Maryam tace ai kana fama wallahi da wanan mai kama da goyon kakan bakin nan ba komai sai bakar magana a cikin sa. Yace maryam ina yi yaya na iya ga abinda nake so nace gulma ke nan wani abinda kake so sallon yaudara dai naka maryam kin ga ba wanan ba yace. Alfarama nazo nema a gurin ki da fatan zaki min shi tace Allah yasa wanda zan iyane insha Allahu zan maka yallabai. Ni mamakin yawan girman da maryam ke bashi nakeyi don ni har yanzu haukana bai barni na san ko shi waye ba alakarmu dashi kawai nake duba. Tafiya zanyi yau nake son ki dan zauna min da madam na kwana biyu a gidan dafatan ban takura maki ba ga hakan. Lah don wanan ai babu komai wallahi zan zauna da ita har zuwa lokacin da zaka dawo kada kaji komai yallabai tace. Nace ai kyazo ki hadu da buzayen gidan shi tun a kofa zasu tare ki da halin shi tace ba komai tunda basu maki komai ba nima ba zasuyi min ba nasani. Haushi ta bani don naso tace bata samun zuwa ya yarda in zauna dakina na hostel har zuwa lokacin da zai dawo daga tafiyan shi. Godiya yai mata tare da rokon ta kada mu shiga harkan kowa a gidan matukar ba sun takale mu bane ya kare da cewa zanso kuyi hakkuri da duk abinda zasu yi maku don zasuyi da gayya ganin ban kasan. Tace insha Allahu zamu kiyayye kada ya damu komai ba zai faru ba bayan mun tsaya ya dakatar da ita tare da debo kudi ya bata tafita tana mai godiya. Wasu ya dibo ya miko min kai na kada mai tare da fadin ka barshi cikin basarwa nace ina da kudi a hannu na yace nasani ai baki zama dani ki zauna ba kudi a hannun ki ki rike wanan din ko wani abu ka taso bayana sai ki lalura dashi. Nagode nace ina saka kudin a cikin jakka ta na zuge zif din na rufe ina kokarin fita a motar ba tare da nayi magana ba. Zan fita ya riko ni yana fadin haka zakiyi sallama da maigida idan zaiyi tafiya Allah ya kai lafiya nace ina kokarin fita daga motar naji ya sake rikoni ta baya na sake juyowa . Saida ya lumshe idanuwan shi yace min I gone miss you deedar give me a hug please jikina na ne naji yayi sanyi nace cikin daurewa sai kace ba zaka dawo ba kana wani kashe min ido sallon yaudara kuma. Murmushi ya danyi cikin ciki yace cikin daurewan fuska please bazaki min ba ya wani marairaice fuska na turo baki tare da fadin ni wanan abin ya isheni gaskiya. Tare da juyowa gare shi na rungumay shi din dayake so a hakali rikene yayi shima yana murmushi a bayan fuskana ya kara rungumay ni na dan wani lokaci ya dan buga min baya tare da fadin take care yana sake ni. Jikina ne yayi sanyi na fice daga motar ina jin wani irin ba dadi a raina banko juyo ba najiya ta da motar tare da yi min horn ya bar gurin. Muna shiga school raina nake jin yana min ba dadi har zuwa lokacin da muka fito daga lectures kamar yadda yace lamban drivern ya turo min idan na gama in kirashi yazo ya dauke mu. Hostel muka shiga maryam ta dauki abinda zata dauka ranan na bayar da kayan amfanina ga wa yanda mukai zaman arziki dasu a hostel din sai godiya suke min drivern na kira ina fada mai mun gama. Ba a dauki lokaci ba sai gashi ya kirani yana fadin yana bakin hostel din yana jirana muka fito tare da maryam muka shiga ya wuce damu zuwa gida. Yamma yayi koda muka iso gidan mun samu gida a cike ashe su madam ne suka zo ziyaran ta muna shigowa naji sunyi tsit kamar ba mutanen da mukaji hayaniyar su bane da zamu shigo. Bamuyi masu sallama ba kai tsaye part dina muka nufa ina dauke da jakkar maryam a hannu na ita kuma tana dauke da ledojin da muka sawo kayan makulashe a cikin sa. Mun shiga mun huta ina ciki ina cire kayan da ke jikina Samiha, ta shigo tana fadin wai matar gidan tace tana kirana. Kaina na nuna tare da tambayan ni kuwa tace eh ke tace in kira mata koba kece amaryam maigidan nan ba ta juya ta fita har ta kai kofa na ce mata ki koma ki tambayo ta kila bakiji da kyau bane. Ta fita ta bar mu ina mamakin kiran da take min yau din maryam na fadin kije kila wani abin ne ya taso na gida zata fada maki. Nace maryam baki san wannan matar ba inda kike zato daban yanzu bai wuce wani sherin zatai min ba kila amma bari muji har yar sakon ta dawo. Samiha ce ta dawo dakin tana fadin tace wai bata sanki bane ke take nufi nace Allah ko na dauka ai bata san kalana ba ma kice da ita ina zowa idan na rarage. Banje ba sai da nayi wanka nasa wani bubu redmaid ne haka yazo da dan kwalin shi na bare chewing gun na saka a bakina na nufi falon gidan inda suke zaune ina tauna chewinggun din. Ban masu sallama ba ko wanan karon duk da chewing gun din dake bakina addua bai katse min ba a bakin dana tun kare su don yawan jin faduwan gaban da nake ji indan mun hade da ita. Na karaso na zo har tsakiyan su na tsaya ina fadin gani ance kina nema na gaba dayan su ido suka zuba min suna kallona. May kike takama dashine a gidan nan da zaki shigo min gida dake da kawar ki babu sallama kina ganin abokan arzikina ba zaki iya gaida su ba kizo ki wuce mutane kina takama. Sai da na tauna chewing gun yabada kara kasss nace oh ashe abokan arzikin ki ne nan bako sani ba ke da haka ya shafa badai kin gaida su ba. Na kalle su na ya tsune fuska tare da fadin abokan arzikin ki iyayyenane ko iyayyen mijina da za,a ce dole sai an gaida su. Gida kuma dana shigo ke idon ki ke ma gizo haka don gidan miji ba gidan uban kowa bane gidan kazo nazo ne bai da mata tabbata ga kowan mu nan. Ke karamar yar iska karya kike wallahi baki iya fitsara ba koyo kike yi ke wacece da zaki zo ina fadi kina fadi har ki tsaya tsakiyan mu kina bani amsa a cikin gatse tana magana cikin hausanta dake da surkin harshe. Madam ce ta katseta da fadin tun farko da kun bi shawarana da baku kirata ba wallahi don wanan idon ta a tsaye yake tun farko na fada maku. Irin wa yan nan ba ta wanan hanyar ake fito maku ba nace who d hell are da zaku kirani kuna son raina min wayo na juye harshe cikin turanci na shiga surfa masu zagi har da hauka. Tasowa Nafisa tayi wai zata mare ni madam ne ta riketa ta bayan ta tana fadin Nafisa mu ba munzo don tashin hankali bane farin ciki ne ya kawo mu gidan ku. Na samun cikin da kika yi na juya tare da tafa hannuna nace Allah sakone to za a fada masu ashe kin samu karuwa ne Allah dai ya raba lafiya. Ciki ai yanzun ba abin kuri bane adaiji da wahalan shi tukun nan baku fada ma kowa ba don ni ko a jikina wallahi inkin iyama ki haihu duk sati don ko a jikin khadi. Na juyo nabar wurin ina jin suna hayaniya ban juya gare su ba na shige abina madam ta juya tace wanan yar takai fitsarara wallahi jifa zancen cikin nan ko a jiki ta ma. Wata tace karya ne wallahi ba zamu gane hakan ba sai idan Samad ya dawo munga bata dauki wani mataki ba sanan zamu san bai damay ta ba. Ina shiga daki na zube a saman kujeran falon ina maida numfashi maryam ta kalleni tace ban taba jin kalar kishin gidan ku nan ba khadi kishi haka har da su hauka. Nace ashe kina jin mu tace ba dole in bi bayan ki ba kada su maki na jaki ke kadai wai har da ciki har sai anyi wa mutum gatsen shi kuma. Nace sunyi ma banza wallahi inya iya ya bata ciki duk sati ko a jikin dije don haka yake gareni ban damu da shirmay su ba ni daga shi har ita shi kuma munafukin zai dawo ai ya samay ni. Idan ya dawo may zaki ce dashi ai yadda kika nuna masu nan koshi haka zaki nuna mashi idan kin bi ta nawa shida kanshi zai ji kunyar haka wallahi. Don dama sunyi hakane don hadin hasumi a tsakanin ki dashi tunda sun san sherin da suka kulla a kan . Sun hana wani mu,amula a tsakanin ku dashi ita ta samu ciki a hakan zasu nuna maki ke ba mace bane a gurin shi wallahi sai yanzu nake ganin gaskiyar Fati uwargidan shi khadija. Ina zata iya da wanan abin haka kishi harda mutanen waje bayan yan uwanta dake gidan ana gwabzawa dasu. Wayana dake ringing ne ya dauke min hankali ina duban mai kirana a wanan lokacin slnomban South Africa na gani da mamaki na daga wayan da sallama a baki na muryan shi naji yana fadin my Deedar mun iso yanzu muna south africa sai lokacin na gane baya kasan ma gaba daya don ni wautana bai barni na tambaye shi inda zai tafi ba. Maryam ne ta kalleni tana min signal da ido nace kun sauka lafiya yaya hanya naga tayi ajiyan zuciya daga inda take zaune. Ya amsa min da lafiya ya muka barku I hope ba matsalan komai dai nace lafiya muke ya tambayi maryam nace gata zaune tana assingment . Ba wani hira bane sai dai fada min wahalan hanyan da suka sha wai jirgin su ya masu dely din lokacin da zasu sauka. Bayan mun gama wayan ne maryam ta kalle ni tace ki tafi haka dashi har ya dawo khadi kada ki yarda korafi na fitowa a gurin ki sai abinda idon shi ya ganan mashi ko yaji. Saukin abin ma kina da baki da baki magana ne abin zai maki yawa ya cuta maki kuma ba ganewa mutane zasuyi ba. Waike maryam duk a ina kika san wanan rayuwar hakane kamar wata matar aure tace wallahi zama da yan uwa yasani sanin haka. Na fada maki ai nice auta a gidan mu koda yake kin ki zuwa ma balle ki san gidan mu gidan mu gidan yawa ne khadi so nasan irin wanan rayuwan ne ga zamantakewa a cikin yanuwa kowa da tashi kalar kaddaran dakan zo mashi. Kuma nima da kike gani fa na taba aure sai dai zaman baiyi ba don ko tarewa kishiyar bata bari nayi gidan mijin ba aka watse. Wani kallo nayi mata tare da tambayan kin taba aure fa kikace maryam shine duk zamana dake baki taba fada min wanan zancen ba. Dariya tayi tace ba maganar da zaka fada bane tunda ba dadin ji zancen ke dashi ba wataran zan zauna in baki labari kada ki damu. Washegari da muka tashi da safe bayan mun shirya ne muka zauna mu karya lokacin na kira malam musa driver ina sanar mashi da mun shirya. Sai dai wayan shi bai shiga a wanan lokacin ana fada min wai not reacherble nace babban magana wayan mutumin nan baya shiga fa maryam. Gamu kuma da test ranan da safe tace mu gama sai mu fita waje mu gani ko yana nan yana jiran mun kin san kila matsalar services ne. Bayan mun gama mun fito motar shi baya waje sai motocin maigidan na alfarma da suke rufe a cikin innuwa. Kallon juna mukayi da maryam tace mu koma tunda bayanan nace akan may zamu koma wa yasan lokacin da zai dawo gidan kawai muje titi mu shiga mota takarasa damu. Don ba zan yarda in rasa test dina yau ba hayan fita get din gidan muka nufa kamar ance in juyo baya Yanyala ne da Samiha a tsaye suna kallon mu suna yare suna dariya ban wa maryam magana ba har muka samu mota muka tafi. Shidda daidai na kira malam musa ga waya na ringin sai dai bai daga ba raina ya baci nace ma maryam mu tafi titi mu samu mota. Mun dawo gidan suna falo kamar kullun ranan har da Nafisan bata fita ba suna ganin mu suka kwashe da dariya suna yare can cikin hausa naji tana fadin. Matar permsec ne yau a motar haya haka shine daidai da yar tallakawa dama an ga motoci a gida an biyo banza kamar in koma in bata amsa maryam tace ba banza a jiyar ta dama nasan da manufa haka ya faru bandai maki magana bane. Nace na sani tun ganin su da nayi da safe suna muna dariya tace ashe kin gansu kema abin ya kona min rai sai dai na kyale tun wanan ranan ban sake gigin kiran malam musa ba ya zo ya dauke mu ba. Kullun da safe wani mai Napep zai zo ya dauke mu ya kuma je ya dauko mu don muna bashi kudi masu yawa. Mun dawo muna daki da maryam da dare nace da ita ina zuwa kitchen na shiga na dauko yuka da gishiri na fice gidan. Allah ya taimake ni hankalin mazan dake waje yana kan butar shayin da suka dora a wuta hankalin su ya dauke dashi ga kidan yaren su sun saka suna bi suna rayawa. Da karfin halina na suce tayon motacin dake aiki a gidan tare da zuba gishiri yadda ba zasu moru ba sai an zuyarci kani kawa. Na juyo cikin duhun na koma part dina ba tare da na bari wani ya ganni ba da safe ko da muka fito suna gurin tsaye cirko cirko cikin tashin hankali bamu bi ta kansu ba ko kallon abin bamuyi ba muka fice gidan. Sai da muka dauki hanya nace suma suji inda dadi abinda mukaji maryam ta juyo tace may ne wai nake fada mata abinda nayi baki ta rike tace khadi kin kai can ban sani ba. Har na wuce nan ma itama ta iya sheri balle wani kafin mu dawo maigidan ya kirani hankali a tashe yana tambayana ashe abinda ya faru ke nan ? Nace may akayi yace wai an shigo gidan jiya da dare an taba motoci nace banda labari don ni yanzun haka ina school. Yace da wani mota kika je nace wanda na saba zuwa dashi dashi na tafi yana fadin bai gane ba na kama fadin hello hello ban jin ka fa na kashe wayan. Bayan mun fito ne muka dan ratse sayayya a wani shago muna gab da gamawa ne naji ance wanan ba matar oga AA bace ban tsaya ba sai maryam ne ta ba mashi amsa ashe tare yake da matar shi . Maryam ne ta tsayar dani tana fada min tare da nuna matar a gareni yace aishi yaron AA ne ya taba ganin tare shiyasa ya shedani. Mun gaisa dasu zai biya muna kudi nace ya barshi mun gode muna da kudi mun fito zamu shiga Napep ne suma sun fito ya gan mu yana mamakin shigar mu napep ya hana dole shi da matar shi suka kawo mu gida. Muna zaune a dakin mun barbaje kayan da muka sayo muna kallo aka turo kofan dakin hankalin mune yakai ga mai shigowa dakin. Kayan dake kasa a barbaje ta kare ma kallo yayin da muma ita din muke kallo muji may ya kawo ta dakin a wanan lokaci. Tace ban san ke muguwa bace muke zaune dake sai yau abu ya samay mu a gidan ki nuna muna halin ko in kula. Nace au da ke sai yau kika san ni muguwa ce komai ai halin ki ne nake koyo ba wani ba don kin san ance dan koyo yafi mai hali iyawa. Sai dai har kullun ina garga din ki da shigo min shiya haka gaba gadi don haka kowa ya tsaya iyakan shi. Ke uwatace ko may da kullun kike min kallon wace zaki ba commad a gida ke abin ya shafa ni bai shefe ni ba kin ji koma may nene tace dama nasan ba son shi kike tsakani da Allah ba anga dukiya an shigo aci banza. Nace kamar yadda kika biyo don jin dadin wuri kika kwaso yan garin ku kaf azo a sauke yunwa a nan ko. Dani dake sai ki tunanen waya biyo dukiya yanzu ni da nazo ni kadai ko wanda ya kwaso yan uwan shi ya cika a gidan miji babu kunya ba tsoron Allah kin kakace gida da komai na gidan. Bakin cikin ki yanzu shine kin samu wace zaku raba daidai da ita ke kuma baki son ki bude ido kiga haka din a gidan. Sai dai kare ya mutu da haushin kura don na shigo ke nan ba fita gareni wanan kuma damuwan kine can . Lalai wanan yar iskan ana zuwa dake haka dama nake son ganin karamin kwazon ki a fiki wanda bai kai ko cikon cukali ba a wurina zaki gane kin shiga hurumin da ba naki ba kwanan nan ta juya ta fice daga dakin . Maryam da ke kallon ta tun shigowa tace wai khadi haka kuke kullun da wanan matar ashe da gaskiya ne da ake fadin bakin mitar tsiya gare su kamar mayu. Allah ya taimake ki kina da baki da wanan ai ko sati ba zakiyi a gidan nan sai kin gudu don wanan kishin harda na hauka a cikin sa. Nace na fahince ta so take ta juyani kamar wata yar cikin ta bata san ta makaro ba duk sirin iskancin ta yana a tafin hannuna. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Shida da wani abu ya shigo part din nawa a lokacin ina kitchen ina karasa miyan da na dora a kan gas wanda zai isheni ci na kwana biyu. Banji shigowan shi kitchen din ba sai ji nayi mutum ya rugumoni ta baya na tare da dora kan shi saman bayana yana fadin may malaman tawa take girka muna ne? Zabura nayi a firgice ina batun sake cibin miyan dake hannuna yace relax baby nine wa kike tunanen zai shigo makinan in ba niba. Nace na sani tunda gidan cike yake da garadan kati nagani ko wani ne yai min shige tunda sun ganni bare a cikin su. Da naci uban maishi kuwa duk wanda yayi gigin shigo min part din amaryana bada izinina ba basai ka masu haka ba tunda gidan baida security na gani ni dai zan daukarwa kaina mataki tunda kai baka saba daukar masu ba. Juyoni yayi muna fuskan tar juna dani dashi kawar da idona nayi daga gare shi sai lokacin na gane. Ya sauya kayan jikin shi zuwa jallabiya fara kal a jikin shi hakan yasa na gane cewa ba shigowan shi gidan ke nan ba a lokacin. Rikoni naji naji ya kara yi a jikin shi kallon sakeni nayi mashi maimakon ya sake ni din sai ma ya kara rikoni a jikin shi yana shakan kamshin jikina a hankali. Wani turare kike amfani dashi ne haka mai kamshi kamar banji mai yake fadi ba nace malam sake ni don Allah. Idan na sake ki ai dana shiga uku nace don ka sakeni zaka shiga uku yace tun ban furta maki kalman da kike son in furta maki ba zan sakeki. Kai kasan wanan nace dashi ina kokarin kwace jikina daga rikon da yai min din kamar mai rada yake magana. Idan mun idar da sallah zamu zauna daku a falo don haka ki zauna a cikin shiri zan kiraki naji nace dashi kawai ya sakeni yana gyara hannun rigan dake jikin shi. Ya juya nace dashi dama sai kuma nai shiru yajuyo tare da takowa zuwa inda nake yana fadin dama may sunkuyar da kaina nayi kasa tare da fadin. Idan na gama abinci a ina zan kaima naka yayi murmushi tare da kallona a cikin mamaki abinda bai samu a gidan shi yau ya samu ana mai tayin abinci dare da zaici. Haka gaisuwan da nayi mai yaji shi wani iri don bai saba aimashi ina kwana ko wuni ba idan ya tashi. Yace kin san ban saba cin abinci a gidana ba sai dai zaki iya kai min a dining din dake sama anan zan samu inci hankali kwance don wanan dining din na kasa ya zama na kowa yanzu. Nace ko in aje maka anan idan ka shigo sai kaci yace hakan ma yana da kyau nagode ya fada daga haka bai tsaya ba ya fita. Ajiyan zuciya na sauke bayan fitar shi daga part din nawa ina mamaki mutum da gidan shi baida daman ya wala yadda yake so komai a make zaiyi shi don wani akida nasu na daban. Gaskiya akwai aiki ja a gabana yadda zamu zauna da mutanen nan su da yawa ni kadai a cikin su ya zama dole gare ni in jajirce sosai in kwatar wa kaina inci garesu. Wanka nayi na saka atamfan zani da riga a jikina sai da na zauna na gyara fuskana a jikin mirrow nakawo dan kwalina na kafa daurin ture kaga tsiya nayi sai daurin yai min kyau sosai ya kara fito dani. Ga gashina dsa yasha kitso a baya daure da ribon ya fito fili yana sheki karan wayana naji daga inda nake zaune na mike zuwa inda wayan ke jikin caji. Sunan da nayi seving din nomban shi dashi nagani a wayan sai da ya kusa katsewa na daga wayan muryan shi ne yana fadami in fito ni suke jira tundazun. Nace naji kawai na kashe wayan turare kusan kala biyar na feshe jikina dashi kafin in fita nakawo takalma masu hill na saka a kafana kamar mai shirin fita unguwa sai kara suke sakewa na tada hankali . Tun fitowa na naga kallon da matan buzaye dake zaune a falon gidan sun tasa wani abu ga buta sama suna rike da kofuna a hannun su, suna min wani kallo kamar sun ga abin mamaki a tare dani. Babu wace taimin magana daga cikin su nima haka na nuna ban san da zaman su a falon ba nabi kwatancen da yai min na haye sama dauke da basket din abinci a hannu na. Da sallama na shiga falon da baikai wancan dake kasa girma ba zaune na hango su saman three seater kamar su manne ma juna dashi da ita. Na karaso da sallama mana ta dago ta dubeni daga samana har kasana ta kawar da kanta gefe daga kallona dining din na nufa na fara jera abinci a sama dining ne na glass mai kujera shida. Sabanin wanda nake gani babba a falon kasa wanda kujerun shi zai kai takwas ko fiye da hakan gaba sai faduwa yakeyi amma na dake don in nuna mata ban damu dasu ba. Sai da nagama na juyo inda suke zaune nace ga abinci nan na shirya maka yayi murmushi tare da fadin sannu da kokari na gode. Wanan godiyan da yake min tsakani jiya da yau yasa na kasa fahintar halin ko zan iya kiran shi da mutum mai saukin kai ko akasin hakan. Ya dubi inda Nafisa take a gefen shi zaune yace bissimilah mu fara cin abinci ko ina ganin zai fi sauki kafin muje ga abinda ya tara mu a nan. Kallon ta na danyi da gefen ido na dauka zatace wani abu sai naga ta rigashi mikewa tsaye ba tare da tayi magana ba ta nufi gurin table din. Tana isa ta fara bude kulolin abincin tana tabe baki har tagama ta jawo kujera takai zaune shima ya taso ya ja daya ya zauna a kusa da ita. Sai da na bari sun kai zaune na karaso gurin na ja wanda ke dayan gefen shi na zauna muka sashi a tsakiya. Kallona tayi kamar zatai magana sai kuma naga tayi shiru ta fara zuba abincin da plate idin dake gaban ta. Ganin haka sai na mike na bude kulan na jawo plate din gaban shi na fara serving din shi na sai da na kusan rabin plate din da abincin nace akara ko ya isa hakana ? Yace is ok wanan yayi min sannan na zuba kadan a plate don kada suce banci ba na koma na zauna nayi bissimilah na fara ci a hankali. Saici yake ya na wani lumshe idanuwan shi ban sani ba ko haka yaba ta haushi sai ta turo plate din ta da karfi tana jan tsuki ya dubeta yace ya akayi ne bazaki ci abincin bane ? Ta wani yamutsa fuska tana fadin dama tun farko kamshin abincin bai mun ba kuma dandanon shi babu dadi. Yakai loma a bakin shi zaiyi magana nariga shi fadin saukin abin wanda na girka kan shi yayi mashi dandano don naga yana kai hannu baka hannu akushi. Yayi mashi na dole ko kamar yadda akai mashi dole a kanki ya kwaso yakawo min ke cikin gidana ke naga zubin ki na marasa kunya ne fa. Murmushi nayi sai da nakai lomar da na diba a bakina na kora da ruwa nace saukin abin dai shine kin gani da idon ki ai kowa akaiwa dole a cikin mu. Kin taba ganin inda aikawa gwabjejen kwato kamar mijin mu auren dole kuma namijin ya kalli macen dole nan take. Enough don Allah ya isa haka bashi na dauko nan kuyi min ba abinci dai bai maki ba bakici shikenan ya isa haka ban son jin hayaniyar nan kuma. Shiru nayi ban kara magana ba itako tana saman bakin ta sai abinda ta manta gurin fadin bakar magana don in nuna mata nazo da shirin biyayya ga iyayyena da wanda yayi sanadin zuwa na gidan ban sake kulata ba har muka kare na tattara kayan a cikin basket tana kallona kamar ta shake ni. Bayan ya gama ya mike ya dawo saman kujera ya zauna ta taso ta dawo inda yake da sauri ta zaina sai da na gama hada kayan na dawo saman three seater din da suke zaune yana ganin haka ya gyara min wuri nima na zauna. Nafisa irin matan nan ne da basu iya danne kishinsu sai ta fitar a fili angane nufin ta a take na fara gane takon ta. Yayi gyaran murya ya soma magana Nafisa gadai kawar ki nan na kawo maki gidan nan sai kiyi hakkuri da ita ku zauna lafiya. Ban son in, , , tare shi tayi da fadin kanwa ta ko kishiya ta kace ga kishiya ta ka kawo yan uwan ka sun auro maka mata da zata zo ta ci min mutunci muna zaune kalau. Wanda su kuma shine basu son su gani a gare mu ni kuma ba wanan ba ko goman ta zaka dauko bazata taba girgizani ba indai Nafisa ce. Murmushi yayi a cikin rashi yace mudai samu mu iya da wanan din mai gira saman ido tukun. Ya juya gefe na yace Khadija kinga yar uwar zaman ki Nafisa ina fatan zakiyi mata biyayya a matsayin ta na wace kika sama gaba dake a gidan nan. Sanan akwai masu aiki duk wanda kika gani a gidan nan da sunan aiki yake zaune nan tare damu babu abinda zakiyi hatta gyaran daki da wanki bayin ki duk sune zasuyi maki daga cikin su akwai masu girki sai dai duk abin da kike so kya iya sanar dasu su girka maki. Zan sa a saka maki waya da duk kike bukatan wani zaki iya kiran masu aiki suzo saboda bukatan ki. Ko in kinyi baki haka kodai wata matsala aikin ki daya ne a gidan nan shine gyara min dakina watau shifidana don ban yarda wani dan aiki ya shiga min daki saboda sirina. Zaici gaba da magana tace Samad wai kana nufin yan uwan nawa kake kira da yan aikin da zasuyiwa wanan aiki ko may ? Yace yan uwanki ba a matsayin mai,aikatan gidana kika dauko su nan ba ina biyan su duk wata kuma da albashi mai tsoka ban cutata masu ba ko kadan. Ta sake duban shi da mamaki kamar zatayi magana ya rigata fadin ko kina nufin duk wanan taron haka zasu zauna damu a gidan nan a yadda suke so. Tace to wallahi baku isa ba daga kai har ita baku kai min can ba babu wacce zatayi ma wanan aiki a gidan nan aure tazo yi tayi aikin ta da kanta zamana suke a gidan nan kuma ni kadai zasuyiwa aiki idan ina so. Murmushi ya yi kadan yace ashe ko idan har ba zasuyi wa matana da na dauko aiki ba sai tayi da kanta zasu ko bar min gida kada kice ban fada maki ba. Yaci gaba da magana yace sai kuma zancen kwana idan khadija ta gama satin ta na addini da aka tanada namiji yayi a dakin matar shi ina son jin yadda zaku raba kwana a tsakanin ku, ? Don in sani saboda shiga hakkin wani ya kare da cewa ina sauraren ku shiru dakin yayi don ita wani gurin take kallo da alama ma hankalin ta bai a girin lokacin ta lula duniyan tunane. Ya ce uhumm ku nake saurare fa dare nayi ina son in je in kwanta ne don magaji da yawa hidimar bukin nan bai fita jikina ba. Sai lokacin ta kallo shi tace kana nufin har kwana bakwai zakayi a gurin ta ko mai ? Yace haka addine ya kidanya muna tunda ba bazawara bace ita mikewa tayi tsaye tace baka isa ba wallahi ta nuna mu ds yatsa tace dukkan ku kunyi min kadan. Wanan ai son danne hakkin wanine ya girgiza kai yace bani fatan in danne ma kowace daga cikin ku hakkin ta don kowa son shi nake na kawo shi nan mu zauna tare dani. Ganin zancen yana ta nisa a tsakanin su yasa nayi magana nace idan zancen kwanane a barshi a kwana bibiyu ina ga hakan zaifi sauki. Ta juyo da sauri tace ke wacece da zaki tsara muna yadda zamuyi kwana a gidan nan na bude baki zanyi magana ya daga min hannu naja baki na nayi shiru. Yace idan na kwana biyu zakuyi ba kwana nawa kike son kuyi ba wani nauyin baki tace mashi daya. Yace dayan yayi maki hakana yana kallo na nace yadda kuka tsara duk dayane a gareni banda matsala ni agurin haka. Yace idan haka yayi maku kuna iya tafiya Allah ya kauda shedan a tsakanin mu nace amin sai dai banji ka fada muna wani magana daya dace ace mun san dashi ba. Da sauri suka kalloni a lokaci daya duk su biyun yace may ke nan na manta nace a cikin maganan ka ka manta ka fada muna lokacin da zaka dinga tafiya kaduna ziyaran uwar gidan ka uwar yayan ka sai nake gani ya kamata musan da wanan yanzu. Daga inda Nafisa take zaune ta watso min wani kallo shi kuma gogan murmushi yayi a ranshi yace kin fara baiyana min manufar su hajiya mama akan ki ke nan. A fili kuma cewa yayi hakan ma shawara ne mai kyau zan iya zuwa karshen kowani wata in duba su shike nan ko ya tambaya na gyada mai kai badon hakan yayi min ba yace Allah ya taimakemu ya bamu sa,a yana shirin mikewa. Ita ta rigashi mikewa batare da tayi magana ba ta nufi hanyar fita daga part din nashi rai a bace nima mikewa nayi don in bar gurin da tunane kalakala araina. Na sauko saman a hankali ban samu kowa a falon kasan ba lokacin da na fito na shige part dina na rufo kofana, . Abinda ya soma dagawa Nafisa hankali shine zancen yan uwan ta da yayi sai kuma zancen Fati da taji a baki na yanzu nawa iskancin tana daukan shi wasa don har taga ta magance shi ko a wurin ta. Tun wanan lokacin da akai maganan ni ban ma gwada kiran kowa ba daga cikin su don ba yarda nayi dasu ba har cikin raina. Koda ya shigo dakin har na gama abinda nakeyi na kwanta a can cikin barci na naji shi a bayana kamar karamin yaro yana karkaduwa alaman baida lafiya. Zubur na mike tare da kunna wutan dakin ina binshi da kallo idanuwan shi suna a rufe nace baka da lafiya ne kai kawai ya gyada min alaman eh. Nace wani taimako zanmaka yanzu yace ki kara rufa min wani bargo don Allah mikewa nayi na sauka a saman gadon na jawo bargo cikin wardrobe dina na rufa mashi ina mashi sannu. Na koma gefe nakura mashi idanu kawai ina kallon yadda yake kaduwa a cikin bargon tare da tunanen wai yau nice a gado daya tare da AA a matsayin miji da mata dadai naga tunane ba zai fitar dani ba na fara yi mashi addua daga inda nake zaune . Ayyatulqursiyu na fara karanto mashi sanan falaki da nasi da kulhuwallahu na tofa mai tare da gyara mashi rufa. Da kyat barci barawo ya dauke ni na koma barcin alam din da nayi setting ne ya tayar damu daga barcin. Ina tashi nagashi zaune kamar bashi bane ke kaduwan sanyi da dare na kalle shi ina kokarin tashi nace ya jikin da sauki yace yana sauka saman gadon ya shiga bandakin. Sai da yafito na shiga na kewaya ruwan zafi na watsa ma jikina na dauro alwala nafito na samu ya na sallah . Ban bi ta kanshi ba na fara gabatar da nawa sallah sai da muka idar ya tashi ya koma saman gadon ya kwanta ban koma saman gado ba anan inda nayi sallah na dan kwanta bayan na gama azakar din da zanyi. Sai takwas ya falka lokacin har na hada mashi abin abin karyawa ina jiran shi ya tashi yana falkawa yakai kallon shi ga agogon dakin yana fadin khadija shine baki tayar dani ba don zuwa office. Nace gani nayi daren jiya bakai barci ba yasa na kyale ka kadan runtsa kafin yai wani magana nace dashi ina kwana ya jikin kuma ? Lafiya yace yana sauka saman gadon na sake cewa ga abin karyawan ka nan idan ka shirya nagode yace barin dan je in watsa ma jikina ruwa in shirya zan dawo yana fadin haka yafita daga dakin. Ni abinda ke ban mamaki a cikin kwanakin da yayi a dakin sai dare yayi a haka muke kwana dashi a wahalce ba sauki sai gari ya waye zai tashi kamar bashi ba sai dai ban kawo komai a raina ba na dauko yanayin ciwon ne yazo mashi a haka. Gashi a dadafe yakai sati daya a wurina don nagaji da gorin Nafisa da kawayen ta dake shigowa ganin amarya suzo su karanta min haukan su su wuce do ni na dauke shi haukane sukeyi. Abinda ke daga ma Nafisa hankali bai wuce kullun tana saka kunne taji fada a tsakanin mu da maigidan sai taga in gari ya waye shiru mun tashi kamar babu komai dake faru damu. Idan ta kira madam tana fada mata sai tace nafisa baki da hakkuri wallahi komai ba asannu ake binshi ba. Tace madam ni sai ina ganin kamar abin bai aiki yana kwana da itane a fake tace zan shigo gidan zan dan bugi cikin ta muji. A nawa bangare duk da babu wani abinda ya taba shiga tsakanina da AA kuma bai taba nuna min yana bukatan wani abu a gurina ba. Hakan bai taba damuna ba a raina don ban kawo wanan a tare dani ba yanzu abinda yafi damuna shine karatuna don shike cikin raina. Yadda naga yana nunawa hakan nima nake nunawa a gidan zai shigo da rana mu gaisa yadan min wasan zolayar daya saba ina mashi tsiwa inyi mai girki yaci yana min godiya. Tun zuwa gidan yaune karo na farko da nake son shiga dakin maigidan don in gyara mai kamar yadda ya umurta ai mashi don ban ke daya a hannu na. Wani super nawa ne da mijin ya Amina yai min last sallah a jikina wanda akai min dinkin buje da riga din yana min kyau sosai a jikina. Na dauko wani dan gyale na yafa tare da zura takalma a kafana nafito na rufe part dina do ban yarda koda wasa in bar part din a bude idan zan fito. Sai da na kwataci bai gida na nufi part din suna zaune falo duk suka bini da ido caaa na wuce ba tare da nayi masu magana ba kamar kulun. Dakin a hautsane yake sai da na tsaya na kare ma dakin kallo sannan na fara takawa zuwa ciki na rasa ta ina zan fara da dakin. A gadon na fara na yaye zanin gadon na kakabe gadon tare da share kasan dakin ina mamakin yadda yake rayuwa haka acin wanan dakin . Ban ga takaici ba sai da na shiga bayin nan naja nayi tsaye ina mamaki duk gayen shi a haka yake rayuwa a tauye. Kwal nayiwa ban dakin tare da wanke gajajerun wandunan shi da ya tara da singlet na bazasu a waje kasa don su bushe dawuri. Na dawo na gyara ko ina na dakin tare da saka room fresh din da nagani a aje nagama na nado mai inner din shi nakai cikin wardroveb na jera mai wanda bai bushe ba na baza a bandakin. Koda na dawo dakina na gaji don haka wuri na samu na kwanta don in huta sai barci mai nauyi ya dsukeni a gurin ban tashi ba sai uku da wani abu a gagauce na mike naje nayi alwala na dawo na tada sallah . Koda ya dawo ya shiga part din shi abin ya bashi mamaki yadda dakin ya canza a lokaci guda ga kamshi da kyali yana tashi a dakin. Har part dina ya shigo yana min godiyan canjin da yagani a dakin nashi ya samay ni a kwance falo ina karatu ina saye da wando da riga sun matse min jikina . Yayi min kallon tsab idon shi ya sauka saman kirjina ya dago ido ya mayar a fuskana da yasha kwalliya. Yace ce sannu da kokari na samu wuri na yau ya samu gyaran da ya dade bai samu ba sai yau a wurin ki. Bai gama magana ba sai ga Nafisa ta fado muna dakin tana huci tare da zare ido. May kazo yi dakin wanan ko ka manta da sauran lokacina har yanzu tunda magariba baiyi ba yace ke kada ki kuskura ki kara shigo mata shiya da sunan haukan kishin ki. Wanan wani irin shashanci ne zaki fado ma mutane daki babu ko sallama tace nice shashan yau samad yace idan ba shashamci ba yanzu may kikayi haka. Ya nuna mata kofan dakin da hannu yace ta fice tace ba inda zan tafi sai ka fito mun fita tare idan ba haka ba sai dai mukarasa lokaci mu anan. Daga inda nake zaune ina kallon su ina rike da littafina da nake da nake bita ciki nace saukin abindai yau yake naki anjima nawa har zuwa gobe iwar haka sai ki kama. Kin ga ke nan kin rage tunda har zaki iya sakar ma wata shi na wani dan lokaci koma in ce wasu dakike son haka may yasa bakije kin auri mijin ki ba. Kika zo kika auri mijin wata watan ma har da kari kuma kika samu ai irin wanan ki aurin mijin ki na kan ki ba mijin mamu duka ba. Zagi ta fara jefo min tana fadin sai taga bayana a gidan nan nan bada jimawa ba nace ta Allah bataki ba gani nan bari nan takalmin kaza. Ya fice ta bishi ta tasa shi gaba tana zagi dariya nayi nace kun fi kusa ku karata can tare na samay ku ai. Da dare na gama shirya komai a basket ina cikin wasu english wear na mata dogon rigane irin mai bin jikin nan ya fitar maka da sura sai dan gyalen da na dora a saman kaina nayi rolling din kaina dashi. Bayan na gama jera mai abincin ne na nufi daki in gani ko yana ciki muyi maganan daya kawo ni wurin shi. Kofan a bude take na tura tare da sallama na shiga zaune na hangoshi saman sofan din dakin ya tasa laptop din shi a gaba yana aiki a cikin sa. Ganin haka na juya zan koma naji yace yaya zaki koma kuma shigo mana ke da dakin mijin ki dazun fa naji kin ce ma Nafisa anjima ke dani. Wani kallo nayi mashi nace idan ka gama abinci yana jiran ka a falo yace sannu da kokari sai na dan tsaya jin ya kara dagowa ya dubeni. Ki zauna mana yace nace mmmh dama ba zama nazo yi ba nazone in tuna maka batun karatuna don yanzu sati ke nan da muka koma. Yace ina sane amma na dauka hutun aure kikeyi ai yanzu wani kallo na aika mashi yace naga kamar zaman aure yafi maki wanan karatun da kikeyi yanzu. Nace aini ba zaman aure nake yi ba don ban yi kama da masu aure ba a yanzu haka don Allah na fada ma monday nake son shiga. Wani kallo yayi min na mamakin jin abinda na fadi nace kana mamaki ne aure aure fa na dauka sai wanda yaji yagani shine aure ba irin wanan nawa da nake zaman biyayya ga iyayye ba. Murmushin karfin hali yayi sanan yace makaranta zaki koma idan kin gama hutun ki sai munje kaduna karshen satin nan mun gaida su idan mun dawo zanyi shawara in gani yaushe yakamata ki koma. Shiru nayi tare da dan tsayawa sai na juya zan fita yana rufe laptop din nashi yake fadin ina kuma zaki zan tashi inzo ki bani abinci kuma zaki tafi aina dauka kin zo kwanan da kuke ma fada ke nan. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Ranan monday na fito daga wanka na samay shi zaune a dakina bina yayi da kallo kunya ne ya kamani na yadda ya riskeni. Kamar zan koma bayin sai kuma na dake naje wurin wardrobe dina na bude na dauko zani na koma bayi na daura tare da yafo tawul dina saman jikina. Yana zaune ya kallon abinda nakeyi zuwa nayi na zauna a saman dan stoll din mirrow ina sauraren shi. Murmushin nan nashi ya sake mai kama da manufa idan yayi kallon shi nima nakeyi ba tare da nayi magana ba. Yace dank kin gama boye boyen naki muyi maganan da ya kawo ni sai dana dan ja lokaci nace kai nake sauren ai. Yace to ki shirya idan zan fita sai mu sauke ki a school din idan an tashi kuma ki min waya zan zo in dauke ki. Nace naji kawai ya mike kamar zai fita a dakin sai kuma ya juyo zuwa gareni baya na fara ja har na hade da jikin mirrow . Anan ya samay ya matse yana fadin muga wurin kudu yanzu kuma wai may kike dauka nane da kike wanan gudun kina boye min kan ki. Cikin karfin hali nace dashi may zan ma gudu gare ka tunda kai ba dodo bane kawai dai ina kare mutuncina ne. Ido ya kura min sai na kasa jimirin kallon sa ido cikin ido na kawar da kaina daga kallon da yake min din. Ji nayi yana kokarin kama bakina ya hada da nashi nayi saurin zille mashi amma hakan bai yuyuba don ya riga da ya kamani ko ina kokarin zille mashi nan muka fara kokawa dashi har ya samu ya matse ni yadda yake so don karfin mu ba daya ba dashi. Jin abinda yake so ya tabbatar yayi ya dako yana kallon fuskana tare da fadin wa kikewa karyan fashin sallah ? Nace kamar ya karya dama nina fada ma ina fashin sallah ko gane ganen ka ya gano maka ni wallahi irin wanan abinda kake min ban son shi don kaga, , , , Jinayi ya kara hada bakin shi da nawa a ciki na karasa fadin magana na don bakin shi da ya hade da nawa a lokacin. Don kanshi ya gaji ya sake ni tawul din dake jikina nasa ina goge bakina dashi ya wani waro idanuwa waje yana kallona da mamaki na abinda nakeyi din. Kai ya girgiza min ya fita daga dakin ba tare da yayi magana ba shirin na fara yi don kada su tsaya jirana na gama na dawo falo na zauna ko karyawa banyi ba saboda zumudi. Shi ya shigo a cikin shirin fita office yana saye da suit baka da wandon su sai farar riga daga cikin suit din daya fito fili da necktie. Sai kamshi yake zubawa kallo daya nayi mashi tare da kawar da gaina gefe daya saida ya karewa shiga na kallo don babu ta inda zai kushe min shigar tawa don shiga na kamilanci da nayi ga mayafin dana yafa har saman kaina na dora shi. Idan kin shirya mu tafi naji muryan shi yana fadin haka da sauri na mike don tafiyan tare da dauko handa bag dina nabi bayan shi. Suna zaune a falo sai hayaniya sukeyi karan takalmana ne ya dawo da hankalin su daga part dina suka kura ma wurin ido. Yana gaba ina bin shi a baya har muka iso daidai inda zamu dan gwauta su muryan nafisace ke fadin yaya kuma haka naga ka fito da ita zaku fita tare . Wurin da suke na dan kalla tare da wurga masu harara naci gaba da tafiyana hankali kwance shima din naga bai tsaya bata amsa ba don haka ta mike ta biyo bayan mu. Driver yana ganin fitowan mu ya bude kofar motar yana jiran isowan mu bude mata other side din yace ma driven sai ya zagaya ya bude min na shiga. Ina zama shima ya zauna sai ga Nafisa ta iso gurin daga ita sai rigar barci a jikin ta wanda ta kwana dashi ta dora zani a sama kanta babu dan kwali. Kofar motar ta rike tana fadin sai ka fada min inda zaka da ita munafuki macuci azallaumi dan cin amana nidai ina zaune ina kallon su kalman dai dayace da yake yawan fada mata ko yaushe. Nafisa zan saba maki idan baki shiga hankalin ki ba wallahi ban san dalilin da maganar yake kashe mata jiki ba sai inga ta yi laushi idan ya fada mata hakana. Yanzun ma daya fada mata sai ta sake kofan motan taci gaba da surfa mai zagi har motocin suka daga suka bar gurin bata daina ba kuma bata shiga ciki ba. Hannun shi daya yasa ya dafe goshin shi dashi sai faman tsuki yake ja motar na tafiya ban juyo na kalleshi ba sai kallon inda muke wucewa nakeyi. Har cikin school din ya shiga inda ake aje motoci suka sauke ni zan fita naji ya rikoni juyowa nayi na kalle shi sai kuma na sauke ido na don banda jimirin jure kallon nan nashi. Jinayi yace behaviors self kin ji ko kai kawai na gyada mashi nace naji a fili zan kara fita naji ya jawo hand bag dina ya cusa min wani abu a ciki. Ban duba ba sai dai na fita ina gyara gyale na saman kaina na fara tafiya a hankali zuwa department din mu. Tun farkon haduwa da wa yanda na sani suke min murnan auren da nayi ina fadin na gode kawai. Ko dana isa na samu an fara lectures saukin abin wanaan malamin dake ciki baida tsanani sosai ina shiga idon kowa a kaina caaaa har abin ya ban mamaki. Wurina samu can baya na zauna ina noke kaina don kunya Allah, Allah wasu keyi ya fita su fara min sheri don bani ba harsu course mate dina ba wanda ya dauka zanyi aure a yanzu din. Bayan an gama lectures ne suka fara fadin amarya amarya nan ma wanda basu san nayi aure ba suka sani. Ranan dai nasha sheri a gurin su shiru nayi sai fadi suke wai aure ya mai dani silent na koma wata shiru shiru dani yanzu. Bayan mun raraagene na fito na samu maryam tana ganina ta saka ihun murna muka rungumay juna zuwa hostel muna shiga dakina na bude ban san lokacin da wasu hawaye suka zubo min ba. Maryam ta shigo dakin tana bina da ido tare da fadin barin kawo maki abinci ki dan ci kai na girgiza mata tace nasan fa baki karya ba murna zuwa makaranta ba zai barki ba. Nace kamar kin sani wallahi ban son in ciye maki abincin hostel ne tace ko dai baki son warin shi yanzu tana kokarin kai hannun ta saman ciki na tana shafawa. Saurin buge mata hannun nayi ina hararan ta tace ba ssni ko har kwallo ya shiga raga ko kike min wanan sabon surfi haka. Dukka na kai mata tana kaucewa tana dariya tace wallahi bawan Allah nan ya iya kiwo ji yadda kika koma cikin kwana biyun nan da ban ganki ba. Ni ina nan ina tausaya maki ashe ke kina can kina sheke ayan ki a gidan mijin ki tashi tayi ta dauko min wani leda tace antyn ta ce tace ta kawo min shine gudun mawarta gare ni tunda anyi aure bata nan. Nafi yaba dogon rigar dake cikin kayan da mayafin shi sauran kuma maganin mata na zamani bayan na gama duba rigar na koma ga maganin ina kallo ina tabe baki. Nace ni sai ciki ni da wanan abubuwan akeyi kuma basu da amfani a gare ni dariya tayi tace da saura ki kenan ashe. Wai kina nufin har yanzu baki mallaka ma wanan bawan Allah kan ki ba komai kike nufi ne wai shima AA din har da laifin shi daya kyale ki yana kallon ki haka. Nace idan bai kalleni ba mai zai min kike so tace kema ai kin sani don baki fi karfin shi ba kyalle ki dai yake yi kwance nakai ina fadin kanki ake ji ni barin huta ina kaiwa kwance wayana yana kara na dauka. Ganin sunan shi yasa na kalli maryam ina fadin mutumin ki ne ban san may zai fada min ba daya kirani. Har wayan ya kusa katsewa na daga tare da sallama a bakina bayan ya amsa min ne yake fadi har yanzun baku tashi bane daga lectures din. Mun tashi yanzu gani nan na shigo hostel wurin maryam zan dan dauki wani abune yace da izzinin wa sai nayi shiru. Kashe wayan yayi na kalli maryam ina fadin jimin wanan mutumin fa kamar bashi bane buzuwar matar shi kewa yadda take so a gida . Ina ruwan ki khadi ramin ta daban naki daban kowa ya gyara nasa kada ki daka ta tata don ba tarbiyan ku daya ba. Bani daka ta ai maryam nasan abinda nake yi don haka ne nake dan daga mashi kafa kada mu zama daya da ita Allah maryam yanzu har tausayi yake bani idan tana mashi wani abin. Gwamma da kika fadi da kan ki yanzun lokaci yayi da zaki fara bashi salama ya samu saukin wanan tsiwan a gurin ki. Nace Allah maryam ko nayi niya sai inji na kasa don irin abinda nake gani matar sa na mashi a gaban idona kuma bai daukan mataki ga hakan. Wallahi khadija sanyin hali kega AA din nan naki bawai ya kasa daukan mataki ba shu,uman mata iri su Nafisa wuyan sha,ani ke gare su sai an bi abin a sannu . Don girman Allah ki sauke wanan halin hakana khadija ki rungumi mijin ki ku ba mara da kunya dan kin san yana son ki yanzu dai. Dama nasan da hakkan maryam amma zuciya ta ce ta kasa natsuwa dashi ban san may yasa hakan ba nima naso ace ko ba don komai ba nayi wa iyayyena biyayya don samun haske na gobe kiyama. Addu,a zaki dage dayi da sadaka da sai kiga komai ya zo maki a cikin sauki ina nan ina kokartawa maryam ki dai tayani da addua. Ko nayi niyar kyau tata mashi idan ina kallon abinda wanan matar ke mashi sai inji komai ya fita raina. Baki tunane ba khadija aiki ne fa ja a gaban ki yanzu don Allah idan kin mutu a wanan irin yanayin fa may zaki je ki fadawa Allah zaki ce akan wata buzuwa ne kika kasa cika naki ibadan. Kafin in wani magana ya sake kirana karo na biyu na dauka yace fito mu tafi gani a waje kallon maryam nayi nace kinji wai gashi waje. Tace da sauri mike mike don Allah kada yaga kin dade kuma kiyi laifi a wuri shi ni dariya ma ta bani don har ta rigani mikewa tana fadin kada ki manta da abin nan da Anty ta baki tace in fada maki kiyi amfani dashi yadda ya dace. Naji nace kice mata na gode sai nazo in Allah ya yarda tace don Allah maryam ki natsu ki yi tunane akan maganan nan. Mun fito mun samay shi a mota wanan karon shine mai jan motar ba driver ba kuma mota daya ba kamar yadda muka zo ba. Sannu da zuwa taimai ya amsa mata fuska a sake tace dashi ya aiki lafiya kawai yace da ita ya bude min kofan dirkekiyar jeep da yake ciki zaune na juya wurin maryam ina mata sallama. Mun fara hanya ya juyo yana fadin waya baki izinin zuwa nan da kika zo shiru nayi mashi ina kallon window motar ya sake fadin badake nake magana bane ? Na fada ma daukan wani takarda nazo yi a dakina wanda zanyi amfani dashi amma in haka ya bata ma rai kayi hakkuri. Kallin mamaki yayi min jin kalman hakkuri ya fito a baki na sai naji baiyi magana ba sai tuki yake yi mun kusa kawa gidan naji yace yusuf yaje kaduna yace su hajiyan mu na gaida ke. Sai lokacin na juyo nace mai ya koma bayan zuwan mu kuma yace ai yanzu kin san zuwa ya kama shi tunda bukin su ya kusa. Au har bukin ya zo ne ai na dauka sai ta karasa karatun ta yace ke kin kare ne da kikai aure shiru nayi mashi ya sake tambayana nace ai kafi kowa sanin amsa. Amsan ki nake son ji kin koya ma zainab ana aure ko ba a kare karatu ba don haka itama zata kwaikwaiye ki ne nace nima ai dole akai min ba da sona ba. Wa yai maki dole ya fada yana murmushi nace kafi wacce kake tambaya sanin amsa ai na dauka maryam tai maki nasiha ne jin kalman hakurin da kika bani dazun don nasan ba halin ki bane aro kikayi. Kai har yaushe kasan wani halina tunda ba zama cutship mukayi da kai ba balle ka sani kasan komai nawa. Wani irin cutship kike son muyi dake bayan wanda mukayi dake a baya ban samu bashi amsa ba motar shi ta shigo get din gidan wani dogon mutum fari kanshi ako yaushe a cikin nadi yana rataye da takobi always a kafadan shi ya taso ya wagale get din muka shiga. Motar mu na danna kai motar Nafisa na kokarin fitowa a gidan wanda dama ashe ita buzu mai gadi ya bude ma kofar fita daga gidan. Sau daya na kalleta na kawar da kaina gefe daya ban kara kallon ta ba shima kallon nata yayi ya kawar dakai, ganin shi bai sa ta dawo ba ko ta tsaya sai ta fice a gida. Kanshi ya girgiza a cikin takaici batare da yayi magana ba ya samu wuri ya parker motar nayi sauri kama kofan zan bude amma sai naji kofar a rufe take. Na juyo na kalle shi ya zaune yayi shiru yana kallo na nace bude min in fita yace mana yace ban gama dake ba tukun zama na gyara ina sauraren shi. Iska ya dan furzo daga bakin shi tare da sauke numfashin shi yace kin san yau ranan girkin ki ne ko na juyo na kalle shi tare da fadin ina da ranan girki ne a gidan ka ? Ko matar ka ta yarda ne a bani girkin ta gama cin ramuwar girkin ta da naci mata ya dan murmusa tare da fadin ko can bata ci wani ranan girkin ba don ni ba jahili bane. Nasan abinda nakeyi fa khadija wanan haukan da take bawai zai rudar dani bani in afka sherin shedan na daina shiga gurin ki ne don naga kina lalura yasa na daga maki kafa. Baki na turo gaba tare da kara yunkurin bude kofar motar ina son fita daga cikin ta naji ya danna abu kofan yayi kara yace kin dai ji na fada maki. Fita nayi ba tare da ns juyo gare shi ba na fice daga cikin motar yabi ni da kallo har na shige ciki da sallama a bakina. Suna falo zaune kamar kullun suna hiran su babu wace ta karba min sallama na nima kuma ban damu da sai sun karba min din ba na fara wuce wurin da suke zaune. Suna gani na sai sukai tsit da farko da na dan wuce su sai suka saka dariya irin wanda ke sa mutum ya tsargu din nan haka bai sa na juyo gare su ba sai dana kai kofana na juyo na dawo gare su duk suka maida hankalin su gare ni Nayi masu kallon tsab gaba dayan su tare da fadin wacece mai share share a gidan nan shiru sukayi suna kallona ga baki dayan su. Na sake fadin mai shara nake tambaya a cikin ku da wace ke girki don za ai min gyaran daki ne da girki yanzu. Yanyalace ta amsa min da babu wata mai aiki a cikin mu da zatai maki aiki a karkashin Nafisa muke zaune nan dukan kan mu yarinya. Shigowan shi a bayana yasa na juya wurin shi ina kallon shi tambayan may ke faruwa ne ya tsaya yi nace kai kace min yan aiki ne su idan ina da bukatan wani abu in kira mai yi tayi min yace kwarai da gaske. Yanzu ya akayi nace na bukaci mai shara da mai girki sun ce babu a cikin su asali ma su a karkashin Nafisa suke zaune. Yace haka ne tare da kallon su yace tunda a karshinta kuke ba aikin gidan nan kuka zauna kuyi ba sai ta zo ta sama maku wurin da zaku zauna daga yau din nan ba sai gobe ba. Yana fadin haka ya juya ya fara tafiya muryan wata daga cikin su ne take tambayan wani guri zasu share min na nuna mata falon gaba daya nace nan nake son a share a gyara bana son daga yau in kara samun falon haka. Sai mai girki idan akwai zaso ta biyoni taji may za a girka muna a gidan kowa yaci ina fadin haka na juya na fara tafiya ban tsaya sauraren may zasu ce ba. Na bude part dina tare da addua a bakina na shiga sai dana aje tarkacen takarduna da na shigo dasu na fada bandaki na watso ruwa na sauya tifafin jikina dan karamin kitchen dina dake manne a part dina wanda nake dan yin aikin abinda zanci na bude na shiga. Motsi na ji a falon yasa na fito wata buzuwa nagani tsaye tana fadin zancen girkin da kikayi ne ya kawo ni. Nace da ita abinci zaki girka wanda mutanen da ke gidan nan zasu ci ganinan fitowa yanzu zan duba abinda za a dafa. Ta juya ta fita ni kuma naci gaba da abinda nakeyi a kitchen din nawa na dora komai na fito na samay ta tare da wata nan muka fara aiki dasu cikin dan lokaci kadan muka girka tuwo da miya wanda zai wadaci wa yan da ke gidan. Ga mamakin su ban tsaya diba ba sai dai na zubawa duk wani dan aiki suna fada min muka gama lokacin magariba yayi ko. Part dina na koma na samu cow tail din da na dora ya dahu yadda nake so na sauke na zuma warmer tare da dora wutan tuwon alkama nake son tuka mashi sai miyan yauki da zan danyi a hada da ja miyar cowtail din dana dafa kafin takwas da rabi na gama komai naje nayi wanka na fito na fara gabatar da sallah na dan dade a zaune ina addua kafin in tashi in shirya kaina. Abinda antyn Maryam ta aiko min na bude na karanta bayanin su turaren na shafa tare da bin ko wani gabban jikina na goga kadan na dauko wani Ethopian abaya na saka a jiki. Sai da na gama na fara tunanen yadda zamu kwashe da buzuwa yau a gidan gashi nabi shawaran maryam nayi yadda tace amma kuma matsalan shine buxuwa yanzu. Nace a raina dole ne Anty Fati ta kasa jure wanan fitinan na buzuwa tabar mata gidan duk da mijin wanda nai fahince tane ashe ke ganin laifin ta. Sai yanzu dana shiga wanan tarkon nake kara fahintar dalilin ta na bar ma wata mijin ta da gidan ta gaba daya ta zabi zama a inda bata samun kulawan shi yadda ya kamata acan. Mikewa nayi yare da fadin Allah ya haudani kan wanan matar shu,uma ta gidan nan kamshin humran da body spary na oud dana shafe jikina dashi ne ya amsa ko ina na gilma a gidan. Na shirya komai da zan bukata a basket na jawo kofan part dina nayi mashi key turaren ne ya jawo hankalin su inda suke zaune suna cin abincin da muka girka in general na gidan. Araina nace algungumai ashe suna son cin abincin gashi yanzu duk suna cin abincin da suka tsaya min iskanci. Sama na haye zuwa wurin maigidan basket din na aje ba tare dana jera ba na nufi cikin dakin kai tsaye inda na samay shi ya fito daga wanka kenan yana goge jikin shi. Juyawa nayi da sauri zan koma muryan shi naji yana tsayar dani a inda nake yana fadin ina kuma zaki ba kinzo cika ladan ki bane kuma zaki koma. Nace ni bashi ya kawo ni ba zuwa nayi in gyara ma guri daku abinci dana kawo yana tsaye na nufo inda yake ya tsaya yana kallon na a zaton shi gurin shi zan zo sai yaga na wuce na shige bathroom din na rufo gyara nayi sosai ban so yi da dare ba amma banda lokacin yi don na makara gayin hakan. Koda na fito na samu ya gama ya sauka kasa na gyara mai dakin na goge ko ina ina gap da karasawa ya shigo dakin dauke da jakar da ya ke fita aiki dashi yana fito da laptop din shi ciki. Na gama nace dashj abincin fa don ni zan koma part dina dayake shi dan zolaye ne a noke sai cewa yayi wanan kwaliyan da kamshin wa zaki kai ya shaka ko ya gani. Kaina nayiwa kwaliya ba wani ba yace karya kike wallahi ni ki kawai kuma ban gama gani ba da shaka don ban biya ki ladan yi ba. Kaidai ka sani na fada na kara dacewa kai dama ba,ayi ma abin arziki ai a wanye lafiya sai ka samu abinda kace wa mutum. Yanzu kuma laifine don naga abin sha,awa a matata na yaba ko ba yabon baki kike so in maki bane ? Fita nayi ban bashi amsa ba sai da nakai kofa nace idan ka gama abinci yana danning yana jiran ka ni sai da safe na gama nawa yace kada ki soma ki bar part din nan don baki gama ba. Fita nayi zuwa dinnig din na jera mai abincin ina cikin jerawa ne ya fito daga dakin ban ji fitowan shi ba sai jin hannuwanshi nayi saman weast dina yana min chakulkuli da wani irin zabura na dago na watsa mai harara tare da fadin ka bar min haka please. Zama yayi yana fadin ina da doka ne ajan abina kuma karki manta fa kayana ne a gurin bansan may yasa yake son min irin maganan nan dake sakani jin kunya ba. Bandago kaina ba don na fahinci shi baisan kunya ba ganin ya zauna na jawo plate din na fara zuba mai abincin yana zaune yayi balance saman kujeran da yake zaune yana kallon abincin da nake zuba mai baiyi magana ba jin bai tanka min ba yasa na dogo kaina ina kallon shi tare da fadin ya isa ko in kara ? Yace idan zamu iya cinye wanan din ki barshi hakana ko kuma ki kara idan ba zai ishe mu ba don tare zamuci. Da sauri na dago kai nace dashi nifa na koshi don naci abinci a gurin maryam dazun. Yace wanan ba reason bane ki zauna kici abinci nace ban cin abinci sau biyu a wuni haka ka,idana yake ki koyi ci daga yau ya fadi. Gani nayi kamar bai yarda dani bane yasa na je kura daya na zauna a kusa dashi tare da wanke hannu na soma ci yana zaune ya harde hannayen shi saman chest din shi ya kura min ido. Dago kai nayi na dan kalle shi ganin bai fara cin abincin ba bakin shi ya bude min sai na dan harara shi. Yace baki son in ci abincin ke nan ashe nace kai ni wallahi kana takura min har abuncin ma na girka ci ma bazakayi da kanka ba sai anbaka a baki ? Ganin da gaske ba zai ci ba na debo katon loma na nufi bakin shi dashi sai da yayi murmushin ganin loman dana debo din ya bude bakin shi da nufin in sa mai. Nafisa ce ta shigo tana watsa muna harara dagani har shi tace karuwancin da ake ma ke nan tun a waje har ya rude ka ashe , ? Eh yace mata ashe kema kin gane yanzu akwai wace ta damu da cina dashana a gidan nan tunda gashi kin gani kinyi magana. Loman da ya barni dashi a hannu na mika mashi ya bude baki ya hade abincin takai ma kallo tace wanan karyan bai rudani. Nazo ne jin dalilin da matar ka zata sa min yan uwana aiki haka a gidan a wani dalili nata zata saka su suyi mata aiki. Yan uwan ki ko yan aikin gidana kike nufi don biyan su nakeyi kuma inda suke zama tasa su gyara abinci kuma naga suma sunci da suka girka sai kuma may ya saura. Samad da bakin ka yau kake fada min haka akan yan uwana a gaban wanan fitsarariyar mara kunyar yarinyar mai son katsalan dan to bari kaji Ban dauko su gidan anan don wata shegiyar matar ka cen ta dinga saka min su aiki ba don bukatan kaina na kawo su nan ba nawani ba can daban. Yace idan dai zasuci gaba da zama gidan nan ya zama waji bi su yi duk wani abinda kowa na gidan nan zai saka su suyi mudin kina son zaman su a gidan nan kuwa. Wallahi wanan ba zata saka su komai ba daga yau su sake mata ko wanan da sukayi don bani gidan ne aka samu yin hakan. Yace ashe ko karshen zaman su a gidan nan yazo ke nan don muddin ta saka su wani abin basu yi ba zaman su ya kare a gidan nan na fada maki. Tace akan matar ka kake fada min haka bazasuyi ba kuma ba zasu bar gidan nan ba sai dai ita tabar min gidana wallahi. In ba haka ba sai dai mu tafi tare dasu idan ma korar su zaka yi daga gidan kaji na fada maka yace da ita haka yafi nono fari a gurina idan zsku tafi duka har dake. Ido waje take fadin Samad akan wanan abar kake fada min wa yan nan bakaken maganganun haka har da cewa sai dai muta tare dasu din. Kwarai kuwa mudin ba zakubi abinda na umarce ku dashi ba kuwa nima a shirye nake da matakin da zaki dauka din. Tace ke kuma bari kiji Samad a tafin hannu na yake idan kina takama da guntun asirin da kukayo mashine na baki kwana bakwai a gidan nan. Idan kin taba zama kin zauna in baki taba zama ba baki taba dashi don wanan dandana haukace na bari kikayi na zana dashi din. Yace tana barin gidan nan ki tabbatar da tare zaku barshi don kin san ni ba saki ko wani abu a gidana duk wani abin da zaki mata ki tabbatar da kafin ya samay ta kece ta farko da zai sama. Kai na girgiza ina murmushi nace bude baki kaci abincin kada yai sanyi ka tsaya kana magana akan abinda bai da ma,ana . Bude bakin yayi kamar wani yaro naci gaba da zuba mai abincin yana ci ta dan tsaya tana kallon mu sai masifa take surfa mashi ni dai ina murmushi ta nufo wurin yace idan kika kuskura kika taba wani abu anan bakin auren ki kenan dani wallahi. Ido waje take kallon shi sai ta juya ta fita a fusace ta bar gurin tana fita na tsamay hannu na ga abincin ina wankewa tare da mikewa kai ya girgiza min tare da fadin nace dake na koshi ne ? Nagama baka ka karasa da kan ka wanan masifar taku ya isheni haka wallahi mace kamar a kanta aka fara kishiya. Na fara tafiya sai naji ya kamomi hannu na zuwa jikin shi wani irin shock ne ya ziyar ce ni a lokaci daya cikin karfin hali nace dashi ka sake ni don Allah. Murmushi naji yayi na kara jin haushi a raina nace a fili kasan ba ka iya gidan haka ka dauko ni don ku bata min kurciyana komay ? Jawoni yayi na kara fadawa saman jikin shi da kyau ina kokarin zilewa ya matseni har ban iya motsin komai . ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Ina kara rokon ku da ku taimaka ku rike min amanan wanan novel din da albarkan Allah da Annabinsa. Wace kuma ta yi sakaci da amana na roki ubangijin mu Allah alfarman wanan rana ta jumma,a ya hanata farin ciki a rayuwan ta har abada kwantan kwancin abinda na roke ta dashi taki darajan Allah da Annabi. Tunda na tashi na shiga kitchen goge nan wanko can har na gama na dora abin breakfast duk laraba bata fito ba har matar gidan. Na kusa gama abinda nake girkawa ne laraba ta shigo kitchen din tana fadin a cikin barci nake jin kamshi a hannci na ashe ke ce a kitchen din hajiya. Gaida ita da kwana nayi ta amsa cikkin jin dadi tana godiya tare da kallon kitchen din yadda na gyara shi komai tas sai walkiya gurin keyi. Sai da muka gama jera komai a inda ya dace na koma daki don in watsa ma jikina ruwa in shirya na fito daga wanka har na saka ma jikina tufafi sai gashi a dakin nawa gaida shi na yi sai dai fuskan shi duk da ya tashi daga barci ne babu walwala a cikin fiskan shi. Daga inda yake tsaye yace ki shirya zamu koma Abuja yau din nan dago kai nayi da sauri ina kallon shi. Yace kinji may nace ai ko nace ni da zaka barni in badon karatuna ba sai in ce kabarni nan kaduna don Allah don wallahi nafi jin dadin zama a nan. Wani kallo yayi min sai baiyi magana ba bayan fitan shine na fara shirin kaya duk da ba wasu kaya mai yawa nazo dasu. Bayan na gama shiryawa ne na sauko kasa ban samu anty a falo ba don haka na nufi dakin ta don in fada mata zamu tafi yau inji maigidan. A kofa na tsaya ina sallama ta amsa min daga ciki na sakai na shiga har wanan lokacin tana kwance jikin ta ba riga batayi wanka ba. Gaida ita da kwana na fara yi tare da tambayan yaran ta tayi murmushi tace yanzu na kora su zuwa islamiya don yau basu shiga boko. Abinda na lura dashi shine maganan diyan ta yana sakata farin ciki shi kawai zakai mata kaga farin ciki a fuskan ta. Daga inda nake tsaye nace anty Fati ya fada maki yau zamu koma wai don nima yanzu ya shiga yana sheda min batun tafiya. Gashi kuma su Affan basu nan zamu tafi kila don Allah anty zanso idan an masu hutu suzo Abuja wurin mu suyi hutu tare da mu. Zaune ta mike tana fadin a, a Amarya ban maki wanan alkawarin ba gaskiya yaran da ko wanda ya haife su ba wani damuwa yayi da al,amarun su ba ina zan tura su zuwa can suje su zama abin tausayi. Muna tare dasu ma yaya aka kare ballantana sun tafi su kaida tare ta nayi da fadin haba anty ban son ki fadi hakan karki manta gidan uban su zasu tafi hutun fa ba wani gida ba. Daga inda take take gyara zama tare da gyara daurin zanin jikinta a gaba da kyau tana fadin Amarya ke nan wallahi zan iya tura maki yara na ko zuwa ina ne don na yarda dake sosai dan kwana biyun da mukayi tare. Bayan haka kuma ina da labarin halinki da komai naki gurin su mommy da su Bintu sai dai matsala daya ne daba zan turo maki yara zuwa Abuja ba gaskiya matsalan kuma kin sani itace Nafisa. Na dago kai na kalle ta nace Nafisa kuma anty tace kwarai kuwa don na fiki sanin waye Nafisa ke yanzun kika shigo kila baki fara sanin halinta ba ko wani abu nata. Halin ki kawai khadija yasa na aminta da dake da diya na wanda idan Nafisa ce ko na minti daya bz zan aminta da ita da hakan. Kiyi hakkuri nace da ita kawai don taban tausayi a yadda take maganan nata Amarya matar da bata kauna na da diyana ko na second daya taki jinin ta bude ido tagamun tare da mahaifin su a gidan nan. Idan itace fa tazo yadda kukazo da mijin nan ban isa in saka shi a ido ba yanzun ma ne da abin ya danyi sauki har zai iya dan kwana a dakin mu da zara gari ya waye kuma bazan kara ganin shi ba sai wani jikon. Sannan zan tura yarana inda take ai duk abinda tayi masu a can nina ja don ni nayi sake suka tafi. Nace anty ai ba wurin ta suka zo ba gurina suka zo kuma gida gidan uban su ne ba wanda zai hanna su abinda suke son yi da zakiyi hakkuri ki turo min su ko kuzo muna hutu tare dasu ki gani babu abinda zai faru wallahi. Tace ummh,ummmh amarya bazan je ba suma ba zasu zo ba barsu dai nan inda nake shiya fi ni wallahi na gode da abinda kikai min don ko yanzu kin nuna min ke mai kaunar mu ce. Ko ba komai ki nuna min so tunda kin so diya na ni kin gama yi min komai wallahi shiru nayi sai can nace amma ya kamata ace kuna zuwa hutu Abuja duk lokacin da yaran suka samu hutu sai kuzo sai nake ganin kamar haka zai kara kawo masu shakuwa da mahaifin su. Tace hakane kuma amma gaskiya ba zan iya zuwa ba ke dai kawai abar maganan nan zaifi sauki. Nace idan ke ba, , , , , shine ya shigo dakin ya samay mu a ciki yana muna kallo mai kama da zargi ganin mu a tare muna magana. Saidai ganin shin bai hanani karasa maganar da zan fada ba din nace in ba zaki zo ba sai ki barsu su suzo suyi min hutu a can. Tayi dan dariyan nan nata a gyatsire tace zasu zo wata rana ai tunda kin kwadaita masu zuwan zasu shiga damu na ne don dama suna son zuwa. Nace to yayi anty sai na gansu ke nan idan ma basu zo ba ni zan zo nan in masu hutun ba shike nan ba na juya zan bar daki yana tsaye yana duba wayan shi bai muna magana ba. Nan na barshi na fita zuwa dakina ina bugawa Ya Amina waya cewa wai yau zamu koma Abuja inji shi. Tace yau kuma Khadi gashi baki ko shigo wurina munyi magana ba nace ai haka kuka zaba min a tauyeni a hanani dama na. Dariya tayi min tace aure ne khadi aure kuma yakin mata ne kin sani nasan dai idan zaku wuce zaku ratso nan ai shi ya shigo yana fadin in fito mu tafi in kule dakin in bar key din a wurina shine dakina a gidan. Ya sa hannu ya dauki dan trolley din da na aje a tsakar dakin yayi waje dashi mikewa nayi na dauki hand bag dina na yima dakin kallo na rufo na sauko kasa. Anty Fati tana kasan anan na samay ta tana jiran saukowana na taka zuwa inda take ina gyara mayafin da ke a kaina tare da fadin anty zamu tafi. Ta dan kakaro murmushi tace khadija na gode sai kuma wata rana ke nan nace ai zanzowa su Affan hutu tunda su basu zuwa shiko yana tsaye yayi kicin kicin da fuskan shi bai annuri. A waje muka samu Yusuf da sauran drivers din suna magana suna diban dayan motar ya fito yana fadin da matsalane Yusuf ? Yusuf din ya juyo yana fadin iska kawai zai kara mata idan mun fita yanzu kafin mu fara hanya rai bace ya ce ma drivern motar kasan ban son irin haka shiyasa nake cewa kowa ya duba motar shi kafin muyi tafiya. Yallabai ban san yau zamu koma ba da tun jiya nazo na dauke ta na kai an kara mata iskan. A family house din su muka tsaya sai da muka tsaya muke gaisawa da Yusuf din don suna ta fada da driver. Niko sai kallon su nake ina cewa a raina samun duniya ma wani wahala ne ji yadda yake ma dattijon nan fada don Allah ? Mun shiga ciki muka gaisa da mutanen gidan dakin hajiya mama kamar kullun muka shiga karshe. Gaisawa da ita nayi na mike na shiga wurin su Binta nayi haka ne don in barshi ya gana da mahaifiyar shi din. Hira mukayi sosai ina jadda ma Binta zancen zuwan da tace zatayi wurin mu tayi IT zainab tace dani don kinji tana fadi kawai wa zai barta tazo . Fitowa mukayi falon don tafiya yana zaune har yanzu a gaban hajiyar su daidai lokacin da take fadin kasan dole sai ka mata lefen ts kamar kowa don iyayyen ta sun dubi korafin mu sun aura maka ita a haka bashi zai sa ka dauki lokaci ba wurin bata hakkin ta. Tsam mukaja muka tsaya sai kuma nayi niyar komawa dakin da muka fito din tace dawo ki zauna ai ba wani magana bane magana muke akan zancen lefen ki da bai maki ba har yanzu tunda anyi auren ba wani shiri a duka bangaren biyu. Kaina na sada kasa don kunya kan ai iyayyena sun gama sayae min da daraja na a idon kowa sai dai biyayya ya rage min don ni ban ma ko tuna da zancen wani lefe ba can. Ta juyo kaina tana fadin khadija bamu da abinda zamu saka maki dashi dake da iyayyen ki sai addu,a don mahaifan kin sun nuna muna harcin da ba kowa ne zai maka shi ba a wanan zamanin. Don Allah kada naji wani abin assha ya fito daga bangaren ki ko kadan yadda mukayi hadin nan a cikin aminci muna fatan zaku ba marada kunya dukkan ku biyun. Mommy ne ta shigo dakin da wani leda mai ruwa blue mai dan girma a hannun ta tana fadin masu tafiyan nan babu sallama ga dai dan abinda kika samu ayi hakkuri dashi na rubuta duk bayani a cikin ko wani idan kin duba. Godiya nayi na karbi ledan daga hannun ta na kara sada kaina kasa ina jin kamar hawaye zai zubo min tace to babangida gadai amanar diyana nan muna kara danka maka muna maku fatan alheri ke kuma ki bi mijin ki amana yi nayi bari na bari. Muryan shi naji cikin rashin tsammani yana fadin mommu ku dai kara ja mata kunne ta fita harkan Nafisa don Nafisa takala ita kuma tace sai ta mayar da martani. A , a tun yanzu har sun fara ne inji hajiya mama yace mama ai kin san halin Nafisa akan kishi zuwan nan da mukayi ba irin kirana da batayi tana zagina ba. Nasan in min koma akwai tsiya shiyasa nake son a ja mata kunne don Allah kada ta dinga biye ma haukan ta. Ina zaki tsaya bin ta kan wanan da bata san ida ke mata ciwo ba mommy tace kada ki soma inji haka na faruwa dake khadija. Ba zata taba son ki ba haka sukayi da Fati a baya yanzun kuma ta dawo gare ki hajiya mama tace bazaku zo daya ba khadija don ke mai ilimi ce kiyi amfani da ilimin ki ku saman ma yaron nan kwanciyan hankali don Allah wayan shi yai kara ya mike ya fice daga dakin. Hajiya mama tace khadija nace a sanyaye na,am mama tace don Allah ku sama ma mijin nan na ku lafiya ya natsu ya dawo kan hanya. Idan kin duba da halin da ake ciki shi kan shi yanzu bai san abinda yake yi ba kin ga ko wanan maganan na tana zagin shi da yafada yanzu abin ne ya ishe shi har mukaji. Mun sa ayi auren nan naku ne don muna fatan samun sauyi daga gare ki a gidan don ke din mai ilimice da ko wani gida ake sin samun irin ta. Kin ga mu nan idan kika shigo kika gan mu a haka sai ki dauka ba wani kishi a tsakanin mu amma akwai shi. Kaina na dago na kalle ta tace kwarai akwashi mana a tsakanin mu sai dai muna kishin mu da ilimi ne bamu wanda za ai Allah waddai damu. Don haka ki natsu ki karanci waye Nafisa ki san ta inda zaki bulloma haukan ta don ban dauke ta cikin mutanen kirki ba ni kina da ilimin ki na boko dana addini ki dinga kai kukan ki ga Allah kina neman kariya daga sherin ta in Allah ya yarda bata komai dake da yardan Allah. Nan dai sukai tamin fada ya aiko daga falon Abba in fito mu tafi muka fito da su mommy banda hajiya mama da tai muna Allah ya kiyaye daga dakin don kawaici. A falon Abban muka samay su dukan su ya dan taba muna nasiha mukai mashi sallama muka fito muka dauki hanya sai Abuja. Tunda muka dauki hanya na lunshe idona har barci ya dauke ni a hakana mun shigo Abuja da dan sauran rana kai tsaye gidan muka nufa. Nikan ina fitowa kai tsaye na nufi cikin gidan da addua dauke a bakina basu falon don haka na samu na shige ciki kai tsaye na bude part dina na shiga. Sai da na shiga na dakatar da addu,an dake bakina ban zauna ba ina aje handbag dina ban daki na fada don a matse nake a lokacin pad din dake jikina ya damay ni. Wanka nayi na canza wani pad kafin in fito koda na fito na samu an shigo min da kayana dankin nawa na gama kintsawa na zo na kawar da kayan inda ya dace. Ban huta ba na shiga gyaran part din don dan kwana biyun da nayi naga wurin ya dan min kura ina cikin gyara ne ya shigo ya samay ni ina gyaran dakin. Yace ke baki huta ba wani aiki kika daukowa kan ki na fada maki fa akwai may wanan aikin a gidan nan bakiji ba. Sai lokacin na dago nace dashi in don dan wanan aikin ne zan iyayi wa kaina sannan kuma a gaban ka fa kaji tace in samo nawa yan aikin da zasuyi min ba yan uwan ta ba. Ni kuma ko banza banga dalilin da zai sa in saka yan uwanta su gyara min daki ba da raina da lafiya na bai bani amsa ba sai cewan da yayi may zakici zan fita yanzu in sayo muna abinda zamuci ne. Ban jin cin komai na bashi amsa tare da mayar da hankalina ga abinda nake yi da farko kallona ya dan yi yaga yadda fuskana yake daure tun fitowan mu daga gidan su. Ni kuma haushin shi nake ji wanda ina ganin zancen lefen da naji hajiya mama tana mashine a kaina na kudiri koda ya kawo lefen ma bazan karba ba insha Allahu. Bai dawo ba sai wani lokaci sai gashi dauke da ledoji a hannun shi ya shigo ina inner room ya samay ni a zaune ina nayi shiru na sadda kaina kasa ina tunane. Yace may ke faruwa na gane ki a hakan dagowa na yi na kalle shi tare da kawar da kaina daga kallon shi nace ba komai yace ga abinci nan ki ci idan kin gama tunanen ki ya sa kai ya fice na bishi da kallon haushi. Ban bude ledan ba sai bayan magariba dayake ina fashin sallah na gama addu,a na na jawo ledan na dara budewa. Fredrice da barin kaza sai wani leda mai gasasa kaza a ciki dayan kuma kayan sanyi ne acikin sa cikin kwalaye. Abincin na dan taba kadan na raja,a a cin kazan wayana yai kara na dauko na duba maryam ne a layin take kirana. Na dauka da fadin yaya akayi ne yan mata tace ahhaye matan aure ke nan wai ke watau kin samu miji kina kokarin watsar da karatun ki ko ? Nace to may akayi da maza inji dan daudu ina nada miji yanzu may zanyi da wani karatu kuma ? Ke khadija ban son sheri wallahi muyi maganar gaskiya nace ke nake saurare tace yaushe wai zaku dawo kaduna ance fa monday kuna da test department din ku dazu na hadu da Ruth take fada min. Nikan ina kaduna muna holewar mu inani ina wani test yanzu wallahi ki dawo khadija ki covering din abinda kika rasa nace sai wani sati maryam ihu tayi tace what ? Nace da gaske tace wallahi kada kijawa kan ki caryover nace yau she kuma ni ban ma san ta inda zan fara ba wallahi ki dai dawo a cikin satin nan don Allah nace in Allah ya yarda ma na dawo don ni yanzun haka ina cikin garin Abuja ko. Tace wai da gaske kike khadija nace da dawasa zan fada maki haka wallahi ina abuja nace mata tayi ajiyan zuciya tare da fadin da safe ki dubi hanya na zan shigo. Nace ki barshi ba sai kinzo kin damay ni ba ina hutawa da mijina taja tsuki tana fadin Allah yasa da gaske kikeyi ba cika baki bane. Nace ba abinda kuka kowo ni kenan in yi mai ba mai zaisa in cika baki kuma tace shegiya mai dadin bakin tsiya Allah sa da gaske kikeyi dai nace sai kin zo zaki gani. Ina dago kai nagan shi a tsaye daga kofan yana saurena fuska na daure kamar ba ni nayi magana yanzu ba. Maryam ce a layin naji ya tambaya nace dole sai kasan da wanda nake waya ne don bai cikin dokokin da aka fada min da zan shigo nan. Matsala ta dake kenan baki san maganar arziki ba ke sai kin wa mutum wanan tsiwar taki nace ban mashi magana ba sai wasa da naman dana rike nakeyi a hannu na. Kici abincin ki ni fita zan yi nazo yi maki saida safe ne don nagaji ina son in huta yanzu ban ce dashi komai ya juya zai bar dakin sai kuma ya juyo yana fadin wanan abin naku yaushe zaki gama shi ne ? Wani abu na dago na kalle shi cikin jin haushin maganar shi yace abinda ke saki ciwon mara mana nace ban sani ba don sirina ne. Dariya yayi ya fita daga dakin na ja guntun tsuki tare da fara tatara kayan abincin na mike don in kawar dasu a wurin. Kofana na rufe daga nan tare da bin kusurwan dakin ina tofewa da addu, a don i zuwa yanzu ina matukar jin tsoron lamarin Nafisa ta yadda kowa bai fadin alherin ta sai akasin hakan. Ina mamaki a raina wani irin kishi ke gareta haka kamar tafi kowa sanin dadin miji nace a raina Allah yaba Anty Fati boyar Allah hakkuri. Barci ya dan fara daukana can a cikin barcin sama sama nake jin kamar hayaniya a gidan kasa kunne na nayi na kara saurarawa. Haniya ne gami da kururuwa ke tashi a zabure na mike zaune jin hayaniyar yai yawa yasa na fito falona a tsorace na dubi lokaci naga goma na dare saura. Ihun kamar babu lafiya na bude kofa na fito daidai lokacin da yake jibganta daga sama suna saukowa kasa tana buga mai duk abinda yazo gaban ta. Ga sauran yan uwanta tsaye cirko cirko suna kallo sai tsuma sukeyi har zan juya naji sun dauki kururuwa na juyo da sauri inga abinda suke ma ihun lokaci daya haka. Nafisa ne ta dauko flower vase ta nufe dashi shi kuma ya murde ta ya kwace yana dukan ta na karaso da sauri ina fadin ka sake ta mana kasheta zakayi ne. Don Allah ka barta hakana zaka biyewa mace ne kayi kisan kai a gidan ka ya juyo ya kalle ita ko bata saduda ba nan yan uwanta sukayo kan su suna batun banbaranta ajikin shi ta yi wuuu dasu dashi ya kara sheke ta tana fadin zai kasheni mugu kawai. Shakeshi su yanyala sukayi daga baya ya juya gurin su yana fadin ku sake ni sai na fahinci shigar mata sukayi. Ranan naga tashin hankali sosai a gidan don dukan su ya shiga yi mazan suka yo kanshi suma cikin kuka take yare da ban jin abinda take fada sai naga sun dare nasan warning dinsu tayi da hakan. Dakina shiga na kira Yusuf cikin tashin hankali nake fadin kazo yanzu don Allah babu lafiya a gidan nan fa na kashe wayan . Ba,a dauki lokaci ba sai ga Yusuf din ya shigo ban san irin gudun dayayi a hanya hanya ba ya iso gidan yana shigowa kai tsaye wurin AA din ya nufa sai lokacin na karasa kusa dashi nima ina fadin ga jini nan yana zuba ma a hannu da gefen goshin ka yayana kuje asibiti don Allah kabar gidan nan dashi please . Wurina ta juya da masifanta tana fadin akan ki akai min haka wallahi dake dashi kun nemi rashin kwanciyan hankali a gidan nan kun samu muci gaba da haka dani daku yadda ya zubar min da jini nima sai na zubar maki da naki a gidan nan duk kayan dake jikin su sun yaga su. Kada ki soma kice zaki kawo haukan ki ga yar mutane kinji na fada maki duk ranan da kikai gigintaba ta sai kin kwana a cell wallahi don ba zan nuna maki sanaya ba. Tace narin doke ta a gaban ka sai in kwana a cell din tun yanzu tayo kaina a sukwane Yusuf yayi sauri shiga tsakanin mu shida AA din. Nace barta barta ta gwada haukan ta a kaina yau ta rena kan ta a gidan wallahi ke wallahi ki kiyayyeni kina ganina haka nafiki hauka wallahi don ke ba masifa kika iya ba sai hauka. Kallona ta kama yi ido bude ba ita kadai ba har dasu dake falon don idona ya gama rufewa da ita a lokacin . Ke Deedar shiga dakin ki nace karki kara fitowa nan wajen yana fadi cikin bani commad kamar zanyi magana sai kuma na juya na tafi tare da sa ma kofa na sakata na barsu a wurin. Ranan sai dai barci dayake barawo ya dauke ni ban sani ba amma da zaran na rufe ido su nake gani a cikin yanayin dana gansu suna fitinan. Bayan Yusuf ya kaishi asibiti an mashi dressing din ciwon ya dawo dashi gida sun dade a mota suna maganan dashi yana fada masu wai murde mai gaban shi Nafisa taso tayi yana barci. Gaskiya wanan matar taka bata da hankali kasheka taso tayi ne ko may idan taja maka wani matsala fa kuma ? Nifa wanan matar tsoro ta soma bani AA gaskiya kasan nayi tun wuri yace haukanta na banza ne ya motsa kawai wai tana zargin naje na sadu da sauran matan nawa shine duk wanan haukan da kaga tanayi fa. Da mamaki ya kalleshi yace da may take nufi ita kadaine mace ko may yace ban san wanan haukan ba nima shike damuna ai. Lalai akwai matsala kuwa ina ga taga khadija ta fara haihuwa a gidan nan ai sai ta hade ranta ke nan. Na gama komai a part din sai dai na kasa bude kofana har lokacin zaman kadaici kuma ya damay ni jinayi ana kwakwasa min kofa part din. Tashi nayi naje na bude kofan shine a tsaye a saka mai plaster a gushin shi da kuma inda yaji ciwo a hannun daga kofan ban kauce ba nace ina kwana hannu ya mika ya jaye ni a hanya ya shiga part din kamshi ne ya daki hancin shi mai dadin shaka. Daga kofa zaki gaida ni ko kina korata a dakin naki ne nace ba koranka nakeyi ba ina dai guje ma abinda zai kawo fitina ne a tsakanin ku da matar ka tunda mune bata son taga ka mame mu. Wanan ne dalilin ki na dakatar dani daga waje kuna da banbanci ne da ita ko may nace ai yadda ta nuna akwai banbanci sosai kuwa don kai nata ne ita kadai don haka don Allah ka kula. Yace damay ko shiyasa da suke duka na naga kin damu kin so ki shigar min don baki sona ko ? Kallon shi nayi sai na rasa abinda zance dashi har na juya sai kuma na waigo nace mashi saura kiris ai su kashe ka da baka fisu karfi ba kan ban san yadda zaku kwashe ba. Uhhmm yace ashe na baki sha,awa,ke nan ko na burge ki tunda har kika fada nace fada da matan shine burgewa komay kayi ? Gaskiya idan haka zaka biye mata kuna wanan fitina kamar gidan wasu madanbata aibin baiyi ba wallahi ya girgiza kai yana fadin kin san may ta aikata min har na doketa haka. Nace ban sani ba wanan tsakanin ka ne da matar ka ban kuma son in sani don ba abinda ya safe ni bane. Nasan zaki tunanen haka halina yake dama dukan mata akan may zanyi tunanen hakan ai da kana dukan mata da zanji tun baka aure ni ba. Bincike kikayi akaina ke nan akan may zan bincike don banda aikin yi ko may maganar duniya ai bai boyowa kamar yadda naji a kan matar ka gashi Allah ya nuna min. Wanan bakin zanso inga ranan da zai mutu nace akan fadin gaskiya ko may ya dan jima a dakin muna fafatawa wanda shi hakan yana mashi dadi. Yai ta zolayana niko in hakikance ina mayar da martani kamar gaske ya gaji ya fita yana dariya dake ban haushi. Maryam ne ta shigo da sallamanta a dakin tana fadin Khadija kunyi accident ne ko may naga AA din ki da plaster a goshin shi. Kai gulma ajali shiya kawo ki ko duba ni tace wallahi abin ya ban tsoro ne wallahi ke dallah can ni barmin wanan zancen kinji nayi missing din ki zaki zo min da wani zance kuma. Khadija don Allah ina fatan bake kikai mashi wanan abin ba wani kallo nayi mata tare da fadin may kika maidani wai nifa nasan abinda nakeyi can tsakanin shi da matar shine. Nan dai na kora mata iya abinda na sani tace duk saboda ya tafi kd dake tayi wanan abin haka ko may, ? Nace wa ya sanar mata don ni ban damu da in sani ba ba abinda ya shafeni da rikicin su ni yanzu zancen karatuna ne a gaba na don ban san may yake nufi dani ba. Khadija kibi shi a hankali shima ai yasan kina karatu koda ya aure ki kawai halin su na mazane sai yaja maki aji akan hakan tunda yasan kina so. Nace wallahi bai isa yace zai hanani karatuna ba maryam tunda a haka yaganeni ya aure ni banji zan iya bari ba kuma. Idan yace ki bari ai dole ki bari din shine saukin ki ki dai lalabashi don Allah ya barki ki koma nace ina ruwana dashi maryam zaman dai kawai nake a gidan wanda ni banga dalili ba kawai dai don ya kuntatamin ne yai min haka na karasa cikin bacin rai. Tace da amfani mana tunda yana hutu a jikin ki wani kallo nayi mata tare da fadin wani hutu cabdi jam yana dai hutu a wurin matan shi. Kina nufin har yanzu komai bai shiga tsakanin ki da shiba komay komai kamar yaya dama ance maki sona yakeyi ne don fa ya kuntata min ya kawo ni gidan shi yaga yadda zanyi niko bazan taba karya ba har yagane mu tafi a hakana dashi. Gaskiya khadija ban taba zaton haka ba wallahi don nasan AA yana son ki kuma shi namiji ne da ko wace mace zata so kece dai kike mashi rowa shi kuma ya biye maki yaga iya gudun ki. Anya khadija ba sherin wanan buzuwan bane kuwa nace kamar yaya tace tai maku asirin akan haka mana khadija wanan fa yana faruwa a tsakanin kishiyo da basu da imani . Da zaran namiji yazo ga matar shi sai yaji shi ya koma tankar mace ba zai iya tabuka mata komai da dai sauran abubuwa da zai gusar mashi da sha,awanta gare shi. Shiru nayi ina sauraren ta tunda ta fara bayanin ts sai da ta nace haba dai tana iya yin Abin da Allah bai tashi yi bane kawai dai hakan ra,ayin shi ne maryam. Nace kuma fa maganar ki yana da kamshin gaskiya don abubuwan dake faruwa a tsakanin abin akwai ayan tambaya. Nan dai na koro mata labarin komai tun zuwa na gidan ban boye mata komai ba har hiran da naji mommy da ya Amina sunayi sun dauka barci nake a lokacin. Tace Khadija gaskiya kibar sakaci da ibadan ki idan ma kinayi to ki kara duk da sherin ta kada ki bari ta fahinci halin da kuke ciki dashi. Ki nuna mata ke fa kin san kan ki ta ko ina ba kishin hauka irin nata zaki tsaya yi da ita kamar wata bagidajiya duk da ansan asiri gaskiyane. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Naji dadin kasancewa da maryam a dan wanan lokaci kamar yadda ta fini da shekaru haka ma na fahinci ta san hikima irin ta matan zamanin nan sosai. Bayi mamakin ganin haka daga gare ta ba don fada min auren da tayi a baya inda ta hadu da kishiya yar bala,i da bata ko barta ta tare a gidan mijin ba. Cikin hikima take hada min komai da zai inganta jikin mace da cikowan ni,ima ban san kaiba don haka sai nake dauka kayan kwadai ne kawai take ban da kuma na tsari. Na ciki sosai a cikin dan sati biyun nan da mukayi da ita a gidan ba tare dashi ba ni kaina ina jin dadin zaman mu a haka ni da maryam sai dai muci musha muje makaranta mu dawo. Buzuwa kumz ko yauahe bata rasa fitinar da zata takalo min dashi a gidan sai da nagaji muka saka mata ido itama ta kyale mu a haka . Bata fita da motocin don maigidan yace abari har yazo yaga abinda ya faru da motocin dole yanzu duk wanda zai fita sai a motar haya hakan yasa Nafisa ta rage yawan fitan da takeyi ko yaushe akai akai. Cikin hikima da dabara maryam ke kawo min hiran iri daban daban da har naji zuciyata ta natsu da abinda take koyar dani. Haka yasa na raya a raina da zaran ya dawo zai samu canji sosai daga wurina sai dai a can kasan zuciyata ina kwankwanton anya kuwa zan iya haka a gare shi. Mutumin da bata kaina yake ba ta matar shi yake zama nake dashi a gidan kamar kiwo na yake yi. Yau mun tashi da niyar zuwa gyaran jiki don maigidan yace zai dawo daga tafiya a karshen satin nan gidan yar maryam muka fara zuwa gaida ita don ta dawo da mura daga Dubai. Mu shiga gidan tana bedroom din ta maryam tace mu samay ta a dakin naso tsayawa falon sai taja hannuna zuwa saman inda dakin yar nata yake. Shigar maryam har ta fara fada da maryam din tana cewa wai sai yau taga daman zuwa ta dubata bayan ta fada mata ta dawo da matsanecin mura daga tafiya. Ganin da tayi min na shigo a bayan maryam da sallama yasa ta tsagaita da fadan nata ga maryam tana fadin yau amaryace a gidan namu. Nan muka shiga gaisawa da ita yadda naga suna yi da maryam din suka ban sha,awa sosai don sai kace itace ta haifi maryam din Kallona tayi bayan maryam ta mike zuwa wurin kayan da ta dawo dashi din tana fadin khadija gaskiya aure ya karbe ki sosai. Kaina na sada kasa ina murmushi ta sake fadin ance ana gane bikin mace indan yayi kyau a cikin satin da ta haihu ne kamar yadda kuma ake gane kyau dakin mace idan ta dace a jikin ta. Daga inda maryam take tana daga kayan tace wani kyaun daki tayi anty wanan kanwar taki ai sai kin hada da bulala kila don bata daukan shawara . Kallona tayi sosai tana fadin ban gane ba khadija abinda take fada da gaske ne saurin kada mata kai nayi ina fadin bs gaskiya bane anty kada ki dauki maganan maryam. Maryam din ta sake cewa wallahi anty gatanan dai yau a gaban ki gaki gata har yau din nan fa babu abinda ya taba shiga tsakanin ta da mijin ta . Da sauri ta wani waro ido tana fadin Khadija kina da lafiya kuwa kunya naji sosai nayi kasa da kaina dan shiru tayi sai can tace dani Khadija dago muyi magana dake ta fahinta ina son ki dauke ni tankar yar uwar ki ta jini a gare ki kai na gyada mata. Fada min may nene matsalan ki don idan irin haka ya faru dole akwai matsala a ta wani bangare walau a gurin ki ko a gurin mijin naki. Murmushi nayi ina fadin anty ni banda matsalan komai wallahi a bangare ne a iya sani na ko yana tare dani ina iya tursasa zuciyana wurin ganin na mashi biyayya da ya dace dashi. Sai dai ban san dalilin shi ba na kyale nin da yake yi wanda nima hakan ba damuna yake ba don nafi jin dadin hakan da muke dashi. Subbahanallahi ta fadi da sauri a hankali cikin hikima irin ta matan da suka san kansu take min tambaya ina bata amsa har muka kai inda take son fahinta. Naga ta wurgar da hannaye ta biyu saman gado tana fadin shike nan ta cuce ku yar iskan mata mara imani maryam ai ki bar ganin laifin kawar ki don matsalan ba daga gare ta yake ba. Asiri akai masu wanda in ba wanda yasani ba ba zai iya fahintar komai ba anan sai irin matan dake wanan asirin suka san haka. Tace wani asirine da ake hadawa da kaucen albasa da jijiyan dabba idan anyi wanan abin aka haka a ranan girkin macen da ba a son miji ya kwana da ita sai wani akasi yazo ya gitta masu wanda zai ji ba zai iya kaiwa ga matar shi ba komai kuwa sha,awan da ya motsa mashi na matar. Irin shi ke sa sai zargin miji ya shiga zuciyar dayan da akaiwa asirin taga yar uwa da miji ta suna sha,anin su ita kuma an bake ta a gefe sai kaga kishiyar wani lokaci ita kadai zata dinga samun ciki. Maryam tayi saurin fadi wallahi ko kamar kin sani anty don yanzun haka har da kiran khady tayi suna sheda mata wai ciki ke gare ta nan dai ta kora mata labari komai da ya faru harda hana mu shiga motar da yadda nima nayiwa motoci gidan illa babu mai amfani a yanzu . Dariya anty tayi tace ta koya maki kema kin iya ke nan don gashi har zaki jawa maigidan hasara a lokaci daya. Ta dago ta kalleni tana fadin ki kwantar da hankalin ki khadija wanan ba wani matsala bane insha Allahu yau din nan zanyi waya a sama muna makarin wanan abin. Ai idan tasan wata bata san wata ba komai shu,umancin ta kuwa ta samay ki yarinyace shi yasa har abin ya dade yana tasiri a kan ku. Daga yau kada kiji nauyi ko kunya na duk abinda ya shige maki a duhu ba sai kin kira gida kin tada masu da hankali ba ki tuntube ni nan kinji na fada maki ko. Kai na gyada mata tace akwai abubuwan da nima zan hada maki a nan da zakije kiyi amfani dasu idan ya dawo zata sha mamakin ki da yardan Allah. Don irin su nasan yanzu ta shirya sosai ma dawowan shi ai irin mazan ku mace bata shiga gidan su haka kai tsaye yanzu sai an shirya ta kima godema Allah don kila kina da tsari ne a jikin ki da har kike iya tsayawa ki mayar mata da amsa kai tsaye. Wallahi da watace ai wane ke dasu madam fa take hurda a kasan nan wanan kungiyar tasu ko mutum da ransa akace zasu iya birnewa ba abin mamaki bane gare su don tsafin su. In Allah ya yarda tama zasu barki mu zuba dani da shegu ai sun sani na san su ba yau ba ko wani kallon gani gani tayi maki kada kiji nauyi ko kunya kirani ki fada min karta san kar dani dasu. Jin ta kawai nakeyi ban iya yin magana ba don mamaki nake na yadda mata a wanan zamanin suka dauki yin asiri kamar wani ibada can gare su. Kamar tasan abinda nake tunane a raina tace yanzu idan kina son zaman dakin auren ki sai da yan dabaru wallahi don da kinyi sake yanzu wace ta iya zata zo ta kwace maki maji kina ji kina gani ba yadda za,kiyi babban abin ke dai kawai ki dage da addu,a sosai da zan baki da kuma yawaita sadaka ga mabukata da dai sauran aiyukan Allah da zasu iya tsare ki daga duk wani abin ki. Nasan abune mai wuya ki iya yin su anan to zaki iya bada kudi gida ga wanda kika yadda dashi a dinga maki wa yan nan abubuwan a saukake. Na gode naji bakina yana furta mata tare da dan marairaice da zama a gaban manya tana mikewa take fadin bari ma in tashi don kila ba lalai bane ku dawo ta nan din don naji kunce gurin gyaran jiki zaku tafi. Wardrobe din kayan ta ta bude tayi tone tone a ciki tare da fito da wani jakka ta dawo ta zauna tana fadin ba fa a wanan kadai zaki dogara ba khadija. Ya zama dole yanzu ki nuna ma mijin ku kin fi kowa damuwa da damuwan shi kallon ta nayi don son karin bayani tace eh na farko shine ki kula da kulawan shi kin dai san abinda maza suka fiso gun matan su. To kiyi kokari ki fahinci may ye weak din ita wanan matar a gurin shi sai kiyi kokari ke kuma ki toshe girin da halin ki na gari da zai sa yaji ba wata sai ke a gare shi. Ko akwai asirin wani lokaci har da sakacin mu na mata hakan ke yawan faruwa ga mace cin shi shan shi fitar shi da uwa uba kwanciyan ku ya kasance ke naki sallon yazo a daban gare shi. Maryam da tai kasake tana sauraren mu tace Allah yasa tayi kin ganta nan anty ba abinda ban lurar da ita ba akai. Anty tace rufa min baki ai duk kun ne kema ba a garin sakacin ki kika bari bayaleraba ta kwace maki mijin da tun kuna yara kuke tare ba. Kinji khadija don Allah badon niba kiyi kokari ki gyara auren ki idan ya dawo inji wayan alheri bana na kasa anty ba don wallahi bani shiri da macen da ke da sanyi ga mijin ta . Dariya nayi lokacin da take magana ina jin wani irin nadama na shiga raina yanzun kan na shirya yaki akan mijina ta kowani hali yazo min. Ba wasu abubuwa ne masu yawa ba sai dai ta fada min abinda ta ban shu,umai ne a gurin aiki da kariya ga jikin mutum. Dan haka nayi mata godiya sosai tare da fadin insha Allahu anty zanyi duk yadda kika umurce ni dayi din zan kuma zo maki da kyakyawan labari in Allah ya yarda. Tace sai kin jajirce sosai don akwai yaki babba a gare ki idan buzuwa nan ta fahinci mijin ki ya mayar da hankali a gare ki yanzu don haka banda sakaci da addu,a ko yaushe. Nace insha Allahu anty na gode na saka abubuwan a jakkana mukai sallama da ita muka fito zuwa wurin gyaran jikin. Daga kaina jikina har zuwa kafafuwana sai da suka koma sol don gyaran da suka samu maryam da yan saloon din sai faman wasani suke yi. Mun gama muka dawo gida da yamma lis tun a waje muka sayo abinda zamu ci mu kwanta don ma Friday duk kan mu ba mu shiga school ranan. Ba wani magana kai tsaye wurin na muka nufa yatin da wa yanda muka sama a folon suka biyo mu da ido caaa a kan mu. Maryam ne ke rada min cewa suma shegu sunga canji yau gare ki dama ko yaushe haka kike wanan gyaran jikin kina dada ruda yar iskan buzuwan nan da bata iya gyara ba kullun cikin shadda doga ga zani. Na shiga bayan na bude part din ina fadin ke maryam banda kishi wallahi kin san haka shigarsu take shada suka ba amana a kasan su sosai. Tace yanzu wake ta shada komai kwalliyan shi ke nifa bakiga haushin da kika bani ba dakice masa baki son lefen da zai maki baki san irin hasaran da kika tabka ba wallahi. Nace shima baida niyar yi don kada ran matar shi ya baci ne kinji rabu da dan rainin wayo kawai tace dani Allah khadi kin ki bada hadin kai ne da ba karamin abu zaki tara a wurin shi ba. Tsuki naja nace mata ke wanan ya dama don ni abinshi baya gaba na rokona Allah shine ya barni in aiki in more ma kararuna don naji ya fara fadin ko nayi karatun ba aiki zai barni nayi ba. Aa ya dai fada ne kawai amma aikin ku ai yana da kyau sosai wallahi karatun ne naku kawai da wahala kamar na likita. Can falo kuma gulma aka kaiwa Nafisa na yadda na gyara jikina kwal dani ta tabe baki tana fadin duk ga banza don iya karta da miji sai gani sai hange. Don ba karamin shiri nayi masu ba wanan karon in batai hankali ba gidan ma gaba daya sai ta barshi shegiya taurin tsiyace gare ta inayi kamar bana yi a kan ta. Sai naga zancin ma nasara sai inga abu ya juye sun koma daran da miji kamar mai iraizai akai yanyala tace wanan wa yasani ko tana dasu ne don kyaunta itama yayi yawa wallahi. Wani kallo ta watsa ma yanyala din don taki jinin taji wani ya furta wai nima ina da kyau a gaban ta ita abinda ta dauko sune kawai kyawawan mata a duniya. Da sauri yanyala ta gyara zancenta don ganin ran uwargijiyar tasu ya baci ga maganan ta tace komai kyaunta ai a gaban ki mumuna take don kin dara ta ga komai wallahi ina ma za a hada tsarin ku da ita. Bata ganni ba taso ta gannin din taga abinda su yanyala ke ta yabo a gurina tace yanzu shigiya na san ta hau akan zancen cikin nan dake jikina. Da nayi wauta don na tashi zubar da shege ne don ban yarda in tsufa yanzu kan haihuwa madam ce ta kawo shawaran na barshi ko don amaryan nan na samu makami a kanta. Waahe gari karfe shidda na safiyan jumma,a ya iso gidan lokacin muna kwance don ba zamu shiga school ba a ranan. Mun sakata muna barcin mu tun bayan da muka tashi mukai sallah muka koma gado ni a kasa ma nake kwance a inda na idar da sallah. Bugun kofan da akeyi ne ya sani tashi a gigice ina kallon lokaci tare da mamaki a iya sani na ko zamu kai wata daya bamu bude dakin ba ba mai buga muna shi a wanan lokacin. Jin dukan kofan yayi yawa na mike ina saye a cikin bakar doguwan rigar da na saka jiya zuwa sallon da a suba da zanyi sallah na dauko shi na kara sakawa a jikina don nasan baida matsalar komai. Fuska a daure na bude kofan cikin hasala tare da shirin taron abinda akazo min dashi tunda farar safiyan nan haka. Shine a tsaye a bakin kofa yana saye da rigar sanyi a jikin shi tare da zura hannayen shi a aljihun wandon shi yana min wani irin kallo daga inda yake dan diriricewa nayi don banyi expectig din ganin shi a wanan lokacin ba. Ganin kallon mamakin da nake mashi ya dan sake murmushi bansan lokacin da nace mashi sannu da zuwa ba. Tsaye yake har lokacin yadda yake yana kallona tare da fadin irin taron da zaki min ke nan a kunyace nace wani irin taro kake so kuma hannayen shi ya ware min tare da fadin come on my friend give a hug cikin wani tako na kai gare shi tare da shigewa jikin shi ya mayar da hannayen shi ya dora a jikina yana maida numfashi. Wani irin abune ya ziyarci jikina kamar shock a lokacin nima numfashin nake saukewa jinayi yana rada min kiyi a hankali fa kin san amare tsotsayi gare ku. Nace amare ai suna inda suke dashi zaka fara kuma ko ya kara matse ni a jikin shi yace au daga fadin gaskiya kuma kokarin jayewa nayi daga jikin shi amma sai naji ya kara matse ni gam a jikin shi a hankali na ce mai kafa san maryam tana nan. And so what idan tana nan zata hanani rungumar matana ne komai maryam kuma ba ruwan ta kin sani to nidai sake ni tarbon ya isa hakana nace tare da kara kokarin zare jikina daga nashi. Khadija kina da tausayi kuwa kwana nawa ban ji kamshin ki ba yanzu kuma shine zaki min rowar shakar abina halin maza dai wa ya sani ko kana can da wace tafi mu kamshin bamu sani ba Murmushin nan nashi naji yayi tare da sakeni yana fadin wanan kin san ba halina bane don da akan ki zan fara tunda ke kika fara koya min soyayya. Baya naja na fara tafiya tare da fadin wani sabon magana ni din nan har yaushe na shiga rayuwan ka da zaka fadi haka yace tun a ranan da na fara ganin ki falon hajiyan mu ai kika so ki bata ni. Dariya abin yaso bani sai dai na kumay dariyan a cikin raina falo muka iso ya zauna saman kujare da kyat yana fadin kiramin maryam mu gaisa nace barci takeyi yanzu nima shi nake ka tasheni. Yau baku shiga school din ne ya tambaya cikin kafe da idanuwan shi nace yau muna up dukan mu sai dai gobe ita ta dan shiga. Zama nayi tare da fadin kun dawo lafiya yaya hanya yaya jamma,an can yace suna gaida da ku cikin wani irin kasalalen murya tare da fadin ina son in watsa ruwa in samu abinda naci tun two na ranan jiya rabon da in saka wani abu a cikina. May zakaci yanzu na tambaye shi yace duk abinda ya sauwaka zanci don yunwa nake ji bansan wanda zai bani abinci ba a cikin ku. Shiru nayi ina kallon shi tare da fadin kada nayi ma wani abu yanzu ya zama laifi a gare ni kuma don abin laifi bai wuya a gidan nan. Don kin tare ni da abinci kuma sai ya zama laifi tunda ba bani za ayi ba idan baki ba madin sai dai in zauna da yunwar hakana. Nace to bani yan mintina kafin kafito wanka in hada maka amma sai dai in a nan zakaci don banson abinda zai iya kawo rigima daga dawowan ka yace ba matsala indan har zan samu barin je in watso ruwa in fito kafin nan kila maryam ta tashi. Fita yayi da mamakin sauyin da ya gani a fuskana a tunanen shi baiyi zaton samun taro haka a wurina ba. Sai gashi yaga sauyin da bai tsamana ba ya samu a tare dani a dan lokaci kadan yaga gaba daya na sauya mashi ga komai . Wanda ganin nawa ya kara sashi a wani hali da nauyina da kunya kuma na yadda ya kasa cika min alkawarin aure a kaina. Yasan ya rageni da abubuwa da dama da suka shafi aure wanda daga cikin babban abin da yafi daga mai hankali shine raya sunna ma,aiki da ya kasa yi min. Kuma ban taba nuna bacin raina ga hakan da ya kasa aiwatar min ba bai taba ganin wani akasin kan hakan ba kodai yarinyar nan ta gane halin da nake ciki ne da ita. Dakina shiga inda na samu maryam a zaune tana ganina tace sai naji kamar muryan mijin ki khadija nace ba tare dana kalle ta ba shine ya dawo. Tafiyan dare sukayi ke nan ta fada nace lalai kan tunda kika ganshi yanzu ai kema kin sani yazo min wai yana jin yunwa ne in sama mashi abinda yaci tin jiya rabon shi da abinci. Tace yi maza ki sama mashi barin tashi mu shiga kitchen din don kiyi sauri ta fada tana mikewa daga inda take zaune a saman gadon. Kitchen muka nufa a tare muna shiga nace mata ni wallahi ban ma san abinda zan girka mai ba a yanzu don yace tun two na ranan jiya rabin da yaci wani abu. A, a dole zakiyi mai wani abu mai dan ruwa da zai kama mai ciki don yanzu ba zai iya cin abu mai nauyi ba ke nan nace may zanyi to ? Tace ki dama orth sai ferfesun mai dan kamshin kayan yaji don cikin shi ya bude ina ga zai ji dadin hakan ai. Nace ni ban ma san abinda yafi so da safe ba irin haka bari dai muyi din ko zai so shi nan muka shiga kiciniyar hada abinda mukai niyar yi mashi din. Kafin wani lokaci mun hada tace jeki wanka sai in karasa kafin nan kin shirya taron sa kada ya dawo ya kara samun ki ba shiri. Na dan dauki lokaci a bandakin na fito ina shafa mai saiga maryam din ta shigo tana fadin ta kammala komai in gama in kai mai nace ai a nan zaici don gudun fitinan wanan matar tashi. Tace a,a ita batayi ba kuma anyi mai tace zatayi fitina a ka ida ma idan bakece zaki karbi girki ba yau ki kwana dashi to yazama dole kece dashi har zuwa yamma. Nace su ka,ida suke bi kedai kawai ayi shani maryam wai an cuci na kauye duk da hakan mudin ta gashi nasan akwai rigima wallahi. Tace wani rigima zatayi kuma ga yadda abu yake don nasan da wuya ta bar maki shi ya kwana a wurin ki gaskiya yana da wuya nace mata. Na sake cewa ai barta kin kawo min point idan zatai masifan ta ga wanan maganan naki zan dogara don wallahi yanzu kika fahintar dani na tuna haka din ne. Shiryawa nayi cikin wasu lace brown dinkin buje da riga kayan sun matukar karban jikina sosai maryam tana gefe tana kara gyara min inda baiyi ba tace barin je in wanka in je gida in karbo maki abinda anty tace zata ba da sai dai kafin in je barin dan tuntube ta a waya muji ta kirata tana fada mata dawowan shi tare da tambayanta ko abinda tace din ya samu tace tazo ta karba jiya da dare aka kawo mata abin. Har maryam ta fito ta shirya zata fita a lokacin ya shigo part din saye da wandon jeans baki da rigar t-shirts ja mai guntun hannu fuskan shi dauke da annuri askin da yayi a can ya fitar mai da kurciyar shi a fili. Ganin maryan yasa ya dan sake murmushi tare da fadin a maryam kin tashi ashe mun samay ku lafiya itama yi mashi sannu da zuwa tayi. Bayan sun gaisa na ya fara mata godiya tace ba komai wallahi tace dani tana zuwa zata fita yace maryam ina kuma zaki tace zan dan karbo abune nan in dawo yanzu. Adawo lafiya yai mata tare da mayar da hankalin shi a kaina yana fadin masha Allah gaskiya nafi kowa more mata a garin nan irin wanan kwalliyan haka duk ni akaiwa shi. Dan harara shi nayi nace zaka fara zolayan ka ke nan ni a kaina nayiwa ba kai ba don kasan dama ni haka nake a cikin kwalliyana ko yaushe. Zaiyi magana nace malam yunwa fa kace kana ji kuma ka tsaya fadin abinda ba a tambaye ka ba. Yace za a hanani kallon matana ne ko may nace matan ka dai suna inda suke ni kan ai yar kanwar kace kaima ka sani. Zama yayi a saman dan dining table din dake falon na shiga kitchen cikin wani tako na fara fito mai da abincin na jera a gaban shi har lokacin bai kara magana ba ya soma ci. Annurirn fuskan shi dai naga ya sauya ya zauna yaci abincin sosai sai da ya kusa kammalawa sai ga Nafisa a part din babu sallama kamar kullun ta tsaya a kan shi tana fadin. Samad kai wani irin makirin mutum ne yanzun ma daga dawowan ka ka sudada kazo nan wurin karuwan matar ka tasaka a daki tana maka karuwan ci data saba yi ma. Nafisa kin san may kike fada kuwa matar tawa ta sunna zaki kira da karuwa a gaba na tace in ba karuwa ba may take da zata tura ka daki tana baka abinci yanzu anan. Alhalin kaida ita kunsan ba itace da girki ba yau kafin yai magana nace hakane fa na manta afuwan don Allah bani ke dakai ba yanzun sai anjima da yamma nake dakai. Sororo yayi yana kallon mu cikin wani huci tace dani karya kike karamar yar iska nice da girki yau don ko Allah yace idan miji yai tafiya ya dauki kwanaki ya dawo ya sauka a inda yake so. Nace kin yarda ke nan ya sauka a dakin wacce yake so yanzu ko sai ki zabi guda ko yanzu din ko sai anjima da yamma in sakar maki shi yanxun kuma ya zama mallakina. Ke makirar yarinyace wallahi tanan kuma kika bullo watau nace ai kin san haka abin yake tunda shigan safe yayi yazo inda yake so sai ki barshi ya huta da abin kaunar shi ko kuma ya tashi anjima din ni in karbe shi don haka take gare ni ko ina ta fada rataya ne. Samad kana jin abinda take fada ba zakai magana ba yace ai gaskiya kuka fada dake da ita yanzu sai ki zaba wane kika su yanzu din ko sai anjima kamar yadda tace. Makiri kawai macuci ai ba haka ka saba yi min ba yanzu kuma wani sabon yaudara ka dauko don ka samu sakewa da wanan karuwan yarinyar. Mikewa yayi tsaye yana nuna ta da yatsa yace ke bari kiji duk ranan da kika kara aibanta min mata da wanan kalman a gaba ranan ko maigarin garin ku bai kwatar ki a wurina wallahi. Ki bace min dagani anan ke wace irin mace ce da baki son a zauna lafiya ne wai ko na tsaya awurin naki yanzu wani abu zaki tsinana min haka. Kutawa tayi tana fadin zaka shigo hannuna wallahi zaku raina kan ku dakai da ita dani kake wasa wallahi bana ba da bashi ka sani ta juya ta fita rai a bace. Bai kara magana ba nima ban yi ba sai ci gaba da cin abincin sa dayayi ya kusa gamawa ne wayan shi yai kara ya dauka naji yana fadin barin in fito yanzu. Ashe kayan shi ne ya iso da Yusuf ya kwaso masu a airport ya fita ya gani idan sun cika ya barni ina tattara kayan maryam ne ta shigo nake fadin har kin dawo. Tace zan zaunane na sani ko da ranan nan komai ya kan kama yadda ake so da sauri nace mata ke kamar wasu jarabbabu can tace may za a tsaya jira idan ya nemi ki bamu san inda sa,a yake ba fa ko anan za a dace komai ya wuce. Dariya nayi mata daki muka shiga taimin bayanin komai wani dan ruwan turare na a cikin wani dan kwalba wai shafawa kawai zanyi a jikina na bude na sunsuna tare da dan gogawa inji kamshin shi a jikina. Dakin ya dauki wani irin kamshi sosai na mayar da kwalban na rufe na bude wardrobe dina na tura a jakkar dana ta nada don irin aje siri din nan. An dan jima mukaji ana shigo da akwatina a falon fitowa nayi don ganin may nene a ke shigowa dashi din naga set din akwatina ne garadan gidan ke aje min a falona. Kallon maryam dake bayana nayi ita ma ta kalleni tare da fadin ayyuririii yau lefen mu ya iso ke nan can sai gashi ya shigo part din yana fadin maryam ga lefen ku nan na sawo muka acan sai ku duba kuga abinda ban saka aciki ba kuyi min magana. Maryam din ta samu bakin mashi godiya ta isa wurin kayan nikan komawa nayi kuryan dakin nawa biyo ni yayi ciki yana fadin. Deedar ko ba irin wanan kike son a saya maki bane naga baki tsaya kun diba kayan ba juyowa nayi da niyar mashi magana ashe ya iso inda nake sai maganar nawa ya sarke jinshi danayi a jikina. Deeadar wanan wani irin turarene haka mai kamshin dadi kika saka don Allah turare ne kawai mana ni ban ji kamshin shi ba nace. Kara jawoni yayi zuwa jikin shi yana dan sunsuna jiki tare da lumshe idanuwan shi da naga sun sauya sunyi ja dasu huging dina yayi sosai a jikin shi tare da fadin kamshin yayi min dadi sosai wallahi. Na gode nace ina kokarin kwatar kaina daga rikon da naji yayin kamar wani zai raba mu a lokacin shiga aika min da kiss yayi kamar wani zarare dakyat na iya bude bakina nace mai kasan dai maryam na dakin nan ko ? Nasani kuma sai akace may yana kokarin yin wasu abubuwan can na daban maryam na kwalawa kira yai saurin sakina da sauri ya fita daga dakin bai ko juyo ba. Yana fita maryam din ta shigo dakin tana fadin lafiya na shiga uku maryam kardai ace turaren nan har ya fara aikin sa ne bakiga irin yadda yai min ba yanzu wai kamshi turaren yai mai dadi. Tace an fada maki anty hauwa ta wasa ne tana dariya tace ai shi yasa kikaga na matsa inje in karbo don ba abin mamaki bane yau din ta lula kuma wani wuri ta manta damu. Wayana dake saman gado ne yai ringin na dauka shine a layin yake fadin kizo ki samay yanzun deedar a dakina please. Tsaro naji na kallo maryam a firgice ina fadin kinji abinda yace wai inzo yanzu in samay shi a part din shi tace welldone anty maggi ya haukan zabo ke nan yarinya yau kin shiga hannu. Don Allah maryam ki bari wallahi ni tsoro ma nake ji wanan wani irin shu,umin turare ne haka mai karfi tace jeki don Allah kada ki bata mashi lokaci kin ji . Ban bar dakin ba don shirin da maryam din ke min sai daya kara kirana kusan sau biyu ban dauki wayan shi ba wanka na sake yi tare da sauya kayan jikina zuwa simple dongon riga daga cikin dogayen rigunan da ya zuba min a kwati ta dauko guda. Ni kaina sai dana ji ko ina nawa ya canza a lokacin mara na kamar zai tsage don sai danakai awa daya da kusan rabi zauma nayi saman gado ina kallon kaina tare da fadin wallahi maryam tsoro nake ji ba zan iya zuwa wurin shi ba yau. Tace haba khadija mijin ki ne fa may ye na kunya ko tsoro don Allah ki daure kije ki bar daukan ma kanki zunubi haka tunda dama ya samu yanzu. Har falo ta rakoni tana min dariyar keta hakana na daure dai na fita tana fadin yau kan yau ne Allah ba da hassan da hussaini. Ina fita tasaka ma kofan key don tsoron gidan da takeyi gani take kamar za a shigo a rutsata a cikin dakin ne akwai mutane a falon ban bi ta kasu ba na nufi part din nasa. Na samu zai sauko ya kara biyo ni sai gani ya sauke ajiyan zuciya tare da rike min hannu muka shiga ciki muna shiga ya juyo yayi wa kofan key. Ina tsaye ina kallon shi nace dashi yaya haka baiyi magana ba sai kara rike min hannu da yayi muka nufi saman gadon da dama a gyare yake tin ranan da yace zai dawo na gyara mai bai kuma dawo ba. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Assalamu Alaikum yan uwa makaranta novel dina ina mika godiya na a gare ku akoda yaushe a bisa da goyon bayan da kuke bane har kullin ina alfari da ku yan uwa. Wace kuma ke fitar min da novel ubangiji yasa ta gane nauyi da da sakacin da tayi da kallaman da tai wasa dashi wanda ko ba dan musulmi bane mutum aka hadashi da darajan Allah da Annabi yasan girman su da mutucin su. Idan tana da rabon gane nauyi da girman wanan abinda take yi Allah ya ganar da ita da gagawa idan kuma ba mai imani ce ba bazata shiryu ba Allah ka nisanta mu da ita. Kallon yadda yake rawan jiki nakeyi wai shine har da rike min hannu zuwa bakin gado mu zauna bayan mun zauna ne yake fadin . Ai niyata inje har dakin in dauko ki tunda kunyan zuwa kike yi ke, da sauri nace haba dai sai kace kafi kowa yace nafi kowa may ? Dukar da kaina nayi na kasa kallon shi don ban iya jure ma kallon da yake min a lokaci ban yi aune ba naji hannuwan shi a saman jikina yana kare rugumay ni cikin jikin shi. Tare da dora fuskan shi a saman kaina yana shakkan kamshin gashin kaina da yasha gyara jiya naji ya kai hannun shi saman kitson yana tambayana hannu ne yai maki wanan kitson ko injin. Dariya sosai abin ya bani dole sai da na murmusa kadan a cikin raina kitson kan nawa naji yana dan wasa da shi a hankali. Da sauri na rike mai hannu don yarda nake jin tsikar jikina yana tashi a lokacin nace don Allah ka daina min haka kabari in tafi . Ina fadin haka kamar wanda na tunzura shi ga abinda yake yi din juyo ni yayi muna fuskantar juna dani dashi da kyat na iya furta mai don Allah dai ka bari kaga rana ne yanzu kada wani ya shigo ya samay mu haka fa. Kamar na kara masa karfi ne a lokacin a hakali muka fada saman gado daga inda muke tsaye din ina jin yana kokarin daga min rigar dake jikina ya kasa don jikin shi da ya dauki rawa a lokacin. Na sake yunkurin fadin don Allah ka bari mai nene haka wai kake, , , , shiiii naji yace tare da dora bakin shi a cikin nawa. Yayin da hannun shi ke safara a jikina tun ina zillewa har na rasa kuzarin yin mashi gardama ya samu ya balle aninan rigar take kirjina ya baiyana a fili. Don maryam ta hanani saka komai a jikina bayan rigan da na saka kawai a lokacin gaba daya naji jikin shi ya dauki rawa da ganin kirjina da yayi. Tun yana aika masu sako da hannayen shi har yakai bakin shi sama take wani yanayi yasani bankaro mashi gaban nawa da ban san nayi hakan ba gareshi. Yadda kika san kossashen dan akuya yana tunin ko tsutson nonon uwarshi haka AA ya sani a gaba yana tsotsewa. Ban san yaya akayi ba sai da naji wani irin zafi mai kama an dora min reza ana yanka min karkashi na ya sani sakin ihun da ban shirya ba a lokacin. Da sauri ya manna min bakin shi a cikin nawa ya hana sautin ihun fita a fili ji nayi kamar an dora min nauyi duniyar nan akaina don wahalan da nake sha. Tun ina kukan wahala da sai hawaye ke fita a idona har nagaji na sake lankwas ina hadiya;wahala a raina bai san ina yi ya rude kamar tsohon driver da ya samo tsohuwa akori kura yana tuki , Sai daya gaji don kan shi ya kyale ni lokacin ba komai a idona sai ambaliyan hawayen da ke fita min a idon nawa na wahala. Kallon fuska na yayi daga inda yake kwance tare da dan kai min kiss saman goshina har lokacin yanayin shi bai dawo daidai ba. Deedar ya furta a can kasan makoshin shi zaka ce bashi bane ya kirani a lokacin dan yana a ciki wani irin yanayi da shi kanshi ba zai ce ga yadda yake ji ba. Ban iya yin magana ba don baki na ya mutu a lokacin mutus daga furta ko wani irin kallama ganin ba zan amsa mashi bane naji ya mike yana barin gadon . Duk da idanuwana suna arufe bai hana in gane bathroom din dakin nashi ya shiga ba don jin karan kofan daya bude din. Sai lokacin nayi kokarin bude idanuwa na dake rufe a hankali gani na danayi naked ba komai a jikina rigan da ke jikina yana yashe a kasa. Nayi saurin rufe idona ina tattaro bargon gadon dake ture a gefe na ina rufe jikina dashi don kada ya fito ya kara samu na a hakan da nake. Ya dan dauki lokaci a ciki naji fitowan shi daga ban dakin inda nake kwance ya nufo da tawul a hannun shi ya yaye bargon ya rufa min tawul din. Zama yayi a bakin gadon tare da jawo ni zuwa jikin shi yana fadin haba deedar kukan bai isa haka ba kada ki jawa kan ki wani ciwo kuma fa. Tashi kije kiyi wanka ki zo muyi magana ban motsa ba a yadda nake muryan shi naji yana fadin ki daure ki tashi please kin san zama da janaba bai da kyau ga addini da haka kuma ga lafiyan ki. Hakan da naji yasa ni yunkurin motsawa daga inda nake sai kuma na tuna da yanayin da nake ciki na koma na kwanta tare da kara jawo tawul din ina rufe jikina da kyau. Ya fahinci abinda nake nufi din sai naji ya sake murmushin nan nasa ya saka karfin shi ya ture tawul din tare da dagoni gaba daya ya nufi bathroom din dani. Na samu ya hada min ruwa a kwatamin wanka shiga nayi a hankali gani ban son zafi ko kadan amma ba yadda na iya haka na daure na shiga zafi sai ya zamay min ina jin dadin shi a karkashina. Na fita na tsiyaye ruwan tare da zuba wani na kara gasa jikina dakayau naji dasin hakan da nayi na fito nayi wankan tsarki kamar yadda na koya a isilamiyan mu wanda kusan na iya tunda ina na haila. Yadda zan fito dagani sai dan tawul a jikina nake ji ba yadda na iya haka na daure na fito daga ban dakin na samay shi ya kwanta tare da kura ma kofan ban dakin idon. Jinayi kamar in koma ciki sai dai na daure na nufi rigana da na bari a kasa yanzu ya mayar min dashi saman gadon. Dauka nayi na saka a gurguje na na nufi gurin mirrow shi na shafa man da nagani a wurin ba tare da na tsaya karanta sunan man ba don gudun bushewar jikina. Muryan shi naji yana fadin ai da baki maida rigar a jikin ki ba sai idan zaki fita don yanzu kwantawa ya kamata kiyi ki samu dan hutu nima in kara watsakewa daga gajiyan da kika saukar min. Ban tanka shi ba sai kokarin daura dan kwalin da nake a kaina don sanyin kan yana shiga jikina a lokacin. Ya sake fadin wai haka kike nufin zaki fita da wanan tafiyan da kike yi ai sai mutanen gidan su gane abinda kika zo kikayi a dakina wanda kike boye masu. Hararan shi nayi tare da fadi nine ma na sauke maka gajiyan ba kai ka dora min ba yace mun dai dorawa juna ko ? NAFISA Zaune suke a falon madam tun da safe da ta fita daga gidan don karbo abinda za a hada mata wanda zataiwa maidagida amfani dashi da dare. Matar da ta kawo masu kayan tana ta kokarin hada sauran kayan da basu dauka ba a gurin ta wanda da shegen tsada ta sayar masu dashi. Nafisa dake zaune a kasa tana kallon kayan ne taja wani irin uban tsuki tana fadin wallahi madam na tsani in bude ido inga shegiyar yarinyar nan a gidan nan wallahi. Yadda na tsani mutuwa na haka na tsani wanan yarinyar a rayuwana ban son inga tana kusanci da samad hankalina tashi yake wallahi. Haba Nafisa komai fa a sannu ake bin shi keda aka rike ma kan maciji kina wasa da bindin shi samad ya rike maki komai daga miliyan daya zuwa dari idan kika bukata zai maki maganin shi a take. Ga Namando shi kuma tsaye a kan lamarin ki yana maki aikin komai a tsanake zama fa kawai suke amma ba wani moriya a garesu sai dai gani sai kuma hange. Dariya sukayi suka tafa hannayen su tace dazun kin san wai ita yar iska makiran yarinya ban fito gidan nan ba sai da suka bata min rai ita da samad. Nan ta koro mata yadda mukayi da ita da sauri madam tace ke wani kika zaba a ciki tace kema ai kin sani. Ina zan zabi zama dashi da ranan nan nabar banza dashi ta yuni tana kallon shi kamad hoto yadda take so niko sai dare yayi ya tsiyaye min abinda ya adana kwana da kwana ki a jikin shi. Wani irin shewa suka dauka tare da fadin kinyi daidai mutumiyar ai babu abin haushi ga kishiya ko ta kwarai ce. Ace miji ya dawo bai sauka wurin ki ba sai a gurin yar uwarki ranan da bakin ciki take kwana don tasan duk wani gajiya anriga da an sauke ma yar uwarta shi sai dai ta samu ragowa saura. Mai maganin ne tace balle wanan abinda na baki yanzu ai sai dai ta sha takaici koda ya koma a wurin ta don haka zai jita salaf kamar miyar da ba maggi a cikin sa. Shewa suka dauka tace nasan tana can yanzu ta tasahi a gaba kamar hoto don babu abinda zai iya tsinanawa yar banza. Madam tace yarinyar nan tana da dan banzan wayo shiyasa ake gudin auro mace mai ilimin da ta dara ka don komai wayon ka sai ta dan munafince ka gun miji. Haka nake karantowa gun wanan yarinyar don wanan tarkon da muka dana mata na zancen cikin jikin ki ban dauka zata tare shi da mutunci ba har tana fada akan shi. Kyale yan iska dani suke zancen komai jarabansu sai dai sukali juna kamar photo don ko hannun ta ba zai rikaba in tace naci ta iya yaya muka kwashe da fati a baya. Wani irin dariya suka sa sun dade suna tataunawa kafin ta mike tace zata gida taga rawan kan yar iska don sai haka din a tsakanin su. Har waje mota madam ta rakota tana kara mata bayanin yadda zatayi da maganin da ta karba din tare da fadin sai mun sha labari da safe mutumiyar. Ta iso gida a gajiye a falo ta zube nan yaranta suka rufa mata suna tambayan ta abinda da ta sayo masu tace ba ta tsaya ba sun rufa ta suna lalaban jakarta inda suka ga babu komai a cikin jakar sai ledan maganin da ta shigo dashi. Yanyala da su Samiha suka fito daga dakunan su suna gaida ita da dawowa bayan ta gaisa sun zauna take tambayan su samad ya fita ne ko yana gun yar iskan nan har yanzu. Yanyala take cewa da ita ina ganin baya gidan nan fa don tun safe banji duriyan shi a gidan nan ba tace nasan ai ba zai zauna yasha takaicin yar iska ba tunda ta hana shi ya wala inda yake so. Hira suke tayi a gurin har akai kiran sallah azahar basu mike ba don sallah dama baya damay su bane. KHADIJA Can cikin barci nake jin agogon dakin na nuna alaman biyu tayi tashi nayi a wahalce ina kallon yadda muke kwance dashi . Duk rabin jikina yana manne da nashi kokarin zare jikina nake a cikin nashi ya bude idanun shi tare da sauke su a kaina kawar da kai nayi gefe ina fadin lokacin sallah yayi fa. Har lokaci yayi ya fada yana kokarin kallon agogon dake dakin yace shiga ki fara alwala sai kin fito zan shiga. Adakina zanje inyi na bashi amsa ina kokarin sauka a gadon yace bari ki dan kara gasa kanki anan kada ki fita kina wanan tatatan ana kallon ki. Mikewa nayi na sauka daga saman gadon na nufi bandakin don shawaran kwarai ya bani nayi kamar yadda yace na fito na samay a zaune yana dakon fitowa na tare da fadin akwai hijjab a wardrobe dina ki duba ya fada yana mikewa daga saman gadon. Kallon mamaki nake mashi yace kina mamakin hakane na tanadar maku shine don gudun hakan gashi kuma yai muna amfani ko ya fadi yana wani kashe min ido. Shima shiga yayi ya dauro alwala ya samu har na tayar da sallah ina nafila ina idarwa ya jamu sallah . Mun idar muna addua sai da ya shafa naji muryan shi yana fadin Deedar ban san godiyan da zan maki ba ga wanan tanadin da kikai min wanda na amsa a gurin ki yau. Fatana Allah ya bamu zama lafiya a tsakanin tare da samun zuri,a masu albarka da fahintar juna a cikin raina na amsa da amin. Deedar nasan kinyi hakkuri dani wanda ba kowa ce mace ne zata iya irin abinda kikai min ba batare da anji tsakanin mu ba. Ina son ki kasance da wanan hali naki na hakkuri da rikon amna ki bani hankalin ki don yanzu lokaci yayi da zamu fahinci juna dani dake . Deedar kin fi kowa sanin ina son ki don da ban son ki ba zan kawo ki gidana mu zauna tare ba duk da kalubalin da nasan zan samu a gurin ku. Ina son ki sani ni ba mutum bane mai son yawan hayaniya amma sai Allah ya hadani da mata masu son rashin zaman lafiya a gida. Zanso ace kin san ko waye Nafisa yanzu da yan uwanta dake gidan nan wanda kulun a cikin kwaso min su take sai dai idan bataje garin su ba. Don Allah kiyi hakkuri ki yaki zuciyar ki ki kawar da idon ki akan alamuran su ki dan bani lokaci har zuwa lokacin da na gama shirina akan su. Ya kare da fadin ina fatan kin fahinci may nake nufi da magana na kai na gyada mai tare da fadin insha Allahu zaka samay ni mai biyayya ga abinda ka umurce ni dayi matukar ba shiga harkans sukayi ba wanan kan ban maka alkawarin shi ba don zan maida martani akan hakan. Yace wanan kina da daman yin hakan mudin kina da gaskiya akan maganan nima a shirye nake da daukan mataki akan hakan. Dan shiru ne ya biyo baya ya gyara zama yana fadin yunwa nake ji zan dan fita na samo muna abinda zamuci don kin sa ni yau cin abinci sau biyu a wuni. Hararan shi nayi ina fadin nasan maryam zata girka muna abinci tunda taga ban fito ba har wanan lokacin. Kai maryam tana da kirki sosai wallahi tun farko na karance ta da tana da matsala da tuni na rabaki da ita ai ba kamar waccan kawar taki da na taba gani ba yar garin ku. Mikewa nayi ina gyara dankwali dake saman gado ina kokarin daurawa a kaina nace ni zan sauka sai ka fito. Yace kibi a hankali don kin san idon kowa yanzu a kan ki yake kamar in ce dashi kai kuma kana tsoron hakan ne sai dai na wuce ba tare da nayi mai magana ba ina tunane a raina. Ba dama mutane su sake a gidan ke nan mutum yayi abinda yake so sai idon jamma,a ya sauka a kan shi kamar gidan haya. Karan bude kofan danayi ne ya jawo hankali su a falon suka bi hanyar stairs din da ido a hankali nake saukowa daga saman yayin da idanuwan su yake a kaina. Fuskana ya nuna daga barci na tashi a lokacin har na sauko basu dauke idanuwan su a kaina ba tare da kallon yanayi na. Ban kula su ba nazo na wuce su tsuki naji aje tare da jin muryan nafisa na yare da yan uwan ta banji may take fadi ba don ba yaren nake ji ba nasu. Na dai ga ta mike a fusace ta nufi saman ban tsaya ta kanta ba na shige part dina inda na jishi a rufe gam kwakwasawa na tsaya yi abinda ya dan dakatar dani a wurin ke nan na dan wani lokaci kafin maryam ta bude kofan. Tambaya ta tsaya yi nace don Allah bude nice matsoraciya ta bude tana dariya na shige ta mayar da kofan ta rufe. Wani kallo take min ban tsaya ta kanta ba na fada kan doguwar kujeran dake falon ina fadin maryam kin cuce ni yau wallahi. Dariya ta koma sakewa tare da guda tana fadin amarya ta ango yar shagali yar biyan bukata yar garali makulin mota ke aka ba harara na aika mata tare da fadin. Idan ba a bani makulin mota ba ai an bani na wahala daga haka na mayar da kaina saman kujera tare da kara hannuna saman fuskana. Don wani yanayi nake ji na zazzabi nason kamani a lokacin in kawo maki abinci kici ne kai na girgiza mata tare da fadin banjin cin komai yanzu wallahi. Shidai yace yana jin yunwa yanzu zai sauko yazo yaci yace daga haka na rufe idona dan ban son yawan magana a lokacin. Zama tayi tana fuskanta tare da fadin wallahi yau kun burgeni sosai wallahi ko ba komai mun nuna ma buzuwa karya take wallahi. Allah ya fita yafi sherin ta sai dai taji a salansa yanzu kan shetin ta ya kare a gidan nan wallahi daga yau kun zama daidai da kowa a gidan nan abinda bata so ya faru ko. Tana magana bance da ita kanzil ba jin nayi shiru ne ta fahinci ina cikin wani yanayi wasa wasa ko zazzabine mai karfi ya rufe ni a gurin. Kamani tayi zuwa ciki ta rufa min wani bargo tare da tambayana maganin da zansha tasan ban son magani haka kuma allura don haka nake ciwo na idan ya tashi a wahalce. NAFISA Wani irin bugun zuciya take ji a ranta har ta isa dakin nashi ta tura kofan da karfi ta shiga don tabbatar da abinda take zargi da idon ta ya ganan mata. Yarinyar nan wai may take nufi danine a gidan nan duk da hanasun da nayi sakewa sai ta iza min bakin ciki take nufi ko may wallahi bata isa ta walla a gidan nan ba yadda take so. Jin yadda aka turo kofan yasa shi juyowa da sauri yana kallon kofan yaga mai shigowa don bai tunanen nice na dawo a lokacin. Ganin ta yasa ya daure fuskan shi don yasan abinda ya kawo ta ba alheri bane bai wuce taga fitowa na daga dakin ne tazo masifa. Idon ta a saman gado ya sauka ta ga yadda gadon yake sequzing ya nuna alaman wani abu ya faru saukin abin ma data gani mun canza zanin gadon kafin mu kwanta don sai dana matsa mashi ya yarda na sauya tare da taimakon shi. Samad samad mai idona ke shirin gani ta fadi tana karasowa a cikin dakin cikin wani irin yanayi na da bata san inda kanta yake mata ba. Samad dama kana dakin nan tare da wanan shegiyar yarinyar a gidan nan ban sani ba may idona ke son nuna min ne wai ? Yace abinda idon ki ya nuna maki haka ba matana bace matar wani ne kikaga na kebe da ita komay ? May kake nufi da maganar ka yace yadda kika dauke shi kinga ban son wanan shirmay naki idan shi ya kawo ki ki bace ki bani guri hutu nake so yanzu. Ido waje take kallon shi tare da fadin watau hutu ma kake so yanzu may kaiwa yarinyar nan yanzu da rana tsaka yace may ake dake idan kin shigo. Bata bari ya kare maganan shi ba ta saki wani ihu tare da fadin karya kake wallahi ka fada min don ban fahince ka ba. Yace may kuma kike son in fada maki uwata banda wanda kika ce idon ki ya gane maki kuma na fada maki hakane. Ya juya yana son daukan wayan shi shaka yaji takai mashi tana fadin wallahi karyane baku isa kuyi komai ba a gidan nan. Juyowa yayi a hasale tare da kwashe ta da mari yana fadin kina da hankali kuwa ni zaki rikewa riga ta baya haka duk iskancin ki na fada maki ya daina zuwa a jikina don zan saba maki. Wallahi baka isa ba daga kai har ita wallahi ita takai wata mace ce da zakace wai ka huta da itane har kana bukatan hutu yanzu. Ta kara yowa cikin shi ya kawaice wa rikon da tayo mashi tare da fadin idan kika taba again zan saba maki a gidan nan. Wallahi sai ka fada min dan iska mayaudari azzalumi watau gani sakarai ashe kana ciki kun kule da ita uwar wa zaka nema a gurin ta. Shine manufar ku na yi min wayau kuce in zabi guda ashe kasan sharin da kuka kulla da ita muna fuka yau zamu hadu a gidan nan ko ni ko ku wallahi . Har ina macen da za a huta da ita a gurin nan mace haka da fari kamar zabaya yace ashe kin san tana da farin bari kiji idan kika kuskura kika taba yarinyar nan yau a gidan nan raki zai matukar baci wallahi. Kamar kada ya fadi haka ta juya a sukwane ta nufi dakina sai dai kafin ta sauka ya riko ta ta baya yana dakatar da ita. Fisgewa take yi tana fadin wallahi yau sai naci uban ta a gidan nan ita har ta isa ta kebe dakai cikin wanan yanayin ta bata min rai. Ko kuwa ne ya kaure a tsakanin su sosai har ya jawo hankalin su yanyala a garesu suka mike da yare suke mata magana akan ta sake shi. Yanyala ta hadashi da Allah ya kyale ta ya sake ta yana huci yana batun komawa dakin shi yaga ta nufi part dina a sukwane ya bi bayan ta. Ina kwance a daki hayaniyar su ne ya falkal dani daga barcin wahalan dana dan samu din maryam ma hakali a tashe take kallona daga inda take a zaune gefe na tana charting. Ina ganin fitina suke akan ki fa khadija nace kyalesu suci kan su ni ba abinda ya damay ni da shirmay su ta kaina nake yanzu na kara jan bargo na rufe kaina dashi tare da lumshe idanuwa na. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU KU SAKANI GA ADDU,AN KU A DAREN YAU DON ALLAH YAN UWA MUSULMAI. 1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Tun ina jiyo hayaniyar su sama sama bandai fita ba har wani barci ya kara daukana na dade ina barcin a dakina. Kwance ya samay ni rijib a cikin bargo na rufe har zuwa kaina sai kaduwan dari da nake yi. Muryan shi ne ya tayar dani a cikin barci yana fadin subbuhanallahi tun yaushe take haka maryam na bashi amsa tana fadin tun shigowanta dakin nan take kwance. Tambayar maryam din ya sakeyi da dama bata da lafiya ne ko may tace gaskiya yau daine ta tashi da wanan zazzabin haka amma lafiya lau muka tashi. Ji nayi yana taba min goshina har zuwa jikina da nake ji kamar garwashin wuta a lokacin ga wani irin sanyi dake damu na. Tallaboni yayi ina tashi da kyat saboda ciwon da jikina ke yi, idanuwa na sun kada sunyi jawur dasu . Wayan shi ya lalubu yana kiran Yusuf tare da fada mashi yazo su kaini asibiti banda lafiya sosai Yusuf din yace subbahanallahi da sauki dai ko yace da sauki ka dai zo yanzu. Ba, a dauki lokaci ba Yusuf ya iso har lokacin yana dakin zaune bakin gadona ya tsura min ido sai tunane yake a zuciyan shi. A hankali ya lumshe idanuwan shi ya fara tunanen abinda ya faru a tsakani mu ya san ba banza Allah ya dora mashi sona a ranshi ba. Don yarinyar tana da wani baiwa da Allah yai mata ta zai amfana daga gare ta ya kara bude idon shi ya sauke su a gare ni ina kwancen ban san inda nake ba nikan a lokacin. Wani shu,umin murmushi ya sake yana godiya ga Allah da ya mallaka mashi ni a wanan ranan ta jumma,a yana godiya ga Allah tare da fatan samun zuri,a masu albarka daga gareni. Karan wayan shi ne ya katse shi Yusuf ne ke kiran shi yana fada mashi isowan shi tashi yayi da sauri ya fita falon maryam na zaune yace ta gyara min jiki muje asibiti. Suna zaune a falo da tawaganta madam na tsakiyar su tana bata magana duka ga fitowan mu daga dakin yana tallabe dani a jikin shi. Ido suka zuba min madam ne cikin kisa tana ganin mu take fadin lafiya kuwa yallabai samad yace bata da lafiya ne zamu asibiti ne da ita daga haka muka fice daga gidan. Kallon Nafisa tayi tana fadin baga irin ta nan ba ashe ma ko lafiya yarinyar bata dashi shiyasa suka shige daki yana jinyar ta. Ke ko da baki da fahinta kishi ya rufe maki ido kina naki haukan kishi haukane wai Nafisa ke bazaki bar abin kunya ba kullun danbe da miji akan kishiya. Yanzu don Allah duba ashe wace kikewa haukan ma ba lafiya ne gare ta ba baki tsaya kin bin cika ba kin hau fadan hauka.. Ajiyan zuciya ta sauke tare da fadin wallahi madam ban san abin haka yake ba wallahi don idona ne ya rufe a lokacin. Ta ja tsuki tare da fadin yanzu ai sai ki san yadda zakiyi ki gyara don kin ji irin hukuncin da ya yanke akan ki da yan uwan ki gyara ya saura gare ki. Don dole ranshi ya baci kina mashi zargin abinda ba shine ba. Da wani kike son yaji don kinsan dama yana cike da haushin rashin samun matar shi da baya yi sai suka sa dariya harda tabawa. Yanzu hanya guda ne ya zama dole gareki ki kwanta mashi ki nuna kin sauko sosai kinyi nadama idan sun dawo yana dakin kije ki gaida ita in ma da hali ki yafe mata shi na yau tunda kin san ba komai ne zai wakana a tsakanin su ba. Da sauri tace zan dai je in gaida ita din ko shi don yaudara zan tafi kuma don kin ce inyi haka amma aini banki yar iska ta mutu ba ma. Nan dai sukai ta kitsa sherin su har suka gaji suka watse a gurin rai bace basu cin ma manufa don maigidan yace ta barmai gidan ita da yan uwan ta baison kowa a gidan nashi. Mun isa asibitin likita mace ce muka gani doctor Rahama itace ta dubani yan tambayoyi taimin ina bata amsa ta fahinci matsala don dagani sai itace a office din su suna waje. Magunguna da allurai ta rubuta min ta bashi yaje ya sawo basu dade ba suka dawo d taimin alluran da kanta tare da fada min abinda zanyi in kara samun lafiya tace wasu mata da yawa hakan na faruwa dasu don rashin sabo da abinda farga ba. Ba laifi na dan fara jin sauki tun a hanyan Yusuf ne ke min zaune daga inda yake yana jan motar murmushi naji shi ya sauke tare da dan juyo gare ni yana fadin. Wanan kaunar taka fa da alama raguwa za ayi anan mace haka sai bakin raki ina ga in zata haihu wayasan irin rakin da zataiwa mutane. Dan lumshi idona nayi cikin yanayin ciwo na dan harareshi cikin yana yin ciwo ina gyara zama na daga inda nake zaune. Babu je gida ba sai da suka tsaya wani shago Yusuf din ne ya fita ya shiga shagon ko kaina ban iya dagawa ba a lokacin don yadda bake jin kaina. Hannun shi yakai ya jawo ni zuwa jikin shi yana fadin mai baki dama bai iya raki ba daga dan tabaki kadan sai ki fadi ciwo haka kina ma mutane makyarkyata. Yana magana yana kokarin rungume ni a jikin shi cikin karfin hali na furta don Allah ka bari jikin nan nawa kamar gyabo nake jin shi yau. Na karasa fadi cikin wani irin kasalalen murya mai tatare da rauni a gare ni yace da sanu zaki saba da hakan kuma har da rakin banza da son jiki irin naki. Naji nace ina mai da kaina saman kujeran motar tare da lumshe idona a hankali muryan shi naji yana fadin kodai na zama shape shorter ne har na aika sakona na ya shiga. Kasalalen murmushi na sauke tare da damtse baki na a hankali ina tunane a cikin raina Yusuf ne ya fito daga shagon ya bude mota ya aje lodojin da ya fito dasu daga shagon. Sai da ya zauna yake fadin kana nan kana damar min yar kaunata da zolaya ko bayan kasan ka mata laifi yau. Wani irin nauyi da kunya ne suka rufe ni a lokacin don ban zaci Yusuf ya fahinci abinda ke damu na ba a lokacin. Mun shigo gidan babu kowa a falo sai Samiha tana ganin mu ta fara min sannu ni dai ban iya amsawa ba don wurin kwaci nake bida a lokacin. Shima ciki ciki naji ya amsa mata gaisuwan da taimin din muka shige part dina tare dashi Yusuf ya shigo da ledojin har cikin part din nawa yana kara yi min sannu da jiki. A falo na kwanta saman dogon kujeran falon tare da lumshe idanuwa na a hankali zama yayi yana kokatin bare min maganin da zan sha a lokacin. Sai jin sallama Nafisa mukayi a falon su shigo ita da Yanyala ban bude idona ga yadda nake ba sai dai ina sauraren abinda ya kawo ta dakin a lokacin . Ji nayi tace ya mai jikin yadda ya amsa mata ba abin mamaki bane don yanayin bacin rai da suke ciki ita dashi. Tace ummmh wanan ya jikin fa Allah ya sauwaka ya kawo sauki maryam ne ta amsa masu da amin shiko yana kokarin dago ni ya bani maganin a baki. Juyawa sukayi suka bar dakin ranta a bace yake na abinda ta gani wai yau samad din ta ne ke faman rungumar wata mace a gaban ta bata iya yin komai ba. Ta na fita dakin ta shiga wani irin huci tana fadin wanan akwai makirar yanrinya ji yadda take wani narkewa a gaban shi ita a dole ga mara lafiya miji na jinyan ta a haukace. Iya abinda zai iya mata ke nan dai lalashi amma badai yakai a gareta ba yar iska wanan ba don ta samay ni a tsaye ba da ba karamin yar iska za ayi ba. Ya dade zaune a dakin yana rarashina inci wani abu dan fresh milk din daya zuba min a cup ban iya shan koda rabin cup din ba ina batun aje cup din ya karba daga hannu yana fadin. Miko min in sha tubarlakin ki tunda nima jiyan ake a tare dani ai ya karbi cup din yana shan milk din yana wani irin lumshe idanuwan shi. Girgiza kai nayi ina kokarin komawa in kwanta yace a a bafa kwanci zakiyi ba zama zakiyi muci naman nan tare ko ba haka ba Yusuf. Don Allah malam ka tashi mu fita kada ka damar min da kanwa ta hutu take so yanzu haba nima ku tausaya min mana. Ya fada yana mikewa tare da fadin amarya zan dan raka wanan sarkin nacin ya tafi ya bamu wuri nazo muyi jinyar a tare. Maryam don Allah idan ya fita ki rufe muna kofa please so yake sai wanan matar tashi ta dawo ta karanta muna haukan ta kuma ina fama da kaina. Haba ai yau bazatayi halin nata ba ba yanzu tazo ta gaidake ba anan ai ta saduda yanzu da alama. Yusuf yace kaiya wanan duk ladabin shegune da wata dai a kasa Nafisa ce zata shigo don Allah wai gaida khadija. Fita sukayi sai da suka fitane yake koro ma Yusuf abinda ke faru a gidan tsakanin shi da Nafisa din inda yake fada mashi ya basu kwana daya su kwashe nasu i nasu subar mashi gidan shi. Bai son ya sake ganin su a gidan don suna yawan takura ma rayuwan shi yanzu kuma ga khadija duk da batai magana ba yasan zaman nasu a gidan a takure take dasu. Yusuf yace tun farko ban so ka aje khadija a wanan gidan ba amma wanan makiran matar taka ta kawo sallon yaudar ta tace dole sai a nan zaka aje khadija din don kawai su takura ma rayuwan ta ita da yan uwanta. Dakin mu maryam ne ta lalaba don in watsa ruwan dumi ko jikin nawa zai kara sake min inji dadin barci da dare. Ban ki ta taba bayan ta hada ne tazo tana fada min in tashi in je in watsa ruwan yana bayi ta shirya min. Naji dadin wankan da nayi din alokacin don nakara jin jikina ya sake min sosai ina fitowa dsshi na fara arba zaune a bakin gado yana jirana a lokacin . Kin fito yace min ciki ciki na karba mai tare da fadin eh kawai na nufi wurin mirrow ina bude mai na lakato zan shafa ma jiki. Hannu na naji ya rike tare da karban man ya fara murza min a jikina a hankali ina runtse idanuwa na don yanayin na shigana sosai duk da halin da nake ciki . Cikin dauriya murya makale nace dashi don Allah ka bari mana jikina ciwo yake min wallahi zai daina yace min ki bari in karasa sai ki kwanta. Dole na kyale shi ya karasa shafa min man tare da dauko nightgown ya saka min da kashi sai da yaga na kwanta na dunkule a wuri daya ina runtse idanuwana. Ji nayi ya zauna a kusa dani tare da fadin sannu ko Allah ya sauwaka, daga dan murzan ki saudaya wanan irin ciwon haka kuma. Don Allah ka fits matar ka tana jiran ka please yace in fita inje ina anan zan kwana jiyan amarya na zanyi yau. Bude ido nayi ina fadin yaya Abdulsamad don Allah ka fita kafa san haka ba kyau don shiga hakine hakan tunda ba lokaci na bane yanzu ka sani. Ido ya kura min sai na dukar da kaina kasa don ban iya hada ido dashi yinin yau wani irin kunyan shi nake ji can naji yace Korata kike ko may na kara dan marairaicewa ina fadin ba wai koranka nake ba kasan fa hakan da kake yana iya kawo rashin zaman lafiya a gidan nan don zata dauka wani abu muke kullawa. Yace kodai fushi kike dani ne Deedar kiyi hakkuri don Allah dama dole ne zaman aure sai ancin ma wanan ranan. Shiru yayi yana kallon yanayin da nake maganan in serious ya dan jima a zaune baiyi magana ba sai dan wani lokaci naji ya mike yana fadin take care zan tafi Allah ya sauka. Ciki ciki nace amin ya fita ajiyan zuciya na sauke ina gyara kwanciya na dakyau tare da lumshe idanuwa na ina jin wani iri a raina. Barci na son daukana naji muryan maryam a kaina tana fadin ki tashi khadi ki dan sha tea ko zakiji nauyi a cikin ki don Allah. Idona na bude ina bata fuska tare da fadin maryam wallahi baki nane ba dadi ban jin zan iya cin wani abu a yanzu. Kafana taja dake saman gadon tana fadin don't be a lazy tun yanzu mijin ku mai karfi ne in kin ce haka zaki dinga yi aikuwa aiki ya samay ki khadi don ko gobe ma karawa zaiyi ba fashi. Da sauri na dago ina kallon ta tare da watsa mata harara ina fadin tunda gani jaka ko may ni wallahi yanzu ko muryan shi naji tsoro nake ji daurewa kawai nake yi. Dariya ta dinga yi tare da fadin kajiki inda ana jin tsoron maza haka ai da ba a haife mu ba yanzu haka nace wasu suna tausayawa ai ba irin nashin nan ba gaskiya. Tace ke don Allah kin faye raki wallahi dama masu bakin nan haka kuke da shegen raki ai wallahi kada ki bari ya gano kina da rauni a wurin nan don dai buxuwa tafiki fada a gurin shi kan dan wanan abin da kika raina. Miko min tea din tayi ta kafe ni da ido dole na daure na sha fiye da rabi na miko mata cup din na dan zauna don ya fada min kafin in kwanta mun dade muna hira a gurin kafin mu kwanta. A,A yana shiga part din shi ya rufo kofan dakin shi da key ruwa ya shiga ya watsa ma jikin shi ya fito Nafisa tana kula da shi tana ganin ya fito tayi saurin komawa ta shirya zuwa dakin nashi don ta shirya bashi hakkuri acin daren nan. Kofan ta tura taji yai mashi ke ta shiga dan bubuga kofan a hankali yana daga inda yake tsaye yake tambayan waye ? Tace nice bude min mana tsuki ya ja mata ya kyale ta a wurin yaci gaba da shirin kwanciya da yakeyi ta kara buga kofan bai sa ya je ya bude mata ba. Sai ma hauwa gadon da yayi yana kashe wutan dakin don ya kwanta anan ya fita batun ta tare da shigewa bargo don ya huta. Barci yake son yi sai dai tunanen duniya ya hana shi a lokacin alamarin Nafisa ne ke damun shi a rai duk abinda yake wanan damuwar na mashi yawo a zuciyar shi daurewa kawai yake yi abin yana damun shi sosai a rayuwan shi. Duk yadda ake son mutum da hakkuri da iyalin shi yana iyakar hakkuri da Nafisa amma ita bata ganin hakan da yake mata. Sai kokarin daukan shi macuci mayaudari da takeyi shi baiga wani abinda yai mata ba in ma cutarwa ne Fati da khadija yake cuta . Don tana da motar shigs amma Fati tun zuwan da yayi bukin kannen ta motar ta ya samu matsala bai sa an gyara mata ba kuma yana sane da hakan. Ga wanan yarinyar shiga da ficen da Nafisa keyi a cikin dukiyar shi bai taba tsone mata ido tai mashi gori a kan hakan ba. Kafin barci ya dauke shi yayi tunane kala kala a wurin kafin barci ya sace shi ya manta da komai da ya faru a wanan wunin. Washe gari bayan yai sallah asuba bai kwanta ba yana zaune yana addua a gurin don neman mafita ga Allah akan damuwar shi. Sai da rana ya dan haska ne ya daga ya sauko daga sama zuwa part din mu don ya duba jikin nawa ya samu kofan mu yana a rufe ba,a bude ba yai nocking yaji shiru haka ya sa ya gane muna barci har lokacin don da mun bude mai. Part din shi ya koma ya shiga wanka ya kimtsa cikin kananan kaya kamar kullun yana shirin fitane yaji an turo kofan daki. Ba sai ya juya ba don yanzu ya fara banbance yanayin shigowan mu dakin don zai fahinci wasu abu ga yanayin kowacen mu. Samad ina kwana tace mai daga inda take tsaye ta kasa karasowa inda yake lafiya ya amsa mata fuska daure. Don Allah na zo ne dama in baka hakkuri ga abinda ya faru jiya kuskuren fahinta ne wallahi. Idona ya rufe ina ganin kamar wani abu ya faru ne a tsakanin ku a lokacin ashe ba haka abin yake ba don Allah kayi, , , , , Katse ta yayi da fadin idan ma wani abu ya faru a tsakanin zaki hanane ba mata na bane ita kamar yadda kema kike matana. Ko ansa min dokan cewa dake kadai zan zauna in dinga mu,amula in bar sauran nagaji da wanan halin naki Nafisa ba zan iya daukan shi ba kuma. Daya ke shiri take so a lokacin sai ta kwantar dakai tana bashi hakkuri don dai kawai ya kyale su ita da yan uwanta a gidan. Duk fadan da yayi ranan bata bashi kwararar amsa ba don gudun abinda zai yi jawo mata fita yayi karshe daga dakin duk da bai taba ganin ns damarta irin haka ba amma baisa ya nuna mata ya hakura da bukatan ta ba. A falo ya samay mu ina kwance maryam tana hada tea a kofi shigowan shi part din maryam ta rude ta shiga gaida shi. Daga inda nake zaune na gaida tare da fadin ina kwana yace lafiya ya jikin naki nace da sauki cikin lumshe ido. Kinsha magani ya tambaya yana mai kura min idanuwan shi yanzu zan sha idan na karya nazo dazun baku bude kofa ba. Bamu dade da tashi ba na bashi amsa ya karaso gap dani yana taba jikin nawa tare da fadin zazzabin ya wuce ke nan ko ? Kai na gyada mashi alaman eh don magana ma nauyin yin sa nake yi a lokacin yace raguwa kawai zan so inga ranan haihuwan ki. Ban bashi amsa ba don maryam dake falon ta gama hada min tana miko min kofin zata shige yace maryam da zan dan samu ruwan zafin nan yanzu da nasha kafin in fita tace to barin hada maka. Sai lokacin nayi kwakwaran magana nace haba maryam kada fa yin haka ya jawo muna matsala kuma kin dai san halin matar shi da kishi. Zama yayi a kusa dani yana fadin ke baki kishin nawa ne komay don nagani a idon ki yanzun haka. Dariya maryam tayi ta shige kitchen ta barmu a wurin kokarin taba ni yake ina kaucewa tare da fadin yaya samad ka bari don Allah. Da sauri yace what kema zaki bi jahilcin Nafisa ne kina kira na da Samad bayan kin san ma,anan sunan . Is better idan zaki fara kirana da wani sunan na daban ba wanan ba don kin san mai sunan haukanta ne yasa take kirana da hakan nasha warning din ta da tabari takine. Maryam ne ta fito kitchen din rike da ture a hannun ta wanda ta shiryo mashi kayan karyawa a ciki ta aje a gaban mu. Yun kurawa nayi na mike don in hada mashi yace zauna abin ki na hutar dake na yau zan hada da kaina. Kallon yadda yake hadawa nakeyi har ya gama ya fara kurbawa a hankali ya dago ya kalleni yana fadin bazaki sha naki ba sai yayi sanyi . Dauka nayi na fara kurbawa naji yana fadin wani irin mota kike so a rayuwan ki don zan sa a duba maku. Nace wanda kaga ya dace dani ko wani iri ne na gode Allah saka da alheri yace ba godiya a tsakanin mu don ba zan iya biyan ku ba sai Allah. Bai dade a zaune ba ya kube tea din ya mike kudi ya miko min na dago kai ina tambayan shi na may nene yace ki karba tukun nasa hannu biyu na karba ina sauraren shi. Kudin ce fane ne da zaki da na sauran abubuwan da baki dashi a part din ki a shirya min abinci mai dadi don Allah. Nace amma sai naga ai wanan kudin sunyi yawa ga cefane kawai da kara biyu don ni ina da komai a nan kallona yake daga inda yake tsaye yana fadin. No haka dabia na yake mai girki zan bata kudi da zai ishe ta lalurata har ta amfana da sauran sai na dawo yace dani baysn ya tsureni sai da yaga nasha maganin. Tunda ya fita bai dawo ba ga maryam ta nace akan ita zata wuce tunda na samu lafiya na kirashi a waya yace ta dakance shi ya dawo don Allah. Da taimakon ta na hada girki ta bani kwarin gwiwan zuwa gyara mashi part din shi kafin six na kammala komai da zanyi a bangare na. Koda ya shigo dare yayi a lokacin hakan yasa maryam bata wuce ba a ranan tun fitan shi dakin maryam ta damay ni sai in je gurin shi kada in barshi shi kadai a daki. Na nuna mata tsoro nake ji wallahi tace haba mai zai maki yau bayan yasan baki da lafiya kuma. Haka dole na shirya na fita zuwa wurin shi nakai mai abinci ban dade ba na dawo na kara shirya nai mata sai da safe na wuce part din shi. Su Nafisa suna zaune a falon duk wanan sintirin da nake suna kallona tana ji kamar ta hade ranta a lokacin. Na samu har ya gama ya kwanta ya kashe wutan dakin ina ganin haka na dauka yayi barci da sanda na isa bakin gadon na kwanta a hankali kada motsina ya tayar dashi. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Tana tsaye a bakin window dakin ta tana kallona sanda na shiga dakin wani irin shu,umin murmushi ta sauke ta juya da sauri zuwa karkashi gadon ta tare da jawo roban da ta saka. Wani kallon mamaki takewa kayan nata ganin yadda abin ya rikide ya koma bakikkirin dashi da fargaba ta dauka tana dubawa a hankali tana mamakin ganin sauyawan abin a dan kwanakin da ta dauka bata dubashi ba. Gabata ne ya kara faduwa sai dai bata saduda ba kara haka shi tayi kamar yadda ta saba hakawa a kulun nayau ma yafi tankuwa da kyau. Ta gama surukulen ta ta kwanta tana murmushi a ranta tare da dariyan mugun ta tana tunane haka barci yai gaba da ita. Jin saukan hannun a saman jikina yana gyara kwanciya tare ds sauke ajiyan zuciya yasani razana don tsoro. Muryan shi naji yana fadin kin cika tsoro Deedar ina kallon ki tun shigowar ki fa kamar wata mara gaskiya dake. Ai na dauka ba zaki zo bane inje in dauko ki a dakin sai lokacin nayi motsi tare da fadin tunda kai kafi kowa rashin ta ido. Matseni naji yayi cikin jikin shi ina jin shi yana shakan kamshin gashin kaina yana sauke numfashi yakai hannun shi tare da cire ribon din da na daure kaina dashi. Yana wasa da kitson dake kaina a hankali naji yace kitso yana ma mata kyau idan sunyi sai dai ku matan yanzu baku son kitso na gani. Idan bamu so da zaka ga nayi kazamai ne da raggaye kawai basu son yin kitso don kiyya amma ai kitso karin lafiyan mace ne da fitan surar ta. Au to sura yake fitarwa ashe barin fara duba yarda ya fitar maki da naki suran tun yanzu inda comment in fada maki ki gyara jinayi ya kuna dim light din dakin yana kallon fuskana. Da sauri na runtse idanuwa na daga kallon shi ina fadin don Allah ka bari kasan fa banda lafiya yau. Yace bamu da lafiya dai ai tare muke ciwon raki dai kika fini don ni ban nuna ba yinin yau kai nayi fama dashi sosai wallahi. Na dan yi kokarin juyawa ina fadin ba dole ba mutum ya dawo tafiya bai huta ba ya tsaya ja, , , sai nayi shiru matse ni ya sake yi yana fadin na tsaya may ki karasa maganan ki mana. Ban tanka mashi ba don jin yadda ya matse ni a lokacin a jikin shi hannuwan shi naji a saman kirjina zabura nayi ina kaduwa. Yace Deedar mai yasa kika cika rakine ko tsoro haka da yawa wai ina bakin nan naki ya tafi ne mai tsiwan tsiya da fadar bakan magana yau. Duk wanan abin yana magana kamar mai rada yana shafa na yakeyin shi niko sai faman runtse ido nake cikin wahala. Naji ya ci gaba da fadin kin shayar dani ziman da ban iya mantawa a safiyan jiya Deedar ina son yadda kika shayar dani zuman ki a jiya ki kasan ce mai shayar dani a koda yaushe wanan ni,imar taki da Allah yai maki. Yadda kika kasanci mace mai saukin kai da biyayya tun farko a gareni ya kasance ako wani lokaci haka halaiyan ki zai kasance a gareni da kowa na tare damu. Wasu hawaye naji suna bin fuskana da bansan fitowar su ba hannu yakai yana fadin kuka kuma Deedar godiya yakamata kiyi wa Allah ba kuka ba. Ki gode ma Allah da ya nufeki da da samun wanan baiwar har kikai tanadin shi yakai a inda ya kamata ina mai fatan samun zuria masu kwatancin tarbiyan ko fiye ma da yadda kika samu a wurin iyayyen ki don ni sheda ne kuma na gani. Kukan nawa ne ya tsananta naji ya shiga aika min da kiss yana murmushin da nake jin zafin shi a lokacin. Ta ko ina yake jagwalgwalani kamar wanda yayi sabon hauka akan haka ranan yai dai yi wasa da jikina kamar ba gobe amma bai shiga jikina ba kamar yadda nake gudu yayi. Da safe ma bai bari na fito da wuri ba daga dakin barcin safe mukayi a tare kasancewa safiyan lahadi ne ranan bai fita ko ina nima ban fita ranan. Sai tara saura na fito daga dakin lokacin Nafisa da tawagan ta suna a main falo tanayi tana kallon lokaci da kofan dakin don tana da tabbacin bamu fito ba har lokacin. Jin motsina fitowa ne yasa ta kafe hanyar da idanuwan ta caraf idona suka sauka a nata bata kawar ba nima ban kawar da nawa ba a nata. Shu,umin murmushi ta sake min ta gefen fuska tare da kada kai alaman kinsha haushi nima nuna mata nayi da alama aiko a jikina. Na wuce su na shige part dina don na samu maryam yau ta bude min ba kamar jiya ba da na samu wurin a rufe. Da sallama na shigo na samu ta gyara ko ina yadda ya dace tana jiran shigowa na ta wuce zaune na samay ta a falon ta jirana. Kallon juna mukayi ta sake min murmushin shakiyanci na kawar da kaina tare da fadawa saman kujera tace amarya kina kamshi fa. Sake aika mata da harara nayi tare da fadin kun dai cuta min wallahi mutum baida freedom din kan shi yanzu sai ace bai yi dai dai ba. Dariya ta sake tana fadin may kuma akai maki yanzu ai gara da ke aikin lada kikeyi mu fa kun barmu sai fake maki shiya. Ni dama ke nake jira ki fito zan tafi ke nan da sauri na dago nace haba wasa dai kike wallahi tace Allah da gaske nake yi dama ke kawai nake jira badon ma in tafi ba in bar maki shiya ga muggayen nan aida kin zo kin samu na tafi. Nace a lalace ki tafi bamu duba kayan nan da ya kawo ba ki dauki abinda yai maki a ciki don ni yanzu basu gaba wallahi. Da sauri ta tare ni da fadin ke ko suke gaban ki don yanzu kwalliya yake gare ki kina da wanan kishiyar haka zaki zauna ba kwalliya. Kin san fa kwalliya na daga cikin abinda mazan yanzu suke so da kuma gyaran gida da daki gami da babban dakin hutun su. Nace ina ni ina babban dakin hutun shi buxuwa da yan uwanta sun mai dashi wurin zaunawan su ko yaushe fa a lokan nan zaki samay su zaune. Tace ke tafi can wake maganan wanan falon da ya zama na masaukin buzaye ana maganan HQ taki kina min wani zancen falo can. Nace Allah dai ya shirye ki maryam mijin ki na da aiki wallahi tace wa zai zauna yanzu ai mashi sake anshani daya baza a kara ba. Wai ke ai ba falo ba wallahi yanzu gidan naku da mutum ya shigo falon ai wani tsamin buzaye yake tariyan hancin mutum da doyin sakesakin su. Sai fa kinyi da gaske a gidan nan kafin ki cin ma manufarki don akwai aiki ja a gaban ki khadija duk wani abu wanda kika san ba halin mu bane nan kiyi kokarin kawar dashi a cikin hikima da basira ba a cikin garaje ba. Da sannu komai zai zo ya daidaita idan kin jajirce baki biye ma halin su kun zama daya ba sai kiga abubuwa na tafiya daidai. Shiru nayi ina sauraren maganan ta tana ta fada min yadda zan bullowa nafisa a cikin hikima da basira ake gudanar da kishin yanzu ba a haukan da take yi ba. Kallon ta nayi nace ki jaye tafiyan ki yau sai gobe idan zan shiga school a sauke mu tare ina ganin zai fi ta kalleni nace Allah ko haka nake ganin zaifi sauki. Tace kan ki ake ji ai nikan bari ki gani yanzu ma zan tafi don ina da aiki a daki dana bari gashi gobe akwai shiga school shiyasa nake son komawa yanzu. Shigowan shi ya katse muna maganan yake fadin yanzun da safen nan zaki tafi maryam ba zaki bari sai yamma mu kaiki ba. A kunyace tace yanzun nake son komawa don akwai abinda zanyi idan na koma gashi gobe monday akwai shiga school. Yace OK bari mu karya ga Yusuf nan yazo sai ya sauke ki a school din idan ya gama ya juya gurina yana fadin akwai abin karyawan ko na sa a sawo muna ne ? Nace na samu ta hada kafin in shigo a ina za a kai maku kaimun falon sama yace tare da fito da kudi daga aljihun shi yana mika ma maryam din tare da yi mata godiya akan abinda tai muna. Kai ta girgiza tare da fadin bazata karba don mun wuce haka wurin ta fatan ta dai Allah ya bamu zaman lafiya mai dorewa da zuria masu albarka . Amin ya amsa mata yana kara mata godiya tare da fadin kusan halin ku daya da kawar ki baku son amsan alherin mutum ko wanan wani sirine bamu sani ba ? Mikewa nayi daga inda nake na dauki kayan karin na mara mai baya zuwa sama ban samu Nafisa a falon ba nake ganin ta shige part din ta a lokacin. Na gama zan fito ne sai ga su tare da Yusuf suna hawowa saman da rabewa nayi ina basu hanya tare da gaida Yusuf din yana min yaya jiki nace da sauki. AA yace ai kasan maganin ta jiya ta shashi sosai shiyasa kaga ta kara samun sauki hararan shi nayi na wuce abina ban tsaya wurin su ba don nasan in na tsaya kunya zai ta bani a gaban Yusuf din. Na koma muka bude kayan da Maryam sai faman yabon kyawon su take yi nidai ina sauraren ta wani dogon riga da muke ganin yaimin kadan kawai ta dauka daga cikin kayan tana min Allah sa a kashe lafiya. Ita da kanta ta jera min su a gefe inda ya dace gefen wardrobe dina mun dan dauki lokaci sai gashi ya shigo part din yana fadin ta fito su tafi. Har bakin mota na rako maryam din tare da fadin sai mun hadu gobe a school na dauka da shi zasu fita sai naga sabanin hakan . Komawa nayi part dina nayi wanka kafin in fara shawaran abinda zan girka muna na rana sai da na kusa hadawa naji wani abu kamar kaurin hayaki yana shiga hancina. Allah ne ya bani ikon fadin innalillahi wa, inna alaihim rajjiun a uzubikalamatillahi tamat min shedanin rajin. Karan fashewan abu naji kamar ya fadi daga saitin window kitchen din part din da sauri na jawo buner dina na debo turaren wuta na saka sai warin abin ya daina. Garwashi na hada tare da zunbuda turaren wuta na hayake part dina dashi na fito har falo ina yi Nafisa ce naga ta fito dakin ta da sauri sai yanyala da suka hade tare tana bude gwiwan ta taji ciwo sosai a kafan nata. Bina sukayi da kallo ban tsaya ta kansu ba na ci gaba da turare gidan da kamshin turaren wuta muryan Nafisa ne a kaina tana fadin. May kike nufi kike muna haka a gida sallon wani sihirin ne haka duk ki hayake mu a gidan ko may ? Ci gaba nayi da tafiya sako sako lungu lungu ina saka kamshin yana tashi tare da ba falon wani yanayi mai dadi dama turen na waje ne anty Hauwa ta bani shi lokacin aure na. Ganin ban fasa abinda nake yi ba aiko ta hau fada tare da shewa abinda ya dawo da hankalin AA falon ke nan a lokacin. Da sauri ya fito daga part din shi yana fadin may nene may ya faru kuma wai may ke faruwa ne haka daku. Daras nake a cikin kwaliyan atamfar buje da rigar da nasa na daura dan kwalin ture kaga tsiya a kaina juyawa tayi wurin shi tana fadin. Ni wanan zata raina ma wayo a gidan nan ta fito tana wani turare muna gida haka da rana tsaka don ta raina ma mutane wayo ta samo wani sihirin ta ta saka a ciki zata zo tana muna hillan hayankin turaren wuta take saka muna. Khadija may ke faruwa ne wai don banji abin dauka ba a wanan zancen nace wani wari nake ji shine na saka turaren wuta warin ya wuce shine ita kuma ta mayar abin fada. Yace nima naji wanan warin ba dadi a hanci na sai kuma daga baya na daina ji ya juya gare ta yana fadin. Yanzu may ye abin fada da wani zargi a nan fisabilillahi don an saka kamshi a gidan nan ke baki saka ba an saka zaki tsaya fada haka ba kunya yanzu ko ke baki ji dadin kamshin nan ba a hancin ki. Zata yi magana sai ga yarta karaman ta fito daga waje tana wasa tana fadin Abbi Yanyala taje saka hayaki a bayan window amaryan ka ta fadi kasa yanzu muna ta dariyan ta a waje dasu mai gadi. Juyawa yayi yana kallon ta da mamaki tare da mayar da hankalin shi gare ta yayin da uwar ke buge ma yarinyar baki ta saka kuka da karfin najin zafin bugun da tayimata din. Kallon Nafisa yayi rai a bace yana fadin may kika tura a saka mata a window din dakin ta Nafisa tace ka dauki maganar ihisan da gaskiya ne. Yace in ba da gaskiya bane may ya saka kika bugeta yanzu ita kuma yanyala mai ya samay ta naga taji ciwo haka a kwaurin ta. Da sauri Yanyala ta sake dogon rigan da ta rike don zafin da wurin ke mata nikan juyawa nayi zuwa part dina ina rokon Allah tsari. Ban san yaya suka kare ba a falon na dai ga ya shigo part din nawa ina zaune a falo bai mun magana ba ya wuce kitchen ya duduba ya fito yana tambayana banjin komai ko. Daga inda nake zaune a harde kafa cikin kafa ina karatu nace dashi ban jin komai Allah dai ya kara tsare mu da tsarewan shi yace dani amin yana kaiwa zaune ya dafe kanshi da hannun shi daya yana tunane. Dago kai nayi ina kallon shi naga yadda ya zurfafa a cikin tunane nace a hankali wani abin ne kuma ya faru ? Sauke ajiyan zuciya yayi yana kallo na yaga har cikin raina ban nuna damuwan abinda ya faru din ba kuma nayi hakane don kada ya fahinci na razana da abinda ya faru din yanzu a falon. Wa yan nan mutane Deedar zaman su a gidan nan yana takura ma rayuwana gasu basu da zuciya nayi korar su sun ki tafiya su barni. A raina nace baka kore su ba dai kana gudun bacin ran yar uwar su ina ko zakai masu koran da zasu barka amma a fili cewa nayi dashi haba dai ai bakon ka annabin ka ba a korar mutum hakana. Yan uwar matar kane fa in ma baka son zaman su anan ne aiba korar su haka zakayi ba sai a cikin hikima kada dai ince don dan wanan abin kake bata rai haka. Deedar baki ganewa ne akwai abubuwa da dama da nake hango ma zaman su a gidan zai haifar zuwa gaba . Nace da baka hango wanan ba sai yanzu ni dai kada, kasa zarge ni su ga laifina su dauka nice ke zuga ka a kansu. Yace kin taba min maganar daya daga cikin su ne tun shigowan ki gidan nan idan kai kasan ban taba ba amma su sun san da hakane. Yinin ranan AA yana makale dani bai fita ko ina ba kamar a kaina ya fara aure niko kunyan shi nake ji don tunawa da abubuwan da na dinga mashi a baya sai inji kunya ya kama gashi a yan kwana kin nan duk wanda yace zai rabani dashi ai ya samu mai shi. Dan zaman weekend din nan da mukayi a tare na fahinci AA mutum ne mai saukin kai sosai ashe yana da addini sabanin yadda na dauke shi lokacin sallah nayi bai bari ya wuce mu. Nafisa ko tun lokacin da suka gama rikici ta dauki motar ta zuwa gidan madam uwar daba mai arna ta samay ta da wasu kawayen su biyu suna hiran nasu kishiyoyin sai gata. Yanayin ta kawai madam ta kalla ta fahinci tana cikin wani yanayi ta ta fahinci sunyo tsiyan a gidan ta tare ta da fadin yau mutumiyar da wace aka tashi kuma. Don yanzu gidan ki ya zama gidan danja kulun fitina ne ba daga kafa zama tayi tana jan tsuki tare da fadin ba dole ba wanan matsiyaciyar yarinyar kamar mai ira,izai da ke ture min shiri na. Au har kin manta da abinda na Mando ya fada muna ranan cewa tana da masu kariya sai munyi da gaske a kanta. Naga alama tace wai duk kudin dana kashe akan yar iska abin bai yi ba na tura yanyala ta turara yar iska ta baya sai gashi ita ta fito ta gaba tana turarani a gidan. Ddon iskancin yanyala kuma a gaban idon su Ihisan taje yin abu sai gata wai taji kamar tafiya a bayan ta taje waigawa ta fadi duk ta kuje kanta ta kone. Dariya sosai suka dauka ita ko tasha toka don bata ga abin dariya ba anan taci gaba da fadiin na nuna mata na gane turaren da take yi sai gashi ya fito kamar zaki yana tambaya shi a dole mai lalashin ta kada ta gudu. Ba sai ga ihisan ta fito tana fada ma uban abin da Yanyala taje yi ba ta fadi yau ai ba karamin rikici muka kwasa dashi ba a gidan. Sai dana murje mai ido kada inji kunya na dinga zabga masifan karya sanan ya rabu dani ai da ban san inda rikicin zai tsaya ba. Dayar matar dake zaune hamshakiya ne ta karbe maganan da fadin kin ga irin abinda yasa ban tura kowa yai min aiki ni nake abina da kaina ba tare dana saka wani ba yaje yai min shirmay. Tace ai dan ba kari mutanen banza ne wallahi ace dan karamin aiki haka sai mutum yayi shirmay a cikin sa wai fa yau sai kusan goma suka fito daga kwana. Matar guda dake ta faman kada kafan ta tana jin mulki ta amshe da fadin wuri kika basu wallahi ni akawi yar iskan kishiyar da zata kai ko biyar na safe da miji a daki. Ai da ranan sai tasan ta shiga hurumin da ba nata ba a gidan nan sai na saba mata kamar yadda ta saba min sai dai suyi tsiyar can a sace ban gani ba. Ke in fada maki ma fa dayar ma sai idan bani gari yake samun sakewa da ita idan ko ina nan basu isa ba wallahi har shi din. Hankalin Nafisa ya koma wurin mai maganan taji kamar ace itace ta samu irin wanan irin mulki tace haka nake so wallahi yar uwa. Tace a mai za a fasa mutuwa ko hisabi ni ban daukan raini ga kishiya wallahi balle su duka ukun na girmay masu ga shekaru mijin ma kanshi na girmay shi balle su. Kina nufin dama sune a gaban ki ta tambaya cikin son karin bayani gare ta tace wlh in fada maki ina ganin shi yai min kawai na aure shi duk da shima yana da abin hannun shi do ya fini nisa ba kusa ba gaskiya. Badai haihuwa yanzu nake nema ba sai rufin asirin don haka nake juya su yadda raina ke so a gidan ba wace ta isa ta mai tak a cikin su tayi waje road. Don wace nake bi har ta gwada min iya shege nasa miji ya yanka mata jan kati sai gidan su sani Allah sani Annabi ta samu ta dawo cikin yayan ta. Madam tace amma sai da kika bari kikai nazarin su kafin ki fara aiwatar da shirin ki ko tace sosai kuwa da farko ai da fuskan musulma nazo masu. Nice son diyan su nice nuna masu ban damu da miji ba nama fisu son kan su da sauran abubuwa sai da na gama karance su tsab na fara fito masu da kalata. Da uwargidan na fara don na jata a jikina sosai naji komai na gidan da yadda yake guda ai in fada maki akanta na fara ranan. Ba baki don ta gama fada min duk sirin gidan na sani kuma tana jin kunyar aji a gurin ta naji komai dole sai lalabawa da biyayya gare ni. Madam tace to abinda Nafisa bata iyawa ke nan na fada mata ta nasu ta gama fahintar ida suka dosa amma ta kasa hakan don kishi. Ai in kina son ki san kan gida kafin ki fara aiki fara kama kan uwar gida je mata da fuskan musulma ki nuna kina ra,ayin ta kina tausayin ta yanzu zaki fahinci komai a wurin ta. Don su gani suke cutar su miji ke yi ko yaushe yafi maida hankali ga amare basu san duk kanwar jace ba kishiya kishiya ce ba mai son taga yar uwa tafita ga miji. Kai Nafisa ta gyada tare da fadin ni gaskiya ba zan iya jan kowa a jiki na ba duk daya na dauke su ai kafin in zauna da amaryan da uwargidan muka fara. Wanan fa irin kishin kasar su tazo muna dashi nan bata san abin ba haka yake ba a nan sai ka hada da kissa da kisisina da kutungwila zaka ci riba. Nafisa tace gaba daya nike masu bugun diyan kadanya don ban yarda da kowan su ba ni mijin nake son in kama ko ta halin kaka abin ya faskara gare ni kuma. Sai naga kamar zan kama shi sai abu yazo ya jagwule min daga baya yanzu fa yan kwanakin nan samad bai jin kunyar fadin mu bar mashi gida dani da yan uwana. Matar tace duk ke kikaja hakan tunda ya riga da ya fahince ki baki kaunar ko daya daga cikin su don may zai zauna zaman goyon bayan ki koda yaushe. Bafa ko yaushe asiri ke tasirin akan mutum ba madam ta karbe da fadin shi nake fada mata ai bata gane ba. Matar tace kamar ni nan ai da farko wani na samu na kamashi a hannu wani last done ne wallahi har ina ganin na kama shi ashe matar shi ta fini iya duniya. In fada maki tana ji ba ai sati ba ta shiga ta fita sai batun kake ji yar iska ta kama abinta tamau ta rike ai ke madam kin san labarin don da ke mukai ta bugawa a lokacin. Madam tace kwarai kuwa na sani Hauwa black yar jos ko kin san har yau kuwa a kule take damu ranan mun hadu a gidan buki baki ga yadda take wasa da naira ba tana muna hura kai. Ba dole ba yar iskan mata miji ya rike mata kan maciji tana wasa da bindin shi duk tarin dukiyan shi fa ita kadai ce matar shi har yanzu gashi matashi mai ji da lokaci. Kedai bari yar uwa yanzun ai ba a sanya don wace za ka sama sheri ke da zaki shigo kuma da naki shitin ba, a shiga hannu sake yanzu kowa tsaye yake kamar laya. Tambayan Nafisa tayi may ye matsalan ta yanzu akan kishiyar tane sai da ta rufe ido ta bude kai tsaye tace wallahi hajiya ni gaba daya naki jin kishine a rayuwa. Don na kasa tsayawa in fahinci takon yar iska ai in san ta inda zan fito mata don yarinyar gata karamace amma akwai bakin wayo gare ta. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Washe gari bai so in shiga school ba wai sai na karkare murmurewa in fara zuwa rokon shi nayi ya bari in shiga don muna da test washegari tuesday. Bamu hadu da maryam ba sai da muka fito sallah a zahar muka hade a masallaci da ita kallona kawai tayi ta kwashe da dariya. Oh kinga abin dariys a jikina ke nan na fada a hasale tace ban gani ba sai dai kina dashi ne khadi daga dan haduwa guda shine har kika wani fada haka. Kallon jikina nayi na tabe baki nace dama haka kike son gani aka hada baki dake ai wlh ki san da sani konci bashin haka a gurina sai na rama nima. Yarinya ai sai dai ki ramay wurin ramawa nikan ai ba zanyi wanan rakin irin naki ba kin sani mun dauki lokaci a gurin kafin mu koma ciki. Biyar da rabi muna fitowa motar shi na iso wa don haka ban samu kara kebewa da maryam din ba na wuce . Tunda na shiga motar naga shi rai bace ban damu in tambaye shi ba don ba abinda ya shafi gida bane kila. Mun dan taba tafiya kadan ne naji muryan shi yana tambaya maganan da ya daure min kai dagowa nayi ina kallon fuskan shi ya kara maimaita tambayan shi gare ni. Nace ina kika je a Napep ke da maryam da bana gari shuru na dan karayi sai kuma nace ban je ko ina ba sai wurin gyaran kai dakuma shago na sawo kayan bukatana don banda mai sawo min. Khadija kin ko san darajan ki a yanzu garin nan da zaki je shiga Napep da mutuncin ki da kimar ki na matar aure matar ma tawa . Wai kin san wanda kike aure kuwa khadija idan ma baki sani ba bari yau in fada maki ni ko waye don ki sani. Wanan aikin da kikaga ina yin shi nake don cika gurin iyayyena a yadda suke so suka kuma gina ni akai ina kokarin ganin akoda yaushe na farantawa iyayyena ransu. Idan ba haka ba ba abinda zanyi da wanan aikin da kike gani inayi anan kin san wasan polo ko wasan kwalon doki da akeyi . Kai na gyada alaman na sani yace to ina daga cikin wanda duniya ke alfahari dashi a wanan wasan kin san jackpot na girgiza mai kai yayi dan murmushi yace ki bincika don yafi komai kawowa rayuwana kudi sai dai banson yi idan ba yama min dole ba wanda idan na buga kusan duk abokan karawan nawa sai na doke su. Ni business man ne ina shigo da karafuna da part na motoci a kasan nan sai dai duk inayin wanan ne a cikin boyen kurwa don idon jamma,a akaina. Don Allah don Annabi for god sake mai zai sa kije shiga motar haya bayan na aje maki daya daga cikkin motocin shiga na a dinga kai ki duk inda kike so. Ba wai naki saya maki mota bane tun kafin muyi aure ko mota nawa kike so a gare ni zan iya saya maki Deedar sai dai ina duban abinda haka zai jawo maki ne a gida da idon jamma,a. Ranan da Nafisa tayi maki gori naji zafin abin don har barci abin ya hana ni samu issashe saboda raina da ya baci da zancen. Don Allah may yasa kikayi min haka har yaron wajen aikin mu dashi da matar shi suka rage maku hanya yau yake fada min banji dadin jin haka ba wallahi. Gyalen kaina na gyara tare da gyara zamana ina fadin ni kada kaga laifina akan hakan fa. Yace a harzuke don may ba zanga laifin ki ba Deedar sunana kike son batawa a bugani a jarida anga matana a motar haya a garin nan. Ko Fati da take cen duk inda zata da motar hajiyan mu take tafita na kuma kyaleta ne ban sai mata wani ba saboda careless din ta dayai yawa. Don Allah ka daina zargi kan haka don ko ba laifina ba ka tambayi driver ka ko maryam zasu fada ma idan nice mai matsalan. Motar da tun ranan da ka tafi iyakar mu da ita kenan a gidan ka ban kara ganin driver ba sai yau da muka fito din nan naganshi a waje yana noke kai. A dai yi min munafunci ne don ba,a son aga kwanciyar hankalin mu tare da kai shiyasa ban bi ta kan motar ba na ci gaba da tsagogina. Da ina da power a gidan ka ba za a hanani shiga motar ka ko taba kayan ka ba a gidan nan. Shiru yayi yana saurarena har na gama san nan yace kina nufin hana mashi umurnin da na bashi akayi komay nace ai ka tambaye shi kaji daga bakin shi ko kuma idan baka yarda ba zaka iya tambayar maryam yanzu ma ba sai gobe ba. Shiru yayi bai sake magana ba har muka isa gidan ban tsaya ba na kwashi takarduna zuwa ciki na barshi a motar ya biyo ni da kallo. Part dina na bude na shiga har kullun baki na dauke da addua don nema tsari ga Allah har nayi sallah la,asar na idar part din shi na je na gyara na saka kamshi ko ina tare da wanke unders din shi na shanya mai ta bayan benen shi na fito zuwa nawa dakin na dora girkin abinda zamu ci da dare. Ban sa lallai dole zaici abincin ba sai dai na girka dashine kawai don nice mai alhakin bashi abinci a ranan duk da ba wani girki mai yawa nakeyi ba. Na gama na shiga wanka lokacin har magarina ya dan gwauta na fito na tayar da sallah bayan na gama ne na zauna na gyara jikina tare da hayewa saman gadona na kwanta. Tara saura ya shigo part din nawa daga shi sai wandon crazy fari da farar riga armless ajikin shi sai kamshi yake zubawa haka yasa na fahinci yayi wanka ko a lokacin. Ban daga daga inda nake ba ina kwance a yadda nake sallama ma dayayi ciki ciki na karba mashi ya iso bakin gadon ya zauna yana fuskanta na tare da cire min handout din da nike karantawa da na dora saman cikina ya dan duba. Ba tare da ya kalle ni ba idon shi na kan takarda naji yace dani wai fushi kike dani akan maganar da nayi maki dazun ko may ? Na dan juyo tare da fadin wa ni don may zanyi fushi tunda ina da gaskiya na akan may zan dauki zafi dakai kuma hutawa dai nake kawai. Murmushi naji yayi tare da fadin ba gaskiya bane idan da baki fushi may ya hanaki zuwa wurina ki dubani ko ki kawo min abincina a can ko baki girka abincin bane ?. Na girka mana nace dashi tare da kokarin mikewa zaune sai naji ya mayar dani a yadda nake kwance da ya shigo. Ido na kafa mai shima haka sai nayi saurin jaye nawa idon daga nasa ina sauraren shi inji abinda zai fadi fuskan shi ya sauko zuwa kasa yana nufan nawa dashi. Kokarin kawar da kaina nayi gefe sai dai ya riga kai fuskan shi din a nawa yana neman bakina ya hade da nasa ban samu kaucewa ba har ya kawo bakin sa a gare ni ya shiga tsotse ni tun ban biye mai har na fara biye mashi na fara mayar mashi da martanin abinda yake min din. Mun dauki lokaci a hakan kafin ya sake ni ya mirgina gefena yana sauke numfashi a hankali dan gyarawa nayi tare da kokarin tashi saman gadon naji ya rike min hannu na. Dole na juyo ina dan kallon shi kafin yace ina kuma zaki yanzu nace abinci zanje na hada maka kafin ka fito ko a nan zakaci yace dani duk inda kika bani a shirye nake inci banda matsala ga hakan. Mikewa nayi zuwa hada mashi abincin a nan falona muka zauna mukaci tare dashi ina jiran ya kara min maganan shiga motar sai naga ya sake yana ta wayan shi ina zaune gefe ina kallon shi har lokacin da ya gama ya mike yana fadin bari in dan leka dakina sai kin shigo. Don Allah dai ka barni in kwana a dakina mana tunda ka jagule ni ya juyo yana fadin wayo kima zaki min Deedar shiyasa kika taimaka min. Nace na taimaka ka da may kadai jagule ni kaimin wayon manya kuma kace sai nazo dakin ka may nayi maki ai hakkurine wanan na soma baki don naga kina son fushi dani. Sai da na karasa hada komai na bar dakin nawa na kashe wuta na fito tare da rufe part din na nufi wurin shi. Koda na shiga dakin yana zaune a bakin gadon shi ya tasa laptop din shi a gaba yana aiki a cikin sa jin sallamana ne ya dan dago yana amsa min. Dan zama nayi a gefen shi shiru banyi magana na sai ji nayi yace ina son shiga kaduna wanan satin in Allah ya kaimu. Da sauri na nuna mashi farin cikina nace Allah sarki ashe anty Fati na da bako ranan don Allah idan an masu AFFAN hutu azo min dasu. Yace idan nazo dasu ni yaya zakiyi dani ina cin amarci na juyawa nayi na kyaleshi ba tare da nayi magana ba kuma. Dan dariya yayi yace don nace ina cin amarcina laifine kuma nace wanan ne cin amarcin gida tab da yan sa ido. Dariya ya soma min tare da fadin nafa lura wanan amaryan tawa wurine bata samu ba da amarcin yafi nan da zan samu ashe. Yana fadin haka tare da rufe system din nashi ya hawo gadon tare da runguma na zuwa jikin shi ranan kan bai sarara min ba sai da ya debi rabon shi a jikina son ranshi. Duk da ba wani gudun mawa na taimakamashi dashi ba amma hakan bai hana shi yai min sheri ba nikan wai yaya zanyi da wanan mutumin ne wai. Ashe shi yana min hakane don tsokana yaji tsiwa na sai dai bai sani ba yanzu baki ya mutu kunyan shi da nauyin shi nake ji yanzu sosai. Ana gobe zai wuce ne na tura maryam kasu don ban iya zuwa ta sawo min tsaraban da zai kai min kaduna din. Banyi tunanen komai ba na shirya tsaraban kamar yadda nake bukatan su jira nake ya shigo in fada mai wayana yai kara shine a layin ya kirani falo. Da mamaki na tashi ban fita sai da na tsaya gaban mirrow na kalli fuskana tare da fesa kamshi a jiki na fito shar dani. Sai dai may ina fito na samay shi zaune a falon ga Nafisa a gefen shi tana kada kafa daya saman daya ta mike kafafuwan ta kofana dukkan su suka zura ma ido su ga fitowana. Tunda na tun karo falon na samay su a haka nima na gyara fuska na nadaure shi da kyau nazo da sallama na, shiya dago yana amsa min tare da nuna min kujera da in zauna. Da bissimillah na kai zaune ina mai sauraren su sai can naji ya ce kowan ku nan ina son ku bani hankalinku ku saurare ni . Ai kai muke sauraro tace cikin kada kafan da takeyi har lokacin ta yace ina son ku sani kowa a nan auro ta nayi don mu zauna tare mu raya sunna ma,aiki SAW nidai kai kawai na iya gyadawa sai faman tunane nake mai ya kawo wanan maganan haka. Wani hararan shi takeyi da yake wanan maganan batare da itama tayi magana ba yace Nafisa kin san dai Na sai maki motar ki akan wanan auren na Deedar kika ce baki son wanda na saya maki din kika dauki daya daga cikin wanda nake shiga ban kuma hanaki ko yi maki magana a kan hakan. Yanzu may ya kawo wanan maganan agaban wace ba ayi da ita ba tun farko yace maganan ya shafe ta ne dole ayi shi da ita tunda haka kike so. Yace kin san da haka ko baki sani ba tace na sani mana kuma wanan ra,ayinane haka shi nake so shiyasa na dauke ta yace good. To akan may ita zanyi tafiya nace malam musa driver ya dinga kaita makaranta kika hana shi alhalin kin san itama din mata ta tace tana da ikon yin yadda kikayi a gidan nan. Ta kalle shi tace eh ni na hanashi din ya kai ta don ban san da wanan maganan ba saboda baka fada min komai akan haka ba. Kaga ke nan ina da ikon da zan hana wani yin abuda kayan ka a gidan don nice za ka tambaya akan haka idan wani abu ya faru. Yace malam musa bai fada maki nine na saka shi yin hakan bane da kikai mashi warning akan dauka Deedar a motana. Ina son ji idan bake bace sai in kira shi yanzu gashi nan a bakin kofa yazo ya fada muna nashi dalilin da zan sa shi abu yakiyi ko yau yabar min gidana da aikina don ba zan dauki wulkanci akan iyali na ba ga kowa. Samad na fada maka nice na hana a fita da motar nan akan na hana matar ka shiga mota ne wai ka zaunar dani anan ina wani magana ne can na daban. Yace wanan din naki dauke shi wani magana ba ke nan idan anyi maki hakan zakiji dadi a ranki ki fada min eh ko a, a ya tambaye ta. Mikewa tayi tana fadin akan matar ka ta fada ma na hana ta fita a mota shine ka zaunar dani nan taga ka wullakanta ni ko may. Yace baki son gaskiya ke dama do baki san shi ba to bari kuji dukkan ku abina abina nane idan ban ma kowa shamaki da abina daga yau kada wata ta kara yiwa yar uwar ta shamaki dashi. Dama ai arzikin ta biyo taci ba kuma zataci komai ba daga gare ka sai dan karen wahala kafin ta kara gaba munafuka har kin iya shigewa daki da miji kiyi gulman wani dashi jin dasin may kika samu a gurin shi. Zagin ne naji yai min yawa har na kasa daure don karshe cewa tayi dole in fita in bar mata gidanta in koma wurin matsayitan iyayyena makwadaita. Dani dake waya fi tsiya Nafisa ai yanzu ba sai an bincika wanda yafi wani talauci ba anan don ke mai arzikin ne da baki fada ba wallahi. Ko mutum ya shigo gidan ba sai ya tambaya don ku yunwa ya koro dake da yan uwan ki kuka samu wurin lebewa ki bari kiyi prouding da abinda kika ne ma da kan ki ba abin miji na kowa ba. Sannan da kike fadi sai na bar gidan nan ki tuna ke ba Allah bace ba kuma kowa kike ba da kin isa ko shigowa ma gidan banyi balle in zauna kina gani na kuma baki da abinda zaki min. In har kin ga na bar gidan nan sai dai gawa na wallahi amma badon ke da sherin ki ba don kunyi min kadan dake da duk da abinda kike takama a gidan. Karya kike kema kin san nafi karfiki wallahi don banga abinda zan tsaya ma fada ba nan nace balle ni da banga abinda zan ma kishi ba nan iliterat din banza dake sai shegen bakin karya da cika baki. Gani fitan naso yai yawa ne yasa shi dakatar damu da tsaya tare da fadin ya isa hakana ban kira ku nan ba don kuyi min fitina na kiraku ne don in ja maku kunne. Bayan haka zanyi tafiya gobe zuwa gida ban son in dawo in samu kunyi wani fitina a tsakanin idan haka ya faru nayi bincike ko wacece mai laifi zan hukunta ta wallahi. Ya sa hannu a aljihun shi yana ciro kudi ya aza a saman table din gaban shi ya juya gurin ta yana fadin dauki gudu wani kallo tayi mashi tare da watsa ma kudin harara tana fadin kudin ma da zaka ban sai a gabants zaka bani kuma daidai da nata ko may yace. Eh nayi hakane don fita daga zargin ku na mata ya kirgo wani yana mika mata tare da fadin wanan dubu goma ne kiyi wa ihisan lalura dashi kafin in dawo . Yana fadin haka ya mike ya fara tafiya ya juyo yana fadin shike nan kuna iya tafiya bangane muna iya tafiya ba sauran jamma,a yaya kake son inyi dasu wanan matsalan ki ne yace yana tafiya cikin daga murya bayan na kwashi kudin na mike nake fadin mungode Allah umfana arziki. Nan na barta tana ta masifa wai bai mata kara ba yarsa kawai ya sani ita dayan fa afa yai mata sai yanzu ne da aka hure mashi kunne zaice bai ma sauran lalura sai ita tayi masu ko may ? Ni kan sai a lokacin ma nake sanin dayar yarinyar mai tsiwan ba diyar shi bace dama abin na daure min kai ina mamakin lokacin da suka haifi yar da ta kai haka girma. Nafisa ji take kamar ta mayar mai da kudin shi gashi kuma tana bukatan kudi a hannun ta da zaitai sabon lalura ita tai girki ranan don haka sai da ta saka shi daki ta lalashe shi ya kara masu wani abu. Washe gari tun da safe suka bar garin zuwa kd don yana son zuwa kano ya dawo kaduna a ranan shine dalilin yin sammakon su. Wanan karon ni kadai ce a gidan tunda na dawo school ban fita koda falo ba ina part dina yau kallo na kunna ina yi tunda ba wani girki zanyi ba ranan. Idan bai part dina bana wahal da kaina gurin girki sai dai in samu dan snack inci in kwanta jin anturo kofan dakin na kalli kofa ihisan ce ta shigo da kanta boya an tsefe ba kitso ta shigo wurina. Nace a, a Ihisan ke ce tazo har gurina da surutun ta irin na yara fadi wanan fadi wofi muna hira yarinyar na dan debe min kewa har tayi barci a dakin kwane a jikina. A hankali nayi dabaran kama kanta ina mata kitso kalaba nayi mata manya irin na yara don bata kwaso uwarta ba ubanta ta fi daukowa sosai ha halitta. Kalaban yai mata kyau na mike na dauko man kitso a dakina da yan ribos na kama mata kan har lokacin bata falka daga barcin da takeyi ba. Ashe suna can suna neman yarinyar a falo dakuna har wajen gidan basu ganta ba hankalin su ya tashi sosai har suka buga ma uwar waye ta baro inda take zuwa gida hankali tashe. Tun a hanya ta kira AA tana fada mashi batan yarinyar shima hankalin shi ya tashi sosai sai fama buge bugen waya yake a duba yarinyar wurare da dama. Yusuf da yaga yadda duk ya firgice gashi suna garin kano yamma yai masu basu gama abinda ya kaisu garin ba shima ya shiga damuwar batan yarinyar sosai. Yusuf din ne yace khadija ko tasan abinda ake ciki a gidan naji bata bugo maka waya ba sai lokacin ya tuna ya kira layina. Hankali a tashe yana fadin kina ina nace gida yace bakiji ihisan ta bace ba ne baki bugo min ba nace kamar yaya ta bace ga ihisan a gurina tayi barci tun Four muke dakin nan da ita fa. Ajiyan zuciya naji ya sauke ya ja tsuki yana fadin kaji fa ashe tana part din Deedar tana barci tun karfe hudu mahaukatan baza basu duba ba sunce sun duba ko ina a gidan kuma. Kiran uwar yayi yana fada mata yarinyar na nan gurina tana barci suje su dauke ta tace may uban wa yace ta daukar min yarinya. Idan tai mata wani sheri fa wani irin magana kike fada Nafisa sherin may zatai mata kuma Deedar fa nace maki ta gidana. Tsuki taja ta kashe wayan tana isa gidan part dina tayo direct ba sallama ta banko kofan dakin idon ta akan yarinyar dake barci saman kujera. Direct wurin yarinyar ta nufa ta dago ta tare da fadin uban wa yace ki dauko min diya wani sheri kika kawo tanan ki na mata yar bakin ciki, yar nawa guda daya da Allah ya bani itama neman ta kike da sheri ko may. Idan haihuwa banza ne ki haifi naki mana ki dinga kallo idan kina son yara a dakin ki daga yau kada ki sake taba min yarinya a gidan idan ba haka ba ranki zai baci kin aza haka ake samun haihuwa a ruwa ko may ke da haihuwa ai sai daki kalla in kin ce naci kika iya. Ban iya mata magana ba sai kallon ta da nakeyi ina mamakin wanan haukan nata ta dauko yarinyar da karfi tana dube dube a jikin kamar may neman wani abu. Har takai kofa fita da yarinyar a sabale saman kafadan ta ta juyo tana fadin kuma bari kiji idan wani abu ya samu ya ta nan da sati daya wallahi sai mun shiga kotu dake. Baki da hankali nace mata kina tunanen kowa ma irin ki ne muguwa ke kika san wanan zancen ni ban san shi yar ki ta kawo kanta inda nake bani na dauko taba kuma ko gobe tazo wuri na bazan koreta ba don ni ba mahaukaciya bace irin ki. Kije ki mutu ranan don tazo wurin makiyiyar ki, don Allah fice min da haukan ki na banza mara dalili ki sa ido ki gani idan na shiga harkan yar ki in dai ba ita tazo inda nake . Tace zaki gane baki da wayo duk ranan da wani abu ya samu ya ta, wama ya sani ko saceta kikai niyar ki yi Allah ya tona maki asiri kika fito da ita. Har ta fita mamakin kishi irin na Nafisa mai kama da kishin hauka nakeyi yanzu may na yarinya a cikin kishin mu bafa ni na dauko ta itace ta kawo kanta inda nake. Idona na lumshe maganganun ta suna min zafi a rai na nace ya Allah kana gani kuma kana jin Allah kai min mafita akan wanan aure. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Bayan sun dawo daga kano Yusuf ne dauke da kaya niki niki zai shiga gida dashi ya bishi da kallo tare da fadin wanan kaysn kuma haka daga ina suke. Yusuf din yace dashi sako ne aka bani inzo ma mutanen gidan dashi bishin ya sake yi da kallo yana mamakin ida kayan suka fito sai dai bayi magana ba suka shiga. Bayan sun gaisa da Fati ne Yusuf din ya mika mata leda tare da fadin wanan khadijja ce tace azo ma su AFFAN dashi wai akwai wani leda a ciki naki ne tanaa gaida ku. Dagaa inda take zaune ta tace tauuu, ta mika hannu ta karbi kayan tare an gode kallon mamaki ne a fuskan AA ddin karara sai kuma baiyi magana ba ya basar. Ba wani sako bane a ciki sai takalman makaranta da school baga har da littafai da warmers na makarantan yara masu kyau. Tun a gaban su ta bude kayan tana kallo murmushin da ta sake a fuuskan tane ya bashi mamaki tace to ashe monday akwai rigima wurin babana sai nayi wa kayan sheda. Taci gaba da bude dayan ledan turararuka ne a cikin na jiki humra dana daki masu kamashi sosai don ana bude su falon ya dauki kamshi. Allah yasa ai amfani dashi AA ya fada yana mai tabe baki tare da komawa saman kujera yayi balancen da kyau. Malam bafa kai ka sayo su ba balle kace wani abu yar kanwar tace ta aiko mata da tsara ta shafa. Rai fati ta hade da sauri saboda akwai ta da saurin yin fushi da mutum, don haka yana fadin wanan magana ta fuske, dashi ba tare da tayi magana ba. Yaran ne suka dawo daga gidan mahaifan shi suna ganin shi suka dan zabura don jin dadin gani shi komay suka tuna kuma sai suka ja suka tsaya suna fadin sannu da zuwa Abba. Kamar yadda ya saba yi da yaran cikin rashin sakewa ya amsa masu Yusuf ne yace a,a Affan an dawo ke nan sai suka nufi wurin shi idon su yana kan school bag din da suka gani a gaban uwar su. Karamin ne ya rarafa wurin uwar yana tambayan ta cikin kashe murya yana fadin mama Abba ne ya sayo muna ? Cikin muryan ta a yadda take magana kamar an sata yi dole tace wa yaron Anty ku ce ta sayo maku har da takalma da cooler. Dayan yaron ma yaje gurin yana tambayan ta mama wace antyn mu ta sayo muna ? Yusuf ya ce da yaran mommy ku amaryan Abban ku da tazo wancan karon tace a kawo maku murna yaran suka shiga yi tare da fadin mama itace tace zamu hutu Abuja ko ? Wani tsawa ta daka ma yaron sai da ya gigice tace kai rabani da maganan banza don Allah, ku magana baya isan ku . Kallon ta mijin yayi yaga yadda ta hade fuska ya fahinci fushin maganan dayayi take yi har wanan karon zata sauke ga yaran . Kallon yaran yayi shima cikin daure fuska tare da fadin kai ku kwashi kaya ku ku shige ciki ban son yawan surutu fon Allah. Yaran suka shige gwanin ban tausayi tare da daukan kayan su ita bata dauki lokaci ba ta mike ta mara ma yaran baya. Nuna ta yayi ga Yusuf yana fadin duba don Allah mutum ya zo daga tafiya ko ruwa ba zata iya bashi ba wai matar mutunce haka tun tasowan mu da safe fa na buga mata waya amma bai sa mu samu taro a wurin ta ba. Yusuf gajeren murmushi kawai yayi tare da fadin ina ruwan fati ita dai bata taba canzawa haka rayuwan ta yake sai hakuri kawai irin haka. Kai AA ya girgiza tare da fadin rashin sanin ciwon kaine yanzu ita deedar baga ta can tana hakkuri da halin Nafisa ba tasan komai fa amma bata taba nuna min hakan ko anyi mata sai dain in suyi a gaban idona. Bata fita kurciya ne sa ba kusa ba Yusuf yace ai ba zaka hafa Fati da khadija ba don yanayin su ba daya bane matsalan ita Fati akwai saurin fushi da kowa kuma bata da sakewa. Ya karbe Yusuf din da fadin nakasa ne kawai da wulkanci ita ds kowa haka take kamar mai jin warin mutane. Na fadi shafa turaren zatayi ko ajewa yara su bata wani itin turare ne ban sayo mata da haka zata barshi batai amfani dashi ba yara su zubar ko wani yazo ya dauka. Ya kare maganan shi cikin jan tsaki yana kiran Affan daga inda yake zaune sai ga yaro yazo da gudun shi yace kace ma laraba ta kawo muna abinci. Yaron ya kalli uban yace Abba laraba tayi tafiya bata nan da dadewa in fada ma mama ne yace barshi ya mike ya samay ta a daki yace da ita. Tana kwance baki sa muna abinci bane tace nasa amma ni tunda rana nayi kuma banji kace a kawo maku ba juyawa yayi inda ya fito ya samu Yusuf zaune yana waya. Ba sai ya tambaya ba yasan bai wuce da zainab yake wayan kallon shi yayi tare da fadin muje gurin hajiyan mu muci abinci don Allah. Katse wayan Yusuf yayi yana fadin bata girkaz bane ko may yace muje don Allah don yunwa na soma ji rabona da abinci kasan tun safe. Suna zaune a falon mahaifiyar shi wance ta gama fada da halin Fati din suna cin abinci wayan shi yai kara ya dauka yana dibawa. Nombana ya gani yayi received din call din tare da fadin slm nace wlsm an wuni lafiya ya hanya ya amsa da fadin Alhamdullahi nace ya su mama da sauran mutanen gidan an samay su lafiya ko? Lfy ya amsa dashi nace agaida min da su ya su Affan da baba yadda naji suna kiran yaron dashi yace duk suna lfy a huta gajiya a gayar min da anty Fati don Allah, dama na kira inji lafiyan su ne in maka sai da safe yace ya gode ya kashe wayan shi. Yana aje wayan hajiyan su tana fadin wacece yace khadija ce wai tana gaida ku dan murmusawa tayi tana mai jin dadi har cikin ranta. KHADIJA Muna gama wayan dashi na gyara kwanciya dama a kwancen nake don har na kashe wuta ko tun karfe shida da rabi na rufe kofan part dina. Fruit kawai nasha sai naji na koshi a lokacin sallah nayi na watsa ma jikina ruwa, na haye gadona shine na kirashi. Tofe jikina nayi da adduan neman tsari a wurin Allah na gama na tofa a hannu na tare da shafe hannaye ga jikina na gyara kwanciya na. Allah yasa washe gari ban shiga school haka yasa na sha barci na da safe ban ko tashi na nema ma cikina abinda zanci ba. Sai da yunwa ya damay ni cikin barcin nawa na mike na shiga bathroom nayi brush tare da kewayawa na fito na fada kitchen. Simple abinci na hada na fito falo dashi na zauna ina ci na bar wayana a kuryan daki ashe yai min har three miscall ina falon ban sani ba. Sai dana gama na shigo inyi wankane naga kiran nashi diban lokaci nayi naga rana yayi tunane nayi yana ganawa da iyayyen shi a daidai wanan lokacin. NAFISA Tana zaune falo gidan tare da yan uwanta fada take masu akan sunki kokarin su kama wani namiji daga irin mazajen birnin nan da suke zuwa wurin AA itama ta samu ta huta da nauyin su haka. Tunda yanzu duk maganar samad daya biyu zaice ta kwashe yan uwan ta tabar mashi gidan shi tunda bata son a zauna lafiya. Duk wanda ya ganta zaune a falon yasan Nafisa na cikin wani yanayi dan kwanakin nan. Kalo daya zakai mata ka hango matsala a tattare da ita wai a cikin ma tana karfin hali ke nan tunda tana samun yadda take so a gidan har yanzu. Sai dai matsalan ta daya ne shi kuma abinda ke bata mamaki da haushi da takaici mamakin ta da haushinta ta ko shi wai ashe dama zata iya zama da kishiya a gidan nan kwana da kwanaki. Bata taba zaton ko yar yaren su na buzaye ta shigo gidan ta zata dauki kwanaki a tare da mijin ta ba. Yau sai gashi yar nigeria ce ta shigo mata gida duk kudin da ta kashe da irin maganin da take banka ma Samad bai hana wanan shegiyar yarinyan ta zauna mata da miji har su kwana a gado daya dashi ba. Wani irin yawun takaici ta hade a mokoshin ta tare da fadin a fili lalai ya kamata in nuna ma wanan yarinyar ni bata wasa bace. Idan tsubu ta iya ko tsafi zata nuna mata karya suka iya don bata kaita iyawa ba ita bata taba daukan akwai wata macen kasar nan da zata iya ja da ita ba a zauna lafiya. Wanan tunane da take yi ne yasa ta rashin jin karan da wayan ta keyi kiran mijinta na shigo mata a lokacin. Wanan tunanen dashi take kwana dashi take tashi don bata kaunar ta bude ido taga har yanzu yarinyar nan ta saura a gidan ta. Ta sha alwashin ko ta halin kaka sai taga bayan khadija a gidan nan kuma ta kama mijin a tafin hannun ta idan ta gama da khadija din. Daga kai tayi tana kallon kofan shiga part dina taji kamar ni take kallo ta watsa ma kofan nawa harara aiko yayi daidai da fitowana daga part dina. Zan tafi wurin gyaran kai da sauran part din jikina don kusan wata ban gyara jikina ba kaina ya fara min kyakayi don har na sance kitson a haka nake daure shi yanzu da ribon ni kuma ba gwanar barin kai ba kitso bane tare dani. Sannu fa nace da ita ban sani ba ko ta karba min sannun da nayi mata din nidai na fice ba tare dana kara kallon inda nake ba. Ita a ganin ta rangwada nakeyi mata bata san haka halittan diya matan yake da rausaya ba ko a banza. Na dauki lokaci ban dawo ba don na dan biya nayi sayayyan kayan amfani wanda na sawo pad saboda expecting din period dina da nakeyi a cikin satin. Ko da na dawo gida yamma yayi sosai ban wahal da kaina ba wanka nayi nai sallah na nemi wuri na kwanta . Waya na dinga yi da yan gidan mu munfi dadewa da ya Amina a wayan muna hira akan yaran ta don akwai ni da son yara sosai a rayuwana. Har barci ya dauke ni gari ya waye nasan maigidan zai dawo ranan kuma nice zan karbi girki don haka na shiga kitchem tun karfe hudu na fara hada mashi girkin da zaici. Dakin shi na shiga na gyara komai na fito bandade da fitowa ba Nafisa ta shigo gidan daga unguwa. Na fito falon gidan ma na bada umurnin a gyara na koma na kammala girkina shida saura suka iso gidan. Banji dawowan shi ba sai da Yusuf yazo part dina kawo min sakon mommy nasan sun dawo bayan Yusuf ya fita wurina ne na nufi part din shi. Na samu ya fito daga ban daki yana ganina I a dan sake murmushi yana gyara hannun rigar dake jikin shi haka yasa na fahunci alwala yayi a lokacin. Gaida shi nayi ban tsaya ba na koma part dina don bin ka,ida sunna don lokacin shiga girki na baiyi ba a lokacin sai bakwai na marance zan shiga lokacina. Sai bayan sallah isha,i na gama shiryawa kwalliya na zauna na tsara ma fuskana atamfan super na sa wanda maryam ta karbo min su daga wurin dinki kayan sun matukar karbuwan jikina don sun fitar min da surana sosai na jikina Kallon kaina nayi a mirrow na naga yadda komai nawa ya zauna cas na kara feshe jikina dakyau da kayan kamshi. Na dauki basket din tare da kulle part dina zuwa wurin shi dauke da basket din dana shirya abincin shi a ciki . Falon sama din na tsaya sai da na shirya abincin komai na aje inda ya kamata daga baya na naji an rungumo ni. Dan firgita nayi tare da juyowa ina kallon shi kaina na dan langabar da kaina tare da fadin wallahi kaban tsoro yace Allah ko sake ni yayi bayan ya murza min hannu yace mai aka girka min cikin sakewa da jin dadin ganin haka yake magana. Abinda na fahinci kafi so ne na girka maka ko zakaci ban sani ba ya fara bude warmer din ke nan sai ga Nafisa a gaban mu tana fadin. Samad ya naga haka ke may kikeyi anan ta juyo gare ni tans tambaya na tana aje kulan dafa dukan da ta shigo mai dashi da plate. Ta fara fadin wai may kuke nufi ne a gidan nan ya karba da fadin kamar na may fa? May ya kawo wanan wurin nan yanzu may tazo nema a wurin ka ko iskancin nata da samun wuri har yakai haka ban sani ba. Ke ban fahinci maganar ki ba fa Nafisa ki fito fili ki min magana yadda zan fahince ki kin tsaya kina wani sharfi haka. Tace amma kasan a ka,ida nice da girki yau don ko yau ka dawo daga tafiyar da kayi kaga ke nan nice zan karbe ka yau. Yace wani makamin ne ya koyar dake hakan ina ranan jumma,a nabar garin nan da safe da yamman ranan ya kamata Deedar tayi giri bana gari . Washegarin asabar sai wa zaiyi tace ita yace idan gari ya waye fa tace ita ya kamata tayi yace kin ba kanki amsa yanzu. Tace wallahi baka isa nice ya kamata nayi tunda daga tafiya ka dawo yaudin don haka a wurina zaka sauka ke nan. Wai hauka kike yi ne Nafisa ko mai tace kaidai ke haukan don gashi kuna son ku dulmiye ni akan hakkina. Tsaye nake gefen su mamaki ya hanani yin magana don naga haukar kishi a filin Allah yau sai kallon su nake ina sauraren su. Ke wace irin dakikiyace wai amfada maki ana haka ne idan kinga anyi hakan tafiyace ya kama mutum da zai share lokaci bakuma ance lalai dole mutum sai ya sauka dakin babba ko karami ba. Zaka iya sauka a ida zuciyar ka ke so ko wancen karon na sauka wurin ki ne badon komai ba sai don a zauna lafiya badon wani abu. Don may ita zata fahince ni ke ba zaki tsaya ki natsu ki gane mai addini ke nufi da hakan ba sai shirmay ban za. Tace yanzun kana nufi a wurinta ke nan zaka sauka ko may yace ba itace dani ba yau don may ko ba zan sauka wurin ta ba. Samad amma kai macucine ashe har zaka iya rufe ido akan wanan mai ruwan fulanin ka tozartani a gaban ta. Uban may zata tsinana maka a dakin banda kwaciya tana shafa ma janbaki tana bata gado da katifa. Bayan wanan akwai wani abinda zai shiga tsakanin ku ne da ita bayan na gane hakkuri kake da ita tunda aka kawo ta. Yace yaya kikayi kiks san hakan ko labe kike zuwa kina muna ban sani ba koko ita ta fada maki photo nake ganin ta ba mace ba. Ina macen take anan wanan ai mun sani farin mai ne wanda matan ku ke shafawa an shafo don a gwada dani aja hankalin ka. Ko gashin dokin da take karawa ne ya rufe maka ido kake ganin days muke a wurin ka dariya sosai maganan ya bani ban san lokacin da nace da itaba. Au haka kike tunane a she diba ki gani yadda Allah ya baki fari da komai haka nima ya albarkace ni da abina kamar ku idan ma gashi na doki ne ai yana samun gyara akai akai ko ? Ba kamar nake da ke cushe a guri daya ba sai doyi balle Allah ya tsareni da kari a kaina don ni musulmace ina tsoron haduwa da Allah na tunda ya sani. Tace ina musulma a nan dida karki bata min suna kamar yadda kike bata mashi nashi don ni khadija nake. Ki koma makaranta don Allah ki fara sanin Allah kafin kizo kina karanta ma mutane kishin ki na jahilai. Jahila na gidan ku kin bari a hasale na juyo gare ta dan jin abinda ta fadi wanda nasan uwata take nufi da jahila. Nafisa kina haukane wai da zaki zagi iyayyen ta tace na zage ta ko zaka rama matane ina sauraren ka. Nace shi ba jahila bane irin ki don yasan abinda yake yi ki koma makaranta da wanan jahilicin naki hakana ko zaki san abinda kikeyi nan gaba. Tace Ke da ke zuwa makarantar may kika karu dashi banda bin maza da kike fitayi wanan kuma kanki kike fada ma don ke ce kullun a hanya ke ba kasuwanci ba aikin office ba wawiya mai fitsari taye ba kama ruwa ko tsarki don haka banga laifin ki ba idan kina haukan ko zargin wani. Abinci ne yau ko zaki mutu nice da miji sai yaci kuma mu kwana tare da baki so ki gani kije ki mutu ko ki fada ruwa ki hade ran ki. Zata fara ihun ta yace Nafisa bar nan gurin tun muna sheda juna dani dake tunda kin san ba gurin ki nake ba yau. Agaban ka kake jin zagin da matar ka take min yace waya fara zagin wani dake da ita ki bace min dagani nace kafin ranki ya baci. Tace bazata fita ba yazo ya ja mikewa yayi ina kallon shi ya ficiki hannun ta tana turjewa zuwa waje ya wurgata tare da rufo kofan saman gaba daya ya dawo ya zauna yana huci tare da rike kan shi. Da fashi nayi don in nuna mashi bai damay ni ba nace kan wanan abin zaka bata ranka kafa saba da halin matar ka ba komai ya kawo ta ba don kawai ta bata maka farin cikin kane ko nawa. Ajiyan zuciya ya sauke tare da fadin wanan bansan ranan da matsalanta zai kare ba a gidan nan . Nace hakkuri zakayi damu don haka halin wasu mata yake akan kishi tunda ba mai kaunar kishiya a tare dashi. Cikin zolaya yace har dake kenan ashe nace ni ba mace bace da zance ban kishi ko wace mace ai tana da kishi sai dai na wata yafi na watane. Ranan mun sha zagi a gurin nafisa da kyar yan uwanta suka lalabata bayan tayi masu bayani suka ce itace bata lissafa da kyau ba. Suma sun sha fitina a gurin ta kafin taja kafan ta zuwa daki tana jin maranta yana masifan ciwo a lokacin. Yau AA ya sha mamaki duk cikin kawar da fushi a zuciyar shi kamar yadda nafisa ke son ta bata muna daren mu dashi yasa na zage nayi mai abinda ban taba yi mashi ba tun fara aurataya na dashi. Wanda na barshi da mamakin hakan a cikin ranshi can gabsnin asubs ne mukaji dukan kofa da karfi cikin tashin hankali. Rigan shi ya zura a jikin shi ya nufi kofan yana tabayan waye a kofan muryan Yanyala ce take fadin Nafisa ce ba lafiya jini ne ya balle mata. Hankali tashi ya bude kofan yafita daga dakin binshi da kallo nayi tare da fadi a fili ikon Allah Allah ka kareni daga sherin wanan matar lafiya a cikin kwanciyan hakali ka, ka haushe ni akan ta ko da yaushe. Jin shi shiru yasa na tashi da daura zani a gaba na saka hijjab dina na fito daga dakin. Kowan su hankali shi a tashe yake na dan karasa part din nata sai dai ba isa kusa ba a daidai lokacin da ya fito da ita rungumay a jikin shi cikkn gala baita suka fice daga gidan. Su samihane suka shiga ba tare da yanyala ba a gurin su nake ji wai cikin jikin tane yake son ya bare Allah ya sauwaka nai masu na dawo saman wanka na yi a cikin daren nan tare da dauro alwala na fito na tayar da sallah. Ban kwanta ba sai da akai kiran sallah asuba nayi sallah tare da jawo wayana na kira layin shi ina tambayan shi mai jikin yace da sauki. Am bata gado ana son cikin jikin nata ya tsaya Allah ya sauwaka nayi mai ban kwanta ba na fito na nufi part dina. Kafin dan lokaci na gama abinda nakeyi ganin bai dawo ba had lokacin yasa nafito ko zan samu mai sauke ni a school. Nakoyi sa,a don su Samiha zasu asibitin nai ma driver magana ya sauke ni a school yacs ba damuwa hajiya. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Tunda na isa school hankali na wurin su ban cikin natsuwa don a yadsa naga sun fita da ita ta matukar ban tausayi. Sai dai abinda ba,a saka ka ciki ba kuma nasan ko na saka kaina ba zanyi fari a gurin Nafisa ba idan ma banyi hankali ba zata iya cewa nice na jefeta da wani asirin haka ya samay ta. Sai dai na kudurta a raina idan na fito zan ji halin da take ciki in gaida ita kafin nan na yanke a raina ya kamata in fara neman shawaran maryam ance wanda ya riga kwana yana rigaka tashi inji hausawa. Don haka maryan zata fi ni sanin dacewa inje ko in bari sai ta dawo gida mu gaisa da haka naci gaba da daukan darasins a class. Sai a zahar muka fito daga lectures a masalaci kamar kullun muka hadu na rigata zuwa har na kusa idar da sallah sai ga maryam din ta iso na gama na dade ina addua kafin in bar gurin zuwa waje na zauna ina gyara jikina sai ga maryam din ta fito. Muryan ta naji a bayana tana fadin amarsu ta ango yau lafiya kike kuwa tun dazu nake tsaye ina kallon ki kina tunane ko anyi halin naku ne agidan. Ajiyan zuciya na sauke ina shafa weat lips a bakina tare da fadin Allah dai ya kyauta maryam amma fasawa za, ayi tunda Allah ya kawoni gidan matsala. Dafani tayi tana kaiwa zaune tare da fadin AA ya dawo ke nan daga tafiyan ko ? Tana mai tsura min ido taji amsa nace cikin yar murya karama ke dai ya dawo jiya maryam kuma har munyi halin namu. Nan dai na koro mata da abinda ya faru a daren jiya din tsakanin mu da Nafisa da wanda ya faru da ita din zuwa safe har zuwa na school. Ikon Allah wai ko khadi matar nan tana sallah kuwa nace waya sanar mata tunda ba part din mu daya ba nace balle ma nasan tanayi tunda nasan shi ba kyaleta zaiyi ba. Sai dai ibadan ragaggene na sani ba cika shi akeyi yadda ya dace ayi ba Allah dai ya kyauta kawai kedai maryam tace amin. Nace ni yanzu shawaran ki nake nema shin in tafi asibitin ne idan tana can har yanzu ko in bari sai idan ta dawo gida in gaida ita don kin san ita bahaguwar mace ce maryam ba ai mata daidai kin sani. Shi AA din ya kiraki ne da sukaje asibitin nace bai kirani ba nice dai ma na kirashi ina tambayan jikin nata a guriin shi. Tace matsalan maza ke nan wallahi ai kamata yayi kafin ma su fita ya sanar dake amma yasa kafa kamar baisan akwaiki a gidan ba akala da suka isa komai yayi daidai ai sai ya kiraki yai maki bayanin halin da ake ciki ko. Nace ni wanan bai damay ni ba don sun fi kusa shiyasa kike ganin duk irin fitinan da zasuyi bai zurfi a cikin sa dan kai zasu bari a cikin idan ka shiga. Yanzu zasuyi masifa kamar su kashe junan su amma minti goma yayi yawa ki samu sun shirya don may zan tsaya ina wahal da kaina akan su nidai hakkina na tsare kawai don kada wullakanci da raini yai min yawa. Tace kin kyauta ma kanki wallahi don irin auren jaraban nan idan kana gidan da akeyin shi wallahi sai su daure maka kai don ga abin haushe na faruwa saidai kai kaji musu haushin kawai su basu damu ba. Ni yanzu shawaran da zan baki shine ki fara bincikawa idan tana asibitin sai muje can mu gaida ita ai ba don ta zaki ba don Allah ne da shi kuma AA din. Sanan kuma hakan wani makami ne a gurin ki don gaba koda magana ya taso dai kina da abinda zaki fada masu wanda ita ba zata iya maki shi ba. Na nisa tare da fadin gaskiya maryam ba zan iya kiran AA ba tunda shi baiyi tunanen ya kirani ba insan halin da ake ciki. Tace kada ki kirashi nima ban goyi bayan ki kirashi ba ai maza suke gyarawa kuma suke bata gidan su idan sun tashi. Barin kira Yusuf muji halin da suke ciki kiin ga sai mu san abin yi ko kai kawai na gyada mata ina matse jikina da hannaye na wuri daya ina tunaane tare da takurewa a ida nake. Kira uku ya dauki waya tare da fadin maryam kuna tare da kanwa tace khadija tace eh muna tare itace ma ta sa in kiraka muji halin da mutanen gidan su suke ciki a asibitin. Yace eh suna can har yanzu don likita ya bata gado na kwanaki har aga halin da cikin zai yi tukun maryam tace dama muna son jin ida suke ne sai taje ta gaida su. Yace yanzu kuna free ne ko sai anjima inzo in kaiku tace bamu gama ba amma zaka iya zuwa muje ai ba matsala kada yamma yayi. Yace kujirani ganinan zuwa insha Allahu tace sai kazo Allah ya tsare take care ta kashe wayan tana kallona tare da fadin ke kinji bama zancen dawowa gida bane fa. Don an kwantar da itane acan sai anga yadda hali zaiyi idona na lumshe ina tunane rayuwa na sake budewa nace oh mata suna ganin abu akan ciki kamar ba ita bace lafiya jiya fa. Tace ikon Allah ko mutuwa akace maki tayi yanzu ai ba abin mamaki bane don ikon Allah yafi danan nace kwarai kuwa maryam. Tace aini abinda nake ji zata zauna ta iya yin bedrest din nan a asibiti wanan matar da take kamar shanshani wurin yawon tsiya. Zata iya mana idan ya kama tayi dole don lafiyan ta sai dai idan cikin bai damay ta bane mun dan dauki lokaci a gurin kafin Yusuf yazo. Da ya iso wayan maryam din ya kira yana sheda muna zuwan shi muka samay shi a gurin da yai muna kwatance din. Baya na shiga maryam a gaba ta zauna dashi sai da ya fara tuki nake gaida shi ya amsa da yaya gida jiya mun iso ban samu shigowa cikin ba ina sauri. Nace kun dawo lafiya ya mutanen gida yace suna gaida ku Fati tace ai maki godiya sosai sun gode nace kai sai kace wani abu na basu mai yawa. Yace kin yi kokari sosai khadija ai baki san wani abu ba wallahi macen kwarai ke kula yaranta har tayi masu alheri irin haka. Ina ta samu haka a baya banda ma idan mijin zai yi idan har Nafisa ta sani hanawa takeyi ko ta amshe kudin da sunan zata saya masu abin sai labarin ga. Maryam tace wallahi wanan abokin naka yana bukatan gyara a rayuwan shi wallahi ta yaya kana tare da mutum abu ya samay ka bazaka iya fada mai ba. Yace maganan da muka gama dashi kenan kuka kirani wai cewa yayi ai khadija ta sani kuma ta wuce school bada izzinin shi ba. Murmushi nayi nace ni ina na kara ganin shi ma yayana tun fa da aka buga kofa ya fita ban sake ganin shi ba har yanzu. Zan zauna ne akan lalurar wata in bar nawa yace na fada mashi ai da yake fada nace kai ka kirata kai mata bayani halin da kuke ciki shine yai min shiru. Ki dai kara hakkuri kanwata wata rana sai labari insha Allah irin wa yan nan matan ba abokan zams bane wallahi. Yanzu a asibiti sai da suka kwashi rikici sosai da ita wai ita bazata zauna ba har tsawon wani lokaci da kyat likitan tayi mata bayanin halin da take ciki kafin ta yarda ta kwanta din. Allah dai ya bata lafiya nace idan tayi hakkuri kwana nawa ne in ta samu lafiyan ta ba sai ta dawo gida ba duk da an san zaman asibiti ba dadi wallahi. Yusuf yace lafiyan ta yafi komai fa khadija ita wata irin mace ce da bata da ganewa ne mace har da kanta takewa kyata haka. Nidai shiru nayi suna ta maganan su a hanya wurin masu fruits ya tsaya ya fita sai gashi da ledojin fruits an biyoshi dasu zuwa wurin mota yace zaku shiga mata dashi kada kuje hannu sake. Godiya mukai mai yana zama nace ummmhmm ni nasan ko kallon wanan ba zatayi ba zatace wani abu muka saka mata aciki don ko yanzu ba fita zanyi ba a gurin ta. Kada ki damu da wanan don ko baki fada ba sai ta fada idan kuma baki kai badin ma fada zatayi don halinta ne haka. Mun isa asibitin motar AA mukai tozali dashi a haraban wurin aje motocin muka fito Yusuf na gaba muna biye dashi a baya shi ya dauki ledan tsaraban kayan dubiyar da ya saya muna din. Lokacin ganin mara lafiya ne a lokacin ga yan uwanta da kawayen ta harda ma wa yanda ban sani ba a gurin. Suna hango mu kamar ba asibiti ba idanuwan su ya dawo gare mu caaa sai kuskus ake yi a gurin bani ba ko maryam bata tsaya binta nasu ba muka shige dakin da take kwance a ciki. Ita kadai ce a cikin dakin ba,a hadata da kowa a dakin ba komai akwai a dakin na jin dadin rayuwan dan adam aciki. Yana zaune bakin gadon da take kwance ga su madam a gefen zaune ya rike mata hannu suna magana muka shiga dakin. Yusuf ne ya aje kayan yana gaida ita da jiki muka karaso wurin sai dakin yai tsit a lokacin suna kallon mu. A bakin gadon muka tsaya muna mata ya jiki bata amsa muna ba sai shi dake zaune ke fadin baki jisu bane ? Ta wani dako kai tana fadin najisu mana ba tazo ta gani da idon ta ba ban mutu ba yadda taso in halaka. Murmushi nayi tare da fadin Allah dai ya baki lafiya ya tsare gaba mu duba lafiyan ki ne ya kawo mu ba wanan ba. Allah ya sauwa ka nace tare da fadin mu tafi ma maryam muka juya mun fara tafiya naji muryan ta a cikin hausan ta dake da surki tana fadin ku zo ku dauki kayan tsiyar ku, ku tafi da sherin ku baku ganni cikin mugun hali ba. Madam ne tace haba matar Samad wanan wani irin haline ai kya bari ki koma gida duk abinda kike ji kuyi shi a can amma ba anan ba. Duk wanda yazo gaida kai koda na munafunci ne ai yayi kokari tunda tsabgan gaban shi ya bari yazo ko. Mudai mun fita daga cikin mu ba wanda yai magana har muka kai bakin mota muka tsaya jiran yusuf ya fito mu tafi. Ashe a ciki sun kwasa da Yusuf din a kan mu da yaji zagin yai yawa yace mata irin hakane kike jawa kan ki matsala may zata saka maki a cikin ayaba da lemo ko kankana yanzun fa suka sa na tsaya hanya suka saye shi. Tace koshi an fada mashi yarda tayi dashi idan akwai wanda zai kashe ta farko ai shine don ta dade da sanin haka . AA ne ya mike tare da jan tsuki ya yiwa Yusuf magana su fita daga dakin tace kai kuma ina zaka ko binta zakayi ne ? Yace idan na bita laifi ne yasa kai suka fito sun samay mu a tsaye ba mai magana a cikin mu kowa da kalar tunanen da yake yi. Bayan fitan mu madam ne ta ja tsuki tare da fadin Nafisa ina ganin tafiyan mu ba zaizo daidai da ke ba gaskiya. Yanzu wa ya saura irin wanan kishin da kike haka koma may ye kin ga yanzun tafiki gaskiya ga mijin ku don tazo dubaki a gaban shi kin mata rashin mutunci kuma. Yanzu abinda kikai din nan yayi daidai ke nan har karamar yarinya tazo tafiki wayau ta nuna maki hillan mata da kissa. An san akwai zafi tunda a sanadin ta haka ya samay ki sai ki barin har kiga lafiyan ki tukun na sai kin koma gida ki nuna mata halin ki. Tace madam ke ma kin san ba zan iya ba wallahi uban wa tazo nema a gurina in ba zuwa tayi tagani ko zan mutu ko ina cikin wani hali ? Dadai kin koyi boye wani hali a gaban miji don ranan fadin magana tace ba wani ranan fadar magana in ba bayan wanan yar iskan nayi da mijina ba. Ledan kayan fruit madam ta jawo ta fara budewa tana fadin mukan bari muci tunda bada sunan mu akai aikin ba komai ba zai samay mu ba. Nan suka far ma kayan da ci kamar jira suke itako wani irin bakin ciki take ji a ranta na bin bayan mu da yayi. Sai lokacin yake gaisawa da maryam ta amsa tana tambayan shi ya mai jikin yace da sauki ni dai ko kallon shi banyi ba ina kallon wani wurin. School din zaku koma ko gida maryam tace ni dai zan koma itakan gida zata yanzu ai yamma yayi ko mun koma ba wani dadewa zamuyi ba a tashi. Barin sauke ku yace nace da sauri da ka tsaya kada kuma kayi laifi yaya Yusuf sai ya sauke mu Yusuf ne yace lalai kan don abu kadan yanzu laifine ga mai ciki. Tsaye yayi sororo yana kallona ina magana ga mamakina nayi zaton zai yi magana amma sai ya kyale Yusuf din ya tafi damu har muka kai gidan ba sa baki a hiran su ba. Wanda duk hiran akan Nafisa ne suke yin shi muka kawo nayi wa Yusuf godiya na bude na fita ban san ya sukayi ba naji muryan maryam tana kirana na tsaya tare da juyowa. Ganin tana magana yasa na koma wurin motar inji mai zata fada min sai naji Yusuf na fadin kanwata don Allah kada ki sa komai a ranki halin Nafisa dai yanzu ba bakon abu bane a wurin ki. Na dan yi dariyar yake ina fadin ba komai wallahi nagode yace ke dai kici gaba da addua don Allah shine kawai mafita ga wanan shu,umar abokiyar zaman taki. Murmushi na sakeyi ina fadin ba komai na gode nayi masu sai anjima na wuce ciki zuciya na cike da damuwa ina isa na shiga babu kowa a gidan sai mutum daya da yara a gidan. Ihsan na ganina ta sheko da gudu ta rungumay ni wanan matar dake gida da suke kira da gambo tazo da sauri tana kokarin daukan yarinyar taki zuwa yar Nafisa babba tayi mata yare naga ta bar ta dani. Dakina muka nufa da ita tana min yare na bude muka shiga kayan zaki na bata irin na yara ta fita da gudu zuwa waje murmushi nayi na tube don in watsa ruwa a jikina. Sai da na fito nayi sallah na koma na zauna na gyara jikina a gaban mirrow kitchen na shiga don nemawa kaina abinda zanci may dan karfi don yanzu ina ci abinci sosai gashi tun safe ban ci wani abu a cikina har na fara galabaita. Lafiyayyen nodles na hada wanda yaji kayan hadi don ya cika min ciki na na debo nazo falo zama sai ga Ihsan ta dawo dakin wurina. Tayi nayi mata tace zataci na dibar mata waje ta nufa dashi na zauna na fara cin wanda na zuba ma kaina. Yar wurin Nafisa ne ta shigo sai ranan ta fara gaidani a gidan tana tambayana idan abincin da na dafa ya rage in diba mata yunwa take ji. Kallon ta nayi kamar zanyi magana sai dai na mike na shiga kitchen din na juyo mata wanda ya saura gaba daya. Ta karba batare da furta komai ba ta fita bayan na gama ne na fito don gyara part din msigidan na samay su zaune dukan su harda mai tsaron su a gidan suna ci. Na shiga dakin yana a yadda na barshi da safe sai kayan barcin da ya cire a saman gado ko tsaban rudewa yasa yau ya barshi a wurin ban sani ba. Wanko ban dakin na fara yi inda na dawo dakin na gyara mai komai tsab na rufo kofan kamar yadda na samay shi na dawo part dina. Har akai magariba banji ya shigo gidan ba har tara na dare barci ya fara dauka na tashi nayi na kule part din na don na dauka a asibitin zai kwana ke nan. Sai sha daya da wani abu ya dawo gidan bayan sun gama tsiya da Nafisa daga kwancen amma bata barshi ba don cewa tayi bata yarda ya kwana a gidan ba don ranan girkita ne. Kada yaje wurina don baiga idon ta ba da alkwari da komai ta barshi ya tafi gida shi dai sai lalabata yakeyi kada cikin jikin ta ya samo matsala dai. Koda ya shigo gidan ba kowa a falon sai dai wuta a kunne yake har lokacin kallon kofan part dina yayi ya ganshi shima rufe. Kofan gidan ya rufo ya nufi part din shi don ya watsa ruwa Allah ya taimake shi yayi duka sallah a cikin jamm,i wanka ya rage mai sai dan abinda zaici. Ya fito yana saye da bathrobe ya tsaya gaban mirrow dakin har ya gama shiryawa cikin pjarm din shi ya sauko zuwa part dina ya murda hardles din yaji kofan a rufe kara murdawa yayi sosai ya ji a key kofan yake . Gashi yana gudun buga kofan yan uwan Nafisa su jishi sukai mata labarin sun ji shi yana bugun kofa na dole ya juya ya koma part din shi zuciyar shi a cunkushe. Ban falkaba sai asuba karan agogon dakin ya ta dani duban lokaci nayi tare da saukowa saman gadon na nufi bathroom din daki. Alwala nayi bayan tsarkin da nayi na fito na tayar da sallah ban kara kwantawa ba kitchen na fada don ina son in dan dafa wani abu in rika wanda zanci don jiya nasha wahala sosai a school din. Saida na gama hada abincin ne na shiga wanka tare da zuba wanda zan dan karya dashi kafin in fita yau tafa na sa a jikina zani da riga da yake zamay min wahalan idan na daura amma haka nake koyon sabawa da daura zani yanzu. Falon na dawo a cikin shirina na zauna cin abincin ban jima da zaunawa sai gashi ya shigo dakin dago kai nayi na kalle shi na kawar da kaina naci gaba da cin abincin da nakeci. Sai da yazo gab dani na ce dashi ina kwana bai amsa ba sai da yakai zaune ya amsa da lafiya maimakon in ci gaba da cin abincin sai na koma wasa da cibin. Amsan cibin yayi daga hannu ya debi abincin yakai bakin shi tambayan daya jeho min ne yasani dago kai in kalle shi. Yanzun kika dafa abincin ko may da eh na bashi amsa kawai ina nawa abincin yake ya tambaya cikin tsure ni da ido . Nace ban dauka zakaci ba nawa kawai na dafa na bashi amsa yace saboda may koni ba zanci abincin bane naji ya fada. Nace na dauka a asibiti zakaci naka ai daga haka na mike na shige ciki na barshi a wurin bin bayana yayi da kallo yana murmushi. Koda na fito a ciki shirina na samu ya cinye abincin gaba daya dana bari kujeran dake gefe na samu na zauna akai ba tare da nayi magana ba. May yasa jiya kika fita baki kirani ba kuma waya sauke ki school din da kika tafi nace ban san amsan da zan bashi ba don haushi sai nayi shiru. Yace tambayan ki nakeyi kin kyale nace yan uwan matarka da zasu fita na roka su sauke tare dasu muka fita yace OK da izzinin wa kuma kika bisu ? Amma kasan ina karatun ko da ka aure ni ko yanzun ne kuma zaka ce baka san ina fita zuwa makaranta ba din. To yau ki zauna babu inda zaki daga haka ya mike ya bar falon binshi nayi da kallon mamaki ban samu magana ba. Kofa na mike na rufe bayan fitan shi na koma uwar daki na cire gyale tare da aje jakkana na haye gadona ina tunane a raina. Ba komai nake tunane ba sai hanani fita da yayi don ban san ko may yake nufi da hakan da yai min din ba. Waya na dauko na kira maryam kafin ta shiga class ina fada mata abinda ke faruwa tace dani kyale shi sa mai ido zanje department din ku in masu complain baki da lafiya . Amma maryam saboda may zai hanani tsabgar gaba bayan yasan ina karatu ya aure na hakana tace kiyi hakkuri. Gwada ki yakeyi ko zaki fita ko ba zaki fita ba din ya samu bakin magana idan kin fita kin ga gara da kika kyaleshi ya fita baki magana ba yasan wa yake aure. Idan mun fito da yamma zan leko ki sai mukarasa maganan nace to nagode na kashe wayan. Barci ne ya dauke ni a wurin da nake da tsakiyan tunanen sabon rayuwan da nake fuskan ta din a gidan. Saida ya gama abinda zaiyi ya fito zuwa asibiti kallon part dina yayi ya ganshi a rufe ranshi ne ya baci ya nasa watau fita nayi da ya hana fitan. Har yaje asibiti ya duba su da kwana nafisa sai korafi take mai yaki zuwa da sassafe ya dubata sai yanzu na barshi yazo ganin ta . Yana zaune office rai bace yana tunanen iri hukuncin da zai yanke min ji yake kamar ya hana karatun gaba daya yaga tsiya ko bai hanani ba sai ya bata min rai kamar yadda na bata mai. Zai nuna min a karkashinshi nake a yanzu ba karkashin wani ba yana wanan halin ne Yusuf ya shigo office din ya samay shi a haka. Sun gaisa ne ya kalli yanayin shi yaga bai a cikin dadin rai yake tambayan shi ko jikin nafisa din ne ya tsanan ta haka. Kai ya girgiza mai yana fadin taji sauki sosai dani da Deedar ne wanan karon ban san may yarinyar nan ta dauke ni ba . Wani abu ya faru ne yace zai dai faru don zan saba mata sosai wallah har zance mata kada tayi abu tayi shi. Yusuf yace ita khadija da kanta ko dai bata fahince ka bane don banyi tsamanin zatayi haka ba gaskiya yace OK karya ke nan nake maka. Jiya na dawo na samu ta rufe kofa bata aje min abinci ba naje kofanta a rufe da safe kuma again wai bata girka dani ba ta dauka a asibiti zanci ina mata magana kuma tashige daki ta barni a zaune. Sai gashi ta fito wai school zata nace ba zata tafi ba shine ina fita daga dakin ta fita bansan may yasa take son cudanya da maza suna daukan ta a mota ba ta san kuma ban son haka. Hannu yusuf ya daga mashi yana fadin kai malam gyara zancen ka don Allah kada wani yaji ya dauka wani harkan banza take yi na daban. Har wasu maza suka dauke ta ba dai driver gidan ka bane kokai kuma kana bada wanan go ahead din. Kenan su ba maza bane ya tambayi yusuf din cikin bacin rai yace jiya kayi ta kanta ne ko ka bugo mata waya gaka nan tafe kakai ta daba zata bi wasu ba. Yanzun ma da kake wanan magana ka tabbatar da bata gidan tana makaranta ko a gaban idon ka kags fitan ta yace dashi a hasale nasan fita tayi tunda na samu part din ta a rufe. Waya Yusuf ya ciro daga aljihun shi ya kira layina a cikin barci naji kiran na dauka da sallama bayan mun gaisa ne yace . Kanwata kina ina yanzu don Allah nace ina gida yayana yace yau ban fita school ban san may yake nufi da hakan ba gashi yanzu lokacin tsananin karatun mu yake. Yace ok zan mashi magana ya barki kiji yanzu zai zo ya dauke ki nace No ka barshi kawai yayana na riga na makara yau. Na kare da fadin wani abune ka kirani dama yace amma barshi kawai na dauka kin fitane in baki sako wurin maryam. Dan murmushi nayi nace kai yayana kada ku sani tsaka fa ga sister inlaw kuma ga friend yaya kuke son in yi da raina yace haka shine karin zumunci ai na kashe waya ina dariya. Kallon AA din yayi cikin zafin rai yana fadin kada ku cutawa yar mutane kai mata wasu suyi maka jiya a gaban ka yarinyar nan tabar karatunta taje gaida matar ka sukaci mata mutunci a gaban ka bakai komai ba. Yanzu kuma ka nemo wani fitina kana kokarin haddasa fitina a tsakanin ku tun bata iya yiba kazo ka koya mata maka mussu. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Darajan Allah da Annabinsa ya fi komai nauyi ga musulmi koda yaro karami ne yasan darajan wanan kallaman mai muhinmanci ga musulmi ko kafiri yasan daraja da nauyin wanan kalman. Balle dan musulmi baligi ko baliga har yanzu ba zan gaji da daure ku agun Allah ba da wanan kalman don darajan Allah da annabinsa kada ki fitar min idan ma an fitar yar uwa musulma kada ki karan ta idan baki biya ba don darajan Allah da Annabisa musulman kwarai ce kadai zata fahinci hakan Idan kuma kin nace da karanta hakkin wani Allah yasan tsakannin ki dashi akan haka don na sauke nayina na fada na kara fada don darajan Allah kada ki karanta hakkina idan baki biya. Inagama daukan wayan Yusuf kiran ya Amina yana shigo min mun gaisa na tambayi yara ita ta tambaye ni muna lafiya dai? Nace lafiya muke anty tace jiya ta shiga cikin gidan su mommy ake fada mata cewa Nafisa bata da lafiya an kwakaina da ita asibiti. Nace eh hakane anty an bata bedrest a asibiti yau kwanan ta biyu a can tace da nace idan su mommy zasu zo zan biyo su inzo in gaida ita. Da sauri nace No kada kizo ya Amina ban son kowa nawa yazo gaida wanan matar don gudun matsala. Haba khadija daga gaisuwa kuma sai matsala ina laifin wanda yazo gaishe ka ai komai abinta ba zata ce sheri ya kawo ni ba ko ? Naga yin haka kamar sayen mutuncin ki ne a gurin su ita da mijin ta nace ya Amina na fada maki kada kizo don Allah don ba irin wanan matar akewa haka ba gaskiya. Idan ita bata gani ba ai mijin ya san don shi aka zo ko nace harshi din anty halin su daya don ko a gaban shi sai ta ci maki mutunci ba abinda zai yi don haka kawai ki zauna. Tace kina ganin hakan zaifi nace kwarai kuwa ina hawaye duk da ba ganina take yi ba amma zuciyar ta ya bata ban cikin dadin rai. Khadija hakkuri zaki aure ya gaji haka don dan kalubali ne aure wata rana ka wayi gari a cikin dadin rai watarana akasin hakan. Koda kuwa baka da kishi balle ke mai kishiyoyi da yawa don haka sai kin hada da hakkuri da addua kina yawaita kai kukan ki ga Allah. Sai komai yazo maki da sauki a cikin alamuran ki don Allah yana tare da masu hakkuri da yaiwata ibada a gare shi. Hawayen dake fuskana na goge tare fadin bakomai ya na gode kudin da na turo sun kare na sadaka ko in turo wasu tace da saura a hannu na sosai kullun ana maki sadaka dashi. Maryam ta tambayeni nace yau bamu hadu ba don ban shiga school ba tace lafiya nan shiga ba nace banda lectures ne yau na tsaya in hutane. Dan nasiha kamar kullun tai min tare da kara min karfin gwiwa a zaman takewan rayuwan aure nayi mata godiya tare da kashe wayan mukai sallama da juna. Kwallan dake fuskana na share tare da gyara kwaciyana ina tunanen yanzu may ye matsalana ko laifina a hakan da yai min . Ni da ya wullakanta akan matar shi ya manta dani banyi fushi ba sai shine mai daukan mataki a kaina wani abu sai ko aure yakai haka ga mutum. Kayan jikina na tashi na sauya tunda ba fita zanyi ba kuma ni kadaice a gidan wando da yar riga armless sai kaina da na daure da ribon ko dan kwali ban aza a kan nawa ba. Falo na dawo bayan nayi sallah azahar na dauko cake da drinks na aje a gabana na kunna tv ina kallo ina kora drinks din a hankali. Motsin da naji kamar wani zai shigo part din yasani dago ido ina kallon kofan jin an kara murda kofan yasa na mike na nufi kofan tare da cire key a kofan . Gardawan samarin nan ne buzayen gidan suke shigowa da kayan masarufi zuwa kitchen dina da sauri na koma daga kuryan dakin na zauna harsu bar part din. Sai da naji na daina jin motsin su na fito na zauna a inda nake ba tare da na kara rufe kofan ba ban kuma je na duba abinda suka shigo dashi din ba. Sai dai ina tunane a raina ina dadin wanan kayan da ake jibga min babu kwanciyar hankali a tare da zuciya na ko kadan. Shi ya shigo da sallaman shi a dakin daidai lokacin da na dauki kwalin drinks ina korawa a bakina yana sabale da corth din shi a kafadan shi, sallaman na karba mai tare da kawar da kaina daga kallon shi. Shima ni din ya tsurawa ido yana kokarin samun wuri yakai zaune don daga ganin shi a gajiye yake a lokacin muryan shi naji yana fadin dauko min drinks mai sanyi in kora. Ba tare da nai magana ba na mike zuwa kitchen din anan na samu kayan da masu karfin nan suka shigo min dashi a tsakar kitchen din nawa. Bin kayan nayi da kallo na wuce zuwa wurin fridge na dauko kwanlin five alive da kofi na nufo falon dashi a hannu na. Gaban shi nazo na dire da zan dago na rusunna irin al,adan mutanen Niger din nan ko mai zakayiwa na gaba da kai sai ka dan bashi girman shi duk da addini ya rage wani abu da wayewan kai kuma. Wanan dabi,an kowa ya san mutanen Niger da irin sa wurin ba na gaba girma da girmamawa ba su da wari a gurin nan . Kanshi a sama dage ya furta thanks tare da sauke kanshi hannu na naji ya kamo zuwa baya na fada a jikin shi. Kokaein kwacewa nake ga jikin nasa yaki bari na kurce mai ji nayi yace kamar mai rada fushi kike dani don na hanaki fita yau ko mai ? Akan may zan yi fushi tunda a karkashin ka nake kace ba zan fita ba ai dole in zauna fushi na may zanyi tunda nasan yau baka ra,ayin fitan nawa ne. Kaina ya tallabo ya hada da goshin yana sauke ajiyan zuciya tare da fadin kin dai huce daga fushin naki. Kokarin mikewa nakeyi tare da fadin wani yace dakai ina fushi dakai dama ni dai naga hakan don ko abin sha sai dana roka yanzu a wurin ki. Dama ina da niyar dauko maka idan ka bukata kuma ka bukata na dauko ma salin alim shine kuma abin fushi din. Yanzun dai ba wanan ba zowa nayi inji idan akwai wani abin amfani da ba,a sawo maki ba wanan watan sai ki fada min a sayo yanzu. Komai akwai na gode nace yaushe kika duba kayan da kike min godiya a kan su nace ko ban duba ba nasan zaka sayo muna komai na bukata ai. Kwalin juice din ya dauka tare da balle marfin kwalin ya kafa a bakin shi ya fara sha hakana bada cup ba sai da yasha kusan rabi ya aje kwalin ya mike tsaye yana fadin zan koma asibiti in duba su idan na bar nan kafin in isa office Allah ya sauwaka nace ina kokarin dauke kayan da suke falon. Zuwan maryam ranan yasa na basar da komai dake raina don hiran mu da ita yasa na manta da duk wani damuwa na. Tana gidan har sai da tayi sallah isha,i ta bar gidan nayi nayi ta kwana tace zamu dai hadu gobe insha Allahu. Bai dawo gidan ba sai sha daya Nafisa ta barshi ya dawo gida lokacin har nayi barci a dakina don banji motsin shi ba na dauka a can yake kwana. Wayana ya kira sai da yai min call biyu na falka daga barcin da nayi nisa ga yin shi bude min kofa ya fada bayan na dauki wayan. Nataso da sauran barci a idona na bude mai kofan dakin ya shigo shima da ganin shi a gajiye yake a lokacin. Sai dai yayi wanka don alama ya nuna hakan saboda ya sauya kayan jikin shi zuwa dogon riga sabanin yadda ya fita gida da rana. Abinci fa ko baki aje min ba kitchen din na nufa na dauko mai abincin nakawo tare da fadin sama zan kai ma ko nan zakaci ? Aje min in ci nan ya bani amsa hankalin shi yana ga wayan shi saida na gama jera mai komai nace na hada ya dago yana kallo na tare da fadin kin rufe kofan nan ? Kallon shi nayi da mamaki nace na dauka yanzun zaka fita yace yana nuna kofan rufe kawai na tashi ina mamaki a raina tare da rufo kofan. Mikewa yayi ya nufi dan table din mai kujeran mutum biya ya zauna zuwa nayi na fara zuba mai abincin nagama nakoma dayan kujeran na zauna tare da harde hannaye na ina kallon shi. Abincin har lokacin da zafin shi sosai tuwo na tuka mashi na farar shimkafa da miyar kuka da naman rago nayi amfani da kayan yaji sai man shanu dana zuba a sama. Tunda ya fara cin abincin baiyi magana ba har ya kare na mike ina tattara kayan don idona cike yake da barci a lokacin. Bayan na kawar da kayan ne na dawo falo da zumar zama naga ya mike ya shiga kuryan dakin kashe wutan ko ina nayi falon na shiga dakin . Na samu yana cire rigar shi daga kofa inda nake nake fadi amma baka fada min a nan zaka kwana ba yau ban gyara wurin yadda ya kamata ba. Baiyi magana ba sai da ya zauna a gadon yake fadin may ye laufin shi a hakan ai a gyare yake yana fadi ya haye gado ya kwanta. Juyawa nayi zuwa falon bakomai nake yi ba sai dai na dauki lokaci ban dawo cikin dakin ba sai can na shigo. A zato yayi barci ne yadda na ganshi a gajiye don haka na dan tako a hankali zuwa gadon can na kwanta na takure a wuri daya. Can naji shi yana shafa addua a jikin shi tare da sauke ajiyan zuciya ni dai ina wuri daya a takure sai rokon Allah nake a zuciya na kada yace zai taba ni alokacin. Saukan hannun shi naji a jikina dan zabura nayi a firgice tare da lumshe idona ina jin yadda hannun shi yake yawo a saman jikina. Sai faman runtse idanuwa na nakeyi kokarin rabani da dan rigar barcin dake jikina yakeyi a hankali na iya furta don Allah ka barni please. Why naji yace dani kamar mai yin rada nace banjin dadin jikinane kawai shiru yayi na dan wani lokaci sai naji ya matse ni a jikin shi yana sauke numfashi a hankali. Bai mun komai ba haka muka kwanta da sassafe na tashi bayan nayi sallah kitchen na fada don sama muna abin karyawa. Nan na barshi zaune yana addua na shige kitchen din don gudun makaran shiga school da nake tsamanin zuwa yau din. Sai da na gama in son shiga wanka sai gashi ya shigo dakin har yayi wanka a lokacin yayi shirin fita sai lokacin na gaida shi da kwana. Ya amsa min yana kallon fuskana tare da tambayana yaya jikin naki nace naji sauki cikin wani murya. Ni zan fita yace yanzun suka kirani daga asibiti wai ana nema na a can dago kai nayi na kalleshi tare da fadin abinci fa nagama hadawa. Yace banda time din karyawa yanzu sai dana kalleshi nace idan ka tafi wa zai sauke ni school ? Yace wani school ke da ba dadin jikin ki kike ji ba zaki fita ki zauna ki huta a gida har ki kara walwalewa. Don girman Allah ka bari in shiga yau kada nayi hadaran point dina jiya banje ba yau kuma kace haka. Yace eh yana tafiya yana fadin haka naga yafi ga lafiyan ki don ki samu sauki sosai ina kallon shi ya fita naji kamar in saka hannu a kai in kurma ihu a wurin. Tunane kalakala nayi shi a cikin dan lokaci kan kankani wankan da ban iya shiga nayi ba ke nan ban kuma iya kallon abincin dake gabana ba. Na dan dauki lokaci a wurin zaune ban iya ko motsawa daga inda nake zaune ba naji wayana daga daki yana ringing kamar in share wayan. Sai kuma nayi tunanen kila maryam ce ke nema na a layina don haka na tashi zuwa daukan wayan kafin in isa kiran ya katse. Na duba naga shine a layin kokarin aje wayan nake wani kira ya shigo min nashi na dauka yana fadin kina ina haka waya ke ringing baki dauka ba ? Ina falo na bashi amsa yace ki shirya min breakfast yanzo zan aiko a daukar min ke kuma ki shirya ya sauke ki a school din idan zaki iya zuwa. Kamar in ce mai ba zan tafi ba sai naga kaina zanwa sheri nace dashi to kawai ba tare dana furta wani abu ba shima naji ya kashe wayan diban lokaci nayi naga ina da sauran lokaci. Mikewa nayi na fada bandaki ina tunane a raina ashe haka mata suke fama da ikon maza a kan su mace ita shike nan bata da wani right din kanta sai inda akayi da ita. A gurguje na shirya tare da shirya mai komai sai ga driver ya iso shiya kirani yana fada min driver na waje yana jirana . Ban tsaya bata lokaci ba na fito a cikin shirna a waje na samu driver yana jirana fitowa tayi ya karbi kayan hannu na ta sa a motar ya bude min na shiga muka fara hanya. Tunda ya gaida ni bai kara magana ba sai da na gama tunane nace dashi yana asibiti ne ko office yanzu. Yace yanzu na sauke shi office ya baro asibiti a raina nace watau akan zuwa asibiti duba matar shine yasa ya fita ba tare da ya jirani ba komay. Ko kuma wanin sallon ne suka fito dashi a gidan yanzu ya daina saukeni don an hanashi fita dani da wanan tunanen har muka isa school. Na sauka tare da yima driver godiya na shige ciki na samu har an fara lectures malamin bai hanani shiga ba don ya ganni saye da hijab. Saboda yana respecting din mata aure sosai yace lalura ke tsayar dasu a wani lokacin haka yasa yake dan rangwanta ma matan aure. Ban fito ba har sai da mukaje break daidai lokacin sallah azahar wanda a lokacin ne muke dan samun lokacin cin abinci da sauran su. Yau ma kamar kullun a masallaci muka hade da maryam ina alwala naji tana fadin matar manya yau kin samu fitowa ashe. Saida na gama na mike nake cewa da ita nikan ai naga iko maryam yanzu na fara ganin matsalan da aure keda shi wallahi. Bayan mun fito daga sallah muka zauna a inda mukan dan huta idan mun ffito daga sallah kafin mu koma lectures din. Sai lokacin na fito da abincin da na dan zuba don in karya idan nazo yau kuma abinci zaki ci nace. Ban karaya ba maryam yau AA yayi bala,in bata min rai sosai wallahi nan dai nake fada mata yadda mukayi dashi. Dariya naji tana min tare da fadin ai ma ya raga maki cewa fa kikayi bakijin dadin jikin ki. Kin hana ma bawan Allah hakin shi kice ba zai dauki mataki a kan ki ba ya gane rowa kike mashj ai kyale ki dai yayi wallahi. Wayana na naji yana verviration na dauko naga sunan shi nace kamar wani wandaa ya damu dani don Allah kirana na may yake yanzu kuma, ? Ina dauka naji yana fadin yawa kina jina wai su mommy ne suka zo ban san da zuwan su ba yanzun suke sanar dani tasowan su. Kallon maryam nayi yaci gaba da fadin idan kina free sai ki koma gida yanzu su samay ki a gida idan sun iso. To kawai na amsa mai dashi na kashe wayan kallon maryam din nayi nake fada mata tace ai dole kije ku gyara gidan ki dan yi masu wani abu ko ? Tare muka tafi don driver shi ya dawo ya dauke mu zuwa gidan tunda muka isa gidan bamu zauna ba falon gidan ne kawai ban taba ba don ko na gyara buzaye zasu bata shine. NAFISA Duk da tana kwance asibiti ba abinda ya rage a cikin halin ta madam na shigowa dakin bayan sun gaisa ne tace madam. Duk da nasan wanan dan bakan a tamke yake ban cire shi ba a yadda yake tun ranan don gudun su faki idon ya amfa mata yasana barshi a hake. Yanzun ma jiya da dare nake jin likitocin nan suna magana wai zan kara kwana ki anan na nuna masu bazan iya ba gwamma na koma gida na fake yan iskan nan da idona. Kai nafisa akwai ki da shirmay wallahi ba zaki batun lafiyan ki ba yanzu ta wani shirmay kike can wai kishiya. Kishiyar da kika san babu abinda zai taba faru a tsakanin gaban ki ko bayan ki duk dayane a gare su tun da kin dane shegu. Tayi dariya tare da fadin kai nafisa kin san kan sheri wallahi yanzu kirikiri kin hana komai ya wakana a tsakanin wayan nan mutanen. Tace ina zan barsu yar iskan koni ta samu haka zata hake ni kin sani tunda ba kishiyar dake son ganin dingo karuwa ga yar uwar zaman ta ai. Ta kasheni ko in kashe ta shine aure zamanin nan ai don kowace hake take da yar uwarta kowa na sukar dan uwa. Wallahi indai nice haka zata kare a gidan nan bata gane komai yar iska harta tafi don wanan da ace ta samu ranke ranke ce ni da yanzu taimin yadda naiwa fati. Da ita da ban za duk daya a gurin miji wallahi madam naki jini a lokacin in bude ido inga wanan bakar fatin gidan samad da yaran ta. Ina murnan sun tafi ashe zaune bata kare min ba yaje ya kwaso min jikan mayu ya kawo min gida ina hadiyan takaici. Idan naga yarinyar nan kamar in shake yar iska nake ji a rayuwa na ga shegen feleke wai ita yar boko a dole. Madam ne tai dariya tare da fadin watau ma waine ko baki tabbatar ba ke nan ke madam tace yanzun kina ganin babu abinda ke faruwa a tsakanin su har yanzu. Daga inda take zaune tana fuskantar madam din tace ban tsan mani ba duk rawan kan dakikaga yana mata a yanzu wani tsigane na lalashi kada ta tona mashi asiri ace bakai namiji ba. Dariya suka dauka tare da tafawa kamar ba a asibiti suke suna jinya ba sai faman hanya kulla sheri suke na yarda zasu kasara rayuna da na Fati gidan ya koma nata. Wanan ai kin gano takon shegeya mai ido a tsaye don idan kika bari har ta fara dandana maki miji ta samu ciki ja dake zatayi sosai a gidan nan don a bude idon ta yake. Gaban Nafisa ne ya fadi jin abinda madam diin ta fadi a gamay dani na zancen haihuwa da sauri tace madam ranan ko da anyi aika aika ba kadan ba a gidan nan. Don wallahi na tsani samad ace yana da wasu diya shiyasa ko wa yan nan yaran ban yarda ya saka su a ranshi ba. Da karfi da yaji sai da naga gaba daya hankalin shi ya fita a gare su bai ko ambanta sunan su ako ina yake yanzu. Ai mutumiyar baki da wasa wallahi kin huta ganin takaici ba mai maki sallon haihuwan da na namiji har biyu tace shiyasa nake son wanan cikin don in haifi namiji nima. Badon haka ba ai da tuni na bar da shege na huta da wanan wahalan da nakeyi haka nifa ba haihuwan nake so ba haihuwan namiji kawai nake kwadayi dashi. Shigowan wasu matar abokan aikin shi ne ya katse masu hiran nasu idan ko nan bata bar halinta ba sai wani jiji dakai tana basarwa take masu. Basu dade ba sukai masu sallama tare da Allah ya sauwaka suka fice matsn sheri ko wanan bakin Nafisa da madsn basu barsu ba sai gulman su suka dasa kuma a wurin. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Abinci lafiyayye na shirya ma su mommy da ban san su nawa ne tafe ba sa,a na shine ina da komai da muke bukata a gida. Zakace abincin restaurant ne yadda muka kawa ta komai tuwon faran shimka shine nafiso a rayuwana don haka ban rabuwa da abin sarrafa shi a duk inda nake. Yauma bayan na tuka tuwon na daure a cikin farar leda ba wasu manyan kwasa nayi ba daidai yadda mutum zai iya cinye kwasar nayi. Miyar a laihu da manja sai egusi dana daure miyan wanda nama ciki na yankashi da girma yadda zai cika miyar a plate idan anzuba. Bayan mun gama na shiga wanka nafito na gyara jikina a cikin dogon ringa dinkin kasar Dubai yaji duwatsu har kasa atamfar super ce akaiwa pattern din kwalliya da stone masu kala. Maryam ma wani dogon riga ta saka a jikin ta muka zauna zaman jiransu ashe sun iso suna asibiti . Bai samu zuwa ba a lokacin don haka ya tura wani dan ma,aikatan su yayi masu iso inda Nafisa take kwance. Bai samu sheda mata zuwan su ba don ranan yana busy da baki a office shiyasa ya manta nima zai shiga ne kiran da Abba yai mai cewa sun taso sai yayi tunanen irin taron da zasu samu a gidan idan ban nan shine ya kirani. Tana zaune saman gado ta baje tana cin kaza gassa da aka kawo mata su madam ma kazar suke yaga daga inda suke sai hira ake kwasa da dararaku irin na shakiyan ci daga bakunan su. Sallama sukaji a kofan dakin suka waiga don ganin masu shigowa ds sallaman idon tane ya sauka akan anty Amarya dake gaba mommy tana bi mata sai anty Fauziya da Anty Faiza da ya Amina a bayan su. Take yanayin fuskan ta ya sauya daga dariya zuwa daurewa don batai maraba da zuwan su ba a lokacin don bata ga dalilin zuwan su ba. Ta dauki zuwan su da munafunci ya kawo su don su zo suga halin da take ciki su koma su baza a dangi ga halin da take ciki. Don haka ta shiya masu cin mutunci a wurin don sai sun raina kan su da zuwan da sukayi din anty amarya dake gaba dama nafisa ta dade da fahintar son shige mata da take son yi. Anty amarya cikin kulawa da nuna damuwa a gare ta take fadin Nafisa sannu ashe kuma haka abin ya zo da akasi kuma. Kazar dake gaban ta ta kawar gefe tana fadin akasi kuma anty wanan ai matsalan ciki ne duk mace mai haihuwa na tare da wanan laurar. Mommy ne ta yi kamar basu fahinci abinda take nufi ba tace Nafisa ya jikin Allah yasa haka ya zamo alheri ubangiji ya baki lafiya ki koma cikin iyalan ki. Wanan magana na mommy yai mata tsauri don addua mai kyau mommy tayi mata sai ta amsa da amin mommy faiza da fauziya da kamar zuwan dole sukayi dama sukace sannu Allah ya baki lafiya. Tace ai lafiya ya samu don gashi kun ganin a cikin sa yanzun ma muna jiran likita ya dawo ne ya bamu sallama mu koma gida. Fauziya tace ashe ma yadda ake fadi kina jin jikin bai kai yadda yayan mu ya ruda mu ba eh baikai ba tunda ba a jikin ku ciwon yake ba. Shi kuma da ya damu din ban aike shi shela na a duniya ga halin da nake ciki ba a,a may ya kawo wanan magana kuma haka daga zuwan mu gaida ke inji Fauziya. Nafisa tace wanan haka yake ai maganar gaskiya na fada daga dan ciwo zai kama tallatani a duniya kamar wani matsala babba. Allah dai ya baki lafiya inji ya Amina dake kallon ta gaban ta ne ya fadi don kamar da tagani nawa ga ya Amina din sai ta kafe ta da ido. Mommy ne ta kula da hakan tace ga yar uwar amaryan ki nan makwaciyar mu ne tazo ta gaida ke da taga zamu zo . Au itama ashe gulma ya kawo ta tazo ta ga ko zan mutu ko ai ban farga ba tun farko har da dangin mayu kuka zo min su karasa ni tana fadi tana jan zani dake jikin ta tana rufe cikin ta da jikin ta. Haba Nafisa wanan wani magana ne kuma kina nufin gulma ya kawo mu ko may idan ma kin mata ki sani abinda ke cikin ki yana da alaka damu don haka dole muzo muga lafiyan ki. A, mommy ki dai gyara zancen ki abinda ke cikina da Samad yake da alaka don ko wace ke fili a yanzu ba damuwa kukayi da ita ba a cikin ku. Kin nuna mata mu yan uwan ubanta ne aka kita don da kin gwada mata mu ai da kinga gatan dakin a gare ta mufa ba don ke muka zo wurin nan ba don mijin ki ne da Abba da yace mu zo mu duba ki. Kuka dai zo ganin halin da nake ciki amma wace ba a damu da ita da abinda ta haifa a cikin ku ba har aure akai ma Samad aga yadda zan nakasa a gurin shi ko in koma baya don tsabar kiyayyan da ake nuna min. Anty amarya zatai magana mommy ta tare da fadin bamu san kina kule damu ba ai nafisa da bamu zo ba sai idan kin huce kin fahinci mu ba makiyar ki bane sannan mu zo dubaki. Don bamu dauke kina rike damu ba a ranki haka sannan ki sani shi aure da samad yayi ra,ayin kanshi ne yayi haka ba ra,ayin mu ba. Don ba mu zamu zauna mashi da ita ba aure ya nema kuma muja bashi goyon bayan hakan sai dai kiyi hakkuri da kaddara don aure kan anyi shi ba rabuwa sai fatan alheri ta juya tana fadin mu tafin ku Allah ya sauwaka. Suka juya Faiza ta juyo tana fadin ke kan ki canza halin ki don kina tare da wahala kan ki kika wullakan ta bamu ba don dai Ya AA zai iya rabuwa dake mukuma yana tare da mu har abada. Nan suka fice suka barta tana jefan su da bakaken magana masu zafi suna fita faiza tace kunga abinda nake fadi tun a gida akaki yarda da magana na yanzu ai gashi kun gani. Suna mota hanyar zuwa gidan sai masifa suke ya Amina dai shiru tayi mamaki ya cika mata zuciya halin nafisa ya bata tsoro yadda taciwa su mommy mutunci. Ina gani wani irin zama na keyi a gidan dasu ga yan uwan ta tab a gidan niko ni kadai babu ko abokin hira a tare dani. Sun iso gidan basu yi mamakin ganin gidan hakana ba gyara ba don yawan mutanen dake ciki zaune ba masu moriya bane. Don sun dade da sanin halin su ba yauba don haka yanayin da suka samu gidan bai basu mamaki ba. Part dina yana rufe kamar kullun nan suka nufa ina jin an kwankwasa muna zaune tare da maryam muna hira jin motsin kofan nace da maryam ko sune suka iso maryam ne ta bude kofan sune a tsaye. Da murana na mike na tare su ina masu sannu da zuwa duk na rude da ganin su in gaida wanan in gaida waccen suna karba min. Idanuwan su na akaina sai da suka zauna ne na shiga kitchen maryam ta biyo ni abin sha muka fara gabatar masu sai abinci ya biyo baya. Bayan na gama gabatae masune mommy tace sallah zasu fara kafin su zauna cin abinci din dakin na yi masu jagora suka shiga ana suka fara gabatar da alwala da sallah daya bayan daya. Bayan su idar ne suka zauna cin abinci yar gurin Faiza ce dauke a hannu na ina mata wasa naji sun sako zancen rashin mutuncin da Nafisa tayi masu a asibiti. Murmushi nayi ina sauraren abinda suke fadi maryam ce tace ikon Allah ina laifi wanda yazo ya gaida kai gari ya gari haka. Ni shi yasa ban daukan wanan matar a cikin masu hankali Fauziya tace wai haka kuke fama da ita da wanan bakin halin nata . Nidai murmushin karfin hali nayi mata ba tare da nayi magana ba haka yasa suka san akwai matsala boye masu dai nake yi a hakan. Anty amarya dake zuba abinci tace ni ai mamaki ya hana ni magana mata kamar tana jirace damu haka na dauka yanzu fa ta canza. A wurin ku wanan yake abin mamaki inji mommy tace ni da na zauna nan da iyan bawa ai mu muka ga abu a lokacin bata da yarda ko kadan ga bakin zargi da sheri. Ya Amina tace ai yau mun ga inda ake kishi a filin wai muna dangin mayu kuma ikon Allah bai karewa a duniya wallahi kishi haka harda na hauka. Anty ina kika sani ai muma haka tai muna shekaran jiya da muka je gaida ita wallahi baki ga irin wullakancin da tai muna ba a gaban abokan ta. Kamar dai yadda tai muna ke nan inji Faiza tace yau ai munga mamaki wallahi Fauziya tace ai bari ya AA din ya dawo wallahi zan fada mai idan sha,anin nafisa ya sake tashi kada ya kara neman mu a ciki. Mommy tace ai ba, a haka ba don ta mukeyi ba don dan uwan ku muke yi yasan kuma muna mashi ai don gashi ya kira yana fadin abinda ya samay ta. Ba gashi mun zo ba ko bamu samu taron arziki a gurin ta ba bagashi yanzun mun samu anan ba dadin auren ke nan ai da yanzu ina muka san zamu dosa idan ba khadija a gidan. Anty Amarya tace yanzu ai na kara fahintar manufar yaya na jajirce ma karin auren shi yanzu kin ga ai zaman khadija gidan mudai yai muna rana. Sai zuwa yamma sosai ya shigo gidan don da su niyar su su juya a ranan su koma kaduna rashin dasowan shi da wuri yasa dole su kwana. Ya shigo muna zaune a falo ana hira bayan na dora masu girkin dare maryam tana taimaka min don kusan aikin itace mai yin shi. Zama yayi suna gaisawa yana tambayan su gajiyan hanya da mutanen gida suka amsa da lafiya yace ashe har kun baro asibitin na buga akace min baku can. Ai dole mu barcan yaya AA mu da bamu ko zauna ba aka tare mu da rashin mutunci da hauka a asibitin wai munzo leken asirine ba zuwan girma da arziki ne ya kawo mu ba. Haba dai Fauziya nafa sanki da daukan zafi akan dan abu karami ina jin ya fadi haka nace uhmm na mike daga inda nake. Bina yayi da ido ina dauke da yarinyar a hannu na taci gaba da fada mashi abinda ya faru dasu da nafisa a asibitin. Wani irin zafi da kunyan su mommy yaji na kokarin da suke mai amma Nafisa tana gwace mai wai shi yaya zaiyi da Nafisa ne a rayuwan shi yake tambayan kanshi. Mommy ne ta katse shi tana fadin kada wanan abin ya damay ka mudai domin Allah muka zo da kuma kai in ma tayi ne don wata manufa nata tayi karya. Yace hakane mommy kuyi hakkuri don Allah kuyi hakkuri Nafisa bata da mutunci idan ta tashi halin ta. Ai tayi da masu yi wallahi sai ta rena kan ta watarana a wurin mu don dai ni ba kyaleta zanyi ba wallahi kallon ta yayi ya girgiza kai. Ya mike yana fadin barin dan shiga ciki in watsa ruwa in fito lokacin na fito daga kitchen din ina fadin akawo abinci ne yanzu. Ya dan juyo yana fadin bari har zuwa dare yanzu hutu kawai nake so anty tace da ka dawo da wuri babangida da yau zamu juya gida. Juyowa yayi yana fadin anty munyi magana da Abba na fada mai yayi hakkuri sai gobe ku dawo saboda yanayin hanyar yanzu. Ya fadin haka ya fice daga dakin nima kitchen na koma wurin gurki bayan na kammala hadawa na dawo wurin su ina fadin amma zaku shiga kasuwa gobe kafin ku wuce . Mommy tace dani bamu son dare yai muna a hanya banjin zamu shiga kasuwan nan sai anty Faiza tace mommy don Allah mu dan shiga ko a gurguje mana bamu rasa abin saye a can. Har lokacin ban samu kebewa da yar uwata ba fita nayi zuwa wurin shi na samu baya dakin na dawo part din na samay su. Mommy mace mai fahinta tace kuje daki khadija Amina zata baki sako acan nace to mommy tashi mukayi zuwa dakin. Anan muka samu kebewa da ya Amina din tambayan farko data yi min shi ne Khadija haka kike fama da wanan matar haka, ? Nace to yaya zanyi ya Amina tunda haka daddy daku kuka zabar min yi kada kice haka khadija muna taya ki da addua a kulun wallahi. Yanzu yaya yanayin zaman naku yake a gidan nace da dama ya Amina tace komai dai yai sauki a bangaren ki dashi har yanzu ko murmushi nayi mata tare da kama hannun yarinyar dake hannuna. Nace yayi ke nan amma a yadda na fahince shi komai a tsorace yake yin shi kamar hanyanzu ita Nafisan bata fahinci yana kawai gareni ba don yawan lafazin ta a kullun shine haks zamu zauna sai kallo a tsakanin mu. Dan dariya tayi tana fadin wawiya ai haka yafi sauki don tana ganewa ba kyale ku zatayi ba wani shirin zata sake kuma. Nace na fada maki yar maryam ne ta samo min taimakon da abinda tayi muna ya karye ai kila da har yanzun ba abinda ke shiga tsakanina dashi. Tace ai naso ace ba,a taro muka zo ba da naje gidan nata nace ko yanzu zaki iya zuwa sai mu tafi da daren nan ai anty wayayiyar mace ce bazata nuna wani abu ba sai ku ce kunzo gaida ita ne. Gaskiya ya kamata inje in mata godiya kuma in ganta don wanan matar takai wallahi nace ai sai ma kin ganta zaki san takai. Idan munyi sallah sai mu tafi ai ba wani nisa ne sosai da mu ba ci gaba da bani shawara tayi har lokacin sallah yayi muka mike zuwa sallah. Ina idar da sallah na dauki waya na kirashi ina sheda mai zancen fitar mu din yace kai yakamata dai in sama maki mota haka khadija barin nemo driver da zai kaiku yanzu. Driver din yazo na fada ma su mommy ina son su dan raka Ya Amina gidan su maryam su gaisa kowan su bai ki ba suka shirya muka fito nan falo ina rufe kofan part dina muka samu su Samiha zaune gaba dayan su sai yanyaka ce dake asibiti bata gurin. Nan suka samu ganin Ihisan suka tsaya suna tambayan lafiyan yarinyar tare da dan taba ta duk da ran buzayen bai so haka ba. Wurin shi na haura sama na na sallamay shi na fito muka fita Fauziya ce ke fadi bayan fitar mu daga gidan take cewa yanzu khadija har yanzu wanan taron na nan maku haka a gidan nan. Maryam tace ai ma sai abinda ya karu wallahi motan biyu ya tanadar ma fitan namu. Mun kai gidan maryam ta riga fita taima maigadi magana ya bude kofan muka shiga da motacin mu. Mun shiga gidan anty hauwa suna babban falon su a lokacin ganin mu tare da jamma,a yasa ta dan yin fara,a tana taron mu. Bayan gaisawa ne maryam ta fara gabatar da su ya Amina a gurin ta dasu mommy sai da ta kalli ya Amina da kyau tace mata kanwa dai tafi ki kyau duk da akwai kama gare ku. Dariya mukayi falon tace ma mommy amma sai nake ganin kamar na sanki a baya mommy tace ba abin mamaki bane hakan. Kila mun taba haduwa a wani guri a can baya tace sai nake ganin kamar a federal school na maiduguri na sanki ko ? Mommy tace kwarai kuwa don can nagama tace kwarai kuwa don nima acan na kare sai dai ban zato mate muke daku don kamar muna gaban ku da shekara daya. Sai lokacin mommy ta tuna tace sister hauwa black jos tace kwarai kuwa nice nan suka fara hiran yaushe rabo a tsakanin su tana tambayan mommy yan kadunan da ta sani tana bata labarin su. Maryam tace yanzun dai ashe mommy muka rako wurin sister ta sanun sannu har aka dauko hiran Nafisa nan anty hauwa je basu labarin kungiyar su nafisa din a gari . Tace ai sai matar da bata san ciwon kanta bane take shiga wanan kungiya ko last week kafin wanan abin ya faru mun hade dasu a wani buki. Sun ganin na gansu sai dai ba dama su shiga harkana don kar ta san kar dani dasu kuma har yanzu ina ganin basu san nasan ita khadija ba. Tace aike khadija baki san kan wa yan nan buzaye bane don har yanzu da sauran kurciya a tare dake da sannu dai zamu kai can insha Allahu Nafisan may can don Allah. Da ita dasu madam din aini duk a tafin hannuna nake kallon su maganin shegiya koku a gare ku dangin miji ku nuna mata idan tana iskancin ta kunsan asakin ta ai basu kaunar a tuna masu asalin na gida don yanzu sun waye. Basu sha mamakin anty hauwa ba sai da zasu wuce ta bisu da abun arziki na irin kayan da take sayarwa nan suka mutu da mamakin ta. Zamu fitane take fadin ida na samu lokaci tana son ganina nace to anty zan zo idan Allah yarda mukai mata godiya muka bar gidan. Ko da muka dawo baya gidan yana asibiti wurin nafisa yaje ya dubata a lokacin tare da maryam muka dawo don tace ina da baki zata taimaka min da aiki da safe. Suna zama ledan da taba kowa suka shiga budewa atamfofine masu kyau da tsada na mommy ne super daga ciki sai hiranta sukeyi suna yaba kirkin ta. Daki na shiga na watsa ruwa kafin dare yayi sosai sha daya da rabi kamar kullun ya dawo daga asibitin . Waya ya bugo min don bakin da ke akwai a shiyan nawa yana fada min in kawo mai abinci cikin shiri na fita na barsu a part din. Ledan da ya dawo masu dashi ya bani in kai masu bayan na gama jera mai abincin na samu suna ta hira na aje masu ledan tare da fada masu sakon shi ban dade ba nayi ma maryam signal da ido na zan tafi tace mu tashi lafiya. Ina fita ta rufe part din na samu ya gama cin abinci yana zaune saman kujera yana duban laptop din shi na shigo sai da na shiga ban daki na yi lalura na fito. Ban tsaya ba na haye saman gadon don a gaskiya na gaji sosai ranan ban dade da kwanciya ba ya rufe laptop din ya hawo yana fadin ina ganin gobe za a sallamo nafisa don taki yarda ta zauna acan yadda suka bukata. Allah ya kaimu lafiya nace yaci gaba da fadin don Allah Deedar abinda nake so dake shine ki kawar da idon ki akan nafisa da duk wani iya shegen da takeyi a gidan nan . Don ita ba ciwon kanta ta sani ba bazata damu da abunda hakan zai iya haifa ma rayuwan ta ba don naga cikin bai damay ta ba. Ni dai ina sauraren shi banyi magana ba don abinsu tsoro ma ya fara bani yanzu yace banji kinyi magana ba mana ? Nace may zan ce yanzu kuma may zance tunda na fahinci maganan ka kamar nice mai takakan ta ba ita ba. Yace ba haka nake nufi ba nayi maki magana ne don nasan ke zaki iya fahintar manufa akan haka idan tayi taga baki biye mata ai bari zatayi dole gyara kwanciya na nayi ina juya mashi baya. Shiru yayi yana tunanen yanzun kuma may ye laifin shi daga fadin gaskiya nayi fushi kokatin rugumoni yakeyi na koma mai kamar dutse. Har yai abinda zaiyi ya gama ban muda mai ba naji ya mike ya shiga bandaki ya yi wanka ya fito nima mikewa nayi zuwa bandakin na watso ruwa na wanke najasan dake jikina. A can asibiti kuma bayan sun gama rigima da Nafisa yafito duban yanyala tayi tana fadin dole gobe ki shirya zuwa gida wurin Fatumay don karbo min sakon da aka hada min. Yanyala ta kalleta tace gobe goben nan kallon tayi a wullakance tana fadin koba zaki je bane in nemi wani ? Da sauri yanyala ta amsa da Allah ya kaimu don tasan kwanan wasan don ko su ba dadin ta suke ji ba kwadiyi ne kawai irin nasu da son jin dadin rayuwa. Waya ta dauka tana kirsn madam tare da fada mata yadda suka kwashe da AA din tace idan ba kinyi da gaske ba Nafisa samad na gab da juya maki baya. Ba komai kuma zai kawo haka ba sai yadda baki da hakkuri akan komai ke baki iya hade magana a cikin ki. Ai na fada maki bai kamata kiyi wa yan uwanshi da kishiyoyin mahaifiyar shi haka ba namiji fa duk yadda kake ganin ka kama kafan shi idan ka taba yan uwanshi ba kyale ka zaiyi ba. Ai duk yadda kike ganin kin kama shi kada ki yarda ki nuna yan uwan shi basu da mutunci a gurin ki don zai ji abin har cikin ranshi. Balle Samad da hsr yanzu ba gama kamashi a hannu kikayi ba yadda kike so ni wanan mijin naki har tsoro yake bani wani lokaci mutum kamar dutse haka anayi kamar ba ayi. Ni dai ina ganin ko zama da wanan kishiyar taki kamar dai boyon kurwa yake muna wallahi. Nafisa tace madam kin fi kowa sanin abinda nake kashewa akan samad duk rabin samuna agurin shi akan shi yake zuwa. Ni wanan fannin banda matsala don nasan shirin da nayi masu ai shiya nake son komawa gida kada ina nan abin yazo ya karye ya lalaba ya taushe yar iska kin san rana da hauka zan maki. Don wanan zuman na samad sai ni nasan kan lasan abina badai wata mace tazo ta lasa man ba. Madam tace sai ko fati ko don itama ta rigaki lasawa tace ko ta lasa ta manta kalar zakin shi don shegiya warin jaba na sakar mata bashi ba zuwa kusa da ita. Haka sukai ta shirmay su na surkule basu san a lokacin har zuman ya fara fita kaina ba don banda jimiri a wanan fanin ko kadan yanzu don dole nake daurewa saboda hudubar mutaneba kaina ko yaushe. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Ga Allah na dogara shine mai komai mai kowa ubangiji ya sada mu da rahamomin sa masu albarka duniya da rahira. Barkan mu da safiyan jumma ubangiji yasa muga haske a rayuwan mu ta yau da kullun. Washe gari na samu har maryam ta gama hada abin karyawa jira kawai take ya kara sulala ta sauke na shigo. Kitchen din na fara zuwa don jin motsinta danayi nan tana gani na ta dan sakar min murmushi tare da fadin amarya kina kamshi fa wurin gas din na nufa na fara bude tukwanen dake sama. Kamshine da tururin abincin suka doki fuska na nace mutum haka kamar injin gurin aiki tun yaushe kika fara wanan aikin haka. Ni ina can ina sauri in zo mu dora masu girki ashe ke kin dora ko kin koyi barci wanan aikin haka ? Na juyo ina tambayan ta harara tayi tare da fadin saurin may kina can kinyi filo ds kirjin mijin ki kin manta da baki. Ke dai kika sani na bata amsa tare da saurin juya maganan nace Allah kin yi saurin wanan aiki haka yanzu fa shida ke batun yi. A wurin ku ma,aurata kikaga saurin hakan mukan ai safiya ya dade da yi ko tunda kinga har nagama aikina yanzu saura naki. Shiga ki kintsa ki fito a fara zuba masu kafin su tashi mun gama komai dakina na shiga inda ya Amina da anty fauziya suka kwana su mommy na cikin dayan dakin da ban faye amfani dashi ba. Suna kwance suna barci na shiga na shirya a hankali ina shirin fitowa ne ya Amina ta falka ina kwana nayi mata muka dan tsaya hira. Maryam ta shigo dakin tana kirana na fita na samay ta a falo tana fada min tana jin hayaniya kamar Nafisa ce ta dawo. Nace da safen nan kila dai muryan yan uwanta kika ji sai dai kuma ba abin mamaki bane don yace yau za,a sallamo ta dama. Tace kamar mai tsoron asibiti zata dako wanan sammakon haka ta dawo gida ke ko wake son zaman asibiti idan ba dole ya kama ka ba. Mun ci gaba da zuba abinci ba tare da mun kara bi ta kanta ba jin muryan su mommy a dakin da suka kwana suna hirane yasa nasan sun tashi. Dakin na shiga da sallamana suka karba min cikin zubo idon su a kofan dakin fuskokin su a sake tare da fadin khadija kun tashi nace eh mommy ina kaiwa kasa tare da fadin ina kwanan ku mommy ? Lafiya ya gajiyan da dauwai niya mun kawo maku bakun tan na bazata anty amarya ne ta dan dago daga inda take kwance tana fadin wallahi fa. Sannu da kokari kinji ina murmushi na mike daga tsugunin da nake nace mommy kuyi wanka abinci na falo. Kin gani ba haka muke so Alhamdullahi gida ya gyaru yanzu tunda mutun zai zo ya samu tarbo haka ke da ki kara hakkuri don yanzu kishi ko wani iri yin shi zata yi na fili dana boye Alkah dai ya dada kare muna ku. A raina na amsa da amin na mike zuwa ban dakin wanko masu shi na yi tare da kunna masu ruwan zafi na fito har lokacin magana sukeyi akan gidan ban tsaya na fito daga dakin. Can na koma dakin kwana na na wanke ban dakin yadda zasuji dadin yin wanka a cikin sa duk da shima ba wani ddatin da yayi. Muna falo na ce da maryam barin leka shi idan ya tashi in gani na fice daga dakin ina zuwa falo na samu buzaye mazan su da matan su sun saka nafisa a tsakiya. Nace a, a ashe kin dawo sannu da dawowa ya jikin idan ke dake nesa kin karba min nafisa ta karba min ban tsaya ba nai murmushi ina haurawa sama naji tace Allah waddai cusa kai babu kwarjini. Sanin muna da baki a gidan yasa ban tsaya ta kanta ba na haye sama abina kofan dakin shi na tura naji kofan a rufe na dan murda shiru. Harna juya zan fito ina tsanmani ya fita daga dakin naya na sai naji ana murda kofan dakin shine ya bude tare da fadin waye fuskan shi a daure. Ganina yasa naga ya koma yana bude kofan na mara mai baya zuwa cikin dakin ina shiga yake fadin marasa hankalin na rufe na kofa. Ina kwance sai ga Samiha min a daki wai Nafisace ta turo ta karban abu wurina ban bashi amsan maganan shi sai kokarin fadin da nakeyi kayi wanka ne ko in hada ma ruwa ? Banyi ba yanzun dai nake shirin yi danaga baki dawo ba don kwance nake tun dazu na gane may yake nufi amma na basar dashi kamar ban gane may yake nufi ba. Nagama abinda zan mai na fito daga dakin daya shiga wanka har lojacin suna nan a inda na barsu zaune din. Ban kula su ba na shige part dina a falo na samu bakina sun fito maryam ta na gabatar masu da abin kari. Mun zauna ana karyawa ana hira ne ya shigo a cikin shirin fita yana gaida su mommy din da yaya Amina dake mai sarakuta. Tambayan shi mai jiki mommy tayi yace ai ta dawo da safen nan Anty amarya tace har an sallamo tane yace tadai sallamo kanta dai. Ikon Allah duk shiru sukayi falon suna mamaki sai Fauziya ne tace wai ko yayan mu Nafisa nada hankali murmushi yayi yana mikewa daga inda yake tare da fadin tana da shi mana tsaban wautane mata. Da kuma zafin kishi inji Faiza ta badi tana kama yar ta dawowan gida mai zatayi banda zaman saka ido da fitina kana ma kokari wallahi. Kallin ta ya danyi ya kawar da kai zuwa gareni ban ko dago na kallesu ba ina dan shan tea dake gaba na a hankali. Zan fita in dawo Allah ya tsare nace dashi tare da kawar da kaina gefe daya akan tea dina bayan ya fita ne suka sa topic din Nafisa a dakin. Fauziya da Faiza sukace ba zasu gaida ita ba don sai sun nuna mata ba kowa take ba yanzun kan basu shayin rama komai zatai masu. Maryam nabi a daki nazauna a wurin ta a nan ya Amina ta samay mu sai lokacin nake nuna mata kayan da ya sayo min na lefe fita tayi da kayan falo wurin su mommy tana nuna masu. Nan suka shiga kallon kayan tare da yaba kyauwon su ashe mu kallon tsoro mukaiwa kayan sai yau muka fahinci may ke cikin akwatunan. Mommy ne ta jawo sarka da awarwaro na zinare har kala uku da wasu set din agoggaya masu masifan kyau kala uku suma kallon juna mukayi da maryam din na sada kaina kasa . Su mommy ne bayan sun gama kallon kayan sun sa albarka suka fita waje gaida Nafisa da dawowa basu jima ba suka dawo dakin. Basu ko zauna ba Faiza ke tambayan su idan nafisa ta amsa masu gaiuwa dariya ne ya dan kamani alokacin haka na kumay shi ba hali in fitar aji. Haka dai har suka shirya tare da maryam su Faiza da fauziya da Anty amarya suka shiga kasuwa suka barni da su mommy da ya Amina a gida. Bayan fitar su ne mommy ta fara magana tace dama naki binsu ne don mu samu kyabewa dake Khadija da sauri na dago kai ina kallon mommy din. Tace khadija nasan irin zaman hakkurin da kike da wanan matan don haka ki kara ga wanda kike dashi kada ki yarda daidai da rana taya ta gane kin karaya da alamarin ta. Don ta haka zata gano takon ki a gidan nan ki zama jarumar mace a gidan ta kamar sauran jarumai matan da suka sha gwalgwalmaya a gidajen auren su kafin su tsaya a kafan su. Sannu a hankali idan kinyi hakkuri kuma kikaci gaba da wanan dabiar take zaki cin ma nasaran ki da yardan Allah. Sai dai abin ne dakamar wuya don akwai tafiya amma sai dai kamar gobe a wurin Allah in dai da rayuwa . Ba wanda ya tsamani zaki samu sauki a wurin mijin ku haka sai gashi Allah da ikon shi na fahinci biyayyan ki gare shi ya jawo maki mutunci da kima a idon shi. Bawai kwanciyar aure bane kawai jin dadin aure a, a har da yi nayi bari na bari da gyara da hakkuri da rayuwa ga abokan zama. Ni a fahintar Nafisa danayi ta ta,allakane kawai da kwanciyar aure a tsakan su ba wai ta damu da kula da rayuwan miji bane. Shi namiji kana sace zuciyar shi ta fanni daban daban irin kyautatawa da kulawa a gareshi da nuna damuwar ki nasan duk kin san da wa yan nan abubuwa amma sakaci dashi da wasu mata a yanzu sukeyi ne ke yawan jawo masu matsala a gidajen su. Kinga kamar fati ansan akwai asiri amma asiri ya cin ma hali dama don ko banza haka take kamar dutse babu marmari a tare da ita. Yanzu daman ki ne khadija da zaki nuna naki bajin ta ga kowa na babangida asan ba auren banza ya kara ba. Ko wace mace dama da dalilin auro a gidan mijin ta amma dan akasi kadan zai iya bata ta ga kowa ba wai ga mijin shi kadai ba kadai ba a, a har ga kowa dake tare dashi. Don Allah khadija kin dai ga kannen mijin ki a tsatsaye suke ko gare mu matan uban su wani lokaci sai mun hada da hakkuri da su. Haka ke ma nake mai jan kunnen ki a kansu kada ki yarda ki samu matsala dasu ta ko wani fanni na zamantakewar ku dasu don Allah. Ko dan zaman nan da mukayi tsakanin jiya da yau ya kamata ki fahinci wani abu daga gare su irin halaiyan su da sauran kalaman su zuwa ga nafisa. To ke sai kiyi amfani da wanan damar ki toshe wanan kafar da ta sake daman ta a gare su ki gyara ta yadda zai zama kin kawar da duk wani shakku na gidan nan a zuciyar su. Ina fada maki hakane don daukar ki danayi tankar yar uwata ta jini don albarkacin Amina gata nan shawaran Amina har gobe baya wuce ni da kika ganmu nan . Haka nima nawa bai wuce ta a haka muke zaune muna rufawa kan su asiri ga matsolalin mu . Akwai canji kwarai da aka samu a gidan nan ta dalilin ki ne kuma sai ki daure ki rungumi Allah da mijin ki banda yawan fushi kan abinda bai kai ya kawo ba a dauke shi da zafi. Har yar uwar zama ta fahinci kuna da matsala da mijin ki taji dadi ko a bainan jamma, a yai maki abinda ba daidai ba kada ki yarda ki nuna har mutane su gane hakan gare ki. Ajiyan zuciya na sauke bayan ta kare maganan ta da fadin Allah yai muna jagora ya shige muna gaba da amin. Nace mommy na gode in sha Allahu zan kiyayye da yarda Allah ya Amina ne ta karbe da fadin don Allah khadi kiyi amfani da maganganun da mutane suke fada maki ko da yaushe ki jajirce a gidan nan ki mai da komai ba komai ba . Dawowan su Anty amarya yayi daidai da isowan shi gidan ya dawo ya sallamay shi sai da yasa aka cika masu bayan motar su da tsaraba sukai muna sallama suka tafi. Bayan tafiyan su ne ya dan shigo bai zauna ba saman dakin shi ya shiga bai dade ba ya fito su nafisa na zaune a falon ya dan tsaya da ita yai magana daga nan ya shigo part dina ya samay mu. Ina gyaran wuri ya gaida maryam dake kitchen tana wanke kayan da mukai amfani dasu ga bakin mu yace dani ya kamata a samo mai taimaka maki da aikin nan haka. Nace zan sa hajiya mama ta duba min a kaduna idan za a samu a turo min yace ba zaki magana a samo maki a gida ba. Fuska na ya mutsa nace mai zan dai fi so a kadunan don can gaskiya ban san wata wace za,a dauko min ba yanzu kan. Ok zan mata magana muji ko akwai wace za,a turo maki din ni ni zan koma office sai yamma idan na dawo. Allah ya tsare a dawo lafiya nace mai yanzun na dan sasauta daure fuskan da nake mai kwana biyu a gidan. Na jin zafin abinda yai min ajan nafisa don ni jin zafina shine bai kulani ba kamar ba mutunce ya bari a daki ya fita ba. Sai kuma fadan da yai min don may na fita school a ranan duk da na fada mai a motar gida na fita kuma yake ganin laifina dayin hakan. Bayan mun gama komai ne mun zauna da maryam muka danyi hira har barci mukayi after four tace zata koma school ban so ba sai dai ba yadda zan yi da ita don dole ta koma din. Bayan tafiyan marya sai naji zaman ba dadi ban kuryan daki ban falo a karshe dai na dawo falo na zauna da takarduna ina dubawa a hankali. Lokacin aiyukane amma sanin cewa ba nice da girki ba sai ban damu da in aiwatar da komai a gidan ba don ba hurmi na bane yin hakan yau. Waya na dake gefena yai kara na dauka ya Amina ce ke kirana na dauka take fada min bayan mun gaisa wai sun isa tun dazu yanzun take shigowa gida. Nace sannun ku da hanya su boy dai nasan sai zuwa gobe za a dauko su ko tace nace a kawo min su yau don gidan yai shiru basu. Nace wallahi haka nake fama da kadaici yanzun haka dazun nan ma bayan wucewar ku yake min maganan ai in samo mai aiki da zata debe min kewa. Ni kuma nace ba wadda zan samo sai dai yaima hajiya mama ko mommy su sama muna tace kina ganin a dauko maki wata ta fanin su zaifi. Nace ni haka nake gani anty don kin ga irin korafin da akeyi akan nafisa da yan uwan ta a gidan ko yaushe to sai kuma ni inje in dauko nawa in kawo gidan anty ? Ke diban hauka zakiyi irin nata ai ba zai wuce mutum biyo ko uku ba ko nace wai anty na kaisu ina data ma ta isheni ai ya Amina ina zan kai har mutum uku haka anan. Tace yanzun dai zamu tatauna da mommy muji inda ya dace a sama maki din amma ai ko can gida ba za a rasa irin yan kauyen Doko din nan ba masu neman aiki. Munyi sallama da ita na kashe wayan tare da tunane a raina mikewa nahi na shiga daga ciki don in watsa ruwa kafin lokacin sallah yayi. Misalin takwas ya karaso gidan nan falo ya samu nafisa da iyalan ta zaune tana waya gaida shi suka danyi bawani cikin kulawa ba. Kare wayan tayi tana dago kai gare shi yace da ita ya jikin naki tace da sauki tana kokarin mike kafar ta a kan dan stol dake gaban ta. Bai tsaya ba yace barin shiga daga ciki in watsa ruwa ya sa kai ya fara tafiya ta kira sunan shi da fadin Samad ya juyo yana kallon ta. Tace banji kayi min maganan kudin dana tambaye ka ba dazun da zaka fita yai mata wani irin kallo tare da sauke nauyayan ajiyan zuciya. Cikin bacin rai ya dan runtse idon shi na dan dakikoki sannan ya bude tare da kallon su gaba daya da yan uwan ta yace. Nafisa na sha fada maki ban son irin wanan dabiar da kike min ke wai kullun baki da zance ga mutum sai na maganar kudi shi kudin nan ko ginar shi mutum ke yi ai yana wahala gurin gina ko ? Tace idan ban tambayeka ba wa kake son in tambaya ya bani in yi lalurar gabana dashi yace saboda ke baki da wayau ko ya watsa mata hara ya barta gurin. Har ya shiga wanka yana tunane a ransa alamarin Nafisa yana daure mashi kai ya rasa abinda take yawan yi da kudi haka don kullun cikin jero mashi lalurar kudi take a gidan. Babu abinda ke cikin zuciyar ta sai zancen kudi bata san ta sauke hakkin ta na aure ba gare shi. Duk kokarin da yake yi a kanta da yan uwanta a gidan ya lura Nafisa bata ganin haka may ye amfanin bata kudin matar da batasan kimar shi ba. Ganin alamarin nason damun shi a rai yayi gagawan cire tunanen ta a ran shi ya watsa ruwa agurguje ya fito bai tsaya dogon shiri ba ya nufo part dina don ganin halin da yake ciki don baiji motsina ba a gidan. Kai tsaye da ya fito part dina ya nufa nafisa da ke zaune tabishi da mayattacen kallo cike da jin hayshin shi da zargi a fuskanta. Shigowa yayi lokacin ina falo zaune a kasa tv na aiki ga cup din tea da cake a gefe ina rike da takarduna ina assignment. Kaina na dago ina kallon shi tare da mashi sannu da zuwa ya samu wuri ya zauna tare da fadin dauko min abinci in ci anan. Kallon shi nayi cikin mamaki nace ba nan kake ba yau ai shiyasa banyi girki ba yace kenan baki girka komai ba ? Nace cikin girgiza kaina gaskiya banyi komai ba yanzun ma tea na dan hada kada in kwana da yunwa a cikina. Yace amma kin san dai nafisa jinya take yi ko don haka ba hujja ba ne kice baki girka min abinci ba inba ba, a nan zaci ba ke cikin ki bazaki ci bane ? Najira ya gama fada in fada mashi dalili na na kin yin girki danayi don yin zai kawo wani fitina tunda dai ita batace ba zata iya yin girki din ba saida ya gama. Nace ina gujewa abinda zai haifar da wani fitina ne agidan nan tunda ba ita tace ba zata iya hidima da kai ba kuma ni naga ni kadaice yau shiyasa ban girka komai ba tea din ma zai isheni in kwanta ai. Yar gurin Nafisa ce ta shigo babu sallama ya daka mata tsawa yace ta koma tayi sallama kafin fa shigo. Ta koma baya sai taiyi sallama ta shigo tace maman su na kirnshi a falo yace yaji koda ta fita ya dan dade zaune a gurin yai waya yana bada sakon abinda za a sawo mai yaci. Ya mike tare da fadin ina zuwa yana fitowa ya samay ta tacika fam tana jiran shi a gaban yan uwanta ta haushi da fada. Akan may zai tafi dakina bayan banice da girki ba ita bata son cin amana don an raina mata zai zo gabanta gaban kowa ya shige dakina ya zauna. Nafisa wai may kika dauki kanki bazan shiga dakin matana ba don kina zaune ko may ina mutanen da kike fadi a gaban su na shige. Take taji zafin zancen shi don wata ita da yan uwanta ya raina ma hankali yake fadin ina mutanen da zaiji nauyin su. Tace to barin fada maka in ma mayaudariyar bata fada ma yau nice da girki a gidan nan kaima ka sani don haka banga dalikin shiga dakin ta ba yanzu. Wai ke kina da hankali kuwa banda shi kamar yadda ke kirana kullun mara hankali sai kai min yace ta yaya za a sallamo ki daga asibiti yau kan lalura kuma likita ya fada maki dokokin da zaki tsare kice wai zakiyi wani girki can a gidan nan. Dama nasan hada baki kayi da likita ya fada min haka don ka samu damar kebewa da matar ka kun mai dani bi can ko ? Idan mun hada baki da likita ya fada maki haka hada baki nayi dashi jini ya zubo maki sai tace mai waya sani ma ko hakanen. Wai kaima baka da zuciya ne may kake tsunta wurin wanan yarinyar daka rasa a wurina bada taya ka kwanan banza da takeyi kullun. Amma banga laifin ka ba don kayi haka tunda dole ka rarashe ta kada asirin ka ya tono ta gane kai mace ne a gurin ta. Yace eh lallai Nafisa na yarda yau tunda kin fada da bakin ki ashe kin san sherin da kikayi a haka tace banyi komai ba amma nasan hakane ma. Idan taya ni kwana takeyi ya zama laifi ne tayi kokari tunda tasan hakkina a kanta ta taimaka min. Yau dai ba inda zaka tafi ta rike taimakonta an yafe don mai abu ta dawo yanzu ke don Allah ban iya shirmay ki kullun fada a kan abu daya. Yarinyar nan bata ko san kina wanan haukan ba don ita tana da hankali tafiki kaifin tunane tace don ta fini iya kissa ba. Ciki dai ne tare dakai mukayi kuma tare zamu raine shi a gidan nan kaji na fada ma ga inda iyalin ka suke suna bukatan taimakon ka zaka shige wurin mara moriya. Juyawa yayu ya wuce ya barta na baiyi nisa ga tafiyan shi ba mai sakon shi yayi sallama dauke da sako a hannun sa ya karba ya aje masu leda daya ya wuce da sauran part dina. Bata fasa fada ba dashi tana saman bakin ta yashi ya mika mun keda yana fadin gyara min daya in ci . Yanzun dai kaima kaji dai da kunnen ka ji da kunnuwan ka abinda nake fada ma yanzu waya ta buga mai yai ta ringing yaji dauka sai cin naman shi yake yi ya kyale wayan yana ta ruri a gefen shi. ZAINAN IDRIS MAKAWA SEENABu 1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Ni dai suna cikin rikicin su n rufo kofan part dina na barsu can suna yi barci nayi ranan sosai saboda dan nauyin mutane dana sha kwana biyu. Ban samu zuwa gidan anty hauwa ba sai da aka kwana hudu don jigilan karatu da nake fama dashi gashi yanzu girki da nawa da ba nawa ba duk ya zama min dole inyi saboda a part dina yake cin abinci. Duk da Nafisa tana zaune a gida tana bedrest amma haka bai hanata aiwatar da sherin ta na sheri kamar yadda ta saba akan maigidan da ni. Burin ta kullun shine ta wayi gari taga ta daina gani na acikin gidan gz baki daya don haka ne kawai take gani samun kwanciyan hankalin ta da ta rasa. Yanyala ta isa lafiya a cikin kwana biyu da tayi a gida mai ma nafisa aiki ya gama hada masu surukulen da zai bata ta kawo wa Nafisa din inda ya jadda mata zasu ga haske sosai ga aikin su . Bata kara kwana kauyen ba ta shigo mota ta juyo Nigeria cike da gajiya da bautar uwar gijiyan nata. Bata iso abuja ba sai washe gari bayan ta sha bakar wahala a hanya ta iso gidan a gajiye da ita. Ina kofar gida na shirya zan tafi gidan anty hauwa naga isowar ta alaman rashin gaskiya karara a tare da ita nikan kallo daya nai mata naji gabana ya fadi. Lah, illaha illah, anta subbahanaka inni kuntun minal zalumin, na fadi. Ta gwautani kamar mara gaskiya da ita ta shige na bita da kallo ta gefen ido sai kamay kamay take yi. Driver yana jirana mu tafi na bude mota na shiga har mun danyi nisa da gida sai na tuna ban dauki tsaraban da na sayawa anty hauwa ba. Nace ya juya nayi mantuwa a gidan ya juya kan motar muka koma gida na fita don in dauko tsaraban. Suna falo zaune yadda na barsu sai yanyala dake ta fitar da maganunuwa daga cikin jakka ta tana ma nafisa baya su . Daidai ta daga wani farin kwalba da ruwa a ciki sa fari tana mika ma Nafisan na shigo falon gaba dayan su sai da suka razana da ganina a wanan lokacin. Ban bi ta kan su ba na bude part dina na shiga na dauki abin da zan dauka na fito ina rufe kofan ina karanta addunan neman tsari da kariya a wurin Allah. Na sake ficewa ba tare da na kula suba na samu driver muka wuce har lokacin gaba na bai bar faduwa ba har muka isa gidan anty hauwa da ba wani nisa don a unguwa daya muke dasu sai dai akwai dan jayawa kadan. Na samu bata nan sai yar ta da tazo hutu daga saudiya da muka zauna da ita muna hira dama mun saba tun a waya da ita idan maryam ta kira ta takan bani mu gaisa da haka har muka saba din da ita. Sosai muke jin dadin hiran mu wanda ba wani hira bane sai na yanayin karatun nan kasar mu da inda take karatu a saudiya. Mahaifiyar ta da ta buga ma waya ta sheda mata zuwa na ne ta dawo da fara,anta a fuska take taro na har kasa nakai ina gaida ita zuwa tayi inda nake tana fadin. Kai haba khadija zauna mana ke fa yanzu ba bakuwar gidan nan bace don gashi ma yanzu naji mamakin ganin wanan mai kama da kura ta sake jiki dake haka har kuna dariya. Hummaira tace lah mami na san anty khadija fa tun a waya mukan gaisa da ita time to time har zancen auren ta na sani. Ledan da na shigo dashi ne na mika ma anty a cikin ladani ina fadin ga dan tsaraba nan ba yawa na riko maki anty. Karban ledan tayi tana budewa da sauri ta dago kai tana fadin kai kai kai khadija wanan tsaraban manya haka duk ani daya. Gaskiya wanan ba abin fitarwa bane kowa ya gani wanan sai idan na shiga daki ni kadai hummaira dake kallon uwar nata tace mami idan naji kin fadi haka rowa kike son muna. Anty khadija may kika kawo ma mami take kokarin yi min rowa ta mike zuwa wurin uwar sai ta dauke ledan ta boye nan suka kama yar boya da uwar. Sun bani sha,awa sosai yadda sukeyi da uwar nata kamar kawayen juna karshe dai sai ta bude ledan hummaira nagani ta fada jikin uwar tana murna tare da fadin. Wai mami ashe da rabon zanci wanan abin tambayar yar tayi may ye sunan abin ina kallon su ina dariya daga inda nake zaune. Juyowa anty tayi inda nake tana fadin khadija fada mata sunan shi murmusawa nayi ina fadin kilishi wanan anty ba na nan bane a kebbi na aika aka sawo min don yafi dadi. Kai bari mu dana muji tace tana bude ledan ta balla kadan ta mika ma hummaira din wai anty tace bayan ta gutsura ta tauna tace wanan wani gari ake yin sa don Allah nace wata course mate din mu ce take sawo shi mijin ta dan can ne wai kilishin gwandu. Gaskiya wanan yaci sunan sa ainihin kilishi irin na da wanda muka sani ke nan sallaman maryam mukaji muka amsa anty tana kokarin boye ledan a bayan ta don ganin shigowar maryam din. Nace anty ai ba sai kin boye ba don na dibar mata nata jiya da aka kawo min shi wanan naki ne na kawo maki. Zama maryam din tayi kusa da ita suka sa ta a tsakiya nan suka far ma kilishin da ci maryam ne take fadin ta buzuwa ashe kin samu shigowa din. Hararan ta nayi nace ba buzuwa buzaye anty tace kin ga na manta wanan yar kwadan ta cika ni da surutun banza wai ya kuke a gidan. Murmushi nayi tare da fadin muna nan dai anty humamaira ne ta mike tana fadin mami kawo ledan in kai maki daki boye ledan tayi a karshinta tare da cewa sai mun raba na dibarwa daddyn ku nasa kin san yana son shi sosai shima. Hummaira ta shige a shagwabe uwar ta juyo gare ni tana fadin kedai ina jinki kanwata nace suna can yanzu ma nabarsu kamar kullun nan nake labarta masu abinda na gani yanzu kafin in fito. Tace ai indai wa yan nan ne aikin su ke nan ba fasawa zasuyi ba ko basu cin riba ke dai dama abinda yasa nake neman ba wani abu bane sai in kara fada maki ki kula sosai. Ina son ki kuma classic lady sosai khadija kin ga kwalliyan nan yana daukan hankali maza sosai tundai irin mazan nan naku da suke yara ga kuma sanadarin a hannun su, shine kudi. Ki dage sosai kada ki ji kiuyan komai ki dinga masa abincin da yafi so kina daurewa a gurin shimfida kinuna mai cewa ke ma gwanace ta wanan famnin har kin fishi iyawa. Dariya maryam tayi tare da fadin Allah yasa anty wanan kamar kifin rijiya take fa ba abinda ban fada mata ba. Wanan kuma wani abune dake kara haska kwarjin mace ga miji khadija shiyasa zaki ga wasu mata ba kyaune dasu ba amma miji yanaji dasu kamar ya lashe a gida. Kin san fa maza su a wanan fannin basu da wasa ko ita buxuwan ai da wanan abin take samun galabarshi ba komai ba. Don idan ba kin tsaya wasa ba ai duk inda wata buzuwa zata tsaya khadija zaki iya tsayawa may ake so gun mace gyara da wayewa yanzu duk kina dasu sai lafabin aure wanda nasan ko rantsuwa nayi bani kaffaran haka. Kin fi wanan buzuwa ladabin aure a gare shi So kina da dama da zakiyi amfani da naki baiwan wurin gwada mata ita ba komai bace a idon ki . Idan har kin rike wanan abin dana fada maki babban makamin ki ya zamo Allah shi zaki sa a gaba ya taimaka maki akan komai da zakiyi. Wallahi khadija ni na fada maki zakiji buzuwan nan tadawo tana fadin kin kwace mata miji ne da asiri ko wani abu. Yanzu akwai wata kawata yar libiya ce matar zan turaku wurin ta zata baki training akan komai na rayuwa na riga da na mata magana akan matsalan ki. Don haka ki daure ki dan yi sequzy din kan ki ki rage lokacin don ki samu ganawa da ita a kullun just three week ko four kawai ya isa ki haddace komai da kike so. Zan shiga dubai zan hado maki duk wani abinda zaki bukata maryam tace akwai wasu kayan lates da mijin ta ya sawo mata a matsayin kayan lefe. Tace ok ku kwaso mu bada dinkun nan su a modern design suyi maki express masu kyau na gani na fada najan ra,ayi . Ki gani idan baki haukata wanan buzuwan da makarabanta ba suma su madam din ai ba don Allah suke tare da ita ba . Abin hannun ta da mijin ku, ke sake mata ne suke gwadayi a wurin ta dan bata san ciwon kanta ba sam. Yanzu abinda nake kara son ki dashi shine ki koyi dabara ta tanadin abinda kike samu daga gare shi ta yadda ke ma zaki iya gina kan ki ki zauna a kafan ki, ki kafu. Shawara mai amfani ranan tayi min sosai wanda ni ban kawo wutan yin shi ba a raina nace ashe magani ne a gonar yaro ba sai nabi wani hanya ba can nike da maganin a tare dani. Sai da nayi sallah la,asar a gidan tasa drivern su ya kaini gida tare da maryam muka fito zuwa gidan namu. Mun samu su madam a gidan ana shewa da hayaniya an barbaje ana ciye ciye maryam na biye dani a bayana muna tafe muna hira. Zan taka falon naji gabana ya fadi addua nayi saurin kawowa a bakina da sallama mara sauti na shiga sai dana karanto adduan . Alama nagani daga na garin magani a kofan shiga part din da sauri na rike maryam ina mata nuni da abinda na gani idanuwa suka watso muna suna Allah Allah in taka abin da aka barbada din. Sai sukaga naja na tsaya fita mukayi da maryam din a waje muka tsaya muna shawaran abin yi maryam ce ta kawo shawaran may zai hana mu shiga makwabtan mu muyi fitsari mu zuba. Dariya ta bani nace kina ganin haka zai yuyu tace ba ance yana kara asiri ba nace ban fa taba shiga gidan kowa ba anan maryam asalima ba wanda ya sanmu. Yanzu dai bari ki gani ashe suna leken mu maryam ne ta gansu take fada min adduan neman tsari na karanto naji gabana ya daina faduwa shiga muka sakeyi main kitchen din gidan na nufa na dako tsintsiya da mofa suna kallo na share abin maryam na zuba ruwa. Muka bude part din muka shiga muna shiga maryam tace wai Allah ya somu yau khadija kina da kula wallahi da nice ai afkawa zanyi hakana batare dana halkanta ba. Nace maryam kullun ido akan komai yake a gidan nan bakina kuma bai daina karanto addua don sanin halin wace muke zaune da ita. Idan naji gabana yana yawan faduwa maryam tun ina gidan mu nai nitice din haka wani abune mara kyau ke shirin faruwa dani. Kin san ance ko wani mutum yana da sing din shi na gane abu kula da hakan ne kawai mutane basu yi. Amma yanzu kin ji zuciyana wasai nake jin shi alaman abin ya gushe ke nan a gare ni Allah ya tsare ya kare maryam tace nace amin. Madam ta fara magana a falon bayan shigan mu wurina tace Nafisa anya wanan kishiyar taki ita kadaine kuwa. Ko dai tana da aljannun da ke nuna mata abune haka ji yarinyar nan yanzu abinda tai muna fa ta nuna muna ta gane may mukayi mata. Kin manta ne madam jikar mayune fa tana ganin har hanji banyi mamakin haka ba don dama malam ya fada muna haka kin manta ne ? Idan tasan wata ai bata san wata ba don wanan da zan saka a kasan gadon dakin shi yafi zama shu,umi a gare su don ko ta mutu ko hauka kota kwanta ciwon da ba magani. Ina da tabbacin sosai ga wanan aikin yanzu shigar su kawai nake jira dakin su kwanta da ta kwanta shegiya sai buxunta ba ita ba. Bayan mun hutane nacewa maryam ta dora min girki zan tafi dakin shi in dan gyara na fito ina saye a cikin dogon rika na zaman gida. Na daura dan kwalin rigar a kaina rigar free ce don shan iska akayi shi baida wani nauyi sosai. Na tura kofan da sallama na nashiga dakin nabi da kallo a hankali gadon dakin naga alaman an daga take sai gabana ya harba min dammm. Wurin na nufa kamar wace ake turawa sai kawai na daga gadon na shiga dubawa abubuwa ne ba zaka gane akwaisu ba a dakin an nade a cikin farin leda a ka cusa can; daga gefe daya. Ban dakin na shiga nayo fitsari na zuba mai na sharo abin sai dai ban zubar ba na aje a cikon dusbin sai ya dawo in tambaye shi idan ba nasa bane. Na gyaro dakin ko ina na rufo mai na fito basu falon a lokacin har na koma part dina na samu maryam tayi nisa ga aikin da take min. Bata tafi ba sai da mukai sallah magariba ta dauki kayan da zata kaiwa anty ta tafi ya saura ni kadaice a part din . Na dade a gurin zaune ina tunanen kalaman anty a raina lalai ya zama dole gare ni na gyara komai nawa kamar yadda anty tace min ga magani a gonar yaro baisan kan sa ba ke nan. Shigowan shi ke nan ya nufi gurin nafisa ya dubata yayo dakina daga can daga ida nake zaune a kasa saman center carpet na mike kafafuwa. Jin an turo kofan ne yasani daga kai na kalle shi sannu da zuwa nai mai tare da fadin ka dawo ? Na dawo khadija yau ban tsaya kusa ba munyi balaguro ne zuwa keffi acan muka bata lokacin mu yanzu sai wanka ke nan tunda ka kwaso wanan gajiya. Kinyi tunane mai kyau gaskiya barin dan watsa ruwa in fito kafin nan nasan abinci na ya kammala. Insha Allahu na bashi amsa ina kokarin mikewa daga inda nake zaune dukawa yayi ya debi corn din danake ci a gefe na. Har ya kai kofa ya juyo yana fadin hajiyan mu tace a fada maki za a kawo lefen zainab a karshen satin nan insha Allahu. Da murna na dago ina fadin masha Allah gaskiya nayi murnan jin hakan wallahi ashe zainab ta kusa bin layin mu bada jimawa tunda har lefe zaizo. Baki ya tabe mi yace kinji dadi ke nan za ai mata yadda akai maki koda yake kawaye kuke waya sani ko matsin ku yasa akai maku hakama. Wani kallo na watsa mai tare da fadin kana da gaskiyan ka tunda ka tauye ni. Dariya ya wuce yanayi har ya fita kitchen na shiga na hada mai abincin shi na tsaya na gyara komai yadda ya kamata in yi na fita zuwa wurin shi. Sai da na aje abincin na shiga daki wurin shi tsaye na samay shi yana juya kwalban da wasu abubuwan da na tsinto a karkashin gadon shi. Yana ganin na shigo ya juyo gare ni yana fadin wanan may ye kuma haka Deedar ? A karkashin gadon ka na jawo shi dazu nan dai na fada mai yadda akayi tun dawowana gidan ni da maryam. Kai kai yace yana zama saman gadon tare da fadin wanan abin wai da may yayi kama haka nace waya kawo shi nan to ? Yace wa zai kawo kuwa banda daya daga cikin ku tunda daga ni sai kune keda alhakin bude dakin nan yanzu. Allah ya kyauta nace na dago ina fadin kayi wankan ne yace shi zan shiga ai naga wanan abin a kofa nace nina aje don kazo ka gani da idon ka. Ya juya ya samu leda ya saka tare da adana abin jirani in fito dakin ki zamu koma sai nayi bincike akan wanan abin. Yana shiga ban dakin ban zauna a gadon ba na juya inda na hada kayan abincin dana shigo mai dasu a cikin basket. Ya fito a gurguje ya shirya muka bar dakin zuwa nawa ranan a can muka kwana wanda ina jin dadin hakan don ina sakewa sosai idan yana dakin nawa. Asuban farko dukan kofan nafisa ne ya falkar damu cikin sababi take fadin iya shegen da kake yi a gidan nan yayi yawa. Samad kaine ma mai biyo mace dakin ta ka kwana yana son fita na girgiza mai kai nace dashi kyale ta please. Ya koma ya kwanta sai da akai kiran sallah muka tashi a dakin shima yayi sallah bai fito daga dakin ba sai bakwai da rabi. Ashe tana falo zaune zaman jiran shi yana fitowa ta fara mai ihu da sowa wai yaji kunya gotaigotai dashi yana bin karamar yarinya dakin ta yana kwana. Nafisa kina da hankali kuwa ke ba dakin ki nake binki ba yanzu tace idan ka bini ai da amfanina ko dan yanzu da nake cikin wanan halin. Ita bata da amfanine gareni tace ina taga amfani banda ci takai masai mai take tsinana maka kai nafa san komai na fada ma duk wanan rufa rufan da kakeyi nasani. Ashe dai har yanzu ke nan labe kike muna kenan tunda har kin san haka gashi yanzu ma alama ya nuna kan shi tunda har kin san a dakin ta nake kwance. Na sani samad don na damu dakai ne nake haka yace ban saki damuwa dani ba tunda kin san bake kadai ke dani ba. Wallahi baka isa ba samad sai ka dawo kana fadi da bakin ka a tsakar gidan nan ka kwaso mai farar kafa mara moriya a gare ka. Yace ban yi mamaki ba don kin san sheri da kika kula zaki ko sha kunya a gidan nan wallahi don babu ida zata tafi. Banyi mamaki ba don jikar mayu ka aura ta kama ma kurwa baka ganin laifinta a yanzu do an gama dakai ko. Yace ke mahaukaciya ce kula ki ma hasara ne kiji da hakin da kike ciki zai fi maki alheri sakarai kawai ya shige . Cikin daga murya take fadin zaka gane baka da wayau samda karka manta a tadin hannuna kake wallahi bai kula ta ba ya shige abinshi ya barta a wurin. Ranshi a bace har ya karasa shirin shi ya zo ya karya bai kara bi ta kanta ba don ya gane idan ya biye mata zasu sai da haline kawai a gurin. Koda muka fito yau a tare muka jero dashi don fita zuwa school shi kuma zai shige office abinsa nafisa da tawagan ta suna zaune falon nan ta dasa sabon balai kamar yadda bai kulata ba ni haka nazo cikin shiri na wuce su a inda suke zaune suna banbami. Tunda muka shiga motar takaici da haushin tozarcin da tai mai ya hana shi magana nima ban bi ta kansu ba hankali na na mayar a wayana. Mun isa suka sauke ni a kasalance yai magana da cewa yau ma ina ganin keffi zamu je wani aiki da wuya in dawo gida yau. Allah ya tsare hanya nai mai da a dawo lafiya ina kokarin bude mota naji ya rike ni tare da fadin wai fushi kike ko may ? Kallon shi nayi tare da dan murmusawa nace fushi akan may ? may ya hadani da maganar ku da zanyi fushi kuma? No khadija idan ya kira full name dina nasan magana ce ta serious zai yi don haka na mayar da hankali a gare shi ina sauraren shi. Kada kiji wanan yar fitinar na fadin wai ina kwana a dakin ta ki dauke shi wani abu wallahi banyi hakan don wani manufa ba. Sai don tsaron lafiyan abinda ke cikin ta kawai nayi haka don hawa saman ta sauko zai iya jawo mata wani matsala again. Don wanan tunanen yasa, , , , haba dai ni fa wanan ba matsalata bace asalima ban san da wanan zancen ba a rayuwa na. Tunda ba hakkina ka dauka ka kai mata ba ban damu da duk wani rayuwan da kuke yi a cikin gidan nan ba idan ba wanda ya shafi bangarena bane. Murmushi yayi yana hade wani kololon bakin ciki tare da fadin take care tunda ya kula ban son maganar da ya dauko min din nace dashi insha Allah. Na sauka daga motar ya ja suka wuce ni kuma na shige ciki duk da nayi kokarin wanan maganan amma sai naji wani bangaren zuciyana yana kokarin kishin hakan ga Nafisa. Da sauri na kawar da wanan zancen a bangare nace damuwa na may tunda ba hakkina yakai mata ba alhalin kuma gashi yanzun ma ya fadi dalilin shi na yin haka gare ta. Ni komai nene suje suyi tayi ai tare na gansu na kuma san gidan da na shigo dole ne sai na yaki zuciyana daga wasu abubu na kawar da kaina gare su . Muddin ina son kwanciyar hankali a tare dani da salama yawan sa rai ga zamantakewar kishiya da miji da saka ido ga abinda sukeyi shike kawo rashin kwancinyar a zukatan kishiyoyi. Kamar yadda ita take yawan saka ido akan duk wani motsi nawa shine silar hanata samun salama a zuciyar ta. Idan na biye ma wanan halin nata nace zan dau fansa a gare ta nice zan sha wahalan haka tunda ance wanda ya rigaka kwanci yana riga ka tashi . Da wanan shawaran na shiga ciki na kama normal life dina na school mun dauki lectures muna fito wa sallah muka nufi gidan wanan matar da anty hawau ta hadani da ita. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Akwai mata duniya don gaskiya nayi mamakin ganin wanan matar da anty hauwa ta turani gidan ta daukan darasin rayuwa a gurin ta. Bayan mun gaisa da matar take tambaya tare da maida hankalin ta a gare mu tana fadin daga cikin ku wacece mai daukan darasin nawa ? Maryam ne ta bata amsa da fadin dukkan ne anty don duk muna da bukatan hakan dariya matar tayi cikin hausanta da bai biye ba tace wacece matar auren maryam ta nuna mata ni da hannu. Ta kalle ni tare da fadin very nice ai dukkan ku kina da quality din da namiji zai so ku a take idan kin iya rike miji kwana nawa ne kin kama abinki ga hannu basai ki tsaya wanan hali na matan kasar nan ba bin bokaye da malamai bashine mafita ga mace ba. Sai dai wa yanda suka yarda da wanan akidar a wurin su yake mafita gare su amma idan mace zata zauna tayi amfani da hikimar ta da basira da Allah yaba mata sai taga ta kama mijin ta da hannun ta a saukake. Ba wani abu mu matan waje mukafiku dashi dan banbancin kadan ne a tsakanin mu daku ku matan nahiyar nan kunya ne ko girman kai yake yawan damun ku. Zaki ga mace na jin nauyi ko shakkan idon jamma,a ba zata iya sauke nauyin da Allah ya dora mataa kan mijinta ba. Unlike mu kinga ni nan ko a gaban iyayyena nake ban shakan sauke nauyi mijina a gaban su No bawai kinji nace haka ki tunanen ina nufin kiyi fitara a gaban mutane bane, Abinda nake nufi shi namiji yana son a riritashi ako wani lokaci ko agaban waye amma sai kiga mace sam bata damu da jawo mijin ta a gareta ba irin haka ne mata da yawa suke samun matsala a gidajen su. Sai kiga namiji yayi aure daga baya matar tazo tana mashi abinda ke kika yi sake dashi a baya can wanda hakan laifin ki ne. Ki cire kunya da nauyi kowa a idon ki ki tuna kuma kisa a ranki bautar Allah kike a hakan don babu waani wanda zaki daraja bayan iyayyen ki sai mijin ki. Aljannan ki fa akace yana ga tafin kafar mijin ki ashe ko bazaki bada karfin ki da lokacin ki wurin ganin kin gina aljannan ki da hannun ki ba. Zama muka gyara tare da ajiyan zuciya muna sauratlren wanan matar mai bada nashina kamar lectures taci gaba da fadin. Ke bazakiyi tunanen irin nasa nauyin da yake sauke wa kanshi na hakkin ba kiyi tunanen wani abu zaki masa kwatankwacin wanda shima yake masa ki farauta masa rai. Ashe ko duk wani abinda muka san zai sasu farin ciki ya zama wajibi muyi shi namiji shine zai ciyar dake ya tufatar dake ya biya maki dukkan bukatun ki nayau da kulun naki dana yan uwan ki. Ke har da rabo idan ya ratsa a tsakanin ku koda yake ke ina ganin amaryace yanzu ko muka amsa mata da eh. Tace to Allah ya baku zuria dayyaba muka amsa da amin tace kada kiji na zake ina maki wanan nasiha haka ke da kika zo in koyar dake dabarun mata. Na dauko maki tunatarwa ne daga farko ta yadda zaki iya fahintar abinda zan fada maki a gaba da fatan kun fahince ni maryam ne ta amsa da kwarai anty muna biye dake ai. Tace Alhamdullahi tunda kun fahinci inda na dosa taci gaba da fadin shi namiji da kike gani da zaran aure ya kullu a tsakanin ku daga ranan an bude maki wani sabon babin rayuwa ke nan. Don haka wani jiji dakai da ko musu da sauri fushi ya kare a gare ki daga wanan ranan dole ne ki zama mai biyayya a gareshi. Duk wani abinda muka san zai saka zuciyar su a farin ciki ya zamo dole mace ta juri yi ma maji shi muddin abin bai kaucewa shari,a ba. Maryam tace kwarai anty tace kin gane ke nan shin kun san abinda yasa mazan ku na wanan kasar suke son auren matan waje ko wata kabila ta daban da naku ? Wanan abin yana daga cikin abinda suke kwadayi wanda akasarin matan su sun yarda shi saboda kunya da dahun kai kan aure . Suna hangen kwaraiwan wasu da kwadayin halaiyarsu na iya tatalin mazajen su da kwantar da kai a gare su. Ladabi da biyayya ga miji tare da mutunta juna gami da sadaukar taimako tare da jajircewa a cikin zamantakewan aure. Kun ga wanan abinda na lissafa maku bakomai bane auren facewa wanan gishin kin rayuwan da nai maganan su yanzu idan kin rike wayan takar kin rike kan maciji ne da hanuwan ki don ana son mace tazamo mai wanan halin a rayuwan ta. Sai kiga ba mijin ba kadai da kowa nasa kin gama dasu a lokaci daya sai dai fa wani kari daya zuwa biyu dana manta ban fada maku ba sune. Karbi, karbi ga dangin miji da abokai yana kara haska mace a gidan mijin ta sosai haka kuma godiya ga alheri zuwa ga miji yana daukaka darajan mace. Sannan shi yawan bukata kullun ki ce saya min wancan babu wanan sai ta girgiza kai tare da fadin kin ga abu mai muni dake saurin durkushe mata yanzu. Duban lokocin da maryam tayi a wayan ta yasa tace damu barin barku haka idan kun kara shigowa ma karasa sauran bayanin kafin mu kai ga darasin mu. Amma kafin ki tafi yanzu barin baki wani abu don baji amaryan tana kamshi irin na rikakaun amare ba mikewa tayi tashiga daga ciki. Maryam ta kalle ni tare da fadin kam uban nan duk wanan kamshin da kike zabgawa kinji matar nan wai bai yi ba nace maryam aini yau naji abu wallahi. Fitowa tayi dauke da kwalayen a hannun ta tana kokarin sakawa a wani leda blue ta miko mun tace wanan idan kin karanta akwai sauran bayani a cikin sa kafin gobe ku shigo ko jibi. Godiya mukai mata muka miki tsaye don barin gidan Nepep muka shiga muka koma school don acan za a zo a dauke ni. Har naje gida maganganun ta suna min yawo a zuciyana da yake bai nan tun shigana na rufo part dina tunda nasan ba kara fita zanyi ba ranan. Ban dade ba barci ya dauke ni a can cikin barcin nawa nai mafalki da Nafisa wai ina duke ban san da zuwan ta bayana ba tayi kokarin turani cikin wani rami Allah ya taimake ni na rike wani farin abu mai tsawo kafana yana daga cikin ramin ban riga da na fada ba. Na dago na kalleta tare da fadin bazaki taba cin nasara akaina in Allah ya yarda sai ta kara yunkuri turani a ramin razana yasani ambata inna lillah da karfi. Zubar na mike daga barcin ina yanka wani iri zufa a goshina tsoro ne matuka ya kama ni gashi ni kadai ke a dakin. Wani irin tsoro nake ji yana rufe ni a lokacin addua na fara karantowa sai wajajen asuba barci ya dauke ni har nakai ga makara. Wanan mafalkin ya tsaya min a rai sosai haka har na gama shirina na fito ranan nayi mamakin yadda ban samay su a falo ba kamar kullun. Na isa school na samu an shiga sai dai malamin yana gab da shigowa a lokacin wuri na samu na zauna ina mai ci gaba da nazarin wanan mafalkin a raina. Har malamin ya fito yayi abinda zai muna muka gama lectures ranan jikina banda wani kuzari sosai . Haduwan mu da maryam yasa na dan sake kadai sai dai idan na tuna da mafalki nakan karatun Allahuma ajirni fi masibati wa,akalifli hairun min ha. Bayan mun sallamay sallah da yake ban karya ba a lokacin sai nake jin kamar zan fadi don yunwa maryam ce ta sawo min lemon kwalba da snack na dan sha rabin goran na aje sai dai ko ina bai kai ba na amaye shi duk. Kin san baki ci komai ba dole sai abu mai dan zafi ne zai zauna maki a ciki dole mikewa mukayi da jikina yadan sake muka nufi gidan anty Salbiya don karin ilimin da muke so na zaman duniya. Bamu dauki lokaci ba muka isa gidan anty Salbiyan saida akai muna iso saboda tsaron da gidan ke dashi duk da gidan bai kokai rabin gidan AA tsaruwa ba da fasali. Sai dai rashin tsari da yawan jamma,a da gidan namu ke dashi ya jawo baida wani tsari yanzu ga kowa. Bamu dade zaune ba ta fito fuska da fara,a da alaman daga barci ta tashi lokacin gaishe ta muka fara tana murmushi ta zauna tare da fadin kun shigo. Eh inji maryam tana kara gaida matar nima na gaida da ta tace jiya ai nayi mantuwa ban tabayi sunayen ku ba har kuka tafi. Maryam ta gabatar mata da sunan ta sannan ni na biyo baya tace duk sunayen ku sunane masu dadi ko a addinance ana alfahari da wanan sunan. Tace amarya zance ko khadija nayi murmushi tace da fatan aikin mu ya fara tun jiya dai cikin kunya nace gaskiya bai fara ba don maigidan bayanan yayi tafiya. Ok lailai ashe akwai taro kuwa don ya kamata ki haddace lokacin dawowan mijin ki gida kafin nan da rabin awa ya zamanto lalai kina a cikin shiri bawai yazo ya samay ki a ya mutse ba har ya fahinci halin ki ne hakan. Ya kamata ya samay ki a cikin kwalliya kina zaune falo kina dakon zuwa sa yana shigowa zaki mike a cikin naki irin sallon kina masa sannu da zuwa tare da karban jakkan hannun sa ko leda ko wani abu dai daya shigo dashi gidan a hannun sa kina mai sannu da zuwa da sauran maganganun jan hankali a gare ki. Nayi mantuwa ban fada maki ba ya kamata ace shi yana waje gurin aiki ke kina gida akalla zaki kirashi cikin ko wani a wa daya kiji lafiyan shi da sauran su. Har lokacin da zai dawo gidan wanan yana kara kawo shakuwa sosai tsakanin mata da miji don Allah ki kula khadija nace in sha Allahu anty. Ina fatan dai kina hakan kaina na noke tare da fadin anty ni ba wani shakuwa na soyayya mukayi da maigidan ba sanan kuma yanzu bamu fi wata uku da aure ba dashi. Maryam tace a cikin na hudu kuke fa yanzu khadija hararan ta nayi Anty Salbiya tace amma ko kin ban mamaki don duk macen da tai jami,a ai ya kamata tasan wanan koda kadan ne. Aure wata kusan hudu khadija amma baki maida komai serious ba haka a hakan har zaki saci zuciyar mijin naki ina kina da kishiya ko ? Maryam tace kwarai kuwa kuma buzuwa ce yar Niger ce ta asali don ko hausa bata ji sosai har yanzu Antyn tace ashe irin mu ce sai dai muna da banbanci sosai dasu yanayin mune kawai shigen iri daya dasu don su ma haka suke kamar larabawa ke din ma ai zubin ki baza a ce yar kasan nan bace idan an ganki don kin fi kama da yan kasar Ethopian sosai. Nakan fada mata amma sai ta dauka zolaya ne nake mata No ba wasa gaskiya nima farko jiya da kuka shigo ban dauka ke hausa bace sai dai da yake ko a cikin hausawan mafi akasarin su ai kyawawa ne kula ne dai da basuyi da kansu yadda ya dace suyi. Sai kiga mace haihuwa biyu ko uku sun jemay sun fita hayacin su kamar mai shekaru da yawa. Naga kamar lokaci tafiyan ku yayi ina fatan yau zaki fara daga cikin abinda na koyar dake koda kadan ne don Allah nace in Allah ya yarda anty. Sosai ta kara yi min yan nasihohi wanda hakan ba karamin tasiri yayi a zuciyana ba don a cikin hikima ta dinga fadakar dani abinda ya dace. Mukai mata sallama zamu tafi ta dan tako muna har zuwa waje tana fadin gobe insha Allahu zan fadakar dake akan kishiya ko yadda zaki zauna da ita acikin salama don kin san yanzu anbar kinshin fili sai na boye. Maryam ta amsa da wai banda wanan kishiyar na khadija mai kishin hauka anty bakiga ba fa yadda suke abinsu kirikiri ranan mun dawo daga unguwa kirikiri magani da wani abu muka samu yabe yabe a kofan shiga part din nan dai ta bata labarin abinda ya faru a gidan ranan. Na dora da fada masu abinda na tono a karkashin gadon AA duk a ranan ko maryam sai a lokacin take ji tana yaba zurfin ciki irin nawa. Ajiyan zuciya Anty Salbiya ta sauke tace to Allah ya kyauta anan kuma na dora da fada masu urin mafakin da nayi ranan akan Nafisa din wanda abin yake cina har yanzun a zuciyana. Tace gaskiya sai kin dage da addua tare da yawaita irin su sadaka kyautata da sauran don kin san irin wanan abin ya taimakawa mutum ta ida bai zata ba. A sanyaye na furta ina yi anty tace da hannun ki kike badaw ko sakawa kike ai maki dai nace cikin murmushi sakawa nake ai min tace shine matsalan mu ai. Baki san adduan mutum da bakin sa yafi saurin kamawa ba haka kuma abinda kika bayar da hannun ki yafi saurin karbuwa a wurin biyan bukata. Sauraren ta mukeyi a cikin fahintar abinda take fada muna din, maryan tace anty ai inda mutum zai samu irin wa yan nan mabukatan ne anan har ya basu shine ai. Kai ta girgiza tana fadin baku dai nema ba maryam amma idan kuka je irin su madala ko maraba nan ma a cikin gwagwalada akwaisu. Ba wai sai mu saki ba irin masu karamin karfi din nan duk zaku iya basu don ko suna bukata Allah yasan a inda yan amin suke. Mun rabu da ita cikin farin ciki da kauna muka bar gidan ta wurin anty muka biya nan mukai sallah la,asar mukaci abinci sai dana dan huta na dauko waya na nakira shi. Kamar kiran zai katse aka dauka da sallama na karba mai yace cikin wani murya a kasalan ce Deedar ya akayi ne ajiyan zuciya na sauke ta yadda har yajini nace dashi ba komai. Nadai kiraka ne in ji lafiyan ka yace realy nace may ye kuma na mamaki don na kira ka yanzun kuma ? Ai dole inyi mamaki yau ni Abdulsamad Deedar zata kira kodai kin yi kewan kayan ki ne tsakanin jiya da yau ? A hasale nace ban sani ba na kashe wayan yana ta kiran layin nawa inaji naki dauka maryam da muka fito take fadin . Wai wake ta kiranki ne haka kike rejecting din call haka nace kyale shi don Allah shi ai dama ba ai mashi abin kirki yafi son kowa ya zauna kamar yadda matan shi suke ko yaushe. Ba zaki zauna ba kuwa da sannu zaki gyara komai koda ace ko basu koya ba ke zakici gaba da dasa mai naki akidar a zuciyar shi. Tun hanya muka rabu yau ban koma school ba na kira driver na fada mai ba sai yazo ba na samu an rage min hanya na dawo gida. Ina shiga gidan massage din shi na shigo min yana fada min yana saman hanya yanzu an jima kadan zasu iso insha Allahu. Su nafisa na samu a falo na wuce ba tare dana gaida su ba suma kamar yadda basu min sannu da shigowa ba na wuce hanyar part dina kai tsaye na bude na shiga. Sai da na canza kaya na fada kitchen tare da tunanen abinda zan girka mai yaci idan ya dawo din ruwa na dora na dauko garin alkama na fara tankadewa. Na gama na gyara kayan miya fresh na wanke na ciro nama na yanka tare da dorawa akan wuta. Allah da ikon sa har na karasa aiki basu shigo ba part din har na gyara komai yadda ya dace wanka nayi na shirya sai naji kawai in fara aiwatar da huduban mutane mana yau. Iya gwargwado dai nasha nasihan zamatakewar rayuwa da fadakar wa ya kamata ni ma in fara amfani dashi hakana in kawar da duk wani nauyi da kunya a tare dani. Turaren da Anty Salbiya ta bani na shafa na shirya a cikin wasu atamfa mai launin jan watau red colour da dan fari fari a cikin sa. Skirts and blulawars ne dinkin shi sai dan kwalin dana daura na kawo shi gaba kadan na kara kallon kaina a mirrrow na fito tsab. Har zan fita daga falon na koma na dauko chewagun mint na bare na saka a baki na direct falon gidan na nufa inda su nafisa suke zaune da tawagan ta a can barin hago inda dakin ta yake. Wurin dayan set din na nufa tun fitowa na kowan su ya sako min ido caaa suna kallon ikon Allah don wanan shine karo na farko da na taba fitowa falon gidan na zauna tun shigowana gidan. Zama nayi na dauki kafa na daya na dora saman daya ina taunan chewing gun din a hankali yana bada dan sauti mai kara . Hankalina yana a wayan dake hannu na ina dakilar wayan ba tare da na kula kowa dake falon ba a lokacin su kuma basu daina kallona suna mamaki ba da tunanen abinda ya kawo nin falon a wanan lokacin. Yar wurin Nafisa Ihisan ne tayo wurina da gudun ta ta fada min a jiki na dan zabura ina shafa kanta muryan Nafisa naji cikin wani irin kara tana fadin . Ke, ke , ke kada ki fara ki taba min yarinyar ki kama mata kurwa na fada maki idan kina so ke ma sai ki dage ki haifi naki a gidan. Ban kula ta ba kuma ban sake yarinyar ba muna magana da yare taiwa Samiha magana tazo ta dauko mata yar ta a wurina. Samiha ta taso zukwai zukwai taja hannun yarinya ta figeta ta wuce da ita inda suke zaune uwar tace tauraruwa mai wutsiya ganin ki ba alheri ba. Kin kulla ta nayi don kada ta rushe min plain din kada ya shigo ya samay mu muna fada ko minti biyar ba,ayi ba sai naji dirin motocin shi sun iso gidan. Ba wanda ya kula daga cikin su da dawowan shi tun a cikin cotton na hango shi tafe ya sagale rigar shi ta sama a kafadan shi. Mikewa nayi tsam daga inda nake na tare shi bayan ya karasa shigowa daga ciki din a lokacin na mike na nufe shi. Aiko idanuwan su caa a kaina kamar su cinye ni danya a lokacin hugging nakai mashi tare da sunbatan shi ina mashi sannu da zuwa. Sai ya rugumoni sosai zuwa jikin shi tare da fadin Miss you deedar wanan kyau da kika sha haka fa nace is for you ya kara kai min kiss shima a tsakiyan kaina. Mutuwar eacin gadi tayi da kyat ta iya tataro courage din ta tace yau kuma wani karuwanci ne haka a fili ? Komai dai jarabar mutun dole ya bari har ranan girkin shi yayi jakka shi na zuwa aiki driver ya shigo dashi na karba daga hannun driver din. Na wuce gaba yana biye dani a bayan shi part din shi na nufa har lokacin banda Nafisan ba wanda ya iya wani kwakwaran motsi daga cikin su. Ganin na doshi hanyar part din ta mike tsaye tare da fadin malama kya bari sai girkin ki kiyi wanan sallon karuwancin kauyen ko ? Murmushi nayi ban tsaya ta kanta ba na haye sama abina na barsu a nan tace a hasale dashi. Samad amma kana kallon takalar yarinyar nan shishigin ta yayi yawa a gidan nan girkin ma yanzu kokari kwacewa take nufin yi a gare ni ko may ? Da mamaki ya kalle ta yace kamar ya zata ci girkin ki ina yau itace dani kuma time din karban ta yayi har ya shuda yana magana yana kallon agogon hannun shi. May kaku nufi da maganar ka ina jiya baka kwana gida ba don haka ni ya kamata in karbe ka a yau ai. Wai Nafisa ke wata irin mace ce da baki da lissafi a rayuwan ki ban fa son irin wanan rikicin kin ji na fada maki. Amma ai kasan haka muka saba yi a baya dakai idan ka dawo daga tafiyan yanzun ne zaka canza muna tsarin ko may ? Yace da kika ce ba yanzu ita taga tana iya bar maki nata waccen da kike magana wanan ko tasan right din ta. Hannayen ta ta taba tare da fadin yau ko zanga yadda za a dulmuye ni ina ji ina gani tsuki yaja ya nufi saman abinshi ya barta nan. A dakin ruwan wanka nake kokarin hada mashi a ban daki naji shigowan shi dakin ko da na fito yana tsaye a tsakar dakin yana kokarin sasauta nicktie din wuyan zai kwance. Na fito daga ban daki takowa nayi inda yake na rike mai hannu karban cire mai tie din nayi ina kokarin cirewa sai kallon mamaki yake min yana wani lumshe ido Ban san shigowan ta dakin ba sai ji nayi an bangaje ni ta baya da karfi sai da na fada saman jikin shi ya tallabe ni da hannun sa. Tare da fadin kina hauka ne wai Nafisa may ya shigo dake dakin nan wanan lokaci haka ko kishi haukane wai ? Mace baki son zaman lafiya ko yaushe sai dai ayi fitina shine gurin ki kin sani sarai ba lokacin ki bane yanzu don may zaki tayar wa mutane da hankali haka wai , ? Zan nuna maku haukan da kake yawan kira min ne azzalumai kawai kuna ganin zaku juyani ne a gidan nan ne komai yadda muka saba idan ka dawo haka za a ba wanda ya isa ya canza min tsari na. Hannuna na daga ina kokarin karasa cire mai tie din ta daga hannu zata kai min duka ne ko mari ya rike hannun ta da sauri tare da fadin. Dukan ta zakiyi komay nace barta kin ci albarkancin cikin nan dake jikin ki da yau kin gane baki da wayo da nanuna maki tawa kalar haukan kin gani. Don ni ban tsayawa fadan baki haka kanki zaki tsunta a waje eh lalai ba laifin ki bane wuri kika samu. Gashi yanzu kirkiri a gabana kuna son ku dulmuye min hakki na macuta mayaudara ba irin Nafisa ake cuta a zauna lafiya ba. Ciki kuma da kike maganar sa kokarina ne ya bani shi don ni ba juya bace mai ci takai masai kullun zufana ne kike gani don haka kada bakin bakin ki ya kara tofa zance akan cikin jikina. Jan hannun ta yayi zuwa waje yana fadin ki koma kasa idan na sauko sai muyi magana amma ba nan ba a cikin hakkin wata. Samad ni kake kora a dakin ka kan wanan kwailar karuwan yarinyar da ka dauko mai kama da matan titi. Nafisa yace cikin wani irin tsawa ba ita dake gaban shi ba har ni sai da na kadu daga inda nake ina kallon su ya daga hannun kamar zai make ta sai kuma ya sauke yaja hannun ta zuwa wajw tana turjewa. Sai zagi take zuba min na cin mutunci da tozarci na fallasa irin na tantiran kishiyoyi din nan suka fice daga dakin ajiyan zuciya na sauke ina binsu da kallo. Abinda ya fara zuwa min a rai shine ashe wanan akidar ke nan sukewa Fati dole ne Fati ta kasa zama a gidan don wanan irin dabancin na Nafisa kishi da buzuwa sai basira da hankali sai kuma an daure. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Wanan novel fitar dashi cin amana ne karanta shi ba tare da biya ba rike hakkin wani ne akan ki don Allah yan uwa musulmai mu kula da hakkin wani akan mu. Ki tuna wanan online novel ne kika saya ba booklet don haka ka,idar shi ki karanta ki barshi nan kiyi tunanen wanan maganan yar uwa dubara ya saura ga mai tsoron Allah. Dakin ya dawo rai bace ya shiga wanka bayan shigar shi wankan, sauka nayi zuwa kasa na kammala duk wani abinda zanyi na rufe part dina na nufo wurin shi a cikin wasu rigar barci masu daukan hankali sosai. A D/table na samay shi zaune ya fito daga wankan tunda na nufo gurin ya mayar da hankalin shi gare ni ga waya yana yi a hannun sa. Kulolin na bude na fara zuba mai tuwon da miyar kubewa sai kamshi kaya yaji da sanadarin miya ke tashi. Ke ba zaki ci bane ya na jan plate din zuwa gaban shi ya dago yana tambaya na ban jin cin komai yanzu don naci abinci around four dazun a koshe nake sosai. Na lura baki damu da abincin ba sai yan kayan zaki da sauran tarkace kamar sha zumami dan murmusawan dole nayi don abinda ya fadi din. Sai kuma naci gaba da tunanen da nakeyi a raina ina tausar zuciya akan abinda nake gani anayi akai na, ko yaushe a gidan. Na zauna a gaban shi yana cin abincin a hankali ido na kura mai zaka ce hankalina yana gurin shi ne a lokacin a yadda muke zaune. Kula yayi da zurfin tunanen da shiga wanda ba tunanen komai bane sai na rayuwan matar gidan da muke zaune tare, kullun a cikin fitina babu ranan sulhu ko shiryawa a gare mu. Muryan shi naji tare da dan kada hannayen shi daidai fuskana, na dago kai ina murmushi tare da fadin ina jira ka kanmalane in kwashe kayan a gurin . May kike tunane haka Deedar har ina magana baki jini ba ajiyan zuciya na sauke tare da mayar da hankalina a gurin shi. Abinda ya faru yanzun kika sa a ranki ko mai na dan rausaya kaina tare da fadin abin ne kawai yake ban mamaki don naga babu tsarin Allah a cikin harkan ta. Murmushi kawai yayi ya dauki tsokan nama dake cikin miyan ya kai a bakin shi ya fara taunawa ba tare da yayi magana ba. Sai da ya lashe abincin tare da turo min plate din a gabana yana fadin kin sani over feeding yau da yawa don girkin yayi dadi sosai. Haka nake so shiyasa na bata lokacina na girka mashi don nasan zaka so shi saboda na kula da kana son abincin gargaji ya sosai. Ashe kin fara fahintar halayena yanzu kwarai ina son irin girkin nan idan zan samu don dashi nayi wayau a gidan mu kin sani. Mikewa nayi ina hada kayan abincin tare da tambayan shi ya zancen da hajiya mama tace tace ka fada na kawo kayan zainab din idan da hali ina son inje ayi sha,anin dani. Mikewa yayi shima daga inda yake zaune yana fadin ba fa buki bane ko wani abu kayan lefe ne kawai za a kai masu. Nace ai yanzu kasan an maida abin kamar buki ne duk wani dan uwa na kusa yakan je a tari kayan dashi sai naga zai yi kyau ace wata daga cikin mu ta tafi wurin. Ita Fati dake can idan taje bai isa ba sai ku dake nan kunje sai dai idan akwai wani abinda zai kaiki dama ba wanan zancen ba. Ko daya wallahi ban sa ran zuwa yanzu ba ko don karatun dake gaba a wanan lokacin ganin dacewan zuwan mu dai guri. Dakin shi ya shige ya barni gurin ina gyarawa ba tare da yai min magana ba na gaba hada kayan a cikin basket na shiga na samay shi a dakin. Ko da na shigo dakin yana zaune yana latsan laptop din shi har na shigo na kara kawar da komai na dakin a inda ya kamata. Maimakon in hau gadon in kwants kamar yadda na saba yi a kullun sai yana zauna a gefen shi tare da dan kwanto jikina a saman nashi ina sauke ajiyan zuciya. Muryan shi naji yana fadin Deedar yau may ke faruwa dake ne haka naga wasu sauyi a gare ki. Ba wani sauyi da ka gani a gare ni dama can haka nake ko ka manta ne da halina kawai dai irin rayuwan da gidan naka ke ciki ne bai gamshe ni ba. Sosai magana ta taso bashi dariya amma sai ya daure yace dani cikin juyowa yana kallona tare tare da fadin look at me Deedar. Kallon nasa nayi kamar yadda ya bukata nayi yace gida na ba halin sa ke nan ba ki dai ce matar gidan da kika sama ce halin ta bai maki ba. Deedar kin san kowa da yadda Allah yayi sa da kuma irin fahintar shi ita rayuwan ta ne haka da zafin kishi irin na rashin fahinta rayuwa nata kawai ta sani bata damu da damuwar wani ba . Na karbe da fadin wuri dai ta samu nayin hakan don da kunnen ka kaji abinda ta fadi a baya kuna yi watau da kai da ita kun hade kai kuna tauye ma Fati hakkin ta yasa yanzu da ka canza take ganin muna yaudaran ta ko cutar ta. Murmushi naji yayi tare da fadin kada ki min mumunan fahinta anan mata suke da alhakin saita gida a tsakanin su idan daya ta bada daman da dayar zata taushe jaruntar ta sai alkibilan komai ya koma ga yar uwarta duk kokarin namiji akan yaga yayi adalci a tsakanin su. Tunda naji kalaman shi na fahinci abinda zancen shi ke nufi watau idan mace tayi sakaci da daman ta sai abokiyar zaman ta ta kwace komai daga miji har gidan a hannun ta yanzu ke nan dabara ya saura gare ni ke nan akan buzuwa. Bayan dan zurfafa danayi a cikin tunane na sauke ajiyan zuciya ina kokarin mikewa daga inda nake zaune don tuni tun da muka fara magana na raba jikina da nasa ko. Na juya naji ya riko hannuna ya rike ba yadsa zan iya tafiya naji yace ina son ki fahinci magana ta da kunnen basiri a yadda nai maki shi a dunkule da fatan zaki fahinci mai nake nufi. Na fahinta na fadi cikin daurewa don nakai iya wuya a lokacin yace ba ina nufin ki biye mata ku dinga hauka irin nata da sunan kishi bane. Ina son ki gane kamar yadda na auro ta a gidan nan da sunan so a gare ni haka kema na auro ki na kawo gidan nan da sunan so a gare ni. Sai dai kada ku mata ni namiji ne ina da wanan daman da zan kara kawo wata agaba ta zauna a cikin ku ku zama ku hudu ke nan a gare ni. Kallon da nai mashi yadan kara jawo ni a gare shi yace ni mijin mace hudu ne Allah ya bani wanan daman kuma ya hore min abinda zan iya karawa dashi ai kin san aure kuma sunna ce ta Annabin rahama. Don haka ne nake son ki fahinci zama da hali mai kyau ko akasin haka mafitane a ko wacen ku idan Nafisa tana da wani hali da bai gamshe ki ba a gidan nan. Kina da daman dake zaki amfani dashi wurin toshe wanan kafan ki dora hakin ki na gari ki gyara min wanan gurbin da taba da kafa a gare shi. Shiru nayi ina sauraren maganar shi wanda yake min kamar nasiha ko fadakarwa a gare ni kokarin janye hannaye na nayi daga nasa sai naji ya rike ni gam ya ki raba hannuna daga nasa. Yace Deedar ki sa a ranki wanan ne kaddaran ta farko da kika fara fuskanta da fatan zaki rugumi rayuwa a yadda yazo muna. Yanayin rayuwan zama na da nafisa kowa ya gani zai dauka ta fi karfi na ko wani abu makamancin haka ni na bar wa cikina wanan dalilin. Yanzu naga kamar magana ta tasa zuciyar ki ta fara kishina jin zan iya karo wata a bayan ki kuma nan gaba. Yanzu wanan zancen da zai sa ki lalabanj kina ririta ni duk wata mace dake gidan nan dama wace zata zo ki nuna masu cewa ke din ta daban ce daga cikin su. Fisge hannuna nayi daga gare shi na haye gadon na kwanta tare da juya baya a gare shi can naji ya gama abinda yake ya hawo gadon ya kwanta. Hannun shi yakai a jikina na lumshe idanuwa na muryan shi naji yana fadin Deedar badai maganar fahintar a tsakanin yasaki shiga wani yanayi ba. Na juyo a cikin wani courage dana samu ina fadin na rungumi kaddarana tun ranan da na shigo gidan a sunar matar sunna a gare ka . Zanso ace na kasance daga ciki diyan albarka masu biyayya ga iyayyen ga duk halin da suka riski kan su a ciki. Don haka ni na dade zama da shirin duk wani rintsin da zan fuskanta a gidan nan ko wace kallace matukar ban saba wa mahalici na ba da hakan. Wani kallo yake aika min ina maganan a take idanuwan suka canza launi ganin haka na so juyawa in koma yadda nake da farko naji ya riko ni. Kokawa irin ta ma aurata muka fara a lokacin nayi nasara haye ruwa cikin shi nan wasan tamu ya canza sallo a dakin mun dauki lokaci a tare muna farauta wa juna rai a inda ya sha mamakina a wanan dare. Ko da gari ya waye ranan mun makara daga tashi sallah a gurguje na karasa duk wani abunda zanyi na fito bayan mun karya muka bar gidan. Ban hadu da Nafisa ba a falo ashe bata gidan nan ne tayi asubacin batin gidan zuwa wurin madam kan matsalan da take fuskanta. Ban makara daga shiga lectures ba a ranan duk da lating da nake gani nayi a lokacin sai dai jikina nake jin yawan kasala yana damu na sosai ga wani barci da nake ji wurin kwantawa kawai nake bukatan in samu. NAFISA a falo madam cikin takaici take magana kan sauyin da take gani ga madam sai data gama fadin maganan da ke tafe da ita iya son ranta madam din ta karbe maganan da fadin. Nafisa kema kin san wanan yarinyar fa ba irin ta farkon bace don wanan kina ganin ta duk da tana da karancin shegaru idanuwan ta wallahi a bude suke. Banyi zaton ta shigo gareki a banza ba yanzun dai matsalar mu ai wanan cikin da kika samu ne gashi yazo maki da lalurar rashin yin motsi mai karfi da sai mu bazama mushige duniya can kasashen yarbawa da iyamurai kin san su aikin su tsafi ne kamar yanka ne. Nafisa ta kalli madam tace ke nifa ciki ba zai hanani yin komai ba wallahi idan zamuje a shirye nake ko yanzu kan wanan yar iskan. Wai fa a gaba a kan idona na samu wai tana balle samad anineyar rigan shi shiko yayi tsaye kamar wani soko dashi. Dariya madam tayi tana fadin ke makin san halin maza ai idan suka samu sabon sauyi sai fa kinga abinda ba daidai ba a idon ki. Ni yanzu shawaran da zan baki shine ki bari har ki haife sai mu san abin yi don yanzu koda munyi wani abin walahi barnan kudin ki kawai zakiyi. Keda, keda dama yanzu da zaki ta karban kudi da suna cikin jikin ki kina tara ma tafiyan mu kin ga kafin nan kinyi muna tanadi mai kyau da zamu ci kaniyar su da tushe. Jin maganan kudi ya shigo yasa Nafisa washe baki tare da fadin kin kawo magana madam don ni ban ko kawo wanan ba a raina ina dan banzan hauka kamar yadda yake kirana dashi. Madam tace kin fahince ni mutumiyar ai ba karamin shiri zamuyi wa shegiya ba sai ta raina kanta da ta shiga ragan da ba nata ba. Wallahi madam na tsanin wanan yarinyar ban taba dauka samad zai ga wata mace har ya ta so rikita shi ba haka. Madam ki duba min may na rasa a jikina wanda yasa samad yin aure madam tace ikon Allah kin fasan halin namiji fa nafisa. Balle shi da iyayye suka bada tasu gudunmawa ga auren shi baki ga sai da suka darje suka zabo mashi mai irin zubin ki ba ta yadda zai iya fudewa a kanta ya barki ba . Basu san wasa suke damu ba jin mu suke basu san sherin mu ya wuce haka ba ke zan iya cewa gara da yai maki ita yanzu ba sai daga baya ba lokacin girma ya kama ki baki da moriya sosai ba. Ai babu auren nakasa ga mace kamar sai lokacin da girma ya fara kama ka a auro maki kishiya da zata zo tana haihuwa kina kallon ta. Badon kin ma yar iska wanan dan bakan ba ai da yanzu tana nab da kunshi a gaban ta wai ciki. Da sauri nafisa tace dakun daure ni ranan don bansan inda zan saka raina ba shiyasa na haka ma yan iska shi ban sake bi ta kanshi ba. Shine daidai wallahi don gudun bacin rana kizo baki haka ba azo a samu akasi ya haye yar iska tazo ta dauki ciki asirin mu ya tonu . Ina ai ba zan ma yarda haka ya faru ba a tsakanin sai dai gani da hange badai wanan ba nasan don haka ne ai yake lalaba shegiya don kada ta tona mashi asiri mutuncin shi ya zube a gane shi mace ce. Kin gane ke nan amma ya kamata fa ki duba bakan nan don kin dade da haka shi ko yana a haken har yanzu kada azo a samu matsala kuma. Zan duba yau din nan dana je gida amma inda na aje shi ai banyi tsanmanin wani zai iya ganin ba ma ga kuma kwalban dan agadas shine ma banga wani tasirin shi ba koda yake ai yau suka fara kwana dakin tare. Dan iskan kamar yasan abinda nasa ranan sukaki kwana a dakin sai dakin ta suka je suka kwana shiyasa nake fada maki ai da shiri shegeya ta shigo maki. Sun dade suna magana daya a karshe dai ta yarda da shawaran madam din na sai ta haihu kafin su yi wani yunkuri a kaina da maigidan. KHADIJA. Tunda nayi sallah nakai kwance sanan carpet din masallacin ina jin dadin yanayin wurin na dan shiga na a hankali. Maryam ta idar da sallah ta juyo gare ni tana fadin yau yaya dai madam nace wallahi maryam wani irin barci nake ji sosai jikina duk kasala sa nakeji. Yau ko zamu samu leka anty salbiya ke nan nace zamu bari dai in dan kara hutawa gashi kuma yau ina son attending din last lectures dina wallahi. Tashi mukayi muja shiga gun lectures din yana fita muka nufi gidan salbiya din don jin dan karuwan da zamu samu a gurin ta. A gidan anty salbiya ma kwance nake ina sauraren bayanin da take min ka kwalliya da yadda zan dinga shiga wai ko wani lokaci ya kamata ace mace tana yabayin shigar da takeyi tundai idan oga yana gida tare da iyalin shi . Ta juyo gare ni tana fadin idan kin bi wanan hanyar zaki ci galaban kishiya sosai wallahi don ko wani kasa suna da kalar tufafin da suke jin dadin sakawa a jikin su. Ashe kin ga ku matan kasar nan ko wani shiga kukayi yana daukan jikin ku sosai don baku dogara yanzu da kayan aladan ku ba. Kin ga kuma su mazan yanzu abinda ke kara ingizasu kenan gun wasu matan sai ki dage wurin saka tufafi masu jan hankalin namiji nasan ko tace zata koye ki abin ba zai dore ba gare ta don ko bata saba ba da hakan idan ma ta saba ke zaki iya kirkiro naki sallon kiyi. Yanzu dai kinga ko anan ai mun samu wani babban mafita akanta ko mukace hakane anty sannan ta juya da fadin sai gyaran muhali. Yazanan to part din ki yana da wani kamshi da sai a gunki za a ji wanan kamshi naki ne ke kadai komai na gurin ki ya karba da wanan kamshin. Ina mai tabbatar maki duk lokacin da yaji wani kamshi makamancin haka zai tuno dake a ranshi haka nau,in abincin ki ya zaman to kina canza shi lokaci lokaci ba kulun abincin ragayen mata ba irin su indomie taliya da sauran su din nan. Ke koshi miji fa yana bukatan gyaran kansa daga gare ki kamar kula da tufafin sa da undies din maigida da sauran abin amfanin shi irin su takalma da sauran su bawai sai tufafin jikin shi ba kawai zaki kula akan su ba. Wani amai ne ya taso min na toshe baki na da sauri na nufi toilet din dake falon su banyi wani abin kirki ba na dawo idanuwan su a kaina har na zauna. Tace ikon Allah anyah amarya bakin halbu bane kuwa wanan irin amai kuma haka fa nace anty ina ganin rashin karyawa ne da bana yi sosai ya jawo min ulcer. Dariya sukayi anty salbiya tana fadin Allah yasa ulcer mai tushe ne ya samu to yanzu barin barku kije gida ki huta don kina bukatsn hutu a tare dake. Don tun shigowan ku na fahinci hakan ki daure dai ki adana wanan sirin idan son samu ne sai idan ya fito a gani a jikin ki. Don shi ciki kamar hasken rana idan ya haska babu abinda ke boye shi ko mijin ki ki bari sai ya gani da idon sa . Don wasu mazan yawan doki na saka su jawa mace matsala akan sauran al,umma basai kishiya kawai ke kishin haka ba. Idan baki yai yawa gun abu sai kiga abin na zuwa da matsala sosai don baka san bakin wani ba don baki dafi ne sosai wallahi. Nace ba komai yanzu anty hasashen kune kawai hakan amma dai zan kula din idan haka ya faru maryam kan bata samu bakin magana ba sai kallo na take yi. Mun bargidan ganin banjin dadi yasa maryam ta biyo ni gida yau tunda ba nice da girki ba mun huta ina zaune a falo ya kira layi na. Nakai hannu na da kyar na dauki wayan tambayana yake idan mun gama lectures din a zo a dauke ni na amsa mai da kyat da gani nan na dawo gida yau banjin dadin jikina ne. Yadda yaji murya na yace da sauri may ke damun ki nace ulcer ne yace kin gani ba dama nasan haka zai iya faruwa ai na fada maki ki dinga cin abinci bakya ci. Nace da kyat bafa rashin cin abinci bane ulcer ciwo ne kawai yace yanzun dai ke dayane kuma gashi aiki nakeyi nace muna tare da maryam ne ta rakoni gidan sai ta zauna dani. Ok maryam ta kyauta ki samu abinda kika ci idan zan dawo zanzo maki da maganin ulcer din kisha mu gani nace nagode . Yace Ok bye bye take care nace nagode I will ya kashe wayan maryam tana zaune ta kafa min ido sai da naje wayan tace dani. Karfa kisha magani khadija azo ana magani daban ciwo daban nace yau na fara wanan kuma maryam don Allah bari zancen nan inani ina ciki yanzu ai abin zai min yawa. Ok kina planing ke nan nace akan may zanyi planing maryam don cikin wai na masan ba zan yi shi a yanzu ba tace ok tana dan murmushi. Kafin ya dawo yai min kira yakai uku tare da tambayan har yanzun maryam din tana tare dake dai ko nace eh ai anan zata kwana. Warin tafarnuwa nake ji har cikin part dina da ake girki dashi a part din nafisa yake shigo min a part dina sai ya saka zuciyana wani irin tashi dole na mike ina cewa maryam don Allah mu shiga daga ciki. Sai dai ban fada mata may nake ji ba wanka nayi nayi sallah ina sallamay wa na haye gado na kwanta abina. Bai shigo ba sai nine na dare ya shigo dagani ko part din shi bai je ba a dakin ina kwance maryam zaune tana karatu ya shigo.. Gaisuwa sukayi da maryam din tare da tambayan ta jikina tace da sauki ulcern ai ya fada mata tun dazu barci tace tanaji yanzu. Wurin gadin ya nufo maryam ta mike ta fita daga dakin kafa na ya ja na falka firgigit ina kallon shi sai kuma na dan sake murmushi tare da fadin sannu da dawowa. Zama yayi yana fadin ya jikin naki naji sauki na bashi amsa yakai hannun shi saman wuyana yana dan tabawa tare da miko min maganin ulcer masu tsada a leda na karba ina fadin nagode. May kikaci yanzu ya tambaye ni nace tea nasha da cake wani kallo yai min yace may zakuci a samo maki yanzu nace sai dai maryam amma ni na koshi. No yace yana mikewa tare da fadin barin fita yanzu idan nayi wanka kada ku rufe ku jirani in dawo nace a dawo lafiya ya fita. Falon na tashi na dawo na samu maryam din bata nan ashe tana dayan dakin ta kwanta nan na samay ta kwanta na shigo na samay ta na zauna. Hiran anty salbiya muka dauko take fadin naji maganar mamaki yau ai watau dai ita mace da bauta aka santa a rayuwanta. Da zaran an daura ma aure baka da wani lokacin kan ka isashe a gidan ka saina bautan miji ke nan wallahi khadija ina fanin kokarin ki sosai. Ni dake tare dake kadai nasan wanan amma gaskiya kina kokari sosai don ba za a dauke a karamar jaruma ba kan don ko zama gidan nan ai sai mutum ya shirya. Amma ke gani zaune ba abinda ya damay ki murmushi nayi nace to maryam yaya zanyi abinda yafi karfin ka ai sai ido. Tace hakane mun kai kusan awa biyu da wani abu ya shigo dauke da ledoji a hannun shi ya miko min tare da fadin. Kici kisha magani don Allah maryam ki tabbatar da ta sha maganin nan kafin ta kwanta don nasan ta da tsoron shan magani . Tace zata sha ya dan lakato min hanci na tare da fadin raguwa kawai ji yadda kika fada yau kawai da dan ciwon nan . Nace yau dai ka sani amma ni na dade yana damu na ai yace to asibiti zan kaiki gobe idan Allah ya kai mu ko yanzun ma don dare yayi ne da munje. Ya fita yana muna sai da safe muka karba da Allah ya bamu alheri na mike nabi bayan shi don rufo kofa maryam ta nufi kitchen bai fita dakin ba sai da ya dan matseni a jikin shi na zille da dabar na samu ya fita na rufe kofan ina dariya. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Tunda ta shigo gidan ta dan zauna falo tare da tambayan su abubuwa na gidan kamar yadda take masu dan kwana bibiyu . Hankalin ta ne ya koma kan abinda take son yi tsam ta mike zuwa dakin ta ta barsu a gurin tana fadin zan shiga ciki in huta ban son damuwa yau. Sun san idan ta fadi haka tana son kebewa ne ita kadai shigan ta dakin ta daga gado ta jawo ruban da ta saka dan bakan da ta haka muna. Yana nan yadda ta ajeshi sai dai yayi wani abu kamar hunhuna ya shamuke ya bushe sosai ba yadda ta saba ganin shi ba. Ganin shi a hake yasa tasan daurin da tayi mai yana nan yana aiki a kan mu ke nan ta sauke wani shu,umin murmushi ita kadai a dakin. Ta mayar dashi dakyau bayan ta kakabe abin yadda ta saba aje shi ta aje tana fadi a zuciyar ta shegiya dangin makwadaita a haka zaki kare a gadin don nafiku maita wallahi ga abinda nake so. Ba zan zauna ina kallo kizo ki mun kutse a gida ba kiyi yarda kike so sai dai ki gaji ki bar min gida yar iska yarinya kawai. Gyara kwanciya tayi tana jan tsuki duk da abinda samad din yake mata akan wanan yarinyar da take ji kamar ta shake yar banza ta huta da bakin nacin yarinyar. Lalai ya zama dole yau su kasance tare da samad ba zata tsaya wani bin dokar likita ba can ita da ko haihuwa tayi da anyi suna take like da mijin ta yanzu za, a kawo mata wani sharudda a kafa mata. In banda wanan yar banzar yarinyar da tai mata shigen bazata a rayuwan samad har ake wani wai raba kwana shi kuma ya biye mata ina zata iya hakkuri dashi haka, . Yanzun ma tasan don yakan dayi wasanni da yarinyar ne amma ai ba dai a cikin wani gamsuwa ba tunda tasan ta gama daure shi ta ko ina. Don har yanzu idan sunyi fada yakan dawo ya lalashe ta su koma daidai ta sauke murmushi tana gyara kwanciyar ta tasan babu wata mace da zata shiga rayuwan shi ya gamsu da ita idan ba ita dai Nafisan ba. Itako indai tana jin dumus a hantu da account din ta ai komai zata iya yiwa samad din don a zauna lafiya bazata taba yarda wata ta kwace mata wanan dama nata ba har takai ga lasan zuman shi. Haka ta wuni a kwance duk wani shiri tayi shi a gurin don daren yau tana son ta kasance tare da samad din tane saboda tayi kewan shi sosai. Da dare bayan ya dawo ne yakai muna kaji da drinks da sauran tarkacen ciye ciye ciyen da ya sawo muna ya dawo falo ya dauki nata ya nufi dakin ta dashi. A kwance ya samay ta tana waya a cikin yaren su ya fahinci da mutanen su ne take waya a lokacin wanda idan ta fara wayan ba kasafai take aje wayan ba. Don haka ya a je mata ledojin yana shirin juyawa ya fita ta katse wayan tare da fadin ina kuma zaka again yace daki zan koma ga dan abin tabawa nan na shigo maki dasu ya sake juyawa kamar zai fita daga dakin. Amma kasan a nan yau zaka kwana dai ko wani kallo yai mata kafin yace kin manta cewa kin kashe wanan ranan da na kwana a dakin Deedar don wani dalili. May kake nufi da fadan haka amma kuma ni kasan dalilin kwanan ka anan yanzun ai akan matsalana ne ko ? Wani matsala ina kin samu lafiyan da zaki iya hawa sama yanzu tunda har kina iya hawa ki tafi yin masifa sai zuwa kwana gurina ne zai gagare ki kuma ? Ban gane inda maganar ka ya dosa ba fa kana nufin don na hau ranan shike nan ina da karfin hauwa ko yaushe. Yace wanan maganan haka yake a zuciya na don ba zan zauna in tauyewa diyar mutane hakkin ta ba ko yaushe a kan ki ba. Wani hakki take dashi a kanta idan ma kun kwana din wata tsiya take iya tsinana mata bayan bakar fitinar da ta shigo muna dashi gida tana kokarin mai dakai mace mara amfani ga mata. Wani kallon mamaki yai mata ya bude baki zai yi magana sai kuma ya fasa fadan abinda zai fadi din yadan girkiza kai ya juya tace dakai fa nake magana. Yace naji ki kuma naji abinda kika fada ai koma bata yi min komai amma ai dole in tsare mata hakkin ta ko. Tace tunda kai ka zama dan son ba mace dadi ta ko wani hanya ko to wanan dai ka sani bazaka taba jin dandanon ta ba har ta gaji ta fice don nan ba gidan zaman ta bane. Yace da kyau kinyi kokari kin san sheri da kikayi ke nan shiya sa kike fadar haka ko wani lokaci ashe , ? To koma may ye haka naganta nake son zama da ita ko da ko bazan taba more mata din ba balle ma ina morewa a wanin fannin. May kake nufi ta waro ido waje yace kwana da ita da nake yi ina jin kamshi don ta iya gyaran jikin ta a gurin miji ba sai zata fita take gyara ba. Ga kuma girki da ladabi da nake samu a gurin ta ga natsuwa da sanin ya kamata da wanan halin kike son in barta haka ba tare da kulawa ba. Ai kema ki mata adalci mana wanda ke baka wanan abin ai bai kamata ka wofunta shi ba Nafisa . Kema da zaki daure ku hada kai ku shirya da ita nasan da kin karu da wasu daga cikin ni,imomin ta ai. Samad ta kira sunan shi da karfi tana fadin agabana kake lissafo min wai abinda kake ji a kishiya ta . Wallahi maganan nan naka yanzu yasa nake jin kamar in shake yar iskar yar banzan yarinyar nan ta mutu kowa ma ya huta shegiya diyan makwaidaita kawai. Wani murmushi yayi yana fadin dama na fada maki kadan daga abinda nake samu a wurin ta ne don ki ji haushi kema ki gyara halin ki. Don duk waban abinda na lissafo Deedar dashi Nafisa baki da ko daya a gurina da sunan kinayi miji yaji dadi. Filo ta dauka ta jefa mai ya cabe tana dube duben wani abin ta jefa mai ya fice dakin yana dariya samun sa,anta da yayi har taji haushi. Muryan ta yaji tana fadin zanzo dakin in samay ka ai yanzu kafin da safe ita kuma yar banza in san abinyi akan shegiya. Kafin tazo ta hanashi hutawa ma ya sa ma kofar shi key ya rufe ya zauna yaci dan abinda ya riko ma kanshi ya kwanta tunda ba girki take mai ba sai sa,a . Kuma ko tayi ba iya ci yake yi ba don abincin baya gamsuwar shi a bakin shi yasa kullun gikin ta dole sai ya samu wa kansa dan abinda zai ci. Taje dakin nashi kamar yadda tace ta samu kuma arufe ta soma buga kofan da karfi tana kiran sunan shi ta yarda kowa zai iya jin ta. Da fushi ya zo ya bude mata dakin ta shiga tana huce ta fara fada dashi akan may zai rufe mata kofa tunda yasan zata shigo. Ko don yaki kwana a dakin ta kuma bai barta da takaicin hakan ba ya fada mata magana son ranshi ya fito yana zaton zata kyale shine wanan karuwan gidan nashi ta shigo inda yake. Dariya maganan yaso bashi yace yanzu dai ba kinzo ba may ye kuma nasai kin zagi diyar mutane a cikin maganan mu. Hararan shi tayi tana kaiwa kwance tace idan ba ka sallami wanan yar banzan ba kaima kasan ba zaka taba samun kwanciyar hankali a gurina ba ai. Don na tsani na bode ido naga wanan yarinyar a gidan nan kuma kasan ba haka mukai alkawari da kai ba tun farko. Yace da na aure ki munyi rijejeniyar ban kara aure ne ko may ko yanzu wata zan karo idan naga wace tai min ita ma na fada mata hakan ta kuma sani. Aure fa kace zaka kara again yace kwarai kuwa Nafisa ina son in gado mahaifina kuma inyi koyi da sunnan ma,aikina ne. Tofar da yawun ka akan wanan magana ko wanan kul ba dade kul ba jima sai ta fita gidan nan ina fada maka kana dauka wasa ne. Yace ki tabbatar da ranan tare zaku fita da ita don son ta nake na auro ta haka kema so da tausayin ki ne yasa na aure ki ai. Shiru tayi ta bashi baya tana tunane a ranta ya dauka ma tayi barci ne sai can yaji tace wai samad may kake nema ne a gurin wasu matan wanda ni banda shi a tare dani . Yace kina da komai na mata Nafisa amma kuma ai kin sa ra,ayin maza ne haka akwai wasu abubuwa da namiji kan hango gun mace yaji yana son kasancewa a gidan shi da ita. Banga abinda wanan da ka kwaso zata nuna min ba yace a naki ganin ke nan amma tana da quality din da nake son mace ta kasance dashi. Haushi maganan shi ke bata idan taji yana fadin magana a kaina don haka ta kyale shi ba tare da tai magana ba. Kwanciya ya gyara ya kwanta sai saukan hannun shi yaji a ga jikin shi murmushi yayi tare da fadin kin san kina cikin dokan likita dai. Tace likita shi Allah ne ko ubana ne da zai kafa min wani doka yau na fara cikin in kwana tare da kai ko mai. Da zamu tsaya bin wani dokan shi can muki farautawa ran mu abinda muke so ni tsausayin ka naji tunda nasan kana bukatan hakan kaga nazo da ba haka ba sai in kyale ka da wacan mara moriyan inga iya gudun ka. Sai dai ina gudun kaje wajen wata kayi abinda ka kasayi a gidane alhalin ina nan ina da abin a jikina nima. Har suka gama abinda zasuyi yana mamakin karfin halin Nafisa da bata iya boye zuciyar ta ko kadan don ta fito fili karara ta nuna ita ke da hannu kuma bako shakkan fadin hakan da takeyi. Yanzun ita a zaton ta ba abinda ke shiga tsakanin shi da Deedar yake zaune haka da ita don haukan ta da zafin kishi ya hana ta kwantar da hankalin ta ta fahinci komai akan haka. KHADIJA Mun tashi mun yin sallah akan lokaci sai dai bamu kara kwantawa ba don nemawa cikin mu abinda zamu ci. Yau tunda na tashi da kewan yan uwa na da iyayyena na tashi har na kasa boyewa nayi wa maryam magana a kan su. Tace ba kuna waya ba nace ba kullun ba don daddy ya kafa muna dokan kiran su ko yaushe yace idan suna son magana damu su zasu kira mu. Maryam tace kai daddy ho wallahi da daddy ya fito cikin mutanen da, da yayi tsanani sosai nace ai ko yanzun ma akwai tsanani don duk da aure muke bai hana daddy kafa muna doka ba kuma dole mu bi. Tace ina son irin su daddy masu tsayawa tsaye a kan iyalin su amma wanan mazan yanzu ai adaiyi dai ne wallahi. Kamar kin sani abinda nake tunane ke nan irin du AA ai ko tarbiyan yaran su basu da lokacin bayarwa kullun ana gurin aiki. Tace ashe kema kina wanan tunanen nace ba dole ba maryam tunda ruwa ya gaurayu da jini yanzu ke dai Allah ya shige muna gaba kawai. Tace AA fa saukin kan shi ne yakai har wanan matar ta samu wuri haka wallahi irin su basu damu da matsa ma iyali ba komai akayi mai kyawo ne hali ne na rayuwan turai kowa na da independent din kan shi. Nace halin banza ba maryam mutum ya yarda addinin shi da al,ada ya kama na wasu shi abin nasa ma har yai yawa wallahi. Da na dauka diyan Fati kawai yake kin kulawa sai yanzu nake fahintar ko yar nafisan ma ba wani damuwa yayi da ita ba iyakan shi da ita ya dan kama mata hannun yai mata wasa a tsatsaye ya wuce. Niko kin ga ba haka na saba dashi ba duk tsananin daddy da kike gani wallahi yana da lokacin iyalin shi maryam idan kin gan mu dashi zakice ba shi bane. Sai dai idan kayi ba daidai ba yanzu zaka sha hukuncin da bakai tsammani ba a gurin shi komai girman ka kuwa. Mun karya mun shirya har lokacin bai shigo dakin ba waya na dauka na buga mai ina sallama ya amsa min tare da fadin Deedar kun shirya ne ? Na amsa da eh tun dazun kai muke jira wallahi yace sorry dear wallahi yau na dan makara ne amma gani nan fitowa ku bani minti goma. Kallon wayan nayi na kashe maryam dake jin abinda ya fadi tace yau ko dai buzuwa ta murda kambun sarauta ne haka ? Tsuki nayi ina saka wayan a cikin jakka na tare da diban time din agogon daki naga takwas ya dan gwauta kadan. Ban dade da aje wayan ba ya sake kara na dauko daga cikin jakka ina dubawa sunan shi na gani again na dauka tare da fadiin hello dear. Ke ba dear ba abu kazar uban ki kada ki kara gigin kiiran wayaan shi idan kin san muna tare da ke ke har waya baki wanan matsayin da kike son kai kan ki ne a gidan nan ? Sai da nayi dan murmushi takaici nace wani matayi kike jira kuma in kai tunda abinda ya kawo ki gidan nan shi ya kawo ni nima. AA ne kuma dole ko kin ki ko kin do mu cudanye shi tare da ke ko kina so ko baki so yadda ya ke murzan ki haka yake murzana son rashi dole kuma anjima ki bar min shi ya murjeni son ranshi. Karya kike wallahi karuwan cin ki bai kai can ba in fada maki sai dai kije gurin wasu su murje ki amma badai samad ba don wanan kayan yafi karfin irin ki. Ke dashi sai gani sai hange nace a tunanen ki ke nan ruwa ya dade da gaurayewa da jini zatai magana naji ya wafce wayan a hanunta yana fadin. Wanan wani irin hauka ne wai wanan wani shashanci ne haka zaki dauki wayana ki kirata kina zaginta wai nafisa kishi haukane halan. Nace idan kun gama muna jiran ka please sai lokacin ya tuna bai kashe wayan ba ya kashe. Kallon maryam nayi nace wanan mahaukaciyace wallahi bata da wayau ko kadan ana kira mata hauka yana binta. Kara zagewa ki nuna mata ke ma fa matar gidan nan ne don Allah cire wani tsoro da kawaici ki din ga nuna mata ke ma kina da power a gidan nan. Haba abin yai yawa wallahi har da kiran mijin mutun sai an saka mashi dokan haka kuma wanan abin yai yawa wallahi. Maryam fitinane banso wallahi kuma shi din ya rokeni akan in dinga kyale ta idan tana yi kinga idan ina biye mata sai mu koma daidai da ita. Tace wani ain ake kyalewa maryam wani kan idan an maka shi yafi gaban kyalewa wallahi tunda ba garejewa yake yana rama maki ba. Daukan wa kanki mata ki a fito a gwabza tasan kema mace ne kamar ta amma wanan abin nata yayi yawa wallahi. Maryam nima bashi ba ke damuna sai yawan fadin da take min wai ni dashi sai gani sai hange din shine yake daure min kai da ita wallahi. Yau idan munje wurin anty Salbiya zan fada mata wanan kalamin ta sama muna mafita akan shi don fadin dz takeyi yayi yawa. A kin san a tunanen ai tariga da ta shiga tsakanin ki dashi ba zai iya aiwatar da komai na kwanciyar aure dake ba abin da take nufi kenan ba wani abu ba. Dariya nayi nace badai wanan mugun mijin nata ba da bai san daga kafa ga mace ba da kulun sai ya lalabe ni ya kwashi rabon shi. Kyale ta surprise zamu bata sai tasha mamaki a gidan nan tasan an dade da tsere mata tun 1900 ita ta makara take haukanta da bugun daji. Yana gama shiri a gurguje yasan ba abin karyawa zai samu kusan tare suka fito daga dakin sai dai ta riga shi saukowa ne ta zauna falo tana dakon shi. Yana fitowa ya tunkari kofan part dina tace tana mikewa tsaye samad ina zaka kuma yace gun Deedar mana mu gaisa kuma in fada mata nagama su fito mu tafi. Daga haka ya sa kai ya shiga ya samay mu muna zaune muna dakon shigowan shi dakin sai gashi gaida shi muka fara na nuna mai kamar komai bai faru ba damu. Shiko sai kallon fuskana yake ko zaiga na daure mai fuska akan abinda tayi min din nace zamu makara sosai yau wallahi don an kusa shiga lectures yanzun haka. Muje yace dani tare da fadin maryam kuyi hakkuri don Allah wallahi yau makara nayi yana gaba muna biye dashi muka fito daga part din. Har lokacin tana tsaye cikin jin fitina shiga na ta fara kallo tana ana mazuru ana shahu da sunan karatu mai zuwa daukan darasine aa hakan mu da muka ga turawa basu bamu tsoro ba. Juyowa nayi ina mata gwalo kan aiko ta fara sababi da zagi tana goranta min wai a haka zan kare yadda na shigo haka zan fita cikin labani kullun a mota. Tundaa muka fara tafiya bai wanda yai magana a motar sai can naji yace ki shirya jibine tafiyan mu da safe . Naa juyo nace Allah ya kaimu lafiya ya sake fadin akwai yan sayayyan da nake son ai su hajiya yau ko gobe zan turo maki da list ki duba ki gani wanda baiyi ba sai ki gyara naji nace dashi. Amma yau ba zan dawo da wuri ba don zan tafi gyara kaina tunda muna da tafiya a gabana idan nace sai gobe zan iya makara gashi kace zan maka sayayya kuma. Mun isa maryam ta bude motar ta fita na bude zann fita baji yasa lock din motar na juyo na dube shi da sauri. Dan langabar da kan shi yayi yana fadin kiyi hakkuri Deedar nasan ba, a kyauta maki ba wallahi bada sanina ta dauki wayana ba na shiga wanka a lokacin. Ai na sani nace dashi ba komai wallahi zata zo ta daina wata rana da yardan Allah kaidai kai muna addua kan hakan don Allah ji nayi ya rugumoni da sauri nace na makara fa yallabai kadubi lokaci ka gani. Ina fadi ina aika mai da hararan wasa nace bari matar ka ta biyo ka ta ganka haka yace da haukan ta yayi yawa ai idan ta biyo ni nan. Zan sauka yace miss you nace miss you too na sauka na rufo mai motar tare da jan guntun tsuki ina fadin munafuncvin maza kawai wani miss dina zakayi can adai tafi a hakan kawai. Yau ma mun dade cikin makarantar don exam ne ke gabato muna baifi sati uku ba mu fara hakane yasa muke dan jimawa yanzu sai yamma lis zamu dawo gida. A gurguje na biya gidan anty Salbiya ina sheda mata kwana biyu ba zata jini ba daga nan na wuce wurin gyaran kai haka yasani kai dare ban dawo gidan ba gashi kuma nice zan karbi girki a ranan. A salon din shiya biya suka dauko ni muka juyo gida dasu tun a mota yake faman matse min hannu na a cikin nasa yana yaba kyau da nayi da gyaran da akai min din. Mun shiga gida kowa ya nufi part din shi dan rage kayan jikin mu sallah nayi na fito na shiga kitchen don kada mukwana da yunwa. Cus,cus na dafa muna sai cabage dana yanka da albasa mai yawa acikin don yaba da ma,ana mai dadi. Soyayyan nama nayi amfani dashi sama sama a ciki ina gaf da kamalawa ne ya shigo kitchen din ya samay ni a ciki. Saukan hannuwan shi naji a saman weast dina sai na dan zabura kadan tare da juyowa in kalleshi fuskan mu ne ya hade a wuri daya yake fadin may kikeyi yanzu anan ? Nace abinci na hada muna kada ka kwana da yunwa ya juyo ni gare shi yana fadin wa yace dake zan kwana da yunwa bayan gaki. Murmushi na sauke tare da girgiza kaina ina fadin kadai baka jin kunya wallahi kana wanan maganan haka a gabana. Yace au ke kin saura da kunya na ashe har yanzu shiyasa kike son ko yaushe mu kasance a cikin duhu idan kina lalabana ko ? Ikon Allah nine kuma nake lalabanka ma ashe bakai ba hannu na dana mika in gani idan dahuwana ya sulala yasa shi sake ni a lokacin. Sai da na kashe gas din na gyara wurin har lokacin yana tsaye yana kallon yadda nake aikin yana tsaye ya jikina jikin shi daga kofan shigowa kitchen din. Juyowa nayi nima ina kallon yadda ya tsaya din yana saye cikin three quarter fari da rigan armless na shan iska murmushi na sauke a fuska na tare da fadin dan gidan hajiya mama ko yunwa ne haka ya fara damun ka ? Kai ya girgiza min yace gyara zancen kice dan gidan mommy don hajiyan mu kan na bar maku ke dasu zainab da Binta. Nace realy yace of course don kun fini fada a gurin ta nace halin kane bata so yasa kuke yawan fada tunda ka zama yaro mai lefi kullun. Murmushi yayi yana karasowa inda nake na fara ja baya tare da rike kunnuwa har bayana ya tsaya a jikin sink din kitchen din. Yace fada min laifin da kika san ina mata in ji yanzu don kunfi kusa ni dai ban san ina mata laifi ba nace kayi tunane mana da kan ka. Hannu yakai kamar zai danko ni na zille daga kasa na fice falo ina mashi dariya falon ya fito yana murmushi tare da girgiza kan shi. Yace zan kama ki ai sai kin fada min mara kunyar karya kawai ya juya ya fice dariya nayi na girgiza kaina kitchen na koma na hado mai abinci nasa a basket . Falo na fito nazo na shiga daki wanka nayi na fito na zauna na gyara jikina tare da shafe kusurwan jikina ko ina da turarukan da ke saman mirrow dina. Na dauko rigar barcina na saka tare da zanin da zanyi sallah asubah dashi da hijjab na daura zanin hijjab din kuma na sa a wani jakka tare da sauran tarkace na na bukata. Basket din na dauka na kashe wutan part din na rufo kofan gurin na nufi sashen nashi yan gidan suna falo har kullun basu gajiya da aikin saka min ido idan zan tafi gurin shi. Yauma hakan ne ya kasance dasu kamshi da shiga na ya dauke masu hankali Ihisan ce ta nufo ni tana hausanta da ya dan surku da yaren uwarta. Dayake akwai kaya a hannu na ban samu taba taba nadai kira sunan ta tare da dan mata wasa na wuce ashe yarinyar ta biyo ni a baya. Ina jin suna hada baki gurin kwala mata kira ina bude part din uban ta fada ciki da gudu Samiha ce ta biyo bayan mu. Zaune muka samay shi a dinning di ya tasa laptop din shi a gaba yana aiki a cikin sa jin hayaniyar mu ne yasa ya dago kai yana kallon mu tare da fadin wai may ye haka ne ? Fuska a daure ya juya ga Samiha din yana fadin may kike nema a nan cikin dan tsarguwa take fadin dama ihisan ne tabiyo wanan nazo daukan ta. Wani kallo yai mata ta juya da sauri tabar part din ni dai ina tsaye ina jera kayan abincin saman table ihisan din ke fadin Abincine zata ci. Tare da iban taso suci yaki kulawa nina jawo ta na fara bata a baki tana ci muna hira dasu jefi jefi taci abincin sosai har uban ya tsaya yana kallon ta. Shigowan Nafisa ke nan gidan aka fada mata yarta na sama wurina sai gata a sukwane ta fado dakin tana huci. Ke ban yata nan idan kin yi zuciya ki haifi naki yanzun nan an gaya maki haka ake samun diyan a nakashe ko asha a ruwa. Daga yau nayi maki kashedin taba min diyana sai ranki ya baci a gidan nan kin jawo ta nan don ki lashe mata kurwa kamar yadda kika lashe ma ubanta nashi kurwan. To kurwan mu kur a kanki mai bakar aniya kawai kina son burge miji ai ba ga diyana zaki burge ba sai ki zage ki haifi naki ki burge shi dasu. Hankaka maida dan wani naki kin zama bata irin macen sai ci akai masai kullun kinga nan ta nuna cikin jikin ta tace mai kika gani. To dake dashi a gidan nan sai irin haka watau hange an shigo aci gado a baza diya a gidan to gaba ba a nan ba yar iska mai kutsen tsiya mai hana farin ciki a gida. Ina zaune na harde hannaye na saman kirji na sai kallon ta nakeyi ina murmushi mai dauke da takaici sai da ta gama nace zakiko sha kallo a gidan nan. Idan ban sha kallo ba zan sha dariya ai ki matsa idan kin ce naci ne zakiga tsiya a gidan nan yadda kika shigo haka zaki fita daga ke sai ke wallahi. Murmushi nayi na mike ina hada kayan abincin ta bimu da harara ta matso zata dauki yar ta data dafe uban nata ya dago da idanuwan shi da sukai ja yace kina taba ta ina marin ki wurin nan sai kin raina kan ki. Ki bace min da gani daga wurin nan kafin in makeki yanzu yarki ce ko tawa idan kuma kika ce tak akan yar nan sai na shayar dake mamaki ke da ita sai idan ta girma ta nemay ki. Samad akan yata dana haifa a cikina kake fada min haka idan kana son ta rike ya ai kun san yadda ake samu dan kuyi mana kusamu kuma. Anga ya yar tubul, tubul son kowa kin wanda ya rasa ake son lashe min kurwanta watau kowa ma ya rasa ke nan ko wallahi ba zan jure daukan wanan hukuncin ba a kan ya ta a gidan. Tana kokarin jan yar ya mike da sauri nace haba dear kabar mata yarta mana Allah yaba kowa nasa ba shike nan ba akan may za, a tsaya ana fada akan ya abinda Allah baison hakan. Ta juyo gareni tana fadin may kike nufi da haka kanaji ko kaine sheda idan wani abu ya samu yata kotu ne zai rabani da wanan ta nuna ni. Ta fice da diyar tana kuka wani iri naji a raina amma a fili na wayance ina fadin kai Allah dai ya kyauta naci gaba da hada kayan. Muna kwanciya yace yarinya bagaki ba yanzu may kika fadi dazun a dakin ki maimaita yanzu mana da bakin ki. Dariya nayi nace ai maganar ya wuce ko don munyi shi tun acan ai yace to be frack Deedar na rasa may yasa hajiyan mu take min wasu abubuwa na daban wallahi. Nace ka fasan halin iyayyen mu da alkunyar dan fari ba wani matsala bane kawai kawaici ne take maka a hakan amma ni ban dauke shi wani abin damuwa ba. Bazaki gane bane Deedar idan ba muna tare da Yusuf ba bazan taba ganin fara,ar hajiya a tare dani ba tun ina jin wani abu har yakai yanzun na saba da haka. Shine dalili dayasa kikaga ina shuga da Yusuf idan zan tafi nace kai ya kamata ace ka bata hakkin ka na uwa a gare ta. Har gobe fa kai yaro ne a gurin ta wani shawara da ita ya dace ka zauna kayi shi amma kana nuna kamar kana gudun ta yanzu da shawaranta. Ya kamata ace kaja yan uwan haihunka a jiki ta wanan hanyar na tabbatar da idan ka gwada zakaji dadin ta sosai amma ba dadi ace naka nada shi a gida amma baiwa yan uwan sa abinda ya dace. Sun bukaci wani abu ne a gurina ban masu ba a, a gaskiya yaya AA kasan fa irin tarbiyan gidan ku bazasu taba rokon abu ba kaima ka sani. Iska naji ya furzar daga bakin ya sauke ajiyan zuciya yace na yarda da maganan ki don Bintace ta taba rokona in saya mata laptop tun farkon shigar su school. Ban san abinda ya matar dani daga saya mata sai yanzun nake tuna wanan abin nace ka gani kuma nasan hajiyar ce zata kwaba mata kada ta sake ma magana tunda ta fada ma da farko. Idon shi ya lumshe na tsawon wani lokaci shiru dakin yayi na wasun sa,oi kafin yace wai ke ina kika san wanan abubuwane haka ? Baristet khadija Adamu ce a kusa dakai yace natuna dama ance nine farko da za a fara lauyewa idan an zama barister nace dane ai. Yace au yanzu kin fasa ke nan nace kila don ban tabbatar ba ya kara sauke ajiyan zuciya yace think before tommorow may ya dace in wa Fauziya da Fa,iza . Wai ka bani aiki mai wahala saboda ba sabawa nayi dasu ba kamar binta da zainab don ko gidajen su ban sani ba. Amma ina ganin zaiyi kyau inda hali kakaisu saudiya ko ka gyara masu dakunan su da dai sauran su yace insha Allahu da halin yin duka ma don yan uwana da iyalina nake neman kudina da zufa na. Nace amma may yasa bakai wanan tunanen ba tun farko sai yanzu yace nima ban san dalili ba Deedar yanzu dai ne da muke wanan magana abin yazo min a rai na. Allah ya kyauta nace mai yace amin yana kamoni jikin shi dasafe da muka tashi bayan mun idar da sallah ne na duka na gaida shi kamar kulun yace kibani accout din ki zan tura maki kudi ai sayayya azumi ko nan ko idan munje kaduna. Don ban sa zan koma ba kafin azumi Allah ya saka da alheri idan mun dawo sai ki saya ma mutanen Niger nasu driver yakai masu can. Shiru nayi nama kasa magana a lokacin sai can nace angode ubangiji ya kara ma arziki albarka yace amin mikewa nayi na fice daga dakin zuwa part dina. Yinin ranan busy nake sai yamma na dawo a gajiye ga jikina banjin dadin shi amma haka na daure naiyi ta zirga zirgan tafiyan da zamu gobe. Washegari na shirya tsab shi kawai nake jira sai da ya leka office din su ya dawo muka dauki hanyar kaduna wanda kafin mu tafi din sai da suka kwasa da nafisa a gidan. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Kamar kullun yau ma shigan dare mukayi garin inda kai tsaye gidan shi muka nufa da kyat naga mun kawo kaduna din don wani irin amai dake taso min a motar yayi magana na nuna mai kaina ke ciwo kawai. Motar na tsayawa na fitaa da sauri na rigashi shiga gidan don jirin da nake ji a lokacin banyi tsammanin anty Fati tasan da zuwan mu ba don yadda muka samay ta ba a cikin shiri ba. Ganin mu yasa ta fara dan kamay kamay tana fadin ashe kuna hanya tafe ne yau nace eh ina zama saman kujera. Dafe da hannu na akaina karshe ma kwantawa nayi don jirin ya sake ni shigowwaan shi gidan idon shi ya sauka a kaina. Dashi da Yusuf suka shigo wanda ya wataa biyu bai abuja a lokacin yana waje wurin wani business da AA din ya tura shi yai masu. Lafiya may ke faruwa yake tambayana cikin kura ma inda nake ido har suka kara so gare ni Fati tana mashi sannu da zuwa ya amsa mata sama sama. Har ya iso inda nake kwance ya dan duka yana taba jikina tare da fadin may ke damun ki ne kuma ? Yusuf ya tambaya dama banda lafiya ne da muka fito gida yace lafiya take sai dai ina ganin tun a motar ne bata jin dadi zuwa yanzu. Yaran ne suka fito daga dakunan su ganin mu yasa su jin dadi sukazo wurin uwar su suka tsaya suna kallona suma. Har lokacin ban iya daga kaina ba ina a yadda nake kwance ko muje asibiti ne Yusuf ya fada sai lokacin da naji ya ambaci asibiti na dago kaina da idanuna da suka kada sukai ja nace jiri nake gani kawai amma lafiya ta kalau. Ok zai sake wani lokaci haka yakewa mutum ai idan ya kwana biyu baiyi tafiya ba ya hada min da fadin sannu na gyada mai kai. Daga inda Fati take zaune ta jefo min sannu na amsa mata tare da karfin halin fadin Affan kuna lafiya ina mika masu hannu su zo gareni. Affan kawai yazo shi karamin yaki zuwa inda nake din na rike hannun Affan din ina gaida shi sai yayi saurin fadin sannu anty ya jiki. Murmushi nayi nace da sauki Affan kunyi hutu ne yaron ya gyada min kai tare da fadin eh munyi hutu last week. Zama AA din yayi saman kujera ina jin ta kara gaida shi ya amsa gaisuwan nata ya kara maida haankalin shi a inda nake kwancen yace. Ko ruwa baki samu kisha ba don gidan ba,a iya ba boko ruwa ba ki daure ki shiga ciki kidan watsa ruwa ko jikin naki zai sake maki. Namike batare da bata lokaci ba na nufi hanyar hawa saman ida dakunan kwanan gidan suke tare da ciro key a cikin hand bag dina na bude dakina na shiga. Dakin yana nan kamar yadda yake sai kura da yayi saboda rashin mutum a cikin sa na kwana biyu da ba a zauna ba na bi dakin da kallo na rasa ta ina zan fara da dakin. Zanin dake saman gadon a shimfide ya yaye na jefa ga abin zuba wanki dake gefe daya aje a dakin na nufi ban dakin akwai ruwa kamar ko yaushe duk da yanayina sai dana wanke bandakin don in akwai abinda na tsana shine rashin gyara bandaki. Na fito na dauki tsitsiyar dakin na share jakkana ba bude na fito da sabon zanin gado a ciki na shimfida na feshe dakin da room fresh ya dauki kamshi a lokaciya daya. Ban daki na shiga a can na tube kayan jikina wanka nayi tare da dauro alwala na fito na tada sallah ina gamawa na haye gado na kwanta duk da yunwar da nake ji a lokacin. Barci ne ke son dauka na naji an shigo dakin tun daga kofa ya fara magana yana fadin har kin kwanta ne ko ? Kin ci wani abune da kika kwanta haka na da yunwa ? Ko baki jin yunwa ne yanzu da kika kwanta hakana ? Ya karaso bakin gadon tare da zama yana dan taba min jiki nace ai ba zazzabi nake yi ba gajiya ce dai kawai ya kama ni kamar yadda yayana Yusuf yace. Har wani tafiya zakima gajiya haka kamar wace taje Egypt da kafan ta akawai dai wani abinda ke damun ki may be ulcer din kine ke son tashi maki kuma. It may be don yanzu danayi some a hours banci abinci a kan lokaci ba haka yake min naji yace kai wanan ulcer da tonon asiri yake bai tashi kamaki ba sai yanzu da kike gida. Ya sake kai hannun shi saman wuya na cikin dan shagaba nace dashi haba ya AA don Allah ka bari barci nake son yi fa yace ba zakiyi barci ba sai kin samu a binda kika sa a cikin ki tukun na. Bari Yusuf ya dawo yanzun nan ya fita ya samo muna abinda mukaci nace laifin ka ne ai dabaka bugawa Anty Fati waya kana tafe ba yau da ta maka tanadin abinda zamuci. Tsuki naji ya buga tare da dagawa daga rankwafen da yake a kaina yace wai ma ko kin sha ruwa da muka iso nace banjin kishin ruwa ai dana sha ko. Fita yayi daga dakin sai gashi ya dawo dauke da goran ruwa da cup a hannun shi ya zauna a bakin gadon tare da fadin oya tashi kisha ruwa ko da kadan ne. Cikin yanayin jin jiki nace har yanzu fa jiri nake dan ji ban son in daga sosai wallahi yai kamar ya tallaboni na mike da sauri tare da fadin kana son mushiga hakkin da ba namu ba ke nan. May ye kuma na cin wani hakki anan din na karbi goran ruwan ba tare da nayi mashi magana ba na tsiya na shanye na mika mai cup din. Ina kawai kwance kallo ya bini dashi har na kwanta ya ja tsuki tare da fadin kai dana san wanan tafiyan haka zai zama maki ai da banzo dake ba wallahi. Zanyi magana wayan shi yai kara ya duba tare da mikewa tsaye ya bar dakin bai dade ba sai gashi ya dawo dauke da leda a hannun shi. Take away ne na karba tare da godiya ya tsureni da ido yana fadin tashi mana kici sai ki kwanta dole na tashi na sauko a kan gadon bandaki na shiga na kurkure bakina na wanko hannu na fito na samay shi a zaune. Sai da yaga na zauna kasa ina bude ledan ya tashi ya fita daga cikin dakin tare da fadin kici sosai fa don Allah sai da safe nace yace ba yanzu ba ai. Kilama anan zan kwana tare da ke da sauri nace rufa min asiri don Allah mu rabu lafiya da anty Fati yadda nazo yace ita bata san ciwo bane halan ? Yana fita na mike nayi ma kofar key na dawo na zauna ban iya cin abincin ba don dandanon shi bai min ba na ture gefe drinks din na dan sha namike na kurkure baki na kashe wutan dakin na kwanta bayan nasha magani na . WASHEGARI Wasai na tashi banji komai ba bayan nayi sallah na koma na kwanta har inji motsin mutanen gidan in fito mu gaisa dasu. Anan kuma barci ya kara dauka na gurin bani na tashi ba sai goma da wani abu mamakin barcin da nayi haka naji na mike na shiga wanka na fito har na shafa mai ina shiryawa naji ana kwankwasa min kofa. Na tuna tun jiya kofan yana rufe na bude Laraba mai aikin gidan nagani tsaye a kofan tana dauke da kayan abinci a hannun ta kula guda biyu. Murmushi na sakar mata tare da kai hannu in karbi kulan tace haba hajiya aiki na ke nan ai gidan nan ta shiga dashi ciki ta aje tare da fadin yaya karfin jikin jiya kun iso ance baki da lafiya. Nace nace naji sauki mama na gode ta juya zata fice daga dakin nace mama don Allah fita da wanan kayan abawa mai ci shi a waje. Ta duka tana daukan kayan ta dan bude tace a, a hajiya ai ba sai ankai waje ba ma ni nan ina da bukatan shi yaushe rabon da inci nama haka a gidan nan sai idan Alhajin gidan nan yana gari koshi baifi inci tsoka biyu ba don matar gidan kan raba idan na gama. Murmushi nayi nace ayyah dauka to kije dashi amma sai kin dumama shi don yayi sanyi tace bama zan tsaya dumamawa ba wani ya ganni dashi. Ta fice ta barni da mamaki a raina tare da tambayan kaina amsan da ba mai bani shi a lokacin na gama shiri na bude kulan abincin data aje min doya nagani busashe sai dan kwai a ciki da baida yawa. Dayan kulan kuma jeloup din taliya ne ne kai na girgiza don ban iya cin ko daya daga cikin su dama akwai kayan tea ne sai insha tea din in tashi. Bakin gado na koma na zauna na tasa kayan a gaba ina tunane kala kala a raina naji an turo kofan dakin AA ne ya shigo dakin. Da alama ba daga barci ya tashi ba ya nufo inda nake zaune kafin ya karaso nace ina kwana bai amsa ba sai da ya karaso inda nake. Kin tashi lafiya yace yana taba fuskana tare da fadin ya jikin naki da sauki nace ina dago kaina gare shi. Hajiyan mu tana gaida ke da jikin da sauri na dago ina fadin ka fada mata ne kai ko yace eh nace tare muka zo amma tunda muka iso baki jin dadin jikin ki ne kina kwance. Nakan naji sauki nace dashi yanzun ma nake son shiga can in gaida su daga nan in wuce gidan ya Amina itama in gaishe ta. Har kinji saukin yawo haka ne nace naji ai dama ba ciwo nakeyi ba gajiya ce kawai ta kamani dama. Idan kin shirya sai ki magana a kaiki yace kin ma karya kuwa yana kallon kaya abincin kai na girgiza mai tare da fadin banjin cin wanan da akayi sai idan naje gurin mama zanci. Tsuki yaja tare da nufar kulan yana budewa sai ya daga ya kara jan tsuki bai iya magana ba ya fice daga daki bin shi nayi da kallo har yafita na sauke ajiyan zuciya na mike na dan kara gyara jikina na dauki hand bag dina na fita. Ina sauka faln na samu ya fito daga dakin Anty Fati rai a bace na fito nace dashi ya dago ya kalle ni idanuwan shi sun canza launi a lokacin. Ya amsa min da kyat tare da fadin muje in sauke ki ban gaisa da anty ba nace mai bai yi magana ba sai kama hanyar fita waje da yayi. Ni kuma na wuce dakin anty Fati din da sallama na shiga dakin tana zaune saman dogon kujeran dake dakin nata tana gani na ta kakaro murmushi a fuskanta da kyat. Cikin dan rusunnawa na gaida ita da kwana ta amsa min da lafiya nace zan shiga gidan su hajiya in gaida su tace min a dawo lafiya karamin dan nata yana zaune yana cin irin doyan da aka kai min din. Nace daddy ba magana ko san mun doya inci ya dauki kwanan ya nufi uwar shi tare da jingina jikin shi da nata sai na dawo nace mata. A waje na samay shi zaune cikin mota yana jirana na bude na shiga ya ja motar muka tafi duk da bawani nisa bane a hankali yake jan motar. Mun kai na bude motar zan fita naji yace dani kayan da kika zo dashi suna nan a cikin mota sai kin dawo ki zauna ki kasafa. Nice mai kasafa kayan kuma ya gyada min kai da alama har lokacin yana a cikin fushin da yake yi don shirun da naji yayi min har muka zo gidan banda wanan maganan bai kara wani ba. Fita nayi daga motar na shiga ciki ba tare da na tsaya wani abu da Anty amarya na fara cin karo a gidan tace a, a khadija ashe tare kuke da babangida . Nakai kasa ina gaida ita daga nan bayan mun gama gaisawa na nufi dakin hajiya umma na gaida ita a na dan kai minti goma na fito zuwa dakin mommy . A gurin mommy na dade don na samu ya buga mata waya ta hada min abin karyawa don ban karya ba na fito don haka na samu kafin in shigo wurin ta tana hada min breakfast. Ban fita gurin ta ba saida ta tsare ni na karya muna hira da ita wanda hiran bai shafi komai na rayuwan zamana gidan AA ba ko wani nasa sai hiran Abuja dana karatuna. Nagama nace barin gaida hajiya mama tace ai tasan kina nan kina karyawa tun a kofa nake jin hayanin su zainab da Binta. Da sallama na shiga duk suna zaune a falon da ihu Binta ta taso ta rungumay tana fadin tun dazu naso zuwa dakin mommy wai zamu hanaki karyawa da kyau. Kasa nakai na fara gaida sarakuwan nawa tana amsa min cikin dadin rai cike da kulawa a gare ni bayan gama gaisuwan ne zan juya wurin zainab hajiya mama tace min. Khadija kina sakaci da cin abinci kina haka kada wani ciwo ya samay ki fa mace mai lalura karami irin naki ba,a son tana wasa da cin abinci. Duk ido suka zubo min ni kaina ban fahinci mai hajiya ke nufi ba a lokacin tace wanan abin abin farin ciki ne aure a bazata haka gashi kuma an samu karuwa. Na dago kai na kalli hajiya mama da sauri sai kuma na dukar da kaina kasa cikin kunya. Binta da ke manne danu tace min ko kuma zaki ma hajiyan mu mussun haka ne kin fa san hajiya ko cikin kwana daya ne tana ganewa a jikin mutum. Dakuwa hajiya tai mata ta rufe baki tana dariya sai hajiyan ta kawar da zancen da fadin nace ya fada maki zancen kawo kayan zainab da za,ayi gobe. Nace eh mama ya fada min shine ma nace dashi ina son zuwa ta karbe da fadin sai ya hanaki ko ya kirani kuma yana fada min wai zaki zo amma ya hana. Dana san kina cikin wanan halin haka ai da ban sakaki wahala ba wallahi tunda lefe ne kawai za a kawo ba wani buki za a yi ba. Mama nu fa lafiya nake shine ya fada maku banda lafiya don gajiyan motan da na iso jiya dashi kawai ya dauka wani ciwo ne. Ikon Allah irin wanan lalurar ai ciwo ne babba khadija Allah dai ya rabaku lafiya ya bamu mai albarka ai kinyi kokarin zuwa haka wallahi. Kunya da nauyi ne ya kamani sosai a gurin kamar kasa ya bude in shiga naji alokacin ta lura da hakan tace gashi kin zo khadija. Idan yan uwan ki sun karaso sai ku tatauna abinda za, a tari bakin dashi gobe koda yake gida ne duka amma hakan ai ba zai hana ai masu wani abu ba. Tunda yanzu abin ya zama kamar al,adan aure , wasu ma saboda wanan zasu matsa idan za a kai kaya aje dasu . Nace mama akwai kayan da muka zo dashi wanda yace na azumi ne za,a raba suna cikin mota har yanzun ba,a sauke ba. Ya fada min Allah dai yai maku albarka ya kara yawan arziki ta hanyar alheri nace amin mama tace yace kece kika san kan kayan idan kin huta sai a ba kowa nasa kamar yadda kuka tsara nace mama dadai akawo nan din sai a raba zaifi. Tace da sauri a,a ku barshi can idan kin samu lokaci ku raba a can a aiko ma kowa da nasa idan kun kawo nan ganin laifin juna za, a dinga yi . Shiru nayi ina nazarin maganan ta sai dai a fili cewa nayi to mama ta katse min tunena da cewa Allah dai yayi albarka ya rabaki da cikin nan lafiya kin yi kokari khadija kwai mafalkina yana shirin zama gaskiya a kan ku. Tun yanzu na fara hango alherin wanan auren a tsakanin ku yau ga babangida a dakina tun safe har wani lokaci muna hiran matsalan shi dani. Kin san bai iya boyo ba shi da yasan ina mamaki ganin ya dade a zaune tare damu sai cewa yayi wai ke kika saka shi kin san halin mijin naku haka yake abu kamar dan fari ashe shi. Muka sa dariya da Binta zainab ta dago tana kare dan uwan nata dacewa hai hajiyan mu kina fada mata kuma don ta raina shi. Binta ta cabe da fadin ai khadija ba ta da raini ga mai rena shi dai can yar haure hankaka maida dan wani naka sai lokacin hajiya take tambaya cikin katse muna dariya. Tace tasan da cikin jikin ki kaina dukar kasa tare da fadin ban sani ba nima mama na dan kwanta jikin Binta ina fadin nii fa banda komai wallahi. Binta tace hajiya kinji mai take fada wai bata da komai wallahi kiban dakine ko inji hajiya mama duk muka sa dariya. Shigowan su anty Fauziya ya katse muna hiran wanda dama na matsu abar zancen sai dai cikin zuciyana tunane fal ke damuna kan maganan cikin da mama ta ambata min. Gaisaw mukayi dasu suna min yaya hanya Anty Faiza tace ina buzuwar gidan ku yar sheri nace tana lafiya sun shiga aibanta tane hajiya ta katse su da fadin ku bar wanan dabi,an tunda zaune take da dan uwan ku. Kuma ta fatan shiryuwa idan zata shiryu banji kowan ku ya tabayi yar ta ba wanda jinin ku ne ita ai laifin uwarta bazai shafi yarta ba ko. Tunda yar jinin ku ne ita don haka ta samu ragowan wanan yar da abinda ke cikin ta yanzu tunda dan uwanku ya dauko yaya za a yi sai hakkuri kowa da halinsa ake zama dashi. Dazun ya tashi nan ya kawo min karan Fati sun zo bata basu abinci ba yau da safe kuma tasa laraba masu abincin banza. Kunga ke nan kowa da nasa halin ake zama dashi araina nace saura ni aji nawa problem din gaba tunda yanzu anji nasu su. Dangin miji akwai matsala sai naji hajiyan tace wanda kuma anan ita fati ta fishi gaskiya don dana kirata ina mata fada cewa tayi bai fada mata zuwan su ba. Kinga ta fishi gaskiya laifin ta daya da bata tashi cikin daren ta sama masu abinda zasu ci ba ta bari aka je waje sayowa. Hajiyan mu kin san halinta fa da shegen mako yanzun haka bata saya ba ma sai dai a turo mata da kudi ta haye sama ta zauna tabar yara da yunwa inji Faiziya. Fa,iza tace ita kan tana da matsala wallahi bata ci bata bari na tare da ita yaci kuma ba a gani a jikin ta shine matsalanta. Hajiya mama tace Allah dai ya kyauta haka abubuwa sukan zowa mutum wani lokaci ta baibai binta tai caraf tace saura musan matsalan khadija kuma. Hajiya tace diyata bata da matsala insha Allahu sai dai wanda ba,a rasaba yanzun dai kuyi abinda ya kawo ku muji yaya za, a yi. Hajiya yaya kika tsara abin ne inji Faiza tana tambayan mahaifiyar tasu wani abu zan tsara kuma yanzu gaku ga khadija sai dai inda gyara in gyara maku idan kun da bukatan hakan. Sunyi ta tsara abinda zasuyi ni dai ina sauraren su tunda ban san kai ba sai in sun tambaye ni ince yayi daida. Karshe nayi masu sallama akan zan leka gidan ya Amina na barsu a dakin zainab da binta suka taka min muka tafi. Ya Amina ta riga da tasan da zuwa na garin a gidan suka barni bayan mun dan zauna dasu suna fita ya Amina ta kalle ni tace khadija ciki ne dake ? Kai ya Amina haka ma mama fa tace min yanzu ina ciki don Allah anan banda abin ku tace cikin murmushi gashi ko har ya fito ana gani. Ganin may kuma ina shafa tunbina da hannu tace wai ke da gaske baki da komai ko may don Allah ki fada min gaskiya duk alamomin ki sun nuna ciki a jikin ki wallahi. Gabana ya fadi ina kara kallon kaina nace haka fa kowa ke fada min ya Amina tun a abuja tace rabon ki da mesturation wata nawa yanzu ? Nace nima har na manta wallahi kin san tun ina gida yakan min haka wani lokaci ai shiyasa ni ban damu ba. Tace kajiki da wani shirmay yanzun a gida kike ko a gidan mijin ki da zaki fadi haka tsaya inzo tace tana mikewa tsaye ta shiga dakin ta. Sai gata ta fito da wani takarda fari mai dan tsawo a hannun ta ta kokarin yaga ledan tace na sawo shine da nake ganin kamar cikine dani. Sai kuma kafin in amfani dashi sai ga jini yazo min na aje ashe da rabon ke za aiwa gwaji dashi tashi kiyi fitsri mugani ki dan debo cikin wani abu mu gani. Nace fitsarin nawa kuma ya Amina tace eh mana tunda ke har yanzu yarinya ce baki san komai ba don wauta irin naki . Kina kwana da namiji ki tsaya gardaman abu gashi kirikiri ana ganin shigar ciki a jikin ki kina gardama kuma. Shiga nayi ban dakin nayi na kawo mata kamar yadda ta bukata ta saka tsinken ciki sai gashi ya nuna alaman wata uku ke na yanzu. Nashiga uku na furta tare da kara tambayan ya Amina din nace ya Amina wai ciki ya nuna ina dauke dashi don Allah ? Tace bagashi kin gani ba da idin ki kina tambaya kuma tana fadi tana dariya kai na girgiza mata ina fadin wallahi ya Amina da matsala. Ni ina zankai wani ciki can yanzu ina tsaka da wanan karatun na ga rikicin wanan gidan nashi ba mai karewa bane kullun. Kai amma khadija ke har yanzun dai yarinyace wallahi shiyasa nake matukar tausaya maki a gidan nan wallahi iyakar ki baki amma idan kinyi wani abu sai mutum yaji kamar ya mangareki don haushi. Yanzun saboda karatu zakiki gina rayuwan ki ko saboda matsalan gidan mijin ki sai ke ki, ki haihuwa yadda kowa ya haihu dashi a gidan. Idan kina barin wanan wautar ki bari tun wuri kada ki kuskura ki bari mijin ku yaji wanan shashancin naki don duk yadda yake son ki zaku samu matsala dashi. Ya Amina ni bama zan yarda ya sani ba sai dai idan wani ya fada mashi ko ya gani da idon shi ni kunya ma ai ba zai barni na yi maganan dashi ba gaskiya. Shawara tayi ta bani barci nayi sosai har yayi ta kirana a waya ban sani ba sai dana tashi yin sallah ne nags kiran shi a wayana har uku. Na kira shi fada ya fara dani wai ina na shiga haka waya na ruri ban dauka ba tun dazu nace barci nake kuma wayan na cikin jakata ba, a ji. Yace ok yanzu kina ina nace gidan ya Amina na nake yace ok ganiman zuwa daukan ki ki dawo gida hakana tunda baki jin dadin jikin ki. Naji sauki fa nan kuma ai gidane gare ni ya kashe wayan dole na fara shirin komawa gidan ba a dauki lokaci ba sai gashi har ciki ya shigo ranan suka gaisa yai mata alheri muka tafi. Ina shiga motar ya kalle ni baya ya zauna yake fadin kinga yar uwar ki kin manta da mutane ko nace kai da ke ganin naka kullun fa. Gidan ya kaini bai bari na shiga gidan su ba in masu sallama gidan shi muka nufa a falo na samu su Anty na dan zauna nagaida su na haura sama dakina . Kayan jikina na rage na dauko wani dongon riga baki nasaka irin mai matse jiki din nan watau hook gaban mirrow naje na kalli kaina ina mamaki kai ni daya a dakin. Kallon cikina nayi naga yana nan a lefe nace abin da mamaki wallahi ya za, ace wai cikine dani ina shafan cikin nawa. Wani abu naji cikin ciki na da jikina gaba daya ya amsa min abin na motsi bol bol daidai inda na dora hannu na akai. Tsoro naji nayi saurin cire hannu na saman cikin ina mamaki da abinda naji yayi din na kara dora hannuna ya dan kara yin hakan again. Nafisa buzuwa ce ta fado min a rai ashe duk gorin da take min Allah ya riga da yayi nasa ikon akai na ko ita ke nata kalar shirmay. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Yau da wuri na tashi na fada kitchen sai da na gyara komai na dora girki lafiyayyen abin karyawa na dora da dan abinda na gani a kicltchen din ina aiki zuciyata fam da tunanen yadda na samu kitchen din nasu. Na rasa ta inda laifin yake shin daga bangaren AA ne ko na anty Fati sai dai zuciyana tafi bashi laifi don shi nake zargi da rashin basu kulawan da ya dace dasu. Tausayin uwar da yayan tane ya kamani a raina na duba yadda acan yake aje muna komai amma nan ba makamancin irin sa kafin wani abin yakai rabi ya kara labto muna irin sa don amfani. Sai nazo na samu anan ba haka abin yake masu ba a store kan gaskiya ba laifi don akwai komai na kayan masarufi sai dai a kitchen ne irin su nama mai wadattace da saura kayan amfanin gida ga mace duk sai a hankali. Muryan Laraba ne ya katse min tunane tana fadin hajiya ashe har kin fito ina jiran fitowar uwar dakina ne ta fada min abinda zan yi shiyasa ban fito ba. Nace basu fito ba nima karanbanin nayi na shigo aikin don kada a makara hajiya hakan ba karan bani bane tace min don hakan na da kyau Allah yasa a dore da hakan . Murmushi nayi nace mama laraba don wanan aikin ai ba komai bane don mun riga da mun horu da aiki tun a gida. Nace yanzu ko za, a samu masu kayan miya don naman kai nake son a sayo muna ta amshe da may zai hana hajiya yanzun sai in je nan bakin kasuwa zan samay su sun fito. Daki na koma na dauko kudi na bata tare da lissafa mata abinda zata sayo muna kudin ta kalla tare da fadin hajiya kudin sun yi yawa ai. Nace ki je dashi ki sawo na yadda ya dace don gobe ma da jibi sauran canji kyayi amfani dashi tace kai madallah barin yi sauri in dawo. Ta juya zata fita nace kuma kada muyi rashin hankali da ki dan saurara matar gidan ta fito muji ra,ayin ta. Kai hajiya dai ai tasan da irin hakan dole ne idan miji yana gari dole a gyara mai balle irin mijin ku mai yawan jama,a nan barin yi sauri in tafi. Nace to shike nan sai kin dawo naci gaba da aikin gabana cus, cus nayi na da ganye don shi nake ganin zai dan ciwo da safe ga kowa sai ferfesun sauran kayan cikin ragon da na gani a fridge din. Daga baya na dora ruwa tea wanda na saka kayan kamshi a cikin sa sallaman mama laraba ne da har ta dawo daga aiken da nai mata din. Nace mama abin ba wuya har kin dawo tace aikin abin hawa ne ai kuma a nan kasuwan cikin unguwa na tsaya don in sauri. Nace na gode mama ga abin karyawa nan na hada sai ki dibi mai isar ki ki zuba wa kanki kafin in kwashe ma saura tace ai ayi haka dadai kin zuba min yadda aka saba zai fi. Tana miko min canjin da ta dawo dashi nace kai mama banace ki bar canjin ba yanzu dai nuna min kulan da kuke zubawa direbobin abinci idan sun zo dana maigidan. Ta nuna min wani karamin kula nace kai haba mama su uku ne fa wanan ko mutum daya ba zai isa ba ai na jawo wani babban kula na zuba masu a ciki karamin shi na zuba masi ferfesun kayan cikin. Nace mama sai akai masu ko tace to yar albarka ta dauka ta fita na gyara kulan da na zuba masu AA da Yusuf tare da na Anty Fati da yaran ta sai kuma laraba a karshe na cika mata kulan data nuna min na direbobi da farko. Sai kayan tea din da na gani na ce idan tazo sai ta dauka mu a dauko wani ai amfani dashi cikin wanda za a rabawa mutane da muka zo dashi. Ta dawo nace ga ruwan zafi nan akai masu sai kice su dauki gwangwani madara da millo a mota da suga na amfanin su ne tace to hajiya tana washe baki. Ta dauka suka hade da Anty Fati take tambayan ta ina kuma zaki da wanan tace aike na akayi hajiya amaryan ku tana kitchen din. Bin laraba tayi da harara ta nufi kitchen din ganin ledan cus cus a dustbin din kicin din cike ya hanata min sallama sai cewa tayi wanan ai barna ne duk wanan ledan cus,cus din may akayi dashi haka ne ? Fuska dauke da murmushi na juyo gare ta ina fadin anty kin tashi ina kwana ta amsa min sai kuma ta kara maimaita maganan ta gare ni wanan cus cus haka da aka dafa fa? Nace anty amfani nayi dashi wurin hada breakfast tace amma wanan duk ina za a kaishi haka kamar abin ya zama barna nace yi hakkuri anty gani nayi kamar zai isa . Ta nufi kitchen din tana bude kulan abincin na fara mata bayanin komai ok kawai tace fuska a daure ta juya wurin ledan sakon da laraba ta sayo min tana fadin wanan kuma fa. Nace wanda zan muna amfani dashi ne da rana tace shiya bada kudin ko ya sayo nayi kasa da murya nace nice na aiki laraba ta sayo su yanzu shi bai fito ba ai. Tace Ok tana ja da baya sai gashi kitchen din da kansa yace na duba daki bakya ciki ashe kina nan ina kwana nace mai ya nufo ni ba tare da ya amsa min ba. Ya dan kai hannun shi a saman wuya na yace jikin yayi sauki ko nace tun jiya ai na watsake sosai wanan aikin da kikayi haka ai yanuna alama. Yanzu kuma may kike yi nace abincin rana zamu dora don kasan bamu da time yau sosai laraba ta shigo ganin da gwangwanayen kayan tea danace ta dauko a mota tana ganin su sai zata juya nace. Yawwa mama sai ki aje a dinning barin fito da wanan kayan nace da ita anty fati tace da ki bari tazo ta kwashe ai yana fita ya juyo yace mata sai aikin bada commad baki iya motsa jikin ki ke ko kadan. Nace ai ni kamata inyi tunda ina nan ita kuma ta huta ko ya wuce bai ce komai ba waje ya nufa nasan gun direbobin shi ya nufa su gaisa. Mun gama jera komai muka dora girki abincin ranan da za a ci suna falon ya turo Affan ya kirani nazo. Zaune suke sin fara karyawa na gaida Yusuf da kwana yace a, a kanwata wanan irin girkin haka tun da safe gaskiya naga wuyan mutumina yana dada kauri yanzu. Murmushi nayi nace aikin su anty na ne da buzuwa idan kaga haka tana gefe zaune da yaranta suna cin abincin su hankali kwance tace wata fati aikin kune dai amare masu lokaci. Murmushi nayi nace ni inani ina wanan aikin haka na samu abiku da a cikin yanayin sa AA ne yace ke zauna ki karya nace nasha tea a kitchen yanzu na gama karyawa. Wani kallo yai min nayi saurin fadin Allah ko baka yarda bane anty fati tace may nagaya ma Yusuf yanzu ka gani shine ma mai sata ta karya ai. Kamshi a duke baiyi magana ba sai nine nace ai anty ya rigaki ne don ke ya kamata ki min maganan karin. Tace to angon ki ya rigani ai don shi yasan zafin ki fiye da kowa anan gane manufar maganan ta yasa nayi dariya tare da wasance maganar nace ni abincin daddy zanci ina nufar inda yaron yake zaune yana ta aika cibi a cikin shi. Yana ganin na nufo shi ya jaye plate din shi yana fadin banyi banyi dariya aka kwaishe dashi Yusuf yace in banda abinka daddy ai ita ta girka ma zakai mata rowa kuma ko baka son ta karama wani ne. Sai ya miko min plate din nace na koshi ci abincin ka baba na fada ina juyawa zan bar wurin yace kunyi magana time din da za a shigo da kayan Yusuf nasan sani don zamu zaria ne yau ? Nace eh to naji kamar suna fadin Four na yamma ko yace ok lokacin mun dawo ke nan don naga yayan naki a zumude yake yau. Nace kada kaga laifin yayana kai kariga da ka tara naka a gida ko Yusuf yace kyaleshi kanwata ni biyu ma zan yi kusan lokaci daya. Nace kai haba dai yayana tun kawata bata gama cin amarcin ta ba zakai mata kishiya yace wanan an fada maki da gaske yake yi ne bafa jarumin gaske bane shi. Yusuf Yace I mean it ku bari ku gani kuwa zan baku mamaki ai ita zainab ta sani don na fada mata komai tasan da maganan . Jikina ne yayi sanyi da jin maganar shi ban iya furta komai ba na nufi kitchen din zuciya ta yana tunane itama zainab ke nan irin rayuwa na zata fada zama da kishiya. Sai da na dora komai na haura sama inyi wanka na fito ina zaune ina shafa mai ya shigo dakin ya fito daga gidan iyayyen shi. Inda nake zaune a gaban mirrow ya nufo yana fadin daga wurin su hajiya nake tafe yanzu nayi mata maganan mai aikin ki tace zata diba ta gani idan za a samu kafin mu tafi. Nace tare da su Affan nake son zuwa suyi min hutu a can tunda zan samu hutu in two weeks coming sai su dan debe min kewan zaman gida. Yace kunyi magana da hajiya ne nace banyi na dai fadawa maman su wancen zuwan da mukayi yace ok bari zan mata magana muji sai dai kin san ni zuwan su zai takura min. Nace wani takura kuma duk mutanen dake gidan ka basu takura maka sai wa yan nan yaran kananane zasu takura ma. Baiyi magana ba sai hannun shi dayakai saman wuyana ya shafa na dan noke yace zan bar maki driver guda da zakuyi zirgazirga dashi don aike. To nace tare da furta angode kada ki manta da yan uwan hajiyan mu fa na zaria a wurin rabo nace ni ina nasan su yaya, ? Yace waye yayan naki ya tambaya yana matsowa inda nake again nace cikin dariya gaka kuwa ko zaka banbantani da su zainab da binta na tunda ka zama kifi yanzu, , , , Bakina ya kaima cafka ban samu karasa zance na ba ya ce shiyasa naman shi keda dadin don da yan uwansa ya girma. Karni dai na bashi amsa bakina yana makure da hannun shi yace wanan bakin zanga ranan da tsiwan sa zai kare ? Sai ranan da ka bar tsokana na zai daina tsiwa nace mai tare da fadin da su anty Fauziya da Anty faiza da antyn nan gidan ai zamu kasafa kayan yace kin yi daidai. Ruguma ya kai min daidai ina mikewa zuwa wurin jakkan kayana ajyan zuciya na sauke da ban san yazo min ba tare da lumshe idona. Yace you miss my hug ko two days nace na fada ma haka tunda na saba an hanani auren mara mata a inda zan samu kulawan mijin ko yaushe a kaina. Murmushi yayi ya sake ni tare da fadin kin makaro yarinya sai dai diyan ki su samu kila au dazun hajiya take wani magana da ban gane kansa ba nace na may fa ? Dauka kamar suke kina da ciki ko nace haka suks ce min nima basu san canjin yanayi bane kawai yai dariya ya fice dakin. Nagama shirina na sauko kasa lokacin shima ya fito da shirin shi zasu wuce ke nan a falo inda na bar anty na samay ta zaune. Na gaida ita tare da dan zama a gurin ta nace anty dama akwai kayan da muka zo dashi na rabon azumi da yace su anty Fauziya da anty Faiza zasu shigo sai a raba. Tace wanan aikin ki ne ai khadija tunda bai taba yin haka ba na gani nace anty ai yin hakan yana da kyau may ne amfanin kana da baka yi wa yan uwanka abinda ya dace dasu. Ko mutum nada hali ai yana son kari ko tace wanan kuma dai yanzu naki shawaran ke nan dai nace bai yi bane anty tace yana dakyau hakan ai. Nace ko dacen sai nake ganin laifin ki ne da baki lurar dashi abinda ya dace yayi wa yan uwa da abokan arziki wai laifina kike nufi mutumin da baida lokacin kansa balle na wani . Nace ko yanzun haka yake anty a haka dai zaki matsa ki ta saka shi a hanya daya dace tayi murmushi a gitsire a fuskan ta. Kitchen na nufa wurin girkin miyan dana dora na bar ma laraba dafa shin kafa fara na samu komai yayi yadda nake so. Wutan na kara ragewa na kara ruwa na barshi ya dahu da kyau daki na koma na kira binta take cewa gamu tafe munga yanzun mijin ki ya bar nan ai zai tafi zaria. Nace ni ida ma kuzuwa bashi na kiraki ba tunda nasan zamana daku yanzu kiran ki nayi ki ban lamban anty Fauziya don Allah. Maimakon tayi magana sai kara ma anty Fauziya waya a kunne tayi naji tace hello khadija yanzun muke maganan ki da hajiyan mu ai. Nace Allah sarki anty dama ina son ku shigone akan zancen kayan nan da muka zo dashi na azumi tace yar halas yanzun hajiyan mu ke min bayani gamu tafe gidan. Sun ji dadin wanan abin don da farko har sun fara zance na suna fadin ni kuma da iyawa na shigo sai nice zan raba masu abu sai gashi na kirasu akan maganan. Hajiyan mama tace baku da hakkuri akan abu wallahi ni nasan baza tai haka ba don yarinyace da zuciyar manya tasan ya kamata sosai ai. Sun shigo gidan a lokacin kowan mu na dakin ta sai laraba dake gyaran wuri sama suka hau suka fara shiga wurin anty Fati daga nan suka shigo dakina. Mun da jima muna hira suna fada min komai ya kammala na taron baki da suka tanada sai zuwan su ake dako yanzu. Falo muka fito na tura laraba ta kira driver da zai shigo muna da kayan ciki ni da kaina na shiga dakin anty Fati na kira ta tana kwance nake fada mata ita ake jira ta sauko. Tace muje a raba kawai dan jimm nayi tare da fadin anty ina fatan ba fushi kikayi ba akan haka idan ma kin dauka wani abu ne Allah yaga zuciyana wallahi. Ban shigo cikin ku da zuciya biyu ba sai alheri tsakanina dake don baki min komai ba a rayuwana tarkan yayata na dauke ki a gurin na. Don haka ina mai baki hakkuri idan ni na saba maki badon niba sai don Allah ki daure ki fito ki bada umurni a matsayin ki na uwar gidan nan. Kada ki sakaci da daman da Allah ya baki a kan mu Allah ya gani ba zan taba shige maki gaba a kan hakkin ki ba a gidan nan da yardan Allah. Murmushin nan irin nata tayi kamar dole tace khadija na gode na kuma fahince ki sai dai nima bana fadi haka da wani manufa bane gaskiya na fada maki ban son irin wanan abin ganin laifin ne. Nace yaya zakiyi Allah ya baki wanan girman sai dai ina kara baki shawara badon nakai ba ko na cancanci na fada maki kina sakaci da daman ki don ko ke ce babba a cikin mu kamata yayi wani abin ke ce mai daurewa ki fada koda ba zai dauka ba a lokacin nasan zai duba daga baya yai amfani dashi. Yanzun dai khadija na fahinci dole sai naje kasa ke nan ko nace haka nake so anty don ke ya kamata ki komai a matsayin ki na matar gidan nan . Kinga yanzun ana ta shirin kawo kayan zainab alhalin hajiya mama ta kiraki baki kuma leka ba har yanzu. Mikewa tayi daga kwancen da take tana fadin gaskiya ta fada min kamar kwana bakwai da ya wuce sai dai ban samu lekasu ba din. Nace anty yin haka kamar kina sakaci ne da daman ki da Allah ya dora maki tunda ko banza wanan abin ai ya shafe ki amma ki gafarce ni idan na fadi ba daidai ba. Tare muka fito da ita daga dakin zuwa kasa inda na samu su Anty Fauziya sun kulu da dadewan mu a ciki. Nice na basu hakkuri nace na samu tana bayine na tsaya jiran ta anty Faiza tace na dai dauka tana halin nata ne data saba ai don dukkan su sun girmay ta ga shekaru. List din nabawa anty Fati tun muna saukowa nayi mata bayanin komai ta karba ta zuwa kuma sai ta mikawa anty Faiza anan na fahinci halin ta irin mutanen nan dake da halin ko in kula akan abu. Na suka shiga bin komai yadda ya kamata tun nan suka tayar da binta da driver aka fara mika na mutanen cikin gidan su kafin wani lokaci a kaiwa kowa wanda ya kamata anyi yadda ya dace. Kitchen na koma na duba girkin yayi na shiga rabo tare da laraba tana mikawa a falon karshe na fito ma laraba da nata . Abin ya daure ma laraba kai sosai tace hajiya har dani sai kin biyo ni da nawa kason kuma nan ai da ki barshi a can in dauko. Nace haba dai mama kina gaba dani zan bar maki abinci acan ki dauka karma ki koma irin maganan nan don Allah kije ki huta yau mun aikatu da yawa sai zuwa anjima a kai makarde shikafa da zamuyi sinasir dashi. Ta karbi abincin tana godiya nace sai dai kada ki manta da markaden don ya dan samu rana ya tashi. Tace yanzun kuwa dana gama zan mika insha Allah jinayi anty Faiza tace uhumm, ummm laraba yau ke ma dai kin ga canji a gidan ku ko. Yanzun dai Fati dabara ya saura gare ki duk da baki son afadi matsalan ki ya zama dole ko mu fadi don ke din dole mu ce. Yanzu dai ga abokiyar zama kin samu kamata yayi ku hade kan ku ko bazan kune yan kasa al,adan ku daya kabila daya kin ga komai zai zo maku da sauki idan kan ku yana hade. Anty Fauziya ta karbe da fadin naji dadi danaji yayan mu na fadin da yaran Khadija zata tafi suje can suyi hutu a gurin ta haka ya nuna ita mai son muce mai kuma kaunar mu. Don ance wanda duk yaso yayan ka ya gama son ka a duniya koda kuwa ya nuna kai bai kaunar ka balle gashi yanzu mun gani rabon kayan nan ki duba fa bata yarda an taba komai ba sai da taje ta kira ki dakin ki kizo aka fara. Sanan kuma muma gare mu abin farin ciki ne ace yau gamu gamu gidan dan uwan mu muna raba abin arzikin da ya fito a hannun shi may yafi wanan farin cikin a ran mu sauran sukace babu wallahi. Mu dai fatan mu yanzu ku hada kai sosai ku jawo muna hankalin dan uwan mu ya dawo jikin shi ko kwata muna shi daga kaidin wanan shedaniyar matar tashi. Anty Fati tai wani murmushi tace kayyah anty wanan wazai iya da ita a cikin mu kike gani kun fasan duk ta girmay muna a shekaru ba kusa ba. Zainab tace bari fadin haka mana Anty Fati ita tayi kamar Allah ne ga Allah duk damu daku za,a dukufa wurin kai kuka mu ga Allah. Ai tunda har khadija takai haka a gidan nan tare da Nafisa alama ya nuna hakan Allah yana karban adduan mu. Yanzu dai mu hadin kan ku muke fatan don kada kuma kawunan ku ku yazo bai hadu ba abin yafi nan lalacewa kuma. Nan dai sukai ta magana wanda yawan maganan duk akan anty fati yafi yawa don inda take da sakaci duk basu boye mata ba a gurin ranan. Karfe uku daidai suka bar gidan zuwa cikin gidan su nace zamu shigo da anty Fati idan mun shirya da ga baya. Fitan su gidan yai daidai da dawowan su AA da Yusuf bayan mun tare su ne na shige daki na shirya ban fito ba sai da nayi sallah la,asar na fito na samay su a falon har lokacin bata shirya ba. Nace anty lokaci yana gabatowa fa shima Yusuf din mikewa yayi yana fadin zai je ya shirya motan da zasuyi amfani dashi ya bar gidan . Falon ya rage daga ni sai shi a zaune ina jiran ta tashiga yace dani zo nan Deedar hanya hawa saman na kalla inda tabi sai na mike na isa gurin shi din. Jawo ni yayi zuwa jikin shi tare da fadin wanan kwalliyan yai maki kyau sosai na gode nace ina kokarin dagawa saman jikin shi din. Ji nayi ya kara riko ni da kyau ya kokarin kai min kiss nace kaima Allah ya AA ka bari kada anty ta fito ta samay mu a haka kasan ranta ba zaiyi dadi ba fa. Yace and so what idan ta samay mu a haka budurwa taga na rungumay ko farkana nace koma dai may don Allah ka daina don ba dadi irin hakan aiwa mutum sake ni yayi yana sauke ajiyan zuciya tare da fadin yau dai kin san ke ce da girki ko ? Da sauri nace dashi girkin may kuma ana zaune kalau may zai sa in yi girki anan bayan ba lokacin mu bane kada ki kawo min wanan zancen anan don ba a kanki aka fara haka ba. Nace ni kaina na sani ai abinda banso kuma bazan ma wani ba bai kara kulani ba tunda na fadi haka sai ya share ni ya mike zuwa sallah. Fitowa tayi muka fice daga gidan mun samu yan uwan haihuwan su kaf sun zo a lokacin muna shiga suka hau yi wa fati sheri kamar yadda dangin miji kanyi wa uwar gida wani lokaci. Part din hajiya Umma aka gyara don taron bakin masu kawo kaya muna dakin mommy zaune na mukaji shigowan su gidan . Ba bada wani yawa suka zo ba su shidda ne kawai an tare su a cikin mutunci suka gabatar da kayan ga manya akai masu godiya suka bada kudin dinki dubu dari biyu tare da fadin suna so jin lokacin buki. Daga inda nake nayi murmushi naji hajiya Umma tace wanan maganar maza ne idan an shirya za a sanar dasu lokacin nan dai aka gabatar masu da drinks da su snack da kajin da aka soya don su tare da basu tukwaicin alherin da suka zo dashi aka rabu lafiya da kowa a wurin. Yan gida suka shiga duba kayan suna yaba kyaushi da yawan shi suna sa albarka tare da fadin abu yayi kyau wallahi. Dakin hajiya mama na shige na samu zainab ita kadai na fara mata guda akai tare da fadin amaryam mu na gobe ta dan hararane tare da samun wuri na zauna a kusa da ita. Ta kalle ni tace ai amaren suna da yawa khadija don ya ce ba ni kadai zai aura ba wai kina nufin wanan maganan da yake da gaske har ke ya fadama shi. Tace a kasale cikin wani murya haka yake fada min wai kuma ke kin san ko wace matar kuma kin san halinta don haka in kwantar da hankalina. Gabana ne ya fadi nace a fili ni ni din nan nasanta yace maki tace kwarai kuwa da sauri nace wallahi haram idan bashi bane da sai ince yai min sheri don ya hada ni dake yace hakan. Murmushi tayi tace indon nice fa khadija kada ki damu da wanan don nima kamarki ce auren biyayya mukeyi wanda muke fatan muga riban hakan. Don haka wallahi kadama ki damu khadija kin san dai ni ba zan taba fadawa wani wanan maganan ba idan bashi ya fadi ba akaji. Jikina ne yayi sanyi don ta kawar da hiran sai ce min tayi kinga ni yanzu ba wanan ba wani shiri kika tsara akan bukin kafin lokaci yayi. Ajiyan zuciya na sauke nace Allah dai ya kaimu lokacin lafiya don shine mai wuya tace ai shine fa shigowan Binta dakin yasa mukai shiru a lokacin don ta shigo tana yaba kyau kayan da aka kawo. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENAB 1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Sai daga baya ne bayan mun dawo gida na lura da AA yana fushi dani kan maganar da mukayi na girki ina gama cin abincin da na girka na shige daki tare da kargamay kofana. Da safe shiya tayar dani daga barci wai a ranan zamu koma Abuja bance komai ba illa gaida shi da nayi da kwana har yakai kofa nace ina son shiga gun yaya Amina kafin mu tafi. A,a yace min ya fita kawai dakin wani irin bakin ciki naji a raina kan hananin da yayi dole sai a waya na kirata mukai maganan da zamuyi. Muna a falon hajiya mama zaune a gaban ta yana gurin Abbasu suna magana dashi mama tace dani ya kuma banga kun fito da yaran ba nace ban san may ya hana ashirya su ba. Ta dauki waya takira anty fati tare da fada mata cewa ta shiryo yara yanzun da laraba ta turo su gidan ta ina son ganin laraba yanzu. Labara suka shigo tare da yaran tace ina ita fatin take binta maza kira min ita ai maganan ya shafe ta yanzu. Fatin suka shigo tare da Binta suka gaisa tace dani ashe baku tafi ba har yanzu nace eh yana tare da Abba ne. Hajiya mama tace dama kiran ki nayi in fada maki cewa yaran nan yanzu dasu khadija zata wuce suje can suyi mata hutu a can idan hutu ya kare su dawo. Sai maganan Laraba da nake son yi yanzu kin san kwanaki mun taba magana kanta cewa kin gaji da zama da ita kina son a kawo maki yarinya har karo biyu kina min wanan korafin akan laraba ina baki hakkuri. To yau Allah ya kawo iyakar zaman ku da Laraba don kin san Laraba yar uwatace ta jini bazan cire ta a cikin jini ba kamar yadda nasha fada maki haka ita din jinina ne ita din. Don haka yanzu zaman laraba zai koma Abuja wurin khadija ke kuma sai ki dauko wanan yarinyar da kika ce an maki magana a kanta. Shiru tayi sai can tace amma hajiya da an fada min a shirya su ko yanzu gaskiya basu da shiri don ko wanki ban masu ba. Shirmay banza ke nan ai in don wanki ne idan kin yi tunda Yusuf yana hanya ko yaushe sai ya kai masu . Laraba aka kira hajiyan ta sheda mata zancen zuwan ta a gaban mu tace tau hajiya can kuma Allah ya maida zama na tace eh don ita din can yanzu tana da bukatan mai taimaka mata da wasu abubuwan gama kin ga yanzu gashi azumi ne tafe kuma ga yara zata dasu. Kinga zaki dan rage mata wani abin a can tace hajiya banda zabi duk yadda kuka ce haka za ayi yanzu zan dan je in kwaso komatse na sai nazo mu tafi sai dai zan bar sauran kayana sai a aika dasu gida daga nan wurin ki. Tashi tayi zuwa shiri inda ta bar anty fati zaune bata ce komai ba sai zuwa can ta mike tana fadin zata je ta hado kayan yaran. A gaskiya banji dasin yadda akai mata din ba sai dai babu halin magana a wurin don ba wurin magana bane. Amma a gaskiya ta yaya ta zaune da ita kalau yanzu kuma a dawo ace ta koma gurin kishiyar ta ke nan nima watarana za a iya rabata da wurina din don bata yin kanta sai yadda aka juya ta ke nan. Muryan hajiya ne ya katse min tunane na tana fadin kada ki damu dama zaman Laraba da Fati ya ishe ita Fati din don tasha min korafi yar uwata ce Laraba ta gurin uwa kin ga ita din jini na ce sosai. Ba zanso kaita inda baza a kula min da ita ba yadda ya kamata ba dai sai na fada maki komai ba a yanzu zaki komai a gurin Laraban. A raina nace ai kaji matsalan nikan an barni a ciki dana sani in dauko a bangare na kamar yadda ya bukata inyi tun farko. Mikewa hajiya mama tayi ta samay shi a falon Abba tana mashi bayanin halin da ake ciki na zancen tafiyan da ta tsara yanzu. Ba wanda ya musa mata don bayanin da tai masu akan haka sai Allah tsare hanya da Abban yayiwa jikokin nasa a lokacin. Fati bata aiko wa yaran da wani kayan kirki ba hajiyan ta fara fada ina shigowa daga dakin mommy dana fito wurin ya Amina da ta shigo nace ai babu komai Allah dai ya kaimu lafiya. Tunda muka fara hanya ba wanda yai magana a motar sai da mukai nisa ne daddy yace zai sha ruwa na dauko goran swarm na bude na bashi ya soma barci. Allah ya sauke mu lafiya duk da gajiya muka fito daga motar tundai ni dana jirkita irin na ranan da muka je kaduna wanan dalilin yasa yai min magana ya sauke fushin da yake dani akan kin amsar girki a kaduna da banyi ba. Muna shigowa na bude part dina muka shiga kafin kace may labari ya samu Nafisa na dawowan mu gidan har da yara muka dawo da wata mace. Tace what in dai ba Fati bace tazo wa zaizo gurina da yara kuma mun shiga inda na barsu zaune a falo ban daki na fada sai da na amaye dan abinda ke cikina na karin safe danayi na samu sa,ida a raina. Duk da yamma yayi sosai a gagauce nayi sallah na fito daga dakon na samay su har laraban zaune a takure falo. Nace don Allah mama kuyi hakkuri na dan shiga ciki rage lalura ne ku taso muje daki ina kokarin shiga dayan dakin da kayan ta. Tashi tayi ta biyo bayana inda na aje kayan tare da cewa sannu da shigowa sabon rayuwa mama ubangiji ya kawar da shedan a tsakanin mu ya bamu zaman lafiya da juna tace amin yar nan. Kitchen na koma na dora girki a gagauce na hada muna abinci duk da dare ne bai hana in girka abinci mai inganci ba a lokacin. Sai tara saura ya shigo dakin muna zaune a falona muna cin abinci a plate daya da yaran sai mama laraba dake gefe daya tanas cin nata ita kadai. Wuri ya samu ya zauna saman kujera ya fara gaida mama laraban da gajiyan tafiya sai ya juyo gare ni yace ya jikin naki yanzu ? Da sauki na bashi amsa ina ci gaba da cin abincin da nake wanda dama bawani ci nake ba tsakura nakeyi don ma in dan ci yasa na hada hannu da yaran muna ci. Yace mama yau gaki Allah yai dawowan ki Abuja kuma da fatan za a zauna lafiya da kowa a cikin amana da yarda tace insha Allahu. Ya mike bayan ya gama maganan da zai yi ya fita nayi mai saida safe nace yara suyi mai suma sukace mai saida safe Abba ya amsa ya fita. Laraba dake gefe tace uhumm sai dai kin koya masu ai sannu a hankali zasu iya ai din babu wannan shakuwar a tsakanin su irin haka. Murmushi nayi nace komai yanzu sai a hankali ai mama bamu jima ba muka shige kwana. Washegari ko da na tashi jikina ya matukar mutuwa sosai yai min nauyi ga kasala da kyat na iya fitowa na hada masu abin karyawa suka karya nikan daki na koma na dunkule. Barci nayi sosai a wurin har mama taiwa yaran wanka ta shirya su ban fito ba sai da AA ya shigo ne yana tambayan ina cikine mama ke fada mai ai tun safe na shige banjin dadin jikin ne take gani. Dakin ya shigo tun daga kofa ya tsura ma yadda nake kwance ido har ya karaso gare ni inda nake kwance bargon dana rufa ya yaye na bude idona da yai min ja na sauke a kan shi. Yace may ke damun kine Deedar nace a kasalance jikina dai ke ciwo na kwanta in huta yace oright idan dai wani abin kike ji ki fada min muje asibiti a duba ki nace lafiya ta kalau. Mikewa yayi yana fadin yau bazaki shiga school ke nan ba nace sai dai gobe idan Allah ya kaimu gaskiya . Ni zan fita yace idan akwai abinda kuke so sai ki kirani a waya nace idan zaka dawo dai ka riko muna pop corn wasu daddy da sauran abin yara dan Allah ? Kallona yayi ya girgiza kai nace da kyat please don Allah kaga yau ni ban fita zanyi ba yace yaji Allah ya sauwaka ya fita. Mikewa nayi na shiga ban daki na fito wayana yana kara na dauka maryam ce a layin ina dauka take fadin ke yar dadi miji yau ke nan ba zaki fito school ba ko ? Wallahi maryam jikin nan nawa yau sai a hankali sai dai gobe idan Allah ya kaimu tace ai ganinan zuwa na dubaki idan mun fito sai kinzo nace na kashe wayan ina kallon lokaci. Sha biyu da wani abu na rana nace kai ashe lokaci ya shige ne tashi nayi zuwa falo na samu su laraba da yaran a zaune ko tv basu kunna ba. Gaida su nayi nace mama shine ba a tayar dani ba ga har rana yayi sosai kallon yaran nayi ina tambayan su may za a dafa masu abincin rana ne ? Wanan yace indomie wanan yace taliya nace bari mu raba gardama yanzun barin maku taliya din gobe sai ayi indomie din. Na juya wurin Laraba ina fadin mama ai zakici taliyan ko tace zanci mana uwar dakina may ye bamu ci acan mu. Kitchen na shiga na hada kayan miya na jajjaga tare da dauko tukunya na zuba ruwa na dora kan gas din fridge na bude na dauko nama na yanyayanka na wanke na zuba a tukunyar tare da zuba gishiri na kawo albaaa na yanka a sama Haka dai har na hada abincin yadda nake so na rage gudun gas din nawa na fito falo wurin su na zauna muna hira dasu. Gaskiya ko ba komai ashe zama da mutum dadi gare shi ga yau kawai naji dadin kasancewa dasu a tare dani part din. Da ko sai ni kadai zan zauna idan ba waya ba ko tv banda abokin fira a a part din shigowan maryam yasa muka mayar da hankali a gare ta tace ke shegun buzayen nan su tare ni waje sai tambayoyi suke min wai may na dauko a jakata sai na bude masu sun gani don basu yarda dani ba. Nace ga yan wulakanci zanyi maganin shegu kuwa tace bakiga yadda suke wani zare min ido ba wallahi har tsoro ne ya kamani. Mikewa nayi na fita zuwa wurin su a bakin get din ko hijab ban tsaya sawa ba a jikina tun daga nesa nake kwala ma wanda nagani a kofar kira ya wani nuna kan shi wai shi. Zuwa nayi a bakin get din nace wa ya baku ikon bakona idan zai shigo gidan nan sai kun caje min shi yace hajja dokane muka samu yin hakan daga sama. Wayan dake hannuna na kira AA dashi suna kallo na nace da ya dauka kai kaba wa yan nan buzayen dake get din gidan ka doka idan bakuwa tazo wurina su caje ta don yanzun haka sukai ma maryam har da so taba jikin ta. Yace what wa ya basu wanan dokan haka gurin bakin ki nace haka sukace ina juyawa ciki bayan na gama masu masifa da warning din su don nasan inda dokan ya fito yanzu. Ina shiga rike da hannun daddy dayan su shima ya shigo ya nufi gurin nafisa dake zaune falo yanzu cikin jikin ta ya girma sosai. Na barshi nan ya duka yana fada mata sai gashi wai ta aiko in je kin zuwa nayi don nasan maganan banza zanji idan naje din abinci na juyo muna na na kawo falo. Mun baje muna cikin cin abinci sai gata ta shigo falon da kanta ba sallama kamar kulun na dauki wanan dabianta ne haka ta saba shiga guri tunda har mijin ta naji yana korafin hakan. Zata fara magana na dakatar da ita da fadin malama may ye haka kamar wace ta shiga church babu sallama kuma. Tunda zuwan ki nan ba alheri bane ki fice min daga shiya don bakiga kafana a gurin ki ba ke fitsarariyar mara kunya nace dakata may kika gani anan yara ko. Don Allah kada ki bata ma yaran nan tarbiya da halin nan naki mara kyau kamar yadda kika bata wa naki tarbiya kallo takai ga yaran da laraba tace aikin banza sai kuma ta fasa fadan daya kawo ta tace. Idan mutum ya isa ai ya haifi nasa ya daina karice karicen diyan mutane a furin shi a haka dai zaki kara da kalar diya a shiya badai ki haihu ba. Nace idan na haihu tunda kece Allah sai ki kashe diyan mu gani gaki bakar manya kike kiran wani maye ashe tunda har kin san gaibu. Ta hayyako na mike tsaye ina fadin Maryam rufo min kofa nan don Allah yau in koya ma matar nan hankali a gidan nan . Jin haka yasa ta fara ja da baya baya tana fadin dama an fada min haka kuke yan cin mazan mutane idan kunga anfi karfin ku sai ku nuna karfin doya ga mutum. Har ta fice da wayo tabar dakin dariya muka sa maryam tace shegiya yau kin gano takon yar iska a gidan nan ai ashe dama tana da tsoro haka take iskanci. Laraba tace ina ina za a hada girman jikin su ba daya ba idan uwar dakina ta danke ta aisai buzunta dama haka hajiya uwar yaran nan ke tsayawa ta kwaci yancin ta ai da abin bakai haka ba. Amma yadda kika san uwa da yar ta haka muka zauna a gidan nan a baya lokacin ba a nan muke ba dawowan munan kuma abin ya kara lalacewa tsakanin su da maigidan. Maryam tace ai ma kasa ki yarda ki hada jiki da yar iska don ance tsiya yake kawo wa a gida fada kana hada jiki da kishiya haka. Nace nima ai hauka nai mata ina zan fara taba ta da wanan tsohon ciki haka a samu na bin gari dani ana nayi kashin kai. Ashe tana fita ta kirashi ta kwashi karya da gaskiya ta fada mai sai gashi ya kirani yana fada da daukan wayana babu ko sallama sai fadin Deedar kina haukane da zaki biyewa Nafisa da tsohon cikin ta ki nakasata ki mai da ni baya. Duk abinda tai maki bazaki jira in dawo gida ba sai ki far mata da fada har kina shirin dukan ta a wanan yanayin da take ciki haka. Sannu mai mata nace mai tare da fadin ai bansan mijin tace kake ba sai ka nuna min yau na kashe wayan abina. Maryam tace wa mama laraba kin gani ko kirashin fa tayi yanzu ta kwashi karya da gaskiya ta fada mai shi kuma ya hau ke nan. Nace idan ma ya hau ai sauka zaiyi don ba zan yarda da rainin wayon kowa ba a cikin su yai min kira yafi a girga naki daukan wayan ina gani ban daga ba. Muna gidan da maryam sai bayan magariba ta bar gidan zuwa gidan anty ta tace acan zata kwana don yanzu zaman hostel din bai mata dadi da ban nan. Sai dare kamar yadda ya saba shigowa ya dawo gidan sai da ya watsa ruwa ya sa jallabiya ya shigo dakin namu rike da ledan popcorn daya sayo yana shigowa ya mikawa yaran sun karba babu godiya nace baku godewa Abba mana ko ya karbe abinshi ne sukace sun gode suna hada baki wurin fada. Gaida laraba yayi ya juya ya na fadin kai min abinci nace naji ya juya ya fita daga dakin nawa sai da ya dan jima na mike na shirya bayan nace mama ta rufe ta ciki idan na dawo zan kwankwasa sau biyu tace to. Na riga da nayi warning din yaran da kada su fita ko ina idan ba dani ba koda wani na fice zuwa wurin shi kai mashi abincin. Yana zaune a d/table din na shigo da sallama ya amsa min ciki ciki na isa na fara jerawa baiyi magana ba sai dana gama na juya nima ba tare da na yi mashi magana ba naji yace. Ina zaki na juyo nace mai daki zan tafi yace dawo ki zuba min ina zubawa har na kusa gamawa yace don may nake kiranki baki daga waya ba. Ban kusane ina kitchen na bashi amsa yace da kikazo kikaga miscall dina fa shiru nayi mai ban tanka shi ba. Ya ja plate ya fara kai abincin sakwara ne da miyar agushi maryam ta taimaka mukayi tunda nafisa tai maganan doya muka sha dariya. Shiru wurin ya dauka ba wanda yai magana a cikin mu wurin sai da ya kusa gamawa ya dago kai yace nice mijin tace ko ? Nace in ba haka ba daga jin magana ta bangare daya zaka hauni da bugu don ni naza juyan da take fada min ko may ? Haka kawai zan zauna ta shigo min har part dina da cin mutunci amma naka laifinta ba sai ni da ta sama din tunda ni ban san daukan ciki ba ko ? Kinga bashi na kiraki nan ki min ba yanzu sai dai abinda nake son ki dashi shine ki kula da halin da take ciki yanzu da hankalin ki zaki far mata da duka. Au ka dai yarda da dukan ta nayi niyar yi ke nan daga haka naja bakina nayi shiru yana gamawa na kwashe kayan zuwa kasa na barshi a gurin zaune. Koda na koma dakina ban fito ba na zauna muna hira da laraba har sai da yara sukai barci na kaisu daki bayan na saka sunyi fitsari daki na koma don in shirya na samu waya na ruri. Dauka nayi na duba shine a layin ban daga ba sai da na gama shirina tsab na fito naiwa laraba sai da safe nace ta rufe kofa tayi addua kuma ta kashe wutan dakin . Ina shiga yana zaune a bakin gadon shi ya tasa laptop din shi gaba sai dai ba dakila yake yi ba har na aje jakkan hijab da zanin sallah na na kwanta bance dashi komai ba. Jin sauka hannun shi nayi bayan ya hawo gadon ya kwanta ba kula shiba yai abinda zai yi ya tashi kamar yana taba dutse. Shima bai min magana ba ya mike zuwa ban daki yana fitowa nima na mike na shige ina fitowa na tsaya nayi na fila ban kwanta ba sai da na kwanta naji murya shi na fadin. Wanan magana yasa kije min haka idan ban yi maki magana akan aikata ta,asan da kike son jefa kanki a ciki so kike in kyale ki kiyi. Ban iya magana a lokacin sai dai a raina nace lalai namiji sai dai a barshi da halin shi yanzu yana nufi ya dauki maganan Nafisa da muhinmanci akan abinda taimin ko don ban haihu dashi bako kuma da gaskiya dai din Nafisa ce kawai a gabam shi. Da asuba tunda mukai sallah na sauko daga dakin shi duk wanan sakkon da nayi na samu mama laraba ta gama gyara part dina. Sai kamshi ke tashi komai tsab ta gyara har na shiga dakina nan ma komai tsab har toilet din ta gyara sai kamshi ke tashi. A raina nace lalai tafiyan mu zaiyi kyau da mama Laraba fitowa nayi zuwa falo muka hade da ita a falon ta fito kitchen nace a, a mama aiki haka da wanan safen. Tace uwar dakina ai tun kan a kira sallah nake idona biyu ina idarwa na hau abinda ya kawo ni yanzun ma kitchen na gama gyarawa. Sai dai ban san may zaki girka ba yau amma dai duk da haka na dora maki ruwan zafi a wuta har ya tafasa ina ji nace kai nako gode mama gashi kuma guri ya dauki kyau haka. Tace to uwar dakina shifa ya kawo ni nan yanzun ma zajen nan nawa kawai nake jiran tashin su in masu wanka. Nace gaskiya mama nagode fa aiki haka gwanin yabawa Allah yasa mu dore a hakan tsakanin mu. Tace insha Allahu mun riga da mun saba da wanan ai ko can abinda ke yawan hada mu da hajiya ta kaduna cewa take na faye kakalen aikin da ba a sakani ba ni kuma ban iya keta ba a rayuwana. Kitchen na nufa na dora girki har wanda zasuci da rana idan na fita farar shimkafa na dafa sai da yayi wara wara na sauke yasha kayan hadi sosai su karas da koren wake da kabeji dahuwar tayi kyau sosai don haka na kwashena zuba a inda ya dace ma kowa. Na samu tsoka zalla na yanka na tafasa da gishiri da maggi bayan ya dahu na dauko attarudu da tatasai albasa na dan daka su a turmi nayi miyar jajage don yafi dadin cin shimkafa. Sai cooker outh dana dama na hado da madara zuwa falo su karya dashi don bai sayo muna sabon bread ba ranan idan zai dawo da dare yake shigowa dasu gidan. Na samu an gama ma yaran wanka har ta shirya su cikin wasu kayan da uwar su tabayar da zamu zo nan falo na zaunar dasu suna karyawa na shige wanka a gurguje na fito na shirya don kada ya girshe ni. Zamama ke nan zan karya sai gashi part din suka gaisa da laraba yaran nace ma ga Abba ku gaisa mana suka ce ina kwana. Ya amsa masu tare da zama in kawo maka breakfast ne nan yace eh sai dai kiyi sauri kin san zaki makara fa na wuce zuwa kitchen na hado mai na kawo mai ya karya suna dan hira da laraba sama sama. Muna gamawa ya mike ya fara fita ban fita ba sai dana kara jawa yaran kun ne na tsorata su nakuma yiwa laraba magan akan su rufe kofa kada su budewa kowa kofan. Tace a tsorace ai ko murai ban budewa nasan halin gidan ba yau ba ai nayi masu sallama na tafi ta kargamay kofan ta ciki. Mun dauki hanya shiru ina kallon titi naji muryan shi yana fadin wai ke kina nufin dan maganan da nayi maki kike wanan hura hancin haka. Ko kina nufin a barki ki yi yadda ranku ke so ki biye nata ku zama daya kuyi aikin rashin hankali tunda kin san bakin ki take nema. To wallahi bari kiji ban yarda da fadan duka ba ko babu lalurar ciki kaddara akewa gudu ai don ba karfin ku daya ba kema kin sani. Kuyi na farko kunyi na karshe kada ku mayar dani sakaran namiji mana da baisan ciwon kansa ace gida ana irin wanan fadan. Na dago kai na kalle shi sai na kawar da kaina gefe don kwar jinin da yai min a fuska da na kalle shi yadda ya dake fuska yana min fada acikin serious voice . Muka isa na fita ranan bance dashi komai ba ya ja motar shi yabar gurin na shige cikin school din kai tsaye. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: A falon anty Salbiya muke zaune bayan barin mu makaranta mun gaisa na mika mata tsaraba da nazo mata dashi tai min godiya tare da tambayana mutanen gida. Suna lafiya na bata amsa dashi kawai naci gaba da sauraren su ba tare da nayi magana ba bayan dan hiran kadunan da sukayi ta dubeni tace yau ko lafiya kike nace lafiya anty. Tace to mu fara abinda ya kawo ku don nima fita nake son yi dan anjima kadan zan shiga barka anan makwabtan mu ne. Kai na rausaya tare da sake dan guntun tsuki nace dama dai an barshi anty don ni banga amfanin yin hakan ba gaskiya. Subbahanallahi tace dama kallon ki nake kawai don nasan da matsala tunda na ganki a haka nace anty may amfanin kai kaita kokarin gyarawa namiji rai shi bai san kanayi ba ma. Dariya tayi tace zaka ko gyara kanwa ta don su din Allah ya dorasu akan mu dama haka zaman aure ya gada ko da kuwa baka da kishiya balle ke mai kishiya kishiyan ma kuma buzuwa buzuwa ko yar baruwan mu ce ba abin yarda bace kice ki bar mata miji don ke zaki sha tarin takaici. Yanzun dai may ke faruwa nace wallahi anty mutumin nan mijin tace ne nan dai na kwashe labarin abinda ya faru tun a kaduna har dawowan mu nan Abuja na fada mata komai. Allah sarki kanwa ta yo ai haka halin maza yake al,amarin sun dama sai hakkuri zaki ga abin magana su bashine abin yi a wurin su ba tun dai na miji irin naku da kullun a cikin ci da sha yake na saddabarun mata. Yau da kin samu kanshi gobe juyewa zai yi kamar bashi ba sai ke ce mai tarin takaici shi bai san yana yi ba ai kamata yayi ki kara kaimi ba kice wai kin jaye ba kamar yadda kikace yanzu. Ke ki fa gode ma Allah don wallahi kishi da wa yan nan mutuane ba abin wasa bane ke gashi har kin samu miji na kulaki bata samu yadda take so gaba daya ba a gurin ku. Gyara kan da addua ai yanzun kika sa hannu khadija don ba fasawa zakiyi ba don shi gyaran nan da muke yi yana hana wani abu ko don kimar hakan da kake dashi. Gaki a ganuwan cin ribar auren ki kike yanzu idan shakuwa da kauna bai shiga tsakanin ku ba a yanzu yaushe kike tunanen zakuyi shi sai gaba kun fara tara iyali kike ganin wanan abu zai yiyu a tsakanin ku komay. Ke ki bar maza a inda kika gansu wallahi halin sai Allah daya halicce su don komai iyawan mace sai sun lasa mata wannan nakin cikin da namijin da suke dashi. Ajiyan zucita na sauke nace nasa abin ne yai yawa wallahi anty anty tace nasa dai kike gani shida kike zaune dashi idan wata ta zauna dake ta fada maki halin nata mijin sai kiga aike mowa ce a gidan ki. Mike ki gyara ki tofe shi da addua komai zaizo sai Allah ya kawo abin a cikin sauki gare ki ko yanzun ai ba haka taso abin ya tsaya a tsakanin ku ba kika san shirin da akai maku dan wanan tafiya na kwana biyu da kuka yi. Akwai abinda yafi ciwa kishiya rai kamar miji yai tafiya da yar uwanta koda da yardan ta ne sai ya dan sosheta a rai wanan kishi a jinin mata yake sai dai ana son idan zakayi kada kayi na wuce wuri. Yanzun missalin in tambaye ki tsakani da Allah ki fada min ke baki kishin su a ziciyar ko kadan don Allah ta fada tana kallon cikin fuskana da idonuwan ta. Murmushi nayi na dukar dakai ina dariya tace kin gani haka abin yake ai kamar fagen yaki ne aure sai idan inda karfin mace ya kare ga mijin ta. Ai tunda kika ga ko wani kabila na kishi akan mazan su to ki ji tsoron kalman nan ta kishi da kike ji don kishi na iya kai mace aljanna yana iya kaita wuta Allah yasa mu dace muka amsa da Amin. Don haka barin baki wasu sirika yau irin na kasan mu banan nan ba sai dai zan fassara maki sunayen su da amfanin su a cikin kalman hausa yadda zaki gane muhinmancin su dakyau. Ta mike ta shiga ciki sai gata ta dawo hannun ta dauke da wani jakka mai ruwan zaiba ta zauna ta dauko wani kwalba da aka nade da takarda mai ruwan gold tace cikin kallon inda nake kin ga wanan. Na gyada mata kai tace shi muke kira ina gaban ki uwargida da yaren mu turare ne na sihiri ana shafa shi a wuya da duk wani gabobi na jikin ki amma banda gurin mamanki don gudun kansa gare ki. Sai zaki gun maigida zaki shafa shi zaki iya gwadashi ko yau idan zaki girki ki gani kin gashi aikin shi shine yana sa dadin saduwa a tsakanin ku. Idan kina amfani da wanan zaki mallaki mijin ki don sai yaji duniyar nan babu kamar ki zai dawo hannun ki ba sai kin je gun malami ba don hadi ne na sosai akayi shi ba kowa ne yasan shi ba ko ke don na soye maki ne kuma da wace ta turoki gareni akwai mutunci da yarda sosai a tsakanin mu Shafa shi kuma yana sa wa mutum farin jini da kwarjini yana kara kafiyar soyayya a tsakanin miji da matar sa sosai dama wa yanda suke mu,amula tare. Tamika min na karba ina kara juya dan kwalban a hannu na sai naga tayi murmushi ta dauko wani ta miko min na karba. Tace muna kiran sa da bilkisu ma,ana sarauniya bilkisu ana dan zizara shi ne bayan kin shafa kwali karyan mutum yace zai kalli idon ki ya gaya maki maganan banza don kwar jini yake sa mace mai amfani dashi. Ana amfani da shi ne musanmam mace mai irin kishiyar ki don ki rika yiwa kishiya kwarjini ko idan zaki shiga taro ko wurin dangin miji . Zakiga suna haba haba dake ba wanda ya isa ya rainaki ko yai maki kallon wullakanci saka shi a idon ki kinga zai saka kaunar ki a gurin maigida yasa ki mallake shi a hannu ya samaki farin jini a gare shi. Ajiyan zuciya na sauke ina jin kamar har na kama AA ga hannu nane kamar yadda take bayani yanzu tayi murmushi ta dauko min wani leda da akai siling din shi baka ganin abinda ke cikin sa sai ka bude. Bayan na karba ina dan juya ledan a hannu na tace kin ganshi nan muna kiransa da mujallabul sheri ma,ana da turan ci back to sender. Shima dafa,i ne sosai hayaki zakiyi dashi karfi gare shi sosai wallahi akwai na ruwan sa kamar turare da sabulun sa sai dai ban samu ba a lokacin da naje kasar mu. Iddan kika turara shi a jikin ki duk wani aike da akai mike ko dako bakin aljani ke jikin ki sai ya kone shi ssamu ko sihiri ke ko tsafi ne akan ki idan kinyi hayaki dashi sai ya karye. Yana magance duk wata matsala na cuta da ba,asan yana ajikin mutum ba yawan hayaki dashi yana kawo waraka da ikon Allah ga mutum. Sai wanan da ace kina sana,a ne zaki ga fa,idar sa sosai shi sunan sa majabul khairi hayaki ne karfi gare shi sosai shima yana sa ka tara jama,a idan kina harkan kasuwanci kina amfani dashi jama,a zasu zasu rika tururuwa wajen sayen sana,ar ki. Yin hayaki dashi a yadda kike zuwa makarantar nan da yadda mijin ki yake da jama, a idan baiyi hankali ba duk zasu dawo wurin ki don haka yawan hayaki dashi yana kawo ki rika samun alheri ta inda baki zata ba ma. Tana kawai nan ta koma da jikin ta ga makarin kujera ta jingina tana murmushi tace ki gwada wa yan nan mugani akan su duk abinda kika gani kizo ki ban labari don zan yi tafiya zuwa sudan bukin yar uwata dake can. Ajiyan zuciya na sauke tare da fadin na gode anty maryam tace anty mun gode amma nima gaskiya da anbani don abu ga hannu shine abu. Dariya muka saka mata tace ke da baki aure ba tukun tace anty ai yin zanyi nan bada dadewa ba idan Allah ya yarda. Tace to bari lokaci yayi kilama a lokacin naje kasar mu kinga sai in maki hadi mai kyau daga can tace to shike nan amma fa kin san alkawari kika dauka tace na sani. Bamu dade ba mukka fitoo naso zuwa gaida anty hauwa don na kwana biyu ban je gidan ba saboda zuwa wurin anty Salbiyan da muke yanzu. Ko da na dawo sai dana kwankwasa kofa sau biyu kamar yadda na fadama laraba amma hakan bai sa ta bude min ba sai da ta tambaya waye nace mama nice khadija ta bude tana min sannu da dawowa na amsa ina shiga. Zama nayi a falo wurin su Affan ina tambayan su idan suna da damuwa laraba tace sai dai shi wanan mai kiriniyar ba wai sai in bude mai yaje waje nace dashi ya rufa min asiri ina zan sake dan mutane cikin wanan gardawan haka ni laraba. Nace mama ai da kin bude mai sai ku fita tare ku dan sha iska amma yanzu barin dan kaisu su sha iska kin san ba yadda zaka iya tauye yaro a guri daya haka ai. Idan ya kama sai ka iya uwar daki na sai ayi ai kin san komai daurowa ne Fati bata da yarda balle yadda tasan halin matar gidan nan a baya shine abinda takewa jiyewa zuwan su nan din ai kikaga tun farko bata yarda ba. Yanzu ma ai don hajiya ta nuna mata fin karfi ne ga hakan don tafita tunane zuwan su nan zai kara kawo shakuwa tsakanin su da mahaifin su kamar yadda naga kinayi din nan. Nace mama ashe kin gane manufana nazuwa dasu nan da nayi a yanzu tace duk wani mahankali da hange zai hango hakan ai yar nan. Ciki na shiga na dan kewaya na fito na samay su zaune a falo nace ku tashi mu dan ja waje da sauri yaran suka mike tsaye. Bamu tsaya falo ba na zaga dasu wajen gidan har inda nima ban taba kai kafana ba tun shiga na gidan mun taka da yaran ranan don dai su dan sake jikin su. Leken mu naga Samiha tanayi ta window falon tsayawa nayi nace da ita duk da ta sake labulen falon idan an turo ki ne ko ke kika sa kanki gulma je ki karas da abinda kika gani yanzu kada dan kuda ya riga ki. Bayan mun dawo a falo inda suke na zauna dasu wani tasha aka kai suna yaren su kuma babu mai kallo a lokacin. Mikewa nayi na dauki remote din tv na mayar masu mbc cartoon suna kallo ganin wata garmaka daga cikin su ta mike ta shiga ciki yasa ni gyara zama da yaran ina jiran tsammani. Talge baki shan rada sai ko gasu tare sun fito da ita daga dakin remote din tv na a hannu na rike tana zuwa ta tsaya a kaina tana fadin . Ke may ye hujjan ki na canza masu chanal da kikayi suna kallo ko son iko da mulkin naki har yakawo akan yan uwana ya tashi ga maigidan kuma ya dawo gare mu ne. Ban ko kalli inda take ba balle in san Allah yai ruwanta a wurin ta sake maimaita maganan ta a cikin tsawa nace ke ke ke wai wata irin fitinaniyar mace ce. Ina nan dai gidan yaran nan ne kuma don jin dadin iyalin shi ba wasu ba ya saka wanan kayan haka na nuna mata kayan falon da hannu. Ahhaye nanaye inji yan mata naki ikon da mulkin ke nan dadin abindai baki cikin gadon gidan nan idan ma don iyalin shi ne ba dai don ke ba bakar manya mai bakin nacin tsiya. A haka zaki kare wurin kalan diya kina fadan gado dasu gadon da bazaki ci ko sisi a cikin sa ba kuma ki sani gidan nan gidanane kije can ki nemi gidan ki. Nace gado gado yan cin gado manya to kin sani ko ki riga mai dukiyan mutuwa ko a lahira zakici gadon naki ke nan. Bakar manya kurwa na kur akan ki ko kina yawo da maita a fili ne nafi karfin kamun ki wallahi ke har kin isa kizo ki samay ni kice ga yadda kike so a gidan nan. Nace gashi kuwa na nuna maki isa ta a gare ki idan kin isa zoki kwata da karfi ki canza masu inda suke so din na juya wurin munafukar nace ke kuma sa aranki kamar kin bar gidan nan kun gama zama mu zuba dani daku agani. Na kama karkada kafana daya tana kallon bata bar wurin ba sai da nasha gori ta kare da fadin bari samad ya dawo yau in san inshi ya baki wanan damar na takamu yadda kike so nace Allah dawo dashi lafiya. Sai gab da magariba muka shige ciki ga yarinyar ta nason zuwa wurin yan uwanta amma sun hana karshe ma suka turata part din uwar nata aka rufe. Abinci na dora muna dayake indomie zanyi dama yasa ban dora da wuri ba na fita da yaran shan iska waje. Sai da nayi sallah na fito na dora ban fito ba sai da dahu na kwashe muna a babban plate ni dasu na zubawa laraba nata daban muna zaune muna ci ya shigo falon yana gyara nicktie din wuyan shi zuwa sasautawa. Gaidashi da zuwa mukayi dani da laraba sai Affa ya gaida shi ya kalli karamin yace kai ba zaka gaida ni ba nacewa yaron daddy ka gaida Abba mana kamar yadda suke kiranshi. Ina sauraren yai min magana akan Nafisa sai naji shiru bai ce kala ba ya juya ya fita daga dakin nan na fara ba laraba labarin abinda ya faru a falon. Tace ikon Allah mata da son kai haka diyan gida ma ba zaki barsu suyi yadda suke so da gidan uban su ba. Nace shine dalilin da yasa kikaga ban son su fita idan bangidan su kadai haka kuma rufe kofan da nake saki yi sanin halinta da nayi ne don zata iya shigo maku tace kunyi mata wani abin can daban. Yanzun jiran shi nake ta fada mai yazo inji abinda zai fada kuma tunda bata laifi ita a gurin shi sai naga laraba tayi murmushi tare da fadin uhumm uwar dakina ai abin naki da sauki ke. Ga yadda ta shigo gidan nan ta mayar da uwar yaran nan ko wata bora tafi ta albarka a gidan nan amma ke gashi har yana shigowa duba ki kuna tafiya a tare har kina iya mayar mata da martani ai abin naki da sauki sosai wallahi. Ita fa mai gaba daya tai mata a gidan nan daga ita har yaran na ko ya koma bai ma kaunar ganin su ga baki daya sai da uwar shi ta tashi tsaye sosai fa akan lamarin. Nace ko may akace wanan matar tana yi ai ba a mussu da hakan don ban taba fanin karfin halin kishi irin nata ba ni dai. Shiru shiru har aka kwana biyu banji yayi magana ba kuma kullun idan na dawo zan kai yara su sha iska a wajen gidan. Ashe abinda ban sani ba shine tun ranan tayi mai magana yace so kike in hana yara na jin dadin rayuwa in in ganta yan uwan ki a kan su . Wai ke may yasa baki tunane kafin ki aikata abune don Allah nan dai suka dan kwasa da ga karshe ya fice ya bar mata part din ta. Wanan dalilin ne ya sare mata gwiwa bata sake tayar da zancen ba sai dai zaman yaran a gidan yana matukar dagz mata hankali sosai da ta kalle su sai taji wani irun bakin cikin da ba gaira ba ta dalili ya rufe mata zuciyar ta . Gidan madam ta nufa duk da cikin jikinta yayi nauyi yanzu madam ta tare da sheri ta ga ranta a bace yake take tambayan ta may kuma ke faruwa ne wai ? Ta cire dan karamin gyalen da ta yafe a jikin ta tana fadin na gane wanan shegiyar yarinyar idan banyi da gaske ba a gidan nan madam wata rana zata iya cin duduniyata. Wai ki duba yar iska da wayon banza zuwa tayi ta kwaso diyan samad daga kaduna wai sun zo mata hutu anan garin da sauri madam ke tambayan yaushe haka ya faru ? Tace ba nakiraki nace sunyi tafiya ba satin can a aiko min da abinda zan saka ma shegiya a kofan ta madam ta tambaya tace kin saka din taja tsuki tace na saka mana amma banga komai ba wallahi. Shegiya banda kyau da kara bajewa ba abinda take yanzu ni kaina na hango abinda samad yasa y auro ta ashe. Madam ta kumshe dariyan ta tace lalai wanan yarinyar ba karamar yar duniya bace kinga hakan da tayi zai saka ta haskawa a idon shi yo wanda ke son dan ka ai yana son ka ke nan. Kinga tafi mu dabara dauko yaran nan da tayi sai yanzu nima na kara gaskanta maganar Sabuwa na ranan da tace muna ganin ta hakana tunda tayi karatu kada ji mamakin tafi mu wayo . Nafisa dake gefe tace komai aka ban inyi a kanta nayi amma banga wani ci gaban hakan ba dole yanzu sai idan na haihu in dire ma shegiya Niger ayita ta kare acan wata kila ma kafin in dawo ta kara gaba. Ke yanzu ma fa zuwan nan gidan ki da nayi akan yadda take kokarin juya zuciyar shi da zancen yan uwana ne nazo. Don indai yace sai ya kore min su to lalai nima ba zan zauna ba dama ni zaman ya zamay min kamar dole ne an takura min wallahi. Kai haba Nafisa may ye matsalan ki yanzu a duniyan nan banda zancen kishiyan nan komai kika nema kin samu a gurin shi yai maki yaiwa yan uwan ki aiko Alhamdullahi ko. Ta tabe baki tare da fadin hakane kuma inda wanan da wanan gaskiya ba abinda na nema a gurin shi da bai mun ba . Gashi har yau asiri na aiki kan yar iska ko motar shiga ya kasa sai ma yar banza wai duk da haka baisa tayi ziciya ba ta fita. Tana ganin yadda nake shiga ina fita ina saka gwalagwalai a gidan ina yadda raina ke so itako iyakarta part din sai kuma idan zata fita ya sauke ko yasa driver ya sauke ta. Madam tace to mai yafi rai dadi ga hakan aiko wanan abin alfahari ne gare ki kinga taso muje ma wani guri da aka fada min wani kafirin kasan Togo ne yazo aka ban labarin shi ina Allah Allah dama in fada maki sai gashi kin shigo ma. Da sauri tace shine baki sanar dani ba tun wuri ai irin su sun fi dadin aiki tunda kikaga har an dauko shi a kasan nan kin san ko yakai aiki kenan. Suna a gaban arnen togo ya baza farin kudi irin na da da yake aiki dasu a gaban shi suna kallo mai mashi fassara yana gefen su zaune. Sai da ya duba ya kada kai ba tare da sun mashi bayanin abinda ya kawo su ba ya fara bayani mai fassara mashi na fada masu. Jikin Nafisa har rawa yake sai da ya gama bayanin shi tace ita dai kafin ma in kai ga ciki din har in haihu tana son in fice daga gida gaba daya. A sa masu tsanar junan su ta daina burge shi yaji komai sunan ta aka kira a gaban shi ya tsane ta suka baje mai kudi ya basu iya sanin sa sukai godiya suka fita yace sati daya ya bata zan bar gidan nan kafin sati ya cika idan aiki baiyi ba zai bata kudin ta . Jikina tsuma suka bar wurin arnen da farin ciki don zumudi ko gidan madam bata samu komawa ba ta wuce gida don fara aiwatar da abinda arnen yace tayi. A dai dai lokacin ne kuma muke zaune a dakina da maryam take tambayana ko na aiwatar da abinda anty Salbiya ta bani inyi. Nace kai maryam ni fa yanzu komai ya fita min rai wallahi irin abubuwan nan ni ba cika son su nake yi don ba yarda nayi dasu ba. Wani kallo tayi min tace amma ke din nan to ki sani samu yaci annabawan Allah balle ke din nan khadija idan kina tashi tsaye ki tashi tun kan dare yai maki a gidan nan don wanan matar ba zaune take ba akan ki. Nace taje tai tayi mana indai mijine gata gashi ai tayi ta kayan shi kai maryam ta girgiza tace lalai ba banza kila ta barki ba. Nace kai maryam har kina ban dariya wallahi nifa duk abinda zatayi taje tai tayi ina kaya suke maryam ta tambaya nace suna a cikin jakkar da na fita dashi ranan har yau ban cire su a ciki ba wallahi. Miko min su nan idan baki so nace kwasa duka ki ta kaya don Allah dauko min to nako mike na dauko mata ta duba sai naga ta falke ledan wanan hayakin ta mike boner din saka turaren wuta ta dauko a falo ta dawo kuryan ta turara min har yana hawa min kai sosai. Nace gaskiya maryam ke ma shuumace dama anan zaki saka kikace in baki zaunar dani tayi ta fadakar dani sosai akan zamana da nafisa din a gidan har sai da jikina yai sanyi sosai. Nace in Allah ya yarda yau din nan zanyi amfani da sauran ni da sabulai da na gyaran gashi kawai nake amdani dasu wanan din wagalan yi nake gani gare su. Da dare bayan na gama komai a gaban maryam nayi amfani da komai yadda tace inyi dasu don a gidan maryam zata kwana tare damu. ZAINAB IDRI MAKAWA SEENABU 1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Madam zaune a dakin Nafisa sun baje suna shan ferfesu da aka sayo masu don ko tace su Samiha su dafa yanzu da take da cikin nan sai ta dinga jin karnin shi a bakin ta. Madam tace wai shi wanan mai auren budurwan dai yau kwanaki sun kusa cika naji shiru mana . Nafisa tace au kin dauka mu din na wasa ne ai wasa yake damu wallahi don haka zata bar gidan nan batare da ya san yar iska diya mace ba. Dan bakar da na dana ma shegu na nan dam na aikin shi har yau dan yadda na daure su ko kallon yar iska da sha,awa bai iya. Dariya suka sa madam tace aini na kosa inga yadda yar iska zata bar gidan nan ranan insha dariya don Allah da an fara ki kirani inzo insha kallo. Ai tafiyan nan da yayi kwana biyu ne ya kofsa muna da yanzun kila ta dade da ficewa gidan nan kema Nafisa wani lokaci akwai ki da sanya wallahi ai da tun yana nan kikai ta masu overdoze din shi wallahi. Samad akwaishi da shegen wayau wallahi ko ranan ina hayaki ya rutsa ni sai da na wayance mai da fadin turaren maiduguri nake bulawa gida. Kin san ina ganin ganeni yayi sai dai baiyi magana ba don shi haka yake bai faye saurin magana akan abu ba da sauri.. Nan madam ta kara kitsa mata yadda zatayi abin yai mata aikin sauri ba tare da bata lokaci ba tace ai da ya dawo za,ayi ta ta kare gidan nan. Daddyn mu ne ya kirani awaya yana sheda min alherin da AA yai masu na alheri tunda daddyna ya fara bayani ban iya magana ba shiru nayi ina sauraren shi. Ajiya zuciya na sauke tare da fadin bai fada min ba daddy bai sanar dani wanan alherin da zai maku ba. Daddy yace haka ake so khadija biyayan ki ne ya kaimu ga haka ai idan baiji dadin zama dake ba hakan ba zai samu ba kidai muna godiya don Allah sosai a gurin shi. Mun gama waya da daddy ina mamaki a raina yadda AA yai wa iyayye na alheri bai sanar dani ba duk da daure mai danakeyi a kwanakin nan . Gashi yanzu bai gari sun tafi jos wani aiki filin gwaunati da yace zasuyi acan kwana biyu kafin ya dawo wanan godiya ba awaya ya dace in mashi shiba sai idan Allah ya dawo dashi lafiya. Yau tunda na tashi banjin karfin jikina tun cikin dare zazzabi da amai ya damay ni sosai har washe garin ranan monday din gashi zamu fara exam a ranan. Dole haka na daure na fita na rubuta exam din cikin rashin walwala na juyo na dawo gida a falo na zube maryam da ta fito ta kirani nace da ita gani gida kwance banda lafiya. Hankalin maryam ya tashi cewa tayi gata nan tafe hankalin laraba ya tashi sosai sai amai nake kwarawa a gurin. Maryam ta shigo fitowan ta ke nan daga gurin exam bata je hostel ba ta wuto gidan daga school. Tana zaune ta tsura min ido wayana dake gefena yai kara har ya katse ban iya dagawa ba wani kira ya sake shigowa again da kyar na amshi wayan hannun maryam da ta dauka tai recieving tana fadin AA ne fa. Da kyat na dauki wayan na kara a kunne na da sallama da kyat shima na iya yi don yadda nake a galabaice kasan ties din falon. Yadda yaji muryana yasa yace da sauri Deedar lafiya kike kuwa kafin in bashi amsa wani amai ne yazo min na mike da sauri don zuwa yi a toilet. Maryam ne ta dauki wayan tai mashi bayanin halin da nake ciki yace please maryam ki taimaka kuje asibiti zan ma driver waya yanzu yazo ya dauke ku. Ba a jima ba driver yazo muka fita zuwa asibitin Nafisa dake daki har labari ya samay ta dariya tayi tace wa Yanyala kilama mutuwa zan yi don ta hadani da wani katon bakin arne ne yai min aiki. Dariya suka sa a lokaci daya Yanyala tace ita dama zamana a gidan yakai mata ko ina tana gudun inzo watarana in fara zama wani abu a gidan. Yadda jikin nawa yake yasa dole aka daura min ruwa sai dai sunce ba kwana zanyi ba idan ya kare sunga yadda jikin yayi zasu iya sallamana inda sauki. Yana jos ya matsa ma Yusuf sai su taso ranan da sauran abokan tafiyan shi dole suka kamo hanya dawowa Abuja din ba shiri. Barci na samu sosai nayi da aka samin drip din tunda na falka around five na sake mayar da barcin sai yanzun da na falka kuma lokacin tara da wani abu na dare. Tsaye suke a kaina shida Yusuf da wani daya da ban san shi ba sai laraba da yaran dake zaune a gefe na tayi tagumi maryam kuma tana shigowa dauke da kulan abinci daga kofa. Dan murmushin karfin hali nai mashi tare da fadi da kyat yaushe ka dawo ne ? Yace yanzun muka iso khadija ya jikin naki nace da sauki cikin rufe idona ina yunkurawa kamar zan tashi da sauri suke hada baki gurin fadin yi a hankali fa akwai ruwa har yanzun a hannun ki. Kallon hannun da yai min nauyi nayi na mayar da idona ga sauran ruwan daya rage saura kadan ai Yusuf yace. Maryam AA din ya juya ya duba tare da tambayan ta mai likitan yace yana damun ta ne ? Tace Allah dai ya rabasu lafiya tace mai tana dariya Yusuf ne yace da ita kina nufin aure yai albarka ke nan dai tace insha Allahu ciki har ya girma haka. Hararan ta nayi na lumshe idanuwa na cikin jin nauyi da kunya daya rufe ni a lokaci daya tambaya ya sake mata da cewa shi likitan ne ya fadi haka maryam ? Yusuf yace muje mana muga likitan zaifi sauki ji a bakin shi suka juya zuwa wurin likitan tare da maryam da tai masu rakiya. Likita yai masu bayanin yadda zasu gane yake sheda masu stress ne yai min yawa sai dan maleria da ya kamani amma sunyi min alluran maleria din insha Allahu zan samu lafiya ko yanzu idan ruwan ya kare zasu iya tafiya dani gida. AA yace wa likita da sauri da dai an barni har zuwa gobe a gani likita yace ba damuwa zamu iya komawa gida ai. Sai sha daya saura muka dawo gidan har shi don sai lokacin Nafisa tasan da dawowan shi garin. Da yake ba nice da girki ba a ranan muna shiga muka rufo kofan part dina daki na shiga nayi wanka na fito ban jima ba zaune na kwanta sai safe. Koda gari ya waye maryam da laraba suna kitchen har lokacin ban iya fitowa ba gashi dole in shiga school don exam din da nake dashi ranan. A dakin ya samay ni kwance ya tako zuwa bakin gadon da nake kwance idanuwa na suna a rufe jin an shigo dakin na bude idona. Sai da ya zauna yake tambayana jikin tare da kura min idon shi a kaina nace naji sauki ina son shiga school in anjima don ina da exam yau. Haba Deedar ciwo fa ya kawar da komai a yadda kike din nan har kina tunanen wani yin exam can a ran ki. Banson in missing din wanan exam din don muhinmancin shi a gareni bansan may zakiyi da karatun nan ba haka da har kike son wahal min da baby na haka akan wanan karatu. Dan harara nakai mai nace da abina kuka ganni don haka ku barni in karasa don Allah na hada da kalman roko gare shi saboda kada ya hanani. Yace shike nan amma sai idan kin kara jin sauki zuwa anjima zan kaiki don ina gida yau zanyi jinya baby na tare da ke yana kokarin cusa hannun shi a sanan cikina . Nace wai wa ya fada ma cikin gareni don Allah na fada a shagwabe ina kawar da kaina gefe daya dan murmushi ya sauke yayin da hannun nashi ya sauka saman cikin nawa yace. Yanzu Khadija kin kyauta min ke nan da kika ki sanar dani zancen ciki nan har saida ya girma haka naji gun wasu ? Yana kokarin juyo fuskan shi gare ni nace to ni may kake son in fada ma akan haka tunda bashi ne na farkon ciki a gidan ka ba. Amma a wurin ki shine farko ai ko don may ba zaki sanar dani wanan abin alherin da ya samay ni ba muyi farin cikin shi a tare. Nace nima bansan da cikin ba sai zuwan mu kadunan nan ne hajiyan ka ta fara fada min a gurin ta na fara ji. Yace serious har hajiya ta sani ni ban sani ba ashe zancen da take min ke nan ban fahince ta ba ranan da take fadin kina bukatan taimako a yanzu shiyasa ta bamu laraba muzo da ita. Nace ashe kuma alherin da ka aikawa su daddy ke nan ranan sun bugo min suna sanar dani an gode Allah ya karawa arziki albarka yace amin yana ja min hanci na. Tare da fadin ba sai kin min godiya ba deedar don nima yanzu iyayyenane su yanzun dai ki kwantar da hankalin ki ku rage yawan fitinan nan ki renan min cikina cikin koshin lafiya don Allah. Nace cikin dan marairaice murya na ai kasan ni ban shiga alamarin kowa a gidan nan sai dai idan an tabani ne ban kyalewa. Yace yanzu ina rokon ki da ki kyale don ni deedar ina matukar son haihuwa a gidana sosai yasa kikaga ina kafakafa da ciki jikin Nafisa ma. Banyi magana ba shima shiru ya dan yi a inda yake zaune muryan Nafisa ne a falona tana fadin wanan wani sabon cin amana ne ya dauko komay a gidan. Mikewa yayi zuwa falon inda ya samay ta tana sababi yace lafiya may ke faruwa ne wai ? Tace nifa gaskiya ba zan yarda da wanan halin ba ka shigo dakin wanan ka dauki lokaci haka a ciki kansan kuma nice da girki wani rainin hankali kake son ka jawo min a wurinta ko may ? Har kuna wani shigewa kuna shiru a haka wani lalashin ta zakayi a daki tunda bata da moriya a gurin ka sai ci takai a masai. Mamaki ya kama shi sosai yace wai nafisa wanan wani irin kishi ne haka harda bata da lafiya din ban da halin in zo in duba halin da ta kwana ke nan ? A wurin ki ne kila bata da mori a wurina kar kiyi mamaki inkinji irin moriyan da take min tabe baki tayi tace banda abincin da take girka ma kana ci kana santi wani moriya take ma bayan shi. Zaki gani da idon ki idan lokacin haka yayi yanzun dai ki fice mata a shiya tunda ke baki da tausayin gaida mara lafiya idan yar uwarki bata da lafiya. Yace ni dana jawo mata rashin lafiya aikin ga nazo in duba abina ko don haka ki fice muje kada ki damay su da surutun ki. Gaba ta sashi suka fice kamar yaro suna fitane maryam ta shigo dakin ta kawo min tea na tashi na dan sha kadan mikewa nayi ina zufa na shiga wanka don gudun kada mu makara. Hakana na daure na shirya muka tafi school cikin yanayin rashin jin dadin jikina ko a mota sai korafi yake min nashi fa kada inje wani abu ya samu cikin shi. Nidai ban iya magana ba sai kaina dana dora saman glass din motar ina sauraren shi da kyat na gama ranan sauki na daya banda wani exam kuma sai wani monday. Shi da kanshi yazo ya dauke ni muka koma gida ban iya komai kwana biyu naji jiki sosai na samu na murmure namike tun lokacin kuma ban kara jin komai ba tare dani. Na murmure nayi wani irin fresh dani kyau na ya kara fitowa farina yayi wani fau kamar wata halfcas dani. Damun kebe dashi zai shiga yaba irin kyau din dana yi a lokacin yana zuzutani irin na maza masu mata biyu zuwa hudu yadda suke wa mace idan suna su kadai. Sai na lura ko a gabankowa muke dashi zai bini da manyatacen kallon shi yana mamaki irin canzawan da nayi wanda dagani sai maryam muka san sirin abin. Ga wani ni,imtacen kamshi da nakeyi koda kuwa na bar guri ne zai dade yana bada kamshin jikina hakan na yawan haifar mai da kasala . Wanan kamshin ko may yake dana ratso zai dago yakalle ni duk abinda yake zai iya dakatar dashi a lokacin . Gulma haka su yanyala suka kai mata haka yasa ta zauna ta kula da abinda ke wakana a tsakanin mu ta sa ido ta gane ma idon ta fitina. Ranan sunyi tashin hankali dashi sosai a gidan ranan suyi tujara a cikin dare ni dai ina part dina gashi ana batun fara azumi a washe garin muna ciki muna shirin abinda zamuyi sahur dashi. Sai da suka gama ne ya shigo dakin namu ina zaune a kasa dogon rigan body hock a jikina rigar ya kama jikina daram ya fitar da suran jikina a waje dan cikina ya baiyana a fili kaina ba dan kwali baida kitso na daure shi a baya. Daddy yayi barci yayi filo da cinya na sai da ya kalli inda yaron yake kwance yace dani wanan ai sun maki nauyi a jiki ko ? Nace barshi so nake barcin shi yai nisa yanzun ya gama min fitina kallon yaron dake barci yayi yana makale da goran bobo da yake sha yai barci. Dukawa yayi ya dauki yaron zuwa saman kujera ya shimfide shi tare da fadin zanga yadda yaran nan zasuyi idan sun koma wurin uwar su duk kin bi kin shagwaba su yanzu da riritawan ki barci ma sai yaro yayi a jikin ki. Dan murmushi nayi nake fadin haba dai kamar daddy kuma za, a ce wai an bata duka shekarun sa nawa a duniya. Yanzu dai may kike kuma a zaune haka nace haba yaya kasan fa azumi za a dauka gobe kuma ma kaida ke can kuma sha,anin ku da matarka falo. Ya harare ni tare da fadin niba shirmay na tambaye ki ba idan kin gama kizo ina jira ki a ciki yana shigewa bed room dina nace na dauka ai an hanaka shiga nan idan ba nice dakai ba. Aiko bai karasa shiga ba sai ga Nafisa a dakin ni dai ranan naga masifa saidai duk fitinan ta idon ta yana akaina yadda nake zaune da kammanina take kallo. Da kyat taga safiya tun da safe gidan madam ta yiwa tsinke madam dake barcin safe na masu azumi take kwalawa kira. Dole ta fito a gigice daga dakin ta zani na sabule mata tana fadin lafiya Nafisa anyi mutuwa ne komay naganki haka. Madam ai da mutuwa akayi min nasan maishi ya tafi ke nan ko madam ta kara tambayan ta ko aikin mune yaci tace don Allah madam bar wanan shirmay naki yanzu ki saurare ni. Mu zauna tace mata tana nuna mata kujera tun kan sukai zaune take fadin madam jiya banyi barci ba wallahi ina Allah Allah gari ta waye in zo nan. Ki tayani duba madam yariyar nan wai bata da aljannu kuwa don ni abinta yana ban tsoro wallahi kinga yadda yarinya take nema ta zuzutani nida gidana kuwa. Madam ina yi kamar banyi nan dai ta koro mata komai madam tace bari tai wanka taje gidan don ita bata fahinci wanan zuzutawan da nafisa ke nufi ba. Ina daki sai ga Samiha wai inzo ga madam tazo gaida mu mu gaisa nace yau madam ta saba zuwa da za ace in fito mu gaisa tafice taje ta fada mata. Zuwan anty hauwa yau kenan na farko gidan mu tazo dubani da jiki ita da anty Salbiya sun kawo min tsaranban tafiyan da sukayi. Mun dan jima a dakin muka fito na raka su kafin in dawo su na falo a zaune dukan su ina shigowa idanuwan su a kaina ya sauka. Na wuce ciki rike da hannun daddy dake biye dani kamar bindi shiga madam tayi sauri mayar da hankakinta ga Nafisa tana fadin shike nan kuma yanzu Nafisa kun zama daya da wanan yariyar a gidan nan. Tace don ta sauya shine zama mu daya da ita ko may tace kina nufin baki ga abinda na gani ba komay kuna gida daya da ita. Tace nifa har yanzu ban fahince ki ba madam ki fito fili ki magana yadda zan fahince ki tace bakiga abinda idona ya gano ba ke nan . Ban gani ba tace mata cikin rike habanta tace nafisa ai ciki ke ga amaryan ki tsoho ko don har ya tasa sosai gashi a na gani a filin Allah. Madam ci may tace wallahi ciki don ko ba gizo idona ke min ba ciki na gani a jikin ta yanzun tunda nafisa ta dafe kirjin ta maranta ya yanka bai daina ciwo ba sai gaba abu ke mata wasa wasa duk suna kanta. Har aka kai ga kiran mijin ta yazo suka kwasa zuwa asibiti can suka rike ta don sunce cikin bai isa haihuwa ba a lokacin. Bata san inda take ba don drip di ruwan munje gaida da ita da laraba har lokacin tana barci bamu zauna ba muka dawo gidan don an kusa shan ruwa. Sai da tai kwana bata san inda take ba ta falka washe gari sai dai har yanzu da damuwa a ranta sosai farkon maganan ta shine AA na shigowa tace dashi baya ya gasheta. Samad ciki ne ga matan ka komai sai a lokacin ya gane asalin ciwon ta yace cikin wayan cewa ciki kuma wata matar tawa wai kike nufi.? Ajiyan zuciya yaga ta sauke ta mayar da idanuwan ta ta lumshe bata kara budewa ba saj da ya fita daga dakin Yanyala dake zaune gefen ta ta tambaya a cijin yare ko ta ga ciki a jikina itama. Yanyala tace ita dai taga na sauya mata ainun ba kamar yadda nake ba a baya ko cikar dakine nayi hakana itama bata sani ba gaskiya. Fada ta hau yanyalsn dashi wai dama haka suke basu mayar mata da hankali kan abu har sai abu ya lalace hakkuri ta shiga bata a wurin sai da ta gaji tayi shiru. Samihace ke fada mata wai ai mun zo dubata tana barci fa kuma hausu da fada don may suka bari na shigo inda suke tai masu fada sosai a wurin . Har da fadin su basu ganin laraba iya inda na tsayar da ita take tsayawa bata gusawa a gurin dana ajeta idon ta na saman aikina. Kwana biyu tayi asibitin ta matsa zata dawo gida aka sallamay ta ta dawo zuwa madam tayi tace anya babu hannu ga wanan matsalan naki. Tace na dade da sanin haka madam ina kuma kokarina ga hakan wanan shegiyar badon nafi karfinta ba ai da yanzu ta halakani gidan nan don da karfi ta shigo min gidan nan. Ko mafalkin ta zanyi ba mai dadi bane gareni shiyasa kike ganina tsaya kyam a kanta kamar layan wuya . Madam tace kinyi bincike akan cikin ne a jikin ta ko kibane tayi ido ta lumshe tare da fadin na binke shi yace bai san da zancen cikin ba. Zai fada maki gaskiya ne kike tunane ko may namiji ai makiri ne kila ma dashi aka hada baki a rufe maki kada ki sani ki dauki mataki tun farko. Yanzu isan ya kosa ai ba wani abinda zamu iys sai dai idan ta haife mu illanta diyar ko dan cikin wani murya tace don Allah madam kibar wanan magana don ma ba cikin bane ni dana daure su daga shi har ita ina wani zancen ciki kuma zai fito gare ta yanzu. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Azumi da kwana goma Nafisa ta haihu lokacin muna gida mun fara hutu hayaniya dana ji cikin ji muryoyin su, kamar waka a falon, yasa ni laikawa waje. Ashe itace ke labour zasu asibiti suke addua hakana banyi gigin zuwa inda suke ba na dai yi mata adduan Allah ya raba su lafiya. Diya ce mace aka fitar mata sai dai kuma yar tazo da lalura don haka hankalin kowa ya tashi saukin abin uban yar na da hali tun tashi farko sai da ya zube kudi masu yawa aka fara mata amfani dashi. Mu dai samu labarin ta haihu don da farko theater aka tashi mata sai Allah ya kawo saukin abin ta haife da kanta a cikin sauki. Maryam ne tazo min da labarin halin da ake ciki na matukar tausayawa baby da iyayyen ta acikin dan lokacin kankani na shiga damuwa a raina. Ban ko tsaya mamaki ina maryam ta samu wanan labarin ba sai halin da yarinyar ke ciki nake tausayawa. Haihuwan safe ta yi don haka ranan tun fitan su da safen ban kara ganin AA ba yana asibitin gurin su sai bayan sallan la,asar ya shigo part din namu. Lokacin mun rarage girkin da zamuyi don shan ruwa ya shigo falon da sallama a bakin shi na dago kai ina amsa mai sallaman tare da mashi sannu da zuwa. Sai da ya kai zaune ya amsa min tare da tambayan ya muke nace da Alhamdullahi laraba ta fito kitchen ta gama gyara min zobon da zan hada muna na shan ruwa tace Babangida barka da arziki ashe an sauka lafiya. Yace barkan mu dai laraba ya gida ya aiki kuma yanzun ma na dawo ne ko zan samu ai min kunun tsamiya in buda baki dashi. Kallon mamaki nayi mai da abinda naji yace din sai naga duk ya fada min a lokaci daya daganin shi kasan yana cikin tashin hankali. Laraba ta kalle ni nace akwai sauran garin ai bari tashi in dama mai ki huta don tasan nafi son in girka mai abinda zaici da hannu na ban son wani yai masa. Nace bari idan na tashi zan dama mai yace ok nace mai barka fa ashe an sauka Allah ya raya muna yasa dadin musulmine yace amin sai dai yarinyar bata da koshin lafiya haka tazo da lalura. Subbahanallah nace da sauri tare da tausayawa ga maganan nan na jero mata adduan samun lafiya ga Allah yace amin tare da fadin. Likita yace kila sai an fita da ita waje a acan kila a samu nasaran mata surgerier don matsalan da abin ke da. Nace Allah yasa a dace yace amin yana dagawa daga inda yake zaune din a kasalance ya nufi hanyar fita part din cikin damuwa. Ya dade da fita ina a inda ya barni zaune cikin jimamay maganan da ya fada min din laraba data zo ta zauna baya fitan shi tace irin wanan abin ishara ne ga mutum wani lokaci. Sai dai yanzu uwar daki na karshe akan ki maganan zai dawo don kin san ance mai kishiya bata mutuwar Allah dama. Nace ni may ye nawa a ciki kuma mama tace kin manta da halin matar gidan nan ne da rashi yarda da Allah bata san kadara ba fa irin su. Nace hakane fa mama maganan ki dutse wallahi Allah ya gani banje ko ina ba akan ta balle yar da bata ko zo duniya bna Tace ai zama da irin matan nan sai su bace su batar da na tare dasu don shirka da yai masu yawa yanzun haka wurin shige shigen ta da tsohon ciki taje ta hadu da gamon ta can Allah ya sauwaka nace na mike zuwa kitchen do dama masa kunun da yace. Sai da na dora na jira ya tafasa na dama na na zuba mai a jug gundun kada ya huce duk da lokaci ya karaso sosai na shan ruwa. Daga kitchen na fito zuwa part din shi na gyara mai ko ina tunda yau ni kadaice a gidan dole aikin komai nasa ya dawo kaina. Duk da dama ita ba wai tana gyara mai part din bane iyakan ta ta kwanta ta tashi shike nan nata girki ma ba kullun yake samu ba sai idan tana da bukatan yaci wani abu ne zata sa a girka mai ta barbade shi da abinda zata sa mai shi kuma ya lamshe cikin rashin sanin kai. Zaune suke shi da Yusuf wanda tunda aka fara azumi a tare suke shan ruwa yanzun ma daga asibiti suka yo nan tare don buda baki. Da sallama na isa gurin su suka amsa min gaida su nayi da shan ruwa tare da kara tambayan su ya mutanen asibiti sukace da sauki. Yusuf ne yace kanwata kina yin azumin nan akai akai ga lalurar ciki kuma ki dan sahirta ma ki dinga dan hutawa ko kwana bibiyu ne mana. Murmushi nayi ina kaiwa zaune nace banda matsalan komai yayana bari kawai in bi sahun jamma,a in sauke nauyin shi a kaina. Yace na fada mata bata jin magane na yanzu kinga inda rashin jin maganan Nafisa ya kai ta taja wa yarinya wahala don rashin tausayi. Amma ai kaji ita basu yarda rashin kulane kamar yadda likita ya fada ba ya jawo haka ita ba dauka take wai wani ne ya sa mata hannu kamar wai sheri akai mata na sihiri. AA yace kyale ma haukaciya naji duk haukan da take fadi ai, yau aka fara haihuwan diya da wanan matsalan haka. An fada mata ta yi bedrest don ciki ya samu ya tsayu yarda ake so amma matar nan ta tayar da hankali wai ita gida zata dawo ta dawo gidan kuma bata zauna ba kullun tana cikin yawo in ma wani abune ai ita tajawa kanta shi wurin bakin yawace yawacen ta na banza. Tunda ya fara magana nayi kasake tare da tagumi ina sauraren shi tare da son in gano wani matsala ne ga yarinyar har yanzu banji sun fada ba. Kin ci wani abune da aka sha ruwa naga baki debi abincin kin ci ba tundazun yace min yana kallo na sai lokacin nayi ajiyan zuciya nace wallahi tausayin yarinyar dai nake yi a raina. Yar jaririya tana wahala irin haka abin akwai ban tausayi sosai wallahi Yusuf yace indan an bi yadda likitan yace ai ana iya mata aikin kan da cibiyar nata insha Allahu. Wani irin tsoro naji har cikin raina ya mamaye ni sai nake ganin nima wata kila haka zan haifo abinda ke cikina da matsala din kamar yadda nafisa ta haifi nata. Sun kula da yadda na shiga damuwa a lokacin Yusuf ne ke fadin kada fa wanan abin ya tayar maki da hankalin ki yanzu ki jawa kanki wani matsala kuma. AA yace tambayan ki nayi kinci abinci yanzu ko kuwa idan baki cin abinci fa zan dakatar dake ga azumin nan tunda Allah da kanshi ya sawaka ma mai irin laluran ki yin azumi. Yanzun zan je in ci na basu amsa ina kokarin mikewa tsaye jawo plate yayi ya fara zuba min farar shimkafa da kayan hadi ya turo min gaba na yace zauna nan kici in gani. Dole na fara ci kira ne ta shigo a waya shi ya dauka banji may ake fadi ba sai dai na fahinci Nafisa ce akan layin tunda ya kasa kunne sauraren ta yake baiyi magana ba. Sai data gama yace nafisa so kike nima in fadi da ciwo ne komai ina yanzun nabar gurin naku da zaki ce nazo gida na zauna na manta daku. Kashe wayan tayi naga yabi wayan da kallo sai Yusuf ne yayi dan murmushi yace ita matsalan ta ke nan idan abu yazo bata binsa a hankali. Wayan yake kallo baiyi magana ba sai dai yanayin fuskan shi daya nuna bacin rai karara a lokacin ya gama kallon wayan ya dago ya kalli Yusuf din yana fadin. Idan ka gama muje muyi sallah daga can sai mu wuce tace wai likitan yazo yana nema na yanzu. Yana fadin haka ya mike tsaye dama ba cin abincin nake yi ba tunda nayi cibi uku naji ya fita raina bazan iya ci ba yace ki tabbatar da kin cinye wanan abincin kai kawai na gyada mashi. Sun fita na tatara kayan gurin da sukai amfani dashi na kwaso zuwa kasa ina shiga dasu laraba dake zaune ta taso zata karba nace mama barshi ki zauna ki huta ke ma hakana. Juyawa nayi na fita zuwa kwaso sauran kayan da na bari sai ga samira yar wurin nafisa babbban tace anty akwai abinci a gurin ki ki bamu yau basu girka muna komai ba suna asibiti kuma an rufe store din. Akwai abinci nace mata tare da tambayan ta da ku nawane kije can mama tana ciki ta zuba maku na wuce zuwa sama sauran katan da zaiyi amfani dashi idan ya dawo na sa a dakin na sauko kasan . Na samu ta karbo abincin suna zaune su hudu a falo suna ci ban tanka su ba na wuce abina zuwa part dina mama zaune da yaran suna kallo Affan ya tasa fruit's a gaba yana sha. Sai dana tsinki aya daya na zauna ina barewa naji laraba tana fadin kudai yaran yanzu baku da tadan abinci idan dane ai ba zakici wanan ayaban ba don cewa ake yana saka turken yaro yayi tauri cibi yaki faduwa da wuri. Da sauri na mikawa daddy ayaban dana bare din ya karba duk da ban fahinci maganan nata sosai ba sai dai banci din ba. Tace waini wani irin lalura aka haifi yar dashi ne na sauke ajiyan zuciya ina fadin mama ban tambaya ba don gudun magana. Saidai ina ganin matsalan a kaine da cibin da kike magana yanzu a yadda na fahinci maganan su sunayi shida Yusuf yanzu. Allah ya sauwaka tace tare da fadin Allah yasa wanan abin ya zama mata ishara ta daina halin banza nace amin . Gobe idan Allah ya kaimu ai zamu shiga mu gaida su duk da dai nasan zuwan nawa wurin ba zata so shi ba amma ai dole in lekasu ko dan mijin ta kada yaga rashin kyautawa na ko mama ? Tace kwarai kuwa yar nan ai ba don ta zakiyi ba don Allah zakiyi da mijin naku amma in don itace ai ba kya je ko ina ba wallahi. Waya na dauko ina kiran maryam nake fada mata da safe idan tana da lokaci ta shigo muje asibiti mu gaidasu. Khadija ke baki da zuciyane komay matar da za, a ja gayarwa taiwa mutane tijara zaki ce mu koma gaishe ta kuma. Nace maryam ba don ta zanje gurin nan ba kin sani saboda Allah da mijin mu zan tafi don kinga rashin zuwa na bai dace ba gaskiya tace sai kin dawo ta kashe wayan ta barni da kallon wayan a hannu na. Bai dawo ba ni kuma nayi kwanciyana a part dina saida asuba na shiga na tayar dashi don sahur saboda nasan ba zai kwana dai a can ba. Fada yai man na rashin zuwana dakin nace baka nan dawa kake son in zo inzauna anan ka dai so dora min laifi ne. Na fito na barshi a dakin bayan na gama hada mai abinda zaiyi sahur din dashi yana bandaki na fice part din. Nayi masa hakane don yasan abinda yayi din bai kyauta min ba don ya gyara saboda har sha biyu da rabi ya wuce muka kwanta da mama laraba bai dawo gidan ba har lokacin. Idan kuma na kyalesu ga sanin halin Nafisa da nayi don burin ta shine taga ta kuntatamin ta ko wani hali a gidan. Washe gari da safe sai da muka gama gyara part din mukai waka muka kwanta har lokacin yaran na barci basu tashi ba yasa muma muka kara kwantawa bayan tanadar masu abinda zasuci idan sun tashi din. Sun sake jiki sosai dama karamin ne ya so yai fitina daga baya kuma ya daina ya sake jiki sosai dani ga kuma mama laraba da tun farko sun bude ido da ita akwai sabo a tsakanin su sosai. Ina cikin barci muryan maryam ne ya falkar dani daga barci tana fadin iyyeh kin hanani barci akan wanan bakar kishiyan taki ke gaki kina abinki hankali kwance. Idona bude da sukai min nauyi ina fadin ai na dauka baki zuwa din tunda kin fadi haka takai zaune a bakin gadon tana fadin. Ai ba don ta zan je ba don AA din ki ne kawai wallahi saboda mutuncin dake akwai a tsakanin mu da banje wurin yar iska ba yanzun dai ai taga ishara akan ta bakin halin ta ya jawa yar cikin ta matsala dama irin su a haka suke ganin abinsu. Allah dai ta sawaka nace da ita ina kokarin mikewa zaune nace ai jiya mama ta lurar dani wani zance maryam nan dai nake fada mata yadda mukayi da laraban. Tace ai dama kema kin san abinda zai biyo baya ke nan ga zancen din dauka suke kowa haka yake kamar su ai ke dai yanzu ki kula da addua Allah ya sauke ki lafiya. Nace ina yi maryam ke nima auren dai matsala ne wallahi yanzu shi yasa nake tausayin yan mata idan suna rawan kai wai su zasuyi aure kiga yarinya yanzu ba kunya tana fitsara. Tace rashin sanin ciwon kaine mana tunda hankali bai kai ba sai idan an shiga ido ya raina fata kuma don mazan yanzu ko wata ba a rufewa za a fara saida hali idan kuma ka samu kishiya tace dawa Allah ya hada ta bada ke ba irin naku din nan. Wurin wardrobe dina na nufo na fito da wasu material da zan saka a jikina tsab na shirya a cikin su ni kaina nasan kayan sun matukar karban jikina. Tace gara da kika saka kayan nan don nasan yanzu gurin nan kamar kasuwa da a bokanta yan duniya irin ta. Waya na dauko na kirashi ina fada mai zan fita yace ki jira driver yazo yanzu ya kashe a yadda ya amsa min wayan yasa na fahinci a gaban Nafisa yake a lokacin. Don idan suna tare muna waya dashi yanzu ina ganewa ga yanayin da yake amsa min wayan daban ne da idan bata a kusa dashi. Bamu dade da jira ba driver ya iso yace mu fito tare da laraba da yaran muka nufi asibitin gida tsit kamar ba kowa a cikin sa. Maganan mu ya zama gaskiya don muna zuwa driver ne yai muna jagora dakin da suke tun daga nisa muke hagon su sun sako idanuwan su akan mu. Canjin yanayina gaba daya ya basu mamaki don zakace ko baturiyar asalice tayi shigan hausa yadda komai nawa ya bude a lokaci guda ga traning din anty Salbiya da anty Hauwa na aiki. Nayi masu kwarjini sosai a idon su yaran da mama larabane a gaba suna bin driver sai ni da maryam a baya da muka jero tare muna magana. Gab da zamu shiga dakin ne wata buzuwa da ban santa ba take muna magana tana fadin ba,a fa barin kowa ya shiga daga nan ake mika masu gaisuwan su. Ni kan mamaki nake na yadda naga yan yaren su a gurin da yawa haka ashe suna da hadin kai ne haka sosai nan dai gasu madan dasu sabuwa a gurin su ma. Tsayin mu yayi daidai da fitowan Yusuf ciki yana ganin mu ya washe baki tare da fadin a kune tafe ashe ku shigo mana ko suna ciki AA din ma yana nan yanzu muka shigo. Nace wa yan nan sunce ai ba a shiga inda suke ko yace akan wani dalili ba gaida ita kukazo yi bane mujen ku dan Allah ya fada yana fara tafiya muka bishi a baya. Ya tura kofan dakin da sallama muna biye dashi na hango AA ya zaune da hannun nafisa dake kwance a saman gado duk ta sauya saboda damuwa. Ga yar a kwance a gefen ta an rufeta da shorwel fari kallo daya nayi wa yar da sauri na kawar da idona shiko duk yai wani daburcewa da ganin mu. Gaida ita muka fara yi tare da mata barka da arziki tayi kamar bata jimu ba shine yadan matsi hannun ta yace bakijin su Deedar na gaida ke ne ? Ta dago kai ta kalle mu wani iri ta watsar tace kai ka san su don ni ban gaiyace su ba tunda nasan gulma ya kawo ai don suzo suga abinda ake fadin na haifa din. Murmushi nayi ina gyara tsayina tare da dafa gadon nace mu bashi ya kawo mu ba don inda sabo mun saba da wanan zuwa mukayi muyi maki barka kuma mu gaida babyn mu. Hannun ta ya sake ya nufi yar zai dauko ya bamu tace kabar min ya a inda take duk da take hakan tana ganin banson abina inson ta a hakan. Nace dama ka barta ai tana barcin ta, ke banda abinki ina kika taba ganin jujin yara kowa ya haifi da ai yana son abinshi ya haifa. Dauko yar yayi ya mikawa laraba ita tace yanzun ma zuwa kikayi nan ki karasa ta komay tunda baki so yar ta fito duniya tana numfashi duk da sherin da kikai mata tun a ciki. Ba laifin ki bane hakan da Allah kike son yin jayaya mu bashi ya kawo mu ba daidai laraba na mike mun yar kamar kada in karbe ta nadai sa hannu na karbi yar tare da fadin ubangiji Allah ya baki lafiya kinji. Na mikawa maryam sai sababi take muna muka mika mashi yar muka ce Allah ya raya muka juya yace wanan wai wani irin haukane akan yaran ma fada zakuyi ko may yarinya nata kanta cikin wanan halin. Tace idan haihuwa yana da dadi tayi mana mu gani na juyo ina fadin zaki gani idan muna raye kwana nawa ya rage inji maye . Haihuwa kan tunda ina tare da mijina ai yin sa zanyi da yardan Allah yadda kowa yayi shi kuma ki dai gani anayi nace yaushe kuma Allah ya fiki don dan zaki ya girma ko na nuna mata cikina na fita. Samad wai may yarinyar nan ke nufi ne da maganan ta yace abinda kika tambaye ta ne ta baki amsa da nuna maki mana tunda ke baki san yakamata ba. Kina cikin wanan halin haka har kinga wurin fada bazaki ji da abinda Allah ya jarabi mutum dashi ba wai kana nufin itama ciki gare ta komay yace baga shi kinga ta nuna maki ba. Kururuwan ta ne yasa yan wajen saurin shiga dakin hankali tashe suka samay su taci kwalan mijin tana fadin wasau maganga nu da bata san tana fafi ba a lokacin. Ya banbare hannunwanta daga jikin shi yana fadin wawiya mara hankali bazakiji da abinda ke gaban mutane sai kin jajibo wani fitinan kuma. Ita din ba matana bace da ba zata haihu dani ba komay da kishi zai rufe maki ido kina wanan hauka haka yanzu ai kinji ma kanki wani tashin hankalin tunda haka kike so. Samad Allah ya isa tsakanina dakai da yan uwanka yadda kukai min sai Allah yai maku shi kuma munafukin banza kawai azzalumi. Madam ne tayi mai magana akan yaiwa Allah ya fice daga dakin ya kyale ta yan uwanta buzaye kuma na magana a cikin yare suna fadin may ye haka take yi ne wai. Ciki ina bama zai yuyu ba wallahi tasan dai inda ta kwaso cikin ta take son kakaba maka kaiko daba kasan ciwon kan ka ka yarda dashi. Ya juyo a fusace yana fadin gada ki soma sheganta min cikin jikin matana don nike da abina ni nasan kuma zafin abina. Munyi dake ne idan na aure ta ban haihuwa da ita ko may ke da nake haihuwa dake fa madam ta samu ya fice dakin da kyat a lokacin mu har yusuf ya saka mun bar asibitin ko. Yafito a hasale yana fadin shine dalilin da kaji nace muzo wurin nan yanzu don sanin halin Nafisa da nayi don kada suzo ta nemi salwanta min wani cikin kuma ta gama yiwa nata ta,adi. Don Allah ka daina biye mata kuna haka mana AA a bainin jama,a tunda kasan halin abinka yace ina amfanin kullun a boye mata cikin jikin Deedar Yusuf ai gara ta sani idan ma mutuwa zatayi taje tayi wanan matar halinta ya isheni yanzu. Hakkuri zakayi ka san halin mata akan kishi yanzu wanan abin kunyan da take damay yai kama AA yace ita ta sani yana tsuki. Yanzun Nafisa kin tabbatar tun kwanaki nake fada maki ciki ne da yarinyar nan kika ce Samad yace ba ciki bane shi baisan tana da ciki ba a ina ta samo ciki. Ai yanzun dai kinji ga bakunan su ko madam tace duk da cikin ne mun tabbatar din ai mu kwantar da hankalin mu muga cikin to mujira hauhuwan shi mukagani mana. Damu take wasa ba har tana iya nuna wai ita mai ciki bane shi a dole ga mijin mai cikin fari a haihu din mu gani in shari ne ai kowa ya iya ko. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Tafiya muke a motar babu mai magana a cikin mu kowa da abinda zuciyar shi ke saka mai a lokacin duk mu a cikin motar sai maryam ne ta kawar da shirun da motar yayi a lokacin. Khadi tunda kuke fada da buzuwan nan a gabana baki taba burge niba irin yau mace haka bata san Allah ba ita. Ko wanan yar dake gabanta haka saye da naura bai ishe ta ishara taji tsoron Allah ba a zuciyan ta abinta ne fa Allah ya fara nuna mata. Laraba ne ta karbe zancen da fadi ai irin uwar dakina sune daidai da irin wanan matar ina fada kullun don macen da ke nuna masu tsoro sai su kara zama shedanu a gurin su. Ba karin abu muka gani a wurin taba wancan zaman da mukayi da ita da hajiya uwar gidan saboda ita sam bata da baki a gurin ta. Idan sun fara sai dai mu shige daki ba dama mu leko ko na minti daya yanzun zatace dawa Allah ya hada ta ba da mu ba. Ba girma ba arziki muka koma kaduna da zama don abin har yaso taba ta a lokacin sosai wallahi Allah dai ya gyara da yake iyayyen miji suna bayan ta ai da yanzu basu tare. Don gaba daya ta juya kan babangida ga kowa ko iyayyen sai da suka tashi tsaye akan shi don gaba daya ya juya masu baya ne a lokacin. Kowa yayi mamakin jin zai kara auren uwar dakina damaganan ya fito fili sai ana ganin ko ita ba zata iya dasu ba ai. Abin mamaki laraba na rufe baki driver ya karbe zancen ta yace ai ba karamin dadi naji ba yanzun da naga hakan don mun sha wuya a gurin wanan matar. Kafin ta fara tuka mota irin yadda muke fita daku din da zaran mun fita da ita sai mun sha fada a gurin oga ranan don sherin da zata kulla muna tace mun mata abu kaza. Shi kuma ya rufe ido yaci muna mutunci ido rufe a kan ta kuma fa ba gurin alheri mutum zai kai ta ba. Matar dake tambayan mu idan musan wurin wani mai asiri mu kai ta ko nawa yake aiki zata biya mu idan mun kai ta. Wanan mace ai shu,umace kwanaki akan oga yasa musa ya dinga kaiki school da yai tafiya Allah dai ya gyara ba a kore shi ba sai da muka bi ta kan oga yusuf muka kai maganan shi muka samu yai wa ogan namu magana aka barshi sai dai aka maida shi office. Kinga kuma zama office ba so shi muke yi ba don irin haka mutum yafi samu don idan anyi tafiya dakai ko aike wani guri zaka samu alheri dabaka zata ba a gurin shi. Mussanman ke hajiya da kowan mu ke son ace ya kaiki wani guri saboda Alherin ki da girmamawa a gare mu. Laraba tace komai akace tayi zata iya ba sheri a cikin sa don halin ta ne ake fadi ko ita hajiyan tawa tace ai ba kanwar lasa bace ita ma guri ne bata samu ba dai yanzun. Dariya driver yayi yace hajiyan can kan gaskiya akwai rowa ba abinci ba kuma kulawa a gare ta sai nakasa. Gaskiya yanzun kan muma muna fadin oga yakai ga mata kulun muna rokon Allah yasa wanan matar ta barki ki zauna a gidan nan don tsaye take a kan ki sosai yanzu. Emanuel yace min ya kaisu wani guri da wanan kawar nata bakar nan mai jiki ya je ya kai mata wayan da ta bari a mota yaji tsoron inda ya gansu kuma ya samu ana maganan ki a cikin bukkan da ya shiga. Muushi nayi daga inda nake zaune sai dai ban masu magana ba illa cewa danayi malam sani kaimu sahad don Allah daga nan mu dan yo sayayya a can. Nau,in kayan girki na gwagwani da na kwalba zuwa na leda na sayo don Azumin da muke ciki akwai yawan amfani da kaya da muke kai da kai. Gurin kayan yara na nufa na zabo ma yaran yan tufafi da takalma don na fara rage hanya sai yar baby daa nayiwa sayayya itama daga nan muka wuce wurin kayan sha dana ci muka dan taba muka fito zuwa gida don har da maryam can zamu tafi don anty ta bata gari. Maryam ne take cewa wai kina nufin har da yaran wanan matar kika sayawa kaya komay ? Nace maryam da yara nake kishi ko da uwar su gani nayi na sayawa wa yan kada yaga ban sai ma nata ba kin ga ba dadi zaiga na banbanta a tsakanin su. Shiru tayi batace dani komai ba har muka kai gida ta lura ban jin magana don duk maganan da suke tun farko ban tanka masu ba. Don irin yadda nake ji aa zuciya na ba dadi na farko yarinyar dana gani a cikin wani hali na biyu kuma zancen mu da Nafisa a asibiti yadda ta rufe ido tayi muna cin mutunci az bainar jamma,a kamar wace tayi cikin daba na sunna ba. Zaman mu a a falon bamu jima da zama ba na fara fitar da kayan da muka sayo muna kallo daidai nan ya shigo falon fuska a daure. Bin kayan dake baje a kasa yayi da ido sai kuma ya dago yana bi mu da kallo har lokacin fuskan shi babu walwala a cikin sa. Nima daure fuska nayi ban ko samu gaida shi da dawowa ba sai laraba ce ta fara mai sannu da zuwa tana kokarin tatara kayan dake gurin a kasa. Wuri ya samu ya zauna daga gefe haka yasa maryam dake daga kwance mikiewa zata shige daga ciki ya dakatar da ita da fadin zauna abin ki maryam ba wani abu bane ai. Ya joyu gare ni yana fadin Deedar may yasa baku da hakkuri ne dukkan ku kunje asibiti kuna sayar min da hali a gaban mutane da matan abokaina. Yaya AA nine ma mai rashin hankalin ke nan ba ita da mukaje gaiyarwa ba ta tare mu da bakar magana yace a fusace dukkan ku baku da hankali. Na gane ni kuke son tozartawa a idon duniya idan ita bata da hankali ke baki da shine don may ba zaki kyale ta ku fito bakin ku alaikum ba tunda kin san halin ta. Wani irin takaici da bakin ciki ya zo min a wuya ya tokare ina jin wani bacin rai na zo min kamar zan fashe. A cikin wani irin murya nace a fusace ni wanan abin ya isheni ya isheni wallahi kulun mutum shine mai laifi a furin ku baka ganin irin cin mutuncin da take min ko yaushe magana ya taso sai kayi kokarin dora laifi a gare ni. Gaskiya na gaji da wanan halin abin yai min yawa a gidan nan da wannen kuke son inji wai daga ciki ? Yace ni ba ruwa na da abinda ke a tsakanin ku mutunci nane ba zan yarda kuna zubar min a idon jamma,a ba ko yaushe. Idan ita bata da hakkuri bata dauki girman ta ba don may ke da ilimin ki zaki tsaya kuna irin wanan sai da halin akan titi haka. Yanzun dai nice mai laifin kake nufi ke nan tunda ance inda fata yafi taushi nan ake duka ta gama karanto maka hauka kazo ka sauke a gurina ko . Hawaye ne ya kawo min bayan na gama maganan mikewa yayi a hasale yana fadin ban son irin wanan halin da kuke na zubar min da mutuci a baiyanan jamma,a Har yakai kofa nace cikin daga murya mutunci kan ai koda nazo na samay shi a zube gidan nan ya juyo ya kalle ni ya girgiza kan sa ya fice. Labara dake daga kofan kitchen tana sauraren mu tace kayya uwar dakina ai da baki biye mai kunyi haka ba shifa hakkuri bai baci. Nace ina hawaye mama na gaji ne da abinda mutumin nan yake min yanzu fa a gaban ku akai komai da ya faru, amma yanzu kin gani akaina yake son ya maida maganan. Tace indan wanan ne fa kinyi kuskure babba domin ba wani abin halitta da rayuwa take zuwa mai daidai a yadda yake son ta. Ba tare da ganin akasin ta ba kuma may zaisa ki damun kanki da abinda yace yanzu ai gaskiya ya fada don ke mai ilimi ce gaba da baya. Ke din yake gani zai wa magana yaji sanyi ke kuma din yanzu kin bultsaye masa ina kuke son ya dafa yaji saukin wanan alamarin. Ga ya masa mara lafiya a asibiti cikin halin ka, in dana in ku kuma ga taku rikicin yanzu kin san iya irin bala,in da sukayi a bayan mu kan zancen cikin jikin ki ne ? Sha,anin kishiya ko ba irin wanan ba sai mutum ya hada da hakkuri yakanci riba duk mai gaskiya fa ki tuna shike da riba akan komai . Don haka kada ki kara wanan irin gangancin da kikayi yanzu ai komai ake a sane yake ina jiye mata ranan da zasu hadu mutum mai hakkuri ba a iya kaisa bango ba. Dama ita amarya a duk inda ta samu kanta dole sai tayi hakkuri da biyayya kan takai ga gina kanta yadda take so. Kaina na duke kasa ina share hawaye nace nagode mama tace nice ai da godiya da kika fahince ni kikai amfani da magana ta. Don haka kada wanan magana kice zaki rike shi a rai inda kukayi shi ku barshi gama kin ga cikin wata mai alfarma da muke. Ita bata tsaya ta nemi falalan sa ba ke da keyi ta kawo maki cikas acikin sa dama kuma burin ta ke nan taga ta dakushe ki a wurin miji ko ta halin kaka. Maryam da sai yanzu tai magana tace dadin zama a kusa da manya ke nan don ni har na goyi bayan yadda khadija din tai mai yanzu amma maganan ki mama ya sa na hasaso wani abu a yanzun haka. Ganin yake idan khadija tana kyaleta a bainan jamma,a zaifi da su dinga saida hali ana masu daukan baidaya . Kin gane ke nan yar nan ai ki rabu da shu,umar mace a gurin kishi Allah dai ya tsare ya kare kawai za a ce. Ranan ban shiga kitchen ba su sukai aikin komai yadda ya kamata tun kan ya dawo na shiga part din na gyara na jera komai yadda ya kamata na shan ruwa. Samira ma tazo ta dauki nasu zuwa part din su a falo ya hadu da ita dauke da kayan abinci ta fito daga part dina zuwa nasu ya shige bayan ta gaida shi a tsartsaye. Yana shiga yaga ranan har na aje mai kayan abincin sa ko ba kamar yadda na saba ba idan nayi girki sai ya dawo nake kawowa part din. Wanka ya shiga kafin a kira sallah sufita inda suke sallah dasu yusuf mama laraba takai masu kayan buda bakin su acan sai sun isha,i suke shigowa suci abinci su dan taba hira kafin su watse. Sai dai yanzu da zancen asibiti yazo ne naga da sunci abinci sai su bar gidan zuwa asibitin wurin Nafisa. Mun idar da sallah a nan falo nayi sallah kasancewar azumine ina zama nan muyi buda bakin mu gaba daya wanda bayan ruwa sai diyan ice dana kan danci sai zuwa dare kuma in dan sha tea shine abinda nakan iya ci kawai in kwanta ban dogon hira sosai don nakan gaji da ansha ruwa nakan kwanta wani lokaci a falo sai idan sun gama kallo mama ta tadani. Ranan da nake da girki kuma ban jimawa sosai a part dina nakan shige wurin shi in kwanta yakan so matsa min da sai naci wani abu ganin idan ya matsa min din naci ina wahala yasa ya kyale ni hakana. Yau da shan ruwan su yace suje asibiti ya duba su suna zuwa tana zaune har lokacin cikin ba sakewa tare da ita yanayin ta ya nuna tana cikin tashin hankali. Yusuf ne ya iya gaida su tare da tambayan jikin yarinyar sauran mutanen dake gurin ne suka karba mai da sauki har tasha nono da likita yace a bata. AA ya zagaya ya dauki yarinyar ya dan dubata ya dade da ita a hannu kafin ya mayar da ita ya shimfide ta saman gadon ya dago yana cewa Yusuf su tafi. Sai lokacin tayi magana kamar cikin fada tana fadin ku tafi ina kuma yanzu yace zamu gida ko da magana ne kuma. Ba laifin ka bane hakan tunda ka auro makirar mace gidan ka ana fada min ban yarda ba sai yanzu na kara tabbatar da hakan jikan mayu . Idan suna takama da maita gida tazo don sai na nuna mata ita ba kowa bane a garin nan don sai na wullakanta ta kafin ta kai ga nufin ta a kaina. Ganin Yusuf bada niyar tafiya ne ya fara tafiya ba tare da yayi magana ba Yusuf din yace Allah ya sauwaka yabi bayan shi ko minyi talatin basuyi ba a cikin asibitin suka fito. Direct ciki suka shigo sai bayan sun zauna ne Yusuf ke fadin yau banga kanwata tazo gaida mu ba mana yace tana ciki da maryam. Au tana gidan nan ke nan har yanzu yace ina ganin haka bayan sun gama cin abincin Yusuf bai dade ba yace zai tafi don ganin yanayin abokin nasa yau ba dadi. Jin cewa suna gida har yanzu a wurin laraba da tafita dauko kayan da sukai buda baki dashi waje yasa nayi mamaki a raina. Har wani lokaci na kara tabbatar da yana gidan bai fita ba kamar in share shi ganin ina hamma don ranan na wuce lokacin da nake kwaciya idona biyu muna hira da maryam. Laraba tace dani da kinje ki kwanta don barci kike ji wanan mijin nawa ko kawar daga mai son jiki ne sosai. Ba yadda zanyi in share shi haka na daure na shiga na shirya na fito nayi masu sai da safe suka rufe kofan part din mu ni kuma na tafi wurin shi. Koda na shiga dakin na samu shima ya kwanta sai dai baiyi barci ba don na ga fuskan shi a dum light din dake kunne a dakin dake dan haska dakin kofan nayiwa key na nufo gadon na kwata dan can nesa dashi. Shiru ne ya biyo dakin na tsawon wani lokaci daga cikin mu kuma babu wanda yayi barci a lokacin. Sai can naji muryan shi kamar daga sama yana fadin ya kamata ki sauke wanan fushin karki haifar min diya masu fushi irin ki ko su dara ki. Kanzil bace dashi ba sai gyara kwanciyar danayi na bashi baya yace na dauka ke din mai ilimice da zaki fahinci saidai na manta da halin mata da haka kuke komai ilimin ku. Shiru nayi mai yace bakya jinane dake fa nake magana Deedar ina matsayin mijin ki ina magana kin bani baya wanan tarbiyan a ina kika samo shi ? Ya mirgino yana taba ni nace kada ka tabani don Allah ka barni inji da abinda ya damay ni please . Dan shiru yayi sai kuma naji yace becouse of what zan daina taba ki kina matana da zaki ce in daina taba ki ina a matsayin mijin a gare ki kuma. Nace kadai san inda matan ka suke da suke bata ma wasu rai ka goyi bayan su kuma dama ba sona ake ba nuna fin karfi da iko yasa aka kawo ni gidan nan ba don so ba. Sai don cin ma wani manufa taka ta daban a kaina kada kuma kaga na zauna a gidan ka kace zaku hade da matar ka ku gasa ni cikin ruwan sanyi yadda kuke so. Na zauna gidan ka ne saboda biyayya ga magabata har ka ganin haka don haka enough is enough dakai da matar ka don kun fara kaini makura kada ka dauke ni yarinya kace ko ban gane inda ka dosa bane dani. Shiru yayi yana sauraron kalamai na da nake fadin cikin zafin rai da yaji nayi shiru yace kin gama maganar ki nace yanzu na fara yace to karya kike fada da kikace wai zaman biyayyan iyayye kike dani. Don kowa yasan da kina so na ai ba haka ake zaman biyayyan iyayye ba dakikace kina fada a kaina kice wai ba son ki ake ba ko baki sona. Kyale shi nayi na bashi baya ba tare da na juyo ba balle in nuna naji maganar shi yace hakkina zaki ban kafin ki kai ga barci ni shine bukata na yanzu ba wani abu ba. Dama baka da zancen da ya wuce wanan ai a gare ni don shine kawai tsakanin mu dakai murmushi baiyanane yayi ina iya jin shi daga inda nake kwance. Ranan dai ban yarda na bashi abinda yake so din ba duk da maganan da yake min cikin sanyin rai sai na dauka yaudara ce kawai irin ta maza idan suna son kasancewa da matan su. Duk sayin nan bai a cikin natsuwa abubuwa sun taru sun rikice masa a kai ga wurin Nafisa ba dadi sai fitina take masa da yaje asibitin akan cewa da yayi sai an sallace zasu fita da yarinyar waje. Nan ta haushi da masifa tana fadin don ciwon ba ajiki shi yake ba yasa yace hakan don kawai yana da ida yake rage dare a gidan sa. Gashi kuma har lokacin ba wani sakin fuskan da nake mai a bangare na kamar baya ko magana daga eh sai a, a idan yai tsowo kuma ba mai yawa bane. A dole nima ina son jan nawa kambun na mata ina nuna nima mace ce ban san haka halin sa yake ba mussanman ma idan mace tana da ciki. Yana matukar tausaya mata sosai don acewar shi bakanta wa mace mai ciki yana jawowa yaron dake ciki matsalane. Har wanan lokacin babu wani dan uwan sa da yazo daga kaduna duba su Nafisa din don Abba yace ba wanda zai sake zuwa harka idan na Nafisa ne gidan shi. Sai lokacin kumane abin ya bata mata rai take yawan korafin akan haka tana fadin dama nasan ba,a sona da kai tunda gashi har na haihu ko dan aikin gidan ku ba,a turo min ba. Yakance da ita laifin wa da suke zuwa dubaki kina masu wullakanci su ba zuciya ke gare su ba da zaki dinga koje su suna biye dake. Dama don ni suke zuwa yanzun kuma sun gaji sun ba kan su lafiya ga irin wullakancin da kike masu din don haka kada kiga laifin su. A gun maryam na fara jin wai wani sati zasuyi tafiyan su nai mamaki rmtare da tambayan ta ina taji wanan magana haka ? Tace min a bakin da baya karya taji don har angama shirin tafiyan su yanzu haka lokaci kawai ake jira sai ban dauki maganan da wani muhinmanci ba a raina. Tunda nasan da gaskiya ne da ya fada min ai sai shirin sallah da aka fara inda yasa in mai list din abubuwan da zamu bukata da wanda zai aika gidan su. Banyi sanyi a gwiwa ba na zauna nayi list din duk abubuwan da yace din nayi zaton zai rage daga ciki sai banji yayi korafin ko daya ba sai cewa da yayi zai min kari a sama koda bukata hakan ka taso. Daga haka muka bar zancen sai bayan kwana biyu ne ina zaune naji alent ya shigo min na duba naga irin kudin da ya turo min ga account kirasa nayi ko bani yai niyar turowa kudin ba yace shiya turo idan ya dawo gida zai min bayanin komai. Bayan ya dawo gidane Yusuf ya zo sunyi buda baki ya wuce mun shiga kwanciya yana zaune yana aiki a laptop di yace dazun kinga kudi ko ? Nace eh sai dai bansan ko na may ba kudin yace zancen list din da nace ki min shekaranjiya ne sune na turo maki don jibi zamu fita da yarinyar nan zuwa india a dubata. So kiga banda wani time issashe da zance zan leka kaduna kuma tun da tafiya ya kamani tunda ya fara maganan bance tak ba har ya gama nace Allah bata lafiya na gyara kwanciyana . Yace baki ce komai ba mana ina magana kinyi shiru nace bayan Allah ya bata lafiyan dana fada kuma may kake son ince kuma ? Murmushi yayi yace at list ai zakice kudin sunyi ko ba zasu isheku ba har in dawo ko nace zasu isa din ai daga haka bance komai ba yakara cewa babu ko Allah ya dawo damu lafiya ? Baka so in fadi haka ba ai daka fada min tun farko bawai sai yanzu da tafiya yazo kusa ana gobe zaku tashi. Kai mata may kuma kike son in fada maki bayan wanan yanzu ba gashi na sanar dake zancen tafiyan ba. Ban face komai kar kuma ace ina bakin ciki ko kishi akan za a kai yarinya wurin neman magani. Ida ni mai halice nima da naba da nawa gudun mawar kaita asamo mata lafiya yarinya mai taimin ita yar mala,ilar Allah da ita nima kaina mai maganan ai ban wuce nan ba ga Allah. Amma ai ya kamata ki muna fatan samun nasara kk dana fada maki yanzu din nace bayan wanda na furta idan bakina kake son ji kan haka bazakaji komai ba ubangiji Allah ya bata lafiya yasa aje a cikin nasaran ubangiji yace amin haka nake son ji tun farko. Kyale shi nayi na kakaro ma kaina barcin dole kafin ya gama abinda yakeyi din sai nasari na yaji a bayan shi na fara barci. Bai zauna ba washe gari tun safe da ya fita yana wurin fafitukar tafiyan su laraba ne ke tambayan shi nace kin san zasu fita gobe da yarinyar nan zuwa india nasan yana can yana shirin tafiya ne. Bamu dade da magana ba ya shigo lokacin har an sha ruwa anyi sallah ko part din mu ya nufo yaran suna rige rigen gaida shi ya amsa ya samu wuri ya zauna anan falon. Laraba ta gaidashi ya amsa ta tabaye shi ya mai jiki yace da sauki Gobe in sha Allahu da safe zamu fita zuwa waje da ita da yardan Allah takama addua da fatan samun sa,a. Ina kallon shi ya dan kalle tare da fadin madam ya gida kuma nace muna lafiya yace ce kun gani sai yanzu matsala aka samu kan pasphot din yarinyar ya dan kawo muna tsaiko. Nace yanzun an gama komai ko yace insha Allahu yana mikewa tare da fadin to mama nasan da safe koda zan fita baku tashi ba. Tace hakane ubagiji Allah ya kaiku lafiya yasa ai farar tafiya ya amsa da amin nace Affan kuyi sallama da Abba zaiyi tafiya gobe suka shiga ce mai Abba Allah yakai lafiya ya amsa da amin. Sai da ya dan jima da tafiya na samay shi a dakin har yayi wanka yana cin abinci nace yau ina yayana yake baizo cin abinci ba. Yace tare muke yanzu ya wuce gida ya huta don kowan mu ya gaji yau ina hada kayan abinci guri daya yake tambayana ba wani matsala a kara muna kudi ? Nace ba kudi bane matsala ta ni don haka kabar kudin ka nagama hada kaya na shige nabarshi yana mamakina a gurin. Sai da ya shigo ya kwanta naji yace ke may matsakar ki ne wai khadija nasan maganan serious ne tunda naji ya ambaci sunana in full nace bada matsalan komai illa a dinga bani hakki na a yadda ya dace ba amai dani wata bican ba cikin ku. Sai da kuka gama shirya tafiyan ku ne zanji daga shanun talla wanan abin da kake min kai mun adalci ke nan yace shine kawai matalar taki. Na kyale shi shima shiru yayi haka muka kwanta kowa da abinda ke a zuciyar shi hudu saura ya fara shirin tafiya ina jin sa na kyale shi har ya shirya sai lokacin ya tashe ni inyi sahur da ruwa da nake sha. Nace zanyi dan ajima kadan kafana naji yaja tare da fadin ni zan tafi Yusuf yana waje suna jirana na bude ido tare da mikewa zaune nace Allah ya kai lafiya yasa aje a sa,a. Yace amin ya dauki dan case din shi ya rataya bai dauki wasu kaya ba taee dashi ya tako zuwa inda nake yace ki kula da kanki da gida nace insha Allahu. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Tun tafiya shi ban koma barci ba karshe ma na tataro na dawo part dina sai dana dade ina dan kwankwasawa mama laraba ta bude min. Ina shiga tana fadin masu tafiya sun tafi ke nan eh kawai na bata amsa dashi na shige ciki ban tsaya ba. Na isa dakina kan gado na kwanta ban koma barci ba don lokacin sallah da ya gabato mamaki ne fal a cikin zuciya na da tunanen a haka zan zauna da wanan mutmin ba wani kima da daraja sai idan na biyan bukatane tsakanin miji da mata kawai. May yasa zai min haka bayan ina zaman zama na a gidan mu yasa aka zarga mashi aure dani alhalin yasan matar shi ba bari zatayi ya zauna da wata mace ba a rayuwan su. Duk wani abinda aka ce inyi na jan hankalin miji daidai gwargwado ina kokari yin sa don dai inga na jawo hankalin shi a gare ni. Sai naga saukin daga wurin shi lokaci daya kuma sai abin ya kara birkicewa a tsakanin mu nace a raina wanan wani irin zamane haka. Gaskiya sai aka kamar kishiya ta tsoron kishiyar ta ko mijin ta bazata iya mata komai ba idan tana iya shege a kan su da miji kamar yadda nake gani da da ban shigo gidan ba. Sai nake ganin Fatine kawai ke kyale ta don haka ta samu wuri tana iya shage ban san cewa abin bada nan bane ashe da zaran miji ya goya ma mai iya shege baya dole ke ki zama yar bi a tsakanin su don a zauna lafiya. Nace a raina ba komai yaje idan ma wanan matar tashi ce da yake rawan kafa a kanta nasan da wuya su kare lafiya a can din. Ina cin wanan tunane ne agogona ya buka na mike na shiga bandaki na dauro alwala nazo na tayar da sallah. Ina tsaka da sallah ne laraba tazo dakin ta tayar dani sai ta samu ina sallah ta juya ta fita ta koma falo don tafi zama a nan. Na idar na dade zaune ina kai kukana ga Allah wanda yawan addua,a na yanzu biyu ne Allah sauke ni lafiya ya ban komay ke cikina mai albarka sai kuma fatan in ci jerabawa na dake gaba na yanzu. Na dade zaune sai da gari ya haska sosai na tashi na koma saman gado na kwanta barci ya dauke ni wanda na jima inayin sa a dakin. INDIA Saun sauka lafiya basu tsaya neman masauki ba asibiti suka nufa direct daga nan airport din already an riga da an masu bucking din likitan da zai duba yarinyar acan. Haka yasa basu wani sha wahala ba sosai sai dai wanda ba a rasa ba kawai a garin da ba naka ba idan kaje. Likitan ya duba yarinyar inda ya tabbatar masu zasu iya mata aikin a wuein cibiyar ta yanzu sai na kai din ne zasu dan duba su gani idan zai yuyu ai mata shi yanzu saba da kankantan ta. Gado aka ba su wanda uwar zata dinga shigowa bayan awa bibiyu tana bata nono tare da duba yar sai bayan kwana uku idan sun gama aune aune zasu yi mata aiki su rufe gurin da yake bude din wanda tun a Nigeria likitoci suka so suyi mata aikin uwar tace bata yarda da hakan ba sai dai suje waje. Masauki suka nema wanda baida nisa da asibitin don samun saukin zirga zirgan su zuwa duba yar tasu dake cikin halin hau,ila,i yanzu. Wanka ya fito ya canza kayan jikin shi i zuwa masu sauki da ya saya da saukan su indian don bai dauko wasu tufafin kirki ba da zasu zo don gudun wahala dasu. Abinci yai masu odo aka kawo masu ga abincin ba wai dandanon shi ya mai bane cusawa kawai yake kada ya zauna da yunwa ga azumi da yayi . Sai dai zuciyar shi yana cikin damuwa damuwar yarsa dake cikin wani hali sai kuma damuwa akan yadda muka rabu dashi ba a cikin dadin rai ba duk da na yi kokarin nuna mai da babu komai. In ya tuno yadda ko rakiya ban mashi ba da zai bargidan ina daga gado zaune tankar ba wani guri zai tafi nisa da gida ba. Ke nan kishi nake akan zuwan su ko fushine haka na duk da yasan da na fadi korafina akan rashin fada min da baiyi ba da wuri sai da tafiya tazo masu gap ya fada min. Idan kishi nake akan ya kawo yarshi asibiti nayi hakan may yasa ban kishi akan su Affan illar cusa yaran da nake kokarin a gurin shi. Ya kuma yi tunane zaman Nafisa a asibiti daga part dina yaran nafisa da yan uwanta suke dauko abinci suci ai duk da halin zaman da nakeyi da uwar su din don haka ba akan fita da yarinyar nakewa ba sai dai fushine na ba gaira ba dalili irin namu na mata nake tsira mai. Don haka yace a ranshi bari yaga iya guduna ba zai kira ba sai idan nice na nema shi ya kwanta yana kokarin share zancen a ranshi. Yusuf kawai ya kira ya sheda mai isar su sai kuma bayanin da yai mai na abinda likitoci suka ce akan yarinyar. Yayi mashi fatan samun sauki tare da nasara a guri aiki yace zai kira da safe yaji halin da suke ciki kashe gari sukai sallama ya kashe wayan. Nafisa dake ta waya kwance a gefen shi sai hira take da madam akan wata da za,a hada ta da ita a india tai mata iso wurin wani bokan indiya . Shiyasa ma ta nace akan sai sunyi tafiyan don tana ganin kamar a kasan ne sa,an ta yake don yanzu idan tana son mutuwar ta to tana son zamana a gidan AA. Ko nawa ne zata kashe don ta riko kudi sosai a tare da ita wanda tasan zasu isheta shige da fice a kasan na indiya. Zancen yar ta ma bai damay ta ba don bata ki yar ta mutu ba ta huta don tana ganin ba wani rayuwa zatayi ba a hakan da take ta manta da Allah ne mai yin komai yadda ya so. KHADIJA Ko dana tashi na yi mamakin barcin da nayi ranan don har sha biyu ya gwauta ko sai dai damuwar da na kwanta dashi ya rage a zuciyana don tun barci bai dauke ni ba na yanke wa kaina shawara gara inji da abinda ke gabana in fita batun su can. Wanka nayi na fito falo na zauna laraba suna cikin daki da yaran ina jiyo hayaniyar su daga inda nake zaune tv na kunna wanda karan tv ya jawo hankalin su gare ni. Sai gasu sun fito daddy ne sarkin son jiki yana fitowa ya nufo ni na dan rugumay shi a jikina tare da fadin daddy mama an tashi lafiya , ? Laraba tace daddy ko sarkin rigima wanan tsohon naku akai fitina yanzu wai shi dole sai rigar dan uwan shi zai sa a jikin shi bai son nasa tun dazun rikicin da mukeyi ke nan dasu. Nace ina jawo yaron jikina kyale mama kaji da Affan idan mun fita zan sawo ma sabbi kasa kai kadai bada Affan ba. Haka yasa yaji dadi sai ya murmusa ya sake ranshi sosai naga kaman shi da mahaifin su da ya dan murmusa din da da Affan nake ganin suna kama da AA din kawai. AA ne ya fado min a raina nace ko a wani hali suke ciki yanzu a can Allah dai yasa su dace ai wa yarinyar nan wani abu a can din da sukaje. Mama ne take fadin yau kan kinsha barci ai zasu tayar dake nace don Allah su barki ki dan runtsa don ana son mai ciki tana samun barci irin haka. Nace aiko na runtsa din sosai wallahi mama dama ga gajiyan jerabawan da nayi yana bina ban samu hutawa ba wanan zancen haihuwan yazo kuma. Tace suna can dai ko a wani hali suke ciki yanzu ko kunyi waya da sune kiji ko sun isa nace idan bashi ta kiramu na samu lanban shi tace ba ai waya bai yi a tsakanin mu yanzu. Tace hakane abin ashe ai dana dauka zai yiyu ki kirasu ki samay su a can da tasu nomban ta nan da suke amfani dashi ai. Nace sai dole su sa na kasan idan sun kira mun samu layin su da suke amfani dashi can ne zamu samay su. Tace amfanin bokon ke nan ai dariya nayi nace mama ke ko dan primary din nan bakiyi bane ashe tace wa ya bamu wanan gatan a kauyen mu lokacin mun ai mata basu karatu sosai har zagin masu yi din akeyi a lokacin. Nace ikon Allah gaskiya da anyi abu wanda diya matane akafi cutawa ga rashin barin aikararun din don su maza ai sunayi ba a faye sa masu ido ba kamar diya mace. Wayana yai kara na duba hajiya mama na gani nace a fili yau hajiya ce ta kirani kuma wanda dama nice kwana bibiyu nakan kirata mu gaisa. Na dauki wayan da sallama tare da gaida ita ta karba min da fara,a tare da tambayana yara da mama laraba. Nace suna lafiya gamu tare ma dasu tace ki gaida mun su nace zasuji insha Allahu. Dan shiru ne ya biyu baya sai can tace sai kuma nake jin wai mijin naku ashe sunyi tafiya zuwa kasan waje ne kai yarsu asibiti shine bai sanar da kowa ba. Mamaki naji a raina nace wai may AA yake son ya zamane duk ya rude akan wanan matar tashi yar matsala. Sai dai a fili cewa nayi mama kila tafiyan a bazata yazo mai don nima sai da tafiyan tazo gap ne na samu labari a wurin shi. Yanzu khadija abinda yaron nan yake yana kyautawa kan shi dani ke nan sam bai dauke mu da wani muhinmanci ba a rayuwan shi. Wanan bakar matar tashi tana kokatin sai ta rabashi da kowa nasa ta huta shine farin cikin ta ita. To idan haka take so sai ta zuba ruwa kasa tasha don ta samu yaje tunda ita ya zaba akan mu sai yaje gata gashi mun bar mata. Sai dai abinda zance dake shine ki kara hakkuri a zaman ki a cikin su nasan kinayi sai dai ince ki kara din. Nace mama na gode sai dai don Allah zan baki hakkuri kan danki kada kice haka don samun haske a gare shi ko yaushe udan kince haka mama kamar kin yafe shi ke nan a cikin diyan ki baki daya. Tace khadija idan bance hakan ba may zance shi kadai ne da namiji da Allah ya hore min yanzun baki ganin Suraj kanin sa ne na baya amma baya wuce magana da shawara da mahaifiyar shi. Mama don Allah kiyi hakkuri insha Allahu shima zai dawo kamar yadda kike so har ma ya dara duk wani a gidan . Murmushi naji tayi tana fadin kai kina son ki kare mijin ki ne a gurina khadija bayan kema a yanzun kina shirin zama uwa ga wasu kin kuma san sherin kishiya yadda yake. Yaya ba zan saka damuwa a kan haka ba kin san ko ba ai magana a fili ba dole ne ayi shi a boye yau bakiji urin bacin ran da nake ciki ba dana samu wanan labarin. Nace mama kiyi hakkuri bai kyauta ba kan gaskiya don ko bai kira kowa ba ya kamata ya kiraki tun farko ya sheda maki halin da ake ciki ku sani adduan ku ai shine jagora a gare mu. Tace ke kika san wanan amma babagida sam narasa gane inda ya dosa da irin wanan rayuwar tashi baiko tunanen shima ya fara tara iyali a bangaren shi yanzu. Ni dai hakkuri na bata don banda shi ba abinda zan iya cewa nasan kuma duk maganan ta gaskiya take fadi. Don babu uwar da zata so ta haifi da yace bai shawaran komai da ita komay kuwa ya zama a duniya. Laraba ke fadin hajiya ranta ya baci ne hakan akan maigidan ku kuma nace abin ne sai hakkuri mama don kyautawa bai kyauta ba gaskiya. Ni ina ganin bai kyauta min ba ashe ga idan bai kyauta ba din da tushe Allah dai ya sa ya gane gaskiya ya daina hakan don mama tana da gaskiya wallahi . Ai yanzu kin samu abu yayi sauki ke nan idan da sabo ai yakamata itama hajiyan ta saba ni nake ganin kamar dai haka rayuwan shi take ba mai son yawan magana ba ne shi . Shiru nayi ina tunane kafin in mike tsaye tare da fadin Affan kuzo mu dan zaga kafin a kira sallah ko. Muka fice daga part din muna fita falo buzayen nan suna zaune ga butar shayi sun dora a tsakiyar falon yana tafasa sai abin ya ban mamaki a raina har na kasa daurewa nayi masu magana. Wanan wani irin dabi a ce haka kuke wa mutane wanan ai ya zama ganganci a gare ku koda baku san zafin kayan dake cikin falon nan ba ai kuma kun san zafin amfani dashi tunda kun fi kowa marar abinda ke cikin falon don kullun kune a cikin sa zaune. Dije munyi wanin abinda bai dace bane kike fadar haka inji yanyala tana dagowa daga kwance nace yanzu don Allah haka ya dace ku saka wanan abin anan haka ? Ko da masu gidan basa nan ai ku kuna nan ko kuma kuna amfani da kayan wuta a gurin tace yo ai in wanan ne ko masu gidan da suke nan muna amfani da abin mu. Don haka dabiar mu yake buzu baya yayi sai da shayi kowa ya sani nace idan ma bakuyi sai da shayi sai kuyi a cikin kitchen don ban lamunci kuyi shi a nan ba din. Idan kuma kunce ba haka ba yau sai a raba falon in san bangare na da naku yanzu a cikin wanan watan da muke mai albarka a wanan lokacin ne mace zata fito tana shan abu da rana kiri kiri haka. Tace yo Dije sai dai idan wani zancen na daban kike nema a kan mu ko Alhajin dake da gidan ya gamu ya kyale mu a hakan. Nace yau ni ba zan kyale ba don ban taba ganin kuna haka ba cikin yare naji samiha tana magana wanda na fahinci tsageranci take son yi. Zuwa nayi with full confidence na dauke abin wutan a gaban su zuwa kitchen din gida wanda tsami da dauda ya cika shi na kai na aje na fito. Na dawo falon na zauna ina jin suna zuba yare akaina wanda nasan zagi na sukeyi ban kula su ba sai sai samiha ce tace wanan dai jan magana kike son yi a gare mu. Kin san kuma ba kyale ki zamuyi ba tunda kafin ki shigo gidan nan kin samay mu da yar uwan mu a nan ne don haka ganin bata nan zaki zo ki kafa muna naki ikon a kan mu. Nace yar uwar taku gidan ta ne nan ko may yadda take a gidan nan haka nake auro ta akayi auroni akayi don haka ba fina tayi ba ga maigidan. Duk abinda kuke bawai tsoron ku nake ji ba kyale ku nake yi don kawai a zauna lafiya idan kuma wata tace zata fada min maganan banza yanzu zaku gane kalana a gidan nan. Wasa wasa maganan ke girma gare mu na ko haukace masu a gurin har yakai mama laraba fitowa a part din mu ta tsoma baki akan su bari don samiha ta dauko dahuwar tasu ta dawo dashi falon wai taga abinda zanyi. Cikin ikon Allah muna haka sai ga Yusuf kamar wanda aka kira ya shigo gidan duba mu ya samu ana wanan fitinan . Rai bace ya daka masu tsawa yace baku da hankali ne mace da ciki haka zaku tarar mata wanan samun wurin yayi yawa haka gare ku. Ya zama dole yau a raba falon nan kowa cen ku ta rike bangare ta har maigidan ya dawo yasan yadda zaiyi daku a gidan nan ku ishi wanan yarinyar tana hakkuri da halin ku dana yar uwar ku amma duk baku ganin hakan. Bai bar gidan ba sai da ya kira wasu da ban sani ba yace suzo gidan har wajen karfe hudu ana magana daya a gidan dole aka raba set din kujerun biyu aka bar hanya a tsakiya yace ba zai kore su ba yanzu don maigidan yai tafiya amma su kwana da shirin idan ya dawo dole ne asan abinyi kan su tunda ba don Allah ya kawo shi ba da bai san abinda zasu yi min ba. Yai masu iyaka da mu da komai na fanni na yace idan yaji wani abu ya taso kuma zai dauki mataki sosai a kan su don sai ya sa an daure su. Karshe dai sukace don yaga yar uwar su bata nan ne ya wullakan ta su yace idan da tana nan ma abinda zai masu daya fi wanan don da basu kwana a gidan bai mai zuwa shida sai gashi da yan sanda mutum biyu yace su zauna a get din gidan su kula da komai na gidan. Wanan abin ya kara tayar da hankalin su sosai madam suka nema suka fada mata halin da ake ciki shawara ta basu akan sai sunyi hankali don Yusuf din nan kamar ya shanye maigidan ne. Don haka suyi hakkuri su bimu yadda muke so har yar uwar su ta dawo gidan yanzu ba komai ya daga masu hankali ba sai yan sanda dake gadi a kofan gidan da bindigogin su shine tashin hankalin su. Ya kuma kira maigidan yace yai wa nafisa ma gana idan yan uwan ta suka taba ni sai ya masu wulakanci sosai tare da mashi bayanin komai dake faruwa. Ranshi ne ya baci ya samu nafisa di yai mata tas dama kuma gashi suna rikici a tsakanin su da zuwan ta ta tsiri yawo har lokacin zuwa ba yarinya nono yayi bata a masaukin su. Kiran su tayi ta tambaya yadda akayi suka fada mata ashe dama ta basu go ahead idan nai masu wani gani gani su doke ni har sai cikin jikina ya zube idan kuma sunyi ban kulasu ba din su san yadda zasu tsoratani a gidan. Sai gashi kafin suyi din ni na fara magana da har yakai akai min iyaka dasu komai zai faru da mutum idan ba mai kyau ba sai ubagiji ya kare shi ta wani hanya. Sudai gurin su yanzu shine yadda zan rasa cikin da ya baiyyana a jikina yanzu shine babban bakin cikin duk wani na tare da Nafisa din. Suna kallo na da yara muna shige da ficen mu a gidan babu yadda zasuyi shima yusuf bai faye zuwa ba don yace yana gudun sherin su. Sai dai yazo ya tsaya a waje ya turo a kai mai abimcin buda baki ya tafi dashi idan ya gama da safe ya bayar da kayan a shigo min dashi ciki. Tafiyan su da kwana uku na fita muka tafi yin sayaya kamar yadda ya umurce ni da motar shi muka fita tare da maryam harda ihisan da yanzu ta lake min da ba uwar ta a gida. Sayaya mukayi sosai komai kamar yadda yace don Yusuf ne zai kai ma mutanen kaduna nasu idan zai tafi weekend. Can kuna nafisa ne da ta dawo a fusace tana fada dashi don may zai bar min makulin motar shi inyi amfani dashi. Yace ke da na saya maki mota kin fita ne ko may a wurina kada kiga ban sai mata mota ba har ki dauka wani abu ne ya hana bari nayi har ta gama karatun ta kada ya dauke mata hankali. Kuma har yau ita bata san da manufana akan haka ba bata kuma taba nuna min bacin ranta kan rashin sai mata mota da banyi ba kamar yadda ke kika nuna min a baya. Don haka itama matatace tana da iko da abina kamar yadda kike da iko dashi kuma ki fada ma yan uwan ki da suke bugo maki waya don gulma in ba suyi hankali ba abin akan su zai koma don nagaji wallahi ba akan ki bane faraun kishiya don ke ma wata ki ka shigo kika sama a gidan. Kada ki dauki kamar wani daki ko wanda bai san abinda yakeyi ba nan dai sukai barsm baram da ita a dakin hotel din da suka sauka din. Washe gari akai ma yarinyar aiki har lokavin kuma bai kirani ba sai dai da yayi tunanen ai banda layin shi koda yaso ya kamani da laifi tanan ne ya sa shi kiran layin nawa. Muna zaune dukkan mu a falon da na dawo na samu samiha akwance tana barci tayi ale ale da ita na buga kujera ta tashi gani na ta da marairaice tace kanta ke ciwo tazo nan kada a damay ta a can. Ban mata magana ba illar alama da nayi mata da ta bar gurin ta wuce muka zauna sai ga kiran shi ya shigo min. Ba kuwar nomba dana gani na kasar waje ne yasa na gane shine a layin har kiran ya katse ban daga waya ba na share shi. Ya kara kira kusan zai katse na daga da sallama wani iri yaji dajin muryan ya amsa yana fadin watau ke idan ba,a kiraki ba bazaki nemi mutane kiji saukan su ba ko ? Nace cikin dakewa tunda naji shiru nasan tafiya yai dadi ne don ance shiru alaman lafiyace ya mai jikin da fatan an yi nasara ga tafiyan. Yace jiki da sauki yanzu aka fito da ita gurin theater an dinke cikin dake bude din kan ne dai sukace bazasu taba ba yanzu saboda tayi kankanta da aikin shi sai idan Allah ya raya ta ta tasa nan gaba zasu taba ta. Nace Allah ya bata lafiya yace amin ya wajen su mama da yaran nace duk lafiya muke sai yayi shiru. Kawar da shirun nayi da fadin ka kira mama ka fada mata halin da ake ciki ko don su sani ? Yace ban samu kiran ta ba har yanzu nace amma dai kasan baka kyata ba iyayye fa ba abin wasa bane mussanman uwa da Aljannan ka ke karkashin ta. Yace may ya kawo wanan maganan Deedar nace gani nayi baka kyauta bane dai yace ai sun san na fada masu an haifa min ya mai lalura ko ? Wa yazo dubata daga cikin su nace amma kuma kai kasan halin matar ka ai suzo kuma tace gulman ganin yar ya kawo su kamar yadda tai masu a baya. Shiru yayi yace na fahinci dai kunyi waya da hajiyan mu ke nan ko nace ni ba muyi waya ba sanin halin ka dai nayi ba zakai tunanen ka kirata ka fada mata halin da ake ciki ba ka kuma san a karkashin wani take ga ta da abokan zama. Naji zan kira yanzu idan mun gama waya sai na kara kira nace agaida su muna masu fatan alheri duk da nasan ba fada mata din zaiyi ba nadai fada ne kawai. Yace zasuji ya kashe wayan nima na bi wayan da kallo na sauke ajiyan zuciya tare da gode ma Allah dana taushi zuciya nayi mai magana yadda zai fahinta. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Idan kin san darajan Allah kuma kina tsoron haduwa dashi kada ki karanta idan baki biya ba kyale mai cin amana taci ita kadai don ramin kowan daban ne kada ta halaka kan ta ta halaka ki yar uwa. Ina falo zaune wayana yai kara na dauka hajiya mace a layin bayan mun gaisa ne take fadin kunyi waya ne da mijin ki don ya kirani yau. Nace a, a mama ya kwana biyu bai kiramu ba nan tace haba khadija nasan kece zaki mai magana ya kirani ai. Don yanzu ya kira yana min dadin baki na zage shi tas tunda shi har yanzu bai san ciwon kanshi ba. Nace mama ayi hakkuri don Allah in Allah ya yarda zamu gyara haka ba zai sake faruwa ba tace idan ma ya ga haka shine daidai yaje yai tayi ai duniyace ita ta ishi kowa. Nan dai na dinga bata hakkuri ta bar zancen tare da min kuma godiya a karshe tana fadin nagode khadija duk da kin boye bakece kika mai magana ba amma ni nasan ke din ce don wanan ba dabara shi bane. Nace wallahi mama ban san cewa yana irin wanan dabi,ar ba da tuntuni na nuna mai kuskuren hakan da yake yi tace fushin shi na banza wa yake son yazo a wullakanta dama dai mommy ku ce mai wanan kokarin ita kuma Alhaji yayi mata iya ka da al,amarin Nafisa din tun wancan zuwa da sukayi don haka ne bata kula ba ma wanan karon. Idan dai sun dawo zanyi kokari in zo da kaina in duba su in gani koni ma din zatai min rashin mutuncin nata data saba ne. Nace wane ita mama dako ni ranan na isheta ai da takai karshen rashin mutunci gidan nan hakan dana fada ne yasa ta sake murmushi har ina iya jin ta mukai sallama na kashe wayan. Sai shirin sallah muke ta faman yi da yanzu baifi sati daya ba idan Allah ya kai mu duk wani shiri da zanyi a bangare na nayi shi . Yau muna zaune muka kira Anty Fati a waya bayan mun gaisa ne na ba yaran waya su gaisa da ita take tambayan su yaushe zasu dawo ne ? Daddy yace da ita mama ni anan zan tsaya wurin anty tana kaimu yawo tana sai muna abin dadi ina ci kuma tana muna karatu a gida. Daddy kaida kanka kace baka dawowa gurin maman ka yace eh mama ni anan zan zauna muna zuwa masallaci da Abban mu. Dariya muka sawa yaron ta gama gaisawa da Affan ya miko min wayan nace ina nan kawo maki daddy ki mun maso muzo nan muyi maki sallah ne sai kuma ga zancen tafiyan mai gidan india. Tace haka dai nake ji dana shiga wurin hajiya ashe kuma haka abin yazowa Nafisa wanan karon nace wlh anty ikon Allah yafi da nan ai. Tace ta dai gani ga rabon ta dama idan mutum yace aikin sa yiwa mutane sheri ne da bin bokaye tafar ganin sherin ta na fita mata ai. Tayi nisa Allah dai ya taro ta don ko wanan abin daya samay ta baisa jikin ta yai la,asar ba ta tuba ta daina wanin abin sai ma ai abinda ya karu gare ta ita. Khadija ai ina ganin kokarin ki da kika iya zama a tsakiyan wanan nan mutanen don ta riga da ta gama da maigidan shiyasa kika gani gaba daya ma lamarin shi ya fice min a raina yanzu. Nace hakkuri zakiyi ai don goben ki anty ki bar duba da tuna abinda sukai maki a baya ki dube gaban ki ki gyara goben ki. Don ita dama gurin ta ke nan abar mata shi ita kadai ta yi yadda take so dashi tace bazan tsaya bata lokaci na akan su ba ni gaskiya nace anty nima na iya hakan balle ke don Allah dai ki gyara tsakanin ki da mijin ki da yan uwan shi tace nagode sai na kara kiran ku mukai sallama ta kashe wayan. Laraba dake gefe tace wani abin ne baya mantuwa ga mutum ai amma in kana duban wanan sai kaima ka bata goben ka a banza. Gwama da kike iya fada mata gaskiya ake lamarin ki yana da kyau don ka zauna da mutum tsakani da Allah kuma ka fada mashi gaskiya a idan yake da gyara ai shine kyau. Muna a gurin muna zancen maryam ta shigo sun gaisa da mama ta juyo gare ni tana fadin ke uwar biyu zaki ko iya fita anty Salbiya ta neman mu fa yanzu mukai waya da ita. Nace yau din nan banjin fita ta tace naga alama yadda kika zauna turus din dake kamar wanda ta kumsa cikin diya goma wallahi cikin nan kamar kada a bayana shi naga ya kara maki wani bunkasa yanzu. Duk kin wani koma jagwal yanzu gaba daya nace ai ko biyu na haifa da a gidan zaki tare tace zancen kike so lokacin kika sani ko ina gidan nawa mijin nima ? Nace Allah dai ya nuna muna ranan wanan auren da aka ta fata kuma ni banga ana da niyar yin shi ba a zahiri. Ke wallahi ni yanzu tsoron maza nake yi anshani farko banji dadin su ba ina zan yarda su kara shana. Dariya nayi ina mikewa nace aure kuma dole yarinya tayi ba don ko ba fashi a gare ta tace haka dai antyn ki ke ce min. Daki na shiga sai dana watsa ruwa a jikina na shirya na fito mukai ma mama sallama muka nufi gidan anty Salbiya din. Mun samu tana falo muka shiga ta tare mu da murna ta fadin khadija kin yi wuyan gani a garin nan komai yayi daidai ke nan dai da alama. Zama nayi ina fadin wanan shu,umar ai halin ta sai ita anty yanzun haka ba su kasan nan daga ita har mijin sun na indiya sun kai yar su da bata da lafiya nan dai nake fada mata abindake faruwa. Ta tausayawa yarinyar sosai tayi mata adduan samun lafiya tace dama irin masu bakar asirin nan ai haka ke faruwa dasu sosai amma sai kiga kamar ana bushe masu zuciya ne. Yanzu dai ai ba zancen biye biye tana fama da yar ta nace Allah yasa ni tunda suka tafi wlh hakalina ba akwace yake ba da ita don da zaran na kwanta ita nake ganin taza min a wani irin yanayi da ba dadi fassarawa. Nace yanzu ko sunan ta aka kira wlh gaba sai yai mugun faduwa tun rikicen gida da mukayi da yan uwanta anty Salbiya tace dani. Kina ko ibadan ki yadda ya dace don kin san irin yanayin nan da kike ciki yana sa mace raggata yin ibada sosai sai kin kara jajircewa. San nan yanzun haka kiran nan danayi maku an turo min da kaya da na ba da sako ne kasar mu ke ce farkon fado min a raina wlh barin dauko maki ku gani don Allah kada ki wasa da amfani dasu don tunda kike yawan wanan mafalkin da ita dole akwai abinda take shiryawa ne a kan ki. Kema nasan kina da farfarun mabiyane dake sanar dake suke baki kariya daga sherin nata shiyasa kike ganin wasu abubuwan a cikin mafalki haka. Mikewa tayi zuwa dakin nata sai gata dauke da wani katon jaka dake da rubutun arbiya a jikin shi tazo ta aje a gaban ta mudai muna kallon ta ta fara fitar wa daga cikin jakkar nata tare da fara muna bayanin shi. Tamiko tana fadin wanan da kike gani aikin sa shine koda ace irin yadda mijin nan naki yake da mata da yawa ne idan kina matsa wanan din a jikin zai ji koda yaje gurin wata matar tai mai dandano na daban. Hakama idan namiji yana da yawan neman mata insha Allah zai dogara gake matar shi ta gida da yardan Allah don duk inda yaje sai yaji dandanon bai gamshe shi ba sai ya dawo gurin ki. Ta kara dauko wani tace wanan sabulune na hadi da akayi na gargajiya bake ba ko yaran da zaki haifa idan kika malaki wanan kuna amfani dashi zai maku aiki sosai matuka gaya. Ko yau kika haifi yar ki ko yaron ki kina gudun irin wani abu na sihiri ya shafe shi zaki iya lakata dan kadan a wanke al,auran yaro dashi haka ma ke ma fa dan kadan zaki diba amma kada ki amfani da wanan a yanzu don yanayin cikin dake tare da ke baida wani chemical a cikin sa kayan gargajiyane masu karfi aka hada dashi. Yana da kwai sosai matukar kina amfani dashi ko da kishi tana jifar ki da sihiri ne da yardan Allah bazai yi tasiri akan ki ba. Ta kara dauko wani tace ga wanan kuma poweder ne kamar irin da ake fadar aljani ya shafe ka ko kuma wani sihiri haka zaki iya amfani da wanan din wurin karya shi musanman ke mai kishiyoyi hakan nan zaki iya amfani dashi ki shafa a hammatarki da wuya da sauran gurare na jikin ki haka da yardan Allah zaki ga na miji yana bin ki sau da kafa da sauran su. Wanan kuma da kifi ake cin sa mallaka ne sosai sahihi idan kikai amfani dashi sau uku zaki raba shi zaki iya yin miyar kifi ko soyayyen ki ki dan barbada a sama wallahi yana da kyau da amfani sosai don mutum zai dinga jin shakkan ka da kuma baya iya ketera maganar ka ko diyan zaman nan ke gare ki zaki ya masu amfani dashi bazasu iya ketare maganar ki ba. Ajiyan zuciya na sauke tare da fadin ni ya su a raina yanzu dole aure ya koma sai da irin wanan abin idan kana son zaman lafiya da maigida ke nan. Ta miko wani tana fadin wanan turaren wuta ne shi ake kira da turaren sakata zaki dan zuba a kaskon garwa shi kizo karkashin gadon da kuke kwana ki aje sai turaren yabi ko ina ya dauka. Zaki cire abin hayakin a wurin hmmm idan kina amfani da wanan a hankali a hankali in Allah yayi duniya don manzon sa sai an wayi gari yaji ba wata mace a ransa saike. Shiya bamu son ba mai kishiya wanan din amma ke ya zama dole mu baki shi don wanan shu,umar sai da hakan gare ki don ke ma baki san iya sherin da take maki ba ai. Ta aje ta dauko wani tana fadin kinga wanan kuma shi muke kira da dan lalai idan zaki kumshi zaki dan zuba kadan a ciki ki kwaba ki kumsa idan kiyi yana jawo yawan alheri gun namiji sosai zuwa ga matar shi. Wanan kuma turare ne ana kiran sa dan mara zaki shafa ga maranki da goshin ki yana da matukar amfani sosai yana saka dandanon jima,i sosai tsakanin miji da matar shi. Wanan matan da suka san kan su sosai suke amfani dashi ko a kasan mu saboda yana da wuyar samu sosai kin ganshi nan. Sai hummara da zan baki da turare da powder da kwali na fari jini both yan mata da matan aure zasu iya amfani dashi don saka kwarjini a idon jama, a so kinga idan har kin daure kinyi amfani da wanan zamu zubawa sarautar Allah ido mu gani Allah yasa mu dace ya kare mu daga miyagun kadarori. Muka amsa da amin ta fada min kidin su naji shi a sawake don na tabbatar ita Nafisa Allah kadai yasan irin makuden kudin da take zubawa a kaina don dai kawai in bar gida. Tace akwai addu,oi da zan baki wanda zaki tsare sosai ki dage a gurin yin su shi addua kin san shine gaba da komai wa yan nan munayin su don Allah yace tashi in taimake ka. Idan gari ya waye kafin ki ci komai zaki komai kuma kafin ki magana da wani zaki dinga karanta li,ilafi kafa tara ko wace da bissimillah ki nayi kina tofa a tafin hannun ki. Da kin kammala sai ki shafe jikin ki daga kai zuwa har tafin kafan ki da yarda Allah idan kika juri yin haka sai ubangiji ya fifita ki kan makiya ya kuma sanya masu tsoron ki a zukatan su. Ina fatan kin yi karatun arabic sai maryam tace malamace wurin nan ai anty don na gani da mukaje garin su bukin ta abin har mamaki ya bani. Tace to masha Allahu to lazimci karanta tabara kulun idan zaki kwanta don yana daga darajan mace a vikin kishiyoyin ta. Komai aka nufike dashi zai koma akan maishi da yarda Allah ko a makaranta ko wurin aiki duk yana da amfani ga mutum ya dinga yin sa idan kika daure kina wanan abinda na fada maki dayardan Allah duk wani sheri zai koma kantane. Nayi mata godiya sosai tare da bata kudi duk da nasan nadai bata sune ba wai kudin kayan bane don ma batayi niyar amsa ba sai da nace tasai wa yara abin sallah ta karba. Maryam ne har mun daga tace wanan jirgin dankaro Allah yasa tai amfani da su ko tayi abinda kika ce din yanzu duk ta sukurkuce ga baki daya wallahi. Nan Anty Salbiya tace haba kamar fa kina abakin kura ne da wanan kishiyar taki ko bakin rami ko ta turaki ko ki turata haka abin yake yanzu gidaje da yawa wallahi ko da baka da kishiya ma. Wata tana waje tana maka hassada da bakin cikin zaman da kake yi da mijin ka akace ko kana da kyau ka kara da wanka. Idan ita tana shirka tana kaucewa mahaliccin mu ke a saukake zaki kama mijin ki kuma kauce wa kai,din ta da yarda Allah don Allah ki kula ki yi amfani dashi kamar yadda nayi maki bayanin komai. Ai yanzune daidai kiyi su don bata gidan kinga kafin ta dawo duk abin ya fara zama jikin ki insha Allahu. Gidan anty hauwa naje na gaida ita don nasan da wuya in kara fitowa a yadda nakejin kai na kafin sallah kuma nan na samu sakon ya iso na kwaso wanda kayan yara ne sai nawa da na su mommy mamana da su ya Amina da hajiya dana saya masu. Ko da na dawo gida sai naji zancen ta ya tsaya min a rai gama yadda ta hada ni da Allah in amfani da abinda ta ban yau din dama wa yan can na farkon. Bayan nayi sallah na zauna in lakaci wancen in shafa in goga wanan na fito falo na samu laraba ta dora girki abinda zasuyi buda baki dashi. Na fito zuwa kitchen din wurin ta a nan na tsaya muna hira da ita ina dan tayata gyara ganyen da naga ta fitar zatai amfani dashi. Kusan a tare mukai aikin da ita muka gama na shiga sallah la,asar ne naji shigowan ihisan part din nan na fito na samay su da yan uwanta suna wasa nace ta kira min samira yar ta yarinyar ta fice da gudu zuwa kiran Samira din. Sai gasu sun dawo a tare nan na bude kayan sallah su da na sayo masu amma fa da kudin miji na bawa ko wace nata har na su yanyala nace takai masu. Abin mamaki bai karewa ina zaton ba zasu karba sai gasu har part dina sun zo min godiya nace ba komai suka fita anan suka bar samira da ihisan a wurina suna kara duba kayan su din. Anty da maman mu tana garin nan ba zata bari mu karbi kayan nan ba ko su yanyala sun fada yanzu da na kai masu nasu sunce kada mu bari maman mu taji doin idan ta sani zatace a mayar da kayan ni kuma wallahi ina son abina don bazata saya muna irin wanan ba na sani. Nace idan tace kada kusa sai ku dawo min da abina ina da wa yanda zabawa su saka tace nima ina son abina wallahi. Abinci laraba ta debowa yaran zasu suci sai samira tace itama zataci nace haba samira babba dake baki koyon azumi har yanzu tace aiko su samiha basu azumi wai basu isa yi ba sai sun haihu biyar zasu fara azumi. Abinda ko maman mu bata kanyi tace bata isa fara azumi ba sai ta yi haihuwa biyar ko fiya da haka zata fara. Innalillahi nai ta maimaitawa har yarinyar ta rude tace ko sallah fa sai da malamin mu na islamiya ya koya mun ne nake koyawa maman mu dasu samiha suma basu sallah. Gabana ne ya fadi a raina nace ashe dole abin yaiwa Nafisa yawa don babu kusanci tsakanin ta da Allah har yanzu. Mamakin mijin mi ne ya kamani a raina nace yanzu yaya yake zama haka da mutanen da basu sallah a gida nai tsoron Allah ya tambaye shi wanan abin gobe kiya yaya irin macen nan zatayiwa yayan ka tarbiya mai kyau a haka ? Ranan dai da wanan damuwan na kwana a raina har dare ina kara nanata maganan ga mama laraba tace ai haka suke har mazan su idan kinga namiji ya fara sallah wai sai ya aske gashin kansa nan na kitson su ya fita samar taka ke nan imani ya fara zuwa mai. Ikon Allah ni kuma nan Allah ya kawo ni idan baka mutu ba baga gama ganin duniya ba ashe tsoron al,amarin naji a raina sosai ranan nayi nadaman kasancewa na da su a gida daya. Bayan kwana biyu sallah saura kwana biyar muna zaune da dare falo sai ganin mutum mukayi kamar anjefo shi ina kwance a kasa a wurin da nayi sallah naga shigowar shi sai da naji gabana ya fadi. Don ban sa zasu dawo a wanan lkacin ba tunda sunce an wa yarinyar aiki ne na dauka sai bayan sallah kamar da sati biyu zasu dawo sai gasu. Addu,oin tsara naja daga inda nake kwance din ina mikewa zaune da kyat yara na mashi sannu da zuwa da laraba. Har inda nake ya karaso ya zo ya tsugun na daidai saitin fuskana tare da fadin ya akayi ne nagan ki haka har yanzu kina azumin ke nan baki hutawa ko ? Nace tafiya irin haka babu sanarwa kuma sai kuyiwa mutane girshi yace hakan nake tafiyana ba sai wani ya sani ba ko Yusuf yanzu na kirashi suzo su dauko mu a airport shima korafin da yake min ke nan. Nace dole yai maka korafi ai sannun ku da zuwa ya hanya ya kuma mai jikin ina kallon fuskan shi inji may zai fada don a zatona ko yarinyar ta rasu ne ma. Yace lafiya kalau take ta samu sauki sosai shima kan yana dan ragewa don sun bada maganin da za, a rika mata amfani dashi idan munzo nan sunce kan zai rage girma. Ya mike tsaye yana fadin barin dan watsa ruwa ko zan rage jin wanan gajiyan dana debo na hanya mikewa nayi bayan fitar shi na mara mai baya. Na samay shi a falon bai shiga part din nashi ba yana fadan don may aka kai mai kaya part din Nafisa a dauko mai kayan shi. Nidai na wuce shi nan na nufi saman yana a rufe har lokacin na bude da key din wurina dakin yana a gyara sai kamshin turaren dana bude dakin dashi ke tashi ciki. Bandakin na shiga na hada mai ruwan wanka na fito na samu suna shigo da kyan dake daure kamar na mahajjata yadda aka daure su. Ga ruwa na na hada sai dai yau mama tuwo ta girka masu wai shi suke son ci mai za a dafa ma yanzu kaci ? Yace tuwon ma ai is ok zanci ai in akwaishi don ya zama abin marmari a gare ni yanzu da wancan cimar nasu da na baro yanzu kai wanka kafin ka fito na hada ma abincin. Na barshi ya fara cire kayan jikin shi na fita daga dakin zuwa hada mashi abinci lokacin an gama shigo da kayan ban ko kali inda kayan suke ba na fice. Sai da na dan jima a part dina don mun tsaya hada mai da dan abu mara nauyi da zai sha muka gama na shiga na gyara kaina na nufi part din. Ina shiga na rufo kofan na samay shi zaune da waya a hannun shi yanayi na jera komai a inda ya dace a jera din na samay shi ija fada mai na hada abincin ko. Ina zaune gefen sai da ya gama baiyi magana ba har ya kare na hada kayan na samay shi a dakin guri na samu nakai kwance don tunda ya dawo amsa waya yake yi har lokacin. Acikin wayan da yake yin din ne na fahinci dawowan baram baram sukayi da Nafisa din don yana fadin ace mutum baisan ciwon kansa ba kamar ba itace ta haifi yar da cikin ta take cikin wanan lalurar. Bansan Nafisa tayi nisa haka ba sai wanan karon wai zaka yarda har gurin boka taje a india wai ya duba mata ya akayi ta haifi yar haka ? Wani iri naji a raina daga inda nake kwance yace wallahi alamarin nafisa ya fara fita min rai don bata san Allah ba sam a rayuwan ta in dai taje boka ta iya bi ai tajiyo makanta matsala a can daya tada mata da hankali banji may wanda suke wayan ba yace sai dai shi danaji yace. Ni ina zan yarda da wanan shirkan da shashanci iri nasu na mata wa take zargi yanzu tace ya hurhura mata yar yanzu. Ya gama na sauke ajiyan zuciya dama yanayin sa ya nuna ba dadin rai ya dawo don yadda na ganshi a cikin rashin walwala a fuskan shi. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Bamu yi nisa ga barci ba tazo tana dukan kofa hankali tashe na farka naji muryan shi yana fadin kwanta abinki tayi abinda zatayi din. Da safe ko da na sauko lokacin tara na safe ya gwauta a falo na samay ta zaune ta harde a cikin masifa da bala,i take ban muna arba ta soke kanta a kasa. Na shige ban mata magana ba sai da naje nayi wanka na shirya na fito na nufi part din ta cikin rashin dadara nayi sallama na shiga. Tana zaune ta jingina bayan ta a gado kafanta a harde tana waya kamar bata son aji maganan sai gani nayi sallama har kuryan dakin inda take. Wayan ta kashe da sauri ta dago tana kallo na nace maman ihisan sannun ku da zuwa kun dawo lafiya ya mai jikin kuma ? Tace lafiya kan muka dawo tunda kin ga miji har kin iya shigewa wurin shi kin san kuma bake ce dashi ba mai jiki kuma gata nan idan za a karasa ta ne da zai fi. Murmushi nayi nace wanan kuma Allah ne kadai yakai can Allah ya bata lafiya yasa kafara ne gare ta . Dama nazo in gaida ku da hanya ne in kuma dubs mamana Tani da jiki Allah ya sauwa ka na juya ina jin tana fadin muna funcin banza da wofi idan ma karasata kika zo yi ai gaki gata da yafi min wanan wahalan da kuka samu ciki. Na kada kaina ina murmushi na wuce nace kodai ba komai na sauke nauyin da Allah yace ka sauke tsakanin ka da abokin zama. Dakina na dawo na shige na kwanta barci nayi sosai ban falka ba sai wuraren karfe dayan rana na tashi don lokacin sallah da yayi. Ban fito falo ba sai da nayi sallah na fito na samu mama laraba a falon yaran sun fita laraba ke fada min shigowan shi biyu part din nawa ya samu ina barci. Zama nayi ina tambayan ta yaran tace yanzu baban su Yusuf yazo suka bishi tace kina barci ba an tayar da fitinan kujerun falo da aka raba ba gidan nan Yusuf yana zuwa yace a mayar dasu yadda suke a gyara . Tace na fita in gyara wurin mu ne sai gata ta fito a cikin masifa kai wanan yarinyar bata da mutunci wai ni zatacewa maza in gyara kujerun a yadda suke a da can. Tsoro da ya kamani yadda naga ta fito min dole na juya na shigo nan na barta tana ruwan bala,i a falon nasan tasa an warga zasu ne sai dazun da Yusuf ya shigo ne yake tambaya wanda ya hadesu tace itace tasa a yi hakan. Yace yan uwanta su gyara a yadda suke anan gurin namu suka zauna yanzun haka badon sun tafi sallah ba tun dazu nan yake karban mutanen shi ai yau mutanen ki sun samu fita falo suna yadda suke so. Nace ashe yau daddy ya samu sake, sai kinji ke nan dama abinda yake so ke nan a rayuwan shi dan ni har tausayi suke ban duk a takure suke dama. Ai kina ma kokari tunda kina dan fita dasu acan in dai ba gurin kakan su ta turasu ba ko cen ko yaushe suna gida kumshe. Shine ya shigo part din yake fadin kin tashi ke nan nace eh yace idan kin huta kije dakina kaya na nan saman gado ki dauko. Tsaraban ki ne nace mun gode na bashi amsa yana fita na mike zuwa dakin a nan na suma kayan indian sari ne zube a saman gadon da kayan yara a cikin buhun nan na saka su na mayar na dawo na kira mama tazo ta dauka muka nufi part dina da kayan . Nan dai muka baje ina duba daya bayan daya kayan suna da matukar kyau sosai da gani suna da tsada sosai sai set na dan kune da sarka masu kyau suma har guda uku. Na gode sosai don kayan sun min kyau sosai gashi lokaci ya kure sosai duk da ina da kayan da suka fisu a dakin ke. Zaman dai babu dadi sam don duk da mutanen da ke shigowa gaida su da dawowa bai hana Nafisa yin halin ta ba a bainan jamma,a duk dai a kan cikin dake jikina ne. Shi da kan shi a wani safiya da ta tayar da fitina yace dani kada in kara kulata idan ta isa ta zuba da cikin a gani tace wai yana fada akan cikin da ba shine yayi min ba don tasan ba yadda za ayi ya iya min ciki din. Yace saboda kin san sherin da kikayi yasa kike fadin haka to na dade da gane hakan sherin ki baiyi tasiri akan mu ba. Fadan hauka ta fara yi dashi wai ita zaiwa kazafi yace kazafin may tunda yanzu ta fada kowa yaji bayan sun gama ta shiga daki sai gata ta kwaso kayan sallah dana sayawa yaran ta nufo dakina dashi yaran na biye da ita suna kuka. Kukan yaran ne ya fito dashi yana tambayan su may ke faruwa nan samira ke fada mai abinda uwar ke niyar yi part din ya nufa ya samu an bude kofan ke nan tana shirin shiga ya dakatar da ita yana fadin. Ba yaran nan kayan su idan ba so kike ranki yau ya baci a gidan nan ba tace akan kayan raina zai baci yace kwarai kuwa. Ganin da gaske yake ga ihisan tana fisge kayan ta a hannun uwar ta rugumay su a jikin ta ta koma bayan uban ta tsaya. Diya nane ko naka yace yar ki da nawa tace to kayi iko da yarka kabar min nawa yace haka kika ce tace eh na fada yace yau ko idan kin hana ta amfani da wanan kayan sai dai samira ta bar min gida. Eh lalai Samad an wanke an baka kasha ka tsuma to bari kuji wallahi ko damay take tsafi sai na nuna mata tsafin ki karya ne kada kiga kin salwantar min da wanan da na haifa ki dauka na kyale ki ne kin ci bulus. Yanzu ma kin saka miji ya yi min gori akan wanan kuma yadda kika saka yai min ki dauka kinci bashi ne a guri na idan na tashi nawa na fiki iya sheri. Duk wanan hayaniyar muna jin su don kofan har lokacin a bude yake bamu rufe ba tace yau har kana ikirarin Samira ta barma gidan ka saboda na hanata saka rigan tsafi a jikin ta ko ? Tsafi kece mai yi ai tunda har kika iya zuwa wurin boka a india don rashin imani irin naki kina dauka kowa haka yake kamarki komay to ke da bukan kunyi kadan ku juya ni yadda kuke so. Kinji na fada maki kaya ne idan har samira kika hanata amfani da wanan kayan ni kuma ki tabbatar da tabar min gidana ta gama har abada. Sai dai ta koma gidan ubanta can ta zauna ni hadin kai nake so a gidana ba watsewar kai ba yadda kika kasa wata tazo tanayi ya zamay maki kuma abin bakin ciki da sheri tunda ke baki iya hakan. Nan ya fice ya barta tana jidali tare da ihuce ihuce can naji hayaniyar su da yan uwan ta ana ta koke koke ashe baiyi nisa sai gashi ya shigo gidan rai bace yace duk su fito daga su bar maigida. Nan ya tsaya lalai ranan ba zata zauna mai a gidan shi ba daga ita har yan uwar nata duk yadda ta bada hakkuri yaki amincewa da hakan karshe ya fice tare da ba yan sandan bakin get baki akan su tabbatar da kafin biyar na yamma. Ranan kan sun gamu da halin shi ashe Yusuf ne ya yi mai tas yace badon Allah ya kawo shi ranan ba da yaya zai samu anyi ni kadai sai laraba suka wuri su shida a kaina . AA kan san kuna daukan alhakin wanan yarinyar duk da bata magana akan haka kyale ku fa tayi ta barka ga Allah idan kun cuce ta. Kuma sai Allah ya kama ka da laifi akan hakan don kaine ka tauye ta ba wani ba nan dai ya kawo musalan irin tauye nin da zaman su ke yi a gidan. Ashe shine turje matan da yayi dayazo ya samu tana fada dasu wai don sun karbi kayan sallah a hannu na shine dalilin fadan ta dasu tayi masu yankar kauna. Dole ta kwashi angayan ta maza da mata suka wuce gidan madam madam tana gani su tace yo ni Nafisa ina zan kaiku duka haka. Wanan dawainiyar ai sai mijin ki shi daya dauka abinda nake fada maki ke nan kin kasa ganewa gashi gobe jajibirin sallah. Don may ba zaki hakkuri dakomai ke cikin ranki ba abinshi a sannu har hankali ya kwanta da sannu gani Allah ta samu ta karbi matan da ita ga yar tana ta tsala ihu tana neman nono. Haushi ne ya kamata tace yar banza mai cin tsiya da shegen taurin rai ta mutu taki mutuwa tana lake dani. Madam tace nafisa baki da hakkuri ne ga yar nan ko bukin suna ba ai mata ba kin debi rabon ki dako ta wanan yar idan kin kwantar da hankali ai sai ki cuta ma khadija. Cikine fa a jikin ta take dauke dashi da kinyi dabara nuna mata bakomai a zuciyar ki ki tsiri tura yar wurin ta da itama haka zata haifo cikin ta tankar wanan yar na hannun ki. Kin manta ace mace mai ciki wanda take arba dashi duk safiya kamar shi sak take haihu dakin daure kina iza mata yar ai da itama sai ta haifi sherin ta taji inda dadi. Amma ina kin kasa hakkuri don zafin kishin da baki iya boyewa kin kaiga yadda ba a son akai yo ko ciyar daku yau kawai ai aiki ne gun mutum. Wurin kwana kan zan iya baku sai dai ki nema muna abinda zamuci dagani harku a gidan nan yau gobe ki samu ki lalaba mijin ki ki koma dakin ki yafi sauki. Tayi mamakin jin kalaman madam din sai dai ba yadda ta iya tunda duk yan uwanta da saka shigo ta gujesu yanzu tunda tana ganin ta fisu yanzu. Don haka abin kunya ne ta nemay su akan su taimaka mata ta kwamace ta zauna hakanan wurin madam din in yasoda safe zata nemi mijin ta su shirya dashi. A gidan kuma ban san har sun fice daga gidan ba sai da laraba ta fita har sau biyu bata ga ko dayan su ba ta dawo tana fada min. Fita nayi na duba sai banji dadin hakan ba da yai masu ko don yar nan mara lafiya da take dauke da ita nasan ko yayane dole tana jin zafin kasancewar yar ga hakan. Maryam na fara nema ina fada mata dariya ta kwashe dashi tana fadin dama a ce ina gidan da zasu tafi in dauke su in watsa shegiya a duniya. Tace ke tsaya kin yi amfani da wanan abin sai nace nayi wasu banyi wasu ba sunan aje tace kai ke wai wata iri ce khady wanan matar fa ke taso aiwa haka rashe ya juye da mojiya sherin da ta dauko ya koma kanta. Ke bari dai yau komai dare gani nan zuwa gidan wallahi gaba zan sakaki sai kinyi amfani dasu dariya nake mata nace maryam baki da tausayi wallahi. Mata da danyen jegon ta zaki ce kinji dadin tafiyan ta ki kwanta haka da kan ki fa idan kece bazaki ji dadin hakan ba ai. Tace amma ke ai da cikin taso kibar gidan ki koma gidan ku ki kayan goyo da ciki tana jin dadi don nasan wallahi idan itace ba zata tausaya maki ba ko kadan. Nace wanan kuma ita ta sani nidai da zuciya daya nake zaune da ita a gidan nan tace ita kuma da zuciya biyu take zaune dake ba. Karfe bakwai da wani abu ta iso gidan tun daga kofa take fadin wai Alhamdullahi Allah mun gode ma yau gidan nan kamar bashi ba wallahi. Laraba ta dinga mata dariya tace don Allah mama ki tayani gani dajin wanan matar ko itama ba mamaki buzuwan nan ta shanye tane dai bamu sani ba wai fa mama tausayin wanan matar take harda kirana ta fada min maganan takaici. Nidai ina zaune ina tasbihi ina kallonta ina murmushi na shafa nace ke dai baki da tausayi wallahi ni banga abun farin ciki ba a nan. Laraba tace ni ai tun dazun ina zaune imani ya kashe ni wallahi wanan da ba a nan nake zaune sai in ce yar nan itama takai ta isa. Amma sanin ko waye ita yasa na kara tsoron alamarin ubangiji yanzu duk balain da matar na ta dauko a kasan yan tsafin nan yau sai gashi abin ya juye da ita a gidan nan. Shiyasa aka ce mutum wanda ya dogara da Allah baya taba kunya a duniyan nan don Allah yana tare dashi a ko wani lokaci. Matan nan saboda bakin fitinan irin nata tun ranan da suka dawo take sama da jidali a gidan nan har rana mai kamar tayau bakin ta bai huta ba kan wanan boyar Allah. Maryam tace ai yanzu ta kai ga yadda take so don da tsamani take mijin ba zai iya mata komai ba tana ganin ta gama dashi . Bata san Allah ba ai mashi haka ba sai ya girgiza bawan sa ta inda bai zata ba Allah dai yasa ta tafi ke nan yar iska daga ita har angayan nata kowa ya huta. Tara maryam tabar gida har lokacin kuma bsi dawo ba sai goma ya shigo part din mu ya nufo ya gaida mama da shan ruwa na fita na bishi da ga bayan don dama nakai mai komai na jera acan . Koda na shiga na samu yana sallah sai dai baiyi wanka ba a lokacin na shiga na hada mai ruwa na fito ya rarage sallah yana zaune fanin na fito ya mike yana rage kayan jikin shi ya shiga ban dakin har ya fito ina zaune da waya na a hannu ina dubawa muna charting da binta. Nan ya barni zaune ya nufi dinning na mike nasamay shi a girin abincin na fara zuba mai kafin in zauna yace kina ganin yau zan iya cinye wanan abincin haka mai yawa ? Nace haka fa na saba zuba ma sai dai yau idan baka jin ci abincin ne kawai in rage ma yace barshi mu gani tunda kin zuba ko. Idona koma gefe na zubs mai tare da harde hanaye na wuri daya na zuba mai ido yana ta cin abincin shi hankali a kwance. Can ya dago kai yace min lafiya kikai shiru haka nace hakkuri nake baka bisa ga abinda ya faru yau a gidan nan don wallahi ban yi zaton zaku dawo bane yanzu kuyi sallah a gida yasa na hada dasu nasai masu kayan cikin kudin ds ka bar muna ai amfani dashi din.. Ai ba laifi bane don kin yi hakan yace ba tare da ya dago kan shi gare ni ba ya kalle ni nima shiru nayi na dan lokaci sai kuma na sake fadin. Don Allah kayi hakkuri su dawo gida hakana ko don yaran ka dake wurin su din sai naga kamar hakan da kayi bai dace ba gaskiya. Don , , , , hannu ya daga min tare da fadin ya isa haka don Allah koma may ye ya riga da ya faru ai ban son wanan maganan again. Yaci gaba da cin abinvin sa sai can yace gobe kaduna zamu a can zamuyi sallah in Allah ya yarda. Yana fadin haka ya dauki cup ruwa ya kora ya jawo tiesui yana goge bakin shi dashi ya mike binshi nayi da kallo har ya shige ciki. Sai lokacin daya shige nake mamaki watau dai halin shine hakan na tafiya babu sanarwa sai yazo yaiwa mutum girshi Allah yasa ina da dan shiri na sai kuma goben zamu shiga in karo abinda nake so. Mikewa nayi na shiga dakin na samay shi zaune yana waya gado na hau na lafe kamar yar mage ya dade yana wayan kafin ya gama. Yace shirin sati daya zakiyi don ina son indan huta idan munje can na sati daya idan haka ya samu a gare ni. Allah ya kaimu nace tare da fadin sai a shirya su Affan ke nan su koma gaba daya don hutun su ya kare one week after sallah zasu koma school. Akwai wani abinda zaki kara sai masu ne ya tambaya yana hawowa gadon nace sai dai sayayyan school da nake son yimasu da dan abinda ba a rasa din ba dai. Ok yace yana jan bargo tare da fadin kada muje can kuma kice zaki kawo min kabali da badi din da kika saba fada min idan munje don hutu nake son muje ba bacin rayukan mu ba a can. Ciki ciki nai magana ina fadin mutum dai ya rika shuka gaskiya a lamarin sa shine kyau yace may ne may kika ce nace ai kajini. Murmushi naji yayi nace ai dama kaji may ye na bukatan in maimaita kuma kin dai ji na fada maki tun anan ko in nuna maki kala na acan. Nace ko yanzu ai nasan kalan ka don ka zama sabo da kaza bai hana yankata ina jiye min ranan da nima zaka iya korana da abinda zan haifa dakai a gidan ka. Tunanen ki ke nan dama dako kinyi kuskure don ba haka nake ba hukunci nakan yanke dai abinda mutum yayi ne. Ba mamaki idan halin ki ya sauya in yake maki makamancin hukunci da kike ganin banyi daidai ba kansa. Shiru nayi ina nazarin maganan har lokacin da naji ya rungumoni zuwa jikin shi yana fadin ku dai mata ba a gane gaban ku na gaskiya ko ? Washe gari banyi wani barcin safe isashe ba na shirya muka fita mun dan taba sayaya muka dawo muka kara shiri kusan maryam ne ta hada min komai da zan bukata acan idan mun tafi. Duk damuwan rabuwa da yaran da zanyi yana cin raina suko ba abinda ya damay su sai ma murna zasu kaduna da sukeyi. Karfe sha biyu da rabi muka bar garin Abuja zuwa kaduna baysn yasa an rufe gidan ya bada umurnin kada a bude ma kowa gidan idan bashi ya dawo ba. Yai masu ihisani muka tafi bamufi minti ashirin da dagawa ba Nafisa dasu madam suka iso gidan tare da wasu yan yaren su dattije da wasu da madam taiwa magana su zo aba shi hakkuri abindai a wullaknace. Nan sojan dake gadin kofan yai masu nuni da su koma da hannu kada su karaso kofan sai da kyat suka samu ya saurare su yace masu gidan sunyi tafiya. Tace ina suka je cikin tshin hankali take tambayan shi gashi ko kayan sakawan yaranta bata dauka ba suka tafi. Yace shima bai sani ba amma da gani zasu dade inda suka tafi din ya kuma ce suyi maza subar kofan kafin ranshi ya baci dole suka bar kofan gidan. Tunda suka shigo motsa madam ke fadin da sake gaskiya don sun damay ta da hayaniya a gidan tace nafisa abinda nake fada maki ke nan kullun baki ganewa. Na fada maki ki bi alamarin nan a sannu tunda kikaga yarinyar nan ta shigo gidan nan da karfin ta ta shigo kikaga kinyi asiri bai yi wani tasiri akan ta ba har wanan lokaacin to ki bita a sannu. Yanzu gashi kinjawa kan ki komawa baya a gaban idon ta ya nuna mata ke ba kowa bace a gurin ta wanan abin damay yai kama ? Duk rashin hakkurin ke ne yaja muna wanan koma bayan yanzu ina kike son in kaiku kuda yawa hakan nan a gida na ? Bakin magana Nafisa bata samu ba a lokacin abin mamaki da alajabi yake bata wai yau itane ake tagaririya da ita ana mata wanan wullakancin haka a gidan samad. Ita ce samad ya wullakanta a kan wata abin ita har yanzu kamar a mafalki take ganin sa a idon ta ba wai ta yarda samad ne yai mata haka ba. Ta tuno ko a indiya kudin da ta kashe zai iya sai mata gida da abin hawa a garin Abuja su zauna ita da ya uwanta ba sai sin rabo a gidan wata ba ana masu wullakancin akan abinda tafi karfi shi a yan shekarun da suka shude kai bama shekuru ba a jiya jiyan nan ma. Dole ta fidda da kudi da madam din ta bukata masu yawa wanda zasuyi amfani dashi domin sallah da ake sa ran za a tashi dashi gobe. Mun isa kaduna a wahalce duk dauriyan da nake yi sai da ya gane ina cikin wani hali sai ga amai da ya biyo baya da kyat naga mun kai garin kaduna din. Yau ma kaman wancam karon a jirkice na iso garin muna shiga na nufi sama amai nayi ta shega yasa wai dole in kara azumin dake baki na nace naji yasa laraba ta hado min tea kafin ys shigo na dan kai rabin bayi na koma na lafe kamar nasha tea din sai barcin wahala da ya dauke ni. Bayan nayi sallah na dade ina barci sai da aka kira sallah magariba na tashi nayi buda baki wanka nayi nazo nai sallah ban dade ba kuma na koma na kwanta. Bani na samu kaina ba sai washe garin sallah da akai sanarwa da anga wata garuruwa daban daban na kasan nan dama wasu kasashen duniya Ga kayan da muka zo dashi ba a bude ba don rashin lafiyan das nna iso gartin dashi dole na fito a cikinn karfin hali na bude kayan ya bawa kowa nasa tun da safe. Abinda ke ban mamaki ya daure min kai shine lamarin anty fati ko wancen zuwan da nazo a haka matan nnan bata tako dakina dubs ni da jiki ba haka kuma batai min sannun kirki ba. Hakane ma wanan karon tunda na shiga bata leko ni ba a dakin har zuwa lokacin da na fito ina bawa kowa abinda muka zo dashi garin. ZAINAB IiDRIS MAKAWA SEENABU 1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: ZAINAB IDRIS MAKAWA 08036959275 Kitabbatar da hakkina a kan ki idan kin karanta baki biya ba kibar wace bata san darajan Allah da Annabisa da hakkin data dauka kada son zuciya ke ma yakai ki ga halaka alhaki bin maishi yake ta inda baiyi zato ba. Ina kara jaddada wanan maganan don akwai ranan tambaya yana tafe kan mu ko yau ko gobe ko kuma yanzun da kike karanta hakkin da ba naki ba . Musulumin baya so ma dan uwan sa abinda shi baya so akan sa ba shiyasa a kulun nake maku wanan tunin a matsayin ku na musulmai da suka isa dauka hakki akansu. Na gama abinda nake na koma dakina na kwanta don har lokacin jikin ba ya gama warwale min bane waya nayi gida ina sheda ma daddyn mu mun sauka lafiya jiya mun iso bana jin dadin jikina ne ban samu kiran su ba daga nan kuma inda nake na kira ya Amina ina sheda mata halin da nake ciki. To wai idan kin ce kin biya ya zama naki kina da ikon kiba wanda kike so amma ko da kin jahilci sharudan ciniki wanan a haka yazo don online novel ne mai shi tace ga ka,idan abinta dake mai tsoron Allah ce ai ba zaki biya ki saya ba sai ki barta da kayan ta tunda karatun novel dai ba ibada bane. Muna cikin waya da ya Amina nake danji murya alaman fada a kasa da sauri na aje wayan ina saurare daga ina maganan ke fitowa nan na fahinci a falon kasa ne dai a cikin gidan kuma. Jin abin bai kare ba yasa na sauko kasa don gane ma idona abin dake faruwa a gidan kuma da wanan safiyar sallah da kowa ke cikin fari ciki da barka da buda baki na wanan shekaran da Allah ya nuna muna lafiya wanda wasu Allah bai nufa suga shi ba. Wasu sunga farkon shi amma Allah bai nufa suga karshen shi ubangiji ya gafartawa magabatan mu na kusa dana nesa idan namu yazo mucika da kyau da imani. Kina ban dariya wai karfin hali barawo da sallama shi malamin da yace haka kin masa bayani ga yadda mukayi dake kafin ki saya akwai ka,ida a tsakanin online ne ba takarda bane da zaki dauka ki kaiwa wasu. Yanzu dai idan kin nace da fitarwa alkalin mu Allah da ku don duk abinda akace abarwa Allah idan kana da hankali da imani kaiwa kanka hisabi tun nan cikin duniya. Hakina na ban fara ba sai dana roki Allah akan hakan na fara a cikin baiwar sa na kuma samu a cikin iyawarsa yanzu zabi ya saura gare ki dake damasu biye maki ku halaka ku halaka zurian ku akan novel din da ba ibada bane. Isowana yayi daidai da furcin shi yana fadin nawa na turo maki akan sallah nan dubu dari biyar nasa Yusuf ya kawo maki don ban san halin da tafiyan mu zaiyi ba acan . Shine yanzu zaki tare ni da wanan maganan banzan wai ba a sai komai na aikin abincin sallah ba don baki san zamu zo nan sallah ba. Idan ma banzo ba ai ina da iyayye da yan uwa da zaki ba abincin sallah ke kanki ba don karki gani ga wani na tura maki kudi haka Fati ni na rasa gane may kike da kudi ne haka wai. Ke ba a gani a jikin ki ba ba a gani ga diyan ki balle dan uwa kowa korafi yake da rowan ki ba wanda ke tare dake yake jin dadin ki saboda bakin halin ki na tsiya. Tace idan ka bani ne don kasan abinda nake dashi kabar bani mana yace haka kika ce ko tace hakane mana tunda kabani kaba kowa na sani yanzu kan wanan magana danayi zaka aza min wanan tujaran haka. Yace oh baki komai ba ke nan ko tayi shiru yace yau zaki gane baki da wayau baki san kalman da ya dace ki fadawa mutum ba komai ya fito bakin ki zaki iya fada ma mutum shi kai tsaye. Wanan dalilin yasa baki taba ganin fuskana don a gaban kowa ba abin kunya bane gareki ki disga ni baki san komai ba sai bakin rai da hassada dake cin ki. Don Allah dai ku bar wanan magana na fada daga inda nake tsaye nace indai don wanan kuke wanan abin kuyi hakkuri ga komai nan nazo dashi wanda na saya can a zatona acan zamuyi sallah da naga nan ne na ce mama ta kwaso muzo dashi nan ga baki daya don girman Allah dai kuyi hakkuri wanan maganan ya wuce. Inda nake ya kalla ya nuna ni da hannu tare da fadin you see kinji abinda tace kinji ma kunnuwan ki kudin dana bata baiko kai wanda ke na turo maki kuyi hidima dashi ba nan. Amma ji irin abinda ta sayawa yaran ki suka dawo dashi ke da kanki kike nuna min yanzu babu ko kunya wanda ke kin kasa yi masu hakan kuma ke kika haifi abinki fa. Yaya don Allah kayi hakkuri kabar gurin nan idan ba ka kauce ba zancen baya karewa a tsakanin ku itakuma fadi take wanan munafuncin ni ban iya ba. Wani sheri ne na kishiya mitum bai sani ba kuma yace idan munafunci ne yin haka ke kiyi mana a gani ai shima ribar zamane. Kince Nafisa bata da kula bata son ki bata son diyan ki wanan kuma kin kirata da munafuka ke wace kala ce to a cikin ku yanzu. Tace dama idan ba kaci min mutunci ba ai hankalin ka baya kwanciya yace idan magana akan gaskiyata ce cin mutunci naci maki din sai ki abinda zakiyi. Kitchen na wuce na kyale su kayan da mukazo dashi nake tambayan laraba da take tsaye a cikin damuwa wajen kitchen din ta fito tana fadin gasu canbda aka shigo dasu aka aje su daga can. Nufar kayan nayi don mu fitar a dora girki dasu nan dai muka shiga aiki da laraba ban san lokacin da suka gama suka watse ba. Na fito naga Affan zaune a cikin damuwa daddy kuma yana wasa nace Affan ba zaku je ku shirya kubi abba masallaci ba ne ? Yaron yace maman mu batai muna wanka na nace ku tashi muje kuyi wanka da sauri na wuce suka bini a baya zuwa dakina na gama masu nace su karbo kayan su in saka masu sai ga shi ya dawo yana fadin maman mu ta koro ni. Mikewa nayi na nufi dakin da sallama a baki na ta dago kai ta kalle ni nace anty kiyi hakkuri don Allah kada ki sa wanan abin a ranki mana. Bani kayan yaran in shirya su kada su rasa falalan wanan ranan ta wuce su ko kuma a rasa wanda zasu bi zuwa sallah idan shi ya wuce. Kayan ta nuna min saman gado na nufa farar shadda da maryam takai aka dinka masu na dauko da hullan nan su na fice daga dakin. Bina tayi da kallo mai kama da harara taja tsuki nikan tsab na shirya yaran suna fitowa daidai shima ya gama shiri ya fito da sauri kada ya makara. Nace ga su zasu bi dan kallon mu yayi batare da yai magana ba suka fice nace adawo lafiya banji ba ko ya amsa kitchen na koma na samu laraba mukaci gaba da aiki. Kafin wani lokaci mun hada tuwon farar shinkafa sai miyar ganye kadan stew yafi yawa da kaji da akaiwa yakan ci muga iyakar ka nan fa akeyin ta don babu kula na kwarai da zan kai abinci cikin gidan su. Ba kuma dama in tambayi matar gidan da tahau ta cika nasan ko na tambaya bakar magana ce rabona sai wanan karon naji nima ya kamata in samu kayan aiki a gidan fa. Don nima ai yanzu matar gidace dai mama ta gane may ne tunawa bayan mun gama saka tuwon a leda mun cika babban kulan da nazo dashi shake da nama a cikin sa. Wayana na dauko nayi wa ya Amina bayani tace barin shiga nan makwabta na dubo maki akwai matar da sana,anta ke nan sai in hado maki da wanda nake dasu anan. Ba a dauki lokaci ba ko sai ga shi anyi sallama wata yar matashiyar budurwa ne tazo da set uku na kula duka na saye nace ta karo min biyu idan akwai. Ta fice tana murna mai girma daga ciki guda biyu na cika da abinci nace wa mama daya na Abba daya na cikin gida ne dayan kulan kuma na sawa su AA a ciki don yafi kyau da tsada. Kafin masu shigo gidan don nasan sun tsaya cikin gidan su ne su gaisa da mutane yasa basu shigo ba har lokacin. Yar uwa ina typing ne wa jama,an Annabi masu tsoron hakkin wani fa don hakkin su da ke kaina ina son in sauke nayi kina damuna da zancen bati. Idan kinga zaki iya da hakkin wani ki ta karantawa ba nawa na duk wace zaki iya karanta ki dai sani akwai nauyi babba a kanki na mutumin da baki san ida zaku hadu ba kila sai a gaban ubangijin talikai wanan sarkin kowa da komai da aka hadaki dashi kika yiwa daranjan saboda son zuciya don Allah ki barni haka zabi ya rage akan ki yanzu ko yaron yasan akwai ranan haduwan shi da Allah. Yana zaune dakin hajiyan su laraba ta shigo da kayan abincin tare da mommy duk yan gidan sai magana sukeyi a tsakar gida suna fadin ikon Allah yau abincin sallah gidan babangida ne a gidan nan. Hajiya mama daga daki da aka dosa da kayan tace kai mommy yara kuje can kuji dashi da ai ba abincin gidan shi muke ci mu san munyi sallah ba ko. Mommy ta karaso ciki tana fadin ina zan dashi ai sai kin gani kin sa albarka wanan sabon sauyi da ya samay mu haka ko hajiya ummu tasa bakin albarka gata can tana addua ai. Yana zaune yana murmushi daga inda yake tace yanzu kai wanan abin don Allah bai ma dadi ba kokai fa yanzu shine muhinmanci auren wace ta san darajan iyayye din da muke nuna maka haka tun farko. Yace yanzun mai tun da safe muka kwasa da fati hajiya da mommy na hada baki suri fadin kai don Allah bar zancen wanan sakaran da bata san inda ke mata ciwo ba fati kan bansan halin ta ba wallahi. Nan dai ya kora ma su bacin randa sukayi da ita ya kuma labarta masu halin da suke ciki da Nafisa kafin yazo. Hajiya mama tace dama kai ka barta tana iya shege nidai abinda zan fada ma shine kada su kuskura su taba lafiyan diyar mutane don Amana take gare mu girma da darajan iyayyen ka yasa aka bada ita ba tare da wani dogon bincike ba . Shiru yayi yana sauraren bayanin da mahaifiyar shi ke mashi din Yusuf ne yayi karfin halin yin magana yace insha Allahu hajiya hakan ba zaima faru ba. Don yanzu ai dole ya ya dauki mataki a gidan tunda iyali khadija itama zata fara ajewa kinga ko barin su haka a gidan ai bazai yuyu ba don ko yaran nan da sukaje mata hutu sai kafa kafa take dasu a gidan saboda su. Tace to don Allah ji yara da gidan uban su basu da dama suyi wani dogon motsi wallahi kaji na fada ma ya zama dole yanzu ka dauki mataki akan alamarin gidan ka. Ita kuma wanan mara wayon ko wanan kokarin da yarinyar nan tayiwa yaran nan bai sa ta kawar da duk abinda ke ranta ba. Ta yi kokarin itama gyara auren ta don abin ita nata miskilanci ne shitasa na dawo daga rakiyan ta yanzu don ba yar goyo bace lalaci da son kai yai mata yawa a rayuwa har bata iya tsinana wa kanta komai na rayuwa na ci gaba. Sun dai dade a zaune gurin hajiyan suka mike zuwa gida ban samu shiga gaida su ba a ranan don muna gama girki nayi wanka na kwanta sai barci. Damana na aje masu komai da zasu bukata na kuma aje na sauran mutane duk na halartawa laraba na shige na kwanta. Can cikin barci nake jin yana ja min kafa na a hankali na bude idanuwa na sauke a kanshi yana tsaye saman kaina yace kizo zaku gaisa da childship dina mikewa nayi zaune. Zaki iya tashi yace min na kada mai kai ya fita ban fito ba sai da nai makeup a fuskana na dan gyara tare da dora gyale a kaina. Tun ina saukowa suka sako min idanuwa naji suna magana kasa kasa har na karaso inda suke su biyar ne bakin namu. Ina zuwa nayi sallama tare da dafa kujaran da yake zaune a kai na zube kasa ina gaida su da zuwa tare da masu barka da sallah. Masha Allah naji sin fada tare da fadin maye gaskiya Allah yakaimu ga danshin ka wanan zukeke haka ga ladabi da sanin ya kamata gaskiya kai muna wayo ka kuma falkar damu ko muma Niger state zamu koma ne ? Suka sa dariya wa wanda ke maganan mikewa nayi na shiga kitchen na hado masu abinsha da naman kajin da akai pepeying sai cake din da maryam ta ai min. Na fito masu dashi wani daga cikin su ke fadin wanan ai ba maraba da buzuwar taka har ma ince tafi buzuwan taka komai gaskiya ka gode ma Allah. Ban sake fuska ba don maganan su ya nuna yan duniya ne ba kunya gare su ba don basuki in zauna cikin su mu taba ba idan sun hadu da yar duniya kamar su da sai in biye ai ta darawa. Kitchen na koma bayan na gama gabatar masu da abin sha din usualy mama laraba dama kamar a kitchen din ne wurin zaman ta. Tambayan ta nayi idan yaran sun ci abinci da suka shigo tace ta basu sunci sai dai uwar su ce bata fito ba tun dazun nace mama ki shiga ki huta daga ciki mana. Tayi murmushi tace ai banda hutu yar nan kamar can umurni ne haka daga uwargidan nan tace in dinga zama nan kusa da kitchen kada in nisa da nan irin wanan lokacin . Na juyo nace haba mama mutum ai anason shi da hutu wanan aikin da muka sha kuma ba zaki zauna ki huta ba hakana. Ta danyi murmushi tace haka na saba ai shiyasa da naje guri ki can ai naji daban do kin dauke ni kamar ta jikin ki. Mama kada kice haka ke fa uwace a gare mu kuma ko banza ma kin haife ni don haka ki bar wanan tunanen ki daina daukan kanki a matsayin yar aiki a gidan nan ke uwa ce a gurin mu. Muryan AA ke kira na daga falo na amsa da naam na nufi falon wurin su tire din dake gaban su yace in shiga dashi ciki na kwashe kayan zuwa kitchen. Dakin anty na shiga na samay ta a kwance tana waya nace anty baki fito ba har yanzu abinci fa ko a kawo maki nan daki ne ? Tace bayan amsa sallaman barshi ai yanzi zan sauko idan nayi wanka nace to barkan mu da sallah Allah ya kara maimaita muna tace amin daddy nagani yana barci a kasa nace daddy barci kayi ne ai na dauka kana gurin hajiya ne tace yana nan tunda suka dawo yaci abinci yazo ya kwanta. Ban san sun dawo ba fa su nake jira su dawo muci abinci ashe har sun shigo ina barci na fita bata kara min magana ba dai. Inda na idar da sallah ina zaune AA ya shigo da kudi masu yawa a hannun shi yana fadin bakin ki sun wuce sunce a baki wanan yana miko min kudin. Anty ya kamata kakai wa nace dashi wani kallo yai min ya nufi gado yana aje min kudin tare da fadin idan kin ga zaki iya bata sai ki bata wanan dai ni ke sukace a bawa na dawainiyar da kikai masu ne . Ya fice daga dakin ina idar da sallah kasa na sauka muka gyara ko ina na gidan har kitchen na feshe ko ina da kamshi ferfesu na dora don nasan ba abinci za a iya ci ba da dare. Four ya gauta na gama komai na dawo na shiga wanka na kara sa wasu tufafi sai dai kayan nawa nasaka wanan karon don atamfar da na saka ya damay ni. Rigar yai matukar karban jikina har zaka iya gano cikin jikina da ya baiyana yanzu falo na sauko muka zauna da mama laraba muna hira. Binta da zainab suka shigo gidan muna ganin juna muka dauki ihu dasu sai kuma na juya da fadin Binta ai nayi fushi tace tambayi zainab Abba ne ya hanani zuwa. Saboda gidan ku baida dadin zuwa ga mutum don babu kwanciyar hankali inji Abba nace kada ki dorawa Abba laifi Binta tace kin tambayi zainab idan baki yarda ba. Mun gaisa na mike na shiga kitchen na hado masu tire na kawo gaban su na aje ina zama Binta tace ashe abin har ya fito haka ne ? Nace ya fito sai ki shirya dama kece uban shi ai tace ko yanzu shiga daki ki haihu ki gani idan banda shiri nace uhumm kwana nawa ne Allah yasa Abba yace auren ki dana zainab za a hada inga tsiyar wanan bakin. Muna gidan tare dasu har dare sai da sukayi sallah isha,i suka tafi tafiyan su da kama minti biyar bakin mu suka shigo gidan. Ina kara gyara falon babu sallama sai ganin mutum nayi ta fado gidan har na firgita nace a, a sannun ku da zuwa ashe kuna hanya tafe ? Kamar ba zata karba min ba sai kuma naji tace eh Ihisan na gani na tayo gurina da gudu ta fada min a jiki nace Ihisan nayi missing dinki. Wani yare taiwa yarinyar naga ta kara makale min a jiki na rike ta tare da fadin tafi gun mamaki kinji. Sama ta nufa ta bude dakinta ta shiga ruwa na dauka damai sanyi da mara sanyi nakai mata a dakin sai dai ban shiga daga ciki ba. Yanyala ta fito ta karbi ruwan tana fadin angode na juya na fito Ihsan ta kara biyo ni karo na biyu muka sauko kasa. Nan suka hade da daddy suna wasa irin ta yara Anty Fati da tun safe sai wanan lokacin ta fito muka gaisa ta kalli yarinyar tana fadin wanan fa? Nace yar gurin Nafisa ce yanzu suka iso tace cikin wani irin yanayi ai sunzo ne suma ina Affan yace min basu gidan koda kuka taso. Nace haka ne daga shi ban kara magana ba ita ma haka ta zauna tana cin abinci da bataci sai yanzu da tafito din Sai tara ya shigo gidan yana shigowa idon shi akan Ihisan ya sauka yace ke kedawa kika zo tana ganin shi ta ruga wurin shi ta rungumay shi. Hannun ta ya rike suka hau sama zuwa dakin su a daidai lokacin Samira tafito tana ce min anty Abinci yunwa nake ji tare da zama a hannun kujaran da nake zaune rabin jikin ta a nawa. Nace barin hada maki kikaiwa wa su Ami din ki ko tace No a nan zaci gurin ki tana gyara zama kitchen na nufa na hada masu abinci naba ta takai lokacin yana tsaye suna fafatawa da ita a gurin. Yana zuwa ya tura kofan tana zaune tana waya saman gadon ta yace ke wa ya baki izzinin shigo min gida cikin iyalina ? Banza tayi dashi sai da ya kara maimaita abinda yace mata din ta juyo tana fadin naga nims gidan miji nane kuma gidan uban diyana. Rai bace yace ku fice min daga gida kafin rayukan ku ya baci yanzu awanan lokacin samira ta shigo da abincin dakin ya bita da harara. Tace gidan miji nane don haka babu inda zan tafi yace ok haka kika ce tace eh yace ok barin zo yanzu ki gani ya juya ya fita. Kallon abincin tayi tana tambayar yarinyar wa ya bada abinci tace anty ce tace in kawo maku wani irin bacin rai taji a zuciyan ta cikin yare tace yar iska munafuka zanyi maganin ki a gidan nan. Yana fita ya kira waya ba,a dauki lokaci ba sai ga yan sanda har biyar mata biyu maza uku sun shigo gidan kai tsaye yana gaba suna biye a bayan shi Muna ganin haka muka bisu da kallo yaran dai suna gurina suna cin abinci hakalin su kwance can mukaji hayaniya daga sama inda dakunan suke. Nan yan sandan mata suka taso su a gaba kamar a falki sai ga Nafisa tana share hawaye yanyala na goye da yar baby a bayan ta Nafisa ce a falon ta kalli yaran take fadin su taso Samira tace Ami na gaji da wanan yawon haka ku tafi ku barni gurin anty don Allah har ku gama. Yace maza ta tashi tabi uwar ta da sauri nace please yaya kada kusa yara a cikin zancen ku dan Allah wani kallo ya watso min sai da na dukar da kaina kasa. Ya kuta ya bi bayan su tana kan zagin shi na fitar arziki Allah ya kyauta nace Anty Fati daga inda take zaune take fadin Allah nagode ma da ka nuna min wanan ranan da raina da lafiyata. Can rikici ya kaure masu tace bazata shiga motan yan sanda ba tunda gidan shi yace ta fito ta fita ai sai da yaga wucewanan su daga unguwar ya koma cikin gida bai tsaya falon ba ya shige dakin shi muna zaune munyi tsit a inda ya barmu zaune sai dai wanan karon ihisan ta gama cin abinci ta kwanta tayi filo da jikina da ita da daddy. Ashe bata wuce ba Family house din su ta shiga gurin iyayyen shi da kuka tace tazo ya kore ta gidan shi ko tausayin yarsu da take fama da ita baiji ba. Don inda yanyala tabi tanata da sun bar yar a gidan bata tafi da ita ba ga yarinyar tana callara ihu gwanin ban tausayi amma haka ya rufe ido ya kora su daga gidan. Mommy hajiya mama ta aika a kira don dare ne kowa na part din sai ga mommy don binta ta fada mata ga buzuwa tazo yayan su ya korata daga gidan shi. Har su umma an kira sun zo da anty amarya Biinta ta shige daki ta kira yayyun su tana labarta masu dan abinda ta sani daga cikin zancen. Mommy ne tayi karfin halin magana bayan ta karbi yar daga hannun yanyala ta dubata tana fadin Allahu Akbar Allah mai iko sai kuma ta dago kai ta kalli nafisa tace To Nafisa abinda ake gudu ke nan ya faru samun wuri yasa kin wuce iyakar ki kina taka kowa yadda kike so baki tuna akwai Allah. Nan muka je gaida ke akan lalurar rashin lafiyan cikin yarinyar nan kika rufe ido kikai muna cin mutunci a gaban kawayen ki da kowa. Mu dai mun san babangida namu komai ko ya faru bazai taba kin mu ba don mune dai iyayyen sa mudin da kika wullakanta. Yanzu kuma ki dauko kafan ki kice kin zo wurin mu wai neman sulhu ko kin manta da maganar ki na ranan da kikayi akan zuwan mu. Anty Amarya tace irin wanan ranan akewa gudu duk abinda bawa keyi Allah yana kallon shi ai don yanzu tun a duniya Allah yake fara hisabinsa. Ke baki zauna lafiya da miji ba, haka kuma yan uwan zama ki baki zauna lafiya dasu ba kin bi gida duk kin burkuce mai da bakar fitinan ki. Ga magana suna ta zuba mata babu daman ta basu amsa don ita yanzu bukatan ta kawai a samu a shawo mata kan Samad din ta takeyi daga baya sai ta san abinyi. Hajiya umma ne tai magana karo na farko bayan ta gama kallon yar tace yanzu da kika zon nan din may kike son muyi maki ? Wanda ke zama dake ya gaji da halin ki yace baiyi mu may ye namu a ciki ko lokacin da ta auro ki ya kawo ki gidan shi mun sani ne ? Ba irin wullakancin da baki wa yaran gidan nan dama yan uwan mijin ku suda gidan dan uwansu kin hanasu zuwa kin tare gaba kin tare baya. Yanzu ki koma don mu ba abinda zamu iya maki tunda kince ba son ki muke yi ba sai kije gun masu son ki su gyara maku zancen tana fadin haka ta mike ta bar dakin. Hajiya mama tace kin ji abinda yaya tace don haka ki koma inda kika fito yaje can ya samay ki shida yaji yana iyawa don yanzu ban san may zan fada ba don in ina tuna abubuwa raina kara baci yakeyi. Hajiya umma ne ta dawo dakin tana fadin ki taso Alhaji na kiranki ta juya tace hajiya Binta ku taso muje gurin Alhajin . Suka fito banda yanyala da bata bisu ta zauna a dakin hajiya mama din don ita hajiyan tace babu inda zata. Yanyala ta kala bayan fitar su tace kunci abinci tace yanzu Dija amarya ta aika muna dashi muna shirin ci yazo ya kore mu daga gidan. Dabiar yar uwaku baida kyau bai kuma da dadin ji samun wuri ai ba hauka bane tana ganin dama Allah bazai tambaye ta wanan fitsaran da take bane wa mutane. Yanyala tace hajiya hakkuri zakuyi don Allah ku taimaka muna mun sha wallah sosai tsakanin shekaran jiya zuwa yau abin ba dadin fada. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Washe gari na tunda safe na hada breakfast ina gamawa na aika laraba ta mikawa kowa nasa don guje wa fitina kuma. Girkin rana na dora don firlta hakkin mutane kada in fita banyi ba alhaki ya hau kaina a gurguje na gama komai na zuba again takai masu. Wanka nayi na shirya na nufi cikin gidan su part part na shiga nagaida kowa na dawo gurin hajiyar su. Mun dade a falon tare da ita tana kara min godiya irin canji da take gani a tare da dan nata take fadin sai kin kara jajircewa don wanan matar tashi ban yarda da nadamar ta ba har yanzu. Babu komai nace mama adai taya mu da addua tace fauziya suna fada min abin arzikin da ya samay su jiya sai dai kin san ba abu bane da za ai saurin bayyanawa a fili sai in maganar ya tabbata ko ? Nace gaskiya ne hajiya tace banson ko mommy ku taji wanan labarin sai idan abin ya tabbata gaskiya ya mika masu takardun a hannu kowa ya sani. Don mijin nan naku ne baida tabbas a al,amarin shi yasha yin alkawari irin haka karshe ya barni ana yaba min magana a fakaice. Mama ki kara hakkuri don Allah muma haka muke dashi alamarin nasa sai da addu gaskiya don zakaga ya bi hanya kwana biyu kuma sai ya kauce kamar bashi ba a rasa gane kan shi. Sai naji tace Alhamdullahi dana samu wace ta fahinci hakan gare shi wanan abin yana ci min tuwo a kwarya khadija yanzu ki duba dan wurin hajiya yaya ummar ku nan. Surajo ai ba kaishi yayi ba ga komai amma yadda yake kula da mahaifiyar shi da yan uwan shi a dakin su sai abin ya baka sha,awa ni nawa sai sunan kudi amma babu amfani gare mu daman ma yanzu ne nake dan ganin haske abin. Tausayi ta bani yadda ta zauna tana fada min damuwar ta nasab abin yana cin ta sosai a rai tunda har ta iya zama dani tana fada min hakan. Tace bandamu da sai yai min ba amma ya dinga kulawa da mahaifin shi da yan uwan shi bawai dole sai nawa ba a,a duk dan da ke cikin gidan nan yanzu shine babba a gare su ai yakamata ace suna alfahari da abinsa ai. Shiru ni dai nayi ina sauraren ta tana kuma ban tausayi ga maganan ta wanda gaskiya take fada koda ba a cikin kishiyoyi ko take ba kowa nason ace nasa na kwarai ne. Mun gama nake cewa zan leka gidan anty na in gaidasu da sallah tace to a dawo lafiya zaki leko ta nan ne kafin ki koma gida ko nace insha Allah mama. Har na fita gidan ina tunanen wanan magana Binta ce ta rakani don zainab tana kwance tun safe wai bata jin dadin jikin ta. A kofar gidan Ya Amina muka hade da mijin ta a get zai fita tun daga nesa yake min dariya na karaso inda yake nace ya Adam abin dariya kuma na zama gare ka ko yanzu ? Yace mamaki nake wai yar khadijace haka ruku ruku da ciki nace ai haka kuke son gani na dama kuka lakaka min aure binta ne ta amshe auren bagaki kin sake ba kin zama wata basaraka dake. Baki na tabe yace kyale ta binta kinji tana matar last done haka takewa mutane korafi yanzun zaki koma ko kina nan zanje gidan hajiya in dauko yara ne dama sun maysa a dauko su suzo wurin ki tunda sukaji kina gari. Nace ina nan har dare tare daku yace barin je in dawo mu sha hira ashe iya matar manya duk kin wani canza ga baki daya wallahi. Nan dai na wuce ya na barshi ya shiga mota yana min sheri muna shiga na samu anty tana gyara falo su tana ganin mu ta washe baki tace mutanen Abuja. Wallahi yanzu na gama magana yau idan azahar tayi ban ganki ba zanje gidan naku in ganki nace ai gani nazo yanzu. Muna waje da mijin ki yana min sherin shi da ya saba ina ganin sai munyi fada dashi zai daina yanzu ma fa dariya ya dinga yimin a waje. Binta ne ta gaida ita yasa bata bani amsa ba suka tsaya gaisawa ta tambaye ta mutanen gida tace suna lafiya bata tsaya ba ta mike tana fadin madam ni zan tafi sai kin dawo ke nan. Nace madam kan ai tana abuja suna bushasha wata kawar buzuwa ce uwar dakin su suke kira madam tace ko wata garmakar mace haka karfafa nace ita ashe kin santa ma ? Tace na santa mana lokacin da mukaje sunan ihisan sukayi muna tsiya suka kulle abinci Allah yasa da mommy na gidan ta saka aka kawo muna a wani gida. Dariya nayi nace kai Nafisa ai ta tsula tsiya gidan nan kuma har yanzu akan yi take don ku jiya sai da muka kwasa da ita ai bayan fitar ku. Kai khadija wallahi kina kokari mun dawo gida muna maganan ki da hajiyan mu take cewa ai tunda batayi galaba a kan ki ba yanzu bazata taba yi ba da yardan Allah. Ke dai adai yi sha,ani wai ancuci na kauye ni abin nata gani shi nake kamar mai motsi akai tace babu motsi wallahi inji ya Amina haukan kishine irin nasu kawai su haka suke kishin su a haukace. Nan gaba idan taga abin ma bai mata ba taga ba ci kokari zatayi ta wawashe mijin naku ta gudu kasar su bai kuma samun labarin ta. To Allah ya kyauta nace ina dora kafana saman kujeran da nake zaune akai Binta tace wai khadija wallahi ba don na sanki ba da sai in ce baki taka kasa wallahi. Duk kin canza gaba daya komai naki yayi fresh nace tafi yar sheri wanki da ko mota ya kasa sai min don tsoron buzuwa wani kasa zakice ban takawa kuma. In dai mota ne tafe yake ai ki dai haihu ki gani har abinda yafi mota zamu saya maki nace oh haka kuke ashe kowa yaci ladan kuturu yasha dungu ko ? Ta fice tana dariya ya Amina ta zauna gefe na tana fadin abindai da sauki yanzu ko na mede baki nace wani sauki dukkan su biyu fa anty ba wani sauki don ko anty fati ba baya ba ashe. Tace ita fatin nace dama mana nidai kawai ban bin ta nasu ne don kawai a zauna lafiya amma ko ita ba kanwar lasa bace. Tace zata iya indai Fatice don ba wanda ke jin dadin ta a gidan nan ko kwanaki na iske suna rikici da na shiga wai motar ta ya baci ta sayar bata fada ma kowa ba kuma an nemay kudin an rasa su. Wai to Ya Amina may take da kudine sai naga tayi dariya tace ke ma ai ba sai kin tambaya ba ni dai abinda nake so dake khady shine. Kada ki yarda da cewa wani zai iya maki wani abu ki yarda da Allah shine maiyin komai a rayuwa ki idan rokon Allah ne ki tashi da kan ki Allah maji rokon bawan sa ne. Ki dai dage da gyaran jikin ki kina kara ma kanki daraja a furin mijin ki wanan kan ban hanaki yin sa don yana taimaka wa mace a rayuwan auren ta. Amma bin boka ko malam kin san ba dabiar gidan mu bane kullun da wanan zancen nake kwana ina tashi ina kuma maki rokon Allah kema kada kiga suna yi kice zaki kauce ma hanya yanzu da abinda yan uwan Fati suke mata korafi ke nan. Sai dai kuma dole ne yasa Fatin yin haka don tana ganin shine kawai mafita a gareta ta manta da Allah shine mai yin komai. Nace anty ni jiya na kara yarda da halin ta da ake fadi ai wai fa kin yin girki tayi don kawai na taimaka nayi mata girkin sallah ranan danaga suna rikici da miji. Ashe ta kulle ni a rai ta aje shine jiya taki girkawa da yai magana tace wai ai nice mai girka mai may yasa ba zai tambaye ni ba. Tace ai da kin sani ki kyale su a zauna hakana mana ba ita zata sha wuya ba ita dake da yara ke haka fa take bata dadi da kowa bata shiga mutane ta waye. Ai mijin nan naku yana da mata wallahi ga mutum har mutum amma bai samu abokan rayuwa a gidan shi ba shiyasa yake kara yin abu a dabbale wallahi. Don mace na kara gyara namiji ta hanyoyi daban daban sai idan ba ai dace ba zaki namiji bai kullawa yan uwan shi komai. Nan nake fada mata hiran mu da hajiya tace matar tana a cikin damuwa ne khadija yau ba maison ace nashi baida kirki ai. Mijin ku fa yadda nake ji ba karamin mai kudi ba ne a garin nan shi ma rigima ne dai kawai da baida shi amma kinga yan uwa sai korafi sukeyi akansa. Waini ya Amina yanzun haka zan zauna ban leka mama ba idan shi Daddy bai son ganinna ita mama fa da ya tauye mu da ganin juna. Tace kin manta haka halin daddy yake ne ko suwaiba dake cikin gari ai dai kinga yadda suke kwashe wa dashi idan ta jera sati uku tsakani tazo gida. Halin su ne na filani ya dauko yake wanan akidar haka ko kuma tsabar izzala ce ta haushi haka ban sani ba kiyi hakkuri kwana nawa ya rage idan kin haihu zaki gan su. Ya Amina har wanan lokacin ban je gida ba gaskiya nikan da mun koma din nan zan matsa mashi zani gida ne don banzama har wanan lokacin ban leka su ba. Shigowan yaran da ihun sune ya dakatar damu da hiran sukayo kaina na rungumay su a jikina Allah ya dora min son yara a rayuwana tun kan yayan ya Amina din. Karamar da bata saba dani bane taki zuwa wurina dole na yunkura ina fadin zo nan yar bura uba mai shege kiuya kawai wai ita nan bata san ni ba. Uwar tace ke ko ina zata sanki tunda aka haifeta ba zuwa kike sosai ba kuma datai wayon na kinyi aure ba zuwa kike yi ba tana ganin ki. Mijin tane ya shigo gida yana fadin matar manya ke nan gani na dawo nace wata matar manya can kodai matar wahala may ke gidan ban da tarin fitina kullun safe da kalar da za a tashi dashi. Yace mijin ki fa last done ne wurin kudi khadija bazaki fadi haka ba ai mana nace ya Adam kudi ai basune farin ciki ba ko ? Yace hakanane kuma kin fini gaskiya tanan har ina cewa zan kawo wani ogana da ya dade yana neman fili a wurin shi yasa mashi hannu yaki ki muna hanya asa. Tsuki naja nace wanan idan yaki abu ai ya kishi ne sai dai mu gwada mu gani idan zamu ci sa, a kawai amma bansa zai yi ba wallahi. Yace kai dako kin kyauta muna wallahi khadija bashi ba harni nan da na warke idan wanan abin ya yuyu ai aje aki gaba daya zanyi in fara business. Nace kai yaya Adam wanan wani irin abune da zaisa harka aje aikin ka kanshi kuwa yace wallahi khadija muddin muka samu ya sa ma takardan nan hannu mur warke har abada. Ina fada maki AA ba karamin mutum bane fa sa hannun shine kawai ya gagara wata kila kuma da rabon mune har abin ya biyo ta wurin mu yanzu. Ogana wani dan jalingo amma lagos yake zaune yayi ritaya shine ke ta binshi shekara da shekaru yaki saka mai hannu a takardan nan. Shiru nayi ina tunane har banjin may yake fadi sai can naji yana fadin ai kinsan da ina da sister wace ta rasu din nan a lagos farkon auren mu da yayan ki nace eh yace to ai mijin tane nake maki zance nace in Allah yaso zan masa magana sai dai nasan zamu kwasa dashi koda zai yarda din ma. Ya Amina tace ki daibi a hankali kada wanan maganan ya hada ku nace insha Allahu ko maryam kawana ta taba min korafin nan yaki saka ma mijin yayan ta hannu. Ya Amina tace ashe haka yake dai sai mijin ta yace aikin nasu ne akwai hatsari a cikin sa da yanzu yana saka hannu barkatai da sun yi waje dashi tuntuni. Ko jiya da dare naga matasan masu kudi garin nan sun parke motocin su a kofar gidan shi nasan wani harkan business sukeyi kinsan shi fa dan kasuwa ne kuma yana wasanni da dama ta idan kudi ke zo mai ke nan ai sai dai akwashi da boyon kurwa ne sosai wallahi. Ina gidan tare dasu har dare anan na wuni sai baya magariba ne ya kirani yace wai kina inane nace gidan yaya na amma yanzu mijin ta zai sauke ni gida idan ya dawo sallah. Yace No ki jirani in zo akwai inda nake son muje daga nan nace dashi sai kazo ya kashe wayan yaran ya Amina na rabawa goron sallah. Kudi ns girka masu yawa na aje mata a gefen inda take zaune tare da kara kirga wani na sake aje mata nace naki ne da yaya Adam kuyi hakkuri dashi baida yawa. Ita ya Suwaiba nace ta bude account taki har yanzu kuma tana raina sosai don nasan irin wahalan da suke ciki idan ta bude ai kinga zan dan rika tura mata da wani abu lokaci lokaci. Tace zan ma daddy magana a bude mata din kin san halinta nako in kula da abu ai gaskiya kan tana bukatan taimako nace aishine kullun zaka bata abu sai ta hannun daddy dole shi kuma ya dinga fada da mutum wai kana rikon mijin ka kudine. Ni kuma wallahi anty ban iya cewa ya bani kudi idan bashi ya dauka karan kanshi ya bani ba tunda muna samu a gurin girki idan zakayi dubu goman nan sai ya zube ma shi kafin ya fita. Tace yanzu wanan din da kika bamu baiyi yawa ba khadija nace idan ban baku ba wazan ba anty tunda kune dole na. Bandai ba dangin shi kudi kai tsaye sai dai in saya masu wani abu in basu gudun yawan magana da zargi tace haka shine daidai ai. Don wallahi zargin ki zasuyi akan yana sakar maki kudi su bai basu ba tace kina da dabara da yanzu an fara kusun kusun kin san gidan yawa. Wayana ne yayi kara na duba shine a layin ina dauka yace fito mu tafi nace a, a bazaka shigo ku gaisa ba ke nan kuma sai naji ya kashe wayan. Tare da yaya Adam suka shigo gidan har cikin falon ta suka shigo suka shiga gaisawa tana mai barka da sallah. Yaran suka zo suka rusunna suna gaida shi ina ganin yaji dadin hakane naga ya shafa kan yar karamar yana tambayan ta sunan ta. Kudi ya debo ya basu tare da ajewa ya Amina nata a gefe ya mike yana fadin zai mu tafi zamu unguwar dosa ne. Yaya Adam sai wani haba haba yake mai abin ni sai mamaki nakeyi na mike ina cewa ya Amina sai na kara shigowa tace yaushe zaku koma ne nace muna nan tukun ba rana. Tace tafiyan ku ai kamar na filani ne idan ya tashi ko ba shiri ranan tafiya zakuyi nace to ya muka iya sai bi har wajen dirkekiyar motar shi suka raka mu ita da yara mijin ta yana tsaye dashi a waje nayi masu sallama na shiga muka tafi. Yace yau kin kawo mata dawainiya ko nace wani dawainiya kuma mutum da dan uwan shi ina dawainiya ina zamune wai haka ban ko zata ba. Yace baki da shiri ne mu koma nace ban ce ba ina dai tsoron ka saida nine kawai dariya ya dan sake yace dasun sai mai baki kan. Gidan gwagona zani kanwar Abba tayi ciwo ance tana ta magana na ko yaushe can nake son muje mu gaishe ta don yau nake da lokacin zuwa. Allah sarki ashe dai daddy yana da yan uwane da yawa haka yace sosai kuwa suna da yawa fa sosai don ma wasun su sun rasu ko . Mun isa gidan da ganin gidan ya dauki shekaru don ba wani gida bane can irin dai gidan tallakawan ne kamar mu. Da haba haba dattijuwar ta karbe mu tana fadin maraba da babana yau kaine a gidan ashe da rabon zamu kara haduwa dakai yace yana shiga dakin gwago kiyi hakkuri wallahi ban faye zama kasan bane muka shiga dakin tana kokarin kawar da tsumakaran saman kuje ta gyara mai wuri tana fadin zauna zauna baba ubangiji yai maku albarka da ka tuna dani yau. Ina tsaye daga kofa ta kawar da kayan saman gadon gefe tare da fadin karaso kinji yar albarka tana nuna min inda zan zauna. Na kai kasa saman carpet din sallah ta tare da fadin babba nan ma yayi mun ai aka shiga gaisawa tana ta tambayan shi mutanen gidan su da iyalin shi. Ta juyo tana kallo na nayi murmushi ina gaida ita ce itace buzuwar ko sabuwar ce ta garin nufawa yace sabuwar ce gwago. Ta kamo min hannu tana fadin sannu kinji yar albarka ki rike min ubana da kyau kinji kinsa mata suke gyara gida ina murmushi nace to babba . Nan sarakanta da yara ta suka fara shigowa gaida shi suna mashi sheri bai iya wasan tobashi ba sai kamay kamay yake masu yadda na lura dashi. Matar tana da kirki a yadda na kula ga addini magana kadan ta kawo Allah tana nuni da rikon zumunci a gare su. Yace Ahmed fa yana inane yanzu sai da ta dan bata rai tace yana nan gida kasan shanin aikin su na Nepa ashe basu da tabbas. Yana cikin wa yanda aka kora daga aiki kwana ki ga iyali ya tara kamar ka shima mata uku gare shi sai dai yadara ka don yanzu diyan shi goma ga ba aikin yi kuma. Yace wai ikon Allah yanzu Ahmed din ke da diya goma gwago tace ga na shadaya nan a ciki ana maganan shi sai gashi ya shigo tace kaga dan halas nan ya shigo. Kallon juna sukayi sai suka dara yace wai mama yau kodai dan naki yayi batan kaine yau baban ku ne a gidan ki gaskiya ranan yau ta dabance. Sun dade rike da hannun juna suna shammatar junan su sai daga karshe yake fadin yanzu nake ji wurin gwago abinda ya samay ka. Yace wallahi ya za ayi da sha,anin kasarnan tamu sai hakkuri yace haba Ahmed shi ne baka leka ni ba yace kasan ganin irin ku idan baku kuka nemi mutum ba abu mai wuyane sosai. Yanzu ai cikin hukuncin Allah gashi kai ka nemay mu ka kwashe ladan dazun naji Altine na maganan su hada kafa suje gaida kawu da sallah nace mata mu mun je tunda aka sauko idi. AA yace haba ya bamu hadu ba daku yace wallahi ana saukowa mukaje muka gaida shi kasan mu bamu wasa da kawun mu yace ai na ga alama. Gwagon tace Alhaji banda kamar Alhaji ga yan uwa duka kaf har gobe Alhaji duk da girma ga iyali yana tsaye ga alamarina garin nan sai ta fashe da kuka. Wani iri naji a raina dukar da kaina nayi kasa ina kokarin maida hawayen da yazo min a lokacin gwago kiyi hakkuri haka rayuwa yake AA yace mata ya ciro kudi ya aje mata tare da fadin gwago mu zamu tafi zan maida wanan gida don yanzun bata dogon hira ta fara tsufa. Hararan shi nayi sai lokacin Ahmed din ya juyo gare ni yace amaryan ne ko buzuwar yace amaryan ce yace ikon Allah aiko ita buxuwan ce sak. Yana washe baki ya mike tare da fadin muje waje muyi magana ina Altine ne tazo in bata goron sallah kada ta cini da bakin nan nata gwago zakiji yadda zamuyi da Ahmed din insha Allah. Sai lokacin na mike tare da fito da kudi cikin jakkana na mika mata nima tana ta saka muna albarka muka bar gidan. Sun dan dade da Ahmed din a waje suna magana ni kuma muna tsaye da wace aka kira da Altine din da sauran yan uwanta muna hira sukace zasu shigo kafin mu koma Abuja sai kunzo nace na shiga mota suna ta janshi da ba a tace sai munzo Abuja suna idan matar ka ta haihu yace kada kiyi mamakin ma kije can ki zauna har ta haihu din. Ahmed din yace dako abu yayi kyawo wallahi tunda ba aure takeyi ba yace ai shine taki aure ba sai ki koma zama da mu ba muka wuce suna daga muna hannu . Ajiyan zuciya na sauke ya juyo yana fadin ya akayi ne nace ummm, umm gani nayi ashe dai kuna da yan uwa ne haka da yawa garin nan yace wanan da kike gani uwar su daya da Abban mu da ita da Iyan bawa ok baki santa bako lokacin haihuwan Ihisan ne ta zauna damu acan Abuja. Nace ok wanan tsohuwar da suka zauna da mommy yace ita ok inji kin ji don su binta lokacin nace naje mana matarka tai muna hauka kai ya girgiza yace yanzun ma tana can ai na barta tana haukan ne . Wai ita girki zata karba yau nace ai da kabarta ta karba din tunda ita taga zata iya yace in kaita ina idan ta karba din ko ta cika min daki da fitina. Nace da ina kake kaita da kuke daki daya kefa baki da kunya nace I'm sorry big brother tuba nake yace hauka ta dai takeyi. Allah da ka barta tayi ai tunda zata iya din ko ba wani matsala bane shiru yayi min bai bani amsa ba nima shirun nayi mai sai can nace yawwa don Allah ko kasan wani AS Hamza jalingo wai. Sai da ya waigo ni yace cikin dakewa ina kika san shi ke nace mijin yayan Adam ne mijin anty Amina da ta rasu tabar mai yara biyar. Yace nasan shi may ya faru shiru na danyi kafin in ce wai alfarma suke so a wurin ka don Allah badon mu ba sai dan yan maratun diyan nan ka saka masu hannu a takardan da yake so ka saka mai hannu. Yace aikin da suka baki ke nan kuma nace a, a wallahi basu bani wani aiki ba magana daine ta taso har naji amma ni basu sani ma magana ba. Shi AS jalingo din ne baida abin duban marayu ko shirmay ki din ne yasa kika fadi haka nace kai kullun ai banda wayo ne a giri ka yace abinda nake so dake daga yau kada wani hurda aikina ya kara hada ki da kowa kinji na fada maki. Don ban daukan wanan shashanci abi ta matana ace ana neman wani abu a gurina haka don yaudara ko may ? Don Allah kayi hakkuri bansan maganan zai bata maka rai haka ba da banyi mashi ba amma ban karawa da yardan Allah kayi hakkuri ka yafe min idan na bata ma raine. Ni abinda yasa kaji nama maga hakane kawai zanyi in rama itin halarcin da yaya Adam din yai min a rayuwana wanda dashi nake tunkaho yanzu do badon shi da yai min tsaye a karatuna ba da iyakata secondry school don daddy baida halin kaini gaba. Amma ya Adam shiyayi tsaye har sai da nayi aure ya daina sa hannu a zancen karatuna shine kawai yasa kaji nayi ma maganan nan. Huci naji ya furzo dana gama maganan bai sake tanka min ba har aka wagale get din gidan muka shiga muna tsayawa ya bude motar nafita yace dauki ledan na daya ki shiga dashi wurin ki na juya baya na dauka kamar yadda yace nace Allah bamu alheri ban tsaya ba na wuce. Ina shiga falon yaran nata wasa suka sheko suka rike ni suna mi oyoyo nace miss you guys ina ihisan na tambaya tana gurin uwar ta na karasa dasu a rike a hannu na na gaida Anty Fati da tayi kamar bata ganni ba. Mama laraba ta fito daga inda take tana sannu da zuwa an dawo nace na dawo mama ya gida tace muna lafiya wajen antyn taki suna gaida ku nace tare da fadin barin dan watsa ruwa mama tace kudai baku da tada ko wani lokaci wanka kuke bamu gujewa wahala da cikin ki da tsohon daren nan zaki wanka. Idan ban watsa ruwa bane banjin dadi mama nace mata ina dariya na wuce dauke da leda a hannu na har na fara hawa sama nace mama in akwai ruwa a flasks akawo min don ban iya saukowa kuma. Tace barin in duba lokacin naji yaran na mashi sannu da zuwa na shige abina ban tsaya ba ina shiga na tube na shiga bandaki daidai fitowa na sai ga mama laraba dauke da ruwan zafi a cup tana fadin banga flasks din ba ina ganin mai abune ta dauke abinta nace tofa kuma wata sabuwa ashe ? ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Kallon yarinyar Abba yayi tare da dan jujuya ta ya dago yana fadin Allahu akbar ya mika wa hajiya umma yar yace yanzu da wanan yar haka babangida ya turaki waje a cikin daren nan ? Bai tausayawa yar shi ba saboda saboda halin da zata iya shiga yana magana yana duban wayan shi bayan ya gama kafa glass din ido shi. Umma tace ai fushin uwar ne ya shafi yar amma ai ba zaiki yar shi ba tunda ya iya kaita har waje cikin wata mai alfarma da kowa ke son ya natsu yayi ibada a cikin sa. Murmushi tsohon yayi yana danna kira a wayan shi ya kafa a kunnen shi tare da alaman saurarawa. Muna zaune falo bayan na gabatar mai da abinci yana shan ferfesun kajin danayi a matsayin abincin dare ihisan da daddy ne a gefen shi suna wasa. Sai ni da anty Fati da Affan da muke hira daga can wurin kujerun da muke zaune mukaji yace hello Abba. Duk muka dago muka kalle shi cikin kashe murya anty Fati tace yar iskan kila itace yanzu haka takai karanshi gurin Abba ai dai ta fara ganin sheri ga kaya ta. Sauren wayan yake yi ba tare da yayi magana ba mukaji yace naji Abba nagode ya kashe wayan ya dan kallo mu yana mikewa yabar gurin tare da nufar hanyar fita waje. Wallahi ban taba tausayin wanan matar a rayuwa na khadija don ban iya manta abubuwan da tai min a rayuwa na har in koma ga mahalici na kuwa. Hakuri za a Anty ai ita bata bar kowa ba nidai ban mata sheri ba indan kuma ta nufe ni dashi ya koma saman kanta insha Allahu. Tace kiri kiri mata ta hanani zama a dakina ta fito fili ta fada min kuma wai kadan na gani daga sherin ta shine yanzu zan tausaya mata ai mata ma yafi haka wallahi. Allah ya kama su daga shi har ita abinda na gani akan wanan matar nawa sane kiri kiri zasu garin nan tare tace bazan yi girki ba har su gama kwanakin su su koma suna tare. Ai wurin nan kan shagoce a wurin kwana da miji ko ni can shine yawan matsalan mu don ba shiga harkanta nake ba tun farko don haka ne abubuwa suka zo min da sauki. Don bamu taba zama haka yadda muke dake din nan ba tunda na shiga gidan nan har rana ita yau kuwa don yar rainin wayo ce tana ganin ita tafi kowa ko shi kan shi gani take tafi shi bata san namiji ki sabo ne ba idan halin shi ya tashi dan abu kadan sai ya kaskanta ka akan shi. Tace Allah ne fa ya kama su khadija ina fada maki koshi ba kanwar lasa bane wurin wullakanci bata kai karshe ba sai gashi a gaban mu don duk bamu farga da shigowan shi ba lokacin. May kike fada ya tsure fati da ido ta kasa magana ya kara maimaita maganan shi tare da kallo inda nake nace bafa maganar ka ake ba da Affan take kutawa yayi ya wuce sama. Nan yafi auki ai don nan zai iya zare idanu can ko ko mussu bai iya yi nace anty wa ya fada maki wallahi yana yi yar iskan matace dai ya hadu da ita. Sallaman su mommy ne da Anty amarya yasa muka mayar da hankalin mu gurin taron su muna gaida su da shigo tare da masu barka da sallah. Mommy suka kai kallo a gare mu yaran duk suna a kujeran da nake zaune two seater sai samira dake barci gajiya a dayan kujeran dake gefe na ta rankofo jikin ta wuri na. Mommy tace don Allah duba saboda Allah may yafi wanan Nafisa kina can kina fada akan wanan yarinyar duba yaran ki a tare da ita. Anty Amarya tace yaro ai dama fuska yake bi idan bata basu fuska ba ai ba zasu bita haka ba dukkan su. Yanzu ba Fati da khadija muka samu a tare ba suna hiran su gwanin ban sha,awa amma ke kice da kowa ba za a zauna lafiya ba. Muryan AA mukaji daga baya yana fadin mommy kun shigo tace eh babangida don Allah kai hakkuri don Alhaji da ya saka baki a cikin maganan nan kada wani abu kuma ya kara samun wanan yar. Kallon Nafisa da take tsaye tun lokacin nayi mommy tana sance yarinyar a bayan ta tana kokarin mikawa Anty Fati da ta gane haka sai tayi saurin mikewa tare da fadin tana zuwa tayi hanyar kitchen duk muka bita da kallo don kowa ya dago ta. Ni mommy ta mikowa yarinyar tana fadin karbar ta khadija nasa hannu bayan na jaye ihisan a jikina na karbi yarinyar tana ta barcin ta ba wasu kayan kirki a jikin ta duk da sanyin kaduna da akeyi din. Zama sukayi tare da fadin Nafisa ki zauna mana ayi magana tana wani harare harare ta zauna tare da yanyala. Mommy tace Alhaji ne yace idan munzo dama mu tara ku sai gashi Allah yasa mun samay ku a nan din baki dayan ku. Tau Nafisa duk da Alhaji baiji ta bakin mijin ku ba yanzu dai wanan abin ya ishe ki ishara baka shigowa wuri kace kai kan ka kasani kai kadai. Ihisan da ta kara hawa jikina anty amarya tace wai ku bakuga uwar taku cikin wani hali bane ku barta ta huta mana hakana. Shiya karbe da fadin laifin tane ai anty ko yaushe yaran nan suna saman jikin ta hatta idan abinci zata ci sai dasu take ci nayi fada bai sa sun daina ba. Tace kin zama uwar yara khadija mommy tace in dai khadija ce haka take ai tun gida da yara ita yaro baya isanta ai. Fada mai kama da nasiha sukai muna a gurin tare da jawa kowa kunne a cikin mu sukai muna sallama suka tafi suna fita yanyala ta mika hannu ta karbi yar daga hannu na suka shige dakin su. Don shi ya raka su mommy har bakin motar da sukazo dashi an daiji kunya idan an santa angama cika baki gashi tun ba,a je ko ina ba anfara gani. Anty Fati ce ke wanan maganan bayan wucewar nafisa din ciki ta ce ni ai ba zan taba yarda da kishiya ba har dai irin nafisa mara imani. A raina nace hardani ke nan dama ban ce sai kin yarda dani ba ai banda ma kowa sheri idan kun min kuma insha Allahu ya koma kan mace. Bamu dade ba na tayar da Samira na kora ihisan zuwa dakin su nima na shige nawa na barta da yaran ta a gurin. Washe gari na tashi da son zuwa gidan Ya Amina don can nake son wuni idan na shiga na gaida su hajiya da sallah daga can sai in wuce wurin ta. Sai dai hakan bai samu ba don bakin dake shigo muna su Anty fauziya ne tare dasu binta suka shigo muna gaida dan uwan su da sallah basu samay shi gida ba. Har lokacin ba duriyan Nafisa ko wani nata hatta ihisan banga ta fito ba yau abin karyawa ma yanyala ce ta fito ta karbi ruwan shayi ta koma. A dakina muke zaune tare dasu bayan sun fito wurin Anty Fati nan suka zauna muna hira sosai da su wanda hiran na zancen auren zainab ne. Sai gashi ya turo kofa suka shiga gaida shi ina dan tsaya a jikin mirrro sai dai duwawo na dake saman mirrow na zauna akai. Gaidashi da dawowa nayi ya mayar da kallon shi gare ni yana fadin bazaki zauna da kyau ba wanan tsayin da kikayi fa haka ? Gyara tsayawa nayi da kyau yace dani yau dakin nan nawa yana bukatan gyara don tunda nazo haka yake da kyakyami nake zama a cikin sa. Nace zaka bar key ne a gyara maka yace eh ina ma gida ban fita sai anjima idan Yusuf ya shigo. Ya fice Anty Fa,iza tace kai daga Yusuf dai sai yayan mu Allah ya hada amintaka a wurin nan nan suka shiga tuna labarin su na baya suna dariya. Nace ai gaskiya zainab tayi dacen miji wallahi don idan ta iya zama dashi zata ji dadi wallahi Fa,iza tace ai kema kinyi dace don yayan shima yana da hali mai kyau. Baki na mere masu nace kai anty kina dai son zance ne kawai wanan gidan gidan danger ko yaushe a cikin fitina ake. Wallahi anty wani lokaci sai inji kamar in bude ido na in ganni gidan mu don fitinan yayi yawa wallahi tace ai dazun hajiya ke bamu labarin abinda ya faru jiya nace eh tana nan ta dawo zaku shiga ne. Ina anty faiuziya ta fadi da sauri nace wurin ta anty ina dariya tace ban tashi jin bakar magana ba yau da farin ciki na fito gidana. Dakin Nafisa kuwa har lokacin tana kwace a dunkule wuri daya sai kiyasta yadda zata dau fansa akan mu baki daya take a zuciyar ta. Wai yau itace har iyayyen mijin da ta tsana sukai mata alfarman dawowa da ita gidan samad don albarkacin wanan yar data haifa a haka cikin wani yanayi. Zuciyar ta ke mata soya tun safe gashi ta hana kowa fita sai da yaran suka damay tane ta tura yanyala gurina ta karbo masu abin karyawa. Taba yaran sun sha amma har yanzu a takure suke a dakin tagane nufin su so suke ta barsu suje gun waccan yar isakan mayaudariyar yarinyar dija yar gidan malamai. Waya sani ma ko duk ta asirce har da yaran nata ne bako daya irin wanan kulawa da shakuwa dake son shiga masu don ma tana tsaye a guri daya dasu da abinta tasan zaifi haka. Madam ta kira a waya tana sheda mata duk yadda akayi tace dama ai malam ya fada muna zai karbe ki idan kin je tace kayya da kinga irin wullakantan danayi a gurin su madam sai kin tausaya min. Wanan yarinyar na yarda ba a banza ta shigo gidan nan ba ga iya kissa kamar tsohuwar karuwa tasan kan sheri har ta gaji. Yanzu so nake da komai ya daidai in shege kasar mu kafin yar iska ta haihu in yi waje da ita ta haihu can a gidan su ta dandana bacin ran data sani ciki ita ma taji idan da dadi. Madam tace injin kin tuna da kai mata wanan yarinyar wurin ta shegiya muga karyan jan yara a jiki idan zata yarda ta mamay ta a haka yadda take. Don nasan shegiya da wayon tsiya ba karbar yar zatayi ba zata samo wani abinda tace tana mata ta guje ma ganin ta kusa da ita. Ai ko ta guje tura mata zanyi shegiya sai ta haifi irin ta itama ko wace ta fita idan tace sheri ta iya mu zuba dani da ita a gidan nan baki da dama wallahi nafisa madam tace. Kofan ya turo tayi saurin kashe waya tana kallon shi yace dawa zaku zuba a gidan nan kina da aiki don ko yanzun kika kara gigin min iskanci ba kyale ki zanyi ba don nagaji da halinki nafisa. Tace nasan ai ba yin kanka bane duk abinda zaka fada yanzu kana da daman fadi duk abinda kaga dama a kaina yanzu. Yace ki bi sannu wallahi kin san zaman da kike a gidan nan don haka ki natsu kamar yadda kowa ta natsu don ba fin wata kikayi a gidan nan ba duk abu daya ya kawo ku gidana. Idan akwai abinda ta tsani ji shine yace duk daya suke da sauran matan shi har da wanan da ta shigo kamar jiya a rayuwan shi dama fati abin banza da bata da wani kira na mata da ake so. Juyawa yayi wurin su samira yacewa ihisan may takewa kuka samira ne ta bashi amsa da fadin wurin anty take son zuwa Ami ta hanata fita. Common taso kije don may zaki tsare yarinya haka a daki ki hanata walwala tace don ya tace ita din yace yanzu kin daina fadin tayi zuciya ta haifi nata ne ? Ya rike hannun Ihisan suka fita a cikin yare ta fadawa samira ta dauki baby takai min ita tare da feeder din ta ta mike dama itama fita take son yi ta sukuci yarinyar suka fito daga dakin. Muna zaune dasu anty Faiza muna hira ya shigo rike da Ihisan yana fadi gata nan wai zata zo wurin ki uwarta ta hanata. Fauziya ne tace ikon Allah har yara ma a cikin kishi wanan mace dai Allah mana tsari da irin su wallahi faiza tace ai abinda mutum keyi sai yaga kamar shi kowa ke yi. Fauziya ta fada maki abinda ta roka maku kun tatauna da ita kuwa wani irin kallo nayi mai ina mamakin shi wani irin mutum ne haka da baya boyon magana kai tsaye yake fadin abinsa. Kallo na sukayi tare da mayar da kallo a gare shi tana fadin bata fada muna baz yayan mu khadija alheri ne ya samay mu komay ? Zanyi magana Samira ta shigo dauke da baby a hannun ta tana fadin anty ance in kawo maki ita nan na mika hannu ita fadin mama na Allah sarki na karbi yarinyar. Nadan dubata tare da nufar anty Fauziya da ita na mika mata yarinyar tana ganin katon kai tace subbahanallahi haka take nace eh abin tausayi ne yarinyar yana tsaye a dakin har lokacin yana ma yar gurin Faiza wasa. Nace ki duba cikin ta inda akai mata aiki da wurin a bude yake tayi saurin bude cikin yarinyar ta gani ta mayar da sauri don har yanzu akwai wani roba a jikin ta. Da ta dago kai tana kallon yayan nata dake tsaye tace yaya haka aka haifeta ashe yace wallahi abin akwai tausayi sosai saura suka mike zuwa ganin yarinyar. Yake cewa su Ikilima dai basu damu da zuwa wurin mutane ba Faiza da ta sauke ajiyan zuciya tace yayan mu kasan su ai da nuna akidar wariya dakin su har yanzu haka muke dasu ba abinda ya canza. Yaran dakin mommy ne can zaka ga an kawo su suce sun zo ziyara ne kwana bibiyu suna zuwa wallahi yace shiyasa nake so mommy halin matar nan yana min wallahi. Motsin da yarinyar tayi ne ta miko min ita da sauri yana kallon mu nace barin goya ta ko zata dade tana barcin yace likita ya fada mata haka daga ita har yan uwan nata raggaye ne. Ina goyan yarinya Binta dake zaune fuskanta wani iri tace ke da cikin ki hakan nan zaki goya wanan yarinya don Allah ki bada ta amaida mata da abinta. Dariya nayi nace may kike tsoro kada a kara haifo maki haka ko may ai mutum baya kaucewa kadaran shi ko ina yake. Baiyi magana ba sai dan girgiza kai yayi ya fice daga dakin Faiza tace ai gaskiya ne khadija ko ita sheri yasa tabayar akawo maki don tasan kina da ciki. Allah dai ya sauwa ka idan mada wani manufa tabada tayi wa kanta ai, ai itama Allah ya bata yar hakana da take kin ta a kusa da ita. Khadija fada muna abin alherin don Allah don a kage nake tun dazun inji don yace kece zaki fada muna mu baki goron albishir. Nace ina ganin bana zaku sauke farali ne don sharan dana bashi yace ko gyaran daki ko wanan nace dashi duka dai baidai ban amsa ba har yanzu. Don mun dade dayin maganan tunda ya tayar da zancen yanzo nasan akwai maganar tafiyan ku ke nan tace ko shi yasa Yusuf ya amshi passphot din mu kwanaki nace shine. Murna suka fara yi ba basu jima ba sukace gidan hajiyar su zasu tafi nace yau naso shiga mugaisa kuma gashi ban samu fita ba ko da zuwa dare ne zan shiga. Bayan sun fita ne nayi waya da maryam ina fada mata zancen dawowan Nafisa gidan tai ta kunduma mata ashar nace kai maryam baki da kyau wallahi. Dakin shi na nufa wanda wanan ne karo na buyu dana taba shiga dakin sai da na tsaya na kare wa dakin kallo tare da mamakin yadda akwai mace a gida dakin miji yake a haka. Naga kokarin shi da ya iya zama haka a wanan dakin sai dai abinda na kula dashi shine iyaka a dan gyara fadon da za a kwanta akai. Ga goyon yarinya haka na zage na gyaro ko ina na dakin har ban daki ina yi ina sauraren numfashin yar da ke bayana data take yin shiba wahalce. Kacar nagama na fito daidai yarinyar ta falka nakai wa uwar itadaga kofa na tsaya ban shiga daga ciki ba na tsaya daga kofa. Na sallamay sallah ya shigo dakin yana gaida ni da aiki tare da fadin yanzu hajiyan mu ta kirani a waya wai taji abin alherin da ya samu yayan ta sun koma mata da murna. Yaya ka biya masu din ne na tambaye shi sai da yace nifa ba yayan ki bane nace inawa su Zainab kara ne ai nima nasan ba yayana kake ba yanzu. Yace yana zama sun tsorata da ganin yar nan ai don naji binta na maki magana nace ita dama ai matsoraciyace . Yanzu na maida ita nazo in yi sallah ya mike yana fadin ki girka abinci da dan dama don ina ganin su chezer zaso gidan nan don muna da meeting yau. Nace anty ya kamata ka fadawa don itace mai gidan don ni ba girki nake yi ba yace amma kin san yadda mukayi dake tun Abuja ko. Sanan idan ma ba kece da girki ba may zai sa in fada mata tunda ba kunya zata iya fitar dani ba nasu banda kayan haushi. Haba yaya AA kaima fa kana da laifi akan anty gaskiya bai dace kuna haka ba ga yara girma suke suna ganin abinda kuke yi kuma. Baice dani komai ba sai fitan da yayi daga dakin ganin banda lokaci yasa na mike lokacin kyautan da abokan shi sukai min jiya . Wardrobe na bude na fito da kudin sai da na ware ido daga inda nake zaune don ganin yawan kudin har zuciyana tana zargin wace irin sana,a sukeyi hakane wai. Da wanan tunanen a raina na fito zuwa kitchen din wanda banyi tsamanin an dafa wani abu ba a cikin sa da rana laraba tana zaune dan lungun kitchen din kamar marainiya nace mama kun koyi abinci da rana gidan nan tace to shine nake nan ai a cikin damuwa. Na tambayi hajiya tace wai na tambaye ki aike ce mai mashi girki ba ita ba nace kuma da sauri tace tau haka dai tace min da naje gurin ta dazun. Allah ya kyauta nace ko wani gauta ja sai dai in bai sha rana ba yadda take so zan bita mu tafi a haka tunda itama alamarin ta ba baya bane. Aiki muka hau yi gadan gadan sai gashi yafito yana fadin wai ba ai abinci bane da rana ko may ? Shiru nayi ban tanka mai ba tana zaune a falo yake sake tambaya tace ba,ayi ba don na dauka khadija zatayi ne yace itace mai girki ? Ita naga tanayi ai da kuka zo OK kawai yace ya kira yara shi suka fice daga gidan Samira ne tazo ta samay ni a kitchen din tana fadin anty yunwa tana taba cikin ta. Nace bari dafa maki indomie kusan a tare mukai aiki da ita don bata koma dakin su ba again. Sai yamma lis suka dawo gida da yaran nan suke fadin wurin hajiya mama suka tafi ashe kafin magariba na gama hada masu komai abinci ne tuwon alkama da miyar yauki sai jar miya da na dafa na cow tail ya dafu sosai sai dafa duka da yaji cabeji da kayan hadi nayi amfani da zaukaken nama daban soya ba sai kayan ganishin dana yi a sama. Bayan nan kuma na hada masu zobo da yaji kayan kamshi da kayan hadin shi dadai sauran tarkace na motsa baki na aje masu sai da na gama jerawa na haye sama na bar gurin bayan na mutanen gidan dana saka daban na nuna ma laraba wanda ke so ya diba. Ina shigewa Nafisa na fitowa ta nufi abincin zata diba Laraba ta fada mata abindanace tace ita wanan din nasu zasu diba din don nasan sherin da nayi a ciki yasa nace hakan komay ? Kamar an fada min sai gashi na manta wayana a kitchen na sauko in dauka na samu zata bude mama ihisan kada ki taba wanan din . Muryana taji daga bayan ya yasa ta juyo tana fadin akan may ba zan debi wanan din ba nace saboda maigidan da bakin shi na girka ba don ke ba. Tace kin dai san sherin da kikayi a cikin sa don haka sai na diba din sai dai ki mutu idan na diba na karasa wurin ina fadi bazaki diba ba tunda iri dayane da wancan dana aje din . Kai may ye Nafisa wai kina da hankali kuwa tace sai ka koya min na gaji da wanan rashin hankalin da kake kira min a gidan ka ka wanan yarinyar. Na kira maki don ko baki da alaman shi da baki tsaya kina wanan abin kunyar da kikeyi a gidan nan ba. Bar wurin nan yanzu kafin ranki yakai ga baci anty Fati dake tsaye tana sauraro tace ikon Allah a ranta ashe Allah zai gwada min faduwan buzuwanan haka ingani da idona. Samad an wanke an baka kasha diyar matsafa ta gama dakai ka fita hayacin ka baka cikin hankalin ka baka ganin kowa a gaban ka sai ita yanzu. Yace ashe kema da don ban ganin kowa a gaba kikewa mutane yadda ranki yaso ke nan to yanzu itace a gaban nawa kamar yadda kika ce din. Sunyi tsiya sosai dashi duk da haka na dauka bazata debi abincin ba sai gata tana diba abinci ta haye sama dashi tana sababi ita kadai don shi har ya shige ko ya barta a gurin. Idan dane na tabbatar da sai anyi dayan biyu ko ta kifar da abincin ko kuma ta diba tunda tace shi din dai zata diba din. Abin duniya ya taru yai mata yawa a rai gashi ganin da tayi muna mu biyu tsaye a falon ya kara tayar mata da hankali sosai wai ace duk biyun nan da Samad suke kai ina ba zai yuyu ba wallahi. Bakin shi sunzo sai da ya fada ma kowa yana tare da abokan shi a falo sai dai bai leka wufin Nafisa don kofan ta a rufe yake. Suna tsaka da tataunawa ne sai ganinta yayi gaban su bata damu da duk wanda ke gurin ba bata kuma gaida su ba sai jin ta kira sunan shi gatsal sukayi. Tace Samad ina son ka sawo min magani yanzu kakuma sayo ma yarinyar nan permpers tare da magani itama don mura take yi. Yace baki da hankali ne baki gani tare da mutane bane ko baki da hankali ne tace idan na ganka da duniya ne ni may ya damay ni dasu tunda wurin ka nazo. Nafisa wai baki da hankali ne komay Yusuf dake rubutu ya dakatar yana fadin haka yace kin fi saura yan uwan ki ne da suka natsa kansu a dakunan su komai. Dayan ya kalle ta yace ai dama tare kuka zo ne ashe yana tambayan AA din da yakai iya wuya da abinda tayi mashi din. Bai bashi amsa ba sai mikewan da yayi ya nufi hanyar sama tabishi tana maganganu itama bai tsaya ba sai dakin ta. Tana shigowa yakai hannun zai wanka mata mari ta gwauce mai tace akan dan wanan maganan da naje ma dashi zaka mare ni ? Baki da hankali ne ko baki ganni da baki bane da ba zaki iya jirana su wuce ba ko sai kin zubar min da kims ta a ko ina zaki ji dadi ? Daga yau idan ina da baki a gidan nan kada ki kara zuwa inda suke idan bani na bukaci kizo ba ke wata irin mace ce da baki da tunanen abinda ya kamata haka ? Ai basai kai mun haka ba zan san ka auro diyar matsafa ta canza ma tsari da ai naga ko bakin may baka shayin in fito a gaban su. Sai yanzu ne zaka tsiro min da wanan dokar naka mara amfani ko haka ta tsara maka yanzu kuma a gidan. Yace eh haka ta tsara min don ta fiki hankali da tunane abinda ya kamata ne ga addini na ta tsara min hakan. Wani dariya tayi tace wai abin mamaki bai karewa a duniya haushi yake ji cikin ranshi kamar ya shaketa yake ji a ransa. Don bakin da ke gidan ne ya juya yafice daga dakin baice mata komai ya zauna gurin su rai bace dashi. Yana zama dayan yace sai kai mijin buzaye wanan matar taka ashe halinta na nan yadda yake ada bata canza ba har yanzu. Sai daya yace cool down my friend mun saba da halin irin matan nan na ketare ko salis gashi nan haka yasha wuya da nasa kafin ta yaye shi tayi gaba Allah yasa yana da karfi arziki da yanzu ta gama dashi yanzu kai muke jiwa dan uwa. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Zan iya cewa Alhamdullahi a zaman mu na dan wanan lokacin a kaduna don zaman ya kara haska min hanya sosai a gidan AA na fahinci wasu abubuwa daga halaiyyan mutan gidan daga mijin har matansa da ma yan uwan uwashi. Yanzu na gama tanadar abinda nake son fahinta daga gare su sai dai wanda ya kara boye halin shi bai fitar a fili na gani ba kan shine ban samu nazarin sa ba. Na fahinci zaman akwai rikici na son mallakan miji ta ko wani hanya musanman daga wirin buzuwa. Ida ita kuma fati ta kasa daukan girman ta ne a gidan sabado abuwa kamar biyu zuwa uku dana fahinta. Na farko akwaita da son jiki don ko kanta bata iya yiwa komai balle danta ko mijin ta amma kuma a hakan take son jin girman ta. Sai abu na biyu dana fahinta gare ta shine tana da kishi irin na matan da da basu iya boye kishinsu a zuciya sai sun bari abokiyar zama ta fahinci hakan gare su. Na uku tanada fadar magana kamar wace taci kashi bata tsayawa ta auna magana ga ko waye zata fada mai kai tsaye cikin halin ko in kula yai ma dadi ko kada yayi tadai fadi zuciyar ta. Ga bason mutane a kusa da ita don zaka iya zama da ita wuri daya idan bataga dama ba taima magana sai ku wuni a hakana da ita atakaice akwai ta da nakasa ga kowa. Irin matan nan ne da ba,a gane samun su don ko yaushe jiya i yau ce gare su bawani canji tare da ita haka yasa mutane ma basu damu da ita ba sosai don har yau da ake bukin sallah banga wani bako kodaga gidan su yazo. Ita kuma buzuwa gaba daya har mijin na fahinci ba dadi a tsakanin su burin ta kawai ta ba kowa iko kowa iko a gidan mu koma sai bi sai yarda tayi da kowa. Ba ta kaunar taga wata ta rabi shi ko magana yayi da wata anjima kadan zakaji su sun rikeci dashi suna jidali kan hakan. Ga rashin yarda da kowa kowa ta dauke shi mai tsafi idan kayi sallama sai ta tura aga mai ka shigo gidan dashi idan kuma ba gurin ta kazo ba bata taba amsa ba sallama balle su gaisa da mutum. Kai abindai gashi nan sai gyaran Allah bana mutum ba don haka ne idan nayi sallah nakan roki Allah ya haudani kan su ga baki daya don shine kawai mafita yanzu gare ni. Tun dana fahinci gaba dayan su suna adawa dani na fara kama kaina ga kowa a gidan. Yau ma da aka wayi gari haka yasa ban fito ba tun safe ina daki na don Fati ce tayi girki don haka na zauna daki. Banji motsin kowan su ba haka kuma baisa na fito ba dana gaji da kwanci na gyara daki nayi wanka bayan na shirya na haye gado na jawo waya ina kiran yan uwa na muna gaisawa dasu. Karshe maryam ce na kira tana min korafin na tafi na barta don su abuja sukayi sallah tace ba inda ta fita tana jin garin ba dadi. Nace mu kan muna nan don banga ya saka ranan dawowa ba gare mu kamar da abinda yakeyi ne a garin don bai faye zama a gida ba kuma kullun cikin meeting suke. Jin an turo kofa dakin yasa nakai kallo na ga kofan inda naga shine ya shigo dakin ido na zuba mai har lokacin da ya karaso inda nake kwance din. Ina kwana na tare shi dashi ya amsa min yana zama tare da fadin lafiya kike kuwa nace lafiya ta kalau may ka gani halan ? Ajiyan zuciya ya sauke tare da bin dakin da kallo yana fadin naga baki fita bane har yanzu ko yau baku abin karyawa ne a gidan ? Bani ce da girki ba ai ko ka manta ne na bashi amsa yace ok yana mikewa maryam na gaida kai nace mashi yace a itace ta bugo waya nace eh tana min korafin yaushe zamu dawo na barta can ita kadai. Yace ba yanzu ba gaskiya don ban gama abinda nakeyi ba a nan kofa sati daya ma bamu kaiba garin nan kike wanan zancen. Yau Friday idan mun dawo daga mosque ina son zamu fita daku gaba dayan ku zaria zamu tafi mu gaida su. Allah ya kaimu nace ina kwantawa ya juyo ya kalle ni yana fadin ba zaki tashi ki nemi abinda kikaciwa cikin ki ba kin san fa kina da ulcer ga kuma lalurar ciki a jikin ki yanzu. Nace ina gudun in fita in jawa kaina wani magana ne kuma nima yunwar na fara ji yanzu yace you see maganan may zaki jawa kan ki don kin nemi abinda zaki ciwa cikin ki. Common taso mu fita ki girkawa kan ki abinda kike so kici dole na mike na bi bayan shi muka fito babu kowa a falon suna ciki suna barci laraba kawai muka samu rakube a gefen kitchen din tayi tagumi. Tana ganin mu ta dan zabura tana sauke ajiyan zuciya tare da fadin yau uwar dakina naji gidan shiru dama kece mai fitowa mu dora girki kuma sai naga baki fito ba kema yau. Ganin shi a bayana ta fara gaida shi ya amsa tare muka shiga kitchen din dashi yana tambaya na abinda zanci nace orth zan dama don jiya da zan kwanta nasha tea idan nasha yau kuma zai damay ni ne. Sai da yaga na dora ya fice kitchen din laraba ta shigo tana fadin yau har karfe takwas ya gwauta ba wanda ya fito daga cikin ku. Nace kin san banice da girki ba don ba zan kara dora komai don yaran ta suci ko mijin ta ba ta dawo tana nuna min bacin ranta a kan hakan kuma. Tace aishi Alhaji ya saba idan da sabo da halin matan shi girki fa ba wai ya damay su bane gidan nan a gurguje na karasa abinda nakeyi na wanke har tukunyar nace ma laraba ta kai min daki tajirani a can kuma. A dakin na samay ta nace mama ki hada kisha iya yadda kike iyawa ki zauna a nan din har ki gama tace nagode tana murna. Sai da tagama zubawa naja tire nima na hada nawa nan muka zauna tana sha muna hira har muka shanye zata fita da kayan nace ta dan dakata har yabi cikin ta. Hira mukayi sosai tana debe min kewa sai gashi ya fito a cikin shirin shi zai fita yana fadin mama kina nan ne tace eh zata mike yace zauna a binki fita zanyi nace ka karya ne yace zan karya a gurin hajiya idan naje can. Ido na runtse tare da fadin mutum da mata uku kuma bai daina cin abincin mama ba har yanzu yace kun bani ne nace idan zaka sha sai in baka ai don akwashi. Zama yayi anan ya sha cup daya dana hada mai ya fice sai guraren goma mama ta fito tana fadin bari ta sauka kasa kada abar falon ba kowa. Fitan ta bata dade ba naji karan bude kofan wani daki a cikin su ashe anty Fatine ta fito yaran sun damay ta suna jin yunwa ta fito ta duba idan an gama sai taga kitchen din ba komai. Laraba ta kwalawa kira a dan hasale tana tambayan ta ba,a dafa komai bane a gidan ta ce yau hajiya bata sauko ba tun dazun. Tsuki taja ta kalli Laraba din tana fadin yanzun ya take son muyi ke nan har wanan lokaci ace ba,a karya ba sai dai idan na rana zaku dora gaba daya ke nan . Laraba tace hajiya yadda kikace haka za,ayi ai ko sai dai gaskiya ban tsammanin zata fito yanzu ba kila tunda takai wanan lokacin bata fito ba. Ki kirata muji ko may ya hanata fitowa laraba ta nufi daki na lokacin har na kwanta in huta sai gata nace tace mata ba komai kawai ta juya zuwa fadin sakon. Bayan ta fada mata ne ta bata rai batare da ta fadi komai ba ruwan tea ta dora masu suka karya dashi su kuma sauran part din bansan yadda suka karata ba. Darana ma wai ta tsaya jirana ko zan fito sai da laraba tazo tambayanta may zata dafa tace ban fito bane tace hajiya ina ganin fa maganan da kikayi ne ya bata mata rai ta daina girkawa yanzun. Don wanan dan maganan dana fada zatace tayi fushi ko may tace laraba ta su shiga kitchen din jeloup ta hada masu wanda a gurin dahuwa yai half done. Ya bude zaci ya kasa ranan tasha fada ni dai ina sama ban fito ba har sukaci suka sude abin su ban san ma sunyi ba daga baya ne nake ji. Karfe biyu mun shirya zuwa Zaria da ya sanar ma kowan mu kusan nice karshen fitowa inda na samu anty Fati da yaran a falo ban san abinda nake jira ba. Na fito muka fita a tare Laraba da Yanyala kadai muka bari a gidan suna gadin gida Nafisa ce ta kamay a gaban mota inda muda yaran zamu zauna a baya. Tunda muka hada ido sau daya na kawar da kai sai naji yace da ita bayan ya shiga motar ke ya haka ki koma baya mana wurin yan uwar ki. Ki bar yaran nan gaba da Yusuf sai da tayi dan jim ta bude kofan motar ta fito maimakon ta shiga sai ta sa kai ta koma cikin gida a hasale. Na dauka zai bita ne don ko ita haka ta zata sai yace mu shiga mu wuce kawai . A kofan gidan su Yusuf ya tsaya ya dauke shi muka wuce sai zaria inda muka samu taro sosai a gurin su. Sai yamma lis ana kiran sallah magariba mu ka shigo garin kaduna duk daurewa nake a yadda nake duk da ba wani tafiya mai nisa bane amma sai da na wahala. Yana yi daga inda suke gaba shi da Yusuf yana juyowa yana min sannu har Yusuf din anty Fati da muke a guri daya batace min kala ba har muka shigo gida. Nan kuma muka samu Nafisa ita ma ta hau ta cika dashi wai ya wullakantata a gaban iyalin shi ai da ba haka sukeyi ba a gaban mota take shiga tare dashi sai yanzu ne zai tsuro da wani munafunci ko dole ne sai yaje da Yusuf duk inda zai tafi da iyalin shi. Already na yi miya kagin mu wuce nabarwa laraba tuwo ta tuka min ta kwashe a leda ta sa a cikin kula har mu dawo. Mun dawo sallah nayi na fito hakana cikin yanayi na rashin jin dadi jikina na raba takaiwa kowa nasa sai na mai gidan dana shirya mai a falo saman d/table. Falon kuma laraba ta gyara shi kwal kamar yadda muke gyara namu nacan Abuja sai kamshi ke tashi cikin shi. Tun da na sauko ban koma sama ba ina zaune tare da shine yana cin abinci ta samay shi da wanan fitinar haka. Sai data gama maganan ta yace akwai wanda kikafi ne daga cikin su ko may dasu basuyi min korafin rashin shiga gaban mota ba sai ke. Ko wani abin zaki tsunta a gaban motar udan kin zauna din Yusuf kuma na sha fada maki baki isa ki raba ni da shi ba tun farko a tare kika samay mu ko iyayyena basu ce zasu raba ni da Yusuf ba balle ke. Tace tunda yasan abinda yai ma ba aikai bazaka gane hakan ba ne yace kamar yadda kema kika san abinda kikai min Allah ya kubutar dani daga sherin ki ko ? Ni dai ina zaune na harde hannaye saman kirji ina kallon su tare da kada kafana tace ai nasan duk bayin kan ka bane saboda an birkice ma kwakwalwa yanzu. Ke kika birkita min kowa yace mata a zafafe yana kallon ta tace ai kafi kowa sanin amsan wanan din yace ban sani ba sai kin fada min tace nadai fada ma gobe ni zanyi girki a gidan nan din ku sani. Yace bazakiyi ba don ba haka aladan mu yake ba sai lokacin nasa baki ga zancen su wanda nasan karfin zancen akaina take yin shi dama. May zaisa kace bata yi tunda tana iyawa wanan ai dama al,adane kawai ba shari,a ba ko Allah ya kaimu goben nace ina mikewa. Ko baki ce ba ai gobe zanyi din ne don haka ki kama min bakin ki a gurin nan don baki isheni ba ke ta fadi tana karsawa a hasale. Maganar ta shafe ni ne yasa na saka baki don wanda bai shafeni ba ai bakiji na sa maku baki a ciki ba ko ? Lalai wuyan ki ya isa yanka a gidan nan amma na baki dan lokaci kadan indai samad ne inda saniyar gaba tasha ruwa ko na baya intazo anan zata sha. Ba dai ta kawar da kishin ruwan nata ba ko yadda shanun gaba ta kawar da nata tace sai dai ta kawar a burkutacen ruwa nace ruwa ruwa ne komai daudan shi dai ai ruwa ne don ba za a kira shi da wani suna ba can. Kai ya fada cikin tsawa tare da fadin ya ishe ku hakana ban son kara jin bakin wani a gurin nan kuma. Sai da na juya ne na ga ashe har anty Fati tana falon zaune ita ma tana sauraren mu nagama abinda nake na haye sama ita kuma tana zaune suna fafatawa dashi. Wanka nayi na shirya na nufi part din dole sai da na tsaya gyaran part din don ban iya kwaci a hakan ina gamawa na kwanta ban jira shigowan shi dakin ba. Har barci ya fara daukana can cikin barcin naji hannun shi saman cikina yana shafa a hankali dan gyara kwanciya nayi na shige a cikin jikin shi. Yace ya naji jikin ki haka da zafi nace banjin dadin jikina na ne sosai na kwanta kin sha magani ya tambaya nace basai na sha magani ba zai bari. Ina duban yarda zamu koma abuja a haka dake cikin wanan yanayin ina ga sai dai mubi jirgi daku sauran su biyo mota zaifi zan iya na bashi amsa ba tare da na bude idanuwa na ba. No bazaki iya ba gaskiya ko bukin zainab bazaki zo ba don wanan wahalan da kikeyi idan kin shiga mota nace mama tace zai bari ai ko. Bai mun magana ba sai can naji yace ki fada ma Adam gobe ina son ganin shi around ten kan maganan AS Jalingo din. Da sauri na bude idanuwana na sauke a kan shi ya gyara kwanciya yana dan taba kaina tare da fadin wanan na fada maki ya zama na farko yazama na karshe a gare ki don ba haka nake aikina ba ko wanan ina da dalilin yinsa. Nace koma may ye dalilin duk da ban sani ba dai na gode tunda na samu abinda na saka ma yaya Adam dashi a rayuwa na nima. Eh hakan na daga cikin dalili na sai na biyu wanan ne karon ki na farko da kika taba rokona wani abu tun haduwa na dake nasha gwada ki ta hanya da dama kina cinye gwajin ki gare ni. Sai kuma shi kanshi Adam din da nake son in taimakawa wanan ne dalilin da yasa nace ki masa magana yazo mu gana dashi. Ya Ahmed fa da naji kayiwa alkawari don tunda naji laraban shi abin ya tsaya mun a raina wallahi wani Ahmed nace na unguwar Dosa da mukaji. Kai Deedar kina da abin mamaki Ahmed kuma ai na gama da zancen shi tun jiya yazo mun yi magana kwagila na sama mashi wanda zai daga shi idan ya iya tanadi. Mutum ya cika gida da iyali haka tun yanzu wani tanadi kike tsamanin zai iyawa kan sa nan gaba tunda akan haihuwa yake har gobe. Nace hmmm nan ma kwana nawa ne zamu cika gidan nan yazamanto ko inda zaka zauna babu yace bissimillah udan zaku iya ai ina da bukatan hakan nima. Ranan ina Allah Allah gari ya waye in bugama Ya Amina waya ya Adam yazo su gana bai bari na fito sashen nashi da wuri ba sai misalin tara na safe. Ban san may ya kawo Nafisa falo ba ta zauna anan na samay ta har Yanyala da yaranta kitchen na shiga na hada abin karyawa wa kowa a gidan . Sai dana gama na shiga nayi wanka na gyara jikina lace na saka duk da akwai ciki a jikina bai hana kayan su karbe ni ba. Ruwan wanka na shiga na hada mai na fito na gyara dakin yadda ya dace mace idan zata fita girki tayi bata bar ma yar uwa daki don sheri tazo tana gyara rai bace ba. Kamar yadda ni na samu anayi a gidan abin ba kyau don har unders sai ace an manta dashi sai dai kai idan kazo gyara ka kawar inda ya dace. Wanan nafisa tafi yi min don ita Anty fati sau daya ta barshi na kawar mata Nafisa kuma dana gane abin nata kissa ne idan ta barshi a gurin idan nagama gyara nake bar mata abinta yanzu. Gashi dai yau tace zata karbi girki a gidan inda kwanan ta ashirin da wani abu yanzu da haihu tana tasan ma yin arbain ke nan yanzu. A tare muka fito falon dashi muna jere zuwa falon tun muna akan steps din take bin mu da kallo har zuwa saukowan mu kasan. Wurin table muka nufa inda sai da ya ja min kujera na zauna shima ya ja ya zauna a guda daga inda take tace idan baka mutu ba dai zaka sha kallo. Wanan bokan naki yaci biya wanan rawan kan da jiji da kulawan kan ai sai mota za akai biya gurin tsafi. Gidan mu bama tsafi bama shirka idan dai kince ayar Allah na aiki na yarda da wanan kan don bamu wasa da karanta shi don neman tsari ga shedanu irin ku. Tsiyan abindai mutum bai taba samun yadda yake so nace kamar yadda ke ma ba zaki kara samun irin na da ba a rayuwan ki har a bada kenan. Yan kwana ki na deba maki a gidan nan gaba daya idan kin dauka wasa ne sai mu zuba na bude baki zanyi magana ya bugi table din da karfi tare da fadin enough. Nafisa barnan tun raki bai baci ba ke ma kuma idan kika kara tanka ta haka a gabana kuna wanan shashancin ranki zai matukar baci. Duk wace ta fasa daukana sukutun takai gidan boka ta raina Allah yanzun ma ku dauke ni ku kai iyakarta ke nan Mata baki da aiki sai sa ido da jan maganagirkin nan ina ba hakkin ki bane yau kin zo nan kin kashe mu da ido kina ganin zaman ki a nan din zai sa mu fasa abinda zamuyi ne komay , ? Idan naki yazo kin bukaci ai maki banyi ba shine zakiyi magana ba wanan takanar fadan ba haka na hauka zalla da kike yi ina jiyewa wanan bakin naki watarana. Shiru nayi ban kara magana ba har ya gama fadan shi ya fara cin abincin shi masa na aika laraba ta sayo shina dan diba naci kwara biyu nasha ruwa don ya isheni. Daki nakoma na barshi a gurin na kira yaya Amina na fada mata tace gashi ko zai fita barin fada mai wayan na a hannun ta naji tana fada mai sakon. Ina ji yana hamdalla a wayan tare da zuka min addua har na gaji na kashe wayan sai gashi ya kira layina da kan shi. Yana tambayana nace eh to ina ganin maganan ne sai dai kuma bashi bane kadai zakuyi sai dai idan kazo zakaji ko may nene daga bakin shi. Yai min godiya ya kashe wayan na wurga wayan gefe na kwanta ina maijin kunan maganan Nafisa a kaina da tayi min a gaban shi duk da na bata amsa dai. Amma sai lokacin nake dana sani ban bata amsar dayafi wanan ba zafi yadda itama zataji zafin da naji a ranta. Amma nasan dai idan itace ko yau ma ba gobe ba karawa zatayi don haka na tanadar mata amsan da zan bata mai zafi daidai da maganan ta din gare ni. Shigowan shi dakin ina kwance na dago ina kallon shi da fuskana dake nuna damuwa a cikin sa yace kin kira Adam din don ban son ya wuce lokacin dana bashi. Nace na fada mai yana hanya tafe insha Allahu yace ai mai godiya kafin yazo ba wani matsala yace yana juyawa. Sai kuma ya sake juyowa lokacin har na mayar da kaina saman filo yace may yasa kike son mayar da kanki daya da Nafisa ne a gidan nan ko yaushe ? Nace amma kaji ai ita ta fara takala na da zancen ko sai taja mutum idan ya bada amsa kuma yayi laifi a gurin ka. Tana dauka kowa yadda take yake idan bata daina kirana da diyan matsafa ba ni zan dauki mataki da kaina a gidan nan. Tunda ta fada daya ta fada biyu taga ba wani mataki dana dauka akan hakan yasa take ci gaba da aibantani yadda take so idan kuma na rama ace ba haka ba. Sai daya dan kada kai ya murmusa yace ke na kun zama daya yanzu da ita don may ba zaki fita batun ta yadda Fati take fita batun ta ba idan tanayi. Ban yi magana ba sai runtse idona danayi ina jin kuna a cikin zuciya na naji yana fadin ban son irin wanan fitinar kinji na fada maki gaskiya. Ido na bude nace ita ma ka fada mata ta daina shiga harkata tunda ban shiga nata ba ni kin shiga kan tunda kin auri mijin ta yace. Nace ba sai in bar mata mijin ba indai shine zaman lafiyan ku tunda na fito na ganta a wurin nasan tsiya take ji yau a gidan nan. Yace tunda har kin fahinci hakan mai zai sa ki biye mata ku zama daya da ita kuna saida hali a gaban yara suna kallon ku. Juyawa nayi na kyale shi naji ya fita daga dakin can ya dan jima da fita wayana yai kara ya Adam ne na dauka yana fada min gashi a kofan gida mu. Nace to yaya barin fada mai kazo yanzu namike zuwa fada mai dakin shi na samay shi yana duba abu a cikin computer shi jin na shigo ya dab dago yana kallo na nace ya Adam ne yazo yana waje wai yace kice ya shigo mana ki bashi wuri kafin in fito. Har waje na leka na samay shi zaune a motar shi muka gaisa na fada mai ya shigo tare muka shigo gidan dashi dama kafin in fita na fada masu bako zai shigo falon. Nan anty fati ta mike kafin in dawo tare da yaran ta sai nafisa muka shigo muka sama zaune lokacin shima yana saukowa ke nan. Tun bai karaso ba yake fadin bata fada maku akwai bako zai shigo bane batai mai magana ba kuma bata tashi daga inda take zaune ba. Ya sauko yana fadin baki jini bane tace gani nayi itama ai bata shige ba ko yace you're very stupid Nafisa ina magana kina yi. Yadda ya hasala yasa ta mike kitchen na koma na hado kayan taron bako na kawo mai tare da dan zama muka kara gaisawa daga nan na shige ciki. Sai lokacin ya kalli ya Adam yace bissimillah mana ga ruwa nan kasha yayi godiya tare da balle marfin drinks din ya dan tsiyayya yace kai hakkuri fa kasan matsalan mata yadda yake haka muke fama dasu. Yace a, a ba matsala ko mu masu daya ma wani lokaci ai sai hakkuri su haka Allah yai halin su da karamin tunane. Tsuki yaja yana fadin wanan nasu yafi na kowa ba a haduwa wuri daya bai jidali ba kowa na jirace da dan uwan shi. Allah ya sauwaka yace yana gyara zama tare da fadin ta fada min abinda ke nan sai dai da farko zanso inji alakan ku da wanan mutumin dan shiru yaya Adam yayi yana aje cup din da ya kurba drink's a cikin shi. Can Yace a gaskiya zan iya kiran shi da uban gidana da kuma mijin yar uwata da tarasu shekarun baya auren mu bai dade da ita yar khadija din ba a lokacin. Ta rasu ta barshi da yaran su guda biyar a tsakanin shi da ita sai daga bayane ya auri wata yar kasar su yanzun haka ita ke gidan zaune dashi da yaran. Kuma zan iya cewa yanzu dai shine jigon da muke dashi duk da ba yar uwana a gidan yana taimaka min sosai ta fannin aikina don shine ma ya samo min wanan aikin Nepa da nakeyi yanzu. AA yace madalla na fahinci abinda nake son ji daga gare ka sai dai banji dadin ta yadda ka biyo min ta hanyar ita deedar din ba gaskiya. Yanzu ai mun zama daya koma may ye zaka iya tunkara na gaba da gaba kai min magana don ni ban faye son abi ta gurin iyalina ba kamar yadda kukai min. Ba zan boye ma ba ita Deedar ta cancanci in mata alfarma ko wani iri tazo dashi don tsawon zama na da ita bata taba rokona wani abu a duniya na rayuwan ta ba. Idan na bata ta gode idan kuma ban bata ba koda tana da bukatan wanan abin bazata taba min magana da tana son abin ba. Ya Adam yace alhamdullahi naji dadi kwarai da ta samu wanan shedan daga gare ta don kusan sai ince haka halin su yake daga ita har yan uwan ta . Wanan halin ne yasa kaga ban kyashin in mata in ma yan uwanta daidai gwargwadin halina yanzu kuma kaima gashi ka shedi khadija da wanan halin wanda na san tarbiyan da suka samu ne daga iyayyen su haka. AA Yace to yanzu dai maganan shi AS kamar an gama ne sai dai zan so in zauna dashi muyi magana tsakani na dashi kan fili. Sai kuma kai naka da nake son ka bar aikin nan in da halin bari in sama ma kwangila wanda zai tallafa maka ka gina kan ka dashi da iyalin ka don nima ina son in rama alherin da kukai min dakai da iyalin ka wanda ban manta dashi ba kuma ina afahari dashi yanzu. Godiya ya Adam yai mai inda bai tashi ba sai da suka aje lokaci a tsakanin su akan ya samay shi idan ya koma Abuja. Suka rabu da farinciki da jin dasin juna ya adam ya koma gida yana sheda ma Ya Amina yadda zaman nasu ya kasan ce a tsakanin su ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: A dadafe mukai kwana goma sha daya kwatsam da yamma ya shigo yana fadin gobe jirgin bakwai na safe zamu bi zuwa Abuja. Da mamaki na kalle shi nace gobe goben nan kuma yaya yace eh halama zaman kd din ya maki dadi haka nace wallahi. Da dai kun tafi kun barni nan har hutuna ya kare sai in samay ku daga baya don nan din mutum yafi sakewa ga yan uwa kuma kana gani. Baki da hankali Deedar kina ganin zan wuce in barki garin nan ne komai karfin tafiyan goben ma donki zanyi shi ai don ina son muje asibiti idan mun koma. Baga asibiti masu kyau anan din ba ku tafi kawai zanje ni da ya Amina na cikin magana mai kamar fada yace tunda Amina ke auren min ke. Har ya fara tafiya ya juyo yace wai may kike tsunta a garin nan da baki son komawa Abuja naga idan na biye maki garin nan zaki dawo dani baki daya da zama. Nace a yadda muke full house din nan yana min dadi ne don ba wani zaman part ga mutum yana yadda yaso a cikin gida. Yace can din wa yahana maki yin hakan nace kaima kasan inda matsala take ai don yanzu muna komawa angayan buzaye ka zasu cika muna gida ne. Wani kallo yai min baiyi magana ba ya juya ya fita dakatar dashi nayi cikin dan gudu ina fadin yaya sai ya juyo nace don Allah zan shiga wurin ya Amina da cikin gida in masu sallama kada in girshe su kuma. Ya kalli agogon hannun shi tare da fadin a wanan lokacin zaki fita nace please yace shirya in sauke ki idan kin gama ki kirani in dauko ki kuma. Nidai na juya da sauri hijjab kawai na zura a kaina na jawo kofan dakina na rufe a falo na samu Nafisa zaune da wanan yar uwar tashi suna kus kus fitowa suka zuba min ido. Ban tanka su ba na fice ina jin Nafisa na jan tsuki a waje Affan ya tare ni yana fadin anty zan biki nace gidan hajiya zan tafi affan yace eh zanje. Na kama hannun shi muka nufi wurin mota shi ya dakatar damu da fadin ina kuma zaki dashi haka nace cewa yayi zai bini. Common shige ciki ya dakawa yaron tsawa ya juya da sauri motar na bude na shiga ya tayar na dan kalle shi nace yaro ne fa kana masu haka basu jin dadin ka ai. Yace kin sagarta yaran nan idan kin koma zasuji daban nace ba sai in koma dasu ba ko muje da maman su gaba dayan mu. Da sauri ya juyo yana fuskantana tare da fadin ina nace can Abujan mana ko itama ba gidan mijin ta bane can. Yace ke baki san komai ba da data dawo nan waya koro ta can ta zauna nan tunda haka taga yafi mata nace ai ba tanata za a bi ba yaran yakamata ka dubawa makomar su. Yaro fa sai da tarbiyan uba a kusa sai dai idan ya rasa su ne ya dauki maraici hakana. Kofan gidan ya Amina ya tsayar da mota yace idan kin fito ki kirani nace to na fita ya wuce. Ina shiga yaran ta suka tare ni da murnan su mun gaisa na shiga dasu ciki tace daga ina haka da yamman nan da cikin ki tsoho nace daga gida zuwa gidan yar uwata mana. Baki san ba a son mai ciki tana fitar yamma haka ba nace daurowa fitan nawa yayi nazo maki sallama ne na fadi ina zama. Yaushe zaku koma nace wai fa yanzu yazo yana fadin gobe goben nan da bakwai na safe in Allah ya kaimu. Shiko may yasa yake hakane nace haka yasaba dashi yanzu shirin da zan maki ina zan samu yinsa da yamma haka nace nidai idan na samu yaji ya wadatar dani kibar ssuran shirin ai ba zamu dade ba zamu dawo bukin zainab don kafin sallah babbane akace bukin. Wayana yai kara na dauka maryam ne akan layin take fadin wai yaushe zaku dawo ne kin barni nan abubuwa na son cabe min nace kaji ki da wani zance kamar may shirin aure. Tace don Allah yaushe zaku dawo wallahi ina bukatan ki khadija sosai nace ke gidan mijina fa nake dariya tayi sosai tace ana muna kuri da auren nan muma dai mun kusa bin layin ku ai muhuta gorin auren nan hakana. Kiyi yau idan kinyi fushi mana tace banyi yau amma zan baki mamaki don sai kin sha mamaki na. Dariya ta bani nace gobe idan Allah ya kaimu muna nan tafe korafi ya kare ni kina ban mamaki mace da mijin ta kuma a dinga damuwan ta wai ta dawo . Ko kun hada baki ne da buzuwa wai tace shegiyar tana ina ne wai nace kd mana muna nan tare da ita. What naji tace wai mijin nan naku wani irin sokon mijine shi maryam mijin nawa ne soko na katse ta tace hannu a kunne na madam kada a yankani . Yau kuma AA ake shigar ma fada nace ya son ranki yar mata tace daina rage min aji kice KARAMAR BAZAWARA. Dariya mukayi sosai da ita tace sai dai kinzo don akwai labari gaskiya nace kamar yau ne insha Allahu tara ina dakina da yardan Allah. Mun gama waya da ita ya Amina ta kalle ni tace aure zatayi ne nace bar ta da shimay ta ba aure zatayi ba so take dai in koma mu shiririce can da ita. Ina gidan ya Amina anan nayi sallah sai baya magariba na bar gidan nida ya Amina muka shiga cikin gida. Mun gaida Anty amarya dake farko shigowa sai umma da ke kusa da part din Abba su hajiya mama da mommy sune daga ciki part din su yana kallon juna. Wurin mommy muka shiga nan take jun zancen tafiyan mu tace waishi babangida wani irin bahagon mutum ne haka bai fadin abu sai a kuraren lokaci. Ya Amina tace shi nake fada mata yanzu ai wai yaji take so ni kuma ban riga da na aika ba ai mata mai hadin nan. Mommu tace in don yaji ne akwashi nan gurin a koba na sadiyan shehu ba tace shi take so wai taci shi ranan tace dandanon yai mata. Mikewa nayi nace barin gaida mama tace yakamata kada taji kin shigo tun dazun baki lekata ba kuma. Tana zaune tana lazumi na shiga dakin ganin tana lazimi na shige wurin su Binta a kwace na samu zainab gaisawa mukayi dasu Binta tace daga ina haka da daren nan nace gida nazo sallaman ku ne. What don Allah har zaku koma ke nan nace wallahi haka yace dazun da yamman nan sai lokacin zainab tace yanzu nima yaya ya ke fada min amma yace ku jirgi zaku bi ai nace eh tafiya safe zamuyi shine nazo sallama don goben nasan a gurguje zamu shigo. Zainab yakama ta fa ki koyi sakewa da mutane hakan wanan shirun baiyi maki a wanan zamanin don ni naga ranan bakina nace na juya ina kallon ta. Murmushi tayi tace kaji ki da wani zance haka halina fa yake Binta tace tana sin komawa anty fati ne kila nace Allah rabaki da halin anty Fati . Mutum bai iya maida hatsi sufe kullun jiya ayau ita kodan kiza kizan na fa batayi na mata hajiya mama ce ta bude labulen dakin take fadin. Khadija kece da daren nan nace eh mama nazo in sallamaku ne yace gobe zamu koma wai tace ikon Allah gobe goben nan kuma nace haka yace mama kuma tafiyan safe zamuyi . Nace aiko kuna nan har bukin zainab tunda ba nisa nace nima naso haka mama tunda muna hutu ne yanzu amma yace a, a. Daga inda zainab take tace hajiyan ki tuna mata zancen set din kada ki manta Binta tace mara kunya zancen kayan ma ke ce mai tuni ashe ba a ko bari mu, mu tuna. Nace kunyawa zata ji kan abinda take so kuma kece dai mara kunya ai da kika sa baki a zancen manya dariya ta kwashe dashi lokacin da taga na dafe baki tace ai kin gama. Kunyar may zakiji dama in ina fadin kina da baki sai tace wai kazafi nake maki yanzu ai gaki kin gani hajiya da idon ki. Murnushi hajiya tayi tana fita tace in kin gama ina falo nace to hajiya tana fita na mike Binta tace ina kuma zaki nace wurin hajiya mana ko so kike in zama mai zunubi kuma na fice. Zama nayi kasa daga gefen ta na fara gaida ita bayan gama gausuwan mu ne tace dama akan kayan zainab ne wanda aka saya tace bata son irin sa . Nace ta fadawa dan uwan ta wai ita kunya take ji nikuma magana irin haka baya hadamu dashi don zaiga kamar umurni ne nake bashi akan dole. Shiyasa nake son kuyi magana dashi udan da hali sai ya kara mata wani su zama biyu dana alhaji din dayai mata. Zanyi magana wayana yai kara na dauka shine a layin yace kina ina baya na dauka nace gani wurin hajiya yace ok ya kashe waya. Nace mama ina ganin in anyi mai magana ai ba zai ki ba zai canza mata din tunda dai bata son wancan din da akai mata hajiya tace matsalan ai Abban ku yabawa kudin komai a hannun sa. Sallaman dayayine ya katse mu ya shigo dakin yadda ya samay mu a zaune ya fahinci wani magana muke yace karana takawo ko ? Yana zama yake fadin haka hajiyatace kai mata wani abin ke nan ko tana kallona nace shawara muke na uwa da yar ta kawai ka tsargu. Yace ashe nazo daidai sai ai shawaran dani ke nan tunda nazo murmushi hajiya tayi irin na manya da yake baiyana jin dadi a gare su. Dama kazo a daidai magana muke kan zancen kayan zainab sai gaka yace ina mun gama maganan da Abba ko na bada duk wani abinda za a bukata ta bagaren shi. Ka gama hajiya tace sai dai ita zainab din take korafin kayan yanzu yace hajiya mu yarinyar nan ta samu wuri korafi kuma kan kayan da Abba yasai mata ko may ? Nace yaya ba haka ake nufi ba ana magana ne kan abinda ake yayi kasan shi Abba din bawai yasan kan kayan bane yace ke kikasan kan su ke nan ko ? Ya fadi yana harara na hajiya tace kada kaga laifin yar mutane itama yanzu ta san da zancen kasan hajiya umma zai sata zabo ita kuma kasan sai ta samu riban sai ta zabo mata mai karamin kudi. Yace kai umma tana nan da halin nan hajiya tace may za a fasa kadai san halin bakina suke son ji kawai akan zancen har alhajin. Tunda ina yar tane baiba kowa ita yake ba dai tawo masu abinda ransu ke so mu kima kaga namu iya bi. Yanzun ya kuke son ayi tunda an riga da ansaye din tace shine ka samu muna magana anan yazon shawaran da muke ke nan ai. Nace ni sai naga a bar wancan din a matsayin na Alhaji sai ka saya mata wani mai kyau a matsayin naka ko na hajiya din. Hajiya tace a dai barshi a matsayin nasa din zaifi yace idan mun koma sai taje ta duba mata komai acan a bata list din duk wani abinda za a bukata daga can din yana magana yana sa hannu aljihun shi hakan yasa nace mun gode yayan mu ina mikewa. Hajiya tayi murmshi tace kema dai yayan naki ke nan zama nidai na shige ina masu dariya a can muka zauna ina fada masu yadda mukayi zainab naji ta dungumay ni nace kamata yayi ki shigo mu zagaya dake ina ganin zaifi. Ban dauki lokaci ba ya gama ganawa da mahaufiyar shi yace in fito mu tafi nayi masu sallama tare da zuwa dakin mommy na yima su anty Amina sallama suma muka tafi. Duk wani shiri da zanyi nayisa a cikin daren nan mama laraba zata biyo motane zuwa abuja sai da safe na samu anty fati bayan nagama shirya nake cewa anty a gafarce mu idan munyi ba daidai mu zamu tafi ke nan tace yau ne tafiyan nace eh haka yace ai tace dukan ku kenan zaku tafi nace eh Affan najin haka ya mike da sauri yana fadin anty mu fa nace zan dawo in dauke ku ai yanzu zan tafi yin wani abu a can ne in dawo. Karfe tara kamar yadda nace wa maryam muna cikin garin Abuja har na huta na gyara part dina ba kowa a gidan sai mu kadai. Don shima muna isowa ya nufi office ya barmu ba kowa a gidan sai mu kadai abinci na girka da zanci don rashin karyawa da banyi ba can. Ina zaune a falo sai ga Samira ta shigo tana tambaya na abinci nace ta jira ya dahu tana zaune sai ga uwar ta turo kofa tana fadin may samira tazo yi guri na yarinyar tace Ami yunwa nake ji ke kuma baki girka ba nazo gurin anty taban. Idan ban girka ba ke ba zaki iyaba da zaki zo nan a tsafe min ke nace cikin wani murya mai kaushi ke ya ishe ki ya isa haka idan bakin ki ya kara kirana da matsafiya zaki gane kuren ki a gidan nan. Da dasuke cin ban tsafe su sai yau ne zan tsafe maki su da sherin ki wanan kalman ya isa hakana daga bakin ki daga taimako zaki dinga aibanta ni haka ke wata irin mace ce da baki da lissafi. Ke kina ganin budar idon ki a kaina zai razani ko may ko umurni kike ban karya na fada ke ba yar matsafa bane ko may duk tsafin da kuke dake da iyayyen ki a kune yake ai. Nace kin dauka kowa irin kine jikan mayu masu yawo da maita suna sayarwa kuna yat ga ganye kuna kuma tallan kan ku. Nafa san komai harda zuwa gidan dakike gun tsohon mijin ki da kika bari a gida sai shekara shekara zagayo shi. Ni din ta fada a rude nace ke mun san komai fa da na dauka abin naki na wasa ne zaki gane ki dawo hanya amma yanzu nagane baki san ana maki ragowa ba. Yunwa da kika saba zama cikin sa yasa ko girkin abinci bazaki iyawa yaran ki suci ba sai yawo bin boka da malamai saboda bakin yunwa har dangin kaf kika kwaso zuwa gidan mijin ki don baku gaji kunya ba. Ina ma akasan shi balle a jishi uwa da uba duk a gidan suki zaune an fada maki ana bara ana karuwa kin dauka ban san yanyala uwar ki ce data haife ki tsohon dake bakin get kuma da kuke kira da Ruwa shine mahaifin ki. Ban aune ba sai ganin ta nayi a gaba na wai zata doke ni ban san ina da wanan azaman ba a yadda nake jin jikina da nauyi sai ji kake kau kau kau na zuba mata maru biyu masu kyau ta yunkura Allah yaban sa, an ta nan na mata dukan banza a dakin. Na turata waje ashe har yanzu samira na dakin muryan ta naji tana fadin idan kun gama ki bani abincin anty. Kitchen na shiga nasamu abinci har ya tsane yana son kuna na zuba mata tafita a falo ta tsaya taci abinta inda uwar na daki tana fama da bugun waya wa miji da su madam. Samad kazo gida yanzu daga magana matarka ta daga hannun ta mare ni yace what tace kazo tun kan ayi barna a gidan nan don ba yarda zanyi ba. Ta kasheta kira madam tana fadin a turo mata yan uwanta yanzu gidan don babu lafiya wanan bakar banufan ta na son kashe ni. A zabure madam da tasa yan uwanta a taso azo gidan sai dai sunzo bakin get masu gadi sun tare su waya madam ta buga mata tace gata fitowa. Shafin hannu na kwance a kumcin ta magana tayiwa yan sandan kofar gidan suka ba shiga doka ne daga maigidan nan ta shiga dura masu ashar har bakin layin dayan yan sanda ya raka su da bindigan shi. Abin sai ya taru ya zama mata biyu ga na cikin gida ga kuma namiji ya hana kowa nata shiga gidan . Ciki ta koma a haukace tana tatara kayan ta wai ita ba zata zauna a kashe ta ba a gidan sai yasan yadda zai yi yau a gidan. Nikan ina zaune bayan na dan cakula abinci don yunwar da nake ji ya bace min na daina jin shi kuma yanzu ina sauraren zuwan maigidan inji irin hukunci da zai dauka saboda irin haukan da take tana sababi. Zuwan su laraba da Yanyala da kayan mu ne yasani fitowa waje tun lokacin sai dai na samu suna rikici a bakin get masu gadi sun hana yanyala shiga gidan. Nace ma security din ya barta tashiga mama da harshe turanci muke magana dashi yace oga yace kada subar wani froriner ya shigo mai gida. Ga Nafisa a tsaye sai surfa ma zagi take yi masu akan may zasu hana yanyala shiga gida zasu bar Laraba fa shigo. Nace a cikin hausa ku bari wanan ta shiga don uwar matar oga ne ita ma daga kd take tafe sai yace ok ma tare da sarawa ya bude mata get din. Tunda na fadi haka nacewa driver ha shiga muna da kayan mu cikin gida na barta a wurin tana masifa. Saida ya fito ya shiga masu da kayan su ciki suma mun zauna da mama a falo muna fira abincin dana aje mata na dauko mata tana ci muna hira. Sai four ya shigo gidan kai tsaye dakin shi ya nufa ya watsa ruwa dayake ranan muka dawo ban sawa raina wani yin girki ba duk danice zan karba. Sai na kyaleta ita tayi don gudun jan wani fitina sai dai mun girka a part din mu don gudun ta taso a gaba. Part din Nafisa ya fara shiga yanyala ce zaune a falon ta ya gaida ita da dawowa ya nufi cikin dakin inda ya samu yar tana kuka ga uwar a zaune bata kula mata ba. Wurin yarinyar ya nufa ya dauke ta yana fadin sadiya ya akayine mai ke damun ta ne kin kyale ta tana kuka haka. Idon ta da ya kade yai ja tace samad yau ina son ka raba muna gida da wanan yarinyar idan ba zaka dauki mataki ga abinda tai mun ba. Haka kawai zatai min wanan aikin haka na kiraka kuma bakazo baka dauki wani mataki ba a kai sai yanzu ka ga daman shigowa gidan. Kallon mamaki yake mata yace oh dama so kike da na dawo in shigo gida in rama maki dukan ko may ? Ke may kike da har ta mare ki baki rama ba sai ni kike son inzo in tare maki fada komay yanzun haka ko ban tambaya ba nasan kece kika fara wanan fitinan. Kamar kada taji haka daga bakin shi tace shike nan dama na sani ta wanke tabaka kashanye ta kaika gurin matsafan iyayyen ta an tsafe ka. Ka sani yau ban zama a gidan nan da wanan gajar matar taka mai karfin doki ta illantani a banza tunda ita fadan mahaukata takeyi. Yace kije duk inda zaki tafi kofa a bude take maki idan ke ba zaki tsaya ki rama ba sai ni ke son in zo in rama maki ko ? Yana fadin haka ya aje yarinyar zai fita tace kazo ka dauki yar ka nagaji da wahala banza hakana yace ki barta ta mutu dama ba son ta kike yi ba ai. Ya fita dakin sai samira ne ta shiga ta dauko yarinyar ta kawowa yanyala ita itako har kofa tabishi tana fitina bai juyo gare ta ba yaci gaba da tafiya . Hiran daddy mukeyi muna dariya sai gashi ya shigo part dina daga unda nake zaune nayi mai sannu da zuwa ya amsa . Labara na gaidashi yace laraba ku iso lafiya ta hanya tace da godiya Alhaji ya naku hanya da aiki kuma yace Alhamdullahi. Daga haka bai kara magana ba ya fita nima kuma ban bi bayan shi ba don yadda na ganshi bai walwala yasa ban bishi ba don nasan yasan da batun fadan namu. Sauraren shi nakeyi inji mai zace min akan zancen sai naga bai min magana ba ya fita har dare bai nemay ni ba nima ban je inda yake ba don ban kara jin duriyan shi ba ma. Washe gari da safe da ya shigo har lokacin yana cikin tamke fuska gaisawa mukayi ya juya ya fita zuwa maryam yasa na manta da zancen a raina. Har kwana uku banji yai min magana ba kuma babu wani sakin fuska a gare ni ga gidan ya koma muna tsit kamar ba gidan nashi ba. Wani lokaci ashe mutum yana da rana ko shigowan da nake ina ganin su a falon ashe wani abune ga Laraba a yan kwanakin tana gyaran gidan sosai yai kyau da wani haske kamar dai ba gidan ba. Zaman doya da manjan da yake damu ya ishi nafisa da kanta ta nemi shiri don taga haukan bazai fisheta ba dashi. Na idar da sallah na fito falo na zauna wayana dake gefe yai kara na duba shine a layin na dauka da sallama ciki ciki yace ba tare da ya karba sallaman ba. Bazaki kawo min abinci bane ko may nace dashi ban san ka shigo bane ya kashe wayan sai da na dan dauki lokaci namike na shiga kitchen na hada abincin shi na fita. Bai gurin cin abincin bayan na jera ne na shiga dakin yana zaune nace na hada abincin gani tafe yace ba tare daya dago kan shi ba gare ni. Komawa nayi saman kujeran dininng din ina jiran fitowan shi sai can ya fito har ya zauna bai yi magana ba na zuba na juya zan wuce yace ina zaki na dawo na zauna. Abincin ya fara ci ba tare da ya kula dani a wurin ba sai da ya kusa karewa yace may ya hadaki da nafisa har yakai kuka hada jikin ku a wanan yanayin da kike ? Shiru nayi ban bashi amsa ba ya dago yace ba tambayan ki nake nake yi bane nace ban san amsar da zan baka ba yanzu don ban san may ta fada ma ba kake fushi dani. A hasale ya aje cibin yace ashe kin san ina fushi dake ke nan ko dana dauka kina da hankali ashe ban sani ba duk kanwar jace halin ku daya ga baki dayan ku. Kina a wanan irin yanayin har zaki tsaya irin wanan fada kuna tijara wa junan ku nace dama nasan laifina zaka gani kan wanan maganan. Fadan ku bai damay ni ba sai cikin dake jikin ki idan ke baki san zafin kan ki ba nina sani don idan har wani abu ya samay ki ni zaku daukowa magana. Baki da hankali ne ko halin Nafisa ne ya zama maki bako kuma nace har part dina fa tabi ni zata dake ni bayan zagin da take min kuma. Ta dake ki mana idan tayi hauka ne ta dake ki din idan rashin hankalin ta ya kai can tunda ita bata dake ki ba aike kin dake ta din. Najirane inji kin ce wani gurin naki yana maki ciwo na shirya abin da zan maki kan haka sai Allah ya taimake ki banji kin min korafin komai ba. Ranan dai naga bacin ranshi sosai a gare ni don yai min fadan da bai taba yi ba a gidan har sai da nayi kuka a wurin. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Laraba mace mai kwazo da sanin ya kamata ga kawar da kai ga abin mutum ga aiki a tsakani da Allah idan nace wani halinta wanda bai mun ba nayi karya illa da farko dana fara ja baya da ita. Don yawan complain din Fati da takan mun don idan ta dauko zancen Fati shiru nakanyi in nuna mata banson zance. Amma yanzu da muka dauki dan lokaci tare da ita saina fahinci wasu abubuwa a gamay da halinta, na farko dai tana korafinn akan zaman su da Fati. Sai na biyu tana son ja na da maganan da ya shafi cikin family house din su AA sai daga baya na fahinci abida yasa take hakan. Yau na fito da niyar zuwa gidan su maryam mu gaida anty hauwa dani da mama laraba zamu fita budan part din mu naci kararo da su Samiha sun dawo gidan. Madam ta gargadoso don bazata iya ba sun isheta a gida shine mafarin ladabin shegun da Nafisa take ma AA akan yayi hakkuri idan anyi sunan yarta tayi arbain zata gida ta wuce dasu. Ya amince mata da su dawo su zauna a gidan kafin lokacin data ce din dan hakan akace tsakanin mata da miji sai Allah don haka ta san kan abinta bata samu matsala wurin jawo hankalin shi ba. A raina na hade mamakin ganin su zaune a falon har falon ya fara komawa yadda yake da da tarkace da shara komai akaci anan za a aje falon. Ko kallon gefen su bamuyi ba muka fice daga gidan driver yana waje yana jiran mu ya kaimu unguwa. Sai da motar ta fara tafiya laraba tace abin mamaki bai karewa a duniya mutanen nan dawowa sukayi kuma gidan nan again. Murmushi na dan sake tare da fadin sun dawo mana mama tunda gasu nan har mazan su a gidan tace ikon Allah sai dai kuma ina ganin shigan dare sukai ma gidan don kafin mu kwanta ban gansu gidan nan ba danazo kwaso kayan da security sukaci abinci. Dama haka suke kamar bakin sheri basu sauka gari da rana sai a cikin dare a wayi garin dasu ba mai cewa ya san saukan buzu a gari sai dai ka wayi gari ka gane shi. Nace mama kin san su basu yarda da kan su ba balle wani don haka komai nasu a cikin munafunci sukeyin sa . Munje gidan anty hauwa a can muka wuni gidan mun sha hira sai yamma lis muka dawo gida ba mu girka komai ba don mun ciko ciki a can gidan da muka fito. Kamar gidan buki haka naga gidan ya koma min ga hasken kwayakwayan wuta ya haska falon sai hiran su ke tashi wasu kuma na waka har da tafin hannayen su. Wani iri naji tankar a kaina suke wanan hayaniyar duk da naji kewan rashin su amma yanzu sai na tsunci kaina ina bakin ciki sake ganin su a gidan da nayi zamu zauna dasu kuma. Bamu karasa shiga part din ba naji sun sake wani irin dariya har da guda irin shigen na matan larabawa. Tirkashi nace raina ya baci sosai don nasan dani suke haka na daure ido rufe na bude part din muka shiga muryan laraba naji tana fadin oho wanan masifafun sin dawo ke nan kuma. Ban iya bata amsa ba kai tsaye bed room na shiga na rage kayan dake jikina zuwa dogon riga na daura dankwalin shi a kaina na dawo falon na samu laraba. Nace mama ko a dan dafa maki wani abu ne ki dora akai kada ki kwana da yunwa tace kai yan nan wanan koshi da nayi haka sai dai gobe idan Allah ya kai mu dai ko ? Nace bari dai mu dora da dan ruwan tea a kai don kwanan nan mama sai dare yayi wani masifan yunwa yake damuna sosai. Sai da tayi dariya tace yar nan banda abinki yunwa ai yana maki da sauki na gani mace mai ciki da ake so taci ta koshi amma ke har yanzu cakulan abinci naga kinayi. Haba mama aiko yanzu ina ci da yawa fa a kwanakin nan har mamnakin kaina nake yi irin wana cin tace a hakan shine ci kada fa ki haifo min miji ko kishiya a ramay nace mama kishiyar dai don ku ji dadin kishi dakyau irin na gidan nan. Laraba tace kedai bari yar nan ai har na sallamay sallah ina mamakin wana abin ke dai da gani kin san ba banza bane wanan abin haka. Ace wai yadda aka rabu baram baram din nan wai Alhaji ya iya dawo da mutanen nan gidan nan haka kai da gani kasan ba abin kai sake bane wanan wanan. Kai mama kai sake kuwa ya dawo da ita kin san bai iya saba mata a hakan yadda yake tsoron alamarin ta aiko hajiyan su baya shaku haka nan. Tace yar na yanzu ma cikin abi yayi sauki ke nan ai idan dane ai bai isa yai mata hakan ba ma gaskiya kowa na ganin kokarin ki sosai da kike iya fuskantar matsalan wanan matar a zauna lafiya. Ko can sai da hajiya Fati tai magana ranan ganin kun fita da shi tana zaune bata iya cewa komai ba a kai. Nace mama ai abin nasa ne sai kaga kamar ya kubuta daga kaidin ta kwana buyu kuma sai kiga ya kara dulmiyewa a ciki sosai. Ai bata barshi haka ba kullun irin su a cikin tushi aikin su suke yi suyi nan suyi can ko yaushe a cikin kauce hanya ake don dai kawai aga an kuntata ma abokiyar zama ta muzanta a gurin miji. Aike bata samu yadda take so a kanki ba har yanzu nace Allah kuma ba zai taba bata sa, a akaina ba har ta mutu. Shiru nayi ina tunane a raina yanzun haka zamuyi ta rayuwa a cikin wa yan nan mutane kai ke nan ba wani rayuwan jin dadi dakai da miji gaskiya nikan da ake cewa wai ka gani ka daure ba zan iya cin fuskan Nafisa ba wani lokacin har da miji. Juyowa nayi nace mama ina ganin bread din nan tun na jiya ne ba zan iya cin sa ba gaskiya ko zamu fita in samu wani na aike sa ya sawo muna. Tace bari dai ni in leka idan masu gadin nan su nanan sai in basu su sayo muna ko na mike na shiga na fito mata da kudin bread din. Shiru shiru zanga laraba ban ganta ba gashi kuma ba wayane da ita ba dole na fito zuwa duba ta na samun har an datse get din gidan ta baya. Karasawa nayi gurin get din ina tambaya buzanyen waya rufe get din gidan daga ciki ne karfe takwas da wani abu. Don security din bakin get di basu nan su ma ina ta mamaki a raina babu wanda ya tanka min nasa hannu na bude get din . Laraba da security din nan biyu ne a waje ina bude kofan motar shi na isowa gurin da mamaki ya shigo yana kallon mu ko kallon inda yake ban tsaya yi ba. Na ba security din hakkuri muka shige da mama a ciki ina shiga ban tsaya jiran komai ba na jawo akwatuna na nafara hada kaya na da suke nawa sai da na shake akwatunana kaf ina jan zip ya shigo dakin . Kallon akatunan dana dora a saman godo yake yi ya dago ya kalle ni tare da fadin wanan kayan fa na may ye kuma. Ban bashi amsa ba na nufi gurin wardrobe na bude na tono handbag dina da nake dasu na fara saka kayan shafe na a ciki yana tsaye yana kallo na. Yace bake nake tambaya ba ina zaki haka kike hada kaya saida na gama na sauke akwatunan kasa na dauki hijjab dina yace ina kike nufin zuwa bada izinina ba sai lokaci na dago nace gidan ubana zan tafi yau insha Allahu komai dare kuwa. Murmushi yayi yace a wanan lokacin kin ko san karfe nawa muke yanzu da kike wanan haukan wai ma da izinin wa zaki tafiyan. Wani kallo da ban taba mai ba cikin bacin rai nace izini izini zan nema a gurin wa gurin mutumin da aka hada kai dashi aga bayana zan nemi izini ko may ? Cikin mamaki yace aka hada kai dani aga bayan ki akan may nace koma may ye ku kuka sani na fara jan jakkan zuwa falo rike ni yayi daga baya yace zaki bar wanan haukan da kikeyi kosai ranki ya baci. Ki tsaha ki min magana yadda zan fahinta rashin kunya ya hanaki tsaya kina ganin wanan ne mafita ga komay nene kike shirin yi din. Yanzu akan idon ka Allah ya nuna maka abinda sukai muna ni zaman su a nan tare daku bai damay ni ba kuma ba zai taba damu na ba din. Lafiya ta da na boyar Allah dake zama don ni a gidan nan najawa nagaji wallahi nagaji da irin wanan zaman gara na tafi inda ake sona da kaunana ida kansan zafi na yafi min. Malalacin Murmushi ya sake tare da fadin akan dawowan mutanen nan kike wanan haukan ashe idona ya ciko da hawaye nace dawowan su gidan nan bai tare min komai ba don a tare na samay ka dasu. Lafiya ta na jawa don gaba ban san irin abinda zasu iya min ba ina cikin wanan hali gara na koma ida aka san zafi na da ciwo yafi mun sauke. Kallon yadda nake zubar da hawaye yayi sai naga ya fita zuwa falon yace mama wani abu ya faru ne bayana. Laraba dake zaune tayi tagumi a takure guri daya tace Alhaji mutanen nan dai ne da suka dawo sin saka mu a gaba da dariya yanzun kuma na fita zuwa sayo mata bread ina ba masu gadi sako suka rufe mu ta baya. Yace rufewa fa yana fadin haka na fito ya kalle ni baice komai ba ya nufi kofan fita daga part din har ya fita ya dawo ya cire key di dake lake a jikin kofan ya rufe mu ta baya ya wuce. Zama nayi a gurin ban iya magana ba sai kukan da nakeyi part din nafisa ya nufa suka hade da ita tana fitowa. Nafisa wa yarufe kofan gidan nan da mama laraba a waje sai da taimai wani kallo tace nice nace su rufe don ko bazan yarda ana fita a wanan lokacin ba tana kebewa da wasu maza a dauka yan uwana ne dake gidan suke haka ? Nafisa kin san yarda muke da laraba kuwa tace ko ya kuke ai aiki take a gidan nan kuma a karkashin ka take. Kallon mamaki yake mata don yadda take maganan sai dai yana jin ba zai iya mata masifan daya shiryo yai mata ba suna hada ido yaji wani irin abu a tare dashi ya soki zuciyar shi. Wanda yazo da fada sai gashi yana maganan lumana haba wanan ai kin san bai dace ba kamar laraba ce za ace ta fita yin zance a waje ko may ? Samad kaga idan matar ka ta turo kane kai min cin mutunci in sani don bazaka zo nan ka tsare ni ba kana fada min wanan magana. Zuwa tayi gidan nan ta samay mu bata isa ta ce zata juya kowa yadda take so ba dokane na bayar ko itace ta fita wanan lokacin zance a rufe gidan nan ne. Ta fada tana wuce shi ya bita da kallo sai yaji bai iya musa mata da komai a lokacin suko yan uwanta sunyi tsit suna sauraron su. Yaja kafan shi ya bar gurin zuwa part din shi bai iya aiwatar da komai ba don kwarjin da Nafisa tai mashi. Yusuf na kira ina kuka ina fada mashi yai mashi magana ya bude muna kofa don ya rufe ni ta baya . Hankali tashe Yusuf yake tambayana abinda ke faruwa nace Yusuf nagaji da auren mijin wata wallahi bazan iya zama a gidan nan ba gaskiya. Yace yi hakkuri gani nan zuwa yanzu don Allah kanwata kada ki fita a cikin daren nan kin san halin da kike ciki fa yanzu. Hali ba zai hanani kwatar inci na ba nagaji ne sai kaga abu kamar yai sauke gare ka sai kuma a bulo da wani abin ban iyawa wallahi yace zaki iya insha Allahu khadija ki kara daurewa dai please. Maryam na kira muna gama waya nace tazo ta dauke ni jin ina kuka yasa taba anty waya tana tambayana ban boye mats komai ba abinda ke faruwa. Tace wai shi wani irin mutum ne da bazai iya tashi tsaye ba akan gidan shi yanzu kiyi hakkuri khadija dare ya riga da yayi sosai . Ki bari gobe idan Allah ya kaimu zamu shigo mu samay shi dole ne yasan tsarin da zaiwa gidan shi duk abinda take ji kowa ya iya sa ai. Da kyar ta samu ta lalashe ni na bar kukan da nakeyi din taita bani magana akan inyi hakkuri in bari har suzo. Yusuf ne ya iso gidan tun waje ya fara mamakin ganin buzayen sun dawo gidan don bai fada mai cewa sun dawo din ba sai da yazo ya gansu. Nan ya fahinci inda matsalan take ciki ya shiga ya samu matan sai raha suke a tsakanin su bai tanka su ba ya nufi part din mai gidan kai tsaye. Muryan Nafisa ne daga inda take zaune take fadin kai waye da zaka shigo min gida haka kai tsaye ka wuce sashen maigidan baka nemi iso ba. Ya juyo da zuman ya fada mata bakar magana wani iri yaji a ransa da sauki ya ambato Lah, illah,ha illah muhammadan rasullilah sau uku yaji wasai a ranshi yace ke baki isa ba wallahi kuma sherin ki yayi kadan a kaina. Yana fadin haka ya wuce part din azaune falon sama inda ya ke zama ya huta ko yaci abinci ya samay shi zaune. Lafiya na ganka a wanan lokacin Yusuf yace ba dole in taso ba kanwa ta takirani hankali a tashe zata bar gidan ka. Sai yanzu danazo kuma na fahinci abinda yake faruwa a gidan AA yaushe ka dawo da mutanen na gidan nan baka sanar dani ba. Yusuf ashe abinda ake fadi gaskiya ne kakai kanka inda ka wuce iyakar ka matsalan na nida iyalina harshi dole sai ka sani ko may ? Kallon mamaki Yusuf yake mashi yace gaskiyane na wuce iyakana a gare ka amma kayi hakkuri nayi kuskuren yin hakan. In Allah ya yarda kuma hakan ba zai kara faruwa ba don nima na sani matsalan iyalin ka baidace in shiga ba. Amma ka sani matsalan wanda ya shafi khadija ya zama dole in saka baki a cikin shi don matsalanta a gidan nan ya shafeni. Yusuf ya fadi a kakausar harshe yace ban min gidana tun muna sheda juna dani dakai a gurin nan matsalan Deedar ya isheni nima. Tunda na aureta ban zauna lafiya da matana ba kullun a cikin jidali muke a gidan nan ba wani kwanciyar hankali dana samu a cikin gidan nan. Yace naji wanan kuma kai kajawa kan ka haka tunda baka iya tsayawa kayi adalci a gidan ka ka bar mace ta shige maka a gaba kan komai. Ni ba zaka fada min wai khadija ta shigo ka rasa kwanciyar hankali a gidan ka ba don nafi kowa sanin gudun mawar da shigowan ta gidan nan ya baka. Tun kan khadija ta shigo gida ka baku da kwanciyar hankali da matar ka haka ta shigo ta samay ku da tarin matsalan ku a gidan nan. Yusuf ka tafi ka barni a yadda nake jin din nan idan ma zaka tafi da ita ne ga key can ka dauka ka kwashe ta ku tafi duk inda zaka kaita da daren nan sai kun dawo. Inda ya nuna mashi key din ya dauka ya fice baiko kalle shi ba ya ja tsuki a kofan suka hade da Nafisa tana shigowa tace mu zuba dani dakai agani. Yace ko mun zuba indai ni Yusuf ne baki kwashe komai wallahi don nafi karfin tsafin ki ko wani shirka daga inda AA yake zaune yace Yusuf ka fice min a gida nace maka. Yusuf ya fice bai ce mai komai ba part dina ya nufa ya bude muna falo ba wanda ke magana a cikin mu inajin an bude kofan na mike a zatona shine ya shigo. Sai naga Yusuf na zauna naji wasu hawaye suna zubo min na takaici da kunan rai yace khadija yi hakkuri ba sai kin fada min komai ba na fahinci duk abinda ke faruwa a gidan nan ko. Daga wurin shi nake yanzu wanan shu,umar matar ta riga da ta asirice shi da sihirin ta yanzu maganar ta wuce yadda ma kike zato ga AA din. Kuma dan dawowan nan da kukayi ne komai ya faru ina kuka nace ni ba zan zauna ba yayana dama can zaman hakkuri nake don ba sona yake ba har ga Allah. Yace ki bar fadin haka khadija don so wallahi ni nasan AA yana son ki fin karfin shi da asiri ne kawai akayi yanzu kuma insha Allahu zamu kwatoshi daga halakan ta. Sai dai abinda nake so dake yanzu don Allah ki jaye wanan maganan ficewa daga gidan nan da kike fadi idan kinyi haka kamar kin nunawa Nafisa nasaran ta a fili ne. Kin ga kina dauke da tsohon ciki haka tare dake sai taji dadi dama nasan akan abinda akai wanan aikin ke nan yadda yai masu din nan nasan ba zasu kyale shi ba nasani . AA mutum ne dake da yawan sakaci yasan halin matar shi amma shi bai damu da neman kubuta daga sherin ta ba zan kira hajiyan su yanzu insanar da ita abindake faru ta kara baki hakkuri takuma dage gurin yi masa addua itama don yadda na fahinci abin aikin gagawa aikai masa. Nan kafin in magana ya fara neman layin hajiyan ta dauka suka gaisa bai boye mata komai ba ya sheda mata harda abinda ya faru yanzu a tsakanin su. Hajiya sai innalillahi take maimaitawa yace ga khadijan hajiya kuyi magana tace kana gidan ke nan yace eh don ban fita ba ina gurin ita khadijan yanzu haka. Miko min wayan yayi bayan tace ya bata hakkuri ta shiga bani ba abinda nake sai kuka sai fadin take don Allah in rufa mata asiri kada inje ko ina zasu san abinda sukayi tace in ba yusuf din wayan don kuka da yaci karfina na bashi ban san may tace mai ba naji yana fadin in Allah ya yarda hajiya zan shigo din. Sai kuma ya mikawa laraba wayan ta karba itama sai fadin take insha Allahu hajiya ina tare da ita ko wani lokaci zan bata hakkuri in Allah ya yarda. Ya dai dan kara min nasiha da nuna min kuskuren tafiyan da nake son yi din tare da ban shawaran in kara dagewa wurin mika lamarina a gurin Allah. Karshe dai yai muna sallama ya fita muka rufe kofan part din nan laraba itama ta shiga bani baki tana lurar dani illan da fitar mace gidan mijin ta ke jawo mata a gurin kishi. Da barin ta fahinci halin da muke ciki kamar nuna mata samun nasaranta ne a kaina kukan ma da nake ya daina zo min sai tunanen maganan da Yusuf ya fada ma hajiya sunyi a kaina nakeyi. Ranan sai dai barci barawo ne ya sace ni ban dade ba na falka gajikin ba dadi abu gamai ciki haka na daure na gabatar da nafila na dade zaune ina mika kuka na a wurin Allah da fatan ya sauke ni lafiya. Washe gari tunda na tashi nayi sallah na gaida laraba na koma na kwanta ban fito dakin ba barci da ya soma dauka na laraba ta shigo tana fada min ina da baki a falo. Nafito na samu anty Hauwa da wata kawar tane da nake gani tare da ita ko yaushe ina fitowa tace khadija badai kuka kika tsaya yi akan wanan kishiryar taki ba. Dayan matan tace ai kuka baima irin matan nan ki dake ki nuna mata duniyan ci in kin yi kuka har ta gane ai abinda take son gani ke nan dama daga gare ki. Duk namijin da kikaga ya zauna da mace so ne yasa ya kawo ta gidan shi kinga zomu zauna zo mu saba idan ita tana asiri ke kuma ki nuna mata karfin Allah a kan ki. Anty Hauwa tace bamun zo nan bane don mu hadaki da mijin ki muyi magana yin hakan yanzu gare mu kamar tonuwar asirin ki ne tsakanin ki dashi a gareta. Shawara mukazo mu baki babu inda zaki kinji na gaya maki a gidan nan dai da bata son ganin ki zaki zauna ki haihu lafiya lau a dakin ki. Idan kinji na kuda daure ki kirani ko ban gari akwai matar da zan turo tazo nan gida ta karbi haihuwan ki haihuwar ki a cikin gidan nan shi zai kawo nasaran cin galaban ki a gurin wanan matar. Don matane basu gane ba sun dauka zuwa asibiti a haihu wani abin adone yanzu haihu yanzu ga saporters nan suna zuwa har gida su karbi haihuwa jinin nan da zaki zubar a cikin gidan nan shi zai karya duk wani asirin da ta binne a gidan nan. Sai abu ya gagara ne ya kama aje asibiti da mata sun sani irin haka ko sau daya ne da sun daure sun haihu a dakunan su don samun sauki a rayuwan su. Sun min magana mai tsawo wanda har naji na fahinta da zancen su nayi masu godiya anty hauwa ta mike tana fadin mu zamu tafi dama na zo ne don nayi maki alkawarin zuwa yau din. Matar tace zauna ki gyagije adakin ki kamar ba ayi ba kuma kada ki biyewa ciki ki zama raguwa a gurin miji. Ki nuna masa dashi da ita basu isheki ba ki fuskanci rayuwan dake gaban ki da kanshi zai dawo ya koma kunyar ki a gidan nan zaki ce na fada maki watarana. Gani da komai da namiji ke so a gurin mace gyagije ki koya mata hillan mu na mata ki nuna mata ke ma kin iya fa. Muka fito muna dariya suna zaune da su madam suna kwasan kanu labarai a gurin nafisa sai gamu mun fito madam tunda ta kyala ido taga anty Hauwa tasha jinin jikin ta muna fita daga falon tace. Nafisa may ya kawo hauwa black din JJ gurin wanan yarinyar kuma Nafisa tace waye ita din sai da ta kalli kofan da muka bi tace ashe akwai shegiyar kuwa. Indai wanan yarinyar da Hauwan JJ take hurda a garin nan idan baki mike tsaye da kyau ba watarana sunan ki sorry a gidan nan. Nafisa ta dafe kirji tace kin barni a duhu sai zuba kike yi haka tace itace fa hajiya sabuwa ranan take bamu labarin ta wurin hatsabin banci ga kudi amma ba wanda ya isa ya rabi mijin ta yanzu har gida zata ci mashi mutunci. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Na dawo daga raka su anty a yadda na samay su falon ya nuna min suna wani magana mai muhinmanci ne. Har na dan shige naji muryan Nafisa tana fadin ba wata hauwa zaki jira ba ko uwar hauwa ce bani shayin ta kamar in wuce sai na dawo baya. Ke karamar shu,uma kin tsargune da ganin anty hauwa gidan nan gida kan dole ta shigo cikin sa tunda yar uwarta na cikin sa. Ba a hana guzamay irin wa yan nan shigowa ba na nuna su madam da yan uwanta nace sai matan kirki irin su anty hauwa za a hana . Ai in kin ga bakina sun daina shiga gidan nan tabbatar da nice bani gidan nan barin gidan nan kuma gare ku tankar hasaran ku ne kuma don a tare zamu fita daku. Karya kike wallahi ai wanda ya riga kwana ya riga ka tashi na cabe da fadin ke nan zaki rigani fita kenan ko ? Tunda kin rigani shiga ke mai gayyan tsiya ba ai magana ba sai ni dana tarkato baki alheri zaki magana. Bakina yan yar arzikine irin alheri ko ruwan gidan AA bai ishesu kallo ba balle abinci gidan shi wanan sai yan yunwa irin ku masu gayar har dangin su da abikan bushasha a zo ataya su cin arziki banza ta fadi. Ke yarinya kada kice zaki fada min magana inji madam to uwata kin tsargune ko kin sha ruwan gidan nan ne ke ma ? Na wuce ina dariyan ke ta nan nafisa da yan uwanta suka shiga magana ina jin su ban tsaya bin ta kansu ba na shige part dina. Ina shiga ban tsaya falo ba daki na shige na dauro alwala na fito na fara sallah nakai wani lokaci ina sallatus tasbihi ga ubangijina na gama na bude kur,anina na shiga tulawa a gurin. Sai sha biyu da wani abu na daga wurin falo na shiga na samu laraba zaune tana kallo zama nayi ina fadin mama yunwa nake ji ban karya ba yau. Tace na gama abinci naga kina son dafa duka mai ganye shina dafa muna uwar dakina naji dadin ganin ki haka kin maida komai ba komai ba yanzu ki barsu da halin su. Allah bai barci bai gyangyadi yana kallon kowa da halin sa ne mai hakkuri shike da riba wata rana ai ta mike ta zubo min abincin ba laifi naji dadin abinvin sosai. Nafisa ta kalli madam bata damu da wa yanda ke falon ba a lokacin tace ni na rasa jinin wanan shigiyar ko wani irine madam. Jifa abinda arnen bokan na ya fada shekaran jiya nashikan naga fa,idar shi sosai don jiya sun kwasa da Yusuf amma wanan kamar abin bai haukan ta ba ita. Madam tace irin su shegu basu shigowa ai sai sun shirya ba a banza suke shigowa duniya ba ki dai bi a sannu har ta haihu kinji boka yace sai ta haihu zata hudu . Samira dake zaune tana ma baby wasa ta dan dago ta kalle su sai kuma taci gaba da yin wasa da hannun yarinyar. Na idar da sallah a zahar ina zaune sai ga Samira da ihisan a dakin sun samay ni falo ihisan tace abinci anty. Nace maman ki zatai fada ida kinci abinci nan Samira tace anan zamuci ban son abincin part din mu ba dadi kamar naki. Laraba nace ra dibo masu sun zauna sun fara ci Samira tace anty haihuwan baby zakiyi irin na Ami din mu nace wa ya fada maki. Tace Amin mu da madam naji suna magana dazun wai sai kin haihu zasu huda ki su huda baby anty kada ki haifi irin baby Ami don Allah. Ami bata son baby nan nata tayi ta dukanta tana zagi wai jinin ki nada karfi ba a iya hudaki yanzu inji madam ta dago tana tambayana. Eh Samira sai na haihu tare da Amin din ku za, a hudamu idan na haihu amma itace zataji ciwo ai idan an huda mu din fuska ta bata. Tace shiyasa sukace ke boka yace baki huduwa da sauki sai Abbi din don shi tun shekarajiya an huda shi. Duk da gabana yana faduwa da zance yarinyar amma sai na biyewa shirmay ta ina fahintar wani abu hartace wai a filon Abbi ansaka mai abu shiyasa ya hudu da sauri. Shigowan maryam ya katse muna hiran yaran da muke sauraran abi boye daga shirmay su na fahinci iyayyan suna hira ne a gaban su. Maryam ta bisu da harara nace ya haka kuma ta zauna tana aje jakka da gyalenta a gefe suna gamawa suka mike anan suka bar kayan da sukaci abincin suka fice. Shegu suma sun iya kwadai irin iyayye su nace maryam ai zuwan ki ya katse muna jin laraba ne yau nan dai na kora mata abinda yarinyar tace. Ido waje maryam tace mun shiga uku wanan matar dai a haka zata mutu ga bin bokaye da yan tsubbu yanzu ya za ayi nace shinake tunane. Maryam ni na dade da sanin haka tun fadan mu da ita na rasa gane kan AA a gidan nan magana ma sama sama yake hada mu yauma karewa fita yayi bai shigo part din nan ba. Yanzun kin gane ni sai naga ki bari sai idan yana gida kije dakin gyara mai ki bude filon a gaban shi ki nuna mai tare da tambayan shi wanan nasa ne idan kin gani amma kafin nan ki fara dubawa idan gaskiya ne. Duk wanan sakacin ki ne da mijin ki khadija kallon ta nayi tare da fadin sakacina kamar ya fa tace wallahi sakacin ku ne khadija. Khady ke malama ce kin iya karantawa ki rubuta da kanki yanzun bansan matsalanki ba khady duk kin yi laushi da yawa baki irin wanan kiza kizan naki. Laraba tace ayyah ai abin ba hakana bane ke dai kada Allah ya hada ki da irin wa yan nan matan shu,umai barin ta banza akayi kike zato. Jifa fa ba fasa yinsa ake ba a kullun jifanka ake amma ai uwar dakina tana kokari wuri ibada sosai wallahi. Nan dai muke ana ta tataunawa kan matsalan har yamma ta tafi kamar yadda bai damu ta duba mu ba nima haka na dage mai kafa har ya gama borensa. Ina daga daki wayana dake falo ya dauki ruri laraba ta kawo min dakin hajiya mamace kan layi mun gaisa ta tambaye ni jiki na ce alhamdullahi mama. Tace to yaya ina akwai canji fa alamarin gidan naku ko yanzu nace akwai mama tace ban kirashi ba shima bai kira ba tun ranan. Nace mama kiyi hakkuri abin sai a sannu da addua don kullun halinta kara baiyana yake na sheri. Nagama waya na kashe falo na fito naji ana sallama laraba ce ta leka security din gidan ta gani a kofa na yace Alhaji na da boko waje yace a kira masa daya daga cikin matan gidan nan. Nace bakon ya fadi haka yace eh sai dai naga suna da zubi da Alhajin gidan nan sosai sai dai na gidan nan yafi shi tsayi da haske sosai. Daki na koma na dako hijjab na fita duk da ban san shi ba amma ganin shi da kakin soja yasa na fahinci shine. Da fara,a a fuskana nace yaya Suraj kaine a gidan mu yau sannu da zuwa ya amsa min tare da fadin ko kece amaryan ta mu nadan yi murmushi nace bissimillah ka tsaya nan mana. Yace nazo security din kun sunce maigidan yayi tafiya duk da ban sani ba nace eh yace ok yanzu muka sauka shine nazo nan in dan watsa ruwa kafin in samu masauki. Ashe maigida ma baya nan nace ko bayanan aimu muna nan yaya shigo daga ciki na fara tafiya ya biyo ni zuwa ciki part din AA na nufa dashi na bude dayan dakin nace ya shiga tare da fadin barin je in hada ma abinci yaya. Yace ya gode nafice a falo muka hade da Nafisa tana huci tare da fadin dama na sani har kwasan mazan naki yakai ki dauki kato ki kai sashen miji na. Waye kato naji ya fada daga bayan mu ashe ya fito yaba da sakon a sawo mai katin waya ya samu muna magana. Sai da naga kaduwa a tare da ita data ganshi ya nunata yana fadin har yanzu wanan halin tsiyar taki yana nan ashe yace to na dawo kasan zamu zuba dake a gidan nan don a nan zan zauna daku kwana biyu kafin in kama gida. Naji dadin har cikin raina ya sake nuna ta yace ki natsu a dan zaman da zanyi a gidan nan tare da ku don ko mijin ki ya takani yasan halina ba raga mai zanyi ba balle ke. Murmushi nayi na wuce part dina naje nace wa laraba mama yau muna da bako yaya Suraj ne ya dawo anan zai zauna tare damu kwana biyu. Abinci lafiyayye muka hada mai takar wanda nake hada ma AA na kai mai a dinning na aje na kwankwasa kofan nace abinci na kan table. Ya dan leko yana fadin ya gode na fita saida na koma nake fada ma laraba ashe wai maigidan yai tafiya ne tace ikon Allah kuma shine babu ko sanarwa haka ? Nace ba komai mama ni dai Allah ya sauke ni lafiya shine addua na ko yaushe yanzun banda lokacin komai a rayuwana. Nafisa ko a bangaren ta tun fafatawan ta da Suraj ta shige daki sukuku tana kiran madam ta dauka tace madam kina ina yanzu ? Madam tace wani matsalane kuma ya faru yanzu tace wanan dan iskan ne yau yazo gidan mu bakiga yadda nake kaduwa ba don tsoron shegen mutumin nan nake a rayuwa na. Madam tace ke ki debe wanan tsoron ki nuna masa shi din may har yaushe zaki tsaya wani kanin miji yana baki tsoro kamarki yanzu kuma. Nan dai ta bata karfin gwiwa akan zaman da zaiyi a gidan kan kada ta sarara mai don tasan AA bazai yarda ba ai mata wullakaci. Iyakata dashi in kai mai abin karyawa kafin ya fita idan ya dawo da dare kuma in kai may yau weekend bai fita ba yana dakin shi kwance. Daga can yake jin dararakun su ya sauko ya samu wani buzu zaune yana sharara masu labari sai dariya suke kwasa saukowa yayi daga sama tun kan benen yake fadin kai may ye haka su waye hakan kuma. Gaba daya suka maida kallon su gare shi har ya sauko kasa yace wa yan nan fa daga ina suke haka ne ? Ya nuna namiji yace kai tashi ka fice cikin karfin hali tace ya fice gidan ka ne gidan dan uwana ne fa yace ok belt din jikin shi yake zarewa a hankali. Kagin buzun yai azaman tashi har ya make shi a kasa ko ya nana kasa ya fara kai mai belt da shuri duk matan suka mike suka fara kururuwa. Ihun su muka ji nida Labara muna rigen fitowa abinda muka gani yasa mu ja baya daga kofa na muka tsaya kallo abinda ke faruwa. Sauran mazan dake waje suna dafa shayi suka shigo gidan nan ya hada dasu yai ta aika masu shuri da bugu da belt. Hankalina ya tashi na fara rokon shi yayi hakkuri Nafisa ko wuri daya ta manne da yan uwan ta suna kyarma ya na huci ya nunata yace sai nayi maganin ki a gidan nan shegun karuwai kawai. Wani dadi naji a raina yau ga mai maganin shegu yazo gidan juyawa yayi wurina yace duk wa yan nan a nan suke ne kai na gyada mai ya waro ido yace duk wanan taron a gun mutum daya yake mutum kusan ashirin da wani abu. AA wani irin mutum ne shi da baida tunane yaya gidan ka zai zama happy family da wanan kwama calan haka zai dawo zamu hadu dashi gidan nan. A daidai wanan lokacin ne maryam ta shigo ta samu an gama rikicin yana masu sababi duk sun shige daki sun boye. Part dina muka shiga ba abinda muke sai labarin muna dariya mukaji anyi nocking din kofa. Laraba ta mike tana dubawa shine tsaye a kofan yake tambaya ina ina tace gani a ciki yace kice mata zan shigo. Ta juya ta fada min da sauri muka gyara ya shigo da sallaman shi waban karon ya canza kayan jikin shi zuwa jallabiya. Wuri ya samu ya zauna tun ban mai iso ba yace madam gurin ki nazo sai dai naga kamar kina da bakuwa yanzu din nace kawatace ba bakuwa bace ai yaya. Yace good zan so in tambaye ki wani abu gamay da gidan nan dafatan zaki ban amsa yadda nake so ba tare da kin boye min komai ba. Nace insha Allahu yaya idan na sani zan fada ma yace good buzayen su nawane a gidan nan nace gaskiya ban san adadin su ba yaya kai ya gyada ya sake fadin kina ganin sun kai how long a nan nace ban sani ba don nima anan na samay su gaskiya. Yace kina nufin duk dadewan nan suna gidan nan tare daku nace eh yace wanan wani irin rayuwa ne haka ina mutum zaiji dasin rayuwan sa a haka ? AA wani irin mutum ya zama da baida lissafi wallahi dan zama nan mutanen nan suna takura min sosai ba dama mutum ya dawo da gajiya ya huta sai sun damay shi. Kada ki damu zanyi maganin abin insha Allahu maryam tace mun gode yaya wallahi da abin yai dadi gidan sam babu kwanciyar hankali ko kadan . Yace kada ku damu ku dan bani time mu gani har ya dawo ya mike ya fita yanufi kofan fita wajen gidan kiran wani buzu yayi yace ya kidaya mashi su nawa ne a gidan nan. Na fito rakiyar maryam yana zaune saman motar shi muka gaida shi yake fadin zata koma ke nan nace eh yace barin sauke ta don nima gari zan shiga nayi mata sallama na fita. Gidan ya koma shiru kamar ba taron nan a cikin sa nace wuta soja ga wuta ga halbi don dole yau kowa ya natsu badon Allah ba. Ashe bayan sun fita ya bugi ciki maryam yaji komai na gidan tunda ya fahinci na boye mai wani abu ba gidan dake faruwa. Washe gari nayi bakin course mate dina tun da nai aure zuwan su na fako ke nan gurina mun dade dasu sun fito na rakasu zasu tafi lokacin motar AA ya shigo gidan ban ko kalli inda motar take ba balle sannu da zuwa. Shima kallon mamaki yake aika min daga inda nake muka gama magana suka ja motar su muna dariya suka tafi ni kuma na juya na shiga ciki ban kara bi ta kan sa ba kuma. Wai ashe hakan da nai mai yaji zafi kodana shiga ban fada ma mama ya dawo ba na shige ciki don yin sallah la,asar. Ina sallah ya shigo dakin bai ko sauya kayan jikin shi ba muryan shi naji suna gaisawa da laraba a falo tana mai sannu da zuwa ya leko dakin ina sallah tsaye yai min dakin ni kuma danaga haka ban yi saurin katse sallah ba. Sai dana gama addua na shafa na mike ina ninke sallaya na gurin muryan shi naji yana fadin ke baki san nayi tafiya bane da baki iya yiwa mutum sannu da dawowa ba ? Da zaka tafi ka fada min nai maka Allah ya tsare hanya ne da zaka zo ka tsare ni yanzu Allah dai na ganin ka duk abinda kuyi a gidan shine gata na. Na fadi ina nufar side drower dina don aje carpet din sallah yace kina nufin sai na biyo ki nan na fada maki zanyi tafiya kin min wullakancin da kika saba yi min zaki gaida ni da dawowa komay ? Zama nayi a bakin gadon batare da nace mai komai ba yace kina ganin wanan rayuwan da kika dauko shine zai fisheki a gurina komay ? Ni dai ban mashi magana ba ya buga tsuki ya fita a hasale na bishi da harara tare da fadin karfin hali wai barawo da sallama ke nan. Yanzun kuma wai laifina mutumin nan zai gani yanzu ban masan kan girkin gidan ba yanzu tunda na daina bin komai. Falo na fito na samu laraba tana ganina tace injin dai ba wani abu tace kinyi ba kuma naga mai gidan ya fita a hasale mama rabu dashi rainin wayo yake son yi min wai ni ban mai sannu da zuwa ba. Lokacin da zaiyi tafiyan shi ya sallamay ni balle yanzu in tare shi da dawowa tace ai da kin tare sa din ba komai bane Aljannan ki kikaiwa hakan. Mama har zancen wani Aljanna ake a gidan nan da babu tsari dole in masa haka mama ai idan na gaida shi gobe ma fiya da haka zangani garesa . Yaba nufin zan zaman bisa ne yana min wullakanci ina bishi shi yana bin umurnin wata saboda ya gyara mata raine yaki sallama na ai yasan dani a gidan. Watau yanzu hankalin shi ya fara dawowa gare shi idon shi ya bude zai zo ya lalashi banza ko ban cikin matan da zasu dinga bin namiji yana cusguna masu cikin nan ne kawai ya kawo min cikas a gidan nan. Ki dai yi hakkuri tunda ya sauko yanzu ba gashi har ya biyo ki dakin ki ba inda yana tsoron ta ne ai ba zaizo nan din ba ko yanzu. Allah ne ya karba muna adduan mu ya kawo saukin lamarin nan kurkusa har ya gane hakan nace bai gane komai ba wallahi mama ki barni dasu kawai a gidan nan. Dana haihu sai an nemay ni don ba zan zauna ina cin wanan kashin ba da kurciyana su bata min lokaci na a banza. Sai dai iyayyena da nasa suyi hakkuri tunda basu ke zama min ba nice nasan abinda ake min don haka ni zan wa kaina mafita a gidan nan. Abincin dare muka gama na dauka bayan nayi sallah na kaiwa Suraj tare na samay su zaune a falon sama din dagani dukkan su rayukan su a bace yake. Muryan nafisa naji tana fadin akan may zaki kawo mai abinci a gurin ki yake ne ko may kayya ke zaman shi gurin ki ya dama a rayuwan ki ni yaya Suraj na kawowa abinci. Ke waya kiraki gurin nan ko an fada maki sa,annin ki ne zaune girin nan suraj ya fadi a hasale yana kallon ta. Tace amma dai kasan a gidan mijina kake ko ina da daman shiga ko ina naga dama a gidan nan ba wanda zai min shamaki. Ai na dauka gidan ubanki ne nan din ba ita ba harni saida na waro ido waje ya nuna mata kofa yace fice nan tun ranki bai baci ba ko yanzu in tatakaki a gaban mijin naki yana kallo. Don shi ya daure maki gindin iya shegen da kikeyi gidan nan saboda samun wuri yayi maki yawa har kishiya kike son juyawa ko ? Kallon AA tayi don yai magana yace Nafisa ki fita kin san halin suraj tunda kikaji ya fadi zai iya aikata maki abinda yace yanzu. Ta juya yace dawo da sauri ta tsaya yace waye da girki ranan da ya tafi a cikin ku kallona nayi na dukar da kaina kasa ya sake maimaita maganan shi. Nace itace don nima ban san yayi tafiya ba ya dago yana kallon dan uwan nasa tare da fadin why brother why kabari haka na faruwa a gidan ka. Kan wanan mara mutuncin zaka watsar da matan ka na kirki ka kama banza can wanan da kake gani cin kasuwa ne ya kawota wurin ku munsan irin case din su da dama. And kuma gobe goben nan ina son duk taron buzayen nan subar gidan nan tun suna sheda kansu ko in turo a kwashe min su kaf wallahi. Ke kuma kin zauna wanan banza tana juya ku kamar ta samu waina daga yau ni suraj nace ki mike da tai maki tsiya kikirani ina garin nan yanzu . Dama nasan zuwa ka nan ba alheri bane an turo kane ka koreni ko ta halin kaka a gidan nan ba inda zan tafi yan uwa na kuma ba zasu tafi ko ina ba tunda ina gidan nan. Ai bakai nake aure ba dan uwanka nake aure yace zaki gane baki da wayo ranan ma kyale ki nayi don mijin naki baya kusa yanzu ya dawo a gaban shi zan lalatsaki son raina. Ganin yana magana AA baiko dago kai ya kalle mu ba sai wayar shi yake latsawa a binsa kamar hankalin shi bai gurin draman da akeyi. Har na bar gurin ina cike da mamakin wai shi AA wani irin mutum ne haka wanda bai iya yin katabus a gidan sa kanin ka yazo yana shimfida doka a gidan ka kana zaune kana sauraro batare da ka furta wani magana ba. Har na kasa boyewa na fada ma laraba abinda ke faruwa tayi dariya tace bazaki shiga tsakan su ba tun suna yara ance haka suka taso su uku da Yusuf da yanzu ya zama dan gida shima garesu. Idan ma da ta matsa a kanta zaimai da haushin rashin mutuncin idan tayiwa dan uwan nasa sai kunji mamakin shi. Allah ne ya karba adduan mu ya jefo aikin shi nan kuma har ya zabi zama daku mutumin da baida sauki ko kadan kowa yasan shi da rashin mutunci ai. Washe gari ina daki kwance naji kururuwa yana tashi muka fito ciki da sauri ashe nafisa ne shiko yana tsaye murtuk da fuska yasa bakin glass cikin kakin su na sojoji. Sai umurni yake bayarwa nafisa na Fadin sai dai ta bisu yace tafi nono fari amma yau babu buzun da zai kwana a gidan nan. Kaf mazan su da matan su aka kwashe a gidan karo na biyu ina fatan daga wanan tafiya kada Allah ya dawo muna dasu gidan kuma. Ranan laraba taita aiki a falon yasa duk a kwashe kujerun falon aka saka wani su tv da komai na nu,ora aka canza na gidan nafisa tunda ta fita banji duriyan ta ba haka shima mai gidan ashe wuri suka nema masu can wani unguwa da zasu zauna. Sai dare bayan goma ya shigo lokacin ni har na kwanta mun rufe part din mu yazo yana kwankwasawa don waya a kashe take tunda zan kwanta. Laraba dake falo ne ta taso ta bude mashi part din ya shigo yana fadin tana ina tace tana daki a nan ya samay ni kwance saidai na falka daga barcin dana fara. Har kun kwanta yace eh kawai na iya bashi amsa don haushin shi da takaici da nake ji a raina yasa ban ganin dan sauran girman shi da nake gani dama. Ashe abinda ni ban sani ba shine waya suraj sukayi da hajiya yana tambayan AA zai zo abuja yana son sauka gidan shi shine kafin ya samu wuri. Hajiya tayi murmushi tace anya zaka iya zama a gidan dan uwanka yanzu yace saboda may hajiya tace gidan ya koma kamar tashan buzaye kowa yaje bai marmarin komawa kuma. Nan dai ta kora mai duk halin da dan uwan ki ciki yace kada ta damu zai ma abin magani in sha Allahu shine mafarin wanan turjin da yazo yi a gidan ya watsa kowa don bai barta da kowa ba yace idan tana son mai aiki a nema mata yar kasan nan. Ranan kan sun sha zagi su da dangin su kaf a gurin su da abikan ta inda suka tasa AA a gaba saida ya basu wani gida nashi suka tare a cikin sa wai kafin su gama shiri su koma gida. 1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Yanzu gidan AA tankar babu kowa a cikin sa ne don shirun da gidan ya koma wani lokaci muna fitowa falo anan zamu zauna muyi hira da mama sai yaran Nafisa da in ta fita ta barsu a gidan. Da farko dasu take fita zuwa unguwa daga baya kuma ban ya akayi ba take barin su gidan ta fita haka zasu wuni da yunwa sai idan ni na basu abinci. Babu wani dogon shiri tsakanina da maigidan tun wanan Clash din ya faru Yusuf ma yanzu ya dauke kafan sa a gidan. Gida nake son zuwa nakai sati ina binshi da zancen yana ja min rai akan zuwa na gida wai sai na haihu zan tafi na dage akan maganan bai dai ban amsa ba kan tafiya. Sai yau da ya dawo ya same mu a babban falon gidan muna hira Samira ne ke bamu labari ina rike da yar gurin Nafisa a jikina abinci nake bata. Ya shigo kamar yadda ya saba idan ya dawo gurin aiki a kasalance muna gaida shi ya samu guri ya zauna Ihisan ya tambaya maman su tace ta fita tunda safe. Kai ya girgiza yana fadin ina son ranan Friday din nan zan yi tafiya sai ki shirya kuje gida ki dubasu kwana uku ai is ok ya fada yana kallon fuskana. Kwana uku wanan dadewan da nayi banje gida ba haka one week dai dan dama ke nan yace idan zaki wuce kwana ukun ki fasa ki bari sai idan kin haihu. Tun ranan na fara shiri na shiga kasuwa da maryam muka sai tsaraban da zamu kai gida tare da mama laraba zan tafi don barin ta gidan ba zai yuyu gare ni ba. Nafisa bata san da zancen tafiya na ba sai ranan da zamu wuce naje sallaman ta har dakin ta na samay ta nace mu zamu tafi ai muna gafara. Tace na aikeki ne da zaki sallamay ni dariya nayi nace akwai rai akwai mutuwa don haka ba don ki na zo ba nazo sauke nauyin hakkin makwabtakane gare ki. Daga haka na fito abina na samu mama a kofa tana jirana a waje muna fita na samu AA a gurin motar . Motar shigan shi ce ya bamu zamu tafi dashi nan dai ya kara jaddawa driver da yaja mu a sannu kada yai gudu damu. A raina nace kaji kitihin maza kamar wata wace ya damu da ita a gidan abin mamaki harda hilux na biye damu a bayan mu dauke da kayan tsaraban da ya saya muna . Ban san da wanan sayayyan ba sai yanzu da motar mu zai tashi yace tsaraban ki na dayan motar. Ban samu godiya ba muka daga daga wurin ina mamakin shi wa zai ganni da tarin arzikin nan yace wai ba zaman lafiya a gidan shi. Shike nan ya gama daure ni ta wanan fannin kai maza sun sa takon sheri nace dole in ja bakina in tsuke kan wani matsala nawa ke nan don babu wanda zai yarda da wanan. Duk da fadan da yai ma driver bai hana shi sharara gudu ba dan kankanin lokaci sai gamu garin minna wani dadi naji a raina daya sakani lumshe idanuwa. Ina mai jin dadi a raina gidan mu ba bakon wuri bane ga driver nayi mamaki ba tare da kwatance ba ya kaimu har kofan gidan. Sai dai nayi mamakin ganin sauyin da gaban gidan ya samu sosai an rushe ginan dana sani anyi na zamani a yanzu. Da mamaki na fito daga ciki motar sai kallon tsarin da akaiwa gidan nake yi gaisuwa nake samu daga wurin samarin dake zama opposite din gidan mu suna zaman kashe wando. Wa yan nan samarin da suka taso ne suka yi kokarin shiga muna da kayan mu cikin gida sai ga yaran gidan mu a guje sun fito taron mu. Nan dai muka rungumay juna dasu muna murnan gani junan mu na yaushe rabo ciki muka shiga laraba tana biye damu a baya. Maman mu tana tsaye ta kasa boye farin cikin ta gare mu sai fara,a take a fuskan ta da dan gudu na karaso na rungumay ta cikin farin ciki. Ke da hankalin ki kuwa kike wanan gudun da tsohon cikin ki nace mama don Allah bari mana ina cikin yake ina kallon kaina na sake rungumay ta ina jin wani irin abu har cikin raina. Mun shiga ciki inda samarin ke ta faman jibga kayan a tsakar gidan mu kallon dakin mama nayi nace mama nifa na kasa fahinta wanan sauyin da na gani a gidan nan yanzu. Tace bari ki huta mana ai zakiji komai dake gudana ko a bakin baban ku idan ya shigo nima haka naga wanan aikin. Allah sarki dan uwa mai dadi sai ga kanina Nasir da gudu ya sawo min banbara da ta waska wai abin tarban shi ya kawo min. Nan na baje falon mama na ci bambarana sosai na kora ruwa sama iskan fanka na buguna sai barci ya dauke ni a gurin. Barci nayi sosai a gurin sai da mama ta tayar dani in sallah na tuna da driver da muka zo dashi nace mama ankaiwa driver ruwa kuwa ? Tace yanzun kika tuna dashi ankai mai har abinci sun ci suna can da Alhassan ya kai su su samu inda zasu sauka. Laraba fa na tambaya tace tana can dakin tana sallah na mike nima don zuwa sallah amma cikin nan naki ya girma da yawa anya ba batan wata kikayi ba kuwa baku kidaya da kyau ba. Ai ina zuwa awo mama su suka fada min cikin yayi girma kamar ba cikin fari ba ne na gani kai mama bar wanan magana kina sa ina jin kunya sosai wallahi. Tace ikon Allah shi zancen cikin ne abin kunya kamar bamai uba ba ciki ciki da gatan shi zaki wani kama noke noke haka. Bayan nayi sallah ne daddy mu ya shigo gidan da murna na taso na tare shi shima yaji dadin gani na da yayi yace that is my girl khadija ke ce haka kika zama wata big mama. O lord daddy har dakai cikin min sheri yace common zo nan in kara ganin ki nayi dariya naje gab dashi na zauna sai kallona yake yana jin dadin ganina. Mun dauki lokaci dashi muna hira anan yake fada min irin alherin da AA yake masu a raina nace munafuki yar ku nacan yana gana mata tasko yazo nan yana wani kyautata maku. Yanzu ni zan fara kawo korafin zanan da muke a gidan nan a gaban su dole in ja baki na in shiru ko kuma in kebe da mama da take ita mace ce ta taimaka min da shawara.. Sai washe gari aka fara raba tsara na nesa ni na shirya zuwa gidajen su kai masu don ba lokacin da zan ja dole na shirya ban hutaba na fita. Gidan ya suwaiba ne karshen zuwa acan muke har karfe takwas muka dawo gida ranan na samu kebewa da mamana itace ta fara kawo min maganan tana fadin. Naji dadin ganin ki a haka khadija kullun ina kwana da zancen ki a raina dashi kuma nake tashi nasha mafalki da farko mara dadi a kan ki. Sai da naje gida maikunkele na karasa har beji naga baba nacan ya ban addua da zandinga yi akan ku yace idan kin zo a sanar mashi tun jiya da kuka iso na tayar da Alkassim ya tafi ya sanar mashi da zuwan ku. Shine yaba da sako a kawo maki kinga sakon nan ta mike tana daukowa tace rubutu ne da hayaki yace kiyi shi tun nan gida dama ina Allah kizo ba sai kin kaiga haihuwa kamar yadda yace ba. Nace mama nasan kin damu da rashin zuwa na ai sai dai ai kin san ba laifina bane tsoron daddy nake ji kan umurnin daya bani da za a kaini. Dadin ku haka yake ai ni ban san halin shi ba idan na matsa da magana sai yace ina son kashe maku aure ne komay ? Mama zuwan nan da nayi akan haihuwa na ne na matsa in zo don irin abinda za a aiwatar idan na haihu din na ce nazo da kudi da zan bar maku ai lalurar haihuwan dashi in Allah ya sauke ni lafiya. Maganin da ta dauko ta fara min bayanin su tare da fadin yanzu idan kin gama sai in debo maki garwashi ki hayakin yace idan kin kwanta zaki mafalki da wani abu duk abinda ya tsaya maki a rai to kiyi taka tsatsan da abin nan. Ruwan rubutu ta miko min tace wanan idan kin gama wanka kiyi hayakin sai ki shanye gaba daya ki shafa sauran a jikin ki sai ki dora da hayakin. Ga ruwa can ki watsa kafin dare yayi sosai ta fadi tana mikewa na tashi na wanka kamar yadda mama tace ina fitowa na samu tana zaune tana jirana da garwashi a gaban ta. Rubutun ta miko min nasha na shafe jikina da saura na shiga yin hayakin sai da yabi jikina da kyau na cire rufin danayi mun dan taba hira nan cikin daren naba kudin nace ta boye su zan ba daddy nasa da wani don kada ya fahinci wani abu. Albarka tai ta saka min tare da kara min nasiha kan hakkuri da juriya a gidan miji har barci ya dauke ni ban sani ba ta fito ta barni don in samu barcin. Washe gari tunda na tashi nake baki masu shigo taro na don an kai masu tsaraban da nazo dashi suna tambayan yaushe zan koma sai ace masu gobe. Duk wanan bai sa zancen mafalkin da nayi da madam da yanyala ya fita raina ba da wata mace da ban sani ba mama ta lura da damuwan da nake ciki sai da muka kebe nake fada mata abinda na gani a cikin mafalkin nawa. Da farko dai ana taro ne a dakina sai gasu sun shigo fuskan madam ya canza ta karbi wata yarinya ta barin wurin yarinyar ta koma wani kala kamar abin tsoro. Yanyala kuma ganin ta nayi tare da nafisa suna bina da gudu ina kama yara sai ga AA yazo ya tare mu sai suka juya da sauri.. Ajiyan zuciya mama ta sauke tace ke nan akwai wani fitina a boye da zai taso nan gaba ki yabada lambar wayan shi mu kirashi mu fada mai abinda kika gani din. Nace nima zan so na samu lambar inje dashi don ko wani abu ka taso mun a can sai in kirashi in mai bayani. Mama ta kirashi sun gaisa yace a bani waya bayan dan wasan jika da kaka da muka taba dashi ya fara tamnayana ko nayi mafalkin nace eh tare da mashi bayanin komai dala,dala ya sauke ajiyan zuciya tare da fadin ikon Allah. To Allah ya kyauta ya tsare ya kare kuma mafalkin farko yana nufin suna da mugun manufa akan abida zaki haifa nan gaba sai kiyi taka tsatsan da su sosai lokacin haihuwar naki don akwai wani sheri da suka kula. Sai nabiyu dake da zurian dkine suke bi da sherri wanan daya tare ku shine zai taimaka maki a nan gaba akan sherin nasu. Yaushe ne tafiyan ku nace gobe yace da wuri haka nace kwanakin da akan bake nan inyi yace ba damuwa tunda bada safe kwarai zaku tafi ba ai nace eh malam. Yace to goben zan ba yarda abu akawo maki kafin ku wuce sai ki kirani a waya zan maki bayanin komai Allah ya kara tsarewa nace amin nagode muka kashe wayan. Shikan daddy ba abinda ya damay shi sai harkan shi yake dani da mamane muke kashewa muke binnewa mu kadai ba tare da yasan komai ba sai kuma ya Amina da wayanta ke kai yana kawowa akan mu. Sai da mukai waya da tsohon na danji sanyi a raina yadda ya kwantar min da hankali sai shirin ake min yayin da nake jin raina ba dadi na komawan nawa. Don bansan kuma damay zasu tare ni kuma don yanzu tsoron su nake ji sosai abin yayi yawa sosai kullun babu sasauci ga alamarin nafisa din. Abuja tun ranan da muka bar gidan ta fita ta bar yaran sun kadai a gidan har mijin ya dawo basu dawo ba ashe sunje wani kauyen kefi ne dare yai masu acan. Ranan yai mata masifs sosai yakuma sa mata kulle ance mai kishiya bata mutuwar Allah ni da ban gari amma laifina Nafisa ta gani. Wai na kai AA wurin tsafi an tsafe shi tun kan in dawo gidan dole ta mike don tasan ina can gida ina sabon shiri a kan ta da mijin ta. Da rarashi da komai taciyo kanshi ya yarda yanyala ta dawo ita kadai ta zauna dasu don kula da yara nan suka hade sukai ta binne binnen su a gidan yadda suke so. Saboda sakon da za a kawo min muka dan bata lokaci gashi sai kira yake muna ina bamu taso ba har yanzu muna may a minna har wanan lokacin. Banbi ta nasa ba sai dana karbi sakona muka kama hanyar Abuja uku da wani abu muka shigo garin da shirina na dunfari kofan ina adduoi a bakina banji fargaban komai ba na shiga gidan ba kowa a falo sai tv dake aiki shi kadai. Part dina na bude ana samun kayan da akai min tsaraba daga gida ciki Ihisan ce ta fito taga laraba ta shigo da wasu kaya ta sake ihun ganin mu shiya hankaltar da iyayyen suka san mun dawo. Dakin ta nufo tana jikina tana zuba surutu sai ga Yanyala ta shigo tana kiranta nayi mamaki kwarai da gani yanyala ta dawo gidan sai dai ban tankata ba taja yar suka fita. Mikewa nayi zuwa uwar dakina na fara tube kayan jikina sai ga Laraba ta leko tana fadin uwar dakina maza a barsu kawai kinga matar nan ashe sun dawo gidan nan kuma. Nace mayu ne basu da zuciya wace Suraj yaiwa koran wullakanci irin haka ko kofan gidan nan in nine ai ba zan kara kallo ba. Tace kin san su da bakin nacin tsiya ai in sun samu guri kamar gidan gado suka samu ta fita na mede baki ina fadin shi dai ya sani mina fuki. Kansu zai kare shida ya dauko jaraba gidan shi ya sani ana wani labewa ga asiri yanzun dai ban kara yarda da cin kashin kowa daga cikin su. Wanka nayi nayi sallah ban fito ba sai da nayi la,asar nafito falo bambarana na diba naci mai isata na saka saura a cikin fridge. Biyar daidai ya shigo part din mu da mama suka fara gaisawa yana tambagan ta ya hanya da mutanen gida. Ya juyo inda nake dan cin sauran bambaran dana rage yana fadin kun iso ashe nace eh yaya mutanen gida sunce suna gaishe ka sun gode. Bai yi magana ba sai kallo na dayake yi sai kuma ya tuntsure da dariya yace haka kika je masu da katon cikin nan kowa na kallon ki dashi. Nace ai sin san ba laifina bane don bada shi nazo nan ba da farko yana kallon abinda nake ci tare da fadin maye wanan haka kuma kike ci nace cimar mu ne na yan Niger. Ko zakaci ne in dibama na tambaye shi ina kallon shi tare da fadin ga doya can daddy yasa muzo ma dashi nace ya barshi muna dashi yace a, a. Yace nako gode ai doyan ku daban take da namu na nan tana sakwara mai kyau sosai akace nace in diba ma bambaran ne ya bata fuska tare da fadin ci abinki na gode. Ya fita naso ranan in huta amna hakan bai samu ba sai da ya saka ni in mashi sakwara da miyar egushi yace yana so dole muka daka mai shi. Zan kai mai abinci na hadu da nafisa tana saukowa saman harara ne ya raba mu yadda naga ranta a bace nasan sunyi tsiyane ta fito. Shima a haka na samay shi ban kula ba ban kuma tambaya ba shine naji yana tambayana da cewa idan mace ta dawo tafiya kafin yamma ba ita bace da girki sai idan yamma yayine lokacin amsan girki ya wuce ta iso bazatai girki ba. Nace eh haka naga anayi sai lokacin na fahinci may sukewa rigima nakuma fahinci dalilin shi na matsa muna mu taso da wurin da yake yi tun muna minna. Nace idan girkin take son yi ka barta mana tayi ba shike nan ba nasan dai ina gidan zuwan ta gida sau biyu kuma bantaba cewa zan karbi girki a ranan da ta dawo ba. Don haka na kulle a raina nasan abinda zan mata nan gaba idan tayi tafiya ai abin ba tsoro bane don taga ina daga mata kafa ne ta dauka duk asiri ne ke cina. Ranan wani munafukin soyyaya gwada min in da na dabe komai a raina nima na gwada mai nayi missing din shi. Washe gari ban fito ba har goma muna dakin muna barci wanan abin shi ya bakanta wa Nafisa rai sosai don tana falo tun bakwai tana dakon fitowan nawa. Bayan na fito ne na samay su zaune a falon na shige ina jin tana buga wani uban tsuki nace sai dai shi kan yanzu. Dakin ta nufa ta samay shi ya fito wanka gadon ta kalla na gyara shi fes kamar bamu kwanta ba tace dan dadin abu kazan mace. Anje gida an tsuma anzo maka dashi ka rude harda kaiwa karfe goma da mace cikin daki baka fito ba may kake nufi da hakan ko tafi kowa dadi ne wai. Yace baki ganewa ke wanan sirina ne kuma nakai karfe goma din kema kije ki tsuma naki idan kina son in sha daya dake. Yana magana yana nuna mata lokaci da hannun tace Samad ni kake fada ma haka akan wanan yar duniyar matar taka yace na fada maki ke may ye na shigowa ki mun wanan maganan haka. Ko ke ba a kwana dake ne wani yahanaki kai wanan lokacin ne a dakin nan kullun ke ke nan amaki ba daidai ba cikin korafi. Na dauki hakkin kine na kai mata ko ita ta saka ido akan abinda mukeyi dake ne a gidan nan barin fada maki nagaji da wanan halin naki wallahi. May na rage ki dashi na rayuwa akan wanan yarinyar ne a gidan nan kina da abinda bata dashi tayi hakuri dani ta zauna dani duk da tasan ina tauye ta din akanki. Ko finta kikayi a gurinanr wai tace tana gyada kai lalai Samad shike nan an kaika wurin dodon Nufawa sun asirice ka tunda har ka iya fada min wanan magana ko duk zaki kazane yasaka sake wanan santin. Yace ashe kin gane nasha dasin da ban taba shan irin sa ba jiya kuma ki bace min da gani dakin nan kafin ranki ya baci sororo tayi tana kallon shi yau. Don tana da tabbacin aikin da taimay ba zai iya taba daga ido ya musaya mata maganan ta ba sai gashi jiya jiya da dawowa na gida taga sauyi mai yawa a tatare dashi din. Bata iya kara magana ba juyawa tayi tafita a hasale shikuma yaci gaba da shirin sa hankali kwance tana zuwa daki ta rarumi waya tare da danna wa madam kira. Tana dauka tace ayyah madam na shiga uku wanan yarinyar ibilishiya ce ta gama min da miji kin san wai sai yanzu suka fito tun jiya da suka shiga barci nayi mai magana baki ji irin santin kaza da Samad ke min ba yau. Madam tace waya aikeki wayasa ki ki masa magana Nafisa nafa fara gajiya da wanan halin naki kema kin san idan mace tayi dan tafiya bata gida namiji dokin ta yake yi kamar tayi tafiyan shekara ne. Tace madam abin ne da ban haushi wallahi yun jiya fa sai yanzun suka sako kasa ji irin kudin da muka kai kefin nan fa duk akan shegiya ta dawo mai makon inga sauyi sai bacin rai. A bangare na na shirya mai abin karyawa wanan duk yana daga ciki huduban dana samu wurin mama Tani harda dadewa ban fito badanayi daga gurin shi din. Sai da ya gama shiri ya sauko ganin ban kawo mai abin karyawan ba yasa ya biyo part dina nan na zaunar dashi muka karya ina jan shi da dan hira ya bata lokacin shi a gurina. Yana fitowa ta wani kafe shi da ido sai gani na fito dakin dauke da case din shi a hannuna tare muka jera zuwa waje sai da motar shi ya bar gurin na juya na shiga ciki. Barci nayi sosai sai bayan sallah na fito falon gidan na zauna tare da kuna tv bayan nasa laraba ta gyara min falon don wurin kamar tunda mukai tafiya ba a gyara shi ba. Suna daya gefen zaune nace Samira ta miko min remote na canza canal nakai muna mbc 2 muna kallon fin can na rage sautin tv na danna kiran layin shi ya dauka. Hira mukayi sosai dashi duk hankalin ta na gurin mu tana ji kamar ta taso ta shake ni a furin takeji a ranta. Da gangan nayi mata haka karshe kasa zama tayi a falon ta shige ciki tare da kiran yaran ta suka barmu a gurin bamu tashi ba sai yamma muka shige part dina . ZAINAB IDRIS MAKAWA 1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Ni kaina canzawan da nayi a gidan cikin dan kwana biyun danayi da dawowa yana buurgeni don a sannu ina samun kulawa daga maigidan ta yadda ban zata ba. Ashe gaskiyar maryam da take fada min ciki bai saka rage komai gun miji sai dai ma ya kara maku farin ciki . Don ni a wautana na dauka cikin da nayi saurin samu ba zai barni inyi yadda raina zai so ba ko samun kulawan maigidan a kaina ashe abin ba haka yake ba sai yanzu da nayi amfani da nasihar mama tani dake fadin indan baan dadage ba zasu daga min nono a cikin wasa. Ba miji kulawa yana kawo shakuwa da yarda a tsakanin ku sai yanzu na kara yarda da wanan maganan don na gani a kaina. San kulawan da nake nuna mai da yawan manne mai idan muna tare yasa na fara zama kamar wata abokiyar shawaran sa. Koda ban je gurin shi ba shi da kansa zai zo part dina mu dade muna hira dashi wanda haka nasha kama su da Nafisa suna fitin akan hakan. Duk da har yanzu bawai power ta ya kare a gidan bane akwai dan shakkunta a tare dashi ban damuwa da hakan kokarin kafa kaina nake a gare shi. Yanzu ma na dawo daga rakiyar shine zai tafi office nan muka wuce su a falo zaune kamar kullun idan ina da girki hakan take miin wanda nasan ba zaman banza take a gurin ba zaman saka idone akan mu. Ina shigowa tace karuwanciin banza indai na miji ne can muka fito muma talkaman ya tsunke baan yarda na kyale ta ba najuyo nace ashe takalman naku dama tsoho ne kuka saka harda ya tsunke din. May kike nufi da maganar ki nace amsar maganar kice na baki ai dama tsohon gindn kika kawo mai wanda mazan buzaye suka gama dashi ashe shiyasa kikai saurin daukewa. Wa, iyazu billah nan naga tijara iyayyena sun sha zagi ranan a haukace ta tashi kamar zata dukeni sai tazo kusa dani kuma komay take tunawa sai ta dan ja baya. Nace kiyi naki kibar na Allah wanan kan an hade mutu ka raba takalmin kaza ba abinda zai sashi tsunkewa da kike tunane yanzu muka fara wasa dake a gidan nan. Idan kin fada min biyar sai na fada maki goma don haka shege ka fasa dani dake na shige dakina ma barta tana masifa. Karshe na fito wanka sai ga kiran shi ya shigo min yana tambayana wai may kuma ya hada mu da Nafisa ne bayan fitar shi yanzun ta kirashi tana tashin hankali. Murmushi nayi nace yaya kadai san halin matar ka magana ta fada min na bata amsa shine ya zama tashin hankali nina fita batun ta ai tunda na bata amsa ai. Deedar bakya dai ji baki fita zancen ta wai nace ai na fita nikan tunda ban tsaya kulata ba yadan gama babatin shi ya kashe wayan na kali wayan nace Waire inji yarbawa. Da yake ba abincin rana yake dawowa ci ba don haka na samu issashe barci na dakyau da rana sai bayan sallah la,asar na fito falo da laraba muka zauna. Babu kowa a falon sai baby ita kadai a kwance falon tana tsala kuka kamar in share yarinya na dai daure nace laraba ta dauko min ita. Allah sarki yarinyar tana kara girma kanta ma yana kara wani yin gingiringin dashi ga wani dan molo dayayi a gaba idan ka kalle ta sau daya bakaa son ka kara kallon ta karo na biyu. Na duba tayi kashi da amai nace laraba ta duba yanyala ta bata yarinyar ta duba babu kowa a part din yana a rufe gashi tana kuka da alama abinci take so a bata. Dole laraba ce nasa ta wanke mata kashin ta kawo min ita shiru shiru basu dawo ba nan kira AA ya shigo min muna waya yana jin kukan yarinyar. Yace sadiya ce a gurin ki nace eh yanzu na fito falo na samay ta ita kadai a kwance tana kuka mun duba part din babu kowa da alama ma yunwa take ji. Tayi kashi an wanke mata sai dai ba abincin ta a kusa yace gashi nan zuwa yanzu AA yana kokarin kula da yarinyar sosai don yafi uwar kula da ita gaskiya in dai yana gida zai dauke ta su tafi part din shi. Amma uwar da wuya kaga ta dauki sadiya a jikin ta ba a dade baa sai gashi ya shigo dauke da madaran da ake mata amfani yana zaune aka bata tasha sai barci ya dauke ta. Ajiyan zuciya ya sauke tare da kada kai yace wanan wani irin rashin imani ne haka ga Nafisa na lura sam bata son yarinyar nan tunda aka haife ta hakan nan. Take kyamkyamin ta sai wani maganan banza wai an hurhura mata yarta ne donn likita yace mata namiji zata haifa sai gashi ra haifi mace macen wai musaka acewar ta. Laraba dake gyarawa yarinyar kwanciya tace da Allah take jayaiya ke nan kuma irin yaran nan in suyi lafiya ai su ke zama wani abu wata rana. Ya mike yana fadin ina hankalin ta zaisa ta gane hakan yanzu tana can wurin bakin yawon ta mara dalili daga haka ya haura sama. Sai da ya dan jima da shiga na mike na samay shi a dakin yana kwance rigingine na karaso na zauna a gaban shi ajiyan zuciya naji ya sauke. Dan kwantawa nayi saman jikin shi tare da kokarin kawar mashi da tunanen shi wanda nasan akan Nafisa din yake yin shi nace. Bazaka koma wurin aikin ke nan ba ya sake sauke ajiyan zuciya yana dora hannun shi a saman ciki na yace banjin komawa na gama na yau sai dai gobe. Zan zauna inga dawowan wanan mara mutuncin ne nace haba zakuyi halin kuma ke nan ka kyale ta tunda kun saba da hakan. Yawon nan na fisa yakai min ko ina ko aikin gwaunati take iyakar ta ke nan kai ko aiki take ai ba zata kai haka ba dai. Ta saba ne tun farko babu hanawa a gurin ta amma da tun farko akwai dokan hakan a gidan ka bazata yi ba ai yanzu ko abin wuyan tankwarawa zai yi a furin ka. Zan ko baki mama idan ba zata iya zama gida ba sai dai mu rabu wallahi dagawa nayi daga jikin shi don jin kalamin shi da yayi nace. Haba yaya kada kai fatan rabuwa da uwar yayan ka don abin ba zai damay ka ba sai gaba idan yara sun tasa babu uwar su a cikin gidan ka nan fitinan haka ke taso wa. Ka saba hakkuri da abinka kayi hakkuri da abin ka sai dai ka zama na miji akan hakan ka nuna mata kai ke auren mu bamu ke auren ka ba ka nuna kaine maigida a gidan ka shine nake gani solution din haka. Samad amma kasan yau ba ranan girkin wanan bace da kuka shige daki da ita haka da sauri na dago saman jikin shi sai dai shi hannun shi na saman ciki na din har lokacin. Kallon ta nayi daga gani ko daki bata shiga ba dawowan ta ke nan taga motar shi tasan yana gidan ta hawo sama. Malama a koyi yin sallama idan za a shiga wuri gada kizo ki samu ba daidai ba tace gidan ku su koya min sallama din . Zama na gyara tace tashi ki fice daga dakin nan nace koke ki fice min daga dakin nan na kalli agogo kiga lokaci idan kin iya karfe nawa yanzu ko kuma kwancen girkin da kika saba zaki min yanzu kuma. Tace an ki a kalla din wai kokarin kike ki jaye mai hankali zuwa gare ki wai yarinya kin makara samad nawa ne don haka kije ki nemo mijin ki. Ke bakiji kunyar fadann maganan nan ba wai yaya Abdulsamad namu duka ne da naki ne ke kadai da baki wanan haukan da kikeyi ba don Allah ki ficewa mutane daga daki na fadi a dake. Muryan shi a dake ya daka muna tsaya yace ke kifice min nan tun ban bata maki rai ba gidan ubanwa kika fito yanzu kin bar yarinya a wullakace ita kadai a gida. Wai Nafisa anya kina da burbushin imani a zuciyar ki kuwa tace sasai ka saman naka ina kake son in fita da wanan yar haka a nuna ni a gari. Yace lalai yanzu na kara tabbatar da koke wacece na yarda baki da imani tunda har kina iya yayya da hukuncin Allah akan abinda yaso gare mu. Inajin sun kaure na mike tsam da zumar in bar masu dakin suci kansu sai naji tace duk munafukin da ya fada ma na tafi na barta sai ya rungumay ta ai dama may yarage ba ai mata ba . An riga da an shiga an fita tun tana ciki an hakakala ta sai ki karasa abinda ya rage gatanan na bar maki ita babu inda zan fita da ita a dinga nuna ni. Kin san dai inda kika shiga aka hurhura maki yarki kaikayine ya koma kan mashekiyar sa ai kowa ya dai bo da zafi bakin sa. Ki bari ki ga kema abin da zaki haifa ga cikin jikin kin ki da yardan Allah sai kin haifi wanda tafi wanan munu nace Allah ya bani sai in rugumi abina da hannu biyu watarana sai ya bani mai kyau. Zaki gani dani kike wasa a gidan nan nace inga Alherin Allah a tare dani don bakiyi kamar Allah ba ai yace wai nafisa kina da hankali kuwa ? Yar uwar zaman ki kikewa wanan fatan haka tace yar uwar zamana na ina yar uwar zaman ka ai da tai min sherin ai banga ka dauki wani mataki ba ga hakan. Yace mai tayi maki da zan dauki mata ki a kanta ko itace mai bayarwa ba Allah ba har kina ikirarin sheri da bakin ki a gaba na kuma. Wallahi duk abinda ya saman min jinina nan gaba ba zan barki akan hakan ba don ki sani tunda kiyi ikirarin haka da bakiin ki. Oh ashe da yafi dane tun dan baizo duniya ba kana ikirarin daure ni ai ban san da yafi da dadi ba sai yanzu daka nuna nace ni ba abinda zaki iya min da yardan ubangiji na don ga Allah na dogara baga wani ba. Ina fadar haka na fice na barsu a dakin nafito rai bace zuwa daki na laraba na gani na haka duk ta damu dan zama nayi da ita gurin na mikewa zuwa yin sallah ina idar da sallah ns kira mamana ina fada mata abinda tace min din. Mama tace ds yardan ubangiji lafiya zaki haihu mai albarka wanda zamu aika ita batayii kamar Allah ba duk cika baki ne irin na wanda bai san Allah ba. Kada kisa zancen ta arai ya damay ki lafiya lau zaki haihu cikin hukuncin ubangiji nace to mama tace kira kakan ki fada mai yadda kukayi kiji may zaice. Muna gama waya ba kirashi don gaskiya na tsorata da zancen nafisa don nasan shuuma ce tunda har ta furta zata iya din. Mun gaisa yana min wasan jika da kaka nace Bado akwai matsala fa yace na sani ai tunda naga kin kirani murmushi nayi nace ai da banda layin kane ban kiran ka. Yace to yaya akwai sauki dakika koma din nan ko abin yana nan har yazu nace Bado akwai sauki sosai wallahi tsakani da miji ba wanan yawan fitinan yanzu sai dai ita abokiyar zaman nawa ne. Nan dai na kora mashi halin da ake ciki naji yayi dariya tare da fadin hadizatu kin yarda Allah nace kwarai Bado yace to kisa yarda kika yarda da Allah kika kuma imani dashi ba abinda zata aiko maki ya kara galaba a kanki insha Allahu. Ki kwantar da hankalin ki kidai ci gaba da yawaita addua da yawan sadaka da kyautatawa mabukata na kasa dake in sha Allah duk abinda ta dauko a kanta zai koma idan ta mata zata ga ba daidai ba a rayuwan ta. Mukai sallama dashi na kashe wayana sai danayi isha,i na fito falo na samu laraba zaune ita kadai a cikin damuwa nace mama anan zaune ne ? Tace to uwar dakina banda zaman bamu da wani aikin yi sai kallo ba kamar can da yan aiyukan wata rana har suka fi karfina bane. Zama nayi nace an karbo kayan guga wuri mai wankin nan tace an karbo sai dai yazo min da wani zance wai an yagi zanin ki ta kasa jiya ba haka ya wanke shi ba. Nace ikon Allah wata sabuwa ke nan kuma zani na may zasuyi dashi kuma tace sheri mana yar nan ai haka masu bakar bidan asiri suke da yawan surkulen su. Yanzu wani katon mushirinkin bokan ne nasan ya bukaci a kawo mai yankin zanin ki nace wallahi mama haka aka taba min kafin ki zo garin nan ban fada ma kowa ba sai maryam dana nuna kayan. Sai tace injin dai baki saka kayan ba nace wallahi na saka tace ashe idan har Allah ya nuna ma sheri ka gani ga idon ka ai sai kayi taka tsamtsam kinga kwanaki kafin muje garin nan naku. Nace tace Yanyala na samu tana kakabe carpet din kofan nan tana tara kasan a zata zuba a cikin wani leda sai gani munyi rikici sosai da ita ban fada maki bane don gudun fitina bakiga na dauke carpet din a wurin ba. Nace ikon Allah wai duk akan in bar gidan suke wanan abin haka tace ko ki nakasa ba ba sherin da yan bakar bida basu iyawa yar uwanzaman su ba ai Allah dai ya tsare ya kare nace Amin. Mama dauko zanin da aka yanka din mu gani nace wa laraba ta mike taje daukowa sai ga AA ya shigo dakin yana fada min wai Abba ya daga bukin zainab sai gaba. Da sauri nace mai subbahanallahi yace eh dalilin da ya bayar yana da kyau kin san ta kusa kara karatun yace idan ta karasa sai ayi ya wuto da ita nan gaba daya. Nace Allah yasa haka yafi zama alheri ai ni abin zai mun dadi gashi an fara fadin dama ba zan tafi yanzu yai min daidai ke nan. Ni dai ban san abinda yasa yayana Yusuf ya daina zuwa gidan nan ba yanzu na tambaye shi kallo na yayi zaiyi magana. Laraba ce ta shigo dauke da kayan a hannun ta ina gani na manta yana gurin nace wanan sabon kayane fa mama sai ya juya yana kallo. May ya faru yace nace nakai wanki ne yanzu mai wanki ya aiko min wai yazo guga ya samu an yankar min zani na da mamaki yace yankar zani kuma may za a yi dashi idan an yan ka din. Laraba bata san sanda ta bashi amsa ba da fadin asiri mana Alhaji yace ta miko mai zanin tana mika mai tare da nuna mai gurin da aka yanka din. Fita yayi da zanin a hannun shi laraba ta fice part din yana fita tana zaune falo yace Nafisa waya yankawa Deedar zanin ta gidan nan. Tace wanan ai tambayan banza ne zaka zo ka sani a gaba kana tambayana wa ya yankawa matar ka zanin ta kafin yai magana Ihisan tace Ami ne Abbi tare da Yanyala muka je da Ami ta tsare yanyala ta yanka da suka aiki mai wanki. Dawo da kallon shi yayi gurin Nafisa din yace kin gani yarki ta fadi gaskiya zaki lalata min ya da bakar bidan asirin ko har da ita kike zuwa. Ihisan kamar mai wasa tace Abbi an kai wa wanan mutumin da baida riga har ya shafa min wani abu a jikina jikake dim dim uwar takai ma yarinyar duka sai da ta kife kasa daga saman kujeran. Yana karasowa shima ya dauke ta da mari kauuu sai data duka ya tallabo yarinyar yana rarashin ta yaja hannun ta suka nufi part din shi. A gaban laraba akai komai tana labarta min abinda ya faru nace Allah ke nan dayake ban da amanan ta ya fitar min da hakki na Allah ya gani ina matukar son kayan nan. Ban ji duriya shi ba haka yasa na fahinci yana cikin bacin rai sai da safe ya shigo part dina yana fadin shi zai fita nawa zanin yake ya biyani nace ka barshi tunda ina da wasu dama cikin wanda ka saya min na lefe ne na dinka shi. Kudi ya fito dashi koda ban kalla ba nasan kudin yana da yawa yace gashi in za a samu irin sa a nan sai ki saya a kara dinka maki kalarsa. Nace daka barshi ai don ba yau suka fara min haka ba a gidan nan karo na biyu ke nan wallahi yace ga Ihisan ta fadi yadda sukayi wani gardama zatai min kuma. Har fa da yata suka tafi gurin shirkan su aka shafa mata wani abu bayan bokan yai mata tsirara wai da ita da Samira duk jiya ihisan din ke fada min. Allah ya kyauta shine kallama ga sherin ta ko yanzu din shina kara maimaitawa a bakina ya fice nace monday zamu koma school fa. Ya juyo yana fadin monday din nan mai zuwa nace insha Allah sai yai dan shiru yaja tsuki tare da fadin Allah ya kaimu nace Amin komawan kakewa tsuki kuma ? Yace No naso kafin ki koma motocin mu sunzo ne don akwai naki a ciki ban son wanan toiries din gare ki kwanaki naba da sako sai ba a samo wanda nake so ba. Nace ai ba komai tunda ana kaini ba wani matsala bane duk lokacin da suka shigo sai a bani yace shike nan . Sai ki min list din abinda ake bukata mu gani kafin monday din in baki daga haka yasa kai ya fita a dawo lafiya nayi masa daga gurin da nake zaune din. Kudin da ya aje min na dauka na kirga sai da nayi mamaki tare da fadi a raina wanan kudin har da toshin baki dai kada naja zancen da nisa watau. Ina adana kudin maryam na shigowa gidan sai da ta kalle ni ta tuntsire da dariya tace wanan ciki ya kara maidake wata babba mace haka. Nace da ba babban nake ba may nake tace ai na manta tana kaiwa zaune tace yau banga buzuwar gidan ku falo ba don haka take zama kullun kamar mai gadi. Yau Allah ya tona mata asirine ai nan dai na kwashe maganan na fada mata tace muguwa Allah yaki aniyar yar iska da Allah kadai yasan sherin da zasuyi dashi. Nace wallahi shiya ban saka yaran nan a cikin zancen mu da ace ina masu mugun hali a rayuwan su bazasuga ana cuta min suyi magana ba tace wallahi da ba,a jin komai haka don koyo zasuyi suma yau da gobe bai bar komai ba ai. Nace bata da kunya ai don wanan ba shine farko tsura ta ba kin manta zacen layun da aka gani cikin filo daya kirata cewa tayi sheri ake son mata dai. Maryam tace shi wanan din ma sheri ne yar nata ta fada ai tayiwa kanta don idan tasan kunya taji shi muna cikin zancen laraba ta shigo tana fadin ga gugumanmun nan su shigo da sauri muke tambayan ta tace tace magajiya ko madam ake ce mata. Dariya muka kwashe dashi nace kai mama kin iya sawa mutum suna wallahi maryam tace ai magajiyar ce kin sani ko har kauce hanya anayi wanan irin abu nasu haka. Nice na kawar da zacen da jefo da maganan komawan mu makaranta tace wallahi na dauka kafin mu koma kin haihu nace haba dai yanzu fa nake a takwas. Tace ni dai rokona kada ki haihu muna exam don wanan karon ba wani dadewa zamuyi ba sosai nace to gani nan dai ni san abin zaizo min ne a rikice wallahi. Kana naka Allah na nasa ne ban taba daukan haka a gare ni ba wallahi maryam tace ai haka abin yake muna cikin hira mukaji ihun Ihisah kamar ancire mata rai. Zan daga maryam taja tsuki tana fadin ina kuma zaki don baki da zuciya ta kashe ta mana ba ita ta haifi abinta ba ki kyalesu su kashe ta in sun isa sai can muka tsinkayi muryan namiji yana fada nace yadawo ne gidan. Mama laraba tace kamar muryan Soja nake ji maryam tace shine ma don munyi waya yace min yana hanya zai shigo kallon ta nayi da mamaki nace maryam yaushe kuka dinke dashi kuma ban sani ba. Tace kece zaune ai tun yaushe muke tare tun wannan ranan daya rage min hanya fa ai da badon Allah ya gyara ya kawo sojan ku da kila mun samu matsala dake don saura kiris kijini ana min guda. Kallon ta nayi da mamaki nace wa ke din tace wallahi saboda ke nayi ta daga ma zancen kafa don ban san yadda zasu dauke ki ba idan zancen ya fasu anji. Wa da zaki aure na tambaya cikin tsure ta da ido tace yayan ki mana Yusuf sai da naji gabana ya fadi nace ina zuwa daki na shiga na kewaya na fito. Tana kwance saman digon kujeran falon nace maryam wai wani Yusuf dai kike nufi tace kina son kara kewayawan ke nan Yusuf dai da kika sani mana. Na dafe kirji tare da fadin haba biri yayi kama da mutum ashe shiyasa zainab ke min hannun ka mai sanda tace ai bata san ko wacece ba don ko AA bai bari ya sani ba. Maryam da kin daure ni wallahi dakin sakani tsaka mai wuya a tsakanin ku da barin gidan nan zanyi tace don may saboda kawai na auri mijin sister inlaw din ki zaki bar gida. Nace ai idan nayi rantsuwa dubu bazan fita ba sai suce dani aka kulla zancen tace dasun dauki alhakin ki wallahi yanzun haka muna rikici dashi ne ai. Wai wallahi nayi kadan na fada mai ai ko rikici suraj ya fishi shima kwakwan da yake kenan yasan ko waye aka saka muna rana a kd din. Nace wallahi baki da kirki maryam harda saka rana ban sani ba tace yes don bamu son ki sani ki bata muna zance ba nace to Allah ya sani ai. Tace yanzun haka yazo ne mu tsayar da magana a sa mai lokaci wai baison ya zauna nan ba mata nace zaki iya da yaran hajiya umma kuwa ? Tace da ita zan zauna bafa gari daya zamu zauna ba waike baki murnan zamuyi aure a gida daya dake ne ina ruwa na da wata umma can. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Monday da muka shiga makaran ta da kyat na samu zuwa don yanayin da nake jin kaina ranan dai a dadafe nayi komai daya kaini. Asibiti na wuce sun dubanu suka ce wai juyawa ne yasa nake jin haka ko wani month din zai juya sai mace ta dan ji jiki magani pain killer suka bani muka dawo maryam ce ta raka ni. Two ina gida ruwa na watsa a jikina nayi sallah na kwanta can cikin barci nake jin laraba na kirana sama sama na bude idona. Tace baki kike dasu a falo da kyat na tashi sai dana dan jima a zaune na mike zuwa falon mata ne da ban san su ba su biyu zaune. Tun kan na zauna nace laraba kawo masu abin sha mana na juyo ina masu sannu da zuwa ina kaiwa zaune. Gaida su na fara suna amsawa laraba ta kawo masu drinks din kwali da cups ta aje a gaban su matar tace sun gode. Ai da kin barshi muzo maki godiya ne dama maigidana ne ya turo ni ai mai godiya a wurin ki nasan baki san mu ba ko ? Nace wallahi ban sheda ku ba tace matar SJ jalingo ce da sauri na dago kai ina kallon ta nace ayya ban san ku bane na fara gaida ita tare da tambaya ya gida. Tace yaso muzo tare dashi yai maki godiya kan alherin da kukai mai keda maigida shine ya fara turo mu. Nace ai babu komai idan wanan ne ai don yaya Adam akayi tunda ba sanin ku nayi ba sai dai mun sha rigima yace a nan kuka biyo mai kuma. Matar tace ya fada muna ranan da mukaje office din shi yace abinda mukai mai baiji dadin shi ba ai ko wurin Adam muka bi zai muna din. Murmushi nayi nace haka yake shi nace hajiya baku sha ruwan ba tace no ki barshi a koshe muke nace haba ko kun raina ne da sauri tace haba dai. Wallahi tun dazun muka so zuwa sai wanda yasan gidan zai kawo mu ya dan bata muna lokaci nace Allah sarki ba komai hajiya ai ba sai kunzo ba. Don yanzu mun zama daya daku tace hakane ashe cikine dake haka nayi murmushi tace Allah ya raba lafiya wace suke tare ne ta karba da Amin. A raina na amsa mata tace a, a kina kunya irin namu na fulani ne sai dayan da batai magana ba tace nima zubinta yai min na fulani tunda muka shigo. Nace mu fulani ne asalin mu sai dai bama jin fulanci ne tace haba kinyi kama da fulani sosai wallahi suka mike tana fadin ana jiran mu a waje ga wanan maigida yace a kawo maki. Da sauri na kada kai nace a, a wallahi hajiya bazan karbi ko kwandalan ku ba don Allah nayi maku Allah yasa a more . Da mamaki ta tsaya tana kallo na tace haba dai kanwata idan kinyi haka ba zamuji dadi ba ai nace wallahi hajiya bazan karba ba tace to shike nan ban layin ki don in kin haihu muji muzo barka. Na karanto mata layin nawa tasa a wayan ta har wajen gida na raka su motar shigan su kawai ma abin kallo ne daidai nan nafisa ta danno gidan da motar ta idon ta a kan baki na. Ta fito ta shige da yaran ta ina tsaye matar tace wanan fa kardai ince kishiyar ki ce don mun taba hadewa a gurin wani buki da ita. Murmushi nayi nace kishiyatace hajiya ta kada kai kawai tace bari zamuyi waya tunda ina da layin ki don kin min sosai wallahi. Nace na gode suka ja motar su suka tafi na shigo cikin gidan Ihisan ta sheko ta rike ni nace ihisan kun dawo ya school tace cikin shirmay yara uncle din mu yace ban iya karatu ba zata fara zuba sai ga uwar ta fito. Wani tsawa ta daka ma yar tace maza ta bar gurin ta shiga sake yare nan na fahinci tana koyawa yaran yaren su. Ta juya da hausa tana fadin idan ba mutum ya haifar min yaraba ya barnmin abina mana wanan wani irin bakin naci ne haka. Nace kinga kafana agun yar ki sai dai su biyo ni idan kuma sun zo bazan koresu ba don ni ba irin ki bace mara hankali don ni banda lokacin ki yanzu. Na shige na barta awurin kalamin ta yasani tsayawa cak tace munga ciki sau ra muga haihuwan shi kuma in don shi kike taka kowa yarda kika ga dama. Najuyo nace ke jahila ce ta karshe wallahi mai jayayya da ikon Allah ni bazan biye maki ba mu koma daidai don haukanki yafi karfi na na rufo kofan part dina na barta nan. Maganganun ta suna matukar ci mun rai sosai wallahi wanan ko haihuwar nayi gidan nan yaya yaran nawa zasu taso a cikin wanan rayuwan gida kullun fitina haka. Duk da anty hauwa tace in yi kokari in haihu a cikin gidan nan ammani ina jiyo ma kaina abinda kaje ya dawo ne idan na haihu a cikin wa yan nan kurayen dake farauta na haka. Zan mai magana ya barni in koma gida ko kaduna da zaran month dina ya kama wata zuciya tace min karatun ki fa. Ajiyan zuciya na sauke nace kuma dai dole fa inyi hakkuri da wanan karatun in sama ma kaina lafiya a gidan nan tukun zai fi in da hali ni kan ya canza min gida ma da yafi. Ranan da nayi girki ina son mashi maganan kaini gida sai gashi ya rigani fadin gobe zamu Niger da Nafisa babanta baida lafiya. Cak na tsaya ina fadin goben nan yaya yace eh in Allah ya kaimu sai dai a can zan barsu in dawo sai tayi kwanaki ta gama ganin su ita zata dawo. Antan cikina ne ya kada sai da naji abincikina yana juya min lokaci guda don mamaki abinda ya fada min. Dama haka maza suke munafukai ne wai ni naje gida bai kaini ba sai driver yasa ya kaini ya dauko ni. Lalai na miji ba dan goyo bane ba a kuma bashi amana ni ke nan iyayyena basu kai yaje ya gaida su ba ke nan har ya kare bayanin shi ban kara fahintar may yake fada min ba . Ya lura da sauyawa na amma sai ya dake kamar wanda bai fahinci wani abu ba daga gare ni a dadafe naga gari ya waye min na fice daga dakin. Bai kulani ba ya gama shiri ina jin hayaniyar su ya gaure gidan na shige na dakina can sai gashi ya shigo ina kwance a kuryana. Yasha wani shadda sai maiko take zubawa duk da shi ba gwanin saka kaya hausawa bane sai kayan sukai matukar karban jikin shi sosai . Amma ni sai kyau di ya koma min duhu a idona ya karaso inda nake ya samu bakin gado ya zauna. Mamaki yake yadda tunda yayi sallama ban karba mai ba gashi na nuna ma ban san shigowan shi ba dakin. Muryan shi naji yana fadi bakyajin dadi ko yau ba zaki shiga school bane na ganki a kwance haka shiru nayi mai ya kara tambaya bakya jin dadi ne wai Deedar. Nace lafiyata kalau yace ki fada min mana udan bakyajin dadin jikin ki ne a kaiki asibiti nace idan ma banjin dadi ne ai wanan ni ya shafa ko ba kai ba. Yace may kuma yakawo wanan magana haka nace don Allah malam kaje kaji da abinda ke gaban ka ka barni in ji da nawa zancen matar ka shine a gaban ka ni da ban da galihu a gurin ka ai ban samu wanan gatan ba. Ko asibiti sai idan nakai kaina don jin lafiya ta baka damu da ka san lalurana ba sam a gidan nan ajiyan zuciya ya sauke tare da fadin. Duk akan tafiyan da zanyi da Nafisa ne kike fada min haka nace Allah dai yakai lafiya umma ta gaida assha na mike na shige ban daki na barshi a gurin. Ya dade zaune gurin yana jijina magana a ranshi kafin ya mike ya nufi kofan ban daki ya murda yaji shi a rufe gam ina daga ciki ina jiyo muryan shi yana fadin. Deedar ki fito muyi magana na fahinta dake shiru ban bude kofan ba har yagaji da jira ya fita danaji shiru na bude daki na fito gidan ms tsit a laman sun tafi ke nan. Ina tsaye ina sa kaya a jikina kiran wayan shi ya shigo min ban daga ba har kiran ya katse ya sake kira karo na biyu hakana kyale wayan ya tsuke. Nagama shiri na fito na samu driver a waje wai yana jirana nace ayya ka huta abinka zanbi kawata ne ta sauke mu sai ga maryam ta iso ta bude min na shiga. Kallona take yi tare da kallon titi wai may ke damun ki ne khady yau na ganki kinyi wani so weak dake mana haka ina AA yake bai saukeki ba kuma ? Ban kalle ta ba na bata amsa da fadin ya tafi Niger da Nafisa yau da safen nan da sauri ta juyo tace Ni may khady don Allah ki bar wanan wasan . Nace wallahi maryam yau da safen nan suka tafi tace amma dai maza shegu ne wallahi yanzu shi baiji kunya yin hakan ba khady. Nace kunyar may zaiji ba matar shi bace ni don yaje garin su ba shine damuwa ba banbancin da yake nunamin a filin Allah maryam shine ya fara isata wallahi. Ki duba ni da naje gida maryam ba shi ya kaini ba bai kuma je dauko ni yanzun ma bai fada min zancen tafiyan ba sai jiya da daddare yake fada min. Tace ya fada maki yasan bai shuka gaskiya ba ta yaya zai fito maki da zancen da wuri ki tayar mai da hankali ya fasa. Koda yake itama baki san irin kwaram din da suka sha da ita ma kafin suyi tafiyan ki kyalesu su suka sani indai sune ko acan sai sun sayar da hali ai. Nifa tafiyan bai damay ni ba maryam sai dai ni da yake nuna mata ba kowa bace a gare shi nan dai na kora mata yadda akayi muna shiga school tace kyale shi kada ki daga sai kin ja masa rai sosai. Mun shiga lectures bacin rai bai barni nayi abin kwarai ba ranan da kyat naga mun taso ta dauko ni ta kawo gida. Gidan naga yai min mu kadai dagani sai laraba kadai a gidan da dare ma na samu ya kira ni bandaga wayan ba karshe ma kashe wayan na kwanta abina. Kwana uku ban bude waya ba ina amfani da waya ta tada da layin dabai sani ba maryam na sauke ni motar Yusuf tana shawo kwanan gidan. Tsayawa mukayi muna dakon zuwan shi gaidashi mukayi ina fadin haba yayana ka manta da kanwan ka gaba daya. Yace ba hakana bane khadija aiyuka ne sukai muna yawa ban kuma samun zama yanzu sosai nace Allah sarki maryam tayi min horn tace zata wuce nace sai gobe. Hararan ta yayi yace kece mai daurewa karya gindi ko kin hanata bin umurnin mijin ta tana biye maki ko ? Nace haba yayana maryam bata da laifi binta shine sauki a gare ni tunda wanda nake nan don shi baisan muhinmaci na ba. Yace a, a kanwata kada kice haka don Allah don ba haka zancen yake ba gaskiya daga cikin mota maryam tace baku da gaskiya wallahi. Ke rufa muna baki don Allah tsigar da yake magana da ita na fahinci wani abu yace yanzu khadija ya dace ace mijin ki yayi tafiya baki kirashi kinji saukarshi ba har wanan lokacin. Ai ba tafiyana yayi ba yayana tafiyar matar sa yayi kuma suna tare kiran mai zan mai kumani yanzu Allah dai ya dawo dasu lafiya maryam tace shike nan kuwa. Yace ki daina bin zancen wanan mara gaskiyan zata kaiki ta baro wallahi nace yayana maryam din ne kuma yau zatakaini ta baro ? Yace kin ga mubar zancen nan muyi na gaskiya don wallahi baki kyauta ba khadija mahaifin Nafisa ne bai da lafiya suka je gaida shi. Daga cikin motar ta kara fadin shikenan kuwa ke dan Allah barnan ai surikin kine zan fada mai kece mai zuga mai mata tace rufa min asiri tana kokarin jan motar ta ta bar gurin. Yace tsaya ai magana ta fahinta ai abokin kuka ba a boye mai damuwa abinda kikayi ai ba daidai bane khadija dayakiraki ai sai ki dauki wayan kiji korafin shi ko. Amma yana can kin saka shi a damuwa gashi kin ki daukan waya ga kuma kinki bari driver ya kaiki school gaki a cikin yanayi. Nace ai yanayin nawa bai gaban shi nice da kaya ni ya dama ya kada kai yace ba hakana bane khadija ku na ma maza fahinta baibai wani lokaci. Lalurar ciwo ya kawar da komai yanzun haka sai da yaje ne suka kai tsohon asibiti duk wanan ciwon ba wanda ya kaisa asibiti ashe. Nace eh hakan yana da kyau sosai yanzu dai barin in kirashi kuyi magana yaji lafiyar ki don Allah ko hankali shi zai kwanta. Nace akwance hankalin shi yake tunda yana tare da farin cikn shi ai basai yaji tawa ba baza ki min ba ke nan sai naja na tsaya daga cikin mota maryam tace ki saurare shi kiji may zaice din. Bashi ke nan ba baidai wuce dadin bakin su na maza zai maki tunda kina sokuwa sai ki yarda Yusuf yace khadija ki saurare ni nan kiji may zan fada maki. Wallahi wallahi duk mu nan musan AA yana son ki shuumancin matar shi kawai ke damun ku khadija kin yi hakuri a gidan nan kowa ya sani kuma kina kan yi . Kinyi abinda bako wace mace zata daure mayin sa ba saura kiris ya rage khadija buzuwa takai karshen ta a gidan nan. Yanzun dai ga wayan saura bayani zan maki idan kun gama wayan yana kira ya miko min na karba muryan shine yake sallama na amsa. Yace kuna lafiya nace kalau yusuf ya zagaya gurin maryam ya barni a gurin muna wayan ba wani magana mai tsawo mukayi ba ya tambayi lafiya tace da dalilin da yasa na ki daukan waya nace ba komai sai anjima na kashe wayan nace wa Yusuf dake duke ga wayar shi ya karba yana fadin har kun gaisa nace eh nagode. Yace ki kara hakkuri aimu ko hanzu bukatan mu ya biya khadija kin shigo gaki har da cikin a gidan nan. Wanda ba wanda yai tsamanin hakan a gidan nan haihuwan ki gidan nan shine babban masifan dake addaban Nafisa a yanzu don nike jin irin wayan da sukeyi dashi idan muna tare. Don haka don Allah ki kara daurewa khadija ansan abinda zafi nima na nuna mashi abinda yayi bai kyauta ba yakawo min uzurin rashin lafiyan tsohon na yarda. Haka dai muka dan dauki lokaci dasu a gurin karshe mukai sallama suka tafi na shigo ciki na samu laraba a babban falon gidan gana kallo. Nan na zube falin muna dan taba hira tace ta kawo min abinci ne nace ta kawo min amma kadan na mike ina fadin bari mu shiga ciki dayani in rage kayan jikina. Sai da na watsa ruwa na fito falon na samu ta aje min kulan abinci na zauna naci muna gurin akai sallah a nan nayi sallah tara muka shige daki. Cikin dare na falka da tunanen mafalkin da nayi a gidan maganan tsoho bado ne ya fado min a raina tashi nayi na gabatar da nafila ban kwanta ba sai da aka kira sallah bayan na sallamay na fito ina kiran laraba tafito a dan gigice tana fadin lafiya uwar dakina ko jikin ne. Zama nayi ina fadin mama wani malki nayi a gidan nan jiya yau yakai kwana uku a gurin mugudanan ruwan dakin maigidan nan ko dai akwai wani abune da aka boye a gurin nan mama ? Tace bazance a a ba don kin san wani lokaci mafalki na zama gaskiyane tunda idan mutum nada tsarin mutanen a kanshi zasu iya nuna mai haka ko kuma Allah da nasa ikon idan zai yake ma mutum wahala sai ta baiyana maka abu ta inda baka zata ba. Nace yanzun yaya ke nan tace idan kina gane wurin muje mana zan ma mai gadi magana tunda muna shiri dasu sai mu tona mu gani tunda mu kadai ne a gidan. Tunda safen nan muka fita zuwa baya tare da dayan maigadin dataiwa magana naga kokarin mutumin nan daya iya tona wurin baiji kazantaba sai gashi ya ciro wani kwallaba dake da layu da yawa a cikin sa. Mamakine ya kama mu sosai jikina har rawa yakeyi yace zai tafi da kwalban a bincika masa ko na maye a ciki muna shiga falon akwai wani carpet wuri hawa step din saman AA nan ma nace wa laraba ban yarda da gurin ba. Ta sake kiran maigadin ya shigo suka daga yace akwai rami bayan daken din ya tona saida naji tsoro nan ma wani abune an cacaka mai allurai sunfi a kirga aka bine. Maigadin yace wanan matar takai shuuma wallahi sai ya cire abu har gurin kofan ta ya fita dashi gidan haka na wuni sukuku a gidan. Sai AA ya kwashe kwana shidda a Niger bai dawo ba ya kama jumma tunda maryam ta sauke ni na shiga gida tace zata shigo da dare ta kawo min sako dana bata tazo mun dade muna hira ta wuce. Washe gari har mun rufe gida akai ta bugawa muka bude AA ne ya dawo a cikin dare nidai ina dakin ban fito ba sai gashi ya shigo ba laifi nayi mai sannu da zuwa da tambayan mai jiki. Yace da sauki tare da tambayana lafiya ta nace Alhamdullahi haka muke zaune a gidan ba wani sakin fuska a tare dani sai wani rawan kai da yake min ban kula ba don nasan don matar bata nan ne. Sai da ta share sati biyu ta dawo da yamma ina jin hayaniyar su nasan ta dawo ke nan sai ga ihisan ta shigo min har part dina. Ban fita taron ta ba tunda da zasu tafi bata sallamay ni ba ita ma na gama abinci na kai mai muna zaune sai gata ta shigo part din shi da kayan dake jikinta data dawo dashi wani shadda ne blue yasha aiki da zare yellow. Abinci yake ci ina zaune a gefen shi ina game da waya na ta shigo ta samu wuri ta zauna can naji tace ke ban dago ba don kiran rainin da tayi min ta sake fadin dake nake magana fa. Nace ki je gun yaysn da kika haifa ki magana dasu hakana ba dai ni khadija ba tace kin san abinda kika yi ai nace ko da ban sani ba na sani din don nasan ba alheri bane ya kawo ki nan yanzu. Tace amma dai kin san na dawo yau ko may zaisa ki kawo masa abincin ki kuma nace kin duba lokacin da kika dawo ko ko tsoron ki zanji in canza lokaci in bar maki shi. Table din ta buga da hannu ta saida kayan sama suka girgiza tace wallahi kinyi kadan ke baki isa ba wallahi nace isar ke nan kikaga haka ke wacece da za a ji tsoron ki wai. Ya dago rai bace yace mata Nafisa bar nan tun kan na bata maki rai ina mun gama wana maganan tun dazu tace wallahi ba zata bari ba don ita zatai girki tunda ta dawo yau. Yace sai kiyi mu gani tunda jidali kika dawo dashi ke wata irin mace ce da bata da godiyan Allah kwana nawa ina can tare dake bata bata ranta ba kan haka yanzun ma kin dawo din ba zaki bari a zauna lafiya ba . Nidai ban sake kula ta ba nan suka gama sa insa din su har ta gaji ta fice tunda na kwanta ban motasa ba shima bai nemay ni ba nasan yana cike da bacin rai ne. Tunda na koma part dina banjin dadi don haka na samu guri na kwanta can cikin barcin da na dan samu ya dauke ni naji mara na ya yanka min. Tun ina ji kamar mafalki nake har yakai na bude idona na dan saurare sai ya dan lafa min na sake rufe idona sai kuma ya dan kara cunkula na na bude ido ciwo sosai yake min dabaran kiran maryam nayi a waya . Sai dai wayan ta yana busy naja tsuki na wurgar da wayan ga maran yana addabata da ciwo irin wanda ban taba jin sa ba. A hankali na mike zaune daidai lokacin da naji ya lafa min din na sauko na nufi falo in duba laraba na samu laraba din ta fita bata nan cikin part din kitchen na nufa don in duba kanwa na daiga kanwar najika na nufo falo sai naji kafata ya rike min lokacin laraba ta shigo dauke da kayan wanki a hannun ta . Tana ganina tace subbahanallahi uwar dakina lafiya dai ko nace mama marata ke min ciwo yanzun kuma kafata ya rike min sosai ban iya dagawa. Tace ubangiji ya sauke ki lafiya ko in fada ma Alhaji don na barshi a waje yanzu kaina girgiza mata na samu kafan ya sake min na karaso gurin kujera na zauna cikin karfin hali. Na dauki kanwar nasha ina aje cup din yana shigowa falon kallon yanayina yayi ya fahinci banjin dadi yace lafiya kike kuwa Deedar ga AC kuma kina zufa haka. Na goge zufan cikin karfin hali nace haka na yake min kwanan nan cikin ya kara murda min na nade wuri daya yace nace baki da lafiya ko muje asibitii ne na girgiza kai nace ba komai ai zai bari. Yadan dade tsaye a kaina yana kallona ya juya fita daga dakin da kyar na samu na daga zuwa dakina laraba tana tsaye ta kallona har na shige maryam na samu tana kirana da kyar na daga wayan nace maryam kizo da saurin don Allah cikin wani irin murya mai ban tausyi. Tace haihuwa ne ko may khady nace nima ban sani ba ki dai zo don Allah tace gata zuwa yanzu ta kashe wayan. Ya lafa min ya taso ba a dauki lokaci ba sai ga maryam ta shigo ta samay ni ina yarfar da hannu ta iso gurin a rude tana fadin haihuwar ne khady ban sani ba maryam ko shine yazo wani irin ciwon mara dai nake ji maryam. Can ya yanka min nace wayo maryam zan mutu wallahi ta rude tace barin in kira mama kila tasan haihuwa ita laraba na shigowa dakin tana kallon yanayina tace wanan kan haihuwa ne sai dai kila da sauran lokaci. Waya maryam ta dauka tra kira anty Hauwa tai mata bayani tace bari ta turo sister Larai ta dubani ba ajima ba aka kira maryam ta dauki waya sai ta fita. Tare suka shigo da matar da aka kira da sister larai din tana zuwa tace in kwanta ta dubani tana dubawa tace haihuwa ne yazo sosai a dan ban tea ko kunu in sha don ba a so nakuda da yunwa. Da sauri laraba ta hado min tea mai zafi ta kawo na karba na sha da kyat do ni ba gwanan shan tea bace na sha na dire cup din kasa ina kallo sister din ta gyara guri a dakin leda ta shinfida sabo da ta bare shi a gaban mu. Tace su dan fita daga falo su jira mu ta hada allurai tayi min cikin ikon Allah tana min alluran kamar ta jawo nakudan kusa ne na koma ba zama ba tsayi. Maryam ta kira tana tambayan ta akwai leda a kusa yadda maryam taga ina cije baki itama ta fara kamar mai nakudan tace don Allah fita wanan rakin ki har yafi na mai nakudan gaskiya ai. Da ya wani taso min tace kwanta kwata da sauri da taimakon ta na nisa da karfi tana kiran oya push pushi niko Allah nake kira a bakina. AA yana shigowa falon don ya dubani a yarda ya barni kuka yaro yana gauraye falon yaja ya tsaya yana kallon maryam data rude sai kuma ya nufi kuryan dakin ya daga labulen dakin . Don ya tabbatar maryam na fadin Alhamdullahi ta haihu ta hau murna laraba ma sai hamdala take zubawa a gurin da mamaki ya sake labulen dakin yana fadin dama haihuwa zatayi ne mama tace eh Alhaji. Haihuwar ce tazo da sauki wallahi kiran ds ka kwala wa maryam daga ciki ta shigo da sauri dakin tace karbi yaron miko min wani zani again jikins rawq ta bude wardrobe dina ta dauko zani. Tana mika wa ta fito yana tsaye ya kasa zama a dakin ta mikawa laraba yaron mai matukar kama da uban sa sai dai shi farine sol yafi uban fari. Mikewa yayi da sauri ya karaso wurin laraba kamar zai karbi yaron Laraba tace bari a goge shi Alhaji. Yace to to mama ikon Allah haka abin yazo da sauki kuma ikon Allah sai hamdala yake zubawa ban dauki lokaci ba macen ta fito sai kuka take zuba har yafi na namijin kamar yai tsuntsuwa ya fada dakin yace wani again ? Kafin wani lokaci matar da yake aikin su ne ta saba ta ta gyara yarinyar ta aza saman gado ta kwala wa maryam kira ta shigo tace dauki baby girl din ki bamu wuri. AA kan kasa hakkuri yayi sai da ya karbi yaran tun ba ai masu wanka ba yai masu addu a ya fito ya bari ana gyara muna jiki. Direct wurin Nafisa ya nufa yana washe baki yace ki min murna mata na ta haihu yanzu tace may kace yace nace Khadija ta haihu yanzu ta zabura ta mike tsaye tare da fadin ina yace a dakin ta mana. Kana gidan nan ta haihu Samad yace yanzun na shiga in dubata na samu ta haihu tace nashigs uku ya zaro ido yace haihuwan kika shiga uku ko may ? Hannun ta yana saman kirjin ta tace ka barni don Allah da abinda ya samay ni a gidan nan can kuma tace may aka samu yace mace da namiji ta zube saman kujera kamar ba kashi a jikin ta jagwab ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Daga inda yake tsaye a gurin ya buga ma mommy waya yana sanar da ita zancen haihuwan sai yusuf da ya kira tare da kiran mahaifana ya sheda masu. Tana zaune ta zuba mai ido tana sauraren abinda yake fadi a cikin murna tun tana sheda shi har ta dinga ganin ya koma mata wani abin,ki a zuciyar ta. Jirin da take jine yasata dafe kanta da hannun ta daya sai rintse idanuwanta da tayi tana jin shi sama sama yana farin ciki. Fitowan laraba part dina yasa ta bude ido ta sauke kanta tana fatan raba tace ai yaran sun mutu ko sai taji laraba na fadin Alhaji matar data karbi haihu tana bukatan ganin ka. Yana cikin fara,a yake fadin to, to mama gani nan zuwa ya dakatar da wayan da yakeyi suna zaune tare da bakin da tazo dasu sai yanyala da itama hankalin ta a tashe yake wurin. Yana barin gurin ta kalli yan uwan nata a cikin yare take magana rai bace tana fadin shike nan ta kara min asiraina dana binne a gidan nan . Dayar tace asiri kika birni Addah tunawa da wace take maganar ko wacece ta ja tsuki tayi daki yanyala ta mike ta bi bayan ta zuwa dakin. Samun ta tayi tana safa da marwa a tsakiyar dakin tare da dan bubuga dundun hannuta wani saman wani tana jin motsiyan yanyala ta juya da sauri tana kallon kofan. Yanyala wanan yarinyar ta gama dani a gidan nan an fada min kada in yarda a zubar da jinin haihuwa a gidan don komai da nasha wahalan nema na girka kaina zai lalace yanzu ga wanan banzan tazo ta haihu min a cikin gida na shiga uku ban san ta ina zan fara ba kai na ya daure da yawa yanyala. Yanyala tace madam ya kamata a kira tun lokacin bai kure ba muji shawaran ta don ba abinda za aiwa sanyin jiki bane. Kira biyu madam ta dauki wayan ta fara mata kirari tana fadin sai ke manyan mata a gidan Abdulsamad ba wata bayan ke a gidan nan. Madam yau ba wanan a gare ni madam kashina ya bushe a garin nan yarinyar nan ta gama dani a gidan nan. Cikin tsoro madam ke tambayan may ya faru kuma wani abin tai maki daga dawowanki jiyan nan tace madam yarinyar na shu,umace ta haihu min a cikin gida madam ta kara min duk wani abu danake tunkaho dashi a gidan nan na kwarai. Ta haihu madam tace hankali tashe tana tambayan Nafisan tace gashi na fada maki kinji wallahi ta haihu ko minti talatin ba a yiba. Cikin rudewa madam tace gani nan zuwa yanzu ki jirani don Allah ki natsu Nafisa har in zo musan abinyi tace ina jiran ki ai ban iya komai saura kiris in fasa ihu Allah ya kare ni. Koda ya shiga dakin ya samu na shiga wanka muna ciki da nurse din data karbi haihuwan nawa jin shigowan shi maryam tai mata magana gashi ya shigo sai ta fito daga bayin ta barni a ciki. Takardan da ta rubuta magani ta dauka ta mika mai tana sharce zufan da tayi na wahala tare da fadin wanan nake son a sawo min zan mata ne ta dan samu saukin tsamin da jikin ta yayi sai dana gyara jikina na fito daga bayin ta shiga gyara yaran wankan farko tayi masu ta kawo zaitun ta goge jikin su dashi kafin ta kara masu wanka na biyu sai ihu suke calarawa. Daga inda nake ina shafa mai ina mamaki a raina wai nice na haihu haka yau na dandani abinda ake fadi gamay da haihu. Wai cikin suna fadin abin yazo min da sauki ke nan gaskiya nagaida mata a gaisheku iyayyen gida don dai kune gidan. Komai ya kamala sai wani irin barci da nake ji yasa na kwanta nurse din nan ba karamin kokari tayi min ba sai data gyara ni ta gyara yara ta dawo kan daki laraba na fadin ta bari ta gyara tace aikin ta take yi ai. Mahaifa ne suke muhawaran inda za a rufe maryam da laraba ke kuskus din rufewa inda buzuwa ba zata gani ba don tana iya wani sheri dashi. Laraba ne tace bari taiwa sabo security magana taji nan ta fita gurin su ya tare ta yana washe baki tare da fadin ashe uwar dakin mu ta sauka yanzu maigida ke fada muna wanan abin farin cikin daya samay mu yau . Ta gaya mai abinda take bukata dashi yace akwai ko yadda za ayi sosai ma nan ya nuna mata bayan gidan engine din wutan gida na stand by yace yasan yarda zaiyi ta fita tazo mai dashi ya faki idon mutane ya nufi gurin ya rufe ya mayar da kasa kamar ba a taba gurin ba da farko. Madam ne tsaye tana rike haba tana tafa hannayen ta tace ai rudewa ya kasa barin in tambaya mai shegiya ta dire mai nasan itama bazai wuce mace ba tunda an fada muna sannan yaya halittan yarinyar yazo ? Daga inda Yanyala take zaune take fadin biyu fa ta haifa madam data dafe kirji sai da takai zaune bata sani ba tace tagwaye matane zallah ko? Mace da namiji naji yana bugawa iyayyen sa kaita fara girgizawa tana fadin shike nan ko a yanzun ta ci galaban mu gurin wanan. Madam shine damuwa ji irin kudin dana narka wurin cikin yarinyar nan kan in haifi namiji kowa kuma na fada min namiji ne a ciki na ashe shegiyar yarinyar nan ta sa an musaya mata da dana. Yanzu abinda nake son ki dashi ki kwantar da hankalin ki ina wanan abinda na dutse ya bayar tace yana nan tace gobe idan Allah ya kaimu zan shigo sai mu amfani dashi. Bar yan iska ba suna murnan an haifi namiji da mace ba to sai mun lalata ruyuwan yaran su koma dolaye ko sakarkaru sai muga yadda za ayi kuma. Ajiyan zuciya Nafisa ta sauke tana fadin sai yanzu hankali na ya kwanta don da har na mance da zancen maganin nan. Yanzu ko har naji sanyi a raina shegiya sai ta kare rayuwanta wurin yawon neman magani wa yaran bata gane komai ba. Don Allah madam kada ki wuce goben baki shigo ba don kin san ka,idan maganin an haihu gari ya waye ne kowa ya gama ganin lafiyayyen da sai aga ya sauya daga baya kuma. Karki damu badon yau munyi da hornarable zai shigo ba ai da anan ma zan kwana wallahi tace ke dai da wanan hornor din naki mutu karaba ke nan. Tana mikewa tace ya za, ayi da tsohon zuma ake magani abu tun muna da jajayen sawo idan da ban gama da dan baza ba da yanzu bai dade da gudu ba ya barni tunda yaci moriyar ganga ya samu rabon shi suka tafa. Ina kwance barci nake ji saidai ban iya yiba a lokacin don yadda nake jin jikina wani kala inayi ina shafa cikina tare da tuno abinda ya wuce dan awanin da suka shige. Muryan AA ne dakin yana fadin wanan ne maganin don yace akwai wanda babu sunan sa sai dai akwai irin shi kudin su daya da wancan din. Ta karba ta duba tare da fadin sune inda nake kwance ya dan kalla yana fadin barci take ne ? Sai lokacin na motsa tun shigowan shi dakin ya karaso bakin gadon yana mai kura min ido kaina na sada kasa don na kasa jure kallon da yake min din. Deedar ya jikin ba dai inda kike ji yanzu ko ya tambaya yana kokarin taba min jiki nace lafiya nake nurse din dake dakin bai hanashi tabani ba yana fadin maman twin's ke nan ? Murmushi nayi masa na turo baki nace ban san ya akayi na dauko wanan hannun ba ko ita dake da gadon abinta bata haifa sai ni. Yace nowarder nikan ina mamaki ina kika dauko tagwaye kuma nace maman mu ce tagwayen itama namiji ne abokin tagwacin ta ai. Amma mama ta kyauta min wallahi don nike da wanan baiwan data sam baku a zurianta gashi ita bata samu ba ni na samu ta sanadin ta. Maryam ne ta shigo dauke da yaran a hannun ta da suka sha kayan sanyi da farin showel tace ga kyautar Allah ka rika dazu ka dauke su ba ai masu wanka ba. Sai da ya karbi yaran ya dade yana masu kallon kwab dukkan su biyu ya dago yace wa maryam wanan sun dara uwar su ma fari nake gani tace shi muke fada da mama yanzu. Wa yan nan gaskiya kamar diyan wasu halfcase dasu ya kara maimaitawa yana mikawa maryam su nace daga inda nake maryam dan ban ruwa in hade maganin nan. Ta kwantar da yaran a gefe na yace ruwan zafi fa zaki bata tasha kada ki debo mata na sanyi shiyasa nace mommy ta taso yau din nan tazo. Nace a wanan lokacin yace jirgin yamma zasu biyo ita da Altine zasu zo da sauri nace ashe baka manta da alkawrin da kai mata ba ke nan yace yana raina ai. Don naso tazo tun kan a haihu don ban dauka tarbon wata zaki yi haka ba na dauka ko sai irin tsakiyan wata din nan ne haihuwan idan naje sai in zo da ita. Har yakai kofa zai fita bayan ya tsare ni da ido nasha maganin sai ya juyo yana fadin Nafisa ko ta shigo dakin nan na tare da fadin kasan ba a kimtsa ba kila tana jiran a rarage ne ta shigo. Kai ya girgiza ya fita maryam ce ta kalle ni tana fadin kai namiji ji mutumin nan yadda yake rawan kai da samun yaran nan yanzu. Nace haka yake ai idan an mai haihuwa sai dai son yaran nasa a baki ne kawai ai baida jan diyan shi a jikin shi shi. Tace to ke zaki yarda ne aikrce zaki koya ma yaran manne masa ko baiso kuwa don idan ma baki koya masu ba sai wata tazo kiga yana nan nan da diyan ta kina kallo. Ajiyan zuciya na sauke tun yanzu zan fara fuskantar wani abu kuma akan yaran da basufi awa daya da fadowa duniya ta mu ba mai cike da rikici a cikin ta. Sai lokacin nace maryam ta miko min yaran don in masu addua na karanta masu adduoin tsari tare da bude farinjin su na karanto masu adduan tsari daga zina. Biyar laraba ta gama abinci har lokacin nurse din nan mai kirki tana gidan tana ta koya mun komai da zanyi akaina da babeis din. Abincin suka debo min nurse din nan ta sani a gaba ina ci mommy suka iso gidan ina jin muryan su sai gasu dakin da murnan su suka shigo sai naga har da ya Aminana suka zo. Ina ganin ta nayi narai narai da idanu kamar zanyi kuka saboda dadin ganin ta da nayi gaishe su na fara yi mommy ta karaso inda yaran suke tana fadin khadija aike ke da sannu yara manya haka dasu kamar ba tagwaye ba don Allah. Nan dai ake anata hira sai ga Laraba tazo tana kirana dagani maganane da ita haka na mike mommy tace dawo ki saka hijjabin ki ko nan da falo zaki yanzu ki kula da hakan. Na samu laraba take cewa muje kitchen naga abinda aka shigo dashi sai dana dan duba nace mommy za a kira ta san yadda za ayi dasu ai. Nama ne mai yawan gaske sai kan shanu har biyu da kafafuwan su da sauran tarkace ya kwaso dakin na koma suna zaune nace mommy Laraba na magana dake da Anty Altine a falon. Mikewa sukayi sun samay ta ta nuna masu kayan da abinda nace mommy ta duba tace dayake akwai frezer sai a saka zuwa gobe amma kayan cikin a dan diba ke Altine ai mata ferfusu da zata sha kafin ta kwanta yau. Bayan sun gama adana komai yadda ya dace mommy na shigowa dakin tace ikon Allah ance naka sai naka yau mune a gidan babangida ake halarta muna komai a matsayin mu na manyan shi. Ance ma hakurci mawadaci abinda muke mashi nuni dashi ke nan tuntuni ya kasa fahinta na tuna da mukazo zaman yar nan Ihisan irin taskun da Nafisa ta nuna muna a gidan nan lokacin. Altine ce ta tambaya ina take ne mommy tace tana kasansu ai nace ta dawo jiya mommy tace jiya jiyan nan dai nace eh jiya suka dawo daga can. Altine ta kara tambaya tashigo taga tagwaye ko laraba ne ta basu amsa da ko leke ba wanda ya shigo daga sashen ta tana fadi ta fita. Lokacin na bata rai nace ban ma son su shigo din mommy don mafalkin danayi kafin in haihu nan dai na koro masu abinda nake tajiwa akan yaran nace mafalkin hakan nayi da Nafisa din. Da sauri Altine tace indai ina gidan nan kuwa ba zasu ga yaran nan ba har su dauka don wallahi kemaymay zan masu idan sun shigo . Mommy tace dole muyi taka tsantsan kan haka don hajiya mama saida ta fada min haka dana shiga muyi sallama da ita wallahi tace don Allah musa ido kan shu,umar matar shi ashe kinga da batu ke nan a gidan nan. Ya Amina da ba gwanar magana ba sai fadi take Allah to ya kare yanzu mommy kina ganin zamu iya hana mata su ta dauke su din nace in dai har anyi suna basu sanu taba su shike nan ai. Anty Altine kamar yadda nake kiranta tace har bayan suna indai ina gidan nan bazata dauke su ba may ye amfanin boye mata an san manufar ta ne. Ai gara a nuna mata tunda itama haka take wa mutune idan ta haihu har yanzu wayasan diyan ta a cikin dangi. Nan dai suka sha hira akan nafisa din har wani lokaci sai kafin in kwanta nace ma mommy yaya zasu kwanciya. Tace bari taje dakin da ba kowa su sauka a ciki nace ya Amina tace a a mommy ke ce dai zaki zauna dasu nan mana ni da Altine sai muje can dakin ko dakin laraba. Mommy tace dake dai Amina zamu tsaya nan din don dare da sauran lalura don bamu san yaran ko suna fitinan dare ba. Ni barci ya cika min ido koda AA ya shigo masu da ledan kaji gassasu ya dan duba yaran suka gaisa da baki yadan yi hira da Altine tana tambayan shi ina tarin buzayen gidan shi . Dariya yayi yana nuna ta ya fita ya Amina ce ta tayar dani wai in tashi in kewaya kafin a kwanta don inji dadin barci da dadi ruwa ta surka min na shiga na fito take fada min wai ga kajinan in ci na gyada kai nace bazan iya ci ba anty mommy ta hauni da fada tana fadin zaki yi jagon wasa khadija jego fa baison hakana daure kici ko kadan ne da dan ruwan tea sai ki kwanta. Badon naso ba haka na daure na sha tea din na kwanta can cikin dare nake jin muryan su wai namijin ya hana su barci yana kuka. Ruwa suka bashi sai ya dan fara barci kuma yasa kuka ya falka sai da mommy ta goya shi suka dan samu barci tana fadin yunwa yake ji yasa bai runtsa ba. Washegari koda bakwai yayi har nayi wanka na shirya ko suna ta hada hadan wanka da hada abin karyawa zuwa tara duk mun karya muna zaune sai ga Nafisa da madam sun shigo dakin . Sai da naji gabana ya fadi Altine dake kitchen ne ta shigo dakin da saurin ta taja ta tsaye a bakin gado. Bayan sun gaisa dasu mommy tace ga kawayen ta sunzo suga babies su gaida mai jego tana wani fara an dole ta nufi bakin gadon da yaran ke kwace suna barci. Altine tace dakata kada ki taba su don Allah barci suke yi ta riga nafisa dukawa gurin da yaran su wani kallo Nafisa tayi mata tace nice zaki hana daukan yaran ? Tace ban hanaki ba amma aladan mune ba a taba yaro idan baiyi sati da haihuwa ba don haka barsu nan har zuwa gaba madam tace amma ai itama uwace a gurin su ko ko baki sheda ta bace. Haka umurnin yake daga kakanin yaran komu nan ai kin ga daukan su mukeyi ba dai ko zargina kike son yi komay nafisa ta fada. Babu zancen zargi anan amma ki barsu nan ikon Allah yaran ma rowan su akeyi ke nan nidai kaina na duke ina cin ferfesun da aka aje min yaji kayan yaji na gargajiya sai kamshi yake yi. Kiri kiri sukai wa juna sai da Altine tayi masu na mahaukata ta nuna masu ita tsohuwar yar barikice itama suka fice baram baram a part din . Mommy tace yau Altine kin cece mu da muna kadai a dakin nan ai kyale su zamuyi su dauki yaran ajiyan zuciya na sauke baya fitar su. Mommy tace falo zamu koma duk wanda yazo muce suna ciki don zasu iya biyo muna ta wani hanya kuma tunda sun fahinci an gane su. Laraba ce ta shigo tana fadin abin mamaki yau naga bakuwa a gidan nan cikin buzayen da suka zo tana sallah har sallah walha take yi. Jiya ma tunda tai magariba take zaune tana karatun kur,ani wurin har aka kira sallah isha,i tanayi mommy ne ta bata amsa da fadin ke ance maki duka suka taru suka zama daya akwai na Allah a cikin su ai sosai ma yanzu wayewan kai na addini ina ne bai ratsaba. Kukan da babyn mace tayi ne yasa hankalin su ya koma kanta mommy ke fadin yaran nan yunwa suke ji ya kamata su fara kama nono haka na Amina kara gyara nonon nan a basu su sha . Fuska na tabe shigowan maryam dakin na mayar da hankalina gare ta gaisawa tayi dasu mommy ta mike ta nufo ni da yarinyar. Falo suka koma naji dadin hakan nan suka barni da ya Amina da maryam ina koya min yadda zan rika yaran. Haka dai na daure yarinyar tana kamawa tana sakewa sai barci ta koma kuma na samu saida. Ya Amina ne tacewa maryam kin makara maryam baki samu rikicin buzuwan ku da Altine ba kan daukan yaran nan da sauri maryam tace sun dauke su ne ? Tace ai Altine ta hana su yau munga hauka badon Altine ba kan da mukan ai bamu iya tijaran su don yadda suka hakikance sai sun dauki yaran. Nan dai ta bata labarin abinda ya faru tace mun dai gode Altinen na nan nace yar mijin ki ne fa sai ta harare ni kallon mu ya Amina tayi tace ta ina tazama yar mijin ta kuma ? Maryam tace tambaye ta dai yaya nace ta sojan gidan su mommy da sauri tace Suraj nace shifa in Allah ya yarda tace ko shine naji ana rikici da uwar ya samu mata Abuja tace bata yarda ba yar yar uwanta zata hada shi da ita. Wata sabuwa ke nan dama nasan sai an kwasa da Umma don da ganin ta irin matan nan ne dake mulkin diyan su sosai. Muna cikin maganan mommy ta shigo dakin sai mukai shiru tace in fita kuna siri ne ya Amina tace a, a mommy ashe maryam din khadija ne Suraj ke so nan Abuja. Da sauri mommy tace wace maryam nace wanan maryam dai tawa mommy ta sake fara a tana fadin dako yayi dacen mata wallahi dama shi irin ku yake so ai wayyyayu mata kamar shi. Duk wace uwar ta kawo yace batai mai ba ita kuma taki bari ya kawo wace yake so idan mijin kine ubangiji Allah ya ingata tsakanin ku. Suraj yana da kirki wallahi bai biyo halin sauran yaran dakin ba da nuna banbanci uwar ce dai matsala yanzu yana nan kan ya dage. Ko zuwan nan dayayi last naga sun zauna wurin Alhaji nasan ko zancen ne ya Amina tace ita bata ganin yadda ya girma baiyi aure ba mommy tace wa yaya Allah dai ya kyauta. Shine ai take ganin laifin hajiya mama wai ita ke sakewa diyan ta itakan ai bata da wasa ga yaro ko auren yayi ko yana under control din ta ne. Suraj din daine ma bai faye bin dokan ta ba sani lokaci nace Allah dai ya shawo muna kan ta da abin baiyi dadi bako gaskiya. Shiru maryam tayi na fahinci ta dan shiga damuwa mommy tace idan kina son abinki yana son ki in Allah yayi ai dole ta hakkura saukin abin daya ne idan taji ace ke din yar masu hali ne zata iya yarda daga baya. Fita tayi tana rufo kofa muka kwashe da dariya nace mun zama yan kurkuku ke nan kofan ma sai an rufe mu a ciki ya Amina tace dole ni yanzu ma yadda in an watse zaku kwashe da ita nake ji ai. Nace idan mommy bazasu zauna ba wallahi saidai in koma gida ban iya masifan wanan matar gaskiya yanzun dai sai yadda shawara ya tsaya ai don ban tsamani baban maigidan zai yarda ta zauna har arbain ba saboda gudun yadda akayi wancan karon. AA ne ya budo dakin ya shigo gaisawa sukayi da ya Amina sai maryam data gaida shi ya amsa ya Amina ta mike zata fita yace zauna fita zanyi ai maryam kira min mommy falo. Maryam ta mike zuwa kiran mommy din daga can bata dawo dakin ba momy ta shigo tana fadin kai Altine akwai tsiya wallahi. Yana duke yana duba yaran yana kare masu kallo yace nurse din nan ne data karbi haihuwan yaran ta bugo min wai za a kaisu su amshi riga kafi yanzu can asibitin su. Dama ashe kiranta wai yar maryam tayi makwabtane tayi kokari sosai wallahi matar kuma na tambaye ta mai za a bata tace wai ai gida ne tunda yar maryam ta turo ta sai ku fadi abinda za a bata mommy. And kuma mommy ya akayi ina office yanzu nafisa ta kirani tana kuka wai tazo ganin yaran an hanata daukan su ita da kawayen ta. Kafin mommy tayi magana sai ga Altine kamar an turo ta dakin momy nacewa ba hanata daukan su ai mukayi ba kasan ai haka ba zai yuyu ba babangida. Altine ta cabe da fadin haka tace ma an hanata dauka idan bata da wani manufa may ye don ance suna barci a barsu sai bayan suna zata matsa sai sun dauke su. Yace ke mahaukaciya da uwata nake magana tace ni kuma yarana nake karewa ba wallahi tsohon su yanzun an daina hakana irin hakane sai abu ya zo ya samu yaro a haife shi lafiya sai daga baya a rasa gane kan yaro . Amma idan anyi suna yaro yasha addua duk wanda zai dauka ya dauka ana ta fadakarwa akan hakan yanzun duniya ya lalace wallahi ba a gane mugu a fuska barci suke akace su barsu don jiya basu bari anyi barci ba da dadi dan namijin yanata kuka da dare. Yanzun dai na fahinci kece mai rashin mutuncin wa mata na ke nan ke kika sakata kuka ko wai harda kuka tayi don an ce su bari su tashi kila tana da wani manufa kenan akan su. Taga yara bulbul gwanin ban sha,awa ta kwaso wani gaiyan buzayen ta suzo lashe min diya kai ya girgiza yace ke mahaukaciya ce tace naji dai ita wake daukan nata idan ta haifa ai ta sani sherin matane kawai irin namu. Muko nan mun san komai wallahi sai anyi suna zamu bari kowa ya dauke su yace ke kada ki aibanta min mata fa an fada maki matana muguwa ce . Bansan lokacin da na saka masu baki ga zancen su ba nace may ye na naci idan bata san sherin data kulla ba tun jiya ai na haihu bata shigo sai yau zata kwaso munafukan ta su zo min. Wurina ya juya yana nuna ni yace mommy ki ji a gaban ku take fada kan yaranta ya juya zai fita yana fadin Altine ji mana ta bishi baya suka fita daga dakin. Momy tace aini na gode da zuwan Altine dako Alhaji bai so a zo da ita ba sai da akace babangidan ne yace tazo ya yarda tazo. Irin su ne daidai dasu ai momy don ta nuna masu ita ma ta iya ya fita sun dade sai ga Altine ta dawo dakin tana fadin ikon Allah. Ina kawar buzuwa da suka shigo dazun bakar matar nan mai zubin yan duniya yanzun suna fitowa wallahi muna tsaye da tsohon su kawai mu kaga ta yanke jiki ta fadi. Adaga ta wai tayi kariya a kafan ta daga faduwa fa a gaban gidan nan su momy suka mike suna fadin subbahanallahi yanzu tace gata can za a kwashe ta ai duk sun tada hankalin su a waje. Gurin nace aniya mako miya wallahi kinga mugun abinda suka riko ne ya koma masu nan suka barmu zaune suka fita sai ya Amina ne bata fita ba dakin ta zauna dani a dakin da yara. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Yadda naga maryam tana ta faman shirya ma sunan yasani tambayar ta wai har suwa zasu zo ne take wanan shirin haka ne ? Tace idan ke baki da mutane yaran da mutanen su suka zo duniya don haka ki barni in shiryawa bakin su ke baki san abinda kika haifa ba ina gani. Ga mijin ki shi sai faman shiri yake keko kin zauna sai kumshe kai a cikin daki gobe dai ki shirya mai sallon na tafe gidan nan suyi maki gyaran kai. Murmushi nayi mata nace to maman biyu Allah ya kaimu goben lafiya saura kwana biyu suna babu zama don abubuwa sun yiwa kowa yawa don an gyara ko ina na gidan. Yusuf ne ke gabatar da komai shikan AA nasa bayar da kudine kawai washegari yan kaduna suna isowa basu dade da zuwa ba mutanen minna suka iso mota daya doguwar motar maikatan lafiya nasu mama tani aka basu. Duk gidan ya cika da jama,a hotel AA ya kama ma bakin namu mai kyau da tsada sai yabawa suke yi yara sunyi goshi inji momy tunda har hajiya umma tazo Abuja suna hajiya mama kawai aka bari a gida. Naji mamakin rashin zuwan Anty Fati da batayi ba sai dai sakon da ta bayar a kawo min yaran dai sun zo da wasu yan uwanta mata biyu nasan su don suna zuwa gidan idan naje kaduna. Duk wani abinda za a gabatar sune masu gabatar dshi su Fauziya basu samu zuwa ba don suna tsamanin kira binta da zainab dai sun zo sun hade da maryam da wasu kawayen mu biyu da muke zaman mutunci a hostel. Baiyi shawaran komai dani ba da iyayyen shi da yan uwanshi yake shawaran shi nima kuma hakan bai damay ni ba. Ban baku labarin sunan yar gurin Nafisa da sukai shagali ba bayan dawowan mu inda mata yan duniya suka barje gumin su ranan akai ta muna iya shege agida dasu haibaici da gori. Sai ga Nafisa yanzu fitowa waje yana son ya gagareta don nuna tan da akeyi tana gani ana cin arzikin mijinta babu dama tai magana. Muna nan da daren nan muka samu labarin hajjata mata an hanasu tafiya don a shekaran akai doka saudiya sai mace taje da muharamin ta zata shiga saudiya. Wanan abu ya tayar muna da hankali sosai don muna ganin bazasu samu dagawa ba zuwa makka sai da yusuf ya shigo yana muna bayanin wai AA ya biyawa Ahmed shine zai tafi tare dasu da yar wurin umma daya su hudu ke nan. Washe gari aka tashi da hidimar buki a gidan inda ake ta shigowa da kulolin abinci gida yana waje sai ganin Nafisa yayi ta fito da yaran ta da yan uwanta wai zasu bar gidan har taro ya watse yace babu inda zata tafi mai da yara inda zata tafi ita daya bai hanata ba. Dole ta juya ciki dasu bata dade ba ta fito ita kadai ta fita ta barsu da yan uwan ta su Fatiya a gidan. Sai abin arziki nake samu daga matan da ban sani ba wai matan abokan shi da yan gurin aikin su ne ke zuwa muna murna. AA ya yanka ma yara raguna biyu na suna sai shanayen da aka yanka don aukin nama Umma da momy ne suka zo kiran su mama Tani su fito falo ga kayan suna za a gabatar masu. Duk wanda yazo ina bashi kulawa da tallaka da mai arziki don abu daya ne ya tara su a gurin don haka nake ba kowa kulawan daya dace don kada wani yace na fifita wani. Ihun dana a falo ne yass mu yin shiru ashe cikin kayan sunan ya saka min makulin motana sabuwa dal baka kal da ita wata jeep dirkekiya na mata new desgn. Maryam ta shigo dakin da murnan ta tana rawa tace kin kai ga mota khady AA ya bada ki kyautar mota albarkacin su yan biyu. Baki na tabe nace in dai don su zai ban mota ya bari ban so suka shiga min shakiyanci a gurin amma kasan raina nace may wanan mutumin ke nufi danine dama daya kasa saya min mota kullun yana min wake. Nafisa ne suka shigo da kawayen ta gidan kallo ya koma wurin su don shigar su sun nuna hali da gadara sosai a jikin su. Sai zuwa rana Anty hauwa ta danno da tawaganta sai motoci ake fakawa a gidan bata dade da zuwa ba hajiya laila SJJ ta iso itama wuri ya dauki manyan mata don su shidda ne ita ma . Kyautar da suka kawo ne ya girgiza kowa a gurin motace Parado fara na mata mai kyau dashi sai da jikina ya mutu na kasa magana a gurin. Tace yayan ku ne yace a kawo maki ita albarkamcin su yan biyu ki karba don Allah don yasan halin ki su momy da Umma aka kira don karban wanan kyautar sai manya. Anty hauwa ta karba tace ai godiya wurin maigida su yan biyu sun gode nikan na rasa may zance don nasan akwai rigima gurin AA idan yaji. Walima aka shirya zuwz hudu aka hallara babban falon gidan Nafisa suna ciki ana cacakan AA dani da yaran sai mugun baki suke muna. Labarin kyautar wata motar ya kai gare su ranan da kyat su Badosa suka shawo kan nafisa ta haukace wai an nuna mata banbamci annuna mata ita ba yar kasa bace. Da kyat aka samu ta fito wirin walima suka zauna sai wani sallo suke suna ganin su anty hauwa da mutanen ta sai kuma ga matar Sjj sun fito sunga karyan naira inda take aiki a gurin. Sai suka koma kuskus ina na samu mutane ne haka irin kudin da ake ba malamar da gudun mawan da tace ana nema marayu wurin ya firgita Nafisa ta fara mikewa zuwa dakin sauran ma suka bita. Malam ta gama sai Fatiya tace a dan bata lokaci akwai kiran da zatayi mata yan mintuna kadan don Allah. Tunda ta karbi abin magana ta fara wurin yayi tsit inda tai nasiha kan hakkin yaya zuwa iyayyen su kafin su girma da inda illoli ke fitowa daga iyayye mata wurin tarbiyan yara yanzu. Kowa ya yaba da hankalinta sosai kudin data samu tace a hada a bawa malaman batayi don karban komai ba sai ta rufe akan jin tsoron Allah a zukata saboda mata sun shagala da yawa. Coure mate dina sunyi kokari sosai don ku san musulmai da Christian duk sun halarta harda wa yanda ba course din mu daya dasu ba sunzo. Anci an sha araba jakkuna dake dauke da kayan buki a ciki mai hoton yaran su biyu taro dai ya watse lafiya ana sam barka. Can kuwa kawai Nafisa ne ke kara zugata har yaushe na shigo gidan da zan bunkasa haka a cikin dan kankanin lokaci kai mutane akwai munafunci dasu. Don neman fada ne a gurin mijin ki yasa suka tara mata wanan abin arzikin haka mai yawa wata tace ni ba shiba kun ko ga sarkan wuyan ta a wirin waliman nan zai tasan ma milayan kusan biyu ko uku fa. Kai kai ina wanan yar talakawan ta gama min yakar kauna a gidan nan yaushe nasa sarka makamancin haka a wuyana wata tace kece baki so lokaci daya sai ya mallaka maki wanda ma yafi wanan kudi. Banda abinda zancewa Anty hauwa da maryam sai godiya don itace ta hada kan sarkunan ta canzo min wanan a Dubai a matsayin kaddara ana gama taro ta rada min a kunne in adana sarkan nan don ya tsone ma kowa ido a gurin sosai. Yara sunci suna don na Mijin an saka mai muhammadu Aminu-lah kanin Abban su daya rasu, sai mace da aka radawa sunan hajiyan su Aisha humaira tun haihuwan Ihisan yaso sawa tace bata yarda ba don ba wani ya haifa mata diyar ba. Ko zuwa dare ban samu kaina ba duk da ciwon da kaina ke min don bakin kaduna dana Minna dake gidan zakace ba a watse ba. Yana shigowa get din gidan idon shi akan motar da aka kawo min kyauta ya yaba da motar sai dai ya dauka mai shi na cikin gidan ne tazo buki. Yana shiga Nafisa dake dakon shigowan shi tana mara mai baya kusan a tare suka shiga dakin lokacin. Ganin yanayin ta yasan tana da magana a bakin ta don haka ya sashi daure fuska jin muryan ta yayi tana fadin macuci azzalumi ya juyo da zauri yana kallon ta tare da fadin may nayi maki kuma daga shigowa na yanzu. Tace azzalumi zakace baka san cutar da kaimin ba wai kai zaka nuna ma duniya niba kowa bace yace to wa kike nafisa shugaban kasa kike ko matar shugaban kasan ? Tace ban ko daya yace to ki tsaya a matsayin ki na matar Abdulsamad yafi maki cutan da kike cewa nayi sai ki fada min inda na cuce ki kuma ? Tace wani cuta ne bakai min ba kuma na taba haihuwa ka sai min sarkan gwal ko na taba haihuwane ka bani mota a matsayin kyautar haihuwa. Kai ya girgiza yace lalai Nafisa ke butuluce ta karshe sarka wani irin ne ban sawo maki ba duk naje turai shine tsaraban ki kina amfani dashi a gidan nan ne idan na saya maki ban ganin shi. Mota kuma shigowan ki gidan nan mota uku na saya maki kina kadarwa wanan ma yanzu da kike shiga nawa ne kika dauka a matsayin dannan kirjin ki bayan kudi da kika saka in baki na fati ko ita khadijan ? Tun suna fada su biyu a dakin har yakai sun fito falo a bainan jamma,a suna yi umma ta fito tare da gwagwanin shi suka kada kan shi ya fice ya barta. Yace umma wanan matar kashe ni take son yi haihuwan nan da tana da halin murde yaran nan da uwar su da tuni ta murde su sun mutu kowa ya huta. Akan ki ne kishiya ta fara haihu a zauna lafiya may wanan matar take nufi da nine kamar itace ta haife ni ko ta ajeni a gidan nan haka ? Fitan su bai sa ta yi shiru sai tonawa kanta asiri da miji take a gurin yan uwan shi kowa na tirda halin ta. Ban samu kebewa dashi ba sai washe gari don fada mai zancen motar tunda nayi wanka na shirya cikin wasu atamfan exclusive na sillace jiki zuwa wurin shi. Yana kwance har lokacin sai dai ba barci yake yiba kuma yana kwance rai rai kamar wanda ke tunane a lokacin sallama nane yasa shi dan dagowa gare ni. Tun ban kai zaune ba nace yaya lafiya ko ina zama a kusa dashi ya dan gyara min na zauna da kyau yace matsalan kune da baya kare wa nake tunane. Nace mun kuma da mamaki ina kallon shi kafin in kara fadin, wani abin mukai maka kuma yace zaku fasa ne gaba dayan ku na rasa gane inda kuka dosa da rayuwana. Allah ya kyauta nace don ban san may mukai mashi ba yai wanan jam,in haka gare mu nace godiya nazo in wa su yan biyu akan kokarin da akai muna mun gode Allah ya kara rufa asiri yasa a fi nan karfi. Kamar ba zai karba min ba sai can yace amin ke kin iya godiya idan an maki alheri nace kowa ma ai ya iya tunda bamune muke nema ma arzikin naka ba sai yadan yi murmushin yake. Yace ina yaran suke nace ana masu wanka sai dai naji umma na fadin kamar yau zasu koma fa yace yau din nan nace haka naji ta fadi jiya dai don wai Abba yace kada su wuce yau idan sun zo. Komawan su ba zaiyi yau ba sai dai gobe har yan Minna din nace harsu yace eh haka nake so idan sin dan huta sai kowa ya kama hanya kisa Altine ta kirga min ko su nawa ne daga minna haka ma yan kaduna. Nace nabarka lafiya har na daga na dawo nace ai na manta kaga bakuwar mota a waje gidan nan ko ? Yace eh to akwai dai motoci a gurin gaskiya nace wata parado fara yace ok da wani flawer kamar gift ko nace eh ita yace naganta tun jiya a packer gurin. Nac to ita ma wasu yan biyu aka kawo wa kyautan ta mikewa yayi da sauri yace wa ya kawo masu kyautar mota haka nace wanan dai matar mutumin nan dan uwan yaya Adam dakaiwa alheri sune suka zo dashi. Nan dai na fada mai yadda akayi tun kawo kudin su da bankarba da kuma zuwan su jiya da mota da har anty hauwa ta karba. Abinda nayi tsamani ne ya faru don lokaci daya idon shi ya canza min ya hauni da fada khadija jin ya ambaci sunana na asali yasa na fahinci maganan takai magana gurin shi. Ban fada maki rayuwana ba haka yake ba cin hanci ke nan suka kawo maki komay yau idan badon nasan halin ki nasan ko ke waye ba da ba abinda zai hana in saba maki a gidan nan. Nace yaya kada kaga laifina a hakan nayi duk iya kokari na in kaucewa hakan don gudun bacin ranka sai suka biyo min ta wanan tsigar kuma. Banda yadda zanyi a cikin mutane ga maganan da ta fadi wai kanwa nake gare shi do haka su yan biyu yabawa mota bani ba yace ni zai gwada wa mota komay ? Ko gidana bai gannin da motoci bane da zai dauko wanan motar ya kawo maki motar nawa na saya maki da kikaji nafisa na fada akan shi jiya. Ke bari kiji idan kin shigo rayuwanane ki lalata min suna wallahi baki isa ba duk fadan da yake yi kaina na kasa ban san lokacin da hawaye yazo min ba cikin wani irin murya mai sanyi nace. Ni yaya Abdulsamad nice na shigo rayuwan ka don in bata ma suna ni khadija Adamu danladi dini sai na mike hannun na naji ya riko min ta baya. Na koma na zauna a inda nake yace ki fahince ni Deedar wanan ba rayuwana bane cin hanci da rashawa da ina wanan halin da yanzu nafi haka a garin nan. Cikin kuka nace na sani yaya amma ni may ye laifina a ciki yanzu tunda ba rokon sa nayi ba sun nuna min wanda ya rigaka kwana ya rigaka tashi ne da ban karbi kudin su ba sai suka biyo min ta nan kuma. Amma idan kaga laifina a cikin wanan maganan har kake ganin za a hada kai dani a cuce ka kayi hakkuri zan kirasu suzo su dauki abinsu tunda ni ban san gidan su ba ma. Ki barni dashi zan kirashi inji dalilin yin haka a gareni don banga dalilin saka mata na ga maganar business din mu dashi ba. Shiru nayi hawaye yana zuba min sai can danaji ya tsagaita fadan na mike na fice a dakin ina share hawayen fuskana da bayan hannu na. Bayana yabi da kallo har na fice daga dakin ya sauke a jiyan zuciya tare da jan guntun tsuki ya mike a inda yake yaka ya shiga yanayi yana tunane abinda ya faru tsakan mu yanzu har na bar dakin. Sai yaga rashin kyauta min da kalamin shi don a gaskiya bai ga laifina a cikin zancen ba don ko gidan su ma bawai na sani bane kamar yadda nace mai. Ina shiga daki na samu a nata hada hadan wanka da shirya abin karyawa wa baki na samu ya Amina tayi wa su Affan wanka tana shirya su na shigo tace ga diyan ki nan wai ba zasu tafi ba yau suka ce. Nace ina ganin ba yau bane tafiyan su duka ai ganin yanayi na yasa ta fadin wani abin ne ya faru kuma ? Ina kuka nake fada mata abinda ya faru tace ikon Allah wanan mijin naku halin shi sai shi may ye a cikin haka ba karuwa ya samu aka kawo gudun mawa ba. Ina share hawaye gajiye ta fado dakin itama tsayawa tayi tana tamnaya ya Amina tace uhmmm ita da mijin su ne akan motar da aka bata jiya ne suke jidali nan dai ta fada mata komai. Tace shikan wanan shiya kwaso mai sunan nashi da komai wallahi to ba za a mayar ba wa ya taba wanan halin don Allah dai shifa wani irin bahagon mutum ne shiyasa yai daidai da kalar matan shi ai. Fita tayi kafin wani lokaci sai fa momy ta shigo dakin tana fadin yanzu nake jin wani magana gurin Altine ya Amina ne ta fada mata komai. Tace haba babangida yaushe kuma aka taba yin haka in bakai mai godiya ba ai sai ka kyalesu da wace aka ba din ko ? Tace umma tace zatayi mashi magana ai idan ya shigo nace Allah yasa ma bai buga mai ba kamar yadda yace zai kirashi din. Altine na kalla nace yace wai ki kirga mai mutanen da suka zo daga kaduna da minna ko mutum nawa ne suma yasan mutum nawa suka zo tace dan gidan momy ke nan ga dadi ga wuyan sha,ani. Sai zuwa goma da wani abu ya sauko kasa koshi tare da Yusuf suka shigo part din su gaida mutane a can dakin dasu umma suke ne bayan ya gaida su tace babangida sai muke jin wani zance kuma mara dadi. Idan baku samu karuwa ba kun ga wani ya kawo abin arzikin shi gidan nan a baya arzikin diyan ka ne ya jawo maku alheri don may zakace a mayar da kyautan motan da aka baku. In ma kana ganin da wata manufa ya baka ai samun hanyar da zaka mayar mai dashi kaima zakayi ba wai a dauka kai tsaye ace amayar haka ba. Kallon shi Yusuf yayi yana son karin bayani yace Umma ba wai hakana bane sun biyo ta wanan hanyar ne don suga sun bata min tsarina tace idan da haka ne ai ba zasu hada da matanka harda diya ba ko ? Kayi hakkuri abinda ya wuce abarshi akan ya wuce sai a faki gaba kuma yace to shike nan umma ya wuce ai tunda kinyi magana. Tace ta gode nan yace naji ance yau zaku koma wai munyi waya da Abba nace dashi gobe zan sallamo ku kudawo gida tace to shike nan Allah ya kaimu goben lafiya yau da gobe duk daya ne a gurin Allah ai. Ya barin wurin su dakina ya shiga inda nake zaune da yan uwa suka gaisa dasu ya fada masu yana son su bar tafiyan su har gobe mama Tani tace bai zama dawainiya ba tunda angama abinda ya kawo mu. Sai dai kuma dama muna son magana akan ita khadijan wai muna rokon ko za a bamu ita mu tafi da ita taje gida tasha ruwan zafi sai su dawo. Dan murmushi yayi tare da fadin mama kuyi hakkuri a barta a dakin ta don mu gidan mu ba a hakana sai dai idan wata zata zo ta zauna da ita nan ne babu damuwa. Mama Tani tace to shike nan zamuyi shawara mu gani abinda shawara ya yanke zakaji yace karatun ta ma sati biyu kawai suka bata leave. Yana fita na turo baki nace ni gida zan koma gaskiya ban iya zama ni kadai anan inyi jego da yaran har biyu haka a gabana. Yafi mu gaskiya mama Tani tace don kinga idan kinje gida yaya zakiyi da karatun ki kuma yace komawa gida ba aladan gidan su bane dole dai kiyi hakkuri sai a turo maki wace zata kula dake nan. Ban so haka ba don ni na sama raina zuwa gida inyi wanka a can ban taba tunanen zai kawo min cikas ga zuwa gidan da na kwalfawa rai ba. Wunin ranan dai haka nayi shi ba dadin rai sun shiga gari har yan kadunan yan tsiraru aka barmu dasu a gida da yamma ya dawo ya kirani falo na fita na samay shi zaune. Yace wanan sallaman yan minna ne wanan kuma na yan kaduna ko akwai sauran wani abinda za a basu ne nace babu an gode. Ina shirin mikewa yace min ya na ganki haka wani abin yana damun ki ne shiru nayi sai da ya kara maimaita maganar shi nace gida nake son zuwa in sha ruwan zafi. Nan da kike ruwan sanyi kike sha kafin in magana sai fa Nafisa a gaban mu tace samad kasan yarinyar nan bata da girki tunda ta haihu ko ? Yace wani abin kika ga munayi da ita anan tace ban yarda kana ke bewa da ita ba haka don hakkina ne yanzu. Nace au hakane to tunda abin haka gobe zan karbi girki na a gidan nan ko ba za a ban ba inji tace wallahi baki isa ba don sai kinyi arbain. Nace tunda ke ke iko dani sai mu gani idan ban insa ba din ko kin manta ke ma haka kikayi baki arbain din ba kika karbi girki ki ko kinfi wani ne a gidan nan. Don haka nima zan karba kamar yadda kika karba kina nufin dani zaki takara a gidan nan nace da abin kwarai kikeyi da nayi koyi dashi sosai kuwa amma girki a gidan nan gobe kamar nayi shi na gama ne. Ina fadin haka na dauki kudin tare da kiran laraba ta shigo min da kayan na barsu a gurin suna fafatawa da ita na shige ciki ban san yadda suka karata ba. Nasha alwashin dama sai na rama hakan a raina idan ita tayi a kuraren lokaci wancan karon ni da wuri zan mata nawa iya shegen nima tunda da gangan take yin tsiyar ta don ta nuna tafi wani iya iskanci. Momy na kira na danka ma kayan su na yan kaduna mutanen minna kuma na ba mama Tani nasu a hannun ta. Washe gari baki sun watse sai su momy da Altine sai ya Amina muka saura a part din maryam ne ta shigo zuwa yamma muka shige daki muna hira damu uku. Anan nake fada masu yadda mukayi da Nafisa da jiya maryam tace kwarai kuwa gwama da kika ce hakan ko ba zaki dakin shi ba nuna mata kowa ya iya iya shegen ai. Girki nasa Altine su shirya dashi zuwa biyar ya shigo gidan ya dan jima zaune a falo gurin su kafin ya shigo wurina ciki. Ganin shi maryam ta fita ya samu wuri ya zauna yace ya batun girkin naki yau nace yana nan kamar yadda nace yace cikin marairaicewa bazaki bari yaran nan su kara kwari ba. Nace cewa nayi zasu hanani yin girki din dama haka zanyi tunda tace bata san nasiha ba muje zuwa ga haka. Ya ga dai da gaske nake magana ba wasa a cikin harkan don ashe ita ce ta tayar mashi da hankali ya mike jiki ba karfi ya fice dakin. Can ta samay shi ranan dai sunyi bala,i sosai yace ai ita ta fara tunda nace zan rama sai ta kyale ni da ta kyaleni bata fito da cin mutunci ba yasan da ban karbi girki a yanzu ba. Dare yayi da kaina nakai mai abincin shi na zauna sai da ya gama na kwashe kayan yace ina yaran suna daki na bashi amsa fuska a daure murmushi kawai yayi yace a can zasu kwana ne ? Nace tare da wa nima ai ba anan din zan kwana rashin mutunci tai min nima na rama in nuna mata ba tsoron ta ake ji ba nasan da gangan ta take iskancin ta. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: An buga ma yan uwa da abokan arziki zancen haihuwana na kusa da na nesa sai kiran waya nake faman karbawa na mutane. Sallama akayi a kofan falon za a shigo duk muka maryam da hankalin mu wurin mai shigowa da sallama da murya a natsune haka. Wata bakuwar fuskane daga cikin buzayen mai sallaman tana gaba rike da hannun Ihisah sai wata daya dake bayan ta sai daga bana ya fadi don ganin kamar su da Nafisa da yaiwa take na daure fuskana don ganin su. Bani kadai naga wanan kamar ba duk wanda ke falon ya san Nafisa yaga kamarsu da wanan buzuwan wani sallaman ta kara muna a karo na biyu muka sake karba masu. Ihisan ce ta shiko gurina ganina rugumay da baby a hannuna tana fadin anty baby babyan mu ne nace eh Ihisan banganki ba tun da kuka dawo sai yau. Wuri momy ta basu suka zauna mai kama da Nafisan bata zauna ba saida tayi bissimillah a tsigar kamala takai zaune. Tare da fara gaida mutane da ta samu a gurin tace dani kece maijegon nace eh tace tubarkallah masha Allah Allah ya raya muna su akan tafarkin addinin musulinci. Allah ya tsare mina suna daga duk wani aikin shedan daga mutun ko aljan da duk wani abinki masheranci muna fadin Amin. Tace munzo mun samay ku lafiya don muna zuwa washe gari sai mukaji haihuwa nace bari mu barki ki huta sai mu shigo mugaida ke. Nace na gode dan shiru ne ya biyo falon sai ihisan dake zuba surutu wai a bata baby ta dauka nace ina Samira sai matar tace tana kwance gajiyan hanya ya saukar mata da zazzabi jiya. Allah sarki gaskiya dai banganta ba tace eh ai tana yawan ban labarin ki sosai tace kina basu abinci mai dadi kina dai kyautata masu sosai. Yarinyar dake hannun maryam ne ta danyi kuka kamar irin mafalkin nan da yara kanyi tace idan sunyi haka ku karanta masu kalman sha hada a kunnen su kunnen hagu kuma ai masu auzu billahi mina shetanin rajjim. Ki dinga shafa masu man zaitun sai da dare idan zaku kwanta ki shafa masu man habba da safe ma hakane don kariya daga duk wani abin sherin daga gare su. Nagode nace tace ba damuwa Allah ya raya ya inganta cikin hausan su na ayan Niger take magana mai kama da kananci ko sakwatanci. Mikewa tayi tana fadin mun gaishe ku dama nace bari mu shigo mu gaisa muyi barka kuma to na gode sai dai ban sanki ba gaskiya. Tace tana dariya wanan ne karona na farko da nazo Nigeria a Niger nake aure mijina ya rasu shekara biyu ke nan yanzi na dan zo ganin ku ne in koma kwana biyu. Nace munko gode wallahi tace ba komai nace baki dauki yaran ba don naji nauyin matar sosai ganin kamalanta ya cika min ido tace a, a barsu har gaba ai muna nan daku kwana biyu. Dayan matar tace wa Ihisan tazo suje tace ki barta mana tana wurin uwarta ne ai sai dayan tayi yare sai ita ta juya da hausa tana fadin. Za a rabata da yan uwanta ne wanan ai duk shirmay ne don sune dai nata din kinga don Allah mu tafi maryam tace baki dai fada muna sunan ki ba har yanzu. Tace hakane sunana Fatiha wanan kuma Zakiya ita ubane muka hada da ita amma uwarta ta rasu ita ta kare karatun ta ne batayi aure ba niko nayi aure har ina da yara biyu sai dai basu tare dani suna gurin mahaifiyar uban su can Cameron don acan nayi aure. Da fatan zamuji dadin kasancewa daku na dan lokaci a gidan nan nace insha Allahu mun gode kwarai tace sai mun kara shigowa ke nan. Suka fice tare da rufo muna kofan a yadda yake kowa gulma ya cishi a falon marym ta fara magana tana fadin ikon Allah ashe akwai na Allah haka a cikin su ? Momy tace haba maryam akwaisu ma sosai kuwa ai irin masu shigowan nan jahilan su ne da talauci yaiwa katutu suke shigowa nan. Ko a cikin sun kuma akwai na kwarai sosai laraba tace itace mai ibandan nan dana fada maku ko yaushe ka wuce su suna sallah ko karatun kur,ani a falo suke zama abinsu har dare. Ikon Allah gashi kuma abu daya suke da Nafisa ita ta fito daban inji ya Amina sai momy tace haka abin yake ai wani lokaci. Mun kai wani lokaci muna hira a kansu kafin in mike zuwa cikin dakin in kewaya koda na fito ban koma falon ba wurin su na zauna a daki. Ya Amina ne ta shigo dakin tana fadin in hada maki tea ki shane ko kunun zaki sha nace bani kunun don yai min dadi sosai. Tace Adam ya bugo waya kin kewaya nace sai yanzun zai kirani ai nayi fushi wallahi tace ke ko ai ya kirani jiya da muka iso mana. Muna zancen shi ne wanan matar SJJ ta fado min a rai nayi salati nace kinga na manta da matar mutumin nan tazo nan kafin in haihu kwanaki har taban layin ta tace idan na haihu in sheda mata kinga na manta ban fada mata ba ko. Tace tazo gidan nan fa nace wallahi tazo har da kudi maigidan ya bayar a bani sai dai ban karbi kudin su ba nace don yaya Adam ne nayi masu hanya. Tace amma dai Khadija nan don may baki karba ba su wayan nan ai ko nawa ne baki ragesu ba wallahi bacin ribar ma da sukaci dake ai da kin karbi abin ki wallahi. Nace haba dai ya Amina sai kace ba training din ki ba da su daddy don may zan karbi kudin su haba dai tace kirata don Allah ko don in santa ma don ban santa ba Allah yasa tana kasan ma indai itace bata faye zama nan ba sosai kullun tana waje. Kunun da ta zuba min nasha sai na dauko wayana na danna kiranta watace ta dauki wayan mun gaisa nake fadin nice sister din matar Adam. Tace ok wacce muka zo gidan ta da anty ko nace eh anty na kuss ki fada mata na haihu jiya tace masha Allahu anty ko tayi tafiya amma zan kira ta in fada mata insha Allahu. Mukai sallama bayan tayi min barka muka kashe wayan Altine ta shigo dauke da kwanan abinci ta dire min a gabana sai da naji gaba ya fadi sauko ki ci kada huce nace anty ba yanzu ba yanzun nan nagama shan kunu kinga kofin nan. Tana kokarin bude kulan ta zuba min abincin tuwon farar shikafa da miyan shuwaka sukayi naga tazuba da yawa na bata raina nace haba anty ina zankai wanan abincin haka. AA ne ya shigo dakin fuskan dana bata yake kallo Altine na fadin duka zaki cinye shi fa yace bazataci abincin bane ko may naga ta bata fuska ? Nace haba yaya ya zanyi in cinye wanan abincin data zuba min yace haka kuwa zaki cinyesa duka sai kun kula don bata cin abinci sai kayan kwadai. Cikin marairaicewa da yanayin shagwaba nace ni dai wallahi ana takura min mafarin a saka mutum yin babban tunbi ke nan. Yace tunbi kan ai tunda diya biyu suka fito a cikin ki sai kin yi shi in zakici abinci ki sauka ki ci Altine tace kaima baban jegon in dauko ma filet ne a zuba ma yace Altine kamar kin san tun safe ban karya ba wallahi. Tace kana may haka har wanan lokacin tsohon su bakaci abinci ba ina momy taji dan ta bai karya ba wai har wanan lokacin. Yace wallahi muna can wurin kai wanan matar asibiti ne ashe a cinya ta kare fa da kuma kafa abindai ba a magana wallahi. Nace wai garin ya ta fadi ne tayi wanan kariyan haka yace abinne ikon Allah tace wai taga kamar abu ya gitta a gaban ta sai taga duhu bata san lokacin da ta fadi ba. Altine tace mugun abin su ne ya koma masu balle tagwaye da kofi yace nima dai abinda nayi tunane yanzu ke nan wallahi don yanzun na dawo security ke ban wani abu wai a jikin ta ya fado lokacin da za a dauke ta. Altine tace kaga abinda nake fada ma jifa muna tsaye dakai kasan kamar an kifa ta a kasa ne yadda ta fadi kofin yaran ne ta gani ba wani abu ba. A nan zakaci tare da matar ka ko a hada ma naka akawo ma karkuma buzuwan matar ka tace an mata shishigi yace indan ma tace bani zatayi yaushe ma ta zauna gidan balle ta dafa. Tana can suna zancen wanan matar na barsu can nayi masu abinda zan masu tunda a gidana ta fadi na barsu can. Yusuf yana tafe yanzu ya dawo zai karaso sai muci daga falo momy ta shigo dauke da yaron yafi fitina sosai tace khadija sai fa kin karawa yaron nan nono yasha don tun dazun yaki shiru. Na tabe fuska nace momy a bashi ruwa don Allah yace saboda may za a bashi ruwa ko nono sayarwa zakiyi ne ? Karban yaron yayi daga hannun momy ya dora min a cinya na yana fadin gyara ki bashi ya sha kinji. Raina bata sosai ya Amina daga inda take zaune tun shigowan shi dakin batai magana ba tace dole sai kin daure kafin su saba don ita kamun nan take jiwa zafi. Dukawa yayi bai damu da suna dakin ba yana kokarin bude min riga nayi saurin budewa shi ya gyarawa yaron kai ya tallabo shi ya sa mai nonon a baki yadda zai iya kamawa. Shi kuwa yaron ya cabe ya kama ja ban san lokacin da nace wayyo Allah na ba don zafi cikin tsigar lalashi yace min daure zafin zai bari na dan lokaci ne kawai yana rike da kan yaron ya duka yana kallon yadda yaron ke shan nonon. Ya samu ya zuka sosai ina faman runtse idanuwa na don zafi da nake ji har cikin raina yana ganin yaron ya kama da kyau ya mike tare da fadin barin dan shiga ciki in fito idan Yusuf ya karaso. Ya fice daga dakin momy tayi murmushi tace ikon Allah komai nason kwanciyan hankali wallahi ji babangida kamar bashi bane ke wanan abin. Altine tace gaskiya tsohon ku ya sauya gaba daya wallahi gashi yanzu har za a sake dashi ayi hira da komai dashi ya sauke wanan jin kan nashi na da can. Momy tace yarinyar nan ai ba karamin kokari tayi a cikin ruwan sanyi take ganar dashi hanya ba a garaje ba indai mace zata iya bin namiji a saukake sannu sannu zasu kai ga manufan da ake nema. Ya Amina tace yanzu idan mace na samun itin kulawan nan ga namiji mai zai dame ka kuma da zancen wani kishi can indai za a baka hakkin ka. Hakkuri ai bai bar komai ba yanzu datayi hakkuri gashi Allah ya bata wa yan nan yara haka masu kyau dasu da sha,awan dauka. Samira ne ta shigo dakin da sallama sai da nayi mamaki nace Samira ashe baki da lafiya ne ta zube a gabana tace anty wai kin haihu nazo in ga baby ne. Yaron dake hannu na take dan tabawa tana mai wasa ta dago tace ance biyu kika haifa anty nace eh ga dayar can hannun maryam ta juya tana kallon ta daga inda take durkushe ta juyo tana fadin so cute . Anty yaran nan nada masifan kyau sun fi baby Ami kyau sosai nace itama tana da nata kyau din ciwo daine ya mayar da ita hakana ai. Tace hummm that mumu girl sai kuma ta bata fuska tana fadin zanci abinci anty nace tuwo ne fa kin ga kalar shi ta dan ya mutsa fuska sai can tace zanci a ban . Nace baku dafa abinci bane tace wai Ami ta wuce da key din kitchen kin sai ance that madam ta fadi and she break her leg . Allah sarki nace mata tana mikewa daga durkushen da take tace anty kina tausayin ta ne ke ni ban son ta muguwa ce sosai ita da Ami yau naji suna magana kan twins din nan fa zasu kashe su ni kuma ban yarda a kashe yaran nan masu kyau haka dasu su kashe momo din Amin dai amma ba wanan ba. Bani ba duk wanda ke dakin sai da hankalin shi ya daga nace cikin karfin hali ke Samira kada ki masu shiri tace wallahi anty naji ne sai Amin mu ta kore ni dakin. Nace ikon to Allah ya tsare laraba na kira nace a ba su abinci har da sauran dake part fin Tin samira bata fita dakin ba Altine tace suyi a hankali don sun fara ganin kohin tagwaye a kan su tun yanzu in sunce sheri suka iya sun kai karshe ai. Yarinyar dai ta kalle ta ta fita dauke da abincin da laraba ta mika mata momy tace wanan zancen ba na kyalewa bane fa babangida zanwa magana ya binkici yarinyar yaji komai wanan karon. Don gaskiya ba maganan kyalewa bane wanan don mutum mugu ne tunda tayi niyar masu cuta tasan duk hanyar da zata bi ta cuta masu din Nace anya ko an fada mai zai yarda don kirikiri yasha kamata da makamancin case din nan ni banga yana daukan wani mataki ba akanta sai ma abinda ya karu don agaban shi sai tayi ikirarin halaka mutum bai kuma daukan matakin komai wallahi. Altine tace ko ba zai dauka ba wanan kan dole a fada mai komai don ya sani ya bincika yarinyar yaji da kunnen shi mana. Momy tace kai abin ne da daure kai wallahi ya Amina tace momy kun san fa ba banza ta barshi ba wallahi aikin banza nayin haka ina sai dai asiri kan inji maryam. Tare da Yusuf suka shigo part din falo na fito na samay su Yusuf yana min barka tare da yaba kyaun yaran sosai Altine ce tace dama kai muke jiran shigowan ka tun dazun. Yace shi tace eh sai momy ta karbe tace dazun muke jin abin mamaki a gurin yar nan diyar Nafisa babban sai Altine tace yar agolan gidan ka dai. Kai ya girgiza yace ke baki barin sheri dai momy ta kwashe abinda mukaji a wurin samira din ta fada masu bude bakin shi yace kai shine abin damuwa momy ? Nafisa bata da hankali wallahi zafin kishin ta ne kawai amma may zata iya yiwa yaran nan don tasan ba kyale ta zanyi ba itama. Yusuf ne yace a, a AA wanan ba karamin magana bane ya zama dole wanan karon ka nuna mata an fasan abinda take yi kafa san halin Nafisa sosai wallahi don may zaka tsaya yin gardama kan abinda ka sani kuma. Shiru yayi yana sauraren maganan kowa yanzun zan bikici yarinyar inji komai kafin in mata magana sai lokacin na sauke ajiyan zuciya jin zai dauki mataki akan zancen. Abinci aka fita masu dashi yaci sai da ya sallami Yusuf yazo ya kira Samira cikin dabara ya fito mata da zancen ya shiga jin har abinda bai tsamani ba daga gurin yaran yana recoding a wayar shi. Ta dawo yawon gantalin ta a falo ta zube karfe takwas da wani abu tun safe da ta fita abin ya faru da madam suna can wurin jinyar ta. Ya sauko daga sama fuskan shi a daure yace ina kika fito a wanan lokacin tace amma dai kasan abinda ya faru da madam gidan ko ? Na sani sherin ku ne da kuka dauko ya fara fada maku ai tace ban gane sherin mu ba yace Fatiha ina son ku saurara kuji ya kuna oudio daya dauka na hiran shi da yaran ta. Ba Nafisa ba har yan uwanta da yanyala kanwar uwarta sai da suka kadu dajin komai tiryan tiryan yadda ya fara tambayan yaran yace kuga sabbin kannin ku ko yaran suka ce mun gani Abbi har biyu suna ta shirmay su yana dariya. Yace ai za a sace maku sune Ihisan tace in kashe wanda zai sace su in yanka shi sai Samira tace ko Ami ban yarda ta kashe su yace takashe su kuma samira tace eh Abbi naji suna magana da Madam din nan ai ta kwashe komai ta fada mai. Oudio na karewa ya dago kai yace may zakice kan wanan yar uwarta ta hawaye yazo ma tace amma ke kan halin ki ya fita daban a cikin mu. Ban san may kika dauki duniyan nan ba wallahi shiyasa nace wurin bakar bidan asirin ki kika dauko yar nan dakika tsana. Tace Fatiya kada ki fada min maganan banza don bake ke min zaman aure ba zan shigo kasar su ina bare su kyale ni ne ? Don wanan hiran yara da ya dauka har zaki dauka gaskiya ne in shirya masu akayi suce haka kafin a dauka fa baki tunanen haka ke ? AA ya kaleta yace nine zan shirya maki sheri ko may yace bari kiji wanan recoding din zai kashe ga hukuma ne yanzu don su sani ko ciwon kai daya daga cikin diya na yayi wallahi ke ce. Lokacin da kuke kulin sherin ku idon ki ya rufe da bakin kishi kin manta da yaran suna kusa dake bakin san abinda kike fadi ba. Su yarane suna nan suna koyi daduk abinda kike yi a gaban su don haka ba zan lamunci wanan ba ga diya na ita Samira yar kice komai zaki koya mata banki ba don yarkice nai maki kara kuma a kanta. Fatiya tace yanzu dai wanan kadai ai ya isheki ishara don babu abin kunyan dayafi wanan idan mutanen nan suji wanan zancen fa. Yace yaushe kuma shiyasa suka hana mata yara an mayar dake mujiya maciya abin tsoro don sherin ki ta harzuka tace suji mana suma ba sherin suke min ba. Ko ban san abinda take aikatawa a gare ni bane har canza min diya a ciki da tayi na sani amma baka dauki mataki ba sai wanan zancen yaran zakazo ka tsure ni da zancen banza haka. Yace an cen za maki ya kamar yaya cikin tsure ta da idanuwan shi yace kowa yaga yaran nan ansan ba nata bane wallahi diya nane ta sa aka sauya mata zuwa nata. Kana dauka zan yarda da hakane ko may yace Nafisa anya baki da tabin hankali kuwa kin san ko abinda kike fada nan dai kanwar tayi mata kaca kaca tace gobe zata koma Niger ina zata da wanan abin kunyar haka ? Azo ana nuna su a tare kishi haukane ko may kin samu gidan da zaki huta mu huta rashin hankali ya hana ki kwantar da hankalin ki. Cikin murje ido taciwa yar uwar nata mutunci tace ta tafi mana an tsare ta ne nan dama bata isa ta nuna mata ga abinda za tayi ba. Don ba ita ke mata zaman auren ta ba ya mike yace zanyi maganin ki don haka ki shirya ki koma kasar ku don ba zan zauna da wace bata tsoron Allah ba a gidana. Nan dai su fatiya suka shiga bani hakkuri da ban baki suka farar mata dole tayi shiru ya fice gidan gaba daya. Duk abinda ya faru akan idon laraba itace ta shigo tana bada labari hankalin shi ya tashi sosai har yaji auren nafisan gaba daya ya fice mashi a rai. Mun ci gaba da hada hadan shirin suna wanda maryam bata da hutu itace ke zirga zirga ka karatu AA da kan shi yace ya daukar min excuse a school inda suka ban sati biyu. Yana jin dadin yadda yake shigowa gidan ya samu ana ta harkan arxiki da raha da dariya sai yake ganin gidan tankar ba nasa ba. Part din nawa yayi masi karami don haka Altine ta mayar masu da zama can babban falon gidan inda gidan baya tsinkewa da kafar yan barka. Abokan karatuna sun zo min barka lokaci daya suka hada kafa akazo don akwai hadin kai sosai a tsakanin mu lokacin Nafisa suna zaune a falon su ma. Har falon gidan daya sha gyara kwana biyu da haihuwa an canza har labulayan falon da kujeru duk da ba a dade da suraj yasa aka gyara ba amma AA yace dole su sake wasu don bakin da ke shigowa barka. Bayan sun ga yaran na fito muka gaisa dasu suna min barka da ba,a suna kirana da maman twin's. Maryam ta dauko drinks ta kawo masu da zasu tafi suka bada gift din da suka zo min dashi matan sunce sai sun dawo suna su nace ko wanan ma na gode. Tana zaune daga barin part din ta da yan uwan ta ganin yadda muke harkan da course mate dina ta tabe baki har suka fice ana wasa da dariya bayan sun dauki babies din. Nan na dan tsaya muna hira da Altine sai naji tace idan da mutum bai haihu bane zai ga takaici saukin abin dai nabaya aka samu. Murmushi nayi na girgiza kaina tare da fadin banda lokacin ki don ba finane yanzu a gabana ba abin arzikine a gabana. Nasani ai tunda kin shiga kin fita kinyi musaya diyan da ba naki bane kowa ya duba ya sani ban san lokacin da Altine ta shigo ba tace kai amma ke katuwar jahilan inace haka. Ke a tarihi kin taba jin wanan zancen naki na masu tabin hankali kinje gun tsafe tsafen kin sun fada maki karya tunda yaran ki ne ta juya zuwa nata sai kiyi yadda zakiyi ga yaran nan a gabanki ai. Ke wai wa kike ne a cikin wanan zancen yar kalan dangi kawai na fada ko kun dauka bamu san komai bane tace a,a kin sani don naga alama tai mata alaman mara hankali da hannu. Wasa wasa fadan su da nafisa yayi tsawo ranan Nafisa taga tujara taga zari agurin Altine yar duniyar mata don da wanda tayi da kazafi duk ta hada mata sai ga Nafisa na kuka da hawayen ta wai yan uwan Samad basu kaunar ta basu kaunar diyan ta. Tunda ga Altine ta sheganta mata yaran da ta haifa dashi yau ya dawo ya fada mata matsayin ta a gidan dana diyan ta. Da kyat dai su momy da yan uwanta suka samu suka rabasu ni dai har na gaji na shige ciki na bar gurin don ban iya tsayawa sauraren su. AA ya dawo ya samu sun lafa Nafisa ta same shi yace ke ki barni da wanan haukan inji da abinda ya samay ina fama da abinda ke gaba. Yana ce ta fice mai daki bai son kananan magana diya dai diyanane ba na wani ba tace ai baka damu da yaran ba wa yan da ka damu da zuwan su gashi kana rawan kafa an haifa ma yan gwal. Ke may yasa baki haifa min ba in rawa kafa kan su kamar wa yan nan din yace ya kara hasalata nayi rawan kafa don an haifa min abinda ke kika kasa samar min a gidana. May na kasa samu kana nufin namiji ai duk rawan kan da kuke nasan don shi ne kukeyi haka yace yan gwal din dai da kikace an haifa min. Kinga rashin kyau gori ba abinda baki fada ma yarinyar nan ba a gidan nan kan haihuwa tana hakkuri da Allah ya tashi nuna maki abunki sai gashi ya bata biyu a lokaci daya kuma kyawawa har sun saki hauka. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: As usual na tashi tun da safe nayi wanka na shirya tsab dani kafin in fito laraba ta shigo min da abin karyawa ta aje sai dana gama shiri na zauna don shan kunun kanwar da yanzu na saba sha don nafi son shi da tea. Altine ne ta shigo dakin zata dauki kayan yara ta kaiwa momy da tai masu wanka take fada min ga yar uwar Nafisa a falo tana magana dani. Nace tace ta shigo daga ciki can sao gata ta shigo da sallaman ta fuskanta dauke da fara,a tace maijego sai kunun kanwa ina aje cup din nace Anty Fatiha kece ashe tace eh. Ban samu shigowa ba ranan da aka kai muna kayan buki don jama,a sunyi yawa a lokacin nace kai haba ba komai ai muka gaisa ta tambayi yara nace ana masu wanka ne a dayan dakin. Tace to idan sun fito ki shafa min kansu Allah yai masu albarka nace amin na gode sai naga ta gyara tsayu nace bissimila zauna mana tace ba sai na zauna sai dai magana nake son muyi dake dama. Nace to ai gani tace don Allah ina fatan zaki fahince ni ki fahinci zuciyana kuma nace insha Allahu. Tace kin san zama da mai ilimi da wanda baida sai anyi hakuri don zaka ga wanda bai da ilimi yana abu wani lokaci kamar zararre nace gaskiya. Tace kiwa Allah kiyi hakkuri da yar uwata uwar mu daya uban mu daya amma mu kan mu mun sani abinda take bata yin sa a kan gaskiya. Duk wanda ya yarda da Allah kuma yai imani dashi ina tabbatar maki baya taba tabewa a duniya Dija nasan kina da ilimin zamani dana addini gwargwado kima bazamu ce duk ba don kowa dan koyo ne. Nace gaskiya ne tace a gaskiya ga abinda dan zama na ya hango min a gidan nan dan zuwan danayi na zauna daku din nan. Na fahinci dukkan ku kuna da rauni sosai kina sani fa ba mai iya maka wani abu a rayuwan ka bayan Allah in ma har wani abu ya samay ka tabbatar wanan abin kaddararene a gare ka dama kuma bamu iya kauce wa kaddaran mu. Zaman gidan nan yana bukatan gyara daga gare ku ko in ce daga gareki ki tuna abinda ya kawo yar uwana gidan nan shiya kawo ki ke ma ta yaya zaku zauna kuna kona kanku saboda son zuciyar mutum daya tak. Ta girgiza kai tace gaba dayan ku gidan kuna tsoron ta har mijin naku an san akwai asiri tabbas yaci annabawa Allah balle mu da ba kowan Allah ba face bayin sa. Kina da makami a tare dake kin iya karanta shi don may ba zaki bi dare kibi rana ba wurin kwatoku har ita daga halaka. Ki dage ki bata duk wani lokacin ki kina da dama yanzu ba sai kin dauki Alkur,ani maigirma ba a hannun ki yanzun ne lokacin da kike hutawa ki dinga aikwa ubangini kina fada mashi matsalolin ku sai ki ga sauki ta inda baki zata ba. Amma duk kun biye mata ana wai asiri asiri da ita dake zuwa da wanda ke mata wakeyi in ba Allah ba ba wani abinda zata iya maki muddin kin koma ga Allah . Ita kanta wallahi tasan kinfi karfin ta ga komai yanzu don ta fada na sani kuma haka ne mutumin da kullun kake binshi da sheri munana yana tsalkewa ai kasan yafi karfin ka. Kada kiji ina wanan magana ki fassara min magana da wani manufa ina yin shi a matsayin ku na yan uwana musulmai har maigidan na zauna dashi jiya na fada mai inda yake da kuskure da rauni ya kuma fahince ni . Da fatan ke ma zaki fahince ni na barki da saura a zuciyar ki sai ki nemo mafita amma ku gyara gidan ku don Allah inda kake fa shine wurin ka ba nawani ba. Tana fadin haka tace nagode da kika bani lokacin ki kuma kika aurare ni da fatan zaki kula da abinda nace ma,assalam. Tana fadin haka ta juya tafita daga dakin ajiyan zuciya na sauke tare da fadawa tunanen abinda tace min din. Ya Amina ne ta shigo nake fada mata yadda mukayi da yar uwar Nafisa din tace ikon Allah Allah daya gari bambam ke nan. Gasu uwa daya uba daya amma yanayin su ya bbambamta wurin hali ai gaskiya ta fada maki ba karya a ciki kjadija wallahi kija mijin ki a jiki yanzu ki nuna mai so. Ba dai inda zaki yanzu kibar wa yan nan yaran wa wata ta rainar maki su da wani tarbiya na daban don haka wallahi khadija ki sa tsoron Allah ga alamarin ki ki bar wanan wautar da kike ki rugumi mijin ki da yayan ki kin dai ji abinda mama Tani ta fada maki ai. Ga yara kamar diyan larabawa kyawawa dasu kamar mutum ya sace uban sai rawan kai yake yana alfahari da abinsa ko da kike cewa wai bai damu da yara ba wallahi nikan naga ya damu da wayan nan sosai. Idan ya shigo ko hannun wa suke sai ya taba su kafin ya fito don yaran akwai su da shiga ido shiyasa mama tani tace a dan saka masu zuben azurfa don bakin mutane naji maryam tace zata nema masu sai ki tuna mata. Hmmm nace nama rasa abinda zance sai na juya da fadin ya Amina ki duba kayan a fitar da wanda zasuyi amfani dashi yanzu zannuwa kuma sai ki cire min wanda kika ga ya dace saura a fitarwa laraba da Altine da mommy sai a cirewa hajiya mama ita ma. Tace wanan aiki bari har maryam tazo don ba zan iya ba ni kadai wallahi kayan ne gasu nan kamar shago za a bude. Gaskiya mijin ku yana son ki wanan buzuwan ne dai kawai da tai maku shamaki tsakanin ku da ba karamin abu zakuyi a gidan nan ba. Wayana dake ruri ya dakatar damu na duba sai da na kalli ya Amina nace hajiya mamace fa ke kirana. Na daga kiran da sallama muka gaisa tace kun tashi lafiya khadija ya su takwara na dasu momy ku da sauran su nace suna lafiya mama. Tace dama na kiraki ne in tambaye ki may ke faruwa a gidan ku don Nafisa ta kirani ta kuma kira Alhaji a karo na farko ta kawo karan ku wurin mu. Murmushi nayi nace mama may tace kuma mun yi tace eh to ke dai lafin ki shine wai kince zaki karbi girki yanzu shi kuma mijin naku wai yai maki abinda bai mata ba idan ta haihu. Alhajin ya nemi layin shi a gabana ya kirashi yai mashi bayani yadda abin yake wai idan zata haihu jinga sukeyi ashe ya bata kudin komai da komai daya shafi haihuwa. Yanzu kuma da taga a girin ki ba haka abin yake ba shi yayi komai bugun gaban shi shine take kiran shi da azzalumi da macuci. Sai naki matsalan yace itace ta fara yin hakana yanzu kuma kema kika ce zaki rama nace hakana ne mama tace to kinga aikin gagawa inda yake kai mutum ai. A lokacin ita gani take dama ne ta samu na yin duk abinda ta ga dama bata tunanen abin da zai je ya dawo gare ta yanzu gashi tayi a lokacin taji dadi yanzun kuma na wani yazo tana yin korafi. Abinda nake so daga gare ki shine ki natsu don Allah ki dubi yaran ki kada ki biyewa shirmay ta ku koma daya da ita ki dauke idon ki ga komai da takeyi a gidan kinji ko nace naji mama na gode. Mun gama wayan na kalli yaya Amina tace wanan bata da hankali wallahi yaya zaki kira sarakanki da wanan magana bayan baki da gaskiya ta ko ina. Nace ya Amina wuyan sha,ani ke gareta ga wanda bai gane halinta ba idan tayi tana jin dadi yanzu ramawa ai sai taji zafi lokacin da ta karbe kudin ta wa ya sani. Tace wanan ko yadda yai maki din nan yafi zafi ba don ko kudin daya bata masu yawa ne dole taji zafin ganin abinda ya sai maku don zaku dade kuna amfana dashi . Ita karshe ma kila kudin a banza zai tafi gun bokaye da malamai nace tun yaushe wallahi ni abinta ma yanzu ya daina bani mamaki sam. Ita fa yanzun na fahince ta gaba dayan mu bata son kowa ya rabe shi ne sai ita kadai ko uwar da ta haife shi tana kokarin nisanta shi dasu ne dan kowa bata son ya raba shi. Yanzu ai sai dai ta mutu don karshen rabuwa har da rabo biyu a tsakani ai kinga dole ta ganku tare munyi hiran sosai karshe muka koma hiran maryam tana yaba kirkinta gare ni. AA ne ya shigo dakin ya Amina ta fice wurin su momy yanayin shi ya nuna daga barci ya taso lokacin nace ina kwana daga inda nake bai amsa ba sai da yazo kusa dani ya lakutan min hanci yace . Shine kika shayani jiya ina jiran amaryan jego tazo tayani kwana in sha karni murmushi nayi nace wane ni in ka ganin dakin ka mun yi arba,una ne. Yace kai mata nace ai itace ta fara don haka kar kaga laifi na yace banga laifin ki ba ga hakan tunda bashi kike biyan . Dan kallon shi nayi nace haka ka dauka ko yace tunda anci gashi zaki karba kuwa tunda kin iya daru ke ma. Nace ni har wani daru gare ni ka san dai inda daru yake yace darun ki a cikin ruwan sanyi kike abinki babu fada balle hayani don haka yanzu nake tsoron fadawa tarkon ki. Murmushi nayi nace sunan da na samu yanzu ke nan kuma aina gode tunda shedan mai sauki akai min. Ya dan jima a dakkin muna magana akan sunan da taron da akayi muna kafin ya fice a gurina a falo ya samu Nafisa da yan uwanta zaune suna duban waya. Jin motsin shi ya fito yasa su daga kai suna kallon shi Ihisan ne ta mike zuwa wurin shi uwar ta daka mata wani irin uban tsawa sai da yarinyar ta kado. Da mamaki ya kalleta yace don may zaki hanata zuwa wurina tace don ni ke da yata ba wani ba yace ok ashe yar taki ce ke kadai kin san inda kika samo ta ke nan ? Yau ka fada min abinda dana dade ina jiran ji daga bakin ka kamar yadda yan uwanka suke fada min game da yarana a gidan nan. Fatiya ce tayi gyaran murya ta katse lazumin da take yi tace wanan wani irin abu kuke haka gabsn yara ko da yau kuke na kulluyaumin gidan ku babu zaman lafiya sai anyi fitina kamar kananan yara. Yanzu ina amfanin wanan abin kece fa kika fara jan maganan nan ya baki amsa kince ina yafito kima kanki fada don Allah yaran ku girma sukeyi suna ganin abinda kuke yi. Tace oya Ihisan jeki gurin Abban ki kinji yarinyar tana kallon uwar su don tsoro yace ta zauna abinta fita zanyi ya kalli nafisa yace kin kaini bango yanzu kan ya fita. Tace ba laifin ka bane laifina ne dana yarda na nuna maka son kwarai har cikin zuciyata yanzun kam ya kare ai. Kai Fatiya ta girgiza mata ta hau yar uwan da fada a cikin yare don laraba dake falon tana gyaran bangaren mu. Zama tayi tana tunane a ranta bayan fitan shi wai itace kuwa Nafisa ita nafisan da suke rayuwa kamar ba gobe da mijin ta tana juya abinta yadda take so. Ya gwada ma yar da tazo dashi gata har zuwa Ihisan dinta yanzun tana kokarin zama dodo a gare shi akan wata wai ita ake wa haka akan kishiya da take ma kallon bata kai mace ba. Yau tana kallo ba dan ta rasa kudin yin sihiri a gareta tana ba kuma rashin masu mata aikin ba sai dai gani take abin baya tasiri a kan su ne yanzu gaba dayan su har samad din. Maganar da zatai mashi da ya bata hakkuri akan shi yanzu kafin ta gama fadi ya bata amsa gaskiya dole ne ta kara danmara a gidan ta ta gasa masu kwakwa a hannun su. Ya zama dole ta dauki mataki akan wanan yarinyar data shigo jiya jiya gidan nan tana kokarin ta taushe ta da karfi da yaji a gidan. Kwana biyu ya Amina ta tafi sai momy da Altine momy ma sati biyu kacal Abba ya bata da kyat ya yarda tai muna satin biyun ta dawo. Tafiyan ya Amina ya saukar min da kadaici sosai don kwana biyun da mukayi a tare ba karamin dadi nake ji a raina ba. Wucewan ta yasa momy ta dawo dakin ita da Altine muna zama Laraba ko ance ta shigo bata sake jiki a cikin mu sosai tafi gane ma zaman falo ko tana wani aikin. Gashi idan tayi wankin yara bata shigowa sai kayan sun sha iska take dawowa part din don dai kawai tsaron lafiyan su da take yi. Na samu hutu sosai don idan suna falo barci nake samu inyi sosai sukan kyale ni har lokacin dana tashi ko yaran suna neman nono. Maryam ko cewa nayi ta bude kayan ta dauki duk abinda ranta ke so ba wani kaya ta dauka ba sai turmin zani guda daya wai shine ya bata sha,awa a cikin kayan. Madam kafa ya kiya har lokacin tana kwance a asibiti tana jinyar kafan basu sani ba ashe daurin da akai mata bai dauru ba da kyau dole aka samce aka gyara wani sabon dauri din iya wuya ta ci shi. Ga rashin ganin kulawan da take Nafisa batai mata da takan shigo sau daya ta dubata har ta koma bayan kwana daya take shigowa gidan. Ya kai yanzu sai ta share kwanaki bata leko ta ba sun dinki da sabuwa aminiyar madam din na baya da sukai fada tana kwance labari yazo mata. Ta kudurta a ranta zatai wa Nafisa magana akan hakan duk ranan da tazo dubata din sai bayan kwana uku tazo a gurguje tana sauri tana wani sham kamshi. Bayan sun gaisa take fadin akwai ida zata sauri take yi madam tace dama ina son magana dake don naji wani maganan da tsamace shi ba a gare ki Nafisa. Tana wani taunan chewing gun tace ins jinki ai yanzu nafisa ki rasa wanda zaki hurda dashi sai sabuwa makiya na zaki dinki da ita. Nace tace may ye a ciki madam business ne fa dama tsakanin mu ba wai haka kawai kike min ba yanzun kuma kina kwance kina jiyan zama kike son inyi kar in nemi wanda zai haska min hanya ko may ? Ita ma sabuwa abinda kike min take min a yanzu kema idan Allah ya baki lafiya sai mu dora a inda muka tsaya ko ba shike nan ba. Matsalan ku da sabuwa ku ya shafa bai shafeni ba kowa kudi nake bashi yadda ya bukata yaje min guri ko ya rakani inje. Madam ta ce haka kikace tace ai haka maganan yake madam sai idan kin so juya shine a wani tsigar kuma wanan kam. Tana fadin haka ta aje mata dubu biyar a gefen filon ta tace sai anjima don ni akwai inda zan tafi daga nan kallo madam ta bita dashi tana kallon takon ta tare da kutawa . Ta raya a ranta sai ta dauki famsa in har ta mike akan Sabuwa da Nafisa kan abinda sukai mata din tace ai in kun san wata baku san wata ba dani kuke wasan. Tana fita ta samu sabuwa a mota suka dauki hanyan zuwa jos ranan suke son zuwa su dawo a ranan kuma a gida dai ta bar yan uwanta da yara tace dasu zata dan je wani wuri ta dawo. Bayan fitan da kamar awa daya sadiya ta fara kuka sunyi lalashi taki yin shiru tun suna lalashinta da girma da arziki har abu yafi karfin su. Sai ga Fatiha dauke da ita ta nufo ni ina falona lokacin ina cin abinci tace Dija ko zaki duba muna yarinyar nan uwarta ta fita yau dai sai kuka take muna mun rasa gane kanta. Karbar yarinyar nayi daga hannun ta ina lalashi ta muka samu ta dan yi shiru nace ina abincin ta tace bari ta dauko. Ta dawo dauke da feeder ta ta miko min a na dan bata taja kadan sai kuma taci gaba da kuka nace yau halima lafiya kike kuwa na fara dan taba mata jiki zuwa kai naji kan yai zafi sosai. Na dago nace mata ina ganin yarinyar nan bata da lafiya ne yau ina maganin ta yake a bata tace sai ta tambayi Yanyala. Ta fita da yarinyar kasa cin abinci nayi na wanke hannu na samay su a falon suna tambaban wanda zasu bata daga ciki. Karba nayi na karanta na mika masu paracetamol si bata ina tsaye ina kallon yadda suke bata maganin sai kuka yarinyar ke yi. Su goyata nace ko zata yi barci Yanyala ta fara fadin ko sun goya ta kanta ba tsayawa yake yi ba ai nace haba dai sai kusa abu ku tare kan ta baya mana. Fatiha ce ta goya ta na nuna mata yadda zata tare kan sai kan nata ya tsaya tana dan jijigata har tayi shiru barci ya dan dauke ta nace Allah ya sauwaka. Na koma part dina na shige bayan kamar rabin awa ta falka kuma kukan ta muna ji har part dina muka fito dasu momy falon muka samay su. Nan ma munyi munyi taki shiru momy tace su kira uwan mana wai sun kirata wayan baya shiga sai momy ta kira layin AA take fada mai abinda ke faru yace gashi tafe. Kafin yazo yayi ta gwada layin ta ana fadin not reachable sai ya kashe ya iso gidan ya samay mu a kanta ya tambaya may ke samun ta ne ? Suka ce haka kawai suka ga ta fara kuka momy tace jikin nata ai ya gashe ma ya dago yana tambayan Yanyala ina Nafisa taje ne tace tace masu zata nan ta dawo ta fita. Momy a shirya mu kaita asibiti yace a dubata momy ta shiga ta fito tare da yanyala suka tafi likita yace zazzabi ne da kuma karancin jini ke damun ta. Take aka bada gado ranshi idan yai dubu ya baci sai gwada layin ta yake faman yi baya zuwa shi ya dawo gida daukan abinda zasu bukata asibitin. Yana shigo yace wa Fatiya bata dawo ba tace ,a,a har lokacin bata dawo yake fada masu an ba yarinyar gado wai bata da jini a jikin ta. Tace duk kwanan tun da suka dawo gida yarinyar bata cika lafiya ba sosai ga uwar bata zama koma ta zauna ba nono take bata a kan lokaci sai taga dama. Ya shigo wurina yana fada muna an aba yarinyar gado mukai mashi Allah ya sauwaka ya dauki abinda zai dauka ya bar gidan ranshi a bace. Tara ya shigo gidan ya kara tambaya still bata dawo ba ya fita ya kira wayan ts yafi a kirga bai samu layin nata ba har wanan lokacin. Altine dasu Fatiya suka shirya zuwa asibitin don kaiwa su momy abinci tunda har wanan lokacin basu dawo gida ba shir shiru har guraren sha daya da rabi suka shigo har lokacin ba Nafisa ba labarin ta ba a san inda ta tafi ba. Tun yana jin haushi har ya koma fargaba idan ba wani abin bane ya samay ta can wurin bakin yawon ta don bai dauki wanan abin na kai sake ne ba. Inda momy tayi sallah ta kira hajiya mama tana fada mata halinda ake ciki ranta ya baci sosai ta kirashi a waya tayi mashi tas ranan . Sai ga su Altine sun dawo muna da labarin har yanzu ba a ga Nafisa kuma wayan ta baya shiga idan an kirata nan muka zauna jigun jigun damu a falona. Nafisa sun samu layi a gurin boka haka yasa suka bi sahun masu jiran su gana dashi din sai biyar suka samu ganin bokan shirgegen mushiriki dashi yana zaune daga shi sai lagen bakin zanin daya yafa a jikin shi. Ta fara bayani ya dakatar da ita ya kora masu abinda ke tafe dasu Nafisa irin su take so dama tace hakane boka shine mukazo wurin ka idan da taimakon da za a bani kanta. Boka naki jinin in bude ido in ganta a gidan nan yace kada ki damu tunda kinzo nan zamu diba mu gani a cikin karfin tsafin mu. Yadan yi surukullen shi ya dago yana dubanta tare da fadin kai haba dai gaskiyane kina aiki kamar bakiyi don wanan yarinyar itama hatsabibiyar kanta ne sosai. Nafisa tace haba nikan na sani idan ka ganta kamar ta Allah da ita ni dama nasan ba banza ta barni ba ya kada kai yace a, a ba yadda kike nufi bane. Ita irin masu baiwa din nan ne asiri baya saurin kamata gaskiya ga kuma tana da rikon addinin ta da wuya a aika mata ya samay ta gaskiya. Sai dai idan munce zamu mata aiki kema akwai aiki a gaban ki gaskiya don sai kin bar komai daya shafi naki addinin zamu samu aiki ya kai gare ta. Kallon juna sukayi da Sabuwa sai sabuwa ta kada mata kai Nafisa ta juya gurin boka tana fadin boka na amince da ko may ne zaka fada min zanyi. Don na tsani wanan yarinyar naki jinin in bude ido in ganta a gidan nan wallahi ya ki kwantar da hankalin ki tunda kin zo nan. Zakiga aiki maikyau sosai tace boka ko nawane indai bukata zai biya zan baka sabuwa tace ko akashe muna ita har yaran nata ko kuma a haukata ta tabi daji a manta da ita gaba daya. Boka yace irin su na fada maki ba,a zuwa masu yadda kuke nufi din nan domin Aljanin da zamu tura ba zai samu aiwatar da aikin shi ba sai ya samu bata cikin ibada. Ko bata sallah gata nan nagani tana yawan ambatan abin bautar ku koda yaushe a bakin ta gatanan anan gurin ina kallonta yace. Ya mika mata wani ruwa a dan wani roba fari na yought yana fadi wanan kiyi kokari yau din nan ki yayafa ida kika san zata bi daga ita har mijin idan kin samu washe gari sun taka. Yayi wani iri da hannuwan shi alaman mun raba hanya ke nan da AA yace ba sauran zaman lafiya a gare su karshe auren zai watse babu wanda zai tuhumay ki. Sai wanan ya mika mata wani dan kuli yace zaki gina rami daidai bayan dakin ta ki binne a cikin ramin ki kawo babban dutse ki taushe gurin zata dinga jin gidan gaba daya ya fita ranta ga baki daya sai ta barshi ba shiri. Wanan kuma a inda ake girki zaki saka da zaran zafin wuta yana dukan shi bata da kwanciyan hankali a zuciyanta tsana da ganin bakin mijin zata ji. Idan kinyi haka yau ba tare da samun akasiba ina mai tabbatar maki bata kai wata daya a gidan nan komai tsananin ibadan ta. Boka mun gode zakaji dasin aiki damu sosai nan gaba dama ai rashin sanin wurine yasa baka ganmu ba da tuni munzo ai. Sai dai ya matsalan mijin nata ne kai ya kada yace wanan gaskiya samun shi shima yanzu ba abune mai sauki gare mu ba don uwar shi tsaye take akan dan ta. Kai har uban ma yana tsaye sosai akan diyan shi amma da zaki iya samo muna dan kwalin kan uwar shi da kasan kafanta akwai aikin da zan hada maki zai ci sosai kuwa. Sabuwa tace boka mun gode in Allah yaso zakaji nan bada dadewa Nafisa ta balle jakka ta fito da kudi masu yawa don jin dadin abinda yai masu alkawari ta bashi tare da fadin sai sun juyo. Sai lokacin da suka fitone suka dubi lokaci hankalin Nafisa ya dan tashi don bata san gurin yana da nisa haka ba da ta dauko yanyala da yar Aljannan ta sun taho ta raya a ranta don haka take kiran sadiya dashi. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 1/2/21, 10:23 AM - Xxxxx: Garin Allah ya waye hankalin kowa a gidan a tashe yake tun shida da wani abu ya bargidan zuwa asibiti ya dubasu inda ya samu jikin yarinyar ya danyi sauki. Za a kara sa mata wani jinin na biyu ya dan dade tsaye yana kallon ta yana mai jin wani iri har cikin ranshi sosai. Yusuf ne ya iso ya samay shi a asibitin inda ya dan duba yarinyar kafin su fita zuwa police station su sanar da bacewan Nafisa din. Dawowan su asibitin yayi daidai da isowa tare da Altine da Fatiha munzo masu da abin karyawa ida nake jan motar da aka ban gift gidan SJJ . Tsayawa yayi da mamaki yana kallon mu yadda nake tuka motar cikin gwanan cewa da iya tukin bai taba kawowa a ranshi ina driveing ba da farko don ban taba nuna mashi iyawana ba. Sai da muka firfito daga motar na rufe muka nufo inda suke tsaye a cikin jimamay tare da gaida su inda muke hada baki gurin tambayan anko gano inda nafisa din take. Yusuf ne ya bamu amsa cewa wallahi har yanzun shiru ba a ji komai ba gamay da ita har na fara tafiya nace wai ba za a gwada tambayan wanan matar madan aji ko tasan idan taje . AA yace wanan dabaran bai fado min ba sam wallahi don shawara ne babba yace ma Yusuf suje su tambaye tana cikin asibitin ai. Suka nufi dakin da madam din take kwance sun fara gaida ita da tambayan ya jikin tace da sauki sosai sai tayi shiru. Yusuf yace munzo mu tambaye ki ne ko kina da masaniyar inda Nafisa ta shiga tun jiya da safe da ta fita ba a ganta ba har wanan lokacin. Tace cikin farga tun jiya fa yace kwarai sai tayi dan shiru ido suka kafe ta dashi yadda take nazarin wani abu a danta ke tunane a ranta sai can tace . A bunkici Sabuwa idan basu tare don jiya tazo nan da safe dubani tace suna sauri zasu tafi wani guri tare da Sabuwa bata tsaya ba tafita duk ko da nuna matan danayi yin haka kuskure na. Wacece Sabuwa AA ya katse madam da ta fara zuba cikin tsana tace wata aminiyar tane datayi sabuwa tana zama uguwar Nyanya ne. Ki muna kwantace idan kina da layin ta kuma ki bamu cikin rawan jiki tace ina da layin ta sosai kuwa bari in duba maku mu gani. Ta kira masu layin yasa a waya tare da danna ma layin kira sai dai amsa dayane kamar na wayan Nafisa din dai har itama. Kallon juna sukayi da Yusuf yace itama not rechable ke nan wani abu dai yana faruwa dasu duk yadda akayi. Kara kwatacen gidan Sabuwa tayi masu suka juya suka wuce batare da mata godiya ba sai AA ne da ya juyo yace idan a nason karin bayani zamu kara dawowa gurin ki kuma. Wani irin takaici da bakin ciki mai tatare da Nadama ne ya rufe madam a lokaci daya har kwallan takaici suka zubo mata tana kiyas ta wani a cikin ranta. Mun duba yarinyar shigowan likita yasa bamu wani dade a gurin ba ko da muka fito daga dakin motar su AA baya gurin nake cewa da su Altine ai anan ne madam din take ko ? Fatiya tace eh don ranan sun zo da dare sun gaida ita da yar uwarta muka sa kai zuwa dakin don mu dubata. Tana zaune da ganin idanuwan ta tayi kuka lokacin mukai mata sallama tare da gaida ita da mata ya jikin tace da sauki tana mamaki a ranta mai ya kawo mu asibitin wanan lokacin. Nace ya kafan da sauki dai ko tace da sauki ta gode na bude jakka na na ciro mata kudi na bata dubu goma sai ta fashe da kuka. Fatiya ce tace ba kuka zakiyi ba kiyi tawakkali ga Allah da kaddaran da ya jarabce ki dashi ai tace dole ne in kuka yar nan kuka dole ne gare ni ai. Wanan yar tai min abinda ban zata ba gashi duk da abinda nake mata tazo dubani da zuciya daya har da alherin ta gare ni haka. Ba komai nace da zuciya daya nake tare dakowan ku ni na juya tace yanzu maigidan ku ya barnan yana fada min Nafisa ta bata tun jiya ba a san ida take ba. Ni dai jiya tazo nan a gurguje to ba abin alheri bane inda zasu koda bata fada min ba nasan wani kawai zasu da sabuwa don yanzu itace sabuwar amiyar ta. May yuyuwa basu kasan nan ko kuma wani abu ya samay su a hanyar zuwa bamu dai fatan hakan amma ba a raba daya biyu daga cikin wanan dai. Fatiha tace kauye kuma suka tafi yin may tabar yarinyar ta jinjira a gida zata tafi kauye ta barta yar a gida. Madam tace ke dai Allah ya yafe muna kawai ni yanzu nayi na dama wanan karayar yaza min kamar ishara ne a kan duniya. Idan mutum bai nufe ka da share ba kace kai zaka nufa tun a nan duniya Allah ke nuna maka abinka yanzu ba sai anje can ba. Yanzu kudin nan da yariyar nan ta bani ya kara sa rayuwana a cikin nadama sosai wallahi muna binki da sheri kina saka muna da alheri. Murmushi nayi na juya na fara tafiya Altine ta biyo ni Fatiha muka tsaya jira a cikin mota ta fito muka dauki hanyar gida. Cikin mu babu wanda ya iya magana tunda muka fara tafiya har tsawon wani lokaci kafin Altine ta kawar da shirun da fadin ita wanan matar taga aya ke nan ga rayuwan ta ? Fatiha tace aini imanin su ya cika min zuciya mutane babu imani a tare dasu yanzu idan wani abu mumuna ya faru dasu a hanyar mai zasu fadawa Allah kan hakan. Har suka gama maganan su ban samu bakin magana ba ni kadai nasan abinda nake kiyastawa a raina wanda godiya nake wa Allah da bai min wanan halin na yawon bin bokaye da malamai ba wanda karshen shi nadama ne ke tare da mai wanan halin. A A kan zuwa ya samu gidan sabuwa a rufe ya kara tayar mai da hankali inda ya tambayi makwabta sukace tun jiya rabon su da ganin ta suma a garin. Sun kuma tabbatar masu sunga fitan su tare da nafisa din a yadda akai masu kwantacen ta sukace tabbas tare suka fita daga gidan. Bai shigo ba sai karfe hudu na yamma ya shigo gidan a gajiye don yai wanka part dina ya fara shiga ko da wani labarin ya sani. Yadda ya shigo na kalle shi ina falo zaune ina shayar da yara nono ya shigo muna gaida shi muka fara tare da tambayan shi anganta da jikin yarinyar. Yace har yanzu dai ba wani labarin su sai dai makwantan wanan dayan matan sun sheda masu sun gansu a safiyan jiya tare wai zasu tafi wani kauye ne yanzu dai an bamu layin wata mu kirata muji ko tasan inda sukaje. Wayan ta yana ringin bata dauki waya ba har yanzu nace oh wanan abin tashin hankalin da mai yai kama haka ne ? Zaki fita zuwa nesa ai sai ki fada wa mutane don gudun irin haka ko akalla dai an san inda ka tafi ai. Altine tace ai yanzu wanan yarinyar ne abin tausayi wallahi an rabata da nono da karfi da yaji haka gashi bata isa yaye ba ma. Wallahi nima abinda nake tunane ke nan nace Allah yasa dai duk inda take suna lafiya shine fatan mu dai yanzu. Dariya mai kama da yake yayi yana dagawa daga inda yake zaune kusa dani yace bari indan watsa ma jikina ruwa inji dadi. Nace abinci fa ina ganin ko karyawa bakayi ba tunda ka fita gidan nan yace lemo nasha dazun da naji yunwa barin watsa ruwan inci abinci dai ko zanji dama ya mike ya fice daga part din. Wanan matar akwai tsinanna wallahi, ji yadda ta saka bawan Allah nan cikin wani hali tsakanin jiya da yau din nan har ya fada . Nace dole hankalin shi ya tashi ko don wanan yarinyar karama dake kwance asibiti cikin wani hali tace dama ba son yarinyar take yi ba ai kin ga idan ta mutu an huta ai. Amma ke khadija ni sai ina gani kamar gudu tayi yadda suke ma maza idan sun gama dashi sai dai kuma zata gudu ta bar yan uwanta da diyan ta haka ? Don idan zasu gudu ai shammatar namiji suke yi sai sun gama yaye komai na mutum sai su gudu su barshi daga baya. Nace Allah dai yasa duk inda take tana lafiya sai Altine tace kai wanan baki san takaici ba wallahi banga abin tausayi wurin wanan matar bani. NAFISA Sun kamo hanya da ga yamma yayi masu inda suka dauki mota shata zuwa Abuja tun basu kai ko ina ba dare yayi masu tafiya driver ke yi kamar ai aike shi. Sai kwasan su yake da uban gudu a daji tun suna firan bokan da sukaje gurin shi har suka gaji sukai shiru da bakin su driver na ta faman tukin mota. Sun dan wuce kaduna kadan suka hango haske a tsakiyan titi driver su ne ya fara fadin yaushe aka fara checking wurin nan sai ya rage gudu bai kai ga karasawa ba ya gane yan fashine a hanya. Salatin da ya saka ne ya fargar dasu abinda ke faruwa a titin yan fashin sun tare wani mota suna operiton sai suka hango motar su nafisa tafe. Driver yayi saurin yin kwana garin juyawa sai motar tashi ta leka da sauri yace dasu kowa ya ta kanshi ya fita ya zura daji da gudu suka mara mai baya suma a guje cikin dajin . Nan yan fashin suka farwa motar da suka bari da bincike suka kwashe duk abinda suka sama a cikin motar sukai gaba suko wurin gudu sin fadi sun jirji ciwo a jikin da kyat suka samu wani dan kauyen da suka bari a baya suka kwana a tsaye don mutanen garin sun shige gidajen su ko. Sai washe gari mutane suka fito suka samay su a gurin ga mutanen da yan Fashin suka tare hanya motaci an taru a gurin wasu an kashe wasu kuma sun jirgita. Basu suka samu isa wurin motar su ba sai da wani ya taimake su suna zuwa suka samu an masu dadaya da kaya duk an watsar da komai a daji. Tsananin firgicin da ta kwana ciki yasa ta fita yacin ta ga gurin gudu ta gwauce a kafanta haka dai suka samu aka taimaka masu aka kwaso su garin kaduna akai dan bincike basu bar kaduna sai uku na rana koda suka iso Abuja lokacin yamma yayi sosai gidan Sabuwa suka fara zuwa. Suka kitsa abinda Nafisa din zata fada a gida kafin ta wuce zuwa gida daidai AA ya fito yana magana da yusuf da security din gidan mota ya tsaya da ita. Kallon mamaki suka fara mata yadda ta koma gaba daya ga jikin ta ko ina ya guje tana tangadi tun da ta dumfaro gidan gaban ta ke faduwa. Ganin su cirko cirko a kofan gidan bai hanata kokarin shigewa ciki ba wani irin tsawa ya daga mata daga inda take sai da ta kadu. Yace ke tsaya nan ina kika fito haka zaki shiga min gida ki koma can inda kika fito yawon tanbadan ki kada ki fara shiga min gida. Yusuf yace ka barta ta karaso muji in da ta shiga aiko tace cikin dakewa kai wani irin mara tausayi ne Samad mutum ya dawo a wani irin yanayi baka bincike ni zaka fara min fada. Yace na fada maki kada ki soma shiga min gida ya kalli security din yana fadin kada ku bari wanan matar ta shiga min gida daga yau. Security suka ce angama oga yace yayi bai tsaya ba ya shiga mota suka wuce zuwa asibiti ganin ya wuce ta doshi gidan . Security din suka taso mata nan gardama ya kaure a tsakanin su a gurin muna ciki laraba tazo tana fada muna abinda ke faru. Muna fitowa falo Fatiya yadda ta gan mu ta zabura tana fadin lafiya dai ko Altine tace yar uwarkice akace ta dawo tana bakin get an hanata shiga gidan. Gaba dayan mu muka fita zuwa waje a yadda muka samay ta a gurin munyi mamaki duk bata da dadin gani mun karasa ina tambayan security din suka ce umarni ne daga maigidan ya basu. Jin haka nayi mata wani kallo nace yanzu sai kiyi hakkuri ki nemi maigidan ya basu izzini ki shiga nan muka bar su Fatiha a gurin ta muka juta zuwa ciki. Fatiha ce ke tambayan ta ina ta shiga hankalin mutane ya baci ga rashin ganin ta tun safiyan jiya ga yarta tun jiyan bayan fitanta tana asibiti bata da lafiya. Tace wace yar tawa ciki suka ce Sadiya yar jaririysn ta sai tayi wani iri a fuskanta na ko in kula da hakan tace kin san iya hankalin da aka shiga a gidan nan na batar ki kuwa ? Sun dauki lokaci wurin har lokacin bai dawo ba nan dai cikin hikima suka lalashe ta take fada masu abinda ya faru da su a daji har suka kwana tace wayan ta da jakkarta duk yan Fashin sun kwashe acan haka ta dawo gidan. Ga kafarta da tayi targade yana mata ciwo sosai don yayi tsami zuwa tanzu tambayan da fatiha ta jefo mata ya bata haushi. Addah gurin bin bokayen da kika saba kukaje ke nan kuka hadu da wanan kadaran sai yaushe zaki ma kanki fada akan wanan abinda kike aikatawa ne. Ke ko abinda ya samu matar nan a gidan nan ranan bai isheki kiwa kanki fada ba yanzun wanan abin da kikayi yaya kike son diyan ki da mijin ki su dauke. Kin wuce kin watsar da diyan ki gashi kin rufe kitchen kin barmu da yunwa in badon wanan baiwar Allah dake gidan nan mun samu ta bamu kulawa da yaya kike son muyi. Tsawa ta daka ma Fatiya tace wanan ya isheki haka na gane idan na barki a gidan nan watarana zan dawo in samu kun dinke da wanan matar a gidan nan. Kai ta gyada mata tace ba zan taba cin amanan kowa ba sai dai daga ke har ita zan fada ma duk wanda yayi ba daidai ba gaskiya. Kiwa kanki fada ga wanan halin da kike yi don zai kaiki a inda baki tsamani ba don daukan alhakin yayi yawa. Abu wasa wasa har dare suna wajen ganin bai dawo bane yasa suka yanke shawaran zuwa asibiti su duba idan yana can ita da yar uwarta dayan Fatiha tana ciki tana sallah a lokacin. A asibitin ma sin sha bambam a can basu samu ganin shi ba sun dai duba yarinyar suka juyo zuwa gida sai dai sun samu ya koma gida. Yana zuwa gida ya shiga gida tare da bada umurnin su rufe maigidan shi bai kara fita ba sai safe don ranan yana da bukatan hutu a tare dashi. Nashiga gurin shi na samu har ya kwanta a lokacin na karasa yana kwance ya kifa ciki shi kadai a dakin na shigo zuwa bakin gadon na zauna. Juyowa yayi da fuskan shi yana kallo na nace sannu da dawowa ashe anka maman Ihisan din yace ta dawo dai tunda ta gaba abinda taje yi. Kallon shi nayi cikin dan mamaki nace wani abin taje yi ashe ina tambaya ina kallon fuskan shi yace idan ba wani abu ina zata tafi tabar yarta mai shan nono. Ajiyan zuciya na sauke don banda abinda zance cikin fadan mijin da mata nace abinci fa naga har ka kwanta ko yace bar abincin nan bana jin yunwa. Nace kada ka dinga sa zancen mata a rai ka jawa kanka matsala kuma ki hado min tea kawai zansha na daga har na kai kofa nace ka bada umurini ta shigo ko. Kallo na yayi ya kawar da kai saina dan tsargu da kallon da yai min din na fice daga dakin zuwa dafa ruwan zafin. Ban dauki lokaci ba na kawo mai sai da ya sha na kawar da kayan na sauko ba tare da na kara mai maganan komai ba shima dai din bai mun ba. Ina sauka na shige muka rufe Altine ce take tambayana ko Nafisa din ta shigo gidan daya dawo nace ban sani ba amma ina tsamanin ta shigo ai. Mikewa nayi zuwa ciki na dan kewa ya ban daki na fito na gyara jikina ban fita falo ba na shirin kwanciya sai ga laraba ta shigo da mami na karbeta na shayar da ita. Bayan mun kwanta ne har barci ya fara dauka na sai ga Altine a dakin tana fada min ashe Nafisa ba shigo gidan ba. Karshe ma maigida yace a rufe mai gidan shi tunda ya dawo ta na waje tana hauka da yar uwarta nace badai Fatiha ba tace dayan ai Fatiha ce tazo tana fadi wai ai maki magana ko zakiwa maigida magana don ance yana gidan nace mata kin kwanta tun dazun kin yi barci. Yau ma Altine yana nufin matar nan awaje zai barta ta kwana ke nan ko may tace wa yaja Khadija itafa tajawa kanta komai Allah ke tambayan ta. Tun da safe ina karyawa sai gashi a dakin yace zai fita asibiti ya duba su nace adawo lafiya yakai kofa ya juyo yana fadin jiya ya akayi kika shiga motar nan , ? Baki shiga wanda na baki ba sai wanda aka baki kyauta kikai amfani dashi kin nuna min kin fi bukatan wanan din ke nan ko ? Kaina na dan girgiza nace wanda na gani a kasa ai dashi zanyi amfani ko don har yau banga wanda ka bani din ba a gidan nan. May maganan ki ke nufi ke nan ban baki shi a kasa din ba ke nan ko nace bance ba tambayana kayi ai na baka amsa ko ? Yaushe ma kika iya tuki haka ne ban sani ba nace ni tun ina kaduna nake driving motar ya Adam ai ko don bamu da mota gidan mu kake mamaki haka ? Wanan kuma maganar kine don zance na bai kai can ba kuma yanzun na fahince ki ai daga zancen ki yana fadin haka ya fita nabi bayan shi da kallo. Nace a fili tunda ina yar tallaka kana mamakin tukina ko ai samu yafi iyawa yanzu baga iyawan yai min dadi ba. Matar ka daka wayar kamai da ita mutum a cikin mutane bakai mamakin iyawan ta ba sai nawa ai itace maganin ka a gidan nan. Tayi yadda take so kuma a zauna lafiya yanzu ai zanga matakin da zaka dauka akan ta gidan nan don wallahi ba yarda zanyi ba. Yana fita daga gidan asibiti ya nufa sai da ya duba yarinyar ya fito ya leka office bai dade da zuwa office din ba security din gidan ya kira shi. Kan Nafisa tazo gidan da tashin hankali sai ta shiga gidan fita yayi zuwa gidan inda ya samay a cikin tashin hankali sosai da masu tsaron get din. Yana bude kofa yace ke wata irin mace ce mara hankali zaki zo ki tara min jama,a a kofar gida na haka ne. Tace don may zaka hanani shiga gida na don wani dalili naka can yace gidan ki fa kika ce tace idan nan ba gida bane ina kake son in tafi ? Ida kika fito yace ke ni dai na auro ki ko to kije na sake ki saki daya yau ban son komai naki a gidan nan ki tatara ki kwashe awa daya na baki ki barmin gidana. Ya juya gurin security din yace kada ku bari ta tafi min da diyana ko ina Nafisa da tayi mutuwar tsaye tun lokacin da ya furta ya sake ta sai da taji yace diya ta iya magana. Tace diya kan nagama tafiya da abina bandaki wanan musakan zan iya barma ba yace mu zuba ni dake ki gani a garin nan. Ya shiga motar shi ya tafi ya barta a gurin a cikin tashin hankali ina daki zaune naji hayani ashe itace ta kuma dora laifin a kaina. Falo na fito na ce ma su Altine don Allah su kyale ta kada su tanka ta abokin mutuwa take nema sai lokacin Altine ke fada min wai ai ya sake tane a gaban kowa. Da sauri nace subbahanallahi shiko yaya don may zai yi haka da hankalin shi kuma Altine tace ke kan ban san irin zuciyar ki ba wallahi. Altine ba hakana bane nace wanan abin bashi ya dace da ita ba ai ba a yanke hukunci haka a cikin fushi sakin aure fa ba dadi ne gare shi ba. Tace ke ai farin ciki yakamata ace kinyi nace saboda an sake ta din tace kwarai kuwa an huta da bakar daga a cikin mu. Nace Altine ke fa mace ce bai dace ki farin ciki don aure ya mutu ba ko ta bar gidan nan bashi zai sa ta gyara halin ta ba sai ma ta nusa ga halinta mara kyau. Kin ga kuma ga haihuwa a tsakanin su dole dai ko yaya ta koma a kira ta da uwar yayan shi a garin nan amma in yayi hakkuri ya ladabtata a cikin gidan shi kila idan tana da rabo sai ta gyara halin ta. Amma saki baida wani alfanu ga namiji zuwa ga mace yanzu ma ko nayi murna ta tafi ai wata zai kara kwasowa gidan nan ko don haka banga abin farin ciki a wanan ba gaskiya. Laraba tace gakiya ne uwar dakina na gamsu da maganar ki don baka san kalar da za a kwaso maka ba kuma don mazan nan da zaran sun dadana zama da mace fiye da daya a gida ba fasa aure zasuyi ba. Gara wace ko ka santa kasan halin ta yafi ace a auro maka watacan daban sai dai ita din ce ba abin a tausaya mata ba ko kadan saboda halin tan nan duk da abinda ya faru da ita din. Altine da magana na bai gamshe ta kitchen ta shige ta barmu a gurin muna magana da laraba ina gurin zaune ina jimamay sai ga Fatiha ta shigo part din. Bayan mun gaisa take fadin nazo ne ki taimaka min da daysn layin mijin ku don wancen dana sani baya zuwa na ba wanda zata iya samun shi taimin godiya zata fita. Saita juyo take ce min kin dai ji abin daya ke faru damu ko a gidan nan koda yake banga laifin mijin ku ba gaskiya. Don yayi iya hakkurin da ake son namiji dashi don haka tsuntsun da yaja ruwa shi ruwa ka doka nace naji zaman jimamay nake a nan din kika samay ni yanzu. Nayi iya kokari na tun jiya yai min iyaka da zancen su yasa kikaga na sa masu ido tana murshi tace ai ba komai don kinyi yadda duk akeyi don nasan da itace ba zataiwa naki yadda kikai muna ba. Allah dai ya kyauta har abada ba zan taba goyon bayan karya ba nawa bai kona ni ba nawani kuma ba zai kona ni ba har ga Allah. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 1/4/21, 9:38 PM - Xxxxx: Ban san ya sukayi da shida Fatiha ba na dai gan su a gidan bayan wasu awowi gaba dayan su sai shige da fice sukeyi a gidan. Ranan dai gidan ya koma na buzaye kowa ka gani fuska babu walwala a cikin su alamun bacin rai a tare dasu ba sai an tsaya fadi ba. Shikuma tun da abin ya faru ya tafi bai dawo gidan ba har wanan lokacin magana nayi wa su Altine akan su fita batun su su daina zirga zirgan da suke a wajen gidan ma. Don kada su dauka ko muna farin ciki da hakan ne gare su Altine tace kai ni kina ban mamaki akan wanan buzuwa ta dauka haka din ne mana. Idan kece haka ya cika da ke tausaya maki zatayi akan hakan ba nan falon zata fito tana darawa ba murmushi nayi tare da fadin aimu ba ita bace sai mu nuna mata mu din masu tarbiya ne ko. Baki ta tabe tamike zuwa ciki tana fadin ko dai duk tsoron nata ne haka daga ke har mijin ku shima tunda wanan abin ya faru ya bar gidan nan bai leko ba. Nace ai kin fi kowa sanin ba matsoraci bane yanzu tunda ya nuna maki namiji yake dake da kawar ki buzuwa ta shige tana dariya ciki. Mun yi saurin rufe part dina ranan don haka bamu san halin da suke ciki ba sai da safe ne naji ana buga kofan part dina da karfi ina zaune ina karyawa Altine ce taje ta bude kofan. Shine a tsaye zata jashi da wasan ba,a tace ina khadija tana ciki ta bashi amsa ya wuce ta ya turo kofan ina kafa kai a cup din da nake shan kunun da Laraba ta dama min. Ina kwana na fara mai yace Deedar waya balla min dayan dakin nan ya shiga nace tunda na haihu ban taba zuwa gyaran wanan dakin ba asalima ai bakaji na karbi key din ba da sunan zan gyara shi. Wani iri yanayin fuskan shi yayi a lokaci guda ya furta Nafisa nafiki iskanci wallahi ya juya ya fita da sauri dakin. Mikewa nayi na fito falo motsin da naji a kitchen na leka inga wace ke ciki Altine ce a kitchen din itama ganina ta juyo tana fadin mijin ki lafiya yake kuwa naga ya shigo a fusace yau ya kuma fita a hakan. Nace shine nima abinda ya fito dani yanzu don ina ganin anmai barna a dakin shi da yake aje kayan sirin shi ne tace dan gado baya barin gado. Wa zai mai inba wanan matar tashi ba suna fita a gida haka banza ne dama ai sai sun samu barnan da sukayiwa miji suke tafiya. Tun jiya naso ince mu saka ido akan komai sai kuma maganan da kikaimuna ya sare min kafa da zancen nace yanzu ai ya fita. Sanan may zaki iyayi akai Altine wanan tsakanin su ne don yafi kowan mu sanin halin matar shi ai . Tunda ya fita da safen nan sai daya ya dawo yana shigowa muna falo zaune sai wayan shi yai kara ya daga kafin ya amsa muna gaisuwa. Naji yana fadin OK ok yayi kyau an karbo yarinyar da kayan ko ya tsaya saurara sai yace No yarinyar dai da kayan zaku karbo min ku barsu su tafi su. Ina ita Sadiya bakina ya subuce ya tambaya sai da ya gama sauraron mai wayan yace min tana asibiti dasu momy yau za a sallamota dai. Wanan bata da imani tafiya tayi tabar maka yar jaririyan anan ? Zama yayi a daya daga kujerun falon yana cewa kudina dake gidan nan dawasu abin amfani na ta kwashe zata tafi dasu. Haka suke ai dama inji Altine sai sunyiwa gida tas suke tafiya su tsiyata mutum gaba daya Allah ne ya taimake ka ai. Hannun shi yakai a goshi yana fadin bari Altine yadda matan nan tasan ina aje abu haka a gurin nan yake ban mamaki kuma ba ita kadai ta budeshi ba dole da taimakon maza ta iya bude gurin nan. Wanka yayi ya fita ya dauko su momy daga asibiti sai yarinyar ta baka tausayi sai gashi ya shigo dauke da kwalayen madara wanda za a dinga bawa yarinyar tasha. Zuwa dare su Ihisan suka shigo gidan tare da Samira munyi mamakin ganin samira tare dasu shima yana fitowa yace yarinya daya ya ba da umurnin a dauko sukai mai bayanin taki bin uwar ne anyi rigima sosai tace bazata bi uwae ba suka tafi suka barta nan shine dalilin dauko ta. Ni dai tunda yaran suka shigo banyi magana ba sai ma Ihisan datazo gurina ta kwanta ita kuma samira ta kwanta saman dogon kujera. Tunane nake na abubuwa da dama a raina har dare yayi ina son kwantawa ga yaran banji yace wani abu a kan su ba. Momy ne ta ce sani ki shige abinki ki kwanta bar mu dasu a nan har safe muji abinda ya yanke a kan su din. Cikin dare ma banyi barci ba sai tunane nake barkatai sai wani lokaci na samu barci ya dauke ni a gurin. Kukan yaran ne ya falkar dani daga barci na tashi na samu momy na rarashin su na zauna ba karbi yarinyar momy dake zaune a gefe na tace ni wanan matar alamarin ta ya daure min kai yafi karfin mamaki. Anya barin yarinyar nan datayi ba da biyu tayishi ba don shu,umancin ta yawa ke gare shi nace momy ni abin ne ma na kasa fasarashi wallahi. Nan ta fara bani labarin a cikin dare yanyala ta gudu ta falka ta nemay ta bata ganta ba a asibitin sai da safe ne da yaje yake fada mata abinda ke faruwa. Nace raina ya bani zata dawo gidan ai tace nima dai haka nake tunane a raina tun dazun don dawowan yarinyar nan da biyu ne gaskiya. Mun dauki lokaci a dakin muna maganan da momy kafin in koma barci ita kuma ta mike zuwa sallah. Da safe ya shigo gaida su momy ne yake fada mata zai bayar da Samira a ranan abi uwarta da ita koda ma bata je gida bane a je mata ita can garin su don bai dauka gida ta tafi ba. Don a maiduguri aka kama su aka karbo mai kayan shi da yarshi ya ce wanan matar ta fita raina kwata kwata momy don bata da dadi tako ina. A raina nace yanzu ko lokacin da ake fada ma ai baka ganin laifin ta sai na masu fada ma gaskiya ni ko a jikina kan wanan zancen. Muryan shi naji yana tambaya na jikin Sadiya din nace tana barci har wanan lokacin a daki sai bai kara magana ba. Kamar yadda yace haka ya fita da Samira a gidan ashe tafiyan ke nan bai dawo ba sai dare momy ke tambayan shi yar yace yaba da kudin jirgi an kaita Niger ai. Allah ya kyauta momy tace mai ya fice zuwa part din shi sai dana dan jima a zaune na mike tare da daukan kayan abincin shi na samay shi a dakin. Na shigo yana amsa call dan haka na samu wuri na zauna a gefen shi ya dan dauki lokaci yana amsa wayan. Ya gama ya juyo yana ce min na san kina da hankali Deedar zaki fahinci halin da nake ciki a yanzu ki taimaka ma momy ku rike min yaran nan a dan zaman da momy zatayi kafin ta wuce wani sati. Zuwa lokacin na gama yanke shara akan yaran na samu wace zata rainan min su a gidan nan don banson inyi nisa da yara nan ko kadan. Nace yara ai na kowa ne sai dai ina gudun abinda kaje ya dawo ga zaman su a wurina a matsayin su na diyan kishiya na kishiyar kuma irin matar ka da bayarda da Allah tayi ba. Cikin tsigar rarashi ya soma magana tana fadin kece hope dina yanzu kan yaran nan don nasan zasu samu kula yadda ya kamata a gurin ki. Idan kin rike min su da zuciya daya Allah zai baki lada akan riko da kikai masu din darajan ki kuma agun yaran zai karu ne. Nasan kina kokari akan iyalina khadija ina son ki kara duk da kalubalin da zaki samu duk da haka ina son ki daure ki rike min su amana. Ni dai tunda ya fara magana ban yi magana ba sai sauraren shi nake yi na rasa may zance mai don yadda nake ji din a lokacin. Wani nayi ya dauko ya kara dorawa a kaina har yaushe nakai munzalin daukan wanan nauyin ya dora min kuma akaina. Shirun da nayi sai naji ya rungumoni ta baya ya zauna dab da ni ya kare matse ni a jikin shi da alama hakan yana rage mashi itin radadin da yake ji a zuciyar shi a lokacin. Can dana ji shirun yai yawa na daure nace dashi ga abinci can na hada ma a dinning cikin karfin hali ya mike zuwa wajen abincin ya dan taba yace ya koshi. Har na fita na barshi baida walwala a tare dashi nima dai haka nake sai dai na dan dake nabar abin a raina ne kawai in ga iya gudun zancen kafin in maganta kada in yi saurin fasa cikina yai min wani fassara na daban. Don halin maza sai su laifi nasu ne amma sai su so su dulmiya mace a cikin shi su barta karshe da laifi. Wanan tunanen ne yazo min na nuna mai kamar ba komai a raina kan maganan da mukayi din kafin in samu mafitawa kaina. Har na mike zan wuce yace baki ce komai ba ga zancen yaran danayi maki dan murmushin yake na kakaro a fuskana nace Allah ya taya mu duban su ai da na kowa ne ba a san mai kama wani ba cikin mu dasu nan gaba daga haka na juya na fita. Daki na koma na kira maryam tazo da magana a gidan mu da safe tace zata idan ta fito school tace may ke faruwa ne dan fara fada min dai. Nace sai dai idan kin zo din mayi maganan zai fi na kashe wayan falo na koma don kada damuwa ya isheni a daki ni kadai a ciki. Ina zama Altine na fadin ita bata san yadda zata bawa Sadiya abinci ba ta karba nace ta miko min yarinyar in bata tana bani na fara gyara kan yarinyar yadda abincin zai zaunu mata da kyau bai dawo ba na fara bata tana karba. Ina cikin bata ya shigo dakin cikin shirin barcin shi yana kallon yadda na ke ba yarinyar abinci tana hadiya ya dade a kan mu yana kallon mu kafin yai muna saida safe ya fita. Zaune nake da maryam a dakina na gama fada mata yadda mukayi dashi tace cabdi jam akwai magana sosai a wurin nan. Khadija ina zaki iya rika yaran wanan matar yadda yake nufi wani abu yaje can ya samay su ace kece kikai masu sheri don suna diyan kishiyan ki. Shi kan shi uban ba yarda zaiyi ba idan kin masu wani abinda bai gamsheshi ba duk kokarin da kikeyi rana daya sai ya goge. A mararaice nace maryam abinda nake tunane ke nan nima wallahi tace idan gaskiya ne don may ba zai kaisu gurin hajiyar shi ba ? Nace maryam ni ban iya furta mai komai ba har ya kare naganar shi don ni abin ya daure min kai muna maganan sai ga momy ta shigo dakin. Ganin mu shiru yasa zata juya muna hada baki gurin fadin momy shigo mana ai ba wani magana mukeyi ba. Tana zama nace momy dama akan zancen yaran nan ne na buzuwa sai nake fada mata zancen da mukayi da AA din . Katseni tayi tana fadin ai nasan ba zai fara ya dumfari hajiya da yaran nan ba tun jiya maganan da muke ke nan da ita karshe ma ta fada ma Alhaji ya datse zancen da ba a gidan shi ba. Hakkuri zakiyi don inda tanice wallahi zan iya kama yaran nan may ye a cikin rika su din ai duk yiwa kai ne amma matsalan shine Alhaji. Karshe dai ba mafita momy tace in bishi a sannu tunda yace zai samu wace zata kula mashi da yaran a gidan sai in daure in kama mashi na dan lokaci a gani. Satin dana koma schools a satin momy ta barmu ta koma kamar yadda mijin ta ya umurce su data dawo gida ga babban sallah daya gabato saura yan kwanaki ayi sallah a lokacin. Ban sa rai cewa zamu kaduna sallah ba shiyasa banyi wani yunkurin zuwa ba na dawo daga school ne na samu bakuwa a gidan. Suna zaune a falo tare dasu Altine na shigo muka gaisa nadan dube ta cikin rashin gane ta ko daga ina take Altine ce tace min ai itace matar da zata kula dasu Ihisan itama yar uwar su daga can kaduna tazo. Dan kallon ta na karayi ina mata sannu da zuwa ta amsa min tare da cewa mun samay ku lafiya ? Nace lafiya kalau da fatan zamu samu kulawan ki yadda ya kamata tace insha Allahu zata kwatanta. Sai yamma ya shigo gidan bayan ya dan huta ya fito kafin magariba ya shigo part din yana fadin Altine bazawarin ki ya bugo min waya wai na dauke mai bazawara shi. Dariya tayi tace ai da ina dashi ba zaka rike ni a nan ba sun gama ba an su ya shigo dakin ya samay yace kin shigo ina wanka. Nace eh naje in gaida kaine da dawowa yace ya gidan lafiya muke na bashi amsa yace kin ga matar da momy ta samo muna ko ita ma dai yar uwar mu ce kamar Altine sai dai ita a kauye take zaune mijin ta ya rasu ne a baya ta aurar da diyan ta. Kinga ba yarinya bace itama don Allah ki daure kuyi zaman mutunci da ita kikuma sa ido ga irin kulawan da take ba yaran nan a gidan nan. Yanzu a ina zata zauna sai lokacin na sauke ajiyan zuciya nace mai sai mu zauna a nan ba na dan lokaci ba ne har uwarsu ta dawo bai ban amsa ba ya fita. Yana fita nace na shiga uku ni kan a gidan nan baka gama wanan ba ka fada a cikin wanan waini ko wace mace haka take rayuwa irin nawa ne a gidan ta. Matar mai suna Shatu bata da yawan hayaniya sai dai kamar tana da zafin rai da yake ni ba zama nake ba ban san wani hali nata na boye ba. Zaune muke a falo maryam ta sayo min abinda zamuyi amfani dashi na sallan ita da Altine suka fita zuwa kasuwan don ban yarda naje kasuwa ba banyi arba,in ba. Laraba ce take kokarin kwashe kayan ta dauki kwandon tumatir take fadin shatu ta dan kama mata. Ta cewa laraba ita ba aikin girki aka dauko ta tayi ba gidan don haka ta fitar da ita a cikin zancen aikin su a gidan nan. Dukkan mu kallon mamaki mukai mata daga can laraba dake fitowa tace amma idan an girka kina ci ko ? Dakatar dasu nayi da zancen nace haba mama Shatu bai kamata kuna haka ba da girman ku Laraba ki rage sai ki diba zuwa kitchen din. Tun wanan dole na mayar da hankali ga takon shatu a gidan don yadda take nuna hasala da sauri zata iya cutawa yaran da take kulawa dasu. Da safe ina shiri nake jin kukan ihisan har dakina na fito da sauri da ga daki ina tambayan may ya samay ta take fadin wai daga shirya tane take wanan kukan haka. Dan tsayawa nayi ina nazarin yarinyar na kama hannun ta zuwa daki ina tambayan ta take fada min dukan ta tayi da zatai mata wanka yanzun kuma ta kara dukan ta din. Dan shiru nayi a raina nace matsala ga wanan ga wancan yaya zan fito ma wanan matar don dai a haife ta haife ni kuma gata da rashin fahinta . Sai da muka dawo da yamma ranan muka rufe don sallah da za a yi a gobe shi kuma zai tafi sallah gida nace mama Shatu dama ina son magana dake don Allah dai kinga yaran nan kanana ne sosai duka bai dace dasu ba a yanzu. Don Ihisan ta fada min dazun kina dukan ta don Allah mama a bar dukan nan inda hali a tsawata mata dai yafi duka sauki ga yaro. Yar nan kina tuhuma nane komay ko wani sheri kuma ake son a laka min don hadin ga wanan magana don nasan fada maki wanan zancen akayi. Nan dai na lurar da ita na kota gane ban sani ba sai dai ina tune a raina idan ma nice ke rikon yaran haka dan abu kadan a kansu zai iya jawo min matsala tsakani da maigidan ke nan. Washe gari ya tafi ya barmu a Abuja a nan zamuyi sallah mu tunda ba school a gida nake ban fita zuwa ko ina sai dai zaman su Altine ya debe min kewa a gidan sosai. Sai shirin hada abinci muke yi muna kitchen gaba dayan mu in ka debe shatu dake daki gurin Sadiya da tai kashi tana canza mata pampers. Sallama kayi aka shigo gidan laraba ce ta leka don ganin mai sallama sai gata ta dawo da sauri tana fadin uwar dakina yau fa muna da baki a gidan. Su waye na tambaya tace wanan kawar Nafisa din nance tazo tana falo a zaune hannu na na dauraye na fita ina zuwa naga wanan Sabuwa din ne tazo ashe. Mun gaisa take fadin gurin yara tazo ta duba nace to bari a kawo su ku gaisa na shiga nace Shatu ta fito da yaran. Tana ganin su tace Ihisan ke ce kika ramay haka kika lalace kamar bake ba daga inda nake zaune ina kallon ta ina dan karkada kafa na. Wanan ai basai an fada ba yaran nan a cikin kunci hajiya duban yaran ki kazo ko kin zo ne ki fada muna magana a kan yaran nan. Tace gaskiya nake fada kin san dai yaran nan sun lalace ba haka uwarsu ta barsu ba nace da baku son su lalace ai sai ku tsaya ku duba abin ku ko. Ta mike tana wani tafiys tare da fadin ita zata tafi dama Nafisa ne tace ta shigo ta duba mata yaran taga lafiyan su. Sai ki je ki fada mata abinda idon ki ya ganan maki a kan yaran nace mama Shatu shaga da yaran ciki Allah ya baki ladan riko . Taja tsuki ta fita tana zage zage har kofa na fita na kira security na nuna masu ita kan kada su kara barin ta shigo muna gida don Allah don ba alheri ke kawo ta gidan ba ta buga motar ta ta fita. Altine tace mai yasa ba a kira ta ba ta yi daidai da yar iska nace ko makiyin Allah yasan yaran nan suna samun kulawa a gidan nan yanzu. Aikin mu muka karasa maryam ta shigo min da dinkunan na fitar ma kowa nasa na bashi ranan sallah mukayi abin ci da sha iya mu sai security a gidan. Zaune muke muna hira sai faman ciye ciye suke yi duk abinda ran mutum ke so ba wani sha maki ga kowa dama kuma haka muke ban saka masu ido ga abinda sukeyi. Yana can bayan sun fito sallah wayan shi yai kara ya dauka ba sallama sai masifa data fara mai ya hada kai dani ana zaluntar diyanta duk yara sun lalace sun fige. Kashe wayan yayi yana kashewa ya kirani yana tambayan wacece tazo gidan nan bayan shi nace kawar Nafisa ce . Ina fadin haka ya hauni da fada inda yake shiga ba nan yake fita ba nayi shiru ina sauraren shi ba tare da nayi magana ba na kashe wayan. Komay ya tuna kuma sai gashi ya sake kira ban daga ba har kiran ya katse yai kira uku ban dauka ba ina zaune ina ba Sadiya abinci ina gani naki dagawa. Na gama na dauki yarana muka koma daki ban dade da shiga ba sau ga Altine ta shigo tana mika min waya tare da fadin mijin ki yace yana kiran layin ki baki daga ba. Ta miko min wayan na karba ina karba yana fadin ina kike waya na ringing baki daga ba nace ina zaune a daki ne yace ok. Kin gane daga yau ban son a kara barin kowa ya shigo min gida da sunan duban yaran nan ban dai tanka mai ba kawai ina sauraren shi. Naji yace ana magana sai ki kyale mutu kamar bakyajin shi nakai iya wuya dashi nace wanan ba matsala na bane kuma na kashe wayan. A gaban hajiyan shi yake suna gaisawa tace ma dama ina son ganin ka don may zaka hada yar mutane tana fama da kanta ka dauko wani wahala ka dora mata. Hajiya banda yadda zanyi ne shiyasa na barwa deedar su a gida amma kasan itama tana da nata diyan ko so kake a tauye ta don kawai tana da hakkuri ? Nan dai yayi mata bayanin an dauko mai kula da yaran Shatu nacan gurin su tana duba su ai tace duk da haka ai a karkashin ta suke su duka. Kada kace zaka sa ido da son diya arai har ka kasa ganin kyautatawan da yarinyar nan ke maka Yace hajiya don haka ne na dauko wace zata kula dasu na musanman a gidan Tace ka dai ji hukuncin da Alhaji ya yanke akan yaran nan don haka kasa yadda zaka bi da gidan ka a samu zaman lafiya. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 1/6/21, 8:09 AM - Xxxxx: Zaune dai nake ina washe baki a cikin su amma ta ciki na ciki ina tunanen wayan mu dashi ga sadiya kamar mai wayau idan bani ba bata yarda wani yai mata wani abin. Ni har na fara tsorata da lamarinta a raina yadda yarinyar tasan dimin jikina da hannu na ko guri nake idan ana gurin da ita zata fara kokarin juya kanta gare ni. Sai na shiga tsarguwa a raina kodai maganan Nafisa gaskiya ne ita ya tace aka sauya mata to ta yaya na kawar da wanan jahilcin a raina irin nata. Ga dai su yan biyu zakace bani na haife su ba don kyau da kwarjin yara kara fita yake a idon mutane kulan da suke samu ya saka suna komawa kamar diyan larabawa dasu don shegen kyau. Fari dai nasan ba nawa bane kadai haka girman jiki sun dauko shi duka biyu don AA da yan uwan shi jajir suke suma haka hajitan su take. Duk da manyata ya kama ta amma haka bai sa farin ta ya gushe ba sai dai idan ya tsaya a cikin mu ne farin shi ke gushewa. Tunda nayi sallah ban fito ba don na fara sallah ina dakina zaune anan Altine ta samay ni mun dan taba hira da Altine din ta sako zancen Nafisa ina kaucewa. Don ni yanzu ban ma son zancen a tare dani da naji ta matsa ne nace Altine ni fa gara ta dawo ta dubi yaran ta yafi mun don ko ban samu matsala akan komai da magidan nan ba akan yaran nan nasan zamu samu saboda yadda yake ganin bamu basu kulawa da ya dace dasu. Tace kafin in kai ayya kai yana soma shi kulan da kike basu ko yaran ki kin tsaya kin basu shi yaushe shi ko uwar yaran da take nan ta kula dasu hakane. Ke harfa laifin ki nake gani akan haka wallahi yaushe zan tsaya kula wasu diyan kishiya in bar nawa can su girma suce nice makiyar su nina kore masu uwa gida. Nan nake fada mata laifina da ya gani tace amma mijin kan buzuwan wanan ta gama dashi ta ko ina wallahi. Ke nifa tun kan yaran can biyu da bai damu dasu ba kamar ba diyan shi ba wallahi idan kana da matsala da uwar su yaran ba naka bane da zai dinga kin kula su yadda ya dace. Laraba ce ta shigo muka maida kallon mu gare ta tana dauke da Alamin a jikinta tace uwar dakina yau fa kamar yaron nan baijin dadin jikin shi. Nace mama nima na kula da hakan tunda yamma yana kuka na bashi nono yaki kamawa sai kuka yakeyi cshine kikaga na goya shi yayi barci dazun. Tun dare baiyi ba mu kaishi asibiti a duba shi Altine ta fada nace yanzu kan ai dare yayi ina zamu fita da wanan sanyin haka ? Laraba tace ko in daka albasa mu shafe mai jiki kila mura ke damun shi zai dan sa ya sake zuwa safe mu gani falon muka fito dukan mu muka zauna. Ina kallon yadda take murzawa yaron albasa a jikin shi da kyau tace insha Allah zai samu sauki don ciwon yara bai wuce mura da ciwon ciki ba wani lokacin. Sai da ta gama shafe shi tare da shaka mashi hannun ta a hannci ya shaki gafin albasan sosai ta mayar mai da tufafin a jikin shi ta bashi magani. Shatu ne ta fito daga dakin da take dauke da Sadiya tana fadin yar nan taki barci hajiya tun dazun nake lalashin ta taki shiru. Tana kokarin miko min ita na rasa yadda zanyi da raina a loacin karban yar nayi daga hannun ta Altine tace a shafa albasan mata ita ma mu gani ai. Nace Anty lamarin Sadiya ne akwai wuya kin san ita komai nata dan ka,ida ne jikinta ma har yanzu bai tsaya daidai irin na yara ba. Tace ban ita nan a shafa mata tafi dan uwanta ne da aka shafa mai ta karbi yarinyar daga hannu na tace laraba ta dako mata wani albasan ta shafa mata. Shine muka samu yaran sukayi barci bayan an masu na gargajiya a gida ko da gari ya waye laraba tayiwa su yan biyu wanka ta kara shafa masu albasan a jiki dukan su aka goya su. Ya kira wayana har sau biyu ban samu dagawa ba don ban kusa da wayan a lokacin na shigo na samu miscall din. Wanka nayi na shirya tsab na fita mai falo din gidan dake a gyara tsab sai kamshi yake saboda gyaran dayake samu yanzu. Nan suka fito suka samay ni muka zauna gaba dayan mu sai laraba dake girkin rana wanda zamu ci take dan tashi lokaci lokaci. Hira dasu yana dan rage min damuwan dake raina wani lokacin sai dai hiran tasu ce kamar gugan juna don kowa a hasale yake da dan uwa. Dan gara laraba da Altine akwai dan shiri a tsakanin su sosai daya da wani abu mukaji dirin motoci a hara ban gidan ban kawo shi bane sai da ya shigo. Da mamaki muke kallon shi ba wanda ya tsamaci dawowan shi a ranan don mun dauka zai dan jima a can ne sannu mukai mai sai dai duk da yana amsa muna hankalin shi yana gun sadiya dake kwance tana kuka. Ya nufi wurin yarinyar yana fadin yaya kuka barta tana kuka haka yana kokarin dauko ta zuwa jikin shi. Altine tace yanzu uwar ta aje ta tayi sallah shine ta fara kuka ashe tayi kashi Shatu taje hada ruwa ta wanke mata ne. Yace shine za a kyale ta tana kuka haka kuma ba wanda ya dauke ta ya juya inda nake yana fadin shiyasa na dawo don hankali bai kwanta ba kan yarinyar nan. Yanzu ai sai ka kula da ita tunda ka dawo din don hankalinka ya kwanta ko yace wani irin magana kike fada min haka shiru nayi ban bashi amsa ba ya dan kura min ido zuwa dan wani lokaci sai ya kawar. Ya aje yarinyar ya fara tafiya yace ina twins ban bashi amsa ba Altine ce tace suna lafiya jiya dai ne Al,amin baiji dadin jikin shi ba. Yace yaya akayi yanzu yana kallona Altine ce tace mai jiyan dai an bashi magani sai kuma Laraba ta shafa mai magani sai jikin yai sanyi. Baice zai ga yadon ba ya wuce zuwa sama yayin da ake shigo da kayan shi ciki nidai ina zaune a inda nake imani ya cika ni. Altine tace lalai tsohon nan nasu bai nemi zaman lafiya da iyalin shi ba irin wanan halin daya dauko yana sa mutum sanyi ga abinda yai niya akan yaran. Ban samu tofa komai a zancen da takeyi sai sauke ajiyan danayi ina mikewa daga inda nake daki na na shige ina shiga Laraba ta kawo min Al,amin wai jikin shi ya fara zafi. Maryam na kira ina fada mata tace tunda an fada mai bari muga abinda zaiyi idan bai dauki mataki ba sai mu kai yaron asibiti. Sai wani lokaci ya fito ya fice daga gidan dama nasa Laraba ta kula min da hakan yana ko fita ta sanar min na kira maryam din tace in shirya mu je asibiti da yaron. Mun kai yaron asibiti sun duba shi suka rubuta maganin da za a bawa yaron sai da na sayo na dawo gida ina hanya naji ya kirani na dauka. Kina ina ne nace hanya sai naji ya kashe wayan ba tare da yayi magana ba yana kashe wayan nabi wayan da harara na aje gefe na. Na dawo gida dauke da yaron a kafada na nashigo gidan hannu daya dauke da ledan maganin da na sayo part dina na shiga don babu kowa a falon babba. Ban jima da dawowa ba ta shigo dakin yana fadin ina kika fito na shigo na samu kin fita ina kokarin dago yaron dake kuka saman gado nace na kaishi asibiti ne. Duban yaron yayi ya karaso yana taba yaron yace may ke damun shi ne wani haushin shi nake ji a raina ban iya bashi amsa ba sai kokarin dura ma yaron magani da nake shirin yi. Wani tsawa ya daka min yana fadin bake nake tambaya ba kinyi shiru dago kai nayi nace ni ba likita bace don haka bansan abinda ke damun shi ba. Naci gaba da bawa yaron maganin da nakeyi din ba tare da na kula shiba yace ok wani zance kike so ke nan kuma. Har ya kai kofa nace zancen iyakar ka kace in tafi gidan mu nima tunda ban ba diyan ka kulawa yadda kake so ba ko ? Juyowa yayi yace shi kike shawa wanan kamahin dama don kawai na tambaya akan sadiya nace bazaka tambaye ni ba ai tunda bani ce kaba kula da ita ba. Duk abinda zaki fada ki fadi nasan haliku na mata duk halin ku dayane a wurin kishi ko kuma don kawai na tambaya shine abin wani zance can ? Ya fita sai da nagama dura ma yaron maganin nayi tunane idan banyi da gaske ba akwai abinda ke shirin faruwa akaina da yaran nan. Don yanzu hankalin shi na gurin yaran Nafisa kawai kamar su kadai ne yara a gidan yanzu dayake jini ya dawo min sai ban daga ba don jin lokacin sallah da yayi. Ina ciki ina hada abinci a dinnng din shi ya shigo gidan na gama na dauka ya shige ashe yana tsaye yana kallo na. Ina gamawa na juya zan sauka kasa naji yace ina kuma zaki yanzu nace part dina zan koma sai naga ya matso inda nake yace Deedar may yasa kike son bani matsala ne yanzu ? Dagowa nayi na kalle shi ido cikin ido nace wani abin na sake ma yanzu kuma, ko da yake kasan duk halin mu daya wurin rashin kirki ai. Murmshi yayi yace kin canza min gaba daya yanzu na rasa may ke damun zuciyar ki a gidan nan gaba daya kin canza dabiun ki gare ni. Nace dama haka nake ai ko ka manta ne jawoni yayi zuwa jikin shi yace muje ki bani abinci kamar yadda kika saba bani a baya. Da ke nan yanzu ka san ina da yaran da nake kulawa ma,ana yarana dana haifa don suna bukatana a kusa dasu. Saboda yaran ne ba zan samu kulawanki ba yanzu nace koya min akayi hakan yasa na iya don kowa nasa ya sani murmushi yayi yace ki ban abinci dai yanzu don yunwa nake ji . Table din na nufa na fara zuba mai abincin kamar yadda ya bukata yaja kujera ya zauna yana kallon yadda nake zuba mai abincin. Nagama zan wuce yace ki zauna in gama mana kamar zanyi magana sai kuma naja na zauna a daya daga kujerun wurin. Kura ma kofa ido nayi hankalina ya tafi ga tunane yace gaya min mai ye matsalan ki danine yanzu da ya kamata ace na samu jin dadi a wurin ki. Maimakon in magana sai na fara kuka wiwi nace nagaji da wanan zaman haka nagaji nima ka sauwaka min tun yanzu yafi min alheri da zaman ukubar da nake yi a nan. Shiru yayi baice komai ba sai abincin shi yaci gaba da ci hankali yana sauraren kukan da nakeyi. Sai atukar mamaki maganar dana yi yake a zuciyar shi jin baiyi magana ba yasa na mike zan wuce sai lokacin na ji yace ki fada min laifin da nake maki har kika iya furta hakan a gare ni gabana kuma. Baka san halin da ka jefa rayuwana a cikin gidan ba a yan kwanakin nan saboda fitinar gidan nan bankai lokacin daukan wanan kwaram din a lokacin nan ba. Kasan girman nauyin da ka dauka ka dora min duk kokarin da nake a gaban kowa kake nuna mani rashin godiyan ka baka damu da damuwana dana yara na ba ina tsoron abinda nake gudu tun farko ya faru dani a gidan nan. Mutum ya tara yara dashi dasu su koma banza a gurin ka gara tun wuri a rabu don ba zan iya daukan wanan wullakancin ba da kurciyana haka. Ajiyan zuciya naji ya sauke yace yanzu na fahinci kina nufin ban ganin kokarin ki wurin kyautatawa su Ihisan da sadiya. May zai sa inga rashin kyautatawan ki gare su bayan uwar da ta haifesu ta tsalka ta barsu iyayyena sun kasa rika min ke da kika zauna min dasu ba tare da gardaman komai ba ince baki kyauta min ba kuma. Ko kinga na nuna bambaci akan yara nane da kike fadin ba zaki dauki wullakaci ba akan diyan ki kasa magana nayi ban iya furta wani abuba. Yaci gaba da fadin wace tayi min haka ta yaya zan kuntata maki idan ban gode maki ba kin san yara nan kanana ne suna bukatan kulawa don su manta da uwar su a ran su. Hawayen dake zubamin nake kokarin gogewa da bayan hannu na ina nazarin magananganun da yake min na dadin baki irin ta maza. Karshe naji yace kiyi hakuri ke uwace yanzu a gare mu kada ki yarda wani yaga sarewan ki tun yanzu a kan gidan nan har a raina maki wayo kan hakan. Kada ki dauki abinda nakewa yaran da wani manufa na daban kulawa ne kawai wanda ya dace su samu daga uwar su da basu samu ba yasa nake hakan. Runtse idanuwa na nayi na sauke ajiyan zuciya ina mikewa zan bar wurin naji yace ki zauna mu gama maganar mu kada ki fita haka a fahunci kinyi kuka anan su dauka wani abin ne ya faru tsakanin mu. Komawa nayi na zauna inda na tashi banji yai magana ba har wani lokaci na dauko na dan kalleshi naga ya mayar da kanshi a saman masangalin kujera yana tunane. Jikin shi yai sanyi da maganan da na fada farko yasan kawai na kyaleshi ne da kamay kamay da yake min din amma a gaskiya yasan ko waye dole yaji zafin abinda ya nuna min kan yarana Bai taba kawowa a ranshi nima yanzu na haihu a gidan kuma rashin ba yarana kulawan da ya daina zai iya haddasa wani a zuciyana ba kan yaran balle yai tunanen da yake bai dace ba a fili har kowa ya fahince shi. Sai yanzu da nayi wanan maganan yake nazarin wanan abin zai iya jawo matsala sosai a tsakanin mu har abin ya shafi yara a gaba. Gashi tun yanzu shakuwan da muka fara samu a tsakanin mu ya fara raguwa don yadda nake nuna mai din. Wasu hawaye ne na bakin ciki naji sun kara zuwa min lokaci guda ina kokarin mayar dasu a idona. Naji ya sauke ajiyan zuciya yace kukan nan da kike haka yana daga min hankalina idan hakkurin dana baki bai gamshe ki bane ki fada min in akwai wani matsala ne sai in sani. Na dago na dan kalle shi nace rayuwan gidan nan gaba daya ba tsari a cikin sa nike nan a haka zan zaune a cikin kuncin miji dana kishiyoyi ko ina ba dadi. Mace bata ganin fuskan miji a farin ciki taji dadi ko miji ya zauna da iyalin shi yaji damuwar matar shi kullun sai a dan kuraren lokaci za a zowa mutum sai nayi shiru. Murmushi yayi yana fadin ina sauraren shi wanan ne kawai damuwar taki a gidan nan ko da saura don ina son in sani ida nake da gyara in gyara nan gaba kamar yadda kike so. Don wanan kalamin naki naji shi har cikin raina da kika iya budan baki kina ikirarin ke ba zaki iya zama ki reni yaran ki a gidan nan ba. Ban taba tunanen jin wanan maganan a gareki ba khadija bana jin dadin ganin ki a cikin takura hakan sai inga ban maki adalci ba ban kuma yiwa iyayyen ki ba suma. Don Allah ki fada min duk damuwan ki dani a gidan nan a shirye nake da in gyara matukar bai saba ma addini ba a gidan nan. Khadija abinda baki sani ba shine zama dake ya fadakar dani abubuwa na rayuwana da dama da na rasasu abaya a matsayi na namijin mace fiye da daya a gidana. Ki yarda dani deedar bazan taba cutar ki ko wani naki ba balle diyan dana haifa da zufana don haka ki fada min komay ye damuwar ki kikuma bani second chance da zamu gyara matsalolin gidan nan da kike ganin tauyewa ne a gare ku. Ajiyan zuciya na sauke don jin yadda yake kalaman shi a gare ni a cikin tausasawa ina jin zuciya ta tana min sayin radadin da nake ji nasa din da farko. Tunane nake a raina may zan fada mai kuma wanda yai wanan maganan gare ni haka may yasaura in fada mai wanda shi bai san shi akan iyalin shi. Kallona yake ban sani ba ganin na zurfafa ga tunane nima ya dan hura min iskan bakin sa na bude idona na sauke a kanshi. Saurin kawar da fuskana nayi gare shi ina sauke ajiyan zuciya yace ke nake saurare deedar nace a hankali ba komai indai zamu samu kulawan ka a matsayin iyalin ka ya wadatar min ga komai. In dai wanan ne kawai damuwar ki a gidan nan kisa kin samu dama don karatun kine da lalurar ciki yakawo hakan amma kuma nima fa an rageni a gurare da dama kin kuma sani. Kallon shi nayi da saurin don jin abinda ya fada din yace yes nima indai wanan ne sai ince ni aka kuntatawa don ba a bani kulawan daya dace sai an fara ai min rowa kuma daga baya. Murmushin karfin hali nayi nace da wanan bataliyan buzayen na gidan ka kake son a baka kulawa komai mutum ke yi idon su akan shi yake. Murmushi yayi yana mikewa zuwa inda nake yana fadin yanzu ai bataliyan ki suka rage a gidan nan kadai ko su yaya zakiyi dasu kuma ? Shiru nayi na dan harare shi yace kinyi shiru bakice komai ba nace wanan ai ba su saka ido irin wa yan cen. Dukawa yayi daidai inda nake zaune yace wani iri naji har cikin raina kamar mai rada yace kin san may kai kawai na girgiza mai khadija ke kadai ce matar da zan zauna da ita muyi magana ta fahinta har mu fahinci juna a natse babu wani hayaniya a gidan nan. Kalamin ki na yanzu sun sakani jin kunya kaina da nauyin ki a idona ki gafarce ni deedar nasan ban kyauta maki ba har ga Allah kin fada min yaro baida lafiya ban kula ban duba shi ba ni kaina ban san abinda ya dauke min hankali gayin hakan ba. Ya kara dukowa gab dani yana fadin kiyi hakkuri ki tayani da addua duk da nasan kina min amma ki kara kwanan duk abinda nake Nafisa sai yaran ta nake gani a idona. Wani iri naji gabana ya fadi sai dai na dake hakan a cikin raina yace na san kowa cece Nafisa nasan ba zata barni in zauna lafiya wanan tafiyan nasan tana can tana shiri akaina sosai fiye dana farko. Cikin karfin halina nace mai idan sihiri kake tunanen tanayi shi din ma takeyi don duk wanda ke hada wanin Allah da Allah ya zama mushirki. Kai may zai hana ka dage kana da sani gwargwado na addini yaya idan ka dage komai zata dauko maka akan ta zai koma. Maganar gaskiya kana da rauni a gurin tsayawa kayi addinin ka kafi bada karfi a girin neman duniya wanda duk abinda ka samu iyakarshi a nan duniya. Sai nake ganin harda sakacin ka gurin bata dama tana wasu abubuwan da takeyi a gidan nan kiriri zaka kama ta da laifin da ya shafi haka amma babu wani matakin da ka taba dauka kwakwara a kanta don may kuwa baxata ji dadin ta mai da kaimi ga sherin da takeyi ba tunda ta dauka shine mafita a gare ta. Ka kafa mata tsauraran matakai ka dage gurin ganin addini ya wanzu a gidan ka dole ko batawa Allah ta rage wasu abubuwan da take yi din. Ka duba yadda Alhajin ku yake tsaye a gudan sa bai ba ko wace mace dama da zata raina shi a matsayin shi na maigida ba garesu. Kaiko duk wanan abin kayi watsi dasu ka kama akidar turawa da wanda ba naka ba don kawai so da ya rufe ma ido. Yatsun hannu na ya ja da karfi ina fadin wanan maganan sai da na dan sake kara dan zafin da naji a lokacin. Yace kika kara fadin haka sai na maki fiye da hakan yace akwai wata wace nake so da har son ta zai rufe min idona bayan ke. Ko kin mata kece maganin Nafisa a gidan nan kin fada tun kan ki shigo gidan nan kuma na sheda hakan a gare tunda gashi yau kin koreta. Dan dagowa nayi na kalleshi nace nine ma na koreta ke nan ba kai ba yace akan wa ta bar gidan nan to akan kine ke Deedar dama tace yar matsafa kike kinga kuwa tsafin ki yafi nata ke nan yanzu. Murmushi nayi don jin abinda ya fada din nace wata sabuwa ke nan yace ai sinan ki yakai har inda baki tsamani ba. Ni din nace yace yes yana dagawa daga dukawan da yayi a kaina yace yanzu dai jeki shirya don naga kin fara sallah kinga dama kin mata bukulu kin karbi girkin ki tun farko. Nace ni ban fara sallah ba don ko yanzu wallahi banda tsarki a tare dani yace har da fadin wallahi nace ba karya nakeyi ba ai gaskiya na fada ma. Mikewa nayi ina fadin ni zan tafi kada yaran su tashi a nemay ni kasa sai dai idan maganan da nayi dazun ya bata ma rai kayi hakkuri don Allah ka gafarce ni. Haba dai zuciyar ki kika fada min fa kuma gaskiya kika fada idan kin bar abin a dunkule ai ba zan farga haka da saurin in gyara muna kuskuren mu ba. Baki taba yimin musu ba iyakar ki bakar magana wanda na saba da wanan tun waje baki tsalake umurnina akan wanan maganan ba zan taba ganin laifin ki ba. Nace Allah ya sauka don Allah a kula da ibada wanda zai zama garkuwa a gare mu da yayan mu nan gaba yace in sha Allah. Ina kokarin hada kayan wurin yace barin in biki in duba Al,amin da yani nace mun hutar dakai ka bari har da safe idan Allah ya kaimu kaganshi. Yace rowan dan nawa zaki min nace ban maka rowa ba sai ka dawo a tare muka sauka zuwa kasan don ya duba yaron sai dai mun samu sunyi barci da laraba a daki na ko yasa yai muna saida safe ya koma. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 1/8/21, 8:34 AM - Xxxxx: Tun dana dawo part dina na kasa barci saboda maganan daya fada min na Nafisa dake mai gizo a ido ke nan Nafisa bata bar bibiyan shi ba ko a can. Tunanen samun mafita ga wanan alamarin nakeyi a raina har nakai wani lokaci dare ya raba sosai san nan na tsaya ga shawaran dana yanke a raina. Ya zama dole in tsaya tsayin daka in koma ga mahallicin mu Allah in dukufa dakai kuka na gare shi in dukufa da fada mai damuwan mu gaba daya don samun mafita a gare shi. Da farko dai na yanke shawaran zan kula da maigidan in mayar da hankali akan aure na sai kuma in kaifafa katfin ibada na dare da rana in yawaita karatin kur,ani da sadaka da taimakon wanda nafi mabukaci. Da ire iren wanan shawaran ne nakai karshe har barci yazo ya dauke ni ban sani ba a gurin. Kamar yadda nasa a raina haka na mike gabanin asuba da yake ba sallah nake ba na zauna na dinga tasbihi har zuwa bayan sallah asuba. Wanka nayi ban kwanta ba, sai dana gama shirina na fito zuwa hada breakfast koda Laraba ta fito ta samu har na kusa hasawa dan wanke wanke da goge wuri ta tayani. Part din shi na nufa nakai abin karyawa na jera mai kofan dakin shi yana rufe har lokacin don haka na sauko kada in tayar dashi tunda ba aiki zai fita ba ranan. Na dawo na samu laraba ta gama shirya yaran nan na zauna falo gurin ta muna hira sai gashi ya sauko yana saye da dogon jalabiya baka a jikin shi mai taushi. Sallaman shi muka karba tare da gaida shi ya karasa inda nake zaune ya karbi yaron a hannu na yana tambayan yaya jikin nasa ? Nace jiya yayi barci sosai baiyi wani fitina ba yau kuma koda ya tashi babu alaman zazzabin a tare dashi kuma. Dan wasa yayi mai kafin ya ajeshi ya dauki mami a hannun Laraba yana fadin Laraba wanan yarinyar kamar tana fin babana girma fa. Tace ai ya dan fada ne saboda dan zazzabin nan dayayi kwana biyu amma ba wani finshi tayi ba gasunan kamar su kadai ake kiwo a gidan nonon uwar tasu yana da kyau sosai sai kace madara ake basu. Daga inda nake nace mama kamar kin san nakusa fara basu madara tundai tsotson daren nan da suke yana damuna sosai wallahi. Juyowa yayi inda nake zaune yana fadin idan kin hana su abincin su saidawa zaki yi komay ba wani madara da za a basu tunda suna jin dadin wanda Allah ya wadatar dasu din. Nace don bakai ake wa wanan tsotson bane yace ki dai daure ki barsu su sha abinsu don Allah ban faye son wanan madaran ba da akeba yara yanzu. Altine ce daga bayan shi data fito take fadin ina kwana tsohon su yace a, a manyan mata sai yanzu aka tashi ke nan. Tace na dan koma na kwanta yau matar ka ce ta girka muna abin karyawa da kanta ta fara kyarkyaran mijin ta ke nan . Nace kai haba Anty daga na taimaka maku kuma kudan huta bagashi shiga kitchen dina yasa kin dan samu runtsawan safe ba yau. Sadiya basu tashi bane ya tambaya nace da safe dai ta falka an bata abinci ta koma barci Ihisan ko sai zuwa goma don ba school tana hutawa. Ya juya dauke da yarinyar a hannun shi ya fita daga part din sai dan wani lokaci kiran shi ya shigo min na daga yace breakfast zaki bani nace ok gani nan zuwa. A zaune suke a dinning din suke zaune yana ma yarinyar wasa na karaso ya tsura min ido har na iso gare su ina fadin yau kuma abincin sai nazo za a ci. Yace ba haka kika saba min ba da sanyayyar murmushi na sauke a fuska na don jin may yace din yace koba gaskiya na fada ba. Murmushi na sake yi na bude warmer din na fara zuba mai abincin ido ya kura min yayin da hannun shi ke ma yarinyar wasa nazarin nayake sosai yadda ban nuna abu a cikin wasan dadi sai abin yai mugun damuna. Daren jiya shima ya dade yana tunanen magana na yayi nazari yagano rashin kyatawan shi sosai don yasan ida Nafisa ce yaiwa hakan da wani ya jisu a gidan tuni. Sai yaji ba dadi a ranshi irin yadda yake min abubuwa ina hadewa ba tare da nuna damuwa ba sai dai indan yaba baka in bar maganan. Dagowa nayi da niyar in tambaye shi idan abincin ya isa hakana sai naga ni yake kallo cikin wani irin yanayi na damuwa murmushi muka sauke wa juna nace wani abin nayi kuma ko kake min wanan kallo ? Yace har yanzu hakkuri nake son kara baki Deedar kiyi hakkuri da abubuwan da suka faru tsakanin mu in Allah ya yarda hakan ba zai kara faruwa ba. Kallon shi nayi ido cikin ido na nufe inda yake na mika hannu zan karbi yarinyar nace wanan ya wuce ai tun jiya ni ban rikon magana dama kasani tunda mun fahinci juna. Sai dai wani bukata daya danake dashi akan Anty Fati don Allah idan da hali may zai hana itama ta dawo nan da zama yanzu mu zauna tare tunda can din ba ko yaushe kake samun zuwa ba akai akai. Kina son kawo wanin zance ke nan a tsakanin mu yanzu kuma nace ba haka bane yaya kawai dai naga kamar shima wani nauyi ne a kan ka. Sai dai naga kamar dawowan nasu nan zai sai kuma nayi shiru don irin kallon da yake min din yasa na kasa karasa abinda zan fadi din. Ki bar wanan zancen don baki gama sanin ko waye Fati har yanzu nace koma may ye dai iyalinka ne itama diyan ka ake cutawa don sune har yanzu ba shakuwa a tsakanin ku. To yanzu may kike son inyi ita fa ta zabi zaman kaduna bani na mayar da ita dole ba can so ki bar wanan zancen don Allah nace Allah ya kyauta. Ya juya ya fara cin abincin shi hankali kwance ba tare da ya kara magana ba na mike da yarinyar a hannu na na nufi inda yake na kai mai kiss nace hucewan ka lafiya yayan mu. Murmushi ya sauke yana fadin kin kuru wanan ya fanshe ki gare ni don dana bata maki rai kan wanan maganan nace a dai yi hakuri damu dan Allah. Na fice ina fadin barin sauka kafin Altine ta fara min sherin data iya don bai mata wuya yanzu gashi ta fara fadi ko. Yace kina tsoron ta ke nan indai Altine ce sai kin gaji kin fara bata amsa ai a gidan nan na fice ina dariya na barshi zai shige daki shima. Na samu maryam tazo duba jikin Al,amin a falon gidan na samay su nan muka zauna muna hira dasu sai gashi ya fito cikin wani shadda Gezenah mai kyau ruwan sky color kalan yayi matukar karban jikin shi sosai. Gaida shi maryam tayi ya amsa tare da fadin yana gyaran hulan shi yace zan fita zamu dan je wani guri da abokina nace na dauka ai gurin budurwa zaka wanan shigar haka ? Altine ta cabe da cewa da baki fadi ba ai ke dai kice shigar tayi maki kyau sosai ko nace kamar kin sani anty don bai faye saka kayan gargajiya haka ba sai irin wanan lokacin na sallah . Murmushi yayi ya fice mukai mashi sai ya dawo sai da ya fita maryam tace ai laufin ki ne da baki tsayawa ya shirya a gaban ki idan kin zabo mai yasa mai zai hana ya saka tunda kina sonsu. Nace kina ganin idan na shiga dakin nakai dan wani lokaci ban fito ba yanzu Nafisa zata kutsa ciki taga may muke yi kedai maryam Allah ya kyauta kawai. Don ko yanzu ban debe rai da zata dawo gidan nan ba nan dai nake fada mata abinda yace a gamay da ita din tace dama na sani khadija wanan matar ba kyale shi zatayi ba. Ya zama dole yanzu gare ki kafinta dawo in ma dawowa zatayi gidan nan din kin kafa gwaunatin ki a zuciyar mijin ku ya zama kin mamaye ko ina a gidan nan ta yadda zata rasa gane kan gidan da komai. Maryam ina kokarta hakan sai dai kin san shi da bahagon hali shima maryam amma zan kokarta in gani don aikine ja a gabana na yin hakan. Don gaba daya sun sukurkuta mashi lissafin rayuwan shi maryam yana bukatan sai saiti sai dai na fahinci yana da saukin kai a wurin fahinta idan an sashi a hanya. Sai yamma ya shigo gidan tunda ya fita daidai lokacin naci kwaliya ina zaune a falon gidan ya shigo idon shi a kaina na kada manyan idanuwa na ina mashi sannu da dawowa ya amsa. Sadiya dake gefe na ya nufa yana mata wasa tare da dan daukan ta ya dan yi mata wasa ya aje ta tare da tambayan ina su mami na ? Nace suna ciki ana masu wanka yace kinyi kyau sosai da wanan shigar nace na gode tunda ka yaba min dama don kai nayi shi ai. Yace idan zan samu haka kullun zan yi godiya a kullun duk da dama kina yi amma shigan kananan kaya kamar sun fi karban ki ai. Sai bayan sallah isha,i na shirya cikin wani arabian gown daga cikin kayan lefena rigar baka ce sai aikin da akai mata a gaba har kasa ya dane jikina dakyau har zaka iya ganin suran jikina dakyau. Na shiga wurin shi yana zaune yana aiki a dakin shi ya dago yana amsa min sallama na nace barka da yamma ya gajiya ina zaunawa a gefen shi. Yace ya kuke nace lafiyan mu kalau yaya dan murmushi yayi yace ba zaki daina kirana da yayan nan ba ko sallon ki yaudare ni da wanan kalman yayan naki. Nace to yaya zance cikin dan marairaicewa yace wanda ya dace dani mana nace baban twince ko yace kamar wani tsoho can nace a dan shagwabe to nikan yaya zance ma don Allah bayan wanan. Ke kika sani duk maganan da yake kanshi yana a duke bai dago ba sai murmushin da yake a baiyane a fuskan shi jin yadda nai magana ya dago kai yana kallo na. Sai naji yai murmushi yace oya ki fadi ina sauraren ki nace sai nayi shawara zan fada ma juyowa yayi ya harare ni da sauri na kawar da kaina ina dariyan kasa kasa. Mikewa nayi da zumar barin shi ya karasa aikin shi sai naji ya jawo ni da hannun shi guda yana fadin yarinya ni zakiwa wayo. Juyowa yayi da kyau gare ni yabar abinda yakr yace ki tausaya min hakana khadija ina cikin matsuwa don Allah idan kin san kin fara sallah ki fada min please? Ya kara matso da fuskan shi ya tokare gadon dani a tsakiyan shi har hancin mu yana gogan na juna magana kamar mai rada ya kara fadin in matse dake wallahi. Nace wallahi yaya bana sallah dadi yakai ma bakina yace waye yayan naki sai kuma yaci gaba da fadin kamar in kara dokan Allah in badon tsoron shi ba da nake ji. Nace tunda ya fara daukewa mai zaisa ka kara dokan ubangijin nasan nan da kamar sati biyu ko uku zai dauke gaba daya ne. Ya goga fuskan shi saman nawa yace baki da tausayi wlh kin ma rainani har tsawon sati biyu kice jiya kika haihu ma. Dariya nayi ya sake matso dani a jikin shi yace Allah bakiga yadda kika koma bane jegon nan yai maki kyau kamar in hadiye ki nake ji. Nace kai ka taba ganin inda aka hade mutum da ransa yace da wuya in ba a fara kaina ba yanzu nace da ka amayar dani ba shiri idan matan ka suka gane hakan. Juyawa yayi ya mike zaune ya koma inda yake yaci gaba da aikin shi na mike zaune naji yace yaushe ne zaku samu hutu. Nace kasan bamu wani dade da komawa ba ai ina ga sai nan da wata da wata biyu mai zuwa yace ok na dauka ai ba zaifi wata daya mai zuwa ba don ina son mu fita da kune waje. Nace da yaran nan kanana haka gara dai a bari idan sun kara wayau ko yace yara zasu hanamu jin dadi ne a can sai dai idan baki son zuwa ne kawai. Zanso fita mana tunda ban taba fita wajen kasan nan ba ai nakai wani lokaci a gurin shi muna hira kafin na mike na bar dakin . Rayuwa jin dadi da so da kauna muke nuna ma juna a gidan yana nuna muna matukar kulawa ni kuma ina kokari wurin kyautata mashi. Har na yi wanka na fara sallah ranan da na fara zuwa gare shi yayi murna sosai da hakan ranan ya tabbatar da kewan da yake fadi na gaske ne har cikin ranshi. Sai dai banje da yara dakin ba nan na barsu da gwagon su Altine da laraba suka kwana a wirin su sai ma mami ne ta danyi kuka ana bata ruwa ta koma barci. Muna kwance bayan mun gama azzakar yake fada min zuwa next week zaiyi tafiya kasan waje zai dan dauki lokaci a can bai dawo ba sai dai kuma idan bai samu yadda yake so ba. Nace idan alheri ne Allah ya tabbatar da tafiyan yace amin yace ina son kiyi min list din abinda zaku bukata a gidan nan. Nace gaskiya ban tsanmani akwai abinda bamu dashi ba dai a yanzu amma ya bari zan duba in ga abinda za a kara muna. Yace kina ban mamaki deedar ke wai baki san kice bari ki karba irin na wasu matan nace may ye riba na a cikin yin haka tunda nasan wata rana za,a tambaye ni kan hakan. Ban taba tsamanin hakan daga gare ki ba idan mutum ya ganki ganin farko sai ya dauka idon ki a bude yake kan komai. Dan murmushi nayi nace saboda may za ai min kallon hakan yace da anganki anga wayyan yar boko sai dai idan anzo magana mutum zai sha baka sai ya gane halin ki zai fahinci wanan a jinin ki yake. Na dauki lokaci a dakin muna hira dashi ina sauraren sai jefi nakan dan amsa mashi sai naga ina fahintar wani abin da ban sani ba a gamay dashi. Ta yadda zan warware matsalolin dake gaba a gidan sai bakwai da rabi na fito inda na samu Altine tana soya muna Irish da kwai na karyawa. Dakina na shiga nayi wanka na shirya na fito bayan na gama kimtsa jikina na nufi falo anan na zauna na shayar da yara nono nan Altine ta gama hada komai ta samay ni a zaune. Yau kan amaryan jego sai kyali haka Allah naga dare daya kin sake min ga komai gaba dayan ki murmushi na sauke a fuskana nace kai Anty Altine akwai ki da zolaya sosai yau yau da shiga turaka har kin hango wani canji a tare dani hakan. Magana take yayin da na shiga tunanen a raina na san dai na gwada amfani da abinda anty Salbiya ta bani abaya ciki ya hanani amfani dashi a lokacin. Duk da ban son in kasance macen da bata dogara da baiwan da Allah yai mata ba daga ni,imomin mu na mata da muke dashi a jikin mu don ko wace na da nata baiwan da Allah yai mata wanda zata gamsar da mijin ta dashi. Ina son in fahinci ina ne nake da rauni a cikin halittana bai ko da yaushe in dogara da amfani da abubuwan da ban san abinda aka hada dashi ba. Idanuwa na nalumshe a hankali ina tuna irin yadda muka kasance dashi a daren jiya din duk da ban yarda cewa abinda nayi amfani dashi din bane ya gigita min AA ba kawai. Har da gudun mawan dana cire kunya na zake nayi yadda namiji ke bukatan jin mace na bayar da gudunmawa a gurin saduwan su. Abunda na yarda dashi shine ruwan dumin dana ba amana wurin kula da kaina a lokacin da nake jego ya taimakamin matuka wurin kara hade ni kamar yadda ake bukatan mace ta kasance din. Sai dai duk da hakan na yarda da kayan Anty salbiya din dari bisa dari don zama babu caji yana kara durkusa da mace a gurin mijin ta sai dai yana da kyau mace tasan may zatai amfani dashi wanda ba zai cutar da ita ba a jikin ta. Shine ya shigo dakin ya katse min tunanen da nakeyi a lokacin yana saye da kananan kaya a jikin shi da suke kara fitar mai da suran shi na cikakken namiji a fili. Ihisan tana jikina tana wasa da mami dake shan nono sai sadiya dake wasanta ita kadai a gefe na Altine dake kasa saman carpet ta fara gaida shi. Ya kallin kayan karin dake gaban ta yace duk wanan ke kadai Altine shiyasa kike wanan kibar kamar wata curi dake tace dan wanan dana zubu har wani kama min ciki zai yi . So nake in gama dashi in koma ciki in dumama sauran tuwo in dora a kai sai in kara jin dama yace kice in kara yawan abincin da nake kawo muku ke nan a gidan nan tunda na aje acici a gidana yanzu. Dariya tayi tace ka dauka kowa irin wanan matar taka ne da take wasa da ci ni ina zan iya zama da ciki da yunwa ai sai in zubu rana guda. Ya juyo gare ni yana fadin ki ban abin kari na tun kan wanan acicin ta hada da nawa robon ta cinye baki sani ba dariya na danyi nace ai tasan dole ta zuba ma naka yana aje wa yan nan diyan nata da suka kwaso ta da ci natsaya ba nono su sha. Yace ai gara dai suci ko su kara kumari don ina son in gansu ko yaushe bulbul dasu kamar kajin agric a gidan nan ihisan ce ta dago tana fadin Abbi kalli yadda waban ke zukar nono ba kamar sadiya ba. Ya dan lakuci kumatun ihisan yace itama sadiya ai ta iya tsotson samun nonon dai ne bata yi a bata ya duka yana ma Sadiyan wasa kafin ya dago yace wai ina Shatu ne ? Altine ce ta tabe baki tace bata tashi ba ke nan tunda kaga ta turo yaran wurin uwar su da safen nan wanan kan bata san may ya kawo ta gidan nan ba ai. Fita yayi nabi bayan shi da abincin inda na samay shi zaune yana waya na hada mai abincin har na gama bai daina wayan ba. Dan gwauta shi nayi zan wuce ya jawo ni zuwa jikin shi yace deear kin sakani a wani yanayi jiya zuwa yau nace kana son dawo da abinda ya wuce baya ke nan. Jayoni ya kara yi zuwa jikin shi yana sunsunan wuyana yace kamshin ki daban ne yanzu deedar wanan kamshin ina son shi wallahi. Dan murmushi na sake nace kaci abinci kada yayi sanyi please yace ba abinci ne a gaba na ba yanzu deeder juyowa nayi na kalle shi tare da fadin may ye a gaban ka din ba yanzu kace in kawo ma abincin ba kaci. Sake ni yayi ya dangana da kujera yana kallo na alama nayi masa da ido yaci abin cin ya sauke ajiyan zuciya ya jawo plate din zuwa gaban shi ya fara ci. Ina zaune na kura mai ido yana cin abincin hankali kwance sai da ya ishe shi yajawo abin goge baki yana goge wa yace abincin nan nadai shine bai min dadi ba yadda nake jin test din naki girkin. Kai yaya AA har da girkin na Altine zakai wa sheri yace tunda kika fada min ita ta girka naji abincin ya fice min a rai baki san ina gane girkin ki bane a gidan nan. Sai idan kin so muna sheri sai ki bar wasu su girka abincin da mutum bai iya ci nace yanzu ai shike nan sai in dinga girkawan dama taimakona ai tayi tunda taga ka wahal dani daren jiya din. Murmyshi ya sauke kawai yana sauke ajiyan zuciya yace tafiyan dana fada maki zanyi sun mai dashi nan kusa ina ganin gobe da dare zan bar gaein nan zuwa lagos don yanzu dole ta can zan tashi. Nace kusa haka kuma yace ko in fasa ne mu zauna da sauri nace haba dai idan baka fita nemo muna na kan mu ai za mu durkushe ne kuma. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 1/11/21, 8:35 AM - Xxxxx: Washe gari da karfe uku ya dawo gida ya dade zaune a part dina yana hira da Altine da shatu sai mama dani dake gafe ina dan saka masu baki a hiran su. Yaran shi na saman jikin shi duka hudun yana wasa dasu sai dai yakai wani lokaci a wurin mu ya dan dube agogon hannun shi ya mike yana fadin Altine bari na shirya lokaci na gaba towa na tafiya na. Sai lokacin Altine tace au tafiya zakayi yau ashe yace eh tare da dan kallo inda nake yace kuma zan dan jima acan idan na tafi din. Fatan aje lafiya a dawo lafiya sukai mai dukkan su ukun ya mike yana aje Al,amin da lakuto kumatun Sadiya a gefen shi. Murmushin jin dadi nayi a baiyyane wanda ya nuna farin cikina a lokacin ya daga min gira ya fita sauke ajitan zuciya nayi bayan fitar nashi a din nawa na dan dade zaune na mike don tuno da signal din da yaimin kafin ya fita par din Mikewa nayi na binshi nayi dakin bayan ya dan dade da fita daga dakinawa na yafe gyalen kayan dake jikina tare da murza humra a part din jikina na nufi part din nasa. Ya na tsaye wurin wardrobe din shi yana ciro wasu kaya nayi sallama a kofan dakin nasa hankalina yana wurin abinda yake yi din na karaso wurin da yake tsaye din . Bayan shi da bani na rungmay ta baya na kwantar da kaina ina fadin wanan dai kasan ba aikin bane nawa ne don may zaka wahal da kanka gayi ? Ajiyan zuciya ya sauke don jin jikin mu daya hade a guri daya yace ina son ki huta haka nane nima nasan ba aikina bane ai. Dan pick kiss nakai ma bayan tare da fadin nace ma nagaji da bautar ubangijina kai dai kaimin wayo don kar in samu wanan ladan na yau dai. Na raba jikin mu ina karban kayan kala biyu daya dauko nace wanan kawai zaka tafi dasu kai da kace zaka dade a can ? Ban son tafiya da kaya masu yawa idan zanyi tafiya don kin san ina fita nakan sawo kayan sawana a can nafi gane ma hakan. Yana magana yana tsure ni da ido nace hakan na da kyau ai don rage wahala tare da fadin na hada ma ruwan wanka kaji dadin tafiyan ke nan ko ? Jinshi nayi a baya na ya rike min weast dina yana fadin kin san dai ba zanyi wankan bazan ba haka kawai a wanan lokacin ina dariyan maganan shi na dago ina fadin akwai wankan banza ne kuma ni ban sani ba ai don, , , . Kasa karasa maganan nayi don jin jikin mu daya hade wuri daya yana kokarin sunsunar wuya na yace kema kin sani ai wankan da baida dalili ai ba wanka bane ko ? Bakina yake kokarin lalaba ina kokarin zulewa tare da yar dariya ina fadin kai yaya so kake kabi hanya kana jin gajiya a jikin ka kuma ? Sai da yai nasaran cabka mun dade tsaye muna farautawa juna rai inda na debe nauyi da kunya da girman kai na yi mashi abinda ya kamata ta yadda ba zai manta dani ba idan ya tafi. Mun dade a tare kowa na nuna ma dan uwa kaunan a fili da kyat ya barni ya jaye jikin shi daga nawa yana sauke ajiyan zuciya na gamauwa da abinda nayi mashi din. Yace kin biyani bashina da ke kanki deedar nace ai ban san da bashin ka a kaina ba dana dade da biya in huta da nauyin shi a kaina. Yace ko wanan din da kika fara bani ai na gode nace da saura ke nan dai ban sani ba na fada ina kokarin tsure shi da ido yace dayawa ma tunda an barni maraye a baya sai uwa ta mai sona momy. Murmushi na sauke ina kokarin dagowa daga inda naya da kaina nace ke nan ka kashe Abba da hajiyan mu damu kannen ka yace kuna raye amma baku damu da damuwa na ba ai. Mikewa nayi daga gadon kafin ya fadi wani abu na nufi bandakin saida nayi tsarki da ruwan dumi sosai na wanke gurin na hada mai ruwan wanka. Yana a kwance nace ga ruwan can na hada ma kada ka makara yace sai biyar da rabi zan bar gidan fa don haka ki bari in gama abinda nake tukun don in tafi da dadin rai. Na nufe shi ina kokarin daga shi don yaje yai wanka ya kara jawo ni saman jikin shi na fada sai tsawon wani lokaci ya kyale ni yana mikewa tare da dariyan mugunta ya nufi bandakin har yakai kofa. Sai ya juyo yana fafin tasowa zakiyi fa ki min wankan nan tunda ke kika tara min wani gajiyan kuma yanzu duk nacin shi akan hakan ban yarda naje din ba don wankar sarkin da zaiyi din a lokacin yana bukatan natsuwa. Ya fito na shiga na tsarkake jikina na shirya a nan dakin ban yarda na sauka ba a lokacin zaka dauka banyi komai ba don kaina dana tsane na rufe abinda gyale na saboda manyan matan da nake zaune dasu kada su fahinci komai ga hakan. Yana zaune a bakin gado koda na gama na juyo gare shi kudi na samu yana faman lissafawa saman gadon na karaso inda yake din zaune. Ba tare da ya dago ba yace min bissimilah zauna in maki bayanin su kudin na kalla daga inda nake yace wanan Altine zaki ba dubu talatin ne ta rike sai wanan laraba da Shatu su rike ashirin da biyar kan na dawo suma a hannun su. Godiya na ari bakin su na fara yi yana murmushi yana gidaya ya hada bandur din kudin wuri daya yace wanan ki rike don lalurar ki dana yara kema. Kallon kudin nayi ba tare dana karba ba nace sai dai kamar sunyi yawa mana yace cikin girgiza kai ba wasu kudi bane masu yawa ki karba ku aje don amfanin ku na fada maki zan dan jima a can din. Don wurin kasa uku zan ziyar ta zuwa hudu mika hannu nayi ina godiya na karbi kudin daga hannun shi ina mashi godiya ya buge min baki. Wanan godiyan yai yawa haka nifa zaki taimaka dashi kaina na tsune a saman kirjin shi nace yabawa ga alheri shine yin godiya don haka kabari in gode ma don ka sani na sani wanan kudin yafi karfin aiwatar da wani hidiman gida gare ni ai. Murmushi ya sauke wayan daya karba yasa na samu silalewa a dakin na nufi wurin yara na in duba su na samu Al,amin yana kuka sai gani karban shi nayi na bashi nono inda na karbi mami ita ma na bata nonon. Ina gama bata sai sadiya dana daga ina bata abincin ta tasha sosai duk da wahalan da bata abincin yake dashi nakan daure in bata lokaci na wurin bata abinci sai ta koshi. Nan ya samay ni ina goge mata baki da jikin ta ya dan dade tsaye yana kallon mu kafin yace wani abu akai yace wanan dai dake ta bude ido a gidan nan. Laraba tace kasan yaro kamar dabba yake mai kula shi yake sabawa dashi tun dai idan yana karami da mai bashi abinci yake bude ido ai. Yace wanan ai gaba daya ma bata san uwar ta ba sai wanan don ba kulawa take bata ba ko da take nan din, idan ba don Deedar ba da bansan yadda zanyi da wanan yarinyar ba mama ya karasa fadi a cikin yanayin damuwa da tausayawa yarinyar yanayin ta. Bai samu maganan da ya kawo shi ba Yusuf ya shigo gidan yasa shi fita wurin shi sai bayan fitan shi ne na basu Altine da tafito sakon shi nan suka shiga washe baki suna farin ciki. Shatu na daki nasa laraba ta mika mata nata a dakin da take bata son fitowa a zauna da ita don irin mutanen nan ne masu saurin fushi ga dan magana kadan sai tayi yar zukut da mutane. Kai mata kudin yasa ta fitowa dakin tazo inda nake tana fadin munga sako hadiza Allah ya saka da alherin sa ya umfana arziki nace amin mama. Daga nan bata furta komai ba ko kallon yar renon nata dake wasa a gefena bata yi ba ta mike ta koma dakin su laraba ne ta bita da kallon takaici nayi kamar ban ganta ba ban kuma san may take nufi ba. Shida saura suka bar gidan inda muka raka shi har bakin mota muna mashi a Allah ya tsare a dawo lafiya. Yace Amin ya daga yana muna sai ya dawo idanuwa na na lumshe bayan na gama kallon motar tasu data wuce muka juyo zuwa ciki. Sadiya ce ke dan kuka nake fadin ina shatu ta dauraye yarinyar nan dare na yi kada sanyi ya kama ta shatun na kira sai dai bata karba ba. Sai can gata ta fito cikin daure fuska tana fadin gata tazo ta tsaya akaina nace lafiya Shatu zaki zo ki tsaya min a kai haka kamar mai shirin fada. Tace kiran raki ne naji shi kamar da manufa a gare ni yasa na fito jin ba, asin hakan cikin mamaki na girgiza kai tare da fadin dama ba komai nake kiran ki dashi ba so nake ki daureye wanan yarinyar a saka mata kayan sanyin a jikin ta don dare. Tace duk kokarin da nake a kan yaran nan ba,a gani a gidan nan dazin ma ina jin maigidan nan ke yake yabo a kan su ai. Bani ba har su Altine dake falon a zaune sai da suka bude baki sona mamakin kalamin ta nace Shatu ban ko iya kiranta da mama din da nake saya masu a gaban su ita da laraba ba lokacin. Nace kishi kike akan abinda ke wakana tsakanina da mijina a gidan nan komay kuma don wanan maganan naki ya na da manufa. Tace konayi kishi ai gidan dan uwana ne ko nace idan kuma nace yau ba zan zauna dake gidan dan uwan naki ba ya zaunu a hakan ko. Tace waban kuma fadi ne don ba yau ba nasan baki da ra, ayina a gidan nan don irin banbacin da kike nunawa tsakani na dasu Altine nasan komai ko sako aka bayar ki bani sai ya fito a hannun su. Altine tace dani ke nan kike jayayya a gidan nan ni da kika sama a gidan kike bakin ciki da kasancewa na a gidan tunda kika zo kika samay ni a gidan nan kike wanan bakin ciki dama na san ku da bakin hassada. Nan dai fada ya kaure a tsakanin su waya na daga na kira layin momy bai jima yana ringing ba ta daga kiran na fara gaida ita bata gama amsawa ba nace. Momy akan shatu na kiraki a gidan nan don gaskiya na fahinci namu dai bai zo daya da ita ba a gidan nan. Subbahanallahi tace tare da fadin mai yai zafi khadija ban san ki da korafi ba dole akwai abinda ke faruwa ke nan tsakanin ku. Momy kawai dai ba zan iya zama da ita bane don kauce wa matsala murmushi naji tayi yayin da sukai shiru suna sauraren wayan nawa. Nace momy ba zamu jittu da ita ba a hakkura kawai indon yara ne a barsu a tsakanin mu zamu rike su insha Allahu. Tace bani Shatu din idan tana kusa zan mata magana nace momy ba sai anyi ba don na riga na yanke a raina ba zan zauna ana fitina har abin ya kai akaina ba wata rana nake ma gudu momy. Tace zanyi magana da ita bata kusane nace eh don ban son bata wayana ma yadda nake jin zafinta a raina na kashe wayan tare da mike na nufi daki na har nakai kofa na juyo nace mama laraba kiwa Sadiya wanka don jikin ta ya baci. Na shiga daki ya Amina na kira na fada mata halin da ake ciki tare da fadin matar nan ba abokiyar zama bane ya don za,a iya hada kai da ita gaba a cuta min tace kwarai kuwa zan samu momy in fada mata abinda ke faruwa don ta sani. Bayan min gama wayan na jima a dakin sai da zan kwanta na fito nace Altine ku dauki yaran nan ki kwana dasu a wurin ki don Allah. Tace angama hajiyan mu na daiyi murmushi na ce laraba ta shige min da yara daki muka kwanta ita ko tana dauka da wasa sai can dare ta fito daukan yaran basu falon duk mun shige mun rufe dakunan mu. Don haka bata san wani daki yaran suke ciki ba da safe ban kulata ba dana shirya muka fice zuwa school bayan na yi wa laraba magana kada ta kulata don Allah idan tana fitina. Sai yamma muka shigo gidan ihisan ma bata jima da dawowa ba gidan ina shigowa Laraba tana Sadiya wanka na leka su nafito daga dakin dakina na fada na fara kwabe kayan jikina da tare da watsa ruwa a jikina. Sallah nayi na fito falon ban jima da zama ba sai ga Shatu ta fito tace nazo ne in baki hakkuri kan abinda ya faru jiya don hajiya Binta ta kirani. Ni arziki nazo ci ba zuwa nayi nan don wani abubu naga kuna son hada min kai ai min bakin ciki ga samun da nake yi gidan nan. Ikon Allah Altine dake zaune tana lazumi ta fadi nace Altine ya isa don Allah ban son fitinan nan haka na daga haka ban kara cewa komai ba. Ta juya zata tafi tana maganganu nace shatu ki shirya da safe za a kaiki gida tace wanan kuma sai idan dan uwana ya dawo daga tafiya yace in barmai gida zan bari nace yayi. Ta dauka wasa nakeyi da safe sai ga kiran wayan shi yace ta shirya a kaita gida zata fara magana ta kashe wayan sai da nagama shirina na fito falona na zauna ina karyawa. Kudi da abu a leda na mikawa laraba ta ba shatu nace driver zaizo ya dauke ta zuwa kaduna har gida za a kaita daga haka na dauki hand bag dina dake gefe na rataya tare da daukan mami zuwa waje Altine ta dauki Al,amin muka fice. Da Laraba taga mun fita an kule ko ina ta rufe kitchen ta shige dakin ta ta fito tayi cin mutunci a tsakar falon ta fice driver ya dauke ta zuwa kaduna. Mun dawo da yamma na samu ta wuce hankalina ya kwanta dan zama da ita ba alheri bane ga yadda na hango abubuwa da dama a gareta. A kulun muna waya dashi lafiya zai kira ya tambayi lafiyan mu mudan taba hira maganan shatu ne ya saka na kirashi kawai ranan don banson damuwan shi bansan halin da yake ciki ba. Yau tun daya tashi hankalin shi ke wurin nafisa ya kasa zaune ya kasa tsaye duk yinin ranan ji yake yana son kawai yayi arba da Nafisa a idanun shi haka yasa washe gari ya katse duk wani abindake gaban shi ya juyo zuwa gida. Ba wanda yasan da zuwan shi don ranan yana da kwana takwas da tafiya muna hira da dare sai ganin shi mukayi kwatsan ya dawo daga tafiyan. Kallo daya nayi mai na fahinci akwai damuwa a tare dashi sai na dauka gajiya ne ya kwaso mun tare shi da zuwa ba wani walwala a tare dashi ya juya ya nufi part din shi. Wanka ya fito mun gama hada mai abinda zaici na nufi gurin shi da abincin sai da nagama jera mai na nufi dakin yana tsaye yana fida riga a wardrobe din shi. Sallama na yasa ya dan juyo gare ni nasha kwalliya a jikina na nufo shi ina murmushi ta baya na dan rugumay shi ina mashi sannu da zuwa. Bai wani nuna jin dadin gani na ba a lokacin sai cewan da yayi kuna lafiya yana kokarin kwacewa a inda muke tsayen. Da mamaki na bishi da kallo tare da fadin lafiya ko kake yaya yace may kika gani yana kokarin saka riga a jikin shi. Tsaye nayi sororo ina kallon shi cikin mamaki hakan bai sa na dadara ba na bishi bakin gadon na zauna tare da fadin sai naga kamar kana cikin damuwa ? Yace khadija ban son damuwa nan haka da yawa ki barni in huta don ina bukatan hutu ne na dan dade a zaune ba tare da nayi magana ba sai can na mike nace abinci na a dininng na shirya ma. Yace bazan ci ba a koshe nake jin abinda yace na dago na kalleshi don duk halinda yake ciki idan nayi mai tayin abinci zai dan tsaya yaci. Sai dai yau naga akasin hakan gare shi gashi ba fuska balle in matsa da tambayan shi na juya zan fita nace ubangiji Allah yai muna saukin koma may nene ke damuwan ka. Nakai kofa naji yace bar abincin indan ci kamar wanda dama ya matsu in bar dakin nashi dan kallon shi nayi na juya na fita daga dakin. Ina fita yaji ba dadi kuma a ransa sai dai yadda yake ji din fitan nawa dakin ne alheri a gare shi don wani irin haushi da takaicina yake ji a ranshi lokacin. Dakina na koma a cikin damuwa sai dai ban iyajin zan koma wurin shi kuma idan ba shine ya nemay ni ba a lokacin cikin dare ma dana kasa barci tashi nayi na dauro alwala nazo zan tayar da sallah. Ina kallon Labara dake barci da yaran makale a jikin ta na tayar da sallah na laraba sai barcin su suke hankali kwance a raina nace kin huta da jidalin duniya na mazan yanzu. Salatu tasbihi nayi Allah ya ban sa, a daga laraba har yaran babu wanda ya tashi a lokacin a raka,an karshe ne da nayi sujada na dade duke ina rokon Allah bukatuna daga ciki ko har da sherin kishiya da makiya na duniya a kaina da yayana. Ina idar da sallah na mike zaune ina ma Allah kirari da sunayen shi tsarkakkaku na dade a wurin kafin in ji kukan mami dama itace mai kwakwan shan nonon dare. Kukan ta yasa laraba falkawa daga barcin tana dan bubugata nace ta miko min ita a inda nake zaune ga kamashin turare ya karade gurin yana tashi. Nakai wani lokaci kafin mu koma saman gado da yarinyar mu kwanta da gari ya waye ba school zan shiga ba don weekend ne na kwanta ina ramuwar barcin da ban samu ba da dare. Sai dai ina jin zuciyana wasai don ba kunci a tare da ni ko kadan a lokacin da ko har jin wani iri nake tun abinda yai min a dakin na fito idan natuna kamar nice bai son gani lokacin. Gashi ban san abinda ke faruwa dashi ba sai dai hango tsanana karara a fuskan shi da kwayan idon shi a lokacin can cikin barcin dana samu mai dadi nake jin ana dan ja min kafana. Zubur na bude idona na sauke a kanshi inda yake tsaye yayi kwaliya da gani wuri mai muhinmaci zai tafi lokacin . Gyara kwanciya na nayi ina fuskantar ya dube fuska a daure yace tashi magana nazo muyi dake jin haka yasa na tashi kaina babu dan kwali ko hulla sai gashina dana daure a baya da ribon sai wanda yadan zubo min daga gaba kadan ina gyarawa. Ganin na natsu ina sauraren shi don jin abinda zai fada min din nasan abune mai muhinmaci daya shafe mu nidashi. Ganin na dago ina kallon shi yace Niger zan tafi yanzu in dawo da Nafisa don zata dawo dakin ta wurin yaran ta dani. Allah ya tsare hanya nace mai ban kara tanka mai ba yace ban son ki dauki dawowan ta da wani fahinta don dama kin san komai. Nasa kuwa sosai Allah yasa aje lafiya a dawo lafiya na kara bashi amsa tsaye yake a kaina komay yake tunane ban sani ba yaga ina kokarin tashi saman gadon daga zaune. Sai da na mike da kyau nace mai ko wani abin ne kuma don zan shiga ban daki in watsa ruwa ajiyan zuciya naji ya sauke yace zan kara rokon ki idan Nafisa ta dawo gidan nan ban son tashin hankali don Allah ku barni in huta please. Ka san ni da tashin hankali ne yaya AA inda dai zaka ya kamata ka tsawata tun a can amma ni may ye nawa na wani tashin hankali kuma. Tare fa na shigo na samay ku a gidan nan idan naga abin da bai min ba ba matsala bane sai in tatara nawa i nawa in kara gaba inda nafi wayau a zauna lafiya idan dai nice matsalan ku dama. Wanan kuma wani zance kike son ki dauka kuma ni dai kinji abinda na fadi yanzu na tafi a sauka lafiya na bashi amsa dashi ban iya shiga wankan ba na zauna a bakin gadon. Tunane nake wanan abin ko na kai sake ne ko kirane dabara ya fado min na jawo wayana dake gefe na kira kakana Bado bayan mun gaisa nake fada mai matsalana. Yace duk da dai kina kirana akaikai nasan wanan kiran na yau ba banza bane nace kamar ka sani tsoho don wallahi abokin nan dai naka ke son ya dauko min wani fitina kuma. Yace na sani dama kuma na fada maki zai dawo da matar shi kada ki tayar da hankalin ki ko kadan halinki nagari gare su ba zai barsu su samu nasara a kanki ba da yardan Allah. Ki bari ta dawo din mu ga abinda zata dawo dashi idan zai yi tasiri a kan ki ke dai ki dage da rokon Allah zan sa ai maki saukan alkurani anan da sadakoki yadda ya dace ayi. Godiya nayi mai mukai sallama bayan yan nasihohi da yai min akan zaman aure da hakkuri tare da kawar da ido ga komai don aikin asiri bamai dorewa bane yace ko anga nasara akan shi na dan lokaci ne kadan. Idan da hali yace kwana nawa nake zaton zaiyi a can nace bai wuce kwana biyu Bado yace barin gani idan zai yuyu zan shigo gaein naku yau din nan insha Allahu. Haka yasa naji dadi muna kashe wayan na ji kamar na kara samun warakan da kunan da zuciyana ke min a lokacin Mikewa nayi nashiga wanka na fito falo wurin su Altine muna hira tana tsokana na wai taga mijina ya dawo yana daure fuska yau ko ba an da take mai yaki karba mata. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 1/12/21, 6:57 AM - Xxxxx: Murmushi na sauke a fuskana ina sauraren maganar Altine yayin da cikin zuciyana nake dauke da tarin damuwa ina ji wani iri a raina sai dai ban baiyana hakan a fili ba ta yadda zasu fahince ni. Nace Altine dan uwan ki ba hushi yake yi da mu ba, damuwa ce tayi mai yawa yana da tarin damuwa yana cikin wani hali da yake bukatan adduan ku a yanzu. Da sauri ta dago daga ita har laraba dake ba Alamin ruwa tace cikin nuna damuwa ga magana na tace may ke faruwa dashi ne haka wallahi nima naga alaman hakan a tare dashi ai. Nace buzuwa tayi kiran shi tun daga Canada ya juyo ba shiri zuwa Niger yana can ya tafi ya dawo da ita zuwa jibi nasan zasu iso nan din insha Allahu. Sai naga Altine har laraba sun wani dafe kirji a cikin damuwa da firgici suna hada baki wurin fadin zata dawo fa kika ce hajiya ? Nace kwarai kuwa don ko har ya tafi can din don yazo da ita din sai dai idan wani akasi aka samu ne zai sa ba zai dawo da ita din ba. Nan dai suka shiga fadin albarkacin bakin su akan zancen ni dai ina zaune ina sauraren su ina nazarin maganan su ban yarda na nuna masu damuwa na ba a fili. Don su din duka dangin miji ne a gare ni watarana nakewa gudu akan su don abu na iya juyewa a tsakanin mu kamar yadda shatu tayi min zuwanta. Don dangin miji ba abin yarda ba ga matar dan uwan su idan mace nada hankali don duk yadda suke sonta suna da kyashi a kanta a zuciyar su sai dai abar na ciki a ciki. Ban yarda su san sitin na daya shafi rayuwana sai dai abinda ya shafi cikin gida da sauran su na zahirine zamu zauna muyi hiran shi dasu. Don kada in shiga daki zuciya ta ta hana ni barci yasa na daure na zauna a falon dasu suna debe min kewa akan damuwan nawa. Mun kai wani lokaci a falon muna zaune can waya na yayi kara na dauka tsoho Bado ne a layin yana fada min suna hanya zuwa wurina yau yana son min kafi a gidan. Nace Allah ya kawo su lafiya yace amin muka kashe wayan fita nayi na zuwa bakin get na samu Sanusi security don shi namu yazo daya dashi sosai a gidan. Nayi mai bayanin komai yace kada in damu idan yazo zai san yadda zai kula da sauran kada su fahinci wani abu akai nayi mai godiya na dawo ciki. Shi da kansa ya gyara inda kaka Bado zai zauna idan yazo din ya fada masu oga yace bako zai zo su kula dashi idan yazo. Wurin uku na rana Bado ya iso tare da Al,kassim dayai mashi jagora zuwa gidan namu don shi yasan gidan sun samu taro sosai a wurin mu tunda Bado ya shiga part din naje na gaida shi bai fito ba yana ciki yana aikin da ya kawo shi sai faman fadin yake ayyah kai kasa haba haka da yawa abin yai yawa a gidan nan. Nidai ba sanin abinda yake nufi nayi ba sai dai binshi da idanu kawai da nake yi. NIGER REPULIC Ta gama shiga da fice tana sauraren zuwan shi kamar yadda Yalliya mai magani ya gama tsara mata zuwan shi a duk inda yake a cikin satin. Ta fito daga cikin dan bukkan gidan su ta zo bakin layin su ta sai dan abinda zata karya dashi don tun safe bata kai komai a cikin ta ba don babu abinda zata ci. Tafiya take a hankali wasu mata biyu da suka santa suka dan gwauta juna suna gulmanta tunda suka hangota tafe da yar leda a hannun ta. Taji abunda suke fadi duk da bata ji sosai ba tasan gulman ne akan yadda ta lalace ta zabge kamar ba ita ba ce ke zuwa da motoci tana yadda taga dama a dan kauyen nasu. Wuce su tayi ba tare da sun gaisa ba duk da tasan su dariya suka saka ta juyo tana kallon su rai bace kamar zatai masu magana sai dai ta kyale su. Don fada yanzu ba nata bane abinda ke gabanta ya ishe ta a lokhaka ta koma ta dan samu dan kwano ta zauna a tsakar gidan nasu tana cin dan abincin su na kauye data saye. Fatiha ce ta fito ta kalli yar uwan nata tace dama daga kin gaskiya sai bata kina cikin rufin asirin ki babu ne baki samu a gidan ki. Kin dauki son duniya kin dorawa zuciyar ki yanzun da haka ta cika dake wa ya kwana a ciki ke kin rasa muda muke ci a inwar ki mun rasa. Babu takaici kamar yadda kika debo mai kaya kika sa aka tozarta mu a kasan da ba namu ba yanzu ban san da idon da zan kalli mijin ki dashi ba. Nafisa da sai abincin ta take ci bata kula yar uwan nata ba sai can dai tace Saboda wanan abinda ya amshe ban tsira da komai ba nake son komawa in debi rabona sai nayi mashi tas zan barsu da takaici. Kallon ta fatiha tayi tace har yanzun dai baki dadara da bin bokaye da malamai ba Adda duk kin sai da dan abinda kika samu kin koma kamar wata almajira dake. Na tabbatar da zaki dogara da abinda kika samo acan zai isheki rayuwa mai inganci har na bayan ki su samu amma duk kin bi komai kin sayar kin mika ma malamai kudi suna maki karyan sihiri. Tace idan bakin fata kike zaki koyi kunya Fatiha don gidan Samad dai sai na koma Fatiha tace idan ba komawan Allah da Annabi zakiyi mai ba ko yanzu idan kin koma gidan jiya zaki samu. Don wanan da kike yi kanta tafi karfin ki saboda ta fiki rike makami a hannun ta na tabbatar da in har ta dogara ga Allah ba zaki taba cin galaba a kanta ba. Maganan yai matukar bata wa Nafisa rai sosai haka yasa ta harzuka ta hau fada ma Fatiha magana cikin bacin rai ita ma. Har take fadin ta gane da ita makiya ke mata dariya dama ta fahinci tana tare dani ai nan dai sukayi kaca kaca da junan su sai da kyar uwarsu ta samu ta raba su. Bayan kamar awa hudu da fadan su kowa ya kama gaban shi tana zaune saman wani matacen tabarma wani yaron dan makwabatan su ya fara shigo da kayan abincin da AA ya tsaya ya sai masu a hanya da ya shigo kasan Niger din. Ido ta zubawa yaron dake sintirin shigo da kayan Fatiha ce tayi karfin halin tambayan yaron wa ke da wanan kayan haka yaron yace bako sukayi a gidan. Nafisa ko sai tunanen maganan malaminta yalliya take yi a ranta sai zuba ma kofan dan gidan nasu wanda ba wani gida bane ido. Sallaman da yayi ne ya shigo gidan yasa gaban ta faduwa don sai take ganin kamar mafalki take yi bashi bane ya shigo gidan ba. Fatiha dake tsaye a gaban kayan ne ta iya taron shi tana fadin sannu da zuwa ashe kana hanya maraba da babban bakon mu. Kallon Nafisa yake yadda ta ramay tayi baki duk ta jemay ka wani kwano a gabanta da bussashe tuwo a cikin shi da akaci wanda alama ya nuna itace taci abincin ta kasa kawar da kwanon a wurin don kiuya. Kawar da kai yayi daga kallon ta ya mayar ga mahaifiyar ta data fito daga dan bukkan ta tana son itama ta ganewa idon ta. Dakin iyayyen su Fatiha tayi mai shimfidan ta barma mahaifin su dake kwance a gefe yana jinya ya dago da kyat shima yana masu sannu da zuwa. A gurin da akai mai shimfidan ya zauna tare da gaida dan tsohon da yunwa ke barazanar aikwa dashi lahira ga kuma ciwon dake damun shi. Nafisa na ganin ya shiga daki ta mike da sauri ta fada dakin su tare da saurin canza kayan da ya samay ta dasu don ita kanta taji kunyan a yadda ya samayta ya samu gidan nasu kuma. Don zuwan karshe da sukayi duba jikin uban ya bata kudi da za ai masu gina a canza gidan amma ta hada ta dunkule ta koma Nigeria da kudin ta halakasu wurin bokaye da malamanta. Tana shiyawa a cikin sauri wanan zancen ya fado mata a zuciya bata san yadda zai dauki wanan abin ba tunda bata sa zai dawo zuwa yanzu ya gane ma idon shi bata aikata abunda yace tayi ma iyayyenta din ba. Nan dai ta zauna a dakin don matukar kunya da nauyin samad din ne ya kamata yadda ya samay ta da kuma gidan nasu da iyayyen nasu. Fatiha ce ta shigo dakin tace lalai bokayen ki sun iya aiki don aiki ya biya sai dai bamu san irin kamun da zakiyi ba a yanzu kuma. Nan dai fada ya kaure kuma dole taja bakin ta don kada AA din yaji hayaniyan su ya kara raina mata hankali kamar yadda yasha yi mata. Fatiha tace yazo da maganan maida auren ku ne duk da dama a shiye kike da hakan don da sanin ki hakan zai faru. Sai dai ina mai baki shawara ki bi a sannu wanan karon ki rike darajan auren ki ku zauna lafiya da kowa a gidan. Fatiha taci gaba da fadin ba komai da kake so kake samu ba kai tsaye ki dogara ga Allah daya umurce shi da tara mata iya adadin yadda yake so a gidan shi. Ko ba a fada maki ba wanan da kike tayar da hankali a kanta tafiki da komai wallahi kece dai ba ki yarda da hakan ba a zuciyar ki. Kinyi saa idon da zuciyar mijin ku ya makance a kan ki nafisa har bai iya hango illar ki a gidan shi don abinda yasa nace ta fiki ilimi da sanin kai shine agaba ke makin sani. Don haka ne nake cewa tafi ki ga komai wallahi don tana da ilimin da take amfani dashi gare ki da mijin naku a cikin hikima da basira wanda ni na dade da hango haka a gare ku. Tace zaki uya zuwa ku gaisa yana dakin soro yana jiran ki idan kin dawo zamu karasa magana da muka fara tace da yar uwan nata. Ta mike jiki a sanyayye ta fita dakin zuwa dan dakin da yake din ta shiga da sallaman ta dakin yana zaune yana kallon ta ta shigo. A daidai lokacin kuma tsoho bado na can yana aikin cire kafi da sihirin da bokayen ta suka tura a gidan don bai zauna ba tunda ya shigo. Take gaban shi ya fadi ya rasa may ma ya kawo shi nan yanzu shida ya rabu da kaya a baya hankalin shi a kwance yanzu a gidan shi yazo ya jajibar wa kansa wani wahalan nafisa kuma again. Sai ya tuna don yaran ta ne kuma shi din ba wai baya son ta bane a ranshi kallon da yai mata ne ya dan razana ta don ba haka yalliya ya fada mata zai faru ba a tsakanin su idan yazo. Cewa yayi zaiyi kuka ya gurfana mata yaji duniya babu sauran mace sai ita kodai hakan bai faru ba ita dai idan ya dawo da ita din zai fi mata sauki. Cikin sanyin murya take mai sannu da zuwa tare da gaida shi da hanya cikin sanyin jiki. Ya dago ya kalleta yace yanzu ke kin ga wanan zaman yafi maki a nan haka dukar da kanta tayi kasa don nauyin shi da kunya da take ji yanzu baki ya mutu murus bana fadi kuma. Tace nasan nayi ba daidai ba a baya abinda nayi na nuna son kai da bin shawaran kawayen bariki a kasan ku wanda ashe abin ba haka yake ba. Nai ma alkawari idan na koma yanzu zaka ga canji a gidan ka a tare dani idan Allah ya yarda cikin nadama da zai iya yarda da tuban ta. Yace idan kin yi hakan kin kyautawa kanki na baki yau zuwa gobe ki gama shirin ki mu koma tare dake. Wani irin ajiyan zuciya ta sauke don jin abinda ya fada ya mike ba tare daya tsaya sauraren abinda zata ce ba don yana son yaje yayi sallah a lokacin. Yana fita ta bishi da kallo don ya cika mata ido a gurin ta sauke ajiyan zuciya taga ya koma fari ya zama wani kato har dan tunbi ya aje tace a ranta dan barin ta gidan ashe bai damu da ita ba ke nan tunda had ya samu kwanciyan hankali a tare dashi haka. Wai shi samad wani irin muyum ne malamin ta ya tabbatar mata cewa ga abunda zaiyi idan yazo sai bata ko digon girgiza da nadaman rabuwa da ita ba a tare dashi banda shan kamshin da yake mata. Tace ba komai a ranta ta samu din ta koma tunda har yazo din zata dasa a inda ta tsaya sai taga bayan wanan yar iskan da harda yar uwan ta ke ikirarin ta fita wai da munafukan iyayyen sa masu daure mata gindi a gidan. Don ba karamin shiri tayi akan komawan nata ba don ga haske ta fara gani tunda har yazo din wurin ta. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU Kuyi hakkuri yau ba yawa kun san ranan yau ina gajiya sosai . 1/13/21, 7:23 AM - Fatima Amarya: Ranan Bado bai kwanta ba sai da yayi duk wani abinda yake son yi a gidan zuwa safe ya gama hada komai koda na shiga gaida shi bayan sun karya yake ce min su zasu koma. Da mamaki na kalleshi tare da fadin tun yau kaka Bado yace to may zan tsaya yi na gama maki abinda ya kawo mu ai sai dai gaskiya duk wanda yai wanan aikin dana cire a gidan nan yana da karfin zuciya sosai. Ki gode ma Allah dake baki kariya akan hakan don da wanan asirin dana gani a gidan yana aiki a kanki da yanzu sai buzun ki. Nan dai ya fada min maganganu masu firgitawa yace harda wanda aka tura ai muna a yanzu duk ya karya su insha Allahu. Ya kuma dasa nasa don neman kariya a gare mu a gidan ya kara da ce min kada kiji komai akan duk wani abinda zatayi akan ku akan ta zai koma komai ta dauko maku. Ke dai ki kara dagewa da neman tsari a wurin Allah da gafaran sa shine babban mafita a gare ku nayi mai godiya sosai na koma ciki na hado mai tsaraban da zan basu na kawo mai yace a, a ko kufin motar ki ni ba zan karba ba mu dai fatan mu ku zauna lafiya da mazajen ku ku tara muna iyali masu albarka. Murmushi nayi tare da masa godiya nace da Alkasim zan bashi sako na muka fita nace ya dauka idan sun isa ya bashi a can ya kara min godiya. Suka tafi suka barni da kewan su a gidan tun tafiyan su na fara aiwatar da abinda ya bamu a kaina da yara na a cikin da bara nake aiwatar wa. Ya dade a tsaye yana jiran ta don ance tun safe ta bar gidan zuwa wani guri da ba,a sani ba a lokacin ne Fatiha ta samu kebewa dashi. Tace ka ga farce ni ga abinda ya faru a bayan wallahi bada sani na haka ya faru ba sai da wa yan nan mutanen suka tsayar damu ne na san abinda ke faruwa. Yace ba komai Fatiha tace duk da haka sai ka kara hakkuri da Adda don bawai ta canza hali bane sai ma abinda ya karu mata daga halin ta daka sani a baya. Murmushi ya sauke a fuskan shi yace Fatiha na saba da halin Nafisa banga wani abu da zatai min yanzu wanda ban sani ba daga halin ta kuma. Allah ya kyauta tace don tasan ba yin hankalin shi bane bai a cikin hankalin shi don koda ganin yadda Nafisa ta koma ba zai kalle ta ba ai. Tunda ta tun karo gidan gidan ta hango motar shi a kofan gidan gabanta ya fadi tsayawa tayi nisa da gidan tana tunanen abinda zata fada masu don tun asuba tabar gidan zuwa wurin malam boka Yalliya don da nisa sosai da kauyen su zuwa wurun shi. Hango AA ya fito daga gidan ya kara fadar mata da gaba ta karaso don babu yadda ta iya tana ganin kamar tafiya zaiyi ya barta kuma. Simi simi ta karaso tana kokatin boye ledan data dawo dashi cikin jikin ta da ganin ta kasan bata da gaskiya a yanayin da take tafe. Daga ina kike haka ya fada fuska a daure yana kallon ta ta dago kai ta dan kalle shi tace daga gidan yan uwa na nake can cikin gari naje in ban kwana dasu ne. Yadda take in,inaya yasa ya fahinci bata da gaskiya yace shine baki danar da kowa inda zaki ba da zaki fita tace koda na fita babu kowa a kusa lokacin. Yace ke dai kika sani tunda ba zaki daina wanan halin da kika sawa ranki ba na biye biyen bokaye da malamai sai dai ki sani indan ni kike wanan shirmay babu abinda zan fasa. Tace wanda yace ma na fito wanan wurin bai fada ma daidai ba ni sada zumunci na tafi yi a gari yace ki shirya don kin san da asuba zamu wuce ban son inzo in samau baki shirya ba kuma. Tace Allah ya kai mu ta shige gida tana ta kokarin boye galon din ruwan rubutun da ta dauko a hannun ta. Tana shiga ta nemi wuri ta aje kayan hannun ta tace wa fatiha ina kika fada ma Samad naje ? Fatiha tace ina maki hani da kiran mijin ki da sunan nan na Samad don Allah kadai takai can a kirashi da hakan don zunubi kike daukarwa kan ki. Idan na kirasa da haka ki hana shi ya amsa min yar sa ido duk sherin da zaki kulla min an rigaki ko don bakin ciki kinga zan komawa mijina zaki kulla min sheri cewa naje gidan bokaye. Kai Fatiha ta kada tace ai hannun ka bai rubewa ka yanke ka yar sai dai kaita kayan shi hakana a jikin ka. Ni ban fada mai komai ba tunda ba hauka nake yi ba da zan bata maki auren ki nassn abinda nake kece dai ke dauka na makiyar ki don fadin gaskiya na gare ki. Nasan a yau zasu dawo don haka tun tashin mu nasa laraba ta gyara muna falo da ko ina na gidan inda naje dakin shi na gyara da kaina. Mun gama na saka kamshi a ko ina na gidan tare da abinda tsoho bado ya ban in hayake gidan dashi gaba daya. Daga nan muka dawo part dina muka gyara komai a ranan na canza komai na part din aikin maryam ne wanan komai sai kyali yake kamar ranan aka kawo ni gidan. Sai zuwa hudu da wani abu muka rage aikin komai ya kammalu karmar yadda nake son shi wanan karon launin purple da fari ne a part din nawa. Komai ya canza gaba daya sai mutum ya dauka sabon wuri ne muka koma ga kayan da ta karbo min wurin dinki data kai express akwana biyu aka gama min su. Sai turare dan arab iri iri data kwaso min da kayan make,up abinci lafiyayye Altine ta girka da abin sha zuwa biyar duk mun hada komai mun kara gyara gidan da part fina duk da baiyi wani datti ba. Shida da rabi suka diro gidan tare da yanyala da samiha sai samira da tai wani baki sai hakora da dogon gashi ya rage a jikin ta. Suna zuwa part dina ta nufa da murnan ta sai kuma taja ta tsaya tana bin ko ina da kallo ta sauke ajiyan zuciya. Na tare ta sosai tare da murnan ganin ta ta dan dade zaune a wurina nake tambayan ta ko tayi ciwo ne tace batai ciwo ba yunwa daine don ba abinci kamar nan ba kulawa da sauran su. Tausayi ta bani sosai da take min bayanin sai gata tana kuka tana fadin ita ba zata kara komawa can ba. Hakkuri na bata tare da fadin taje tayi wanka tazo taci abinci tace zataci kafin tayi wanka haka nasa a debo mata abinci ta zauna ta fara ci. Sai da ta kusan gamawa ne sai ga samiha ta shigo kiran samira din da wanan halin nata na rashin sallama idan zata shigo wuri cikin tsawa na dakatar da ita da fadin ke idan ba zaki sallama ba maza ki fice min a part din nan. Sai da ta dan kadu tace Sallamu Alaikum na amsa a hasale tare da fadin wanan dabi,an baida kyau don Allah mutum kamar ba musulmi ba shiga wuri ba sallama. Tace a cikin yaresu uwar samira na kiran ta sai yarinyar ta bata rai nace jeki kiji kiran da ake maki sai ki dawo ta mike zuwa amsa kiran da uwar take mata. Shiru shiru banji ya shigo ba na daure na mike zuwa part din shi in mai sannu da zuwa dauke da Al,amin a kafada na. Na shiga da sallama na samu ya fito daga wanka yana saka riga a jikin shi ya amsa muna sallaman tare dan juyowa ya kalle ni ya mayar da kan shi ga abinda yake yi din. A hankali na tako na karasa shiga dakin na tsaya daga bayan shi ina fadin sannun ku da zuwa an dawo lafiya ya mutanen can ? Lafiya ya amsa lokacin da yake karasa saka rigar a wuyan shi yace ba tare da ya kallo ni ba fuska ba yabo ba fallasa yace waye kika dauko nace Al,amin ne yace ina mami sai lokacin ya juyo yana fuskanta na. Nace tana barci bayan Laraba bai sake magana ba sai ya dauki turare yana fesawa jikin shi tsarguwa da mamakin shi ne ya kama ni a lokacin. Shiru dakin ya dauka na dan wani lokaci juyawa nayi zan fice daga dakin don jin shirun yayi yawa akwai abinda zanci ya fada a takaice. Akwaishi idan zakaci na girka maku dama don ina sa ran dawowan ku yau au har kirga kwanaki kika tsaya yi ke nan ? Ban gane ba idan nayi hakan kuma laifi ne komay nace dashi a dan hasale don wani irin mamakin shi nake ji lokacin. Dan kallona yayi kamar zaiyi magana sai kuma ya basar yace bashi na tambaye ki ba abinci nace ki kawo min dan Allah. Nace ba laifin ka bane kuma banyi mamaki da ganin haka ko jin haka a gare ka ba yanzu don nasan inda ka fito ai. Ina fadin haka na sa kai na fita daga dakin jikin shi ne yayi sanyi don yasan ban nuna kishi ba ga dawowan nasu tunda har nazo na tare shi da dawowa. Amma shi bai san dalilin daya sa tun kan ya tafi baya kaunar gani na ba yanzu yasan ina iya kokarina amma shiya rasa laifin da nai mashi din yake jin haka akaina. Ina komawa ina jin zuciyana yana min kuna na aje yaron na hada mai abincin nakai na aje mai nafito don yana daki har lokacin bai fito ba. Na dawo part dina ban zauna falo ba na shige daki na da yasha gyara na alfarma wani iri nake ji kamar zuciyana zai fashe duk karfin halin da naso yi in dake a lokacin na kasa. Zuciyana ta kasa daina tuna irin kallon tsanar da yake min tun kan yayi tafiya har zuwa yanzu da naje gaida shi din ya na min wanan kallon na rainin hankali. Tambayan kaina nakeyi may nayi masa wanda ban sani ba may yasa bai min adalci ne idan halin shi na wulakanci ya tashi akaina ya kamata yai min uzuri ko don wani abu. Hawaye naji yana silalo min a fuskana nace a hankali a fili may nayi ma AA yake son ya tsiro da abinda zai kawo fitina a tsakanin mu . Why why duk hakkuri na da dauriya baka gani a idon ka ne share hawayen nayi da sauri na jawo waya ina neman layin tsoho bado in fada mai. Sai da ya gama sauraro na yace kasa hadizatu kada ki damu da wanan don ba haka aka so ba a tsakanin ku kibi komai a sannu da yarda Allah duk wanan abinda yake ji a kanki zai daina jin shi. Bafa karamin aiki akayi maku a gidan nan ba don har jaki baki da bakar akuya masu rai aka birne don ku aka hada fatar kura dana kare dana bakin maciji akai asiri dashi duk akan ku. Ni kaina da nayi aikin cire kafin nan ba karanin wahala nasha ba a jikina don bakin Aljannin da aka turo yana maku aiki a gida. Komai ya wuce da yardan Allah don ba karamin kwaran muka kwasa dasu ba a cikin daren nan danayi aikin a gidan naku. Ki saki ranki ga kowa kada ki bari kowa ya fahinci kariyan ki har mijin naku da sauran wa yanda ke gidan kafin aikin mu ya shiga kansa. Jin shiru ga almuru ya yayi sosai a lokacin ya fito a dininng din ya samu na jera mashi komai yadda ya kamata ya bude yaga sakwara ne a ciki. Sai kulan miyan da ke dauke da dan ganye akushi yafi yawa sai nama dake ciki manyan yanka dasu sai kamshi ke tashi daya buda zama yayi ya fara diba yana zubawa a plate. Ya fara ci a hankali yaji dadin girkin har cikin ranshi ya lumshe ido a hankali yaci gaba da ci ya kusa gamawa ne sai ga Nafisa ta shigo part din batayi wanka ba har lokacin balle ta canza suturan jikinta daya sha hanya. Samad kai ka samu abinda kaci mu har yanzu bamu samu komai munci a cikin mu ba yunwa muke ji sosai wallahi. Kallon ta yayi yace ba abin dafawa a shiyan ki ne yanzu tace da wanan gajiyan hanyar da muka kwaso zamu tsaya dafa abinci yanzu ? Yanzu kai baga shi ka samu abinda kaci ba har don bamu da gata mu an barmu a zube hakana ni da tan uwa na. Ya isa dan Allah ban son tsiro da fitina tun yanzu don Allah idan da tasan kina ci may zai hana ta baku tunda ta dafa abincin. Yana fadin haka ya mike ya shige dakinshi ya barta a gurin abincin ta bude don yunwan da take ji gashi abincin yana daukan hankalin ta andade ba a gamu ba ta zauna ta cinye sauran daya raga tas har miyar bata bar komai ba. Ta na isa dakin ta ta samu na aiko masu da nasu tace su samiha suci su kwaso mata naman ciki su saka guda guda a nasu suci ta zauna ta kara azawa a wanda taci din a wurin shi. Sai da ta koshi nak tasha ruwa ta getse tace koma da ta zuba muna wani abu ba zai taba kama mu ba don don mun fi karfinta wallahi. Yar wahala ina jira in huta ne in karbe yarinya na a gurin ta munafukar banza da wofi kawai wai ita uwar kinibibi da kissa itace gwanar rike mashi yara idan an barsu. Yanyala tace ai Ihisan ta ban mamaki ji yadda ta nuna kamar ma bata san mu ba a gidan nan hankalin ta duk yana can gurin ta. Ran Nafisa yai mugun baci tace ashe kuma kun lura da hakan nasan wani sheri tayi ma yaran ta raba ni dasu don ta gaje min su . Idan da wanan Aljannar ce sadiya kawai ko kallon ta ba zanyi ba taje taita kayan wahala dama ni ban sata a jerin diyana ba can, don taulalin wahala ne kawai. Yana zaune dakin bayan ya gama salolin shi ya dan duba laptop din shi ya koma saman gadon shi ya kwanta a rigingine yana kallon agogo. Ba wanda ya shigo dakin a cikin mu har wanan lokacin wani zafi yaji a ranshi ita Deedar tunda ta fice bata shigo ba haka kuma Nafisa bata zo ba har lokacin. May ye na fushi ga dan maganan nan yace to shima may yasa ya fada min wanan maganan ne don bai kamata ya nuna min hakan ba don ai kulawa dashi na nuna a fili. Ya dan juya tare da jan tsuki yana ci gaba da tunanen shi sai ga Nagisa ta shigo dakin yana cikin yanayin jin komai bai mashi dadi. Ya dan juyo ya kalle ta har lokacin ba wani wankan da tayi a jikin ta don yanayin ta kawai ya isa mutum ya gane hakan. Zama tayi a bakin gadon tana fadin na dauka gajiya yasa ka barci ai ya katseta da fafin may ya hanaki wanka tun dazun da muka dawo har wanan lokacin ? Ta kai hannun ta saman jikin shi da zuman taba shi ya gwauce yace cikin dakewa tashi ki shiga ki watsa ruwa tace bazan iya wanka yanzu ba don gudun daukan mura. Kyaleta yayi dole suka kwanta haka na badon yaso ba sai dan tsamin daudan da takeyi sama sama don yanzu ya saba da shakan kamshi ga jikin mace. Nikan tunda na koma part dina mukayi magana da tsoho bado naji wani kwarin gwiwa yazo min na fito nace akai masu abinci don nasan dare yayi ba zasu girka ba. Tunda laraba takai mata abincin ta dawo nasa ta rufe part din namu bankara fitowa ba sai washe gari na shirya tsab na nufi part din nafisa na samay su kaca kaca a zaune. Sai hira suke zubawa a cikin yare suna dariya nayi sallama na shiga gaban Nafisa ne ya fadi don gaba daya na sauya mata na koma mata wata hamshakiya dani a idon ta. Sannun ku da zuwa nace mata tare da tambayan mutanen gida magana nake tana kallona a cikin mamakin sauyi na da yanayin magana na. Na juya cikin wani tako da take ganin yanga da sallo nake mata na fice abina ta dade a zaune kafin ta sake wani irin ajiyan zuciya. Tace duniya ku tabani idan ba mafalki nake yi ba don Allah yaushe nayi sake yarinyar nan ta zama haka a dan lokaci kadan a dan watan nin da nayi bana gidan nan. Yanyala tace ashe bake kadai kikaga hakan ba nima mamakin sauyawan ta nake a raina gaba daya ta koma wata babban mace da ita. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 1/15/21, 8:23 AM - Fatima Amarya: Yayi mamaki da yafito ya samu breakfast din shi a dininng na aje mai komai na tafi koda ya sauko zuwa part dina ya samu duk mun fice a gidan kofa a rufe. Ya tsaya yana mamaki inda mukaje haka ya kira waya bai shiga ba ya kira na Altine ya shiga yace Altine ina kuka ke kuka rufe gidan. Tace muna nan makarantar su khadija suna wani taro ya kashe wayan tare da kutawa a fili ya koma part din Nafisa a falo inda laraba ta aje Sadiya tana gurin tana ta tsala ihu har zuwa wanan lokacin. Daukan yarinyar yayi ya nufi cikin dakin nafisa dake kwance tana ramuwar barcin ta hankali kwance ya bita da kallon takaici tare da bugun ta yayi a hasale ta falka a gigice tana kallon shi. Yace yanzu kin kyauta ke nan kina nan kina barci kin bar Sadiya ita kadai a falo tana ta faman tsala kuka baki damu da damuwanta ba. Tace Sadiya may ye hadina da ita a yanzu ai na riga na mayar da ita hannun uwarta na ainihi ke nan idan ba diyar ta bace ta yaya zata rike min ita haka kawai. Wa kallo yai mata na takaici yace Nafisa kina da hankali kuwa wai wanan haukan da kike yi a ina kika taba jin anyi haka ko duk jahilcin ne wannan ina laifin yarinyar nan khadija da ta sa hannu ta rungumay maki diya abayan ki tsakani da Allah. Wani dariya ne ta sake tare da fadin kai may ka sani ta dai rike yar ta amma wanan mai zubin yan ruwan kan na yafe mata ita harga Allah. Yace idan kin ce haka zaki yi kuwa ba sadiya ba har ihisan din duk a wurin khadija zasu zauna su biyu tunda ke baki da hankali nagane yana fadin haka ya fita dauke da yarinyar a kafadan shi yana lalashin ta zuwa part din shi. Bamu dawo gidan ba sai after two ina saye da rigan mu na lauyoyi a jikina na tsayar da mota yana tsaye suna magana da Yusuf su Altine suka fito suna dauke da yarana. Fuskan shi a kaina har na fito daga motar gaida su nima nayi kamar yadda su Altine suka gaida su sai dai ban tsaya ba Yusuf ne yace yau kin fara fitowa lauyan ki na ainihi ke nan nace wallahi kasan muna gab da gamawa yanzu ba hutu a gare mu. Daga haka na shige abina Yusuf ya karbi mami hannun Altine mun shiga da gajiya a falo muka ya da zango dukkan mu. Abinci muke ci ya shigo part din dauke da Sadiya ban dago na kalle shi ba yace tun dazun yar nan tana gurina da kyat na samu ta dan ja fida kadan. Altine ku karbe ta ku bata wani abu taci don nasan yunwa take ji ga bata abinci da wahala Altine tace ba uwarta ta dawo ba ai an kaita da safe da zamu fita. Fuska ya bata tare da fadin Altine ku barta a nan gurin ku don Allah fadin hakan da yayi yasa na dago kai da sauri ina kallon shi tare da fadin ta zauna a nan kuma bayan uwarta ta dawo. Ina don uwar bata nan ne muka rike ta anan din yace kin ji magana na ai nan nake bukatan su zauna dukan su su biyun yanzu yana fadin haka ya juya ya fita daga dakin. Bin bayan shi da kallon mamaki nayi tare da sauke ajiyan zuciya sai laraba ne tayi magana take fadin ina ganin dai wani abin ne ya faru akan yaran kun san ba kirki ne da ita ba. To amma mama an taba yin haka don Allah ina don uwar bata nan ne na rike su a nan wurina yanzu kuma zai zo da wanan maganan haka. Altine tace maganan Laraba ne dai dole akwai abin da ya faru nace ni gaskiya Anty matsalan gidan nan ya isheni haka wallahi. Hakkuri suka shiga bani tare da fadin don yaga kina rika masa ne a gurin ki ne kadai yake ganin yaran zasu ji dadi kuma su samu tarbiya ni dai shi nake gani kamar hakan ne. Shiru nayi na kasa ci gaba da cin anincin dake gaba na duk da yunwar da na kwaso a lokacin na mike zuwa dakina wanka na shiga na fito na gyara jikina tare da saka bubu a jikina redmade mai laushi daidai zaman gida. Falon na fito don kada damuwa ya damay ni ni kadai ban dade da zama ba sai ga text ya shigo min shine ya turo min wai in mashi list din abinda muke bukata a gidan. Share zancen nayi naci gaba da abinda nake yi nace Anty yau naga kun wahala ina ga zan bar fita yanzu da yaran nan a gida zan dinga barin ku tunda sunyi wayo ko ? Altine tace wa yan nan diyan nawa dake da yawan tsotso haka zasu yarda su zauna a gida nace idan sun samu madara zasu zauna sai mu gwada a satin nan mu gani. Tacevto shike nan idai mahaifin su ba zai yi fada akan haka ba nace satin nan ba zamu zauna a cikin makaranta ba don zamu shiga kotu muyi aiki ne a can kin ga ko fita dasu ba zai yuyu gare ni ba ai ke nan. Laraba ne da gulma yaci ta shigo take fadin ina ganin da mutum biyu kawai aka dawo Altine tace ni tun da suka dawo ban ga ko dayan su ba har ita uwar gayyan tasu. Ihisan ce ta shigo part din namu da kukan ta sai ga uban ya shigo shima yana zare mata ido yace idan na sake ganin kafan ki gurin su saina balbala ki a gidan nan. Yana fita sai ga Nafisa a part din nawa ta shigo da zuman masifa sai kuma taja tayi tsaye tana bin part din da kallon mamaki can sai ta basar tace Ihisan fito muje. Ba zaki zauna gurin wanan matsafiyar ba ya dai bar wanan data sauya ta karasata a nan idan ta iya tayi gunduwa gunduwa da namar ta kafin gobe. Sai yarinyar ta make hannu taki zuwa tana matsowa da zumar janta ta yanka wani ihu ta nufo gurina tana kuka tsayawa tayi tana kallon mu nace Ihisan jeki gun uwar ki kin ji. Aiko baki fada ba zata zo ne tunda bake kika haifar min ita ba nace ina yanzu gorin haihuwan nan ya wuce a gurin ki tunda kin tabbatar ni din ba juya bace. Ina magana kamar banbson yi tare da ahafan kan yarinyar dake kwance a jikina tana kuka au don wa yan nan diyan da kike ganin kin haifa mai masu zubin diyan ke tare wa ya sani ko wani bayahuden kika je yai maki cikin su. Nayi murmushi nace ba wani baya hude yai min cikin su ba wanan dai da kike hauka a kansa ne yai min. Wata kila baki iya kwancin bane yasa kika haifo naki a haka don haka ki fice min daga shiya kafin ranki ya baci yanzu a gidan nan don zan maki abinda sai kinyi jinyar jikin ki. Ya dai ba taki bace tawa ce kuma dole ki bani abina nace diyan ki dai don naji kina magana akan Ihisan kadai kwashi tarkacilen diyan ki ku tafi don Allah banson yawan hayaniyar nan naki a nan kina daman min yara dake barci. Haushi da takaicin magana na ya kamata a wurin tace don wayan nan diyan da kike ganin kin haifa kibar daga kai a kansu kibari kiga girman su. Ta Allah ba taki ba in sha Allah idan da rai da lafiya kamar gobe ne kin gani sha kurumin yadda kowa ya girma su ma girman zasuyi da yan uwan su gidan nan. Ta rasa may zatace ta fice daga part din Altine tace dama na fada maki akwai wata a kasa kyalesu muga iya gudun su gidan nan. Ko yanzu ki gode ma Allah don ta wullakanta ai ga saki ga yaranta kiri kiri miji ya hanasu zama a gurin ta ko haka ai ci gaba ne a gare ki don ya yaba da ke ke nan. Wanan yabon kan ai da wahala Anty ace an dauki taulalin yara an dora ma sai sun girma su kama uwar su. Tace ke dai din ce ba mai son hayaniya ba amma sai naga ko sanan riba ce a gare ki ai tunda duk wani kudin lalurar su yana a hannun su. Murmushin takaici na sauke nace wanan bai a gaba na sam don ni ga Allah na dogara da lamarina idan rabona ya koka a wurin shi ko bai da niyar bani sai ya bani. Shiru falon yayi na dan wani lokaci na mike ina fadin bari na dan huta a daki idan nayi sallah. Na mike suka bini da kallo sai dana shiga ne laraba tace mace mai hakkuri komai tana gani a gidan auren ta don kin san dai wanan maganan ba gaskiya a cikin sa fada ne ba halin ayi kawai. Altine tace hakkurin yarinyar nan yai yawa wallahi ba zakace zaka samu yaran yanzu da wanan halin ba. Nan dai suka zauna suna zancen ina ciki bayan na idar na jawo wayana ina fada ma maryam abinda ke faruwa don bamu samu kebewa ba a school. Ina gama wayan daidai lokacin ya dakin ba sallama balle inji shigowan shi sai muryan shi naji yana fadin baki ga sako na bane dazun. Nagani nacea takaice tare da juyar da kaina gefe daya na bar kallon shi yace dake nake magana ai . Nace don banda bukatan komai yasa ban amsa ba idan ma ina da bukata ai kasan duk abinda ya dace a saya a gidan ko ? Bai iya furta komai ba don yadda yake jin zuciyar shi a lokacin kamar zai tafi yace ba haka na saba ba don haka ki fada min abinda kuke da bukata nace. Shiru nayi mai ban bashi amsa ba na matsu ya fice min daga dakin ya sake fadin bakiji bane ina magana dake ya fada a hasale. Nace ka sayo muna abinda ka sai muna last time kafin ka yi tafiya shike nan ko sai madaran yara da za a saya masu kuma. Barin fada maki ban daukan wanan tsiwan naki yanzu bai kai karshe ba nace ai ba sai ka fada ba don alama ya nuna kansa. Don ko ganina baka kaunar yi a kusa dakai don haka nima na kama kaina da kai tunda ba dole dama zaman biyayya nake a gidan nan ai. Kana ja min tashin hankali na ba gaira ba dalili a cikin gidan nan ina zaune ban shiga shirgin ku ba duk da hakan ban tsira a gare ku ba. Duk hakkuri da dauriya da biyayyan da nake maku kai kan ka baka ganin hakan sai ka cisguna min ka wullakanta ni yadda kake so. Menene laifina may nayi maka da zaka dauki karan tsina ka dora a kaina don kawai ka cusa min bakin ciki da tashin hankali a zuciyana. Ya isa haka kin fadi abinda kike son fadi kin gaji dani yasa kike fadan haka sai dai ki sani zama a gidan nan kamar yanzun kika fara don gida ba fita a cikin shi kin shigo cikin shi ke nan. Murmushin takaici nayi nace tunda kaine autar maza kake ganin idan an shigo ba fita ka sani ni ba irin tarkacen matan ka bane dake tsayawa yin asiri ko wani abu a kan ka. Yace nasa don nasan ko wacece ke har da halin da baki san kina dashi ba nasani kaita sani mana wanan kai ta shafa kamar yadda kace baza ka dauki halina ba a yanzu nima haka ba zan dauki naku ba a yanzu daidai zamuyi da kowa a cikin ku. Khadija wuyan ki ya isa yanka nace har datsa ma ya isa ba yanka ba sai ka shirya ka datse shi din ki shirya min abinci irin na jiya don banda lokacin wanan a yanzu. Kaje matar ka ta shirya ma ita da kake ganin idon ta da kwali a gare ka yanzu dama ku maza haka kuke kun fi son macen da ke latsaku a zauna lafiya. Yakai kofa ya juyo yace ashe shiyasa kema kike son ki gwada latsa ni din to bari kiji idan kinyi haka ke wuya zaki ji a gurina wallahi. Haka kace yace ai kin ji na fadi yanzu sanan may ye dalilin ki na kin shiga motar dana saya maki nace don bada zuciya daya ka saya min ba ai ba don ni ka saya ba may ye mutum bai sani ba. Kallon mamaki yai min yace haka kika ce to in kara ganin kin shiga wanan motar dake ci mun rai idan ran ki bai baci ba a gidan nan. Wanan din dai da aka bani da zuciya daya zan shiga tunda bakai ka saya min shi ba OK zamu gani dani dake a gidan nan kuwa. Ya tura kofan ya fita a hasale nace mijin tace kawai matar ka ta bata ma rai kazo nan zaka fashe a kaina don nice marainiyar ka . Da safe na fito zan fita sai wayau don babu motar a gurin na juya a hasale na shiga gidan zuwa part din shi banyi mamakin ganin kofan a bude ba lokacin don kila haka ya kwana yana jirana. Yana kwance yana waya na banko kofar dakin wani kallo yai min ya ci gaba da maganar shi na koma gefe na tsaya cikin fushi ina jiran ya gama. Ina jin ya gama nace ina motana yake don na fito yanzu ban gan shi ba yace nasa an fitar min dashi a gida don nace bazaki kara shigar shi ba ai. Wani kake son in shiga ina wanda na saya maki din bazan shige shi ba na fada ma baki son fita ke nan gidan nan key din babbar motar shi dake aje na dauka na fita. Dashi na fita zuwa school din in da zamu kotu yin wani gwaji sai dana biya school na ga maryam na wuce zuwa kotun. Ranan sai five muka dawo gida Nafisa na samu tana magana a waje da wasu bakin ta yun shigowa na kallon su ya dawo gare ni na fito a gajiye ina rataye da jakana da rigan mu na lauyoyi a dayan hannu na na wuce su. Uhuumm naji wata tace tace kin ga illar barwa kishiya gida ke nan Nafisa tace ai ni wanan shegiyar yarinyar ban san yadda zanyi da ita ba. Yaya ko zakiyi da ita banda ki kawar da shegiya ai taki kawowa ne wata tace kafin nan ai shi mijin naku zaki tun kara da yaba ta wanan daman haka kina may har haka yake faruwa ga matar da tazo ta samay ki a daga baya. AA ya shigo ke nan yana kokarin shiga wanka sai gata ta shigo a hasale tace samad abin naku har yakai can kaba wanan yar iskan motar ka tana shiga don an mai dani banza ko may ? Amma dai kin san ita din mata tace don haka tana da iko da abina kamar yadda kema kika matsa sai da kika dauki wanda nake amfani dashi a baya. Tace ke nan don taga na dauka yasa ta dauka yace a ganin ki ba mota dai nawace don haka banga dalilin zuwan ki nan kisani a gaba ba haka. Yana fadin haka ya shige bandaki ya barta a wurin ina sam wallahi ba zai yuyu ba ta shiga motar dani ban shiga ba yana jin ta tana haukan ta ya kyale ta. Part dina ta nufa sai ganin ta ta fado muna lokacin ina rungumay da yar ta sadiya ina bata abinci tace ke bani key din motar da kika fita dashi. Ke kina da hankali kuwa zaki fado min daki haka kamar mara hankali idan kina da karfin kwata kizo ki kwata an ki baki din mota kuma ta zama mallakina daga yau. Na gane kina jayayya danine a gidan nan nace ashe sai yanzu kika gane hakan ke jayayya ai ya kare tunda na mallaki abinda ke kika kasa mallaka din. Tace kina nufin don kin haifi na miji gidan nan har zaki min gori a kan hakan nace kaji jahila haihuwan namijin kuma shine abin tsone maki ido ni ban kai can ba. Bani shige ma Allah a gaba idan kina da karfin kwatan key din kizo ki diba na karfi ne a hannuna kaji min mata ko kin ki ko kin son abin miji na kowa ne a gidan nan. Barin fada maki tace duk yadda kike gani kin kai ga shige shige a gidan nan na damaki na wuce gurin nace may shige shigen naki ya haifar maki ban da saki. Ni ga Allah na dogara da alamarina ke da kike ganin wani zai baki abinda Allah bai tashi baki ba sai kije kitayi mota dai ce sai dai ki mutu a kan shi. Tayi zage zagen ta ba wanda ya kula ta Altine ce taso kula ta tunda na daga mata hannu tayi shiru bata kara tanka taba har taci tagaji ta fita kowa yai banza da ita. Yana zaune sai gata ta dawo cikin tsawa ya kore ta a dakin yace tasan shi tasan halin shi zai saba mata yanzu akan maganan nan idan ta damay shi. Da mamaki take kallon shi tare da tunanen irin kudin data kashe a kan shi gashi komai sai kara lalace mata take ganin yana yi a gidan tun daaowan nata. Fitinan yau daban na gobe daban duk dako malam yace zata ga canji sosai a gidan idan ta koma ba abinda ta gani daga cikin aikin malamin sai sa, an dawowa gidan kawai data gani. Daki ta koma ta kira malam Yalliyan tana fada mai halin da take ciki yace har yaushe ta koma gidan idan da bai mata aikin kwarai ba har yaushe zata koma gidan. Hakkuri ta shiga bashi akan gajin hakkurin da ta gani a gidan ta kashe wayan tana sauke ajiyan zuciya tare da tunanen wani mataki zata dauka kafin maganin ya fara mata aiki kan wanan yar iskan Banufar. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 1/16/21, 5:48 AM - Xxxxx: Har sati biyu ina amfani da motar AA bai taba tambaya na don may ba nima kuma da yake ba zama nake ba ban kula da lamarin kowa a gidan. Yau na dawo a gajiye ba abinda nake so sai in yi wanka in dan kwanta shigana ke da wuya waka na fara yi ina saka riga sai gashi ya fado dakin. A cikin yanayin daure fuska nagaida shi ya amsa tare da fadin may ye hujjan ki na fita kibar yaran nan a gida. Naga ai sunyi wayo yanzu yasa na barsu tunda ina da masu kama min su a nan din don wahala nake dasu idan na fita gashi satin nan duk bamu zauna a cikin sulchool ba tun wancan satin muke shiga kotu. Ban dai son hakan may yaran zasu hanaki yi idan kin je dasu din tunda ba ciki zaki shiga dasu ba ya fada cikin daure fuska shima. Nace don ba kai suke tsotso ba amma barin su gida aiko su saukin su ne hakan nagani zaki fasa fita ke nan muddin kika ce ba zaki fita dasu ba kuwa. In fasa karatu fa kace yace haka nace don naga kin dauki karatun fiye da komai a zuciyar ki yara kan a gida zan barsu don shine sauki a gare ni yace ki barsu din idan kin isa. Washe gari na fice ba tare da yaran ba kira uku nagani nasa ban daga ba sai da aka gama wani sharia da muke saurare na fita na kira shi. Yace may na fada maki jiya khadija nace may kafa da min fa yace ban ce kada ki fita gidan nan kibar yaran nan a gida ba. Nace ka fada min to don may kika ketare doka na tunda kin nuna ban da muhinmanci daga yau ba zaki kara fita ba wayan na kalla ba tare da nayi magana ba sai na kashe wayan. Mamaki ne ya kamani don naga dai karatin nan da abina ya ganni ciki don may yanzu yake son tsiro min da wata fitina kuma. Duk abinda akeyi sai faman tunane nake a raina karshe dai na yanke shawara da zai fitar dani ba tare dana fada ma kowa ba layin Alkasim na kira. Don tunda ya kare COE mina yake zaune gida ba aikin yi shi nakan kira idan ina da bukatan wani abu nace kada ka fada ma kowa zaka zo wurina ina son yau ka shigo Abuja akwai inda zaka kai ni. Mun fito ban tsaya ba na nufo gida direct tsab na shiga shiri ba tare da kowa ya gane mai nake shiryawa ba komai da zan bukata na saka a mota da sunan zan kai wanki. Alkasim ya iso ya sanar dani nace ya samu hotel ya kama da asuba zan fito mu hadu hanya na koma kamar ba komai naci gaba da mu,amula na da mutane. Ya dawo yazo part din ina zaune ina ba yara nono ya su Altine suka shiga gaida shi da dawowa ya kalloni tare da fadin kin mai da magana na zancen banza ko? Na dago kai na kalle shi tare da mayar da kaina ga yarinyar dake shan nono bance dashi ufan ba ganin haka su Altine suka mike suka bar wurin. Kara matsowa yayi inda nake tare da rage tsawon shi kadan ya fara zazaga masifan shi tare da kara nanata min ba inda zan kara fita in bar mai yara da wahala. Ido rufe nace kai nagaji da wanan auren wahalan nagaji wallahi don ina gidan ka sai ai ta min abinda aka ga dama don kawai an ga ban magana . Allah dai yasa kasan ni ba yar iska bace balle ka dauka yawon banza nake zuwa ina barin yara a gida kasan inda ka dauko ni ka kawo ni nan don ku taru ku cuta min. Kullun kai ke nan mutum bai maka daidai a rayuwan sa na gaji wallahi da karatuna ka ganni ka ce kaji ka gani yanzun na kusa kamala abina zakace wai ba zan sake fita ba. Shiru yayi yana kallona da mamaki na yadda na buda mai wuta, don ban taba mashi irin na yau ba sai can yace idan makaranta ne na fada daga yau kin daina ke nan a gidan nan. Tunda banga amfanin karatun da kike yi ba karatu kika zo yi ko zaman aure a gida don haka na kashe wanan karatun Na share shi ba tare da na kula shi ba ya gaji ya fita daga part din wani irin hawaye ne ke silalowa daga idona . Altine ce ta fito ta samay ni a haka tace asha khadija halin namiji kike ma kuka tunda ya fada maki kin fada mashi sai abarshi haka. Har ta kare maganganun ta ban tanka mata ba da wuri na kwanta don nasan abinda na shirya a raina sai sakawa nake ina kwancewa har barci ya dan sace ni asuban farko na tashi na kamala komai da zanyi. Zuwa karfe bakwai nace laraba ta biyo ni da Alamin na dauki mami takai min su wurin mota tana fadin ko tazo muje don babu mai kama min yaron nace yanzu zamu dawo ki jira ni ba dadewa zamuyi ba ai. Tace Allah ya tsare nace amin ta aje min yaran a jiki na bar gidan karan bude get din gidan yaji sai dai yana mamaki wanda ya fita da safe haka don yasan yasa muna dokan talala a gidan. Ita Nafisa ya hanata fita ko ina tunda ta dawo haka kuma ni ya kashe min fita makaranta wanda nasan yayi haka ne don kawai ya gyarawa matar sa rai a kaina. Don haka ne ban yarda ba da wanan dokan da ya kafa min zai min salalan tsiya da karatuna gashi muna gab da gamawa yanzu. A inda nace Alkasim ya jirani na samay shi tsaye yana jirana na fito na bashi key muka dauki hanya sai jahar kebbi jahar da dagani har shi bamu taba zuwa ba labari kawai muke ji. Sai da yagama shiri ya nufi wurin nafisa suka gaisa yayi sallama da ita ya fito zuwa part dina sun gaisa da su Altine ya nufi kofana dake rufe Altine tace dashi na fita tun da safe ai. Ya tsaya yana kallon ta da mamaki tare da tambayan yaran fa tace dasu ta fita yakai kofa ya juyo tare da fadin wa zai kama mata yaran a can da bataje da ko gudan ku ba ? Altine tace zancen da muke ke nan yanzu ka shigo kila dai ba makarantar ta shiga ba sai dai in wani wurin ta tafi kai ya girgiza yace yayi kyau ya fita. Yana jin zafi a ranshi wayan shi ya dauko yana neman layina akace a kashe wayan yake bai kawo komai a ranshi ba ya wuce zuwa office. Tun muna tafiyan dadi har kowa ya ja bakin shi yai shiru a motar mun shiga jahar kebbi a nan muka fara tambayan garin KA,OJE. Ana muna kwatance muna bi har dai Allah ya kawo mu garin lafiya da karfe biyar na yamma muka shiga garin. Gidan Liman Hamza tsoho muka tambaya akai muna kwatance har gidan a kofan gidan muka tsaya da motar mu. Ganin basu san mu ba aka tsaya tambayan daga ina muke wasun su ko hausa basu ji sosai sai yaren filace suke yi. Dan gajeren bayani mukai masu suka gane nan take aka shiga muna sannu da zuwa wuri ya kaure da murnan yar wurin dan uwan su dake Niger state ce tazo gida. Part din tsohon gidan aka kaimu direct anan aka sauke mu daga ni har yaran da Alkasim duk mun gaji. Sunyi murna sosai da ganin mu inda aka shiga dawai niya damu da yaran sai nuna min yan uwa akeyi duk wanda yazo gaida mu. AA ya shigo gidan ya kalli inda nake fakin baiga motana ba a wurin ga gajiyan daya debo ga yunwa na damun sa part din shi ya shige ya fara watsa ruwa ya fito. Sai bayan magariba ya shigo part dina sin gaisa yana tambayan Altine ina nake ne tace ai tun fitan da nayi da safe ban dawo ba. Da mamaki ya maimaita abinda tace yace bata dawo ba fa ina tashiga haka da yaran kuma ai shine Altine ta bashi amsa. Yayi yace ya juya ya fita daga dakin ya kara jin bacin rai fiye dana safe din wayana ya kara gwadawa bai shiga ya haura part din shi. Abin duniya ya taru yai mai yawa a rai yasha alwashin sai ya bata min rai ranan idan na dawo don bai yarda da fita irin haka . Kara shigowa yayi part din tara saura ya tambaya suma hankalin su a tashe yake don laraba tace ban taba fita irin haka ba tunda suka ce mai ban dawo ba. Gaban shi ne ya bada dam yana fadin ina na shiga a cikin ran shi a fili ko cewa yayi OK idan ta shigo kice ta samay ni a wurina. Abinci Altine ta taya mai don ranan nice da girki duk da ban nan sun girka abinci sun saka mai nashi. Yace a hada ya tafi dashi shiru shiru ban shigo ba ya kara trying din layina a kashe wayan yake har lokacin haka yasa ya kira momy yana tambayan ta nazo kaduna ne ? Momy tace dashi bata gane ni ba sai dai idan ina gidan su ya Amina ne amma bata tsammanin hakan don da ya Amina ta kira ta fada mata nazo. Ta sake tambayan wani abu ya faru ne babangida da zata wuto baka san inda taje ba tun yaushe ta fita gidan ma ? Kasa amsa mata tambayan nata yayi don yadda yake ji a ransa yace zan kira momy kada ki fada ma hajiyan mu don Allah ko Abba zan maki bayani daga baya. Tace to shike nan gashi baida lamban maryam kuma yana son ya kirata ba hali Yusuf ne ya fado mai a rai yasan da wuya idan baida layin maryam din don yaga suna dasawa da ita. Ya kirashi ya tambaya yace yana dashi inji dai lafiya nan dai yake fada mai abinda ke faruwa yace shine baka nemay ta tun dazu ba man. Yanzu fa fast ten muke yace shiyasa hankali na ya tashi ai nan dai suka dan taba magana yace bari ya kira maryam din bayan ya turo mai layin ta. Maryam tayi mamakin jin ban gida tace kuma wallahi ban fada mata komai ba balle ta san inda na tafi din itama dai hankalin ta ya tashi sosai. Tace idan ansan inda nake don Allah a kirata yana dauka wasa ne sai ga abu ya zama gaskiya don har safe ban gidan ranan hankali tashe ya kwana. Sai tunane yake ina nashiga don da minna naje da daddy mu ya kirashi ya sheda mai mun sauka lafiya ai. Tun da safe ya kira daddy bayan sun gaisa sai ya rasa abinda zai fada mai daddy na ya tambayi yan jikokin shi yace daddy su na kira inji ko sun zo gidane ? Bata gidan ne daddy ya tambaya da sauri yace daga dan magana kadan akan karatun ta tun jiya ta fice gidan da safe bata dawo ba har yanzu. Hankali daddy ya tashi sosai sai dai ya kwantar ma AA da nasa hankalin yace ka barta duk inda taje nasan gida ne saboda nasan halin khadija. Ba zata inda zamu ce asha ba da ziwanta zan kirata in gani yace daddy wayan ta a kashe yake tun jiya bai shiga. Shiyasa na kira ina tsoro idan ba wani mugun abin bane ya samay ta a can don yanzu duniya ya lalace da fitina. Sun rabar da Daddy zai zaga cikin yan uqa yaji ko ina can daddu ya kashe wayan ya fada tunane bayan sun gama magana da daddy ya ce khadija ba matar da ta taba min haka a gidan sai ke. Yaushe wanan bakin shawaran yazo maki har kika aikata hakan ki fita min da yara haka ban san inda kika tafi ba. Hankalin shi idan yai dubu a tashe yake ranan ya har zuwa karfe hudu baiji wani labari ba kuma wayan baya shiga. Lokaci daya ya zabge dashi don yana cikin tashin hankali kwana mu uku na raba tsaranba da na saya masu tsohon gidan yake tambayana yaushe ne komawan mu sai nayi shi. Haka yasa ya gane ba lafiya muka zo ba gidan nan cikin hikima yake tambayana ban boye mai komai ba na fada masu abinda ke faruwa . Sukace in zauna in kyale su zasu kirashi daga baya su fada mai kamar illa ina kuna wayana kiran maryam yana shigo min. Na dauka naji tana fadin khadija ne kina ina don Allah haka kika tayar da hankalin mutane nace ina garin mu Minna tace nace minna garin mu ne. Asalin mu dai nazo don nasan in naje minna ba zasu share min hawaye na ba niko kin san ba zan bar karatuna ba don shi. Khadija ai da sai ki tsaya ku fahinci juna nace kina ganin zai saurare ni yadda ya hau din nan bari ke dai in mashi hakan. Muna gama waya ta dana ma AA kira suna tare da Yusuf ya dauki wayan tare da sallama tace yanzu mukai magana da khadija. Cikin sauri yace tana inane haka tace wai garin su ta tafi a jahar kebbi garin yake yace what yaya akayi har taje can din Yusuf yana tambayan shi an ganta dai ko ya kada mashi kai kawai. Sun gama magana da maryam ya dubi Yusuf yaja tsoki tare da fadin wai kaji wanan yarinyar kebbi fa ta tafi don hauka irin nata da yaran nan. Yusuf yace tunda dai an san inda suke ai yanzu hankali ya kwanta dai ko da ba a san inda suke bane kaga shine tashin hankalin mu ka tafi Niger ma don mace balle nan da kebbi cikin kasan nan. May ye marabin kebbin da Niger Yusuf ai kusan nisan su dayane dan bambamcin kadan ne ya fada yana jan tsoki. Yusuf yace dama su khadija yan kebbi ne ashe yace ta taba fada min hakan amma basu san gida ba garin su wai fulani ne su tace min tun kan muyi aure ta fada min hakan. Daddy ya kira ya fada mai komai sai da Daddy yakai zaune a inda yake tsaye tsakar gidan mu yace kebbi fa kace yace haka ta fada ma kawar ta . Suna gama waya da daddy na kiran hajiyan su na shigo mai don momy ta gaji da boye mata kada tayi laifi momy bata bar dakin ba hajiya ta daga waya ta kirata. Fada ta fara mai tana fadin duk inda yar mutane ta shiga ka nemo masu yar su tunda kai baka san mutunci ba yanzun haka akan wanan bakar matar taka yarinyar nan ta bar gidan ka. Yace hajiya an gasu wai suna kebbi can ta tafi garin su wurin yan uwan mahaifin ta na can fada sosai hajiya tayi mai ta nuna mashi bacin ranta na yarda ya bari har haka ya faru tsakanin mu. Bata bari yai mata bayanin komai ba tace gobe goben nan kaje ka dawo da yarinyar nan ko in saba maka hankalin shine ya kara tashi da fadan hajiyan tasu sosai. Agida ko cewa yayi wasu Altine gida naje in gan su ai badon sun yarda ba suka bar maganan a hanka duk yadda suka so su samu layina a ranan ba wanda ya kamani. Don muna gama waya da maryam na kara kashe wayan dama itama don ta daukan min excuse ne a school na kirata. Da ko ita ba zata samay ni ba don naso in barsu sai sun sha wahalan sosai ba wanda yasan inda na tafi har yan gidan mu din. Tunda mukai waya da maryam din ta fada min yadda ya tayar da hankalin shi kan rashin sanin inda muka shiga nace ai duk tsiyan shi sai ya sake ni don ba zan koma gidan shi ba tunda ba sona yakeyi ba. Tace keke wanan haukan mukan ai mun tabbatar da son ki a ranshi a fili don yadda ya tayar da hankalin shi ga batan ki. Nace yaran shi dai yakewa amma ba niba zata damay na kashe wayan na barta tare da danna ma wayan off gaba daya. Nasan zasu ta nema na don fada ma maryam din duk da nace kada ta fadawa kowa inda nake aikin banza ne sai ta fada yasa na kashe wayan nawa gaba daya. Washe gari ban san irin sakkon da sukayi ba karfe hudu da wani abu suna cikin kaoje tare da Yusuf da wani dan uwan daddy na suka zo har da daddy. Muna hira a lungun sarakan kakan namu naji wani saurayi yazo yana fadin ga baki nan daga Abuja sun zo wuri na sai naji gaba ta fadi. Don ban taba zaton zuwan su ba da wuri hakan nan dayar matar tace karya yake yi yace wallahi suka kalle ni sukace mijin ki ne yazo tafiya ya tashi. Nace ban zuwa ko ina nazo gida ke nan suka sa min dariya sai da suka huta aka tare su da abin arziki sai da suka huta akaiwa su daddy korafi rashin zuwan su gida. Sai aka dauko zancen mu kuma nan dai aka kirani nazo a cikin hijjab dina har kasa na zauna gaida su da zuwa. Daddy na dauka zaiyi fushi dani amma sai naji yace kai khadi idon ki ke nan ke mai iyayye kin kwaso kafa kinzo gidan ku ko. Dan murmushi nayi na noke kaina nan dai kakan namu ya fara magana yace to Alhaji Abdulsamad ga matar ka nan ta kawo muna korafi duk da kawaici irin namu na fulani korafin ta ya zama dole mu duba mata. Kasan tana karatu ka aure ta komu nan yan kauye yanzu mun san mahinmacin boko ga diya mace don yaran mu nayi sosai balle ita yar birni. Don haka muna son ji a nan may ye matsalanka ga karatun nata don mu san makomar ta akai ya gyara zama don tunda na shigo ya daga kai ya kalleni ya sunkuyar da kan shi kasa. Sai yanzu ya dago yana fadin ba manufa in hanata karatun ta ba tunda dashi na samay ta ni matsalana da ita akan yaran da bata fita dasu ne. Yara ko nan ai naga basu fita dasu zuwa daukan darasi a gida suke barin su don Allah kayi hakkuri yarinyar nan ta samu ta karasa karatun ta yace ba komai malam in Allah ya yarda an wuce maganan. Yace shi zancen kishiya da zamantakewan gida ba zan ce maka komai ba mu hilani ba a san mu da raki kan kishiya ba ko kadan balle wata buzuwa can ta tayar mata da hankali. Don haka ba zamu taba wanan zancen ba amma don Allah duk da haka a kula a tsare hakki abawa kowa hakkin sa a daidaita adalci a tsakani. Sai zancen yaran da tace ka kwace hannun kishiya ka bata wanan bamu dan dalilin ka nayin hakan ba na bata hakkuri akan haka ta sa maku ido dole kana da manufa akan haka. Nasiha sosai yai muna sun so su juya ranan don Yusuf ne ya tambaya yace ai ba tare kuka zo ba sai ku bari idan mun shiryata zuwa karshen sati zatazo da yan uwa aga inda kuke da zama don sada zumunci. Mu wanan yarinyar tai muna komai a rayuwan mu don ta farfado muna da abinda muka kasa yi a tsakanin mu sada zumunci tunda tsofin mu suka kare. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 1/17/21, 6:30 AM - Xxxxx: Yusuf da sai faman murmushi yake saukewa a fuskan shi tunda tsohon ya fara magana AA dake kula dashi ya fahinci murmushin may Yusuf din ke yi. Saida suka fito don yin magariba yake sake dan guntun tsoki alokacin Yusuf ya fadada murmushin shi mai sauti yace dama ai na fada maka khadija ta daban ce gashi ko kagani yanzu. Kai a tunanen ka baka ga macen da zata barka don kanta ba ko wani abu sai idan kai ka saka kan ka binta . To yanzu ka gani mata suna suka tara don khadija dai ta nuna maka ita ba dukiyan ka ne a gaban ta ba nata take nema da incin kanta. Zama yayi ya fara tatara hannun rigan dake jikin shi don jin dadin alwalan da zai gabatar a lokacin. Yace kana tunanen don ta nazo nan din ko may yace ina son sanin wanda kayi uwar tafiyan nan don shi din yace kaima kasan saboda yara na ne don ban san halin da zasu shiga ba idan na barsu nan. Yaran wa ya haife su ko ka dauki yaran ka tafi dasu man ka barta ai ita gida take gaji irin yabon da ta samu kan zuwan nata ai. Kyale yusuf din yayi ya fara gabatar da alwalan shi yana tunanen maganan Yusuf din lalai khadija fassarata da wuya ita sam abin da ke gaban saurran bai gabanta kullun ita sai yakin neman wakanta mafita take. Bayan sun dawo daga massalaci ne a gabatar masu da abinci ida idan sun ci zasu wuce birnin kebbi su kwana washe gari su kama hanya. Wani yayana ne yazo da kanshi ya kirani wai in je mu gaisa kafin su tafi nace ai ba ni na kirasu ba ya barsu kawai. Yace ke ko ayi hakan bakin mu ne fa har dake dole daya matsa min na fita zuwa wurin su don mu gaisa. Na samay tsaye a bakin motar su nayi sallama ciki ciki ba tare da furta komai ba na ja na tsaya Yusuf ne yace maman biyu idon ki ke nan ? Kin gudo muna da diyan mu ba tare da sanin mu ba nan ma da suka zo ai gidane na bashi amsa a takaice. Hummm naji AA ya fada kawai tare da fadin gida ne amma ba gidan su ba nace dole dai kamar yadda za a ce gidan uban su nan ma ace gidan uwar su ce ai. Yanzun dai kada ki saka fulanin garin nan su sauke muna sanda a kai duk inda bi gari ba kaji komai sai kodin kodin ba hausa mai dadi. A haka aka gansu har aka nace masu Yusuf wanda ke gefe dariyan mumuke yake ma converstion din mu yace wai ni yaran ma ba za a bari mu gansu bane ko fushin mu ya shafe su suma ? Suna wurin yan uwa na ni kuma ba zan iya cewa a kawo su ba yace gaskiya ne kin nuna muna ke bafullatan asalice wurin kawaici. Yanzun dai gamu a kasa muna kara bada hakkuri bisa ga laifin da mukayi don Allah a yi hakkuri a dawo a cikin lokacin da aka saka din ko don karatun ki ke ma. Ai ba damuwa da karatun nawa kukayi ba tunda ku kun kama naku yasa kuke son yi min sakaci da nawa. Yusuf zaiyi magana ya tare shi da daga mai hannu yana fadin haka naki tunanen yake sai nake ganin kamar sauki na neman maki ashe ke a gurin ki ba haka abin yake ba. Nace sauki may sauki da zama da jahilci akai ko sauki da gadara da abinda ba na ka ba kai kadai ban yarda da wanan saukin na dan lokaci ba nafi bukatan in sama ma kaina mafita da zufa na nima. Yusuf muje dare na muna don ance akwai dan nisa tsakanin nan da garin kebbi din mu tafi kada dare yai muna anan. Yaushe kuma ai dare ya riga yai muku nan don almuru ya wuce ko sai kuma na gobe duk da yasan magana na fada mai bai bani amsa ba sukai min sallama wanda Yusuf ne ya samu yin sallama din suka tafi. Sunyi nisa ga tafiya yace yarinyar nan ta samu damana da yawa Yusuf ya dan nisa yace dama haka abin yake ai ba kullun ake hawa gado ba. Ya maida kan shi ga seat din da yake zaune yana lumshe idanu sai tunane take a zuciyar shi lalai maganan Yusuf gaskiya ne. Mata suna suka tara wai yau shine mace ta bar gidan shi don wani dalili nata can bai taba zaton akwai macen da zata iya tsallake shi da abinda yake dashi ba tace nata zabin ta zaba. Kudi kyau ilimi wayewa da duk wani abinda mata ke so yana dashi don haka yake daukan ko dun dole mace ta bushi ya juya ta yadda yake so. Sai gashi ita wanan abin ba haka yake gareta ba duk wanan abin daya lissafa ta ketare shi ta wuce don wani dalili nata na banza. Allah yaso Deedar yana son ta har cikin ranshi haka ma hajiyan mu tana son ta da na nuna mata nafita tsiya wallahi. Guntun tsuki yaja a fili har Yusuf ya dan juyo yana fadin yaya akayi ne mutumina ? Wallahi Yusuf yarinyar nan nake tunane a raina ban san ya akayi ta samu waje haka a zuciya na ba har batinta gidan ya sa nake jin gidan kamar ba kowa a cikin sa. Yusuf yace ba sake kayi ba halin khadija ne ya ja mata haka yanzu in ka bibiya ko su Altine kamar su kama da wuta suke don rashin ta a gidan. Ai mutum mai mutunci haka yake idan yabar guri sai kowa yaji daban a gidan yace na yarda da dan ko sadiya da take yarinya tasan khadija bata gidan. Yau din nan Altine ke fada min ta daina karban abinci ko wani abu idan an bata sai fitina take masu kaga ko yaro yasan mai kyauta mai ashe inji Yusuf. Ban san kunyi haka ba wallahi da na fada ma hakan da zakai mata ba daidai bane ko don kyau cika alkawarin da ka daukawa iyayyen ta kafin ai aure. Bai iya magana ba sai dafe kanshi da yayi da hannun shi daya yana ci gaba da tunane a ranshi don baiji irin haka da Nafisa ta tafi ba in ba jin da yayi a lokaci daya yana son ya dawo da ita gidan ba.. Na yarda gyara na wurin yan hausa don ni kaina ina jin canji a jikina don irin shaye shayen da akai ta dura min nasu da suke amfani dashi na gida wanda suka sani sukan san ingamcin sa. Bawai abinda basu san komai aka hada dashi ba wanda suke amfani tun iyayye da kakanni wanda duk wata mace a can ba abin kunya bane a gare ta amfani dashi. Wancan ta kawo wanan ta kawo duk kuma kakana tana tsare ni sai nayi amfani dasu ba wani zancen boka da malam ko yawan cushe cushe a gaba da zaija wa mutum illa. Wanan sai ma ya gyara ma jiki fata yai haske ka kara dan magurjin jiki daidaiwa daita da mata biyu zamuyi tafiyan sune zasuyi min rakiya sai wani yayan mu na miji da zamu tafi dashi. Tun da safe muka dauki hanya har da kuka na na barin su da zanyi don ina jin wani iri a raina ba dadi a lokacin. Mun sha tafiya sosai sai karfe biyar muka shigo garin har zuwan mu gidan kafin shida na yamma mun shiga gidan. Da murna su Altine suka tare ni tare da baki na suka bani abinci kamar sun san da zuwan mu a ranan. Sai tambayan mutanen gida sukeyi ina fadin suna lafiya a yadda na fahinta a cikin hiran mu dasu basu gane yaji nayi ba don shi abinda ya fada masu daban. Naji dadin boye min sirina da yayi sai naji mutuncin shi ya darsu a zuciyana koba komai ya rufa min wanan asirin dama ina tunanen da wani ido zan kalle su. Kafin wani lokaci Laraba ta gyara min dakina tsab da dakin da baki na zasu sauka Altine ta gyara yaran sun goya su bai shigo gidan ba sai bayan sallah ishai ya shigo. Suna falo ana fira yayi muna sannu da zuwa tare da tambayan su mutanen gida sukace suna gaida shi. Daki ya shiga wurina ina waya da maryam sai kyalkyatan dariya nake ni kadai a dakin kamshin turaren shi ne ya ziyarci hanci na na dago kai ina kallon shi. Tare da fadin maryam sai anjima na kashe wayan ido ya kura min na dan wani lokaci cikin dakiya nace wanan kallon fa yace ai nasan baki da kunya. Duk iya gudun naki bagashi yanzu kin dawo ba nace an dai dawo dani indon ta nice ai natafi ke nan ban dawowa wanan gidan da ba a san darajan mace ba. Maimakon inga ranshi ya baci sai naga yayi murmushi yace goya ki kike son in dinga yi ke nan a bayana ina yawo dake ina fadin ga matar so na komay ? Ka taba ganin wanda ke goya matar shi a baya ya nuna ma duniya don yana son ta sai dai ya nuna ma duniya kulawa da matan shi a fili. Kai ya kada min kawai yana fadin wanan bakin mai farsan sa bata farshe da kyau ba gurin wanka. Bayan fitan shine haniyan su ta kirani na dauka da kunya tare da gaida ita take ce min khadija ashe kun dawo yanzu yake fada min dawowan ku. Nace eh mama mun dawo dazun tace daga yau na hane ki da barin gidan mijin ki idan ma wani abune ki kirani ko kizo nan wurin mu. Nayi mamaki da kikai hakan khadija kin nuna min baki dauke ni uwa gare ki ba har yanzu da zaki sa kafa ki fita zuwa wurin yan uwan ki wani kasa. Nace mama ba hakana bane ta tare ni da fadin kada dai ki sake yin wanan gangancin barin gida da yara haka koma may ye ki fada min ko ki zo wurina. Nace na gode mama don Allah kiyi hakkuri tace ya wuce ki faki gaba mukai sallama na kashe wayan tare da fadi a fili nace ina zan iya haka mama ai abin kunya ne a gare ni in kai korafin dakin wurin ki ko yaushe. Washe gari maryam tazo tunda safe ganin yan uwana ta dade dasu tana fira kafin mu koma dakina da ita. Muna shiga tace min yar iskan mata kin sa mijin ku karamin haukacewa duk da boyen hakan da yake yi wa mutane amma kana ganin shi ko jin maganan shi zaka san baya cikin hankalin shi. Gado na fada nace ai ke kan gulman ki yayi yawa wallahi duk kin rushe min plan dina naso sai ya wahala sosai kafin ya gane inda nake din. Tace da ya kwanta asibiti ke kinga yadda ya tayar da hankalin shi ai Yusuf yace min kece maganin shi don ba a taba yi mai haka ba. Nace maryam kin san da na yarda shike nan haka zai min sheri ya hanani karatuna na zauna nayi nazari sai na fahinci don ya hana Nafisa fita ne ya kirkiro da wanan dokan a kaina. Tace shima dai wallahi ina zai hada ki da wanan jahilan zaman gida ba ilimi sai tarin jahilci ai karatun mace bawai don aiki kawai ake son tayi ba. Yana taimakawa rayuwan yayan ta dana mijin ta da ma alumma baki daya karatu ga mace kamar ba gari tallafine. Nace barshi kawai shi bai gane hakan gani yake kudi suna iya sayen komai da kowa ni bai san zuciya na bai mutu ga abun wani ba. Wallahi maryam harga Allah ban so dawowana gidan nan ba don komai ya fita raina wallahi tace ke ki bari ko dai yar buzaye ta gama dake ne. Kai na kada nace ba zan dauki alhakin ta ba koda tayi ban sheda ba kuma ni kin gani nan yanzu duk wani zancen wani asiri ya fita min a kai don Allah keyi ba mutum ba. Kawai dai ni rayuwan tsarin gidan ne bai mun ba maryam ace mace bata da sani rana ga miji ko wani jin dadi sai idan miji yana da bukatan ta. Maryam bai fa san damuwan mutum ba shi ko ka fada shi yana ganin kudi sune maganin ko wani matsala na mutum a gidan nan . Maryam kin sanni kin san halina ni mace ce mai son a kulani amma shi sam rayuwan shi bai san ya lalashi mace ba ko a wuri bukata duk wani abinda ke fada da shawara da ake bani nayi maryam duk a banza. Sai yanzu nake gane cewa haka yasaba dashi ga matan shi na farko bai da wani damuwa dasu sai ta kudi baida lokacin su ko na diyan su sai dai ya baka kudi kayi ko may nene . Nasan akwai matan da haka rayuwan su take su dai bukatan su ga namiji shine kudi babu wani jin dadin rayuwa. Kudi kan nasan akwai su don yanzun haka ina da kudi a dakin nan ni kaina ban san ko nawa bane haka kuma ga account dina don baida keta wurin kudi gaskiya to amma a baka kulawa mana. Na nuna mashi ni kudi basu bane matsalata ba ranan da namiji zai ware ya baka kulawan shi sai kullun cikin uzuri dare ne kawai zaka kebe da mutun ko shi a uzurce ne. Tace ikon Allah wai ni khadija ban san halin ki ba wasu nacan suna neman hakan ke kuma ga kudin hakan bai maki ba koda yake banga laifin ki ba tunda ba auren kudi kikai mai ma ba. Yanzun ai dole ya canza nace Allah yasa sun riga da sun koya mashi haka lokacun da mukaje kaduna sallah da yake dan zama a gida tare damu. Da kunne na naji Fati tana gulmana wai ni kamar wata fitsarara banjin kunyan zama da miji ko yaushe ina makale dashi. Maryam tace ke wani amsa kika bata nace bance mata komai ba don nafahinci bata san ciwon kanta ba ita. Naso mu zauna mu fahinci juna amma hakan bai yuyuba a tsakanin mu don ita bata yarda da kowa ba. Mun dade muna hiran matsalolina da maryam inda ta dan bani shawara sai dai ban fada mata komai ga irin abinda na fahinta dan zuwa garin mu danayi ba. Bayan tafiyan maryam na fito wurin bakin na muka dan taba hira akai kiran sallah naje nayi la,asar na fito na shiga kitchen laraba ta biyo ni. Nan muna aiki muna hira take banu labarin ai babu zaman lafiya tunda na tafi tsakanin shi da Nafisa kulun jidali ne akan yara da kuma zancen fita. Yasa tsauraran matakai ashe akanta ranan da bakin ta take fadin wai ke ce kikai mata asiri dan kada ta zauna lafiya da mijin ta. Nace kuma dai ita bata da aiki saina asirine a gidan nan wai wani riba ta samu akan hakane da har yanzu bata saduda ba. Mun gama mun gyara part din na wuce zuwa part din shi na gyara ko ina banyi mamakin samun part din kamar tun gyaran karshe dana yi yake haka ba ba wani gyara a cikin shi. Sai da na gyaro ko ina nasaka kamshi don har karni naji dakin yana min na rufo kofan ashe ban sani ba yanzu ni kadai ce keda key din dakin a hannu na. Sai da na fito naji nafisa na fadin aiko a kwaita wato ni nawa key din ya karbe ya barwa wanan banza nata a hannun ta zai dawo ya fada min abunda yake nufi. Kamar in wuce ta sai wata zuciya tace daina kyaleta na juyo nace ba komai yake nufi ba illa dai yarda ne ban taba daukan mashi komai a dakin ba kila ke bai yarda dake bace yasa ya karbe key din shi. Kin san mutum shike sayawa kan shi mutunci idan bai sa ido ga abin wani ba waya sani ko kin masa halin bera ne a dakin. Tashin hankali nan ko ta hau jidali zaginta dama irin na tab tasha ne daga zagin iyayye sai bakar ashar mai muni nace baki da maraba da yan tasha zama dake ma zunubi ne wallahi Mace ba sanin Allah ba addini ba ilimi sai jahilci dake cin ki da bakin kishi ki koma ki san Allah zai fi maki ko dan tarbiyan yaran ki. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 1/19/21, 6:32 AM - Xxxxx: Bayan na gama tanadar komai dana san zaiyi amfani dashi har abinci na jera mashi saman d/table na dawo part dina na samu yan uwana bakina dasu Altine suna hira. Zama nayi a wurin su kafin lokacin sallah ya karaso ban wani dade da zama ba time yayi na mike na shiga daki wanka bayi kafin alwala na fito. Bayan na idar da har isha,i na zauna na gyara jikina tsab a cikin doguwar rigar mai kyau don sune kaya na in bada naje kebbi nake kokarin saka atamfa kulun ba a dan kwana goma sha danayi can. Laraba ce ta kawo Al,amin wai yana rikici na karbe shi muka fito falon muka zauna muna dasa fira Altine tace yaron nan fa yanzu wayo yayi sosai don yasan yayi kwana biyu ba tare da mu ba. Ina kokarin ciro nono in ba yaron nake fadin wai baba kayi wayo inji gwago kasan dangin uwar ka yanzu ko kabar su gwago. Na dago kaina ina dariya a yadda Altine ta tsura min ido yasa na fasa dariyan ina kallon ta tace wanan tafiya kamar an canza ki ne baki daya. Haka ake son mutum yaje gida aga canji a tare da shi ba irin zuwa gidan buzuwa ba dariya zancen ta ya bani nace kai anty ho. Bamu dade da zama a gurin ba Altine na cikin magana sai ya shigo part din namu gaida baki na tare da tambayan su ba dai wani matsala ko ? . Bayan sun gaisa ne ya juya ya fita mukaci gaba da hiran mu bai dauki wani lokaci ba mai tsawo da fita sai fa kiran shi ya shigo min a lokacin kira uku gana hudu na daga kiran da sallama. Yace ki zo ki bani abinci mana sai ya kashe wayan ina shirin fadin ai abinci da duk wani abinda zaka bukata yana nan na aji mashi su sai naji ya kashe wayan nan take ban samu bakin magana ba. Sai da ba dan bata lokaci wurin har na dan ci abinci na mike zuwa bedroom dina dogon rigan jikina na shafa ma oud kala kala sai body spray dana fesa a gabobin jikina dakyau. Na fito na nufi wurin shi inda na samu yana waya na juya zan wuce bayan na dan tsaya bai gama wayan ba. Muryan shi naji yana fadin ina kuma zaki je bayan nace ki kawo min abinci in ci abinci na d/table tundazun na fada a wani irin yanayi. Yace ba gani ki zuba min mana na fice daga dakin na barshi a ciki ban dade a gurin ba sai gashi ya fito daga dakin . Ya abincin baci gaba da zuba mai na gama tare da hada sauran kayan a guri daya sai jug din zobo dana sabo garin mu dana hada mai na matsa mai dashi a gaban shi. Ya kalli jug din tare da fadin wanan may ye a cikin nan din zan bashi amsa sai ga Nafisa ta fado gurin kamar an jefo ta dakin tace Samad gurin ku nazo dama dakai da wanan yarinyar. Don ke baki iya sallama bane idan zaki shiga wuri ko may ye hakan kikayi yanzu tace ba a koya min ba don bashi ta kawo ni nan ba yanzu. Nace amma dai ke jan a binciki addinin ki don ragage ne kin ga don Allah malama ki bar nan don na gane manufar ki da kike muna hakan a ranan girkina ne kadai kike muna wanan dabian haka. Do kawai kiga kin birkita muna farin cikin mu zuwa bacin rai saboda haka yau dai baki zo a sa,a don nariga da na gane nufinki a hakan Ji wanan dama har wani farin ciki kike dashi a gidan nan miji dai kike kokarin cusa kanki a gare shi kuma baya yi dake yar iska. Dani dake yanzu ai ansa wa miji ya daina yayi a gidan nan don ko makaho ta laluba yasan gwanatin ki ta kife a gidan nan sai yan dabaru kuma. Oh dama burin ki ke nan wallahi komai asirin ki dole ki barni don na damaki na shanye yarinya na juya gurin shi nace kaji ke nan da kunnen ka har tana ikirarin da asiri a gaban kowa haka ? Yace ke ku rabani da wanan shirmay haka Nafisa bar nan don Allah don ba lokacin ki bane yanzu tace nasan ba lokacina bane amma kasan ina da daman shigowa nan duk lokacin da na ga dama. Wallahi karya ne baki isa ba idan kuma kin ce karya ne ki kara muna haka kiga abinda zan maki a gidan nan. Kin mata kike kika saka wanan dokan a gidan nan kuma dayake nasan gaskiyan hakan na tsare wanan dokan don may ke ko yaushe kike karya wanan dokan. Lalai wuyan ki yayi kauri a gidan nan har ni zaki kafa ma dokan ganin mijina komay kai wanan matar da abin dariya kike mijin ki ko mijin mu dai miji kan ai ya tashi a naki sai dai a jam,i don mata uku cur take mallaka daidai kuma kike da kimar kowa a cikin mu har ma mun daraki a wani fannin a gurin shi. Wani irin bakin ciki da takaicina ya rufe ta a lokaci daya nan ta fara irin zaginta na yan iska zagin banza da baida dadin saurara ko fada. Ke ya ishe ki kifice nan ai gaskiya khadija ta fada kin zo nan don ki bata muna farin cikin mu ne kawai tace zuwa nayi don in ji dalilin da zaka bar mata key din sashen ka ka karbe min na wurina. Gyaran part din kike ko may iyakan ki kizo ki kwanta ki tashi ki barshi a haka na ko so kike in bar maki key din ki kwashe min duk wani abin kwarai kiyi gaba dashi. Iyakar ki min sata ko bincike ki samu abinda na aje ki gaba dashi wani kallo tayi mai kamar zatayi magana sai kuma tayi shiru don babu abin fada. Yanzu sherin da zakai min ke nan yace may ye sheri a cikin wanan maganan ba gaskiya na fada ba ko kina tunanen ni mahaukaci ne da zan bar maki key dina yanzu ? Ke nan itace mai gaskiya a gare ka don baka san barnan da take maka ba a boye yace ban taba gani ba ko ji ke ko fa na gani kuma na sani. Dama tunda an riga da an gama dakai yanzu ai baka ganin laifin ta tunda ta asirce ka ta gama. Wai ke may kika gane da zancen asirin nan ne baki da tawakkali ga Allah sai zancen asiri may asirin naki ya tsinana maki a rayuwa ki wai ? Ki yarda da Allah shine mai yin yadda yaso ba wani can ba wanan ma abin kunya ne kina fadan haka a bainan jama,a ke baki jin nauyin haka ko kunya ? Kunya may zanji ga abinda nasan kinayi ina yi duk akan mutum guda kuma muke tin shi nace kike dai yi don ni banda lokacin haka ga Allah na dogara da al,amarina . Karya kike yar iska muna fuka karuwan cikin gida mai kwatar mazan mutane nace ikon Allah ai kwace miji ke aka sani da wanan. Ke da kika raba miji da matar shi har da uwar shi da iyayyen shi Allah bai yarda ba yanzu kike ganin baki na kan hakan. Ke kana jin abinda take fadi banyi mamaki ba don ke kin fada tunda dama haka ake fadi nace ba gaskiya aka fada ba yanzu mai kika zo yi nan din ? Ke karamar yar iska dake da wa yanda suka turo ki kimin fitsara duk maganin ku zanyi a gidan nan mu zuba dani daku a gani. Nace muga alheri gida dai na shigo shi ba fita sai dai ki mutu akan kishi ba abinda za a fasa kuma tace. Wallahi karya kikeyi sai kin bar gidan nan koda tsiya anga wuein ci an lake kamar kaska ko to fita kamar gobe ne wallahi don, , , , . Ke dan Allah ya isa haka ban son wanan shirmay tunda kin fadi abinda ya kawo ki kuma kinji amsan ki. Ki fice min daga shiya tun kan ranki ya baci a gisan nan tace bayi kan ka bane don kai min haka a yanzu zaka dawo a hannuna mu zuba dani daku a ga wanda zai fasa. Ta juya ta fita daga part din ya juyo yana kallo na ina zaune na harde hannaye na saman kirji na nima ido na zuba mai yace ke ma na lura kun zama daya da ita yanzu. Nace yar rainin hankali ce bata tashi fitinan ta sai ranan da tasan nice da girki na dade da fahintar haka a gare ta dama. Ke din yanzu rai kike gyara min da kike guduns komay ni ba gudun ka nake ba kaucewa nayi ma abinda nasan zai iya jawo muna matsala ai. Yace oh tunanen ki ke nan ashe nace haka shine mafita ba tare da samun sabani a tsakanin mu ba tunda ka hau a lokacin. Na tura mai plate din abincin da na zuba a gaban shi nace amma bai dace kace tana maka sata haka a gaba na ba ya ja plate din dakyau a gaban shi tare da fadin ke daban ne a gare mu ai gara kiji ki san may ke gudana don ki kula. Lokacin da ta yaye ni ta tafi dashi ai kina gidan nan amma baki sani ba don haka kina gama abinda kike yi ki dinga rufe min kofa na don Allah. Haba sai kace ba matan ka ba dai ai yanzu ba zata kara ba tunda tasan ka gane hakan har ka dauki mataki yace baki san halin Nafisa bane. Zama nayi ina kallon shi tana cin abincin shi hankali kwance na tsiyaya mai ruwan zobin a kofi na mika mai ya ansa ya kurba tare da lumshe idon shi yace ke kika hada wanan din nace eh baiyi bane yace yayi mana sosai. Akwai abinda zaki hada da hannun ki baiyi dadi bane ya karasa kurbe sauran dake cikin cup din ya aje min lokacin ne nace mai gidan SJJ sun aiko min da katin gaiyatan bukin gidan su wani sati. Kamar baiji abinda nake fadi ba ganin ya gama ya turo min plate din a gabana na mike tare da fara tattara kayan abincin. Kallona yake yana jin wani irin son kasancewa dani a lokacin wani abu yake ji yana fisgan shi na dago kai nace ka gama da wanan jug din ne in dauke. Bar min zan kara anjima yace amma dai kin san babu inda zaki yanzo ko nace kamar ya ba abinci kace inzo in baka ba dama, na kuma baka. Ke nan har yanzu baki hakkura ba daga gudurin ki na dauka wanan zancen ya wuce ai. Dago kaina nayi na kalle shi da zuman in bashi amsa sai dai yadda ta tsure ni da idanuwan shi yasa nayi saurin dukar da idona kasa. Ina sauraren ki idan hakkurin da mukaje har gafin ku muka baki bai maki ba yanzu sai ki fada min abinda kike son inyi kuma , ? Deedar nasan wani lokaci ban kyauta maki amma kuma ni ina ganin duk abinda kikaga nayi da dalilin yin shi gare ki sai dai ke kin kasa fahinta na ne ko kadan kina ganin haka kamar tauye hakkin ki ne a gare ni. Har cikin zuciya na na dauka ke kadai ce macen da zan iya sakata tayi abu tayi shi ba tare da korafi ba, ina alfahiri dake a ko ina Deedar bana son rashin fahinta haka yana shiga tsakanin mu akoda yaushe. Ki tausaya min don ceto rayuwana daga halaka ke kadai ce kike iya tsayawa ki fada min gaskiya in fahinta ya zama min alheri kuma idan nabi shawaran ki. Kada ki ruguje muna tubakin da muka fara dorawa dake a gidan nan wanda nake fanin zamu girbi alheri nan da dan lokaci kadan idan Allah ya yarda. Ki daina fadin kalman banson ki khadija ina son ki ina matukar kaunar ki babu macen da keda kaso irin naki a zuciyana. Na yarda dake dari bisa dari khadija ke din jaruma ce da bakowa ke gane hakan ba sai wanda ke tare dake yasan hakan ki yarda dani khadija don jiki nake kamar ba a matsyin matana kawai na dauke ki ba a matsayin yar uwa ta jini da zata share min hawaye. Ban kara gaskanta hakan ba sai rike min wa tan nan yaran da kike ganin kamar na cuta maki ne ga yin hakan ni kadai nasan manufata nayin hakan danayi gare ki don ingancin tarbiyan da yaran nan zasu samu daga gare ki nake kwadayi wanda Alhamdullahi yanzu na fara ganin hasken hakan a gare su sosai. Ajiyan zuciya na sauke daga inda nake zaune don jin yadda yake tsaro min magana daga bakin shi wanda ko wacece dole ta hakkura da wanan kalaman nashi. Sai naji bazan iya fada mai komai ba a lokacin tunda har ya zauna yana fada min zuciyar shi haka yau ga kuma kalamin dana dade ina son ji a gare shi ya furta min da fatar bakin shi. Sai naji bai kakata in rike shi haka yadda nayi niya ba a zuciya na don duk sai naji ya wanke laifin shi a gare ni ya zama dole gare ni in kara hajircewa gurin taimakashi a gidan. Ba zan so in dawo da abinda ya wuce ba gare mu yanzu sai dai mu dora a inda muka tashi a faki gaba kuma don nasha alwashin ba zan sake kyale Nafisa tana juya mu yadda taga dama ba a gidan. Ganin nayi nisa a tunane yasa ya dan rankwafo inda nake zaune tare da hura min iska yana fadin ko baki yarda da duk abinda na fada maki bane yanzu. A sanyaye nace na fahinci manufar ka yaya AA insha Allahu ni kuma nayi maka alkawarin duk naga gyara a lamarin mu zan sanar dakai koda a cikin hikima ne da yardan Allah yadda zaka gane. Rungumini yayi zuwa jikin shi yana mai sauke nunfashi tare da matse ni sosai a jikin shi kamar wani zai kwace ni a jikin nasa. Wani iri duniya muka lula naji tankar ace daga ni sai shine a wana rayuwan babu sauran wata a bayan mu in gwada mashi so na sahihi duk da ko a yanzu ma hakan bai baci ba ai don kowa gyara kansa yake a gurin miji tunda har na fara samun wanan yabo a bakin shi. Sake ni yayi yana fadin kai kayan nan ki kara ba yara nono ki dawo daga kai nayi na kalle shi ido cikin ido wani irin abu naji a zuciyana nayi saurin dukar da kaina kasa. Don nauyin shi da kunya daya kama ni a lokaci guda da kyar na iya bude bakina nace daka bari har yan uwan nan nawa su wuce zaifi. Ummm, ummmu yace kada ki kawo wanan maganan yanzu ai sun san gidan ki suka zo kuma aure kike yi jin dadin hakan ne ma yasa kika gansu nan. Nace to shike nan amma nima kayi hakkuri da abinda nai maka a baya ba daidai ba matsalan rashin fahintar junane na fada a cikin sanyin murya tare da dan marairaicewa. Rungumo ni naji yayi cike da tausayin junan mu yana fadin ki yarda dani Deedar ban rike ki da wani manufa ba a raina idan kin ga haka ki fahinci inda na dosa kafin ki yanke hukunci ina sane da komai da ke faruwa a gidan nan. Sai dai ban taba daukan zaki dauki hakan a cutarwa ba gare ki don haka don Allah ki gafarce don baki taba min musu irin haka ba har da guduna zuwa wata uwar duniyan. I am so sorry ga abinda ya faru ba wai na fada don in hana ki karatu ki bane ya isa haka yaya AA na fahinci komai wallahi kaima don Allah ka yafe min . Kai ya girgiza min yana murmushi yace khadija ke nan babu abinda kikai min na batanci da zaki ce in yafe maki komai kikai min kina da dalilin yin shi tunda ban fada maki manufana ba. Idan ma kin man na yafe maki har ga Allah don ban taba rikeki da magana ba kara lafewa nayi a jikin shi ina sauke numfashi. Can na sake shi nace zan duba yaran yaya kada suga na dade ban dawo ba yace ke dai kina gudun sherin mai shegen saka idon nan Altine. Da kyat na samu na bar wurin shi zuwa kasa ya bini da kallo yana sauke murmushi a fuskan shi tare da kada kai yana fadin kai mata sai a hankali kamar ba ita bace ta so ta birkice min yanzu. Koda na koma na samu ma yaran suna goye a bayan su don haka na shiga nayi wanka na kimtsa jikina dakyau naso in kara ba yaran nono amma sai Altine tace in wuce ai akwai madaran su yana nan idan sun tashi. Koda na shiga motsin shi naji a bayi yasa nagane yana ciki wurin daya dan baci na kara gyarawa sai lokacin naga zoben shi dana tsunta a kasan gado danake shara yana fitowa da bathrobe a jikin shi sai dan karamin towal da yake tsane ruwan kan shi dashi yace har kin dawo ashe. Nayi sauri nace mai sai yai saurin fadin bance ba don Allah a rufa min asiri kada asani kwana maraya kuma nace da momy da ranta da Abba zaka kwana maraya kuma . Yace ai sin yayeni tuni yanzu sabbin uwaye na samu kuma wanan zoben naka ne na kawar da zancen da tambayan shi. Kallo zoben yayi yana mamaki yace ina kikaga wanan zoben dana dade ina neman shi a dakin nan karkashin gado na gan shi dazun ina shara na bashi amsa. Takowa yayi zuwa inda nake ya karba yana juya zoben yace nasan ba kowa yai min wanan aikin ba sai Nafisa zobe ne na tsari da aka bani ta sani takuma san amfanun shi sosai gare ni ya karba yana sa zoben a yatsan hannun shi naga yana wani addua lokacin da yake zura zoben. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 1/20/21, 6:35 AM - Xxxxx: Satin bakina daya suka koma gida da rarin abin arziki daga gare mu sai albarka suke saka muna mun rabu tare da kewan juna inda suke kara jadda min kula da zumunci. Bukin gidan SJJ ya tashi ban dauka yana tune da zancen ba sai ana gobe yake ce min daya shigo part dina da dare, kin fasa zuwa yiwa Adam din ne kara ? Ni na dauka baka barni bane ai yace ai ba zan hanaki zuwa rama abinda akai maki ba kema sai dai kin san dole zaki kai abin buki ko ? Nace ai shine kuma don dai kasan wanan ba taran kudi suke nema gudun mawa ba yanzu yace idan kinyi tunane sai ki fada min. Abinda zaki kai godiya nayi mai ya fita tun wanan lokacin nake shawaran abinda zan kai wa amarya gudun mawa idan zan tafi. Altine da nake fadaw tace shine matsalan mu yanzu sai mutum yace sai ya rama alherin da akai mai nace ba wanan a tsari na abu dai wanda ba zasu zata ba nake tunane komai kankantan shi. Karshe dai mun yi shawara na hada kaya masu kyau irin na Anty Salbiya sai wani sarkan gold mai kyau da tsada da awarwaro a cikin kit din su da zan ba amarya gudun mawa. Maryam ta shigo washe gari muka shirya har laraba da Altine zuwa gidan bukin mun samu taron sosai wurin hajiyan gidan. Ban dade ba muka mika abinda muka zo dashi tare da fadin zamu tafi tace haba tun yanzu jana tayi har dakin ta dani da maryam tare da su Altine. Muka zauna tace naga kamar wanan sakon naki mai muhinmanci ne a gare mu tana magana tana bude ledan ta ga abinda ke ciki. Ikon Allah duk wanan abin haka kin ga mutane basu fahinci hakan ba don ba wanda ya maida hankali gurin gyara min kawan tawa. Don Allah kiyi hakkuri ki dan muna bayanin komai kafin ki tafi na fara mata bayani a cikin kunya tana fahinta na sai godiya take min kan hakan. Ta bude ledan da akai wraping din sarka da awarwaro a cikin sa sai naga ta bude ido tana fadin wanan ma ya isa khadija ki koma da sarkan nan ko ni ban saya mata shi ba don mijin ta ya saka mata su a laife sosai. Anty ai wanan nawa ne don ta na kawo shi tayi dan shiru kamar za tai magana sai kuma taja baki tayi shiru ta mike ta fita dan jima kadan sai gata ta dawo dakin tare da amaryam da wasu dauke da kayan motsa baki a cikin tire. Bayan sun fitane tace da amaryam na kira kine kiwa anty khadija godiya kinga abinda ta kawo maki tana nuna mata kayan. Murmushi tayi tana zama sai da ta shafa sarkan ta dago tace kai anty nagode sosai wallahi wanan yana da kyau matuka. Ta shiga godiya kayan ne hajiyan ta fara mata bayani tana sune kai don kunya ta kara fadin anty nagode. Bamu taba komai ba daga cikin abinda suka kawo muna a dakin nace zamu tafi tace haba wai kodai har yanzu baki sake damu bane a yan uwa muka dauke ki fa gidan nan. Nace ba haka bane anty a koshe dai muke shiysa tace to tunda ankawo saidai ku tafi dashi ranan jumma,a akwai walima da yinin buki don Allah kuzo khadija don ranan zan hada ki da Alhaji ku gaisa. Don bai sanki ba sai dai yana jin labarin ki a gurina nace Allah ya kaimu mukai mata sallama muka tafi tana muna godiya. Maryam ce ke jan mu a motar sai da muka dauki hanya tace humm,umm masu kudi suna inda suke wallahi duk wanan gidan ita kadai ke mulkansa. Altine tace nima abinda nake ta tunane a raina ke nan tun dazu don Allah ji daki kamar wani shagon sai da kaya. Ni ba abinda ya ban mamaki sai yadda suke ta yaba kyautan ki gare su nace nima maryam shine ke bani mamaki ai. Muna shiga gidan buzuwa ta fito zasu fita ita da wata maryam tace wanan ashe ta fara fita bakar yawon nata ko nace dama ina zai iya tsare ta a gida ko yaushe tunda ta riga ta saba da fita kullun. Ranan Jumma,a bamu je gidan SJJ da wuri ba sai bayan azahar muka isa gidan yau ma kamar ranan haka aka tare mu tana nuna ga yan uwa da abokanta wai ni sister din marigayitace kishiyar ta kuma yar uwar su. Mun fito wurin waliman ne mun saurari nasiha da akayi inda aka fara hada hadan buki bayan waliman mai kidan kwarya suka dauko ta kida inda mata ke ta rawa da sauran su mudai muna gefe daya a zaune. Sai abubuwan karamawa ake shigo muna dashi ina magana da Altine maryam ta ya futo ni tare da fadin kinga buzuwan ki gidan nan gaba daya muke kallon inda suke zaune. Ita da wasu mata da gani masu ji da kansu ne a garin nan suka dasa hiran ta sai naji na tsawala a gurin don kasancewan Nafisa itama a gidan bukin. Maryam ce ta fahinci hakan tace ita sai ta tambaya taji alakansu da ita nace haba dai akan may zaki tambaya. Ashe zancen na a ran maryam sai ji nayi tana tambayan hajiyan ta juya tace wacan kike nufi tace eh wallahi ban san ta ba sai dai ina ganin gayan wata yar uwar maigidan nan ne sabuwa. Maryam tace itace kishiyar khadija ai tace ita wanan din haba ashe a gidan ku na taba ganin ta ina ta tunanen a ina na santa tunda na ganta dazun tun shekaran jiya tana gidan nan yaude ne suka jima haka ai. Bayan fitan hajiyan ne maryam tace yanzu ai munji dahir can mukaji ana sanarwa daga na hannun daman hajiya wai ana bukatar khadija matar AA perm sec ta fito fili nata ne. Wani iri naji a gurin maryam tace da gaiya hajiya ta sa a fadi hakan don ki fito Nafisa ta ganki wuri yayi tsit ana sauraren fitowana a filin ga masu kwaraya sai kirari suke min. Hajiya da kanta tazo taja hannun zuwa filin take na balle jakka ba dai wani rawa nakeyi ba na azo a gani amma sai wuri ta dauki ihu Allah ya taimake ni nazo da kudi a jakka na ina zubawa ana zuba min. Koda na fito filin rawan ba Nafisa a inda suke daga ita har kawayen nata sun bar gurin mun dan dauki lokaci a gidan kafin ai muna iso gurin maigidan mu gaisa. Yana ta zuba min godiya tare da fadin ki saki jiki kin zama yar gida kin bamu abinda ba kowa zai iya bamu ba a dalilin ki. A raina nace badon ka nayi ba ai da zaka taimakawa yaya Adam ya daga zai fi min wanan godiyan da kake min a yanzu duk da yanzu AA na ma ya Adam din kokari sosai sun fita cikin gangin talauci ana danawa dasu sosai. Biyar daida mu ka dawo gidan motar Nafisa da take amfani dashi muka gani a haraba don ta sayar da wancan na farko daya bata yanzu wani ya kara bata sai dai ko kusa bai kai nawa kudi da daukan idon jamma,a ba. Muna shiga falon su Altine dauke da kaya niki niki itace zaune falon da mutanen ta kai ba dan kwali sai hayaniyan su ke tashi gidan. Jin motsin mu shigowa ya dawo da hankalin su a gare mu har mun dan wuce ta tace yau ni naga inda ake cusa kai babu kwarjini a garin nan. Nace ashe ke makin san gayyan na anya kika je babu gaiyata don kin gani da idon ki kai abin takaici wai mutun yaje bukin da babu gaiyata don rashin sanin ciwon kai. Wallahi karya kike wai har ke za a kira da matar Samad a fili a cikin matan shi wa kike nace ai da aka kira keda kike wata tsiya a gurin shi sai ki fito tsakiyan filin. Wata ce ke tare ta da fadin kaiya Nafisa wanan ai ba zancen fasawa bane don rai ya baci ai ita ma tasan ba zata hada kanta da ke ba. Ke kuma wacece a cikin kayan miya na tambayi matar nace koda yake ba abin mamaki bane an gama cin kasuwa da madam yanzu kuma ku aka jaji bo muna. Haka dai zaku kare wurin akaita sheri har da bukin da babu gaiyata kai girma dai ya fadi idan an sanshi maryam sai yau ta saka baki a zancen mu tace da an san dashi ne ai. Tsiyan abin ba a san kunya ba da girma ai da ba, a zubar da mutumci ba ku dai kan kunyi hasara wallahi abin kunya masu buki suce basu san wanda ya gaiyato ku ba. Ke har kina da bakin magana kullun kina yawo gidan kawa kuna fita yawon iskan cin ku da kuka saba wanan sai dai a fada maku ai. Don mun san komai har gidan bokaye kuke zuwa suna amfani daku don kawai su biya maku bukata da bai yuyuwa. Wanan maganan ya ci masu rai sosai take gida ya kaure da fitina security ya shigo yace su zo su fice a gidan Nafisa tace ba wanda ya isa ya kore mata mutanen ta. Waya ya daga ya kira AA a fusace yace kada su bar mace ko daya a gidan nan kafin yazo nan suka tasa su a gaba sai da suka bar gidan cikin kunya sai faman zage zage sukeyi. Wai an wulakanta su maryam bata dade ba ta tafi sai bayan sallah magariba ya shigo gidan rai bace falo ya kira mu ya tara mu yana tambaya. Ta koro mai karya da gaskiya ta fada mai ya juyo gare ni jin tun da ta fara bayani banyi magana ba yace naji nata ke ya akayi fada min naki. Nan na kora mai duk abinda ya faru ya juya wurin ta a hasale yace banta sanin ke sakarai bace haka sai yau. Wai ma uban wa kika tambaya da zaki fita Nafisa na fada maki ba zan dauki wanan shashanci ba na yawon banza a gidana. Nafisa wai ke wata irin mace ce da baki da tunane har kije gurin bukin da ba a gaiyace ki ba kina zubar da kimar ki ana maki gori akan shi. Ke baki san komai ba a rayuwan ki sai shashanci da tambadewa kina bin tsofin zawarawa kuna zubar da mutuncin ku a gari. Kana nufin goyan bayanta zakayi ne ko may yace kina rufe min baki ki barni da abinda nake jina raina ko sai ranki ya baci wurin nan. Mace bata iya ba kanta tarbiya ba ta yaya zata ba yaranta ta tarbiya tace yanzu ne kasan banda tarbiya ko may ? Na dade da sanin haka ya fada a hasale zatai magana ya daka mata wani uban tsawa wanda yasa har ni ma na kadu a wurin. Mikewa tayi zata bar wurin yace dawo mara mutunci kawai wace bata san ciwon kanta ba bari kuji duk da ke kadai ce a cikin su ke da wanan halin duk ranan da irin haka ya sake faruwa da dayan ku sai na ba maishi mamaki a gidan nan. Ku bace min da gani ya fadi daga karshe kowan mu ta mike zuwa part din ta yana gurin yana ta fada a cikin hasala har muka shige. Nasan tasan bata da gaskiya ne ko may ta gani tayi shiru don bata zaci abin zai juye haka da ita ba idan da dane ba zaiyi wani fada na azo a gani ba. Sai bayan sati biyu ne yake fada min wai yana ganin bukin Zainab ya tashi nayi mamakin jin haka don ni gida naso inyi hutun da muka samu sai ga zancen bukin zainab kuma ya taso. Jin da sauran lokaci yasa na yi amfani da damana na shirya zuwa gida in duba su shiri sosai nayi inda na so su Altine ma suje gida da laraba su duba gida kafin buki sai dai ba zai yuyu ba haka muka fara shirin tafiya tunda nayi sa,a ya barni. Sati mai kewayowa muka ziyarci gida da yarana sadiya kawai muka zo da ita bamu zo da Ihisan ba don suna makaranta har lokacin. Munji dasin zuwa gida don muna da lokaci har sati daya ya bani inyi a gida haka ya bani daman ziyartan tan uwa da abokan arziki da aka dade ba a hadu ba. Tafiyan mu da kwana biyu ne ya dawo gidan ta shigo tana fada mai wai ta dafa mai abinci yayi mamaki amma sai ya dauka don bani gari ne take son burge shi da hakan ita ma. Tana zaune a gefe bayan ta zuba mai duk da abincin bai cika mai ido ba haka ya daure zai ci ya jawo plate din zuwa gaban shi bayan ya wanke hannun shi da ruwa. Allah Allah take taga ya fara ci yana saka hannu kamar ance ya dubi zoben nan daya saka wanda na tsinto mashi a kasan gadon shi. Wani sirirn hayaki yaga yana fita daga jikin zoben sai da gaban shi ya fadi sai ya dake ya kara kai hannu zai dibi abincin karo na biyu. Abinda ya faru da farko ya kara faruwa dashi zoben yana fitar da hayaki yace wanan tsohon yayi gaskiya. Plate din ya tura mata gabanta yace bisimillah ki fara ci don naga kamar baki ci ba ke ta kakaro murmushin yake tace nikan ai dam nake yanzu naka ne kawai ya rage. Ido ya tsura mata tare da mikewa ya zagayo inda take ya duka ya dibi abincin tana zaune tana kallon shi. Zuwa lokavin tayi mutuwan zaune ya dibi ya kai mata a bakin ta kai ta girgiza mashi take ya daure fuska yace ko kici ko in saba maki yanzu wurin nan. Hakkuri ta fara bashi akan ba zata ci ba yace Nafisa kashe ni kike son yi ko may da kika zuba min mugun abu cikin abinci na ? Ta fara kamay kamay ita bata zuba mashi komay ba watau ita bai yarda da ita ba ke nan ko ? Nan suka fara rikici a tsakanin su yace kina tunanen yanzu zaki iya shamta nane ki yaudare ni kar nake kallon ku a gidan nan. Duk wace ke sheri na sani kyale ki kawai nake yi nan dai ta hau borin kunya inda take shiga banan take fita ba yace kici idan kin san baki zuba wani mugun abu a ciki ba . Karshe dai ya kore ta dakin yace kada ta kara zo mai daki idan bashi ya nemay ta ba tunda ke jahila ce baki dogara ga Allah ba. Ranan dai kunya ma ya hanata ko wani dogon motsi a gidan wayan sabuwa ta nema tana fada mata abinda ya faru. Tace ke yaya akayi ya gane amma wanan mijin naku na yarda da madam ke fadin wahalan banza muke akansu gaskiyane asiri baya kamasu tunda har ya gane wanan shirin namu. Nandai na sha zagi a wurin su sun dade suna kulawa da warwarewa a tsakanin su shiko yana can rai bace ya rasa matakin da zai daukar mata ya huce. Kasheni Nafisa take son yi ko may may na rage su dashi a gidab nan da take neman rayuwana tabbas Yusuf dasu hajiya sunyi gaskiya. Yau ba don na kasance da khadija a rayuwana ba da Allah kadai yasan irin cuta min da Nafisa zataci gaba dayi ba tare dana sani ba gidan nan. Barci rabi da rabi ya yi shi ranan tun safe ya fice gidan tare da taurara mataki akan Nafisa ba tare data sani ba. Yusuf yana ganin shi ya fito da safe haka yake tambayan shi ko lafiya kasa fada mai yayi a lokacin don bai san may zaice mai ba. Sai zuwa yamma ne da Yusuf yaga damuwa yayi mai yawa ya tasa shi a gaba take fada ma Yusuf din abinda ya faru. Yusuf yace kaga zoben tsohon nan ke nan ya wani yamuste fuska yace Deedar ta tsinto min shi a kasan gadona nasan kuma hakan sherin Nafisa ne ba kowa ba. Yanzu wani mataki ka daukan mata don ya kamata ka daukan mata mataki yanzu tunda bata da niyar bari. Na riga na dauki mataki ko sai ta raina kanta a gidan nan don ba saki a tsarina wancen ma danayi bakaji irin fadan da Abba yai min ba ranan. Don haka a cikin ruwan sanyi zangasa ta sai ta raina kanta gidan nan Allah yasa ta bari indai Nafisa ne ina ganin da shi idon ta ya bude dama yusuf yace. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 1/21/21, 7:42 AM - Fatima Amarya: Satin mu daya a gida muka dawo sai dai tunda na dawo naga sauyin gidan ya juya a yanzu gaba daya na rasa fahintar komai daga mutanen gidan. Ban kara gaskata hakan ba sai da ta shigo wurina da safe yana fadin kulun ku dinga saka min abincin dare a part din nan. Saurin dago kai nayi don jin abinda ya fadi kasa hakuri nayi sai da nayi magana nace wanan kasan ba zai yuyu ba tunda ga matar ka a gidan. Bani kadai bace matarka kasani sai dai idan wani fitina kake son ka dauko min kuma ga yin hakan yace idan ba zakiyi abindana sakaki ba sai ki bari. Zan fita waje na dinga ci a can nace idan hakan yayi maki nace indon abincin da zakaci ne ba sai ka fita kaci waje ba. Yace shi zai fita fuskan shi babu walwala a cikin shi da alama ma bai karya ba zai fita gidan lokacin bishi nayi da kallo ina nazarin shi a raina. Ajiyan zuciya na sauke tare da fadi a fili Allah ya kyauta koma may nene don banda amsa komai a yanzu. Naki tasowa da wuri ne don kada in karbi girki a ranan yasa sai biyar muka taso na dare dayake motar mai lafiya ce Alkasim ne driver ya iso da wuri bayan gudun dayai ta shararawa damu a hanya mun iso ana sallah magariba. Haka yasa ban damu da wani girki ba a ranan duk da nasan idan na tashi yi koda tsiya yadda takeyi zanyi nima. Wanka nayi na shirya na fito falo wurin su laraba dake faman cire tsaraban da muka dawo dashi tana adana shi inda ya dace. Zama nayi a cikin rashin walwala a tare dani sadiya da ke kwance nake kallo yadda yarinyar ke dada girma yanzu shi kuma kan dake da matsala yana kara girma sosai. Naji tausayin ta sosai a raina ga ta dai yarinya ce duk da ba tada alhakin kowa a kanta amma Ubangiji ya jerabe ta da wanan lalurar a rayuwan ta. Altine ce ta fito daga dakin du tana dauke da mami a hannun ta wuri ta samu ta zauna a gefe na tana fadin kamar in koma minnan nan naku nake ji. Ban taba zuwa jahan ba a baya sunan girin kaidai nake ji ashe gaein babba ne haka ban sani ba gaku da abunci kala kala a garin. Duk da naga kunfi maida hankali ga doya itace abincin mutanen garin sosai duk gidan da mukaje shine za a sarafa muna a wani launi. Nace haba dai inda dai muka je kikaga hakan ai yanzu wasu saboda wayewan kai basu faye son doyan ba sai dai abincin zamani . Bayan mun dan taba hira ne na mike na fita daga part din nawa gidan nake zagayawa inda tun a falon naga yadda ya koma tankar babu mata a cikin shi. Din ina ganin ko kara ba a taba a gidan baya dada shara da kazantar da akayi ko ina na gidan kai na girgiza, tare da kwala wa Altine kira tana fitowa nace tazo ta gane min wanan wulakancin. Nan Altine ta shiga zuga ni har naji raina yana tafasa sosai kira ba kwala ma samiha dake kwance a dakin su taki amsawa. Part din na fada nace samiha da yanyala su fito tare da su Altine su gyara gidan nan tas ku wasu irin kazamai ne haka kamar ba mata ba zakuyi rayuwa haka a cikin kazanta. Ku ke nan baku iya gyaran wuri sai dai ku bata kuna jira azo a gyara maku don haka ku fito ku taru ku gyara gidan nan yanzu. Daga bayana naji muryan Nafisa tana fadin ba zasu gyara ba ke wacece da zaki shigo har nan ki basu umurni wai suzo suyi maki aiki. Aiki aina kowa ne don su suka bata amma na saka su Altine da laraba a taru a gyara tace wanan ke ya dama don mu ba matsalan mu bane. Waya na daga na kira AA ya dauka bayan ya dan dade yana ringing yana dauka nace mai cikin ladabi dama na kiraka ne don kaiwa matar ka magana gidan yayi mugun datti ko da muka dawo. Mun samay shi ba a gyara ba tun tafiyan mu shine yanzu na saka samiha da yanyala dasu Altine su gyara amma ga Nafisa tace wai ba zasu gyara ba. Yace bata wayan ko ki saka wayan a hand free yadda zata tajini na saka ban yarda na bata wayan ba yace Nafisa kina jina idan mutanen nan bazasu aiki ba kamar yadda aka sakasu suyi su bar min gidana kafin in dawo. Yana gama magana na juya na fita na barta a wurin da takaici na ba abinda take kallo sai sauyin da take gani a gareni. Sai mamakin yadda na juye a lokaci daya komai nawa ya canza kamar ma kada inje garin mu taga na wani kara kiba da haske sosai sai yau take ganin abinda su madam suka sha fada mata a kaina. Wani iri taji a ranta tare da fadin shike nan bakin bakin su madam yaja min tabbatar wanan abin ga yarinyar nan yanzu yaushe har ta bunkashe haka ne wai ? Lalai tayi sake da yawa da idon ta ya rufe bata hango haka ba tunda wuri anya yanzu kuwa zata iya taron wanan da take gani a gaban ta zata iya shawo kanta kuwa ? Don idan batayi da gaske ba tana kallo zata kwace mata komai nata a gidan tasan dai idan kyau ne ko fari take rudan mutane dashi wanan ma ba baya ba haka kuma ga ilimin da take dashi wanda take gani dashi take kara amfani wurin ganin bayan ta a gidan. Kai anya nan gama ko zata iya karawa da Dijan nan da yanzu gaba daya komai nata ya sauya ya zama na hamshakan matan da ake iya damawa da ita. Duk kokarin ta wurin taga ta shiga sahun matan manyan abuja abun ya faskara sai ta dan jona dasu kwana biyu sai su bare ko don suna daukan ta bare ne ita haka ke faruwa. Dama ance mutum bai ganin illar shi abinda bata gane ba shine halinta na rasgin tauhidi ke kore mata mutane. Don da ta dan kwana biyu da kawance da mace zakaji ta fito mata da kudirin ta tana tambayan ta ko tasan gidan wani boka ko malami da aikin shi ke ci kamar yanka ? Ko tace ita kishiyanta take son kashewa ko ta haukata ta ko ta batar da ita ta shiga duniya a manta da ita gaba daya ire iren wanan maganan ke ba matan da take son mamuwa tsoro suke gudun ta kwana biyu ta daina jin su. Hakane yasa ta kula da mata masu zaman kansu a Abuja don su basu da lasisi haka take gare su ko ina ta fada rataya ne. Ina tsaye har suka gyara falon zuwa wajen gidan da ko ina dake da bukatan gyara a gidan suka feshe ko ina da kamshi gidan ya dawo daidai. Nafisa ko tana daki ta kasa fitowa sai tunane take tana sakawa tana sancewa don komai ya juye mata a lokaci guda a gidan ga samad dake wanan fushin ko kallon inda take baya yi. Har Ihisan laifin take ganin ya shafa don ya shigo yarinyar na kiriniya ya daka mata tsawa taki dainawa ya kamata yai mata dukan tsiya a gabanta. Idan da dane sai dai yayi dariya ya wuce idan tana irin wanan halin ta manta ita abinda taiwa uwa da yaranta a baya data hanasu shakuwa ma da uban su gaba daya. Idan ya shigo ko kallon yarinyar baiyi yanzu sai dai ta sha alwashin ba zata yarda ya mayar mata da ya wani part ba da abinta zata zauna. Nikan muna shiga nayi wanka tare da dauro alwala nayi sallah nafito kitchen na nufa don dora girkin dare da kaina don ina son burge maigidan yau. Komai na hada sai da akai la,asar ne na fito na koma daki na dan jima a ciki kafin in fito in duba girki na sai da na tabbatar komai yayi yadda nake so. Na dawo falo wurin su Altine muka zauna kallo suke wanda ni ba gane kan kallon ban dade da zama ba na mike zuwa ciki don gwada wani abinda Anty salbiya ta taba bani ban taba amfani dashi ba. Sai yau tunda nice zan karbi girki a gidan nayi kamar yadda tace min ina gamawa na zauna bakin gadona don inyi waya da maryam don naga bata shigo ba. Mun dan dade muna wayan inda take fada min zancen su da Suraj ya tabbata don karshen satin nan zasu je gurin iyayyen ta a tsayar da magana. Murna nayi mata sosai tare da fatan alheri gare ta nace zamu koma a innuwa daya ke nan tace ke dai bari ni abin mamaki ma yake bani. Ba a mamaki da ikon Allah nace baki ganina yanzu Allah ya dora ni akan Nafisa a gidan nan abinda kowa ke min fargaba a baya. Idan Yusuf yana fadin zan iya sai inga ta ina zan iya da wanan shedaniyar ashe abin daga Allah ne kaidai ka dogara gare shi kaga aiki da cikawa. Khadija in banda abinki in bamake ba ai wanan buzuwan tana da saurin kawarwa don gata nan da abubuwan fada kala kala tare da ita. Matar da bautan ubangiji ma sai taga dama takeyin sa bata san wani abu ba sai shirka da bata ina cikin sauraren maryam ne ban san shigowan shi dakin ba don ban masan lokaci yaja haka ba. Fuskana na kallon cikin dakin na shagala da wayan sai ji nayi an dafa ni ta baya a firgice na juya yana shi na gani a tsaye yana min wani irin kallo a cikin gajiya. Dawa kike waya haka kika shagala nace maryam ce na kira muke waya don naga bata shigo ba yau tasan kuma mun dawo. Tana fada maki ke nan wanan satin za a je zancen su ko ban bashi amsa ba nace sannu da dawowa don ban yarda yaji akan may muke magana. Jin bai amsa ba yasa na dago kaina ina kallon shi shima kallon nawa yakeyi nace lafiya kake min wanan kallon ko wani laifin nayi kuma ? Ba tare da ya amsa min ba shima yace wai may kika ci haka a gidane kika bun kasa da yawa kin wani koma wata big madam dake , ? Kallon shi nayi ina murmushi nace kila dai idon ka ne ya gane maka hakan ni ban wani canza ba ai danaji a jikina ko ? Kara matsowa yayi kusa dani yana gyara corth din shi daya rataya a kafadan shi da kyau yana wani lumshe idanuwan shi yace. Kun gudu kun barni ina kewan ku daga ke har yaran ya fada yana zama a kusa dani nace ai gamu mun dawo ko har wani dadewa mukayi balle kace kayi kewan mu. Kanshi ya dora akan kafada na kamar wani karamin yaro yana sauke ajiyan zuciya yace nayi kewan ki wallahi a kusa dani ban taba sanin dadin mata biyu ba sai wanan tafiyan da kukayi. Najini kamar wani maraya can Deedar ajiyan zuciya na sauke tare da fadin kai yaya banda abinka kai dake da wata a gida shine zakace mun barka maraya kuma. Tura fuskanshi yayi cikin kaina yana sunsunan dadaden man kitson da akai min kitso dashi tarre da rike min hannaye na. Yace kowa da matsayin sa a gare ni don haka ki yarda dani I miss you kwana biyun nan da kukayi sosai wallahi. Wani iri naji har cikin raina a lokacin ina mai jin dadin wanan furcin nasa a gare ni sai naji kamar ba wanda ya kaini a gare shi a lokacin. Muryan shi naji cikin sarkewa yana fadin wanan kamshin naki yai min dadi wallahi yana kara dora kanshi a saman kaina yana shaka. Kai na girgiza tare da kokarin jaye kaina daga gare shi ina fadin ka tashi ka watsa ruwa ka ji dadin jikin ka kada wani yazo nan ya samay mu a haka kuma. Korata kike yine daga nan da sauri nace don may zan kore ka gani dai nayi ka gaji kana bukatan hutu yanzu kafin a kira sallah. Murmushi yayi tare da mikewa tsaye yana gyara kayan jikin shi da suka dan takure daya zauna ina mamakin yawan tsabatan shi har nakan yi tunane wai yaya yake da matan shi masu kazantar tsiya ? Mace tun zanin safe dashi zata wuni a jiki wata kila ma ta kwanta haka dashi don ko washe gari dashi zaki ganta ta tashi. Muryan shi ne ya katse min tunane na da yace may zan samu inci ne yau tun safe rabo na da saka wani abu a cikina dana sha dan cock . Nace abinci na nan na girka ma sai dai idan wani abin kake so kuma a dafa ma yanzu yace zan dan sha tea kadan idan zan samu kafin anjima inci abincin don hanji na ya warware. Nace barin kawo maka kafin ka fito wanka yace dakin kyauta min ya juya ya fice daga dakin ajiyan zuciya na sauke bayan fitar shi dakin. Wai yau nice AA ke fadin yayi kewan mu da bakin shi yake fada min hakan tare da nuna min da gaskiya yake fadi yadda naga jikin shi yana mutuwa dan zaman da yayi a kusa dani. Mikewa nayi zuwa kitchen na hada mai ruwan tea tare da daukan kayan na nufi part din shi baya ciki yana bayi sai kamshin mai dadi ke tashi a dakin. Kayan daya cire na kwashe na aje inda muke aje kayan dauda ina shirin fita daga dakin ne ya fito daga wankan muryan shi yasani juyowa yana tambayan ina tea din yake ? Nace yana dinning na aje ma nan zaki kawo min in sha yunwa nake ji sosai nace kai mai mata har uku biyu a gari zaice yana jin yunwa haka. Kallona yake mai kama da harara na fice ina dariya yace zaki dawo ai yana murmushi na dawo dauke da kayan a gaba shi na hada mai komai ya zauna a bakin gado ya na sha muna dan taba hira sama sama. Na dauka Nafisa zata shigo tace na shiga mata lokacin ta duk da saura yan mintuna lokacina ya cika sai dai banda yadda zanyi dole in bi umurnin shi. Na mike bayan ya gama sha ya miko min kofin yana fadin yagode sai dan zufan daya fara tunane nayi nace wai ita wanan wata irin mace ce da zata bar miji haka ya zauna da yunwa. Allah kadai yasan yadda yake zama da yunwa da take ita kadai a gidan gasu da yawa saidai yawan ya zama na banza gareshi don babu mai iya dora abinci idan ba yunwa yaci su ba sun kwamce suyi tashan ruwan bakin shayi. Ina fita ya sauke ajiyan zuciya tare da tunane a ranshi irin saukin kan dake gare ni a dai barni da fadin magana ko yaya yazo min a bakina kuma yanzu ya saba da wanan. Wanda maganan nawa daidai yake da amsan abinda zaka fada min sai dai ya lura yanzu ina dan rage yaba magana kamar da can baya. Daki na koma na kara shiyawa don yau nasan zan dadana kuda na a wurin shi yadda yake mazarin nan akaina sai Allah. Ana sallami isha,i ya dawo gida ranan shiya kirani da kansa kwaliya na caba sosai kamar mai shirin fita wani wuri a lokacin. Na dauki kayan abincin shi zan fita Altine ce ke min wasa wai su rufe kofa ne na tafi ke nan ina dariya na juyo nace lalai kan idan kunji shiru ku rufe. Zaune yake a dinning din tunda na shigo ya kura min ido kamar tsohon maye har na iso gareshi da sallama a bakina. Kallona yake tundaga samana har kasa ya dawo da idon a fuskana na fara gaida shi da wuni ya amsa min tare da fadin in kama maki ne. Ina iyawa na bashi amsa na aje kayan tare da jan kujera daya na zauna akai nace may zan fara zuba maka bayan na gama jera mai abincin . Yace koma may na samu don yau ina son in cika cikina da wanan girkin danayi missing na kwana biyu daga nan sai in dora da abinda aka hanani din dazun. Abinci kadan na zuba mai don nasan ba zai ci ba tunda yana ganin naman kai a gaban shi don yana son shi sosai da bindin sa. Plate din abincin ya jawo a gaban shi yana fadin kin kara kyau sosai wanan kwaliyan kamar mai zuwa buki nace bako bukin zan tafi ba duk wanan kwalliyan don ka nayi ko zan koma amarya yau. Kai ya gigizs yana fadin har kina tunanen komawa wata amarya ce ke da kulun sabuwar amarya kike a gurina ban taba ganin macen da ta haihu ba kuna komai nata yana nan a yadda yake. Wani kallo nayi mai nace dama tunanen ka ke nan ashe barin kara zake damtse na furin gyara kada watarana kaga gazawana . Ban tunanen akwai wanan ranan a rayuwana ya bani amsa yana debo abincin sai naga ya dan tsaya yana dube duben hannun shi can ya girgiza kai yakai loma a bakin shi tare da bissimillah. Ashe aune abincin yakeyi ko nima na masa wani sihiri sai baiga komai ba don yanzu tsoron kaidin mata yake gaba daya ba Nafisa kawai zata iya mai sheri ba kowane akan wanan. Yana ci muna hira wanda hiran akan yan uwanane yake tambayana a cikin hikima nan yake fadin na hana Alkasim din ki komawa ne don a sama mashi aiki ya fara daga baya sai ya koma ya karo karatun shi. Naji dadin jin wanan maganan don zan su mutanen da muke tare da dadewa suyi alfahari da samu na nima a duniya tun yanzu. Bayan ya gama na kwashe kayan zuwa part dina na rage wanan kayan zuwa kayan barci na gyara duk wani sassan jikina nayi masu saida safe na fito. Yana kwance yana jira na ban bata lokaci ba wurin ba bori kai ya hau ranan nice na nuna masa gwanintana ya rasa duniyan da yake ciki sai wani lokaci muka sarara ma junan mu nan ma bamu kwanta ba hira muka dasa akan bukin da zamu tafi. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 1/23/21, 7:58 AM - Fatima Amarya: Mamaki nake a raina yadda naga Nafisa ta koma wata saliha a dan kwana biyun gashi kuma ba wani hurda dake hadashi da ita a gidan. Rana girkin nafisa ne duk da na saka mai abinci kamar yadda ya umurce ni sai dai ban kai ba har karfe tara na dare sai ga wayan shi ya tambayan abincin shi. Dan jim nayi kafin in ce ina zuwa bayan wayan na mike na dauki basket na nufi part din shi a falo na wuce su suna hira na hau sama wurin shi da abincin. Kallon mamaki ta bini dashi har na shige waya ta dauka ta kira Sabuwa tana fada mata cin fuskan da yake shirin mata don ita a zaton ta har da kwanan ta ya bani duka. Ki bishi a sanun mu gane mai yake nufi da dakatar dake da yayi a girki tunda bamu san manufar shi ba kan hakan yanzu. Kuka ta saka mata tana fadin sabuwa Samad ya cuce ni idan yace haka zai min yanzu kan wanan yarinyar baya ganin kowa da mutumci sai ita kadai a gidan nan ga laifin nawa har yana son shafuwar ya ta yanzu don har ihisan haushin ta yake ji gaba dayan mu yanzu. Ke ma kin san wanan aikin asiri ne idan tace tanan harda yara zata hada sai muma mu koma kanta da yaran ta ga baki daya mu zuba mu gani. Sai dai ke ma kina da laifi Nafisa don may zaki haifi ya kuma ki nuna mai kina kyamatan ta haka a fili ko Allah zai iya jarabtan ki kan wulakanta wanan yar da kika yi ai. Sabuwa na kasa saka yarinyar a raina don zuciyata ta kasa hakkura da ita a matsayin ya ta ki duba yadda yaran nan nata yanzu suke tasowa a gidan nan kamar wasu diyan turawa dasu . Shegu ko kaine wa bakai masu kallo daya ka kawar da kan ka garesu saboda shiga rai da yaran ke dashi farat daya na rasa gane wa suka biyu da wanan kyau din cikin uwar da uban. Nakasa shegu zamuyi su koma abin kyamata suma ga jama, a ba tana sallo ta haifi na miji ba mu kai dan banza a sakar mashi illa a rayuwan shi. Yadda uban ma zaiji dan ya fita rashin gaba daya kinga dake da ita mai kurin tana da namiji kun zama daya ke nan sai dai idan samad ya mutu a yanzu kan dan ko mun nakasa shi tafiki kaso a gidan. Nan dai sukai ta kula sheri wanda kullun cikin kulawa suke basu ganin alfanun shi kuma bai sa sun daina abinda sukeyi din ba. Tunda na shiga falon na aje mai abincin tare da gaida shi da wuni na juya zan koma part dina naji ya ce dani dawo ki zauna har in gama ki tafi. Wani kallo nayi mai a cikin mamaki ya sake fadin ki zauna nace in gama ko nace amma kasan in munyi haka mun wuce gona da iri don ba hakki na bane yin hakan. Babu ruwan ki umurni na baki ba neman ba,asi ba ko wani dogon bayani ya fada don katse wani zance daga gurina din . Don dole na ja kujara na zauna ina fuskantar shi yana cin abincin ba tare da wani yayi magana a cikin mu ba. Na yanke zan tambaye shi may ye dalilin sakani yin hakan bayan ya san banice da alhakin kulawa dashi ba ranan ina yi ina dan satan kallon kofan dan barin Nafisa a falo da nayi nasan kuma zata biyoni itama taji dalilina nayi mata hakan. Sai dai har ya kusa kammalawa bata babu dalilin ta yasa na kara gaskanta da wani abu akasa wanda ni ban sani ba dayake faruwa a tsakanin su. Yana gamawa na mike jikina ba kuzari yace idan kin hada kizo ki dan matsa min wuya na don yai min tsami yau sosai wanan kan ban san lokacin da nace haba yaya AA kafasan bani ce da alhakin yi maka komai ba a yau. Kada mu shiga hakkin wata koni idan an min hakan ba zanji dadi a raina ba gaskiya don may kuma zan biye maka mu fasa halaka. Yace kin fini sanin Allah ne khadija nasan maganan mai girma ce tunda ya ambaci sunana haka yau na bude baki da kyar nace na daiga ba zata ji dasin ganin haka bane idan ta shigo ta samay ni a nan din. Zaman ta kikeyi ko nawa nace naka a sanyayye yace idan ba zaki min abinda na bukata ba to ki fice min don Allah ban son dogon magana yanzu. Daukan kayan nayi da niyar fita yace ba zaki mun massage din ba ke nan dole na aje kayan hannu na na nufi inda yake gabana sai faduwa yake kamar wani zai kamani a lokacin Dan jin nayi kafin in fara sai dai can na dora hannu na a hankali na fara mai sai naga ya gyara zama yana wani lushe ido sama kanshi ya nuna min ba tare da yai magana ba na kai hannu saman kan ina dan cakula mai a hankali. Jin shitun yayi yawa yasa shi yin magana na dai ga kamar dole kike min kina iya tafiya yanzu yace yana mai sauke ajiyan zuciya. Nace gaskiya kan a tukure nake tunda nasan ba hakkina bane yi maka haka yau don gudun zargi ina mun dade da gama wanan maganan . Ai na dauka kina da fahinta amma tunda bayani kike son ji jeki zan maki bayani indan na shirya sai dai ba yanzu ba don kin gama bata min rai da gardaman ki nan. Akan gaskiyana nake magana don ko ni ba zanso kai min haka ba kaga yanzu da Allah yasa ta shigo duk abinda ta fada a kan mu bamu da gaskiya ai. Shiru yai min bai ce komai ba don ya matukar kuluwa da ni a lokacin dukawa nayi na dauke basket din kayan dana hada nafita daga dakin. Kai ya girgiza bayan fitana tare da nisawa yace watau ita komai nata akan tsari yake ke nan da Nafisa ce dadin hakan zata ji sosai ba wani tunanen wani abu. A falo na samay su zaune da yan uwanta ina fitowa tace Allah dai ya tsine wa mai satan kwana kiyi abinki yanzu lokaci ne gobe ko ance kiyi ba zaki gwada yi ba ai. Ban kulata ba don dama nasan haka ne zai biyo baya don babu gaskiya ga wanan maganan saboda ta fimu gaskiya yanzu. Ina shiga su Altine dake zaune suna hira tace kin dawo nace eh sai da nakai kayan kitchen na wanke na fito ina zama nace gaskiya dan uwan ki na son ya ja min magana in rasa bakin bada amsa. Ya dai san yau banice da girki ba amma ya saka min dokan nice zan dinga bashi abinci ba tare da yai min bayanin komai yadda zan fihinta ba . Yanzu gashi ina fitowa ta fara zargina tana fada min magana kan hakan dole na kyale ta don banda bakin bata amsa tunda babu gaskiya a ciki. Maman biyu tunda kinga haka dole akwai wata a kasa gaskiya haka kawai da hankalin shi ba zai ce maki hakan ba ya kamata ki gane hakan. Itama fa wurine bata samu ba da hakan zatai maki ai koda kuwa babu wani dalilin mai kwari zata so tai maki hakan Allah ne ya taimakeki ya doraki a kanta ai. Don haka zagewa zakiyi yanzu ki nuna mai naki daman akan shi koda sun shirya a tsakanin su kin riga da kin kara kafa gwaunatin ki a zuciyar shi. Ke dai mace ce mai ilimi ba sai na fada maki abubuwan da zakiyi ba yanzu dama naki ne a gidan nan ki fito da kalar ki ta gaskiya ga kowa na gidan nan ta yadda zasu fahinci rayuwan ki. Akoma ana kyamatar ta acikin wana zuri,an ga baki daya kowa ya gane cewa gwaunatin buzuwa na kama karyane a baya tayiwa mutane. Maganan Altine ya tsaya min sosai a raina don haka na fara neman mafitan hanyar da zanbi in nuna nawa hikimar data ce. Ban dade ba na shige don in kwanta sai dai barcin yaki zuwa min da wuri yadda nake so sai can dare na samu yazo min duk da haka na samu tashi nayi nafila na mika bukatana a wurin Allah. Washegari tunda ba school muke fita ba kitchen na fada na hada mai lafiyayen breakfast kafin wani lokaci na gama duk abinda zanyi. Wanka na shiga na fito na shirya tsab dani falo na fito na samu sanyi ya hanasu fitowa daga daki tunda yau din san ina kitchen din. Dakin na leka nayi masu ina kwana suna kwance tare da yaran sai dai ba barci sukeyi ba suna kwance ne suna hira nake fada masu zan hau sama a fito lafiya sukai min. Na samay shi yana shirin jikin shi sai da na karaso inda yake nayi mai ina kwana ya juyo yana amsa min tare da fadin ya kuka tashi lafiya nace mai ina isa inda yake sa botturn din rigar shi. Amsa nayi na karasa saka mai yana tsaye yana kallona na mika mai ties din shi yana sakawa na nufi gurin takalma na dauko mai wanda ya dace da shigar shi sai dana dan goge na aje mai a gaban shi. Kallon takalman yayi yana dan murmushi nace ko takalman basuyi ma bane yace sunyi mana ina dai mamakin yadda kika san su zan saka. Na sani mana tunda nasan shigar ka yanzu dan zama da kai a gidsn nan abinci na table yana jiran ka idan ka shirya. Ai baki karasa shirya ni ba may ya saura na tambaye shi yace turare ko na juya gaban mirrow din shi na dauko turaren da yake amfani dashi idan zai fita na fara fesa mai a jiki. Na gama tare da dago kai na kalle shi ni yake kallo na dan daga mai yatsu na biyu alaman yayi kyau yace ya gode na juya zan fita dakin ina kuma zaki yace yana kallo na. Na gama abinda ya kawo ni ai kada in zake da yawa ba aikina bane taimaka maka kawai nayi ai juyawa nayi zan fice naji ya jawo ni zuwa jikin shi yana fadin ai baki isa ba sai kin karasa na fada maki. Jin zafin yadda ya juyo ni nayi yasa na dan sake kara kadan nace wasshh mane ni yayi a kirjin shi yana fadin abu biyu zuwa uku ya rage maki ai kafin ki tafi nace. Ai da ina zaton ka gama shiryawan ne ya sake ni yana miko min tsitsiyar hannun shi alaman in daura mai agogo a hannun nakama hannun na daura mai. Bayan nagama nace sai na biyun kuma yace muje dining ki bani abincin tare muka fits zuwa dining din sai dana zuba mai ya fara ci ba dama in tafi don nasan wani matsala ne kuma yana cin abincin shi a tsanake har ya kare ya goge bakin shi. Mikewa yayi nima na mike tare da fadin na ukun fa ko nagama ke nan yace da sauran ki saura nan yana mai nuno min gefen kumatun shi tare da fadin saura sallama. Na gane nufin shi amma sai nace ba yanzu naga ka goge bakin ba ki ban kiss in tafi kina sani makara fa ba a kuma sanni da makara ba. Kai na girgiza na nufi fuskan shi in mashi yadda yake so din ina kai bakina na sake mai kiss na juyo Nafisa na shigowa gurin. Take ya daure fuska yana fadin may ya kawo ki nan may na fada maki akan part dina zaki fice muna ko sai na bata maki rai yanzu gurin nan. Kamar zatai magana sai kuma ta juyo ta kalle ni ta juya ta fita rai bace nace haba yaya ko mai tayi maka bataci wanan hukinci ba daka dauka haka akanta. Wani kallo ya watso min nace haba dai kuma a gabana kake fada mata wanan kalaman haka yaya babu kishiyan da zata so ai mata haka a gaban kishiyan ta fa. Yace ni zan tafi sai na dawo a dawo lafiya nayi mai ina ci gaba da tattara kayan abincin zuciyana fam da tunane na dauko zuwa kasa. Nafisa ce a main falo ta cika tayi fam da ita ina karasowa take fadin gurin ki ya cika an wulakantani a gaban ki yadda kike so. Sai kijira zuwan naki ke ma don ba kyale ki zanyi ba akan hakan nace duk da ban san tsakanin ku ba idan kin tashi sai ki dauki raina tunda a hannun ki iko yake. Kin gani nan nasan abinda nakeyi don ni ba jahila bace irin ki da za aiwa dan uwa abu inji dadi don nasan kambun namiji murdawa ne nima ban wuce haka a gare shi ba. Amma ki sani umurni nake bi ni yanzu don mijinane a inda ya tsayar dani anan zan tsaya ban kari ko ragi don haka ki shiga taitayin ki ki lalaba ku shirya da mijin ki don ni ban san tsakanin ku ba yanzu haka. Daga haka ban jira in ji amsanta ba na shige part dina na barta nan tana bakaken magana tana amaye zuciyar ta ko zata ji sanyi daga abinda take fuskanta. Karyawa nayi na kwanta barci na samu nayi sosai sai zuwa sha biyu saura na falka tare da duban lokaci ga har rana yayi ke nan. Wayan dake gefena na dauka ina dubawa sai naji ina son kiran shi a lokacin samun kaina nayi da danna mai kira wata zuciya tace mayvzan fada mai idan nakirashi din har wayan ya shiga ban sani ba ina can ina tunane a raina. Sai muryan shi naji yana fadin Deedar ya akayi ne nayi saurin fadin ya aiki yace gashi muna tabawa lafiya kuke nace eh dama na kiraka ne in tambaya may za, a dafa maka yau. Dan murmushi naji ys sauke yace duk abinda kika dafa min zanci don nasan mai dadi ne kamar mai dahuwan nace wani zance ke nan kuma. Ai gaskiya na fada yau dai nasan ba cin haki ai ko don haka a dafa min komai yayi zamzam yadda zan gamsu dakyau don Allah don shekaran jiya am barni ina santi . Sai anjima don naji kana son sakin layi ni bashi nakira ka fada min ba dana ni ko a yaushe zamzam nake don haka Allah yayi halittana. Ai basai kin fada ba da zaki bar girki ki zauna ki samu hutu ai ni dakin kyauta min wallahi kin ga idan na dawo sai nima in raba in samu wanan ni,imar daki ka kwasa. Dip na kashe wayan don kalaman shi sunfi karfin sauraren kunnuwana bai kokai ga aje wayan ba kiran shi ya kara shigo min sai da ya kusa katsewa na dauka. Yace don may zaki kashe min waya ina magana nace wayan ne ai ya mutu yace to ya na hutar daku girkin komai za a kawo maku abinda zamuci da daren idan kuma akwai abinda kuke so sai ki min text kafin in bar office din nace mun gode na kashe wayan. Ranan haka muka wuni muna hira bamuyi aikin komai ba don nace kada su girka komai a gidan basu dai tambaye ni ba suka kyale ni. Da ya dawo ne aka shigo muna da ledoji kala kala lokacin ina daki laraba tazo ta kirani take fada min an shigo da sako don bata bude ko may nene sai idan nafito nace a bude. Bayan na fito naga ledojin ne na umurcesu dasu bude nama ne na kaji sun sha hadi sai na rago da sauran kayan shaye shaye sai take away kala kala aka hado muna. Ganin kayan sun muna yawa nasa laraba takai ma su Nafisa wanda na ware masu ita da Ihisan suka dauka na dauka zata bayar a dawo min dashi sai naga laraba ta dawo ba tare dasu ba. Shirin tafiya buki muka shiga yi tun ana saura kwana uku mu wuce sai faman shiri muke part dina yayin da ita part din su ko a jikin ta. Sanin halinta yasa ban damu da ita ba don zama muke ba mai shiga harkan wani a gidan ba ina kwana ba sanin halin da dan uwa yake ciki zama dai irin wanda bai dace ba ga addini. Banda yadda zanyi don dole nima na koya na iya koda kuwa dan uwa zaiga abin cutawa dan uwa na har gara nima nakan dan tanka idan naga wani abinda bai kamata ba a gare su. Ana gobe tafiyan mu ne ya kiramu a falon kasa kan tafiyan nan dai ta nuna ita bata san da zancen ba ai yace ba dole sai kin sani ba kamar yadda kika ce saidai ya zama dole duk wanda ke gidan nan yayi tafiyan. Saboda haka ya saura gareki gobe karfe takwas zaku kama hanya ni sai alhamis ko jumma,a zan shi go idan Allah ya kaimu ban son jin komai ya fito daga gare ku kuje kuyi abinda ya kaiku ku dawo. Ya bude briefcase din shi ya fara ciro kudi a ciki ya mika mata sannan ya miko min nace mu gode Allah ya kara rufa asiri. Kallo ida take zaune tana faman juya kudin yayi yace yanzu ke bakiji kunya ba mutum haka baisan komai ba sai gadara da jahilci. Yanzun kuma may nayi yace a gidan ku ba a koya maki godiya bane ko baki ji yadda yar uwar ki tayi godiya ba yanzu. Samad har abin yakai ka zage ni a gaban wanan yace wanan din tafiki mitumci da sanin ya kamata don gashi tayi a gaban ki. Yana fadin haka ya mike yabar gurin ta bishi da kallon mamaki kafin ta juyo kaina tace gurin ki yau ya cika a gidan nan sai dai naki kadan ne na baki nan da dan lokaci kadan. Dariya nayi nace tunda ke ce da lokacin a hannun ki ga lokacin nan yana fadin kanshi wanan shirmay na fada maki yanzu ba shine mafita ba gare ki. Da zaki koma gs Allah ki dawo hanya madaidaciya a zauna lafiya mutaru mu rufawa kan mu asiri da mijin mu da zaifi maki. Ina fadin haka na mike ina cewa mudai mun gode Allah ya kara rufa mai asiri duniya dalahira don gobe akara muna. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 1/24/21, 7:50 AM - Fatima Amarya: Duk yadda yaso mu tashi da wuri hakan bai samu ba don fitan da mukayi tun safe zuwa gurin motar da zata daukan muna kayan dakin zainab din da kayan sobaniya da na hada a nan wanda ba wanda yasan dashi maryam ce kadai ta san da wanan sai yau da ake daure kayan ya gani baidai yi magana ba. Set biyu yai mata inda idan mun dawo dayan nan gidan ta zamu gyara da dayan don haka shi bamu dauke shi ba. Sai shabiyu da wani abu muka bar garin da tawaga na na bar maryam a wurin kayan wace ita daga baya zata samay mu kaduna idan an fara buki. Ban tsaya bin ta kan Nafisa ba don banga alaman kamar zata tafi ba Al,kasim ne zai jamu sai dayan hilux dake dauke da kaya da zata bimu don haka duk a motana mukayi tafiyan . Mun sauka kaduna lafiya sai dai nayi mamakin ganin duk zumudin zuwan da mukeyi acan kamar ba wani abinda ke faruwa. Wanan ne karon farko da nazo tun bayan haihuwana wanda yanzu yakai wata ni masu yawa don yarana suna batun shekara daya ne sunyi wayo dosai do , har sun fara takawa. Abinda yasa ban zuwa kaduna bai wuce abu daya ba shine rashin barkan da Fati batai min har wanan lokacin har wanan lokacin dama a lokkacin da na haihu din ta bugo waya tana fadin ashe an sauka to barka ba wani Allah ya raya ko wani abu. Hakan baisa na fita zancen yaranta ba don duk karshen wata idan zai tafi nakan bada sakon da za,a kai wa su Affan din da daddy. Hajiya mama tayi lorafin rashin zuwan mu har ta gaji sai in fake da yanzu karatuna yayi zafi banda halin tafiya ne niko naga zuwan nawa yana takurawa Fati shiyasa na kara dauke kafana. Ban damu da rashin taron mu da batayi ba don dama da shirin mu muka zo da abinci mu da komai har abin sha mun tanada a bangarena. Sai dai naji dadin don ashe su Fauziya na gidan hajiyan su ana cewa mun iso sai suka dira a gidan namu har lokacin anty Fati bata fito ba mune kaidai ke ta bidirin mu a ciki. Baifi awa biyu ba Nafisa da tawaganta suka iso suma sunyi daidai mun gama abincin da nasa a girka aka diba aka kai masu. Nan gidan ya kici may da hayaniya na riga na fada ma Laraba ta saka ido akan yarana kafin yan uwa na da zasu zo su kara kulamin da diya na don haka ne na hutar da ita ko wani aiki sai kula da yaran kawai. Munyi sallah na shirya su zasu shiga cikin gida da laraba su gaisa da su momy da Abba inda zasu rika kai dare a can badon komai nayi haka ba don sherin kishiyoyina nayi wanan gudu nai wanan dabaran. Kamar zuwa na su Fauziya ke jira inda muka fara tsara abinda zamuyi kan bukin sai can ga Fati ta shigo wai ita daga barci ta tashi. Fauziya ce tace ai da ki bari sai gobe kwa gaisa wanan halin dai naki baiyi ba wallahi ace mutum kullun alamarin sa sai kara lalacewa yake. Ni dai gaisuwa mutumci mukayi da ita sai da zata fita ne take tambayan yaran nace sun fita kawai. Daga haka ta fice a dakin kodai ba komai na dan rage jin zafin ta da nake ji a raina din tunda ta tambayi yara ai. Amma duk da haka batayi wani dadani ba zainab ce ba kunya ta kawar min da tunane na tana tambayana kan kayan da aka saya mata waya na dauko na fara nuna mata inda sauran duk suka rufu muna kallon kayan ina masu bayini. Binta tace har biyu nace daya a Abuja za a aje mata gidan ta nacan sai dayan azo nan dashi kai amma yayan mu ya fidda zainab inji binta. Anty Faiza tace har da ita mai bayanin ai badon khadijan ba kina tunanen akwai wanda zai takwasa shi kan haka tunda yaba Abba kudin yin komai. Ko yanzu Allah kadai yasan irin kai ruwa ranan da sukayi dashi kafin hakan nace wallahi ko anty kamar kin sani harda su kukana sai da nasha da gaba. Tace ai na san halin mazan nan yanzu sosai don haka muke fama muma dasu ai gara ke ma mun samu yana sauraren shawaran ki ni nawa idan nai mashi zancen sai mun kwashe kwanaki ba shiri tsakanin mu ga ganin laifina da suke duk abinda suka ganin dashi sai suce dan uwan su ne ya saya min shi. Ban san lokacin da nace dangin miji ai sai a slow ba sai dai idan ka iya zama dasu ne akwai dadi wallahi matsala kaidai kada abinka ya rufe maka ido. Binta tace watau mu ke nan ko duk aka kwashe da dariya a dakin nace kuka ai yan uwa nane ba dagin miji ba yanzu. Faiza tace lalai kam don khadija haihuwan tane kawai hajiya mu batayi ba yadda take son ki ma yanzu dukkan mu babu mai fadan nan a gurin ta. Fauziya tace halin mutum ne ke ja masa so ai don bata so kanta da gidan su ta bar yan uwanta ba nace ni yanzu sai dai idan yaiwa gidan mu alheri su bugo suna fada min amma ban taba bude baki nace kaiwa wani nawa alheri ba duk ko da talaucin gidan namu na rike masu mutuncin su a gurin shi. Muna ciki motar kaya ta iso gidan nan muka fita zuwa ganin yadda za a sauke kayan sai dai sun bada shawaran a wuce da kayan can gidan Yusuf wanda shima dai a cikin unguwar namu yake. Sai sauran kayana dake sama suka sauke a gidan na shiga karban key a hannun anty fati na dakin da babu komai ta gama ja min rai ta bani key din dakin akusa da dakin da su laraba suke ciki. Fita mukayi zuwa gidan Yusuf din dake dan bayan mu kadan aka sauke kayan a gaban mu suna Allah Allah suga kyau kayan. Sai da na shigo ne zan shiga daki najiyo muryan su na leka dakin ina masu sannu da zuwa ihisan dake dakin tana ganina ta nufo ni sai uwar ta daka mata tsawa . Kai kina wani shirmay wallahi ina tare muka zo da ita da zan cuta mata da tuni na gama cuta mata ai ba yanzu da alheri ya kawo mu nan ba. Tace waya sani ko kin cuta mata din don wanan kokarin rabani da diyana da kikeyi haka nace abinda kakeyi shi kake zargin kowa nayi kin gani nan ni ga Allah mahalicina na dogara ba ga wani mutum can ba da shima yake nema a gurin Allah. Ina fadin haka na juya na bar dakin tare da tunanen yaushe ne wanan matar zata sauya ne tayi saduda tasan Allah dayane a zuciyar ta. Allah gani gare ka don ina cikin tsaka mai wuya ga Fati babu alaman hadin kai a gurin ta yadda take faman sharewa da basarwa a fuskan ta. Sai bayan sallah isha,i ne su laraba suka dawo bisa jagorancin momy data rako su gidan sai wani jiji dasu ake a cikin dagi wanda hakan ba karamin dadi yake min ba a raina tunda kowa na son jini na a gidan. Har umma daba kula kowa take ba momy tace a wurinta sukai magariba zata kwace mata mijin ta don haka take cewa Al,amin. Washegari bayan mun huta ne naba Laraba tsaraban su ta shiga masu dashi gidan inda babba da yaro kowa ya samu tsaraba na a gidan. Sai gasu suna layi wurin zuwa yi min godiya tare da sannu da zuwa wanda hakan ba karamin bakanta ran abokan zama na yayi ba sosai. A raina nace indai kana son a soka ashe gaskiyan Anty hauwa da tace min idan ina son in rabu da kowa lafiya kada in matse hannu na gurin alheri musan man dagin mijina da abokan arzikin su. Sako har na mutanen zaria dangin hajiya mama sun samu na bada akai mata sai albarka take saka min kan hakan. Niko da a zatona ban dauka haka abin yake ba don ban so nuna masu haka ba wai don gada su gane ina samu a gurin shi sai take ce min ai matar dake cikin daula ansan tana samu ko yaya ne don haka nuna masu a daula kike don rashin bayarwan shi kan shi matsala ne yin hakan sai yanzu na gane wanda ya riga kwana yana rigaka tashi. Ban samu shiga gaida sarakaina ba sai washe gari na samu shiga gidan muka gaisa dakin hajiya mama na yadda zango. Bayan mun gaisa take fadin haba khadija kin dauke kafa gare mu haka har ina murna kin dawo da hankalin mijin ki gida sai gashi ke kuma kina kokarin gudun mu yanzu. Ina kaduna ina Abuja bafa wani nisa ne a tsakanin mu ba kwarai amma kuke wanan dadewan baku zo gida ba ko yan jikokin nan namu yanzu don su saba damu ai kyazo dasu su san yan uwa ko ? Hakkuri na bata ban kawo korafin komai ba don taimin uzuri sai hakkurin da na bata akan zamu gyara insha Allahu. Zancen bukin ta dauko min inda take fadin yara sun zo suna fada min kokarin da kukayi ke da mijin ki sosai an gode Allah yasa albarka ya kara daukaka da nisan kwana a kunyace na amsa da amin mama. Nace sai zancen gara shine ma ya saka muka zo da wuri don a gudanar da komai yadda ya kamata akan lokaci yace a lissafa abinda ake so gaba daya idan yaso sai ya turo da kudi kafin yazo a saya don shi sai karshen sati yace zai shigo. Madalla duk da nasan Alhaji ne mai wanan nauyin amma hakan yana da kyau don yanzu lokaci yayi da zasu dauke mai wanan nauyi zan fadawa Alhajin sai ai shawaran abinda za a kai masu. Nan dai su anty Faiza suka samay ni gurin hajiyan mukaci gaba da shirin da zamuyi dasu haka dai zuwan ya zama min busy bamu da hutu na kan mu sai dare. Duk yadda nasu in zulle masu indan huta hakan bai samu ba a gare ni don a cikin kwanakin ne akaje yiwa zainab gyaran dakin ta sai dai ina kokarin leka ya Amina na duk wanan ritsin. Abin gidan yawa sai abin ya koma gulma kuma wai dani kadai suke shawara sun bake sauran yan uwana basuyi dasu. Yau ya kasance ranan kamun zainab yan uwa da abokan arziki sun hallara a gidan gida ya cike da yan uwa zainab tana gidan mu ana shirya ta don mai makeup tazo. Wasu yan mata da matasa a gidan namu suke zaune duk wace akacewa zainab tana gidan mu nan suke shigowa. Sai abin sha dana dan tauna baki muke rabawa wanda Yusuf ne ya sawo ya kawo muna a raba ma baki don Binta ta kirashi take fada mai komai. Wanda ya rage na sa a dayan dakin muka rufe muka fito zuwa gurin kamun wanda kafin in isa har mun iske an fara program din ko. A daidai wanan lokacin ne AA ya shigo kaduna ranan yammacin alhamis sai dai yayi mamaki ganin dandazon mata a kofar gidan iyayyen sai gashi ya iso gida ya samu Fati a gida. Ya haura sama nan ma su Nafisa da yan uwanta suna gida zaune a binsu sai shan bakin tea suke saboda sanyin da akeyi a kadunan lokacin. Ihisan da ta fara hangoshi tayo wurin shi da murna tana taron shi fuska ba saki ya rikewa yarinyar hannu yana fadin . Ihisan ya baki je gurin kamun gwagon ki ba ke tace Abba Amin mu tace kada in bi momy ne ya dago kai ya kalle ta daga inda take kwance baiyi magana ba ya wuce dakin shi ya dan jima a ciki ya fito daga kofa ya tsaya ya kwalawa yarinyar kira ta fito. Ya rike mata hannu suka fita tare zuwa gidan duk yawan matan dake gidan haka ya kusa yana rike da hannun Ihisan zuwa dakin mahaifiyar shi. Ya samay ta zaune da wasu dattijan mata a dakin yan uwanta da abokan arzikin ta bayan sun gaisa ne hajiyan tace da yarinyar ashe suma sunzo akace yake fadin basu shigo gaida ku ba ke nan tunda suka zo? Tace mun dai ga khadija da yaran ta don su ko yaushe a nan suke tare damu koda uwar bata gidan har sun saba da mutane hajiya ina Deedar take ya tambaya. Yanzu kan ai tana cikin wanan taron don sune keda bukin ai wanan yarinyar na kawo mata na samu uwar ta ta hanata fitowa wai. Hannu hajiya ta mikawa yarinyar duk da tana da wayau sai taki zuwa tana shigewa jikin uban tace ina zata zo tunda bata san mu ba. Tsawa ya daka mata cikin harshen turanci yace taje gurin grandma don tsoron shi ta taka a sanyaye zuwa gurin ta. Ai daka barta tunda ba sanina tayi ba daya daga cikin matan dakin ke fadi akan may zai barta ai gara a nuna masu ku su sanku ko. Wani irin ba dadi AA yaji a ranshi sai yanzu yake dana sanin auren bare wanda babu wani alfanu a cikin sa sai jin dadin rayuwa karshen abin ba kyau yake yi ba ga mutum. Wai ace yayan shi basu san mahaifiyan shi ba haka kamar an jefo momy dakin tare da su yan biyu dake gurin ta don zata fita ta shigo da yaran gurin hajiya su zauna. Suna ganin uban zube a kasan carpet din dakin mahaifiyar shi sukayo kan shi da murnan ganin shi aka dauki dariya a dakin. Ihisan ta baro wurin hajiyan zuwa wurin da suke tana kiran sunan su tare da dariya suma dayake sun saba da juna sai gasu suna wasa a jikin uban da junan su. Yanzu kan kin san yan uwan ki ai gashi kije gurin su ba tayi anan ya barsu ya fice daga gidan ranshi yana mashi ba dadi. Ya rasa dalilin matan nashi na kin shiga sha,anin bukin shi sai da zai fita ne yaga shigowan Fati gidan ita da wasu yan uwan ta ya dauke kai kamar bai gansu ba. Mota ya shiga ya nufi inda su Yusuf ke jiran shi sai dai kafin yaje yayi tunane kala kala tare da hango abinda bai taba yin tunane a kansa ba sai yanzu. Ya rasa gane may yasa Nafisa bata son zancen yan uwan shi bata mu,amula da kowa daga cikin su duk da kokarin da yake na ganin ya kokarta ma yan uwanta a koda yaushe. Amma haka baisa ta dauki nashi da mutunci ba kokari ma take ko yaushe ta nisanta shi da yan uwan shi sai lokacin yake tuna wasu abubuwan da suka faru a baya kai ya girgiza yana furta kalman innalillahi har yakai wurin da zai tafi din. Ya samu su Yusuf din na shirin zuwa wurin kamun ba yadda zaiyi duk da zainab kanwar shi ce yasani amma zuwa wurin ya zama mai dole don kokarin Yusuf a gare shi. Wuri ya dauka ga angwane sun iso ban san da zuwan shi ba don na dauka sai washe gari zai shigo sai dai kawai na hango shi yana ma Yusuf da zainab liki a tsakiyan fili. Daga inda muke tsaye ina rike da mami sai Alamin dake hannun laraba ihisan tana tsaye rike da hannu na daya, muna hango shi na kare mai kallo har na shagala ban san ya karaso inda muke tsaye ba sai ganin shi nayi yana muna liki kallo ya dawo gare mu mata nata kokawan kwasan yan dubu dubun da yake manna muna. Abokan nasu har Yusuf suka dawo kaina da yaran suna manna muna kudi ina kare kaina don kunya ya jawo mu ya rugumay wuri ya kara rudewa. Ya fice yana muna dariyan keta don ya gama bani kunya a bainan jamma,a ya wuce nan kannen sa da aboka wasa suka shiga min sheri a gurin. Sai bayan magariba muka dawo gidan ina daki ina cire kaya Alamin yana kukan da ban san may ke damun shi ba don haka yake kwana bibiyu da ciwo shi macen tafishi dama. Ya shigo dakin shima da ganin shi a gajiye yake lokacin yake yaron dake kuka ya kama sai ga laraba ta shigo da madaran da ta hado ma yaron daki. Yana tambaya may ke damun shi nace nasan sanyin garin nan ne ya kama shi tunda acan ba fita suke haka ba ko yaushe. Yace ki bashi nono ba wanan abin ba yaya zaki gane halin da yake ciki baki mamay shi ba a jikin ki ban ki ta nasa ba na dauki yaron ina kokarin zama dagani sai zanin da daura gaba a jikina. Yana tsaye yana kallon yadda yaron ya kama nonon ya sauke ajiyan zuciya ya juya ya fita daga dakin . Bakai dakin shi ba Nafisa dake dagon shigowan shi ta tsare shi a hanya tace dama kai nake jira ka shigo inji idan kai ka ce kada a fitar da komai abawa kowa nasa don ban san dalilin matar ka na kule kayan da aka zo dashi ba a daki tana amfani dashi ita kadai don samun wuri. Wasu kaya ya tambaya da mamaki karara a fuskan shi tace kayan da ka saya aka zo dashi mana ko wani sallon wulakanci ne ka dauko kuma haka yasa kace sai munzo . Ke ban san zancen kayan da kikeyi ba don haka ban son wanan haukan naki idan cin mutuncin ki ya taso ne in sani. Idan ma na sawo kayan tayi amfani dashi ke bukin ne ya kawo ki nan ko may ina gida kike baki je gurin abinda ya kawo ki din ba. Yana fadin haka ya wuce tana fadi cikin daga murya may zanje yi gurin mutanen da basu sona sai dai suga bayana shine fatan su. A cikin daren nan taje gurin Abban su AA da korafi wai ya hanasu komai sai ni kadai ce nake gudanar da komai a gidan kan bukin. Abba yace ta koma zai nemi AA din yaji kan maganan idan haka ne kuma bai kyauta ba ya dai bata hakkuri ta wuce zuwa gida. Washe gari da safe Abban su AA ya tako zuwa gidan mu ya samu su laraba yace a sallama mashi dan nashi sai da AA yayi mamakin jin ga Abba a gidan nashi yau yazo da kan sa. Yana kiran wayan shi don su laraba sun fada mai cewa basu tashi ba a lokacin yasa shi kiran wayan shi. Ya sauko da sauri zuwa kasa ya samu mahaifin nasa a kasa ya zauna don girmama mahaifin nashi da yakeyi yace ya tashi ya zauna magana zasuyi dashi. Bayan ya zauna ne mahaifin nasa ya fara mai da nasiha da wa,azi akan zama da mace fiye da daya sai daga baya yake cewa dashi jiya matar ka ta samay mu da korafin kana tauye masu hakkin su. Ya dago kai da mamaki yana kallon mahaifin nasa yace kamar ya Abba yace eh kasan maza wasun mu haka suke wani lokaci hankalin su sai ya raja,a agurin mace daya ya manta da hakkin sauran matan nasa. Don haka ina ga ka saba bata ta halartar da komai yanzun kuma ka janye daga hakan kaga ko dole ka samu wanan korafin. Nan dai ya kora ma dan abinda tazo mai dashi ya rantse ma uban baisan da zancen komai ba akai Abban yasa laraba ta kiramu dukkan mu a falon. Nice kusan ta karshen fitowa koda na karaso suna jirana na iso da sallama dauke a bakina na samu wuri gefen kujeran da anty Fati ke zaune na zauna ina gaida Abba da kwana da gajiyan jamma,a. Kai Abban ya kada ya amsa min ya danyi gyaran murya tare da kallon inda nafisa take zaune yace jiya kin je kin samay ni da korafi akan mijin ku tace hakane Abba. Don ko gaba daya wanan ta kulle dakin da kayan ke ciki yadda kowan mu nan baizayi amfani da abinda aka sayo ba don bukin. Dago kai nayi ina kallon ta da mamaki sai na duka don Abban bai gama magana ba a lokacin. Ya juya gurin dan yace kai kaji maganan ta yaya akayi ka halarta wa mutum daya yace Abba ban san da wanan maganan ba ni. Ya juyo gare ni yace gwagona yaya akayi muna son bayani na hade miyau dakyat don takaici nace Abba ba shi ya saya min komai dana zo dashi ba. Sai dai kudin da ya bamu ne nayi amfani dashi don nasan yawancin jama, a anan gurin mu zasu sauka nayi wanan dabaran shima baisan da zancen komai ba. Ya dago kai yace kinji abinda suka fada ya baku kudin ko bai baku ba kuma tace ya bani da zamu zo Abba yace masha Allah. Abinda nake son ji gareki ke nan dama AA tace ita kuma Fati gata nan shekaran jiya na turo mata nata nayi mata bayanin komai. Amma Abba sai nazo gidan nan na samu matan nan ba wanda ya tafi gurin kamun zainab jiya din ni banyi fushi kan haka ba sai ita mai son banza zatayi wani korafi can. Abba yace a nan dai na fahinci gwago na tafiku da bara da sanin ya kamata tunda mutumin nan ya baku ne don ku fitar dashi da kan ku kunya. Shiru kowa yayi a falon yace da har nazo da zuman ci ma mijin ku mutumci akan may zai dauki girma da nauyi ya ba karama a cikin ku ashe ita ta sayawa kanta mutuncin komai. Ba wurin shi ba har gurin mu mu iyayyen shi irin matan da Allah yace ka aura ke nan macen da zata iya rufa ma asiri. Wanan maganan da Abba yayi yasa Nafisa taji haushin shi sosai watau abinduniya ya rufe masu ido ke nan. Ta ce Abba ai na dauka don bukatan kan mu ya bamu wanan bukin shi ta shafa don may daga baya za a ce muyi hidima dashi kuma. Ke rufawa mutane baki a gurin nan kada in kara jin muryan ki a nan don ke fitsararace dama yana fadin haka ta ce Abba na gode ta bar gurin. Abba wanan ta isheni a gidan nan wallahi don ku nake zaune da ita har wanan lokacin haka ka ganta ka auro ta yanzun ne kake gano illar auren irin su. Baka da wani kwakwaran dalilin cewa ka gaji da ita a yanzu halin ta ne kai zaka gyara abinka sannu a hankali ta koma kamar kowa. Ita dai wanan khadija ta nuna muna ita yar tarbiyace ko daga yanayin kamalan ta da mu,amula da mutane mutum zai gano haka gare ta ya dan muna nasiha yayi muna sallama ya tafi suka fita tare da AA. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 1/25/21, 9:22 AM - Fatima Amarya: Ranan duk yadda naso inyi walwala raina ya baci na kasa tsayawa in yi komai ga anty fauziya sai aiko min in fito mu tafi gidan zainab. Kiran da maryam tayi min ne tana sheda min tasowan su ita da wasu abokaina yasani fara tunane. Dama don haka ne na garje nayi wanan don Anty hauwa muna firan bukin a gabanbta tace to kinga shawara zan baki yanzu. Duk yadda zakiyi ki kokarin a wurin nan ki zage ki fishi nuna damuwa da sha,anin bukin fa blood sister din shi ne za a yi. Ke kuma sai ki hikimar da zaki kara haska kanki ga kowa a gidan dama zuciyar mijin ki muna hada baki gurin tambayan ta may zanyi ? Tace bude aljihun ki ki basu mamaki ki shanmaci kowa a gurin kiyi gifts ki bada karfin ki koda ba a son hakan gare ki. Nace nasai robobi da zan raba a nawa bangaren taja tsuki tare da fadin mijin ki mai hali ne fa khadija kudin nan badaga aljihun ki zai fito ba don may ba zakiyi abinda sai sunji mamakin ba ki nuna kin fishi son yan uwanshi. Idan kika kama zuciyar uwar miji dana yan uwan miji don dole miji yai maka ragowa kema kuma naki yan uwan da iyayye su kara haske a gare shi. Wanan daman mata da yawa suke sakaci dashi gurin mallake miji a tsaya ga asiri ba wani hikima a ciki ni kon gani nan tambayi maryam kiji idan sha,ani ya taso a gidan su man yadda yake zama nawa. Robolan banza abu zakuyi wanda ya banbanta dana kowa da zai ba mutane mamaki har shi kanshi mijin naki ai ba don komai zaki haka ba sai don daga darajan ki dana diyan ki da yan uwan ki gare su ko ba a wa Allah dole a yi dake. Itace ta ban shara duk wani abinda zanyi tace ga haushin da kishiyoyin ki zasu ji kan hakan sai a koma gulman kin malake miji shiko yasan ba haka bane. Ina cikin wanan tunanen ne ya shigo dakin nawa daga ni sai yara na a dakin sai sadiya dake gwalanniyan ta daga kwance. Har ya karaso inda muke kwance ya dan ja kafana tare da fadin yau ba buki ne na ganki a kwance har wanan lokacin. Ganin yana kokarin zama yasa na dan matsa mashi kadan ya zauna yace ko dan maganan wanan mara hankalin ne yasa jikin ki yai sanyi ? Kokarin mikewa zaune nayi nace maganan ta bai sani jin komai ba sai ma dadin da naji don haka ya bata daman gyarawa itama. Yace idan suna da niya ko ke baki san wa yan nan matan bane sune matan da ake kira da masu hana miji mu,amula da yan uwan shi. Barin fayace maki abinda kila baki fahinta ba dasu don ni yanzu na gama gane halin kowan ku ita dai Fati da kike ganin ta. Mace ce shasha wace ko kanta bata iya hasala ma komai ki duba fa yanzu buki ake ji yadda take zama a gidan nan ita dai butin ta a bata kudi ta kimshe su. Ko tabi wani hanya dasu na daban wanda ba wanda yasan abinda takeyi dasu sai ita don ba a gani a jikin ta ba ba a kuma gani ga wani nata ba. Sai bakin hali da bakin ciki ga zurfin ciki ko kaine wa baka gane cikin ta don ma bata yarda da kowa ba ita kowa macuci ne gare ta. Ita ko nafisa ba a maganan ta don ke kanki kin fahinci wasu hali nata burin ta shine ta mallake kowa ya koma karkashin ta harni sai yadda tayi dani ta juyani yadda ranta ke so ita zaki iya kiranta da yar tallaka da gadara. Da farko kan ta samu yadda take so dani amma shigowan ki a rayuwan mu ya maida ita baya sosai don ta kasa juya ki yadda ta samu daman juya Fati. Don ke baki dauki wajan ba a gareta da kin yarda ta juyaki da an zauna lafiya ko ki bar gidan nan don bata yarda taga ina mu,amula da wata mace. Nace tunda don ita kadai aka halice ka ko yace rayuwan ta ke nan sai dai ta juyani da duk wani wanda ke karkashina yadda take so. Ban san lokacin da nace nifa murmushi yayi ya juyo ya lakuci hanci na tare da fadin gaki nan dai har yanzu na kasa kai karshe ga alamarin ki sai dai nasan komai da zuciya daya kikeyi wa mutum ke. Aiko na samu sheda mai kyau yace tukunna dai ai ba, a gama shedan mutum cikin yan shekaru sai nan gaba idan na karo maki kishiya in gama gane halinki. Wasa yuka a gaban doki baya tayar da hankalin doki ai yace eyyeh haka kika ce nace kwarai kuwa. Su wayan nan dake gidan ka muke zama tare ai kidhiyoyinane haka kuma wace zata zo bayana ita ma kishiya ta ce mai zai sa daga baya in tsiro da halin da ba nawa ba sai dai itama idan tazo min da akidar rashin gaskiya. Ko yanzu kai niya sai ka kara ni ba matsalana bane kaine mai aiki kaida ka dauko abinka wace ta shigo ta samu mata biyu a gaban ta haka wata kishiya kuma zata razana ni yanzu. Lalai shiyasa nace ban gama tantace halin ki ba sai na kusa kammalawa sai ki tsiro da wani halin da ban sanki dashi ba. Yanzu dai nazo in ji nawa kika kashe a cikin wanan hidimar in baki kudin ki kamar yadda kowa zai amfana da nasa. Badon ka biya nayi ba nayi ne saboda Allah dakai da diyana da kuma mama da zainab din ko ka manta zainab kawatace nima kamar yadda Yusuf yake aminka . To tunda kin ce haka zan kara maki gudun mawa na wuri hidimar bukin hakan yai maki ko nace yanzu kayi magana ya mike yana sa hannu a aljihun jallabiyan dake jikin shi ya fito da rafan yan dubu dubu guda biyu ya dora min saman jikina sai da na zaro ido. Zanyi magana ya dora yatsa a bakin shi yace min shiiii alaman in kyale duk da haka sai da nayi mai godiya ko abindana kashe din bai kai nan ba ai. Riba biyu ke nan na samu a gare shi a lokaci daya na anyana a raina yakai kofa yace yau kece da girki kin sani kada ki shagala da buki ki manta dani. Kafin in magana ya fice a dakin ya barni da tunane koda zanyi girki garin nan ai bani ya kamata in karbi girki ba yau da na gaji da tunane na mike na bar gurin na fada bandakin don yin wanka. Bayan na fito na shirya ban dauki lokaci ba na fito na samu laraba ma sun shirya sai dai Alamin wai yana gudawa. Dakin Anty Fati na shiga na gaida ita nake fada mata zan shiga cikin gida tace yanzu nace eh tace sai ta shigo na fice. A coridor din sama muka hade da Nafisa ta watso min uwar harara ban damu ba nayi mata ina kwana kamar ba zata tanka ba sai dai ta amsa min cikiciki na wuce. Altine kwana biyu tana gidan su, sai na samu sun shigo da yan uwanta muka gaisa sukai min ya gajiyan buki. Tare dasu muka bar gidan bayan mun rufe duk dakunan da nake da makullin su ka shiga cikin gida inda muka gaisa nake fada ma momy zancen Alamin din da baida lafiya . Anan gurin momy na barsu muka wuce zuwa gidan zainab da za a kaita don karasa yan gyare gyare sai lokacin ne mutane ke ganin wanan kayan da AA ya saya mata wanda ba kowa ne ya sani ba. Don ranan farko sunki zuwa gyaran dakin yau ko harda su anty Amarya muka zo gidan da wasu yan uwa da yawa. Kafin mu koma fida har zance ya kai kunnen Abba murmushi yayi yace shine samun ai kasamu dan uwanka ya san ka samu. Umma taso jan zance da tsawo sai Abba din ya katse maganan yana fadin abinda zamuyi farin ciki yaya kuke kokarin maidashi abin tsegumi ne wai. Ina da kune masu korafin yaron nan bai komai ga kowa yanzu kuma an samu hankalin shi ya dawo gida za a kuma ce bai kyauta ba. Umma tace Alhaji nina ga ba haka aka saba ba ai a gidan nan hannu ya daga mata tare da Anbatan sunan ta. Yace ina son ki gane mutum bai lokacin shi yace kuma sai yayi na wasu ku godewa Allah da yanzu nake da mai taimaka min tace amma Alhaji kasan dai an munafunce mu ko. Yace a cikin zancen nan waya munafunce ki rakiya sai tayi shiru kada ta zake da yawa a gane manufanta hakan yasa ta kulle hajiya mama a ranta. Suka shiga yar tsama da juna da akazo kai gara aka kirata tace ai an tsamay su a ciki don yin abu ake ba a shawara dasu cikin wanan rikicin muka dawo gida muka samay su a hakan. Bayan mun gama saurare ne ni dai naja kafana zuwa dakin momy inda na samu ya Amina dasu momy na cire gyale na na shiga sallah. Har na fito suna magana guda a raina nace manya ke nan suma da tasu kalar kishin ko ina dai abin ba dama ashe yanzun kuma may ye a cikin wanan ? Dakin hajiya mama na nufa bayan na gama ba yara nono na samay ta da yan uwanta na zaria sun shigo ina shiga muka fara gaisawa. Hajiya mama take tambayana ko naci abunci nace yanzu dai zanci mama na shige ciki gurin da yayan ta duka suke dakin banda zainab da Binta tace suna gidan mu tare da kawayen su. Ban dade da zama ba suma dai anan din zance gudane kan bakin cikin da ikon hajiya mama suke ta nanata maganan tambayan su nayi yanzu don bata saka baki ba ba za a kai kayan yau ba ke nan ? Faiza tace min don may ba za a kai ba ga yan uwan Abba can dana hajiyan mu su zamu fitar sukai a raina nace ashe maryam nada aikin sarakuta da wanan matar da kowa ke fadin halin ta. Hajiya mama mace ce mai kawaici da girmamawa tasan abinda umma ke nufi amma haka ta shanye maganan a ranta ta hana ma ayi maganan sai murmushi take sakewa a fuskan ta. Duk yadda hajiya Umma taso taga auren zainab kasa dana diyan ta hakan bai samu ba gare ta don Allah yayi zainab zataci daga arzikin dan uwanta da ake tsegumin bai masu komai a baya sai gashi ya garje ya fitar da yar uwanshi da uwar shi kunya don har da motar shiga mai tsada ya danka mata . Ban samu dawowa gida ba sai goma na dare na dawo na samu ya cika fam dani kan rashin dawowa in karbi girki kuma ya hana nafisa yin girki sai anty Fati ce tayi girki a ranan. Isowan bakina ne ya kara sani zama busy a gidan tare dasu muka dawo gida inda na sauke su a dakina su hudu ne suka zo tun zuwan su nasa laraba ta dawo gida don shirya muna abinci da gurin kwana. Ga zainab gidan tare da kawayen mu ban samu ganin shi ba sai washegari da safe ina kitchen ina hada ma bakin mu abin karyawa ya shigo kitchen din. A tsorace na juyo don jin mutum gab dani ina juyawa na ganshi nayi mai ina kwana sai ya basar dani kamar bai jini ba yace kin kyauta watau ke van isa yanzu ince ga abinda zakiyi kiyi min ba ko ? Nace kamar ban gane may yake nufi ba may kuma nayi ma yaya AA au ke baki san abinda kikai min ba ke nan ko ? Wallahi ban sani ba na bashi amsa may nace dake jiya akan girki sai na dan sake murmushi a fuskana nace a, a ba hakana bane yaya gani nayi ai bani ya dace in karba jiyan Nafisa ce zata karba sai ni ko ? Ke zaki gwada min yadda zanyi dani da gidana matan ki ko nawa ni na aje kowa a cikin ku sau nawa zan fada maki ki bar zancen nafisa a yanzu ko so kike ki bata min rai. Kayi hakkuri ban san haka zancen yake ba in Allah ya yarda yau zan ma girki idan kin ga dama kada kiyi wanan ba matsalata bace ai. Murmushi mai kama da takaici na sauke a fuskana laraba ta shigo dauke da flask a hannun ta shiyasa har ya bar kitchen din ba wanda yai magana a cikin mu. Bakina sunci sun sha da yan matan zainab da suka kwana a gidan mu duk nayi ta fama da dawainiya da su har sha biyun rana muka gama shiryawa zuwa cikin gida. Kallon da hajiya umma tayi muna ne yasa duk muka tsargu da ita muka bar part din ta zuwa sauran part din gidan a dakin momy na aje bakina don dakin hajiya mama cike yake da mutane. Karfe biyun rana da rabi shine lokacin daurin aure tun cikin dare na saka zainab shan abubuwa har zuwa wanan lokacin ina bata a fakaice tana sha. Adakin momy gaba dayan mu muke har su Faiza da tawagan su anan anty Fati ta shigo ta samay mu gidan sukayi kanta da korafi. Sai buda baki tace ai ga amaryan ku nan tana maku yadda kuke so ko don haka ba sai mun shigo da wuri ba mu. Ina jin su ban son abin rashin mutunci ya shiga tsakanin mu ko kadan sai nayi shiru ina dan dariya. Taci gaba da fadin kin san ku ko wace amarya tazo maku daa kalan rawan ta wanan da alama ta shigo da kafan dama don baga yayan ku kawai abin ya tsaya ba har ku ta gama kwashe kafan ku. Fauziya tace mu khadija kin san ta wuce matar dan uwa a gurin mu don tun kan ta shigo take yar gidan nan ita ma don haka bata yada mu muma bazamu yadda ita ba. Faiza ta dora da fadin khadija bata son kanta bane a cikin mu don tayi kokarin abinda ku kuka kasa yi tun farko akan gidan dan uwan mu don aljihun ku kawai kuka sani. Nan dai abin yaso ya zama masu fada a tsakanin su sai da momy da yan uwanta suka shiga tsakanin su don ta fara fada masu bakaken magana wanda duk a fakaice dani take yin zancen suna mayar mata da amsa. Nafisa bata shigo ba sai karfe uku na rana da wani abu ta shigo gidan da yan uwan ta ba wanda ya kalle ta yadda take shigo masu da izza abaya sai gashi wanan karon ta shigo gidan bata samu kulawan kowa ba agidan duk kuwa da adon da tasha na fitar buki irin nasu na kasan su. Bata dade da shigowa ba don ko haduwa bamuyi ba muka koma gidan don shiryawa na samu laraba ta gama girki data koma ta hada miya na karasa hadawa kafin mu shirya ina san ran ya karasa. Dama tun safe kafin in fita na hada komai yadda nake son yi hankalina ya kasu biyu ga girki n miji ga sha,anin buki. Laraba ta kyauta min don abinci tayi wadatattace da zai ishi kowa har a raga a gidan sai gashi ya kirani a kuraren lokaci akwai baki da zasuci abinci a gidan na dare. Shigowan mu daidai ana wankin amarya muka shigo filin shigar mu kawai ya dauke hankalin kowa a gurin don shiga ce ta alfarma. Alkasim na gefe a mota dake jibge da kayan da zan raba a gurin Altine da fauziya ce zasu raba don su suka san mutanen su. Da ganin an fara rabo hankalin mutane ya koma can har ana batun rufe su dakyat na kusa nasa Alkasim rufe kofan motar gabadaya. Nace ya koma gida kawai ta bar gurin duk wanda ya karbi jakka ko roban sai ya karanta hoton yan biyu ne da sadiya suna dariya aka dauka. Tun maryan da sauran kawayena na nema muka wuce gida ban koma cikin gidan ba sai da muka shiga ne a cikin dare na tura laraba da duk wani gifts din bukin takaiwa matan gidan su AA wanda na ware masu. Bayan isha,i ne bakin shi suka shigo gidan ga shirin zuwa diner da zamu banda halin zuwa don AA na gidan da bakin shi. Bakina dasu laraba ne suka wuce a mota na don ban sa ran zuwa guri ba sai gashi yana fada muna mu shirya don tare dashi zamu tafi dukkan mu. Shiri sosai kowan mu yayi dama akwai kayan da anty hauwa ta sayo min a dubai suna saka sai sai gashi shigan mu yazo kusan daya dashi farin yadin mazane a jikin shi mai tsada. Anty fati ta fara fitowa sai nafisa na dan bata lokaci don tsayawa gyara sadiya data bata jikin ta da yake yarana suna da kafan su shiya rike su a hannun shi biyu zuwa wuri mota. Ni kuma na dauko sadiya a kafada na kowa satan kallon shigan dan uwa yakeyi munzo shiga mota a raina nace zanga yadda za ayi yau. Sai naji yace Fati ke ki shigo gaba su zauna a baya su kamar nafisa ba zata shiga ba sai dai taja ta shiga ya tayar da motar fati sai sauke ajiyan zuciya take yi. Yaran suna gaba a wurin su zan iya cewa wannan ne karon farko data dauki yarana a jikin ta kota kulasu. Mun shiga wurin wuri ya cika da mutane yana neman gurin da zamu zauna ne naji muryan Altine na fadin kawo sadiya in kama maki dama sai da nayi tunanen barin ki da mukayi da ita ai. Ni naga karfin hali a gurin Nafisa ko kallo yar bata isheta ba wai ita ala dole ta barmin yarinyar don nawa ne dama. Mc da yake abokin su ne ya shiga baradawa ga AA abokin ango yayan amarya da iyalin shi sun iso kallo ya dawo gare mu. Daga can gefe gulma ya tashi yana gaba tare da nafisa ya dawo muka jera daniyar daukan mami sai yace in dauki Alamin muka jera tare da anty Fati da muke tafe tare muka sakashi a tsakiya sai da ta juyo ne ta gamun a hakan tafe ba yadda zatayi haka muka kai mazaunin mu. Nan ma yana kusa dani sai dai mun sashi a tsakiya dani da nafisa din Fati tana daga gefe na don ban dauka wani magana yana hadata da buzuwa ba. Dan rankwafowa yayi yana fadin yau kinga yayan ki baki yaki rufuwa Altine ne ta karaso tana rada min wai su maryam basu samu wurin zama ba. Tambayana yake yasa ya dan duko min ina fada mai abinda ta fada min sai jin hasken wutan camera mukayi a kan mu ana dauka mu hotuna. Wani ya yafito yazo ya danyi mai magana bada jimawa ba sai ga wani sit ana gadawa a gurin. Aka nemo su cikin loundspeaker ana neman su suzo ga gurin zaman su kusa damu suka zauna maryam don gulma ta zauna a setin mu. Duk wanan abinda ake sai sakon harara yake samu daga wurin nafisa itama fatin ba wani walwala a tare da ita turanci da nuna wayewa ke tashi a gurin. Duk wanda yazo dani zamu gaisa sai fati dakan dan saka baki gefe zakaga mutum na fadin ya muke ya iyalin mu sai in buge da bada amsa. Dinner yayi kyau sosai sai dai bai bari an tashi ba yasa mu bar gurin don yara saboda sanyi tayi yawa a gurin don haka muka bar gurin a cikin lokaci. Baya munyi hotuna da amarya da ango muka bar gurin zuwa gida saboda laraba da muka baro gurin bukin don haka ko da muka dawo ban huta ba don shirin yaran da nakeyi na kwashe su zuwa dakin shi. Sai gasu maryam sun dawo nadan dade a gurin su sai daina basu komsi don sunce tea zasu sha kafin su kwanta larabs na saka ta dubamin su. Na samu ya gyara min kwanciyan yaran guri daya ya ajesu su uku don haka muka manne da junan mu a gefe daya mundanyi fira kafin komai ya kan kama muna mukai barci cikin jin dadin kasancewa da junan mu ga yan diyan mu a tsakiyan mu. Washegari da wuri na fito don shirya abincin baki saboda ranan su maryam zasu juya Abuja ina tsakiyan aikin ne hayaniya ya taso a sama ashe fitowa na nafisa ta shiga dakin shi. A fusace taje da tambaya may ye matsayin ta a gurin shi ne do bata gane ba don may zai ban girki bayan ita gata yace don tana matana ita din. May kake nufi da ita matar kace nifa a matsayin may nake gurin ka yace wanan kuma yanzu ba zan iya fada maki ba sai nayi shawara nan gaba. Nan har yakai suka fara sa in sa har yakai ya mike ya fara jibgan ta suna tonon asiri ga junan su duk wanda ke gidan ya fito. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 1/27/21, 6:51 AM - Xxxxx: Yanzu kokarin kammala karatun mu mukeyi wanda muna a matakin karshe haka ya jawo min rashin zama sosai a gida. Sai yamma lis nake dawowa gidan da na dawo kuma na dan huta bayan na gama ibada sai in shege barci don gajiya. Duk yadda Altine kan so muyi hira hakan bai samuwa a gare ni ban san may yakai Nafisa garin mu ba ranan na fito don zuwa school ina sauri sai ji nayi tana fadin iyayyen ki na gaida ke mun biya munga gidan ku . Mamakine ya kamani don jin kalamin ta matar da ba wani hurdan arziki yake hada mu ba may ya kaita gidan mu kuma. Nagode Allah ya bani ikon amsa mata dashi na fice ba tare dana dora wani magana ba akai sai dai a raina ina mamakin zuwan ta minna din da tayi. Banda lokacin wanan don haka ban tsaya bin ta nata ba kuma Allah ya taimake ni mun gama komai na project nayi sumiting. Na fara jin shakat a tare dani yasa ina dan zama gida yanzu a cikin iyalina yanzu muna da masu aiki dake girka abincin gida gaba daya wa kowa don haka ba wani aikin komai mukeyi ba mu. Arzikin AA ya bun kasa sosai bai damu da tsayawa yayi aikin nan gida Nigeria ba ko yaushe yana waje mu kan mu ba kullun ne muke ganin shi ba nan. Sai dai idan ya zone kasan ba mai hutu a cikin mu don yawan aikin da muke na fama dashi da bakin shi dole sai mutum ya leka kitchen din ya duba abinda sukeyi. Na fada ma masu aiki abinda zasu girka min yau kafin in fita sai na dawo na samu wai Nafisa ta shiga tace dasu kada suyi abinda nace sai wanda ta fada masu din. Raina ya baci gashi muna saka ran dawowan maigidan a ranan kuma nice da girki idan ya dawo ga auren maryam daya taso kwatsam a satin da zamu kare satin za a fara bukin. Part din Nafisa na shiga wanda zance tun da akai wanan gyaran ban shige shi ba sai ranan nayi mamaki ganin part din dam da buzaye yan uwan ta wanda ban san lokacin da suka zo ba ma. Da farko naji dan shakka yin maganan da ya kaini amma ganin sun gani nashigo ya sa na dake na karasa dakin ta don tsarin ginan iri daya ne da nawa na kwankwasa kofa na shiga. Tana zaune da bakuwa sun baje kaya a gaban su ana mata bayani wanda ashe akan yarana akai wanan tafiyan ban sani ba ni. Allah ya taimake ni ban wasa da ibadana duk ko da daulan da Allah ya kaini a cikin sa na dawo khadija na ta farko sosai ban yarda na shagala ba da addinina. Shima kan shi maigidan yanzu ya canza sosai don koda zan falka zan samu ya rigani tashi yana gabatar da nafila a cikin dare. Daz mamaki suka kalloni nan ta fara fadan borin kunya wai may na shigo mata shiya yi bata shiga girina va don may zan shigo mata. Suna kokarin boye kayan da na samu an baje ana kula sheri farin kudine sai dodon alkwato da kan wasu mushen halittan daban san ko may ye ba. Na gama kare ma kayan kallo a cikin second nace zuwa nayi nima inji dalilin daya sa na bada kalar abincin da za ai min kika shiga kika ce kada su girka min shi. Jimun wanan yar matsiyatan don Allah zuwa kikayi yanzu ki makure ni ko may ta fada tana min wani irin kallo nace zuwa dai nayi in maki kashedi akaina da komai nawa. A matsayin ki nawa a gidan nan ke yanzu fa nasan komai akan ki don haka baki da wani bakin da zaki mun maganan banza a gidan nan. Don naje har kuryan dakin uwarki na gani naga abinda kike mun tunkaho dashi ba komai banda tsiya a gidan naku. Alhamdullahi tunda muna da gida har kinje ashe nafiki don iyayyena dai ban barsu a kango zaune ba ko bukka ta kwashe da dariya tace karya ke nan wallahi kowa ya ganin yasan gidan dana fito ai. Dama na nemi gidan ku ne don in kashe maki wanan alfaharin naki a gidan nan don na samu abin fada maki watarana nace nafi kowa sanin haka ai don ba zuwan alheri ya kaiki gidan mu ba. Sai dai nasan duk yadda gidan mu yake nan yafi gidan ubanki sau dubu albarka koda banje ba ina da labarin komai a kunne na ga wayanda sukaje suka gani. Ban fito ba sai da muka fada ma juna magana son ran mu na fito dakin da farko abin yaso ya damay ni a raina sai daga baya maryam tace dani akan dan maganan nan zaki damu kanki dashi. Cin tuwon kishiya fa ranko ne ko birnin masar take sai munje mun gano gidan su wallahi don taji inda dadi hakan balle banga abin kushewa a gidan ku ba ai. Sherin kishiya yanzu khadija wani iri ne baki sani ba kuma har da wanda batayi niyar yiba kin sani banga abinda zai damay ki ba ni. Haushinta dai daya yanzu duniya ta daina yi da ita babu bakin cikin ta sai ta bude ido ta ganki a cikin gidan nan dake da yaran ki. Da wanan maganan na maryam na manta da zancen ranan sai Allah ya taimaka bai dawo ba a ranan ya dage tafiyan sai wani sati mai zuwa zai dawo. Tun lokacin da muka fara bukin maryam banjin dadin jikina sam zazzabi nake fama dashi sosai dole na samu time naje asibiti don a dubani sai dai result din ya ban mamaki jin wai ciki ne dani. Sun bani magani na dawo gida na boye takardan naci gaba da ahan magani na banje kaduna na ba jos na wuce inda a can za ai bukin maryam din. Wanan yasa hajiya umma yin korafi akaina wai na fifita gidan kawa na sama dasu don shi kanshi AA baiso in tafi jos din ba sai danayi ta magiya ya yarda na tafi. Wahalce nakai jos kwanan mu uku ana shan shagalin buki muka juyo zuwa kaduna a dadafe na shigo kaduna don jikina daya kiya min tuncan. Fada ya fara wai ai saida ya fada min karnayi nafiyan nan na nace sai nayi dole ya tasa ni gaba zuwa asibiti a cikin daren muka je. Tambayan farko shine ko ina da ciki ne ya wani kura min idanuwan shi don son jin amsan da zan bayar a sanyaye na daga ma likitan kai alaman eh. Zama ya gyara yana saurare na likitan yace wata nawa nace biyu sai ya rubuta min magani yace tafiya da jigilan bukin danayi ne ya sa min wanan zazzabi haka. A raina nace koma may zai fada ya fadi yanzu dama don kada ya hanani sha,anin buki naki fada mai zancen cikin da wuri. Har muka dawo gida bai min magana ba sai da zan fita mota naji yace baki son cikin jikin naki ne da alama don tunane na ya nuna min hakan. Dan kallon shi nayi banda bakin magana don yanayin da nake ciki nace ban iya magana yanzu don Allah ina kokarin fita daga motar . Mun samu masu zuwa gurin dinner nata kokarin zuwa nikan nasan ba halin haka gare ni ina shiga na shige dakina na dunkule. Laraba ya kira ta hada min tea in sha insha maganin da aka bani tunda ya fita bai kara lekowa ba nasan sun tafi gurin dinner din ne sai ni da laraba kadai muka rage a gida. Can ma hankalin shi bai kwanta ba don haka ya dawo gida sai dai ya samu ina barci na hankali kwance tare da yarana su uku a dakin. Sai laraba data gama gyara bandakin dana bata tana saka kamshi a dakin ya shigo baidade ba tunda ta fada mai nasha maganin sai dai nayi ta amai daga baya. Jamma suna tambayana ake fada masu na dawo banda lafiya ina gida kwance haka yasa mutane da yawa sukaji rashin lafiyan nawa. Da safe na dan tashi jikin nawa da dama don haka nayi wanka na gyara jikina na koma na kwanta muna waya da maryam din nan nake sheda mata abindake damu na. Tayi mamaki nace nasan ki da baki tsiya dana fada maki tun farko dayan zu ba ai bukin nan dani ba don idan ya sani ba inda zanje kema kin sani. Shine ya shigo dakin nace zan kirata daga baya yana wani shan toka a fuskan shi ina kwana nayi mashi tare da tambayan shi gajiyan jamma,a . Bai amsa min ba sai tambayan da yayi na karya insha magani nace laraba ta fita ta samo min kosai don shine kadai nake ci ya zauna min a ciki yanzu da dan kunun kamu. Ina taje samuwa nace ban sani ba wallahi ta dai fita ko zata samu yanzu kina sakaci da rayuwan ki da tun farko nasan da zancen cikin nan ba inda zaki je wallahi. Har ya kare rigiman shi ya fita ban iya tanka mai ba na kyale shi ya fita a cikin fushi laraba ta dawo min da sako na na tashi na danci na koma na kwanta . Shigowan su hajiya mama da momy ne ya sa na tashi daga barcin da nake muka gaisa suna min yaya jikin nace naji sauki. Momy tace baki da lafiya haka kika tafi gurin buki ai ciwo ya kawar da komai ga ran mijin ki ya baci sosai wallahi. Hajiya mama tace tasan ba zai barta zuwa bane ta boye mai amma kuma ai lafiyan ki dana abun cikin ki yafi komai khadija kada ki kara irin wanan gangancin don Allah nan gaba. Kai na gyada mata kawai tace zainab ma halin da take ciki ke nan ya hanata halartan bukin da kyau. Sai lokacin nayi magana nace zainab cikine da ita ashe tace cikine irin naki itama mai wahala takeyi yanzu dai naji yace ai zaku fita ne ko ? Don bukin nan ya dawo dashi dama nayi saurin dagowa ina kallon mama din momy tace kin san babangida ai tun da ya kafe da ita zai wuce har yaran shike nan kuma ai. Da kyat na bude bakina nace don Allah momy a rokar min shi ban son zuwa kasan nan wallahi ya barni nan zan kula da kaina. Basu wani jima ba suka tafi sai lokacin Fati ta shigo dakin tana fadin ashe bakiji dadi bane sai yanzu da su momy suka shigo nake ji. Nace zazzabine naji sauki ai tace Allah ya sauwaka wanan karon Nafisa ba shigo ba wurin bukin sai lokacin nake ji bata shigo ba ashe. Banyi mamaki ba don karamin aikin tane don ba shiri suke da Suraj din ba ko banza fa kuma maryam da ta tsana a rayuwan ta. Don gani takw babu abinda muke da maryam sai shige shige akanta da mallake miji shine aikin mu kamar yadda take da kawayen hurdan ta. Kwana uku muka kara a kaduna su maryam har sun bar garin ko ita da angonta zuwa cin amarcin su tun kwana biyu da tarewan ta. Mun iso lafiya nan ma dai ba a cikin dadi nayi tafiyan ba don keta kuma ya ki saya min ticket din jirgi in bi ko da nida shine. Tunda na dawo ban leka waje ba ina ciki kwance gashi shi ba zama yake ba don Yusuf bai dawo Abuja ba shi kadai ke komai a nan yanzu. Ya dawo a cikin dare ya shigo gurina ya dubani sai yake fada min cewa wai zamuyi tafiya nan da kwana biyu in shirya kuma zamu dan dade a can din. Fuska na bata tare da fadin gaskiya sai dai kaje kai kadai don ba inda zan tafi a hankan da nake ko ka dauki wata kuje tare. Kin san abinda kike fadi kuwa ya tambaye ni ni ince kiyi abu har ki tsaya kina min korafi akai wanan tafiyan ya zama dole kiyishi don ba zan zauna acan ni kadai ba alhalin ina da mata. Dawa kike son in wanan tafiyan cikin ku bayake duk cikin ku akwai mai ilimin da zata taimaka min da wasu abubuwa a can ne ? Shiru bayi tunda ya fara magana don jin abinda ya fada din nace kasan wata mai zuwa kuma zamuyi buki a gida shine dalilina. Buki ba wanda zasuyi ne idan kin tafi wai may yasa kike son ja danine kina tsanmani ko kina nan za ai bukin zan barki kije ne a hakan yadda kike din nan don haka ku shirya harsu Altine don yara zamu tafi. Jin dasu Altine yasa hankalina ya dan kwanta da tafiyan sai dai banso rashin samun bukin yar mama Tani da za a yi ba haka yasa washe gari na tura ma mama tani din kudi masu yawa tare da bata hakkurin rashin halartan bukin da baczan samu yi ba. Nafisa ta so ta tayar da rigima yake ce mata idan kin je can wanu aiki zaki min a can ita aiki ne zai kaita ba shakatawa ba. Wani aiki ta iya da zatayi a can yace idan taje zaki gani lokaci ya kure mata don da bata yarda da wanan tafiyan da za ayi dani ba ta nasa a ranta. Ba tare da na samu sallama da kowa ba mukai wanan tafiyan zuwa waje kasan hongkong muka nufa ba sai na fada maki yadda naga kasar ba kacar dani . Sai nake ganin rashin tausayin shi da ya jajirce akan sai nayi wanan tafiyan ko ta halin kaka sai na tafi tare dashi can. Da farko don laulayin da nake yasa banji dadin garin ba amma da bazo ina samun kulawa sosai sai na fara jin dadin yanayin garin a jikina. Sannu sannu na gane dalilin shi na zuwa dani da farko dai doin kare lafiyan shi da mutuncin iyalin shi sai na biyu don yaran shi yana kusa dasu. Sannu sannu alamura suka fara canzawa yayin da cikin jikina ke kara girma yana fitowa ba zan iya cewa Nafisa ta san da zancen cikin ba. Sai dai nasan tana kiran shi suna fina kan rashin zuwan shi Nigeria din wurin ta muna da wata uku da zuwa ya barmu can yazo nageria. Sai da ya share wata daya ya dawo gurin mu karatuna na koma ina business inda bake turowa Ya Amina da zainab dasu Faiza kaya suna sayar min a tura min kudina in sake turo wasu. Tsayawa in fadi canzawa na a yanzu bata lokaci ne don gaba daya na sauya na zama wayayiyar mace mai aiki da zamani ga ilimi dana samu a can. Watan cikin jikina tara yanzu ban fita ko ina sai zuwa daukan darasi kawai ke fitar dani ban ketare wata tara ba na haife dana mai kama da diyana sak yazo duniya. Allah ya taimakeni yana kasan bai fita ba na haihu nasa rai zamu dawo gida don sunan dan sai cewa yayi ba inda zan tafi karatun yaran shi ya samu tsaiko. Ya dai buga waya ya sheda ma mutane na haifi Abdulsamad jinior kamar daga sama Nafisa ta samu labarin haihuwa na daga bakin shi. Ba karamin fitina tayi ba har da dan kukan ta wai ta gane dai yanzu bai son ta har nayi wani ciki na haihu ita ko bata n wata bata kara yi ba har yanzu. Wayan ya kashe don bai iya sauraren shirmay ta yanzu ya kira fati ya fada mata tayi kokari wurin boye kishinta tayi addua akan jaririn da aka haifa din wanda hakan ya kara daga daranjanta a idon shi. Hajiya mama da momy ne suka zo dubani inda watan su daya a wurin mu yana nuna masu gata bayan wata daya suka shirya suka dawo Nigeria, Zainab ma ta haihu ta haifi dan ta namiji ita ma sai maryam suke fada min cikin ta ya girma amma sau daya suka zo kaduna gaida su basu sha da dadi ba wurin umma ya dauki matar shi suka koma tun kwanakin da zasuyi basu cika ba tun wanan lokacin basu sake dawowa ba inji momy. Hajiya mama ba mau son hayaniya bane sai dai tayi ta kallon mu tana murmushi wanda hakan ke nuna farin cikin ta a fili. Ana saura kwana biyu ta koma ne take fada min cewa sunyi magana da AA yace yana son akai su Affan karatu saudiya. Nayi murna kwarai ya yarda da shawaran dana dade ina binshi akai ke nan sai dai maimakon ya kaisu inda nace sai canzawa yayi zuwa kasan saudiya wanda hakan yayi min dadi sosai. Ban nuna mashi naji ba sai bayan tafiyan su hajiyane yake mun magana na nuna mai farin ciki na sosai yace zai shiga Nageria don shirn yaran karshen wata zai dan dauki lokaci don wani aiki da ake mai a can yanzu. Ya barmu can yazo sai dai tun zuwan shi Altine ta tayar da gankalinta akan ita fa zaman garin ya isheta hakana gida take son ta dawo. Na kirashi ina fada mai yayi mamaki yace ko dai wani abune ya hada mu da ita nace ba abinda ya hada mu gaskiya gida daine ya biyo mata a rai. Yace a bata wayan suyi magana ya dan rarashe ta akan ta bari har ya dawo ai zamu zo gida muma bada dadewa ba. Niko nasan dan ci gaban data samu ne yasa tayi wanan maganan don taje ta shana a kaduna asan itama ta faso gari don gwargwado AA ba maketaci bane. Yana kyautata ma duk wanda yake kasa dashi yadda ya kamata dan kudin da suke samu ne ba basu shawaran su dinga juyawa suma suna samun ci gaba. To wanan daman data samu take ganin yanzu ta wuce zama rainon yara ita ma zata iya tsawa da kafan ta yanzu. Ya dawo da sati biyu tare da Anty Fati daga wurin kai yara suka wuto zuwa gurin mu, Altine ta barmu can ta dawo Nigeria wurin yan uwanta ban wani shan wahala ba don Laraba mace ce data cancanci yabo ga Anty fati ba laifi tana dan taya mu kula da yaran. Tare muka zo Nigeria lokacin tana da wata biyu da zuwa wurin mu ko yaron dana haifa ya girma yayi wayau sosai yana rarafe ne yanzu . Tun isowan mu Abuja Nafisa ta kyala ido ta ganmu don bata san da zuwan Fati ba hankalin ta yayi matukar tashi sosai yau tana ji tana gani matan da tafi tsana a rayuwan ta suna can ashe suna holewa da mijin ta. Ita tana nan an yada ita kamar wata bora ko taron arziki bai samu ba a guri ta hankalinta ya tashi sosai ga yadda taji labarin nakoma da yarana. Bai bi ta kanta ba ya fice ga dayan part din da aka budewa fati ta shige ciki shiya kara daga mata hankali sosai don bata gama da batuna ba, ga kuma wata tazo. Wai may ke faruwa da itane haka komai nata yana shirin lalacewa gare ta sai taga kamar zatai nasara sai abu yazo gaba daya ya rikice mata. Fatin da take ganin ta gama da batunta a rayuwan su yanzun kuma ta sake dawowa cikin lamarinta kardai aikin ta yatashi ke nan ita ma kan sanadiyar wanan fitsararan da bata jin jifa a kanta. Daidai lokacin ne da take wanan nazarin laraba ta fito da yaran tana masu burgan turancin data samu a can tana wa yaran. Galala Nafisa tayi tana kallon laraba ko yaran dake dan wasan su cikin rashin kula da ita a gurin bata taba nadaman rashin karatun ta ba sai ranan don tana ganin da kyau shine nasaba ga komai a gareta. Dakin ta ta koma cike da bakin ciki da takaicin yaran data gani a jere su uku wai duk wanan yar nufawan keda haihuwan su a gidan. Ya zama dole ta mike tasan inda take ba zata tsaya kallon ruwa ba balle kwado ya rigata tsalle haka kawai daga shigowa na har na sake diya uku tana zaune dabas. Kaji jahila wace bata san Allah ke yi ba waya ta jawo tana kiran kande sabuwar aminiyan ta na yanzu Kande dake tare da madam datazo wurin ta maula. Tana sauraren bayanin su da Nafisa har suka gama tunda Kanden tayi mata alkawarin zuwa Cameron kafin mu koma zata san yadda zata sai dai zance na ya sha ruwa a gidan. Muna da sati biyu da zuwa naje gida na ziyarce su kowa yaji dadin zuwa na ya Amina tazo muka hade nan da ita ranan raba dare mukayi nuna hira da ita. Nayi sa, an zuwa don gap da bukin yar mama Tani ta biyu ce sai na roka ya barni sai da muka sha buki muka dawo ranan Fati ce da girki a gidan na samu sun gama fitina da Nafisa. Duk da rashin son hayaniyar ta ranan saida ta kai karshen ta sukai sa in sa kowa ya gama jin su a gidan don nafisa tace ba zata zauna ba da fati sai dai takoma kaduna da zama. Ita ko tun a can na kara mata karfin gwiwa gara ta dawo Abuja ta zauna tunda ba kowa a gabanta yanzu da haka harta yarda. Shine ita kuma nafisan ganin bata da niyar komawa ta tada wanan fitinan na bata yarda da zaman Fati ba a Abuja. Muna gidan maigidan ya dawo ta tayar da fitina yace akan may kada fa ta daga mai hankali don shi yanzu mace ba dole bane a gare shi. Dama can bashi ya maida fati kaduna ba itace ta zabi zama can yanzu kuma tace ta dawo nan don haka dakin ta na nan a gidan. Wayo buzuwa ina wuta ta saka AA ranan don bamu kishiyoyin ta ba har shi maigidan tsanan shi take ji a ranta tayi tunane kala kala ta rasa na dafawa. Don yanzu bazata iya zama kasan su ba don wacen zaman datayi bata sha da dadi ba ga gorin yan garin daya isheta sai da Allah ya taimaketa yazo ya dawo da ita. Yanzu yaya zatayi ga duk kawayen ta na farko dake mata shige shige yanzu duk sun gujeta sun koma ga wayan da suke ganin sun fita bayarda ihisani. Dole dai madam zata nemo ta dawo a rayuwan ta su dora a inda suka tsaya da wanan shawaran ta kwanta tana jiran gari ya waye ta lalubo madam din taji yadda za a yi. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 1/28/21, 6:23 AM - Xxxxx: Washe gari da dawowan mu kururuwan Nafisa ne ya tayar damu a gidan ta samu waya Allah yaiwa mahaifin ta cikawa da yammacin jiya. Duk wanda ke gidan ya tausaya mata da wanan rashin da tayi don mahaifa ba wasa bane gaskiya ko da ban san tsohon ba a yadda ake fadin yana jinya shekara da shekaru dole mutum ya tausaya mai da iyalin shi. Har dakin ta na shiga nayi mata gaisuwa na dan dade a zaune babu mai magana a cikin mu kafin in fito na bar part din. Gurin Anty Fati na shiga don mu gaisa nake fada mata dagagurin Nafisa nake naje nai mata gaisuwa ne tace zan dai yi daga nan indan yana kai ga mamacin amma ba zan mata gaisuwa ba ita. Don ko uwata data mutu bata sani ba amma idan cin mutuncin ta ya tashi gidan nan lokacin uwara dake kwance a kabarin ta itace abin zagin ta kullun. Naji ba dadi a raina amma dai na kara bata hakkuri a fili nace ba a binta nata ai don zama ya hada mu tare komai mutum zaiyi sai ya gyara ramin sa don ba ruwan Allah da kishin mu hakkin zama zai tambaye mu. Wanan nasihan danayi mata yasa jikin ta sanyi na dora da fadin wanan isan mutum nabin ta nata sai ta kona kanta ta kona ka ai. A falo muka hadu da AA din nayi mai ina kwana tare da fadin ashe rashi akayi haka kuma yau yace wallahi Fatiha jiya ta kirani da dare tana fada min ya kare. Allah ya jikan shi yai mashi rahama nace ya amsa da amin tare da jan guntun tsuki yana fadin yanzu abubuwan mutum zasu tsaya ke nan kuma. Nace wanan ai ya kawar da komai don dole aje akan lokaci yace hakane garin nasu ne ba dadin zuwa ke gare shi ba ai nace ko yaya ne ya kamata aje da wuri dai. Wayan shine yai kara ya dauka nikan na shige part dina na barshi gurin ya nufi hanyan part din shi yana wayan. Ashe Fati tace tai mata gaisuwan da rana ina falona zaune na kira maryam bayan mun gaisa ne nake ce mata ke yau fa rasuwa akai muna a gidan. A kidimay take fadin innalillahi wa ya rasu kuma khadija banji dear na na fadi ba kuma nace mahaifin Nafisa ne ya kare jiya da yamma wani irin tsuki taja tare da fadin har kin sa gabana faduwa wallahi. Nace maryam musulmi ne fa dan uwan mu tace don haka aishi zan ma addua ba itaba sai kuma tace ashe zuwa ya kama mu Niger. Da sauri nace kedawa tace dake wallahi ai wanan dama ne ya samu zamuje muma muga gidan su wanan karon sai ta jimu wallahi. Sai kin dawo nace mata yanzu fa AA ya gama fadin garin ba dadin zuwa jiki da wani shirmay don Allah ba dadi shi yake zuwa wallahi nina fada maki sai munje mun gani in ba irin wanan sanan ba yaushe zamu samu zuwa. Sai kin dawo nace mata tace sai dai na shigo yanzu aiki nake yi yace zau dawo yaci abincin rana shine nake girki amma idan na gama ganinan zuwa gidan. Mukai sallama ta kashe wayan ta barni ina mamakin karfin halin ta don ban dauki zancen da wani gaskiya ba aiki yana ma laraba yawa haka yasa nace akawo min yarinya daga gida irin Nufawan doko din nan. Sai wata yar maman mu tace ga yaran ta nan mata har uku in dauki guda daga ciki ko nawa ma nake so na barsu zasuyi shawara na dawo. Itace ta iso da ranan haka yasa na manta da zancen Maryam din naci gaba da harkokina a gidan zuwa hudu sai ga maryam din ta shigo. Bayan mun gaisa ne nayi mata jagora zuwa dakin Nafisa tayi mata gaisuwa inda muka samu suna ta faman shirin tafiya washe gari zasu tafi. Muna fitowa maryam tace kinga mu kuma sai mu dora idan sun tafi nace wai ke da gaske kikeyi ne don Allah tace insha Allah sai munje munga gidan su muma don mu maida martani. Ai shege akewa bai rama ba mamaki zamu basu don nasan idan kin fadawa mijin ku ba zai yarda mu je ba don haka kyaleshi kedai kawai ki tambaya muna yadda ake zuwa garin. Haka akayi dan a cikin hikima na tambayi maigidan yake fada min duk yadda za ayi aje garin washe gari suka tafi tunda asuba mu kuma muka fara shirin tafiya don anty Fati ma tace zata tafi tunda gulma ne. Momy na fadawa shirin mu tace gata tafe dama tana tunanen yadda za ayi sai gata ta shigo garin da yamma da sunan gaisuwa tazo yi a Abuja. Muma tunda asuba muka dauki hanyan doso da motar Suraj ya hada mu da sojoji guda biyu muka tafi tun muna tafiyan dadi sai gashi ido ya fara raina fata. Kowan mu ya gaji da wanan tafiyan shiru mukayi dukkan mu a motar sai da muka fara shiga garuruwan kasar ne muka fara magana muka dauki hanyan tawa inda acan ne zamu nausa a sahara zuwa kauyen nasu. Ga namu watau mun dauka tafiyan mara nisa ne sai gamu har guraren uku bamu kai garin ba sai da muka bar gari da nisa muka iso garin. Da tambaya muka samu wanda yasan gidan har akai muna kwatance munga karyan buzaye a wanan garin kowa da dan kitso a gaban kai mazansu da matan su da shiga irin tasu. Kofan wani gida shi ba gidana ba full ba a kuma kiranshi da bukka gashi nan dai ga kamar shi sai da na raina ma AA ba buzuwa ba kawai. Yana zaune suna karban gaisuwa muka iso yabi motar da kallo shida yusuf ne yana mamakin motar don daga Nigeria take kuma lamban depences na Nigeria ne. Momy ce da ta fara fitowa dauke da daddy a hannun ta yana kuka yasa AA dan zabura daga inda yake zaune sai gamu muna fitowa daga cikin motar. Mamaki zaiyi ko takaicin zuwan mu na wanan kasadan shigo wanan kasar da mukayi hikiman Zuwa da momy ya taimake mu don bai iya muna wani magana ba a wurin sai cewa da yayi momy kune tafe haka ? Bayan mun gaisa ya nuna muna hanyar shiga cikin gidan muka nufa kai tsaye kowa na baza idon wurin kallon kwam suna ciki da mutane da ba yawa a gidan. Mukai sallama sai da ta girgiza momy ce dai gaba sai fati maryam na bi ina bayan su gaba daya matan dake gidan suka dawo da kallon su gare mu. Fatiha ce tayi karfin halin iya magana tana fadin lalai marhabin kune tafe ashe kuna hanya bamu sani ba tana taron mu a cikin jin dadi. Ita ko nafisa tayi mutuwan zaune ta zuba muna ido ana kokarin shimfida muna ta barma ina kallon maryam bata zauna ba sai da ta goge tabarman da aka shimfida muna don jan magana. Nan aka debo muna wani jan ruwa a tukunyar kasa aka kawo muna kowan mu kallon ruwan yayi ya kawar da kai. Za,a ba dan wurina dake rikici ruwan maryam tayi saurin fadin a,a aida ruwan mu a jakka ta dauko ta mika ma Fatiha fatihan tace ai nasan ba zaku iya shan ruwan mu ba. Gaisuwa muka fara tare da tambayan mu yaya hanya nice nace ina mama mu gaida ita aka nuna muna wani bukka babba tana ciki Fatiha tace mu zo mu gaisa da ita. Kai maryam da ta kallama ita da fati suka shiga bukkan sai ni da momy ne muka tsaya cire takalman mu muka shiga dakin . Mun gaida matar da wahala ya sata tsufan dole tare da mata gaisuwa don bata jin ko zo in kashe ka da hausa sai yaren su na buzaye. Bamu dade ba muka fito don zamu juya sai lokacin nafisa da bayan gaisuwan da mukayi bata kara magana ba tace ashe yanzu zaku juya ? Eh don ba kwana zamuyu ba anan nice a kofan su muke magana da Fatiha nake tambayan ta ko zamu samu ninon rakumi a wurin su. Tace sosai kuwa ai yanzu lokacin sa ne ma na bata kudi akan a samu muna idan ba zai dauki lokaci ba tace nan bayan su akwai inda zata samo muna. Shije ya dan bata muna lokaci har muka dan makara mun fito zamu tafi inda naba uwar su kudin mu na Nigeria masu yawa da su Fatiha sai godiya suke zabga min muka fito . AA da ransa in yai dubu ya baci yace ma momy badai juyawa zaku yi ba yanzu momy tace munzo munyi gaisuwa ai gara mu juya komai dare insha Allahu yau gida zamu kwana. Baiso tafiyan mu ba yaso akaimu cikin gari wai mu kwana da safe mu dauki hanya sai sojojin nan sukace ba damuwa tunda muna tare dasu ai don suma basu son su kwana a kauyen. Bamu muka kawo Abuja ba sai daya na dare suka sauke mu gida suka tafi wanka nayi na rama sallah dake kaina na kwanta. Don gajiyan da muka debo sai dai AA yana kiran mu har muka shigo abuja hankalin shi ya kwanta da safe ban fito ba don gajiyan da muka debo acan ko tsaranban da muka saya ban bi ta kanshi ba. Kwanan shi uku da akai sadakan ukun ya dawo a cikin dare sai dai ba kamar namu tafiyan ba na dare sosai jin dawowan shi ne na fito don har lokacin ina da gajiyan zaman mota a jikina. Yana waya na shigo ganin yana waya yasa nayi mai sannu da zuwa na juya da zan fita ne yake cewa dakata na juyo dani yake din yace hada min ruwan wanka. Banki ba na hada mai na fito na samu ya gama wayan yace ku yan kasada may yakai ku Niger ne da mamaki nake kallon shi nace kai may yakaika don Allah ? Ni kike tambaya nace naga dai abinda ya shafe ka ya shafe mu ai ko zuwan namu kuma laifi ne idan kuma bamu je ba a ce bamu tafi ba don bamu damu ba tunda ba uban mu bane ya mutu. Bakin nan naki ai sai ke ni dai ban son hakana kuma banji dadin zuwan ku ba tunda baku sanar min ba idan muyi laifi kayi hakkuri bamu sake hakan na fadi tare da barin dakin waini nayi fushi. A raina nace mun dai je munga abinda ake boye muna din idan shine ba a son mu gani ashe bayan tafiyan mu sai da sukayi kaca kaca da Nafisa a can . Wai ya munafunce ta bai fada mata zuwan mu ba sai ganin mu tayi kwatsan yaja mata abin fada a gurin mu ke nan shima ya rufe ido yayi mata cin mutumci a gurin sai da aka raba su. Shine karin takaicin shi damu fati ma da ta shigo sai da sukayi fada tace baka son muje ka hada mu yace gulma dai ya kaimu tace in ma gulman ne mun dai tafi din. Haka yai ta shan mur shi kadai ba wanda ya kula shi a cikin mu dama momy ta koma tin kan ya dawo don haka bai samay ta ba a gidan. Ya gaji donn kan shi ya sauko ta nemi shiri damu ni kuma na hau ranan nice da girki sama sama nake dashi na aje mai abinci zan fita yace wai ke mai kike shawa wanan kamshin ne haka. Nace kamshi akan may inma kamshi ne aikai ka fara sha muda muka sadaukar da ran mu muka bata lokacin mu zuwa maka kara baka gode ba sai ganin laifin mu . Ashe zuwa gidan kishiya baida dadi ka bari taje namu gidajen sai itane don munje mata abin arziki zakace bamu kyauta ba. Kin san yadda mukayi da ita dans san taje nifa akan yaran da kuka wahalar min nake wanan ba don komai ba in ma ba gaisuwa kuka tafi ba ai kanku kukaiwa. Ni ki zauna ki zuba min abinci naci don yunwa nake ji yanzu nace bakai bane a raina, ina zubawa ne yake fadin ya kamata ku koma haka na don karatun yaran nan kada ya lalace. Kofa wata daya kwakwara bamu cika ba ina gani gaskiya nikan ba yanzu zan koma ba sai nayi wata uku a gida kafi in koma wanan kasan. Zance dai kike so don naga ke karatun yaran bai damay ki ba ko kadan in ma ya damay ni sai na tauye kaina don su. Ban kara magana ba na zuba naja kujera na zauna tare da fadin yarinyar da zamu da ita tananan ta iso yace ok Altine din ba zata koma ba ke nan. Nace naji kamar momy tace aure zata daura fa don tunda muka dawo ta bugo min waya sau daya sai ko da mahaifin nafisa ya rasu ta kira bata kara kirana ba. Yayi murmushi yace ita tana ganin tayiwa kanta mafita ke nan duk da dai ba a hana aure amma auren ta nawa idan tayi wanan don tun ban karasa cika saurayi ba take aure. Don ma bata haihu da yawa bane jikin ta bai nunawa aida yanzu ta ragwabe suma mazan dake auren nata ne basu da aikin yi ai. Nace bakaji masu iya magana sunce guban wani zuman wani kai ke ganin ta ta tsufa sukan shar suke ganin ta ai. Hiran yasa gaba dayan mu muka mata da zancen fushin da mukeyi da juna muka buge da zancen Altine har wani lokaci. Zaman mu da fati akwai fahinta sosai don ina guje ma abinda zai kawo wani baraka a tsakanin mu don haka ne muke zaune lafiya da ita bani shiga zancen ta idan ba itace ta sakani ba. Satin nafisa biyu ta dawo abuja da yan uwan ta gidan ya koma cike kuma sabanin da muke mu kadai sai yaran mu nidai ba a samu matsala dani ba sai dai da AntyFati ne suke dan tabawa akai kai. Sai da maigidan ya dan tsawata masu kan hakan suka dan bari amma suna dan tabawa a boye don Nafisa ta tsani zaman fati a Abuja. Na fito da safe mukai kicibis da wasu mata sun fito gurin nafiss ban son tankasu ba sai da naji dayan tace min hajiya khadija mun tashi lafiya ? Na dakata ina kallon matar kamar na taba sanin ta sai tayi murmushi tana fadin nasan baki gane ni ba ko ? Nace na dai sanki amma wallahi na manta inda nasan ki tace kin manta da madam mai zuwa gurin Nafisa a baya can. Nace a, a mama kece wallahi mun dade bamu hadu ba tace wallahi kwanaki nazo akace yanzu waje kike zama da maigidan. Nace hakane yaya bayan rabo tace sai Alheri dama ina tason mu hadu in rokeki gafaran akan abubuwan da suka faru a baya. Mota zan shiga don har na bude ne na tsaya muna gaisawa dasu nace baki min komai ba mama in makin min to na yafe maki. Sai ta fara sharan kwalla nace tafiya zakuyi ne in rage maku hanya don fita zanyi tace dako mun gode don wurin nan naku ba a sanun abin hauwa wasan dadi. Mun dauki hanya har lokacin tana dan sharan kwalla a fuskan ta sai naji dayan tayi magana tana fadin ki fada mata gaskiya don baki san ranan da zaku kara haduwa ba. Dan juyowa nayi nace wani abune mama datan tace wai gafaran ki dai take son roka akan abinda sukayi a baya akan ki. Sai madam ta karbe tana fadin don Allah hajiya kiyafe min nasan alhakin ki na cikin abinda ke bibiyana yanzu don tun wanan ranan dana fadi a gidan ku ban kara lafiya ba har yau din nan da muke magana. A ranan ma mun yo daukan asiri ne da zamu shafawa diyan ki sai abin ya juye a kaina nan dai ta shiga bani labarin abinda ya faru a ranan da ita. Tace yanzun ma tazo don nafisa a baya ta gujeta sai yanzun kuma ta nemay ta wai tana son suci gaba da harkan su na baya. Tana son a illanta yayana dani kaina da kuma fati a rabata da gidan ga baki daya sai dai na fada mata yanzu ba da bane bazan koma wanan harkan ba shine tayi muna koran kare kona mota bata bamu ba. Zaki iya fadin wanan maganan a gaban maigidan mu mama na katseta da tambaya don jin may zata ce zan iya idan har hakan zai sa Allah ya gafarta min . Don nasan koda banyi mata ba wata zata nema tayi mata wanan aikin nikuma nasha alwashin fada maki gaskiya dama don ko ban ganki a yanzu ba zanyi kokari in nemay ki. Ni mama ga Allah na dogara babu ab inda zata iya min da yardan ubangijina duk abinda take nufa akaina na sheri akanta zai koma. Tace kawarai kuwa niko nasan hakan don irin daukan da muke a kan ki kina katarewa abin akwai mamaki don ba karamin tsari ke jikin ki ba. Yaran nan naki ma saai ince sun fiki tsari don su kila kokuwan su na tagwaye ne ya hade danaki yake aiki a kansu. Kada kiji komai mama ni ina tare da Allah ko da yaushe don gare shi na dogara ga duk alamurana ban shigo gidan mijina da wani sihiri ba ko magani da ayar Allah dai na shigo a bakina. Na sauke su bayan nayi alkawarin zan nemay ta ta bani nomban wayan ta na bata kudi zai kai dubu hamsin nace tasha magani dashi tana tayi min godiya da fatan Allah ta tsare ni da diyana. Na wuce gidan maryam ina tunane a raina kan Nafisa wai ita wata irin mace ce kamar dutse wurin tauri ita watau mutuwar mahaifin ta bai shige ta ba ke nan ko. Ina shiga gidan maryam tunanen yarana da banyi warning kada a bari su fita ba ya fado min a rai nan nakira laraba ina tambayan ta yaran. Take fada min wai suna waje gurin security suna wasa nan na hauta da fada maryam na falin na shigo ina fada da laraba tana saurare na. Bata taba jin ina daga ma laraba murya haka ba irin yau bayan na gama ne na aje wayan take tambayana. Nan nake fada mata abindake faruwa dani duk abinda madam din ta fada min dan lokacin daya wuce tace wai wanan matar may take nema a gare ku ne da har yanzu batai saduda ba. Nace may ko take nema banda ran mu dai take so maryam idan ta lalata min yara ko tayi masu wani mugun abu wa gari ya waya. Wanan katon bazan yarda ba maryam idan matar nan tayi comfention bai yarda da ni da kaina wallahi zan dauki mata a kan su. Wa zai ji wanan abin bai dauki mataki ba sau nawa ake wanan maryam wani mataki kika taba ganin ya dauka a kanta koda ma ya dauka din ai na dan kwana biyu ne ya bari. Na dade a gidan maryam kafin in dawo gida na samu yaran na falo suna kallo kan su na shafa kagin in zauna ina fadin. Laraba kin jini hankali a tashe na kiraki ko nan dai nake labarta mata komai ta rike haba tana salati tace haba ina nan ina fadin may na nayiwa hajita yau. Sai na koma ganin bakin nafisa ko maganan ta ban son a dauko a gidan sai dai ban gama yanke shawaran abinda zanyi ba akan abinda madam din ta fada min. Ranan dana karbi girki ne ina gurin shi ne muna hira na jeho mashi zancen nace kasan matar nan madam aminiyar nafisa ta da lokacin da ina amarya. Yace wanan bakar matar wai tana inane yanzu nace ranan na ganta a gidan nan ta fara fada min wasu magana da ban fahinta ba nace ta bari zan nemo ta ta fadi a gaban ka gamay da yaran nan. Yara kuma may ya samu yaran ya tambaya cikin kura min ido yana son jin ba asin maganan nacw wani magana take fada min wanda ni ban fahince shi ba. Yace ki gayyato ta gobe tazo karfe biyu zan dawo mu saurare ta muji abinda zata ce amma ina mamakin may ya hadata da yaran kuma. Nifa ban yarda da wanan matar ba tuncan bata a cikin tsarina haye jayen nafisa ne kawai ta dauko muna ita amna dai ai ka bari tazo muji may take son fada muna ne , . Na fada maki gobe tazo karfe biyu sai dai don Allah ki una min gobe din idan Allah ta kaimu don gudun mantuwa karna manta da zance. Allah ya kaimu nace ina kokarin tashi daga inda nake zaune naji ya ja wani uban tsuki na juyo yace ban son cakwalin mata wallahi. Nima shine ai nake gudu amma tunda ita ta nemo mu ai mu saurareta muji abinda zata ce tazo din muji ai na kwashe kayan nabar dakin zuwa part dina don na samu abinda nake so. Don haka n fara nemo shawaran anty hauwa tace bafa sakwa sakwa zakiyi ba khadija Allah ya kawo lokacin tonon asirin ta gaban Jamma,a ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 1/30/21, 6:21 AM - Fatima Amarya: Yau bai fita ba yana zaune a falo tare da yaran shi sadiyace a kusa dashi kwance sai idan taga wanda ta sani yana mata wasa ta kama dariya. Anan yake karban bakin shi yau kasancewar bai leka ko ina ba sai ko buge bugen wayan da yakeyi daga inda yake zaune. Hakan yasa Nafisa jin haushin rashin fitan shi ta samay shi gurin a dakile take mai magana yau girkin yar so ne ba a leka ko ina ke nan? Ya dago daga abinda yakeyi tare da fadin ashe akwai yar so a gidan da wa yanda ba a so ke nan sai da kika fada na sani ai yanzu. Akwai mana yanzu ga zahiri nan ya nuna da kan sa yau take sabuwar amarci a gare ku ke nan kuma ko wani sabon shirine haka ya taso ma ban sani ba. Ke kinga ban son daukan magana ke ko yaushe mutum bai maki daidai ne sai kin samu abinda kika daure mutum dashi. Bake ya kamata ki fadi maganan nan ba tace don may an mun ba daidai ba zan yi magana ba yace ke akwai wanda yakaiki samun dama na a gidan nan bayan ki. Tace zancen da ke nan kake mun ba yanzu ba da ake kirana banda ilimi bayan ansan bada illimi ka aure ni haka na. Yace sau nawa ina cewa zan maida ke karatu kina nuna min baki so, haka sai yanzu ne zaki zo da wanan maganan. Dama can ba so kake inyi ba don kasan abinda kake nufi dani sai yanzu na gane hakan daga yanayin ka. Yace tunda kin gane may ye na magana yanzun kuma sai a barshi a yadda kika fahinci manufana din suna cikin wanan takkadaman ne na fito na samay su a falo . Kokarin, zama nakeyi ina sauraren su gani na baisa ta fasa fadin maganan da take fadi ba a lokacin take cewa wai wa nafi boko da wayewa da zai dauke ni ya fita dani waje ni kadai. Kokana tsanman bamu fahinci nufin ka bane wai duk tsiyan mutum dai wani yafi shi boko da wayewa don ba a kanta farau boko ba. Ina jin su nace yanzu kuma na daina tsafin da boko nake maki sallo ke nan idan kin yi fushi ai sai ki fara yau koda yaki da jahilci ne ko zaki san Annabi ya faku. Kece jahila da baki amfani da ilimin ki sai kin hada da tsafi da asiri kin kama miji dan ya fita zancen kowa idan kin kama su shida wanan bakar matar tashi ni ba zaki taba kamani ba kin sani. Wacece bakar mata muryan Fati ne dake fitowa take tambayan ta a bayan mu tace duk sherin ki Nafisa sai kin gani a gidan nan. Ke ba a kyamace ki ba sai kece wai zaki kyamaci mutane alkadaein rinki ya dade da karyewa a gidan nan tunda Khadija ta shigo gidan nan ko. Don duk wani abinda kike takama dashi khadija dai tafiki shi a yanzu don ko kumbar kafanta baki kama ba a wurin komai wallahi. Tace karya kike wallahi gashi nan ki tambaye shi don ita ma tasan bata kama kafana ba a gidan nan nace gurin sheri ba lalai kam ban kama kafan ki ba kan wanan. Sai dai duk sherin ki ki sani bai tasiri akaina koda na ke ma fada dake tsayawa bata baki ne ai don matar da bata san Allah ba may zai sa a tsaya bata lokaci a kanta. Sai dai ki sani idan baki bar shige shige a kaina ba kina gab da haukacewa wallahi tace samad kadai ji may tace da bakin ta. Barin fada maki in har kin je gun malaman ki ne sun fada maki haka to nafi karfin ki da malaman naki don kar nake kallon ki duk wani iya shegen da kike tunanen kin iya na damaki na shanye a gidan nan. Kai ya isa haka yace yau dai duk karyan mai sheri zai kare ai don gaskiya zatai halinta don in har naji wani abu da bai kamance ni ba zanyi maganin ko wanene a gidan nan. Baku kadai bane mata a garin nan kuma ban ce zan zauna da mace daya ba a cikin ku da kowan ku ta aure ni ta samay ni da iyalina duk abinda kuke yi na sani tara maku nakeyi kawai. Ya dauki waya yana fadin zaki iya shigowa yanzu yana fadin haka ya kashe wayan tare da cewa duk ina son ku natsu ku bani gankalin ku ga baki nan tafe yanzu. Kowa ya dauka wasu baki ne zasu shigo sai ni da na san zancen ko ni kuma ban dauka cewa ita din bace a lokacin zata shigo. Mun dai kai wani lokaci ba mai magana a falon sai harare hararen juna mukeyiwa junan mu daga inda kowa yake zaune a hasale da dan uwa. Sadiya tafara dan fitina ya juyo inda nake yana fadin ki dubata kila wani kazantar tayi kin santa da tsabtan banza naji wani iri a raina sai can na dan mike zuwa wirin yarinyar. Na fara duba permpers din jikin ta na samu fitsari tayi shine yake damun ta ina kokarin cire mata ne na kai zaune dama da wani a hannuna da na dauko in canza mata uwar sai wani tabe baki take faman yi. A lokacin madam da wanan matar sukai sallama ya karba masu Nafisa dake zaune ta wani dan zabura sai kuma ta dake tana fadin may kuma ya kawo ku gidan nan yanzu na fada maku ban son bakin nacin tsiyar nan fa kubar mutum ya huta hakana don Allah. Sai ga madam ta zube a kasa da kyat tana fadin barkan ku da hutawa Alhaji ya amsa mata fuska ba wani walwala sai Nafisa tace wanan akwai makwaidaita. Mutum baida wani moriya sai bakin nacin tsiya haka ke rufa min baki don ba gurin ki suka zo ba ko ta ce gunki tazo da zaki tare da wullakanci. Watau kinci moriyar ta yanzu Allah ya mayar da ita haka kike gudun ta ko ke ko kunya baki ji na yiwa wanan matar data rike ki amana da can waya san tsakanin ku. Madam dake dan share kwalla tace wallahi Alhaji wanan abin yasani yin nadaman sanin wanan matar a yanzu don a sanadinta ne naci karo da wanan halin rayuwan da nake ciki a yanzu. Nafisa tace da kike min wahala ba biyan ki nake a lokacin ba ko a banza kike min duk abinda kike min din a lokacin. Haka kika dauka ke wanan dalilin yasa nazo gurin Alhaji yau in fada mai komai da mukayi dake a baya ko Allah zai sausauta min halin da nake ciki yai min rangwamay a halin da nake ciki. Ta kare magana tana sharan hawaye da gefen gyalen ta yace ke nan kun dade kuna aikata wani abu wanda bai dace ba har kike ganin yana daga cikin abinda zai sa ki samu lafiyan ki idan mun yafe maki. Tace kwarai kuwa Alhaji Abdul samad don wallahi mun aikata maka abubuwa da dama kai da iyalin ka sai hajiya khadija ce tafi katfin mu. Don dama an fada muna tun da zancen auren ku ya taso da ita kan idan muka matsa zamu iya ganin ba daidai ba kasan abinda zuciya ke so ni kuma dan abinda take bani a lokacin yana rudina sai idon mu ya rufe ala dole sai munga bayan ta tabar gidan nan da karfi da yaji. Nafisa ne ta tare ta tana fadin sheri kika zo ki min ki kashe min aure na ko may ke kinki aure don nace na tuba bana wanan harkan yanzu kike son ki kulla min sheri. Babu sheri a cikin zance na yanzu ke ma kin sani don shekaran jiyan nan kika kirani akan mu dora a inda muka tsaya kina son in sa a lalata rayuwan yaran hajiya khadija ko ta halin kaka. Mazan a maidasu yan shaye shaye da sata macen kuma a lalata mata rayuwa ta dinga bin maza dakata don Allah yace a hasale. Madam taja bakin ta tayi shiru ya juya wirin nafisa yana fadin kunyi haka da ita ko bakuyi ba tace yaushe rabona da wanan matar samad. Tun kan natafi Niger din nan da muka samu matsala dakai na tafi tun lokacin ban kara ganin ta ba sai yanzu yace bata zo gidan nan ba shekaran jiya tace tazo kuma na koreta. Madam ta dago kai tana fadin kai kiji tsoron Allah matar nan kece kika kirani da inzo kira hudu kikai min kafin wanan yar uwan tawa tace muzo muji may kike nema na dashi. Tana kokarin ciro wayan ta daga post din ta tace gashi ga kiranki a wayana har yanzu idan karya nake maki tana kokarin nuna mashi kiran a wayan ta. Ya dan karba ya duba ya kada kai ya kallo nafisa tare da fadin gashi kece kika kirata ya fara fadin lokaci da rana ya sake dago kai ya kalle ta. Madam tace ba wanan ba ai ina da record din maganan da mukayi dake a ranan don shedan haka don nasan koda ban maki ba wata zaki sa tayi maki tunda kinyi niyar hakan. Kuna muna recording din muji yace ba tare da ya kalli kowan su ba dan lokaci ta dauko tana neman recording din ta miko mai wayan. Nafisa ce ta mike zubur tana fadin Allah ya isa tsakanina dake madam sherin da zaki min ke nan bayan yadda na dauke ki a zuciyana. Zaki rufa muna baki ko sai na bata maki rai taja bakin ta tayi shiru tana mazurai zaune nake na harde hannaye na saman kirjina ina kada kafa a gefen shi tunda na sakawa sadiya permpers nake gurin ban daga ba. Bayan gaisuwa ta fara fadin dama na kiraki ne mu dora inda muka tsaya don na gane su sabuwa kudina kawai suke ci a banza yanzu. Aiki dake yafi min dadi sai madam din tace hajiya aiko da ban guje ki ba ban kuma yi tsanmanin zaki min hakan da kikayi kika guje ni ba. Yanzun dai kada mutsaya dogon bayani dake wanan yar banzan yarinyar nake son a shiga tsakanin ta da maigidan nan suyi rabuwan wullakanci da junan su don ba zan zauna ina kallo yana tafiya da ita ba ina zaune. Sai yaranta da nake son a lalata masu rayuwan su tun yanzu su danbale ya kasa tsaron su don ba zance ayi yadda akaiwa fati da diyan ta ba don gashi yanzu itama bata zauna ba tana kokarin dawowa cikin rayuwan shi har daukan diyan yayi yakai waje karatu. Madam haka zan zauna duk buri ba akan Samad ya tafi a banza ina son in gama da wanan fitsarar kafin in dawo kanshi shi maigidan. Madam tace hajiya Nafisa ba zan maki karya ba gaskiya na daina wanan harkan yanzu wanda ma nayi a baya ina rokan Allah ya gafarta min ne. Kema da zaki bi shawarana da kin daina wanan harkan na bata don babu komai a cikin sa sai tarin nadama da dana sani mai tarin yawa a cikin sa don ni sheda ce kuma na gani. Katse ta Nafisa tayi tana fadin dakata madam ba wa,azi nakiraki ki min ba anan taimako na nema a gare ki idan ba zaki iyaba sai in nemo wata tayi min abin kudi ba fa kyauta zaki min ba kin sani. Haka kawai don guntun wa,azin ki in zauna ina kallon gida nason fita a hannu na tun shigowan wanan fitsararan yar matsafan na kasa gane kan gidan nan ga baki dayan shi. A nan recording din ya katse sai madam ta dora da fadin nayi mata wa,azi yadda zata fahince ni karshe ma sai koran kare tayi min da mugun fata ta hanani kudin mota. Haka muka fito muna tunanen yadda zamu koma gida don ko na zuwa aro tace inyi muzo sai Allah ya turo muna hajiya khadija zata unguwa itace ta taimaka muna ta sauke mu a gida. Shine dalilin da naji ya kamata in nemaku in fada maku gaskiyan irin kuskuren da muka tafka a baya ni da ita don ni gaskiya yanzu na tuba nabi Allah na daina wanan halin ga baki daya wallahi. Munyi sanadin rabaka da iyayyen ka mun raba tsakanin ka da matanka fati gata nan da diyan ka da ma kokarin rabaka da khadija wace ta buwaye mu ita da yaranta sai aminin ka babba abokin ka yusuf shima mun sha zuwa guri kanshi muga mun shiga tsakanin ku. Khadija mun hana aurataya a faru a tsakanin ku dayake Allahku yafi namu sai aune da ciki mukayi a jikinta a lokacin gun wanan lokacin na tsuke da lamatin khadijan. Dama ana fada muna duk inda muka je cewa ita tsaye take ga kai kukanta a gurin Allah ko yaushe ba zamu iyata ba kaji dan abinda na ke da niyar fada ma dama don Allah ku gafarce ni ga baki dayan ku ko zan samu sa,ida a raina. Bayan ya nisa yace da da fa kikace hajiya wanan zancen ya wuce dan labari ai don rayuwana gaba daya kuka gurgunta dana iyalina Nafisa may nayi maki a rayuwana kike nema kiga bayana. Shiru tayi sai kwallan da take matsa a fuskanta yace ba kuka zakiyi ba bayanin zaki min yadda zan fahinta. Shiru falon yayi na dan wani lokaci sai fati ne tace tsakani na dake nafisa Allah ya isa wallahi don ba zan taba yafe maki ba. A baya ina zargin khadija da tazo ta mallake mijin ita da tazo daga baya ta samu fifiko akan mu da komai sai daga bayane nazo na gane ba haka rayuwanta yake ba. Ita di mai kaunane da yara na ban kai ga tabbatar da haka ba sai da yazo da zancen zai kai yara karatu madina inda ni da yan uwana muka zauna suka kara fahintar dani kan khadija din sosai. Dan zaman mu da khadija ta fitar dani daga wani kangin rayuwan da na shiga a baya na gane tana kokarin kusantani da mijinane sabanin ke dake kokarin nisantani dashi a baya. Zuwan mu can inda suke zaune ya kara gaskanta mun tunane a kanta yadda ta rike ni kamar ba kishiya ba har girki ta bani acan da kuma muka dawo nan ta kwadaita min zama daku a guri daya. Ke ko fa ba wani alheri ga shigowan ki a rayuwan mu sai komawa baya tirda hali irin naki wallahi madam tace baku gane ta bane tun farko don ta taba fada min a baya so take ta kammala mijin ku ta kwashe komai nasa ta koma kasan su da zama don tasan ba zai bita can ba ya zauna. Nafisa kinji duk abinda aka fada ba karya a cikin sa halin ki ne kuma zaki iya yin shi ke kuma madam na dawo gare ki kafin in san irin hukuncin da zan yanke a kanta. Yanzu wanan abinda ya samay ki idan kina da tunane ya isheki ishara akan sa tace kwarai kuwa Alhaji na dade da nadama batun yau ba. Don ni nasan abinda nagani kan son mu halaka yaran nan kokuwan su ya dawo gare ni shine har yau ban kara lafiya ba don dama ance tagwaye akwaisu da kokuwa a tare da su. Ba tagwaye na ba kawai duk dana koni duk wanda yayi gigin tabamu a gidan nan zai ga abinsa don banyi wa kowa sheri ba don haka wanda ya nufo ni dashi a kansa zai koma. Karya kike wallahi an fada min yadda nake tsaye kema haka kike tsaye a gidan nan madam ce ta ba ta amsa tace don ance muna tana tsaye ba ana nufin abinda mukeyi shi takeyi ba na dade da fada maki hakan amma kin ki kiji. Nafisa you are very stupid har kina ganin kin samu bakin magana a gurin nan yanzu kin san girman abinda kikayi kuwa. Rayuwan mu ne fa gaba daya gidan nan kike nema a hannun ki don baki da kunya har zaki dauka kinci bulus ke nan ko ba zan sake ki ba ko in kore ki kin ci albarkacin wa yan nan diyan da muka haifa dake. Amma zaki zauna a gidan nan zama na dake da babu duk daya a gurin kowa kada kiyi tsamanin zan barki ki gudu ba gudu ko zuwa wani guri a wuri ki. Don duk inda kika shiga a duniyan nan sai na tonoki ki zauna yadda kika so ganin sauran ke ki zauna a haka kuma zan kara fada maki wasu dokoki da zan kafa maki. Amma kafin nan yanzu barin sallami wanan matan mutanen ki yace su tashi su fita suka mike suna muna sallama suka bi bayan shi. Ya dan jima waje tare da su kafin ya dawo ya samay mu sai zuba habaici anty Fati keyiwa nafisa bata samu bakin maganan ramawa ba. Koda ya dawo bai furtawa kowa komai ba ya haura sama ya barmu a gurin naso jin matakin da zai dauka amma sai ya bar mu a duhu ga zancen. Itace ya kamata tayi girki a ranan sai yace fati ta karba nidai ido na sa mashi har in fahinci may yake nufi da mu kan zancen. Sai bayan kwana biyu ne na fara fahintar komai don haka zai dawo ya zauna damu a babban falon gidan da yaran mu nan zamu zube ai ta hira da raha ita kuma tana daki da yan uwanta ba wani walwala ko ni shadi a tare da ita. Ga Ihisan daya hana ta zuwa gurin Nafisa din koda wasa yarinyar ta tsorata sosai dashi bata zuwa wurin nafisa din koda baya gida. Haka yasa samira ma ta dawo mu,amula damu idan muna falo itama anan zata zauna gurin mu koda uwar ta kirata minti biyu yayi yawa zata dawo inda muke din. Har komawan mu yayi wanan karon da Ihisan muka tafi Nafisa ta tayar da hankalinta sosai har takai karan shi gurin iyayyen shi. Abba ya kirashi nan dai ranan ya warware ma Abba komai na zaman su da nafisa din bayan ya gama sauraran shine yace ka kyauta da bakai saurin sakin ta ba. Don idan mace ta kauce irin haka ba saki ne abin yi gare taba kamata yayi namiji ya horata a gida ko zata gane ta dawo hanya madaidaiciya ta gyara halin ta. Idan ta gyara zaka gane idan kuma ba mai gyaruwa bace zata koma ma halinta kaga a wanan lokacin duk matakin daka dauka a kanta shine daidai. Amma sakin baida wani amfani gare ta sai kaga mace bata hakkura ba ta koma ga wani hali wanda bai dace ba yanzu dai idan tana da hankali zata gyara halinta tunda ta gwada taga ba wani riba ga mace mai irin halinta. Shi saurin saki illa ne gama ga haihuwa a tsakanin ku duk inda tabi dole mutane suyi kwatance da kai suna fadin tsohowar matar wani ne uwar yayan shi. Sai yara su taso basu san abinda ya hada iyayye fada ba sai su dauka don wance aka saki uwar mu ba sauran shiri tsakanin su da wanan matar ta gida kaga an samu akasi a gurin. Don haka na gamsu da bayanin ka don ba matar da za a barma diya ta tarbiyartan dasu bane da wanan halin nata. Yayiwa Abba godiya washe gari muka daga muka bar kasan nan muka barsu da Fati a abuja zaune ba wanda ke shiga alamarin dan uwa. Bayan wata uku yake shigowa ya koma wanan tafiyan mun dauki lokaci sosai bamu zo Nigeria ba har muka kai sadiya asibiti akai mata aiki a kanta watan mu daya a can Anty Fati ne tazo ta zauna muna da yara har mu dawo. Alhamdullahi aiki yayi kyau sosai don an gyara kan ya koma daidai yanzu ta fara tafiya bata san uwarta data haife ta ba sai ni ba wani ban bancin da nake nunawa a tsakanin su da diyan dana haifa. Sai dana kara haihuwa ya bari nazo Nigeria lokacin na bunkasa sosai na kara ilimi yadda ya dace ko wanan zuwa munyi shi ba a cikin dadin raiba don jikin Abba da ya kiya yana asibiti kwance. Na daukarwa yarana hutu muka shigo Nigeria yarinyar da nake riko itama ina jin dadin ta ban barta ta zauna haka ba sai da tayi karatu a can. Mun zo da kwana daya muka wuce kaduna duba Abba ranan yayi fada da anty fati na rashin zuwan su duba Abba din don cewa tayi bai bada bakin su tafi bane. Don haka bamu je tare dasu ba yara kawai muka aje a gidan wurin Binta muka nufi asibiti inda muka samu Abban a cikin wani yanayi na jin jiki sosai. Yana ganin mu duk da sunce bai magana sai gashi yana murmushi yana son ya yunkura ya tashi ya kasa. Mun dade a gurin Abba din kafin mu dawo gida washe gari su maryam suka iso da safe da yaranta biyu . Sai su Anty Fati da Nafisa da suka zo suma ga zainab da yaranta muka cika a gurin Abba din don yace muzo mashi da yaran ya gansu. Ranan anyi murna kwarai da jin saukin Abba din don alama ya nuna ya dan samu lafiya ina hada mai abincin da zai kara mai kuzari ya kara jin katfin jikin shi sai gripe water irin na yara da nake sa momy ko anty amarya su bashi. Don yana taimakawa sosai gurin mutumin da ya dan manyanta ya ji karfin jikin shi ba wani hayaniya sai dai na kula da Nafisa dake son jan yaranta a jikin ta. Yaran daine basu bude ido da ita ba don haka basu damu da al,amarinta ba ko inda take basu zuwa. Ga na kula har lokacin ba yarda a tsakanin ta da maigidan da ma yan uwanshi dake yawan hattaran ta a kusa dasu. Satin mu daya Abba yace ga garin ku muka tashi a cikin tashin hankali don ban tabs ganin AA ya shiga irin halin da ya shiga ba a ranan. Anyi zaman makoki na kwana uku mutane suka watse har mutanen Niger ( minna) sunzo mota uku yan uwa da abokan arzikin mu da yan uwana na Ka,oje suma sai da suka ciko bus sun zo min gaisuwa don muna zumunci sosai dasu. Satin mu uku kaduna muka dawo Abuja inda yanzu nauyi ya karu akan AA din Allah ya taimaka yana da karfi sosai ya kawo saukin abin. Don bamu dawo ba sai da ya hada kan gidan nasu ya ba wa kowa abinda yake bukata ya biya wa yan makaranta kudi school fees. Nan ya gane tsohon ba karamin kokari yake akan iyalin shi ba gashi ya hada kan zurian shi guri daya kafin ya tafi ba wani baraka a tsakanin su sai dai wanda ba,a rasa ba din. Ranan da muka dawo don su Nafisa sun rigamu dawowa ita da Fati sai daga baya muka dawo nafisa tayi abinci amma da muka iso tace tabar min girki nace a a tayi abinta. Nasan yana daga cikin halin da take son nuna mashi ne na nadaman ta a yanzu sai dai duk wanan abin bata burge shi ba don tsanan ta ya riga da ya darsu a zuciyar shi ko. Zaman dai suke hakana bai yarda wani daga cikin mu ya nuna mai banbanci a gida ko kadan wanan abin yana damun nafisa don kishi a zuciya yake haline na halitan mace sai dai na wata yafi na watane kawai. Idan ya tuna da maganan Abba yakan ji jikin shi yayi sanyi akanta yaso yayi koyi da abinda Abba din ya koyar dashi. Da alama ba zamu koma kasan waje ba don yaran daya nemawa makaranta anan yanzu suna falo zaune na fito da yara zan kaisu islamiya ko wanin su yasha fararan kaya da hula. Sai sadiya data rike min hannu muka fito tare tana min shagwaba nayi masu sai mun dawo nafita da yaran ta bimu da kallo. Lokacin maigidan baya gari yayi tafiya washe gari koda na fito banga motar nafisa ba yasa nasan tafita ne har na dawo gidan maryam ina zaune ina cin abinci wayana yayi kara na dauka. Yusuf ne muka gaisa yake tambayana ko akwai wace ta fita ne a cikin mu nace ban tsan mani ba sai dai barin sa Sadiqa ta duba min. Ta dawo tace ance nafisa ce ta fita na kirashi ina fada mai yace to sunyi accident yanzu aka kirashi ana fada mai hanyan keffi. Na maimaita kefi kuma yace eh gashi ma yazo asibitin da aka kawo su sai dai ance a motar wasu sun mutu wasu kuma sunji ciwo sosai. Hankalina ya tashi na mike na fito ina fada ma fati tace subbahanallahi. Dama tunda naga ta fita ko sai dawo batai muna ba nake zargin wani abu Allah dama ba azzalumin kowa bane yanzu haka wurin bakar biye biyen bokayen su ne haka ta faru dasu. Nace kada tace haka ya kamata musan da wa yanda ta fita samiha tace da yanyala suka fita dawata kawar su. Munje asibitin mun samu tana a wani hali ba a bari mun ganta ba sai yake fada muna sauran sun rasu ko take a gurin da abun ya faru. Ita ma dai tana a wani yanayi ya kira AA bai samay shi ba yana dai trying din layin shi har yanzu salati na saka tare da fadin yanyala ce wanan dattijuwar da suke tare. Sai dare ya samu layin AA din yake fada mashi abindake faruwa yace gamu tare a gurin su yace a bamu wayan ko ya saka a handfree kowa yaji. Ya fara fadin may yasa kuka fito bada sani na ba ku koma gida kada kuma wace ta kara zuwa asibitin nan a cikin ku dama amana ai gudace na fada mata duk wanda yaci amanan wani a cikin mu Allah ya baiyana shi. Yanzu gashi ashe bata bar wanan halin nata ba zanyi magana ya kashe wayab shi dole muka dawo gida kamar yadda yace don bin umurnin shi. Sai dai ina tura laraba ko Sadiqa sukai masu abinci acan saboda Allah bayan kwana biyu ya dawo garin abincin ma daya gane ya hana kuma baije asibitin ba ya dubasu. Kafanta ance sai an fita da ita waje har kano aka tura su sunce bazasu iya ba sai dai idan yanke mata zasuyi a nan. Yan uwan ta sunzo daga Niger sani Allah sani Annabi ya yarda ya bada kudi koshi don hajitan su ne data saka baki ya yarda aka fita da ita waje. Watan su hudu a can ta dawo saman keken ta ba kafa ba zuwa gurin boka miji kuma bai kulata tana dai zama a gidan zaman takaici da dana sani. Tana kuma kallon gata da ranta anayi bada ita ba ga duniyan ga komai amma jin dadi yafi karfin ta yanzu sai dai ido. Nikan sai yara nake zubawa a gidan sai dana haihu bakwai dashi na dakatar da haihuwa badon ya so ba ga aiki da nake dan tabawa ina aiki da humanright yanzu. Masha Allah da fatan kun fahinci darasin da wanan sakon ya kawo maku badon kowa zai gamsu ba sai wanda Allah ya ba ikon gamsuwa da hakan dogara ga Allah shine mafita, ga bawa. Kyau ko nasaba bashi zai kai mu ga abinda muke burin samu ba kyakyawan hali da dogara ga ubangijin mu shine alfanu gare mu da fatan zaku yafe min kurakuren da na rubuta a ciki sai mun hadu a sabon labarin mu mai suna kanin ajali Nagode kwarai da kaunar da kuka nuna min wanda ba hikima na bane abin daga Allah ne don Allah mu yafe ma junan mu yan uwa. Taku har kullun zainab din ku labarina dai sai anyi hakkuri dashi akan zamantakewan rayuwan mu na yau da kullun ne a gidajen mu na hausawa. Nagode nagode nagode da kaunar ku gare ni da fatan zakuyi hakkuri danu hakana. Sai mun hadu ma,assalam ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU