[10/8, 18:30] Badiat Ibrahim: NA FAƊO DAGA BENE... NA ZARCE RIJIYA Hakkin mallakar Badi'at Ibrahim Mrs Bukhari b4b gidan ƙamshi Gawurtattu uku Lamba ta 1 Samfoti! Samfoti!! Samfoti!!! ( ƊANƊANO) Ƙabilar Hausa dai, ƙabilace dake zaune a arewa maso yammacin taraiyar najeriya da kudu maso yammacin jamhuriyyar Nijar. Ƙabilace mai ɗimbin Al'umma, amman kuma a al'adance mai matuƙar haɗaka, a ƙalla akwai mutane miliyan hamsin da harshen yake asali gare su. A tarihi an ce ƙabilar hausawa na tattare a salasalar ko manyan birane. Hausawa dai sun samu kafa daularsu ne tun daga shekarar 1300's, sa'adda suka samu nasarori da dauloli kamar daular Mali songhai, Borno da kuma fulani. A wasu lokutan Hausawa sun samu gagarumin ikon mulki da haɗaka ta kau da baƙi ƴan neman ruwa da tsaki, da kuma neman aringizo a cikinta, da kuma halƙallar ko cinikin bayi. A farko_ farkon shekaru na 1900's, a sa'adda ƙabilar Hausa ke ƙoƙarin kawar da mulkin aringizo da Fulani , sai turawan mulkin mallaka na burtaniya suka mamaye arewacin Najeriya da kuma kafa manufofin mulkin bayan gida, a bisa ƙarƙashin mulkin burtaniya, ƴan mulkin mallaka sai suka marawa fulani baya naci gaba da manufofin aringizon siyasarsu. Wannan haɗakar gamin gambizar an farota ne tun asali a matsayin fulani su ɗare madafan ikon a tsararren tsarin siyasar arewa. Akasarin masu mulki na fulani sun kasance a yanzu al'adance Hausawa gwamitse ko da yake Hausawa na farko_farko maharbane, amma ya zuwan addinin islama da kuma karɓansa da hannu bibbiyu ya sanya labari ya sha bam_bam. Ginshiƙoƙin al'adun Hausawa na da matuƙar zaranta, kwarewa da kuma sanaiya fiye da sauran al'ummar dake kewayenta. Sha'anin noma ita ce babbar sana'ar hausawa inda Hausawa ke ma sana'ar noma kirari da cewa, na doke tsohon ciniki kowa yazo duniya kai yatarar, akwai kuma wasu sana'o'in kamar su sha'anin jima watau harkar fatu, rini, saka da ƙira. Fannonin dake mutukar samun cigaba a harkokin sana'o'in hausawa. Hausawa dai sun jima da shahara wajen harkar fatauci kana kuma masu arziki na taka rawa a sha'anin yau da kullum, tare da masu mulki da masana. Harshen Hausa shine mafi girma da mafi sanaiyar harshe a nahiyar Afirka. Harshen Hausa ya aro wasu kalmomi daga wasu harsuna musamman larabci kana kuma harshen na tafiya tare yanayin mu na zamani bisa al'adar cuɗeni_ in _cuɗeka. Harshen Hausa dai ya zama harshen yau da kullum ga miliyoyin jama'a da ba Hausawa bane a nahiyar Afirka. Bugu da kari akwai cincirindon al'ummar Hausawa a manyan biranen yammacin Afirka da arewacinta da kuma yankunan cinikayyar al'ummar Hausawa da kuma yankunan da Hausawa suka jima suna bi a hanyar ta zuwa aikin hajji. Akwai kuma rubutattun adabi masu zurfi da kasidodi da kuma rubuce-rubuce a rubutun ajami da aka buga tun kafin zuwan turawa ƴan mulkin mallaka na burtaniya. Har ila yau kuma wani tsarin rubutu a ajami da aka ƙirƙiro tun kafin zuwan turawa da ba kasafai ake amfani da shi ba yanzu. Wannan shine takaitaccen tarihin Hausawa. Jihar Filato (Jos) Jihar filato, jihace mai sanyin gaske, garine mai ni'ima, dan Lokacin damina ana samun wadataccen ruwan sama masha Allah, sannan babu yawaitar zafi sam ko da lokacin zafi ne ya shigo. A da yankin Haifam, wannan yanki na Haifam tsabar sanyi ance har dusar ƙanƙara tana zubowa, amman wannan labarin da jimawa sosai tun duniya na kwance. Wannan dalilin yasa turawa suka miƙe ƙafarsu a garin jos . Gasu da arzikin kuza, da noma. Kowa ya sani garin jos sune dankalin turawa, dankalin hauwa ( dandikwali, ko fasa ƙirji), da kayan gwari. Suke raba ma garuruwa da dama kaya, musamman kudu. Suna da atile, suna da risga, suna da lemun tsuntsu, akwai tsada, akwai bado, da sauran kayayyakin ciye ciye iri_iri. Garine mai cuɗanyar yarirrika masu tarin yawa kamar irin su. Hausawa, yarbawa, inyamurai Fulani. Sai kuma ƴan ƙasa irin yaren birom, angas, tsala, tubi, maguzawa, Arago, da dai sauransu. Ada ana zaune zaman lafiya da amana tsakanin ƙabilu mabanbatan ra'ayi da addini, ana rayuwa a cakuɗe cikin soyayya da yardar juna. Daga shekarar 2001 rikece_rikicen faɗan addini ya kunno kai jihar ta filato, wannan tashin hankula shine ya daƙile tattalin arzikin jihar, ya kuma jefa tsoro da fargaba a zukatan mazauna jihar, har ta kai ta kawo, kirista na tsoron gamuwa da musulmai, musulmai na tsoron gamuwa da kirista, sabili da kisan mummuƙe da suke yi a junansu. Yaƙin farko da aka soma gudanarwa an yishi ne ranar juma'a a wata anguwa da ake kiranta ( kongo rosha, a babban masallacin juma'a na gidan Alh jojibes) wannan rana itace ta zama tamkar matattakalar rikici, domin wata kirista aka wakilta tayo shiga irinta banza, tazo ta wuce ta gaban Sallah. Al'amarin daya tada zaune tsaye kenan, an zubar da jini, an yi kashe_kashen rayuka a wannan rana daga ƙarshe aka saka dokar ta ɓaci na ba shiga ba fita tsawon awa ashirin da huɗu. Har izuwa yanzu jihar filato bawai ta zauna lafiya bane. Har gobe ana rikici a tsakankanin fulani makiyaya, da kirista manoma. A baya ma an yiyyi irin wannan tashin hankula tsakanin Fulani da makiyaya a ƙauyan ( dogo na hauwa) Duk ƙasar da babu zaman lafiya talauci ke mata dabaibayi, haka talauci yaima garin filato dabaibayi, talakawa su suka fi yawa a jihar filato, masu kuɗin cikin nasu basu da yawan azo a gani. Sakamakon ƙone babbar kasuwar taminos data kasance kasuwa ta uku a fannin kasuwanci da hada_hada, musamman kasuwancin gwanjo. Kuma har gobe wannan kasuwa a ƙone take, sakamakon ƙone kasuwarnan ya sanya Al'umma da dama a cikin ƙangin talauci, hakan ya sake taɓarɓara tattalin arzikin jihar, sakamakon hakan jihar ta samu ci baya sosai, kuma baƙi ƴan cirani sun rage shiga jihar sasakai. LAYIN ƊAN MARAYA JOS. Layine da marigayi Alh Adamu ɗan maraya wannan shahararren mawakin na gargajiya ɗaya tamkar da dubu ya zauna, kuma har gobe gidanshi yana cikin wannan layi. A bayan gidanshi akwai rafi wanda wannan rafin shima an yi mishi inkiya da ( rafin ɗan maraya) Unguwace mai cike da ɗumbin tarihin gaske. ( Allah Ubangiji yai mishi Rahama yasa Aljanna ta zamto makoma a gareshi Ameen) Gidane madaidaici mai ƙaramar ƙofar shiga da dogon zaune, a cikin zauren akwai ɗaki falle ɗaya a ciki wanda anan mutan gidan suke ajjiye shirginsu. Daga cikin gidan kuma filin tsakar gida na hango madaidaici wanda yaji sumunti sumul sumul, daga gefe akwai rijiya da murfinta. Ɗakuna uku ne a jejjere ko wanne ɗaki ciki da falo ne, sai wani ɗaki falle ɗaya daga can gefe daban. Ga bayan gida a tsakar gidan da kicin duk a tsakar gidan. Tsakar gidan duk datti da tulin kwanukan wanke_wanke harda ma tsunmokaran kayan wanki. TANI: Yau da kwalima na tashi kasancewar yau jajiberin babbar sallah ce, gidan ya kacame da tarkacen kwanuka da kayayyakinmu na wanki ni da yaran. Unguwa kuma ta kacame da toye_toyen kayan fulawa da suyar kaji, da suyan miyar sallah, kamshi kamar zai kashe mu. Katifar yara na kinkimo na fito da'ita tana yararin ruwan fitsari, ta jikin bangon ɗakina na jingine katifar dan rana in ta fito ta doketa ko Allah zai sa ta bushe kafin wani daren a kuma jiƙeta ta fitsari sharkab. Hajiyayye dake bakin kofarta ita da ƙannenta suna faman murzar fulawa zata yi toye_toyen Sallah, tayi maza ta toshe hancinta tare da sakin wani tsaki mai ɗan banzan ƙara. A ƙirjina naji dirƙar tsakin na abokiyar zamana, amman sai nayi biris tamkar kurma haka dama nake zaune a gidan. Hindatu ƙanwar facalarmu ce ta fito daga ɗaki hannunta riƙe da baƙin bokiti shaƙe da daƙwa_daƙwa kajin gidan gona. Gawayi ta shiga jerawa a kan kurfo dinta, tana yi tana ƴan waƙe_waƙenta dan Hindatu gwanace wajen rero waƙoƙin ƴan wasan Hausa, musamman waƙoƙin mawaƙi ado gwanja. Balaraba ce ta ja zanina tace. "Umma Sulaiman ya gama tsefe mun kan ya wanke mun?" Murmushi guntu nayi mata na dubi gashinta nace. Ki zauna ki jirani zan duba miki ko ƙwarƙwatar kan ki sun mutu" Dariya Balaraba tayi tana susa kanta tace. "Umma ai Yaya Sulaiman ya cire mun guda goma suna ƙirgawa da Sani." To kije kice mishi yaci gaba da cire miki kafin in gama wanke kwanukannan." Da gudu ta koma ciki, ni kuma na zauna a kujera ƴar tsugunno da ƙyar abinka da mai ciki, kuma cikin ya girma sosai. Ina wanke ƙwanukannan ina tunanin rayuwa, ni tunani nake yi shin Aure ne bai karɓeni ba, ko kuwa haka yanzu mazan hausawan suka zama ne, Aure da saki ya zama tamkar ado a ƙasar Hausa ko ince a ƙabilar Hausawa. Yarinya ƙarama sai ki ganta ashe bazawarace, ko kuma yau ayi aure ringiɗi_ringiɗi gobe a sako mace, na kuma rasa a ina matsalar take daga mazan ƙabilar hausawa ne, ko daga matan ƙabilar Hausawan ne? Wannan amsar ita na gagara samu, amman zukatan mata da iyaye yana soyuwa da wannan yawan mace_macen auren, kuma a kullum abun sake ta'azzara kawai yake yi, ina malamai da hukumomine shin basa ganin halin da ƙabilar Hausawa ke ciki ne ko yaya?. Ajjiyar zuchiya na sauke kaina sai sarawa yake yi, cikin kankanin lokaci na game wanke ƙwanukannan tas na shanyasu a kan tabarma dan su bushe. A gurguje na farma wanki, wankin yana da yawan gaske, dan har sai da ta kai ta kawo bamu da wankakken kaya ko guda ɗaya daga ni har yaran. Sabulun nera saba'in da omon hamsin bazai mun ko kwatan wankin ba, zan dai yi iyakar wanda ya sauwaƙa sauran kuma in koma dasu ciki. Ina cikin wankin Sulaiman babban yarona ya fito shi da ƙannenshi. "Umma na gama kashe musu ƙwarƙwatar, kan Amina babu sosai, kan Balaraba da Hauwa na kashe yafi hamsin umma." To sannu yaron kirki, yanzu bari in baka nera ɗari ka siyo kumfar los maza, sai in wanke musu kan maza suje layin kitso." Ɗarin dana daɗe da tanadarta dan wannan ranar na kunto a bakin zanina na miƙa ma Sulaiman ya fita da gudu shi da mai binshi Shafi'i. Su Balaraba kuma suka nufi wajan Hajiyayye data cika gidan da ƙamshin suyan meat pie, ga cincin ma ƙannenta nata taya ta yankawa da almakashi, can gefe ga Hindatu na tafashen kaji, Sani kuma yana zaune a bakin ƙofa sai sannu yake mun. Fatattakosu Hajiyayye tayi har tana toshe hancinta wai kar su sata amai wari suke yi. Murmushi kawai nayi na dubeta da kyau da ƙaton cikinta itama a gaba, ga ƴarta Samira a zaune a can wajen rijiya tana tsefe mata kanta suna hira da Hindatu dake dakan yajin sallah. Kai kawai na girgiza bance komai ba. Ina cikin shanyar kayan dana ɗauraye Sulaiman suka shigo a guje da ledar kumfar los a hannunsu. To ku ƙarashe mun shanyar, kai Sulaiman ka dinga ɗaurayewa shi yana shanyawa. Ruwan zafin dake kan kurfo ɗina na juye a bokiti, na ɗauki bokitin da tukunyar zuwa bakin rijiya, ruwa na jawo na cika tukunyar na mayar wuta kana na surka ruwan bokitin na dawo inda nake wankin. To tawo Balaraban umma in soma sa miki ko?" Abunka da yarinta da gudu ta tawo har tana zamewa, na shasshafa mata kunfar los ɗinnan sama_sama ina gamawa na wanke mata tas, sannan na shafa ma Amina, sai autata Hauwa ƴar wata takwas da ɗoriya itama na shafa mata na wanke da sauri, dan ance mun tana maganin ƙwarƙwatane ma shi yasa na shafa musu ko Allah zai sa mu rabu da ƙwarƙwatar. Basilin na shafa musu a kan bayan ya bushe na taje musu shi tas, babu laifi suna da gashi sosai dan ma baya samun kulawa. Bayan yara sun game mun shanya ni kuma na share ruwan tas, sai na zari mayafina nace. Muje in saku a layin kitson sai in dawo in ci gaba da aikina, ku kuma ku je ai muku aski Sani tawo muje." Dai_dai zan fita nace. Hajiyayye na fita zan kai yara kitso, Hindatu na fita" Ni dai banji sanda Hajiyayye tace wani abun ba. Na dai ji Hindatu tace sai na dawo. Fita mu ka yi fararam_fararam zuwa gidan kitso, mazan suka suce shagon aski kayan jikinmu duk datti duƙun_duƙun damu. A hannun mai kitso na danƙasu na ciro ɗari biyar na miƙa mata, ɓata rai tayi tace "Gaskiya umman Sulaiman wannan yaran kitsonsu yafi ɗari biyar, gashinsu da yawa fa yara har uku, ace kitson sallah ne za'a bani ɗari biyar." Haka mai kitsonnan ta tsinkani a gaban yaran mata sa'annina da waɗanda basu kaini shekaru ba. Amman tunda ni nake nema a wajenta dole na karya wuya nace. Haba Aisha mai kitso ki taimaka, kinsan garin ya ci wuta ba kuɗi, ko guda nawa ne ayi musu nasan kuɗin nawa ya gaza ayi musu a hakan" Da ƙyar a hakan ma ta yarda, ajjiye Hauwa nayi a cinyar Amina ni kuma na fito. Ina tafe ina cizon yatsa harna isa gidan. Tun daga zaure nake jiyo muryar Hajiyayye tana ma Hindatu tsegumi. "Allah ya kiyaye tun yaushe Kaila ya dena yarda su haɗa shinfiɗa da ita, wari fa take yi yace, kuma nima wallahi ina jin warin, daga ita har yaranta, har Allah _Allah yake yi girki ya dawo hannuna dan ya more ƙuruciyarshi." Hindatu kuma ta saka shewa tace. "Ahayye daɗi, ai ko ni shigarki ta yamma ta taran mai gida in kika yi tana burgeni balle wanda akayi domunshi. Shi fa kanshi in ya shigo tsakar gidannan ya ganki, kasa gane kan shi yake yi " Jingina nayi a jikin bangon zauren ina haki, har wani duhu_duhu nake gani tsabar tashin hankalin dana tsinci kaina a ciki. Na jima cikin irin wannan yanayin da naji hirar ta lafa sai nayi sallama na shiga. "Ahh har kin dawo nayi tunanin ai zaki jira a gama musu ne?" Cewar Hindatu kenan cikin fara'a take mun magana" A"a Amina zata kula dasu ni zan ƙarashe kwalima ne. Ɗakina na shige na soma kintsa kayayyaki, babu komai a ɗakin a falo dai ledar tsakar ɗakine shinfiɗe kawai sai tarkacen kayan sawan yara, bangon ɗakin cike da jinin kuɗin cizo da yara ke kashewa a bango, haka uwar ɗakin ma take, katifa ce yashe a ƙasa sai buhunhunan kayan sawata dana yara. Share ko'ina nayi na tattare kayayyakin yara na ɗura a buhu, in banda zarni babu abunda ɗakin yake yi. Tawa katifar na kinkimo na fito da'ita. Hoɗar kuɗin cizo na dinga zazzagama katifun. Ina cikin wannan aiki mai kitso da lalle tazo yi ma Hajiyayye. Nan da nan aka soma yarfa mata jan lalle mai kyau sosai, ni kam in kai mari in kai gwauro inata mayar da kwanuka kichin ɗinmu ina jerasa a gefe ta inda kwandona yake da tukwanena. Bayan na gama na jawo tran silver da salateb da reza na soma yankama yara wanda zanyi musu lalle zuwa dare. Hajiyayye har an gama yarfa mata kitso lallen ya bushe wankewa ma take yi. Ado ne yaron aikin Kaila ya shigo kici_kici da buhun bako har guda biyu, ɗayan sai ɗigar da jini yake yi. Gaisawa mu ka yi ya wuce ƙofar ɗakin Hajiyayye ya dire mata" "Amarya gashi in ji Oga Kaila kaji ne sai tumaturi na miya da su magi, wannan kuma yace in baki kuɗin niƙa " Karɓan kuɗin tayi tana washe bakinta Ado yayi mana sallama ya fice. Nan Hajiyayye ta shiga kacaniyar wanke kayan miya, bayan ta gama wanke kaji ta ɗaura tafashensu a babbar tukunya. Ƙanwarta ce ta kai mata niƙa yayin da ita kuma ta soma jera gawayi a wani kurfo ɗin. Ina zaune sai ga sallamar Habu ƙanina da leda mai zane a hannunshi. Baki na washe dana ganshi Habu kaine a tafe daga ina haka?" "Daga wajan bara Inno tace in kawo miki nama ne da muka samu a wajan sadaka da yawa shine ta ɗibar muku, harda tumaturi" Haƙiƙatan nayi farin cikin samuwar namannan da tumatur matuƙa. Baki na washe nace. Ai kuwa na gode sosai. Habu wanke mun kayan miyan ka kai mun niƙan shi su Sulaiman sun tafi layin aski babu wanda yasan yaushe zasu shigo gidan" Bai yi musu ba ya juye kayan miyan a ƙaramin bahun ya ja ruwa a rijiya ya zuba. Tas ya wanke kayan miyar, na ɗebo tafarnuwa da ɗanyar citta dana gyara su yanzu na watsa. Bai jira kuɗin niƙa ba ya fice, nasan akwai kuɗi a jikinshi dan ba ƙaramin kuɗi suke samu a wajan bara ba. Naman na juye a ƙaramar tukunyar miya ta, naman kuwa cikin tukunyar dam, ɗaurawa nayi a wuta nasa magi da su citta da tafannuwa na rufe. Alwala nayi na shiga ɗaki na gabatar da sallar azahar ina zaune ina tasbihi Habu ya shigo da sallama. Kallonshi nayi futu_futu dashi fuskarnan tashi duk waskane ƙayayau_ƙayayau. Inno dawa ka barta a wajan barar Habu?" Ita kaɗai na bari tace kar in zauna, Indo tana wajan barar Baffa tana mishi jagora, da tare muke zuwa bara da Baffa, amman sai yai ta dukana da sanda shine mu kai canje da Indo" Kai kawai na girgiza haka kam Baffa yake, muma wanne irin duka da sanda ne bamu sha ba, in mun rakashi yawon bara daga ƙarshe Yaya Use dena yima Baffa jagora tayi. Dubu ɗaya ya ciro a aljihunshi ya mika mun. "Inno tace in baki ayi ma su Balaraba kitson sallah. Yaya Tani ni kam na tafi sai kunzo wunin sallah" Godiya nayi ma Habu har zaure na rakashi, ina tsaye ina kallonshi sai sauri yake yi, ƙafarnan tashi ba ko takalmin arziki, wasu hawaye masu ɗumi suka sulalo mun, da sauri na juyo na shigo cikin gidan. Har zuwa yamma sakaliya aiki muke yi a tsakar gidan bamu daina ba, har masu zuwa aski suka iskeni ina suyan nama, nan farin ciki ya lulluɓesu har suna tsalle tare da yin waƙar gobe sallah zamu ci naman Baba Dauda. Da dariya na bisu nima soyayyar miya nayi na juye namannan a ciki dab magriba sai ga masu kitso sun shigo an ko rangaɗo musu kitson gaba da shiku, Tubarakalla sunyi kyau abinsu. Ina gama kaye_kaye na mu ka ɗaura alwala ni da su Balaraba muka shige ɗaki, su Sulaiman kuma suka tafi masallaci. Muna sallah da yara Hajiyayye ta bankado labule ta ajjiyemun kular da take zuba mana abinci in girkinta ne, ta fice abunta. Ko da na sallame nayi mamakin abunda ya sa Hajiyayye ta kawo abincin da kanta, dan yara take kira su zo su ɗauka, sau biyu Hajiyayye ta taɓa shigowa ɗakina, lokacin haihuwar Balaraba da Lokacin haihuwar Hauwa sai kuma yau." Amina kije kichin ki ɗakko mana tran silver da muke cin abinci muci, in mu ka yi sallar isha sai kuma muyi lalle ko" Amina tace. "Umma an sha ruwa lafiya?" Shaf na mance ina yin azumin arfa da ba dan Amina ta tunamun ba, ba fa lallai in tuna ba. Sai da na sha ruwa sannan nace mata. Lafiya lau Aminana" Fita tayi daga ɗakin, sai ga su Sulaiman sun shigo. Jallof ɗin shinkafa da makaroni Hajiyayye tayi, sai soyayyen nama data ƙirgamu ta watso, daga fika fiki sai wuya, kwankwaso harda kai da ƙafa. Juye mana dukka abincin nayi mu kai bismillah muka soma ci. Ni dai ci kawai nake yi amman zuchiyata tamkar an ɗaura mun bulo haka nake jin nauyinta, kaɗan naci naji na ƙoshi ma. Kai da ƙafan na ɗauka naci, na bar musu sauran muna zaune a wajan har isha. Ina jiyo mashin ɗin Kaila daga tsakar gida. Sulaiman yace. "Baba ya dawo Umma" Bance mishi ci kan ka ba nace. Ku tashi oya aje ayi sallah maza a dawo banda wasa." Da sauri suka fice, ina jiyo Kaila yana tambayarsu ina zasu je su ka ce masallaci zasu je. Korosu yayi ya shiga sababin cewar. "Da wannan dattin kayan zaku je masallaci kuna tafe kuna zarni, uwarku bata da aiki sai son ganin ta zubar mun da kimata. Maza ku wuce ciki kafin in dokeku" A guje suka dawo ciki, ni kuma na miƙe tsaye da ƙyar nace. Ku yi sallar a gida ina zuwa bari in yi ma Babanku sannu da dawowa" Fita nayi tsakar gidan ina turo ciki gaba. A bakin rijiya na hangoshi Hajiyayye tana haskamai tocila yana ɗaure ƙaton ragon laiya" Sannu da dawowa Kaila" Kafin yayi magana aka kawo wutar nefa ta haske tsakar gidan tarwai. Hajiyayye tana sanye da gajeren wando iyakarshi guiwa da wata riga mai hannun shimi, kannan yasha man kitso sai ƙyalli yake yi, lallennan ya zauna a fatarta ɗas, sai ƙamshi take faman busawa, ko ni ta bani sha'awa ballantana Kaila mijinta. Shi kuwa Gogan namu yana saye cikin ƙananun kaya masu tsada da gani a ido, idanunshi saye da tabarau fari mai kyau, sai ƙamshin turaren 212 yake yi. Kaila ƙyalli kenan ƙyalli shine inkiyar shi, wanka kam akwaishi a wajan Kaila ga iya direshi, in ya ci wanka babu mai cewa yana da aure ma balle a yi tunanin yaranshi sun kai Bakwai" "Yanzu Shanono yarannan a haka kika turasu masallaci ɗazu? Kinga kayan jikinsu kuwa, in banda zarni babu abunda suke yi. Wannan ai wulaƙanta ni kika son yi Shanono" Ɗan Murmushin dole na ƙwaƙwulo nace. Kayi haƙuri kayan nasu masu daman ka gansu a shanya basu bushe bane shi yasa, amman baza'a sake ba. Rago muka samu? To Allah ya ba da lada" "Ameen Shanono" Yana faɗar haka suka tafi suka barni a tsaye, hannunshi riƙe da ƙugun Hajiyayye suka nufi turakarshi. Hannuna na wanke na koma ɗaki, bayan nayi sallah na shigo mana da katifinmu ciki. Sannan muka shige ƙurya ni da matan. Lalle na soma yi musu, kafin ma in gama musu duk sun yi bacci. Kwanciyar na gyara musu. Sannan na shiga jera seletab a ƙafata, bani na kammmala lallennan ba sai wajen sha biyu da rabi na dare. Ina zaune a gefen katifa tunani yai mun yawa, kaina sai aikin saramun yake yi. Ni bansan lokacin da bacci yayi awon gaba dani ba, sai kiraye_kirayen sallar asuba ne ya farkar dani. Lalle na na cire yako yi shar dashi. Gishirin lalle na kwaɓa da toka na shafa, yaranma na kwashe musu lallen na sa musu gishirin lallen. Cikin minti goma yayi baƙiƙƙirin gwanin sha'awa. Nan fa yara duk suka tashi muka shiga yin alwala. Muna tsakar gida na jiyo ƙamshin turaren Kaila ta bayana, wucewa yaxo yayi da sauri yana saye da farar jallabiya mai ɗaukar idanu. Hajiyayye kuma ta fito riƙe da ƙatuwar buta a hannunta tana waƙe_waƙen data saba yi in dai Kaila yayi mu'amalar aure da'ita. Ɗaki muka shige da yara mu kai Sallah. Na fito na hura wuta na ɗaura ruwan wanka. Kafin shidan safe tsakar gidan ya kacame da ƙamshin girkin Hajiyayye da Hindatu, mu kuma sai wanka muke yi. Nice karshen shiga wankan. Ina fitowa naga Hajiyayye da wani lafiyayyen leshi mai taushi ɗinkin doguwar riga, tasha ɗan kunne da sarƙa da zobe da awarwaro harda agogo tayi kyau sosai. Samira kuma tana cikin wasu riga da wando na kanti sababbi fil, kanta yasha bit itama ba laifi tana da gashi. Fati da Zulaihat da Tasi'u yaran Hindatu matar ƙanin Kaila suma suka fito cikin ankon shadda mai ruwan ƙasa su da uwarsu kowa yayi kyau. Gaisawa na tsaya mu ka yi dasu kafin na wuce, yara suna jira in fito in basu kayan da zasu saka. Kowa ya shafa mai. Wata bulu ɗin yadi na zaro ma Sulaiman da Shafi'i da Sani, Inno aka ba sadakarshi ta kawo mun, basu taɓa sawa ba, kuma sabone fil. Su kuma su Balaraba atampa na ciro musu wacce na dinga musu da ƙaramar sallah atampa roba, kowa yasa kayanshi, na basu sababbin hijabansu duk suka sa harda Hauwa, su kuma su Sulaiman suka saka baƙar hularsu ( gobe da mandiri) wacce na siya musu a kasuwar mai shafi da azumi ɗari bibbiyu. Ficewa su ka yi tsakar gida suma suka shige cikin ƴan uwansu. Ni kuma na shiga ciki na zaro wata abaya irin ƴan italiyannan itama Inno ce ta kawo mun ita tare da kayan su Sulaiman harda takalmi mai kyau ta haɗomun dashi duk da dai takalmin ya yi mun yawa kaɗan. Bayan na shafa mai na zura rigarnan doguwa mai kyau, na saka dan kunne da awarwarona, sai jar hoda Zainab dana ɗan barbaɗa akan tsumma na shafa, na bi farin idona da kwalli. Hijabina baƙi na ɗakko na maka na daƙko baƙin takalmina na saka abuna. "Shanono shanono ki fito mana in kina zuwa, in kuma bakya zuwa mu tafi" Kaila ne yake mun magana murya a sama. Ba shiri na fito da ƴar posa ta baƙa a hannuna, ɗakin na kulle na samesu a ƙofar gida. Kaila yaci ado da wata farar shadda mai kyau, ya kafa hula da sabon takalmi fil, idanunshi saye da tabarau baƙi. Motar Abokinshi Isa na gani a ƙofar gidan. Shiga nayi kamar yadda naga Hindatu a ciki, mandiya hamshaƙiyar kuma tana gaban mota da ƴarta ta sa wani mayafi shara_shara. A bayan mun matsu sosai sabida yara amman a haka dai muka tafi zuwa masallacin idi. Yaya kuka ji wannan salon tafiyar kuma? Tafiyace mai tsayin gaske, labarine mai tsawon gaske, ku bini a sannu sannu domin ganin yadda zata kaya. Ƙofa a buɗe take ga masu son magana dani. Wannan littafin zai soma zuwa muku 20 ga wannan watan in sha Allah. GAWURTATTU UKU 👠👠👠 1 _KWAI A BAKA_ *(UMMU AFFAN)* 2 _ZULFA_ *(UMMU MAHEER MISS GREEN)* 3 _NA FAƊO DAGA BENE..._ _NA ZARCE RIJIYA_ *(BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI)* MRS BUKHARI CE https://chat.whatsapp.com/Dqaioj0tydVHQGo5zoG0lm [10/8, 18:30] Badiat Ibrahim: NA FADO DAGA BENE...... NA ZARCE RIJIYA hakkin mallakar Badi'at Ibrahim Mrs Bukhari b4b gidan ƙamshi. Gawurtattu uku *ASSALAMU ALAIKUM MASOYAN GAWURTATTU UKU, MASOYAN BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI. GAMU MUN FITO DA ZAFINMU A BISA ROƘO DA ƘORAFIN MASOYA DA MUKA SAURARA AYI KARATU LAFIYA. NA SOMA DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN ƘAI. GODIYA DA TABBATA GA MAMALLAKIN RAINA, WANDA YAI MUN HANCI DAN SHAN ISKA. SAƘON GODIYA. INA MIƘA SAƘON GODIYATA GA ƊAUKACIN MASOYAN RUBUTUNA. HAƘIƘA NAGA ƘAUNA. SHAFI ƊAYA NA WALLAFA NA LITTAFINA, AMMAN A RANAR NA SAMU WAYAYO DA SAƘONNIN MASOYA BILA ADADIN. HAƘIƘA WANNAN LITTAFIN YAZO DA WANI IRIN FARIN JINI NA MUSAMMAN. SHANONO TACE IN MIƘA MATA GAISUWA GA MASOYAN LABARINTA. SADAUKARWA: NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA KO WACCE BAZAWARA TA ƘASAR HAUSA. NA SAKE SADAUKAR DA WANI KASO DA MATAN AURE IYAYE. GAWURTATTU UKU UMMU AFFAN (ƘWAI A BAKA) UMMU MAHEER MISS GREEN ( ZULFA) MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI ( NA FAƊO DAGA BENE NA ZARCE RIJIYA) Lamba ta 2 A filin masallacin idi mu ka yi sallar idinmu, zukatan al'ummar musulmi cike yake da farin cikin wannan rana. Yara da manya kowa ka kalla a cikin ado da kwalliya yake. Inata kallon yara ƴan gata yara sa'annin Balaraba da Amina da jaka da agogo harda tabarau na yara duk an sai musu, kansu cike da bit kamar ba da kuɗi ake siye ba. Kaila ne ya iso inda muke muna jiranshi shi da Abokinshi Isa. Gaggaisawa akayi, nan Isa ya bi ko wanne yaro da goron salla na sababbin ɗari biyar_biyar, mu kuma ya bamu dubu ɗaɗɗaya. An gode Baban Nana Allah ya saka da Alkhairi " Idanu Kaila ya ƙuramun cikin kallonshi na yaudara, nayi saurin kawar da kaina, yaran duk suka mimmiƙo mun kuɗin hannunsu. Muna tafe zamu je inda muka ajjiye mota Balaraba tace. "Umma siya mana askirin" Dariya nayi mata, Hindatu ta shiga yi mata tsiya. Ɗari biyar na zaro na ba Sani nace. Yaya maza siyo muku dukkanku na duka." Jikinshi har rawa yake yi ya karɓi kuɗin ya zura da gudu ya siyo musu. Mota muka shiga muka koma gida. Muna isa Hajiyayye ta shiga rabon abinci. "Umma! umman Samira tace ki kawo kular abincinki, da kwanon da zata zuba miki nama da cincin" Cewar Shafi'i. Yana gama faɗa ya fice a guje. Mayafin doguwar rigar jikina na yafa na fito a lokacin Kaila na kiciniyar fita da rago. Yaran kuma ashe Hundatu ce ta zuba musu shinkafa da miya a katon trai suna ta ci, harda zoɓo mai sanyi. Kula na shiga kitchen na ɗakko da kwanon nama na kai bakin ƙofar ɗakin Hajiyayye. Tana fitowa data ganni da doguwar rigarnan sai tayi wani turus ta kasa ɓoye mamakinta dan rigace mai kyau da gani kuma zata yi tsada. Kafata ta kalla sai ta haɗe ranta tace. "Hmmmm" Ni dai ina tsaye ta zuba mun fried rice ɗinnan da koslow a kwano. Sai naman kaza da cincin, da meat pie. Cike da mamaki na dubeta ganin nama da kayan fulawar data zuba mun kamar ni kaɗaice a ɗakina banda yara. Hajiyayye ki ɗan karamun naman da kayan fulawar kinsan muna da yawa" "Dan kuna da yawa? Ai ba dan ku nayi ba, nayi ne sabida Baby da abokanshi ba sabida ke da yaranki nayi ba, mtwss" Taja tsaki. Ban tanka ta ba na ɗauki kwanon naman na ɗaura a saman kular abincin, na sa kwanon koslow ɗin akan kwanon naman na ɗauka. Sai ga Shafi'i ya biyo ni da lemon kwalba 7up guda huɗu. Ajjiyewa yayi na dubeshi nace. Maza kuci abincin kuzo ku tafi ku kai ma su Inno abincin Sallah maza. Nan Shafi'i ya shiga murna a guje ya kirawosu, sai gasu har suna rige_rigen shigowa. Ƙatuwar samira ta kasan na cika ma Inno da abinci dam, samirar tsakiyan kuma nasa mata nama da meat pie. Na samu ɗankwali mai ɗawisu na kulle musu samirun dashi, na samu leda ɓaka mai ƙarfi na zura samirun a ciki, na ɗakko 7up guda biyu na zuba. Ragowar meat pie da lemun kwalbar nace musu su ci kafin su tafi, dan in sun tafi sai an gama bikin sallah ranar da naje wunin sallah na gida nake tarkatosu mu dawo tare. Suna gama ci su kai mun sallama suka fice. Hauwa kuma sai bacci take yi. Zama nayi na zuba abinci a plate na soma ci, gaskiya abincin yayi daɗi sosai, Hajiyayye ta fini iya girki nesa ba kusa ba. Bayan na gama cin abincin saina ɗan shingiɗa a bakin katifa har bacci ya soma ɗibata na jiyo muryar Kaila a tsakiyar kaina. "Shanono ki taso ki gasa mun hanta ga kayan ciki nan na shigo dashi ki soma aiki. Kallonshi nayi nace Kaila ai girkina sai zuwa bayan la'asar zai shiga Hajiyayye ce da kai har yanzu" "Ke dai babu dama ayi magana ki ce to. To Hajiyayye tana can tana zuba ma abokaina abinci, kuma ta gaji ita tai ta yin hidima jiya, in zaki taso ki taso ni dallah sai shegen sa'insa mata ba dama ace mata abu ɗaya. Allah yana gani ni nayi nadamar auroki da nayi" Ficewa yayi fuu. Babu shiri na biyo bayanshi, har sun gama aikin ragon, yana jikin bangon ɗakin Hajiyayye a banƙare. Wuta na haɗa a korfo, na shiga cakuɗa hanta da maggi da yaji da kayan ƙamshi, nan na shiga gashi. Ina jiyo shewar Kaila a ɗakin Hajiyayye da abokanshi, harda shewar Hajiyayye Babu kowa a tsakar gidan sai ni, Hindatu tana ɗaki da mijinta suna kallon wakokin ado gwanja. Haka na gasa hantarnan tas nayi sallama a ƙofar ɗakin Hajiyayye. Fitowa tayi ta karɓi plate ɗin ta shige ciki. Nan na duƙufa gyaran kayan ciki, nazo na yayyanka bayan na gama na zuba a tukunya na aza bisa wuta, na zuzzuba duk abinda ya dace, na koma ɗaki ina nishin gajiya, na tarar Hauwa ta farka sai kuka take yi. Ɗaukarta nayi na zura mata nono a baki, nan ta shiga tsotso tana sauke ajjiyar zuchiya. Nima ajjiyar zuchiyar nake saukewa zuchiyata cike da tunanin shin haka mazan ƙabilar Hausawa da yawansu suka lalace wai, so suke ƙarfi da yaji su mayar da mata baya can zamanin jahiliyyah. Kuma abun takaicin shine ba ga masu sanin ba, ba ga jahilan ba. Tunda ni na auri malami na gani, jahilin ma na aure shi shima naga kalar tashi rawar, ga tsaka tsaki shima na aura naga irin tashi rawar da yake takawa. Wai mu mata ina zamu tsulma ranmu ne muji sanyi, haba maza iyayenmu ya kuke son mu yi da ranmu ne? Gashi in ƙaddara ta samu mace tayi aure ɗaya zuwa biyu ta fito, sai ƙabilar Hausa su sa mata jakar tsaba, wasu su kirata da maras tarbiyya, wasu suce mata mai ruwan ido, wasu su kirata da kwaɗayayya. A gidanku ma baka huta ba a wajan iyaye da ƙanne, tsangwama daga ko wanne ɓangare babu daɗi. Wannan dalilin shike tilastama wasu mata zaman dole wanda ka iya zama ajalinsu, ko silar shigarsu wuta. Ni kaina a wannan auren nawa karo na biyar na ɗau alƙawarin duk rintsi duk wuya zan zauna ko da wuya da ciwon zuchiya za sui ajalina. Tuno mazajena na baya na yi da dalilan mutuwar Aurarrakina. Numfashi naja mai ƙarfi dana tuno da yanda akayi na haɗu da Kaila a hanyar kasuwar taminus wajan da Baffa yake zaman Bara a masallacin ƴan taya. Wasu zafafan hawayene suka gangaro kumatuna. Ƙauri na soma jiyowa da sauri na fita na sauke tafashen kayan cikin. Man gyaɗa na gani kwalba biyu a kofar ɗakina an ajjiye mun a wulaƙance. Ɗaukowa nayi na juye a bojuwar suya na soma suyan kayan ciki. Hindatu itama tana tsakar gidan tana suyar hanji wanda Kaila ya dibar musu. Wani kurfo na dakko ƙarami na zuba gawayi da gaushi a kai. Ina suyar nan na tsai da sanwar miyar tuwon dare, na ɗebi tafashasshen kayan cikinnan na zuba a cikin ruwan miyar da ruwan tafashen. Zuwa bayan la'asar na kammala suya tas na juye a roba mai murfi bayan ya huce. Assalamu alaikum Hajiyayye dan Allah ɗan miƙo mun key ɗin turaka zan ajjiye namannan ne" Naji shiru dama a rufe naga ƙofar amman dake na saba ganin hakan a wajen Hajiyayye sai ta saka Kaila a ɗaki ta rufe shi da ranar Allah gida fal yara bata ko jin nauyi. Hindatu ce ta fito daga bayan gida take ce mun. "Ai basu daɗe da fita ba, ɗazu da kika shiga ɗaki ɗakko robar da kika juye kayan ciki tai mun sallama sun fita." Dawowa nayi da robar naman a hannuna, basu tasarma fita ba sai da suka ga kwanana ya shiga. Roba na samu na cika ma Hindatu da kayan ciki duk da nasan an bata ɗanye. Kunyace tasa ina dawowa ta biyo ni da cincin da soyayyen naman kaza harda zoɓo mai ɗan karen sanyi. Godiya nayi mata na ajjiye a ɗaki. Sallar la'asar nayi na jawo wayata inga ko an kirani, ai kuwa miss call ɗin Yaya Use na gani. Ina jiyo muryar Zulaihat a tsakar gida na fita da nera ta ɗari. Zulaihat zo ki siyo mun katin glo a shagon mahi" Da gudu tazo ta karɓa taje siyo mun. Ni kuma na shiga yin talgen tuwo. Ina zaune a dokin ƙofata ina cin kayan ciki da zoɓo sassanya Zulaihat ta dawo daga siyo katin, na ganta da alkaki cike da baƙar leda tace mun. "Maman Zuhura ce tace in kawo miki wai zata shigo inta gama tuwo. Kuncewa nayi na bata guda uku nace ta kaima ummanta. Sai da na tuƙa tuwo na kwashe a leda na mayar da ruwan wanka sannan na saka katin a wayata, na ɗan sake share falona sama_sama. Ban zauna yin wayarnan ba sai da na fito wanka na kintsa tsab. Sanye nake da riga da skirt na gwanjo da azumi na siya a wajan tafsir ɗin mai shafi. Ni dama ba kananun kaya nake sawa ba, na ga kananun kaya sunfi burge Kaila ne shiyasa ma na cire ɗari ukuna na siya." Danna kiran layin Yaya Use nayi, bayan ta ɗaga nayi mata barka da Sallah mu ka ɗan taɓa hira na kashe wayata. Layin Inno na kira nayi musu barka da Sallah, daga ƙarshe na kira Yaya Karima itama mu ka yi gaisuwar sallah. Har zuwa bayan magriba ba su Kaila babu dalilinsu. whatApp na ɗan leƙa da bonus na data da glo ta bani, dan in ɗan ɗebema kaina kewa, group ɗin ƴar aljanna na leƙa mata sai turo hotunan sallansu suke su da yaransu, wasu a irin tabka_tabkan falukannan na gani a faɗe, wasu kuma a tsakar gida ma suka ɗauka, wasu a filin idi. Gasu nan dai birjik, wasu na buɗe na kashe ƙwarƙwatar idona, wasu kuma wucesu nayi. Wasu matan harda mazajensu a cikin hotunan. fita nayi a group ɗin baki ɗaya sabida naji anata kiran sallar isha. Har nayi Sallah ni dai banji motsin shigowar su Kaila ba. whatApp ɗin na koma ina hawa na ganni a cikin wani sabon group mai suna ( FGGC BAUCHI) dariya da mamaki na soma yi lokaci guda. Ina shiga na soma ganin sunayen ƴan ajinmu. Mariya Habibi, Habiba Bala, Fatima Bello, Aisha Aliyu musa Biu da dai sauransu, sauran ban sansu ba dake jiniyo kaɗai nayi daga zuwa huto aka cireni a makarantar nan komawar da ban sake yi ba kenan. Ni mamakina ma ina suka samu number wayata, duk mutanenannan ya akayi aka tattarosu" Daga farko na soma bin hirarrakinsu Habiba Bala ce ta buɗe gidan. Wani dogon voice note tayi, jikina yana rawa na danna, muryarta ce wallahi tana nan yadda nasan muryar. Nan ta faɗi manufofin buɗe group ɗin domun zumunci da ƙarfafa juna, ta bada labarin yanda akayi ta haɗo numbobinmu da dama a cikinmu, Fatima Sunusi ce ta bata number na. Mun taɓa haɗuwa da'ita ta shigo jos, lokacin ina aure a wani gidan ba gidan Kaila ba har ta ziyarceni. Haka na dinga bin saƙonnin mutane wasu a rubuce wasu voice har sai da na gaji, dan sunyi surutu fin dubu ɗaya da wani abun. Sai cigiyata ƴan ɗakinmu suke yi. Voice nayi nima na soma da gaisuwa tare da nuna farin cikina a bisa wannan gida da Habiba Bala ta zama silar assasashi, nayi musu alƙawarin in sha Allah zan halarci taron da aka haɗa domun tattaunawa na ido da ido, wanda suka tsaida rana ran huɗun Sallah,za'ayi taron a zaranda hotel. Ina turawa da saƙo duk suka fito nan muka ɓalle da hirar yaushe gamo, muna ta tuno abubbuwan dariya da suka shuɗe a lokacin baya. Ina cikin haka na jiyo muryar Hajiyayye a tsakar gidan. Sallama nayi musu kuma na miƙe. Abincinta na zuba mata na fita. Duk da nasan abune mai matuƙar wahalar gaske taci abincinnan. Ba kasafai ta fiye cin abincina ba. Nayi sallamar duniya a ƙofar ɗakin nata ba'a amsa mun ba. Ta kasan labule na tura hannuna na ajjiye mata abincin na komo ɗaki. Abincin Kaila dake jere a tire mai murtala duk tsatsa na ɗauka na fito. Da sallama na tura ɗakin Kaila na shiga. Take ƙafafuwana suka shiga rawa, ƙirjina na dokawa. Tunda nake ko a waya ban taɓa ganin tsaraici ba face na mazajen dana aura , sai gashi nayi tozali da Hajiyayye tsirara haihuwar uwarta da ubanta a saman Kaila, shi kuma sai sambatu yake yi idanunshi a kulle. Ƙaran faɗiwar tiran hannunane ya dawo dasu cikin Haiyacinsu. Da sauri na fita ina haki sai Allah kawai nake ambato, tsigar jikina sai tashi take yi. A guje na faɗa ɗakina na danna sakata ina haki. Jiyo bugun ƙofar Kaila nayi daga bayana. Ina jingine da jikin ƙofar ina tsiyayar hawaye, hoton tsaraicin Hajiyayye ƙam a idona. "Shanono ki buɗe ƙofar nan nace miki, bakya ji nane Shanono, kinga buɗe kiji" Da ƙyar na rarrafa na shige uwar ɗaki na kwanta a katifa na rushe da kuka ina tambayar kaina wai ni mai nayi ma maza ne suke ƙoƙarin ganin sun rabani da rayuwata ne?" Nayi kuka a wannan daren wanda bansan iyakarshi ba, bansan sanda baccin wahala yayi sama da faɗi dani ba. Na dai farka da asuba idandunana sunyi luɓu_luɓu. Ina fitowa tsakar gida da buta a hannu naci karo da Kaila, sai wani kallona a ido a ido yake yi. Ni kuwa nayi biris tamkar ban ma ganshi ba. Waƙe_ waƙen Hajiyayye na jiyo daga bayana, ina juyowa nayi tozali da'ita ta fito daga turakar Kaila daga ita sai rigar bacci iya cinya, bata ko jin kunyar bayyanar tsaraicinta. Wani ƙududune ya tokare mun maƙoshina. Bayan gida na shiga nayo fitsari na fito. Kwanukan tuwona dana kai ɗakin Kaila na gani a dokin ƙofata da tuwon da miyar duk an zube mun su a cikin tiran. Shigarwa ciki nayi na ta da Sallah. Ina sallah ina tsiyayar hawaye. Ruwan tea na haɗa shi kaɗai na iya sha da alkakin da ƙawata ta aiko mun dashi jiya. Ina jiyo ƙwaramniyar matan gida, ni dai ban bi takan kowa ba, kuma da har nayi niyyar hana Kaila abinci tunda bani na kwana dashi ba. Sai kuma na zuba ruwan tea da alkaki da naman kaza a tire na fita na kai mishi harda robar kayan ciki dana soya. Na sameshi yana waya ƙasa_ƙasa yana ganina ya sauke wayar a kunnenshi. "Shanono ai nayi tunanin ba zaki kawo mun kayan karyawa bane, dan naga kin ƙaro wulaƙanci. Dan kuturun wulaƙanci kina fa jina ina buga ƙofa kikai biris dani sai kace wacce tazo ta kama ni ina zina da karuwa. Kai ku mata kishinku dai yayi yawa." Kallonshi kawai nayi yana gamawa nasa kai zan fice abuna. Sai yace. "Ki same ni a ɗakin Hajiyayye yanzu inason zan yi muhimmiyar magana daku dukka kuma yanzu. Danni fita zanyi, wannan kayan karin naki ki koma dashi Hajiyayye ta kawo mun tea da biredi da ƙwoyi. Ɗaukan turan nayi na fita ba tare da nace dashi ci kan ka ba. Ina jiyo takun tafiyarshi daga bayana. Ko dana shiga ɗaki sai da na yi kuka sosai kafin na goya Hauwa a bayana na fita zuwa ɗakin Hajiyayye. Da sallama na shiga ɗakin. Suna zaune akan 3sitter na same su suna hirarsu faram_faram. A kan 1 aitter na zauna a rakuɓe bance musu komai ba, vidiyon tsaraicin Hajiyayye sai yawo yake yi a kaina, gata dai da kaya a jikinta amman ni tsirara nake kallonta. Ɗakinnan a gyare tsab sai ƙamshi yake yi. Ga kujerunta masu taushi, ga kayan kallo ga kafet mai taushe malala a ƙasa, harda buna ta turaren wuta na ƴan gayu sosai mai wuta, an juna turaren wuta yana ta buso kamshi. Gyaran murya naji Kaila yayi. Wata leda viva ya miƙo mun yace. "Ungo nan Shanono kafin in yi muku bayani" Hannu nasa na karɓi ledar daga hannunshi kaina na ƙasa, dan mugun kunyarsu nake ji. "Baby riƙe naki kema ko?" Ya miƙama Hajiyayye ledarnan irin tawa. Zama ya gyara ya tattaro dukkan nutsuwarshi garemu, sai wani wauware idanu yake yi kamar wanda ya wanke makanta........✍🏻 *Akwai set na kayan ƙamshi, musamman domin masoyan wannan littafin. Zaku same su cikin rahusa da izinin Allah* ga masu buƙata sai su tuntuɓeni. Amman iyaka masoyan wannan littafi kaɗai zan siyarma, garaɓasar taku ce, promo nayi muku domin in faranta ranku kwatankwacin yanda kuka faranta nawa ran [10/8, 18:30] Badiat Ibrahim: NA FAƊO DAGA BENE..... NA ZARCE RIJIYA HAKKIN MALLAKAR BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI GAWURTATTU UKU LAMBA TA 3. *ASSALAMU ALAIKUM BARKAN MU DA SAFIYAR LITININ. HAƘIƘA BANSAN DA WACCE SIGA ZAN MIƘO SAƘON GODIYATA A GAREKI BA HAJIYA SUMAYYA. KE ƊIN MASOYIYACE TA HAƘIƘA CIKAKKIYA. SAƘON DA KIKA TURO MIN DASHI, NA KARƁA YA ISO GARENI, BANSAN WACCE IRIN GODIYA ZAN MIƘA MIKI BA, SAI DAI ADDA'AR KHAIRIRO. ALLAH YA BARMU TARE YA ƘARA MANA SOYAYYAR JUNA* *HAƘIƘA WANNAN LITTAFIN YA KAINI WANI MATSAYI DA BAN TAƁA MAFARKIN RISKAR KAINA A KAI BA. BABU ABINDA ZANCE DA ALLAH SAI GODIYA. BABU ABINDA ZANCE DA MASOYANA SILAR MURMUSHINA, SAI FATAN ALKHAIRI* Bayan ya gyara zama yace. "Waɗannan ledojin kayane a ciki. Atampa guda ɗaya , sai mayafi, da takalmi, harda ɗan kunne da sarƙa, da nera dubu da ɗari biyar_biyar kuɗin ɗinki. Fasali ya ja kafin ya ɗaura da cewa. "Dalilin wannan kaya kuwa shine. Aure zan ƙara nan da sati biyu masu zuwannan in Allah ya nufa. Kayane na faɗar kishiya ake ce musu ko me oho dai? Ɗanyan gwal Bilkisa ce ma na bata kuɗin ta siyo muku dan ta bala'in sanin kaya da kala." "Kanbu Kaila Aure fa kace zaka yo a cikin gidannan, ni za kai ma kishiya Kaila? Wallahi in ka isa me nake, kinji fa umman Sulaiman baki ce komai ba Aure fa yake cewa zaiyo?" Ni dariya ma ta bani yanda naga ta haƙiƙance tana kumfar baki, harda miƙewa tsaye. Saina tuno da iriyar muguwar wulaƙancin dana fuskanta a lokacin da Kaila yake neman aurenta. Waya babu dare babu rana, a kan kunnena suke musayar kalaman da suka shige ƙa'ida yana fallasa mata asirin zuchiyarshi da inda gangar jikinshi ke mararin jin duminta. Daga yanda suke wayar basa jin kunyar yin batsa hakan ya sake tabbatarmun suna haɗuwa su watse, in dai Kaila bai kusanceta a waje ba, to haƙiƙa babu inda bai zakuɗa hannunshi a jikinta ba. Amman haka duk na ɗauka na jure, duk dan in samu wannan auren nawa na biyar ya ɗore. Ni banma samu arzikin kayan faɗar kishiya ba, kazalika bai zaunar dani baki da baki ya sanar dani bikinshi ba. Da lokaci yayi kawai ganin ƴan Akwanga nayi dangin mahaifiyarshi sun cika gidan tab, dangin mahaifinshi suma suka yo nasu zugar daga wudil. Haka na shiga cikin jama'ar biki akayi dani. Tunda aka auro Hajiyayye bata sake barin zuchiyata ta samu nutsuwa ba. Ga shigar banza da rashin kunya, a gabana take tsotse Kaila. Shi namiji dama kunya ba isarshi tayi ba ko a jikinshi. " "Umman Sulaiman baki ce komai ba fa wai Aure zaiyi. Yaushe_yaushe na shigo cikin gidan ciki na biyu ne a jikina fa. KAILA ashe kai mayaudarine ban sani ba? Ka mance alƙawarurrukan da kaimun a waje cewar daga ni babu ƙari nice maganin matsalarka kana son mace ƴar gaye?" Kaila yace. "Sabida son mace ƴar gayen ne yasa zanyi wannan Auren. Bayan na sameki ne saina gane ba mace ƴar gaye kaɗai nake da buƙataba. Ina son mace mai aji ƴar jami'i ƴar kwalisa. Allah cikin ikonshi Ɗanyan gwal Bilkisa duk ta haɗa dukkan wannan abun da nake nema, fiye da ma abinda nake nema. Dan a yanzu hakannan da nake magana Bilkisa ma'aikaciyar jinyace, unguwar zoma ce ta asibiti, ƴar gaye mai turanci kamar a fadar Queen alizabet sarauniyar Ingila aka yayeta, kinga ke iyakarki sakandare, ita kuwa Shanono iyakarta ƙaramar sakandare bata samu damar kammala karatun sakandaren ba ma ita, kunga ai iliminku in aka haɗa bai wuce rabin cokali ba ko?" Dariya ce taso kubce mun yanda naga Hajiyayye na ƙanƙance idanta, kafin ya gama ta shiga lailayo ruwan ashar tana dannama Kaila. Dana fuskanci ranshi ya soma ɓaci sai nace. To ka gama dani ne in tafi?" Dubana yayi yace. "Tukunna dai Shanono. Abunda nake so dake shine ɗakin ki da kike ciki nake buƙata a nan zan saka Ɗanyan gwal Bilkisa, da wancan ɗakin zauren zan gyara mata. Amman tace mun tana da kaya da yawa kinga ɗaki ɗaya bazaiyi mata ba. Bugu da ƙari ƴar manyan mutane ce, Babanta babban mai kudine. Tunda ke babu uwar komai a ɗakin ki sai tsummoki da gaiyar kuɗin cizo da ƙwarƙwata, ku tattare ke da yaran ku koma ɗakin zaure, nan da kwana biyu haka, dan masu gyaran wajen jibi zasu zo. Zan sa su yi miki fenti in sun zo. Ɗakin ma ko kin fita sai an yi mishi wankan maganin kuɗin cizo" Dim naji gabana ya tattake ya faɗi. Ni dai na rasa me nayi ma maza basu karɓeni ba . Wai yau ni Kaila yake cema in koma ɗakin zaure ni da yara mu rai takwas. Me Yasa baice Hajiyayye ta koma ba ita mai ƴa ɗaya? Nice ba mace mai daraja ba ko, ko dan a bazawara ya auroni ne shi yasa? Murmushin takaici nayi nace. To shikenan babu komai zan koma yau ba sai gobe ba ma. Sannan inaso Hajiyayye taci gaba da kulawa da kai har zuwa lokacin da Allah zai saukeni lafiya tunda sai na haihu zata haihu, ita da Amarya sai suci gaba da kulawa da kai. Allah ya sanya alkairi yasa abokiyar zamanka ce na har abada" "Lallai umman Sulaiman ban san ke wawuya bace sai yau, ashe rashin ajin naki har ya kai ki dinga ma miji fatan alkhairi dan zai ƙaro aure?" Cikin gatse nace. Ke da kike da ajin ai bai hana ya hango wata zai auro ba ai ko, ba'a aure ke aka auroki kika zo kika miƙe ƙafarki kuma? Yarinya meye matsalarki da aurenshi? Ta huɗu ma tana ƙofar gida ai in dai namiji ne" Ina kaiwa nan na fita abuna. Ɗaki na koma na saki kukan baƙin ciki. Hajiyayye kuwa muryarta har dakina ina jiyowa, daga karshe Kaila ya fice fu a gidan ya barta tana ta zage_zage a tsakar gida tana faɗin bai isa ya kawo mata wata ƴar iska a matsayin kishiya ba. Mikewa tsaye nayi na shiga aikin sintiri a filin tsakar ɗakina, ina tuna farkon haɗuwarmu da Kaila, da kalma mafi soyuwa daya faɗamun yasa na sakankance zan samu farin ciki mai dorewa a gidanshi. A lokacin da nake Amarya sai da Kaila ya maisheni sarauniyar mata tsabar so, ko da yaushe yana liƙe dani muna zuba soyayyarmu. Amman jibi yanzu yanda bolar gidana ta fini daraja da kima. Kaila ya mance meye ya zama silar kafuwar sana'arshi, har shi kanshi ya samu nutsuwa a cikin rayuwarshi. Gashi sakayyar da zai mun ba'a iya yin kishiyoyi ya tsaya ba harda tozarci da ƙasƙantar dani. Iyayena suna gani sunyi biris kullum kalmar da Inno take faɗamun shine duk rintsi kar in kuskura ace aurena ya sake mutuwa a karo na biyar. Mahaifina kuwa cewa yayi duk randa na sake na kaso aurena sai dai in nemi wasu iyayen da wasu dangin ba dai su ba. Gani suke kamar ni nake yin laifin da mazan suke sakina. Ni kuma a iyakacin zamana da mazajena huɗu na baya bazan iya cewa ga laifin da nayi ma ɗaya daga cikinsu ba wanda shine yai silar mutuwar auren ba. Ko su kansu basu isa sunce ga laifin da nayi musu suka sake ni ba. Ni kawai mazan ne basu karɓeni ba, ko kuma mazan ƙabilar Hausawa ne basu ɗauki saki da mace a bakin komai ba mafiya yawansu. Ni na kasa gane kan wannan zamantakewa da kabilar Hausawa ke gudanarwa a gidajensu, ko kun ɗauka an halicci mata ne su zo duniya domun kawai su zama bayinsu? Na gane mace bata da daraja amfaninta baya wuce a samu nutsuwa da'ita, ta haifi yara ta rene su. Dai_dai da ciwo in ya kamata wasu mazan saki suke yi, ko kuma su tura mace gida iyayenta su nema mata lafiya, da zaran ta samu lafiya ya lallaɓo a bashi matarshi. Hawayena na share, a zuchiye na soma fito da kayana daga cikin wannan ɗakin. Hajiyayye tana dokin ƙofarta tayi tagumi idanunta sun yi ɓulu_ɓulu. Ni kuwa aiki na shiga yi kace_kace. "Umman Sulaiman lafiya kuwa, naga shekaran jiyannan kika gama kwalimar sallah, ko ɓera ne ya mutu a ɗakin?" A'a Hindatu zan sauya ɗakine kawai" Nan na barta da riƙe haɓa, ai kamar jira Hajiyayye take yi. Nan ta shiga ƙundumama Kaila ruwan ashariya nan ta labartama Hindatu halin da ake ciki. Ni dai bance musu komai ba ɗakin zaure na buɗe, ƴan shirgunan ɗakin yawanci na Hindatu ne, harda wata kujerarta 2 sitter da yadin ya yayyage. Fito da komai na ɗakin nayi na kaɗa omo. Ga ciki ga goyo, amman tsabar jin haushi bana jin nauyin komai. Wanke ɗakin nayi har bango na tsane ruwan da tsumma, na wangale windon ɗakin. Alwalar azahar nayo, na shinfida daddumata nayi sallah a tsakar gidan. Hajiyayye uwar karaɗi yau ko wanka ta kasa sabuntawa tana zaune da rigar bacci a jikinta. Dumamen tuwo na ɗaura ina kan ɗumamen ƙanin Kaila ya shigo ya shiga aikin sara rago. Yana gamawa na duƙufa aikin suya. Dana gama cin abinci na ba Hauwa taci. Sai na soma shigar da kayana ɗakin zaure. Amadudu mijin Hindatu yace. "Yaya Tani Allah dai yasa lafiya ba auren naki bane ya sake mutuwa a karo na barkatai?" Naji zafi da ciwon maganar Amadudu amman na riga na san mazauna Akwanga, Lafiya, da makurɗi basu iya tauna zance ba, kamar fitan zawo suke Magana. Ban kai da bashi amsa ba Hindatu ta labarta mai Abunda yake faruwa. Kayana naci gaba da shigarwa cikin ɗakin. Katifata na shinfiɗa a ƙasa, katifar yara kuma na jingineta daga bango ɗaya. Buhunhunan kayanmu kuma na lodasu lungun dake ɗan gefen katifata babu laifi filin tsakar ɗakin ya ishemi. Amman kenan a haka zamu dinga gwamutsuwa dani da yara a ɗaki ɗaya, taya hankalina zai kwanta gani ga yarana a cakuɗe a ɗaki ɗaya. Irin wannan sakaiyar Kaila zaimun babu komai. Sai magriba na gama suyan naman laiyannan. A take na raba na fitarma da kowa nashi. Na ba Hajiyayye nata dana Yariman nata nace ta ajjiye mishi, na ƙullama ƴarta a leda kamar yadda na ƙullawa su Sulaiman, na miƙama Hindatu nasu nayi shigewata ɗaki. Ina zaune ina shan shayi da nama na jiyo muryar kawata tana tambayar bana gidanne. Ina jin Hajiyayye tana faɗa mata cewar. "Ta koma ɗakin zaure Aure mai gidan zaiyi zai sa amaryarshi a nan ɗakin" muryarta fes cikin nishaɗi dama nasan wannan rashin darajar da Kaila yai mun dole zai faranta mata. Da sallama maman Zuhura ta shigo ɗakin da nake, taci ado irin na asalin mata gaske waɗanda maza suka amshesu har suka samu yardarsu. "Tani kece haka a cikin wannan ɗakin mai kama da akurki?" Murmushi nayi mata kawai. Waje ta samu ta zauna, shayi na zuba mata, na miƙo mata nama leda ɗaya. Bismillah jiya kika ce zaki shigo baki shigo ba, bismillah zauna a bakin katifa mana" Zama tayi a sanyaye. "Tani kuma kin yarda kin amince Kaila ya fitar dake a ɗakin ki kina uwar gidanshi yasa amarya a ɗakin ki? Ya kasa bari kici albarkacin yara ma, bacin in ya mutu a halin yanzu sai dai a tsakurama matanshi da sauran yaran wani ɗan abu. Ai kinci gidan taya zaki rayu a irin wannan ɗakin ke da yara? Me yasa ba zakiy tsaiwar daka wajan ganin kin kwaci ƴancin kan ki ba, bari kiji iyayenmu bafa zasu goyi bayanki su barki ki ƙwaci ƴancinki ba ma, balle kiyi tunanin su da kansu su ƙwatar miki ƴancinki. Ya da jininki a jiki zaki zauna baƙin ciki Kaila dana kishiya ya halakaki? Yanzu fa Hajiyayye fa cikin farin ciki take faɗamun abunda ya faru. Shigowa nayi na samu suna gulma da facalarki fa. Kema Tani ƙazantarki tayi yawa, dubi jikin ki fa, ji nono yanda ya ɓata miki riga, ko rigar mama bakya sawa, kullum ke kenan cikin riga daban zani daban. Ko kitson sallah ma baki samu yi ba, kin kama ƙafarki data yara kin muku baƙin lalle wanda ake sama gishirin lalle. Wallahi in baki gyara ba, ke ma fa ba zaki ga da kyau ba. Sannan tunda kun dawo ɗakinnan kuɗin cizo ku dena kasheshi a bango dan Allah, ki ke gyara jikin ki ko kema zaki samu iska mai kyau" Ajjiyar zuchiya na sauke cikin nauyin ƙirji nace. "Sabira bari in faɗa miki na jima da tsanar gidannan da mai gidan baki ɗaya, bani da kuzarin iya gyaran jikina, kina gani kullum zaki ganni da goyo da ciki, ni fa sai in yi wata ban kama nera biyar ma tawa ba, miji baya yi da kai, kowa ma haka ni yaya akeso in yi ne. amman yaya zanyi ne da rayuwata Aure na huɗu ne suka mutu wannan shine na biyar. Iyayena basu da wani burin daya wuce suga ina zaune a ƙarƙashin inuwar aure. Sabira dukka wannan aurarrakin da nayi suka mutu. Mahaifina ya ɗaura alhakin mutuwarsu a kaina. Gani suke rashin haƙuri ne, da kai mazajen bango yasa duk aka koroni. Dauda dana bari a Shanono tunda na bar Shanono ban sake sashi a idanuna ba Sabira. Inno dai tana zuwa dubashi in suka je ganin gida, kuma ina mai aiken duk abunda Allah ya hore mun. Yaronnan yana tsakiyar shan nono mahaifinshi ya tsigeshi a kan cinyata bazan mance ba, ya danƙashi ga kishiyata Tamaulidi ni kuma yai mun korar kare. Naga abubbuwa da dama da bana so ma in shiga labarin. Wadannan yaran zamansu nake yi bana so su yi maraici kamar yanda Dauda ya taso cikin maraicin uwa, kuma an faɗamun ba ƙaramin azaba matar uban take gana mishi ba. Inno tace in zata je wannan karon in mun je zata kaini in ganshi. "Amman Tani ni ina ganin akan yara bai kamata mu dinga nuna ma maza dole sai mun rayu dasu ba. Kinga wannan maganar zaman yaran da aka ƙirƙireshi a cikin kabilar Hausawa ita ta ja kusan rabi da kwatan matsalolin matar Bahaushe. Da ace yanda kika haƙura kika tafi kika bar Dauda kuma baki sake waiwayarshi ba, da hakan ki kai ma Kaila ki zube mishi yaranshi ki samu ki shaƙi iskar ƴanci" Murmushi nayi mata wasu hawaye suka surnano mun. Sabira bata san raɗaɗin dake zukatan iyayen da suke rayuwa a wata duniya, ƴaranta suma suna rayuwa a wata duniyar ba ne. Da tasan irin tashin hankali da uƙubar dazan tarar a gida, da irin tsangwamar da ƙabilar Hausawa ke ma bazawara da bazata ce in kashe auren ba. Nashiga kunci rayuwa kashi daban_daban wannan yasa banason shiga cikin ainihin rayuwar dana tsinci kaina a gidajen sauran mazajen nawa huɗu. Mahaifina har cemun yayi na zama karuwa in ɗanɗana wannan namijin, in fito in ɗanɗana wani, auren sha'awa kawai nake yi da mazajen. Babu sanda aka taɓa jana a jika domun in samu sauƙin zugin zuchiyata. Haka Sabira tai ta bani baki tana bani haƙuri akan cewar wataran sai labari. Ni kaina ina roƙon Allah yaimun tsawon ran da zanga ranar labarin. Sai da ta ɗan kwantar mun da hankali sannan tace mun zata tafi. Samosa ta kawo mun cikin leda, har bakin ƙofar gida na rakata ta tafi. Ina jiyo Kaila da Hajiyayye suna cin uwar sabada, a wannan daren Kaila yayi jaraba da masifa tamkar zai doki Hajiyayye ina ji yana cewa gobe ta tafi gidansu taje ta koyo tarbiya. Ina kwance ina fama da marurun zuchiyata. Sassafe Kaila ya ƙanƙasamun ƙofa ya miƙo mun Samira har zai wuce nace. Zanje wunin gida yau. Sannan dan Allah inason zuwa gobe zani Bauchi akwai wani taron ƴan makarantarmu da za'ayi." Ranshi a haɗe ya juyo yace. "Ni dai bani da kuɗin dazan baki zuwa wani Bauchi hidimar aure ce a gabana, in kina da kuɗin mota ki je in baki dashi ki haƙura." Ina dashi dama izini nake nema" Nace a sanyaye. "To kije kwana nawa zaki yi to?" Nace mishi. Bazan wuce kwana ɗaya ba ƙarƙari ƙwana biyu zan dawo" umarnin zuwa ya bani, nayi mishi godiya. Da wurwuri na kammala aikina nayi wanka naima Hauwa. Goyata nayi a bayana na saka hijabina na fito hannuna riƙe da leda da Samira. Kulle kofata nayi, na miƙa ma Hindatu Samira. Nan taso ta neme ni da gulma, tana son sanar dani abinda ya faru, tafiyata nayi na barta nan da Samira a hannu. Ina isa titi na tari keke napep zuwa layin idi mai barkono (Allah ya jaddada rahamarshi gareshi). Tun daga titi na soma gaisawa da maza_mazan anguwar da suka sanni nazo na wuce gidan mariyagi idi mai barkono a raina nace Allah sarki iya ta lungu mai maganin gargajiya na kashin jarirai alkhairin Allah ya kai miki. Da sallama na shiga gidan namu. Da Baffa naci karo shi da Habu yana mishi jagora da dukkan halama bara zasu fita. Yana jin muryata ya caɓe abunka da makawo akwaisu da gane murya ballanta na kuma muryata. "Tani kema kin iso kenan? Yanzu shigowar Use kamar tare kuke." Tsugunnawa nayi har ƙasa na gaisheshi duk da nasan ba gani yake yi ba. Da fara'a ya amsa mun gaisuwar tawa. "Ya mai gidan naki Kaila ince dai kina zaune lafiya kuma kina mishi biyayya ko? Gara ma ki haƙura ki dena wannan auren ɗanɗanen dan wallahi duk ranar da kika zo mun gidannan da sunan yaji ma, wallahi zaki sha mamakin abunda zanyi miki Tani. In auren kika kaso karma ki nufo gidannan dan wallahi zaki sani in aikata miki abunda ƙila sai dai in ƙarashe rayuwata a firzin." Ni dai da to Baffa naita binshi harya gama mun nasihar. Bara zaku je ne Habu, har hutun sallar ya ƙare?" Baffa yace. "To in bamu fita ba Tani wa zai bamu abinci? Kwana biyunnan dana zauna a gidan duk babu daɗi sam, dan ma matan gida da maƙota sun kawo mana abinci da sadakar nama shi yasa na ɗan huta. In muka zauna a gida babu mai bamu muci. Rannan ma Kaila ya biyo ta wajan barata ya bani ɗari ko Habu ɗari biyar ce ko?" Habu yace. "E Baffa ɗari biyar ya ajjiye mana a kwanon barar" "To kinji kya yi mishi godiya" Wasu hawayene suka gangaro akan kumatuna shar_shar_shar, cijewa nayi nace da Baffa. Zan yi mishi godiya sai kun dawo Baffa. Ga wannan ɗari biyar ɗin kwa yi cefane" Karɓa yayi yana ta yi mun addu'o'in masu daɗi. Shiga cikin gidan nayi na samu su Yaya Use a barandar ƙofar ɗaki a zaune akan tabarma suna dabdalar cin farfesun kan rago. Mu namu kan ragon Hajiyayye aka ba takai ma iyayenta da fatar ragon waccen laiyar ma ita aka ba. "Kaga matar Kaila mai tukubar gashin kajin gidan gona da zabuwa" Cewar Yaya Use kenan uwar barkwanci da tsokana. Dariya nayi mata na zauna a hankali na sakko da Hauwa ja'ira idanta biyu akan cinyar Inno na ajjiyeta. "Inno ina wuni anyi Sallah lafiya?" "Lafiya ƙalau ya mai gidan da abokiyar zamanki, da facalarku kowa lafiya dai ko?" Dariya nayi nace Lafiya lau Inno, ina yaran suke?" Inno tace. "Na aikesu ƴan dankali gidan wata Hajiya kira tayi a waya tace in tura Indo tayi kwalima ta karɓo mun kaya. Shine fa yarannan su kaita magiyar su sai sun bita shine fa na basu kuɗin abun hawa suka tafi." Kai kawai na girgiza na juya muka gaisa da Yaya Use da Yaya Karime. Yaya Use tace. "Tani rannan Baban Abas ya siyo mana kaza a tukubar Kaila gaskiya dole ma Kaila ya dinga uban ciniki gaskiya ya iya gashi sosai." Dariya nayi mata nace. Babu laifi kam ya iya ciniki kam yana yi gaskiya tunda yanzu da kanshi ma yake kiwata kajin nashi, zabi da kajin gidan kuma daga ƙauye mahaifiyarshi ke turo mishi da yajin gashin ma duk ita take aiko mishi dashi. Yaya Karime matar babban direba Baban jafaru ya dawo kuwa?" Murmushi tayi ita ba mai son magana bace tace. "Ya dawo a gida yayi Sallah, amman yanzu haka motarshi tana kan layi a farar gada ana mai lodin kayan gwari zuwa Port Harcourt, ai matan direbobin manyan mota, da matan masu kaki sai dai mu yi ta haƙuri kawai." Nan na shige cikin ƴan uwa mu kai ta hira, da dariya Inno tayi ta binmu, wanda ya kama tasa baki takan sa. Farfesun kan ragonnan nima na zuba kaɗan na sha yayi daɗi gashi yaji kayan ƙamshi. Ana haka sai ga Indo dasu Sulaiman da kaya niƙi_niƙi a buhunhuna sun shigo. Nan na shiga washe baki dan nasan zamu samu kwance ko da ɗaɗɗayane, dan yawancin kayan nawa Inno ce take bani kwancensu. Dan tunda na haifi Balaraba Kaila bai sake mun zani ba, ko na sallah baya yi mun, sai wanda ya bamu jiya na faɗar kishiya. Yara suna ganina suka shiga murna. Anan tsakar gidan Inno ta zazzage kayan tana wawwarewa, gaskiya wannan karon kayan suna da kyau sosai, harda su mayafai na ƴan gayu da takalma. Carab na riƙe wani mayafi baƙi mai kyau, ashe Yaya Use itama ta hangoshi ganin na rigata ɗauka yasa ta bar mun. Atampa da leshi Inno ta miƙo mun da ƙarin mayafi ɗaya. Na karɓa ina murna dan kayan kamar sababbi, gashi ɗinkunan jikin kayan bana banza bane ɗinkunane masu tsada. Ta wari wani ta miƙa ma Yaya Use, ta sake warema Yaya Karime nata itama. Ta ware ma Indo ma. Daga baya ta sake ƙara mana kala bibbiyu, ni nawa riga da skirt na wani jan yadi ta bani, da shadda mai surfani a jiki, na samu mayafai har uku takalmi kala ɗaya ne yayi daidai da ƙafata wani ɓaki. Yaya Use ce ta more takalma dake ita ƙafarta da girma naji daɗin kayannan sosai dama harna tawo da ƴar atamfar da Kaila ya bamu ta faɗar kishiya zan ba wata maƙociyarmu ta ɗinka mun in samu na zuwa Bauchi dan bani da wasu kayan fitar kunya in ba wannan abayar dana sa ran sallah ba. Sai gashi na samu kaya masu kyau sosai. Haka dai muka wuni na ba su Yaya Use ɗan ƙullin nama tsoka uku uku, na ba Inno nata itama ba wani yawa nawa kason ne ma na bata ni na haƙura, su Yaya Use kuma a cikin na yaran na cira musu. "Tani saura sati biyu bikin Momiyo ƴar wajan Shafa ƙanwata ya kamata wannan karon aje Shanono dake, daga nan dai mu je kiga Dauda. Daɗi sosai naji a raina dan ina kwaɗayin son ganin Dauda sosai dannewa nake dan gudun kar in jawo ma kaina jangwam." Allah ya kaimu. Nima gobe nake son zan je Bauchi. Ɗaliban makarantar kwana ta Bauchi da nayi ne suka haɗa taron ƙarfafa juna shine zani. Kuma sati biyu masu zuwa Kaila zai ƙara Aure." Su Yaya Use ne su ka ji wani iri, Inno kuwa saima washe baki da tayi tace. "Ayya namijin duniya to Allah ya baku zaman lafiya. Kar dai kice zaki yi wani zafin kishi ki je ya sako ki a banza. Wallahi in ma ya sakoki kisan tayi dan Baffanku yana jirace ne dake, nima a wannan karon ba barinki zanyi ba. Aure biyar fa sai kace wata karya. Babu abinda yara suka sani na biyayyar aure in banda sakarci da hauragiya. In ce dai da yardar shi zaki je wani Bauchi ko? Dan na sanki sarai da ƙulafacin son makarantar yahudawa." Jiki a mace nace. E da yardar shi zanje. Kuma in sha Allah babu abinda zai sa in bar wannan gidan sai in gawata za'a fitar, in dai yi nayi bari na bari shine aure to da izinin Allah sai dai a fitar da gawata, ko na mutu Lokacin mutuwar baiyi ba, ko kuma wa'adinane ya cika" Ai da faɗar haka Inno tace ina wuta ta tsolma ni. Nan ta shiga mun faɗa tana cewa dama duk take_takena ya nuna so nake Aure na biyar ɗin ma ya mutu in sake auran wani, wai na gaji da ɗanɗana Kaila inason ɗanɗana wani. Nayi kuka ainun wannan kalmar fa iyayena ke jifana dashi bansan kuma mai mutanen waje zasu ce dani ba. Ban karashe wunin da daɗi ba, kafin magriba duk mu ka ɗauki haramar komawa gidajen mazajenmu, har zuwa lokacin Baffa da Habu basu shigo gida ba, har barar dare suke yi wani sa'inma a bakin kasuwar suke kwana ko bakin masallacin ƴan taya a cikin ƴan cirani dake dako a ƴan kwalli.....✍🏻 [10/8, 18:30] Badiat Ibrahim: NA FADO DAGA BENE.... NA ZARCE RIJIYA HAKKIN MALLAKAR BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI GAWURTATTU UKU LAMBA TA 4. Anan na bar yaran akan in na dawo zan yo kiran waya Habu ko Indo su rakosu." A titi muka rabu da su Yaya Use kowa ya nufi gidan mijinshi. Ina shiga na hango Hajiyayye a zaune a tsakar gida tana alwalar magriba idanun nata taci kuka na fitar hayyaci da gani. "Kin dawo umman Sulaiman?" Ni mamaki ma nayi sosai dan Hajiyayye ko ni na kulata sai ta ga dama take kulani. Nadawo Hajiyayye sannunku da gida. Key na ɗakko na buɗe ɗakina na shiga na ko ci sa'a akwai wutar nefa. Shinfiɗe Hauwa nayi na fito tsakar gidan dan yin alwala. Ina zaune akan sallaya na idar da sallah sai ga Hajiyayye ta shigo da sallamarta, waje ta samu a bakin katifa ta zauna. Da ido kawai na bita, to yau Hajiyayye ce a zaune a ƙazamar katifata mai wari?". "Umman Sulaiman ni dake so nake mu haɗe kanmu ta hanyar gasa Kaila a cikin gidannan duk inda ya yi yaji babu daɗi, nifa ina gani bazan bar wata macen ta shigo gidannan ba ko da tsirara zanyi yawo. Kuma ita matsiyaciyar da yake nema zan ɗakko mana number ta mu yi mata kashedi da barazana mai ƙarfi na tabbatar zata fasa auren. Wannan bazai faru ba sai na samu haɗin kanki. Jiya da daddare sabida na fasa mishi wayarshi suna waya shine fa Kaila yasa hannu ya wankeni da mari, har nayi yaji ma na je gida, dawo dani akayi a bisa tilas ba son raina ba. Yanzu in banda maza da shegen kwaɗayi bamu isheshi ba mu biyu? Gamu farare babu wacce za'ace tana da muni jibi yawan gashin kanki dana yaranki fa me Kaila yake nema ne?" Ai ya faɗa miki abunda yake nema da irin macen da yake burin son mallaka. Kinga kuwa dani dake in aka haɗemu bamu kaita ba ko kusa. Ni da zan baki shawara ki ɗauka ko, da kin fita sha'anin batun aurennan in dai kina son tsira da igiyoyin aurenki. A lokacin da Kaila zai auroki da ban kwantar da hankali ba da tuni bana cikin gidannan. Naga hanyar da kike son bi ba mai ɓullewa bace, in Kaila zai kwana yana waya da budurwa ke kuma sai ki kwana Sallah. Kin mance lokacin da yake nemanki kusan kwana waya kuke yi ne, ai a lokacin kinsan yana da mata a gida, yanzu dan yayi menene ai ke kika lalatashi kika kuma nuna mai hakan wayewa ce. Ni kin ganni ina lallaɓa igiyar aurenane babu ruwana da duk abunda zaki yi akan hana Kaila Aure" "Au haka zaki ce ma dan kinga nazo inason mu haɗe kanmu?" Haka na ce ma Hajiyayye." Ina faɗar haka na miƙe na tada kabbarar sallar isha. Fuu Hajiyayye ta fice. Bayan na idar na zauna nayi azkhar sannan na jawo wayata na buɗe data na faɗa group ɗinmu na FGGC. Anata magana da tsare_tsaren yanda za'a gabatar da taron. Magana nayi musu akan goben zan shigo nima dani za'ayi taron" Sunji daɗi ainun nan su kai ta nuna farin cikinsu. Mayafi na yafa na shiga cikin gidan a tsakar gida na samu Kaila a gaban lifan ɗanshi yana duba tayunsu. Sannu da dawowa" Shine kalmar dana ce dashi. "Yauwa Shanono " Iyakar abunda shima yace kenan. Wajan Hindatu naje na aro dutsen guga. A daren na goge kayan da Inno ta bani dukka ƙaramar jakar tafiyata na ɗakko nasa leshi kala ɗaya da mayafi a ciki, nasa ma hauwa kaya kala biyu da famfams guda uku dana tsaya na siya a bakin layinmu, ɗayan kuma na ajjiyeshi gobe in zamu tafi zan sa mata. Na daɗe a kwance ina tunanin yanzu shikenan rayuwata ta mutu a haka zanta rayuwa kenan ni. Nice har karfe ɗayan dare ban runtsaba. Dana ga dai baccin ya ƙauracema idanuna saina miƙe na fito dan ɗaura alwala. Abun mamaki na jiyo tashin muryoyin Kaila da Hajiyayye, yana ambaton. "Ki bani wayata, wallahi kika sake fasamun waya a bakacin aurenki. Wawuya mahaukaciya kinga Shanono tana irin wannan haukar ne? Ko da aka auroki kin taɓa ganin ranar da ku kai cacar baki ne. Amman kin kira yarinya a waya kunyi zage_zage sabida ki nuna mata kin rainani ina cikin wayata kin fisge." Baki na taɓe na tuno wata rana da daddare da muna mu'amular Aure ni da Kaila Hajiyayye tayo kiran wayarshi lokacin suna ganiyar soyayyarsu. Haka Kaila jiki na rawa ya zare jikinshi a nawa ya shiga amsa wayar Hajiyayye kwanciyar da ba'a gamata ba kenan. Har batsa yake yi da'ita a waya a gabana. Ina gani suna waya gabanshi zai miƙe ƙyam sabida musayar maganganun batsa da suke yi da junansu. Hmm ashe wanzami bai son jarfa. Alwala nayi na shige ɗaki abina, na dinga gurgura Sallah, dan ɗan karatun sallan ba wasu masu yawa na iyaba, ko izifi biyu ban cika ba, ɗan abinda na haddace dasu nake gudanar da ibadar tawa. Washe gari sassafe nayi wanka naima ƴata wanka. Masa na siyo a gidan maƙota ta ɗari biyu muka ci ni da Hauwa. Nasa mata pampas da kaya. Wannan atampar ta jiya da inno ta bani na saka ɗinkin riga da zani ne. Nayi ɗaurin ɗankwali na maryam babangida. Na ɗauki baƙin mayafin jiya na yafa a kaina, na ciro baƙar ɗaya_ɗayar jakata na ɗan zuba kuɗaɗena a ciki da ƴan tarkace, wayata, chaja, da dai sauransu. Banyi kwalliyar komai ba ko turare ni bani dashi, bama ni da kuɗin saye. Kayan kwalliyar ma bani dasu kwalli kaɗai nake murzawa, in banda jar hoda ta zazzzage Zainab da rannan Yaya Use tazo ta mance da'ita shine na samu na ɗan barbaɗawa, haka nake yin wani janƙau in na shafata. Fitowa nayi na rufe ɗakina Hauwa tana baya. Jakata a ajjiye a zauren na shiga cikin gidan Kaila yana tsakar gidan yana zaune akan kujerar tsugunno yana waya sai wani ƙanƙance idanu yake yi, wandonshi na kalla ya cika fam. Hmm maza mutanen mu. Banza nayi dashi na wuce Hindatu nayi ma sallama zani Bauchi. Na dawo nayi sallama a ƙofar ɗakin Hajiyayye tana fitowa naga sai bin ƙasan zanina da kallo take yi cike da mamaki tace. "Yaushe kika ɗinka kayannan umman Sulaiman, sunyi miki kyau?" Da sallarnan na ɗinka. Nagode" Na bata amsa kafin na ɗaura da cewa Ni zanje Bauchi sallama nazo yi miki." Nan da nan naga ta murtuke fuska ta shiga jijjiga kai ni dai wuce ta nayi a tsaye a wajan. Nazo zan wuce Kaila ya ɗaga mun hannu dan gudun kar in yi magana budurwar tashi taji in kwabsa mishi. Haka ya dinga mun lokacin Hajiyayye gashi lokaci yayi ana rama ma kura aniyarta. Fita nayi abuna zuwa Bauchi road a gefen hanya na samu motoci masu zuwa Bauchi nera dubu. Shiga nayi baya mu uku ne a ciki dukka mata mutum ɗaya ake jira na gaban mota sai mu kama hanya. Gaggaisawa nayi da matan motar. Wayata ta shiga ruri ina ɗagawa naga Habiba Bala ce ke kirana. Karawa nayi a kunne. Habiba Bala kin ganni na shiga motar Bauchi kenan amman motar mu bata tashi ba tukunna." Daga cikin wayar Habiba Bala tace. "To Shanono Allah ya kawo ku lafiya karfa ki mance a zaranda hotel zasu ajjiyeki in kika sauka a bakin hotel ɗin sai ki kira ni zan zo in shigo dake ƙarfe tara muka sa lokacin taron gamu kusan dukka mun hallara ku biyu ne baku ƙarasoba Halima Bawa daga Gombe take tawowa amman tun asubar fari ta tawo duk yanda ake ciki nasan ta kusan shigowa Bauchi. To Allah ya tsare." Sallama mu ka yi akan saina kirata. Ko da na sauke wayar saina shiga mamakin yadda Habiba Bala take magana a mugun yangance. Ni dai da sanin dana mata ƴar karaɗice da son aba hammata iska. Dan ko rigima muka kwaso ita ke shigewa gaba ta tare mana. Gata da kuri kuma ƙatuwace a lokacin mai ƙiba sosai, ɗalibai na jin tsoronta. Ɗan guntun murmushi nayi dana tuno rayuwa. Ban jima da zama ba motarmu ta cika muka biya kuɗi muka kama hanyar Bauchi. Tafiyar awa ɗaya da rabi ne cib ya kaini Bauchi. A dai_dai zaranda hotel na sauka. Ina sauka na ga Halima Bawa tsaye da goyo a bayanta. Duk da ta zama babbar mace amman kamanninta yana nan yanda na santa. Halima Bawa kaddai sai yanzu kema kika samu isowa?" Na yi magana ina nufota. Da sauri ta juyo sai kawai ta ganni. Baki ta washe tana tafa hannuwa. "La'ilaha illallah mahammadun rasulillah sallallahu alaihi Wasallama Shanono ashe da rabon zamu gana? Kai Allah yaima Habiba Bala albarka ta da yi ƙoƙarin sake haɗemu waje guda a karo na biyu." Ɗan rungumar juna muka yi ta kafaɗa muna cike da farin cikin ganin juna, ƙamshi jikin Halima Bawa yake yi sosai, gata shar_shar da'ita cikin kwalliya da ado. "Ga ciki ga goyo kuma Shanono? Dama har yanzu ana haihuwar konika a wannan tsadar rayuwar da muke ciki. Kai Shanono har yanzu kina nan da ƙauyancinki wai?" Kafin in bata amsa muka hango wata mota ta tsaya a gabanmu. Baki dukkanmu muka sake muna kallon Habiba Bala. Ni dai da idanuwanta kawai na ganeta dan wallahi na ɗauka wata balarabiyace ta sauka daga masar. Ni sanin da nayi mata mai ƙiba ce sosai, kuma bata kai haka haske ba. Sai kuma yanzu na ganta ƴar madaidaiciya da'ita, ga mota tana ja. "Habiba Bala kece kika zama Hajiya haka?" Cewar halima Bawa. Dariya tayi mana haƙoran matanta biyu sama da ƙasa suka bayyana tace. "To ya sanki? Shegiya Halima Bawa kina nan yadda kike babu abinda ya sauya. Ke kuma Shanono dan ubanki meya kawo wannan ƙanjamewar haka?" Dariya dukka mu ka yi. Motar muka shiga Habiba Bala ta canja akalar motar zuwa get ɗin shiga hotel din. Halima Bawa tace. "Ba dole shanono ta rame ba. Kinga fa ga ciki tulele a gaba, ga ɗanyen goyo kuma fa. Nima ina ganinta na dirar mata" Ni farin ciki ya hanani magana ma sai dariya kawai nake yi. A wajan ajjiye motoci muka tsaya dukkanmu muka fito. Habiba Bala ta karɓi jakunkunan mu tace. "Bari in taimaka muku da jakar. Tana tafe muna biye da'ita zuwa sama. A sama ta huɗu muka tsaya a bakin wani ɗaki. Tura ƙofar tayi tana gaba muna biye da'ita a baya. Tangamemen falone babba sosai muka shiga. Ƴan set ɗinmu na soma cin karo dasu. Wasu sun canja irin Habiba Bala, wasu kuma sun lalace ire_irena. Amman kowacce ta zama babbar mace sosai da sosai. Waje na samu na zube a ƙasan kafet ɗin daya malale katon falon. Nan aka shiga gaggaisawa, duk da na ga baƙin fuska har wajan rai biyar. "Kinga waɗannan daga siniya suka shigo. Lokacin kin gudu gidan aure daga zuwa hutun gama jiniya. Fatima wannan itace Shanono" Allah sarki sannunku sannunmu. Barkanmu da zuwa dukkanmu ita Habiba Bala Allah ya saka mata a alkhairi a bisa wannan zumunci data kuma haɗawa. Hakan yasa na tuno rayuwarmu a baya lokacin duniyar tana kwance." Nan fa hirar makaranta ta ɓalle. Hauwa na zaro a bayana na miƙa ma Habiba Bala ita. Fatima B Bello kuma ta fita samo mana abinci. Jallof din taliya da kifi sadin muka ci da lemon kwalba. Bayan mun ɗan nutsa kuma sai Habiba ta miƙe tsaye har zuwa lokacin Hauwa tana hannunta. "Assalamu alaikum ƴan uwana abokan karatuna ina mana sallama irin ta addinin musulunci. Ba komai bane yasa na dage na yi ƙoƙarin ganin na haɗa mu waje ɗaya sai san zumunci da tallafin juna. Duba da yanzu yanda Aure ya taɓarɓare a ƙasashen Hausa. Sai dai muce innalillahiwainnailaihilrajiun kawai. Naso ace na samu damar tattaro kanmu duka. Amman ƴan ajinmu na A ma kaɗan na samu na iya tarkatowa. Kafin in ɗaura jawabina inaso wata ta taso ta buɗe mana wannan taro mai albarka da adda'a" Wani jin daɗi ne mara musaltuwa naji yana lulluɓeni sai nake ganin kamar zan samu sassauci matsalolina ko da da iya shawari ne, kuma ƙila in samu waɗanda zasu fahimtar dani inda maganin matsalata take. Halima Bawa Amirar mu a makaranta ita ta tashi ta buɗe mana taron da adda'a. Kafin kuma Habiba Bala ta ɗaura. "To kamar dai yadda na faɗa dalilin assasa taronnan badan komai bane sai dan mu dinga zumunci da ƙarfafar junanmu, da ba juna shawarwari masu kyau. Sannan inason mu ware wani asusu na taimakon kai da kai. Ta hanyar ajjiye wasu ƴan kuɗaɗen da zamu taimaki junanmu dashi. Gwargwadon abunda kake dashi shi zaka zuba tunda ba adashe bane, in ma baka da halin zubawa mun ɗauke maka, hakan bazai sa mu kasa taimakonka a lokacin da buƙatar hakan ta taso ba. Ba komai bane yasa nayi wannan tunanin ba face ɗan matsalolin dana ɗan shiga a baya wanda wani sirrina ne, amman alhamdulillah komai yanzu ya dai_daita wannan halin ne yasa na tuno daku. Nasam yanzu mata kaso casa'in na gidan aure haƙuri suke yi kawai. A wannan zamanin ba ko wanne namiji ne yake iya sauke dukkan hakkokin da suka rataya a wuyanshi ba. Kaso hamsin daga cikin mazan talauci ne yai musu katutu, ko yawan yara da tarin mata daya zube a gida yasan bashi da halin kula dasu. Kaso hamsin ɗin kuma mugunta ce da som ganin sun tauye matayen aurensu yake sawa su kasa sauke hakkokinsu. Bance duka aka zama ɗaya ba kar maza su samu jakar tsaba. Mu kuma matan bama yi ma kanmu adalci. Mun shigo zamanin da bayan zaman auren dole kina da buƙatat sana'ar da zaki dinga juya taro ya koma sisi. Ko kuma kiyi karatu ki yi aiki. Ta hakane zamu tsira da mutuncinmu a gidajen aure a dena ganinmu a tagaiyare a haɗu a rufa ma kai asiri. In ya kawo ayi, in ma bai kawo ba ke zaki ɗauka da kanki kiyi. Amman fa in ma Allah ya haɗamu da mazaje masu tsoron Allah, nagartattun mazan da suka san darajar mace kuma basa son suga mace tayi kuka ko ta shiga damuwa ba. To zama haka fa bai ganmu ba. In kina da ƴan canjinki wani wulaƙancin ma namiji bazai iya tunkaro inda kike dashi ba. Amman mazan yanzu in ba kya aiki ba kya kasuwanci ganinki suke a matsayin nauyi a kansu. In talaucinshi ya bugoshi ya dawo gida ya sauke miki buhun rashin mutunci. Ni kiran da zanyi mana shine ilimi yana da matuƙar mahimmanci ilimin addini dana zamani, ko zamu haɗa da sana'a mata ya kamata mu yi ilimi ko da mijinki bazai barki kiyi aiki ba, ke a_kan_ karan _kankin_ kanki zaki zauna lafiya jahilci ai babban ciwo ne. Ni nayi karatu na karanta fannin ilimin limitanci ni likitan mata ce ina aiki a babban asibitin Bauchi. Bari in ga waɗanda da suka ci gaba da karatu bayan gama sakandare" Cikin zolaya tayi maganar tata. Naji daɗin maganganunta sosai wallahi, na yarda rashin ilimi bai yi ba a rayuwa, ni dai na addinin ma iyakata makarantar allo da nayi a shanono ina dai dana Sallah. Boko a ƙaramar sakandare na tsaya, kuma na taso da hazaƙa da son ganin nayi karatu mai zurfi. Amman Baffa ya dakatar mun da karatuna yai mun aure. Ƙalilan ne daga cikinmu suka gama jami'a suke aiki. Sune suka fita daban ko a cikinmu. Halima Bawa atampar dake jikina tafi tata kyau a ido. Amman dake ƴar makaranta ce tana da wayewa sai ta fini haskawa, ni ko kashe ma kayan kyau ma nayi. Mu sauran irin su Fatima B Bello iyayene mazauna gida. Habiba Bala tace. "To ku da ba ku ci gaba da karatun ba bakwa sha'awar karatunne ko sana'a dai kuke yi?" Nice nayi Magana nace. Ni dai bana siyar da komai Habiba Bala. Ina zaune a gida kusan duk shekara sai na haihu. Yarana bakwai ga na takwas a cikina. Amman yanzu naji ina sha'awar karatun addini dama kasuwancin ko da sai da daddawa da kanwa a cikin gida ne" Ai kamar na buɗe ƙofa ne, wannan tace itama sana'ar take son tayi, sai masu son komawa islamiyya nan dai muhawara ta ɓalle." "To duk abinda kuke son yi zaku yi da izinin Allah, kusa a ranku zaku yi. Zamu dinga tara kuɗi duk wata, sai a dinga raba ma mutum biyu. Duk abinda Allah ya hore muku ku kawo a soma tarawa. Sannan zan ajjiye muku account number ɗina ta cikin group in wata yayi ko ɗari biyu ne da ke turo. In baku dashi an yafe miki. Masu son makaranta kuma zamu yi magana in sha Allah. In akwai me abun cewa tace sai mu rufe taron da adda'a" Da ƙyar na yunƙura na tashi tsaye sunai mun tsiyar duk shekara da nace saina haihu, wasu daga ciki sai jinjina mun suke yi. Hakika na ji daɗin wannan taron, kuma zuchiyata tayi mun fari tamkar audiga. Kuma taron ya haskamun wata hanya wacce ta zamto hanyar cikar burina. Allah ya sani ina da son karatu ku abokan karatuna kun sani. Wannan buri nawa bai cika ba a baya nazo mahaifina ya turani gidan aure domin neman aljannata da ɗanyen shekaruna sharab. Amman in sha Allah zan shiga makaranta in yi yaƙi da jahilci ƴar sakandare ɗinnan in kammaleta sai in ci gaba da zuwa ta muhammadiyya kuma. Sana'ar ma in sha Allah zan soma kamar sai da daddawa ko kanwa da kuka. Madallah da abokan karatu irinku. Kamar yadda muka haɗu a ɗakin hotel ɗinnan Allah ya haɗamu a Aljanna haka" Ɗan tafa mun su ka yi. Nan aka tsai da matsaya mai kyau mu da bama karatu muke son ci gaba Habiba Bala ta bimu da dubu biyar biyar bayan kowa ya bada kuɗin shi na wannan watan kenan. Ɗari biyar na zaro na danƙa mata. Kafin ta bimu da wannan kuɗin tace mu samu islamiyya mu soma zuwa tukunna, ni da nake son in karashe sakandare kuma tace zamu yi magana. Ledoji viva ta bi kowa dashi ciccike kai Habiba Bala tayi ƙoƙari. Mun kai bayan azahar kafin muka gama, mun rufe taron da adda'a sai da mu kai sallar azahar, muka ɓalle da hirar yaushe gamu, kuma aka shiga haramar komawa. Musamman ƴan nesa da mazauna ƙauyen Bauchi. Da dukkan alamu babu mai kwana dan ƴan cikin. Garin ma kowacce ta yafa mayafinta a ka. "Wai kuna nufin har kowa zai tafi kenan. Halima Bawa, Shanono kuma tafiya zaku yi yau. Mai makon ku bari sai gobe sai ku tafi, sai mu je gidana mu kwana ai, akwai waje fa. Ni kam har ga Allah dama banyi niyar komawa yau ba sam, ni da so samu ne in kwana biyu ma zuchiyata ta huta tukunna kafin in koma. Ni da da niyyar kwana biyu ma nazo kinga jakata fa. Halima Bawa muje mu kwana a gidan Habiba Bala mana" Itama Halima Bawa bata ja ba da dukkan Alamu da shirin kwanan tazo, kuma itama tamkar cikin damuwa take. Dukkanmu muka ɗunguma zuwa waje. A wajan ajjiye motocin muka tsaya jiran Habiba Bala. Aisha Aliyu itama mota take ja ashe, ita da Karinatu Jibril sai Habiba Bala. Mutane duk suka ɗuɗɗura a mota muka fice a tare bayan mun yi sallama da juna. Zukata sun yi sanyi, kowa yaji daɗin ganin kowa. Sai da muka shisshiga gidajen su Fatima a tsattsaye dai haka bayan mun gama saukesu mu kai sallama Habiba Bala ta nufi hanyar gidanta dake bayan tsohuwar Airport. Ni dai muna tafe na lula cikin tunani mai zurfin gaske. Hoton tsaraicin Hajiyayye yana yawan dawo mun, dana tuno sai gabana ya faɗi naji tsigar jikina ya tashi. Haka ina hango wandon Kaila yanda ya cika dan kawai yana waya da budurwa. Magidanci mai yara takwas, shine da irin wannan aiki, mazanmu na hausawa sun ɗaura zuchiyoyinsu a son tara mata da kula mata, da zantuttukan batsa marasa daɗin ji. Ka rasa ina matsalar take laifin mazan ne, ko laifin ƴan matan ne, ko kuwa laifin matan cikin gidane, a'a ko kuwa laifi na iyayene?" "Shanono....." Wannan tunani haka lafiya meke damunki ne haka?" Cewar Habiba Bala kenan. Har motar ta tsaya ashe ni ban sani ba ina can duniyar tunani. "Ki yi iya ƙoƙarinki wajan ganin ɗa namiji bai sa zuchiyarki tayi bindiga ba, yaranki ne zasu yi maraici shi kuwa bashi da asara." Idanu na zuba mata ƙur ban da zarafin iya furta komai. Fitowa nayi ina ƙarema haɗaɗɗen gidan kallo. Muna baya tana jagorantarmu har zuwa cikin matsakaicin falo mai kyau mara shirgi da hayaniya. Setin kujerune dak blue a falon irin ƴan ƙanana na zamani. Sai tv na bango dake ajjiye akan t v sitan, sai kafet na tsakar ɗaki wanda ya dace da kujerun, haka ma labulen falon ya dace da kujerun. Sai wani guntun firji a gefe da disfensa ta shan ruwan sanyi ko tea iyakar abunda ke cikin falon kenan ya fito yayi ƙwasƙwas sai sheƙi tayil ɗin falon yake yi. Zama nayi a kujera ina kallon Habiba Bala da maɗaukakin farin ciki yalwacce akan fuskata .......✍🏻 [10/8, 18:30] Badiat Ibrahim: NA FAƊO DAGA BENE.... NA ZARCE RIJIYA HAKKIN MALLAKAR BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI GAWURTATTU UKU. 5 Cikin fara'a nace Masha Allah rayuwa tayi albarka Habiba Bala. Irin wannan daula da kike ciki haka. Ah abun yayi kyau" Murmushi ta sakar mun kawai ta nemi ɗaya daga cikin kujerun falon ta zauna. Muma zama mu ka yi. Halima Bawa tace. "Ni banji motsin kowa ba a gidan, kaddai baki samu rabo bane Habiba Bala?" Wani murmushi tayi mana irin na manyan mata kana tace. "Na samu rabo yarana uku dukka maza" Tare muka haɗe baki wajan cewa. Masha Allah." Halima Bawa tace. "Ismaliyya suka tafi ne, ko gidan kakanninsu nasan dai ana hutun Sallah?" "Halima Bawa kina nan a ƴar bin diddiginnan dana sani, aikin jarida zai fi dacewa dake. To yara suna Jigawa gidan Babansu. Bani da Aure a halin yanzu. Ni kaɗai nake zama a gidannan sai Iya mai taya ni gyaran gida da jire mun gidan, ni kuma ina zuwa asibiti kamar yadda na faɗa muku a cikin taro" Jijjukannanmu gabaki ɗaya sai yayi sanyi laƙwas. Wato wannan mace_macen auren ya karaɗe Arewa sosai? Ada ƙabilar Hausa an san mazansu da riƙon Aure da haƙuri. Kamar yadda matan suke da kunya, kawaici, gami da yakana. Ni dai na rasa gane a inda matsalar take. Furucin Halima Bawa ne ya dawo dani daga zancen zuchin da ya jima da aurena. "Hmm mazan ƙabilar Hausa na wannan ƙarnin sun maida saki tamkar ya da ledar fiya wata. Nakan yi mamaki da tunanin mai ya taɓa malam bahaushe ne haka, wannan aure da sakin yayi yawa, yawan zawarawa a ko da yaushe sake hauhawa yake yi a ƙasar Hausa, hakan yasa zinace_zinace yai yawa, duk da zina yanzu ta zama ruwan dare game duniya. Su kuma al'ummar Hausawa basa yi ma bazawara kallon tausayi, sai kallon maras tarbiyya, maras haƙuri. A cikin gidanku ma sai mahaifanka su kasa yi ma uziri, ai ta hantararka, in Aure ya mutu to fa macen itace mai lafi. Da tayi aure ɗaya biyu sai a sa mata suna, wata ma taƙi auruwa. Amman shi Namiji a kan dukkan abinda yake a kai ƙarfafa mishi guiwa jinsinshi suke, in aure goma zai yi, ij yaje nema za'a wanke a bashi. Haka Namiji da mace zasu aikata zina, ita macen ya zame mata masifa, taƙi auruwa aita goranta mata. Shi kuwa namiji sai ace mishi duk abinda yayi adone. Zina ashe zata iya zamewa ado? Wa'iyazubillah. Nima na ɗanɗani wannan rayuwar, sai da na shekara takwas ina zawarci. Duk wanda yazo wajena da iskanci yake zuwar mun. Ko ku ga da girmana yara ƙanana masu soyayyar shan minti suna zuwa. Wannan dalilin yasa na yi fatali da surutun iyaye da dangi, sai na koma makaranta na yi karatun jami'a, ban yi aure ba sai da na dafi aikina mai kyau a hannunna. Ko yau aka sake koroka a ƙalla ba zaka tagaiyara ba, kana da abun yi, ba zaka bada jikinka dan ka biya buƙatar kan ka na yau da kullum ba" Idanuwanta take suka ciko da ruwan hawayen tuno da wasu ƙunci da suka shuɗe mata a baya. Ni kuma leɓe nake cijewa kawai, irin azabar da rijalu suka ɗanɗana ma ruhina bana wasa bane. Hmmm Allah ya kyauta" Shine abun da na iya cewa, amman tabbas Halima Bawa ta taɓo inda yake mana ƙaiƙayi ainun. "Halima Bawa kenan. Ke aure ɗaya ma kika yi kika fito a ɗan labarin da kika bamu. Kin ganni mazaje uku na aura amman zaman yana ƙin yiwuwa. Ku dai mu shiga daga ciki ku ɗan watsa ruwa ku huta. In muka nutsa zan dan baku a taƙaice, amman naci wuya. Jagora tayi mana i zuwa cikin ɗakinta wanda ya kasance haɗaɗɗe. Ga takalma a jajjere sunfi sawu talatin, jakunkuna suma gasu nan kaya guda a rarrataye a abun rataye jaka. Ɗakin sai wani irin ni'imtaccen turaren wuta ke tashi wanda ban taɓa jin ƙamshi turare mai sanyi irin wannan ba. ( In kina son ɗakin ki ke ma ya dinga ƙamshin gidan sarakai ki neme ni, zaki samu dukkannin nau'ikan turaruka masu sanyin daɗi 08179523215) A 3sitter dake uwar ɗakin na zauna. Hauwa na sinto a baya na na shinfiɗeta a gefe baccinta take ta shantakawa. Halima Bawa kuma mayafinta ta yaye ta yi zamanta akan gadon Habiba Bala wanda yasha shinfiɗa lallausa." "Ga bayan gida nan akwai ruwan zafi a ciki. Ku yi wanka, sai ku yi Sallah. Bari in samu Iya a kitchin inga mai take dafawa yau ina da manyan baƙi" A haka ta fita ta barmu hatta Halima Bawa kallon sha'awa take yi mata ballantana kuma ni tukururu. Wanka mu ka yi dukkanmu tare da ɗauro alwala. Kayan jikina ni dai na mayar na yafa mayafina ina tunanin to ina ne gabas ina son gabatar da sallar la'asar wacce aka jima da yin ta. Dan yanzu ƙarfe biyar ma ta gota, amman har yanzu lokacin sallar bai wuce ba. Ina cikin wannan tunanin Habiba Bala ta shigo da ƙaton tire shaƙe da kayan abinci. Nuna mana gabas mu yi sallah Habiba Bala." Gabas ta nuna mun, da mamaki ta dube ni tace. "Wai da ki ka yi wankan kayan jikin ki kika mayar Shanono, har yanzu kina nan da halinki na adankiya ko? Wannan fa ƙazantace, kin sako kaya tun daga gida, kin ciyo uwar tafiya yanzu kinyi wanka kin sake mayarwa jikin ki, to meye ma amfanin wankan naki in banda abinki, baki zo da wasu kaya masu sauƙi bane na shan iska haka?" Gaskiya banzo da kayan shan iska ba." Dariya tayi tace. "To yi sallar bari in kawo miki ƴar doguwar riga ta shan iska ko kema kya ji dama_dama. Bauchi ana zafi ba kamar Jos bane da zaki ji sanyi kamar a masko." Dariya mu ka yi dukka. Bayan mun idar da Sallah, muna zaune, Halima Bawa tana saye da ƴar doguwar riga ta shan iska mai kyau. Habiba Bala ta shigo rike da riga ta miƙo mun. Na saka rigarnan ɗas dani gwanin sha'awa ga cikina ya sake fitowa sosai a kayan. Soyayyar shinkafa da pepper chicken Habiba Bala tasa ayi mana shinkafar taji kayan lambu da yankakkun hanta ƙananu, ga masar Bauchi da ƙuli_ƙuli shima, sai lemon kwali na tatacciyar abarba mai shegen sanyi. Ni dai sai cika bakina nake yi. Har ga Allah tunda nake ban taɓa cin shinkafa mai daɗin wannan ba. Lemon tatacciyar abarba na kora dashi. Habiba Bala tace. ""Shanono watan yarinyarki nawa ne, naga cikin naki tsoho shima ga yarinya ƙarama?" Sai da na haɗiye naman kazan dana yaga nace. Watan ta dai to tara zance kawai duk da bata ƙarashe ba shi kuma cikin wata takwas zance. Dan Allah a matsayinki na likitar mata wacce hanya zanbi dan ganin na kauce ma samuwar ciki ina shayarwa? Ke ni yaran ma sun isheni haka inason in huta ma rayuwata, Kaila sabon Aure ma zai kuma zai sake samun sababbin ƴaƴa ƴan gaban goshi, tunda iyayen nasu suma ƴan gaban goshin ne" Tataccen ruwan abarba ta kora kafin tace. "Akwai hanyoyi da dama da mace zata yi tsarin iyali, domun jikin mace yana da buƙatar hutu da hakanne komaɗar mace zai dawo. Amman ta yaya ma zaki zama ƴar gaban goshi a wajan miji. Kullum cikin ciki da goyo, yau ƙarnin jinin biki, gobe ƙarnin nono haba. Akwai allura ta tsarin iyali, akwai wanda ake sawa, sannan akwai ƙwayoyin da ake haɗiya, duk in ba wannan ba akwai hanyar da zaki iya yin tsarin iyali ta hanyar ƙirgen kwanaki, ina nufin kwanakin sakkowar ƙwai, in muka ƙirga kwanakin al'adarki zan ɗauraki a kan hanya in wannan ɗin kike so. Kinsan mutane da dama na gudun matsalolin da tsarin iyali suke haifarwa ga lafiya. Amman yana da kyau tsarin iyali musamman a wannan ƙarnin da muke ciki na yawan mace_macen aure, da kuma yanda a wannan zamanin mazanmu na Hausawa basu cika tsaiwa akan ƴaƴa ba, hakan shi ya jefa Arewa a cikin musibu iri daban_daban." Gaskiya ne dukkan maganganun Habiba Bala, a raina naji na gamsu zan yi tsarin iyali ko dan nima jinin jikina ya dawo, so nake in daure in zama ƴar kallo a tsakankanin Kaila da abokan zamana. Duk da dama ƴar kallon ce. Hakan zai yiwu ne in na dakatar da haihuwa zuwa wani lokacin, suma su miƙe ƙafa suita zubo yaran, wala Allah su ya kula dasu da kyau, ni kuma in ci gaba da kulawa da nawa yaran." Halima Bawa tace. "Wallahi hakane maganarki Dr Habiba Bala. Ni kaina daga wannan haihuwar dai in sha Allah ni na dena haihuwar baki ɗaya ma, wallahi da da hali ma mahaifar zan juya, wadanda na samu ma Allah ya raya mana su da imani. Yanzu mazan mu basa iya sauke ratayayyen hakkunan iyalansu daya rataya a wuyansu, mafi yawancinsu duk haka mazan suke, ɗaiɗaikune na kirki. Babban abinda yake bani tsoro shine ba ga gidan mai sani ba, ba ga gidan jahili ba, mata kuka suke ta ko ta ina kawai. Allah dai ya iyar mana kawai." Habiba Bala tace. "Ni zan faɗa miki wannan Halima Bawa. Kun ganni aurena na fari malami na aura, wanda yake da sani sosai ta ɓangaren addini. Ni abinda ya fara jan hankalina a game dashi ma kenan. Sabida a tsari da zubinshi bai yi mun ba har ga Allah. Tunanin samun kwanciyar hankali, da kwaɗayin gurje soyayya yasa na shiga wannan gidan, dan kunsan ance ustazai akwaisu akwai iya soyayya da kwantar da hankalin mace" Dariya muka kwashe dashi ni ko har da tuntsurawata. Sai da mu ka yi mai isarmu sannan ta ɗaura da cewa. "Amman dana shiga gidan nashi abun mamaki ashe ni nawa kallon kitse naima rogo (na ɗauka irin dacen da Mrs Bukhari tayi nima irinshi nayi. Dan nata ustaz ɗin sune mayun soyayya da tsantsar sanin darajar mace irin na ustazan asali) Wata na farko dana biyu duk lafiya. Daga wata na uku muka soma samun saɓani. In kwananane sai yayi ƙundumbala ya faɗa ɗakin uwar gidana, ni kuma babu haƙuri dan wannan ai rainin hankaline tsantsa, kuma duk macen da akaima haka tabbas sai ta zargi kanta da cewar ANYA NI CIKAKKIYAR MACACE KUWA? In na shiga na same shi yana cin abinci a ɗakin uwar gidanshi, da nayi mishi magana cewar kwanan nawa ne fa, sai yace ya sha'afa amman in yi haƙuri tunda yaci abincinta gobe ya shigo ɗakina. Daga haka matsala ta soma tun yana shigowa ɗakina wallahi har ta kai ta kawo ko iya ɗaga ido ya kalleni bayayi. Da nayi magana sai zagi da hantara, har ya dinga ce mun shi aurena bai amfaneshi da komai ba tunda ni ba haihuwa nake yi ba. Bazai dinga asarar ruwan jikinshi ta hanyar yin mu'amular Aure dani ba, ina mai asarar ruwa a banza yana bin rariya. Sai da na shekara biyu cib a gidanshi baya ko ɗaga labulen ɗakina. Abinci sai Babanmu ke aiko su Mansura su kawo mini. Dana je gida, sai su dawo dani raɓe_raɓe tare da faɗar wannan kalmar ta gadon mata (ko wacce mace zaman haƙuri take yi a gidanta. Amman duk macen da kika ganta a gidan mijinta akwai wani abun da mijinta yake yi mata wanda bata so) haka za'a tusoni gaba in dawo. Daga ƙarshe dai yai mun sakin tozarci. Yaronshi ɗan shekara uku ya aiko mun da takaddar sakina saki uku. Sai na dawo gida. Nan ƴan uwa da dangi suka dira a kaina. Biki ko suna sai da suka gagareni shiga. Mahaifiyata kuwa wallahi kamar sauyamun ita akayi, wani irin tsanata tayi, ko gaisuwata bata amsawa. Shekara guda nayi a gida sai na samu bazawari. Sakamakon tsangwama da son barin gaban iyayena yasa na auri wannan miji daya nuna yana sona. Dan ko bincike ba'aiba aka wankeni aka kaini gidan miji. Ashe madokine shi kuma. Ga matanshi tamkar karnuka kullum cikin haushi suke. Daya zo sai ya haɗa mu yaita labta tamkar Allah ne ya aiko shi. Ba dama kuyi magana ta arziki. To watan aurennan biyar ya mutu mus. Hmmmm" Hawaye ne ya gangaro a kumatun Habiba Bala, ni kuma nayi jigum ina saurarenta dan ko kwatan kwatan azabar da nasha a hannu maza bata ci ba sam, ni bana ma ƙaunar tuno da baya, banga abinda zai sa in zauna ba da labarin aurarrakin da nayi a baya ba. Na tabbatar labarin zai karya zukatan al'umma da dama, mata zasu zubar mun da hawaye sosai, maza da suke tunanin matsalar a mata ne, zasu sama ma mata lafiya. Habiba Bala ta share hawayenta taci gaba" "Dana koma gida, na miƙa ma mahaifiyata takaddar sakina. Sai ta fashe da kuka, ni kaina kukan nake yi, shikenan na dawo gidan jiya. Ni ba mutuwar auren bane yafi ɗaga mun hankali ba, a'a irin zaman da zanyi da mahaifiyata da ƙannena shi nake tunani, dan hatta maƙota in suka shigo gidanmu sai sun yada mun habaici kafin su fita. Mahaifina a ranar ko runtsawa ya kasa yi, ni dai haka naci gaba da rayuwa a cikin gidanmu. Rana tsaka mahaifiyata take sanar dani mahaifina ya janye duk wani taimako da yake mun. Dangin su sabulu, man shafa, abinci, suttura. A ranar nayi kuka ainun, amman ya zanyi, sai na nemi mai gidan wani abinci ina mata wanke_wanke tana biyana ɗari biyu da abinci dafaffe. Da ɗari biyunnan zan sai sabulun wanki, dashi nake wanka, da ɗan man kaɗanya ko man alaiyadi su nake shafawa. Ina cikin wannan halin kwatsam wan mahaifina yazo daga ƙauye can Jigawa. Anan ya samu labarin mutuwar aurena na biyu. Ni dai bansan yanda suka ƙareba, bayan kwana biyu da tafiyarshi, sai ga Asabahu ɗanshi wai an turoshi ne ya ganni, in nayi mishi sai mu sasanta, in ban yi mishi ba to" hmmm Asabahu yace banyi mishi ba, wallahi mahaifiyata ta zaunar dashi ta dinga cewa ya rufa mata asiri, dangi sun sata a gaba ita kaza_ita kaza. Da haka ta jawo hankalin Asabahu ya amince da aurena. Ni ina gefe kamar yajin ƙosai, bani da bakin furta komai. Haka aka sa rana, aka kawo kayan aure a cikin baƙar leda viva. Ranar wata asabar aka ɗaura aure. Babanmu da kanshi ya kaini har wannan ƙauye. Dama nasan ƙauyen ni ba baƙuwa bace a ƙauyan. Nayi kuka sosai ganin yanda mahaifana suke neman kai dani. Ina cikin maraya haifaffiyar maraya sabida kawai ba sa son a zagesu ace sun kasa bani tarbiyyar da zanyi zaman Aure, shine suka kawoni ƙauye suka juye. Iya wuya naci wuya nice daka, nice zuwa gona, nice_nice_nice dai, ga ƙauye da gori wannan tambarin aure biyu fa yana nan anata yaɓa mini magana. Ni dai nasa audiga na toshe kunnena. Ta ɓangaren Asabahu babu daɗi, ta ɓangaren abokan zamana kuwa lafiya muke zaune dasu sosai. Shi kuwa babu dama yayi ba dai_dai ba in yi magana sai yace shifa dole akayi mishi alfarma yayi mun. Haka naita wannan zama na alfarma harna haihu. Sannan iyayena suka sake dani a bisa doron fishi da suke yi dani. Akayi suna ƴan uwa da suka zo daga Bauchi suka koma. Ni kuma naci gaba da shayar da Sani. Watan sani huɗu na samu wani cikin. Laulayi da raino ya haɗe mun. Hmm karfa ku mance a lokacin ni har ma nafi ƴan ƙauyannan munin kama wallahi, sabida rayuwar babu daɗi. Wata tara na haifi Auwal. Daga nan kishiyoyi suka sani gaba, wai na haifi maza biyu, nazo ina baƙuwa inason kwace dukiyar Asabahu. Hmm gashi shi kuma ya ɗauki son duniya ya ɗaurama Sani da Auwalu. Ni dai dama bani da wata daraja a wajanshi, bani kaɗaiba irin dai wannan ɗab'ar ta da yawan maza ta raina ƴaƴa mata, gani suke amfaninmu shine su huta damu suyi mana ciki, mu renan musu ƴaƴa. Daga lokacin da abokan zamana suka sauya mun, sai matsatsin gidan ya takureni, dan su suke debe mun kewa, mu yi daka tare, mu je roro tare. Sani da da shekara biyar na sake haihuwar ɗa Namiji ranar suna yaci sunan mahaifina Tasi'u ( Bala) Aifa nan komai ya caɓe mun. Ai mun ai ma yarana, yara babu damar su fita tsakar gida dan bala'i fa. Shi kanshi Asabahun bashi da aiki sai zaginsu da dukansu, da hantara kuma duk wannan son su da yake ya dena. Kullum a cikin kuka da lallaminsu nake. Haka kurum Asabahu ya sake ni da wata farar safiya saki biyu a karo na uku. Kuma zan tafi suka hanani ɗa ko ɗaya, yarana suna kuka ina kuka haka na baro ƙauyannan. Tunda na sauka a tashar Bauchi gabana yake ta dokawa hankalina a tashe nasan abun da zan tarar a gidan ba mai daɗi bane. Ai kuwa ilai abunda ya faru kenan. Kwararam_kwararam na shiga gida da tulin tsummokina ina kukan fitar rai ko zasu ji ƙaina su sassauta mun. Abun mamaki mahaifina nan ya rufe ni da duka, ya farfasamun jikina ko ganin girmana bai yi ba. Sabida baƙin ciki da takaici na sai da hawan jini ya kama shi. Ni kuwa na kasance tamkar mujiya, ko sallama akayi za'a shigo Mama sai ta turani ɗaki bata son mutane su ganni sabida su basason su ji kunya a wajan mutane. Sun dai zaɓi ni su karya mun zuchiya. Ga rashin iya zaman Aure, ga tsangwamar irin wacce kabilar Hausawa suke ma Bazawara, ga rashin ƴaƴana, shi kanshi jawarcin raɗaɗine dashi. ( Zawarawane kaɗai zasu gane wannan batun. Zawarci fa bashi da daɗi sam. Shi yasa wasu matan suke kashe kansu a gidan Aure, sabida gudun zawarci, da gujema tsangwama) Haka nai ta rayuwata babu wani mashin shini, na zama tamkar bora a gidanmu, aiki ake ledamun tamkar jaka, kuma fa haka na koma wannan gidan abincin na ci gaba da wanke_wanke tana bani wannan abinci dafaffe sai ƙarin albashi da tayi mun daga ɗari biyu zuwa ɗari biyar. Wannan shine labarin halin dana shiga a baya" kai na jinjina nace. Yaya batun komawarki makaranta ya akayi kika samu wannan damar, har kike kan matsayin da kike a yanzu?" Dariya tayi mun, idanunta sun yi jawur......... [10/8, 18:30] Badiat Ibrahim: NA FAƊO DAGA BENE..... NA ZARCE RIJIYA HAKKIN MALLAKAR BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI GAWURTATTU UKU 6 Batun komawata makaranta ya samo asaline ta dalilin Hajiya Hari mai gidan abincin da nake yi ma wanke_wanke. Wata farar rana da bazan mance da'ita ba itace ranar da hajiya Hari take shaidamun ta samomun aiki a gidan wata Hajiya ƴar boko ce, kuma ta kasance mai son tsabta. Ganin tsabtata ne yasa ta zaɓeni a inje can gidan nata in yi aiki. Za'a dinga biyana albashin nera dubu biyar. Wannan labari sai naji tamkar in zuba ruwa a ƙasa in shanye dan murna. Hajiya Hari ta kaini gidan wannan Hajiya ƴar boko ta damƙani gareta. "Habiba kin yi karatune, ko kuma matar Aure ce ke a zaune a gida?" Kafin in ce wani abun Hajiya Hari ta tari numfashina da cewa. "Bazawarace nan mai ƴaƴa uku. Aurenta uku zaman yaƙi yiwuwa, shine ta fito neman na kai, ko dan bukatun yau da kullum" Numfasawa wannan Hajiyan tayi kawai, sai cewa tayi." "Kinason komawa makaranta ne, ko me kika tsarama kan ki?" Inaso Hajiya, dan auren ya gama fice mun a raina." Na bata amsa da haka. Ta umarceni gobe in zan zo in tawo da takadduna zata gani, kuma tayi mun alƙawarin zata taimakamun. Ashe wannan Hajiyar gidauniyace da ita domun tallafin mata da basu jari, masu son komawa makaranta ta sasu a makaranta. Ko da na dawo gida bance ma kowa komai ba, washe gari na kai ma Hajiya Boko takadduna ta gani, ta ajjiye a wajanta. Wata biyu da soma aiki a ƙarƙashinta na samu gurbin karatun likitanci a jami'ar Jos. Lokacin da zan tafi mahaifina ya dage akan shi ba da yawunshi ba, za'ace ya barni na tafi karuwanci Jos. Sai da amininshi maƙocinmu ya dinga bashi baki. In baku a taƙaice Amininshi ne ya bani umarnin tafiya tare da shi mun albarka. Kunji yadda akayi na zama haka kenan." Halima Bawa tace. "To batun aure kuma fa Habiba Bala tunda dai yanzu duk namijin da zai aureki ma sai ya shirya?" Dariya mu ka yi dukka, Habiba Bala tace" "Ina da tarin tulin zawarawa a ƙasa wanda suke jin kamar zasu mutu a kaina tsabar so. To ina lallaɓawa dai in sha Allah akwai wanda nake ganin kamar zamu iya dai_daitawa, sai dai yawan shekarunshi ne dai yake tsorata ni. Duk da nasan nafi ƙarfin ƴan matasa haka waɗanda da kadan suka haura arba'in." Hirarmu dai haka tai ta tafiya. Mu yi sallah mu dawo mu zauna mu sake baje hira. Sai da mu ka kusan raba dare muna hira, daga ƙarshe duk a ƙasa mu kai bacci saman kafet. Washe gari da rana Habiba Bala ta fita damu muka sake ziyartar sauran ƙawayenmu, ta kaimu shopping mall tayo mana siyayya sosai, sai mahriba muka dawo gida. Bayan munci abinci mun yi sallar Isha sai na ɗan shiga tattare kayana dan gobe da wuri nake son shiga Jos, ta gida zan sauka in tawo da yaran. "Shanono kar kice na rainaki ƴan kayayyakinane nayi miki kwalimarsu, atampopi da ƴan ƙananan kaya na shan iska, da fatan kina so ko? Ke kuma Halima Bawa ga wannan babu yawa" Ta miƙa mata kuɗi ni kuma ta miƙo mun babbar leda, baki a yashe nace. Gaskiya na gode sosai. Kin ji ki da faɗe Habiba Bala ai wanda ya fika ya fika. Kinga na ɗan samu na sawa, gashi kishiya za'ayo mana dama. Nagode sosai Allah ya bar zumunci" Kuɗi ta kuma bani, na dangane da batun komawa karatu ta cika mu da goma sha tara ta arziki. Washe gari ta fita damu, ni a titi ma na samu motar Jos na shiga, su kuma suka wuce zata kai Halima Bawa tashar Gombe. Idanu na lumshe motarmu sai shatata uban gudu take yi a titi. Mamaki nake yi duk da ba wannan bane na farko ba, Kaila ya saba nuna mun halin ko in kula, duk inda zani baya hanani, bazai kuma kirani a waya ba ko da shekara zanyi ban dawo ba. Ya kamata in san abunyi tun kafin Kaila ya gaji da bani ɗakin kwana da abinci ya koroni rayuwata ta sake tagaiyara a karo na biyar. Amman ba lallai abinda nake tunani ya yiwu harya tabbata ba, domun bani da wata madogara sai Allah, bani da mai taimakona ƙila iyayena su gwasaleni su ƙi ban goyon baya ma. Kaila dai nasan ba sona yake yi ba balle kishina ya ratsa ƙirjinshi ya hanani cikar burina. Wannan burin burine wanda ya daɗe da samun muhalli mai kyau a zuchiyata, mahaifane suka ruguje mun burina da nake mafarki. Kuma ba wai na yasar da burin dan son raina bane, face dan bani da yanda zanyi, bansan ta ina zan soma ba. Amman lokaci yayi da zan soma koma ta inane da izinin Allah, kuma inna soma in sha Allah sai na idasa zan tsaya, abu ɗaya ne zai yi mini cikas wannan cikin dake jikina, amman zan jinkirta har zuwa lokacin da Allah zai saukeni lafiya." "Hajiya mun iso fa, ke kaɗai kika rage a motarnan" Cewar direban motarmu. Sakkowa nayi ina sauke ajjiyar zuchiya. Keke napep na tara zuwa layin idi mai barkono. Na kuwa taki sa'a a kofar gida na samu Inno ita da su Sulaiman, Shafi'i na riƙe da buhun bararta. Balaraba tana ganina ta rungumeni tana murnar ganina, Sani sai dariya yake yi na murna. Nima naji daɗin ganinsu sosai. Inno tace " Ƴar nema du wannan murnar ganin uwar taki ce lallai kuwa. Dama Amina ce tawa da su Sulaimanu." Inno bara zaku tafi, ni nama yi tunanin ba lallai in same ku a gidan ba" "Wallahi kuwa yaranki ne suka makarar dani, amman ai da tuni ina can, Baffanku tun shidan safe suka fice da su Habu da Indo. Yarannan dai ki tafi da su Balaraba, Amman Shafi'i da Sulaimanu, da sani zasu rakani bara, inna taso komai dare zan dawo miki dasu.." Su Amina suma suka kafe sai sun bi inno .Turus nayi domun akwai lokacin da Kaila ya taɓa wucewa ta masallacin ƴan taya ya ga su Sulaiman tare da Inno suna bara yaran sun bita daga gida lokacin ana hutun makaranta. Ranar nasha baƙaƙen maganganu da zagi iri_iri, kuma yayi mun mugun gargaɗi akan kar hakan ta sake faruwa ba za'a mayar mishi da yara mabarata masu matacciyar zuchiya ba. Ni kuma bazan iya hana mahaifiyata tafiya da yarana ba. Koma yaya take uwa uwace. To shikenan Inno sai kun dawo, ni zan tafi gida. Kwa gaishe da Baffa." Tare muka fito titi Inno na cogala ƙafarta, Inno irin masu ƙafa ɗaya da rabinnan ce, a duƙe take tafiya hannunta ɗaya dafe da ƙafar mai lalura. Shi kuma Baffana makawone, a wajan yawon bararsu tun a Shanono suka haɗu Allah ya ƙaddari aurensu. Mun zauna a garuruwa da dama wanda yawon bara ke kaimu. Amman tunda muka zo Jos Baffa yaji sanyi da daɗin garin yace yaga wajan zama, a lokacin muna yara Yaya Use ce kawai babba a wannan lokaci. Keke napep na tara muka zo muka wuce su, Su Sulaiman suna ɗaga mun hannu. Dan Inno basa hawa abun hawa duk inda zata a ƙafa take zuwa tana yi tana bara, Indo na mata waƙa. Ina jiyo sautin muryoyin su Shafi'i suna ma Inno amshin waƙar bara. Wacce muma muka taso da ƙwarewarta. Hawayene ya gangaro a kumatuna, da sauri nasa gefen mayafina na sharce hawayen. A bakin layinmu na sauka na ƙarasa. Tun daga baƙin ƙofar shiga cikin gidan nake jiyo muryar Ba Rammai Mahaifiyar Kaila, da hausarta irin ta Hausawa mazauna Akwanga , maganarta dama a sama take yi da tsawa da hargowa, kuma ba faɗa bane. In kuwa faɗan zata yi duk maƙota sai sun fito. Gabana ya yanke ya faɗi dan bata da sauƙi musamman a kaina. Ajjiye kayana nayi a ɗaki na shigo da sallama cikin gidan. A kan taburma na samu Baba Rammai da Kaila, Hajiyayye tana daga bakin ƙofarta, Hindatu kuma tana aikin sharar tsakar gida, yaran na wasansu." Sannu da zuwa Baba Rammai kece a tafe, maraba" Ban kai da zama a kan taburmar ba, cikin hausarta ta Akwanga tace. "Yau ga burun ubaaa ni kike cema a tafe sai kace sa'ar gurguwar uwarki Inno? Lallai Kaila ka yi ƙoƙari da kaci gaba da ajjiye wannan tsohuwar bazawarar da taga maza kala_kala." Turus nayi a durƙushe a gabanta, ji nayi kamar ta ɗauki wuƙa ta luma mun a cikina. Wai mai Hausawa suka ɗauki kalmar zawarci ne da aure_aure? Ni naga ko karuwai basu cika fuskantar irin matsin da Bazawara ko mace mai caccanja miji take fuskanta ba. Buɗar bakin Kaila sai yace mata. "Wallahi Rammai sabida yaranta nake ɗaga mata ƙafa, bana son in ɗauketa a kansu dan babu wanda zai kula mata dasu sai dai itan. Wannan dalilin ne yasa na bata ɗakin zaure ita da yaran, ita kuma Bilkisa na bar mata nata kuma yafi ko wanne daki girma" Haƙiƙa maganar Kaila yayi dai dai da zafin fitar rai daga gangar jiki. Wato ni amfanina ciki da rainone, da ba dan hakan ba da tuni a karo na biyar ɗin ma koroni za'ayi. Ya Allah ka bani jumurin dauriyar ci gaba da zaman gidannan ko dan in bama yarana tarbiyyar data dace, sune kaɗai sanyin idaniyata, Dauda ma dana fita a gidan mahaifinshi na barshi ina mishi adda'a da fatan nasara a rayuwa. Iska na fesar na ɗago muka haɗa idanu da Hajiyayye wani irin Murmushin nasara take yi mun, Idanuna ya kaɗa yai kamar gauta. Da ƙyar na haɗiye wani kakkauran yawu kana nace. Ina kwana Baba Rammai kin zo lafiya?" Sai da tayi tsaki sannan tace. "Su yaran fa suna ina?" Kaila daya kafeni da mayaudaran idanunshi waɗanda ada suke da matukar tasiri gareni yace. "Ai na ɗauka ta gidan zaki biya ki tawo dasu ko? sai nagan ki ke kaɗai ya'isa haka ai ko. Ni kar aje ma a dinga fita ma da yara yawon tumasanci suje zuchiyarsu ta mutu su ce sunga sana'a" Duk dauriyar da na dinga yi gudun kar in yi kuka a gaban kishiya, da facala, sai da zuchiyata ta gaza tayi wani irin raunin da bansan sanda na fashe da kuka ba. Hauwa'u na sauke na dangwarar musu na tafi ɗakina. Ina jiyo shewar Hajiyayye, ita kuma Baba Rammai ta shiga farfaɗan miyagun maganganu akan bara, ina ji tana cewa daga ranar kar a kuma kai mata jikoki gidan guragu da makafi kar a koya musu maula. A kan katifata na kwanta a rigingine ina kallon rufin ɗakin, hawaye kuwa sai makanta ganina yake yi. Wallahi bansan rashin darajata a rayuwar Kaila ya kai hakan ba, yau da ba dan gudun tsinuwar iyaye, da gudun tofin Allah ya tsine daga bakunan mutane ba, wallahi da babu abinda zai sa in ƙara ko awa ɗaya a cikin gidannan" "Ke Shanono dan wulaƙanci Rammai tana magana bata sallameki ba shine kika dangwarar mun da ƴa kika yi tafiyarki, wato ga mahaukaciya ko? To nagode Allah mahaifiyata ba mabaraciya bace mai kwana a bakin masallaci ba. Yara kuma ki yi waya a dawo mun dasu. Sannan muddin kinason kici gaba da amsa sunan matar Kaila, ki je ki tsugunna ki ba Rammai haƙuri har sai ta hakura sannan. Abu na gaba wannan kayan da kika saka a jikin ki ranar da zaki Bauchi ki fito mun dasu ki kawo mun, muna ɗakin Hajiyayye " Yana kai ƙarshen maganarshi ya fice kamar kububuwa. Sai da nayi kukana ma'ishi na kusan minti ashirin, sannan na share hawayena zuchiyarnan a cunkushe babu wani sassauci dana samu. Maganganun Kaila na ɗazu dana yanzu su suke ta faman yi mun amsa kuwa. Jakata na buɗe na zaro wannan kaya da Inno ta bani na fito. A tsakar gida na samu Hindatu tana ta waƙar kujerar tsakar gida. "Umman Sulaiman sannu da dawowa, ina aka baro mana su Sulaiman?" Yauwa sannu." Iyakar abunda nace mata kenan, ai tasan inda suke kuma duk abinda aketa taunawa ba tana ji ba." "Tohh iko sai Allah wai na kwance ya faɗi. Me yayi zafi shi ba wuta ba, ai bani na kar zomon ba rataya aka bani." Shigewata nayi ɗakin Hajiyayye da sallama. Hajiyayye na tsugunne tana haɗa ma Rammai tea. Ga yarinyar Hajiyayyen a cinyarta, Hauwa kuma tana yashe a ƙasa, harta soma ɗan kuka, Kaila yana harɗe a kujera yana aikin daddanna wayarshi. A gaban Baba Rammai na durƙusa bakina na ɓari. Baba Rammai dan Allah kiyi haƙuri. Nayi kuskure bazan sake ba in sha Allah, Allah ya huci zuchiyarki." Ai nan tace ina wuta ta tsoma ni. Ta dinga faɗa tana ihun da babu makawa maƙota duk suna jiyowa, ta dinga dawo da bara bana. Ai rannan da tazo ma banko yi mata fara'a ba bani da kunya dake na saba da maza, kuma idona ya buɗe da rashin kunya irin na yara ƴan jagora. Ni dai kaina na ƙasa ina haɗiɗiye zuchiyata, Hajiyayye ranta fes dashi har Murmushi take yi, ni dai ban gushe ba har sai da tace ta haƙura na mata godiya, wajan Kaila na wuya. Kaila ga kayan" Bai ɗago ya kalleni ba, sai yace. "Hajiyayye karɓi kayannan, shikenan rigima ta ƙare dai ko?" Ni kuwa binsu nayi da idanu cikin ɗaurewar kai ban gane rigima ta ƙare ba, rigima tayi akan kayan shine ya sa na kawo dan ya bata ita tasa ko me suke nufi?" "Rigima ta ƙare Baby, ai kayanne suna da tsada super ce fa kuma babbar" Kallon Hajiyayye kawai nayi na sauke kaina ƙasa. Rammai ce tace. "Ɗauki ƴarki kuje ya'isa haka kuma" Dama zaman ya gundureni gudun kar in kuma yin laifine yasa na zauna ina kwasar baƙin ciki, Hajiyayye kamar zata koma cikin jikin Kaila, shi kuma sai wani lallashinta yake yi. Hauwa na sunkuya na ɗauka tare da fice wuf a ɗakin, ina shiga ɗakina na kuma ɓallewa da kuka. To mai Kaila yake nufi ne dani, meye dalilin da zai karɓarmun zani ya ba matarshi alhalin ni bashi ya sai mun ba? Kuma wai har ake faɗin rigima ta ƙare, ita kuma tana faɗin kayanne da tsada super ce. Dole na ture wannan damuwar domun akwai matsalolin da suke da mahimmanci fiye da wannan su suka fi damuna. Haka na wuni cir a ɗakina a takure, ragowar soyayyen naman sallana naci na sha ruwa, Hauwa kuma bacci take yi. Wajajen biyar na yamma dai na daure na fito tsakar gidan dan ɗaura girkin dare, Hauwa sai kuka take yi na rasa kukan na meye dan har jikinta ya soma zafi. Ni kaina jikina ya ɗau zafin zazzaɓi kau, ga wani irin mugun ciwon kai dake damuna. Zulaihat na aika shago ta siyo mun omo. Ni kuma na zauna ina jiran wuta ta ruru, Baba Rammai tana kwance tayi bacci a kan taburmar, Hajiyayye Hindatu kuwa sai shewa suke yi. "Gobe nima yace za'a haɗa da ɗakina ayi fentin. Kuma zai sake mun kujeru, kinga inna siyar da wannan kujerun na ɗakina, nima sai in yo suturu duk da jiya ya kawo mun kala shidda. Amman zan ƙaro wasu ni da tsinanniyar amaryar tashi sai dai mu zuba, bata isa ture mun matsayina a zuchiyar Kaila ba" Cewar Hajiyayye kenan. Hindatu tayi shewa suka tafa tace. "Ai naga sai bala'i kuke yi, jiya ma fa haka kika fashe mai wayarshi sai wata ya siyo. Naga duk ya rikirkice sai lallaɓaki yake yi" Ni dai ina jin hirarsu amman harkokin gabana nake yi. Zulaihat ce ta shigo ta kawo mun omon dana aiketa. Ina tsaka da tsintar shinkafa na jiyo muryar Kaila daga zaure yana rangaɗamun gigitaccen kira. Kafin in miƙe har ya shigo cikin gidan abunka da tashi da ƙyar zama da ƙyar. Ihun kiran sunanane ya farkar da Baba Rammai. Bol yayi da tiran dake hannuna Allah yaso na juye rabin shinkafar a roba. Tirannan ya faɗi ƙasa gwangwarangwannnnnnnn...... Ƴar ragowar shinkafar ta tarwatse. Ya cika gidan da ƙara yana huci yace mun. "Sabida kin ɗaukeni ɗan iska shine zaki tura mun yara gidanku su dunga fita yawon bara kamar ni Shanono? Yanzu na dawo daga ƴan taya, wucewa nazo yi Shafi'i ya riƙe mun riga yana ce mun babiye Allah ba tare da yasan ko wa ya riƙe ba, ina juyowa ya ganni, Sulaiman shima yana can wani kirista na bashi sadakar nera ɗari. Dan iskanci da raini sau nawa na faɗa miki kar a sake zuwanmun da yara wajan bara?" Ni dai tunda ya soma wannan tonon sililin jikina ke rawa, ada in ma masifar ce a ɗaki yake yi mun kisan mummuƙe, amman a yanzu a gaban kowa tozartani yake yi, yau na ji na mugun muzanta a idanun kishiya da, facala. Salati suka shiga rabkawa dukka Baba Rammai harda tattafa hannaye. Hakan ya kuma tunzurashi yace. "Kar a kuma ɗaukar mun yaro a kai mun shi gidan makafi ni dai na faɗa miki. Ke daya zame miki dole sai ki je. Kuma yanzu_yanzu ki je ƴan taya ki ɗakko mun yarana wallahi in ba haka ba a gidanku zaki kwana, bara harda su Balaraba an baza su a titi ana son kashe musu zuchiyarsu. Wannan wanne irin masifa ce nayi ni dai nadamar auro ki da nayi, wannan ai kece kara da kiyashi." Baba Rammai tace. "Ɗaukar marar sani ba. Ai ni tunda kace mun aurenta huɗu nasan ba za'ayi abun arziki ba. Amman dake a lokacin sun yi ma asiri kana saurayinka da kai zarkaɗeɗe a rasa wacce zaka auro sai bazawara mai Aure huɗu mai yaro. Ke kuma ai sai ki bi umarnin mijinki ki je ki ɗebo mishi yaranshi tun kafin ya sallameki a koma kwana a ƙarƙashin gada. Ai dama ance mana a ƙasan gadar legas aka haifeki da rana" Ji nayi zuchiyata na harbawa da ƙarfi, jinin da take watsawa ya wuce kima. Ƙafafuna sun gaza motawa kaina kamar zai tarwatse nama rasa wanne irin tunani ma zanyi. Ana cikin haka na jiyo muryar Inno tayi sallama da yaran. Shigowa tayi da sallamarta, tana duƙe riƙe da ƙafarta kamar yadda take. Ganin Baba Rammai ya faɗaɗa fara'arta tace . "Rammai kece a garin? Maraba lale ga jikokin naku na kawo miki su, nima duk sun isheni suna san ganin uwasu." Sama da ƙasa Baba Rammai tayi ma Inno wani kallon wulaƙanci, cikin ba'a tace. "Ai fa ga jikokina, daga yawon barar kuke ne naga duk kun haɗa zufa Inno ƙafafunku duk ƙura" Da dariyar wulaƙanci ta ƙarashe maganar tana jayo hannun Balaraba. Inno da bata san ba'a tayi mata ba tace. "Wallahi daga bara muke can muka wuni dasu, shine dai nace bari in kawo su" Hindatu ce ta ƙaraso inda muke dan gulma ta gaisa da Inno. Kaila kuwa bai ma kalli inda inuwar Inno take ba yayi shigewarshi ɗaki. Baba Rammai taja hannun su Sulaiman suka zauna a tabarma, Hauwa da rarrafe ta bisu tana murna taga ƴan uwan nata. Inno muje daga ciki kici abinci ko?" Baki Inno ta washe tace "Kamar kuwa kinsan yinwa nake ji wallahi, dan tun fitarmu rogo na sai mana na nera ɗari kawai" Ɗakina na da tayi ƙoƙarin shiga cikin dakiya nace Inno na canja ɗaki kin mance ne?" Bata ce dani komai ba, na shige ta biyo bayana. Sai ga Hajiyayye da wata koɗaɗɗiyar nera ishirin ɗinta a hannu, muna haɗa idanu ta wani yamutse fuska. "Inno ga sadaka ko?" Juyowa Inno tayi ta kalli Hajiyayye kana ta dawo da kallonta gareni. Sai lokacin ta fahimci halin da nake ciki. Ajjiyar zuchiya inno ta sauke ta kalli Hajiyayye a karo na biyu tace. "Allah shi karɓa Allah yasa a mizani ƴannan, amman ki bar kuɗinki ai kema ƴata ce. Rammai Allah ya bamu alkhairi ni zan koma" Baki Hajiyayye ta taɓe tayi komawarta tana ƴan surutan da bazan ce ga abinda take cewa ba. Sallama Inno tayi da Baba Rammai. Muna shiga zaure tace. "Me kika yi musu haka Tani, in ce dai ba Auren kike son kuma kashewa ba a karo na biyar? Ki buɗe kunnenki da kyau a wannan karon in kika sake aurenki ya mutu sai dai ki nemi wasu iyayen ba mu ba, Baffa ma zai iya tsine miki kibi duniya. Ina fatan ba akan auran da Kaila zai ƙara bane ko? Hawayene suke fita a idanuna wasu kan wasu sai kai kawai na girgiza ma Inno amman na kasa magana. "Abincin ki samun ko a leda ne in naje gida maci da ƙannenki, ni bazan shiga ba kar uwar mijinki ta zargi wani abun, ni da nasan tazo ma babu abinda zai kawo ni gidan" Bance mata komai ba na shiga ɗaki na zuba mata abinci a kula dukka na juye musu, nasa musu miya da nama ban ma ko ɗumama miyar ba tunda na dawo, dake soyayyar miya ce babu abinda ya sameta.na fito da ledar abincin a hannuna." Inno ina zuwa bari in tambayi izinin Kaila sai in kai ki gida dan ba zaki iya riƙe kayan ba" Kafin tace wani abun sai ga shi ma ya shigo zauren shi da su Sulaiman da dukkan alama masallaci zasu je, dan anata kiraye_kirayen sallah. Kaila dan Allah zan raka Inno gida kaga dare yayi hankalina bazai kwanta ba in ta tafi ita kaɗai" Sake shan kunu yayi ba tare da girmamawa ba yace. "Wanne irin zaki rakata kuma, naga har dare kuke kaiwa a wajan bara, kuma da ƙafa kuke zuwa gida kuna tafe kuna bara. Yau kuma sai kin rakata? To adawo lafiya" Yana dasa aya ya raɓa ta bayan Inno ya wuce, yaran suka bishi a baya, dake Sani yaro ne mai hankali naga ranshi bai yi mishi daɗi ba. Kuka mai sauti na saki da naga fitarmu. "Banda kuka Tani, kiyi haƙuri ba komai bane ai wannan mu dai in zai riƙe mana ke ai shikenan, wuce muje ki rakani titi in kika sani a abun hawa ma ya'isa inna sauka a kan layinmu zan samu matasa su kai mun ledar gida" kiran Balaraba nayi, da gudu tazo nace. Ku zauna a wajan Baba Rammai zan kai Inno gida. In Yaya suka dawo daga sallah ku jirani a cikin nan ɗakin kinji ko? Wannan shine ɗakinmu yanzu" Fita mu ka yi ni da Inno, muna zuwa titi na tara mana abun hawa mu ka shiga. Babu mai iya cewa komai tsakanin ni da ita. Ita kanta cikin tunani take. Ban bar Inno ba sai da na kaita har gida nayi sallar magriba kafin nayi mata sallama a gurguje su Baffa basa gidan basu dawo ba tukunna. Tun daga ɗan nesa da gidanmu nake jiyo kukan Hauwa hakanne yasa na ƙara sauri dan in shiga gidan. Ina shiga na ji kukan a cikin ɗaki da sauri na shiga. Hauwa na bayan Sani yana jijjigata sai kuka take ta haɗa hawaye da majina. Sauran yaran suna zaune jigum daga gefen katifarsu. Zare Hauwa nayi a bayan Sani na nemi kujerar tsakar gida na zauna, sai da na zura mata nono tayi shiru sai ajjiyar zuchiya take faman yi, nima ajjiyar zuchiyar nake ta faman saukewa. Ga haki daya dame ni.......... MRS BUKHARI [10/8, 18:33] Badiat Ibrahim: NA FAƊO DAGA BENE... NA ZARCE RIJIYA HAKKIN MALLAKAR BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI GAWURTATTU UKU 7 *Ina miƙa ɗinbun miliyoyin godiya ga duk ɗaukacin masoyana, masoyan Shanono. Haƙiƙa littafinnan yayi karɓuwar da ni kaina banyi tunanin zai yi ba. Ta dalilin wannan labarin manyan mutane sun kirani a waya sun jinjina mun. Zawarawa suma sun kira sunce na taɓo musu inda yake musu ƙaiƙayi. Ina godiya ga duk makaranta wannan littafin, Mrs Bukhari gidan ƙamshi taku ce* *Yana da kyau ko wacce mace ta karanta littafinnan tun daga farkonshi izuwa ƙarshenshi. Domin makaranta ne mai zaman kanshi wannan labarin* Me yasa baka kaita ko da wajan Baba Rammai bane ka barta tana ta kuka?" Sulaiman ya dube ni yace. "Koro mu tayi har Abba yana ce mana jikokin makafi da guragu. Umma Hajiyayye kuma ta daki Balaraba dan tace yinwa take ji" Da sauri na miƙe na fita tsakar gidan, ruwan wanka dana ɗaura a wuta yana ta tafasa har ya ƙune kusan rabi. Saɓa Hauwa nayi a baya na sauke tukunyar na girgije kurbo ɗin na ƙara gawayi, kana na mayar da tukunyar kan wuta. Taliya na ɗakko a kitchen guda ɗaya na zuba a ruwannan. Sai da nayi sallar isha na juye musu taliyarnana a babban faranti da miya. Sai da suka ci sannan su kai Sallah. Ni ko ruwa na kasa kurɓa sam. Ina zaune a bakin katifa yara duk sun yi bacci, mazan katifarsu daban, matan kuma muna katifa ɗaya. Kaina ya ɗaure da tunani nama rasa wanne irin tunani zanyi ma. Ga yinwa data addabeni yaron dake cikina sai juyi yake yi, ni kuwa ko ruwa bazan ma iya kurɓa ba, hawaye kawai nake zubarwa. Ina tuno irin so da kulawar dana samu a wajan Kaila a lokacin farkon aurenmu. Wallahi in wani ne yace mun Kaila zai ƙyamace ni har haka bazan yarda ba. A yau na gane nadamar aurena yake yi, ko ko in ce nadamar haɗa tsatso yake yi da ɗiyar mabarata wanda ubanta yake makawo, uwarta kuma take gurguwa, ni Shanono wacce aka haifa a ƙarƙashin gadar legas a tsakiyar kutare da guragu, da makafi. Ni na yarda wannan itace ƙaddarata, na aminta cewar maza basu karɓeni ba, Aure biyar amman babu wanda naji daɗinshi, gashi wannan ma lilo yake yi. Ban taɓa yarda da masu cewa yanda suka ga rana haka suka ga dare ba, sai lokacin da matsalolin gidajen aurena suka farma rayuwata. Kamar kullum yau ɗinma banko iya runtsawa ba. Washe gari na tashi da zazzaɓi da ciwon mara mai tsanani ko tashi bana iya yi." Sani zaka iya hura mun wuta?" Na tambayeshi cikin muryar tsananin ciwo, yaran duk sun kewayeni sai sannu suke yi mini. "Umma zan iya, nasan yadda akeyi" To ka hura mun wutar, sai ka ce da Ammanku dan Allah tazo banda lafiya" Da sauri Sani ya fita, ni kuma naci gaba da juyi a tsakar ɗaki. Kamar minti goma sha biyar da fitarshi sai ga Kaila ya buɗe labulen ɗakin yana tsaye a kaina sai wani ajjiyar zuchiya yake faman yi. "Lafiya kike neman Hajiyayye? Mun kwana gida ɗaya baki iya fitowa kun gaisa da Rammai ba balle ki dafo abinci ki kawo mata ko? Jiya haka kika kwashi abinci tab leda mai zane kika ba Inno, amman ita Rammai baki iya bata ba ai." Baki na cije nace. Kai haƙuri bani da lafiya ne, shi yasa ma nace a kira mun Hajiyayye ta taimaka ko asibiti ne ta raka ni" "Allah ya ƙara sauƙi ko haihuwar ce?" Sai kuma ya sassauta murya ganin halin da nake ciki. Wallahi ban sani ba, Amman zai iya yiwuwa haihuwarce wata takwas da ɗan ɗoriya ne. Naga sai cikina ya kusan wata goma nake haihuwa ne" Baki ya taɓe. "To bari in kira unguwar zoma zaifi, in ma asibitinne sai ku tafi tare. Kike wani raki haihuwa ke da kika ɗauketa kamar ki saki ƙaton kashi. Ba za'a fi wata biyu ba zaki sake shiga wani laulayin ai in dai kece Shanono ciki da goyo shi kadai kika iya ai, duk wani abun arziki baki sanshi ba. Ga shegiyar ƙazanta ɗaki sai warin annakiya da tsummokin bara " Ana cikin wannan halin Hajiyayye ta iso, ganinshi a bakin ƙofar ne yasa tace. "Baby lafiya kuwa inata jiranka karyawa fa kake yi?" Murmushi yayi mata. "Kinga naƙuda inaga take yi, ki kira mata Rammai. Yaran kuma ki ja su basu karyaba zan shigo musu da masa sa ci nasan kin gaji. Bari ina zuwa, sannu Shanono Allah ya raba lafiya " Nan ya fice ya barni a tsakar ɗaki. Ji nake dama zan iya haɗiye zuchiyata in mutu ko na huta" Sulaiman ka kira mun Sabira maza" Da gudu Sulaiman ya fita, Hajiyayye ta wuce cikin gida da sauran yaran ko uffan ta kasa ce mun. Har sai da Sabira ta ƙaraso kafin Baba Rammai ta leƙo, a dokin ƙofa ta doge." "To tunda kin iso ma ai shikenan, kinga ni surukace, Hajiyayye kuma kishiyace, Hindatu kishin sauri, kinga ba sa ga tsaraicinta ba sai dole." Tana idasa faɗa ta saki labulen, ba sannu, ba Allah ya raba lafiya. Haka naita gumurzu Sabira na yi mun sannu. Anguwar zoma ce ta shigo ɗakin jikinta saye da fararen kaya na ma'aikatan asibiti. "Tun yaushe kika soma jin halamun naƙudar?" Ta tambayeni tana duba ni" Da safennan ne kamar wasa naji ciwon sai tsananta yake kuma yi. Cikin bai kai haihuwa ba amma" Dubani tayi da kyau tace. "Ai kuwa ba haihuwa bace juyi ne. Amman ki je Asibiti likitoci su duba ki." Kaila ne ya leƙo ɗakin. Ba shiri Sabira ta rufe wuyanta zuwa ƙirjinta da gyalenta, shi kuwa yaƙi ɗauke ido a kanta. Ni kuma ina zaune zaman ɗabaro a ƙasa, marar na lafawa kaɗan_kaɗan. "Yaya akayi haihuwarce dai ko?" Ya tambayi unguwar zoma. "A'a bazai wuce juyi ba, ba haihuwar bace. Amman ya kamata taje asibiti" Hanya Kaila ya bata ta fita dan sauri take yi da gani wajen aiki zata. Tsaki Kaila yayi yace. "Sabida shegen raki irin naki juyin cikin kike ma murƙususu haka sai kace mai haihuwar fari, haihuwa ta barkatai? Allah ya kyauta, sai ki fito da tsunmokin ki ai, da gaiyar kuɗin cizo masu fenti in sun gama na ɗakin Bilkisa sai su yi miki kamar yadda nayi alƙawari." Ni dai na ma rasa ta cewa, Sabira kanta a sauke har Kaila ya gama magana ya tafi. Ita ta fitar mun da komai na ɗakin nawa zuwa tsakar gida, ni kuma ina zaune akan taburma a tsakar gidan. Baba Rammai ce ta fito daga ɗakin Kaila da waya riƙe a hannunta tana waya da amaryar Kaila. Masu fentin ɗakin Amarya suna ta tayi, wasu suna fentin tsakar gidan namu. Har haf door akayi a ƙofar ɗakin Amarya, daga gefen ɗakin kuma kafinta na buga kitchen irin na langa_langa, da dukkan Alamu Kaila na ji da wannan Amarya dan shima kwalima yake yi a ɗakinshi. Ana gama fentin ɗakin Amarya aka shiga fente ɗakin ango. Hajiyayye sai kumbure_kumbure take yi, motsi ɗaya ta jibgi ɗiyarta. Ni dai ina zaune jigum, Sabira ce ta kama yaran tayi musu wanka suka yi ficewarsu waje. Ita ta ɗaura abincin masu aikin fenti da Kaila yazo yace in ɗaura. Amadudu da Baba Rammai kuma fita su ka yi zuwa kasuwa. Ni dai ina kwance a kan taburma ciwon jiki dana zuchiya na neman rayuwata. Bayan masu aiki sun gama aikinsu Sabira ta zuba musu abincinsu, ni kuma sai da nayi Sallah na ɗan taɓa abincin, ta haɗe yaran du ta zuba musu abincinsu. Kaila yana ta kai kawo tsakan kanin ɗakinshi da ɗakin Hajiyayye dan fishi take yi dashi sosai, shi kuma babban tashin hankali ne fishinta gareshi, har sabunta mata fenti itama akayi. A haka dai ya shirya ya fice a gidan. Ko awa bai yi ba sai muka jiyo sallamsrshi da wasu maza suna kiciniyar shigowa da setin gado. Gado da wadrope Kaila ya sake filla_filla daga kamfanin ɗan sogai. Tsofaffin kuma aka fice dasu. Sabira kuwa sai hidima take yi dani, ita ta share mun ɗaki ta goge ƙasan ɗakin Sani da Sulaiman su ka kama mata suka shigar da katifun da buhunhunan tsunmokaranmu. Sabira nagode sosai Allah ya bar zumunci. Ya kamata ki tafi gida kinga magriba ta kawo kai, kije ki ɗaura ma mai gidan Abinci, ragowar abincin dake cikin tukunya zai ishi yaran, naga ma kin dumama musu." Murmushi tayi tace. "Babu komai ai Tani, in ruwan wankan naki yayi zafi sai ki sa Sulaiman ko Sani su juye miki. Su Balaraba kuma zan aiko Mustapha zuwa bayan isha ya zo ya tawo mun dasu gidana, zuwa gobe sa dawo kya samu kiyi bacci sosai " Sabira ƙawace wacce samun irinsu da wuya a wannan zamanin. Godiya marar iyaka nayi mata, sallama tayi mun ta tafi, ni kuma na lallaɓa na tashi. Fitowata daga banɗaki kenan Baba Rammai suka shigo ita da Amadudu kici_kici da kaya, harda su katan_katan na ruwa da lemo. Sannu da zuwa nayi musu zan wuce, Baba Rammai tace. "Ungo wadannan ledojin kayan miya da kayan lambu ne a ciki, wannan kuma kaji ne an fige an yanka ma. Gobe sassafe sai ku tashi da aikin ƴan jere zasu tawo daga Zaria kuma fitowar safe zasu yi." Ledojin na karɓa a hannunta, sauran suna ƙasa. Kayan ruwa da lemun kuma Amadudu ya shiga dashi ɗakinshi. Ɗaki na kai kayan sai da nayi har sallar isha sannan na aika Shafi'i kitchen ya ɗauko mun bahun ƙarami. Kajin na juye sai da suka cika madaidaicin bahun dam. Haka na kinkima da ƙyar zuwa tsakar gida na shiga aikin gyaran kaji nan. Mustapha yayi sallama ya tafi da su Sulaiman Hauwa kawai suka bar mun. Ina wanke kajinnan marata na karta mun. Gawayi na haɗa na ɗaura tafashen kajinnan a ƙatuwar tukunya dan kajin sun yi guda takwas masu abun ne to da abunsu kura da kallabin kitse. A kan kujerar tsugunno Kaila ya shigo ya same ni, ni ni kaɗai a tsakar gidan gashi ba wuta, sai hasken waya na kunna. Sannu da zuwan da nayi mishi ma da ƙyar ya amsa ni, yayi shigewarshi ɗakin ƴar gwal. Sai goman dare na sauke tafashe na tafi dashi ɗaki, ko lomar tuwo ban kai bakina ba. Haka na kwana ina ciwon mara, washe gari kuma na shiga hidimar aikin ƴan jere, Hindatu da Hajiyayye babu wanda yayi yinƙurin taya ni. Tun sassafe na kira Anty Use da Anty Karime a waya na sanar musu da batun abincin jeren, sun ce zasu zo da safen su taya ni aikin. Kuma na aika ma Sabira. Zuwa ƙarfe taran safe duk suka hallara, har mun soma tuyan kaji, Sabira kuma tana zaune tana gyaran kayan lambu. Ganin su Yaya Use ne yasa Hindatu zuwa ta kama mana aikin. Kayan miya ta gyara yara suka tafi kai niƙa, ni kuma ina gefe ina ɓarar maggi ina cije leɓe na ciwo. "Tani ki je ki tambayo Rammai me za'a girka ma baƙin kinga na gama da suyar naman." To kawai nace, na yi sallama a ɗakin Hindatu Baba Rammai na can. Bayan mun gaisa nake tambayarta mai za'a girka" "Wannan ai ya rage naki Tani. Komai na hannunki du abunda kuka san zai burge baƙin sai kuyi. Dan Allah ayi abinci mai daɗi dai ga kaji nan wadatattu mutanennan masu arziki ne sosai, a kamanta musu." To shikenan Baba Rammai" Fitowa nayi na same su. To tace mu yi koma meye, ya kuke gani me za'a girka?" Yaya Use tace. "To ni dai ban san kalolin abincin zamani ba, ban iya ba ko ba gaskiya ba, nafi ƙwarewa a abincin gargajiya." Yaya Karime tace. "Nima dai wallahi ko jallof ɗin taliya ban iya girkata ba, in nayi duk sai ta raɓe a cikin romon" Sabira tace. "Babu damuwa ni na iya, sai ku taya ni muyi. Party jallof rice za mu yi, da pepper chicken, sai ayi musu coslow tunda akwai kayan lambu da yawa" To da taimakon Sabira data kasance kan gama komai muka kammala girke_girken mu. Ni dai bani da manyan kuloli na zamani, Hajiyayye nayi_nayi da'ita ta ba da nata a zuba abincin taƙi, daga ƙarshe da Baba Rammai tasa baki sai kawai ta fashe da kuka ta kuma rantse ba zata bayar ba. Sai Sabira ce ta je gidanta ta ɗakko mana manyan kuloli na Alfarma, tsabar ƙyalli ras nake ganin fuskata a kular nan. Bayan mun kammala komai Baba Rammai tace a kai ɗakin Hindatu a ajjiye abincin. Yaya Use ce ta shigar da komai, a tsakar gidan suka zauna suna cin nasu abincin. Ni kuma na shiga wanka, ina fitowa na shiga ɗaki na saka riga da zani na atampa wanda Habiba Bala ta bani. Babu abinda na shafa a fuskata. Dirin motoci da ihun yara na jiyo a dai_dai window na suna faɗin "Kayan amarya ek_ek" Sai naji zuchiyata na son leƙawa in ga waɗanne irine matan da suka tawo jeren. Ai kuwa da sauri na matsa bakin windon na leƙa. Wasu manyan mata ƙosassun ƴan boko na gani a tsaye a bakin motar kaya, sai turanci suke yi a tsakaninsu da juna. Kaila na hango cikin girmamawa ya isa garesu, sai ɗan guntun turanci suke yi mai, shi kuma yana zare idanu gudun kar su kai shi maƙura, dan ɗan turanci nashi bai wuce cikin cokali ba, shima ya iyane a sanadiyyar zaman shagon wani inyamuri a bayan banki, shagon takalma da jakunkuna. Kamar akan gidan suke yi mishi magana dai, dan naga suna kallon gidan suna yamutse fuska, ajjiyar zuchiya na sauke na bar windon. Su Yaya Use ne da Sabira suka shigo, a tsaye suka ganni da wannan riga da zani na atampa, rigar tayi mun yawa har wuyan na zamewa. "Baƙin ku sun iso Tani, ni naji sai turanci suke ta zazzagawa a waje." Kafin in kai da magana muka jiyo sallamarsu da wasu muryoyi masu daɗi, daga ɓangarena Yaya Use ce ta amsa musu. Suka ƙarasa zuwa cikin gidan Baba Rammai da Hindatu suka tarbesu. Daga haka muka soma jiyo muryoyin maza da shige da ficensu. Yaya Use ce ta fita, ni ko waje na samu na zauna ina fama da marurun zuchiyata. Bata jima ba sai gata ta shigo. "Tabb lallai Kaila ya ɗebo matar da tafi ƙarfinshi gaba da baya. Yarinyarnan da zai aura daga gani ƴar masu dashi ne. Kunga kaya irin na gani da faɗe kuwa. Hmmm daga kamfanin da aka sai kayan ma aka tawo da ma'aikata maza su suke gyara ɗakin. Ji nayi wata Baturiya tana faɗama Rammai." Baki ni dai na taɓe abina. Baba Rammai ce ta ɗaga labulen ɗakina tace. "Ai ya kamata ace kin zo kin tarbi baƙi ko Tani? Sannan ki basu abincinsu sun shawo hanya" Da To na bita tare da yunƙurawa na tashi tsaye. "Muje in taimaka miki ke da ba ishasshiyar lafiya ba" Harara Baba Rammai ta sakar ma Sabira, taja tsaki ta saki labulen tayi gaba abunta. A ɗakin Hindatu aka sauƙi baƙin, Hajiyayye tace dangin kishiya basu isa sun zauna a ɗakinta ba. Tun muna aikin abinci tayi ficewarta daga gidan, amman ba zata wuce maƙota ba gidan ƙawayenta. Da sallama muka shiga cikin abun mamaki a cikin baƙin babu wacce ta amsa sallamarmu sai Yes kawai suka ce mana. Dauriya na aro na yafa na zauna aka gaggaisa, Baba Rammai ta nuna ni da cewa. "Hajiya kinga wannan itace uwar gidan Kaila. Amman bazawarace ya aureta." Naji zafi sosai, baƙin a wulaƙance suka shiga bina da kallo, ni ko murmushi nake yi, abinci muka gabatar musu da abun sha, kana muka fice a lokacin idanuna ya cika tab da ruwan hawaye. Sai zuwa yamma lis suka gama abinda ya kawo su, su kai mana sallama. Sai magriba su Yaya Use suka tafi bayan sun yi mun girki suma sunci, Sabira kuma ta ɗan jima da tafiya itama zata je ta kula da nata iyalan. Da su Sulaiman ta sake tafiya. Ina zaune muna cin abinci ni da Hauwa nake jiyo hayaniyar Kaila da Hajiyayye a tsakar gida, wannan karon hayaniyar tayi tsamari, dan ina jiyo yanda Kaila ke kutuntumama Hajiyayye ashariya, dama Kaila gwanine wajan rashin daraja, akwai shi da ruwan ashariya. Da ƙyar dai fitinar ta lafa ni ko ina ɗaki a kwance abuna ban ko leko ba ƙofata ma rufe take na saka sakata. Haka ranaku su kai ta shuɗewa ana saura kwana uku biki, gida ya cika da ƴan Wudil dangin mahaifin Kaila, da ƴan Akwanga dangin Baba Rammai. Ƙannen ƙanin Mahaifin Kaila ne kacal suka sauka a ɗakina, yara kuma suna gidan Sabira acan suke kwana. Aikin girki kuwa nice gaba_gaba taimakamun kawai jama'ar bikin ke yi, amman in ban ɗaura sanwa ba babu wanda zai fito ya ɗaura. Ana jibi ɗaurin aure aka tashi mutum huɗu biyu daga ɓarayin Baba Rammai , biyun kuma ƴan Wudil ne domun kai akwatin Amarya wanda dama ita yaba kuɗin ta sai komai domin irin yanda take ba gaye hakkinshi. Sassafe suka kama hanya domun a ranar suke son dawowa, basu suka shigo gida ba sai taran dare. Washe gari aka shiga hidimar biki gadan_gadan wanda a ranar Kaila da mutanenshi suka nufi Zaria acan zasu kwana in an ɗaura aure su tawo da Amarya da danginta. Ranar juma'a gida ya cika da maƙota ƴan uwa da abokan arziki duk sun hallara, Yaya Use da Yaya Karime tun taran safe. Mu mu kai ruwa mu kai tsaki a girkin ƴan biki. Tuwon shinkafa miyar taushe mu ka yi, sai jallof ɗin shinkafa da kaji da akai ma masu kawo amarya da abokan ango. Saye nake cikin wani lashi ɗinkin doguwar riga, yana daga cikin kayan da Habiba Bala ta bani, babu ko kwalli a idona balle in shafa mai. Yara kuma nasa musu kayan sallansu, abunka da yara sai murna da ƙiriniya suke ana biki a gidansu. Hajiyayye ma ɗakinta cike dam da ƴan uwanta da ƙawayenta na anguwa. Taci ado kamar itace Amaryar, ƙawayenta sai koɗata suke faman yi, an yi saloon, an yi ƙunshi, duk da na sallah da tayi bai gama fita ba amman akai akayi mata, har me kwalliya ƙawayenta suka ɗakko mata. Misalin ƙarfe shida da rabi na yamma motocin kawo Amarya suka soma tsayuwa a dai dai bakin windo na. Cikin ƴan mintuna yiriri_yiriri ya shiga tashi a kofar gidan. A wannan lokacin ina kwance ina hutawa ne, su Yaya Use kuma suna cikin gida suna rabon tuwon dare. Tuwon masara miyar bushasshiyar kuɓewa su ka yi. Ina jiyo takun dangin Amarya, a kunnena najiyo wata ƴar tsohuwa tana faɗin ki shiga ɗakin ki da ƙafar dama, ki yi adda'a kamar yadda muka shigo dake gidannan Allah yasa sai dai a fitar da gawarki. Murmushi kawai nayi ina dafe da cikina dake mun juyin waina. Bayan hayaniyar mata ta lafa ne na soma jiyo hayaniyar Kaila da abokanshi. Ina jiyo sallamarshi Amman bakina yayi nauyi na kasa amsawa sam. "Shanono ki sa yara su shigar mana da Abincinmu cikin gidan Tanimu acan zamu ci, yanzu dai sallah zamu je mu yi" Da ido na bishi, sai naga kamar an sake Kaila tsabar yanda yake ƙyalli da sheƙi, saye yake da farar shadda sol sai maiƙo shaddar take faman yi, ɗinkin malum_malum na matasan zamani ce a jikinshi, kanshi saye da hula zanna bukar, ƙafarshi saye da takalmi haf koba baƙi, ga baƙin zobe ga baƙin agogon fata, idanunshi kuma saye da sabon farin tabarau, sai ƙamshin shi na tun asali yake yi ƙamshin turaren lailatus sahra, duk sanda na shaƙi wannan ƙamshi sai ƙwaƙwalwata ta shiga tariyomun faifayin bidiyon irin romon soyayyar da muka dangwala ni da Kaila. Kai kawai na ɗaga mishi halamar naji, shi ko ko a jikinshi bai damu da yasan meke damuna ba ya saki labulen yayi gaba. Zafafan hawayene suka gangaromun, sallamar Hajiyayye ne yasa nayi saurin goge fuskata, na amsa mata sallamarta. Sai gata ta shigo cikin wata jar sabuwar atampa mai kyau ta sake shiga a karo na uku. Hannunta riƙe da ƙananun bokatan roba har uku. A bakin katifata ta dure mun. "Umman Sulaiman ga naki ke da jama'arki, dangin Amarya ne suka bamu" An gode Allah ya ba da zaman lafiya" Baki ta taɓe tace. "Hmm har wani roƙon zaman lafiya ma kike yi? Ni ko zuchiyata saura ƙiris ta ƙone ma baki ɗaya. Kaila ya je ya kwaso mana ƴar gidan masu kuɗi." Murmushi kawai nayi mata. Ta ja dogon tsaki ta fita abunta, tare da Yaya Use su ka ci karo, ita zata fita, ita kuma zata shigo. Ga kayan cin_cin nan in ji dangin Amarya, ku ɗibi naku" Bubbuɗe robibin tayi. Ɗaya cike da cin_cin ɗayar cike da alkaki, ɗayar cike da nakiya sai ƙamsin kayan ƙamshi take zabgawa. Leda Yaya Use ta ɗakko ta zuba nata dana Yaya Use, ta ƙulla na Sabira dana Inno, sauran ta bar mana ni da yara. Ƴan uwa masu daɗi sai bayan isha suka mun sallama suka tafi, bayan Yaya Use ta sallami Kaila da abokanshi da abinci. Ni ko ina yin sallar isha na ɗan ci tuwo na ba Hauwa taci ta ƙoshi, dani da'itan a wajan mu kai bacci ko hannu ban wanke ba, balle in wanke bakina. Dake na gaji ainun ban farka ba har sai da asuba, kuɗin cizo sun sha jinunmu sosai hakama sauro. Mayar da Hauwa nayi kan katifa ni kuma na fita dan ɗauro alwala. Mata ƴan biki duk sun firfito anata alwala, nima alwalar nayi na gabatar da salla, kana na fita na bi ɗaki_ɗaki ina gaisawa da dangin Kaila. Da gari yayi sha kuma na dafa tea na toya wainar ƙwai na dangin Amarya. Yaran ƙanwar Baba Rammai ce suka kai musu. Mu kuma ruwan bunu muka sha da biredi. Ni dai ina gamawa na yi komawata ɗakina. Yara basu suka shigo gidan ba sai wajajen goman safe Sabira ta tusosu gaba suka tawo. Ina zaune zaman taɓaro a ƙasa Suka shigo. "Uwar gida sarautar mata, banga kin yi wanka kin fito shar dake ba. Na hango wulgawar Hajiyayye ta sha kamfala da ɗankwalin ashoke, ke ko ina ƙunshe a ɗaki. Balaraba ce ta zauna kusa dani. "Umma ina kwana?" Lafiya lau ƴan albarka" Nan suka shiga gaisheni ɗaya bayan ɗaya. Maza ku shiga cikin gida ku gaishe da iyayenku." Da sauri suka fita harda rige_rigensu. Ledar kayan filawa da Yaya Use ta ƙulla mata nata na jawo na miƙa mata. Ga naki kayan garar Amaryar kwa tauna ke da yara. Ina so in faɗa miki ma jibi zamu yi tafiya dasu Inno zuwa Shanono can garinmu, bikin ƴar ƙanwar Inno." "Dukka wannan garar amarya leda guda haka, ai yayi yawa Tani. Murmushi nayi nace. Haba Sabira ai ko duka na zuba miki kin cancanci hakan ne. Kuma kinga fa bokatannan cike aka kawo mun, wannan amarya akwai maiko a hannun iyayenta gaskiya " Dariya tayi mun tace. "Gaskiya kam ai ko da ganin danginta, da gani basu san meye talauci ba ma sam. Batun komawar yara makaranta fa? Naji ana sanarwa a gidan rediyo cewar ran monday makarantun gwamnati zasu koma karatu, to yaran zaki barsu a wajena amman ko? In an Koma makaranta sai su soma zuwa kafin su dawo, ga islamiyya ma ran monday zasu koma" Ni kam babu abinda zance da Sabira da mijinta sai dai adda'ar kairiro, domun maƙotane na gari sosai. Shi ya soma kama hannun su Sulaiman ya jefa su a makarantar gwamnati mai suna islamiyya pilot primary school makaranta ce ta gwamnati, to bayan yayi hakan ne, Kaila ya sai musu fensir da takadda...........✍🏻 MRS BUKHARI [10/8, 18:33] Badiat Ibrahim: NA FADO DAGA BENE.... NA ZARCE RIJIYA HAKKIN MALLAKAR BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI GAWURTATTU UKU 8 _*AMMA ARAB!AMMA ARAB!!AMMA ARAB!!!*_ _kai daga jin sunan kasan sunan ya amsa sunansa,AMMA ARAB ta kawo muku wani supplement na gyaran jiki mai sanya daɗi da ƙamshi AMMA ARAB gidan ƙamshi_ *MUSUK* *MADARAR TURARE* *KAJIJI* *ROT* *SANDAL* *HUMFUR* *SANDAL FLASK* *SANDAL WUD* *AALUT* *GAF-GAF* *JANNAMI* *ƘWALAKCA* *MAHAHABSUFYAN* *WANNAN SHINE GRP ƊINA NA WHATSAPP,KI ANTAYO SABODA KADA AYI BABU KE* 👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻 https://chat.whatsapp.com/BrUXmBHnDN6KUJYnkBDT7S *ADDRESS👇🏻👇🏻👇🏻* Zaria road kwankwasiyya sabon gari dangwauro house number 224 *AƘWAI WANI SUPPLEMENTA NA GYARAN JIKI DA TAZO MUKU DASHI KE DA KANKI IDAN KIKA YI ZAKISAN EH LALLAI ZAKI GIGITA ME GIDA,KINSAN MAZA SAI DA ƘAMSHI DUK MATAR DA BATA SAYI WANNAN SUPPLEMENT ƊIN BA TO AN BARTA A BAYA* *AƘWAI BABBAN MAGANI NA INFECTION,WANDA ZAI DAWO MIKI DA MARTABARKI NA ƳA MACE,ZAI CIKO MIKI DA NI'IMARKI KI KOMA ƳAR GATAN MEGIDA* *AƘWAI BABBAR KAMBASA,TA TURARA KAYA HAJIYA KI BUƊE BAKIN ALJIHU KI JIƘO DA ƘAMSHI,KINA ZAMA AN SAN KIN ISA MACE HAJIYA DON AMMA ARAB TA SHARA SOSAI WAJEN KAWO MUKU KAYAN GYARA NA MATA* *AƘWAI SABULAN GYARAN JIKI SUNE KAMAR* *MULATO SOAP* *FACE CREAM* *FACE SOAP* *MULATO WHITENING LOTION* *HAIR GROW OIL* *HAIR GROW CREAM* *KAR-KAR OIL* *MINT LEAVE OIL* *ANTI PIMPUS SOAP* *AƘWAI SABULUN NANKARWA* sannan ina harkar👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻 *ABIN BUKI* *ABINCIN OFFICE* *SNACK* KAMARSU👇🏻👇🏻 *WAINAR MASA* *SINASIR* *MEAT PIE* *CINCIN ƊAN LAUSHI* *CUP CAKE* DA DAI SAURANSU. AMMA ARAB GIDAN GYARAN AURE😄👏🏻 Hatta inifom mijin Sabira ne ya ɗinga musu, da basa zuwa ko ina sai gararamba a unguwa. Haka zalika shi ya sanyasu a islamiyya irin ta cikin anguwa, duk sati suna tafiya da nera hamsin, shima wannan ko da Kaila yaga suna zuwa bai ce dani komai ba, nima ban tanka mishi ba. Ajjiyar zuchiya na sauke na dubi Sabira a karo na barkatai nace. To zan bar miki su, zan haɗo inifom ɗinsu Sani zai kawo miki. Zaki sha bari_bari kenan bakin ki sai yayi tsini ashe kafin in dawo. Dariya tayi tace. "Su Mustapha da Umar fa da kike ganinsu wallahi sun fi Shafi'i da Sulaiman rigima, Sani shi bai da yawan ƙiriniya magana ma bata isheshi ba. Kullum a cikin raba dambe nake." Hmm suma ko da yaushe aikin Kenan." Mun jima muna tattaunawa kafin muka fita domun ɗora girkin rana. Ƴan Wudil kam har sun fito tsab zasu koma, ƴan Akwanga suma ina ji suna cewa da sun yi azahar zasu tafi. Sallama nayi ma ƴan Wudil, muka shiga hidimar abincin rana. Girkin dangin Amarya daban Sabira tayi shi. Tuwon shinkafa miyar ganye tayi musu da kaji. Ita tayi komai da komai, kuma ta ɗauka ta kai musu. Bata jima ba ta fito. Ƴan Akwanga suna cin abinci suma suka kama gabansu, harda Baba Rammai dan an bogo waya an yi musu haihuwa. Sabira da Hindatu ne suka yi wanke wanke da gyaran gidan. Fes suka wanke tsakar gidan yayi kyau sosai. Misalin huɗun yamma muna tsakar gidan ina ɗaura sanwar miyar dare. Sai ga dangin Amarya su biyu, sun sa Amarya a tsakiya. Suna zuwa in da muke suka tsaya. "Bayin Allah muna neman ɗakin uwar gidan gidanne, zamu kai amarya bisa doron al'ada." Sabira ce tayi musu jagora zuwa ɗakina ta nuna musu taburma. Ni kuma na kirawo Hajiyayye da Hindatu, tare muka shiga ɗakin, na shiga na same su sai yamutse fuska suke yi, ba shakka zarni ne ya ishesu. Bayan an yi ƴan gaishe_gaishe wata farar mata tace. "Wacece uwar gidanne a cikinku?" Hindatu ce ta nuna ni tana dariyar ƙeta, ta nuna Hajiyayye a matsayin ta tsakiya. Baki suka sake su kansu, ƙila sun yi tunanin mai aikin gidan Kaila ce ni, dan sun gagganni face_face ina shan uban aiki kamar jakka tun zuwansu." "To uwar gida kece babba ga Bilkisa mun kawota domun ku gana, ba Domin mun kawo muku amanarta ba, amanarta na hannun wanda ya rabota da garinta da ahalinta. Bilkisa ki buɗe fuskarki abokan zamanki su ganki ki gansu" Bilkisa tana saye da wata lafaya mai adon duwatsu faca_faca hannu tasa tayi baya da mayafin. Wallahi bani ba hatta Hajiyayye da take jin ita shahararriyace sai da ta ƙware. Bilkisa gaskiya tana cikin sahun kyawawan matan hausa fulani, uwa uba gata da haske sosai, ga iya kwalliya da zabin kalar daya dace da launin fatarta. "Ina yininku Anty da Anty?" Wani ƙwallon kishi na haɗiye nace. Lafiya lau Amarya Bilkisa ya baƙunta?" Murmushi kawai tayi mun bata ce komai ba. Iyakar abinda ya faru kenan, sai shaida mana cewar yanzu zasu tafi da suka yi. Fatan sauka lafiya nayi musu Hajiyayye dai in kun tanka ku masu karatu to itama ta tanka, tunda Bilkisa ta buɗe fuskarta Hajiyayye ta daskare a zaune. Ana cikin haka Kaila yayo sallama ya shigo, sai faman dariya yake yi, yana doro. "Anty Zinaru baku wuce ba ashe?" Sai wani dariya yake yi harda wani sin_sin da kai. Ita wacce ya kira da Zinaru tace. "Munkaila yanzu zamu tafi, ka kula da Bilkisa sosai kar ka manta da sharaɗin da Mahaifinta ya gindayama tun kafin ma tafiyarku ma tayi nisa. Bayan kwana bakwai zata ci gaba da zuwa aikinta, an yi magana an gama mata komai aikin kawai zata soma zuwa." Dariya yayi yace. "Babu ai komai Anty Zinaru ni dama ƴar bokon naso shi yasa na biyota kuma na aminta da komai. Zuwanta cikin rayuwata aikhairine mai girma, gidan zai ɗau saiti sosai, nifa yanzu ne na san nayi auren kece raini. Ina godiya sosai da karramawa" Nan su kai mana sallama suka fice, ni maza sun dena bani mamaki tuni. Hajiyayye ce tayi kasaƙe tana kwasar ruwan mamakin Kaila. Fitar Amarya da ƴan uwanta ke da wuya Hajiyayye ta miƙe tsaye tace. "Aikin banza aikin wofi ni Kaila zai wulaƙanta sabida ya auro ƴar boko, wallahi zaman lafiyar Kaila da kilakin daya auro ya ƙare. Fuuu ta fice kamar kububuwa, Hindatu ta bi bayanta tana faɗin. "Allah ya kyauta, wannan cin fuska dame yai kama ne ni ƴasu?" Sabira ta dubeni, nima ita nake kallo, murmushi nayi mata kawai muka koma bakin aikin mu, amman zuchiyata a cushe take ainun. Zuwa yamma gidan babu kowa sai mu mazauna gidan, yara suna gidan Sabira ta haɗe kansu dasu Mustapha sun tafi, Hauwa tana bayana. Ina kan yin shanyar kayan Hauwa dana ɗan ɗauraye sai ga Kaila ya shigo gidan, kici_kici da manyan ledoji yana shirin wucewa ɗakin Amarya. Sannu da shigowa *Ango* Jin na kirayeshi da Ango yasa ya washe mun bakinshi har kunne. "Sannu Shanono da hidima da jama'a fa" Murmushi nayi mishi, Hajiyayye tace. "Inason yin magana da kai Kaila kafin ka shiga ɗakin Baturiya" Dubanta yayi yana nazartarta kafin yayi wani malalacin murmushi wanda ni nasan na muguntace. "To yau dai kwanan Amaryane baki da hurumin da zaki ce dole sai kin yi magana dani." Yana kaiwa nan ya burma ɗakin Amarya ya rufo ƙofa garam. Numfashi kawai naja, ina gama abunda nake yi na yi alwalar magriba nayi shigewata ɗaki na danna sakata." KAILA: Yana shiga ya tarar da Amarya a harɗe a kan kujera tana kallon tashar Mbc action, ana wani film na soyayya. Baki ya buɗe yana dariya. Itama juyowa tayi ta yi mai murmushi mai burgewa. "Amarya bakya laifi ko kin kashe ɗan masu gida. Ni na ɗauka zan zo in tarar dake akan gado a harɗe kin rufa da mayafi kina jiran in sai bakin ki?" Dariya tayi mai tace. "Siyan baki kuma? Sai kace wadda bata waye ba. Ai ni na ɗauki wannan abun a matsayin ƙauyanci, Shekara guda muna soyayya sai yau kawai in rufe maka fuskata haba mana Ƙyalli " Murmushi yayi haƙiƙa Kaila sai ya ji Bilkisa ta sake burgeshi, irin macen daya jima yana nema kenan. Amma a baya bashi da damar mallakar irinsu, duba da yanayin rashi da yake ciki. Amman a yanzu sai hamdala, sana'arshi dai shine gashin kajin gidan gona, kuma wajan gashin nashi babbane, a rana ya kan siyar da kaji guda ashirin ko sama da haka, banda masu siyan pat_pat irin su cinya, ƙirji, kai da ƙafa da sauransu. Kuma shike kiwata kajin a gidan gonarshi da kanshi, ga kashin kajin da yake siyarwa buhu_buhu. Zama yayi a kusa da'ita yasa hannu ya jawota jikinshi tare da lumshe idandunanshi. Itama idan nata a rufe yake, taushin fatarta da irin ɗumin jikinta yayi daban da na matanshi baki ɗaya. Iya hakan ya fitar dashi daga hayyacinshi sosai. Bilkisa ba tai aune ba taji Kaila yai ma bakinta riƙon alawar yara. Abunka da wayayyar mace tuni itama ta fara mayar mishi da nata martanin, cikin wani irin salo mai gigitarwa. Kaila kusan suman zaune ya kusan yi yanda yaji Bilkisa na wasa da harshenta a cikin bakinshi. Kota ina a jikinta ƙamshine har bakinta, hatta numfashi in ta fitar ƙamshi yake korowa. Wannan masoya sun jima suna shaƙar ɗumin juna, dana bisani Kaila ya zare bakinshi a nata ya zuba mata idanunshi da suka narke dan jaraba irin tasu ta maza musamman ma sabon ango. "Ɗanyan gwal. Barka da shigowa cikin rayuwata da fatan zaki kula dani fiye da irin kulawar da kika bani a baya? Ki ɗaukeni tamkar jariri sabuwar haihuwa kinga kuwa yana buƙatar kulawa mai yawan gaske. Ɗan wannan zaman da nayi dake a yanzu ya sake dulmiyani cikin soyayyarki. Mata ma suna suka tara ashe?, bari in fito fili in fyeɗe miki biri har wutsiya. Tunda nake ban taɓa shan yawu mai ɗanɗanon naki ba, haka ban taɓa jin fata mai nagartar taki ba, ga ɗumi, madallah da samun ki a matsayin abokiyar rayuwata." Murmushi Bilkisa tayi tace. "Amman Gwanda ni gaskiya bazan iya shiga bayan gidan tsakar gida ba, ni tunda nake ban taɓa amfani da bayan gidan gargajiya ba. Kuma kamar ni Gwanda sai kawai a ganni na fito zan je wanka? Ina gaskiya bazan iyaba wallahi, su Anty Zinaru ma sunyi magana, ni ina ganin zan yima Dady magana kawai ya kama mun haya kusa da asibiti kawai, daman hakan yaso, amman ganin ka fi sha'awar haɗe mu waje gudane yasa na tausheshi har ya haƙura" Zama Kaila ya gyara yace. "Kin fi ƙarfin wannan bayan gidan ai Ɗanyan gwal. Ki kwantar da hankalinki zan sa a yanka miki banɗaki a cikin uwar ɗakin ki, sai dai bazai kasance babba ba sai kiyi haƙuri kafin in ƙarashe ginina, ke zan fara kaiwa gidan ki zaɓi in da yayi miki. Amman kafin azo a soma aikin bayan gidan sai ki yi amfani da nawa na cikin turakata, ni kaɗai nake amfani dashi dama, zan yi gaggawar ƙarashe sabon gida, wannan da muke ciki ma inaga a kasuwa zan sa shi, kuɗin sai in ƙundume a sabon gidan, wannan sabon gidan dama dake ya dace, da ace tun farko na tuno da batun sai da wannan tsohon gidan, da yanzu ma muna sabon gida." Jin za'a tayar da salla ne yasa Kaila ya miƙe cikin kasala. "Ɗanyan gwal bari in je sallah kinji har za'a shiga Masallaci. Ga keyn turaka zaki iya komawarki can, waɗannan ledojin ki tafi dasu" Yana gama faɗar haka ya ajjiye mata keyn turaka ya fice. Da Hajiyayye yaci karo a tsakar gida, bangazarta yayi, yayi ficewarshi yana faɗin. "Aikin banza aikik wofi duk jarabarki ke baki isa kin hanani shan man Amarya ba" Nan ya barta a tsaye tana cizon yatsanta, dan data ganshi hanya ta tare mishi. Bayan sallar magriba ta kafa ta tsare tana jiran shigowar Kaila domun ta mayar mishi da martanin cizon yatsan da yasa tayi. Shinkafa da miya da nama da latas take ci. Sai taji haf door ɗin ɗakin Amarya yayi kara, juyawar da tayi tayi tazali da Bilkisa cikin wasu fararen riga da wando masu shegen kyau, kanta babu ko kallabi fuskarta sai sheƙi take faman yi. Take numfashin Hajiyayye ya nemi dakatawa, yuu daga ita har Hindatu suka bita da kallon mamaki. Far tayi da idanunta tace. "Barkan ku dai da gida" Ba ta yi maganar domun lallai sai sun bata amsaba, duba da yanayin sigar ta tayi maganar, kuma tana yi ta nufi turakar Kaila. Ɗan mabuɗi tasa ta buɗe ɗakin ta shiga. Hajiyayye bata dawo daga cikin duniyar mamaki da ruɗu ba Amaryar Kaila ta sake fitowa daga turaka ta nufi ɗakinta. "Lallai da gani wannan amarya bata da kunya, har tsakar gida bako kallabi, ace amarya daga kawoki har kin soma nuna isa da turakar miji." Ƙuta Hajiyayye tayi. Bilkisa ta sake fitowa daga ɗakinta da ƙaramin akwatinta ja na aure. Tasa kwaɗo ta datse ɗakin nata tayi shigewarta turaka. Abincin da Hajiyayye ta kasa ƙarashe ci kenan. Ajjiye kwanon tayi ta shige ɗakinta. Hajiyayye: Tunda ta shiga ta kasa zaune ta kasa tsaye. Kishi kawai ke ɗawainiya da zuchiyarta. Bata san sanda ta fashe da kukan baƙin ciki ba. Bata taɓa tunanin Kaila zai ji marmarin yin wani aure nan kusa ba. Domin a tunaninta da kuma abinda Kaila ya faɗa mata a yayin da yake kan karagar sonta cewa yayi. Tani bata iya gamsar da sha'awarshi in ya shigeta baya ko jin alama, sabida yawan haihuwa ta zama fanko maras amfani a gado. Shi yasa yake son yayi auren kece raini, kuma yana sha'awar mace wayayya wacce zata latatashi a shinfiɗa so yake a dinga lasarshi kamar alawa, kuma mai jin turanci da iya gaye yake so. Hajiyayye tayi tunanin itace mace mafi soyuwa a zuchiyar Kaila, ganin tayi dai_dai da irin macen da Kaila ke ra'ayi. Duk da cewar ita iyakarta sakandare ne kawai, amman tana ɗan jin turanci kuma tana iya mayarwa babu laifi, kana ta iya rubutun turanci, kuma tana karance_karancen littafin Hausa. Tun tana gidansu take bama Kaila dukkan kulawar da yake buƙata. Sau biyu Kaila na kwanciya da'ita a wani shagon abokinshi. Ya kuma nuna mata babu wata mace a zata iya kere mata a matsayi. Sai gashi tun kafin aje ko ina ya nuna mata kalarshi. Zama tayi a kujera tana tuno ranar da Kaila ya fara ribatarta ya jata zuwa shagon abokinshi, ranar daya rabata da darajarta kenan. Irin kalaman soyayya da irin alƙawarurrukan da Kaila yai mata a wannan ranar abun ba'a cewa komai. Kuka ta sake fashewa dashi tace. "Kaila ka cuceni. Amman wallahi bazan barka kaci amarcinnan lafiya ba, saina ja maka masifa" Wata zuchiyar tai mata gargadi da cewar. "A'a Hajiyayye kar garin kishi kije zuchiya tasa ki aikata abunda zaki zo kina ɗan daka ce baki aikata ba." Shiru tayi tana nazari. " "Tani ko tana ɗakinta kamar bata ma gidan. To wai wacce iriyar zuchiyace a ƙirjin Tani, ita bata san ciwon kanta bane ko yaya? Na tatama Tani rashin mutunci da cushen baƙin ciki iri_iri. Amman a tsakanina da'ita sai dai tayi mun murmushi kawai. Tana cikin wannan sambatun Kaila ya ɗaga labulen ɗakin nata, ya zuba mata mayaudaran idanunshi yana nazartar yanayinta. "Ni zan shiga daga ciki Hajiyayye babu wata matsala dai ko?" Ai Hajiyayye dama kamar jiranshi take ya dasa aya ta miƙe." "Ai ba sai ka zo kayi mun sallama bane zansan cewar zaka kwana da mace ba. Wanne darene jemage bai gani ba, ƙila itama ka gama shan romon amarcin nata tun daga zauren gidansu, ba girin_girin ba dai tayi mai" Idanun Kaila har ƙanƙancewa su ka yi dan ɓacin rai, ita kanta Hajiyayye data kalleshi sai da tasha jinin jikinta. Amman a zuchiyarta kuma taji sanyi sosai da taga ɓacin rai a shinfiɗe a fuskarshi. Harararshi tayi ta ƙule ƙuryar ɗakinta ta barshi riƙe da labule yana mata kallon mamaki." Dariyar mugunta yayi, bai bi ta kanta ba ya ƙule turaka wajan amaryarshi. A wannan daren Kaila ya tsunduma wata duniya iriyar duniyar da bai taɓa tsintar kanshi a ciki ba. Me yasa? Sabida wannan shine karon farko daya ɓare matarshi ta sunna dal a leda. Hajiyayye ba wai bai sameta a cikakkiyar budurwa bane, ko ɗaya. Sai dai kawai sun gudunar da kwanciyarne babu nutsuwa da kwanciyar hankali a tattare dasu. Kuma kasancewar tasu bata zama mai armashiba domun sun kauce ma shari'a( Ƙalubale a gareku ƴan mata masu miƙa ma saurayi kai tun kafin a shiga daga ciki) Duk wata hadda dake kan Kaila a wannan daren sai da Ɗanyan gwal ta kankare mishi Tani: Bayan nayi sallar isha, sai na shiga tunanin yanda zaman gidannan zai sake yi mun zafi. Amman inason da zaran Allah ya saukeni lafiya in tashi tsaye domun cikar burina. Duk da nasan fitowar burina ka iya haifar da matsaloli masu tarin yawan da ni kaina bansan su ba. Amman gani nake yi muddin naci gaba da rayuwa a haka haƙiƙa baƙin ciki da damuwar gidan Kaila ce zata zame mun ajalina. Kaila ya mayar dani tamkar wata jakkar gidansu. Dangin Baba Rammai babu mai ganina da kima, Hajiyayye wanne irin baƙin cikine bata cusa mun ba, ga Amarya kuma bansan ita da wanne salon tazo ba. Ni duk wannan fafutukar inayi ne domin yarana, bana fatan abinda zai sa in tsallake in barsu, nasan babu mai iya kularmun dasu, ƙarshe gararamba zasu ci gaba dayi a anguwa kawai. Wayata ce tayi ƙara ta katsemun tunanina. Yaya Use ke kirana, nayi mamakin kiran duk da dai dare bai yi sosai ba, goman dare ne. Assalamu alaikum Yaya Use kece da daddarennan haka, Allah yasa dai lafiya?" Dariya Yaya Use tayi daga ɓangarenta tace. "Babu komai. Inno ce tace in sanar miki gobe zamu tafi ashe ba jibin ba. Tace kizo da sassafe, mun samu mota har gida. Lauwali maƙocinmu direban bektira ɗinnan motarshi zamu bi har Shanono in sha Allah. Yayi mana sauƙi sosai, sai ki soma shiri tun yanzu sai da safe" Sallama tayi mun ta datse wayarta babu shiri na miƙe na shiga zaƙulo kaya. Kayan da Habiba Bala ta bani na ciri kala uku na saka a jaka. Sai lokacin na jawo ledar data rarraba mana a wajan taron. Sabulan wanki dana wanka ne a ciki, sai omon wanki, da turaren wuta, da humra, harda turaren ɗaki na fesawa da ƙaton basilin. Murmushi nayi na jinjina kaina lallai Habiba Bala akwaita da kirki. Kayana dana Hauwa na haɗa tsab, na ware mana wanda zamu saka in zamu tafi, a lokacin wani bacci mai nauyi yayi gaba dani, bani na farka ba sai asuba. Fitowa nayi ina hamma gefe_gefen bakina duk yawun bacci, idanuna kuwa cike da kwantsa bana ko iya buɗe idon sosai. Banɗaki na faɗa na kama ruwa na fito. Ina tsakar gida ina alwala Kaila ya fito da sauri ya fita zuwa Masallaci. Ina gama alwalar na shige ɗaki nayi sallah, na fito na hura wuta dan in ɗaura ruwan wanka. Hindatu ma ta fito tana bakin rijiya tana jan ruwa. Kaila ne ya shigo gidan, boll yayi da butar da nayi alwala na barta a kan hanya. Taje ta haɗu da garu ta fashe, da ido nabi butar, sannan na dawo da kallona wajan Kaila Wanda shima ni yake kallo rai a ɗaure, ni kuwa ko a jikina. Ina kwana Kaila, an tashi lafiya, ya kwanan baƙuwa?" Jin na ambaci kwanan baƙuwane yasa Kaila ɗan sakin fuska har ya iya tsayawa muka gaisa. Dama inason in roƙi alfarma, amman ban samu ganinka irin haka ba sai yau" Sai nayi shiru. "Ina jinki mana Shanono ki faɗi abunda kikeson faɗa, na bar ƴar mutane ita kaɗai a ɗaki" Shanono dama zamu je dasu Inno biki. Kuma yau zamu tafi shine nake neman izininka" "Ba Shanono zaku ba, ko bangon duniya zaku je shanono ƙofa a buɗe take, duk inda kike son zuwa ba sai kin tambayeni ba kije abunki" Yana kaiwa nan ya wuce ya barni da sakakken baki. To me Kaila yake nufi dani ne, duk inda nake son zuwa in yi tafiyata ba sai na tambaya ba, sai kace wacce take zaman kanta?" Kai na gyaɗa kawai na juye ruwan wankana a bokiti, a gurguje na ɗan diddirza jikina na watsa ruwa na fito. Hauwa nayi ma wanka na shiryata tsab. Har Yaya Use ta soma kiran wayata. A gurguje na saka kaya na fito da jakar kayana da jakar mata ta zuwa anguwa. Ɗakina na rufe na shiga cikin gidan nai ma Hindatu sallama, na bata sallahun faɗama Hajiyayye in ta fito. Gidan Sabira ma a tsaitsaye na shiga nayi sallama da yaran, na ba Sabira key ɗin ɗakina na nufi gida. Na isa gida na samu har sun shisshiga mota, Baffa yana daga ƙofar shiga gaba dafe da Habu sai faɗa yake yi. "In dai Tani ce kun santa da shauni, Inno shi yasa nace muku aba Lauwali haƙuri ya kaimu gidan nata mu ɗakkota acan." Inno tace. "To Baffa faɗan ya ƙare ga Tanin nan ta iso sai mu tafi, kai kuma Lauwali kayi haƙuri kasan sha'anin lafiya da mata" Shiga motar nayi, Baffa ma ya shiga gidan gaba shi da Habu. Sai da mota ta soma tafiya sannan muka gaggaisa, Baffa yace. "Abokan nawa suna gida, na ɗauka zaki riƙo hannun Inno ƙarama a tafi da'ita." Dariya nayi nace. Suna gida Baffa na barsu, ita kanta Hauwa dan dai babu mai riƙe mun ita ne da har da ita zan bari." Muna tafe munata taɓa hirar ta zumunci. Hakan ya tuno mun lokacin da muka yo ƙaura daga garin kogi zuwa Ibadan, a lokacin mabaratan koji basu fiye samun kuɗi ba, manyan mabarata daga cikinsu suka zauna domun neman mafita irin su Baffa dan Baffa na ɗaya daga cikin manyan mabarata masu ƙarfin iko. Kasancewar daɗewarshi a bara da gogayya da yarika iri_iri. Allah sarki rayuwa, mun sha yawo gari_gari yawon bara, hakanne yasa babu wacce a cikin mu tayi ilimin addini, mun dai samu na sallah a wata makarantar almajirai, muna jin yaruka da dama, domin duk garin da muka je da irin harshensu muke bara, ko da dai ba zamu iya doguwar hira da yaren ba, zamu iya roƙonsu. Kuma waɗanda ba musulmai ba sun fi ƙoƙari wajan bada manyan kuɗi ma mabarata fiye da Musulmai. Sai kaga Alh ya tsaya a ƙatuwar motarshi, mabarata sun rufeshi ana mai bara. Amman bazai wuce ya raba sababbin nera ashirin_ashirin ba, masu ƙoƙarin ciki suke raba hamsin_hamsin. Haka ƙwaƙwalwata tai ta yawo dani a cikin labarina, wani abun inna tuno in yi ƙwal_ƙwal, wani abun inna tuno na yi murmushi, wani kuma babu yabo babu fallasa. Motarmu tai ta lulawa, misalin sha biyun rana muka ɗan dakata a wani ƙauyen da bansan sunanshi ba. Baffa ya sai mana abinci. Shinkafa garau_garau ce ya siya mana akan wani ɗan tallah. An yi mata zubin ɗari_ɗari, kowa ya ɗauki ƙwano ɗaya. Wata rumfa muka nufa anan muka yi zaman dirshan. Hauwa na sakko daga baya, sai da ta ƙoshi sannan na ci abincin na bi da ruwan leda guda ɗaya. Inno tace. "Baffa ni kam zan kama ruwa, kaga Shanono daga nan da tafiya sosai, gara in rage marata, Indo muje ki rakani mu nemi wajan ciyayi haka sai in yi." Ai Inno na faɗin haka duk muka miƙe ko wacce da guntun fitsarinta ga mararta. Wani gida muka samu daga bayan wasu rumfuna, a gidan muka kama ruwan, sannan muka shiga mota, bamu tsaya a ko inaba sai a Shanono. Idanu na lumshe na shiga tuno irin rayuwar auren dana gudanar a shanono, duk su ka dinga dawomin. Tuno da Dauda ɗana ne yasa na ɗan saki ajjiyar zuchiya. Baffa ne ya katse mun tunanina da cewa. "Inno acan gida zamu sauka, jiya ina wajan bara Jafaru ya kirani, nace ya buɗe ɗaki ya ƙyara mana. In yaso ko zuwa yamma ai sai ku kintsa kuje gidan Deluwan ko?" Inno tace. "Tunda ka yanke hukunci ai shikenan Baffa. Amman ni kam ai so samuna daga nan sai gidan Deluwa, ana can anata sha'anin biki ka sani. Tun shekaran jiya ya kamata ace na iso garinnan fa haba Baffa" Da ihu_ihu Baffa yake magana kamar faɗa irin na makafi, sake ƙwalla muryar tashi yayi yace. "Da wannan tulin tsarabar kike son ki je gidan biki, shingin duk abi a sace, bazai yiwu ba. Use nuna mishi hanya kinji mu je unguwar Shakogi." Yaya Use tace. "To Baffa. Lauwali kwana zaka yi, ka miƙe har gaba da ceɗiyar can. Kana yin kwana gidan kenan"........ Mrs Bukhari ce Sai Allah ya sadamu ni da ku ranar Monday. Bana posting ranar asabar da lahadi [10/8, 18:33] Badiat Ibrahim: NA FAƊO DAGA BENE.... NA ZARCE RIJIYA HAKKIN MALLAKAR BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI GAWURTATTU UKU 9 Asalin garin Shanono. Fulanine na usil waɗanda sukai fice ta ɓangaren noma da kiwo. Suna da mata kyawawa ga gashi sosai, kuma ba ƙauye bane irin ƙayau ɗinnan ba, dan suna da kwalta, akwai ruwan, suna da lantarki, asibitoci, kana suna da makarantu masu dama, kuma yara suna zuwa makaranta ba kamar sauran ƙauyuka da muka ji su a baya ba. (Ƙaramar hukumar shanono) an kafa garin shanono zuwa ga sanannun ƴan uwa biyu. Jaukere da shanu, waɗannan ƴan uwa biyun. Suna zuwa ƙasar domin yin kiwo, ana kuma kyautata zaton sun fito ne daga garin Hadejiya dake jihar jigawan dutse a yanzu. Ganin cewa ƙasar tana da tile kuma tana da kyau ga dabbobinsu suna kiwo manyansu sun zauna a wurin a ƙalla shekara ɗaya kafin su ci gaba, amma da lura da yanayin yankin daya dace, sai suka yanke shawarar ci gaba da zama a wurin tare da dabbobin nasu. Bayan samun wurin da ya fi dacewa sai SHANU ya yanke shawarar komawa baya kaɗan don gabatar da garin Shanono ya bar JAULERE ɗan uwansa a wurin. (JAULERE TA YANZU) ya zo ya kafa aikin sa (riga) a garin shanono na yanzu har zuwa yanzu Rijiyar taushe a shanono. Garin a halin yanzu ana ganinsa a zahiri. Ga jerin mutane da sarakunan da su ka milki Shanono. Kabiru isyaku ( ɗan shanono na yanzu dakaci shanono) akwai Hakimi. Tun da Shanono ta zama ƙaramar hukuma suka fita daga ƙaramar hukumar Gwarzo a 1989 sunansa Alhaji Bello Abubakar kambun bunun Kano daga 2004 zuwa yanzu. Shanono na da yanki na 697 km2 da yawan jama'a ² a ƙidayar 2006. Lambar gidan waya na yankin ita ce 704(1) manyan mutanen garin sun haɗa da marigayi Alhaji Ibrahim aka Ibrahim ( ɗan kasuwa) Marigayi Alhaji Barau (Ɗan kasuwa) Marigayi Alhaji Haruna Muhammad Shanono. Mariga Alhaji Bawa Mashin (Man0mi) marigayi Ɗan Anni ( Ɗan siyasa) marigayi Alhaji Haruna Naganga ( cocas chairman) marigayi Alhaji Shehu Shanono. Farfesa Nura ( masan kwamfuta) dandalin matasa na shanono ( ƙungiyar ci gaba) da dai sauran fitattu a Shanono da lokaci bazai bani damar jero su ba. Shanono: A daidai ƙofar gidan su Baffa Lauwali ya tsaida motarshi. Ai kuwa Baffa Jafaru, da Baffa Yusuf suna gano mu suka miƙe daga kan kututturen da suke zaune, suna shan iska a kasan bishiyar durumi. Rana ake kwanɗawa sosai da sosai, matasa gasu nan daba_daba sunata afkin fira, kasancewar da rani ne, babu noma sai kiwo." " Naroro, Inno kune da tsakar rana haka, maraba da baƙin birrni. Use, Karime, Tani, Habu, Indo. Sannunku da hanya. Babban direba sannu" Da murmushi a fuskata nace. Barka da gida Baffa Jafaru da Baffa Yusuf." Baffa yace. "Kuna gida baku je aikin hatsi ba Jafaru, ko su Tanimu kuka tura?" Inno tace. "Lauwali mu je ciki kaci abinci, in kayi sallah Allah bashi sai ka kama hanya. Jafaru muna da kaya a mota ku shigo mana dashi ku da su Use." Inno tayi shigewarta ciki, tana ta cogala ƙafarta. Tausayi ta bani dan ƙasar da zafi sosai, gashi ko takalmi babu a ƙafar Inno. Allah ya hore mini in sai ma Inno keke ta huta da zafin rana, ko sanda." Da tulin kaya muka shiga babban gidan mai yalwar filin tsakar gida da yalwar matan gida da yaran gida. Dan Baffa su rai ashirin cib mahaifinsu ya haifa malam Jauro Ja'e. Kuma a cikin ƴaƴa ashirin ɗinnan macen su ɗaya ce itace Goggo Ige. ( Hausawa na kiran sunan Ige ne ga macen da ta biyo maza zuryan) "Ah Inno maraba lale kune da rana haka, an tawo biki ko? Tani ashe ƙafafuwanki zasu sake taka ƙasar garin Shanono idanunki kenan?" Inji Baba mai riga matar Baffa Jafaru, mace mai faram_faram da son zumunci kenan. Dan duk da yawan yawonmu baisa ta dena ziyartarmu a duk garin da muka ya da zango ba. Ɗakinta ma ta ja mu baki ɗayanmu. Baffa kuma su Baffa Jafaru suka janyeshi shi da Lauwali. Bayan mun zauna mun sha ruwa. Nan fa ɗakin Baba mai riga ya cika maƙil da matan ƙannen Baffa, da sabbin idandunan da ban sansu ba, da yara rututu. Gaisuwa da taɗin yaushe gamo yaƙi ƙarewa. Da ƙyar muka yakice mu ka rama sallah. Baba mai riga ta saukemu da kwaɗon ganyen dimkin yaji albasa da ƙuli. Baba Marka ta kawo mana damammiyar fura da nono wacce ta ji zuma. Kowa ya bar gida gida ya barshi. Haƙiƙa garin Shanono garine mai tsaiwa a rai sosai. Suna da son zumunci, da son taimako. Kuma bugu da ƙari kusan kowa ɗan uwan kowane a Shanono. Inno tace. "Oh Marka ni ko banga matar Katagi ba, shi kanshi Katagin ban ganshi ba" Ɗan dariya Baba marka tayi tace. "Wannan yaron ai yana legas da iyalin nashi, ya samu aiki a wani babban gidan abinci. Shekararshi guda da tafiya, wallahi dawowarshi gida na uku, sai Baffansu ya bashi shawarar ya tafi da ita iyalin nashi." Kasancewarshi Ɗan fari a wajanta yasa tai mishi alkunya da wannan yaron, kamar yadda yazo a al'adar malam bahaushe. Hausawan zamanin da an sansu da yakana da kunya, haɗe da kawaici da kara. Amman kwaikwayon al'adun wasu ne yasa tamu al'adun suka samu tawaya, daga wannan lokacin mace macen aure yayi yawa a ƙasar Hausa. Gabana ya yanke ya faɗi da jin an ambaci Katagi. Katagi ya nuna kwaɗayin aurena a fili, ni kuma Allah yana gani tsanar da naima Narani ce ta shafi Katagi, da tuno da Kaila da nayi, da irin kulawar da Kaila yake bani a dai_dai wannan lokacin muna matsayin saurayi da budurwa kuma a lokacin soyayyarmu da Kaila tayi zurfin da bazan iya juya mishi baya ba, kuma ina jin maganarshi fiye da maganar kowa a duniyata. Allah yayi Kaila mutum ne shi mai daɗin baki da iya tsara zance. Daga baya ne na gane ashe tantirin gogaggen mayaudarine. Gashi da iya ɗaukar wanka aljihu babu ko sisi. ( Wannan kuma ɗabi'ace ta samarin Jos. Allah yayi da dama a cikinsu mayaudara masu iya layancewa. Bugu da ƙari akwai iya wanka ba ko tasi a aljihu. A jos ne zaku ga gaye iya gaye, yayi wanka iya wanka, amman yana kan titin salisu Adamu yana tafe ɗai_ɗai kamar bazai taka ƙasa ba. Jasawa ayi haƙuri nima ƴar Jos ce na rayu a Jos sama da shekaru ashirin, nasan komai ). Muryar Baba mai riga ce ta katseni. "Uhm Inno ai Katagi ya zama babban mutum, gonakin shi a shanono ai sunyi goma. Kuma duk nomesu yake yi tsab, irin wannan yanayi na rani yake fitar da abincinshi cikin garin Kano. Yananan yana ɗanɗasa gida a gaba dasu Tabawa kaɗan. Kuma yaron gashi da zuchiyar yi, in ya tashi yo aikennan baki gani ba, baya mancewa da kab iyayen nashi. Yama kusan ƙarin aure, mai Anguwar anguwar gabanmu ya bashi babbar ƴarshi." Ni dai nayi tsumu_tsumu dani. Su kai ta rabtako zancen Katagi da irin samunshi. Baba Marka ce tace. "Tani ai ko Dauda yana yawan zuwa gidannan. Su Tasi'u ne abokan wasan nashi. Kinsan Narani ya sashi a gareji, to garejin nasu yana nan anguwar. Amman an kwana biyu baya zuwa wallahi. In ce dai zaki daure ki mance da duk abinda ya faru kije ki ga ɗanki ko shima zaiji daɗi? Tani rayuwar haƙuri akeyi, wallahi duk wacce kike ganinta a cikin ɗakin aure. Imma babba ko yarinyar mace, zaman bazai yiwu mata ba madamar batai haƙuri ba. Yara_yaran cikin gidannan da suka ɗaɗɗauko mata. Kusan rabinsu da kwata du sun yi saki, sakin fa a cikin ƙabilar Hausawa ya zame ma mazan kamar wani ado. Face maza na gari da suka kasance sun san abinda suke yi. Kuma ba rashin addini ba, ba rashin kyawawan al'aduba, face watsi da mu kai da koyarwar Arrasul Sallallahu alaihi Wasallama, mu kasa ƙafa muka shure al'adunmu, muke hanyen turawa da mutanen kudu waɗanda addini da al'adarmu suka banbanta. Mu da ƙabilar Hausawa bamu san wani yawan mutuwar aure ba. Sai kiga mace sama da shekaru saba'in tana tare da mijinta na lalle. Ta ba gamu ba mun doshi shekaru sittin a ɗakin aure, ɗuwawu duk ya dame da kashi, amman anata bugawa dai. Ke mu fa a al'adar malam bahaushen da, ko anguwa bama fita da rana. Da asussuba muke fita, sai dare ya rufa muke dawowa. Ko kuma mu fita da daddare. Sabida kunya, da killace mace irin na malam bahaushen da, ba irin na yanzu ba." Take kawaye ya soma shatata a kumatuna. Sufa duk a ganinsu, nice nake ƙure duk mazajen da nake aure har take kaimu ga macewar Auren. Da an magana suce mace tayi haƙuri. Sai hawan jini ko ciwon zuchiya ya rabketa ta mutu suce Allah yayi, kwananta ne ya ƙare. Alhalin baƙin ciki ne yai sanadin katse mata numfashinta. Wani sa'in macen ma nason ta zauna a gidan nata duk rintsi duk wuya, amman mazajen basaso, duk hakkinta daya gama ɗauka, da gallaza mata daya dinga yi, bazai isheshiba hakan, sai yayi mata tukuicin saki, wata ma harda tagonashin duka, ko karɓe yaro, irin yadda Narani yayi mun akan Dauda. Inno tace." "Kune iyayen nata ku dai sake faɗa mata. Dan ubanta ya lashi takobi a wannan karon in ta kaso aurenta, to ba dai gidanshi ba, ba dai Shanono ba. Kuma ita tasan waye Baffa, shi a makafin ma kafiyarshi irin ta kutarece, ga mitar tsiya. Dan a yanzu haka nasan Tani bata ƙi wannan auren ya kuma turguɗewa ba. Kullum tazo gida da abinda zata ƙirƙiro ta faɗa. Sai da uban wata rana data tawo raɓe_raɓe da ciki da goyo wai tayo yaji. Wallahi dukan da Baffa yayi mata ban zaci yarinyarnan gata ba zata haihu a take a wajan ba dan tsabar duka. To da taji fa babu daɗine shine ta dena ƙorafi shekara uku kenan. Sai dai kullum a rame kamar ita ake yanka ana miya" Kuka nake rerawa mai fitar da amon muzanta da tozarta. Jina nake wata ta daban a cikin ƴan uwana mata. Dangi duk sun bugamun hatimin rashin zaman aure. Wasu ma suna kirana da mai auren sha'awa. Wasu suce mun mai ruwan ido. Sunaye maras daɗi dai. Akuyata ta riga da tayi kuka a cikin dangi. Nina kafe tarihin aure biyar, bana fatan wata ta kafa irin tarihina." Baba Marka daga baya su kai ta rarrashina. Inno kuwa wanka tayo ta shirya tsab, tana rabon tsaraba tana sake jaddada musu labarun da in haddace sun riga da sun daɗe da haddacewa. Yadda suke ji, da irin halin da suke shiga, da irin tsangwamar duk da suke shiga in ina gabansu ina zawarci. Wai me yasa iyaye da jama'ar gari basa yi ma BAZAWARA uzirine? Har ta gama rabon tsarabar batai shiru ba. "To ni kam zan wuce gidan bikinnan. Ke Tani Karime ta raka ki ku je ku dubo Dauda. In yaso kwa same ni a can gidan bikin zamu tafi da su Use. In shi Naranin ya amince muku sai ku ɗauko Daudan ya ɗan zauna dake kafin mu tafi. In bai amince ba ku bar mishi abunshi" Ajjiyar zuchiya na sauke, naji sanyi a raina sosai. Tare da adda'ar Allah yasa Narani ya amince ya ɗan bar mun Daudan mu ɗan zanta" Da haka muka shirya. Na cire tsarabar da nayo ma Dauda na kwancen kaya da takalmi na riƙe. Muka kama hanyar Unguwar Marabutawa. Muna kusantar gidan ina hangoni a lokacin danai fitowar ƙarshe babu ko mayafi balle kallabi. Ina kuka, ina ambaton Ɗana kar ka raba ni da gudan jinina Narani" Abubbuwa da yawa suka shiga yi mun yawo. Bansan sanda na yar da ledar hannuna na wuya ba. Ji nayi na fasa shiga cikin wannan gidan mai ɗumbin tarihi, gidan da anan matsalata ta soma. Gidan dana zama ɗanya ina wari sabida wanka da ruwan sanyi da ɗanyan jego. Gidan da na kusan rasa hankalina tsabar damuwar ɗa namiji." Kuka nake yi mai ciwo, irin kukan wacce ta fama wani babban gyanbon daya daɗe yana ruruwa a ƙasan zuchiyarta. Yaya Karime ce ta dafa ni. "Haba Tani wai ke dan Allah ba kya mantuwane? Duk abunda ya faru ai ya riga da ya faru. Yanzu yaro muka zo gani, Narani bai isa ya koro mu ba, bai kuma isa hana ki ganawa ko keɓewa da ɗanki ba. Ki cije mu shiga gidannan ki ga ɗanki. Ki sani shima yana da hakki a kanki, ba kya tsoron shi yaron ya girma ya dinga tunanin kamar kin watsar dashi ne?" Numfashi naja, tabbas shima yana da hakki a kaina. Hawayena na share zuchiyata da hantar cikina nata kaɗawa haka muka shiga gidan a bisa jagorancin Yaya Karime. Sai na tuno sanda aka kawoni gidan a matsayin Amarya, su Baba marka na cewa in shiga da bismillah kuma da ƙafar dama. Duk wani taku dai dai yake da bugawar zuchiyata. Sallamar Yaya Karime ce tasa hankulan matan gidan ya karkato izuwa garemu. Na san da dama, da dama ban sansu ba, basu sanni ba. Sai dai nayi imani ba zasu gaza samun labarina ba. "Sannun ku, mun same ku lafiya?" Cewar Yaya Karime. Kallon ƙuda muke yi ni da Ta Maulidi. Tana ganina ta datse annurin dake shimfiɗe a kan fuskarta, tsaki taja taci gaba da dakan masarar yin tuwo, wanda ya zama ta'adar gidan. Fiddausi da Ɗausiyya matan ƙannan Narani ne suka ce. "Tani ashe rai kan ga rai, umman Dauda ashe baki mance da mu ba?" Ɗan murmushi na ƙaƙaro cike da ƙarfin hali da juriya nace." Ba gashi yau rai ya ga rai ba. Ɗausiyya na same ku lafiya ya bayan rabuwa?" "Sai Alkhairi Tani. Ku ƙaraso daga ciki Iya mai Fura tana ciki" Naga mun gaggaisa da kowa cikin fara'a banda Ta Maulidi wacce take ta waƙa tana shilla taɓarya tana cafewa" "Ina wuni Ta Maulidi, na same ku lafiya?" Harara Yaya Karime ta zuga mun tace. "In ma ba lafiya kika same su ba, meye naki?" Ai Yaya Karime na faɗar haka Tamaulidi ta soma tafi tana dukan cinya. Habaici da gori dai mun shashi, ƴaƴan mabarata. Da kyar na jaye Yaya Karime muka shiga ciki. Iya mai Fura tana zaune tana cura fura muka shiga da sallama. Idanunta ƙifi_ƙifi duk ya dame irin na tsofaffin fulani. Amman ras Iya mai Fura ta gane mu fes. Bayan mun gaisa Iya mai Fura tace. "Tani ni na ɗauka kin haƙura da Dauda ne ai. Kin tafi babu ko waiwaye, kuma ke iyayenki fulanin tashi ne, ballantana mu mu neme ku mu kai muku shi yayi ziyara. Inno dai tana zuwa ganinshi duk randa ta shigo Shanono. Kuma ana kawo mishi saƙo, kuma ana faɗa mishi daga wajan gyatumarshi ne. Wacce Fatsumar ce a bayanki?" Yaya Karime tayi dariya tace. "Wannan Hauwa ce ba Fatsume ba?" Baki ta turo tayi zunɗe harda kashe ido tace. "Duk shegiyar ɗarin ce, itama tsohuwarce ita ta haifi gyatumina" Dariya muka yi dukkan mu. Tace. "Tamaulidi ta nuna muku Daudan ne? Yanzu ma ya gama bacci a tsakar gidan fa" A'a bamu ganshi ba" Tashi tayi tasa ƴan uwanshi nemoshi a waje. Fura ta dama ta bamu." "Ai yana ko almajirci a can wani ƙauye mai nisa, yanzu haka ma sun kusan tafiya. Dan sauran ƴan uwan nashi ma har sun yi gaba. Sun ɗan jima a Shanono wannan karon, tun fa damuna suke, an ƙare noma abinci ya dawo gida, sai azamar komawa bakin karatu" ƙirjina naji ya doka da ƙarfi data ambaci almajirci, yanzu Daudan ne yake ɗaukar nauyin cin shi da shan shi da lafiyarshi? Bakina na rawa nace. Ai na ɗauka yana zuwa makarantar boko, ta allon na ɗauka makarantar malam babba zai yi ai Iya?" "E hakane, hakanne ya dace kuma. Da har ya shiga makarantar yana aji uku a firamare, sai uban yace bazai iya ba ya cireshi, sakamakon faɗuwa jarabawa da yake yi. Kinji yadda akayi, ko a ta allon fa bai da ƙoƙari ƙannenshi ma sun wuce shi, amman shi shekara guda yana wai Abasa wata wallah. An sashi a garejin ma, ogan ya hana shi zuwa baya gane komai sai shegen wasa da niman tsokana a cikin Dauda. Ga yawo" Tana cikin faɗar haka wani ɗan yaro ya shigo da yagaggun kaya, yayi futu_futu, sai jan ƙafarashi yake yi. Ga sumar kanshi daka gani kasan fulanine, amman kora ta cinye fatar kan." "Tani kin ganshi nan ja'iri. Ga uwarka tazo dubaka" Ƙura mishi idanu nayi, ina jin motsin sonshi a dukkan jikina, wani irin so nake yi ma Dauda so irin na yaran fari, so irin na uwar data soma haihuwar ɗanta ta buɗe idanu ta ganshi a matsayin mallakinta fid duniya wal akira. Shima ni yake kallo tamfar ya sanni. Fuskarshi ta yaiwatu da fara'ar data kusan karya kuzarin dana aro na yafa. Sai nake ji kamar bazan iya tafiya in bar Dauda a cikin garin Shanono ba. Hannu na miƙa mishi. Tawo gun ummanka Dauda" Dariya yayi har wawalonshi ya bayyana, da halama famfara ya soma. Cikin ɗingishi da yanayi na azabar ciwo ya iso gareni. Riƙe mishi hannu nayi dam. Siraran hawayene suka gangaro a idanuna. Ji nake sake rabani da Dauda a karo na biyu tamkar zare mun munfashine, ma'ana nabar doron duniya. A halin yanzu hankalina ya dawo kan Dauda, kuma inason in da so samu ne yaci gaba da rayuwa a gabana, in sashi a boko, wala Allah ko su sa samu damar cika mun burina, tunda ni aure, da yawan yara ya danne burina." Baka da lafiya ne Dauda, na ga ka kasa zama?" Runtse idanu yayi yana ta ƙoƙarin son zama, amman ya kasa. Cikin nutsuwa na miƙar dashi tsaye na juya bayanshi, na ga jini a bayan rigarshi. Gabana ne ya yanke ya faɗi ras. Hannuna na rawa na ɗaga mishi rigar, wandonshi ma da jinin a jiki. Zuchiyata na tsalle na sa hannu zan zame wandon nashi, cike da tsoro Dauda ya riƙe mun hannuna. "Innata da zafi karki cire mun. Kema irin abinda Alh Zangina yake yi mun zaki mun? Ciwo nake ji" Rugujewa zuchiyata take shirin yi. Cikin fitar hayyaci nace. Ba irin abinda yake ma zan yi ma ba, gani zanyi, naga jini a wandonka" Iya mai Fura tace. "Kaji mun ɗan baɗo, zaka cika mata hannu ko sai na buge hannun da sanda?" A firgice ya cikan hannuna. Jikina a mace na zare mai wandon ina jawo numfashi daga cikin huhuna da ƙyar. Abunda na gani ya gigitamun lissafina. Tunanina ya gurɓace. Fata_fata takashin Dauda take, ga wani irin mugun wari, ga ɗiwa, harda tsirarin tsutsotsi in ba dai haukacewa nayi ba. Innalillahiwainnailaihilrajiun innalillahiwainnailaihilrajiun kawai nake ta faman ambato. Yaya Karime ta fashe da kuka. Ni a wannan lokacin wallahi kukan ma ƙin zuwar mun yayi. "Tashi Tani maza mu tafi asibiti kar yaronnan ya mutu. Iya ku kuna ina wannan al'amari ya faru, ɗan mutum ya ruɓe ba ruwanku. A ruɗe Iya tana kuka tace" "Wallahi bansan komai ba Karime Tani. Bari matar Shehulle ta fito kuje" Ba wanda ya bi ta kansu. Yaya Karime ta goya Dauda a bayanta. Ina biye dasu ina haki, ga ciki ga goyo, ga numfashina na fita da nauyi. babban Asibitin gwamnati na Shanono muka shiga. Ganin yadda Yaya Karime ta ruɗe da kuka. Ba shiri ma'aikatan jinya suka amshi Dauda suka shige dashi wani ɗaku. Mu kuma akace mu jira a waje" MRS BUKHARI✍🏻 [10/8, 18:33] Badiat Ibrahim: NA FAƊO DAGA BENE... NA ZARCE RIJIYA HAKKIN MALLAKAR BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI GAWURTATTU UKU 10 *INA MIƘA DUMBIN GODIYA GA DUK ƊAUKACIN MASOYA WANNAN LITTAFIN. HAKIƘA SAƘONNINKU SUNA ZUWA GARENI. KUMA INA GANIN WAYOYINKU DAGA GARI_GARI ƘASA_ƘASA. WAƊANDA BAN SAMU DAMAR ƊAUKAR WAYOYINSU BA, SUIMUN UZIRI ABINNE DA YAWA. WAƊANDA BAN SAMU DAMAR BASU AMSOSHIN WASIƘUNSU BA, SUIMUN AFUWA SUMA DAN ALLAH. ZAN AJJIYE LINK ƊIN GROUP ƊIN LITTAFIN NA FAƊO DAGA BENE NA ZARCE RIJIYA, MAI SON KASANCEWA TARE DANI SAI YA SHIGA. KU SANI INASONKU MASOYANA A DUK INDA KUKE.* Kaila: wani irin farin ciki Kaila yake ciki marar musaltuwa. Tun dawowarshi da asuba, ya dawo ya samu Balkisa ta fesa ado da wata jar atampa ɗinkin riga da siket. Kayannan sun zauna mata ɗas a jikinta, kirjinta ya bayyana sosai, sai wannan hasken Amarcin irin na amaren kwana ɗaya tare da miji take yi. Kaila na ganin Bilkisa a cikin wannan ado, tuni ya mance da takaicin ganin Tani da yayi a tsakar gida. Dan bayan ya gama magana da Tani, fata yayi a ranshi dama ace Tani kar ta dawo in ta fita ta fita kenan, ko kuma ya ji labarin motarsu tayi dungure babu wanda yayi rai. Da wannan mummunan tunanin ya shigo, ganin Balkisa ya yaye mishi dukkannin cunkushewar zuchiyarshi. Tuni ya washe bakinshi tare da ware ma Bilkisa hannunshi. Da shagwaɓa ta faɗa jikin Kaila, shima ƙamshin yake zubawa kafin ya fita Masallaci sai da yayi wankan soso bayan wankan Sallah. Kan gadon suka faɗa suna dariya. Cikin so Kaila yace. "Jina nake kamar nafi sauran maza sa'a. In ana cin ɓaure ba'a tona cikinshi Ɗanyan gwal, amman abunda zance miki shine kin sabunta mun jinina, kin sake mayar dani fresh. Dan ƙazantar su Shanono saura ƙiris ta shafe ni, ke kika ceceni. Matane gasu dai a gida, daga mai warin dauɗa da kuɗin cizo, sai mai warin baki. In Hajiyayye ta yi magana bakinta kamar shadda fa. Ke kuwa naji har yawunki ƙamshi yake yi" Dariya Bilkisa tayi na farin ciki. Ko wacce mace ta fi son mijinta a kalleta a matsayin TA FI SU, shi yasa da yawan mata basa iya takama maza burki in sun kwaso gulmar kishiya sun kawo musu. Sai dai tai ta zura miji shi kuma yana sakin layi. To ki sani yin hakan tamkar cikin ki ki ka daɓa ma wuƙa, yau ga wani gobe gareka, musamman sha'anin maza. "Gwanda amman dai bakwa sumbatar juna in kun zo mu'amular Aure ko? Kyama har ta kama ni, ji nake uwa in yi amai" Dariyar yaudara Kaila yayi, ya gyara mata kwanciyar tata, tare da faɗin. "Ai komai baya yiwuwa kamar yadda na faɗa miki tun kafin kizo. Ni fa duk wani soyayya da tarairayar miji a gado ban sanshi ba. Ke baki ga hakan a haɗuwarmu ta jiya ba? So fa kika yi ki buɗe mun kai" Dariya tayi mishi tace. "Tarairaya Gwanda ai baka ga ma komai ba. Ni dai fatana shine kaci gaba da sona har izuwa ƙarshen rayuwata. Ni kuma zan baka duk wata kulawa." Nan suka shiga musayar kalaman ƙauna masu zafi, tamkar zasu koma ruwa, amman ina cikinsu na kiran ciroma, ba shiri Kaila ya miƙe dan bashi da juriyar yunwar ciki da yunwar mace. "Bari in shiga gidan in samo mana abinda zamu ci ko?" Baki ta taɓe tace. "To Allah yasa dai in iya ci Gwanda" Fita yayi daga ɗakin. Akan idon Hajiyayye Kaila ke ta faman jan rigarshi a ƙoƙarinshi na san dai_daita kanshi daga fitinar dake cin ƙasan ranshi. Wandon shi da yayi tudu tabi da idanunta. In da Hindatu take zaune tana wanki tabi da kallo, itama Kaila take kallo harda riƙe haɓa. Wani ƙaton malolon baƙin kishi ne ya tokare mata maƙoshi. Bata dawo daga duniyar takaici da zafin zuchiya ba, taji saukar sautin Kaila yana faɗin. "Ina abincin karin Amarya Hajiyayye na ɗauka sassafe za'a shigar mata dashi, kinsan dole da yinwa ake wayar gari" Ji tayi muryarta ta dashe, ashar tayi niyyar lailayowa da ƙyar ta danne, taci gaba da wankin da ta tashi dashi yau. "Ba dake nake ba Hajiyayye dan rashin son albarka shine kina jina ki kai mun kunnen uwar shegu, ko an faɗa miki ni sa'an wasanki ne?" "Abinci dai banyi ba, kuma in sai Bilkisa taci abincina zata rayu sai dai ta mutu. Kayi haƙuri Kaila bana son ka taɓo ni in fa ba haka ba zaka ga jajjagen rashin mutunci, alo tsiya alo......." Tas ya wanketa ta wawan tafi. Da sauri ta dafe kuncinta tana mamaki, miƙewa tsaye tsaye tayi dafe da kunci. Shi kuma ya haɗe rai ya kumbura jiran ƙiris yake ya fashe. "Ni ka mara Kaila sabida ƴar iskar Amaryarka?" "In kika kuma kiranta ƴar iska sai na saki a cikin dana sani wallahi " "An faɗa ƴar iska, an kuma ƴar iska" Cikin ɗaga murya da hargagi yace. "Kije gidanku na sake ki. Tunda ke bakya ji, baki isa ki hanani sakewa da matata ba. Ki je gida kawai" Kuka Hajiyayye ta ruguje dashi. Wannan kukan sakin ya zame ma mata dole. Ko da mace ita ta nemi sakin, da zaran miji ya furta kalmar sai zuchiya tayi rawa gami da raunata. Amman dake Hajiyayye itama A ce, kuma ita tayi dai_dai da Kaila. Bai yi aune ba ta juye mai ruwan wankin da take yi a ka. Ta jiƙashi sharaf. Bilkisa da Amadudu tare suka fito a guje tsakar gidan, a sakamakon hargagin Kaila da Hajiyayye. Da mugun gudu yabi Hajiyayye jikinshi har yana ɓari. A guje ta fella bako mayafi daga ita sai doguwar riga. Kaila bai bar binta da gudu suna ratsa mutanen anguwa ba. Sai da Hajiyayye ta faɗa cikin wani gida jikinta na rawa. Yanda taga ɓacin rai a fuskar Kaila bata san me zai yi mata ba daya kamata. A ƙofar gidan ya tsaya yana cizon yatsanshi. Amadudu ne ya iso da sauri wajan, dashi da Baban Mustapha mijin Sabira, da wani dattijo maƙocinsu. Wannan dattijon ne yace. "Haba Baban Sani, ya zaka take ka biyo mace da tsohon ciki waje, kana gudu tana gudu ko mayafi babu. Ai koma meye tayi maka bai dace ku fito titi ku fallashi kan ku ba. Ka duba yadda anguwa ta cika da mata, jibi can mata ne daga katanga suke leƙe fa" Kallon katangar da dattijon ya nuna musu suka yi. Mata uku suka gani sai leƙe suke yi. Anguwar ts soma cika da mutane. Dan da dama sun jiyo sautin muryar Kaila a lokacin da ya furta ma Hajiyayye saki. Haka dai wannan Dattijo ya taushi Kaila ba dan haka ranshi yaso ba ya bar ƙofar gidan yana ƙuta. Yana shiga gidan bai zarce ko ina ba sai banɗakinshi, dan takaicin bai gurje bakin Hajiyayye ba da ruwan sanyi yayo wanka. Yana fitowa ya kintsa, Bilkisa dai tana zaune tana kallonshi, so take ta bashi haƙuri amman tana jin tsoro. Ita yawan fara'ar Kaila da kashasshiyar muryarshi ta yaudara kawai ta sani. Sai gashi yau taji muryar cikakkun maza tattare dashi" Kai tsaye Kaila wajan mai indommie ya je. Kwai yasa aka toya mishi guda huɗu, ya sai kayan tea da ƙaton biredi ya dawo gida. A inda ya fita ya bar Bilkisa anan ya sameta a harɗe, jira yake ta amshi ledar hannunshi amman yaga ko gezau batai ba. Ba ta mishi ko sannu da zuwa ba. Amman dake amarya ance bata laifi ko ta kashe ɗan masu gida, haka ya barta. "Ga kayan tea na siyo, ki dafa ruwa ko a kettle ne ki haɗa mana tea, akwai soyayyen ƙwai a ciki sai mu haɗa da kazar jiya" A yangance ta ɗauki ledar ta fita zuwa kitchen ɗinta na langa langa. Bata jima ba sai gata da trai a hannunta ta sako komai a kai, harda kaza mai turiri da halama ta dumamata a oven ne ko microwave, dan an danƙara mata kayan wuta iri_iri. Suna zaune suna karyawa babu mai cewa da kowa komai, sai da suka kusan kammalawa Bilkisa tace. "Gwanda kayi haƙuri da Hajiyayye ka dawo da'ita ɗakinta, ga ciki kuma naga ƴarta ƙaramace, ɗazu ma daka fita ina jiyo kukanta a tsakar gida. In ka rabu da'ita waye zai riƙe mata yaranta" Ƙur Kaila ya mata da mayaudaran idanunshi yace. "Tunda fa na sanar musu da batun aurenki, bata taɓa barina nayi bacci mai kyau ba. Dama fa fitinar Hajiyayye yawa ce da'ita. Ki barta kawai ta je gidan. Ala bashi in iyayenta su ka yi tunanin dawo da'ita ɗakinta shikenan." Kai Bilkisa ta gyaɗa tace. "To shikenan ba damuwa. Abu na gaba kuma ya batun mai aiki da kayi mun alƙawarin zaka ɗauka mun washe garin ranar dana tare, kaga yau kenan. Dan gaskiya bazan iya haɗa tarairayarka da shiga kitchen ba, ga aiki in na soma zuwa. Bani ma da wannan lokacin gaskiya" Murmushi Kaila yayi yace. "Yanzu bari in kammala karyawa sai in fita, in sha Allah da ƴar aiki zan dawo cikin gidannan. Ai ba wuya suke yi ba masu aikin. Gaskiya Ɗanyan gwal kina ji dani fa, sabida tsabar tarairayata da kike son yine kika ji girkin ma ba zaki iya yi ba." Nan dai su kak ta faman tattaunawa, daga ƙarshe Kaila ya fita, Bilkisa kuma ta koma ɗakinta. Babu abinda ta taɓa a ɗakin, kayan da su ka yi kari suna wajan, kayan da Kaila ya cire suna zube a kan gadon. Kafin azahar sai ga Kaila da ƴar aiki ya kawo ma Bilkisa. Tana harɗe a falonta tana kallo suka shigo. "Ɗanyan gwal, wannan sabunta kwalliya haka, kai gaskiya ina morewa idona. To yanzu dai ga ƴar aiki nan na samo miki ita, sai ki faɗa mata aiyukan da zata dinga miki, da kuɗin da za'a biyata ko?" Bilkisa ta murmusa tace. "Godiya nake ɗan maraƙin jimina gagara ɗaukar shawo. Ke me sunanki" Yarinyar tace. "Sunana Shamwila Hajiya" "Okey Shamwila, aikinki shine, girki duk ran girkina, wanke wanke, wankin kayana da kayan mijina duk randa yake ɗakina. Sai gyaran ɗakina da turakar mijina, sai aika haka in ya kama zan dinga yi miki. Ina ga shikenan iya aikin. Zamu dinga biyanki duk wata nera dubu bakwai. Amman fa bana son fashi in ce dai gidanku babu nisa da nan ɗin ko?" Kaila ya shiga ruɗu da mamakin yanda yaji Bilkisa ta lissafo harda gyaran turakarshi da wankin kayanshi ranar girkinta, ya soma tantamar tana da hankali kuwa? Ta ya zata sakar ma ƴar aiki girkin mijinta, da gyaran turakarshi, harma da wanki? Yarinya matashiya, mai jini a jika, kuma kyakkyawa irin haka. Shiru yayi ya ƙudurce zai taka mata burkine. Muryar Shamwila ce ta dawo dashi daga taɗin zuchin da yake ta faman yi da zuchiyarshi. "Gaskiya ina da nisa Anty. Kuma dole sai dai in dinga tawowa da ƙafa, dan in nace kullum zan cire kuɗin abun hawa kuɗin zai ƙare, kuma ni ke kula da mahaifana da ƙannena" Shiru Bilkisa tayi tana nazari. Kaila yace. "A wacce unguwa kike haka, sannan mahaifinki bashi da rai ne da yarinya ƙarama dake nauyin iyayenki da ƙannenki yake wuyanki?" Shamwila sai ta saka fuskar tausayi tace. "Mahaifina yana kwance ba lafiya shekaru biyar kenan. Kuma mu masu ƙaramin ƙarfine sosai. mahaifiyata girma ya kamata. Shine nake buga _buga ina ciyar damu, danginmu dukka suna Niger mu Sadaka yalla ne, waɗanda ake mana laƙabi da muna bara muna karuwa. A layin ƴan ƙarya muke da zama can kusa da babtis." Kaila ya girgiza kan shi kawai. Balikisa tace. "To a gida za'a barki ki dawo nan da kwana, in yaso ranakun asabar da lahadi kya dinga komawa gida? Sabida yanayin nisa, duba da cewar kuna cikin wani hali, zan baki nera dubu goma duk wata, amman zaki samu ƙarin aiki" Shamwila ta zube tana ta faman godiya. Kaila shi kuma aka barshi da mamaki. "A ina zata dinga kwana kenan to?" Balkisa da take magana a gadarance tace. "A ɗakina ga falo wadatacce, Gwanda sai ta dinga kwananta a kujera ai, tunda kai kana da turaka" Kai ya jinjina yana tunanin taya kyakkyawar budurwa haka za'a turota aiki harda kwana a gidan aiki? Tsabar haushi a wajan ya fice ya barsu. Shamwila kuma ta kama aikinta ka'in da na'in. Dan a wannan rana ita ta gyare ɗakin Kaila tai ma ɗakin turaren wuta, ta wanke toilet, da kayan da suka cire. Tayi sharar tsakar gidan da wanke_wanke fes. Hindatu sai kallon ikon Allah kawai take yi. Bayan ta kammala ta tsugunna a gaban Bilkisa da take kwance tana charting da Kaila tana tambayarshi wai ina ya tafi ne tun safe?. "Anty inaso zanje in kwaso kayana kuma in faɗa ma Ummata." "Yauwa Shamwila dama inason zan miki aike kasuwa. Kaza nake son ki siya mun, da kayan miya, sai kayan lambu" Bilkisa ta lissafama ma Shamwila duk abinda take buƙata, ta bata kuɗin mota ɗari biyar. Ba'afi awa biyu ba, sai ga Shamwila niƙi_niƙi da boron kayanta gari guda, da ledar cefane. Bilkisa ta nuna mata bayan lungun show glass ɗinta tace sai dai ta ajjiye a nan. "Inason ki dafa mun jallof ɗin soyayyar taliya da pepper chicken. Akwai kayan zoɓo a kitchen ki mun zoɓo mai daɗi" Nan Bilkisa ta tusa Shamwila a gaba suka shiga kitchen ta nunnuna mata abinda ya dace ta nuna mata. Anan ta bar Shamwila tana mamakin yanda aka narkama kitchen ɗin langa_langa dukiya haka, da tunane_tunane, da burika fal ranta ta shiga aikinta ka'in da na'in. Cikin ƙanƙanin lokacin gida ya soma tashin ƙamshin albasa da tafarnuwa." SHANONO: TANI: Allah kawai nake ambato, naƙuda ma nake ji kamar inayi. Matan ƙannen Narani ne suka Iso, Shehulle na biye dasu faram_faram, ga Iya mai Fura itama tana tafe. Ni kuwa zuchiyata sai tsalle kawai take yi. "Ina Daudan yake, a wanne halin yake?" Cewar Shehulle kenan cikin ɗaga murya. Yaya Karime ce ta mishi bayani, tare da nuna mishi inda aka shiga da Daudan. Ni ko hawaye kawai nake fitarwa bana ko iya ganin gabana, kaina naji yayi wani gingiringin. Wata ma'aikaciyar jinyace ta fito daga cikin ɗakin da aka shiga da Dauda. Ina gani duk suka rufu kanta, ni ko ina zaune ina haki, dishi_dishi ma nake ganinta. "Wannan yaron bashi da iyayene, ko dai tsintarshi kuka yi. Ya yaro kamar wannan za'a bari ta kashinshi ta zazzage har ta lalace haka? Ina mahaifiyarshi take?" Take Shehulle ya nuno ni. Wani kallon tsana wannan ma'aikaciyar jinya tai mun tace. "Ke kuwa baiwar Allah kiji tsoron Allah. Shin a matsayinki na uwa, har kin mance da rainon ciki da lauwaye_laulayanshi, shin bakiyi ƙwannafi da amai bane, ina kika mance da zafin fitar kan yaro daga jikin uwa, ina kika bar buɗuwar da kwankwaso yakeyi yaro ya faɗo. Ga raino, ga shayarwa? Kina ma yaronnan wanka ace har baki san halin da yake ciki ba, har sai da ya soma tsutsa da ɗiwa tukunna? Anya kece kika haifeshi kuwa?" Duk illahirin jikina babu inda baya rawa. Maganganun ma'aikaciyar jinyarnan sai huda mun tsoka yake yi, take tsigar jikina ta soma tashi yar_yar_yar." "A'a kar ki zargi mahaifiyarshi. Domin tun yana tsumman jinjirantaka ubanshi ya kwaceshi. A hannun matar uba yake. Ita ta hofantar da rayuwarshi. Dan Allah yarinya yanzu meye abinyi, wanne taimako ya dace abashi?" Yaya Karime ke magana cikin taushin murya. Dangin Narani kuwa kamar ruwa ya cinyesu haka suka dawo. "Aiki za'ayi mishi. Amman aikin zai lashe kuɗi masu yawa. Shawarar da zan baku shine ayi gaggawar kaishi cikin gari, domin sun fimu ƙwararrun likitoci, da kayan aiki. Muna bashi agajin gaggawa dai a yanzu. Ke kuma baiwar Allah kiyi haƙuri, wallahi na zaci sakaci ne irin namu. Ashe muguntace irin ta iyayen riƙo. Amman duk wanda yai ma yaronnan wannan aika_aikan ya kamata lallai ku haɗashi da hukuma" Nan aka shiga ciku_cikun yanda zamu kai Dauda asibitin Birni. Baffa da Inno tuni sunji labari. Inno da Kawu Junaidu har sun tawo. Shehulle kuma ya fita samo mota. Ranga_ranga aka sa Dauda a mota, yana jikina sai ajjiyar zuchiya yake yi, ni kuma na rungumeshi kamar jariri. Hauwa tana bayan Yaya Karime. Da Yaya Use zamu, sai Shehulle. Su kuma su Inno banda su. Ta tagar mota Inno ta zuro kanta, ta danƙama Yaya Use dubu huɗu tace. "Gashi in ji Baffanku yace in baki Use. Sai munzo. Ke kuma Tani kar ki tashi hankalinki kinga juna gareki. Naranin yana ma cikin garin Kanon yace zaku haɗu a asibiti." Ido na lumshe kawai, idona yayi jawur dashi nama rasa abinda ke mun daɗi. Ga marata sai faman ɗaurewa take yi. Haka muka kama hanyar Kano, baka jin ko tari a cikin motar, sai ajjiyar zuchiya da nake faman saukewa a kufi_a kufi. A farfajiyar asibitin Murtala muka haɗu da Narani yana jiranmu. Dauda ya zare a hannuna suka yi ciki shi da Shehulle. Mu kuma muna biye dasu a baya. Wallahi har nafi Yaya Use dauriya, dan tunda muka tawo take rera kuka mai sauti. Cikin wani dogon falo muka shiga, a lokacin Narani sun shige ɗakin jinya shi da wani ma'aikacin jinya, Shehulle da halama dakatar dashi sukayi. "Shehu cewa su kayi ka tsaya anan?" Cewar Yaya Use, Shehulle yace. "E Narani kawai suka ba damar shiga. Dauda ya faɗi wanda yai mishi wannan aikin?" Banza nayi dashi dan kowa haushinshi nake ji a gidansu Shehulle. Dan su su kai ruwa da tsaki wajan banƙaremun hannuna a ƙwace Dauda a yayin da akeson raba uwa da ɗanta. "Ya faɗa Shehu. Amman baza mu yadda ba, dole hukuma tayi aikinta. Duk da dai mu marasa ƙarfine, amman ya kamata ace ko yayane mun ƙwato ma yaron hakkinshi." Kai Shehu ya jinjina yace. "Me sunan wanda yayi mishi hakan wai? Mu bamu san komai ba, kullum kuma zaki ga Dauda yana baccinshi a tsakar gida, ko a ɗakin iya." Cikin jin haushi nace. Alh Zangina ne wai yake yi mishi, haka yace" Ido Shehu ya zare yace. "Alh Zangina fa? Wallahi zai aikata dan yana shiga da yara gidan gonarshi cike da mota. Kuma ko ɓatan ɗan liman an yi zargin dasa hannunshi. An tasarma maganar, ana cewa hukuma zata yi aiki. Wallahi Alh Zangina yabi dare yaje ya samu malam Liman ya cika shi da barazana. Maganar bata sake tashi ba. a wata ruwayar ma cewa akayi yace in yayi magana sai ya ɓatar dashi. Ku rufama kan ku asiri damu kanmu maganar nan ta mutu kawai. Karma ku sake kama sunan Alh Zangina wallahi, in dai kuna son kan ku da arziki" Mun tsorata sosai da jin wannan labarin. Haƙiƙa nasan mai ƙarfi ma sai ya shirya zai iya tunkarar Alh Zangina da irin wannan maganar. Dan shahararren mai kuɗine sosai, yana da gonakai da wani irin wawakeken gidan gona. Abun dubawan Alh Zangina babu wanda yasan mutumin inane daga kuma wanne nahiya yake. Kuka na fashe dashi nace. Na barshi da faɗuwar rana da tsaiwarta. Allah kana ganin abinda wannan bawa naka yaima Dauda, mala'ikun Allah ku shaida, Allah ya saka ma Dauda, ubangiji Allah ka tagaiyara Alh Zangina ka haɗashi da jafa'in duniya kafin ya tarar dana ƙiyama" Yaya Use ma kuka take yi sosai. Muna cikin wannan tashin hankali Narani ya fito a gaggauce ya nufomu sai yarfe zufa yake yi. "Yaya ake ciki Narani?" "Wallahi Use a taƙaice dai sun bamu gado. Jibi za'ayi mishi aiki, kuma sunce bama zasu taɓashi ba har sai mun biya kuɗin aikin. Amman suna maganane akan wasu mahaukatan kuɗin da ni banma taɓa riƙe irinsu a rayuwata ba. Ni harma nace su sallamemu mu koma gida sai ayi na hausa mu jaraba ko Allah zai sa a dace." Nunfarfashi na shiga ja da saukewa. Yanzu Daudan da yake buƙatar taimako shi za'a mayar gida? Ya Ubangiji Allah ka kawo mana agaji" Yaya Use tace. "Har nawa ne kuɗin haka Narani da zaka ce a komar da yaro gida? Shakirar tashi fa naga tayi fata fata har ɗiwa take fitarwa, ya zaka ce haka" A rainace cikin ɗiban albarka Narani ya soma magana da Yaya Use. "Magana suke akan sai an sauke duɓu ɗari biyu da hamshin kwatan miliyan kafin ma a taɓashi, banda kuɗin gado da magani. Lissafin rabin miliyan suke yi mini. Dani daku nayi imana har mu mutu hanyar inda kuɗaɗennan suke bama zamu gansu ba wallahi. Yaro dai ɗanane gida zan koma dashi ayi mishi na gargajiya. Ni dama tun farko da aka sanar dani gaku a hanyar asibitin Birni, sai da nace ma a sanar muku ku koma. Kai Shehulle shiga ka fito da yaron mu koma gida." Fuu Shehulle ya shige ɗakin da aka shigar da Dauda. Sai gashi saɓe dashi a wuyanshi. "Ka saukeshi ɗan ƙwal uba ai yana iya tafiya. Ba sai da aka nemo shi a waje ba ma" Shehulle da jin haka ya dire Dauda a ƙasa. Ni kuwa sai tsiyayar ruwan hawaye kawai nake yi. Na kasa cewa komai, Yaya Use ma ta kasa magana. Fuu suka wuce suka barmu a tsaye. Dauda sai waigena yake yi, shima kukan yake yi. Sai da na dena ganinsu sannan na sake fashewa da wani irin kuka mai kama da fitar rai. Duk waɗanda suka zo wucewa sai sun tsaya sun tambaya lafiya ko rasuwa akayi mana ne? Da "E" Yaya Use take amsa musu. "Tani daure ki lallaɓa mu koma Shanono. Kinga mu kanmu bamu da kuɗin da zamu iya lura da Dauda ko da da maganin gargajiyanne, ballantana wannan maɗuɗun kuɗin da lukitoci suka yanko. Mu yi ta mishi adda'a, zo mu tafi" Da jan ƙafa na bar asibitin. Muna cikin motar komawa Shanono Baffa yayo kiran wayar Yaya Use " "Use Yaya kun isa asibitin dai ko, yaya jikin yaron?" Cewar Baffa da yake magana ihu ihu. Ajjiyar zuchiya Yaya Use tayi tace. "E Baffa, amman gamu a hanyar komowa Shanonon ma." Baffa yace. "Dashi Daudan ko an kwantarku ne?" "Dashi zamu dawo, sai mun dawo zaka ji komai" Gidan su Baffa muka wuce kai tsaye, a lokacin naƙuda ta kawo kai, ba shiri su Goggo mai riga suka rufeni a ɗakin Goggo Marka. Nan na shiga sabuwar azabar naƙuda. Duk zafi irin na naƙuda, da fita hayyaci da akeyi, sai wannan karon yazo mun da sauƙi. Dan raɗaɗin dake cinye ƙasan zuchiyarta yafi naƙudarnan zafi. Cikin gumurzun awa uku na suntulo ɗana namiji ƙato dashi lafiyayye. Cikin da babu awo bare shan ƙwayar bature ta masu ciki. Amman cikin hukuncin Allah gashi na sauka lafiya, shima yaron yana cikin ƙoshin lafiya, dan ya karaɗe gidan da inya_inya. Yara_yaran gidan sai murna suke an siyo musu jariri wai. Ni kuwa sai jinyar zuchiyata nake yi.....✍🏻 https://chat.whatsapp.com/Dqaioj0tydVHQGo5zoG0lm [10/8, 18:33] Badiat Ibrahim: NA FAƊO DAGA BENE.... NA ZARCE RIJIYA HAKKIN MALLAKAR BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI GAWURTATTU UKU 11 https://chat.whatsapp.com/Dqaioj0tydVHQGo5zoG0lm Bayan nayo wanka na dawo. Na tarar da Goggo Marka tana gasama Jariri cibi, an sa mishi kayan jirajirai yayi kyau abinshi, yana duƙunƙune a cikin zanina. Ina zama Inno ta shigo da ɗumamen tuwo da kunun tsamiya. "Shanono maza ki yayyanki tuwonnan da zafi_zafi. Ni kuma bari in kira Kaila in sanar dashi haihuwar." Dubanta nayi bayan na tusa tuwon a gaba nace. Inno inason inna gama cin tuwon in koma can gidansu wannan yaron dan in ji me ake ciki dan Allah Inno kar ki hanani." "Da ɗanyan jiki zaki fita Tani, ko Use da take can kina nufin kin fita iyawa, Karime ma tana can gidan tama riga Use yin gaba." Goggo Mai riga ce tace. "A'a Inno kada mu tauyeta in ta gama ta goya jaririnta taje ɗin tunda Allah ya sauketa lafiya. Hankalinta ba kwanciya zaiyi ba muddin bata je taga yaron ba. Ke kuma Tani batun shigar da ƙarar Alh Zangina wallahi karma ku kuskura a ta da zancan. A burne wannan maganar a cikin gida, wanda yaji ya riga da yaji, waɗanda basu ji ba kuma shikenan , kuyi Allah ya isa kawai" Ni dai sanyi naji da har suka fahimceni kuma basu hanani fita ba. Batun shigar da ƙara tuni mun tsorata har mun haƙura .A gurguje na cinye tuwon na sha kunun rabi. Goggo Marka ta goya mun baƙon duniya ta lulluɓemun shi da zani biyu lub_lub. Sallama nayi musu zan fita, ina jiyo sanda Inno take waya da Kaila tana sanar dashi an samu ƙaruwa, jibi ma zan tarkato in komo. Ni dai nayi ficewata, ina tafe Kaila ya kirawo wayata, sai da na samu gefe na rakuɓe sannan na amsa wayar. Assalamu alaikum Abban Sulaiman barka da yamma an wuni lafiya?" A daƙile yace. "Lafiya lau. Yanzu Inno take faɗamin kin haihu, Allah ya raya, dan haka gobe sai ki kamo hanya ki tawo gida ki nutsu." Da sauri na tari numfashinshi dan naji yana shirin kashe wayarshi. Abban Sulaiman dan Allah ka barni zuwa jibi kaji? Wallahi jibi zan dawo, jikin nawa bashi da ƙwari. Ne ina gudun yin tafiya mai nisa." Katseni yayi da cewa. "Ko kuma baki gajiya da kallon tsohon mijinki wannan baƙauyen ɗan uwanki baƙauyiya ba ko, ko so kike ki goma gidan tsohon mijinki? Ai in hakan kikeso yanzu sai in rubuto miki takaddarki ta waya kinga ba ma sai kin dawo ba ko? Sai dai in zo in karɓi ɗana" Ƙit ya datse wayarshi. Zuchiyata ta shiga harbawa da sauri, tarihi na shirin maimaita kanshi. Da ƙyar na saisaita kaina naci gaba da lafiya. Ina shiga cikin gidansu Dauda na tarar ana rikici ko wacce daga cikin matan gidan sunce babu wanda zai iya riƙe Dauda sabida wari yake yi, kowa yace ba za'a shigar mishi da yaron ɗakinshi ba. Yaya Use da Yaya Karime sai basu baki suke yi, amman kowa yaƙi, babu ma wanda yasan na shigo sai jiyo muryarta suka yi cikin sanyi ina cewa In ba'a samu wacce zata riƙe Dauda ba, ina ganin mahaifiyarshi ita tafi cancanta ta kula da abinta. Idan da Dauda zai narke ya zama tsitsotsi ni inason yarona. Narani na roƙeka a karo na barkatai ka bani yarona, ko shari'a ta mallaka mun Dauda. Tunda yaronnan bashi da lafiya a bani kayana" Kowa na tsakar gidan suka zuba mun idanu. Yaya Use da tasan ni kaina a dofane nake a gidan Kaila tace. "Baki da hankaline Tani, in kika ɗauki Dauda a cikin irin wannan halin kiyi yaya dashi, kina da kuɗin da zaki yi mishi maganine ko yaya, sannan kin tambayi mijinki yace miki zai iya riƙe agola ne?" Yawu na haɗiye nasan tabbas Kaila bazai yarda Dauda ya zauna a gidanshi dindindin ba. Amman a matsayina na uwa ina ganin ban kyauta ma yaron ba in na barshi a cikin irin wannan halin na ciwo. Gashi da dukkan halamu inda za'a barshi ya zauna ai mishi jinyar ma babu. Gani nake kamar in na barshi mutuwa zaiyi, kuma alhakin mutuwarshi gani nake kamar a kaina zai rayata, tunda nice uwarshi, kuma hausawa sunce Inna nafi uba ko da uban sarkine" "Can dasu gada zomo ya jiyo kiɗan farauta. Gara ma ka bata ɗanta taje ta kula dashi. Dan ba mahaukaciya bace ta yayeni da zan shigar da Dauda ɗakina yana tsaye yana ɓirɓishin tsutsotsi, ɗiwa na gudana" Cewar Ta maulidi kenan. Tana magana tana fari da idanuwa. Iya mai Fura tace. "Ni gashi ba ƙarfi ba balle ince ni a bani. Nima kula dani akeyi" Shi kuwa gogan duk wannan maganar bai ce komai ba, yana tsaye sai hunhuna yake yi. Na tuno ranar da aka ƙwace Dauda a hannuna yana tsumman goyo a wannan tsakar gidan. Yau gamu a tsakar gidan dai ina shirin karɓar ɗana bayan tarbiyarshi ta samu tawaya ga halin jinya da yake ciki a sakamakon rashin mahaifiyarshi a kusa. Ire_ iren waɗannan dalilinne ke sa iyaye su kasance ma yaransu a matsayin madoraga, ko in ce kendir mai ƙone kanshi dan ya haske wasu. Cikin buyagi Narani ya finciko Dauda ya dire shi a gaban Yaya Use yace. "Gashi nan ku je dashi, tunda taji zata zame mai biyu a ɗaya ( 2 in 1) Amman ta sani muddin tasa ƙafa ta fita da Dauda daga cikin ahalinshi, to yafita kenan har abada. In Dauda ya gwamutsa sunanshi da sunana ko inkiyar ahalina Allah ya isa ban yafe ba. Aurenki in banda bala'i babu abinda ya haifarmun mai farar ƙafa kawai, tunda na haifi Dauda asarori su kai ta bibiyar rayuwata kuje ko na huta" Hannun Dauda na kama a raunace shi kuma kuka ya fashe dashi, daga ni har Yaya Use kuka muke yi. Yaya Karime me ce idanunta a soye, sai mamakin Narani da irin hukuncin daya zartar mai zafi take yi. Ni kuwa ɗana na riƙe nace. Tawo mu tafi Dauda in sha Allah ni Tani Naroro Shanono zan tsaya ma a rayuwarka, zan zame ma tsayayyar uwa." Juyawa muka yi zamu fita, idanuna ya rufe bana ji bana gani." "Tani ki bar yaronnan a gidan mahaifinshi ina jiye miki kar Dauda ya zama sanadin mutuwar aurenki. Kinsan furucin da Baffa yayi. Kaila bazai yarda ya riƙe Dauda ba" Cewar Yaya Use da take ƙoƙarin farkar dani, dan a tunaninta na saki layi. Ni kaina zuchiyata cike take tab cikin taraddadin me kaje kaxo. Sai dai ina roƙon Allah yai mun mafita ya kareni daga sharrin Kaila" Dauda yace. "Iyata dan Allah kar ki barni, ni zan biki." Murmushi nayi na share hawayena, wani irin ƙarfin guiwane ya zo mun. Fuu na fice a cikin gidan riƙe da Dauda a hannun dama na. Ban nufi gida ba. Wajen maganin gargajiya na nufa, ban ko bi ta kan su Yaya Use ba. Bayan na sa Dauda a layi, sai da na keɓe kaina na ragema zuchiyata nauyi. Nayi kuka kamar bazan dena ba. Sai da nayi ma'ishina sannan na fito daga ciyayin dana ɓuya na dawo kan layi. Sai wajajen magriba muka samu shiga ɗakin maganin. Cikin ikon Allah jaririn dake bayana tunda na goyashi yake bacci, sai dai yana ɗan motsi lokaci zuwa lokaci. Malam Mamuda Maƙeri ya zame ma Dauda wandonshi ya duddubashi. Sai toshe hancinshi yake yi da tsumma. Bayan ya gama dubashi ya mayar mishi da wandon nashi. "Ciwonshi mai girmane kuma yana buƙatar kuɗi da jajircewa wajan bin ƙa'idar shan magani. Zan baku na sha da shafawa kamar na kimanin wata ɗaya. In maganin ya ƙare sai ku dawo." Har ƙasa na zube ina godiya, cikin rauni nace. Malam meye abun sadaka to?" Murmushi yayi yace. "Hala yau shine karonki na farko na zuwa karɓar magani ko?" Tsurewa nayi, cikin dibibicewa nace. E hakane, yau ne ranar farko Malam " "To shi yasa. Ai ko ƙwandala bana karɓa har sai marar lafiya ya gama shan magani, in ya warke sai in yanka abinda za'a bani. In kuma bai samu waraka ba bana cin sisin kobo. Amman sau ɗaya na taɓa bada magani ba'a samu waraka ba. Shima ajaline ya cin mishi. Shekarata hamsin ina aikin ceto" Wani sanyi naji a raina sosai. Godiya nayi mishi na fito. Muna tafe raɓe_raɓe da Dauda, duk inda muka wuce sai wari buu, ga kudade sai bibiyarmu suke yi. Baƙon duniya sai lokacin ya saki wani irin kuka mai zafi, inaji yai ta canyarawa. Abun hawa muka hau muka nufi gida. A ƙofar gida naga su Inno harda Baffa sun yi cirko_cirko. Yaya Use tana hangoni tace. "Baffa ai ga Tani nan zuwa ita da Daudan" Ina isowa Baffa ya ɗaga sandarshi ya rabɗamun ita a goshina, ji kake gab. Take wajan ya fashe jini ya soma wanke mun fuskata, jini har cikin ƙwayar idandunana. Kuka na fashe dashi kawai, ina jiran me Baffa zaice. Cikin ɗaga murya yace." "Wallahi muddin ki kai sake akan Dauda auranki ya mutu a karo na biyar. Kwarankwatsa Tani tsine miki zanyi kibi duniya, ba za ki yi albarka ba tunda kin kasa faranta mun raina. Ke ba ma zaki tafi da Dauda ko ina ba. Kai Muttaƙa ka kama hannun yaronnan kai da junaidu, Ige ta raka ku." Ni dai ina dafe da kaina sai kuka nake yi, hannuna rike da Dauda. Ige ce tace. "Naroro ni gaskiya ina ganin kabar ma yarinyar nan ɗanta tai mishi jinya. Ala bashi in ya warke sarai sai ta dawo dashi gidan ubanshi. Ke Tani karma ki sanar ma Kaila cewar riƙon Dauda zaki yi sam. Ki faɗa mishi jinya kika tawo dashi ki yi mishi, yay haƙuri da zaran ya warke shikenan, sai ki dawo dashi. Ni da kaina zan mayar dashi. Junaidu Yusufu, Muttaƙa, me kuka ce ko ba gaskiya ba?" Akan hakan duk su kai na'am Inno ta jawo hannuna muka shiga ciki yarare_yarare jini na bina. Sai lokacin na samu ɗan kuzari har nayo wanka da ruwa mai zafin gaske, kafin in fito daga wankan goshina ya kumbura yai suntun, kaina dan ciwo kamar zai dare gida biyu. A tsakar gida na tadda Inno ta tuɓe Dauda zata yi mishi wanka. Sai toshe hancinta take faman yi, tsutsotsi sai yawo suke ɗaiɗaiku a gefe_da_gefen cinyarshi. Kasa tafiya nayi har sai da Baba Marka taje. "Ki shigo daga ciki sanyi na kaɗaki da ɗanyan jiki" Sannan na shiga ciki na sake kaya, aka bani tuwo naci, sai bacci ya shiga yanko mun. Amman tunanin yadda zamu yi da Kaila in yayi tozali da Dauda tuni ya yakice mun baccin. Nan kuma na harba duniyar tunani. Su Inno suka yi tafiyarsu zuwa gidan biki. Ni kuwa maƙota sai abkin shigowa yi mun barka su ke yi. Dauda yana ɗakin yaran gidan a kwance, Baba Marka ce ta kaishi tace ya kwanta acan, dan duk matan da suka shigo barka sai sun tambaya abune ya mace a ɗakin ne yaketa busa wari. Ni a karan kan kin kaina warin isata yake yi, nima kenan uwa, ballantana kuma su Baba marka. Allah sarki rayuwa Allah ka kawo mun sauyi na alkhairi a cikin rayuwata, kasa goben yarana tayi kyau, a wajensu kawai nake fatan samun salama. Sune kaɗai zasu ji ƙaina su sani Murmushi. JOS KWATA TA YAMMA DA BAUCHI: GIDAN KAILA: Anty Maryam ce ƙanwar mahaifiyar Hajiyayye ta tusota a gaba dab magriba suka shigo gidan. Idanun Hajiyayye yayi luɓu_luɓu da halama anci kuka an ƙoshi, rannan nata a mugun murtuke. Shigowarsu tayi dai_dai da fitowar Bilkisa daga cikin turakar Kaila. Taci wani irin uban kwalliyar da ba mijinta Kaila kaɗai bane zai gwaɗa. Duk wani mai idanu muddin ya gani tabbas yasan anba kyau hakkinshi ta hanyar ƙara ƙawatashi da kayan ƙawa. Sanye take cikin gajeren baƙin wando iyakarshi guiwarta. Sai wata riga ɓaka ɗamammiya mai hannu ɗaya. Gashinnan yasha gyaran Amarci sai sheƙi yake yi, babu ko ɗankwali a kanta, da baƙin ribbon ta tubke sumar tata. Ba wani gashi gareta can ba, tana dai da nayin kwalliya, da yake ta gyarashi tsab sai yayi mata mugun kyau. Fuskarta tasha janbaki da hoda, sai ƙamshi kawai take. Hatta tsakar gidan ya cika tab da ƙamshin turaren wutan da aka sa Shamwila ta bunka a ɗakin Kaila. ( Turaren wuta ne na matan aure, wanda ake kunnawa da yamma domin jawo hankalin da nutsuwar mai gida. Matan Kanuri suna saka wannan haɗin turaren in suka kintati dai_dai lokacin dawowar mai gida sai su kunna. Da zaran mai gida ya shigo gida da gajiya ko ɓacin rai. Yana shaƙar wannan ƙamshin sai yaji wata iriyar nutsuwa na gangaromai. Hakanne yake sa miji ko a ina aka ɓata mishi rai Allah _Allah yake yi ya dawo gida dan ya samu nutsuwa. Ga masu buƙatar wannan turare sui mun magana) Cikin yanga Bilkisa ta dubesu tace. "Sannunku da zuwa, Maman Samira kin dawo?" Wata uwar harara Hajiyayye ta sakar mata kamar idanunta zasu faɗo ta ja tsaki. Murmushin cusa haushi Bilkisa ta sakar mata. Anty Maryam ce ta amsa ma Bilkisa gaisuwarta tana ƙarema shigarta kallo." "Shamwila" Ta kira Shamwila da ɗan ƙarfi. Da sauri ta fito daga kitchen ɗin. "Anty gani" "Ki kai plate da cokali ɗakin Gwanda, in kin kai sai ki rufo ƙofar ki same ni a ɗakina" Tana idasa faɗa ta shige ciki, ta bar Hajiyayye da sakakken baki. Motsi wannan Hajiyayye ta kasa yi. Yanayin Bilkisa ya firgitata ainun. Bilkisa tafi ƙarfinta tako ta ina, in ma gasa tace zata yi da'ita ta'ina zata soma? Duk inda take jin tana da buɗewar ido. Bilkisa ita nata idon tsabar yagewa ɗayan ya haɗe da ɗayan. Da jan ƙafa Hajiyayye ta nufi ɗakinta da ko rufewa bata yi ba. Anty Maryam tace. "Hiye irin matar da Kaila ya auro kenan ƴar boko maras kunya? Danƙari Hajiyayye akwai gagarumin aiki babba a gabanki. Domin kishi da macen data fi ƙarfinka aikine ja. Amman abinda zan faɗa miki shine kar ma ki sake ku sake hayaniya da Kaila har ta kai ki da dawowa gida. Mijin da yake da irin wannan Amaryar taku ko ya rabu daku duka kune da asara. Ni dai fatana Allah yasa kafin Babanku ya iso muji labari mai kyau" Hajiyayye tana zaune sai jijjiga kawai take ta dunƙule hannunta ɗaya tana nausan tafin hannunta dashi. Chaji kawai kanta yake ɗauka. Tunani take ta wacce hanya zata fitar da Bilkisa a gidan, dan in ita Hajiyayyen bata fitar da'ita ba. To zahiri ita zata fitar da'ita. Ita Shanono ba'a sata a lissafi dan bata ma san ciwon kanta ba, a cewar Hajiyayye wacce tayi zurfi cikin zancan zuchi. "Ita Shamwilar da aka aika turaka da'ita tazo ne a saman gara koko yaya?" "Ni ban sanma tsinannu ba. Nima yanda kika ganta haka nima na ganta. Anty Maryam amman kinga irin shigar da Amaryar kwana ɗaya tayi kuwa?" Anty Maryam tayi dariya tace. "Na gani sarai kuwa. Ke dai ki kwantar da hankalinki ki nutsu ki zaƙulo salo_salon kissa da hilatar miji ki ƙara akan yaƙin ki da Uwargidanku, dan wannan yaƙin shine asalin yaƙi, kinsan wannan kam sai dai ku fafata dan sai inda ƙarfinta ya ƙare. Amman ki kiyaye abinda zai taɓa igiyar aurenki, kinji dai furucin mahaifinki kunsanshi da zafi dai akan irin waɗannan maganganun. Rabi kina gani da mijin ya sakota ta dawo gida, da duka mahaifinku ya rakata har ɗakinta, wallahi ki kiyaye kema dan sunan gyatumarmu ne dake da kin yaba ma aya zaƙinta." Suna cikin wannan tattaunawa suka jiyo Sallamar malam Tsaiha mahaifi ga Hajiyayye. Ita da kanta ta fita tayo mishi iso har ciki. Rannan nashi a murtuke, bayan ya zauna ne yayi shiru kamar mai tunani har na tsawon minti biyu. Daga bisani kuma yace. "To da ƙyar da siɗin goshi mijinki ya aminta ya dawo dake ɗakin ki. A hakannma sabida darajarmu ne. Yace tunda ya bijiro da batun aurennan baki sake barinshi yayi bacci ba. Kiji fa Maryam har sau biyu tana fasama bawan Allah wayarshi salula. Sabida kawai ƙazamin kishi, ko haka taga iyayenta suna yi ohon mata. Ni gidana ko kara na ajjiye ai cikin iyayenta ba wacce ta isa ta tsallake wannan karar gabanta gaɗi. Wallahi in baki yi wasa ba sai in miki baki tunda baki da mutunci, so kike ki mayar dani dattijon banza ake ganina a matsayin wanda ya gaza wajan baku tarbiyya? Jibi abinda Rabi ta aikata itama fa. Kinci sa'a ke uwatace wallahi da sai na dakaki a cikin ɗakinnan tunda baki da hankali. Ke baki rasa ci ba, baki rasa sha ba, baki rasa suturaba da an taɓo ku ku dawo mana gida, alhalin iyayenki duk sun rasa abinda ke baki rasa ba a naki gidan mijin. Matar Bahaushe kenan, ire_irenku ke sa adadin yawan zawarawa yake sake hauhawa a ƙasar Hausa, da gangan ake ɗaura mana laifin kacokam, ai in ɓera da sata daddawa da warinta. in zaki bi mijinki ki bi mijinki, kin ganni nan aure zan ƙaro ni kaina nan da sati biyu masu zuwa, kuma yarinyace bata shige sa'arki ba. Yaushe za'aita zama da tsofaffin guzuma bayan Allah ya bamu damar da zamu more rayuwarmu." Ta inda mahaifin Hajiyayye ya shiga ba ta nan yake shiga ba. Shi ba kuɗi ba, sana'ar tashi ba wata ta kawo makudan kuɗi ba amman yana maganar cikace mata ta huɗu. Matanshi uku, yara kuwa sunfi ashirin, shagon siyar da gwanjo na yara yake dashi a kasuwar gwanjo dake katako. Yanayin sana'ar tasu hawa da sauka ne. Haka su Hajiyayye suka taso babu yabo babu fallasa, abincin da zasu ci wani sa'in sau biyu kacal yake iya ciyar da iyalanshi, na ukun sai dai iyayen su yi buga bugarsu a ƙuƙuta aci. Ko makaranta yaran da dama iyayensu mata su suka ɗau ɗawainiyar makarantar yaran nasu. Matsalolin yau daban na gobe daban. Amman a hakan yake neman yayo ƙarin Aure da ƙaramar yarinya sa'ar Hajiyayye. Mahaifin Hajiyayye yana ɗaya daga cikin mazan ƙabilar Hausa masu cisgunawa matansu da yaransu. Dalilina kuwa shine, ƙarfin samunshi bai wuce na mata ɗaya da ɗan yara ƙalilan ba. Kuma shima yasan da haka, amman dake babu sunnar da Hausawa suka fi ɗabbakawa sama data ƙarin aure a hayayyafa dan manzon Allah yai alfahari dasu ranar ƙiyama. Fahimtarsu ce ba dai_dai ba. Domin babu a inda akace a haifi yaran iska, a kasa basu tarbiyyar islama kuma ayi tunanin wai wannan yaron zai zama abun alfahiri ranar ƙiyama. Ai ko ku da kuke iyayenshi ba za kuy aifahari dashi ba. Sannan babu a inda akace sai an auri mata biyu, uku, huɗu dole, akwai mazan da auren ma ya sauka a kansu baki ɗayanshi. In kana da halin ɗaukar nauyin lalurorin mata huɗu da yaransu, kuma kana da lafiyar jiki da zaka dinga iya biyan buƙatunsu, kana da dukiyar da zaka ɗauki nauyin karatu da tarbiyyar yaranka, zaka kwatanta adalci a tsakaninsu. Alh ai baka da matsala sai kayi mata huɗu abinka. Gargadi muddin kasan baka da wannan halin to maganin kar ayi kar a soma, ko dan gudun haifar ƴaƴan iska masu addabar anguwa da sace_sace da harkar daba, fyaɗe, da sauran gurɓatattun abubbuwa. In kunne ya ji jikinmu ya tsira. Haka mahaifin Hajiyayye yay mata tas, sai kukan baƙin ciki take yi. Tafiya su kay suka barta a cikin damuwa da tashin hankali. Rana zafi inuwa ƙuna. Gida ba daɗi, iyayenta haƙuri su ke yi da Babansu. Gidan Auren ma babu daɗi Kaila ya ƙaro samfurin rashin mutunci. Tana zaune dirshan a tsakiyar ɗakinta ta jiyo dirin shigowar lifan ɗin Kaila. Da harara tabishi ta labule ba dan tana ganinshi ba. A cikin kunnuwanta take jiyo oyoyon da Kaila ke ma Bilkisa, itama tana mishi oyoyon cikin muryar kirsa irin tamu ta mata. Yatsa Hajiyayye ta ciza. Tana ta jiran shigowar Kaila yau zai shigo, gobe ne, ko jibi. Har bayan isha bata jiyoshi ba. Ba shiri ta miƙe da cikinta a gaba ta nufi turakar Kaila. Kaila: Shi kuma Kaila a dai_dai wannan lokacin yana zaune Bilkisa na bashi abinci a baki. Sai washe mata baki yake yi. Yana shigowa gidan ta jashi bayan gidan ɗakinshi, dama tasa Shamwila ta haɗa mai ruwan wanka. Yana fitowa ya wuce masallaci, bai shigo ba sai da akayi isha. "Amman Ɗanyan gwal yarinyar ta iya abinci babu laifi. Ni tunda nake ban ma taɓa cin soyayyar taliya ba, ga kazar ta ɗau maggi da tafarnuwa." Murmushi kawai tayi mishi tace. "Nima da na ci abincin na yaba mata. Kaga bani da wata fargaba ko ran girgikina in na samu aikin kwana, Shamwila zata yi maka duk abinda ya dace, ba tare da na shiga hakkin abokan zamana na ɗaura musu hakkin da ba nasu ba." Dariya yayi yace. " Ƙwarai ma da gaske, Shamwila za tai mun komai da komai daya dace. Da kike maganar ɗaura hakki, ai Shanono ce kaɗai zata iya yarda tayi wannan aiki ko ba ranar kwananta ba. Hajiyayye ai baza ta taɓa yarda ma tayi ba. Wannan da kike ganinta ƙwayar boris ce zafi gareta fa sosai." "E babu shakka an zauna ana kwance mun zani a gaban kishiya. Tur da kai Kaila wallahi . " Suka jiyo saukar muryar Hajiyayye a kansu, sai jijjiga take faman yi, basu ji shigowar tata ba ma. Kaila yace "Zaki fita a ɗakinnan ko sai na turaki gidan tsoho kin je kin ɗan ja koriyar miya ne? Nifa shi yasa naso a barki a gida, ko nima na huta amman mahaifinki ya dinga mun magiya darajarshi na duba har kika ganki a tsaye a kanmu" Hajiyayye tsabar kunya sai taji kamar ƙasa ta tsage ta faɗa. Masu iya magana na cewa, in baki yasan me zai furta, bai san me za'a mayar mishi ba. Jibi yanda Kaila ya tsinkata a gaban kishiya yana jifanta da kalaman da zasu zubar mata da mutuncinta. Cikin borin kunya ta ɗaura hannunta a bakinta ta shiga yi mishi ele. "Woooo woooo wooo kaji kunya Kaila kaji kunya. Yarinyar da na yi imani sai da ka gama zakuɗa hannunka cikin ramar kayi kwaɗo kafin ka kawota cikin gidan kamar yadda nima kayi mi...." A mugun fusace Kaila ya dakatar da'ita da cewa. "Ƙarashe kalmar da kike son fesarwa dai_dai yake da saki Hajiyayye. Baki da hankali ne, ni zaki ci ma mutunci a gaban iyalina?"........✍🏻 NA FADO DAGA BENE.... NA ZARCE RIJIYA HAKKIN MALLAKAR BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI GAWURTATTU UKU 8 _*AMMA ARAB!AMMA ARAB!!AMMA ARAB!!!*_ _kai daga jin sunan kasan sunan ya amsa sunansa,AMMA ARAB ta kawo muku wani supplement na gyaran jiki mai sanya daɗi da ƙamshi AMMA ARAB gidan ƙamshi_ *MUSUK* *MADARAR TURARE* *KAJIJI* *ROT* *SANDAL* *HUMFUR* *SANDAL FLASK* *SANDAL WUD* *AALUT* *GAF-GAF* *JANNAMI* *ƘWALAKCA* *MAHAHABSUFYAN* *WANNAN SHINE GRP ƊINA NA WHATSAPP,KI ANTAYO SABODA KADA AYI BABU KE* 👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻 https://chat.whatsapp.com/BrUXmBHnDN6KUJYnkBDT7S *ADDRESS👇🏻👇🏻👇🏻* Zaria road kwankwasiyya sabon gari dangwauro house number 224 *AƘWAI WANI SUPPLEMENTA NA GYARAN JIKI DA TAZO MUKU DASHI KE DA KANKI IDAN KIKA YI ZAKISAN EH LALLAI ZAKI GIGITA ME GIDA,KINSAN MAZA SAI DA ƘAMSHI DUK MATAR DA BATA SAYI WANNAN SUPPLEMENT ƊIN BA TO AN BARTA A BAYA* *AƘWAI BABBAN MAGANI NA INFECTION,WANDA ZAI DAWO MIKI DA MARTABARKI NA ƳA MACE,ZAI CIKO MIKI DA NI'IMARKI KI KOMA ƳAR GATAN MEGIDA* *AƘWAI BABBAR KAMBASA,TA TURARA KAYA HAJIYA KI BUƊE BAKIN ALJIHU KI JIƘO DA ƘAMSHI,KINA ZAMA AN SAN KIN ISA MACE HAJIYA DON AMMA ARAB TA SHARA SOSAI WAJEN KAWO MUKU KAYAN GYARA NA MATA* *AƘWAI SABULAN GYARAN JIKI SUNE KAMAR* *MULATO SOAP* *FACE CREAM* *FACE SOAP* *MULATO WHITENING LOTION* *HAIR GROW OIL* *HAIR GROW CREAM* *KAR-KAR OIL* *MINT LEAVE OIL* *ANTI PIMPUS SOAP* *AƘWAI SABULUN NANKARWA* sannan ina harkar👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻 *ABIN BUKI* *ABINCIN OFFICE* *SNACK* KAMARSU👇🏻👇🏻 *WAINAR MASA* *SINASIR* *MEAT PIE* *CINCIN ƊAN LAUSHI* *CUP CAKE* DA DAI SAURANSU. AMMA ARAB GIDAN GYARAN AURE😄👏🏻 Hatta inifom mijin Sabira ne ya ɗinga musu, da basa zuwa ko ina sai gararamba a unguwa. Haka zalika shi ya sanyasu a islamiyya irin ta cikin anguwa, duk sati suna tafiya da nera hamsin, shima wannan ko da Kaila yaga suna zuwa bai ce dani komai ba, nima ban tanka mishi ba. Ajjiyar zuchiya na sauke na dubi Sabira a karo na barkatai nace. To zan bar miki su, zan haɗo inifom ɗinsu Sani zai kawo miki. Zaki sha bari_bari kenan bakin ki sai yayi tsini ashe kafin in dawo. Dariya tayi tace. "Su Mustapha da Umar fa da kike ganinsu wallahi sun fi Shafi'i da Sulaiman rigima, Sani shi bai da yawan ƙiriniya magana ma bata isheshi ba. Kullum a cikin raba dambe nake." Hmm suma ko da yaushe aikin Kenan." Mun jima muna tattaunawa kafin muka fita domun ɗora girkin rana. Ƴan Wudil kam har sun fito tsab zasu koma, ƴan Akwanga suma ina ji suna cewa da sun yi azahar zasu tafi. Sallama nayi ma ƴan Wudil, muka shiga hidimar abincin rana. Girkin dangin Amarya daban Sabira tayi shi. Tuwon shinkafa miyar ganye tayi musu da kaji. Ita tayi komai da komai, kuma ta ɗauka ta kai musu. Bata jima ba ta fito. Ƴan Akwanga suna cin abinci suma suka kama gabansu, harda Baba Rammai dan an bogo waya an yi musu haihuwa. Sabira da Hindatu ne suka yi wanke wanke da gyaran gidan. Fes suka wanke tsakar gidan yayi kyau sosai. Misalin huɗun yamma muna tsakar gidan ina ɗaura sanwar miyar dare. Sai ga dangin Amarya su biyu, sun sa Amarya a tsakiya. Suna zuwa in da muke suka tsaya. "Bayin Allah muna neman ɗakin uwar gidan gidanne, zamu kai amarya bisa doron al'ada." Sabira ce tayi musu jagora zuwa ɗakina ta nuna musu taburma. Ni kuma na kirawo Hajiyayye da Hindatu, tare muka shiga ɗakin, na shiga na same su sai yamutse fuska suke yi, ba shakka zarni ne ya ishesu. Bayan an yi ƴan gaishe_gaishe wata farar mata tace. "Wacece uwar gidanne a cikinku?" Hindatu ce ta nuna ni tana dariyar ƙeta, ta nuna Hajiyayye a matsayin ta tsakiya. Baki suka sake su kansu, ƙila sun yi tunanin mai aikin gidan Kaila ce ni, dan sun gagganni face_face ina shan uban aiki kamar jakka tun zuwansu." "To uwar gida kece babba ga Bilkisa mun kawota domun ku gana, ba Domin mun kawo muku amanarta ba, amanarta na hannun wanda ya rabota da garinta da ahalinta. Bilkisa ki buɗe fuskarki abokan zamanki su ganki ki gansu" Bilkisa tana saye da wata lafaya mai adon duwatsu faca_faca hannu tasa tayi baya da mayafin. Wallahi bani ba hatta Hajiyayye da take jin ita shahararriyace sai da ta ƙware. Bilkisa gaskiya tana cikin sahun kyawawan matan hausa fulani, uwa uba gata da haske sosai, ga iya kwalliya da zabin kalar daya dace da launin fatarta. "Ina yininku Anty da Anty?" Wani ƙwallon kishi na haɗiye nace. Lafiya lau Amarya Bilkisa ya baƙunta?" Murmushi kawai tayi mun bata ce komai ba. Iyakar abinda ya faru kenan, sai shaida mana cewar yanzu zasu tafi da suka yi. Fatan sauka lafiya nayi musu Hajiyayye dai in kun tanka ku masu karatu to itama ta tanka, tunda Bilkisa ta buɗe fuskarta Hajiyayye ta daskare a zaune. Ana cikin haka Kaila yayo sallama ya shigo, sai faman dariya yake yi, yana doro. "Anty Zinaru baku wuce ba ashe?" Sai wani dariya yake yi harda wani sin_sin da kai. Ita wacce ya kira da Zinaru tace. "Munkaila yanzu zamu tafi, ka kula da Bilkisa sosai kar ka manta da sharaɗin da Mahaifinta ya gindayama tun kafin ma tafiyarku ma tayi nisa. Bayan kwana bakwai zata ci gaba da zuwa aikinta, an yi magana an gama mata komai aikin kawai zata soma zuwa." Dariya yayi yace. "Babu ai komai Anty Zinaru ni dama ƴar bokon naso shi yasa na biyota kuma na aminta da komai. Zuwanta cikin rayuwata aikhairine mai girma, gidan zai ɗau saiti sosai, nifa yanzu ne na san nayi auren kece raini. Ina godiya sosai da karramawa" Nan su kai mana sallama suka fice, ni maza sun dena bani mamaki tuni. Hajiyayye ce tayi kasaƙe tana kwasar ruwan mamakin Kaila. Fitar Amarya da ƴan uwanta ke da wuya Hajiyayye ta miƙe tsaye tace. "Aikin banza aikin wofi ni Kaila zai wulaƙanta sabida ya auro ƴar boko, wallahi zaman lafiyar Kaila da kilakin daya auro ya ƙare. Fuuu ta fice kamar kububuwa, Hindatu ta bi bayanta tana faɗin. "Allah ya kyauta, wannan cin fuska dame yai kama ne ni ƴasu?" Sabira ta dubeni, nima ita nake kallo, murmushi nayi mata kawai muka koma bakin aikin mu, amman zuchiyata a cushe take ainun. Zuwa yamma gidan babu kowa sai mu mazauna gidan, yara suna gidan Sabira ta haɗe kansu dasu Mustapha sun tafi, Hauwa tana bayana. Ina kan yin shanyar kayan Hauwa dana ɗan ɗauraye sai ga Kaila ya shigo gidan, kici_kici da manyan ledoji yana shirin wucewa ɗakin Amarya. Sannu da shigowa *Ango* Jin na kirayeshi da Ango yasa ya washe mun bakinshi har kunne. "Sannu Shanono da hidima da jama'a fa" Murmushi nayi mishi, Hajiyayye tace. "Inason yin magana da kai Kaila kafin ka shiga ɗakin Baturiya" Dubanta yayi yana nazartarta kafin yayi wani malalacin murmushi wanda ni nasan na muguntace. "To yau dai kwanan Amaryane baki da hurumin da zaki ce dole sai kin yi magana dani." Yana kaiwa nan ya burma ɗakin Amarya ya rufo ƙofa garam. Numfashi kawai naja, ina gama abunda nake yi na yi alwalar magriba nayi shigewata ɗaki na danna sakata." KAILA: Yana shiga ya tarar da Amarya a harɗe a kan kujera tana kallon tashar Mbc action, ana wani film na soyayya. Baki ya buɗe yana dariya. Itama juyowa tayi ta yi mai murmushi mai burgewa. "Amarya bakya laifi ko kin kashe ɗan masu gida. Ni na ɗauka zan zo in tarar dake akan gado a harɗe kin rufa da mayafi kina jiran in sai bakin ki?" Dariya tayi mai tace. "Siyan baki kuma? Sai kace wadda bata waye ba. Ai ni na ɗauki wannan abun a matsayin ƙauyanci, Shekara guda muna soyayya sai yau kawai in rufe maka fuskata haba mana Ƙyalli " Murmushi yayi haƙiƙa Kaila sai ya ji Bilkisa ta sake burgeshi, irin macen daya jima yana nema kenan. Amma a baya bashi da damar mallakar irinsu, duba da yanayin rashi da yake ciki. Amman a yanzu sai hamdala, sana'arshi dai shine gashin kajin gidan gona, kuma wajan gashin nashi babbane, a rana ya kan siyar da kaji guda ashirin ko sama da haka, banda masu siyan pat_pat irin su cinya, ƙirji, kai da ƙafa da sauransu. Kuma shike kiwata kajin a gidan gonarshi da kanshi, ga kashin kajin da yake siyarwa buhu_buhu. Zama yayi a kusa da'ita yasa hannu ya jawota jikinshi tare da lumshe idandunanshi. Itama idan nata a rufe yake, taushin fatarta da irin ɗumin jikinta yayi daban da na matanshi baki ɗaya. Iya hakan ya fitar dashi daga hayyacinshi sosai. Bilkisa ba tai aune ba taji Kaila yai ma bakinta riƙon alawar yara. Abunka da wayayyar mace tuni itama ta fara mayar mishi da nata martanin, cikin wani irin salo mai gigitarwa. Kaila kusan suman zaune ya kusan yi yanda yaji Bilkisa na wasa da harshenta a cikin bakinshi. Kota ina a jikinta ƙamshine har bakinta, hatta numfashi in ta fitar ƙamshi yake korowa. Wannan masoya sun jima suna shaƙar ɗumin juna, dana bisani Kaila ya zare bakinshi a nata ya zuba mata idanunshi da suka narke dan jaraba irin tasu ta maza musamman ma sabon ango. "Ɗanyan gwal. Barka da shigowa cikin rayuwata da fatan zaki kula dani fiye da irin kulawar da kika bani a baya? Ki ɗaukeni tamkar jariri sabuwar haihuwa kinga kuwa yana buƙatar kulawa mai yawan gaske. Ɗan wannan zaman da nayi dake a yanzu ya sake dulmiyani cikin soyayyarki. Mata ma suna suka tara ashe?, bari in fito fili in fyeɗe miki biri har wutsiya. Tunda nake ban taɓa shan yawu mai ɗanɗanon naki ba, haka ban taɓa jin fata mai nagartar taki ba, ga ɗumi, madallah da samun ki a matsayin abokiyar rayuwata." Murmushi Bilkisa tayi tace. "Amman Gwanda ni gaskiya bazan iya shiga bayan gidan tsakar gida ba, ni tunda nake ban taɓa amfani da bayan gidan gargajiya ba. Kuma kamar ni Gwanda sai kawai a ganni na fito zan je wanka? Ina gaskiya bazan iyaba wallahi, su Anty Zinaru ma sunyi magana, ni ina ganin zan yima Dady magana kawai ya kama mun haya kusa da asibiti kawai, daman hakan yaso, amman ganin ka fi sha'awar haɗe mu waje gudane yasa na tausheshi har ya haƙura" Zama Kaila ya gyara yace. "Kin fi ƙarfin wannan bayan gidan ai Ɗanyan gwal. Ki kwantar da hankalinki zan sa a yanka miki banɗaki a cikin uwar ɗakin ki, sai dai bazai kasance babba ba sai kiyi haƙuri kafin in ƙarashe ginina, ke zan fara kaiwa gidan ki zaɓi in da yayi miki. Amman kafin azo a soma aikin bayan gidan sai ki yi amfani da nawa na cikin turakata, ni kaɗai nake amfani dashi dama, zan yi gaggawar ƙarashe sabon gida, wannan da muke ciki ma inaga a kasuwa zan sa shi, kuɗin sai in ƙundume a sabon gidan, wannan sabon gidan dama dake ya dace, da ace tun farko na tuno da batun sai da wannan tsohon gidan, da yanzu ma muna sabon gida." Jin za'a tayar da salla ne yasa Kaila ya miƙe cikin kasala. "Ɗanyan gwal bari in je sallah kinji har za'a shiga Masallaci. Ga keyn turaka zaki iya komawarki can, waɗannan ledojin ki tafi dasu" Yana gama faɗar haka ya ajjiye mata keyn turaka ya fice. Da Hajiyayye yaci karo a tsakar gida, bangazarta yayi, yayi ficewarshi yana faɗin. "Aikin banza aikik wofi duk jarabarki ke baki isa kin hanani shan man Amarya ba" Nan ya barta a tsaye tana cizon yatsanta, dan data ganshi hanya ta tare mishi. Bayan sallar magriba ta kafa ta tsare tana jiran shigowar Kaila domun ta mayar mishi da martanin cizon yatsan da yasa tayi. Shinkafa da miya da nama da latas take ci. Sai taji haf door ɗin ɗakin Amarya yayi kara, juyawar da tayi tayi tazali da Bilkisa cikin wasu fararen riga da wando masu shegen kyau, kanta babu ko kallabi fuskarta sai sheƙi take faman yi. Take numfashin Hajiyayye ya nemi dakatawa, yuu daga ita har Hindatu suka bita da kallon mamaki. Far tayi da idanunta tace. "Barkan ku dai da gida" Ba ta yi maganar domun lallai sai sun bata amsaba, duba da yanayin sigar ta tayi maganar, kuma tana yi ta nufi turakar Kaila. Ɗan mabuɗi tasa ta buɗe ɗakin ta shiga. Hajiyayye bata dawo daga cikin duniyar mamaki da ruɗu ba Amaryar Kaila ta sake fitowa daga turaka ta nufi ɗakinta. "Lallai da gani wannan amarya bata da kunya, har tsakar gida bako kallabi, ace amarya daga kawoki har kin soma nuna isa da turakar miji." Ƙuta Hajiyayye tayi. Bilkisa ta sake fitowa daga ɗakinta da ƙaramin akwatinta ja na aure. Tasa kwaɗo ta datse ɗakin nata tayi shigewarta turaka. Abincin da Hajiyayye ta kasa ƙarashe ci kenan. Ajjiye kwanon tayi ta shige ɗakinta. Hajiyayye: Tunda ta shiga ta kasa zaune ta kasa tsaye. Kishi kawai ke ɗawainiya da zuchiyarta. Bata san sanda ta fashe da kukan baƙin ciki ba. Bata taɓa tunanin Kaila zai ji marmarin yin wani aure nan kusa ba. Domin a tunaninta da kuma abinda Kaila ya faɗa mata a yayin da yake kan karagar sonta cewa yayi. Tani bata iya gamsar da sha'awarshi in ya shigeta baya ko jin alama, sabida yawan haihuwa ta zama fanko maras amfani a gado. Shi yasa yake son yayi auren kece raini, kuma yana sha'awar mace wayayya wacce zata latatashi a shinfiɗa so yake a dinga lasarshi kamar alawa, kuma mai jin turanci da iya gaye yake so. Hajiyayye tayi tunanin itace mace mafi soyuwa a zuchiyar Kaila, ganin tayi dai_dai da irin macen da Kaila ke ra'ayi. Duk da cewar ita iyakarta sakandare ne kawai, amman tana ɗan jin turanci kuma tana iya mayarwa babu laifi, kana ta iya rubutun turanci, kuma tana karance_karancen littafin Hausa. Tun tana gidansu take bama Kaila dukkan kulawar da yake buƙata. Sau biyu Kaila na kwanciya da'ita a wani shagon abokinshi. Ya kuma nuna mata babu wata mace a zata iya kere mata a matsayi. Sai gashi tun kafin aje ko ina ya nuna mata kalarshi. Zama tayi a kujera tana tuno ranar da Kaila ya fara ribatarta ya jata zuwa shagon abokinshi, ranar daya rabata da darajarta kenan. Irin kalaman soyayya da irin alƙawarurrukan da Kaila yai mata a wannan ranar abun ba'a cewa komai. Kuka ta sake fashewa dashi tace. "Kaila ka cuceni. Amman wallahi bazan barka kaci amarcinnan lafiya ba, saina ja maka masifa" Wata zuchiyar tai mata gargadi da cewar. "A'a Hajiyayye kar garin kishi kije zuchiya tasa ki aikata abunda zaki zo kina ɗan daka ce baki aikata ba." Shiru tayi tana nazari. " "Tani ko tana ɗakinta kamar bata ma gidan. To wai wacce iriyar zuchiyace a ƙirjin Tani, ita bata san ciwon kanta bane ko yaya? Na tatama Tani rashin mutunci da cushen baƙin ciki iri_iri. Amman a tsakanina da'ita sai dai tayi mun murmushi kawai. Tana cikin wannan sambatun Kaila ya ɗaga labulen ɗakin nata, ya zuba mata mayaudaran idanunshi yana nazartar yanayinta. "Ni zan shiga daga ciki Hajiyayye babu wata matsala dai ko?" Ai Hajiyayye dama kamar jiranshi take ya dasa aya ta miƙe." "Ai ba sai ka zo kayi mun sallama bane zansan cewar zaka kwana da mace ba. Wanne darene jemage bai gani ba, ƙila itama ka gama shan romon amarcin nata tun daga zauren gidansu, ba girin_girin ba dai tayi mai" Idanun Kaila har ƙanƙancewa su ka yi dan ɓacin rai, ita kanta Hajiyayye data kalleshi sai da tasha jinin jikinta. Amman a zuchiyarta kuma taji sanyi sosai da taga ɓacin rai a shinfiɗe a fuskarshi. Harararshi tayi ta ƙule ƙuryar ɗakinta ta barshi riƙe da labule yana mata kallon mamaki." Dariyar mugunta yayi, bai bi ta kanta ba ya ƙule turaka wajan amaryarshi. A wannan daren Kaila ya tsunduma wata duniya iriyar duniyar da bai taɓa tsintar kanshi a ciki ba. Me yasa? Sabida wannan shine karon farko daya ɓare matarshi ta sunna dal a leda. Hajiyayye ba wai bai sameta a cikakkiyar budurwa bane, ko ɗaya. Sai dai kawai sun gudunar da kwanciyarne babu nutsuwa da kwanciyar hankali a tattare dasu. Kuma kasancewar tasu bata zama mai armashiba domun sun kauce ma shari'a( Ƙalubale a gareku ƴan mata masu miƙa ma saurayi kai tun kafin a shiga daga ciki) Duk wata hadda dake kan Kaila a wannan daren sai da Ɗanyan gwal ta kankare mishi Tani: Bayan nayi sallar isha, sai na shiga tunanin yanda zaman gidannan zai sake yi mun zafi. Amman inason da zaran Allah ya saukeni lafiya in tashi tsaye domun cikar burina. Duk da nasan fitowar burina ka iya haifar da matsaloli masu tarin yawan da ni kaina bansan su ba. Amman gani nake yi muddin naci gaba da rayuwa a haka haƙiƙa baƙin ciki da damuwar gidan Kaila ce zata zame mun ajalina. Kaila ya mayar dani tamkar wata jakkar gidansu. Dangin Baba Rammai babu mai ganina da kima, Hajiyayye wanne irin baƙin cikine bata cusa mun ba, ga Amarya kuma bansan ita da wanne salon tazo ba. Ni duk wannan fafutukar inayi ne domin yarana, bana fatan abinda zai sa in tsallake in barsu, nasan babu mai iya kularmun dasu, ƙarshe gararamba zasu ci gaba dayi a anguwa kawai. Wayata ce tayi ƙara ta katsemun tunanina. Yaya Use ke kirana, nayi mamakin kiran duk da dai dare bai yi sosai ba, goman dare ne. Assalamu alaikum Yaya Use kece da daddarennan haka, Allah yasa dai lafiya?" Dariya Yaya Use tayi daga ɓangarenta tace. "Babu komai. Inno ce tace in sanar miki gobe zamu tafi ashe ba jibin ba. Tace kizo da sassafe, mun samu mota har gida. Lauwali maƙocinmu direban bektira ɗinnan motarshi zamu bi har Shanono in sha Allah. Yayi mana sauƙi sosai, sai ki soma shiri tun yanzu sai da safe" Sallama tayi mun ta datse wayarta babu shiri na miƙe na shiga zaƙulo kaya. Kayan da Habiba Bala ta bani na ciri kala uku na saka a jaka. Sai lokacin na jawo ledar data rarraba mana a wajan taron. Sabulan wanki dana wanka ne a ciki, sai omon wanki, da turaren wuta, da humra, harda turaren ɗaki na fesawa da ƙaton basilin. Murmushi nayi na jinjina kaina lallai Habiba Bala akwaita da kirki. Kayana dana Hauwa na haɗa tsab, na ware mana wanda zamu saka in zamu tafi, a lokacin wani bacci mai nauyi yayi gaba dani, bani na farka ba sai asuba. Fitowa nayi ina hamma gefe_gefen bakina duk yawun bacci, idanuna kuwa cike da kwantsa bana ko iya buɗe idon sosai. Banɗaki na faɗa na kama ruwa na fito. Ina tsakar gida ina alwala Kaila ya fito da sauri ya fita zuwa Masallaci. Ina gama alwalar na shige ɗaki nayi sallah, na fito na hura wuta dan in ɗaura ruwan wanka. Hindatu ma ta fito tana bakin rijiya tana jan ruwa. Kaila ne ya shigo gidan, boll yayi da butar da nayi alwala na barta a kan hanya. Taje ta haɗu da garu ta fashe, da ido nabi butar, sannan na dawo da kallona wajan Kaila Wanda shima ni yake kallo rai a ɗaure, ni kuwa ko a jikina. Ina kwana Kaila, an tashi lafiya, ya kwanan baƙuwa?" Jin na ambaci kwanan baƙuwane yasa Kaila ɗan sakin fuska har ya iya tsayawa muka gaisa. Dama inason in roƙi alfarma, amman ban samu ganinka irin haka ba sai yau" Sai nayi shiru. "Ina jinki mana Shanono ki faɗi abunda kikeson faɗa, na bar ƴar mutane ita kaɗai a ɗaki" Shanono dama zamu je dasu Inno biki. Kuma yau zamu tafi shine nake neman izininka" "Ba Shanono zaku ba, ko bangon duniya zaku je shanono ƙofa a buɗe take, duk inda kike son zuwa ba sai kin tambayeni ba kije abunki" Yana kaiwa nan ya wuce ya barni da sakakken baki. To me Kaila yake nufi dani ne, duk inda nake son zuwa in yi tafiyata ba sai na tambaya ba, sai kace wacce take zaman kanta?" Kai na gyaɗa kawai na juye ruwan wankana a bokiti, a gurguje na ɗan diddirza jikina na watsa ruwa na fito. Hauwa nayi ma wanka na shiryata tsab. Har Yaya Use ta soma kiran wayata. A gurguje na saka kaya na fito da jakar kayana da jakar mata ta zuwa anguwa. Ɗakina na rufe na shiga cikin gidan nai ma Hindatu sallama, na bata sallahun faɗama Hajiyayye in ta fito. Gidan Sabira ma a tsaitsaye na shiga nayi sallama da yaran, na ba Sabira key ɗin ɗakina na nufi gida. Na isa gida na samu har sun shisshiga mota, Baffa yana daga ƙofar shiga gaba dafe da Habu sai faɗa yake yi. "In dai Tani ce kun santa da shauni, Inno shi yasa nace muku aba Lauwali haƙuri ya kaimu gidan nata mu ɗakkota acan." Inno tace. "To Baffa faɗan ya ƙare ga Tanin nan ta iso sai mu tafi, kai kuma Lauwali kayi haƙuri kasan sha'anin lafiya da mata" Shiga motar nayi, Baffa ma ya shiga gidan gaba shi da Habu. Sai da mota ta soma tafiya sannan muka gaggaisa, Baffa yace. "Abokan nawa suna gida, na ɗauka zaki riƙo hannun Inno ƙarama a tafi da'ita." Dariya nayi nace. Suna gida Baffa na barsu, ita kanta Hauwa dan dai babu mai riƙe mun ita ne da har da ita zan bari." Muna tafe munata taɓa hirar ta zumunci. Hakan ya tuno mun lokacin da muka yo ƙaura daga garin kogi zuwa Ibadan, a lokacin mabaratan koji basu fiye samun kuɗi ba, manyan mabarata daga cikinsu suka zauna domun neman mafita irin su Baffa dan Baffa na ɗaya daga cikin manyan mabarata masu ƙarfin iko. Kasancewar daɗewarshi a bara da gogayya da yarika iri_iri. Allah sarki rayuwa, mun sha yawo gari_gari yawon bara, hakanne yasa babu wacce a cikin mu tayi ilimin addini, mun dai samu na sallah a wata makarantar almajirai, muna jin yaruka da dama, domin duk garin da muka je da irin harshensu muke bara, ko da dai ba zamu iya doguwar hira da yaren ba, zamu iya roƙonsu. Kuma waɗanda ba musulmai ba sun fi ƙoƙari wajan bada manyan kuɗi ma mabarata fiye da Musulmai. Sai kaga Alh ya tsaya a ƙatuwar motarshi, mabarata sun rufeshi ana mai bara. Amman bazai wuce ya raba sababbin nera ashirin_ashirin ba, masu ƙoƙarin ciki suke raba hamsin_hamsin. Haka ƙwaƙwalwata tai ta yawo dani a cikin labarina, wani abun inna tuno in yi ƙwal_ƙwal, wani abun inna tuno na yi murmushi, wani kuma babu yabo babu fallasa. Motarmu tai ta lulawa, misalin sha biyun rana muka ɗan dakata a wani ƙauyen da bansan sunanshi ba. Baffa ya sai mana abinci. Shinkafa garau_garau ce ya siya mana akan wani ɗan tallah. An yi mata zubin ɗari_ɗari, kowa ya ɗauki ƙwano ɗaya. Wata rumfa muka nufa anan muka yi zaman dirshan. Hauwa na sakko daga baya, sai da ta ƙoshi sannan na ci abincin na bi da ruwan leda guda ɗaya. Inno tace. "Baffa ni kam zan kama ruwa, kaga Shanono daga nan da tafiya sosai, gara in rage marata, Indo muje ki rakani mu nemi wajan ciyayi haka sai in yi." Ai Inno na faɗin haka duk muka miƙe ko wacce da guntun fitsarinta ga mararta. Wani gida muka samu daga bayan wasu rumfuna, a gidan muka kama ruwan, sannan muka shiga mota, bamu tsaya a ko inaba sai a Shanono. Idanu na lumshe na shiga tuno irin rayuwar auren dana gudanar a shanono, duk su ka dinga dawomin. Tuno da Dauda ɗana ne yasa na ɗan saki ajjiyar zuchiya. Baffa ne ya katse mun tunanina da cewa. "Inno acan gida zamu sauka, jiya ina wajan bara Jafaru ya kirani, nace ya buɗe ɗaki ya ƙyara mana. In yaso ko zuwa yamma ai sai ku kintsa kuje gidan Deluwan ko?" Inno tace. "Tunda ka yanke hukunci ai shikenan Baffa. Amman ni kam ai so samuna daga nan sai gidan Deluwa, ana can anata sha'anin biki ka sani. Tun shekaran jiya ya kamata ace na iso garinnan fa haba Baffa" Da ihu_ihu Baffa yake magana kamar faɗa irin na makafi, sake ƙwalla muryar tashi yayi yace. "Da wannan tulin tsarabar kike son ki je gidan biki, shingin duk abi a sace, bazai yiwu ba. Use nuna mishi hanya kinji mu je unguwar Shakogi." Yaya Use tace. "To Baffa. Lauwali kwana zaka yi, ka miƙe har gaba da ceɗiyar can. Kana yin kwana gidan kenan"........ [10/8, 18:33] Badiat Ibrahim: NA FAƊO DAGA BENE.... NA ZARCE RIJIYA HAKKIN MALLAKAR BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI GAWURTATTU UKU 12 _*AMMA ARAB!AMMA ARAB!!AMMA ARAB!!!*_ _kai daga jin sunan kasan sunan ya amsa sunansa,AMMA ARAB ta kawo muku wani supplement na gyaran jiki mai sanya daɗi da ƙamshi AMMA ARAB gidan ƙamshi_ *MUSUK* *MADARAR TURARE* *KAJIJI* *ROT* *SANDAL* *HUMFUR* *SANDAL FLASK* *SANDAL WUD* *AALUT* *GAF-GAF* *JANNAMI* *ƘWALAKCA* *MAHAHABSUFYAN* *WANNAN SHINE GRP ƊINA NA WHATSAPP,KI ANTAYO SABODA KADA AYI BABU KE* 👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻 https://chat.whatsapp.com/BrUXmBHnDN6KUJYnkBDT7S *ADDRESS👇🏻👇🏻👇🏻* Zaria road kwankwasiyya sabon gari dangwauro house number 224 *AƘWAI WANI SUPPLEMENTA NA GYARAN JIKI DA TAZO MUKU DASHI KE DA KANKI IDAN KIKA YI ZAKISAN EH LALLAI ZAKI GIGITA ME GIDA,KINSAN MAZA SAI DA ƘAMSHI DUK MATAR DA BATA SAYI WANNAN SUPPLEMENT ƊIN BA TO AN BARTA A BAYA* *AƘWAI BABBAN MAGANI NA INFECTION,WANDA ZAI DAWO MIKI DA MARTABARKI NA ƳA MACE,ZAI CIKO MIKI DA NI'IMARKI KI KOMA ƳAR GATAN MEGIDA* *AƘWAI BABBAR KAMBASA,TA TURARA KAYA HAJIYA KI BUƊE BAKIN ALJIHU KI JIƘO DA ƘAMSHI,KINA ZAMA AN SAN KIN ISA MACE HAJIYA DON AMMA ARAB TA SHARA SOSAI WAJEN KAWO MUKU KAYAN GYARA NA MATA* *AƘWAI SABULAN GYARAN JIKI SUNE KAMAR* *MULATO SOAP* *FACE CREAM* *FACE SOAP* *MULATO WHITENING LOTION* *HAIR GROW OIL* *HAIR GROW CREAM* *KAR-KAR OIL* *MINT LEAVE OIL* *ANTI PIMPUS SOAP* *AƘWAI SABULUN NANKARWA* sannan ina harkar👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻 *ABIN BUKI* *ABINCIN OFFICE* *SNACK* KAMARSU👇🏻👇🏻 *WAINAR MASA* *SINASIR* *MEAT PIE* *CINCIN ƊAN LAUSHI* *CUP CAKE* DA DAI SAURANSU. AMMA ARAB GIDAN GYARAN AURE😄👏🏻 "IYALI kake magana, wannan ƴar marasa tarbiyyar itace iyalin? A zafafe take magana cikin rufewar idanu. Bilkisa wacce tunda suke abinsu bata ce komai ba, sai yanzu da taji ana neman taɓa mutuncin iyayenta shine tace "Kul kalmar aibanta iyayena ya sake fitowa daga bakin ki. Dan ko wanda ya haɗamu ni da ke bai isa ya aibanta iyayena ba. Dan sun yi mishi riga da wanda bashi ni da su kayi. Ko ba haka ba Gwanda?" Ta ƙarke maganar cikin rausaya murya. Dariyar mugunta Kaila yayi, yana ganin anzo gaɓar da zai sa Hajiyayye ta fita da ƙafafuwanta." "Ƙwarai kuwa kuwa ɗanyan gwal, Dady ai yayi mun sutura daya bani cikakkiyar buduwa ba ɓari ba. Ba irin matan da samarin sawo ke luguiguitawa ba. Ga mamannan a cikkike gwanin banƙawa. Ni mai zance da Dady sai adda'a ai" "Allah ya isa tsakanina da kai Kaila macuci ka....." Bata ƙarashe zancan ba taga Kaila ya jefa Bilkisa gado yana neman danneta, da mugun gudu ta fita har tana tuntuɓe, tana tsoron ganin tsaraicin Bilkisa. Zuchiyarta sai fat_fat take yi. Kai ta gyaɗa tana jinjinama ƙarfin zuchiyar Tani ita data gansu tsirara ma, kuma ranar kwananta, amman washe gari kamar ma ba'ai komai ba" Nadamar ba ma Kaila jikinta ya shigeta, yau ga Kaila da su ka watse tare shi yake mata shaguɓe kuma abun takaicin shine a gaban kishiya. Ta lura sai ta sassauta kishinta zata kai ga cimma manufarta akan Bilkisa. Amman in ta ga Bilkisan ne sai taji zuchiyarta na ingizata. Sai dai muce da Hajiyayye kash ta bar kari tun ran tubani daga ranar da ta fisge waya a hannun Kaila su kai zage_zage da Bilkisa, daga ranar raini ya shiga tsakaninsu babu sauran ragowar mutunci ( uwayen gida ƙalubale a gareku) Haka dai daren ya kasancema Hajiyayye ko rintsawa ta kasa yi, tana kwance tana ƙirgen silin ɗin ɗakinta. Yayin da Kaila yake jikin matarshi suna aikin samun lada. Haka ta ɓangaren Tani ba ta iya bacci ba a wannan dare. ALLAH YAYI DARE GARI YA WAYE: SHANONO: Tun duku_duku nayi wanka fes. Inno ta kama Dauda ta wankeshi tsab, farin ruwan ciwo sai fitowa yake daga shakirarshi, shi ke haddasa mishi wari mai shiga har maƙogoro. Zuwa karfe taran safe har mun fito, Yaya Use ce za tai mun rakiya zuwa Jos ɗin. Su Inno kuma sai wa'adin da suka yanke ma kansu ya cika zasu dawo gida. Sallama mu kai ma kowa a gidan muka fita. Mashin ne ya kaimu har zuwa bakin titi. Baffa Janaidu bai barmu ba har saida motarmu ta cika dam misalin sha ɗayan rana Sannan ya tafi. Tunda na zauna a motar nan gabana ke faɗuwa domin bansan me zan je gidan in tarar ba ma, bansan ta inda zan yi ma Kaila bayani ya fahimce ni ba. Dauda yana zaune a cinyata, jaririna yana bayan Yaya Use. Sai mutsu_mutsu Dauda yake yi, baya iya zama waje guda, sabida tsutsotsin dake fitowa a shakirarshi suna ci mishi jiki, musamman dana sanya mishi ƙunzugu. Hankalina take ya kuma tashi sai kuka. "Wai meye hakan Tani? Kin tusa yaro a gaba sai aukin kuka kike yi. Kiyi haƙuri kiyi ta mishi adda'a Allah zai bashi lafiya da yardar sa, harma ya zama tarihi. Kaila kuma kafin in koma gida zan same shi mu yi magana, dan zan ɗan miki kwana biyu kafin in koma gida. Baban yara ma bai san ina hanyar dawowa ba." Allah sarki ɗan uwa rabin jiki, ɗan uwa abun wuya. Muna tafe Yaya Use tana ta bani kalma, sai tausata take yi. Sai na ɗan ji dama_dama a raina kaɗan. Fargabata yanzu biyu ce. Na farko Kaila ne, na biyu ciwon Dauda ne. Matsalolina na jingenesu a gefe ba ta su nake yi ba. Domin na yanke ma kaina wani hukunci da nake ganin shi zai fiye mun alkhairi, kuma hakan zai taimaka ƙila Kaila ya amince yaci gaba da zama dani. Motarmu sai gudu take yi. Maza da mata sai hira suke yi. Kowa na kalla sai in ganshi yana dariya, ko in ganshi cikin walwala. Allah sarki walwala ko sai yaushe zata sake kawo min ziyara cikin rayuwata oho. Ƙila ni da walwala munyi hannun riga har abada. Amman ina fatan ƴaƴana su dawo mun da walwala cikin rayuwata. Allah ka bani damar da zan dama har in tsaya akan karatun yarana su zama wani abun. Allah ka dubeni yaran sune kaɗai sanyin idaniyata. Da yamma sakaliya muka iso tashar farar gada, daga nan muka hau abun hawa zuwa gida, ni dai gabana sai faɗuwa yake yi kawai, hankalina duk a tashe yake. Da sallama a bakunanmu muka shiga cikin gidan. "Shiga ciki ke Tani, Bani keyn ɗakin naki mu mu shiga, bai dace ki shiga da Dauda ciki ba. Ya kamata Kaila ya fara sani tukunna." Ɗan mabuɗin na bata ta buɗe, ni kuma na shiga cikin gidan. Hajiyayye tana zaune tana soya miyar tumatur taci uban kwalliya da atampar da Kaila ya ƙwace a wajena ya bata. Lamarin da ya matuƙar bani mamaki kenan,dan ni sai yanzu ma naga kyan atampar. "Me zan gani Umman Sulaiman haihuwa ki kayi kome, naga babu ciki a jikinki? Yaya Use ce ta shigo ciki da fara'a ta dubi Hindatu da take tambayata, hannunta riƙe da jariri tace. "Haihuwa tayi, Shanono na biyu yazo. Sannunku da gida mun same ku lafiya?" Hajiyayye tana juya miya tace. "Ikon Allah wai na kwance ya faɗi. Ai kuwa bamu ji ko labarin haihuwarnan ba, kuma mai gidan shi ya sani?" Yaya Use ta dubi Hajiyayye, sai naga ta kalleni da mamaki, nasan bazai wuce ganin atampar jikin Hajiyayye ba ne. Daurewa tayi tace. "Ya sani, shine ma yace ta dawo ai" "Allah ya raya mace ko Namiji?" Cewar Hajiyayye. "Namiji aka samu, Hauwa an fita daga kan nono" Ta ƙarashe maganar tana yaƙe. Babu wanda yayi yunƙurin tasowa ya ga jaririn balle su ɗaukeshi, komawa ɗakina mu ka yi. "Tani atampar jikin Hajiyayye kamar itace atampar da Inno ta bakinnan cikin bikin Sallah ko?" Yaƙe nayi nace. A'a irinta ce dai, me zai kai kayana jikin kishiya" Ƙuramin idanu tayi tace. "Wallahi itace Tani ɓoye mun zaki yi dai kawai. Amman akan me zaki ɗauka ki bata Inno ce fa ta baki dan tasan baki da wasu kayan fita, dan neman wajan zama shine kika ɗauka kika ba Hajiyayye matar da bata da burin daya wuce taga zubar hawayenki?" Nasan babu wata ƙarya dana isa in yi ma Yaya Use, dan tana da ƙwaƙwa sosai, tun sanda muke yara tana da saurin ɗago abu. Sai kawai na zaɓi faɗa mata gaskiya. "Kusun uwa har lalacewar taki a cikin gidan ta kai kaila ya karɓi kaya a hannunki ya ba matarshi, ke kuma da yake lusarace sai kika bata ko, shi bai siya miki ba, wanda aka baki ya amsa? Bari kiji wallahi sai na sa Hajiyayye ta cire kayannan ta bani. In ma ke ba zaki yi amfani dashi ba, to itama bata isa tayi ba. Uwarmu ce ta nemo ta bamu domin tanason ganinmu muma fes. Wato yafi son yaga matarshi cikin ado, ke kuma ko oho." Shirin fita tayi da sauri na riƙo hannunta tsorona Allah tsorona kar Kaila ya yi zuchiya ya rabu dani, yarana bazan iya barinsu a gidannan ba. Sannan ina tsoron kar rikicin ya taɓa zaman Dauda a gidannan." Kafin in yi magana mu ka jiyo sallama da wata siririyar murya. Amsawa Yaya Use tayi, tare da ba da izinin shigowa. Bilkisa ce ta shigo, tana saye da wasu ƙananun kaya riga da wando na yadi, amman basu kamata ba, sun yi mata kyau, sai da ta cika ɗakinnan da ƙamshinta dam. "Sannunku Anty Tani kun dawo? Maraba" Hannu tasa ta karɓi jaririn dake hannun yaya Use, amman tana ɗaukarshi tayi maza ta miƙa mata shi. "Masha Allah, Allah ya raya shi, dama ina kwance ne a ɗakin gwanda na jiyo shigowarku shine nace bari in zo in yi muku barka, ni zan koma" Nagode sosai Bilkisa, Allah ya saka da Alkhairi" Fita tayi da sauri, nasan hakan na da nasaba da zarni, da kuma warin da Dauda yake yi, da ƙarnin nono da jaririn shima yake yi. Yaya Use nai ma kallon kiyi mun rai. Wucewa tayi fuu zuwa tsakar gida, kai na dafe, na zauna a kusa da Dauda na shiga sauke numfashi. Banaso yaya Use tayi wani abun da zai sake jefa ni a matsala, kuma in aurena ya mutu sune na farko_farko wajan ƙyamatata da ɗaure mun fuska, amman yanzu gashi taje tana son yin rigima da Hajiyayye akan kaya. Kuma nasan rashin kunyar Hajiyayye bana wasa bane. Fitowarta daga ɗaki kenan Yaya Use ta fito. "Hajiyayye mu shiga daga ciki zamu yi magana in babu damuwa" Wani kallon banza Hajiyayye tayi mata dan ta riga da tasan akan abinda tazo. "Nan ma ai ya isa, babu bare a cikin gidan, ba irin gidanku na haya bane, gidan mai gidanmu ne. Yawu Yaya Use ta haɗiye tace. "Tunda haka kika ce ai shikenan. Kayan dake jikinki nake son ki cire mun bakin ki alaikum ki miko su." Cikin gatsali Hajiyayye tace. "In kuma ba haka ba fa?" "Sai in tuɓe ki in ga uban daya isa ya ji dalili dan kutumar ubanki" Ina cikin ɗaki nake jiyo wannan gurmi. Ba shiri na miƙe. Dauda ina zuwa kaji ko? Kar ka fito. Da gudu na fito, na samu Hindatu tazo ta shiga tsakaninsu. "Hindatu ki matsa, ni ba karamin aikina bane in yima Hajiyayye zigidir a tsakar gidannan. Kaya dai ba nata bane kaya na Tani ne. Ya zama dole ta cire ta miƙo su" "Ai Kaila ne ya bani, dan haka in kina son a cire miki kayanku, sai ki jira in yazo sai ya bani umarni amman ba dai ke ba. Kuma ni bazan haɗa kirji dake ba, ni ba fitsarariya bace wacce take yawo kwararo kwararo na bara, dama ance ƴan jagora basu da kamun kai." Abinda nake gudu shi yake shirin faruwa. Bilkisa ce ta fito daga turakar Kaila, ita da wata budurwar farar yarinya sol. Bilkisa ta shige ɗaki ita kuma yarinyar ta soma shanya. Abinda ya ɗaure mun kai gajerun wandon kaila da singiletinshi take shanyawa. To wacece wannan kuma? " Ƙaran marin da naji ne ya dawo dani hayyacina. Hajiyayye na gani dafe da kunci. Hannu Yaya Use tasa ta fincike Hindatu kefe. Dama Yaya Use irin ƙatuwar macece, gata da ƙiba sosai. Kamo Hajiyayye tayi, nayi maza na shiga tsakani. Hajiyayye na ganin haka ta kawo naushi ya sauka a gadon bayana. Wallahi sai da ƴan hangina suka motsa tsabar zafin naushin. Nasan tana sane sarai ta naushe ni. Ni kuma nasan in na barta da Yaya Use abun bazai yi kyau ba, ga ciki a jikinta." Zagi Hajiyayye ta soma narko mana, tana haɗawa da su Inno. Idanun Yaya Use ya rufe, nan kokawa ta kaure a tsakani. Jikake tutur_tutur. Ni da Hindatu muka kasa raba wannan dambarwa, gashi har Yaya Use ta keta ma Hajiyayye riga har nonuwanta sun bayyana. Kuma bakinta bai mutu ba. "Shegiya tsinannu masu baƙin jini. Yaran mabarata ƴan jagora karuwai waɗanda suka saba tambaɗewa" Wannan kalmar yasa Yaya Use ta raɗa Hajiyayye da ƙasa, mazaunanta suka zauna daɓas a ƙasa zaman daɓaro take jini ya ɓalle mata" Bako ɗankwali a kaina haka na fita na kirawo maƙota, a guje suka shigo. Da ƙyar aka ɓanɓare Yaya Use a jikin Hajiyayye, ta cire mata riga da zanin jikinta. Daga ita sai sikel ɗin ciki, nonuwanta gasu a waje duƙwai. Hajiyayye da taga jini na malala a jikinta sai ta shiga murƙususu tana cewa "Nashiga uku ta kashe mun yaro a ciki, shikenan sun kashe mun ɗan cikina, a ciki ta dinga naushina. Na mutu, ku kira mun Kaila" Sabida tsabaragen makirci ba sai Hajiyayye ta sandare ba, ta soma kakkafe idanuwanta. Ita kanta yaya Use hankalinta ya tashi ainun. Kuma tsoro ya kamata. Ni kam dama nasan hukunci saki ya tabbata a kaina. Ba shiri aka kinkimi Hajiyayye sai asibiti, Hindatu ma ta bisu. Duk wannan abun da akeyi Bilkisa bata ko keƙo ba, balle tace kuyi haƙuri. Gida ya cika da mata, sai ba Yaya Use rashin gaskiya akeyi. Danme zata daki mai tsowon ciki, a ciki. Ita kuma sai rantsuwar ai ita sam bata daki cikinta ba take ta afkin yin. Jikina a sanyaye na shiga ɗaki. Sai lokacin na samu zarafin yin kuka. Shikenan aurena ya mutu. Sai da na hanaki amman kika ƙi hanuwa, yanzu wa gari ya waya? Allah kaɗai yasan irin sharrin da Hajiyayye zata yi a wajan Kaila. Ba'ayi abu ba ma ta ƙirƙira tace anyi, kaila ya ci zarafina akai, balle an yin" Yaya Use nan ta shiga zagina tana hargagi. "Dalla rufa mun baki, ni banje da zummar dukanta ba. Amman wallahi bata isa ta zagi iyayenmu in tsaya ina kallonta ba. Kina jin mugayen maganganun da take fesarwa, ni zata nuna ma rashin kunya ina ƴar gajora?" Gani da tayi hankalina ya tashi da yawa ne yasa ta sassauta murya ta shiga lallashina. "Ki fito da maganin Dauda a dafa, zuwa anjima ya soma amfani dashi. Wadannan kayan kuma ki adana." A'a Yaya Use, ki tafi dasu dai." Jakata na buɗe na bata ƙullin magangunan. Tare muka fita, kurfo biyu muka ɗaura, ni na ɗaura sanwar girki ita kuma ta ɗaura ruwan zafi. Sabira ce ta shigo da sallamarta, da alama daga anguwa take" "Maraba lale umman Sulaiman an dawo? Yaya Use ke aka bari da ɗaura ruwan jegon?" Yaya Use tayi yaƙe kawai, dan hankalinta baya tare da'ita. "Tani abunda naji a anguwa gaskiya ne, wai kun haɗu ke da yaya Use kun zauna a ruwan cikin Hajiyayye zaku kasheta? Wai ranga_ranga aka kaita asibiti, ance ma sai an yi mata tiyata" Daga ni har Yaya Use salati muka saka, jikina yana rawa. Wallahi Sabira ba haka zancan yake ba" Nan yaya Use ta labarta mata yadda akayi" "Hmmm da kin sani baki neme ta da faɗa ba. Muguwar makirace. Kuma kinga Tani a dofane take a cikin gidannan, wannan maganar zata iya zama babba sosai ta ɓangaren Baban su Sulaiman dama dangin ita Hajiyayyen, dan na lura yayyenta suna da fitina sosai" Tare muka haɗu mu ka shiga jimami a tsakar gidannan. Sai zuwa can bayan isha sai ga su Sani sun shigo. Sai murnar ganina suke yi, ni kuwa sai dariyar yaƙe nake yi musu. Sallama Sabira tayi mana akan sai gobe zata shigo. Taliya na ɓararraka musu, na baje musu ita a tire. Yaya maza kuje ku ci, Dauda Yayanku yana cikin ɗaki a kwance bai da lafiya, kuje ku ci tare" Shafi'i yace. "Umma dama ba Yaya Sani bane babban yayanmu ba?" Murmushin dole nayi nace. Dauda ya girmi Sani sosai ma, ɗan uwanku ne ni na haifeshi, kuje ku ganshi " Sani yace. "Umma shi Babanshi da ban ko?" Wannan maganar ta daki zuchiyata sosai da sosai, amman haka na kanne nace. E Babanku ba ɗaya ba. Amman duka ni na haifeku" Shafi'i zai sake jefo tambaya, Yaya Use ta koresu. Jikin Yaya Use a sanyaye tace. "Tani je ki watsa ruwa ki fito ki samu kici abinci. In sha Allah sharrin Hajiyayye kanta zai koma. Kuma banyi da niyyar in jefa ki a matsala ba. Asalima nayi ne domin ƙwato miki ƴanci ta yanda gaba ba zasu yi miki milkin mallaka ba, daga ita har Baban Sulaiman ɗin. Amman kiyi haƙuri ƙanwata" zuchiyarta ce ta sake tsinkewa, bance komai ba na je nayo wanka na fito. Hindatu ce ta shigo da sallamarta. Da sauri na isa kusa da'ita. Yaya jikin nata Hindatu dan Allah?" Hindatu ta yi mun wani kallon wulaƙanci tace. "Na baro su an shiga da'ita ɗakin tiyata, sakamakon hallakata da Use ta kusan yi. Ran danginta yayi zafi, dan sun yi rantsuwar baza su yarda ba. Kinsan dai Hajiyayye da gatanta. Kaila ma yana hanyar dawowa gidan yanzu" A nan ta tafi ta barni da wannan. Jikina ya mutu murus, hantar cikina sai kaɗawa take yi. Yaya Use dake zaune da abinci a gabanta, itama tayi kasaƙe ta kasa ƙara sa loma a bakinta. "Tani kiyi haƙuri, da sharri suke neman mu shi yasa, ta Allah ba tasu ba. Mu je ɗaki" Hannuna taja zuwa ciki, yara sai jan Dauda da surutu suke yi. Shi kuma ya takure a kuryar katifa, sai mutsi_mutsu yake yi. "Zauna ki daure kici abinci, jego kike yi kin sani. Dauda tawo muje in maka wanka ko ka samu ƙarfin jikin, sai a shafa maka maganin, ka sha kuma na shan." Hannunshi ta riƙe suka fita. Shafi'i ya rufe hancinshi yace. "Umma Dauda wari yake yi kamar yayi kashin wando" Carab Amina tace. "Ni shi yasa ma naƙi zama a kusa dashi" Ni dai ina zaune jigum na rasa abinda yake yi mun daɗi a rayuwata, nasan ba lalle bane in kwana da igiyar aure a kaina. Ina ganin rayuwa fitintinu daga wannan sai in faɗa wannan, ya Allah kafi ni sanin abinda ke jawo wannan matsalar kai mun zaɓin alkhairi, in Kaila ya sake ni Allah kai mun mafita, bani da kowa sai kai ya Allah. Ita kuma Hajiyayye sharrin da take nema na dashi Allah ka mayar mata abinta. Duk wannan magana a zuchiyata nake yi. Ga abinci a gabana na kasa ci sam. A inda su Yaya Use suka fita suka barni a haka suka dawo suka same ni." "Kun yi sallar isha ne?" Sani yace. "Mun yi Mama. Mama amman ba'a katifarmu Dauda zai kwana ba ko?" Yaya Use ta dubeni, kana ta dubi Sani tace. "Anan zai kwanta ɗan uwanku ne fa Sani, wanka ne" Baki Sani ya turo gaba yace. "Wallahi wani abune a jikinshi yake wari sosai, mu gaskiya bazai kwanta mana a katifa ba. Zata yi magana na katseta da cewa. "A kusa dani zai kwanta, katifar ai ba zata isheku ba." Shine fa su kai shiru, da ƙyar Yaya Use ta dinga rarrashina sannan na samu na tuttura abincin. Ina zaune cikin zulumi na jiyo tsaiwar lifan ɗin Kaila a ƙofar gida. Tun daga ƙofar gida ina jiyoshi yana ta faman jaraba, kamar tare da Isa abokinshi yake. "Shanono, Shanono zo nan?" Na jiyo muryarshi a cikin zauren, a zabure na miƙe, Yaya Use ta ce. "Jira bari in je in mishi bayani na fahimta tukunna" Tana kaiwa nan ta fita da Hijabinta a hannu. "Kaila sannunku" Wani irin haɗe rai yayi yace. "Ita shanonon bata ji ina kiranta ne? Ko nima kin fito ki dake ni ne, tunda ba'a koya muku tarbiyya ba? To ina ma aka nutsu da za'a koya muku tarbiyya? A kwararo fa....." "Kai Kaila dakata kaji ko, kul ka kawo wannan zancan. Ni ba sa'arka bace, ka sani ba ƙanwar Tani bace ni, yarta ce ko ince uwarta ce ni. Dan ina da mai shekarunta a gidan miji" Maganganun Kaila yayi dai dai da saukar aradu a kaina. Ji nayi wani abu ya tokare mun maƙoshi, sai lokacin na samu zarafin yin kuka, kukane ya turniƙeni mai ɗacin gaske. Ina jiyo muryar Yaya Use da Kaila a sama. "To Use bari kiji, ni na fiki tashanci wallahi, a kwararrafa na girma, har za'a nuna ma ɗan kwararrafa iya shege ne? Iyayen Hajiyayye sunce ba zasu yarda da abinda ku kai ma ƴarsu ba, zasu shigar da kararku, wallahi babu abinda ya dameni tsuntsun da yaja ruwa shi ruwa kan doka. Kuma ki fice mun daga gida kar ki kuma zuwan mun, tunda zuwan naki ba alkhairi bane." Muryar Isa naji yana faɗin. "Kaila baka kyauta ba. Tun a asibiti ina faɗa maka kabi komai a sannu kaƙi. Kayi haƙuri mana, abinda ya faru ya riga daya faru. Allah ya ƙaddari Yaya Use ita zata kashe yaron dake cikin Hajiyayye. Yaya Use gaskiya kema kin yi kuskure, ai ko Hajiyayye ce ta cakaleki da faɗa kya ɗaga mata ƙafa. To sakamakon dukan cikinta da kika yi, yaron ya mutu mata a ciki, an yi tiyata an ciro mata shi ba rai, kin ganshi a kwali. Danginta sunce bazasu taɓa yarda ba ƙara zasu shigar. Nayi iya yina ma a kashe maganar a gida, wallahi basu yarda ba..............✍🏻 MRS BUKHARI Sai jibi in Allah ya kaimu da rai da lafiya " [10/8, 18:33] Badiat Ibrahim: NA FAƊO DAGA BENE.... NA ZARCE RIJIYA HAKKIN MALLAKAR BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI GAWURTATTU UKU 13 Bansan sanda na fito zauren kamar zautacciya ba. Idanu muka haɗa da Kaila, ya jefe ni da wani kallon tsana. "Nayi ɗan daka ce ban je masallacin ƴan taya na ganku a wajan bara ba. Nayi nadamar wannan haɗuwar tamu na farko. Na auro mata marar tarbiyya ƙazama, wacce babu abinda ta sani sai ƙazanta da haihuwa. Ki faɗama Yarki ta bar mun gidana wallahi in ta ƙara shigo mun gida kotu ce zata raba ni da'ita. Ke kuma zaki ga irin mummunan hukuncin da zan yanke miki akan wannan aika_aikar da kishi ya rufe miki ido kuka yi. Nan gaba ni zaku kashe ba ɗana ba ai" Jikina tsuma yake ta ta yi. Kuka kawai nake yi, Yaya Use kuma ta yi kasaƙe tana kallona, bata ce komai ba tasa hijabinta ta ratsa ta gaban Kaila ta fita, har jikinsu na gugar na juna, dan Kaila ya ƙi mazawa, ita kuma na santa da zuchiya, dan Yaya Use asalin irin halin ƴan jagora gareta, girmane yasa ta yi sanyi. Namiji kuma ya ƙara seseta mata nutsuwa. Da harara Kaila ya bi yaya Use. "Aikin banza aikin hofi. In banda tashanci taya wannan buhun fulawar zata yi faɗa da Hajiyayye ba dai dama shiryawa su ka yi ba. Ke kuma na dawo gareki Shanono." Nuna ni yake yi da ɗan yatsa jikinshi har rawa yake yi, tunda nake ban taɓa ganin Kaila a cikin ɓacin rai makamancin wannan ba. Ba shiri na durƙushe a gabanshi ina kuka. Hannayena na haɗe waje guda cikin sigar ban haƙuri. Amman Wallahi in buɗe baki in yi magana na kasa. Babu irin zagin da Kaila bai yi mun ba, ya buɗe baki yace uwarki Inno da ubanki Nanoma ne kawai baice ba. Amman ya zage su tas. Hakan bai mishi ba yasa ƙafa ya shureni sai da na shige ɗaki. Sai gani a tsakiyar yarana. Kuka na kuma sakawa, ganin ashe kuka suke yi. Hauwa da Balaraba ne kawai basa kuka, amman suma sun yi shiru kamar ruwa ya cinyesu. Ban yi aune ba, Kaila ya shigo da bulala mai baki biyu. Yanda yake dukan Sani da Sulaiman in sun mishi laifi haka ya shiga tabkata. Tsabar zafin duka da gigicewa sai da na kusa tsirara a gaban Isa dake ta faman kokawar ƙwace dorinar a hannun Kaila, amman ya kasa. Amadudu ne ya shigo da gudu da ƙyar suka ɓanɓare kaila a ɗakin. "Zaki ci ubanki ne ƴar iska ƴar mabarata, ni zaku kashe ma ɗa dan baƙin hali." Allah kawai nake ambato har zuwa lokacin ina jin zugin dukan na ratsa jikina. Yarana duk sun takure a lungon katifa sun cure waje guda sai kuka suke yi. Jaririna dana tumirmushe na ɗauka da sauri. Ashe shiɗewa yayi. Sai da na jijjigashi da ƙarfi sannan ya saki wani irin kuka mai karaɗe kunnuwa. Nima na sake sakin kuka. Ina jiyo Bilkisa tana yima Kaila magana akan rashin dacewar dukana da yayi. Sai faɗa yake yi kamar zai ari baki. Yana ta tsinkani a wajan Bilkisa, yana faɗa mata a kwaroro ya tsinceni ya wankeni ya aureni ina bazawara mai aure huɗu, shi kuma yana saurayi fil. Jaririna na duba, sai ajjiyar zuchiya yake yi, nono yake ja a hankali. Su Sani na duba, haƙiƙa ƙaddarar zuwansu duniya ne ya haɗa aurena da Kaila. Dani dashi bamu da tsimi bamu da dabara. Wannan shine karon farko da Kaila ya sa madoki ya dokeni. Ya kan mareni, ko ya sa hannu ya hankaɗeni in faɗi, amman bai taɓa mun mugun duka irin wannan ba. Da ƙyar na lallaɓa na rarrashi yaran su kai shiru. Ina zaune ina karanta wasiƙar jaki har wajajen sha biyun dare, na rasa inda zan tsoma raina, fargabar abinda kaje kazo nake yi. Na san zaman gidannan ya ƙaremun, to yarana fa wazai riƙe mun su? Jibi rayuwar Dauda yadda ta samu giɓi sakamakon rashin uwa majingina a tare dashi. Taya zan tafi in bar gidannan, in tsallake yarana ababen alfaharina? Ina cikin wannan taɗin zuchi wayata tayi kuka Yaya Use ke kira da sauri na ɗaga" "Tani ince dai babu wata matsala data biyo baya ko?" Babu Yaya Use, kiyi haƙuri da abinda Kaila yayi miki" "Hmmm Tani kenan, akwai ranar da zan mayar ma da Kaila wannan cin kashin da yayi mun. Halin da kike ciki shi yafi damuna a yanzu, rintsawa wannan na kasa yi. Baban yara sai tambayata yake yi, jikina yayi sanyi. Ki yarda dani Tani wallahi ban daki Hajiyayye a ciki ba, makircine kawai irin namu na mata. In ce dai ƴan uwanta basu zo ɗaukar fansar dukan ƴar uwarsu da akayi ba ko?" Ajjiyar zuchiya na sauke kana nace. Basu zo ba, amman a cikin zulumi sosai nake Yaya Use, dan ƴan uwanta sunce ba zasu yarda ba. Kuma Yaya Use makircin Hajiyayye yafi da haka wallahi, tayi mun abubbuwan da bansan iyakarsu ba a rayuwa. Amman babu komai, kema nasan kin yi ne domin ki ƙwatar mun ƴanci ba dan ki jefa ni cikin matsala ba. Amman tsorona tsinuwar da Baffa zai mun in ya ji mutuwar aurena a karo na biyar. Dan ina da yaƙinin Kaila sakina zaiyi, Ɗa ba wasa bane yaya Use " Mun jima muna tattaunawar da ba zata fisshemu ba, face mu ɓata bakunanmu da ƙone katin waya kawai. A taƙaice kwana nayi kusan a zaune, kafin asuba jikina ya kumbura yai suntum, ko idona bana iya buɗewa sosai. Kasancewar jikin nawa ɗanyene kuma gashi na daku iya duka. Ko da na tashi yara su yi Sallah, da suka ga fuskata sai tambayata suke yi banda lafiya ne? Ni kuwa shiru nayi musu kawai, Dauda kuma yayi ƙuri abun tausayi. A ranar dai a ɗaki nayi ma Dauda wankan magani a cikin bawo, na shafe mishi takashinshi da man da mai maganin ya bamu. Abun tausayi har wani ajjiyar zuchiya Dauda yake ta saukewa, wari kuwa ya cika ɗakin fam. Ruwan wankan na fita dashi a bawo na zubar. Nan da nan tsakar gidan ta kaure da ɗoyi ina jiyo Amadudu daga ɗaki yana faɗama Hindatu. "Ina bara gurbi ne ya fashe a maƙota kinji wani azabar wari?" Ina jin haka na koma ɗaki da gudu gudun karma su fito su ganni. Ina cikin yima jaririna wanka na jiyo tsaiwar mota a dai_dai windo na, ni dai na jiyo muryar mace tana cewa. "Ga gidannan, mun yi waya da mai gidan yana ciki" Sai muka jiyo sallama a zaure da wata ƙatuwar murya. Ba'a jima ba na jiyo takun tafiyar Kaila. Ni ko gudawa harya taru mun. Yara su kai tsuru_tsuru duk a cikin tsoro muke. Kaila ne ya bankaɗe labulen ɗakina. Ba shiri ya toshe hancinshi harda runtse idanunshi. Tabbas na san warin da Dauda yake yi ya kai ayi fin hakan ma. Nima dake uwace shi yasa ko a jikina. "Ke kam ba dai ƙazanta ba. Ji warin da ɗakinnan yake yi. Ashe dama warin da Ɗanyan gwal tace mun ta jiyo a tsakar gida daga nan yake fitowa? Ko da yake ba abinda ya kawo ni ba kenan. Ƴan sanda na jiranki a waje sai ki goyo ɗanki ku je, nima zan biyo bayanku" Miƙewa tsaye nayi a zabure ina kuka nace. Kaila kayi mun rai dan Allah. Wallahi Allah Yaya Use bata naushi Hajiyayye a ciki ba. Kaga jego nake yi banda lafiya, ka tausaya mun dan Allah kar ka bari su tozarta ni" "Kinga dakata Shanono. Dangin Hajiyayye suna da hakkin yin shari'a daku akan ƴar uwarsu. Dan baki san girman laifin naku bane shi yasa ma har kike wannan magiyar ai. Wuce dallah" Kaila ya hankaɗoni waje, sai gani a zaure kusa da wata ƴar doka macr. Goyona ya miƙo mun na ɗamare shi, jikina fa bai daina kakkarwa ba. Yara suka fito suna kuka. Sai a lokacin kaila ya kula da Dauda. "Shi kuma wannan yaron fa Shanono daga wacce duniyar yake?" Ruɗun sai ya ƙaru mun, in yi magana na kasa. Ƴar doka ce ta katse mana uzuri, wanda ni hakan yayi mun daɗi. "Wannan kuma maganarku ce ta cikin gida. In ta dawo kwa tattauna, muje baiwar Allah " A gaba ƴar dokar nan ta tusani, ina jiyo kukan Hauwa a kunnuwana, dukkansu yaran kuka suke suna ambaton. "Umma Umma" Babbar yar su Hajiyayye na gani a ƙofar gidan, da ƙaninsu Namiji. Haka aka sani a motar ƴan sanda kamar ɓarauniya. Kai tsaye hanyar gidan su Yaya Use muka nufa. Labarin daya sake tunzura tashin hankalina. Damuwata ta ƙaru ainun. Ai kuwa sai gamu a ƙofar gidan su Yaya Use. Basu jima da shiga gidan ba, sai gasu da ita an taso ƙeyarta. Ganin Fatima yasa nace. "Fatima ki je gida ki kula mun da su Sani. Dauda ma yananan, Saudat ta kula da su Inno" Yaya Use sai kuka take yi. Ni ko idanuna a bushe, haka mu kai ta tafiya tiryan tiryan har caji office. Bamu taɓa shiga caji office ba sai yau. Haka aka zube mu bayan kanta. Suka ci gaba da aikinsu. Mu dai muna zaune jigum. "Tani me ya same ki, naga jikin ki yayi ja ja ja halamun shatin bulala kaddai Kaila ne ya dokeki da ɗanyan jego a jikinki? Kinga yanda halittarki ta canja kuwa Tani. Ga wajan da Baffa ya kwaɗa miki sanda ma ya sake aunewa" Kafin in bata amsa Babbar yar su Hajiyayye ta shigo ita da ƙaninsu, Kaila na biye dasu. Ya ɗau wanka sai ƙamshi yake yi, ba ka ce kaila mijina bane. Shi yasa ma bai son a dangantasho dani, na sani yafi karfina nesa ba kusa ba." Zuwansu ne yasa har aka kulamu. Nan yar Hajiyayye ta shiga ba da labari ma ƴan doka. Yaya Use tace. "A'a Ta bizaro kar ki bada wannan shaidar. Wallahi ban naushi Hajiyayye a ciki ba. Tsautsayine da ƙaddara su ka kashe abinda ke cikinta" Buɗar bakin Kaila yace. "Zaki ga tsautsayi ganin idanki. Tsautsayi da ƙaddara su zasu kai ki gidan kaso kema" Yaya Use tai ma Kaila kallon banza tace. "In aka sani a gidan kaso a baka mukullin a jefa a bahar maliya. Kaga in ba zamu tsaya a gaban Ubangiji ba... Wata ƴar sanda ce ta daki teburi tace. "Kuyi mana shiru anan. Ke kina bayan kanta amman bakin ki bai mutu ba ko? Zaki yi bayani ai. Ku taso ko wacce ta rubuta statement, kuma ku sani duk abinda kuka rubuta zai iya zama hujjarku a gaban kotu. " Cikina ne ya juya da naji ta ambaci kotu. Yaya Use tace. "Mu bamu iya rubutu ba" Ƴar sandar nan tace. "Zan dinga rubuta muku kuna faɗa mun. Sannan in kuna da lauya ku neme shi, dan ba ma zamu ba da belin ku ba, dan maganar kisa akeyi. Ita kanta me jegon bama tasan in da kanta yake ba har yanzu. Dan haka ku nemi lauya dan tattare bayananku zamu yi mu miƙa ku kotu." Muryata na rawa na dinga karanto iya abinda na sani. Ƴar sandar nan nata rubutu. Haka na gama Yaya Use tayi nata. Ana cikin haka sai ga Sabira da Baban Mustapha sun shigo. Sabira ƙawa ta gari tana ganina ta fashe da kuka. Baban Mustapha kuma yayi iyakar ƙoƙarinshi a bashi ko da belinane wallahi su ka ƙi. Sha'anin hukumomin ƙasarnan sai adda'a. "Tani ki bani jaririn in tafi dashi, kema ki samu kiji da kanki. Zan dinga bashi madarar yara. Su Sani ma suna gidana, harda yaronki Dauda" "Dauda yaronta? Kut lallai Shanono kin ci ƙarya kin kwana da yunwa, nine ɗan iskan da kike tunanin zam riƙe miki agolan ɗanki, bacin ubanshi yana da rai? Ai ko bashi da rai wallahi bazan riƙe agola ba, kina fitowa daga gidan yari ki tattare ki mayar da yaro gidan ubanshi. In kuma kina son ku koma gidan uban nashi tare ne ai shikenan Shanono" Yana dasa aya ya fice. Baban Mustapha ne ya bishi da sauri. Ni kuma na sunto goyona na ba Sabira. Sabira wayata tana ɗaki, ki duba zaki ga number Habiba Bala a ciki. Ki kirata ki mata bayanin halin da nake ciki dan Allah, nayi imani zata zo yau ɗinnan." "Shikenan Tani, zan kirata. Kuma in Allah ya yarda ba zaku kwana a tsare ba" Keyarmu aka tasa cikin. Zama nayi a ƙasa ina murmushi kawai. Yaya Use tace. "Sai da na faɗa miki kar ki ɗakko Dauda Tani. Kinga yanzu abinda ya faru ko. Yanzu yaya yaronnan za'ayi dashi? In kika ce gidansu Inno zaki mayar dashi bara zai dinga zuwa kema kin sani. Mu ma kuma kinga halin da muke ciki. Amman wacece ita Habiba Balan da kika ce a kirata?" A taƙaice na faɗa mata wacece Habiba Bala. "To Allah ya rufa asiri. Baban yara yana ciki fa. Amman Sabida ɓacin rai ko kallona yaƙi yi. Shi yasa ma baki ganshi ya fito ba. Kuma nasan ko ɗaureni za'ayi igiya tayi saura bazai zo ba........... [10/8, 18:33] Badiat Ibrahim: NA FAƊO DAGA BENE.... NA ZARCE RIJIYA HAKKIN MALLAKAR BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI 15 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 *(Assalamu alaikum masoyana. Haƙiƙatan naji daɗin yanda kuke yaba rubutuna, da yanda nake tafiyar da salon labaraina. Babu abunda zance daku sai kodiya. Yau na tashi sai wasu uziri suka same ni, wanda bazai bani zarafin yin typing akan kari ba. Sai na yanke hukuncin sanar da masu bibiyar rubutuna cewar su yi haƙuri ina da uziri, ba zasu samu jina ba har sai na samu al'amura sun warware mun. Allah cikin ikonshi jim kaɗan da yin wannan maganar, saina soma samun kiraye_kirayen waya daga masoyana. Na kuma dinga cin karo da saƙonninsu wanda in na karanta wani ban isa na karanta wani ba. Duk dai ƙorafinsu shine, in taimaka zasu yi kewar Shanono. Wata tace tana cikin ɗakin jarabawa amman hankalinta na kan wayarta. Duk wanda zai yi ma rubutunka haka ai ba ƙaramin masoyinka bane. Ummu nabeeha, da su Khadija Amarya, Maman Amal, Khadija mai doki, Salma musa, Mamagee, da duk members na cikin zauren NA FAƊO DAGA BENE NA ZARCE RIJIYA. duk sun tashi hankulansu. To ga page 15 na baku. Amman zai iya kaini mako guda kafin in gama uzirin dake gaba. In sha Allah zan dawo da zafi. Nagode)* SHANONO Bance da Hajiyayye komai ba, sai buyagi take yi. Nazo nayi wucewata ko sake kallonta ban yi ba. Ina jiyo Yayarsu tana ƙunduma manyan zagi a tsakar gidan. Sabira ce ta shigo ɗakina da sallama, hannunta riƙe da kwanon abinci. Wayata ce ta shiga ruri a karo na biyu. Yaya Karime ce take kirana, dagawa nayi tare da kara wayar a kunnena. Yaya Karime ina wuni?" Daga cikin wayar akace. "Inno ce Tani. Yaya kun isa gida lafiya dai ko?" Lafiya lau Inno yaya biki?" Dariya tayi tace. "Ƴan uwanki sun so ganin ki. Barinma ƙawarki Shafa, yaranta goma fa yanzu, jin labarin kin shigo Shanono sai gata a gidan biki. Yaya Kaila ya yarda da zaman Dauda ba wata matsala ko?" Tsintar kaina nayi da cewa. E ya yarda Inno." Baki ta washe tace. "To barka ni dama dalilin da yasa na kira inji kenan. in na dawo zan zo in ɗaukeshi. Sai mu yawata dashi muna bara ina nuna ma mutane ciwon nashi. Ba karamin kuɗi zamu samu ba, kinga muma ma samu a jikinshi. In muka tattare kan kuɗin ko asibitin miya barkatai ai sai a kaishi su yi mishi aikin ko Tani?" Idanu na lumshe na tuno lokacin da muka sauka a Bamaina dake jihar jigawa, Inno ta ɗaure mun ƙafata, ta samo jini a kwata ta kwara mun a kafata, haka mu ka fita mu kaita neman kuɗi a haka. Na sha wuya sosai, Amman mun samu kuɗi sosai. Watanmu biyar kullum sai Inno tayi mun haka A'a Inno ai Dauda wata ƙawata da mu kai karatu a Bauchi ta ɗauki nauyin biyan kuɗin aikin nashi. Yanzu haka ma suna Bauchi tare." Inno ta yi sanyi da murya, a maimakon taji daɗi, sai ma ta nuna irin ita tafison ta yawata da Dauda, sabida ba karamin kuɗi zata samu ba. Yaya Karime ce ta karɓi wayarta muka gaisa. Daga ƙarshe su kai mun sallama tare da kashe wayarsu. "Tani ga abinci maza kici. Wai Hauwa tana Shanono ne a wajan su Inno?" Hmm tana can, sai sun dawo zasu kawo mun ita. Nagode da hidima Sabira " farfesun kan saniya ta zuba mun da farar shinkafa. Ai kuwa naci sosai, ta bani magungunana na sha suma. Sannan nace mata. Habiba Bala ta bani kuɗi in koma makarantar islamiyya, da boko. Kuma nima dama na riga na ƙuduri niyyar hakan. Dama jira nake in haihu, zaman rashin karatu bazai fissheni ba Sabira. Kinga kuɗin" Ƙasan fulon da nake kwance na bankaɗa na ciro kuɗin, na ba Sabira a hannunta. Kinga kuɗin ko. Tace abinda ya ragu sai in soma ƴar sana'a domin dogaro da kai. Ke meye shawararki akan hakan? Wacce makaranta kike ganin ya dace in shiga?" Sabira dake riƙe da kuɗin a hannunta tana jujjuyasu tace. "To tunda naga kuɗin da yawa. Inaga a shawarce ki shiga islamiyyar matan aure *UMMAHAT* Ta cikin al'iman. Kinga Mrs Bukhari ma makarantar tayi, nima gashi ita nake zuwa. Jumma'a, asabar, lahadi ne ranakun zuwan, kinga bazai taɓa makarantar bokonki ba. Kuma zaki ji larabci sosai dan ba'a Hausa, ( Allah sarki malama musriyya, malama Hajara, malama Zarah, mun sha larabci) zaki haɗu da mata wayayyu ƴan ƙarya. Nima gaskiya makarantar ta sake gogar dani na sake fahimtar yanda zan mallake Baban Mustapha. Bokon kuma zamu bincika wata makarantar matan aure dake cikin shaƙura, can unguwar rogo ƴan kwaba. Akwai wata makarantar matan aure masu jajayen wando sai mu bincika. Maganar islamiyya kuma zan sa Baban Mustapha yai ma abokinshi magana suna ɗarasawa da munir director ɗin makarantar asamu a saki a aji ɗaya. Kinga in kika gama makarantar nan har zuwa aji shida? To zaki samu takaddar zaria, zaria suke kiran takaddar, da wannan takaddar zaki iya samu admission a jami'a kai tsaye in islamic studys kike son karanta. Mu kinga saura shekara ɗaya mu gama." Ajjiyar zuchiya na sauke nace. To sabira Nagode sosai. Yanzu ni gobennan nake son mu je shaƙuran mu ji yaya za'ayi in samu makarantar nan. Tunda dai kuɗin sun samu, ba'a bori da sanyin jiki." "Ke zaki iya fita ne da wannan kumburarriyar fuskar Tani?" Da sauri nace. Ai ko yanzu kika ce mu je, miƙewa zanyi kawai" Dariya tayi tace. "Goben sai mu je sassafe in Allah ya kaimu. Batun sana'a kuma mu cire sati guda mu yi tunani tukunna. Dubawa zamu yi muga menene a cikin anguwarnan yake da wuyar samu,wanda har sai mun dangana da titi, koma kasuwar ƴan tifa ( new market)? Kayan miya, musamman attarihu da albasa" Na ce mata. "To kinga shikenan sai ki soma zuwa farar gada kina sarosu, shikenan ma muma mun huta. Kuma zaki sha ciniki sosai." "Ɗazu da ki ka yi bacci ai gida na shiga Baban Mustapha ya dawo. Shine yake faɗa mun jiya ya ba Baban Sulaiman aron million biyu, yana son zai ƙareshi abubbuwan da bai yi ba a sabon gidanku. Wai yana son nan da sati ɗaya ku koma sabon gida. Sabida wai Baban Bilkisa ya kirashi wai ita Bilkisan ta yi ma mahaifinta ƙorafin ita wannan gidan ba zata iya rayuwa a cikin shi ba. Shine na ba Baban Mustapha shawarar tunda Baban Sulaiman ɗin siyar da nan gidan da kuke zaiyi, to ya siya kawai tunda dama zai siyar ne dan ya biya shi kuɗinshi. Na taya ki murnar zaki rabu da wannan akurkin, tunda kince a sabon gidan yara ma suna da ɗakinsu. Amman Tani zan yi rashinki da yaran baki ɗaya. Sauƙinta ma zaki soma zuwa makarantar mu" Ni dai kai kawai na gyaɗa ma Sabira, tamkar ya jin ƙosai na kasance wato a rayuwar Kaila. Ada har sai na kori Kaila yake iya zuwa gareji. Ni tunda nake aure, ban taɓa haɗuwa da masoyi irin Kaila ba. Amman jibi yanda komai ya juya, duk a sanadiyyar shigowar Hajiyayye rayuwarmu. Yawu na haɗiye kawai. Mun jima muna tattaunawa ni da Sabira. Na ce mata ta riƙe wannan kuɗin a hannunta tukunna. Sai da aka fito sallar magriba ta tafi. Bayan ta shigo mun da katifuna. Bata jima da fita ba yaran suka shigo. Nan suka dame ni da haya_haya. Bayan isha sai ga Kaila bayan har yaran sun soma bacci. Idanu ya ƙura mun kawai, yana tsaye ƙerere a tsakiyar kwanyata. "Shanono kenan. Yaya akayi kika dawo gida, kuma wa yayi belinki?" Ikon Allah" Iyakar abinda nace dashi kenan. "Shi yaron da kika ɗakko a Shanono kin fitar mun dashi ne ko kuwa yana nan? In kuwa yana nan wallahi daga ke har shi baku isa kun kwana mun a gidaba. Dan bazan iya riƙe agola ba. Kema da kike zaune a gidannan dan yarane fa, amman wallahi da baki isa amsa sunan matar Kaila ba." Kayi haƙuri, Dauda baya nan. Amma zai dawo. Kayi ma Allah kaila ka barni in rayu da Dauda. Yaron yana cikin damuwane. Fyaɗe akayi mishi kuma acan gidan Baban nashi an rasa wanda zai iya kulawa dashi ne. Yaron yana buƙatata. Dan Allah Kaila. Ƙur yayi mun da idanu yace. "Hiye ba shakka Shanono. Acan gidan uban nashi an kasa riƙeshi sai ni ne zan riƙe shi ko? To sai ki zaɓa ai ko riƙe yaronki da kika haifa a Shanono. Ko riƙe su Sani, zaɓi ya rage gareki. Shawara ta rage ga mai shiga rijiya. Bani yaro in mishi huɗuba ni, wani irin tunani irin na jahilan ƙauye" Jiki a sanyaya na miƙo mishi yaronshi, ina tsugunne a wajan ko tausayina zai taɓa zuchiyarshi. Huɗuba yai ma yaron ya miƙo mun yace. "Na sama yaro suna Salis, sunan mahaifin Bilkisa. Kuma bana buƙatar wani taron suna, in sun zo ma nan da wata tara zasu sake zuwa wani taron. To na gaji, kya bari kuma in ji da bikin sunan haihuwar Bilkisa in ta samu ciki, da Hajiyayye " Hannu nasa na karɓi ɗana. Shima ya fice. Mamaki nake yadda za'a sa ma ɗana sunan uban kishiyata sabida mulkin mallaka, ko turawan mulkin mallaka ai ba zasu yi wannan kama karyan ba. Da wannan surkullen tunanin nayi bacci. Nayi bacci a wannan daren sosai, irin baccin da na daɗe banyi irinshi ba. Magungunana akwai masu saka bacci. Washe gari. Tun sassafe nayi duk kaye_kayen daya dace. Ko da na fito tsakar gidan, sai banga buhunhunan tsunmokaranmu ba. Sai Sani ne yake faɗa mun Sabira ce ta fita dashi, su suka rakata gidan wankau ta kai mana kayan. Yarona nayi ma wanka. Ni kuma ko wankan banyi ba, bakina kawai na goge da gawayi da gishir, sai ƙunzugu dana sake. Na ɗan yi kwaskwarima na shirɓina mai mai gurguwa sai walƙiya nake yi. Ina cikin goya Salis Sabira ta shigo. "Oya fito muje, dan ina da islamiyya yau" nera ɗari uku na ba Sani. Ungo ka siyo muku masa kuci. Sai ku fitar da katifar fitsarinku ku sa ruwa. Mu sai mun dawo." Adawo lafiya su kai mun, muna zuwa titi mu ka hau napep na unguwar rogo. "Tani. Ga shawara akan lamarin fitsarin yarannan. Ni ina ganin kinga katifunku dukka ko? Ki siyar dasu gaskiya sai a sai wasu na hannu a bayan masallaci, tunda Habiba Bala ta baki isassun kuɗi. Sai mu sai ledar fitsarin kwance, yarannan kuma Tani ki dinga daurewa kina tashinsu yin fitsari mana. Kayanku na kai gidan wanki, saida na yayyafa musu fiya_fiya kinga kuɗin cizo yanda suke gudu a kayan kuwa? In an wanko sai ki tsince waɗanda suka yayyage dan Allah ki zubar ko ki ba almajirai. Ni bana son kuje sabon gida da kuɗin cizo kuna ɓata bango, maganar gaskiya ran kaila fa ba zai yi daɗi ba. Ga makaranta zaki shiga. Kina zuwa a ƙazance daga malaman har ɗaliban rainaki zasu yi, ki gyara ke ma kiji daɗi mana" To Sabira in sha Allah zan gyara." Haka mu kai ta tafiya har zuwa bakin lungun da zamu ɓulle zuwa cikin makarantar. Muna tafe ina adda'ar Allah yasa su ɗauke ni. Makarantace ta gwamnati babba, mai suna G S S UNGUWAR ROGO. amman sabida yanda sha'anin kasar tamu ta zama ne yasa ake kiran makarantar da suna shaƙura, tsabar yanda malamai suka ƙi tsaiwa su yi aikinsu, sai dai ɗalibai sui ta buga tamaula. Itama gwamnati taƙi tsaiwar daka wajan ware kuɗin malamai. Sai makarantar ta zama gata_gata. Duk fa da haka ɗaliban shaƙura sunfi ɗari, in aka tashi cika titin mota suke haka zaku gansu kamar fari. To ita wannan makaranta ta matan aure a cikin shaƙurar take. Wasu malamai masu zaman kansu ne suke kula da makarantar, sai in ɗaliban shaƙura sun tashi misalin ƙarfe biyun rana. Sai makarantar matan auren a soma biyu da rabi, zuwa ƙarfe biyar a tashi. Kamar yadda wani malami yake yi mana bayani. Form muka yanke nera ɗari biyar, yace in cike ran monday ma zan iya soma zuwa, sai in dawo da fom da fasfo guda biyu. Na biya kuɗin karatu na zango na ɗaya wato S S 1nera goma. Sai jerin littafai daya rubuto mana wanda zamu je bayan banki mu siya, dana rubutu dana katatu. Muka gama komai tas. Kai tsaye sai gamu a bayan banki. A wajan inyamuran bayan banki muka sisiyi littattafan da aka rubuta mana duka, na sai jakar gwanjo, da baƙin sandal shima na gwanjo, da safunana biyu farare tas. A wajan mu ka yanki yadin inifom jan wando, farar riga da farin hijabi. Sabira ta ban shawarin yankan yadin inifom ɗin islamiyya shi kuma mai ruwan toka ne duka, sai baƙar safa da baƙin takalmi, sai ta kaini akai mun fasfo. Dan murna zuchiyata har tsalle take yi. Duk muka sai abunda ya samu. Sha Allah sai muka dira a gidan mai ɗinki, ta mun duk gwajin daya dace. Kuɗinta dubu da ɗari biyu ta cajemu. Muka yi da'ita gobe da yamma Mustapha yazo ya karɓa mana. Bamu muka shigo gida ba sai tara da rabi. A bakin ƙofar gida mu kai sallama da Sabira, dan tayi lattin makaranta tara dai dai suke soma kilas. Ina sa ƙafa ina shiga cikin zauren Kaila ya hankaɗoni waje, na tafi taga_taga amman cikin ikon Allah ban faɗi ba. Sai ji nayi Bilkisa tace. "Baki ji ciwo ba ko umman Sulaiman?" Ashe tare suke taci ado na tada gari, kallon kaila nayi, ashe farin takalminshi na na taka mishi. Gashi hatta kafata ƙurane bajaja balle takalmina. Ajjiyar zuchiya nayi nace. Banji ciwo ba Bilkisa. Kaila kayi haƙuri bansan ka tawo ba. Da sauri na zamo kallabin kaina ina shirin goge mai takalmin dan gujema tozarcinshi ya dakatar dani cikin ɗaga murya. "Kar ki sake ki ba ɗa mun ƙwarlwata. Jeki nagode, kece kina tafe bazar bazar, kamar akuyar ballagaza, kinga kuwa ina akuyar ballagaza zata samu nutsuwa?" Tsaki ya ja ya dubi Bilkisa yace. "Ɗanyan gwal jirani in sako takalmi. Wannan ɗin sai a ba Shamwila ta wanke." Buu ya shige ciki. Bilkisa tace. "Kiyi haƙuri dan Allah ummun Sulaiman. Banji daɗin abinda yayi miki ba" Ɗan dariya nayi mata nace. La ai babu komai. Ai ibadar aure ta ƙunshi abubbuwa masu tarin yawa." Ɗan murmushi tayi itama tace. "Dama Gwanda ne yace yana son ya kaini gidan da yake ginawa in gani. Kinsan ai sati mai zuwa zamu koma sabon gida ko, kuma kinsan ya siyar da wannan gidan ko?" Dariya nayi nace. Na ji dai a bakin ki yanzu. To Allah ya sanya alkairi yasa a koma a sa'a." Ina faɗin haka na shiga ciki tare da cewa da'ita. Sai kun dawo." *KAILA* Yana shiga ya tarar da Shamwila ɗare_ɗare a kan gadonshi tayi goho tana lailaye mishi. Mazaunanta yabi da idanu, sai wani muskutasu take yi suna tanjan_tanjan. A zuwan bata san da shigowar Kaila ba. Kuma tana sane fes. Jikinshi taji ya haɗe da nata. Tayi wata iriyar zaburar da babu inda bai kaɗa ba a jikinta ba. Tsam Kaila ya ƙanƙameta yana kokawa da numfashinshi wanda yake shirin ɗaukewa. Da ƙyar ya lalubi kunnenta yace. "Kaila ne. Kar ki yi ihu nine. Grayan gado kike yi?" Yanda yake jan maganar ba ƙaramin gigita Shamwila yayi ba. Dama Kaila gwanine wajan iya sace zuchiya. Saurin fisge jikinta tayi a nashi, tare da faɗawa kan gadonshi, tana wani irin ja da baya, ga wawan zama da tayi. Ba shiri Kaila ya bita. Ƙaran wayarshi ne ya ankarar dashi aika aikar da yake shirin yi. Babu shiri ya fasa bin Shamwila ba dan hakan yaso ba. Wayarshi ya miƙa mata. "Samun number ki anan. Zan kiraki anjima ki je A 1 ki same ni ko S F C." Da sauri Shamwila ta tiyfa mishi numbernta ta bashi wayar, bayan ta tabbatar hannunsu sun haɗe dana juna. Takalmi ya sake a gurguje ya fice." Kama hanyar filin sukuwa su ka yi anguwar da Kaila yai gini kenan. Unguwar masu kuɗi da amare, unguwa mai tsari marar hayaniya. Da a wajan ake yin polo ( KWALLON DOKI) A lokacin turawa ke yin wasan. Sai masu talle da ke ai kayan sana'arsu. Daga baya gwamnati ta yanka filin, jama'a su kai ta tururuwar saye. Cikin ikon Allah unguwar sai ta shahara, ta zama babu irin unguwar a cikin garin jos, sai dai ta bayan gari can. A wannan unguwa Allah ya hore ma kaila katafaren gida mai ɓarayi uku. Sai ɗakuna falle falle guda uku. Nan ya kai Bilkisa ta dinga yabon gidan. Ɓarayin da yafi ko wanne ɓarayi tsaruwa har da na shi kanshi mai gidan nan Bilkisa ta zaɓa. Masu aiki suna ta gabatar da aikinsu, gobe fenti za'ayi kuma. Suna gamawa da nan Kaila ya kai Bilkisa gida, shi kuma ya wuce wajan sana'arshi cike da zabarin son kiran Shamwila dan jin shanyayyar muryarta. Ai kuwa yana samun sarari ya danƙoro ma Shamwila kira, tare da karonto mata adireshin inda zata same shi. Shamwila a lokacin tana kitchen ta gama abincin rana kenan. Dama a shirye take tsab. A gaban Bilkisa ta tsugguna. "Anty ummanmu ce ta kira ni jikin Babanmu ya tashi, suna bukatar in je zan kai musu kuɗi" Bilkisa ta dubeta ta watsar, dan ita irin masu adankiya ne ( I don't care) Jaka ta ɗakko ta bata dubu biyar. "Gashi kwa ƙara. Amman kar ki daɗe, sabida girkin dare ko? Shi kuma Allah ya bashi lafiya." Da "Ameen" Shamwila ta amsa mata. Tasa kafa ta fice. Sai A1. A harɗe a kan kujera ta samu Kaila sai cika baki da guggurun A1 yake yi, bakinshi duk madara.( Jiki duk madara 🤣🤣) Yana hango Shamwila ya shiga yashe bakinshi, harda wani kashe idanu. Waje ta samu ta zauna. "Barka da hutawa" Baki ya kuma washe mata mata. "Shamwila, Shamwila, kin samu karasowa kinga yanda ki ka yi bala'in kyau kuwa. Zauna da kyau yau ai rana ta ce. Me kike son a kawo miki, gugguru, ko abinci?" Fari tayi da idanunta tace. "Soma gabatar da abinda yasa ka kirani. Dan Ɗanyan gwal taka lokaci ta bani. Abincin darenka na bisa wuyana" Murmushi yayi mai ƙayatarwa, ya kashe mata idanu yace. "Ai sabida tsabar son abincinki da nake yi. Inason da zaran mun koma sabon gida zan sa ki dinga mun girki ko da yaushe. Ko wacce mata tayi girkinta da yaranta, nawa girkin da ban." Ido ta zare tace. "Tayaya hakan zai faru to, alhalin Ɗanyan gwal ce ta ɗaukeni aiki?" Ƙur ya bi tsakiyar fararen dara daran idanunta da mayataccen kallo, mai firgita ƴan mata, da narkar da zuchiyar mata. "Ni zan ƙirƙiri hakan ya faru. Ke dai naki ido Ɗanyan jini." Dariya tayi mai burgewa tace. "Nawa sunan kenan ɗanyan jini? Ina godiya da wannan suna. Amman har yanzu fa banji dalilin zamana a gabanka ba" "Ɗanyan jini. Sonki nake yi har cikin jijiyata. Tun kallon farko da nayi miki na jaraftu. Kuma ni aurenki zanyi, amman sai zuwa nan da shekara ɗaya. Amman zaki zama matata ta bayan fage kin gane yhah?" Yana magana irin na cikakkun ƴan duniya, waɗanda suka ga jiya su ka ga yau." "Taya hakan zata faru, bayan matanka uku, sai dai mu yi sabgarmu a waje ina tsoro gaskiya" Gugguru ya watsa tare da taunawa, kana yace. "Ai kema matar gidance, yanda zan turmushesu a turaka ai kema ya kamata in turmusheki a turaka" Kai ta gyaɗa tace. "Ko in turmusheka ba, ai ni nafi karfin kab matanka" Daga haka suka shiga musayar kalaman da suka shige ka'ida. Kafin su ankara har biyar na yamma ta gota." A zabure ta miƙe. Kaila ya riƙo hannunta ya tafa mata dubu talatin, su kai sallama kowa ya kama gabanshi." SHANONO: Yau haka na wuni cikin farin ciki da nishaɗi, Allah _Allah nake yi monday tayi in soma zuwa makaranta. Ina ta shirye_shiryen makaranta, na zube littattafaina duka a cikin jakata. Yaran kansu suma cikin walwala suke sakamakon walwalar da suka gani tattare dani. Kuma daɗin daɗawar farin cikina shine, waya da nayi da Habiba Bala take sanar dani, zuwa gobe za'a yima Dauda tiyata yana asibiti yana karɓar kulawa ta musamman, ƴar aikinta na kula dashi a asibiti" Sai naji zuchiyata ta yi wasai. Tamkar bana cikin wata matsala. Sani da Shafi'i sai guje_guje suke yi. Allah sarki uwa, farin cikinta da walwalarta shine taga yaranta a cikin nishaɗi, haka suma yaran ganin mahaifiyarsu a cikin walwala na sanya su kazar_kazar. Haka dai yau muka wuni cikin annuri. A tire ɗaya mu ka ci tuwon dare. Bayan sun je sallar isha sun dawo muka kulle ƙofarmu. Dan tun da Hajiyayye ta dawo wuni tayi tana ƙunduma zagi iri_iri, so take in tanka ta jawo ni ta huce haushinta a kaina. Washe gari ma muka tashi zuchiyata fes. Sai dai zuwa sha biyun rana sai ga sammaci an aiko mun daga kotu. Hakanne yai silar mutuwar jikina, sukuku na wuni, sai jan ƙafa nake yi, bansan yanda shari'ar zata kaya ba. Sati biyu alƙali ya yanka mana zamu soma shiga kotu. Shikenan gidan yari za'a aimu kenan ko? Tunda da kisa ake tuhumarmu. Ban ɗaki na shiga naci kuka na na gode Allah. Da yamma Sabira ta shigo ina tsakar gida ina kaɗa miyar kuka. Sai gata da ledar inifom ta kawo mun. Ganin idona yayi jawur ne yasa tace. "Wata matsalar ce ta afku ko me? Ba dai wani abun ya haɗaki da Hajiyayye bane, dan ina jiyo buyaginta ina tsakar gida ina wanke ganye" Hmm daga kotu aka aiko mun sammaci, nan da sati biyu za'a gurfanar damu. Shine jikina duk yayi sanyi, kinsan sharia tamkar mace mai ciki ne, babu wanda yasan me zata haifa, sai abinda Allah ya bata." Dafani Sabira tayi. "Da yardar Allah Alkhairi zamu ji. Tunda dai ba Yaya Use bace ta kashe yaron Hajiyayye ba. Ke dai ki dage da kai kukanki gun ubangiji Allah zai sa a dace. Kin kira Habiba Bala kin sanar mata? A'a zan kirata dai yanzu, so nake in sauke miya." Sabira ita tai ta tausar zuchiyata. Tare da'ita muka kira Habiba Bala a waya. Hankali itama ta kwantar mun. Ta sanar dani cewar jibi zata shigo ita da lauyan da ta ɗaukar mana. Ina kashe wayar sai ga Yaya Use tana kirana. Itama jikinta duk ya mutu. Haka na kwanta cikin zulumi. Ban samu barci ba, gashi zani makaranta. Haka na tashi tun kafin asuba, tsabar zumuɗi. Duk da batun kotu ya ture mun murnar da nake yi. Yara na shirin makaranta, ni kuma ina bakin gawayi ina dumamen tuwo. Sani ne ya fito da katifarsu ya jingina yana kwara mata ruwa. Ya ɗaga butar zai sheƙa ruwan kenan. Ashe kaila ya doso. Ai kuwa yana watsa ruwannan ruwan fitsarin yai tsalle sai a jiki da fuskar Kaila. Ihu ya sake harda cewa. "Wayyo Allah Shanono zata halakani nima"......✍🏻 [10/8, 18:33] Badiat Ibrahim: NA FAƊO DAGA BENE....... NA ZARCE RIJIYA HAKKIN MALLAKAR BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI GAWURTATTU UKU 16 Assalamu alaikum. Allah ya nufeni na dawo. Nagode da jumurin jira. A ɗan hutun dana tafi naga zahirin irin soyayyar da kuke ma wannan littafin. Ina godiya. *(Domin soyayyarku gareni da rubutuna. Akwai promo da zanyi muku na turarukan wuta da humra setine mai bala'in kyau. Kunsan dai Kanuri mune turaren wuta da humra, namu da banne, ke kanki in kika yi amfani da waɗannan set zaki gode mun. Akan farashin 10k kacal na bar muku farashin promo domin ku. Mutum ishirin kaɗai zan cire suke da damar mallakar wannan setin mai sanyin daɗi. Kuma iyakar ƴan paid group ɗina ne kaɗai zasu samu wannan garaɓasar. Ku yi hanzari duk mai buƙata ta kasance a cikin mutum ashirin da zan ɗiba.)* Da sauri na miƙe tsaye kamar ba ni bace na wuni sukuku. Baki na riƙe kawai ina kallon Kaila. A guje Bilkisa da Hajiyayye suka fito. Hajiyayye tana ganin abinda ya faru taja wani irin dogon tsaki tayi komawarta ɗaki. Dama ɗakin nata cike yake da ƴan uwanta. Kamar yinwataccen zaki haka Kaila ya dira a wuyan Sani ya far mishi da mahaukacin duka, tamkar yana dukan ƙato. Dama haka yake musu irin wannan dukan. Bilkisa ta isa a guje ita da Hindatu, amman sun kasa ƙwatar Sani a hannun kaila. Har ya fashe mishi ɗan bakin nashi. Tsam na miƙe na koma ɗaki. Yaran suka biyoni ɗuu. Zaunar dasu nayi, ni ko na kasa zaune na kasa tsaye, ina jiyo Sani yana kirana. "Umma ki ceceni zai kasheni, wayyo Baba wallahi bansan kana zuwa bane, wayyyooo" Kuka na fashe dashi, har muryar Sani ta dashe. Baban Mustapha ne ya burmo gidan namu. Ina jiyo muryarshi tun daga zaure. Shine ya ƙwaci Sani a hannun Kaila. Da mugun gudu Sani ya shigo bakinshi na zubar da jini da yawu, gefen idanshi ya kumbura. Ƙanƙameni yayi tsam sai cusa kanshi yake a jikina. Hannuna na ɗaura a saman kanshi ina shafawa. Ya'isa kayi shiru kaji Yaya. Babu komai, ai mahaifinka ne hukunci yayi maka. Muje in wanke maka bakinka, ku ci dumame ku kama hanyar makaranta, kayi shiru ya'isa" Da ƙyar a ranar nasa Sani ya yarda ya tafi makaranta, bakin shi ma ya aune sosai. Ko bayan tafiyar su Sani makaranta na jima a ɗaki ni kaina bansan zaman me nake yi ba. Ni ba tunani ba, ni bansan adda'ar da zan dinga yi domin kore damuwa da baƙin ciki ba. Habiba Bala ce ta sanyaya mun raina data kira take sanar dani an yi ma Dauda tiyata cikin nasara, amman yana bacci a lokacin. Wani irin farin ciki ne ya sauka a zuchiyata. Kawai na sau ma Habiba Bala kukan farin ciki, sai jero mata godiya nake yi, ita kuma tana ta rarrashina, da haka mu kai sallama. Ina dai zaune, bani na fito ba sai wajajen goman safe. Kiki_kiki na ɗaura miyar dare, tana tafasa na kaɗa. Miyar kuɓewa nayi bushasshiya, Sai na mayar da ruwan wanka kan wutar, na soma yanke farata na, waɗanda suka cika da datti, sunyi baƙiƙƙirin dasu. Tas na yanke farcen ƙafata dana hannuna, na faɗa bayan gida, ina cuɗawa na bi da ruwa na fito. Misalin dayan rana sai ga su Sani sun shigo hajaran majaran sai warin rana suke dokawa." "Umma yinwa" Cewar Shafi'i dama shi kam ba mai jurar yinwa bane sam. Sani da Sulaiman ne dai masu dama dama. Balaraba ita bata zuwa boko, islamiyya kaɗai take zuwa. Abinci na zuba musu su ka ci, dan zumudi ni ko abincin na kasa ci. Ƙarfe biyu bata cika ba na saka inifom ɗina har nayi goyo. Yara suka kalleni suka kwashe da dariya, Sani har yana ƙwarewa. Nima dariyar nayi bance uffan ba. Farin hijabina na saka na rataye jakata. To maza ku yi ku gama mana. Ku je gidan su Mustapha ku yi wasanku, in lokacin islamiyya yayi sai ku je tare. Sani banda zuwa wanka rafi, dan Mustapha ya faɗa mun kana bin yaran gidan Rahilu. Ni zan je makaranta ku yi mun adda'ar samun nasara." Adda'a su kai ta mun. Raina fes na fito zauren, dai_dai Hajiyayye ta rako ƴan uwanta zaure. Turus Hajiyayye tayi kawai tana kallona. Ni ko da ganinsu gabana ya yanke ya faɗi. Dan banso nayo arba da kowa ba. Da sauri na ɗauke kaina, ina rufe ɗakina na jefa ɗan mabuɗin a jakata na fice. Yara su ka bi bayana. Da sallama mu ka shigarma Sabira. Tana ganina ta soma tafa hannaye. "Ga ƴar makaranta, ga ƴar makaranta" Dani da yara duka muka tuntsire da dariya. Sabira baki da dama. Ga yarannan. Sabida in na barsu a gida ba lallai suje islamiyyar ba." Sabira tace. "Yau bana nan na fita, sai da na dawo Abban Mustapha yake faɗa mun irin dukan da Abban Sulaiman yayi ma Sani. Gashi idanunshi sun tara jini." Na ƙwafe wannan dukan sosai a raina. Sosai nake jin zafin dukan, har bana so ayi zancan. Bagarar da hirar nayi ta hanyar juyawa da gudu_gudu. Sai a zaure mu kai sallama na kama hanyar makaranta. Aji ya cika bundin, ni dai bancin ƙarshen aji na samu, mu biyu ne a bincin ni da wata dattijuwa. Mata sai hira suke yi ana tafi. Malami bai shigo ajin ba, shewa kawai kike ji yana tashi. Ni kuma sai kallonsu nake yi, ina mamakin wai yau nice a zaune a aji a karo na biyu. Bayan haihuwa ta takwas, Allah mai iko, Allah ya bani nasarar karatu. Ina cikin tunanin nan sai naji ajin ya yi tsit, ashe malamine ya shigo. "Sababbin zuwan mu su je ajin ƴan B su mayar da form dinsu da fasfo, za'a rubuta sunansu a rijista. Ni dai na taso amman sai harɗewa nake yi. Duk inda na walga kallona mata suke yi kamar wata baƙuwar halitta. Har na fita na jiyo Muryar wata mata na faɗin. "Baiwar Allah kuɗin cizo suna bin hijabinki ta baya" Da sauri na waiga bayan nawa ai kuwa na gansu har uku, yatsana manuniya nasa a baki na dangwalo yawu na kamo kuɗaɗen cizonnan na kashesu a ƙasa. Kab ajin ni suke kallo. Ni kuma ina ɗagowa nabi ayarin mata biyun da suka nufi B likas dan mayar da fom. Muka mayar da fom sunanmu ya shiga rijista. Da darasin lissafi muka soma ( maths) Nan dai na shiga rubutu hannuna na kakkarwa, har wani zufa hannuna ke yi dan tsoro. Abubbuwan dai gasu nan ga kamarsu gani nake tamkar ban taɓa shiga aji ba. Ko malamin turanci daya shigo ni dai ina zaune dunkum kawai. Gashi sai aikin gida suke bamu ( home work) Ni dai kwafewa kawai nake yi, wasu abun dai nakan haɗa in furta kamar mai koyon magana. Ana cikin yin darasin gona, agiric Salis ya soma kuka. "Wacece ɗanta yake kuka? Ta fita waje in ma ta shayar dashi, ko ta rarrasheshi. Ya kamata ku dinga zuwa da mataimaka da zasu dinga kula muku da yaranku, iyakarku dasu ku fita ku basu Mama ko ruwa" Da sauri na fita, dama fitsari nake ji. Sai da na nemi ban ɗakin makaranta, ashe basu da banɗaki sai na malamai, ɗalibai sai dai su shiga maƙota. Nima maƙotan na shiga na soma yo fitsarin. Ina dawowa makaranta ana buga ƙararrawar yin hutu. Gefe na samu na yaye hijabina na dumbulama Salis nono. Yayi maza ya cabka ya shigo tsotso yana sauke ajjiyar zuchiya. hutun minti talatin muka yi. Ina gani mata sai siyayyar ƙwalam suke yi, ni kam inaa. Aji muka koma muka ci gaba da ɗaukar darasi, wallahi ji nayi bana iya fahimta, ƙwaƙwalwata ta toshe sosai. Har ƙwalla sai da na tsiyayar dana tuno ƙoƙarina wajan karatu da naci. Duk abinda ya gagari su Habiba Bala da su Halima Bawa, ni ake kawo ma, har mayya suke ce mun. Dan ina da ƙwaƙwa ko darasi akayi mana komawa ɗaki nake in ta bitar karatunnan, ko kuma in shiga ɗakin karatu na cikin makatanta wanda aka tanada domin ɗaliba, ni dai ku barni da ƙazanta kawai. Kuma ni ban ɗauka abinda nake yi ƙazanta bane, dan a haka na taso na tarar da mahaifana, da yayyena. Amman yau gani a aji bana ko gane komai. Dattijuwar dake gefena ta taɓoni. "Baiwar Allah an tashi fa, bani wuri in wuce" jakata na raruma na matsa mata, nan na shiga kiciniyar goyon Salis, wannan dattijuwar ta dubeni tace. "Wannan goyon ai ɗanyene, kuma zai barki kina fahimtar karatun kuwa?" Ɗan murmushi nayi nace. To zan jaraba dai, amman ban fahimci duk abinda akayi ba ma yau. Ƙila sabida na daɗe rabona da shiga aji " "To ki dinga tawowa da wacce zata dinga miki renon yaron. Ke kuma sai ki nutsa kiyi karatun dan yana da matuƙar mahimmanci sosai. Kuma nan ai makaranta ce duk wanda kika gani koyo yazo yi. Duk abinda ya shige miki ki yi tambaya ko malami ko ɗaliban ilimi. Sai gobe ko?" Godiya nayi mata, muka fita a tare kowa ya kama gabanshi. Inata ta tafe, kwasham_kwasham bani na samu abun hawa ba har sai da na nazo kan babban titin zangon baƙi tukunna, Minti goma ne ya kawo ni bakin layinmu. Da shigata gidan nayi maza na buɗe ƙofata na ƙule bana son kowa ma ya ganni. Kayan makarantar na tuɓe na mayar da kayan gida. Salis yana kwance yana baccinshi rai ɗaya. Da Bilkisa naci karo tana riƙe da ƙatuwar leda. "Umman Sulaiman kin dawo ashe? Nazo har sau biyu baki nan" Yangar maganar Bilkisa burgeni yake yi, harma nake jin kamar tafi kowa iya sarrafa harshe. Duk da naji Habiba Bala ma haka take karya murya. Na dawo yanzu" Na bata amsa. Kaila ne ya nufo mu sai ƙamshi yake yi, cikin ado da kwalliya yake. Yana ganinmu tare ya dubeta yace. "Wai me yake kawo ki wajan Shanono ne Ɗanyan gwal? Ni sai in ga kina shige mata da yawa ai" Da zafin harshe ya fesar da kalamin. Wani mugun kallo ta watso mishi tare da ƙare mai kallon sama da ƙasa. "Kar ka sake ka sake ɗaga mun murya. Ko mun yi da kai duk abinda zan yi sai ka sani ne? Ni fa ko a gida banga uban da ya isa ya takura mun ba." Baki ya sake yana kallon Bilkisa data mugun haɗe ranta, kallona tayi tace. "Kaya ne dama na fitar suna nayi miki ke da Dady na. Mummy ma tace in miki Barka ranar suna ƙanwata zata zo suna. Allah ya raya Dady." Da dariya na karɓi ledar. Kai amman na gode sosai Bilkisa amman babu ma suna kar ki wahalar da me zuwa." "Amman me yasa ba suna?" Ta jefo mun tambayar amman idanunta na kan Kaila wanda ya ƙula ainun. Murmushi nayi nace. Babu kawai dai, haihuwa bata fari ba, taron bikin suna ai sai ku" Baki ta taɓe ta yi wucewarta. Tana shiga cikin gida nima na faɗa ɗakina. Kaila ya bita fuuu zuwa turakarshi. KAILA: Tsabar jaraba har baya iya gani. A hargitse ya shiga ɗakin ya tarar da Bilkisa a tsaye ta riƙe ƙugu. "Ke Bilkisa yanzu dai_ dai kenan a gaban shanono ki dinga nuna ban isa dake ba? Ni fa duk na soma gajiya da lamarin zaman aurennan wallahi. Mu kenan bama kwana biyu cikin jin daɗi. Jiya ina ji ina gani kika hanani kanki a shinfiɗa............... Dakatar dashi tayi da cewa. "Dakata mun, ni ba'a mun faɗa, kuma na gaji da aurenka tafiyata zanyi gidanmu, na gama aurenka kenan. Bansan dama kai ba adali bane a gidanka ba da bazan shigo ba ma" Hanyar fita ta shiga nema. Carab Kaila ya riƙeta ƙam. Shine harda tsugunnawa yana roƙonta tayi haƙuri, da ƙyar ta haƙura, da taga kaila na shirin zubar da hawaye. Amman sai ta shiga fishi dashi. Kiran sallar magriba ne yasa ya fice daga ɗakin jiki a mace. SHANONO. Ina tsakar gida ina jiran ruwan tuwo ya tafasa in zuba talge. Littafin lissafi ne a hannuna ina duba shafin da akayi mana, ina bin misalan ciki a hankali a hankali. Haya_hayar yara ce tasa na rufe littafin na kallesu. Yaya akayi yinwa ko Sulaiman?" "Lefi yayi ma malam shine ya zane shi" Cewar Amina uwar kanzagi kenan. Shi Sulaiman ashe a wuya yake, sai yasa hannu ya shararama Amina mari. Tas naji sauran hannun kaila a fuskar Sulaiman. Yaron ya fashe da kuka ya durƙusa. Tsaki Kaila yayi tare da bin mu da kallo yana muzurai. "Kizo shanono mu yi magana" Jin yace haka sai Hajiyayye ta ɓata rai daga dariyar data gama yi ina ganinta. Nasan tatsuniyar gizo bata wuce ta ƙoƙi, ilai kuwa ina zuwa na same shi a tsaye kamar soja. "Bani kayan da Bilkisa ta baki maza" Suna kan katifa dama. Ɗakkowa nayi na bashi abinsu. "To daga yau sai yau in kika sake tsaiwar minti uku da Bilkisa ranki zai ɓaci. Wallahi Shanono ki fita sabgarta in kina son aurenki ya tsira" Yana kaiwa nan ya fita. Kaila na lura barazanarshi gareni bata wuce ta saki. Domin yasan babu abinda na ƙi jini irin saki. Kuma yasan wahalhalun da na shiga sanadiyyar mutuwar aure. Wannan dalilin ya riƙa yake tsorata duniyata da kalmar saki. Sabida ya lura zaman auren nake so, burina in zauna da daɗi babu daɗi. Kai na girgiza kawai, na fita nayi talge abuna, na ci gaba da duba littafina. "Ni da su Gwamma, oh ni Hajiyayye in da ranka ka sha kallo, an koma makarantar balagaggu, dan miji ya auro kishiya likita." Ni dai hankalina yana kan littafina domin na soma fahimtar yadda abun yake, saura ƙiris in gano bakin zaren. Amman in na kwashe tuwo zan leƙa Sabira ta ɗan ƙara ɗaurani bisa layi. Kafin isha na game tuwo na baje ma yara a faranti, nima na zuba nawa. Sai da naci na yi ƙat, na goge miyar a kaina tas na mayar da ɗankwalina. Sai na miƙe na goya Salis. Yaya ka kula dasu zan je in dubo Sabira. Haka dai kiki_kiki Sabira ta koya mun abinda ya samu, sai taran dare na baro gidan. Duk aikin gida da aka bamu a makaranta sai da mu ka yi tukunna. Ko da na shigo gida yara sun jima da Bacci. Amina harta tsula fitsari tana cikinshi. Salis na sauke a baya a daddafe nima na haye katifar nan nayi kwanciyata. Gaga_gaga dai anata rayuwa a haka, kullum da sabon tashin hankalin da kaila zai sani a ciki, bayan kwana biyu da kawo sammaci. Habiba Bala tazo mana da lauya. A gidan yaya Use mu ka haɗu, acan muka tattauna, yai mana tambaoyi cikin ƙwarewar aiki. Iyakar abinda muka sani muka sanar mishi. Shi kuma ya ɗaura mu a kan matsaya ɗaya. Habiba Bala bata daɗe ba ta koma, sabida Dauda. Ranar dana kwana bakwai da haihuwa da safe ina ɗaki yara duk sun tafi makaranta. Nima aikin gida da malamar Physics ta bamu nake yi, da kuma aikin gida da aka bamu a islamiyya, Baƙaƙen larabci zamu rubuta daga farko zuwa ƙarshe, inata fama na barbaje sai cin rubutu nake yi. Makaranta da daɗi sosai, naji daɗin makarantar islamiyya dana je sosai, gashi muna da yawa ainun, akwai ƴan mata da matan aure, harma da zawarawa. Ga manyan mata ƴan gayu sosai a ajinmu, ko wacce tas da'ita. A bencinmu mu uku ne, dukkanmu muna da goyon yara ƙanana, kuma naci sa'a suma sababbin zuwanne, sai kowa ya sake da kowa dai. Kaila ya ɗago labule ba ko sallama yace. "Ki shirya kaya nan da awa biyu motar ɗiban kaya zata iso. Za'a kwashi kayanku zuwa sabon gida" Kafin in yi magana ya saki labule ya ficewarshi. Ina jiyo dirin lifan ɗinshi." Ba shiri na haɗe littattafan sai gidan Sabira. A falo na sameta tana turarashi da kayan ƙamshi daga Mrs Bukhari. Ko ina tsab sai ƙamshin daɗi. Ka ga mata ƴan lelen miji. Wallahi kya yi Sabira Abban Mustapha yana yabawa kuma yana ba da gudunmawa" Zama nayi a kujerarta, ita kuma ta ajjiye kaskon tace. "Yaya karatun, yanzu na kira Habiba Bala na ji jikin Dauda, mun gama wayar kenan na soma turara gidan sai ga ki" Hmmm yau zamu tashi Sabira. Yanzu ya leƙo ɗakina yake sanar mini. Wai nan da awa ɗaya motar ɗiban kaya zata iso." Waya kawai naga Sabira ta zara, ta yi danne dannenta ta kara a kunne. Jim kaɗan ta soma magana. "Hello Ahmad kana ina yanzu haka? Kaya nake son ka ɗaukar mun daga gida zuwa masallacin ƴan dankali. Wajan masu sai da kaya na hanu.? " Daga wayar ina jiyo Ahmad na cewa. "To Anty motar ma tana ƙofar gidanki, in shigo in ɗebi kayanne?" Da jin haka Sabira ta miƙe tsaye. "Mu je Tani maza bamu da lokaci sosai." Fita mu ka yi, Ahmad ya taimaka mana muka saka katifunnan a mota. Yayi gaba dasu, mu kuma mu ka bi bayanshi a Napep. Da waɗannan katifun guda biyu Sabira ta amsar mun gado 6 by 6. Sai mu ka sai katifu guda biyu a cikin kuɗin da Habiba Bala ta bani. Sabira ta siyamun kafet na hannu mai kyau ja da kuɗinta. Cikin awa guda muka gama siyan komai Ahmad ya dawo damu. Motar mu na tsaiwa motar ɗiban Kaya itama ta tsaya. Kaila ne a gaba a lifan ɗinshi. Kamar bai ganmu ba haka yayi. "Ahmad ga motar nan, ka zuba kayan a ciki. In ka zuba ka shiga ɗakin su Mustapha zaka ga doguwar kujera ka fito da'ita ka haɗa mata." Godiya naso yi, amman Sabira ta doka mun harara ta ja hannuna zuwa ciki. A lokacin me motar kaya da Kaila, da Amadudu sun soma fitar da kaya waje. Sabira ta zazzage tsunmokaranmu tas a ƙasa ta sake zaɓewa, ta cire mana marasa yawa, sauran kam ni kaina nasan babu amfanin da za'ayi dasu. Tsabar sabo da tulin tsunmokine kawai. A buhu ɗaya ta haɗe ma yara kayansu. Ni kuma nawa ta je gidanta sai gata da katuwar jaka. A ciki ta shirya mun kayana. Ta kirawo Ahmad ya fita dasu. Kayana dana Bilkisa su kai gaba. Kayan Hajiyayye da Hindatu kuma sai an dawo. Hajiyayye ta kai wuya kuwa da ita da ƴan uwanta da tayo gayyarsu. Itama Bilkisa ƴan uwanta biyu sun zo jiya daga Zaria, ga me aikinta kuma. Allah sarki, ni ko daga ni sai Sabira, Yaya Use sai dai waya kawai mu ka yi da'ita nake sanar mata. Habiba Bala kuma, dana kirata ɗazu a wajan siyo katifa tace in yi haƙuri sai gobe zata iya shigowa.........✍🏻 *OUM SOOFEEYYER GRAPHIC AND DATA* *INA Marubuta da masu business* *Maza ku hanzarta mun shirya tsaf domin kayatar da ku da graphics kalakala Kuma cikin farashi me sauki* Logo 2d Logo Flyer Invitation card Invitation vedio Save the date card Save the date vedio Book cover Account sticker Makeup Flyer Business Flyer Da dai sauransu Sannan Kuma Ina koyarwa ga duk me bukata cikin sauki 08069638776 *All netwk Data is available* _*AMMA ARAB!AMMA ARAB!!AMMA ARAB!!!*_ _kai daga jin sunan kasan sunan ya amsa sunansa,AMMA ARAB ta kawo muku wani supplement na gyaran jiki mai sanya daɗi da ƙamshi AMMA ARAB gidan ƙamshi_ *MUSUK* *MADARAR TURARE* *KAJIJI* *ROT* *SANDAL* *HUMFUR* *SANDAL FLASK* *SANDAL WUD* *AALUT* *GAF-GAF* *JANNAMI* *ƘWALAKCA* *MAHAHABSUFYAN* *WANNAN SHINE GRP ƊINA NA WHATSAPP,KI ANTAYO SABODA KADA AYI BABU KE* 👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻 https://chat.whatsapp.com/BrUXmBHnDN6KUJYnkBDT7S *ADDRESS👇🏻👇🏻👇🏻* Zaria road kwankwasiyya sabon gari dangwauro house number 224 *AƘWAI WANI SUPPLEMENTA NA GYARAN JIKI DA TAZO MUKU DASHI KE DA KANKI IDAN KIKA YI ZAKISAN EH LALLAI ZAKI GIGITA ME GIDA,KINSAN MAZA SAI DA ƘAMSHI DUK MATAR DA BATA SAYI WANNAN SUPPLEMENT ƊIN BA TO AN BARTA A BAYA* *AƘWAI BABBAN MAGANI NA INFECTION,WANDA ZAI DAWO MIKI DA MARTABARKI NA ƳA MACE,ZAI CIKO MIKI DA NI'IMARKI KI KOMA ƳAR GATAN MEGIDA* *AƘWAI BABBAR KAMBASA,TA TURARA KAYA HAJIYA KI BUƊE BAKIN ALJIHU KI JIƘO DA ƘAMSHI,KINA ZAMA AN SAN KIN ISA MACE HAJIYA DON AMMA ARAB TA SHARA SOSAI WAJEN KAWO MUKU KAYAN GYARA NA MATA* *AƘWAI SABULAN GYARAN JIKI SUNE KAMAR* *MULATO SOAP* *FACE CREAM* *FACE SOAP* *MULATO WHITENING LOTION* *HAIR GROW OIL* *HAIR GROW CREAM* *KAR-KAR OIL* *MINT LEAVE OIL* *ANTI PIMPUS SOAP* *AƘWAI SABULUN NANKARWA* sannan ina harkar👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻 *ABIN BUKI* *ABINCIN OFFICE* *SNACK* KAMARSU👇🏻👇🏻 *WAINAR MASA* *SINASIR* *MEAT PIE* *CINCIN ƊAN LAUSHI* *CUP CAKE* DA DAI SAURANSU. AMMA ARAB GIDAN GYARAN AURE😄👏🏻 [10/8, 18:33] Badiat Ibrahim: NA FAƊO DAGA BENE..... NA ZARCE RIJIYA HAKKIN MALLAKAR BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI GAWURTATTU UKU 17 Ana cikin wannan Gaga_gaga sai ga ƴan makaranta sun dawo. Ganin mu a tsakar gidane yasa suma suka shigo ɗu. Amina ta kusan murjema ƙanwar Hajiyayye ƙafa. Ai kuwa ta lailayo ashariya ta mako mata ta ɗaura da cewa. "Shegiya mai kama da uwarta, dangin ƴan maula, masu kwana a bakin masallaci" Wani zafi naji a zuchiyata, nasan haushi suke ji da abinda ya faru da Yaya Use da Hajiyayye, da kuma haushin an soma tafiya da kayana ita nata gasu nan jibge a tsakar gidan. Ina ganin haka na miƙe dan take takensu so suke a tanka su yi buyagi a tsakar gidannan. Su ja mun sale salin tsiya. Sabira mu soma yi ma maƙota sallama, kafin lokacin tafiyar tamu tayi, yau dai ba zuwa islamiyya sai kuma gobe." Fita mu ka yi a gidan har da yaran. Bilkisa tana ɗakin Kaila ita da ƴan uwanta. Muna fita mu ka samu isa a waje isowarshi kenan da matarshi uwar gidanshi Jamila. Itace muke mutunci, amaryarta kuma ƙawar Hajiyayye ce unguwarsu ma ɗaya. Jamila kece a tafe? Gashi kin zo zamu shiga yawon sallama da maƙota" Ɗan dariya tayi tace. "Ai sai mu je. Da fatan ba ki yi fishi ba. Kin haihu ko barka banzo ba, an muku amarya ma banzo ba" Babu komai. Isa barka da rana" Muka gaisa da Isa tare da mun murnar komawa sabon gida. "Kaila ne yace in soma kai ku can gidan. Ku shiga maƙotan ku fito sai mu wuce in soma ajjiyeku, sai in kwashi sauran matan nashi" Tare da Jamila mu kai ta bin maƙota muna musu sallama. Sai Allah sanya alkairi suke yi mana. Muna fitowa Isa ya figemu a mota sai sabon gida. Kaila ne ya buɗe mana get da sauri, ni naga sai dariya yake yi. Muna haɗa idanu ya gintse dariyar tashi, ya sau get ɗin. Masha Allah gida yayi kyau ya sha fenti mai ruwan ƙasa, ga filin tsakar gida masha Allah. Muna firfitowa Kaila ya soma masifa. "Haba isa dana san haka zaka yi mun ai da ni zan ɗauki motar in je in ɗakkosu. Bilkisa baka ganin baƙine suka zo mata daga Zaria? Da direba ma suke tafe, direban nasu yaje Bauchi ɗakko wani saƙone. Da sai ka bar su Shanono su zama ƙarshe." Isa ya hararashi yace. "Kai dai kaji kunya. Shanonon zan kawo a ƙarshe gidan da tare kuka zaɓi yanda fasalin gidan kuke son ya kasance. Ko ka mance tare kuka dinga zuwa sauke block ne? Duk wani wahalar ginin gidannan da itafa akayi. Dan kawai kayi amarya shikenan sai itace zata zama ƙarshen shiga gidan?" Ni dai ina gefe kamar yajin ƙosai. Yara kuwa guje_gujensu ma suke faman yi a tsakar gidan. Isa ya nuna mana hanyar babban falo, inda shine mahaɗar ko wanne pat na cikin gidan. "Bismillah ku shiga daga ciki, ai kinsan ɗakinki" Sai lokacin Kaila yayi magana yace. "In kin shiga ki jirani a falo in na dawo zan nuna miki ɗakin ki. Kai kuma ka bani keyn mota in ka gama soki burutsun zancan" Fisge keyn motar yayi a hannun me shi. Isa ya koma ɓarayin mai zaman banza ya zauna, suka fita a gidan. Mu kuma muka shiga ciki. Masha Allah, ko ina yaji tayil, ga ƴan kayayyakina a gefe a cikin babban falon, amman banga na bilkisa ba. Kuma duk ƙofofin ɓangarorin uku a rufe suke da ƙwaɗo, dan Jamila sai da ta murɗa ko wacce ƙofa ta ji ta gam. Doguwar kujerar da Sabira ta bani akai muka zauna, jikina kamar an watsa ma kaza gishiri haka nake ji. Sai haɗiɗiyar yawu kawai nake yi. Minti ashirin bayan zuwanmu sai ga Kaila da Isa motarsu ta shigo. Sabira ce ta leƙo take sanar mana. "Gama su nan sun dawo, Amarya a motar da ƴan uwanta suka zo aka kawo su, Abban Sulaiman kuma ya ɗebo Hajiyayye da ƴan uwanta. Ni dai ina zaune jigum, har su Bilkisa da tawagarta suka shigo. Hajiyayye kuma suna wajan motar kaya data shigo yanzu. Ƴan uwanta suka shigo cikin falon da muke, tare da Kaila. Key ya jefo mun cinyata, tare da nuna mun ƙofar ɗakin dake gefe can. Ciki biyu da falo ne ɗakin sai bayan gidu a ko wanne ɗaki in ban manta ba Dan da sunan Amadudu aka yanki ginin ɗakin. Ashe ni zan zauna a ciki. Hajiyayye kuma ya miƙa mata keyn ɗakin da a da nasan turakarshi ne, Bilkisa kuma ya buɗe mata ɗakin da aka gina shi da sunana, ɗaki mai babban falo da ɗakuna har uku, bayan gida biyu, ga kitchen yalwatacce, har kantocin cikin kitchen ɗin ni da kaina na zaɓi samfurin wanda nake so, ashe rabon wata ne. Wannan shine kura da shan bugu gardi da ƙwace kuɗi. Ana cikin haka sai ga Amadudu da Hindatu sun shigo babban falon da sallama. Key ya miƙa ma Amadudu. "Ɗakunan dake tsakar gida, kai da Hindatu sai ku jera kayanku a ciki. Ɗayan yaranku sai su dinga kwana a ciki. Ɗayan kuma Shamwila sai ta dinga kwana a ciki " Gaba mu ka yi abin mu, Jamila ta buɗe ƙofar ɗakin muka shiga. Dukkanmu tsuru_tsuru mu ka yi a tsakar ɗakin muna kallon abun mamaki, ni ko hawaye ne kawai yake gudana a Idanuna tsabar damuwa har wani jiri ne yake ɗibata. Jan fentin mai kaila ya shirɓinamun a ɗakunan nawa babu ko sofane kalar jinin kare ( maron). Ni ɗakin ma tsoro ya bani wallahi, dan tunda uwata ta haife ni ban taɓa ganin fenti mai kalar jinin kare ido da idoba sai yau. Numfashi na ja mai zafi. Sabira ta kawar da tunanina da faɗin. "Kai Tabarakalla masha Allah. Waje yayi kyau. Tani Allah ya sanya alheri, Jamila mu soma shigo da kaya ciki ko, mu kafa mata gado?" A tsaye suka fice suka barni ina kalle kalle. Ɗayan ɗakin ma an toshe ƙofarshi da bulo ga halama nan ana gani. Shi yasa naga wata ƙofar a cikin falon, kuma wannan ɗakin da aka toshe yafi girma, bayan gidan ɗakin kuma yafi kyau. A wannan gidan ɗinma a falo yarana zasu dinga kwana kenan, gashi su Hindatu har nasu yaran sun samu ɗakin kwana, Allah mai iko" Kama musu na yi mu kai ta shigo da kaya. Dake kayan nawa babu yawa cikin ƙanƙanin lokaci muka kammala komai. Durowar dake jikin bangon uwar ɗakina Sabira suka buɗe suna ta jera kayan yara. Ni kuma ina saman turmi ina buga labule da ƙusa dan bani da ƙarfen labule amman mancewa nayi da zan siya na hannu a masallaci. Zama nayi a kujera ina ba Salis Mama. Jamila tace. "Umman Sulaiman me za'a dafa ne ya kamata ace an ɗaura abinci, naga gidan ya soma ɗinkewa da mutane." To Jamila bari in nemi Abban Sulaiman tukunna riƙe mun yaronnan ina zuwa" Kafin ta karɓi yaron sai ga sallamar Bilkisa daga bakin ƙofa. "Umman Sulaiman ki kawo kwano a zuba miki abinci ke da jama'arki" To Bilkisa zan aiko yara su kawo" Komawa nayi na zauna. Sabira ce ta ɗakko wata kwaraɓaɓɓiyar kulata babba ta kira yara ta basu su ka kai. Sai gasu da masa da miyar gyaɗa, harda sinasir, da lemukan roba har katan biyu, da fiya wata leda biyu. Yaran Sabira ta soma cira ma, su kuma sai da su kai sallar la'asar sannan suka zuba mana namu a tare muna ci suna hirarsu har da dariya. Duniya lallai ta nai musu daɗi. Ga ƴan uwan Hajiyayye ma a babban falo sai shewa da surutu suke yi. Dan Hajiyayye tayo gayya sosai, har maƙotanmu ƙawayenta duk sun zo. Ni ce dai koma baya akan komai, komai nawa yana zuwar mun ba irin na gama gari ba. Yau da Kaila bai hana Yaya Use zuwa inda nake ba da yanzu tana nan, yaranta. Nayi_nayi ta turo mun su ma taƙi gudun fitina, ga shi Yaya Karime tana Shanono sai jibi zasu dawo. "Tani kayayyakin kitchen ɗinki ina zamu jera miki ne, naga kitchen a falo ko nan ne zamu jera naki kayan?" Cewar Jamila ba tun yau ba na fahimci Jamila tana da son dukan cikin mutum dan taji zance. Murmushi kawai nayi mata nace. Ku barshi ai kuma kun gaji, kayan kitchen ɗin ba wani kaya ba, ni kaɗai ma in na nutsa zan gyara, dan akwai gyaran da ba'a ƙarasa a kitchen ɗin ba" Ni kuma harga Allah tsoro nake ji in ba da umarni a jera mun kayan kitchen a kitchen ɗin falo in zo Kaila yai mun watsi da kaya a gaban kishiyoyina, ya tsinkani kamar yadda ya saba. Gaga_gaga haka mu ka wuni cur muna abu guda. Sai yamma lis Jamila, Isa ya zo ya mayar dasu gida, ashe Amaryar a gidan ta wuni a ɓarayin Hajiyayye. Har gaban mota na kai Jamila sai godiya nake yi mata. Jamila ta kawo mun gudumawar kofunan roba dozin guda. Ban jima da shigowa ba Sabira ma tai mun sallama, sai kuma gobe in mun haɗu a makaranta. Abun sha'awa yara sai facaka suke da ruwan fanfo a bayan gida, su shiga ciki da gudu, su fito da gudu, wannan rigimar harda Hauwa akeyi. Tana biye dasu tana ihu da dariya. A babban falo kuma ina ta jiyo hayaniyar maza da muryar Kaila. Har zuwa bayan Isha, nan fa yunwa ta soma sasuƙar yara, ni bansan tudun da zan dafa ba. Ragowar masa guda goma sha biyu na basu, na juye musu miyar a kai. Nan da nan suka cinye, ba sai sun ce mun basu ƙoshi ba, ni kaina nasan basu ƙoshi ba. Lallaɓasu kawai nayi. Ku yi haƙuri babu abinci ne a gidan. Ai kuna gani yau muka dawo sabon gida ko? Sai gobe zamu soma ɗaura sanwa." Buɗar bakin Sani yace. "Umma Munga su Samira, da Jaxuli suna cin tuwo ɗazu" Sai nayi jigum nace. To bari in leƙa in tambayo muku in bai ƙare ba." Salis na saɓa a kafadata yinwa kamar zata kayar dani, na nufi ɓarayin Bilkisa. Ashe mugun gyara akaima falon namu. Wasu ɗima_ɗiman kujeru aka baje, da ƙaton kafet, harda kayan kallo, ko ina sai hasken wuta. Gargaɗin dana tuno Kaila yayi mun ne yasa na canja akalata zuwa ɓarayin Hajiyayye. Jama'a sun soma sassautawa a ɓarayin nata. Da sallama na shiga falon. Abun mamaki ƴan uwanta suka watso mun wani kallo. Daga masu jan tsaki, sai masu cewa wari suke ji, harma da masu toshe hanci. Wani ƙududu na haɗiye ya faɗa cikina da zafi. Da ƙyar na buɗe bakina, dan jikina yayi mugun sanyi. Da ba dan bana son yarana su kwanta da yinwa ba, da juyawa ma zanyi in haƙura. Amman yaya zan yi, wanda bashi da gata ai yana ruwa. Hajiyayye dan Allah abinci zaki sanmun in ba yaran yinwa suke ji." Wani banzan kallo tayi mun. Ita da danginta suka saka shewa, kafin tace. "Wannan abincin ba Kaila bane ya kawo aka dafa. Balle kice suma suna da hakki akai. Daga gidan ubana ƴan uwana abun alfahari na suka yo aka tawo mun dashi kin gane ko? Sabida haka bazan bayar ba." Yayarta Ta Bizaaro tace. "Zamu haɗu a kotu nan da kwanaki zaki san kishi ba hauka bane. Gobe ba zaki sake yin kisan kai ba. Tani baki ma da kunya, kinga ƙannenmu sai haƙuri aka basu dan dakaki ma su ka so yi, nice na taushesu" Daurewa nayi dan bana fatan suga zubar hawayena. Juyawa kawai nayi da sauri. Kiciɓis nayi da Kaila a ƙofar shigowa ɓarayin Hajiyayye. Idanu muka zuba ma juna. Sai lokacin hawayen da na shanye suka shiga suntiri a kumatuna. Ƙur yayi da idanunshi a kaina, bai tanka ba, nima ban tanka ba muna tsaye dukkanmu. Kaina na sauke ƙasa nace. Yara yinwa suke ji Kaila. Bansan da wanne kitchen zanyi amfani ba. Sannan bansan kuma inda kayan abincin suke ba waɗanda aka ɗebo daga can gidan.. "Dakata Shanono. Wannan gidan ba irin wancan tsohon gidan da muka baro bane. Duk wani tsari ya canja. Zuwa gobe zan tara ku kuji sabon tsarin da zan fitar. Kayan abinci kuma ki tambayi Hajiyayye yana store ɗin kitchen ɗinta. Kitchen ɗin falonnan zaki iya jera dattin tarkacenki, amman ki sani ba kitchen bane na kunna gawaye ba. Yana da ƙofar waje, sai ki dinga fita da gawayin ta waje. Wallahi muddin naga wani ƙazanta a cikin kitchen ɗin, to zaki koma girki a cikin ɗakin ki zai fi mun sauƙi." Yana kaiwa nan ya wuce ni, bai faɗa mun yanda zanyi da yaran ba. Nayi iya dubana ko gawayi babu ban gani ba. Haka dole na koma ɗakina. Na samu ma yara mazan sunyi bacci a katifarsu wacce aka sa ma rigar leda. Ajjiyar zuchiya na sauke, ina shiga ciki na tarar da matan ma sun yi bacci. Ni ko a darennan tunanika babu irin waɗanda basu zo kaina ba. Na gaji da irin wannan rayuwar ƙasƙancin da nake yi a gidan kaila. Na fahimci tozarcin da nake fuskanta shafi_shafi ne, kuma ko wanne shafi da salon shi. Rayuwa kenan. Babu damuwa watarana sai labari, zaman gidannan inayine domin goben yarana kawai, amman nayi imani baƙin ciki da ciwon zuchiya su za sui ajalina. Haka na kusan raba dare ina kuka da tunano rayuwar da nayi a baya. Da irin mazajen dana aura, da irin jarrabawar dana fuskanta, dama darasi, da ƙaddarar dake cikin ko wanne aurena biyar. Aure da sha'anin maza ya gama fitar mun a kaina sam. Washe gari. Haka gari ya waye muka tashi cikin yinwa, ni kuwa cikina ƙullewa yayi sosai, da ƙyar na tashi, na tashi yaran dan su ɗauraye jikinsu su yi sallah. Ni kuma na shiga aikin fitsari. Ruwa na yayyafa a katifun duka biyu, nasa tsumma na goggoge,abun daɗin, rigar ledar da aka rufe katifar bai ba fitsarin damar taɓa katifar ba. na fito dasu, ruwan fitsari na yarari. Kaila da Hajiyayye suna babban falo, da dukkan halama Hajiyayye itace da Kaila. Ta ɗauki wanka tayi kyau abinta. Da idanu suka bini harna fice da katifun duk biyu, na wanke zannuwan gadon da zallan ruwa na yaɓa a katanga. Ina shigowa Hajiyayye tace. "Ruwan fitsarinnan kisa tsumma ki gogeshi, wallahi Baby bazan iya ba. Yanzu ta babban falonnan zata dinga fitar da katifa kullum?" Ina tsaye ina kallon Hajiyayye, da irin kallon tsanar da kaila ke jifana dashi. Ko da ya tashi, da zagi ya rufeni, idona ya bushe babu ko sofanen hawayen ma. Tsumma na ɗakko na goge, na basu haƙuri dukkansu na koma ɗaki. Salis na tarar a hannun Sani sai kuka yake yi. Tun cikin dare yake jan nono, amman babu ruwan nonon, kukan yinwane kawai. Sauran yaran ma sun yi jigum sai kallona suke yi, irin kallon ki yi mana rai" Salis na saɓa a baya. Idanuna duk kwantsa, kumatukana duk busassun yawun bacci na fice a gidan da karamar jakata. Jefa ƙafata kawai nake yi bansan inda ma na dosa ba. Wannan masifa dame tai kama. Ni dai na kama tafiya sai nausawa nake yi, kafin in zo titi ma ba ƙaramar tafiya bace, haka nai ta fama, ina tafe faram_faram Salis sai kuka yake yi........✍🏻 _*AMMA ARAB!AMMA ARAB!!AMMA ARAB!!!*_ _kai daga jin sunan kasan sunan ya amsa sunansa,AMMA ARAB ta kawo muku wani supplement na gyaran jiki mai sanya daɗi da ƙamshi AMMA ARAB gidan ƙamshi_ *MUSUK* *MADARAR TURARE* *KAJIJI* *ROT* *SANDAL* *HUMFUR* *SANDAL FLASK* *SANDAL WUD* *AALUT* *GAF-GAF* *JANNAMI* *ƘWALAKCA* *MAHAHABSUFYAN* *WANNAN SHINE GRP ƊINA NA WHATSAPP,KI ANTAYO SABODA KADA AYI BABU KE* 👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻 https://chat.whatsapp.com/BrUXmBHnDN6KUJYnkBDT7S *ADDRESS👇🏻👇🏻👇🏻* Zaria road kwankwasiyya sabon gari dangwauro house number 224 *AƘWAI WANI SUPPLEMENTA NA GYARAN JIKI DA TAZO MUKU DASHI KE DA KANKI IDAN KIKA YI ZAKISAN EH LALLAI ZAKI GIGITA ME GIDA,KINSAN MAZA SAI DA ƘAMSHI DUK MATAR DA BATA SAYI WANNAN SUPPLEMENT ƊIN BA TO AN BARTA A BAYA* *AƘWAI BABBAN MAGANI NA INFECTION,WANDA ZAI DAWO MIKI DA MARTABARKI NA ƳA MACE,ZAI CIKO MIKI DA NI'IMARKI KI KOMA ƳAR GATAN MEGIDA* *AƘWAI BABBAR KAMBASA,TA TURARA KAYA HAJIYA KI BUƊE BAKIN ALJIHU KI JIƘO DA ƘAMSHI,KINA ZAMA AN SAN KIN ISA MACE HAJIYA DON AMMA ARAB TA SHARA SOSAI WAJEN KAWO MUKU KAYAN GYARA NA MATA* *AƘWAI SABULAN GYARAN JIKI SUNE KAMAR* *MULATO SOAP* *FACE CREAM* *FACE SOAP* *MULATO WHITENING LOTION* *HAIR GROW OIL* *HAIR GROW CREAM* *KAR-KAR OIL* *MINT LEAVE OIL* *ANTI PIMPUS SOAP* *AƘWAI SABULUN NANKARWA* sannan ina harkar👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻 *ABIN BUKI* *ABINCIN OFFICE* *SNACK* KAMARSU👇🏻👇🏻 *WAINAR MASA* *SINASIR* *MEAT PIE* *CINCIN ƊAN LAUSHI* *CUP CAKE* DA DAI SAURANSU. AMMA ARAB GIDAN GYARAN AURE😄👏🏻 [10/8, 18:33] Badiat Ibrahim: NA FAƊO DAGA BENE..... NA ZARCE RIJIYA. HAKKIN MALLAKAR BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI GAWURTATTU UKU 18 Na ci tafiya sosai. Ƙafafuna su kai busu_busu dasu. Da ƙyar na ga wani shagon yarbawa yana kallon asibitin Salman dake cikin anguwar. Na ko yi sa'a suna da gawayi, da komai. Kayan miya, da taliya, maggi, manja na siya. Dubu ɗaya na kashe, na kuma juyawa faram_faram ina haƙi. A tsakar gida na tarar da su Shafi'i suna wasan tsere ban bi ta kansu ba, na shige ciki na fito da kurfot ɗina, ta bayan lungun inda ɗakina yake a wajan na hura gawayi. Kayan miyan kuma na wanke na zuba a turmi, Sani na kira yana jajjage ni kuma ina ɗebo kayan kitchen ɗina. Babban teburina dake kitchen ɗinmu na tsohon gidanmu na jawo. Akai na jejjera ƴan tukwanena, da kwandon wanke_wankenmu. Kurfot ɗinma na kinkima na aza a saman teburin. A daren jiya na yanke hukuncin bazan yi amfani da wannan kitchen ɗin na falo ba, dan akan kitchen ɗin Kaila zai iya ƙila dukana ma, gara in kiyaye kaina in janye jikina in ƙara komawa gofe, tunda ina da iyaka a cikin rayuwar Kaila. Taliya na ɓararraka mana na baje mana ita gabaki ɗaya a tire. Ina gaba Sani na biye dani. A tsakar gida mu ka ci karo da Hindatu tana wanke wanke a bakin famfon tsakar gidan. An kawata wajan da fararen tayil masu haske. Gaisawa mu ka yi. "Ya sabon gida Umman Sulaiman?" Alhamdulillah sabon gida yayi kyau, yayi daɗi" Iyakar abinda nace kenan nabi bayan su Amina da suka bi Sani ɗu sunga abinci. Muna shiga falon na tarar da su Bilkisa, da kaila, da Hajiyayye" "Shanono ki zo ke muke jira, zan yi magana daku" Nufosu nayi na samu ƙasan kafet na zauna kaina a ƙasa, su ko dake ƴan gaban goshin mijine, ɗaya na hannun daman Kaila, ɗaya na ɓarayin hagu a saman kujera. Bilkisa na sanye da kayan aikin likitanci, da halama aiki zata wuce. Itace ta gaisheni. Da fara'a na amsa mata gaisuwarta. "Dubi idanki duk ƙwantsa Shanono. Kai Allah ya sauwaƙe miki." Ƙasa na kuma yi da kaina. "To dalilin da yasa na tara ku anan ba komai bane face canja tsare _tsare da zanyi a gidannan. Daga yau ko wacce mace ta dinga girkin abinda take so, ko wacce zan bata kuɗin cefanenta na wata, ta sai duk abinda yai mata. Amman na dena cin abincin ko wacce mata, Shamwila ce zata dinga mun girki a kwanan ko wacce Mata. Sannan na bata ɗakin tsakar gida, zata gyara ta zauna a can. Kuma ita zata dinga gyara mun ɗakina, da wankina kamar yadda Ɗanyan gwal take sata. Ko wacce mata ta gyara ɗakinta, tayi wankinta dana yaranta. In akwai me magana tayi" Yayi shiru yana sauraren mai magana. Ni dai ai yasan banda ta cewa, ni banga ma ta inda wannan maganar ta shafeni ba da har aka tara har da ni. "Gwanda lokaci zai ƙure, kaga ina da nisa da asibiti sai na dawo." Cewar Bilkisa wacce ta miƙe tsaye tana kallon agogon hannunta. "Naga ƙannenki kince sun tafi sassafe, amman kuma motar da suka tawo da'ita tana tsakar gida." Idanu ya ƙura mata. Sai da ta kai bakin ƙofar fita waje kana tace. "Dad ne ya aiko mun da'ita in ci gaba da jigilar zuwa aiki" Tana kaiwa nan ta fice. Kaila ya daɗe sosai a zaune yana bin ƙofar da kallo, har motar Bilkisa ta fice a gidan baice komai ba. Abinda na lura shine ranshi ya ɓaci. Hajiyayye ce ta katse shirun ta hanyar cewa. "Baby me kake nufi. Yarinyar da matarka ƴar boko ta kawo cikin gida a matsayin ƴar aikinta itace zata ci gaba da yi ma girki ko ba ranar girkin uwargijiyarta ba? To ina da ja gaskiya, irin ƴan iskan yarannan ne zaka sakar ma girki, da gyaran turaka, harda wankin miji." "Hukunci dai na riga na yanke. Yayi daɗi ko karma yayi dai dole abi. Wacce taji ba zata iyaba sai ta tafi gidansu ai." Zuruf Hajiyayye ta miƙe tace. "Zan ko tafin. Ai gara in san aurenta kake yi zai fi mun. In san gumurzun kishi nake yi da'ita" Fuu ta wuce abunta ta bugo ƙofar ɓarayinta. Ni dai bance uffan ba na miƙe na bar Kaila a zaune yana ƙananun maganganunshi. Ni ko dan yinwa ko gani bana yi sosai haka na shiga ɗakina. Nako ci sa'a sun rage mun taliyar, na dira akai nan da nan na lashe. Ko wanke baki cikinmu babu wanda yayi. Miƙewa nayi na shiga banɗaki nayo kwaskwarima, na wanke tsumman jini, na shanya a windo. Ban wanke bakin ba, sauri nake yi in na dawo na wanke. Yaran dai na miƙo musu roba mai murfi da muke zuba gawayi dakakke da gishiri na wanke baki. Ku goge bakin ku Sani. Ke kuma Amina ki fita waje ki yi mun wanke_wanke. Da kin gama ku dawo ɗaki ku kulle, dan Allah kar ku fita babban falo kar ku ja mun abun faɗe, ni sai na dawo." Fita nayi, na hau abun hawa sai makaranta. KAILA: Bayan watsewar su Tani a falon. Sai ya shiga ɗakinshi, wanda yake manne da falon shanono.wanka ya shiga yayo. Ya fito ya cakuɗe jikinshi da kamshi. Ya ciro wasu ƙananun kaya masu kyau. Duk da kasancewar kayan na gwanjone, a wajan Baban Hajiyayye ya siya, amman a gwanjon ma su masu tsada ne, dan giredi ne sosai. Wani silifas yasa mai taushi, shima na gwanjonne. Ya ɓare ledar cingam ya jefa a bakinshi, ya shiga tsuna kamar tsohuwar kilaki. Wayarshi ya ɗaga ya danna number Shamwila. Ringin ɗaya wayar tayi zuruf aka ɗaga. Ita kanta dama zaman jiran wayar tashi take yi, tunda ta ji fitar Bilkisa. "Ɗanyan jini mu haɗu dake yanzu a moonshine hotel, kinsan wajan ko, ta wajan cobe?" Murmushi tayi mishi tace. "Ai na karaɗe hotels da dama a garinnan. Gani nan fitowa, ƙila in rigaka ƙila ka rigani" Sallama su kaima juna. Ita ta rigashi fita, amman kuma shi ya rigata isa tunda shi a abun hawa na gida yake. A wannan ranar Kaila yai rub da ciki akan Shamwila. Wa'iyazubullah a wannan ranar kaila da Shamwila sun aikata abubbuwa masu yawan gaske. Amman dake Shamwila mai wayo ce, sai da ya bata kuɗi masu tarin yawan gaske, kafin ta bashi kai bori ya hau. Abunka da aikin shaiɗan nan take yaji dukkan matanshi ashe salab suke shi bai sani ba, sai daya haɗu da gogaggiyar ƴar bariki sannan ya sani. Nan Kaila ya shiga rawar jiki akan Shamwila. Tsugunnawa yayi akan guiwarshi . "Ɗanyan jini yaushe zaki kaini wajan Abba ne? Wallahi a yau ne nake jin dai_dai da kwana ɗaya bazan iya jure rashinki ba. Ni gara muyi aure hankali a kwance." Dariya tayi mishi. "To ya maganar ginin ɓarayina, ba kace zaka yi mun ginin daya zarce wanda kwashi kwarab ɗin matanka suke ciki? Aure kam ai zamu yi ka soma gamawa da ginin tukunna" Shiru Kaila yayi yasan a yanzu baida kuɗin soma yin wani gini, nan da shekara guda ma ba lallai ya samu kuɗin soma yin sabon gini ba. Wannan ɗin ma daya aka ƙare. Rarrashin shi Shamwila ta shiga yi, tare da yi mishi alƙawin kasancewa tare dashi a duk daren duniya. Haka ne kuwa yaci gaba da kasance. SHANONO: Ina dawowa daga islamiyya na samu Kaila ya ba Sani dubu uku wai kuɗin abincinmu ni da yara na wata ɗaya. Ban dai yarda da abinda Sani yace ba, na adana kuɗin ina jiran in ya dawo in tambayeshi. Na riga nayo mana cefanen ɗan kayan masarufi daya sauwaƙa. Garin rogo da ƙuli kuwa na siyo su da yawa sosai. Gari na jiƙa mana, muna cikin sha Habiba Bala ta kira ni. Gata ta shigo jos. Kwatance na dinga yo mata harta iso. Itama ta zo mana da tsarabar sabulan wanki, dana wanka, harda man shafawa. Nako ji daɗi sosai, dan harna siyo sabulu da omo na wanki a cefanen da muka yi. Video call ta kira mai aikinta, suka haɗa ni da Dauda. Yana kwance ya sake ramewa, da gani yana jin jiki, dan sai da na zubar mishi da hawaye. Yaran na kira duk su kai mishi ya jiki. Sai tambayata yayi. "Innata yaushe zaki zo?" Daurewa nayi na haɗiye kukana nace. Zan zo Dauda kaji. Allah ya baka lafiya mai ɗorewa, ubangiji Allah ka raya wannan bawa naka" Habiba Bala ta kashe wayarta. A wajanmu ta wuni cur. "Sabon gida ba zarni sai kaɗan Shanono. Akwai turaren wutan tsinke na sako miki ki yi kokari ki dinga kunnawa. Kuma ki yi kokarin gyarawa, ki dage da karatu. Sannan ki binciki sana'ar data dace dake" Godiya nayi mata sosai. Tayi mana sallama akan sai mun haɗu a kotu gobe." Wunin ranar sukuku nayi shi dan tsoron zuwa kotu gobe. Ko da Yaya Use ta kirani itama jikinta duk a sanyaye haka dai mu ka yi wayar. Da yamma lis nasa yara mazan su yi wanka. Ni kuma na tafi baya dan yin girki. Wuta na hura na dawo ciki. Hauwa da Salis nai ma wanka, su Amina da Balaraba da kansu suke yi. Ni da kaina na ciro musu kayan da zasu saka, ba kamar yadda na saba barinsu su zazzage buhun kayan a ƙasa ba. Dana tsayar da sanwar miya, nima sai na shiga bayan gidan nayo wanka, nayi wankin tsumma. Wajajen magriba na haɗu da kaila a tsakar gida, ni kuma na fito daga baya da tukunyar miya a riƙe. "Shanono Sani ya baki dubu uku ko?" E ya bani. "To sai ki jalauta kuɗin abincinku na wata guda kenan. Sai kisan yanda zaki tanana ya kai muku. Kina sane da batun zaman farko a kotu gobe ko?" Numfashi na ja. E ina sane Allah ya nuna mana. An gode Allah ya saka da Alkhairi " Na wuce ciki abuna. Ni fa a wannan daren Wallahi masu karatu banko runtsaba, nayi kukan harna gaji. Na yi tashin hankalin, har zazzaɓi sai da ya ci nasarar kama ni dan farbaga......✍🏻 _*AMMA ARAB!AMMA ARAB!!AMMA ARAB!!!*_ _kai daga jin sunan kasan sunan ya amsa sunansa,AMMA ARAB ta kawo muku wani supplement na gyaran jiki mai sanya daɗi da ƙamshi AMMA ARAB gidan ƙamshi_ *MUSUK* *MADARAR TURARE* *KAJIJI* *ROT* *SANDAL* *HUMFUR* *SANDAL FLASK* *SANDAL WUD* *AALUT* *GAF-GAF* *JANNAMI* *ƘWALAKCA* *MAHAHABSUFYAN* *WANNAN SHINE GRP ƊINA NA WHATSAPP,KI ANTAYO SABODA KADA AYI BABU KE* 👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻 https://chat.whatsapp.com/BrUXmBHnDN6KUJYnkBDT7S *ADDRESS👇🏻👇🏻👇🏻* Zaria road kwankwasiyya sabon gari dangwauro house number 224 *AƘWAI WANI SUPPLEMENTA NA GYARAN JIKI DA TAZO MUKU DASHI KE DA KANKI IDAN KIKA YI ZAKISAN EH LALLAI ZAKI GIGITA ME GIDA,KINSAN MAZA SAI DA ƘAMSHI DUK MATAR DA BATA SAYI WANNAN SUPPLEMENT ƊIN BA TO AN BARTA A BAYA* *AƘWAI BABBAN MAGANI NA INFECTION,WANDA ZAI DAWO MIKI DA MARTABARKI NA ƳA MACE,ZAI CIKO MIKI DA NI'IMARKI KI KOMA ƳAR GATAN MEGIDA* *AƘWAI BABBAR KAMBASA,TA TURARA KAYA HAJIYA KI BUƊE BAKIN ALJIHU KI JIƘO DA ƘAMSHI,KINA ZAMA AN SAN KIN ISA MACE HAJIYA DON AMMA ARAB TA SHARA SOSAI WAJEN KAWO MUKU KAYAN GYARA NA MATA* *AƘWAI SABULAN GYARAN JIKI SUNE KAMAR* *MULATO SOAP* *FACE CREAM* *FACE SOAP* *MULATO WHITENING LOTION* *HAIR GROW OIL* *HAIR GROW CREAM* *KAR-KAR OIL* *MINT LEAVE OIL* *ANTI PIMPUS SOAP* *AƘWAI SABULUN NANKARWA* sannan ina harkar👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻 *ABIN BUKI* *ABINCIN OFFICE* *SNACK* KAMARSU👇🏻👇🏻 *WAINAR MASA* *SINASIR* *MEAT PIE* *CINCIN ƊAN LAUSHI* *CUP CAKE* DA DAI SAURANSU. AMMA ARAB GIDAN GYARAN AURE😄👏🏻 [10/8, 18:33] Badiat Ibrahim: NA FAƊO DAGA BENE..... NA ZARCE RIJIYA HAKKIN MALLAKAR BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI GAWURTATTU UKU 19 Washe gari sassafe ni da yaran muka fice a gidan. Basu ci gaba da zuwa makaranta da islamiyya ba sai gobe in Allah ya nuna mana. Ni kaina ba lalle bane in iya zuwa school yau ba. Dan zazzaɓine magashiyan a jikina, ga wani irin sanyin mashasshara da nake ji. Gidan Yaya Use muka wuce. A tsakar gida na same su harda Baban yara. Yaya Use tana raba ma yara kokko. Ganin mu yasa aka ƙara yawan kofuna. Aliyu ne ya shigo da ledar ƙosai. Kowa ta danƙa mai kosai bibbiyu a hannu. Nima ta miƙo mun nawa kokko da ƙosan. Baban yara ina kwana" Nace a sanyaye. "Lafiya Tani. Za'a soma shiga kotun ko?" Kai na iya gyaɗa mishi kawai, dan harshena yayi nauyi. Ya nuna Yaya Use wacce idanunta su kai zuru_zuru yace. "Kin ganta tun daren jiya take faman yin gudawa, har wayewar garin yau. Sabida tsabar tsoron zaman kotu. Idandunanta har sun faɗa. Ai irin abinda dama nake guje mata kenan. Itafa bata da aiki sai rigima da zafi, duk da a hakanma tayi sanyi" Kai ya girgiza yace. "Allah ya kyauta. Sai kun dawo ni na fita kasuwa" Na dubi yaya Use nace. Nima tun daren jiya zazzaɓi me zafi ya rufe ni. Gashi yau su Inno zasu dawo, ai in Baffa yaji wannan labarin daga ni har ke mun shiga uku. Barenma ni da abun lefi baya mun wuya." "Tani na tsorata, gani nake yi bazan kuɓuta ba wallahi. Sabida tabbas na daki Hajiyayye, amman tabbas ban daki cikinta ba. Amman wa zai fitar dani a wannan ƙullin sai Allah " Kafin in yi magana Habiba Bala ta kirayi wayata. "Shanono in shigo cikin gidan Yaya Usen ne?" E Habiba Bala shigo muna ciki" iyakar abinda nace mata kenan. Na datse wayar. A hankali nake ɗan kurɓan kokkon. Ƙosan ma danƙama Hauwa ɗaya nayi, Balaraba ɗaya. Ruwan kokkon ma ya isheni. Da sallama Habiba Bala ta shigo. Tana sanye cikin riga doguwa fara mai shegen kyau. Ƙamshi take yi mai kwantar da zuchiyar mai shaƙa. "Maraba Habiba Bala. Zauna ga waje dan Allah" A ɗofane Habiba Bala ta zauna. Ta faɗaɗa murmushinta suka gaisa sosai da Yaya Use. Ni kuma ta dube ni. "Shanono lafiya dai, naga jikin naki babu ƙwari sam. Menene damuwar?" Hmmm babu Habiba Bala. Ya hanya?" "To ya kamata ace ki yi wanka sai mu je ko, Yaya Use ku shirya, lokacin yayi mana a gaban kotun." Yaya Use tace. "Kayya Habiba Bala. Tani dai ta shiga tayo wankan in zata iya. Ni kam har sai na ji yadda shari'ar zata kaya. Babban damuwata in da gaske alƙali ya tura mu gidan kaso, ni Use ya zanyi da raina Habiba Bala yarannan ina zamu kaisu?" Habiba Bala ta dube mu tace. "Ko ɗaya Yaya Use, ai in Hajiyayye ta san farkon shari'a bata san ƙarshenta ba. Ku dai ku shirya kawai mu tafi" Da ƙyar na tashi nayo wankan na fito. Kayan jikina na mayar, ina fitowa Yaya Use ta shige ɗaki danta kintsa. "Shanono na lura duk nasihar da nake yi miki akan ƙazanta baki dena ba. Kinsan Allah in na zuchiya ko wallahi bazan sake tako inda ma kike ba. Ke fa macece, ya kamata ki nutsu ko dan ummu nabeeha ki gyara. Na tabbatar sabida ƙazantarki ne yasa mijinku yayi miki jan fenti. Gashi ni nayi cinikin kujeru inaso in sai muku ko dan farin cikin yaranki, amman ƙila kujerun barinsu zaki yi yara su lalata a banza. Jibi kayan jikin ki, ba koɗewarba, ji dattinsu kin yi wanka tsabar iskanci kin kuma damɓarawa, meye amfanin wankan naki to? Jibi kanki dana yara duk datti. Ji Hauwa yarinya ƙarama ji tarin tulin ƙasa a kanta. Shanono sai fa kin miƙe zaki iya kwatar ƴancinki a idan duniya ma. Ki ajjiye damuwa da komai a gefe ki gyara kanki da yaranki, ki nutsu ki basu tarbiyya. Yaranki mata in kikai sake suka taso a haka wallahi kin kashe su. Suma fa korosu za'a dinga yi a gidan miji.?" Tabbas maganganun Habiba Bala sun ratsa duk jijiyoyin jikina. Kuma tabbas ita da Sabira burinsu shine su ganni cikin rayuwa da yanayi mai kyau. Nima ya kamata in faranta musu kamar yadda suke faranta mun. Kiyi haƙuri Habiba Bala in sha Allah Shanono daga yau ta canja, bazan sake ba, zaku sha mamakin haɗuwarmu ta gaba" Ina faɗin haka na miƙe zuwa ɗakin Yaya Use." Yaya Use ki ban wasu kaya da zasu yi dai dai da jikina" Ba tai mun musu ba ta zaro wata doguwar riga "Kinga wata Inno ce ta hado mun a kayan data aiko mun. Dama ke naso ba ko Karime " Godiya nayi mata tare da saka wannan kayan. Na ari hijabin ƴan matan Yaya Use na saka. Na fito, Habiba Bala tayi murmushi tace. "Koke fa. Kema kya ji daɗin jikin ki ai ƙazanta fa babu kyau Shanono, haka ki kai ta bamu wahala a makaranta, kai kin cutar damu da warin hammata irin na sabon balagarnan. Dariya mu ka yi duka. Sai ta tuno mun da wannan Dattijuwar da muke zaman benci ɗaya a makaranta. Ranar laraba daya kasance zuwana makatanta na uku, bayan an tashi na fito daga aji, hijabina duk jirwayen ruwan nono, muna ƙarni. Wannan dattijuwa sai ta tare ni tace. "Ƴata in babu damuwa bari in baki shawara. Muddin ki kai amfani da ita zaki ji daɗi." Tsaiwa na gyara. "Kin ganni nan yara ɗaiɗai sai da na haifi yara goma sha bakwai a cikinnan nawa. Ƴan bibbiyu sai da na yisu sau uku. Amman bamu yi ƙarni ni da yaran irin yanda kike wannan ƙarnin ba. Ke ƴata ce, yadda zan ma ƴar cikina haka zan yi miki. Kinga ajinmu duk gulmarki suke yi. Sabida cika ajin kike da ƙarni da warin rana da kin shigo. Ƴata ki dinga tsabtace jikinki, ko dan lafiyar ki da lafiyar jaririnki. Jiya da tsarabar kuɗin cizo na koma gida, kuma nayi alƙawarin yau zan yi miki magana. Ƙazantarki tayi yawa, jibi hijabinki duk datti, littafin turanci jiya da muka haɗa aka kaima malamin da ya bamu aikin gida a ciki. Naki fa da kika ciro duk manja. Tani Shanono ki dena kin ji ko ƴata?" Ta mun jan kunne, da nuni masu dama, amman nasa ƙafa na shure. Ni ganina nake tamkar ba mace ba, gani nake yi ni kowa ma ya tsaneni, wallahi bansan abinda ke damuna ba, amman ko iyakar cunkushewar zuchiya da haki dake yawan taso mun aka barni dashi shima jarabawane. Yaya Use ce data fito ta katse mun tunanina. "Mu janku. Ku kuma ku kula da gidan banda yawo kune manya" Adda'a yaran su ka yi mana. Manyan kuwa sai da suka ga ɓacewar motarmu tukunna. Damuwa duk ta damesu, kamar yadda muma ta damemu. Shiru kuke ji a cikin motar babu motsin komai sai ƙaran Ac da Habiba Bala ta babbaka mana. Tafiyar minti goma sha biyu ce ta kawo mu kotun wajen amingo. Muna fitowa muka ga su Hajiyayye da tawagar ƴan gidansu birjik a zaune a gefen kotun. Kaila kuma yana gefe yana waya, da ganin yanda yake suntiri na gano yayi wata sabuwar budurwar kenan. Gefe guda muka ja muka zauna. Dangin Hajiyayye suna ganinmu suka soma tsaki da harare_harare. Babu wanda ma yabi ta kansu damuwar dake damun mu ma ta ishemu... NA FAƊO DAGA BENE..... NA ZARCE RIJIYA. HAKKIN MALLAKAR BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI GAWURTATTU UKU 20. Gefe guda muka samu mu ka zauna. Kaila sai yawo yake a filin kotun yana ta wayarshi. Can lauyanmu ya ƙaraso a gurguje. Isowarshi ke da wuya aka buɗe kotu tare da bamu umarnin shiga. Wallahi ƙafafuna da ƙyar suka ɗauke ni izuwa cikin kotun. Wannan shine karon farko dana shiga kotu, ina fatan na ƙarshe in sha Allah. Kujeru ne a jejjere kamar makaranta. Sai wani gidan katako daga sama, da ɗan akwaku a gefe. Kowa ya nemi waje ya zauna. Lauyoyi suna gefen wajan zamansu. "A yau ashirin da biyar ga wata. Wannan kotu mai alfarma zata yi shari'ar Hajiyayye wacce take unguwar layin ɗanmaraya, gida mai lamba Z2110. Inda ta shigar da ƙaran kishiyarta Tani, da Yar kishiyarta Use, akan kashe mata yaro da su ka yi a ciki sanadiyyar lakaɗa mata na jaki da su ka yi" Yaya Use ta zare idanu tare da riƙe ciki. "Gudawa nake ji Tani. Nashiga uku" Cikin raɗa take magana. Kafin in san abinda zance sai mu ka jiyo Alƙali na faɗin. "Lauyoyin duka ɓanrarorin biyu in sun halarci zaman su gabatar mana da kansu, kafin mu soma amsar hujjoji" Lauyan su Hajiyayye ya miƙe. "Sunana Barister Safwan Sammani. Lauyan gwamnati, nine wanda nake kare waɗanda suke ƙara. Nagode mai shari'a" Zama yayi. Lauyan da Habiba Bala ta ɗaukar mana ya miƙe. "Sunana Barista Suwiɗi Zakariyya, daga Aminci chamba. Nine wanda yake kare waɗanda akayi ƙara" Shima yana gama faɗar haka ya zauna. Bayan shiru na sakwanni ya wakana, sai Alƙali yace. "Akwai wani jawabi da lauyan masu ƙara zai mana a matsayin shinfiɗa?" Ni dai jikina ya gama jiƙewa sharkab da zufa. Habiba Bala sai ƙarfafani take yi. Yaya Use kuwa ta durƙusa cikinta ya gama birgewa. "Ina da shi ya mai shari'a. Hajiyayye dai har ƙofar ɗakinta Use ta je ta sameta, kuma ta cakaleta da dambe, suka haɗu ita da ƙanwarta Tani suka zaune Hajiyayye da tsohon ciki, basu suka ɗagata ba sai da su ka ga jini na zuba tukunna. Ya mai shari'a ina son wannan kotu mai alfarma ta kwato ma Hajiyayye hakkinta, a biyata hakkin jinin ɗanta daya salwanta. Likitoci sun tabbatar mana buguwa tayi a cikinta dalilin mutuwar yaron kenan. Wanda hakan yasa sai tiyata akayi mata aka cire mata gawar yaro. Nagode ya mai shari'a " Lauyan su Hajiyayye ya zauna. Kuka mara sauti na fashe dashi, shikenan mai fitar damu a cikin wannan matsalar sai Allah. Ƙila su Baffa da muke gudun su sani dole su sani, tunda in aka kullemu a gidan yari dole labari zai je har shanono ma. Lauyan mu ya mike yace. "Ya mai shari'a ina da ja a bisa jawabin abokin aikina. Domin har yanzu zargi akeyi ba'a tabbatar ba. Bai kamata ya dinga jingina laifin ga waɗanda ake tuhuma ba kai tsaye. Sannan abinda yai sanadiyyar har Use ta daki Hajiyayye shine. Hajiyayye cikin kaifin harshe ta zazzagi iyayen su Use tare da aibantasu dan kawai sun kasance nakasassu. Ya mai girma mai shari'a, kowa yasan duk wani ɗa na halas yana kishin iyayenshi ko da kuwa iyayennan nashi masu taɓin hankaline. Wannan lamarin shi ya haddasa turka_turka a tsakanin Use da Hajiyayye. Amman Tani bata sa hannu a jikin Hajiyayye ba. Ita kanta Use bata zauna a ruwan cikin Hajiyayye ba, kuma bata naushi cikinta ba." "Ina da ja ya mai shari'a. Use ta zauna a kan ruwan cikin Hajiyayye, a tsakar gida akayi abun. Maƙota sun shigo a daidai lokacin da Hajiyayye take kwance a ƙasa jini na tsiyaya a jikinta. Sannan a gaban matar Ƙanin mijinsu mai suna Hindatu akayi. In kotu na son in gayyato mata Hindatu, a zama na gaba zata zo. Domin ta faɗi abinda ta sani game da hakan. Akwai takaddar asibiti data tabbatar da cewar buguwa Hajiyayye tayi shine yai sanadiyyar mutuwar abinda ke cikin nata." Lauyan su Hajiyayye ya miƙa takaddar asibitin i zuwa ga mai shari'a. Bayan ya duba takaddar sai yace. "Zamu je hutu na minti talatin kafin mu dora" Daga nan ya buga guduma, mu ka miƙe tsaye dukkanmu. Sai da ya shige wata ƴar ƙofa kafin muka soma fita. Yaya Use da gudu ta fita, mu ka bi bayanta. Wani gidan sama dake jikin kotun ta shiga da mugun gudu. Gudawace ta koreta. Muna zama na sau kuka mai sauti. "Lallai Hajiyayye sun shirya ganin sun kai ku ƙasa sosai. Kuma mun yi magana da Suwiɗi fa akan daga zaman kotun ya ƙare zamu je asibitin da suka karɓi haihuwar Hajiyayye. Suwiɗinne ya iso inda muke, duk muka miƙe tsaye. "Tani ki dena kuka. Amman abunda na fahimta da wannan shari'ar, shari'ace wacce akeson ganin an kaiku ƙasa, dan kes ɗin yana da girma. Amman mun miƙa ma Allah lamarinmu, ku yi ta adda'a. Habiba Bala ita kanta jikinta yayi sanyi balle ni Shanono. Habiba Bala tace. "Amman barista kana ganin zamu yi nasara? Likitoci fa sun tabbatar da cewar buguwace tai sanadiyyar mutuwar yaron a ciki." Dariya yayi yace. "Ke dai ku kwantar da hankulanku, zamu yi iya yinmu, Allah shi ne zai iya mana. Ina Use?" Sai lokacin muka hangota tana tafe tana ɗingishi. Su Hajiyayye ma magana suke da nasu lauyan. Kaila ma yana tsaye a kusa dasu. Sabira muka hango tafe. Yaya Use ta ƙaraso in da muke. "Ni nasan ma kurkuku zasu kaimu. Wallahi narantse da wa billahillazi huwarrahmanu ban daki Hajiyayye a ciki ba. Na dai fyaɗa ta da ƙasa. Idonane ya rufe kuimun rai " Sai kuka. Sabira ta iso wajanmu jikinta a sanyaye sakamakon yanda taga idanuwanmu sun yi jawur, dan hatta Habiba Bala a yau sai da hawayen idanunta suka zuba. Minti talatin na cika muka koma ciki. Kafinnan fa sai da yaya Use tayo gudawa sau biyu. Gabaki ɗaya ta galabaita ta fice a hayyacinta. Lauyanmu ne ya soma magana. "My lord inaso wanna kotu mai alfarma ta duba lamarinnan, tayi duba a kanshi. Sannan ina neman alfarmar wannan kotu mai alfarma data ɗage shati'arnan zuwa wani lokaci, domin tattaro hujjoji. Nagode my lord" Lauyan su Hajiyayye ya miƙe tsaye. "My lord, nima ina roƙo kamar yadda ɗan uwana ya roƙa a sake saka mana lokaci. Kafinnan inason kotu ta tsare Tani, da Use a gidan kaso har zuwa ranar da za'a dawo zama na biyu. Domin su masu lefine, kuma kisan kai ake tuhumarsu dashi my lord. Ko belinsu da aka bayar ba bisa ƙundin tsarin doka aka ba da belin nasu ba." Baki dukkanmu muka buɗe. Zuruf lauyanmu ya miƙe tsaye. "My lord ina da ja" Shima lauyan su Hajiyayye ya miƙe a zabure yace. "Nima ina da ja. Bai kamata ace su Tani su yi kisan kai ba kuma a barsu suna bacci a gida hankalinsu kwance. Wanda in da yazo da ƙarar kwana ita kanta uwar jaririn zata iya rasa rayuwata" Lauyanmu yace. "Ya mai girma mai shari'a. Inaso wannan kotu mai alfarma ta ji ƙan su Tani ta barsu a gidajensu. Tunda har yanzu ba'a tabbatar su su kai kisan kan ba. Ta yiwu wani abunne da ban ya kashe yaron su kuma suka taka sawun ɓarawo. Ta yiwu yaron ma ya jima da mutuwa a cikinta. My lord ina roƙar musu alfarma a matsayinsu na mata masu rauni. Kuma dukkansu a halin yanzu ba ishasshiyar lafiya garesu ba, sannan ita Malama Tani tana da ɗanyan goyo, ƴan satittika tayi da haihuwa, sanyi zai iya illata mata lafiyarta, sannan a dubi shi jaririn" Alƙali ya dube shi yace. "Wannan kotu ta ɗage wannan ƙara zuwa ashirin ga sabon watan da zai tsaya. Wanda zai kama ranar laraba. Zaman zai kasance na ƙarshe, dan haka lauyoyin duka ɓangare biyu ko wanne ya tanadi hujjojinshi. Duba da dubi da wannan kotu tayi, da nazari da tayi. Kotu zata sa a tsare Tani, da Use a gidan yari zuwa ranar da za'a yi zaman ƙarshe..........." ANAN NA KAWO ƘARSHEN LITTAFI NA ƊAYA 1 WANDA KUMA YAYI DAIDAI DA KAMMALA FREE PAGE ƊINA. DUK MAI SON JIN KARASHEN LABARIN SHANONO, SAI MU TARA DASHI A PAID GROUP, IN DA ZAN KAWO MUKU BOOK 2, DA BOOK 3. TAFIYAR FA NA FAƊA MUKU TANA DA TSAYIN GASKE. YANZU NE ZAMU SOMA LABARIN MA. KAR KU MANCE SHANONO BATA LABARTA MANA TARIHIN RAYUWARTA, DA TARIHIN AURE_AURENTA BA. KUMA NA SAN KOWA NA SON JI. MU HAƊU DAKU A GROUP ƊIN KARATU. NAGODE. GA NUMBER NA GA DUKKAN MASOYA MASU SON YI MUN GYARA, KO MASU YABON ALƘALAMINA, DAMA MASU SUKAR ALƘALAMIN DUK ƘOFA A BUƊE TAKE. MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI TAKU CE. 08179523215 DOMIN SAMUNA KAI TSAYE GA NUMBER NA. *SANNAN INA ƘARA JADDADA MUKU PROMO NA TURAREN TSUGUNNO, DA TURAREN TURAREN ƊAKI, DA TURAREN TURAREN TURARA KAYA, DA HUMRAR GASHI, DA HUMRAR FESAWA A KAYA IN ZAKA TURARASU, DA HUMRAR MATAN AURE, SUNE SETINMU DA NA FITAR MUKU DA PROMO AKAN 10K DUKKA SETIN KACAL. GARAƁASANE GA MASOYAN ALƘALAMINA IYAKAR ƳAN PAID GROUP ƊINA KAƊAI KE DA DAMAR MALLAKAR WANNAN TURARUKA MASU SIRRIN DAƊI, KUNSAN MU KANURI MUNSAN SURRUKAN ƘAMSHI IRI IRI. NA MUTUM 20 KACAL ZANYI SETIN IN SHA ALLAH. KI YI HANZARI KAR A BARKI DA CIZON YATSA. GAWURTATTU UKU 👠👠👠 1 _KWAI A BAKA_ *(UMMU AFFAN)* 2 _ZULFA_ *(UMMU MAHEER MISS GREEN)* 3 _NA FAƊO DAGA BENE..._ _NA ZARCE RIJIYA_ *(BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI)* _Littafi ɗaya; 400_ _Littafi biyu; 800_ _Littafi uku; 1000_ Ga masu son turo kuɗinsu ta account sai su tura a wannan account ɗin 👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻 0037219728 Fatima Rabi'u Sunusi StanbicIBTC Bank Sai ku tura da shaidar biya ta wannan number 👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻 08104335144 Masu tura kati kuma sai su turo screenshot na katinsu Mtn ta wannan number 👇🏻 08104335144 *GA MASU SON A TALLATA MUSU HAJARSU A DUKKANNIN SHAFINMU NA Facebook, whatApp, telegram, YouTube, groups, status, zamu tallata muku ne a kan farashi mai rahusa 10k ne kacal sai ku tuntuɓi numbobinmu kamar haka 👇🏻 08104335144 07068606171 08179523215 Domin tallata muku hajojinku a cikin na sati guda ya kama👇🏻 2k kacal Sati biyu 3k ne Idan kuma kanason har mu gama book mu dinga ɗaura maka ya kama 10k kacal. Muna godiya da zaɓar GAWURTATTU UKU ako da yaushe. Siyan nagari mai da ƙudi 🙏🏻. https://chat.whatsapp.com/Dqaioj0tydVHQGo5zoG0lm _*AMMA ARAB!AMMA ARAB!!AMMA ARAB!!!*_ _kai daga jin sunan kasan sunan ya amsa sunansa,AMMA ARAB ta kawo muku wani supplement na gyaran jiki mai sanya daɗi da ƙamshi AMMA ARAB gidan ƙamshi_ *MUSUK* *MADARAR TURARE* *KAJIJI* *ROT* *SANDAL* *HUMFUR* *SANDAL FLASK* *SANDAL WUD* *AALUT* *GAF-GAF* *JANNAMI* *ƘWALAKCA* *MAHAHABSUFYAN* *WANNAN SHINE GRP ƊINA NA WHATSAPP,KI ANTAYO SABODA KADA AYI BABU KE* 👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻 https://chat.whatsapp.com/BrUXmBHnDN6KUJYnkBDT7S *ADDRESS👇🏻👇🏻👇🏻* Zaria road kwankwasiyya sabon gari dangwauro house number 224 *AƘWAI WANI SUPPLEMENTA NA GYARAN JIKI DA TAZO MUKU DASHI KE DA KANKI IDAN KIKA YI ZAKISAN EH LALLAI ZAKI GIGITA ME GIDA,KINSAN MAZA SAI DA ƘAMSHI DUK MATAR DA BATA SAYI WANNAN SUPPLEMENT ƊIN BA TO AN BARTA A BAYA* *AƘWAI BABBAN MAGANI NA INFECTION,WANDA ZAI DAWO MIKI DA MARTABARKI NA ƳA MACE,ZAI CIKO MIKI DA NI'IMARKI KI KOMA ƳAR GATAN MEGIDA* *AƘWAI BABBAR KAMBASA,TA TURARA KAYA HAJIYA KI BUƊE BAKIN ALJIHU KI JIƘO DA ƘAMSHI,KINA ZAMA AN SAN KIN ISA MACE HAJIYA DON AMMA ARAB TA SHARA SOSAI WAJEN KAWO MUKU KAYAN GYARA NA MATA* *AƘWAI SABULAN GYARAN JIKI SUNE KAMAR* *MULATO SOAP* *FACE CREAM* *FACE SOAP* *MULATO WHITENING LOTION* *HAIR GROW OIL* *HAIR GROW CREAM* *KAR-KAR OIL* *MINT LEAVE OIL* *ANTI PIMPUS SOAP* *AƘWAI SABULUN NANKARWA* sannan ina harkar👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻 *ABIN BUKI* *ABINCIN OFFICE* *SNACK* KAMARSU👇🏻👇🏻 *WAINAR MASA* *SINASIR* *MEAT PIE* *CINCIN ƊAN LAUSHI* *CUP CAKE* DA DAI SAURANSU. AMMA ARAB GIDAN GYARAN AURE😄👏🏻