[9/23, 12:35 PM] BintubatulBintUmarAbbale👄: 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 _*GIMBIYA BALARABA*_ 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 _*NA*_ _BINTA UMAR ABBALE_ *®BINTUBATULA👄* ```MARUBUCIYAR``` *NANA KHADIJA* *YARO DA KUD'I* *GIMBIYA BALARABA* *TSANTSAR BUTULCI* _*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*_ _________________________ ```We are here to educate, motivate and entertain aur Reades``` _________________________ _*DEDIGATED*_ _*TO*_ _RAHAMA ALIYU_ *NA GAISHE KU* 💝💝💝💝💝💝💝 ```AISHA SHAKA``` ```AISHA IBARAHIM``` ```ASIYA KEBBI``` ```AUNTY BABY``` ```FARIDA SK``` ```DOTANA MAHILLAH KDN``` ```MAMAN HANIF``` ```MAMAN KHAUSAR``` ```MAMAN SUHAIMAT``` ```MAMA QUIN``` ```MUM BASMA``` ```NAFISA IBRAHIM``` ```NANA AYSHA KDN``` ```NAFISA AHAMAD``` ```PREETY``` ```IBNAT BARHAM``` ```SEEMA ATIKU``` ```ZAHRA``` ```MAMAN UMMYTA``` ```CIMA KADI``` ```SHAFCYN SAFNY``` ```HAFSAT USUMAN``` *KUNA DA YAWA YASIN, WANDA BAI JI SUNAN SA, YAYI HAKURI GURIN COMMENT YASA NAKE GANE WANDA YAKE BIBIYAR LITTAFIN, NAGODE K'WARAI DA GASKE* *🅿106* Part hud'u ne a shashen nasa guda biyu a jere, biyu na kallon juna, gurin zaman mutum hudu. kenan, dama tuntuni Mama tasa an gyarawa Balaraba wanda yake kusa da nasa sauran biyun kuma Halisa da Azima,, ko wacce danginta sun kashe mata kudi sosai duk da da akwai wani abubuwan da suka tarar a ciki,, ko wacce tana tare da bayin ta kasancewar su "yayan mulki, Mama ta had'a Balaraba da bayi mata gudu biyu ko sa dunga d'ebe mata kewa Balaraba babu yadda zatayi ne , amma da don ita ne, bata bukatar wasu bayi,, dakanta ta rako ta har d'akinta,, tana k'ara yi mata nasiha. To su Shahid suka gama barkwancin su suka d'ebi matansu suka tafi,, suka barshi shi kadai a falo yana sak'e-sak'e daga bisani ya mike ya haura sama domin ya watsa ruwa. Gimbiya Halisa bayan " yan rakiyar ta sun tafi sai ta mike ta shiga toilet ta sake sabon wanka da turaririka masu kamshi ta futo ta goge jikinta sosai ta mulka turaran fata ta d'auko wasu kayan bacci masu dogon wando ta sanya a jikinta ta d'auki hula ta sanya, hijab din da take sallah ta zura ta kulle shashen ta, kai tsaye nasa ta nufa. Yana sama lokacin da ta shiga falon tsitt bakajin komai sai sautin Ac, sama ta hau gabanta na fad'uwa wai ango na kai kansa ga amarya yau ita ya kawo kanta. Yana zaune kan kujerar miroow yana gyara sumar shi tayi sallama ta shiga,, amsa mata yayi yana daure igiyar rigar baccin sa,, zama tayi gefan gado Kamar munafuka, ya kalle ta tw cikin madubi yana b'oye dariya yace "Kin gama fushin kin zo" Sakin fuska tayi tana wani fari da ido, ya d'auke kansa yana girgiza kai ya cigaba da taje sumar sa, ajiyar zuciya ta sauke lokacin da ta kalle shi,, wani irin shauki yana tsirga mata, mik'ewa tayi yace"Je ki dauro Alwala muyi nafila ta godiya ga Allah". Gyara zama tayi tace"Da Alwala ta" "Babu laifi sai ki tashi muyi" mik'ewa tayi ta gyara shimfidar dadduma suka tada sallama, ya jima sosai yana addu'a kamar yarda addini ya tana ya shafa itama ta shafa, mik'ewa yayi ya kashe futular dakin domin wani sa'in baya son haske mussaman in zai kwanta ya zauna gefan gado yana Dan kallonta babu yabo babu fallasa yace"Kinci abunci" daga kai tayi yace"To zo ki kwanta,, Halisa ta mike tare da cire hijab din ta ta haye kusa dashi tana nanak'ar shi,, shiru yayi yana shakar kamshi ta, mutsu-mutsu ta dunga yi , ya jawo ta jikinsa ya rungume yana sauke ajiyar zuciya, to takaice dai anan labari ya sauya suka shiga soyayya. Halisa ta gurzu gurin Yallab'ai wanda tazo tana da ta sani jikinta duk ya shika Sai nishi,take to itama dai Kamar Azima ne bata fuskanci Komai sai bak'ar azaba. Babu laifi ya samu nutsuwa da ita,, amma dai duk da haka yana jin zai iya k'arawa tausaya mata kawai yayi ya rabu da ita,, abunka da mara jiki kafun Safiya ta kara zabgewa, da kanta taje gasa jikinta da ruwan zafi ta futo daure da alwala lokacin ya shirya tsaf yana k'okarin sauka kasa, ba tare da,ya kalle ta ba yace"In kin gama ki sakko k'asa" Kallo ta bishi dashi wato ita bazai tsaya ya riketa ba kamar yadda ya rike Azima aikwa bazata sauka ba,, Ma'aikatan sa ne suke aikin gyara gurin an gyara komai yadda ya dace, abun kari ma na kan daining gwanin sha'awa, yana saukowa suka dunga kwasar gaisuwa yana amsa musu Cikin nutsuwa suka futa,, minti goma tsakani Azima ta shigo cikin Uwar kwalliya sai baza k'amshin take ga gwal ko ta Ina, kusa dashi tazo ta zaune tana masa k'yataccan murmushi,, tace"Yallab'ai barka da Safiya fatan ka tashi lafiya"? Kwalliyar tata tayi masa kyau ya juyo yana kallonta fuska a sake yace"Lafiya Lou na tashi, kefa"? Tayi wani fari da ido tace"Ni ma haka" hannunsa ta rike tana wasa da zoban dake hannunsa, Cikin dubara tana cirowa tana mayar wa cikin wani irin salo"" sosai abun yake tab'ashi ,tsigar jikinsa ta hau tashi,, Sarki! Mutum ne mai Lafiya da kuzari ko Yaya yaji mace a kusa dashi sai yanayin jikinsa ya sauya, ya rik'e hannunta yana murzawa kad'an-kad'an, Azima ta samu abunda take so,, sai tw hau zuba masa hirara cikin sigar Jan hankali. Cikin nutsuwa tayi sallama ta shigo,, duk su biyun suka daga kai suna kallonta, k'asan mak'oshi ya amsa,, yana d'auka kansa kamar Wanda bai ji dadin ganinta ba,, itama d'auke kanta tayi har ta k'arasa in da suke, ta zauna kujerar dake kallonsu, fuskarta a sake, tamkar bata ga abunda suke ba, tace"Barkanku da Safiya Yallab'ai fatan ka tashi lafiya"? Ido da ido suke kallon juna ita dashi, itace ta fara kauda kanta,, ya amsa da "Lafiya nake kefa"? " Nima Lafiya lau na tashi" "To masha Allah" Cikin kissa Azima tace"Yar uwa ya kike"? Balaraba ta saki fuska tace"Ina lafiya lau" daga haka taja bakin ta tayi shiru, Azima ta cigaba da yi masa surutu shiko hankalinsa na kan Balaraba, gyaran murya yayi yace"Jimana" Balaraba har tasaba da wannan sunan, idonta ta d'ago tana kallonsa, baza ka tab'a tantance abunda yake zuciyarta ba. Cikin bada Umarni yace"Ki hau sama ki kira Halisa" Kallonsa tayi cikin mamaki, shima ita yake kallo,, zuciyarta tace "Kibi umarninsa ki dakewa zuciyar ki" mik'ewa tayi a nutse ta fara tafiya, ya bita da wani mayan kallo, dama abunda yake so kenan yaga kwalliyar ta,, tana sanye da atamfa "yar ingila dinkin Riga da zani ne simple sai dai rigar " yar k'arama ce,sosai iya kacinta cikinta bata rufe mata mazaunai ba,, tayi amfani da siririn mayafi tayi rolling din kanta dashi,, sannu-sannu take taka k'afar bene jikinta na motsawa as'usuel,, tanayi bada wata manufa sai dai hakan da ya zama nutural d'inta ta shige dakin" daga tashin ta har shiga dakin a kan idonsa ya dunga mik'a wuya yana lek'en ta sam ya manta da wata Azima dake zaune a kusa dashi,, ajiyar zuciya ya sauke ya dawo hayyacin sa,, Azima ta muzanta sosai ganin yadda kamaninsa suka sauya sosai jikinta yayi sanyi tarasa wace irin masifa ce wannan, ta lura fa mutumin nan ya kwallafa rai akan Balaraba ko dame ta fisu oho, Suna had'a ido dashi ya b'ata fuska gami da waskewa yana kallon agogon hannunsa kamar Wanda zashi wani guri, ya mike ya nufi daining cikin k'asaita, bayansa tabi jiki a sanyaye. Tare suka sauko Halisa sai ya mutse fuska take,, kai tsaye daining din suka nufa,,,, kallonta yayi yace"Ke da nace ki sauko k'asa shine kika zauna". Karyar da kai tayi tana fad'in"Jiri nake ji shine na koma na kwanta shiru tayi kawai yana kallon Balaraba da ido yayi mata magana wai ta had'a musu abunci, ta gane Abunda yake nufi sai ta share shi zuciyarta na zugata kar tayi wato Dan yaga ita ba "yar sarauta bace shine yake sanya ta Aiki.. " Nace ki had'amin abunci gimbiya" Abunda ya furta kenan ya waske tamkar bashi ba,, Dan kar ta bashi kunya yasa ta fara had'a musu abuncin cikin nutsuwa tana addu'ar Allah yasa kar ya k'ara tsuro mata da wata futinar. *INA LABARIN WAZIRI DA TSITO KULU ME D'AKIN KUDU* MUJE ZUWA. [9/24, 5:59 PM] BintubatulBintUmarAbbale👄: 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 _*GIMBIYA BALARABA*_ 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 _*NA*_ _BINTA UMAR ABBALE_ *®BINTUBATULA👄* ```MARUBUCIYAR``` *NANA KHADIJA* *YARO DA KUD'I* *GIMBIYA BALARABA* *TSANTSAR BUTULCI* _*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*_ _________________________ ```We are here to educate, motivate and entertain aur Reades``` _________________________ _*DEDIGATED*_ _*TO*_ _RAHAMA ALIYU_ _*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR RAHIM*_ *🅿106* Hannuwan ta ya zubawa ido kurr!! Sun sha uban Jan lalle wanda yayi jajazur har ya fara yin b'aki, sosai abun ya burge shi kuma ya bashi sha'awa,, nata duk ya fi tafiya da imaninsa, nasu Halisa bak'i ne, irin wanda ake zanawa shima yayi kyau babu laifi, kowa da kalar nashi,Cikin nutsuwa ta had'a plate uku kowa da nashi,, ta mik'a masa nashi tana fad'in "Bisimillah" Ajiyar zuciya ya sauke yana lumshe ido yace"Ke ina naki plate d'in, kin had'awa kowa nashi" babu yabo babu fallasa tace"Na ci abunci kafin na futo,, kai tsaye yace"Ko kinci dole kici na nan, ka'ida tace, wannan" Cikin mamaki ta kalle shi, ganin yanda ya b'ata fuska yasa ta fara zuba abuncin domin bata son ayi ta Jan magana,,Shiru gurin yayi, sai motsin cokola, satar kallonsa take yanda yake cin abunci kamar baya so,, ita kanta taunar sa ma abun kallo ne, Halisa kanta ya k'ara girma ganin yanda yake kula da ita domin shine ma ya tsiyaya mata ruwa,, ya mik'a mata lokacin da ta k'ware ganin, yana sanya Balaraba aiki yasa suka kara mike kafa suna ganin sun fita daraja a gurin shi kuma yasan su dama basu saba da aikin wahala ba,, shine ya fara mik'ewa daga gurin,, ganin ya tashi yasa ta mike da sauri ta gudu part d'inta... To Azima ma da ta kammala mik'ewa tayi ta wuce part din ta, aka bar Halisa tunda itace take da miji a hannu jiya da yau. ******************** ******************** Tsito da Waziri ne zaune cikin duhu,, Aljani Mak'asudu ya hauro kan Tsito nan suka fara magana da Waziri,, yana fad'a masa buk'atun sa, Mak'asudu yace"Akwai alkwarina a kanka na k'afa biyu kar kace na manta da wannan alk'awarin ina sane dashi, kuma sai na bi jinina,, wannan buk'ata kuma da kawo mana, zata biya amma da sharad'i idan ka kuskura ka kauce sharad'in da muka gindaya maka to sharrin zai koma kanka kaji!!!!!!! Ko"!!!!!!!? Waziri yace"Arne ya dafa maka ai duk sharad'in da kuka gindaya min ina me tabbatar maka da cewar zan bishi bazan kauce ba" Mak'asudu yasa dariya yana fad'in"Shikkenan ni zan jirge!! Yanzu amma zan Sanar da Tsito duk sharad'inmu sai ya fad'a maka" Waziri yace"A sauka lafiya Mak'asudu me mukulin mulki mak'asudu d'an gidan K'azaza gaba salamun baya salamun Ubana"" Tsito ya dunga wata irin katantanwa a tsakiyar d'akin yana wani irin ihu!!!!!! D'if dakin yayi shiru kamar anyi ruwa an d'auke. Wajan minti goma Tsito ya dawo dai-dai cikin duhu ya kalli Waziri yace"Da alama d'azu muna magana da kai Mak'asudu ya hauro ko"? Waziri ya gyad'a kai yace"Akwai sak'on da yace zai fada maka ka fada min" Shiru Tsito yayi yana sauraron Mak'usudu sai gyad'a kai yake alamun yana sauroro,, bayan ya gama sauraron Mak'asud'u ya kalli Waziri yana fad'in"Yace"Mu nemo bak'ar kulb'a da bak'ar kunama sai bak'in b'era dunka sai tsohon kadan gare Wanda ya soma sab'a saboda tsufa, duk a yanka su a cire musu fatar jikinsu,, a shanya ta bushe, sai ka kafa kusa a d'akin ka, duk ka kafe fatocin bango d'aya ka samu Jan yanki kasa a tsakiya, bayan nan kuma hanjin su,, a had'a shi guri guda a sanya su su bushe a dake lukwi sai a zuba masa a abunci, da iziinsa sai ya mutu idan bai mutu ba to zai rasa wani b'angare na jikinsa, sannan in ka kuskura mutum ko guda ne, ya shiga dakin Da ka kafe fatocin nan to abun zai dawo kanka,,sai magana ta k'arshe yace"Ka tafi bakin kogi da k'aton rago me tozali ka yanka masa zai shanye jinin" Waziri yace"Duk za'ayi da izininsa mutukar bukatar zata biya, yanzu yanda za'ayi na samu wad'annan dabbobin shine abun dubawa" Tsito yace"Wannan babu matsala gobe sai ka futa dani a mota ni zan samo maka,, sai dai ka ware min lada na" Waziri yace"Duk kar ka damu zan maka kyauta ta ban mamaki in zaka tafi" Nan sukayi sallama Waziri ya futa yana godiya ga Mak'asudu. ************************* ************************* Kwanan Sallau Uku a asibiti yace ga garin ku nan, Lantana ta dunga kuka kamar ranta zai futa,, Uwa! Ma duk da ya sake ta ta koko da mutuwar Sallau,, Shamsiyya kuwa tun sanda ta dawo daga gidan Arrama ta kwanta ciwo kariris,, Amai da zazzab'i duk ta rame ta jeme sai uban zubar da miyau da takeyi,, jama'a 'yan zaman makoki dayawa duk San fahimci ciki ne da ita Uwa! Ta gane da sauran mutan gidan rudanin mutuwa ya hanasu nuna b'acin ransu domin hausawa nacewa wani tashin hankalin yafi wani,,, Lokacin da Balaraba taji mutuwar Sallau kuka ta dungayi sosai, Mama tai ta rarrashin ta, tare suka tafi Da ita da du Halisa Madabo ma taje,, Sarki kuwa dashi akayi jana'izar Sallau, unguwar ta d'auka wanda ma bai yi niyyar zama gurin mutuwar ba dalilin zaman Sarki! A gurin ya zauna,, ya sa aka kafa rumfuna sosai mutane suka zo suna kwasar girgi harda wadanda suka futa kasuwa, sai su dawo domin su kwashi abuncin gidan mutuwa, kullum sai sun zo har a kayi sadakar uku,, Balaraba suka dawo gida cikin jamami,, tayi mamaki da har aka share zaman makoki bata ga Iro da Mabaruka ba, har dai ta gaza hakuri ta tambayi Iya ina suke, sai tace"Mabaruka dai tafi sati hudu rabon ta da gida, shi ko Iro tun kafin ki bar gidanan aka neme shi aka rasa, tace"Shamsiyya fa"? Iya ta girgiza kai tana goge kwalla tace"Tana cikin daki ta d'auko abun kunya shiyasa take buyarwa jama'a" Balaraba ta dunga share hawaye tana tausayawa rayuwar su,, Shamsiyya kuwa tana jin ance ga Balaraba tazo zata dunga lekowa tana taga tana kallonta tana fad'in ina ma itace. ************************* ************************* Duk abubuwan da Mak'asudu ya ce a nemo sun nemo kuma sun aiwatar da aikin kamar yarda yace d'in abunda ya rage wa Waziri shine zuwa bakin ruwa ya yanka rago shima ya sa d'amba gobe da Asuba zai futo domin an samo ragon irin wanda Mak'asudu ya buk'ata... Yau ne girki Balaraba ya kama,, duk dama wancan kwanakin ya na Cikon na Halisa ne, sai Azima da yayiwa kwana uku, wannan mutuwar da akayi yasa Balaraba taga kamar kwanakin sunyi sauri, ita fa bata lissafin komai yanzu duk bata cikin hayyacin ta domin mutuwar Sallau sai ta dawo mata da ta iyayen ta sabuwa,, jiki a sanyaye take yin komai, k'arfe shida ta kammala girki mai rai da lafiya tayi Wankanta gami da fesa turare ko ina a jikinta, tana sanye da wani material sky blue yayi mata masifar kyau, inda tayi amfani da k'aramin mayafi tayi rolling dashi,, anyi mata kitso ta tattare shi a tsaki ta sanya manya-manya ribom sai ya zama kamar a cuci tayi kyau sosai d'inkin Riga da sket ne,, tayi fuskarta fayau,, ko kwalli babu sai mai leb'e da ta goga,, a nutse ta dunga d'ibar kayan abuncin tana kaiwa part d'insa,, su Amina da Hadiza bayinta sukayi-sukayi ta barsu su d'aukar mata tak'i tace"su barshi itama ladan take so, sai suka hak'ura suka k'yaleta ,, lokacin yana sama ta gama shige da fucen ta, ta koma part d'inta sai bayan tayi Sallahr magariba ne, sannan ta kimtsa, da niyar komawa part din nasa. Da shirin zuwa masalaci ya sauko hankalin sa bai kai kan daining ba, sai Mai dafa masa abunci fa ya gani a tsaye tsakiyar falo ya sunkuyar dakai kasa, gyaran murya yayi da sauri ya dago yana masa barka da sakkowa, Yace"Kana tsaye gashi ana shirya-shiryen tayar da sallah" Yace"Allah ya taimaka ke Nazo zan jera abunci na ga an jera wani nace Allah yasa ba laifi nayi ba" Kallon daining teble din yayi yaga wasu had'addan kuloli ba Wanda aka saba zuba masa abunci ba,, girgiza kai yayi kawai, yasan aikin Gimbiya ne, yana k'okarin tafiya yace"Yau an hutar sheka, gobe ma kar kayi gudun asara ka futar muku da Wanda ka girka" Yana gama maganar ya futa,, Shi kuma ya koma kicin, cikin zuciyarsa take cewa amma wannan matar tasa ta tarbiyantu ba kamar sauran ba, Allah ya kyauta. [9/25, 7:58 PM] BintubatulBintUmarAbbale👄: 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 _*GIMBIYA BALARABA*_ 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 _*NA*_ _BINTA UMAR ABBALE_ *®BINTUBATULA👄* ```MARUBUCIYAR``` *NANA KHADIJA* *YARO DA KUD'I* *GIMBIYA BALARABA* *TSANTSAR BUTULCI* _*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*_ _________________________ ```We are here to educate, motivate and entertain aur Reades``` _________________________ _*DEDIGATED*_ _*TO*_ _RAHAMA ALIYU_ _*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR RAHIM*_ *🅿108* Sai bayan sallahr Isha'i ya shigo, zama yayi a falo da carbi a hannunsa yana ja,, a hankali ya dunga jin wani sanyayyen k'amshi na ziyartar hancin sa, d'aga kansa yayi yana kallon inda yake jin motsi, Balaraba ce take saukowa daga matattakala cikin nutsuwa, a sirance ya sauke ajiyar zuciya ya su kunyar da kansa wani Abu na tsunkullin sa,, ta k'arasa daining cikin nutsuwa ta gyara komai ta tako a hankali ta zauna kujerar dake kallon sa, kansa na k'asa bai dago ba, a hankali tace"Barka da dare" d'ago kansa yayi yana kallon ta, minti biyu yace"Barka kin wuni lafiya"? "Lafiya Lou ta fada'a tana wasa da hannunta,, yace" Ya k'arin hakuri kuma" ? "Alhamdullahi" Shiri falon yayi sak'e-sak'e take a zuciyarta, shi kuma yana k'okarin ya cika carbin sa,, sai da ya kammala sannan ya aje ya d'auki wayar sa, numbar Halisa ya kira tans d'auka yace"Ki futo muci abunci " kashewa yayi ba tare da ya saurari abunda zata CE,ba, numbar Azima yake nema, sai gata ta shigo cikin uban kwalliya ta k'ananun kaya wanda suka d'ame ta,, b'ata fuska yayi lokacin da yayi arba da ita, kusa dashi ta zauna tana gaishe shi cikin wani irin salo,, a dakile ya amsa, yace"Wannan wane irin iskanci ne zaki futo da wannan kayan na jikin ki"? Azima ta sunkuyar da kai tana fad'in 'Yallab'ai me ye laifin su" A fusace! Yace"Ba duguwar magana na nema ba,, magana ta farko ta k'arshe kar ki sake futowa da irin wannan kayan in zaki saka kayan ki ki saka Ke ka dai a daki ba sai kin nunawa jama'a ba, gida cike da mutane ki futo min da wannan shashancin" Ganin ransa ya b'aci yasa ta fara bashi hakuri , ko sauraron ta baiyi ba ya mike ya nufi gurin cin abunci ransa in yayi dubu ya baci"! Balaraba kuwa taji dadin abunda yayi wa Azima ta lura tayi shigar ne Dan Taja hankalin sa, a randa ba girkin ta ba, dariya kawai take mata Cikin zuciyarta tace"Wallahi wani lokacin mutumin nan na burge ni da halinsa baudadden mutum ne! Gyaran murya yayi Balaraba ta mike da sauri kar ta samu rabon ta,, Azima ma ta mike jiki a sanyaye,zama tayi, daya daga cikin kujera ita kuma ta fara zubawa kowa nashi cikin nutsuwa, Halisa tayi sallama ta shigo,,, itama ansha kwalliya kamar masu zuwa gasar fidda kyau!! Gwara ita material ne, a jikinta dinkin riga da sket kusan irin na Balaraba kala ce kawai ta banbanta,, gaishe shi tayi ya amsa ba tare da ya kalle ta ba,, sama-sama suka gaisa da junansu ko wacce na danne Kishi a zuciyarta. Balaraba ta zubawa kowa nashi ta zauna ta fara cin nata cikin nutsuwa. Sarki! Yaji dad'in girkin Balaraba sosai ya bude ciki ya ci ya k'oshi ya yagi tissue ya goge bakin sa,, da kuzari a jikinsa ya mike daga gurin, falo ya koma ya zauna,, to suma dai su Halisa sunji dadin girkin shiyasa babu wacce tayi k'orafi suka cinye plate din tass ko wacce ta tashi tana goge bakinta,, Balaraba ta gyara gurin tsaff!! Ta isa in da suke,, k'asa-k'asa yake kallon ta ganin tana k'okarin futa,, yace"Ina zakiji kuma? Duk gashi muna zaune da juna" A takure take jin jikinta kasan cewar tana cikin halin rashin tsarki,, wannan motsa jikinta da tayi Duk pad din ta ta jik'e haka take a rana sai ta sanya sau biyar,, tace"Yanzu zan dawo zan Dan watsa ruwa ne"" Nan ma akwai toilet kin shigo kenan ki dawo ki zauna" wannan halin nasa yana bata haushi wallahi, to in ta dawo ta zauna yana da pad din da zai bata oho masa,,, zama tayi kujerar dake daf da bakin kofa ranta a bace, duk ya lura da yanayin da take ciki,, Azima sai watsa mata d'an iskan kallo take,, Ita ko Halisa sai hira take masa yana biye mata,, goma shaura, sukayi masa sallama ko wacce ta wuce part d'inta, falon yayi shiru da shi sai ita mik'ewa yayi ya nufo inda take zaune,, Balaraba ta sunkuyar da kanta tana jiran taga me zaiyi,, kulle k'ofar yayi ya cire key din,,, ta kalle shi bakin ta na rawa tace"imm... Ina da Uziri a gurina fa,, yanzu zan futane in je in dawo naga kuma ka kulle kofar" Tsayuwa yayi a kanta yayi mata rumfa! Cikin wani irin voice yace"Me zaki je kiyi? Uhumm kin ce wanka nan babu toilet ne"? Girgiza kai tayi yace"To kin gani, tashi muje ki gyara min shimfid'a ta"" ta d'ago dararan daran idonta tana kallonsa,, lallai akwai rigima kenan mutuk'ar ya san halin da take ciki, yaya za'ayi ta fada masa,,, hannunta ya kama ya mikar da ita tsaye,, zura hannusa yayi ya rungumo k'ugunta suka fara tafiya, a haka suka dunga hawa mattatakala duk rabin jikinsa na jikinta,, lokaci guda ya soma neman nutsuwar sa,,, zama tayi gefen gado ya shiga toilet ya futo daure da alwala yace"Ki shiga kiyi wankan sai ki dauro alwala kizo muyi nafila" babu musu ta mike ta shiga toilet din,, Wanka tayi sosai,, ta sanya towol ta goge jikinta ta maida kayan jikin ta,, tana futowa taga ya shimfid'a dadduma yana tsaye yana jiran ta,, hijab ya mik'a mata, ta karb'a amma bata sanya ba,, ik'ama yake so ya tayar ya kalle ta yana fad'in"Ki sanya mana" A nutse tace"Bani da tsark" Yaji wani irin fad'uwar gaba, amma dake Namijin duniya ne,, sai ya maze Dan kar ta gane,, yayi minti biyu yana nazarin ta daga bisani ya tada sallahar shi,, zama tayi gefan gado jikinta a sanyaye , Ya dade kan dadduma yana addu'a har ta fara gyangyad'i,, ya mike a nutse ya kashe wutan dakin,, bed din ya nufa Balaraba tayi tsuro tana kallon inuwar sa,, sai da yw zauna sannan ya cire jallabiyar da take jikinsa,, babu zato taji ya jawo ta jikinsa, gabanta ya dunga fad'uwa duf!!duf!! Zif din yake k'okarin zugewa tayi saurin dafe hannusa,, kansa ya zura tsakanin wuyanta yana sakin ajiyar zuciya daki-daki,, k'okarin hanashi take, amma sai da yayi nasarar zuge mata zuf din ya cire rigar ya jefar kwantar da ita yayi k'asan shi yayi mata rumfa, Balaraba sai motsi take da bakinta taka cewa komai duk inda ya kai hannunsa sai ta kai nata duk a k'okarin ta na hana shi abunda yakeyi ya ta kasa,, sai ma jikinta da yayi la'asar sakamakon uban soyayyan da yake zuba mata,, Balaraba taji kamar ba a duniya take ba,, ta shagala Wanda ba san ma yayi nasarar cire mata brziyya ba,, aikuwa ta gigice amma yanai mata wani salo tuni ta bada kai bori ya hau suka hau soyayyar su irin ta ma'aurata,, Sarki! Ya sha mutukar wahala lafin ya samu nutsuwa,, Balaraba kam jin ta take a sama, ta manta a wace duniyar take, ita dashi sai sauke nuffashi suke,,,,, wani irin kullewa mararsa take,, shi kansa yasan ba duka ya zubar da abun ba, yanzu shine damuwar sa, zai iya shiga mugun hali, mutukar bai samu yayi sex ba, domin shine katt! Shine za samu sukuni,, a galabaice ya kira sunanta, ta amsa murya na rawa yace"Ki yarje min na je gurin "yar Uwar ki na biya buk'ata ta, ina Cikin wani hali" Sosai ta tausaya masa,, cikin raunin murya tace"Babu damuwa, ai dama amfaninmu kenan, na yarje maka kaje kawai" mik'ewa yayi yana zura jallabiyar sa,, Albarka kawai yake sa mata,,, sauka yayi daga bed din ya d'auki key zai futa, ta kira sunansa juyo wa yayi yace"Menene uhumm? Kiyi hakuri Yanzu zan dawo"' shiru tayi haka kawai taji kwallah na k'okarin zubo mata,, ya fuce da sauri,, Azima tafi Halisa dauriya, saboda haka shashen ta ya nufa Cikin duhun dare, dam ma akwai hasken futulu a wasu guraran,, Azima na zaune a gefen gado ta zabga uban tagumi sai tunani take kana kallonta kasan akwai abunda yake damunta,, taji ana bugu tana k'okarin tashi taji karar wayarta,, tana dubawa taga Sarki! Ne hannu na rawa ta d'auka, yace"Bude min kofa" jiki na rawa ta je ta bud'e masa ya shigo ta mayar da kofar ta rufe,, kai tsaye bed din ta ya nufa,, ta bishi a baya,, tana shiga ta ganshi yana k'okarin cire Riga, tace"Lafiya Yallab'ai "? Kwanciya yayi bed din ta yace" Zo" Azima ta gane me ke da akwai,, zuciyar tace mata Allah ya kawo miki shi har dakin ki,, da sauri ta nufi friji ta d'auko Lemo mai sanyi ta k'araso kusa dashi,, tace"Yallab'ai tashi ka fara shan Lemo nasan ranka a b'ace yake"" sama-sama yake jinta ya mike ya karb'i lemon dake hannuta ta bud'e masa ya shanye Tass! Ta karb'i robar ta aje,, kashe futular tayi ta rungume shi,,, cikin mawuyacin hali ya biya ma kanshi buk'ata,, yana gamawa yaji wata irin muguwar kasala ta rufe shi,, da k'yar ya koma part d'insa, Balaraba na zaune ta rafka tagumi jiran dawowar sa kawai take, ya shigo ta bishi da kallo ya shigowa ya kwanta babu abunda yace mata,, kusa dashi taje ta kwanta gabanta na fad'uwa,,, da k'yar bacci ya dauketa mai cike da mafarkai! Asubah ya farka tare!dashi, ya d'aga kafa zai sauka k'afar tak'i d'aguwa yayi-yayi taki motsi sai wani yammmmmmmmm!!! Take masa. [9/26, 8:47 PM] BintubatulBintUmarAbbale👄: 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 _*GIMBIYA BALARABA*_ 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 _*NA*_ _BINTA UMAR ABBALE_ *®BINTUBATULA👄* ```MARUBUCIYAR``` *NANA KHADIJA* *YARO DA KUD'I* *GIMBIYA BALARABA* *TSANTSAR BUTULCI* _*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*_ _________________________ ```We are here to educate, motivate and entertain aur Reades``` _________________________ _*DEDIGATED*_ _*TO*_ _RAHAMA ALIYU_ _*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR RAHIM*_ *🅿109* Kalmar Innalillahi wa'ina ilahi raji'un itace ta futo daga bakin sa, yunk'urin d'aga k'afar ya kuma yi a karo na uku, tak'i motsawa,, hannu yasa ya d'agota yaji wani Yammmmmmmm! Mara dad'i Dole tasa yayi saurin aje ta saboda ji yayi abun har tsakiyar kansa,,, zufa duk ta jik'a masa jiki kamar babu sanyi asubah,, salatin da yake ne,, ya farkar da Balaraba ta mike a zabure itama bakin ta na fad'ar kalmar Innalillahi wa'ina ilahi raji'un, saboda wani irin mumman mafarki da tayi,, hannuta ya Kamo ya rik'e tamm!! Suka tsurawa juna ido,,, gumi taga goshin sa nayi,, yana ta cije baki!! Bakinta na rawa tace"Yallab'ai baka da lafiya ne"? Da k'yar ya gyda mata kansa, yace"K'afata ta rike min" gabanta ya fad'in,, cikin zuciyarta tace"Kar dai mafarkina ya zama gaskiya,, hannu takai kafar tana shafawa idanunta har sun soma zubar da ruwan hawaye,, a hankali yace" cire hannun ki babu dad'i" da sauri ta cire hannun nata tana kallonsa,, cikin dauriya yace"Yaya za'ayi nayi sallah" tace" Ko in kama ka mik'e"? Gyad'a kai yayi yana murmushi me ciwo yace"Baza ki iya ba,, mik'omin waya ta""" sauka tayi da sauri ta d'auko wayar ta mik'a masa,,, numbar Shatima ya kira,,,, ya fada masa halin da yake ciki,, cikin tashin hankali Shatima ya futo daga gida,, kai tsaye gidan sarautar ya nufa lokacin har an idar da sallahr asubah,, Balabara na durkushe a gabansa jikinta sanye da hijab,, ba ta cire ba,, Shatima yayi sallama ya shigo,, zama yayi yana duba k'afar,, cike da alhini yace"Kurum wayar gari kayi kaji k'afar taki ta kuwa"? Sarki! Ta girgiza kai shi kadai yasan ciwon da yake ji yace"Da sauk'i ai idan kin takuwa tayi,, taki motsi fa" Shatima ya Dora hannunsa k'afar yana salati,, wayarsa ya Ciro yana kiran dector dake duba Sarki!! Yace"yazo yanzu yanzu,,, "Kamani in mik'e in kama ruwa sai in d'aura alwala inyi sallah". Shatima ya mike yana kici-kici ya samu ya mik'e inda Allah ya rufa asiri ma k'afa d'aya ta taku itama da k'yar da dafa bango suka je toilet yayi uzirin sa, kana ya dauro alwala suka futo,, dadduma ta shimfuda masa,,, cikin zuciyarta sai tasbihi take Allah ya gajar ta musu wahala [9/26, 8:42 PM] BintubatulBintUmarAbbale👄: Da Jan k'afa suka k'araso gurin yayi nufin ya tsaya abun ya gagara,, sai ya zauna a nutse yayi sallahr sa,, duk suna tsaye suna kallonsa Balaraba sai goge hawaye take,, Shatima ko ya kira numbar Shahid yafi Sau a kirga bai d'auka mybe baya kusa,, dector ya shigo da kayan aiki,, cikin girmamawa ya gaida shi ya amsa a nutse ya fara yi masa tambayoyi,, Sarki! Ya fada masa duk abunda ya faru,,, A hankali ya kama k'afar yana dubawa,, lafiya Lou da ita a ido,, matsata yayi sarki! Ya cije baki!! Yace"Kar ka k'ara matsawa,, dector ya cire hannunsa da sauri yana neman afuwa,, yace"Yallab'ai ina ganin dole zamuje hospital dakai domin mu auna k'afar dole kuma a d'auke hoton ta, domin sanin maganin da ya dace da ita" Gyad'a kai kurum yayi,, Shatima yace" Bari insanar da Mama Halin da ake ciki,, babu Wanda yace masa komai,, yana sauka k'asa suka ci karo da Halisa ta shigo,, da fara'a ta tsaya suna gaisawa da alama batasan abunda yake faruwa ba,, Shatima ya wuce bai fada mata ba,, kai tsaye sama ta nufa cikin k'asaita! Tana shiga taga Balaraba durk'ushe gaban shi tana kuka, ga dector a tsaye a gefe yayi shiru fuskar sa ta kalla taga alamun alhini ta k'arasa da sauri kusa dashi,, cikin kid'ima tace"Hubby menene wai naga duk kuna cikin damuwa!" Kallon ta yayi zuciyarsa a dake!! Yace"Babu komai ke me kika gani" ? Baki na rawa tace"Tashin hankali na gani"" d'auke kansa yayi baice mata komai,, Balaraba ta kalla tace"Menene "? Kafar sa ta nuna mata, tana kuka! Halisa ta kalli k'afar da sauri,, taga ta Dan kumbura" jiki a sanyaye tace"Ciwo take masa"? Balaraba ta girgiza kai tana fad'in "Idan ciwo ne da sauk'i yau tunda ya tashi ya kasa tafiya da ita tak'i motsi d'azu da k'yar aka kai shi toilet yayi alwala " Halisa tace"Innalillahi wa ina ilahi raji'un kuka ta fashe dashi tana k'unshe baki tace"Wannan wace irin masifa CE"???? Tsawa!! Ya daka mata yana fad'in"Bana son shashanci da koke -koke addu'a zakuyi min""""" a gigice ! Ta mike tana fad'in"Au! Da gaske ne Ashe? Sai ta kalli Balaraba Cikin daga murya tace"Ke nake zargi! Munafuka meye ribar ki anan, me yasa ranar da ya kwanta damu haka bata faru ba,, me kike nufi, bak'ar algumguma wato kina so ki kashe ki samu tumunin takaba"? Taji kamar ta watsa mata ruwan zafi,, a jiki ta dago jajayen idonta da suka rine!! Bakin ta na rawa tace"Mey...... Ka tsaye ta yayi ta hanyar daga mata hannu sai tayi shiru gami da toshe bakinta da gefen hijab dinta tana k'okarin b'oye kukan da yake k'okarin kufce mata a karo Mara adadi,,,, Halisa yake kallo cikin tsantsar b'acin rai da takaici. [9/27, 4:53 PM] BintubatulBintUmarAbbale👄: 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 _*GIMBIYA BALARABA*_ 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 _*NA*_ _BINTA UMAR ABBALE_ *®BINTUBATULA👄* ```MARUBUCIYAR``` *NANA KHADIJA* *YARO DA KUD'I* *GIMBIYA BALARABA* *TSANTSAR BUTULCI* _*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*_ _________________________ ```We are here to educate, motivate and entertain aur Reades``` _________________________ _*DEDIGATED*_ _*TO*_ _RAHAMA ALIYU_ _ALHERIN ALLAH YA ZO INDA KIKE_ *NANA AISHATU KADUNA* _Hak'ika inajin dadin comment dinki ubangiji Allah ya kara kauna da aminci nagode sosai ina miki fatan alkairi a rayuwar ki🥰_ _*Kuyi hakuri yau pege din babu yawa zazzab'i ne ke damuna wallahi Ku sanya ni cikin addu'ar Ku*_ _*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR RAHIM*_ *🅿110* Suna had'a ido dashi ta kara rikicewa tana fad'in"Wallahi Hubby kar ka yarda da ita,, itace Silar faruwan wannan al'amari ko mara kunne ne yaji wannan abun yasan da akwai lauje cikin nadi,, shiyasa hausawa suke cewa idan takalan mutum mugun ice ne, idan ya samu guri yafi mai kudi iko,wallahi yanzu na daina ganin laifin masu kud'in da suke gudun talaka domin halin su ne ya ja mus............."Halisaaaa!!! Rufe min bakin ki anan gurin"" ya katse ta cikin wata muguwar tsawa"" gum! Tayi da bakin ta tana shashshekar kuka,, Balaraba na durkushe a gurin kai a kasa tana zurarar da hawayen bakin ciki,, murya a cunkushe! Yace"Duk futa bana son ganin Ku" da sauri dector ya futa Halisa ta futa simi-simi,, mik'ewa tayi kwata-kwata jikinta babu lak'a, suka had'a ido saurin d'auke kansa yayi ransa a bace kalaman Halisa ba k'aramin kona masa rai sukayi ba,, wuce tayi tana waigen sa, duk yana kallonta,,, tana futa ya sauke ajiyar zuciya me zafi. Tana sauka taga Halisa da Azima suna maganganu k'asa-k'asa suna ganinta suka hau rafka mata harara, d'auke kanta kawai tayi,, Mama ce ta shigo bayanta Jakadiya da Shatima Shahid da Madabo cikin tashin hankali ta nufi sama suka rufa mata baya,, kansa a kasa yaji shigowar su,murya Maman shi yaji a kansa, ya d'ago idonsa,, da sauri ta tsuguna kusa dashi tana masa magana,, cikin nutsuwa ya warware mata duk abunda ya faru,, cikin tawakkali tace"Allah yana ji yana kallo ko wane hali da kake ciki abunda za za'ayi yanzu muje hospital din ayi hoton kamar yadda dector ya fada insha Allahu komai mai sauk'i ne" A nutse ta ce da dector "Je ka d'auko while chair,, a d'auke shi,, da sauri ya futa, shiru dakin babu Wanda yayi magana har dector ya dawo su Shahid ne suka kama shi suka Dora shi kai, a hankali suka dunga sauka dashi, daga kafar bene, Mama na bayansu tans goge hawaye a fakaice. Balaraba ta mike da sauri ta tsaya har suka k'araso gurin,, kallonta yayi yaga duk ta tayar da hankalin ta, ta bashi tausayi wannan alama ce da ta nuna tana cikin damuwa kuma ta damu dashi sosai,, babu yabo babu fallasa yace da ita"Wannan kukan da kike ya isa haka, cuta fa ba mutuwa bace, shikkenan ni Allah bazai jarrabe ni, ba Wannan ba yana nufin shikkenan bazan kara taka k'afafu na ba, insha Allahu inaji ajikina wannan abun na lokaci kankani ne saboda haka Wannan koke-koken da kukeyi ya Isa haka" Balaraba tayi shiru tana gyad'a kai, Azima kuwa ai batayi shiru ba sai cewa tayi "Duk ba anan take ba Yallab'ai dole muyi kuka Hak'ika an zalince ka kuma bazamu bari ba,, wallahi ka gurgunce sai mun d'auki mummanan mataki akanta " duk jama'ar gurin suka bita da kallo cikin mamaki,,,!! Mama tace "Ku muje mu wannan tsayuwar bata da amfani,, Azima da Halisa suka rufa musu baya, Balaraba aka bari a baya tana tafiya salau-salau babu kuzari ko na kwabo a jikinta. Buba direba ya bud'e bayan mota suka d'auke shi suka saka ciki da gyara masa zama sosai sannan kowa ya shiga ya zauna,, ganin Matan nasa na k'okarin shiga ne ya dakatar da Buba,, kallonsu yayi cikin bada umarni yace " Ko wacce ta koma gurin ta""" umarni ya bawa Buba ya tada mota suka futa,, dake safiya CE, babu jama'a sosai a harabar gurin sai dai-dai Ku, motar na fucewa suka yo kan Balaraba da bala'i kowa na fad'in albarkacin bakinta,, Balaraba lalurar mijinta itace a gabanta shiyasa bata tanka musu ba,, wucewa tayi ta barsu a gurin suna zagin ta ta uwa ta uba.. Sun jima a gurin suna maida magana daga bisani kowa ya koma part d'insa,,, Azima labewa tayi sai da taga Halisa ta shige ta kulle kofa sannan ta futo kai tsaye b'angaran Waziri Zayyanu ta nufa... Da futowar su da shigar su mota da futar su daga gidan sarautar duk akan idon Waziri da Tsito ,, Tsito ya kwashe da dariya yana fad'in kaga aikin Mak'asudu ko, ai inda alkawairi to da cikawa,, kai kuma sai ka kula da haradin da ya gindaya maka" Waziri ya kece!! Da wata mahaukaciyar dariya" hahahahahaha"" Mak'asudu ka cika alk'awarina na yarda dakai akan aikin ka, daga yau zan fara mulkina cikin kwanciyar hankali da nutsuwa nasan wancan yaron ya zama musaki,, ka lalata masa k'afafu ya gama aiki, Hahahahaha""" [9/28, 5:55 PM] BintubatulBintUmarAbbale👄: 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 _*GIMBIYA BALARABA*_ 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 _*NA*_ _BINTA UMAR ABBALE_ *®BINTUBATULA👄* ```MARUBUCIYAR``` *NANA KHADIJA* *YARO DA KUD'I* *GIMBIYA BALARABA* *TSANTSAR BUTULCI* _*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*_ _________________________ ```We are here to educate, motivate and entertain aur Reades``` _________________________ _*DEDIGATED*_ _*TO*_ _RAHAMA ALIYU_ _*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR RAHIM*_ *🅿111* Zuwan Azima gurin yasa Waziri ya bar dariyar da yake yi,ya d'ora hannunsa akanta fuskarsa cike da walwala da farin ciki yace"Kin gama min komai yarinya ta, hak'ika kin cika "yar halak d'iyar abokina aminina ya iya haihuwa ki fad'i duk abunda kike buk'ata zan yi miki". Jiki a sanyaye Azima tace." Nifa na soma nadamar abunda nayi gaskiya yanzu ina dana sani" Waziri da Tsito suka kalli juna, Tsito yayi wani murmushi, Yace." Ki daina nadamar abunda kika aikata idan kuma kina jin tsoro kar sunan ki ya futo ranar da asiri ya tuno to duk ki daina, aiki inda Mak'asudu a ciki baya karyewa sai dai Idan wanda yayi aikin ne ya kar ya doka saboda kije ki kwantar da hankalin ki,babu abunda zai faru,daga yau ma zan fara aiki domin zan daure wa duk mutan gidan baki" Azima ta sauke ajiyar zuciya gaskiya halin da taga mijinta a jiki ya bata tsoro amma aikin gama ya Riga ya gama, Waziri yace"Shiga ciki ganin zuwa" simi-simi ta shige cikin gidan nasa. To duk wani alk'awari da Waziri yayi wa Tsito sai da yq cika masa mota guda akaiwa Tsito da tashi da ta kayan arzki ya tafi garin su, Hajiya Kulu ma tayi masa kyautar bajinta dake ba sosai take zama a gida ba shiyasa duk bata San abunda yake faruwa ba sai da Waziri ya shiga har gurin ta da sassafe ya sanar mata, murna ta dunga yi mak'iyinta ya gurgunce dama ita babban bakin cikinta shine kar yayi mulki tunda ita Allah bai bata 'ya'ya mata ba. Babu irin aune-aunen da ba'ayi ba, abu d'aya yake nunawa k'afafun shi lafiya suke, cike da dumbun mamaki da al'ajabi suka dawo gida suna tunanin meye abun yi, Waziri kuwa bayan sun rabu da Tsito gida ya koma ya shiga keb'antaccen d'akinsa da ya rataye fatocin su k'adan gare, Kunama da kulb'a gami da b'eran dunka bango guda ya kafe su, tsakiyar su wani Jan yanki ne a n daure wani Abu a tsakiyar sa, shiri yayi sosai ya nufi fada yana wani irin taku na k'asaita shiga Sarki aikuwa fada na cike da mutanan sa munafukai ya zauna suka fara aikin zugashi da wasashi shi kuma yana jin dad'i. ****** Yanda aka futa dashi haka aka shigo dashi dama tun safe Labari yaje kunnensu Limam da Galadima da Wambai don haka suna tsaye aka futo dashi daga motar, suna kallon ikon Allah kowanne yana mamaki da tu'ajibi k'afafun Sarki! Sun kumbura sosai, ba kamar d'azu da safe ba. A daran ranar mai girma governor yazo suka zauna da Sarki! Duk aka basu guri, dake akwai sha kuwa a tsakanin su, Governor yace."Ina ganin wannan ciwon naka tafarar d'aya anya ba jifa bane? Nifa ka sanni da lek'e-lek'e saboda yadda yanayin al'amarin namu yake, gaskiya ina zargin jifa ne kuma duk wanda yayi maka makusancin ka ne" Sarki! Yace."Kaga ni kuma bana wannan tunanin kawai nafi gazgata cewar jarraba ce daga Allah" Governor ya gyad'a kai yana tunani minti biyu yace."Shikkenan yanzu dai na sanya ayi mana vizar dani da kai dasu Shatima zamuje Saudi'a akwai k'wararun likitoci islamic a can insha Allahu kome ye zamu gane zamu samu sassauci" Gyad'a kai kurum yayi, . shiga don duk sun damu ne, amma sam baya jin wani ciwo a k'afar shi, illa kawai motsa ta da ya kasa yi duk da haka yanaji zai iya yin duk abunda mai lafiya zaiyi. Sallama sukayi governor ya mike ya futa mutanan sa suka rufa masa baya. To a can babban falon Fulani ma Ashe tattauwar da ake kenan Liman ne ya bada sha'warar suje saudi'a wannan Asibitin dai da governor yake magana akai. Ko da Halisa ta shiga part d'insa tun kafin ta zauna ya fattatake ta, jiki babu k'wari ta futa, tana da tasanin shirman da tayi masa d'azu. Balaraba kuwa abunda tasan zata d'auka taje ta d'auko a part d'inta ta kullo ta dawo gurinsa, kula take dashi sosai tana jin wani irin tausayin sa, kallonta kawai yake yana mamaki ashe tana sonsa. Yana zaune gefan gado da k'aramin littafi a hannunshi yana dubawa idonsa sanye da glass d'insa na fama ta futo daga toilet d'inshi jikinta daure da towol din sa,da wani akanta ta nannad'e kanta, had'a ido sukayi da sauri ya kauda kansa, ita yanzu kunyar sa ta ragu lafiyar sa kawai take so shiyasa bata jin kunyar saka kaya a gabansa ba, so take tagama abunda take taje gurinsa taji ko da akwai abunda zatayi masa, yau tayi Wanka tsarki dadduma ta shimfid'a ta tayar da sallahr isha'i ,, dago kansa yayi yana kallonta sosai, zuciyarsa yace"Tayi Tsarki kenan hummmm! Lallai yau akwai budiri😍 *Bari muga yaya za'a buga kwallon😂* [9/29, 5:57 PM] BintubatulBintUmarAbbale👄: 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 _*GIMBIYA BALARABA*_ 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 _*NA*_ _BINTA UMAR ABBALE_ *®BINTUBATULA👄* ```MARUBUCIYAR``` *NANA KHADIJA* *YARO DA KUD'I* *GIMBIYA BALARABA* *TSANTSAR BUTULCI* _*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*_ _________________________ ```We are here to educate, motivate and entertain aur Reades``` _________________________ *DEDICATED* *TO* *RAHAMA ALIYU* _*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR RAHIM*_ *🅿112* Saurin kauda kansa yayi daga kanta ganin tana zuwa gurin sa, kallon littafin dake hannunsa yake,sai ka rantse da Allah bai san da zuwan ta gurin ba, zama tayi kusa dashi ta d'an tsurawa littafin dake hannusa ido, ta lura yana da son karanta littafan addini,nan ta tuna da program d'insa da yake duk ranar juma'a, ake sanyawa tashoshin redio, a nutse tace."Ya jikin" ? Hankalinsa na kan littafin yace." Alhamdullahi " shiru dakin yayi minti biyu tsakani tace."Ko kana buk'atar wani Abu"? girgiza kai kurum yayi,kallonsa tayi zuciyar ta tace."Ubangiji Allah ya baka lafiya" k'asa-k'asa yace." Kashe mana hasken futular nan, na duba dana wayata" Mik'ewa tayi a nutse ya bita da kallo cike da so da sha'awa, futular ta kashe dakin yayi duhu sai hasken wayar sa, kad'an, zama tayi inda ta tashi tayi shiru tana zancan zuciya. Yace." Ki kwanta mana" a hankali tace." Idan na kwanta kuma kai zaka kwanta ban sani ba ko da wani taimako da zanyi maka kar bacci ya d'auke ni". Murmushi yayi iya kacinsa leb'ansa yace."Hakane, kawai kiyi kwanciyar ki, idan ina buk'atar wani abu zan ta she ki" Hawa bed din tayi sosai taja bargo ta rufe iya kacin k'irjinta fuskarta a bude. Sai misali k'arfe goma sha biyu da rabi ya rufe littafin ya aje shi, hannusa ya sa ya jawo while chair d'insa da ke gefe ya sai ta sosai cikin k'arfin hali ya hau ya nufi toilet, a nutse yayi uzirinsa ya futo, kai tsaye mirrow ya nufa, turaririka ya fesa sosai a jikinshi, motsin sa taji yasa ta bude ido sai taga yana k'okarin sauka daga while chair d'in, da sauri ta sauko ta ruk'e hannunsa ya zauna bed din sosai, ta sanya hannunwan ta ta d'auko k'afarshi ta Dora a hankali haka tayiwa d'ayar ma, a raunane tace."Shiyasa fa nace ko kana da uziri me yasa baka tashe ni ba".? Cikin duhun d'akin yake, ganin yadda fuskarta ta nuna alamun jimami da tausayi, gyaran murya yayi yace." Kar ki damu toilet na shiga kuma na futo Cikin hukuncin Allah". Ajiyar zuciya ta sauke a hankali ta koma ta kwanta tana kallon shi yana k'okarin gyara kwanciya, lumshe ido kawai tayi tana shak'ar k'amshin tura ransa masu sanyi duk jikinta ya mutu jin saukar nuffashin sa a kusa da ita, babu zato taji hannusa a jikinta yana k'okarin jawo ta ya rungume, kallon fuskarsa tayi sai taga idonsa a lumshe, tanaji ya jawo ta jikinsa ya rungume k'am, gami da cusa fuskarsa tsakanin wuyanta, shiru tayi tsigar jikinta tana tashi, nuffashi ya dunga saukewa akai-akai taji yana k'okarin cire mata rigar bacci, hannusa ta dafe takasa dago kai ta kalle shi.....har sai da yayi nasarar cire mata rigar jikinta, ya d'auke ta ya d'ora ruwan cikinsu, fuskokinsu suka had'u guri guda, rintse ido tayi tana mugun jin kunyar sa da mamakin abunda yake lallai bashi da dama, abu yake tamkar mai cikkakiyar lafiya, wuyanta ya rik'o da hannushi guda, muryarshi bata futa sosai yace"Kiss me plaesa". Balaraba ta dinga jin kanta yana wani irin juyawa saboda lokacin da yayi maganar wani mugun kamshi mai dad'i ne ya futo daga bakin sa, cikin sigar jan hankali mace ya k'ank'antar da muryar shi yace." Ki kula dani kin ce in ina da buk'ata nayi miki magana, toum ke nake buk'ata a yanzu, yanayin yadda yake mata wasa da gadon bayanta ne ya furgitata, sai ta hau kufce-kufce zata sauka daga kansa, ya rike ta sosai yana k'okarin b'alle mata briziyya, murya a sark'e tace."Kayi hakuri kai da baka da lafiy..... Ka tsata yayi ta hanyar fad'in" Lafiya k'alau mutukar a wannan fannin ne babu abunda bazan iya ba" Shiru tayi masa tana jinsa yayi dubara ya zare mata brziyya jikinta ya wani kara damk'e ta sosai yana sakin wata irin azabbabiyar ajiyar zuciya jin taushin brast d'inta a tsakiyar k'irjinsa, a gigice ya lalubo bakinta ya had'a da nasa ya farai mata lafiyyan kisses masu wahalar mantawa, Balaraba taji kamar ba'a cikin duniya take ba jin wani mugun dad'i da shauki yana dibanta, ga gashin k'irjinsa yana tsikarar ta a jiki, nan take ta sakar masa jiki, suka fara shan soyyayarsu irin ta ma'aurata. Nan na futo na barsu domin ganin sirrin wasu bashi da amfani.......Cikin dabara da hikima irin tashi ya dinga lallab'ata har ya samu ya mayar da ita cikkakiyar mace, Balaraba tayi kuka sosai kuma ta razana da jarumtar sa, cikin zuciyarta take fad'in"Babu Lafiya ma yayi mata wannan aiki ina ga idan ya samu sauk'i .. Ni ko nace Balarana kenan Sarki! fa lafiyansa lau kawai matsalar shi rashin k'afa babu wani Abu da mai cikkakiyar lafiya zai nuna masa. Cikin jin kunya da nauyi ta tashi da safe jikinta duk yayi tsami da nauyi da k'yar ta shiga toilet ta gasa jikinta ta futo lokacin shi yana zaune kan dadduma har ya idar da sallah tayi ta mamakin yaya akayi ya tashi yayi wanka haka har ya shirya jikinsa, dadduma ta hau tayi sallah bayan ta idar tayi addu'a yanda ya sauwak'a, jiki babu kuzari ta mike tana cire bedshirt din domin duk ya b'aci da jini, gyaran murya yayi, ta Dan kalle shi kad'an, ta d'auke kanta da sauri, can taji muryarsa yana fad'in"Ki bari kar ki bawa kanki wahala zasu zo su gyara" batasan sanda ta kwad'a masa harara ba, Murmushi ya saki yana girgiza kai toilet ta wuce da bedshirt din a hannu ta cikin zuciyar ta na fad'in "Abun kunya ne in bari wani ko wata ya ga sirrina da mijina komai sai na gyara da kaina. Tsaf ta wanke shi ta rataye ta kara wanke toilet din, a nutse ta futo, taka had'a ido dashi, shi kuma sai kallonta yake yana sakin k'ayattacan murmushi yarinyar ta gama masa komai yanzu baya jin wata damuwa a tare dashi mararsa sakayau kamar anyi masa wankin Mara,sab'anin jiya da shekaran jiya da take damunsa ko jiya da ya taki Azima ya rage wani abun ne, amma yau Balaraba ta gamsar dashi sosai don haka bakinsa bazai tab'a gajiya da shi mata albarka ba, Gurin da ta aje kayan ta ta nufa ta d'auko wata duguwar riga mai hula rigar ta gaji da haduwa sosai kalar sky blue ce, dogon wando ta zura sannan ta Dora rigar ,duk idonsa akanta, cikin zuciyarsa yake fad'in" Yarinyar nan nason abu sky kamar tasan ina son shi. [9/30, 10:12 AM] BintubatulBintUmarAbbale👄: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation *🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚* *🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀K'WADAGA🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀* *NA* _BINTA UMAR ABBALE_ ~*®BINTUBATULA👄*~ *MARUBUCIYAR* ```NANA KHADIJA``` ```YARO DA KUDI``` ```GIMBIYA BALARABA``` ```TSANTSAR BUTULCI``` _*LOODING:*_ _*{LADIDI K'WADAGA🌚}*_ _*ZAMANI WRITES ASSOCIATION🤝🏻*_ _______________________ ```We are here to educate motivate and entertain aur reades``` _______________________ _Alhmdullahi jiki yayi sauk'i_ *Gaskiya naji dad'i sosai da kularwar ku akaina nagode masu kirana a waya kuna yimin ya jiki da fatan samu lafiya,masu min sannu ta pravite wanda na sani da wanda ban sani ba nagode sosai da sosai ina muku fatan alkairi* *Jan kunne⚠* _Ban yarda a d'aukar min d'aya daga cikin book d'ina a siyar min ba, duk mai buk'atarsu ya nemi numbar ta, Idan ka/ ki siyar min da littafi ba da sanina ba, Wallahi tallahi ban yafe ba, kuma sai mun tsaya gaban Ubangiji kan haka, hattara dai!! Masu satar fasaha a kiyaye kowa yaje yaci gumin sa, kane mi halak d'inka shi yafi amfani a gare ka_ *DEDIGATED* *TO* *RAHAMA ALIYU* _*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_ *🅿13* Cikin sauri Yusuf ya k'araso gurin da Ladidi take kwance, ya bud'e ruwan,ya fara zuba mata a fuskar ta furgice! ta mik'e zaune ta k'wala k'ara! Waige-waige take tana neman Hakkim a gurin, Salima ta rik'e hannunta tana son tayi mata magana. Fuzge hannunta tayi da sauri ta mik'e tsaye tana fad'in" Yana ina."? Duk suka mik'e suna kallonta, Yusuf yace." Ke yarinya me ya shigo dake gurin nan?,da har kika jawo wa kanki suma." Banza kallo tayi masa ta murgud'a bakinta, bata ce masa komai ba, ta bar gurin bagazan-bagazan! kallo suka bita dashi, Yusuf ya kalli Salima yace." Anya kuwa yarinyar nan me lafiya ce"? Salima ta k'unshe dariya tace." Lafiyan ta lau. Kamar ka manta da a k'auye kake dole kaga haka." Yusuf ya girgiza kai yace." Ni abunda ya bani mamaki da ita shine yadda ta shigo gurin nan wallahi". "Gaskiya nima nayi mamaki." Salima tafad'a yayin da suke k'okarin futa dafa gurin. ******** Ta inda ta shiga gurin tanan ta haura ta futa Hakkim na kallonta tun futowar ta har lokacin da take haure katangar yana gani, zuciyar sa yana mamakin ibilicin yarinyar, yau d'in nan zai sanya a kewaye katangar gurin, da waya mai k'ayoyi, duk saboda ita dole kuma a zuba masu gadi a gurin. tuni ya cire kayan da ta b'ata masa ya watsar dasu harabar gurin, domin mugun k'yamk'yami ne dashi, idan ya tuno halittar yarinyar sai yaji zuciyarsa tana wani irin tashi! sosai zuciyar sa take masa zafi, tunda yake a rayuwarsa babu wanda ya tab'ai masa irin abunda yarinyar tayi masa dole ne ya d'auki mataki akanta mutukar ya kara ganin k'afarta a gidan, karya ta zaiyi kawai kowa ya huta. Su Yusuf suka k'araso gurinshi ya sha kunnu domin baya son ma yayi masa maganar, Simi-simi Salima ta shiga ciki, Yusuf ya samu kujera ya zauna yana kallon Hakkim d'in, da yake k'ara yin kicin-kicin da fuska, yace." Zauna zamuyi magana da kai". A fusace! Ya juyo yana fad'in"Ubana ne kai zaka bani umarni". Yusuf ya kalleshi , da alama zuciyar sa har yanzu batayi sanyi ba. Yace." A'a ba ubanka bane". "To ka fad'i duk abunda zaka fad'a kunne na yana ji". Ya k'arashe maganar yana juya masa baya. Yusuf ya mik'e ya k'arasa inda yake, kafad'arsa ya dafa cikin taushin murya yace." Aboki wai me ya faru tsakanin ka da yarinyar nan? Wallahi hankalina ya tashi sosai domin ta dad'e kafin ta farfad'o,haka kurum daga zuwanmu guri zakayi kisan kai saboda zafin zuciya". Hakkim ya juyo yana fuskantar sa, cikin kaushin murya ya fara fad'a masa abunda ya faru. Yusuf ya sauke ajiyar zuciya yace." Gaskiya kam yarinyar ba tayi maka dai-dai ba,amma kai ma bai kamata kayi mata irin wannan dukan ba,saboda yadda na lura da ita kamar irin yaran nan masu lalurar k'wak'walwa kasan k'auye ko d'ansu na cuta basa mai da hankali sai abu yayi tsanani, sannan zaka gansu sun nufi asibiti hankali a tashe." Zuciyarsa ce fara sanyi ya zauna kan kujera guda Yusuf ma ya zauna kusa dashi, yace." Ka bari kawai Yaro wallahi zuciyata a lokacin ji nake tamkar na kashe ta na huta da b'akin ciki." "Kayi hakuri don Allah ka rage zafin zuciya." Yusuf yafad'a yana dukan kafad'unsa. Salima ya k'walawa kira, tana can ta shagala da kallon yadda aka tsara falo da kayan jin dad'i da more rayuwa, har ta kunna kallo tanayi taji kiran big broth amsawa tayi ta mik'e da sauri, tana zuwa yace." Ki shiga kchin kiyi mana abunci." "Angama big broth" tafad'a cike da bin umarni, kai tsaye kichin d'in ta nufa, gashinan komai akwai na amfani nan take ta fara aikinta. ********** To can gidan su Ladidiya kuwa Mai koko ta saddak'ar ta fawwala wa Allah cewar Ladidi ta mutu cikin rijiyar don haka mutane sun cika gidan ana yi mata ta'aziyya, Jama'a sun kewaye ta, tana zaune da carbi a hannu ga idonta yayi jajazur! taci kuka ta k'oshi, D'alha na waje da mutane zazzaune kan tabarma, sam yak'i yadda cewar Ladidiya ta mutu cikin rijiya k'wak'walwar sa tafi tunanin yarinyar tana can gurin gantalin ta, shiyasa ya kasa zaune ya kasa tsaye sai zurga-zurga yake a gurin. Duk Wanda yazo gurin sai ya hau yi masa gaisuwa, ko kallon su baya yi ********* Tafiya take fakam-fakam!! sak'e-sak'e kawai take a zuciyarta da tunanin d'aukar fansa kan, d'an burni,sunan da ta sama sa kenan, wallahi bai dake ta a banza,sai ta rama duk hanyar da zata bi ta sani, leb'anta ta tab'a da hannunta, cire hannuta tayi tana girgiza kai! a fili tace."Wallahi he na rama idan ubanka ne shugaban k'asa he na rama, nima sai na fasa maka baki,hummm!! Zaka san ka tab'o Ladidi jikar Mai koko, bana barin takwana kuma bana manta ranar d'aukar fansa." Da tafiyar ta ya gane i tace jiki na rawa ya k'wala mata kira,"Ladidi" da sauri ta juyo tana waigen idan taji ana kiranta. Kakanta ne D'an fulani, yake tawo wa inda take, yana can gurin kiwo labari ya same shi na mutuwar ta,shine ya tawo cikin tashin hankali! Abun mamaki kuma sai gashi ya ganta a hanya, yana k'arasowa inda take ya damk'i hannuta, bai ce mata komai ba suka fara tafiya, zub'uro baki tayi tace." Ni ka sake ni ka rik'e min hannu da k'arfi ai gida zani ba wani guri ba." D'an Fulani yayi mata shiru, shi dai k'okarin shi kawai yaga ya danganata da gida,hankalin kowa ya kwanta. Tun daga nesa jama'ar dake gurin suka hango tawowar su, sai aka fara kallon-kallo tsakanin su, da suka tabbatar da cewar itace sai kowa ya fara zura silafas d'insa yana guduwa, D'alha ya juya yaga wayam! babu kowa a gurin, girgiza kai kurum yayi yana jin wani d'aci cikin zuciyarsa wato Ladidi ta zama abun tsoro kenan? D'an Fulani ya d'amk'ata a hannunsa yana fad'in"Gatanan can wajejan titi na gano ta tana tafiya ita kad'ai." D'alha ya sauke ajiyar zuciya yace."Alhamdullahi, dama ni jiki na bani yarinyar nan tana raye,amma jama'ar gari suna ta fad'in ta mutu a cikin ruwa,Allah nagode maka daka bayyana mana ita ko hankalin Mai koko ya kwanta." Sai sanan Ladidi ta tuna da abunda ya faru d'azu tsakaninta da Mai koko, dariya ta kece dashi,hahahaha! D'alha ya gaura mata mari! Yana fad'in"Rufe miki don buhun ubanki, shashasha, shakatafe, naga ranar da zakiyi hankali dai" D'an Fulani kuwa a'lamarin Ladidi ya fara bashi tsoro,don haka yace."D'alha mu shiga cikin gidan sai mu San abun yi." Kai tsaye cikin gidan suka shiga. *Tofaa ko ya zata kasance idan jama'ar gidan sukaga Ladidi Wanda suka dauka ta mutu cikin rijiya,ko yaya Mai koko zatayi in taga Ladidi? To Ku cigaba da bina dai cikin labarin domin in warware muku* *COMMENT VOTE AND SHARE* [10/1, 10:04 PM] BintubatulBintUmarAbbale👄: 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 _*GIMBIYA BALARABA*_ 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 ~*NA*~ _BINTA UMAR ABBALE_ *BINTUBATULA👄* *MARUBUCIYAR* ```NANA KHADIJA``` ```YARO DA KUDI``` ```GIMBIYA BALARABA``` ```TSANTSAR BUTULCI``` ```LADIDI K'WADAGA``` _*ZAMANI WRITES ASSOCIATON🤝🏻*_ _____________________ ```We are here to educate motivate and entertain aur reades``` _______________________ *ALHAMDULILAH* *HAUWA S ZARI'A* _Maman Usuwan_ *Ina taya ki murna na kallama littafin ki HAKA ALLAHA YA NUFA* _KADDARA TACE_ *UBANGIJI ALLAH YA K'ARA BASIRA YA SA SAK'ON KI YA ISA INDA KIKE SO* _________________________ *JAN KUNNE⚠* _*Ban yarda a siyar min da d'aya daga cikin books d'in ba, duk mai buk'atarsu sai ya nemi numbar ta, ban yarda ka/ki siyar min da littafi to wallahi tallahi ban yafe ba kuma zamu tsaya gaban Ubangiji kan hakan, hattara!! Masu satar fasaha, ka nemi halak d'in ka yafi kaci da gumin wani, halak d'in ka shine mafi alkairi a gare ka.*_ *DEDICATED* ~*TO*~ *RAHAMA ALIYU* ~*ABUJA*~ _*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_ *🅿113* K'ok'arin futa take daga d'akin, ba tare da ta k'ara kallon inda yake zaune ba, cikin nutsuwa yace." Ina zakije kuma"? D'an juyo wa tayi tace."Zan je in kawo maka abun kari" k'asa yayi da kansa cikin so da k'aunarta yace."Na huttashe ki dawo ki zauna, domin yau bana jin yinwa saboda kin cika min ciki da so da k'aunar ki, hak'ik'a ina alfahari dake cikin matana Balaraba kece Gimbiya ta." Lumshe idonta tayi tana jin wani yarrr! a jikinta gaskiya taji dadin yabon da yayi mata, itama yanzu ta fara jinsa cikin zuciyarta, yace." Dawo ki zauna muyi hira" Simi-simi ta dawo ta zauna nesa dashi,sai kauda kai take cike da kunya, shi kuma ya k'ura mata ido yana sakin k'yatattacan murmushin sa, cikin shagwaba'a tace." Ka daina kallona haka inajin babu dad'i a jikina."Lumshe ido yayi ya bud'e tare sa zuba mata su yace." Haka nake so ai da alama kin fara sona, ko da yake ma, jiya naga alamu daddare an karb'eni hannun biyu" rufe fuskarta tayi ta mik'e da sauri ta bude dakin ta futa cike da kunyar sa. Karo! Suka buga da Halisa ta d'ebe ta ta watsar! tab'e baki tayi tamkar taga kashi tace." Ke kuma wannan shashan cin fa? dube ki don Allah abun tausayi dake wai har kece zaki shigo cikinmi ki nakasa min miji,to bari kiji wallahi Duk irin k'ulunboton ki baki isa ki kashe min mijina ba, domin kici dukiya sai dai Idan mu, mu kashe ki, kar ki manta da cewar mun San kece silar mutuwa d'an uwanmu Moddibo, to wallahi Sarki! Almansur yafi k'arfin ki, jaka kawai, 'yar talakawa" Wani mugun b'acin rai! Ya turnek'e zuciyar Balaraba, tabbas Halisa taci albarkacin mijinsu da bashi da lafiya, amma da badan wannan ba, da sai ta k'ara nuna mata ita wacece, da alama ta manta karon su da ita na farko, amma taci al'washin duk randa ta k'ara yi mata magana irin wannan tabbas sai ta nuna mata kuskuran ta. Azima ce ta k'araso inda suke tsaye ta buge k'afad'ar Balaraba tana zabga tsaki! Hannun juna suka rike suka wuce ta cikin wata irin tafiya ta k'asaita. Kallo ta bisu dashi zuciyarta tana zafi,! Lallai ruwa ya daki babban zakara, ita kad'ai take fad'in haka a zuciyar ta, idan da ba haka ba wallahi da sai sun gane kuransu. Yana zaune inda yake tun futar Balaraba, fuskarsa cike da annuri suka same shi, amsa musu sallama yayi ya nuna musu gurin zama, jiki a sanyaye ko waccen su ta zauna, babban abunda ya sa jikinsu yayi sanyi shine ganin da sukayi yana cikin farin ciki da annushuwa kamar yadda suka ga fuskar Balaraba haka, wani irin kishin Balaraba ya damu zuciyarsu, sanin halinsa na rashin d'aukar raini yasa ko wacce tayi shiru da bakin ta, gai dashi sukayi sunayi masa ya jiki, ya amsa da walwala, Azima tace."Yau zaku tafi ne"? " Eh insha Allahu sha biyu na rana" Shiru sukayi. Halisa tace." Tunda ita wannan ta futa daga girkin ta, zan shiga nawa ina ganin ya kamata a tafi dani ko da wani taimakon da zanyi maka." Harararta yayi, ta sunkuyar da kanta da sauri, a hankali yace." Ke ko za'a tafi da wani waye zai tafi dake guri kije kiyiwa mutane shirme" Azima taji dad'in maganar sa, ji wani son kai na Halisa take fada a zuciyar ta, muryar shi sukaji yana fad'in"Duk Ku kwantar da hankalin ku babu da wanda zani, sai kace wani Yaro,ku munje ma ba wani zama za muyi ba." Azima tace." Nima dai abunda nagani kenan." Halisa kuwa sai yak'e take ta lura mutumin nata haushinta yake ji, domin yak'i sakin jiki da ita hirarasu suke da Azima tamkar babu ita a gurin. Wayar shi tafara k'ara ta mike da sauri ta d'auko masa, karb'a yayi ba tare da yace mata komai ba, Governor na ne, suka gaisa yace." Fatan jikin da sauk'i, duk wasu shirya-shirye angama insha Allahu da kaina zan zo in d'auke ka cikin mota har filin jirgi" Sarki! Yace." Jiki alhamdullahi ni kam bani da matsala sai ta rashin k'afafu shima na wani lokaci ne insha Allahu, zamu zauna cikin shiri insha Allahu" Governor yace." Naji muryar ka rad'au da alama kana cikin nishadi kasan fa duk namiji da yake da mace sama da daya to mutukar suna kula dashi da kwantar masa da hankali babu Wanda ya kaishi dacewa". Murmushi yayi yace." maganar ka haka take, Aboki" dariya Governor yasa yace." Dole dai na koya maka surutu ko"? Yace." To ya na iya fa halin ka." Haka dai sukai barkwamci kafin suyi sallama suka kashe wayar, Azima da Halisa kuwa ganin babu fuska ko wacce taje zata je tayi Wanka, suka sauka babu wacce ta kara kula 'yar uwar ta. [10/2, 9:21 PM] BintubatulBintUmarAbbale👄: 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 _*GIMBIYA BALARABA*_ 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 ~*NA*~ _BINTA UMAR ABBALE_ *BINTUBATULA👄* *MARUBUCIYAR* ```NANA KHADIJA``` ```YARO DA KUDI``` ```GIMBIYA BALARABA``` ```TSANTSAR BUTULCI``` ```LADIDI K'WADAGA``` _*ZAMANI WRITES ASSOCIATON🤝🏻*_ _____________________ ```We are here to educate motivate and entertain aur reades``` _______________________ *JAN KUNNE⚠* _*Ban yarda a siyar min da d'aya daga cikin books d'in ba, duk mai buk'atarsu sai ya nemi numbar ta, ban yarda ka/ki siyar min da littafi to wallahi tallahi ban yafe ba kuma zamu tsaya gaban Ubangiji kan hakan, hattara!! Masu satar fasaha, ka nemi halak d'in ka yafi kaci da gumin wani, halak d'in ka shine mafi alkairi a gare ka.*_ *DEDICATED* ~*TO*~ *RAHAMA ALIYU* ~*ABUJA*~ _*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_ *🅿114* To Balaraba ma lokacin da suka rabu dasu Halisa gurin ta, ta nufa wanka ta shiga a gurguje ta futo ta kimtsa jikinta, ta kasance mace me son atampa duk ya wanci kayan ta itace doguwar riga, da Riga da siket da zani basu da yawa, yanzu ma wata 'yar Ghana ta saka doguwar riga ce, sosai kasa ya bud'e daga iya kwankwanson ta ya matse da kirjin rigar komai ya futa har madauri ne da ita daga baya, d'ankwali ta d'aura dai-dai misali ta shiga kicin dinta dole tana ganin sai tayi masa abu motsa baki, cake ta fara had'a ma, zuciyar ta tace ki had'a masa Dambu nama ko yana so, nan take ta futo da zallar tsokar Neman sa cikin firji ta Dora kan wuta bayan ta sanya albasa da kayan k'amshi, ta cigaba da had'a cake din ciki k'warewa. Balaraba ta k'aware sosai gurin had'a dambun nama shiyasa sam bai bata wahala ba, nan ta had'a komai cikin abunda bai fi awa guda ba, k'amshi ne kawai yake tashi kicin d'in, zuba shi tayi cikin warmers ko wanne ta aje ta samu wani had'ad'an akushi irin na gidan sarauta ta cika shi da cake d'in da Dambu nama,wannan ta aje shi ne sai zasu tafi zata bashi, ruwa ta d'ora a wuta ta zuba kayan tea masu sa kamsh gahwa na'ana'a citta kanifari kimba da dai sauran su sai da ya gaja da tafasa sannan ta kashe gas d'in ta tace sosai ruwan tea d'in yayi kyau sai kamshi yake ta juye cikin fulas mai kyau. D'auka tayi ta kai falonta ta aje ta dawo ta gyara kicin din tas! Sannan ta dawo ta d'auki, d'auki abunda ta aje, kai tsaye part din shi ta nufa. Lokacin har su Shahid sun zo sun d'auko dashi k'asa yayi wanka shar dashi kana ganinsa kaga ango sosai yake walwala Shatima na tsokanar sa wai farin cikin me yake, shi kuma yana basarwa. A nutse tayi sallama ta shigo, da sauri ya dago kanshi yana kallonta, saurin sunkuyar da kanta tayi, cikin mamaki ya bi hannuta da kallo, yana kallon yanayin tafiyar ta, Shatima ya amsa yana fad'in"Gimbiya sannu ki da zuw..... Katse shi yayi ta hanyar fad'in"Ka tsaya kana surutu ka karb'i abun hannuta mana,bata da lafiya" Balaraba tayi saurin kallonsa, cikin mamaki, da sauri ta wuce Shatima ya bi bayanta yana fad'in"Ayya! Gimbiya sannu da kokari kawo in aje miki daining d'in." Murmushi k'arfin hali tayi tace." Ka rabu dashi don ni lafiya talau fa." 'Yar dariya yayi yace." Ai naga alama gashi kin sha aiki domin ki faranta ran maigidan ki mybe yana so ki huta ne shiyasa Yace in karb'e ki" Shiru kawai tayi masa tana sunkuyar da kanta cike da kunya,wato Dole dai sai ya tona mata asiri gurin abokan shi,kome amfanin fad'a musu haka oho masa. Gyara gurin tayi sosai, Shahid ya kawo shi har gurin, idonsa a kanta yace." Wato nace kije ki huta shine kika wahalar da kanki ko." K'asa tayi da kanta kurum domin bata so tayi wata magar ya lafto wacce zai sa har su Shatima su gane. "Jimana" yafad'a yana tsare ta da ido, a nutse ta watsa masa wani kallo, Wanda ya shiga jikinsa,amma da yake ya saba karb'arsa sa'i da lokaci a gurin ta,sai ya dake! Yace." Bayan wahalar da kika sha jiya shine zaki na wahalar da jikin ki yanzu,wai ke bakya son hutu ne." ? Taikacinsa ya hanata cewa komai, sai aukin futo da warmers take, Shatima ya doki kafad'arsa yana fad'in." Kai kanai mata bak'in cikin ladan da zata samu ne, ina ruwan ka."? Shahid ya b'oye dariya yana fad'in"Lallai hausawa da sunyi gaskiya cikin karin maganar su, inda suke fad'in"Gurgu yafi...........Sarki! Ya galla masa harara! Dariya suka saka Shatima ya bashi hannu suka taga!Balaraba kamar ta nutse don kunya, simi-simi tabar gurin tana da ta sanin dawo da tasan tonan silili zai mata da bata dawo ba, dab da zata futa sai ga Mama ta shigo da jama'ar ta, sai ta tsaya tana murmushi , itama Mama murmushi ne a fuskarta, suka zauna cikin kujera Balaraba ta durkusa har kasa ta gaishe ta, cikin sakin fuska mama ta amsa tana tambayar me jiki, tace "Jiki alhamdullahi wallahi gashi yana k'okarin Mama muna sa ran samun nasara wannan tafiyar insha Allahu, Mama tace." Hakane dama babu abunda yafi k'arfin addu'a ai, jiya munyi waya da aminiya ta, Matar Sarkin Yalwa sosai mahaifinta dake Malami ne yasa yara 'yan makaranta na addu'a jiya an sauke al'kurani babu adadi" Mama ta cigaba da cewa." Insha Allahu tanan zuwa itama,kin san bata samu damar zuwa gurin bukin ku ba tun dai da tazo lokacin mutuwar me Martaba." Balaraba tace." Kai angode sosai wallahi ai Mama alk'urani mai girma yana tattare da waraka ko wace iri ce ,mutukar mutum zai rike shi, to ya rike babban kundi." Mama tace." Haka maganar ki take Balaraba." Su Shahid ne suka k'araso gurin cikin nutsuwa suka tsuguna suna gaishe da ita, ta amsa musu da walwala a fuskarta tace." Ya mai jiki? Domin Ku zan tambaya." Shahid yace." Jiki alhamdullahi Mama kin ganshi zaune k'alau dashi,wannan kuma aikin Gimbiya ne ga tanan kusa dake." Cikin farin ciki Mama tace." Nasan zata aikata fiye da haka, k'okarin tura while chair d'in yake, da sauri Shatima yace." Kabari mana inzo." Ko saurarensa baiyi ba ya cigaba da turawa ya k'araso kusa dashi gami da kama while chair din yana fad'in"Da ka bari an turaka." "Akan me zan bari hannuna aikin me yake." Yafad'a ciki-ciki murmushi kawai Shatima yayi yana fad'in" Dama kai ai babu me iyawa da kai sai Balaraba." [10/4, 12:54 AM] BintubatulBintUmarAbbale👄: 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 _*GIMBIYA BALARABA*_ 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 ~*NA*~ _BINTA UMAR ABBALE_ *BINTUBATULA👄* *MARUBUCIYAR* ```NANA KHADIJA``` ```YARO DA KUDI``` ```GIMBIYA BALARABA``` ```TSANTSAR BUTULCI``` ```LADIDI K'WADAGA``` _*ZAMANI WRITES ASSOCIATON🤝🏻*_ _____________________ ```We are here to educate motivate and entertain aur reades``` _______________________ *JAN KUNNE⚠* _*Ban yarda a siyar min da d'aya daga cikin books d'in ba, duk mai buk'atarsu sai ya nemi numbar ta, ban yarda ka/ki siyar min da littafi to wallahi tallahi ban yafe ba kuma zamu tsaya gaban Ubangiji kan hakan, hattara!! Masu satar fasaha, ka nemi halak d'in ka yafi kaci da gumin wani, halak d'in ka shine mafi alkairi a gare ka.*_ *DEDICATED* ~*TO*~ *RAHAMA ALIYU* ~*ABUJA*~ _*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_ *🅿115* Shiru yayi masa har suka k'arasa kusa da Mama,ya fara k'okarin saukowa Mama tace." A'a kayi zaman ka kawai mu gaisa a haka lallai jiki yayi kyau,naji dadin ganin ka cikin walwala ubangiji Allah ya k'ara lafiya." Suka amsa da "Ameen" Cikin kauna irin ta d'a da uwarsa yace." Mama kin tashi lafiya."? Tace."Lafiya lau na tashi amma na kwanta da tunanin ka, shiyasa da na shigo na ganka cikin koshin lafiya naji dad'i kuma na godewa Balaraba." Sunkyar da kai kurrum yayi yana murmushi,tace." Ina fatan ka karya ko."? Balaraba tace." Ga kayan karin can kan daining." " To maza je ki d'auko masa in ga yaci a gabana." Kallon ta yayi yace." Mama sai kace wani k'aramin yaro." Murmushi tayi tace." K'aramin Yaro kake a gurina." Shahid yace." Wallahi hakane Mama mu yara ne a gaban iyayemu, Sarki! Shiru yayi yana kallon ikon Allah Mama tasa Balaraba ta had'a tea me kauri tace."fara bashi ya d'umama cikinsa." Balaraba ta mik'a masa kofin tae sai yak'i karb'a Mama tace." Ki cika ladanki mana." Sunkuyar da kanta tayi cike da kunya ta nufi bakinsa da cup d'in, a hankali ya bud'e bakinsa ya fara kurb'ar tea d'in, ji yayi sugar yayi yawa ga madara tayi yawa baya son k'arni, a hankali yace." Ki aje Wannan ki had'a min bak'i." Ajewa tayi kamar yadda yace ta fara had'a masa wani,hannu ya mik'a ya d'auki cake guda d'aya ya fara ci, sosai yayi masa dad'i a baki sai da ya cinye guda uku kafin taga ma motsa tea d'in yadda zai fi masa dad'i a baki ta fara bashi cike da kunya a idon Mama da su Shatima, Mama sam hankalin ta baya Kansu tana can tana magana da Jakadiyar ta, Su Shahid sai tsokanar sa suke yak'i tanka musu, a hankali ta dinga bashi yana kurba yana gutsirar cake d'in, sai da ya ci guda shida sannan ya d'aga mata hannu alamun ya ishe shi, tissue yake k'okarin yagowa, ta ya ciro masa mik'ewa tayi tana goge masa gefan bakinsa,ya tsura mata ido yana kallo, ita ko taki yadda su had'a ido dashi, Halisa da Azima ne suka shigo cikin wannan hali, turus sukayi ganin abunda yake faruwa kowacce jikinta yayi sanyi ga Mama a zaune ga uban tafiyar zaune cikin shiri Balaraba ta had'u sosai domin shigar ta ta yau tayi mata kyau, tana tsaye kusa dashi tana goge masa gefan bakinsa . Suka zazzauna jiki babu k'wari suna gaishe da Mama ta amsa musu a sake tana tambayar su me jiki, Azima da yake tafi Halisa wayo ta b'oye damuwar ta ta saki jiki suna hira dasu Shatima,har tana sa Balaraba a ciki kamar ba itace ta bangaje ta d'azu ba, ita ko Halisa sai shan kunu take tana hira da Mama kawai, cikin wannan hali me girma governor ya iso, suka gaisa da Mama cikin girmamawa, Halisa ta kalli Mama k'asa-k'asa tace." Mama ina gani tafiyar nan ayi ta dani domin yau girki na ne, kinga sai in kula dashi" Mama tace."aikuwa kin kawo shawara me kyau dama ya kamata a d'auki daya daga cikinku a tafi da ita, to amma kinga Balaraba bata futa daga lokacin ta ba, ina ganin da ita za'a tafi, in yaso in ya dawo sai ya sauka a dakin ki, kin gane ko"? Halisa ta b'ata fuska bata ce komai. Me girma governor yaji dadin ganin jikin shi yayi kyau, sosai ba tare da wani b'ata lokaci ba, suka mik'e domin tafiya Shahid shine yake tura shi har suka futa harabar gidan jama'a a tsatstsaye Suna sauraron futuwarsu kowa na addu'a da fatan alkairi, tare da samun lafiya. Waziri na fada zaune shi da mutanan sa labari ya riske shi cewa gashi can an futo da Sarki! Zasu tafi Saudi'a sai ya kece da dariya yana fadin "Duk inda zasuje suje su dawo shida ya taka doran kasa da k'afafunshi to sai dai idan lahira yaje" mutanan sa suka ce "Wannan haka yake,takawar ka lafiya gyara kintsi dai!!!!!! Wani mugun dad'i ya rufe shi, jin yadda suke faman zuba masa kirari,abunda yake mutuwar so kenan a rayuwarsa. Azima da Halisa, na tsaye sai gani sukayi kawai Mama ta rik'o hannun Balaraba ta zaunar da ita bayan mota kusa da Sarki! Ta maida kofa ta rufe, fad'i take." Ubangiji Allah ya bada nasara a rayuwa Yarona ka dawo da k'afafun ka.' Sarki! Yayi mamakin abunda Mama tayi,sam ba son daya daga cikinsu ta bishi saboda ya San rigima ce, yana kallon b'acin rai da zallahr kishi a idon Halisa, amma bai san manufar Mamanshi ba, Wambai da Galadima da Liman suka shiga motar su,suna dagawa Mama hannu, Shahid da Shatima motar me girma governor suka shiga, shi kuma tashi daga shi sai Balaraba sai direba, d'ayan bayan d'aya suka futa daga gidan da niyyar zuwa eirport. Addu'a sosai Mama takeyi, har suka futa, ta dawo da hankalinta Kansu Halisa kamar su d'aura hannu aka don bakin ciki, nan ta basu umarnin ko wacce ta koma shashen ta. ********** Bayan awa biyu da tafiyar su. B'angaran Waziri Zayyanu, Khalifa ne da Ansar, Suna zaune a falo suna ciye-ciye sai dariya sukeyi da alama suna jin dad'i saboda yanda Babansu ya sakar musu kudi Sosai saboda duk cikin 'yayansa yafi son su, sune zai ce suyi Abu kai tsaye suyi babu gar dama, Khalida ya kalli d'an uwansa yana fadin"Kai wai ya kabarin wancan gurgun ne,? Wallahi naso ma mutuwa yayi shege Dan asara,wato shi da yana zaune yana jiran mulki, kakansa yayi ubansa yayi Dan rashin imani,shine yake so yayi shima, ko an fada masa muma ba 'yan sarautar bane oho,ai yanzu kuma mulki ya dawo hannunmu Dan uwarsa sai dai yaga anayi sai mun kashe shi da bakin cikin mu." Ansar yace." Kaii manta da wannan, sai muga da wace k'afar zai hau kujerar mulki ballantana ya zauna." Hahahahahaha!!suka kwashe da dariya, kamar da wasa sai Khalifa ya k'ware ya fara tari!! Ansar ya mik'a masa ruwa ya kurb'a tarin yak'i tsayawa idonsa yayi jajazur har yana k'okarin fad'uwa daga kujerar ya damk'e k'irjinsa sosai yana ta tari idanunsa duk sun futo waje, Hajiya Kattime ta futo daga dakin taga abunda yake faruwa da sauri ta k'arasa gurin tana salati, har ya fado daga kan kujerar ya kifa sosai ya galabaita, Ansar duk ya gigice' yan uwansa dasu kenan sunyi tsaye a kanshi, ji sukayi kamar anyi ruwa an d'auke, da saurin Al'amin ya d'ago shi, sai yaga wuyansa ya karye ya tafi luuuuuu ya fad'i kasa, salati suka saka, Hajiya Kattine tace." Innalillahi, waina'ilahi raji'un.! Khalifana babana ka mutu ka barni babana kabi Dan uwan ka Moddibo, ya Allah ya jikanka Khalifa na." Tana share hawaye take fadin Wannan maganar, aikuwa gida ya rude da kuka sosai, mutuwar ta girgiza su mussaman dai Ansar da suke, hira dashi, da sauri Al'amin ya nufi fada domin ya sanar da mahaifin su halin da ake ciki. [10/4, 1:59 PM] BintubatulBintUmarAbbale👄: 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 _*GIMBIYA BALARABA*_ 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 ~*NA*~ _BINTA UMAR ABBALE_ *BINTUBATULA👄* *MARUBUCIYAR* ```NANA KHADIJA``` ```YARO DA KUDI``` ```GIMBIYA BALARABA``` ```TSANTSAR BUTULCI``` ```LADIDI K'WADAGA``` _*ZAMANI WRITES ASSOCIATON🤝🏻*_ _____________________ ```We are here to educate motivate and entertain aur reades``` _______________________ *JAN KUNNE⚠* _*Ban yarda a siyar min da d'aya daga cikin books d'in ba, duk mai buk'atarsu sai ya nemi numbar ta, ban yarda ka/ki siyar min da littafi to wallahi tallahi ban yafe ba kuma zamu tsaya gaban Ubangiji kan hakan, hattara!! Masu satar fasaha, ka nemi halak d'in ka yafi kaci da gumin wani, halak d'in ka shine mafi alkairi a gare ka.*_ *DEDICATED* ~*TO*~ *RAHAMA ALIYU* ~*ABUJA*~ _*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_ *🅿116* Waziri na zaune a fada sai bada umarni yake cike da izza! magana ma da k'yar yake yin ta,wai shi dole ga Sarki, Al'amin ya shigo cikin tashin hankali ya zube gaban mahaifinsa ya fara Sanar dashi halin da ake ciki. Hankali a tashe ya mik'e fadawansa suka rufa masa baya,kwata-kwata ya manta da alkwarinsu da Mak'asudu, yana isa ya Tarar dasu hankali a tashe mussaman Hajiya Kattime da ta kusa zautuwa domin. Bayan tafiyar Al'amin shima Ansar d'in fad'uwa kawai suka ga yayi yana rike cikin sa kafin su ankara sukaga jini na b'ulb'ulowa ta bakinsa da hancin sa,gaba ki daya sun rasa wanda taimako zasuyi masa, Khalifa kuwa tuni Allah yayi masa rasuwa kafin Waziri ya k'araso mutuwar Ansar din ta afuku a gabansa, zaman dirshan yayi a gaban gawawwakin 'yayansa ya sunkuyar da kansa kasa yana kukan zuci,kamar daga sama yaji wata murya kamar ta Mak'asudu yana fad'in." Kar ka manta da alk'awari mu dakai,yau na cika shi shiyasa ma na shanye jinin 'yayan ka saka fi so da kauna."!!! Zumbur!!! Ya mik'e tsaye idonsa yayi jazur ya kalli sauran 'yayan nasa yace." A shirya yi musu suttura." Yana gama fad'in haka ya shige asirtaccan d'akinsa, Hajiya Kattime ta bishi da kallo cikin mamaki ganin bai damu ba, yanzu tafara zargin sa, Sosai take zargin wannan dakin da ya kulle ya hana kowa shiga,dole tafara bunkice a kansa. Kafin kace kwabo mutuwar su Khalifa ta watsu a gida da waje, su Sarki! Ma labari ya same su,sunyi mamaki sosai daga bisani Sarki yace." Ba'a mamaki da ikon Allah, Galadima da me girma governor ne suka dunga tur da halayyan Waziri domin su sun San abunda yake faruwa saboda mulki babu abunda Waziri bazai yi ba. Mama ce ta dinga d'ebe wa Kattime kewa har akayi sadakar uku kowa ya watse Hajiya Kattime ta kudiri aniyar bibbiyar mijinta da abunda yake aikatawa tana fatan asirinsa ya tuno a duniya shine sanadin mutuwar 'yayan ta uku, tayi da tasani data aure shi. Saboda mugun bakin halinsa. Waziri kuwa yana shiga d'akin sirrinsa ya kulle da mukulli ya zube bakin kofar yana warware nadin dake kansa, gumi na tashin hankali kawai takeyi wasu zafaffan hawaye ne suka fara zubo masa, lokaci guda yayi rashin 'ya'yan shi biyu lallai Mak'asudu ya shammace shi, kuka yayi sosai daga bisani ya miki ya maida rawaninsa ya futa daga dakin, yanzu yasan kuma Mak'asudu baya binsa wani bashi tunda ya biya shi. *Niko nace haka kake gani Waziri aljan ba'a iya masa sai Allah* ********* Uwa! na zaune tsakar gida ta zabga uban tagumi tunanin rayuwa kawai take, duk ta rame ta ko jale,Shamsiyya ce ta futo daga ban daki hannunta rike da buta cikin ta ya tsofa sosai duk ta kumbura, Sadiya matar Kawu na hangota tace." Ki dinga tafiya a a hankali da gurin nan kar ki fad'i saboda santsi." Shamsiyya ta d'aga kanta cikin tausayin kanta taje kusa da uwarta ta zauna da k'yar.Uwa! Ta sauke ajiyar zuciya tace." Shikkenan yanzu kamar yanda na fidda rai da Iro haka zan hak'ura da Mabaruka, anyi neman duniya ba'aganta ba." Shamsiyya tace." Jiya fa Walidi yake ce miki ya samu labari gurin wani abokin kasuwanci sa wai ya ganta cab portarcouht ita da saurayin ta." Uwa! ta share hawaye tana fadin ." Allah ya dawo da ita gida ubangiji Allah ka shirye ta kasa ta gane duniya ba mattabata bace." Cikin sanyi murya Shamsiyya tace." Ameen" Lantana ta futo daga d'akinta ta zauna suna Tisa maganar,Lantana Duk tayi sanyi,kusan kullum tana daki tana Jan carbi sallar walha bata wuce ta, ta koma ga Allah sosai domin mutuwar Sallau ta gigirgaza ta, yanzu basa cikin k'angin rashi Walidi na tsaye a Kansu basu da yunwa,kuma daga gidan Sarauta Mama nayi musu aike duk wata. ********** Alhmdullahi yau satin su guda A k'asa me tsarki, sauk'i ya soma zuwa da izinin ubangiji duk Wannan kumburi da k'afafun sukayi ya sab'e kwanan su biyu da zuwa aka fara yi masa amfani da magunguna na islaminc masu d'auke da ayoyin Allah a ciki, yasha a shafa k'afafun nasa, dasu yanzu yana iya motsa su, amma bai iya taka su,yayi wata kib'a sosai saboda samun kulawa daga my life d'in shi Balaraba soyayyar sa yake sha sosai idan yaga babu idonsu su Shatima, dake su in Safiya tayi suna tafiya harami su yini sai yamma suke dawo wa, wannan damar da ya samu ya dinga more amarcin sa, Balaraba ta saki jiki dashi sosai tana bashi kulawa, shi kuma sai yayi tayi mata shagwaba yana lanjarewa, da dare yayi zata ga ya watsake yana Mata kallon love, tun bata gane wayon sa ba har ta gane shi, sai dai kawai tayi masa dariya, suna samun waya sosai daga gurin Mama, taji dad'i da taji jiki yayi kyau, Balaraba ta sha addu'a a gurina. Daga Wanka ta futo daure da towol cinyoyinta duk a waje ga kanta sai d'igar ruwa yake, yana zaune gefen gado daga shi sai k'aramin wando, da alama angama love ne, bude mata hannuwan sa yayi wai ta zo. A hankali ta k'arasa amma me makon ta shiga jikinsa kamar yadda ya buk'ata sai ta zauna gefan gadon tana ya mutse fuska, Ka fad'ar ta ya kamo ya Dan matsa kad'an k'asa-k'asa yace." Menene hummm."? Lumshe ido tayi tace." Bana jin dadin. Jikina yanzu na fara zargin kaina saboda banga period d'in ba, wannan lokacin nake yi shiru bai zo ba." [10/5, 9:29 PM] BintubatulBintUmarAbbale👄: 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 _*GIMBIYA BALARABA*_ 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 ~*NA*~ _BINTA UMAR ABBALE_ *BINTUBATULA👄* *MARUBUCIYAR* ```NANA KHADIJA``` ```YARO DA KUDI``` ```GIMBIYA BALARABA``` ```TSANTSAR BUTULCI``` ```LADIDI K'WADAGA``` _*ZAMANI WRITES ASSOCIATON🤝🏻*_ _____________________ ```We are here to educate motivate and entertain aur reades``` _______________________ *JAN KUNNE⚠* _*Ban yarda a siyar min da d'aya daga cikin books d'in ba, duk mai buk'atarsu sai ya nemi numbar ta, ban yarda ka/ki siyar min da littafi to wallahi tallahi ban yafe ba kuma zamu tsaya gaban Ubangiji kan hakan, hattara!! Masu satar fasaha, ka nemi halak d'in ka yafi kaci da gumin wani, halak d'in ka shine mafi alkairi a gare ka.*_ *DEDICATED* ~*TO*~ *RAHAMA ALIYU* ~*ABUJA*~ _*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_ *🅿117* Hannunsa ya sanya ya rungumo k'ugunta fuskarsa d'auke da wani kyakykyawan murmushi yace." Lallai Allah ya amsa min addu'a ta da wuri Ubangiji Allah yasa ciki ne dake, idan hakane zan yi farin ciki sosai da sosai." Sunkuyar da kanta tayi tana jin kunyar sa a hankali tace." Gaskiya ina zargin haka domin ban tab'a batan wata ba,ko lokaci nayi nake amma wannan kwana hud'u akai gaskiya da akwai alamun tambaya." Cikin farin ciki yace." Yanzu nan zan auna ki domin in tabbatar da hakan." Towol din yake k'okarin cirewa ta rike hannunsa cike da tsoro! Kallon ta yayi yana lumshe ido,tace." Wai kai baka gajiya ne."? Kanne mata idonsa yayi yace." Kece ai kamar zuma kike sam bakya gimsa ta." Nauyin maganar sa taji yasa ya juya baya tana girgiza kai. Ya rungume ta k'am! Yana sakin ajiyar zuciya yace." Ki barni in gaisa da babyna." Shiru tayi, sai ya zura hannunsa yana shafo cikin tamkar Wanda yake mata tafiyar tsutsa ya dinga shafa mata mara lumshe idonta tayi tana sauke ajiyar zuciya, ni dai nan na futo na barsu. ******* Hajiya Kattime ce zaune a falo tana jiran futowar mijinta, sai gashi ya futo cikin shirin zaman fada, tace."Allah ya taimake ka ina da magana da kai." A k'asaince yace." Ina sauraron ki,zan shiga fada ne." Zama ta gyara tana fuskantar sa sosai tace." Dama tambaya nake so in maka." Yace." Ina sauraron ki." "Me yasa da yaran ka suka a mutu baka nuna damuwar ka ba? Kuma me yasa baka so a shiga wancan dakin na kulle."? A hasale! Yace." Ke saurara min da maganar banza haka." Shiru Kattime tayi ya cigaba da cewa." Idan mala'ikan d'aukar rai yazo kan 'yayana sai in hanashi kan wane dalili zan tashi hankalina zaki mutu zan mutu zamuje inda sukaje,saboda haka babu dalili da zai sa in tada hankalina, bayan wannan kuma kina maganar wancan dakin dake kulle dakin sirri na ne,ko da wasa kar ki kuskura ki kai kanki gurin zan iya sakin ki a kan hakan." Kattime ta saki baki tana kallonsa cike da mamaki. Futa yayi ya bar ta da tunani. ********* Mabaruka ne da saurin ta cikin mota zasu dawo gida, duk suna cikin maye, Alhaji Ashiru sai fafara gudu yake, ba tare da bin ka'idar tuki ba, wata k'atuwar mota ta buge su,suka gangara cikin daji,ihu!! Mabaruka take kurmawa tana k'okarin futowa ta fado kasa motar ta bi ta kan kafafunta, ta cillata can gefe, motar ta cigaba da katantanwa a gurin, tayi raga-raga Alhaji Saminu kansa ya fashe take ya amsa kiran ubangiji ita kuma Mabaruka ta suma. ******** Hajiya Kattime na zaune a inda take tun bayan futar mijin nata take tunani kan yadda zata yaudare shi har ta samu nasarar shiga dakin sirrin shi, murmushi tayi lokacin da ta tuno abunda zatayi masa, gyad'a kai tayi a fili tace." Insha Allah sai asirin ka ya tuno mutukar ba abun kirki kake shukawa ba." 'Yan a gaji ne suka kawo dauki gurin, ba tare da b'ata lokaci ba,a ka dauki Mabaruka a kaita asibiti ,shi kuma Alhaji Saminu cikin motar suka duba suka ga katin sa da shaidar garin da yake, nan suka saka gawar sa a mota domin su kaishi dangin sa. ******* Ranar Sarki! Da Balaraba sun sha soyayya sosai ji suke tamkar su kadai suke rayuwa a duniyar Balaraba har fargaba take su koma gida, in ta tuno da masifaffan kishiyoyinta wanda ko anan ma sun dunga damunsa da kiran waya babu dare babu rana. Sai k'arfe shida shu Shahid suka shigo gidan,dama me girma governor ya koma lokacin da yayi kwana uku, nan sukayi sallahr magariba, suka zauna suna cin abunci suna hira, Shatima ya futo da magunguna ya mik'a masa, b'ata fuska yayi yak'i karb'a.Balaraba na kallonsa, ta kalli Shatima a hankali tace." Ka bari zan bashi in anjima har na shafarwar ma." Shahid yace." Hakan yayi ke in kika bashi sai yafi karb'a mu kam kullum sai ya bamu wahala." Murmushi tayi kawai. Gyaran murya yayi yace. " Na fa gaji da zaman gidan nan, Dole gobe nima na futa in kusanta kaina ga Allah don haka sai Ku shirya futa dani." Shahid yace." Allah ya kaimu goben muna fatan a sanya mu cikin addu'a." Yace." Jikina na bani insha Allahu da k'afafu na zan koma gida." Shatima yace." Idan Allah ya yarda kuwa haka muke so." Nan suka cigaba da hira suna kallo, sai k'arfe goma da rabi sannan sukayi sallama kowa ya shige makwancin sa. Balaraba ce ta tura shi bedrom ta d'auko masa kayan bacci, ta taimaka masa ya sa, ta sanya nata sukayi kwanciyar su, cikin so da kaunar junan su. [10/6, 5:29 PM] BintubatulBintUmarAbbale👄: 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 _*GIMBIYA BALARABA*_ 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 ~*NA*~ _BINTA UMAR ABBALE_ *BINTUBATULA👄* *MARUBUCIYAR* ```NANA KHADIJA``` ```YARO DA KUDI``` ```GIMBIYA BALARABA``` ```TSANTSAR BUTULCI``` ```LADIDI K'WADAGA``` _*ZAMANI WRITES ASSOCIATON🤝🏻*_ _____________________ ```We are here to educate motivate and entertain aur reades``` _______________________ *JAN KUNNE⚠* _*Ban yarda a siyar min da d'aya daga cikin books d'in ba, duk mai buk'atarsu sai ya nemi numbar ta, ban yarda ka/ki siyar min da littafi to wallahi tallahi ban yafe ba kuma zamu tsaya gaban Ubangiji kan hakan, hattara!! Masu satar fasaha, ka nemi halak d'in ka yafi kaci da gumin wani, halak d'in ka shine mafi alkairi a gare ka.*_ *DEDICATED* ~*TO*~ *RAHAMA ALIYU* ~*ABUJA*~ _*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_ *🅿114* To bayan likitoci sun gama binkicen su a kan Mabaruka nan suka yanke shawarar yanke mata k'afafu domin babu wani sauran dubara da ta rage k'afafun Mabaruka duk sun karye karaya mafi muni! Wanda ko dori akayi baza su k'ara amfani ba, Mabaruka tana ji tana gani aka yanke mata k'afafu, ta futa daga cikin hayyacin ta saboda azaba fatan mutuwar ta kawai take. *********** Ranar Juma'a da misalin k'arfe d'aya shaura na rana, Waziri ya shigo cikin gidan, cikin sauri ya bude dakin sirrin shi ya shiga tare da kullewa, Hajiya Kattime na zaune a falo tana kallonsa, ya shiga ya fi minti goma a ciki sai gashi ya futo da sauri, yaja kofar tare da murza mata mukulli ya cire ya futa ba tare da ya kalli inda take ba. Kamar wacce aka bawa umarni ta mike Zumbur! Kofar dakin taje tana murza wa, abun mamaki kofar ta bude, bata tsaya tunanin komai ba ta afka cikin dakin, abunda ta gani yayi mutukar gigita mata tunani,nan take sai kanta ya fara juyawa ta zube a gurin a sume.! ******* Tsaf! Ta shirya shi cikin wani parkinstan irin na maza sunyi masa kyau sosai kanshi sanye da hula irin ta Larabawa tsaf idan ya shiga cikinsu zai saje, turare ta d'auko tana fesa masa, ya rike hannunta yana murzawa, murmushi tayi tace." Ka bari in fesa maka fa kar Ku makara gasu Shatima na jiran ka." A kasalance yace." Kece duk kin gajiyar dani jikina duk ciwo yake." Hararsa tayi kad'an tace." Kana da Neman magana ko." Murmushi yayi tare da lakuce mata hanci yace." Gaskiya ne ai." While chair d'in ta kama tana k'okarin tura shi domin ta futa dashi farlo, yace." Bari ki gani da izinin Allah yanzu zan taka k'afafuna." Balaraba ta matsa gefe tana kallon ikon Allah, ya yunkura bakinsa d'auke da Addu'a sai gashi tsaye da kafafunsa, cikin mutukar farin ciki ta furta "Alhamdullahi ala kullu halin." Shima cikin farin ciki yace." Allah ne abun godiya." K'okarin futa take yi ya rike hannunta da sauri yana fad'in " INA zakije kece 'yar jagora ta fa." Cike da farin ciki tace." Wallahi duk na rasa ya zanyi saboda farin ciki,hak'ika ubangiji naji rokan bawansa ne." Yace." Hakane mutukar bawa zai mik'a lamarin shi ga ubangijinsa to babu shakka dukanin Matsalar sa ta kare." Rungume shi tayi sosai tana sauke ajiyar zuciya, cire ta yayi daga jikinsa yana Dan murmushi yace." In kika karya min alwala fa , zamuje massalaci yanzu in mun dawo kiyi min tanadi me kyau." Ta sinne kanta kafadar shi suka futa a haka Su Shahid na zaune suna jiran futowar sa,kawai suka ganshi ya futo da k'afafun sa,tare suka mike tsaye cikin mamaki ! Shatima yace." Alhmdullahi Alhmdullahi ala kulli halin, yaushe ka mike ka fara tafiya." Suka fada a tare. Balaraba tace." Yanzu ne kamar da wasa wallahi ya mike." Shahid ya zube gurin yana sujjadar godiya ga Allah,shiko Shatima waya ya futo da ita zai kira mutan gida, Yace." Ka bari tukkuna muje mu dawo ko meye sai ya biyo baya in ka kira mutane yanzu zasu hana mu ibada." Shahid yace." Hakane bari muje mu dawo kawai, tare suka futa har da Balaraba tana sanye da dogun hijabinta fari tass dashi mijinta ya rike mata hannu suka fara tayi,dake gidan da suke bashi da nisa da harami da kafa suka tafi, Bayan an idar da sallahr jama'a suka zauna massalaci suna add'a tare da karatun alkur'ani me girma. ********** Waziri Zayyanu kuwa yana futa fadawansa suka rufa masa baya tare da kareshi da lema saboda rana sai baza babbar riga sukeyi, kamar daga sama yaji wani irin ihu!! A kunnensa ,zabura! Yayi yana kalle-kalle, wani ihun yaji Wanda yafi na d'azu, can yaji gurnanin Mak'asudu sama-sama yaji muryar shi yana fad'in "Aiki ya lalaceee!!!!! Ka janyo min ka janyowa kanka, ihuuuuuuuu!! Shikadai yake jin wannan ihu,ya tsaya yana dira-dira Wani bafade yace." Gyara kimtsi daiiii!!! Allah yaja zamaninka ko kayi mantuwa ne." Waziri ya girgiza masa kai a mutukar tsorace!! Yake, tuni jikinsa ya fara tsiyayar da gumi! Ya juya zai goma gida, k'afafun sa suka sark'e suka lauye suka kwalmad'e ba tare da bata lokaci ba ya zube a gurin, yanda k'afafun sa sukayi haka hannuwan sa sukayi, bakinsa ya kar kace idonsa ya wurkile, hallitunsa suka sauya gaba ki daya. Fadawansa suka saka salati tare da d'aukar sa domin kai shi cikin gida. Ko da suka shiga dashi cikin gidan suka tarar da tashin hankali domin sauran 'yayan ne tsaye kan Mahaifiyar su suna k'okarin ceto rayuwar ta. ********* Shamsiyya ce cikin kuryan d'akinsa tunda ta tashi da safe take jin ciwon ciki tayi shiru bata fada ba,sai da taga wani abu me kama da jini yana zubawa daga gabanta shine fa ta kira mahaifiyar ta ta fada mata, Uwa ta kira Lantana hankali a tashe! Tasan haihuwa CE,nan suka fara bata taimako ganin yadda take yunk'urin da alama haihuwar a kusa take. ******** Tashin hankalin da iyalin Waziri suka shiga ba a fad'ar sa, ganin yadda hallitun ubansu ya sauya ya munana ya jirkita sai kace ba mutum ba, tuni wasu suka fara kuka mussaman mata, da k'yar aka samu Kattime ta dawo hayyacin ta, ta kallin mijinata da ya koma kamar tsumma! Lokaci guda ubangiji ya tagayarashi tace." Alhamdullahi Allah na gode maka da ya mayar da kai haka hak'ika mutuwar ita tafi amfani da RAYUWAR ka, ka cucu ni ka cuci 'yayanka saboda son zuciya irin taka, ka kashe rai Wanda bamu San adadi ba, hak'ika nayi nadamar auranka bana fatan ko a lahira ubangiji ya had'a fuskoinmu" Tana gama maganar ta fashe da kuka me cin rai! Nan fa fadawan da suka kawo shi suka dinga silalewa suna futa cike da kunya. ******** Cikin hukuncin ubangiji Shamsiyya ta haihu lafiya inda ta haifi d'anta namiji yaro lafiyyaye dashi me kama da ubansa sak!!! Kuka sosai take uwa na tayata wai yau itace zata Goya Dan shege rayuwa kenan, haka Lantana ta dafa ruwan zafi tayiwa jinjiri Wanka tas ta shirya shi cikin kaya,ta goyashi tana daure zuciyarta itama amma kukan zuciya kam kullum sai tayi shi. ****** To ranar bayan sun dawo daga massalaci Shatima ya kira wayar mama ya Sanar mata halin da ake ciki, murna sosai Mama tayi ta dinga godewa Allah da ya kawo wa yaron ta sauk'i cikin lokaci kankani lallai duk Wanda ya dogara ga Allah yayi dace duniya da lahira Me girma governor kuwa yana ganin kamar yafi kowa farin ciki, don haka nan take yasa mutanan sa afara shirye-shiryen nad'i domin a cewarsa me Martaba Sarki!Almansur na biyu na dawowa za'a fara shagalin nadin sarauta, aikuwa gari ya d'auka da murna,dama labarin halin da Waziri yake ciki ya karad'e ko ina cike da waje harda wajan gari ma kowa yaji wasu na turr dashi wasu kuma na tausaya masa halin da yake ciki. Yau Litinin Wanda yayi dai-dai da sati uku kenan da tafiyar su saudi'a a yau din ne kuma suke d'aura niyyar dawowa gida cikin farin ciki da samun nasara, Balaraba tayi wani fresh da ita kyallin ciki duk ya bayyana a tattare da ita, ta kara cika da kwarjini sosai duk Wanda yasan mace me ciki ya kalleta a lokacin sai ya gane, shiko uban tafiyar tamkar ba Wanda yaje jinya ba ya had'a wata kiba fatarshi tayi sumul-sumul sai shek'i take,shida Balaraba har nasara Wanda yafi wani kyau da gogewa ****** Can gida kuwa ya hautsine da shagali gami da kid'e-kid'e da busa ko INA ka kalla jama'a ne suke kai kawo kowa yana cike da farin cikin dawowar me Martaba cikin aminci da koshin lafiya. Halisa da Azima sai kintse-kintse sukeyi kowacce tana k'okarin tayi abunda zata fi 'yar uwarta dashi, Azima kokari kawai take tana ji ajikinta kamar asirinta zai tuno tunda dai gashi Waziri yana cikin wani hali shine dama ya yaudare ta, gashi yanzu tana mutukar son auranta addu'a kawai take Allah ya rufa mata asiri. Fili jirgi a cike da a yarin gidan sarauta tare da ayarin me girma governor suna jiran saukar jirgin su, Sha biyu dai-dai jirgi ya sauka Shahid da Shatima ne a gaba, sai Sarki! Da BALARABA a bayansu ya rungomo ta jikinsa, tuni gadawan gurin suka fara zubewa suna kwasar gaisuwa, cike da kunya take k'okarin kwace jikinta ya ki s'akinta,cikin walwala suke gaisa da jama'arshi su Governor da Galadima da sauransu mota ta mussaman aka bude masa ya shiga ya zauna Balaraba ta shiga direba ya shiga domin su Kansu su Shahid wata motar daban suka shiga, direba yaja su suka nufi gida ***** Tsabar hayaniya jama'a tasa kansa ya fara ciwo nan take yace. da Babu direba su huce can shashen Maman shi, amma duk da haka jama'a bin motar suke suna banbadan ci tare da roko da kid'a kowa na fadin albarka cin bakinsa, Sarki ya futo cikin walwala ya dinga daga musu hannu ya rike hannun matar shi tamm!!fadawa suka dunga sanya duka da bulala da k'yar dai ya samu ya tattatka suka shige gurin Maman shi, wacce take tsaye gurin wani k'aton window tana ganin abunda yake faruwa, ganin yaron ta yayi kiba da lafiya gashi kamar ba Wanda ya tafi jinya ba,yasa ta godewa Allah sosai yana shigowa ya rungume ta, Balaraba ta koma gefe tana murmushi, Mama ta rik'o hannunta tana fadin"Zonan yarinyar ta hak'ika ke alkairi ce a tare damu kin zama Wani jigo na rayuwar mu, Balaraba ina jinki a cikin jinana tamkar nice na haifeki ubangiji Allah ya sauke ki lafiya." Balaraba tayi saurin sunkuyar da kanta cike da kunya, lallaima ashe sai da ya fadawa Mama halin da take ciki" Mama ta cigaba da cewa." Duk irin dawainiyar da kikayi da mijinki ina da labari, babu abunda zan iya saka miki dashi sai dai addu'a ladan ki na gurin Allah domin kinyi ibada kin bautatawa mijinki ubangiji Allah ya jikan iyayaenki yayi miki albarka a rayuwar ki." Balaraba ta sunkuyar da kai kasa tana amsawa da amin kwalla duk ta cika mata ido. Sadiya da Usuman ne tsaye can gefe suna kallonsu Mama ta kirasu tace." Kuzo ga aunty ta dawo,. " BALARABA ta daga Kai tana kallon yaran sunyi kyau sosai sun murje sun kara girma Sosai Mama take kula dasu, makaranta suke zuwa me tsada su saka suttura masu tsada babu. Shakka babu abunda zatace da Mama Fulani bisa alkairin ta a garesu. Nan b'angaran Mama suka biyo shi Halisa da Azima kowacce tana wace wannan gurin ado gwal sai walwali yake a jikinsu, Balaraba ta basu gurin ganin yadda sukeyi I junansu tamkar su bangaji juna,duk wannan k'awancan babu shi, kowacce ta kwaci kanta, Halisa duk ta kanainaye shi, a cewar ta ai girkin ta ne yau don haka duk su matsa gefe, shidai kawai kallonsu yake, yana tunanin halin da zai shiga zai kwana ba tare da gimbiyar sa ba, ya Riga ya saba da dumin jikinta da shagwaba shi da take sosai da soayyarsu duk dare, to itama b'angaran ta hakan take duk tayi sanyi tana tunanin ta yaya zatayi bacci bataji kanta a kirjinsa ba yana mata wassanin kamar yanda suka saba a saud'ia. *Daga wannan pege din sai na k'arshe Ku zauna cikin shiri*❤❤❤❤ [10/7, 12:25 PM] BintubatulBintUmarAbbale👄: 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 _*GIMBIYA BALARABA*_ 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 ~*NA*~ _BINTA UMAR ABBALE_ *BINTUBATULA👄* *MARUBUCIYAR* ```NANA KHADIJA``` ```YARO DA KUDI``` ```GIMBIYA BALARABA``` ```TSANTSAR BUTULCI``` ```LADIDI K'WADAGA``` _*ZAMANI WRITES ASSOCIATON🤝🏻*_ _____________________ ```We are here to educate motivate and entertain aur reades``` _______________________ *JAN KUNNE⚠* _*Ban yarda a siyar min da d'aya daga cikin books d'in ba, duk mai buk'atarsu sai ya nemi numbar ta, ban yarda ka/ki siyar min da littafi to wallahi tallahi ban yafe ba kuma zamu tsaya gaban Ubangiji kan hakan, hattara!! Masu satar fasaha, ka nemi halak d'in ka yafi kaci da gumin wani, halak d'in ka shine mafi alkairi a gare ka.*_ *DEDICATED* ~*TO*~ *RAHAMA ALIYU* ~*ABUJA*~ _*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_ 🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚 *🅿115* Da k'yar ya samu ya kufce daga hannun Halisa ya gudu part d'insa inda su Shahid suke zaman jiransa,nan kama kafin ya tafi sai ya gargade su kar wacce ta bishi, saboda hutawa zaiyi Balaraba cikin zuciyarta tace." Dama ni ko ka neme ni ba zuwa zanyi ba, zama zanyi inyi jinyar zuciyata da zatayi kwana hudu ba tare da Kai ba. Nan gurin Mama suka zauna dukaninsu, kallon Balaraba sukeyi a fakaice ganin yanda tayi Wani mugun kyau, tayar ta kamar ka tab'a jini ya futo ta kara cika da kwarjini, wani kyashi da bakin ciki ya damu zuciyarsu babu abunda ya kara daga musu hankali sai yanda Mama take kula da ita, tana kaf-kaf da ita da tayi motsi zatace "Ya akayi in dai akwai abunda kike sha'awar ci kiyi magana akawo miki." Girgikai kai kurum take cike da kunyar Maman, Halisa ta kalli Mama da jiki a sanyaye tace." Bata da lafiya ne."? Murmushi tayi tace." Cutar ta arziki ce ai insha Allahu kun kusa samun baby." Ita da Azima ban San wanda yafi wani shiga rud'u da tashin hankali ba, neman miyau tayi ta rasa abakin ta, idonta ya ciko da ruwan hawaye, Balaraba na da ciki,cikin kuma na masoyinta Wanda taci burin ita zata fara Haifa masa 'yaya, to wai abun tambaya anan, shine mutumin da ya tafi Neman lafiya ta yaya har ya iya kwanciyar aure babban abun tambaya yaya akai shi da bashi da kafa ya sarrafa kansa. *Dariya nayi nace lallai Halisa kin cika hamaguwa😄* To tunani da take shi Azima take duk sun shiga tashin hankali Lallai BALARABA tayi musu fintinkau tayi musu zarra,yanzu meye abunyi? Halisa take tambayar zuciyar ta, wani b'angare na zuciyar tata Yace mata,kawai yau kema ki matsa masa yayi miki ciki ki haihu, aikuwa ta yarda da wannan shawarar ta zuciyar tata. ******* Walidi ne ya siyowa Shamsiyya atamfa guda biyu dinkakkau ya siyo rago ranar suna yaro yaci sunan mahaifin su,wato Sallau, Salihu kenan, a ranar ne kuma labarin Mabaruka ya same su, ta hanyar k'afafun yada labarai, an nuno ta kwance gadon asibiti babu k'afafu, ana cigiyar danginta harda Lamar waya aka kawo wa Walidi aikuwa atake ya kira wayar yayi musu kwantan inda suke, ba tare da bata lokaci ba aka sako Mabaruka a mota tare da keken guragunta tana kuka tana da tasani abunda tayi, Ranar kwana sukai kuka Iya da Sadiya matar Maman suna ta tausar zuciyar su. ****** Ana kiran idar da sallahr Isha'i Halisa ta dura a part din Sarki! Cikin shirin ko ta kwana, tayi kwalliya iya kwalliya, sama ta hau domin baya farlo,shima tunda su Shahid suka tafi ya hau sama domin ya huta, bude kofar tayi ta shiga bakinta d'auke da sallama ya amsa babu yabo babu fallasa, zama tayi kusa dashi, tana sak'e-sak'en maganar da zata yi masa, yace." Halisa mun same Ku lafiya ko."? Cikin dauriya tace." Lafiya lau Yallab'ai." Shiru yana sauraron ta yasan da akwai magana a bakinta, yace." Wane tanadi kikayi min."? Yake tayi kawai tace." Ni wane tanadi zanyi maka,nice ma Nazo kayi min tanada kamar yanda kayiwa Balaraba." Bai gane hausarta ba yace." Wane tanadi nayi Mata." Inda-inda ta fara yace." Ke nake saurare." Tace.'Nima ciki nake so kamun.' Cikin mamaki yake kallonta. Yace." Ciki Allah ne ke ba dashi ba mutum ba, sai kice ni in zama silar shi." Kuka ya fara yi sosai harda sharb'ar majina." Yace." Meye abun kuka, kuma." Tace." Ina jin takaicin yadda wata zata fara haihuwa dakai bani ba." Tsaki yaja yana girgiza kai yace." Matsalata dake rashin wayo da dubara ni dake da balaraba babu Wanda ya Isa ya hana Allah ikonsa akanmu Balaraba zata fara haihuwa dani haka Allah ya tsara.'' Kuka sosai takeyi takasa cewa komai ta kwanta kan bed din tana Jan ajiyar zuciya, tausayinta ne ya kamashi,ya kashe futal dakin tare da aje k'aramin littafin hannunsa ya rungume ta yana fada mata daddadan kalamai, nan labari ya sha BABBAN, na futo na barsu ina fatan samun nasara da 'yaya masu albarka. To sarki! Ya biya Halisa domin dai jiya ya kashe ta da soyayyar sa mai wahalar mantawa lokaci kad'an ta manta da damuwar ta,ta cigaba da kyautatata masa. ****** Tsito ne ya dura a gidan kamar tsohon mahaukaci ya nufi b'angaran Hajiya Kulu me dakin kudu, yazo domin ya karb'i sauran kud'in aikin sa. Nan ya samu babu. Kowa a shashen nata sai hadiman ta, suka ce masa satin ta biyu bata gida,hakanan yaranta suma ba kullum suke kwana a gida ba, haka ya futo yana tunanin ina zashi,domin yanzu duk aljanun da suke kanshi sun dare sun gudu baya iya yin aikin komai watarana ma da yunwa yake kwana, ya tabbatar da cewa abunda suka aikata da Waziri ne ta shafe shi, zuciyarsa ta bashi shawarar kawai yaje ya nemi afuwar iyalin Waziri ko Allah zai sa ya gama da duniya lafiya, sannan suyi masa iso gurin Sarki! Almansur domin ya nemi gafarar sa Halin da yaga Waziri a ciki ya bashi tsoro bakinsa ya dinga rawa ya rasa abun cewa,Hajiya Kattime tace." Bawan Allah daga ina haka domin banga ne ka ba."? Tsito ya fashe da kuka yana fad'in." Yanzu haka Waziri ya koma oo ni Tsito." Kattime tace." Kayi min bayani mana, yace." Nine Tsito wanda nayi ma mijin ki aiki duk Dan yayi mulki nan ya warware mata duk abunda ya faru, yaran ta suka taso domin suyi masa duka ta hanasu, tace." Ku kyale shi shima zai ga karshen sa, nan Tsito yayi dasu su masa iso gurin me Martaba Kattime ta hana, haka suka tarkatashi suka futa dashi fadawa suka tasa keyarsa har waje, yana futa ya kasa gane hanya kawai sai ya dauki wata haya ta daban yana tafiya yana tsayawa bola-bola yana tsince-tsince duk ledar da ya gani sai ya d'auka ya sa a bakinsa yana taunawa. *Ubangiji Allah kasa muyi kyakyawan k'arshe* ******* Kwana biyu da Halisa tayi ta samu kulawa sosai a gurinsa ganin yanda ta kwantar masa da kai tana kula dashi komai sai tace idan BALARABA ta haihu za'ayi kaza da kaza, hakan ne yasa ya Sakar mata jiki suka sha soyayya. Azima ya ta karb'i girki sai girin gidishi take tasha magunguna mata kamar banza mararta sai kullewa take jira kawai take dare yayi ta shiga part din Yallab'ai a kashe boss. ***** Hajiya Kattime ce tayi sallama ta shiga a nutsue Mama ta amsa Jakadiya ta gyara mata gurin zama,sannan ta futa ta basu guri, Kattime ta gyara zama tana fadin ." Fulani magana nake tafe da ita." Mama tace." Ai tunda naga fuskar ki nasan akwai magana." Kattime tace." Wallahi kuwa, jiya na samu wani labari da bakin da ya fada min bazai k'arya kai asalima shine ya asassa al'amarin." Mama ta zuba mata ido, Kattime ta cigaba da cewa." Kin san Azima da ita aka had'a baki gurin cutar da Almansur." Mama ta mike zaune sosai tana kallon ta cikin mamaki! Kattime ta cigaba da cewa.' Jiya Tsito mashirikin da yayi aikin yazo ya warware min komai, saboda haka Nazo na fada miki auran Azima da Almansur dama da wata manufa aka had'a shi don haka ki umarce shi da ya rabu da ita tun wuri." Mama jikinta yayi sanyi sosai da sosai tace." Dama ni kaina banyi na'am da wannan hadin ba wallahi oh! Mugu bashi da kama yanzu Azima itace ta bawa yarona guba yaci domin ya nakasa."? Kattime tace." Kina mamakin wannan duniyar wallahi." Mama tace." Yanzu zan sanya ayi min kiran su ki zauna a gaban ki za'ayi komai, Jakadiya ta kira ta umarce ta ta kira mata Azima da Halisa BALARABA Wayar ta ta d'auka ta kira uban gayyar, suna tare da me girma governor suna shirye-shuiyen yanda za'a gudanar da nadin sarauta,domin an tsai da rana jama'azuwa ,Yaga kiran Mama a nutse ya d'auka tace." Kazo yanzu shashena." "Insha Allahu ganin zuwa." Ya fada yana kashe wayar. Sallama sukayi da governor suka futo tare me girma ya shiga mota tare da mutanansa shi kuma ya. Nufi shashen Maman shi tare da jama'ar sa, duk suna zaune suna jiran isowarsa yayi sallama ya shiga duk suka amsa, matansa na rige-rigen gaishe ya amsa mu a nutse ya zauna, yana gaida Maman shi tare da Hajiya Kattime, Fulani tace." Kattime yi musu bayani da bakin ki." Nan Kattime ta fara fada masa duk abunda ya faru tun daga farko har k'arshe da manufar Waziri akan auransa da Azima. Nan take Sarki! Ya tuno da ranar da ya shiga gurin Azima da daddare har yayi Tara da ita tunda lokacin nan ya tashi da wannan ciwo, Azima tayi tsuru-tsuru tuni hawaye ya soma ambaliya a fuskarta tayi da tasani yagi cikin kwando shikkenan yanzu tasan karshen zamanta dashi ya kare ganin yadda ransa yayi mugun b'aci, shiru farlo na minti biyar yayi gyaran murya yana goge gumn da ke tsatsafo masa, yace." Mama ki gafarce ni, da abunda zan aikata yanzu hak'ika zama da Azima babbar musiba ce saboda haka na sawwake mata igiya guda taje in ta samu miji tayi aure." Yana gama fadin haka ya mike ya futa zuciyarsa babu dad'i. Babu Wanda yace komai cikinsu,Azima ta dunga kuka tana rokan Mama ta sanya shi ya janye sakin Mama tayi shiru da rarrafe taje ta rike k'afafun Halisa tana rokonta Halisa ta fuzge kafarta tana maka mata harara tace." Wallahi na tsane ki Azima muguwar azzalima kawai." Cikin kuka Takarasa kusa da Balaraba tana rokonta wai tabawa Sarki hakuri Balaraba tayi shiru kawai tana Mamakin halin Dan Adam. Fadawan dake waje mama ta umarta tace su futa da Azima kuma su tsaya kanta ta had'a duk wani ko matsanta ta kama gabanta. Aikuwa haka akayi aka tasa Azima a gaba har garin su. ******** 🔕📣📣📣🔊🔊🔊🔊📢🔱🔱🔱🔱🔱🎶🎶🎶🎶🎶🎶🎶🎶🎶🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌙💥💥💥💥💥💥💥💥🧝🏼‍♀🤴🏻🤴🏻👸🏻👸🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🧝🏼‍♀ *Rana bata karya* Yau juma'a uku ga watan uku, yau aka gudanar da shagalin nadin sarauta. Wannan nad'i ya samu halartar dubban mutane kama daga shugabanin kasa she,governor ni shahararun malamai da limamai da shahararun 'yan kasuwa duk sun samu damar halarta nad'in sarautar Sarki! Almansur YARO me dattako me halin manya me nagarta da sanin abunda takeyi kowa na masa fatan alkari tare da jagoranci me cikin adalci, lokacin da ake gudanar da wannan nad'i Waziri na kwance yana zurarar da hawaye duk an d'ad'e an barshi shi kadai kuka yake tukuro gami da nadamar abunda ya aikata,, labari ya riske cewar ga Almansur can an mik'a masa sandar mulki, ihu!!! Ya kurma yana buga kansa a bango nan take ya futa daga hayyacinsa . Balaraba takasa nutsuwa sai shige da fuce take da hidima da mutane duk 'yan gidansu sunzo tare da wasu 'yan unguwar su, Wanda suke mata wani irin ladabi da biyayya tamkar zasuyi mata sujjada, ita kam sam bata son abunda suke mata. Lantana ce me sallamar baki da taga Balaraba ta motsa zata hanata wai saboda cikin jikinta, su Uwa da Iyalinta na gefe guda gwanin tausayi, Mabaruka kadai aka bari a gida saboda babu k'afafu, Shamsiyya kuwa danta ya girma har yana rarrafe, Walidi dashi ake komai yana can waje cikin jama'a yana shige da fuce. Har magariba gidan sarautar babu masaka tsinke, shi kanshi me Martabar bai samu damat shigowa gida ba tun safe da ya futa sai bayan sallahr Isha'i lokacin jama'a sunyi sanyi, ya nufi part d'insa tare da dakarunsa. Balaraba da Halisa sun shirya masa guri sosai suna tsaye bakin kofar shigowa sun ci uwar kwalliya ba'a magana, yana shigowa suka fara watsa masa wani abu me kyalkyali yana takawa wani. A jikinsa, murmushi yayi ya rungumo su gefan kafad'unsa yana manna musu kisses cike da so da kauna yace." Allah yayi muku albarka."suka amsa da amin. Sama suka nufa suna rungume a jikinsa. ***** Kulu me dakin kudu kuwa tun da taji labarin abunda ya faru da Waziri ta tattara inata-inata ta gudu domin tana jin tsoron tunowar asirinta, ba karamar sata ta labta ba, Sarki! Da ya samu labari yaji ciwon abun sosai saboda 'yan uwansa su Shukura dole duk inda suka shiga ya sanya a nemo su. ***** Kwana biyu kura ta lafa me Martaba ya fara zama a fada cikin aminci yana gudanar da mulki cikin adalci da yanda Allah yace aikuwa jama'ar gari suka fara kiransa da "D'an karaminsu babansu, Babansu kuma a cikin sarakai mulki azo a koya a gurin shi, Sarki! Ya zama mutum na matasa na tsofaffi na dattijai na yara kanana. ***** Balaraba ciki ya tsufa sosai ya shiga wata tara yayin da Halisa ma NATA yake da wata shida,me Martaba kullum cikin sarauraren haihuwar ta yake tayi kib'a sosai ga wani girma da cikin yayi shiyasa sai ya shiga gida sau uku a rana har India lya futa sallah baya komawa fada sai ya koma ya ga jikin nata. ***** Ranar litinin misalin k'arfe goma da rabi na safe Allah y sauke ta lafiya inda ta haifi 'yaya uku rigis duk maza, cikin hukuncin Ubangiji haihuwa tazo mata cikin sauk'i ba tare da tasha wahala me tsanani ba, Ubangiji kenan me bayarwa da hanawa Allah ya azurta me Martaba da 'yaya uku lokaci guda, gida ya d'auka gari ya d'auka tunda ga ranar aka fara shagali babu kama hannun YARO,Mama kullum a tafe take gurin 'yayanku kullum cikin yi musu hidima take, shi kam me Martaba ai da k'yar yanzu yake zaman fada, kullum yana nanike da baby's din sa tare da Queen d'inshi da yake jin yanzu ta zame masa wani b'angare na RAYUWAR sa, ranar suna yara suka ci sunan Abdullahi Abdulraham Abudr jabbar, shagali da aka gudanar har sai da na wajan gari ya San dashi domin gidanan tv ne suka dinga d'auka suna watsa shi duniya me jego da 'yayanta tare da me girma Me martaba sunga kauna da soyayyar mutan gari,. Iya ce ta zauna mata har sai da akayi arba'in, sannan aka had'a mata shatara ta arziki aka kaita har gida, tare dasu Sadiya da Usuman zasuje Hutu kafin a koma makaranta. Tofaaa! Yallab'ai fa na ganin ta fara sallah ya bud'e huta domin can gurin Halisa babu bayani cikinta ya tsufa gashi daman can raguwa ce bata d'aukar laluransa, Balaraba ta karbe shi hannu biyu ta fara shayar dashi madara da Zuma irin na aure, sai ga Yallab'ai yana kin zuwa fada, kullum yana kan aiki 😄Balaraba tace batasan wannan ba, sai da yaga ranta ya b'aci sannan ya cigaba da zaman fada, hakan ma tana raya masa zai gudu ya biya buktarsa sannan yayi Wanka ya koma, aikuwa ciki ya samu babu shiri. Watansu Abdulrrahan uku Halisa ta haihu 'yan ta gwaye duk mata, Wai-wai murna gurin Yallab'ai ya samu 'yan mata masu kama dashi, ranar suna an dagargaji buki babs suka ci sunansu Hasana da husaina. Balaraba kuwa ta fahimci wani cikin ne da ita sai ta fara Neman yaya zatayi gudun karsu Abudul su sha ciki.nan family dector dinsu yace babu matsala zata cigaba da shayar dasu da nonon ta, amma cikin na kaiwa wata shida dole ta cire su daga nono sai a dorasu kan madara me kyau. Aikuwa haka akayi yara suka cigaba da shan nono Mamansu cikin koshin lafiya, inda Yallab'ai ya durfafe ta, ganin yadda yake kwasar gara, kunsan dai mace me yaron ciki abun marmari ce ga mijinta. *Alhamdullahi* *Alhmdullahi* *Alhmdullahi* Nan na kawo karshen wannan littafin Ubangiji Allah ka yafe min kurakurana abunda na rubuta dai dai Allah kasa a amfana ka sanyamu cikin ladan baki d'aya 👏🏻👏🏻 *🦹🏼‍♂BABBAN YARO🦹🏼‍♂* Cigaban littafin. _*Yaro da kud'i💵💵*_ *WASA FARIN GIRKI📲* *INA KUKE MASOYA LITTAFIN YARO DA KUD'I, TO MAZA KU GARZAYO KU CASKALO KU ANTAYO KU SAMU CIGABAN YARO DA KUD'I WATO BABBAN YARO WASA FARIN GIRKI, YANZU AKA FARA KAFCEN, WANNAN DABAN YAKE DA SAURAN DOMIN YAZO MUKU DA SABON SALO ME SANYA KU NISHAD'I, BABBAN YARO LITTAFI NE ME K'UNSHE DA RIKITA-RIKITA, BABBAN YARO!!!!! BABU SHAKKA YA AMSA SUNAN SA🦹🏼‍♂💷 BABBAN YARO YA ZO DA SABON SALO MAI SAKA NISHAD'I MAZA KU GARZAYO KU SAMU NAKU KAN KUD'I NAIRA D'ARI UKU KACAL KU BIYA KU SAMU BABBAN YARO DOMIN KU GA YA KAFCAN YAKE🦹🏼‍♂. Hummmm!!! KAR KU BARI A BAKU LABARI...... DUK ME BUK'ATA ZAI NEMI TA WANNAN NUMBAR KAMAR HAKA* 08089965176 07084653262 *NI CE DAI HAR ILA YAU* _BINTA UMAR ABBALE_ ```MARUBUCIYAR WANNAN LITTATAFAN``` *NANA KHADIJA* *YARO DA KUDI* *GIMBIYA BALARABA* *TSANTSAR BUTULCI* *LADIDI K'WADAGA* *MUJE ZUWA MASOYA NA* A KAFTA!!!!!!!!!!!!!! *BABBAN YARO CIGABAN LITTAFIN YARO DA KUDI🦹🏼‍♂💵💵💵💵* Kar Ku bari a baku labari