🐎 *BAƘAR MASARAUTA* 🐎 👑👑 🦋 🦅🕊🦆 🐍🎠🐄🏹 _*NA*_ UMAR FARUQ*D* *BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM* *BAƘAR MASAURATA YASHA BAMBAN DA SAURAN LABARAN, LABARI NE IRIN WANDA BAKU TAƁA CIKIN KARO DA KALAR SABA.* *DUK ABUN DA ZAKU GANI ACIKIN LABARIN NAN ƘIR-ƘIRARRE NE, KAMA DAGA SUNAYEN GARURUWA HAR IZUWA NA MASARAUTU, KAMAR YACCE DUKA LABARIN YA KASAN CE ƘIR-ƘIRARRE.* *BAN YARDA WANI KO WATA BA SU JUYAMUN LABARI TA KOWACE SIGA BA TARE DA IZININA BA.* *PAGE 01* _SHIMFIƊA_ *ƘASAR HAUSA* Ƙasa ce mai tsantsar girma da faɗi, ƙasace wacce Allah ya azurta ta da mayawaitan al'umma, maban-ban ta ƙabilu da mazaunai daban daban, ƙasa ce mai ɗauke da jahohi 30 cif acikin ta, yayin da jahohin suka kasan ce ayanku na daban daban, ƙasa ce wacce ta kasan ce ƙasar hausawa, duk da dai basu kaɗai bane suka kasan ce acikin ta, sai dai kuma mafi yawan jahohin da suke acikin ƙasar yawan cin su duka na hausawa da fulani ne, wato dai sune masu ƙasar. *MASARAUTAR WASAI* Ɗaya daga cikin manyan masarautun da suke aƙarƙashin ƙasar hausa kenan. JAHAR WASAI Jahace mai matuƙar girma da faɗi, jahace wacce take ɗaya daga cikin manya-manyan jahohin da suke a ƙar-ƙashin ƙasar hausa, jaha ce ta musulunci da musulmai, jaha ce wacce take da manyan ƴan kasuwa tare da manyan kasuwani acikin ta, domin ko itace ta kasan ce cibiyar kasuwan ci ta ƙasar hausa. Yayin da ita kuma masauratar wasai ta kasan ce ɗaya daga cikin manya manyan masarautun da suke acikin ƙasar hausa, sannan kuma ta kasan ce masarauta ɗaya acikin jahar wasai, wato dai itace mamallakiyar jahar gaba ɗaya. Masarautar wasai masarauta ce mai tsantsar girma da ƙarfin mulki, masarauta ce wacce ta kafa tarihi acikin ƙasar hausa, masaurata ce mai ƙarfin mulki wacce ake ji da ita aduk faɗin ƙasar hausa harma da ƙasashen da suke maƙota ka da ƙasar. *** *JAHAR KAGUL* Itama dai jahar kagul ta kasan ce dlɗaya daga cikin manyan jahohi ne da suke aƙasar hausa, sai dai ita kuma jahar kagul tana ayankin yammacin ƙasar hausa ne, saɓanin jarah wasai da take a arewacin ƙasar hausa. Jahar kagul ta kasan ce jahar fulani ce ita, wato dai kusan duk mazaunan cikin ta sun kasan ce fulani makiyaya ne, sai dai ita kuma ta kasan ce ɗaya daga cikin jahohin da addinin musulunci baiyi zurfi acikin ta ba, domin kuwa mafiya yawan mazaunan cikin ƙasar ko karatun sallah basu iya ba bare aje ga sanin tauhidi da hadisai, kai ataƙaice ma dai sallahr duka bata dame su ba, domin ko hatta da gidan sarautar dake cikin ƙasar shima babu addinin acikin sa, dan kuwa babu abun da suka sanya agaba sai tsafi da harkar kula da dabbobin su, kasan cewar itace babbar jahar kiwo aƙasar hausa, domin kuwa kusan duk wasu shanu da ake kadawa acikin jahohi talatin da suke aƙasar hausa suna futowa ne daga jahar kagul. Hakan yasa ɗaukacin mutanen dake cikin jahar suka maida hankulan su akan kiwo da asirce asricen da zasu bawa dabbobin su kariya fiye da komai agidan duniya, ciki kuwa har da addinin su, wato dai in taƙaice muku zance jahar kagul itace cibiyar kiwo ta ƙasar hausa. *MASARAUTAR FULƊE* Masarauta ɗaya ƙwal dake acikin jahar kagul, wato dai itace mammallakiyar jahar gaba ɗaya. Masauratar fulɗe tana ɗaya daga cikin masarautu masu tarin dukiya da kafaffen tarihi acikin ƙasar hausa, masarauta ce ta fulani wacce ta kafa tarihi ta fannin harkar kiwo, domin kuwa duk wasu makiyaya da suke acikin ƙasar hausa kusan suna aƙar-ƙashin mulkin masarautar fulɗe ne. Masaurata ce wacce ta haɗa wasu irin mutane acikin ta, waƴan da ko kaɗan babu Allah azuciyar su, duk da dai suna iƙirarin su musulmai ne ako da yaushe, sai dai gaba ɗaya jama'ar cikin masarautar babu wanda zaka tambaye sa wani abu akan addini ya iya baka amsa, ciki kuwa har da sarki mai ci, bar su dai su ta fannin tsaface tsaface anan suka fi ƙarfi, domin kuwa hatta da ɗan ƙaramin yaro dake cikin masarautar zaka same sa ɗauke da tsafin sa ne, wato ya iya tsafuka kala kala ankoya masa an kuma basa tun yana ƙarami, ga su kuma da wata irin baƙar zuciya wacce bata tanƙwaru wa, wato dai idan suka ce hakan za suyi babu wanda ya isa ya canza su daga hakan, haka kuma idan suka ce baza suyi ba to fa babu wanda ya isa ya sasu suyi, sannan kuma basa yafiya ga mutumin da ya zalince su ko kuma yake shirin cutar da su, ko yake farautar wani abu nasu muddin suka gano sa. Hakan yasan ya babu wasu da suke iya shigo musu cikin ƙasa suyi musu satar dabbobi, duk da dai ansha kawo hara-hare daga jahohi daban daban, sai dai ako da yaushe idan ɓarayin sun shiryo sunzo babu wata riba da suke samu sai dai ma akarɓi ransu anan tsabar ƙarfin asirin su. Gaba ɗaya mutanen cikin jahar kusan sun kasan ce fararen fata ne, masu matukar kyawun hallitar jiki da fuska, tare da yalwataccen gashi, kama daga mazan su har matan su, hakan yasa masu kuɗin ƙasar hausa suke yawan zuwa jahar ta kagul neman aure cikin ta, sai dai kuma koda sun je ɗin duk da yawan dukiyar da suke da ita ba afiya basu ba, kasan cewar su mutane waƴan da basu fiye yadda da wani bare ba musamman ma bahaushen mutum, balle kuma har su sake da shi. **** *ƘASAR MALIN* YAN KIN JAHAR KARFUZ. Jahar karfuz ta kasance jaha mai matuƙar girma da faɗi, jahace wacce take aƙar-ƙashin ƙasar malin, jahace wacce Allah yayi ta da yawan manya-manyan ruwaye, tare da dogayen bishiyu da duwarwatsu, domin kuwa duk inda zaka bulla acikin jahar kusan zaka yanka ne ta tsakan-kanin dogayen korayen itatuwa tare da manya manyan ruwaye masu kwaranya. Ba afiya yi musu rana ba duka ajahar tasu, koma nace kusan aƙasar tasu ta malin baki daya, sai dai kuma aduk lokacin da aka tashi yi musu to bata zuwar musu da sauƙi, dan ko hatta futa ba kowa ke iyayi ba idan ba dare ne yayi ba a'irin yana yin. Ita dai jahar karfuz ta kasan ce jahar da babu musulunci acikin ta ko kaɗan, asalima gaba ɗaya basu san mene ne musuluncin ba, mutane ne su waƴan da suke bautar gumaka, huta, ruwa da rana, wato dai gaba ɗayan su basu san Allah ba. *BAƘAR MASARAUTA* Masarauta ɗaya ƙwal dake cikin jahar karfuz, masarautar da basu san Allah ba bare suyi aiki da faɗar sa, masarautar da basu mai da kisan rai abakin komai ba, masarautar da rashin imani da yahudanci ya tattaru ya ƙare acikin ta, masarautar da suka mai da zubar da jinin mutum tamkar zubar da jinin rago. Masarautar da take da matuƙar girma tare da ƙarfin mulki da iko, tsantsar zalunci da tarin yahudanci, dan ko ataƙaice su ko sallah ma basu san ta ba balle su san falalar ta har suyi ta. Wannan kenan. Tafe take cikin takun ta na tsantsar izza, isa tare da ji da kai. Kyakkyawa ce ajin farko, duk da dai bata kasance farar fata ba, sai dai kuma baƙin ta shima bai zamto na muni ba, irin baƙin nan ne wanda hausawa kewa laƙabi da wankan tarwatsa. Tana da tsayi tare da faɗi da tudun jiki dai dai misali irin wanda kowa ke so. Tana da manya manyan idanuwa farare masu matuƙar kyau da ɗaukar hankali, yayin da bakin ta kuma ya kasance ɗan tsukut da shi mai ɗauke da jajayen laɓɓa akan sa, sai dogon hancin ta siriri da yake tsaye cak akan fuskar ta yarce kasan ɗora sa tayi. Kai ataƙaice dai gaba ɗayan ta bata da makusa tako ina, dan ko hatta da gashin dake kan idanuwan ta idan ba ƙura mata ido kayi ba sai ka rantse kace ɗora sa tayi, sabo da yarce suke da matuƙar tsayi. GIMBIYA TASMIR kennan, ƴa mace ƙwalli ɗaya ƙwal ga sarki barbaru shugaban baƙar masarauta, gimbiya mai matuƙar kwarjini, wacce sautin takun ta kawai ke girgiza zuciyoyin bayi, gimbiyar da da zarar ta biyo hanya to babu wanda ya isa ya bayyana awurin idan aka cire ƴan rakiyar ta muddin bata kai ga wucewa ba tsabar ƙarfin ikon ta, gimbiyar da sautn muryar ta ke hautsina ƙwaƙwalen bayi, duk da dai ba fiye yin maganar tayi bama, dan azahirin gaskiya magana ma matuƙar wahalar da ita take yi, domin kuwa sai akawana atashi ba tare da ta furta koda kalma ɗaya ba ga kowa. Sanye take da wata doguwar riga baƙa mai matuƙar tsayi da faɗi, tayar ce har take sharar ƙasar duk wurin da ta taka, yayin wasu matasan ƴammata guda biyu suke riƙe da wasu yankuna na daga jikin rigar sabo da ta rage sharar ƙasa. Ɗaure suke da baƙin ƙyalle aƙugun su, wanda duka tsayin sa ya tsaya a'iyakar gwiwoyin su, sai wasu ƴan ɓingilallun fararen riguna na yadi masu matuƙar faɗi babu tsayi sanye ajikin su, yayin da jikin rigunan kuma daga gaban su suka kasan ce ɗauke da zanen tambarin masarautar tasu, wanda aka ɗinka sa da baƙin zare adai dai ƙirjin su, sai fuskokin su suma zane suke da tambarin masarautar da sukayi ado da kwalli ta ko ina. Yayin da gefe da gefen su harma da bayan su kuma wasu irin danƙara- danƙaran maza ke biye da su, hannuwan su ɗauke da zura zuran bulalai tare da takubbai soke aƙugunan su, wanda hakan ke nuni da sune dakarun ta, babu wanda ke sanye da riga ajikin sa, sai baƙin ƙyalle mai haɗe da gajeran wando iyakar gwiwa dake ɗaure aƙugun su, gaba ɗaya jikin su zane yake da tambarin masarautar tasu ta ko ina da akayi sa da baƙin fenti tun daga fuska har ƙafa. Kallo ɗaya zaka musu kayi matuƙar razana idan baka saba ganin su ba, sabo da yarce ƙwayoyin idanuwan su suka kasan ce jajaye, gasu su kuma baƙaƙe huluk dasu, duk wanda ya gansu ba sai anfaɗa masa ba zai san babu imani tattare da su, kai ataƙaice ma basu san saba ko kaɗan. Sosai wurin yayi tsit yarce kasan ba ataɓa hallitar mutum ba, kamar yacce kowane wuri yake kasan cewa aduk lokacin da ta kasan ce ashi, babu sautin da ake ji yana tashi sai na takun ta. Kallo ɗaya zaka mata ka fahimci ranta amatuƙar ɓace yake, sabo da yarce fuskar ta me ɗauke da zannen tambarin nasarautar su agaban goshin ta take amugun ɗaure, ko kaɗan babu alamun annuri tattare da ita, bare har asa ran samun rahama daga gare ta. Sun yi tafiya mai ɗan tsayi daga cikin gidan sarautar, tukun suka ɓulla cikin wani ƙaton wuri mai ɗauke da dogayen bishiyu da duwar-warsu zageye dashi. Kai tsaye ta doshi ƙofar dake kallo su idanuwan ta ƙur akan ta, yayin da suma dakarun nata ke biye da ita har suka ƙarasa bakin jibgegiyar ƙofar dake da matuƙar girma da kauri. Tsaye tayi cak daga gaban ƙofar ita batayi gaba ba sannan kuma ita batai baya ba, yayin da su kuma ƴammatan nan da suke riƙe da rigar ta sukayi hanzarin sakin rigar, suna masu zube gwiwoyin su tare da durƙusar da kansu ƙasa. Hannun daman ta tamiƙar tana mai buɗe tafin sa ba tare da tace ƙala ba. Dasauri ɗaya daga cikin jibga-jibgan mutanen nan da yake daga bayan ta ya juya baya, tukun ya fara tafiya da baya da baya yana mai yin inda take har sai da ya ƙarasa kusa da ita, kana ya zube gwiwoyin sa aƙasa tare da durƙusar da kansa ƙasa, sannan ya zaro wata zureriyar jar takobi ajikin sa yana mai miƙa mata ita, har lokacin kuma bai bari idanuwan sa sun kalli koda fuskar ta ba balle su shiga cikin nata. Ba tare da ta ɗago ta kalli inda yake ba ta ƙara ware tafin hannun ta, tukun shi kuma wannan ba dakaren ya ɗora mata takobin akan tafin hannun nata, kana tamai da yatsun ta tana mai dunƙule takobin acikin su. Dasauri badakaran ya ƙara juya mata baya, tukun ya miƙe yana mai cigaba da tafiya da baya da baya har ya koma inda yake, sannan ya ƙara tsayawa cak ya koma tamkar bishiyar da aka dasa. Rumtse idanuwan ta tayi da ƙarfi, tukun daga bisani ta buɗe su akan ƙofar dake kallon ta, kana ta ɗaga zureriyar jar takobin dake dunƙule atafin hannun ta tana mai nuna ƙofar da ita, tukun ta buɗe bakin ta cikin kakkausar muryar ta mai matuƙar sauti tana mai faɗin. "Gargabiluuuu!" Take jikin bayin nan mata ya ɗauki rawa yarce kasan mazari, gumi na yanko musu sabo da yarce sautin muryar ta ya daki zuciyar su ba tare da sunyi zato ba, yayin da su kuma jibga jibgan dakarun nan maza suka sake ƙamewa cak a'inda suke yarce kasan icci na. Ahankali -ahankali murfin ƙofar ya fara buɗewa har ya buɗe duka akan idanuwan ta, tukun daga bisani ta janye ƙwayar idanuwan nata daga kan ƙofar tana mai mai dasu kan tafin hannun ta da yake ɗauke da zureriyar jar takobin nan, sannan ta sake miƙar da hannun gefe ba tare da tace komai ba. Dasauri wannan badakaran da yakawo mata takobin ya sake tawowa da baya da baya har ya ƙaraso inda take, kana ya zube guiwoyin sa aƙasa, sannan ya miƙa hannu ya ɗauki takobin ba tare da ya kalli fuskar ta ba yanzu ma. Sake miƙewa yayi ya koma da baya da bayan sa kamar yacce yazo. Sai da ta ɗauki kimanin daƙiƙa goma atsaye awurin tana kallon ɗakin da yake kallon ta wanda yake baƙiƙƙirin da duhu, ba ahangen komai na cikin sa, tukun daga bisani ta fara ɗaga ƙafafuwan ta masu sanye da sarƙoƙin gwal ajiki waƴan da suke futar da sauti aduk lokacin da take tafiya, tana mai dosar ɗakin gadan -gadan. Cak ta tsaya adai dai bakin ƙofar ɗakin ba tare da ta shiga ciki ba. Dunƙule tafin hannun ta tayi tana mai yin wasu surutai, tukun daga bisani ta buɗe sa tana mai watsa wasu abubuwa da suka bayyana akan sa zuwa cikin ɗakin. Take kuwa haske ya bayyana acikin sa, tukun ta sake ɗaga ƙafafuwan ta tana mai tura kanta cikin sa. Ɗan ƙaramin ɗaki ne wanda idan da mutane zasu zauna aciki duka baifi yaci shimfiɗun mutum biyu ba zai cike, sai wasu kaskwayen huta (randina) da suke ajiye akowace kusurwa ta ɗakin huta na tashi daga cikin su, wacce tayi matuƙar zafafa ɗakin tako ina. Tsaye tai daga bakin ƙofa tana mai kallon yarce yake tsaye awurin, gaba ɗayan sa ya jiƙe sharkaf har yana ɗiga da gumi, kai idan baka sani ba zaka rantse kace daga cikin ruwa aka zarosa tsabar yacce ruwan ke sauka akowacce kafa ta jikin sa. Matashin saurayi ne mai kimanin shekaru talatin aduniya, ɗaure yake jikin wasu ƙarafa masu matuƙar girma, yayin da jikin sa ya kasan ce babu ko riga akai, sai ɗan ƙaramin farin yadi dake ɗaure aƙugun sa kawai. BEER Ahankali ta fara ɗaga ƙafafuwan ta tana mai dosar inda yake idanuwan ta ƙur akan sa. Tun lokacin da ta ƙaraso bakin wurin yaji alamun zuwan nata ajikin sa kamar yacce yake ji aduk lokacin da sukai kusanci da ita, sai dai kuma ayarce kansa ke ɗage asama idanuwan sa na kallon rufin dake saman ɗakin kai bazaka taɓa cewa yasan da wanzuwar mutum awurin ba, domin kuwa motsi baiyi ba daga yarce yake tunda ta shigo balle har ya ɗago kai ya kalle ta. Cigaba da takowa tayi har ta ƙaraso kusa da inda yake, tukun taja ta tsaya tana mai kafe sa da manya manyan idanuwan ta ba tare da tace komai ba, yayin da har lokacin shima kansa ke ɗage asama ba tare da ya ɗago ya kalle ta ba. Sai da suka ɗauki kimanin minti goma ahaka, tukun ta fara ɗaga laɓɓan ta cikin zazzaƙar muryar ta mai matuƙar kaushi tana mai faɗin. "Ina amsar tambaya ta?" Tukun ta ƙara mai da baki ta tsuke tana kallon sa. Sai da yay kamar bazai yi magana ba, domin ko ita kanta har ta fara fudda tsamannin zai bata amsa, tukun daga bisani ya saukar da kansa daga kallon saman da yake yana mai juyo da manya manyan idanuwan sa zuwa kan fuskar ta. Lumshe idanuwan sa yayi bayan ya kalle ta ba tare da yace komai ba, tukun daga bisani ya sake wara su yana mai watsa ƙwayoyin su acikin tsakiyar nata, kana ya gumtse baki yayi shiru ba tare da yace ƙala ba. Sosai ranta ya ƙara bala'in ɓaci ta dalilin banzan da ya mata, da kuma yarce ya tsaya ya kafe ta da idanuwa yarce kasan sa'ar sa. Cikin zafin rai da tafasar zuciya ta ƙara buɗe baki tana mai faɗin. "Nace maka ina amsa ta ƙasƙantacce!" Ta faɗa da wani irin ƙaraji tana mai kallon cikin idanuwan sa. Murmushi gafen baki ya saki yana mai ƙare kafeta da dara -daran idanuwan sa, tukun daga bisani ya ɗaga laɓɓan sa cikin kakkausar muryar sa shima yana mai furta cewar. "Ke ɗin yarin ce har yanzu, shiyasa har kika gaza samun amsar tambayar ki ke da kan ki, amma ba damuwa, shima girman lokaci ne da shi, kuma ina mai tabbatar miki idam naki lokacin girman yayi keda kan ki zaki samo amsar ki." Ya faɗa cikin kaushi yana mai ƙareshe maganar tasa da sakin murmushi, har kuma lokacin ƙwayar idanuwan sa suna cikin nata yana aika mata da wani irin kallo. Da matuƙar ƙarfi ta rumtse idanuwan ta jikin ta na tsantsar rawa, tsabar yarce maganar sa tayi matauƙar ƙona mata rai, tukun daga bisani ta buɗe su tana mai sake watsa su acikin nasa. Lokaci ɗaya duka idanuwan nata suka rikiɗe daga launin fari zuwa na ja, jan ma irin jajahur ɗin nan tsabar ɓacin rai, wani irin huci take futarwa daga cikin bakin ta yarce kasan wacce tayi tseren gudu, yayin da jijiyoyin kanta kuma suka futo sukai ruɗu-ruɗu agaban goshin ta duk ta sanadin furucin sa. Ta fannin sa kuwa har lokacin bai ɗauke idanuwan sa daga kan fuskar ta ba, kamar yacce bai dena jifan ta da kyakkyawan murmushin sa ba da yake yi, da alama dai shi ko kaɗan yana yin da ya ganta aciki bai razana saba, duk da dai kallo ɗaya zaka masa ka tabbatar da ba ƙaramun jigatuwa yayi ba, koma ace yana kan jigatuwa sabo da yarce gumi ke tsattsafowa daga cikin gashin kansa yana dira akan kafaɗun sa da fuskar sa. "Tabbas azaba mai raɗaɗi zata hau kanka fiye da wacce kake ciki muddin ka bari daƙiƙa huɗu suka shige agaba ba tare da na jiyo abun da nake san ji daga gare ka b...." "Azaba? Shin dama har akwai wata azaba da zata zamto sabuwa gare ni ne acikin *BAƘAR MASARAUTA*? Shin koko kin manta ita kanta azabar acikin ta na taso na samu kaina ne?" Ya katse mata maganar da take kanyi da faɗin haka yana mai sakin numfarfashin wahala ba tare da ya bari yaji ƙarshen abun da zata faɗa ba, har lokacin kuma idanuwan sa suna acikin nata kamar yacce ita ɗin ma take kallon sa tana sakin huci da nata jajayen idanun. Harshe yasa ya kamo leɓen sa na ƙasa da shi, tukun ya sanya haƙwaran sa na sama dana ƙasa yana mai cige leɓen tare da sakin murmushi, har kuma lokacin bai bar kallon ta ba. Wani irin ɓacin rai gimbiya tasmir taji ya ƙara cakar zuciyar ta, lokaci ɗaya jikin ta ya fara rawa idanun ta na sake rikiɗewa suna yin ja. Cikin zafin nama ta ɗago tafin hannun ta na dama tana mai dunƙule ƴan yatsun ta cikin sa, sannan ta ɗaga ƙafar ta ta hagu tayi ball da kaskon hutar dake ci agaban ta ya tuntsire ƙasa ya fashe, kana ta rumtse idanuwan ta da ƙarfi tana mai buɗe baki cikin tsantsar sauti tace. "Rai Rai buuuu Hooo Reee!" Tukun ta wara tafin hannun nata bayan ta buɗe jajayen idanuwan ta tana mai watsa wasu abubuwa da suka bayyana acikin sa akan fuskar Beer. Wani irin baƙin hayaƙi ne ya tashi awurin yana mai lulluɓe masa duka jiki. Wata irin gigitattar ƙara ya buga wacce tasanya gaba ɗaya komai dake wurin amsawa. Juyawa tayi cikin tsantsar ɓacin rai tana mai dosar hanyar waje, banda sautin sarƙoƙin gwal ɗin dake sanye aƙafafuwan ta babu abun da akeji yana tashi awaurin. Tana fucewa waje gaba ɗaya dakarun nan dasu da ƴammatan bayin suka zube wanwar aƙasa suna masu yin ribda ciki. Ba tare da ta ɗaga kai ta kalli ko mutum ɗaya daga cikin su ba ta cigaba da tafiya har ta ƙarasa wurin da ta tsaya kafun ta shiga ɗakin nan. Sai da ta ɗauki tsayin minti biyar da tsayuwa, tukun dukan su suka mimmiƙe suna masu durƙusar da kansu ƙasa. Hannun daman ta ta miƙar gefe ba tare da tace tak ba. Kamar yacce ya faru ɗazu haka yanzu ma wannan badakaran ya tawo da baya baya har ya ƙarso inda take. Tukun ya zube guiwoyin sa aƙasa, sannan ya zaro takobin nan daga cikin jikin sa yana mai ɗora mata ita akan tafin hannun ta. Dunƙule ta tayi gam acikin hannun, tukun ta miƙar da ita tana mai nuna ɗakin da huƙar, kana daga bisani ta buɗe baki tana mai faɗin. "Gargabiluuu." Ahankali ƙofar ta fara rufewa har ta rufe gaba ɗayan ta, sannan ta ƙara miƙar da hannun ta gefe shi kuma wannan badakaran ya miƙa hannu ya ɗauki takobin. Tashi yayi ya koma inda yake da baya da baya kamar yacce yazo. Juyi tayi cikin zafin nama ba tare da ta kalli kowa acikin su ba, har lokacin bata bar sakin huci ba tana mai kallon hanyar da suka biyo sukazo wurin. Dasauri waƴan nan ƴammatan bayin suka mimmiƙe daga durƙushen da suke suna masu kama wasu sashika daga jikin rigar dake sanye ajikin ta, sannan ta fara ɗaga ƙafafuwan ta tana mai dosar hanyar da suka biyo sukazo cikin sauri. Gaba ɗaya suma dakarun nata rufa mata baya sukai cikin sauri suna binta. *ƘASAR HAUSA CIKIN MASARAUTAR WASAI* Tun daga bakin masarautar mutum zai fahimci yau ɗin ana wani gagarumin bikin ne aciki basai an faɗa masa ba. Sabo da yarce sautin kaɗe-kaɗe da bushe-bushen algaitu, sarewa, kakaki, tambura, kalangu, harma da kiɗin ƙwarya ke tashi awurare daban daban acikin masarautar, ga kuma yarce jama'a keta kai kawo, wasu asaman doki, wasu akan motocin su, yayin da wasu kuma suke tafe akan ƙafafuwan su. Ko ina ka kalla hadimai ne da sarakai kawai suke giftawa kowanne da kalar shigar dake sanye ajikin sa. Tsaya yake gaban tamfatsetsen mudubin dake manne jikin bangon ɗakin wankan nasa yana mai kallon fuskar sa ta cikin sa. Ɗaure yake da towel aƙugun sa bako riga jikin sa, yayin da hannun sa kuma ya kasance riƙe da wani ɗan ƙaramin towel ɗin yana tsane lallausar sumar dake kwance akansa tana ɗigar ruwa. Ya ɗauki kimanin minti goma tsaye gaban mirrown yana kallon kansa, tare da cigaba da tsane sassan jikin sa da towel ɗin dake ɗauke ahannun sa ba tare da ya gama ba. Ahankali ya juya bayan sa yana mai kai fararen ƙwayoyin idanuwan sa kan ƙofar bathroom ɗin, sabo da yarce sautin noking keta tashi ta yarce har ya fara takura masa, domin kuwa an ɗauki tsayin minti huɗu ana yin sa kenan. Mtseww! Yaja ɗan ƙaramin tsaki yana mai yamutsa fuska, tukun daga bisani ya janye idanuwan sa daga kan ƙofar ba tare da ya tankawa mai ƙwan-ƙwasowar ba, sai ma juyawa da yayi yana mai zuwa ya ya saƙale ɗan ƙaramin towel ɗin dake riƙe ahannun sa ajikin ƙarfen saƙale kaya, kana ya juya yana mai komawa ɗayan ɓarin inda wata azababbar wadrobe mai matuƙar kyau da ɗaukar hankali ke manne ajikin bango take, ya tsaya gaban ta yana kallon ta, tukun daga bisani ya lumshe fararen idanuwan sa, kana ya buɗe su yana mai saka zara-zaran yatsun hannun sa masu ɗauke da kwantaccen gashi akan su, ya dire su akan murƙar jikin wadrobe ɗin, kana ya bude ta. Gida ukku wadrobe ɗin ta kasu. Gida na farko gaba ɗayan sa ɗauke yake da designers bathroob jere aciki kala-kala masu masutuƙar kyau, sai gida na biyu kuma jere yake da designers boxers da singlet gaba ɗayan su sababbi fidigil suma, sai kuma side na ƙarshe da ya kasance ɗauke da haɗaɗɗar loka mai zaman kanta, wacce take ɗauke da haɗaɗɗen murfin roba fari ƙal da aka ƙawata sa da zanen flower's akan sa. Sake kai yatsun sa yayi kan murfin lokar yana mai buɗe ta. Gaba ɗayan ta cike take da tooth brush sababbi fidigil acikin kwalayen su tare da maclean masu matuƙar tsada. Hannu yasa ya ɗauki brush ɗaya tare da maclean, tukun ya maida locar ya rufe, kana ya mai da murfin wadrobe ɗin ya rufe ta duka, sannan ya juya yana mai yin wurin wani haɗaɗɗen sink bathroom da yake manne akan canter yana facing ɗin wadrobe ɗin nan, yana tafiya yana yage kwalin brush din dake ɗauke ahannun sa. Cilla kwalin brush ɗin yayi cikin dustbin ɗin da yake ajiye awuri ɗaya daga can gefe, tukun ya buɗe sabon maclean ɗin da ya ɗauko ya matsa sa ajikin brush ɗin, kana ya ƙarasa yana mai sa hannu ya kunna tap ɗin da yake manne jikin sink ɗin bayan ya aje maclean ɗin gefe. Ya dauki kimanin minti shida zuwa bakwai akan brush ɗin kawai yana ta dirzar haƙwara yarce kasan wanda zai canza su, tukun daga ƙarshe yasa ruwa ya ɗauraye bakin sa da shi, sannan ya juya ɓarin da kwandon sharar nan yake yana mai cilla brush ɗin da ya gama amfani da shi aciki, tukun ya juya yana mai dosar ƙofar da zata futar dashi daga cikin toilet ɗin wacce ake ta faman ƙwan-ƙwasawa tun ɗazu, cikin takun sa na tsantsar isa da izza, wanda yake nuni da shi ɗin cikakken jinin sarauta ne. Ɗan gajeran tsaki ya sake ja yana mai ɗan cije lower lips ɗin sa ahankali, tukun daga bisani ya ɗora hannun sa akan jamlock ɗin jikin ƙofar yana mai murɗa sa ta buɗe. Tunda yaji motsin sa abakin ƙofar yana shirin futowa ya ɗaure fuska, kana ya ture sistem ɗin dake ɗauke akan cinyar sa yana opereting ɗin ta zuwa kan kujera, tukun ya kafe ƙofar da kallo yana mai jiran futowar sa. Koda ya futo daga bathroom ɗin inda yake bai kalla ba ya doshi bakin dressing mirrow, kai bakace yasan da wanzuwar mutum ba ma acikin ɗakin, sabo da yarce bai ko kalli kujerar da yake zaune akai ba balle har ya tambaye sa yaji dalilin da yasa yake ƙwan-ƙwan sa masa ƙofa. Yana ƙarasawa gaban mirrow yaja kujera ya zauna akai, tukun ya sanya hannu yana mai janyo haɗaɗɗen man da yake shafawa, wacce robar sa kaɗai ma abar kallo ce, ya fara matsar sa atafin hannun sa yana murza sa, sannan ya shafe akan lallausar fatar jikin sa, wacce take lulluɓe da kwantaccen baƙin gashi akan ta hankali kwance. Ƙwafa saurayin dake zaune akan kujera ya buga da ƙarfi, cikin jin haushin yarce abokin nasa ya nuna halin ko inkula dashi da yay, bayan yasan tun ɗazu shi yake ta zaman jira acikin ɗakin, tukun daga bisani ya buɗe baki yana mai faɗin. "Amma dai gaskiya guy baka da mutunci ko kaɗan wallahi, wato tsabar iskanci tun ɗazu ina nan zaune ina zaman jiran ka, amma ka futo shine ko darajar kallo ma bazan samu daga gare kaba balle harka tanka mun ko?" Ya ƙarashe maganar yana mai sake buga ƙwafa tare da buga masa harara ta cikin mirrow, duk da dai shi har yanzu bai nuna yasan da shi bama. Inda yake bai ɗago ya kalla ba balle harya samu ya tanka masa, cikin kwanciyar hankali ya cigaba da shafa mai asassan jikin sa ba tare da ya juyo ba. Sai da ya gama mutssike ko ina na jikin sa da mayukan, sannan ya janyo body spray ya shafe ko wanne lungu da saƙo na jikin sa da shi, tukun ya mai dasu ya aje akan mirrown kamar yacce suke tun farko, kama ya miƙe daga kan kujerar da yake azaune yana mai juyawa ya doshi bakin tamfatsetsen royal bed ɗin da yake kwance atsakiyar ɗakin mai tsananin kyau, har kuma lokacin bai juya ya kalli wurin saurayin nan ba balle ya kula sa. "Please ASAD kayiwa Allah kai maza ka shirya, ko mayi mu ƙarasa cikin fadar nan muma, dan nasan yanzu duk kowa na can mu kaɗai ne bamu ƙarasa ba." Cewar matashin saurayin nan yana mai kallon Yarima Asad, tare da haɗe tafukan hannuwan sa wuri ɗaya alamun roƙo, domin ko yasan har dai ba lallaɓa sa yayi ba to bazai taɓa yin sauri ya shirya ba kamar yacce idan zai kwana yana masifa bazai nuna yasan yana wurin ba balle ya tanka mai. "Kash!" Yarima Asad ya faɗa yana mai yamutsa fuska tare da dago idanuwan sa ya watsa su akan fuskar abokin nasa, tukun daga bisani ya ɗaga laɓɓan sa cikin muryar sa wacce har dai ba mugun nutsuwa kayi ba ka saurare sa ba zaka taɓa jin abun da yake faɗe ba yana mai cewa. "Uhmm Al'AMIN kake da suna kowa ma? Shi wai na tsare ka ne anan ɗin, ko kuwa nace maka kajira ni ne da zaka tsaya kana mun ihu acikin kunnuwa tun ɗazu." Ya faɗa yana mai janye idanuwan sa daga kan fuskar sa, tukun ya cigaba da dosar bakin bed ɗin nan inda ya hango kaya ajiye awurin, alamun Abokin nasa ne ya zaɓo masa su amatsayin waƴan da zai sanya. "Ɗan iska mara mutunci, haka ma zakace kenna ko?" Abokin nasa ya faɗa yana mai ɗaure fuska takaici fal ransa. Ko kallon sa Yarima Asad bai ba ya ƙara sa bakin bed ɗin yana mai bin kayan da ya gani ajiye akai da idanuwa. Tattausan farin yadi ne ƙal mai matuƙar kyau, wanda yake ɗauke da irin aikin da ake yiwa rigunan sarakai da baƙin zare mai matuƙar kyau, kai ko baka san kaya ba idan ka kalli wannan yadin tare da aikin dake manne ajikin gaban rigar sa zaka san ba ƙananan kuɗi aka ɓatar ba kafun asamar da shi, agefen yadin kuma wata azababbar alkyabba ce fara mai matukar kyau da ɗaukar idanu, sai baƙin takalmi sandal tare da baƙar hula wacce take ɗauke da sirkin farin zare ajikin ta, waƴan da suma basai an faɗa maka ba kana kallon su zaka san bana ƙananan mutane bane, bayan su kuma sai farin rawani da yake ajiye agefe gaba ɗayan su anjere su akan gadon ne gwanin sha'awa da su. Wani irin matsiyacin kallo Yarima Asad ya dinga bin kayan da shi yana mai yaƙuna fuska yarce kasan wanda yaga kashi, tukun daga baya ya ɗago kai yana mai watsa idanuwan sa ɓarin da Al'amin yake zaune, wanda shima ɗin shi yake kallo yana mai addu'a Allah yasa ya sanya kayan nan acikin ransa. Danna lower lips ɗin sa yayi cikin baki yana mai taune sa da haƙora tare da lumshe idanuwa, tukun daga bisani ya wara su akan fuskar Al'amin yana mai buɗe baki yace. "Ina fatan dai ba wai ka ajiye waƴan nan shirgin bane anan wurin, da nufin nine zan sanya su ajiki na ko?" Ya faɗa yana mai sake yamutsa fuska tare da mai da idanuwan sa ya sake lumashe su. "Dan Allah Yarima Asad ka daure yau kaɗai ka taimaka kasanya kayan nan muje fada please." Al'amin ya faɗa yana mai haɗe tafukan hannuwan sa wuri ɗaya tare da kallon fuskar Yarima Asad a marai-raice. "Uhm! Amma gaskiya ina ganin da alamu kafara samun taɓin hankali ne guy, imagin ni Asad kake cewa in sanya waƴan nan kayan, ni, ni Asad zan sanya waƴan nan blankets ɗin ajiki na. Tirr god forbid." Ya faɗa yana mai sake juyawa ɓarin da kayan suke ya watsa musu wani matsiyacin kallo. "Haba Asad, koda baka son irin waƴan nan kayan bai kamata ace a irin rana tayau da ake bikin naɗa babban Yaya Ciroman gida ka ƙisu, domin ko kasan duk masarautar nan babu mai maka irin son da yake ma ko? Dan haka ni a gani na ya kama ta ace wannan ce irin shigar da zakayi ayau kaɗai domin ka taya masoyin ka farin ciki." Al'amin ya fada cikin sanyi yana mai fatan Allah yasa Yarima Asad ya fahimce sa yasan ya kayan nan acikin ransa. Mtswww!!! Yarima Asad yaja dogon tsaki yana mai wucewa gaban wadrobe ba tare da ya sake tankawa Al'amin ba. Buɗe wadrobe ɗin yayi yana mai zaro wani black creazy jeans, tare da farar long sleev t shirt sababbi gadagal ya aje akan bed ɗin, tukun ya sake sa hannu ya zaro wani farin ƙyalle mai kama da hirami yana mai diresa akan bed ɗin shima, kana ya rufe nan yana mai juyawa zuwa inda wata ƴar ƙaramar loka take manne ajikin bango ya buɗe ta. Wasu irin azababbun agoguna ne masu matuƙar kyau da sarƙoƙin huya suka bayyan aciki, hannu ya sanya ya ɗakko wani baƙin agogo tare da sarƙa mai matuƙar ƙyalli aciki, tukun ya mai da lokar ya rufe ta, kana ya juya zuwa inda kayan suke ba tare da ya sake ɗaga kai ya kalli Al'amin ba yana mai ware su ya fara sanya su ajikin sa. Cikin mintinan da basu huce biyar ba duka ya sanya creazy jens ɗin tare da farar rigar da tayi matuƙar kama jikin sa, tayarce har ta bayanna hallitar ƙarfin sa, domin kuwa ko singlet bai sanya aciki ba zallar rigar kawai ya ɗora. Ɗaukar hiramin nan yayi yana mai ware sa ahannun sa, tukun daga bisani ya lanƙwasa sa yana mai nin kasa gida biyu, kana ya ɗago sa yana mai dire sa akan sa ya haɗa da kunnuwan sa ya ɗaure sumar tas, wato dai ya ɗaure kan yarce kasan ɗan kwali, kana ya sake buɗe wata loka yana mai janyo wasu sababbin fararen boot masu matuƙar kyau da girma ya sanya fararen ƙafafuwan sa acikin su, kana ya ɗago yana mai hucewa gaban mirrow hannun sa riƙe da silin sarƙar nan. Buɗe bakin ta yayi, tukun ya ɗora ta akan huyan sa, kana ya maida bakin nata ya haɗe, sannan ya sake ɗaukar parforms ya feshe ko ina na jikin sa da su, tukun ya juya ɓarin da Al'amin yake zaune sake da baki yana mai karkace kai, tare da ƙanƙantar da idanuwa akan sa yana kallon sa. Farine ƙal yarce kasan ataɓa sa jini ya ɓullo, faffaɗa ne mai matuƙar tsayi da kauri dai dai misali, yana da doguwar fuska wacce take ɗauke da siririn dogon hanci tare da ɗan ƙaramin baki akan ta, sai fararen idanuwan sa da suka kasan ce su ba manya can ba, sannan kuma su ba ƙanana ba, yayin da gefe da gefen fuskar tasa kuma take ɗauke da kwantaccen baƙin gashi da yabi har ta tsakan-kanin saman bakin sa zuwa haɓar sa, mai matuƙar taushi da yayi matuƙar ƙara haska ka fuskar tasa, sosai sajen nasa yasha gyara yay gwanin ban sha'awa, kai kana ganin sa kasan ba ƙaramun ji yake da sajen ba, sabo da yarce yake futar da wani irin walwali da sheƙi akan fuskar tasa. Cikin tsantsar ɓacin rai Al'amin ya buɗe baki yana mai faɗin. "Am............✍ *FOLLOW ME ON WATPPAD @umarfaruqD pls.* *#COMMENTS* *#VOTE AND SHARE FISABILALLAH* 🐎 *BAƘAR MASARAUTA* 🐎 👑👑 🦋 🦅🕊🦆 🐍🎠🐄🏹 _*NA*_ UMAR FARUQ*D* *BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM* *PAGE 02* "Amma kai da kanka kasan hakan da kai bai dace ba ko Asad, domin ko hatta mai martaba idan ya ganka acikin wannan shigar arana irin tayau wacce sarakunan garuruwa da dama suka halarci gidan nan kasan ransa ba ƙaramun ɓaci zai yi ba ko, ina ma laifin ace kasanya iyakar manyan kayan basai kasa alkyabbar ba, in yaso bayan an gama shagali sai kazo kacire su ka maida irin wanda kake so ko." Al'amin ya ƙarashe maganar cikin sanyi kamar bashi ne ya fara ta cikin fushi ba, domin ko yasan har dai bata lallami yabi Abokin nasa ba to ko kallo ma bai ishesa ba balle har yayi amfani da abun da yake faɗe . Kallon sa Yarin Asad ya cigaba dayi har sai da ya bari ya kai ƙarshen maganar sa, tukun ya ɗan taɓe baki yana mai juyawa ya doshi bakin bed ba tare da ya tanka masa ba. Nannauyar ajiyar zuciya Al'amin ya sauke yana mai sakin murmushi, sabo da yarce yaga Yarima Asad ya nufi inda waƴan can kayan suke, amma sai dai ko gama murmushin nasa bai ba ya koma ya ɗinke fuska yana mai bin Asad da ido, sabo da yarce yaga ya huce ta gaban kayan ko kallon su baiyi ba balle ya dauka ya sanya. Direct yayi saitin inda pillow'n sa yaka yana mai zuwa ya ɗauki makullin motar sa tare da wayar sa ƙirar iphone 13 pro max ya riƙe, tukun daga bisani ya juya yana mai dosar ƙofar da zata sadasa da waje ba tare da ya sake kallon inda Al'amin yake ba, yayin da shi kuma Al'amin har lokacin yake binsa da kallo yana mai jin-jina girman rainin hankalin Asad acikin ransa. Sai da yaje har bakin ƙofa tukun ya tsaya yana mai juyowa ya sake jifan kayan nan da kallon ƙas-ƙanci, tukun daga bisani ya janye ƙwayoyin idanuwan sa daga kansu yana mai -mai dasu kan kujerar da Al'amin yake zaune yana kallon sa baki sake shima. "Katabbatar ka kwashe waƴannan shirgin banzan naka kafun na dawo, and then idan ka gama abun da kake kana iya rufe mun ɗaki ka ƙara gaba." Ya faɗa yana mai juyawa ya sanya kai ya fuce ba tare da ya tsaya jin abun da Al'amin zai ce ba. "Kuttt, Amma wallahi sai kaci ubanka Asad, yanzu duk awannin dana ɓata ina jiran ka kagama shiryawa mutafi tare shine har zaka huce ka barni, to dan uwarka baza a kwashe kayan ba kayi duk abun da zakayi." Al'amin ya faɗa da ƙarfi yarce Asad ɗin zai jiyo sa yana mai miƙewa cikin jin haushin sa yabi bayan sa. "Barka da futowa yaya." Wasu kyawawan ƴammata da suke zaune akan haɗaɗɗun kujerun da suke jere acikin tamfatse-tsen fallon suka faɗa, suna masu kallon Yarima Asad da ya futo daga ɓarin sa. "Ina mamy take ne?" Ya faɗa idanuwan sa akan waya ba tare da ya amsa gaisuwar da sukai masa ba. Da sauri ɗaya daga cikin su ta buɗe baki tana mai cewa. "Mamy na part ɗin ta, amma bari baby taje ta kira maka ita." Ta ƙarashe maganar cikin wani irin salo wanda yake nuni da tayi hakan ne domin ya ɗago ya kalle ta, amma sai dai ko motsi bai canza ba daga kalar wanda yake yi balle har ya kallo tan, yayin da ita kuma wacce aka kira da baby ta miƙe tsaye da sauri tana mai faɗin. "Ok bara nayi sauri." "To yaya ga wuri kazauna mana, kafin mamy'n ta ƙaraso ko." Ta faɗa tana mai far-fara idanuwa tare da ɗan buɗa space akusa da inda take idanuwan ta akan fuskar sa. Taune lips ɗin sa na ƙasa yayi yana mai yamutsa fuska ba tare da yace tak ba, domin kuwa ita bata sani ba ba ƙaramun takura masa tayi ba da surutun da take tayi ma. Ba tare da ya ɗaga kai ya kalli ko kujerar da take zaune akai ba duk da yarce take ta faman gyara zama tana kwar-kwasa kala kala ya juya yana shirin fucewa daga cikin falon, akuma lokacin ne Al'amin ya ƙaraso falon yana ta faman masifa. Baice ƙala ba duk da yaji abun da Al'amin ke faɗa, sai ma taɓe baki da yayi yana mai cigaba da tafiyar sa hankali kwance. Yana fucewa daga cikin part ɗin nasu ya tsaya cak abakin ƙofa, yana mai kallon yarce jama'a keta hucewa cikin irin banzar shigar da Al'amin ya aje masa da sunan yasa ta shima. Tsaye yay awurin yana mai ƙan-ƙantar da idanuwan sa tare da kar-katar da kai yana mai bin duk masu hucewa da kallo, yi yake yana taɓe baki tare da yamutsa fuska, ji yay gaba ɗaya bazai iya zama acikin gidan ba idan har baza'a dena waƴan nan kaɗaɗen ƙauyen cin da ake yi ba, domin ko shi ba ƙaramun takura masa sukayi ba, gaba ɗaya bai ɗauki irin waƴan nan bushe bushen ba amatsayin abubuwan nishaɗi, sai zallar gida danci da rashin waye wa kawai yake gani. "Kai yanzu dan Allah mutanen nan da suke hucewa cikin shigar nan basu burge kaba?" Al'amin ya faɗa alokacin da ya ƙaraso wurin yana kallon sa. Uhm! Yace kawai yana mai yin parkin space. Da sauri zagagen da suke tsai-tsaye a area wurin suka taso suna masuyo kan su. Tun daga nesa suka fara faɗin. "Barka da futowa ɗan sarki jikan sarki, takawar ka lafiya bujimin maza, takawar ka lafiya jinin mulki, gaba salamun baya salamun Asadullahi ikon Allah, ɗa ga sarki Abdallah, shalele wurin sarauniya kuma gimbiyar matan hausa, jika ga sarki Ahmadu ƙani ga ciroma uban.... Cak suka tsaya a'inda suke suna masuyin shiru dukan su, sabo da yarce ya ɗaga musu hannu sama yana mai dakatar dasu, ba tare da ya waigo ya kalli ko mutum ɗaya daga cikin su ba. Juyawa suka farayi suna masu komawa wuraren da suke, yayin da shi kuma ya cigaba da takawa cikin takusan sa da shi kaɗai ke hautsina ƙwaƙwalen ƴan mata su muto akan sa, yana mai dosar inda wata azababbar farar mota take, wacce take ɗauke da number mai suna YARIMA ASAD 08 sabuwa fidigil da ita. Tun daga nesa ya sanye remote ya buɗe ta, shi yasa yana ƙarasawa wurin ya sanya hannu ya buɗe murfin yana mai shigewa ciki ya zauna akujerar direba. Da sauri shima Al'amin ya ƙaraso wurin yana mai buɗe murfin ya shiga. Lumshe ido Yarima Asad yayi yana mai ɗora tafukan hannayen sa akan stiyarin motar bayan yayi mata key. "Wai yana ga kayo nan ne Asad, bayan kuma kasan fada zamuje ko?" Al'amin ya faɗa yana kallon fuskar sa. Ƙala bai ce masa ba sai ma buɗe idanuwan sa da yayi yana mai janyo wayar sa ƙirar iphone 13 pro max ya fara shafawa. "Da kai fa nake Asad kamun banza." "To kai ɗin ubane ne da bazan ma banza ba, ko kuwa na maka dole ne akan sai ka biyo ni inda zani." Ya faɗa ƙasa ƙasa yana mai cigaba da danna wayar sa ba tare da ya ɗago ya kalle sa ba. "Me kake nufi da hakan? Idan na fahimta kamar kana so kace ba fada mukai daga nan ba ko?" "Kai ka juyo kuma." Yarima Asad ya faɗa yana mai danna giyar motar bayan ya rufe motar gam. Da wani irin mahaukacin ƙarfi ya take ta yana mai lailaya kanta atsakan-kanin wurin da suke ya juya ta. Tukun ya ɗebe ta atamanin yana mai ɗauke hanyar da zata sada sa da main get, ko mutanen da suke faman kai kawo aharabar gidan nasu bai lura dasu ba. "Wai dallacan Asad me kake shirin yi haka ne?" Al'amin ya faɗa cikin ƙaraji yana mai dukan kujerar motar ransa amatuƙar ɓace. Inda yake Asad bai ɗago ya kalla ba balle ya tanka masa, saima sake take motar da yayi ahaukace yana cigaba da dosar get ɗin da zai sada su da wajen gidan sarautar. "Kaga malam dallacan samu wuri ka sauke ni anan." Al'amin ya sake faɗa cikin fushi yana mai jin kamar ya mammake fuskar Yarima Asad tsabar takaici. "Ai kana iya buɗewa ka futa yanzu ma tunda ba ɗaure ka nayi ba, kuma da kake cewa na tsaya na sauke ka ai ina ce da ɗin bani na ɗora ka aciki ba ko?" Yarima Asad ya faɗa adai dai lokacin da ya shilla kan motar sa titi aguje. Gaba ɗaya mutanen dake abakin titi harma da waƴan da suke acikin motocin su bin motar Yarima Asad sukayi da idanu, manya banda zagin sa da shegan tasa babu abun da suke yi, yayin da matasa kuma keta faman kambaba sa suna faɗin guy ɗin na burge su, sabo da yarce yayi matuƙar iya hannun sa. Acan cikin mota kuwa Al'amin ne ya kalli Yarima Asad yana mai faɗin. "Amma Asad kai atinanin ka hakan da kayi ka kyautawa babban yaya kuwa?" Murmushi Yarima Asad yayi wanda yayi matuƙar ƙara masa kyau, tukun daga bisani ya lumshe idanuwan sa ko damuwa bai ba da cewar kan titi yake duk da uban gudun da yake kwara-rawa, kana ya wara su daga baya yana mai buɗe baki yace. "Shin wai dan Allah ni nace ka biyo ni ne guy, koka na buɗe baki nace Al'amin kar kaje fada kallon naɗi ne?" Ya faɗa yana mai sake sakin murmushi hankali kwance. Yayin da shi kuma Al'amin yayi matuƙar ƙulewa, sabo da yarce yaga shi ko ajikin sa bai damu bama. "Amma dai ai kasan ban san nan kayo ba da babu abun da zai sa inbar hawan da zamuyi in biyo ka ko?" Uhm! "To ai yanzu ma bata baci ba idan naje inda zani na tsaya sai ka futo kasamu mota ka juya, domin kuwa kasan ni dai bazan tsaya akan hanya ba, kuma kasan bazan iya zama acikin gidan can ba ana waƴan can kaɗaɗe da bushe -bushen banzan can na gidadanci." "To karka tsaya ɗin mana ɗan iskan banza kawai." Al'amin ya faɗa cikin zafi yana mai buga ƙwafa, yayin da shi kuma yarima Asad yay shiru yana mai mai da hankali akan tuƙin haukar da yake hankali kwance. *ASADULLAH PALACE* Shi ne sunan da aka rubuta daga saman azababben building ɗin daya tunkara da motar tasa wanda get ɗin wurin kaɗai abun kallo ne bama ginin ba. Tun daga nesa ya danna horn ɗaya daga nan kuma bai sake yin wani ba. Da sauri wani matashin saurayi ya wangale tamfatse-tsen get ɗin yana mai kauce wa. A hankali ya fara taka motar yarce kasan ba zai tafi ba yana tunkarar cikin wurin, kai idan har ba sani kayi ba ka gansa akan titi yanzu kuma akace maka shine yake irin wannan tafiyar sai ka rantse da Allah kace ƙarya ne, domin kuwa ko mutum dake tafe aƙafa sai ya hucewa sa sosai a'irin yarce yake taka ta yanzu! *JAHAR KAGUL CIKIN MASARAUTAR FULƊE* Da gudu ƴar ƙaramar yarinyar mai kimanin shekaru bakwai aduniya ta afka cikin ɗakin tana ta faman numfar-fashi, alamun ba ƙaramun gudu tayi ba kenan. Durƙushewa tayi akan guiwoyin ta tana ta faman zare ido tare da sakin numfar-fashi. Ahankali kyakkyawar budurwar da take zaune agefen wani azababben gadon ƙarfe mai matuƙar kyau, wasu matasan ƴammata guda biyu da suke sanye da kayan fulani na tufke mata uban gashin da yake ɗauke akan ta mai tsananin yawa, tsayi da baƙi ta ɗago dara-daran fararen idanuwan ta tana mai watsa su akan ƴar yarin yar data shigo aguje. Kallon yarin yar tafarayi tun daga sama har ƙasa ba tare da tace komai ba. Yayin da ita kuma ƴar yarinyar har lokacin take durƙushe aƙasa tana sakin nishi. Ɗaya daga cikin ƴammatan da suke gyarawa budurwar nan gashi ne ta ɗago kai tana kallon yarinyar fuskar ta ɗauke da murmushi, tukun daga bisani ta buɗe baki cikin harshen fulatanci tana mai faɗin. "Shin me ya faru ne uwar gijiya ta beldo?" Ɗago kai yarinyar tayi tana mai kallon ta, tukun tace. "Ba hulin ki nazo ba." Kana ta mai da idanuwan ta kan fuskar budurwar da ake gyarawa gashi tana mai cewa. "Adda ta gote ki duka sun tashi sun gudu, yanzu naje ansho fulata wani ya kal-kaɗamun jelar sa afuska ta ya tashi sama, kinga kenan gwalo yayi mun ko?" Yarinyar ta faɗa tana mai kallon budurwar bayan tazaro manya manyan idanuwan ta waje, alamun dai abun ba ƙaramun firgita ta yayi ba. Yayin da waƴan nan ƴammatan bayin guda biyu suka tuntsire da dariya suna kallon ta. Ita ko uwar gayyar wacce aka kawowa labarin taɓe baki tayi tana kallon ƴar yarinyar, kana daga bisani ta ɗaga laɓɓan ta cikin zazzaƙar muryar ta mai matuƙar daɗi tana mai faɗin. "To uwar shirme ni wuce ki bani wuri." Ta faɗa tana ɗauke kai daga kan yarinyar, yayin da ita kuma yarin yar ta ɗaure fuska tana mai miƙewa tsaye ranta aɓace ta juya ta tafi, sai da taje bakin ƙofar futa daga ɗakin, tukun ta juyo tana mai kallon yayar tata, sannan daga bisani ta buɗe baki tana cewa. "Bama zan ƙala baki labari na ba, kuma Allah yasha kalsu dawo ma." Ta ƙarashe maganar da murguɗa baki, tukun ta juya tana mai fucewa daga cikin ɗakin. Murmushi dukan su su ukkun sukayi har ita ba tare da sunce komai ba. Sun ɗauki dogon lokaci suna gyaran gashin tukun suka kammala. Gefe guda suka koma suka tsaya kawunan su durƙushe aƙasa, ko wacce hannun ta riƙe da cumb. Gyara zaman ta tayi akan gadon da take, tukun daga bisani ta buɗe baki tana mai faɗin. "Kuna iya tafiya sai na sake neman ku kuma." Ta faɗa tana mai miƙewa daga kan gadon. "Tom ranki shi daɗe Allah ya ƙara lafiya." Suka haɗa baki wurin faɗin haka, tukun suka juya suna masu fucewa daga cikin ɗakin. Tafiya tayi zuwa bakin mudubin da yake maƙale ajikin bangon ɗakin, wanda gefe da gefen sa yake ɗauke da ƙarafa masu adon flawoyi kalar ruwan zuma, kamar yacce duka kayan ɗakin suke. Tsaye tayi agaban sa tana mai kallon kanta acikin madubin. Sanye take da kayan fulani irin na sarauta, riga da zani ne farare masu ɗauke da adon ja da koren zare ajikin su, sai ƙafar ta kuma da take sanye da plat farin half cover shoe na fata mai ɗauke da adon gashi ajikin sa mai tsananin kyau, yayin da kanta kuma ya kasan ce abuɗe ba ɗankwali akai, sai uban gashin da aka gama gyarawa da aka rabasa gida biyu, aka kikkitse jelolin suka zubo har kan cikin ta baƙiƙƙirin dasu gwanin ban sha'awa. Farace tas kamar ataɓa ta jini ya ɓullo, tana da tsayi tare da ƴar ƙiba dai dai misali, irin waƴan da ake so mace ta kasan ce dasu, tana da dara daran idanuwa masu ɗauke da blue black ɗin ƙwaya acikin su, sai siririn hancin ta da yake zaune daram akan fuskar ta wanda baza'a kira sa da dogo can ba kuma baza ace nasa ɗan guntu ba, yayin da bakin ta kuma ya kasan ce ɗan tsukut dashi ɗauke da pink lips akan sa suna ta faman ƙyalli. Ba wata kwalliya ce ɗauke afuskar ta ba sai kawai zallar powder data shafa, daga nan kuma bata ƙara komai akai ba sai suturar dake sanye ajikin ta da sukayi matuƙar zama das da su. GIMABIYYA HADDIYAL kenan. Ƴa mace ta farko ga Lamiɗon masarautar fulɗe, gimbiya ƴar gata wacce ake tsananin ji da ita, gimbiyar da take da matuƙar izza da kwarjini irin na ƴaƴan sarauta. Gimbiyar da ta maida tsun-tsaye da shanaye abokan rayuwar ta fiye da komai acikin masarautar tasu, hakan ya sanya har mahaifin ta Lamiɗo ya bata sarautar tsun-tsaye ta duka masarautar. Lumshe idanuwan ta tayi agaban madubin fuskar ta ɗauke da sassanyan murmushi, babu abun da take hange acikin idanuwan ta sai kyakkyawar fuskar sa yana aiko mata da sassanyan murmushin sa kamar yacce take ganin sa aduk lokacin da taso ganin sa muddin ta kulle idanuwa ko kuma ta kwanta bacci. Ta ɗauki tsayin mintina biyar rufe da idanuwan tana sakin murmushi, tukun daga bisani ta buɗe su tana mai sake duban kanta ajikin madubin, kana ta juya tana mai dosar ƙofar da zata sadata da waje cikin takun ta wanda yake nuni da ita ɗin wata ce basai anfaɗa ba. Wani danƙareren fallow ne mai tsananin kyau, wanda aka ƙawa tasa da kujerun ƙarafa masu ruwan zuma ta ɓulla cikin sa. Gaba ɗaya bangon fallow'n zagaye yake da adon ja da bluen stara masu tsananin kyau, yayin da daga saman starorin kuma aka kafe wasu haɗaɗɗun ƙwarare da luwade harma da faifayen kaba kala kala akan su. Kallo ɗaya mutum zaiwa wurin ko da bai san saba yasan tabbas ya shigo cikin babbar masarautar fulani waƴan da suke ji da Al'adun su, sabo da yarce aka ƙawata ko ina da kayan ado irin na fulani. Kai tsaye ta tunkari inda wata farar dattijuwar mace mai kimanin shekaru hamsin da ƴan kai take, kishingiɗe take akan tabarmar kaba wacce saman ta take ɗauke da lallausar sarrafaffar fata akai, sai wasu tum-tum da suke ajiye agefe da gefen shimfiɗar, yayin da ita kuma matar take kishingiɗe akan tum-tum ɗin ta miƙe ƙafafuwan ta duka akan kafet ɗin. sanye take da kayan fulani farare kar da su, sai al'kyabba wacce itama take ta mahaɗin kayan fara mai adon baƙi sanye ajikin ta. Kallo ɗaya zaka yiwa matar ka gane itace ta haifi Gimbiya Haddiyal, sabo da tsananin kamar da suke yi, riƙe take da wani haɗaɗɗen kofin silba ahannun ta, wanda cikin sa ya kasan ce cike danƙam da madarar shanu mai matuƙar dumi tana sha. Sai daga can wuraren ƙafafuwan ta kuma wata dattijiwar mata ce mai kimanin shekaru kusan hamsin da biyar aduniya take riƙe da ƙafafuwan ta tana ta aikin mammatsa su. Tunda ta hango tawowar ƴarta ta take ta faman sakin murmushi tana kallon fuskar ta har ta ƙaraso wurin da suke. Cire takalman dake sanye aƙafafuwan ta tayi, tukun ta hau kan kafet ɗin tana mai zama ta tanƙwashe ƙafafuwan ta akai. Dasauri wannan dattijuwar matar dake aikin lallatsa ƙafafuwa ta buɗe baki har tana ɗan ranƙwafa jiki wurin faɗin. "Barka da futowa ranki ya daɗe." "Yawwa barkan ki dai Iya." Gimbiya Haddiyal ta faɗa fuskarta ɗauke da murmushi, tukun ta juya ɓarin da mahaifiyar tata take tana mai buɗe baki cikin sanyi, bayan ta durƙusar da kanta ƙasa tace. "Barka da hutawa dadde na." Janye kofin madarar da takai baki tayi bayan ta ɗan kurɓe ta, tukun ta miƙawa dattijuwar matar nan da take zaune tana matsa mata ƙafafuwa shi. Dasauri matar ta karɓa tana mai ajiye kofin agefe bayan ta rufe sa da murfin sa. Lumshe idanuwan ta tayi, kana ta buɗe su akan fuskar ƴar tata, tukun daga bisani ta buɗe baki fuskar ta ɗauke da murmushi tana mai faɗin. "Yawwa Bello (kyakkyawa) ta." Tukun daga bisani ta ɗora da cewar. "Me ɗazu Innahuro ta tamiki da kika mata rashin mutunci, tazo tashe mun bazata ƙara kula ki ba ta dena baki labari daga yau babu ruwan ta dake." Mahaifiyar tata ta faɗa har lokacin tana kallon fuskar ta. Zaro idanuwa Gimbiya Haddiyal tayi tana sakin murmushi, tukun daga bisani tace. "Wai haka tashe miki kenan, barni da ita Dadde na ita da kanta zata zo har inda nake da anjima." Ta faɗa tana mai miƙewa tsaye. "To yanzu kuma sai ina?" Mahaifiyar tata ta faɗa tana kallon ta. Zan zaga bayan nan ne."Cewar Gimbiya Haddiyal" tana mai sanya takalman ta aƙafa. "To adawo lafiya." Mahaifiyar tata da dattijuwar matar nan suka haɗa baki wurin faɗin haka. Juyawa Gimbiya Haddiyal tayi tana mai kama hanyar waje. Tsaye tai daga bakin ƙofa bayan ta futa tana mai kallon ɗirka ɗirkan shanun da ake shigewa dasu ta gaban ta. Gaba ɗaya ginunuwa ne irin na fulani masarautar gare ta, ko ina ka kalla share yake ƙal babu alamun datti ko kaɗan. Sai da har tagama kallon shigewar shanayen nan tukun ta sauka daga kan daɓen part ɗin nasu tana mai kama wata hanya ta miƙe ta samɓel tana tafiya. Tafe take tana lumshe idanuwan ta tare da sakin murmushi akai akai, sabo da yarce take ganin fuskar sa aduk lokacin data lumshe idon, ga kuma yarce take jin daɗin yana yin garin nayau da ya kasan ce babu rana ko kaɗan, sai wata irin sassanyar iska dake kaɗawa tana dukan jikin ta, tayar ce har jelar gashin dake kitse kwance akan cikin ta suke juyawa. Sai da tayi tafiya mai nisa daga cikin gidan sarautar tasu, tukun ta ɓulla cikin wani tafke-ken wuri wanda yake ɗauke da bishiyu kala-kala acikin sa, sosai wurin yake da tsananin kyau, sabo da yarce aka ƙawata sa da itatuwa iri daban daban akuma jere atsare, ga wata irin sassanyar iska da take kaɗawa mai matuƙar ƙamshin ganyaye tana dukan fuskar ta. Wuri ne mai matuƙar girma, domin kuwa aƙalla idan akace mutun ya zagaye sa ataiƙace zaiyi tafiyar kusan awa biyar aƙafa kafun yaje ko ina na ciki. Banda sautin kukan tsuntsaye iri iri babu abun da akeji yana tashi awurin. Kai tsaye ta doshi wani wuri da yake daga can gaba wanda aka zagaye sa da iccina, mai ɗauke da haɗaɗɗun bishiyu acikin sa. Lumshe idanuwan ta tayi abakin wurin tana mai sakin murmushi, badan komai ba sai dan kawai sautin kukan abubuwan data fiso da taji yana dukan kunnuwan ta. Ahankali ta fara ɗaga ƙafafuwan ta tana dosar cikin wurin bayan ta buɗe idanuwan ta, har kuma lokacin bata fasa sakin murmushi ba. "Shale am!" (tsun-tsaye na). Ta faɗa cikin zazzaƙar muryar ta da matuƙar ƙarfi. Aiko ko minti ɗaya batayi ba da rufe baki sai ga dan-dazon tsun-tsaye nan da matuƙar gudu sunyo wurin da take ko wanne na kalar kukan sa. Tsaye sukai asaitin ta wasu daga bayan ta wasu kusa da fuskar ta, yayin da wasu kuma suke daga saman kanta kowanne da kalar kukan da yake, suna yi suna kar-kaɗa jela da fuka fukai, alamun suna farin ciki da zuwan nata kenan. Lumshe idanuwan ta tayi cikin tsantsar shauƙin da take ji, tukun daga bisani ta buɗe su tana mai sakin murmushi, kana ta ɗaga laɓɓan ta cikin yin ƙasa -ƙasa da murya tana mai faɗin. "Kun san me, yau akwai babban labari da zan baku, labari ne mai daɗi wanda yafi duk na baya daɗi akan Giɗaɗo am." Ta ƙarashe maganar cikin murmushi tana mai girgizawa tsun-tsayen nan kai, take awurin ko suma suka ƙara sautin kukan su suna masu cigaba da karkaɗa jelina da sauri da sauri alamun farin ciki kenan. Tukun ta juya tayi gaba suma duka suka biyo ta abaya da matuƙar yawan su, sannan kuma kaloli daban- daban. Bata tsaya ba har sai da taje wani haɗaɗɗen wuri wanda yake ɗauke da ruwa mai matuƙar girma acikin sa, tukun taja ta tsaya agaban wata shimfiɗar fata mai ɗauke da tum-tum da take agaban ruwan, yayin da cikin ruwan kuma ya kasan ce ɗauke da agwagi kala kala suna ta faman iyo aciki. Suna ganin zuwan ta suma gaba ɗayan su sukayo bakin ruwan da gudu suna ta faman yin kuka tare da luma kawunan su acikin ruwa, wanda hakan ke nuni dasu ɗin ma farin ciki suke kenan. Tukun daga ƙarshe kuma sai ga dan-dazon kaji masu tsantsar kyau gaba ɗayan su jikin lukui-lukui dasu sunyo inda take suma suna nasu kukan. Cire takalman ta tayi tana mai hawa kan shimfiɗar nan ta kishingiɗa akan tum-tum. Dasauri tsun-tsaye nan suka mar-matso saitin shimfiɗar suna masu maƙal ƙalewa ajikin itatuwan bishiyun da suka yiwa ruwan da shimfidar rumfa gaba ɗayan su, sai ɗawisu kuma guda ɗaya babbar cikin su da ita kuma ta haye kan tum-tum ɗaya wanda yake kusa da wanda Gimbiya Haddiyal ta kishingiɗa tana mai ƙure ta da idanun ta. Yayin da su kuma agwagi nan suka jajjeru acikin ruwan daga bakin sa, suma cikin su akwai wata fara da tafi duk sauran kyau da take agaban su, sai kuma sauran duka suka hau layi abayan ta. Sai daga gefen shimfiɗun kuma kaji ne jera reras mazan su da matan su duk sun duddurƙusa suna kallon ta, suma acikin su akwai wacce take agaba fara, sai sauran abayan ta ajere. Wato dai waƴan nan na gaban sune shuwagabbanin da Gimbiya Hadiyyal ta naɗa acikin iyalan nata, kuma ako da yaushe hakan suke idan har zasu gana da ita. Lumshe idanuwan ta tayi bayan ta ɗaga kai sama tana mai sakin murmushi, yayin da su kuma tsuntsayen nan duka sukayi shiru tsit suna kallon ta, tukun daga bisani ta sauke kan nata ƙasa tana mai wara idanuwan ta akan tsun-tsaye nan, kana ta buɗe baki cikin zazzaƙar muryar ta, har kuma lokacin tana sakin murmushi tana mai faɗin. _"Babban wuri ne mai tsananin girma da kyawu, zagaye yake da korayen furanni masu matuƙar ƙamshi da ƙyalli, yayin da jinsin kyawawan tsun-tsaye suka kasan ce kewaye da wurin mazan su da matan su ko wanne yana harkokin sa, sai sassanyan ruwa fari kar dashi yana kwaranya acikin rami. Zaune yake acikin ruwan yana ta faman ɗaga sa sama da hannun sa, sannan sai ya watsa sa ajikin sa, yayin da ni kuma na kasan ce zaune agefen ruwan ina shan madara idanuwa na akan sa, ban an'kara ba banyi tsammani ba sai jinai an watso mun ruwa akan fuska, ina ɗago kai dan naga ko waye sai nayi ido huɗu da shi agabana yana sakar mun murmushin sa mai tsananin kyau, murmushin nima nayi masa ina mai ɗaukar yatsa ta na dunguri dogon hancin sa da shi, kana daga baya na buɗe baki ina mai cewa. Ina sanka Giɗaɗo na._ _Murmushi shima yayi mun, tukun ya sake komawa cikin ruwan yana mai yin nitso ya cigaba da wankan sa ba tare da ya bani amsa ba, daga nan kuma sai na tashi daga bacci na."_ Ta ƙarashe maganar idanuwan ta akan tsun-tsaye, kaji da agwagin nan, yayin da su kuma gaba ɗayan su suka fara sakin kuka suna masu jujjuya jiki alamun suna taya uwar ɗakin nasu farin ciki kenan. "Tom kunji inda labari na na yau ya tsaya, sai kuma gobe idan na dawo zan baku sabon da zanyi yau, dan haka kowa yana iya komawa wurin sa masoya na." Ta faɗa tana mai miƙewa tsaye daga kan shimfiɗar. Sosai tsun-tsaye suka rikice da ihu suna ta faman shawagi akan ta, wasu har suna dan gwalar ta da jelar su, tukun sai suyi gaba, suma kaji juyawa sukai agurguje suna masu komawa wurin da suke, yayin da agwagi ma suka sake yin nutso cikin ruwa suna cigaba da harkokin su. Zura ƙafafuwan ta tayi cikin tattausan takalmin fatar ta, tukun ta juya tana mai sake ɗaukar wata hanyar duk acikin wurin. Tayi tafiya mai nisa, kana ta isa bakin wani farin ruwa da yake wucewa ƙal-ƙal da shi, yayin da gefe da gefen ruwan kuma wasu irin korayen ciyayi suka masa ƙawanya yayi gwanin ban sha'awa. Zama tayi agefen ruwan kan ciyayin tana mai cire takalman dake sanye aƙafar ta, tukun ta zura ƙafafuwan nata cikin ruwan tana mai kar-kaɗa su tare da lumshe idanuwa, kana ta ɗaga laɓɓan cikin sanyi tana mai faɗin. "Shin sai yaushe ne zaka bayyana gare ni, sai yaushe ne zan ganka azahiri kaima ka ganni, nayi iyakar yina akan ka amma na kasa, sai dai ina so kasani muddin rai da numfashi suna tattare agangar jikin Gimbiya Haddiya, to soyayyar kama tana nan daram, haka kuma muddin zuciya na cigaba da bugu aƙirjin Haddiyal, to kasani koda yaushe ƙaunar ka na sake sambun ta ne. Kamatso gare ni ya kai masoyi na, ka tawo gare ni yakai abun ƙauna ta, shin sai yaushe ne zan ganka ka ganni Giɗaɗo na? Ban sanka ba, ban taɓa ganin ka azahiri ba, amma na kamu da ƙaunar ka azuciya ta. Shin kai ɗin ma kasan da zama na ko ko ni kaɗai ce nake hauka akan ka? To kasani koda baka san dani ba babu wata mace da ta isa ta kasance agefen ka bayan ni! Har yau ba ahallici wacce zata soka ba bayan ni! Mutane na cewa kai ɗin ba mutum bane, amma ni na daɗe da sanin kai ɗin mutum ne kuma na daban acikin mutanen ma, ina son kaso ni kamar yacce na soka Giɗaɗo na, jiki na na bani zan ganka na kusa na sadu da kai nan kusa ba da daɗe wa ba." Ta ƙarashe maganar ƙwalla na tsiyayowa ta gefen idanuwan ta, tukun daga bisani ta wara idanuwan ta tana mai sakin murmushi, kana ta zare ƙafafuwan ta acikin ruwan tana mai miƙewa tsaye. Takalmanta ta sanya aƙafa, sannan ta sake yin wurin wasu korayen ganye har lokacin fuskar ta ɗauke da murmushi. Tsaye tai agaban su tana mai sanya hannu ta fara bubbuga ganyayyakin. Take kuwa Malam buɗa mana littafi (buterfly) suka mimmiƙe daga kan ganyayyakin masu tsananin kyau kala kala suna hawa kan jikin ta. Dariya ta kwashe da ita tayarce har sai da sautin ta ya ɗan futo, tukun ta buɗe tafin hannuwan ta duka biyun, yayin da su kuma birbillo nan (malam buda mana littafi) suka hau kan tafin hannuwan nata suna ta jujjuyawa. Zagaye ta farayi awurin tana hajijiya tare da sakin dariya mai sauti, tukun daga bisani ta tsaida dariyar tana mai faɗin. "Kuyi haƙuri masoya na, ban so nayi muku kishiya ba, sai dai kuma nima ban san lokacin da soyayyar sa ta hudan zuciya ba, abu ɗaya kawai dana sani shine amafarki nasan sa, kuma amafarki nake gannin sa, amma sai da ina mugun kaunar sa, dan haka kuma ina san kuso sa masoya na, na muku al'ƙawarin kune na biyu acikin zuciyar Gimbiya Haddiyal daga ku babu ƙari." Ta faɗa tana mai cigaba da shawagi da dariya ahaka har ta koma bakin ruwan nan data taso. *ƘASAR MALIN, YANKIN JAHAR KARFUZ, CIKIN BAƘAR MASARAUTA* Cikin tsantsar fushi da tafasar rai ta ƙarasa bakin ƙofar dake sada mutum da cikin gidan nasu. Tsaye tayi ƙam abakin wurin, yayin da su kuma waƴan nan ƴammatan bayin da dakarun sukayi saurin zube guiwoyin su aƙasa. Miƙar da hannun ta tayi gefe ba tare da tace komai ba, yayin da idanuwan ta kuma da ɓacin rai ya mayar dasu ja suka kasan ce kafe akan ƙofar dake kallon su. Dasauri wannan badakaran ya tawo da baya da baya har ya ƙaraso inda take, tukun ya zube gwuiwoyin sa aƙasa yana mai durƙusar da kai ƙasa, kana ya sanya hannu ya zaro takobin nan tata yana mai ɗora mata ita akan tafin hannu. Damƙeta tayi da ƙarfi fiye da irin riƙon da take mata abaya, yayin da shi kuma wannan badakaran yayi saurin miƙewa yana mai juya baya ya koma inda yake ya tsaya. Cikin tsantsar izza ta fara ɗaga ƙafafuwan ta da suke futar da sautin gwalagwalai tana mai dosar ƙofar dake kallon ta. Cak ta tsaya adai dai lokacin data ɓulla cikin tafkeken falon da yake zagaye da kayan alatu tare da Tambarin masarautar tasu tako ina acikin sa, sabo da abun da idanuwan ta suka gane mata daga shigar tata. Sosai kanta ya kulle, mamaki da tinanin abun da ya kawo sa cikin falon su awannan lokacin yayi matuƙar ɗaure mata kai, tayarce har ta kasa buɗar baki tayi magana kamar yacce ta kasa ɗaga ƙafa tai gaba. Cikin tsantsar fushin da bata taɓa ganin sa acikin sa ba tun lokacin da tazo duniya tagan sa adai dai lokacin da ya juyo ɓarin da take yana mai watsa jajayen idanuwan sa cikin nata! Wata irin faɗuwar gaba ta samu kanta aciki, sabo da tunda take bata taɓa ganin idanuwan sa sun sauya haka ba, yayin da shi kuma ya fara tinkaro inda take cikin takun sa wanda yake nuni dashi ɗin ko waye fuskar sa amatuƙar ɗaure. Rawa jikin ta ya kamayi sabo da yarce taga ya nufo ta gadan gadan, abun da tunda take bata taɓa tsintsar kanta aciki ba, wato tsoron da ya ziyarci zuciyar ta yanzu! Cak ya tsaya agaban ta yana mai ɗan ranƙwafowa ya rage tsayin sa fuskar sa ta kasan ce dai dai tata fuskar, tukun ya buɗe baki yana mai faɗin. "Sh.............✍ 🐎 *BAƘAR MASARAUTA* 🐎 👑👑 🦋 🦅🕊🦆 🐍🎠🐄🏹 _*NA*_ UMAR FARUQ*D* *BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM* *PAGE 03* "Shin ashe dama har akwai lokacin da zaizo wanda ƴa zata yaƙi ubanta! Wato ke yanzu har kinyi girman da zaki iya ja dani, sannan ki rushe mun ginin da na ɗauki tsawon shekara da shekaru ina yin sa! Shin kin san kalar hanyar dana bi kuwa kafun na samu wannan mafutar da ke kike shirin wargazata yanzu?" Ya faɗa cikin ƙaraji jajajyen idanuwan sa duk sunyo waje yana mai kafe ta da su. Yayin da ita kuma jikin ta ya ɗauki wata irin kakkarwa, hankalin ta idan yay dubu sai da duka ya tashi, domin ko ko kaɗan bata fahimci inda maganar mahaifin nata ta dosa ba balle har ta gano kalar laifin data aikata masa. Sake gyara tsayuwa yayi agaban ta yana mai sake fuskantar ta fuskar nan tasa babu alamun rahama tattare da ta, tukun daga bisani ya sake buɗe baki yana mai faɗin. "Labarin dogo ne, tarihin murɗaɗɗe ne, al'amarin kuma mai girma ne, sannan kuma rikitacce ne wanda yafi ƙarfin iko na! Tsahon shekara talatin kenan da Ubangiji mai girma Gargabilu ya samar mun da mafuta, amma sai gashi rana tsaka ƴata ta ciki na tana shirin rushe duk mafutar da aka samar tun kafun wanzuwar cikin ta agidan duniya!" Ya faɗa yana mai sake watsa idanuwan sa cikin nata. Cikin tsantsar ruɗu da firgici Gimbiya Tasmir ta buɗe baki tana mai faɗin. "Tuba nake yakai mahaifina, tuba nake ranka ya daɗe, labarin ka yazo mun atayarce bazan taɓa fahimtar me yake nufi ba, karatun ka ya girmi ƙwa-ƙwalwar Gimbiya Tasmir tayarce har yake shirin tarwatsa ta, nazari na da hangen nesa na bakai wurin da kake son yaje ba! Na roƙeka da abun bauta Gargabilu katai maka kamun yarce zan ɗauka!" Ta ƙarashe maganar cikin wata irin murya tana mai girgiza kai, yayin da manya manyan idanuwan ta kuma suka sake rikiɗewa suna masu komawa kamar garwashi dan firgici. Juya mata baya yay ba tare da ya tanka mata ba, tukun yayi taku ɗaya, biyu, zuwa ukku daga wurin da yake, kana ya sake juyowa yana mai kafe ta da jajayen idanuwan sa, tukun ya sake ɗaga laɓɓa cikin kakkausar muryar sa yana mai faɗin. "Na same sa ta tsaura-rarriyar hanya ce ba sauƙaƙƙa ba, na same sa alokacin dana futar da tsammanin samun sa, na same sa ta hanyar taimakon abun bauta Gargabili, ba da ban haka ba dako ke ba asamu wanzuwar ki aduniya ba balle har akawo yau." Ya ƙarashe maganar yana mai fara ɗaga ƙafafuwan sa ya doso inda take. Tsaye ya sake yi a'inda ya tsaya tun farko, wato gab da ita, tukun ya sake saita idanuwan sa cikin nata, sannan ya buɗe baki cikin kaushi yana mai faɗin. "Umarni ne nake baki ba shawara ba, ki gaggauta zuwa ki kwance yaron nan tun kafin komai nawa ya lalace, domin ko wannan yaron da kike gani shine gaba ɗaya duniya ta, sannan kuma shine duniyar ki! Wannan yaron dai da kike hukuntawa bada ban samuwar sa ba da tuni babu sauran tarihin BAƘAR MASARAUTA ayanzu, da tuni kafaffen tarihin mu ya rushe, da tini labarin mu ya shafe, dan haka na baki daƙiƙa daga ɗaya zuwa biyar, karki kuskura ki bari sukai shida balle har su tsallaka goma ba tare da kin kwance saba, muddin kuwa kika watsar da magana ta to ina mai tabbatar miki dake kan ki ƙarshen ki yazo, sannan kuma babin mu ya shafe, domin ko faɗan bani kaɗai yafi ƙarfi ba, hatta da abun bauta Gargabilu yafi ƙarfin sa, cewar boka mai HUTAR KASKO!" Ya ƙarashe maganar da ƙarfi, tukun ya janye kansa daga saitin fuskar ta, kana ya juya cikin takun sa wanda yake nuni da tsantsar jarumtakar sa ya futa. SARKI BARBARU kenan, shugaban BAƁAR MASARAUTA wanda yake akan karagar mulkin tsawon shekaru arba'in baya kenan har kawo yanzu. Sarki mai tsantsar girman jiki da kauri, sarkin da sautin tafiyar sa kawai ke razana zuciyoyin Al'ummar da suke ƙarƙashin mulkin sa! Wani irin tashin hankaki Gimbiya Tasmir ta samu kanta aciki irin wanda tunda tazo duniya bata taɓa riskar kanta aciki ba. Ɗaga ƙafafuwan ta ta farayi tana mai zaga tanƙashe-shen falon da yakasan ce tsit da shi, kanta asama tana kallon rufin falon, so take ta gano inda zantukan mahaifin ta suka dosa da kuma abun da suke nufi amma gaba ɗaya ta kasa, ko kaɗan bata fahimci inda tsauraran kalaman sa suka dosa ba, abu ɗaya kawai da ta sani shine ransa yayi matuƙar ɓaci irin ɓacin da bata taɓa ganin sa acikin sa ba, tun da take da shi bai taɓa yi mata ko da tsawa ba, sabo da irin mugun ƙaunar da yake mata, amma sai gashi yau har ihu ya mata acikin kunnuwan ta akan wani ƙas-ƙantaccen bawa mara galihu. Dunƙule tafin hannun ta tayi da ƙarfi bayan ta rumtse idanuwan ta, sabo da yarce sautin muryar mahaifin nata take ta mata amsa kuwwa acikin kunnuwa yana faɗin. _"Na baki daƙiƙa daga ɗaya zuwa biyar, karki kuskura sukai shida balle har su tsallaka goma ba tare da kin kwance sa ba!"_ "Inaaaa!! Tayaya ma!! Shin me hakan ke nufi kenan?" Ta faɗa da mugun ƙaraji idanuwan ta na furfutowa waje, yayin da jijiyoyin kanta suka futo sukai raɗa raɗa akan goshin ta, tukun daga bisani ta fara ɗaga ƙafafuwan ta cikin sauri tana mai dosar hanyar da zata sada ta da waje takobin ta damƙe acikin tafin hannun ta, har kuma lokacin kalaman mahaifin na basu dena mata amsa kuwwa acikin kunnan ta ba. Tana futa gaba ɗaya bayi da dakarun da suke acikin harabar wurin suka zube wanwar aƙasa suna masuyin ribda ciki, amma sai dai ko inda suke bata kalla ba balle har ta tsaya cak kamar yacce ta saba, tai shigewar ta gaba cikin sauri kamar ta kifa ƙasa. Cikin tsantsar sauri dakarun nan nata suka mimmiƙe tsaye, sabo da ganin da sukayi ta shige ba tare da tsaya sun gama gaishe ta ba, balle har ta bawa mariƙi takobin ta suyi gaba. Dasauri suka fara ɗaga ƙafafuwan su suna masu dosar inda tayi, sai dai tun kafin su ƙaraso wurin da take tayi saurin ɗaga musu tafin hannun ta sama tana mai dakatar da su ba tare da tace ƙala ba, tukun ta cigaba da ɗaga ƙafafuwan ta tana mai dosar inda wani garken dokuna suke. Bata dakata ba har sai da taccima gaban wani ɗirkeken baƙin doki da yake atsaye yana cin ciyawa. Wani irin mugun tsalle ta buga tana mai ɗanewa kansa, tukun tasanya hannun ta na hagu tana mai damƙar linzamin dake rataye awuyan sa da shi, kana tasa dunduniyar ƙafar ta tana mai dukan cikin sa da matuƙar ƙarfi da ita. Wata irin haniniya dokin ya saki da matuƙar ƙarfi, tukun ya zabura da mugun gudu yana mai dosar yamma. Gudu yake ba gudun wasa ba, yayin da ita kuma Gimbiya Tasmir ta kasance zaune asaman sa jajayen idanuwan ta kafe akan hanya, yayin da iska ke kaɗa mayawaicin baƙin gashin dake kanta yana tashi sama, ga kuma jibgegiyar rigar ta da ƴammatan bayi keta aikin riƙewa ɗazu da take ta faman tashi sama itama, sabo da irin tsantsar gudun da dokin yake yi. Cikin lokacin da bai huce daƙiƙa ukku ba duka suka bayyana adai-dai bakin ƙofar ɗakin azaba. Cak dokin ya tsaya awurin sabo da yarce ta matse linzamin dake jikin sa da hannu. Sakin linzamin dokin tayi, sannan ta durko daga kansa zuwa ƙasa. Kana ta miƙar da takobin dake ɗauke ahannun ta tana mai nuna ƙofar nan da ita, sannan ta buɗe baki cikin tsantsar sauti tana mai faɗin. "Gargabiluuuuuuu!" Take awurin ko ƙofar nan ta fara ɗagawa sama har ta buɗe duka. Wani irin baƙin hayaƙi ne ke futo daga cikin ta da matuƙar gudu. Sauke takobin tata ƙasa tayi tana mai cake tsinin ta acikin ƙasa, tukun ta sake rumtse idanuwan ta tana mai yin wasu irin surutai, sannan daga bisani ta buɗe su tana mai buɗe tafin hannun nata ta watsa abubuwan da suka bayyana acikin sa zuwa cikin ɗakin. Take haske ya bayyana acikin sa, sai dai kuma duk da haka hayaƙin nan dake futowa bai fasa futowa ba da matuƙar tururi. Ɗaga ƙafafuwan ta ta farayi tana mai matsawa jikin ƙofar. Sake rumtse idanuwan ta tayi tana mai dunƙule tafin hannun ta, sannan ta sake buɗe baki tana mai faɗin. "Rai Rai Rai Buuu Hooo Reeee!!!" Da tsantsar ƙarfi. Take awurin hayaƙin nan duka ya ɓace ɓat, tukun ta juya baya tana mai zuwa ta funciki takobin ta daga jikin ƙasar da ta cake ta, sannan ta juya tana mai sake nufar cikin ɗakin gadan-gadan. Tsaye yake ajikin ƙarafan nan da yake ɗaure jikin sa nata faman kar-karwa, yayin da gumi ya jiƙa sa yay masa sharkaf yarce kasan wanda aka tsamo daga cikin ruwa, banda layi da girgiza kai babu abun da yake iya yi, sai kuma buɗe baki da yake ta aikin yi gaba ɗaya leɓun kasa sun bushe sun yi baƙiƙƙirin dasu! Kallo ɗaya zaka masa ka fahimci ba ƙaramun jigatuwa yayi ba, sabo da yarce duka yana yin hallitar sa ta sauya. Cigaba da taka ƙafafuwan ta tayi tana mai dosar wurin da yake. Sai da taje har gab da shi tukun taja ta tsaya tana mai ƙare masa kallo, yayin da shi kuma har lokacin kansa ke ɗage asama yana ta faman aikin girgiza sa. Shiru tai ba tare da tace komai ba, sai kawai idanuwa da take binsa da su tana mai jin tamkar ta shaƙe masa huya ya faɗi ya mutu, ko taji sassaucin baƙin cikin da take ji acikin ranta ta sanadin sa. Sauke kansa ya farayi ƙasa -ƙasa har ya sauke idanuwan sa duka acikin nata. Wani irin murmushi ya ƙaƙalo yana mai jifan ta da shi duk da irin wahalar da yake ciki, kana daga bisani ya buɗe baki cikin muryar sa da take tsantsar rawa, sabo da azabar dake sauka ajikin sa yana mai faɗin. "Gimbiyar mu Gimbiyar BAƘAR MASARAUTA... Ya da dawowa yanzu kuma?" Ya ƙarashe maganar yana mai sake jifan ta da murmushi, yayin da har lokacin kuma gumi ke cigaba da tsats-tsafowa ta kowace kafar gashi dake jikin sa. "Kai ɗin wane ne? Wane ubanka? Wace kuma uwarka acikin BAƘAR MASARAUTA da har kake ja da iko na?" Ta faɗa cikin ƙaraji tana mai sanya idanuwan ta acikin nasa ita ma. Murmushi ya sake yi yana kallon ta, tukun daga bisani ya buɗe baki yana mai faɗin. "Abun da na daɗe ina son sani kenan tsahon shekara da shekaru acikin baƙar masarauta, amma ba damuwa, tunda har kema kin buƙaci ki sani yanzu, shikenan na barki da aikin neman, in yaso duk randa kika gano ko suwaye sai inzo ki faɗamun su nima!" Ya ƙarashe maganar yana mai zaro harshe ya lashi busassun laɓɓan sa, har kuma lokacin bai fasa jifan ta da murmushin da yake aikin yi ba. "Wat...! _"Na baki daƙiƙa daga ɗaya zuwa biyar, karki kuskura sukai shida balle har su tsallaka goma ba tare da kin kwance sa ba!" Muryar mahaifin ta ta sake dukan kunnen ta da matuƙar ƙarfi, tayarce har tai sanadin tsinkewar maganar da take kanyi ba tare da ta kai ba. Danna lips ɗin ta na ƙasa tayi cikin baki tana mai taune sa da mugun ƙarfi tare da kafe Beer da jajayen idanuwan ta da suke sake rikiɗewa, tukun daga bisani ta ɗaga takobin ta sama tana mai nuna ƙarafan da yake ɗaure ajikin su da ita, sannan ta buɗe baki da matuƙar ƙarfi tana mai yin wasu irin surutai. Ko rufe baki bata kaiga yi ba ƙarafan nan suka fara buɗewa wani irin sauti na tashi. Timm! Kake jin ƙarar faɗuwar Bir ƙasa alokacin da ƙarafan suka gama sakin jikin sa. Wani irin nishi yake saki yana daga kife aƙasa, yayin da ita kuma ta juya tana mai dosar hanyar waje cikin tsantsar sauri, banda sautin ƙarar sarƙoƙin gwal ɗin da suke sanye aƙafar ta babu sautin dake tashi awurin. Dasauri shima Bir ya fara jan jiki yana mai bin bayan ta gudun karta sake rufe sa acikin ɗakin. Tana fucewa bata tsaya wata wata ba ta daka tsalle tana mai hayewa saman dokin nan, tukun ta ɗaga takon dake riƙe ahannun ta tana mai nuna ƙofar da ita, akuma dai dai lokacin shima Bir ya futo waje da jan jikin da yake yana ta faman sakin nishi da ƙarfi. Sosai farar fatar sa tayi wani irin dabbara dabbaran baƙi awurare daban -daban, yayin da jajayen laɓɓan sa kuma sukai wani iri duk ta sanadin wahalar da ta basa da huta. Dogo ne sosai mai ƙirar ƙarafa, yana da faffaɗan ƙirji wanda yake cike da kwantacce gashi mai matuƙar taushi akan sa. Yana da dara daran idanuwa tare da dogon hanci dashe akan fuskar sa, sai ɗan ƙaramin bakin sa kuma da ya kasance ɗauke da jajayen laɓɓa da suke matuƙar ƙara masa kyau suma, yayin da sumar kansa kuma ta kasance mayalwaciya mai matuƙar taushi da santsi. "Gargabiluuuu!" Ta faɗa da ƙarfi tana mai nuna ƙofar da takobin. Take kuwa ta koma ta rufe gam, tukun tasanya hannun hagun ta tana mai jan linzamin dokin, tare dasa dunduniyar ƙafar ta ta daki cikin sa da ita. Haniniya dokin ya ƙara saki, tukun ya fara ɗaga ƙafafuwan sa yana mai ƙara danna kansa gaba. Bata tsayar da shi ba har sai da suka ɓulla wani wuri da yake da dogayen bishiyu tare da duwar-watsu tako ina, agefe kuma ga wani tafkeken ruwa da yake ta faman tawowa daga saman wani dutse yana sauka acikin wani ƙaton rami. Durowa tayi akan dokin, tukun ta samu wani wuri da yake da yashi tana mai cake takobin ta agun, kana ta fara dosar inda wani dutse yake gadan gadan, jajayen idanuwan ta kafe akan sa. Sai da taje gab da shi, tukun taja ta tsaya cak, kana ta rumtse idanuwan ta da ƙarfi tana mai dunƙule duka tafukan hannayen ta. "Kai!! Inaaa!! Bazai yuwu ba wallahi!" Ta faɗa da matuƙar ƙaraji tana mai girgiza kanta, tukun daga bisani ta buɗe idanuwan ta da suka sake rikiɗewa suna masu ƙarayin jajajir, sannan ta fara ɗaga ƙafafuwan ta tana mai komawa wurin da ta cake takobin ta. Funcikar ta tayi da ƙarfi adai dai lokacin da taje wurin, tukun ta sake ɗaga ƙafafuwan ta tana mai dosar gaban ruwan nan idanuwan ta ƙur akan sa. "Yau kimanin shekaru Ashirin da biyu, da wata biyu, da kwana biyu da zuwa na duniya mahaifina bai taɓa yimun koda kallon banza ba balle harya yimun tsawa sai yau. Shin wai shi ɗin wane ne ma? Me gare shi, wane kalar tarihi ne da har zai hana hukunci na yin aiki akan sa? Inaaa! Hakan bazai taɓa yiwu ba wallahi." Ta faɗa tana mai tsayawa agaban ruwan idanuwan ta ƙur akan sa. Tukun daga bisani ta ɗaga takobin ta tana mai nuna ruwan nan da shi, sannan ta buɗe murya cikin sauti tana mai faɗin. "Shairama!!!" Take wata wata tamfatse-tsiyar macijiya ta bayanna acikin ruwan kanta fashe tana mai karkaɗa harshe! "Shairama!!" Ta sake faɗe da ƙarfi tana mai nuna gefen ruwan daga waje da takobin. Wani irin tsalle macijiyar nan ta daka, sai gata ta dira adai dai wurin data nuna da takobin tana mai karkaɗa harshen ta. Yayin da ita kuma ta sake neman wuri ta cake takobin, kana ta fara ɗaga ƙafar ta tana mai dosar inda macijiyar take gadan -gadan. Hannu tasa ta damƙi kanta da matuƙar ƙarfi, tana mai zaro idanuwan ta bayan ta durƙusa agaban ta! *ƘASAR HAUSA JAHAR WASAI* ASADULLAH PALACE Babban wuri ne mai matuƙar girma da yalwa, gaba ɗayan sa wurin shimfiɗe yake da wata haɗaɗɗiyar ciyawar roba koriya shar da ita, yayin akabi aka ƙawata ko ina da furanni kala kala masu matuƙar kyau da suka yi matuƙar ƙara haska ka wurin. Agefe guda kuma wani haɗaɗɗen building ne mai kimanin hawa biyu, wanda cikin sa yake jera da ɗakuna, sai daga ɓangare ɗaya kuma wani tafkeken swimming pool ne ɗauke da wasu tayoyin roba tare da bluen ruwa acikin sa, yayin da bakin swimming pool ɗin kuma aka bi aka zagaye sa da wasu haɗaɗɗun kujeru masu kama da gadaje, bayan kujerun kuma wasu irin haɗaɗɗun furanni ne adashe, sai daga can cikin wurin kuma wasu kujeru ne na roba kakkefe da mutane suka kasan ce zazzaune akan su, wasu na cin abinci, yayin da wasu kuma suke shan drinks. Kusan duk wanda zaka kalla awurin zaka gansa ne tare da budurwar sa suna zaune. Anan cikin swimming pool ɗin ma wasu ƴammata ne da samari suke ta faman wanka suna watsawa juna ruwa. Sanye mazan suke da boxer kawai wanda jikin sa aka rubuta Asadullah palace, yayin da su kuma matan suka kasan ce sanye da wasu ƴan ƙana-nan riguna, tare da gajerun wandina waƴan da suma duka jikin su yake zane da Asadullah palace. Daga kan kujerun da suke abakin ruwan nan ma wasu ƴammata da samarin ne ɗaure da towel aƙugunan su, kishingiɗe suke kowan ne hannun sa riƙe da cup ɗin lemo. Duk wanda ka kalla acikin wurin nan basai an faɗa maka ba zaka san yayi matuƙar tarawa, ko kuma an tara masa, duba da kalar motocin da suke ajiye a parking space da kuma yarce skin ɗin jikin su take. Ahankali ya cigaba da taka motar yarce kasan bazai tafi ba, tunda ya shigo gaba ɗaya jama'ar dake cikin wurin hankulan su ya dawo kansa, yayin da ƴammatan da suka kasance acikin wurin waƴan da mafi yawan su tare da samarin su suke suka fara mimmiƙewa tsaye suna masu gyara jikin su, kana suka fara tattakawa suna masu dosar inda motar sa take. Wani haɗɗaɗen get da yake daga can cikin wurin ya tunkara da motar tasa gadan gadan. Kallon yarce haɗaɗɗun ƴammata keta zuwa suna giftawa Al'amin yayi, tukun ya buɗe baki yana mai faɗin. "Ɗan iskan banza kawai, wato kai da ka zauna ayi hawa da kai ka gwammace ka tawo wurin da zaka lodarwa kan ka zunubi ko?" Murmushi Yarima Asad yayi adai dai lokacin da suka ƙarasa bakin get ɗin nan, tukun daga bisani ya buɗe baki yana mai faɗin. "Hausawa dai kance Abokin ɗan iska ɗan iska ne, kaga kenan daga ni har kai duk samma kar, kuma idan ka isa har mu shiga wurin nan mu futa karka kuskura ka ɗaga kai kakalli wata yarinyar." "Dallacan malam rufemun baki tunda ni ba dutse bane dan uwarka!" Al'amin ya faɗa yana mai sakin ƙwafa da ƙarfi, domin shi har yanzu haushin Asad yake ji, sabo da yayi matuƙar tama ranar yau ɗin amma gashi lokaci ɗaya duk ya rushe masa ita. "Malam ni sauke ni anan na ƙaraso daga baya, domin ko ga zafafan ciks nan suna buƙatar ataya." Al'amin ya faɗa yana mai kallon yarce haɗaɗɗun ƴammata keta kai kawo asaitin inda motar su take ta cikin glass ɗin daya kasan ce ɗauke da baƙin tinteck ajikin sa. Taɓe baki Yarima Asad yayi ba tare da yace komai ba, haka kuma bai buɗe masa murfin motar ba, saima danna hancin ta da yayi zuwa cikin haɗaɗɗen wurin da aka wangale masa get ɗin sa. Plat building ne mai tsananin kyau da ɗaukar hankali agefe guda na cikin wurin. Yayin da gefen sa kuma wani tafkeken swimming pool wanda gefen sa yake zagaye da ƴan gadaje ya kasan ce. Sosai wurin yayi matuƙar haɗuwa fiye da na farkon, sai dai shi wannan bai kai wancan girma ba, kuma babu ko mutum ɗaya acikin sa sai su da suka shigo yanzu kawai. Daga can ƙarshen wurin kuma daga jikin bango wasu danƙara danƙara kosassun dokuna ne fari da maroon ɗaure ajikin garken su suna cin dusa. Direct yayi parkin space da motar sa. Ɗan gajeren tsaki ya saki yana mai lumshe idanuwan sa, sabo da yarce Al'amin ya fara takura masa da masifar sa. Ahankali yasa hannu ya buɗe murfin motar, tukun ya zura ƙafafuwan sa daga waje bayan ya ɗauki wayar sa ba tare da ya tankawa Al'amin ba, kana ya fuce duka yana mai juyawa ya doshi bakin ruwan nan kai tsaye. Budewa shima Al'amin yay ya futo yana mai juyawa ya doshi get din da suka shigo, danmiyar yaje ya dubo wata cikin yammatan da suka huce awaje tukun su dawo. "Banza kawai ballagaji mara aji." Yarima Asad ya faɗa alokacin da ya zauna kan ɗan gadon da yake bakin swimming ɗin yana mai kallon Al'amin, tukum daga bisani ya mai da idanuwan sa kan wayar sa yana mai fara shafata. Wata irin azababbiyar mota ce sabuwa gadagal ta danno kanta cikin wurin. Direct ta huce inda aka tana da dan ajiye motoci, parking mamallakin motar yayi, tukun daga bisani aka buɗe murfin ta. Fararen ƙafafuwan ta da suke sanye da wani mugun hill shoe ta fara zurowa waje, tukun daga bisani ta futo duka tana mai sa hannu ta rufe murfin, sannan ta juya tana mai kai idanuwan ta bakin ruwan nan. Murmushi ta saki sabo da yarce ta hango sa zaune cikin shigar sa da take mugun tafiya da ita, wacce akullum idan ta gansa acikin ta sai ta ƙarajin ta tsundum acikin kogin ƙaunar sa. Farace doguwa siririya, tana da dogon hanci tare da ƴan madai daitan idanuwa akan fuskar ta, sai bakin ta da ya kasance shi baza ace masa ƙarami ba haka kuma baza'a kira sa da tafkeke ba, wato ataƙaice dai tana da kyanta dai dai misali. Sanye take da blue crazy jeans da yayi matuƙar kama jikin ta, sai red t shirt mai gajeran hannu wacce take ɗauke da kwalliyar flawoyi akan ta, yayin da kanta kuma ya kasance abuɗe ko darajar ɗankwali bai samu ba, sai uban jan gashin atach da yake zube agadon bayan ta yana reto. Riƙe take da ƴar ƙaramar jakar ta wacce ta kanace kala ɗaya da takalmin dake sanye aƙafar ta mai matuƙar tsini da sirantaka, yayin da ɗayan hannun nata kuma ya kasan ce riƙe da wayar ta ƙirar iphon 13 pro max itama. BILKISU ABUBAKAR SARDAUNA kenan, wacce ƙawayen ta suke kiran ta da Billy Baby. Ƴa ga gwamnan Jahar Wasai mai ci ayanzu, sun haɗu da Yarima Asad ne a oxford university dake ingla, alokacin shi yana mastering degree ɗin sa, yayin da ita kuma take degree, tun daga ranar data ɗora idanuwan ta akan sa gaba ɗaya komai nata ya sauya, duka lissafin ta ya rikice take masa wani irin mugun so, ita da kanta takai kanta wurin sa tun suna can, har kuma ya gama karatun sa ya dawo gida basu rabu ba. Tunda ta tawo har ta ƙaraso wurin bai ɗaga kai daga kan wayar sa ballanta harya kallo ta, duk da yaji zuwan nata sarai. "Hello baby!" Ta faɗa cikin yauƙi tana mai zama akusa dashi, tukun daga bisani ta faɗa jikin sa tana mai rungumar sa, kana ta kamo wayar da yake aikin shafawa tana mai kai idanuwan ta kanta. Murmushi ta saki, sabo da ganin da tayi ba tare da wata yake awayar ba, kamar yacce dama batayi tsammanin ganin hakan ba, sabo da yarce tasan sa da mugun jan aji akan ƴammata, domin ko ko ita sai da taci baƙar wuya kafun ta samu ya fara kula ta. Ƙala baice mata ba, sai ma janye idanuwan sa da yayi daga kanta yana mai ɗaure fuska, sabo da wayar sa data karɓar masa. "Wai meya faru ne Beb, naga kana ta faman ɗaure fuska ko kallo na ma baka yi ba?" Ta faɗa cikin muryar shagwaɓa tana mai sake kwanciya ajikin sa tare da ɗaukar hannun ta ta ɗora akan ƙirjin sa tana shafawa. Bige mata hannu yayi yana mai janye ta daga cikin jikin sa, kana yaja dan guntun tsaki. Kallon kanta ta farayi baki sake, tana mai son sanin laifin da ta masa da har yake ture ta yana mata tsaki. "Kashh! I'm sorry Baby, wallahi ni bawai na amshi wayar ka bane dan nayi maka bincike." Ta faɗa tana mai marai-raicewa, sabo da tino laifin ta da tayi gare sa. "Ke har kin isa ki hanani kula wata ne idan naso yin hakan?" Ya faɗa cikin kaushi yana mai kafe ta da idanuwan sa. Da sauri ta girgiza masa kai, duk da dai baƙaramun baƙin ciki taji da kalaman nasa ba, sai dai kuma idan da sabo yaci ace zuwa yanzu ta saba da irin waƴan nan magan ganun nasa, domin kuwa tun farkon haɗuwar su yake mata haka, sannan kuma har kawo yau bai taɓa buɗar baki yace yana sonta ba sai dai ita ta furta masa, dama kuma shi ta fannin sa haka yake, tunda yake bai taɓa kallon wata ɗiya mace ba yace yana santa sai dai su suce suna san sa, danko shi acewar sa yace ba'a haifi ƴa macen da zai buɗe baki yace yana sonta ba, kuma baza'a taɓa haiwuwar ta ba aduniya ko ƴar gidan uban wace kuwa. "I'm sorry baby, i promise i would never do that againe." Ta faɗa tana mai durƙusawa ƙasa ta kama kunnuwan ta agaban sa, bayan ta marai raice fuska. "Its you're own concern." Ya faɗa ba tare da ya kalle ta ba yana mai taɓe baki. Murmushi tayi da jin hakan daga gare sa, domin kuwa tasan ya riga da ya huce tunda harta furta haka, hakan yasa ta miƙewa da sauri tana mai faɗawa jikin sa ta rungume sa ƙam-ƙam, tukun ta ɗau fuskar ta tana mai kaita saitin tasa fuskar ta haɗe su huri ɗaya, sannan ta ɗan ɗaga lips ɗin ta kaɗan tana mai hura masa iskar bakin ta akan fuska, kana daga bisani ta buɗe bakin ta tana mai faɗin. "I love you so much My Prince!" Ƙala baice mata ba sai kallon cikin idanuwan ta kawai da yake yi shima. Ahankali ta cigaba da matsar da fuskar ta saitin tasa har ta samu damar haɗe tsinin hancin ta dana sa, tukun ta matsar da lips ɗin ta tana mai ɗora su akan nasa, kana ta zaro harshen ta tana shirin lasar nasa. Da sauri ya janye fuskar sa daga jikin tata yana mai juyar da kai gefe. Galala ta bisa da kallo baki asake, sannan kuma hankali atashe, sabo da baicika yi mata irin haka ba sai har idan yana son suyi faɗa da ita. Cikin rawar murya ta buɗe baki tana mai faɗin. "What happened againe Baby?" "I'm not in the mood!" Ya faɗa yana mai jan wayar sa ya cigaba da shafawa ba tare da ya kalle ta ba. "Please Baby i said I'm sorry!" Ta sake faɗe tana mai ƙara faɗawa jikin sa. Uhm! Ya faɗa ba tare da ya kalle tan ba dai. "To please ka tsaya kaji." Ta faɗa tana mai sake kai lips ɗin ta kan nasa ta haɗe su wuri ɗaya. Bai hana taba yanzu sai dai kuma bai taya ta ba, sai ita kaɗai kawai ya bari tana ta faman aikin ta. Ganin da tai yaƙi ya ware kamar yacce take sone ya sanya ta ƙara dabai-baye sa sosai acikin jikin ta, tukun ta fara jansa da ƙarfi ba tare da ta sakar masa bakin sa ba daga cikin nata ba. Binta ya fara yi ba tare da yay mata musu ba har tasamu nasarar matso da su bakin kujerar nan, tukun ta cigaba da kissing ɗin bakin sa cikin sauri, kana daga bisani ta shammace sa tana mai funcikar sa suka afka cikin swimming pool ɗin nan atare. *BABBAN ZAURE LOCUS* Unguwace wacce take agaban gidan slSarkin Wasai, Unguwace ta masu hannu da shuni dai dai gwargwado. Duk gida jen da suke acikin unguwar sun kasan ce manyan ginin-nika ne na bene, sai dai kuma ahakan wani yafi wani girma. Wani ɗan madaidl-daicin gida mai matsakaicin girma baƙar motar ƙirar coralla Lx ta danna kanta cikin get ɗin sa da yake abuɗe. Farfajiyace mai girma dai dai misali acikin gidan, yayin da akabi aka ƙawata ta da wasu haɗaɗɗun kujerun silver daga can gefe. Zagaye compound ɗin yake da furanni masu natuƙar kyau da ɗaukar hankali. Direct matuƙin motar ya huce parkin space inda wasu motocin har guda biyu suke fake acikin sa da ita, tukun ya parka ta awurin ta, kana ya buɗe murfin motar ya futo hannun sa riƙe da jakar sa. Farin ne dogo mai kimanin shekaru arba'in aduniya. Sanye yake da dack bluen shadda tare da baƙar wula akan sa, yayin da takalman kafar sa ma suka kasance baƙaƙe, sai tsintsiyar hannun sa kuma da take ɗaure da baƙin agogon fata mai tsananin kyau itama. Ɗaga kai sama yayi yana mai kallon yarce giza-gizai keta haɗuwa, alamun ruwa na kusa kenan kasancewar yana yin damuna da ake ciki, tukun daga bisani ya sauke kan nasa ƙasa, yana mai kai tafin hannun sa kan fuskar sa ya shafi sajen da yake kwance lup-lup akan ta har zuwa dogon gemun dake manne ajikin haɓar sa da yasha gyara yana ta faman shignin, kana daga bisani ya fara ɗaga ƙafafuwan sa yana mai dosar ƙofar da zata sada sa da cikin gidan nasu. Da sallama ɗauke abakin sa ya danna kansa cikin ɗan madai -daicin falon da yake ɗauke da kujerun ƙasar turki acikin sa. "Wa'alaikumu salam!" Datijjon mutumin da shekarun sa zasu kai sittin da biyar aduniya ya amsa masa, tare da wata tsohuwa da take zaune akan kujera dattijon mutumin na ɓare ayaba yana bata. "Barka da hutawa Abba, ina yini." Matashin mutumin ya faɗa yana mai zama akan kujerar da take facing ɗin wacce suke akai. "Lafiya ƙalau Malam Ahmad, fatan ka dawo lafiya kaima." Dattijon ya faɗa yana mai sakarwa ɗan nasa murmushi. "Lafiya ƙalau wallahi Abba, sai dai kawai gajiya dana kwaso sosai." Shima mutumin da aka kira da Ahmad ɗin ya faɗa yana mai ɗan yamutsa fuska. "To ai dama gajiya ta zama dole, tunda anyi aikin da za'a gajin ai." Mahaifin nasa ya faɗa yana kallon sa. "Kai dallacan rufen baki kaima, gajiya ko ko zallar ragwanta irin tasa." Tsowuwar matar dake zaune akan kujera tana cin ayaba ta faɗa tana harar wanda aka kira da Ahmad. Tukun ta ɗora da cewar. "Yanzu Abdulkarimu kana gani ɗanka ya shigo har inda nake, amma bai gaishe niba sai kai kaɗai ya gaisar, shine ko kayi masa faɗa tsabar duniya ta lalace ko." Ta faɗa tana mai marai-raicewa kamar zata saki kuka. "A'a Umma ta kiyi haƙuri, ai yanzu shima zai gaishe ki, kinga magana muke yine shiyasa baiyi ba tun farko." Ya faɗa yana kallon ta. Tukun ya juya ɓarin da ɗan nasa yake yana mai sakin murmushi yace. "Kai gaishe mun da uwata tun kafin ranka ya ɓaci yanzu yanzu." "Ina ai abun bama zaije da haka ba Abbana." Ya faɗa yana sakin murmushi, tukun ya sake buɗe baki yana mai faɗin. "Kaka ta ina yini, barka da gida ya akaji da tsufa kuma?" Ɗaure fuska tayi tamau ba tare data amsa masa ba, sai wata muguwar uwar harara data bugo masa, tukun daga bisani ta buɗe baki tana mai faɗin. "Amma ai da uwarka kake gaisarwa ba zakace mata ya tsufa ba." Taɓe baki yay shima ba tare da ya tanka mata ba, yayin da shi kuma mahaifin nasa yake ta faman gumtse dariya, domin ko shida kansa yasan Umman tasa bata so jikokan ta suna ce mata ya tsufa. "Ina Ummi take ne Abba?" Shekh Ahmad ya faɗa yana mai kallon mahaifin nasa. "Tana sama tana ai'kin tinanin ta na sabo daka tafi kabar ta cikin sa mana." Mahaifin nasa ya faɗa yanayin sa na sauyawa lokaci guda. Shima Sheikh Ahmad gaba ɗaya sauyawa yay, jikin sa duk yay mugun yin sanyi, yayin da ita kuma kakar tasu ta buɗe baki tana mai faɗin. "Aini na rasa gane wace irin mace ce Ai'shatu, ace shekaru ɗai-ɗai ɗai-ɗai har kimanin shekaru talatin da faruwar abu amma kullum jiya iyau abu yaƙi hucewa." "To duk wace sila, da kinbi ta maganar Abba da yace baza taba ai'da duk hakan bata faru ba." Sheikh Ahmad ya faɗa yana mai miƙewa ya doshi hanyar stairs. "To mara kunya fitsararre, daka tsaya baka tashi ba mana kaga yarce zansa yanzu yanzu ubanka ya mammake mun kai, sha-sha-shan yaro kawai, Sheikh ɗin ƙarya Malamin kwali kawai." Tsohuwar ta faɗa da ƙarfi tana mai bugawa bayan sa harara. "Ke kika jiyo dai." Sheikh Ahmad ya faɗi haka ƙasa ƙasa yana mai ƙarasa hayewa sama. "Gunguni kake min ko, ai'ko wallahi zaka futo ne kasame ni ina nan babu inda zan matsa daga ni har baban naka, ai dai nasan ba kwana zakai aciki ba dole ka futo ka tafi wurin bursun-sunar matar nan taka da ko ɗaurin zani bata iya ba." Sheikh Ahmad ya jiyo sautin kakar tasa tana faɗin haka adai dai lokacin da yake shirin shiga ɗakin mahaifiyar tasa. Taɓe baki yay yana mai danna kansa cikin ɗakin. Zaune ya hange ta acan ƙarshen gado sanye da maroon ɗin hijab ta haɗa kai da guiwa. Tsaye yay daga bakin ƙofar yana mai kallon ta ba tare da yace komai ba. Sosai yake jin ciwo acikin rai da zuciyar sa aduk lokacin da zai tadda mahaifiyar tasa cikin damuwa, ji yake ina ace yana da yarce zaiyi ya yaye mata damuwar ta, tabbas da ko kwana ɗaya baza'a sake ba sai ya samar mata da abun da take so, kafun ta koma ga mahallicin ta. "Assalamu alaikum ya Ummi na." Ya faɗa da sauti cikin tattausar muryar sa daga inda yake. Ahankali ta janye kanta daga tsakan-kanin cinyoyin ta, tukun ta ɗago fuskar ta ɗauke da murmushi wanda kallo ɗaya zaka mata kasan na yaƙe ne tana mai faɗin. "Wa'alaikumu salam yaro na!" Ajiye jakar dake ɗauke ahannun sa yayi akan kujerar da take agefen sa, tukun ya fara ɗaga ƙafafuwan sa ahankali yana mai dosar gadon. Hawa yayi kan gadon yana mai matsawa kusa da inda mahahifiyar tasa take ya zamto suna facing ɗin juna, tukun ya tanƙwashe ƙafafuwan sa agaban ta, kana ya miƙa hannuwan sa yana mai kamo tafukan hannayen ta ya haɗa dana sa ya rumtse su wuri ɗaya, tukun ya ɗaga idanuwan sa yana mai kallon ta, kamar yacce ita ɗin ma take kallon sa ƙwalla na tattaruwa acikin nata idanun, kana ya buɗe baki cikin sanyin murya da taushi yana mai faɗin. "Sh...............✍ #COMMENTS ND SHARE PLS 🐎 *BAƘAR MASARAUTA* 🐎 👑👑 🦋 🦅🕊🦆 🐍🎠🐄🏹 _*NA*_ UMAR FARUQ*D* *BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM* *PAGE 04* "Shin har sai zuwa wane lokacin ne zakicire damuwa aranki ummi na?" Ya faɗa yana mai kallon ta tare da murza tafin hannhn ta dake cikin nasa ahankali -ahankali. "Har sai ranar da rabbi samawati wal'ard ya karɓi rai da ruhina." Ta faɗa tana mai kallon cikin idanuwan ɗan nata ƙwalla na tsinkewa daga cikin idanuwan ta. "Subahanallah! Ummi na me yasa zakice haka? Ina al'ƙawarin da kika mun na cewar ba zaki ƙara kuka ba?" Ya faɗi haka muryar sa na rawa shima. Yayin da ita kuma ta buɗe baki tana mai faɗin. "Kayi haƙuri yaro na, domin ko na kasa cika sa, sannan kuma bana tinanin zan'iya cika sa! Ba daga ni ɗin bace ba, ƙaddara tace tazo da hakan yaro na." "Tabbas na sani ƙaddarar kice tazo da haka Ummi na, amma ya kamata ace kinyi abun da zaki cinye ta, ko dan kisamu tagomashi awurin ubangijin mu, domin ko duk musulmi na ƙwarai mumini ansan sa da yarda da ƙaddar mummuna da kyakkyawa ne Ummi na, shin me yasa kema ba zaki rungumi taki da hannu bibbiyu ba, zuwa yanzu kibarwa Allah komai." Sheikh Ahmad ya faɗa yana mai cigaba da murza tafin hannun ta, tukun daga bisani ya ɗora da cewar. "Dan Allah Ummi na ki taimaka ki rage sanya kanki acikin damuwa ko domin lafiyar ki, kinga gaba ɗaya yau satin ki biyu da baro asibiti duk ta sanadin damuwar da kike yawan yi, dan haka dan Allah ina son kimun al'ƙawarin bazaki ƙara yin kuka ba, ko kuma zama wuri ɗaya kina tinane-tinane Ummi na." Ya ƙarasa maganar cikin sanyi yana mai kallon ta. Murmushin yaƙe ta saki tana mai kallon sa itama, tukun daga bisani ta buɗe baki tana mai faɗin. "Na gaji da ɗaukar al'ƙawain dana san bazan iya cika sa ba, idan har nace na maka al'ƙawarin bazan ƙara tinani ba daga yau ba to kasani tabbas ƙaryace kawai na faɗa, domin ko koda nayi ƙoƙarin yin hakan ako da yaushe bana iyawa, ko kaɗan nima ba'ason raina nake haka ba, kuma bawai dan hakan na rage mun raɗaɗin abun da nake ji azuciya ta ba, sai dai babu yarce zanyi tinani agareni ya zama dole Yaro na. Akullum ako da yaushe idan na tuna yarce aka rabani da jariri na ta ƙarfi, awurin dana haife sa ba tare dako ɗaukar sa nayi ba, ina mai jin zuciya ta na wata irin suya ne, ina mai jin raina na tsan-tsar tafasa da ƙuna, ina mai jin ƙwaƙwalwa ta na zafi, hankalina na sake tashi, komai na dawo mun sabo in dinga ganin kamar alokacin abun ke faruwa! Abu na biyu kuma da yake ƙara sanya ni cikin damuwa shine, canzawar mafarkin dana sabayi akan matashin da nake faɗa maka daga mai daɗi zuwa akasin sa, rabon da nace maka nayi bacci mai daɗi ni kaina har na manta Yaro na, domin ko da zarar na kwanta nake ganin sa acikin mugun yanayi yana mai miƙo mun hannun sa dan na taimake sa, amma sai dai da zarar na matsa wurin sai nima awurgar dani gefe, sannan aja sa ai gaba. To ko taya ya kake ganin zan iya dena tunani da shiga damuwa Ahmad?" Mahaifiyar tasa ta faɗa ƙwalla na jiƙa mata fuska, har kuma lokacin bata fasa kallon saba kamar yacce shima bai fasa kallon ta ba. Shi kanshi sheikh Ahmad wani irin raɗaɗi da suya yake jin zuciyar sa nayi masa. Cikin sanyi ya sake buɗe baki yana mai faɗin. "Zaki iya denawa Ummi na, addu'a kawai zaki dingayi kamar yacce kika kasance kina yi abaya, sannan kuma aduk lokacin da zakiji abun na faɗo miki arai, to ki yawaita ambatar. *Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, lahaula walaƙuwwata illah billah! Allahumma ajirni fi musibati, wa'aklifni kairan minha! Hazbunallahu wani'imal wakil.* Da izinin Allah zaki samu sauƙin raɗaɗin da kike ji azuciyar ki tsawon shekara da shekaru, dan haka yanzu ki tashi mu tafi fallo wurin Abba da Kaka, sabo da idan kina zama cikin murtane shine bazaki dinga tinawa da abun ba akai-akai ba. Ya ƙarshe maganar yana mai ɗaukar yatsun hannun sa ya fara ɗauke mata hawayen da suke kwance akan fuskar ta. "Allah yayi maka albarka Yaro na, rabbi yasa kaima ƴaƴan ka suji ƙanka kamar yacce kake jin ƙanmu muma." Ta faɗa tana mai sakarwa Sheikh Ahmad murmushi, yayin da shi kuma ya miƙe tsaye yana mai sauka daga kan gadon fuskar sa ɗauke da murmushin shima, tukun ya sake miƙa mata tafin hannun sa ta riƙe sa, sannan itama ta sauko suka kama hanyar da zata sadasu da waje tare. *JAHAR KAGUL, MASARAUTAR FULƊE.* Sai da ta gama shawagin ta tare da abubuwan nishaɗin ta, tukun ta juya cikin takun ta wanda shi kaɗai abun kallo ne, tana mai kama hanyar da ta biyo. Tayi nisa sosai tana shirin fucewa daga cikin wurin, sai ga wani mutumi nan mai kimanin shekaru arba'in ya dunfaro inda take da matuƙar sauri har yana ɗan haɗawa da gudu gudu. "Ranki ya daɗe!" Mutumin dake sanye da kayan fulani rataye da sanda akafaɗar sa ya faɗa da ƙarfi, sabo da ganin da yayi tana shirin yin nisa, kasancewar shi ta ɓangaren kudu ya ɓullo wurin, saɓanin ita kuma da take yin gabas. Juyawa tai baya dan taga ko wanene. Murmushi ta saki daga inda take sabo da fuskar da tai arba da ita, tukun ta koma jikin wata bishiya da take kusanci da ita tana mai jingina da ita tare da ɗaga kanta sama. "Barka da warhaka kyakkyawar Gimbiyar Masarautar Fulɗe, Sarauniya kuma ga tsuntsayen Masarautar Fulɗe." Ya faɗa adai-dai lokacin da ya ƙaraso gaban ta yana mai durƙusar da kai ƙasa. "Barkan ka dai amintacce na." Ta fada tana mai kallon sa itama, tukun ta ɗora da cewar. "Ya aka kwana ne, me ake ciki dan gane da binciken ka tun daga na jiya har kawo na yau?" Ta faɗa idanuwan ta ƙur akan sa. Sake durƙusar da kansa ƙasa yay, tukun ya buɗe baki yana mai faɗin. "Amsar dai duk itace take mai-maita kanta ya shugaba ta, ma'ana jiya da yau ɗin ma duk Duhu ne yake bayanna amai makon ganin wurin da yakasnce ashi, amma sai dai abu ɗaya dana sake ganowa shine, tabbas mutum ne shi ɗin ba Aljan ba." Ya ƙarashe maganar yana mai sake durƙusar da kai ƙasa. Yayin da ita kuma Gimbiya Haddiyal ta fara ɗaga ƙafafuwan ta tana mai juya baya ta fara taku daga inda take zuwa gaba, sai dai tayi yayi taku biyar, tukun ta tsaya cak awurin da take tana mai juyowa ta sake fuskantar mutumin nan da ta kira da Amintaccen ta. Sannan ta buɗe baki cikin kaushi tana mai faɗin. "Na riga na daɗe da sanin Giɗaɗo am mutum ne ba Aljan ba, dan haka daga yau bana buƙatar sake jin wannan daga gare ka, yanzu kai zaka iya tafiya, amma katabbatar ka ƙara azama wurin tayani binciken inda yake agaba, domin ko gaba ɗaya shine duniya ta ayanzu, sannan kuma ina jin muddin ban same saba to komai na iya faruwa dani." Ta faɗa tana mai rumtse idanuwan ta da ƙarfi. "Insha Allahu zama asame sa nan kusa bada jimawa ba kyakkyawar Gimbiya." Ya faɗa yana mai miƙewa tsaye daga durƙushen da yake, tukun ya juya yana mai sake bin hanyar da ya biyo yazo wurin. Yayin da ita kuma Gimbiya Haddiyal ta juya tana mai sake ɗaukar wata hanyar ba wacce take kan biba, fuksar nan ta ta aɗaure yarce kasan ba ita bace take aikin sheƙa dariya ɗazu ba. Ba wata doguwar tafiya tayi ba ta ɓulla wani huri mai kama da daji-daji. Gaban wani kogo dake jikn wata shirgegiyar bishiyar ɗorawa ta ƙarasa tana mai tsugunnawa, kana ta miƙa hannun ta tana mai janyo wani baƙin kasko aciki ta ajesa agefe, tukun ta sake zura hannu ciki, sai gashi ta ƙara janyo wata ƙatuwar gora wacce take cike da wani yellon ruwa itama ta ajeta kusa da kaskon, sake mai da hannun ta tayi ciki, wasu irin layoyi, tsummokarai da iccina ne masu matuƙar yawa ta sake zarowa aciki, kana suma ta ajesu agaban kaskon. Buɗe gorar ruwan nan tayi tana mai tsiyaya yellon ruwan dake cikin ta acikin baƙin kaskon nan, sannan ta janyo wani tsumma mai matuƙar ƙura tana mai buɗe sa, wasu irin ciyayi -ciyayi tare da wata kalar ƙasa ne suka bayyana aciki, suma ɗibar su tayi ta zuba su acikin kaskon, kana ta ɗauki layun da suke awurin su kuma ta maƙalasu abakin kaskon. Take ruwan nan ya fara juyawa da matuƙar gudu kalar sa na sauyawa daga yellow zuwa fari-fari. Miƙewa tayi tsaye bayan ta ɗauki wata laya tare da wani icce ta rumtse su acikin tafin hannun ta, tukun ta rufe idanuwan ta da ƙarfi tana mai fara zaga wurin tare da buɗe baki cikin sauti tana faɗin. "Zaiba! Zaiba!! Zaiba!!!" Wani irin hautsinawa ruwan dake cikin tukunyar nan ya farayi da matuƙar gudu, cigaba da furucin ta tayi cikin ƙarfi tana zaga kaskon, har lokacin kuma idanuwan ta arufe suke bata buɗe suba. Wani irin hayaƙi ne baƙiƙƙirin ya fara futa daga cikin tukunyar yana mai tashi sama. Dasauri ta buɗe idanuwan ta akan tukunyar tana mai zaro su waje tare da ja baya. "Inaaa!!! Wallahi kai ɗin nawa ne ni kaɗai, babu wata mace da zata kasance mallakin ka aduka duniya bayan ni! Shin har sai zuwa wane lokaci ne zan gano inda kake ne Giɗaɗo am?" Ta faɗa da ƙaraji tana mai girgiza kanta, idanuwan ta akan wannan kaskon da yake futar da hayaƙi, tukun daga bisani ta ɗora da cewar. "Akan me zanga baƙin hayaƙi bayan farin ruwa nake buƙatar gani wanda zai hasko mun hanyar da zanbi zuwa gare ka? Akan me duk lokcin da naso gano inda kake abun baya yiwuwa? Shin me yasa kake bani wahala bayan babu wani abu da na taɓa so ya zamto mai wahala agare ni!" Ta ƙarasa faɗe da ƙarfi tana mai matsawa kusa da kasokon ruwan nan ta tuntsirar da shi aƙasa ya kife. Sakin layar dake dunƙule acikin tafin hannun ta tayi hawaye na ɓallewa daga cikin idanuwan ta, tukun ta juya tana mai yin taku biyu daga inda take zuwa gaba, kana ta tsaya cak tana mai buɗe baki cikin kakkausar murya tace. "Ko ita ɗin wace ce, ko waye ubanta, koda ko tare kukazo gidan duniya da ita, muddin ya tabbata kuna soyayya dole ne kabarta kasoni ni kaɗai Giɗaɗo am! Ni Gimbiya Haddiyal Ɗiyar Lamiɗon Masarautar Fulɗe nayi rantsuwa da mahallicin Shanu da Mutane sai ka zamto nawa, bazan taɓa gazawa ba wurin neman ka kamar yacce soyayyar ka baza ta taɓa yin gibi acikin zuciya ta ba, tabbas idan har tsafi gaskiya ne to ka sani zanyi amfani da wanda ya kasance acikin jiki na tun zuwa na gidan duniya domin na gano ka, haɗuwar bazata taɓa tsayawa cikin mafarki ba, tunda har na tabbatar da kai ɗin ba Aljan bane mutum ne kamar kowa." Ta ƙarasahe maganar muryar ta na rawa kamar ba itace ta fara ta ba akausashe, tukun daga bisani ta sake juyowa tana mai yowa wurin kaskon nan. "Ina sonka Giɗaɗo am, kai ɗin ka zamto wani tsagi na daga tsagin zuciyar Haddiyal." Ta faɗa cikin sanyi hawaye na sauka daga cikin idanuwan ta, tukun ta durƙusa gaban kayan tsafin ta tafara haɗasu wuri ɗaya. Sai da ta haɗe kansu tsaf, sannan ta mayar da su cikin kogon nan, kana ta tashi jiki atsan-tsar saɓule tana mai dosar hanyar da zata sadata da gidan sarautar nasu. Duk inda ta gifta sai bayi sun zube suna kwasar gaisuwa, amma ko kallo basu isheta ba balle ta amsa, ahaka har ta ƙarasa cikin tamfatsetsen falon su kanta durƙushe aƙasa, ba tare da ta kalli kowa dake cikin falon ba ta doshi hanyar ɗakin ta kai tsaye. "Haddiyal!" Cak ta tsaya adai dai bakin ƙofar ɗakin nata da take shirin shiga sabo da muryar mahaifiyar ta data daki dodon kunnuwan ta, lokaci ɗaya taji wata irin faɗuwar gaba ta ziyar ceta, sabo da mahaifiyar tata bata fiye kiran ta da Haddiyal ba, sai idan zata faɗa mata wani abu mai muhimmanci ko kuma zata mata faɗa. Cikin sanyi ta juyo tana mai kai duban ta inda tajiyo sautin muryar mahaifiyar tata. Zaune take akan kujera yanzu hannun ta riƙe sa tufa tana ci, yayin da innahuro kuma take zaune agafen ta ta ɗora kanta akan kafaɗar mahaifiyar tasu tana cin inibi ita kuma. "Gani Dadde na." Gimibiya Haddiyal ta faɗa adai dai lokacin da ta ƙaraso inda suke bayan ta samu wuri ta zauna itama. "Me ya sameki ne naga idanuwan ki sunyi ja?" Mahaifiyar tata ta watso mata tambaya tana mai kafeta da idanu. Uhm! "Dama.. Damm.. Fuffiken shale ne ya taɓan ido." Ta faɗa cikin in-ina tana mai sake sunnar da kai ƙasa. Shiru mahaifiyar tata tayi ba tare da tace mata komai ba, sai idanu kawai da tacigaba da bin ta dasu. Ta fannin haddiyal kuwa ta futar da tsamannin Dadden nata zata ƙara magana, sai daga bisani kuma ta tsunkayo sautin ta asama da yayi matauƙar hautsina zuciya da ƙwaƙwalwar ta tana mai faɗin. "Aɗazu bayan tafiyar ki Mahaifinki Lamiɗo ya shigo, yace in sanar miki atanadi madara da kayan itatuwa, gobe zakiyi baƙo ɗan Lamiɗon Masarautar Yamma zaizo batun auren ku, dan haka sai kitashi kije ki fara gyarawa!" *** *ƘASAR MALIN, JAHAR KARFUZ CIKIN BAƘAR MASARAUTA* Sai da suka tabbatar da tabar duka yankin, tukun suka dumfaro inda suka hangi Bir kwance cikin ƙasa da gudun su. 🐎 *BAƘAR MASARAUTA* 🐎 👑👑 🦋 🦅🕊🦆 🐍🎠🐄🏹 _*NA*_ UMAR FARUQ*D* *BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM* *PAGE 05* Durƙusawa sukayi ƙasa suna masu kamo sa, yayin da shi kuma yake ta faman juya kai har lokacin yana mai taune leɓen sa na ƙasa. Ɗagosa sama sukayi ya zamto yana jingine ajikin su, tukun suka fara ɗaga ƙafafuwan su suna masu dosar kudu tare da jera masa sannu. Sanye suke suma da fararen gajerun wandina na yadi kamar yacce shi ɗin ma ya kasance babu riga ajikin su, sai uban zanen tambarin masarautar tasu da ya kasance manne akan fatar su tako ina. "Sannu ɗan uwa Bir, dama sabo da gudun shiga irin wannan matsalar ya sanya kullum nake ce maka kadena shigewa Gimbiya, amma sai dai kai ɗin ko kaɗan bakaji, to yanzu wa gari ya waya kenan, dubeka kaga yarce ka koma, gashi kuma kariga da kasan jibi -jibin nan ne ranar zagayowar bikin godiya ga Abun Bauta Gargabilu, kuma kasan muddin kana cikin BAƘAR MASARAUTA babu ruwan wani da larurar ka ko wace kalace ,sai ka ɗauki iccina har dai bikin godiya ya zagayo." Ɗaya daga cikin matsan da suke dafe da Bir waƴan da zasu iya yin sa'anni a shekaru ya faɗa suna masu cigaba da dosar inda wasu ɗakuna da aka haɗasu da iccina suke jera da matuƙar yawa. "Ai dama ka dena wahalar da bakin ka ɗan uwa Mauzum, domin kuwa duk abun da zakace akan Bir ya dena shish-shigewa Gimbiya kayi abanza ne, dan ko ba saurara yake ba balle harya dauka ma, shiyasa ni yanzu tsakani na dashi kawai idone babu ruwa na, sabo da karma ya gogamun laifin da ban janyo ba." Cewar ɗayan yana mai kallon ɗan uwan nasa. Yayin da shi kuma Bir ya lumshe dara daran idanuwan sa yana mai yin shiru ba tare da ya tanka musu ba, duk da dai yana jinsu sai aikin kawai taunar leɓan ƙasan bakin sa da yake yi da haƙoran sa ahankali, ahaka har suka ƙarasa wurin da ɗakunan itacen nan suke ajere re-ras ta kowanne ɓangare. Sai da suka shigar dashi har cikin wani ɗan ƙaramin ɗaki dako daɓe babu akasan sa, sai ƙasa da kuma shimfiɗun tsummokara waƴan da suke kwanciya akan su, tukun suka ajesa. Miƙewa tsaye sukai suna kallon sa, yayin da shi kuma yake akwance rigin-gine idanuwan sa na kallon iccinan da aka jera asama wurin rufin ɗakin. "To Bir bara mu muje musanarwa Iya cewar kadawo, domin kuwa tun lokacin da Gimbiya ta rufeka hankalin ta yake atashe ko abinci bata ƙara ciba." Suka faɗa suna masu juyawa suka fuce daga cikin ɗakin. Ahankali Bir ya miƙe daga kwancen da yake yana mai taune laɓen sa tare da yamutsa fuska, alamun har yanzu jikin nasa nayi masa ciwo kenan. Waige waige ya farayi acikin ɗakin nasu har idanuwan sa suka sauka akan wasu curin kaya da suke ƙulle wuri ɗaya. Jan jiki ya farayi har ya ƙarasa inda kayan suke, tukun ya sanya hannu yana mai bubbuɗasu, kana ya janyo wata ƙatuwar kwari da gwafa daga cikin kayan yana mai riƙe ta ya jujjuya ahannun sa yana kallon ta, tukun ya miƙe tsaye ahankali yana mai dafa katakwayen da suka kasance bangon ɗakin, kana ya fara ɗingisa ƙafafuwan sa yana mai dosar hanyar waje. Yana futa ya ɗauki hanyar dake kallon kudu yana mai miƙar ta, tafe yake yana dingishi tare da cije lips ahanka har yayi tafiya mai nisa daga inda yake, tukun ya ɓulla wani huri wanda za'a iya kiran sa da daji sabo da bishiyun da suka kasance awurin masu matuƙar yawa ta koina, banda sautin kukan tsunysaye babu sautin da akeji yana tashi awurin. Jingina yayi jikin wata bishiya yana mai ɗaga kansa sama tare da lumshe idanuwan sa. Kana ya ɗaga laɓɓan sa ahankali yana mai faɗin. "Iya tace ba'a taɓa yin nasara daga zaune, sannan kuma daɗi bai zuwa sai bayan ansha gumurzu, dan haka na ɗauri aniyar zama jarumi har zuwa lokacin da zancimma buri na, zan jure kowace kalar wahala daga gareki yake Gimbiyar BAƘAR MASARAUTA, zan ɗauki ko wane kalar wulaƙanci da ƙasƙanci muddin zan samu abun da zuciya ta take muradi agaba, zan tabbatarwa duniyar BAƘAR MASARAUTA cewa Iya batai ƙarya ba data kirani da suna JARUMI." Ya ƙarashe maganar yana mai buɗe idanuwan sa tare da sauke kansa ƙasa, tukun yakai duban sa kan tafin hannun sa da yake riƙe da kwari da gwafa, sannan ya matsa daga jikin bishiyar nan yana mai ɗaukar kwarin ya maƙala sa ajikin gwafar, tukun ya saita wata shirgegiya bishiya da take nesa dashi sosai, yana mai jan gwafar tukun ya sake ta. Fit!!! Kake jin sautin futar tsinken daga jikin gwafar da matauƙar gudu yana mai zuwa ya cake cak ajikin bishiyar. Cigaba da saki yayi baji ba gani yana yi yana tangaɗi tare da buɗe baki, sabo da yarce yake jin wata irin hajijiya na ɗibar sa, amma duk da haka ko kaɗan bashi da alamar zai tsaya. Kallo ɗaya zakai nasa ka fahimci ba'a ƙaramun jigace yake ba, sabo da yarce gumi ke cigaba da tsiyaya daga jikin sa da yake tsantsar rawa, ga laɓɓan sa da sukayi matuƙar buahewa tare da yin baƙi, alamun ba ƙaramar ishirwa yake ji ba kenan! "Kai Jarumi! Jarumi!! Jarumi!!! Shin meye hakan kake yi?" Sautin muryar iyar bayi ya daki dodon kunnen sa cikin firgici, amma duk da haka bai waiga ya kalli inda yajiyo sautin ba balle harya tsaya daga abun da yake, sai uban tangaɗi da yake yi kawai! Da gudu Abokan nan nasa guda biyu da suka kai sa ɗaki suka ƙaraso inda yake suna masu sanya hannu suka rirriƙe sa, tukun Mauzum ya anshe kwari da gwafar daga hannun sa yana mai dire su aƙasa. "Shin me yasa zaka baro ɗaki kayo nan, bayan kasan ɗauke kake da raunika ajikin ka Jarumi?" Cewar Iyar bayi tana mai durƙusawa ta aje ƙatuwar ƙwaryar dake rumgume ahannun ta agefe, tukun ta matsa inda su Mauzum suke zaune aƙasa, rungume da Bir da yake ta faman sakin numfarfshi idanuwan sa na kakafewa ahannun su. Zama tayi tana mai tanƙwashe ƙafafuwan ta agaban sa, tukun ta tallabo kansa tana mai ɗora sa akan cinyar ta, kana ta buɗe tafin hannun ta tana mai ɗan marin fuskar sa sama-sama bakin ta na furta kalmar. "Kai Jarumi! Jarumi!! Jarumi na!!!" Amma sai dai ko kallon ta baiba sai idanuwan sa da suke cigaba da kakkafewa numfashin sa na fuzga da ƙarfi. "Kai Mauzum maza yi sauri ka miƙo mun ƙwaryaccan." Iyar Bayi ta faɗa hankali tashe tana mai cigaba da marin fuskar Bir tare da faɗin Jarumi. Dasauri suka mike su duka biyun har suna gware da juna wurin tashi, tukun Mauzum yay maza yaje ya ɗauko ƙwaryar da take cike da ruwa tare da kofi acikin ta yana mai zuwa ya ajeta agaban Iyar Bayi. Dasauri ta sanya hannu ta ɗauki moɗar dake cikin ruwan tana mai kwaso ruwan da shi, tsiyaya sa tayi atafin hannun ta, tukun ta yarfawa Bir shi akan fuska tana mai cigaba da kiran sunan sa. Ajiyar zuciya ya fara saukewa akai-akai yana mai lumshe idanuwan sa. Hakan da Iyar Bayi ta gani ne yasan ya ta sa hannu ta ɗago kansa, tukun ta ɗora masa moɗar ruwan akan laɓɓa tana mai faɗin. "Sha ruwa Jarumi na." Bai musa mata ba ya buɗe bakin sa ruwan ya fara wucewa da sauri da sauri. Tas ya shanye ruwan yana mai buɗe idanuwan sa, sake maida moɗar ruwan tayi cikin ƙwaryar ta ƙara kamfato sa, tukun ta ƙara ɗora masa akan baki ya shanye sa tas. Sannan ya sake maida kansa kan cinyar Iya yana mai lumshe idanuwan sa. "Shin sai yaushe ne zake dena shigewa Gimbiya Jarumi? Kullum abun da nake gudar ma kenan amma ko kaɗan bakaji, to yanzu wagari ya waya kenan, gashi kuma kasan Jibi ne bikin ranar zagayowar godiya ga abun Bauta Gargabilu, amma kuma babu abun da ka tanada, ko iccen da zaka ɗauka baka tanada ba, kuma kasan ko awane irin hali kake ciki babu wanda zai yarje maka sai ka futo kaima." Iyar bayi ta faɗa tana mai bin fatar jikin sa da tayi wani irin dabbara-dabbaran baƙi da ja yarce kasan wanda ya ƙone da idanu. Yayin da shiko Bir har lokacin yake lumshe da idanuwan sa ba tare da yace mata komai ba. Hannu tasa ahaɓar zanin ta tana mai ciro wani ƙullin tsuma, tukun ta fara kwance sa bayan ta sake matso da ƙwaryar ruwan nan gaban ta. Ƙullikan wasu tsummokaran ne har guda biyu acikin babban ƙullin. Ɗaukar na farkon tayi ta fara kwance sa. Gishiri ne ya bayyana acikin sa, buɗe tafin hannun ta tayi tana mai tsiyaya gishirin da yawa akan sa, tukun ta juye sa acikin ruwan ƙwaryar, sannan ta sake kwance ɗayan ɗaurin wanda yake ɗauke da garin magani acikin sa. Shima ɗibar sa tayi ta zuba acikin ruwan, kana ta sake ƙulle su tana mai mai dasu jikin haɓar zanin ta ta ɗaure, tukun ta sanya hannun ta cikin ruwan tana mai jujjuya sa. Kana ta tsunduma kofin nan tana mai kamfato ruwan da shi, tukun ta juye sa ajikin Bir. Rumtse idanuwan sa yayi da ƙarfi yana mai taune leɓen sa na ƙasa, sabo da yarce ruwan yake ratsa ciwukan dake jikin sa yana kwanciya. "Ina mai roƙon ka da abun bauta Gargabilu ka taimake ni ka kuma taimaki kan ka futa daga harkar Gimbiya, muddin baso kake muyi kukan rashin ka ba nan kusa." Iyar bayi ta faɗa tana mai cigaba da watsa masa ruwan ajiki. Sai da ta gama sanya masa ruwan ta tabbatar da ya taɓa ko ina na jikin sa, tukun ta miƙe tsaye tana mai gyara ɗaurin baƙin ƙyallen da yake aƙugun ta, kana ta kalle su tana mai faɗin. "Yanzu ba zama zakuyi ba, ku tashi ku kama Jarumi kutaya sa yo nasa itacen ɗaukar shima, dan ko muddin bakuyi hakan ba to ni nasan wannan azabar tayau ba komai bace akan wacce Boka mai Hutar Kasko zai sa ayimasa aranar Biki." Ta ƙarasa maganar tana mai juyawa ta doshi hanyar data biyo. "Shin har sai zuwa wane lokaci ne zaki cikan alk'warin da kika d'aukar mun ne Iya?" Bir ya fad'a da k'arfi yana mai mik'ewa tsaye, tukun ya fara d'aga k'afafuwan sa yana mai dosar inda iyar bayi take. Yayin da ita kuma Iyar Bayi ta tsaya cak ai'nda take jikin ta na matuk'ar rawa ba tare data iya furta komai ba, tukun daga bisani ta fara waige- waige tana mai duba gabas da yamma, kudu da arewa, domin taga ko akwai wani wanda yaji furucin Bir bayan su. Sai da ta tabbatar da babu wani mahaluk'i dake wurin bayan su, tukun ta juyo inda Bir yake takowa da d'an gyashi jikin ta na tsantsar karkarwa. "Shin mene zai sanya kayi irin wannan furucin awuri irin wannan jarumi?" Iyar Bayi ta fad'a k'asa k'asa tana mai matsawa inda Bir yake ta dafa kafad'ar sa. "To iya s.... "Shiiiit!" Iya ta fad'a tana mai d'ora yatsa akan baki tare da zaro idanuwa, jikin ta na tsantsar rawa, yayin da shi kuma Bir ya bita da idanu yana kallon ta, tukun daga bisani ta janye yatsar ta daga kan la'b'ban ta tana mai bud'e baki ahankali tace. "Muddin baso kake in bak'unci k'asa ba ayau, to na rok'eka da abun bauta Gargabilu ka temakeni karna sake jin makamancin furuci irin wannan anan wurin." "Amm..." "A'a Jarumi kawai kayi abun da na sanya ku, ka tafi, ka tafi kuje kufara samo icci na." Cewar iyar bayi jikin ta na tsantsar kyarma. Yayin da shi kuma Bir ya rumtse idanuwan sa da matuk'ar k'arfi tare da taune leb'en sa na k'asa, tukun ya juya yana mai fara d'aga k'afafuwan sa ya doshi inda ya baro ba tare da ya sake cewa komai ba. Wata irin nannauyar ajiyar zuciya Iyar bayi ta saki tana mi dafe k'irjin ta da hannu, tukun itama ta juya cikin tsantsar sauri tana mai dosar inda ta futo, har lokacin kuma jikin ta bai bar kyarmar da yake yiba. Acan b'angaren Gimbiya Tsamir kuwa cikin zafin rai ta damk'i kan macijiyar nan da ke karkad'a harshen ta bayan ta durk'ushe agaban ta tare da rumtse idanuwan ta da k'arfi. Tukun daga bisani ta bud'e baki cikin kaushi tana mai fad'in. "Shin meke shirin faruwa dani ce Shairama? Wane laifi nayiwa abun bauta Gargabilu da har yake shirin hukunta ni ta wannan hanyar? Kamar ni! Kamar ni!! Ni Gimbiya Tasmir har zan yiwa wani can k'as-k'antanccen bawa hukunci asa na sake sa! Shin ina k'arfin iko na ya tafi ne? Me Baba yake nufi dani ce akan wancan k'ask'antaccen banzan mara galihu Shairma?" Ta fad'a da k'araji tana mai sakin kan macjiyar ta mik'ewa tsaye. Taku ta farayi daga inda take zuwa gaba, sai da tayi taku ya kai biyar, tukun taja tsaya tana mai sakin wasu irin numfar-fashi, kana daga bisani ta juyo tana mai dawowa wurin yashin da ta cake takobin ta ta funcike ta da matuk'ar k'arfi. Sake d'aga k'afafuwan ta tayi tana mai yin wurin da macijiya nan take akai. Tana k'arasawa wurin ta zube gwiwoyin ta tare da cake Takobin da matuk'ar k'arfi ak'asa idanuwan ta akan macijiyar nan da take kallon ta, tukun daga bisani ta bud'e baki tana mai fad'in. "Ina mai rantsuwa da Gargabilu sai naga bayan sa Shairama, ina mai rantsuwa da gargabilu sai ya fuskanci azaba irin azabar da bai tab'a fuskantar makamanciyar taba aduniya tunda harya bud'e baki yace mun wace kalar azaba ce bai santa ba acikin BAK'AR MASARAUTA! Zan masa azaba da ruwa, sannan kuma zan masa azaba da k'asa, kana kuma in masa azaba da huta muddin ban samu amsar tambaya ta daga bakin sa ba! Zanyi amfani da ranar jibi wacce ta kasance ranar godiya gare ka abun bauta Gargabilu, wurin gana masa azaba mafi muni daga cikin azabobi na! Tabbas ranar jibi zata zamto rana irin wacce baka tab'a yin taba agidan duniya k'ask'antacce! Tabbas ranar jibi zata kasance rana mafi k'uncin rana gareka gidan duniya, tunda har kasanya mahaifina yamun tsawa ayau! Daga rana ta jibi zan kawo k'arshen rashin kunyar ka ta hanyar gille sauran lalatacciyar rayuwar ka agidan duniya! Wannan alk'wari ne na d'aukarwa kaina, kuma nayi rantsuwa da ubangiji Gargabilu sai na cika sa Shairama kece sheda ta kuma!" Ta k'arasa maganar cikin k'araji, kana da matuk'ar sauti. Tukun ta sake mik'ewa tsaye tana mai matsawa gaban ruwan nan ta kafesa da dara-daran idanuwan ta da suka koma jajajir dasu, sabo da b'acin rai, sannan ta k'ara bud'e baki tana mai fad'in. "Tabbas kome zai faru sai dai ya faru, danko bazan tab'a iya barin wannan lalataccen bawan yaci banza ba, shine na farko da aka fara samu acikin BAK'AR MASARAUTA! Dan haka nayi rantsuwa da Gargabilu bazan tab'a barin sa shi kansa yay k'arko ba balle har asamu na biyun sa agaba!" Ta k'arasa maganar da matuk'ar k'araji tana mai juyawa ta doshi wurin da takobin ta take acake gaban macijiyar nan. Hannu tasa tana mai funcikar ta daga cikin k'asa, tukun ta juya tana mai dosar inda dokin ta yake atsaye da matuk'ar sauri. Tsalle ta buga adai dai lokacin da taje gaban sa tana mai hayewa kansa, tukun ta damik'i linzamin sa da hannu hagunta da matuk'ar k'arfi, kana ta mik'ar da takobin nan ahannun ta tana mai nuna macijiyar nan da ita, sannan ta bud'e baki cikin sauti tana mai fad'in. "Shairama!!!" Take awurin macijiyar ta b'ace bat kamar ba atab'a yin taba awurin, yayin da ita kuma Gimbiya Tasmir ta saki linzamin dokin tana mai dukan cikin sa da matuk'ar k'arfi. Haniniya dokin ya saki da k'arfi, tukun ya zabura da mugun gudu yana mai dosar hanyar daya biyo sukazo wurin. *K'ASAR HAUSA, JAHAR WASAI* *ASADULLAH PALACE.* Ba zato ba tsammani yarima Asad ya jisa tujum acikin swiming pool din nan! Yayin da ita kuma Billy ta sake damk'ar lips d'in sa da matuk'ar sauri tana tsotsar su tare da dannan tongue d'in ta cikin asalin bakin sa kamar mayya. Ta fannin Yarima Asad kuwa damƙar gashin atach d'in dake kanta yayi da matuk'ar k'arfi yana mai ɗago da fuskar ta sama, bayan ya zame lips ɗin sa daga cikin bakin, yayin da ɗayan hannun nasa kuma yake dafe da ƙugunta yana mai kallon cikin idanuwan ta, kamar yacce itama take kallon nasa, tukun daga bisani ya fara matsar da fuskar sa yana mai dosar tata, tayar ce har kowanne daga cikin su yake jin dirar numfashin ɗan uwansa akan fuskar sa. Cikin tsantsar shauƙin da Billy ta tsinci kanta aciki tayi wani irin lumshe idantuwa ta, tana mai jiran taji saukar lips ɗin sa akan nata, amma sai jitai ya sake damƙar gashin kanta yana mai ma.................✍ 🐎 *BAƘAR MASARAUTA* 🐎 👑👑 🦋 🦅🕊🦆 🐍🎠🐄🏹 _*NA*_ UMAR FARUQ*D* *BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM* *PAGE 06* Yana mai masa wata irin cakuma, tukun daga bisani ya funcikesa da matuƙar ƙarfi yana mai hullata cikin ruwan, ji lake tunjum! Ƙarar faɗawar ta. Wata irin gigitattar ƙara Billy ta saki sabo da azabar da taji ta ratsa har tsakiyar ƙwaƙwalwar ta asanadin fuzgar gashin kanta da yay, yayin da shi kuma ya juya ba tare da ya tsaya duban halin da take ciki ba yana mai kama ƙarfen dake manne jikin ramin ya futo waje. Ƙarasawa yay gaban ɗan gadon nan da yake daga bakin ruwan yana mai sa hannu ya ɗauki wayar sa, tukun ya juya yana mai dosar haɗɗaɗen building ɗin dake cikin wurin hankali kwance. Yayin da ita kuma Billy tayi suman tsaye daga cikin swimming pool ɗin ba tare da ta iya futowa ba, tana mai bin bayan sa da kallo, kafin daga bisani kuma wasu irin hawaye masu matuƙar gudu suka tsinke daga cikin idanuwan ta suna dira akan kuncin ta. Sai da har taga shigewar sa duka, tukun ta fara ɗaga ƙafafuwan ta jiki asaɓule tana mai yowa bakin ruwan. Wucewa tayi gaban gadon nan, tukun tasa hannu tana mai ɗaukar hand bag ɗin ta da wayar ta, banda ɗigar ruwa babu abun da jikin ta yake yi. Juyawa tayi ɓarin da building ɗin da da Yarima Asad ya shiga tayi tana mai kafe haɗaɗɗiyar ƙofar dake wurin da idanuwan ta da suke tsiyayar hawaye har lokacin, tukun daga bisani ta buɗe baki cikin kaushi tana mai faɗin. "Wallahi! Wallahi!! Wallahi!!! Sai nasa kayi nadamar hulaƙanta ni da kake yi Prince Asad, sai nayi fatali da duk wani jiji da kai tare da izzar da ka, sai na maida kai bawa gareni mai mun bauta, sai na nuna maka bam-bancin dake tsakanin girman kujerar Gwamna da ta Sarki! Zanyi amfani da ikona da matsayi na na ƴar Gwamana kuma ƴar gata wurin ganin na mallakeka Prince Asad, sannan aƙarshe in rabaka da duk wata ɗiya mace da ka kasance kana da kusanci da ita, domin ko an halliceka ne domin ni kaɗai Asad, an halliceka ne sabo da kazamto miji gareni ni kaɗai, dan haka babu tayarce za'ayi ka iya gujemun Prince Asad! Wallahi dani kake wasan ne Prince, kai ka fara amma nice zan ƙarashe sa. Yarima Asad kake ɗan Sarki Abdallah jikan Sarki Ahmadu agarin Wasai, ni kuma Bilikisu Abubakar Sardauna nake ɗiyar Gwamnan Wasai, dan haka muzuba mugani ni da kai ɗan halak kafasa! Ta faɗa cikin kaushi tana mai taune leɓen ta na ƙasa da ƙarfi, kana ta janye idanuwan ta daga kan mofar tana mai juyawa ta doshi parkim space cikin sauri. Bata damu da yarce ruwa ke ɗiga ajikin ta ba ta buɗe murfin motar tata tana mai faɗawa cikin ta, tukun tayi mata key tana mai lailaya kanta acikin wurin ta juya ta, kana ta take ta aɗari da ashirin tana mai dosar bakin get ɗin nan atsiyace. Da gudu get man ɗin dake zaune abakin wurin ya miƙe yana mai wangale mata get ɗin, tukun ya kauce da sauri sabo da yarce yaga tana shirin bi takansa. Gaba ɗaya ɗaukacin mutanen da suke aɗayan wurin nan na farko bin motar Billy sukayi da ido baki sake, sabo da yarce suka ga ta futo amugun tsiyace, anan ɗin ma tun kafin ta ƙaraso aka wangale mata get ɗin, tukun tazo ta huce tana mai hayewa kantiti aguje ba tare da ta tsaya duban hanya ba. Acan cikin Masarautar Wasai kuwa, tun acikin fada lokacin da ake naɗi Babban Yaya yake ta ɗaga idanuwa yana mai wurga su awurare daban -daban domin ya hango ƙanin nasa. Amma sai dai har akai naɗi aka gama baiga ko Al'amin ba ballantana yasa ran ganin sa, hakan ko ba ƙaramun sosa masa rai yayi ba. Koda aka gama naɗi mimmiƙewa akayi domin aje afara aiwatar da shagul gulan da aka shirya kamar yacce aka saba. Sosai taro yay taro, wuri ya cika da manya manyan Sarakai, masu kuɗi, harma da Gwamnoni na garuruwa daban-daban, ko wanne da kalar shigar dake sanye ajikin sa. Yayin da shi kuma Ciroma, wato Babban yaya yake sanye da wani ɗanyen farin yadi mai matuƙar taushi da haske, anyi masa ɗinkin doguwar riga tare da dogon wando, ɗauke yake da wata azababbiyar hula baƙa mai sirkin adon fari ajikin ta, yayin da daga saman hular kuma aka bita da naɗin farin rawanin da yayi matuƙar ƙarawa shigar tasa kyau, sai takalmin dake sanye aƙafar sa da ya kasance half cover shoe baƙi irin na Sarakai, yayin da tsintsiyar hannun sa kuma take ɗaure da wani ɗan ubansun agogon fata mai tsananin kyau, sai wata uwar baƙar Al'kyabba mai ɗauke da adon fari da take sanye ajikin sa tana ta faman walwali da ɗaukar ido. Dogon mutum ne sosai kanar yacce Yarima Asad ya kasance dogo, sai dai shi kuma yayi biyun Yarima Asad ajiki, kamar yacce ya basa tazarar shekaru goma a haihuwa, domin ko shi ayanzu yana da shekara arba'in ne aduniya, tare da mata ɗaya da kuma yara huɗu, maza biyu mata biyu, yayin da shi kuma Yarima Asad yake da shekara talatin da ƴan watanni aduniya. Kamar su ɗaya sak da Yarima Asad, bam-bancin su kawai shine shi Babban yaya bai kai Yarima Asad haske ba, duk da dai shima bai zamto baƙi ba, amma bayan wannan basu da wani bam-banci sai na shekaru, dan ko hatta da sajen dake ɗauke ahaɓar su duk iri ɗaya ne. Tafe suke suna masu dosar inda dawakai suke, kasancewar yanzu ne lokacin da za'a fara hawa. Zagaye yake da maroƙa da zagage suna ta faman yi masa kirari tare da kaɗa-kaɗe da bushe-bushe, suna masu faɗin. "Ciroma Sarki! Ciroma Yarima! Gagayya Ciroma! Yarima damisan Ƴan Sarki! Ɗan uban gabasawa!" Sai wasu irin bushe-bushe da kaɗa-kaɗe kawai ke tashi awurin, yayin da shi kuma ko kaɗan baya tasu, sai aikin wurga idanuwa da yake tayi awurare daban daban dan yaga ta inda zai hango ƙanin nasa. Dum! Dum!! Dum!!! Kakejin sautin ƙarar harbin bindigu na tashi da matuƙar ƙarfi, kasancewa tawowa da Sarki yayi tare da tawagar sa. Zagaye yake atsakiyar Fadawa da Dogarai, hannuwan su ɗauke da wasu irin zura-zuran bulalai suna ta aikin buɗa hanya, tare da hankaɗe duk wani wanda ya kasance tsaye agaban su. Yayin da fadawa kuma ke aikin sakin kirari da matuƙar karfi yarce kasan zasu tsaga wurin, suna masu fadin. "Takawarka lafiya garƙami wandon ƙarfe! Lafiya jinjirin wata shakallo! Lafiya jijjigen Addini! Lafiya maida garin wani kango! Lafiya darzaza amalen Sarakuna! Lafiya bango madafar Bayi! Lafiya mai kiran gabas da yamma ta amsa! Lafiya numfashin duniya! Lafiya ubangijin Bawa da Baiwa! Sannu alafiya Alfanda bawanda! Sannu alafiya Amalen Sarakuna! Sannu Alafiya toya matsafa! Lafiya mai ado da kurar yaƙi! Lafiya mai ado da kurar yaƙi!! Lafiya mai ado da kurar yaƙi!!! Amin zulillah! Amin kigon gabas maci yammawa! Lafiya mai shari'ah daf da wuya! Hifzullahi na Allah! Kanzullahi bawanda! Amincinka yafi ga linzami! Ciki sannu alafiya uban gyayya!" Haka suke ta aikin yi masa kirari da matuƙar ƙarfi suna masu dosar hanyar futa daga cikin fada. Yayin da maroƙa suma keta aikin sakin kiɗa da busa suna masu faɗin. "Abdullahi jikan Abdullahi! Majina gishirin yaro! Dariyanka kukan yaro! Tsawa mai ratsa gidan Arna! Dan Ahmadu Autan Abdullahi! Balaraben sarakuna jikan Abdullahi! Ɗan Massalacin juma'a jikan Massalacin juma'a!" Haka suma suke ta faɗe suna masu busa algaitu da kakaki. Yayin da shi kuma Sarki Abdallah yake tafe atsakiyar su jikin sa sanye da wata azababbar alkyabba ruwan ƙwai mai matuƙar kyau, sai kansa da yake ɗaure da farin rawanin da yayi matuƙar ƙara futo da kwarjinin sa. Shi kansa hulla idanuwan sa yake acikin jama'a duk da gaba ɗaya fadawa da dogarai sun zagaye sa, dan yaga ta inda zai hango ɗan nasa mafi soyuwa aransa. Ahaka suka ƙarasa bakin ƙofa gaban wasu danƙara danƙaran dawakuna da suka gaji da jin Ado ajikin su. Tukun fadawan nan suka baza rigunan su suna masu sake rufe sarki tare da faɗin. "Bisa haikawa da alheri, bisa dafkawa, bisa maikawa." Basu dena faɗe ba har sai da suka tabbatar da ya hau kan dokin, tukun suka saki rigunan su ƴan lufudi kuma suka matso hannuwan su riƙe da bulalai suna masu buɗa hanya. Yayin da ta fannin Babban yaya shima ya haye saman nasa dokin tini suna masu yin gaba, kasancewar sai bayan sun huce tukun Sarki zai huce, sai dai kuma har lokacin bai fasa faman wurga idanuwan sa cikin mutane ba dan ya hango ƙanin nasa, amma sai dai har suka ƙarasa filin hawa aka fara wasa da dokuna baiga ko Al'amin ba balle har yasa ran zaiga Asad, hakan yasa ya ƙudurta aransa da zarar sun gama hawan nan zai huce wurin Gimbiya Fulani Mamyn su, domin su tattauna da ita akan shawarar da ya yanke akan Yarima Asad, danko ba ƙaramun ciwo sukeji ba acikin ransu na hallayar sa shi da mahaifiyar su. Ba'a tashi gama hawa ba sai gabannin magariba, tukun jama'a sukai ta watsewa kowa na komawa inda ya futo. Afannin Babban yaya shima yana sauka daga kan doki ya huce masallacin su na nan cikin Masarautar. Ko da aka idar da Sallah bai tsaya ko ina ba ya huce sashin mamyn su kai tsaye, domin yaje su tattauna akan yarce zasu ɓullowa Asad kamar yacce suke kanyi kullum. *JAHAR KAGUL, CIKIN MASARAUTAR FULDE.* Cikin tsantsar firgici da ruɗu Gimbiya Haddiyal ta ɗago kanta tana mai watsa manya manyan idanuwan ta da suka sake yowa waje akan fuskar Dadden tata. Tukun daga bisani ta fara ɗaga laɓɓanta tana mai girgiza kai, wasu irin hawaye na ɓallewa daga cikin idanuwan ta, yayin da ita kuma mahaifiyar tata ta janye idanuwan ta daga kan ta tana mai mayar dasu wurin Innahuro da take manne ajikin ta, ta fara shafa gashin kanta. Zumbur Gimbiya Haddiyal ta miƙe tsaye yarce kasan wacce aka tsikara, jikin ta na tsantsar rawa, banda ai'kin girgiza kai da ɗaga laɓɓa babu abun da take iyayi, sai idanuwa data kefa mahaifiyar tata dasu, tukun daga bisani ta juya da matuƙar sauri yarce kasan zata kifa aƙasa tana mai dosar hanyar ɗakin ta. Uhm! Mahaifiyar tata ta sauke ɗan gajeran numfashi tana mai bin bayan Gimbiya Haddiyal da idanuwa, tukun daga bisani ta taɓe baki tana mai girgiza kai, kana ta janye idanuwan ta daga kan hanyar tana mai ɗaukar inibin dake cike acikin ƙwarya wanda Innahuro keci ta fara ci itama. Cilla ƙafafuwan ta kawai take aduk inda ya samu ba tare da tana lura ba, sabo da tsantsar tashin hankalin da take ciki, ahaka har Allah yakai ta cikin ɗakin ta lafiya. Kai tsaye ta doshi gaban tanƙashe-shen mudubin da yake manne ajikin bango ɗakin, tana ƙarasawa gaban sa taja ta tsaya tana mai ɗora hannuwan ta akan sa ta dafa sa. Kallon kanta ta farayi acikin madubin tana cigaba da girgiza kai, kana har lokacin kuma hawaye basu bar tseren gudu ba daga cikin idanuwan ta, tukun daga bisani ta buɗe baki cikin kaushi tana mai faɗin. "Shin me Baffah ke nufi ne da zuwan Jauro (Yarima) Masarautar Yamma? Shin ina zan kai shi Gaɗaɗo am kuma? Inyi ya ya da soyayyar sa dake cunkushe aƙasan zuciya da ruhina? Inaaa hakan bazai taɓa yuwuwa ba wallahi, babu wani ɗa namijin da yakai in kulasa balle har ya zamto miji gareni bayan Giɗaɗo am! Ni Gimbiya Haddiya an halicceni ne domin Giɗaɗo am kaɗai kamar yacce aka hallice sa domin ni, dan haka babu tayarce za'ai in bari wani mahaluƙi ya zamto shamaki atsakanin mu, Wallahi! Wallahi Jauro'n Yamma kayi kaɗan na zamto taka, domin ko fatar ka bazata taɓa jure zafin bulalar shaɗin aure na ba, darajarkar bata kai ka mallaki ko takalmin ƙafata ba balle har na zamto mallakin ka, zanyi amfani da ƙarfin ikona wurin ganin na lalata gaba ɗaya shirin ku akaina." Ta ƙarasa maganar da ƙaraji tana mai kaiwa bango duka, tukun ta juya tana mai yin taku biyu daga inda take, kana ta sake ja ta tsaya cak awuri ɗaya, tukun ta sake ɗaga laɓɓa cikin kaushi tana mai faɗin. "Kai da kanka zaka koma kace musu banyi ba Jauron Yamma, domin ko bazan taɓa yimaka ba kamar yacce ba ayini dan nayiwa wani ba bayan Giɗaɗo am." Ta ƙarasa maganar tana mai fara ɗaga ƙafafuwan ta ta doshi bakin gadon ta. Zama tayi akai tana mai buga uban tagumi da hannu bibbiyu, tare da kafe bangon dake kallon ta da idanuwa. *JAHAR WASAI* Anan cikin Masarautar wasai kuwa baki ɗauke da sallama Babban yaya ya tura kansa cikin bedroom ɗin Mamy'n tasu, kasancewar bai sameta afallo ba shiyasa yayo nan ciki. Zaune ya hangeta akan darduma tafukan hannayen ta ɗage asama tana addu'a, da alamun yanzu ta idar da sallah itama. Wucewa yayi can ciki yana mai ƙarasawa bakin gado ya zauna tare da ɗaga tafukana hannayen sa shima suka ƙarasa addu'ar tare. Ɗago kai tayi tana mai kai idanuwan ta inda yake. Dasauri ya sakko ƙasa yana mai ƙarasowa kusa da ita ya zauna, tare da tanƙwashe ƙafafuwan sa akan haɗɗaɗen kafet ɗin da yake shimfiɗe aƙasan ɗakin, tukun daga bisani ya buɗe baki cikin tsantsar ladabi da biyayya yana mai faɗin. "Barka da hutawa, tare da fatan kina yini lafiya Mamy na." Murmushin ta wanda ya zamto kalar nasa dana Asad kamar yacce kamannin su suka zamto ɗaya sak ta sakar masa tana mai kallon sa, tukun daga bisani ta buɗe baki tana mai faɗin. "Alhamdulillah, fatan kuma duka kuna lafiya." "Kowa lafiya ƙalau wallahi mamy na." Ya faɗa yana mai sakar mata murmushi, yayin da ita kuma ta sake gyara zama tana mai ƙara fuskantar sa, tukun daga bisani ta buɗe baki tana mai faɗin. "Ya kuma taro ya tashi." "Alhmdulillah Mamy." Ya faɗa shima yana mai sake fuskantar ta. Gyaran murya tayi, tukun daga bisani ta buɗe baki tana mai faɗin. "To ni dai nasihar da zan maka amatsayina na mahaifiyar ka kan wannan jagorancin da aka baka itace. Atakaice shidai shugabanci ba wani abu bane face wani babban nauyi da Allah yake ɗorawa mutum, dan haka nake shawartar ka da ka zamto adalin shugaba wanda al'umnar sa zasuyi alfahari da shi, kayi koyi da shugabanci irin wanda fiyayyen halitta Annabi Muhammad Sallalahu Alaihi Wassallam yay. Domin ko ita shugaba garkuwace da ake yaƙi abayan ta, ake kariya da ita, dan haka idan shugaba yayi umarni da tsoron Allah yayi adailci to yana da lada, in kuwa ya ai'kata saɓanin haka to wannan laifi yana kansa. Bukharine ya rawaito. Hakanan kuma wajibi ne shugaba ya zama mai adalci tsakanin sa da talakawan sa, sabo da adalci shine tushen rayuwa, kuma sai da adalci ne al'amura ke dai-daita duniya da lahira. Sannan kuma Sheikhul Islam Ibni taimiyya yana cewa. Al'amuran mutane na duniya suna dai-daita ne da adalci da yake haɗe da nau'ika na zalunci, fiye da yadda al'amura zasu miƙe da zalunci acikin haƙƙoƙi, ko da kuwa basuyi tarayya azunubi ba, dan haka akace Allah yana tsayar da daular mai adalci koda kuwa musulma ce, hakanan akace duniya tana dawwama da adalci da kafirci, amma bata dawwama da zalunci da musulunci." Ta faɗa idanuwan ta akan sa, yayin da shi kuma babban yaya ya durƙusar da kansa ƙasa yana mai sauraran ta jikin sa na tsantsar ƙara yin sanyi, kana kuma yana godiya ga Allah da ya azurtasa da uwa tagari acikin zuciyar sa. Zama ta sake gyarawa tana mai ƙara fuskantar sa, tukun ta ƙara gyara zaman hijab ɗin dake sanye ajikin ta, sannan ta ɗora da cewa. "Manzon Allah Sallalahu Alaihi Wassallam yana cewa. Babu wani zunubi daya fi sanya azaba da wuri fiye da zalunci da yanke zumunci. Azzalumi ana bugeshi aduniya koda kuwa an masa gafara da rahama alahira, sabo da adalci tsarine acikin komai da komai, idan aka tsayar da al'amarin duniya akan adalci sai komai ya tsaya, koda kuwa ma'abocin duniyar nan bashi da rabo alahira, idan kuwa ba atsayar da al'amuran duniya akan adalci ba, to lamarin bazai tsaya ba, koda kuwa ma'abocin sa yana da imani da zai ishesa alahira. (Duba maj'mu'ul fatawa 28/146). Hakanan shugaba ya zama ƙarfi wajen zartar da abun da yake gaskiya ne acikin talakawan sa, ya nisanci zalunci, da ƙarya, da cin amana, da ha'inci da sauran munanan halaye. Wannan sune kaɗan daga cikin haƙƙoƙin talakawa akan shuwagabannin su, dan haka wajibi ne akan shuwagabanni su kiyaye waƴan nan haƙƙoƙin, sabo da al'amuran talakawan su amana ce awuyan su, kuma Allah zai tambaye su abun da ya basu kiwo daga bayin sa." Ta ƙarashe maganar tana mai sa hannu ta zame hijab ɗin dake sanye ajikin ta, tukun ta miƙe daga kan prayer mat ɗin da take kai tana mai komawa bakin gado ta zauna. "Nagode sosai Mamy na, Allah ya saka da alkhairi, rabbi yayi mana jagora cikin duka harkokin mu albarkacin fiyayyen halitta." Babban yaya ya faɗa yana mai miƙewa ya koma kan wata mayyar royal chair da take kafe daga jikin bango. "Amin ya rabbi." Mahaifiyar tasa ta faɗa tana kallon sa, tukun daga biani ta ɗora da faɗin. "Ina ƙanin naka yake ne, rabon da muhaɗu tun safe yau, ɗazu kuma Baby take cemun yace mata ta kirani tazo bata saman ba?" "Uhm! Mamy ai Asad ɗin naki ne sai dai addu'a kawai, amma yaron nan kullum girma yake ƙarawa amaimakon yayi hankali sai dai wani sabon salon shirmen da yake ƙara futowa da shi, dama yanzu haka ma akan batun sa nazo wurin ki." Babban Yaya ya faɗa yana mai kallon mahaifiyar tasa. Yayin da ita kuma ta girgiza kai tana mai lumshe idanuwan ta ba tare da tace komai ba, sai dai kuma kallo ɗaya kawai zaka mata kasan akwai damuwa aƙasan ranta, sabo da yarce yanayin fuskar ta ya nuna, tukun daga bisani ta buɗe idanuwan nata akan fuskar Ciroma tana mai faɗin. "To yanzu kai me kazo da shi akan batun kenan?" Wai Mamy ace Asad ko bakin fada bai jeba balle harya hau doki ayi hawa da shi, kai ataƙaice ma duka baya cikin gidan nan ya fuce ya tafi yawon sa. "Cewar Babban Yaya" ransa duk ba daɗi. Murmushi mahaifiyar tasu ta saki, wanda kana ganin sa basai anfaɗa maka ba zaka san na yaƙe ne, tukun daga bisani ta buɗe baki idanuwan ta akan Ciroma tana mai faɗin. "Kaima fa abun da ka riga kasani ne, babu tayarce za'ayi ZAKI yaje fada, tunda yasan irin mutanen da zai tarar aciki da kuma kalar shigar da kowa keyi wacce shi yake ganin ƙauyanci ce agaresa idan yayi ta, sannan kuma shi kansa wurin hawan kasan ba zaije saba duk yarce yake da maitar doki, ko da ko bai bar cikin gidan nan ba, tunda yasan ana kaɗa-kaɗe da bushe-bushen da bai son jin kalar su." Ta faɗa tana mai cigaba da sakin murmushin yaƙe, tukun daga bisani ta tsayar da murmushin da take yin tana mai ɗorawa da faɗin. "Akullm akuma kowane daren duniya sai na kai goshina ƙasa ina roƙon Allah ya canza masa dabi'un sa, ya dawo mutumin ƙwairai kamar kowa, amma shiru kake ji har yanzu." Ta ƙarasa maganar jikin ta na yin sanyi. "Ki kwantar da hankalin ki Mamy na, akwai mafuta da nazo mana da ita, wacce sheikh Ahmad ya samar mun da ita, sannan kuma ina tinanin insha Allah idan har nayi aiki da ita komai zai zo ƙarshe bi'izinillah." Babban Yaya ya faɗa yana mai gyara zaman sa akan kujerar da yake kai. Cikin sauri mahaifiyar tasa ta buɗe baki tana mai faɗin. "Shin wata kalar mafuta ce kenan?" "Ashekaranjiya da muka zauna karatu da sheikh Ahmad, bayan mun gama sai nake kora masa bayanai akan hallayar yaron nan, to shine ya cemun tunda har ni kaɗai ne wanda yake ganin girma na, sannan kuma duk abun da nace yayi yake yi baya iya ƙetarewa, kana kuma akwai tsantsar shaƙuwa da ƙaunar juna tsakanin mu, to kamata yay ya zamto koda yaushe yana gefe na, ma'ana dai in janyo sa ajiki na ya zamto duk inda zani in dinga jansa yana rakani, haka kuma aduk lokacin da na kasance ina cikin gida to in zamto ina kusa da shi koda kuwa awurin cin abinci ne, hakan shine zai sa ya rage yin wasu abubuwan da yake yi, sannan kuma zan samu damar ɗora sa akan hanyar da nake son yabi cikin sauƙi. To bayan na dawo gida da na zauna na sake nazari akan magan-ganun sa, sai naga tabbas hakan itace mafita, dan haka shiyasa tun jiya na yanke hukuncin cewar zan fara aikina na farko amatsayina na Ciroman gida tare da shi, wato jibi zan jasa mutafi JAHAR KAGUL, CIKIN MASARAUTAR FULƊE domin siyo shanun da za'ayi layya dasu acikin gida, kasancewar an aika musu da saƙon zuwan mu tun awancan satin daya huce." Babban yaya ya faɗa yana kallon mahaifiyar tasa. "Masha Allah, tabbas hakan yayi sosai, sai dai kawai muyi fatan Allah ya shige mana gaba, dan nima na goyi bayan hakan ɗari bisa ɗari." Ta fada tana mai jin daɗi aranta, sai kace wacce take da tabbacin idan sukayi hakan zasuyi nasara. *WASHE GARI.* *JAHAR KAGUL MASARAUTAR FULƊE.* Yau tun safe aketa shirya -shiryan tarbar Yariman Masarautar Yamma acikin masarautar fulɗe. Yayin da ita uwar gayya wacce za'ayi zuwan domin ta ta kwana cikin tsantsar ƙunci da damuwa. Zaune take agefen gado sanye da wasu haɗaɗɗun kayan fulani koraye irin na sarakai ajikin ta. Yayin da gefe da gefen ta kuma wasu Ƴammatan bayi suka kasance zaune awurin suna masu aikin gyara mata mayawaicin baƙin gashin dake ɗauke akan ta. Kallo ɗaya zaka mata kasan ko kaɗan bata farin ciki, sabo da yarce fuskar ta take amatuƙar ɗaure, babu alamun annuri tattare da ita, sai dai kuma duk da ɗaure fuskar da tai hakan bai hana tsantsar kyawun da Allah yayi ta da shi ba bayanna. Sanye ƙafafuwan ta suke cikin wani plat shoe mai tsanin taushi da kyawu, yayin da hannuwan ta kuma suke sanye da wasu azababbun jajayen awar-waraye na fulani amma sarakai, sai wuyan ta da yake damɓare da wata haɗaɗɗiyar sarƙar duwatsu ja zaune akan sa. Gida ukku suka kasa gashin kan nata, tukun ko wacce ta kama kaso ɗaya na gefe da gefe suna masu kitse sa sukayi duk baya da su, sannan suka sake raba na tsakiyar gida biyu shima, kana ko wacce ta sake kama kaso ɗaya suna masu kitse sa shi kuma yayi duk gaba, tayarce jelolin suka biyo takan goshin ta, tukun suka sauka akan kafaɗun ta suna masu hucewa har kan cikin ta. Ɗauke duk abubuwan da sukayi amfani dasu wurin yin kitson sukayi, tukun suka koma gefe guda suna masu tsayawa cirko -cirko tare da durƙusar da kawunan su ƙasa. Sai da sukayi tsayuwar kimanin mintina goma ba tare da ta ɗaga kai takalli ɗaya daga cikin su ba, tukun daga bisani ta ɗaga laɓɓa tana mai faɗin. "Kuna iya zuwa ku shirya kafin su ƙaraso." Acan cikin. Amma da yake hankulan su da nutsuwar su duka suna gare ta shiyasa tana faɗin haka suka ɗan durƙusa atare suna masu faɗin. "Mun barki lafiya Gimbiya." Sannan suka juya suna masu fucewa daga cikin ɗakin nata. Acan ɓangaren Lamiɗo mahaifin Gimbiya Haddiyal kuwa, shi da kansa ya sanya aka gyara wurin da ɗiyar tasa tare da sirikin sa zasu zauna idan ya iso, sannan yasa aka kai shimfiɗa ta al'farma da suke da ita acikin masarautar aka shimfiɗa, kana ya cewa Mahafiyar Gimbiya Haddiyal ta tura ƴan matan da zasu je su shirya ta aje afara shirya ta, ba dan komai ba kuma yake haka sai dan kasancewar su Aminai da shi da Lamidon Yamma. Misalin ƙarfe shaɗaya na safe dai dai wata baiwa dake sanye da kayan fulani ta shigo ɗakin Gimbiya Haddiyal bakin ta ɗauke da sallama. Amsa mata sallamar tayi daga kan gadon da take zaune ba tare da ta ɗago ta kalle ta ba. "Allah ya taimakeki yake Gimbiyar Masarautar Fulɗe, Ance in sanar dake Jauro'n Yamma ya ƙaraso." Baiwar ta faɗa kanta duƙe aƙasa. Yayin da ita kuma Gimbiya Haddiyal taji wata irin faɗuwar gaba ta ziyarce ta, tukun daga bisani ta lumshe dara-daran idanuwan ta ba tare da tace komai ba, kana ta buɗe su akan baiwar nan dake tsaye agaban ta tana mai kallon fuskar ta, kafin daga bisani kuma ta miƙe tsaye tana mai tsayawa akan ƙafafuwan ta. Sosai tayi bala'in kyau cikin shigar dake sanye jikin ta. Dasauri ƴammatan bayin da suke tsai-tsaiye agefen ta suka matso kusa da ita suna masu sa hannu suka ɗauki wata haɗaɗɗiyar jar alkyabba irin ta fulani mai adon duwatsu ajikin ta suna masu ɗora mata ita akan jikin ta, tukun suka koma daga bayan ta suna masu tsayawa, gaba ɗayan su suma sanye suke da kayan fulani na mata babu ko takalmi aƙafafuwan su. Yayin da ita kuma wannan ɗayar data kawo rahoto tai saurin juyawa tana mai fucewa daga cikin ɗakin. Cikin takun ta na isa da izza ta fara ɗaga ƙafafuwan ta tana mai dosar bakin ƙofar ta, tukun su kuma ƴammatan bayin nan suka rufa mata baya suna masu ɗora ƙafafuwan su aduk inda ta cire nata, ahaka har suka ƙarasa tanƙashe-shen falon nan. Kishingiɗe ta hangi mahaifiyar ta aƙasa kan tum-tum ana ta aikin mammatsa mata ƙafafuwa. Direct ta doshi inda take fuskar nan tata babu alamun annuri bare far'ah. "Barka da wutawa Dadde am." Ta faɗa tana mai durƙusawa aƙasa bayan sun gama gaisawa da matar dake yiwa mahaifiyar tata tausa kanta duƙe aƙasa. "Yawwa Bello ta, fatan kin fito lafiya." Mahaifiyar tata ta faɗa tana mai kallon ta fuskarta ɗauke da murmushi, domin kuwa ba Lamiɗo kaɗai kesan haɗin nan da za'ayi ba hatta ita tana so, sabo da aganin ta hakan shine zai sanya ɗiyar tata ta haƙura da soyayyar aljanin dake zuwar mata amafarki acewar su. Jijjiga kai kawai Gimbiya Haddiyal tayi ba tare da tace komai ba, tukun daga bisani ta miƙe tsaye daga durƙushen da take tana mai faɗin. "To Dadde ni zan huce." "Tom shikenan ki tabbatar kinyi abun da ya dace, kar ki kuskura wani labari mara daɗin ji yazo wurin mu bayan tafiyar sa." Mahaifiyar tata ta faɗa tana kallon ta. Jijjiga kai kawai tayi tana mai jin ranta na mata wani irin suya da raɗaɗi, tukun ta juya tana mai dosar hanyar da zata sadata da waje Ƴammatan bayin nan na biye da ita abaya. Acan kuwa ɓangaren Jauron Yamma ƙarfe shaɗaya dai dai suka ƙaraso cikin masarautar Fulɗe, da shi da mutanen sa akan dawakan su da sukaji uban Ado. Koda suka iso kai tsaye aka zarce dasu zuwa fada suka kaiwa Lamiɗo gaisuwa, tukun daga bisani ya bada umarnin ayiwa Yarima jagora zuwa wurin da zasu haɗu da Gimbiya Haddiyal, sa'annan ya tura jakadiyar sa kan taje ta sanya afaɗawa Gimbiya Haddiyal cewar Yarima ya ƙaraso. Dogo ne sosai mai ƙirar ƙarafan mutane, sanye yake da kayan fulani na maza, amma irin nasu na sarauta waƴan da sukayi matuƙar amsar jikin sa. Yana da kyawun sa dai dai misali shima, yana da hasken fata duk da dai bai kasance irin farin nan tas ba. Yayin da fuskar sa kuma ta kasance aɗaure babu alamun annuri tattare da ita. Tafe suke shi asaman doki, su kuma jama'ar sa da kuma waƴan da aka sa sukai sa wurin da zasu gana da Gimbiya akan ƙafafuwan su. Wani tafkeken lambu mai cike da korayen ganyayyaki tare da ni'imtacciyar iska da inuwa acikin sa suka shiga. Direct suka doshi inda wata shimfiɗar fata mai matuƙar taushi da kyawu take, yayin da saman shimfiɗar kuma aka ajiye tum-tum tum-tum daga kowace kusurwa, sai daga kan shimfiɗar kuma gaba ɗaya jere take da kayan itatuwa acikin wasu ƴan kwandinan kaba masu tsananin kyau, waƴan da suka haɗa dangin su ayaba, lemo, inibi, tufa, kankana, da dai sauran su, sai akusa dasu kuma wani rantsetstsen kofin silba ne ruwan zuma da yayi matuƙar haɗuwa cike danƙam da madarar shanu mai matuƙar dumi, ga kuma ɗan ƙaramin kofi na tsiyaya akife akan plate ɗin silban da babban yake akai, sai abu na gaba kuma da ya kasance dammamar fura da nono ɗauke acikin wata haɗaɗɗiyar ƙwaryar da aka sanya ludayin duma acikin ta, sai kuma fai-fain kaba da aka rufe ƙwaryar da shi, sai abu na karshe kuma da ya kasance naman kaji da ƴan shila banƙararru acikin wata ƙatuwar roba mai tsaninin kyau da ake yi mata murfi da fai-fai itama. Riƙe dokin nasa akayi tukun ya sauko akai. Kana wanda ya riƙe dokin yaja sa suna masu juyawa tare da sauran ƴan rakiyar duka suka bar wurin, yayin da shi kuma Yariman Yamma ya saɓule takaman fatar dake sanye aƙafafuwan sa, tukun ya hau kan shimfiɗar nan yana mai kishingiɗa akan tum-tum, kana ya ƙure hanyar da yake tsammanin tana nan zata ɓullo da idanuwa. Zaman sa baifi da minti goma ba Gimbiya Haddiyal da tawagar ta suka ɓullo wurin. Tunda suka bullo ya kafe ta da idanuwa daga nesa yana kallon ta bako ƙiftawa, wani irin kallo yake aika mata dashi tun daga nesa, wanda duk wanda ya gansa basai an faɗa masa ba zai san yayi nisa cikin kogin ƙaunar ta. Cak ta tsaya a'inda take daga ɗan nesa da shi ba tare da ta cigaba da takowa ba. Tsaye suma ƴammatan bayin nan sukayi abayan ta cak, tukun daga bisani ta ɗaga musu hannu ta sama ta baya ba tare da ta juya ta kalle su ba. "Afuto lafiya Gimbiya." Suka faɗa suna masu juyawa suka doshi hanyar da suka biyo. Ba ita ta cigaba da tafiya ba har sai da ta tabbatar da tabar jin motsin su tas, alamun sun bar cikin wurin, tukun ta fara ɗaga ƙafafuwan ta tana mai dosar kan shimfiɗar da Yariman Yamma yake kishingiɗe akai, idanuwan ta kafe ƙur akan fuskar sa kamar yacce shima ya kafe ta da nasa, sai dai ita kuma ba irin kallon da yake mata ba take masa, tana masa kallo ne na tsantsar -tsanar sa da take ji aranta tare da ƙin sa, ahaka har ta ƙarasa bakin shimfiɗar da yake kai. Lumshe idanuwan sa yayi yana mai sake gyara kishingiɗar sa yayi balance ransa face, domin kuwa sai yanzu data matso wurin sa ya ƙara tabbatarwa da kansa lallai ba ƙaramun dace yayi ba, muddin ya mallaki wannan babbar kadarar aduniya amatsayin abokiyar rayuwar sa. Tukun daga bisani ya sake wara idanuwan sa akan fuskar ta da take cunkushe tsaye agaban sa, kana ya buɗe baki cikin yin ƙasa da murya yana mai faɗin. "Barka da isowa Gimbiyar Jauron Yamma, Sarauniya kuma ga tsuntsaye da shanu na Masarautar Fulɗe." Ya faɗa fuskar sa ɗauke da annuri. Yayin da ita kuma taji saukar furucin sa na Gimbiyar Jauron Yamma da wani irin azabar raɗaɗi acikin ranta, tayarce har sai da ta rumtse idanuwan ta da ƙarfi tare da taune lower lips ɗin ta. Tukun daga bisani ta warasu akan fuskar sa kamar yacce shima yake kallon ta gaba ɗaya har sun fara canza launi suna yin ja. Sannan ta tuɓe takalman da suke sanye aƙafar ta tana mai dosar kan shimfiɗar da yake kishingiɗe akai, zuciyar ta na tsantsar turiri. Tsaye tayi agaban sa tana mai aika masa da wani irin matsiyacin kallo, tukun daga bisani ta ɗaga laɓɓan ta cikin kaushi, tana mai faɗin. "Shin wa...............✍ *HAK'IK'A INA GAB DA DAKATAWA GABA D'AYA MUDDIN BAZAKU DINGA YIN COMMENT BA.* 🐎 *BAƘAR MASARAUTA* 🐎 👑👑 🦋 🦅🕊🦆 🐍🎠🐄🏹 _*NA*_ UMAR FARUQ*D* *BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM* *PAGE 07* "Shin waya sanar da kai wannan tatsuniyar da har kake shelantawa duniya cewar ni ɗin takace?" Ta faɗa cikin kaushi tana mai kafesa da dara-daran idanuwan ta, tukun daga bisani ta ɗora da faɗin. "To idan ma mafarki kake ina son kayi gaggawar farkwa, domin kuwa ni ɗin nan daka gani an hallice ni ne domin mutum ɗaya, haka kuma na daɗe da zamtowa mallakin sa, dan haka ina mai shawartar ka akan kayi gaggawar komawa wurin waƴan da suka aiko ka zuwa gare ni kasanar musu da cewar banyi ba, domin ko bazan taɓa yi maka ba har abada, kamar yacce kaima bakai mun ba, kuma baka da abubuwan da zanyi tinanin zakayi mun ko agaba!" Ta ƙarsahe maganar ƙasa-ƙasa tana mai jifan sa da wani irin matsayacin kallo, tukun daga bisani ta juya tana mai sauka daga kan shmfiɗar, sannan ta sanya takalmam ta, tukun ta fara ɗaga ƙafafuwan ta tana mai dosar hanyar da ta biyo ba tare da ta tsaya jin ta bakin sa ba. Yayin da shi kuma Yariman Yamma lokaci ɗaya yana yin sa ya sauya, kana gaba ɗaya annurin dake kan fuskar sa ya ɓace ɓat, idanuwan sa kuma suka kaɗa sukai jajajir yana mai kallon ta, kafin daga bisani kuma ya buɗe baki cikin kaushi yana mai faɗin. "Shin waya baki izinin tafiya ne da har kika juya kika tafi?" Cak Gimbiya Haddiyal ta tsaya daga inda take, sabo da furucin sa da taji ya daki dodon kunenn ta da ƙarfi, rumtse idanuwan ta tayi daga inda take ba tare da ta juyo ba, haka kuma bata cigaba da tafiya ba, sai zallar turiri kawai da take jin ranta na mata, tana mai tinanin kalar amsar da zata basa idan ta juyo. Yayin da shi kuma ya miƙe daga kishingiɗen da yake yana mai zuwa ya sanya takalman sa, tukun ya fara ɗaga ƙafa cikin takun sa na isa yana mai dosar inda take. Direct ya huce bayan ta yana mai zagayawa ya tsaya daga gaban ta gab da ita, tukun ya ranƙwafo da kansa yana mai rage tsayin sa ya zamto fuskar sa ta dawo saitin tata fuskar, tayarce har suke jin dirar numfashin junan su. Kallon-kallo suka fara aikawa junan su da shi ba tare da wani daga cikin su yace tak ba, tukun daga bisani shi Yariman Yamma ya buɗe baki cikin kakkausar muryar sa yana mai faɗin. "Ke atinanin ki har akwai wani jarumin ne bayan ni aduk faɗin jahar nan da ƙetaren ta, ko ko azaton ki akwai wani mutum wanda zai iya jure raɗaɗin tsumagiya ta? Shin shi ɗin ɗan wace masarauta ne ma da farko?" Ya faɗa ƙasa-ƙasa tayarce ita kaɗai ce zata ji yana mai kafeta da idanuwan sa, kamar yacce itama ta kafesa da nata, tukun daga bisani ya saki wani shu'umin murmushin da yayi ai'nahin futo da kyawun sa, sannan ya ɗora da cewar. "Agaskiya nayi matuƙar jin daɗin sauraron wannan labarin daga bakin ki, domin ko ada ina tinanin bani da abokin karawa wanda zamu gwada ƙwanji tsakanin ni da shi wurin neman ki, amma sai gashi yau naji cewar akwai sa daga bakin ki, hakan kuwa ki sani ba ƙaramun farin ciki ya sanya ni ba, sai dai kuma ina son ki shaida masa cewar ni Yariman Yamma, tun farkon kafuwar ahalin mu ba'a taɓa yin wani wanda yay bugun shaɗi ba tare da yayi nasara ba, dan haka sai shima ya ƙara shiri akan wanda yake yi, domin kuwa ke ɗin tawace ni kaɗai, kuma an halkice kine domin n... "Dakata Malam!" Ta faɗa da ƙarfi tana mai ɗaga masa hannu sama, tukun ta buɗe baki tana mai sakin wani irin wuci tare da faɗin. "Kar ka kuskura ka ƙara gigin furta kalmar cewar ni ɗin takace muddin baso kake na datse harshen ka ba kafun kabar wurin nan, domin kuwa wannan kalmar mutum ɗaya ne kawai ya halatta ya faɗe ta aduk faɗin duniya, kuma wallahi wallahi ni ɗin tasa ce kamar yacce shi ɗin yake nawa, bayan shi kuma babu wani agefen sa." Ta ƙarasa maganar tana mai juyawa daniyyar tafiya. Caraf taji Yarima ya cafki yatsun hannuwan ta adai dai lokacin da ta ɗaga ƙafa danniyar yin gaba. Cak ta tsaya ai'nda take ba tare data juyo ba ranta na tsantsar ƙuna, yayin da shi kuma ya saki yatsun hannun nata yana mai sake komawa daga gaban ta. Ɗauke kai tayi daga kansa tana mai kallon gefe tare da sakin huci, domin kuwa aduk lokacin da zata kalli fuskar sa ji take tamkar ta shaƙesa ya mutu dan baƙin ciki. "Ya da jin haushi haka kuma Gimbiya ta, ko kuwa har kin sare ne tun yanzu sabo da kin san nine dana sara?" Ya faɗa yana mai jifan ta da murmushi, tukun ya sake ranƙwafawa dai dai saitin fuskar ta yana mai yin ƙasa-ƙasa da murya tare da faɗin. "Ki sani ina sonki, kuma akan sonki babu abun da bazan iya ai'katawa ba dan ganin na mallakeki, dan haka ina mai sake sanar miki da ki shaidawa shi wancan ɗin ya fara shiryawa, domin ko haɗuwa ta da tasa bazata taɓa yin kyau ba, nima kuma da zarar na koma gida zan sanarwa da Lamiɗon mu cewa na samu abokin karawa." Ya ƙarasa maganar yana mai matsawa gefe ya bata hanya. Sai lokacin ta ɗago kai tana mai jifan sa da wani irin matsiyacin kallo. Wata irin tsanar sa take ji aranta irin wacce bata taɓa yiwa wani mahaluki ita ba aduniya, sabo da ganin sa da take amatsayin barazana gare ta akan soyayyar ra da Giɗaɗon ta, tukun daga bisani ta janye idanuwan ta tana mai ɗaga ƙafafuwan ta tayi gaba ba tare da ta sake tanka masa ba. Amai-makon tayi hanyar da zata sadata da gida sai kawai ta doshi hanyar wurin da tsuntsayen ta suke ranta atsantsar ɓace. Yayin da shi kuma Yariman Yamma ya juya yana mai komawa kan shimfiɗar nan ya zauna zuciyar sa na tsantsar tururi, sabo da ganin irin tarbar da tayi masa amatsayin sa na wanda zai zamto miji gare ta. Taune lips ɗin sa na ƙasa yayi da ƙarfi yana mai girgiza kansa tare da rumtse idanuwan sa, tukun daga bisani ya buɗe su yana mai buɗe baki yace. "Tabbas ko kai wane ne sai na sanya ka kayi nadamar soyayyar da ka fara da wacce nake muradin aure, sai nasa kayi dana sanin-sanin ta amatsayin ƴa mace balle har kasota, domin ko wallahi wallahi Haddiyal tawace ni kaɗai!" Ya faɗa cikin kaushi yana mai sake rumtse idanuwan sa, zuciyar sa na tsantsar tururi da ƙuna. *ƘASAR MALIN, JAHAR KARFUZ, CIKIN BAƘAR MASARAUTA.* Sosai shirye shiryen bikin godiya ga abun bauta Gargabilu da za'ayi ajibi ya kan-kama da gasken gaske acikin baƙar masarauta. Gaba ɗaya an sake sabon fenti akowane wuri tare da sabon tambari acikin masarautar, yayin da ko wane bawa da baiwa suka kasance suna ta shiri kuma har yau suna kan shirywa. Acan filin biki ma bayi ne suke ta aikin share share da jera kujeru acikin sa. Yayin da wasu kuma suke ta faman wucewa da wasu mahaukatan iccina ɗauke akafaɗun su suna masu kai su wani fili su aje. Acan wurin su Bir kuwa zaune yake agaban Iyar Bayi ya tanƙwashe ƙafafuwan sa suna tattaunawa. Sake matsawa kusa da Bir Iyar Bayi tayi tana mai miƙa yatsun hannun ta ta riƙo nasa da su. Ɗago idanuwan sa yayi ya kalleta kamar yacce ita ɗin ma take kallon sa, tukun daga bisani ta buɗe baki tana mai faɗin. "Al'farma nake roƙo awurin ka Jarumi na, ina son gobe ka zamto yaro nitsats-tse kamar yacce sauran yara suke, kayi abun da yake agaban ka karka kuskura ka kalli ko inda Gimbiya take balle har kaje wurin ta kajawa kanka bala'i kaji." Uhm! "Iya ta kenan, to ni dama ai bawai ina zuwa wurin ta bane, itace dai take biyowa hanyar data kasance hanyar mu, ni kuma abu ɗaya dana sani shine banga abun da yake tattare da itaba wanda har zai firgita dan tazo wuri in gudu in ɓuya, wannan dalilin ne yasan ya aduk lokacin da tazo giftawa nake ƙara matsawa inda take domin naga ƙarshen ikon ta." Bir ya faɗa yana mai sakin murmushi idanuwan sa akan fuskar Iyar Bayi, yayin da ƙwaƙwalwar sa kuma ke hasko masa kyawun fuskar Gimbiya Tasmir tare da kyawun surar jikin ta. "To wa gari ya waya kuma, wane yake wahala bayan kai Jarumi?" Iyar Bayi ta faɗa tana mai cigaba da kallon sa, tukun ta daga bisani ta ɗora da faɗin. "Tun kafuwar tarihin BAƘAR MASARAUTA ba ataɓa yin zamanin da ɗan sarki ko sarki yake zuwa giftawa ta wuri ba, asamu wata hallita da ke kasancewa awurin ba tare da sun gudu ba bayan ƴan rakiyar su kawai sai akan ka Jarumi, shin kai ɗin me zai hana kazamto kamar sauran ƴan uwanka bayi ko domin lafiyar ka Jarumi, domin ko kasan akan wannan abun da kake ai'katawa tsaf har ranka kana iya rasawa acikin BAƘAR MASARAUTA." "Iya ta kenan, bazaki fahimci yarce nake ji bane kwata-kwata, sai dai kuma abun da zan faɗa miki shine, wallahi bazan iya nisantar ta ba, bazan iya jurewa jin sautin taba ba tare da na ɗaga ido na kalle ta ba." Bir ya faɗa yana mai kallon Iya, yayin da ita kuma Iya ta saki baki cikin firgici tana mai zaro idanuwa waje, tukun daga bisani ta fara ɗaga laɓɓa bakin ta na tsantsar rawa tana mai faɗin. "Shin kasan abun da kake faɗe kuwa Jarumi? Shin wai anya ma kana cikin hankalin kane Jarumi, to wai ma mekake nufi da bazaka iya jure jin sautin taba ba tare da ka ɗaga ido ka kalle ta ba?" Iyar bayi ta watso masa tambaya amatuƙar ruɗe tana mai futo da idanuwa waje. "Shiyasa tun farko nace miki bazaki fahimta ba Iya, amma ba komai kawai ki kwantar da hankalin ki akwai lokacin da bake kaɗai ba hatta da sauran mutanen dake cikin masarautar nan zaku fahimta." Ya faɗa yana mai lumshe idanuwan sa, tukun daga bisani ya wara su yana mai zame ƴan yatsun hannuwan sa daga cikin na Iyar Bayi da ta saki baki take aikin kallon sa, kana ya miƙe tsaye yana mai juyawa zai tafi. "Jarumi!" Iyar Bayi ta faɗa tana mai miƙewa tsaye itama. Cak Bir ya tsaya a'inda yake ba tare da ya juyo ba, yayin da ita kuma Iya ta fara ɗaga ƙafafuwan ta tana mai nufar inda yake. Gaban sa ta ƙarasa ta tsaya tana mai kallon fuskar sa. Lumshe idanuwan sa yayi agaban Iya ba tare da yace komai ba, domin ko yasan duk abun da zata faɗa masa ayanzu bama fahimta zai ba. "Na roƙe ka Jarumi badan ni ba, na roƙe da abun bauta Gargabilu ka futa daga harkar Gimbiya Tasmir, domin ko tsaf ana iya fille kanka muddin irin wannan furucin da kayi ayanzu zai cigaba da futa daga cikin bakin ka acikin BAƘAR MASARAUTA." Hmmmm! "Ki kwantar da hankalin ki Iya ta, ni da kaina na faɗa miki babu damuwa, sannan kuma babu abun da zai faru." "To idan har hakane da gaske ina son yanzu kamun al'ƙwarin babu abun da zai haɗaka da Gimbiya Tasmir gobe." Iya ta faɗa tana kallon sa. "To ai dama Iya ba daga ni bane matsalar, tambaya ce kawai take mun akan rayuwar ta ni kuma nake yarce naso da ita ta hakan, wannan fa shine kawai abun da ke faruwa." "To amma mai zai hana ka bata amsar tambayar da taimakan idan ka sani ko domin hutun ka?" "Iya kenan, shiyasa tun farko nace miki bazaki fahimta ba, amma ba komai yanzu dai na miki al'ƙwarin bazan ko kalli inda take ba gobe balle har wani abu ya shiga tsakanin mu Iya ta." Ya faɗa yana mai juayawa ya cigaba da tafiyar sa hankali kwance, yayin da ita kuma Iya ta juya tana mai komawa ta zauna tare da buga uban tagumi da hannu bibbiyu. Acan ɓangaren Gimbiya Tasmir kuwa sosai ake shirya ta tun yau, wani irin gyara ake yiwa gashin kanta, yayin da ƙafafuwam ta da hannuwan ta kuma aka ƙunshe su da ƙunshi irin na jan lalle da yay tsananin yi mata kyau. Zaune take akan wata kujerar ƙarfe mai azabar kyau ana mata gyaran gashi. Sosai ta ƙagara ranar gobe tazo, domin kuwa gobe ne take ganin ranar da zata wuce duk baƙin cikin da wancan ƙas-ƙantaccen bawan ya ƙunsa mata cikin sauƙi! *ƘASAR HAUSA JAHAR WASAI, CIKIN MASARAUTAR WASAI.* Misalin ƙarfe goma na safe dai dai Babban yaya ya tura kansa cikin ɗakin Asad bakin sa ɗauke da sallama. Kwance ya hange sa akan gado gaba ɗaya ya ƙudun dune jikin sa da eskimo, sai fuskar sa kawai da ya bari awaje yana shara-rar bacci. Kallon haɗaɗɗen agogon bangon da yake manne ajikin bangon ɗakin Babban yaya yayi, sabo da ganin da yay har yanzu Asad bai tashi ba. Girgiza kai yayi bayan ya janye idanuwan sa daga kan agogon, tukun ya cigaba da takawa yana mai dosar bakin bed ɗin. Wuri ya samu daga gefen gadon ya zauna, tukun yakai tafin hannun sa zuwa jikin Yarima Asad yana mai ɗan bubbugasa, bakin sa na furta kalmar. "Kai Asad! Asad!! Asa..." "Wai kai dallacan me yasa mugun jarababben mutum ne kai!" Yarima Asad ya faɗa aharzuƙe yana mai buɗe idanuwan sa tare da miƙewa zaune. Ƙam ya tsaya ayarce yake yana mai zaro idanuwa tare da buɗe baki, sabo da fuskar da yay araba da ita wacce ko kaɗan bai kawo cewar itan zai gani ba, kafin daga bisani kuma ya fara ɗan sosa ƙeya yana mai sakin yaƙe tare da faɗin. "Ashe Babban yaya nane ban sani ba." Uhm! Babban yaya ya sauke ɗan gajeren numfashi yana mai kafesa da idanuwa. Sake sosa ƙeya yayi, sabo da yarce yaga yaƙi ya ɗauke ido daga kan sa, tukun daga bisani yace. "Kayi haƙuri Yaya na wallah na zata wancan masifaffen al'amin ɗin ne yazo, shiyasa kaji na faɗi haka." Taɓe baki babbayn yaya yayi ba tare da yace komai ba, tukun daga bisani ya buɗe baki yana mai faɗin. "Ina fatan dai kayi sallah, ba wai sai yanzu ka tashi ba ko?" "Haba dai ai acikin masallaci nai sallah ma Babban Yaya." Asad ya faɗa yana mai gyara zaman sa, tukun daga bisani ya ɗora da faɗin. "Ina kwana Yaya na." "Alhamdulillah." Babban Yaya ya faɗa yana mai miƙewa tsaye, tukun ya sake fuskantar ƙanin nasa yana mai faɗin. "Dama zuwa nai na sanar maka ka kasance cikin shiri, gobe misalin ƙarfe tara na safe zakamun rakiya zuwa MASARAUTAR FULƊE ta cikin JAHAR KAGUL." "Amma Yaya masarautar fulɗe?" Yarima Asad ya faɗa yana mai sosa kai, kana far'ar kan fuskar sa na gushewa, tukun daga bisani ya ɗora da faɗin. "Da kuma akawai wani wuri da zamuje gobe ni da Al'amin fa Yaya." "Sai ku ɗaga taku tafiyar zuwa jibi idan mun dawo, domin kuwa wannan tare na shirya mana ita ku duka biyun, kuma har mai martaba ma yasan da shirin." "Kuma shima Abban ya yadda atafi dani?" Yarima Asad ya faɗa yana mai ɗan zaro idanuwa, sabo da sanin mahaifin nasa da yay baya taɓa yanke masa hukunci sai ya fara tambayar sa yaji yana son abun ko ko, badan komai ba kuwa sai dan kawai tsananin ƙaunar da yake mai, wanda hakan yana ɗaya daga cikin abubuwan da sukayi sanadin ƙara lalata sa. "Kai Asad wannan fa umarni ne nake baka ba shawara ba da har kake shirin cika ni da tambayoyi, dan haka katabbatar gobe kun shirya da wuri daga kai har Al'amin ɗin tun kafin na futo." Babban Yaya ya faɗa yana mai ɗan ɗaure fuska, sabo da ganin da yay sakin fuskar tasa na shirin sanyawa yace bazai bisa ba, domin ko ya riga daya sani muddin yaje ya samu mai martaba ya faɗa masa baya son zuwa to shikenan fa zuwan ya fasaya sa shi. "Tom shikenan Allah ya kaimu Yaya na." Yarima Asad ya faɗa badan ransa yaso ba. Yayin da shi kuma Babban Yaya ya juya yana mai dosar waje bakin sa na furta cewar. Katabbatar kuma ka futo kayi break, sannan kaje ka nagaisar da Mamy yanzu." "Oh shirt!" Yarima Asad ya faɗa yana mai dukan fillow alokacin da ya tabbatar da Yayan nasa ya futa, tukun daga bisani ya ɗora da faɗin. "Aiko wallahi babu wanda ya isa yasan ya ni nasa blanket ajiki sai dai afasa zuwan dani." Tukun yasa hannu yana mai yaye eskimon dake jikin sa zuwa gefe, sannan ya zuro dogayen fararen ƙafafuwan sa da suke lulluɓe da kwantaccen baƙin gashi akan su zuwa ƙasa. Babu komai a jikin sa sai ɗan ƙaramin boxer da ya tsaya masa asaman guiwoyin sa. Janyo takalman dake ajiye agafen gadon yayi yana mai zura kafafuwan sa acikin su, tukun ya miƙe tsaye duka yana mai dosar hanyar toilet cikin takun sa wanda shi kaɗai ke zautar da Ƴammatan dake binsa. *GIDAN GWAMNAN JAHAR WASAI.* Tunda Billy ta baro Asadullah palace har kawo yau bata bar ƙunci ba tare da jin takaicin abun da Yarima Asad yayi mata. Sanye take cikin engilsh wear na black ɗin wando jeans da yayi matuƙar kama jikin ta ƙam-ƙam, sai ƴar ƙaramar jar riga mai ɗan guntun hannu da take sanye ajikin ta wacce ta zamto kusan da ita da babu duk ɗaya, domin kuwa bata hana komai bayyana ba na daga surar jikin ta. Yayin da kanta kuma yake ɗauke da farin gashin atarch ta tufkesa, sai wani uban hill shoe da yake sanye aƙafar ta tana mai sakkowa daga kan stairs. Direct ta doshi dining area ɗin da mahaifin ta da kuma mahaifiyar ta suke zaune akan kujeru, da alamun ita ɗin suke jira ta ƙaraso dama. "Morning Dad! Morning Mom!" Ta faɗa tana mai jan kujera ɗaya sannan ta zauna akai. "Morning daughter, fatan kin tashi lafiya." Mom ɗin tata ta faɗa tana mai bubbuɗe kulolin da suke agaban ta waƴan da suke ɗauke da kala-kalan abinci cikin su danniyar tayi serving ɗin su. Yayin da shi kuma Dad ɗin nata ya bita da idanuwa kawai ba tare da ya amsa gaisuwar da ta masa ba. Mai da idanuwan ta tayi kan wayar ta dake riƙe ahannun ta tana mai fara shafata. "Dear meke damun daughter ne, gaba ɗaya tun jiya naga duka yanayin ta ya sauya, kwata-kwata bata walwala kamar yacce ta saba, shin meke faruwa ne mara daɗi da bansan da shi ba?" Mahaifin nata ya faɗa yana mai kallon mahaifiyar tata alamun ita ɗin yake tambaya ba ƴar ba. Uhm! Ta sauke ɗan gajeren numfashi, tukun daga bisani ta buɗe baki tana mai faɗin. "To gatanan dai, sai dai yanzu kaima ka ɗora daga inda na tsaya, domin kuwa tun jiya data fuce daga gidan nan ita kaɗai ba tare da guard's ba ta dawo gaba ɗaya abirkice, kuma babu kalar tambayar da ban mata ba akan ta faɗamun abun da ke faruwa amma tace mun wai babu, shi yasa na rabu da ita da zummar yau idan kai ka tambaye ta ta faɗa maka muji." Mom ɗin tata ta faɗa tana mai kallon sa. "Subhanallahi, wai dama ba na hanaki futa bane ke kaɗai daughter, shin mene ne ma yafaru ajiyan, wane ya taɓaki kuma mai yay miki, sannan waye ubansa afaɗin Jahar Wasai?" Dad ɗin nata ya faɗa ahargitse yana mai kallon ta. Ajiye wayar dake ɗauke ahannun ta tayi akan table ɗin dake gaban ta tana mai shash-shake fuska ba tare da tace komai ba." "Kwantar da hankalin ki daughter ki yimun bayanin damuwar ki, ni kuma na miki al'ƙawarin muddin bata ƙarfi na ba zan yaye miki ita ayau yau ɗin nan." Ya faɗa yana mai miƙa hannu ya riƙo tafukan hannayen ta cikin nasa. "Yarima Asad ne Dady!" "Yayi miki me? Ba dai ya sake wulaƙanta ki bane kamar yarce kika faɗamun ya miki a kwanaki ba ko?" "Ai da Dady da kalar na kwanaki ne ma dako sani ba zakuyi ba, domin ko shi ba komai bane akan wanda yamun jiya." "Dukan ki yay ko ko zagin ki yay ne?" Mahaifin nata ya faɗa da ƙarfi yana mai miƙewa tsaye jijiyoyin kansa na futowa raɗa-raɗa akan goshin sa. "Kusan hakan Dad, domin kuwa har hankaɗe ni yay na faɗa cikin swimming pool, dan bada ban Allah yasa na iya ruwa ba da shikenan sai dai akawo muku gawata!" Ta faɗa tana mai matso ƙwalla daga cikin idanuwan ta. "Ina!!! Ai ko wallahi sai yayi nadamar abun da ya ai'kata, zanje in samu uban sa ayau yau basai gobe ba domin ajasa masa kunn... "A'a Dad ba haka nake so ayi ba." Ta katse baban nata da faɗin haka ba tare da ta bari yakai ƙarshen maganar saba. "Kamar ya ba haka kike so ayi ba daughter, ko ko kina nufin kice mun na barsa ne awannan karan nan gaba kuma ya illatamun ke yacuce ni, shin shi agidan ubanwa aka faɗa masa haka ake soyayya, ko kuwa haka yaga ubansa nawa uwarsa tsawa da duka, to wallahi daga yau anyi an gama kema, dan ke kanki bazan saurare ki ba ballan tana har ki sanyani na yafe masa." "Nima bawai ina nufin ayafe masa bane Dad." Ta faɗa tana mai kallon mahaifin nata. "To ya kike so amasa ne daughter?" Ya faɗa shima yana mai komawa ya zauan akan kujerar da ya tashi, yayin da ita kuma mahaifiyar tata tai shiru ba tare da tace komai ba, sai abincin ta da take ci kawai tana kallon su. "Wani shegen murmushi Billy ta saki tana mai ɗan tane lower lips ɗin ta, tukun daga bisani ta buɗe baki bayan ta miƙa hannu ta riƙo hannun mahaifin nata cikin nata tana mai faɗin. "S................✍ 🐎 *BAƘAR MASARAUTA* 🐎 👑👑 🦋 🦅🕊🦆 🐍🎠🐄🏹 _*NA*_ UMAR FARUQ*D* *BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM* *FREE PAGE 08* "So nake abi masa ta hanyar da bai taɓa zato ba Dad, ma'ana kawai ka samu iyayen sa kayi musu magana akan auren mu, nasan idan akayi hakan dole ya dena mun hulaƙacin da yake yi mun, kamar yacce nasan babu tayarce za'ai mahaifin sa yaƙi yin komai kace yayi." Ta faɗa tana mai kallin baban nata, yayin da shi kuma yayi shiru ba tare da yace komai ba, sai kansa da ya ɗaga sama yana mai kallon haɗaɗɗen rufun dake cikin ɗakin, tukun daga bisani ya sauke kan nasa ƙasa yana mai watsa ƙwayar idanuwan sa akan fuskar ƴar tasa, sannan ya buɗe baki yana mai faɗin. "Tabbas na gamsu da zancen ki ɗari bisa ɗari my Daughter, Dan haka ayau yau ɗin nan zan turawa mahafin nasa da saƙon zuwa na gare sa, domin kuwa agobe-goben nan nake son ayi duk mai yuhuwa, sannan kuma aƙarshe in faɗawa mahaifin sa aja masa kunne, sabo da ya kiyaye kar bayan anyi aure ya cigaba da abun da yake yi yanzu." Ya faɗa still idanuwan sa akan fuskar ƴar tasa. Yayin da ita kuma tayi wata irin miƙewa tana mai matawa kusa da shi, tukun tayi hugging ɗin sa daga zaunen da yake da matuƙar ƙarfi tana mai faɗin. "Yess my Dad, that's why akullum nake ƙara son ka, sabo da kaima kana son abun da nake so." Ta ƙarasa maganar da sakar masa kiss akan goshin sa, tukun ta juya aguje tana mai kama hanyar stair's cikin tsantsar farin ciki. Yayin da shi kuma mahaifin nata ya bita da idanuwa fuskar sa ɗauke da yalwataccen murmushi shima. *WASHEGARI* ƘASAR MALIN, JAHAR KARFUZ CIKIN BAƘAR MASARAUTA. Tun daga bakin tafkeken ruwan da yayiwa jahar karfuz ƙawanya mutum zai fahimci yau ɗin ana wani gagarumin taro ne acikin sa basai an faɗa masa ba, sabo da yarce jama'a na garuruwa daban- daban suke ta shigowa suna wucewa, wasu akan dokuna, yayin da wasu kuma suke akan ƙafafuwan su, ga kuma yarce akabi aka zagye gefen ruwan da yake abakin garin, wanda dole sai mutum ya tsallake sa kafin ya shiga jahar karfuz da wuta acikin kaskwaye tanaci bal-bal-bal! Acan cikin Baƙar Masarauta kuwa ban da sautin kiɗa babu abun da akeji yana tashi, domin kuwa tun cikin dare aka gama shirya filin biki tas, sannan kuma aka zageye sa da kayan kiɗa masu matuƙar sauti, tare da kaskwayen Huta waƴan da suke ɗauke da iccina suna ci acikin su. Yayin da daga can gefen filin kuma wani tamfatsetsen farin ruwa mai wucewa yake. Sosai aka ƙawata wurin da ado kala-kala, yayin da tambarin masarautar tasu kuma ya kasance manne akowane wuri, acan ƙarshen filin kuwa daga jikin bango wata irin haɗaɗɗiyar ƙatuwar kujerar ƙarfe ce aka jere awurin, yayin da gefe da gefen ta kuma aka aje wasu ƙananan kujerun masu azababben kyau suma na ƙarfe masu dauke da tambarin baƙar masarauta ajikin su, yayin da tsakiyar filin kuwa aka ƙawata sa fiye da yarce aka ƙawata ko wane wuri. Wani tafkeken daɓe (floor) ne akayi awuri mai matuƙar tudu da tsairs ajikin sa, gaba ɗayan sa zage yake da randinan da suke ɗauke da Huta acikin su suna matuƙar ci sosai, yayin da saman daɓen kuma aka ajiye wani danƙareran gunkin da akayi sa da taɓo da basa da kyan gani ko kaɗan, yayin da gefe da gefen sa kuma ya kasance ɗauke da fulawoyi zube aƙasa zageye da shi masu matuƙar yawa da wal-wali, sai kuma tambarin baƙar masarauta da aka bi aka manna sa aduka ƙasan daɓen. Acan ɓangaren bayi kuwa ko wanne shiryawa yake cikin kalar shigar sa. Yayin da ɓangaren Gimbiya Tasmir kuwa ta kasance zaune akan wata ar'niyar kujerar ƙarfe mai azabar kyau da sheƙi acikin ɗakin ta, yayin da wasu ƴammata da suke ɗaure da ɗan guntun baƙin ƙyalle iya guiwar su tare da ƙatuwar farar rigar yadi ajikin su mai ɗauke zanen tambarin masarautar tasu suke aikin tsan-tsara mata wata irin azababbiyar kwalliya mai matuƙar kyau da ɗaukar hankali, kallo ɗaya zaka musu katabbatar da amatuƙar tsorace suke, sannan kuma ko kaɗan basa cikin nutsuwar su, sabo da yarce suke aikin wasu sassa na jikin su na kar-karwa. Yayin da ita kuma ta kasance lumshe da idanuwan ta tana mai ɗan taune leɓen ta na ƙasa ahankali, tare da ɗan sakin murmushi lokaci bayan lokaci, wanda yayi matuƙar bawa ƴammatan da suke yi mata kwalliya mamaki, domin kuwa zasu iya cewa tunda suke da ita basu taɓa ganin ta tana murmushi irin haka ba sai yau, duk da dai dama bawai suna iya kallon fuskar ta bane ba ada, yanzun ma dan suna mata kwalliya ne shiyasa har suka samu wannan damar kallon ta, amma sai dai tun da suke basu taɓa jin ko alabari ba ance tayi murmushi sai yau da suka gani azahiri . Afannin ta kuwa ba komai ne ke sata murmushi ba sai tunawa da take yi yauce ranar da zata koyawa ƙasƙantaccen ƙazamin bawan can Bir da yake ganinta tamkar tsaran sa hankali, domin kuwa ta tanadi azabobi kala kala waƴan da zata yi masa su ayau fiye da duk sauran da ta masa abaya muddin bai bata amsar tambayar ta ba. Sanye take da wata doguwar riga mara kafaɗa wacce ta kasance ruwan ƙasa mai duhu sosai, yayin da kanta kuma ya kasance ɗaure da abun ɗaurin ɗan kwali kalar ruwan zuma da aka mata ɗauri irin mai hawa hawa da shi, sai sarƙar goshi mai azababben kyau ta goal da take zagaye akan ta. Yayin da ƙafafuwan ta da hannuwan ta harma da wuyan ta suka kasance ɗauke da sarƙoƙin goal masu matuƙar kyau da tsada suna ƙyalli. Sosai tayi matuƙar kyau tana ta faman sheƙi ta ko ina. Acan ɓangaren su Bir kuwa tun cikin dare Iyar Bayi ta sake zaunar da shi tana mai sake roƙon sa akan karya ko kalli fuskar Gimbiya Tasmir, balle har tai masa wani abun. Da tom ya amsa mata shima yana mai ƙudurtawa ransa cewar zaiyi yarce Iyar tasa ta roƙe sa yayi ko domin farin cikin ta, amma bawai dan yana tsoron wani abu da Gimbiya Tasmir zata masa ba, asalima yasan sai yayi tsantsar kai zuciyar sa nesa, tukun zai iya haƙura ya kasa ɗaga kai ya kalle ta muddin sukai kusanci da juna, gashi kuma yasan wajibine suyi kusancin, tunda akwai gaisuwa ta daban da Bayi suke kaiwa ahalin Sarki aduk irin wannan ranar. *ƘASAR HAUSA, JAHAR WASAI CIKIN BAƘAR MASARAUTA.* Tun misalin ƙarfe takwas da minti arba'in Yarima Asad ya gama shirin sa tsaf kamar yacce Babban yaya ya umarce sa akan ya shirya da wuri. Sai dai kuma irin shigar da yay ta yau tafi ta kusan koda yaushe muni, domin ko sanye yake da wani farin wando three quarter wanda yake akekkece daga saitin cinyoyin sa, tayarce har ake hangen farin net boxer ɗin dake sanye jikin sa, wato crazy, sai wata baƙar t shirt mai ɗan guntun hannu da take sanye ajikin sa da tayi matuƙar kama jikin sa, tayarce har ta bayyana gaba ɗaya murɗaɗɗiyar surar sa. Yayin da sumar dake ɗauke akansa sa mai tsananin yawa kuma ta kasance atsage gida biyu, banda wal-wali da sheƙi babu abun da take yi, sabo da ruwan mayukan da ya mulketa dasu har zuwa ƙasumbar sa, sai wuyan sa kuma da yake ɗauke da wani silin sarƙar goal mai matuƙar ƙyalli, yayin da hannun sa ɗaya kuma ya kasance ɗaure da wani azababben baƙin agogo yayi matuƙar ƙara haskaka fatar hannun, sai kuma ɗayan hannun da ya bisa da wasu abun hannuwa na roba suma baƙaƙe. Banda faman ciccin magani yana kumbura babu abun da yake aikin yi, donin ko koda Al'amin yazo yana masa magana ma ko kai bai ɗaga ya kalle sa ba balle ya tanka masa, hakan da Al'amin ya gani ne, sannan kuma ya fahimci dalilin fushin nasa ya sanya yake ta faman tsokanar sa yana sheƙar uwar dariya, domin ko shi sanye yake da manyan kaya ɗinkin riga da wando na shadda. Ƙarasawa yayi zuwa inda takalman sa suke yana mai sa hannu ya ɗauko wani sabon baƙin boot yana mai sanya ƙafafuwan sa acikin su, tukun ya janyo wayar sa ya riƙe ahannun sa yana mai komawa gefen bed ɗin sa ya zauna tare da mai da idanuwan sa kanta. Ko minti biyu baiyi ba da zama sautin ringing ya fara tashi daga cikin wayar tasa. Yamutsa fuska yayi yana mai sake ɗaure fuska, sabo da sunan da yaga yana yawo akan screen ɗin wayar tasa, wato Yaya na. Tukun daga bisani yayi picking yana mai kai wayar kan kunnen sa. Lumshe idanuwan sa yayi yana mai ɗan taune lower lips ɗin sa da haƙora ba tare da yace komai ba, da alamun dai yana sauraran abun da ake faɗe ne daga can, tukun daga bisani ya buɗe baki yana mai faɗin. "Tom shikenan gamunan." Daga can ƙasan makoshin sa, kana ya janye wayar daga kan kunnen sa yana mai miƙewa tsaye. "Ka taso Malam ana jiran mu." Ya faɗi haka yana mai yin gaba. Murmushi Al'amin yayi ba tare da yace komai ba shima, tukun shima ya miƙe yana mai bin bayan sa. Acan ɓangaren Babban yaya kuwa sanye yake da manyan kaya harda alkyabba ajikin sa. Tsaye suke agaban wasu arnayen motoci da suke ta faman ɗaukar ido, tare da dogaran sa da suke sanye da uniform da zura zuran bulalai riƙe ahannun su, suna masu kallon hanyar da su Yarima Asad zasu ɓullo, alamun su ɗin kawai suke jira kenan. Al'amin ne ya fara ɓullowa tukun Yarima Asad ya biyo bayan sa, tun daga nesa Babban yaya ya saki baki tare da zuba idanuwa akan ƙanin nasa saboda shigar da ya hango sanye ajikin sa, yayin da suma dakarun nan gaba ɗaya suka bisa da kallo, duk da dai hakan ba sabon abu bane awurin su, sai dai amma gaba ɗaya cikin su babu wanda yay zaton ganin sa ahaka yau, duba da wurin da suka san zasuje. Tafe suke babu mai cewa wani ƙala daga shi har Al'amin, dan shi Yarima Asad ma kansa sunkuye yake aƙasa, ahaka har suka ƙaraso bakin motocin nan. "Ina kwana Yaya." Al'amin da Yarima Asad suka faɗa adai dai lokacin da suka ƙaraso gaban Ciroma. "Da alamu ka manta sunan wurin dana faɗa maka zamuje ne, ko kuma ka kurmance alokacin da nake faɗa maka jiya, shiyasa har ka sanyo waƴan nan ƴan iskan kayan ajikin ka ko?" Babban yaya ya faɗi haka ransa aɓace ba tare da ya amsa gaisuwar da suka masa ba, sai idanuwa kawai da ya kafe yarima Asad dasu yana kallon sa. Yayin da shi kuma ya sake gyara tsayuwar sa awurin da yake yana mai ɗaure fuska tare da ɗaukar yastun hannuwan sa ya kai kan ƙeyar sa yana sosawa ba tare da yace komai ba. "Wai ba magana nake maka bane da kamun shiru kana bina da idanuwa?" Babban Yaya ya faɗa da ƙarfi ransa na ƙara tafar fasa. Yayin da shi kuma Yarima Asad ya rumtse idanuwan sa da ƙarfi yana mai danna lower lips ɗin sa cikin baki ya cije su, sabo da tsawar da yayan nasa yamasa ransa na ɓaci shima, tukun daga bisani ya buɗe baki still yana sosa ƙeya tare da faɗin. "Am dama Yay.... "Kamun shiru, bana son jin duk wani shirmen banzan da zai futo daga bakin ka, dan haka yanzu yanzu ka huce kaje ka canzo kayan nan kasanya kayan mutunci, minti biyar kawai na baka ina jiran ka anan." Ya katse sa da faɗin haka cikin tsawa ba tare da ya bari yaji ƙarshen abun da zai ce ba. "Girgiza kai Yarima Asad yayi tare da sake rumtse ido ransa na ƙara ɓaci, domin kuwa aduk duniya idan da akwai wani abu da yafi tsana to ya biyo bayan tsawa da takura, hakan yasa lokaci ɗaya yaji gaba ɗaya tafiyar ta gama fuce masa arai, tayarce har ya ƙudiri aniyar cewa muddin ya koma to wallahi babu abun da zai sanya sa ya dawo, domin kuwa bazai taɓa sanya barguna ajikin sa ba, sai dai komai zai faru ya faru. Yayin da shi kuma Babban Yaya ya buɗe murfin motar dake gaban sa yana mai shigewa ya zauna ransa na tsantsar ɓaci. Sai da ya ɗauki kimanin minti biyu daga tsayen da yake rumtse da idanuwan sa, tukun daga bisani ya buɗe su gaba ɗaya har launin su ya fara sauyawa daga fari zuwa ja, kana ya juya yana mai dosar hanyar da suka biyo suka zo daniyyar ko yaje bazai dawo ba wallahi. Acikin mota kuwa cikin tsantsar takaicin hallayar ƙanin nasa da yake ji aƙasan ransa ya lumshe idanuwan sa, yana mai jingina da jikin kujerar tare da ɗaga kansa sama, kafin daga bisani kuma ya miƙe zumbur yana mai gyara zaman sa akan kujerar, sabo da tino wasu daga cikin shawar-warin Sheikh Ahmad da yayi da yake cewa muddin yana son buƙatar sa ta biya ta ɗora ƙanin nasa akan hanyar dai dai, to dole sai yana binsa ahankali, domin kuwa idan har yace zai masa ta zafi ko kuma yace zai na cewa yayi komai kai tsaye, to bazai taɓa samun yarce yake so ba, face shaƙuwar dake tsakanin su ma ta samu tangarɗa, dan haka muddin yana son yay abun da yake so, to dole sai yana jan sa ajiki tare da lallaɓa sa. Hakan da ya tina ne kuwa ya sanya sa miƙewa zumbur daga kishingiɗen da yake jikin kujera, tukun daga bisani ya miƙa hannu yana mai janyo wayar sa da take ajiye agefen sa, sannan ya shiga contacts yana mai nemo number ƙanin nasa da ya rubuta My Asad ajiki da ɓaro-ɓaron baki ya doka masa kira, tare da karata akan kunnen sa. Aɓangaren Asad kuwa yana shirin shiga cikin apartment ɗin nasu yaji sautin wayar sa dake riƙe ahannun sa. Bai ɗago ta ba balle ya kalle ta har tai ringing ɗin ta ta gama tas. Ko minti ɗaya batai da katsewa ba sai ga wani kiran nan ya sake shigowa. Mtswwww! Yaja wani dogon tsaki yana mai dakatawa awurin da yake tare da lumshe idanuwan sa, tukun daga bisani ya warasa yana mai ɗago hannun sa yakai idanuwan sa kan wayar tasa. BIG BROS Shine sunan da ya gani yana yawo akan screen ɗin wayar ɓaro-ɓaro da manyan baki. "What againe kuma?" Ya faɗa yana mai taune lowar lips ɗin sa tare da yamutsa fuska, tukun daga bisani yay pickin ɗin call ɗin lokacin da yake dab da katsewa yana mai kai ta kan kunnen sa. Shiru yayi ba tare da yace komai ba, sai faman hanci da yake hurawa kawai. Yayin da acan ɓangaren Babban Yaya kuma yayi gyaran murya yana mai yin shiru ba tare da yace komai ba shima. Sun ɗauki kimanin mintina biyu ahaka sai sautin futar numfashin junan su da suke ji kawai, tukun daga bisani shi Babban Yaya ya buɗe baki cikin sanyin murya yana mai faɗin. "Ƙanina." Kana yay shiru ba tare da ya ƙara furta komai ba. "Uhm!" Kawai Asad ya faɗa ba tare da yace ƙala ba. Murmushi Babban Yaya yayi daga can ɓarin da yake sabo da fahimta da yay ƙanin nasa na fushi da shi ne, tukun daga bisani ya buɗe baki yana mai faɗin. "Kana ina ne ƙani na?" "Cikin ɗaki." Ya faɗa acan ƙasan maƙoshi tayarce shi kansa Babban Yaya sai da ƙyar ya iya jiyo sautin furucin nasa. "Ka cire kayan naka ne?" Ya sake faɗa agajarce har lokacin muryar sa ɗauke da murmushi. "A'a." Yarima Asad ya faɗa still daga can ƙasan maƙoshi. "To kawai kabar abun ka basai kacanza ba, nima sai bayan ka tafi naga ne ba ƙaramun kyau kayi ahakan ba, dan haka yanzu kayi sauri katawo mutafi kai kaɗai muke jira." Baban Yaya ya faɗa ahankali muryar sa ɗauke da murmushi har lokacin. Yayin da shi kuma Yarima Asad yayi wani irin haɗ..................✍ *SAI DA NA GAMA TYPPING ƊIN 6K WORDS (READ MORE GOMA) INA EDITING DUKA YA GOGE, SO KUYI HAƘURI DA WANNAN KUYI MANAGE, INSHA ALLAH IDAN NA SAMU LOKACI ZA KUGA PAGE 9 ZUWA DARE.* 😭 🐎 *BAƘAR MASARAUTA* 🐎 👑👑 🦋 🦅🕊🦆 🐍🎠🐄🏹 _*NA*_ UMAR FARUQ*D* *BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM* *FREE PAGE 09* Haɗe rai yana mai ɗaukar tafin hannun sa ya kaisa kan goshin sa ya dafe sa tare da rumtse idanuwan sa da ƙarfi, yana mai jin takaicin kiran sa da yayan nasa yayi, tukun daga bisani ya buɗe idanuwan nasa yana mai juyawa ya koma hanyar da ya biyo. Yana ƙarasawa wurin da suke, suka buɗe murafan wata haɗaɗɗiyar mota ba wacce Babban Yaya yake aciki ba shi da al'amin suna masu zama daga gidan baya. Tukun matuƙan motocin sukayi musu key suna masu ɗaukar hanyar da zata futar dasu daga cikin masarautar. Ƙarasawar su bakin get yayi dai dai da isowar motocin Gwamnan Wasai tare da tawagar sa, ba tare da sun tsaya sauraran junan su ba bare su gaisa ko wanne yayi gaba, su suka shilla zuwa kan titi, yayin da motocin da gwaman da ƴan rakiyar sa suke aciki su kuma suka hulla kan motocin su zuwa cikin masarautar. *JAHAR KAGUL, CIKIN MASARAUTAR FULƊE* Tun daga lokacin da tayi arba da fuskar Yariman Yamma take cikin baƙin ciki tare da ƙunci, tayarce har takasa sanya komai acikin ta, domin kuwa ko alamun yunwa bataji ba balle har tayi ƙoƙarin cin abincin, duk da yarce aka jere mata su kala kala agaban ta kuwa, sabo da tsantsar baƙin cikin da take ciki. Babu abun da yafi ƙona mata rai da sanyawa ta sake jin ta tsanar sa fiye da kowa, sai irin kalaman da ya dinga faɗa mata na cewar ita ɗin tasace. Koda ta kwanta bacci cikin dare mafarki tayi wai gata kan saman wani tafkeken dutse. Yayin da ƙasan dutsen kuma ya zamto zagaye da wani farin ruwa mai matuƙar girma da haske, sai daga can gaban ruwan kuma ta dinga jiyo wani irin sautin busa mai tsantsar daɗi da kwanciya arai yana tashi. Hakan yasa tai ta shawagi akan dutsen fuskar ta ɗauke da murumushi, yayin da idanuwan ta kuma suka kasance kafe akan ruwan nan tana mai tinanin ta hanyar da zatabi ta tsallake sa, domin ta ƙarasa wurin da daddaɗan sautin da ke dukan kunnen ta yake. Sanye take da kayan fulani bana sarauta ba yau, wato irin waƴan da kowa ke sanyawa farare ajikin ta, yayin da kanta kuma ya kasance ɗauke da wasu manya manyan kitso guda biyu ƙwal akai, sai sandar gadon ta ta tsafi da take riƙe ahannun ta tana mai cigaba da juyi asaman dutsen nan. Babu abunda yafi mata daɗi awurin sai yarce wata irin sassanyar iska mai matuƙar daɗi take tashi tana dukan jikin ta awurin, ga kuma ƙamshin korayen ciyayin da suke dashe agefen dutsen, waƴan da suka ƙara sanya ta cikin shauƙi. Ta ɗauki kimanin daƙiƙa kusan talatin asaman dutsen tana mai neman hanyar da zata sauka daga kansa, domin tabi ta cikin ruwan nan ta ƙarasa wurin da take jiyo sautin busar, amma bata samu ba. Lokaci ɗaya yanayin ta ya fara sauyawa, gaba ɗaya jikin ta ya farayin sanyi, sabo da rasa hanyar da zatabi ta sauka daga kan dutsen da tayi, sai can taga wasu kyawawan tsuntsaye guda biyo sun tawo aguje suna masu zuwa suka gogi gefen fuskar ta da fuka-fukan su, tukun daga bisani suka ƙara yin gaba suna masu tsayawa asaitin fuskar ta tare da karɗada jelinan su. Wani irin murmushi ne ya suɓuce mata take awurin, sabo da ganin tsuntsayen nan da tayi, tukun daga bisani ta gayara tsayuwar ta awurin tana mai ɗaukar sandar dake riƙe ahannun ta ta maƙale ta akan ƙafadar ta, sannan ta buɗe baki cikin tsantsar shauƙi tana mai faɗin. "Barkan ku da zuwa gareni masoya na." Ta faɗa tana mai sakin murmushi tare da lumshe kyawawan idanuwan ta, tukun daga bisani ta buɗe su tana mai ɗorawa da cewa. "Dama ni nasan bazaku taɓa barina cikin wani hali ba, duk inda mafuta take zaku samo mun ita Shale am, dan haka idan kun shirya nima na shirya, muje ku nuna mun hanyar da zata kaini wurin wancan daddaɗan sautin." Ta faɗa tana mai sake gyara tsayuwar ta tana kallon su tare da sakin murmushi, yayin da suma ɗin suka juyo ɓarin da take suna masu shawagi akan ta tare da sakin kuka, alamun suna amsa batun ta kenan, tukun daga bisani suka juya atare suna masu dosar wata hanya dake akan dutsen. Bin su itama tayi abaya cikin takun ta wanda shi kaɗai ke ɗaukar hankulan jama'u akan ta. Wata hanya suka ɓulla da ita akan dutsen wacce ta kasan ce gangare ce, tukun suka sauka daga sama suna masu sauka akan dutsen, suka fara ɗan tsallawa da ƙafafuwan su suna masu sauka daga kan dutsen. Binsu itama tayi abaya idanuwan ta ƙur akan hanyar da take jiyo sautin busar nan cikin tsantsar farin ciki, ahaka har suka sauka daga kan tafkeken dutsen nan dukan su suna masu tsayuwa agaban makeken ruwan nan, tukun daga bisani tsuntsayen suka ƙara tashi sama suna masu dawowa dai dai saitin fuskar ta, sanann suka karkaɗa mata jelolin su tare da shafar gefen fuskar ta da fuka fukan su. "Shin ina kuma zaku tafi kubarni ba tare da kun nuna mun hanyar da zanbi in tsallaka wannan ruwan ba." Ta faɗa tana mai marai-raice fuska idanuwan ta akan su. Cigaba da zagaya ta sukayi suna masu sakin ɗan kuka, tukun daga bisani suka tashi sama gaba ɗayan su atare suna masu yin gaba suka barta awurin. Lumshe idanuwan ta tayi tana mai shaƙar sassanyar iskar dake wurin, tare da ƙamshin turare. Ta ɗauki kimanin mintina biyu ahaka, tukun daga bisani ta buɗe idanuwan ta fuskar ta ɗauke da tsantsar murmushi, sabo da tinawa da tayi da Birbillon ta (malam buda mana littafi) Hakan yasa ta juyawa da sauri tana mai dosar wurin da wasu korayen ciyayi suke dashe agafen ruwna nan, fuskar ta ɗauke da murmushi, yayin da har lokacin hannun ta yake riƙe da sandar nan ta. Durƙusawa tayi aƙasa gaban furannin bayan ta aje sandar ta agefen ta, tukun ta lumshe idanuwanta tana mai kai tafin hannun ta ta bugi korayen ciyayin nan da shi, tukun ta buɗe tafin hannun tana mai ɗora sa akan ciyayin. Take wasu irin kyawawan malam buɗa mana littafi kala-kala suka taso suna masu yin shawagi adai dai saitin fuskar ta, tukun sai su koma su haye kan tafin hannun ta. Ahakan har sai da suka cika duka tafukan hannayen ta biyu da ta buɗe, tukun daga bisani ta wara fararen idanuwan ta masu ɗauke da blue black ɗin ƙwayar ido akan su. Miƙewa tsaye tayi cikin tsantsar farin ciki tana mai sakin dariya, tukun daga bisani ta buɗe baki tana mai faɗin. "Barkan ku da zuwa Birbillo am masoya na." Ta faɗa tana mai cigaba da sakin dariya, tukun daga bisani ta ɗora da faɗin. "Shin ta wata hanyar kuke ganin zanbi domin na tsallake ruwan nan?" Ta ƙarasa maganar tana mai tsayawa awuri ɗaya tare da zuba idanuwan ta akan su. Rufe bakin ta keda wuya gaba ɗayan su suka tashi daga kan tafukan hannuwan nata suna masu komawa kan sandar ta da take ajiye agefe, tukun suka ƙara tashi daga kan sandar suna masu tafiya zuwa saitin ruwan nan sukayi kamar zasu nutsa cikin sa, sannan suka sake juyawa suna masu sake hayewa kan tafukan hannuwan ta. "Godiya nake masoya na, bada ban kuba da bansan yacce zanyi in tsallaka ruwan nan ba." Ta faɗa tana mai sakin murmushi, tukun ta daga bisani ɗora da cewar. "To sai da anjiman ku masoya na, ni zan ƙarasa wurin Gidado am." Tashi sukayi dukan su suna masu komawa cikin ciyayin nan, yayin da ita kuma ta durƙusa ƙasa tana mai sa hannu ta ɗauki sandar ta dake ajiye aƙasa, tukun ta ɗago ta tana mai riƙe ta ahannun ta, ta miƙar da ita tare da zuba mata idanuwan ta, kana daga bisani kuma ta buɗe baki tana mai faɗin. "Na dogara dake sandar gado ta, dan haka ina fatan bazaki bani kunya ba, kamar yacce akace ba zaki taɓa bani kunya ba arayuwa, zaki kaini zuwa ga Giɗaɗo am." Sannan ta fara ɗaga ƙafafuwan ta tana mai dosar bakin ruwan nan gada-gadan. Tana zuwa gaban sa ta sake dunƙule sandar nan tata da matuƙar ƙarfi acikin tafin hannun ta, tukun ta ɗaga ta tana mai buga ta acikin ruwan nan da matuƙar ƙarfi. Take kuwa ruwan ya dare gida biyu gaba ɗayan sa. Yayin da ta sake jiyo sautin busar nan da matuƙar ƙarfi na cigaba da dukan kunnen ta. Ba tare da ta tsaya wata -wata ba ta fara ɗaga ƙafafuwan ta tana mai dosar hanyar da take atsakiyar ruwa kai tsaye. Sai da tai tafiya mai ɗan tsawo, tukun ta fuce daga cikin ruwan, kana hanyar ta koma ta haɗe gaba ɗayan ta ta zama ruwa kamar da. Yayin da ita kuma Gimbiya Haddiyal tayi tsaye a'inda take tare da buɗe kunnuwa tana mai sauraran sautin busar nan, dan ta fahimci ta inda yake futowa. Murmushi ta saki tana mai lumshe idanuwan ta, tukun daga bisani ta warasu tana mai fara ɗaga ƙafafuwan ta ta doshi hanyar da take tinanin anan zata tarar da mai busar nan. Miƙaƙƙar hanyace mai ɗauke da farin yashi mai matuƙar laushi akan ta, cigaba da tafiya tayi har ta ɓulla zuwa wani ƙaton fili mai ɗauke da duwar-watsu tare da da ƙananan ruwaye zagaye da shi. Zagaye ta farayi aɗan rukunin wurin da take tana mai wara idanuwan ta, domin ta hango ta inda mai busar yake. Tsaye ta hange sa acan bayan wani dutse ya juya baya yana mai karkaɗa kai, tare da cigaba da sakin busar sa da take jin daɗin ta na ratsa har cikin kwanyar ta. Lumshe idanuwan ta tayi awurin da take tana mai sakin murmushi, tukun daga bisani ta sake buɗe su akan bayan sa, kana ta fara ɗaga ƙafafuwan ta tana mai dosar wurin da yake. Tsaye tayi abayan sa tana mai jin wani irin shauƙi na ɗibar ta. Yayin da shi kuma yake cigaba da sakin busar sa hankali kwance ba tare da yasan da tsayuwar ta ba awurin ma. Gyara tsayuwar ta ta sake yi awurin tana mai ɗora sandar ta akan kafaɗar ta, tukun daga bisani ta buɗe baki cikin daddaɗar muryar ta tana mai faɗin. "Yau dai gani gaban ka Giɗaɗo am, ubangijin shanu da mutane ya yayin sanadin haɗuwar mu da juna yau. Ta ƙarasa furucin cikin wani irin shauƙi wanda bata taɓa tsintar kanta amakamancin sa ba, tukun daga bisani ta ɗora da faɗin. "Tabbas yau ɗin ta kasance rana ta musamman gareni ni Gimbiya Haddiyal, yau ɗin ta zamto rana ta daban daga cikin ranakun da nayi arayuwa ta, dan haka juyo ka ganni na ganka Giɗaɗo am, juyo gani masoyi na, juyo kayi arba da wacce aka hallita domin kai, juyo kaga kyakkyawar hallitar da ta daɗe tana tsumayin ganin ka." Ta faɗa fuskar ta ɗauke da murmushi, yayin da shi kuma yayi shiru ba tare da yace komai ba, sai tsayawa da yayi da busar da yake yi. Sake gyara tsayuwa tayi tana mai ɗorawa da faɗin. "Ka sani na soka fiye da kowa da komai dake cikin duniyar nan, na soka kuma ina kan sonka fiye da yarce nake son kaina Giɗaɗo am! Ka sani kai ɗin nawa ne ni kaɗai kamar yacce na kasance taka kai kaɗai kaima, dan haka juyo ka ganni na ganka masoyi na!" Ta ƙarasa maganar still fuskarta ɗauke da tsantsar murmushi. Ahankali shima ya fara juyowa gare ta fuskar sa ɗauke da tsadadden murmushin sa da yayi matuƙar ƙara masa kyau. Kallon ta ya farayi yana mai jifan ta da murmushin sa ba tare da yace mata komai ba. Yayin da ita kuma ta lumshe kyawawan idanuwan ta tana mai cigaba da sakin murmushi, tukun daga bisani ta fara buɗesu ahankali-ahankali, tana mai jin sun nata wani irin nauyi, sai dai kuma suna gama buɗuwa amai-makon taga Giɗaɗo am ɗin ta sai kawai tayi arba da fillown da ta ɗora kanta akan sa tun kafin tayi bacci! Zumbur ta miƙe zaune daga kwancen da ta ka tana mai ɗaukar tafin hannun ta ta dafe goshin ta da shi cikin tsantsar takaici da haushi, sabo da fahimtar da tayi na duk abun da ya faru ba gaske bane ba mafarki ne irin wanda ta saba yin sa akoda yaushe tayi. Ta ɗauki kimanin mintina biyar ahaka tana mai cizon leɓen ta na ƙasa, tukun daga bisani ta janye hanun nata daga kan goshin ta tana mai matsawa bakin gadon tare da zura ƙafafuwan ta ƙasa. Sannan ta miƙe tsaya tana mai yin taku biyu daga inda take, tukun taja ta tsaya tana mai rumtse idanuwan ta da ƙarfi, kana daga bisani ta buɗe su tana mai faɗin. "Wato idan na fahimci dai dai, wannan mafarkin na nufin sandar tsafi na ta gado ce zata nuna mu hanyar da zanbi in gano ka Giɗaɗo am kenan." Ta ƙarasa maganar tana mai girgza kanta tare da sakin murmushi, tukun ta cigaba da ɗaga ƙafafuwan ta cikin kuzari tana mai dosar wani ɗan ƙaramin ɗaki da yake acikin ɗakin baccin nata. Hannu tasa tana mai janyo ƙofar dake wurin, tukun ta danna kanta zuwa cikin ɗakin. Ɗan ƙaramin ɗaki ne sosai, domin ko ko mutum ɗaya bazai ɗauka ba da sunan kwanciya acikin sa. Ɗauke yake da wasu kayan kari-kitai kala kala acikin sa, sai kuma wata doguwar sanda irin ta fulani da take jingine ajikin bango an yafa mata wani farin ƙyalle akan ta. Hannu tasa tana mai janye ƙyallen dake kan sandar, sannan ta damƙe ta cikin tafin hannun ta na hagu da matuƙar ƙarfi, tukun ta ɗago ta tana mai juyowa tayo waje da ita. Hannun daman ta ta sanya ta rufe ƙofar ɗakin da shi, tukun ta juyo tana mai dosar wata ƙofa dake manne jikin bangon ɗakin gadan -gadan. Buɗe ƙofar tayi itama, kana ta zura kanta tana mai dosar cikin wurin. Tafkeken filine mai matuƙar girma da faɗi ya bayyana, ashe wai nan ɗin ma hanya ce wacce take sadar da mutum wani shashi na daga cikin sashikan dake cikin gidan cikin sauƙi. Ɗaukar sandar nan tayi tana mai rataye ta akan kafaɗar ta, tukun ta fara ɗaga ƙafa cikin sauri tana mai dosar wata hanya. Sai da tayi tafiya mai ɗan nisa daga cikin ɗakin ta data futo, kana ta bayyana gaban wani tafkeken farin ruwa wanda ko ƙarshen sa ba ahange. Tsaye tayi agaban sa tana mai rumtse idanuwan ta da matuƙar ƙarfi, tukun ta fara ɗaga laɓɓan ta cikin kakkausar murya wacce batai kama da tata ba tana mai faɗin. Zaibaaaa!!!" Tukun ta ɗaga sandar nan tana mai bugata acikin ruwan da matuƙar ƙarfi, kana ta sake rumtse idanuwan tana mai sake faɗar kalmar Zaiba da matuƙar ƙaraji, tukun ta wara idanuwan nata tana mai kaisu kan ruwan nan gaba ɗaya, sai dai kuma me, take awurin taga gaba ɗaya kalar ruwa na sauya daga farin da yake zuwa baƙiƙƙirin yana wani irin tsalle. Dasauri taja baya tana mai girgiza kai tare da sakin sandar ta aƙasa, tukun daga bisani wasu irin hawaye masu matuƙar gudu suka ɓalle daga cikin idanuwan ta suna dira akan kuncin ta. Ba ta ita ta tsaya da ja da bayan da take ba har sai da ta jita jikin wata tafkekiyar bishiyar ɗorawa, tukun ta jingina da ita tana mai buɗe baki cikin kuka tace. "Shin me yasa irin hakan ke faruwa akowa ne lokaci ne? Shin ita ɗin ƴar gidan uban wace da har take mun katanga da ganin ka Giɗaɗo am? Nayi iya yina, nayi duk abun da zanyi domin na sameka amma duk abanza. Shin wane dalili ne ya sanya akowane lokaci ruwan ke canzawa daga kalar sa zuwa Baƙar kala." Ta faɗa tana mai ɗagowa daga jikin bishiyar da ta jngina, tukun ta farayin taku daga inda take tana mai komawa wurin ruwan nan da taga yana juyawa yana komawa asalin kalar sa. Tsugunnawa tayi awurin da ta yarda sandar tsafin ta tana mai ɗaukar ta ta riƙe acikin tafin hannun ta, tukun ta ƙurawa ruwan nan idanuwa tana mai ɗaure fuskar ta tamau, kana daga bisani ta buɗe baki cikin wata irin kakkausar murya tana mai faɗin. "Ina mai rantsuwa da ubanginin da yay ruwan dake cikin wurin na tare da bishiyun da suke cikin sa sai na tagyaraya ki ko ke ɗin wacece kuwa, tunda har kike ƙoƙarin shiga tsakanina da Giɗaɗo am, domin kuwa an hallice sane domin ni kaɗai badan wata ba, dan haka Wallahi tallahi sai na sanya ki kiny nadamar sanin sa da kikayi arayuwa, domin ko bincike na ya fahimtar dani cewar yana tare da wata ɗiya mace ce bani ba, bayan kuma gaba ɗayan sa anhallice sane domin mukasance atare mu biyu kawai." Ta ƙarasa maganar tana mai sake rumtse idanuwna ta zuciyar na tsantsar ƙuna da ciwo, tukun daga bisani ta warasu da sauri tana mai ɗora hannun ta akan goshin ta ta dafe sa, sabo da tino saƙon mahaifin ta da aka sanar da ita na cewar ta sanya asamar da madara da kayan itatuwa, sabo da baƙi da zasuyi yau daga Masarautar Wasai ta cikin jahar wasai, gashi kuma gaba ɗaya ta manta bata sanya an tatso madarar ba sai yanzu kawai abun ya faɗo mata. Hakan yasa ta janye hannun nata daga kan goshin ta tana mai fara ɗaga ƙafafuwan ta ta doshi hanyar da ta biyo cikin sauri, hannun ta riƙe da sandar ta domin taje ta sanya asamar da madara kafin lokacin zuwan baƙin yayi. *ƘASAR MALIN, JAHAR KARFUZ CIKIN BAƘAR MASARAUTA.* Misalin ƙarfe tara dai dai na safe tawagar Sarki Barbaru tare da iyalan sa suka doso cikin filin bikin da yake cike maƙil da jama'a. Banda sautin kiɗa da bushe-bushe babu abun da ake ji yana tashi awurin. Sanya yake da wa..................✍ 🐎 *BAƘAR MASARAUTA* 🐎 👑👑 🦋 🦅🕊🦆 🐍🎠🐄🏹 https://chat.whatsapp.com/BhlmHQbDexzCA2fi7K6Jtu _*NA*_ UMAR FARUQ*D* *BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM* *PAGE 10* Sanye da wasu jibga-jibgan riguna ajikin sa, yayin da ƙafafuwan sa kuma suke sanye cikin wani irin halp cover takalmi irin na sarakai mai azabar kyau, fuskar sa kuma zane take da tambarin masarautar tasu. Sai Iyalan sa kuma da suke daga gefen sa sun sanya sa atsakiya. Ɓarin daman sa da hagun sa matan sane biyu suma cikin shigar su ta alfarma, sai daga bayan su kuma Gimbiya Tasmir ce sanye da wata doguwar riga mai azabar kyau data futar da surar jikin ta tana jan ƙasa sosai, sai daga bayan ta kuma Yayyan tane maza guda ukku, suma dukan su sanye da shigar alfarma tare da alkyabba yafe asaman jikin su. Gaba ɗayan su babu wata alamun rahama tattare da fuskar su. Yayin da wasu irin danƙara danƙaran mutane da suke sanye da wani baƙin gajeran wando bako riguna ajikin su, hannun su riƙe da wasu irin zura zuran bulallai sukayi musu ƙawanya, gaba ɗaya jikin su zane yake da tambarin masarautar wanda akayi sa da baƙin fenti. Tafe suke cikin takun su wanda shi kaɗai ke hautsina cikin mutanen da suke ƙarƙashin mulkin su, suna masu dosar ƙarshen filin nan inda yake jere da kayan ƙawa tare da wasu irin azababbun kujeru masu matuƙar kyau da ɗaukar hankali. Kai tsaye suka fara zarcewa tsakiyar filin, suna masu tsayawa daga gaban tafkeken daɓen da abun bauta Gargabilu yake akai. Yayin da dakarun nan kuma dukan su suka zube wanwar aƙasa suna masu yin ribda ciki, tukun su kuma tawagar slSarki Barbaru suka juya baya dukan su, kana suka fara ɗaga ƙafafuwan su suna masu fara taka matattakalar da zata sada su da saman daɓen nan da baya da baya, kawunan su durƙushe aƙasa. Ahaka har suka ƙarasa wurin da abun bauta Gargabilu yake, tukun suka zube wanwar aƙasa gaba ɗayan su hatta da shi Sarki, suna masu rumtse idanuwan su tare da buɗe bakunan su atare suna faɗin. "Godiya gare ka yakai abun bauta Gargabilu, godiya gareka ya kai jagoran rayuwar mu, godiya gareka yakai madubun dubawar mu." Kana sukai shiru dukan su aduk lokaci ɗaya, tukun daga bisani suka buɗe idanuwan su akan abun bautar tasu. Sannan suka ɗora da faɗin. "Haska mana gaban mu yakai jagoran mu, godiya muke gareka da ka sake mai-maita mana wannan rana mai albarka." Suka ƙarasa faɗe suna masu mimmiƙewa tsaye daga kwancen da suke. Tukun Sarki Barbaru ya fara ɗaga ƙafafuwan sa yana mai ƙarasawa kusa da abun bauta Gargabilu, sannan ya sanya hannun sa ɗaya acikin aljihun alkyabbar dake jikin sa. Wata irin haɗaɗɗiyar sarƙar gwal ya zaro wacce take sarƙe da fulawoyi ajikin ta, tukun ya ɗan durƙusa agaban abun bauta Gargabilu yana nai sanya masa sarƙar awuyan sa, kana daga bisani ya ɗago yana mai haɗe tafukan hannayen sa biyu ya ɗora su akan ƙirjin sa, tukun ya sake buɗe baki yana mai faɗin. "Godiya muke ubangijin mu maji ƙanmu." Sannan ya juya yana mai komawa wurin da ya baro, tukun matan sa guda biyu suma suka tawo atare suna masu yin kamar yacce mijin nasu yayi, tare da ajiyewa gunkin nasu kyaututtuka, kana suka juya suka koma suma. Haka duka Iyalan nasa suka dinga zuwa wurin abun bautar tasu suna gaishe sa tare da basa kyaututtuka, kana su koma wurin da suke ahaka har kowa yaje. Tukun suka juya da baya da baya suna masu dosar hanyar matattakalar nan, domin su sauka daga kan daɓen. Acan gefen daɓen kuma daga ƙasan sa wani tsohon mutum ne tukuf zaune akan wata shimfiɗa mara kyan gani, daga shi sai ɗan guntun ƙyalle ɗaure aƙugun sa bako riga ajikin sa. Yayin da gefe da gefen sa kuma aka ajiye wasu kaskwayen wuta, ya zamto atsakiyar su suna ta faman bal-bala da huta. Daga gaban sa kuwa akan shimfiɗar da yake wasu irin karikitai ne akan ta kala-kaka, kai ataƙaice dai gaba ɗayan sa basa da kyan gani ko kaɗan, domin kuwa idan mutum ya kalle sa har dai ba sanin ko waye shi yayi ba babu abun da zai hana ya kirasa da mahaukaci tuburan, sabo da yarce jikin sa yake ɗauke da zanen tambarin Baƙar Masarauta ta ko ina, ga kuma wasu irin layoyi da suke rataye awuyan sa, da hannuwan sa harma da ƙafafuwan sa. BOKA MAI HUTAR KASKO KENAN. Suna sauka daga kan daɓen nan suka tsaya cak a'inda suke, yayin da su kuma dakarun nan da suka zuzzube aƙasa suka miƙe da sauri dukan su suna masu fara tafiya da baya da baya, ahaka har suka koma bayan su. Sannan Sarki Barbaru ya fara ɗaga ƙafafuwan sa yana mai yin gaba, kana suma Iyalan nasa suka bisa suna masu dosar wurin da kujerun nan suke. Suna ƙarasawa gaban kujerun gaba ɗaya dakarun nan suka yi sauri suka tsaya daga gaban su, suna masu juya musu baya tare dayi musu rumfa, ya zamto sun rufe su bamai ganin su kwata -kwata, tukun sarki Barbaru ya zauna kan wannan azababbiyar kujerar da ta gaji da haɗuwa, yana mai kamewa wuri ɗaya, kana suma matan sa suka zauna akujerun da suke ajiye jikin wacce ya zauna, tukun ƴaƴan sa maza guda ukku suka zauna, akan waƴan da suke ajiye agefen wacce Iyayen nasu suke akai, sai wata ƴar ƙarama kuma mai azabar kyau, wacce aka ajiye ta daga gaban na iyayen nasu hatta da ta shi sarki Barbaru, da take ɗauke da fulawoyi akan ta, Gimbiya Tasmira ta doshi inda take cikin takun ta wanda yake futar da sautin ƙarar sarƙoƙin gwal ɗin da suke maƙale ajikin ƙafar ta aduk lokacin da ta ɗaga ta ta dire aƙasa. Tsaye tai agaban ta tana mai lumshe idanuwan ta, wani irin nishaɗi take ji aranta wanda ta gaza misalta kalar sa, badan komai ba kuwa sai dan kawai ganin da take yauce ranar da zata yiwa ƙasƙantaccen fitsararren bawan can azaba mai raɗaɗi, agaban dubban jama'ar da suke cikin filin nan, kasancewar aduk rana irin wannan dama su Ƴaƴan Sarki suna da ikon yin duk yarce suka so suyi akan kowane Bawa, sabo da girman ranar agare su, domin kuwa azamanin baya da ya shuɗe, a'irin wannan ranar ce ake kashe duk wani mutum da ya can-can-ci kisa acikin Baƙar Masarauta gaban dubban jama'a. Sai da ta ɗauki kimanin mintina kusan huɗu lumse da idanuwna ta, tukun daga bisani ta buɗe su tana mai komawa ta ɗaure fuska tamau, duk da dama can ɗin ba dariya take ba, sai dai kuma baza'a ce fuskar ta ɗaure take ba, sannan ta zauna akan wannan haɗaɗɗiyar kujerar tana mai ɗora ƙafa ɗaya akan ɗaya, tukun ta ɗago dara-daran fararen idanuwan ta tana mai ɗora su akan hanyar da bayi zasu biyo su shigo filin bikin, kasancewa acikin duka filin babu wani Bawa suna can sashin su suna shiryawa suma. Tana zama akan kujerar salon kiɗan dake tashi acikin wurin duka ya sauya, wani irin kiɗa makaɗan sukeyi da gangunan dake ɗauke ahannun su da tsantsar ƙarfi idanuwan su arufe. Tukun can sai ga Bayi mata nan sun fara shigowa alayi ta wata hanya da baya da baya suna ta faman ɗirkar rawa, yayin da tafukan hannayen su kuma suke ɗauke da kaskwayen wuta waƴan da suke ta faman ci da huta! Wata irin rawa suke yi suna masu shigowa akan layi da baya da baya, bakunan su kuma na aikin furka kalmar. "Gargabilu! Gargabilu!! Gargabilu!!!" Da tsantsar ƙarfi. Ɗaure suke da wani baƙin ƙyalle na yadi ɗaure aƙugun su wanda ya tsaya iyakar guiwoyin su, sai wata ƴar ɓingilar riga da tsayin ta ya huce kan cibin su da kaɗan mai tsantsar faɗi fara ajikin su, gaba ɗaya rigar zane take da tambarin masarautar kamar yacce duka fuskar su take zane da shi, wanda ake bugasa da baƙin fenti, yayin da ƙafafuwan su kuma suka kasance ko takalmi babu akan su, sai uwar ƙura kawai da suke ɗiba. Haka sukai ta shigowa cikin filin suna masu dosar inda abun bauta Gargabilu yake, hannuwan su riƙe da kaskwayen huta da suke ta faman jujjuya sa, alamun ba ƙaramun zafi yake musu ba, domin kuwa kusan dukan su tafukan hannayen su sunyi jajajir yarce kasan zasuyi tsartuwar jini. Ba tare da sun gama shigowa ba suma bayi maza suka fara shigowa da baya da baya akuma kan layi, su kuma ɗauke da damin iccina masu matuƙar yawa akan kafaɗun su, suna ta faman rawa tare da faɗar kalmar. "Gargabilu! Gargabilu!! Gargabilu!!!" Da tsantsar ƙarfi yarce kasan zasu tsaga wurin, ga kuma uban sautin kiɗan ganguna da suke tashi awurin mai matuƙar dadi. Sanye suke su kuma da fararen wandina na yadi masu matuƙar faɗi iyakar guiwoyin su, yayin da gaba ɗaya jikin wandinan kuma suka kasance ɗauke da zanen tambarin masarautar tasu da akayi sa da baƙin fenti, sai fuskar su da fatar jikin su da ta kasance zane da tambarin masarautar tako ina, kasancewar babu wanda yake sanye da riga acikin su. Gaba ɗaya suma nufar hanyar wurin da abun bauta Gargabilu yake sukayi da baya da baya, hannuwan su ɗauke da iccina suna faman aikin dilliƙar rawa, yayin da gumi kuma ke yanko musu ta koce kafar gashi dake jikin su sabo da wahala. ƘASAR HAUSA, JAHAR WASAI CIKIN MASARAUTAR WASAI. Acikin masarautar wasai kuwa tun kafin gwamna da tawagar sa su ƙarasa fada masu tarbar su suka ƙaraso inda suke, kasancewar an riga ansan da zuwan su tun jiya. Cikin girmamawa wasu daga cikin fadawan mai martaba Sarki Abdallah suka da aka turo su tarbar mai girma gwamna suka durƙusar da kai agaban su suna masu miƙa gaisuwar su gare sa. Yayin da shi kuma gwamna da yake zaune agidan baya cikin azababbar motar da suke ke ciki ya sanya drivern sa ya sauke masa glass ɗin motar ƙasa, tukun shima ya ɗagawa dakarun hannu yana mai sakar musu murmushi alamar amsawa kenan, sannan suka juya suna masu dosar hanyar da zata sada su da fada aƙafafuwan su, yayin da suma motocin su gwamna da escort ɗin sa suka bisu abaya, bayan driver'n shi ya mai da glass ɗin motar ya rufe. Ko da suka ɗauki hanyar fada amai-makon su shiga cikin ta sai suka ɗauke hanya suna masu yin wata hanyar wacce zata kai su zuwa ga gidan da mai martaba Sarki Abdallah yake ganawa da manyan baƙin sa, kasancewar tun jiyan da mai girma gwamna ya aiko da saƙon zuwan sa sai da yasa sanarwa da mai martaba cewar babbar magana ce zata kawo su wurin su, sai dai amma ba wacce ta shafi Jaha bace, magana ce wacce ta kasance family issue. Hakan yasa mai mairataba Sarki Abdallah bai sa akai su fada ba sai yace awuce dasu zuwa masaukin baƙin sa direct. Gaban wani haɗɗaɗen plat building fadawan sarki suka tsaya, sannan suma motocin su gwamna akayi parking ɗin su awani wuri da yake ajikin gidan, wanda anyisa ne sa domin aje motocin dama. Dasauri escort ɗin da suke acikin motocin waƴan da suke sanye da uniform kala kala ajikin su suka buɗe murafan motocin su su suna masu furfutowa waje, tukun suka fara ɗaga ƙafafuwan su suna masu dosar wurin motar da mai girma gwamna tare da aminin sa suke aciki, cikin takun su dake nuni da su ɗin cikakkun jarumai ne, yayin da hannuwan su kuma suka kasance riƙe da manya-manyan bindigu. Mutum biyu suka matsa jikin ƙofofin motar suna masu sanya hannu suka buɗe su, yayin da suran escort ɗin kuma sukayi tsai-tsaiye abakin motar cirko-cirko. Ƙafar sa da take sanye da wani azababben cover shoe mai matuƙar kyau da tsada ya fara zurowa waje, tukun daga bisani ya sanyo gangar jikin sa waje yana mai futowa duka. Sanye yake da wata arniyar getzner shadda ash color da take matuƙar ƙyalli da ɗaukar ido, ɗinkin babbar riga ajikin sa. Aɓangaren abokin nasa shima futowa yay yana mai dawowa ɓarin da mai girma gwamna yake, shi ɗin ma sanye yake da shiga ta alfarma ɗinkin babbar riga ajikin sa. Tukun suka fara takawa suna masu dosar ƙofar dake manne jikin haɗaɗɗen building ɗin nan, yayin da suma escort ɗin suka bisu abaya suna ta faman bubbuɗawa. Cak fadawan nan suka tsaya daga bakin ƙofar suna masu komawa gefe suka buɗawa mai girma gwamna wuri. Suna zuwa bakin ƙofa ya ɗagawa escort ɗin dake binsu hannu ba tare da yace musu komai ba. Cak sukai tsaye awurin daga bakin ƙofar suna masu gyara riƙon bindigun dake hannuwan su. Yayin da su kuma su gwamna suka danna kawunan su zuwa cikin ƙofar. Tamfatse-tsen fallo ne wanda ya gaji da haɗuwa da kayan ƙawa da alatu yarce kasan babu mutuwa. Tsit fallon yake babu kowa cikin sa sai sautin futar ac kawai dake tashi acikin sa, tare da wani irin ni'imtacce ƙamshi. Kan wata mayyar royal chair dake zagaye da fallon mai girma gwamna da aminin sa suka samu wuri suka zauna. Yayin da daga gaban kujerar kuma wani tamfatse-tsen center table yake cike maƙil da kayan ciya-ciye, irin su ruwa, fruits, naman kaji, dana rago wanda aka sarrafa sa kala-kala jere akan wani ƙaton tray. Basu jima da zama awurin ba sai ga Waziri da Galadima nan sun futo ta wata ƙofa da take acikin fallon bakunan su ɗauke da sallama. Ƙarasawa sukayi zuwa kan kujerar da take facing ɗin wacce su mai girma gwamna suke akai, tukun suka zauna suna masu fara gaisawa cikin mutunta juna da girmamawa. Zaman su baifi da minti biyar ba sai ga mai martaba Sarki Abdallah nan ya futo ta cikin ƙofar dasu galadima suka futo bakin sa ɗauke da sallama shima. "Wa'alaikumu salam." Gaba ɗayan su suka amsa masa suna masu kai idanuwan su kansa. Sanye yake da shigar sa irin ta koda yaushe, wato manyan kaya tare da alkyabba mai azabar kyau da rawani ɗauke akan sa. Ƙarasawa yayi zuwa gaban kujerar da su mai girma gwamna suke yana mai miƙa musu hannu sukayi musabaha cikin mutunci da girmamawa, kana ya juya yana mai komawa kan kujerar da take agefen wacce su Waziri suke akai ya zauna, sannan ya buɗe baki yana mai faɗin. "Bismillah ga abinci nan ku taɓa mana." Ya ƙarasa maganar yana mai musu nuni da tray'n dake cike da kayan abinci kala kala akan sa da yatsar sa manuniya. "Alhamdulillah! Alhamdulillah wallahi!!" Suka haɗa baki wurin fadɗe suma fuskar su ɗauke da murmushi. Shiru ne ya biyo baya ba tare da wani ya ƙara cewa komai ba acikin su. Tukun daga bisani aminin mai girma gwamna mai suna Alhaji Saleh yayi gyaran murya yana mai ɗago kai ya fuskanci su mai martaba, tukun daga bisani ya fara ɗaga laɓɓan sa yana mai faɗin. "To ataƙaice dai ba komai ne yasan ya mu muka buƙaci zama daku ba sai akan wani muhimmin abu da yake atsakanin yaran mu duka, wanda afannin mu mu muke masa kallon abun alkhairi tare da alfahari garemu gaba ɗaya idan har muka samu ya tabbata." Ya faɗa yana mai gyara zaman sa akan kujera, yayin da su kuma su mai martaba suka zuba masa ido suna masu kallon su tare da sauraran sa fuskar su ɗauke da murmushi, ba tare da sunce komai ba. Tukun shi kuma ya ɗora da faɗin. "Ba komai bane ba kuwa face soyayyar dake atsakanin yarinyar wurin mu, wato bilkisu ƴar wurin mai girma Gwamna, da kuma yaron wurin ku Yarima Asad." "Asad kuma!" Suka haɗa baki su duka ukkun suna masu faɗin haka fuskar su cike da tsantsar mamaki, domin kuwa cikin su duka babu wanda bai san halin Asad ba na rashin son aure, dan kuwa babu yarce ba'ayi ba da shi akan su futar da matan aure amma shi yaƙi sai Al'amin ne kawai ya futar da tasa. "Tabbas kuwa Asad naku da Bilkisu, dan kuwa ataƙaice sun ɗauki tsawon shekaru kusan huɗu suna atare, hakan yasa mukaga amai-makon su zauna suna ta abu ɗaya gwanda ace kawai anyi mai duka kowa ya huta, wannan shine dalilin da yasa muka buƙaci zama daku." Yaƙarasa maganar yana mai sakin murmushi. "Masha Allah! Masha Allah!!" Galadima da Waziri suka faɗa gaba ɗayan su fuskar su ɗauke da murmushi, tukun daga bisani suka sake buɗe baki atare suna masu faɗin. "Haƙiƙa munyi matuƙar jin daɗin wannan labari daga bakin ku, kuma insha Allah abun bazai ɗauke mu ga dogon lokaci ba ba tare da anyi sa ba, tunda har su yaran sun samu fahimtar juna." Suka sake faɗe fuskar su ɗauke da murmushi. Yayin da shi kuma mai martaba ya sake gyara zaman sa akan kujera, kana daga bisani yayi gyaran murya, tukun ya buɗe baki cikin yanayin sa wanda baka isa kace fariciki yake ba ko kuwa akasin sa, yana mai faɗin. "Masha Allah, naji duk abun da aka tattauna akai, kuma nayi farin ciki da jin hakan, dan haka yanzu sai muyi fatan Allah ya tabbatar mana da alkhairi." Ya ƙarasa maganar da sakin murmushin yaƙe, domin kuwa haka kawai yaji bai wani amunta da zancen su mai girma Gwamna ba, na cewar Yarima Asad na san Bilkisu, gashi shi kuma aransa yana mai jin bazai taɓa iya yiwa ɗan nasa mafi soyuwa acikin ransa auren dole ba, sai dai kuma yasan tunda abun ya zamto ahaka to koda tinanin sa ya zamto gaskiya na Asad baya son yarinyar babu yarce zasuyi daga shi har Asad ɗin dole suyi haƙuri ayi, domin ko shi dai bazai iya buɗar baki yace bazai haɗa jini da mai girma Gwamna ba, hakan shine ya sanya gaba ɗaya yaji yana yin sa ya sauya, sannan kuma ya ƙudiri aniyar samun Asad da maganar dan yaji ta bakin sa ayau yau ba sai gobe ba. Ta fannin Alhaji Saleh kuwa cikin farin ciki ya buɗe baki yana mai faɗin. "Amin Amin." Yayin da shi kuma mai girma Gwamna yake ta sakin murmushi ba tare da yace komai ba, duk da yarce yake son tun ɗazu ya buɗe baki yayi wa mai martaba bayanin abun da Yarima Asad yake yiwa Bilkisu tare da kashedin ajamasa kunne, sabo da jin da yay Alhaji saleh baiyi magana akan hakan ba, sai dai kuma da zarar ya kalli mai martaba danniyar ya buɗe baki yay masa magana akan hakan sai yaga ya masa wani irin kwarjini acikin idanuwa, hakan yasa yake ta ruƙon maganar acikin sa tun ɗazu duk da yarce yake son ya furta ta ba tare da yayin ba. Sun ɗauki kimanin mintina talatin zuwa arba'in suna tattaunawa, tukun daga ƙarshe suka yiwa juna sallama su mai girma Gwamna suna masu miƙewa suka doshi hanyar waje. *JAHAR KAGUL CIKIN MASARAUTAR FULƊE.* Cikin sauri Gimbiya Haddiyal ta ƙarasa cikin ɗakin ta, direct ta doshi ƙofar ɗakin da kayan tsafin ta na gado suke aciki, tana mai zuwa ta buɗesa, tukun ta mayar da sandar nan tata awurin data ɗauke ta tana mai ɗaukar farin ƙyallan da ake rufe ta da shi ta lulluɓe ta, sannan ta sake juyawa cikin sayri tana mai fucewa daga cikin ɗakin, kana ta doshi hanyar da zata sadata da fallo dan taje ta sanya atatso madara. "Barka da futowa yake kyakkyawar Gimbiya." Wata matashiyar Baiwa da take share cikin tafkeken falon ta faɗa tana mai ajiye tsintsiyar hannun ta ƙasa tare da zube giuwoyin ta aƙasa alokacin da Gimbiya Haddiya ta futo daga cikin ɗaki. "Am, kiyi maza yanzu-yanzu ki tashi ki tafi wurin majiaɗin shanu, ki sanar da shi cewar ina buƙatar sabuwar madara cikin ƙwarya ukku kafun nan da giftawar da ƙiƙa talatin gaba." Gimbiya Haddiyal ta faɗa tana mai kallon Baiwar dake durƙushe agaban ta ba tare data amsa gaisuwar da tai mata ba. Yayin da ita kuma baiwar ta miƙe da sauri tana mai nufar hanyar da zata sadata da waje. Tukun ita kuma Gimbiya Haddiyal ta juya tana mai komawa cikin ɗakin ta. Tana shiga ta huce gaban wata wadrobe ta ƙarfe mai azabar kyau ruwan zuma da take ajikin bangon ɗakin. Hannu tasa ta buɗe ta tana mai zaro wani farin towel mai ɗauke da lallausan gashi jikin sa, tukun ta maida murfin ta rufe sa, kana ta juya tana mai dosar hanyar da zata sadata da bathroom ɗin da yake acikin bedroom ɗin nata ba tare da ta tsaya cire kayan jikin ta ba, gaba ɗaya tana komai ne cikin sauri duk da yarce ranta yake amatuƙar cunkushe da baƙin ciki. ***** Misalin ƙarfe shaɗaya da rabi na safe motocin su Babban Yaya suka shigo cikin Masarautar Fulɗe, kasancewar gudu sukayi bana wasa ba, domin kuwa tafiyar kusan awa biyar ce har da rabi, amma su sukayi ta acikin awa biyu da ƴan mintinu. Tunda suka shigo garin Yarima Asad yake aikin yamutsa fuska tare da wurga kallon ƙasƙanci acikin sa, domin kuwa gaba ɗaya ji yay bazai taɓa iya rayuwa acikin wannan bagidajen garin ba, wanda ya kasance babu wasu wayayyun mutane acikin sa. Banda aikin yamutsa fuska da taɓe baki babu abun da yake yi, yayin da shi kuma Al'amin yake ta sakin zuba yana mai faɗin. "Agaskiya garin nan yayi, domin kuwa ba ƙaramar ni'ima Allah ya wadata su da ita ba, kaga fa yarce suke da wata irin daddaɗar iska, ga ruwaye da suke ta faman gudu, tabbas mutum na garin nan dole ma fatar jikin sa tai ta ƙare kyau akoda yaushe, domin kuwa daga gani su basu san mece rana bama." Ya faɗa idanuwan sa akan hanyar da suke wucewa yana mai kallon ta ta cikin glass. Yayin da shi kuma Yarima Asad ya rumtse idanuwa yana mai jin tamkar ya mammake Al'amin dan takaicin furucin sa, sabo da shi kwata kwata baiga wani abu da ya birge sa acikin garin ba, sai zallar haushi da ya basa ma, domin kuwa ya fuskanci hatta da mutanen cikin sa kusan dukan su duk ƙauyawa ne. Aƙarshe ma da ya gaji da jin surutun Al'amin earpiece ya zaro acikin aljihun sa yana mai sanya ta cikin kunnuwan sa ya doɗe su da ita. Ahaka har suka ƙarasa cikin Masarautar Fulɗe wacce take cike da abubuwan burgewa da kyan gani acikin ta, sai dai ta fannin Asad kuma har yanzu bai ga abun da ya burge saba acikin Masarautar. Tun daga bakin ƙofa wasu dogarawa suka tarbe su cikin tsantsar girmamawa, sanye suke da kayan fulani, hannuwan su kuma riƙe da sandina, daga nan kuma suka yi musu jagora zuwa fadar Lamiɗon Masarautar Fulɗe. Kallo ɗaya Yarima Asad yayiwa mutanen nan da suka zo tarbar su, daga nan kuma ya ɗauke idanuwan sa akan su ba tare da ya sake kallon wani daga cikin suba, dan ko gaba ɗaya ƙyanƙyamin su ma yaji shi, sabo da suturar dake sanye ajikin su, wacce yayiwa laƙabi da ta mahaukata ayanzu daga kallo ɗaya da yayi musu acikin zuciyar sa. Dasauri Babban Yayan su Gimbiya Haddiyal wanda ake kira da Jauron masarautar Fulɗe yazo ya tarbe su cikin tsantsar mutun tawa, tukun daga nan ya shige gaba suna masu dosar cikin fada da take ɗauke da kayan ado na fulani tako ina gadan gadan. Sosai Masarautar tayi matuƙar birge Al'amin, tayarce har yake jin ina ma ace sai sun kwana biyu tukun zasu barta, yayin da shi kuma Yarima Asad yaji gaba ɗaya wurin ya gundure sa, kana ko kaɗan bai ga wani abun burgewa ba acikin sa sai zallar ƙauyanci da yake gani. Iso akayi musu har gaban Lamiɗo da yake zaune akan wata irin kujerar Al'farma ta ƙarfe mai azabar kyau, sanye yake da kaya irin na fulani, amma na sarauta tare da Alkyabba wacce ta kasance ta fulani ɗauke ajikin sa, sai farin rawani da yake ɗaure akansa, farine tas da shi yarce kasan ataɓasa jini ya ɓullo, kamar yacce duka ƴaƴan sa suka kasance suma. Yayin da gefe da gefen sa kuna da gaban sa mutanen fada suka kasance zaune awurin. Zama su Babban yaya sukayi akan shimfiɗar kafet ɗin da take agaban su suna masu kwasar gaisuwa awurin Lamiɗo. Cikin mutun taka da far'a ya amsa musu fuskar sa ɗauke da tsantsar annuri, sannan daga ƙarshe suka sake gabatar da abun da yake tafe da su. Gyaran murya mai martaba Lamiɗo yayi, tukun ya furta munji komai kamar yacce kuka faɗa arubuce, dan haka yanzu kai Jauro ka tashi ka kai su wurin cin abinci, inyaso idan sun gama sun huta sai su dawo ayi ciniki." Ya faɗa yana mai kallon Babban ɗan sa wanda zai kai kusan shekaru arba'in aduniya. Amsa masa yayi da tom shima, tukun ya miƙe suma su Babban Yaya da su Yarima Asad da yake ta faman yamutsa har lokacin suka take masa baya. Suna futa waje Jauron Masarautar Fulɗe ya hangi ƙanin sa mai suna Habu, mai kimanin shekaru talatin aduniya, wato sa'an su Yarima Asad dai. Ƙwalla masa kira yayi da ƙarfi, cikin sauri Habu ya ƙaraso wurin da suke yana mai faɗin. "Barkan ku da zuwa baƙi." Fuskar sa ɗauke da murmushi yana mai kallon su Yarima Asad. Idan ka gansa kai bazaka taɓacewa ɗan nan cikin Masarautar bane, domin kuwa sosai yake awaye shima, kasancewa yayi karatun boko har matakin degree shi. "Yawwa." Babban yaya da Al'amin suka faɗa cikin far'ah, yayin da shi kuma Yarima Asad ya faɗa ƙasa ƙasa ba tare da ya kalle sa ba. "Yawwa Habu ga abokai nan kaja su ku tafi cikin lambu, sannan ka tabbatar an samar musu abinci da madara yanzu yanzu" "Tom shikenan Hamma." Habu ya faɗa yana mai sake miƙa musu hannu suka sake yin musabaha, tukun yace ku tawo muje ko. Jerawa sukai suka tafi suna tafiya suna hira da shi da Al'amin cikin raha, yarce kasan sun san juna dama. Yayin da shi kuma Yarima Asad yayi shiru yana sauraran su kawai ba tare da yace komai ba, ahaka har suka ƙarasa cikin wani ni'imtaccen lamubu mai ɗauke da korayen ciyayi tare da sanyi acikin sa. Direct sukayi kan wata shimfiɗar Al'farma ta fata da take ɗauke da tum-tum akan ta daga can nesa. Tunda suka shigo masarautar Fulɗe Yarima Asad baiga wurin da ya burge saba sai wannan kaɗai, hakan yasa ya jujjuya yana mai kai idanuwan sa ko wane sashe dake cikin wurin, tukun ya maida idanuwan sa kan shimfiɗar da suka ƙarasa gaban ta yana mai cire takalman dake sanye aƙafar sa ya hau ya zauna, kamar yacce Al'amin da suke uwar hira da Habu suka zauna. Kishingiɗa yayi jikin tum-tum ɗin dake gaban sa yana mai lumshe idanuwan sa ba tare da yace komai ba. Kallon sa Habu yayi fuskar sa ɗauke da murmushi, tukun daga bisani ya buɗe bakin sa yana mai faɗin. "Shin wai kai ɗin Bebe ne amma ko?" Ya ƙarasa maganar cikin raha. Wara idanuwa Yarima Asad yayi akansa yana mai sakar masa murmushin yaƙe, still ba tare da yace komai ba, yayin da shi kuma Al'amin ya buɗe baki yana mai faɗin. "Bebe ko kuma miskili ba." Ya faɗa yana mai hullawa Yarima Asad da ya zaro wayar sa yana shafawa harara. Yayin da shi kuma Habu ya saki dariya yana mai faɗin. "Any way, ga dai abinci nan yanzu kuci tukun sai acigaba da hirar." Ya faɗa yana mai fara buɗe haɗaɗɗun kwanukan da suke jere akan tray. Farfesun naman ciki ne dana kaji da suka gaji da haɗuwa suna ta faman tashin turiri da ƙamshi acikin kwanika biyu da suke daga farko, sai kuma wani haɗaɗɗen kwandon kaba da yake ɗauke da Tufa, Inibi, Ayaba, Lemo, acikin sa da matuƙar yawa. Bubbuɗe kwanukan duka yayi yaga babu madara kwata- kwata awurin. Hakan ne yasa sa miƙewa yana mai kallon su tare da faɗin. "So sorry dan Allah fa, ashe wai basu kawo madaraba, but please ku ɗan jirani yanzu bara naje naji dalilin da yasa ba akawo ba." Ya faɗa yana mai miƙewa ya juya ya tafi ba tare da ya tsaya jin ta bakin su ba. Bai tsaya ako ina ba sai acikin ɗakin Haddiyal da take zaune agaban madubi tana mutsikka mai afatar ta. Da sauri ta juyo bayan ta tana mai kai idanuwan ta bakin ƙofa sabo da motsin da taji. "Mai ya hana kisa akaiwa baƙi madara amatsayin ki na shugabar shanu, bayan kuma nasan an sanar miki da zuwan su tun kafin yau?" Ya faɗa yana mai kafeta da idanuwan sa. "Kayi hakuri dan Allah Hamma, wallahi na sha'afa ne, amma nasa atatso ta tun ɗazu, kuma yanzu haka nasan an gama ma ƙila ma sun shigo da ita, dan haka bara na sanya kaya sai naje nasa akai madarar." Ta faɗa tana mai miƙewa ta doshi gaban wadrobe ɗin ta. "A'a kawai ke yanzu abun da za'ayi shine, idan kin sa kayan kije ki ɗauki madarar ki kaita lambun gaban sa, ni kuma yanzu bara naje na ɗauka na kai lambun yamma inda su Hamma Jauro suke, domin kuwa har baƙin sunzo tun ɗazu gashi ba akai musu madara ba." Ya faɗa yana mai juyawa. "Tom shikenan Hamma Habu." Gimbiya Haddiyal ta faɗa tana mai sanya hannun ta acikin wadrobe ɗin ta. "Ki fa yi sauri, sabo da sun riga sunzo harma sun zauna." Ya faɗa yana mai ƙarasa fucewa daga cikin ɗakin. Yayin da ita kuma ta fara sanya kayan da ta zaro farare na fulani, amma bawai na sarauta ba cikin sauri. Tukun ta ƙarasa gaban mudubi tana mai kama uban gashin kanta da yake baƙiƙƙirin atsafe ta tufke sa wuri ɗaya, sannan ta ɗauki man leɓe kaɗai ta goga akan pink lips ɗin ta. Sosai tayi matuƙar kyau yarce kasan sarauniyar kyawu ta duniya, duk dama ba wata kwalliya ce ke ɗauke afuskar ta ba, yayin da gashin kanta da ta tufke sa kuma ya zubo har gadon bayan ta ya kwanta. Cikin sauri ta juya tana mai kama hanyar da zata sadata da waje, bayan tasanya wani plat shoe aƙafar ta ba tare data ɗaura ɗankwali ba. *ƘASAR MALIN, JAHAR KARFUZ CIKIN BAƘAR MASARAUTA.* Ahaka suka cigaba da shigowa cikin filin kafaɗun su ɗauke da iccina masu matuƙar yawa, suna masu dosar wurin da abun bauta Gargabilu yake. Ahaka har akazo kan Bir da ya shigo shima kafaɗar da ɗauke da nasa iccinan da baya da baya, yana mai faman ɗirkar rawa daga shi sai farin ƙyalle ɗaure aƙugun sa. Wani irin murmushi Gimbiya Tasmir ta saki alokacin da taga shigowar Bir cikin filin, tana mai cije leɓen ta na ƙasa. Yayin da su kuma bayin nan daga mazan su har matan su suka cigaba da nufar wurin da abun bauta Gargabilu yake suna masu faɗin. "Gargabilu! Gargabilu!! Gargabilu!!!" Da matuƙar ƙarfi. Duk wanda yaje gaban daɓen da abun bauta Gargabilu yake akai durƙusawa yake kansa sun kuye aƙasa yana mai faɗin. "Godiya ta tabbata gareka ubangjin mu daka nuna mana wannan rana." Sanna su sake yin juyi agaban sa suyi rawa iyakar rawa, tukun su huce zuwa cikin filin nan suna masu dosar inda Sarki da Iyalan sa suke, domin su kai gaisuwa, har lokacin kuma hannuwan su suna riƙe da kaskwayen hutar nan ne. Dasari Gimbiya Tasmir ta miƙe tsaye daga kan kujerar da take alokacin da taga bayin nan sun fara doso hurin da suke, kamar yacce yayin ta biyu maza suma suka miƙe. Tukun suka doshi wurin da wasu irin zura-zuran bulalai suke masu matuƙar tsayi da kauri cikin wani ruwa, suna masu sa hannu suka ɗauke su, sannan suka juyo suna masu dawowa tsakiyar filin nan ta ɓarin da bayi maza suke tawowa suka tsaya cirki cirko. Ahaka har bayin nan suka fara isowa zuwa wurin da suke. Ɗaga bulalun nan suka farayi cikin tsantsar ƙarfi, suna masu antaya musu ita agadon bayan su da ya kasance ko riga babu akansa! Ana zubawa mutum bulalar yake rumtse idanuwan sa da ƙarfi jikin sa na tsamtsar karkarwa, tukun daga bisani ya buɗe baki cikin ƙaraji yana mai faɗin. "Gargabilu! Gargabilu!! Gargabilu!!! Godiya muke!" Sannan ya huce gaba, shima ɗayan da yake agaba ya sake yi masa irin wacce na gaban sa yay masa, kana su huce gaba inda Gimbiya Tasmir take tsaye itama ta yi musu kamar yacce yayin ta sukai musu ba tare da tausayi ba ko kaɗan aranta, ahaka har aka ƙaraso kan Bir da yake ɗauke da iyayen iccina akan sa, jikin sa na rawa da ɗigar gumi. Haka duk yayyen Gimbiya Tasmir suka masa bulalar nan kamar yacce suka yiwa duk waƴan da suka zo kafin shi, sannan ya huce gaba wurin da Gimbiya Tasmir take idanuwan sa durƙushe aƙasa, aƙoƙarin sa na ganin ya cikawa Iya alƙawarin da ya ɗaukar mata na bazai kalli Gimbiya ba, duk da kuwa yarce yake jin wani irin abu na fusgarsa akan ta, amma ahaka ya daure ba tare da ya ɗago ya kalle taba, ahaka har ya ƙarasa gaban ta. Yayin da ita kuma tayi wani irin rumtse ido da matuƙar ƙarfi tana mai yin wasu irin surutai ahankali, bayan ta dunƙule tafin hannun ta, tukun daga bisani ta buɗe idanuwan nata tare da tafin hannun nata tana mai kaisa kan bulalar dake riƙe ahannun ta ta shafeta da shi. Take awurin bulalar ta ƙara wata irin miƙewa tare da banƙarawa tana motsi yarce kasan abu mai rai, tukun Gimbiya Tasmir ta ɗaga ta da matuƙar ƙarfi bayan ta cije leɓen ta na ƙasa idanuwan ta akan Bir, tana mai zambaɗa masa ita agadon baya! Da ƙarfi ya rumtse idanuwan sa jikin sa na tsantsar rawa da karkarawa, sabo da tsantsar azabar da yaji ta ratsa jikin sa wacce bai taɓa jin makamanciyar ta ba, yayin da jini kuma yayi wani irin tsartuwa daga cikin jikin sa yana mai tsalle aƙasa. "Gargabilu! Gargab..." Maganar ta ɗauke daga cikin bakin yana mai sakin ihu lasa-ƙasa, tayarce ya zamto ita kaɗai taji sabo da yarce ta ƙara zambaɗa masa bulalar agadon bayan sa! Wani irin feshin jini jikin sa ya sake futarwa yarce kasan wanda aka tsaga da reza! Tukun daga bisani ya ɗago kansa amatuƙar firgice yana mai watsa manya-manyan idanuwan sa cikin na Gimbiya Tasmir. Ƙara ɗaga bulalar tayi da iyakacin ƙarfin ta tana mai sakar masa ita asaitin wuyan sa, tare da sakar masa wani irin murmushin mugun ta. Amma amai-makon taji yayi ihu kamar yacce yayi ɗauzu sai kawai taga ya dake yana mai sake watsa ƙwayoyin idanuwan sa da suka canza launi daga fari zuwa ja cikin nata, tare da sakar mata wani irin shegen murmushi shima, tukun daga bisani ya lumshe idanuwan sa yana zaro harshen sa ahankali ya lashi gefen bakin sa da shi, sannan ya sake buɗe idanuwan sa akan ta yana mai sake jifan ta da kyakkyawan murmushin sa! Wani irin baƙin ciki ne taji yazo ya caki zuciyar ta da matuƙar ƙarfi, take awurin kuwa ranta yayi matuƙar ɓaci, tayarce har idanuwan ta suka fara canza launi daga fari zuwa ja, tukun daga bisani ta rumtse tafin hannun ta tare da rufe idanuwan ta tana mai buɗe baki tace. "Rai Rai Rai Buuu Hooo Reee!" Kana ta buɗe sa tana mai watsa masa wasu abubuwa da suka bayyana acikin tafin hannun nata akan jikin sa tare da yin gefe da shi. Take ya fara yin wani irin layi awurin yana mai shirin zubar da iccinan da suke ɗauke akafaɗun sa, tukun daga bisani ya fara tafiya adurƙushe cikin tsantsar azabar dake ratsa jikin sa yana mai fucewa daga cikin filin ya doshi wata hanya can daban, har lokacin ƙafadar sa ɗauke da iccinan yana layi, ganin hakan da Gimbiya Tasmir tayi ne ya sanya ta juyawa itama cikin tsantsar ɓacin rai tana mai nufar hanyar da yabi gadan-gadan! *ƘASAR HAUSA, JAHAR KAGUL CIKIN MASARAUTAR FULƊE.* Tana futa daga cikin babban falon nasu taci karo da wata baiwa, hannun ta ɗauke da wata haɗaɗɗiyar ƙwarya wacce take rufe da fai-fan kaba tare da ludayin duma har guda biyu akan ta. Dasauri Baiwar taja baya tana mai faɗin. "Tuba nake ranki ya daɗe, ban san da zuwan ki ba shiya sa na sanyo kaina ciki." Hannu kawai ta miƙa mata tana mai karɓar ƙwaryar ba tare da ta tanka mata ba, tukun ta juya tana mai dosar hanyar da zata sadata da lambun gabas. Tafiya take iska na kaɗa jikin ta, tayarce har gashin ta yake reto agadon bayan ta, sai dai kuma yau ɗin gaba ɗaya bata jin daɗin yana yin garin ko kaɗan, sabo da yarce take cikin tsantsar baƙin ciki, wanda ba komai ne yasan ya ta cikin sa ba sai zuwan Yariman Yamma jiya wurin ta, da kuma mafarkin ta na yau, tare da abun da ta gani alokacin da tayi bincike. Gaba dayan ta jinta take asaɓule yarce kasan babu laka ajikin ta, ahaka har ta ɓulla cikin lambun gabas ba tare da tasan ta shigo sa bama, sabo da yare tayi nisa aduniyar tinanin hanyar zatabi wacce zata sadata da Giɗaɗon ta. Afannin su Yarima Asad suma dukan su babu wanda ya lura da shigowar ta wurin, domin kuwa shi Al'amin farfesun naman cikin nan kawai yake ci yana lumshe idanuwan sa, yayin da shi kuma Yarima Asad har lokacin kansa yake durƙushe idanuwan sa akan wayar sa da yake aikin shafawa. Tafiyar ta ta cigaba dayi cikin sanyi ba tare da tasan taƙamai mai cikin wurin da take bama, ahaka har ta ƙaraso gab da shimfiɗar da suke bata lura da suba, kamar yacce suma ɗin babu wanda ya lura da ita. "Ashhh!" Ta faɗa da ɗan sauti cikin zazzaƙar muryar ta, sabo da yarce taji tayi tuntuɓe da wani abu wanda batasan ko menene shi ba, ga kuma yarce ƙwaryar madarar da take ɗauke ahannun ta mai ɗumi ta suɓuce daga kan hannun nata duka. Atare dukan su suka ɗago kawunan su, shi Yarima Asad cikin tsantsar zafi da ƙuna rai, sabo da yarce ta kifo masa ƙwaryar madara akan duka cinyar sa, yayin da ita kuma ta ɗago domin taga abun da ya tokare ta ta faɗi, suna masu sanya ƙwayoyin idanuwan su cikin na juna! Ƙurr sukayiwa juna da ido ba tare da wani ya iya ƙiftawa acikin su ba, barin ma Yarima Asad da gaba ɗaya yanayin sa ya sauya, tayarce har idanuwan sa suka farayin ja, yayin da ita kuma take kallon sa tana mai jin wata irin tsanar sa da haushin sa na lulluɓe ilahirin jiki da ruhinta, wacce bata san dalilin taba. Ahankali ya janye idanuwan sa daga kan nata yana mai mayar dasu zuwa kan jikin sa da yayi faca-faca da madarar shanu, tukun daga bisani ya sake ɗago su yana mai sake kafeta da su, kamar yacce har lokacin itama take kallon sa cikin wani irin yana yi, yayin da shi kuma Al'amin ya saki baki tare da ajiye naman dake hannun sa yana mai aikin kallon wannan, sannan ya koma ya kalli wannan ba tare da ya iya furta komai ba! *ƘASAR MALIN, JAHAR KARFUZ CIKIN BAƘAR MASARAUTA.* Gaban wani tafkeken dutse Bir ya watsar da iccinan, yana mai komawa jikin sa daga gefe ya durƙushe aƙasa tare da rumtse idanuwan sa da tsantsar ƙarfi. "Shin ka shirya faɗamun amsar tambaya ta ayau, ko kuwa har yanzu taurin kan naka bai ƙare ba ƙasƙantaccen Bawa mara galihu!" Sautin muryar ta ya daki dodon kunnen sa ba tare da yay zaton jin saba. Take awurin kuwa yaji wata irin jarumta ta zomasa agaba ɗaya ilahirin jikin sa. Ahankali ya fara ɗago ƙwayar idanuwan sa yana mai sauke su akan fuskar ta, tukun daga bisani ya mayar dasu zuwa kan ɗan ƙaramin bakin ta da take futar da munanan kalamai akan sa daga cikin sa. Wani irin abu yaji yana fuzgar sa zuwa gare ta wanda bai taɓa jin makamancin sa ba, hakan ne yasa ya sake kafe ɗan ƙaramin bakin ta da idanuwan sa yana mai cigaba da kallon yarce take motsa su, tare da yarce jajayen laɓɓan dake akan su suke futar da ƙyallin man leɓen da aka shafa musu alokacin da ake mata kwalliya. Ko kaɗan bai san lokacin da ya fara yunƙurin miƙewa ba, sai dai kawai jin sa da yayi tsaye akan ƙafafuwan sa, sabo da yarce yake jin wani irin abu na fuzgar sa zuwa gare ta, ta sanadin jajayen laɓɓan ta da yake kallo. Ahankali ya fara ɗaga ƙafafuwan sa da suke tsartuwa jini yana mai dosar inda take. Yayin da ita kuma ta kafe sa da idanuwa tana mai yin shiru dan taga abun da zai aikata da ya miƙe yayo kanta Ganin da tayi yana gab da haɗe jikin ta da nashi ne ya sanya ta fara ja da baya da baya ba tare da tasan lokacin da ta fara yin hakan ba tana mai kallon cikin idanuwan sa. Yayin da shima ya cigaba da biyo ta har lokacin idanuwan sa ƙur akan laɓɓan ta, ahaka har ta ƙarasa jikin bango. Cigaba da matsawa yayi gare ta gadan -gadan. Dasauri ta kalle sa tun daga saman sa har zuwa ƙasa, tukun ta sake sauke idanuwan ta akan faffaɗan ƙirjin sa da yake cike da yalwatacce gashi akan sa, gashi dama babu riga ajikin sa. Wata irin faɗuwar gaba taji ta ziyarce ta wacce bata taɓa jin makamanciyar taba dan suna tare da shi, hakan yasa ta buɗe baki cikin tsawa tana mai faɗin. "Dakata! Dakata nace maka ƙasƙantacce!!!" Wani irin kyau ya ƙara ganin laɓɓan ta sun masa acikin idanuwan sa, sabo da yarce ta ɗaga su, hakan ne yasa sa cigaba da nufar ta har ya zamto yazo gab da ita, tayarce har ƙirjin sa da nata suka fara tokarar juna. Dasauri tayi gefe tana mai shirin hucewa tanan, amma sai Bir yayi sauri ya sanya hannun sa dake futar da jini akan bangon yana mai tokare hanyar da shi, ya zamto bata da hanyar wucewa ko kaɗan, tukun ya sake sanya ƙirjin sa yana mai danne nata da shi, sannan ya fara matsar da fuskar sa ahankali zuwa ga tata idanuwan sa ƙur akan laɓɓan ta. Da matuƙar ƙarfi ta rumtse idanuwan ta adai dai lokacin da taji saukar tausasan laɓɓan sa akan nata, tukun ta dunƙule tafin hannun ta tana mai yin w.................✍ *KAR MUTUM YA SHIGO MUN GROUOP MUDDIN YASAN BAI IYA COMMNET BA, IDAN KUMA KA SHIGO TO FA TABBAS ZAKAJI KA A WAJE.* *MUYI HUTUN K'ARSHEN MAKO LAFIYA, SAI KUMA RANAR MONDAY.* *BAƘAR MASARAUTA* *NA* UMAR FARUQ*D* *PAGE 11* Wasu irin surutai acikin zuciyar ta jikin ta na tsan-tsar karkarwa, domin kuwa ko kaɗan bai bata damar da zata iya yin wani furuci ba, sabo da yarce ya fara shirin tura harshen sa zuwa cikin bakin ta. Cigaba da surutan da take yi azuciyar ta tayi ranta na sake matuƙar dugunzuma, tukun daga bisani ta wara idanuwan ta akan fuskar sa tana mai buɗe tafin hannun ta ta watsa masa wasu abubuwa da suka bayyana acikin sa. Wata irin gigitattar ƙara Bir ya saki tayarce har sai da duka wurin ya amsa, yana mai sakin bakin ta ya zube aƙasa wanwar. Yayin da ita kuma taja baya da sauri tana mai sakin wani irin huci yarce kasan zakanya, ga idanuwan ta da sukayi wani irin jajahur yarce kasan gauta! Cigaba da kallon sa tayi yana birgima cikin yashin dake wurin cikin zafin rai, tana mai jin wani irin bamin ciki da takaici na sake tokare ƙawon zuciyar ta, tukun daga bisani ta fara ɗaga ƙafafuwan ta da suke futar da sautin saraƙuna tana mai yin wurin da yake. Tana ƙarasawa kusa da shi ta ɗaga ƙafar ta ɗaya tana mai harbin cikin sa da ita da matuƙar ƙarfi, tare da sakin huci. "Ina mai tabbatar maka da ka tarowa kanka bala'in da yafu ƙarfin ka, ka tarowa kanka masifar data ƙarfin duka ahalin ka, domin ko nayi rantsuwa da abun Bauta Gargabilu sai na illata rayuwar ka, tunda har kayi gigin kusantar jiki na." Ta faɗa cikin zafin rai tana mai sake ɗaga ƙafa ta harbi cikin sa da ita. Wata irin ƙara ya saki ƙasa-ƙasa yana mai sanya hannu ya dafe cikin nasa da shi, tukun daga bisani ya fara ɗago kansa ahankali-ahankali harya sauke idanuwan sa akan fuskar ta, da gaba ɗaya ta canza yarce kasan ba ita bace wacce take murmushi ɗazu. Sanya idanuwan sa yayi acikin nata, tukun ya sanya haƙwaran sa yana mai taune leɓen sa na ƙasa da su ahankali, kana daga bisani ya sake su yana mai sakar mata wani shegen murmushi, idanuwan sa akanta. Rumtse idanuwa Gimbiya Tasmir ta sakeyi da ƙarfi tana mai girgiza kanta, tukun daga bisani ta juya tana mai miƙar wata hanya ta tafi ba tare da ta sake kallon sa ba. Yayin da shi kuma ya cigaba da birgima acikin yashin da yake, har lokacin kuma jikin sa bai bar futar da jini ba. Ko minti biyar batayi da tafiya ba sai gatanan ta dawo tare da wasu danƙara-danƙaran baƙaƙen maza da suke sanye da baƙin gajeran wando kawai ajikin su, ga wasu irin murɗaɗɗun bulalai da suke riƙe a hannuwan su suna biye da ita abaya. Kallo ɗaya mutum zaiwa ƙartan nan ya yayi matuƙar firgita muddin ba saba ganin su yayi ba. "Daƙiƙa ukku kawai na baku, ku tabbatar kun ɗauke shi daga wurin nan kun kai shi gidan azaba na gefen taku, sannan ku gana masa azaba irin azabar da baku taɓa yiwa wani mahaluki itaba agidan duniya, ku tsoma kansa acikin ruwa, ku kuma haɗa kansa gware da duwar-watsu, sannan kuma kutabbatar kun baɗe duk jikin sa da gishiri bayan kun gama dukan sa, domin ko ina son koda ya iya tashi ya zamto ya na kasa!" Ta fara bawa mutanen da suke biye abayan ta umarni tun kafin ta ƙaraso inda Bir yake kwance, idanuwan ta ƙur akansa. Dasauri sukayi kansa suna masu funciko sa daga kwancen da yake ya miƙe tsaye, tukun ɗaya daga cikin su ya fara shirin saɓa sa akafaɗar sa. "Kul! Kar ka kuskura ka fara ɗaukar sa, domin kuwa ba daɗi nace kajiyar da shi ba, dan haka maza ka dire sa aƙasa, sannan kafara jansa daga nan har zuwa can, kuma bance akaucewa dutse ko bishiya ba, kamar yacce bance abisa ahankali ba!" Gimbiya Tasmir ta faɗa da matuƙar ƙarfi, tana mai ɗaga ƙafarta ɗaya ta dire ta aƙasa, sabo da yarce taga daya daga cikin mutanen nata na shirin ɗaukar sa. Sakin sa yayi aƙasa daga tsayen da yake, tukun ya durƙusa yana mai cafko ƙafar sa da matuƙar ƙarfi, sannan ya fara jansa acikin wurin mai duwatsu suna masu yin gaba. "Ina bazai yuwu ba! Ba zai yuwu ba wallahi! Ta faɗa da wani irin ƙaraji tana mai dafe goshin ta da hannu, tukun daga bisani ta ɗora da faɗin. "Shin akan me zaka hanani hukun tasa Baba? Wane irin daliline da har zai sa bazai kasu ba? Shin meya sa, meya sa, meya sa nace? Me yasa zan barsa ne haka kawai, bayan akkulum rainin sa ƙara hauhawa yake fiye dana baya? Me yasa zaka hanani hukunta sa Baba, gashi nan kajamun, kajamun raini mafi muni daga cikin rainika Baba!" Ta faɗa da wani irin ƙaraji tana mai kaiwa iska naushi, tukun daga bisani ta durƙushe aƙasa kan guiwoyin ta tana mai fashewa da wani irin kukan baƙin ciki. Ita kanta bazata iya tina tsawon shekrun data ɗauka rabon ta da zubda hawaye ba ko kaɗan, kai zama ta iya cewa rabon ta da zubda hawaye tun kafin ayaye ta, amma sai gashi yau itace har da kuka, kukan ma ba irin kuka na hankali ba, kuka irin na tashin hankali. Wani irin suya da raɗaɗi take jin zuciyar ta na mata, idan har ta tuna da yarce wancan ƙasƙantacce Bawan ya haɗa jikin sa da nata, ita da ko fuskar ta ba'a iya kallo, ita da ko sautin takun ta ba'a son sauraro, ita da ake tseren gudu aduk lokacin da aka hangota daga nesa, amma sai gashi ayau an samu wani ya tsaya agabanta harma ya taɓa jikin ta, ya kuma lashi laɓɓan ta, wani, wanin ma kuma Bawa, Bawan kuma ƙasƙantacce mafi muni daga cikin Bayi, Bawa wanda shi kansa bai san asalin saba shi ya karya alkadarin ta, shi ya take kwarjinin ta, sannan kuma yayi fatali da izzar ta, hakan yasa take jin inama ace ubangiji Gargabilu ya karɓi ranta tuntuni kafin zuwan wannan Baƙar ranar gare ta! Hannu tasa tana mai funcikar gashin kanta ta wargaza sa tas daga curen da yake, tana mai cigaba da sakin kuka! Tukun daga bisani kuma ta miƙe tsaye tana mai juyawa ta kai idanuwan ta zuwa hanyar da sukabi da kallo, kana ta ɗaga laɓɓan ta cikin wata irin murya mai amo tana mai faɗin. "Haƙiƙa zan tabbatar maka dani ɗin ba sa'arka bace, tunda har kayi kuskuren shiga gona ta matsiyacin Bawa!" Ta ƙarasa maganar tana mai janye idanuwan ta daga kan hanyar, kana daga bisani ta fara ɗaga ƙafafuwan ta da take jin sun mata wani irin nauyi, ta doshi hanyar da zata sadata da asalin cikin gidan su ba filin Biki ba, domin kuwa tasan muddin ta koma filin biki ahaka dole ne afahimci halin da take ciki, wanda ita kuma bazata so asan hakan ba, sabo da karma Baban nata ya sake sanya mata idanuwa, har ya gano abun da take shirin yiwa wancan ƙasƙantaccen Bawan ya hana ta. *WAI WAYE ADON TAFIYA INJI MU HAUSAWA, DAN HAKA MU KOMA BAYA DOMIN MUJI TUSHEN LABARIN* ƘASAR MALIN, BAƘAR MASARAUTA. Kamar yacce mukaji tun farko, Baƙar masarauta dai ta kasance masarauta ce wacce basu san musulunci ba ko kaɗan, gaba ɗaya mutanen cikin ta basu san Allah ba, asalima suna bauta ne ga wani gunki wanda aka sassaƙe sa tun azamanin iyaye da kakannin su da yake ajiye, yayin da suke amfani da faɗar Vokan su wanda suka ɗauke sa amatsayin waliyin abun bautar su Gargabilu, domin kuwa shine ke sanar da su duk wani abu da zai faru agaba, da kuma wanda zai faru yanzu ta hanyar duban sa da yake, wanda aduk lokacin da yake aikin duban nasa suke faɗin yana saduwa ne da abun bautar su, amatsayin sa na waliyin sa. Shi kuwa wannan bokan ba kowa bane face BOKA MAI HUTAR KASKO! Tsoho ne tukuf mai kimanin shekaru tamanin da tara aduniya, shima kuma ya gaji bokancin ne awurin mahaifin sa, wanda ya mutu yana da shekaru ɗari da ashirin da biyu aduniya shi, sabo da shi kansa bokancin gado ne a Baƙar Masarauta, domin kuwa acewar su jinin waliyin abun Bauta ne kawai ke iya sake zama waliyin sa, kamar yacce ɗan Sarki ne kawai ke sake zamtowa sarki, kuma gaba ɗayan su suna amfani ne da Huta tare da Ƙasa wurin duban nasu, hakan yasa ake kiran duk wanda yake kan karagar ta bokancin da suna BOKA MAI HUTAR KASKO, sabo da ita wannan hutar dake ci acikin kasko itace mai haska masa gaban sa, kuma itace take fara isar masa da duk wani saƙon Gargabilu ga jama'a, hakan yasa ba'a taɓa barin ta ta mutu, ko da yaushe ake cikin ƙara izata a kowane lokaci. Sarki Barbaru shine sarki na talatin alokacin, yayin da Boka mai hutar Kasko kuma ya zamto Boka na goma shabiyar awannnan lokacin. Ko kaɗan ba aɗauki rai abakin komai ba acikin Baƙar Masauta, dan ko ataƙaice ma babu satin dake zuwa ya huce ba tare da an kashe rai sama da ukku ba acikin masarautar, kuma idan an tashi kisan anayin sane acikin bainar jama'a, gaban kowa da kowa, dan kuwa sai anyi sanarwa ma tukun ake ai'watarwa, kuma mafi akasarin kisan da akeyi bawai anayin sa bane kan an ai'kata wani Babban laifi ne ba, asalima ko Sarki ne yazo giftawa ko kuma ɗan sarki muddin bawa ya kuskura ya biyo hanyar, to hukuncin kisa ne akansa, hakan shine dalilin da ya sanya Bayi ke mugun tsoron Ƴaƴan Sarkin tare da shi kansa Sarkin, ga kuma tsafi da suke da shi na masifa, wanda ake basu shi tun aranar da suka zo duniya. Sarki Barbaru yana da mata biyu ne tare da Ƴaƴa biyu maza awancan lokacin. Gimbya Haiwa itace matar sa ta farko, kuma uwar Ƴaƴan sa maza biyu. Yarima Sauman shine ɗan sa na farko, kamar su ɗaya da uban sa sak, basu da bam-banci ko kaɗan, domin kuwa har halayyar sa ma irin ta ubansa ce tun yana ƙarami. Sai kuma Yarima Sairan wanda ya kasance na biyu kuma ƙaramin su, kasancewar ita amaryar Sarki Barbaru mai suna Gimbiya Salwa bata haihu ba, ita kuma Gimbiya Haiwa Ƴaƴa biyu kawai ta haifa duk maza. Gaba ɗaya matan nasa biyu suma ƴaƴan sarakai ne na wasu masarautun, waƴan da al'adun su suka kasance kusan duk iri ɗaya ne. Sosai Gimbiya Salwa take da sauƙin kai fiye da Gimbiya Haiwa, domin kuwa ita Gimbiya Salwa har ta hanyar Bayi tana iyabi idan ta futo zagaya gida, kuma koda ta haɗu da Bawa ko Baiwa akan hanya bata sanyawa akashe su, sai dai kawai tayi gaba abun ta, saɓanin Gimbiya Haiwa da ko hanyar su bata iya bi, ballan tana har ta iyayi musu gafara idan sun haɗu. Wannan kenan. ƘASAR HAUSA, MASARAUTAR WASAI. Sarki Abdallah shine ya zamto sarki na Ashirin acikin sarakan da suka mulki Jahar Wasai. Kamar yadda aka sani mafi akasarin gidajen Sarauta ana samun rikici, hassada, baƙin ciki, tare da munafurci acikin sa, to hakan ma ya kasance acikin Masarautar Wasai, domin kuwa Sarki Abdallah ya taso ne tare da Ƴan uba, wato yayye da ƙanne waƴan da suke uba ɗaya, amma uwa kowa da tasa, kasancewar Margayi Sarki Ahmadu ya auri mata har kimanin huɗu ne. To hakan yasa koda aka fara shirye shiryen naɗa Sarki Abdallah kan karagar mulki abayan mutuwar Sarki Ahmdu aka sha rikici, tare da ƙulalla-ƙullata ta kowace hanya wurin ganin bai hau kan karagar mulki ba, duk da kasancewar sa babban Ɗa namiji kuwa acikin Ƴaƴan Sarki Ahmadu, amma da yake shi ɗin Allah yace zaiyi, haka sukayi duk mugun abun da zasuyi suka gama, kuma yazo ya hau kan karagar mulki. Yayin da awancan lokacin Galadima da Waziri kuma suka kasance ƙannen baban sa duka biyun, sai bayan sun rasu kuma abayan mutuwar sarki Ahmadu, sannan aka naɗa mutum biyu daga cikin ƙannen Sarki Abdallah, waƴan da suka haɗa uba ɗaya akan muƙaman, wato Alhaji Kabir Galadima, sai kuma Alhaji Nuhu aka basa Waziri, yayin da sauran ƴan uwan nasu suma duka suka zamto suna da tasu sarautar. Sarki Abdallah ya kasance yana da mata Ukku ne cif. Gimbiya Huwaila itace matar sa ta farko, ƴar sarki itama awata masarautar, sai kuma Gimbiya Amina matar sa ta biyu, itama ɗin ɗiyar Sarkin wata masarautar ne, sai amaryar sa kuma Gimbiya Khadija wacce akewa lakabi da Fulani, kasancewar ta bafullatana wacce kallo ɗaya mutum zai mata ya fahimci hakan, sabo da tsantsar kyanta tare da hasken fatar ta, duk da dai shima Sarki Abdallah'n Fulani ne na sali suma. Tun kafin ya hau kan karagar mulki suke tare da Gimbiya Huwaila tsawon shekaru goma shabiyar, ƴayan su huɗu suka haifa, sai dai kuma cikin su duka huɗun mata ne babu namiji ko ɗaya. Yarsu ta farko itace Gimbiya Rahama, sai ta biyu kuma mai suna Hafsat, sai kuma Fatima, daga ita kuma sai ƙaramar su mai suna Suwaiba. Sosai jama'ar gidan suka sanyawa Sarki Abdallah ido tare da yin farinci, sabo da ganin da sukai bai taɓa haihuwar Ɗa namiji ba, wanda hakan yasa kowanne suke ta mafarkin wataran Sarautar tana iya juyewa ta koma ɗakin su. Watan Sarki Abdallah ukku da hawa mulki ya sake yo sabon aure, inda ya auro Gimbiya Amina. Sosai hankalin Gimbiya Huwaila yayi matuƙar tashi alokacin da akai auren, domin kuwa tsoron ta ɗaya, shine kar Gimbiya Amina tazo ta haifi magajin Sarki Abdallah ba tare da ita ta ta haifo ba, amatsayin ta na matar farko, yayin da suma duka dangi suka zuba idanuwa suna jiran sukaga da abun da zata fara ita. Sai dai kuma har tayi haihuwa biyu itama Allah bai bata ɗa namiji ba, duka biyun suka zamto mata, Wato Gimbiya Sumayya da Kuma Gimbiya Hafsat. Sosai hankalin jama'ar gidan nasu masu jiran mulki ya sake kwanciya, sabo da ganin haka da sukayi, yayin da masu yin asiri akan hakan suke ganin aikin su naci sosai. Itama Gimbiya Huwaila sosai taji daɗi, sannan kuma hankalin ta ya kwanta, sabo da ganin yarce Gimbiya Amina ta jero mata duka kamar ita, hakan yasa ta cigaba da fatan ta zamto uwar magajin masarauta. Afannin Sarki Abdallah shima sosai abun ya dame sa, ba kuma wai dan baya son su ƴaƴan nasa mata da ake haifar masa ba, sai dai kuma ko banza shima yan son ace ɗan sane zai ɗora daga inda ya tsaya, kamar yacce ya zamto shima ya ɗora daga wurin da mahaifin sa ya tsaya, sannan kuma ko badan mulki bama, yana son ace ya haɗa ko wanne jinsi daga mazan har matan cikin ƴaƴan sa, domin kuwa ko wanne daga cikin su yana da daɗi tare da amfanin sa. Hakan yasa ko shekara biyar ba'a rufa da auren su da Gimbiya Amina ba ya sake yo wani auren. Wato Gimbiya Khadija wacce ake kira da Fulani. Sosai hankalin jama'ar gidan dana kishiyoyin ta ya sake tashi a lokacin da aka kawo ta gidan, ba dan komai ba kuwa sai dan kar suje ita ta haifo ɗa namiji, hakan yasa kusan duk suka duƙufa wurin ganin ba asamu ɗa nimiji ba, itama ta haifo mace kamar yacce sauran sukai, sai dai kuma suna nasu Allah na tashi, haka kuma muddin Allah yace ga yarce yake to babu wanda ya isa ya canza sa, domin kuwa watan Gimbiya Fulani goma shaɗaya dai dai acikin Masarautar Wasai, ta haifo ɗan ta namiji ƙatoto da shi, sannan kuma kyakkyawa mai tsananin kama da ita. Subahanallah, zo kuga yarce aka nuna baƙin ciki ƙarara tare da hassada, haka jama'ar gidan da basu so hakan ta faru ba suka nuna, domin kuwa cikin su harda waƴan da suka kasa zuwa barka da baƙin ciki, dan ko hatta Gimbiya Huwaila da Gimbiya Amina sai bayan anyi Sallah isha suka iya zuwa ganin Ɗa, bayan kuma haihuwar anyi ta ne tun asubar fari, sosai suke jin baƙin ciki yarce kasan su mutu, dan ko ita kanta bayan ishar ma sunje gudun kar mai Martaba yaji labarin basuje ba ya zargi wani abun aransa. Yayin da ta fannin mai Martaba kuma tare da masoyan sa na cikin gidan suka kasance cikin tsantsar farin ciki mara misaltuwa da samuwar ɗa namijin da sukai Koda ranar suna tazo sosai akai shagali irin wanda ba ataɓa makamancin sa ba aduk sauran haihuwar da matan mai martaba sukayi, domin kuwa ko kilisar da akayi anyi tane ta bugawa ajarida, dan kuwa hatta da mai martaba sai da yayi wasa da doki irin wasan da bai taɓa yin makamancin saba tunda ya yake duniya, wanda hakan kuwa ba ƙaramun sosa ran mutane da yawa yayi ba acikin masarautar, haka akasha shagali aka watasar da kuɗaɗe kamar ba neman su ake ba, bayan jinjiri yaci suna. USMAN. Yayin da masoyan sa kuma masoyan mai martaba waƴan da sukai marhabun da zuwan sa da gasken-gaske suka yi masa laƙabi da BABBAN YAYA tun aranar da aka haife sa. Tunda Gimbiya Fulani ta gano akwai masu ƙin dan nata sosai acikin masarautar ta dage dayi masa addu'a ba dare ba rana, sosai ta dage wurin yi masa azikarai irin waƴan da addini ya koyar har da ita kanta, kasancewar ta mace mai matuƙar ililimi da kuma aiki da shi. Yayin da magauta kuma suka dage wurin ganin sun kassara rayuwar sa. Bayan haihuwar Babban yaya da shekara biyu da rabi Gimbiya Fulani ta sake haihuwa, sai dai kuma wannan karan ƴa mace ta haifa, yarinya taci suna Sumayya, bayan ita kuma da shekara wata biyu da rabin ta sake haihuwar wata ƴar, still mace dai ita kuma taci suna Nafisat. Hakan da magautan ta suka gani ne na bata ƙara haihuwar wani ɗa namijin ba yasan ya hankalin su yayi matuƙar kwanciya, domin kuwa ganin su tunda itama bata sakeyo wani namijin ba to abun yazo musu da sauƙi, tunda da zarar sun ɓarar da rayuwar Babban Yaya, ko kuma suka illatasa shikenan ya zamto babu ko ɗaya. Yayin da ita kuma Gimbiya Fulani ta cigaba da dagewa da yiwa ƴaƴan ta addu'a gaba ɗayan su, sannan ta koyawa Babban Yaya su tun baifi shekara ukku ba, kasancewar yanzu shekarun sa sun kai kimanin biyar aduniya kenan. Bayan haihuwar Gimbiya Nafisat kuma Gimbiya Fulani bata sake haihuwa ba, sai sauran matan Gimbiya Huwaila da kuma Gimbiya Amina da suka haifi wasu ƴaƴa matan, kowacce ɗaya har shekaru suka ja sosai. BABBAN ZAURE LOCUS. Azamanin baya Iyayen sheikh Ahmad ba acikin unguwar Babban Zaure locus suke zaune ba, suna cikin wata unguwace wacce ta kasance geto area, da take anan cikin garin Wasai, wato unguwar Ɗan Tanki. Mahaifin sa mai suna Ishak haifaffan cikin garin Wasai ne. Yayin da mahaifiyar sa Aishatu kuma ta kasance bafullatanar daji, makiyaya da suke yada zango awuri kafun su sake yin gaba kuma. Sun haɗu da Ishak ne a watarana cikin wata kasuwa da take akusa da rugar su Aisha da suka yada zango awurin, ita sunzo siyen takalma silifas ita da ƙanin ta mai suna Aliyu, yayin da shi kuma ya raka wani abokin sa siyo kaji, kasancewar kasuwar irin kasuwannin nan da suke ci sau ɗaya arana, hakan yasa idan kaje a ranar kasuwar kusan zaka samu komai, hatta da akuyoyi masu su suna zuwa siyarwa, kuma suna yin sauƙi fiye da yarce ake samun su acikin gari. Shigar su kasuwar kenan sukaci karo dasu har sun siya takalman suna shirin juyawa ita da ƙanin ta. Aikuwa Ishaƙ na ƙyalle ido ya gansu gaba ɗayan sa ya ruɗe, ataƙaice dai haka ya sanya abokin sa suka bisu abaya, bai bari koda wasa sun ɓace musu ba, kuma basu bari sun fahimci su suke bi ba har suka ƙarasa rugar su. Tun daga nesa su Ishak suka hange ta ita da ƙanin nata sun durƙusa gaban wasu mutane guda biyu da suke zaune akan tabarma ƙarƙashin inuwar darbejiya, tare da kur'anai buɗe agaban su, da alamun karatu sukeyi dai, tukun daga bisani sukaga sun miƙe suna masu shigewa cikin wani gida da aka masa shinge da karare, wanda yake ɗauke da bukkoki acikin sa. Hakan yasa su Ishak suka ƙarasa zuwa wurin mutanen nan da suke zaune suna karatu bakunan su ɗauke da Sallama. Gaba ɗayan su rufe kur'anan su sukayi suna sauraran su, tukun abokin Ishak ya koro musu bayanin abun da ya kawo su. Take ko awurin yanayin mahaifin Aishatu malam Audu ya sauya, sabo da jin da yay sunce wurin ƴarsa sukazo, gashi kuma yaga ko kaɗan basuyi masa kama da mutanne rigar tasu ba. Malam Sammani shi ya biye musu suka tattauna sosai, sannana aƙarshe yace suje su dawo bayan kwana biyu, alokacin sun gama yin tunani. Aikuwa ba tare da gardama ba suka tashi suka tafi, tukun shi kuma ya juya ga malam Audu yana mai yi masa nasihohi tare da nuna masa bam-bancin al'adu ko kuma yare bashi ke nufin babu aure tsakanin mutane ba, domin kuwa duk musulmi ɗan uwan musulmi ne. Haka dai yay ta masa nasihohi tare da kawo masa misalai, kasancewar sa malamin sa da yake ɗaukar karatu awurin sa tun da suka sauka agarin, tukun aƙarshe yace masa bincike akeyi shine ke nuni da ko mutum wanene, ba hakanan kawai kai tsaye ake yanke hukunci ba alamarin aure. Ai kuwa tini ya fahimce sa, da yake dama ya riga ya gama amunta dashi, yasan bazai taɓa cutar dashi ba ko kuma wani nasa amatsayin sa na malami. Bayan kwana biyu nayi sai ga Ishak da Abokin sa nan sun dawo kuwa, ai kuwa aranar dai basu tafi ba har sai da suka gana da Aishatu, kuma Alhamdulilah sun samu fahimtar juna cikin sauƙi, sannan kuma sunga canji sosai awurin mahaifin ta malam Audu, domin kuwa shi da kansa ya kawo musu fura da tabarma ya shimfiɗa musu, sannan kuma aƙarshe ya jasu sukaje wurin malam Sammani aka musu duk tambayoyin da za'ayi musu. Ataƙaice dai duka baifi wata biyu sukai da haɗuwa ba aka ɗaura musu aure, aka tafi da Aishatu cikin garin wasai unguwar Ɗan tanki. Gida ɗaya suke da mahaifan sa, sai dai kuma su nasu part ɗin daban yake, wato dai akwai katanga tsakanin su. Sosai suke zaman lafiya da junan su, sannan kuma mahaifan Ishak suke matuƙar ƙaunar Aishatu yarce kasan ƴar cikin su, barin ma mahaifiyar sa Baba Zulai, wanda hakan ko ba ƙaramun daɗi yayiwa mahaifan Aishatu ba alokacin da sukaji labari daga gare ta, tukun bayan bikin Aisha da shekara ɗaya da rabi kuma iyayen ta suka bar rugar su, suna masu sake yin gaba zuwa sosai, domin kuwa gaba ɗaya Ƙasar Hausa ma suka bari da su da shanayen su zuwa Ƙasar Malin, can wani yanki mai suna Jahar RUMAN, alokacin kuma Aisha ta haifi ɗan ta na farko ita da Ishak da suka sanya masa suna AHMAD, suna masa inkiya da mu'allim. Sosai Aishatu tayi kuka, tayi kuka kamar ranta zai futa alokacin da suka yiwa iyayen ta rakiya zuwa bakin ruwa, kasancewar azamanin ana tafiya mai nisa ne ta cikin ruwa ga mutumin da yake neman sauƙi. Bayan haihuwar Ahmad Allah ya sake azurata su da samun wasu ƴaƴan har guda ukku, amma su kuma duk mata ne. Bilkisu, Maimuna sai kuma ƙaramar su Ruƙayya. Dukan su suna da tazarar shekara bibbiyu har da rabi-rabi ne tsakanin junan su. Afannin iyayen Aishatu kuwa tunda suka koma Kasar Malin yankin Jahar Ruman basu kara canza wuri ba, kasancewar nan ɗin sun same sa da tsantsar ni'ima ga kuma wadatar abincin dabbobi acikin sa, sannan kuma mutanen garin mafi akasarin su Musulamai ne masu san ƴan uwan su musulmai, ba kamar yankin Jahar Karfuz ba. Sau ukku Aishatu da Ishak suna zuwa garin abayan komawar su, domin kuwa zuwa na ƙarshe ma har da ɗan su mu'allim da yake da shekara bakwai da rabi yanzu suka je. JAHAR KAGUL, MASARAUTAR FULƊE. Lamiɗo Sulaiman mahaifin Gimbiya Haddiyal shine sarki na goma acikin Masarautar Fulɗe, yana da mata biyu tare da Ƴaƴa biyar. Matar sa ta farko itace Gimbiya Kaɓel, tana da ƴaƴa ukku, na farko shine Ummaru wanda sukewa laƙabi da Jauron Fulɗe, daga nan kuma bayan shi da shekara huɗu ta sake haifo wani ɗan namiji yaci suna Halilu, amma suna kiran sa da Bammi, bayan shi kuma sai Abubakar wanda suke kira da Buba. Yayin da ita kuma matar sa ta biyu take da suna Gimbiya Maraimu, ita kuma tana da ƴaƴa biyu ne duk maza suma, Habibu shine ɗan ta na fari wanda suke sa'nni da Jauro Ummaru, bayan shi kuma ta sake haihuwar wani yaron mai suna Harisu wanda suke sa'anni da Buba, domin kuwa duka tsiran su baifi tazarar wata ukku ba. Sosai Lamiɗo yake matuƙar son samun ƴa mace, hakama kuma afannin matan nasa da ƴaƴan sa suma duk suna son sugan su da yarin ƴa mace, amma sai dai Allah bai basu ba duka yaran maza ne. Ita dai Masarautar Fulɗe ta kasance masarauta ce wacce ko kaɗan mutanne cikin ta basu da ilimin addini, duk da suna ikirarin su ɗin musulmai ne ako da yaushe, sai dai kuma ko kaɗan basa amfani da faɗar Allah, ataƙaice ma ko tauhidi basu sani ba, dan kuwa sun mayar da tsafi ba komai ba awurin su, domin kuwa babu wani Ɗa dake tasowa acikin gidan sarautar harya girma ba tare da ya iya tsafi kala-kala ba, a cewar su wannan itace kaɗai hanya wacce zasu iya kare kansu daga kowanne irin mugun mutum cikin sauƙi. Basu damu da sai sunyi karatun boko ba, domin kuwa ada kwata-kwata ma basu yarda da ita bokon ba, sai daga baya ne abayan haihuwar Buba da Harisu aka samu wasu turawa tare da haɗin goyon bayan gwamnati sukazo har cikin Masarautar suka ƙarayi musu bayani akan boko tare da muhimmancin sa, kuma Alhamdulillahi alokacin sunyi sa'a, Lamiɗo ya aminta da zancen su duk da kasancewar sa mutum mai kafiya da tsayawa akan magana ɗaya. Hakan yasa koda Habu da Harisu sukai wayo aka ɗauke su aka kaisu wata makarantar kwana, wacce ake biyan maƙudan kuɗaɗe suka fara tun daga farko anan. SHEKARA TALATIN BAYA. 1991..........✍ *SHARHI DA TURAWA NAKE BUƘATA DAGA GAREKU FANS, HAKAN SHI ZAI BANI ƘWARIN GWIWAR CIGABA DA RUBUTO MUKU.* *BAƘAR MASARAUTA* *NA* UMAR FARUQ*D* *PAGE 12* *1991* ƘASAR MALIN, YANKIN JAHAR KARFUZ CIKIN BAƘAR MASARAUTA. Gudu suke tun ƙarfin su yadda kasan waƴan da sukai gamo da mutuwa, banda faman sakin haki babu abun da suke yi, ga kuma wani irin gumi dake yanko musu ta kowace ƙafar gashi dake jikin su. Ƴammata ne guda biyu da suke ɗaure da wani ɗan guntun baƙin ƙyalle tare da ƴar ƙaramar riga ajikin su, wato dai sanye suke da shigar su irin ta bayi ajikin su. Gudu suke sosai tun ƙarfin su suna yi suna kallon sama, ahaka har suka ƙarasa cikin Masarautar tasu, amma duk da haka basu dakata da gudun da suke ba sai da har suka sada kansu da cikin fada. Da matuƙar sauri fadawan Sarki Barbaru da yake zaune akan wata arniyar kujera, sanye da wasu irin manyan kaya ajikin sa suka miƙe tsaye suna masu dakawa ƴammatan nan da suka faɗo cikin fadar arikice wata irin gigitattar tsawa. Amma sai dai ko inda suke Ƴammatan nan basu kalla ba sai da har suka dan gana kansu da gaban kujerar da sarki Barbaru yake zaune akai, tukun suka durƙushe aƙasa suna masu sakin haki da tari. Dasauri Fadawan nan suka sake yowa kansu gadan-gadan cikin tsantsar ɓacin rai, amma sai dai tun kafin su ƙaraso wurin kowanne daga cikin su ya ƙame awurin da yake cak, sabo da yarce Sarki Barbaru ya ɗaga musu hannu sama ba tare da yace ƙala ba, yayin da idanuwan sa kuma suka kasance ƙur akan Ƴamnatan bayin nan, yana mai mamakin abun da ya kawo su cikin fadar sa a irin wannan yanayin. Tafukan hannun su suka sanya suna masu dafe ƙirjin su da shi, tukun daga bisani suka sake sunkuyar da kansu ƙasa idanuwan su akan shimfiɗar kafet ɗin da take awurin, kana suka buɗe baki cikin muryar su wacce take ɗauke da tsantsar tashin hankali suna masu faɗin. "Tuba muke ranka ya daɗe, tuba muke da labarin da bakin mu zai furta, domin kuwa mu kan mu mun san bamai daɗin ji bane." Suka faɗa jikin su na tsantsar rawa. Yayin da wani bafade da yake tsaye agefe ya buga musu wata gigitacciyar tsawa yana mai faɗin. "Ku ƙaz....." Tsit yay da bakin sa ba tare da ya ƙarasa furucin nasa ba, sabo da yarce Sarki Barbaru ya sake dakatar da shi ta hanyar hannun da ya sake ɗaga masa. Komawa bafadan yayi zuwa wurin da yake yana mai tsayawa, yayin da su kuma waƴan nan Ƴammatan suka sake buɗe bakin cikin rawar murya suna masu faɗin. Haƙiƙa labarin ba zaiwa kunnuwa daɗin saurara ba, kamar yacce bai mana kyan gani a idanuwan mu muma ba, hakan yasa muke neman gafara gareka ya shugaban mu, domin kuwa ayau ɗin, akuma yanzu munyi mummunan gani ne, irin wanda bamu taɓa yin sa ba!" Suka ƙarasa maganar da sakin haki kansu durƙushe aƙasa, tukun daga bisani suka ɗora da faɗin. "Munga sama ta juye daga fari zuwa wasu kalolin, giza-gizai na juyewa daga kalar su ta farare suna komawa zuwa jajaye da baƙaƙe, gari nayin duhu tayarce har ba'a iya hangen abun da ke agaba, yayin da ruw...." "Kaiiiii!" Sarki Barbaru ya faɗa da matuƙar ƙaraji yana mai miƙewa tsaye daga kan kujerar da yake cikin tsantsar firgici da ruɗu, yayin da su kuma jikin Ƴammatan Bayin nan ya ɗauki wata mahaukaciyar kyarma, tukun daga bisani ya fara ɗaga laɓɓan sa yana mai faɗin. "Shin me hakan ke nufi kenan? Wane irin mummunan laifin aka aikata da har Ubangiji Gargabilu yake shirin yi mana hukunci ta hanyar juyar da mu?" Ya faɗa da wani irin ƙarfi idanuwan sa duk sun futo waje, tukun daga bisani ya sake buɗe baki cikin ƙaraji yana mai faɗin. "Daƙiƙa ukku kacal na baku, kar ku kus-kura ku bari takai huɗu ba tare da kun samo mun tabbacin labarin nan ba." Ya ƙarasa naganar yana mai watsa idanuwan sa akan fadawan sa da suke tsaye cirko-cirko suma duk arikece, tukun ya sake juyawa ɓarin da Ƴammatan nan suke yana mai faɗin. "Ku sani muddin labarin ya suya daga yarce kunnuwa na suka jiyo sa daga bakunan ku, to awannnan karan ni da hannu na zan luma takobi acikin cikkunan ku!" Ya faɗa cikin ƙaraji, tukun ya juya cikin tsantsar sauri yana mai fucewa daga cikin fadar duka, ya ɗauki hanyar da zata sadasa da wurin Boka mai hutar kasko, domin yaji ko yana da masaniya akan zancen, sabo da shi dai tunda yazo duniya bai taɓa jin wani labari makamancin wannan ba. Yayin da su kuma Ƴammatan Bayin nan hankulan su ya sake bala'in tashi. Da matuƙar ƙarfi suka ruƙun-ƙume junan su kamar zasu shige cikin jikin su, suna masu fashewa da wani irin gigitaccen kuka! ƘASAR HAUSA, JAHAR WASAI CIKIN MASARAUTA WASAI. Tun bayan haihuwar Nafisat Gimbiya Fulani bata sake haihuwa ba, sai yanzu da take ɗauke da tsohon ciki mai kimanin watanni takwas har da sati Biyu ajikin ta. Sosai hankalin magautan ta ya sake matuƙar tashi, fargaba da tsoron karta sake haihuwar Ɗa namiji suka cika zuciya da ruhin su, domin kuwa yanzu hakama kullum ƙoƙarin su shine suga bayan Babban yaya, sai dai kuma har kawo yau da yake da kimanin shekara Goma cif aduniya Allah bai basu nasara ba, wanda hakan kuma ba ƙaramu firgita su yayi ba, domin kuwa babu kalar asirin da basuyi masa ba, amma duk abanza bayaci, danko ataƙaice ma sai kyau da farin jini tare da tsantsar hankali yaron yake ƙarawa awurin jama'a. Tun daga lokacin da cikin jikin Gimbiya Fulani ya bayyana gaba ɗaya hankulan magautan su ya sake tashi, domin kuwa ko kaɗan babu wanda yasan da cikin sai dai kawai lokaci ɗaya suka wayi gari suka gansa ya futo, hakan yasa suka sake bazawa wuraren Bokayen su, domin ganin sun lalata cikin tun kan yazo duniya, sabo da atsoron su kar suje namiji ne ba mace ba, sai dai kuma duk abun da sukayi abanza, ko kaɗan baici ba, domin kuwa gashi nan zuwa yanzu har an fara tsumayen ranar haihuwa. UNGUGUWAR ƊAN TANKI. Zaune Aishatu take akan kujera gaban murhu ɗauke da ƙaton ciki jikin ta tana tuƙin tuhu. Yayin da daga can gefe kuma mu'allim da kakar sa mahaifiyar Ishak suke zaune akan tabarma suna hira tana yanke masa farce. Ayanzu haka yana da shekara goma ne cif aduniya, yayin da ƙannen sa mata suma duka sukai girma tare da wayo sosai sosai, sai dai kuma tun daga kan ƴar ƙaramar su Ruƙayya, Aishatu bata sake haihuwa ba, sai yanzu da take ɗauke da ciki mai kimanin watanni takwas ajikin ta. "Anya kuwa lafiya kike Aishatu, domin kuwa gaba ɗaya tun daga jiya nake lura dake duk kin canza, shin ko dai haihuwar ce ta tawo ne?" Kaka ta faɗa tana mai janye ƙafar Ahmad da take akan cinyar ta tana yanke masa farce daga jikin ta, tare da kai idanuwan ta kan Aishatu da take tuƙin tuwon amatuƙar sanyaye. Murmushi Aishatu tayi tana mai cigaba da tuƙin tuwon ta, tukun daga bisani ta buɗe baki tana mai faɗin. "Wata irin haihuwa kuma Baba, cikin da dukan sa yanzu ya shiga wata na takwas ma, kawai dai gaba ɗaya jikina ne nake jin sa ba daɗi tun jiya, ga kuma zuciya ta da take ta yawan tsinkewa." Ta ƙarasa maganar cikin sanyi sosai. "To ai dama jin daɗin jiki ga mata irin ku sai ahankali, tun...." "Assalamu alaikum." Suka jiyo sautin sallamar Ishaƙ wacce ta sanya gaban Aishatu wata irin muguwar faɗuwa, tayarce har sai da ta rumtse ido, yayin da ita kuma kaka tayi shiru da abun da take faɗe ba tare da takai ƙarshe ba. "Wa'alaikum Salam." Suka faɗa atare cikin sanyi, suna masu binsa da idanuwa, sabo da yarce suka gansa ya shigo ba'a irin yana yin da ya saba shigo musu ba. Yayin da shi kuma Ahmad ya miƙe da sauri yana mai ƙarawa kusa da shi ya riƙe yatsun hannun sa, tare da faɗin. "Sannu da zuwa Abba na." Damƙe tafin hannun Yaron Ishak yayi ba tare da ya amsa masa ba kamar yacce ya saba, sai jansa da ya cigaba dayi har zuwa kan tabarmar da Kaka take azaune da yayi. Cire takalman sa yayi agefen tabarmar, tukun ya hau kai ya zauna yana mai lumshe idanuwan sa ba tare da yace komai ba, yayin da Aishatu kuma da kaka suka juyo ɓarin da yake suna masu zuba masa ido, gaba ɗayan su sun kasa yi masa koda sannu da zuwa, sabo da yarce sukaji wata irin fargaba ta lulluɓe su, sabo da ganin sa da sukayi ahaka. Sai da ya ɗauki kimanin mintina biyu rufe da idanuwan nasa, tukun daga bisani ya buɗe su yana mai juyawa ɓarin da Kaka take ya kalle ta, sannan daga bisani ya buɗe baki yana mai faɗin. "Ina yini Umma ta." "Shin meke faruwa ne ɗan nan?" Kaka ta faɗa ba tare data amsa masa gaisuwar da yake mata ba. Lumshe idanuwan sa ya sakeyi ahankali, tukun daga bisani ya buɗe su yana mai kaisu ɓarin da Aishatu take zaune, kana ya buɗe baki cikin sanyi ba tare da ya bari ya kalli idanuwan ta ba yana mai faɗin. "Tawo baro gaban murhun nan, ga huri kizo nan ki zauna Maman Ahmad." Ya ƙarasa maganar cikin sanyi yana mai ɗaga ido ya kalle ta. Wani sanyi taji jikin ta duka ya mata lokaci ɗaya, yayin da ƙafafuwan ta kuma da suke akan kujera taji sun fara mata karkarawa, tayarce har ta kasa tashi daga kai duk da ƙoƙarin yin hakan da take yi. Ganin hakan da Ishaƙ yayi ne ya sanya sa miƙewa tsaye cikin sanyi, yana mai yin wurin da take. Ahankali ya miƙa hannuwan sa yana mai riƙo tafukan hannayen ta duka biyu da su, tukun daga bisani ya ɗagota yana mai miƙar da ita tsaye, sannan ya saki hannun ta ɗaya yana mai riƙe ɗaya sukayi gaba. Zama yayi akan tabarmar dai dai wurin da ya tashi, yayin da ita kuma Aishatu ta zauna daga gaban sa kusa da Kaka, ya zamto suna facing ɗin junan su da shi. Sake miƙa hannuwan sa yayi ya riƙo nata da su, tukun daga bisani ya buɗe baki cin sanyi idanuwan sa akan ta yana mai faɗin. "Shin wane ke bayarwa Aishatu?" Ya jefo mata tambaya yana mai kallon ta. Yayin da ita kuma ta lumshe idanuwan ta tana mai jin zuciyar ta na wata irin tsinkewa, tukun daga bisani ta wara su akan fuskar sa ahankali tana mai faɗin. "Allah mana." Ta faɗa ƙasa-ƙasa jikin ta na ƙara mutuwa. Yayin da shi kuma Ishaƙ ya girgiza kansa alamar na'am, tukun daga bisani ya ɗora da faɗin. "Nasan dukan mu nan mun san mutuwa gaskiya ce, sannan kuma ko wane rai da yake cikin duniya sai ya ɗan ɗane ta, walau yaro, walau babba, tosho da tsohuwa, haka kuma babu wanda yasan lokacin da tasa zata riske sa, da...." "Haƙiƙa ni ɗin musulmace, wacce ta yadda da ƙaddara mai kyau da mara kyau, dan haka kawai faɗamun kai tsaye, insha Allah zan jure suraron koma mene ne, sannan kuma zan rungumi ƙaddara ta da hannu bibbiyu." Ta katse sa daga maganar da yake da faɗin haka jikin ta na tsantsar rawa, dan kuwa ji tai gaba ɗaya bazata iya jiran sa ba har zuwa lokacin da zai gama bayanin sa. Lumshe idanuwna sa ya sake yi yana mai ƙara damƙar tafin hannun ta, tukun daga bisani ya buɗe su, sannan yayi gayaran murya, kana ya buɗe baki yana mai faɗin. "Allah yayiwa Baffah Rasuwa a shekaran jiya da daddare!" Ya faɗa yana mai yin shiru ba tare da yace komai ba, sai idanuwa kawai da ya bita da su yana mai kallon ta, kamar yacce itama take kallon sa idanuwan ta duka awaje, ba tare da tace masa komai ba, domin kuwa gaba ɗaya ma jitai duka natsuwar ta da komai nata sun ɗauke, ga wani irin dum da taji kunnuwan ta da kanta sun mata, ɗan cikin ta kuma na juyawa. Yayin da Kaka kuma ta buɗe baki tana mai faɗin. "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un. La'ilah Haillalahu Muhammadu Rasulullahi Sallalawu Alaihi Wassallam." Tukun daga bisani kuma wasu irin hawaye suka ɓalle daga cikin idanuwan ta da matuƙar gudu, kana ta sake buɗe baki cikin kuka tana mai faɗin. "Shin a'ina ka jiyo wannan labarin ne Ishaƙ?" "Ɗazu nima ina zaune akasuwa, ɗaya daga cikin mutanen da suke can ƙasar tare yazo mun da labarin, domin kuwa yace ma tun a jiya da sassafe bayan anyi jana'izar sa ya tawo, wuri na ya fara sauka." To yanzu yana ina ne shi ɗin?" Cewar Kaka tana kallon sa. "Na ajiye sa ne a shagon ƙofar gida, sabo da da haka yace ayau zai juyama nine na hana sa tafiya, nace ya bari zuwa gobe sai mu tafi tare." Shiru sukai dukan su ba tare da sunce komai ba, sai uban tagumi da kaka ta buga tana kallon Aishatu data zamto tamkar mutun-mutumi awuirin da take, domin kuwa tun daga lokacin da taji furucin sa na farko bata sake iya motsawa daga yarce take ba, asalima gaba ɗaya bata ji sauran bayanan nasa ba ko kaɗan. Sai da ta ɗauki kimanin mintina kusan goma ahakan, tukun daga bisani ta ɗago afirgice tana mai kai idanuwan ta kan fuskar mijijn nata, sannan ta buɗe baki cikin rawar murya tana mai faɗin. "Shin dagaske ne Baffah na ya rasu Abban Ahmad?" Ta ƙarasa maganar wasu irin hawaye masu matuƙar gudu suna ɓallewa daga cikin idanuwan ta. Miƙewa Kaka tayi tsaye tana mai nufar cikin ɗakin ta, hakan da ishak ya gani ne ya sanya sa miƙewa tsaye shima, tukun ya kamo hannun Aishatu yana mai janta sukayi part ɗin su. ƘASAR MALIN, JAHAR KARFUZ CIKIN BAƘAR MASARAUTA. Cikin tsantsar tashin hankali Sarki Barbaru ya doshi hanyar da zata kaisa wurin Boka mai hutar kasko. Sai dai kuma tun kafin yayi nisa ya hango dan-dazon jama'a na ɓullowa hankali atsan-tsar tashe, ga kuma wani irin sauyawa da yaga sama nayi tana rikiɗewa kamar yacce Ƴammatan Bayin nan suka faɗa. Hakan da ya ganine ya sanya sa juyawa baya da matuƙar sauri yana mai dosar wurin da dokunan su suke. Ko daƙiƙa biyu ba baiyi ba daga wurin da yake zuwa ma'ajiyar dokunan. Wani irin tsalle ya buga tun daga nesa, yarce kasan bashi bane jibge-gen mutumin nan, yana mai hayewa saman wani baƙin doki, tukun ya damiƙi linzamin sa da matuƙar ƙarfi yana mai sa hannu ya daki bayan sa da shi. Wata irin haniniya dokin ya saki da ƙarfi, kana ya fara ɗaga ƙafafuwan sa yana mai fucewa daga cikin wurin da tsantsar gudu. Gudu dokin yake yarce kasan zai tashi sama, yayin da jama'a ke cigaba da furfutowa bakunan su ɗauke da ihu tare da kiran sunan Gargabilu. Cikin daƙiƙun da basu zarta ukku ba duka dokin ya ɓulla kwanar da zata kai sa wurin Boka mai hutar kasko. Da matuƙar sauri Sarki Barbaru ya dire daga kan dokin ba tare da ya tsayar da shi ba, hankalin sa na sake matuƙar tashi, sabo da yarce ya hango B.............✍ By UMAR FARUQ*D* *BAƘAR MASARAUTA* *NA* UMAR FARUQ*D* *PAGE 13* Boka mai wutar kasko ya futo daga cikin ɗakin sa amatuƙar ruɗe, yana mai kallon sama, ga kuma yarce garin ke sake rikiɗewa yana yin duhu. Da matuƙar sauri ya dire daga kan dokin, yana mai yin wurin da ya hangi Boka mai hutar kasko. "Shin meke shirin faruwa damu n ya kai Boka?" Sarki Barbaru ya watsowa Boka mai hutar kasko tambaya cikin kakkausar muryar sa, hankalin sa atsantsar tashe. Yayin da Boka Barbaru kuma ya cigaba da juyi yana kallon sama, ba tare da ya kalli ko inda Sarki Barbaru yake ba, ballan tana ya tanka masa. "Na roƙeƙa da abun bauta Gargabilu ka tsaya kai mun bayanin ta inda mafuta take." Sarki Barbaru ya sake faɗa adai dai lokacin da ya ƙaraso gaban Boka mai hutar kasko. "Ni kai na bansan ta inda zan fara ba, domin kuwa lamarin yazo mun alokacin da ban tsammace sa ba, sabo da ko kaɗan abun bauta Gargabilu bai sanar mun da faruwar hakan ba, gashi kuma afahimta ta ta yanzu naga kamar garin ake shirin rusawa tare da jama'a..." Dakata Boka!" Sarki Barbaru ya katse sa da faɗin haka cikin tsawa, hankalin sa na sake bala'in tashi, tukun daga bisani ya fara ɗaga ƙafafuwan sa yana mai ƙara matsawa kusa da Boka mai hutar kasko, sannan ya buɗe baki yana mai faɗin. "Mafuta nake son ka samar mana Boka, ba wai bayanin abun da yake shirin faruwa damu ba, domin ko tun lokacin da wannan labarin ya iso kunnuwa na na fahimce cewar mun aikata babban laifin ne ga Ubangiji Gargabilu, shiya sa har yake shirin hukun tamu ta wannan hanyar, dan haka duk yanzu ba lokacin dogon jawabi bane, kamata yayi ace ko da na ɓullo wurin nan in hangeka agaban Huta da Ƙasa kana ƙoƙarin nemar mana afuwa ba anan ba." Ya ƙarasa maganar da sakin huci. Yayin da Boka mai Hutar kasko kuma ya buɗe baki cikin zafi shima yana mai faɗin. "Haƙiƙa al'amarin ya huce duk yarce kake.zato, domin kuwa cikin duka abubuwan daka lissafo ayanzu babu ɗaya da ya rage banyi sa ba, amma duk basuyi aiki ba, sabo da ita kanta Hutar kasko Bama ta koma, tana futar da jan hayaƙi, wanda hakan ke nuni da cewar kamar wasu al'ummar ne daga wani yankin suke shirin kawo mana farmaki, wannan dalilin shine ya sanya kazo ka sameni awurin nan, sabo da in duba ne dan na gano ta yadda zan ɓullowa al'amarin!" Boka mai hutar kasko ya ƙarasa maganar yana mai kallon cikin idanuwan Sarki Barbaru. Yayin da shi kuma ya juya yana mai kaiwa iska naushi, tare da faxin. "Kai, kai, kai inaaa! Hakan ba zata taɓa faru dani ba wallahi." Ya faɗa da ƙarfi yana mai juyawa ya fara taku daga inda yake zuwa gaba cikin tsantsar sauri, tukun daga bisani kuma ya sake juyowa ahaukace yana mai dawowa gaban Boka Gargabilu, kana daga bisani ya buɗe baki yana mai faɗin. "To yanzu meye mafuta kenan Boka?" "Zan koma ciki a yanzu domin nayi ƙoƙarin ganin mun sadu da ubangiji Gargabilu ayanzu-yanzu, duk da yau ɗin bata kasance ranar saduwar mu ba, amma sai dai kuma babu yarce zamuyi dole zanje nabi wata hanya, domin ganin na sadu da shi, sabo da ya samar mana da mafuta." "To muje mana kawai kafara Boka, domin kuwa na sani ubangiji Gargabilu bazai taɓa barin mu mutaɓe ba, sabo da mun kasance masu ƙoƙarin yin duk wani abu da ya sanya mu muyi." Sarki Barbaru ya faɗa yana mai bin bayan Boka mai hutar kasko da yayi gaba. Ɗakin iccina ne mai ɗan girma dai dai misali, zagaye yake da bakin ƙyalle wanda aka buga tambarim Baƙar Masarauta tako ina na jikin sa da farin fenti, ga kuma kaskwayen wuta da suke ajiye a kowace kusurwa ta cikin ɗakin suna ci da huta, sai kuma wasu uban kayan kari-kitai kala kala marasa kyan gani da suke ako wane wuri dake cikin ɗakin. Yayin da daga can jikin bango kuma akayi wani ƙaton daɓe mai matuƙar tudu, domin kuwa harda matattakalar hawa manne ajikin sa. Daga saman daɓen kuma Sassaƙen gunkin nan wanda suke kira da abun bautar su ne kafe awuri ɗaya, ɗauke yake da kayan ado kala kala manne ajikin sa, sai daga can gefen sa kuma aka ajiye wata shimfiɗar fata tafkekiya, yayin da kowacce kusurwa dake kan shimfiɗar kuma ta kasance ɗauke da kaskwayen Huta waƴan da suke matuƙar ci da huta, sai dai kuma kamar yacce Boka ya faɗa gaba ɗaya hutar suna futar da jan hayaƙi ne, yayin da kalar hutar kuma ta kasance baƙa! Acan kuwa tsakiyar shimfiɗar mazaunin Boka mai hutar kasko ne awurin. Gaba ɗaya layayoyi ne da ƙulluka kala-kala zagaye da mazaunin nasa, yayin da daga gaban sa kuma aka ajiye wata randa da take faman ci da huta itama, sai akusa da ita kuma aka ajiye wani ƙaton faranti da yake ɗauke da farin yashi acikin sa mai matuƙar yawa. "Shin yanzu ka fahimci abun da nake sanar da kai ko, kaga yadda kalar Hutar kasko ta koma, abun da bai taɓa faruwa ba tun kafuwar mu duniya, wato canzawar Hutar kasko." Boka mai hutar kasko ya faɗa afirgice yana mai kallon Sarki Barbaru. "Tabbas ko al'amari nada matuƙar ruɗarwa, dan haka na roƙe ka da abun Bauta Gargabilu kayi gaggawar fara aikin nan, tun kafin ƙwaƙwalwar kaina ta tarwatse, domin kuwa al'amarin baƙaramun ruɗar dani yayi ba." Cewar Sarki Barbaru awani irin hargitse. Dasauri Boka mai hutar kasko ya cigaba da tafiya yana mai nufar kan daɓen nan. Take masa baya shima Sarki Barbaru yayi cikin sauri. Cikin hanzari yasa hannu yana mai fara fincikar wasu layoyi daga cikin layoyin da suke awurin da matuƙar yawa, adai dai lokacin da ya zauna awurin. Yayin da Sarki Barbaru ma ya samu wuri akan shimfiɗar ya zauna, yana mai cigaba da bin hutar kasko da idanuwa. Wasu manya- manyan layoyi ya ɗauko har guda ukku yana mai ajesu agefe, tukun daga bisani ya juya ɓangaren da wasu karikitai suke yana mai sa hannu ya ɗauki wani ƙaton ƙullin tsumma ya a jesa agefe, sannan ya juya yana mai kai idanuwan sa tare da yatsun sa zuwa cikin farantin dake agaban sa. Akan yashin dake cikin farantin ya ɗora yatsun sa biyu, tukun ya fara wasu zane zane akan yashin yana mai furta wasu kalmomi da ƙarfi, bayan ya rumtse idanuwan sa. Ya ɗauki kimanin daƙiƙa kusan ukku ahaka, tukun ya buɗe idanuwan sa yana mai kaisu kan zanen da yayi. Jijjiga kansa yayi, sabo da ganin da yay abun ya masa kamar yacce yake so, tukun daga bisani ya juya ɓarin da ya ajiye wannan ƙullin tsuman yana mai ɗaukar sa, tare da layoyin da ya aje agefe, tukun ya miƙe tsaye cak yana mai tsayawa agaban hutar dake ci acikin kasko. Kwance ƙullin tsuman nan yayi yana mai riƙe sa da hannu ɗaya, yayin da ɗayan hannun nasa kuma ya danƙule layoyin da ya riƙe acikin sa da matukar Ƙarfi, sannan ya kuma ya rumtse idanuwan sa da ƙarfi, kana ya buɗe baki yana mai fara yin wasu irin surutai, tare da fara tsiyaya wannan garin da yake cikin tsumman sa acikin hutar kasko. Yana fara tsiyayawar gaba ɗaya hutar cikin kaskwayen dake cikin ɗakin duka suka mutu atare! Wata irin gigitattar ƙara Sarki Barbaru ya saki da ganin hakan, wacce tayi sanadin da yasa Boka mai hutar kasko ya buɗe idanuwan sa da tsantsar sauri. Da matuƙar sauri shima yaja baya yana mai sakin tsumman da layoyin da suke riƙe ahannun sa, sabo da yarce yaga gaba ɗaya hutar dake cikin kaskwayen sun mace, aƙoƙarin sa na ganin yayi abun da zai yi sanadin saduwar su da Gargabilu, abun da bai taɓa faruwa ba kenan tun wanzuwar su aduniya, wato mutuwar Hutar kasko, domin kuwa kullum cikin ƙara izata ake yi. "Shin meke shirin faruwa da mune haka, mai ya sanya Hutar kasko zasu mutu ne Boka? Shin wane irin bala'ine yake shirin riskar mu, domin kuwa ko atarihi ban taɓa jin ance hutar kasko ta mutu ba, sai yanzu da abun ya faru agaba na." Sarki Barbaru ya faɗa cikin tsantsar ruɗu da matuƙar tashin hankali, yana mai matsawa kusa da boka mai hutar kasko, da yake ta aikin zare idanuwa shima. "Tabbas ba kai kaɗai ba, koni dana fika shekaru ban taɓa ganin hakan ya faru ba, sannan kuma ko atarihi ban taɓa jin ance akwai ranar da hutar kasko ta taɓa mutuwa ba sai yanzu, wanda hakan kuma shike nufi da cewar wannan abun yafi ƙarfin har abun bauta Gargabilu, domin kuwa ta wannan hanyar ce kawai muke da ikon saduwa da shi harya bamu mafuta, amma sai gashinan gaba ɗaya ta toshe hany...." Sautin ihun da suka jiyo awaje da matuƙar ƙarfi ne ya sanya Boka mai hutar kasko tsayawa da maganar da yake, ba tare da yakai ƙarshen ta ba, tukun daga bisani suka fara ɗaga ƙafa suna masu dosar hanyar futa daga cikin ɗakin cikin sauri, dan suga abun da ke shirin faruwa. *ƘASAR HAUSA, JAHAR WASAI CIKIN UNGUWAR ƊAN TANKI.* _WASHEGARI_ Yadda Aishatu taga dare haka taga rana bata iya rumtsawa ba ko kaɗan, sosai mutuwar mahaifin nata ta girgiza ta, sannan kuma tayi matuƙar gigitata, tayi kuka iya kuka yadda kasan ranta zai futa, bata taɓa sanin haka zafin mutuwar iyaye yake da tsantsar raɗaɗi ba, sai ajiya da abun ya risketa. Kwana sukai cir Ishaƙ na aikin rarrashin ta, aƙarshe ma da yaga takasa yin shiru sai ya sanya ta taje ta ɗauro alwala, tazo tai ta sallolin nafula tana mai roƙawarwa mahaifin ta rahama awurin Ubangiji. Suna futowa daga masallacin asuba Ishaƙ yayo gida danniyar yazo ya shirya kayan sa, sannan suyi sallama da mutan gidan, domin kuwa jirgin dake tashi ƙarfe shida na Ƙasar Malin zasubi ayau ɗin, sai dai kuma me, yana shigowa cikin ɗakin yay tsaye awuri ɗaya yana mai bin Aishatu da idanuwa, sabo da yarce ya ganta zaune akan kujera sanye da hijab, ga kuma jakar kayan ta da nashi ajiye agefe, alamun shi kawai take jira ya ƙaraso su tafi, gashi shi kuma ko kaɗan bai tsara tafiyar da ita ba. To ta ina ma zai fara cewa zata bisa irin wannan doguwar tafiyar, wacce har sai an kwana kusan biyu ahanya, bayan ga halin da take ciki. Ya raya hakan acikin ransa daga bakin ƙofar da yake atsaye, tukun daga bisani ya fara takawa yana mai dosar wurin da take, idanuwan sa akan fuskar ta. Yayin da ita kuma ta durƙusar da kanta ƙasa tana mai wasa da farcen hannun ta. Agafen ta ya zauna yana mai miƙa hannuwan sa duka biyu ya riƙo nata da su, tukun daga bisani ya buɗe baki yana mai faɗin. "Amma dai kin san ba tare zamu tafi ba kina cikin wannan yanayin ko Aishatu, naga kin haɗo jakun kuna har guda biyu." Dasauri ta ɗago kanta tana mai kallon sa, kafin daga bisani kuma hawayen da tasamu ta tsayar da su tun ɗazu suka sake ɓallewa daga cikin idanuwan ta da matuƙar gudu, kana ta buɗe baki cikin dashash-shiyar muryar ta tana mai faɗin. "Dan Allah kar kace bazan bika ba Abban Ahmad, domin kuwa muddin banje ba to bazan taɓa samun natsuwa anan ɗin ba. Ina son naje naga su Dada tare da sauran ahalina, ina son naje nayi ta'aziyyar mahaifina, sannan kuma na karɓi gaisuwar sa. Na roƙeƙa da sunayen Allah kyawawa tsarkaka kar kace bazan bika ba Abban Ahmad." Ta ƙarasa maganar cikin kuka. Yayin da shi kuma ya lumshe idanuwan sa yana mai murza tafin hannun ta da suke a cikin nasa, ba tare da yace komai ba, tukun daga bisani ya buɗe idon sa yana mai faɗin. "In banda ke Ummin Ahmad, ke yanzu ahaka yarce kike ai ko nida kaina nace ki shirya kije ya kamata ki tausayawa kanki kice bazaki ba, dan haka ina son kiyi haƙuri har zuwa lokacin da Allah zai saukeki lafiya, sai na ɗauke ku na kaiku dukan ku har yarama insha Allah, dan kuwa ke da kanki kin riga da kin sani wanda ya rasu ya riga da ya rasu, babu tayarce za'ayi ya dawo, sannan kuma koda bakije ba suma baza suji komai ba, sabo da sun san irin yanayin da kike ciki, sab...." "Assalamu alaikum." Muryar Kaka ta ratsa kunnuwan su daga bakin ƙofa, wacce ta sanya Ishaƙ dakatawa daga zancen da yake ba tare da ya ƙarasa ba, yana mai sakin hannuwan Aishatu. "Wa'alaikumu salam." Ya amsa mata yana mai gyara zaman sa akan kujerar da yake. Yayin da ita kuma kaka ta danno kanta zuwa cikin ɗakin bakin ta na faɗin. "Me kuma ya zaunar da kaine har yanzu, bayan kasan irin tafiyar da zakuyi bata wasa bace ba, tun ɗazu nake jiran naji futowar ka amma naji shiru, shi yasa ya nace bara nazo naga abun da ke faruwa." Kaka ta faɗa tana mai zama akan kujerar da take facing ɗin wacce suke akai. "Wai Aishatu har yanzu kia nufin kice baki dena kukan nan ba?" Kaka ta sake faɗa tana mai kallon ta, fuskar ta cike da tausayin ta. Nannauyan numfashi Ishaƙ ya sauke, tukun ya buɗe baki yana mai faɗin. "Dalilin da ya hanani futowa kenan Umma, wai kin ganta nan ta dage sai mun tafi tare, gashi ma har da haɗa kayan ta tayi." Ya faɗa cikin sanyi yana mai kallon mahaifiyar tasa. Jim tayi itama ba tare da tace komai ba tana kallon Aishatu, tukun daga baya ta buɗe baki cikin sanyi tana mai faɗin. "Aishatu ina so..." "Dan Allah, dan rajara fiyayyen hallita, na roƙeƙi Umma kar kema kice bazan je ba, sabo da ayarce nake ji ayanzu muddin banje ba to bazan taɓa samun sauƙi ba acikin raina. Ina son nima naje akarɓi gaisuwar mahaifina tare dani, sanna kuma naga yarce ahalina suke ciki." Ta faɗa cikin kuka bayan ta sauko daga kan kujerar da take, ta durƙushe akan giuwoyin ta gaban Kaka. Yayin da Kaka kuma tayi shiru ba tare da tace komai ba, sai tinani da ta tafi ma tana kallon Aishatu, tukun daga bisani ta girgiza kanta tana mai juyawa ta kalli Ishaƙ, sannan ta buɗe baki cikin sanyi tana mai faɗin. "Ka barta ku tafi tare Ishaƙ, nina sanya ka." Ta faɗa tana mai rumtse idanuwan ta. "Amma Umma bakya ganin ha..." "Dan Allah karkace komai ishaƙ, domin kuwa komai da kake ganin ya faru agidan duniya muƙaddari ne daga Allah, sannan kuma babu wani abu da yake faruwa face dama can Allah ya rubuto zai faru, dan haka kuje wurin Baban ku kuyi masa bayani, muddin yace ku tafi tare to kuje Allah shine zai kare ku, kuma Insha Allah zaku isa lafiya kamar yacce zaku bar nan lafiya." Kaka ta faɗa cikin sanyi tana mai kallon sa. Taune leɓen sa yayi na ƙasa tare da rumtse idanuwan sa, domin kuwa ko kaɗan shi dai bai so Aishatu zata bisa ba, sai dai kuma babu yarce zaiyi, tunda har mahaifiyar sa tace ya tafi da ita bai isa yaja da umarnin ta ba, sai dai kuma azuciyar sa yana fatan Allah yasa idan sunje wurin mahaifin nasa, shi yace bai aminta ba. Miƙewa tsaye kaka tayi tana mai faɗin. "Ni na tafi, sai ku same ni aɗakin Baban ku, kuma kutabbatar kun gama duk shirin da zakuyi yanzu kun futo, sabo da bana son ku huce yau ba tare da kun shiga cikin Ƙasar Malin ba." Ta ƙarasa maganar tana mai fucewa daga cikin ɗakin. Zaman ta keda wuya sai gasu nan suma sun shigo ɗakin bakunan su ɗauke da Sallama, kasancewar dama gaba ɗaya sun riga da sun gama shiryawa tas. Ko da Ishaƙ ya faɗawa Baba yadda ake ciki, shima ɗin sai ya zamto ya faɗi magana irin wacce Kaka ta faɗa. Hakan yasa ba dan ran Ishaƙ yaso ba ya haƙura ya ɗauki jakun-kunan nasu, bayan sunyi sallama da iyayen nasu suna masu yi musu fatan Alkhairi suka tafi. Ƙarfe shida saura dai dai suka isa bakin ruwa. Lokacin da sukaje sun tarar da har an fara shiryawa, domin kuwa duka -duka baifi minti goma ya rage jirgin ya tashi ba, hakan yasa Ishaƙ ya huce cikin sauri yana mai zuwa wurin da ake biyan kuɗi, tare da sauran abubuwa yayi musu komai su ukkun. Tukun suka shige cikin tafkeken jirgin ruwan da yake ɗauke da komai na buƙata acikin sa. Tafkeke ne jirgin ba kaɗan ba, gaba ɗayan sa rufe yake da tamfol saman sa, wato ba'a iya ganin mutanen da suke cikin sa daga waje. Ƙarfe shida dai dai jirgin nasu ya tashi, yana mai ɗaukar hanyar da zaibi ta kaisa Ƙasar Malin a cikin ruwan nan. ƘASAR MALIN, JAHAR KARFUZ CIKIN BAƘAR MASARAUTA. Dan-dazon mutanen cikin masarautar ne suke ta ɓullowa ta ko ina, hankulan su abala'in tashe, banda ihu tare da sunan Gargabilu babu abun da bakunan su ke iya furtawa, sabo da yarce gaba ɗaya garin ya ƙara rikiɗewa yayi wani irin jajahur daga ɓangaren kudu, yayin da ɓangaren arewa kuma ya kasance baƙiƙƙirin, ga kuma ƙasa da take wani irin tashi sama, ƙura na buɗe ko ina da ina. Cikin tsantsar ɗimuwa Sarki Barbaru ya buɗe baki yana mai faɗin. "Kayi wani abun mana Boka mai hutar kasko, kayi wani abun mana tun kafin komai ya ƙarasa lalace." Ya faɗa cikin hargowa yana mai kallon Boka mai hutar kasko. Yayin da shima Boka ya sake ruɗewa fiye da da, sabo da yadda yaga garin nasu na sake juyewa. Da matuƙar ssuri ya juya yana mai komawa cikin ɗakin sa. Ko daƙiƙa biyu baiyi aciki ba sai gashi nan ya dawo hannuwan sa ɗauke da wasu irin layoyi, tukun ya buɗe baki tun daga inda yake yana mai faɗin. "Na tuna da hanya ɗaya da tarage wacce zanbi, domin na samu ganawa da abun bauta Gargabilu, dan haka yanzu maza maza ka biyo ni zuwa bakin daji gaban ruwan ruwa, domin kuwa anan ne kaɗai zanyi iya ai watar da wannan aikin." Ya faɗa yana mai juyawa ya doshi hanyar ba tare da ya jira Sarki Barbaru ba, yayin da shi kuma Sarki Barbaru ya juya cikin sauri yana mai komawa wurin da dokin sa yake. Tun daga nesa ya buga tsalle yana mai hayewa saman dokin, tukun ya damƙi linzamin sa yana mai saita masa hanya. Wata irin zabura dokin yayi yana mai bin hanyar da mahaukacin gudu, yarce kasan zai tashi sama. Yayin da jama'ar nan kuma suke ta cigaba da ihun kiran Gargabilu, hankulan su na tsantsar sake tashi. Acikin daƙiƙun da basu zarta biyar ba Boka da Sarki Barbaru suka isa bakin daji, wanda yake zagaye da wani irin tafkeken ruwa, da ko ƙarshen sa ba a iya hange ta kowane ɓangare nasa. Gaban wani kogo da yake manne jikin wata danƙareriyar bishiya da take manne a gefen ruwa suka ƙarasa. Hannu Boka mai Hutar kasko ya zira acikin kogon yana mai zaro wani baƙin kasko, yayin da cikin kaskon kuma ya kasance ɗauke da wasu irin karikitai kala-kaka acikin sa. Cikin sauri yasa hannun sa yana mai furfuto da duka abubuwan dake cikin kaskon, sannan ya ɗebi wasu daga cikin su yana mai zubawa aciki, kana ya damƙi wata laya guda ɗaya da take riƙe ahannun sa da matuƙar ƙarfi yana mai rumtse idanuwan sa tare da faɗin. "Gargabiluuuu!" Take awurin kaskon nan ya kama da wuta Bal, bal, bal, yana ci yarce kasan wanda aka zubawa fetir acikin sa, yayin da boka mai hutar kasko kuma ya cigaba da kiran sunan Gargabilu da ƙaraji, ta yarce har wurin ke amsawa yana mai haɗawa da wasu irin surutai, har kuma lokacin bai fasa matse layar dake cikin tafin hannun sa. Ƙara tashi hutar nan tayi tana ci sosai, tukun daga bisani harshen ta ya rabu gida biyu daga tsakiyar su wani irin baƙin hayaƙi na tashi, kana kuma daga saman hayaƙin ya zamto kalar shuɗi. Sosai Hutar ta kasu kala kaka har kimanin kusan kala biyar, yayin da Boka mai hutar kasko kuma yayi shiru daga furucin da yake yana mai durƙushewa awuri ɗaya ya nutsu sosai, sai dai kuma har lokacin bai buɗe idanuwan sa ba, kamar yadda bai buɗe layar dake cikin tafin hannun sa ba. Yayin da ta fannin Sarki Barbaru kuma yaji wani rin daɗi, sabo da fahimtar da yay Boka mai hutar kasko ya samu damar ganawa da abun bautar su. Sai da ya ɗauki kimanin daƙiƙa talatin rumtse da idanuwan nasa, tukun daga bisani ya sake miƙewa tsaye yana mai buɗe idanuwan sa, yayin da kalar Hutar nan kuma ta koma ja kamar yacce take tun farko. "Shin meke faruwa ne Boka?" Sarki Barbaru ya jefowa Boka mai hutar kasko tambaya cikin sauri, yana mai matsawa kusa da shi. "Haƙiƙa Al'amarin babba ne kamar yacce na faɗa maka tun farko, domin kuwa ayarce ubangiji Gargabilu ya sanar mun, sannan kuma nima na gani da idanuwa na, muddin bamuyi da gaske ba to komai na shirin rushewa, idan nace kuma komai ina nufin komai da komai." Boka mai hutar kasko ya faɗa yana mai kallon Sarki Barbaru. Yayin da shi kuma kwata kwata ya kasa fahimtar abun da yake nufi ko kaɗan, hakan ne yasa sa ya buɗe baki cikin sauri yana mai faɗin. "Kamar ya komai kenan Boka, domin kuwa har yanzu ban fahimci komai ba daga cikin abun da kalaman ka suke nufi." "Tabbas bazaka fahimta ba ayanzu dama na sani, sai dai kuma ayanzu yanzu zan sanar maka tayarce zaka gane. Da nace maka komai ina nufin komai namu zai lalace, duniyar mu zatazo ƙarshe, tarihin mu zai shafe tun daga na can baya har kawo na yanzu shafewa ta har abada, sunan Baƙar Masarauta zai ɓace acikin littafin tarihin duniya!" "Shin me kake faɗe ne haka mai tsantsar raɗaɗi acikin kunnuwa Boka? Shin taya ya kake ganin hakan zata faru kuwa?" "Ta hanyar barin Jinjirin adoron duniya, ko kuma kashe sa!" "Har yanzu dai ban fahimce ka ba yakai shugaba Boka, na roƙeka da abun Bauta Gargabilu kayi mun yarce zan gane tun kafin ƙoƙon kaina yay bunduga awurin na." Sarki Barbaru ya sake faɗa amatuƙar rikice, da kuma tsantsar ƙaraji. "Kanka bazai taɓa bunduga ayanzu ba, sai dai ko idan daga baya-bayan ka gama jin bayanin abun da ke faruwa, muddin ba asamu mafuta ba, domin kuwa ni ayanzu zan warware maka komai." Boka mai hutar kasko ya faɗa yana mai juyawa yay taku ɗaya, biyu, zuwa ukku daga wurin da yake, tukun daga bisani ya sake juyowa ɓarin da Sarki Barbaru yake yana mai cewa. "Za'a samu shigowar wani baƙon Jaririn yaro namiji ne cikin ƙasar nan tamu, sannan kuma zai huce ta cikin jahar mu, shi kuma wannan jaririn bakowa bane face musiba da bala'i gare mu, domin kuwa ayarce ubangiji Gargabilu ya sanar mun kuma na gani da idanuwa na, shi yaron zai zamto mana musiba da bala'i acikin masarautar mu, domin kuwa zai wargaza ta, sannan kuma zai rusa gaba ɗaya tarihin mu, zai dawo ya yaƙe mu alokacin da bamuyi tsammani ba bayan ya girma, muddin muka barshi ya wuce ta cikin garin nan, domin kuwa gaba ɗaya wannan yanayin sauyawar garin da aka sama ansa mesa ne ta zuwan da zaiyi ya huce ta cikin kwanakin nan, sai dai kuma ni kaina ban san ko awace ranar zai huce ba, amma ayarce ubangiji Gargabilu ya faɗamun shine daga rana irin ta gobe har zuwa nan da makwanni huɗu masu zuwa zai iya hucewa." Boka mai hutar kasko ya faɗa yana kallon sarki Barbaru. "To amma Boka babu wata hanya wacce zamubi mu hana wannan mummunan abun faruwa?" Ya faɗa ahaukace, sabo da yarce duka magan-ganun Boka mai hutar kasko suka sake haukatar da shi. "Akwai abun da za'ayi wanda zai sa agano sa, wannan abun kuma ba komai bane face binciko hanyar da zai bi ya huce ta ita, sannan akarɓe duk wani jariri da aka samu akan hanyar daga hannun uwarsa, bayan an karɓe sa kuma sai akai sa gaban kaskon huta a ajiye sa, daga nan kuma sai aɗaga kibiya ayi kamar za'a caka masa ita aciki, to muddin shine jinjirin zai sanya ƙafafuwan sa ya ture kaskon hutar nan, tayarce har sai ya rabe gida biyu, idan kuma har bashi bane ba, to bazai iya ture sa ba, dan haka sai kawai acaka masa mashin akashe sa duka, idan kuma shine bayan ya ture kaskon, sai aɗauke sa atafi da shi ya zamto Bawa acikin masarautar mu, hakan da za'ayi itace kawai mafuta garemu, domin shine zai zama aƙarƙashin ikon mu, muddin kuma akai kuskuren barin shi ya futa daga cikin masarautar nan, to wajibi ne zai dawo bayan shuɗewar wasu shekaru ya kuma yaƙe mu, sannan yaci galaba akan mu, haka kuma kashe sa ko ba ayanzu ba shima yana dai dai da tashin duniyar mu ne, domin kuwa bani bama, hatta da abun bauta Gargabilu faɗan yafi ƙarfin sa." Boka mai hutar kasko ya faɗa idanuwan sa akan Sarki Barbaru. "To ta wace hanyace shi jinjirin zaibi ya huce ne yakai Boka?" Cewar Sarki Barbaru cikin tashin hankali. "Abun da nima ban sani ba kenan, sai dai kuma bawai zamu zauna bane, a yanzu tashi zamuyi mubi wata hanyar domin mu gano ta sashin da shi jinjirin zai huce, idan kuma har aka kai gobe bamu gano ba, to kawai zamu sanya dakaru su zagaye mana kowace ƙofa ta shigowa garin nan." Boka mai hutar kasko ya faɗa yana mai yin gaba, tukun shima Sarki Barbaru ya bisa abaya, domin suje su cigaba da binciken hanyar da zasu gano ta inda Jaririn zai huce. Kwana sukai cir suna abu ɗaya amma abanza, babu kalar tsafin da Boka mai hutar kasko baiyi ba dan ya gano ta hanyar da Jaririn zai wuce amma baiyi ba. Har sun yanke hukuncin zasu hakura su subi waccan hanyar ta toshe ko wace ƙofar garin, sai kuma boka mai hutar kasko ya tuno da wata hanya da baibi ba acikin duka tsafin da yay. Hakan yasa cikin sauri ya juya ɓarin da Sarki Barbaru yake yana mai faɗin. "Akwai wata hanyar bayan waƴan da mukabi da muka manta bamu yita ba, dan haka yanzu muyi sauri zuwa gaban ƙaramin rafi, domin kuwa anan ne kawai wurin da zanyi aikin." Dasauri Sarki Barbaru ya bisa abaya hankali atsantsar tashe. Gaban ɗan ƙaramin rafin da yake ɗauke da farin ruwa acikin sa Boka mai hutar kasko ya tsaya. Wasu irin abubuwa ya watsa acikin ruwan, tukun ya fara wasu irin mahaukatan surutai yana mai zagaye rafin. Lokaci ɗaya ruwan ya dinga wata irin hautsinawa da matuƙar sauri, tukun aƙarshe wani irin hoton tafkeken ruwa mai matuƙar girma ya bayyana acikin sa. Dasauri Boka mai hutar kasko ya tsaya da surutan da yake yana mai faɗin. "Tabbas munyi nasara ayanzu, domin kuwa ga hoton hanyar nan tazo. Jiniirin zai biyo ne ta tsakanin hanyar data ratso daga Ƙasar Hausa zuwa jahar ruman, dan haka sai muyi maza-maza yanzu mu koma cikin masarauta, domin ahaɗo kan dakaru da kayan aiki mutafi gaban ruwan, tunda babu wanda yasan lokacin hucewar sa." Ya faɗa suna masu juyawa cikin sauri suka tafi. Acan ɓangaren Jirgin su Ishaƙ da Aishatu kuwa, adai-dai wannan lokacin ya.............✍ *BAƘAR MASARAUTA* *NA* UMAR FARUQ*D* *PAGE 14* Ya huce ta ta cikin Baƙar Masatauta aguje, yana mai ɗaukar hanyar da zata kaisa Jahar Ruman kai tsaye. Yayin da su Sarki Barbaru kuma tare da boka mai wutar kasko suka ƙarasa cikin Masarautar a matuƙar ruɗe. Cikin daƙiƙun da basu zarta goma shabiyar ba duka aka haɗa kan dakarun. Wasu irin jibga jibgan baƙaƙen mutane ne da suke sanye da ƴan gajerun baƙaƙen wandina babu ko roga ajikin su, yayin da idanuwan sa kuma suka kasance jajahur babu kyan gani, ɗauke suke da wasu irin makamai tun daga kan takubba, kibiyoyi da dai sauran dangunan su, kallon su kawai ya isa ya sanya mutum firgici, muddin bai saba ganin suba. Gaba ɗayan su suka juya suna masu dosar bakin ruwan nan. Zagaye sa sukayi ta kowane fanni, ya zamto duk ta inda mutum zai ɓullo sai yaci karo da su kafun ya huce, gaba ɗayan su riƙe suke da mugayen makamai. Tsayuwar su keda wuya awurin wani ƙatoton jirgin ruwa ya tawo zai huce, cikin sauri suka hulla wata igiya mai tsantsar girma, wacce take maƙale da wasu iccina ajikin ta, tayarce jirgin bazai taɓa iya hucewa ba sai ya tsaya. Ai kuwa kamar yacce sukai zato, jirgin yana hangar igiyar ya tsaya cak awurin da yake, yayin da mutanen cikin jirgin kuma hankulan su yayi bala'in tashi, sabo da abun da suka gani, ga kuma wasu irin mutane da basu da kyan gani da suke tun karo su gadan gadan acikin nasu jirgin ruwan. Wasu daga cikin dakarun nan ne suka shige cikin jirgin ruwan Baƙar Masarauta, wanda yake zane da tambbarin ta tako ina ajikin sa, hannuwan su riƙe da makamai. Suna ƙarasawa wurin da jirgin ruwan nan yake suka zare makaman su, suna masu nunawa matuƙan jirgin hanyar da zasu bi. Cikin tsantsar ruɗu, tare da firgici, direbobin jirgin ruwan da suka kasance mutum ukku suka juya kan jirgin nasu, suna masu dosar bakin ruwan nan inda su sarki Barbaru suke atsaye. Suna isa bakin ruwan Sarki Barbaru ya buɗe murya cikin ƙarfi yan mai faɗin. "Ina son kuyi maza maza ku shiga cikin jirgin nan, abincika mun ko ina na cikin sa lungu da saƙo, tare da jikin kowace mata da take cikin sa, muddin aka samu jinjirin yaro namiji, to akarɓo sa akawo mun shi nan, idan kuma har uwarsa tayi gardama wurin badashi, ku caka mata kibiya, sannan ku tawo mun da ɗan nata." Ya faɗa cikin wata irin muraya mai matuƙar amo da firgitarwa, yayin da su kuma mutanen cikin jirgin nan hankulan su ya sake bala'in tashi, tayarce har wasu daga cikIn su suka fara sakin ihu, yayin da wasu kuma suka sassaki fitsari awuraren da suke, musamman ma mata. "Duk matar da taƙara gigin barin amon sautin ihun ta ya daki kunne na, to ta sani tabbas ƙarshen rayuwar tane yazo." Sarki Barbaru ya faɗa cikin tsawa, yana mai kai idanuwan sa kan mutanen da suke acikin jirgjn nan. Take kuwa duka wurin ya ɗauki tsit, sai faman muzurai kawai da mata sukeyi. Yayin da su kuna dakarun nan suka afka cikin jirgin suna masu miƙar da duk matar da suka gani tsaye su duba jikin ta. Sai da suka ɗauki kimanin daƙiƙa kusan arba'in suna abu guda, tukun suka gama da wannan jirgin ba tare da sun samu ko mai ciki acikin sa ba, sannan suka basa hanya ya wuce, kana suka koma kan na gaba da aka tsayar, kasancewar masu binciken daban suke, masu yawo acikin jirgin ruwan Baƙar Masarauta suna kaɗo jirgayen dake wucewa bakin ruwan, suma daban ne. *JAHAR RUMAN* Sai yamma liƙis Ishaƙ da Aishatu suka isa jahar ruman, cikin rugar da ahalin Aishatu suke rayuwa acikin ta, bayan kwana ɗaya da yini ɗaya da sukayi akan hanya. Gari ne mai tsantsar daɗi da ni'ima. Bukkoki ne tsalli-tsalli awurare daban daban da suke acikin rugar da suke. Tun daga nesa suka hango mutane da yawa zaune akan tabarmu, ƙarƙashin inuwar bishiyar darbejiya. Jiki asaɓule suka ƙarasa wurin, suna masu durƙusawa agaban tabarmun. Sosai suka yiwa junan su gaisuwa, tukun suka tashi gaba ɗayan su zuwa cikin gidan. _BAYAN SATI ƊAYA_ Yau ta kasance ranar Al'hamis, wacce tayi dai dai da cikar mahaifin Aishatu kwana goma da rasuwa. Tun jiya suka fara haɗa kayan su, kasancewar yau Al'hamis itace ranar da suka tsara zasu koma, amma zasubi jirgin ƙarfe goma na safe ne. Sosai dangin Aishatu suka haɗa musu tsaraba suka ƙulle ta wuri ɗaya. Gaba ɗaya kowa ka kalla dake cikin gidan jikin sa atsantsar sanyaye yake, domin kuwa har kawo yau mutuwar bata sake suba, jinta suke tamkar sabuwa, barin ma Aishatu da take jin jikinta na sake yin sanyi, wata irin kasala na rufe ta, tana mai jin tamkar su fasa tafiyar daga gobe, su bari sai wani lokacin, ga yarce gaban ta ke yawan faɗuwa tun bayan kwana biyu da suka huce, sai dai kuma babu wanda ta faɗawa kalar yanayin da take ciki, kamar yacce babu wanda ya tambayae tama, sabo da kowa na dan ganta sanyin nata ne da cewa mutuwar ce bata sake taba, yayin da ta fannin ta itama take ganin duk hakan ne. Acan Ɓakar Masarauta kuwa yau kimanin sati ɗaya cir kenan da fara binciken jaririn da sukayi abakin ruwa, ba dare ba rana kullum abu ɗaya sukeyi, domin kuwa ko runtsawa harta da shi sarki Barbaru, sabo da gudun karsu kwanta jirgin da jinjirin yake aciki yazo ya huce basu sani ba. Zuwa yanzu sun kashe jinjirayen mutane sama da ashirin da biyar, sabo da duk cikin yaran da suke samu har yau ba'a samu wanda ya tuntsirar da hutar kasko ba kamar yacce Boka mai hutar kasko yace jinjirin zaiyi. *ƘASAR HAUSA, JAHAR WASAI CIKIN MASARAUTAR WASAI.* Hadimai ne kawai ke giftawa ta ko ina acikin masarautar, wasu ɗauke da abubuwa a hannayen su, yayinda wasu kuma suke share-share da goge-goge. Aɓangaren sashin Gimbiya Huwaila, uwar gidan Sarki Abdallah kuma zaune take agefen gadon dake can cikin ƙuryar ɗakin ta. Kallon matar dake zaune aƙasan gado daga gaban ta tayi ido cikin ido, tana mai miƙa mata wani ƙullin tsuma dake riƙe ahannun ta. Miƙo tafin hannun ta matar mai kimanin shekaru hamsin tayi, itama ɗin idanuwan ta acikin na Gimbiya Huwaila. "Ina son ki buɗe kunnuwan ki ki saurareni Jakadiya, domin kuwa awannan karan ba lallai ne na sake yarda dake ba, muddin kika cemun an samu matsala kamar na baya." Ta faɗa tana mai cigaba da kallon ta. "Na ɗauki nutsuwa ta, hankali na, tare da kunnuwa na na miƙa su zuwa gareki yake Gimbiyar Masarautar Wasai, uwar Sarkin mu na gobe insha Allah, dan haka ki faɗi kome nene, ni kuma ina mai tabbatar miki da babu abun da zai hana sa yuwuwa awanan karan da izinin Allah." Matar data kira da Jakadiya ta faɗa tana mai gyara zaman ta awurin da take. Yayin da ita kuma Gimbiya Huwaila ta lumshe idanuwan ta tana mai sake dunƙule ƙullin tsumman ahannun ta, tukun daga bisani ta warasu akan fuskar Jakadiya, sannan ta buɗe baki tana mai yin ƙasa-ƙasa da murya, yadda kasan ba iya suka ɗai bane acikin ɗakin, wurin faɗin. "Wannan ƙullin da kika gani na baki, ba komai bane acikin sa face layoyi tare da garin magani, wanda nake son ayanzu-yanzu da zarar kin futa daga ɓangaren nan kije ki ai'watar dasu, domin kuwa Boka ya bani tabbacin cewa muddin anyi amfani da shi kamar yacce yace, to babu abun da zai hana duk abun da yake acikin cikin ta mutuwa ko mace ko namiji ne kuwa." Ta faɗa tana mai cigaba da kallon ta, tukun daga bisani ta ɗora da faɗin. "Layoyi ne tare da garin magani aciki, yadda zakiyi ai'kin shine, su layoyin zakije ki ajiye su ne aƙar-ƙashin makwancin ta, wato gadon da take kwana akai ita kaɗai, yayin da shi kuma ƙullin garin maganin, zaki zubasa aduk inda kika san zata taka, kuma ana son ya zamto ta takasa ne har kimanin sau ukku arana, wato safe, rana da kuma dare, muddin kikayi hakan dai-dai, ni kuma na miki alƙwarin mallaka miki kuɗi har kimanin Miliyan talatin, tare da sarƙar gwal babba, da kuma gidaje, kamar yacce na faɗa miki abaya." Ta ƙarasa maganar tana mai buɗe tafin hannun ta ta sakar mata ƙullin maganin acikin sa. "Ina son daga yanzu kisa aranki cewar gawace acikin Gimbiya Fulani, domin kuwa ina mai baki tabbacin babu abun da zai hana wannan abun faruwa, dan kuwa ayanzu haka da zarar na futa daga ɓangeren nan nata zan huce in ajiye layoyin, sannan kuma in barbaɗa wannan ƙullin maganin abakin ƙofar ta, kana kuma idan dare yayi in sake zubasa abakin ƙofar turakar mai Martaba, tunda kin san yau ɗin kwanan tane." Jakadiya ta faɗa tana mai sakin murmushi. "Yawwa bayan an gama da wannan aikin kuma, ki sani akwai wani sabo da zaizo, wanda za'ayi sa akan wancan ɗan iskan yaron da suke kira da Babban yaya, shima kuma ki sani farashin sa daban ne da wannan bawai duk ɗaya ba." Ta ƙarasa maganar da taune laɓen ta na ƙasa, tare da komawa jikin allon haɗaɗɗen gadon da yake acikin ɗakin nata ta jingi na. "Daga yau ina son ki fara kallon sa amatsayin gawa shima, domin kuwa muddin aikin yazo, babu wani abu da zaisa na kasa yinsa nima, dan haka yanzu ma bara na tashi domin naje na aiwatar da wannan ɗin." Jakadiya ta faɗa tana mai miƙewa tsaye. "Da gani sai ke ce maganar nan, bana son bayan mu wani yaji ta ko kuma ya ganta, dan haka sai ki kiyaye." Ta faɗa daga zaunen da take tana mai kallon ta. "Insha Allah Uwar Sarkin gobe." Jakadiya ta faɗa tana kallon ta, tukun daga bisani ta ɗora da faɗin. "Na barki lafiya." Kana ta juya tana mai fucewa daga cikin ɗakin. Acan ɓangaren Gimbiya Fulani kuwa, zaune take akan tattausan kafet ɗin da yake malale acikin bedroom ɗin nata, ta jingina da kujerar da take abayan ta tana mai ɗan cizon lip ɗin ta tare da ya ƙuna fuska, sabo da yarce take jin ciwon bayan data tashi da shi tun bayan tashin ta daga baccin safe na ƙara ƙaruwa fiye da baya, ga kuma yarce take jin marar ta na karta mata, hakan shine ma yasanya ta saukowa daga kan kujera ta zauna akan kafet, sai dai kuma babu wanda yasan halin da take ciki a masarautar, kasancewar babu wanda ta sanarwa. Tana cikin wannan yanayin ta jiyo sautin muryar jakadiya tana mai kwaɗo sallama daga bakin ƙofa. Dasauri ta gyara zamanta tana sakin fuskar ta sosai, tayarce koda jakadiya ta shigo ba zata fuskanci cewar bata da lafiya ba, tukun daga bisani ta buɗe baki tana mai faɗin. "Wa'alaikumu salam, lale marhabun da Jakadiya." Ta ƙarasa maganar fuskar ta ɗauke da murmushi. Yayin da itama Jakadiya ta danno kanta zuwa cikin ɗakin bakin ta amatuƙar washe. Direct ta doshi bakin danƙararen haɗaɗɗen gadon dake cikin ɗakin yake. Wuri ta samu ta zauna tana mai facing ɗin Gimbiya Fulani, tare da jingina da katakon gadon da yake abayan ta, tukun ta buɗe baki cikin tsantsar far'ah tana mai faɗin. "Barka da hutawa Gimbiya Fulani, ɗiyar Sarki jikar Sarki, kana matar Sarki, sannan kuma uwar Sarkin gobe." Ta ƙarasa maganar tana mai kai hannun ta da yake riƙe da layoyin nan bayan ta ta kifesa aƙasan kafet ɗin nan. Yayin da ita kuma Gimbiya Fulani tayi murmushi tana mai buɗe baki tace. "Jakadiyar Sarki kenan, amintacciya kuwa abokiyar shawarar Sarki, wato ke dai ako da yaushe bakya taɓa gajiya da fasawa mutane kai ko?" "Haba dai Gimbiyar mu, ai bawani fasa kai, duk wanda kikaji an faɗa masa to ya kai afaɗa masa ne dama, domin kuwa aduk faɗin gidan nan babu wata ƴar lele bayan ke a wurin mai Martaba, sabo da ke kaɗaice kika ajiye magajin sa acikin gidan nan, kinga kuwa yabo gareki ya zama dole." Jakadiya ta faɗa tana mai sake matsar da hannun ta baya fuskar ta ɗauke da murmushi, ba tare da ta bari Gimbiya Fulani ta lura da itaba ko kaɗan. Yayin da ita kuma Gimbiya Fulani ta ɗan saki gajeran murmushi, sabo da jin kalamin Jakadiya da tayi, bayan kuma tasan da zata futa daga nan ɗin ta tafi wurin wata itama hakan zatai mata, tukun daga bisani ta buɗe baki tana mai faɗin. "To Jakadiya abar dai zancen haka kawai, atafi na gaba kuma." Murmushi Jakadiya tayi tana mai sake kai hannun ta baya tare da gyara zaman ta awurin, tayarce Gimbiya Fulani ba zata gane abun da take yi ba, tukun tace. "Dama mai Martaba ne ya turo ni gareki akan nazo na jiye masa lafiyar jaririn sa, domin kuwa akullum yana faɗin cewa mafarkin sa na nuna masa namiji ne ɗauke acikin ki wannan karan ma." Murmushi itama Gimbiya Fulani tayi tana mai lumshe idanuwan ta, domin kuwa harga Allah ta gaji da surutun Jakadiya, gaba ɗaya ma ta ƙagara ta tashi ta futa ko taji da abun da take ji, tukun daga bisani ta buɗe idanuwan nata tana mai faɗin. "Hmmmm! Mai martaba kenan, to in kin koma sai kisanar dashi cewa, Baby na cikin ƙoshin lafiya." "Tom shikenan ni zan huce, na barki lafiya Uwar Magaji." Ta ƙarasa maganar tana mai hulla layoyin nan ƙarƙashin gadon da sauri, sannan ta miƙe tsaye fuskar ta ɗauke da tsantsar murmushi, tana mai sake faɗin sai da anjima." "Allah ya kaimu na gode." Gimbiya Fulani ta faɗa tana mai miƙar da ƙafafuwan ta akan kafet ɗin nan. Yayin da Jakadiya kuma ta huce ranta fal farin ciki, sabo da ganin da tayi ta samu nasarar aiwatar da abu ɗaya daga cikin abubuwan da zatayi cikin salama. Tana zuwa ƙofar ɗakin tayi sa'a kuwa babu ko mutum ɗaya dake cikin falon. Ganin hakan da tayi ne ya sanya ta fara waige-waige, sai da ta tabbatar da babu ko ƙuda dake kallon ta acikin ɗakin, tukun ta sanya hannun ta jikin haɓar zanin ta tana mai ciro ƙullin maganin nan daga cikin sa. Sake wawwaigawa tayi taga dai still babu kowa, sannan ta kwance sa cikin sauri tana mai zubasa abakin ƙofar ɗakin da matuƙar sauri, tukun ta juya tana mai yin gaba abun ta, bayan ta mayar da maganin cikin haɓar ta da zummar taje ta zuba abakin turakar mai martaba ma. *ƘASAR MALIN, JAHAR RUMAN.* Ƙarfe goma dai dai na safe jirgin su ya ɗaga ta cikin ruwa, yana mai ɗaukar hanyar da zata kaisa Ƙasar Hausa, bayan su Aishatu sun gama koke-koke ita da ƴan uwanta, kana suka mata fatan Allah ya sauke ta lafiya, tare da al'ƙawarin suna nan zuwa idan ta sauka. Sosai zuciyar ta ke cigaba da tsinkewa, gaban ta na wani irin faɗuwa, alokacin da jirgin su ya fara nitsawa cikin hanya. Jin ta take wani iri, gaba ɗaya jikin ta yayi matuƙar yin sanyi, ga kuma zuciyar ta dake cigaba da tsinkewa, yarce kasan ranar da aka sanar mata da mutuwar mahaifin ta. Addu'oi ta fara karantowa acikin zuciyar ta ba tare da ta sanarwa Ishaƙ halin da take ciki ba. Sai dai kuma shima ɗin duka yana lura da sauyawar tata, kasancewar akusa da shi take, amma sai bai kawo komai ba aransa, ya dangana hakan kawai da zafin rabuwa da ahalin tane ya sake sanyawa ta koma haka ba komai ba. *ƘASAR HAUSA, JAHAR WASAI CIKIN MASARAUTAR WASAI.* Ko da Jakadiya ta bar part ɗin Gimbiya fulani direct ta doshi turakar mai martaba, tayi sa'a kuwa babu wanda ta samu a wurin kamar yacce tai fata, hakan yasa ba tare da ta tsaya ɓata lokaci ba ta sake ciro ƙullin tsuman nan ta kwance sa, tana mai baɗasa abakin ƙofar, tukun tayi sauri ta koma baya cikin tsantsar farinciki. Aɓangaren Gimbiya Fulani kuwa, sosai ciwon da take ji ya cigaba da ƙaruwa, barin ma bayan lokacin da aka idar da sallahr magariba amasallacin dake cikin masarautar, amma duk da haka tai shiru da bakin ta ba tare da ta sanarwa kowa ba, haka kuma koda dare yayi bata tafi turakar mai martaba ba, duk da kasancewar itace da shi ɗin yau. Misalin ƙarfe goma ɗaya na dare ciwon naƙuda ya sake turnuƙe ta mai matuƙar tsanani, banda cizon leɓe tare da yarfa hannu babu abun da take ai'kin yi awannan lokacin. Tana cikin wannan yanayin ta jiyo sautin muryar hadimar ta, wacce ta kasance tamkar Uwa ga Ƴaƴan ta, kuma ta zamto aminiya agare ta, tana mai kwaɗo sallama abakin ƙofar ɗakin ta, kasancewar aduk lokacin da take da ciki dama haka Hadimar tata mai suna Larai take ziyarta ta duk dare, dan taga halin da take ciki, domin kuwa wani lokacin ma idan ta shigo sai dai ta juya ba tare da ta same ta ba, idan har ranar ta kasance tana turakar mai Martaba kenan, sannan kuma da zarar ta haihu to kula da yaron da komai nasa yake komawa wurin ta, haka duk ta raini yaran tun daga kan Babban yaya har zuwa Nafisat auta. Babu yarce magauta basuyi ba su janyo ta ajikin su, domin su samu damar kassara rayuwar Babban yaya cikin sauƙi, amma kwata-kwata taƙi, hakan ne yasa gaba ɗaya itama sukabi suka tsane ta, sannan kuma suke jin haushin ta, sai dai kuma babu yadda zasuyi da ita, domin kuwa Gimbiya Fulani ta daɗe da ƴanta ta. Macece mai kimanin shekaru arba'in da ƴan kai aduniya, Ƴaƴa huɗu duka ta haifa, daga nan kuma mahaifin su ya rasu. Tun bayan rasuwar sa bata sake yin wani auren ba, ataƙaice ma tana zaune ne anan ɓangaren Gimbiya Fulani itama data bata ɗaki. Da matuƙar sauri, sannan kuma cikin tsantsar tashin hankali ta ƙarasa wurin ta tana mai faɗin. "Subhanallahi haihuwar ce tazo kenan Mamy'n Yara." Ta ƙarasa maganar tana mai dafata, hankalin ta atsantsar tashe. Yayin da ita kuma Gimbiya Fulani take ta cigaba da cizon yatsa, ba tare da tace mata komai ba. Dasauri ta juya tana mai shirin tafiya, bakin ta na faɗin. "Bara naje na sanarwa Jakadiya ta sanarwa mai Martaba, in yaso ko asibiti ne sai ataf... Caraf taji Gimbiya Fulani ta riƙo yatsun hannun ta, hakan ne yasata juyowa ɓarin da take tana mai kai idanuwna ta kanta. Ido huɗu sukai da junan su alokacin da ta juyo ɗin, tukun daga bisani Gimbiya Fulani ta buɗe baki cikin muryar ta da take nuni da halin da take ciki na tsantsar ciwo tana mai faɗin. "Kar kisanar masa, bana san wani mutum yaji labarin haihuwar nan ayanzu, domin kuwa kin san yarce wasu daga cikin mutanen gidan nan suke, dan haka ki barshi har zuwa nan da asuba muga yarce Allah zaiyi." Ta ƙarasa maganar da ƙyar tana mai cizon leɓe. "Tom shikenan, amma bara naje ɗakina na ɗauko wasu magun-guna dana tanade su sabo ds zuwan wannan ranar." Umma Larai ta faɗa ba tare data tsaya ja da maganar shugabar tata ba, domin kuwa sai dai ta bada labarin magautan cikin gidan nan, ba dai wani ya bata ba, tukun ta juya cikin sauri tana mai fucewa daga cikin ɗakin. *ƘASAR MALIN, CIKIN JIRGIN RUWA.* Dare ya tsala sosai, yayin da gari ya kasance baƙiƙƙirin da duhu, amma duk da haka jirgin nan bai tsaya ba, kasancewar ɗauke yake da futulu masu matuƙar haske tako ina ajikin sa, hakan yasa duk tsayin dare bai sanyawa direbobin su tsaya daga tuƙi, muddin ba abinci aka tsaya siya ba ko sallah. Tini suka daɗe da futa daga cikin Jahar Ruman, dan har sun shiga Jahar Karfuz ma. Tun da suka shigo jahar karfuz Aishatu taji jikin ta ya ƙara matuƙar yin sanyi, ga bugun zuciyar ta kuma da yayi matuƙar ƙaruwa, tayarce har take jin tamkar zata faso ƙirjin ta ta futo, tun tana addu'a acikin zuciyar ta har sai da ta dawo yin ta abayyane, sabo da yarce take jin yanayin na sake hau-hawa fiye da da, tayarce har Ɗan cikin ta shima keta motsi fiye da yarce ya saba yi. Ta fannin Ishaƙ shima sosai yake jin zuciyar sa na cigaba da dukan tara-tara, ga wani irin tsoro da fargaba da suka lulluɓe zuciya da ruhin sa, irin wanda bai taɓa tsintar kansa a makamancin su ba. Hakan ne yasa sa damƙe hannun Aishatu cikin nasa da matuƙar ƙarfi, yana mai karanto duk addu'ar da tazo zuciyar sa azuciyar sa shima. Misalin ƙarfe huɗu da ar'ba'in dai-dai na dare jirgin su ya danna kansa zuwa yankin da ya ratso ta cikin BAƘAR MASARAUTA, wanda shigar tasa kuma tayi dai dai da bugawar da ƙirjin Aishatu yayi da matuƙar tsanani fiye da da, yayin da zuciyar ta kuma ta cigaba da tsinkewa da matuƙar sauri. "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un!" Rabi da kwatan mutanen dake cikin jirgin suka furta cikin tsantsar ruɗu da tashin hankali, sabo da yarce suka hango h.............✍ *BAƘAR MASARAUTA* *NA* UMAR FARUQ*D* *PAGE 15* Hasken futulu masu matuƙar ƙarfi an dallo idanuwan su tun daga can nesa da su. Take a wurin Aishatu ta sake matuƙar rikicewa, jikin ta na tsanstsar rawa da karkarwa, hakan da Ishaƙ ya gani ne ya Sanya sa sake damƙar hannun ta da matuƙar ƙarfi, bakin sa na furta duk addu'oin da suka zo cikin zuciyar sa cikin tsantsar tashin hankali, kamar yadda sauran ɗaukacin mutanen da suke a cikin jirgin suke. Yayinda tawagar mutanne Baƙar Masaruata kuma suka afka cikin jirgin ruwan su da matuƙar sauri, tukun suka doso inda suka hango jirgin su Aishatu, suna masu cigaba da dallewa direbobin tare da mutanen ciki idanuwa da hasken futulun su, bakin su kuma na aikin furta kalmar. "Gargabilu!" Da tsantsar ƙarfi. Cikin daƙiƙun da basu zarta huɗu ba suka ƙaraso wurin da jirgin da su Aishatu suke ciki yake. Ba tare da sun tsaya jan lokaci ba suka zare makaman su daga cikin jikin su, suna masu ɗaga su sama, tukun suka yiwa direbobin jirgin nuni da hanyar da zasu bi. Cikin tsantsar ruɗu kuwa matuƙarn jirgin suka nufi wurin da suke nuna musu hankulan su abala'in tashe, domin kuwa ba iya makaman su bane abun tsoro, su kansu mutanen da suke a cikin jirgin abubuwan firgici ne ga mutumim da bai saba ganin su ba. Yayin da jama'ar dake cikin jirgin kuma suka sanya ihu da matuƙar ƙarfi, suna masu faɗin sun shiga ukku cikin tsantsar tashin hankali. Afannin Aishatu kuwa kallo ɗaya tayiwa mutanen taji cikin ta yayi wata irin murɗawa, sabo da firgita, tukun daga bisani Ɗan cikin nata ya fara wani irin hutsul-hutsul da matuƙar sauri, tayarce har na kusa da ita zai iya lura da motsin sa muddin ya kalli cikin nata. Da matuƙar ƙarfi ta rumtse idanuwan ta, tana mai ɗaukar tafin hannun ta ta dafe cikin ta da shi, zuciyar ta na tsantsar bugawa, yayin da bakinta kuma ke ai'kin furta duk wasu addu'oi da sukazo cikin sa, ba tare da tasan tana yin suba ma. Basu dakata ba har sai da suka turasu gefen ruwan nan, inda su sarki Barbaru da Boka mai hutar kasoko, tare da sauran jama'ar su suke. Shimfiɗar fata ce ajiye daga gefen ruwan, wacce jikinta yake ɗauke da jini faca-faca, ɗauke take da kaskon wuta da yake matuƙar ci da wuta, yayin da gefen kaskon kuma aka aje wata irin kibiya mai matuƙar tsini, sai Boka mai wutar kasko da yake zaune daga gefen shimfiɗar, yayin da Sarki Barbaru kuma yake daga tsaye a bakin ruwan nan, gaba ɗayan sa a wani irin birkice, domin kuwa ko shigar da ke sanye jikin sa tun ta wancan satin ce, ranar da suka fara riskar tashin hankalin nan bai canza ta ba, asalima ko barin hurin kwata kwata baiyi ba har kawo yau, domin kuwa abinci ma a rana baifi sau ɗaya yake cinsa ba, shima sai yaji yunwa na shirin hanasa miƙewa tsaye. Sosai mutanen cikin jirgin nan suka sake matuƙar firgita, suna masu sakin ihu da salati, sabo da irin mutanen da suke sake arba da su agafen ruwan da suka iso yanzu. "Daƙiƙa ɗaya kawai na baku, ko wane mutum ya zamto ya kama bakin sa, muddin kuma kuka bari na sake jin ihun wani cikin kunnuwa na bayan giftawar daƙiƙun, to kusani sunan mutum gawa, ko waye ne shi kuwa." Sarki Barbaru ya faɗa cikin muryar sa mai matuƙar amo, yana mai kallon mutanen cikin jirgin nan. Take kuwa wurin ya ɗauki shiru gaba ɗaya, yarce kasan ba'a taɓa hallitar mutum ba, balle ayi zaton anan wurin ihun ya gama tashi. Yayin da Aishatu kuma ta taune leɓen ta na ƙasa da ƙarfi, tana mai dafe cikin ta da hannu ɗaya, sabo da yadda taji marar ta tayi wani irin kartawa, ga kuma bayan ta da taji lokaci ɗaya ya riƙe gam! Taune leɓenta ta cigaba dayi da ƙarfi, tana mai faman zare idanuwa tare da gumtse baki, gudun kar addu'ar da takeyi a zuciya ta suɓuce ta futo fili, Sarki Barbaru yaji, yayin da shi kuma Ishaƙ yake ta aikin shafa bayan ta a hankali, cikin tsantsar ruɗu shima. "Ku shiga cikin jirgin nan yanzu, ku bincika mana ko ina da ina, lungu da saƙo, ku futo mana da duk wani jinjirin yaro namiji da kuka samu." Sarki Barnaru ya faɗa cikin amo yana mai kallon wasu daga cikin dakarun nan nasu. Yayin da su kuma mutanen cikin jirgin nan hankulan su ya sake bala'in tashi, barin ma matan da suka san suna ɗauke da jariran Ƴaƴa. Dasauri wata mata da take ɗauke da jinjirin ta a hannunta, ta sake danna sa cikin hijabin ta jikin ta na tsantsar rawa, sabo da yadda taga mutanen nan sun tunkaro inda take gadan-gadan, kasancewar sun riga da sun hango ɗan nata tun farko, sabo riƙesan da tayi a hannun ta. Girgiza kanta ta farayi tana mai ja da baya daga zaunen da take, cikin tsantsar tashin hankali da firgici, yayin da su kuma waƴan nan dakarun suka cigaba da doso ta gadan-gadan. Ganin da tayi suna daf da isowa inda take ne, ya sanya ta miƙewa da sauri tana mai shirin rugawa baya, amma sai dai tana ɗaga ƙafarta ɗaya taji ta- ta kife kif a ƙasa, kanta na dukan katakon dake jikin jirgin da matuƙar ƙarfi, sabo da yadda ɗaya daga cikin dakarun ya sanya ƙafarsa ya tatsiye ta da ita. Gadan-gadan ya ƙarasa zuwa wurin da take yana maj sa hannu da niyyar funcikar Ɗan, amma sai tayi sauri ta ƙara ruƙun-ƙume sa acikin jikin ta, tana mai fashewa da wani irin gigitaccen kuka mai ban tausayi, take kuwa shima jaririn ya tsanyare da kuka da matuƙar ƙarfi, sabo da zafin matsar da yaji, wacce uwar tasa tayi masa gudun kar aƙawace mata shi. Tas! Tatas!! Tasss!!! Wasu irin ƙarar marika suka tashi a wurin da matuƙar ƙarfi, waƴan da suka sake sanya mutanen cikin jirgin ruɗewa da firgicewa, suna masu toshe bakunan su da hannu. Badakaran nan ne ya ɗauke matar da wasu gigitattun marika, sabo da yadda yaga yana miƙa hannu zai karɓi Ɗan tana kuma sake ruƙun-ƙume sa, tukun daga bisani ya ɗago tsaye yana mai funciko wata doguwar takobi daga ƙugun sa yayi kan matar da ita. Wata irin gigitattar ƙara matar ta saki, tana mai rumtse idanuwan ta da matuƙar ƙarfi. Funcikar Ɗan ya sakeyi da matuƙar ƙarfi, yana mai mayar da takobin cikin jikin sa ba tare da ya kaita jikin ta ba, sabo da yadda yaga riƙon da tayiwa yaron yayi sakwa-sakwa ta dalilin ihun da ta saki, tukun ya juya jinjirin riƙe a hannun sa, da yake tsala uban kuka yana mai ɗaga kafafuwan sa sama yayi gaba. Dasauri matar nan ta miƙe tsaye tana mai bin bayan sa cikin tsantsar ɗimaucewa. Ƙafar sa ɗaya ya ɗaga yana mai harbin ta da ita ta baya, hakan yasa ta tafi taga taga tana mai kifewa a ƙasa kanta ya sake dukan wani icce, tayadda har sai da ya fashe jini ya futo, amna a haka ta sake miƙewa tana mai sakin kuka Yayin da shi kuma wannan badakaran ya cigaba da tafiyar sa babu ko ɗigon imani tattare da shi, yana mai fucewa daga cikin jirgin. Kai tsaye ya doshi kan shimfiɗar nan mai ɗauke da huta a kanta. Miƙawa Boka mai hutar kasko jinjirin dake tsala uban kuka yayi, yayin da daga can bakin jirgin kuma wani badakaran ya tare wannan matar uwar jinjirin, da take shirin futowa yana mai sanyata ta duƙushe akan guiwoyin ta, tana hangen Ɗan nata daga nesa. Matsawa Sarki Barbaru yayi zuwa gaban kaskon huta shima, yayin da Boka mai hutar kasko kuma ya tashi daga hurin da yake zaune, hannun sa riƙe da jinjirin, yana mai matsawa gaban kaskon nan, tukun ya durƙusa yana mai kwantar da shi a kusa da kaskon. Hutsil-hutsil yaron ya farayi yana mai cigaba da tsanyarewa da kuka, sai dai kuma har bayan shuɗewar daƙiƙa goma ko kaɗan ƙafarsa bata taɓa jikin kaskon nan ba, balle harya tuntsirar da shi, hakan da suka ganine yasan ya Sarki Barbaru buɗe baki cikin muryar sa mai matuƙar amo da firgitarwa, yana mai faɗin. "Bashi bane wannan ma, dan haka matso ka caka nasa kibiyar shima." Ya ƙarasa maganar da kallon wani badakare da yake tsaye agefe. Wata irin ƙara Uwar jinjirin nan ta saki, sabo da jin abun da Sarki Barbaru ya faɗa da tayi, ga kuma ganin da tayi badakaran yayi wurin jinirin gadan-gadan. Da sauri wannan badakaran da yake tsaye a gaban ta ya damƙi tsintsiyar hannun ta, sabo da yadda yaga tana shirin fucewa daga cikin jirgin. Yayin da shi kuma wancan da Sarki Barbaru yayiwa magana ya ƙarasa gaban Jinjirin nan, tukun ya durƙusa ƙasa yana mai sa hannu ya ɗauki kibiyar da take ajiye kusa da kaskon huta, sannan ya ɗago tsaye yana mai ɗaga ta sama, tukun yayi ƙasa da ita yana mai cakata a dai -dai ƙawon zuciyar jaririn! Wata irin gigitattar ƙara Uwar jinjirin nan ta saki, tana mai zubewa a ƙasa sumamma, sabo da yadda taga an yiwa jinjirin nata da bai san hawa ba bare sauka, wanda bashi da haƙƙin kowa a kansa kisan gilla akan idon ta. Yayinda Aishatu kuma ta saki wani irin salati da matuƙar ƙarfi, wanda ya janyo hankalin duka mutanen wurin, tunda ga kan su Sarki Barbaru har zuwa mutanen cikin jirgin nan da suke tare, tana mai rumtse idanuwan ta tare da yarfa hannun ta, sabo da wani irin mugun murɗawa da taji cikin ta yayi, ga kuma bayan ta daya riƙe gam, banda jujjuya kai tare da sakin nishi babu abun da take iyayi. Gumi ke yanko mata ta kowace kafar gashi dake jikin ta, sabo da yadda ciwon naƙuda ya taso mata gadan-gadan, a kuma lokaci ɗaya. Da sauri Ishaƙ ya dafa bayan ta yana mai girgiza kai, hankalin sa a bala'in tashe, kafin daga bisani kuma wasu irin hawaye masu matuƙar gudu suka ɓalle daga cikin idanuwansa suna tsiyaya akan kuncin sa. Yayin da Sarki Barbaru kuma ya buɗe baki cikin amo yana mai faɗin. "Ga wata nan zata haihu yanzu, dan haka ku shiga ciki ku anso mana sauran yaran kafun muga wanda zaizo natan." Ya ƙarasa maganar da kallon dakarun nan nasa. Take kuwa suka tafi zuwa cikin jirgin, domin su anso sauran yaran da suke a ciki, yayin da ita kuma Aishatu take cigaba da sakin nishi, hannun ta dafe da ƙasa tayi durƙushe, yayin da ɗayan hannun nata kuma ya kasance dire akan cikin ta da take jin abun cikin na motsawa, yana neman hanyar futa. Cikin sauri Ishaƙ ya fara buɗe jakar kayan ta da take ajiye a kusa dasu idanun sa na zubar hawaye, nadamar barin Aishatu tazo gaisuwar mahainfin ta na cika zuciya da ruhin sa. Zannuwa ya ɗauko har kimanin guda huɗu. Ninka guda biyu yayi yana mai shimfiɗa su aƙasa, tukun ya sanya hannu yana mai matso da Aishatu da zuwa yanzu bata fahimtar komai, sabo da tsantsar azabar ciwon da take ji zuwa kan shimfiɗar, sannan ya ware guda biyu yana mai miƙewa tsaye ya fara ƙoƙarin yin dabara wurin ganin yayi mata rumfa da zannuwan, ganin hakan da matan cikin jirgin sukayi ne yasan ya wasu daga cikin su har kimanin mutum huɗu sukayo wurin da suke, gaba ɗayan su hankulan su a tsantsar tashe, yayin da idanuwan su kuma ke tsiyayar da ruwan hawaye yadda kasan an buɗe famfo. Karɓar zannunwan matan sukayi a hannun Ishaƙ, tukun biyu daga cikin su suka buɗasu suna masu zagaye Aishatu da shi daga tsaye, ya zamto sun mata ɗan ɗaki kenan, yayin da biyu daga ciki su kuma suka shiga cikin dan ɗakin zannuwan, sabo da su taimaka mata. Acan ɓangaren dakarun nan kuwa, cikin rashin imani suka sake ƙwato wasu yaran har guda biyu a cikin jirgin a hannun iyayen su, suna tsantsar kuka. Ɗaya jinjirin duka watan sa biyu aduniya, yayin ɗayan kuma yake da wata ukku aduniya. Suma ɗin tawowa sukayi da su zuwa kan shimfiɗar nan, tukun aka ajiye na farko a gaban kaskon huta, amma sai dai shima har bayan wucewar daƙiƙa goma da ajiye sa bai bige kaskon nan ba, hakan ne yasa Sarki Barbaru ya sanya aka luma masa kibiyar nan a ƙawon zuciya shima. Wata irin gigitattar ƙara uwar jinjirin ta saki, tana mai miƙewa a zabure zata afka cikin ruwa, amma sai wasu maza guda biyu da suke a gafen wurin da take sukayi saurin kamata suna masu kaita ƙasa, yayin da ihun da ta saki kuma ya daki kunnuwan Aishatu da matuƙar ƙaraji, wanda ya ƙara sanya cikin ta ya ƙara wata irin murɗawa fiye da baya sosai. Cikin tsantsar zafin ciwon da takeji ta sanya hannun ta tana mai dan buɗe zanin da ake zagaye ta da shi, tukun ta zura kanta waje tana mai kai idanuwan ta zuwa wurin da su sarki Barbaru suke, wanda hakan kuma yayi dai-dai da lokacin da wannan badakaran ya sake ɗaga kibiyar nan yana nai cakawa ɗayan jaririn aƙawon zuciya shima, kasancewar bai bige kaskon nan ba shima ɗin. Wata irin gigitattar ƙara Uwar jinjirin tare da Aishatu suka saki a lokaci guda, tukun daga bisani kuma sai ga kukan jinjiri nan ya biyo baya da matuƙar ƙarfi...! *ƘASAR HAUSA, JAHAR WASAI CIKIN MASARAUTAR WASAI.* Acan ɓangaren Gimbiya Fulani kuwa sosai take jin jiki, yayin da hadimar ta Larai kuma ke tsaye akan ta tana ta faman yi mata sannu, tare da sharce mata gumin dake tsats-tsafowa akan goshin ta. Kiran sallah'r da aka kwaɗa a cikin masallacin masarautar yayi dai-dai da bayannar kukan jinjiri da matuƙar ƙarfi. "Alhamdulillahi rabil alami." Gimbiya Fulani ta faɗa tana mai mayar da numfashi, tare da lumshe idanuwan ta, kasancewar abun da ke cikin nata na faɗowa itama mabiyar ta biyo sa. "Ayiri-yiri-yiririiiiiiiiiiiiii!" Hadima Larai ta saki wata mahaukaciyar buɗa mai matuƙar sauti a lokacin data kai idanuwan ta kan gaban jinjirin, sabo da yadda idanuwan ta suka mata arba da santalelen jinjiri Ɗa namiji. Ƙara sakin buɗa tayi da matuƙar sauti, tukun daga bisani ta durƙusa ƙasa tana mai yankewa yaron cibi, sannan ta ɗauke sa tana mai naɗe sa acikin wani lallausan showel, tukun ta juya cikin sauri tana mai kama hanyar waje hannun ta riƙe da yaron. Yayin da ita kuma Gimbiya Fulani ta matsa daga hurin da take tana mai mayar da numfashi, tare da lumshe idanuwan ta. Kai tsaye Hadima Harai ta doshi waje hannun ta ɗauke da jinjirin, sannan kuma har lokacin bata bar sakin buɗar da take yi ba, bakin ta na furta kalmar. "Masha Allahu! Masha Allahu!! Masha Allah da zuwan ka duniya Ɗan albarka!!! Godiya ta tabbata ga Ubangijin talikai mai kowa mai komai. Yau ranar tamuce mu mutanen gida, domin kuwa ƙaruwar tamuce tazo, ƙaruwa irin wacce aka daɗe ana mararinta da jiran ta.... Haihuwar Ɗa namiji ba kowa ba a wanga gida, haihuwar namiji sai ɗiyar sa'a a wanga gida, zama Uwar Sarki sai Ƴar Sarki Jikar Sarki, sannan kuma Matar Marki." Hadima Larai take ta faɗa da tsantsar ƙarfi tana mai cigaba da tafiya tare da sakin buɗa. Yayin da ɗaukacin jama'ar dake rayuwa a ɓangaren Gimbiya Fulani kuma suka furfuto daga cikin ɗakunan su da tsantsar gudu, domim kuwa koda basu san meke faruwa ba muryar hadima Larai kawai ta sanar da su. Aɓangaren Hadima Larai kuwa cigaba da tafiya tayi tana mai sakin kalamai iri-iri, hannun ta ɗauke da jinjirin da yake ta aikin tsala kuka ko wanka ba ayi masa ba, tana mai nufar hanyar da zata sadata da wurin buga Tambarin murna, kasancewar haka al'adar gidan sarautar nasu take, muddin wata daga cikin matan gidan suka haihu, to da zarar an yanke wa abun da aka haifa cibi za'a ɗauke sa a tafi da shi wurin buga Tambari, shi kuma wannan Tambarin shine ke sanar da duk jama'ar dake cikin masarautar haihuwar, sabo da tsananin ƙarar sa, sannan kuma bawai kai tsaye ake bugasa ba da zarar an kai jinjiri, a'a sai sun fara dubawa sun ga namiji ne ko mace, tukun a ɗauki makaɗi a fara bugasa, kasancewar kowane jinsi yana da kalar bugun da ake masa, tayarce da zarar an buga sa mutanen dake cikin gidan suke fahimtar jinsin dlƊan da aka samu, mace ko namji ta hanyar kiɗan. "Ayiri-yiri-yiririiiiiiiiiiiiiii." Hadama Larai ta sake rangaɗa buɗa a dai-dai lokacin da ta shiga wurin, tana mai girgiza jinjirin da yake ta ai'kin tsanyara kuka shima. Kafun kace tak, tuni mutnen da suke zaune cikin wurin sun futo da tsantsar gudu. Tun kafin su ƙaraso wurin da take ta yaye showel ɗin dake ƙudun-dune a jikin jinjirin, tana mai ɗaga jaririn sama tayi musu nuni da shi. Take kuwa wani dattijon tsohon mutum da yake sanye da babbar riga a jikin sa ya juya yana mai dosar wurin da wasu manyan ƙarafuna suke a kafe jikin bango, wato Tambarin murna. Durƙusawa yayi ƙasa yana mai sa hannu ya ɗauki wani ƙarfe mai kama da taɓaryar ƙarfe, amma sai da shi wannan dogo ne sosai, tukun ya ɗago yana mai ɗaga sa ya fara dukan Tambarin farko da yake a ɓangaren wurin da yake a tsaye, wato na namiji kenan. Take kuwa wani irin sauti mai daɗi ya fara tashi da matuƙar ƙarfi, tayarce har sai da ya karaɗe ko ina na cikin masarautar, yayin da su kuma mutanen dake cikin wannan hurin suka toshe kunnuwan su suna rawa tare da kaɗa manyan rigunan su, sabo da yadda sautin yake ratsa har cikin kwanyar su. Ita kuwa Hadima Larai cigaba da ɗaga Jinjirin nan sama tayi tana mai rawa a tsakiyar filin hurin, yayin da shi kuma jaririn keta aikin tsanyara kukan sa. A ɓangaren Gimbiya Huwaila kuwa tashin ta kenan daga kan gado taji sautin bugun tambarin samuwar yaro namiji na dukan kunen ta. Wata irin zabura tayi tana mai miƙewa zaune daga kwancen da take akan gado, tukun daga bisani ta fara girgiza kanta tana mai faɗin. "Inaaa bazai yuwu ba Wallahi Tallahi, shin me bugun tambarin Ɗa namijin da kunnuwa ne suke jiyo mun yake nufi kenan?" Ta faɗa da wani irin ƙaraji tana mai miƙewa tsaye, tukun ta duro daga kan gadon da take yarce kasan wata zararriya. "Ɗa namiji acikin gidan nan kuma? Shin dama akwai wata mai cikin ce bayan Fulani agidan nan ne da har kunnuwa ne suke jiyo mun sautin bugun tambarin Ɗa namiji?" Ta sake faɗa tana mai juyi acikin ɗakin nata cikin tsantsar tashin hankali. "A'a, babu wata bayan ita dake da ciki a cikin gidan nan, kenan hakan na nufin itace ta haifo Yaro namiji kuma yazo da ransa? Inaaaa!!!! Hakan bazai yuwa ba, Wallahi Tallahi ƙarya ne..." Ta faɗa da wani irin ƙaraji tana mai kama hanyar waje! Ɓangaren Gimbiya Suwaiba matar mai martaba ta biyu kuwa, futowar ta kenan daga cikin bathroom bugun tambari samuwar yaro namiji acikin masarautar tasu ya daki dodon kunnen ta. Da matuƙar sauri ta dafe bangon ɗakin ta, sabo da yarce taji ƙafafuwan ta sun zame tana shirin kifawa ƙasa, tukun daga bisani ta koma tana mai zama yaraf a ƙasa, wato zaman daɓaro, tare da ɗora hannuwa biyu aka. A ɓangaren Jakadiya kuwa tamkar a mafarki taji bugun tambarin samuwar Ɗa namiji na dukan kunnuwan ta, kasancewar ita bata kaiga tashi ba a lokacin. Ahankali ta fara buɗa idanuwan ta tana mai yamutsa fuska, kafin daga bisani kuma tayi wata irin miƙewa tsaye daga kwancen da take zumbur tana mai zaro idanuwa waje, tare da dafe ƙirjin ta da hannu, sabo da yadda ta jiyo sautin na dukan kunnen ta da matuƙar ƙarfi, alamun ba mafarki take ba a zahiri abun ke faruwa kenan. "Ɗa namiji?...Gimbiya...Fulani?..ta sake haihuwar sa yanzu ma?" Ta faɗi magan-ganun a rarrabe, sannan kuma ta sigar tambaya, tana mai zaro idanuwanta waje, tukun daga bisani ta juya tana mai miƙa hannun ta ta janyo mayafin ta da tsantsar sauri, sannan ta durƙusa ƙasa tana mai ɗibar takalman ta a hannu ba tare data tsaya sanya su ba, ta doshi hanyar waje tamkar ta kifa a ƙasa sabo da saurin da takeyi. A ɓangaren mai martaba kuwa futowar sa kenan daga bathroom ya ɗauro alwala, sautin bugun tambarin samuwar Ɗa namiji ya daki dodon kunnwan sa. Cak ya tsaya a inda yake yana mai sakin baki da kunnuwa, kai harma da hanci, sabo da yarce yaji abun tamkar al'mara a kunnuwansa, yayin da shi kuma sautin nan ke cigaba da tashi da matuƙar ƙarfi ko kaɗan ba'a da niyyar denawa. Sai da ya ɗauki kimanin mintina tsawo biyar yana tsaye a wuri ɗaya, tukun daga bisani yayi firgigit ya dawo hayyacin sa yana mai furta kalmar. "Al'hamdulillah! Alhamdulillahi!! Alhamdulillah!!!" Kafin daga bisani kuma ya durƙusa ƙasa yana mai kai goshin sa ƙasa yayi sujudu shukur ga rabbil izzati, sannan bayan ya gama ya ɗago idanuwan sa na zubar da ƙwallar murna, tukun daga bisani ya buɗe baki yana mai faɗin. "Masha Allah, ashe nima ina da rabo sake haihuwar Ɗa namiji a duniya, ashe wannan dalilin ne ya hana Fulani zuwa wurina jiya bayan nasa jakadiya ta kira ta, kai Alhmadulillahi rabbil alamin." Ya faɗa cikin tsantsar murna yana mai miƙewa tsaye ya doshi hanyar waje, daga shi sai jallabiya ajikin sa ko al'kyabba bai yafaba kamar yacce ya saba ako da yashe, sabo da tsantsar farin cikin da ya tsinci kansa aciki wanda ya mantar da shi wata alkyabba ma. *ƘASAR MALIN, JAHAR KARFUZ CIKIN BAƘAR MASARAUTA.* Da matuƙar sauri Sarki Barbaru ya buɗe baki yana mai faɗin. "Ta haihu, dan haka kuyi maza maza ku shiga ciki ku anso mun shi tun kafin ta fara sabo da shi, domin kuwa wannan Yaron badan ita Ubangiji Gargabilu yayo saba, yayo sane domin mu." Atare mutanen cikin jirgin suka fashe da kuka hatta da mazan dake ciki, sabo da jin furucin Sarki Barbaru da sukayi yana yi akan Ɗan da ya diro duniya yanzu -yanzu. Yayin da shi kuma jaririn ke aikin tsanyara kuka da matuƙar ƙarfi yana mai ciccila ƙafafuwan sa sama. Cikin sauri matan nan suka fara ƙoƙarin gyarawa Aishatu jikinta, sabo da jin furucin Sarki Barbaru da sukayi, domin kuwa sun san da zarar mutanen sun iso zasu kwaye zannuwan da sukai mata sutura da su. Yayin da ita kuma Aishatu ta miƙa hannu da sauri tana mai shirin ɗaukar ƙatoton farin jaririnta mai tsananin kyau a ƙasa, wanda ada duk suke tinanin cikin sa bai huce wata takwas ba, sai kuma gashi a yanzu take ganin girman Ɗan yafi ƙarfin a kira sa da Ɗan wata twakas. Hannuwan ta suna tsantsar rawa, kamar yadda jikin ta ke rawa ta miƙa su tana shirin ɗaukar jaririn dake cigaba da tsanyara kuka tare da cilla ƴan ƙafafuwa sama, amma sai dai kuma hannun nata yana daf da kaiwa jikin Ɗan taji ansa ƙafa an make sa da matuƙar ƙarfi, tayarce har sai da ta tuntsira baya tana mai faɗawa jikin Ishaƙ da yayi saurin tarota, kasancewar babu ƙwari jikin nata ko kaɗan. Wani danƙareren baƙin badakare ne da yake riƙe da zureriyar takobi a hannunsa, yasa ƙatuwar ƙafar sa ya bige hannun nata da ita, tukun ya durƙusa ƙasa yana mai sa hannu ɗaya ya tallabo jinjirin da yake ɓace da jini zuwa jikin sa. Wata irin gigitattar ƙara Aishatu ta saki tana mai miƙewa tsaye tayi kan mutumin nan, tare da buga tsalle ta shaƙi wuyan sa yadda kasan ba itace ta haihu yanzu ba, domin kuwa lokaci ɗaya gaba ɗaya taji ciwon da takeji a jikin ta ya ɓace ɓat, sai ma wani irin ƙarfi da taji yazo mata, tayarce har take jin zata iya yaƙar uban kowa akan jinjiri nata. Guiwar hannun sa badakaran nan yasa yana mai dukan cikin ta da ita. Take kuwa ta saki wuyan sa tana mai yin baya luuu ta kifa akan jikin Ishaƙ da yayi saurin matsawa wurin da take, a lokacin da take shirin faɗuwa. Banda aikin kuka tamkar ransa zai futa babu abun da yake iyawa, yayin da ita kuma Aishatu ta faɗa jikin sa tana mai wani irin zare idanuwa, tare da taunar leɓen ta da matuƙar ƙarfi, tukun daga bisani ta saki leɓen nata tana mai buɗe baki tana wuri-wuri da idanuwa, gaba ɗayan ta ta fuce daga hayyacinta, sabo da yadda cikin ta yayi wata irin ƙullewa ta sanadin dukan da mutumin nan ya mata. Banda koke-koke babu abun da ke tashi a cikin jirgin, domin kuwa zuwa yanzu babu wani mahaluƙi dake cikin jirgin da ya iya cigaba da riƙe kukan sa. Wata irin ƙara Aishatu ta ƙara saki tana mai sake miƙewa zumbur, a lokacin da idanuwan ta suka hango mata badakaran nan yana tafiya ɗauke da jinjirin ta a hannu da yake ta tsala kuka. Da sauri Ishaƙ ya miƙe tsaye shima yana mai shirin riƙota, amma tuni ta funcike hannun ta tana mai fara ɗaga ƙafafuwan ta a guje ta nufi hurin da ta hangi mutumin nan. Da sauri wani badakare ya tare ta ta hanyar tsayawa a gaban ta, tare da babbake wurin da yayi. Yayin da shi kuma wannan badakaran da yake riƙe da jaririn ya fuce daga cikin jirgin duka yana mai dosar shimfiɗar da Boka mai wutar kasko tare da Sarki Barbaru suke, hakan da Aishatu ta gani ne yasan ta ya ta sake sakin wata irin ƙara mai matuƙar ƙaraji tana mai girgiza kanta, tukun daga bisani ta ɗaga ƙafar ta ɗaya daniyyar ta sake zurawa a guje, amma sai gaba ɗaya ta koma tayi baya luuu, tana mai zubewa a ƙasa sumamma! A wani irin haukace Ishaƙ yayi kanta yana mai sakin wani irin gunjin kuka mai tsantsar sosa rai da ban tausayi, gumi na yanko masa ta ko ina na jikin sa, tayadda har ya jiƙa sa duka sharkaf yadda kasan wanda ya shiga ruwa. Acan ɓangaren badakaran nan kuwa yana ƙarasawa kan shimfiɗar ya miƙawa Boka mai hutar kasko jinjirin. Kallon sa boka mai wutar kasko ya tsaya yi daga tsayen da yake, yana mai yaba kyawun halittar yaron da ya gani aransa, tukun daga bisani ya matsa kusa da kaskon nan dake ci da wuta acikinsa, yana mai ajiye jinjirin da yake tsirara jikin sa ɓace da jini a gaban kaskon, kana yaja baya yana mai komawa ya zuba ido akan sa kamar yadda duka sauran mutanen dake wurin suka zuba nasu idanun. Yana diresa a wurin kuwa jinjirin ya ƙara tsanyarewa da kuka, yana mai kai hannun sa baki ya fara wawurar sa, tukun daga bisani ya fara hahaura ƙafafuwan sa yana mai cillasu sama cikin kukan da yake, hakan da suka gani ne ya sanya su sake zuba idanuwan su akan sa. Yayinda shi kuma jinjirin ya cigaba da harba ƙafafuwan sa har suka dako kaskon wutar nan. Take kuwa a wurin kaskon ya tungule ƙasa yana mai rabewa gida biyu dai-dai.............!!!✍ _KUNA MUGUN SON KARARU TA YADDA HAR IDAN KUKAJI SHIRU BAKWA IYA HAKURI SAI KUN TAMBAYA, AMMA KUMA COMMENT NA KANKANIN LOKACI NA MUGUN YI MUKU WUYA. TO BANA TINANIN ZAKU SAKE GANIN WANI PAGE DIN DAGA WANNAN MUDDIN BANGA COMMENTS DA SHARHI SOSAI BA GASIYA._ *BY* UMAR FARUQ*D* *BAƘAR MASARAUTA* *NA* UMAR FARUQ*D* *PAGE 16* Wani irin ihu su Sarki Barbaru suka saki cikin tsantsar farinciki suna masu ɗaga hannuwansu sama, tare da faɗin. "Gargabilu! Gargabilu!! Gargabilu!!!" Sabo da yadda suka ga gaba ɗaya kaskon nan ya dare gida biyu, kana wutar cikinsa ta mace tas, kamar yadda boka ya faɗa, yayin da su kuma mutanen dake cikin jirgin nan suka sake fashewa da kuka mai sosa rai, shi ko Ishaƙ banda faman girgiza Aishatu yana kiran sunan ta, bayan ya watsa mata ruwa a fuska babu abun da yake iya yi. Wani irin kuka yake jikinsa na tsantsar rawa tamkar ƙaramin yaro. Sarki Barbaru da kansa ya durƙusa a ƙasa, yana mai ɗaukar jaririn dake ta aikin tsala kuka har yanzu a hannun sa, tukun ya buɗe baki cikin muryar sa mai futar da amon sauti, yana mai kallon dakarun sa tare da faɗin. "Ai'ki kuma ya ƙare daga yau, domin ko Ubangiji Gargabilu ya yaye mana wahala, ya aiko mana da mafutar mu, yanzu rayuwar mu zata dawo kyakkyawa ba tare da fargabar komai ba, tamkar yadda muka kasance ada, dan haka ku koremun waƴan nan mutanen, tare da jirgin su gaba ɗaya daga cikin ƙasa ta." Sarki Barbaru ya faɗa yana mai nuna Jirgin su Aishatu. Tukun ya juya ɗauke da Ɗan a hannun sa. Da wata irin gigitattar ƙara Aishatu ta farka da ita tana mai faɗin. "Ɗana! Ɗana!! Ɗana!!! Kuyi haƙuri! Kuyi haƙuri karku kashemun shi, kuyi haƙuri kubani shi ko ɗaukar sa ne nayi, kumun afuwa kubarni inji ɗumin sa yaji ɗumin jiki na shima, kumun gafara ku barni nayi rayuwa da jinjiri na!" Ta faɗa a wani irin haukace tana mai funcike jikin ta daga riƙon da Ishaƙ yayi mata ta sake yin bakin Jirgin aguje tana shirin fucewa, sabo da yadda ta hango Sarki Barbaru ya juya yana tafiya riƙe da jinjirin nata, ga kuma yadda kukan jaririn ke dukan dodon kunnuwan ta. Da sauri wani Badakare da yake abakin hanyar yasan ya hannun sa yana mai hankaɗata baya ta faɗi ƙasa. Tukun suka ƙara zare mahaukatan makaman su suna masu saitawa direbobin jirgin hanya, tare da basu umarnin suyi gaggawar yin gaba tun kafin su canza shawara duka suka kashe su suma. Jin hakan da matuƙan Jirgin nan sukayi kuwa ba ƙaramun sake hatsina musu ƙwaƙwalwa yayi ba, domin kuwa sun tabbatar da babu abun da mutanen nan zasu ce zasuyi sa suka sa yin sa, hakan yasa cikin gaggawa ko wanne ya koma wurin sa, tukun suka sake yin gaba suna masu ɗaukar hanyar su, yayin da suma mutanen Baƙar Masaruta suka ƙara shigewa cikin jirgin su suna masu binsu abaya domin suyi musu rakiya. Tunda wannan Badakaran ya sake hankaɗa Aishatu ta faɗi a ƙasa, sai Ishaƙ ya sake zuwa ya riƙe ta gam, irin riƙon da bazata taɓa iya ƙwatar kanta ba, domin kuwa ya sani muddin zata cigaba da haka to Ba ƙaramun aikin su bane su kashe ta duka itama. Sosai take kuka na tashin hankali mai tsanin ban tausayi daga kwancen da take acikin jirgi, banda raɗaɗi da suya babu abun da take jin zuciyar na nayi mata, tayi nadamar zuwan ta Jahar Ruman gaisuwar mahaifin ta tafi sau dubu, taji inama ace tabi maganar mijin nata tayi haƙuri tabar zuwan, tabbas da tasan babu wani abu wanda zai rabata da Ɗan ta a lokacin da ta haife sa. Sosai take hango kamannin yaron a cikin idanuwan ta, sabo da yarce suka zauna mata a cikin idanuwan nata das, wato kamannin ta kenan sak kamar yacce ta gani akan fuskar jinjirin. Sai da har suka rakasu ƙofar futa daga cikin Ɓakar Masarauta duka, tukun suka juyo da kan nasu Jirgin hankulan su akwance babu damuwar komai tattare da su, yayin da su kuma mutanen cikin Jirgin su Aishatu suka sake fashewa da wani irin azababben kuka, musamman ma waƴan da aka ƙwacewa Ƴaƴa, suna masu kallon hanyar garin, hanyar da suka raɗa mata suna Bakar Hanya, kamar yacce suka raɗawa wannan rana ta Alhamis suna Baƙar Rana, mai tsantsar muni da ƙuna a cikin rayuwar su. Acan ɓangaren su Sarki Barbaru kuwa kai tsaye suka doshi ɓangaren bayi. Tafe suke suna masu furta sunan Gargabilu da matuƙar ƙarfi, yayin da jinjirin nan kuma yake ta cigaba da sakin kuka, har lokacin kuma Sarki Barbaru bai ajiye sa ba. Suna zuwa ɓangaren bayi suka tsaya dukan su a wuri ɗaya, tukun daga bisani wani Bafade ya buɗe baki cikin sauti yana mai faɗin. "Kuna inane ne Ƴaƴan matsiya ta ƙasƙantattu? To kufur-futo ga Uba ga kowa nan ya ƙaraso, ku fur-futo ga bujimin mazaje nan ya ƙaraso, ku fur-futo ga zakin duniya nan na jiran ku." Tun kafin ya kaiga rufe bakin sa sai ga su nan suna futowa da baya da baya daga cikin ɗakunan su na iccina, da matuƙar yawan su mazan su da matan su a guje kuma. Sanye mazan su suke da ƴan gajerun fararen wandina na yadi, babu ko riga ajikin su, yayin da matan su kuma suke ɗaure da wani ɗan guntun baƙin ƙyalke a ƙugun su, tare da wata wargajejiyar rigar yadi ajikin su, gaba ɗayan su babu mai takalmi a ƙafar sa. Da baya da baya suke ƙarasowa har wurin da su Sarki Barbaru suke a tsaye jikin su na karkarwa, tukun sai su juyo ta gaba suna masu zubewa rufda ciki a ƙasa wanwar gaban su Sarki Barbaru. "Ina Iyar Bayi take?" Sarki Barbaru ya faɗa cikin muryar sa da take matuƙar firgitar da su yana kallon su. Wata mata ce mai kimanin shekaru arba'in ta miƙe daga kwancen da take tana mai futowa jikin ta na tsantsar rawa da karkarwa, yayin da kanta kuma yake durƙushe a ƙasa, ta ƙaraso gaban Sarki Barbaru tana mai zube guiwoyin ta a ƙasa. "Tsaye zaki miƙe nan." Sarki Barbaru ya faɗa cikin muryar sa mai firgitarwa yana mai kallon Iyar Bayi da take durƙushe a gaban sa. Yayin da ita kuma ta miƙe tsaye cikin sauri ƙafafunwan ta na wani irin rawa tana mai jin kamar ba zasu ɗauke ta ba, sabo da fargabar laifin da za'ace ta ai'kata da tayi matuƙar lulluɓe ta, domin kuwa ko kaɗan bata lura da ɗan da yake riƙe a hannun Sarki Barbaru ba, duk da kukan da yaron yake tsalawa kuwa tsabar tsoro. Miƙa mata jinjirin dake tsala kuka Sarki Barbaru yayi. Hannuwan ta da suke tsantsar rawa ta miƙa masa su idanuwan ta akan jaririn, tukun shi kuma ya Sarki Barbaru ya ɗora mata Ɗan akan hannun sa. Take kuwa yaron yayi tsit yana zuwa hannun ta, yayin da ita kuma ta zuba masa idanuwan ta tana mai kallon sa tare da yaba kyawun hallitar sa a cikin zuciyar ta. Lokaci guda taji yaron yayi matuƙar shiga ranta, ga kuma wata irin soyayyar sa da taji ta lulluɓe zuciya da ruhinta, tayarce har take jin sa tamkar ita ta haife sa. Sosai ta shagala da kallon sa tana mai ɗan sakin murmushi, domin kuwa ganin kyakkyawan yaron ya sanya ta manta ko a gaban suwa take duka ma. Yayin da shi kuma Sarki Barbaru ya buɗe baki yana mai faɗin. "Ga sabon Ɗa nan na kawo miki shi da kaina, shi kuma wannan jinjirin da kika gani ba kowa bane face rayuwar mu mu dukan mu kamar yadda kukaji labari, hakan yasa nazo da kaina har inda kike na baki shi, dan haka saiki kula mana da Rayuwar mu." Muryar Sarki Barbaru ta daki dodon kunnen Iyar Bayi, wacce tai sanadin dawowa hayyacin ta daga duniyar kallon jinjirin data tafi tana mai faɗin. "Tabbaci tare da alƙawari gare ni zuwa ga kai ya shugabana, babu wani abu da zai faru da wannan yaron, zan kula da shi tamkar yacce na saba kula da sauran Yaran da yardar Ubanguji Gargabilu." Ta ƙarasa maganar muryar ta a ƙasa. Yayin da shi kuma Sarki Barbaru ya juya yana mai tafiya ba tare da yace komai ba. Binsa a baya suma mutanen sa da suka zo tare sukayi. Yayin da su kuma bayin nan duka suka miƙe daga kwancen da suke suna masu yowa wurin da Iyar Bayi take a tsaye, hannun ta ɗauke da jinjirin kowa na kallon sa. Murmushi Iyar Bayi ta sake yi a lokacin da Ɗan ya ƙara tsanyara kuka yana wawurar yatsun sa, tukun daga bisani ta buɗe baki tana mai faɗin. "Wayyo yunwa ma yake ji, dan haka bara naje na haɗa ruwan zafi nai masa wanka, in yaso sai asamo mun madara na basa yasha." Ta ƙarasa maganar tana mai yin gaba zuwa wurin da ɗakin ta yake. *ƘASAR HAUSA, JAHAR WASAI CIKIN MASARAUTAR WASAI.* Shigar mai martaba part ɗin yayi dai -dai da lokacin da Hadima Larai ta dawo hannun ta ɗauke da jinjirin. Da sauri ta zube guiwoyin ta a ƙasa tana mai faɗin. "Barka da futowa Al..." "Bani, bani shi, taso ki bani Baba na na gansa." Mai martaba ya faɗa fuskar sa ɗauke da murmushi, yana mai miƙa mata hannu ba tare da ya tsaya amsa gaisuwar ta ba. Hakan da taji ne ya sanya ta tashi fuskar ta ɗauke da murmushi, sabo da jin da tai har mai martaba ya basa suna, wato sunan mahaifin sa kenan, tana mai miƙa masa Ɗan a hannu. "Masha Allah! Alhmdulillahi Alhamdulillah!." Ya faɗa cikin tsantsar farin ciki yana mai kai hannun sa zuwa kan fuskar Ɗan dako wanka ba'a yi masa ba, ya shafi kumatun sa, tukun daga bisani ya sake buɗe baki yana mai faɗin. "Babban Yaya na biyu kenan ko, wato ita Fulani kawai masu kama da ita take haifowa tsabar san kai kenan." Ya faɗi maganar fuskar ɗauke da murmushi yadda kasan ba Sarki ba, domin kuwa shi kansa bazai iya musalta kalar farin ciki da yake ciki ba, haka kuma yana jin bazai taɓa iya ɓoye saba, koda yana cikin fada ne kuwa. Kallo ɗaya yayiwa jinjirin yaji wata irin soyayyar sa ta lulluɓe duka zuciya da ruhin sa, tayarce har yake jin tamkar bai taɓa haihuwa ba sai akansa, kai ataƙaice dai kallon farko da yayi ga yaron yaji ya shiga ransa fiye duk sauran yaran nasa, har Babban Yaya da yake Ɗan farko namiji gare sa kuwa. "Yanzu ina ita Fulanin take ne?" Mai martaba ya faɗa yana mai miƙawa Hadima Larai jinjirin, sabo da jin da yay ana tada sallah a cikin masallacin Masarauta. "Tana cikin ɗaki lafiya ƙalau." Gimbiya Larai ta faɗa tana karɓar Yaron. "Tom shikenan ki mata sannu yanzu in kin shiga, ni na tafi masallaci bayan an idar da Sallah zan dawo, domin kuwa ban gaji da kallon wannan babbar kyautar da Ubangji yayi mun ita ba." Ya ƙarasa maganar yana mai juyawa yayi gaba. Yayin da ita kuma Hadima Larai ta ƙame a wurin ɗaya tana mai bin bayan mai martaba da kallo, sabo da yadda taji ya tsaya a gaban ta yana dogon surutu, abun da bata taɓa ji ance yayi ba ballan tana kuma ta gani, domin kuwa iyakar su da shi gaisuwa ce kawai ke haɗasu, amma sai gashi yau ya tsaya gaban ta yana zuba da nuna farin ciki, yadda kasan a yanzu aka fara masa haihuwa. "Tabbas ko a kwai badaƙala a cikin gidan nan, muddin mai martaba zai cigaba da rawar ƙafa akan yaron nan ba ƙarama bama kuwa, dan sai dai kawai muyi fatan Allah ya kare." Ta faɗa tana mai yin gaba ta doshi ɗakin Fulani, domin taje ta gyara wurin da a kayi haihuwar da kuma shi kansa jinjirin. Acan ɓangaren Gimbiya Huwaila kuwa tana shirin fucewa daga cikin falon ta sukaci karo da Jakadiya, ita kuma tana danno kanta domin ta shigo, har lokacin takalman ta riƙe suke a hannun ta, da alamun bata sanya su ba a haka ta tawo tun daga can ɗakin ta har nan. Da sauri Jakadiya ta miƙa hannu tana mai riƙo hannun Gimbiya Huwaila, sabo da ganin da tayi tana shirin fucewa kamar bata ganta ba. Janta Jakadiya tayi cikin sauri suna masu nufar ɗakin ta, ba tare da tace mata komai ba. Suna shiga cikin bedroom ɗin Jakadiya ta saki hannun Gimbiya Huwaila tana mai juyawa ta rufe ƙofar bedroom ɗin, tukun ta sake juyowa ga Gimbiya Huwaila data ɗora tafin hannun ta akan goshin ta tana mai sakin numfarfashi, tare da rumtse idanuwan ta, tukun daga bisani ta buɗe su akan fuskar Jakadiya, lokaci ɗaya duka sun canza launi sunyi jajahur yacce kasan gauta. "Shin meye hakan ya faru Jakadiya? Tayaya ma za'a ce Fulani ta haihu, haihuwar ma kuma Ɗa namiji, Ɗa namijin ma kuma mai rai, tayaya hakan ya faru ne Jakadiya?" Gimbiya Huwaila ta faɗa a wani irin haukace tana mai zagaya cikin ɗakin nata. "Nima abun da ya ɗaure mun kai kenan, ya kuma rikita ni Uwar Sarkin Gob..." "Dakata haka Jakadiya!" Gimbiya Huwaila ta faɗa da wani irin ƙaraji tana mai ɗagawa Jakadiya hannu, tare da rumtse idanuwna ta, tukun daga bisani ta buɗe su tana mai faɗin. "Akan me zaki cigaba da kirana da wannan sunan kina samun rai, bayan kuma kin san duk ƙarya ne hakan kuma, bayan kuma keda kunnuwan ki kinji kalar sautin da tamabari ya futar yanzu, bayan kuma wanda ya futar shekaru goma da suka huce baya." Ta ƙarasa maganar da sakin numfarfashi. Yayin da ita kuma Jakadiya ta buɗe baki tana mai faɗin. "Karki fara faɗin haka yake Shugabata, kar kiyi kuskuren cewa zaki sare tun yanzu, domin kuwa haihuwar Yara biyu maza bashi ke nufin an haifo Sarki cikin su ba, dan kuwa sanin kanki ne hawa karagar Sarki sai wanda ya cancanta ko cikin Ƴaƴan Sarkin, sai kuma ya a jiye abubuwa da yawa, tukun yake da damar hawan ta, kinga kenan tunda har akwai waƴan ka'idojin, to ko ba mutuwa kina iya zamtowa Uwar Sarki muddin kin haifo Ɗa namiji kema." Jakadiya ta faɗa tana kallon Gimbiya Huwaila. Yayin da ita kuma tayi shiru tana mai lumshe idanuwan ta, tukun daga bisani ta buɗe su tana mai girgiza kanta, kana ta sake buɗe baki tana mai faɗin. "To duk naji wannan kuma na amun ta da hakan Jakadiya, amma kafun nan, wai taya ma akai hakan ta faru, taya ya za'ace Yaron yazo da rai, bayan kuma kince mun kinyi duk yadda nace kiyi tun a jiyan?" "Ta sanadin ikon Allah mana, domin kuwa cikin duka abubuwan da kika sani babu wanda banyi sa ba, sai dai kuma ko idan ita ɗin ce bata kwanta akan gadon ba, sabo da dama lokacin da naje ɗakin nata na same ta ne zaune agefen kujera kamar yacce na faɗa miki tun jiya, kuma ma ba wannan ba, shin wai kin manta ne haka kikece sai an baɗa mata maganin har kimanin sau ukku arana, sannan kuma ta kwanta aƙar-ƙashin layoyin tukun Ɗan zai mace?" Jakadiya ta faɗa tana kallon ta, yayin da ita kuma Gimbiya Huwaila ta dafe goshin ta da tafin hannun ta tana mai faɗin."Kashhhh!" Tukun ta tafi da baya da baya tana mai zuwa ta zauna yaraf akan gado, tare da cije leɓen ta na ƙasa da ƙarfi. "Ina da wata shawara, wacce nake ganin ko ita kawai akabi zamu cimma burin mu." Jajadiya ta faɗa daga inda take a tsaye, idanuwan ta akan fuskar Gimbiya Huwaila. "Mene abun tsayawa ɓata lokaci, bayan kuma kin san yana gab da ƙare mana, kawai faɗe ta kai tsaye inji ta mana, idan zatayi mai zai hana abita." Gimbiya Huwaila ta faɗa tana kallon Jakadiya. Hmmmm! "To ai sirri ne abun shugabata." Jakadiya ta faɗa bayan ta saki wani shegen murmushi, tukun ta fara ɗaga ƙafafuwan ta tana mai matsawa kusa da Gimbiya Huwaila. Sai da taje har gab da ita, tukun ta ranƙwafa tana mai kai bakin ta dai dai kunnen Gimbiya Huwaila da suke ɗauke da haɗaɗɗen ɗan kunnen gwal, tukun ta fara yi mata raɗa a cikin kunnen nata. Ta ɗauki kusan mintina biyar zuwa shida tana mata raɗan, tukun daga bisani ta janye bakin ta daga kan kunnen ta tana mai miƙewa tsaye fuskar ta ɗauke da murmushi tace. "To ya kika ji?" Shiru Gimbiya Huwaila tayi tana mai ɗan taune lowar lios ɗin ta, ba tare da tace komai ba, tukun daga bisani ta buɗe baki tana mi faɗin. "Hakan ma tabbas zai yin, amma si dai ina son mu fara yin wanda na faɗa miki, idan baiba sai mubi ita wannan hanyar ɗin." Ta ƙarasa maganar itama da sakin murmushi. Haka dai duka haihuwar Ɗa namijin da Fulani tayi ta girgiza gaba ɗaya magautan su na cikin gidan, tare da ɗimauta su, sannan kuma ko wanne ya fara ɗaura ɗamarar sake sabon taku, wurin ganin sun kawar da duka yaran biyu, daga Babban Yaya har shi sabon Jinjirin da aka haifa yau. Yayin da masoyan su kuma murna da farin ciki suka cika su, har suka ransa inda zasu sa kansu, tun kafin agama idar da Sallah Asuba part ɗin Gimbiya Fulani ya fara cika da jama'a, masoya da ma maƙiya, sai dai kuma kowanne da manufar da yake zuwa da ita, su masoya domin taya ta farin ciki, yayin da su kuma maƙiya suke zuwa domin su fara ai'watar da aikin su. _BAYAN KWANA BAKWAI_ *ƘASAR MALIN, JAHAR KARFUZ CIKIN BAƘAR MASARAUTA* Tun daga bakin get ɗin gidan Bayi mutum zai fahimci yau ɗin suna wani gagarumin shagalin ne a ciki, sabo da yadda kiɗa ke tashi da matuƙar sauti tare da daɗi a ɓangaren Bayin, ga kuma manya manyan tukwane da aka ɗora akan duwar-watsu ana aikin basu huta sosai, kasancewar yau ɗin ta kasance sati ɗaya dai-dai da samuwar jinjirin nan, kuma dama a ƙa'idar Baƙar Masarauta koda Bayi ne suka haihu to ana barin su suyi shagalin suna ya junan su, a kuma cikin wurin su, hakan ne yasa tun jiya kuwa suke ai'yika, domin yau ɗin ce takasance ranar sunan sabon yaron da aka kawo musu. Sosai suke cikin farin ciki daga mazan su har matan su, kasancewar sai a irin wannan ranar ta suna idan tazo musu ne kawai suke samu suyi nishaɗi, ayi dariya, a kuma yi kiɗa ai rawa cikin farin ciki da junan su, ba tare da an daki kowa ba a cikin su. Acan ɗakin Iyar Bayi zaune take agefen shimfiɗar ta, rungume da ɗan jaririn a hannun ta tana mai muts-tsika masa mai a jiki, kasancewar yanzu ta gama yi masa wanka, domin kuwa ko ruwan zafin da tai masa wankan da shi ma ba'a janye sa daga wurin ba. Sai da ta gama shafe sa da mai tas, sannan ta ɗauki hoda ta shafa masa akan fuskar sa, tukun ta miƙa sa zuwa hannun wani mutumi da yake zaune a gefen ta shima da irin shigar su ta Bayi. Karɓar yaron yayi a hannun sa, sannan ya juya ɓarin sa na dama yana mai janyo wata ƴar ƙaramar roba a kusa da shi, tukun ya buɗe murfin robar. Wani baƙin abu ne mai kama da baƙin fenti a cikin ta, sai kuma tambarin Baƙar Masarauta ɗan ƙarami na soso, da yake a cikin baƙin fentin. Hannun sa na hagu yasan ya a cikin robar yana mai zaro soson, sannan ya futo da shi waje yana mai manna sa akan farar fatar jinjirin. Take kuwa tambarin masarautar tasu ya futo ɗas a jikin sa baƙiƙƙirin da shi, haka mutumin yay ta manna masa tambarin a fatar sa har kan fuskar sa, sai da ya tabbatar da ko ina tambarin ya futo, tukun ya janyo wani ɗan mitsitsin baƙin wando na yadi irin na jarirai, yana mai ɗago jinjirin, sannan ya sanya masa shi a jikin sa, kana ya buɗe baki yana mai faɗin. "Daga yau za'ana kiran sa da suna BIR, domin kuwa shine sunan da aka raɗa masa." Ya ƙarasa maganar yana mai miƙawa Iyar Bayi shi. Miƙo hannun ta tayi ta karɓe sa fuskar ta ɗauke da tsantsar far'a, tukun ta janyo wani sabon farin yadi tana mai sanya sa a ciki, ba tare da tasa masa ko riga ba, kamar yadda sauran bayi mazan wurin suke duka, babu mai riga a jikin sa. Kallon yaron tayi tana mai sakin murmushi, yayin da shi kuma yake ta faman yin wutsi-wutsil da ƙafafuwan sa, yana mai kallon wurare daban-daban, alamun yana cikin ƙoshin lafiya kenan. Sosai yaron ya ƙara girma da wayo a sati ɗayan da yayi kawai a duniya, ko kaɗan basa da damuwar komai, domin kuwa da zarar yayi kuka Iyar Bayi take ɗaukar madara ta basa, sannan kuma tasa zani ta goye sa a bayan ta idan ya gama sha. Fari ne kar yadda kasan a taɓa sa jini ya ɓullo, kyakkyawa ne sosai, domin kuwa ko kaɗan basa da makusa ta ko ina jinjirin, hakan yasa su kansu sauran Bayin suke matuƙar sonsa, sannan kuma kowa yake mararin ɗaukar sa. Miƙewa Iyar Bayi tayi tsaye da ɗan a hannun ta, tana mai faɗin. "Suna yayi daɗi, dan haka bara muje ashelan tawa jama'a, a kuma shiga tsakiyar fili ai rawar suna da jinjiri." Ta ƙarasa maganar tana mai fucewa daga cikin ɗakin. Kai tsaye ta doshi wurin da sautin kiɗa ke tashi, kasancewar anan ne ta hango dan-dazon jama'a maza da mata suna rawa. Itama rawar ta farayi tun daga wurin da take tana tafiya, a haka har ta ƙarasa cikin filin hannun ta riƙe da Ɗan. "Kai ku gafara nan gamu nan mun iso, suna ya raɗu yaro zama *BIR*." Ta faɗa tana mai kutsawa cikin filin rawar. Take kuwa a wurin kiɗa da rawar da ake suka sauya salo, yayin da jama'ar wurin kuma keta sakin tafi da rawa suna zagaye Iyar Bayi da jinjirin a tsakiyar su, bakunan su na furta. "Barka da zuwan BIR! Marhabun da zuwan BIR." Haka suke ta faɗe suna zagaye Iyar Bayi da jinjirin da matuƙar ƙarfi, sunayi suna sakin tafi. *ƘASAR HAUSA, JAHAR WASAI CIKIN MASARAUTAR WASAI.* Yau take ranar suna a cikin Wasarutar Wasai, hakan yasan ya ko ina ka kalla a cikin Masarautar kake ganin jama'a tun daga kan hadimai, kuyangu suna ta giftawa ta ko ina. Yayin da sautin bushe bushen sarewa, algaitu, kakaki, kiɗan ƙwarya, harma da tambura keta tashi a cikin wurare daban daban na masarautar. Ga kuma yadda bayi keta wucewa da niƙi-niƙin abinci kala-kala afarantai ta ko ina, sannan ga mutane da suke ta hucewa akan dawakuna sunci uban kwaliyya a jikin su, kamar yacce suka tsan-tsarawa dokunan nasu kwalliya. Acan ɓangaren Gimbiya Fulani kuwa, tun daga harabar part ɗin nata zakaci karo da maroƙa suna ta faman sakin kiɗa tare da kirare-kirare da matuƙar ƙarfi. Faɗi suke. "Allah ya raya mana Ahmad ɗan gidan Abdallah jikan Ahmadu, ɗan gidan sa'a haihuwar sa'a jikan sa'a, fari farar aniya, jinin sarauta kafu ƙarfin raini, Ɗa ga gimbiyar mata, shugabar kyawawa kuma uwar Sarkin gobe, Ahmadu jinin alkhairi haihuwar nasara, ƙani ga Sarkin mu na gobe Usmanu Babban Yaya. Allah ya raya mana Ahmadu Asadullahi Zakin Allah, mai Kakkani da yawa, mai Iyaye lodi-lodi, mai Yayye bila adadin. Kakan ka Ɗan Sarki Ubanka Ɗan Sarki, Mamar ka Ƴar Sarki kaima kuma Ɗan Sarki." Haka suke ta sakin kirari da bushe-bushe da matuƙar ƙarfi, kasancewar an riga da an raɗa suna tun asubahi, yaro yaci suna Ahmad, wato sunan Mahaifin mai martaba, hakan yasa tun a wurin mai martaba ya ƙara masa da wani sunan akai wanda za'ana faɗa masa, wato ASAD, ma'an ZAKI kenan. Hakan kuwa ba ƙaramun tafasa zuciyar magautan su ya sakeyi ba, barin ma yadda suka ga mai martaba na wani irin farin ciki da samuwar yaron, yadda kasan akan sa aka farayi masa haihuwa, ga kuma labarin da suka ji yana yawo, na cewar mai martaba da kansa yace yau akwai hawa irin hawan da ba'a taɓa yin sa ba a suna, za'ayi kilisa kalar kilisar da ba'a saba yin ta ba yau da yamma. Hakan kuwa ba ƙaramu sake lona musu rai yayi ba, sannan kuma suka ɗauki alwashin ganin bayan jinjirin nan kota halin ƙaƙa ne. Acan cikin ɗakin Gimbiya Fulani kuwa zaune take a gefen gadon ta taci uban Ado mai tsananin kyau da ɗaukar hankali da abubuwan kuɗi. Sanye take da wani ɗan ubansu farin less, mai ratsin adon baƙi a jikin sa da yayi matuƙar amsar jikin ta, dinƙin riga da zani da ɗan kwali, sai wasu irin saraƙunan gwal da suke manne a jikin kunnuwan ta da wuyan ta, suna ta faman ɗaukar ido, ga wani irin azababben ƙamshin turarruka masu matuƙar daɗi da suke futa daga cikin jikin ta. Yayin fa shi kuma Ɗan jarari Asad yake riƙe a hannun Hadima Larai, da itama taci uban Ado tana mai sake canza masa wasu kayan, sabo da futar da za'a sake yi da shi, harma da Gimbiya Fulani, sabo da yanzu aka aiko cewar mai Martaba yace su shirya su futo harabar gida za'ayi musu hotuna a tare. Hakan yasa ake canza masa wasu sababbun kayan, duk da dai waƴan can na jikin nasa da aka cire masa suma basu fi minti goma ba duka da sanya masa su ɗin. Sosai yaron ya ƙara girma da kyawu asati ɗayan da yayi a duniya. Kamar shi ɗaya sak da mahaifiyar sa, basu da bam-banci ko kaɗan. Cikin ƴan sakanni ta gama sanya masa kayan tas har takalmi, tukun ta ƙara fashe sa da wani haɗaɗɗen turare mai tsananin ƙamshi na jarirai. Tukun ta miƙowa Gimbiya Fulani shi, da itama ta miƙe tsaye tana mai yafa wani haɗaɗɗen mayafi a jikin ta. Karɓar sa tayi a cikin lafiyayen showel ɗin sa, tukun ta fara takawa tana mai dosar hanyar waje. Tana futa tabi wata ƙofa dake a cikin ɗakin nata, wacce zata sadata da part ɗin mai Martaba kai tsaye, domin kuwa da aka tashi tsara ginin gidan, sai da yasa akayi masa hanyoyin da zasu kaisa duka ɓangaren matan nasa ukku daga cikin part ɗin sa, ba tare da ya futa ta babbar ƙofa ba. Baifi minti goma tayi ba da shigar ta, sai ga sunan sun futo a jere ita da mai Martaba, ga kuma Babban yaya da yake daga bayan su da irin shigar mai martaba sak a jikin sa. Sanye suke da farar shadda mai tsananin kyawu da tsada, banda ƙyalli da ɗaukar ido babu abun da take yi, yayin da kawunan su kuma suke ɗauke da baƙaƙen tare da farin rawani, kamar yacce takalman ƙafafuwan su suka kasance baƙaƙe suma, sai kuma wata haɗaɗɗiyar baƙar al'kyabba mai adon fari da take sanye a jikin su, su duka biyun. Haka suka cigaba da takowa mai Martaba rungume da Asad a hannun sa. Suna shigowa Babban falo gaba ɗaya matan dake zaune a cikin sa suka rangaɗa wata mahaukaciyar buɗa mai tsananin ƙara, suna masu miƙewa tsaye. Yayin da masu hotuna kuma suka fara ɗaukar su tun daga nan tare da video, a haka har suka ƙarasa harabar gidan. Suna futowa maroƙa da fadawa sukayo kan su gaba ɗaya, ko wanne da kalar kirarin da yake yi gare su. "Barka da futowa Asadullahi, barka da isowa Zakin Allah, barka da isowa Yariman Wasai! Yarima Damisan Yan Sarki, Yarima Ɗan masu gari, Ɗan bakin ruwa da ciyawa, Ɗan uban gabasawa." Gaba ɗaya maroƙan dake wurin suka faɗa a tare, suna masu sakin kiɗa duk alokaci ɗaya, yayin da su kuma Fadawan Sarki da suke tsaye a harabar wurin suka matso gare su da sauri, suna masu zagaye su, bakunan su na futar kalmomin. "Barka da futowa Sarkin Sarakai, barka da futiwa toron giwa! Sakaka Baban baƙo! Uban gabasawa! Taka lafiya barden mahadi! A Lafiya bahau da wani ba saukan wani! Lafiya hana kangara! Lafiya bango madafar Bayi! Lafiya hadarin ƙasa maganin mai kabiɗo! Lafiya dubu jiran mutum ɗaya! Lafiya gagara gasa! Uban Yarima Usmanu, Uba ga Asadullahi sabon yaro, miji ga kyakkyawar Gimbiya mahaifiyar Sarkin mu na gobe. Taka a lafiya jinjirin wata shakallo." Fadawan keta faɗe suna masu binsu a baya, a haka har suka ƙarasa wurin da za ayi musu hotunan, tukun suka kauce suka bada wuri aka dinga musu hotuna kala-kala, sannan kuma da mutane daban -daban, domin kuwa harda su Gimbiya Huwaila da Gimbiya Amina sai da akayi musu hoton tare, duk da dai ko kaɗan bawai dan ransu yana soba suka tsaya akai hoton, sunyi ne kawai gudun kar suƙi zuwa mai Martaba ya zargi wani abun, kasancewar shi da kansa ya aika a kira su suzo ayi hoton. Haka dai aka yini shan-shagalin suna a cikin gidan har zuwa yamma. Tukun aka sake sabon shiri, sabon wanka, sannan kuma a kayi sabuwar futowa ana tafiya filin Hawa, kasancewar dama da yamna aka tsara za'ayi Hawan sunan. Sosai akayi Hawa a kai wasa da dokuna irin wanda ba'a taɓa yin saba tun da ake Haihuwa a cikin gidan, domin kuwa hatta da shi Mai Martaba sai da yayi wasa da doki irin wasan da bai taɓayin kamar sa ba, wato wasa na ban mamaki, wanda yayi matuƙar ƙayatar da al'ummar wurin, yayin da zuciyoyin magauta kuma suka cika dam da baƙin ciki tamkar sayi bindiga, donin kuwa a cewar su wannan wasa da dokin kawai da sarki yayi shi yake nuni da ada duk ba haihuwa ake masa ba sai a yanzu ne akai masa, sannan kuma Gimbiya Huwaila da Gimbiya Amina matan sa suka sa aransu cewar duka bai ɗauki Ƴaƴan wurin su ba amatsayin Ƴaƴa, tunda a lokacin su su duk bai nuna irin wannan farin cikin ba, hakan yasa suka ƙudiri aniyar ganin bayan Baban Yaya da kuma Ɗan jariri Asad mai farin jinin jama'a. "UNGUWAR ƊAN TANKI.* Tunda su Aishatu suka dawo gida har kawo yau bata dawo hayyacin ta ba, domin kuwa ataƙaice ma har a gadon asibiti sai da aka kwantar da ita, sabo da jinin ta da yayi bala'in hawa. Sosai hankalin duka jama'ar gidan dama duk dangin su yayi matuƙar tashi, a lokacin da labarin abun da ya faru ya riske su. Kaka tayi kuka, tayi kuka kamar ranta zai futa da jin wannan baƙin labarin, tayi tsinuwa bila adadin ga mutanen Baƙar Masarauta, sannan kuma tayi nadamar sanya Ishaƙ ya bar Aishatu da tayi yafi a ƙirga, yayin da ta fannin Mahaifin Ishaƙ shima yaji ina ma ace ya hanasu tafiyar tare, sai dai kuma babu wani bawa da ya isa ya canza abun da Allah ya tsaro. Lokacin da labarin ya riski dangin Aishatu na Jahar Ruman, suma hankulan su ba ƙaramun tashi yayi ba, hakan yasa tun a washegarin ranar suka haɗo kayan su da komai da komai nasu suka sake baro Ƙasar Malin cikin ɗacin rai, suna masu dawowa Ƙasar Hausa, Jahar wasai cikin rugar su da suka bari kafun su koma can. Sosai Aisahtu ta fige ta rame, ta lalace dukan ta, domin kuwa har yau bata dena kuka ba da surutai kala-kala, musamman ma idan akace dare yayi, sannan kuma kullum idan ta kwanta bacci sai tayi mafarkin yaron nata a hannun wata mata tana kula da shi. Ganin da su Ishaƙ sukayi Aishatu taƙi kwantar da hankalin tane ya sa suka fara nemar mata addu'oin dan gana suna bata tana sha, sannan kuma suka sanar a massallatan Unguwar su cewar a taya su da addu'a, kana suma kullum suke kan yin ta, domin kuwa tamkar mahaukaci haka Aishatu take komawa idan tana surutai. Yayin da su Ahmad da sauran ƙannen sa suke sata a gaba suyita aikin kuka, ataƙaice dai gaba ɗaya gidan sun koma abun tausayi. *BAYAN SUƊEWAR SHEKARA HUƊU* *ƘASAR MALIN, JAHAR KARFUZ CIKIN BAƘAR MASARAUTA.* Sosai Bir yayi matuƙar girma tare da wayo da kyawu, domin kuwa idan mutum ya gansa muddin ba sanin shekarun sa yayi ba, sai yayi tinanin yakai irin shekara bakwai ɗin nan, sabo da girman jikin sa, har yanzu kuma yana a wurin Iyar Bayi ne, ita take kula da shi take masa komai, domin shi duk a tinanin sa ma itace Uwar sa, hakan yasa yake kiran ta da Iya ta, yayin da itama a koda yaushe take jin sonsa na ƙara ƙaruwa a cikin zuciyar ta fiye dana baya. Zuwa yanzu shima har ya fara yin wasu abubuwan irin na bayi, waƴan da suka haɗa da ɗibar ruwa da kuma ɗaukar icci na Yanzu haka zaune suke a ƙasan inuwar wata bishiya suna wasa shi da abokan sa guda biyu. Sanye suke d.............✍ *A PAGE ƊIN JIYA NAYI MANTUWA A WURIN FAƊIN SUNAN MATAR SARKIN WASAI TA BIYU MAI SUNA AMINA, YAYIN DA NI KUMA NA SANYA SUWAIBA, DAN HAKA AMINA SHINE SUNAN NATA, SUWAIBA KUMA SUNAN ƊAYA DAGA CIKIN ƳAƳAN HUWAILA NE BABBAR MATAR SARKI ABDALLAH.* *BAƘAR MASARAUTA* *NA* UMAR FARUQ*D* *PAGE 17* Sanye suke da ƴan guntayen baƙaƙen wandina na yadi iyakar guiwoyin su babu ko riguna a jikin su dukan su. Riƙe Bir yake da kwari da gwafa a hannun sa yana mai gyara danƙon jikin ta, kasancewar tana ɗaya daga cikin abubuwan da yake matuƙar so a rayuwar sa. Tun da ya taso yaga mayaƙan Baƙar Masarauta na amfani da ita, sai shima abar take matuƙar birge sa, hakan yasa ko da yasuhe da ya futo daga ɗakin su muddin suna nan yake hucewa wurin su yaje ya tsaya yay ta kallon su, wani lokacin ma har ya ɗauki abar ya fara shirin gwada harbawa shima, hakan da ɗaya daga cikin maharban nasu ya gani ne yasan ya sa haɗawa Bir wata ƴar ƙarama dai-dai da shi ya basa, a ranar kuwa ba ƙaramar murna da farin ciki yayi ba, sannan kuma wuni yay adaji yana harbin tsuntsaye, har sai da Iyar Bayi taje ta kamosa da kanta da taji shiru, domin ko ita ko kaɗan bata son harkar kwari da gwafar da Bir ɗin yake yi, sabo da tana tsoron kar wataran aga ya ƙware da harkar amayar da shi cikin Maharban Masarautar, sabo da idan hakan ta faru to rabin rayuwar sa zata ƙare ne a yawon dajika, sannan kuma koda wani faɗan ya taso to yana ɗaya daga cikin mutanen da za'a na turawa, hakan yasa take ƙin abar sosai, sai dai shi kuma Bir akullum ƙara ƙaunar kwari da gwafar sa yake. Tun yana ɗan ƙaramin sa yake da wata irin halayya ta taurin kai da kafiya, domin kuwa muddin baiyi niyyar yin abuba to ko ance yayi bazai taɓa yin sa ba, ko da za'a dake sa ne kuwa, haka kuma dan an dake san a banza, sabo da baya kuka kwakwata, sai dai mutum yayi ya gama, wannan dalilin ne yasa Iyar Bayi take kiran sa da suna JARUMI, saboda yadda yake da tsantsar jarumtar a ɗan ƙaramin sa. "Jarumi! Jarumi!!" Muryar Iyar Bayi dake tawowa wurin da suke ta daki dodon kunnen Bir da yake shirin harba tsinken gwafar sa jikin bishiya. Da sauri ya juya ɓarin da take yana mai kai dara-daran kyawawan idanuwan sa kan fuskar ta, tukun ya buɗe baki yana mai faɗin. "Me ayi ne Iya yanju ma?" "Wanka da cin abinci mana Jarumi, kaga su Mauzum tun ɗazu nayi musu wanka, gasu nan har sunzo kuna wasa tare, amma kai tun da kafuce tun safe kaƙi ka dawo kana nan kana shirme." Iya Bayi ta faɗa tana mai ƙarasawa kusa da Bir ta riƙo hannun sa. Yayin da shi kuma ya buɗe baki yana mai faɗin. "To a ƙoshi Iya ta, idan a gama halbo cuncuna zanjo kimun wanka, she ki shoya mana shi mucinye ko." Ya ƙarasa maganar yana mai sakar mata dariya, tayarce har sai da kyawawan jerarrun fararen haƙwaran da suke a bakin sa suka bayyana. "A'a Bir bani gwafar nan haka, in yaso bayan na maka wankan kaci abinci sai kadawo ka cigaba da harbo sun, domin kuwa idan ba haka ba nasanka sai ka kai har dare a wurin nan ba tare da ka gama ba." Iyar Bayi ta faɗa tana mai ƙwace kwari da gwafar da suke riƙe a hannun sa, sabo da sanin da tayi muddin ba amsar sun tayi ba to bazai taɓa binta ba. Diddira ƙafafuwan sa ya farayi a wurin yana shirin sakin kuka, sabo da ƙwace masa da tayi. Hakan da Iya ta gani ne yasan ya ta buɗe baki tana mai faɗin. "Haba dai Jarumi da kuka, ka taimaka kar kabani kunya mana, kasa yau mutane suyi mana dariya." Ta ƙarasa maganar tana mai jan hannun sa sukayi gaba. Ba dan Bir yaso tafiya ba yabi Iyar Bayi suka tafi, yayin da suma abokansa su Mauzum suka biyo su a baya. *ƘASAR HAUSA, JAHAR WASAI CIKIN MASARAUTAR WASAI.* A yanzu haka shekarun Babban Yaya goma shahuɗu a duniya, sosai ya ƙara girma tare da nutsuwa da kuma hankali, wanda hakan kuma ba ƙaramun ƙona zuciyar magautan su yake ba, domin kuwa babu kalar asirin da basuyi masa ba amma duk a banza har yau yaƙi cin sa, sai dai kuma suma ɗin har kawo yau basu haƙura sun dena ba, kamar yacce har yau Fulani bata sare ba wurin yiwa Ƴaƴan nata addu'a, sannan kuma suma ta koya musu sukeyi da kansu. Tunda Fulani ta haifi Asad har yau bata sake haihuwa ba, sosai yaron yayi girma bana wasa ba, domin kuwa babu wanda zai gansa yace bai kai shekara bakwai ba a duniya muddin ba sanin sa mutum yayi ba, yayin da kyawunsa kuma a kullum yake ƙara futowa. Gaba ɗaya halayyar sa ba iri ɗaya bace da ta Babban Yaya, dan kuwa shi akwai shi da san yawo, tare da maitar Doki, wanda har hakan da mai Martaba ya gani yasa ya siya masa dawakai har guda ukku ƙanana ƙosassu ana kula masa da su, sannan kuma ake ɗora sa akan su aduk lokacin da za'ayi hawa, ko kuma ranar juma'a, kai wani lokacin ma haka nan kawai ake ɗora sa saman dawakan ayi ta zageye da shi acikin gari, shi kuma yay ta aikin dariya yana jin daɗi, kasancewar sa yaro mai yawan fa'arh da dariya. Yayin da shi kuma Babban Yaya bai damu da shiga mutane ba, asalima ya fison ya gansa a kusa da mahaifiyar su Fulani ako da yaushe, sannan kuma ko kaɗan basa da maitar dokin da Asad yake da ita, dan shi a yanzu haka ma duka dokunan sa guda biyu ne, saɓanin Asad da yake da guda ukku. Sosai sukayi wata irin mahaukaciyar shaƙuwa tsakanin sa da ƙanin nasa, kamannin su ɗaya sak, sai dan hasken fata da Asad yafi Babban Yaya da shi. Ko kaɗan Fulani bata son yawan yawon da Asad yake yi, asonta tafi son ace kullum yana gaban ta tana masa addu'oi kamar yacce suke tare da Babban yaya, sabo da tsaro badan tsoro ba, domin kuwa babu wata hallaya ɗaya ta mutan gidan nasu da bata santa ba, yayin da shi kuma yaran kwata-kwata baya son zama a cikin gida, asalima kullum a Fada yake yini kusa da Mai Martaba suna hira, sabo da ko kaya yanzu haka kullum iri ɗaya suke sawa da shi da Mai Martaba, hatta da alkyabba kuwa, wanda hakan kuwa ba ƙaramar shaƙuwa ce ta ƙara shiga tsakanin sa da Mai Martaba ba, tayarce har yake jin sa fiye da duka sauran yaran sa a zuciyar sa, sannan kuma yake gaza ɓoye soyayyar sa a gaban kowa, wannan dalilin ne yasan ya Fulani bata fiye samun damar yi masa addu'oi ba, kamar yadda take yiwa sauran yaran, sannan kuma shi kansa Asad ba damuwa yayi da addu'ar ba kamar yacce Babban yaya yake yin ta a lokacin da yana ƙarami kamar sa, asalima ko yi masa Fulani zatayi wataran sai ta riƙe sa, tukun take samu ta masa azkar ɗin, idan kuma ba haka ba tana cikin yi zai ruga ya barta a wurin ba tare da ta gama ba, hakan ko ba ƙaramun tsoratata yake ba, sai dai kuma ako da yaushe cikin kaiwa Allah kukan ta take yi. A yanzu haka Abokin Asad guda ɗaya ne, wato Al'amin ɗan gidan Galadima ƙanin Mai Martaba, da aka haife sa bayan haihuwar Asad da wata ukku. Sosai sukayi matuƙar shaƙuwa yaran, yadda kasan waƴan da aka haifa a tare, domin kuwa hatta da abinci tare suke ci ako da yaushe, haka kuma shima Al'amin a cikin Fada yake yini wurin su Mai Martaba, kamar yacce Asad yake yini anan ɗin. Ko hawa aka tashi yi, shiga iri ɗaya ake yi musu su biyun, sannan kuma kusan ajere ake riƙo dawakunan su suna asaman su. Haka mutane zasuyi ta ɗaga musu hannu ana kiran sunan su, barin ma Asad da yake da wani irin farin jinin al'umma tun yana ɗan ƙarami, domin kuwa aduk lokacin da aka futa da shi akan doki sai jama'a sun tsaya suna kallon sa, yayin da shi kuma zakaga yana ta ɗaga musu hannu sama yadda kasan Babban mutum. A ɓangaren magautan su kuwa har yau basu dakata da asirce- asicen da sukeyi ba akan yaran biyu domin ganin bayan su ta kowace hanya, wato Asad da Babban Ƴaƴa, barin ma Asad a yanzu, dan kuwa sunfi tsanar sa sama da Babban Yaya nesa ba kusa ba, sabo da yadda suka ga kaga Mai Martaba naji da shi fiye da Babban Yaya, hakan yasa mutane suka fara zargin tsaf yaron zai iya hawa kan karagar mulki muddin ya ɗore da san zaman Fada har girman sa, wannan dalilin ne yasan ya su suke jin tsanar sa fiye da yadda suke jin ta Babban yaya a zuciyar su, sannan kuma suka mayar da hankali wurin ganin sunga bayan sa ta kowace irin hanya ce, domin kuwa hakan ne kawai zai sama musu salama a rayuwar su. *UNGUWAR ƊAN TANKI.* Sosai su Ishaƙ su kaci wuya akan Aishatu, kafin daga baya kuma Allah ya sanya mata dangana ta sanadin addu'oin da aka dage ana tayi ba dare ba rana, masallatai da cikin gida akan ta, sai dai kuma gaba ɗaya ta canza, halayyar ta dawo sabuwa, domin tun lokacin da abun ya faru ta koma shiru shiru, gaba ɗaya magana ma sai dole ke sata take yi, ako da yaushe sai dai ta shige ƙuryar ɗaki ta zauna kan gado tai ta faman aikin tinani, wani lokacin ma harda kuka. Hakan da ta dawo ɗin kuwa ba ƙaramun sosa zuciyar Ishaƙ da mahaifan sa yake ba, sosai take matuƙar basu tausayi da yarce ta koma ɗin yanzu. Tun bayan haihuwar Ɗan da tayi a cikin jirgi ruwa bata sake yin wata haihuwar ba, yayin da Ahmad kuma yake da shekaru goma shahuɗu dai -dai a duniya yanzu. Sosai yaron yake da matuƙar hankali da nutsuwa, uwa uba kuma ga san addini da ƙoƙari, domin kuwa har ya sauke izu sittin na alƙur'ani akan sa, ga kuma litattafai da yayi matuƙar sani na addini. Afannin boko ma yanzu haka yana matakin ajiki ukku ne na ƙaramar makarantar secondry, wato Jss 3. Sosai halin da mahaifiyar tasa take ciki yake matuƙar damun sa, tayarce har wani lokacin yake zama yay kuka shi kaɗai. A kullum rana ta Allah idan ya same ta zaune a ɗaki tayi tagumi, sai ya zauna gaban ta yay mata nasihohi, sannan kuma ya zauna yay ta kawo mata labarai dan ya ɗauke mata kewa, haka itama kaka take zuwa su haɗu su duka biyu, wani lokacin ma har da sauran Ƴaƴan ta mata ƙannen Ahmad, su sata a gaba suna bada labarai ana shan dariya, to anan ne itama zakaji ta tsoma bakin ta ana hirar da ita, wani lokacin ma har tayi dariyar itama. A kullum rana ta Allah idan ta kwanta bacci sai tayi mafarkin yaron nan da take yi, sai dai kuma yanzu ba'a jariri take ganin sa ba, tana ganin sa ne a ɗan matashin yaro, haka zai ta miƙo mata hannu yana son ta kama sa, amma sai kuma gaba ɗaya taji ta kasa ɗaga ƙafafuwan ta zuwa wurin da yake, gaba ɗaya sai ƙasa ta riƙe su, yayin da shi kuma idan ya tawo domin yazo gare ta, sai wasu irin mutane masu wata kalar siffa mara kyan gani suzo su janye sa suyi gaba da shi, haka zatai ta ɗaga masa hannu shima yana ɗaga mata suna kuka, amma mutanen nan su janye sa suyi gaba da shi, tukun sai ta farka daga baccin ta cikin tsantsar tsoro da firgici. _BAYAN SHUƊEWAR SHEKARA HUƊU._ *ƘASAR HAUSA, JAHAR KAGUL CIKIN MASARAUTAR FULƊE.* Tun bayan haihuwar Buba Gimbiya Kaɓel bata sake haihuwa ba tsawon shekaru takwas kenan, sai yanzu da take ɗauke da tsohon ciki haihuwa yau ko gobe, domin kuwa har ya shiga watan haihuwar sa cikin. Yayin da ita kuma Gimbiya Mairamu matar Lamaiɗo ta biyu ta sake haihuwar ƴaƴa maza har guda biyu a bayan haihuwar hairisu, tayarce Ƴaƴan Lamiɗo suka zamto har su bakwai, amma sai dai cikin su duka babu Ƴa mace gaba ɗayan su maza ne, hakan ne yasa dukan su suke fatan Allah yasa wannan karan Gimbita Kaɓel ta haifo musu ɗiya mace. Sosai suka shiryawa haihuwar, kuma suke zumuɗin ta yadda kasan ba'a taɓa haihuwa ba gidan. *ƘASAR MALIN, YANKIN JAHAR KARFUZ CIKIN BAƘAR MASARAUTA.* Tun bayan haihuwar Yarima Sairan da Gimbiya Haiwa Babar matar Sarki Barbaru tayi har kawo yau tsawon shekaru goma shabiyar bata sake wata haihuwar ba. Yayin da ita kuma Gimbiya Salwa Amarya ta haifi Ɗa namiji mai suna Saufan shekaru tara baya da suka huce kenan, tun daga lokacin kuma bata sake haihuwa ba sai yanzu da take ɗauke da tsohon ciki haihuwa ko yau ko gobe, sosai suke fatan Allah yasa wannan karan ta haifo musu ƴa mace dukan su, domin kuwa ba ƙaramun san Ƴaƴa mata suke ba, hatta da shi Sarki Barbaru. Acan ɓangaren Bayi kuwa yanzu Bir yana da shekaru takwas dai dai aduniya, yayin da wayon sa da girman sa da kuma taurin kansa duk suka zarce shekarun nasa, domin kuwa tun a yanzu bako wane aiki bane ake sa sa yayi sa kai tsaye, sannan kuma muddin akace yaran Bayi sunyi laifi to zaka same sa yana ɗaya daga cikin ƴan laifin, domin kuwa ko kaɗan basa da tsoro, sannan kuma ko wane irin duka za'a masa baya taɓa yin kuka. A yanzu ya fahimci ba Iyar Bayi bace ta haife sa, sabo da yadda wasu daga cikin ƴan uwansa bayi suke goranta masa cewar shi da ma tsunto sa akayi bashi da Iyaye, idan sukayi faɗa, hakan kuwa ba ƙaramun sosa masa rai yake ba, sannan kuma aduk ranar da aka faɗa masa haka to yaran da ya faɗa ɗin ya shiga ukku a wurin sa, domin kuwa baƙaramun duka yake masa ba, sannan kuma haka zaizo ya tasa Iyar Bayi a gaba yana ce mata ta faɗa masa ina babar sa take, su waye suka haifosa, sannan kuma a'ina ta tsinto sa, sai dai kuma koda wasa Iyar Bayi bata taɓa gigin basa amsa ɗaya ba daga cikin amsoshin tambayoyin nasa, asalima idan ya fara yimata tambayar tashi take tana barin wurin, domin kuwa kotace zata lallashe sa ba lallasuwa yake ba, gashi ita kuma tana matuƙar tsoron faɗa masa, sabo da gudun abun da zai faru da ita daga baya, domin kuwa ba ƙaramun gargaɗi Sarki Barbaru yayi mata ba da kansa, akan cewar kar a taɓa barin yaron yasan tarihinsa ko da wasa, saboda kar ko wataran yay gigin cewa zai bar su, muddin kuwa ta bari hakan ya faru, to tasani abakin rayuwar ta. Wannan dalilin shike sanya Iyar Bayi tana tashi tabar wurin Bir aduk lokacin da yazo mata da batun, sannan kuma magan-ganun nasa suke matuƙar firgita ta. Afannin harba kwari da gwafar sa ma kullum abu gaba yake ƙarawa, domin kuwa ba ƙaramun jin daɗin harkar yake ba, sannan kuma baiƙi ba ya yini adaji yana harbe-harbe ba tare da damuwar komai ba aransa. _BAYAN KWAN BIYU_ Yau Gimbiya Salwa ta tashi da masifaffen ciwon naƙuda mai matuƙar tsanani, tun cikin daren jiya take abu ɗaya, amma har kawo yanzu misalin ƙarfe shaɗaya na rana shiru kakeji bata haihu ba. Durƙushe take a cikin ɗakin ta daga gefen gado tana mai faman cize leɓen ta, yayin da gumi kuma ke yanko mata ta ko ina a jikin ta. Agefen ta kuwa wasu dattijan matane tsaye akan ta, ɗaya na aikin yi mata firfita da furta kalmar sannu gare ta, yayin da ɗaya kuma take dafe da bayan ta tana mai faman faɗin. "Yi nishi sosai Gimbiya kin kusa da yardar Ubangiji Gargabilu, yi nishi da ƙarfi kin kusa sannu kinji." Ta faɗa tana mai shafa mata bayan ta, yayin da ita kuma take ta ƙoƙarin yin nishin tana girgiza kanta. Wani irin nishi tayi mai matuƙar ƙarfi, tukun daga bisani kuma sai ga kukan jariri nan ya cika ɗakin da matuƙar sauti ba ƙaƙƙautawa. "Godiya muke abun bauta Gargabilu." Matan nan biyu suka faɗa cikin tsantsar farin ciki, ɗaya daga cikin su na durƙusawa wurin ƴa macen da idanuwan ta suka gane mata kwance tana cilla ƴan ƙafafuwanta sama tare da sakin kuka... *ƘASAR HAUSA, JAHAR KAGUL CIKIN MASARAUTAR FULƊE.* Yau jama'ar cikin Masarautar Fulɗe suka tashi da tsantsar farin ciki, ta sanadin haihuwar da Gimbiya Kaɓel tayi da asuba, kuma abun farincikin shine 'Ya Macen da suke fata a wannan karan ita Allah ya basu. Zo kuga kuwa farin ciki da murna wurin jama'ar gidan tun daga kan Lamiɗo har zuwa kan Bayi da hadiman gidan mazan su da matan su. Kakar su mahaifiyar Lamiɗo kuwa labarin haihuwar na isa kunnen ta ta taso ta tawo daga ɓangaren ta zuwa ɓangaren Gimbiya Kaɓle cikin matuƙar farin ciki. Sosai tayi matuƙar ruɗewa alokacin da idanuwan ta suka yi mata arba da kyakkyawar Ƴar da aka haifo ƙatotuwa da ita fara tas, cikin kayan fulani na jarirai da aka shirya ta. Cikin tsantsar farin ciki ta miƙa hannu tana mai amsar ta ahannun Hadimar Gimbiya Kaɓel, bakin ta na furta kalmar. "Tubarakallah Masha Allah." Tukun daga bisani ta fara rawa a cikin ɗakin ɗauke da ƴar ahannun ta, kana ta ɗora da faɗin. "Amma akan me za'a sanya mata kaya bayan ba a riga an bata kariya ba, dan haka amshe ta nan ayi maza-maza a cire mata kayan nan afuto mun da ita zuwa ɓangarena, ni kuma yanzu zanje na fara haɗa kayan tsafi, domin kuwa ku da kanku kun sani a ranar da yaro yazo duniya muke bashi makari acikin gidan nan." Ta ƙarasa maganar tana mai miƙawa Hadimar nan ƴar. Tukun ita kuma ta juya cikin sauri tana mai gyara ɗaurin zanin da yake a haɓar ta, tare da kama hanyar waje. Yayin da ita kuma wannan Hadimar ta fara cirewa kyakkyawar jinjirar kayan da suke sanye a jikin ta, tukun daga bisani ta miƙe tsaye hannun ta ɗauke da ƴar ba kaya a jikin ta, sai ɗan showel ɗin da ta naɗe ta a cikin sa tana mai kama hanyar waje. Yayin da suma sauran matan da suke a cikin ɗakin duk suka miƙe suka bi bayan ta, sabo da suyi kallon shagalin da za'ayi a ɓangaren tsohuwar mahaifiyar Lamiɗo. Tafkeken wuri ne mai matuƙar kyau da girma. Zagaye yake da ɗakuna irin na fulani a cikin sa. Gaban wata bukka Kaka ta ƙarasa tana mai sa hannu ta buɗe murfin karar da yake a jikinta, tukun ta danna kanta zuwa cikin bukkar. Wasu irin kayan karikitai ta ta futo da su riƙe a hannun ta cikin wani baƙin kasko, tana mai zuwa ta ajiye su a bakin ƙofar bukkar, tukun ta koma ciki-cikin sauri, kana daga bisani sai gata nan ta sake dawowa hannun ta riƙe da wani kaskon, wanda yake ɗauke da ruwa a cikin sa, sannan ta sake juyawa still tana mai komawa cikin bukkar. Bata jima a ciki ba ta k'ara futowa ɗauke da wata Sanda irin ta Fulani a hannunta, tana mai zuwa ta a jiye ta kusa da waƴan can kayan. Tukun ta juya bayan ta tana mai kai idanuwan ta zuwa inda wasu maza suke, da alamun dai Hadimai ne su ɗin, duba da irin suturar dake sanye a jikin su da ta zamto kalar ta Hadiman. Daga nan wurin da take ta buɗe murya cikin ƙarfi tana mai faɗin. "Kai kuyi maza maza kuje gaban rafin gabas, zakuga turamen tsafi na tarihi gaban bishiyar ɗorawa ku ɗauko mun su." Da tom suka amsa mata su duka huɗun, suna masu juyawa cikin sauri suka tafi. Dawowar su daga wurin da ta aike sun tayi dai-dai da lokacin da Hadimar Gimbiya kaɓel tare da tawagar ta suka ɓullo wurin, hannun ta riƙe da jaririyar. Yayin da su kuma Hadiman nan maza suka tawo ɗauke suke da wasu irin manya-manyan turame masu matuƙar girma akafaɗun su. Ƙarasowa wurin da Kaka take sukayi suna masu a jiye su a gaban ta, wurin da kayan nan suke. Yayin da ita kuma ta duƙusa ƙasa da sauri tana mai fara futo da abubuwan da suke a cikin kaskon nan. Wasu irin ƙullikan tsummokarai ta zaro masu matuƙar yawa, tukun ta fara kwance su da ɗai-ɗai da ɗai-ɗai, kana ta ɗibu wasu iccina daga cikin ƙulli ɗaya tana mai zuba su acikin ruwan nan da ya kasance shi ba na zafi ba, sannan kuma shi bamai sanyi ƙarara ba, tukun ta sake ɗibar wani ta zuba sa shima a cikin ruwan. Haka ta dinga ɗibar su tana zubawa a cikin ruwan ɗaya bayan ɗaya har tasa duka, yayin da kalar ruwan kuma duka ta sauya lokaci guda, tana mai komawa ruwan ɗorawa. Miƙewa tsaye tayi bayan ta ɗauki wasu layoyi masu matuƙar yawa ta riƙe su a hannun ta, sannan ta juya ɓarin da mazan nan suke riƙe da abubuwan nan da ta ɗauko su yanzu, tana mai faɗin. "Kuyi maza ku gyara mun turamen nan yanzu, ya zamto sun zagaye wannan kaskon ruwan." Tayi maganar cikin harshen fulatanci, tukun ta juya ɓarin da Hadimar Gimbiya Kaɓel take tana mai sa hannu ta ɗauki jinjirar nan tsirara, ba tare da ta haɗa da showel ɗin ba. Yayin da su kuma Hadiman nan maza suka yiwa turamen kamar yacce tace suyi musu. Layoyin da suke riƙe a hannun ta ta ɗaurawa yarinyar a kan ƙaurin ta duka biyu, kana ta kama damtsen hannuwan ta suma ta sanya musu wasu layoyin, sannan ta durƙusa ƙasa tana mai matsawa gaban kaskon nan, tukun ta rumtse idanuwan ta da ƙarfi tana mai fara yin wasu irin surutai. Take a wurin wani kalar hayaƙi ya fara futa daga cikin ruwan, yana mai wani irin juyawa, tukun ita kuma ta tsunduma ƴar jinjirar nan acikin ruwan tana mai sanya tafin hannunta ɗaya, ta fara ɗebo sa tana zubasa ajikin ƴar tun daga kan gashin kanta. Tsanyarewa da kuka jinjirar tayi da matuƙar ƙarfi, yayin da su kuma waƴan nan makaɗan suka fara buga kayan kiɗan su suna masu fara ɗirkar rawa, tare da zagaye turamun nan suna ɗaga hannuwan su sama cikin tsantsar farin ciki. Ita kuwa kaka har yanzu idanuwan ta a rumtse suke tana aikin sakin wasu irin surutai daga cikin bakin ta, kana kuma tana cigaba da ɗebo ruwan tana zuba sa a jikin jinjirar. Bata ita ta dena surutan ba har sai da taji ruwan nan ya dena juyawar da yake yi tas, sannan kuma ya dena futar da hayaƙin da yake futarwa, tukun ta buɗe idanuwan ta tana mai kaisu zuwa cikin ruwan. Wani irin murmushi ne ya suɓuce mata, sabo da yarce taga ruwan ya koma fari kar, yacce take son yayin dama, domin kuwa komawar tasa farin shine yake nufin ai'kin yayi, wato an bawa yarinyar tsafin kenan itama. Miƙewa tsaye tayi tana mai cilla ƴar jinjirar dake aikin tsala kuka sama, tukun tayi sauri ta caɓe ta, haka tai-tayi mata har kimanin sau ukku, sannan a ƙarshe ta zurata a cikin ɗaya daga cikin turaman nan bayan ta caɓe ta. Tukun ta juya tana mai zuwa wurin da ta ajiye sandar nan da ta futo da ita. Ɗaukar ta tayi a hannun ta tana mai riƙeta gagam, sannan ta buɗe baki cikin harshen fulatanci da ƙarfi bayan ta kalli jama'ar dake wurin, tana mai faɗin. "To Jama'a ku shaida, ni Gimbiya Unau, matar Tsohon Lamiɗon Masarautar Fulɗe, nayi kyautar sandar tsafi na ta gado wacce nima na gaje ta a wurin Kakata ga kyakkyawar jika ta da aka haifomun ita yau halak malak, domin ta zamto mata kariya a rayuwar ta." Ta ƙarasa maganar da sakin murmushi, tana mai matsawa gaban turaman nan. Yayin da su kuma makaɗan nan suka canza salon kiɗi bayan jama'ar hurin sun saki ihu da tafi, a lokacin da Kaka ta gama bayanin ta. Sosai wurin ya sake turnuƙewa da rawa da ihu, sabo da kiɗan da ke tashi mai tsantsar daɗi. Yayin da ita kuma kaka ta ƙarasa zuwa gaban turmin da jinjirar nan take a ciki, sannan ta ɗaga sandar ta tana mai riƙe ta da hannu biyu, tukun ta fara zagaye turaman tana mai yin wasu irin kalamai da ƙarfi, kana daga bisani ta tsaya a gaban wanda jinjirar nan take a ciki, tukun ta ɗan zura sandar cikin turmin tana mai durƙusawa ta kamo hannun jinjirar da yake a dunƙule ta warasa, tukun ta ɗora sandar akan tafin hannun yarinyar. Take kuwa ta ɗan riƙe jikin sandar a ƙoƙarin ta na ta sake rumtse hannun ta. Hakan ya sanya Kaka rangaɗa wata irin buɗa da matuƙar ƙarfi, tukun ta janye sandar daga cikin turmin tana mai faɗin. "Haƙiƙa kyauta ta karɓu, ke kika zamto ƴar gata gare ni, domin kuwa ke kaɗai ce kika samu kyauta mai daraja irin ta sanda ta a wuri na." Ta ƙarasa maganar tana mai a jiye sandar a ƙasa, sannan ta koma ta ɗauko jinjirar a cikin turmin, tukun ta miƙa ta zuwa hannun Hadimar Gimbiya Kaɓel. Amsar ta tayi tana mai sanya ta cikin showel ɗin ta lulluɓe ta da shi, tukun ta juya ita da tawagar ta da suka biyo ta suna masu komawa wurin da suka futo. Yayin da ita kuma Kaka ta fara ɗibar kayan tsafinta tana mai mayar da su cikin bukkar nan, su kuma waƴan nan turamen Hadiman nan suka sake ɗaukar su suna masu tafiya da su wurin da suka ɗauko su. Sai da Kaka ta gama mayar da komai banda sandar nan, tukun ta mai da ƙofar bukkar ta rufe ta, sannan ta juya tana mai ɗaukar sandar ta doshi hanyar ɓangaren Gimbiya Kaɓel, domin taje ta damƙa mata sandar jinjirar tata. *JAHAR WASAI CIKIN MASARAUTAR WASAI.* Yau aka tashi da tsantsar farin ciki a ɓangaren Gimbiya Fulani, sabo da haihuwar Ƴa macen da tayi da asuba itama, bayan shafe shekara takwas da tayi rabon ta da haihuwa, wato tun bayan haihuwar Yarima Asad da yayi matuƙar girma da wayo yanzu kenan. A lokacin da sautin kiɗin tambarin Ƴa mace ya daki kunnen magautan ta ba ƙaramun farin ciki sukayi ba, domin kuwa dukan su dama suna cikin tsantsar fargaba ne ako da yaushe, sabo da tsoron abun da kunnuwan su zasu juyo musu. Yayin da ita kuma a ɓangaren ta sukayi matuƙar farin ciki da samuwar ƴar, wacce ta ɗebo kamannin mai martaba sak, yarce kasan kaki yayi ya tofar. A ɓangaren Asad kuwa yafi kowa farin ciki da murnar haihuwar da Mamayn tasu tayi musu, badan komai ba kuwa sai dan sanin da yay na za'ayi hawan suna a ranar suna, gashi shi kuma dama ya kasance mayen doki, sabo da yaga yacce akayiyyi a lokacin da Gimbiya Huwaila ta sake haihuwar ƴa macen da bata so ba, sannan kuma da lokacin da Gimbiya Amina itama ta ƙara haifo ƴa mace, wannan dalilin yasa yake ta fatan asake yin wata haihuwar a gidan su, sabo da mai martaba yace masa ya bari sai an sake wata haihuwar, tukun sai ya fara yin kilisa, shima a lokacin ya ƙara girma, sabo da yarce yaso abar sa shi kaɗai akan dokin sa shekaru biyu baya da suka huce lokacin da Gimbiya Amina ta haihu, amma mai martba yaƙi, hakan ne yasa yayi matuƙar farin ciki da haihuwar da mamyn tasa tayi fiye da duk sauran yaran, domin kuwa yanzu shi da kansa yake hawa dokunan sa ba tare da wani ya riƙe sa ba. A ɓangaren Babban Yaya sosai yayi ya zama saurayi, domin kuwa a yanzu yana da shekaru goma shatakwas ne a duniya dai -dai, a karatu kuma yana matakin ajin ƙarshe na secondry ne, kuma da zarar ya kammala za atura sa ƙasar turai jami'a, kamar yacce sauran yayyan sa mata da kuma ƴan gidan duka suke karatun su acan. *UNGUWAR ƊAN TANKI.* Sai da Aishatu ta shekara bakwai da haihuwar da tayi a Baƙar Masarauta, tukun ta sake haihuwar wani Ɗa namijin, wanda yake da shekara ɗaya a duniya yanzu kenan, mai suna Salman. Har kawo yau dai tana nan da halayyar ta ta rashin son yin magana da kuma zaman cikin ɗaki, sannan kuma bata bar tinane-tinanen nan da takeyi ba, kamar yacce a kullum daren duniya take mafarkin wannan yaron da koda yaushe yake ƙara girma. Yayin da Ahmda kuma yake da shekara goma shatakwas yanzu a duniya. A fannin karatun boka yana matakin ajin ƙarshe na secondy ne yanzu, yayin da fannin na addini kuma ya sake yin matuƙar zurfi, domin kuwa a yanzu haka har aji yake da shi a Islammiyar su, sannan kuma yake jan sallah a wani sabon masallacin kamsu salawat da aka buɗe anan cikin unguwar tasu aka basa limancin sa, kasancewar duk yafi sauran yaran harma da manyan ilimi a unguwar, hakan kuwa ba ƙaramun farin ciki ya sanya iyayen su ba. *ƘASAR MALIN, YANKIN JAHAR KARFU CIKIN BAƘAR MASARAUTA.* Cikin tsantsar farin ciki ta durƙusa ƙasa, tana mai sa hannu ta ɗauki kyakkyawa jinjirar dake ai'kin tsala kuka da matuƙar ƙarfi, ta ɗora ta akan showel ɗin da yake ninke a gaban ta, bayan ta yanke mata cibi, tukun ta ɗago tsaye tana mai rangaɗa w..............✍ _HAR YANZU LABARIN BAI FARA BA FA. DOGUWAR TAFIYA CE, MAI 'DAUKE DA ABUBUWA KALA-KALA ACIKINTA. AZABABBIYAR SOYAYYA, SADAUKARWA, TSANANIN BAN TAUSAYI, TARE DA MATUK'AR ZALINCI DUK SUKE ACIKIN LABARIN BAK'AR MASARAUTA. AYI COMMENT DA SHARHI HAKAN SHI ZAI SA MUJE HAR ZUWA WURIN DA NAKE FA'DA MUKU._ *BAƘAR MASARAUTA* *NA* UMAR FARUQ*D* *PAGE 18* Wata irin buɗa mai matuƙar sauti, yayin da ita kuma ɗaya ta juya a guje tana mai fucewa daga cikin ɗakin domin taje takai rahoto. Cikin ƙanƙanin lokaci gaba ɗaya labarin haihuwar Ƴa macen da Gimbiya Salwa tayi ta zagaye duka cikin Baƙar Masarauta. Lokacin da labarin ya isa kunnen Sarki Barbaru ba ƙaramun farin ciki yayi ba, domin kuwa tsabar murnar da yayi da jin labarin a take a wurin yayiwa Hadimar da ta kawo masa Albishir ɗin kyautar Raƙumi ɗaya. Tukun ya miƙe daga kan kujerar sa cikin sauri yana mai kama hanyar waje. Ko da ya ƙarasa cikin ɗakin zaune ya samu mahaifiyar sa riƙe da jinjirar a hannunta, tana shafeta da mai. Da sauri ya ƙarasa zuwa inda suke yana mai zube guiwoyin sa a ƙasa, tukun ya buɗe baki cikin tsantsar farin ciki, idanuwan sa a kan fuskar kyakkyawan jinjirar da ya gani, yana mai faɗin. "Shin da gaske ne ba mafarki nake ba, wannan kyakkyawar jinjirar ta wace?" Ya faɗi maganar ta sigar tambaya, yana mai kai yatsun hannuwan sa zuwa kan ƙafar jaririyar ya riƙe. "Tabbas kuwa ɗiyar kace a gaske kake ganin ta ba mafarki ba, haƙiƙa Ubangiji Gargabilu yay mun kyautar jika mace." Tsohuwar matar da take zaune tukuf riƙe da Ƴar ta faɗa tana mai kallon fuskar Sarki Barbaru ɗauke da murmushi a bakin ta. "Godiya ta tabbata ga Ubangiji Gargabilu, haƙiƙa kagamamun komai da kabani kyautar ƴa mace." Sarki Barbaru ya faɗa yana mai miƙa hannu ya ɗauki Ƴar. Zaman sa ya gyara a wurin da yake, yana mai tanƙwashe ƙafafuwan sa, sabo da yaji daɗin riƙon ƴar da kyau, tukun daga bisani ya miƙa hannun sa zuwa inda yaga wata ƴar roba mai matuƙar kyau da take a gaban Mahaifiyar tasa, yana mai janyo ta gaban sa, tukun ya buɗe murfin ta. Baƙin fenti ne tare da soso mai yankan Tambarin Masarautar tasu a cikin sa. Hannu ya sanya yana mai zaro soson daga ciki, bayan ya dangwalo fentin, sannan ya ɗago sa yana mai kai sa kan fuskar yarinyar ya manna mata shi a kan goshi, kana ya sake manna mata akan kumatunan ta duka, har lokacin fuskar sa ɗauke da tsantsar murmushi. Kyakkyawa ce a jin farko jinjirar, gata da wani irin yalwataccen gashi da yake sunƙum tun da ga kan ta har zuwa kan fatar jikin ta. Sosai take da girma yacce kasan wacce tayi irin sati ukkun nan a duniya. Banda wawurar yatsu tana kaiwa baki tare da wuwwurga manya-manyan fararen idanuwan ta masu ɗauke da baƙar ƙwaya huluk a cikin su babu abun da take yi. Ɗago ta Sarki Barbaru yayi, bayan ya gama manna mata tambarin masarautar a jikin ta yana mai riƙe ta a hannun sa, tukun daga bisani ya buɗe baki cikin farin ciki, idanuwan sa ƙur a kan jinjirar, yana mai faɗin. "Shekarau da dama ina zaman jiran zuwan ki, idanuwan sun daɗe suna tsumayen ganin ki, kunnuwa sun jima suna son jin sautin muryar ki, yayin da hannuwa kuma suka ɗau tsawon shekaru suna nararin jinki akan su, amma Ubangiji Gargabilu bai yaddar ba sai yanzu, dan haka na miki alƙawarin zamtowa Uban da babu kamar sa a duk faɗin duniya a gareki, Uban da ko a lokacin baya ba ayi kamar sa ba. Zan baki gata irin gatan da babu ɗiyar data taɓa samun kalar sa a duniya, zan hanaki kuka, sannan kuma na sanyaki dariya ɗiya ta, zan baki kariya irin kariyar da ba'a taɓa baiwa wata ƴa kamar taba a gidan duniya, sannan kuma zaki zamto Jaruma irin Jarumar da babu kamar ta a faɗin duniya, zaki zamto jaruma wacce tarihin ta zaiyi shuwura ya zagaye duk duniya, Jarumar da tarihin ta bazai taɓa gushewa ba, wannan alƙawari ne na ɗaukar miki yake Ƴata." Ya ƙarasa maganar yana mai rungume ta a ƙirjin sa, tukun daga bisani ya janye ta yana mai miƙa ta zuwa hannun mahaifiyar sa, sannan ya miƙe yana mai juyawa ya fuce daga cikin ɗakin. *BAYAN SATI ƊAYA.* Yau ta kasance ranar sunan jinjirar da aka haifa, hakan ne yasa tun daren jiya ake ta shirye-shirye a cikin Baƙar Masarauta, tare da girkuna kala-kala. Duk inda ka gifta banda Bayi Mazan su da Matan su babu abun da ake gani. Yayin da filin da za'ayi bikin suna kuma ake ta aikin shirya sa, wani irin kiɗa mai matuƙar sauti da daɗi na tashi daga cikin sa. Zagaye yake da randina manya manya da suke ci da huta ta ko ina, yayinda daga can jikin bango kuma aka a jiye wasu irin kujeru masu tsananin kyau da suka ji uban ado a jikin su, daga can tsakiyar filin kuwa nan ma ɗin wani ƙatoton kaskon hutar ne a ajiye. Yayinda acan kan wani dakali kuma da yake a gaban filin aka saƙale wasu irin danƙara-danƙara Shanu har kimanin guda goma shabiyu, sai daga gefen sa kuma manya-manyan tukwane ne ɗore akan duwar-watsu suna ci da huta, har kimanin guda takwas, da alamun dai girki akeyi ne a wurin, duba da yarce matan hurin suke ta faman ƙara iza wutar, ga kuma kayan ayukka irin su robobi da fanteku da suke a jiye a gaban su da matuƙar yawa. Misalin ƙarfe goma na safe dai dai salon kiɗan da ake bugawa a wurin ya canza, tukun daga bisani sai ga tawagar Bayi nan Mazan su da Matan su sun fara shigowa cikin filin da rawa, sai dai kuma a wannan karan babu wani abu da yake ɗauke a hannuwan su, kasancewar ba bikin godiya bane ake yi, sai ma tsantsar murmushi da annashuwa ne da suke a kwance a kan fuskokin su. Shigowar su duka baifi da muntina biyar ba, sai ga tawagar su Sarki Barbaru nan sun tawo Dakaru na take musu baya. Sarki Barbaru ne atsakiya kamar yacce suka saba tawowa idan suna taro, sai dai wannan karan kuma hannun sa ɗauke yake da Ƴar jaririyar da aka haifa. Yayin da gafe da gafen sa kuma matan sa biyu Gimbiya Haiwa da kuma Gimbiya Salwa mai jego suka kasance, gaba ɗayan su suma sunci uban ado mai matuƙar ɗaukar hankali da tsada a jikin su, a gefen su kuma yaran su ne maza suke biye da su, yayin da bayan yaran kuma da gefe da gefen su kuma duk dakaru ne, hannuwan su riƙe da bulalai tare da makamai soke a jikin su. Sanye sarki Barbaru yake da wasu irin kaya masu matuƙar kyau da tsada a jikin sa, yayin da jinjirar dake riƙe a hannun sa kuma aka sanya mata wata doguwar riga mai tsananin kywu da tayi mata dai dai a jikin ta, sai wasu ƴan takalma masu tsananin kyau da suke sanye a ƙafar ta. Kai tsaye suka doshi gaban kaskon hutar da yake a tsakiyar fili dukan su. Zagaye kaskon sukayi a dai dai lokacin da suka ƙarasa gaban sa, tukun Sarki Barbaru ya yaye showel ɗin da yake ƙudun-dune jikin jinjirar yana mai cillasa cikin hutar kaskon nan, sannan ya ɗaga ta sama yana mai tsayar da ita asaitin kaskon hutar nan, tukun ya buɗe baki cikin sauti yana mai faɗin. "Gargabilu! Garbailu!! Gargabilu!!!" Da tsantsar ƙarfi. Take kuwa jama'ar dake wurin suma suka ɗaga murya da matuƙar ƙarfi suna masu faɗin hakan, yayin da ita kuma jinjirar na ta tsanyare da kuka. Ƙara gyara riƙon Ƴar Sarki Barbaru yayi a hannun sa, tukun daga bisani ya buɗe baki yana mai faɗin. "Jama'a ina son ku shaida, ni Sarki Barbaru na sanyawa Ƴata mafi soyuwa a raina suna TASMIR, a yau bayan shafewar kwana bakwai da zuwan ta duniya. Na raɗa mata suna Tasmir akan darajar shanu ɗai-ɗai ɗai-ɗai har kimanin guda Goma shabiyu mafiya girma daga cikin shanun da nake da su, sannan kuma nayi Al'ƙwarin bata kariya a yanzu, irin kariyar da babu wata ɗiya mace a duniya da take da kamar ta." "Huuuuuuuuuuu!!!" Ɗakacin Jama'ar dake cikin filin suka sanya ihu da matuƙar ƙarfi, tukun daga bisani Boka mai wutar kasko ya taso daga kan shimfiɗar da yake zaune yana mai yowa wurin da su Sarki Barbaru suke. Hannu ya miƙa yana mai amasar ƴar a hannun Sarki Barbaru a lokacin da yazo, bayan ya gama shirya kayan tsafin sa duka, sannan ya fara saɓulewa jinjirar kayan da suke sanye a jikin ta a bainar jama'a, har ya cire mata su tas, tukun ya rumtse idanuwan sa yana mai kai ta gaban kaskon wuta ya fara sakin wasu irin surutai da matuƙar ƙarfi. Ya jima yana surutan yadda kasan bazai dena ba, tukun daga bisani ya tsaya da surutan da yake yin yana mai buɗe idanuwan sa, sannan ya sake miƙa hannun sa ya ɗauko wani ruwan tsumin magani da yake a cikin kofi, yana mai wanke ƴar tas da shi, tukun ya sake miƙewa tsaye yana mai ɗaga ƴar sama a hannun sa, kana ya buɗe bakin sa bayan yakai ƙwayar idanuwan sa kan jama'a yana mai faɗin. "Haƙiƙa kariya ta tabbata a jikin Gimbiya Tasmir irin kariyar da babu mai kamar ta, kamar yacce ubanta ya buƙaci ta samu, sannan kuma Jarumta da ƙarfin zuciya zasu dawamma a gare ta ta sanadin irin ai'kin da aka yi mata." Ya faɗa yana mai miƙawa Sarki Barbaru ita, yayin da su kuma jama'ar dake wurin suka sake buɗe baki suna masu faɗin. "Gargabilu! Gargabilu!! Gargabilu!!!" Da tsananin k'arfi suna masu ɗaga hannuwansu sama. Amsar ƴar sarki Barbaru yayi, tukun ya juya yana mai kaita kan shimfiɗar fatar da take shimfiɗe a gaban su ya kwantar da ita, tukun ya miƙe tsaye yana mai kai hannun sa zuwa kan ƙugun sa, bayan ya shigar da shi cikin al'kyabbar dake sanye a jikin sa, ya zaro wata irin Takobi mai matuƙar tsawo da ƙyalli. Juyawa yayi gaban mutane yana mai kallon su, bayan ya ɗaga Takobin tasa sama, tukun daga bisani ya buɗe baki cikin muryar sa mai futar da amon sauti yana mai faɗin. "Ni Sarki Barbaru, a yau nayi kyautar Takobin tsafi na tare da macijiya ta wacce Kaka na ya bani su zuwa ga ƴata abar ƙaunata Tasmir, domin su zame mata kariya a rayuwar ta." Ya ƙarasa maganar cikin ƙaraji, yana mai juyawa ya kalli inda ƴar tasa take, tukun daga bisani ya rumtse idanuwan sa da matuƙar ƙarfi, bayan ya ɗaga Takobin tasa ya nuna gefen wurun da jinjirar take a kwance da ita, sannan ya buɗe baki cikin muryar sa mai matuƙar amo yana mai faɗin. "Rai Rai Rai Rai Buuuu Hoooo Reeeeee!" Da tsananin ƙarfi, take kuwa a wurin Takobin nan tayi wani irin kawo farin haske a jikin ta yana walwali. Buɗe idanuwan sa yayi a kan Takobin yana mai girgiza kai, tukun daga bisani ya sake buɗe baki yana mai kallon gefen wurin da Jinjirar take a kwanc,e tare da faɗin. "Shairamaaa!" Da tsananin ƙarfi. Take kuwa wata irin danƙare-riyar macijiya ta bayyana tana mai karkaɗa harshe ta, idanuwan ta ƙur a kan fuskar Sarki Barbaru. Yayin da shima ɗin yake kallon ta da nasa idanuwan ba ƙiftawa, tukun daga bisani ya buɗe baki cikin muryar mai amo yana faɗin. "Shairama ga Ƴata nan Mace ɗaya ƙwal a duniya, ina son daga yau ki koma gare ta, sannan kuma ki zamto mata kariya a bokiyar shawara agare ta kamar yacce kika zamto agare ni, ki kasance mai bayyana a duk lokacin da ta buƙace ki, sannan kuma ki share mata hawayen ta a duk lokacin da takawo miki kukan ta, kamar yacce kikai mun, domin kuwa wannan jinjirar da kike gani a gefen ki itace farin ciki na, ina sonta tamkar yacce nake son rayuwa ta, ina sonta irin soyayyar da nake yiwa abun Bauta Gargabilu, wannan dalilin shine ya sanya na bar mata ke ni kuna na haƙura, domin kuwa ni na sani zata fini buƙatar ki, dan haka gata nan kusa dake daga yau itace shugabar ki ba ni ba." Ya faɗa yana mai matsawa kusa da wurin da jinjirar take kwance ya cake Takobin a gefen ta. Yayin da ita kuma Macijiyar nan tayi wata irin juyawa, tukun ta fara tafiya tana mai zuwa ta fara hawa kan jinjirar ta dinga kanan-naɗe ta, sai da ta gama kanan-naɗe ta tas, tukun ta zaro harshen ta tana mai lasar fuskar jinjirar da shi, sannan daga bisani ta fara barin jinkin jinirar tana mai yin wurin da Takobin nan take a cake. Kanan-naɗe Takobin tayi tas, tukun daga bisani kuma ta ɓace ɓat yarce ƙasan ba a taɓa yin ɗuriyar taba a wurin. Take a wurin kuwa ɗaukacin jama'ar dake wurin harda su Sarki Barbaru da iyalan sa suka sanya ihu, suna masu faɗin. "Gargabilu! Gargabilu!! Gargabilu!!!" Yayinda shi kuma sarki Barbaru ya ƙarasa wurin da huƙar nan take a cake yana mai funcike ta daga cikin ƙasa, sannan yasa hannu ya ɗauki jinjirar tasa, tukun ya juya yana mai kaita wurin Mahaifiyar sa da take tsaye duk a kusa da su. Amsar ta tayi tana mai sanya mata wasu sababbin kayan da wata Hadima ta miƙo mata su yanzu, ba wayan da aka cire mata ba, tukun ta mayarwa Sarki Barbaru ita. Gaba ɗayan su ɗaga ƙafafuwan su suka farayi suna masu dosar wurin da kujerun nan suke a ajiye. Yayin da makaɗa kuma suka cigaba da sakin kiɗi da matuƙar ƙarfi, maraya na ai'kin ɗirkar rawa. Su kuwa Bayi mata Iyaye hucewa sukayi zuwa wurin da tukwanen nan suke, suna masu buɗe su suka fara ɗibar abinci suna zubawa a manya-manyan farantai, yayin da su kuma Ƴammatan Bayi ke ai'kin ɗaukar abincin suna kaiwa mutane su. A ɓangaren Bayi Maza manya kuwa, su hurin da shanun nan suke a saƙale suka huce suna masu ciro su, aka zuba musu kayan haɗi akan su, kana aka kwarara musu mai mai matuƙar yawa, tukun suka matsa da su jikin huta suna masu fara babbake su. Haka dai akai ta shagali a ranar, ana yankan nama anaci tare da kaɗaɗe, maraya na ai'kin dillaƙar rawa kowa cikin tsantsar farin ciki. *ƘASAR HAUSA, JAHAR WASAI CIKIN MASARAUTAR WASAI.* Ko ina ka kalla cikin Masarautar jama'a ne suke giftawa ta ko ina, kowa da kalar shigar dake sanye a jikin sa, kasancewar yau ne sunan jinjirar da Gimbiya Fulani ta haifa. Tun safiya a kayi raɗin suna yarinya taci suna Bilkisu, wato sunan mahaifiya Gimbiya Fulani, hakan yasa Gimbiya Fulani tayi mata laƙabi da BABY. Sosai a keta shagali tun safe, har zuwa yanzu da a kayi sallah la'asar ana shirin yin hawan suna, kamar yacce aka saba ako wace haihuwa da akeyi a cikin Masarautar. Yau Yarima Asad jin ta yake tamkar sallah a wurin sa, koma ace fiye da sallah, kasancewar yau ɗin itace rana ta farko da zai fara yin hawa akan doki ba tare da wani ya riƙe masa dokin sa ba, daga shi har Al'amin. Ana idar Sallahr la'asar a cikin masallacin Masarauta Yarima Asad da al'amin suka futo cikin sauri. Sanye suke da wasu azababbar shadda ɗin kin doguwar riga tare da wando a jikin su, da sukayi matuƙar yi musu kyau iri ɗaya a jikin su. Cikin sauri suka kama hanyar part ɗin mai Martaba, kasancewar anan kayan su da zasu sanya yanzun suke, domin kuwa gaba ɗaya yau ɗin kaya iri ɗaya suka sanya da su da Mai Martaba, duk da dama shi Asad kusan kullum hakan ne yanzu, dan kuwa rabon da Mai Martaba yayi ɗinki shi kaɗai ba tare da an masa ba tun kafun a yaye sa. Suna shiga cikin part ɗin suka ci karo da Jakadiya zaune a kan kujera daga bakin ƙofar ɗakin Mai Martaba, yayin da hannuwan ta kuma suke riƙe da hula da rawanin su tana mai jujjuya su. Da sauri ta waigo ɓarin da suke tawowa, sabo da jin sautin takun tafiyar su da tayi. Washe baki tayi tun kafun su ƙaraso wurin, tukun daga bisani ta laɓɓan ta tana mai faɗin. "A'a ƴan samarin Mai Martaba kuce an futo shiryawar kenan." Ta ƙarasa maganar tana mai riƙe hannun Al'amin a lokacin da suka ƙarao wurin. "Ina yini Jakadiya." Yarima Asad da Al'amin suka haɗa baki wurin faɗi suna masu sakin murmushi. "Lafiya ƙalau shalelen Mai Martaba." Jakadiya ta faɗa tana mai shafa kan Yarima Asad, idanuwan ta ƙur akan sa. Yayinda su kuma suka juya cikin sauri suna masu shirin shigewa cikin ɗakin. Da sauri Jakadiya ta buɗe bakin ta tana mai faɗin. "Am nace ba..." Waigowa Yarima Asad da Al'amin suka yi a tare suna kallon ta, tare da jiran jin abun da zatace ɗin. Hakan da ta ganine ya sanya ta sake washe baki tana mai faɗin. "Idan kun shirya kun gama sanya kayan sai kuzo nan, ga wula da rawani na amsar muku, yau ni da kaina zan sanya muku su Ƴan gaban goshin Mai Martaba." Ta ƙarashe maganar da washe baki tana mai yi musu nuni da wular. Taɓe baki Yarima Asad yayi ba tare da yace komai ba, yana mai juyawa ya shige cikin ɗakin, domin kuwa shi ason samun sa yafi so mai Martaba ya sanya masa hular da rawani da kansa, kamar yacce yake sama sa su ako da yaushe. Yayinda shi kuma Al'amin ya amsawa Jakadiya da "tom", tukun ya juya yana mai shigewa cikin ɗakin shima. Murmushi Jakadiya tayi tana mai ɗan cije leɓen ta na ƙasa, tukun daga bisani ta koma jikin kujerar da take akai tana mai kishingiɗa. A ɓangaren su Yarima Asad kuwa suna shiga cikin ɗakin direct ya huce cikin bedroom ɗin Mai Martaba. Baiyi ko minti biyar da shigar tasa ba sai gashi nan ya futo daga shi sai farar sabuwar singilet tare da sabon farin boxer ajikin sa, yayinda hannuwan sa kuma suke rungume da kayan su waƴan da zasu sanya yanzu, kasancewar da ya shiga cikin baiga Mai Martaba ba sai dai motsin ruwa da ya jiyo a bathroom ɗin sa, shiyasa ya futo musu da kayan nan domin su shirya. Kan haɗaɗɗiyar doguwar kujerar da take a cikin fallon ya ƙarasa yana mai ɗora kayan a kan ta, tukun ya juya ɓarin da Al'amin yake zaune a kan ƴar ƙaramar kujera yana mai faɗin. "Wallahi idan na gama shiryawa ko kallon ka bazan ba, ballan tana na jiraka, tunda naga wuri ka nema kazauna ma." Ya faɗi maganar ƙasa-ƙasa yana mai juyawa ya fara ware kayan nasa. "To masifaffe ai sauƙin ta ma nima nasan wurin inka tafin." Cewar Al'amin yana mai tashi daga kan kujerar da yake ya fara zame kayan jikin sa shima. Yayinda shi kuma Asad ya cigaba da zura kayan sa ba tare da ya sake cewa komai ba. Blue ɗin shadda getzner ce da taji uban aiki irin na sarakai a jikin ta mai matuƙar tsada tana walwali, ɗinkin riga da wando tare da malum-malum suka sanya su a jikin su. Sosai sukayi bala'in kyau acikin kayan, musamman ma Asad shi da ya kasance farar fata. Wasu sababbin fararen takalma na fata suka sanya ƙafafun su a cikin su, tukun shi Asad ya ƙara ɗaukar farar alkyabbar da take a jiye a gefen sa yana mai ɗora ta akan kayan jikin sa. Yayin da shi kuma Al'amin yabar iya babbar rigar jikin sa kawai. "Ɗebo kayan ka muje ka a jiye, daga nan sai mu ƙara sa wani turaren." Yarima Asad ya faɗa yana mai nufar bedroom ɗin Mai Martaba, da niyyar yaje ya sake feso turare, duk da wanda ya fesa a jikin kayan kafun ya futo da su kuwa. Sun ɗauki tsayin mitina biyar zuwa shida a cikin ɗakin, tukun daga bisani sai gasu nan sun futo suna ta faman buga uban ƙamshi mai tsananin daɗi da sanyi. Shafa kai Yarima Asad yayi da tafin hannun sa yana mai sakin guntun tsaki ba tare da yace komai ba, hakan da Al'amin ya ganine ya sanya sa buɗe baki yana mai faɗin. "Mene ne kuma ya faru yanzu?" "Mtswwww! Da yanzu Abba ne zaisa mun rawani na, amma waccan Jadiyar ta ɗauke." Ya faɗa murya acunkushe yana mai fucewa daga cikin ɗakin. Binsa shima Al'amin yayi ba tare da yace komai ba. Suna futowa daga cikin ɗakin Jakadiya tayi saurin miƙewa daga kishingiɗen da take a kan kujera tana mai faɗin. "Kai Masha Allah ƴan samarin mai martaba, a gaskiya kunyi matuƙar yin kyau, dan haka ku maza ku matso nasa muku rawani kafun a fara hawa baku." Ta ƙarasa maganar baki a washe tana mai ɗauko hular ɗaya ta ɗora ta a kan al'amin daya ƙaraso gaban ta. Sanya masa hular da aka riga aka gama naɗa rawanin a jikin ta tayi ta zauna das akan sa, tukun ta buɗe baki tana mai faɗin. "Masha Allah ɗan saurayi ya futo, dan haka matsa a sawa ɗan Uwanka shima." Ta ƙarasa maganar tana mai ɗauko ta Asad ɗin idanuwan ta ƙur akan sa. Kallon ta shima Asad ya tsaya yi ido cikin ido daga wurin da yake ba tare da ya motsa ba. Hakan da ta ganine ya sanya ta buɗe baki cikin rawar murya tana mai faɗin. "Ya dai shalelen Mai Martaba, ko kuwa ka fasa yin hawan ne naga kaƙi ka matso, bayan kasan ƙila yanzu an farama." Ta ƙarasa maganar tana mai sakin wani irin murmushi, wanda za'a iya kiran sa da na yaƙe. Yayinda shi kuma Asad ya sauke wani ɗan gajeren numfashi yana mai janye idanuwan sa daga kanta, tukun daga bisani ya fara ɗaga ƙafafuwan sa yana mai matsawa kusa da ita, sabo da jin furucin nata, kuma yana gudun kar a fara hawan babu shi. "Yawwa ko kaifa Autan Mai Martaba." Jakadiya ta faɗa tana mai fara ɗora masa hular a kan sa idanuwan ta ƙur a kan fuskar sa. Da ƙarfi Yarima Asad ya rumtse idanuwan sa, jijiyoyin kansa na futowa raɗa-raɗa a kan goshin sa, sabo da wani irin mahaukacin nauyi da yaji kan nasa yayi lokacin da Jakadiya ta ɗora masa hular, tukun daga bisani kuma ƙafafuwan sa suka fara wata irin kar-karwa suna rawa. Da sauri Jakadiya ta miƙe tsaye tana mai ƙara cusa hular da take haɗe da rawani cikin kansa idanuwan ta ƙur a kan fuskar sa, tukun ta buɗe baki tana mai faɗin. "Kuyi maza-maza ku tafi ga sautin bindiga can na jiyo, da alamun Mai Martaba ya futa ta ƙofar baya ne muna nan bamu sani ba." Jakadiya ta faɗa da matuƙar sauri tana mai girgiza Asad. Yayinda shi kuma ya taune leɓen sa na ƙasa da matuƙar ƙarfi, tukun daga bisani ya fara bud'e idanuwansa da yake jin sun masa wani irin mahaukacin nauyi a hankali ahankali, harya buɗe su duka a kan fuskar Jakadiya. Da matuƙar sauri Jakadiya ta sake sa tana mai juyawa baya ta fara tafiya, bakin ta na furta kalmar. "Kuyi maza maza ku tafi kar ayi babu ku mana." Ba dan komai ta tafin ba kuwa sai dan yadda taga idanuwan Yarima Asad sun koma Jajahur yarce kasan garwashin huta, a lokacin da ya buɗe sun. Cigaba da tsayuwa Asad yayi a wurin yana mai jin jikin sa na wani rin ɗaukar zafi, yarce kasan ana zuba masa garwashi. Ganin da Al'amin yayi Asad bai motsa daga wurin da yake ba ne ya sanya sa buɗe baki yana mai faɗin. "Muyi sauri mutafi mana aboki, sabo da kaji fa Jakadiya tace amma fara." Ya ƙarasa maganar yana mai jan hannun Yarima Asad yayi gaba ba tare da ya tsaya kallon sa ba, ballantana ya lura da sauyawar da yanayin sa yayi. Jin hakan da Yarima Asad yayi ne da kuma yadda yaji Al'amin na ƙoƙarin jansa ne, yasan ya sa fara ɗaga ƙafafuwan sa da yake jin suna karkarwa yabi bayan sa cikin tsantsar azaba, domin kuwa shi kansa bazai so ace hawan nan da yayi mahaukacin tamasa ba ya huce sa. Tafe suke gumi na yanko masa ta tsakar kansa yana tsiyayowa ta cikin hular dake sanye a kansa zuwa kan fuskar sa sosai, amma a haka ya cigaba da bin bayan Al'amin da yake jan hannun sa ba tare da ya tsaya ba, duk da yadda kuwa yake jin jikin sa na sake ɗaukar zafi tamkar ana hura ta a cikin sa. Basu tsaya ba har sai da sukaje gaban Dokunan su da suke riƙe a hannun wasu mutum biyu daga cikin ƴan sulke, tukun Al'amin ya saki hannun Yarima Asad yana mai faɗin. "Ga naka nan ka hau, nima bari na hau nawa." Ya ƙarasa maganar yana mai matsawa kusa da danƙareren baƙin dokin da yake riƙe a hannun wani mutumi, ba tare da ya kalli fuskar Asad ba har lokacin. Yayinda shi kuma Asad ya sake rumtse idanuwan sa jikin sa na fara karkarwa, tukun daga bisani ya buɗe su a hankali, kana ya fara ɗaga ƙafafuwan sa da yake jin suna ƙara yin nauyi, yana mai matsawa zuwa gaban wani farin danƙareren doki da yaji uban ado ta ko ina a jikin sa, da alama dai shine Dokin nasa. Sosai dokin yake da matuƙar girma, ga kuma fatar jikin sa da takasance fara ƙal, babu ko ɗigon baƙi a jikin ta sai faman shigning da take tana ɗaukar ido, alamun ba ƙaramun hutu dokin yake ciki ba kenan. A hankali ya miƙa hannun sa da yake wata irin rawa yana mai riƙe linzamin dokin da shi, tukun ya fara ɗaga ƙafar sa ɗaya yana mai shirin hawa dokin, amma sai gaba ɗaya yayi baya yana shirin faɗuwa a ƙasa. Ganin haka da wannan mutumin da yake riƙe da dokin nasa yayi ne, ya sanya matsawa kusa da shi da matuƙar sauri yana mai tarosa a hannun sa, sannan ya ƙara cicciɓa sa yana mai ɗora sa a saman dokin ba tare da ya tsaya kallon fuskarsa ba, domin kuwa shi duk atinanin sa ko rashin sabo da hawan da baiyi bane da kansa ya sanya yanzun ma ya kasa hawa. Yayinda shi kuma Asad yana hawa saman dokin nan yaji kansa ya sake yin wani irin bala'in sarawa da matuƙar ƙarfi. Rumtse idanuwansa yayi yana mai ɗanyin zillo akan dokin tare da cije leɓen sa na ƙasa da bala'in ƙarfi, take kuwa leɓen ya futar da wata irin tsartuwar jini, alamun ya fashe kenan! Tukun daga bisani ya fara buɗe idanuwan sa a hankali yana mai jin numfashin sa na wani irin fuzga. Buɗe idanuwan nasa yayi dai-dai da lokacin da Al'amin ya riƙe linzamin dokin sa yana mai ɗan dukan jikin sa da hannu, take kuwa dokin ya zura a guje yana mai yin gaba, kamar yacce na Babban yaya ya riga yayi gaba tini. Ganin hakan da Asad yayi ne ya sanya sa shima miƙa hannun sa ɗaya yana mai damƙar linzamin dokin. Ai'ko kamar jira dokin yake yi ya riƙe sa yayi wata irin zabura yana mai sakin haniniya da matuƙar ƙarfi ya fara sakin gudu. A kuma dai dai lokacin jikin Yarima Asad ya fara wata irin bala'in karkarawa, numfashin sa na wani irin fuzga da matuƙar ƙarfi. Wata irin gigitattar ƙara Babban Yaya ya saki a dai-dai lokacin da ya juya dokin sa yana son yayi wani wasa da shi, sabo da yadda idanuwansa suka hango masa Yarima Asad ya saki linzamin dokinsa dokin na kan gudu, yana mai y....................✍ *A GASKIYA NA DENA SAKIN LINK NA GRUOP 'DINA, SABODA YAWAN B'ATA GARI DA WA'YAN DA BA KARATUN SUKE BA DA SUKE SHIGOWA, DAN HAKA GA DUK MAI SON KASANCEWA ACIKIN GROUP 'DIN B'AKAR MASARAUTA, AMMA FA IDAN YASAN YA IYA COMMENT DA SHARHI SAI KU TUNTUB'ENI TA NUMBER WHATSAPP 'DINA KAMAR HAKA. 08038135929. K'OFA ABUD'E TAKE GA MASU SO A TALLATA MUSU HAJARSU A DUNIYA KUMA ZAKU IYA TUNTU B'ATA TA NUMBER.* *BY* UMAR FARUQ*D* *BAƘAR MASARAUTA* *NA* UMAR FARUQ*D* *PAGE 19* Yin baya gaba ɗayan sa. Da matuƙar sauri Babban Yaya ya dire daga kan dokin sa, yana mai hankaɗe mutanen dake wurin yayi wurin da ƙanin nasa yake da bala'in gudu, kamar yadda mutane da dama suka juya wurin, ta sanadin ihun da yayi da yaja hankulan su zuwa wurin, amma sai dai kash, gaba ɗayan su sun makaro, domin kuwa tun kafin su isa wurin Yarima Asad ya faɗo ƙasa ta baya, kana dokin ya take ƙirjin sa da ƙafafuwan sa yana mai yin gaba! Wata irin zabura yarima Asad Yayi ƙirjinsa na ɗagowa sama adai-dai lokacin da dokin ya taka ƙirjin nasa, tukun daga bisani ya koma yana mai zubewa a ƙasa babu alamun numfashi tattare da shi! Wata irin mahaukaciyar ƙara Babban yaya ya buga alokacin da ya ƙarasa kusa da ƙanin nasa, sabo da yarce ya gansa a sassanƙare, gashi babu ko alamun numfashi tattare da shi, kana daga bisani ya zube guiwoyin sa aƙasa yana mai janyo Asad cikin jikin sa yana girgizasa, tare da kiran sunan sa. "Asad! Asad!! Asad!!!" Babban yaya yake faɗe cikin tsantsar ruɗu yana mai ɗan marin fuskar sa tare da girgiza sa, sabo da yadda yaga gaba ɗaya jikin sa ya sandare ya koma tamkar sanda, domin kuwa babu wata gaɓa da tayi saura wacce ke motsawa a jikin sa. Kafun kace tak tuni wurin ya cika da Al'umma tako ina ana kallon su. Yayin da shi kuma Babban yaya ya fashe da wani irin gigitaccen kuka jikin sa na rawa, gumi na tsattsafo masa cikin jikin sa. "Asad dan Allah ka temake ni ka tashi kar kamutu kabarmu kaji." Ya sake faɗa a gigice yana mai cigaba da girgiza sa. Acan ɓangaren Gimbiya Fulani cikin gida kuwa, tunda akayi sallahr la'asar ta futo daga cikin ɗakin ta tana me neman Asad, ba dan komai ba kuwa sai dan kawai ta sanya sa yayi azkar ɗin yamma, kamar yacce duk ranar duniya take sasu suke yin su, wato azkarul sabahu wal'masah, da suke a cikin hisnul muslim wanda Annabi yake yi ya kuma koyar. Amma sai dai har ta gama duba duk inda yake tsammanin zata gansa bata gansa ba, hakan ne yasata fahimtar yana hurin mai martaba ya tafi ya shirya, ba dan ranta yaso ba ta juya zuwa cikin ɗakin ta jikin ta duk ba daɗi, tana mai fatan Allah yasa yayi azkar ɗin da kansa, domin kuwa tasan sa da wasa muddin basa sa tayi ba haka yake cewa ya manta, ba kamar babban yaya ba da baya taɓa ƙinyi ko a ina yake kuwa, hakan yasa ko kaɗan bata da fargaba akan sa, domin kuwa tariga data sani muddin wani abun ya same sa to muƙaddari ne kawai daga Allah, ba wai dan rashin addu'a ba. Tana nan zaune a cikin ɗakin ta kan tsakiyar gado hannun ta riƙe da Baby, wata kuyanga ta faɗo cikin ɗakin bako sallama a bakin ta, sai faman haki da take ta saki kawai. Da sauri duka mutanen dake a cikin ɗakin suka kai idanuwan su gare ta, yayin da wasu daga cikin su kuma suka buɗe baki suna masu faɗin. "Ke ko lafiya kika faɗowa mutane cikin ɗaki a haka?" Bata iya basu amsa ba, sai gaba da ta cigaba dayi zuwa wurin da Gimbiya Fulani take cikin tsantsar ruɗu da tashin hankali. "Yay...Yarima...ne ya faɗo...daga saman doki afil..." "Me kike son kice mun ne haka, shin wane Yariman ne ma ya faɗo daga saman doki?" Gimbiya fulani ta faɗa a haukace bayan ta diro daga kan gadon da take hannun ta riƙe da ƴar jinjirar ta. Yayin da sauran mutanen dake a cikin ɗakin ma duk suka miƙe tsaye hankula su a bal'in tashe. Da sauri Gimbiya Fulani ta ratsa ta cikin mutanen nan da suke a cikin ɗakin ta tana mai kama hanyar waje, ba tare data ɗau ko da mayafi ba, tsabar ruɗun da take a ciki, domin kuwa hankalin ta idan yayi dubu sai da duka ya tashi. Ganin hakan da sauran matan cikin ɗakin sukayi ne ya sanya su mara mata baya, suma duk hankulan su a matuƙar tashe. Ƙarasawar ta bakin ƙofar futa daga cikin fallon nata yayi dai-dai da lokacin da Babban Yaya ya danno kansa cikin falon, rungume da Asad a ƙirjin sa yana mai sakin wani irin kuka a matuƙar haukace. Take a wurin kuwa jikin Gimbiya Fulani ya ɗauki wata irin karkarwa, kana ta kasa yin gaba ta kasa yin baya, sai mamewa da tayi a wurin da take idanuwan ta ƙur akan Ƴaƴan nata guda biyu, yayin da zuciyar ta kuma ke wani irin gudu fiye da misali, fargaba da tashin hankalin abun da zata gani ta kuma ji sukayi matuƙar lulluɓe ta. "Mamy na dan Allah kicewa Asad kar yatafi ya barni, mamy kice masa ya tashi, dama ni sai da nace masa kar yahau doki bazai iyaba, amma yace ya iya kuma yana hawa ai dama, gashi kuma yanzu ya faɗo dokin ya taka ƙirjin sa." Babban yaya ya faɗa a wani irin haukace yana mai durƙushewa a gaban mamay'n tasu da ya ƙaraso, tare da sakin wani irin gigitacce kuka. Girgiza kai Gimbiya Fulani ta farayi tana mai zube guiwoyin ta a ƙasa Da sauri Hadima Larai ta ƙaraso wurin da take tana mai amshe baby'n hannun ta, sabo da yadda taga tana shirin yadda ta ba tare data sani bama. Cikin sauri ta miƙa hannuwan ta da suke bal'in rawa, tana mai janyo Asad daga jikin Babban Yaya ta dawo da shi kan cinyar ta. Kana ta ɗaga tafin hannun ta ɗaya tana mai ɗan marin fuskar sa, bakin ta na furta kalmar. "Zaki! Zaki!! Zaki!!!" Amma taji shiru ko alamun motsi babu tattare da shi. Hakan ne yasa ta janye tafin hannun nata daga kan fuskar sa tana mai matsar da shi zuwa wurin rawanin da yake sanye a kansa ta tunɓuke sa ƙasa, tana mai cusa ƴan yatsun hannuwan ta a cikin lallausar sumar kansa. Da sauri ta rumtse idanuwan ta tana mai janye ƴan yatsun nata daga cikin sumar sa, sabo da wani irin tururi da taji ya dake su mai tsantsar azabar zafi. "Ku bani ruwa! Ku bani ruwa!! Sun ƙone mun kan yaro da huta!"" Ta faɗa a wani irn haukace tana mai juyawa ta kalli dandazon jama'ar da suke zagaye da su. Cikin ƴan sakanni sai ga wasu mata nan har guda biyu sun miƙo mata ruwayen a cikin jarkokin su kamar yacce ta buƙata Da mtuƙar hanzari ta buɗe murfin jarkar bayan ta warce ta a hannun matar, tukun daga bisani ta ɗaga ta tana mai tsiyaya ruwan a tsakiyar kan Asad, tare da kai yatsun hannuwan ta cikin sumar tasa ta fara cuɗa ta hankali a bala'in tashe. A kuma dai-dai wannan lokacin Mai Martaba Sarki Abdallah ya faɗo cikin falon a matuƙar hargitse, ba tare da yayi ko sallama ba. *JAHAR KAGUL CIKIN MASARAUTAR FULƊE.* Yau take ranar sunan jinjirar da Gimbiya Kaɓel ta haifa, hakan ne yasa ko ina ka kalla a cikin Masarautar kake ganin jama'a iri-iri, tun daga kan Sarakai na wasu masarautun maƙotan su har zuwa hadiman gidan suna ta giftawa, yayin da gaba ɗaya fuskokin su suke ɗauke da tsantsar farin ciki da annashuwa. Tun bayan Sallah asuba aka yanka shanu har kimanin guda takwas narka-narka lafiyayyu a gidan, kana yarinya taci sunan Kakar ta, wato mahaifiyar Lamiɗo, amma za'ana kiran ta da HADDIYAL. Sosai akai shagali irin shagalin da ba ataɓa yin kamar sa ba a cikin gidan, kana aka baiwa jinjirar tsafuka kala-kala, a cewar su hakan shine ƙarshen gatan da zasu yi mata a duniya. *ƘASAR HAUSA, JAHAR WASAI MASARAUTAR WASAI.* Cikin tsantsar ruɗu da tashin hankali mai martaba ya ƙaraso wurin da Gimbiya Fulani take riƙe da Asad, yana mai zube guiwoyin sa a ƙasa, yayin da sauran jama'ar dake wurin kuma suka bubbuɗa fili suna masu matsawa gefe. Janyo Asad yayi daga jikin Gimbiya Fulani yana mai rungume sa a jikin sa, tukun daga bisani ya buɗe baki cikin tsantsar tashin hankali yana mai faɗin. "Baba na! Baba na!! Baba na!!! Asad! Asad!! Asad!!!" Ya faɗa cikin ruɗu da firgici yana mai girgiza sa, gaba ɗayan sa shima ya ruɗe ya firgice yadda kasan ba namiji ba, namijin ma kuma Sarki. Amma sai dai Asad ko motsi baiyi ba, sai ma wata irin sandarewa da jikin sa yake sakeyi tamkar gawa, domin kuwa su kansu banda sunga zuciyar sa na bugawa da babu abun da zai hana suce ya mutu, sai dai kuma ga zuciyar tasa nan tana bugu da sauri da sauri kowa na gani, kasancewar babu kaya a jikin sa sai boxer kaɗai da yayi ragowa, domin kuwa duka sauran kayan Gimbiya Fulani ce ta cire masa su. Cicciɓar sa mai martaba yayi yana mai miƙewa tsaye da shi, kana ya mannasa a ƙirjin sa yana mai masa wata irin runguma, tukun ya juya baya cikin sauri tamkar ya kifa a ƙasa, yana mai fucewa daga cikin falon gaba ɗaya. Direct yayi part ɗin sa da shi yana mai zuwa ya kwantar da shi a kan tamfatse-tsen gadon sa na al'farma. Baifi mintina biyar ya ɗauka da shigowar sa ɗakin ba, sai ga Babban lilkitan su da yake duba su sun shigo cikin bedroom ɗin, tare da su Galadima da Waziri da kuma duk sauran ƴan uwan mai martaba manyan maza. "Yawwa likita matso-matso ka gaggauta dan Allah kayi sauri ka duba sa, bana son na rasa rayuwar Ɗana." Mai Martaba Sarki Abdallah ya faɗa cikin tsantsar ruɗu, yana mai ƙarasawa wurin da Doctor'n yake ya kamo hannun sa. Bai sakar masa hannun nasa ba har sai da ya kawosa gaban gadon da yarima Asad yake yashe akansa, tukun ya cika masa hannun yana mai komawa ɗayan ɓarin ya riƙo tafin hannun Asad ɗaya yana murza sa. Yayin da shi kuma doctor nan ya buɗe box ɗin sa cikin sauri, kana ya fara zaro abubuwan gwaje-gwaje yana mai fara yin abun da ya kamata yayi. Su kuwa su Galadima da sauran jama'ar gaba ɗayan su jugum-jugum sukai suna kallon Asad da yake kwance sheme akan gado yadda kasan gawa, zuciyoyin su cike da al'hinin wannan abu da ya faru lokaci guda, kana ko wanne daga cikin su da akwai abun da yake saƙawa a cikin zuciyar sa. Sai da likitan ya ɗauki kimanin mintina arba'in yana faman bincikar yaron. Kana daga bisani ya miƙe tsaye yana mai sharce gumin dake akan goshin sa, idanuwan sa akan fuskar mai martaba da shima yake kallon sa yana gumin, duk da sanyin A'C'n dake ratsa cikin ɗakin, amma hakan bai hana doctor'n haɗa zufa ba kamar yacce bata hana mai martana yin zufar fa shima. "Ya ake ciki ne doctor? Mene yake damun Asad ɗina? Shin dokin yay masa illa ne?" Mai Martaba ya watsowa likitan tambayoyi a jere a kuma tsantsar ruɗe duk a lokaci ɗaya. Yayin da shi kuma ya sake gyara tsayuwar sa a wurin da yake yana mai yin gyaran murya, tukun daga bisani ya buɗe baki cikin sanyi yana mai faɗin. "Ina ganin wannan abun bazai yuwu anan cikin gida ba, dole sai mun dangana da Asibiti, sabo da acan ne muke da kayan aiki tare da kayan gwaje-gwaje waƴan da zasu taimaka mana wurin gano abun da ke damun sa, sabo da ni dai a yanzu gaba ɗaya ban fahimci komai ba dan gane da ciwon nasa, abu ɗaya kawai dana sani shine yana rayuwa har yanzu a doron duniya, but kuyi hakuri ku kwantar da hankalin ku, insha Allah hakan ba wata matsala bace Babba." Ya ƙarasa maganar cikin sanyi. Gaba ɗayan su suma shiru sukayi babu wanda aka iya samu ya furta komai, domin kuwa ba ƙaramun sanyi jikin su yayi ba duka. Sun ɗauki tsawon minti na biyar a haka, tukun can mai martaba ya miƙe a wani irin zabure yana mai sake ɗaukar Asad, kana ya juya ya kama hanyar waje cikin sauri tamkar ya kifa a ƙasa, ba tare da yace musu komai ba. Hakan da suka ganine ya sanya suma gaba ɗayan su mara masa baya har likitan, suna masu fucewa daga cikin ɗakin. Cikin ƙanƙanin lokaci suka ƙarasa cikin tamfatsetsen private hospital ɗin da yayi bala'in gajiya hurin haɗuwa, domin kuwa tsayawa faɗar kyawun asibitin shi kansa ɓata lokaci ne, amma sai dai kallo ɗaya mutum zai masa ya fahimci cewa ba wurin zuwan ko wane irin mutum bane ba, domin kuwa cikin masu kuɗin ma sai waƴan da suka amasa sunan su na masu kuɗi, wayan da futa ƙasar waje ma ba tai musu huya. Cikin tsantsar hanzari mai martana dake riƙe da Yarima Asad har lokacin a jikin sa ya furo daga cikin motar da wani Bafade ya buɗe masa ita. Ba tare da ya tsaya ɗora sa akan gadon marasa lafiyan da wasu nurses suka kawo wurin ba ya huce gaba rungume da abun sa, ganin hakan da doctor'n yayi ne ya sanya sa bin bayan sa cikin sauri shima. Ko da aka zo shiga da Asad da ya zamto tamkar gawa ɗakin da za'ayi masa gwa-gwajen, dagewa mai martaba yayi yace sai ya shiga shima, amma likitan yay ta basa haƙuri yana mai basa tabbacin zai tashi insha Allah, har ya samu ya shawo kansa ya haƙura da shigar, ta sanadin bakin da ƴan uwan sa suka sanya akan yayi haƙurin. Tukun ya juya yana mai zuwa ya zauna akan kujerar da take a bakin ƙofar ɗakin, tare da ɗaga kansa sama ya lumshe idanuwan sa, yana mai jin zuciyar sa na tsantsar tafasa da ƙuna. Yayin da su kuma likitocin suka shige cikin ɗakin dukan su, domin su fara ai'watar da abun da ya kamata suyi. Acan cikin masarauta kuwa, ɓangaren Gimbiya Fulani, gaba ɗaya mutanen da suke a cikin falon jugum-jugum sukayi a lokacin da Mai Martaba ya fuce da Yarima Asad, yayin da Gimbiya Fulani kuma take wani irin kuka tana mai yiwa ɗan nata addu'oi, domin kuwa ba ƙaramun firgita tayi ba da halin da tagan sa a ciki, barin ma kuma da taji wannan azababben zafin da yake futa daga cikin jikin sa. Shima Babban yaya gefe ya koma ya zauna yana mai aikin rusar kuka, domin kuwa shi duk a tinanin sa ƙanin nasa ya riga da ya mutu. Suna cikin wannan halin sai ga Jakadiya nan ta afko cikin falon a matuƙar ruɗe, tana mai yowa wurin da suke. "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un, yau nayi mummunan ji, naji labarin da ya hargitsa ƙwa-ƙwalwa ta, shin ina ma shi shelelen yake ne yanzu?" Jakadiya ta faɗi haka a hargitse, hannun ta dafe da kanta. Shiru gaba ɗaya mutanen dake wurin sukayi ba tare da wani ya tanka mata ba, jin hakan da tayi ne ya sanya ta sake buɗe baki cikin muryar ta da take tsantsar rawa, alamun kuka na shirin ƙwace mata tace. "Dan Allah kuyi mun magana mana, ku faɗumun inda Shalelen Mai Martaba yake tun kafin zuciyata tai bundiga." "Kiyi haƙuri Jakadiya, Mai Martaba ya ɗauke sa sun tafi asibiti ance." Ɗaya daga cikin matan da suke zaune a wurin jugum-jugum ta faɗa, tana mai dafa kafaɗar Jakadiya da tashin hankali ƙarara ya bayyana akan fuskar ta. Acan Asibiti kuwa sai da har likitocin suka ɗauki tsawon awa ɗaya suna binciken abun da ke damun Asad, amma basu gano komai ba da zasu iya cewa shi yayi sanadin sa-sa sumar, domin kuwa ko ƙirjin nasa da akace doki yabi takai su ba suga wani abun da ya same saba kwata-kwata, wato dai normal ƙirjin nasa yake kamar na kowa, sai dai kuma zuwa yanzu sun samu numfashin sa na futa dai-dai, ta sanadin oxygen da suka sanya masa, kana kuma bugun zuciyar tasa shima ya koma ya saitu kamar yacce yake a baya, sai dai kuma zafin jikin nasa ne har yanzu babu abun da ya ragu a kan na baya, sai ma sake ƙaruwa da yake yi fiye da da. Jiki a tsantsar saɓule Doctor Muhammad ya juya yana mai kama hanyar futa daga cikin room ɗin. Yayin da sauran Nurses ɗin kuma suka samu wuri suna masu zama akan kujeru, kamar yacce tsarin Asibitin yake, wato su da kansu suke jinyar patiant ɗin su ba wai ahalin mutum bane zasu zauna masa, sai dai kuma idan mutum ya takura akan shi zai zauna suna barin sa, tun da dai su baza a fasa basu kuɗin su ba cas, kamar yacce kowa ke bayarwa. Doctor Muhammad na tura kai waje Mai Martaba da yake zaune akan wata haɗaɗɗiyar kujera da take abakin ƙofa anyi-anyi ya shiga office amma yaƙi, ya miƙe tsaye zumbur yana mai faɗin. "Ya jikin nasa doctor, ina fatan dai yaro na yaki sauƙi yanzu ko?" Ya watso masa tambayoyin a jera, sannan kuma a matuƙar ruɗe. "Kayi haƙuri mu ƙarasa zuwa cikin office ranka ya daɗe." Cewar Doctor Muhammad yana mai ɗan durƙusawa ya rage tsayin sa a gaban Mai Martaba, kamar yacce ya saba a koda yaushe. Yayin da shi kuma Mai Martaba ya rumtse idanuwan sa yana mai fesar da wata zazzafar iska daga cikin bakin sa, tukun daga bisani ya buɗe su akan fuskar doctor ba tare a yace komai ba. Ganin hakan da Doctor Muhammad yayi ne ya sanya sa yin gaba yana mai faɗin. "Bismillah'n ku to." Gaba ɗayan su miƙewa sukayi suna masu bin bayan sa, ko wanne a cikin su zuciyar sa cike da son jin abun da ke faruwa, yayin da wasu daga cikin su kuma suke murna da jin daɗi, tare da fatan Allah yasa mutuwa yaron yayi, idan kuma bai ba zaiyi, wato magautan su kenan, munafukai masu fuska biyu, su kuwa masoyan su cike suke da fargabar jin abun da Doctor zai ce. Tamfatse-tsen office ne mai matuƙar girma da kyan tsari. Jere yake da wasu haɗaɗɗun kejeru masu tsanin kyau da taushi acikin sa, yayin da daga can gefe ɗaya na cikin office ɗin kuma wani haɗaɗɗen table yake kafe a wurin, sai daga bayan table ɗin kuma kujera ce mai tsantsar kyau irin wacce ke juyawa da mutum idan yana kai, yayin da saman teburin kuma yake ɗauke da takaddu tare da system akan sa. Direct doctor muhammad ya huce zuwa kan table ɗin, yayin da su kuma su Mai Martaba suka zazzauna akan kujerun nan suna masu fuskantar sa. Gyaran murya yayi yana mai sa yatsun hannun sa ya cire maɓalli ɗaya daga cikin maɓallayan dake jikin gaban rigar sa. Kana daga bisani ya buɗe baki cikin sanyi yana mai faɗin. "Haƙiƙanin gaskiya dai shi ne, munyi iyakar yin mu, sannan kuma munyi amfani da duk abun a ya kamata muyi, domin mugano abun da ke damun sa, amma sai dai kuma gaba ɗaya binciken da mukayi babu wanda yay mana nuni da wata matsala da take tattare da shi, asalima duka result ɗin suna nuna negative ne na duka tests ɗin da mukayi masa, sai dai kuma munyi nasarar dai-dai ta numfashin sa tare da bugun zuciyar sa, but yanayin zafin jikin nasa ne har yanzu babu abun da ya ragu, sannan kuma shima ɗin bai farfaɗo ba." Doctor Muhammad ya ƙarasa maganar cikin sanyi, domin kuwa ya yi iyakar yin sa amatsayin sa na cikakken Medical Doctor, amma bai gano komai na dan gane da abun da ke damun yaron ba, kuma baya tinanin ko sun bar nan sunje wani wurin za adace ɗin, domin kuwa gaba ɗaya kayan ai'yukan da yake amfanni da su a cikin asibitin nasa duk irin na ƙasashen turawa ne, wato irin waƴan da ake amfanni dasu acan ɗin ma idan an kai mutum, kasancewar sa mutum wanda yake da kuɗi, sannan kuma ya taso cikin ruwan kuɗi a gidan su, domin kuwa shi kansa duka karatun nasa ba a Ƙasar Hausa yayi sa ba, hatta da primary kuwa. Wani irin zazzafan numfashi Mai Martaba ya fesar, yana mai jin kansa na sara masa, ga kuma idanuwan sa da sukayi jajajir, alamun ba ƙaramun tashin hankali yake ciki ba. Galadima ne ya buɗe baki cikin sanyi yana mai faɗin. "To yanzu mene abunyi kuma a gaba Doctor, bi ma'ana me kake ganin zaku iya sake yi masa, ko kuma wane wurin kake tinanin zamuje bayan nan wanda suke da kayan aikin da sukafi naku?" Girgiza kai Doctor Muhammad yayi yana mau ɗan yin shiru, tukun daga bisani ya buɗe baki bayan ya ɗago ya kalle su, yana mai faɗin. "Haƙiƙa bazance kuma ga wurin dana sani ba wanda nake da tabbacin yafi nan, domin kuwa a duk faɗin Jahar Wasai babu wani Asibiti da ya kai namu, sabo da mu kaɗai ne muke amfani da kayan aiki irin waƴan da ake afanni da su a Asibitocin mu na ƙasashen waje, amma sai dai kuma ni atawa shawarar sai nake ganin mai zai hana a gwada na Islamic chemist, wato na musulunci ko Allah zai sa adace." Ya faɗa yana mai kallon su. Yayin da su kuma dukan su sukayi shiru ba tare da wani ya iya furta komai ba. Sun ɗauki tsayin mintina biyar a hakan, tukun daga bisani mai martaba ya buɗe bakin sa bayan yasa yatsun hannuwan sa ya sharce gumin dake tsats-tsafowa akan goshin sa, yana mai faɗin. "Ina ganin shawarar taka ita zamubi Doctor, dan haka tun yanzu nake tinanin zamu shirya tafiyar, domin kuwa akwai wani Babban malami na da yake zaune a London, malami ne masanin Al'qur'ani tare da litattafai, da kuma magun-guna irin na Islamic, domin kuwa a wurin sa nayi karatu na a lokacin da nayi zaman Saudiyya, to daga baya ne yanayin ai'ki ya mayar dashi can ƙasar London, dan haka ayau-yau ɗin nan zamubi Private Jet mu tafi." Ya ƙarasa maganar yana mai miƙewa tsaye. Hakan da suka ganine ya sanya su suma dukan su suka miƙe tsayen har doctor, tukun suka juya suna masu fucewa aga cikin ɗakin. Tamkar gawa haka Mai Martaba ya sake ɗakko Asad a hannun sa bayan anyi dischargen nasu, domin kuwa kwata-kwata yaƙi ya bari aɗora sa akan gadon marasa lafiya, shi da kansa yake ɗaukar abun sa. A haka duk suka shige cikin motocin su da dogarawa suka yi musu ƙawanya, tukun matuƙan ciki suka jasu suna masu fucewa daga cikin hospital ɗin. Ba tare da wani ɓata lokaci ba aka fara cuku-cukun tafiyar su Mai Martaba Kasar London. Misalin ƙarfe goma na dare dai-dai Private Jet ɗin da suka kama wanda ya zamto su biyun ne kawai acikin sa, wato daga Mai Martaba sai Asad ɗin, ya ɗaga zuwa sararin samaniya.............✍ _Kadanba na gaji haka_ 😟 *BAƘAR MASARAUTA* *NA* UMAR FARUQ*D* *PAGE 20* Sosai Gimbiya Fulani da duk wani makusancin ta masoyin ta kuma suka shiga cikin matsanan ciyar damuwa, jin abun take tamkar Al'mara, domin kuwa lafiya ƙalau Asad ya bar wurin ta alokacin da aka kira sallahr la'asar, suka tafi masallaci tare da Al'amin, ba tare da yace mata yana ko ciwon kai ba. Kusan duk jama'ar dake cikin masarautar sun shigo sun mata jaje, sai ƙalilan ne kawai basu shigo ba, irin su Gimbiya Huwaila da kuma Gimbiya Amina kishiyoyin ta. Sai dai kuma ko kaɗan abun bai dama ta ba da rashin zuwan nasu, sannan kuma bai bata mamaki ba, domin kuwa tariga da ta daɗe da sanin babu wata mai ƙaunar ƴaƴan nata a cikin su,. Hakan yasa ta duƙufa kaiwa Allah kukan ta, tana mai roƙon sa akan ya tada kafaɗun Ɗan nata. _LONDON_ Sai a washe garin ranar da suka isa, tukun mai martaba ya fara bincikar gidan Sheikh Yaƙub, wato malamin nasa, bai wani sha wata wahala ba wurin neman gidan ya gano sa, sabo da dama ba wannan bane zuwan sa na farko. Cikin girmamawa tare da mutun-tawa sheikh Yaƙub ya tarbi Mai Martaba da hannu bibbiyu a cikin falon sa da yake sauke baƙin sa cikin sa. Bayan sun gama gaisawa ne Sheikh Yaƙub ya buɗe baki idanuwan sa akan Asad da yake kwance a kan cinyar Mai Martaba, tamkar yadda yake jiya yana mai faɗin. "Yaron ba lafiya ne, ko kuwa bacci yayi maka a hanya ne?" Girgiza kai Mai Martaba yayi yana mai kai idanuwan sa kan fuskar Asad ɗin da yayi wata mahaukaciyar rama daga jiya zuwa yau a hakan da yake, tukun daga bisani ya ɗago kai idanuwan sa akan fuskar Sheikh Yaƙub, yana mai faɗin. "Lafiyar ce dai babu Ya Sheikh, domin kuwa tasanadin ta mukazo nan wurin naka ma." Mai Martaba ya faɗa murya asanyaye, cikin harshen larabci kamar yadda suke maganar da shi dama. "Subahanallahi! Meke damun sane haka to?" Shikh Yakub ya tambaya yana mai miƙewa tsaye daga kan kujerar da yake ya nufi wurin su mai martaba. Gyaran murya mai martaba yayi, tukun ya fara bawa Sheikh Yaƙub labarin duk abun da yasan ya faru har zuwa asibitin da sukayi, da kuma shawarar da likitan su ya basu na cewa su haɗa da maganin addini. Girgiza kai Sheikh Yaƙub yayi alokacin da ya gama jin bayanin Mai Martaba, hannun sa riƙe da ƴan yatsun Asad. Tukun daga bisani ya buɗe baki yana mai faɗin. "Tabbas kuwa ba abun mamaki bane hakan ya kasance, domin kuwa mutum babu abun da bazai iya ba, amma in banda rashin imani ma duka-duka nawa wannan yaron yake, me yasa ni ne ma da har za'a cutar da shi irin haka, but ba damuwa insha Allah zai warke tas nan kusa bada jimawa ba." Sheikh Yaƙub ya faɗa yana mai sa hannu ya ɗauki Asad daga kan cinyar mai martaba, tukun ya juya yana mai dosar wata ƙofa da take a cikin fallon, bayan ya cewa Mai Martaba ya biyosa zuwa ciki. Ɗan madai-daicin ɗaki ne mai matsakaicin girma. Ɗauke yake da magun-guna kala-kala irin na addini, tun daga kan na ruwa har zuwa na gari, da suke aje akan kantocin da suka yiwa ɗakin ƙawanya. Yayin da daga ɓari ɗaya kuma aka ajiye wani ɗan gado irin na Asibiti. Direct Sheikh Yaƙub ya huce da Asad zuwa gaban wannan gadon na cikin ɗakin, tukun ya ɗorsa akan sa, kana ya juyo ɓarin da mai martaba yake yana mai masa nuni da wata kujera da take ajiye a gefen gadon, yace ya zauna a kanta. Hannu mai martaba yasa ya matsar da kujerar bakin gadon, tukun ya zauna akai, yana mai riƙo tafin hannun Asad cikin nasa yana murzawa. Sosai yake jin tausayin ɗan nasa na ratsa ko wane lungu da saƙo na jikin sa, yana kwanciya a ɓargon sa. Kana yana mai jin a ransa muddin abun nan ya zamto gaskiya, wato asirin akaiwa ɗan nasa, kuma ya zamto ya gano wanda ya ai'kata masa hakan, to kowaye shi sai yaga ƙarshen fushin sa, sai ya masa hukunci na dai-dai laifin da ya ai'kata masa. Ba tare da wani ɓata lokaci ba Sheikh Yaƙub ya fara haɗa magun-gunan sa, tukun ya matso gaban gadon da Asad yake hannun sa riƙe da wata ƴar kwalba, wacce take ɗauke da wani kalar mai a cikin ta. Dangwalar man ya dinga yi yana mai shafa sa asaman goshin Asad da kuma kan ƴan tsunsa na ƙafa, tukun daga bisani ya juya bayan ya gama shafa masa, yana mai ɗauko wani turare ya zubasa a cikin electric burner ta turaren wuta, bayan ya maƙala ta a jikin socket. Take kuwa ɗakin ya turnuƙe da wani irin hayaƙi mara daɗi ko kaɗan. Ajiye sa yayi agefe yana mai juyawa ya tsiyoyo wani ruwa da yake a cikin jarka a cup, kana ya dawo gaban Asad yana mai zuba ruwan atafin hannun sa, tukun ya yarfa masa shi akan fuskar sa, sannan aƙarshe ya koma ya juye masa ruwan duka a fuska, ɗan sauran da yayi ragowa a cikin kofin kuma ya sanya mai martaba ya ɗago masa da kan sa tare da buɗa masa bakin sa, tukun ya tsiyaya masa shi a ciki yana mai hucewa cikin-cikin Yaron. Yayin da hayaƙin nan kuma ke cigaba da tashi har lokacin yana bugun fuskar Asad. Ruwan na gama shiga cikin-cikin sa ya fara ɗan jujjuya kai idanuwan sa na motsawa, amma bawai sun buɗu bane ba. Ganin hakan da mai martaba yayi ne yasan ya sa zaro idanuwa da sauri, sannan kuma cikin tsantsar farin ciki, tukun daga bisani ya buɗe baki yana mai faɗin. "Malam kagani fa yana motsi da kai yanzu, kuma ma naga kamar idanuwan nasa yake shirin buɗewa. Baba na! Baba na!! Baba na!!! Buɗe idanuwan ka kaganni kaji." Mai Martaba ya faɗa cikin sauri yana mai cigaba da murza tafin hannun Asad. "Hakan shike nuna tabbacin sihiri ne akai masa, kuma Insha Allah ba zaiyi wahalar samun sauƙi ba, amma sai dai kuma wannan motsin da yake bashi ke nufin zai buɗe idanuwan nasa yanzu ba, dan haka ina son ka kwantar da hankalin ka, insha Allah zai warke a nan kusa." Cewar Sheik Yaƙub yana mai dafa kan Mai Martaba da shima duk ya zurma sosai, sabo da tashin hankali da fargabar kar ya rasa ɗan nasa. Jinjina kai Mai Martaba yayi yana mai faɗin. "Allah ya basa lafiya to." "Amin! Amin!!" Sheikh Yaƙub ya faɗa yana mai komawa ya cigaba da haɗa magun-gunan sa. Har suka ɗauki tsawo sati ɗaya da zuwa dai-dai Asad bai buɗe idanuwan sa ba, sai dai kuma akullum motsin sa na ƙara ƙaruwa fiye dana da daga kwancen da yake, domin kuwa yanzu har hannun sa yana ɗagawa ya ɗorsa akan ƙirjin sa, hakan yasa Mai Martaba yake ƙara kwantar da hankakin sa, sabo da cigaban da yake gani shida kansa a kullum. Yayin da shi kuma Sheikh Yaƙub ya duƙufa wurin nemawa yaron magani da gasken-gaske. Acan Ƙasar Hausa kuwa, a Jahar Wasai cikin Masarautar Wasai. Sosai Gimbiya Fulani tayi wata irin kwantsamewa, ta jeme ta rame ta kuma yi duhu, sabo da tsan-tsar fargabar da take ciki, ga abinci da bata iya ci, sannan kuma ga rashin samun ishash-shen bacci, domin kuwa kwanan tsaye take tana kaiwa Allah kukan ta. A ɓangaren Babban Yaya da sauran ƙannen sa suma sosai suka rame suka kwantsa me, barin ma Babban Yaya da shima bai fiye yin wadataccen bacci ba, sabo da yadda yake raba dare yana yiwa ƙanin nasa addu'oi cikin sallolin da yake yi. Fannin Al'amin shima kullum rana sai yayi kukan rashin abokin sa, domin kuwa gaba ɗaya ma baro part ɗin su yayi ya dawo wurin Gimbiya Fulani, acewar sa da zarar su Asad sun dawo shi zai fara ganin sa. Hakan da Gimbiya Fulani ta gani ne yasa tasanya akayi musu visa ta zuwa London su ukku, wato ita, sai Babban Yaya, sai kuma shi Al'amin ɗin, yayin da jirgin nasu zai tashi a sati mai zuwa, wato rana ita yau. Har yau cikin duka kishiyoyin nata biyu babu ɗaya data zo mata jaje, hakan ne yasa gaba ɗaya ta ɗiga alamar tambaya akan su, wato take zargin sune suke da sa hannu akan ciwon ɗan nata, sai dai kuma babu wanda ta faɗawa hakan, kana kuma koshi mai martaba tace bazata faɗa masa basu zo ɗin ba. _BAYAN SATI ƊAYA_ Yau ta kama sati biyu da fara yiwa Asad magani kenan, amma sai dai kuma har yau bai buɗe idanuwan sa ba, sai dai kuma a kullum jikin nasa na ƙara yin kyau daga kwancen da yake, sannan kuma zuwa yanzu gaba ɗaya zafin da jikin sa keyi ya ɓace tas, wato tempreture sa ta dawo dai-dai tamkar ta kowa. Misalin ƙarfe ukku na rana an agogon nan london, su Gimbiya Fulani suka ƙaraso cikin gidan Sheikh Yaƙub, ta sanadin driver'n sa da yaje ya ɗauko su a airport. Sosai dattijuwar matar Sheik Yaƙub ta musu tarbar mutunci cikin sakin fuska. Basu iya cin wani abun kirki ba daga cikin lodin abubuwan da aka ajiye musu a gaban su, suka miƙe tsaye suna masu faɗin wazai kai su wurin su Asad ɗin, kasancewar suna can cikin ɗakin maganin har shi Sheik Yaƙub. Ita da kanta ta sanya hijab ɗin ta tana mai shiga gaba tace su biyo ta. Shigar su cikin ɗakin tayi dai-dai da lokacin da Asad ya fara wani irin girgiza kai da matuƙar ƙarfi, yana mai ƙiƙƙifta idanuwan sa, sabo da wani tirare da Sheikh Yaƙub ya shaƙa masa a cikin hancin sa. Da sauri dukan su suka ƙarasa zuwa gaban gadon suna masu tsayawa cirko-cirko, yayin da wasu irin hawaye masu mugun gudu suka ɓalle daga cikin idanuwan Gimbiya Fulani suna tsiyaya akan kuncin ta, sabo da yadda taga gaba ɗaya ɗan nata ya rame yayi baƙ,i yarce kasan ba kakkyawan Asad ɗin ta ta ɗan gayu ba. Ahankali ya fara buɗe idanuwan sa har ya buɗe su duka akan fuskar jama'ar dake wurin, tukun daga bisani yayi saurin mayar dasu ya rumtse yana mai kai tafin hannun sa ya shafe su, sabo da wani irin haske da ya dalle masa idanuwan alokacin da ya buɗe sun. Yayin da su kuma duka jama'ar a suke wurin suka buɗe baki cikin tsanrsar farin ciki, suna masu faɗin. "Alhamdulillah." Kana Gimbiya Fulani ta ɗaga ƙafafuwan ta cikin sauri tana mai zuwa ta zauna abakin gadon, tukun ta kamo tafin hannun Asad ta riƙe sa a cikin nata tana murzawa, bakin ta na furta kalmar. "Zaki! Zaki!! Zaki!!! Buɗe idanuwan ka ka ganni kaji." A hankali ya fara buɗe idanuwan nasa har ya sake buɗe su tas akan fuskar Mamy'n tasa. Gaba ɗayan su murmushi suka saki suna masu matsowa gaban gadon cikin tsantsar farin ciki. Da sauri Mai Martaba ya matsa kusa da shi yana mai miƙa hannun sa ya riƙo ɗayan tafin hannun Asad da shi, tukun ya buɗe baki cikin farin ciki shima yana mai faɗin. "Baba na! Baba na!! Barkan ka da tashi kaji." A hankali Asad ya sake juyawa yana mai kai idanuwan sa kan fuskar Mai Martaba. Yayin da shi kuma Mai Martaba ya sakar masa murmushi yana mai faɗin. "Sannu kaji Baba na." Amma sai dai kuma gaba ɗaya Asad ɗin baice komai ba tun da ya buɗe idanuwan, sai kallon kawai da yake binsu da shi gaba ɗayan su. Yayin da su kuma suke ta sake matsawa gare sa duka har Al'amin, kowa na yi masa magana. Sai da suka ɗauki tsayin mintina goma suna abu ɗaya amma Asad bai tankawa kowa ba, ganin hakan da Sheikh Yaƙub yayi ne ya sanya sa cewa su ɗan matsa daga bakin gadon su basa wuri. Take kuwa duk suka jajja baya, sai Mai Martaba ne kawai bai kauce ba. "Ina yini malam." Gimbiya Fulani da su Babban Yaya suka faɗa, kasancewar basu samu damar gaishe saba la okacin da suka shigo, sabo da murnar ganin Asad da sukayi ya buɗe musu ido data ɗauke musu hankali. "Lafiya ƙalau, fatan kuma kun iso lafiya." Sheikh Yaƙub ya faɗa yana mai zama abakin gadon. Da lafiya ƙalau suma suka amsa masa, yayin da shi kuma ya miƙa hannun sa ya mai riƙo tafin hannun Asad ɗaya da yake ta kallon sa da shi. Tukun ya buɗe baki cikin sanyi yana mai faɗin. "Asad! Asad!" Ƙala Yarima Asad bai ce masa ba, sai idanuwa kawai da yake binsa da su. "Asad kayi magana mana, ya jikin naka ne?" Sheikh Yaƙub ya sake faɗe yana mai ɗan girgiza sa, amma still dai shiru sai kallon kawai, hakan da ya gani ne yasa ya ɗago sa daga kwancen da yake, tukun ya buɗe baki yana mai faɗin. Sauko ƙasa to kaji." Take kuwa Asad ya fara zuro ƙafafuwan sa ƙasa, amma baice komai ba, ganin hakan da yayi ne yasa yace masa koma kazauna to basai ka sakko ɗin ba kaji." Komawar yayi ya zauna kuwa, yana mai jin gina da bango ya cigaba da binsu da idanuwa. Yayin da shi kuma Sheikh Yaƙub ya juyo gare su, gaba ɗayan su da duk sunyi shiru, yana mai kallon su murya asanyaye yace. "To duk da haka dai Al'hamdullilah zamuce, domin kuwa munga sauƙi sosai fiye da baya, tun da gashi nan yanzu yana ganin kowa kuma yana jin muryar kowa, sannan kuma yana iya motsawa har tafiya ma zaiyi, sai dai kuma inda matsalar take a yanzu itace rashin magana, wato dai a gaskiya baya magana, kuma ba zai iya magana ba a yanzu, sai dai ko a nan gaba." Sheikh Yaƙub ya ƙarasa mganar cikin sanyi. Yayin da su kuma dukan su sukayi shiru, sai hawaye da suka ɓalle daga cikin idanuwan Gimbiya Fulani. "To Alhmdulillah, hakan ma ai yafu da sosai, kuma maganar ma insha Allah muna saran zaiyi ta a nan kusa." Mai Martaba ya Faɗa cikin sanyi yana mai murza hannun Asad ɗin. Yayin da shi kuma Shekh Yaƙub ya miƙe tsage yana mai juyawa ya fuce daga cikin ɗakin da shi da matar sa, sabo da su basu damar tattaunawa. Abu fah kamar ƙarami sai gashi yana shirin zamtowa Babba, domin kuwa har kawo yau da su Gimbiya Fulani suka cika sati ɗaya da zuwa kuma suke shirin juyawa a yau ɗin, Asad baiyi magana ba, wanda hakan kuma ba ƙaramun tayar musu da hankali yayi ba, domin kuwa iyakar su da shi kallo ne kawai. A haka dai rai babu daɗi suka rabu, driver'n Sheikh Yaƙub ya kai su airport, domin su koma Ƙasar Hausa zuciya na zafi da ƙuna. *** Kwanaki sunja watanni sun zo sun shuɗe, tun ana sa ran Yarima Asad zaiyi magana a cikin ƴan satittika sai gashi har ya ɗauki tsawon wata tara ba uhm ba uhm-uhm sai dai kallo da idanuwa kawai. Gaba ɗaya sun fara futar da tsammanin zai sake magana, duk da har lokacin basu bar ƙasar London ba, kwatsam rana ɗaya kawai a daren ranar da zai cika wata goma da fara rashin lafiyar tasa, suna zaune tare da Mai Martaba da ya dawo daga Ƙasar Hausa aranar, kawai sai jin muryar Asad yayi tana dukan kunnen sa ahankali. Da farko basarwa yayi ba tare da ya juyo ɓarin da yake ba, domin kuwa duk atinanin sa amsa kuwwa ne kunnen sa yake masa na muryar tasa kamar yadda ya saba yi masa a kusan kullum. Amma sai yaji Asad ya sake faɗin. "Abba na!" Hakan ne yasa sa juyowa ɓarin da yake da matuƙar sauri, yana mai kallon sa baki buɗe. Yayin da shi kuma Yarima Asad ya lumshe idanuwan sa a hankali, tukun daga bisani ya sake buɗe baki cikin sanyi yana mai faɗin. "Abba na." Zumubur Mai Martaba ya miƙe daga kan kujerar da yake, yana mai nufar wacce Asad yake a kai cikin tsantsar aljabi. Yana ƙarasowa gaban kujerar da yake ya durƙushe a ƙasa yana mai zama akan guiwoyin sa, tukun daga bisani ya buɗe baki cikin rawar murya idanuwan sa akan fuskar Asad, yana mai faɗin. "Shin da gaske ne abun da kunnuwa na suka jiyo mun, kai ɗin ne kake magana da kanka Baba na?" Mai Martaba ya faɗi haka cikin sauri, yana mai kamo tafukan hannayen Yarima Asad duka biyu ya riƙe su da nasa. Yayin da shi kuma Asad ya sake mayar da idanuwan sa yana mai lumshe su, tukun daga bisani ya jin-jinawa Mai Martaba kai alamar Eh. Girgiza kai Mai Martaba ya fara yi yana mai faɗin. "A'a Baba na ba da kai nake son ka amsa mun ba, muryar taka nake son sake ji tamkar yacce naji ta yanzu." "Abba na!" Yarima Asad ya sake faɗe yana mai kallon mahaifin nasa. Yayin da shi kuma Mai Martaba ya buɗe baki cikin tsantsar farin ciki yana mai faɗin. "Shin tun yaushe ne ka fara magana Baba na ban sani ba, ko kuwa dama can kanayi-yin ne baka yi Baba na?" Ya faɗi maganar cikin rawar murya, yana mai shafa lallausar sumar da take kwance sunƙum akan Asad. "Yanzu nima naji nayi maganar." Asad ɗin ya faɗa yana mai sake yin shiru. Da wani irin sauri Mai Martaba ya janyo sa jikin sa yana mai rungume sa ƙam-ƙam a ƙirjin sa yarce kasan zai mayar da shi ciki. Tukun daga bisani ya buɗe baki cikin muryar tsantsar farin ciki, hawaye na tsiyayowa daga cikin idanuwan sa, ya fara faɗin kalmar. "Alhamdulillah." Ba ƙaƙƙautawa. Suna a wannan yana yin ne Sheikh Yaƙub ya danno kansa cikin ɗakin, bakin sa ɗauke da Sallama. Hango su da yayi a hakan ne yasan ya sa ƙarasawa ciki da matuƙar sauri, yana mai faɗin. "Subahanallahi, meke faruwa ne yallaɓai na ganku a haka?" Ya ƙarasa maganar yana mai ƙarasowa gaban su ya tsaya. Yayin da shi kuma Mai Martaba ya saki Asad da sauri yana mai miƙewa tsaye ya rungume Sheikh Yaƙub. Shi kuwa Asad mayar da idanuwan sa yayi ya lumshe su ba tare da yace komai ba, domin kuwa hakanan kawai yaji ko kaɗan baya son yin maganar, amai-makon ace yayi ta yin ta amatsayin sa na wanda ya daɗe bai furta koda kalmar A ba. "Allah ya amshi addu'ar mu ya Sheikh, yau dai Asad ɗina yamun magana, ya kirani ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba." Mai Martaba ya faɗa cikin matsanan ciyar murna. Yayin da shi kuma Sheikh Yaƙub ya furta kalmar. "Alhamdulillah." Cikin tsantsar farin ciki, yana mai sake rungumar Mai Martaba shima, tukun daga bisani ya sake sa yana mai yin wurin da Asad yake, bakin sa ɗauke da tsantsar murna. Zube guiwoyin sa shima yayi a gaban sa yana kallon sa. Tukun daga bisani ya buɗe baki cikin tsantsar farin ciki yana mai faɗin. "Asad! Shin da gaske na kayi magana?" Jin-jina masa kai Asad yayi, tukun daga bisani ya buɗe idanuwan sa da suke a lumshe yana mai faɗin. "Eh nayi magana Ya Sheikh." Ya faɗi hakan cikin sanyi. Yayin da Sheikh Yaƙub kuma yayi saurin janyo sa cikin jikin sa yana mai godiya ga Allah. Haka dai sukai ta farin ciki suna sake sanya Asad yana magana, duk da yadda baya son yin nata shida ko kaɗan. Aranar Mai Martaba ya farayi musu cuku-cukun juyawa Ƙasar Hausa a gobe shida Asad. Ko da dare yayi sosai Mai Martaba yayi bacci har da munshari, irin wanda ya jima baiyi kamar saba, domin kuwa rabon sa da cikakken bacci tun ana gobe Asad zai kamu da ciwon nan, wato tsawon wata goma yanzu kenan. Washe gari kuwa tun da sanyin safiya suka tafi airport. Ƙarfe takwas na safe dai-dai na agogon ƙasar jirgin su ya ɗaga zuwa sararin samaniya. Yayin da Sheikh Yaƙub kuma da Iyalan sa da suka yo musu rakiya suka juya cikin jin kewar tafiyar tasu, suna masu komawa gida. *ƘASAR HAUSA, JAHAR WASAI CIKIN MASARAUTAR WASAI.* Lokacin da labarin dawowar Mai Martaba a yau ya fasu a cikin Masarauta Wasai, ba ƙaramun mamakin abun da zai sanya sa dawowa yau bayan kuma kowa yasan jiya ya tafi bane ya lulluɓe su. Take kuwa maganar ta bazu ako ina dake cikin Masarautar, yayin da jama'a da dama dake cikin Masarautar sukai tinanin ko Asad ɗin ne ya rasu, dan kuwa babu wani wanda yay tinanin ko warkewa yayi ne. Tini kuwa murna ta cika zukatan magautan su gaba ɗaya da tinanin da sukeyi na ko Asad ɗin ne ya rasu, kasancewar Mai Martaba bai sanar da kowa dawowar tasa ba har sai da ya sauka a cikin Wasai Internationl airport, tukun ya sanar musu domin azo atafi da su, amma bawai ya faɗa musu dalilin dawowar tasa bane, sabo da yadda yake son yayi suprising ɗin su. Acan ɓangaren Gimbiya Fulani kuwa tana zaune akan kujera sanye da hijabi a jikin ta tana taz'bihi, ɗaya daga cikin Hadiman ta da suke anan part ɗin nata ta faɗo cikin falon da sauri. Da idanuwa Gimbiya Fulani ta bita bayan ta amsa mata sallamar da tayo, har ta ƙaraso bakin kujerar da take zaune akai. Durƙusar dai ƙasa Hadimar tayi bayan ta zauna akan ƙafafuwan ta, tana mai buɗe baki tace. "Barka da hutawa ranki ya daɗe." "Yawwa barkan ki dai Talatu." Gimbiya Fulani ta faɗa tana mai cigaba da kallon ta. Yayin da ita kuma ta ɗan fara mustu-mutsu a wurin da take tana mai son buɗe baki tayi magana, amma tana tsoron tayarce Gimbiya Fulani zata ɗau zancen, sabo da sun sani gaba ɗayan su bata son gulma, asalima babu abun da ta tsana face mutum ya jiyo wani labarin na wani a cikin gidan yazo yace zai sanar mata, hakan yasa gaba ɗaya ta kasa buɗe baki tayi maganar kai tsaye. "Alamun ki sun nuna akwai magana ɗauke abakin ko, shin meke faruwa ne to?" Gimbiya Fulani ta faɗa tana kallon ta, sabo da lura da tayi da ita tana son yin maganar amma kuma tana shakkar yi. Jin da Hadima Talatu tayi Fulani ta bata dama ne, ya sanya ta ɗago kai cikin rawar murya tana mai faɗin. "Dama wai yanzu ne muma mukejin labarin dawowar Mai Martaba ayau, domin kuwa ance har ya sauka ma an tafi ɗakko sa" Ta ƙarasa maganar da sosa ƙeya. Yayin da ita kuma Fulani tayi suman zaune a wurin da take gaban ta nayin wata irin gigitacciyar faɗuwa, sabo da jin furucin Hadima Talatu da tayi na cewa Mai Martaba ya dawo, sabo da jiya kafun ya tafi ita da kanta ta tambaye sa sai kuma yaushe zai dawo, amma yace mata bai sani ba shima sai yadda hali yayi, sai dai kuma yana tinanin zai ɗauki tsawon sati biyu zuwa ukku kafun ya dawo ɗin, sai gashi kuma yanzu labarin isowar sa yazo kunnen ta. Zumbur ta miƙe tsaye daga kan kujerar da take jikin ta na rawa, yayin da ita kumavwannan hadimar tayi saurin ja da baya daga zaunen da take, sabo da a zaton ta tashi tayi ta make ta ne, duk da dai tasan hakan ba halin ta bane, amma sai taga ta kama hanyar waje cikin ɗimuwa, bakin ta na furta kalmar. "Innalillahi wa'inna ilahir raj..." Cak maganar ta tsaya daga cikin bakin ta tana mai ƙamewa wuri ɗaya, ƙirjin ta na cigaba da dukan tara-tara, sabo da yadda muryar mai martaba ta daki dodon kunnuwan ta yana mai doko sallama shima. Tukun daga bisani sai gashi nan ya danno kansa cikin falon. Kana sai ga Asad nan kuma ya tako masa baya sanye da ƙana nan kaya a jikin sa. Take a wurin Gimbiya Fulani ta fara zare idanuwa jikin ta na cigaba da kar-karwa, yayin da idanuwan ta kuma suka kasance ƙur akan fuskar Asad da tayi arba da shi tana kallon sa. Itama wannan Hadimar tare da su Babban Yaya da sauran ƴan uwan su gaba ɗayan su ƙamewa sukayi a wuri ɗaya suna kallon Asad cikin tsantsar mamaki, ba tare da an iya samun ɗaya daga cikin su ya matsa wurin da yake ba. Yayin da Mai Marataba dake riƙe da hannun Asad kuma yayi tsaye yana kallon Gimbiya Fulani, fuskar ɗauke da wani irin yalwataccen murmushi. Tukun daga bisani ya mayar da idanuwan sa kan fuskar Asad da yake ta faman naniƙe sa, tun lokacin da suka shigo Masarautar, domin kuwa sai da suka ƙaraso ɓangaren Gimbiya Fulani ne ma tukun ya ɗan ware. Fuska ɗauke da murmushi Mai Martaba ya buɗe baki yana mai faɗin. "To Baba na aje a gaida Mamy ko?" Ya ƙarasa maganar yana mai shafa kansa, tare da ɗan turasa gaba. Cikin sanyi Yarima Asad ya fara ɗaga ƙafafuwan sa yana mai tunkarar inda mamy'n tasu take. Ba zato ba tsammani sai jin sautin muryar Asad Gimbiya Fulani da gaba ki ɗaya sauran mutanen dake a cikin falon sukayi yana mai faɗin. "Ina yini Mamy na!" Tukun daga bisani ya faɗa jikin ta yana mai rungume ta. Da sauri itama ta durƙushe a ƙasa tana mai rungume sa ƙam-ƙam a cikin jikin ta, tukun daga bisani ta fashe da wani irin kukan farin ciki wanda batan da tawowar sa ba, sai futowar sa da taji kawai, tana mai faɗin. "Shin da gaske ne ba mafarkin dana saba yi bane nake yi kaine nake jin muryar ka Zaki na?" Ta ƙarasa maganar tana mai ɗago kansa ta kalle sa. Jin-jina mata kai yayi ba tare da yace komai ba. "A'a my Zaki ba da kai nake son ka amsa mun ba, bakin ka zaka buɗe ka sake yi mun magana, hakan shine zai sa na tabbatar da ba mafarki nake yi ba." Ta faɗa tana mai ɗan girgiza sa da hannuwan ta biyu. "Ba mafarki kike ba, Mamy na nine a gaban ki nake magana." Asad ya faɗa yana mai sake faɗawa jikin ta yayi wani irin lafewa. "Alhamdulillahi rabil alamin, Alhamdulillahi rabi samawati wal'ard." Gimbiya Fulani ta faɗa cikin tsantsar farin ciki mara misaltuwa. Yayin da su Baban Yaya da sauran ƴan uwan sa kuma suka saki wani irin ihun murna da matuƙar ƙarfi, suna masu tawowa zuwa wurin da suke aguje. Suna isowa gaba ɗayan su suka faɗa jikin Asad da Mamy'n tasu suna masu rungume juna ƙam-ƙam. Haka dai sukai ta farin ciki suna sanya Asad yana maganar da baya son yin ta ko kaɗan. Barin ma da suka iso cikin gidan, gaba ɗaya sai ya jisa a wani irin takure, ga kuma ƙirjin sa dake ta faɗuwa tunda suka doso Masarautar a mota, wannan dalilin shine ya sanya sa kasa sakewa ko da ƴan uwan nasa. Suna a cikin wannan yana yin na farin ciki sai ga Al'amin nan ya faɗo cikin falon aguje bako sallama a bakin sa. Da matuƙar sauri suka rungume juna shi da Asad suna masu sakarwa junan su murmushi. Tukun Al'amin ya buɗe baki cikin tsantsar murna yana mai cewa. "Yi mun maganar mana inji idan da gaske ne abun da jummai tazo ta faɗa." Al'amin ya faɗa yana mai shafa kan Asad. Yayin da shi kuma ya ɗaure fuska yana mai ture sa daga jikin sa, tare da faɗin. "Bazan yi ba ɗin, dallacan ɗaga ni daga zuwa na har zaka fara danne ni." Ya ƙarasa maganar da hararar Al'amin. Wani irin ihu Al'amin ya saki yana mai faɗin. "To jarabbaben banza ai kayi ma maganar baka sani ba, kuma wallahi bazan ɗaga kan ba." Ya ƙarasa maganar yana mai sake hayewa kansa. Yayin da shi kuma Mai Martaba ya juya yana mai fucewa daga cikin ɗakin cikin tsantsar farin ciki, sabo da ganin da yayi gaba ɗaya sun manta da shi ma. Kafun kece me tini labarin dawowar Asad yana magana ya baza ko na- na cikin Masarautar. Hakan kuwa ba ƙaramun daɗi yayiwa masoyan su ba, yayin da maƙiyan su kuma sukaji tamkar su cinnawa zuciyar su huta dan baƙin ciki. Abu fa kamar wasa na faɗuwar gaban da Asad yake ji, sai gashi yana shirin zamtowa Babba. Domin kuwa bayan Fulani tayi masa wanka yaci abinci sun shirya, sai ga saƙon Mai Martaba nan ya iso wurin sa, na cewar ya tawo faɗa suyi hira idan bai gaji ba. Ai kuwa take awurin Al'amin ya miƙe tsaye yana mai jan hannun sa tare da faɗin. "Taso muje kaji." Kasancewar a lokacin suna zaune ne babu abun da suke yi. Miƙewa Asad ɗin yayi yana mai bin bayan Al'amin suka fuce, sai dai kuma sun dosar hanyar fada yaji gaban sa yayi wata irin mahaukaciyar faɗuwa. Da ƙarfi ya rumtse idanuwan sa yana mai ɗaukar tafin hannun sa ya dafe ƙirjin sa da shi, tukun daga bisani ya cigaba da dɗaga ƙafafuwan sa cikin ƙarfin hali irin nasa suna masu dosar fadar. Adadin yadda yake ɗaga ƙafafuwan nasa yana cigaba da tunkarar Fada, haka adadin faɗuwar da gaban sa yake yi take ƙaruwa. Yayin da Al'amin kuma yake ta masa zuba yana basa labaran abubuwan da suka faru a lokacin da baya nan, ba tare da ya lura da halin da yake ciki ba, ahaka har suka ƙarasa bakin fada. Suna shiga cikin fadar Yarima Asad yaji kansa yayi wata irin mahaukaciyar sarawa, kana daga bisani kuma wata irin hajijiya ta fara ɗibar sa, tukun ya tafi luuu yana mai zubewa a ƙasa sumamme! Cikin tsantsar tashin hankali da firgici daga Mai Martaba har sauran mutanen da suke zaune a cikin fada suka taso suna masuyowa kansa. Yayin da Al'amin kuma ya fashe da wani irin gigitaccen kuka yana mai durƙusawa sa a ƙasa ya fara girgiza sa tare da kiran sunan sa. Da wani irin gudu Mai Martaba ya ƙaraso wurin yana mai h................✍ *BAƘAR MASARAUTA* *NA* UMAR FARUQ*D* *PAGE 21* Hankaɗe mutanen da suke tsaye a gaban sa, ya durƙusa ƙasa yana mai ɗaukar Asad ya ruƙunk'ume sa a jikin sa. Kana daga bisani ya buɗe baki cikin tsantsar tashin hankali, ruɗu had'i da firgici yana mai faɗin. "Baba na! Baba na!! Baba na!!! Asad! Asad!! Asad!!! Zaki! Zaki!! Zaki!!!" Ya dinga kiran sunayen da duk ake faɗa masa a matuƙar ruɗe yana mai girgiza sa. Kafin daga bisani kuma ya miƙe tsaye zumbur ɗauke da shi a hannun sa. Zagaye ya farayi da shi a cikin Fada'r yana mai girgza kansa, gaba ɗayan sa ya ruɗe ya rasa yadda zaiyi, tukun daga bisani kuma ya juya da sauri yana mai fucewa ya kama hanyar pary ɗin sa direct ɗauke da shi a hannun nasa. Yayin da Al'amin kuma ke biye da su a baya cikin tsantsar firgici shima yana kuka. Shimfiɗe sa Mai Martaba yayi akan haɗaɗɗen gadon sa, yana mai cigaba da girgiza sa tare da kiran sunan, kafin daga bisani kuma ya sake miƙewa zumbur yana mai matsawa gaban freezer dake kafe a cikin ɗakin. Buɗe ta yayi yana mai ɗauko ruwa mai sanyi a cikin jarka daga cikin ta, kana ya juyo da sauri yana mai dawowa wurin da Asad yake ya buɗe jarkar ruwan, yana mai fara tsiyaya masa shi akan fuskar sa. Wasu irin ƙarfa-fan ajiyar zuciya Asad ya fara saki da sauri da sauri, tukun daga bisani kuma ya buɗe idanuwan nasa duka akan fuskar Mai Martaba da yake tsaye a gaban sa. Da sauri Mai Martaba yayi cilli da jarkar ruwan da take riƙe a hannun sa a ƙasa, kana ya durƙuso zuwa kan gadon yana mai janyo Asad cikin jikin sa. Da wani irin ƙarfi Asad ya rungume sa jikin sa na rawa, tukun daga bisani ya buɗe baki cikin muryar tsoro yana mai faɗin. "Ina Mamy na Abba na, ni zan tafi wurin Mamy na, ni bana son wurin nan." Ya ƙarasa maganar yana mai shirin zame jikin sa daga cikin na Mai Martaba ya tafi. "Meke damun kane Baba na, me yasa ba zaka zauna anan wuri na ba?" Mai Martaba ya faɗa cikin rawar murya, yana mai sake rungume ɗan nasa da yake jin tamkar shi kaɗai ya haifa a duniya. Wani irin kuka Asad ya fashe da shi jikin sa na matuƙar karkarwa, tukun daga bisani ya fara ƙoƙarin ɓan-ɓare jikin sa daga cikin na Mai Martaba yana mai faɗin. "Abba na mutafi daga gidan nan, mu koma gidan Sheik yafi nan daɗi." Ya ƙarasa maganar yana mai funcike jikin sa daga na Mai Martaba. Yayin da Al'amin kuma keta aikin kuka yana mai riƙe da tafin hannun sa. Ganin hakan da Mai Martaba yayi ne ya sanya sa miƙewa tsaye shima yana mai sake riƙo ɗan nasa, tukun ya buɗe baki cikin sanyi yana mai faɗin. "To muje in kaika wurin Mamy'n taka Baba na." Kana suka juya suna masu kama hanyar da zata sadar dasu ɓarin Gimbiya Fulani, ta cikin wata ƙofa da suka bi da take anan cikin part ɗin su duka ukkun, har zuwa lokacin kuma jikin sa bai bar rawar da yake yi ba. Suna shirin shiga cikin falon sukaci karo da Gimbiya Fulani bako mayafi a jikin ta tana shirin futa cikin tsantsar firgici. Da sauri taja da baya ta tsaya, sabo da jin da tai kanta ya daki ƙirjin mutum, tukun daga bisani ta ɗago kan nata tana mai sauke idanuwan ta akan fuskar Mai Martaba, kafin daga bisani kuma ta sake yin ƙasa da kanta nata, idanuwan ta na dira akar fuskar ɗan nata. Da matuƙar sauri tayi wurin da yake tana mai durƙusawa a ƙasa ta janyo sa cikin jikin ta. Wani irin ƙan-ƙameta shima yayi da matuƙar ƙarfi, jikin sa na karkarwa. "Zaki na aka cemun baka da lafiya, ka sake sumewa a cikin Fada" "Mamy na mutafi-mutafi, ki mayar dani gidan ya Sheikh ni bana son gidan nan." Asad ya faɗa cikin tsantsar ruɗu yana mai fashewa da kuka, ba tare da ya bata amsar tambayar da tayi masa ba. Take kuwa a wurin hankalin su daga ita har Mai Martaba da Babban yaya da ya ƙaraso wurin yanzu yayi bala'in tashi. Da sauri Gimbiya Fulani ta cicciɓe sa a jikin ta tana mai miƙewa tsaye ɗauke da shi, tukun ta juya tana mai kama hanyar bedroom ɗin ta cikin tashin hankali. Rufa mafa baya su Mai Martaba sukayi suma, gaba ɗaya shi yanzu ma ya rikice ya rasa mai ya kamata yayi, domin kuwa gaba ɗaya kansa ya riga da ya gama kullewa da yanayin yadda yaga Asad ɗin ya koma yanzu. Shimfiɗe sa tayi akan gadon ta tana mai fara tofa masa addu'oi. Ƙarasowa su Mai Martaba sukayi ciki suma suna masu hayowa kan gadon, tukun dukan su suka haɗu suna masu karanto addu'oi suna tofa masa. Ba suyi minti biyar da fara addu'oin ba ya fara sauke wasu irin tagwayen ajiyar zuciya ajere-ajere, kana daga bisani kuma wani irin bacci ya fizge sa. A tare daga Gimbiya Fulani har mai martaba suka sauke nannauyar ajiyar zuciya, tukun suka juya suna masu kallon junan su cikin tsantsar aljabi da firgicin abun da ke faruwa. Zaune sukai a wurin gaba ɗayan su jugum-jugum ba mai tankawa wani, sai faman kallon Asad da suke ta ai'kin yi da idanuwa kawai. Acan cikin Masarautar kuwa tini labarin sake suman Asad ya baza ko ina da ina na cikin ta. Sosai kuwa abun yayi matuƙar ɗaurewa jama'a da dama kai, yayin da wasu kuma hakan yayi musu tsantsar daɗi, wasu kuwa gaba ɗaya suma sun firgita da lamarin ba kaɗan ba. Ko da dare yayi ma haka Asad ya farka yana surutai tare da zabure-zabure akan cewa dole sai ya koma wurin Sheikh Yaƙub, shi baizai ƙara zuwa fada ba baya sonta. Sosai hankalin su Mai Martaba ya sake matuƙar tashi, haka su kai ta aikin tofa masa addu'oi da shi da Gimbiya Fulani har su samu yayi bacci kafin ya sake farkwa, kai ataƙaice dai ranar kwanan zaune sukayi dukan su, har Babban Yaya da sauran ƴan uwansa masu girma, domin kuwa shi kansa Al'amin sai bacci ɓarawo ne ya sace sa anan cikin ɗakin Gimbiya Fulani, amma bai koma part ɗin su ba. Washe gari kuwa misalin ƙarfe ɗaya na rana, Abokin Mai Martaba kuma ɗan uwan sa mai suna Alhaji Abubakar ya duro cikin Masarautar Wasai, domin taya murnar samun lafiyar Asad da yaji labari jiya. Alhaji Abubakar nabban ɗan kasuwa ne wanda sunan sa yay shuhura aduniya, domin kuwa ataƙaice dai yanzu haka ma yana Dubai dukan sa da zama da shi da iyalan sa. Sun taso tare da Mai Martaba a matsayin aminai tun suna yara, kasancewar shima ɗin Asalin mahaifin sa ɗan nan cikin Masarautar Wasai ne. Yana shigowa gidan shima ya riski wannan rikicin da ake ta fama da shi na Asad, domin kuwa har kawo yanzu kuka yake yana cewa bazai zauna a cikin Masarautar ba. Shima ɗin shigowa falon Gimbiya Fulani yayi yana mai zama a kusa da kujerar da Mai Martaba yake zaune akai riƙe da Asad. Yayin da ita kuma Gimbiya Fulani take zaune a gefen Mai Martaba, gaba ɗaya idanuwan ta a kumbure, alamun ba ƙaramun kuka taci ba kenan. Ko da Alhaji Abubakar yaga abun Asad ɗin da gaske ne ba wasa ba, sai ya gyara zaman sa akan kujerar da yake yana mai yin gyaran murya. Sautin gyaran muryar sa da su Mai Martaba sukaji ne ya sanya su juyowa ɓarin da yake dukan su suna kallon sa. Fuskantar su shima ɗin yayi sosai, tukun ya buɗe baki cikin nutsuwa yana mai faɗin. "To ni a gani na Alhaji, tunda abun nan yazo da haka shi yaron yana ta faɗin bazai zauna ba, mai zai hana abani shi in tafi da shi can wuri na, in yaso sai ya cigaba da karatun sa acan kafin zuwa wani lokaci muga yarce hali zaiyi." Ya ƙarasa maganar yana mai binsu da idanuwa daga shi har Fulani. Yayin da su kuma gaba ɗayan su sukayi shiru ba tare da wani yace komai ba, tukun daga bisani Fulani tayi ƙarfin halin buɗe baki cikin sanyin murya, tana mai faɗin. "Tabbas hakan ma yayi, domin kuwa ni kaina tun ɗazu tunanin yadda zamuyi da shi nake, sabo da gashi nan daga jiyan da ya dawo zuwa yau har ya rame, dan haka ni na amince ku tafi tare muddin zai samu nutsuwa acan ɗin, in yaso daga baya sai muga yadda za'ayi." Ta ƙarasa maganar cikin sanyi tana mai jin ranta na ɗaci da ƙuna. Jin hakan data faɗa ne ya sanya Mai Martaba shima amicewa, amma bawai dan ransa yaso da hakan ba ko kaɗan, sai dai shima ɗin zai so yaga ɗan nasa ya samu nutsuwa bawai ya cigaba da rayuwa ahaka ba. Hakan ne yasa ya buɗe baki cikin sanyi yana mai faɗin. "Tom shikenan Allah yasa hakan shi yafi alkhairi, amma ni ina ganin idan kun tashi tafiyar sai ahaɗa har da Al'amin ku tafi tare duka, domin kuwa in bahakan akai ba shima bazai taɓa sakewa anan ɗin ba, duba da yadda ya koma alokacin da muke acan London sabo da rashin abokin nasa, kuma shima Asad ɗin zaifu samun sakewa acan ɗin idan suna tare." "To masha Allah hakan ma yayi sosai, Allah kuma ya ƙara masa lafiya." Cewar Alhaji Abubakar cikin sanyi shima. Haka dai ranar ma suka yini cir jugum-jugum sai sallah ce kawai ke tayar da su, domin kuwa ko Fada ma Mai Martaba bai leƙaba kwata-kwata, ahaka har dare ya riske su suna a hakan. Washe gari kuwa tun da sanyin safiya aka shirya Al'amin da Asad tas, misalin ƙarfe goma na safiya aka musu rakiya Airpot, kana ƙarfe shaɗaya na safe dai-dai jirgin su ya ɗaga zuwa ƙasar Dubai, ba tare da sun ɗauki ko da ƙyalle ba na sutura, sai waƴan da suke sanye a jikin su kawai. _Musababbin canzawar rayuwar Asad da Al'amin kenan._ _BAYAN SHUƊEWAR SHEKARU BAKWAI._ *KASAR MALIN JAHAR KARFUZ CIKIN BAƘAR MASARAUTA.*✍ *KUYI MANAGE BANDA CAJI NE YAU.* *BAƘAR MASARAUTA* *NA* UMAR FARUQ*D* *PAGE 22* Tafe Ƴar yarinyar take a cikin tsakiyar wasu garadan maza da suke riƙe da bulalai a hannun su, suna masu tunkarar wata kujera da take kafe a ƙarƙashin wata inuwar bishiya. Yayin da gefe da gefen bishiyar kuma wani irin farin ruwa kar yay mata ƙawanya. Sanye take da wata doguwar riga ruwan hanta mai matuƙar tsayi a jikin ta tana sharar ƙasa, yayin da kanta kuma yake ɗage a sama tana mai yin wani irin taku, babu alamun far'a a fuskar ta ko kaɗan, ƙafafuwan ta kuwa sanye suke da wani irin azababben takalmin fata, yayin da ƙaurikan ƙafafuwan ƙafar ta kuma suke sanye da wasu irin saraƙunan gwal, masu matuƙar ƙyalli da ɗaukar ido suna futar da sauti. Gimbiya Tasmir kanen, Yarinya mai kimanin shekatu bakwai a duniya cif-cif yanzu kenan, Yarinyar da ta-taso da tsantsar Izza, girman kai tare da miskilanci, domin kuwa ba taƙi ta kwana kana kuma ta yini ba ba tare da ta furta komai ba, haka kuma muddin ta biyo hanya to babu wani mahaluki da ya isa ya gifta wannan hanyar, idan aka cire mutanen da suke tare da ita tun a yanzu da take ƴar ƙaramar ta, idan kuma har akayi rashin sa'a mutum bai lura da tawowar ta ba har ta ƙaraso wurin da yake, to fah ranar ya shiga ukku ya lalace, domin kuwa Dakarun ta da suke take mata baya a kowane lokaci take sanyawa su zane masa jikin sa tas sa bulalai. Ko kaɗan bata da tausayi, kuma bata san-sa ba ma, kamar yadda ta taso taga ahalin gidan nasu suke. Ƴar gatace lamaba ɗaya a wurin mahaifin ta Sarki Barbaru, tare da kuma Yayen ta Maza. Duk abunda ta nuna tana so to komun wahalar sa sai an samo mata shi, haka kuma muddin tace bata son abu to fa bata son sa, kuma babu wanda ya isa ya sanya ta taso shi. Ci gaba da tafiya tayi kanta ɗage a sama, yayin da mayawaicin gashin dake ɗauke akan ta kuma yake ta reto a gadon bayan ta. Cak ta tsaya lokaci ɗaya a wurin da take ba tare da ta sake ɗaga ƙafar ta ba, ba wai kuma dan ta cimma wurin da take son zuwan bane, sai dan kawai motsin sautin tafiyar mutum da ta jiyo a cikin kunnuwan ta. A hankali ta fara sauke kanta daga saman da yake, tukun ta juyar da shi ɓarin hannun ta na hagu, tana mai kai idanuwan ta zuwa wurin da take jiyo sautin nan. Take kuwa idanuwan ta sukayi mata arba da matashiyar budurwar da take gudu amatuƙar firgice, tana neman wurin ɓuya, sanye take da kayan Bayi ajikin ta, da alama dai bata lura da tawowar tasu bane da wuri sai da har suka ƙaraso wurin da take, shi yasa ba tayi saurin ɓuya ba. Da sauri dakarun nan suka juya ɓarin da su kaga Gimbiya Tasmir ta kai idanuwan ta, domin kuwa sun sani bata waige idan har tana tafiya, sai idan taji sautin motsin wani abun ne. Take kuwa suma suka hango wannan baiwar da take ƙoƙarin ɓuya hankalin ta atsan-tsar tashe. Ɗaga hannu Gimbiya Tasmir tayi, tana mai yi musu nuni da ita ba tare da tace komai ba, tukun daga bisani ta sauke hannun nata ƙasa, tana mai cigaba da ɗaga ƙafafuwan ta tayi gaba, yayin da su kuma waƴan nan dakarun nata su kayi wurin da suka hangi baiwar nan gadan-gadan. Cikin sakwannin da basu gaza talatin ba duka suka cimmar wa wannan baiwar. Ɗaya daga cikin sune ya miƙa hannun sa zuwa wurin da take yana mai riƙo hannun ta da matuƙar ƙarfi, tukun ya funciko ta yana mai janyo ta ta faɗi a ƙasa, kana ya fara janta a cikin ƙasar yana mai juyawa ya doshi wurin da Gimbiya Tasmir take, suma sauran duka suka take masa baya. Ita kuwa Gimbiya Tasmir cigaba da tafiya tayi har ta ƙarasa ƙar-ƙashin inuwar bishiyar nan, inda wannan haɗaɗɗiyar kujerar take ajiye a kafe. Tsaye tayi a gaban kujerar tana kallon ruwan nan da yake zagaye da bishiyar, wata irin sassanyar iska mai matuƙar daɗi na dukan jikin ta. Kana ahankali ta juyawa kujerar baya, tukun daga bisani ta zauna akan ta tana mai ɗaukar ƙafar ta ɗaya ta ɗora ta akan ɗayar. Kana ta fara girgiza ta a hankali, tana mai lumshe dara-daran fararen idanuwan ta masu matuƙar kyau da ɗaukar hankali . Tukun daga bisani ta wara su akan wannan fuskar baiwar da aka janyo ta cikin ƙasa, jikin ta na wata irin kar-karwa. "Tuba nake ranki ya dade, tuba nake ki mun ai'kin gafara ya shugaba ta." Baiwar nan ta faɗa jikin ta na tsantsar kar-karwa, a lokacin da wannan badakaren ya durƙusar da ita a gaban Gimbiya Tasmir, Yarinyar da a haife ta haife ta. Shiru Gimbiya Tasmir tayi ba tare da tace komai ba, sai kawai fitinannun idanuwan ta da ta ɗora su akan fuskar baiwar nan tana mai jifan ta da wani irin kallon ƙasƙan ci, tukun daga bisani ta janye su daga kanta tana mai kai su wurin farin ruwan nan da yake kwance a cikin tafkeken rami. Kana daga bisani ta ɗaga yatsar hannun ta manuniya, tana mai nuna ruwan nan da ita ba tare da tace komai ba, sannan ta sauke hannun nata ƙasa tana mai sake mayar da idanuwan ta ta lumshe su. Yayin da shi kuma wannan badakaran ya sake cafkar hannun bawair nan da matuƙar ƙarfi, tukun ya cigaba da janta a cikin ƙasa yana mai nufar bakin ruwan nan da ita. Suna ƙarasawa wurin ya ya saki hannun baiwar yana mai damƙar gashin kanta ta da matuƙar ƙarfi, kana ya fara danna kanta a cikin ruwan, sai ya nutsa sa tas a ciki tukun yake zaro sa ya sake mayarwa, a haka har sai da yayi kimanin sau ukku, tukun daga bisani ya futar da ita yana mai yin cilli da ita gefe. Da sauri ta kife a ƙasa tana mai fara tafiya da rarrafe, ta doshi hanyar da zata ɓatar da ita daga wurin tana sakin wani irin tari, yayin da idanuwan ta kuma suka kaɗa sukai jajajir tamkar gauta, alamun ba ƙaramar wuya taci ba kenan, a tsomen da aka mata a cikin ruwan. A ɓangaren Bayi kuwa sosai Bir yayi matuƙar girma, kana ya fara zama saurayi, domin kuwa a yanzu yana da kimanin shekaru goma shabiyar ne a duniya. Kyakkyawa ne lamba ɗaya, dan ko ataƙaice ma shine ya zamto mafi kyawun mutum a cikin duka Bayin dake a cikin Baƙar Masarauta. Har kawo yau yana nan da maitar kwari da gwafar sa, domin kuwa akan ta baiƙi ya yini cir da yunwa ba, dan kuwa mafi akasarin lokuta ma idan ya futa da ita baya dawowa cin abinci, har sai Iyar Bayi ta bisa ta tattago sa. A yanzu haka bashi da wani buri wanda ya huce na haɗuwa da Gimbiya Tasmir domin ya ganta, sabo da tun da yake a cikin Masarautar har yau Allah baisa sun taɓa cin karo da itaba a hanya, kai asalima ganin sa da ita duka sai ya irgu, shima kuma yana faruwa ne aduk lokacin da ake wani taron biki a cikin Baƙar Masarauta, amma bayan wannan bai taɓa cin karo da ita ba, sai dai yaji labarin cewar yau ta huce ta wuri kaza a wurin su Mauzum, haka kuma zai ga sunzo jikin su na tsantsar kar-karwa, kana a kullum sai yaji bayi na labarin kwarjinin ta da rashin tausayin ta, wannan shine kawai dalilin daya sa yaji yana matuƙar son ya haɗu da ita wataran shima, domin ya gwada tsayuwa a gaban ta yaga mai zata masa, ko kuma shima zata masa kwarjini kamar yacce mutane suke faɗin tana musu, kasancewar sa mutun mara tsoro da shakkar kowa, domin kuwa babu wanda bai sansa da wannan halin ba a cikin bayi, kai harma da wasu daga cikin dakarun dake zaune a Baƙar Masarauta, sai dai kuma babu yadda zasuyi da shi, sabo da koda an dake sa ba ya fasa yin abun da yake yi, wato yiwa dakarun rashin kunya, gashi kuma gaba ɗayan su Sarki Barbaru ya shimfiɗa musu sharuɗa akan sa tare da gargaɗi, kana suma dukan su sun san tarihin samuwar sa a cikin masarautar. A kusan kullum sai ya ritsa Iyar Bayi yana mai tambayar ta su waye mahaifan sa, amma sai dai kuma aduk lokacin da ya taso mata da maganar sai yaga gaba ɗayan ta-ta rude ta fuce daga hayyacin ta, a ƙarshe ma sai dai ta-tashi ta basa wurin, ko kuma tai ta roƙon sa akan kar ya ƙara yi mata wanna batun, muddin ba gajiya yayi da ganin ta a duniya ba. To da zarar fa tace masa hakan sai ya haƙura ya tashi yay gaba, amma bawai dan ransa yaso ba, kuma hakan baya hanawa washe gari ya sake taran ta da maganar ma. *ƘASAR HAUSA, JAHAR KAGUL CIKIN MASARAUTAR FULƊE.* Tun bayan haihuwar Gimbiya Haddiyal Gimbiya Kaɓel mahaifiyar ta bata sake wata haihuwar ba, yayin da ita kuma Gimbiya Mairamu ta sake yin wata haihuwar amma ɗa namiji, wato har yanzu dai Gimbiya Haddiyal ce kawai ƴa mace a gidan. Yayin da take da Shekaru bakwai dai-dai a duniya yanzu kenan. Sosai take da wani irin kyawu mai matuƙar ɗaukar hankali tare kwarjini da Izza. Ko kaɗan magana bata dame ta, kamar yacce hayani kuma ke takura mata, domin kuwa hatta da yayyin ta maza idan suka haɗu wuri ɗaya suna hira takura take yi sosai, wannan dalilin ne yasan ya akoda yaushe take ware kanta ta tafi can lambun da jinsin tsun-tsayen masarautar Fulɗe suke rayuwa a cikin sa. Yayin da wurin kuma yafi mata daɗi sama da kowane wuri dake a cikin gidan nasu, hatta da ɗakin ta kuwa, domin kuwa ba ƙaramun birge ta tsun-tsayen suke ba, haka ako da yaushe zata tafi cikin su tun tana da shekara huɗu aduniya ta zaune tana watsa musu gero, kana kuma tai ta kawo labarai tana basu ba tare da tana da tabbacin suna jin abun da take faɗen ba, domin kuwa muddin kana son jin sautin muryar ta to da zarar kazo wurin tsun-tsayen har dai ta kasance itama a wurin, to zakaji hirarar ta har ka gaji, yayin da acikin gida kuma take tamkar kurma a koda yaushe. Ada idan taje wurin tsun-tsayen tun daga nesa suna jin motsin ta gaba ɗayan su suke tashi su gudu, amma a haka zata ƙarasa zuwa mazaunin ta wanda ta saba zama akai, ta zauna ɗauke da ƙwaryar hatsi a hannun ta. Kana ta fara ciko tafin hannun ta tana wats musu shi. Ai kuwa haka gaba ɗaya zakaga sun sauko ahankali-ahankali suna tsintar geron, yayin da ita kuma zata tai kallon su tana sakin mirmushi, tare da lumshe idanuwa. Haka kullum take yi musu ba safiya ba rana, tun tsuntsayen suna guduwa idan tazo wurin, har ya zamto anzo lokacin da suka dena gudun ta gaba ɗaya, wato sun gane ba mai cutarwa bace gare su ita ɗin, domin kuwa gaba ɗaya dawowa sukai suna hangen ta zasu yo wurin da take a guje, kamar yadda dama can kaji da agwagi suka yi saurin sabawa da ita, kuma suke tawowa wurin ta a duk lokacin da taje wurin su, domin kuwa tsun-tsayen da suke a cikin masarautar Fulɗe sun kasance kaloli daban-daban ne, haka kuma babu wata kalar tsuntsuwa da kusan za'ace basu da ita. A duk lokacin da tsuntsayen nan zasuga ta shigo wurin, to haka zasu tawo aguje suna masu yowa kanta ko wanne na sakin nasa kalar kukan, yayin da ita kuma zatai ta ɓaɓɓaka dariya tana mai shafa su tare da shawagi a cikin wurin, cikin tsantsar farin ciki da annashuwa, tukun a ƙarshe kuma ta koma kan shimfiɗar ta-ta zauna, kana suma duka su biyo ta suna masu sauka a gefen shimfiɗar, sannan ta fara ciko tafukan hannyen ta da gero tana watsa musu, tana yi tana basu labarai tare da dariya cikin tsantsar farin ciki. Yayin da shi kuma malam buɗa mana littafi ya zamto abu na farko data fiso sama da komai arayuwar ta idan aka cire ahalin ta, domin kuwa shi yana ɗaya daga cikin abubuwan da suka zamto mahaɗi na tsafin da yake ɗauke a jikin ta, wato muddin tana buƙatar yin wani abun, to da zarar ta buga sandar tsafin ta, ko kuma taje wurin da ciyayi suke ta buge su, zakaga sun taso da yawan su masu tsanin kyau suna hawa kan tafukan hannyen ta, kana kuma idan har tana son su nuna mata wani abun, to da zarar ta faɗa musu buƙar ta zasu tashi su kaita har wurin da abun yake, sannan kuma zata iya cutar da mutum da su muddin taso yin hakan, sai dai kuma ita ɗin ta kasance babu ruwan ta ko kaɗan, domin kuwa ko bayin gidan su ba ƙaramun jin daɗin ta suke yi ba, kana kuma bata damu da sai an mata rakiya ba dan zataje wani wurin, asalima ita tafison tayi tafiyar ta ita kaɗai, sabo da a ganin ta duk ƙarin hayaniya ne dogarawan zasu sanya mata ba wai tsaro zasu bata ba. Wannan dalilin ne ya sanya ko lambu idan zata tafi take tafiyar ta ita kaɗai ba tare da ta bari sun biyo ta ba. Babu yadda ba ayi ba da Lamiɗo akan ya bari akai ta Makarantar Boko dake ac ikin Jahar Wasai ta kwana, wacce aka yita domin ƴaƴan sarakai da kuma ƴaƴan attajirai kawai, amma gaba ɗaya ya yaƙi amicewa, a cewar sa ba zai taɓa barin ta tayi nisa da shi ba amatsayin ta na ɗiyar sa ƴa mace ƙwalli ɗaya ƙwal da yake da ita a duniya, domin kuwa shi afannin sa har yau baiga wani amfani da karatun bokon yake da shi ba, suma kuma su Buba ya yadda an kaisu ne sabo da babu yadda zaiyi, gwamnati ce tace dole sai ya bayar, amma banda haka da ba zai bada su ba. Haka dai akai ta takura masa da naci akan ya kaita amma yaƙi, domin kuwa shi ko karatun addini ma ba damun sa yayi ba balle kuma suce dole sai anyi na bokon, a ƙarshe dai da ƙyar aka samu aka shawo kansa ya bari aka kaita wata makarantar boko da take anan cikin Jahar Kagul, itama ɗin dai ta ƴaƴan masu kuɗin ce, sai dai kuma ya bari ne itama sabo da ance masa bata kwana bace ba, kullum yaro yake zuwa ya koma gida, hakan ne yasa ya tanadi lafiyayyan doki ma tsanin girma da kyawu ya bayar ake kaita akan sa, sannan ajira har a tashi, tukun a ɗakko ta a dawo da ita gida, yayin da masarrafin dokin kuma yake sarrafasa da hannu ɗaya, hannun sa ɗayan kuma yake zamtowa riƙe da lemar da take kare ta daga zafin rana, a haka zasuyi ta tafiya a hankali har sukai makarantar kullum. Yanzu haka zaune take a gefen wani farin ruwa mai tsanin haske, ta zura ƙafafuwan ta biyu a ciki tana ta faman wawwantsala ruwan da su, yayin da gefe da gefen ruwan kuma ya kasance zagaye da wasu irin korayen ciyayi da furanni masu matuƙar kyau da ƙamshi, da suka yiwa ruwan ƙawan ya. Sanye take da fararen kaya irin na fulani da sukayi matuƙar yi mata kyau da amsar jikin ta, yadda kasan dan ita kawai aka ƙir-ƙire su, yayin da gashin kanta kuma ya kasance tufke a wuri ɗaya yana ta faman ƙyalli da ɗaukar ido. Gaba ɗaya gefe da gefen ta tsuntsaye ne a wurin dukan su a diddirƙushe suna kallon ta, yayin da ita kuma take wani irin lumshe idanuwan ta tana mai buɗe su, wani irin farin ciki mara misaltuwa na cigaba da gauraye ilahirin jiki da zuciyar ta, sabo da tino sautin daddaɗar busar sarewar da tayi mafarkin ta adaren jiya mai matuƙar zaki da take mata amsa kuwwa acikin kunnen ta. Tun da take bata taɓa yin irin mafarkin da tayi jiya ba, hakan ne yasa ya mata arai har kawo yanzu ba tare da ya ɓace ba, kuma ba komai bane ya faru a cikin mafarkin nata sai wani irin saurtin daddaɗar busar sarewa, mai matuƙar zaƙi da ta dinga ji yana dukan dodon kunnen ta, yayin da tai ta faman laluben wurin da sautin yake futowa a cikin mafarkin amma bata gano sa ba har zuwa lokacin data farka daga baccin. Shine fa yau tun da safe ana gama shiryata ta tawo wurin tsuntsayen ta tana mai basu labarin zaƙin busar da taji ɗin, wacce ta rasa gano ta inda take futowa, sai dai kuma ko yauma tana fatan ta sake mai-mata irin mafarkin nata na jiya. *JAHAR WASAI CIKIN MASARAUTAR WASAI.* Tun bayan tafiyar su Asad da ƴan kwanaki sai hankalin Gimbiya Fulani ya kwanta sosai, sabo da labarin da sukaji na cewar tunda suka bar cikin Masarautar Wasai bai kuma koda firgita ba balle suma. Hakan ne yasa daga ita har mai martaba sukayi matuƙar jin daɗi, sanan kuma hankulan su ya kwanta, domin kuwa ita Gimbiya Fulani dama damuwar ta tafi ƙarfi ne akan Asad, sabo da shi akafi sanyawa ido fiye da Babban yaya, sannan kuma shine mai wasa da azkar. Tun da suka tafi basu zo ƙasar ba sai bayan cikar su shekara guda da barin ta. Sai dai kuma sunzo ne da sabon salo tare da sabuwar al'ada cikin masarautar, domin kuwa ba ƙaramun rikicewa Gimbiya Fulani ta sake yiba alokacin da taga yadda Asad ɗin nata ya koma. Gaba ɗayan sa ya canza ya koma wani irin miskili, ga wata irin sabuwar al'ada da suka ɗaukko acan garin ta sanya ƙananan kaya, gwanda-gwanda Al'amin ma da yazo yasa manyan kaya akan Asad, domin kuwa shi gaba ɗaya nunawa yayi bama zai iya sa su ba, sannan kuma gaba ɗaya tunda sukazo ɗin bai kalli ko hanyar fada ba, Asalima da Gimbiya Fulani tace suje su gaida mutanne fada nuna mata yayi shi bazai iya zuwa ba, sabo da yana zuwa zasu fara yi masa magana da ƙarfi a cikin kunne, haka tanaji tana gani yaƙi zuwa sai Al'amin ne kawai yaje. Shi kansa Mai Martaba babu yadda baiyi ba da Asad akan yaje Fada, amma ya ƙeƙyashe idanuwan sa yaƙi, domin kuwa shi kansa sai zamtowa yayi idan yana son ganin sa sai dai yazo nan part ɗin Gimbiya Fulani ɗakin sa ya gansa, ko kuma shi Asad ɗin ya yaje part ɗin mai martaba, amma ba dai cikin fada ba. Hankalin mai martaba bai sake tashi ba sai alokacin da ya kawowa Asad sababbun ɗinkunan da yayi musu tare, na wata haɗaɗɗiyar shadda ɗinkin riga da wando tare da malum-malum yace masa ya sanya su ranar wata juma'a. Take a wurin kuwa Asad ya fara bin kayan da wani irin mugun kallo, tukun aƙarshe ya juyar da kansa gefe yana mai buɗar baki yace. A gaskiya ni Abba bazan iya sa waƴan nan manyan kayan ba, haba dai, sai kace wani ɗan ƙauye, kuma mai ai idan nasa waƴan nan zafi ma kusa kashe ni zaiyi." Ya ƙarasa maganar da juyar da kai gefe yana mai ture kayan daga kusa da shi. Sakin baki Mai Martaba yayi yana kallon sa ba tare da ya iya cewa komai ba, tukun daga ƙarshe ya durƙusa a gaban sa yana mai dafa kafaɗun sa ya fara lallaɓa sa dan yasa kayan, amma ƙiri-ƙiri Asad ya nuna shifa bazai iya sasu ba, haka Mai Martaba yana ji yana gani dole ya haƙura ya barsa yasa ƙananan kayan sa. Wata ɗaya cir sukayi a garin, tukun suka juya ƙasar Dubai, kasancewar dama hutun makaranta ne suka yi shiyasa har sukazo ɗin ma. Haka dai abu yay ta tafiya duk zuwan da Asad zaiyi garin baya tabɓa sanya manyan kaya, sannan kuma baya wani shiga cikin mutane, Asalima ko da sunzo lokacin hawa to in'da ake hawan ma baya zuwa, balle har yace zaiyi sa kamar yadda yake maitar sa abaya, kai ataƙaice ma dai idan Al'amin yace masa yazo suje, haka yake cewa Allah ya kiyaye shi da ba bagidaje ba yaje wurin can, duka uwar me ma ake yi a wurin bayan harkar ƙauyanci da iface-iface. A cikin duka abubuwan da ake gudanarwa acikin masarautar abu ɗaya ne kacal bai barsa ba, wato Doki, domin kuwa har yau idan yazo sai ya hau dokunan sa, kamar yadda yake da su acan ma gidan su na Dubai da Alahaji Abubakar ya siya musu su duka, sabo da masifar son sa da yake yi. A ɓangaren Babban yaya sosai shima ya girma ya zama saurayi, domin kuwa ayanzu yana da kimanin shekaru Ashirin da biyar ne aduniya. Yayin da afannin karatun sa kuma yake a matakin masters, kasancewar duka karatun nasa aƙasar turai yayi sa ne shiyasa yay masa matuƙar sauri. A ɓangaren magautan Gimbiya Fulani su kuma sosai sukai farin ciki da yadda Asad ya dawo, domin kuwa sun riga da sun sani muddin ya ɗore a wannan halayyar da yake ta yanzu, to har Abada babu shi babu zama akan karagar kujerar sarki, hakan ko shine yasanya hankulan su sukayi matuƙar kwanciya ta fannin Asad, kana suka koma suka duƙufa akan Babban Yaya da kullum kuma suke abun baya cin sa. Sai dai kuma suna ganin ayanzu an kusa azo lokacin da shima zai cisa, tun da yanzu sun riga da sun gama da babin Yarima Asad, to ko mai da zasuyi akan sa ne shi kaɗai yanzu, domin kuwa su dama burin su karsuyi mulki, kuma sun san Asad ayanzu yayi hannun riga da mulki har abada, tun da aikin su yaci akan sa. *UNGUWAR ƊAN TAKI* Abubuwa da yawa sun fara tun da ga kan marasa daɗi har zuwa kishiyar su, waƴan da cikin su kuwa suka haɗa har da mutuwar mahaifin Ishaƙ da yayi tsawon shekara guda yanzu kenan, da kuma auren Babbar ƴar Aishatu da Ishaƙ da akayi, wato mai bin Ahmad da yanzu kowa ya koma kiran sa da Sheik Ahmad a cikin unguwar su tasu harma da wajen ta, kasancewar sa na Babban matashin malami da ake ji da shi acikin unguwar, domun kuwa yanzu haka yana riƙe da har makarantun islamiyya biyu anan cikin unguwar tasu, yayin da yake koyar da manyan iyaye maza kuma aduk bayan sallar asubahin duniya. A yanzu haka yana da shekaru Ashirin da biyar ne cif aduniya, amma idan mutum ya gansa muddin ba sanin adadin shekarun nasa yayi ba zai ɗauka ya kai irin ashirin da takwas ɗin nan ne, sabo da yadda yake da tsan-tsar nutsuwa, haiba tare da kamala tattare da shi, waƴan da kuma duk sun samu ne ta dalilin ilimin addinin da yake ɗauke da shi acikin kansa, kana kuma yake amfani da shi ako da yaushe. Yayin da a karatun sa na boko kuma yake amatakin level 4 na jami'ar gwamnantin tarayya da take a nan cikin garin wasai. Wato Federal University Wasai, inda ya fara karantar Islami study acikin ta, kafin daga bisani kuna ya koma Qur'anic Hadith, alokacin da yaje lavel 3. Sosai yake da matuƙar ƙwazo fiye da duk sauran ɗaliban da suke a department ɗin nasu, domin kuwa akowane lokaci idan har aka kafe musu exarm makin sa yana fin na duk sauran ɗaliban, wato dai shine over roller na department ɗin nasu gaba ɗaya, wanda hakan kuma yasanya malamai da dama daga cikin malaman su suke bala'in ji da shi. A ɓangaren Aishatu kuwa har kawo yau bata bar tinane-tinane ba tare da zaman cikin ɗaki, domin kuwa ko da tayi kamar zata dena da zarar ta kwanta bacci idan tayi mafatkin yaron nan da ta saba yi, wanda take ganin sa akullum yana ƙara girma, sai taji komai na dawo mata sabo, kana kuma har yau bata futar da tsammanin sake saduwa da ɗan na ta, da ta rabu da shi tun a wurin da ta haife sa, kamar yadda akullum zuciyar ta take bata cewar yana nan araye ba akashe sa ba shi. A fannin kaka kuwa yanzu ta koma masifaffiya lamba ɗaya, domin kuwa a kullum sai tayi faɗa da jikokan nata musamman ma Sheikh Ahmad, kuma ba komai ne yake haɗasu ba sai tsohuwar da yaran suke ce mata, yayin da ita kuma ta tsani a kirata da tsohuwa, duk da ita da kanta tasan tsufan yazo mata. *DUBAI* Tun bayan komawar Asad da Al'amin ƙasar Dubai gaba ɗaya komai nasu ya sauya, domin kuwa ko ɗaki da aka tashi basu ko wanne guda ɗaya tafkeke aka basa, kamar yadda sauran yaran gidan suka kasance kowa acikin nasa ɗakin. Yayin da aka zube musu ruwan kuɗi kuma suke duk yadda ransu yake so da su, ba tare da kwaba ko hantara ba. Kwanan su biyu kacal da zuwa Alhaji abubakar ya ɗauke su ya kai su wata makarantar miliyoyin kuɗi da kansa. Inda anan ɗin kuma suka haɗu da yaran manya irin su, kama daga kan larabawa har zuwa baƙar fata irin su. Satin su ɗaya da fara zuwa sukayi wasu abokai a cikin class ɗin nasu ƴaƴan larabawa, irin waƴan da babu kwaɓa tattare da su ko kaɗan, duk da kasancewar su musulmai kuwa, wato Suhaib da Safuwan. Akullum abun da suke so shi suke samu acikin gidan, haka kuma babu wani mai kwaɓar su da sunyi abun da bai kamata ba, kamar yadda sauran yaran gidan suka kasance, kasancewar su Alhaji Abubakar suna irin rayuwar nan ce wacce turawa da wasu daga cikin larabawa sukeyi agidajen su, wato babu kwaɓa kowa yayi harkar gaban sa. Wannan saken da su Yarima Asad suka samu shine ya sanya akullum suke abun da ransu yake so, ga yawon bala'i daga yau suje wancan park ɗin gobe kuma sai su tafi wancan joint ɗin, ta hanyar abokan su guda biyu da suke biye musu amotacin gidan su su tafi. A yanzu haka daga Yarima Asad har Al'amin ko wanne yana da motar sa ta hawa, mai tsananin kyau da tsada da Alhaji Abubakar ya mallka musu su alokaci guda, tare da ɗan sa mai suna Huzaifah, wanda yake sa'an su shima. Zaune suke akan wasu haɗaɗɗun kujerun silver, masu azabar kyau da suke a cikin wani haɗaɗɗen joint su duka biyar ɗin. Wato Yarima Asad, Al'amin, Huzaifah, Suhaib, da kuma Safwan. Yayin da ga gaban kujerun kuma wani irin tafkeken swimming pool yake. Sosai wurin yake da bala'in kyau da girma, domin kuwa tsayawa faɗin yadda tsaruwa wurin yake kawai ɓata lokaci ne. Ƴammata ne da Samari suke ta giftawa ta ko ina, ko wanne da kalar shigar da take sanye a jikin sa. Yayin da daga cikin swimming pool ɗin nan kuma wasu fararen Ƴammata masu matuƙar kyau suka kasance acikin sa, daga su sai ɗan guntun wando tare da brezia ajikin su, yayin da wasu daga cikin su kuma ya zamto pant ne ajikin nasu ma ba gajeren wando ba. Kusan dukan su tare suke da samarin su acikin ruwan, suna abun da ransu yake so. Yayin da gang ɗin su Asad kuma da dukan su ba zasu haure shekara goma shabiyar ba, suka kasance zaune akan waƴannan haɗaɗɗun kejerun da suka yiwa swimming fool ɗin ƙawanya suna musu hira. Shi kuwa Asad kansa durƙushe yake aƙasa, idanuwan sa akan ƴar wayar sa da aka siya musu ita kwanan-nan, yana aikin latsa ta. Wasu irin haɗaɗɗun Ƴammata ne da suke sanye da ƙananan kaya, da suka futar da siffar jikin su tas su biyu suka zo wuce ta gaban kujerun da su Asad suke zaune akai cikin tsantsar yauki. Take kuwa a wurin idanuwan su gaba ɗaya suka koma kan Ƴammatan nan, banda Asad kawai da kansa yake durƙushe aƙasa yana aikin latsar wayar sa. "Wow!" Safuwan ya faɗa yana mai janye idanuwan sa daga kan Ƴammatan nan ya juya ɓarin da Asad yake. Kana ya buɗe baki cikin zaƙuwa yana mai faɗin. "Hay Prince! Please look at that fine girls." Ya ƙarasa maganar yana mai taɓo Asad ɗin, tukun ya juya yana mai mayar da idanuwan sa kan Ƴammatan nan da suke cigaba da tafiya, kamar yadda su Al'amin ma duk suke kallon sa. Yayin da Asad kuma ya janye idanuwan sa daga kan wayar da yake aikin latsawa, tukun ya fara ɗago kansa ahankali yana mai kai idanuwan sa zuwa wurin da Safwan ya nuna masa. Kallo ɗaya yayiwa Ƴammatan ya janye idanuwan sa daga wurin, yana mai mayar da su kan su Safwan gaba ɗayan su. Kana daga bisani ya buɗe baki cikin muryar sa, wadda yake magana da ita tamkar an masa dole, yana mai faɗin. "Haba dai guys, ku yanzu dan Allah ina abun kallo yake ajikin waƴan nan da duk kukabi kuka zuba musu idanuwa haka, salon kawai ku zubar mana da mutunci." Ya ƙarasa maganar yana mai taɓe baki, kana ya mayar da idanuwan sa kan wayar sa. Da sauri gaba ɗayan su suka zuba masa idanuwa baki a sake, sabo da jin furucin sa da sukayi akan Ƴammatan da duk kyawun mutum yayi kaɗan ya kira su da munana, tukun daga bisani Huzaifah ya buɗe baki cikin tsantsar mamakin halin Asad yana mai faɗin. "Haba guy, anya kuwa kagan su sosai, da har zakace basu kai a kalle su ba." Sake ɗago kai Asad yayi yana mai zuba mayatattun idanuwan su akan su, kamar yadda suma ɗin suke kallon sa, kana daga bisani ya janye su ahankali daga kansu yana mai mayar da su kan hanyar da matan nan suke tafiya, tukun ya sake ɗauke idanuwan sa daga wurin su, yana mai sake watsa su akan abokan nasa, sannan ya buɗe baki yana mai faɗin. "Uhm! Ku kalle su da kyau guys, both of them are bicths fa." Ya ƙarasa maganar yana mai juyar da kai gefe ya tofar da yawu, tukun ya sake mayar da idanuwan sa kan wayar sa. Yayin da Al'amin kuma ya buɗe baki cikin sauri yana mai faɗin. "Kai Asad, wallahi koda suke bitch ƙaryar mutum yace dai basuyi ba, kuma-ma mu dai sun birge mu." Da sauri Asad ya ɗago kansa daga kan wayar da take ahannun sa, sabo da jin furucin da Al'amin yayi yana mai watsa masa wani matsiyacin kallo, tukun daga bisani ya ɗaga laɓɓan sa cikin kausassar murya, yana mai faɗin. "Bu...............✍ *BAK'AR MASARAUTA* *NA* UMAR FARUQ*D* *PAGE 23* "But you know ko da iskancin zanyi nafi ƙarfin na kula bitch ko, ƙazama sauran wani, tirr Allah ya kiyaye." Ya ƙarasa maganar yana mai sake jifan su da wani ɗan iskan kallo, tukun daga bisani ya miƙe tsaye yana mai ɗaukar key'n motar sa ya dumfari parking space. Binsa sukayi da idanuwa gaba ɗayan su ba tare da wani ya iya furta komai ba. Yayin da shi kuma ya shige cikin motar sa yana mai bata huta yayi gaba, ko inda suke bai ƙara kallowa ba. "A gaskiya Prince ɗan iskan gaye ne, ku duba fah ku gani tsabar rainin hankali muzo wuri tare, amma ya tashi yayi tafiyar sa shi kaɗai." Cewar Suhaib yana mai kallon su Al'amin. Yayin da shi kuma Huzaifa ya buɗe baki yana mai faɗin. "Kaɗan daga cikin rashin mutuncin Asad kenan, kuma fa wai shi fa nan yana nufin yaji ne haushi an haɗa sa da bitch, bayan kuma akullum su ɗin yake kallo yana jin daɗi." "Kai guys wallahi ba gida Asad ya tafi ba yanzu, ko kuwa kun manta da yaune birthday ɗin Taslim." Al'amin ya faɗa yana mai kallon abokan nasu, fuskar sa ɗauke da murmushi. Yayin da Safuwan kuma ya buɗe baki cikin tsantsar mamaki yana mai faɗin. "Amma gaskiya kuwa idan haka ne Prince ya raina mana hankali, shegen kullum yay ta nunawa baya son ta, yana faɗin Allah ya kiyaye yaso wata yarinya a cikin class, to yanzu uban mene zai kaisa wurin ta." "Hhhhhh! Lallai ne guy's, wato wai ku haryau baku gane halayyar Prince bane ba ko, to bari kuji in faɗa muku, shi fa ya yadda aso-sa, amma shi ɗin ne dai bazai ce yana so ba, sabo da yana ganin hakanin tamkar zubar da mutuncin sa ne, sannan kuma ya yadda da yayi abota da yarinya, muddin ta kasance kyakkyawa kuma mai tsafta, kana ƴar gayu, dan haka Taslim ma ita take son sa bashi yake sonta ba." Huzaifah ya faɗa yana murmushi. "To kuma uban mene zai kasa wurin taron ta idan haka ne?" Cewar Suhaib yana kallon huzaifah. "Haba dai guy, ya keke irin wannan batun ne tamkar wani villager, kai da kanka kasani ko ba soyayya ai zai rage zafi a wurin." Safuwan ya faɗa yana mai ɗan kashe masa ido ɗaya. Gaba ɗayan su yara ne ɗanyu shakaf, amma sai dai kuma idanuwan su sun riga da sun gama buɗewa da iskanci, ta yadda har suke yiwa kansu kallon cikakkun samari. Ayanzu haka suna ss 1 ne anan makarantar su wacce sukeyi, yayin da Alhaji Abubakar kuma yayi musu Al'ƙawarin kaisu Oxford University Ingla suyi degree ɗin su acan. "Any way, ku tashi kawai mubi bayan ɗan iska, domin muga abun da zai ai'kata da idanuwan mu, ta yadda koda yazo yana cika mana baki zamu samu abun faɗe." Al'amin ya faɗa yana mai miƙewa tsaye. Kana gaba ɗayan su suma suka miƙe tsayen suna masu tunkarar wurin da suka ajiye motocin su. *BAYAN SHUƊEWAR WASU SHEKARU.* Abubuwa da yawa sun faru acikin shekarun da suka gabata waƴan da baki bazai iya furta adadin yawan su ba. Yayin da su Asad kuma suka zama cikakkun samari masu kimanin shekaru Ashirin da takwas zuwa da tara aduniya. Ayanzu haka suna karatun master's degree ɗin su ne a Oxfort University dake Engila, kamar yadda sukayi degree ɗin acan ma. Har kawo yanzu suna nan da hallayar su wacce suka taso da ita, koma ace fiye da waccen ta baya, domin kuwa a yanzu haka har neman matan banza dukan su sunayi, sai dai shi kuma Asad har yau bai taɓa yin zinaba, saɓanin su Al'amin da suka mayar da ita ba komai ba. Shima ɗin kuma bawai yaƙi ta bane sabo da gudun saɓon Allah, a'a kawai dai bai yarda da yin bane, sabo da kallon abun da yake amatsayin ƙazanta, wato ƙyanƙyamin sa da yake mahaukacin yi, abun da kawai ya yadda da shi shine romancing, shima kuma bada ko wace yarinya ba, sai wacca yasan bata mu'amala da wani namijin bayan shi, to fah a wannan fagen ne yayi mugun ƙwarewa, domin kuwa shi ta wannan hanyar yake biyawa kansa buƙatar sa aduk lokacin da yaji ta taso masa, yayin da Ƴammata da dama kuma suke hauka akan sa, tunda ga kan turawa, larabawa, har zuwa hausawa irin sa ƴaƴan attajirai da suke karatu a school ɗin tasu, sai dai kuma shi a wurin sa ko kallo basu ishesa ba, asalima babu wadda tafi cin wuya a wurin sa face wacce zata nuna tana son sa, sabo da ya faɗa ya kuma faɗa har yau ba a haifi yarinyar da takai matsayin ya so ta a cikin zuciyar sa ba, balle kuma har yayi mararin auren ta. Ansha raba Ƴammata faɗa akan sa ba sau ɗaya ba-ba kuma sau biyu a cikin school ɗin tasu. Jin sa yake tamkar yafi kowa aduniya, sabo da azababben kyawun da yaje taƙama da shi, wanda ko su larabawan baza su nuna masa shi ba, ga kuma Uwa Uba giyar ruwan kuɗin da take ɗibar sa, domin kuwa ba ƙaramun kuɗi Alhaji Abubakar da Mai Martaba suke sakar masa ba, kana suma zuwa yanzu duk suna da sanao'in su, yayin da Asad yake da super market's da dama acikin ƙasar Dubai, da kuma cikin ƙasar sa ta haihuwa, wato Ƙasar Hausa, ga kuma wuraren shaƙatawa da yake da su suma, kuma gaba ɗayan su yana sa musu suna Asadullahi ne, kamar irin su Asadullah Palace, da ya gina sa acikin Ƙasar Hausa a Jahar su da wasu Jahohin da suke a cikin ƙasar, da kuma Asadullah Boutique, da shima yake da shi acikin Dubai da Kuma cikin ƙasar hausa, kana ga Asadullah Shoping Mall dukan su a wurare daban-daban. Uwa uba kuma ga jinin Saurata da yake gudanya acikin jinin sa, wanda ta sanadin sa ne kuma ako da yaushe yake ƙara jinsa asama fiye da kowa, domin kuwa ako ina baya ɓoye shi ɗin ko wane ne, duk da dai ayanzu haka babu abun da ya tsana sama da al'adun gidan su, amma sai dai kuma yana jin daɗin a kirasa da Prince ako da yaushe, domin kuwa hakan ba ƙaramun fasa masa kai yake yi ba. Tun lokacin da suka gama Degree ɗin su na farko basu ƙara komawa Dubai da zama ba duka, kamar yadda suke acan ɗin da, sai dai suje ta da ziyara, wato dai yanzu sun koma ƙasar sune, wanda hakan kuma aikin mai martaba ne da Gimbiya Fulani, ba dan komai ba kuwa suka dawo dasu nan ɗin, sai sabo da yadda sukaga gaba ɗaya rayuwar su ta sauya, duk babu wata sauran tarbiyya tattare da su, hakan yasa suka zauna suka tattauna da Alhaji Abubakar, sannan aƙarshe aka gyara musu ɗakunan su na nan, aranar da sukayi graduation Mai Martaba da yazo suka juya tare da su, da kuma Alhaji Abubakar da yayi musu rakiya. A fannin su suma ba siji wani rashin daɗi ba da komowar tasu gidan su, sabo da sun riga da sun san sun dafa ƙasa a yanzu, ko wace ƙasa sukai niyar zuwa zasu tafi aduk lokacin da suka gadama, kana kuma idan duk sati sukayi niyyar zuwa Dubai ɗin to fah zasu je, ba tare da sun cewa wani ya ɗau wani abun ya basu ba. Yanzu hakama cigaban karatu ne ya sake dawo dasu Engila. Zaune yake akan ɗaya daga cikin kujerun da suka yiwa haɗaɗɗen swimming pool ɗin dake wurin ƙawanya. Sanye yake da wani ɗan guntun wandon jeans da tsayin sa ya tsaya masa a iyakar kan guiwoyin sa, yayin da rigar dake sanye ajikin sa kuma ta kasance mara hannu, ta yadda har ake ganin fareren damtsen hannayen sa afili. Sosai baƙar lallausar sumar dake ɗauke a kansa, tare da sajen dake zagaye a fuskar sa suke futar da wani irin ƙyalli suna ɗaukar ido, kallo ɗaya zaka musu kasan ba ƙaramun kuɗi suke ciba. Riƙe yake da mug ɗin copy a hannun sa ɗaya yana siping ɗin sa, yayin da ɗayan hannun nasa kuma ya kasance riƙe da wayar sa ƙirar Iphone 12, yana aikin shafata, idanuwan sa ƙur akan ta. Sosai Ƴammata keta giftawa ta gaban sa, ko wacce da kalar shigar dake sanye ajikin ta, kuma duk suna yin hakan ne ko Allah zaisa su dace ya taya, domin kuwa suna tsoron zuwa gare sa kai tsaye, sabo da kowa yasan halin sa na dizga Ƴammata muddin kasan sa. Yayin da shi kuma ko da wasa bai ɗaga kai ya kalle su ba, sai aikin shafa wayar sa kawai da yake yi, yana sipping ɗin copy ɗin sa. Tun misalin ƙarfe huɗu take zaune a wurin tana jiran zuwan sa, domin kuwa ayau ta ƙudiri aniyar zuwa gare sa ta furta masa abun da ke ranta akan sa, ko Allah zai sa ta dace, amma sai dai kuma yana zuwa ya zauna a wurin gaba ɗaya taji ta kasa tashi daga wurin da take zaunen, balle har ta kai ga ƙarasawa gare sa ta furta masa abun da ke ranta, sabo da tsabar kwarjin da taga ya ƙara yima ayau fiye da kullum da take ganin sa daga nesa. Bilkisu Abubakar Sardauna kenan. Bahaushiya yarinya y'ar gata wacce ta futo daga gidan kud'i, domin kuwa mahaifin ta shine gwamnan da tainuwar sa take ci a cikin Jahar su ta Wasai yanzu. Tana d'aya daga cikin fresh studen d'in da akayi admiting d'in su a wannan shekarar a cikin school d'in. Yarinya ce sangartatta lambar d'aya, kasancewar ita kad'ai ce 'ya mace a wurin mahaifin ta. Satin ta ukku da zuwa makarantar taci karo da Asad a cikin wannan wurin hutawar, da k'awarta ta janyo ta a ranar suka fara zuwan sa, domin suyi wankan ruwa. Sai kuma akayi rashin sa'a adai-dai lokacin da suka shigo idanuwan ta suka yi mata arba da Yarima Asad yana shirin futa daga cikin wurin, domin kuwa acikin wurin Yarima Asad yafi zama sama da ko ina acikin k'asar, dan kuwa har d'aki na mussaman ya kama wanda yake hutawa acikin sa aduk lokacin da yazo, kasancewar wurin Babban wuri ne wanda ya had'a masaukin bak'i da kuma wuraren shak'awa da nishad'i acikin sa, sai dai kuma anan k'asar ma ba kowa ke iya zuwan sa ba, sai wanda ya amsa sunan sa na mai kud'i, domin kuwa wuri ne special wanda babu ruwan wani da wani, kana babu hayani acikin sa kowa na harkar gaban sa ne, kuma mafi akasarin mutanen da suke zuwa wurin duk matasa ne da ga mazan har matan. Cak Billy ta tsaya a wurin da take tana mai bin bayan mayyar motar da ta hango wani had'ad'd'en gaye zaune acikin ta ya fuce daga cikin wurin. Jin shirun da abokiyar tafiyar Billy tayi ne ya sanya ta juyawa b'arin da take, dan taga abun da ya sanya ta yin shirun. A hankali ta janye idanuwan ta daga kan Billy tana mai bin hanyar da taga tana kallo da nata idanuwan, domin taga abun da take kallo wanda har ya janye mata hankali haka. Amma sai kuma taga ba taga komai ba, sai shimfid'ad'ar kwaltar da wasu irin had'ad'd'un furanni suka yi mata k'awanya a wurin. Hakan ne yasa ta sake janye idanuwan ta daga wurin, tana mai mayar da su kan k'awar tata, tukun daga bisani ta d'aga hannun ta tana mai kaisa jikin Billy, bakin ta na fad'in. "Hey Billy!" Ta fad'a tana mai d'an girgiza kafad'ar ta. Firgigit Billy ta juyo b'arin da take tana mai dawo da idanuwan ta kanta, da alamun dai gaba d'aya hankalin ta baya hurin ma da. Yayin da ita kuma k'awar tata ta d'ora da fad'in. "Lafiya kuwa Beb, meke faruwa ne haka?" Ta fad'a tana kallon ta. Lumshe idanuwa Billy tayi tana mai bud'e baki ta fesar da wata sassanyar iska daga cikin sa, tukun daga bisani ta wara idanuwan ta akan fuskar k'awar tata tana mai bud'e baki tace. "Waye shin d'in Zee?" Shiru Zee tayi tana mai kallon Billy tare da d'an cizon lips d'in ta na k'asa a hankali, tukun daga bisani ta sake juyawa bayan ta tana mai k'ara kai idanuwan ta zuwa kan hanyar da taga hucewar Yarima Asad alokacin da suke shigowa, kana ta janye idanuwan nata daga kan hanyar, tana mai sake juyowa ta kalli Billy. Tukun ta bud'e baki tana mai fad'in. "Wai Prince Asad kike nufi?" "Zata iya yuwuwa shi ɗin ne, duk da dai ni ban san sunan saba, amma dai shine guy ɗin da ya fuce a cikin mota alokacin da muke shigowa." Billy ta faɗa idanuwan ta ƙur akan fuskar Zee, tana mai jiran jin amsar ta, kasancewar ita Zee a level 2 take ne yanzu tafi Billy sanin wurin, domin kuwa abotar su tazo ɗaya ne ma sabo da kasancewar Zee ita ƴar shugaban Ƙasar Hausa, yayin da ita kuma ta zamto ƴar Gwamnan Jahar Wasai, kuma jam'iyar iyayen nasu ɗaya, shi yasa tun can suka san juna ma. "Prince Asad kenan." Zee ta faɗa tana mai sake taune leɓen ta na ƙasa, idanuwan ta akan fuskar Billy tana jiran taji abun da zata faɗa. "Ok Prince ne ma kenan?" Cewar Billy fuskar ta ɗauke da murmushi. "Tabbs kuwa, kuma Prince ɗin ma na cikin Jaharku, wato ɗan gidan Sarki Abdallah ne, Sarkin Wasai." Zeee ta faɗa tana mai cigaba da kallon Billy. Yayin da ita kuma ta buɗe baki fuskar ta ɗauke da murmushi, tana mai faɗin. "Kice abun zai zamto mai sauƙi ma a gare ni. To duk ba wannan ba ma, koma waye ne shi ɗin, to yana gab da zama nawa, domin kuwa kallo ɗaya nai masa ya tafi da komai nawa, kuma ayanzu haka ina jin zan iyayin komai akan sa." Wani irin kallon rainin hankali Zee tabi Billy da shi baki asake, tukun daga bisani ta saki wani shegen murmushi, irin wanda ma'anar sa take nufin da wanda aka yiwa shi ɗin bai san kansa ba, wato shi da mahaukaci duk ɗaya suke. Kana daga bisani ta tsaya da murmushin da take tana mai buɗe baki, idanuwan ta a cikin na billy tace. "Shin kin san abun da kike faɗe kuwa Billy? Ko da yake bazan ga laifin ki ba dan kinyi irin wannan furucin akan Asad, sabo da ke ɗin sabuwa ce baki san komai daga cikin halayyar saba, amma shawarar da zan iya baki a yanzu ita ce, ki gaggauta kawar da wannan abun daga cikin zuciyar ki tun kafin yayi zurfi, domin kuwa dubun ki sunyi irin haka, koma nace fiye da haka, kuma har yanzu suna kanyi amma har yau babu nasara akan Prince." Zee ta faɗa babu alamun wasa a cikin magan-ganun nata idanuwan ta a cikin na Billy. Yayin da Billy kuma ta rumtse idanuwan ta da matuƙar ƙarfi tun lokacin da Zee tace akwai dubbanta, kana yanzu ta buɗe su har sun ɗan sauya launi daga fari zuwa ɗan ja, sannan ta buɗe baki cikin muryar gaskiya da gaskiya, tana mai faɗin. "Please Zee daga yau karki ƙara danganta sa da wasu matan muddin ina tsaye a wuri, domin kuwa ni ɗin nan da kika gani ina da zazzafan kishi akan abun da nake so, kana kuma dan su sun buga sun kasa ba shi ke nufin nima zan kasa ba, domin kuwa sunbi nasu salon ne, haka nima zanbi nawa salon wanda kuma ba lallaine ya zamto ɗaya da wanda suka bi ba. Abu ɗaya kawai da zan sake mai maita miki shine, na gansa ina son sa, kuma wallai tallahi sai na bar tarihi tunda har ance wasu sun kasa." Billy ta faɗi haka da tsantsar gaskiyar ta tana mai kallon Zee. Yayin da ita kuma Zee ta fara girgiza kai tana mai jifan Billy da kallon tabbas bakya cikin hayyacin ki, domin kuwa babu wata hallayar Asad wadda bata san labarin ta ba, kana tasan Ƴammata da dama waƴan da sukafi Billy komai da komai da suke hauka akan sa, amma ko kallo basu ishe sa ba, hakan yasa ta buɗe baki tana mai faɗin. "Shin kin san inkiyar sa ma kuwa?" Ta faɗa tana mai ƙara sakin murmushin rainin wayo, tukun ta ɗora da cewar. "Baka so sai dai asoka! Haukata Ƴammata su yini su kwana suna dambe! Sanya ƙawa da ƙawa gaba! Wannan shine iƙirarin da abokanan sa hausawa suke masa a cikin school ɗin nan." "Tabbas kuwa lokacin ɓacewar sunayen ne yazo, domin kuwa tabbaci nake baki akan sai ya koma na Billy bada kan ka asar..." "Hhhhhhhhhhhhhh!" Zee ta kwashe da wata mahaukaciyar dariya wacce ta sanya Billy dakatawa da maganar da take kanyi dan dole tana kallon ta, ba tare da ta kai ƙarshe ba. Tukun daga bisani kuma ta gimtse dariyar ta lokaci guda, kana ta ɗaga kafaɗun ta sama tana mai taɓe baki tace. "Any way naji yanzu kuma zanjira lokaci, dan haka please let us go ko mayi abun da ya kawo mu." Zee ta faɗa tana mai yin gaba. Girgiza kai Billy tayi tana mai bin bayan Zee da kallo, domin kuwa ba ƙaramun shaƙa tayi ba da dariyar da tai mata, tukun daga bisani itama ta ɗaga ƙafafuwan ta tana mai rufa mata baya. Tun daga wannan ranar ta fara bin diddigin Yarima Asad, ya zamto duk wuraren da yake zuwa itama tana nan, haka zataci uban ado da ƙana-nan kaya tazo wurin daniyyar ta tun kare sa da batun abun da ke cikin ranta, amma sai dai kuma har kawo yau da aka ɗauki tsawon wata ɗaya da haɗuwar su ta farko bata iya zuwa ta tsaya ko agaban sa ba, ballan tana ta kaiga faɗar abun da take son faɗen, sabo da wani irin kwarjini da take ganin yana mata akullum idan ta ƙudir ta zuwa gare san. Cigaba da tsayuwa tayi a wurin da take tana mai kallon sa, wata zuciyar nace mata taje kawai koma mai zai faru ya faru, yayin da wata zuciyar kuma take tunasar da ita kalaman Zee akan hallayar Asad da kullum take faɗa mata. Sanye take da black jeans tare da wata ƴar red top ajikin ta, sai wani mahaukacin red hill shoe mai matuƙar tsini da yake sanye aƙafar ta, yayin da gashin atach ɗin da yake tufke akan ta kuma ya kasance zube agadon bayan ta. Yafe take da wani ɗan mitsi-tsin mayafi da ya tsaya iya kar kan ƙirjin ta akan ta, sai ƴar ƙaramar jakarta wacce ta kasance ta mahaɗin takalmin ƙafar ta da take riƙe a hannun ta. Acan kuwa ɓangaren Asad hankali kwance yake sipping ɗin copy ɗin sa, yana yi yana latsa wayar sa, sosai yake matuƙar jin daɗin wurin, sabo da yadda ya kasance tsit babu hayaniya, domin kuwa nan ɗin shine ya kasance vip na cikin wurin, ga kuma yadda wata irin sassanyar iska mai matuƙar daɗi take dukan jikin sa, ta yadda har kwantaciyyar baƙar sumar da tayiwa hannuwan sa da ƙauri-kan sa ƙawanya take kaɗawa. Billy na tsaye awurin nan taga giftawar wata baturiya da taci uban ado ta gaban ta, hakan ne yasa ta bita da kallo domin taga wurin da zatayi, ai'kuwa direct taga ta doshi wurin da Prince Asad yake cikin yauƙi. Take kuwa a wurin Billy taji gaban ta yayi wata irin mahaukaciyar faɗuwa, kana taji wani irin abu ya caki zuciyar ta, bata gama jin wannan baƙin cikin ba idanuwan ta suka hango mata wannan baturiyar a gaban Yarima Asad. Take kuwa jikin ta ya fara wata irin karkarwa, idanuwan ta na canza launi. Yayin da ita kuma wannan baturiyar da ta ƙarasa gaban Yarima Asad, ta miƙa hannun ta ahankali zuwa kan mug ɗin da yake riƙe a hannun sa, tukun ta amshe sa tana mai ajiye sa akan plate ɗin da yake akan table ɗin dake a gaban sa. Yana jin duk abun da take yi kuma ya gane ta, amma yaƙi daga kai ya kalle ta. Yayin da ita kuma ta sake matsawa gare sa, tana mai ɗaukar hannun ta-ta ɗora su akan kafaɗun sa, tukun ta farayin ƙasa da kanta a hankali, tana mai kai fuskarta kan tasa. "Hlo Baby!" Ta faɗa ƙasa-ƙasa tana mai busa masa iskar bakin ta akan fuskar sa, tukun ta cigaba da matsar da fuskar ta zuwa ga tasa tana mai haɗe tsinin hancin ta da nasa, kana ahankali ta juya mazaunan ta tana mai zama akan cinyar sa, tukun ta haɗe lips ɗin ta da nasa wuri ɗaya. Da matuƙar ƙarfi Billy ta rumtse idanuwan ta sabo da abun da ta gani, jikin ta na wata irin karkarwa..! *ƘASAR MALIN, JAHAR KARFUZ CIKIN BAƘAR MASARAUTA.* Abubuwa da yawa sun faru a cikin shekarun da suka gifta, na daɗi dana kishiyar sa a cikin masarautar. A yanzu haka Bir yana da shekaru Ashirin da takwas zuwa da tara ne a duniya. Sosai yake da tsananin kyau mai matuƙar ɗaukar hankalin duk wanda ya gansa, duk da kasancewar sa Bawa. Fari ne kar tamkar a taɓa sa jini ya ɓullo, yana da manya-manyan fararen idanuwa masu ɗauke da baƙar ƙwaya wulik acikin su, yayin da karan hancin sa kuma ya kasance dogo, da yayi matuƙar ƙara ƙawata fuskar tasa, sai kuma ɗan ƙaramin bakin sa da yake ɗauke da jajayen laɓɓa akan sa, yayin da fuskar tasa kuma duka ta kasance zageye da wani irin baƙin saje mai tsananin laushi, da yayi masifar yi masa kyau. Kana yana da wata iriyar suma mai matuƙar yawa da laushi, ga kuma baƙi, duk da dai bata kasance tana samun wani gyara ba, amma a hakan ba ƙaramun kyau take masa ba, domin kuwa tsabar yawan ta har kan kafaɗun sa sai da ta sakko. Har kawo yau yana nan da maitar kwari da gwafar sa, kana kuma afannin taurin kansa ma babu abun da ya sauya. Tun a wancan lokacin na shearun baya da Gimbiya Tasmir ta fara tasawa yake son su haɗu gaba da gaba ita, amma har kawo yau da ita kanta take da kusan shekaru Ashirin a duniya Allah bai haɗa su ba, gashi kuma a yanzu yana jin labarin abubuwan da takeyi da suka ninka na da, hakan ya sanya a kullum yake burin haɗuwar sa da ita gaba da gaba, domin yaga abun da zatayi akan sa. Wannan dalilin ne ma yasan ya-ya samu abokan sa da suke tare ya tambaye su wuraren da take zuwa acikin masarautar, ba dan komai ba kuwa sai domin yaje ya tsaya akan hanyar da take wucewar, kasancewar kusan kullum a daji yake yini wurin harbe-harben sa, shi yasa bai taɓa cin karo da ita ba, sai dai idan ana wani biki acikin masarautar ya ganta, hakan yasa gaba ɗaya ya dena futa daji a ƴan kwanakin -nan, yake zaman sa a wurin su Mauzum, kullum yana hanyar da take bin domin su haɗu, sai dai kuma har kawo yau ita kuma bata biyo hanyar ba, da alamun dai ta kwana biyu bata futo shan'iska ba kamar yadda ta saba. Zaune yake a gaban Iyar Bayi cikin ɗakin ta na iccina ya tanƙwashe ƙafafuwan sa yana kallon ta. Yayin da ita ɗin ma take zaune a gaban sa tana kallon sa, gaba ɗayan ta duk a wani rikice, da alamun dai babu natsuwa tattare da ita a yanzun ko kaɗan. Sake mirginar da kai Bir yayi gefe, yana mai yin narai-narai da idanuwan sa, tukun daga bisani ya ɗaga tafukan hannayen sa duka biyu yana mai haɗe su wuri ɗaya, idanuwan sa akan fuskar Iyar Bayi. Kana ya buɗe baki cikin muryar roƙo yana mai faɗin. "Ki temake ni Iya ta, ina mai tabbatar miki da babu wani abun da zai faru dake. To waima wane ne zai sani bayan daga ni sai ke a cikin wurin nan, ballantana har akai rahoton da kike gudun akai." Girgiza kai Iyar Bayi tayi tana mai rumtse idanuwan ta, tukun daga bisani ta buɗe su akan sa tana mai kallon sa, kana ta buɗe baki cikin muryar raɗa tana mai faɗin. "Amma me yasa kake son dole sai ka sani ne Jarumi? Shin me ma sanin zai amfana maka, bayan kasan ba zaka taɓa ganin su ba, asalima ni ɗin kaina ban san komai ba dan gane da su Jarumi." Girgiza kai shima Bir yayi yana mai ɗan taune leɓen sa na kasa, tukun daga bisani shima ya buɗe baki cikin yin ƙasa da murya, kamar yadda suke yi ako da yaushe idan suna irin wannan batun yana mai cewa. "Kawai ina son jin tushe nane nima, badan komai ba kuwa sai dai in tabbatar da ni ɗin ƙas-ƙantaccen Bawa ne kamar yadda mutane suka sha faɗamun hakan. Ina son ki faɗa mun da gaske ne tsinto ni akayi Iya ta." Bir ya ƙarasa maganar yana mai sauke tafukan hannayen sa daga haɗen da suka ya miƙa su yana mai riƙo na Iyar Bayi a cikin nasa, ya damƙe su wuri ɗaya, yana mai kallon ta da jajayen idanuwan sa. Yayin da Iyar Bayi kuma ta furzar da wata zazzafar iska daga cikin bakin ta, tana mai jin gaban ta na duka tara-tara, tukun daga bisani ta buɗe baki cikin matuƙar sanyi, tana mai faɗin. "Kayi haƙuri Jarumi, haƙiƙa a yanzu bakina bazai taɓa iya furta abun da kunnuwan ka suke son jiba, sai dai kuma ina son kasani akwai lokacin dana tanada domin na faɗa maka, duk da dai zanyi hakan ne ba ason raina ba, dan haka na maka al'ƙwarin muddin lokacin nan yayi to babu abun da zai hana ni baka tsakuren tarihin ka, sai dai kuma ina son kasani, sannan kuma kasa aranka, wannan ranar da bakina zai furta maka labarin da kake son ji, itace kuma zata zamto rana ta-ta ƙarshe a gidan duniya." Ta ƙarasa maganar tana mai zame hannayen ta daga cikin na Bir, kana daga bisani ta miƙe tsaye a hankali tana mai fucewa daga cikin ɗakin, ba tare da ta tsaya jin ta bakin sa ba. Shi kuwa Bir gaba ɗayan sa mutuwar zaune yayi a wurin da yake, sosai yake matuƙar gigicewa aduk lokacin da yaji Iya tayi irin wannan furucin, kana kuma yake jin yana matuƙar ƙara son jin labarin nasa, domin yaji dalilin da ya sanya iyar bayi take tsoron faɗa masan, duk da dai shima ɗin yana matuƙar firgita idan ya tuna da magan-ganun ta, sa yake cewa zata mutu akan tarihin nasa. Ya ɗauki tsawon mitina goma shabiyar zaune a wurin yana mai faman tinane-tinane, tukun daga bisani da yaga abun bazai yi masa ba ya miƙe tsaye cikin sanyi yana mai fucewa daga cikin ɗakin. Dogo ne sosai lamba ɗaya, yana da ƙiba dai-dai misali tare da murɗaɗɗen jiki irin wanda kowa ke so ya kasance da shi. Sanye yake da ɗan gajeran baƙin wandon sa babu riga a jikin sa kamar yadda suka kasance ako da yaushe, duk tsanin sanyi da damina kuwa. Gaba ɗaya ƙirjin sa cike yake da uwar gargasa mai matuƙar laushi da duhu, amma ahaka yake tafiyar sa baya jin kunyar kowa ya gansa, kasancewar hakan al'adar masarautar tasu ta koyar da su, kuma haka ko wane Bawa yake kasancewa a cikin ta. Kai tsaye ya doshi hanyar da aka faɗa masa Gimbiya Tasmir nabi ta ita idan zataje wurin hutun ta. Tafe yake cikin sanyin da kalaman Iyar Bayi suka haifar masa, kansa durƙushe a ƙasa. Yayin da a cikin zuciyar sa kuma yake fatan haɗuwa da Gimbiya Tasmir a futowar tasa ta yanzu. Ai'kuwa ba zato ba tsammani ya jiyo sautin gudun mutane rada-da-da-da ta ko ina, hakan ne yasa sa ɗago kansa cikin sauri domin yaga abun da ke faruwa. Bayi ne suke gudu iyakar ƙarfin su, kama daga mazan su har mata suna masu neman hurin ɓuya. Cikin tsantsar mamaki ya fara waige-waige yana bin su da kallo, domin kuwa shi bai taɓa ganin ana irin wannan gudun ba tun da yake acikin masarautar sai yau. Tsaye yayi a wuri ɗaya yana waige-waige, sabo da yadda yaga cikin ƴan sakanni duka bayin dake a wurin sun ɓace-ɓat. Yana shirin janye idanuwan sa daga kan hanyar da yake kallo ya hangi tawowar mace sanye da wata irin blue'n doguwa riga mai azabar kyau a jikin ta, wacce take manne da adon duwatsu a jikin ta tana jan ƙasa, yayin da wasu irin danƙara-danƙaran mutane waƴan da ba yau ya fara ganin su ba acikin masarautar, amma sai da ya saba ganin su ne aduk lokacin da ake yin hukunci akan wani, dan shima yasha shiga hannun su, suna biye da ita hannuwan su riƙe da mugayen bulalai tare da makaman su. Da sauri ya janye kansa daga wurin da yaga suna tawowa, yana mai yin tamkar bai san da zuwan su ba, ya cigaba da ɗaga ƙafafuwan sa yana tafiyar sa, yayin da a ƙasan zuciyar kuma yake jin wani irin tsoro sama-sama, ga kuma ƙirjin sa dake ɗan bugawa, sabo da sanin muguntar dakarun nan da yayi, sai dai kuma neman fitina irin tasa gaba ɗaya ta sanya ya kasa guduwar shima. Acan kuwa ɓangaren su Gimbiya Tasmir cikin takun ta na tsantsar Izza, wanda shi kaɗai ke nuni da ko ita ɗin wace-ce, ta cigaba da takowa wurin dakarun ta na biya da ita. Sosai tayi matuƙar kyau cikin shigar dake sanye a jikin ta, abunka da mai kyau ɗin dama, shiya sanya duk irin sitirar da tasa a jikin sa sai tayi mata kyau. Kanta ɗaga asama tana kallon hanya fuskar nan tata babu alamun annuri tattare da ita ta cigaba da dumfarar wurin nan. Lokaci ɗaya ta tsaya cak a wurin da take adai-dai lokacin da suka ƙaraso saitin wurin da Bir yake, sabo da motsin sautin tafiyar mutum da taji acikin kunnuwan ta. A ɓangaren Bir kuwa shima ya lura da isowar su wurin da yake ɗin, hakan ne yasa sa durƙusawa ƙasa jikin wata bishiya da take a gefen sa, yana mai ɗaukar wani icce ya fara kakkarya sa ba tare da ya ɗago ya kalli wurin da suke ba. Tsayuwa Gimbiya Tasmir ta cigaba dayi a wurin tana mai jiran taji ƙarar sautin gudu a kunnuwan ta, amma sai dai har ta ɗauki tsawon daƙiƙa ukku a wurin bataji ba, kai asalima sai daina jiyo sautin tafiyar tayi, sai kawai ƙarar karya iccina, wanda hakan kuma ya tabbatar mata da cewar akwai mutum a wurin. Take kuwa ranta yayi matuƙar ɓaci lokaci guda, domin kuwa tunda take futowa ba'a taɓa yi mata haka ba sai yau. Hakan yasa cikin tsantsar ɓacin ran da ya lulluɓe ta lokaci guda ta fara juyar da kanta ɓarin da take jiyo motsin ahankali. Karaf kuwa idanuwan su suka haɗu da na juna, adai-dai lokacin da ya ɗago shima domin yaga ko sun kauce. A hankali ya janye idanuwan nasa daga cikin nata yana mai yin tamkar bai ganta ba, ya cigaba da karya sandar dake riƙe a hannun sa. Yayin da ita kuma ta kafesa da nata idanuwan da suka fara sauya launi tsabar ɓacin rai, tana mai mamaki tare da tinanin abun da ya taka da har ya hanasa guduwa a lokacin da ta tawo, bayan kuma ta tabbatar da yaga lokacin da sauran ƴan uwan sa bayi ke gudu, kana kuma duk wannan laifin da yayi bai ishesa ba sai da ya ƙara sanya idanuwan sa a cikin nata, abun da ba ataɓa samun wani yayi ba bayan ahalin ta a duniya. Cikin tsantsar ɓacin rai ta ɗago hannun ta da yake wata irin kar-karwa tsabar ɓacin rai, tana mai nuna sa daga wurin da take, tukun daga bisani ta ɗaga laɓɓan ta a hankali cikin muryar ta da kafun ajita ake yarawa, tana mai faɗin. "Waye shi ɗin, mai kuma ya taka da har zai ganni ya zauna?" Ta ƙarasa maganar da sakin huci ba tare da ta janye yatsar tata daga nuna san da take yi ba, yayin da shi ɗin ma yake lura da duk abun da take yi ta ƙasan ido da yake kallon ta, kana ta sake buɗe baki cikin fushi tana mai faɗin. "Ina buƙatar ganin sa durƙushe a gabana kafun nan da giftawar daƙiƙa daya kacal".................✍ *BAK'AR MASARAUTA* *NA* UMAR FARUQ*D* *PAGE 24* Ta k'arasa maganar cikin zafi tana mai sakin huci, tukun ta fara d'aga k'afafuwan ta tana mai dosar wurin da kujerar nan take cikin tsantsar zafin rai. Yayin da su kuma dakarun nan sukayi kan Bir aguje ransu atsantsar b'ace da abun da sukaga yayiwa uwar d'akin nasu, domin kuwa zasu iya cewa tun da suke da ita basu tab'a ganin ranar da ranta ya b'aci ba irin na yau. Ko kad'an Bir bai lura da isowar su ba, sai dai kawai hannun sa da yaji an funcika da wani irin k'arfi tamkar za'a cizge sa, ta yadda har sai da ya kife ak'asa wanwar kansa na gwaruwa da wani dutse dake a kusa da shi. Yayin da shi kuma wannan badakaran da ya funcike sa yana mai fara jansa a k'asan wurin da yake d'auke da duwar-watsu da matuk'ar k'arfi. Rumtse idanuwa Bir yayi da k'arfi yana mai jin yadda kansa ke had'uwa da duwar-watsun kan hanyar. Suna k'arasawa gaban kurar da Gimbya Tasmir take a k'ark'ashin bishiyar nan, ya durk'usa yana mai sannu hannu ya damk'o huyan Bir da matuk'ar k'arfi, tukun daga bisani ya d'agosa yana mai durk'usar da shi a kan guiwoyin sa. Yayin da ita kuma Gimbya Tasmir take zaunu akan wannan kujerar ta-ta, ta d'ora k'afa d'aya akan d'aya tana mai girgiza ta. Gaba d'aya babu alamun rahama ko kad'an tattare da fuskar ta. Wani irin abu take ji mai kama da icce na tokare mata k'awon zuciya, aduk lokacin da tuna da yadda Bir ya kalli cikin idanuwan ta. A hankali ta fara sauke idanuwan ta k'asa tana mai kaisu b'arin wurin da Bir yake. Yayin da shi d'in ma kuma adai-dai lokacin ya d'ago nasa idanuwan yana mai kaisu kan fuskar ta. Take kuwa idanuwan su suka sark'e cikin na juna. Yayin da zuciyoyin su kuma sukayi wata irin bugawa a lokaci guda, tukun daga bisani gudun su ya k'aru fiye da yadda suke ada. Cikin wani irin yanayi wanda Gimbiya Tasmir bata tab'a tsintar kanta acikin sa ba ta ji ta, ta sanadin had'uwar da idanuwan nasu sukayi wuri d'aya, ga kuma zuciyar ta dake wani irin bugu da matuk'ar k'arfi, abun da tun da take arayuwar ta bata tab'a sanin sa ba. Wata irin tafar-fasa zuciyar ta take jin tana yi mata, sabo da yadda Bir ya kafeta da tsumammun idanuwan sa baya ko k'itawa. Ita kanta so take ta ja ye nata idanuwan daga cikin nasa, ko ta samu damar yin tinanin kalar hukuncin da ya kamata tayi masa, amma gaba d'aya taji ta kasa, sabo da wasu irin abubuwa da take ganin suna futowa daga cikin idanuwan nasa suna fad'awa cikin nata. A fannin Bir kuwa ko kad'an bai d'aga kansa ba da niyyar ya kafeta da idanuwan sa tamkar yadda yayin, sai dai kuma d'ago idanuwan nasa keda wuya suka fad'a cikin nata, wanda kuma a take a wurin yaji zuciyar sa tayi wata irin matsananciyar harbawa . Yaso ya janye idanuwan nasa daga cikin nata, amma gaba d'aya yaji ya kasa yin hakan kwata-kwata, kai asalima ya kasa koda k'ifta su ne daga kan nata, yadda kasan mayen k'arfe da k'arfe ne suka had'u, domin kuwa wani irin haske yake ganin yana futa daga cikin idanuwan nata yana jonewa da nasa idanun, ta yadda har ya manta matsayin wacce yake durk'ushe a gaban nata, domin kuwa tun da ya taso yayi wayo bai tab'a tsintsar kansa a cikin yanayi mai kama da irin wannan d'in ba. Jini ke tsiyayowa ta cikin gashin kansa sa yana gangarowa ta gefen idanuwan nasa, ta sanadin kansa da ya fashe a lokacin da badakaran nan ke jansa acikin kwazazzaban nan, amma ko kad'an bashi da alamun zai goge sa, gudun karya shigar masa idanun, sai kallon tsakiyar idanuwan Gimbiya Tasmir da ya cigaba dayi zuciyar sa na wani irin bugu da matuk'ar sauri, yayin da tsigar jikin sa kuma ke wani irin tashi, yana mai jin wani irin yanayi a gaba d'aya sassan jikin sa wanda bai saba da shi ba. Cikin tsantsar k'unar rai Gimbiya Tasmir ta cigaba da kallon tsakiyar idanuwan sa, tana mai jin wani rin mugun bak'in ciki na tokare mata zuciya. So take kawai ta janye idanuwan nata daga cikin nasa, amma gaba d'aya taji ta kasa. Babu abun da yafi b'ata mata rai ma sai irin yadda taga shi d'in ma yak'i ya janye nasan, ga kuma zuciyar ta dake wani irin bugu duk ta sanadin kallon-kallon da suke yiwa junan su, abun da bata tab'a jiba kenan dan ta kalli wani mutumin, asalima babu mai iya had'a idanuwa da ita balle har aje ga irin haka. Lokaci d'aya ta mik'e tsaye zumbur daga kan kujerar da take, tana mai tsayawa akan k'afafuwan ta, tukun daga bisani ta fara d'agasu cikin zafin rai, suna masu futar da sautin k'arar gwala-gwalan da suke manne akan su, ta doshi wurin da Bir yake a durk'ushe, har lokacin kuma idanuwan ta na-nan cikin nasa. Ko da ta mik'e'n tsaye amai-makon Bir ya hak'ura dakallon ta tunda tai masa nisa, amma sai ya sake d'aga kansa sama yana mai sake danna idanuwan sa cikin nata. Sai da tazo dab da shi tukun taja ta tsaya tana mai sakin numfarfashi, yayin da zuwa lokacin kuma idanuwan ta suka kad'a sukai jajajir tsabar b'acin rai, duk a tinanin ta idan yaga ta mik'e tsaye zai janye idanuwan nasa daga cikin nata, amma sai taga ya sake d'aga kansa sama yana mai mayar da su ciki, hakan da yayin kuwa ba k'aramun sake dagula mata lissafi yayi ba, kana kuma ranta ya k'ara kaiwa k'ololuwa wurin b'aci, sannan ta fara tinanin to wai shi d'in uban waye ne ma da har zai tsaya a gaban ta yana kallon ta ido cikin ido, sannan kuma mai ya taka da har dan ta kalle sa bugun zuciyar ta ke sauyawa, bayan a yadda ta gansa tariga da tasan Bawa ne k'ask'antaccen mutum gare ta. Hakan ko shi yayi matuk'ar k'ara harzuk'ata, ta yadda har k'wak'walwar ta ta gaza sanar da ita abun da ya kamata tayi masa. Cigaba da kallon sa tayi daga tsayen da take, kafin daga bisani kuma ta durk'ushe a k'asa tana mai cake guiwar k'afar ta d'aya a cikin k'asa, yayin da d'ayar kuma ta dire tafin ta akan k'asa, kana ta dafa k'asa da hannun ta d'aya, yayin da d'ayan kuma ta dunk'ule sa da k'arfi, tana mai cigaba da kallon cikin idanuwan Bir, kamar yadda shim yake kallon nata, zuciyoyin su na wani irin bugu atare, ta yadda har kowanen su ke iya jiyo sautin bugawar zuciyar d'an uwan sa. Bud'e bakin ta tayi tana mai furzar da wata irin zazzafar iska daga cikin sa akan fuskar Bir. Da sauri ya lumshe idanuwna sa ba tare da ya shirya yin hakan ba, sabo da iskar bakin ta mai matuk'ar turiri da ta daki k'wayoyin idanuwan nasa, yayin da ita kuma ta fara d'aga lab'b'an ta cikin kausassar muryar ta da take futa k'asa-k'asa, tana mai fad'in. "Shin waye kai? Waye ubanka? Me kuma ka taka acikin Bak'ar Masarauta?" Ta k'arasa maganar da k'yar, tana mai sakin numfarfashi, gaba d'aya alamun gajiy sun bayyana k'ara-ra akan fuskar ta, kasancewar bata saba yin doguwar magana irin wannan ba aduk lokaci d'aya, sai dai kuma a yadda take jin zuciyar ta na zafi akan wannan mara kunyar Bawan na gaban ta, zata iyayin fiye da haka ma. A hankali Bir ya sake bud'e idanuwan sa akan fuskar ta, tukun daga bisani ya mayar da su ya lumshe yana mai sauke wasu irin tagwayen ajiyar zuciya, tamkar yaron da yaci kuka ya more, kana daga bisani ya sake bud'e su akan fuskar ta yana mai sake watsa su cikin nata da yaga gaba d'aya sun canza launi, daga farin kar d'in da ya gansu d'azu zuwa jajawur yanzu. A hankali ya fara d'aga lab'b'an sa idanuwan sa acikin nata tamkar zaiyi magana, tukun daga bisani kuma ya b'ige da aika mata da wani irin sassanyan murmushi, kana a k'arshe ya k'arasa rufe bakin nasa da hura mata sassanyar iskar dake cikin sa shima, yana mai jin wani irin abu tamkar mayen k'arfe na fuzgar sa zuwa gare ta. Da sauri Gimbiya Tasmir ta lumshe idanuwan ta tana mai sakin wata irin ajiyar zuciya da ko kad'an bata shirya ma yin ta ba, sabo da yadda taji saukar sassanyar iskar bakin sa mai matuk'ar k'amshi akan fuskar ta, ta yadda har sai da ta daki k'wayoyin idanuwan ta. Wanda hakan kuma ba k'aramun sake b'ata mata rai yayi ba. Yayin da su kuma dakarun nan nata gaba d'ayan su sukayi suman tsaye a wurin da suke suna masu bin su da idanuwa, yayin da mamakin k'arfin halin Bir kuma gaba d'aya ya cika zuciya da ruhin su, domin kuwa kosu tun da suke da ita tun tana y'ar k'aramar ta ba a tab'a samun wani ya kalli cikin idanuwan ta ba ko da na second d'aya kuwa, tsabar kwarjinin da take yi musu, amma sai gashi yau sun gani akan idanuwan su wani Bawa wanda ko su suka fisa galihu ya kafe ta da nasa idanuwan. Wata irin kar-karwa jikin Gimbiya Tasmir ya farayi sabo da tsantsar b'acin rai, tukun daga bisani kuma ta wara idanuwan nata tana mai mik'ewa tsaye zumbur tamkar wacce aka tsikara. Kana kuma ta d'aga k'afar ta-ta dama tana mai harbin Bir da ita da matuk'ar k'arfi, ta yadda har sai da yayi baya taga-taga yana shirin fad'uwa akan wani dutse, amma sai yayi sauri ya dafe wani k'aton icce da ya gani agaban sa yana mai sake cake guiwoyin sa acikin k'asa, tukun daga bisani ya d'ago kansa yana mai sanya idanuwan sa a cikin nata, tare fa sakar mata wani irin murmushi mai tafe da ma'anoni da yawa a cikin sa. Da k'arfi Gimbiya Tasmir ta rumtse idanuwan ta da tafukan hannayen ta duk alokaci guda, tukun daga bisani ta bud'e su tana mai juyawa bayanta ta fara waige-waige, tana mai tinanin kalar hukuncin da ya dace da shi. Juyawa tayi b'arin da farin ruwan nan wanda yake zagaye da su yake tana mai kai idanuwan ta kansa, tukun daga bisani kuma ta janye su daga kan ruwan tana mai girgiza kai. Kana ta sake juyawa tana mai kai idanuwan ta kan dakarun nana nata da suke a tsaye cirko-cirko tamkar bishiyu. Sannan ta bud'e baki cikin wata iriyar murya wacce take d'auke da tsantsar b'acin rai a cikin ta tana mai cewa. "Ku d'auke shi ku tafi da shi, a masa azaba mafi muni daga cikin azabobi, a masa azaba irin azabar da baku tab'a yiwa wani makamacin ta ba a duniya, kana idan an tabbatar da jikin sa ya nuna azo asanar mun kafun asake sa." Ta k'arasa maganar tana mai sakin wani irin huci, tukun daga bisani ta juya tana mai fara d'aga k'afafuwan ta cikin sauri, ta doshi hanyar da suka biyo alokacin da suke zuwa wurin. Yayin da su kuma way'an nan dakarun sukayi kan Bir gadan-gadan gaba d'ayan su. Tamkar zasu kacaccala sa suka kai hannuwan su jikin sa, ko wanne daga cikin su yana mai damk'ar wani sassa daga cikin sassan jikin sa. Kana daga bisani sauran suka sake sa suna masu barwa mutum d'aya shi. Shi kuwa wanda aka barwan da hannu d'aya yayi wani irin d'aga Bir sama, tukun ya fara d'aga k'afafuwan sa yana mai nufar bakin ruwan nan da shi, yayin da suma sauran y'an uwan nasa suka rufa masa baya, gaba d'ayan su suma ransu a b'ace da ganin kalar rashin kunyar da yayiwa uwar d'akin nasu. *K'ASAR HAUSA, JAHAR KAGUL CIKIN MASARAUTAR FUL'DE.* Rayuwa taja, a sannu-sannu kwanaki suka dinga zuwa suna wucewa, kana su koma satika, sannan satika suka koma watanni, yayin da watanni kuma suka dinga ninkuwa ahaka har suka zamto shekaru. Abubuwa da yawa sun faru acikin shekarun da suka gaba ta, cikin su kuwa har da haihuwar y'a macen da Gimbiya kab'el ta sake yi, yarinya taci sunan mahaifiyar Lamid'o Gimbiya Unau, amma suna kiran ta da Innahuro, ma'ana uwar masu gida a hausance kenan. Shekaru kusan goma shahud'u ke a tsakanin Gimbiya Haddiya da Inna huro, amma idan mutum yaga yadda Innahuro da take da shekaru biyar zuwa shida yanzu aduniya take yiwa Gimbiya Haddiyal sai ya d'auka baifi tsirayyar shekara d'aya ke tsakanin su ba, domin kuwa ko d'an kunne aka siyawa Haddiya to itama Innahuro sai tace asiya mata shi, wato ta mayar da ita tamkar kishiyar ta dai. Yayin da ita kuma Haddiyal take matuk'ar son k'anwar tata tamkar yadda sauran y'an gidan suke son ta, duk da dai ita Innahuro a kwaita da shegen surutu, ba kamar haddiyal ba da surutu bai dameta ba kwata-kwata. A yanzu haka Gimbiya Haddiyal tana da shekaru Ashirin ne a duniya. Sosai tayi girma ta k'ara yin kyau tamkar ita tayi kanta, domin kuwa babu ta inda Allah ya rage ta aduka hallitar jikin nata. Tini ta kammalla karatun secondry d'in ta a cikin wannan makarantar data farata tun farko, yayin da akai-akai da Lamid'o ya kaita k'asar waje ta cigaba da karatun ta amma gaba d'aya yace bai san da wannan batun ba, wanda tayi na bayan ma shima ya barta ne kawai dan an masa dole, amma bawai dan ransa yaso ba, hakan ne yasa yanzu take zaune a gida babu wurin da take zuwa, sai wurin tsuntsayen ta da tini suka dade da zamtowa abokan rayuwar ta, domin kuwa tsanin son da take yi musu ne ma da Lamid'o ya gani yasan ya ya nad'ata a matsayin sarauniyar su acikin duka masarautar, kana ya bata jagorancin kula da duk shanun da ake d'ibar madara a jikin su acikin masarautar, ta yadda muddin ana buk'atar madara sai an biyo ta wurin ta kafun asame ta. A b'angaren mafarkin ta da tayi na busar sarewa kuwa, haka kullum ta cigaba da yin sa a wancan lokacin, sai dai kuma har ta d'auki tsayin watanni shida tana mafarkin bata tab'a ganin mai busar ba, sai dai sautin ta kawai da take ji, kafin daga baya kuma mutumin dake busar ya bayyana acikin mafarkin nata, sai dai kuma ako da yaushe bata ganin fuskar sa, kawai dai tana ganin sa ne ya juya mata bayan jikin wani k'aton dutse da yake tsayuwa, sanye da shiga irin ta Sarakai a jikin sa, haka zataje ta samu wuri daga bayan sa ta zauna tana mai kallon sa, busar na ratsa ko wane lungu da sak'o na ilahirin jikin ta. A haka har aka shafe sama da shekaru biyu tana wannan mafarkin aduk daran duniya. Kwatsam rana d'aya sai taga mutumin dake busar ya sauya kalar shigar dake sanye a jikin sa ko da yaushe, amai-makon ta gansa da shigar sarauta, sai ta gansa sanye da d'an guntun bakin wando'n da tsayin sa bai huce iyakar guiwar sa ba ajikin sa, sai wani d'an kyalle kuma da yake yafe ajikin sa amai-makon riga, kana kuma babu abun busar rik'e a hannun sa tamkar yadda ta saba ganin sa ako da yaushe yana yin busar. Hakan ne yasa ta fara d'aga k'afafuwan ta cikin sanyi tana mai nufar wurin da yake. Tsaye tayi cak a bayan sa a lokacin da ta matsa dab da shi, tukun daga bisani ta bud'e baki cikin zazzak'ar muryar ta tana mai fad'in. "Yau kimanin tsawon shekaru kenan kullum kana zuwar mun da shigar Sarakai jikin ka, kana sautin daddad'ar busar ka na ratsa gangar jiki da jijiyoyin jiki na, ta yadda har take kwanciya acikin b'argo na. Amma kuma yau sai na ganka da sabon tufa ba waccan ba, kana kuma babu abun busar dake sanyaya mun zuciya ta. Shin ko zan iya sanin abun da ya hanaka zuwar mun da sarewa ta a yau, bayan kuma ka riga da kasabar mun da jin daddad'an sautin ta a cikin kunnuwa na?" Ta k'arasa maganar cikin sanyi, tana mai gyara tsayuwar ta a wurin da take. Amaimakon taji sautin muryar sa yana bata amsar tambayar da tayi masa, sai kawai taga ya fara juyowa gare ta ahankali-ahankali, har ya juyo duka b'arin da take yana mai fuskantar ta tare da jifan ta da wani irin sassanyan murmushin sa, abun da tunda take da shi bai tab'a yi ba kenan, wato juyowa gare ta balle har taga kamannin sa sai yau. Hakan ne kuwa ya sanya ta tayi suma tsaye a wurin da take tana mai binsa sa da dara-daran idanuwanta, kamar yadda taga shima yana kallon ta da nasa idanuwan, tare da sakar mata murmushi. Kyakkywa ne ajin farko, danko atak'aice tana iya cewa tunda take aduniya bata tab'a ganin mai kyan sa ba. Sun d'auki tsayin mintina goma ahaka suna kallon-kallon ba tare da wani daga cikin su yayi magana ba, sai kawai murmushin da suke ai'kawa junan su da shi. Kana daga bisani kuma Gimbiya Haddiyal ta fara d'aga k'afafuwan ta daga wurin da take tana mai sake nufar sa cikin tsantsar farin ciki. Tana dab da zuwa gare sa ne kawai ta farka daga baccin da take. Tun daga wannan ranar kuma take mafarkin sa acikin yanayi daban-daban. Yayin da zuciyar ta kuma ta kamu da wata irin mahaukaciyar k'aunar sa, ta yadda har sai da ko wane mutum na cikin gidan nasu yasan da labarin sa, kana kuma ta fara k'ok'arin ganin ta gano wurin da yake zaune ta hanyar tsafin ta, amma gaba d'aya abun ya cutura. Hakan ne yasa tasan ya d'aya daga cikin bayin gidan nasu data aminta da shi sosai ya fara yi mata bincike akan mutumin mafarkin nata, domin kuwa tun da suke had'uwa da shi tun lokacin data fara zama budurwa har kawo yau bai tab'a furta mata wata kalma ba sai dai kawai murmushi, yayin da ita kuma take zama tayi masa zuba acikin mafarkin nata. A lokacin da labarin mutumin mafarkin Gimbiya Haddiyal ya isa kunnen Lamid'o sosai hankalin sa yayi matuk'ar tashi, domin kuwa duk atinanin sa Aljanu ne suka shafi d'iyar tasa, hakan ne yasa ya fara nemar mata magun-guna gadan-gadan, kana kuma ta ko wacce hanya, amma kuma abanza, domin ko amaimakon abu yayi sauk'i sai haukacewa da kullum Gimbiya Haddiyal take k'arayi akan mutumin cikin mafarkin nata, wanda tai masa lak'abi da Gid'ad'on ta, wato Masoyin ta a harshen hausa kenan. Yanzu haka tsaye take a gaban had'ad'd'iyar wardrobe d'in k'arfen da take manne ajikin bangon d'akin ta, tana mai zaro kayan baccin ta, kasancewar tini dare ya fara nisa, domin kuwa har k'arfe goma ta gota. Cikin sauri ta fara ware had'ad'd'iyar jar doguwa rigar baccin da take rik'e a hannun ta, kafin daga bisani kuma ta zurata a jikin ta. Sosai rigar tayi mata mahaukacin kyau, abun ka da kyakkywar dama, kana ta d'auki hular ta tana mai sanya ta akan ta, bayan ta cusa mayawaicin gashin ta cikin ta. Tukun ta rufe murfin wadrobe d'in tana mai juyawa ta haye kan luntsumemen gadon k'arfen ta na alfarma, mai kalar ruwan zuma, tamkar yadda gaba d'aya sauran kayan d'akin suka kasace kalar. Da sauri ta lumshe idanuwan ta bayan ta janyo lallausan eskimon dake shimfid'e a gadon jikin ta. Tukun ta lumshe idanuwan ta tana mai fatan bacci ya d'auke ta a yanzu-yanzu, domin tayi arba da Gid'ad'on ta farin cikin ranta. Ai kuwa batai ko minti goma da kwanciyar tata ba wani nanauyan bacci mai matuk'ar dad'i ya sure ta. Cikin kyakkywan lambum da suka saba had'uwa da shi ta samu kanta. Sanye take da shigar su ta fulani da tayi matuk'ar amsar jikin, kana ta tai mata bala'in kyau tamkar koda yaushe. Tsaye ta hange sa jikin w...................✍ 08038135929 UMAR Faruq D *BAK'AR MASARAUTA* *NA* UMAR FARUQ*D* *PAGE 25* Wata k'atuwar bishiyar gwanda ya juya baya tamkar koda yaushe. Sanye yake da d'an guntun farin wando na yadi kamar yadda ta saba ganin sa ako da yaushe. Cikin tsantsar shauk'in da ta tsinci kanta a ciki ta cigaba da dosar wurin da yake tsaye, fuskar ta d'auke da tsantsar far'a. Jin ta take tamkar wacce aka yiwa bishara da gidan Aljanna aduk lokacin da zata ganta-gata gasa. Tana masa wani irin so irin wanda ita kanta ba zata iya misaltasa ba, tana mai jin sa tamkar yadda take jin rayuwar ta. Tsaye tayi daga bayan sa a lokacin da ta k'arasa wurin da yake, tana mai lumshe kyawawan idanuwan ta. Tukun daga bisani ta wara su a hankali akan farar-fatar gadon bayan sa da take a bud'e, kana ta bud'e baki cikin sanyi tana mai fad'in. "Tabbas rayuwar da babu kai tamkar mutuwa take a wurin Haddiyal Gid'ad'o am, domin ko zuciya da ruhi sun dad'e da yin nunk'aya a kogin k'aunarka. Ina maka so irin son da ban tab'a yiwa wani mahaluk'i makamancinsa ba a duniya. Kai ne na fara sani a duniyar soyayya, da kai zuciya tayi sabo, duk da a kullum rashin jin sautin muryar ka na matuk'ar rikitamun lissafi, kallon ka gare ni shi ne ya zamto farin ciki na. Shin har sai zuwa wane lokaci ne zaka bud'e baki kayi mun kwatan-kwacin irin kalaman da nake maka Gid'ad'o am? Domin kuwa zuciya ta tana gab da yin bindiga muddin za'a cigaba da tafiya a haka." Ta k'arasa maganar cikin sanyi, tana mai jin wani irin yanayi tattare da ita. Yayin da shi kuma ya fara juyowa a hankali, har juyo b'arin da take gaba d'ayan sa yana mai fuskantar ta, fuskarsa d'auke da tsantsar annuri. Sassanyan murmushin sa na ko da yaushe yake jifan ta da shi, yana mai d'an lumshe idanuwan sa, kana ya sake bud'e su akan ta. "Hak'ik'a ina sonka, kuma zan cigaba da sanka daga nan har zuwa ranar da numfashi na zai tsaya, sannan kuma har zuwa lokacin da zaka bayyana a gareni a zahiri, saboda ni d'in an halliceni ne domin ka, kamar yadda aka hallice ka domin ni." Ta k'arasa maganar itama tana mai jifan sa da nata kyakkyawan murmushin. Kana tana mai jin wani irin farin ciki mara misaltuwa na ratsa ilahirin sassan jikin ta, yana kwanciya a cikin b'argon ta. *JAHAR WASAI CIKIN MASARAUTAR WASAI.* Komai ya sauya a cikin masarautar wasai, tamkar yadda rayuwa take sauyasa ako da yaushe. Tini Gimbiya Fulani ta aurar da 'ya'yanta mata dukan su sai Baby auta kawai da tayi saura. A fannin Babban Yaya shima yayi aure tun yana da shekara ashirin da tara, ta yadda har ya ajiye 'ya'ya ukku yanzu, domin kuwa a yanzu haka shekarun sa sun kai talatin da tara zuwa arbai'n a duniya. A yanzu haka daga shi har mahaifiyar su Gimbiya Fulani basu da wata damuwa face ta hallayar Asad, a kullum basu da aikin yi wanda ya huce addu'oin da suke masa, suna masa fatan Allah ya shirye sa, domin kuwa ba k'aramun sosuwa ransu yake yi ba aduk lokacin da Asad yake gida. A b'angaren Mai Martaba kuwa shima sosai hallayar Asad d'in ke damun sa, domin kuwa bak'aramun d'aci ransa yake masa ba, idan ya tuna yadda suke yin shiga iri d'aya, tare da zama a wuri d'aya da shi da d'an nasa ada, suna hira a koda yaushe tare, amma yanzu gaba d'aya ya canza yak'i komai na baya, babu irin lallab'in da ba yayi masa akan yasa manyan kaya ya kumaje fada amma gaba d'aya a banza, domin kuwa babu abun da Asad ya tsana a halin yanzu irin Fada, yayin da su kuma manyan kaya yake musu kallon barguna. Godiyar sa d'aya ga Allah shine da yariga yasan duk iskancin Asad d'in baya shaye-shaye, sannan kuma baya wasa da Sallah ko kad'an, sai dai kuma bayan ita kuma babu wani abu da ya dame sa na addini. A fannin magautan su kuwa har kawo yau basu fasa jifan su da mugayen abubuwa ba, mussaman ma Babban yaya a yanzu, domin kuwa shi Asad suna ganin sun riga da sun gama da babin sa tun da ya kauce hanyar zama Sarki har abada. Hakan ne yasa suka duk'ufa akan Babban yaya ba dare ba rana, amma sai dai kullum yi suke tamkar basayi, domin kuwa har yau basu tab'a jin ance musu ko ciwon kai yayi ba, gashi har ya fara tara iyali shima, wanda hakan kuwa ba k'aramun k'ona musu rai yake yi ba. Tini Baby autar Gimbiya Fulani ta girma, dan ko a yanzu haka ma karatun degree d'in ta takeyi a cikin d'aya daga cikin k'asashen turawa, ita da 'yar gidan Waziri mai suna Fa'iza, domin kuwa a yanzu haka suna da shekaru goma shatara zuwa ashirin ne a duniya. Sosai Fa'iza take mutuwar san Yarima Asad tamkar ranta, amma sai dai kuma abun takaicin shi ko kallo bata ishesa ba, dan kuwa ko gaisuwar ta ma bako da yaushe yake amsawa ba, sai dai idan suna tare da Baby ne tun daga ranar da ya gane take-taken ta, domim kuwa a cewar sa Allah ya kiyaye ya kula wata daga cikin yaran gidan da sunan soyayya. Haka kuma ba ita kad'ai bace take son sa a cikin 'yammatan gidan nasu, sun kai su kusan Biyar, amma gaba d'ayan su babu wacce take samun darajar kallon arzik'i ma balle ya kulata. *UNGUWAR 'DAN TANKI.* Rayuwa ta canzawa su Aishatu da Iyalanta, ta sanadin aikin da Sheikh Ahmad ya samu na koyarwa a cikin jami'ar su a shekarar da ya gama. Kasancewar ya futa ne da first class, shiyasa makarantar tasu ta rik'e sa amatsayin malami, wato lecture, kana kuma suka basa damar k'aro karatu ta hanyar nauyin sa da duk suka d'auka, hakan ne yasa acikin shekarar da result d'in nasa ya futo ya sake neman gurbin karatun gaba anan cikin jami'ar tasu, wato masters, inda ya d'auki fannin Tauhid. Hakan kuwa ba k'aramun dad'i yayiwa mahaifan sa ba dama duk wani masoyan sa ma. Shekarar sa biyu da fara aikin kacal yayi musu sabon gida na gani na fad'a acikin wata unguwa da take a gaban unguwar su, wacce ta kasance ta masu kud'i, mai suna Babban Zaure Locus, duk da dai gidan nasu ba wai irin tank'ashe-shen nan bane, sai dai kuma a hakan ba k'aramar had'uwa yayi. Part biyu ne a gidan babba da k'arami, babban part d'in mai d'auke da d'akuna sama da k'asa da kuma k'atoton falo shi ya bawa iyayen nasa, yayin da k'aramin kuma da ya kasance plat building shi kuma ya zauna a cikin sa. Kasancewar shekara d'aya kawai su kai da komawa gidan shima yayi aure, inda ya auri d'aya daga cikin d'aliban sa na makarantar islamiyyar sa. A yanzu haka 'ya'yan su biyu shi da ita mace da namiji. Ishak' mai sunan baban sa shine babba, yayin da suke kiran sa da Dady, sai kuma Aishatu mai sunan maman sa da tazo ata biyu, bayan haihuwar Dady da shekara biyu da rabi, ita kuma suna kiran ta da Amira. Sosai sunan Sheikh Ahmad yayi matuk'ar shahara a cikin garin Wasai, domin kuwa a yanzu haka shine limamin juma'a na babban masallacin da yake a cikin garin wasai, idan aka cire na gidan sarki. Sosai girman sa da kwarjinin sa tare da haibar sa harma da kyawun sa suka k'ara futowa, kasancewar a yanzu haka yana da shekaru kusan arba'in ne a duniya. Yana da motocin hawa har guda biyu 'yan madai-daita masu kyau. Yayin da Mahaifin sa Ishak' ma yake da ita, wadda shine ya siya masa da kansa. A yanzu haka matsalar su d'aya ce kawai a gidan duniya, wacce kuma take matuk'ar nuk'ur-k'usar zuciya da ruhikan su, wato Aishatu, domin kuwa har kawo yau bata bar sanya damuwa a ranta ba, ta yadda har ta kamu da ciwon hawan jini mai tsanani, wanda aduk lokacin da ya tashi baya mata da sauk'i ko kad'an. Ako da yaushe sai tayi kamar ta dena tinane-tinanen, kwatsam rana d'aya kuma sai suga ta koma gidan jiya. Wannan damuwar da take ciki itace kawai take hana su sukuni gaba d'ayan su, domin kuwa hatta da kaka da d'akin ta yake anan k'asan bene ba k'aramun damuwa take da yanayin Aishatu ba, haka zata zauna wataran tai ta masifa tana fad'in, ta kasa d'aukar dangana sai kace ba musulma ba, kafin daga k'arshe kuma ta koma tai-ta rarrashin ta, wani lokacin ma har k'walla zakaga tana zubarwa. A fannin fad'an su da Sheikh Ahmad kuwa babu ranar banza da zata zo ta k'are ba tare da sunyi ba, barin ma da aka aurar da k'annen sa mata gaba d'ayan su, ya zamto su biyu ne kawai sukai ragowa shi da autan su mai shekar kusan ashirin da d'aya yanzu take gani, to kullum sai ta takali sheikk Ahmad sunyi ta, domin kuwa shi Auta tasu tazo d'aya da shi sosai, hakan yasa da wuya aji ta fad'i ai'bun sa. Yayin da Sheikh Ahmad kuma abun ya shafi har matar sa, domin kuwa kullum sai ta ai'bata ta tana kushe hallitar jikin ta, duk da kasancewar ta kyakkyawa sosai kuwa tamkar shi. Yanzu haka gaba d'aya Ishak' da Aishatu sun aurar da 'ya'yan su mata. Haka kuma bata sake haihuwa ba tun bayan haihuwar Auta. *ENGLAND* Da matuƙar ƙarfi Billy ta rumtse idanuwan ta sabo da abun da ta gani, jikin ta na wata irin karkarwa! Yayin da ita kuma wannan baturiyar ta k'ara bud'a tafukan hanneyan ta tana mai tallabo k'eyar Yarima Asad da su. Kana ta farasa harshen ta tana mai lasar saman jajayen lips d'in sa da suke matuk'ar birge ta da shi, kafin daga bisani kuma ta fara k'ok'arin tura harshen nata cikin bakin sa. A hankali ya d'ago tafukan hannayen sa duka biyu shima, yana mai dire su akan jan gashin dake kanta, kana ya tallabo k'eyar ta, yana mai zaro tongue d'in sa ya hard'o nata da shi, tukun sukayi wani irin had'e bakunan su wuri d'aya suna masu fara kissing d'in junan su da sauri da sauri. A kuma dai-dai lokacin Billy ta sake bud'e idanuwan ta akan su. Da matuk'ar sauri ta durk'ushe k'asa tana mai sa tafin hannun ta-ta toshe bakin ta da shi, sabo da wani irin azabbaben kuka mai cin rai da taji ya k'wace mata. Wani irin k'una take jin ranta da zuciyar ta suna yi mata. Lokaci d'aya idanuwan ta suka kad'a sukai jajajir yadda kasan gauta, yayin da jikin ta kuma ke wata irin karkarwa tamkar wacce aka sanya acikin ruwa. Cikin zafin rai tayi hurgi da jakar dake rik'e a hannun ta zuwa gefe, tukun ta fara dukan kanta da hannu bibbiyu, tana mai jin tamkar ta tashi taje ta shak'e wuyan baturiyar nan har sai taga ta dena numfashi, sabo da masifar kishin da yake caccakar zuciyar ta. Kana kuma ta k'udirtarwa ranta waji bine itama taje ta same sa daga yau, da ta tsaya tana kallon wasu matan banzan na mu'ama da shi akan idanuwan ta, sai dai kome zai yi mata yayi mata. A fannain su Yarima Asad kuwa cikin tsantsar shauk'i'n da suka tsinci kansu a ciki suka cigaba da abun da suke yi. Kafin daga bisani kuma ya janye tafukan hannayen sa daga saman gashin baturiyar yana mai mayar da su zuwa kan k'ugun ta. Kana ya fara zamar da jikin sa daga kan kujerar da yake yana mai d'an ture ta daga kan cinyar sa, tukun daga k'arshe ya jirkitar da ita ta koma k'asa, yayin da shi kuma ya d'ago zuwa saman ta yana mai yi mata rumfa da faffad'an k'irjin sa, suka cigaba da aikata abun su yadda kasan ba afili suke ba, domin kuwa ko kad'an babuwa ta kunyar tattare da su balle haf suji tsoron kar wani yazo ya gansu a haka. Zumbur Billy ta mik'e tsaye tana mai jujjuya kai, sabo da abun da idanuwan ta suka hango mata Yarima Asad yayi, kafin daga bisani kuma ta fara d'aga k'afafuwan ta cikin tsantsar zafin rai da k'unar zuciya, tana mai futa daga cikin wurin da ta lab'e ta doshi gun da suke gadan-gadan. Tana dab da zuwa wurin taja ta tsaya k'am a wuri d'aya, sabo da yadda taga Yarima Asad ya mik'e daga jikin baturiyar nan zumbur, yana mai yin wani irin jifa da ita a k'asa. Tukun ya fara sakin huci yana mai aika mata wani mugun kallo, da idanuwan sa da gaba d'aya suka riga suka canza launi. Kafin daga bisani kuma ya bud'e baki cikin cunkusassar muryar sa yana mai nuna baturiyar nan da yatsa, tare da fad'in. "How many time did i wand you akan karki k'ara kuskuren kai k'azamin hannun ki jiki na, ko kuwa na fad'a miki dan ina d'an tab'a jikin ki shine yake nufin zamu iyayin komai da ke? To bari kiji in fad'a miki, idan ma kina wannan tinanin, ina mai baki shawarar ki gaggauta kawar da shi a cikin zuciyar ki, because of jiki na ba irin jikin da kike tinanin zai iya kusantar ko wace kalar mace bane, kai impact ma babu ita, kuma ba ayi taba a duniya. Dan haka daga yau babu ni babu ke, ko a hanya kika ganni kikai gangancin nuna kin sanni sai na hulak'antaki. Stupid bitch kawai." Ya k'arasa maganar yana mai sakin nishi tamkar wanda ya futo daga filin dambe, ko kuma na tseren gudu, domin kuwa bai saba yin irin wannan doguwar maganar ba ko acikin sanyi, balle kuma yanzu da yayi ta a cikin zafin rai, hakan ne kuwa ya sanya sa yayi bala'in gajiya. Gaba d'aya yayi furucin nasa ne cikin harshen turanci. Kafin daga bisani kuma ya juya cikin tsantsar b'acinrai bayan yaja wani dogon tsaki, yana mai kama hanyar da zata sada sa da d'akin sa na cikin hotel d'in nan. Yayinda ita kuma baturiyar nan ta fashe da wani irin kuka cikin tsantsar tashin hankali, tana mai tsantsar nadamar abun da ta aikata masa, duk da dama tasan baya so, amma sai dai kuma ko kad'an batayi tinanin zai yanke hukuncin rabuwa da ita ba gaba d'aya a lokaci guda, dama ta gwada sa'ar tane ko Allah zai sa ta dace ayau ya yayada yayi mu'amala da ita, amma sai gashi nan kuma gaba d'aya ta kwafsawa kanta lokaci guda, ta yadda har garin neman gira ta rasa ido. Cikin tsantsar tashin hankali ta bud'e baki a lokacin da taga ya juya zai tafi tana mai fad'in. "Please Please Please Prince don't live me, don't live me, don't do this to me, i promise i will never do that again." Ta k'arasa maganar cikin matsanan cin kuka, tana mai rarrafawa da matuk'ar sauri ta kamo k'afar sa da hannun ta. Cak ya tsaya a wurin da yake zuciyar sa na tsantsar tafasa da k'una, tukun daga bisani ya funcike k'afar sa da k'arfi yana mai juyawa ya kwad'a mata wani irin mugun kallon da ya sanya cikin ta kad'awa, ta yadda har sai da taja baya da sauri, tukun daga bisani kuma ya juya yana mai cigaba da tafiyar sa ba tare da yace mata komai ba. Wani irin gigitaccen kuka ta saki tana mai nadamar abun da ta ai'kata masa a ranta. Abun da ya faru kuwa shine, a lokacin da Asad ya dawo saman ta, sosai ya fara aika mata da salon sa wanda yake matuk'ar gigita duk matan da yake mu'amala da su. Lokaci d'aya gaba d'aya taji ta rud'e ta gigice afagen buk'atar sa, sai dai kuma sanin halin sa da tayi ne na baya tab'a wuce hakan shi ya sanya ta biye masa suka cigaba da kssing d'in junan su, yayin da take jin notikan kanta na sake kwancewa, hakan ne yasa tace bara ta gwada sa'ar ta yau ko Allah zai sa ta dace, tunda taga shima d'in yayi nisa sosai a fagen. Hakan ne yasa ta janye tafin hannun ta d'aya a hankali daga gadon bayan sa, tana mai cusa sa k'ark'ashin ta, wato tsakanin jikin su. Tukun a hankali ta kife sa akan k'irjin sa tana mai fara shafawa, kana ta fara matsar da shi k'asa a hankali tana mai masa wani irin wai-waye da shi, a haka har ta kai ga zuwa kan cikin sa. Cikin tsantsar k'warewa a salon iskanci ta cigaba da yin k'asa da hannun ta har ta k'arasar da shi zuwa kan mararsa dai-dai wurin robar wandon dake jikin sa, kana daga bisani kuma ta fara k'ok'arin tura hannun ta ciki. A kuma dai-dai locin Yarima Asad yaji abun da take shirin yi masa, hakan ne yasa yayi saurin janyewa daga jikin ta yana mai hurgar da ita a k'asa. Tukun ya fara aika mata da ruwan masifar sa cikin tsantsar zafin rai, domin kuwa babu abun da ya tsana sama da yaga yarinya na shirin haike masa, to fa daga wannan ranar ko wacece ke yake rabuwa dake, dan ko acewar sa wai har yau baiga macen da takai matsayin da zaiyi irin wannan mu'amalar da ita ba. Yayinda su kuma su Al'amin da suke yi yake musu kallon shasha-shu marasa aji, inda su kuma suke ce masa daga su har shi d'in basu da bam-banci ko a wurin Allah, tun da dai duk kalar abu d'aya suke ji idan sunyi, dan haka idan zai warema ya cire girman kai ya mori rayuwar sa yayi, idan kuma bazai ba to karya k'ara sanya musu ido, domin kuwa sunfi k'arfin su tsaya a iyakar jagwal-gwalo. Gaba d'aya sun manta da kalar girman zunubin da suke aikatawa. Wata irin mahaukaciyar dariya Billy ta kwashe da ita daga wurin da take, tana mai kallon baturiyar nan da take aikin rusar kuka zaune a k'asa. Tukun daga bisani kuma ta fara d'aga k'afafuwan ta cikin tsantsar farin ciki, tana mai dosar wurin da baturiyar nan take. Tsaye tayi a kanta tana mai aika mata da wani irin matsiyacin kallo, kafin daga bisani kuma ta buga wata irin k'wafa da matuk'ar k'arfi, tana mai juyawa ta tafi, zuciyar ta cike da k'udirin tunkarar Yarima Asad a gobe da nata salon ba gudu baja da baya, babu kuma sauran wani b'oye-b'oye. Yayin da ita kuma wannan baturiyar ta bita da kallo tana mai mamakin abun da yasa tazo gaban ta tsaya, kana kuma tayi mata tsaki da zata tafi, sai dai kuma damuwar da take ciki a yanzu ta rabuwa da Asad tafi bak'in ciki akan abun da Billy tayi mata, shi yasa ma bata bita taji dalilin ta nayin hakan ba, sabo da ba itace a gaban ta ba yanzu. A b'angaren Yarima Asad kuwa cikin tsantsar zafin rai da tafasar zuciya ya murd'a handle d'in k'ofar d'akin yana mai tura kansa ciki, tukun ya mayar da ita ya rufe gam. 'Dan madaidacin falo ne mai matsakacin girma da ya gaji da had'uwa. Duk da dai ba cike yake da kayan tarkace a cikin sa ba. Wasu irin itallian chair's ne masu azabar kyau zagaye a cikin d'akin. Sai wani d'an farin mini freg da yake kafe a wuri d'aya, yayin da k'asan d'akin kuma ya kasance shimfid'e da wani irin lallausan capet kalar yadin kujerun, daga saman capet d'in kuma wani glass center table ne a jiye a wurin. Tun daga bakin k'ofar ya fara cire guntayen kayan jikin sa yana mai fatali da su akan hanya, a haka har ya k'arasa cikin bathroom d'in da ya gaji da had'uwa, a lokacin kawai d'an guntun farin short-nika ne ya rage a jikin sa. Direct ya huce wurin da shower take yana mai zuwa ya kunna ta, tukun daga bisani ya matsa k'ark'ashin ta yana mai lumshe idanuwan sa ruwan ya fara sauka atsakiyar kansa, ba tare da ya cire short-nikan da ya rage a jikin sa ba. Lokaci d'aya ya fara sauke wasu irin tagwayen ajiyar zuciya, sabo da sanyin ruwan da yake sauka akan sa yana harbawa har cikin k'wak'walwar sa, wanda hakan yasa yaji zuciyar sa ta farayin sanyi. Sai da ya d'auki tsayin mintina goma shabiyar ak'ar-k'ashin showar, kana daga bisani ya kauce daga wurin yana mai k'arasa cire sauran sitirar da tayi ragowa a jikin sa, ya koma cikin jakuzie'n da yake cike da ruwan kumfan da ya had'a yayi zaman sa a cikin sa. *K'ASAR MALIN, JAHAR KARFUZ CIKIN BAK'AR MASARAUTA.* Suna k'arasawa gaban ruwan wannan badakaran ya kamo k'afafuwan Bir duka biyun da hannun sa, tukun ya d ago su sama yana mai mayar da kansa k'asa, sannan ya d'aga sa daga tsayen da yake yana mai danna kansa a cikin ruwan nan. Take kuwa Bir ya fara wani irn shure-shure, yana mai hahaura k'afafuwan sa da matuk'ar k'arfi, tare da motsa jikin sa, amma sai dai kuma ko alamun k'wacewa baiyi ba daga hannun dank'are-ren mutumin nan mai sufa da samudawa. Sai da suka d'auki kimanin minti goma, tukun wannan badakaran ya zaro Bir daga cikin ruwan, yana mai yadda shi a gefe. Yayin da idanuwan Bir kuma sukayi wani irin kakkafewa, ga cikin sa kuma da yayi matuk'ar girma, alamum ba k'aramun ruwa yasha ba kenan. Da sauri wani badakare yayi kansa gadan-gadan, a lokacin da wancan d'in yayi cilli da shi a gefe. Yana mai k'arasawa wurin da yake, kana ya d'aga damb'areriyar k'afar sa d'aya, yana mai taka cikin Bir da ita. Take kuwa yayi wata irin d'agowa sama, bakin sa na futar da uban ruwa da matuk'ar yawa. 'Daga k'afa badakaran nan ya sake yi da matuk'ar k'arfi, yana mai direta akan cikin Bir. Wata irin k'ara Bir ya saki k'asa-k'asa, bayan wani ruwan ya sake futa daga cikin bakin sa da matuk'ar yawa, yana mai bud'e idanuwan sa tare da kifewa rufda ciki a k'asa. Da sauri d'ayan badakaran ya sake matsawa wurin da yake yana mai d'aga k'afar sa d'aya yayi wani irin k'wallo da Bir. Ai kuwa yadda kasan iska ta d'aga leda haka Bir yayi gefe yana mai zuwa ya gwaru da wata bishiya, tukun ya fad'i a k'asa. Wani irin jini ne mai matuk'ar gudu ya b'alle daga cikin gashin Bir yana mai tsiyayowa akan fuskar sa. Yayin da shi kuma yake ta sakin nishi da k'yar, yana mai juya juyi a wurin da yake cikin tsantsar azabar da take ratsa jikin sa, ga kuma idanuwan sa da suka furfuto waje tsabar wahala. A tare gaba d'aya dakarun nan suka sake d'aga k'afafuwan su suna masu nufar inda yake. Suna k'arasawa wurin da yake gaba d'ayan su suka zare mahaukatan bulalan su suna masu fara dukan sa da su ta ko ina, yadda kasan sun samu jaki, kai ko jaki ma bai can-canci amasa irin dukan nan ba kasancewar sa abu mai rai, sai dai ace gini ko dutse. Sai da suka yi masa jina-jina, ta yadda har ya zamto sai da k'yar yake iya motsi a wurin da yake, tukun babban cikin su ya kalli k'aramin su yana mai fad'in. "Kayi maza kaje ka sanarwa da Gimbiya cewar anyi tamkar yadda tace, umarnin ta na gaba kawai muke jira." Ya k'arasa maganar yana mai sa k'afa ya shuri Bir da ita. Yayin da shi kuma wannan badakaran da ya aika ya juya da matuk'ar sauri yana mai nufar hanyar da zata sadasa da wurin da Gimbiya Tasmir take. A b'angaren Gimbiya Tasmir kuwa cikin tsantsar zafin rai da k'unar, zuciya ta cigaba da tafiya da matuk'ar sauri tana mai dosar hanyar da zara sadata da b'angaren su. Sosai takejin zuciyar ta na wani rin k'una da tafar fasa idan ta tuna yadda Bir yayi mata k'uri da ido, har da su busa mata iskar bakin sa akan fuska. Wata irin tafar-fasa take jin zuciyar ta nayi mata tsabar b'acin rai, lokaci d'aya taji bata da wanda ta tsana sama da shi. Babu abun da ke k'ara k'ona mata rai sai yadda zuciyar ta ta dinga wani irin bugu a gaban sa, babban abun takaicin kuma shine tana barin wurin da yake d'i taji ta dawo gudu dai-dai, hakan ne yasa taji aranta tana mai son sanin dalilin da yasanya taji haka dan ta tsaya a gaban sa, tana son sanin me ya taka, wana kalar sihiri gare sa da har kallon sa ya sanya ta fad'uwar gaba. Har ta kusa k'arasawa b'angare nasu taja ta tsaya a wuri d'aya, ba tare da ta cigaba da tafiyar ba, tana mai rumtse idanuwan ta da matuk'ar k'arfi, sabo da tinanin da ya fad'o mata aranta, na sanin muddin ta shiga cikin gidan nasu a wannan yanayin na b'acin ran da take dole ne tasan sai wani daga cikin a halin ta ya tambaye ta dalili, wanda idan hakan ta faru take ganin bata da amsar da zata bayar, domin kuwa ba zata tab'a iya bud'e baki tace wani k'ask'antaccen Bawa ne ya b'ata mata rai, sabo da hakan zai zamto babban abun kunya mai muni ne gare ta, wato a matsayin ta na d'iyar Sarki Barbaru yar lelen sa, kuma ace Bawa ya b'ata mata rai, harya sanya bak'in ciki a ckin ranta ta yadda har ya bayyana akan fuskar ta kowa ya gani. Da matukar sauri ta juya baya zuciyar ta na cigaba da tafar-fasa, sabo da wannan tinanin da ya fad'o ranta, domin kuwa data fad'awa wani abun da ya faru da ita cikin 'yan gidan su, tana jin gwanda ta kwana ba a cikin sa ba. Hakan ne yasa ta d'auki hanyar wani lambu da yake acan bayan b'angaren su, wanda nan d'in ma dama yana d'aya daga cikin wuraren da take zama domin hutawa a lokuta da dama, kasancewar ba k'aramun dad'in wurin take ji ba. Kan wata had'ad'd'iyar kujerar gini ta zauna akai, tana mai d'ora k'afa daya akan d'aya, tare da lumshe kyawawan idanuwan ta. Zaman ta baifi da minti Ashirin ba a wurin wannan badakaran da aka aiko sa wurin ta ya k'araso wurin, kasancewar nan d'in ne wurin da ya fara yowa d'in dama, sabo da sanin da yayi na zai iya cin karo da ita a wurin, tunda wurin zaman ta ne dama. Tun daga nesa da ya hange ta zaune akan kujera ya juya baya da sauri, tukun ya fara tawowa da baya da baya yana mai yowa wurin da take, yana mai k'arasowa kusa da ita ya juya kansa sunkuye a k'asa yana mai fad'uwa k'asa wanwar yayi ribda ciki, kana daga bisani kuma ya tashi yana mai cake guiwoyin sa a k'asa, sannan ya bud'e baki cikin k'ank'antar da murya yana mai fad'in. "Anyi duk abun da kikace ayi ranki ya dad'e, yanzu kawai umarnin ki na gaba muke jira." Ya fad'a yana mai yin shiru tare da k'ara sunkuyar da kansa a k'asa. Yayin da ita kuma Gimbiya Tasmir take ta aikin karkad'a k'afarta ba tare da ta bud'e idanuwan ta ba har lokacin. Kana daga bisani bayan shafewar mintina bakwai da gama maganar tasa, ta d'aga masa tafin hannu ba tare da tace komai ba. Hakan da ya ganine ya sanya sa mik'ewa tsaye da sauri, tukun ya bud'e baki yana mai fad'in. "An gama ranki ya dad'e, na barki lafiya." Kana ya juya cikin sauri, yana mai dosar hanyar da ya biyo yazo wurin, domin kuwa tana nufin asake sane da da'ga hannun da tayi, sabo da tinanin da tayi na karta koma wurin kallon fuskar sa ya sanya ranta ya sake b'aci, duk da yadda tayi niyyar zuwa ta gansa bayan an gama masa hukunci a d'azu, shiyasa kawai ta bada izinin asake sa, domin kuwa tariga da ta sani tunda har suka ce an gama, to tasan anyi fiye da yadda take zato ma, wannan dalilin ne ya sanya ta bada izinin a sake san, sabo da tariga da tasan ko yanzu ya gane bam-bancin dake a tsakanin su. Cikin 'yan k'alilan lokaci wannan badakaran ya k'arasa wurin da 'yan uwan sa tare da Bir suke. Tukun ya bud'e baki yana mai fad'in. "Tace asake sa kawai." Hakan da Babban cikin nasu yaji ne ya sanya sa sake d'aga gundumemiyar k'afar sa d'aya, yana mai k'ara yin k'wallo da Bir, tukun suka juya suna masu yin tafiyar su. Yayin da shi kuma Bir ya sake yin sama tukun ya fad'o k'asa, sannan ya fara shirin tashi daga kwancen da yake, cikin tsantsar azabar da yake jin tana ratsa ko ina na ilahirin jikin sa, dan kuwa hatta da idanuwan sa sai da k'yar yake iya bud'e su, ga kuma jini da yake ta zuba a jikin sa. Jin da yayi ya kasa tashi zaune ne ya sanya sa fara jan ciki a wurin da yake, yana mai nufar hanyar da zata sada sa da b'angaren su na bayi, cikin tsantsar azabar da ke cigaba da ratsa jikin sa, amma a hakan fuskar Gimbiya Tasmir kawai yake hange acikin idanuwan sa, tare da d'an k'aramin bakin ta, da kuma dogon hancin ta, yana mai jin ina ma zai sake arba da ita yanzu a gaban sa, domin kuwa ko kad'an baiji ya gaji da ganin kyakkyawar fuskar ta ba, wacce ada bai tab'a tinanin haka take da kyau ba, sai yau da suka yi kusanci da ita dab da dab. Cikin tsantsar tashin hankali su Mauzum sukayo wurin da yake suna masu sakin Ihu tare da kiran sunan Iya, sabo da hango sa da sukayi daga can nesa yana tawowa da jan ciki, ga kuma jini dake bin jikin sa, dama kuma tini tun d'azu an kawo musu labarin ya had'u da Gimbiya bai gudu ba, har hankalin iyar bayi ya tashi. Cikin tsantsar rud'u Iyar Bayi ta futa daga cikin d'an-d'akin ta tana mai gyara d'aurin d'an guntun k'yallen da yake a k'ugun ta. Tukun tayi wurin da ta hangi Bir su Mauzu na shirin d'aukar sa, hankalin ta a tsantsar tashe. Yayin da su kuma su mauzum sukayo wurin da take hannun su d'auke da Bir, gaba d'ayan su suma a rud'e. A k'ark'ashin inuwar Bishiyar darbejiyar da take a gaban d'akin Iyar Bayi suka a jiye Bir. Yayin da Iyar Bayi kuma tayi saurin matsawa kusa da shi jikin ta na tsantsar karkarawa, tukun ta d'ago kansa da tafukan hannayen ta tana mai d'ora sa akan cinyar ta. Kana ta shafa lallausar sumar da take kwance a kansa, tana mai fad'in. "J...............✍ *BAK'AR MASARAUTA* *NA* UMAR FARUQ*D* *PAGE 26* "Jarumi! Jarumi!! Jarumi!!!" Iya ta faɗa cikin tsantsar ruɗu, tana mai shafa lallausar sumar dake kansa tare da bin burɗikan bulalan da suke kwance a jikin sa da idanuwa. "Me yaja maka Jarumi na? Akan me zaka shiga harkar Gimbiya bayan kasan ita ɗin ba tsaran ka bace ba? Wayo ni, wayyo ni na shiga ukku na lalace." Iyar bayi ta sake faɗa a tsantsar ruɗe tana mai jijjiga Bir, gaba ɗaya hankalin ta idan yayi dubu sai da duka ya tashi, domin kuwa tana yiwa Bir wata irin soyayya, fiye da wacce ta kewa duka sauran yaran data raina, tana mai jin sa a cikin ranta tamkar ita ta tsugunna ta haife sa, ita kanta wasu lokutan har mamakin kalar soyayya da take yiwa Bir ɗin take, amma idan ta tuna da itace ta riƙe sa tun ranar da yazo duniya, ta kula da cinsa shan sa wankan sa da komai nasa, sai taga ai dole ne ta jisa a ranta. Shi yasa duk wata damuwarsa take zamtowa tata damuwar itama. Da matuƙar sauri ta jayue kan Bir daga cinyar ta tana mai a jesa a ƙasa, tukun ta miƙe cikin tsantsar ruɗu tana mai kama hanyar ɗakinta. Ko minti biyar ba tayi ba da shiga ɗakin sai gata nan ta futo hannun ta ɗauke da ƙwarya, tana mai sake yowa inda suke. Cikin ƙanƙanin lokaci ta zuba duka ƙullikan magun-gunan data ɗauko na ciwukan a cikin ruwan da yake a cikin ƙwaryar. Sannan ta fara ɗibar ruwan da hannun ta tana mai watsawa Bir shi a jiki. Yayin da gaba ɗaya wurin kuma ya kasance zagaye da ƴan uwan su Bayi suna ta kallon su. Shi kuwa Bir lumshe idanuwansa yayi, yana mai jin yadda ruwan ke ratsa duka ciwukan jikin sa. Amma ko kaɗan ba sune damuwar sa ba, asalima babu abun da yake gani a cikin idanuwansa face kyakkyawar fuskar Gimbiya Tasmir. Yayin da yake ganin ɗan ƙaramin bakin ta a cikin idanuwan sa a lokacin da take motsa sa tana tambayar sa waye shi. Lokaci ɗaya wani irin murmushi ya suɓuce masa ta gefen baki, sabo da tino yadda ranta yayi tsantsar ɓaci da yayi, domin kuwa ba ƙaramun kyau yaga ta sake yi masa ba a hakan. Ji yake inama ace yanzu ma idan yayi wurin zai sake ganin ta, tabbas da babu abun da zai hana sa sake tsayawa a wurin, domin ya ƙara arba da kyakkyawar hallitar ta. Sosai Iyar Bayi ta shafewa Bir duka jikin sa da maganin nan. Kana bayan ta gama ta ɗago kansa tana mai buɗe baki tace. "Shin ma mene ya kai ki shiga sabgar Gimbiya Jarumi na? Yanzu duba fa kaga irin illar data sanya aka yi maka." Ta ƙarasa maganar cikin sanyi, idanuwan ta a kan fuskar Bir da take ganin yana ta sakin murmushi lokaci bayan lokaci. A hankali Bir ya fara buɗe idanuwan sa har ya buɗe su duka akan fuskar Iyar Bayi. Tukun ya saki wani irin murmushin gefen baki yana kallon ta, kana ya buɗe baki cikin yin ƙasa da murya, ta yadda ita kaɗai zataji abun da zaice mata, yana mai faɗin. "Rabo ne Iya ta." "Rabo kuma Jarumi, wannan wana irin rabo ne haka mai tafe da tsantsar tsautsayi?" Iya ta faɗa tana mai kallon Bir, tare da mamakin jin furucin da ya futo daga cikin bakin sa. "Ba zaki taɓa fahimta ba a yanzu Iyata, amma tabbas akwai lokacin yana nan zuwa, wanda ba iya ke kaɗai ba kowa ma zai fahimta." Ya ƙarasa maganar yana mai sake lumshe idanuwan sa, tare da gyara kwanciyar kansa akan cinyar Iyar Bayi. Yayin da ita kuma tayi sakato tana mai binsa da idanuwa, fargaba da tsoron abun da yake shirin aikatawa na cika zuciya da ruhinta, domin kuwa tasan halin ɗan nata, duk abun da yace zaiyi to fa zaiyi san da gaske bada wasa ba. "Koma dai mene ne Jarumi, na roƙeka daga yau akan karka ƙara cewa zaka tsaya akan hanyar Gimbiya tamkar yadda kayi yau, domin kuwa ban shirya yin kukan rashin ka ba anan kusa." Cewar Iyar bayi tana mai cigaba da shafa kansa. *ENGLAND* Cikin tsantsar farin ciki Billy ta koma mazaunin su. Ko da ta koma zaune ta samu Zee a gefen bed tana kwalliya, da alamar futa zatayi itama. Inda take bata kalla ba ballan tana har ta bata labarin abun da ya faru, domin kuwa tun da ta ga Zee bata bata karfin guiwa ba akan son da take yiwa Yarima Asad gaba ɗaya ta dena bata labarin sa, sannan kuma ta kudurta a ranta cewar sai ta bata mamaki, sai ta tabbatar mata da cewa ita Billy'n da ban take da sauran matan, haka kuma tun da ta zo duniya bata taɓa neman abu ta rasa -sa ba. Yayin da Zee kuma ta juyo ɓarin da Billy take fuskar ta ɗauke da far'a, tana mai faɗin. "To ya dai Beb, ina fatan dai yau an dace ko?" Ta ƙarasa maganar tana mai gumtse dariya a cikin bakin ta. Yayin da ita kuma Billy ta kalle ta tana mai faɗin. "Uhm!" Kawai. Kana tayi shiru tana mai ɗaukar wayar ta ta fara shafata. Miƙewa Zee tayi tana mai fucewa daga cikin room ɗin gumtse da dariya a cikin bakin ta, yayin da cikin zuciyar ta kuma takewa Billy kallon ƴar wahala. *WASHEGARI* Da mafarkin YarimaAsad Billy ta kwana, kamar yadda ta kwanta da tinanin sa a ranta. Hakan yasa yau tana ta shi da safe ta shirya shaf-shaf cikin shigar doguwar riga tare da ɗan ƙaramin mayafi akan ta, tana mai fucewa daga cikin room ɗin su ba tare da ta yiwa Zee ko sallama ba. Direct ta huce wani haɗaɗɗen wuri da akayi sa domin gyaran gashi, tun daga kan na maza har zuwa na maza. Sosai wuri yayi bala'in haɗuwa, domin kuwa gaba ɗayan sa anyi sa ne da glass. Ba tare da ɓata lokaci ba aka fara yi mata gyaran gashin tare da wankin ƙafafu, kasancewar wuri ne babba da yake cike da wadatattun ma'aikata, shi yasa ba afiya haɗa dogon layi ba ana jira kafin azo kan mutum. Cikin lokacin da bai zarce awa ɗaya ba aka gama yi mata gyaran gashin nata tare da wankin ƙafafuwan, tukun ta zauna wata baturiya ta fara tsantsara mata wasu irin ƴan mitsi-mistin kitso da gashin dokin da jelolin sa suke saukowa har zuwa gadon bayan ta. Sai da suka ɗauki kimanin awa huɗu suna abu ɗaya tukun aka gama, kuma wai a hakan ma sabo da an yiwa kan nata rubdugu ne, domin kuwa bayan waccan da ta fara yi mata har da wasu matan guda biyu ne suka ƙaru akan ta, wato dai mutum ukku ne suakyi mata kitson. Misalin ƙarfe ukkk na rana ta dawo mazaunin su. Zaune ta tadda Zee akan kujera tana cin abinci. Da sallama ɗauke abakin ta-ta shigo ɗakin. Kana ta huce zuwa kan dining table ɗin da ta hangi food flask ajiye a kansa, tana mai zuwa ta fara zuba abincin da yake ɗauke a cikin su. Yayin da Zee kuma ta juyo gare ta tana mai faɗin. "Ke ko Billy wannan wane irin gyaran kai ne aka miki haka mai jan mugun lokaci." Ta ƙarasa maganar tana mai ture plate ɗin dake kan cinyar ta, tukun ta tashi tana mai dosar wurin da Billy take. Yayin da ita kuma Billy ta buɗe baki daga wurin da take tana mai faɗin. "Da yake ba iya gyaran kan kawai akayi ba, har kisto sai da aka yi." Ta ƙarasa maganar tana mai zame mayafin kanta kitson ya bayyana. "Kai masha Allah, kinga yadda kitson yayi bala'in haɗuwa kuwa Beb. Kai tukunna ma, wai meke faruwa ne haka da na ganki tun jiya kina ta wasu gyara-gyare?" Zee ta faɗa daga wurin da take tsaye idanuwan ta akan kitson Billy, da yayi matuƙar tafiya da ita. "Ba zaki gane bane Beb ko nace zan miki bayani I know, but just wait and see, ina mai tabbatar miki da sai na baki mamaki a yau -yau ɗin nan." Billy ta faɗa in serious toungue, tana mai sakarwa Zee murmushi. Yayin da Zee kuma ta jijjiga kai daga wurin da take tsaye, sabo da fahimtar inda kalaman Billy suka dosa da tayi. Kana daga bisani ta buɗe baki tana mai faɗin. "Can't wait to see, but firstly ina miki fatan Al'khairi." Ta ƙarasa maganar tana mai komawa kan kujerar da ta tashi ta zauna, tare da mayar da idanuwan ta kan tv'n da take kallo. Misalin ƙarfe huɗu na yamma dai-dai Billy ta futo daga cikin bathroom. Ɗaure take da wani lallausan farin towel a jikin ta. Yayin da hannun ta kuma yake riƙe da wani ɗan ƙarami tana mai tsane ruwan jikin ta da shi. Direct ta huce gaban dressing mirrow ɗin da yake cike danƙam da kayan kwalliya kala-kala. Kujerar da take ƙarƙashin sa ta janyo tana mai zama akan ta, tukun tayi wurgi da ɗan ƙaramin towel ɗin da yake riƙe a hannun ta a ƙasa. Kana ta janyo mayukan da take shafawa tana mai fara matso su a cikin tafin hannun ta, tukun ta murza su, kana ta shafe sa akan lallausar fatar jikin ta da take ta faman glowing, alamun ba ƙaramun daɗi ake jiyar da ita ba. Cikin ƙan-ƙanin lokaci ta gama mutsika mayukan, tare da tura-rirrikan jikin da take amfani da su a jikin ta, kasancewar lokacin zaman Asad ya kusa, shi yasa take komai cikin sauri. Ba tayi wata kwalliya ba mai yawa akan fuskar ta, domin kuwa powder kawai ta shafa tare da lips bam akan laɓɓan ta, sai kwallin da ta sanya acikin idanuwan ta, sabo da jin labarin da tayi na cewar kwalliyar cika fuska bata birge Asad ko kaɗan a binciken da tayi akan sa. Mayar da duk abubuwan da tayi amfani da su tayi zuwa mazaunin su, tukun ta miƙe tsaye daga kan kujerar da take akai, tana mai juyawa ta doshi wurin da wadrobe ɗin su take. A gaban haɗaɗɗiyar wadrobe ɗin ta tsaya tana mai ɗora hannun akan murfin ta ta buɗe sa, sannan ta fara bin sababbin ƙananan kayan da suke saƙale a cikin ta da idanuwa. Ta ɗauki tsayin mintina huɗu tana kallon kayan, tukun daga bisani ta miƙa hannun ta zuwa ciki tana mai ɗorasa akan wata haɗɗaɗiyar baƙar riga mai tsananin kyau, da tsayin ta zai iya kai mata har guiwa idan tasa ta. Ɗauko ta tayi tana mai ajiye ta a gefen gado, tukun ta sake mayar da hannun ta ciki tana mai zaro wani white roba jeans shima sabo fidigil, kana ta ciro wani ɗan ƙaramin mayafi da ya kasance fari shima. Sannan ta rufe wardrobe ɗin tana mai dawowa gaban gadon ta tsaya. Ɗaukar rigar tayi tana mai miƙar da ita tsaye tare da jingina ta a jikin ta, tukun ta girgiza kai tana mai sakin murmushi, sabo da sanin da tayi na dole ne ma rigar tayi mata kyau, kamar yadda ta kasance mai kyau itama. Kafin daga bisani kuma ta fara ƙoƙarin zira rigar a jikin ta, bayan ta sanya iner wear's a farko. Sannan ta zame towel ɗin jikin ta tana mai ɗauko wandon shima ta sanya sa. Sosai kayan suka yi matuƙar kama jikin ta-ta ko ina, kasancewar su gaba ɗayan su roba ne. Dauke rigar take da fararen botura masu matuƙar kyau a gaban ta da bayan ta, yayin da daga saitin ƙugun ta kuma take ɗauke da bell ajikin ta. Shi kuwa wandon gaba ɗaya yabi ya matse mata jiki tamkar dama da shi aka hallito ta. Tayi bala'in kyau cikin shigar iyakar kyau. Tafiya tayi zuwa wurin da take ajiye takalmanta da jakun kunan ta, tana mai sa hannu ta ɗauko wani baƙin hill shoe da yake ɗauke da igiyoyi ajikin sa, tare da ƴar ƙaramar baƙar jaka mai tsananin kyau da ta kasance mahaɗin sa. Tukun ta riƙe su a hannun ta tana mai dawowa wurin da mayafin ta yake a jiye shima ta ɗauke sa ta koma gaban dressing mirrow da su. Tsaye tayi a gaban madubin tana mai kama uban gashin dokin da yake kitse akan ta, kana ta sanya masa fararen riborm masu tsanin kyau, sannan ta sake sa ya zubo har kan gadon bayan ta, tukun ta durƙusa ƙasa tana mai cire igiyoyin takalmin nata mai tsanain tsini, ta sanya ƙafafuwan ta a cikin sa. Kana ta sake ɗagowa tana mai ɗaukar mayafin ta ɗora sa akan ta, sannan ta tattare sa daga gaban ƙirjin ta ya zamto a bayyane, tana mai watsa jelolin sa baya. Iyakar kyau tayi kyau, hakan yasa ta fara bin jikin nata da ruwan turarruka tana mai kallon kanta a cikin madubin, tare da sakin murmushi, domin kuwa ita kanta ta yaba da haɗuwar tata ba kaɗan na. Yayin da a zuciyar ta kuma take ta saƙa abubuwan da zata jewa Yarima Asad da su, wanda take tinanin Insha Allah bazai watsar da ita ba. Cikin takun ta na tsantsar ji da kai ta fara ɗaga ƙafafuwan ta tana mai nufar falon su. Ko da ta ƙarasa zuwa cikin falon bata samu Zee aciki ba, hakan ne yasa ta ɗan taɓe baki, tana mai fucewa gaba ɗaya daga cikin sa. Acan ɓangaren Yarima Asad kuwa, misalin ƙarfe huɗu da rabi ya gama shiryawa tsaf cikin shigar sa ta yau da kullum, wato dai black three quarter tare da wata ƴar yololuwa bluen t shirt da tayi matuƙar kama jikin sa, ta yadda har ake ganin gaba ɗaya surar jikin nasa a fili, sai dai kuma fa kwata-kwata baya yiwa kaya sawa biyu, wato da zarar yasa su yau shikenan kuma ya gama da babin su sai wasu sababbin, wanda hakan kuma yana ɗaya daga cikin abubuwan da Fulani bata so na dan gane da halayyar sa, sabo da ganin hakan da take amtsayin zallar almubazzaranci. Wasu tausasan bluen takalma na fata ya sanya fararen ƙafafuwan sa a cikin su, yayin da tsintsiyar hannun sa kuma ta kasance ɗaure da baƙin agogon fata mai tsananin kyau. Cumb ya ɗauka yana mai gyara lallausar sumar da take kwance akan sa mai tsananin yawa, da tasha wani irin shegen aski da yayi bala'in yiasa kyau. Kana daga bisani ya ajiye cumb ɗin akan mirrow'n da yake tsaye a gaban sa, sannan ya lumshe idanuwan sa yana mai shaƙar daddaɗan ƙamshin turaren da yake futa ajikin sa, wanda baya taba gajiya da shi ako da yaushe. Tukun daga bisani ya buɗe idanuwan nasa yana mai fara ɗaga ƙafafuwan sa ya doshi hanyar waje. Tamkar ko da yaushe yau ɗin ma yana zama akan kujerar nan da take a gaban swimming pool ɗin, kyakkyawar baturiyar da take aikin a wurin ta tawo wurin da yake hannuwan ta riƙe da wani ɗan ƙaramim plate mai tsanain kyau, tare da cup da yake rife da murfi akan sa. "Weldon sir." Baturiyar ta faɗa tana mai dire plate ɗin akan table ɗin da yake a gaban sa. Inda take bai ɗago ya kalla ba ballan tana har tasa ran zai tanka mata. A hankali ta ɗauko mug ɗin da yake ɗauke da coppy a cikin sa tana mai sake matowa gaban sa. Tukun ta ɗan durƙusa tana mai miƙa masa shi. Still dai bai ɗago ya kalle ta ba ya miƙa hannun sa yana mai karɓar mug ɗin, sannan ita kuma ta juya tana mai komawa wurin da ta futo. Acan ɓangaren Billy kuwa tun misalin ƙarfe huɗu da rabi dai-dai ta ƙaraso wurin, sai dai kuma yau ɗin ma kamar ko da yaushe, wurin da take zuwa ta laɓe taje ta zauna. Hakan yasa tun tawowar sa wurin take kallon sa har zuwa yanzu da wannan baturiyar ta bar wurin sa. Cikin tsantsar fargabar rashin sanin yadda zai tarbe ta tasa hannu tana mai gyara kiston da ya ɗan sakko kan fuskar ta zuwa baya, sannan ta miƙe tsaye daga wurin da take tana mai ɗaukar jakar ta ta fara takawa. Yayin da take jin zuciyar ta na wani irin bugu aɗari-ɗari, sai dai kuma ta ƙudirtawa ranta cewar ko wane kalar tsoro zataji ayau ɗin sai ta ƙarasa wurin sa, domin gudun kar ta tsaya sanya wata tazo ta bangaje ta, wannan dalili ne ya sanya tayi shahada yanzu tana mai nufar wurin da yake gadan-gadan. Canza taku tayi a lokacin da taga ta kusa zuwa inda yake, tana mai komwa yin wata tafiya mai tsantsar jan hankali. Yayin da fuskar ta kuma take ɗauke da annuri, duk da ba ƙaramun tsoro ne ke danƙare a ƙasan zuciyar ta ba. Cikin wani irin taku na tsantsar jan hankali ta ƙarasa wurin da yake. A hankali kana kuma cikin wata iriyar murya mai matuƙar sanyi ta buɗe baki tana mai faɗin. "Excuse me." Yayin da idanuwan ta kuma suke kasance ƙur akan sa, ƙirjin ta kuwa wani irin bugu yake wanda ba zai misaltu ba. A fannin Yarima Asad kuwa tun lokacin da ta kusa ƙarasowa wurin da yake ya lura da ita, sai dai ko kaɗan batasan ya ganta ba, sabo da yadda taga ko motsi bai canza ba daga yadda yake ballan tana ya ɗago ya kalle ta, yayin da shi kuma yake kallon ta ta ƙasan ido yana mai jiran yaji abun da tazo da shi ita kuma, kafin ya yanke hukunci. Cikin wani irin salo Billy ta ɗan janyo ƴar kujerar robar da take kafe a gaban table ɗin da Yarima Asad yake, wato wacce take fuskantar mazaunin sa tana mai zama akan ta itama. Tukun ta ɗauki ƙafa ɗaya tana mai ɗora ta akan ɗaya, kana ta lumshe idanuwanta bayan ta ɗan ɗaga kanta sama. Tukun daga bisani ta sauke kanta ƙasa tana mai wara idanuwanta a hankali akan fuskar Yarima Asad, kafin daga bisani kuma ta ɗan juyar da kai gefe tana mai fesar da wata sassanyar iska daga cikin bakin ta, sannan ta sake dawo da kallon ta gare sa, tana mai ƙara buɗe baki cikin wata irin murya tace. "I'm Bilkisu Abubakar Sardauna by Name." Ta ƙarasa maganar tana mai lumshe idanuwanta, yayinda shi kuma Asad ya cigaba da sipping ɗin copy ɗin sa ba tare da ya nuna yasan da zamanta a wurin ba har lokacin. Yayinda azahiri kuma yake aikin kallonta ta ƙasan ido, yana mai mamakin ƙarfin halin yarinyar. Ɗan muskutawa Billy ta sakeyi akan kujerar da take bayan ta sake wara idanuwanta akan fuksar Asad. Kana ta sake buɗe baki cikin tattausan lafazi tana mai ɗorawa da cewar. "I was born in Ƙasar Hausa Wasai state. And then the daughter of Wasai Governor." Ta sake yin shiru tana mai ɗan sauke numfashi ƙasa-ƙasa, tare da jifan sa da wani irin shu'umin kallo ta ƙasan idanuwa. Yayinda shi kuma Asad ya janye mug ɗin dake riƙe a hannun sa daga kan bakin sa, kana ya dire sa akan table ɗin nan, sannan ya ɗago kai a hakanli yana mai kai idanuwansa kanta cikin wani irin kallo, azahirin gaskiya tini ya gaji da surutun ta, sa'ar ta ɗaya ma shine ƙasa-ƙasa take maganar itama, sannan kuma aɗan kallon da yayi mata na ƴan daƙiƙu ya fahimci ba bitch bace ita ɗin, domin kuwa yanayin nutsuwar ta wacce ta ara ta yafa kawai yasa ya kawo hakan aransa, amma banda haka da tini ya dakatar da ita ma. Kana daga bisani kuma ya ɗaga laɓɓan sa idanuwansa akan ta cikin yin ƙasa-ƙasa da murya yana mai faɗin. "Then what nex...." Maganar tasa ta yanke yana mai lumshe idanuwan sa, sabo da hango tawowar baturiyar budurwarsa ta jiya da yayi ta nufo wurin da suke cikin tsantsar fushi. Hakan ne ya sanya sa lumshe idanuwansa yana mai tafiya tinanin abun da zaiyi, wanda zai ƙona mata rai tayi nadamar zuwa wurin yanzu-yanzu. Yayinda ita kuma Billy ta ƙara gyara zaman ta akan sit ɗin da take tana mai fuskantar sa, tare da zumuɗin jin abun da zai futo daga bakin sa, domin kuwa tana tinanin tarkon ta ya kama sa. Acan wurin baturiyar na kuwa sosai taciyo uwar kwalliya cikin shigar wasu irin ƴan iskan kaya da suke kusan ɗaya da babu a jikin ta, danniyar ta na zuwa wurin dan ta bawa Asad haƙuri akan abun da tayi masa ko Allah zai sa ya haƙuran, duk da dai tasan hakan abu ne mai tsananin wuya, amma sai kuma tana doso wurin ta hango wata zaune a gaban sa. Lokaci ɗaya kuwa taji wani irin baƙin ciki tare da mugun kishi sun zo sun tokare mata aƙawon zuciya. Bata sake jin ranta ya ƙara matuƙar ɓaci ba sai da ta ƙara kusanto wurin da ta fahimci wacce take zaune agun, wato wannan yarinyar ta jiya da tazo kanta tayi mata tsaki tai gaba, hakan yasa ta fahimtar cewar sonsa take itama, shi yasa jiya har tayi mata tsaki ta huce. Hakan kuwa shi yayi matuƙar harzuƙata, har bata san lokacin da ta durƙusa ƙasa ba tana mai zame takalmin da yake sanye aƙafar ta wanda ya kasance mai matuƙar tsini da tsayi, tana mai riƙo sa a hannunta ta nufo wurin Billy gadan-gadan. Ita kuwa Billy ko kaɗan bata san da tawowar ta ba, domin kuwa hankalin ta gaba ɗaya yana kan Asad ne da take jiran taji yace wani abu. Da wani irin ƙarfi baturiyar nan ta ɗaga tsinin takalmin ta dai-dai lokacin da ta ƙaraso gaban Billy tana mai saita goshin ta da shi, tare da faɗin. "Who the h..." Maganar tace ta tsaya, sabo da yadda taga Yarima Asad yayi wani rin miƙewa tsaye a matuƙar zabure, yayinda Billy kuma ta juya da matuƙar sauri tana mai kai idanuwanta ɓangaren da tajiyo muryar nan, wanda hakan kuma yayi dai-dai da isowar tsinin takalmin gab da goshin ta. Da matuƙar ƙarfi ta rumtse idanuwanta jikin ta na matuƙar rawa, sabo da tabbatarwar da ta riga tayi na an riga da anji mata ciwo. Amma ba zato ba tsammani kawai sai ji tayi anyi wani irin funcikar ta, tana mai kifawa kan lallausan wani abun da bata fahimci ko menene shi ɗin ba. Hakan yasa ta fara buɗe idanuwanta a hankali, tana mai sauke ajiyar zuciya, har ta buɗe idanuwan nata duka akan faffaɗan ƙirjin sa mai matuƙar taushi, da yayi mata rumfa da hannuwansa duka biyu................✍ _MUN KUSA KAMMALA BOOK 1, KAFIN MU SHIGA BOOK 2 KUMA IDAN MUN DAWO DAGA HUTUN SATI ƊAYA._😅 *BY* UMAR FARUQ*D* *BAK'AR MASARAUTA* *NA* UMAR FARUQ*D* *PAGE 27* Wato dai ya rungume ta ƙam-ƙam a cikin ƙirjin sa. Wani irin farin ciki mara misaltuwa Billy ta tsinci kanta acikin sa, hakan ne yasa ta sake maƙal-ƙale sa gam-gam, tana mai sake kwantar da kanta akan ƙirjin sa, yayin da daddaɗan ƙamshin turaren sa ke dukan hancinta yana ratsa har tsakar ƙwaƙwalwar ta. Shi kuwa Yarima Asad tsaye yake a wuri ɗaya rungume da ita a ƙirjin sa, yana mai aikawa wannan baturiyar wani matsiyacin kallo mai kaɗa hanjin ciki. Ita kuwa wannan baturiyar cikin tsantsar baƙin ciki da takaicin yadda taga Asad ya rungume Billy a gaban ta fashe da wani irin kuka, kafin daga bisani kuma ta kaiwa mug ɗin tea ɗin da yake ajiye akan table damƙa, tana mai sake saita goshi Billy ta jefa mata shi. Amma sai Asad ya sake janye Billy daga wurin da matuƙar sauri, kana ya fara tinanin abun da zaiyi wanda zai ƙara ƙona mata rai fiye da yadda take yanzu, domin ta gane cewar shi ɗin muddin ya riga ya bar abu to fa ya barsa kenan har abadan abada, domin kuwa yana faɗa babu wata mace da ta isa ta ɓata masa rai a duniya, ballan tana kuma har ya rarrashe ta. A wani irin haukace baturiyar nan tayi kansu gadan-gadan, bayan ta saki wata irin ƙara. Hakan da Yarima Asad ya gani ne ya sanya sa yin sauri ya suri Billy gaba ɗayan ta a cikin hannunsa, yana mai yi mata ɗaukar jarirai, ba dan komai ba kuma yayi hakan, sai dan kawai ya ƙara harzuƙa zuciyar ta. Yayinda ita kuma Billy tayi wani irin maƙal-ƙale sa, tana mai sa hannuwan ta duka biyu ta saƙalo wuyan sa da su. Kana tana wani irin sakin kukan ƙaryar da take ƙwaƙulo sa, tana nuna cewar a tsorace take sosai. Yayin da azahirin gaskiya kuma wani irin farin ciki mara misaltuwa ya lulluɓe zuciya da ruhinta, domin kuwa tana ganin tamkar ta riga da ta gama mallakar Asad har abada, hakan ne yasa taji ina ma ace tare da Zee suka zo wurin nan, domin ta ganewa idanuwanta, dan tasan yanzu ko taje ta bata labarin abun da ya faru ba lallaine ta yadda ba. Tabbas yau ɗin ta ƙara tabbatar da cewa ita ɗin mai sa'a ce a duniya, kana kuma ta ƙara yadda da cewar babu wani abu da zai taɓa yi mata wuyar samu muddin taso samunsa a duniya. A ɓangaren Asad kuwa ganin da yayi wannan baturiyar ta sake yowa kansu ne, yasa sa wurga mata wani irin matsiyacin kallo daga wurin da yake. Ƙam ta cake a wuri ɗaya kuwa jikin ta na matuƙar karkarwa, domin kuwa ba ƙaramun firgita tayi ba da irin kallon da yake watso mata. Yayin da shi kuma ya juya yana mai fara ɗaga ƙafafuwan sa yayi gaba, hannuwan sa rumgume da billy tamkar jaririya. Wani irin kuka baturiyar nan ta ƙara fashewa da shi, tana mai ɗora hannuwan ta duka biyu aka tare da durƙushewa a ƙasa. Ita kuwa Billy cikin tsantsar farin cikin da ya lulluɓe ta lumshe idanuwan ta, tukun daga bisani ta buɗe su akan fuskar baturiyar nan, bayan ta zuro kanta ta saman kafaɗar Asad. Kana ta zaro harshen ta tana mai yiwa baturiyar nan da itama take kallon ta gwalo, sannan ta sake mayar da kanta cikin ƙirjin Asad, tana mai lumshe idanuwan ta-ta cigaba da shaƙar daddaɗan ƙamshin turaren sa, da yake saukar mata da wata irin nustuwa da kasala a cikin jiki. Wani irin gigitaccen kuka baturiyar nan ta saki tana mai jin tsanar Billy na sake mamaye zuciya da ruhin ta, ta yadda har take jin zata iya kashe ta muddin zata same ta a hannu. Shi kuwa Yarima Asad direct ya doshi room ɗin sa rungume da Billy a ƙirjin sa. Haka nan shima yaji yarinyar ta ɗan kwanta masa arai, ta yadda har yake ganin zai iya dinga kulata, sai dai kuma ba wai yaji yana son ta bane a zuciya, asalima har yau shi baici karo da wadda takai yaso ta ba a cikin ƴammata. Hannun sa ɗaya ya sanya a cikin aljihun wandon sa yana mai zaro key'n ɗakin, sannan ya zura sa yana mai buɗe sa, kana ya murɗa handle ɗin ƙofar yana mai ƙara tura ta da ƙafar sa, sannan ya danna kansa zuwa cikin ɗakin. Da sauri Billy ta lushe idanuwan ta, sabo da daddaɗan ƙamshin turaren da ya daki hancin ta. Tabbas komai nashi na daban ne, tamkar yadda shi kansa ya kasance na daban, haka kuma komai nashi yayi, kamar yadda shima yayi ɗari bisa ɗari. Ta faɗa a cikin ranta tana mai bin kyakkyawan falon nasa da idanuwan ta daga saman hannun san da take. Shi kuwa Yarima Asad yana ƙarasawa cikin ɗakin ya dire Billy a ƙasa ba tare da yace mata komai ba, asalima ko kallon fuskar ta baiyi ba, sai hucewa da yayi zuwa gaban ɗan mini fridge ɗin da yake acikin ɗakin nasa yana mai buɗe sa, kana ya zaro robar ruwa ɗaya aciki mai matuƙar sanyi, yana mai dawowa ya zauna akan kujerar da take kusanci da shi. Sannan ya buɗe murfin jarkar yana mai kafa bakin ta akan ɗan ƙaramin bakin sa ya fara shan sa. Bashi ya ɗauke kai daga kan jarkar ba har sai da yasha kimanin rabin ta, tukun ya ajiye ta akan ɗan mini center table ɗin da yake agafen sa yana mai lumshe idanuwan sa a hankali, tare da sauke wasu tagwayen ajiyar zuciya akai-akai. Ita kuwa Billy jin da tayi ya sauke ta anan ɗin ne, ba tare da kuma ya tanka mata bane ya sanya ta samun wuri akan kujerar da take akusa da ita, wacce ta kasance tana facing ɗin wacce Asad yake akai ta zauna. Kana ta durƙusar da kanta ƙasa tana mai yin wasa da ƴan yatsun hannun ta. Kafin daga bisani kuma ta buɗe baki a hankali tana mai faɗin. "I'm very sorry please." Sannan tayi shiru tana mai cigaba da wasa da ƴan yatsun hannun ta. Yayin da shi kuma Yarima Asad ya buɗe idanuwan sa a hankali yana mai ɗan ɗaga kai ya kalle ta, kana ya ɗan taɓe baki yana mai mayar da idanuwan sa kan wayar sa. Kafin daga bisani kuma a lokacin da Billy ta fara futar da tsammanin zaice wani abu taji sautin daddaɗar muryar sa yana mai faɗin. "Sorry for what?" Duk da har lokacin bai kalle ta ba. Jin hakan da Billy tayi ne ya sanya ta lumshe idanuwanta a hankali, tukun daga bisani ta buɗe su tana mai ɗago kanta ta kalle sa, sannan ta furta cewar. "Da abun da naja wata tayi maka yanzu mana, tun da nasan da banzo wurin ba da ba zata yi hakan ba." Tayi maganar cikin wata irin murya, wacce take tattare da shagwaɓa a cikin ta. A hankali ya ɗan ɗago idanuwansa yana mai kaisu kan fuskar ta tare da ɗan taɓe bakin sa, tukun daga bisani kuma ya basar yana mai yin tamkar bai kalle tan ba, domin kuwa azahirin gaskiya ko ita bata san ya kalle tan ba. Kafin daga bisani kuma ya furta. "Uhm!" "Please! Please!!" Billy ta sake faɗa tana mai sake marairaicewa, tare da haɗe tafukan hannayen ta wuri ɗaya. "Is ok." Ya faɗa a gajarce, kana kuma a saman lips ɗin sa, yana mai miƙewa tsaye da niyyar shigewa cikin bedroom ɗin sa. Hakan da Billy ta gani ne ya sanya ta miƙewa tsaye da sauri itama, kana ta ƙara yin ƙasa-ƙasa da muryar ta tana mai cewa. "Please can i get your phone number?" Ta ƙarasa maganar a hankali, tana mai fatan Allah yasa kar yace a'a azuciyar ta. Yayinda shi kuma ya cigaba da tafiyar sa yana mai yin tamkar baiji abun da ta faɗa ba. Wani irin sanyi Billy taji jikin ta yayi. Gaba ɗaya murnar da take ta fara komawa ciki, sabo da ganin da tayi ya mata banza tamkar bai san da ita ba yana shirin shigewar sa cikin ɗaki. A fannin sa kuma yaji ta sarai amma yay tamkar baijitan ba, sai da har yaje bakin ƙofar da zata sadasa da cikin bedroom ɗin sa, tukun ya tsaya a wurin yana mai zira hannun sa cikin aljihun sa. Kana ya zaro katin sa wanda yake ɗauke da sunan sa da kuma number sa a cikin aljihun sa, yana mai cilla mata shi daga nan wurin da yake ba tare da ya juyo ba, sannan ya buɗe baki cikin maganar sa da sautin ta bai fiye futa ba, yana mai faɗin. "Zaki iya tafiyar ki yanzu ok." Ya ƙarasa maganar yana mai murɗa handle ɗin ƙofar tare da danna kansa ciki. Yayin da Billy kuma ta buɗe baki cikin tsantsar farin ciki tana mai faɗin. "Thank you Prince." Da ɗan ƙarfi yadda zai jiyo, tukun ta matsa wurin da katin sa yake tana mai durƙusawa ƙasa ta ɗauke sa. PRINCE ASAD Shine sunan da yake rubuce ɓaro-ɓaro da manyan baƙi ajikin katin nasa, yayin da special numbers ɗin wayar sa kuma da suka kasance har guda biyu suka biyu a ƙasan sunan. Cikin tsantsar farin ciki mara misaltuwa Billy ta ɗauki katin, kana ta suri jakarta tana mai juyawa ta kama hanyar waje fuskarta ɗauke da tsantsar annuri. Yayin da take jin zuciyar ta kuma tai haske fari ƙal, kana kuma ta ƙagu ta isa wurin Zee, domin ta ƙara tabbatar mata da cewar ita ɗin daban take da sauran fa, tamkar yadda ta faɗa mata bata yadda ba. Rufe masa ƙofar sa tayi bayan ta fuce daga cikin falon, kana tayi gaba abunta tana mai tafiya wurin da lipter take domin ta sauke ta ƙasa, sannan ta huce mazaunin su. *ƘASAR MALIN, YANKIN JAHAR KARFU CIKIN BAƘAR MASARAUTA.* Sosai jikin Bir yayi matuƙar yin tsami sabo da dukan da yaci. Sai dai kuma ko kaɗan hakan bai sa yaji cewar zai iya haƙura da ganin Gimbiya Tasmir ya gudu idan sun haɗu ba, domin kuwa tun abun ya faru a jiya har kawo yau hoton kyakkyawar fuskar ta bai-bar cikin idanuwan sa ba. Asalima da zarar ya buɗe idanuwan ita yake gani durƙushe a gaban sa tana aiko masa da kallon ta, yayin da ko a cikin baccin sa na daren jiya shima ya kasance ɗauke da mafarkin ta gaba ɗayan sa. A takaice dai lokacin ɗaya yaji ta shiga ransa, sannan kuma zai iyayin komai domin ya samu ko kallon tane yayi. Yana jin wasu irin abubuwa dan gane da Gimbiyar irin waƴan da bai taɓa jin makamantan su ba akan wata tun da yazo duniya. Yanzu haka zaune yake a jikin bishiya, hannun sa riƙe da kwari da gwafar sa yayi shiru shi kaɗai. Lokaci bayan lokaci yake ɗan lumshe kyawawan idanuwansa yana mai sakin murmushi. Wani irin shauƙi yake ji tattare da shi, irin wanda bazai misaltu ba. "Haƙiƙa yanzu na fara shiga harkar ki Gimbiyar mu, koma nace yanzu zan fara shiga, saboda ada ban taɓa sanin haka kike da baiwar kyawu ba sai ajiya. Tabbas jiya kin zamto rana mai daraja a gareni, rana irin wadda ta shiga cikin kundin tarihina ta zauna, ranar da aka dakeni acikin BAƘAR MASARAUTA dukan yayi matuƙar sanyaya mun zuciya. Ranar da na fara ganin kyakkyawar fuska irin wacce ban taɓa yin tozali da makamanciyarta ba. Tabbas zan jure duk wata kalar huya da zaki bani, muddin idanuwa na zasu dinga arba da kyakkyawar fuskar ki, domin kuwa jikina na bani cewar ke ɗin zaki zamto hasken zuciya gare ni a wataran Gimbiyar mu." Ya ƙarasa maganar ƙasa-ƙasa fiye da yadda ya fara ta, yana mai sake lumshe dara-daran idanuwan sa. Yayinda yake jin tsigar jikin sa na wani irin mimmiƙewa, wani kalar yanayi na lulluɓe sa, sabo da hango ta da yayi acikin idanuwan nasa. Kafin daga bisani kuma ya wara su a hankali yana mai mikewa tsaye. Da ɗan ƙarfi ya taune leɓen sa na ƙasa, sabo da yadda yaji gaba ɗaya jikin sa a wani irin kakkame, tukun daga bisani ya fara ɗaga ƙafafuwan sa cikin cizon leɓe, yana mai nufar hanyar da yake fatan ta sake sadasa da hasken zuciyar tasa. A ɓangaren Gimbiya Tasmir kuwa ba ita tabar cikin lambun nan ba jiya har sai da gari ya fara dubu. Shima kuma bawai dan taji zuciyar ta tayi sanyi da abun da ƙasƙantaccen bawan can yayi mata ne ba, sai dan kawai sanin da tayi na yanzu za'a fara neman ta muddin aka duba akaga bata nan. Wata irin tafar-fasa take jin zuciyar ta nayi mata aduk lokacin data tuno yadda bugun zuciyar ta ya sauya a gaban sa, ga kuma gizon da yake ta yi mata acikin idanuwan ta aduk lokacin data lumshe su, a lokacin da yake sakar mata kyakkayawan murmushin sa. Wanda hakan kuma shi yake matuƙar ƙara tinzira ta. Cikin tsantsar baƙin ciki ta doshi ɓangaren nasu, tana mai jin zuciyar ta na cigaba da ƙuna. "Haƙiƙa kana gab da shaƙar numfashin ka na ƙarshe acikin duniyar BAƘAR MASARAUTA, muddin har zaka ƙara kuskuren shiga gona ta, domin kuwa ina mai rantsuwa da ubangiji Gargabilu sai na lalata maka wannan koɗaɗɗen jikin naka. Sai na kassara rayuwar ka, ta yadda ko gobe ance ka sake tsayawa akan hanya ta ba zaka yi ba, wannan alƙawari ne na ɗaukarwa kaina akan ka ƙasƙantacce." Ta ƙarasa maganar da ɗan sauti, tana mai danna kanta zuwa cikin tanƙashshen falon su na alfarma. Tayi sa'a kuwa babu kowa acikin falon tamkar yadda tayi fata, hakan ne yasa ta kama hanyar da zata sadata da corridor ɗin da zai kaita ɗakin ta cikin sauri, gudun kar wani ma ya ganta a cikin yanayin da take yanzu. Ko da dare yayi haka tai ta juyi akan tamfatsen-tsen bed ɗin ta bacci yaƙi ya dauke ta, sabo da baƙin cikin abun da yayi mata da yake cigaba da sukar zuciyar ta. Tun da take arayuwar ta bata san wata aba mai suna damuwa ba sai yau, bata sai meye tinanin ba sai yau, haka bata san ɓacin rai ba sai yau data haɗu da wancan ƙasƙantaccen fitsararren bawan mara kunya, hakan yasa take jin ƙarin tsanar sa na ƙara turnuƙe zuciya da ruhin ta aduk bayan wanzuwar wata daƙiƙar. Ba ita ta samu bacci ya ɗauke taba sai misalin ƙarfe ɗaya da rabi na dare, bayan ita ada ƙarfe takwas da ƴan mintuna ma tayi bacci. Haka kuma ko da ta tashi a yau da tinanin abun da yay mata a zuciyar ta tashin. Hakan ne yasa gaba ɗaya yau ɗin taji bata sha'awar futa ko daga cikin ɗakin ta ko kaɗan, balle har ta sake arba da wata fuskar ta ƙarasa tarwatsa mata zuciya da baƙin ciki. Wannan dalilin ne yasa koda Bir yaje kan hanyar ya zauna har ya shafe sama da awa biyar ba tazo ba. Hakan ne yasa ya miƙe cikin sanyi riƙe da kwari da gwafar sa a hannun sa zuciya duk ba dadi, yana mai komawa ɓangaren su. *ENGLAND* Cikin tsantsar farin ciki mara misaltuwa Billy ta tura kanta zuwa cikin ɗakin su. Hango Zee da tayi zaune akan kujera ne ya sanya ta sakin ihu da matuƙar ƙarfi, tana mai yin kanta a guje tare da faɗawa jikin ta tamkar zata karya ta. Da matuƙar sauri Zee ta ɗago gare ta tana mai faɗin. "A Beb meye haka? Lafiyarki ɗaya kuwa da kike shirin karyawa Dady da Momy Autar su?" "Ke Beb i got him! I got Prince Asad! Finally he is my own know!"............... ✍ _CIKIN ABU UKKU TABBAS DAYA ZAI FARU, WATO DAI KO KU GYARA KU DINGA COMMENTS DA SHARHI, KO KUMA BAKAR MASARAUTA BOOK 2 YA ZAMTO NA KUDI, KO NA DENASA GABA DAYA, SABODA HAR YANZU LABARIN BAI DAU ZAFI BAMA, DAN HAKA ZABI YA RAGE GAREKU. KO A ADENA GABA DAYA, KO KUMA YA SAKE KOMAWA NA KUDI, KO KU FARA COMMENTS DA SHARHI_ *GA MASU BUKATAR SHIGA CIKIN GROUP DIN DA AKE POSTING, COMMENT DA SHARHI SAI KU TUNTUBENI TA WHATSAPP NMBER TA KAMAR HAKA. 08038135929* *BY* UMAR FARUQ*D *BAK'AR MASARAUTA* *NA* UMAR FARUQ*D* *PAGE 28* "Kamar ya kin same sa? Waye kike nufin ya zama naki? Please kiyi mun bayani yadda zan gane, saboda kwata-kwata ban fahimci abun da kalamanki suke nufi ba." Zee ta fad'a cikin wani irin yanayi mai nuni da zallar mamaki da aljabin da suka rufe ta, tana mai sa hannu ta d'ago Billy daga jikin ta, tare da kafe ta da idanuwa. Hakan da Billy taji ne ya sanya ta bud'e zip d'in jakar ta cikin sauri, tana mai zaro d'an katin da Yarima Asad ya hullo mata. Kana ta mik'awa Zee shi ba tare da ta furta komai ba, sai zallar farin cikin da yake kance akan fuskar ta ta yadda har ya gaza b'oyuwa a fili. Cikin sakin baki Zee ta mik'a hannu jiki a matuk'ar sanyaye, tana mai amsar katin ta rik'e sa acikin tafin hannun ta, yayin da idanuwan ta kuma suka kasance k'ur akan katin, kafin daga bisani kuma ta d'ago tafin hannun ta tana mai kai sa kan idanuwan ta ta murza su sosai, a cewar ta ko idanuwan nata basu gane mata rubutun da tayi arba da shi ba akan katin dai-dai, domin kuwa ko a mafarki bata tab'a tinanin Billy zata samu karb'uwa a wurin Yarima Asad ba, duba da irin yawan 'yammatan da suke hauka akan sa, amma ko kallo basu ishe sa ba. Sai dai kuma koda ta sake bud'e idanuwan nata bayan ta janye hannun ta daga kai, da abun da ta gani a farko ta sake yin arba. Wato Sunan Yarima Asad akan katin, tare kuma da jerin numbobin sa. Hakan ne yasa ta juyawa b'arin da Billy take cikin sauri, bakin ta har yana rawa wurin fad'in. "Ya akai hakan ta faru ne Beb? Ya ki kai? Me kuma kika basa da har ya baki katin sa? Kai anya ma kuwa da gaske nasan ne Billy?" Zee ta fad'a cikin tsantsar mamaki, yayin da har lokacin kuma take kallon katin nan tana sake juyawa sa a cikin hannun ta, kana kuma ta sake d'ago kai ta kalli tun daga sama har k'asa. Ita kuwa Billy wani irin murmushin farin ciki ta saki, kafin daga bisani kuma ta bud'e baki tana mai fad'in. "Kamar ya anya ma kuwa na san ne? To na tambaye ki mana, dama akwai wani Prince Asad d'in ne bayan shi wanda kika sani." Girgaza kai Zee tayi idanuwan ta akan fuskar Billy, tukun daga bisani ta bud'e baki cikin sanyi tana mai fad'in. "Shi d'in ne dai kawai." "To kinga kenan babu wani zancen kokwaton shine ko ba shi bane ba, kuma ma wai mantawa kikayi da abun da na fad'a miki ne tun a ranar dana fara ganin sa." Billy ta fad'a tana mai gyara zaman ta tare da sake fuskantar Zee sosai. Tukun ta d'ora da cewar. "Idan baki manta ba dama na fad'a miki cewar ni d'in ban tab'a neman abu na rasa sa ba tunda nazo duniya, haka kuma dan wasu sunyi sun kasa ba shi ne yake nufin nima zan kasa ba, domin kuwa kowa yana buga kalar nasa salon wasan ne, wanda kuma gashi naje na bugo nawa, sannan nayi wining acikin sa, dan haka ina san ki cire duk wani mamakin dake a cikin ranki ki fara kira na da Billy'n Asad, domin kuwa ya riga da ya zamto nawan." Ta k'arasa maganar da sakin murmushi, tare da dafa kafad'un Zee. Yayin da ita kuma Zee ta girgiza kanta tana mai sakin murmushi, tukun daga bisani tace. "Tabbas na yadda da batun ki, ke d'in ta daban ce Beb, domin kuwa samun kallo daga wurin Yarima Asad ma kad'ai ba abu bane mai sauk'i, amma sai gashi ke yau daga had'uwar farko kin tawo hadda phone number's d'in sa, dan haka Congratulation Friend." Zee ta k'arasa maganar fuskar ta d'auke da murmushi, kana tana shafa kiston dake d'auke akan Billy, tukun daga bisani ta d'ora da fad'in. "To wai in tambaye ki mana, dan Allah ke kuwa Billy wani irin salo ne kika jewa Prince Asad da shi da har ya bada kai haka da huri. Please kiyi sauri ki fad'a mun na k'agu naji yadda labarin yake." Ta k'arasa maganar tana mai k'ara gyara zaman ta akan kujera. Yayin da itama Billy ta janye cinyoyin ta daga kan na Zee da ta danne ta, tana mai zama sosai akan kujerar ta fuskan ci Zee sossi. Tukun ta fara jero mata duk abun da ya faru tun daga A har Z. Kana tayi shiru tana mai sakin murmushi. "A gaskiya kam da gaske ke d'in 'yar sa'a ce wallahi Beb." Zee ta fad'a tana mai mik'awa Billy hannu suka tafa. Sannan suka d'ora da hirar su cikin tsantsar farin ciki, domin kuwa ko ita Zee tayi natuk'ar taya Billy murna, sabo da yadda taga ta kamu da mahaukacin son sa, sai dai kuma a k'asan zuciyar ta tana mai tausayin irin yadda zata gwaru a wurin Asad, dan kuwa babu labarin da bata sani ba na wahalar da 'yammatan sa suke akan sa, amma kuma dai-dai da kalmar so babu wadda ya tab'a furtawa a cikin su. A cikin hirar tasu ne Zee take cewa Billy. "To yanzu kuma yaushe ne zaki koma wurin nasa?" Shiru Billy tayi tana mai d'aga kanta sama, kafin daga bisani kuma ta sauke sa tana mai watsa idanuwan ta akan fuskar Zee. Sannan ta bud'e baki tana mai fad'in. "Ina ganin kamar nan da kwana ukku zuwa hud'u masu zuwa gaba kenan, duk da dai da son samun abun da zuciya take so ne to yanzu ma bata k'i a sake ganin sa ba, sai dai kuma a yadda naji labarin sa tabbas idan na nuna masa maita-ta tun farko zai watsar da ni, domin zaiga kamar nayi mahaukaciyar damuwa da shi, hakan yasa zan bari har sai zuwa nan da 'yan kwana ki sai in koma, in yaso tunda ina da number sa a hannu na yanzu sai nai ta tura masa da message's na fatan Al'khari harma da kira kafin ranar." "Tabbas hakan ma yayi sosai kuwa, domin kuwa kina komawa gobe ma zai iya fara tinanin ko dama can kin saba mu'amala da maza sosai, da ganan kuma zai fatattake ki, dan kuwa babu abun da ya tsana a rayuwar sa face amasa kishiya, wato kina tare da shi ki kuma ki kula wanin sa, dan haka sai ki kiyaye." Zee ta fad'a tana mai mik'ewa tsaye. Itama Billy mik'ewa tayi tsayen tana mai d'aukar jakar ta-ta doshi hanyar bedroom d'in ta, bakin ta na furta kalmar. "Ai nama kiyaye na gama Beb." *BAYAN SATI 'DAYA.* *K'ASAR MALIN, JAHAR KARFUZ CIKIN BAK'AR MASARAUTA.* Tun bayan had'uwar da Bir yayi da Gimbiya Tasmir har yau Allah bai sa sun sake cin karo ba, duk da yadda yake aikin ziryar bin kan hanyoyin ta ako da yaushe, domin kuwa ba k'aramun matsuwa yayi da ya sake ganin fuskar ta ba, ta yadda har sai da ya d'an fara, sabo da yadda kullum yake yini da tinanin ta, ga kuma mafarkin ta da yake yi a cikin yana yi daban-daban a duk lokacin da ya kwanta bacci. Gaba d'aya ya dena zuwa ko ina hatta da daji wurin harbo abubuwan da ya saba, sabo da yadda yake yini ko da yaushe akan hanyar Gimbjya Tasmir. Babu yadda iya batayi ba da shi akan ya fad'a mata abun da yake damun sa a 'yan kwanakin nan, sabo da ganin da tayi yana ta ramewa, ga kuma yadda ya sake komawa shiru-shiru fiye da da, duk da dai dama shi can ba mutum bane mai hayaniya, amma sai dai kuma a yanzu ya ninka bayan nesa ba kusa ba. Amma Bir yak'i fad'a mata, sai dai yace mata ba komai kawai, sabo da sanin da yayi na muddin taji silar komawar sa hakan to ba k'aramun tashin hankali zata shiga ciki ba, wanda shi kuma bazai tab'a son haka ya faru da ita ba. Wannan dalilin ne ya sanya sa b'oye mata gaskiyar damuwar sa, duk da yadda ya saba fad'a mata komai nasa kuwa. Tsaye yake jingine jikin wata bishi da take akan hanyar da Gimbiya Tasmir take bi lumshe da idanuwan sa. Yayin da yake hangen ta a cikin idanuwan sa tana mai jifan sa da wani irin kyakkyawan murmushi wai. Yana a cikin wannan yanayin ya fara jiyo sautin gudun jama'a acikin kunnuwan sa tamkar a mafarki. Hakan ne yasa sa bud'e idanuwan sa cikin sauri, yana mai bin Bayin da yaga suna aikin gudu da kallo. Kafin daga bisani kuma wani irin murmushin farin ciki ya sub'uce masa daga cikin baki, sabo da fahimtar da yayi na Gimbiya ce zata huce. Take kuwa yaji gaba d'aya zuciyar sa na yin sanyi, ga wani irin nishad'i da yake lullub'e sa ta ko ina. Amai-makon shima ya gudun sai ya koma bayan bishiyar nan da yake jingine da ita, yana mai lab'ewa a jikin ta, ta yadda baza su tab'a hango sa ba a lokacin da suke tawowar har sai dai idan sun k'araso wurin da yake. Yayin.da shi kuma ya tsara abun da zai aiwatar a cikin zuciyar sa kafun su iso gare san. Wannan dalilin shine ya sanya sa b'oyewar. A b'angaren su Gimbiya Tasmir kuwa tun bayan waccan had'uwar tasu ba ta sake futowa tayo nan ba, sabo da ganin da take a kullum tamkar zata gansa ne idan ta futon, hakan yasa gaba d'aya ma ta dena bin hanyar, sai yau data tawo domin zuwa kan kujerar nan tata. Sanye take da irin shigar ta-ta koda yaushe, wato doguwar riga mai jan k'asa, amma ta yau d'in ta kasance blue ce mai azabar kyau. Yayin da gashin kanta kuma ya kasance a bud'e an tufke sa wuri d'aya, sai wasu irin takalman fata da suke sanye a k'afafun ta blue suma, duk da dai ba ganin su ake iya yi sosai bama, sabo da yadda rigar nan ke bin k'asa, a hakan ma wai dan wa'yan nan 'yammatan bayin na rik'e da wani sashi na daga jikin ta ne. Zane fuskar ta take da tambarin masarautar tasu yau da akayi sa da k'walli, sai dai kuma ba k'aramun kyau yayi mata ba. Ko kad'an babu alamun rahama tattare a fuskar ta-ta tamkar ko da yaushe. Cikin takun ta na tsantsar nuna isa da izza tare da tak'ama ta cigaba da tafiya kanta d'age a sama. Yayin da dakarun nan nata na ko da yaushe kuma suke biye da ita a bayan ta. Acan b'angaren Bir kuma ta gefen Bishiyar nan yake ganin su, hakan ne yasa yana ganin sun kusa k'arasowa wurin kawai ya futo kai tsaye yana mai dumfaro inda suke. Ita kuwa Gimbiya Tasmir ba zato ba tsammani taga bayyanar mutum a gaban ta kawai yana tafiya, domin kuwa kwata-kwata bata lura da lokacin da ya tawo ba sai dai kawai ganin sa da tayi. Cak ta tsaya a wurin da take zuciyar ta na wani irin bugu da matuk'ar k'arfi, tamkar yadda ta Bir take yi shima, sabo da idanuwan su da ya sark'e cikin na juna a lokacin da ta kai duban ta gare sa. Wani irin kallon-kallo suka fara aikawa junan su da shi, zuciyoyin su na wani irin gudu a d'ari-d'ari, ta yadda har suke jin tamkar sa fasa k'irji nansu su futo waje. Da k'arfi Gimbiya Tasmir ta rumtse idanuwanta gumi na fara tsats-tsafo mata akan goshin ta. Ga wani irin sarawa da taji kanta yayi lokaci guda, bayan kuma azababbaben b'acin rai mara misaltuwa da ya game ko ina na jikin ta. Lokaci d'aya jikin ta ya d'an fara karkarwa, gumi na cigaba da tsats-tsafo mata akan goshin ta, kafin daga bisani kuma ta sake bud'e idanuwan ta akan fuskar Bir suna masu cigaba da kallon-kallo. Kana ta bud'e bakin ta cikin wata irin murya wacce take k'unshe da b'acin rai a cikin ta, tana mai fad'in. "Kai ne yauma?" Ta k'arasa maganar tana mai cigaba da kafe sa da idanuwan ta da suka canza launi. Yayin da dakarun nan nata kuwa gaba d'ayan su suma sukayi tsaye cirko-cirko suna masu jiran ta basu umarni su far masa. A hankali Bir ya d'an jujjuya kansa, kana daga bisani ya lumshe idanuwansa, sannan ya sake bud'e su akan fuskar Gimbiya Tasmir da yake ganin yau ta k'arayi masa kyau fiye da yadda ya ganta a baya. Kana ya d'an zaro harshen sa yana mai lasar busassun lab'b'an sa da yajisu sun bushen take yanzu, sannan ya d'an jujjuya k'wayoyin idanuwansa. Kana wani irin murmushin farin ciki ya sub'uce masa, yana mai cigaba da kallon fuskar ta, yayin da yake jin zuciyar sa na wani irn sanyi. Tukun daga bisani ya d'an d'aga lab'b'an sa a hankali bayan ya langwab'ar da kansa gefe, idanuwan sa akan ta, yana mai fad'in. "Tabbas nine d'in dai kuwa Gimbiya, kinga yau ma mun sake had'uwa ko. Amma fa kin san me?" Ya fad'a yana mai cigaba da jifan ta da kyakkyawan murmushin sa, wanda ita kuma take jin sa tamkar futar wuta daga cikin bakin sa zuwa zuciyar ta, tsabar yadda take sake tafar-fasa. Kana ya sake lumshe idanuwan sa, sannan ya d'ora da cewa. "Hak'ik'a ke d'in kin kasance ta daban acikin duka matan duniya, domin kuwa kyawun ki ya zarc...." "Dakata! Dakata mun haka k'ask'antacen Bawa mara galihu!" Gimbiya Tasmir ta katse sa da fadin haka cikin wani irin lafazi mai matuk'ar kaushi da sauti, ta yadda har sai da hurin gaba d'aya ya amsa a lokacin da tayi furucin. Yayin da jijiyoyin kanta kuma suka futo sukai rud'u-rud'u akan goshin ta, ga wani irin gumi da ya cigaba da tsats-tsafo mata, ta yadda zuwa yanzu har ya fara d'iga, kana idanuwanta sukayi wani irin jajahur tamkar gauta. Bud'e idanuwanta data rumtse su a lokacin da take furucin tayi akan fuskar sa. Kana daga bisani ta fara d'aga k'afafuwanta da suke futar da sautin sarak'aunan gwal tana mai dosar wurin da yake, cikin wani irin taku wanda shi kad'ai ya isa ya kad'a hanjin cikin matsoraci, amma shi kuwa Bir wani irin farin ciki ne yaji ya sake ziyartar sa a lokacin da ta doso wurin da yaken. Yayin da yake ganin fuskar tasa ta na sake yi masa kyau acikin idanuwansa fiye da baya, ta yadda har yake ganin tamkar canzawa take aduk bayan wasu lokutan. Lumshe idanuwansa yayi adai-dai lokacin da yaji ta iso dab da shi. Kana ya d'ago tafin hannun sa yana mai d'orasa adai-dai saitin zuciyar sa ya dafe ta. Sannan ya bud'e idanuwan nasa wanda hakan kuma yayi dai-dai da tsayuwar ta cak a gaban sa. Cikin muryar ta mai futar da amon b'acin rai ta bud'e baki tana mai fad'in. "Hak'ik'a yau zan tabbatar maka da kayi gangancin shiga gona ta, zan tabbatar maka da ni d'in ko wacece, zan sanya ka ka bambance tazarar da take a tsakanin ni da kai matsiyacin Bawa, domin kuwa nayi rantsuwa da Ubangiji Gargabilu akan sai nasa an maka ninkin ba ninkin abun da akai maka waccan ranar." Ta k'arasa maganar tana mai sakin wani irin huci, ta yadda hucin ke dukan fuskar Bir. Amai-makon taga tsoro ya bayyana akan fuskar Bir sai kawai taga ya sakar mata kyakkyawan murmushin sa yana kallon ta, tukun daga bisani ya bud'e baki yana mai fad'in. "Dama har akwai azaba wacce za'a fad'e ta da har zata firgita Bawan da ya tashi cikin BAK'AR MASARAUTA Gimbiya? Shin wai kin san ma me kuwa iyata take kirana da shi? To bara kiji in fad'a miki. Jarumi shine sunan da iyata ta mun lak'abi da shi tun ina cikin tsumma na. Shi kuma Jarumi kin san ako da yaushe ba raggo bane shi d'in, dan haka ina mai farin cikin sanar miki da cewar Jarumi yana mai maraba da duk wata wahala da zata b'ullo muddin daga gareki ne, domin kuwa ta kan juyawa ta koma dad'i ne, tare da farin ciki a cikin zuciyar Bir." Ya k'arasa maganar da busa mata sauran iskar bakin sa akan fuskar ta, yana mai sakin murmushi mai sauti. Take kuwa a wurin ta lumshe idanuwan ta tana mai sakin ajiyar zuciya. Sosai Bir ya k'yalk'yale da dariya, yana mai d'aga yatsar sa ya nuna ta da ita. Yayin da ita kuma ta bud'e idanuwanta tana mai jin tamkar ta kashe kanta dan bak'in ciki. Cikin wani irin yanayi ta mik'ar da hannunta gefe, tana mai bud'e tafin hannun ta da yake wata irin karkarwa ba tare da tace komai ba. Da sauri badakaran da ke rik'e da takobin tsafinta ta gado ya fara tawowa da baya da baya, yana mai yowa wurin da take. Zube gwuiwoyinsa yayi a k'asa yana mai durk'usar da kai k'asa, tukun daga bisani ya d'ora mata zureriyar takobin nan akan tafin hannun ta. Damk'eta tayi da matuk'ar k'arfi, tare da rumtse idanuwan ta, kana daga bisani kuma ta bud'e su akan fuskar Bir dan taga yadda yanayin sa ya koma. Amma amai-makon taga ya tsorata yanzu sai taga dai still yana cigaba da jefo mata murmushin sa ne. Hakan yasa tayi wani irin ja baya daga wurin da take tana mai nuna sa da takobin nan. Kana ta bud'e baki cikin muryar ta mai matuk'ar amo tana mai fad'in. "Rai Rai Rai Buuuu Hoooo Reeee!" Sannan tayi wani irin kautar da takobin daga kansa tana mai matsar da ita jikin wata bishiya da take a gefen su. Fittt! Kakajein k'arar wucewar Bir asama, yadda kasan wanda iska ta d'auke sa yana mai zuwa ya manne a jikin bishiyar nan. Kana wasu irin igiyoyi suka futo suna masu d'ad'd'aure sa a jikin bishiyar. Sosai gaba d'aya dakarun nan sukayi matuk'ar firgita da abun da suka gani, yayin da su kuma 'yammatan bayin nan jikin su ya kama wata irin karkarwa tsabar tsoro. "Shairamaaa!" Gimbiya Tasmir ta fad'a da k'arfi tana mai nuna gefen bishiyar nan. Take kuwa dank'areriyar macijiya ta bayyana a wurin, tana mai kad'a harshenta. Sake d'aga takobin tayi ta nuna jikin Bir da ita, tana mai fadin. "So nake ki bambance masa tsakani na da shi Shairama." Ai kuwa take wannan macijiyar tayi kansa gadan-gadan. Da matukar k'arfi Bir ya rumtse idanuwansa yana mai jin bugun zuciyar sa na k'aruwa. Yayin da ita kuma wannan macijiyar ta cigaba da tunkarar sa. Tana dab da zuwa gare sa Gimbiya Tasmir ta sake kiran sunan ta da matuk'ar k'arfi, tana mai nuna can gefe wurin da ta baro. Yayin da take sakin wani irin nishi, tamkar wadda taga zaki ko kuma aka biyota za'a kasheta ta samu ta tsira. Ita kuwa wannan macijiyar da wani irin sauri ta juya tana mai komawa wurin ta na farko. Kana daga bisani kuma ta b'ace-b'at, yadda kasan bata tab'a bayyana a wurin ba. Hakan da Gimbiya Tasmir ta gani ne ya sanya ta juyawa b'arin da dakarun ta suke, sannan ta bud'e baki cikin wani irin sauti tana mai fad'in. "Kutsamamamun jikin sa, ta yadda zaiji ina ma baizo duniya ba yanzu-yanzu." Aiko da wani irin sauri suka tunkare sa gaba d'ayan su, suna masu zare bulalan su. Yayin da ita ma ta fara d'aga k'afafuwan ta tana mai nufar bakin bishiyar nan. Su kuwa dakarun nan suna k'arasawa gaban bishiyar suka fara dukan Bir ta ko ina, tamkar suna dukan bishiyar. Yayin da ita kuma Gimbiya Tasmir tayi tsaye a gaban sa tana mai sakin wani irin murmushi aduk lokacin da taji ya saki ihu, sabo da wani irin farin ciki da take jin yana lullub'e zuciya da ruhin ta da ganin sa a hakan da tayi. Su kuwa 'yamnatan bayin nan wata irin karkarwa jikin su yake daga wurin da suke a tsaye. Sosai suka toshe kunnuwan su suna masu durk'usar da kawunan su k'asa, sabo da kar kallon Bir da kuma jin sautin ihun su ya sanya su zubda hawaye, daga nan suma kuma su had'u da nasu hukuncin wurin Gimbiya Tasmir. Basu suka dakata da dukan sa ba har sai da sukaga gaba d'aya ya dena numfashi, a lokacin kuma tini suka huce awa guda da fara dukan sa. Ganin da Gimbiya Tasmir tayi kansa ya tuntsire yayi gefe ne, ga kuma jinin dake tsiyayowa ta ko ina daga jikin sa, tun daga tsakar kansa har zuwa tafukan k'afafuwan sa ne, ya sanya ta dakatar da su. Kana kuma taji bugun zuciyar ta ya sake sauyawa fiye da baya, ga wani irin tsoro da bata san kona mene ne ba da taji ya lullub'e ta, sai dai kuma duk maitar mutum bai isa ya gano halin da take ciki ba dan ya kalle ta. Da wani irin sauri ta d'aga takobin ta tana mai nuna sa da ita, kana ta furta kalmar. "Gargabilu!" Take kuwa igiyoyin nan suka tsits-tsinke gaba d'ayan su, Bir na fad'owa k'asa jikake Tim. Sannan ta juya tana mai nufar hanyar da zata mayar da ita gida ba tare da ta kula wa'yan nan dakarun nata ba. Da sauri suma suka take mata baya suna masu bin ta. Suna b'acewa daga wurin sai ga dan dazon bayi nan hankulan su atsantsar tashe sun yi kan Bir gadan-gadan. Yayin da Iyar Bayi kuma da wasu daga cikin Bayin suke wani irin kuka na tausayin halin da suka samu Bir a ciki. Da k'arfi Mazum ya shek'awa Bir ruwan da yake d'auke a hannun sa a gaba d'aya jikin sa. Take kuwa a wurin yaja wata irin doguwa ajiyar zuciya, yana mai bud'e idanuwansa da sukayi matuk'ar kumbura a hankali. Yayin da bakin sa kuma ke furta kalmar. "Gimbiyata!!!" Ganin jama'ar da yayi zagaye da shi ta ko ina ne ga Iyar Bayi da ta durk'uso gare sa tana rusar kuka ne ya sanya sa yin shiru, yana mai mayar da idanuwan sa ya sake lumshe su. Cikin sauri Iya ta fara basa taimakon gaggawa take a wurin. Har lokacin kuma bata bar kukan tausayin sa ba tana aikin nanata kalmar. "Jarumi! Jarumi!! Jarumi!!!" *ENGLAND* Tun bayan rabuwar su da Yarima Asad a waccan ranar har yau da akayi sati d'aya dai-dai basu k'ara had'uwa ba. Hakan kuma ya faru ne sabo da rashin neman san da ba tayi ba. Amma kuma babu ranar da tazo ta huce a cikin ranakun da bata tura masa da sak'on fatan Alkhairi ba. Sai dai kuma tun da take yin har zuwa yau bai tab'a yo mata replay ba, duk da sunan tan da take rubuta masa aduk lokacin da zata tura masa sak'on. Haka kuma har kiran sa tana yi a kowace rana sau d'aya, amma shima baita yin picking ba. Wannan dalilin ne ya sanya yau ta k'udiri aniyar komawa wurin sa, domin ayi komai a huce wurin. Sosai kuwa taci ado na gani na fad'a cikin shigar k'ana nan kaya. Bluen wando jeans ne da tsayin sa ya tsaya a iyakar k'aurin ta sanye a jikin ta, sai kuma wata farar t shirt mai d'an fad'i tare da kwalliyar duwatsu a gaban ta da take sanye a jikin ta. Kana kuma sai wani blue d'in d'an k'aramin mayafi da ta d'orasa asaman kanta, tare da hulla jelolin sa baya, yayin da k'afafuwan ta kuma suka kasance cikin wani farin toms da yay matuk'ar had'uwa. Sai farin agogon fata da yake d'aure akan tsintsiyar hannun ta da yayi bala'in yi mata kyau. Sosai tayi matuk'ar yin kyau cikin shigar tata. 'Daukar hand bag d'in ta tayi tana mai yiwa Zee sallama, sannan ta fuce daga cikin room d'in su. Acan wurin Yarima Asad kuwa misalin k'arfe hud'u da kwata dai-dai ya futo wurin nasa ya zauna. Sanye yake da wandon jeans nevy blue a jikin sa da yayi matuk'ar yi masa kyau. Yayin da rigar sa kuma ta kasance bak'a mai d'an fad'i. Sai tsitsiyar hannun sa kuma da take d'aure da bak'in agogon fata. K'afafuwan sa kuwa sanye suke da bak'in cover shoe da yayi bala'in had'uwa. Ya d'ora k'afa d'aya akan d'aya yana sipping d'in kofi d'in sa hankali kwance, yayin da d'ayan hannun sa kuma yake aikin shafa wayar sa da shi tamkar koda yaushe. A kullum yana ganin sak'wannin Billy da take turo masa, amma kuma tun da ya karanta na farko har yau bai k'ara karanta wani ba. Sabo da dama shi d'in haka yake, sannan kuma duk bala'in yarinya baki isa ya tura miki da sak'on gaisuwa ba, sai dai idan yana buk'atar ki tukun zai neme ki, shima kuma kawai I'm waiting, zakiga ya turo, domin kuwa shi ababen hutu kawai ya d'auki mata a wurin sa. Zaman sa baifi da minti Ashirin a wurin ba Billy ta k'araso da irin salon ta na wancan satin. "Hello Prince." Ta fad'a k'asa-k'asa a dai-dai lokacin da ta k'araso gaban kujerar da yake, tana mai tsayawa daga gefen sa. Lumshe idanuwa Yarima Asad yayi yana mai shak'ar daddad'an k'amsin turaren da yake sanye a jikin ta ba tare da ya d'ago ya kalle ta ba. Tsaf ya gane ko wacece ta sanadin muryar ta da yaji, wacce ya shaidata tun a waccan ranar da suka fara had'uwa. "Can I sit Please?" Billy ta fad'a cikin wata irin murya mai matuk'ar shiga jiki, kana tana mai d'an had'awa da sakin murmushi a k'arshen maganar tata. Wani irin abu Yarima Asad yaji ya tsarga masa tun daga 'yantsun k'afafuwan sa har zuwa k'wak'walwar sa, ta sanadin muryar da tayi amfani da ita wurin yin maganar, ga kuma k'amshin turaren da yake sanye a jikin ta da suke fara shirin canza masa yanayi. A hankali ya d'ago kansa yana nai watsa yan madai-daitan fararen idanuwan sa akan fuskar ta. Wani irin murmushi Billy ta sakar masa tana mai d'an jujjuya idanuwan ta. Yayin da shi kuma Yarima Asad yayi wani irin lumshe idanuwan sa, yana mai jin wani irin azababben filing na taso masa, sabo da shigar dake sanye a jikin ta da ya sake yin arba da ita. Kana daga bisani kuma ya janye idanuwan sa daga kan ta yana mai fad'in. "Uhm!" Sannan ya juya yana mai kallon gefen sa, tukun ya mayar da idanuwan sa kan wayar sa yana mai cigaba da shafata. Hakan da Billy taga yayi ne ya sanya ta fahimtar yana nufin ta zauna kenan. Ai kuwa cikin tsantsar farin ciki irin wanda ba zai misaltu ta tsinci knata a ciki. "Alhamdulillah." Ta furta acikin ranta tana mai matsawa kusa da shi ta zauna. Ta yadda har k'ugun sa da nata suka a jone wuri d'aya, kana cinyar ta na gugar tasa cinyar. Wanda hakan da tayi kuma ya sake hulla Yarima Asad ciki wani yanayi, sai dai kuma girman kansa yak'i ya bari ya nuna hakan a gare ta kwata-kwata. Cikin wata iriyar murya wacce take tattare da shagwab'a a cikin ta Billy ta bud'e baki, bayan ta d'ora tafin hannun ta akan kafad'ar Yarima Asad, tana mai fad'in. "Tun ranar da na ganka a wurin nan nazo wucewa da nazo wurin ka nayi maka magana, kana kuma nayi maka introducing d'in kai na, amma kai har yau kak'i kace mun komai. Sunan ka ma sai a jikin katin ka kawai na gani, kana daga baya naji labarin ka a wurin k'awata." Ta k'arasa maganar cikin wata irin murya tamkar zata fashe da kuka, kana tana d'an murza kafad'ar sa cikin wani irin salo. Rumtse idanuwa Yarima Asad yayi yana mai d'an sauke wata 'yar gajerar ajiyar zuciya. Tukun daga bisani ya bud'e su gaba d'ayan su har sun fara sauya launi, kana ya juya gefen ta yana mai watsa idanuwan nasa da suka fara canza launi akan fuskar Billy. Tukun ya d'an zaro mata su yana mai d'aukar yatsat hannun sa d'aya ya d'ora ta akan lips d'in sa. Wato dai yayi mata irin yadda ake yiwa yara idan ba aso suyi magana. Kana daga bisani ya janye idanuwan sa daga kanta yana nai d'an fesar da wata zazzafar iska daga cikin bakin sa. Hakan da Billy ta gani ne ya sanya ta sake fad'awa jikin sa tana mai kife tafukan hannayen ta a k'irjin sa, tukun ta fara wani irin shafasa tana mai bud'e baki cikin shagwab'a tace. "Allah yau nima sai kayi mun magana, na gano ka so kake kayi mun rowar muryar ka." Ta k'arasa maganar tana mai d'an diddira k'afafuwan ta a k'asa. Yayin da rabin jikin ta kuma ya kasance akan na Yarima Asad. Ai kuwa take yaji gaba d'ayan da ya sake fad'awa cikin wata duniyar. Hakan ne yasa sa sanya hannuwan sa yana mai d'ago kanta da ta kwantar da shi akan k'irjin ta cikin wani irin yanayi, sannan ya bud'e baki cikin muryar sa da take a matuk'ar shak'e. Yana mai fad'in. "Ke ki mun shiru fa ko kuwa yanzu na mammakeki." Ya k'arasa maganar da zaro mata idanuwan sa. Hakan da Billy ta gani ne ya sanya ta sake b'are baki tana mai cigaba da sakin kukan, tare da mai-maita kalmar sai ka yimun magana ni dai wallahi. Ai kuwa take a wurin Yarima Asad yayi wani irin lumshe idanuwan sa, tukun ya fara yin k'asa da kansa a hankali-ahakali, harya dan gana fuskar sa da tata fuskar, ta yadda har tsinin hanicin su suke tokarar juna. Kafin daga bisani kuma ya d'ora lips d'in sa akan nata. Wasu irin tagwayen ajiyar zuciya Billy sauke tana mai lumshe idanuwan ta. Tukun daga bisani suka fara kissing d'in junan su cikin wani irin yanayi na zak'uwa gaba d'ayan su, ko tinanin cewar a waje suke ma ba suyi ba. Sun d'auki tsayin mintina goma suna abu d'aya a wurin. Kafin daga bisani kuma Yarima Asad ya mik'e tsaye d'auke da Billy a hannun sa tamkar jaririya. Sannan ya juya yana mai dosar hanyar da zata kaisa room d'in sa hannun sa d'auke da Billy. Yayin da ita kuma Billy taji wani irin farin ciki mara misaltuwa na lullub'e zuciya da ruhin ta. Ji take ina ma ace da jama'a a wurin sosai, domin su gani su tabbatar da ita d'in mai sa'a ce, kana kuma ta daban ce, tun da gashi nan tayi abun da dubban mata suka kasa yi, wato sace zuciyar Yarima Asad. Ba shi ya sauke ta ba har sai da ya sadata da had'ad'd'iyar doguwar kujerar da take a cikin falon nasa. Tukun ya dire ta akai yana mai bin ta suka cigaba da aikata masha'ar su, cikin tsantsar nishad'i da jin dad'i................✍ *MUNA GAB DA DAWOWA CIKIN LABARIN MU, SAURA KIRIS YA RAGE KAWAI .👌 DAN HAKA ASAKE WANKE IDANUWA, DOMIN KUWA ANAN NE WASAN ZAI FARA. 😅 *BAK'AR MASARAUTA* *NA* UMAR FARUQ*D* *PAGE 29* Wani irin farin ciki mara misaltuwa Billy take jin kanta a cikinsa, domin kuwa tun daga lokacin data fara soyayyar minti da saurayin ta da yake a k'asar Hausa bata tab'a jin irin abun da take ji a yanzu da take tare da Yarima Asad ba, asalima ko kusa baza a had'a ba, kuma wai a hakan ma ba wani nisa sukayi ba, iyakar su kawai kissing. "To ina ga kuma mun huce can." Billy ta fad'a a cikin ranta tana mai sake cakumar Yarima Asad. Sun d'auki kimanin mintina kusan arba'in, tukun suka samarwa kansu nutsuwa a hakan, wanda hakan kuma yayi dai-dai da lokacin sallah magariba. Da wani irin sauri Yarima Asad ya mik'e daga jikin Billy, sabo da idanuwansa da suka sauka akan had'ad'd'en agogon bangon da yake manne a jikin bangon d'akin. Cikin wani irin yanayi yabi jikinsa da kallo, kafin daga bisani kuma ya juya b'arin da Billy take yana mai watsa idanuwan sa akan ta. Zaune take akan kujerar tana ta faman lumshe idanuwanta, tare da sauke numfarfashi. Haka nan kawai yaji bata da wata sauran k'ima ko kad'an a cikin idanuwansa, domin kuwa ada da farko yayi mata kallon wacce bata san komai ba dan gane da wannan harkar, amma kuma a yanzu da suka buga wasan da ita ya tabbatar da ba wannan ne karon ta na farko ba, domin kuwa ba k'aramun k'warewa ta nuna masa ba. Wannan dalilin ne yasa yaji gaba d'aya babu wata sauran k'imar ta acikin idanuwan sa, sai dai kuma yana ganin zai cigaba da rakawa da ita a hakan, sabo da lura da yayi data san kanta ba laifi, domin kuwa bai ga wani abu na aibu ba tattare da ita tunda suka fara abun su, asalima sai zallar k'amshin turare da yake tashi ta ko ina a jikin ta, shi kuwa dama a wannan fagen yafi auki, wato tsafta da k'amshi. Tabbas duk mai yin su to fa suna shiryawa da ita. _K'alubale gareku 'Yammata, domin kuwa ba a iya novel hakan ke faruwa ba, ko azahiri ma hakane, muddin kikayi gangancin barin saurayin ki ya fara mu'amala da wani sassa na jikinki, to daga wannan ranar duk wani mutunci da yake ganin ki da shi ada zai zube. Zubewa kuma irin warwas d'in nan, ko da kuwa ace shine ya fara nuna miki hakan, kana kuma duk irin mugun son da yake miki, to wallahi daga wannan ranar da kika fara barin sa yana tab'a wani sassa na jikin ki ba tare da kin tsawatar masa ba, to gaba d'aya darajarki ta k'are a cikin idanuwan sa, ta yadda har ba zai ji shakkar fad'a miki ko wane irin kalami ba, kai a k'arshe ma maybe ya bud'e baki ya kiraki da ballagaza a gaban ki._ _Dan haka ku sani babu wata aba soyayyar minti face zallar lalacewa da zubda mutunci, ko da kuwa iya 'yan yastun ki ne zallah saurayin ki ke rik'ewa, to tabbas ki sani fa wani pacentage na daga cikin mutuncinki na raguwa a idanuwansa._ _Allah ka kiyashe mu kasa mufi k'arfin zukatan mu. Rabbi ka shiyar da mu baki d'aya al'ummar musulmi albarkacin Annabi da Al'qur ani. Amin!_ Dan tab'e baki Yarima Asad yayi yana mai ganin yadda take wani irin abu tamkar mai jin bacci, babu ruwan ta da lokacin sallah da ya gabato ma. Kana daga bisani ya juya yana mai dosar hanyar bathroom. Yayin da ya fara watsi da kayan jikin sa tun anan cikin falon. Ita kuwa Billy gaba d'aya wani irin farin ciki ne mara misaltuwa taji yana juyawa da ita. Tana jin lokacin da ya janye jikin sa daga nata, amma ta kasa yin ko da k'wak'k'waran motsi, sabo da yadda take jin wata irin kasala na sauka a jikin ta. Hakan yasa ta cigaba da zama a wurin tana mai cigaba da lumshe idanuwan ta. Acan b'angaren Yarima Asad kuwa cikin sauri yayi wanka, kana a k'arshe ya d'ora da na tsarki. Tukun ya wuce wurin da bathrobe d'in sa take yana mai d'aukar ta ya sanya ta a jikin sa. Kana ya kamo hanyar da zata sadasa da cikin bedroom d'in nasa. Direct ya doshi gaban wardrobe d'in sa. Wasu tausasan kaya ya d'auko masu matuk'ar santsi ya aje a gefen sa. Dogon wando ne tare da rigar sa wacce take da dogon hannu ita. Boxer ya fara sanyawa da farko, tukun ya d'ora dogon wandon a sama. Kana ya cire bathrobe d'in dake sanye ajikin sa yana mai yin hulli da ita, sannan ya kamo hanyar da zata sadasa da fallo, hannun sa rik'e da rigar wandon jikin sa yana mai b'alle mab'allen ta, sabo da saurin da yake na kar atayar da sallah kafun ya k'arasa masallacin nasu da suke sallah. Da sauri Billy ta bud'e idanuwanta akan faffad'an k'irjin sa da yake cike da yalwar bak'in gashi sid'ik, ga wata irin k'ira data gansa da ita irin wacce bata tab'a cin karo da namijin da yake da kamar ta ba. Wani irin yam-yam taji k'wak'walwar ta nayi mata, ga kuma tsigar jikinta da ta fara mimmik'ewa lokaci guda. Da sauri ta lumshe idanuwanta tana mai fesar da numfashi, sabo da ganin da tayi Asad ya d'ora rigar ajikin sa, wanda ko kad'an ba taji dad'in hakan ba, ita taso ace zai zauna a haka ne gaban tai ta kallon sa, sabo da ba k'aramun kyau yayi mata ba a idanuwan ta. Tabbas yanzu ta k'ara tabbatarwa da kanta cewar Asad na daban ne a cikin maza, kana kuma ta gane dalilin da yasa yake juya mata duk yadda ransa yaso, kuma suke binsa a hakan. "Ki tabbatar kin cire k'azantar dake jikin ki, ko kuma kisan inda dare ya miki before na dawo daga masallaci." Taji sautin muryar Yarima Asad acan k'asa-k'asa yana mai fad'in hakan. Hakan ne yasa ta juyawa b'arin da yake da sauri, amma sai taga har ya k'arasa fucewa daga cikin d'akin, kuma da alamun dama yana tafiyar ya watso zancen ba wai tsayawa yayi ya kalle ta ba. Amaimakon taji haushin kalaman da ya gasa mata, sai kawai ta saki murmushi tana mai mik'ewa tsaye. Kana ta bud'e baki tana mai cewa. "Kome zakayi ba zanga laifin ka ba my Prince, domin kuwa ka kai kayi ne guy." Ta k'arasa maganar tana mai dosar hanyar bedroom d'in sa da taga ya futo daga ciki. Sosai tayi kallo tare da jinjina tsafta da kuma gayun Yarima Asad a lokacin da ta shiga cikin bathroom d'in sa, bayan ta gama kalle abubuwan da suke a bedroom d'in nasa. Ji tayi inama ace yace ta dawo wurin sa da zama gaba d'aya, tabbas da tasan ta gama dacewa a rayuwa, kana kuma sunan ta zaiyi k'aura a cikin school d'in tasu, tamkar yadda nasa yayi k'aura. Cikin wani k'aton dustbin ta watsa kayan da ta cire, kamar yadda taga nasa kayan aciki har na jiya data gansa da su, kuma dama ta riga da taji labarin sa na cewar baya tab'a mai-maita kaya idan ya cire, wannan dalilin ne ya sanya itama bata fara gigin adana natan ba. Sosai tayi wanka mai rai da lafiya, tana mai jin wani irin nishad'i na lullub'e ta ta ko ina. Tukun a k'arshe bayan ta gama ta janyo sabuwar bathrobe data gani, tana mai sanya ta ajikin ta ba tare da tasa komai daga k'asanta ba. 'Yan igiyoyin jikin rigar ta kama ta d'aure su, sannan ta d'aura alwala, kana ta juyo tana mai futowa daga cikin bathroom d'in. Gaban dressing mirrow ta huce tana mai shafa had'ad'd'un mayukan da ta gani akan sa, kana a k'arshe ta sake gyara zaman bathrobe d'in da take sanya a jikin ta. Sannan ta mik'e daga kan kujerar tana mai dosar hanyar da zata sadata da falon. A kuma dai dai lokacin shima Yarima Asad ya danno kansa cikin fallon. "Sannu da zuwa honey." Billy ta fad'a tana mai yin wurin da yake, tare da shirin rungumarsa tamkar ba yanzu tayo alwala ba. Amma sai Yarima Asad ya kauce yana mai nufar hanyar bedroom d'in sa ba tare da ko kallon fuskar ta yayi ba. Rumtse idanuwa Billy tayi tana mai jin wani irin a cikin ranta. Kana daga k'arshe ta koma kan kujerar da take a kusa da ita ta zauna. Zaman ta baifi da minti biyar ba sai gashi nan ya sake futowa hannun sa rik'e da kaya. Hullowa Billy su yayi daga wurin da yake a tsaye, kana ya juya yana mai nufar gaban fridge d'in sa. Bud'e sa yayi yana mai zaro robar ruwa d'aya a ciki. Kana ya d'auko d'an glass cup d'in da yake kife a cikin fridge d'in. Sannan ya bud'e murfin jarkar yana mai tsiyaya ruwan a cikin sa, tukun ya juyo yana mai dawowa kan kujera ya zauna hannun sa rik'e da cup d'in. Yayin da yake aikin kallon Billy ta k'asan ido yana mai sake jin sa a cikin wani irin yanayi, sabo da 'yar shigar da ya gani sanye a jikin ta kawai. Ita kuwa Billy cikin sanyi ta mik'a hannun ta zuwa kan ledar kayan da taga ya hullo mata akan jikin ta. Bud'e ledar tayi tana mai zazzage kayan cikin ta akan kujerar. Da matuk'ar sauri ta furta kalmar. "Wow." Tana mai d'an wara idanuwan ta, sabo da arba da tayi da wata had'ad'd'iyar arabian gown tare da iner wear's masu tsananin kyau sun fad'o. Da sauri ta d'aga rigar sama bayan ta mik'e tsaye tana jin wani irin farin ciki na lullub'e ta, kafin daga bisani kuma ta ajiye ta a k'asa tana mai sa hannu ta d'auki pant d'in da ta gani ajiye a wurin. Yayin da shi kuma Yarima Asad yake cigaba da kallon duk abun da take ta k'asan ido. Cikin wani irin salo wanda take fatan yaja hankalin Yarima Asad suyi komai yanzu tayi wani irin cire bathrobe d'in dake sanye a jikin ta. Take kuwa ta koma tik babu komai a jikin ta. Yayin da Yarima Asad kuma ya lumshe idanuwan sa da matuk'ar sauri, yana mai fesar da wata zazzafar iska daga cikin bakin sa. Ita kuwa Billy d'an durk'usawa k'asa tayi bayan ta juyawa Yarima Asad bayan ta, tana mai wara k'afafuwan ta tafara sanya wandon a jikin ta. Tukun ta d'ago ba tare da ta juya b'arin da Yarima Asad yake ba, tana mai sa hannu ta d'auki best d'in da ta kasance mahad'in wandon, sannan itama ta sanya ta a jikin ta. Shi kuwa Yarima Asad cikin wani irin yanayi ya sake bud'e idanuwan sa yana mai dire su akan bayan ta. Jinjina kansa yayi yana mai k'ara tabbatarwa da kansa cewar yarinyar oga ce itama. Yana kallo ta janyo rigar tana mai zurata ajikinta bayan ta d'an jujjuya jiki kafin ta sata. Sosai yayi wata irin mazewa yana mai janye idanuwansa daga kanta, ya mayar da su kan wayar sa yana shafawa. Gaba d'aya ta riga da ta gama rikata sa, amma sai dai kuma ya k'udiri aniyar ba zai nuna mata yasan abun da takeyi ba kwata-kwata, asalima yanzu zai sallame ta, sabo da ta gane shi d'in fa sai ya buk'aci abu yake yi ba wani kesa sa yayi ba. Ita kuwa Billy sai da tagama sanya kayan tas tayi har rolling d'in mayafin abayar, sannan ta juyo b'arin da yake tana mai zama akan kujerar tare da watsa idanuwan ta a kansa. Amma amai-makon ta gansa a yanayin da tayi tinanin zata gansa, sai kawai taga ko kad'an hankalin sa baya kanta ma. Sosai kuwa ta k'ara jinjina k'arfin girman kan Yarima Asad a cikin ranta. Yayin da shi kuma ya d'ago kansa alokacin yana mai watsa lumsassun idanuwansa da suka d'an canza launi akan fuskar ta. Kana daga bisani ya bud'e baki cikin wata irin murya wacce tafi kama data gargad'i, yana mai fad'in. "Muddin mutum yana so yay mu'amala dani, to dole ne ya k'auracewa duk wani banza da yake tare da shi, kana ya kiyayi yimun shish-shigi acikin harkoki na, sannan kuma ya zamto ma'abocin tsafta da k'amshi. To muddin mutum yayi haka zamu shirya da shi, idan kuma aka kauce to fa zamu raba hanya ne, ko d'an gidan uban waye kuwa shi d'in." Ya k'arasa maganar yana mai sanya hannu a cikin aljihun sa ya zaro wrapper dolers, tukun ya hullawa Billy su akan jikin ta daga wurin da yake zaune, yana mai fad'in. "Gasu nan wa'yannan naki ne, zakuma ki iya tafiya yanzu." Ya k'arasa maganar yana mai shirin mik'ewa tsaye. Yayin da ita kuma Billy taji wani irin rashin dad'in yadda yayi mata maganganun, da kuma kud'in daya watso mata a jikinta. _"Ko dan gidan uban waye."_ Ta fad'a acikin ranta tana mai jinjina kanta. Kana daga bisani tasa hannu ta d'auki kud'in tana mai jujjuya su, tukun daga bisani kuma ta d'aga ido tana mai kallon sa adai-dai lokacin daya juya yana tafiya, kana ta bud'e baki tana mai cewa. "Me zanyi da kud'in kuma, a a ka barshi kawai na gode." Ta k'arasa maganar cikin sanyi idanuwanta akan bayan sa. Bai tsaya daga tafiyar da yake ba kamar yadda bai amsa mata ba, har sai da yaje bakin k'ofar bedroom d'in sa, tukun yaja ya tsaya ba tare kuma da ya juyo gare ta ba ya bud'e baki yana mai fad'in. "Hak'k'in ki ne ai su d'in, wato ladan aikin ki kenan." Ya k'arasa maganar yana mai murd'a handle d'in k'ofar, tukun ya tura kansa ciki tare da rufo ta. Ita kuwa Billy rumste idanuwanta tayi da k'arfi, tana mai jin saukar kalamin sa da matuk'ar zafi acikin kunnuwan ta. Kana daga bisani ta bud'e su tana mai fad'in. "Wato karuwa ma ya mayar dani kenan, shiyasa dan mun d'anyi d'an wannan abun kawai zaice zai biyani." Ta k'arasa maganar tana mai mik'ewa tsaye cikin fushi, tare da dire kud'in akan center table d'in da yake a cikin falon, tukun ta juya tana mai kama hanyar da zata sadata da waje. Cak ta tsaya adai-dai bakin k'ofar futa daga cikin d'akin tana mai rumste idanuwan ta, sabo da tinawa da tayi muddin Yarima Asad yazo ya samu kud'in nan anan wurin tsaf zai iya rabuwa da ita daga yau, wanda ita kuma baza ta tab'a son haka ta faru ba, asalima idan hakan ta kasance tana ji ajikin ta tabbas zata iya macewa, sabo da ba k'aramun son sa ta kamu da shi ba. Hakan ne yasa tayi saurin juyawa da sauri tana mai komawa ta suri kud'in nan, sannan ta bud'e zip d'in jakar ta tana mai watsa su ciki. Kana ta juya tana mai fucewa daga cikin d'akin. Tun daga wannan ranar Yarima Asad da Billy sukayi matauk'ar k'ullewa, ta yadda har ya zamto an fara sanin su tare a cikin school d'in ta su. Yayin da har lokacin kuma Yarima Asad bai yadda ya kusanci Billy ba, sai dai kawai romance da sukeyi. Ita kuwa babu kalar dabarar da batayi ba domin ta samu ya zarce duka amma abanza. Sosai take tsananin buk'atar sa, amma take daurewa tana kame kanta, sabo da tino abun da yayiwa baturiyar nan da take yi akan idanuwan ta. Hakan yasa wani lokacin idan ta bar wurin sa dole take sawa ta kira wani saurayin ta da ya kasance shima d'an k'asar hausa, d'an wani shahararren attajiri ya biya mata buk'atar ta, sai dai kuma sosai take yin kaffa-kaffa gudun kar Asad ya gano ta ya rabu da ita, domin kuwa a kullum idan zasu kasance tare da shi sai ya nuna mata shi d'in fa mai kishi ne. Babban abun da yafi bata haushi da Asad shine, rashin sanin darajar ta da baiyi ba ko kad'an, gashi kuma a kullum idan zasu d'anyi wani abun da shi sai ya zaro kud'i ya bata, duk da yadda ta nuna nasa bata son hakan kuwa. Domin kuwa acewar sa ai hak'k'in ta ne, dan haka ya zama dole ya bata, sai dai idan ko ya batan ta zubar da su daga baya. Ga kuma yadda bata isa ta nuna kishi akan sa ba dan ta gansa da wata, yanzu sai yace mata ai ba dole ya mata ba ta kulasa, kai ak'arshe ma shine yake yin fushi, ta tadda har sai taci wuya tukun take samu ta shawo kansa. Har kawo yau bai tab'a yadda ta kwana a wurin sa ba, duk da yadda take mutuwar son yin hakan kuwa, domin kuwa acewar sa bai ga uban da zata zauna tayi masa ba tun da ba wani babban abu yake da ita ba, asalima kuma shi ba d'an iska bane ba, sabo da tun da yake a rayuwar sa har yau baisan wani abu sex ba. B'angaren su Al'amin kuwa sosai suma suka cin karen su ba babbaka, domin kuwa su mai gaba d'aya ma suke yi babu ruwan su da tinanin lahira, a haka har Allah yasa suka kamalla karatun su na master's gaba d'aya, a lokacin kuma itama Billy saura shekara d'aya ta gama degree d'in ta. Haka su Yarima Asad suka tattaro komai nasu suka dawo Ka'sar Hausa, Jahar Wasai Cikin Masarautar su. Inda sukazo suka tarar da ko wanne an sake tsara masa mazaunin sa acikin part d'in mahaifiyar sa, wanda hakan kuma ya zamto duk aikin mai martaba ne, domin kuwa ba k'aramun farin ciki yayi ba da kammala karatun d'an nasa mafi soyuwa a ransa ba, sabo da sanin da yayi na yanzu shikenan ya dawo gaban sa, babu kuma zancen sake yin nisa da shi anan kusa, dan kuwa yace koda zai barsa yayi Phd to sai bayan ya tabbatar da ya nutsu ya dawo tamkar yadda Babban Yaya yake, tukun zai barsa ya k'ara yin nesa da shi, domin kuwa sun d'aura d'amarar ganin sun dawo da shi kan hanya daga shi har Fulani, kai harma da Babban yaya. Watan su biyu da dawowa dai-dai mai martaba da waziri harma da galadima suka same su da zancen aure. Take a wurin Al'amin ya gabatar musu da budurwar sa wadda suka had'u da ita acan school d'in, amma ita yanzu take kanyin degree d'in ta, wato dai mate d'in Billy ce, duka-duka ba zasu k'ara ko shekara d'aya a school d'in ba suma zasu kammala. Yayin da shi kuma Asad ya nuna musu cewar bai san wannan batun ba kwata-kwata, kai atak'aice ma a k'arshe haka yace shi har yau baiga wacce tayi masa ba. Hakan ne yasa waziri ya yanke masa lokaci zuwa nan da shekara d'aya a wadace kenan, sannan yace masa muddin lokacin kuma ya cika bai futar da matar aure ba to ya sani su da kansu zasu zab'a masa cikin 'yammatan su na nan gida da sukaji labarin suna haukar son sa, kana a ka'rshe suka sallame su gaba d'ayan su, bayan sun yanke hukuncin zuwa su nemar wa Al'amin auren yarinyar da yace yana so. Ko kad'an Yarima Asad bai d'auki maganarsu da muhimmanci ba, sai ma ya watsar da ita a wurin da suka gama yinta, tukun ya taso ya baro wurin. _BAYAN SHU'DEWAE WASU WATANNI._ Sosai Yarima Asad yake buga tsiyar sa yanda ransa yake so. Yayin da Babban Yaya, Gimbiya Fulani da Mai Martaba suke k'ok'arin ganin ya dawo kan hanya a kullum amma a banza. Tini Billy sunyi graduation harma ta dawo gida, ta yadda har suka d'ora da mu'amalar su daga wurin da suka tsaya ita da Prince d'in ta. Yayin da sunan Yarima Asad kuma ya karad'e kunnen ko wane mutum da yake da kusanci da Billy, ciki kuwa har da mahaifin ta mai girma gwamna, sai dai kuma har kawo yau bai tab'a zuwa gidan su ba, sai dai ita tazo ta same sa a cikin Asadullah Palace. Yayin da Al'amin kuma akayi maganar auren sa harma da sa rana, inda za'a had'a bikin nasa dana 'yammata da yawa da suke a cikin Masarautar Wasai, cikin su kuwa har da masu hauka akan Yarima Asad da suka gaji suka hak'ura, sabo da ganin da sukayi baya ta su ko kad'an. Yayin da ita kuwa Fa'iza k'awar Baby da suka kammala degree d'in su yanzu take tsantsar haukar sonsa, amma sai dai kuma ko darajar kallo bata samu daga gare sa. Sosai Yarima Asad yayi k'aurin suna acikin garin wasai fiye da duk sauran yaran cikin gidan sarautar, haka kuma kowa yasan halin sa, sabo da yadda ko titi idan ya futo baya sassautawa mota, kamar yadda bai yadda wani ya tuk'asa ba muddin ba tafiyar nesa zaiyi ba. Yayin da motocin sa kuma suka kasance har guda goma shabiyu, gaba d'ayan su masu azabar kyau da tsada na zamani. Ko wacce tana d'auke da number ta mai suna Prince Asad ajikin ta, tun daga kan number 1 har zuwa 12 ta k'arshe. Sosai yake matuk'ar birge Matasa, sannan kuma suke mutuwar son sa da san salon sa, barin ma idan ya futo akan doki, kasancewar har yau yana hawa doki, kana kuma yana da su kusan har guda shida, gaba d'ayan su lafiyayyu k'osassu. Yayin da manyan mutanen da suke a kusa da gidan sarki kuma suke alawadai da hallayar sa, wasu kuma suke masa fatan shiriya, sabo da kowa yasan yadda yake gudun al'adun hausawa yanzu, su kuwa manyan babu abun da suka tsana face irin shigar da yake yi, da kuma yadda suke jin labarin sa a gari na cewar yana da huraren shak'atawa da yake had'a 'yammata da samari kala-kala suna iskancin su. Wannan dalilin ya sanya baya birge su kwata-kwata. Mutuwar Ciroman gida wanda ya kasance k'ani ga mai martaba da yayi bayan wasu 'yan watanni ne ya sanya ake ta shirin nad'a Babban yaya a cikin satin nan, domin ma har an tsaida ranar da za'ayi nad'in, sabo da dubawar da akayi a kaga shine kawai ya cancanta da kujerar, dama kuma ita sarautar ciroma sarauta ce wacce ake bawa 'ya'yan sarki ita. Wannan dalilin ya sanya aka futar da shi a matsayin wanda za'a d'ora akan karagar ta ciroman gida, wanda za'ayi bikin nad'in nan da sati d'aya mai zuwa. *BABBAN ZAURE LOCUS* Tsaye suke a cikin compound d'in gidan nasu, Sheikh Ahmad na furfuto da kayan da suke acikin boot d'in motar tasa irin su fulo, capet, buta, tare da kulolin abinci, wanda hakan ke nuni da cewar sun dawo daga asibiti ne, kuma da alamun sun d'an kwana biyu ne acan d'in da. Yayin da matar sa kuma take rik'e da Aishatu, da yanzu ta koma hajiya Aishatu da sukaje saudiyya sukayi aikin hajji da ita da Ishak', harma da tsohuwa kaka a shekarar da ta huce, wanda Sheikh Ahmad ne ya biya musu gaba d'ayan su kuma, domin kuwa a yanzu sai dai suce Alhmadulillah, sabo iyakar rufin asiri na duniya Allah yayi musu shi, sai dai kawai suyi fatan da cewa da na lahira. Da alamun dai itace mara lafiya da aka dawo da ita daga asibitin, duba da yadda tayi matauk'ar kwantsamewa, sai kuma Alhaji Ishak' mahaifin Sheikh Ahmad da shima ya futo daga gidan gaba. 'Dibar kayan sukayi suna masu shigewa da su cikin gidan gaba d'ayan su. A d'an madai-daicin falon nasu da ya gaji da had'uwa da kayan ado, suka zube akan tausasan kujerun da suke a cikin sa wa'yan da suka kasance na k'asar turkey. "Barka! Barka!! Barkan ku da isowa." Muryar kaka ta ratsa dodon kunnuwan su a lokacin da take futowa daga cikin d'akin ta. "Yawwa Kaka barkan ki da gida." Sheikh Ahmad da matar sa suka fad'a suna masu kallon ta. Yayin da Ishak' da Aishatu kuma suka had'a baki wurin gaishe ta cikin tsantsar ladabi da biyayya. Amsa musu kaka tayi tana mai zama akan kujerar da take facing d'in wacce Aishatu take zaune akai. Kana ta bud'e baki idanuwan ta akan Aishatu tana mai fad'in. "To ya kuma k'arfin jikin naki yanzu 'yannan?" "Alhamdulillah." Aishatu ta fad'a tana mai kallon ta itama. Yayin da ita kuma Kaka ta k'ara gyara zaman ta, tukun ta d'ora da fad'in. "Har yau na rasa gane wace irin macece ke Aishatu, tun kina bani tausayi ina zubar miki da hawaye ada har gashi yanzu kin fara bani haushi. Haba, ace mutum kwata-kwata ya kasa yadda da k'addarar da Allah ya d'oro masa. Yau kimanin kusan shekara talatin da faruwar wannan abun, tun kina da yarinta a jikin ki gashi nan har girma ya fara zuwar miki, amma kullum kina mayar da abu tamkar yanzu yake faruwa, bayan kuma kin san hakan babbar illace gare ki, domin kuwa gashi nan yanzu har likita yace kina gab da kamuwa da ciwon zuciya, bayan kuma tsinannen hawan jinin nan mara imani da yayi miki mugun kamu. To ina ranar damuwar da kike sawa aranki?" Kaka ta fad'a cikin fad'a fad'a tana mai hararar Aishatu. Ita kuwa Aishatu lumshe idanuwan ta tayi tana mai jin furucin kaka na dukan zuciyar ta. Ji take inama ace zata iyayin yadda suke so tayi, tabbas da babu abun da zai hana ta yin hakan, domin kuwa tafi kowa cutuwa da kalar halin da take ciki na yanzu. Amma sai dai kuma ita kanta ta sani babu wanda zai tab'a fahimtar ta, sabo da shekara talatin ba kwana talatin bace ba. Sai dai kuma ita a yanzu ma gaba d'aya ta fara futar da ran sake yin wani murmushi agidan duniya. Sabo da mafarkin matashin kyakkyawan yaron da take yi a yanzu cikin mugun yanayin da yafi na baya sosai sosai, wanda hakan kuma shine musababbin tashin ciwon nata har ya kaita da kwanciya a asibiti na tsawon sati biyu yau kenan. Sai dai kuma tasan babu mai fahimtar halin da take ciki kota fad'a yanzu, sabo da koda ita d'in ce ma ba lallai ta fahimta ba. Sai dai kuma ta riga tabarwa Allah komai nata yanzu, babu abun da take aikin yi face addu'ar Allah yaye mata wannan damuwar, ya sanya mata dangana ko domin farin cikin ahalin ta. Shi kuwa Sheikh Ahmad gyara zaman sa yayi akan kujerar da yake zaune akai yana mai karkata kansa, kana ya watasa dara-daran fararen idanuwan sa akan fuskar Kaka. Sannan ya bud'e baki yana mai fad'in. "Kuji tsohuwar nan dan Allah, to yanzun da kika sata a gaba kina ta masifa dame kike so taji kenan, bayan kuma duk kema kina d'aya daga cikin zamtowa silar abun da ya faru." Ya k'arasa maganar k'asa-k'asa yana mai d'an watsa mata hararar wasa. "Yau na shiga ukku na lalace, yanzu Ahmadu ni kake zagi a haka akan idanuwa na sabo da nayiwa Uwarka fad'a. To Ishak'u kana jifa fitsararren d'anka yana zagi na, amma kayi shiru kana kallon sa. Innalillahi ke duniya ina zaki damu, yau naga abun da yafi k'arfin gani na, sannan naji kalamin da suke shirin toshe mun kunnuwa na." Kaka ta fad'a da k'arfi tana mai fara k'wak'ulo- k'walla a cikin idanuwan ta tana goge ta a hab'ar zanin ta da ta kwanto sa, sabo da Ishak' yayiwa Sheikh Ahmad fad'a. Ai kuwa ta samu yadda take so. Domin kuwa cikin tsantsar zafi Ishak' ya juyo b'arin da Sheikh Ahmad yake yana mai cewa. "Kai dan Ubanka meye hakan kakeyi, bana son shirmen banza da wofi fa, ko kuwa ita d'in tsarar kace da zaka tsaya kana fad'a mata magan-ganu, to kasani har dai zaka iya yi mata rashin kunya nima tsaf zaka yi mun, domin kuwa itace komai nawa a duniyar nan." Ishak ya fad'a cikin zafi yana mai kallon fuskar Sheikh Ahmad. Shi kuwa Sheikh Ahmad kansa ya durk'usar k'asa yana mai d'an murza yatsun hannuwan sa. Yayin da yake jin duk zuciyar sa babu dad'i, sbo da ran mahaifin nasa da yaga ya b'aci. Hakan ne yasa cikin sanyi, kana cikin yin k'asa da murya ya bud'e baki yana mai fad'in. "Kayi hak'uri Abba ka gafarce ni, insha Allah irin haka bazata sake faruwa ba." "Hhhhhhhhhh! Kaji d'an kan Uba ko, ai wallahi ni d'in dai-dai nake da duk wani d'an banza a gidan nan." Kaka ta kwashe da dariya tana mai kallon Sheikh Ahmad, yayin da take jin zuciyar tayi haske k'al. Kana daga bisani kuma ta mayar da idanuwan ta kan matar Sheikh Ahmad da take zaune mai tana fad'in. "Ke kuma lafiya kika zubo mun wa'yan nan mayun idanuwan naki, ke wai a dole mai miji kinji haushi an masa fad'a ko, to ai sai ki matso ki dake ni shine zan san ranki ya b'aci mara kunya matar fitsararre kawai. Malaman k'arya malaman bogi." Durk'usar da kai tayi tana mai d'an sakin murmushin yak'e, kana ta bud'e baki tana mai fad'in. "Allah ya baki hak'uri kakus, ni ba haka nake nufi ba." "Dallacan ni rufemun baki gafara kawai. Kai Allah Sarki Huzaifah na, Allah ya nuna mun taka matar, kai daga gani nasan kyakkyawa 'yar gayu zaka zab'o mana ba irin su d'an ware ba, domin kuwa dama kowa yana d'auko kalar sane." Ta k'arasa maganar tana mai sahafa kan Auta tare da hararar Sheikh Ahmad daga wurin da take zaune. Shi kuwa Sheik Ahmad inda take bai d'ago ya kalla ba, saboda lura da yayi da neman rigima kawai take yi yau d'in, gashi kuma yaji Abban nasa ya biye mata, hakan ne yasa sa kama bakin sa yayi gum da shi ba tare da ya furta komai ba. *JAHAR KAGUL, CIKIN MASARAUTAR FUL'DE.* Babu daren duniyar da zaizo ya tafi ba tare da Gimbiya Haddiyal tayi mafarkin Gid'ad'on ta ba har yau. Yayin da soyayyar sa kuma ta k'ara mamaye gaba d'aya zuciya da ruhin ta, ta yadda har take jin komai zai iya faruwa da ita idan ta rasa sa. A kullum bata da wani labari face nasa, babu abun da tafi son gani face kyakkyawar fuakar sa, hakan yasa ko da yaushe take cikin lumshe idanuwan ta dare da rana, domin kuwa da zarar ta lumshe sun take ganin sa tsaye a gaban ta yana mata murmushin sa. Bata da abokan hira wa'yan da suka huce tsuntsayen ta, domin kuwa sune kad'ai take zama ta bawa labarin Gid'ad'on ta kuma su saurare ta har su taya ta farin ciki. Yayin da sauran mutane kuma suke mata kallon wacce ta fara zaucewa, ta yadda har ake ta aikin samar mata da maganunuwa amma a banza. Sosai ta duk'ufa wurin binciken ganin ta gano mazaunin sa, amma a kullum abun baya yihuwa. Tana da amintaccen Bawa wanda take kiran sa da Buba, wato amintacce ta kenan da fulatanci. Shine kad'ai ya tabbatar da Gid'ad'on ta mutum ne ba aljan ba, sannan kuma ya duk'ufa wurin ganin ya taya ta cimma burin ta. A yanzu haka tana da shekaru Ashirin da biyu ne aduniya, yayin da kyawun halittar ta kuma ako da yaushe yake k'ara bayyana, ta yadda babu mai iyayi mata kallo d'aya ya janye idanuwan sa ba tare da ya sake ba, tun daga kan mace kuwa har namiji. Duk da secondry d'in da tayi batasa ta bar al'adun su na fulani ba da shigar su, kamar yadda ta taso ta ganta acikin ta. Domin kuwa haka masarautar tasu take tafiya har kawo yau da al'adun ta, wannan dalilin ne ma ya sanya ko wasu kayan daban Gimbiya Haddiyal bata sanyawa sai nasu na fulani, duk da kuwa ba su d'in ne kad'ai suka zamto kayan ta ba, domin kuwa Habu da kansa yake siyo mata English wear tare kuma da atamfofi da leces, amma ko kallo basu isheta ba. Iyakaci idan kaga tasa wasu kayan daban to lokacin bacci ne, shine take sanya sleeping dress a jikin ta. Yayin da su kuma kayan nata na fulani suka zamto kala-kala, kana masu matuk'ar yawa, ta yadda har idan tasa wani sai ta shafe sama da wata ukku ba tare da ta zagayo kansa ba, kai wani lokacin ma har mantawa da wasu takeyi. *K'ASAR MALIN, JAHAR KARFUZ CIKIN BAK'AR MASARAUTA* Tun bayan karon da Gimbiya Tamir da Bir da sukayi na biyu da har yau basu sake gamuwa ba, tsawon watanni da yawa kenan, kuma hakan ya faru ne ta dalilin rok'on sa da iyar bayi tai-tayi har da su k'wallar ta akan kar ya k'ara shiga sabgar Gimbiya. Amma sai dai kuma ba k'aramar cutuwa yayi ba da rashin ganin tan da bayayi, domin kuwa babu ranar da zata zo ta shige ba tare da yayi tinanin ta ba, haka kuma aduk daren duniya yana aikin mafarkin ta. Sosai kuwa ya rame kana gaba d'ayan sa ya k'ara komawa shiru-shiru. Haka kawai kwanan nan yaji aduk duniya babu abun da yake son gani sama da fuskar ta, ta yadda har yake jin baik'i ba ace ko kashe sane tasa ayi muddin ya riga ya ganta. Wannan dalilin yasa sa k'udirtawa ransa cewar yau duk runtsi duk huya sai ya isa gare ta, sai dai duk abun da zai faru ya faru bayan ya gantan. Ita kuwa gimbiya Tasmir a b'angaren ta sai da ta d'auki kusan wata tana jin bak'in cikin abun da yayi mata, kafun daga baya kuma komai ya huce. Babu abun da yafi damun ta sai idan ta tuna da yadda bugun zuciyar ta ke sauyawa aduk lokacin da suka had'u. Hakan yasa ta k'udiri aniyar cewa muddin suka k'ara yin gamo da shi sai yayi mata bayanin dalilin da yasa take jin fad'uwar gaba idan ta kasance a gaban sa, sabo da tana zargin ko wani asirin gare sa akan ta, sai dai kuma tun bayan waccan had'uwar tasu ba ta k'ara ganin sa ba. Hakan yasa ta gane cewa ya bam-bance tsakanin ta da shi kenan, shiyasa bai k'ara biyo hanyar ta ba, wanda hakan kuma ba k'aramun dad'i yayi mata ba. Yanzu haka zaune take akan d'irkeken bak'in dokin ta sanye da shigar ta-ta yau da kullum. Yayin da hannun ta d'aya kuma yake r................✍ *AMIN AFUWA ZAKUGA SUNAN MAHAIFIN SHEIKH AHMAD YA CANZA DAGA ABDULKARIM DA NACE A PAGE NA UKKU ZUWA ISHAK', HAKAN YA FARUNE TA DALILIN MANTUWAR DA NAYI.* SAI KUMA NA BIYU YAYAN GIMBIYA HADDIYAL HABU SUNAN SA, BUBA KUMA SUNAN AMINTACCEN BAWAN TANE, SHIMA ABAYA NAYI MISTAKE NA CEWA HABU BUBA, WANDA SAI DAGA BAYA NA FAHIMTA.* UMAR FARUQ.✍ 🐎 *BAƘAR MASARAUTA* 🐎 👑👑 🦋 🦅🕊🦆 🐍🎠🐄🏹 _*NA*_ UMAR FARUQ*D* *BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM* *PAGE 30* _END OF BOOK 1_ Rik'e da zureriyar takobin ta, d'ayan hannun ta kuwa rik'e yake da linzamin dokin ta. A hankali dokin ya fara tafiya, yau da alamun ita kad'ai kawai take sha'awar yawon, duba da yadda babu wani da ya biyo ta a cikin dakarun nata. Tafe suke a saman dokin fuskar ta d'auke da annuri, sab'anin sauran ranakun da ko da yaushe take a d'aure. Yau tun da ta tashi daga bacci take jinta cikin wani irin farin ciki. 'Daga kanta tayi sama tana mai kallon yadda giza-gizai suke a ko ina, ga kuma yadda garin nasu yayi luf-luf tamkar koda yaushe, kana ga wata irin sassanyar iska mai matuk'ar dad'i da take busata ta ko ina, ta yadda har uban bak'in gashin kanta yake d'an d'agawa sama. Ga kuma yadda iskar ke kad'a rigar da ke sanye a jikin ta, tana ta faman bud'ewa, wannan dalilin shine ya sake sanya ta cikin annashuwa sosai. Acan wurin Bir kuwa cikin wani irin yanayi na tsantsar buk'atar ganin fuskar Gimbiya da yaji shi a cikin sa ya mik'e daga bakin bishiyar da yake zaune. 'Daga tafin hannun sa yayi yana mai shafa lallausar sumar dake d'auke akan sa mai matuk'ar yawa. Kafin daga bisani kuma ya d'an saki murmushi, yana mai fatan ya had'u da itan idan ya tafi. Kana ya fara d'aga k'afafuwan sa cikin wani irin kuzarin da yake ji a tattare da shi, yana mai dosar hanyar da yake tsammanin zai iya cin karo da Gimbiyar tasa acan. Sosai yake jin wani irin farin ciki mara misaltuwa tattare da shi. A lokaci d'aya gaba d'ayan su bugun zuciyar su ya sauya, suka fara jin tamkar yadda suke ji aduk lokacin da sukayi kusanci da junan su. Cak Bir ya tsaya a wurin da yake yana mai lumshe idanuwan sa, kana daga bisani ya d'ago tafin hannun sa yana mai dafe saitin zuciyar sa da shi. Yayin da yake jin wani irin farin ciki mara misaltuwa nayi masa bargo a gaba d'aya ilahirin jiki da zuciyar sa, sabo da fahimtar da yayi na tabbas Gimbiyar tasa tana kusa da k'arasowa wurin da yake d'in, wato dai yau yayi futowar sa'a. Kana daga bisani ya cigaba da d'aga k'afafuwan sa yana mai cigaba da bin hanyar, kansa sun kuye a k'asa, acewar sa yana son ta fara kallon sa ne kafin shima ya kalle ta. Ita kuwa Gimbiya Tasmir lokaci d'aya yanayin ta ya sauya, gaba d'aya annurin dake akan fuskar ta ya gushe, ta yadda har launin idanuwan ta suka fara d'an sauyawa, ba dan komai ba kuwa sai sabo da jin da tayi bugun zuciyar ta gaba d'aya ya canza, k'irjin ta na wani irin bugun tara-tara, wanda hakan yasa ta fahimci abun da ke shirin faruwa, wato dai yau ma batayi futowar sa'a ba, tayi gamo da k'ask'antaccen Bawan ta. 'Dan rumtse idanuwan ta tayi da k'arfi, tana mai tinanin kalar hukuncin da zatayi masa idan har bai bata amsar tambayar da zatayi masa yau ba, domin kuwa ta k'udiri aniyar jin dalilin da ya sanya take samun fad'uwar gaba aduk lokacin da zai-zo gare ta. Cikin wani irin yanayi na tsantsar b'acin rai ta sake damk'ar linzamin dokin. Ai kuwa take a wurin ya k'ara gudun sa akan wanda yake yi na baya. Ba zato ba tsamnani kawai sai ganin su sukayi a gaban juna. Ita tana daga saman doki idanuwan ta akan sa. Yayin da shi kuma yake daga k'asa gaban dokin idanuwan sa a cikin natan. Kallon-kallo suka fara jifan junan su da shi daga wuraren da suke tamkar ko da yaushe. Yayin da bugun zuciyoyin su kuna suke sake tsanan ta, ta yadda har suke jin tamkar zasu hudo k'irjin su su futo. Cikin wani irin yanayi Gimbiya Tasmir ta rumtse idanuwan ta, tana mai jin tabbas wannan bawan yana shirin zame mata masifa a rayuwa, kafin daga bisani kuma ta fara aikawa kanta da tambayoyi. "Shin mene yasa bashi da tsoro ne ma shi, wato kenan yana nufin yace duk wahalar da yasha a wancan lokacin bai daddara ba, tun da gashi nan yau ma ya tsare ni agaba yana aiko mun kallo da wa'yan nan mayun idanuwan nasa, tabbas yau d'in kuwa dole ne na san dalilin da yasa kallon sa yake sanya mun fad'uwar gaba." Ta fad'i haka a cikin ranta, kana daga bisani ta bud'e idanuwan nata akan fuskar Bir. Sannan tayi wani irin durowa daga kan dokin, tana mai fara d'aga k'afafuwan ta-ta doshi wurin da yake takobin ta rik'e a hannun ta. A hankali Bir ya d'an fara d'aga k'afafuwan sa yana mai ja baya daga wurin da yake, sabo da yadda yaga ta nufo kansa gadan-gadan. Yayin da har lokacin kuma idanuwan su suke sark'e a cikin na juna. Ba shi ya dakata da ja da bayan da yake ba kamar yadda itama d'in bata daina biyo sa ba, har sai da ya dan gana da jikin wata k'atuwar bishiya, kana ya jingina da ita yana mai lumshe idanuwan sa. Yayin da ita ma ta tsaya cak a wurin, tana mai jin zuciyar ta na cigaba da gudu a d'ari, ga kuma wani irin b'acin rai da tsantsar tsanar wannan bawan na gaban ta da suke taso mata tun daga k'asan zuciyar ta. A hankali Bir ya bud'e idanuwan sa yana mai watsa su akan fuskar ta, kana ya d'an saki murmushin sa mai matuk'ar kyau, ta yadda har sai da fararen hak'waran sa suka bayanna, tukun ya d'an d'aga lab'b'an sa cikin yin k'asa da murya, yana mai fad'in. "Hak'ik'a idanuwa na sunyi kewar ganin wannan kyakkyarwa fuskar taki, mai cike da abubuwan kallon akan ta Gimbiyar mu. Shin wai me...." Maganar tasa ce ta yanke, sabo da yadda yaga lokacin d'aya jikin ta ya d'auki wata irin rawa, ga kuma idanuwanta da ta zuba su akan sa da suke k'ara rikid'ewa suna yin ja, jan ma irin jajahur d'in nan. Yayin da jijiyon kanta kuma suka futo sukai rud'u-rud'u akan goshin ta. "Zan tambaye ka, sai dai kuma kafun nan ina son kasani bana son k'arya, asalima na tsani duk wani mak'aryaci a rayuwata, dan haka amsar tambayata kawai nake buk'atar ji daga gare ka a yau d'in." Gimbiya Tasmir ta fad'a cikin wata irin murya, wacce take nuni da tsantsar kalar b'acin ran da take a cikin sa, ta yadda har iskar bakin ta da ke futowa tana dukan fuskar sa a lokacin da take furucin ta zamto zazzafa matuk'a. Lumshe idanuwa Bir yayi yana mai d'an juyar da kai gefe ya fesar da iska daga cikin bakin sa, kana ya sake juyowa b'arin da take yana mai d'an dage mata girar sa d'aya, alamun yana jin ta to. Yayin da ita kuma ta d'ora da fad'in. "Tunda na taso a rayuwata, ban tab'a sanin wani abu wai shi tsoro ba, sannan kuma ban tab'a sanin b'acin rai ba, kana bansan meye fad'uwar gaba ba, kasan ko me yasa? Sabo da na taso cikin tsaro da kariya, sannan kuma na taso cikin gata. Amma tun a karo na da kai na farko komai nawa ya fara sauyawa, b'acin ran da ban san sa ba kasa nasan sa a ranar, fad'uwar gaban da ban santa ba kasa naji ta a ranar, magana da yinta ke wahalar dani kasa ta zamto abaryina ta dole. Dan haka ayau yau d'in nan, a kuma yanzu-yanzun nan nake son sanin abun da ka taka." Ta fad'a cikin wani irin yanayi, tukun ta fara d'an d'aga k'afafuwan ta tana mai zagayasa a wurin da yake, kana ta sake dawowa gaban sa ta tsaya, tana mai watsa jajayen idanuwan ta a cikin nasa, ta dora da cewar. "Shin me ka taka? Wane kalar sihiri kake tattare da shi ne? Ya sunan bokan daya baka shi? Sannan kuma akan me bugun zuciya ta yake sauyawa a duk lokacin da nayi gamo da kai!!! ?" Ta k'arasa maganar cikin k'araji tana mai d'aga k'afar ta d'aya ta dire ta a k'asa, kana ta d'ora da sakin numfar-fashi idanuwan ta k'ur akan Bir. Shi kuwa Bir wami irin farin ciki mara misaltuwa ne yaji ya lullub'e zuciya da ruhin sa, sabo da fahimtar da yayi ba shi kad'ai bane ya afka kenan. Tabbas sunan da iya ta sanya masa yana gab da zamtowa na gaskiya, wato Jarumi, domin kuwa ya riga da ya sani muddin Gimbiya ta zama tasa to idan da akawai abun da yafi Jarumi ma za'a kira sa da shi. Hakan ne yasa sa sakar mata murmushi kawai, yana mai sake kafeta da tsumammun idanuwan sa da suke d'auke da wani irin sinadari a cikin su amai-makon ya bata amsar ta. Ita kuwa Gimbiya Tasmir yadda kasan saukar tafasash-shen ruwan dalma akan ta haka take jin saukar murmushin sa a cikin jikin ta. Lokaci d'aya jikin ta ya k'ara d'aukar kyarmar b'acin rai, sabo da ganin da tayi tamkar yana shirin raina mata hankali, tunda gashi nan amai-makon ya bata amsar ta sai kafeta da yayi da idanuwan sa yana aiko mata da murmushi ma. "Wallahi! Wallahi Azaba mai rad'ad'i zata hau kanka, irin wadda tun da kazo gidan duniya baka tab'a jin labarin ta ba balle har ka ganta muddin kayi wasa da kalami na, dan haka ka gaggauta bani amsar tambaya ta tun kafin raina ya k'arasa dagulewa, hukunci na ya hau kanka." Gimbiya Tasmir ta sake fad'awa Bir, jijiyoyin kanta na k'ara futowa rad'a-rad'a akan goshin ta. "To idan kuma ban shirya fad'ar amsar ba fa, ko kuma nima nace ban santa ba fa?" Bir ya fad'a cikin tsantsar farinciki, yana mai lumshe idanuwan sa. "Tabbas ko hakan tamkar dai-dai yake da ka kira mutuwar ka kai da kanka zuwa gare ka domin ta d'au ranka, domin kuwa azaba ta ta huce gaban kwatance, dan haka dak'ik'a d'aya kawai na baka, ka gaggauta bani amsa ta ko kuma komai ma ya faru da kai k'ask'antacce mara galihu." "To banda amsar nace miki 'yar gata." Bir ya fad'a yana jifan ta da murmushin sa tamkar ba zagin sa ita tayi ba. Wani irin juyi Gimbiya Tasmir tayi daga wurin da take, tukun ta mik'a hannun ta-tana mai kamo linzamin dokin ta, kana ta d'ane kansa tana mai rumtse idamuwan ta, tare da mik'ar da takobin ta-ta saita Bir da ita. Wasu irin surutai tayi da matuk'ar k'arfi, tana mai nuna Bir da takobin nan tata. Kana ta daki cikin dokin nata da k'afar ta tana mai nuna masa hanyar da zasu bi. Wata irin iska mai matuk'ar k'arfi Bir yaji ta dake sa, kana ta k'udun-dune sa acikin ta, tukun ta fara wani irin fuzgar sa a cikin k'asa, ta yadda kawai yaji sa yana bin bayan dokin Gimbiya Tasmir daga kwancen da yake a guje. Sosai take gudu akan dokin nata tana mai nutsawa wata hanya. Yayin da Bir kuma ke biye da ita abaya iska na jansa da matuk'ar k:arfi, sosai kansa da wasu wurare na jikin sa duk suka farfashe, sabo da duwatsun da yake cin karo da su akan hanyar. A haka har suka b'ulla gaban wani gini wanda yake d'auke da wata irin k'ofa a jikin sa, wato d'akin Azaba. Cak dokin Gimbiya Tasmir ya tsaya a gaban k'ofar d'akin nan. Shima kuwa Bir adai-dai wurin yaji iskar nan ta dena funcikar sa, amma kuma bawai sakin sa tayi gaba d'aya ba, har yanzu dai yana k'udun-dune a cikin ta ne. Ita kuwa Gimbiya Tasmir cikin wani irin yanayi ta duro daga kan dokin nata, tukun ta juya b'arin da Bir yake tana kallon sa, kana ta bud'e baki cikin kaushi tana mai fad'in. "Shin ka shirya bani amsar tambaya ta yanzu ko k..." Maganar ta-tace ta katse, sabo da yadda taga Bir ya girgiza mata kai yana sakar mata murmushi a yadda yake tun kafin takai k'arshen zancen nata ma, alamun bai shirya ba d'in kenan. Hakan ne yasa ta juyawa b'arin da k'ofar nan take da wani irin sauri, kana ta d'aga takobin ta sama tama mai nuna k'afor da ita, sannan ta bud'e baki cikin k'araji, tana mai fad'in. "Gargabiluuu!!!" Take kuwa a wurin k'ofar ta fara bud'ewa har ta bud'e duka. Kana ta sake juyawa b'arin da Bir yake tana mai sake yin wasu surutan. Ai kuwa tini iskar nan ta sake d'ibar sa a guje zuwa cikin d'akin da ya kasance d'an k'arami da shi, mai zagaye da kaskwayen huta a cikin sa suna ta faman ci. D'aga k'afafuwan ta ita tayi tana mai bin bayan sa. Shi kuwa Bir iskar nan bata sake sa ba har sai da ta dangana da shi gaban wasu irin k'arafa, tukun ya jisa sakayau gaba d'ayan sa, ta yadda har ya samu damar mik'ewa tsaye yana mai kallon ciwu, kan jikin sa, amma sai dai kuma ko gama mik'ewar baiyi ba yaji wasu irin k'arafa sun tawo daga sama sun d'ad'd'aure sa gagam a jikin su. Cikin wani irin yanayi na tsantsar firgici da tashin hankali ya d'ago idanuwan sa yana mai watsa su akan fuskar Gimbiya Tasmir da take tsaye a gaban sa, sabo da yadda yaji k'asusuwan jikin sa tamkar zasu warwatse. "Rai Rai Rai Buuuu Hooo Reeee." Gimbiya Tasmir ta fad'a tana mai nunasa da takobinta. Take kuwa yaji wani irin bala'in zafi, irin wanda bai tab'a riskar saba tun da yazo gidan duniya ya lullub'esa, ta yadda har bai san lokacin da ya saki wani irin gigitaccen ihu ba. Ita kuwa Gimbiya Tasmir tana jin ya saki ihun nan ta juya tana mai fara d'aga k'afafuwanta ta doshi hanyar waje. Wasu surutan ta sakeyi a lokacin da ta futa bakin k'ofar d'akin. Ai kuwa take wani irin bak'in duhu ya mamaye gaba d'aya ilahirin cikin d'akin. Tukun ta juya tana mai hayewa saman dokin ta. Sannan ta sake nuna k'ofar da takobin ta tana mai kiran sunan Gargabilu. Take kuwa k'ofar ta koma ta rufe gam. Sannan ta damk'i linzamin dokin ta tana mai juyawa suka doshin hanyar da zata mayar da ita gida da tsananin gudu. _CIGABAN LABARI_ *K'ASAR HAUSA, JAHAR KAGUL CIKIN MASARAUTAR FUL'DE.* Kallon kallo Yarima Asad da Gimbiya Haddiyal suka cigaba da jifan junan su da shi. Yayin da Al'amin kuma ya saki baki yana kallon su, zuciyar sa cike da fargabar abun da Yarima Asad zeyiwa Gimbiya Haddiayl, sabo da yadda yaga gaba d'aya cinyoyin sa sun b'aci da madarar shanun nan. Shi kuwa Yarima Asad a hankali ya k'ara janye idanuwan sa daga kan fuskar ta yana mai sake kallon jikin sa, kana ya k'ara d'agowa yana mai k'ara kafeta da su. Yayin da yake jin zuciyar sa na wani irin bugu da matuk'ar sauri, abun da tun da yake a rayuwar sa bai tab'a ji ba kenan dan ya tsaya da wata yarinya. Ita kuwa Gimbiya Haddiyal haka nan taji wani irin haushin sa ya lullub'e gaba d'aya ilahirin jiki da zuciyar ta. Amai-makon ta basa hak'uri a matsayin ta na wacce tai masa laifi sai tak'i yin hakan gaba d'aya, a karshe ma sai idanuwanta da ta janye daga cikin nasa a hankali. Kana ta mik'e ta juya tana mai fara d'aga k'afafuwan ta da niyyar komawa. Amma sai ji tayi an cafki yastun hannuwan ta da matuk'ar sauri. Cak ta tsaya a wurin da take tana mai rumtse idanuwan ta, sabo da yadda taji wani irin abu ya tsirga mata tun daga tsakiyar kanta har izuwa 'yantsun k'afafuwan ta a lokacin da ya rik'o yatsun hannun nata. Kafin daga bisani kuma ta fara juyowa gare sa fuskar nan ta ta a matuk'ar d'aure. Ido hud'u suka suka sakeyi da shi yana mai cigaba da kallon ta da tsumammun idanuwansa. 'Dauke nata idanuwan tayi daga kan fuskar sa, tana mai mayar da su kan 'yantsun hannuwan sa da suka kasance had'e da nata wuri d'aya. 'Dan taune leb'enta tayi na k'asa da d'an k'arfi, tana mai jin wani irin mugun bak'in ciki da takaici na cakar ta, kafin daga bisani kuma ta janye idanuwanta daga kan 'yantsun nasu, tana mai mayar da su kan fuskar Yarima Asad. Hakan da Yarima Asad ya gani ne ya sanya sa sakin hannun nata da sauri. Yayin da ita kuma ta hurga masa wani irin kallo, kafin ta juya tana mai kama hanyar da ta biyo tazo wurin, ba tare da ta d'auki ko k'waryar ta ba. Lumshe idanuwa Yarima Asad yayi, yana mai jin yadda tsigar jikin sa ke mimmik'ewa, ga kuma yadda yake ganin kyakkyawar fuskar ta a cikin idanuwansa, zai iya cewa tun da yake a rayuwa bai tab'a cin karo da mai kyawun ta ba ko a cikin larabawan da yayi rayuwa da su kuwa. Lokaci d'aya yaji gaba d'aya komai nasa ya sauya a kanta, kayan da suke sanye a jikin ta da yake musu kallon na mahaukata a lokacin da suka shigo cikin masarautar yaga masu su, yanzu kuma sai yaga sunyi bala'in kyau a jikin ta ita. Ko da ba a fad'a masa ba yasan ita d'in bagidajiya ce, duba da yadda yaga yanayin mutanen garin nasu suke, ga kuma kalar shigar da ya gani sanye a jikin ta. To amma mai yasa ta kasa basa hak'uri bayan tasan itace tayi masa laifi. Ya raya haka a cikin ransa yana mai sake d'aga idanuwansa yabi bayanta da kallo. Kafin daga bisani kuma ya mik'e tsaye zumbur daga kan shimfid'ar da yake, yana mai shirin bin bayan ta. Da sauri Al'amin ya mik'a hannun sa yana mai kamo tafin hannun Yarima Asad da shi. Hakan da Yarima Asad yaji ne ya sanya sa dakatawa, yana mai juyowa ya watsa idanuwan sa akan fuskar Al'amin. Girgiza masa kai Al'amin yayi yana mai masa alamar da ya dawo ya zauna da idanuwansa. Yayin da a zuciyar sa kuma mamakin Asad ya gama rufe sa gaba d'aya, domin kuwa k'wayoyin idanuwan sa kawai ya kalla ya fahimci yanayin da yake a ciki. Lumshe idanuwa Yarima Asad yayi ba tare da ya iya cewa Al'amin komai ba, tukun daga bisani ya dawo jiki a sanyaye yana mai komawa wurin da ya tashi ya zauna. Kana ya k'ara bin hanyar da Gimbiya Haddiyal tabi da yanzu har an den hangon ta ma da idanuwan sa. Sosai hoton kyakkyawar fuskar ta ya zauna daram a cikin idanuwan sa, ta yadda har yake jin tamkar har yanzu tana zaune ne a gaban sa. A hankali ya durk'usar da kansa k'asa yana mai k'ara kallon madarar da take kwance akan sitirar jikinsa, kana ya d'an d'aga lab'b'ansa yana mai fesar da wata zazzafar iska daga cikin bakin sa. Yayin da shi kansa yake mamakin abun da ya hanasa hukunta wannan bagidajiyar bak'auyiyar yarinyar, akan wannan laifin da tayi masa har ta juya ta ta tafi. Wai yau shi Asad ne mace tayi masa laifi kuma ya barta ta juya ta tafi ba tare da ta basa ko hak'uri ba, laifi ma babban laifi ba k'arami ba. Shi da mata suke hauka akan sa, suke kuka tare da kaff-kaffan abun da zai b'ata masa ransa, suke jin dad'i aduk lokacin da ya daga ido ya kalle su. Mata masu aji masu ilimi, kana wa'yan da sukafi k'arfin kud'i, amma sai gashi yau wata can 'yar k'auye ta b'ata masa jiki ya kasa yin komai akan ta, asalima ko wani haushin ta baiji ba a ransa, sai zallar kyawun hallitar ta da ta tafi ta barsa da ita a cikin idanuwan sa. Suna a cikin wannan yanayin Habu ya dawo fuskar sa d'auke da murmushi. Amma sai dai kuma yana zuwa gaban shimfid'ar da suke zaune akai yaja ya tsaya cak, murmushin kan fuskar tasa na gushewa, yayin da idanuwan sa kuma suka kasance k'ur akan k'waryar madarar nan, tare da jikin Yarima Asad da ya gansa a b'ace. "Shin meye hakan nake gani? K'waryar madara ta kife a jikin ka? Kar dai kuce mun ba Haddiyal bace ta kawo madarar nan da kanta, wata ta sanya ta kawo muku har tazo ta kifa maka ita a jiki." Habu ya fad'a ransa a tsantsar b'ace. Kafin daga bisani kuma ya fara k'ok'arin juyawa da sauri, da niyyar yaje ya samu Gimbiya Haddiyal dan yaji bayanin abun da ya faru. Amma sai dai ko sauke k'afar sa d'aya da ya d'aga bai kaiga yiba Yarima Asad ya mik'a hannu da sauri yana mai cafko 'yan yatsun sa. Hakan da Habu yaji ne ya sanya sa juyowa gare sa yana mai zuba masa idanuwan akan fuskar sa. Shi kuwa Yarima Asad girgiza masa kai yayi yana mai d'an sakin murmushi, kana ya bud'e baki yana mai cewa. "To yanzu da ka juya cikin fushi ina zaka kenan?" "Zanje wurin ta ne, domin tamun bayanin yadda akai hakan ta faru, bayan ni da kaina nace mata ta amsa ta kawo muku da kanta." Ya k'arasa maganar har lokacin ransa a b'ace, yana shirin zare yasun hannun sa daga cikin na Yarima Asad. Ganin hakan da Yarima Asad yayi ne ya sanya sa sake damk'ar yastun nasa da k'arfi. Tukun ya girgiza masa kansa fuskar sa d'auke da murmushi, kana ya d'aga lab'b'an sa yana mai fad'in. "To idan ita d'in ce ta kawo da kanta kuma fa?" "Ok kana nufin kace mun ita Haddiyal d'in ce ta kifo maka madarar da kanta tsabar tana hauka ko?" Habu shima ya fad'a idanuwan sa akan Yarima Asad. Yayin da shi kuma Yarima Asad ya lumshe nasa idanuwan, yana mai jin gaba d'aya yanayin sa na sauyawa. Kana daga bisani ya sake wara idanuwan nasa akan fuskar Habu, sannan ya bud'e baki yana mai fad'in. "To yanzu dai idan ma hukunci kake son kayi ba kowa ya kamata kayiwa ba face ni, domin kuwa ita har sai da ta juya ta tafi ma tukun na kifar da k'waryar madarar, ta hanyar zamewar da tayi a hannu na a lokacin da na d'auko ta domin nasha." Yarima Asad ya samu kansa da fad'awa Habu haka, ba dan komai ba kuwa sai sabo da yadda yaga ransa ya b'aci, kuma ya fahimci muddin yaje wurin ta bazai mata da sauk'i ba. Wanda sai bayan ya gama fad'ar hakan tukun mamakin abun da yasa sa yayi k'aryar akan waccan kucakar da tayi masa laifi ya lullub'e sa. "To mema ya dameni ne ni, koda kashe ta ma zaiyi idan yaje d'in da har na rufa mata asiri?" Yarima Asad ya fad'i haka a cikin ransa bayan ya gama yiwa Habu bayanin nan. Yayin da Al'amin kuma yayi suman zaune a wurin da yake, idannwan sa akan fuskar Yarima Asad. Gaba d'aya mamaki ya gama cikasa, ko a mafarki akace masa Yarima Asad zai aikata abun da ya aikata yau wallahi tallahi bazai tab'a yadda ba, amma sai gashi nan akan idanuwan sa komai ya faru. Hakan ne yasa sa jinjina kan sa yana mai cigaba da bin Yarima Asad da idanuwa, wanda shi kuma zuwa yanzu ya saki yantsun Habu da ya rik'e yana mai lumshe idanuwan sa. Shi kuwa Habu jinjina kansa yayi yana mai yadda da abun da Yarima Asad ya fad'a masa, domin kuwa ko kad'an dama shi da farko bai kawo k'anwar tasa ce ta kifar da madarar ba, sabo da yadda ya santa da tsantsar nutsuwa. Hakan yasa ya d'an sakin murmushi, kana ya bud'e baki yana mai fad'in. "To yanzu abun da za'ayi shine, tashi zakuyi mutafi part d'in mu sai kayi wanka ka canza kaya, in yaso sai akawo muku wata madarar bayan ka shirya kusha ko." Ya fad'a yana mai rik'o hannun Al'amin. Ba tare da Yarima Asad yace komai ba gaba d'ayan su suka mik'e suna masu bin bayan sa. A b'angaren Gimbiya Haddiyal kuwa, cikin tsantsar k'unar rai ta k'arasa cikin d'akin ta. Direct ta wuce bathroom d'in ta da yake a cikin d'akin. Tana mai zuwa ta kunna ruwa, bayan ta shafe dai-dai saitin wurin da Yarima Asad ya rike na hannun ta da sabulu ta dinga dirzar sa. Tana yi hawayen bak'in ciki na tsiyayowa daga cikin idanuwan ta suna wanke kaykkyawar fuskar ta. Tabbas Yarima Asad ya shigo cikin sahun mutanen da tafi tsana a rayuwa ta sama da komai, ta yadda har ya zamto mutum na farko daga cikin su. Yayin da shi kuma Yariman Yamma ya zamto na biyu. Ba dan komai ba kuwa sai sabo da yadda gaba d'ayan su suka rik'e hannun ta, wanda ko kad'an basu cancanci su zamto wa'yan da zasu kalli ko da fuskar ta ba, hakan yasa take jin tamkar ba tayiwa Gid'ad'on ta adalici ba da ta bari hakan ta faru. A yanzu tafi jin haushin Yarima Asad ma akan Yariman Yamma. Sabo da shi kallo d'aya tayi masa ta fahimci gaba d'ayan sa zubin 'yan iskan samarin nan gare sa, duba da irin sitirar da ta gani sanye a jikin sa, wacce ko kad'an batayi kama da ta d'an musulmi ba, musulmin ma kuma wai hausa fulani, hausa fulanin ma wai d'an Sarki. Wannan dalilin ne ya sanya ta k'arajin haushin sa fiye da yadda take jin na Yariman Yamma, domin kuwa ita ta tsani mu'amala da 'yan iskan mutane a rayuwar ta. Ba ita ta bar dirzar hannun nata ba har sai da taji ya fara yi mata rad'ad'i, tukun ta hak'ura ta barsa haka tana mai juyawa ta doshi k'ofa, yayin da har lokacin kuma idanuwan ta suke cigaba da zubar hawaye. Bata tsaya ba har sai da ta dangana da gaban dressing mirrow d'in ta, kana taja ta tsaya a gaban sa tana mai kallon kanta a cikin sa. Kafin daga bisani kuma ta rumtse idanuwan ta da matuk'ar k'arfi, sannan ta bud'e su tana mai d'aga lab'b'an ta cikin sanyi tace. "Shin har sai zuwa wane lokaci ne zaka bayyana a gareni Gid'ad'o am? Har tsawon wane lokaci zan cigaba da zaman jiran ka? Ka taimake ni, ka taimaki rayuwa ta ka bayyanar mun a zahiri Gid'ad'o am, domin kuwa rashin ganin ka a zahiri tamkar barazana da rayuwata ce a gidan duniya, rashin bayyanar ka ya sanya har wasu mutane can suke k'ok'arin rik'e wani sassa daga jiki na, bayan kuma kai kad'ai ne mutumin da ya dace da rik'e su, domin kuwa kaine kad'ai mammalikin su. Tabbas zuciya ta na gab da tarwasewa muddin rayuwa zata cigaba da had'ani da irin wa'yancan mutanen, wannan dalilin yasa naji na tsane su fiye da yadda na tsani mutuwa ta, domin kuwa ni d'in gaba d'aya na takace, tamkar yadda kaima ka zamto nawa ni kad'ai." Ta k'arasa maganar tana mai durk'ushewa akan guiwoyin ta ta cigaba da sakin kukan ta har da su shash-sheka. Yayin da fuskar Yarima Asad kuma tak'i b'acewa daga cikin idanuwan ta, wanda harda hakan yasa take k'arajin tsanar sa fiye da wacce take yiwa Yariman Yamma, sabo da ada fuskar Gid'ad'on ta kawai ce ke mata gizo acikin idanuwan ta, amma sai gashi yau fuskokin sun zama biyu, wato ta gid'ad'o'n ta da kuma ta waccan mutumin mai siffa da 'yan iska da suka had'u. *K'ASAR MALIN, JAHAR KARFUZ CIKIN BAK'AR MASARAUTA.* Sosai hawaye suke kwaranya daga cikin idanuwan Gimbiya Tasmir tana tafiya. Wani irin rad'ad'i da suya take jin zuciyar ta nayi mata, idan ta tuna yadda wancan k'ask'antaccen bawan ya had'a jikin sa da nata. Ji take inama ace Ubangiji Gargabilu ya d'auki rayuwar ta tun kafin zuwan wannan ranar, ji take inama ace baya na komowa, tabbas da babu abun da zai sa tayi gigin cewa zata dake sa a yau, ballan tana har azo ga wannan d'anyen iskancin da fitsarar daya aikata a mata. Wai ace kamar ita, kamar ita Gimbiya Tasmir, yarinya mai tsantsar kwarjin da Izza, aka samu bawan da ya iya tsayawa a gaban ta ya kalli cikin idanuwan ta, sannan kuma bai ma tsaya a iya kar kallon cikin idanuwan nata ba har sai da ya dangana da had'a jikin sa da nata wuri d'aya. "Inaa! Wallahi hakan bazai yuwu ba! Nayi rantsuwa da Ubangiji Gargabilu sai naga bayan ka, sai dai duk abun da zai faru ya faru, domin kuwa bazan tab'a barin ka ba kaci banza." Gimbiya Tasmir ta fad'a da wani irin k'araji, tana mai durk'ushewa a kasa akan guiwoyin ta, yayin da ruwan hawaye kuma suke cigaba ambaliya daga cikin idanuwan ta tamkar an bud'e famfo. "Shi me yasa rayuwa zakiyi mun haka? Me yasa duniya zaki juyamun a lokaci guda? Me yasa izza ta, kwajini na tare da k'arfin ikona zasu nemi tarwatsewa a lokaci guda? Shin wane laifi na aikata maka Ubangiji Gargabilu da har zaka hukunta ni ta hanyar turo k'ask'antacce bawa gare ni? Me yasa, me yasa zaka hanani hukun tasa Baba? Me yasa hakan zata faru dani?" Ta k'ara fad'a cikin k'araji, hawaye na cigaba da tsiyayowa daga cikin idanuwan ta, abun da ita kanta bazata ce tasan lokacin da ta d'auka rabon ta da kuka ba, sai gashi yau tana yin sa har da k'araji ta sanadin Bawa, Bawan ma kuma k'ask'ancce wanda ko shi kansa bai san suwaye iyayensa ba, Bawan ma d'an tsuntuwa. Kafin daga bisani kuma ta sake mik'ar da takobinta tana mai fad'in. "Shairamaaa!!!" Ta fad'a da wani irin k'araji bayan ta rumtse idanuwan ta. Take kuwa wannan dank'areriyar macijiyar tata ta bayyana tana mai karkad'a harshen ta. Yayin da ita kuma Gimbiya Tasmir ta k'arasa gaban ta da sauri, tana mai durk'usawa k'asa ta damk'i kanta da matuk'ar k'arfi. Tukun daga bisani ta bud'e baki cikin tsantsar kuka tana mai fad'in. "Shin ina taimakon da akace zaki yimun a rayuwa Shairama? Ina Garkuwar da akace zaki zame mun a gidan duniya Shairama? Kana ina hasken da akace zakina haskan gaba na da shi Shairama? Shin wai meye amfanin ki ma agare ni Shairma, bayan gashi nan kina gani ana hulak'anta ni ana take izza ta da kwarjini na akan idanuwan ki ba tare da kin iya komai ba? Shin taya ya zansan dalilin da yasa Baba ya hanani hukunta wancan matsiyacin Bawan, wane irin k'ulli ne yake ak'asa da har hakan zata kasance? Wata irin alak'a ce take a tsakanin su da har take shirin ta ture wacce take tsakani na da shi? Tabbas zan binciko, kuma kome yene amsar muddin na gano sa to sai na tarwatsa sa!" Ta k'arasa maganar tana mai sakin kan macijiyar da ta damk'a tare da sake mik'ewa tsaye zumbur. Kana ta d'ora da fad'in. "Baki da amfani a gareni Shairma, ba kiyi mun komai ba a rayuwa, kana ban ga amfanin zaman ki a tare da ni ba tun da har kin kasa bani kariya akan wancan dak'ik'in Bawan! Tabbas baki da amfani, ki tafi bana bukark'i bana buk'atar ki tattare dani yanzu Shairama." Gimbiya Tasmir ta fad'a da wani irin k'araji tana mai shurin macijiyar nan da k'afa. Take kuwa a wurin ta b'ace b'at tamkar ba'a tab'a yin ta. Yayin da ita kuma Gimbiya Tasmir ta fara d'aga k'afafuwan ta tana mai dosar hanyar da zata sadata da part d'in su ta baya, ba tare da ta koma filin bikin nan ba. Acan cikin filin biki kuma sosai hankalin Iyar Bayi yayi bala'in tashi, jikin ta ya dinga wata irin karkarwa, gumi na yanko mata daga can wurin da take a tsaye, domin kuwa akan idanuwanta komai ya faru na abun da Gimbiya Tasmir tayiwa Bir, har binsa abaya da tayi bayan ya bar filin kuwa. Hawaye ne keta tawo mata tana mayar da su, tare da danne kukan nata tana mai hanasa bayyana afili, domin kuwa muddin aka ganta tana kuka a irin wannan ranar kashin ta ya bushe, sabo da za'ayi zato ko tausayin matasan bayin nan take ji, wanda kuma a k'a'idar Bak'ar Masarauta babu tausayi ga wanda ake yiwa hukunci, ballantana kuma su da ba hukunci ake musu ba duk hakan yana daga cikin murna ne. Sai dai kuma ayau ta k'udirtawa ranta cewar muddin Bir ya tambayeta labarin sa zata fad'a masa, ko da hakan ko zai zamto silar futar numfashi ta da ga gangar jikin ta ne, wato futar rai daga cikin ruhinta. Sabo da tasan tausayin sa ba zai tab'a bari ta sake b'oye masa ba muddin ya tambaye tan, kasancewar tana da matuk'ar rauni akan Bir, asalima shine ya zamto raunin ta a yanzu. A cikin filin Biki kuwa ko kad'an babu wanda ya lura da Gimbiya Tasmir bata wurin hatta da iyayen ta kuwa, hakan ne yasa aka cigaba da d'ibar shagali hankali kwance, ana kid'i da rawa tare da ihun kiran sunan Gargabilu. A b'angaren su Bir kuwa cikin duwarwastun nan dakarun nan suka dinga jansa da matuk'ar k'arfi. Sosai jini ke kwaranya daga jikin sa yana zuba aduk wurin da suka huce tamkar an yanka rago. Amma a hakan ko kad'an ba tasu yake ba, asalima babu abun da yake gani a cikin idanuwan sa face kyakkyawar fuskar Gimbiya Tasmir. Yayinda taushin jajayen lab'b'an ta kuma suka zauna daram akan nasa lab'b'an, k'wayoyin idanuwansa kuwa babu abun da suke hasko masa face k'yallin da lab'b'an nata suke yi tare da dogon karan hancin ta. Yayin da k'ofofin hancinsa kuma suka rik'e k'amshin mayen turaren da yake sanye a jikin ta, ta yadda har yake jin tamkar har yanzu suna tsaye a wuri d'aya ne. A haka har suka k'arasa gaban wannan tafkeken ruwan, wanda aka haifi Bir acikin sa tun a wancan lokacin na baya, wato shekara talatin baya kenan a cikin jirgin ruwa, domin su fara cika umarnin uwargijiyar tasu akan sa anan, kafin kuma suje ga azaba ta gaba.✍ _*RIGIJI GABJ! K'AKA K'ARA K'AK'A. TABBAS YANZU NE WASAN ZAI FARA, DOMIN KUWA ABAYA DUK BURGA CE, DAN HAKA SAI ASAKE GYARA ZAMA*_ _*SHIN ME KUKE TUNANIN ZAI FATU A CIKIN BAK'AR MASARAUTA KASHI NA 2*_ *GA DAI YARIMA ASAD DA GIMBIYA HADDIYAL SUNCI KARO, HAR YAGA ABUN DA BAI TAB'A HANGE BA A JIKIN WATA 'YA MACE AKAN TA.* *SHIN ME KUKE TINANIN ZAI FARU?* *GA KUMA MAI GIRMA GWAMNA YAZO NEMAN AUREN YARIMA ASAD GA 'YARSA, SHIN YAYA YARIMA ASAD ZAI D'AUKI LABARIN IDAN AN FAD'A MASA?* *SHIN ZAI YADDA DA BATUN KO KUWA?* *IDAN KUMA BAI YADDA BA MAI KUKE TINANIN ZAI FARU?* *YA BILLY ZATAYI DA DAKON SOYAYYAR SA DA TAKE TA FAMAN YI.* *SHIN WAI WAYE MA GI'DA'DON NAN NA GIMBIYA HADDIYAL DA KO DA YAUSHE ZANCEN TA YA ZAMTO NASA?* *GASHI DAI BINCIKEN TA YA TABBATR MATA DA SHI 'DIN MUTUM NE, SHIN TO ZATA HA'DU DA SHI D'IN A ZAHIRI TAMKAR YADDA TAKE MURADI?* *IDAN KUMA TA HA'DU DA SHI 'DIN ME KUKE TINAIN ZAI FARU?* *SHIN SHI 'DIN YASAN DA ITAMA TAMKAR YADDA TASAN DA SHI KO KUWA, ZAI SOTA KO KUWA, ZASUYI AURE KO KUWA?* *YA KUMA BATUN YARIMAN YAMMA ZAI KASANCE?* *SHIN IDAN GI'DA'DO YA BAYYANA KUNA TINANIN ZAI YADDA YA SHIGA GASAR SHA'DI KUWA, TAMKAR YADDA HAKAN YA ZAMTO DOLE A AL'ADAR SU?* *TO WAI KUNA MA HANGEN ABUN DA NAKE HANGOWA AKAN GI'DA'DON GIMBIYA HADDIYAL 'DIN NAN KUWA? 😅* *SHIN AISHATU ZATA HA'DU DA JINJIRIN TA DA TA RABU DA SHI TUN A WURIN DA TA HAIFE SA KAFUN TA KOMA GA MAHALLICIN TA KO KUWA?* *SHIN WAYE NE WANNAN YARON DA TAKE YAWAN MAFARKIN SA KUWA?* *SHIN YA K'ARSHEN FA'DAN GIMBIYA TASMIR DA BIR ZAI K'ARE?* *SHIN BURIN BIR AKAN GIMBIYA TASMIR ZAI CIKA KO KUWA?* *SHIN ITA 'DIN ZATA CIKA BURIN TA NA GANIN BAYAN SA?* *GA DAI IYAR BAYI NAN TACE ZATA FA'DAWA BIR LABARIN SA* *SHIN ME KUKE TINANIN ZAI FARU IDAN YAJI LABARIN NASA?* *YANA DA RABON SADUWA DA IYAYEN SA KO KUWA?* *SHIN MEYE ZAI FARU ADUK LOKACIN DA AKACE BIR YA BAR CIKIN BAK'AR MASARAUTA, YA KUKE TINANIN SARKI BARBARU ZAIYI?* *SHIN BINCIKEN BOKA MAI HUTAR KASKO ZAI TABBATA KO KUWA?* *MUTANE DA DAMA SUNA TINAIN ME YASA MASARAUTU SUKA ZAMA DA YAWA, ME YE HA'DIN MASARAUTAR FUL'DE DA KUMA MASARAUTAR WASAI KANA DA BAK'AR MASARAUTA.* *TO KUSANI GABA 'DAYA LABARIN BAK'AR MASARAUTA LABARI NE GUDA 'DAYA, WATO DUNK'ULALLE.* *HAKA KUMA GABA 'DAYA WAYAN NAN AMSOSHIN ZASU ZO MUKU NE A CIKIN LITTAFIN BAK'AR MASARAUTA KASHI NA 2.* *HAKAN YASA NAKE BAKU TABBACIN AKAN DUK WANDA BAI KARANTA BAK'AR MASARAUTA BOOK 2 BA TO TABBAS AN BARSA ABAYA, DAN HAKA KU GAGGAUTA NEMAR NAKU DOMIN ADAMA DAKU. _*ALHAMDULILLAH* _*ANAN NA KAWO K'ARSHEN BAK'AR MASARAUTA BOOK 1*_ _*UMAR DAYYAN.✍*_ _ _