♦️♦️♦️♦️♦️♦️ ♦️♦️♦️♦️♦️♦️ IZGILI ♦️♦️♦️♦️♦️♦️ ♦️♦️♦️♦️♦️♦️ An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT __ Story and written by Fateemah Sunusi Rabee'u (Ummu Affan) Marubuciyar UWANIN QAUYE CIKIN WAYE? NIDA YAYA LAMEER KAINE SANADI NAYI GUDUN GARA... And now IZGILI ________________________________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com Godiya ta tabbata ga Allah da ya bani ikon sake dawo muku da wani littafin nawa me taken IZGILI yadda na farasa lafiya Allah kabani ikon kammalawa lafiya. Wannan littafin banyisa don wani ko wata ba k'irk'irarran lbr ne duk wanda yaji yazo daidai da rayuwarsa arashi ne,Wnn lbr mallakata ne banyarda a juyaminshi ta ko wacce sigaba ba tare da sanina ba, Bazan ta6a mancewa da masoyana ba domin domin ku nake komai da fatan zaku biyoni cikin wannan sabon book nawa kuma ku kar6esa fiye da na baya. Ina roko da addu'ar Allah ka yaye mana wnn cuta ta Corona virus a Nigeria gaba d'aya da duniya baki daya amin, Kuna raina 'yan uwana abokan aiki na Arewa Writers gaisuwa da jinjina gareku ta ban girma, Gaisuwa ta musamman ga Antynmu Anty Hauwa Maman Uswan k'aunarki a gareni ta dabance💖. My qawassss Ummu Inteesar kema jinjina agareki💓 My qanwassss Autar arewa Doctor Maryamah Ibraheem jinjina kema agareki💘 Anty Laurat kema jinjina,Anty Zainab na miko gaisuwa,masu sunan 'yan gayu inji wata😜 Hafscal da Sa'amlad kums jinjina Zee 'yar Antynta ai yar mama kema jinjina,my bros Aliyu da Muhammad da wani Aliyu kuma ina d'aga muku hannu, Wanda baiji sunansa ba amin afuwa❤️Allah ya qara had'a kanmu arewa writers🤝💘 Bismillahir rahmanir rahim 🅿️1️⃣-2️⃣ Haka kawai yau na tashi jikina banajin dadinsa,da k'yar natashi daga kwanciyar da nake,na juro dogayen k'afafuwana a k'asa na tallabe kumatuna wato nayi tagumi,duniyar tunani na fad'a akan abinda ke tsakanina da Yayah Hafeez,mutumin da duk duniya babu wacce ya tsana sama dani,kamar yadda nima araina kwatakwata bana k'aunarsa,dogon numfashi naja kafin na mik'e na fad'a toilet, Wanka nayi,nafito na shafa lesion da powder kadan kasancewar ban ciki son inga na cika fuskata da kwalliya ba ko ja gira banayi barni da inshafa mai sai powder da ban le6e,yanxunma hakan nayi kafin na xura doguwar rigata,snn nayi sallah daman na d'aura alwala, Zaune na iske Ummana tana kallon tashar Arewa24,a hankali na k'araso gurin da take na zauna tare da d'aura kaina bisa cinyarta,muryata cikin sanyi kamar yadda take ako da yaushe nace"Ummana sannu da hutawa,shafa kaina tayi cike da kulawa tace"yauwa kin tashi kenan na lek'a naga kinata barci, Nace"aikuwa Umma kaina ne kemin ciwo amma nasha Panadol zuwa yanxu ya sauka,cikin alamun tausayawa Umma tace"Ayya Allah ya sawak'a,na amsa da amin, Mik'ewa nayi na nufi kitchin,dubawa nayi anyi abinci 6ata rai nayi domin a rayuwata na tsani naci abinci,kuma idan banciba nasan Umma mgn xatamin kadan na zuba snn na nufi dinning table,a hankali nake tsakurar abincin kamar mecin magani,Umma wacce rabin hankalinta na kaina naji ta kira sunana"INTEESAR"da sauri na kalleta cike da marairaice murya nace"Am sorry Ummana,nan take saiga hawaye,kallona take takasa magana,daidai shugowar Yayana Yusuf,da sauri ya k'arasa gareni tare da rok'o hannuna yana tambayata lafiya, Umma na kalla shima ita ya kalla,kamo hannuwa yayi mukazo gurinta muka zauna,yace"wai Umma me yafaru,tace"ka tambayeta mana,kallona yayi kobai fad'aba nasan kallon tambayane,turo baki tayi cike da shagwa6a cikin sanyina nace"Yaya Yusuf wai fa abinci ne...tunda tace haka ya gano inda matsalar take domin sanin kowa ne a gidan babu abinda Inteesar ta tsana sama da abinci,barta dai da kayan zaki danginsu chocolute,minti,sweet,dangin dai irinsu sai kuwa comefulas da su cerelac,to abinda fa takeci kenan a rayuwarta, Murmushi yayi ya kalli Umma yace"don Allah Umma rabu da ita kinsan dai wnn halin nata kamar halittarta kenan,batace komaiba ta mayar da hankalinta ga kallo domin sam batason abinda zai 6atawa marainiyar Allah amma dole ne ta koya mata cin abinci tun farko Yayun nan nata ne suka 6atata,yanxun ma Yusuf aljihun wandonsa yasa hannu saiga tarin su sweet chocolate,ai nan take Inteesar ta saki fara'a tare da rungume Yayan nata tana masa godiya, Girgiza kai kawai Umma tayi tana dubansu,daidai shugowar Yaya HAFEEZ,Ai tuni jikin Inteesar yayi sanyi mik'ewa tayi zatabar farlourn ya wani daka mata tsawa,a gigice ta juyo,tare da zubewa tana masa sannu da zuwa domin sam ta mance da gargad'insa akan idan yadawo saita duka har kasa ta masa sannu, Harara a 6alla mata tare da d'aga mata hannu alamar ya isa,zata mik'e yasakar mata harara da sauri tadawo ta zauna,Tuni Yusuf ya 6ata ransa domin ya tsani abin nan da Yaya Hafeez kewa Inteesar,wnn wanne irin IZGILI ne abin yanaso yayi yawa,ita kanta Umma girgiza kai tayi tare da dubansa, Tace"Hafeez andawo,"Eh Umma ya amsa mata kansa a k'asa,kowa yayi shuru,domin idan yana guri Inteesar natsuwa take domin sosai takejin tsoransa,Umma ita kuma bame hayaniya bace kusan daman Hafeez duk ita ya biyo,Yayin dashi kuma Yusuf me sanyin hali ne, Kallon Inteesar Umma tayi tace"ki had'awa Yayanku abinci,da sauri ta mik'e domin daman ta gaji da dukuwar,kitchin ta wuce,shi kuma Hafeez mik'ewa yayi yace"Umma bari nashiga ciki na watsa ruwa,tace"ok ciki zata kawo maka abin cin,ya amsa da "eh yana haurawa sama cike da Izza da kasaita...。 Plss Share My Fans ku dungamin share fah🙏🥰 Ummu Affan✍️✍️✍️♦️♦️♦️♦️♦️♦️ ♦️♦️♦️♦️♦️♦️ IZGILI ♦️♦️♦️♦️♦️♦️ ♦️♦️♦️♦️♦️♦️ Story and written by Fateemah Sunusi Rabee'u (Ummu Affan) ________________________________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com DEDICATED HUSSAINI ATK gdyrka agareni me yawa ce saidai ince Allah ya biyaka ya kawo mata ta gari amin Bismillahir rahmanir rahim 🅿️3️⃣-4️⃣ Yusuf yabisa da kallo,kafin ya kalli Umma yace"Umma wai ina Hafeez ya gado wnn halin nasa,hararar da ta zuba masa yasa shi k'asa da kai,kafin ya tashi jiki a sanyaye ya koma bedroom nasa daman daga Office yake saman bed ya fad'a ya tsunduma duniyar tunani,daga d'an uwansa har mahaifiyarsu yarasa me ya musu suke masa haka, Mahaifiyarsu k'arara ta nuna tafi k'aunar Hafeez akansa hawaye yaji suna gangaro masa tabbas yana cikin damuwa Inteesar ce kawai ke tausarsa da dad'ad'an kalamanta shiyasa yake k'aunar yarinyar har cikin ransa, Inteesar kuwa a d'arare ta shiga Parlournsa dinning ta nufa da sauri ta ajiye,zata juyo kenan taji tsawarsa,jiki na rawa ta juyo,harara ya zuba mata"ke wacce irin dak'ik'iyar yarinya 'yar k'auye ce,tuni hawaye suka tsinke mata da sauri ta tsugunna tana basa hkr,dinning ya zauna tare da bud'e abincin,cikin tsananin fusata yace"ubanwa zaici wnn abincin?tasowa yayi sai fau kakeji ya tsinka mata mari,tuni ta gigice tana basa hkr miyar abincin ya d'auko ya watsa mata tuni farar atamfar dake jikinta ta 6aci,runtse idanuwanta tayi k'amm tanajin wani tuk'ik'in bak'in ciki a zcyrta, Yace''wawiya kawai karki mance a matsayin 'yar aikina kike me yasa kike 6atamin wllh idan kikaci gaba da bani haushi kinsan tsaf na koreki a gidan nan ba wani abu bane,a hnkl ta bud'e idanuwanta dasukayi ja tsabar bak'in ciki,tace"kayi hkr yaya Hafeez bazan sake ba, Zaunawa yayi yana mayar da numfashi domin bai saba mgn me nisa hk ba sam bayasan surutu amma wnn 'yar k'auyen kullum cikin sashi mgn take,yace "ki kwashe abincinki ki barmin Parlour,da sauri ta mik'e tana tattara kayan ta fice, Yusuf dake cikin bedroom fitowa yayi ya kalli Hafeez domin duk abinda ya faru yana jinsu kasancewar Parlournsu daya,yace"sam abinda kakewa Inteesar bai dacewa Hafeez me yasa kake mata hakan?yarinyar nan idan bakaji tausayinta ba baka zageta ba, A fusace Hafeez ya mik'e yace"kaga Yusuf ban kasa da kaiba wai ina ruwanka da rayuwata ne?,Murmushin takaici Yusuf yayi yace"kadai bi duniya a sannu Hafeez ina tausaya maka wataran, "Yusuf naga take takenka raini keso ya shiga tsakanunmu ko wai bani bane yayanka me yasa ka rainani ne,kallonsa Yusuf yayi na d'an sakonni kafin yace"uhmm sannu Yayana, Umma ce ta shugo domin jin hayaniyar tasu tayi yawa,fuskarta a murtike ta kallesu tace"wai meke damunku ne?ku kullum kuna cikin rigima tunda nake ban ta6a ganin twins marasu had'in kai irinku ba,Kallon Hafeez tayi tace"Hassan kaine babba amma halinka saikai,kallon Hussain tayi wayo Yusuf tace "kai kuma baka basa girmansa shiyasa kullum kuke cikin rigima,Yusuf yace"Umma na basa girma fa kika ce bayan baifi sakonni ba a tsakaninmu kawai ni abinda ke damuna da Hafeez ji dakai IZGILI da rashin mutunci akanme zai dunga wulakanta Inteesar me tamasa, Ai tuni Hafeez ya har zuk'a daman gashi da zcy gadan gadan yayo kan Yusuf,Umma ce ta rik'esa tace"Yusuf kashiga taitayinka banason rashin mutumci shin ina ruwanka da abinda yawa Inteesar na zaci shine ya kawota gidan?,Hafeez da Yusuf suka kalli juna donshi Yusuf yasan komai ko lokacin ai ba Hafeez bane ya kawota Yusuf ne amma ita Umma kullum cikin cewa Hafeez take, Juyawa Hafeez yayi ya koma bedroom ransa a 6Ace,itama Umma kallon Yusuf tayi tace"babu ruwanka da duk abinda Hafeez zaiwa INTEESAR Yusuf ka kiyayeni a cikin gidan nan,bai ce mata komai ba har ta fita zaunawa yayi yayi tagumi lokacin da ya tuna ranar da suka sami INTEESAR Ranar da bazai ta6a mancewa da itaba a rayuwarsa, Tafiya suke cikin mota su biyu tun lokacin basu jituwa da Hafeez su tagwaye ne amma sam halinsu ya banbanta hakan yasa tun suna yara basa ji tuwa,Yusuf ke jan motar makaranta zasu shi kuwa Hafeez yana zaune kujerar me zaman banza ransa a murtuk'e koda cen bashi da fara'a abinda yafi 6ata masa rai mota guda da suke hawa da Yusuf akan me Abbansu bazai sayawa kowa motarsa ba wai sai mota guda zasu dunga hawa idan zasu skul, Sauran kad'an su bige wata mata wacce hannunta rik'e da wata kyakkyawar yarinya tazo zata tsallaka,nan fa YUSUF yaja burki ya fita da sauri yana bata hkr dukda itace ta shigar musu hanya,cikin 6acin rai HAFEEZ ya fito yace"kaga malam kabani key na wuce tunda neman suna zaka tsaya,taya mata tazo ta shigar mana hanya snn zaka tsaya kana wani bata hkr,bai kulasa ba yace"baiwar Allah fatan bakiji ciwo ba tace"a'a yaro na gode sosai da kulawa Allah ya maka albarka ya haskaka rayuwarka ya rabaka da sharrin mak'iya,cike da jin dadi ya amsa da amin, HAFEEZ fitowa yayi yazo gurin ckn masifa yace"bani key na wuce ku.....jin abinda matar kecewa yasashi yin shuru,hannun YUSUF ta kama ta had'a da na yarinyar dake hannunta tace"yaro daga ganinka nasan kafito daga gida na gari ga wnn yarinyar wllh rayuwar na cikin wani k'aton hatsari ka temaka ka tausayawa rayuwarta katemaketa ni kaina aiki akasani akanta ance idan banyi ba za'a kasheni ni kuma wllh bazan iya cutar da INTEESAR ba, Kallon yarinyar yayi wacce itama shi take kallo,kafin ya kalli HAFEEZ da sauri HAFEEZ yace"ina ruwana amma shawarar da zan baka karka amshi yarinyar nan don banyarda da matar nan ba, Juyowar da zasuyi tuni suka nemi mata suka rasa,hankalin YUSUF ya tashi ya fara nemanta amma sama ko k'asa babu mata babu me kama da ita,tsaki HAFEEZ yaja ya koma mota yana wani cika da batsewa dole Yusuf ya komo mota,Hafeez yace"wllh karka shugo mana da wnn aljanar yarinyar domin ni bazan shiga mota daya da itaba,tuni Inteesar ta k'amk'ame Yusuf don ba karin tsoro Hafeex ya bata ba, Gardama suka dungayi HAFEEZ yace wllh bazata shigaba,YUSUF yana da hkr da sanyin hali hakan yasa yabasa key,shi kuma ya hau motar haya zuwa office d'in Abbansu, Bayan ya gama masa bayani,Abban ya d'aga waya ya kira Hafeez yace yazo yanason ganinsa,bayan yazo Abba tace ya fad'a masa yadda suka sami yarinyar nan,kamar yadda Yusuf ya masa bayani shima haka numfashi yaja yace"tabbas ya zama wajibi mu temakawa yarinyar nan,da sauri Hafeez yace"haba Abba ni wllh ban yarda da matar nan ba,Yace"to idan bamu temaka mata ba ya zamuyi da ita kenan tunda matar ta gudu,Hafeez yace akaita police kawai ayi cigiyarta,Yusuf yace"bazai yuwuba domin matar nan ta sanar mana rayuwar yarinyar nan yake nema don haka ni taba amanarta kuma in Allah yayarda zan rik'e mata amanarta, Abba yace"nayarda da maganarka Yusuf kuma hakan za'ayi,sosai Hafeez yaji haushi domin daman duk abinda Yusuf yace shi Abban keyi kamar duk abinda Hafeez yace shi Ummansu keyi, Abba yace"saidai idan munje gida mu sanarwa Ummanku HAFEEZ ne aka bawa amanar yarinyar,daga Hafeez har Yusuf da sauri suka kalli Abba tare da had'a bakinsu wajen tambayar"me yasa Abba?....... Plsss Share Ummu Affan✍️✍️✍️♦️♦️♦️♦️♦️♦️ ♦️♦️♦️♦️♦️♦️ IZGILI ♦️♦️♦️♦️♦️♦️ ♦️♦️♦️♦️♦️♦️ Story and written by Fateemah Sunusi Rabee'u (Ummu Affan) Dedicated to _Hussain Atk_ Special gift to _Anty Hauwa mmn Uswan_ ________________________________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com Bismillahir rahmanir rahim 🅿️5️⃣-6️⃣ Abba yaja numfashi yace"sbd idan mukace Hafeez ne aka bawa yarinyar zata fi d'aukarta da muhimmanci kuma ta amince ta rik'eta nasan kunsan komai ai,dukansu sukan jugum shi kuwa Hafeez aransa yanajin wani tuk'uk'in bak'in ciki,bayan bayason ya musa mgnr Abbansu da yace'a'a, Shima Yusuf shuru yayi tabbas mgnr Abban gsky ce shi kuma daman mai sanyin hali ne yace"hakan yayi Abba,Hafeez mik'ewa yayi,"Ina zaka cewar Abba,yace"zan koma mkrnt ne,Abba yace"mu fara zuwa gida tukun, Abba ya shiga motarsa su kuma suma suka shiga tasu,INTEESAR na jikin Yusuf duk ta kanannad'eshi tunda Hafeez ya mata tsawar nan taji duk duniya bata da abin tsoro kamarsa,bayan sun isa Yusuf bisa kafad'arsa ya d'aura Inteesar yayin da Hafeez yaza wani dogon tsaki yayi gaba,Abba dake bayansa ya girgiza kai tunda yake bai ta6a ganin 'yan biyu marasu had'in kaiba irinsu kuma yasan duk matsalar da gurin Hafeez shine babba amma sam bashi da mutumci sai d'aga kai da IZGILInci yarasa me yasa hakan ke shiga tsakaninsu addu'arsa kullum Allah ya daidaita tsakaninsu amin, A parlour suka iske Umma kusa da ita Hafeez ya zauna zata masa mgn kenan saiga su Yusuf sun shugo,cike da mamaki ta kallesu bakinta na rawa tace"Yusuf me zan gani haka wnn yarinyar waye?ta fad'a tana nuna Inteesar wacce ta sake k'amk'ame Yusuf,zaiyi mgn Abbansu ya rigashi yace"kwantar da hankalinki yarinya ce Allah ya bamu kyautar Allah,nan ya bata labarin komai,cike da tausayin yarinyar taje ta amsheta tana shafa kanta tace"Allah sarki kyakkyawar yarinya wad'an nan anyi muggan mutane yarinya kisha kuriminki zan rik'eki tamkar mahaifiyarki,Yusuf yaji sanyi aransa, Haka rayuwar INTEESAR ta fara a gidan cikin so da kauna kai bazaka kalleta kace ba 'yar gidan bace komai takeso ana mata ba kamar Yusuf komai nata shine,saidai wani abu guda tunda aka kawo Inteesar gidan aka bata abinci tak'ici akayi akayi da ita tak'i bata da abinci sai kayan k'wad'ayi kayan zaqi sune abincinta tun Umma na matsawa har ta rabu da ita ganin yadda yayun nata suka d'aure mata gindin saya mata musamman ma Yusuf wani lokacin kuma Hafeez idan 'yan mutuncin nakai har takai ta kawo kwalayen su sweet minti choculate haka Yusuf ke saya mata, Haka rayuwarta taci gaba a gidan har zuwa lokacin da akasata mkrnt kammala karatun su Yusuf da fara aikinsu,Hafeez Lecturers ne dake koyarwa a jami'ar jahar Kaduna wato Kaduna State University,shi kuma Yusuf Injiniya ne yana aiki a companyn Abbansu sosai suke samun ci gaba, Hafeez da Yusuf kamanninsu guda ne domin wani lokacinma idan ba farin sani kamusu ba bazaka ganesu ba,kyawawan samari masu jini ajika matasan samari yanxu suna da shekaru 32 a duniya,dogaye nesu fatarsu wankan tarwad'a ce su ba farare bane snn baza'a kirasu bak'ak'e ba duk inda kyau yake sun kai,ta inda zaka ganesu shine shi Hafeez sam bashi da fara'a ko kad'an snn fuskarsa ko da yaushe a d'aure take snn yad'anfi Yusuf tsayi kadan,shi kuma Yusuf mutum ne mai sakin fuska da fara'a kowa nasa ne yana da kyirki sosai dason mutane da girmama duk na gaba dashi, Numfasawa Yusuf yayi lokacin da ya gama tuno abinda ya faru tashi yayi ya koma bedroom zcyrsa cike dajin d'acin abinda Hafeez kewa Inteesar d'insa, Ita kuwa Inteesar da gudu ta sauka k'asa tana kuka sosai kai tsaye bedroom d'inta ta fad'a ta haye gado tana kuka sosai tana k'amk'ame jikinta ganin yadda duk ta 6aci da jar miya...... Plssss Share Ummu Affan✍️✍️✍️♦️♦️♦️♦️♦️♦️ ♦️♦️♦️♦️♦️♦️ *IZGILI* ♦️♦️♦️♦️♦️♦️ ♦️♦️♦️♦️♦️♦️ *Story and written by* . *Fateemah Sunusi Rabee'u* *(Ummu Affan)* *Marubuciyar* *UWANIN QAUYE* *CIKIN WAYE?* *NIDA YAYA LAMEER* *KAINE SANADI* *NAYI GUDUN GARA...* *And now* *IZGILI* *DEDICATED TO* *RUKAYYA IBRAHIM LAWAL* . *Ummu Inteesar* *SPECIAL GIFT TO* *Anty Hauwa* *My fans ina godiya da jin dadi sbd yadda kuka amshi wnn littafin hannu bibbuyu kuma inajin dadin yadda kuke suburbudomin comment a cigaba da gashi ina yinku over* ________________________________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com Bismillahir rahmanir rahim 🅿️7️⃣-8️⃣ Saida tayi kukanta me isarta snn ta fad'a toilet,wanka tayi ta fito ta cenxa kaya snn ta fita gurin Baba Kulu me aikinsu,duk lokacin da zatayi aiki ta kan shiga kitchin domin ta temaka mata,tun Umma na hanata har ta gaji ta rabu da ita domin sam Inteesar yarinya ce meson aiki bata da kasala barta dai da rashin cin abinci, Bayan ta gaisheta ta amsa ckn fara'a tace"Uwar dakina kin iso kenan,murmushi tayi tace"na iso Baaba yau me za'ayi a gidan,tace"to Hajiya dai batasanar minba daman kece me za6a murmushi tayi tace ina zuwa, Sama ta hau bedroom d'in Yah Yusuf tashiga zaune yake yana aiki a Computer murmushi tayi ta k'arasa garesa tare da zaunawa gefensa,"yah Yusuf barka da aiki,a hnkl ya juye ya kalleta shima mrmsh ya sakar mata yace"barka dai Kyautar Allah, Lokuta da dama sunan da yake kiranta dashi kenan shida Abba tace"yah Yusuf yau me kakeso kaci,lan gwa6ar da kai yayi yana kallonta da sauri tayi k'asa dakai domin batason yawan kallonsa sbd kwarjininsa yana cika mata ido yace"kome kikayi zanci Amanata,da sauri ta kallesa,lokacin da abin ya faru sam bata da wayau domin shekarunta hudu ne ba komai zata iya tunawa ba,tasan dai tabbas ita ba 'yar gidan bace domin tana hangen abun a kyaunyar kanta saidai bazata iya tuna komi ba byn wnn, Cike da shagwa6ar da take masa tace"pls yah Yusuf yau ka fad'amin za6inka mu girka maka kullum za6ina kakeci,yace"yes sbd nasan duk wani abu da kikayi koda bancinsa to zan iya ci,gyad'a kai tayi shi kenan my Yayanah,ta fita yabi bayanta da kallo tare da jingina kansa jikin bed a fili ya furta Ina k'aunarki Inteesar Allah ya cikamin burina akanki,snn yaci gaba da aikinsa, Tana fita Yah Hafeez na fitowa daga bedroom nasa,ai sauran kad'an ta kifa sbd furgici da tsoro,da sauri tayi niyyar kifawa a guje yace"munafukazo nan,hnkl a tashe taje ta duk'a gabansa tuni ta fara magiyar"don Allah Yah Hafeez kayi hkr wllh.....da sauri ya katseta cike da fusata"kinsan dai banason surutu ko?da sauri ta d'aga kai,Ckn tsawa yace"baki da baki ne,"kayi hkr,mtsuuuww yaja dogon tsaki"ki je ki had'amin coffee sauran kiyisa ba daidai ba, Da sauri ta mik'e kitchin ta koma tasanarwa Baaba kulu abinda zasuyi snn ta had'a masa coffee kamar yadda tasan yanaso snn ta kai masa,tana nan tsugunne harya kul6a ta ga yawani ya mutsa fuska da cikinta ne taji ya bada tsuwwww cike da tsoro ta kallesa ganin baiyi mgn ba kuma bai k'ara kul6a ba aranta tace"shi kenan yau na mutu, Umma ce ta k'wala mata kira hakan yasa tayi saurin kallonsa harara ya zuba mata yace"kin zubamin banzayen idanunki bazakije ba ne?da sauri ta fita aranta tana mitar shidai ba'a iya masa da tashi tayi yace tayi laifi, Bak'i ta gani Umma tayi,da sauri ta k'arasa tana gaishesu ko kallonta matar batayi ba sai wani cin magani take,jiki a sanyaye ta zauna,kusa da Umma,waya Umma ta d'aga ta kira Hafeez da Yusuf ba'a jima ba sai gasu,Hafeez ko kallon matar da yaranta biyu 'yan mata baiyi ba,shi kuwa Yusuf harda gaisheta yayi ta amsa a hankali tana harare harare, Umma tayi gyaran murya tana kallon su Hafeez tace"kun ganeta kuwa?,kafin suyi mgn matar ta katseta da sauri "taya kuwa kuwa zasu ganeni tunda kin mallakemin d'an uwa kin kanainayeshi baya zuwa inda muke bare har yakai 'ya'yansa su sanni, Numfashi Umma taja cike da takaici zatayi mgn saiga sllmr Abba yana ganin Yayarsa ya k'araso da sauri tare da zubewa gabanta"Anty Jummai kece yau a garin barka da zuwa,harara ta zuba masa tace"uhmm Musbahu kenan idunka kenan ko kunya bakaji ba,sai tasa kuka tanacewa"kai kenan kana gindin mace baka tunawa da 'yan uwa,mu kad'ai iyayenmu suka mutu suka bari dagani saikai amma ka mance dani naci kashinka hannuna ka tashi har kayi wnn arzikin amma ka mance dani, Hankalinsa a matuk'ar tashe yace"kiyi hkr Anty Jummai wllh kina raina ko da yaushe,tace"taya zan zauna aranka bayan matar nan taka Hajara ta gama dakai ko yaranka wai basu sanni ba ina matsayin Uwarsu kuma kakarsu tunda ni na raineka da hannuna,hkr kawai yake bata,tace"to Malam dai Allah ya masa cikawa hakan yasa nazo nan kuma anan nakeso na zauna,da sauri yace"Allahu akbar Allah yaji k'ansa Malam mutumin k'yirki, Babban bedroom aka bawa Anty Jummai kamar yadda Abba ke kiranta muma hk muke kiranta domin ko yaranta Maryam da Saima haka suke kiranta,Anty Jummai irin fitinannun matan nance sam bata da kyirki gasa ido,tunda tazo gidan tasaka Umma a gaba da jaraba gashi Abba najin tsoranta sosai saidai ya bawa Umma hkr,tanason Hafeez da Yusuf saidai sunfi shiri da Yusuf kasancewarsa me barkwanci wani lokacin ko masofa take idan ta gansa takan dena domin shid'in daya fadar mata wata mgnr sai hankalinta ya kwanta a rayuwar Yusuf ya maida komai ba komai ba,inda suke samun matsala da shi idan tanawa Inteesar wulak'anci domin duk a gidan ba wacce tafi tsana sama da ita tunda taji asalinta take wulak'antata,haka Saima bata da mutumci ko kad'an ga 'yan aiki amma saidai tasa Inteesar ta mata komi,Maryam kuwa suna mutumci sosai da Inteesar domin ko ashekaru zasuzo guda sai kuma halinsu ya zama iri daya,Anty Jummai da Hafeez basu shiri domin kai tsaye yake gaya mata balle idan yaga tana gayawa Umma mgn,Saima kuwa tunda taga Hafeez ta rud'e a duniya tace bata da mijin da takeso kamarsa,Saima shekarunta 23 ita kuwa Maryam tana da shekaru 15 sa'ar Inteesar ce don itama shekarunta kenan, Su waye Hafeez da Yusuf?, Alhj Musbahu Muhd ne mahaifinsu haifaffan garin Kaduna ne a unguwar shanu shida yayarsa Rabi'atu da ake kira Jummai iyayensu sun dad'e da rasuwa a hannun Yayarsa ya taso,domin tunda iyayensu suka rasu sai 'yan uwa duka suka juya musu baya sai wad'anda ba'a rasaba,haka suka taso rayuwarsu,Anty Jummai tayi sana'a iri da iri domin temakawa rayuwar k'aninta ita tasashi mkrnt amma ita bata zuwa lokacin da takai shekaru 18 Danginsu sukace aure zasu mata suka hadata da wani tshon mutumi ba kauye hk akayi auran bataso aka kaita cen k'auyen me suna Kujama,k'anin babansi yaci gaba da rik'e Musbahu amma sbd rashin abinci ya fille ba'a sake ganinsa ba yayi Kano acenne Allah ya had'ashi da wani ubangida ya mayar dashi mkrnt snn ya rik'esa tamkar d'ansa har ya kammala karatunsa kuma yasa shi a harkar kasuwancin sa,Alhj Hafizu mutum ne me kyirki da tausayin talakawa yana da arziki sosai ganin irin rik'on amanar da Musbahu yake dashi yasa ya aura masa 'yarsa wacce ita kad'ai ya mallaka wato Hajara, Hajara yarinya ce ta gari tamkar mahaifinta saidai miskila ce mgn bata dameta ba,batason hayaniya amma tana da kyirki sosai ga hankali da natsuwa sunyi zaman so da kauna da Musbahu, Wanda shima daga baya Allah ya azurtashi sosai yayi kud'i na kece raini,a yanxu hk har yafi uban gidan nasa kuma surikinsa arziki, Shekarunsu tara da aure snn suka sami haihuwa,sosai sukayi farin ciki da samun yaransu 'yan biyu kyautar Allah,inda Hassan yaci sunan Surinkasa ubangidansa mahaifin matarsa wato HAFEEZ shi kuma Hussaini yaci sunan mahaifinsa wato YUSUF kuma ko wanne ba'a 6oye masa sunansaba........ Muje zuwa Plsss Share Ummu Affan✍️✍️✍️♦️♦️♦️♦️♦️♦️ ♦️♦️♦️♦️♦️♦️ IZGILI ♦️♦️♦️♦️♦️♦️ ♦️♦️♦️♦️♦️♦️ Story and written by Fateemah Sunusi Rabee'u (Ummu Affan) *DEDICATED TO MY FANS* *SPECIAL GIFT TO* . *ALL MEMBERS OF AREWA WRITERS* *SPECIAL THANKS TO* *NURADDEN SHU'AB LIight* *HUSSAIN ABU SAMEER* *NAZHIFI YAREEMAH* *YUSUF NUHU* ________________________________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com Bismillahir rahmanir rahim 🅿️9️⃣-1️⃣0️⃣ Duka yaran sun taso cikin so da kyaunar iyayensu saidai abu guda tun suna yara sam basa ji tuwa,Hafeez zcy garesa abu kad'an zai rufe Yusuf da bugu wataran kuma su bigi juna,snn Tunda iyayen suka gane hk sai basa musu mgn a ganinsu ai yara ne nan gaba idan suka girma zasu bari,sun mance icce tun yana d'anye ake tankwarasa idan ya bushe kuwa saidai ya karye, Haka suka taso wasu irin yara wanda a tarihi ba'a ta6a twins kalarsu ba,gashi dai sunyi kama komai nasu iri daya saidai rashin ji tuwarsu,Tun suna yara Umma ta nuna tafi son Babanta wato Hafeez wnn kuma babban kuskure da iyaye ke nunawa ko kafison wani kamata yayi kabarsa a ckn zcyrka amma k'arara Umma ta nuna tafi kaunar Hafeez akan Yusuf ganin hkn shima Abba ya nuna yafi kaunar Yusuf akan Hafeez tunda kowa ubansa ya dauka,hhhhhh kunji wani rikicin ckn gida sai kace wasu yara k'anana kuma har yaran suka girma akan hakan suke, Sam Alhj Musbahu bai waiwayi gida ba kamar yadda itama Hjy Hajara wato Umma bata ta6a damuwa da sanin halin da dangin mijinta sukeba kuma bata ta6a tambayarsa suba,wata irin rayuwa kawai suke wanda basu damu da damuwar wani ba kansu kawai suka sani sai yaransu,tunda ga kansu kuma basu sake haihuwa ba har zuwa lokacin da suka sami INTEESAR, Ita Anty Jummai ta bazama neman d'an uwanta tunda ta dawo gida sakamakon sakinta da mijinta yayi,wulak'anci dai iri iri tana shansa a gurin danginsu,har zuwa lokacin da wani attajiri ya sake auranta anan Kaduna babban malami ne,daman bata haihuba a cen kauyen,saida takusan shekaru sha biyar da aure snn ta haifi Saima saida kuma Saima ta shekara bakwai snn ta haifi Maryam,hk rayuwa taci gaba har xuwa lokacin da taga Alhj Musbahu a tv ana hira dashi tana ganinsa ta ganesa nan tayi ta kuka har saida Malam mijinta ya kaida garin Kano taga d'an uwanta sunyi murna sosai da zuwanta hk suka dunga zuminci har zuwa lokacin da Malam ya rasu ta dawo gidan sam Alhj Musbahu baiji mutuwarba kasancewar sun dad'e basu had'uba shi kuma sbd tafiye tafiyensa k'asashen k'etare wnn kenan, Anty Jummai ce ke cika da batsewa cikin parlour kallon Alhj Musbahu tayi tace"wai hk rayuwa take yanxu don Allah Musbahu hk zaka zuba idanuwa kana kallon yara sun isa aure ka zuba musu ido to wllh bazai yuwuba idan da aure sukayi yanxu ya isa suna da yara biyu ko uku, Umma shuru tayi ta kasa mgn sbd ita mgn ba damunta tayi ba sam batason fitina a rayuwarta yaranta kuma bazata musu dole ba lokacin da suka shirya aure sai suyi, Abba yace"Anty dukansu ba wanda yace yanason aure su ai ba yara bane idan sunason aure ai zasuyi mgn,rik'e baki tayi kafin ta tafa hannu tana salati tace"yo tunda ka zuba musu ido taya zasuce sunason aure wad'an nan zaratan maza a gida,Mgnrta ta fara isar Hafeez yace"wai Anty Jummai ina ruwanki da rayuwarmu ne ko kuwa sa'ido,tace"Musbahu kanajin abinda Hafeezu ke cemin ko?yanxu sbd tsabar rashin kunya ya kalli idanuwa na yacemin hk,to wllh ko suyi aure ko kuma ni na za6a musu mata da kaina, Kan ubancen Hafeez ya fad'a a zcyrsa aransa yace kamarmu za'ace za'a za6awa mata,Yusuf kuwa murmushi yayi sarkin barkwanci yace"haba dai Anty Jummai sha kuriminki ki ba mu shekaru a qalla biyar zamu kawo miki mata ko da yake bro na yana da wacce yakeso ni kuwa tawa bata isa aure ba,harara Hafeez ya zuba masa da yatuno Yusuf yasan budurwarsa domin tun suna skul suke tare da BAHEERAH yarinyar da yakeso tamkar ransa suna zuba soyayya sosai duk da wani lokacin ita ke haukanta duk tare suka kammala karatu domin shi mutum ne meson mace me ilmi wacce tayi zurfi a karatu kuma me shekaru kusan nasa don beson yarinta Baheerah a qalla shekarunta 29 domin shakara uku rak ya bata a duniya tana matuqar son suyi aure amma shine keja mata aji har yanxu, Anty Jummai tace"da kyau akan yayi daidai kai Hafeez ka shirya sanar da budurwarka za'a turo kai kuma Yusuf kashirya da SAIMA za'ayi,ai gaba d'ayansu suka kalli juna, INTEESAR taji wani irin yarrr gabanta ya buga da qarfi zuciyarta ta mata zafi ta rasa dalili,Yusuf kuwa cewa yayi "haba Anty Jummai kikasan ko da wanda takeso,Saima kuwa wani dadi taji aranta domin burinta daman cikinsu ta auri daya tunda duk kamarsu guda ce wllh tanason YUSUF musammanma shi da yayi k'irki,tace"haba Yaya Yusuf ai kai d'an uwa nane taya zan k'ika,gaba daya akasaka dry idan ka cire mutum biyu Yusuf da Inteesar sai kuwa Hafeez dukda shima ya d'an murmusa don arayuwarsa yanason mace wayayyiya shi kuwa Yusuf a gurinsa ai Saima rashin kunya tayi,Inteesar kuwa k'asa tai dakai hawaye na jirara batasan dalili ba, Abba yace"gsky naji dadi da abin yazo ckn sauqi haka Allah ya qara zuminci,Umma tace"nima abin ya mini dadi na kusan zama suruka,sukasaka dry,Anty Jummai tace"da baku kun zuba musu ido ba ku son 'ya'ya, Inteesar a hnkl ta tashi ta nufi bedroom d'inta wanda yanxu ita da Maryam suke kwana,kan bed ta fad'a tana kuka qasa-qasa,Yusuf yana ganin ta tashi ya mik'e zaibi bynta Anty Jummai tace"sai ina?ko don kaga 'yar gwaltaka ta tashi zaka bita?ransa a jagule yace"ina zuwa, Bedroom d'in yashiga ganin yadda take shashsheqar kuka ya qarasa da sauri tare da d'agota,tana ganin shine ta rungumeshi tare da sakin kuka murya ckn sanyi yace"Inteesar me yasaki kuka?,rasa me zata ce masa tayi tace"uhmm uhmm uhmm nima ban saniba hk kawai naji ina kuka,yace"dole da dalili me yasaku kuka Inteenah?a hankali ta d'ago kai daga qirjinsa karaf suka hada ido ckn raunin murya tace"............ Muze zuwa Plsss Share Ummu Affan✍️✍️✍️♦️♦️♦️♦️♦️♦️ ♦️♦️♦️♦️♦️♦️ IZGILI ♦️♦️♦️♦️♦️♦️ ♦️♦️♦️♦️♦️♦️ Story and written by Fateemah Sunusi Rabee'u (Ummu Affan) Dedicated to _Hussain Atk_ Special gift to _Anty Hauwa Maman Uswan_ ________________________________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com Bismillahir rahmanir rahim 🅿️1️⃣1️⃣-1️⃣2️⃣ Tace"Yaya Yusuf haka nan naji banji dadi ba da akace an baka auran Anty Saima don Allah Yayanah kada ka aureta, Zaiyi mgn saijin tafin hannun Anty Jummai sukayi tana tafa hannu tare da sallallami tana zuwa ta shaqo wuyan Inteesar ta matse qara tasaki tare da rik'e hannun Anty Jummai dake wuyanta tana kuka, Yusuf yace"Anty Jummai meye hk kasheta zakiyi ko me?tace"ai gara na kasheta ko arage mugun iri wllh wnn yrnyr fitinace yarinya qarama sai shegen iyayi da feleqe iye kada ya amince da auran Saima to sannu Hajara da kika kawo Yusuf duniya, Yusuf yace"plss Anty ki sakar mata wuya,da qar ta saketa tana bambamin masifa,jikin Yusuf ta fada tana kuka sosai tana murza wuyanta hura mata wuyan yake yana cewa kiyi hkr INTEESAR,tace"nidai don Allah karka aureta bakaji yadda zcyta kemin ba Yaya Yusuf kai wani jigone na cikin rayuwata inajin hakan a tattare da mu,share mata hawaye ya fara shikansa ji yake kamar ya sakar mata kukan yace"ki dena kuka Inteesar pls ki share hawayenki,tace"to zaka fasa,gyada mata kai kawai yayi alamar eh domin ya kasa mgn tunani ne fal ransa da tambayoyi saidai baida amsoshin,shin itama Inteesar tanajinsa kamar yadda yake jinta kenan?gashi har batason yayi aure?amma kuma taya zai gasgata mgnr nan tabbas qila itama tana qaunarsa kamar yadda yake qaunarta idan kuwa haka ne da yafi kowa sa'a a duniya, Lumshe ido yayi kad'an kana ya bud'e yace"kina sona Inteesar?kallonsa tayi da sauri shi d'inma da sauri ya gara kalamansa domin baiyi zaton a waje yayi mgnr ba, Yace"don Allah ki cire komai aranki banaso nayi jayayya da Anty Jummai sarai kema dai kinsan halinta kuma sai abinda tace"Abba yakeyi,kwantar da kanta tayi bisa kafad'arsa tace"wllh Anty Saima bata da kyirki ne kuma....rufe mata baki yayi yace"karki ce komi nidai nasan ba abinda ta isa tamin, Sosai a zcyrta taji haushin Yaya Yusuf aranta tace"kodai shima yana sonta ne?to amma fa ko mgn taga basu cikayi ba,tashi yayi ya fita zcyrsa cike da rud'u shidai bason Saima yake ba kuma bayajin zaiwa iyayensa gaddama snn ko ba komai ai shima yana buqatar auran snn yasan Inteesar bata isa aure ba ko yace yana sonta yanxu ba aura masa ita za'ayi ba hkn yasa zaibar komai aransa har zuwa lokacin da zata isa auran snn ya sanar da ita yana sonta (uhmmm Yusuf a bari ya huce dai akace shi ke kawo rabon wani), ............................................. An aika gidansu Baheerah an nemi auranta kuma sun basu sosai masoyan ke cikin farin ciki,yauma har office d'insa dake ckn universityn ta je kasancewarsa na babban malami,daman kuwa mafi akasari ita ke zuwa gurinsa zance kafin yaje gidansu sau daya tazo gurinsa fiye da goma,kamar ko da yaushe 'yan mata ne ke ta shawagi ta wajen wundow dinsa domin ko zai taya hk mata ke mugun sonsa dason kawo masa hari saidai ba fuska domin akwai riqe gida gashi ba fara'a ga kuma shegen kwarjinin da yasa 'yan mata ke shakkarsa, K'wankwasawa tayi yace"yes,cikin takunta na kasaita ta shugo,sai yanxu na k'are mata kallo eh baza' kirata mummuna ba amma ba wata kyakkyawa cen bace zamu iya kiranta da hasken fatarta ne ya temaketa domin da baka ce za'aga muni,siririya ce sosai bata da kiba kuma babu wani diri ajikinta hk take sungul kamar kyendir hhhhhh sanye take ckn wani material da yasha wulaqantaccen dinki doguwar rigace amma ta kamata sosai ita kuma babu wani abun nunawa a jikinta domin ko k'irjinta babu wasu manyan nonowa qananu ne ko mayafi bata saba sai jakarta da ta ratayo da dogon takalminta sai wani taunar chingam take, Tana shugowa ta nufi kansa da sauri ya d'aga mata hannu domin shi byn son wani rungume rungume byn ba aure akayi ba sai ta jefashi ckn wani yanayi shi kuma ba neman mata yake ba, Tanan fanninfa ba laifi domin sam Hafeez baya neman mata baya shaye shaye asalima ya tsanesu dukan,zaunawa tayi kujerar dake facing dinsa tana sakar masa smilling,shima yasaki fuskarsa sosai domin gsky byn mahaifiyarsa ba wacce yake sakewa da ita irin Bahira yanasonta sosai wayewarta da iya mgn, Cikin kashe murya da yauqi tace"Honey wllh kwana biyun nan da nayi tafiyar nan ban ganka ba wllh duk hnklna ya tashi sosai kaga kuwa yadda ka qara kyau,murmushi ya saki yace"Baheerah ke ko kyauma na qara ko?byn kinfini kyau,kusa dashi ta matso sosai tace nafika kyau da kuwa bazan sake fitaba,wllh ko rabin kyawunka nayi honey da nafi ko wacce mace kyau,uhmmm kawai yace nan ta dunga zuba masa surutu shidai da uhmmm sai uhmmmm uhmm wani lokacin yayi mrmsh domin yanason Baheerah sosai a zcyrsa irin macen da yakeso kenan me tattare da wayewa, Saida ya tashi daga aiki snnvya d'auketa sukaje supar market daga nan yakaita gida daman idan zatazo gurinsa bata zuwa da mota sbd yadawo da ita, Baheerah d"iyar wani attajiri ce d'an siyasa ne yana da kud'i sosai mahaifiyar Baheerah Hjy A'i macece mafadaciya gason abun duniya dabin malamai Baheerah tana da yayu biyu mata duka sunyi aure yanzu ita kadaice gaban iyayenta sai d'iyar yayarta me suna Sauda da suke tare,To Baheerah dai duk kan halin mahaifiyarta tayi gado tanada fada sosai snn kuma bata da hkr sam batawa iyayenta biyayya domin agefe guda zaman kanta take sosai suke shaye shaye sun shekarunta 29 ta gama karatunta aiki take a wani campany yanxu hk,tun suna mkrnt suke tare da Hafeez,tun wata rana da Hafeez suke fad'a da wani class met dinsa shima fa ya tsula tsiya domin baida hkr sosai suke chachar baki har takaisu ga fashe fashs Baheerah ce tazo ta shiga tsakani tasa aka kama abokin fadan nasa snn shi ta basa hkr duk da shine bashi da gsky tundaga ranar yaji ta burgesa dama itanma da biyu tayi domin tana mugun sonsa ta rasa hanyar dazata biyo masa sai tayi wnn dubarar tun daga nan suka fara mutunci har soyayya ta shiga tsakaninsu,wnn kenan **************** Sosai ake shirye shiryen bikinsu Yusuf inda daga Umma har Anty Jummai shiri suke sosai na bikin komai an hada harda lefe,akwatina dozin doxin komai cikin harkar girma suke yinsa, Inteesar kuwa............ Plsss Share Ummu Affan✍️✍️✍️♦️♦️♦️♦️♦️♦️ ♦️♦️♦️♦️♦️♦️ *IZGILI* ♦️♦️♦️♦️♦️♦️ ♦️♦️♦️♦️♦️♦️ *Story and written by* . *Fateemah Sunusi Rabee'u* *(Ummu Affan)* *Marubuciyar* *UWANIN QAUYE* *CIKIN WAYE?* *NIDA YAYA LAMEER* *KAINE SANADI* *NAYI GUDUN GARA...* *And now* *IZGILI* *DEDICATED TO MY FANS* *SPECIAL GIFT TO ANTY HAUWA MAMAN USWAN* . ________________________________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com _Bismillahir rahmanir rahim_ 🅿️1️⃣3️⃣-1️⃣4️⃣ Inteesar kuwa sosai take cikin tashin hnkl da bikin ita dai batasan yaya Yusuf d'inta yayi aure batasan dalili ba,gashi ba hali ta shiga parlour yanzu sai Anty Jummai ta korota abin nadamunta saidai idan bata gidan snn take fita ita kanta Saima cin mutum cinta take ko da yaushe tana kumshe a daki kamar kayan wanki, Muryar yaya Yusuf taji yana kwala mata kira,da sauri ta mike ta nufi parlour lokacin da ta gansa ta saki murmushi domin kwana biyun nan baya zama sbd hidimar biki,a hnkl ta karaso kusa dashi ckn sanyinta tace"yaya Yusuf sannu da zuwa, Shima kallonta yake cike da soyayyarta yace"yauwa my K'anwata,wasu akwatina yanuna mata guda shida yace"kema ga naki kayan nan,cike da mamaki ta kalli akwatinan snn ta juyo ta kallesa cike da al'ajabi tace"nawa kuma,shhhhhhhh ya daura yatsansa saman labbanta yace"banso kice komai nakine kema da zakiyi fitar biki, Umma tace"ka kyauta kuwa domin nima ina niyyar saya mata sai gashi ka hutassheni, Tayata yayi suka shiga da akwatinan bedroom d'inta kamar wata amarya wai akwati har shida,shima yaya Yusuf ya za6i lokacin ne ya kawo mota domin ya dade da saya baiso Anty Jummai ta gani domin zatayi fada shiyasa saida yaga sunfita da Saima ya d'auko mata wai sunje gyaran amarya, Shi kuwa Hafeez daman bawai kula kowa yake ba,Baheera ta tsarsa kawai take yana mata 6arin kud'i komai tace sai anyi a bikinsu babu harkar qaranta shi d'inma bai ja da ita ba hk ya bata duk wani abu da za'a nema ko fid'a a shagulgular, Akace idan akasaka rana to ranar fa zatazo ana kwana ana tashi bikinsu Hafiz sauran sati guda tun lokacin aka fara shagulgula ba kama hannun yaro,daga gidajen amaren har zuwa na angwayen,sosai akasha shagulgula kala da kala, Har Allah ya kawo ranar kamu ana gobe bikin sosai amare da angwayen sukayi kyau ainun kamshine kawai ke tashi ako ina idan sun gifta,Holl din da'aka tanada domin gabatar da kamun yasha ado kwalliya da abubuwa kyawawa kujerun amare suna sama suna kai,sai shagali ake, Daidai lokacin Inteesar ta shugo sanye take cikin wata had'ad'd'iyar gown tayi mata kyau ta zallar material me kwalli da walwali tasha make-up tayi kyau ga dauri na zamani gefenta Maryam ce itama tati kyau,Maryam cema ta tilasta mata har suka je shagon kwalliya da d'auri aka musu,uhmmm kyawun da Inteesar tayi ba'a mgn kamar ka saceta ka gudu,sbd kyau(nikaina Ummu Affan saida na sake bud'e idanuwana sosai snn na ganeta lolx), Da sauri Yusuf ya mik'e tare da zuba mata idanuwansa,duka kallonsa sukayi domin basu san me yasashi mik'ewa haka ba,Hafeez Baheera da Saima suka kalli inda yake kallo,shi kansa Hafeez saida ya sake kwalalo ido aransa yana tunanin wacece wannan kamar yasanta,lokaci guda ya gane ckn sauri ya kauda kai tare da jan tsaki yana harare harare,Saima ranta yayi mugun 6aci jan hannunsa tayi da sauri ya zauna kafin mutane su fara gane wa yake kallo,ckn 6acin rai tace"haba yah Yusuf meye hkn me waccen yarinyar tafini da kana kallonta ka rud'e hk?,ckn wata sanyaryar murya yace"bazaki gane ba Saima kedai ki tayani da addu'a,kallonsa tayi cike da 6acin rai kafin taja numfashi aranta tana ayyana da zarar ta tare zata rabasa da Inteesar, Ita kanta Baheera wani abu me k'arfi taji ya soki zcyrta lokaci guda taji ta tsani Inteesar duk da batasan wacece ba,sosai taji haushin yarinyar kallon Hafeez tayi tace"Honey wacece waccen?ta nuna masa Inteesar,yace"k'anwar Yusuf ce,shuru tayi na wani lokaci tana tunani kafin tace"kana nufin k'anwarku ce amma ba kasanarmin kuna da qanwa ba,ckn isa yace"ai yanxu kin sani, Cikin gurin kuwa shugowar su Intee yaja hnklin jama'a da dama,Intee k'aramar yarinya ce da har yanzu baza'a sakata cikin 'yan mata ba,amma tana da wani shegen kwarjini ta takewa mutane ga wani asirtaccen kyau da take dashi idan mutum ya kalleta sai yasha wata babbar budurwa ce duk da dai ba wani cika tayi ba amma tana da jikin girma idan akace tana 15y bazaka yarda ba sai kayi zaton takai 18y tayi kyau ainun ita daman da ba kwalliya take ba yau da tayi sai tajama tamkar tauraruwa daman ance idan kana da kyau ka kara da wanka,lallai ni kaina bansan hk Intee take ba saiyau da nasake kallonta da kyau, Doguwa ce da alama ta had'a tsatso da fulani,tana da tsawo sosai irin dogayen nan ce amma bawai cen san 6alba domin idan ta tsaya da yah Hafeez sosai ya kere mata Yusuf ne ma dai tazo kafad'arsa,tana da cikar halitta duk da bata da k'iba ko kad'an siririya ce to ta ina zatayi kiba bacin abinci sai kayan zaki lolx😅 amma akwa hifs hk ba laifi na shanunta a tsaye suke duk da bawata cika tayi ba,gashin kanta baqi ne me santsi shiyasa bata cika kitso ba ga manyan idanuwa hancinta ba laifi bakinta madaidaita Inteesar ba laifi tana cikin kyawawan mata,fuskarta zagayayya me kyau ita kanta bata cika fara'a ba yawacen lukuta zaka ganta ba yabo ba fallasa baza'a kirata me fara'a ba ga hnkl da natsuwa maza da dama hkn kesa su kasa mata mgnr so sbd kwarjininta ga rashin fara'a domin ba wanda zai kalleta yace bata kai 18y ko 20y ba, Yanxun ma duka mazan gurin ita suka sawa ido suna kallo kai harda mata,tuni ta diriri ce,tafiya na gagararta tsayawa tayi cekk tana tunani me yasa ta yarda aka mata wnn kwalliyar gashinan ta jawa kanta abinda ta tsana kallo, Da kyar suka isa gurin zama,hnkln kowa na kanta,tacewa maryam"ki tashi mu wuce gida don Allah,Maryam tace"sorry Sisto bari a fara rawar amare don Allah kinga Abba ya bamu kudin lik'i hk tayi hkr har M.C ya gama surutansa aka fara rawa wato angwaye da amare, A hankali ta mik'e ta nufi ckn fagen rawar,kai tsaye yah Yusuf ta dosa tana murmushi tare da maza rik'in 'yan dari biyar-biyar,murmushi yayi suna kallon juna,kauda fuska yayi Hafeez yayi hkn nan yakejin zafi aransa ba yauba tuntuntuni idan yaga Yusuf da Intee a irin wnn yanayin duk da ya d'au hkn a matsayin trashin kaunar da yake mata da kuma shiri da basayi da d'an uwansa, A hnkl ta juye gurin yah Hafeez gabanta na dukan tara tara karya mata wula k'anci cikin jama'a,daga hannunta keda wuya zata masa liki saijin saukar kud'i tayi ta ko ina ana mata liqi,a rikice ta d'ago fuska, Wani matashin saurayi ne,lik'ii kawai yake mata na rafasss,tuni gurin ya likice da ihu da tafi, Ji tayi an wani finciketa a fusgota da qarfi,sosai ta rud'e,bata gane waye ya mata wnn aikinba sai da taji an wullata a mota an rufe shima ya shugo ba kowa bane face "yah Hafeez,a matuk'ar rud'e ta kallesa ya kalleta......... To my fans wata sabuwa kuma wai inji 'yan chacha ko ya zata kasance sai kun biyoni a page na gaba🥰 Ummu Affan✍️✍️✍️♦️♦️♦️♦️♦️♦️ ♦️♦️♦️♦️♦️♦️ *IZGILI* ♦️♦️♦️♦️♦️♦️ ♦️♦️♦️♦️♦️♦️ *Story and written by* . *Fateemah Sunusi Rabee'u* *(Ummu Affan)* *Marubuciyar* *UWANIN QAUYE* *CIKIN WAYE?* *NIDA YAYA LAMEER* *KAINE SANADI* *NAYI GUDUN GARA...* *And now* *IZGILI* ________________________________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com _Bismillahir rahmanir rahim_ 🅿️1️⃣5️⃣-1️⃣6️⃣ Kallon kallon suke kafin ya d'aure fuska tare da kawar dakai gefe,aransa yana jin haushin me yasa yayi hkn ransa ya 6aci sosai dayin danasanin da yasa yayi hkn, Ita kuwa Intee duk a rud'e take gabanta idan banda bugawa ba abinda yake domin duk a zatonta don tamasa liki ne yasa ya mata hkn shiyasa tun farko bataso masa ba gudun irin faruwar hkn, Ckn sanyin murya kamar yadda take kullum tace"kayi hkr yaya Hafeez wllh dana san ranka zai 6aci da man maka likinba,har ckn ransa yaji sanyi da Intee ta d'auka dalilin hkn yasa ya mata haka,domin karma ta dauka ko wani abu don kar ma raini yashiga tsakaninsu, Sake tamke fuska yayi yace"tashi ki fitarmin mota,hawaye ne kwance a kwayar idanuwanta ta fita,tsaki yaja me k'arfi mtsuuuuwww har saida taji,da sauri harda dan gudunta tayi niyyar komawa ciki,saicin karo sukayi da Baheera,sakamakon irin bangazar da tamata tasata tsayawa cheek cike da tsoro, Kallonta Baheera tayi sama da qasa tace"uhmmmm aini daman tunda Hafeez yace ke qanwarsu ce naji ban yarda ba saida wnn abun ya faru na tambayi Saima naji asalinki ashe tsintacciyar mage ce da bata mage,wani shu'umin murmushi tayi taci gaba dacewa"wllh tallahi billahillazi nice zanga qarshenki,tun farko kallo da na miki naji na tsaneki,wnn abun da Hafeez yayi ya qaramin tsanarki duk duniya ba wacce na tsana sama da ke kuma sainaga bynki, Tunda Baheera ta fara mgn Intee ke kuka,gurin ta zube tana hawayen bakin ciki ita kuma Bahira ta wuce,a zuciyarta take fad'in me yasa rayuwarta tazo mata da hkn me yasa kowa yake tsanarta mutun hudu ke qaunarta a duniyar nan,Abba Umma Maryam sai babban me kaunarta Yusuf duk duniya sune masu k'aunarta(nace kinyi mantuwa Inteesar ga 'yan IZGILI FANS GROUP,Na 1 da na 2 duk fa suna k'aunarki,musamman masu sharhi 😅), Maryam ce tazo ta isketa a wnn yanayin kamata tayi suka koma mota direba yajasu daman shiya kawosu,basusan yadda wnn liyafa ta k'areba sai ciwon kai me tsanani da Intee ke fama dashi, Washe gari aka d'aura auran Hafeez Musbahu Yusuf da amaryarsa Baheerah Khamis,sai Yusuf Musbahu Yusuf da tasa amaryar Saima Muh'd,auran ya tara jama'a sosai ana gama d'aura auran Yusuf gida ya nufa part d'insu ya nufa yana shiga bedroom ya fada kan bed ya fara hawaye,Allah yasani Inteesar yake kauna har cikin ransa burinsa bai wuce ace ita ya aura ba yana sonta bai ta6a son wata tamkar ita ba,ganin ana ta damunsa da kira ya kashe wayar nan take ciwon kai me xafi ya rufesa, Ita ma Inteesar babu abinda takeyi sai rawar sanyi a ckn barko,maryam sai sannu take mata,tun safe suna bedroom su ko wankan bikin basuyi ba sbd zazza6in da ya rufe Intee tun ckn dare hk suka kwana babu barci,gashi Umma tana fama da baqi,Maryam taso ta sanar mata Intisar bata lfy amma ita Intin ta hanata, Shiyasa itama takasa komai gashi tayi tayi taci abinci taqi wanka ma tace tayi taqi sai kuka kawai take hkn ya karama jikin nata zafi,ganin yadda take rawar sanyi hakoranta na had'ewa yasata tashi da gudu ta fita tasanarwa Umma, A rud'e suka hawo saman tare harda mutane ganin halin da take ciki ta rud'e sosai nan ta kinkimeta suka nufi asibiti Anty Jummai sai k'orafi take wai suna tsaka da sha'ani yarinya karama nason ta6ata tace"ciwon k'arya ne kawai take, ................................. Da dareana takiran lambar Yusuf akace gashi za'aje wajen dinner hnklin Saima ya tashi sosai duk inda akayi tunanin za'a gansa ba'a gansa ba,Bahira tace"bakiji ance ankai wnn aljanar yarinyar asibiti ba wayasani ko yana cen, Hankalin Saima ya tashi ranta ya6aci hk ta tafi asibitin ckn fushi saidai taci rashin sa'ar rashin ganinsa, Haka aka gabatar batare dasuba,hnkl bai tashima sai,washe gari domin Saima ko d'akinta ba akaita ba sbd rashin samun wayar Yusuf,duka gida ya rud'e hankali fa yatashi, Hatta Hafeez gidan ya kwana sbd wnn jimami tunani yake ina Yusuf zaije a irin wnn halin,Abba da Umma suma hnklnsu ya tashi su dai Yusuf bai ta6a ce musu bayason auran nan ba balle su d'auka ko guduwa yayi,duk inda ake tunani anje ba'a gansa ba, Kwana biyu aka sallami Inteesar taji sauki amma ba sosai ba likita ya tabbatar harda ciwon yunwa ke damunta yace ta dunga cin abinci sosai,ita dai jinsa kawai take Umma sai fad'a take yarinya kome za'a mata bazataci abinci ba wnn wanne irin rashin yiwa kai adalci ne, Suna komawa gida taji wnn labari,me k'ewa tayi da sauri,zcyrta ta buga da qarfi,kallon k'ofar part d'insu tayi yayin da tayi gurin da sauri da kuma gudu,Abba Umma Anty Jummai Hafeez Maryam Saima suka bita da sauri domin yanayin yadda tayi gaba daya ya basu tsoro, Bedroom d'in Yusuf tashiga da gudu,suma suka rufa mata baya,kwance yake cikin wani irin yanayi na yana da rai ko akasin hkn domin sam bashi numfashi, Cikin tsananin tashin hnkl Hafeez ya kinkimesa da sauri ya fito,Duka suka rufa musu baya,ita ma Inteesar na ganin hk ta zube a gurin dukansu akwa kwasa sai asibiti.......... 😳Tofa me ya faru? Amsar na page na gaba, Please Share🤸‍♀️ Ummu Affan✍️✍️✍️♦️♦️♦️♦️♦️♦️ ♦️♦️♦️♦️♦️♦️ *IZGILI* ♦️♦️♦️♦️♦️♦️ ♦️♦️♦️♦️♦️♦️ *Story and written by* . *Fateemah Sunusi Rabee'u* *(Ummu Affan)* *Marubuciyar* *UWANIN QAUYE* *CIKIN WAYE?* *NIDA YAYA LAMEER* *KAINE SANADI* *NAYI GUDUN GARA...* *And now* *IZGILI* *Godiya ta musamman ga wad'an nan group ina godiya sosai* *NIKE DA GASKIYA FANS* *RIKICIN MASOYA FANS* *AUTAR MATA FANS* *KYAUTAR BUDURCI FANS* *FATIMA KO ZARAH FANS* *DAGA AURENA FANS* *IZGILI FANS GROUP* *IZGILI FANS* *KUNDUN AREWA FANS* *GALADIMA AARIB FANS* *AURAN KWANGILA FANS* Tabbas ina ganin sharhinku akan wnn novels nawa ina matuk'ar gdy da yadda kuke sharhi,snn kuma 'yan facebook bazan barku a baya ba domin kwarai inajin dadin yadda kuka amshi littafin nan ina sonku fiye da tunaninku ngd Ummu Affan taku ce🤝🌷💃💃💃💋 ________________________________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com _Bismillahir rahmanir rahim_ 🅿️1️⃣7️⃣-1️⃣8️⃣ Suna zuwa duka Emergency room aka nufa dasu Yusuf 6angaran maza ita kuma Inteesar 6angaran mata, Inteesar ce tafara farfad'owa ai kuka tasaki doe sai an kaita gurin yaya Yusuf,saida aka mata allurar barci sannan aka huta likitan sai fad'a yake yana cewa"d'azun nan muka sallami yarinyar nan amma kuma sai gata an dawo da ita,Umma dai hkr take basa Anty Jummai taja tsaki tace"waikai likita meye damuwarka ne kaje kaji mana da yaro kazo sai wani fad'an banza da wofi kake da bashida amfani a wajenmu,kallonta yayi zaiyi mgn,yaya Hafeez ya jashi domin yasan ita Anty Jummai don su kwashi 'yan kallo a asibitin ba amuwarta bace, An samu Yusuf ya farfad'o saidai sunan Intee ne kawai a bakinsa,shima allurar barci tasashi shuru byn barcin da ya kwasheshi, Duka hankalinsu ya tashi musamman Abba da Umma,hnkln Abba ya tashi sosai domin yadda yakejin Yusuf a ckn jikinshi abin ya wuce tunanin me tunani,duk ya zama wani iri, Ita kanta Saima na ckn tashin wnn abu yazo mata a bazata mijinta abin sonta amma ga abinda ya faru a daren tarewarsu,kuka tayishi sosai, Saida Yusuf ya kwana biyu snn yadawo cikin hayyacinsa,shi kansa Hafeez sai da yaga Yusuf yadawo hnklinsa snn yaji nasa hnkln ya kwanta,Allah sarki aka d'an uwa rabin jiki duk yadda suke da rashin jituwa a tsakaninsu da yaga wnn abin ya samesa sai hnklnsa ya tashi, Daman kuma hk suke tun suna yara indai dayacknsu zaiyi ciwo yanzun kaga hnkln daya ya tashi,ranar kwana na uku aka sallami Yusuf da Inteesar wanda rana daya sukaji sauqi abin kamar had'in baki ko asiri,shidai Yusuf likitoci sun tabbatar da ciwon tunani ke damunsa wato hawan jini,ita kuwa Intee daman matsalarta ta rashin cin abinci ce,hk suka koma gida kamar basuba,Saima kuwa sbd tsabar bakin ciki ji take kamar ta shaqe Inteesar tabar duniya mijinta na nuna mata halin ko in kula baya ta ita baya zancenta sai fira yake da Inteesar, Suna zuwa gida Abba yasa Hafeez da Yusuf sukayi wani wankan ya basu wasu kayan alfarma iri d'aya yace su saka sunyi kyau sosai,itama Saima tuni ta gama shirinta yace Yusuf ya d'auki matarsa subar gidan shima Hafeez ya tafi gurin tasa matar, Yusuf kamar zaiyi kuka hk ya yi sallama da mutane da kuma Inteesar snn suka tafi,wundow ta la6e tana hangensu har yafita da motarsa ckn harabar gidan kuka me tsanani tasaka tare da zubewa gurin Maryam ce ta kamota tana bata hkr,Hafeez shima fita yayi ya shiga motarsa ya nufi gidansa wanda kusa suke da Yusuf, Baku tambayeni Baheera ba???? ********** Baheera tun byn da aka kaita gidanta k'awayenta sun dad'e suna jiran ango ganin shuru har 11:00pm sai suka mata sallamah suka tafi byn sun gama shaye shayensu, Haka tayi ta jiransa tun tana zaune har ta mik'e hnklnta fa ya tashi da ta tuno irin shaye shayen da tayi sbd wnn ranar dazata tare da masoyinta ranar da taci burin zuwanta, Har wajen daya na dare tana jiransa jinfa shuru hnklinta yayi mugun tashi a gurin ta zube bakin bed tana murkususu domin abinda tasha suna aiki,shaye shaye na magungunan banxa da wofi masu matse mace da sata cikin muguwar sha'awa tasha to ga abinda hkn ya haifar mata domin taci burin ranar ta dade tana jiran ranar shiyasa ta tanaji wnn shiri, Haka ta dunga murk'ususu tana kuka gashi ba damar fita dare yayi bethroom ta fad'a ta sakarwa kanta ruwa tana kuka, Ranar dai yadda taga rana hk taga dare,ko washe gari bata fitoba tana nad'e kan bed kamar wata mara lfy,ganin har yamma tayi Hafeez bai zoba ta k'ullacesa aranta tayi niyyar duk ranar da yadawo zai gane kuransa hkn yasa ta tashi tayi wanka ta sa aka girka mata abinci domin da 'yan aikinta take tafe, snn ta kira saurayinta Sani yazo ya d'ebe mata kewa bazata iya sake kwana ckn wnn yanayinba(😳Bahira byn shaye shaye ashe harda bin maza to Allah ya kyauta), Rana ta uku ma suna tare da kwartonta Sani,Hafeezya danno motarsa cikin gidan.......... Mu had'e a page na gaba,kuyi hkr da wnn plssss🙏, Ummu Affan✍️✍️✍️♦️♦️♦️♦️♦️♦️ ♦️♦️♦️♦️♦️♦️ *IZGILI* ♦️♦️♦️♦️♦️♦️ ♦️♦️♦️♦️♦️♦️ *Story and written by* . *Fateemah Sunusi Rabee'u* *(Ummu Affan)* *Marubuciyar* *UWANIN QAUYE* *CIKIN WAYE?* *NIDA YAYA LAMEER* *KAINE SANADI* *NAYI GUDUN GARA...* *And now* *IZGILI* _My fans ina matuk'ar yinku fiye da tunaninku ina ganin sharhinku sosai akan wnn littafin kumin uxuri don Allah tabbas ina gani kuma ina gdy sosai,IZGILI FANS GROUP kuyi hkr dani gsky daga jiya na fara zama busy amma kuyi hkr kuci gaba da sharhi ina gani duk ranar da nazama free zan biyoku daya bayan daya ngd matuka da soyayya,snn zakuci gaba dajin IZGILI kamar yadda muka saba ngd_ ________________________________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com _Bismillahir rahmanir rahim_ 🅿️1️⃣9️⃣-2️⃣0️⃣ Bayan yayi parking a harabar gidan ya fito cikin takun kasaita da isa ga IZZA ya nufi k'ofar da zata sadashi da parlour,tsitt yaji babu motsinta,d'an Smile yasaki kafin ya nufi bedroom wanda ya tabbatar nasa ne,domin ya watsa ruwa snn yaje ya fad'awa Bahira dalilin da tajisa shuru kuma ko kiranta awaya ya manta yayi, Bahira mik'ewa tayi daga jikin Sani tace"bari na amso mana abinci gurin 'yan aikincen kasan nace karsu kuskura suzomin parlour sbd tsaro,fitowarta tayi daidai da shigar Hafeez cikin bedroom d'insa,zaro ido tayi a matuk'ar gigita ta koma ciki,"Sani"Sani"Sani tashi maza kabar gidan nan mijina ya dawo,shi d'inma a furgice ya mik'e ya zura kayansaya takalmi a hannu ya fito,saida ta kaisa harabar gidan,tasa me gadi ya shiga ciki saida ya fita snn tace ya fitu,shidai baice komai ba domin tun washe garin data tare suka faracin karo da wulakanci irin nata, Ciki ta koma ta fad'a bathroom wanka tayi ta shirya cikin wasu fitinannun kaya ta feshe jikinta da turaruka snn tasha magungunanta na tsuke mace domin matason Hafeez ya gane ita ba cikakkeyar budurwa bace, Parlour ta fito kai tsaye ta nufi bedroom d'insa shima ya shirya cikin k'ananun kaya bedroom dinta zai nufa sai gata ta shugo,jikinsa ta fad'a da sauri tana kukan shagwa6a na k'arya wanda ko kyau bai mata ba(ni kuwa nace wllh mace idan ba aji batayi ba,ko d'an jan class su Bahira Allah ya kyauta), Tace"haba honey yanzu abinda kayi ka kyauta kenan?ace duk buri da tanadin da mukawa rayuwarmu amma ka watsar dashi da nace zan maka hukunci amma kuma ina ganinka sai naji komai ya zube bazan iya maka komai ba wllh ko acikin maxa kai na dabanne ina sonka ina alfahari da samunka a matsayin miji,(Asmy Sa'a juwairiyya,Adama Mmn Khairat,Mmn Imam kuzo kujimin wnn matar wai ko kunyar nan ta daren farko babu sai kace itace Angon irin wnn zumud'i ban saniba ko Asmy kema hk kikayi🤣🤣Lolx), Abinku da miskili gaji da kasaita kamar wanin jinin sarauta ga shegen IZGILI kawai kamata yayi suka zauna bakin bed yace"uhmm Yusuf ne bashida lfy kinsan badon hk ba babu abinda zai hanani xuwa, Nan yake sanar da ita abinda ya faru,ta tausayawa Yusuf aranta tace"shi kenan ashe ita da sauki tunda ankawota gidanta Saima kuwa sai jinya aka tsaya, Jin kiran sallah ya fita masallaci bai dawo ba saida akayi isha'i,dinning ya zauna sukaci abinci,yace"yanzu byn fitata har kinyi girki,zaro ido tayi tana murmushi tace"girki kuma?aini bana girki banma iyaba 'yan aiki ne sukayi,da yake 'yan aikin sunacen B.Q bata basu damar zuwa mata parlour ba saidai idan abinci zasu girka kuma idan suka shiga kitchin babu wacce xata fito sai idan gama girki sukayi suna jerawa a dinning zasu fita wnn qa'idar Bahira kenan shiyasa ko da yazo baisan da wasu 'yan aiki a gidan ba, Uhmmm Hafeez me shegen k'ank'ami ai nan take ya fesar da na bakinsa yasa ruwa abakinsa ya tofar snn ya ya fara kakalin amai da saurari ta dawo gabansa tarik'e hannunsa tace"lfy?meya faru?,da sauri ya tureta da hannunsa ya fizge hannun yace"tunda nake ba'a ta6a cutata ba irin tayau abincin 'yan aiki kuma nifa kin ganninan daga Ummata da Baaba itama don ta iya girki ne(Sirrin daba kasani ba ai Baabar ita da Inteesar sukeyi🤗😜), "taya ke kina matata bazakimin girki ba sai wasu banzaye shiyasa najiGirkin wani iri babu dadi,Kallonsa take da mamaki tace"haba honey wai meye hk nice zan shiga kitchin to bari kaji tunda nake a rayuwata ko ruwan zafi ban ta6a d'aurawa da hannuna ba bare girki hk zalika ban ta6a ganin Mommyna ta shiga kitchin da niyyar girkawa Daddyna abinci ba,sbd hk nima a gidan mijina abinda zanyi kenan shiyasa ma na taho da 'yan aikina, Cike da mamaki yake dubanta,amma bai iya cewa komai ba,sai tashi da yayi yabar mata wajen,ta6e baki tayi sai da ta gama tabi bynsa,nan tafara jansa da hira sbd son da yake mata kawai yasa ya rabu da ita,hk suka kasance cikin farin ciki a daran,duk da dai bai sameta cikakkiyar mace ba kuma yasani sai kawai ya shareta domin son da yake bata kuma shi bamaison mgn bane baison fitina don ya lura k'iris take jira yayi mgn itama tayi nata domin ya lura gani take duk daya take dashi shi kuma yana raga ne sbd soyayya, .................................... 6angaran su Yusuf kuwa,bayan sun isa ko takanta baibiba ya wuce bedroom tsarin gidansa dana Hafeez duk daya ne,wanka yayi byn yadawo sallah yayi kwanciyarsa,itama Saima ganin hk bata bi ta kansa ba wanka tayi tai sallah ta kwanta,washe gari daga gida Anty Jummai ta ai ko musu da abinci,ya fito sunci snn ta basa magungunansa yasha kallonta yayi a hnkl yace"nagode,murmushi tayi tace"haba yah Yusuf ai hakkina ne na kula da lafiyarka,baice komai ba,cikin satin duk daga gida ake aiko musu da abinci tana cika sati kuma aka aiko mata da masu mata aiki,me makon tashiga sun dungayi a'a sai tabar musu ragamar komai ita bata hantararsu suna gaisawa fuska sake amma komi na gidan su keyinsa,dakinta dana Yusuf ne kawai bata barin suna shiga ita ke gyarawa, Haka Yusuf ya cire komai a zcyrsa ya aminta da Saima har suka kasance tare ganin ta kawo masa budurcinta sai yaji ya bata wani kaso a zcyrsa amma dai Intee na nan zaune darammmm, ************* Inteesar ce da Maryam shirye cikin shirin mkrnt marun ne wandonsu sai farar doguwar riga da hijab iya ciki,ta tufke gashin kanta hkn yasa ta k'ara kyau da annuri breakfast sukayi suka fita direba ya kaisu skul, Bayan an tashesu suna tsaye suna jiran direba a bakin gate sai gani sukayi mota tayi parking gabansu wanda ke cikin motar ya fito ya k'araso gabansu da sallama Inteesar bata d'aga ido ta kallesa sai amsawa da tayi cen k'asan mak'oshi Maryam tace"laaah kamar na wayeka fa,murmushi yayi yace"eh nima ina ganinku na ganeku sunana Faisal nine wanda muka had'u daku wajen biki daga miki liki yayanki yajaki kuka fita,ya fada yana kallon Inteesar............ I LUV U ALL MY FANS Ummu Affan✍️✍️✍️♦️♦️♦️♦️♦️♦️ ♦️♦️♦️♦️♦️♦️ *IZGILI* ♦️♦️♦️♦️♦️♦️ ♦️♦️♦️♦️♦️♦️ *Story and written by* . *Fateemah Sunusi Rabee'u* *(Ummu Affan)* *Marubuciyar* *UWANIN QAUYE* *CIKIN WAYE?* *NIDA YAYA LAMEER* *KAINE SANADI* *NAYI GUDUN GARA...* *And now* *IZGILI* DEDICATED TO ZEE 'YAR MAMA k'anwar k'awas,da kuma DOCTOR MARYAMAH inayiinki over k'anwata🥰 ________________________________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com _Bismillahir rahmanir rahim_ 🅿️2️⃣1️⃣-2️⃣5️⃣ A hankali Inteesar ta d'ago fuska lokaci guda daga ita har saurarin me suna Faisal gabansu ya wani buga lokaci guda,kawai tsintar kanta tayi da sakar masa murmushi tace"am dama kaine,gyada kai yayi shima yana murmushin ya d'aura dacewa"kallo daya na miki aranar naji kin kwantamin a rai kallonki nake kamar jinina,"JINI NA ta maimaita aranta,sai tasaki murmushi tace"uhmm nima hk nakeji amma naji ka burgeni,yace"ngd, Maryam kuwa kallonsu kawai take cike da mamaki Inteesar da bata kula kowa asalima mgn wahala take mata itace yau ke kula wani,waninma wanda batasanshi ba, Faisal yace"Inteesar ki bani number d'inki mana,murmushi tayi"Ayya sorry bani da waya dana baka number,cike da mamaki yake dubanta yace"kodai bakison ki bani ne amma taya zan yarda baki da waya,tace"wllh bani da waya,ko Maryam?ta qarashe mgnr ta na tambayar Maryam,tace"eh hk ne yayanmu yace saimun gama karatu zamu fara rik'e waya, Yace"shi kenan amma nidai zan saya miki waya sbd mu dunga gaisawa,tace"kayi hkr ko kasayamin baza'a barni na rik'eba,kawai idan kanason mu gaisa ka dunga zuwa gidanmu,da sauri yace"da gaske,tace"da gaske mana kaima daga yau kazama yayanah ko JININA gaba daya suka tun tsure da dariya Faisal yace"kai Inteesar kin bani dariya,tace"haka kawai naji na aminta dakai nasan bazaka ta6a cutata ba,yace"wnn hk ne JININA,dry suka kuma sawa daidai zuwan direbansu sllm sukawa Faisal snn suka shiga direba yajasu shima bin bynsu yayi a motarsa saida yaga gidansu snn ya wuce, Wani katafaran gida naga yayi hune direba ya wangale masa faskeken gate d'in gidan,gida ne uban ubansu na bugawa a jarida iya haduwa ya hadu da alama gidan wani babban k'usanne a Nigeria,yana parking a faffad'an harabar gidan wanda zai iyacin mota sama da goma,ga kuma motoci kusan shida jere a inda aka tanada domin ajiye motoci,da gudu ya isa ckn gidan da murnarsa, Mum ce zaune akan d'aya daga ckn kujerun alfarma dake Parlourn sai wata matashiyar budurwa da bazata wuce sa'ar Inteesar ba kwance a cinyar matar tana danna waya,shugowarsa yasa suka mayar da hankalinsa gurinsa budurwar ta tashi zaune da sauri tace"Yauwa yah Faisal daman ina nemanka,harararta yayi yace"dalla rufemin baki,Mum albishirinki?,kumburo baki matashiyar budurwar tayi kamar zatayi kuka tace"kai yah Faisal bakasanfa me xan sanar maka ba,yace"to bansonji,Mum nace albishirinki?murmushi tasaki tace"goro fari k'halll my son,ckn zumud'i yace"ina yarinyar da nasanar miki na ganta wajen bikin Anty Baheera to yau nasake ganinta,murmushi tayi tace"to masha Allah my son kace kaga abin kaunarka,murmushi yayi cike dajin kunya, Matashiyar budurwar ta tuntsire da dry tanacewa"wa yaga su yaya an fad'a tabkin soyayya,tashi yayi tare da kai mata bugu da sauri ta goce tare da mik'ewa ta ruga nan suka dunga zagaye babban parlourn da ya gaji da tsaruwa,Mum murmushi kawai take tana binsu da kallo,tsayawa yayi yace yauwa INTEEHAL kinsan sunan budurwata kuwa?,itama tsayawa tayi tana cewa "sai ka fad'a yace"sunanta INTEESAR,ai daga Mum har Inteehal tsayawa sukayi chakk tare da zuba masa ido,yaci gaba dacewa "Inteesar yarinyar tana da hnkl kamar kedai Inteehal girmanku daya tsawonku daya ke kusan komai naku daya ku.......bai k'arasa ba yayi shuru sakamakon hawayen da sukaga Mum nayi da sauri suka k'araso gabanta "me yafaru suke tambayarta,girgiza kai tayi "a'a babu komai nan ta fara share hawayenta,suma dai ganin Mum cikin wnn hali sai sukayi wani iri musamman da suka tuno wani lokaci cen baya, ************ "Inteesar"Inteesar"Inteenah kina ina ne?,muryar yah Yusuf taji dake kwala mata kira,baki ta turo gaba kamar yana ganinta tace"bana zuwa ka gaji ka tafi,6urummm taga ya shugo da sauri ta juya masa baya tace"nidai ka tafi babu ruwana dakai, Da sauri ya zagayo ta gabanta tare da rik'e hannayenta yace"hb Inteenah me na miki?, 6ata rai tayi saiga hawaye nabin kuncinta tace"nidai ka tafi,hannu yasa yana share mata hawaye yace"don Allah Inteenah kiyi hkr me na miki?cikin kuka tace"ba kaine ba tunda kayi aure kusan wata guda kenam baka sake zuwa gidan nan ba saiyau ni nayi fushi babu ruwana dakai, Murmushi yayi yace"wayyo Allah yau Yusuf yayiwa k'anwarsa laifi dole na hukunta kaina amma kafin nan kinsan dai aiki ko wllh aiyuka sunmin yawa Abba ba kullum yake zuwa Office ba duk ni ke aikin bama wnn ba ke komai yayimin zafi kinsan dai Abba gargad'i ya mana kar wanda yazo masa gida sai munyi wata guda,yau watanmu daya ciff wllh shiyasa nayo wnn sammakon domin naga fuskarki kawai ko zcyta tamin sanyi wnn watan wll jina nayi kamar makaho sbd ban alba da Inteenah,hararar wasa tai masa tare da zaunawa ta zuba masa ido,hure mata fuska yayi yace"kallon fa duk anawa,murmushi tayi ta dan turo baki gaba tace"yah Yusuf naga ka k'ara haske ka d'anyi k'iba kad'an me ya kawo hkn, Zuba mata ido yayi yace"wnn wacce irin tambaya ce Intee,6ata rai tayi tace"ai da ba hk kake ba,zaunawa yayi kusa da ita yace"............... Ummu Affan✍️♦️♦️♦️♦️♦️♦️ ♦️♦️♦️♦️♦️♦️ *IZGILI* ♦️♦️♦️♦️♦️♦️ ♦️♦️♦️♦️♦️♦️ *Story and written by* . *Fateemah Sunusi Rabee'u* *(Ummu Affan)* *Marubuciyar* *UWANIN QAUYE* *CIKIN WAYE?* *NIDA YAYA LAMEER* *KAINE SANADI* *NAYI GUDUN GARA...* *And now* *IZGILI* _Am sorry my fans jin kwana2 ba kujin wnn littafi akan ya faru ne sbd wata 'yar matsala amma yanzukomai ya daidaita nagode sosai da yadda kuke ta cigiyar littafin nan,masoyana a duk inda kuke Ummu Affan na k'aunarku iya wuya ana tare_ 💋 ________________________________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com _Bismillahir rahmanir rahim_ 🅿️2️⃣6️⃣-3️⃣0️⃣ Yace"kawai abinci Antynki ke bani me dadi nake cika tunbina,6ata rai tayi tana zun6uro baki tace"kaji yayan nan,tana wani harararsa cikin wasa,hk sukayi hira daga bisani ya wuce office, Kwanci tashi babu wuya a gurin Allah su Intee an zana jarabawar kammala secondry anyi Candy murna gurinsu ita da Maryam ba'a mgn,sosai Inteesar ta k'ara kyau kyawunta ya fito sosai,gashi ta cika sosai daka gantsa ita da Maryam kaga 'yan mata tuni samari sukayo musu chaaa saidai Intee bata bada fuska domin ko fita Islamiyya zata saita d'aura nik'af domin ta tsani kallo, 6an gare guda kuwa sunyi wata muguwar shakuwa da Faisal wanda har zuwa lokacin ya kasa furta mata yana sonta amma sosai suke haduwa, Shekaru biyu ciff kenan da auransu Hafeez,Hafeez ya sami mata kalar da yakeso wayayyi 'yar boko komai nasu cikin tsari sukeyinsa 6angare guda suna zuba soyayya sosai yakeson matarsa da bata kulawar duk da tadace domin shid'in d'an soyayya ne,6angare guda tana mu'amula da Sani saurayinta snn kuma tana shaye-shayenta har xuwa lokacin Hafeez baisan wacece ya aura ba, Baheerah akwai iya zama da mutane hatta su Umma basusan hallinta ba domin sosai take basu girmansu,amma agaban idansu a bayansu kuwa tafi kowa tsanarsu,Sosai Baheera da Saima suuke zuminc domin kansu ya had'e saidai Anty Jummmai babu wacce ta tsana irin Bahira jininsu bai had'u ba ko kadan, Shiyasa kullum idan taga Baheera take mata gorin haihuwa domin Saima yanxu hk ciki tsoho ne da ita haihuwa ko yau ko gobe,sosai Yusuf yake bata kulawa bazaka ta6a kallonsu kace auran had'i aka musu ba saidai har zuwa lokacin Inteesar na kwance a zcyrsa saidai yana mata kallon yarinta karama ko yanxu da ta kammala secondry school dinta gani yake batasan komai ba ya barta sai ta gama karatunta domin jarabawarsu yake jira su fito ya nemar mata addimision taci gaba da karatunta, Kamar yau Bahira da Saima ne sukazo gaishe da su Umma,Anty Jummai ce ke cika da batsewa a parlourn masifa ce kawai ke cinta jira take su Hafeez su shugo ai kuwa tare dasu shugo da Yusuf tun kafin su zauna Anty Jummai tace"wllh kaidai Hafizu kaji kunya yanxu wnn ba abun kunya bane shekara d'ad'd'ai har biyu kana zaune da mata ba ciki ba goyo saidai taci tayi kashi don Allah meye amfanin wnn,dukansu shuru sukayi Hafeez saida ya zauna snn yace"haba Anty Jummai ke kullum hk kike a rayuwarki bakison kiga mutane sun zauna lfy, Kwalla ta fara matsewa cikin kukan k'arya tace"daman Hafizu kai kafi kowa rashin ganina damutumci yanxu sbd na maka mgnr zama da juya kake wnn mgnr kake cimin mutumci amma ba komai bazan fasa sanar maka ka k'ara aure ba,wllh koni ko kai a gidan nan aure zaka k'ara domin bazai yuwu ka zauna da juya ba,du kansu zuba mata ido sukayi cike da tsoro da mamaki musamman Hafeez da Bahira......... Plsss share Ummu Affan✍️✍️✍️♦️♦️♦️♦️♦️♦️ ♦️♦️♦️♦️♦️♦️ *IZGILI* ♦️♦️♦️♦️♦️♦️ ♦️♦️♦️♦️♦️♦️ *Story and written by* . *Fateemah Sunusi Rabee'u* *(Ummu Affan)* *Marubuciyar* *UWANIN QAUYE* *CIKIN WAYE?* *NIDA YAYA LAMEER* *KAINE SANADI* *NAYI GUDUN GARA...* *And now* *IZGILI* ________________________________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com _Bismillahir rahmanir rahim_ 🅿️3️⃣1️⃣-3️⃣5️⃣ Cikin tsananin fusata Hafeez yace"haba Anty Jummai wnn wacce irin mgn ce aure kuma?ana zaune lfy nifa kin ganni nan bani da ra'ayin ajiye mace fiye da d'aya don hk don Allah ki denama wnn mgnr, Baheera kuwa mutuwar zaune tayi bata ta6ajin ta tsani Anty Jummai tsana mai yawa ba sai yau,wani mugun kallo kawai take aika mata, Anty Jummai kuwa jin abinda Hafeez yace saita fashe da kuka tace"yanxu Musbahu kanaji ka gani d'anka na wulakantani a gabanka yanxu bashi nake temako ba yaga kwansa tun yana duniya,Hafeez ne ya katseta da cewa"to wayasan gawar fari ke kenan samu abu ko ke kika haifemu, Ai saijin mari yayi faww da sauri ya rik'e kunci,Abba ne ya maresa cikin fushi yace"Hafeez tun ina raye kenan inaga na mutu 'yar uwar tawa Yayata kuma uwa agareni kake fad'awa mgn hk,to wllh bari kaji na baka wata d'aya ciff ka nemo matar da zaka k'ara aure idan ba hk ba ni xan nemar maka idan kuwa kak'i sai kanemi wani sarkin ma'ana karka dawomin gidana, Umma ce ta tashi fuuwww kamar me cike da fushi tabar falon,Abba ma fita yayi,saura kuwa duk jikinsu yayi sanyi,Anty Jummai ta mik'e tace"ato ni idan ba'aji tawa ba saikaji ta tsohonka shashashan yaro,ta wuce itama tanaci gaba da mita, Hafeez rik'e da kunci,idanuwansa sunyi jawur kamar jan gauta,bawai marin bane ke damunsa ko ke masa zafi ba,abu mafi ciwo tunda yake da mahaifinsa duk da kaunar dayafi nunawa akan Yusuf bai ta6a marinsa ba sai yau, Yusuf ne ya matso kusa dashi tun kafin yayi mgn ya dakatar dashi,ya mik'e kamar wani namijin zaki ya fita daga gidan da sauri Bahira ta bi bayansa, Tun daga ranar yake cikin wani irin hali na tunani,shidai bayason k'ara aure to wama zai aura?kuma bayan san Abba ya nemar masa yarasa madafar dafawa, Ita kuwa Bahira ta na sane da abinda ke damunsa tunda a gabanta akayi komai,mafita kawai take nemar musu kafin ta masa mgn, .............................. Saima ta haihu a wani asibiti na kud'i ta sami 'yarta mace kyakkyawa kamar YUSUF murna a gurin familyn ba'a mgn sosai akayi frn ciki da samun wnn k'aruwa, Inteesar basu sami zuwa asibitin ba saida suka dawo gida da yake nan gidan Umma aka dawo da ita tun ranar Anty Jummai tace"suyo nan don itace gaba a asibitin Yusuf baiso hakan ba amma bashi da yadda zaiyi domin yanxu sai abinda Anty Jummai tace akeyi,Umma sosai abin ke 6ata mata rai amma da yake bame hayaniya bace sai tayi shuru, Cikin d'oki da murna taje gurin me jegon,tana k'ok'arin d'aukar yarinyar kasancewar ta me son yara farin cikine sosai a zcyrta Yusuf d'inta yayi 'ya sunyi yarinya,amma wata tsawa da aka daka mata yasata saurin ja baya jikinta har rawa ake abinku ga mai mugun tsoro, Saima ce tace"wllh duk ranar da kika kuskura kika d'aukarmin yarinya sai na lahira yafiki jin dadi munafuka algunguma,Maryam tace"kai Anty Saima hakan babu kyau ke konsan irin addu'o'in da Inteesar ta tunga miki kina asibiti alwala fa tayi harda sallah raka biyu snn ta zauna tana ta miki addu'a, Harara Saima ta bankawa Maryam tace"dalla cen rufemin baki shaka tafi ni za'a kawowa maganar banza to nasa tane 'yata ce dai bana ra'ayin ta daukarmin,hk jiki a sanyaye ta fita d'akin harda hawayenta, Haka akasha hidima da suna sosai akayi hidindimo na burgewa, Inteesar ce ita da Maryam suka fito harabar gidan daidai lokacin da Bahira tashiga mota zata koma gida,k'urawa Inteesar ido tayi sosai take tunani akanta zuwa cen ta shek'e da dariya a fili ta furta "na sami mafita ta,mafita kuwa me kyau uhmmmmm ai daman nace nice ajalinki kuma wllh sai nayi maganinki,taja mota fuuuuww ta bar gidan, Tana parking ta fita da gudu ko murfin motar bata rufeba,"Honey"honey"honey kawai take kira,Hafeez ne ya sauko daga matattakar bene da sauri Bahira taje ta kama hannunsa suka zauna kan kujera tace"Honey na samo mana mafita akan auran da zakayi na wucin gadi da mun sami abinda mukeso saimu koreta,zaro ido yayi cike da tsoro da mamaki yake kallonta yace"amma dai kinsan bana ra'ayin aure ko?ni nasan abinda zai sanarwa Abba ya hakura, Gyara zama tayi tace"uhmmm honey ai nima baso nake kayi auran ba don bani da yadda zanyi ne so nake ka auri yarinyar nan damun sami abinda mukeso saimu sauta, Kallonta kawai yake kamin yaja numfashi yace"to su iyayenta basu da hankali zasu yarda muyi irin wnn auran da yarsu,tace"kaima da wata mgn to sanar musu zamuyi kaidai ka amince kawai,hk suka dunga gardama har ta shawo kansa snn yace"to a'ina take,kama hannunsa tayi tana murzawa zubawa juna ido sukayi hannunta d'aya tasa saman k'irjinsa tana murza kwantaccen gashin kirjinta tace"................ 😳Bahira fa ta bani tsoro to wai wa take nufin Hafeez zai aura?kodai kodai uhmmmm bari nayi shuru amsar na page na gaba😩😭😭my fans kardai abinda muke tunani ys tabbata har na fara kuka😭😭😭, 🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣I LUV U ALL MY FANS💋❤️ Plss share Ummu Affan✍️✍️✍️♦️♦️♦️♦️♦️♦️ ♦️♦️♦️♦️♦️♦️ *IZGILI* ♦️♦️♦️♦️♦️♦️ ♦️♦️♦️♦️♦️♦️ *Story and written by* . *Fateemah Sunusi Rabee'u* *(Ummu Affan)* *Marubuciyar* *UWANIN QAUYE* *CIKIN WAYE?* *NIDA YAYA LAMEER* *KAINE SANADI* *NAYI GUDUN GARA...* *And now* *IZGILI* ________________________________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com _Bismillahir rahmanir rahim_ 🅿️3️⃣6️⃣-4️⃣0️⃣ Tace"me zai hana ka auri yarinyar gidanku kaga data haifa mana sai ka saketa,ni atawa shawararma da wani tunani da nayi idan ka aureta mubar qasar nan ko ta samu ciki sai ace nice na samu kaga idan ta haihu ace nice ni zan raini d'an idan har ka amince da hkn daga baya sai kasaketa snn muja mata kunne da karta sanarwa kowa, Aransa mamaki yake wnn wanne irin bahagon tunani Bahira take"yace"am wa wa kike nufi Maryam qanwar Saima,girgiza kai ta fara tace"Inteesar!!ai kafin ta dire mgnr ya wani tashi a matuqar furgice a gigice yake kallonta yace"Bahira kinsan abinda kike fad'a kuwa ni bazan iya auran wnn yarinyar ba,mu haihu ba kikace da ita taya zan iya dubanta ma da wani abu kinsan yadda na tsani yarinyar nan kuwa so kike ta rainani ma kenan taji nace zan aureta, Kamo hannunsa tayi suka zauna ruwan sanyi ta kawo masa babu gardama ya amsa yasha kallonsa tayi tana murmushi tace"wnn hanyar ita ce hanyar da zaka nunawa yarinyar nan ka tsaneta idan ka aureta ka wulaqantata yadda kakeso snn ni kaina bawai inason ka kusanci yarinyar nan bane wllh ji nake kamar zcyta zata faso k'irjina idan na tuna saika kusanceta snn zata sami ciki,to babu yadda zamuyi dagani har kai kawai mu cika muradin zcyrmu da kuma wnn muguwar matar Anty Jummai da tasamu gaba kuma kaga Abba shima yabi bynta, Ajiyar numfashi Hafeez ya saki yace"da dad'ewa na lura d'an uwana Yusuf yanaso Inteesar yanzu idan nace zan aureta zansashi ckn tashin hnkl wllh nasan yanason yarinyar nan domin duk mai hnkl zai gane hkn,tace"don Allah kamanta da wani Yusuf idan kuma burinka arabamu ai shikenan,kukan munafurci ta fara tana cewa"kullum burina na gammu ckn frn ciki bana tunanin har abada zamu rabu amma kai na lura bakasan frn cikina,kamota yayi jikinsa cikin sigar rarrashi yace"to yanxu ya kikeso ayi nidai wllh koda wasa bazan iya furtawa wnn qaramar yrnyr wai ina sonta ba bazan iya ba,murmushin samun nasara tayi tace"ai daman ita ko kallonta ma kar kayi gurin Abba zaka kace masa Inteesar kakeso mgn ta qare, Numfashi yaja yace"shikenan gimbiyata abinda kikeso shi za'ayi,gaba daya sukayi murmushi Bahira a zcyrta tace"Inteesar zaki gane wllh keda farin ciki har qarshen rayuwarki, ***************** Da sallama ya shugo parlourn gidan duk kansu suna parlour saidai babu Inteesar da Maryam,shi kansa Yusuf yana gidan,zaunawa yayi gefe kusa da yusuf ya gaishe da iyayensa Umma ce kawai ta amsa tana tambayar bahira yace tana gaishesu Abba kuwa ko kallonsa baiyi ba Anty Jummai ya gayar itama ciki ciki ta amsa snn suka gaisa da Yusuf, Kallon Abba yayi a d'an d'arare yace"Abba kayi hkr yanxu hk ma na samu yarinyar da zan aura,Abba sakin fuska yayi Anty jummai kuwa tuni ta sa dariya tace"d'an keson d'a ko kaifa kaikanka idan ka qara auran hankalinka zaifi kwanciya domin bakayi sa'ar mace ts gariba,shidai baice komai ba harararta yake qasa qasa, Abba yace"a'ina kasami matar?,gabansa ne ya buga sosai muryarsa ad'an d'arare yace"uhmm Abba dama Inteesar ce!!duka gurin suka zuba masa ido,ita kuwa Umma wani sanyi taji aranta ta dad'e tanawa Hafeez sha'awar Intee tasan zaiji dadin auranta sosai domin yarinyace ta gari,shi kuwa Abba bawai baiji dadi ba amma baiyi zaton Intee zaice ba domin Yusuf yaso ya aureta don ya dad'e da sanin irin son da sukewa juna a niyyarsa idan Hafeez baice ga wadda yakeso ba to da Maryam yaso ya aura shi kuma Yusuf ya basa Inteesar domin da rana daya yaso su qara aure,amma tunda Hafeez ya ruga Yusuf furtawa ai shikenan yayi farin ciki,ita kuwa Anty Jummai sam bataso hakanba amma ganin duka iyayen nasu da alamar sunyi na'am saitayi shuru tana wani ciccijewa, Baku tambayeni Malam Yusuf ba?,wayyo Allah a lokacin duk wanda ya kallesa yasan yana cike da tashin hnkl duk kuwa da qoqarinsa na 6oyewa amma Abba da Hafeez saida suka gane,mik'ewar da zaiyi jiri yaji na d'ibarsa sai ya koma ya zauna tare da kallon Hafeez yace"tabbas ina tayaka murna d'an uwana Allah ya tabbatar da alkhairi,Hafeez ji yayi jikinsa yayi sanyi sosai yasan Yusuf yanason Intee shi kuma yanason farantawa matarsa rai yanxu ya zaiyi kodai yace ya fasa,amma yakasa furtawa,Abba kuwa tuni ya miqe yace"saika fara shirye shiryen auranka da Inteesar domin sati guda za'ayi bikin yau juma'a muke rana ita yau za'a daura muku aure............. Tofa qara qaqa qaqa muje zuwa A gaskiya comment d'inku yayi sanyi yanzu,Idan banga sauyi ba kuwa za'a dad'e ba'aga nayi typing ba,don hk idan anason cigaban littafin nan naga cenji shiyasa na dena buku typing kullum bazan dunga wahalar da kaina ina faran tamuku amma ni ku kasa farantamin ta hanyar min sharhi ba aha, Ummu Affan✍️✍️✍️♦️♦️♦️♦️♦️♦️ ♦️♦️♦️♦️♦️♦️ *IZGILI* ♦️♦️♦️♦️♦️♦️ ♦️♦️♦️♦️♦️♦️ *Story and written by* . *Fateemah Sunusi Rabee'u* *(Ummu Affan)* *Marubuciyar* *UWANIN QAUYE* *CIKIN WAYE?* *NIDA YAYA LAMEER* *KAINE SANADI* *NAYI GUDUN GARA...* *K'URUCIYAR SAPNAH* *And now* *IZGILI* ________________________________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com _Bismillahir rahmanir rahim_ 🅿️4️⃣1️⃣-4️⃣5️⃣ Daga Hafeez har Yusuf suka bi Abba da kallo har ya fita daga parlou, Umma ta dubi Hafeez cike da fara'a a fuskarta tace"nayi farin ciki kuma nayi murna Hafeez Allah ya tayaka ruqo wllh na dad'e ina maka sha'awar yarinyar nan ashe kaima kana sonta to Allah ya tabbatar da alkhairi snn kuma don Allah ka riqeta amana kasan dai ko wacece INTEESAR don hk kariqe amanarka da kyau,kallon Umma kawai yake shi yakasa ma mgn, Anty Jummai taja tsaki tace"yo aikin banza Allah yasa itama ba juyar bace domin wnn yarinyar mai fuskar munafukai kamar aljana da ita bazata rasa jinnu ba,Yusuf yace"kai Anty jummai fata dai na gari lamiri don Allah ki dunga kyakkyawan zato, Harara ta banka masa tace"nidai dole na fad'i gsky ace wai kamar mata sun qare shidai Hafeez bai iya za6i ba,da farko ya d'auko me dirin kyendir yanzu kuma ya d'auko me zumin jinnu Allah dai ya kyauta, Sosai mgnrta ta qona ran Hafeez akanme zata cewa matarsa hk yace"eh d'in ko yatake a hk nakeson abata waike Anty jummai duk wani abu da kikasan zai samu farin ciki shi kikeqi wai me muka tare miki a gdn nan ne?, Kuka tasaka tana cewa"Hafeez kafi kowa rainani a gidan nan yanxu bakai nake nemarwa 'yanci dason kasami mata takece raini ba amma bakada wacce kake iya gayawa baqar mgn irina to nagode amma bani kamawa ba kawa Musbahu, Ko kallonta bai kuma ba yabar gidan,a harabar gidan sukaci karo dasu Intee sauran kadan suci karo,wata razananniyar tsawa da ya zuba mata ai batasan lokacin da ta zube a gurinba daga ita har maryam domin sosai suka furgita,tsaki yaja yace"aikin banza kawai zaki ta6ani da wnn tsamamman jikin naki wawiya kawai yaja tsaki tare da barin gurin, Hawaye ne kwance akan manyan idanuwanta suka gangaro zuwa kumatunta,maryam tace"kiyi hkr inteesar wata rana sai lbr,hannu tasa tana goge hawayenta tace"maryam bansan me nawa yah Hafeez ba ya tsanenu hk,tace"uhmm shifa kinsan hk yake koni bakiga hk yakemin ba, Haka suka qarasa ciki,cike da murna ta qarasa gurin yah Yusuf tace"yawwa yah yusuf duba kaga jarabawarmu,da murmushi ta idasa mgnr,amma yayi jiki a sanyaye tabbas inteesar tayi qoqari sosai kuma shi kansa yasan hkn zata faru,yace"kinyi qoqari inteenah, Cike da mamaki take dubansa jiki asanyaye tace"me ya faru yayanah naga kayi wani sanyi ko banyi qoqari bane?,murmushin yaqe yayi yace"kinyi qoqari sosai ma,zaunawa tayi kusa dashi tace"yayanah don Allah kayi hkr idan wani yayi maka laifi idan kuma mgnr karatuna ne idan bakaso wllh na hakura,zzuba mata idanuwa yayi kafin ya tashi da sauri yafita binsa tayi da kallo cike da zullimi to me tayiwa yah yusuf sosai tashiga cikin damuwa, ************* Ko da Hafeez ya koma gida bahira ta tambayesa yasanar mata yadda sukayi da Abba sosai tayi farin ciki,tace sai ka bani kudi da kaina zanje dubai na had'o mata kayan lefe don karma muqiyi suce baka sonta, Kallonta yayi fuska daure yace"Bahira bansan son da kikemin suna ya taraba sai yau yanxu don Allah da kanki kina sani aure snn kuma kice zaki hada mata lefe kina wani rawar jiki sbd tsabar kin dena qaunata, Kama hannunsa tayi cikin nata tana murzawa tace"cool down my honey baza ka gane bane amma wllh son da nake maka yafi na kowa wllh gani nake duk duniya babu wacce take qaunarka fiye dani(kunji wani jahilci Allah ya kyauta bahira ta mance da Umma ne wacce ta kawo hafeez duniya ko kuwa ta mance da Abba mahaifin hafeez ne mata masu irin halin bahira sai ince Allah ya shiryaku), Wani kallo ya mata baice komai ba ya wuce Up step,kallon bayansa tayi ganin ya haura ta wani had'a hannuwanta ta bugi iska tare dasa dry tace watan baqin cikinki ya kama Inteesar(ni kuwa nace ba giringirin ba bahira kardai garin gyaran gira arasa ido aha🤪), Sosai Abba ya fara shirin auran kyautar Allah kamar yadda yake kiranta,hk Umma sosai take gyaran 'yarta ita dai nata ido ta rasa gane me ake yi snn kullum cikin habaicin Anty jummai take,ita ba wnn yafi damunta ba bace tun ranar nan bata sake ganin yusuf yazo gidan ba, Shi kuwa yusuf yanacen kwance babu lfy gashi yasanarwa Saima idan ta fad'awa wani bashi da lfy saiya sa6a mata, Yau alhamis gobene bikin Hafeez da Inteesar kuma a ranar Hafeez da Bahira suka kawo akwatinan lefe,kaya masu kyau da tsada bahira ta za6owa intee batayi qaranta ba domin batason ace ga wani abu laifinta domin nunawa kowa take tafi kowa qaunar auran kunsan FUSKA BIYU gareta, Sosai Umma taji dadin wnn kaya kuma ta tabbatar Hafeez yanason Inteesar tunda kayan lefenta harsunfi na Bahira haduwa, Kowa sai yabawa yakeyi banda Anty Jummai dake tajan tsaki dason samunta ne ace maryam ce aka kawowa wad'an nan kaya ba intee ba sai cewa take kawai albuzaranci ne wnn kawai, Da daren ranar Abba ya kira inteesar domin sanar mata gobe ne bikinta da yayanta Hafeez,cike da na tsuwa ta nufi part d'in Abba domin tun ranar da suka bangaji juna da Hafeez daman gabanta ke faduwa ga kuma fushin da yusuf keyi da ita da batasan dalili ba yau kuma ga kayan da taga su bahira sun kawo,hk tashiga part din jikinta a sanyaye............... Muje zuwa Ummu Affan ce✍️✍️✍️♦️♦️♦️♦️♦️♦️ ♦️♦️♦️♦️♦️♦️ *IZGILI* ♦️♦️♦️♦️♦️♦️ ♦️♦️♦️♦️♦️♦️ *Story and written by* . *Fateemah Sunusi Rabee'u* *(Ummu Affan)* *Marubuciyar* *UWANIN QAUYE* *CIKIN WAYE?* *NIDA YAYA LAMEER* *KAINE SANADI* *NAYI GUDUN GARA...* *And now* *IZGILI* ________________________________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com _Bismillahir rahmanir rahim_ 🅿️4️⃣6️⃣-5️⃣0️⃣ Bayan ta shiga ta iske Abba Umma zaune akan kujerun parloun qasa ta zauna tare da gaishe su,suka amsa cikin fara'a, Da nasiha Abba ya fara inda ya mata nasiha mai shiga rai da zcy,tuni hankalinta ya tashi domin ta gano da wata a qasa,Abba yaci gaba dacewa"Inteesar kiyi hkr domin munyi abu ba tare da saninki ba mun yanke hukunci ba tare da munji ta bakinki ba amma ina da yaqinin bazaki bani kunya ba shiyasa kai tsaye na yanke hukunci, Cikin Intee ya wani bada wata qara aranta tace shikenan anzo gurin gabanta ya tsananta bugawa wa daidai lokacin da taji Abba yace"Hafeez ya nuna mana yana son auranki hkn yasa muka basa ke snn gobe ne bikinku insha Allahu duk wasu shirye shirye da kike ganin munayi a gidan nan akan bikin naku ne, Ai tuni kunnuwan Inteesar suka dod'e samm ta kasa fahimtar ma abinda Abba kecewa ita dai ta fahimci ita ce za'awa aure gobe kuma da yaya Hafeez,tuni hawaye suka tsinkewa idanuwanta damuwa me tsanani ta bayyana akan fuskarta saidai da sauri tayi qasa da fuskarta,komi Abba da Umma sukace bai kamata ta musaba ba Hafeez ba ko waye sukace ta aura bazata iya musa musu ba balle d'an cikinsu mafi soyuwa a garesu, Kawar da damuwarta tayi snn ta goge hawayenta ba tare da sun lura ba,ta d'ago fuskarta cike da murmushin yaqe tace"Abba kenan ai wnn ba wani abu bane wllh ko waye kuka bani zan amince bare Yaya Hafeez d'an uwana na'amince kuma ina murna da wnn had'i, Gaba dayansu sukayi dariya fuskokinsu cike da murna da farin ciki Abba yace"Allah ya miki albarka,Umma kuwa jawota tayi jikinta cike da farin ciki, .................................... "Wai da gaske kike Inteesar abinda Abba yace Hafeez zaki aura,hawaye ne sosai ke zuba a fuskarta tace"zan miki qarya ne maryam ko kuwa baki yarda da ni bane?, Shuru tayi tare dayin tagumi itama tana hawaye maryam tace"wllh ba Hafeez nake jiye miki ba Inteesar sai bahira domin nashi me sauqi ne ke zaki iya dawo dashi hanya amma wnn shed'aniyar matar tasa uhmmmm wllh bata da mutumci, Inteesar kuka taci gaba dayi,daga baya maryam tayi shuru domin sun taru suna tayi sai ta dawo rarrashinta,hk ranar dukansu suka kwana sakaka har garin Allah ya waye Inteesar kwana tayi sallah, *************** Allahu akbar alk'awarin Allah ya cika akace matar mutum kabarinsa duk inda matarka take saika aurota hk miji ma duk inda yake indai shi Allah ya rubuta miki zaki aura to duk tsawon lokaci sai yazo kin auresa, A yau dubbannin jama'a suka shaida auran HAFEEZ MUSBAHU YUSUF,da kuma INTEESAR YUSUF,domin yusuf dama tunda yakaita skul aka tambayi sunanta sai yace Inteesar Yusuf hkn yasa da hk ake kiranta shine matsayin uba agareta kuma hkn ta riqesa yanzu duk da ada taso yaci gaba da zama uba agaretan snn kuma miji wanda zai ji6anci lamarinta saidai kana naka Allah yana nashi,Yusuf yazo d'aurin auran saidai ana d'aurawa ya koma gida, Bayan sun hadu da d'an uwansa ya masa barka,ce masa yayi"Hafeez ina tayaka murnar auran Inteesar duk da nasan ba sonta kake ba amma ni nasani nan gaba ko baka sota ba zaka tausaya mata,duk da basan qudurinka na auranta ba amma zcyta na bani da biyu ka aureta ka aureta ne don cikar wani burin zcyrka ko kuma ka aureta ne domin ka quntatamin sbd ka lura ina sonta kai kuma nasan ka tsaneni tun muna yara,eh ba qarya ba ni naso na auri inteesar saidai qaddara ta riga fata,bazance sakacina ba saidai nace daman cen ita ba matata bace domin idan da matata ce dole ne nifa zan aureta, "Mgnta dakai ta qarshe Hafeez kaji tsoran Allah a ckn lamuranka karka cutar da intee akan wata manufarka ko kasa a cutar da ita ba umarni bane shawara ce domin ni nasan ban isa na umar ce kaba saidai shawarar ita ma idan kayi niyyar amsa,numfashi yaja yana a jiyar zcy hawaye tuni suka gama cika fuskarsa yaja majina tare da dafa kafad'ar Hafeez yace"kai d'an uwana ne bazan ta6a maka baqin ciki akan ka sami inteesar ba saidai har yanzu ina mai sake baka shawara ka riqe yarinyar nan hannu biyu domin ita din ta dabance kuma samun kamarta sai an tona nid'in na sanar maka snn karka d'auka wai har yanzu inason intee a'a na sadaukar maka da soyayyata d'an uwana fatana ka riqemin inteena hannu biyu domin nan gaba zakasan dalilin da yasa nake ce maka hk,shuru yayi tare da sauke hannunsa saga kafad'ar hafeez yace"na barka lfy Allah yabaka zaman lfy da iyalanka ni yaya uba uwa d'an ahli duka hk nake a gurin inteesar,yana gaba fad'a ya fad'a mota ya fuzgeta a guje(Allah sarki yusuf😭🙆‍♀️Allah dai ya kaisa lfy kar yaje garin gudun da yake kar wani abun yasameshi), Hafeez kuwa binsa yayi da kallo jikinsa yayi mugun sanyi d'an uwansa na jini d'an uwansa wanda suka fito ciki daya kuma rana daya uwa uba duka daya d'an uwansa dabaida kamarsa duka fad'in duniya me yasa ya biyewa matarsa ya 6atawa dan uwansa?wani kuka ya fashe dashi tare da shima shiga mota ya fusgeta da gudu.............. 🙄😳Tofa kar ayi biyu babu nidai nayi nan sai mun had'e a page na gaba,idan naga zafafan comment na muku wani gobe idan akasin hk to sai ankwana biyu, An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT __ Ummu Affan✍️✍️✍️