🦜🦜 *RAI DAYA* 🦜🦜 *JAN ZAKI*🐆 *DAGA MARUBUCIYAR :* *KAIKAJAWA KANKA* *KANWATA* *RAYUWAR MA'AURATA* Yanzu gani dauke da sabon littafina *RAI DAYA* inkiya *JAN ZAKI* *Paid book ne* Normal group 500 Special group 1k Acct nomba *3115484026 ikilima Adam first bank* Ko Katin MTN Kan wanna layin 09069080725 Banason VTU 0️⃣2️⃣ Tana kokarin cin kwalar rigar Mahaifin baffa 'tuni Yan gidan suka tattashi suna fadin subuhannallah baiwar Allah kinada hankali kuwa wannann sa'ar Mahaifin ki ne.. Yayar Margayya mai suna Sadiya tana hura hanci tace kutumar bura uban sa'an Mahaifina sun Mika *KANWATA* GA Yan mafiya shine zasu fake da kashe ta akayi shegu taron Mayu kawai.. Dakyar Malam Adamu ya kwaci Mahaifin Baffa hannun Sadiya ... Sauran dake cin bala'i suka ce wallahi sai munyi shari'a daku kujira kuga meze faru daku.. Kuka sossai Mahaifin baffa sukayi shida Mahaifiyar sa Yadiko suka ce daman auren yayan masu kudi akwai wulakanci..... Malam Adamu da autar su Baffa mai suna Lami tace Ah Ah wallahi kowa yasan Amina mutumiyar arziki ce kuma yar gidan Arziki ce iyayen ta Nada tarin dukiya Amma ta zabi auren yaya Sulaiman kuma zamantakewar su bata taba masa gori ko gajiyawa da talaucin sa ba...... Kowa gidan suka ce tabbas Amina ya ce Allah yana fidda rayayye acikin matacce..... Bayan kwana biyu baffa yadan samu lafiya har anbasu sallama sun dawo gida.. Yazama kamar wani wawa be magana abinci ma sai an matsa masa yake ci.. Suna zaune aka kawo musu sammaci daga kotu. Daga dangin Amina.. Shari'a akayi sossai Baffa yace bashine yakashe matar sa ba kazafi suke masa.... Kasantuwa talakawa ne Saida baffa yayi Wata shidda gidan yari... Sannan suka samu kudin daukan lauya har aka sake wani zaman a kotu.. Inda sukayi nasara akayi belin din sa... Dangin Amina sun nemi abasu yaran baffa yace har Abada jinin sa ba zasu zauna da masu zuciyar kafurci ba... Duk da hk Yan uwan Amina sunci Alwashin zasu kwashe yaran su fitar dasu karatu America . Mahaifan Amina sossai sukayi nadaman korar ta da suke yi intazo gidan . Sun zabi mata hakane Dan tagaji ta kashe auren tadawo gare su. suyi mata aure gidan Hutu kasantuwa yar Hutu ce yarinya mai tarin ilimin zamanii Dana Addini.... ***************"**********""""""""""""""" Cigaban labari...... Yau takama Monday tunda ummulkhairi tasan makarantar boko Baffa zekai ta jiya batayi barcin kirki ba har wasu mafarkai taringayi gata acikin makarantar ... Tana horan dalibai . Nan da nan tafito cikin shigar Atamfa ,man Vaseline kadai ta shafa tareda dauko wani yar gyalenta yar shara shara mai Arha ta yafa... Madubi ta dauko tafito kofar dakin ta tana kallon kanta acikin madubin ita kadai take dariyar ta... Cikin washe baki tace Alkur'an nayi kyau yau bakin ciki ze kashe Innaro yayi daidai da fitowar Innaro DAGA bandaki sake da baki take kallon Ummulkhairi da duk hankalin ta yatafi akan wanna madubi da take kallo taji an wabce madubin DAGA hannun ta... Cike da Masifa ta dago kai zatayi Fada... Innaro ta galla Mata harara cikin Jin haushi tace zaaje yawon iskanci ko.... Waike ubanki baze miki aure bane . Yafi ki zauna ki takura Mata da miji ki Hana su zaman lafiya...... Kan ubancen cewar khairi.. Madubina kika kwace sannan kika hada da Zagi harda min gori... Kuka ta fashe dashi tanata shure shure wayyo Allah Baffa shikenan anmun gori ... Tareda daura hannu akai.. Afirgice Baffa yafito daga dakin hannun sa dauke da rigar da yake shirin sakawa... Bakin sa Na rawa yace khairi wacece tamiki gori keda gidan uban ki..... Nuna Innaro tayi da yatsa tana shure shuren tace ba gatanan ba ... Har da cemin wai Na Hana Mata da miji sakewa..... Innaro hararan su take tace nafada saime karya nayi meye ya Hana kahada khairi itada Sultana kai musu aure ai duk girman su DAYA ........ Baffa cikin kunan RAI yace wallahi Safara'u ki fita hanyar yata Ina ruwanki da ita .. Yarinyar nan ba akan ki take ba wallahi akan ta saiki bar gidan nan bafa tsoro bane shiru shiru Na daga miki kafa ne Dan mutane su rage surutun Ina sakin Mata saboda khairi...... Inkika kaini bango babu Abunda baze faru ba ... Innaro jikin ta yayi mugun sanyi Dan duk auren da takeyi saboda rashin haihuwa Ake sakin ta... Shikuma bedamu da haihuwar ba. . Yi hakuri maigida bazan sake ba Amma kaja Mata kunne tasani zaman Uwar ta nake.... Khairi buga kafa tayi kasa tace kutmlesinan ashema zaman uwa ta... Baki isa ba ... Cike da rarrashi baffa yatada khairi daga zaunen Madubin ta . Ta nuna masa hannun Innaro .. Amso Mata yayi ya Mika Mata cike da kwantar da Murya yace kiyi hakuri yau makarantar Jan ZAKI ze dauki manyan dalibai. Murmushi tayi Saida kuncin ta ya lotsa tana fari da idanu tace Baffa kasan me yace Aa saikin Fada khairi Naa..... Tsaki Innaro taja tawuce tabarsu Dan bata iya kallon iya shegen Khairi..... Khairi Tace Baffa wai Makarantar in munje secondary za'a sani ko university....ne tayi tambaya iya gaskiyar ta.. Sossai Baffa ya Dara yace keko khairi yanzu ZAKI Fara karatun fa.. Sunce zasu Amshe Ku Aji shida primary keda Najwa.... Baffa uhmm yau Innaje Ajin nan hatta Malamin saiya jinjina dan har shi Zan koyar.... Sake da baki Baffa ke kallon ta babu daman yace Aa ba haka bane. Yanzu ta tada bori.. Murmushi yayi yace Kwarai kuwa ai kece ZAKI Koya masa... Basu bata lokaci ba wajen yin break koko da kosai . Saida ya tabbatar ta koshi yaja hannun ta suka fice..... Kai tsaye gidan Najwa yatura ta dan kiranta su Tafi... Koda taje iske Najwa tayi har ta shirya... Cike da ladabi ta gaida Rashida Mahaifiyar Najwa..... Mommy Najwa tace yata har kin iso zauna kiyi break ... Aa nakoshi Mommy Kallon ta tamaida akan Najwa dake kokarin zura takalmi a kafar ta... Tace muje danyi Sauri Baffa Na waje Na jiran mu..... Babu bata lokaci sukayi was Mommy sallama itako da adua tabi su cike da tausayin Khairi harda guntun hawayen ta... Tace khairi naso Abban naki yabarni inci gaba da rainon ki bayan na yaye ki... Amma Kash baffa be yarda ba ... Cike da kewar su tashiga fiddo kwanukan wanke wanke............ Tafiya sukayi mai dan nisa kafun su Iso Makarantar..... Najwa itada Khairi Saida suka kalli Juna suka Dara.. . Waoh Najwa ta furta tace wanna makarantar saikace ginin Ajanna... Khairi Tace uhmm ai Makarantar Jan ZAKI ne dole ya hadu.. Matashi ne ko tsoho ne babu Wanda yasani haka naji ana firan sa gidan rediyo..... Ginin Baffa yayi gaba suka take masa baya... Office din headmaster suka nufa. Daman yasan da zuwan su sake da Baki yake kallon Khairi subuhannallah ya Furta acikin zuciyar sa... Yace wanna yarinyar Anya bil'adama ce kuwa irin wanna uban kyau haka ... Ga yar Uwar ta duk da bata kaita ba... Amma itama akwai kyawun halitta... Shagala da kallon nasu yayi... Wanda Yasa khairi ta tsargu shiko Baffa murmushi yake yayi yace Bawan Allah kayi shiru inata magana ... Sau uku ya maimaita maganarr besan yanayi ba.... Khairi daukan takalmin kafar tayi ta kwada Masa Mari dashi. Afirgice yadawo hankalin sa rike da kuncin sa yana Jin zafin Marin.. Yace haba baiwar Allah kina da hankali kuwa Ina shugabar makaranta ki mareni...... Cikin Fada tace an mareka din ya za'a yi ka tsura min idanu kai maye ne?? Baffa cikin ban hakuri yace Yallabai kayi hakuri dan Allah . Bazata sake ba.. Maida kallon sa akan khairi yayi yace yata baa zagin malami ko dukan sa suma kamar iyayen ki ne.... Najwa tace Yi hakuri Malam bazata sake ba... Headmaster murmushi yayi yace azuciyar sa dan ta burgeni ne Zan hakura da Wata gaja ce tamin haka korar ku Zan yi wallahi.. Maida kallon sa yayi akan Baffa yace karka damu yawuce Biro yadauka yasoma rubuce rubuce takardun dake gaban sa... Dago kansa yayi tareda kallon Khairi yace ya sunanki.... Itako turo baki gaba tayi Wanda Yasa yaji kamar ya kwana yana kallon bakin .... Suna Na Ummulkhairi Sulaiman tafada cike da gadara... Itako Najwa yana tambayar ta bata tsaya Wata Wata ba tafada masa sunan ta Najwa Adam.... Nan da nan Baffa yayi Abunda yadace yatafi yabar su...... Khairi zaune suke office din sa . Suna jiran ya gama yayi musu jagora zuwa Ajin nasu.......... . Shiko kyalesu yayi yana ci gaba da Ayyukan sa.... Sallamar da akayi ne yasashi daga kai daga rubutun da yake yi Wani Matashi yaron yagani Fari sol Ajin Karshe..... Tafiyarsa ma abun kallo ce ... Headmaster dake kallon kyakyawan Matashi yace azuciyar sa yau dai ranar kyakyawawa ne.... Kallon sa ya maida akan Matashin yace Bawan Allah daga Ina haka.. Sai asannan ne Khairi da Najwa suka dago kai suna kallon sa... Waouh Najwa ta furta tana mai kare masa kallo ta kasan idanu..... Yana sanye cikin jallabiya Fari , kyakyawa ne Ajin karshe yanada yalwatacen saje a fuskar shi..... Badan sunji yayi Hausa ba zasu iya rantsewa baya ji tsaf kama yake da larabawa jajayen labban sa take kallo da zararan idanun sa mai cike da kwarjini.. Kallon sa ya maida kan headmaster tareda Mika masa takardun hannun sa.... Cikin hanzari ya Amsa ya soma warwarewa . Ganin An Rubuta sakone daga JAN ZAKI...kuma ga sa hannun sa nan akai Haka Yasa shi gyara zaman sa dakyau... Bakin sa Na rawa yace Naga takardan yana magana ne akan kaine mai Koya musu karatun Addini acikin makarantar... Saida Aji shidda ne basuda Malamin Addini.... Matashin Saurayin kayataccen Murmushi yayi dan tunda yashigo dakin kallo DAYA yayi wa khairi da Najwa ya dauke idanun sa.... Yana tabe baki.. Zazzakar Muryan sa mai dauke da sirriku ne sukaji yana Fadin ai babu matsala yafada cike da gamsuwa.... Good Ya furta tareda tambayar sa sunan sa..... Shiru yayi kamar ne nazari... Sannan yace J A Mohamed...... Headmaster ganin bako ne daga Jan ZAKI yace.. Yawwa Mohamed muje in kaika Ajin naku... Kallon sa ya maida akan khairi da kanta yake aduke tun zuwan J A taji wani muguwar Faduwar gaba..... Jiki Asanyaye suka tashi tareda bin bayan nasa J A na bayan headmaster yana karewa Makarantar kallon tsafta sossai yakasa cire idanun sa akan dalibai dake ta safa da marwa acikin makarantar...... Koda suka isa Ajin dalibai da suka gauraye Ajin da surutu kowa yayi tsit ganin headmaster..... Aladabce suka tashi domin gaishe shi hannu yayi musu alamun kowa ya zauna...... Kowannen su zama sukayi idanun su nakan J A dake tsaye rike da takardu hannayen sa.... Khairi kallon Najwa tayi suna magana kasa kasa tace kinga nan ne Ajin Na mu... Najwa cikin yin kasa da murya tace shine Allah Yasa mu iya bokon nan mu ma.....ehee kinsan lauya muke son karanta. Gyaran Murya headmaster yayi yace ywwa wanna dakuke gani ya nuna J A Muhammad shine Malamin daze ringa koyar daku Addini daga gobe zefara koya muku...... InshAllah. Bagabadaya class cikin ladabi sukace barka da zuwa Malam Muhammad. Kayataccen Murmushi yayi yana kallon su cike da kulawa Yace dafatan Na same Ku lafiya suna Na Muhammad Amma anfi kirana da J A.. Ina fatan Zaku bani hadin kai domin koyar daku Abunda Allah yace da manzon sa . Gabadaya Ajin suka dauka da InshAllah Malam J A .. Headmaster dake Murmushin amsar da suka bashi . Kallon sa ya maida akan Khairi da Najwa da suke kus kus.. Yace ywwa ga sabbin dalibai nan hannun sa Yasa ya nuna Wata daliba dake rubutu mai suna Sakina yace tashi tsaye... Hakan Yasa ta ajiye Abunda take ta tashi .. Kinga baki ne yaran nan dan Allah ki ringa dan koya musu Naga alamun kan su naja bazaa Sha wahala ba ashekarun su nan Ajin shine daidai dasu inhar sun maida hankali . Sakina kallo daya tayiwa khairi ta razana da mugun kyawun ta wani mugun yawu ta hadiye tace InshAllah Zan koya musu.. Nuna musu wajen zaman nasu akayi ... Khairi cikin hanzari taje tazauna tana zazzare idanu dan atarihin RAYUWAR ta wanna shine karo na farko data shigo cikin Alumma da sunan karatu har ita Najwa din... Bayan sun zauna kowacce daliba ta maida hankalin ta akan nazarin da suke Amma dukan su hankalin su nakan J A dake tsaye hannayen sa goye a kirjin sa... Kallo daya yayi wa khairi ya dauke idanun sa .. Yana gama magana da headmaster tare suka bar Ajin....... Koda ya Fita wajen makarantar kara juyowa yayi yana karewa Makarantar kallo Na tsafta.. Hannun sa Yasa cikin Aljihun rigar sa . Yana murmushi tareda Fiddo wani ........... *Karku manta paid book ne* *RAI DAYA* *Taku har kullum kyauta daga Allah* 09069080725 🦜🦜 *RAI DAYA*🦜🦜 *JAN ZAKI*🐅 DAGA MARUBUCIYAR Kaikajawa kanka KANWATA RAYUWAR MA'AURATA Yanzu kuma gani dauke da sabon book dina *RAI DAYA* inkiya *JAN ZAKI*🐅 *Paid book ne* Vip 500 Spécial 1k Àcct 3115484026 ikilima adamu fist bank Ko Kuma Katin MTN ta wannan nombar 09069080725 Inayiwa Al'umma musulmi gabakidaya Barka da sallah Allah ya maimaita mana.. Da sunan Allah mai Rahama mai Jin kai nafara wannan littafin ya Allah ka haneni rubuta abunda ze gurbata tarbiyyan Al'umma kabani ladan fad'akarwa. Ya Allah kasa yanda muka fara lafiya mu kare shi lafiya... Ka karemu da yan hassada ka hanemu dayiwa wani hassada... Ka azurtamu da halal ka hanemu da cin haram komin kankartar sa... Ya Allah kasa muyi kyakkyawan karshe ka shirya mana zuri'ar mu......... Kasa Albarka acikin neman mu.... Fitacciya Daga cikin kungiyar Jarumai writ associat IKILIMA ADAM (kyauta Daga Allah) 0️⃣1️⃣ ........... ✍️ Wayyo Allah ! Wayyo ! Allah ! Ataimaka mun gudu take shararawa iya karfin ta cikin dajin Allah babyn dake bayan ta yanata rusa uban kuka Alamun ya jikata........ Mazan dake bin ta wajen su shidda n'a hango 'kowannen su rike da makamai, suna harba bindiga amma baya samun ta... Sai kaucewa take..... D'are ne sossai misalin karfe shabiyun d'are touchla ne hannun ta take haska gaban ta.. Su kuma suna rike da fitilar wayoyin su..... A'cikin wannan yanayin ta buga uban tsalle ta fada wani kango mai cike da kayoyi yaron nata dan wata biyun dake kuka iya karfin sa muryan sa ta shake da gajiyawa da kukan da yake. Allah yataimake ta barci barawo yayi awon gaba dashi..... Su kuma wayanda suke bin sahun ta '' sai zagaye zagaye suke suna nishi sama sama... Ogan tafiyar su cikin tashin hankali yace taya mukayi sake *RAI DAYA* ta gagare mu kamawa..... Cikin su wani yana huci sama sama tareda haska tochla cikin ciyayin nan yace Mun shiga uku mun lalace in shugaba yasan Wannan matar ta kubuce mana bazamu ji da dadi ba.... Wayar babban nasu ne yasoma ring yana dubawa yaga shugaban nasu ne '' cikin tsananin fargaba da tashin hankali d'asuka bayyana a fuskar sa.. Yace Ranka ya dade wallahi gamu cikin jejin nan wallahi ta bace mana babu ita babu Alamun ta Ko kukan dan nata mun daina ji...... Dagacen bangaren cikin tsananin tashin hankali yana ciza labbansa ga wani uban Zufa ne t'a karyo masa nan da nan hantar cikin sa suka kada... Na'urar dake gaban sa yasoma dandannawa yana zufa yace kash amma dai babu waya hannun ta..naso inyi trakin din layin nata insan inda tabuya.... Yaron nasa yace gaskiya oga tun agida tabar wayar nan.. Cikin tsawa Shugaban yace maza kuci gaba da neman ta 'tana cikin jejin nan ku haska wayoyin naku n'a tabbatar kukan dan nata zai sa kusan inda tabuya...... Itakuwa tana cikin wannan kango sai zazzare idanu take' nishi take fitarwa à hankali tareda toshe bakin nata......à hankali taleko kai ba abunda kake gani sai fararen Idanun ta cikin wannan uban duhun take dan lekawa taga Ko sun tafi ne.... Ganin suna d'af da ita ya sata kara cusa kanta cikin kango innaliahi wa'inna ilairajun kadai take maimatawa à zuciyar ta tareda kankame yaron dake sauke ajiyar zuciya akai akai...... Ihu mai firgitarwa sukaji Daga Sama wanda alamu sun nuna kura ce... Ta nufo su Gadan Gadan suna ganin tahowar kuran nan habawa suka ari n'a kare gudu suke tsulawa shima Kuran iya karfin nasa yake bin su..... Suna gudu iya gudu har suka isa kan tsakiyar jeji wannan kuran sai haushi take ta samu nama.... Itakuwa ganin Kura be tsaya ba hakan yasa tasa taci gaba da gudun nata uban kaya suna hannun ta ' wanda sune suke bata matukar wahalar gaske.... ************************************************** Bayan shekara Ashirin da biyar 25 yrs........ Baffa ne zaune kofar gidan nasa zaune yana shawarar yanda zekoma birni dan soma kasuwancin nasa..... Abokin sa malam Adamu ne zaune kusa dashi suna zantawa... Yace baffa kaiko inka je birni wa da wa kasani ne.... Baffa dariya yayi irin tasu ta manya yace ah lallai Adamu kace wani abu ' ina ruwana da sanin wani abirnin nida doya zan ringa kaiwa... Kaga Ummulkhairi so nake in sata boko.. Kuma d'ana bincika bokon ance wai tayi girma tunda yanzu shekarun 13 aduniya shiyasa za'a sata aji shidda din frimari school... Kuma nayi magana da wani malamin dake kula da makaranta sunce su kansu basu taba ganin wanda ya gina makarantar ba komai nasa umarni ne koda ya siya filin ance wasu ne yaturo suma din wayanda yaturo din basu taba ganin sa ba.... Rike da baki Malam Adamu yace ikon Allah yau nakejin sabon Al'amari to taya haka zata kasance ne.... Wai ma ya sunan wanda keda makarantar ne yajefo masa tambaya..... Baffa yace Karma sunce *JAN ZAKI* Kai kai wai daman wannan shahararren makarantar n'a Jan zaki ne.. Habawa shiyasa makarantar tacika haduwa da tsaruwa wallahi ashe ba banza ba... Kuma makaranta ga mugun Arha kamar ta gwanati cewar Malam Adamu...... Ance wannan makaranta shine n'a talatin daya bude À Nigeria kuma dukan su irin gini daya ne ansa Jan zaki........ Ihun Ummul Khairi sukajiyo innaro n'a bugun ta... Baffa ce ya la kamar muryan ummu '' malam Adamu yace ita ce mana.. Babu bata lokaci sukayi cikin gidan koda suka isa gidan iske Innaro sukayi sai dukan ummul Khairi take babu sassauci..... Baffa cike dajin zafin wannan bugun yace ke Safara'u ki sakar mun ya nace... Saboda baki san zafin haihuwa ba shine zakiyi ta dukan marainiyar Allah...... Kuka sossai Innaro ta fashe dashi tana salati tace yau Baffa ni zakawa gorin haihuwa... Malam Adamu cikin takaici yace dole ya miki gorin haihuwa mana jibi har waje akejin karar bugun da kike mata Saboda kin samu jaka Ko ? Wai shin ma laifin me tayi miki ne.... Kallon su suka maida Akan ummul Khairi dake rusa uban kuka iya karfin ta...tana shure shure akasa cikin kukan shagwaba ganin baffa tace wallahi Baffa saika auro wata matar in bahaka ba ni ka kaini gun d'angin uwata sossai take ihu tana shure shure.... Babba durkushewa yayi ya Dago Daga zaune tareda mikar da ita suna face din juna.. Babban rigar sa kodaddiya ya tattaro yana kuka tareda soma goge mata hawayen yace haba Khairi dîna yar Baban ta kiyi hakuri wallahi banson nisa dake ne shiyasa ga yayan ki Saifudeen baya zama gida kullum yana birni gun kai Albasa cikin kasuwar jahar Katsina.... Kara rusa wani uban kuka tayi cike da sakalci tace shikenan baffa ni kadai zanta zama Innaro tana cin zalina takarashe zancen tanama innaro gwalo batareda baffa ya gani ba.... Innaro Salati ta dauka tana yarfe hannun cike da takaicin su tace DUK abunda zakuyi saidai kuyi kuma ni wallahi baki isa kice sai Baffa ya sake ni ya auro wata eheee tana karkada kugu.... Malam Adamu yace ai mugun halin ku ke sakawa a sake ku inban da tsabar mugun ta yarinyar nan batada uwa fa rana daya uwar da kanin ta suka rasu ..... Sossai Baffa da Malam Adamu suka hau Innaro da fada sossai.. Itakuwa Khairi rarrashin ta sukayi.. Dakyar ta yarda zata zauna gidan dan taji Al'kawarin za'a tura ta makarantar boko Jan Zaki........ ************************************************** Wanene Baffa... Baffa sunan sa Ibrahim Mohamed wanda yake cikin garin karamar hukumar Funtua Katsina State..... A unguwar jabiri layin yan bokolo yake zaune inda anan ne gidan iyayen sa suke..... Ya auri Matar sa ta Farko Amina wanda ta haifa masa yaya uku.... Saifudeen Sultana Ummul Khairi Matarsa Amina yar garin Funtua ce itama iyayen ta suna zaune ne a unguwar mata.... Soyayya mai tsananin shakuwa Baffa yayi da matar sa wanda a lokacin iyayen ta bashi suke son ta aura ba kasantuwa talaka ne. beda komai Albasa yake talla... Amina ta hadu da manyan masu Arziki kama Daga kan gwana 'attajirai biris taki yarda da kowa.. Baffa take so bata bukatar soyayyan kowani Attajiri... Mahaifin ta yace tunda tace Mai tallan Albasa take so abata Amma da sharadi babu su babu ita.. Ya za'ayi duk dangin su babu wanda ya auri matsiyaci sai ita... Hakanan dai akayi auren.. Tunda tace taji ta Amince Tun daga wannan lokacin yan uwan ta suka cire hannu kan ta.... Bata isa ta tako kafarta tazo gidan iyayen ta ba... Da tazo korar ta suke hakanan take hakura cikin kuka da bakin ciki Take komawa gidan bukar su n'a Jan kasa..... Baffa Sam baya son wulakancin da ake mata in taje gidan nasu shiyasa ya haramta mata zuwa gidan nasu.... Haka sukayi ta rayuwa cikin tsananin talauci wataran a wuni da yunwa Har Allah ya arzuta su da yaya uku... Washe garin ranar da ta haifi yar ta na ukun Aranar ne baffa ya dauko ta zekai ta Asibiti dan ayiwa yarinyar Allurar rigakafi ... Suka hadu da wasu yan yan iska mutane su Shidda sai fadi suke ita ce... Daya n'a cikin su yace yau shekara 13 kenan kullum sai mun zo unguwar nan. Anya kuwa itace matar da muke bibiya kamar n'a miji take goyo kaga nasan yanzu dan nata ya girma zekai shekaru 12 yanzu fa yake ma yan uwan sa misali. dayan yace Alkur'an itace kuka sani Ko takara wani haihuwa ne awannan kauyen Kuma wallahi mungaji dazuwa unguwar nan shekara shabiyu kenan kila wani auren takara nidai koba ita bace to suna mugun kama. me kuke jira ne...maza ku harbe ta wallahi itace Ko mun huta shekara da shekaru muna abu daya.. Cikin tsananin tashin hankali Amina take kallon su bakin ta na rawa tace wallahi tallahi bansan wacce kuke nema ba. Bani bace kama ce... Dan Allah kumun rai karku kashe ni Kunga mijina Na Nan auren saurayi da budurwa mukayi, cikin gigita take magana tana kokarin ajiye jaririyar ta a kasa. Baffa be Ankara sai jiya yi sun harbawa matar tasa Alburushi daya akan ciki daya akan Fuska.... Nan take ta yanke jiki ta fadi daman koda suka fito sai Fadi take Baffa nifa yau wallahi inajin kamar mummunar Al'amari zefaru dani... Yace mata ah Ah babu komai Adu'a itace maganin musiba... Ganin Amina tana kalmar shahada rike da hannun Baffa dake kuka iya karfin sa jaririyar sai tsala ihu take.... Bebi ta kan ta ba. Cikin muryan wanda rai ke d'af da barin jikin nata Tace Baffa ga Ummul Khairi nan karike ta Amana dan Allah karka bari tayi maraici.. Tana gama fadin haka tayi kalmar shahada nan da nan rai yayi halin sa.. Ganin ta mutu ne suka d'au hoton Jinin jikin nata... Basu tsaya wata wata ba suka haye mashinan su guda uku Kowanne su ya goya dan uwan sa abaya...... Baffa Innaliahi wa'inna yake Furtawa cikin kuka da tashin Hankali ya mugun fita hayyacin sa yana Girgiza ta yana Ihu wayyo Jama'a kuzo ku taimakeni Wayyo ! Wayyo ina jama'a suke yana ihu cikin tsarkewan murya bakin sa na rawa yana Girgiza ta sai Fadi Aminatu dan Allah ki Bude Idanun ki... Dan Allah karki mutu Wayyo Amina n'amiki Mafarkin Jin dadi da Arziki anan gaba zaki tafi ki barni..... Inkika tafi waze raini Ummul Khairi. Kan kace me wajen gabadaya makil da jama'a kowa nata sallallami suna ihun nan da nan suka hau koke koke...... Wata makociyar Amina kuma Aminiyar ta mai suna Rashida cikin kuka take Girgiza Amina datake kwance fuskar wasai cike da Annuri kamar zata budi baki tayi magana gawar ta. Ganin Aminan bata Ko numfashi yasa ta rufe mata idanu nan take wajen kowa yanata fadin ALLAHU Akbar wannan wani irin zalunci ne... A iya sanin mu Amina bata fada kowa nata ne... Wasu Azzalumai ne suka kashe ta me tayi musu ne.... Babu bata lokaci jami'ar tsaro suka iso wajen sossai suka tsora ta ganin wannan matar yanda akayi mata kisan gilla. Aune aune suka shigayi suka gama d'ube duben su awaje kallon su suka maida akan Baffa dake kokarin fita hayyacin Alamun ze sume.... Basuyi wata wata ba suka dauke sa cikin gaggawa kai tsaye Asibiti suka nufa dashi inda Likitoci Gêneral hospital Funtua suka raja'a akan sa..... Itakuwa makociyar Amina daukan Jaririyar tayi takai gidan nasu inda taci gaba da basu nono ita da yar ta datake goyo... Mahaifan Amina labari yaje musu akan Mutuwar yar su '' sossai sukayi sansani suka nufi gidan Baffa koda suka isa wayam babu kowa agidan .. Cikin tashin hankali suka nemi a nuna musu gidan Iyayen Baffa... Awulakance suka Shiga gidan ganin gidan duk laka ne ruwa cike à tsakar gidan bangon gidan da yayi bakin kirin gawayi suke kallo cike da mugun tsana suka karaso gidan nasu.... Mahaifin Baffa yana kuka zaune shida yan uwan sa duk sun jejeru suna kwasar gaisuwa.... Firgit suka tashi ganin d'angin Amina sun shigo da ruwan bala'i sai Fadi suke dangi matsiyata wallahi sai munyi shari'a daku yar ta mu kuka kashe mana... Sossai babban yayar Amina ke kuka tana kokarin cin kwalar rigar........ Taku Har Kullum KYAUTA Daga Allah.. Karku Manta Paid book... Free Page guda goma kacal zan baku... Barkan mu da Sallah Allah ya maimaita mana... Allah yajikan iyayen mu da kakannin mu da dukan musulman duniya Ameen ya Allah 🦜🦜 *RAI DAYA* 🦜🦜 *JAN ZAKI*🐆 *DAGA MARUBUCIYAR :* *KAIKAJAWA KANKA* *KANWATA* *RAYUWAR MA'AURATA* Yanzu gani dauke da sabon littafina *RAI DAYA* inkiya *JAN ZAKI* *Paid book ne* Normal group 300 Special group 500 Acct nomba *3115484026 ikilima Adam first bank* Ko Katin MTN Kan wanna layin 09069080725 Banason VTU 0️⃣4️⃣ Har ogan nasu cikin isa yafito suka bashi hanya Taku yake kamar beson taka kasa. dukar da kai dukan yaran sa sukayi alamun girmamawa . Karasowa yayi daidai inda khairi take tun daga kasa har sama yake bin ta da kallo tareda kau da kansa gefe daya ya maida kallon sa akan Najwa data zuba masa idanu . Karamin tsaki yayi yanda bazasu iya jiyo sa ba. Wanda aka mara yake kallo rike da kuncin sa yana shirin ramawa . Hannun ya daga masa Alamun kada yayi mari. Hakan Yasa cikin kunan rai ya tsaya cak kamar an dasa shi... Itakuwa Khairi sai hura hanci take tana Fadin Aida ka barshi ya Rama Dana nuna muku karamin hauka banza dakiki ni akuya ce ko kaza da kake shirin buge ni da Mota.. Takamar Ku kudi ko . Mu kuma takamar mu Allah ehee Najwa tace wlh babu kodaya yar uwata Zo mu tafi dan Allah jibi kallon da suke jifan mu dashi.... Muryan ogan nasu sukaji yana Fadin dan Allah kuyi hakuri akasi aka samu... Sossai Muryan nasa ya doki kunnuwan su dan babu Wanda yayi zaton zeyi magana hatta yaran sa... Yarinyar dake cikin daya daga cikin jerin motocin ne tafito ranta abace. Tace haba Yaya Aliyu hakurin me zaka bata itace fa tayi laifi . Kutumar bura uban cen khairi ta Furta tareda bude baki tace yau Naga Wata yar iska me shigar banza watau ga awaki ko a buge mu dan ..... Saurin katse khairi yayi ta hanyar daka Mata tsawa Wanda Yasa ita da khairi hantar cikin su ya kada.. Yace stupid girl kinada mental problems ne yanda yayi magana cikin daga Murya gabadaya wajen kowa yayi tsit yarinyar data fito daga jerin motocin cikin hanzari ta koma motar ganin yanda yake a zuciye.... Itakuwa Khairi kuka ta saka tace Najwa dauko biro da papper nasan kin iya rubutu dan Allah rubuta mun Kalmar stupid girl din nan daya furta da kuma Mental problem.. Wallahi Nasan muguwar Kalma ce Alkur'an bazan bari ba . Yasani ya ciwo bashi da baze iya biya ba.. Ganin yana kokarin komawa motar tasa tasha gaban sa.. Cikin tsiwa da fushi tace wallahi Zan nuna maka ba kai kadai ne kayi boko ba ... Sossai kalaman ta suka kara bashi takaici kyaleta yayi batareda ya Amsa Mata ba.. Yashige mota abun sa.. Nan da nan duka sauran yaran sa duk suka shige motocin... Wanda khairi ta Mara yanata Ayyanawa Aran sa saiya dawo ya zane ta . Dan bata mari banza ba... Motocin su nabarin wajen Khairi Tace yawwa Miko min takardan nan in boye ta... Najwa Mika Mata takardan tayi tareda jero Mata sannu. Tace badai kiji ciwo ba ko? Khairi Tace aa banji ciwo ba kawaide Faduwar danayi ne naji azaba danaje gida Na gasa wajen ya wadatar.. Takarashe zancen tana kokarin saka papper acikin jakar ta... Basu bata lokaci ba wajen barin titin kai tsaye gida suka nufa... Daidai kofar gidan su khairi sukaga Baffa da Malam Adamu suna Alwala alamun sallah magrib ce zasu yi... Kallo daya Baffa yayi wa khairi ya fadada Murmushin sa cikin zolaya yace yar auta ta yar Makaranta sai yanzu muke ganin Ku.. Ganin bata Murmushi yasashi Fadin subuhannallah yana mai Kallon Najwa da tayi shiru kamar ruwa ya cita... Malam Adamu cikin halin damuwa yace khairi meya faru ne yar autan mu.. Kuka ta fashe da Wanda Yasa dukan su mikewa tsaye sukayo kanta hannun ta suka kamo tareda zaunar da ita tsakiyar su.. Baffa yace Najwa gayamana Abunda ke Faruwa dan maganar da yake daga ji yanayin Muryan sa ta canza .. Najwa cikin sanyin Murya tashiga basu labarin Abunda yafaru harda kalamin daya batawa Khairi rai... Baffa da Malam Adamu suka hada baki wajen Fadin muga papper .. Mika musu tayi tana kakalo kukan shagwaba tace Alkur'an Baffa wanna mutumin saina Rama nasan mugun Zagi yamin da turan ci.... Baffa karban Papper yayi shida Malam Adamu . suka shiga warware wa duk da rubutun Najwa babu kwarewa aciki Amma tsaf ake iya karanta rubutun nata daya fito daga gabas yayi arewa... Stupid Girl Mental problem Baffa suka furta kusan tare .. Khairi kada kai tayi tace eh haka naji yafada shiyasa nasa ta rubuta kada in manta... Please baffa da Malam Adamu nasan duk kunyi boko kunsan maanar hakan .. Daga Baffa har Malam Adamun sun rasa yanda zasuyi su gayamata dan sunsan kuwa tanajin maanar hakan ankira ruwa.... Baffa ne ya saisaita nutsuwar sa yace khairi Na karki manta malamin Ku yana muku nasiha akan in wani ya zage ka baka Rama ba.. Kansa ya zaga narokeki daughter kiyi hakuri yar auta ta..... Sake hada rai tayi tana kokarin fashewa da kuka tace yanzu bazaku gayamin me Maanar wannan Kalmar ba... Malam Adamu katseta yayi da Fadin yata ai yanzu so muke ki gano da kanki tunda kin zama yar boko kedai kibar Sauri.. Sossai suka shiga lallabata akan ta manta wannan zancen .. Itakuwa sarai tagane wayau suka Mata .. Wayance musu tayi tareda fadin yawu ce.. Karban Papper tayi tace Baffa zanje dashi saboda in ringa koyon hada kalmomi.. Baffa da Malam Adamu kallon Juna sukayi lta kan ta Najwa dake gefe zaune cikin sanyin jiki ta mike tareda fadin Khairi muje ko... Bakin su dauke da sallama suka shiga gidan.. Iske innaro sukayi tana goge kafafun ta da sukayi Faso.. Kallo daya tayi musu ta. Bushe da dariya dan duk firan da suke awaje ta labe zaure tana sauraren su.... Ajiye dutsen gogan kafar tayi tareda Mike wa tsaye tace khairi.. Sai yanzu aka dawo daga zuwa Makaranta sai dare . Khairi ranta abace yake shiyasa bata tanka mata ba Najwa tace innaro munje gidan Anty Sultana ne .. Innaro zazzare idanu tayi tace haba shiyasa Kuka Dade duk gidan da akwai maiko maiko nan ake ganin Ku sarakan kwadayi.... Khairi sossai takara harzuka tace eh gwamma mu gidan Antin mu ne mukaje kwadayin Ke kuma yawon karere kikeyi kina fadin ana barin ki da yunwa bayan karya kike wallahi Baffa yana kashe dukiyar sa akan ki.... Innaro kada kai tayi tace ikon Allah mai karfi Na bara... Shi uban naki har wani dukiya gare shi Banda wahala... Be Tara komai ba.. Gidan da muke ciki da bashi yaita biya har yazama nashi .. Khairi kara fusata tayi tanabin ta da mugun kallo tace ai gwamma shi yaci bashin yasai gida .. Kekuwa gidan iyayen ki Na haya ne kuma.... Saurin katse ta Najwa tayi tace yi hakuri Khairi kidaina biyewa Innaro kema kinsan ba kaunar mu take ba ..ayanda tayi furucin Innaro sossai jikin ta yayi sanyi... Cikin duniyanci irin nata tace nasan Papper ne hannun Ku kunason sanin meye aciki... Dasauri khairi da Najwa suka maida kallosu akan ta dan Sam sun manta tsohuwar malamar Makaranta ce..... Cikin hanzari Khairi taje gun Innaro dan ta mance fadan da suke tace.. Dan Allah Innaro gayamin fassaran wannan kalmomin Fiddo Papper tayi tana warware wa tareda Mika Mata... Innaro Na karba ta karanta ta bushe da dariya tace lallai Khairi ko wanene wlh ya gama dake kyakyawa mace kamar ki ze zaga da kalmar stupid girl.. Harda karawa da Mental problem... Kallon Juna khairi da Najwa sukayi tareda Furta ki gayamana me hakan yake nufi dan Allah .... Innaro tace yana nufin wawiyar yaringa mai tabun hankali .. . sossai suka razana dan tunda ta taso babu Wanda ya taba zagin ta da kalma mai kamanceceniya da wanna sai shi... Najwa dafa Khairi tayi cikin rarrashi tace Baki ji Abunda Baffa ya fada bane.. Kansa ya zaga tunda baki Rama ba..... Khairi Banda tafasa babu abunda zuciyar ta takeyi aguje tayi dakin nata... Tahau gado tareda rushewa da uban kuka mai cin rai... Innaro da Najwa tare suka shigo dakin sossai Innaro ke mamakin zallan shagwaban Khairi saboda an zage ta take wannan sakarcin laifin Baffa ne tafada cikin zuciyar ta..... Afili kuma nuna tausayawa tayi tace khairi dole ne fa .. Ki rama inhar Ummulkhairi Dana sani ce...... Tashi tayi tazauna da rinannun idanun ta da suka kada jajir..... Tace Innaro zauna ki gayamin hanyar da zanbi in Rama .... Bayan sun zauna dukan su ne tashiga musu bayanin dole ne wanna wurin hanyar sa ce. Indai suna bibiyan wajen a time din da suka hadu lallai wataran zasu ganshi..... Najwa ta yarda da shawaran Innaro tace Amma dan Allah karki gayawa su Baffa dan ze iya hana mu... Innaro tace haba taya Zan gayamai nida nakeson inga ta rama... Azuciyar ta sai fadi take uhmm angayamiki masu kudin birni sunada mutunci ne uban ki beda kudin daukan lauya yaro besan wuta ba saiya taka. Saida sukayi Isha'i Khairi ta raka Najwa gidan nasu. Nan ma kara samun waje sukayi suna ta bawa Maman Najwa labarin yanda Makarantar yake itako dariya take cike da so da kaunar su.. Tace Khairi ki kwana nan gidan mana ... Zazzare idanu Khairi tayi tana rike Baki tace Mommy kema kinsan Baffa baze bari ba ... Bayason ina nisa dashi ... Mommy jigum tayi tace khairi in kikayi aure ya Baffa zeyi ne.. Cikin rashin kan gado irin nata da wauta tace aure fa kikace ai babu dalilin dazesa inyi aure Mommy muna nan tare daku nida Najwa gira ta daga wa Najwa tace koba haka bane.. Najwa tace kwarai kuwa Mommy muna nan daram daku ... Murmushi tayi tana kallon nasu adua tayi musu tareda shafe musu jiki dashi.. Khairi ganin dare nayi yasata mikewa agajiye ta dau hanyar gidan nasu ... Da yake Katanga ce ta raba gidan nasu ... Iske Baffa tayi zaune yana fada da Innaro ... Yana Fadin haba wai meyasa bakida tausayi ne Safara'u meye ribar ki . Na fadawa Khairi gaskiyar Abunda aka rubuta ajikin papper ai dukan mu . Mun sani nida Malam Adamu Amma muka lallabata ta.... Dan tabar zancen kinsani Na sani Ummulkhairi tana dauke da Ciwon zuciya ,bana son bacin ran ta ... Allah shike rayawa Amma ban zaci Khairi zata rayu har zuwa wannan lokacin ba.. Ki kiyaye Na gayamiki in ba haka ba Zan sauwake miki in taimaki Wacce take da bukatar kulawa irin ta Mahaifiya ... Cak Khairi ta tsaya daga inda ta labe domin sauraren su... Wasu hawaye masu zafi ne suka shiga silalo Mata daga idanun ta zuwa kan fuskar ta.... Share hawayen nata tayi takarasa shigowa cikin gidan... Baffa najin Sallamar ta ya katse firan da yake cike da kakalo Fara'ar dole.. Yace khairi Na Ashe zaki dawo ki kwana gida... Jiki Asanyaye Tace Baffa aidole indawo kaima kasan bani iya kwana wani gidan in ba naka ba.... Kallon Innaro take da Alamun sossai jikin ta yake amace akan fadan da Baffa yayi Mata... Saida Safe tace musu tayi dakin nata.... Sam bekawo Aran sa taji firan da sukayi ba ya zata gajiya ne yake dawainiya da ita...... ************************** Kashe Gari Tunda sassafe suka shirya domin zuwa Makaranta... Innaro da kanta tashiryawa Khairi brek dan tasoma tsorata da kalaman saki daga bakin Baffa.... Khairi Koda tagama shiryawa cikin uniform din Makaranta blue black din wando da Farin Riga farin hijabi . Sossai sukayi kyau da shigar itada Najwa.. Basu tsaya Wata Wata ba. Suka kama hanyar su tazuwa Makarantar JAN ZAKI.... Sossai suke shan tafiya akasa kasantuwa akwai dan nisa... Khairi cikin gajiya take kallon Najwa tace kinga daga yau aringa bamu kudi muna hawa mashin dan ni nasoma gajiya.... Najwa tace au nifa bana ganin nisa wajen kece dai shagwababbiya bakyason motsa jiki... Khairi Murmushi ta sakar Mata tace naji tunda shedar da zaki min kenan.. Koda suka iso Ajin yayi daidai da shigar malamin nasu ne.... Khairi da Najwa suna kallon yanda yake musu darasi har lokacin tashin nashi yayi ..... Malamin kallon Khairi yake dan ta tafi da imanin sa.... Sakina tana lure dashi hakan Yasa duk ta tsane su batasan uban dayasa aka kawo su Ajin ta ba... Malamin Na kokarin fita daga Ajin yaji Muryan Khairi tana Fadin dan Allah inada tambaya.... Kowa Class din maida kallon su sukayi akan su dan so suke suji me zata fada... Sallamar J A ne Alamun time din karatun sa yayi ... Yaji tana Fadin dan Allah Malam meye Ma'anar Stupid girl da Mental problem.. A J zazzare idanu yayi duk bashi take Mata tambayar ba yace................ *Karku Manta Paid book ne* *Da Free yakare littafin zekoma 1k special group* *Normal kuma 500* *Taku Har Kullum kyauta daga Allah* 🦜🦜 *RAI DAYA* 🦜🦜 *JAN ZAKI*🐆 *DAGA MARUBUCIYAR :* *KAIKAJAWA KANKA* *KANWATA* *RAYUWAR MA'AURATA* Yanzu gani dauke da sabon littafina *RAI DAYA* inkiya *JAN ZAKI* *Paid book ne* Normal group 500 Special group 1k Acct nomba *3115484026 ikilima Adam first bank* Ko Katin MTN Kan wanna layin 09069080725 Banason VTU 0️⃣3️⃣ Tareda Fiddo Biro da pepper samun bangon Makarantar yayi tareda makala pepper yanda ZAKI dadin rubutu yana gamawa ya nade papper cikin Aljihun sa yafice cikin hanzarin yana buga uban Sauri..... ********************** Cikin Ajin kuwa Khairi sake da Baki take kallon malamin dake koyar dasu cike da kwarewa yake koyar dasu darasin mathematics .. Najwa da khairi kallon Juna sukayi Sam basa fahimtar me yake fadi tunda da harshen turanci yake magana... Amma duk Abunda Yake idanun sa nakan Khairi sossai taja hankalin sa . Dan befiye wuce lokacin tashi ba Amma yau Saida dalibai sukayi masa 'tuni.. Karfe daya da kwata ya tashe su... Najwa kallon Sakina tayi dake kokarin fita tace baiwar Allah kece wacce akace ZAKI ringa koya mana darasi... Cak Sakina ta tsaya tareda waigowa 'tabe baki tayi tace eh nice wacce Zan ringa koya muku darasi Amma azuciyar ta sai fadi take zandai kara dulmiyar daku yanda bazaku ringa fahimtar komai ba.... Murmushi tayi tacigaba da Fadin Ku bari zuwa gobe Zan fara horar daku tana Murmushin keta . Khairi daman Sam bata kwanta Mata arai ba .. Tace Najwa muje dan Allah ya kike damun kanki akan sai ankoya mana kedai ki zuba idanu kigani duk wayanda muka samu anan zamu wuce su.... Jan hannun Najwa tayi da karfi tareda barin Ajin cikin kunan rai.. Sakina ikon Allah ta furta rike da bakin ta tace yau Naga mara kunyar yarinya kenan kyawun dan maciji ce batada Kirki. InshAllah Ni Sakina Zan hanaku fahimtar komai masu fararen kafa takarashe zancen tana fita daga Ajin cike da mamakin Kalaman Khairi ... ************************** sunkai su Ashirin zaune cikin office suna karanta sakonni cikin computer Wanda ya nuna Sako ne daga Jan ZAKI... Babban cikin su Yace Kaga Abunda oga yafada kuwa...? Sauran dake latse latsen keyboard sukace eh mun karanta sakonnin sa... Toshi meyasa baze bayyana bane koda agare mu ne.. Babban cikin su Yace nasan yanada kwakwaran dalilin sa.. Amma duk da haka yakamata yazo mugan sa muga yanayin sa ...... Kuma kasan me yake bani mamaki kuwa.. Dayan dake zaune mai Suna Jafar yace saikun Fada.... Gabadaya be taba tozali da wani ma'aikacin sa ba... Kullum sai bada umarni hatta kudade baya turo su ta bank cash yake ajiyewa Yasa aje adauka Anya kuwa mutum ne dayan yafada cike da nuna damuwa akan haka.... Babban nasu yace Mutum ne mana Ku daina damun kan Ku tunda dai yana biyan kowa to meye matsalar Ku .... Hakadai sukaci gaba da amsa sakonnin jan ZAKI Jan ZAKI yana musu bayani akan Babban hospital da yake son abude agarin Funtua cikin gari Asai Filin cikin gaggawa Awa Ashirin da hudu ya basu Su kai masa takardun inda suke aje masa Sako yagani ya tabbatar da komai kuma yasa hannu akai... Sannan Asibitin Wata biyu kacal yake son agama ginin Katafaren Asibiti mai Suna hospital jan ZAKI..... Sossai suka shiga shirin aiwatar da Abunda Yasa su........ ************************** Wayyo Mama yanzu fa Na kwanta cike da shagwaba yake magana... Sake da Baki take kallon sa tace haba Aliyu saika kulle kanka adaki kai kadai .. Ko abincin rana bakaci ba.. Yamutsa fuska yayi yace oh Mama wai ...... Katse shi tayi tana Fadin please Dana tashi Kaci abincin nan so kake inshiga damuwa ne tafada cike da nuna raunin ta... Dago jajayen idanun sa Masu kwarjini yayi yasauke su akan ta... Cikin kwantar da Murya yace yi hakuri Mama. Na tashi tunda haka kike so... Kama hannun nata yayi cikin nasa ahaka har suka karaso falo suka zauna diner table ... Plate din Abincin ta jawo gaban sa tana diban abincin cikin spoon tana bashi abaki... Kwabe fuska yayi yana cin Abinci kamar yana tauna magani. Kadan yaci cikin Muryan shagwaba yace Mama jibi cikina nakoshi ... Murmushi tayi tace kokaifa duk da bamai yawa Kaci ba Amma ka rage mun damuwa.... Nusaiba ce ta iso Falon cike da kulawa take kallon Aliyu dake shan lemun kwali ... Inawuni Yaya ta Furta tareda neman waje ta zauna tana masa kallon Kirilla... Murmushi Mama ta sakar Mata tace yata kinga sai yanzu yafito danma nice Na fiddo shi dole barci ze koma. Nusaiba zare idanu tayi tace haba Yaya sai kayita. Fama da computer 24hrs in rasa me kake shukawa . Duk maganar da take kamar besan da ita.. Kallo daya yayi Mata yadauke idanun sa.... Yace yawwa kishirya bayan laasar zamu fita yakarashe zancen tareda barin Falon... Wani uban tsalle Nusaiba tayi ta rungume Mama ta baya... Mama kinajin wai tare zamu fita .. Murmushi Mama tayi tace ke yar gata ce... Yau dai nasan malamin naku me koyar dake Addini baze Zo ba ko.. Tabe baki tayi tace haba Mama ace mishi naje inga gari inbanda Makarantar boko babu indan kafafuna yake takawa yau babban rana ce awajena.. Mama tace Adawo lafiya nusy ta tana kokarin tattare kwanukan da suka ci Abinci . Cikin hanzari Nusy ta Amshe hannun Mama takai kitchen bata tsaya Wata Wata ba... Kai tsaye dakin nata taje daukan wanka dan tasan shi be jira ze iya wuce wa yabarta... Koda Akayi Sallah Laasar fita yayi yakai kusan Awa daya sannan yadawo cikin dan saurin sa... Kai tsaye dakin sa yanufa yakara daukar wanka tareda saka kanunan kayan sa... Chemis da bakin wando jeans sossai shigar ta Amshe shi glass din sa ya saka yazo gaban mirror yana taje sumar kansa .. Babu bata lokaci yadau abun bukatar sa yasauko ahankali yake taka matakalan step cike da nutsuwa ahankalin Sam yatafi awani tunani Na daban... Koda ya iso Falon iske Nusaiba yayi harta shirya shi take jira dan harga Allah yama mance da ita zefita... Kallon ta yake yace kekuma Ina zakije ne har da yafa gyale.. Sakaka sake da Baki take kallon sa tace Yaya kaine kace inshirya fa kuma yanzu kazo kana mun tambaya.. Dafe kansa yayi yace oh am sorry na mance ne muje ko yafada cike da kulawa...... Gaba tayi shiko kai tsaye sashin Mama ya nufa dan yi Mata sallama.. Koda ya isa kayataccen dakin Wanda ya tsaru iya tsaruwa kallo daya zaka yiwa dakin kasan an narka dukiya awajen musamman gadon da Mama ke zaune kai...... Wani ado irin Na lu'ulu ne kai kace da zinariya akai kayan cikin dakin har tsif din ta.. Lumshe idanun sa yayi sakamakon wani sirritance kamshi daya doki hancin sa..... Ganin shigowarsa Mama ta fadada Murmushin ta .. Tace Dana har kafito ko... Gyada mata kai yayi cike da kulawa hade da zallan shagwaba yace eh nafito kuma Sauri nake... Saidai kwana biyun nan akwai aikin gaggawa daya taso mun kuma kullum Zan ringa fita Banda Asabar da lahadi... Kallon agogon tsintsiyar hannun sa yayi yace mun tafi sai mun dawo ki mana adua . Allah yakareku ta furta tana Murmushin dole... Kuma Allah yataimake ka akan aikin da baa son insan Kona menene ta Fada cike da son tsokano shi ... Murmushi yayi yafice yana girgiza kai koda yafito iske Nusaiba yayi duk ta kumbura kadan ya rage ta fashe dan takaicin barin ta da yayi ya Dade dakin Mama. Nuna rashin damuwa da halin da take ciki yayi kai tsaye yayi hanyar fita ita kuwa cikin hanzarin ta . Ta take masa baya...... ************************** Najwa da Khairi ahanyar su ta dawo gida daga Makarantar suka hadu da Sultana yayar Khairi kasantuwa tana auren wani dan kasuwa kuma gidan nata kan titi yake yasa basu wuce gida kai tsaye ba.... Suka bita gidan ta anan ne suka bata lokaci sossai.. Dan Sultana takira baffa ta gaya masa suna gidan ta agayawa Maman Najwa karta tada hankalin ta... Baffa yace babu matsala tunda gida ne sai sun dawo din. Khairi tabe baki tayi tana sauraren redio da Mijin Sultana ya kunna ..... Inda suka sanya voice din jawaban Jan ZAKI akan harkan kasuwanci da siyasa yake magana da yanda za'a kawo zaman lafiya acikin Al'umma Sossai mijin Sultana ya maida hankalin sa yana jinjina kalaman Jan zakin.. Kallon Sultana yayi yace da ana samun matasa masu fadin gaskiya irin sa da anzauna lafiya da kuma an rage yawan talauci... Yaron nan fa shekarun sa 25 kacal aduniya Amma yana ilimin da wayanda sukayi jika dashi basu dashi...... Murmushi Sultana tayi tana kallon Khairi da ta nutsu wajen sauraron redio tace.... My sister kema kinfara jin dadin jawaban dan ZAKI ne...... Duk ranar litinin karfe uku ake Sako voice din sa kiringa amsar Redio baffa kina saurare ZAKI Karu sossai.. Tabe baki tayi tace ina dadi awajen Wanda keda baki cakwai inkika bibiya maganar fatar baki ce..... Sossai suka Dara har Mijin Sultana da Sultana da Najwa....... Mijin Sultana yace KANWATA jan ZAKI da kike gani yatara yawan magauta saidai abun takaici shine har yanzu babu Wanda ya taba ganin fuskar sa.... Khairi karo na Farko da ta dago kai tana kallon Redio tace a ina suke samun sa suyi magana dashi?? Mijin Sultana Isma'il Yace KANWATA an Dade ana saka voice din sa gidan Redio yanda labari yazo daga majiya mai karfi sunce turo voice din sa yakeyi ta account din sa Na Instagram da Facebook... Khairi da Najwa suka hada baki wajen fadin ikon Allah ... Nidai kam da Wata mai kudi ce Dana bayyana ma duniya fuskar sa mutum saikace mara gaskiya cewar khairi tana turo Baki.... Sultana tace waya sani ko haka dinne Amma kuma an shede shi da taimakon Alumma gidan marayu dari garesa a Nigeria shike daukan nauyin su in kin gansu wlh zaki dauka gaban iyayen su suka taso dan beyarda akai musu wani tallafi ba... Jinjina kai Khairi sukayi itada Najwa.. Suka hada baki wajen Fadin Allah yataimaka. Tashi sukayi cikin sakin Fuska Najwa tace to Antin mu zamu je gida.... Murmushi Sultana tayi tace haba khairi keda Najwa kubari in gama girki mana..... Jin Abunda suke fade Yasa Ismail fadin kinga Sauri suke maza ki Diba musu duka Abunda kikasan ze isheshu dafa irin girkin da kike yi ki basu.. Dan nasan kannena din nan uhmm yan rigima ne..... Dukan su dariya suka sa... Khairi Tace Aa yaya Na yafe Na yau wlh be raina kaima kasan da muna bukata in zata kai nan da isha'i bata gama ba zamu jira ta, ta fadi zancen da shakiyan ci.... Dukan su dariya suka sa.. Sultana dambun nama ta dauko ta cika musu Leda dashi tace to gashi nasan bakin nan naku Yasa ba da ciye ciye.... Cike da murna suka karba suna godiya Sossai Isma'il yake son yawan jin Muryan khairi duk da kanwar Matar sa ce... Amma yana hango wani sirritance Abu a tattare da ita shiyasa take kara shiga ransa yake Mata so Na tsakani da Allah kamar kanwar sa uwa daya uba daya . Har bakin gate suka rakosu tareda musu bye bye.... Najwa kallon Khairi take da duk yanayin ta ya canza lokaci daya tunda akayi firan Jan ZAKI babu Abunda ya burge ta illa maganar marayu da akace yadau nauyin su fiyeda gidaje dari.... Daidai satin kan titi Najwa ta waigo tana kallon Khairi dake tsaye ta Lula duniyar tunani.. Keeee ta Furta da karfi sakamakon ganin wani mota kiris yayo kanta ..... Aguje taje ta Ture ta tafadi kan wasu dutsina yayi daidai da fakin wannan motocin da suka jeru.. Itakuwa Najwa cikin kuka tace azzalumai Zaku kashe min yar uwata ne kuma takama da Arziki takarashe zancen tana mai kokarin daga Khairi. Daya daga cikin jerin motar yafito ransa abace yace haba baiwar Allah kune da laifi Amma kune da Zagi .... Kanya gama rufe bakin sa.... Khairi dake jin jikin azababen Faduwar da tayi tamike cikin karfin Hali ta wanka masa mari ji kake tass... Azabure dukan su wayanda ke cikin motar suka fara fiffitowa Harda ogan nasu cikin.................... *Karku Manta Paid book ne.* *Please in free yakare Na roke Ku karku fitar min da littafi masu son cigaban daga free yakare su shiga Arewa book din karatun ..* *Taku har kullum kyauta daga Allah* 🦜🦜 *RAI DAYA* 🦜🦜 *JAN ZAKI*🐆 *DAGA MARUBUCIYAR :* *KAIKAJAWA KANKA* *KANWATA* *RAYUWAR MA'AURATA* Yanzu gani dauke da sabon littafina *RAI DAYA* inkiya *JAN ZAKI* *Paid book ne* Normal group 500 Special group 1k Acct nomba *3115484026 ikilima Adam first bank* Ko Katin MTN Kan wanna layin 09069080725 Banason VTU 0️⃣6️⃣ Idanun ta ya yi tozali da kafafun dake saukowa daga cikin Motar , kokarin Tashi sukeyi itada Najwa dan akan Juna suka Fad'i. Sukaji Muryan sa yana Fad'in Ku yayan matsiyata ,Banda dabbanci irin naku titin na uban Ku ne Zaku ringa tsayawa. Kuna shashanci? Najwa da Khairi cikin tsananin Tashin hankali suke kallon sa yake doso inda suke cikin zafin nama tareda rufe motar nasa. Cikin Isa da tafiyar takama yakaraso wajen. Wani kallon mai cike da mugun tsana yake bin su dashi ,tareda maida kallon sa akan Khairi Idanun su suka tsarke cikin Juna , hada rai ya yi tamau fuskar sa tamau babu Annuri bare su sa ran tausayi a tattare dashi . Tsawar daya dakawa Khairi ne ,yasa ta razana had'e da zazzare manyan idanun ta mai dauke da digon baki a aciki. "keeee! ballagaza tun daga nesa kan titi na hango ki bayan nawuce Ku shine nayi reverse na dawo, cire gilashin dake Fuskar sa ya yi . Dan su gane waye a gaban su. Khairi da Najwa suka hada baki wajen Fadi kaine ? Kwarai kuwa nine yabata amsa ,ai bazaki manta ni ba karuwa tunda hannun ki ya mari fuska ta. Aranar kinci sa'ar mai gidan mu da wallahi bazaki kara gigicin mari wani ba . Kan ubancen Khairi ta Furta tareda tashi tsaye tana jijjiga cikin ruwan bala'i tace watau sai yanzu na gane ka, kace kazo ka rama Marin danai maka ne raggon namiji dakai nusari yau ka tabbatar mun dakai sakarai ne. Inace ......Najwa ta rufe mata baki cikin tsananin tsoro dan yanda taga idanun sa sun kada tasan kiris yake jira ya yi kasa-kasa da Khairi. A hasale Khairi ta buge hannun Najwa daya rufe mata baki tana huci sama-sama kamar zakanya tace waike Najwa akan wannan banzan zaki rufe mun baki. Sake hada rai tayi tacigaba da Fad'in Abunda take niyar fada. Inace agaban ayarin ka na mareka ,ai kamata ya yi inzaka rama ka rama agaban su , dan su sheda Amma kazo kai kadai kenan ,kana tada kura bayan yaki . Dan Allah Malam matsa kabamu waje ,nazata wani isasshe ne ,ni wallahi kamun kadan a fada uban gidan naka Wanda ya zageni ,shi kawai nake nema wallahi dan beci abanza ba... Mutuwar tsaye Anas ya yi idanun sa sun kad'a jajir kokarin kaiwa Khairi ,naushi yake ,kafun hannun sa yakai kanta ,ji ya yi caraf ta kama hannun sa ,be Ankara ba sai jiyayi ta wanke sa da Wasu lafiyayyun Maruka Masu hasarin gaske . Nan take yaji cen kasan kunnen sa jin sa ya dauke . Arazane yake kallon ta dan ya tabbatar da gaske ita din ce , ganin yanda ta canza kamar ba mace ba tana kokarin Murda masa hannun sa data rike . Yaji Najwa Na Fad'in dan Girman Allah Khairi karki Aikata kefa kika ce kin daina ,inkikayi haka kin saba Alkawari narokeki dan Girman manzon Allah , Albarkacin maman mu dake kwance kasa. Sossai jikin ta yadau rawa , Idanun Khairi ne suka kawo ruwa nan da nan ta saki hannun nasa daya gama masa sanyi duk yanda yaso ya kwace ya kasa. Tana sakin sa Hannun nasa yake bi da kallo yanda yasha damka ,kallon ta yake tana kakkabe kasar daya bata musu jiki itada Yar Uwar ta . Jiyayi Khairi na fadin wallahi da kin barni da shi dayau yazama nakasasshe tareda kama hannun Najwa zasu bar wajen . Har sun kama hanya zasu wuce shi . Khairi tayi return ganin tahowan ta yasa shi yafara Neman hanyar guduwa zuwa motar sa. Dakata ta Furta a tsawace hakan yasa ya tsaya cak batareda ya waigo ba. Inason ka gayamin inane Zan samu uban gidan naka dan wlh saina Rama Abunda yamun ko ana ha maza ha mata, kuma wallahi baka ban amsa ba baka isa kabar wajen nan ba in kace karya ne bismillahi tai masa nuni da hannu. Batareda ya kalle ta ba yace ni kaina bansan daga inda yake fitowa ba ma'ana bansan gidan nasu ba Amma kamar naji yace a Makabarta ne . Zazzare idanu Khairi da Najwa sukayi suna buga Salati , Khairi sossai jikin ta yadau rawa cikin tattaro nutsuwar ta tace karka raina mana hankali kasan me ake kira da Makabarta ta kuwa ? Shiko ya kosa ya bar wajen dan Marin datayi masa yasa kansa na tsananin ciwo kamar zata tsage dan radad'i. Eh nasani shine Amsar daya bata yana k'ok'arin shiga motarsa ,tsintar Muryan ta ya yi tana Fad'in in ma ka boye mun ai zamu hadu ne . Ka gayamin da wani lokaci yake bin wannan titin. Cikin Muryan sa mai cike da takaici yace Sau daya yake bin wannan titin kuma duk karshen Wata ne . Bejira cewar ta ba yashige mota ,be tsaya Wata-Wata ba yatada motar tareda barin unguwar cikin zalama direct hospital Jan ZAKI ya nufa . Tuki yake hankalin sa atashe , dan tunda yake arayuwar sa be taba cin karo da Yarinyar mai tsaurin Ido kamar ta. Tafiya yake Amma yana tunanin hanyar ramuwa dan wannan RAI DAYA bazata gagare shi daukar fansa ba . Khairi da Najwa nan da nan suka bar wajen tareda zuwa sola suka dibo ruwa a jarka koda suka isa gidan su Najwa basu ,bata lokaci ba suka bar gidan. Mommy ta dan so tagane akwai damuwa tattare dasu kasantuwa , khairi bata ba ta damar tayi musu tambaya ba. Ce Mata sukayi,Sultana ce tace suzo su tayata Aiki. Sunsan Mommy bata iya hanawa , Adawo lafiya ta Furta tareda bin su da adua. Tafiya suke Khairi ta juyo tana kallon Najwa tace Kinga wanna dan iskan wai mu zegayawa wannan banzan daya zageni rannan a Makabarta gidan sa yake kinji Rainin wayau fa. Najwa tabe baki tayi ,tace aidaga ji karya ne Amma shawaran da Zan baki , Khairi ki ajiye makaman ki mutanan nan fa ,Masu Arziki ne koda kin hadu dashi na tabbatar babu abunda za ki iya masa bodyguard din sa kad'ai sun ishe ki . Zazzare idanu Khairi tayi tana nazarin Kalaman ta ,cikin takaici take maimaita sunada Arziki ,fuskantar Najwa tayi cikin dan bacin rai ,tace waike me kike d'auki masu Kud'i ne suna iya taka kowa ,suna iya cin mutunci kowa a zauna lafiya?, buga hannun tayi a kirjin ta ,da karfi har tanajin sautin karar buguwar cikin kankanin lokaci launin idanun ta suka canza zuwa ja ,tace wallahi Najwa wannan mutumin ko Dangote ne uban sa Alkur'an saina Rama ni za'a nunawa Arziki Zan nuna masa ko a talakawan akwai isassu Ganin ta fusata sossai Yasa Najwa dafata cikin Muryan rarrashi tace haba Khairi na ,da wasa nake miki har kin dau zafi Harara khairi ta watsa Mata cikin fushi tace wallahi kinban haushi gaba tayi Najwa nabiye da ita abaya cikin hanzari suke tafiya babu Wanda kewa dan uwan sa Magana. ********************** Wani babban maaikata an rubuta *KAMAL ENTERTAINMENT* da manyan bak'i a kasar rubutun sun rubuta welcome . Babban gate ne nahango wasu dattawa su uku sun tsaya , dai-dai kofar shiga suna tsayawa wajen kofar ta bud'e kanta . Suka shige daga ciki. Mai Gadi da su bodyguard cike da girmamawa suka fara barka da zuwa sir. Fuskokin su d'auke da Murmushi suka amsa da yawwa Banda mutum daya acikin su. Wanda shine ogan nasu. Haraban gidan suke bi da kallo babban waje ne cike yake shuke shuken furanni da tsuntsaye dake ta shawagi awajen . Cigaba da takun su sukayi tareda isa daga cikin Maaikatan. Wani office suka shige da Alamu daki ne ,na meeting . Alhaji KAMAL Wanda tun zuwan su yake cikin tsananin bacin rai ,samun wuri ya yi ya zauna hakan yasa dukan su kowannen su ya zauna . Cikin daga Murya yace waiku dan Allah wani yaro ne wannan *JAN ZAKI* na Dad'e da Fad'in kuyi iya kokarin Ku ganin munyi tozali dashi Amma ace kowannen Ku yakasa . Biyun dake zaune Kansu aduke suna sauraren yanda yake magana cikin Fushi da kunan rai. Alhaji Lurwanu Murya a tausashe yace ,wallahi tallahi ranka yadade sanin kanka ne ,mun kai shekara Ashirin zuwa sama muna maka duk Abunda ka samu . Wannan yaron wallahi munyi iya yin mu dan mugano daga ina yake fitowa Abunda ze baka haushi shine ,yana Neman ya karya duk wani kudurin mu akan takaran da muke nema excellent . Alhaji Garba dake , murmushi ,yace haba Alhaji KAMAL kwantar da hankalin ka ,abu nafarko da zamu fara shine mu nemi gidan jaridar da suke saka bayanan sa gidan Redio,sannan mu samu wayanda ake ba kwangilar gine ginen sa... Alhaji KAMAL kallon sa yake yana goge zufan da ya karyo masa ,hade dayin Murmushi yace Amma kai kanka yana ja wallahi ai shiyasa idan dabara ta kare min dole nake nemo Ku kaida Lurwanu ,kuma wallahi nayi naam da shawaran ka . Yanzu gayamana yanda za'ai mukai ga matakin nasara. Alhaji Garba dake kallon Shugaban nasu yace kasan dawa za'ai amfani cikin wasan nan kuwa .. Girgiza kai dukan su ,sukayi cikin kosawa dajin zancen nasa. Ni aganina Asa Sumayya tabi diddigin wannan yaron zazzare idanu dukan su sukayi Alh KAMAL ransa matukar a bace yacxe kako San me kake fad'e kuwa Sumayya Yata ce fa? Kwarai kuwa nasan Yar ka ce dole Saida mace a wannan zaman ,kuma macen ma irin yar ka. Tanada ilimi sossai ta fanni lauya tunda shi take karan ta , koka mance pratical da akai na lauyoyi itace tazo a na daya. Gabadaya dakin saida yadau shiru babu abunda kake ji sai bugawan zuciyoyin su da sanyin Ac Alhaji KAMAL cire gilashin dake Fuskar sa ya yi yana kallon su , cikin yarda da zancen yace Garba ka kawo shawara mai kyau Wanda dukan mu kwakwalwar mu , ta toshe indai Sumayya ce magana takare zamu zauna da ita ,nan dai suka shiga tsare-tsaren yanda Sumayya zata fara aikin da zasu sanya ta.. ************************ Khairi da Najwa zaune gaban akwatin redio suna sauraren bayanan Jan ZAKI akan kula da tarbiyyan yara Matasa musamman yan mata . Jin haka Yasa Sultana murmusawa tace laa yau Jan ZAKI fadakarwar sa akan irin Ku ne Khairi. Najwa da Khairi kallon Juna sukayi , suna jinjina yanda yake magana cikin Muryan sa mai dankaren dad'i mai jan hankalin mai sauraron sa. Najwa tace khairi ya naga duk kin wani nutsu kamar ba ke ba.. Jiki Asanyaye tace wallahi Khairi maganganun sa ,sun matukar tasiri wajen shiga jiki na ,aduk Sanda zanji Muryan Jan ZAKI nan ji nake kamar wani bangare na jiki na ne juyowa tayi tana fuskantar Najwa had'e da ajiye redio akasa takara da cewa wallahi Najwa ina kaunar mai Fad'in gaskiya cike da kamala ,dama ace Jan ZAKI dan gidan mu ne dayaga biyayya dan ban gajiyawa wajen sauraren sa, ba kamar Yaya saifudeen ba shi kullum fad'a takarashe zancen cikin kasalalliyar murya. Najwa tace lallai Khairi kin yaba da hankalin Jan ZAKI ban taba jin kinyi yabo ba sai yau ,kinsan ko a Masu kud'in akwai masu tsoron Allah da bin umarnin sa ,saidai lamarin Jan ZAKI yana matukar bani tsoro yan jaridar ya sukeyi wajen samo rahotannin sa bayan baya zuwa saidai su samu faifan audio na Muryan sa. Khairi tace shiya baiwa kansa sani , nasan yanada dalilin sa, Kinga tashi muje gida kada Yaya saifudeen yazo Bai same mu ba kin San halin sa. Dakyar sukaci abincin gidan Sultana dan sossai Khairi ke tsoron yayan nasu shi Sam baya mata da sauki . Sultana ganin basu da nutsuwa yasa ta rike hannun Khairi cikin sanyin Murya tace inkinje Ku gayawa Yaya saifudeen yakamata muje gidan iyayen Mahaifiyar mu . Hada rai Khairi tayi sossai ,tace haba taya zamuje gidan da baa kaunar Baffa Alkur'an bazan je ba ,kuma din wallahi bakuda zuciya ne bakwa kishin baffa cikin bacin rai take fada ko sallama batayi wa Sultana ba tawuce fuuuu kamar iska . Najwa Ganin fitan Khairi yasata fadin ,anti Sultana Saida Safe aguje tabi bayan Khairi. Itako Sultana sossai tazama kamar Gunki a tsaye tana nazarin yanayin khairi Anya batada Aljanu kuwa . Takai minti Ashirin tsaye tanata sake-sake daga karshe barin wani tunani tayi tareda shiga band'aki dan dauro Alwala. ************************* Dai-dai shiga gidan khairi tajiyo Muryan Innaro tana ba Yaya saifudeen labarin tun safe suka bar gida ,batareda sun Fad'i inda zasu je ba.. Sossai jikin Khairi yad'au rawa ,tana k'ok'arin juyawa dan tayi gidan Mommyn Najwa taji an..................... Taku har kullum kyauta daga Allah Karku Manta paid book ne Ki biya ki karanta cikin salama 🦜🦜 *RAI DAYA* 🦜🦜 *JAN ZAKI*🐆 *DAGA MARUBUCIYAR :* *KAIKAJAWA KANKA* *KANWATA* *RAYUWAR MA'AURATA* Yanzu gani dauke da sabon littafina *RAI DAYA* inkiya *JAN ZAKI* *Paid book ne* Normal group 500 Special group 1k Acct nomba *3115484026 ikilima Adam first bank* Ko Katin MTN Kan wanna layin 09069080725 Banason VTU 0️⃣7️⃣ Taji an fiskota a zafafe cikin tsananin bacin rai yace ,tundazu nasan kina labe nan wajen ,watau ita Najwa guduwa tayi ko har gida zanje in same ta. Ke zakakura shine zaki gudu kije cen ko . Cikin tsananin Tashin hankali khairi ke kallon sa nan da nan idanun ta suka kawo ruwa ,tace wallahi Yaya ba tun safe na bar gidan nan inbaka yarda ba, ka kira Baffa tunda sanda mukayi masa rakiya Innaro bata gidan nan taje barka haihuwar dangin tsiyan ta takarashe zancen tareda banka mata muguwar harara. Innaro dake sauraren su ta buge da salati tana yarfe hannu, cikin kuka tace kaji Abunda ta fada ko wai dangin tsiya? Saif tsawa ya dakawa Khairi yace Amma yau Na tabbatar bakida kunya koba komi ai Innaro Uwar ki ce ,kuma matar baban ki kuma a haife ta haife ki. Turo baki Khairi tayi gaba tace ni wallahi bata haife ni ba ,matar da bata Sona tana min sharri. Kuma wallahi ka bugeni akan ta sai Allah ya..... Rufe mata baki yayi tareda cika ta ,dan bayason ta karasa fadin Abunda tayi Niyar fadi. Dawo da kallon yayi akan Innaro dake kuka yace Innaro kiyi hakuri Khairi yarinya ce karama sossai yayi ta rarrashin Innaro har ta sauko Amma aranra tana kudurin inda tana auran Baffa saitayi sanadin da Khairi zata bar gidan. Itako Khairi Fada yashiga mata tareda bata Umarnin taba Innaro hakuri , Sam taki bata hakuri tace badai Innaro ba tunda bata kaunar ta itako bazata bata hakuri ba koda kuwa ze kashe ta ne. Ganin da gaske take ne yasa shi fadin shige daga ciki kiyi wanka ,kizo inbaki tsaraban Dana kawo miki harda Fara , wani uban tsalle khairi ta yi tace Allah Yaya dagaske kazo min da farar nan mai mugun dadi Na garin nan ,gyada mata kai yayi Alamun eh. Innaro ganin bata ita suke ba taja tsaki tawuce tana magana kasa _kasa tace ai wayannan mutanen akwai mugun son kai jifa yanda ya zaburo kamar Wanda ze Mata hukunci gaskiya Amma gashi ya buge da rarrashi . ************************** Anas yana isa Asibitin Jan ZAKI likitoci sukayi caa akan sa , sossai yake ihu yana Fadin dan Allah Ku dubamin Fuska radadi nakeji ,wayyo kaina ze fashe Ku agaje ni yakarashe zancen yana sakin Kukan radadin Azaban Ciwon da yake ji. Likitoci ganin halin dayake ciki yasa basu tsaya Wata Wata ba sukai masa Alluran barci , ganin yayi barci ne suka shiga duba fuskar sa , sossai shatin hannu suke gani cike da mamaki suke kallon junan su . Cikin Abunda befi minti goma ba sukai masa Alluran daze taimaka masa akan kashe radadi da Ciwon kan dayace yana damun sa. *********** Sultana shiru take tunda su Khairi suka barta ,tana Fadin oh Allah jamaa wai wanna yarinyar kodai magani zanje nema nata ne kullum yarinya sai sangarcewa take tana girma Amma kuma takasa hankali ,mijin ta yashigo yanata kwada sallama bama tasan yanayi ba. Yana shigowa dakin kallon ta yake yanda ta zabga uban tagumi , hannun ta yakama firgit ta dawo hayyacin ta , Murmushin yake tayi tace sannu da zuwa maigida na . Yawwa ya Furta tareda samun waje ya zauna kusa da ita hannun ta , yakama ya hade da nashi hakan yasa ta dago kai tana kallon yanda hannayen su, suke tsarke cikin Juna yace haba Sultana tunanin me kikeyi ne ,karfa ki manta na ce miki in kinada damuwa ki sanar min nine abokin shawaran ki. Ajiyar zuciya ta sauke tace yi hakuri maigida ,bawata matsala bace daya wuce kanwar Khairi, nashiga damuwa nan tashiga bashi labarin Abunda yafaru ,jinjina Al'amarin yayi yace inbanda abun ki Sultana ita Khairi kishin Baffa take karkiga laifin ta yarinyar ce bansan ya akai ba takeda zafin rai saidai mu rakata da adua Amma sainake ganin harda kuruciya zata bari ne, da kalamai Masu dadi yaringa kwantar wa Sultana hankali ,harta saki jikin ta ,tace gobe InshAllah zanje gida inga Yaya saifudeen , mijin nata yace Allah yakaimu ahaka dai suka zauna itada Mijin nata suna Firan su cike da ban shaawa. ********************* Tafiya yake shi kadai cikin jeji yanayi yana waige waige , laptop a hannun sa ,dakuma Wata tsuntsuwar Aku akan kafadar sa . Akun ne yayi masa rada a kunne yace Yallabai ka canza wannan hanyar ,muyi gabas . Aikuwa babu musu ya canza hanya cikin hanzarin sa saidai yayi tafiya mai dan tsawo kafun ya iso daidai wani rami mai uban zurfi ganin ya tsaya awajen ne ,na tsaya kallon me yake shirin yi . Akun dake kafadar sa sai kalle kalle yake gabas da arewa ,kudu ,Yamma , sannan yace Yallabai bismillah . Jin Furucin sa yasashi dago wani murfin karfe tareda taka wani matakala dake cikin ramin yashiga cikin wannan ramin yana shiga yasa hannayen sa yarufe. Ni kaina Ikilima Adam zazzare Idanu nayi dan abun yayi matukar bani mamaki matuka . Daga cikin rami Wata duniya ce na hango babban gida ne sossai cike da ma'aikata da security ,ganin isowar sa ne yasa duk sukayi caa akan sa suna fadin welcome sir ,daga musu hannu yayi yana tafiya cikin Sauri saurin sa, akun na kafadar sa. Kokan yakai hannun sa wajen bude kofar , da kanta tabude kanta ,babu bata lokaci Yasa kai tareda isa babban Falon nasu , Mama ta taso tace haba Aliyu yau akayi kayi dare ne kuma kafita kai kadai wallahi hankalina ya tashi gashi kai baka fita da waya. . kallon ta yake cikin marairace Fuska tareda samun wuri ya zauna kusa da ita , wash ya Furta cikin kasalalliyar Muryan sa mai nuna zallan gajiya yace Am sorry ,Mamy na wallahi yau ayyukan ne ,sun min yawa kuma kinsan gobe Zan fita da safe gun karamin Aiki na. Isowar Nusaiba ne yasasu dago kai suna kallon ta ,fuskar ta dauke da Murmushi tace Yaya na barka da zuwa . Dakyar ya Amsa mata da yawwa tareda maida kallon sa akan Mamy yace ni zanshiga daga ciki , please kada akawo mun abinci na koshi yayi maganar kamar Wanda ke shirin kuka. Akun nasa ya kalla dake makale a kafadar sa yace dan Lele ka sauko mana , gobe mun hadu da safe InshAllah be gama rufe baki ba akun yayi fuffuke ya sauko kan center table tsakiyar daki. Akun ya kalli Mamy yace wash Ku kale ogana yagaji ,dani zakuyi firan . Aliyu Saida Safe yafurtawa Mamy batareda ya kalli , Nusaiba ba data kafe sa da idanu ba. Cikin hanzarin sa yabi corridor dake sadashi da dakin nasa. Yana isa dakin fadawa bandaki yayi kai tsaye tareda yin wanka da ruwan dumi yana wanka yana tunanin wannan labarin dayaji akan wannan yaron nasa da yaji ance Wata ce ta mare shi yana kwance Asibiti ana kara masa ruwa So yake yagano wacece wannan kuma meye alakar su ,kuma shi meyake kallo da har mace zata fi karfin sa ,taron dangi sukayi masa ne . .rasa mai bashi Amsa yashi hanzarta fitowa , tawul din sa mai taushi kamar auduga ya dauko yafara goge jikin nasa . Kayan barci ya saka tareda hawa kan gadon sa , yayi tareda bude system din sa dan ganin Abunda ke Faruwa a labaran duniya. Fadarwar da yayi akan matasan yara yaga ansa agidan jarida , murmushi yayi saida kuncin sa ya lotsa ,tareda lumshe idanun sa ,yana mai cigaba da latsa keyboard din system din sa , yana gama duba labarai be wani tsaya wata Wata kai tsaye yashiga email din sa nan ma yaci karo da sakonni ratata ,binsu yake daki daki yana karantawa Amma babu Wanda yayi wa reply dan yana matukar jin kasala ajikin nasa ,wani Sako ne. Yagani na karshe kasan email din sa , da dukan Alamu sabon email ne kokarin dubawa yake yaji idanun na na masa dishi dishi ahaka har barci barawo yayi awon gaba da shi batareda ya duba ba. Mamy da Nusaiba fira suke akan yakamata ace Aliyu yayi aure zaman ya isa hakanan , Nusaiba cikin yin kasa da murya tace Mamy ni gaskiya da dai da zaki hada aurena da Aliyu dakin taimaka min. Firgit Mamy ke kallon ta ,tace Amma Nusaiba yau Na tabbatar bakida hankali kina mace Amma kece kike Neman a aure ki . Kuma ba wannan ba ,inason Aliyu yayi aure Amma ki sani ba yanzu ba dan akwai wani babban Abunda nake son ganowa cikin yan kwanakin nan inhar Allah Yasa na gano abunnan ,zan duba ingani ko zaki iya auran sa ,inkuma yana da raayin auren ki , bismillah nikam saidai in biku da adua. Sossai Jikin Nusaiba yayi sanyi tareda dukar da kanta kasa , cikin ban hakuri tace Mamy kamar ranki ya bace kiyi hakuri bazan sake ba . Harta tashi zata fice ,Mamy ta dakatar da ita ta hanyar rike mata hannun ta tace dakata yata. Cak ta tsaya tana rintse idanun ta , sauraren me zata ce takeyi. Mamy tace wallahi ina kaunar ki Nusaiba , Amana kike a hannuna ,bazan taba cutar dake ba . Aliyu fa tamkar yar Uwar sa ta jini ciki daya ,ya dauke ki Amma kinsan komai yana iya canzawa ikon Allah yawuce wasa inhar Allah ya karkato hankalin sa , Nina wa fatan Alkhairi Zan muku. Please karkiyi fushi da kalamai na daughter. Sossai jikin Nusaiba yayi sanyi tace InshAllah Mamy nabi shawarar ki tareda yin murmushi ta rungumi Mamy . Ita ma Murmushin tayi mata tareda Fadin tashi ki kira mun yar Aikin nan Asabe ,tazo da daurawa Aliyu ko coffee ne , jin sa nake harda wani fadin kada akawo masa abinci bakiga ko tanka masa banyi ba takarashe zancen cikin kwaikwayon yanda yayi maganar. Sossai Nusaiba ta Dara tace ainasan ba kyale shi zakiyi ba ,sa mishi idanu kikayi mutum sai shegen son rashin cin Abinci . **************** Kashe Gari . Yaya saifudeen, rike da hannun Khairi da Najwa ze kaisu makaranta . Cikin hanzarin yake jansu , khairi tace haba Yaya kajamu a hankali mana saikace barayi . Tsaki yayi yace nasan halin ku sai Kun tsaya tsokana kafun , kuje Makaranta dan haka bazan amince ba indai ina gari.. Har Makarantar yakai su ,Saida ya tabbatar sun shiga Aji sannan yadawo kofar Makarantar yana karanta sunan Makarantar Jan ZAKI. Sallamar da akai abayan sa ne yasashi waigowa . Hannu Muhammad J A yabashi sukayi musabaha. Saifudeen yace inakwana kwana ? Malam ya Amsa da lafiya Lau Alhamdulillah . Saif kallon sa yake cikin farar jallabiya sanye da farin hular saka akan sa , yace sai anjima dama kannena nakawo Makaranta . Amma kamar kaima malami ne a makarantar nan yafada tareda zuba masa idanu. J A yace ya sunan kannnen naka ? Saif yace Ummulkhairi Sulaiman da Najwa Adam. Tunani yake kamar yasan Masu irin wanna sunan. Yace kamar ajina suke ,Amma ban Dade da fara koyar dasu ba . Saifudeen yace MashAllah ya sunan ka Mallam? Jim yayi kamar me nazari tareda dago kansa ya kalli rubutun sunan Jan ZAKI dake rubuce a ajikin Makarantar ajiyar zuciya ya sauke. Yace Sunana Muhammad A J. MashAllah cewar saifudeen tareda yi masa sallama yabar wajen. Ganin Saif harya wuce yasa Shima kai tsaye yayi cikin Makarantar be zarce ko ina ba sai Ajin headmaster. Ganin office din arufe yayi matukar bashi mamaki gashi har time ya gota. Sauran Ajin yakebi bayan daya yana dubawa yaga ,malamai wajen uku duk basa nan. Kai tsaye Ajin su Khairi yashiga inda nan ne wajen zaman sa. Nan ma malamin turancin nasu be iso ba.. Ganin time yatafi yasashi Kallon daliban cikin nutsuwa yafara magana . Yace daman malaman Makarantar nan basa zuwa kan lokaci ne ? Sakina ce ta amsa masa cikin yauki tace eh Akramakallahu basa zuwa dawuri ,wani lokacin ma sai suyi kwana ki basu Zo ba. OK yafurta tareda mata Izinin ta zauna . Sakina sai kallon khairi take tana hararan ta. Caraf suka hada Idanu da Khairi takara banka mata wani hararan. Rike da baki Khairi take fadin oh ni wannan matar Me na tsare mata ne. Najwa ta kalla tace kee! Kin Lura da kallon da waccen banzar ke mana kuwa. Najwa tace eh ina kule da ita barta duk tsiyar ta akwai Na gaba da ita ,kamata yayi mu gyara mata zama tasan , bakin rijiya ba wajen wasan makaho bane. Suka karashe zancen akan yanda zasu fara saita Sakina. Akramakallahu daura su yayi akan karatun turanci inda mamaki yacika daliban ,dan yanda yake fiddo kalmomi turanci a bakin sa ,zakayi tunani a kasar su America ne . Yana cikin basu lecture ,malamin su na turanci ya iso ,hakan yasa malamin cike da mamaki yake kallon Akramakallahu dake basu darasin da ba nashi ba. Musabaha sukayi , murmushi Akramakallahu yayi yace wai naga baka iso dawuri ba , shiyasa nake koya musu turanci kafun kazo ,time din karatuna beyi ba. Malamin yace babu matsala yana tsotsa keya ,na dan je wani wurin ne shiyasa. Sakina Ganin Akramakallahu yafita ,ranta yayi mugun baci tashi tayi dan bin bayan sa. Cikin hanzari take tafiya tana kokarin barin Ajin ,malamin turancin nasu cikin tsawa yace kee Sakina ina zakije ne. Turo baki tayi gaba tace inazuwa uzuri gareni bata jira cewar shi ba ta fice ,ganin saurin nata yayi yawa yayi tunanin ko bahaya zatayi shiyasa bekara fadin komai ba. Koda ta baro Ajin leke leke ta fara inda zata hango shi. Hango shi tayi daga cen nesa Alamun ,yana waya ne ,ya bata baya. Ahankali take taku tana doso inda yake. Shikuwa wayar sa ce tafara kunna danja Alamun akwai Abu abayan sa. Azabure ya waigo cike da tsananin Mamaki yayi tozali da Sakina da take shirin......... Taku har kullum kyauta daga Allah ce 🦜🦜 *RAI DAYA* 🦜🦜 *JAN ZAKI*🐆 *DAGA MARUBUCIYAR :* *KAIKAJAWA KANKA* *KANWATA* *RAYUWAR MA'AURATA* Yanzu gani dauke da sabon littafina *RAI DAYA* inkiya *JAN ZAKI* *Paid book ne* Normal group 500 Special group 1k Acct nomba *3115484026 ikilima Adam first bank* Ko Katin MTN Kan wanna layin 09069080725 Banason VTU 0️⃣5️⃣ Yace yanzu ba lokacin wannan tambayar bane.. Murmushi Malamin turancin nasu yayi yana kallon J A dashi din ma shiyake kallo . Yace kwarai kuwa Akramakallahu ' murmushi yayi yana kallon Khairi da damuwa ya bayyana a fuskar ta .. Yace karki damu daliba ta gobe InshAllah Zan amsa miki inban manta ba.. Ficewa yayi daga Ajin hakan Yasa Khairi komawa ta zauna cike da takaici J A. . J A nashigowa gabadaya class din suka Mike dan gaishe sa Banda khairi da ta cikam fam saura kiris ta fashe... Da Mamaki yake kallon cikin sanyin Muryan sa da Sam babu hayaniya yace Baiwar Allah lafiya kike zaune bayan kowa ya tashi... Gabadaya daliban Maida kallon su sukayi akan ta... Najwa tabata tayi da kafafun su dake hade akasa tana Mata nuni ta tashi itakuwa Fir taki tashi.... A J bawa dalibai damar zama yayi yana mai satar kallon ta cike da mamakin tsaurin idanun ta...... Bismillahi rahmani rahim ya rubuta jikin Allo da harshen larabci... Kowa Class din nutsuwa sukayi ana kallon yanda hannayen ke rubutu cike da kwarewa da nutsuwa yana kai Ayar rubutun nasa yadawo da kallon sa akan Dalibai tareda ajiye alif din kan kujerar mazaunin malami..... Yafara da Fadin kamar yanda kuka gani a rubuce inason Zan fara da koya muku baki ta yanda zakufi saurin fahimtar karatun da ake .. Sanna duk ranar jumaa waazi Zan ringa muku . Zandai tsara jadawalin karattuka Na gare Ku... Gaban Allo yakoma yace ko akwai Wanda ze karanta min Abunda narubuta musamman Ku yan Aji shidda ne nasan Kun sani ko Kun taba karanta a wanna makarantar.... Gabadaya class din rau rau da idanu suke kallon sa.. Dan su ba'a taba koya musu baki ba .. Saidai a koya musu surori.. Khairi ce ta Mike cikin nutsuwa dan sossai rubutun sa yaja hankalin ta musamman ita maabociya son karatun islamiyya ce... Akramakallahu Zan iya karantawa.. Bismillahi yafada cikin son gano ainihin gaskiyar ta... Alif ba'un ta'un. Ta karanto masa har karshen su.... A J sossai yayi mamakin ganin yarinyar da rawan kai yayi Mata yawa har ta iya rike Baki akan ta... MashAllah yafurta tareda ba kowa daman ya taba Mata... Kowa Saida yayi tabi Banda Sakina da wani zuciya ta dibe ta.. Tashi tayi tace Akramakallahu ai bansan fassaran karatun bane Amma tabbas muna ji ana karanta mana . A Makarantar islamiyya... A J kallon ta yake yace yakamata ace kin San shi arubuce sannan ki haddace shi... Sannan asannan Makarantar nan yakamata ace kin San shi inhar karatun akeyi . Sossai taji kunyar Amsar daya bata Wanda shi yafada ne iya gaskiyar sa. Samun wuri tayi tazauna tana hararan Khairi wacce batasan ma tanayi ba.. Kusan Awa biyu yadauka yana koya musu baki. All class din sossai suke gane karatun nasa dan yanayi ne yanda kowa ze fahimta... Koda ya tashe su tsaida Khairi da Najwa yayi ... Su biyun... Khairi da haryanzu take cike da takaicin amsar da ya hana malamin turanci ya basu ta tsaya cike da kosawa..... Kallon Najwa yayi yace Na fahimci Ku baki ne kamar ni... Kuma da dukan Alamu Baku taba yin bokon ba.. In bazaku damu ba zanringa dan koyar daku karatun bokon har Ku iya yana mai tsare Khairi dayaga ta soma dan murmushi.. Khairi cike da Murna ta dafa Najwa tace dan Allah da gaske Akramakallahu zaka ringa koya mana.... Papper dake cikin jakarta ta dauko tace yawwa Najwa karanta mishi Abunda ke ciki dan na mance yanda ake fadi... Najwa Na karban Papper ta karanto masa .. Zazzare idanu yayi cikin firgita yana mai Kallon su Yace ke Khairi kirasa Abunda zaki fara koyon karatun boko dashi sai wayannan kalmomin... Khairi cike da Neman Agaji tace karka damu Akramakallahu nidai ka gayamin matar baba Na ta Fada mun jiya Amma dayake tanada yar Hali shiyasa banyarda da zancen nata dari bisa dari ba A J tana kai karshen zancen nata yace . Stupid girl zagine Shima mental problems haka yake Amma shi yana nufin kamar mai tabuwar hankali .. Rau rau da idanu take kallon sa kamar zatayi kuka sai ta dan ciza labban ta . Tana mai jin radadi da kuna cikin zuciyar ta.. Kallo daya yamata ya fahimci yanda Kalmar ta tsaga bango da duk wani huda Na jikin ta... Be Ankara ba sai yaga hawaye na kwaranya daga idanun ta Shar Shar kamar anbude famfo Agigice Najwa ta dafata tana mai Fadin subuhannallah haba Khairi meye zaki dau zafi dan wani Wanda besan darajan kan sa ba ya zageki.. Inace mun ce zamu dau fansa ko kin manta shawaran da Innaro ta bamu . Shawara ce mai kyau in mukayi amfani da ita.... A J dake kallon su Murmushi yayi kamar zece wani Abu saiya fasa... Kallon Najwa yayi yace itada wa sukayi Fada ne? Sannan meye ya hada su Najwa cike da takaicin Abunda yafaru a ranar ta ringa bashi labari tun daga Farko har karshe.. Mamaki ne yakamashi Matuka yace da kunyi hakuri da dai yafi Alkhairi. Caraf Khairi ta karbi zancen tareda Fadin Allah ya kiyaye nayi hakuri wallahi in kere Na jawo zabo na yawo wataran zasu hadu ne. Ai wannan *RAI DAYA* saina Rama Abunda yafada agaban wayanda yayi zagin saidai Ni ba diyar Sulaiman da Amina bace takarashe zancen tareda kama hannun Najwa zasu bar Ajin... Najwa tace Akramakallahu InshAllah daga gobe zaka fara koya mana Amma dan Allah in dai agarin Na kake me ze hana muringa zuwa gidan naku koyon karatu... A J zazzare idanu yayi yace ai gidan namu da nisa kedai anan Zan ringa koya muku inya muku.. Khairi data kosa subar Makarantar dan suje suyi check din titin ko Allah zesa su hadu wanna bawan Allah.... Tace babu damuwa Akramakallahu zaka ringa koya mana a Makarantar. Barin sa sukayi cikin hanzari tsaye yake yana kallon fitar su . Tsinkayo Muryan Sakina yayi tana magana cike da iyayi sai Fari take da idanu tana bankaro kirji dan ya tabbatar ta cika iya mace .. Akramakallahu dan Allah in bazaka damu ba zanso karinga koyar dani ina biyan ka agidan mu.. Kallon ta yake yana nazartan Kalaman ta cikin kosawa yaje ai iya nan karatuna ya tsaya saidai kibiya in koya miki anan yakarashe zancen tareda barin ta anan tsaye rike da bakin ta tace ikon Allah. Jibe shi talaka dashi Amma sa Girman kai rawanin ni badan kyawun ka wlh baka isa in tsaya kusa da mai kodadden Riga ba takarashe zancen tareda shiga Ajin dan dauko jakar ta......... *********************** Mama zaune gefen sa tana kallon yanda yake lumshe idanun sa lokaci zuwa lokaci..... Cikin halin Damuwa tace Haba Aliyu taya zaka sawa kanka damuwa tun jiya kaki Fadamun Abunda ke Faruwa... Sallamar Nusaiba ne Yasa ta maida kallon nata akan ta .. Fuskar ta dauke da Murmushi tace zonan daughter gayamin Abunda yafaru jiya kila kinsan wani Abun.. Shiru ne ya ratsa dakin dan sossai Nusaiba ke tsoron bawa Mama labari . Abu karami ne yanzu ya hau ta da fada... Mama tace shikenan dukan Ku Kun maidani Mara Amfani ko tun jiya.. Jin Muryan Mama ya canza Alamun bacin rai Yasa Nusaiba ta fara zayyano Mata Abunda yafaru daki daki... . Salati Mama ta dauka tana yarfe hannun rike da bakin ta tace ikon Allah.. Kaiko Aliyu meye ya hadaka fada da mace.. Kalaman ta ne yasashi dan mikewa ya jingina da bangon dakin .. Ahankali yake daga lallabansa cikin sakalci yace haba Mama wuce nan wallahi kawaide Na hadu da yaran kauyen nan ne wayanda basuda kan gado har hakuri fa Na bata . Amma kamar nace cigaba . Ko ba haka akayi ba yana mai Kallon Nusaiba. Kada kai tayi tace kwarai kuwa Mama yarinyar ce kamar Wata tabbabiya... Mama dake sauraren su Murmushi tayi maimakon suga nata ran ya bace.. Haba Aliyu be kamata kubiye Mata ba.. Maybe yarinyar ce tanaji da hayakin kuruciya ne... Kaga Kalmar daka furta Mata ze zauna mata arai... Tabe baki yayi yace yana jinjina zancen. Kallon Nusaiba tayi cike da bada Umarni tace dan bamu waje Zan gana dashi. Sanda Sanda Nusaiba ta fice tana girgiza kai dan atunanin ta fada zesha wajen Mama.... Nusaiba Na fita ta maida kallon ta akan sa.. Haba Aliyu kamance kaine Aliyu mai kokarin kare hakkin mutane.. Kaine Aliyu dake tausayin na kasa dashi.. Atarihin RAYUWAR ka wannan yarinyar itace farkon wacce kuka taba samun sabani please dan Allah irin haka kuringa kiyayewa Yaran naka kaja musu kunne dan sakacin su yakawo hakan.. Aliyu Haidar dake kallon Mahaifiyar sa cikin sanyin Murya yace InshAllah Mama Zan kiyaye. Amma ni fa ba laifina bane yarinyar ce batada kunya ko na second daya. kinga Agajiye Na dawo Zan dan kwanta kafun Anjima ko To Dana Abun Alfaharina takarashe zancen tana kokarin barin dakin nasa daidai kofar fita juyowa tayi tana kallon sa tana girgiza kai shiko kallon yake yana lumshe idanun sa.. ********************* Khairi da Najwa kusan Awan su uku akan titi suna ta kallon titin ko zasu hango irin wayannan motocin na wanna ranar shiru kake ji... Najwa Ganin Yamma tayi tace khairi mu hakura mana mu bari duk Ranar Monday mun ringa gadin hanyar ko nasan haka nasara ne tafada cike da gajiyawa dan batason Khairi ta fahimci ta gaji da gadin titi su ba sallah ba bare cin Abinci.. Kokarin tsallake Titi suke sukajiyo Muryan Mijin Sultana yana Fadin yan halak daga ina kuke ne.. Khairi Murmushin dole sukayi ita da Najwa suka hada baki wajen Fadin . Kaga mun je gidan Wata Kawar mu ce yar ajin mu. Ko gidan Anty Sultana bamu leka.. Dan Allah karka ce Mata ka ganmu kofar Gidan ta dan ranta ze baci ace muna kofar gidan nata bamu leko ba. Karku damu cewar Mijin Sultana yana mai kare musu kallo harsuka fice cikin hanzarin su... Girgiza kai yayi yashige gida Abinsa. Baffa da Malam Adamu duk hankulan su yatashi akan rashin dawowar su dawuri . Har sun kama hanya zasu Neman su. Sukaci karo dasu cike da Razani suke kallon iyayen nasu.. Khairi Tace Baffa ina zakuje ne ? Baffa cikin damuwa yace haba Khairi ai kunsan Neman Ku zamuje . Ina kuka tsaya ne har wannan time din baku dawo ba cewar Malam Adamu cikin Fada dan yasan Baffa baya iya tsawata musu.. Najwa cikin tsoro tace Wata Kawar Ajin mu ce muka je dubata batada lafiya.. Kallon kwayar idanun ta yake tareda nazartan Kalaman ta. Yace Najwa yaushe kika fara Karya ne? Khairi caraf ta karbi zancen da fadin Malam aikuwa gidan Kawar mu ,mukaje Amma daga yau zamu kiyaye . zamu sanar muku duk inda zamuje . Murmushi Baffa yayi shi harga Allah beson bacin ran Khairi Amma kuma baya son hakan yazama silar gurbacewar tarbiyyar ta. shiyasa in Khairi tayi laifi cikin hikima yake ganar da ita kuren ta dayake akwai hankali irin ta manya to sam bata kara maimaita laifin da aka hane ta... Kusan tare suka jiyo inda Khairi tayi gida itama Najwa tayi gidan nasu. Tasha fada wajen Mommy sossai . Khairi nashiga gida taci Karo da Innaro tana tuka tuwon gari da Alama talgi take... Sannu da aiki ta furta mata tareda wuce ta.. Innaro dago kai tayi tana kallon shigewar ta daki.. Tabe baki tayi tace inbanda abun Baffa wannan ma takai ayi mata Aure yarinya saidai in dafa taci kuma bata aikin komai sai taga dama wannan shi ake kira so . Ni kenan nazama baiwa kenan. Cigaba da tukin tuwon tayi tana girgiza kai... Khairi tana shiga dakin fiddo papper tayi cike da bakin cikin rashin samun sa da basuyi ba.. Tashi tayi tadauro Alwala tareda jero sallolin da ke kanta akan sallayar barci yayi awon gaba da ita . Papper yana gefen nata. Da sallama Baffa yashigo dakin nata yana kallon yanda ta buge kan dadduma gyara mata shimfida yayi . Ahankali ya dago ta yadaura ta kan katifar ta.. Itakuwa dan bude idanun ta tayi tana ganin Baffa ne turo baki tayi takoma barcin nata.. ********************** Kashe Gari... Yau babu Makaranta kasantuwa duk Makarantar Jan ZAKI ba'a zuwa Makaranta ranar laraba gwamnati tasan da wannan dokar nashi Amma haryanzu suna son suji dalilin sa . suna da tarin tamboyoyi akan sa.. Amma haryanzu be amsa musu kodaya ba. Baffa tsaf yashirya yau zetafi Birni kai Doya inya tafi saiyakai Sati be dawo ba. Sossai Khairi ke kuka cikin Muryan lallashi Baffa yace kiyi hakuri yar auta ta inazuwa cen yayan ki zezo gida Shima yayi sati aibaki da matsala bakwabe Fuska tayi tasan yayan nata beda sauki duk da yana mugun son ta fiye da kima Amma beson sakarci.. Sallamar Sultana ne yadawo da hankalin su akanta hannun ta rike da bakin leda bakin dauke da Murmushi take kallon Baffa cike da ladabi ta gaishe shi ya Amsa Mata cikin faraa tareda dafata . Khairi Tace Antina duk larabar duniya saikin zo dole saikin ma Baffa sallama ko yayan mu. Murmushi ta sakar Mata tareda maida kallon nata akan Baffa hannun sa tarike tana matso yar kwalla tace Baffa na. Ya Amsa da na'am Sultana yana kallon yanda yanayin ta ya canza lokaci daya.. Baffa banason kana gilan doya daga Funtua zuwa kasuwar Sheme kai inkaje saikayi sati baka dawo ba. Hannun sa tarike tareda saka masa kudade Wanda akalla zasu kai Dubu hamsin tasa cikin hannun sa . Yakai Mahaifina wanna kudin dan Allah karka dawo mun dashi kamar yanda ka saba . Banason kaje Birnin Baffa kayi zaman ka. Kaja jari anan garin ko dan shago kabude ina Sanaa agida Zan dauki nauyin wani Abu na cikin gidan nan, takarashe zancen cikin raunin Muryan wacce take gab da sakin kuka.. Ganin hawaye sun fara kwaranya daga idanun ta ne. Yasa Baffa gigicewa dan kwata kwata baya son Kukan yaran sa. Cikin tsarkewan murya Yace Sultana Zan Amshi kudin dan in Faranta miki rai Amma wanna yazamo shine na farko Dana karshe banaso ki kara kawo mun ko sisi ki barni in nema dakaina InshAllah Allah yana tare da me nema wanna kudin Zan dan siyewa Khairi kaya irin naku na mata ina tara mata koda auren nata yazo kada inji kunya kamar yanda nakusa jin kunya a auren ki ... Kuma maganar shago Sultana Abar shi ,babu sana'ar da banyi ba Amma a banza ne jarin karewa yakeyi yakarashe zancen yana mai matso kwalla a idanun sa tareda Dan bubbuga bayan Sultana data dawo kalan tausayi, wahalar da maihaifin ta yakeyi yayi yawa. Sossai jikin Khairi yayi mugun sanyin gabadaya Baffa yagama bata tausayi . Rungume shi tayi tana Fadin InshAllah Baffa ni Khairi Zan sanya ka kaji dadi kasamu Hutu wataran saidai kabada Umarni amaka batareda ka motsa ba. Murmushi yayi shida Sultana suna kallon zancen nata a shirme . Baffa da Sultana suka hada baki wajen Fadi Allah yacika miki burin ki yar Auta. Sossai ta Dara sai da dimple din ta ya lotsa zararan idanun ta, ta sauke akan Baffa murmushi tayi tareda daukar masa jakar sa tayi gaba . Har waje suka rako sa kasantuwa Innaro bata gidan taje barkan haihuwar kanwar ta..... Suna barin kofar Gidan sukaci karo da Malam Adamu da Najwa zata sola debo ruwa hannun ta dauke da karamar jarkar lita goma. Ganin su Baffa yasa sukayo wajen su ,Malam Adamu yace ah tafiya dai ta tashi yau tun dawuri zaka je kenan yana mai zuba masa idanu tareda basa hannu sukayi musabaha ,gaisawa sukayi cike da dattako irin nasu na manya. Baffa cikin yanayin sa da yayan sa suka gama kashe masa jiki yace . Kwarai kuwa sonake Innaje Dana yadawo gida dawuri tun gari beyi duhu ba. Ana fama da kidnapped a Nigeria ,local government nan barnar tafi yawa. Malam Adamu ya jinjina zancen nasa yace wanna zancen gaskiya ne kayi tunani me kyau. Dukan su rakiya sukayi masa har bakin Titi . Tsaye suke bakin titin suna jiran abun hawa daze kaishi tasha... Sultana sossai tayiwa baffa sallama hade da aduar Allah ya tsare cike da zallan kewa sukayi sallama , kallon Khairi da Najwa tayi tace Zaku Zo gida na sauraren wannan shirin na JAN ZAKI . Khairi tsalle ta daka awajen tace laa kice yau ma laraba ana sakawa aikuwa zamu Zo da Najwa da takai ruwa gida zaki ganmu. Murmushi Sultana tayi tana kallon Najwa dake son yin magana Ganin su Baffa yasa tayi shiru. Najwa tace to Antin mu sai kingan mu. Sultana tace to kannena tareda barin wajen dan zuwa daura girkin rana. tsallaka titi tayi kasantuwa gidan ta a titi yake tareda dagawa su Baffa hannu ,suma hannu suka daga mata suna murmushi. Baffa cikin sa'a ya samu motar daze kaishi babban tasha ,yahau motar tareda rike hannun Khairi yana Mata adua da mata nasiha akan tazauna waje daya yanzu duniyar nan annoba tayi yawa . Tace InshAllah zata kiyaye . Sossai sukayi sallama tana kuka motar ta tashi . Shiko Malam Adamu sai Allah yatsare yake ta Furtawa yana daga masa hannu kallon Najwa da Khairi yayi yace kunga ni Gaba nayi dan haka kuyi maza ku wuce gida . Yafice yabar su nan tsaye. Kokarin juyawa suke Khairi ta hango wannan Motar datake mafarkin haduwa dasu dan daukar fansa, ta tahowa aguje kamar zata tashi sama. Cikin hanzarin su suka matsa daga gefen titin tareda fadawa kan Juna suna fadin subuhannallah cikin tsananin Tashin hankali. Ji suke kiiiiii motar taja wani wawan birki. daidai wajen su.. Cikin Razani Khairi ke kallon motar yayin da taga ana kokarin bude motar idanun ta yayi tozali da ................... Oh Masu Karatu kodawa Khairi tayi tozali ne . Kudai Ku biyomu acikin daddan labarin nan *RAI DAYA* karku Manta paid book ne. *Ku biya Ku karanta cikin salama dan ankusa gama Free page* *09069080725* ko @⁨+229 53 72 61 62⁩ *🦜 RAI DAYA*🦜 *JAN ZAKI 🐆* 🔔📚 *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚* _{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}_ https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo *⚜️©J.A.W📚🖌️* *DAGA MARUBUCIYAR :* *KAIKAJAWA KANKA* *KANWATA* *RAYUWAR MA'AURATA* Yanzu gani dauke da sabon littafina *RAI DAYA* inkiya *JAN ZAKI* *Paid book ne* Normal group 500 Special group 1k Acct nomba *3115484026 ikilima Adam first bank* Ko Katin MTN Kan wanna layin 09069080725 Banason VTU 1️⃣0️⃣ Taji Muryan khairi da Najwa suna fadin Assalam Alaikum. Amsa musu tayi da fara'arta Wanda daga khairi Har Najwa Saida sukayi shock mamaki ne ya kamasu ba kadan ba . Khairi dake da baki tace Innaro inawuni ya gida , Najwa ma gaishe tayi kowannen su , cikin tsananin Mamaki . Haba Khairi sai yanzu kuka dawo , Ku daina dare please Yaya na. Kama hannun Khairi tayi cike da nuna damuwa tace yata yau ina kuka tsaya ne. Najwa ce tabata Amsa da wajen Yadiko mukaje kinsan gidan wannan tsohuwar ba'a zuwa a fito da wuri . Murmushi Innaro tayi tace hakane dafatan Yadiko tana lafiya nima zuwa gobe nakeson zuwa gidan nasu. Khairi kallon Najwa tayi tace muje in rakaki kada mummy tayi miki fada ko tana mai kokarin Jan hannun Najwa. Innaro tace please khairi inkinje kada ki Dade wallahi duk duniya yanzu babu wacce nakeji da kauna irin ki . Kallon juna khairi da Najwa sukayi hakan yasa ta amsa da saina dawo suka fice daga gidan. Itakuwa Innaro cikin tsananin Mamaki tace wannan yarinyar ya zanyi da ita karfa taje ta cika cikin ta agidan Rashida dan nasan bazata kyalesu ba. Khairi suna isa gidan suka Iske Malam Adamu zaune sai fada yake yana Fadin ze dauki mataki akan su ace tun fitar su zuwa Makaranta babu Wanda ya dawo gida Har dare. Mummy tace nasan dai baze wuce gidan Sultana sukaje ba ko gidan Yadiko basuda gidan dayawuce nan . Sallamar su ya katse firan da suke . Mummy ranta abace tace isassu sai yanzu kuka dawo ne tabbatu tana doso inda suke. Malam Adamu yataso cikin tsananin bacin rai yace dan iyayen Ku ban hanaku yawo ,Ku bakwa iya Fadin zakuje wani wurin saidai kuyi gaban kan Ku , sossai yaringa musu fada kamar ze zane su. Wai ma ina Saifudeen yake ne dan Har yasamuku idanu yau beje Makarantar naku bane. Dukan su dukar da kai kasa sukayi cikin Muryan su dake nuna nama sukace Malam kayi hakuri bazamu sake ba InshAllah. Mummy tace to ina Kuka tafi kuka zauna Najwa ce tabata Amsa da gidan Yadiko suka je. Samun wuri sukayi suka zazzauna ,ganin duk jikin su a sanyaye yake yasa Mummy fadin maza kuyi sallah kuzo kuci abinci . Babu bata lokaci suka tashi don dauro Alwala. Wayar Malam Adamu ne yasoma ring yana dubawa yaga Baffa ne ,cikin hanzari ya daga wayar sallama dauke a bakin sa hade da gaisuwa. Dagacen bangaren Baffa ya Amsa masa da lafiya Lau Alhamdulillah. Daman zuwa nan da jibi Zan dawo InshAllah. Kuma wallahi nasamu cigaba sossai dan Har shago nasamu acikin kasuwar kaga mun samu wajen fakewa. Malam Adamu MashAllah yafurta yana washe baki yace kace harka tabude Allah yakaro Arziki da daukaka. Kace Saifudeen ze zama dan gari yahuta da tallah. Kwarai kuwa yahuta cewar Baffa , yawwa ina yayan ka suke ne ? Murmushi yayi yana kallon su , yace Sallah suke yau gidan Yadiko suka wuni . Baffa yace lallai Yadiko tasha Aiki ,in sun idar please ka hadani da Khairi in danjin Muryan ta, yakarashe zancen cikin kankantar da Muryan nasa. Malam Adamu dariya yayi yasan dalilin kiran sa kenan . Daga haka sukayi sallama. Mummy kallon Malam Adamu tayi tace Baffa yasa Khairi aransa kuma dashi bata jin magana Allah dai yashirya su. Da Ameen suka amsa . Su Khairi na idar da sallah abinci ,suka soma ci . Suna cikin ci ne suka jiyo Muryan Innaro tana kwada sallama. Mummy da Malam ne suka amsa mata Sallamar ta cike da mamaki suke kallon ta ,dan suna iya rantsewa tunda Baffa ya auro ta , yau shine karo na farko data shigo gidan. Mummy tace lale lale yau wa nake gani kamar Innaro , cikin sakin Fuska tace nice dakaina tareda gaishe su cike da ladabin dole . Malam Adam fita daga gidan yayi dan zuwa massalaci dan sai an idar da sallah Isha'i ze dawo gida. Yana fita Innaro tace haba Khairi gidan yamin zafi ni kadai ga wayata cajin ya dauke. Mummy tace abinci suka tsaya ci kibari tasha ruwa sai Ku tafi . Wani katutun bakin cikine ya tokare zuciyar Innaro nan take taji zuciyar ta ,na tsanan ta bugawa . Abinci ta maimaita cikin sanyin Murya . Khairi ta amsa da eh abinci nagama ci tareda saka hijab din ta. Tace muje ko tana mai Kallon Innaro dake bin ta da kallo cike da mamaki. Ganin Mummy na kallon su yasata Fadin Saida safe , khairi muje tafada tana kokarin rike mata hannu. Hakan datayi ba karamin dadi yayiwa Mummy ba dan azaton ta Innaro tafara damuwa da damuwar khairi. Suna ficewa daga gidan Mummy ta kalli Najwa dake kokarin gyara inda suka bata ,tace Najwa Kinga Innaro tasoma canja halin ta ko. Najwa tace eh nima haka muka Lura yau da muka dawo daga gidan Yadiko kamar ta hadiye khairi dan so. Sossai Mummy ta daga hannun sama ,tace ya Allah Ina mai godiya agareka daka nuna mun Wannan rana ya Allah kasa ta daure ko yarinyar nan ta samu sukuni wannan cutar Ciwon zuciyar nan ya ragu ajikin ta . ****************** Suna isa gida Innaro takai khairi dakin ta tareda ajiye mata kwanun abinci agaban ta ,tace haba yata be kamata ace inada rai ba kina cin Abinci wani gida ba. Khairi dago kai tayi tana kallon ta tace wallahi Innaro Na koshi ne karki damu daga yau gida kadai Zan ringa ci tafada tana kokarin cire hijab dake jikin ta. Marairaice Fuska Innaro tayi tana kallon Khairi tace dan Girman Allah kici abinci nan saboda ke nayi kuma harda nama da ice cream takarashe zancen tana mai bude mata ledan ice cream din. Khairi Uwar kwadayi tace dan Allah kice harda nama ni yaushe rabona ,ma danaci nama tun a gidan Sultana. Kwanun abinci ta jawo gaban ta . Tareda daukar spoon zata soma ci tajiyo Muryan Yaya saifudeen shida Akramakallahu sun shigo gidan. Kokarin tashi take Innaro tace dan Allah zauna mana Khairi na , ko kina tunanin Zan cutar dake ne. Kada kai Khairi tayi tace A'a naga yaya saifudeen ne yashigo nakeson inje indawo kafun naci aitunda nawa ne zanci kada ki damu. Innaro hada rai tayi cikin cool voice din ta ,tace khairi indai ni uwar ki ce maza ki zauna kici banason rashin biyayya tsakanina dake ki dauke ni kamar Mahaifiyar ki. Tareda rushewa da kukan Munafunci wayyo khairi naso ace na iske Amina agidan nan yanda mutane ke bada sheda akan ta ,ana fadin mutumiyar Arziki ce . Ina fatan nayi koyi da halayen ta. Khairi mutuwar tsaye tayi hakan yasa ta nemi waje tazauna abinci ta bude tanakai lomar farko a bakin ta , taji wani irin juwa na diban ta , Cikin hanzari Innaro ta kama mata hannu ,cikin Damuwa tace khairi lafiya kuwa ? Ganin yanda ta dafe kanta ,cikin karfin Hali Khairi tace babu komai kinsan nayi ciye ciye shiyasa kika ga ina kokarin Faduwa. Abincin taci gaba daci tana santi ,nan da nan ta ture kwanun abinci takoma kan Ice cream din tana Sha cike da Jin dadi . Innaro sossai taji dadin hakan barin dakin tayi tana fadin Alhamdulillah saura nan da kwana uku yarinya uhmm dafa kirjin ta ,tayi tace habawa khairi nawuce tunanin yarinya. Akramakallahu ne yafito hannun rike da bakin leda Wanda kayan kala daya ke ciki. Saifudeen cike da damuwa yace haba Akramakallahu yanzu baka bari sai jibi ba ,katafi gida ba. Akramakallahu dake Murmushi yace yi hakuri gobe Zan dawo da Yamma InshAllah jibi zanje koyarwa makaranta yakarashe zancen tareda Nufo tsakar gidan. Hango Innaro yayi cike da ladabi yagaishe ta tareda sheda mata yau zeje kauyen nasu sai gobe ze dawo. Innaro sake da baki tace kaiko adaren uhmm saide muce Allah yakai ka lafiya. Khairi ce tafito hannun ta dauke da roban ice cream . Kallo daya ya mata ya kauda kansa gefe . Khairi cike da Jin haushin halin ko inkula daya nuna mata ,tace uhmm wasu dai gasu nan baka gane Alkiblan su. Daga Saifudeen Har Akramakallahu kallon ta sukayi , Akramakallahu yasan dashi take hakan yasa shi fadin KANWATA natafi Saida anjima . Khairi samun kanta tayi dafadin Allah yatsare ,shiko Saifudeen kallon Innaro da Khairi yana mai fadin zanje in raka shi saina dawo. Ficewa sukayi daga gidan kai tsaye hanya suka nufa . Tafiya suke ahanya Saifudeen na bin sa abaya yace Kaga garin ya hade kamar hadari. Akramakallahu juyowa yayi yana kallon sa hade dayin Murmushi yace Yaya saifudeen koma gida Zan karasa kaji InshAllah babu damuwa. Saifudeen badan yaso ba yajuya zuwa gida. Shiko Akramakallahu ganin Saif harya juya ,yasashi kara hanzarin tafiyar sa ,yanayi yana waige waige koda ya iso daidai fita kan Titin wayar ce yazaro daga Aljihun rigar ,cike da mamaki nake kallon iPhone 13 max hannun sa ban Ankara ba , naji yana Fadin na iso bakin titi. Mamaki ne yakamani ganin ya kalli Wata bishiya dake bayan sa . Tsalle yayi yabugi wani leda sai gata ta fado kasa. Hannu yasa yadauki ledan nan ,warware ledan yayi ,saiga wasu kaya na Alfarma hade da agogo hannun sa . Babu lokaci ya canza rigar jikin sa . Takalmi ya saka cikin Abunda befi minti daya ba. Motoci shida ne sukayi parking bakin titin gabadayan su fitowa sukayi suna fadin barka da warhaka sir. Be tanka ba yadoso inda suke cikin hanzari aka bude masa ,motar yashiga tareda rufewa. Kallon juna suka shiga yi shida Aminin sa , Salim yace kai meyasa ka biyo su . Salim yace dan inga gari mana kai kadai ne dan Adam yafada yana mai karewa wandon jikin sa kodadde kallo . Ganin kallon da Salim ke jifan sa dashi yasashi hada RAI ,dan yasan yanzu yana iya jefo masa tambaya . Salim numfashi ya fesar yace uhmm watau dai ba'a son inyi magana to yau miskillanci ya tashi kenan. Jin be tanka masa ba yasashi yin shiru. Babu bata lokaci motocin nasu ,suka bar unguwar. ************************ Kashe gari Headmaster ko barcin kirki beyi ba adaren jiya sossai yashiga damuwa ta yanda ze bullowa lamarin . Wata zuciyar na fadin kawai ka Amshi kudin inyaso saikaje ka auro khairi Kaga riba biyu kenan. Murmushi yayi yana tunanin yanda ze basu takardan Koran kuma wani laifi zece sunyi . Tunowa yayi da Khairi ta taba Marin sa ,farkon zuwan su Makarantar . Girgiza kai yayi yana murmushi hannun sa goye a baya yace tabbas wannan kwakwaran hujja ce . Yau kam tun dawuri Innaro ta hadawa Khairi brek itada Saifudeen . Suna gama karyawa tashirya cikin kayan Makarantar ,yau kam harda fesa turare ajikin ta. MashAllah Innaro ta Furta ,tace khairi wallahi kinyi kyau kinata baza kamshi. Kasaitaccen murmushi tayi Saida kuncin ta ya lotsa tace nagode Innaro mun tafi sai mun dawo takarashe zancen tareda fita waje dan Saifudeen yana jiran ta . Fitowar ta yayi daidai da Fitowar Najwa kusan atare suka dau hanya . Saifudeen na bayan su ,sai fadi yake Ku hanzarta mu tafi banson kuyi latti. Kwabe baki Khairi da Najwa sukayi suna fadin ikon Allah, wallahi inhar saif ze rakasu ba karamin wahala suke Sha ba. Adua suke ya Allah Yasa goben tayi dawuri yawuce Baffa yazo . Saifudeen jin suna kus kus yace gulmata kuke ne? Najwa ta zazzare idanu tace gulmarka kuma kawai firan mu , muke fa. OK to naji maza kuyi Sauri banson jin kus_kus din nan yafada iya gaskiyar sa. Suna isa Makarantar daidai kofar shiga yatsaya tareda zaro naira dari daga Aljihun wandon sa , yabasu su biyun godiya sukayi masa tareda shiga Makarantar. Shiko Saifudeen juyawa yayi yana mai adua Allah Yasa su ringa gane karatun su. Koda Khairi suka shiga Aji ,sun iske yau Sakina sai dariya take musu daga ta kalle su sai fashe da mugun dariya tana rike ciki. Wata yar ajin su mai suna Aysha ta kalli khairi cike da tausayawa dan Sakina ta basu labarin Koran da za'a musu ayau. Cikin sanyin Murya tace dan Allah kuyi hakuri karka damu da Abunda take hassada gamai rabo taki ce. Khairi da Najwa sunji dadin Furucin Aysha hakan yasa sukayi shiru basu ko damu da Abunda Sakina takeyi ba. Malamin turanci nasu yana gama musu lecture yafice acewar sa yanzu lokacin Akramakallahu ne. Sallamar headmaster yasa dukan dalibai tashi dan gaishe sa , Banda Sakina dake zaune tana taunan cingam . Headmaster hakan be damesa ba saima kallon Khairi da Najwa yayi yace kuzo Ku sameni a office Daga haka yafice. Khairi da Najwa kallon juna sukayi ,kowani dalibi dawo da kallon akan su ,sukayi suna tambayar ko sunyi laifi ne? Khairi Tace gaskiya bamu sani ba saide munje . Sakina dariya ta fashe dashi tace kila ma korar Ku zeyi karku ja mishi bakin jini . Basu bi ta kanta ba tunda sun dauki shawaran Aysha . Suna isa office din iske shi sukayi yana latse latse wayar shi. Dago kai yayi yana kallon. Su tareda hada rai tamau ,yace ke Ummulkhairi marin da kikamin rannan ban hakura ba . Dan haka ga takardan Koran Ku nan nabaku ,kuje kunemi wani Makarantar Amma ba wannan ba. Bakin Khairi na rawa tace kora fa kace Malam? Daga mata gira yayi Alamun eh hakane. Kan ubancen Khairi ta Furta tun ranar da hakan ta faru baka kore mu ba sai yau . Najwa cikin bacin rai tace Amma kai headmaster munafuki ne wallahi . Irinku karkashin wuta Zaku zauna. Kuma Makarantar nan bana ubanka bane . Wallahi saimunyi karar ka. Headmaster kasa magana yayi yana Kallon su. Azafafe Najwa ta kama hannun Khairi tace muje kyale banza kada ki tanka masa ai zamu koma gida ko. Kuma Akramakallahu da Yamma yace zedawo saimu fada mishi Abunda ke Faruwa. Khairi dan tsananin bacin rai kasa magana tayi dakyar ta Furta Najwa muje kan titi kinsan yau muke sa ran wannan mutumin zebi hanyar nan. Shikuma headmaster kibarshi zeyi nadama zamu gani tsakanin mu dashi Waze bar Makarantar. Cikin hanzarin suka iso kan titi saboda tsabar ranar da ake tsulawa nan da nan kishir ruwa ya kama su. Hango mai tallan pure water sukayi tareda kiran sa . Kowanne leda biyu biyu suka Sha suna maida numfashi . Suna Sallamar me ruwan Khairi tace Allah yasa wannan mutumin ba karya yayi mana ba , bata gama rufe bakin ta ba. Ta hango motocin nasu sun doso kai a aguje . Cikin karfin Hali Khairi ta tsaya tsakiyar titin rike da kugun ta. Motocin jikake kiiiiiiiiii sunja wani wawan birki dake nunin kadan ya rage na gaban ya buge ta . Azafafe suka bude motocin su. Cikin tsananin Tashin hankali ogan nasu yasa abude masa motar sa. Khairi ganin ogan nasu na fitowa yasa ta cikin................ Taku Har kullum kyauta daga Allah 🦜🦜 *RAI DAYA* 🦜🦜 *JAN ZAKI*🐆 *DAGA MARUBUCIYAR :* *KAIKAJAWA KANKA* *KANWATA* *RAYUWAR MA'AURATA* Yanzu gani dauke da sabon littafina *RAI DAYA* inkiya *JAN ZAKI* *Paid book ne* Normal group 500 Special group 1k Acct nomba *3115484026 ikilima Adam first bank* Ko Katin MTN Kan wanna layin 09069080725 Banason VTU 0️⃣9️⃣ Daddy kasan akwai manyan kasa da suka kware a harkan computer Wanda a China sukayi karatun su ,ko su sun kasa sanin daga inda yake fitowa saini ,haba kaima kasan wahalar dani zakuyi akan Abunda babu nasara acikin sa. Takarashe zancen tana mai kokarin barin d'akin . Jin yariko hannun ta ne yasata dago kai ta kalle sa ,cikin marairace Fuska tace gaskiya Daddy bazan iya ba . Sossai Daddy yaji ransa ya yi mugun baci ,nan da nan Muryan sa ta canza launi yace haba Sumayya ina Alfahari da tarin ilimin da Allah yabaki ,indai baki yi wani Abu akai ba , wallahi Zan rasa kujerar mulkina sonake in gana dashi in gayamasa bukatuna a gare shi ,kuma in masa gargadi yadaina tsoma bakin sa akan Abunda yashafi siyasa . . sossai jikin Sumayya ya yi sanyi Allah yasani tana mugun kaunar Mahaifin ta ,kuma batason Abunda zeja ya rasa kujerar mulkin sa na senata yanzu takarar gwamna yake nema . Karka damu Daddy yanzu na fahimce InshAllah zanyi kokarin yin iya kokarina ,kamar a gidan redio ,*Kukan kurciya* akafi saka jawaban sa. Daddy yace kowace gidan Redio na Fad'in Nigeria duk suna sakawa narasa yanda akai maganar sa yake tasiri a zuciyoyin mutane . Murmushi tayi tace karka damu bincike ne zefara ne akan gidan redio *Kukan kurciya* sannan Har Asibitin sa da makarantu zansa idanu akai kaidai barshi in kere Na jawo zabo na yawo wataran zasu hade ba takamar shi ,wayau ba ze hadu da wayanda suka kera shi. Daddy besan sanda ya rungumi Sumayya ba yana murmushi mai sauti ,yata Allah yamiki Albarka yanzu naji zancen ki fadamun Nawa kike bukata na kudi daga millions goma zuwa sama. A'a Daddy karka damu inada kud'i a acct Dina dazaran sun kare Zan maka magana. Mummy ce ta iso Falon ta iske yanda suke magana cike da nishadi . Tace Wai me kuke tattaunawa ne haka ne. Daddy ne yakatse ta da Fad'in muna hira ne tsakanin uba da 'yar sa dan haka banson gulma yafada tareda fita daga Falon domin zuwa aikin sa. Itakuwa Sumayya kallon mummy tayi tace bawani Abu bane ke kinsan Daddy beda burin daya wuce ya gano wanene Jan ZAKI , ni zanshige insamu inyi wanka takarashe zancen tareda barin Falon tayi sashin ta. Mummy rike da baki tace oh ni Rahila wannan wace irin sawa kai Aiki ne ,ina ruwan su da damuwa akan Wanda ma besan sunayi ba . ********* Anas , kwance karin ruwan da aka sa masa yakare ,kwance yake yana mai kokarin bud'e idanun sa ,yaga fuskar Khairi na masa gizo a jikin kanwar sa dake shigowa dakin ,razanannen k'ara ya saki yana Fad'in wayyo Inna gata nan tashigo , arude Inna ta kalli kofar dakin gani Rayya ce kanwar sa ,tace kai Anas bud'e idanun ka ,wannan ai Rayya ce ko mafarki kake ne. Sannu a hankali ya sake bud'e idanun sa yaga lallai Rayya ce ahankali ya fara sauke ajiyar zuciya. Rayya datayi mutuwar tsaye tace Yaya lafiya kuwa kake ihu dan ka ganni . Kallon Inna ya yi yace yakamata ace mun tafi gida nikam na samu ,sauki nan da kwana uku muna Aiki babba . Sallamar babban manager na Asibitin ne yasa su maida kallon su akan sa. Gaishe su yayi cike da ladabi yana sanye cikin fararen kaya nasu na likitoci. Kallon Anas ya yi yace Shugaban wannan Asibitin yaturo Sako ta email yace yana maka yajiki Allah yakara sauki . Sannan yasa adauko million 5 abaka kudin jinya ,kuma gasu nan a hannuna Mika masa ya yi ,cike da mutuntawa. Wani shock sossai Anas yashiga akan wannan kud'in ,cikin mamaki yace ya Akai JAN ZAKI yasan Banda lafiya ,shida baa ganin sa ,bama ganin sa ya akayi yasan da zamana . Make Kafada manager ya yi yace wannan be zama lallai insan Amsar su ba. Abu daya nasani shine duk wani ma'aikacin sa yasan da zaman sa ,koka mance kana cikin wayanda suke fita da motocin sa aduk karshen Wata. Anas yace kwarai muna fita da motocin sa aduk karshen Wata ,tareda ma'aikatar sa , sai dai wani Wanda yake zama cikin mu amatsayin oga wallahi yacika miskillanci ,ta dalilin sa ne wannan abun yafaru dani . Nan yaba manager labarin komai . Jinjina Al'amarin Manager ya yi kai Anas shi wannan Shugaban naku ya sunan sa . Sunan sa Aliyu Shima Jan ZAKI ne yaturo shi badai iko ba ,kuma munyi musan gidan sa ,yace muna a Makabarta ne. Gabadaya dakin zazzare idanu sukayi , manager jin zancen yafi karfin sa yace Kaga nina tafi , babu dole sai mun San inda Jan ZAKI yake ,tunda yana mana Adalci iyakar mu ,mu rike masa Amana kada mu yarda mu fallasa sirrin sa awani wajen. Gyada kai Anas ya yi cikin yarda da zancen nasa . Shiko Manager fita ya yi. Manager na fita Inna ta dawo da kallon akan Anas tace haba meya kaika fad'a da mace kila ma ba mutum bace dan Allah kafita harkan ta. Rayya tace kwarai kuwa Yaya wai kai haryanzu baka daina sa'insa da mata ba . Wani wawan kallo ya yi Mata mai cike da kishiga taitayin ki , maida kallon sa ya yi akan Inna yace InshAllah daga yanzu ban kara bin ta kanta , kuma wannan kud'in Inna ki ajiye awajen ki . Inna fashewa da kuka tayi tace Anas wallahi Jan ZAKI Alkhairi ne a tattare da rayuwar mu ,shine mutum na farko da yacire mu daga kunci zuwa hasken Rayuwa in kaci Amanar sa bazan taba yafe maka ba. Anas yace InshAllah hakan bazata faru ba Inna ta . Likita ne yashigo yaduba jikin nasa yaga dasauki,takardan sallama yabasu ,cike da Jin dajin dad'i suka fara had'a inasu-inasu zasu fice gida. *********************** Innaro cikin hanzarin ta ,tabar gidan dan taje gun malamin ta ,koda ta iso hanya cin karo tayi da J A da Saifudeen ,ganin su yasa ta canza hanya babu bata lokaci tayi hanyar daze sadata da gidan wannan malamin nata . Tafiya tayi mai dan tsayi ,kafun tafara waige-waige tana duba lungu da Sako ganin babu me ganin ta yasa kai tsaye tayi cikin gidan nan. Sallama dauke Abakin ta ,tashiga Malam shehu cikin sakin fuska yace lale da Safara'u sai yau ake ganin ki? Amsa masa tayi da eh kasan mijina akwai sa'ido wallahi fita ,tana min wuya tunda Na aure shi tareda samun wuri ta zauna . Hakane gaskiya kibarshi zamuyi maganin sa . Meke tafe dake yafada yana mai Kallon fuskar ta . Malam Shehu gaskiya kana mun Aiki yanaci yanda nake so kuma bukata ta ,tana biya sai dai wannan karan sonake wannan kwailan amata aure ,danaso tabi duniya Amma sainayi tunani kada Alhakin ya yi yawa gwamma a samu ko me gyaran takalmi ne ,ya aure ta . Watau akwai wani gasa da za'ai na kwallon kafa . Wanda akeyi duk shekara na yan mata Biyar Wanda Allah yaba rabo yaci gasar a kwallon kafa shi za'a Yarinyar farko . Hakanan za'a wuni buga kwallon nan Har aba duka yan mata Biyar din nan. Kasan Mijina Baffa baze taba yarda yasaka sunan yarsa ba Khairi dan yace wannan tallan kai ne . Kuma fadi yake Allah ya tsari zuri'ar da shiga wannan gasar cewar shi ai tallan kai ,saikace an rasa mijin aure . Dariya Malam shehu yayi yace Safara'u idan harna fahimce ce ,kinason in miki Aiki akan khairi wacce da kanta zata kekashe idanun ta ,tace asaka ta cikin yan mata Biyar da Mai gari yake aurar dasu a shekara. Kwarai kuwa ,haka nakeso ,inason inhar baffa ya matsa mata akan ta janye ,ta saka masa Kukan wallahi saide ayi rai a mutu . Karki damu bakida matsala ,wani kwarya yabude agaban tareda had'a ransa yafara karanto adu'oi Masu zafi na lakanin Asiri ,dago kai ya yi ya kalle ta tareda mika mata wani garin magani. Yace wannan maganin saifa kin kula acikin abincin ta za ki ,saka mata. Misali yau inkin sa mata taci sai bayan kwana uku ki sake saka Mata. Duk bayan kwana uku haka za kiyi Kinga kenan nan da kwana tara kingama amfani dashi. Ki saka idanu kiyi kallo tareda bushewa da dariya wallahi za kiyi mamaki amma fa ki tabbatar taci dan inhar ta tsallake daya bata ci ba Aiki ya lalace. Innaro tace haba ai hakan baze faru ba ,cike da Jin dad'i ta bashi kud'i tareda barin wajen sa. **************** Khairi da Najwa suna zaune cikin Ajin nasu inda malamin turancin nasu yake koyar dasu cike bayan yagama musu lecture yanuna yau baze Jima ba yanada uzuri . Amma hankalin sa yana kan Khairi ,kallon ta ya yi yace Ummulkhairi Sulaiman tashi inason insan ko kina fahimtar karatun da ake koya muku duk da Ku baki ne . Khairi cike da Jin dad'i tamike tsaye. Kallon ta yake tareda binda da wani mayataccen kallo ya yi Mata tambaya daya shafi karatun sa. Zazzare idanu khairi tasoma tareda ciza labban ta . Sakina dake zaune murmushi tayi ganin yau za'a kure Khairi. Mamaki ne yakamasu ganin khairi ta bada amsa dai-dai babu tangarda hatta Najwa tacika da mamaki . Malamin kallo yake yace Amma fa kinyi mugun k'ok'ari , murmushi tayi tana maganar zuci luhmm inbanda Akramakallahu yana gidan mu taya Zan iya . Afili kuma fad'i tayi inaywan nazarin karatuttukan da ake koya mana ne . Sakina dafe da kanta tace Kash Amma wannan yarinya abun nata gaba yake inna sake zata wuce ni a komi gwamma insan abunyi . Malamin bada Umarni yayi akan su tafawa Khairi kowa Saida ya yi Banda sakina . Bayan sun tashi daga Ajin ne dan yau Akramakallahu be Zo mamaki ne yacika dalibai dan tunda yake zuwa baya fashi . Direban gidan su Sakina ne yazo hannun sa ,rike da takarda Wanda ke dauke da sunan Ummulkhairi Sulaiman Da Najwa ADAM. Har office d'in headmaster yaje ya Mika masa wanna takardan. Yana karba yace Yallabai wannan takardan fa. Drever yace bude ka gani mana . Warware takardan ya yi yaga ansa Sako daga Alhaji Kamal . Yana son akori Ummulkhairi da Najwa. Sossai headmaster yashiga tashin hankali ,shida yake shirin yaje ya nuna mata yana son ta . Za'a wani ce a kore su. Maido da kallon sa akan drever Sakina da Har ya juya yace dakata dan Allah cikin bacin rai. Wannan takardan na menene yana masa nuni da takardan. Drever yace nikaina bansan meye aciki ba , Sako aka ban kana iya kiran Alhaji ai kanada number sa Sakai ya yi yafice daga Makaranta tareda d'aukan Sakina a motar . Shiko headmaster sossai yashiga tashin hankali dan yasan a dokar Makarantar ba'a kora Saida Izinin Jan ZAKI dakuma sa hannun sa. Kiran Alhaji Kamal ya yi akan maganar cike da damuwa Alh Kamal yace haba headmaster ya zakace kana tsoro kaine ke fad'a Aji kuma JAN ZAKI besan komai akan Abunda ke gudana ba. Millions Biyar Zan baka nidai kacika mun burina a goben nan. Katse wayar ya yi bejira cewar headmaster ba. Shiko headmaster rana zafi inuwa kuna ,wani bangaren kud'in da akai masa tayi ne yafara tunani akai ,sossai kan sa ya kulle rike da kugun sa. Najwa da Khairi ahanyar ta komawa gida suna hiran gobe InshAllah karshen Wata dan haka da shirin su . Zasu je wannan titin da ba kyale shi zasuyi ba. Direct gidan Mahaifiyar Baffa Yadiko suka nufa . Bakin su dauke da sallama suka shigo. Yadiko tana ganin su , ta fadada Fara'ar ta ,tace yau wace rana ce Khairi nake gani. Murmushi kwance akan fuskokin su ,suka karasa ciki tareda samun wuri suka zauna. Khairi Tace Yadiko tunda bakya nemana yau nazo dakaina. Wai me kika dafa ne tafada tareda shiga kitchen din yadiko tana dube-dube. Yadiko rike da baki tace abunci mijina kika dauko khairi tana kwabe baki. Khairi Tace kwarai kuwa nashi zanci ,ya za'ai be bani naci ba Amma kullum saiya baki . Najwa Ganin dagaske Abinci khairi zata ci yasata zuwa wanke hannun ta suka fara ci. Yadiko tace wayyo Allah Ashe baku canza halin Ku ba daga zuwan Ku ,Har Kun dauke abinci Malam. Khairi dake santin shinkafa da wake da mai da yaji tace au haba Ashe abinci Malam ne ,Miko mana yankanken salad din nan mu zuba aciki . Kuma kiyi maza ki dafa mishi wani ko Alkur'an ya kwana da yunwa ina ruwana ni Ummulkhairi idan yakwana beci ba. Sake da baki Yadiko ke kallon ta ,tace lallai yarinya kince wani Abu . To maza kuci kuzo kumun jajjagen kayan Miya in dafa masa koda taliya takarashe zancen tareda shiga kitchen din. ******************** Innaro cikin hanzarin ta ta kamalla girkin ta abinci khairi harda nama ta saka Mata me uban yawa. Saifudeen da Akramakallahu kuwa . Kai musu abincin nasu tayi Har dakin nasu . Kasantuwa yau Saif da Akramakallahu yawo kawai suka tafi cikin gari . Sai kallon agogon hannun ta take ya Akai haryanzu khairi basu dawo ba ganin laasar ta kusa . Wani babban shagon me Saida kayan provision taje ta saiwa khairi lemun kwalba hade da ice cream mai dan Karen sanyi . Komawa gida tayi ,tadau abinci khairi takai dakin ta. Lemun ma da ice cream duka ajiye mata su tayi. Zaune take sai kallon agogon hannun ta ,take shiru kake ji Har magrib. Tana kokarin shiga daki da dauko buta kansatuwa ankira sallah . taji Muryan khairi da Najwa suna........... Taku Har kullum kyauta daga Allah Free page yakusa karewa Ku hanzarta kubiya dan kucigaba da samun littafin . 🦜🦜 *RAI DAYA* 🦜🦜 *JAN ZAKI*🐆 *DAGA MARUBUCIYAR :* *KAIKAJAWA KANKA* *KANWATA* *RAYUWAR MA'AURATA* Yanzu gani dauke da sabon littafina *RAI DAYA* inkiya *JAN ZAKI* *Paid book ne* Normal group 300 Special group 500 Acct nomba *3115484026 ikilima Adam first bank* Ko Katin MTN Kan wanna layin 09069080725 Banason VTU 0️⃣8️⃣ Yayi tozali da Sakina da take shirin dafa bayan sa. Cikin hanzarin sa yabuge hannun ta kafun yakai jikin sa , tareda bin ta da mugun kallo mai cike da mekike nema dani. Cikin rawar Murya da kunyar da ya lullube ta , tace Akramakallahu kayi hakuri ,wani kwaro ne na hango ,nazo inbige maka shi ,bata karasa fadin Abunda takeda Niya ba ,ya daka mata uban tsawa ,Wanda Yasa ta razana kadan ya rage bata saki Fitsari ajikin ta ba. Keeee yafurta cikin kakkausar Murya , wallahi nakara ganin wannan gangancin akaina ,Zan mugun daukan mataki akan ki banason iskanci ,ko na miki kalan yan iska ne . Sakina cike da tsoro kada hankalin mutane yadawo akan su ,tabar wajen cikin Sauri Sauri , bin bayan ta yayi da kallo yana buga uban tsuki akai akai ,tareda kunna hasken wayar sa ,yacigaba da wayar sa ,murya cen kasa kasa. Bayan Malamin turanci yagama musu lecture, Akramakallahu yashiga Ajin ,suna hada idanu da Sakina ya dauke kai ,ita kuwa sossai tasha jinin jikin ta ,tana gudun kada ya fallasa Abunda yafaru . Kallon Dalibai yayi yace yau ba ranar waazi bace Amma zanyi mana waazi game da rayuwar student a school. Nan da nan hantar cikin Sakina ya kada cike da tsoro kada yakawo misali akan ta ,yasa tafara tunanin Mafita Kota fita ne koko dai taboye kanta . Najwa da Khairi hankalin su tsab yana kan Sakina Dan su Lura akwai Abunda ke damun ta ,tun shigowar Akramakallahu. Shikuwa Sam hankalin sa baya kanta bare yasan da halin da take ciki. Tsintar Muryan sa sukayi yana Fadin , a fadin duniyar da muke ciki , Makaranta tana cikin Abunda ake gyara tarbiyya kuma tana cikin hanyar gurbata tarbiyya ,sai Kaga yarinya a makaranta Amma tasan namiji , ko kuma ka samu malami yana amfani da ita dan yabata maki. So yakamata kowace daliba acikin Ku ,ta maida hankalin ta akan Abunda ya taramu ,Ku rufawa iyayen Ku Asiri da suka turo Ku ,dan Ku samu ilimi mai amfani. Tunda yafara magana kan Sakina a duke yake. Yana gama musu nasiha ya maida hankalin sa akan agogon dake makale hannun sa . Ganin Time ya kusa ne yasa shi fadin akwai Mai tambaya acikin Ku ne? Tsit kake ji Ajin ,Lura da Khairi yayi bakin ta na motsi alamun tana son yin magana. Khairi ta daga Hannu tace inada tambaya. Bismillahi yafurta yana mai Kallon ta , idanun su ,suka tsarke cikin Juna ,nan take zuciyoyin su , suka harba , Akramakallahu Subuhannallah ya Furta acikin zuciyar sa. Itakuwa Khairi hannun tasa ta dafa wajen saitin zuciyar ta ,tana jin yanda yake mugun tsananin bugawa . Akramakallahu dauke idanun sa yayi akan Khairi tareda bata daman tayi magana dan yau karo na Farko da sukayi kallon kallo shida ita. Daman inason ka gayamin idan har wani ya cuceka koda da zagine ko duka ,da dai sauran su. Kana son ka rama wani hanza zaka bi. Gabadaya Glass rike da baki kowa ya juyo yana kallon ta. Akramakallahu cikin Muryan sa dake nuni da babu wasa acikin sa yace inhar Cutar da akayi miki ,kina ganin bazaki iya yafewa ba ,toki rama daidai Abunda akai miki ko kibarwa Allah . Mafi Alkhairi acikin mu shine Wanda yabarwa Allah dan yayi masa sakayya. yakarashe zancen yana Fadin ina ganin lokaci yayi zamu tashi tareda sallamar dalibai . Akramakallahu na fita kowace daliba tafara kokarin fita , gabadaya class din firan sa ake akan fadakarwar da yayi. Najwa da Khairi daidai kusa da Sakina suka karaso ,cikin daga Murya khairi tace Kash Amma dai wasu matan basu da Aji wallahi sune ke barin ana muna kudin goro ace ba muda kamun kai. Najwa tace kwarai kuwa ai haka suke da sunga na Miji kamar su cinye shi. Wuce ta sukayi suna dariya rike da baki. Sakina dago kai tayi tana kallon su ,rike da baki tace wayannan yaran dawa suke ne? Rasa me bata amsa yasata bin sahun su ,har waje ta same , su tsaye suna fira. Azafafe tazo wajen su , cikin karaji tace,wani dan iskan ne acikin Ku yake min habaici ? Khairi dake bin ta da mugun kallo tace gani nan ,nice ko akwai Abunda zaki mun ne? Kokarin kai hannu take dan kaiwa Khairi, Mari caraf taji an rike hannun ta. Cikin tsananin Mamaki take kallon Yaya saifudeen da ransa yake a matukar bace ,yace wallahi koda wasa hannun ki ya taba fuskar yar auta na lahira saiya fiki jin dadi ,kuma taimakon ki ,nayi dan wacce kike shirin kaiwa mari ,ba zumar lasa bace , madaci ce yakarashe zancen tareda kama hannun Khairi da Najwa cikin zafin nama yabar school din dasu. Mutuwar tsaye Sakina tayi ,cike da mamakin wayannan yaran da kuma kalaman Yaya saifudeen ,cikin kunan rai tayi hanyar gidan nasu, tana Ayyana aranta sai tayi karar su intaje gidan su. ***************** Yaya saifudeen sunci rabin tafiya daga Makaranta zuwa gida. Hango Akramakallahu yayi zaune gefe yana karantun Alkur'an mai girma. Har sun wuce shi , Najwa tace laa Yaya ga Malamin mu nan mai koya mana karatun Addini . Waigowa Saif yayi suka hada Idanu da Akramakallahu dake shirin rufe Alkur'an. Saifudeen yace kamar dashi muka gaisa da safe , hannun yaba Akramakallahu sukayi musabaha , saif yace Malam kai dan garin nan ne yana mai tsare shi da idanu . Dago kai yayi yana kallon su Khairi da Najwa karamin tsuki yaja ,yamaida kallon sa akan Saif tareda bashi Amsa ni bako ne . Kuma dan Allah ko Zan samu daki haya agarin nan ? Saif yace inhar bakada iyali inaga me ze hana ka sauka a muhallina . Akramakallahu jinjina kalaman sa yayi yace haba kai daga ganin bako saikayi saurin yarda dashi . Eh inada kyakyawar zato akan ka ,kaiba mutumin banza bane . Kuma nasan bazaka taba iya kashe koda kiyashi ba. Murmushi Akramakallahu yayi yace inagodiya Amma kabar ni indai kama hayar zefi, Saif yace dan Girman Allah ka zauna taredani daman kadaici yana damu na ni kadai adakin. Dan Jimm Akramakallahu yayi yana mai satar kallon su Khairi da suke tabe baki akan firan nasu. Na'amince ya Furta Allah yasa Alkhairi acikin zaman da zamuyi . Saidai baka gayamin sunan ka ba. Bashi Amsa yayi da Saifudeen Sulaiman . Khairi ce ta katse firan nasu da Fadin , Yaya kabari zamuyi gaba har Ku gama tattaunawa. Daga musu kai yayi Alamun gamsuwa. Hakan yasa suka wuce suka bar Saif da Akramakallahu tsaye suna tattaunawa. Bakin Titi suka nufa ,Najwa tace khairi kinsa wannan yaron nan yace ,sai karshen Wata yake bin wannan hanyar ki dawo muyi gida . Naga saura kwana biyar karki damu ranar da makaman yakin mu zamu taso ,da wannan kalamin ne , taja hankalin Khairi har ta amince su tafi gida . Innaro zaune adakin ta sai safa da marwa take ita kadai ganin babu mafita ne yasa ta dau wayar ta ,takira Kawar ta ,bugu daya aka daga dagacen bangaren cikin dariya da shewa tace shegiyar mata sai yau kike nema na. Tsuki Innaro taja tana mai fadin kedai wallahi kin bani bazaki bari a gaisa ba. Kwabe baki Biba Kawar ta tayi tace am sorry yakike Safara'u kwana dayawa , bayan sun gaisa ne ,takara da cewa ina wannan nusarin mijin naki da wannan yar tashi sangartaciyya ? Humm Innaro tayi tace ai shegu duk suna nan lafiya ,wannan yarinyar nan inhar banyi hankali ba wallahi saita sa an koreni agidan ,dan Allah ki koma gun Malam shehu ki fadamai Abunda nake bukata Kinga munyi nasarar yin Aiki har aka aurar da Sultana ,itama Khairi takai Aure dan Allah kice masa ayi Abunda za'ayi yarinya da kanta ,tace aure takeso . yau befi saura Wata daya Ayi wasan kwallo na aure da ake bugawa duk shekara. Duk yanda za'ai dan Allah ayi inason Khairi ta bude bakin ta ,tace asaka Sunan ta a wannan gasar . Bushewa da dariyar keta Biba tayi tace shegiya Safara'u kanki yanaja kinsan nama mance gasar nan ta kusa naso in saka yata Amma tunda kinzo da bukata sai asaka shegiyar Yarinyar nan kowa ma yahuta. Sanyayyan Numfashi Innaro tayi wlh sai yanzu naji hankali na yakwanta ace yara su hanaka jin dadin aure , kinsan Baffa indai Khairi na gidan wayyo bazan taba yin haske a idanun sa ba. Da khairi tabar gidan sannan zandawo da sababbin abubuwa agidan kedai kwantar da hankalin koda matsiyaci Amma dai ina hango wasu abubuwa tare dashi. Jin takun tafiya yasa Innaro fadin Biba sai anjima zamuyi waya tareda fitowa tsakar gidan . Kallon su tayi itada Najwa cike da Farin ciki tace yar Baba har andawo .. Sake da baki suke kallon sabon salo , khairi ce ta amsa da mun dawo akwai abunci ne dan yunwa nikeji. Haba yayana ya zaai ina uwar taku abinci saikun nema ,aikunwuce haka awajena nida Zan aurar daku inkun kara girma. Zazzare idanu khairi da Najwa sukayi kusan tare suka furta aure kuma suna zazzare idanu ,ai wallahi ba yanzu ba. Innaro cike da Salo tace Aina sani yayana azuciyar ta sai fadi take wayyo khairi harkin ban tausayi ashekarun ki akai ki dakin Miji bansan me zaki tsinana ba. Sallamar Saifudeen ne da Akramakallahu ne yajawo hankalin su akan sa. Arazane Khairi ke kallon sa agidan su shikuwa kauda kai gefe yayi . Muryan su taji suna gaida Innaro inda ita kuwa sai washe baki take , tace Dana Saif na Allah Ina kasamo wannan farin yaro mai zubin larabawa . Saifudeen murmushi yayi yace uhmm abokina ne kuma bako ne sai ranar asabar zeringa tafiya garin su ,shike koyar dasu Khairi fanni Adinni . Allahu Akbar Innaro ta Furta tace kenan adakin ka ze sauka ,ganin zata cika su da surutu Saif ya katse zancen eh daki daya zamu zauna tareda kama hannun Akramakallahu suka wuce dakin sa dake zaure . Khairi da Najwa cike da mamaki suke kallon Al'ajabi suka hada baki wajen fadin oh ni Yaya saif haryanzu Ashe be bar kwashe kwashe ba . Caraf Kalaman su yafada kunne Akramakallahu da Saif kallon Juna sukayi tareda yin Murmushi dan ya dauke su yara be sasu ajerin Masu hankali ba. Cike da Jin kunya Saif yace please kayi hakuri da Abunda kaji yara ne . Hannun ya masa cikin nuna halin ko inkula da lamarin su Yace nima inada kanne irin su marasa ji. Nuna masa wajen kwamciyar su yayi Wata katuwar katifa . Sossai Akramakallahu ya yaba da tsaftan Saifudeen dan dakin agyare yake komai normal. Kashe gari Sakina cike da bacin rai tafito dakin ta ,tana sanye cikin kayan Makarantar su. Abban su dake tsaye yana mai kare mata kallo yace haba daughter tun jiya naga baki walwala waya tabamun ke. Kuka ta saki cike da shagwaba tace wallahi Daddy wasu yaran Ajin mu ne ,su biyu suke tsokana ta kuma ban musu komai ba , please daddy inason kasa akore su daga Makarantar nan hakan zesa inji dadi. Mummy ta dake sauraron su ta haba Sakina wani irin a kore su , Makarantar ta uban ki ce . Ran daddy Sakina yakai kololuwa wajen baci ,yace waike meyasa bakida zuciya ne ace ana zaluntar yar ki Amma kina Neman ki hana adauki mata ki akai why yafada cikin tsawa . Mummy cikin sassaita nutsuwar ta tace ba haka bane Amma ka sani suma wayancen din Yaya ne kuma abun soyuwar iyayen su , balaifi sukayiwa Allah ba yabarsu a talakawa ba . Tunda Sakina take zuwa Makaranta ni bandaji karatu Abakin ta ba. Saidai inji ta samu sakamako me na tabbatar ba kokarin ne ya bata ba ,haba kudaiji tsoron Allah takarashe zancen tareda barin dakin. Sakina da daddy kallon ta suke suna jinjina kalaman ta . Maida kallon yayi akan Sakina yace karki damu da ita daughter ,gayamin sunan yaran nan wallahi Zan nuna wa iyayen su ba'a tabani a kwana lafiya ni Alhaji KAMAL dan natura ki Makarantar JAN ZAKI akwai dalilin yin haka karki damu ,kwananan nan Zan fitar dake waje karatu. Sakina hada rai tayi cike da fargaba tace haba Dad's waje kuma ,cike da razani kada a rabata da ganin Akramakallahu dan tayi mugun kamuwa da son sa komai zata iyayi . Please Dad's karka canza mun Makaranta kabarni anan kaidai kasa akori wannan yaran shine bukata ta. Wata matashiyar budurwa wacce bazata wuce shekara Ashirin da Biyar bace tashigo Falon hannun ta dauke da wani basketball tana sanye cikin Riga da wandon kwallo . Good morning Dad tafurta tareda karasowa gaban sa ,cikin tsokana tace Sak yadai naganki kamar wacce ke shirin kuka . Daddy ne yabata labarin Abunda akayi wa Sakina ,jinjina lamarin tayi cikin nuna lallai yakamata a dau mataki akan su. Sakina nawuce wa dan drever na zaman jiran ta . A harabar gidan nasu. Daddy kallon matashiyar budurwa yar sa yayi mai suna Sumayya Yace daughter yawwa Zo mu dan zauna muyi magana kullum inason inyi magana dake Amma wani uzurin naki saiya hana. Samun wuri sukayi suka zauna ,cike da son jin Abunda ze Fada ta tattara nutsuwar ta ,tace Daddy inajinka ,tareda daura kafar ta daya kan center table tsakiyar dakin. Sumayya yakira sunan ta ,cikin cool voice din sa. Inason zaki mun Aiki akan JAN ZAKI Firgit ta dago kai ta kalle shi cikin zazzare idanu bakin ta ,na rawa tace Daddy banji Abunda kake fada ba kodai kunne na ,ne ke min gizo da kalaman ka. Girgiza kai yayi yace A'a Sumayya Abunda na fada hakan yake akan sa nakeson son ki mun Aiki ko baki bane yafada cikin daga Murya alamun so yake ya fusata. Zumbur ta Mike tsaye rike da kugun ta tace Daddy kasan............. Taku Har kullum kyauta daga Allah. Ikilima Adam 09069080725 *🦜RAI DAYA* *JAN ZAKI*🐆 Ikilima Adam( kyauta daga Allah) Paid book. 09069080725 1️⃣1️⃣ Ganin ogan nasu na fitowa daga cikin Motar ,yasata hanzartawa ta isa gaban sa , cikin tsananin b'acin rai da suka had'e mata ga na kora da akayi musu daga Makaranta , ga bak'in cikin sa da ta Dade dashi. Kasa hada idanu tayi dashi dan kwarjini ya yi Mata , cikin karfin Hali . Rai ab'ace tace rannan kace mun stupid girl to kaikuma hauka boy , kace mun mental problems to kaine kwakwalwa problem dan na tabbata kwakwalwar taka ba a dai-dai suke ba , shiyasa kake zagin yayan mutane get out tafada jibe shi mutum Shiba kowa ba ,ya tara samudawa yana jawo dashi in katashi zuwa lahira mun gani ko zakuyi kwanciyar kabarin tare dasu nusarin namiji taja tsaki tana mai buga masa uban harara . Ogan nasu tunda tafara zazzaga masa ruwan Masifa babu abunda yake kallo sai bakin ta , ganin takai karshen zancen ta . Yakara takun tafiyar sa izuwa gare ta had'e da shan kunu yace yau kin tabbatar mun dake Stupid girl ce mara hankali inbanda dabbanci an gayamiki ana wasa da Rayuwa ne to bari kiji in gayamaki daga rana ita yau , idan nakara cin karo dake kan Titin nan Zan dauke ki inkai ki gidan zooo inba Kura suyi fata-fata da namar jikin ki yakarashe zancen yana bin ta da kallon kishiga taitayin ki. Tsit kake jin khairi takasa koda kwakwaran motsi arude take kallon sa , tace eh lallai yau na tabbatar da maganar Najwa akan gargadin da ta data janye maganar daukar fansa . Ganin tayi shiru ne Banda hawaye babu abunda ke kwaranya daga idanun ta . Yasa shi Fad'in dan Allah malama bamu hanya In kunne yaji jiki ya tsira. Yaja karamin tsuki. tareda juyawa yayi cikin jerin Motocin. Najwa dake gefe tana kallon Abunda yafaru zuwa tayi tarikota dakyar tana Fad'in khairi kinban mamaki ya za'ai bakin ki ya mutu gaban wannan mutumin . Anas ne yakaraso gaban Khairi yana dariya yace yammata hiiiii yana kashe mata idanu , yakika ga wasan yanzu kin tabbatar sahun giwa ya take na rakumi ko? Khairi da idanu kawai tabishi dan tarasa dalilin dayasa takasa jaa da wannan mutumin , ta tabbatar idan Anas ne da tuni ta dau mugun mataki akan sa. Tsuki taja hade da hararan sa tace Inka isa karama Marin danayi maka rannan agaban su.. Gabakidaya magoya bayan Aliyu dake tsaye Har shi kansa JAN ZAKI duk da yana cikin Motar be hanashi jin Furucin ta ba. Kasa daurewa yayi hakan yasa yafito daga motar karo na biyu cike da kasaita yake tafiya harya iso gaban Anas yana mai masa kallo mai Alaman tambaya . Yace wai kana nufin ,Saida kabiyo wannan yarinyar dan daukar fansa ne. Zazzare idanu Anas yasoma cikin rawar Murya zece A'a . Najwa tace karya yake be kamaceka ba inace biyo mu kayi rannan Har yar uwata ta hukunta ka takarashe zancen tana mai buga masa harara cikin tsawa. Aliyu JAN ZAKI sossai Anas ya yi matukar bashi mamaki Afili kuma kallon sa ya yi yace maza kashiga mota ,yana girgiza kai Alamun akwai Abunda ya Sosa masa rai acikin jawabin Najwa. Yaran sa dake wajen kowanne su yana sake sake akan hukunci da ogan su ze dauka akan Anas . Khairi rike da baki take kallon yanda motocin nasu suka kunna wuta zasu bar wajen . Kamar ance mata waigo aikuwa tana juyawa taga Yaya saifudeen ne . Kuka ta fashe dashi , cikin kidimewa yace lafiya meya faru Khairi na. Nuna masa motar su Aliyu tayi da hannun ta dake shirin hawa kan titi. Dakata yafad'a atsawace ahakan yasa motocin suka dakata cak . Kallon khairi ya yi yace me sukayi miki ne? Cikin kuka tashiga bashi labarin Abunda yafaru Abu daya taboye masa shine bibiyar sa da suke tayi Har yau din nan da suka same shi. Saifudeen isa ya yi wajen motocin yana kallon kowani mota baki wul yace ina ogan naku yake cikin bacin rai. Jin haka Yasa ,Aliyu yabude glass din motar sa yana mai Kallon sa. zazzare idanu Saifudeen ya yi yace kamar nasan fuskar nan. Ganin Aliyu yahada rai yasashi Fad'in bawan Allah me KANWATA tayi muku ,kuji tsoron Allah Arziki ba wayau bane . Bazeyu Ku cutar da marainiyar Allah ba . Akan kuna takama da Arziki yakarashe zancen cikin raunin Murya . Aliyu Saida yashiga shock sossai jin Furucin maraici hakan yasa shi fitowa daga motar nasa shi kadai hannu ya bashi sukayi musabaha. Saifudeen jin taushin hannun sa ya yi yawa yace azuciyar sa uhmm to ansaba kwana Ac ko ina Ac dole jiki ya yi taushi . Maganar Aliyu ne yadawo da hankalin sa kusa . Nan yashiga bashi labarin abunda yafaru tareda bashi hakuri ,nuna masa ya yi yaji haushin Abunda khairi tayi ya za'ai tayi wasa da rayuwar ta harda hawa kan titi akan wani shirmen ta *RAI DAYA* ne daga shi babu Kari dan Allah kaja mata kunnen sossai na Lura yarinya ce yakarashe zancen tareda shigewa motar ,basu bata lokaci ba suka bar wajen cikin hanzari. Saifudeen tsaye ya yi yana kallon motocin nasu Har suka bace masa da gani . Karasowa wajen khairi ya yi wacce take jiran taji meze fad'a sai dai ji tayi ya wanke ta da wawan mari ze kara mata ne. Mijin Sultana ya yi maza yarike masa hannu. Cikin Fushi yace Khairi wai yaushe zakiyi hankali ne ,jibi bawan Allah nan duk da mutum ne mai Arziki Amma yanada hankali da tunani , dan yace miki stupid girl beyi karya ba ,me ce ce ke inba haka ba . Da rayuwar ki kike wasa khairi , ki kashe kanki abanza kisa hawan jini Yakama Baffa. Sossai Khairi ke kuka Har cikin zuciyar ta bawai Marin takewa kuka ba , kuskuren data Aikata wajen tsayuwar titin. Mijin Sultana hakuri yaringa ba Saifudeen ,dakyar ya hak'ura tareda kama hannun Khairi da Najwa yaringa fisgan su kamar yasamu yayan sa. Shiko Isma'il kai tsaye gida yashiga yaba Sultana labarin abunda yafaru kuka ta saki tana salati tace khairi dan Allah ki rufa mana Asiri . Mijin nata yace tunda gobe Baffa zedawo Yakama kije ki mata fad'a sossai . ***************** Suna isa gidan sossai yashiga musu Nasiha khairi da Najwa yana nuna musu muhimmanci hak'uri da Rayuwa . Jiki Asanyaye Khairi tace InshAllah Yaya bazan kara sa'insa da wani ko Wata ba. Murmushi ya yi yana mai Kallon kyakyawar fuskar ta yace koke fa. Najwa tashi tayi zata wuce gida tareda yiwa Khairi sallama. Innaro da sallama tashigo hannun ta dauke da kayan cefane. Gabanta yayi mummunar Faduwa a zaton ta ko khairi taba Yaya saifudeen labarin kan tilasta mata taci abinci ne. Saifudeen ne ya katse mata tunani ta hanyar Fad'i Innaro harkin dawo Kinga Khairi Fad'a nake mata. Ajiyar zuciya Innaro ta sauke tareda zazzare idanu tace Saifudeen meyafaru ? Yana bata labari tashiga sallallami tana yarfe hannu rike da baki tace Khairi karki sake gangancin wasa da rayuwar ki kinji 'yata . Cikin kissa da iya taku taringa bawa Khairi shawara akan ta daina fad'a da Masu Arziki dan ko kotu akaje baza'a iya shari'a dasu ba. Saifudeen yace Innaro maganar ki dutse . Khairi tace Yaya saifudeen ga wannan takardan tareda mika masa , yana karba yashiga warware wa. Kallon sa take yanda yake bin rubutun dake cikin takardan yana kai karshe wani zufa ne ya keto masa . Cikin tsananin bacin rai yace Khairi yaushe zakiyi hankali ne meya kaiki marin Shugaban Makaranta. Cikin kuka khairi tace wallahi ba yau akayi ba nan tashiga bashi labarin tun farkon zuwan su kuma da dalilin mugun kallon dayake jifan ta dashi ne. Ajiyar zuciya ya sauke yace wallahi tallahi be isa shidin banza akwai Abunda yake nufi dake Khairi kuma wlh zesan ya taboni badan antashi ba yanzu da munje Amma kijira Akramakallahu yadawo yace yau zedawo zamu San abunyi shidin banza . Murmushi khairi tayi Saida kuncin ta ya lotsa . Tace Yaya na wallahi nima dai nasan da Wata akasa . ********************* Motocin nasu kai tsaye wani kerarareen gida a JRA suka faka Horne suke ta zubawa ,ahanzarce manyan bodyguard suka fiffito tareda wangale musu gate . Basu bata lokaci ba wajen kusa hancin motocin su a wannan farfajiyar gidan Wanda kana masa kallo daya kasan a narkan kudi ,dukiya ta zauna . Yanayin tsarin gidan da shuke shuken furanni da yawan ma'aikata dake kai komo cikin gidan. Kokan su fito daga cikin motocin gabakidaya maaikatan gidan sun jejjeru kowanne su hannun rike da flawa suna Fad'in barka da zuwa sir ogan mu mai Adalci . Uba goya marayu , maganin kukan mu. Ahanzarce aka bud'e masa kofar yafito daga cikin Motar . Kallo daya ya musu daga mazan Har matan harya sa kai zefice saiya dawo da baya . Ahankali yake bud'e lallabansa yace Ina Nuriyat take ne ? Kowanne zazzare idanu suka shigayi. Cikin su Wata tace tana dakin batada lafiya uban Marayu. Ya sallam ya Furta acikin zuciyar sa. Tareda cigaba da tafiyar sa . Magoya bayan sa suna bin bayan sa. Wow nace lokacin da shiga wannan babban Falon ta Alfarma hatta TV plasma a kewaye shi da ado yalwatacce mai dauke da sunan JAN ZAKI. Kujerun dakin nasa duk inda ake Neman kallo toya kare awajen hade carpet dake malale tsakiyar dakin mai zubin dawisu komai na cikin dakin Hash color ne. Anas yau shine karo na Farko daya shigo wannan Falon zallan mamaki ne yakamashi ganin anrubuta JAN ZAKI .. Arazane yake kallon ogan nasu yana maimaita Jan ZAKI rasa me bashi amsa yayi hakan yasashi Fad'in Yallabai kozan iya tafiya . Cike da tsoron kada ya yi masa Magana akan Abunda Najwa ta fad'a masa. Hannu ya masa Alamun yatafi . Ajiyar zuciya ya sauke had'e da Fad'in Alhamdulillah. be tsaya Wata Wata ba yafita zuwa farfajiyar gidan. Cikin Maaikatan dake zarya wajen yakira mutum daya cikin su. Yace dan Allah wannan bawan Allah shine JAN ZAKI? Murmushi wanda yakira ya yi yace mu kanmu bamuda masaniya Amma dai naji ance wai Jan ZAKI uban gidan sa ne. Kaga dole ne ya yi amfani da sunan sa acikin gidan nan shida , ba'a anan yake kwana ba yana gama uzurin sa zamu nemeshi mu rasa . Da yadauki akun nan nasa mai shegen surutu . Ajiyar zuciya Anas ya sauke yace nidai na fara zargin kamar shine JAN ZAKI fa. Bawan Allah yace kai muma haka muke zargi saboda halayen sa daya da Jan ZAKI duk da bamu taba zama dashi ba. Bodyguard dake kai komowa sukaga firan Anas da wannan mutumin ya yi yawa . Taka musu birki sukayi ta hanyar Fad'in doka be baka damar ka Fad'i wani Abu daga cikin gidan nan ba dan haka akiyaye. Hak'uri suka shiga bashi tareda barin wajen shiko Anas kai tsaye waje ya yi dan taran napep zuwa gida. JAN ZAKI kallon lemukan da ake jera masa agaban sa ya yi , beyi aune ba saiga akun nasa ya iso wajen tareda hawa kan kafadar sa. Kallon akun ya yi yace dan gata sai yanzu kasan na dawo ko? Akun yace A'a inacen ina kallon cikin unguwar ne Uban marayu. Rada yamasa akunne yace kana iya shan lemun nan uban mu. .Babu bata lokaci yadauki kofun dake dauke lemun exotic ya kurba ahankali tareda ajiyewa . Yana tashi magoya bayan sa zasu bishi hannu ya musu yace Akira su Kira Inna Fatima tazo ta kwashe wannan kayan ciye-ciyen da aka jera mishi . Gyada masa kai sukayi . Shiko kai tsaye matakalan step yaringa hawa ahankali Har iso kusa da wasu dakuna . Kallon dakin yake kamar me nazari hakan nan cikin rashin kuzari yabude kofar Yana shiga ya Salam yafurta ganin yanda Nuriyat ke jin jiki sossai yarinya ce da bawata wuce shekaru 16 ba Akun ya kalle shi yace Uban mu , meze hana mu tafi da ita cen Makabarta. Gyada masa kai ya yi Alamun gamsuwa. Amma azuciyar sai wasi wasi yake ya zeyi ya dauke ta ,kuma inyakaita inta samu lafiya saidai ya barta cen dan baze dawo da ita nan ba. Kusan mintina bakwai yana tunani akarshe dai ya yanke shawaran barin ta. Tsintar Muryan sa tayi yana Fadin Nuriyat yanda yaja sunan nata jitayi wani zirrr acikin zuciyar ta. Duk da batada lafiya ne hakan be hanata dagowa ba. Kauda kansa gefe ya yi befiye son kallon kurilla ba , yawwa yajikin naki yafurta . Gyada masa kai tayi alamun dasauki . Shikuwa mikewa ya yi tsaye yace ki zauna cikin shiri zansa akai ki Asibiti duk Abunda kike bukata kiyiwa Inna Fatima magana daga haka be kara cewa komai ba yafice daga dakin. Cikin hanzarin sa yasauko daga kan matakalan step din . Koda ya iso kasan wani daki yashiga Shima dakin akwai Wata kofa acikin Wanda bazaka taba sani ba sai shi da yasan kayan sa. Ahankali yabude kofar yashiga shida akun sa sai gasu tsakiyar titi dan tafiya yayi da bewuce mintina goma ba ya iso dai-dai Wata motar taxi dake ajiye . Kayan jikin sa yasoma rarragewa yashiga motar tareda danna mata key yabar unguwar cikin hanzarin sa. Akun nata masa surutu mai San yanayi ba dan yatara uban gajiya beda burin daya wuce yaje gida ya yi uzurin sa . Yasamu ya sake fitowa dan yin wani Aiki na daban. ******************* Dangin Mahaifiyar Khairi ne suke meeting akan yakamata su dauko khairi daga Hannu baffa . Ya za'ayi ace suna Raye zuria Amina suna wahala . Kakar khairi ta wajen uwa ce zaune take ranta abace duk yanda ya za'ayi a dauko mata khairi. Shima Saifudeen yadawo wajen su akwai ayyuka Masu kyau da kawo kudi da zasu daura shi akai Amma ace abun kunya doya suke tallah a kasuwar Sheme. Da Arzikin mu da komai muga jinin mu na wahala wallahi bazeyuba. Kallon Alhaji Abdul Aziz tayi tace wallahi duk yanda za'ai kayi kokarin amso mana jikar mu. Itama Sultana inda yanda za'ai akashe auren . Yanzu haka wallahi Alhaji hamisu kullum maganar Sultana yake dan haryanzu yana son ta. Alh yace zuwa jibi InshAllah zanje dauko ta. Sai idan ya mana gardama zamu makashi kotu dan bazeyu ba wankan kuturu da sabulu. ********************** Saifudeen zaune adakin shi yanata hada kayan sa daya wanke da agobe zewuce da Baffa yadawo. Jin Sallama ne yasashi fadada murmushin sa . Yace Akramakallahu harka iso tundazu nake ta zuba idanun ka ,shine sai dare zaka Zo ko. Murmushi Akramakallahu ya yi hannun sa rike da jakar sa yace yau hanya akwai go slow ne afuwan yayan mu. Tareda karasa shigowa cikin dakin yazauna . Sukayi musabaha tareda gaida juna cikin mutuntawa da kewar juna. Abinci Saifudeen yakawo masa , yana bude abinci ya hada rai Amma afili ya yi murmushi yace Kash saidai fa harna ci Abinci ahanya nakoshi. Fiddo kayan dake cikin leda yayi ,yafito da gwawanin madara Milo da sugar yace wannan nasu Khairi ne . Wannan kuma namu ne yafada yana kallon saifudeen dayaga murmushi kwance kan fuskar shi. Saifudeen yace harda dawainiya haka MashAllah Allah yasaka maka da Alkhairi Amma ka rage dawainiyar nan haka nasan kaima mabukaci ne irin mu. Amsa masa ya yi da Fad'in karka damu Saifudeen mun zama yan uwa nidakai karka damu. Sallamar Khairi ne yasasu maida kallon akan ta suka amsa mata waalaikum Salam. Khairi Tace Akramakallahu wajen ka nazo tareda karasowa cikin dakin Alamun tarin damuwa kwance akan Fuskar ta . Wani irin Faduwar gaba yaji gab gab gab cikin karfin halin canjin yanayin sa ,ya maida kallon sa akan khairi yace inajin ki Khairi . Shida Saifudeen zuba mata idanu sukayi danjin me zata fad'a. Cikin tsananin damuwa tace Akramakallahu headmaster ne yakoremu daga Makarantar JAN ZAKI babu laifin kwabo in ban mance ranar farko da muka fara haduwa dakai a makarantar cewa headmaster kayi JAN ZAKI ne yaturo ka . Akramakallahu azabure ya tashi tsaye yace kora........? Taku Har kullum kyauta daga Allah 09069070825 *RAI DAYA*🦜 *JAN ZAKI*🐆 Mallakar Ikilima Adam ( Kyauta daga Allah) *Paid book* Page uku yarage ingama free page wayanda basu siya ba ,su hanzarta kada abaku labari. 1️⃣2️⃣ Azabure ya tashi tsaye yace what ? Bangane ya kore Ku ba . Nan da nan duk Wata annurin dake kwance kan fuskar sa ta kau . Ciza labban sa yayi yana mai Kallon ta da idanun sa da suka kada jajir kamar an watsa masa barkono . Khairi ina takardan Koran yake yayi magana cikin kakkausar murya . Saifudeen ne yadauko kusa dashi tareda mika masa . Yana karba yashiga karantawa ,yadade yana kallon Papper kamar mai nazari sannan daga bisani yace Okk babu matsala tareda mika mata takardan yana girgiza kansa . Kallon su yayi yace Ku bari zuwa gobe zanje Na bashi hakuri InshAllah ze barsu. Saifudeen yace inhar be hakura ba tunda khairi tace JAN ZAKI yaturo ka Makarantar please nasan ganin sa zeyi wuya Amma ka kokarta koda ta Sako ne atura masa ,tareda shaida masa Makarantar dake nan cikin Funtua tana Neman Agaji . Akramakallahu kallon sa yayi yana jinjina kalaman sa ,cikin Muryan sa dake nuna raunin sa yace Khairi dan Allah kuyi hakuri. Makaranta kamar Kun koma InshAllah keda yar Uwar ki zanyi iya kokarina . Sossai Khairi da Saifudeen sukaji dadin kalaman sa . Samun kanta tayi da ce masa na gode Saida safe tayi musu tareda fita daga dakin ranta fes da Farin ciki. Rashida Mahaifiyar Najwa ce suke fira da Malam Adamu akan wannan gasar auren da za'ayi . Mummy tace Allah yatsare mana zuria da shiga wannan gasar kamar tallan kai ne. Malam Adamu yace kwarai kuwa , wayanda ma yayan nasu ke shiga gaskiya basu San zafin su ba . Kinga in Allah yayi nan da shekara biyu ko uku zamu aurar da Najwa itada Khairi InshAllah . Mummy cike da jindadi tace wallahi Malam maganar ka gaskiya ce karmuyi gaggawa wajen aurar dasu . Bashi labarin yanda Innaro ke kula da Khairi tayi . Rike da bakin sa yace Anya Matar Nan babu Wata akasa kuwa . Mummy tace haba ya zakace haka ,muyi mata kyakyawar zato Hakane kuma cewar Malam Adamu Allah Yasa dan Allah take yi. Suka amsa da Ameen. ****************** Kashe gari Tunda wuri yau Akramakallahu yatafi makaranta tareda rakiyan Saifudeen. Koda ya isa Makarantar ,kai tsaye be bata lokaci ba shida Saifudeen office din headmaster suka nufa . Kowannen su zaune bakin kofar suna kallon kofar arufe. Saifudeen yace Kaga ni bara inje kila ma ba yanzu ze Zo ba. Akramakallahu ne yakatse shi ta hanyar fadin please ka tsaya ayi komai agaban ka. Jin takun tafiya ne ya tabbatar musu dashi ne. Mamaki ne yacika shi ganin Akramakallahu da Saifudeen kofar office din sa zaune . Suna ganin sa ,suka tashi tareda bashi hannu sukayi musabaha. Sam be kawo komi aran sa ba , akan Neman da suke masa ba. Hakan yasa yabude office din sa . Yana shiga suka take masa baya . Kowanne samun wuri yayi yazauna yana kallon sa. Headmaster cikin iya taku yace Akramakallahu yaushe kafara zuwa Makaranta nan Har kafara fashin zuwa yau kwana biyu kenan baka Zo ba. Kallon Juna sukayi Akramakallahu da Saifudeen . Akramakallahu yace kadauko takarda ta kaduba akwai ranakun da aka sa bazan ringa zuwa koyarwa ba koda akwai Makaranta ba. Headmaster hannu yasa yafara nemo su file dake ajiye na malamai , yana ganin nashi zare shi yayi yasoma karantawa ,ganin inda akasa duk bayan sati biyu kwana biyu zeyi beje ba. Yasa shi ajiyar zuciya yana girgiza kai kan rashin nasaran sa. Akramakallahu yace daman mun zone akan wayannan yaran da kora jiya khairi da Najwa . Kuma nasan a dokar Makarantar babu kora Saida izinin manager ko Shugaban Makaranta. Ya akai kayi gaban kanka? Headmaster murmushi yayi yace ai babu Shugaba daya wuce ni ,kuma laifin yarinya mai girma ne dole ne yasa na kore su. Bakuma Zan Amshe su ba yakarashe zancen yana mai fadin kuna iya fita na sallame ku. Saifudeen cikin bacin rai yace wallahi baka isa ba zakaga Abunda zefaru inbanda zalinci da kun dauki mutane dabbobi laifin me yarinya tayi. Akramakallahu kama Saifudeen yayi yana mai bashi hankuri . Kallon headmaster yayi yace karka damu kanada gaskiya kai akan aikin ka kake . Shikuma akan hakkin sa yake to bari mu gani wa zeyi nasara cikin Ku. kama Saifudeen yayi suka bar Makarantar tareda masa rakiya Har gida sannan yakoma makaranta dan koyarwa . Itakuwa Khairi jin labarin Abunda yafaru yasata rushewa da kuka tana fadin shikenan ya cuce mu. Innaro ta dafa ta ,tace karki damu akwai makarantu dayawa sai acanza muku . Khairi cike da takaici tace ni babu Makarantar danake so fiye da JAN ZAKI . Akramakallahu koda yakoma makaranta cigaba da koyar da dalibai yayi cikin rashin karfin gwuiwa . Test yamusu dan yana son yagane ko suna fahimtar karatun . Duk Ajin tsit kake ji cike da nutsuwa suke rubutun su Banda Sakina dake zaune tana tauna cingam Kara's Kara's haka sautin ke fita. Kallon ta yake yana nazartan yanayin ta , cikin kakkausar murya yace kee Sakina tashi tsaye . Hada rai tayi tana cika tana basewa ta tashi hade da turo baki gaba. Ya sunan ki ? Sunana Sakina Kamal Sossai yashiga nazarin sunan nata ,Mahaifin ki a ina yake da zama babu alamun wasa a tattare dashi. Hakan yasa tace yana zaune unguwar locowst yan wanki. Shiru yayi na wasu dakiku sannan yace inason ganin Mahaifin ki daga nan zuwa gobe . In bazaku Zo tare ba to lallai ki zauna gida Har sai yasamu lokaci dafatan ki gane yana mai daga mata gira. Gabadaya daliban class din ta kasa kasa suke dariya cike da Farin ciki ,yau ansamu malamin daya iya gayawa Sakina magana , sossai suka yaba da jajjircewan Akramakallahu akan aikin sa. Samun kanta tayi da Fadin ni Mahaifina ganin sa ,ba abun wasa bane kafadi Abunda kake bukata ze turo wasu inma kudi ne ,Amma karka sa ran ganin sa agobe . Sossai ran Akramakallahu yabace hakan yasa yace mata get out cikin bacin rai. Yakara da cewa ki tafi gida na sallame ki. Dakyar tafito daga Ajin tana Ayyana aranta wannan wulakanci dayayi mata saita rama , zatasan hanyar da zatabi dan ta aure shi . Shiko tana fita yacigaba da koyar dasu har suka tashi , be bata lokaci ba kai tsaye gidan su khairi ya nufa dan suyi sallama da Saifudeen dake shirin tafiya. Koda ya iso Har saif yashirya zuwan sa kadai yake jira . Cikin tsananin damuwa yace Saif yanzu idan katafi sai nan da sati zaka dawo . Saifudeen yace kwarai kuwa ai munayi muna hutawa ne nida Mahaifina ina isa cen ze baro garin yadawo gida. Akramakallahu yace gaskiya kuna kokari wlh. Innaro ce ta kunna redio tana sauraren sabon fadarkwa JAN ZAKI akan illan cin Amana da zanba cikin aminci . Kwabe baki tayi tace oh wannan Jan zakin Allah Yasa ba Aljani bane . Daga Saifudeen Har Akramakallahu juyowa suka yi suna kallon ta. Khairi dake sauraren Redio tareda ita tace haba Innaro ya zakiyi wannan furucin nifa JAN ZAKI nan yana burgeni , da Allah ze hada ni dashi sujjada zanyiwa Allah dan godiya , Zan iya kwana inajin Muryan sa batareda gajiyawa ba . Innaro zazzare idanu tayi tace khairi kodai kin Kamu da son Jan zaki ne. Eh nakamu da son sa tabata Amsa tana turo baki gaba , tunda haka kike son ji. Kece kikasan me ake kira da so nikam ban sani ba. Akramakallahu cikin karfin Hali yace Khairi Amma da dukan Alamu maganar Innaro gaskiya ce kin Kamu da son Jan zaki . Idanun Khairi ne yacika da kwalla nan da nan suka ciko da kwalla tace Akramakallahu gaskiya na fada bansan meye so ba. Nidai na tsinci kaina da son jin fadakarwar sa . Koda ma ze ganni nasan ko kallon inda nake bazeyi ba. Murmushi Akramakallahu yayi yace to saboda me baze kalleki ba kina kyakyawar mace ? Saboda ni ba Ajin sa bace nidai Abar ma zancen nan kawai tafada tareda tashi tabar wajen. Akramakallahu da Saifudeen dariya sukayi kusan a tare. Saifudeen yace yarinyar nan tana bala'in kaunar duk Abunda ya shafi Jan zaki ,kuruciya ke dawainiya da ita. Innaro ce ta kalle su tace aiko Jan zaki yamata nisa wane mutum inji mutuwa yanzu haka yana tareda manyan Mata Masu Aji da kudi me zeyi da Wata khairi ita kanta tasan tatsuniya takeyi . Saifudeen yace Innaro bafa cewa tayi tana son Jan zaki ba , cewa tayi tana kaunar fadakarwar da yake yawan yi yakamata ki gane . Daman meye ze hada Khairi da Jan ZAKI ko baki fada ba , nasan mu talakawa ne dan haka ki gyara kalaman ki yakarashe zancen yana mai Kallon Akramakallahu yace muje ko? Akramakallahu yace Yaya saifudeen yi hakuri rashin fahimta ne shiyasa tayi maka wannan zargin. Innaro dake sake da baki ganin ran Saif ya baci tace haba Dana da wasa nake Allah ya huci zuciyan maza. Basu bi ta kanta ba suka fice daga gidan . Itako Khairi shiga daki tayi tana tunanin makomar ta inhar bazata koma Makarantar Jan ZAKI ba. Har bakin titi Akramakallahu ya rako Saifudeen tareda masa Alkawarin InshAllah su Khairi zasu koma Makaranta kada ya damu . Hango Sultana tana doso inda suke ne yasa Saifudeen kallon Akramakallahu yace kaga ga kanwata nan Sultana zuwa . Fuskokin su cike da faraa suka ce Mata barka da zuwa. Da yawwa ta amsa musu tace Yaya saifudeen Har zaka wuce ne ? Eh Zan tafi Sultana nayi rana yau . Nuna mata Akramakallahu yayi yace wannan shine malamin su Khairi a makaranta . Kallon sa tayi tareda gaishe shi cike da ladabi Ya Amsa Mata gaisuwar fuska a sake yana mai yaba hankalin ta . Yaga tsantsar kamanni dasuke itada Khairi da dukan Alamu bazata wuce shekaru shabakwai ba. Saifudeen yace Sultana Allah yayi zamu hadu Kinga sauri nake saide ki karasa gida please kije kiga kanwar ki. Allah yatsare ta fada tareda wuce su cikin jin dadi tace na tafi byeee tana mai daga masa hannu shima hannu yake daga mata . Akramakallahu sun dade suna fira akan titin kafun ya samu motar daze kaishi tasha. ******************** Babban gidan redio mai suna *kukan kurciya* wacce tayi zarra acikin garin Katsina . Wata katuwar mota ce tayi parking daidai bakin gate din. Mai gadi najin horn a hanzarce yabude gate . Kai tsaye wannan Motar mai kirar Mercedes kai tsaye tashiga farfajiyar wannan gidan redio. Jamaa dake kai kawo wajen kowa ya zuba idanu yaga waye wannan ko wacece zata shigo . Ahankali ta kashe wutar motar tareda bude motar tafito . Sanye take da Riga da wando irin exgytien marron color tayi rollin din gashin kanta da ribom ,tareda dan karamin gyale marron color , idanun ta dauke da bakin glass . Takalmin ta mai tsini ne yaja hankalin mutanen wajen dake kallon tana rufe motar ta . Suka hada baki wajen fadin MashAllah wannan yarinyar ta hadu ta ko ina. Cike da takama da izzar ta , ta iso inda taga jamaa . Zazzakar Muryan ta sukaji tana fadin barkan Ku da warhaka dan Allah inason ganin manager din gidan redio nan. Daya daga cikin yace gaskiya hajiya indai besan da zuwan ki ba. Ganin sa kai tsaye yana wahala . Hada rai tayi cikin tsananin bacin rai tace kako san dawa kake magana kuwa. To kaje ka gaya masa diyar Alhaj Kamal ce kana Fadin haka yasan ko wacece cikin bacin rai take magana. Angama ranki yadade bara muje mu fada masa. Koda ya iso office din knocking yayi aka bashi damar shigowa. Yana shigowa ya sanar masa da wacce ke Neman sa. Manager cike da mamaki yace diyar Alh Kamal anan wajen . OK jeka shigo da ita yafada cike da tunani me tazo nema. Koda suka iso da ita samun kujerar dake face da nashi tayi tazauna tana mai Kallon sa. Tareda cire madubin tace Ranka yadade barka da Aiki nasan ka kosa kaji meyakawo ni wajen ka. Gyada mata kai yayi yace ina sauraron ki tareda bata duk hankalin sa. Cike da wayau da kissa tace Gidan redio Zan bude Nawa nakaina sainake ganin babu fadakarwa dake Jan hankalin Al'umma sama Dana Jan zaki. In bazaka damu ba zanso Ku sanar dani ta wani hanya kuke bi wajen samun bayanan sa ko ince fadakarwar sa. Ajiyar zuciya mai karfi Manager ya sauke yana mai Kallon ta , yana murmushi yace gaskiya tunda muke samun bayanai akan jan zaki babu takamaimai waje daya da zamu ce nan ne kadai ake ajiye Mp3. Tunda kina bukata kibari da mun samu sai mu baki kema ki saka hakan zefi sauki . No nidai Ku gayamin ta hanyar dakuke bi nima basai na jira Ku ba. Manager dago kai yayi yana kallon ta yace. Sako ne yake zuwa mana ta email akan Jan zaki ya aiko da Mp3 waje kaza . Mu kuma Zuwa muke mu dauka damun kawo sai mu daura duniya taji Kinga yanda muke samu kuma duk gidan redio dake fadin kasar nigeria haka sukeyi wajen samun jawaban sa. Tunda kince zaki bude gidan redio ne . Dakin bude kibamu tallah nasan zeji da kunne sa. Ze saki a layin wayanda ze ringa turowa wannan faifan audio . Zazzare idanu tayi tace uhmm Kaga ni Zan tafi kabani Email din sa. Dauko papper yayi kusa dashi tareda rubuta mata . Jan ZAKI 111 @ gmail.com Cikin tsananin Tashin hankali take kallon email din ,dauka tayi tareda da saka shi a jakar ta . Godiya ta masa sannan tabar office kai tsaye gida ta nufa cikin hanzarin ta kamar zata tashi sama dan sauri. Shiko Manager tana fita ajiyar zuciya ya sauke yace uhmm wannan yarinyar akwai makirci waini zatayiwa wayau . To Ni babu ruwana da fallasa sirrin mutum mai Amana . Koda Sumayya ta isa gidan bata gama daidai ta parking din motar ta ba. Tafito tayi gidan gadan gadan Mai gadi na gaishe ta bama tasan yanayi ba. Kai tsaye babban Falon nasu ta isa , cike da mamaki take kallon Abban su yana magana cikin bacin rai da Sakina. Yace wani dan Iska ne zece dole sai Mahaifin ki yazo zaki koma Makarantar waye uban shi. Sakina tace wallahi dan matsiyata ne kuma wallahi karatun Addini kadai yake koya mana Amma bakaga iyayi ba kyawun sa kadai ya taimake sa. Alhaji KAMAL yace to yayi kadan zesan yataboni ya tafka babban kuskure wallahi. Dawo da kallon kan Sumayya yayi wacce tayi mutuwar tsaye. Yace lafiya kuka tunda kika shigo na ganki sai aslow? Cikin raunin Murya tace Daddy ga email din Jan zaki nasamo tareda mika masa . Yana karba yashiga warware wa cikin tsananin Mamaki yace wannan yaso yayi kama da email din Muhammad marigayi . Sumayya tace kwarai Kuwa banbancin sunan JAN ZAKI da akasa kadai ne. Wani uban zufa ne ya keto masa yace karki damu anjima zamuyi magana . Bata labarin Koran da akayi wa Sakina yayi. Sumayya tace wani mahaukacin malami ne lallai yakira ruwa . Daddy yace kwarai kuwa Kaga dan Iska wai Mahaifin ta yake son gani da kansa. Gobe zantura drever na yaje shida Sakina wallahi yana hanata zaman Aji zega yanda zanyi dashi cikin tsananin bacin rai yake magana. Sakina tace nidai banson a kore shi please dan wallahi na Kamu da son sa. Zazzare idanu Daddy da Sumayya sukayi suna fadin soyayya fa kikace lallai yarinyar nan meye hadin ki da talaka . Mummy dake shigowa falon tace ai suma talakawan mutane ne ,ai babu Wanda yazo duniya da Arziki . Daddy rasa amsar daze bata yasashi yin dogon tsaki tareda barin dakin . Itama Sumayya kai tsaye dakin ta ,ta nufa dan daukan laptop dinta zata saka Email din Jan zaki tareda tura masa Sako . Mummy kallon Sakina tayi tace haba yata meyasa kuka raina talakawa ne dan hakkin daka raina shike tsole maka idanu . Sakina turo baki tayi gaba cikin shagwaba tace mummy ai malamin ne bashida mutunci . ****************** Baffa agajiye yakaraso gida Sallama dauke Abakin sa. Khairi najin Muryan sa aguje tafito daga dakin nata ,be Ankara ba saiji yayi tayi masa wawan runguma tana murmushi oyoyo Baffa kaganka kuwa Baffa wallahi kayi kyau kayi haske da kiba . Sossai ya Dara yana mai shafa kanta yace Alhamdulillah nayi tozali da yar auta na . Innaro tana dakin ta ,tana zuba magani cikin abinci khairi dan yau shine karo na biyu da Khairi zataci abincin nan ,duk da taji Muryan baffa fadi take azuciyar ta Allah Yasa tayi nasara ayau sannan tayi nasara ana ukun daya rage . Ajiye kwanun tayi tareda fitowa tsakar gidan lale lale marhaba da maigida na dafatan ka iso lafiya. Jakar kayan sa dake ajiye ta dauka tayi ciki dashi. Shiko Baffa dakyar ya samu ya banbare Khairi daga jikin sa yana Fadin bara inje inyi wanka ko saimuci abinci tare. Zazzare idanu Innaro tayi jin Furucin sa . Caraf ta karbi zancen habawa aini da Khairi zamu ci Abinci kaikuma kaci naka. Murmushi yayi yana mai Kallon khairi da tayi kasa da kanta . Kai tsaye bandaki yashiga dan yin wanka kokan yafito Innaro ta mikawa Khairi abinci tana mai fadin yata maza muci abincin nan dauko spoon biyu tayi kamar da gaske ci zatayi hakan yasa Khairi tasoma ci . Tana ganin khairi taci kusan rabin kwanun azuciyar ta sai fadin Alhamdulillah take afili kuma tace sauran Nawa ne Khairi maza kije ki share dakin baffa Sam na mance yau zedawo . ********************** Kashe gari Motocine sunkai goma suka paka daidai kofar Makarantar Jan zaki. Ahankali mutanen dake cikin jerin motocin suke fitowa kowannen su sanye cikin bakaken kaya suite . Basu tsaya bata lokaci ba kai tsaye suka cusa Kansu cikin Makarantar. Office din headmaster suka nufa . Iske shi sukayi zaune tareda drever su Sakina akan Koran da Akramakallahu yayi mata. Cikin tsananin Tashin hankali yake bin kowanne su da kallo . Sake da baki yace bayin Allah daga Ina haka? Daya daga cikin su ,yace mu ma'aikata ne , daga Aliyu Jan zaki munzo da............... Taku Har kullum kyauta daga Allah Karku Manta paid book ne . Saura page uku agama free page. 09069080725 *RAI DAYA*🦜 *JAN ZAKI*🐆 Mallakar Marubuciyar KAIKAJAWA KANKA KANWATA RAYUWAR MA'AURATA sabon Salo *Last Free page* Daga wannan na gama na bati duk me bukata ya tuntubi lamba kamar haka. 09069080725 *Duk Wanda zesiye* *littafin nan dan yafitar na roke shi Dan Allah yamin** *magana in dawo masa da kudin sa , ko kuma yake da niyar siya to kada yasiya inhar ze fitar* Kudin karatu ne, ba kudin mallaka ba Karku mun Abunda kukayi a littafin KANWATA please dan Girman Allah na roke Ku. 1️⃣5️⃣ Cikin zazzare idanu yace bawan Allah lafiya kuwa nan fa Makaranta ce wajen koya tarbiyya , ya zakazo kana Aikata badala gaban dalibai . Caraf idanun su ,suka tsarke cikin juna ,wani muguwar Faduwar gaba Akramakallahu yaji zuciyar sa tanayi gab gab gab da karfi. Alhaji KAMAL cikin Razani yake kallon Akramakallahu , Muhammad yafurta ,sannan yafara girgiza kai , yace A'a mafarki nake . Akramakallahu cikin around jarumta yace bakayi karya ba , yar taka ce tagayamaka sunana ko. Ba wannan ba , Makarantar nan dauka na Aiki akayi ,kuma Shugabar Makarantar yaban daman in dauki doka a hannuna . Amatsayin ka na Mahaifin ta , kamata yayi kazo cikin salama sai mu sasanta ta koma Aji ,Amma tunda kazo da rigima daga kai Har yar taka kada inkara tozali da kafafun naku a wannan Makarantar , nasan Kanada tarin tambayoyi sokake kaji uban wa ya bani wannan ikon ko. Uhmmmm Allah shike bada dama da iko ba mutum ba dan haka get out yafada a tsawace Saida jijiyoyin kansa suka mimmike . Alhaji KAMAL da magoya bayan sa , sossai suka rude da lamarin Akramakallahu. Alhaji KAMAL sassaita nutsuwar sa yayi yace kasan dan matsiyata beyi iya samun wuri ba. Jibi suturar dayake jikin ka ,kaikasan talauci be goge ba ajikin ka . Wallahi tallahi indai ni uban Sakina ne Zan nuna maka izzata yakarashe zancen yana fadin kee Sakina Zo muje . Makarantar nan na yayan talakawa ne . Kin wani damu kanki akan matsiyatan malamai . Abokan tafiyar sa , da mamaki suke kallon tsaurin idanun Akramakallahu. Kasaitaccen murmushi Akramakallahu yayi yana kallon yanda yaja hannu yar sa itakuwa tana turjewa batasan tafiya . Hankalin sa yadawo akan Dalibai da kowannen su , yayi cirko suna kallon Abunda ke wakana kwabe baki sukayi . Kowacce da Abunda take fadi akan Sakina da Mahaifin ta. ***************** Sallamar Innaro ne yasa Malam amsa mata , Bismillah yace .. Hakan yasa tashiga tareda samun wuri ta zauna. Cikin tsananin damuwa suka gaisa tace Malam nayi amfani da maganin da kabani wallahi yaci dan ga Yarinya nan ta bushe idanun ta , tace auren Gasa take so. Yanzu kuma wani tunanin nayi Wanda abaya banyi shi ba . Nan tabashi labarin dangin Mahaifiyar ta Masu Arziki ne ,da kuma dalilin dayasa tazo , tanason ya taimaka a warware sihirin daya kama khairi. Malam kallon ta yake yace Safara'u tun ran Gini tun ran zane ,wannan sihirin ba yanda za'ai a warware shi dan wallahi yakamata kenan saidai kawai Ku zuba idanu kuyi kallo. Nan da nan wani uban zufa yafara sassafo wa Innaro cike da damuwa tace wallahi da nasan jikar Masu Arziki ce bazan mata wannan Asirin ba , saidai in samu hanyar da Zan ringa tatsar dangin su . Malam yace Saidai idan tayi auren za'a iya raba auren , tadawo gida. Ko kuma ana daurawa da awa daya ko biyu asa mijin ya sake ta ,Yana sakin ta asirin ze warware jikin ta. Innaro cike da gamsuwa tace tayarda ta da hakan . *********************** Baffa zaune kofar Gidan nasu yana waya da Saifudeen akan yakamata su dau hutun Wata daya basuje kasuwa ba. Saifudeen yace Baffa yanaga yau sai ahankali gayamin yakai Mahaifina wani Abun na damun ka ne? Cikin Damuwa Baffa yashiga bashi labarin Abunda ke Faruwa . Zumbur Saifudeen yatashi daga zaunen dayake yana maimaita auren Gasa tareda daura hannun sa akai yana salati .yace Baffa InshAllah gobe Zan dawo gida tunda kace mu dan huta . Baffa inhar nazo karka hanani hukunta Khairi wannan wace irin yarinya ce , wacce batasan kunya ba. Jiki Asanyaye Baffa yace kana ganin Khairi zataji tsoron ka ta janye ? Kwarai kuwa InshAllah haka nake tunani . Allah yakawo ka lafiya Dana kafun kataho ka sanarwa makota , zamu dau Hutu na wani lokaci . InshAllah Baffa bakada matsala. ********************* Tsohon headmaster yayi shigar shi ta Alfarma tareda daukan motar haya zuwa gidan Alhaji KAMAL. Koda ya isa ya iske shi a farfajiyar gidan zaune tareda manyan abokan sa ,suna shawara akan Akramakallahu. Sallama dauke Abakin sa yakaraso , su kuwa cike da faraa suka tarbe shi tareda yin musabaha ,samun wuri yayi yazauna kusa dasu cikin damuwa ya sanar musu Koran da Jan zaki ya masa akan wannan yar matsiyatan. Alhaji KAMAL yace yanzu kana nufin shi Jan zaki duk Abunda akeyi a makarantar sa yana samun labari kenan , shege saidai baze fitoba burin sa kullum yayi ta jefa mana harsashi . Headmaster samun wuri yayi yazauna yace ranka yadade wallahi korata yayi ,kuma yarinyar nan inason na wulakanta ta . Ita da Alhlin ta . Alhaji Garba dake sauraren sa yace to me zaka mata ne ya tsaresa da idanu cikin tsananin tsoron Furucin sa. Headmaster yace wallahi Fyade Zan mata kawai shine illah da Zan mata da baze taba goguwa a cikin zuciyar ta ba. Dukan su suka sheke da dariya Banda Alhaji Garba daya hada rai . Yace Ku tsaya wannan maganar ba abun dariya bace , kunsan me ake nufi da fyade kuwa. Nasan cikin mu babu Wanda yake son ayiwa yayan sa , sai nake ganin wannan ba ita bace mafita ba. Alhaji KAMAL Kamal yace to menene mafitar ? Nidai Abunda nake gani shine kawai Ya aure ta sannan ya mata duk wani wulakanci hakan zefi , tunda iyayen ta talakawa ne bazasu hana shi ba. . sossai sukayi Naam da shawaran sa . Headmaster yace Alhaji daman nazo na Amshi cikon kudi na , gobe zanyi tafiya sati biyu zanyi indawo Dana dawo kai tsaye gidan su Yarinyar zanje Neman aure . Alhaji KAMAL yace bani account number in saka maka kudin , sannan Inka dawo kazo muyi shawara akan shegen malamin nan dan wallahi bazan kyaleshi ba , dan banza ni zegayawa bakar magana . Cigaba da tattaunawa sukayi akan yanda Sumayya zataci gaba da bibiyar Jan Zaki da kalaman soyayya. *********** Akramakallahu sallama yayiwa Baffa akan zeje yadawo tareda barin su . Tafiya yake cikin hanzarin sa harya kawo bakin titi. Yakai kusan mintina bakwai tsaye yana kalle kalle gefen sa hagu da Dama. Sannan yaciro tsadaddan Wayar kiran iPhone tareda danna number yayi dialling. Buga daya suka daga , cikin Muryan sa mai dauke da sirrika yace Harna iso kuna ina ?cikin Fada yake magana Bejira cewar su ba ya katse wayar yana mai cigaba da kallon agogon hannun sa. Abunda befi minti Biyar ba saiga motocin sun iso tareda parking daidai inda suka gansa. Cikin Yaran sa yace ranka yadade dan Allah kayi hakuri bamu san kataho ba . Beko kalle su ba yasakai yashige motar da dan uwan sa yake ciki. Yana shiga suka rufe motar gam . Adu'oi yafara karantowa yana kallon Salim dake bin sa da kallo alamun tarin tambaya. Salim yace Haidar Amma ba inda zakaje da wannan kayan na jikin ka ,habawa saikace an tsintoka a rami. Akramakallahu tsaki yayi yace a kabari aka hakoni. Maza akaini gidana na JRA zanje nayi wanka na shirya yajikin Nuriyat ne ? Gaskiya Nuriyat taji sauki tunda likitoci sukayi ta bata kulawa harma ta warware fa. OK naji dadin hakan , ni Kaga kadaina samun idanu kasan me yaban mamaki ne? Salim yace saika fada inajin ka. Wallahi yarinya Dana ke kwana gidan su ce ,ta feshe idanun ta wai aure take so ,nifa bantaba ganin fitsararriya irin ta ba. Salim yace Toka aure mana yana mai Kallon yanayin sa. Sossai Akramakallahu yahada rai yasha kunu yace kasan maganar banzan ce banso me zanyi da wannan kwailan , wacce take saka iyayen ta kuka . Ni Mahaifin ta ne abun tausayi dan inta nine , su barta mana tayi auren shasha yarinya kawai. Salim dake kallon reaction din sa yace kaiko yada daukan zafi haka , kodan yayan ta abokin ka ne? Shirune yabiyo baya ya jingina jikin sa da kujerar motar yana mai lumshe idanun sa. Salim ganin Miskillanci yatashi yasa shi fadin mutum sai iyayi kadauko fira mai dadi kana bani daga bisani ka kyaleni ina magana ni kadai nifa tsiyata dakai kenan kasani ko in auri Yarinyar ne. Akramakallahu ko kallon sa beyi ba bare yasa ran ze bashi amsa . ****************** Kwanci tashi asaran mai rai gashi Har lokaci yazo gobe ne za'ayi gasar . Mai shela daga gidan mai gari yakara fitowa yana shela. Jamaa gari mai gari yace a sanar muku gobe ne za'ayi gasar bayan anyi sallah juma'a Allah yaba mai rabo sa'a Duk matasa dasukaji harda khairi aci kowannen su sai fadi yake gaskiya ba za'ayi babu shi ba , yarinya mai kyau da haduwa bazasu bar banza ta fadi ba. Khairi cike da Murna gobe za'ayi gasar Najwa ta kalle ta cikin kuka tace haba Khairi bazaki janye ba kowa yamiki magana kinki sauraren su. Khairi cike da raunin ta ,tace wallahi inajin zafin ganin Baffa da Yaya saifudeen da Sultana suna cikin damuwa saboda ni , Amma wallahi nakasa gane dalilin dayasa na bijire musu wlh Najwa inajin zafin hakan acikin raina. Mummy ce ta taho wajen nasu duk firan dasuke yi akan kunnen ta . Cikin kuka tace khairi nice Na shayar dake inma bakiji maganar kowa ba aikin ji tawa ko. Tashi Khairi tayi tace wallahi Mummy bansan me Ma'anar aure ba , bansan yanda ake zaman gidan Miji ba . Kawai na tsinci kaina da son auren ne ,dan Allah ki yafemun kada kiyi kuka dani Uwata . Rungume Mummy tayi sukaci gaba da rera kuka . Itakuwa Najwa hannu ta daura akai tana fadin shikenan tawa ta kare khairi bazan iya Rayuwa babu ke ,nono daya muka Sha , bansan Waze aure ki anan garin yake kokuwa wani wurin Allah masani . Khairi sakin mummy tayi ta dawo ta rungume Najwa cikin kuka tace kuyafe ni dan Allah. Wallahi bansan meyasa na Aikata haka ba. Malam Adamu ne yashigo yana kallon yanda suke kuka zuciyar sa ta karye jikin sa yayi sanyi yana fadin oh Allah ka kawo mana agajin wannan musiba . Cen bangaren Innaro sossai tashiga damuwa ganin yanda Baffa ya rame duk yafita hayyacin sa . Kudi yafiddo akalla zasu kai Dubu dari yakirawo Saifudeen yace gashi kaje kasuwa kasiyewa Ummulkhairi tukwane da dinkakkun Shadda kala biyu da takalmi da jaka Wanda zata sanya agobe. Sannan yakara bashi Wata dubu hamsin yace wannan kuma Shadda zaka siyo mana nida Malam Adamu Wanda zamu sanya wajen daurin aure. Kowannen mu shaddar dubu goma zakasai mana kasa Amana dinki a kasuwa ,sauran kudin kayi cefane abinci da za'a dafa gobe . Saifudeen da idanun sa , suka kada yace Baffa saidai insiyo kayan Khairi da naku ,Amma cefane sai mata ,zankaiwa mummy kudin sai tayi. Baffa yace hakane To ka kai mata kaji Dana . ********************* Suna iso babban Falon nasu cikin tafiyar sa mai nuna ,kwarjinin sa. Yakaraso Falon tareda samun wuri yazauna . Kallon ma'aikatan da suka kewaye shi yayi , yace ina Nuriyat take . Kokan yagama rufe baki yahangota tana saukowa daga kan matakalan tana sanye cikin bakar habaya tasha makeup hannun ta dauke da awarwao. Kallo daya ya mata yadauke kai. Koda ta iso Falon dukar dakai tayi cike da ladabi tace uban mu maganin kukan mu barka da iso wa. Samun wuri tayi tazauna kujerar dake face din sa ,tace nasan kashiga damuwa akan rashin lafiya ta Amma Alhamdulillah na warke ta dalilin kulawan ka . Allah yasaka maka da Alkhairi. Magoya bayan sa ne ,suka amsa da Ameen , shikuwa cigaba da danne danne wayar sa ,yake . Harta fidda ran zeyi magana saita ga yatashi tareda yi Mata kallo na wasu dakiku ,sannan yace yawwa Inason ki zauna cikin shiri kowani lokaci ,zakiji sakona . Zazzare idanu tayi tace kana nufin ka Amince zaka aureni ne. Kalaman ta , sun matukar girgiza shi yace Nuriyat yaushe muka fara wasa nidake da Har raini yashigo ciki. Dukar da kanta kasa tayi tace Afuwan mistek aka samu . Salim dake shigowa falon yace Nuriyat wai me yake burge mata ne akan wannan miskilin . Kasa magana tayi ganin yana wajen , shikuwa be kalli inda Salim yake ba. Yace idan kagama kazo mu tafi ko. Salim bin bayan sa , yayi sukayi Wannan dakin sirri tare , tareda fita , ta bayan gida kai tsaye motar Taxi dinsu suka hau daze kaisu Har gida cen gidan su dake karkashin kasa. ***************** Mamy zaune adakin ta itada Nusaiba suna hiran gobe ne zata fita zuwa cikin gari Nusaiba tace mummy wallahi kibari in raka ki. Mummy cike da tsoro tace rufan Asiri ni kaina ba karamin artabun muka Sha dashi ba , harya amince , yazo yaji dake zaaje cewa zeyi bazan fita ba . Kinsan kuwa in yahana dole na hakura dan yafini gaskiya. Nusaiba tace Allah yakaimu . Wai yaushe ne zamu koma cikin gari da zama ne Mummy duk da dai anan din ma ,bamuda matsalar komai saidai bamu ganin mutane irin makwata ,kawaye duk babu su. Murmushi Mamy tayi tace InshAllah wataran zakiyi su karki damu . Aliyu Jan zaki , kusan atare suka iso wannan wajen jejin Tareda shiga ramin suka rufe ta ciki. Maaikatan na ganin su , suka fara barka da zuwa ranka yadade . Daga musu hannu yake batareda ya tsaya ba. Kai tsaye falon Mammy yanufa shida Salim , Aku na ganin sa aguje yayo kansa tareda hawa kan kafadar sa yace ranka yadade kana sane kuwa jibi ne zamuje kasar America kan harkokin computer da kake son bude kamfanin sa a Nigeria. Dafa kai yayi yace oh My God wallahi gwamma daka tunanin dan Lele yafada yayin da yake doka sallama adakin Mamy . Lalale lale marhaba da yayana cewar Mamy . Cike da ladabi suka duka Har kasa shida Salim suka gaishe ta . Nusaiba dake kallon yanda yakarayin kyau da haske ,tace gaishe su cike da ladabi amsa mata sukayi . Samun wuri sukayi suka zazzauna inda kukun Aliyu yayi sallama hannun sa dauke da su lemun juice da cincin ya ajiye akan center table dake tsakiyar dakin. Tareda jera musu kofuna gaban su , tsiyaya musu yayi cikin ban girma yace Yallabai ko akwai Abunda kake bukata ne ? Daga masa hannu yayi alamun babu hakan yasa kukun nasa yafice daga dakin. Mamy cike da Jin dadi take kallon su ,suna shan lemu tareda yin gyaran Murya tace Aliyu gobe da karfe Nawa Zan fita ne? Dago kai yayi yana kallon ta ,dan shi Sam yama mance da zancen fitan ta. Dafe kai yayi yace oh Ashe maganar fitan tana nan haryanzu. Eh tana nan haryanzu mana tabashi amsa tace kai nake sauraro ? Shiru yayi kamar me nazarin wani Abu yace ki shirya karfe goma , inason kidawo gida kafun ayi sallah juma'a zanyi wa drever magana da zaran kinshirya.. Cikeda Murna tace Allah yamaka Albarka Dana . Tashi yayi dan agajiye yake yace zamu shiga daga ciki Mamy dan Allah banson akawo abinci har sai na tashi daga barci . .cikin gamsuwa da hakan tace babu matsala , sossai yake Lura da Nusaiba yanda ta rame dan kwana biyun nan yanason yazauna da ita yaji damuwar ta ,Amma kuma yau gajiya ta masa yawa. Dan zuwa dare zekoma cen gidan su khairi . Yana ficewa yabar Salim akun sa,sauka daga kan kafadar sa yayi yadawo kan Mamy yace . Mamy Aliyu fa yana fama da Ciwon zuciya Daga Mamy Har Salim da Nusaiba zazzare idanu ,suka soma yi . Kallon akun tayi tace ya Akai kasan da haka. Shiru yayi yana kalle kalle kada Aliyu yafito yaji Abunda yake fade . Mamy nima waya naji yanayi yana fadin in yatafi Amerika zega likitan sa . Innalillahi wa'innalairajun sukayi ta maimaita wa . Mamy ta fashe da kuka tace haba Aliyu ina uwarka har kanada sirrin dazaka boye mun. In wani Abu yasameka bazan gafartawa kaina ba . Aliyu Banda Miji Amma ka zamemin garkuwa . Salim da idanun sa yaciko da kwalla yace Mamy meye mafita ne . Tunda nake dashi ban taba ganin yasha magani ba hakan yana nuni da be damu da lafiyar sa ba. Amma kibari yau yana fita Zan binciki dakin sa ,inhar akwai maganin dayake Sha Zan dauko in nuna miki muyi masa yan dabaru daze ringa Sha. Mamy cikin gamsuwa da bayanan sa , tace dan Allah kayi kokarin haka . Nikam bazan nuna masa nasan komai ba , harsai kadubo mun shedar da Zan kamashi da hujja. Kashe gari. Babban rana ce mai cike da dumbun tarihi arayuwar Baffa wacce beso tazo masa ahaka. Sossai Gidan Baffa yacika da dumbun jamaa ana ta girke girke dangin mummy duk sun Zo. Sultana kuwa tazo da makwafta ta harda kawaye. Sossai cikin gidan ake ta hada hadan , Dora girki . Akramakallahu tun safe yatafi Makaranta sai kusan karfe daya yadawo gida inda yaci karo da Baffa da Saifudeen ahanya. Cike da mamaki yake kallon su kana ganin su kasan basa cikin hayyacin su. Baffa yace yawwa gashi nan ya iso Karasowa sukayi kusa dashi tareda kama masa hannu shida Saifudeen suka jashi gefe daya. Cike da Mamaki yake kallon su ,sai ganin Baffa yayi yana zubda hawaye Masu zafi daga cikin zuciyar shi. Yace Akramakallahu dan Girman Allah da kaunar ka da manzon Allah . Kataimake mu , dan Allah kashiga gasar nan ,mun San kana shiga zakaci dan kacewa Saifudeen ka iya buga kwallon kafa. Cikin tsananin Tashin hankali Akramakallahu ke kallon su yace me kuke nufi idan Har nashiga gasar . Saifudeen yace inason abuga kwallo kafa dakai na auren Khairi wlh nasan zakaci tunda yan garin nan bawani iyawa sukayi ba , durkushewa kasa yayi tareda rike kafafun sa ,yace koba dan ni ba ,kayi dan Baffa da baya barcin kirki . Dago Saifudeen yayi yace kuna nufin inhar naci Gasar aura min khairi za'ayi aini ban shirya aure ba , Banda sadaki. Baffa yace wallahi inada shi Zan baka , banason khairi ta samu mijin banza a wannan gasar ba Abunda ba mijin kirki ake samu ba . In andaura ko zuwa dare ne , kana iya sakin ta . Kaga dai burina yacika kuma Gasar baza'a maimaita shi ba sai wani shekara. Ajiyar zuciya mai karfi Akramakallahu yasauke yace na amince Baffa karka damu zanshiga Gasar nan kodan in taimake ka. Tunda Kuma Kun taimaka min. Fuskar su , cike da faraa baffa yace Allah Yasa kagama da duniya lafiya nagode InshAllah zakayi nasara arayuwar ka. Sossai yaji dadin kalaman sa , cike da Jin dadi yace muje ko . ********************** Drever ne yashigo da Mamy cikin unguwar yan bokolo inda ta iske dukan garin duk ya hargitse ana ta saurin za'a je gasa bayan an idar da sallah juma'a. Mai gari duk kowa ya isa Filin gasar . Itakuwa Mamy sauka tayi daga cikin Motar tana sanye cikin doguwar Riga ba , fuskar ta dauke da Nikaf tafiya take cikin hanzarin ta . Harta karaso daidai inda ake wannan Gasar rasa wanda zatayiwa tambaya tayi kasantuwa kowa hankalin nakan wasan da za'a fara. Khairi cikin shigar ta , na Alfarma Mummy ta shirya ta , tsaf tareda yi Mata makeup sossai tayi kyau tana baza kamshi. Yadiko na zaune gefen ta. Tace oh khairi ko waye angon namu da zamu aura ne. Murmushi kwance akan Fuskar khairi tace ina Zan sani kibari su dawo su bamu labari ko. Sultana dake tausayin kanwar ta , tace eh lallai Khairi kin girma murna ma kike . Shiru khairi tayi tace Afuwan antina. Sultana tace bakomai tareda Daukar wayar ta , tayi tareda daukan ta Selfi tayi musu itada Najwa . Yadiko ma tace da ita za'a dau hoton . Dole yasa Sultana daukar ta hoto tareda Amarya . Sultana tace khairi zaki ajiye Makarantar ne tunda zaki daura aure. Zazzare idanu khairi tayi tace A'a bazan daina ba . Kullum sai mun tafi ko Sultana tana mai Kallon ta. Sultana da duk jikin ta yake a mace tace hakane InshAllah indai muna kusa. ******************** Saifudeen kayan kwallo yaba Akramakallahu yasa ajikin sa. Suka rakasa wajen gasar daman anyi na sauran na Khairi kadai yarage . Jiran isowar Akramakallahu yasa kowa yayi cirko cirko yana kallon ta inda zefito. Gabakidaya wajen yadauki shewa yayinda yashigo Filin gasar hakan yasa ,mai gabatarwa yace ga dayan ya iso maza ku matsa baya abada fili ayi agama muje massalaci wajen daurin aure . Mamy cikin zazzare idanu tace wannan kamar Aliyu kokarin shiga taron take , Masu tsaron wajen sukace baiwar Allah Ina zakije ne ? Mata basa zuwa wajen dan Allah koma baya yanzu za'a gama ,idan angama kina iya ganin Wanda kike nema. Komawa da baya tayi tana zazzare idanu ,soma kiran sunan sa tayi tana Aliyu Amma ina bayajin ta. Dan hankalin yayi yayi nisa akan kwallon da suke bugawa. Baffa da Saifudeen da Malam Adamu da wasu jamaa sai adua suke Allah yaba Akramakallahu nasara. Ganin wasan yayi nisa babu Wanda ya jefa ball cikin raga yasa hankalin baffa yatashi. Kokan su rufe baki sukaga ansaka ball din cikin raga wani ihu jama'ar wajen suka dauka suna Fadin . J A Akramakallahu yaci gasar auren Ummulkhairi. Cikin Razani Mamy take kallon andaga Aliyu Jan zaki sama . Bakin ta na rawa tana kokarin karasowa wajen sa. Taji an rike mata hannu a razane ta juyo tayi tozali da............. Taku Har kullum kyauta daga Allah *RAI DAYA* 🦜 *JAN ZAKI*🐆 *Saura page daya ingama free page Ku hanzarta kada ayi tafiyar babu ku* *Paid book* Domin karin bayani Ku tuntubi akan wannan number 09069080725 Akwai Group Dina Facebook mai suna . ( Kyauta daga Allah novel's) Kuyi following Dina. 1️⃣4️⃣ Kamar dangin Margayya Amina , Baffa yace sune kam harda Mahaifin ta. Sake da baki suke kallon su Har suka rufe motar su. Kowannen na sanye cikin babban gezner milk color fuskokin su sanye da gilashi. Wani kallo suke bin unguwar da dashi suna yatsine fuska , sannan suka dawo da kallon su akan gidan Baffa tareda Jan dokon tsuki. Alhaji Abdul Aziz cikin bacin rai yace ace shekara da shekaru gida yana nan ayanda yake babu sauyi Allah ya wadaran naka ya lalace . Daga Baffa Har Malam Adamu kallon sa ,suke ganin sun karaso wajen nasu yasa Baffa yin Murmushin yake yace ranka yadade yau kune agarin namu . Bismillah yace yana mai nuna musu gidan. Kwabe baki sukayi dukan su , sukace ina gidan yake da zamu shiga nan ma , ya isa cewar Alhaji Abdul Aziz. Baffa yace Bismillah ina sauraren Ku ? Alhaji Abdul Aziz yace kasan dai Abunda yakawo mu , be wuce na Yaya , Ummulkhairi muke son dauka tareda Saifudeen ita zamu sanyan ta a Makaranta. Shikuma waje zefita taredani kan harkan kasuwanci na. Wannan shi yakawo mu , dan haka kashiga ka fito mana da Ummulkhairi Akira Saifudeen . Sannan Ita Sultana a nuna mana gidan Mijin nata ,mu biya muga lafiyar ta. Tunda yafara magana Baffa dukar dakai yayi kasa yana kukan zuci. Jin yayi shiru ne yasa shi Fadin , Agaskiyar magana bazan taba baku yata ko Dana ba. Saidai kuyi hakuri dan yaran suna dauke da jinina ,bazeyu Ku dauke su ba. Malam Adamu yace gaskiya ne bayin Allah , gaskiya bazamu iya baku yaya ba. Cikin tsananin bacin Rai Alhaji Abdul Aziz ke magana shida kannen sa. Suka ce karfa Ku raina mana wayau dan kunga muna lallaba Ku . To wallahi idan baku bada su ta lalama ba ,Zaku bayar ta tsiya. Fitowar khairi yasa su , hankalin su yakoma kanta tana sanye cikin Wata Riga da zani kodaddiyar Atamfa . Karaso gaban Baffa tayi tace Baffa na lafiya na gansu cikin Tsananin Tashin hankali. Baffa yace Khairi kiji bayin Allah nan dangin Mahaifiyar ki ,nasan kin gane su ,wai sunzo su tafi dake. Kan ubancen Khairi ta Furta tareda fuskantar kakan nata tace , wallahi babu inda zanje , meye hadani daku ,takamar Ku Arziki ,mu kuma takamar mu Allah. Alhaji Abdul Aziz yace Haba Ummulkhairi nifa Na haifi uwar ki Amma kike fada mana haka , nan fa kakannin ki ne. Khairi cikin kwabe baki tace Ai uwata kuka haifa bani ba. Kuma data haifeni anan gidan ta haifan , kuma anan aka raineni nidai bazan taba binku ba takarashe zancen tana mai kama hannun Baffa da Malam Adamu tace muje ko . Duk Abunda akeyi akan kunne Innaro dan ta labe zaure tana saurare. Motar su take bi da kallo tace ikon Allah kenan , Mahaifiyar Amina iyayen ta , Masu Arziki ne. Ganin khairi sunfice tareda Malam Adamu , sunbar bakin nan tsaye yasa ta fito Sadaf Sadaf Ganin suna shirin shiga motar su , cikin bacin rai . Ku dakata Bayin Allah tafada tana mai karasowa wajen su . Kallon ta suke harta karaso , cike da ladabi ta gaishe su ta sanar musu matsayin ta awajen khairi. In bazaku damu ba , zanyi iya kokarina inga na kawo muku khairi Har gida tareda Saifudeen Amma Ku gayamun me Zan samu idan nayi haka. Wani uban kallo suke jifan ta dashi dukan su , Alhaji Abdul Aziz yace matsiyaciya mayun kudi ,kotu ce zata karban mun su bake ba. Cikin kannensa wani yace please kabari muyi yanda tace mana , nasan ko dubu hamsin ka bata zance yakare. Kallon Innaro sukayi da tayi sake da baki yace , bamu lambar wayar ki ,in bukatan haka yataso Zan kira ki. Cike da Murna Ta karanto masa number ta ,tareda tsayawa tana jiran me zasu ce , ganin taki wucewa ne yasa Musa daukan dubu Biyar daga Aljihun rigar sa yabata , cike da murna ta karba tana farin ciki. Ganin suna shirin tada mota tace wallahi Khairi bataci tana koshi gidan nan , meze hana kodan taliya Ku bada kudi asiye aringa dafa mata kafun , Allah yadawo muku da ita. Alhaji Abdul Aziz akaro na biyu kenan daya kalle ta , tareda nazarin kalaman ta , Gefen sa ya kalla ya zaro bandir din kudi ,Wanda akallah zasu kai Dubu dari yace Amshi wannan kudin duk kayan abinci da kika San anaci kisiya ki ajiye , kije gidan Gona kisai kaji guda goma ayanka mata , sauran kudin su Juice da kayan abinci dafatan kin gane ko. Gyada masa kai tayi alamun gamsuwa hakan yasa , taringa musu adua Allah yatsare cike da Jin dadi . Kasa komawa gida tayi harsai da taga tafiyar su , sannan ta daka uban tsalle tayi cikin gida . Zazzare idanu tasoma tace laaa yau nice da bandir din kudi na dubu dari , ga kuma Dubu Biyar cen wayyo dadi. Tsaki tayi data tuno da Baffa tace ana maganar Arziki wake ta tsiya . Khairi Har wajen gonar Baffa tajasu suka tafi , dukan su babu Wanda ya musa mata , kallon kasan wajen tayi , tace Baffa ga ramin da aka binne mahaifiyata cen , kullum kana hanani zuwa wajen dan Allah kabarni inje koda Adua ne inmata takarashe zancen cikin raunin Murya. Daga Baffa Har Malam Adamu Saida kuka ya kwace musu , rungume ta sukayi ,suna fadin haba Yi hakuri Khairin mu , kibari zuwa gaba in kinyi aure mijin ki yaringa wakiltan ki ,kuma adua duk inda kake yana bin mamaci. Khairi dake kuka tace Baffa , dagaske wancen mutumin da muka bari kofar Gidan ka , shiya haifi mahaifiyata . Gyada mata kai sukayi tareda bata amsar shine Mahaifin ta . Sabon kuka ya kwace mata tace Baffa inason ka fiye dasu bansan kowa ba sai kai , dan haka babu mai raba mu nidakai. Baffa Sha fuskar ta yayi yace Khairi ai nan gaba aure zakiyi Kinga dole kibar gida ki koma gidan mijin ki. Zazzare idanu khairi tayi tace aure kuma A'a baffa banason jin wanna zancen . Damar na kawo Ku nan ne saboda naga mutanen cen suna son su tada maka hankali abanza akan Abunda bazeyu ba. Su Alhaji Abdul Aziz daidai suna kokarin hawa kan titi ya hango Sultana ta fito daga wani gida hannun ta rike da ruwa alamun zata zubar ne . Cak ya Saida tukin yace dan Allah Ku dubamin wa nake hangowa cen kamar Sultana. Dukan su suka amsa da itace wallahi. Tsaki yayi yace wannan matsiyacin ya gama damu wallahi ,kuka ya kwace mishi yace yanzu diyar Amina ce cen take wahala ina hango ta. Dukan su shiru sukayi suna jin zafin Abunda suka gani. Kanin sa Musa yace Alhaji kasan me ze faru ne , yace A'a saika fada tunda Kaga gidan Sultana muje kawai zanyi nazari akai , maganar kotu mu ajiye ta agefe saboda Kaga yaran nan sun girma ana iya zaman kotun suce wajen Mahaifin su ,zasu zauna . Wannan karfi da karfi ne zamu hada wajen cimma burin mu . Kaban Sati daya inyi tunanin Mafita , ana samun solution komai zezo karshe. Karma mu tsaya bare ta tsorata da ganin mu. ********************* Su Baffa suna dawo wa gida yayi daidai da zuwan Akramakallahu , cike da Ladabi ya gaishe da Baffa shida Malam Adamu. Baffa yace ko kaine bakon da Saifudeen yace mun , kuna kwana tare . Bashi Amsa yayi da shine . Malam Adamu cikin Sauri yace Baffa bara inje cen cikin gari indawo daga haka yafice . Baffa na masa Allah yatsare ya Amsa da Ameen. Khairi da tun zuwan Akramakallahu idanun ta ke akan sa tace sannu da zuwa Akramakallahu . I Kasamu labarin ansauke headmaster ansaka sabo. Cikin mamaki yake zazzare mata idanu yace dagaske kuwa KANWATA? Eh wallahi dazun Kawar Ajin mu keban labari Kaga gobe dani za'a je Makarantar InshAllah. Murmushi yayi saida kuncin sa ya lotsa yace Allah yakaimu khairi. Baffa ne ya kalle sa yace Amshi makullin dakin naku ko ,maza kaje kayi wanka kahuta . Nasan ka kwaso rana . Godiya yayiwa Baffa hakan yasa yashige daga cikin gidan. Itakuwa Khairi kai tsaye gidan Su Najwa ta nufa. Tana isa gidan ta iske ta zaune tana tankaden garin tuwo , mummy bata nan. Samun wuri tayi tazauna kusa da ita fuskar ta cike da Annuri , Najwa tace Khairi ai mungode wa Allah da zamu koma makaranta wannan dan iskan yaso ya datse mana. Jin Khairi tayi shiru ne Alamun tayi zurfi a tunani tace keee khairi lafiya me kike tunani ne. Bakomai ta bata amsa . . Wallahi Najwa inajin wani bakon Al'amari a tattare dani . Najwa tace kamar me kenan yar uwa gayamin tana fuskantar ta. Yau kwana uku kenan Dana soma jin ina shaawan wani Abu Amma haryanzu ban tabbatar da komene ba . Murmushi Najwa tayi tace kila yanayin Rayuwa ne. Bara indauko mana redio mana . Tana kunnawa yayi daidai da ansaka fadakarwar JAN ZAKI. Tsuki Khairi tayi duk da tanajin dadin haka tace su kullum suke saka bayanan sa ne. Najwa tace inaga maimaici ne tunda magana yake Amma illan cin Amana da zanba cikin aminci . Kasa kunne sukayi suna sauraro. Khairi Tace kinsan me wallahi Muryan Jan zaki yana mun kama da Muryan Dana tabaki ji a kunne na . Najwa tace nima haka nake yawan tunani Amma aikin San ana kamanni a murya . Cigaba da sauraren Redio sukayi. Jin Muryan Innaro tana kwada mata kira ne yasata amsa mata tareda tashi tace Najwa bara inje inga Me matar nan take so ne. Gyada mata kai tayi tareda fadin saikin dawo tawan. Khairi na isa gida iske Innaro tayi rike da kwanun abincin data zubawa maganin karshe tace , zonan yata yau fa baki wani ci Abinci ba. Samun wuri Khairi tayi tazauna tace wallahi kamar kinsan yunwa ne fal aciki na. Innaro shiga daki tayi wayar ta na ring . Itakuwa Khairi abinci ta soma ci , cikin hanzarin dan yau basu karya da abun kirki ba. Innaro waya take da Kawar ta Tana bata labarin dangin uwar khairi. Kawarta tace gaskiya Safara'u ke Shu'uma ce ta karshe . Innaro tace kedai bari angayamiki ana wasa da Masu gidan rana ne. Dagacen bangaren tace Kinga maganar kiyiwa khairi Asiri dan tabar gidan be taso ba. In ma baki bata na karshe ba to karki bata ai hanya ce ta samun kudi tazo miki . Kiyi ta tasar dangin ta Masu Arziki nan ,kan kice me kema kinzama hajiya.. Salati Innaro ta dauka tace wallahi nabata abincin karshen inazuwa tafada tareda katse wayar koda tafito aguje ,iske Khairi tayi harta gama cin abincin ruwa take Sha. Bakin ta na rawa tace khairi Har kin cinye ne . Cike da mamaki khairi ke kallon ta , tace ai cemin kikayi Nawa ne lafiya kuwa ta tambaya cikin son jin zancen? Cikin Tashin hankali Innaro tace ai nayi tunanin tare zamu ci ne . Bakomai anjima zanje gidan mu ,insaida wani Abu na cikin kayana inyo mana cefanen kayan abinci . Khairi Tace ai Baffa yace babu kyau mutum ya dauki abun amfanin sa ya siyar . Innaro tace karki damu sonake mu ma , mu soma cin dadi kamar kowa Har nama Zan ringa soya mana na kaji. Khairi cike da Jin dadi tace wayyo Dadi ! Akramakallahu fa yazo cewar khairi ya kamata akai masa abinci . Innaro tace ayya bansani bara indauko Wanda na rage kije ki kai Masa. Komawa dakin tayi zuciyar ta na kunan abincin da Khairi taci . Tana nazarin ya zatayi ne , batason khairi ta tafi ? Akramakallahu zaune shikadai adakin yana waya da Saifudeen akan yayi kewar sa yakamata ace sun dawo gida. Yaji Sallamar Khairi hannun ta rike da kwanun abinci. Saifudeen yace kamar Muryan khairi nake ji . Amsa masa yayi da itace . Murmushi saifudeen yayi yace kace Amaryan JAN ZAKI ce. Wani mummunar Faduwar gaba ta doki zuciyar Akramakallahu ya maimaita kalaman sa yace Amaryan JAN ZAKI fa kace. Daman tasan shi ne , saifudeen yace A'a zolayarta nake kasan batada Aiki sai sauraren Redio saboda shi . Khairi ganin be amsa mata sallama ba yasa tashigo tareda ajiye kwanun abincin ko kallon inda yake batayi ba , tafice. Akramakallahu dake kallon Fitan khairi yace ai duk wannan Abunda takeyi kuruciya ce . Kuma a maganar ta datayi rannan cewa tayi batasan meye so ba. Daga haka sukaci gaba da hirar su , cike da burgewa. Kashe gari Tun karfe bakwai Safe duka gidan suna karyawa sukaji Muryan dan Sako daga mai gari yana shela. Yana fadin yaku jama'ar gari mai gari ya gaishe Ku ya kuma ya gaishe Ku. Yace a sanar daku nan da sati uku ranar juma'a akwai gasar aure . Duk wacce taga yarta batayi saurin samun Miji ba ,tana iya kai sunan ta. Yan mata Biyar kacal ake bukata , Mai gari yayi Alkawarin daukan nauyin kayan auren su . Khairi dake shan shayi azabure ta tashi kamar an mata joni da wutar lantarki , tace Baffa inason aure inaso asa sunana acikin jerin sunayen matan da za'a gudanar da gasar domin samun zakaran dazeci gasar ya aure su. Cikin zazzare idanu Baffa da Innaro sukace Khairi kinkosan me kike fade kuwa? Kwarai kuwa nasani tafurta cike da isa nace aure nakeso kuna min tambaya bayan kunji Abunda na fada. Akramakallahu dake dakin yana shirin fitowa , zancen nasu yasashi karasowa cikin Gidan. Cikin Kuka Baffa yace haba Khairi dan Allah ki rufa min Asiri inma auren kike so Zan miki Amma ba cikin gasa ba. Khairi da zuciyar ta ke tafasa tace Baffa wallahi tallahi a gasa nakeson asaka aure Na. Kuma babu fashi inhar ka hanani wallahi Zan kashe kaina takarashe zancen tana sakin kuka mai cin rai. Zazzare idanu Akramakallahu yayi yace Khairi Mahaifin ki , kike gayawa aure kike so babu kunya , kuma har kina fadin a gasa kike so a saka auren naki. Murmushi tayi mai ciwo tana kallon shi , tace Akramakallahu aure fa nace inaso ba cewa nayi zanbi duniya ba ,innayi laifi anan wajen awajen Allah Banda laifi . Baffa cikin tsawa yace Khairi bazan saka sunan ki acikin wannan gasar ba . Ki fiddo Miji ko waye shi Zan aura miki koda kuwa ayau ne . Banda tallan kai Khairi. Na rokeki . Akramakallahu mutuwar tsaye yayi yace Khairi ba magana ake miki ba. Tsuki taja tana kallon Akramakallahu tace aisai kuyita yi nina gama Nawa zancen , kafun na wuce Makaranta yanzu zanbiya gidan mai gari in sanar masa da bukata ta. Zazzare idanu suka soma dukan su . Akramakallahu yace Amma ....... Dakata tace mishi ta hanyar daga masa hannu tace Inaruwan ka ne . Daman nasan babu ruwana da harkan ki. Amma Saifudeen yazama jinina dan haka dole inji haushin Abunda kike shirin aikatawa na gangancin. Dan tsabar bakin ciki Baffa fita daga gidan yayi zuciyar sa , na tafarfasa yana Fadin Khairi yaushe ki ka canza bansani ba , khairi sakayyar da zaki mun kenan tafiya yake kamar wani zautacce shikadai ahanya . Akramakallahu kallon Khairi yayi yace muje Makaranta ko indan antashi saikije gidan mai garin ki sanar masa ko yabata amsa cikin jin haushin ta. Gyada masa kai tayi alamun gamsuwa da bayanan sa . Suna fita sukaci karo da Najwa tare suka wuce . Innaro zazzare idanu tasoma tace nashiga uku , kenan magani yakama khairi meye mafita ne ko komawa zanyi gidan Malam ince masa a karya inzeyu da wannan tunanin ta zura hijabin ta. Koda Khairi suka isa Makarantar iske sabon headmaster sukayi inda ya gabatar musu da kansa. Cike da Jin dadi khairi tace yanzu kam mun huta da barazanar kora. Akramakallahu sossai Abunda yafaru agidan su khairi ya hanashi sakat ,hango fuskar Baffa yakeyi a idanun sa , asanda yake kuka. Kallon khairi yayi tareda hada rai yana mai hararan ta ,kasan idanu. Mamaki ne yakamashi ganin shigowar Sakina . Tana sanye cikin kayan Makarantar sai wani hararan sa take tana tauna cingam. Cikin tsawa yace keee! dakata daga ina haka? Shiru tayi ta Gaza magana hakan yasa yakara fadin ki fitar min daga Aji naceee. Tsintar Muryan Mahaifin ta , yayi yana karasowa Ajin cike da izza su uku tareda wasu yace . Nine nan Mahaifin ta Alhaji KAMAL nace tazo tashiga Aji tunda bana ubanka bane . Akramakallahu cikin zazzare idanu yace ..... Saura page daya in gama free Ku hanzarta kada ayi babu Ku. Taku Har kullum kyauta daga Allah *RAI DAYA*🦜 *JAN ZAKI*🐆 Mallakar Ikilima Adam ( kyauta daga Allah) 09069080725 *Paid book* *Saura page biyu ingama free dan Allah duk wacce ta siye littafina dan Allah karki fitar min dashi da zaran nagama free.* *Dakuma wayanda suke da burin siya dan su fitar na roke Ku inkun San fitar dashi zakuyi to dan Allah basai kinsiya ba , kibarni da abuna .* 1️⃣3️⃣ Daga Aliyu Jan zaki munzo ne domin ,mu isar da sakon sa , izuwa gare ka ,kuma yace kaduba emails dinka zakaga Abu daya da irin Wanda mukazo dashi . Nan da nan headmaster ya rikice ,cikin Razani yace wani Sako kenan? Mika masa takarda sukayi tareda yin tsaye cirko cirko suna kallon sa yana karantawa wani uban zufa na karyo masa. Dago kai yayi cikin inda_inda yace bangane ansauke ni daga Aiki ba laifin me na aika ta ? Dukan su make Kafada sukayi sukace bamu zakayi wa wannan tambayar ba. Kaduba emails dinka koma menene ta cen zakaji dalilin haka. Nuno wani daga cikin su sukayi wani Salihin bawan Allah ,sukace wannan shine zai maye gurbin ka . Kallon agogon hannun su ,sukayi sukace Awa daya muka baka ka tattara duk wani Abu dakasan nakane kafice ,gobe InshAllah zamu Zo maka da Albashin ka . Har gidan ka. Drever Sakina sake da baki yake kallon Ikon Allah dan ma , ya mance Abunda yakawo shi. Headmaster yace haba bayin Allah karku mun haka wannan aikin dashi na dogara dashi nake daukan dawainiyar iyayena da duk Abunda ya shafeni dashi na Gina gidana ya kuke son inyi idan Har narasa Aiki na. Cikin su wani yace bakin da Allah yatsaga baya hanashi abinci ,karka bata mana lokaci ,kuma da kake complain ,mu ba laifin mu bane daga Me Makarantar ne shiyasan me aka fada masa game da kai naga makarantun sa dayawa a fadin Nigeria kaine mutum na biyu daya sallama. Cikin Tashin hankali headmaster ke tattara takardun da duk Abunda ya shafe sa. Yana gama hada su yace , nagama hada komi Nawa. Daya daga cikin su yace Miko mana takardun mugani dan kada asamu matsala ka dauki Abunda ba naka ba. Suna karban takardun hannun sa , mamaki ne yakama su ganin check din kudi daga Alhaji Kamal . Sauran file suke bi suna dubawa sukaga harda hoton Khairi tana cikin dalibai ya dauke ta batareda ta sani ba ,haka hoton ya nuna. Zare hoton sukayi daga ciki ,tareda fadin wanna hoton dalibar Makarantar nan kuma da dukan Alama batasan ka dauka ba . Dan haka wannan hoton Har wajen Jan zaki ze isa InshAllah ta email Zan tura masa. Arazane headmaster ke kallon su yace wannan ai cin Fuska ne ,Kun koreni inaruwan Ku dashiga personnel problem Dina. Cikin su wani yace wannan ba personnel problem dinka bane , hakkin mu ne ,mu kare mutunci kowace daliba a makarantar nan. Saida suka tabbatar yafita da Abunda yake nashi sannan suka rufe office din. Sauran Ajin suka nufa ,tareda nuna musu sabon headmaster din su daze ringa kula da su. Dalibai sossai sukayi farin ciki da Faruwan hakan dan ya takura musu da yawan tsanani ga shegen son mata. Sabon headmaster mai Suna Sagir , murmushi yayi yana kallon yanda dalibai ke karatu cike da nutsuwa. Headmaster na isa gida kwalban giya ya jera agaban sa ,yana Sha idanun sa ,sun kada jajir kamar gauta yana Sha yana tuna Abunda akayi masa a makarantar tareda daukan Alwashin duk inda Khairi take saiya nemo ta ,yanada tabbacin daga sune wannan matsalar yafito . Kamar shi Muktar za'a kora a Makaranta , to babu hukunci daya dace da Khairi illah ya mata fyade , wani shu'umin murmushi yayi yana Fadin idan na miki fyade Ummulkhairi dole ne , iyayen ki , su nemi rufa asiri dan kada arasa me auren ki. Kafun na aure ki saina wulakantaki Ummulkhairi keda iyayen ki ,yakarashe zancen nasa cikin Muryan maye. Mahaifiyar sa ce tashigo dakin aguje tace kai Muktar lafiya kake kuwa Naga kanata surutai . Dago rinannun idanun sa yayi yana kallon Mahaifiyar sa tareda buga kirji yace kamar ni ,za'a sauke daga aiki akan mace , yarinyar ma yar matsiyata. Cikin tsananin Tashin hankali mamar sa ta daura hannu akai tace mun shiga uku ,Muktar haryanzu baka canza Hali ba , kaiko Meka Aikata ne haka ne ,nasan ruwa baya tsami banza idanun ta shar da hawaye tace Dan nan ka tona Mana Asiri , dan Allah kanemi hanyar da zakabi asamu amaidaka bakin aikin ka cikin rikicewa take magana. Shiko dayake abuge kasa amsa mata yayi yana kallon ta da idanun maye . **************** Koda aka tashi Makaranta cike da Farin ciki ,Wata daliba mai suna Aisha ta ringa Neman gidan su khairi Har aka nuna mata. Tsaye take bakin kofar Gidan taci karo da Baffa yafito daga gidan Alamun a hanzarce yake . Gaishe sa tayi cike da ladabi tace dan Allah nan ne gidan Ummulkhairi Sulaiman ? Murmushi Baffa yayi dan idan aka danganta sunan khairi da nashi jin sa yake a shauki. Eh nan ne gidan su yabata amsa cikin sakin fuska kina iya shiga da ciki zaki same ta daga haka yasa kai yawuce. Itakuwa kai tsaye gidan tashiga bakin ta dauke da sallama, sake da baki Khairi ke kallon ta , tace laaa Aysha wai kece nan agidan mu ,dan Allah waya kwatanta miki wannan gidan namu . Aysha cike da Jin dadi tace garin masoyi baya nisa da tambaya har aka nuna mun gidan naku . Sossai Aysha ke kallon gidan su khairi ji tayi duk ta bata tausayi dan dagani talakawa ne futuk . Dakin khairi suka shiga tareda samun waje suka zauna ,suna tattauna yaushe gamo Aysha tace Albishirin ki? Khairi Tace goro tana mai Kallon ta ,bata labarin korar da akayi wa headmaster tayi. Wani uban tsalle khairi tayi hade da ihu. hakan yasa Innaro dake barci ta farka tana tsuki marasa adadi , cikin bacin rai tace shegiyar Yarinyar nan yau da bataje Makaranta ba , zata hanani sakewa hade da Jan tsuki taja filo ta daura kanta tareda cigaba da barcin ta. Khairi Tace Alhamdulillah kai naji dadin wannan bayanan naki ,kice gobe ina iya zuwa Aji. Tambayar ta , tayi yau Akramakallahu yazo ne? Aysha tace gaskiya yau bezo ba dan jiya dayazo Sakina ta masa rashin kunya , korar ta yayi yace takawo Mahaifin ta , kila bacin ran ne yahanshi zuwa . Khairi Tace me Sakinan ta masa cikin zazzare idanu . Bata amsa tayi akan Abunda yafaru jiya . Sossai Khairi ta jinjina Al'amarin tace lallai yarinyar nan ba yar gidan tarbiyya bace. Aysha tace aikuwa dai ta hadu da daidai su , ba takamar su Arziki ba . Khairi Tace Allah ya kyauta taso muje wajen Najwa tafada tana mai daukan hijab din ta . ******************** Aliyu zaune afalon sa , laptop dinsa na gaban sa ,Alamu Aiki yakeyi Masu muhimmanci. Kamar an tsukule shi yatuna rannan da yake jin barci akwai wani sako ta email din sa dabe duba ba. Hakan yasa cikin hanzarin sa , yashiga email din sa. Yayi daidai da Sumayya tana gaban laptop din ta itama tana rubuta Sako dazata tura masa. Shiko Aliyu Jan zaki sakon email din sa yabude na wancen ranar yana karantawa . Murmushi yayi saida kuncin sa ya lotsa yana mai kara karanta sakon Wanda ba komai bane aciki . Wani bakon email me dauke da sunan Suyfan yana fadamai yasan inda yake kwana yayi hattara yasan da Wanda zeringa sa'insa ba irin su ba. Yana kokarin fita daga email din yaci karo da sakon Sumayya. Tsaki yayi dan cikin wayanda yake hulda dasu babu mata , me take nema yafada azuciyar sa . Bude sakon ta yayi yaga Sako kamar haka. Aliyu Jan zaki , sunana Sumayya KAMAL Hakika na kasance daga cikin masoyan ka . Yau kimanin shekaru Biyar kenan ina sauraron fadakarwar ka kuma sossai yake shiga jikina. Allah ya jarabce ni da sonka akanka kowa ke kirana na zauce da Allah ka taimake ni ka fidda ni kunya koda lambar wayar ka ce . Dan jamaa su sheda soyayyar da nake maka ,bata wasa bace. Yana gama karanta sakon ta , tsaki yayi be mata reply ba. Ya kashe laptop din . Stupid girl ya furta a Fili . Karar wayar sa ce yadawo da kallon sa akan sa , ganin anrubuta Salim Daga wayar yayi tareda karata akunne . Dagacen bangaren yace Haidar tundazu ina kofar dakin ka nayi knocking shiru baka bude ba haba meye haka ne yana magana cikin Fada. Karamin tsuki yaja tareda tashi cikin tafiyar sa mai daukan hankali hannun rike da remote din TV . Yana bude kofar ,Salim yashigo kamar ze bigeshi sai safa da marwa yake cikin dakin. Akun🦜 Aliyu ne yashigo ahanzarce tareda hawa kan kafadar uban gidan sa. Cikin Tsananin bacin rai Salim yace wai Haidar yaushe zaka ringa daukan magana ta ne. Kullum ina nuna maka ka kiyayi wannan fadakarwar dakake yi labari yazo mun akan wayanda sukayi zaman meeting akan ka , suna son su San dalilin dayasa kake shiga harkan su . Aliyu Jan zaki samun wuri yayi yazauna yana mai cigaba da sauraren Abunda Salim yake fade . Cikin Muryan sa dake nuna bacin ransa yace suwaye sukayi meeting akaina ? Bashi Amsa yayi nadaiji ance . Alhaji KAMAL Alhaji Garba Alhaji Sufyan . Jan zaki girgiza kansa yake cikin tsananin damuwa yace saboda ina fadakarwar ne yasa , suke nema na to su mun me? Ran Salim ne yabashi yace Kash oh My god kai wallahi bansan meyasa baka daukan abubuwa serious ba kayi imagine fa ,ina maka maganar rayuwar ka ,kana nuna mun halin ko inkula akan haka why why cikin tsananin ihu hakan yasa Mamy taji sautin Muryan sa aguje, ta taho dakin cikin Rudewa take kallon Salim tace suwaye suke Neman suga bayan Dana idanun ta sun kada jajir. Fada mata Sunayen yayi yace Mamy Banda Tabbas akan Neman da suke masa , Amma naji suna fadin suna bukatar suyi tozali dashi tareda hanashi wannan fadakarwar da yakeyi dan wannan yana kawo musu cikas acikin harkan su , ta kasuwanci da Siyasa. Mamy sake da baki tace ikon Allah aikuwa Aliyu bazai taba daina fadakarwar nan ba . Tunda yakeyi bantajin ya kama suna ba. Akan me zasu tsargu dashi , ni bansa Aliyu fadakarwa ba dan yayi sa'insa da wani ba. Duk Abunda suke fade zaune yake yana sauraren su kansa aduke zuciyar sa tana tafarfasa . Dago jajayen idanun yayi dasu suka canza kala. Yace Mamy wayannan sunayen daya ambata kamar na San su ko? Mamy tace kwarai kuwa Amma saide bamuda tabbas akan haka. Kallo Salim tayi cikin bada Umarni tace inason ka samo mini hotunan wayannan bayin Allah . Salim yace InshAllah Mamy bakida matsala. Kallon Haidar Mamy tayi tace Dana karka damu da Abunda suke tattauna mudai mun rike Allah , kuma shize cigaba da karemu da dukan sharri . Daman inason Sanar dakai nan da Sati uku zanje Cikin gari Jabiri layin yan bokolo . Cikin tsananin bacin rai yace me zakije yi Mamy ? Gaskiya babu inda zakije yabata amsa adunkule. Haba Aliyu ya zakace babu inda zani akwai wani bawan Allah da nake nema wallahi shekarun baya kana dan yaron ka lokacin naje bansamu ganin sa ba. In banje ba Zan samu matsala acikin zuciyata ba. Kuma bazan taba gafartawa kaina ba takarashe zancen cikin kukan dayake Neman kwace mata. Aliyu Jan zaki shida Salim Har Akun🦜 kallon ta suke cike da tsananin mamakin furucin ta . Gaskiya Mamy bazaki je Kiyi hakuri yabata amsa . Zazzare idanu tasoma tace to ubana ko kuma ince mijina Muhammad . To wallahi sainaje sai lallabaka nake , kana wani tauyeni , shekaru Nawa nayi ban fita ba ,sai fitan da zanyi na yini daya shine ze kawo matsala. Aliyu dake kallon ta cikin gajiyawa da yawan surutun da yayi yace Mamy da kika zauna shekara da shekaru aikin zauna cikin kariyar ubangiji , yanzu so kike ki lalata min duk wani shirina kiyi hakuri Mamy . Ki gayamin sunan Wanda kike nema ko unguwar dayake . Ni Zan Nemo sa. Ran Mamy yakai kololuwa wajen baci tace Kasan Allah dakaina zanje ,Zan sanya nikaf InshAllah bazan baka matsala ba. Shiru yayi na wasu dakiku sannan yace Allah yakaimu ya sa mu wuce lokacin da Ameen ta amsa . Tace wai Aliyu meyasa bazaka tausayawa marainiyar Allah ba. Nusaiba ta Dade tana sonka ina maka magiya dan Allah ka aure ta. Cikin tsananin Tashin hankali da damuwar da sukayi masa yawa yace Mamy babu biyayya agun Aikata sabo agun abokin halitta ko wanene ni fa Nusaiba ina mata kallon ya ne bawai Kanwa ,mune fa muka Raine ta , sannan kuce na aure ta ,inyi amai in lashe kenan yafada cikin jin haushin zancen. Salim yace haba Haidar ya zakace kayi amai ka lashe saikace kaine uban ta . Dan ka raineta menene aciki ,kuma ina tabbacin lokacin da Nusaiba tazo hannun Mamy kaima kana karami , nasan kasan me ake kira Kalmar so inma baka sani ba ,kanaji agari . Azuciye yatashi tsaye hade dayin tsawa Wanda Yasa daga Mamy Har Salim da akun dake kafadar sa fuffuke yayi yakoma kan Salim yana zazzare idanu. Yace me ze hana kai ka aure ta ? Nace mukuuuuu bazan auri Nusaiba ba ko bakwa fahimta ne , ban haifeta ba Amma ta zama kamar jini na ,abun kaunata ,Banda Kani ko Kanwa sai ita kadai inna aure ta , tazama mata ta , kallon da nake mata abaya duk ya kau. Dan haka Ku bar zancen nan haka ya ishe ni wallahi . Maganar aure anan gaba , babu shi . Ni Aliyu Muhammad nace bazan yi aure ba. Bazan yi aure ba. Bazanyi aure ba. Bazanyi aure ba Har Abada yakarashe zancen tareda barin Falon yayi dakin sa , aguje tareda danna mata keyy Wani uban kuka ya saki mai tsuma rai yana Fadin Ni Aliyu Muhammad , ya ilahi ka taimake ni , ya ubangiji na karka barni da iyawata ,ya Allah karka hanani ganin haske . Kuka yake mai tsuma zuciya tareda bude drower din gadon sa. Ya fiddo wani hoto mai dauke da hoton wani Da da dukan Alamu kamar Mahaifin sa ne. Kara sautin kukan sa yayi rungume da hoton yana Fadin wayyo Abbana Wayyo Abbana ! Wayyo Abbana ! Wayyo Abbana! Kuka yake mai tsuma zuciya. Mamy da Salim cikin hanzari suka karaso wajen kofar sai buga kofar suke Amma Sam baya jin su. Dan yashiga bandaki ya sakarwa kansa ruwa ,gashin kansa sun kwanta lub lub ,fadadden kirjin sa mai cike da yalwan gashi duk yake bi da kallo yana mai cigaba da rera kukan sa. Salim yace Mamy wallahi Aliyu yana matukar bani mamaki fa ni kaina inya birkice tsoro yake bani. Akun 🦜 dake bayan su yace harda ni wallahi Ajiyar zuciya Mamy ta sauke tace wannan yaron shine Sak Muhammad babu inda yabar sa halin su daya . Ganin Salim na Neman karin bayani ne . Tace Salim muje InshAllah ze fito indai Aliyu ne . Tunda maganar Nusaiba ba ne bayaso ai babu Kari nikam Murjanatu saidai adua ,Amma zancen yace bashi ba aure tatsuniya ce . ******************** Kashe gari Baffa da Malam Adamu ne zaune inda suka saba zama suna tattaunawa akan Koran da akayi wa yayan su. Baffa yace ai gashi ansauke malamin Tareda musu canji da wani. Malam Adamu yace ai halin sa ne , ya jamasa tunkan yayan mu suje Makarantar ake kuka dashi. Horn da akeyi da mota kofar Gidan sa ne ,yasa shi fadin laa Kaga baki mukayi ko daga ina haka yafada cike da mamaki. Wanda ke cikin Motar ne yagama daidaita parking din motar su wajen uku ne . Suna gama fitowa daga motar Malam Adamu ya kalli baffa dake zazzare idanu yace wayannan kamar........ Taku Har kullum kyauta daga Allah