*SABO DA KAZA* *NA* *SURAYYA DAHIRU* ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.``` ```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️ ____________(�?)______________ https://www.facebook.com/profile.php?id=100069755834980 •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·�? *Godiya ta tabbata ga Allah(S.W.T.). Tsira da aminci su tabba ga Annabin Rahama(S.A.W).* *SADAUKAWA GA IYAYENA GUDA HUDU* *ALHAJI MUHD TUKUR* *HAJ FATIMA LADI ALI* *ALHAJI DAHIRU ALI* *HAJ MARYAM HAMISU KANO* *ALLAH YA JI'KANKU DA RAHMA YA BAKU ALJANNAR FIRDAUSI*. *FATAN ALHERI GA MIJINA* *(M.I. NASHE)*. *JINJINA GA SHUGABAN KUNGIYAR LAFAZI WRITERS* *SADIK ABUBAKAR* *Na gode da kokarinka akan rubutuna*. *Assalamu alaikum sister's! Barkanmu da sake ha'duwa a cikin sabon littafina.* *Hakika na yabawa kaunar da kuka nuna mini akan littafin *Halin Yau*. *Ba abin da zance muku sai dai fatan Ubangiji ya saka muku da mafificin alheri*. *Ina fatan zaku bibiyi wannan labarin sannu a hankali dan jin da wanne sa'kon ya zo.* *Ina addu'ar Allah ya bani ikon rubuta dai dai, ya hana ni rubuta barna*. *JAN HANKALI* *GABA'DAYA WANNAN LABARIN 'KIR'KIRARRE NE (FICTION) BAI FARU BA. HAKAN NAN SUNA DA GARURUWAN DA SUKE CIKI BANA KOWA BANE, NA ZABE SU NE TA YADDA ZASU 'KAWATA LABARIN.* *IDAN KIN CI KARO DA ABIN DA YA YI KAMANCECENIYA DA RAYUWAR KI TO AKASI NE. MANUFAR LABARIN JAN KUNNE DA HANNUNKA MAI SANDA AKAN WANNAN RAYUWAR MAI CIKE DA RU'DANI. BA WAI SHAGUBE GA RAYUWAR WANI KO WATA BA*. 1&2. *Free page.* *Tushe* Asalin kakanmu Alhaji Zubairu Lawal Moriki, 'dan asalin 'kauyen Moriki ta cikin 'karamar hukumar Zurmin jahar Zamfara ne. Bahaushe ne, kuma Bafulatani, domin mahaifiyarsa Bafulatanar daji ce, kyakkawan dattijo fari tas. Ya taso cikin tsari da 'ka'idar tarbiyar Bahaushen Arewa mai tsananin ri'ko da dokokin shari'ar Islama. Fataucin dabbobi ne ya kawo shi garin Kano har ta zame masa tamkar gida. Domin kuwa sannu a hankali ya kwaso iyalinsa suka dawo kano gaba'daya. 'Ya'ya biyar mai dakinsa Maimuna (Adda) ta haifa masa, duk da sun binne wasu da dama a dalilin tana wabi. Hajiya Hafsatu ita ce babba (Yaya ta 'Kwalli) ba ta ta'ba haihuwa ba, sai dai kuma yan'uwan nata ba su ta'ba bari ta ga gurbin rashin haihuwa ba. Sai dai kawai motsawar da zuciya za ta yi idan sha'awar ganin jininka ta motsa. amma ba don kukan wani abu ba, domin 'ya'ya biyu 'yan uwanta suka bata ta goya, ta kuma aurar. Dukkan abin da ya shafi yaran kuwa yana hannunta. Ramla da Ashir. Mace mai zafi idan aka tabo ta, mai son dinke barakar zumunci, duk inda ta ga zumunci zai samu tawaya yanzunan za ta yi dukkan mai yiwuwa ta 'dinke shi. Sai Alhaji Abubakar Moriki (Abba) shi ne na biyu, dattijon arziki mai tsananin ri'ko da ka'idojin shari'a, masoyin zumunci da kyautata shi. Dukkan karatunsa ya yi ne a bangaren addini, a 'kasar Sudan ya yi digirinsa na farko a fannin sanin ilimin Hadisai. (Hadith Science) Daga nan ya wucewa 'kasar Masar ya sake zurfafa iliminsa a kan sanin a fannin Shari'a da rabon gado. Dukkan karatun tallafi ne na gwamnatin tarayyar Najeriya. Daga nan kuma sai ya fa'da harkar kasuwaancin safarar zobo da 'karo a tsakanin 'kasashen Africa. Sosai ya samu daukaka a harkar, ba 'karamin nasibi yake samu ba, domin idan ana lissafa attajirai, babu shakka za a saka Alhaji Abubakar Moriki. Matarsa 'daya Hajiya Saude (Umma). 'Yar asalin garin Yola ta jahar Adamawa ce. Kyakkawar mace fara 'kal mai cikakken diri, mai yalwataccen gashi, sai dai gajeriya ce. Mace ce mai izza da jin 'kai, ta tsani wani ya rabe su, kasancewar mijinta shi ne garkuwa a danginsa. 'Ya'ya shida Ubangiji ya azurta su, biyar 'din farko dukkansu mata ne kyawawan gaske domin dukkansu ita suka biyo, suka sami tsayin mahaifinsu duk da mijin nata ba baya ba ne wurin kyakkawar sifa, sai dai ko kusa ba a hada kyaun mace da namiji, sannan farinta da dogon gashinta baki sidik sun shahara, sai ta zamo tamkar Balarabiya. Haka 'ya'yanta suke farare dogaye, masu gashi, duk irin yadda Ubangiji Ya azurta ta da samun wa'dannan kyawawan yaran kuma masu lafiya, ita ba ta gode ba, domin ba abin da take so irin ta haifi namiji. Hafsat ce babba, wacce ya yi wa yayarsu magajiya, sai Maimuna (Ummu) mai sunan kakarmu, sai Juwairiya, Ramla, Sakina, sai autanta da ya ci sunan sahabin Ma'aiki Abubakar ake ce masa Sadik kasancewar sunan Abbban ke nan, ita kuma ta ce Gudale. Sai Hajiya Binta Moriki (Maman Kebbi) da take aure a Kebbi tana da 'ya'ya uku Shafa'atu, Adnan da Ashir. Sai Alhaji Ssni Moriki (Baban Gusau) da ya kasance dan kasauwa mai sayar da suturu, a cikin babbar kasuwar Gusau, a can kuma yake zaune da iyalinsa. Mutum mai tsauri da fe'de gaskiya, komai 'dacinta, marar daukar wargi. Matarsa 'daya da yara biyar, Fatima, Abubakar, Maimunatu (Ummj), Abbas, da Farisa. Abbas kuma yana tare da mu, tun daga karatun sakandire da ya yi a Science Dawakin Kudu da su Ya Sadik shike nan ya zama dan Kano, duk sa'anni ne da su Ya Al'amin, Kuma duk Gudale ne 'karaminsu. Mahaifina Alh Ibrahim Moriki (Baban Yara) shi ne autansu, kusan Alhaji Abubakar shi ya yi masa komai tunda ga kan hidimar makaranta, har ya zuwa aure. Ma'aikaci ne a hukumar ilimin bai 'Daya. Mahaifiyata Safiyya (Mama) 'yar Kano ce, ta fito daga unguwar Magashi, cikin babbar zuri'a, ina nufin masu haula da yawa ba wai ku'di ba. Matsakaicin kyau ne da ita, sannan tana da dan jiki, da manyan idanuwa dara-dara, sannan wankan tarwada ce, yayin da Baba ya kasance fari tas! Lokacin da aka auro Mamanmu, Umma tana goyon Ramla ne, sosai suke zaman lafiya, domin Mama tana gama gyara bangarenta, matu'kar mijinta ya fita to kuwa za ta rufe ta tafi wurin Umma saboda a gidansu na gado suke zaune wanda Abba ya fadada shi, ya zamanantar da shi, a cikin unguwar Hausawa 'Yan-Babura. Sosai Umma take jin da'din zama da Mama, saboda biyayyar da take yi mata, musamman yadda take hidima da 'ya'yanta, barin Ramla da barci ne kawai yake raba su. Mamanmu ba ta cika shekara a gidan ba ta haifi Abdallah, lamarin da bai yi wa Umma Da'di ba, ta ji babu dadi sai dai ba a samu canjin mua'amala ba. Kafin Mama ta cika shekaru hudu ta hada yara Uku duk maza Abdallah, Azzubair (Babangida) da kuma Ammar. A wannan lokacin kuma Umma ta fito da dukkan munanan dabi'unta, sosai ta dora karan tsana a kan Mama da ya'yanta, babban ba'kin cikinta yadda haihuwa ta tsaya mata cak ga kuma wata ta zo tana haifar maza duk shekara, nan gaba hasken da yake kofarsu zai koma kofar Safiya da Ibrahim. Ta fara hana 'ya'yanta zuwa bangaren kanin mahaifinsu, sannan kuma idan Maman ta zo, ba za ta ga fuska ba, 'dan abu 'kank'anin zai faru za ta fara habaicin har gobe mijinta shi ne garkuwarsu. Sosai Umma ta takura wa Mama har ta kai fargabar ta yi ba'ki take yi, saboda yadda take fuskantar tozarci. Hakurin Mama yasa ko Baba bai fahimci halin da suke ciki da Umma ba, sai da tafiya ta yi nisa. Shi ma rashin ganin su Ramla a gidansa ne, ya kuma lura Mama ta rage shiga wajen Umma. Kasancewar shi ma mai son zumuncin ne, sai ya yi kamar bai fahimci matsalar a wurin matar yayan nasa take ba, yana yi wa tasa matar wayo da dabara ta hanyar cewa ita ce 'karama, sannan ai ya lura ita ta janye daga jikinta, ya lura ba ta zuwa 'kofarta kamar da. Ana cikin haka Umma ta haihu, again dai mace ce, ko ka'dan ba ta yi farinciki a zuciyarta ba balle ta yi godiya. Aka yi sunan Sakina babu wani armashi, saboda ta riga ta dora rai a kan boy ne a dalilin ta yi scanning an tabbatar mata namiji ne, sai kuma ga kyawawar budurwa ta iso. Watan Sakina goma Mama ta sake haihuwar Al'amin, Wohoho! Ina wuta Umma ta jefa ta, a lokacin mahaifiyarmu ta fuskanci wani irin tashin hankali da matsatsi, domin an kai jallin da ko tsakar gidanta ya gagare ta fitowa, kullum tana 'daki, haka 'ya'yanta, sannan duk shedantar Umma ba ta yinta idan maigidanta Abba yana gida, musamman da yake mai yawan tafiye-tafiye ne sai abin nata ya sake bun'kasa. Tashin hankalinta yadda duk tafiya ba ya banbance tsakanin 'ya'yansa da na 'kaninsa, hatta keke da ya ce ba ya son 'ya'yansa mata su hau, duk ya saya wa su Abdallah kowa da nasa, haka indai yana gari to da Abdallah yake yawo ko'ina, daurin aure ne, ko ta'aziyya ko yawo haka, duk dinkin da zai yi tare yake yi da shi. Haka makaranta 'daya suke zuwa da 'yayansa shi ne kuma yake biya gaba'daya. Wannan ya sake ki'dima Umma tana ganin tamkar gazawarta ne yasa ta kasa haifar namiji duk kuwa da ko a fuska mijinta bai ta'ba nuna mata cewar 'ya'ya matan da take haifa masa ya gaji ko baya so ba, duk haihuwa sosai yake murna da hidima ya kuma zaba musu kyawawan suna. Cikin ikon ubangiji watan Al'amin goma. Umma ta haifi 'danta lafiyayye sak ita ya biyo shima, fari kal, mai gashi domin gashin har idonsa yake, tun yana jaririnsa dan tsurut ne babu nauyi, ma'ana ba jiki. Ga mamakin Umma Abba bai yi wani zumudinsa fiye da su Sakina ba, domin har zuciyarsa bai ji yaron ya 'dara Abdallah a wajensa ba, ke nan shi ba yanzu ya yi 'da ba. Wannan al'amarin ya sake tsananta kiyayyar Mamana a zuciyarta, ta gaskata asiri take yi don ta mallake su ga'badaya. Rainon Abubakar ya banbanta da duk 'ya'yan da Umma ta haifa, wani irin gata take nuna masa tamkar dai ba ta samu haihuwa gaba'daya ba sai da ta shekara talatin a dakin miji. Komai na yaron a wajenta mai girma ne, ba ta ha'da shi da komai, tun mijinta na yi mata fa'dan kar ta lalata shi, har ya ha'kura ya koma yi mata addu'a. Shekarar Sadik wanda Umma take'kiransa Gudale biyu aka aurar da Hafsatu 'yar wajen Umma ta farko aka kaita Zariya, saboda nan ne garin mijinta, kuma malami a Jami'ar Ahamadu Bello, daan boko na gaske, tun kafin auren ya sama mata gurbin karatu a Jami'ar inda za ta karanta Tsumi da Tanadi (Economics). Hakan yasa Umma ta 'ki haihuwa tuburan ta dakatar da ita da 'karfin tuwo a cewarta ta barwa Yara. Wani abin da ya damu Umma yadda Sadik ya bijire mata daga hana shi zuwa sashinmu, duk juyin da za ta yi sai ya zo wajen Al'amin, kullum cikin saya masa kayan wasan da za su dauke masa hankali take. Amma da zarar gari ya waye tofa zai tafi, ba zai yarda ya dawo ba, sai ya yi barci sannan Abdallah zai kawo shi. Watarana yana ta kukan zai tafi ta ri'ke shi ta hana, Abba ya gane dalilin kukansa aikuwa cin mutuncinta da ya yi ba ka'dan ba ne, ya ce matu'kar dansa ne to dole kuwa ya so jinin Ibrahim. Shike nan sai ya zama rabi-rabi, har ya fi zama wurin Mamanmu. Mama kuwa tun haihuwar Al'amin ta dinga 'bari, duk cikin da za ta samu sai ya bare, a haka har aka shafe shekaru tara da haihuwar Al'amin yayin da Sadik yake da takwas, shakuwa ce mai tsananin gaske a tsakaninsu, hakan nan sosai Ya Sadik ya shaku da Mamanmu. Na iso duniya ne cikin cire tsammanin haihuwa daga iyayena, sannan ba 'karamin wahalar gaske Mama ta sha wajen haihuwar ba, hakan ya zama sanadin da aka juya mata mahaifa gaba'daya. Idan mai karatu na biye da kyau, zai gane mu biyar ne 'ya'yan Ibarahim Moriki, ni ce kuma 'ya mace tilo da na biyo maza hudu, kamar yadda Ya Sadik ya biyo mata biyar ya zama namiji tilo. Na taso cikin gata iri-iri, ba daga iyayena ba, ba daga yayye ba, haka nan ba daga Abba da iyalinsa ba, kawai Umma ce ba ta sona, take adawa da duk abin da mijinta ko 'ya'yanta za su yi mini. Ta yi juyin duniya Sakina da Sadik su daina kula ni amma ina, domin duk miskililancin Gudale zai dauke ni, shi yasa mafi yawan hotunan muna yara ina hannunsa, ko ina kan cinyarsa, muna da hotuna ni da shi muna yara kala-kala. Wani ikon Allah yadda Ya Sadik ya fi zaman sashinmu, ni kuma na fi zaman sashinsu saboda Sakina, tunda aka yaye ni, na yi wayo kullum ina gurinta, duk zare idon Umma da muzurunta ba na fasa zuwa ko fasa zama, sai idan Sakina tana makaranta, domin duk inda za ta je tare da ni take zuwa. A lokacin an aurar da duka 'ya'yan Umma Sakina ce kawai ta rage. Sakina ita ka'dai ce mace domin tsararrakinta duk maza ne, Al'amin da Sadik. Don hakan shakuwa ce a tsakaninsu ba ka'dan ba. Sai dai ba zai yiwu ta dinga yawo tare da su ko kwana ba, sai ya zamana ta ja ni a jiki duk da karancin shekaruna, tunda shekaru goma ta ba ni cif, tare muke kwana, ita take mini wanka ta shirya ni. Wata irin shakuwa ce ta musamman a tsakaninmu, hakan ba 'karamin da'di yake yiwa Abba ba shi yasa ma ya dawo da ni bangaren gaba'daya. Umma ce take kyashi da hakan, take yawan hantarar Sakina a dalilin ita ta janyo ni. Da wayona da hankalina aka yi bikin Sakina, domin na shekara sha uku a duniya, saboda sai da ta yi karatun Nursing ta gama, a lokacin tana da shekaru ashirin da uku. Tunda aka yi bikin Sakina na kasa jin da'din zaman, saboda ka'daici da rashin samun fuskar yin walwala, na fara a-sha-ruwan-tsuntsaye, idan ba Abba ne a gari ba, ba na kaunar kwanan wurin Umma. A hakan dai rayuwar ta ci gaba da gudana ina kallon irin yadda mahaifiyata take rayuwa cikin zullumi da kaffa-kaffa, saboda takurar da Umma ta yi mata. Musamman da Abban ya sayi wani katon kango da yake jikin gidanmu, ya fasa kofa ta cikin gidan aka yi shuke-shuken su alaiyahu, shuwaka, lemon tsami, zogale da sauran tsirrai. To fa Mama ba ta isa zuwa ta tsinka ko ta aika a ciro mata ba. Na kammala aji uku na sakandire ba dadewa da bikin Sakina, kwatsam sai ga Abba da takardar makarantar kwana ta Sojin Sama ta garin Kaduna, (Air force Staff School Kaduna). Ko ka'dan ban yi murna ba, domin ban ta'ba sha'awar boarding ba, Aunty Ramla ce kawai ta yi boarding a gidanmu, sai su Ya Sadik. 'Karin 'bacin raina Kaduna ta yi mini nisa, da ma a cikin Kano ne da sauki. Hankalina ya tashi, na dinga kuka. Baba ko ya ce ba zai yiwu Abba ya yanke hukunci ya yi masa musu ba. Ya Sadik da ke tsakaninmu da tsakuwa sai murna yake yi yana fa'din, "Na gode wa Abba da ya samo miki boarding wata'kila idan aka yi sa'a kya zazzage wannan tebar da kika ajiye tamkar wata uwar mata, ke kam da wuri za ki tsufa." Wadannan kalaman su ne kullum a bakin Ya Sadik har ya sa na zama very guilty. Ina tunanin laifi ne don na kasance mai jiki. A tsaye nake cak ma'ana ina da tsayi, sannan ina da jiki sai na zama irin giant din nan da suke tafe da tsayinsu da jikinsu, ni din fara ce tas, sannan na yi sa'a ina da manyan idanu dara-dara, hanci ba wani dogo ba ne, amma kuma dai ba laifi akwai, sai dimples a dukkan kumatuna, ko abinci nake ci, suna lotsawa bare na yi murmushi ko dariya. Ina da gashi sosai, sai dai yawa ne da shi ba tsayi, har gaban goshina yake, har wani kamar saje ya yi mini, 'kirjina a cike suke kwarai da gaske, hakan ya janyo ana mini kallon na zarce shekaruna, haka 'kasana a bude yake, kusan ma kibar ta fi shahara daga kuguna. Bangaren halayya kuwa na kasance mai nacin kan abin da na saka a raina, sannan ina da kafiya, sai dai kuma ina da hakuri, da wahalar gaske aji ana fa'da da ni. Ni ko irin fitinar yarinta ban yi ba, ba ni da abokin fa'da sai Yaya Sadik shi ma shi ne mai tsokanar ta hanyar ce mini Yar sukuta, ko Sady bon bon, ko Guduyo, duk cikin sunayen na fi tsanar Guduyo, ban san manufar sunan ba, amma dai na fi zaton saboda ina da jiki ne. Ba yadda ban yi ya daina ba amma ya 'ki, sai na tsiri ce masa Gudale. A farkon abin ba kurarin da bai mini a kan na kiyayi ce masa wannan sunan domin ba sa'ana ba ne. Ban ji ba, don kuwa ban daina ba, tun yana kawo mini duka, har ya hakura. Ni dai tun tashina ban ga fitanannen a gidanmu irinsa ba, domin Umma ta riga ta sangarta shi, komai yake so sai ta yi masa koda kuwa ba daidai ba ne, yanzun nan zai gama yin iyashege amma da zarar ya bukaci abu to ba ta tuna laifukansa za ta yi masa son ransa jikinta na rawa. Kowa nan nan yake da shi, ba ga su Mama da Baba da yafi zaman wurinmu ba, ba ga Ummansa ba, ba ga su Ya Abdallah ba, barin ma Ya Al'amin da komai zai yi a duniya sai da Gudale, wata irin soyayya da shakuwa ce a tsakaninsu tamkar tagwaye, kammaninsu daya sai bannacin shi Al'amin baki ne, sannan mai sanyin hali ne, yayin da Sadik ya zama siriri fari tas, yanayinsa 'daya da Ramadan Both hatta gashin kansu kusan iri 'daya ne saboda ya dauko jinin fulanin Yola. Abba ne kawai ba ya ta Sadik saboda bai son giggiwar da yake yi, ba ya banbanta shi da yayyuna, kusan ma ya fi fifita Ya Abdallah domin ni dai ban taso na same shi a gidan ba, Abba ya kai shi 'kasar Oman yana karantar Law. Haka Yaya Babangida a Sudan ya yi digirinsa akan Arabiya, Ya Ammar kuwa a Jami'ar Nigeria (Nsukka) ya yi karatunsa na (Mass Communication). Dukkansu kuma Abba ne ya yi dawainiyarsu, hakan ba 'karamin damun Umma yake yi ba, sai dai kuma ba yadda za ta yi, tunda duk wani shigi da ficinta bai yi tasirin da ya hana Abba yi wa 'ya'yan 'dan uwansa hidima da zumunci ba. Babban abin da ya sake dagula lamarin Umma a kan mu, a lokacin da su Yaya Sadik suka kammala sakandire, sun riga sun sakankance America ko England za a kai shi karatu, tunda suna ganin ya kai wasu bare kuma tilon 'dansa. Sai dai fir Abba ya tire a kan ba inda zai tura Ya Sadik, a yanzu ma yake yin fitina kala-kala bare kuma ya sake tura shi kasashen da suke da 'yanci, don haka Ya Al'amin da Ya Sadik a Jami'ar Ahamad Bello suka samu gurbin karatu, inda Al'amin ya karanci Halayyar 'Dan Adam (Sociology). Shi kuma Sadik yake karantar Urban And Rural Development. (Tsara Cigaban Birane da Karkara). Yaya Abbas kuma ya samu (Geography). Ba irin rikicin da bai yi ba a kan ba zai yi karatun ba ga'badaya. Ya samu daurin gindin Umma, Abba kuwa ya ja ya kafe ba zai sauya ra'ayinsa ba, tunda ba ya so sai ya yi ta zama, haka ya dauki su Yaya Al'amin ya kai su Zariya, ya damka su a hannun mijin Anty Hafsatu, wacce muke 'kiran ta da Antin Zariya, shi ne Vice Chancellor na makarantar a lokacin. Kan dole Yaya Sadik ya tattara ya tafi Zariya shi ka'dai, ya fara karatunsa,da su Yaya Al'amin a gidan Anti suke da yake cikin kwatsas din makarantar. Yayin da Antin Zaria babbar Ma'aikaciya ce a ma'aikatar E.F.C.C. A lokacin da nake shirin shiga aji hudu na sakandire inda zan tafi makaranta a Kaduna, a wannan shekarar su Ya Sadik suka kammala digirinsu na farko, suka fito da sakamako mai kyau. Ganin a lokacin shekarunsu ba wani yawa suka yi ba, bayan sun kammala bautar kasa, Abba ya tura su digiri na biyu (Masters) a wannan karon ne suka rabu domin Yaya Al'amin a Jami'ar Bayero ya samu, yayin da Sadik da Abbas za su sake komawa Zariya. Yayin da Yaya Ashiru yake karantar pharmacy a B U K. Ba'kin ciki a zuciyar Umma tamkar ta halaka, sai neman tsari da zama tare da dangin miji gida 'daya take yi, domin gani take yi ai don Gudale ya taso a sa'anninsa da yawa yasa Abba bai kai shi karatu waje ba. Tunda Ashir ma a shekara 'daya suka kammala. A haka rayuwar ta ci gaba da gurgurawa, tunda na fara boarding ban sake ganin Ya Sadik ba, domin lokacin zan zo hutu, shi kuma ya tafi, ba mu hadu ba sai da ya kammala, a lokacin ni kuma ina shirin kammala sakandire. # One Love # Ana tare # Surayya Dee ✍️. 2/8/23, 10:22 - Buhainat: 🌺 *SABO DA KAZA* 🌺 *NA* *SURAYYA DAHIRU* ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.``` ```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️ ____________(�?)______________ https://www.facebook.com/profile.php?id=100069755834980 •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·�? *Godiya ta tabbata ga Allah(S.W.T.). Tsira da aminci su tabba ga Annabin Rahama(S.A.W).* *Sadaukawa ga iyayena guda hudu* *Alhaji Muhd Tukur* *Haj Fatima ladi Ali* *Alhaji Dahiru Ali* *Haj Maryam Hamisu Kano* *Allah ya ji'kanku da Rahma ya baku aljannar firdausi*. *Fatan alheri ga Mijina* *(M.I. Nashe)*. *Jinjina ga shugaban kungiyar Lafazi writers* *Sadik Abubakar* *Na gode da kokarinka akan rubutuna*. *Assalamu alaikum sister's! Barkanmu da sake ha'duwa a cikin sabon littafina.* *Hakika na yabawa kaunar da kuka nuna mini akan littafin *Halin Yau*. *Ba abin da zance muku sai dai fatan Ubangiji ya saka muku da mafificin alheri*. *Ina fatan zaku bibiyi wannan labarin sannu a hankali dan jin da wanne sa'kon ya zo.* *Ina addu'ar Allah ya bani ikon rubuta dai dai, ya hana ni rubuta barna*. *BISMILLA HIR RAHMANIR RAHIM* *Shimfi'da* *Farko* Harabar falo ya biyo ni yana fa'din "zo ki ji Halah! Saurare ni mana, sai yaushe za ki yarda da ni? Ai na dauka mun wuce wannan tashin hankalin? na riga na fahimta, na kuma gane bankaura nake yi, ke 'din ce farincikina, ke ce duniyata!" Ya tsahirta da nufin ko zan tanka masa, amma sai na tsuke bakina tamkar gini yake ba yi wa magana. Ya nisa tare da fesar da iska sannan ya ci gaba da cewa, "Ki kalli irin yadda Allah Ya juya al'amarinsa mana komai ya kubuce mini, da kaina na dinga 'karyata kalamaina. Bai kamata ki ci gaba da nuna 'bacin rai ba, tunda Ubangijinki ya yi kishinki, kar fa ki bari ni ma Ya yi kishina, tunda ba a miki sassauci wurin yi mini 'kwangen biyayya ba." Na yi 'kasa da kaina ina jin hawayen takaici na neman kwace mini. Ba komai ke sani jin takaici ba, sai irin yadda ba ni da yar'uwa shakikiya mace. Wacce duk runtsi ba za ta 'ki yi mini adalci ba, wacce na rik'e tamkar cikinmu guda ta nuna mini wata kusar ta fi wata, ta hanyar fifita farincikin 'dan uwanta a kan nawa, duk kuwa da tana sane da irin zaman da na yi da shi, asalima ita ce kan gaba wurin fa'din ha'kurina ya yi yawa, son da nake yi masa ya wuce hankali, ita ba za ta dauki wulakanci namiji irin yadda nake dauka ba. Amma da ya fasa kwalbar ha'kurina! Sai t ta shure dukkan ba'kin cikin da na hadiya a hannunsa, ta bari idonta ya rufe, ta 'ki yi mini kara, duk da ta san ita ce 'yar uwa mafi kusanci a gare ni. Ya sake nanu'kata, yana cewa, "Ni na san ke mai yawan yi mini afuwa ce, wannan taurin zuciyar ba taki ba ce, ba kuma ta dace da ke ba. Kin yi hakuri da ni, na zalunce ki, na shayar da ke gubar ba'kin ciki, na azabtar da ke, na wulakanta ki. Amma don Allah ki ba ni damar da zan gyara na yarda na yi laifi, ina kuma son na gyara, amma kin rufe mini 'kofofofin afuwa. Hawayen idona ya 'balle mini, cikin rishin kuka na ce, "Sau nawa kana yin irin wannan tuban na muzuru? sau nawa ake danne ni saboda kai? Shin laifi ne don na zo a jinsin mata masu 'kiba, na kuma zama uwar 'ya'ya mata?" Kuka ya 'kwace mini kwarai da gaske. Cikin rarrashi tamkar ba ta'kadiri irin Gudale ba, Ya ce, "Kowa ya shaida wannan nadamar tawa har zuciyata ce, sannan ai yanzu bisa sharadin da aka gindaya mini za mu zauna, ni na sani sakayya ce Ubangiji ya yi a tsakaninmu, aka juyar da al'amarinmu ta yadda ban yi zato ba, ina sake rokon ki kar ki bari rashin kirkina, yasa ki yi watsi da kyawawan dabi'unki na ha'kuri da sassauci, Ubangiji da kansa ya ce, "Fa sabir sabaran Jamila." Wato ku yi hakuri, hakuri mai kyau. Ya sake cewa, "A yi wa masu hakuri bushara." Na zuba masa ido tar ina mamakin ashe ya san hakuri dabi'a ce mai kyau? A duk tsayin zamana da shi, kullum na bashi ha'kuri yana ba ni amsa da cewa bai san shi ba, domin shi ba zai yi wani ha'kuri ya cutu ba, ba kuma zai sassauta ba, sai ya yi mini hukuncin da ya yi nufin yi koda kuwa ban yi komai ba. Sai don kawai ya jefa ni cikin 'kunci da bacin rai. Amma yanzu saboda rashin ta ido ya karkace baki yana fa'din falalar ha'kuri, domin shi yake so a yi wa uzurin ha'kurin. Na hasaso irin tsananin da nake fuskanta ta bangaren mahaifiyarsa, take na fashe da kuka mai sauti domin na sani ba abin da zan yi wa Umma ta yi mini adalci. Kishin da take yi da mahaifiyata ne ta tattare ta dawo da shi kaina. Na dinga jin wani irin tashin hankali na shiga ta, tabbas guduwa zan yi domin ba zai yiyu na tabbata cikin 'kunci ba, sanin kowa ne na yi iyakacin hakurin. Zuwa yanzu kuma na riga da na gama dahuwa da 'kunsar ba'kin cikinsu, tura ta kai bango. Shi yasa nake takaicin yadda Sakina ta sake dawo da ni gidan nan, gidan da zan iya kididdige adadin farincikin da na yi a cikinsa, saboda gaba'daya ina rayuwa ne tamkar ta baiwa da mugun maigida. Ya sake 'kaimi wurin rarrashi yana cewa, "Ki yi hakuri ki bari yaranmu su girma a gabanmu, saboda su samu cikakkiyar tarbiya da nutsuwa." Na sassauta kukan na ce "Yaranmu ko kuwa yarana? Shin da ma kana lissafin kana da yara ne?" "Um um Guduyo! Komai girman laifukana ai ban ta'ba barranta kaina da su ba, na sani 'yayana ne, jinina ne, kada ki bari fishi ya rinjaye ki." Kaina ya sara adalilin ba'kin cikin da na sake tunowa na hadiye shi a goyon ciki da kuma haihuwar Afrah! Na zuba masa ido ina kallon sa ina sake hakaito wancan lokacin da ya shu'de, idan da wani ne ya ce mini rashin arzikin Gudale ya kai ya mini abubuwan da ya yi 'din zan 'karyata shi. Sai dai ba na ganin laifin kowa tabbas son zuciyata ne ya mini sanadin wahalar da nake ciki, ba irin hannunka-mai-sanda da Abba da Sakina har ma Al'amin ba su mini a kan bai kamata na auri SADIK ba. Tabbas na gaskata azancin maganar nan duk da ke cewa, sabon da kaza ba zai hana a yanka ta ba. Na goge fuskata wadda ta sake kumubura adalilin kukan da na yini ina yinsa, ido cikin ido na kalle shi, duk wani tsoronsa a yau ban ji shi ba, don haka na sake bude dukkan idanuwana ina fuskantarsa cike da jarumta na ce, "Ka yi mini adalci irin wadda za ka yi wa Sakina. A yau ba na son ka kalle ni a matsayin matarka, ina son ka mini kallon 'kanwarka wadda jini ya hada ku, ma'ana nasabarku ta hadu ne ta wajen uba, gidanmu daya, ko ba ka sona ai za ka yi kishina tunda dai jininmu guda. A ko'ina kai mai wakilta ta ne, mai kare ni daga kowanne irin tozarcin rayuwa. Don haka zan fa'da maka cewa mijina mugu ne, azzalumi ne, bai san komai ba sai son kansa, saboda na haifa masa 'ya'ya mata guda biyu, Allah ka'dai Ya san bala'in da na tsallake wurin cire mini cikin da yake na halal kuma mallakinsa. Yana da arziki, amma ba ya ya wadata ni, ya hana ni aiki, ba sassauci ko kadan a tsakaninmu, asalima yana ganin tamkar alfarma ce tasa yake zaune da ni." Kuka ya so 'kwace mini, amma na hadiye shi. Murya na rawa na ce, "Ya sani ina son sa, ya san ni ina yawan begensa, amma zai iya shafe kwanaki masu yawa bai sauke hakkin auren da ke kansa ba, ba don ba ya so ko sha'awa ba, sai don ya nuna mini ni din ce bai da bu'katar hakan daga gare ni, ba tare da tunanin ni ina cutuwa ba, a hakan kuma yake tsananin azabtar da ni ta hanyar hana ni fita koda kofar gida ne, saboda bai gaskata ni ba. Ya tsananta zargi a kaina, dare da rana, a cikin zullumin sa nake, sannan ban huta a hannun mahaifiyarsa ba. Don Allah fa'da mini wane adalci za ka tsaya ka yi mini a wajen wannan azzalumin mijin da yake neman kashe ni a tsaye? Tunda har yau ban wuce ya doke ni ba, ko da kuwa a gaban 'ya'yana ne." Idonsa ya ka'da sosai tashin hankali ya bayyana karara a dukkan jikinsa, ya rasa kalmomin da zai yi magana su gamsar da ni. Ya sake tsananta matsata, cikin murya marar amo ya ce, "A farko hakuri zan baki Guduyo! Na kuma fa'da miki irin falalar ha'kuri, da irin matsayin da mai yin sa yake rabauta da shi. Sannan na yi wa mijin naki gargadi, idan ya daina shike nan haka muke so, domin duk gatan mace, duk matsayinta aure shi ne rufin asirinta. Na sani duk tsiyar da yake miki, akwai kuma abubuwan da zai miki wanda ni a matsayin 'dan uwanki ba ni da damar yi miki su, ba mahalu'kin da yake son ya ga yar uwarsa a gida da sunan mutuwar aure sai dole, idan kuma ya'ki canjawa to dole ba yadda za mu yi sai a raba ku musamman tunda da zalunci a cikin zamantakewar." Hawaye na zuba na ce, "Ka gaskata ni, ba zan yi wa mijina 'kazafi ba? Ka kuma gamsu akwai cutarwa a zamana da shi?" Da sauri ya ce, "Wallahi Halima na gaskata ki, na kuma yarda ke din adala ce, ba abin da zai fito a bakinki sai gaskiya. Abu 'daya nake so ki yi a yanzu dai dukkanmu 'yan-uwanki kowa ya gamsu ba wacce take ha'kurin da kike yi a gidan aure. To ki 'kara ha'kuri Ubangiji ne ya yi nufin kawo miki mafita shi yasa ya haska lamarinki kowa ya gane halin da kike ciki. Ki 'kara hakuri ki ba wa mijin naki damar da zai gyara kurakuransa, ai yana son ki." Zuciya a dake na ce, "To ai ni ba zan iya ci gaba da zaman ba, domin na riga da na gaji, a yanzu na gamsu, na kuma gane ba abin da nake bu'kata a aure irin kwanciyar hankali, da mutuntunta juna. Na yafe soyayya, na yafe kyau, na yafe dukkan burin zuciya, domin su na biyewa na fa'da cikin halin da nake ciki. Na gane mutuntata juna da tausayi da adalci irin na shari'a su ne tubalin da yafi kowanne tubali 'karko a wurin ri'ke aure cikin salama. Amma ni nawa auren tubalin toka ne, domin so, sha'awa, da kyau su ne suka fi rinjaya ta, shi yasa nake 'dandanar kudata. Na ha'kura! Ba zan iya zaman ba, na gaji matu'ka." Na fa'da cikin kukan da ya kasa 'boyuwa. Hankalinsa ya tashi domin bai ta'ba ganin rikici tsantsa a idona irin haka ba, bai ta'ba ganin jarumta a tare da ni irin hakan ba. Ya sassauta murya sosai ya ce, "Ni na sani mai laifi ne, na kuma yarda da hakan, me yasa ba za ki ba ni damar da zan gyara ba? Me yasa za ki kafe? alhalin Annabi ya ce, "ku yi wa 'yan uwanku uzuri sau sabain." Da sauri na ce, "Na tabbatar na yi maka uzuri saba'in sau biyar, amma a wannan karon ina tabbatar maka wallahi na gaji da hakurin da babu riba ko kawaici a cikinsa, idan kuma ka kafe sai ka ci gaba da ri'ke ni, to kuwa daga yau zan fara addu'ar Ubangiji ya gajarta mini kwana, ba don na san hukuncin wanda ya kashe kansa ba, da sai dai ku wayi gari ku ga na ci abin da zai kubutar da ni da rayuwa tare da kai a kan dole." Ina rufe baki na ga ya zabura ya mike da azama sosai, yana ambaton, "Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun!'' Ya fice, ni kuma na ci gaba da kuka sosai ina ta tunanin na shirya faruwar komai, ko da kuwa zan rasa wanda zai taimake ni. Na dinga hawaye ina tunano matayen da kullum suke cikin fitinar miji, suna kuma da iyaye amma ba za a kai musu dauki ba, sai a bar mace tana ta kwankwadar ba'kin cikin da yake zama ajalinta, duk asibiti idan ka je bangaren masu ciwon hawan jini da ciwon zuciya, mafi yawa matane suke cika wurin ba kuma komai ba ne yake sababa musu wadannan muggan ciwon ba face ba'kin cikin miji ko na rashin kintsuwar 'ya'yansu. Lokaci ya yi da za mu fahimci gaskiya, aure ibadar Allah ne, shi da kansa ya tsara yadda zaman zai kasance cikin tausayi, girmamawa da kuma adalci. Shi yasa Ya kewaye shi da tarin dokoki iri-iri, hatta saki ma sai da Ubangiji Ya kawo matakai hudu kafin a yi shi, amma a yau muna cikin wani irin zamani a kan dan kankanin abu sai ka ji an cewa mace je ki na sake ki, saboda yadda kullum darajar aure take sake karyewa, tamkar ba ilimi ne yake fadada ba. Iyaye mussaman iyayen 'kasar Hausa ba sa ta'ba tsayawa su fahimci matsalar da 'ya'yansu mata suke fuskanta a gidajen aurensu, ko zuwa ta yi da matsala da zarar an tambaye ta shin akwai abinci? Indai ta amsa da e, sai ka ji an ce tashi ki koma, domin kuwa wata ba abincin ma take zaune. Wai shin abinci ne ka'dai hakkin da idan ba a sauke shi ba za a tuhumi miji? A ko'ina mace take za ta samu abinci matu'kar ba zabe za ta yi ba, domin bakin da Allah Ya tsaga ba Ya hana shi abinci. Don akwai wasu hakkokin da shari'a ta tsara ba wanda yake da hakkin sauke su sai miji, ba inda aka yi wa mace halaccin ta same su sai wajen mijinta kawai. Amma abin kaico, a yau mata da yawa suna nan babu wannan hakkin, kunya da kawaici ya hana su yi 'korafi. Da kuma mace za ta bude baki ta koka wannan gingimemiyar matsalar, ba za a yi mata adalci ba, sai ka ji ana fadin wance ai jarababbiya ce, harija ce, marar kunya ce, da sauran sunayen da za ta muzanta ta yi ba'kin ciki. Kuma abin mamakin har da yan'uwa mata wurin irin wadannan kalaman. A yau kowa ya san wannan matsalar ta damu mata da yawa, domin kuwa ta zama ruwan dare ba a tsakanin yara matan ba, ba kuma matasa ba, bare kuma wadanda suka fara manyanta. Ba abin da yake tayar mini da hankali irin yadda maza suke buda 'kofofin da matayensu suka hallaka a dalilin su din ba sa sauke wannan hakkin, wanda rashin kyatatuwar wannan al'amarin manufar auren ma gaba'daya ta lalace. Ina zaune a wajen kawai na ga ya dawo, Sakina na biye da shi da kuma antin Zariya. Suna zama Yaya Abdallah ya shigo. Abin mamaki ban ji 'dar ba, na ganin ya dauko mini antin Zariya da Ya Abdallah, domin ai ba su ne suke mini zaman auren ba, ba da su nake raba bacin ran da nake kwana nake tashi a cikinsa ba. 'Karkari dai su ce ba za su taimake ni ba, idan na kashe aure to na riga da na shirya wa faruwar komai, idan har zan iya jarumtar rabuwa da Sadik, to kuwa sun sani bala'in da nake fuskanta ya kai intaha. Antin Zaria ce ta bude zaman da addu'a don kore shaidanun da suke labe. Cikin rarrashi ta ce, "Haba Guduyon Gudale! Na dauka maganar ta wuce haka nan, kowa ai ya san kin yi hakuri. Dukkanmu kuma ba za mu sake zura ido ba tare da muna bibiyar zamanku ba, na sani akwai guraren da duk yadda kuke zaune lafiya da mijinki sai kin yi hakuri kin kawar da kanki, amma idan kika ga ha'kurin zai zama na zalunci, kar ki fa'da wa kowa, ki fa'da mini, ni din yayarki ce, kin sani kuma na haifi wanda ya fi ki. Don haka ni din uwa ce, idan har kika yi hakuri wannan maganar ta wuce, ni kuma na yi miki al'kawarin ba za ki sake ha'kurin cutarwar da yake miki ba, ni da kaina zan raba ku, na kuma baki mafakar da su Baba suke mana barazanar duk wacce ta kashe aurenta ba ta da gurbin zama a gidanjensu." Hawaye ya balle mini, ina jin tamkar na bude baki na zayyane musu irin ta'addacin da yake yi mini, na kalli Sakina na ce, "Kin fi kowa sanin irin azabar da nake sha a wannan zaman, taimake ni ki fa'da musu, ko su za su ji tausayina." Da sauri ya ce, "Ni da kaina na gamsu ban kyautata miki ba, Sakina ta sani, Ubangiji Ya sani, to mu bar shi a hakan. Ina rantsuwa da Wanda ruhina ke hannunSa na gane kuskurena, na canja, zan kuma gyara, na yarda wadannan mutanen ukun su ne shaida a kan ba zan ci gaba da yin abin da yake cutarwa ne a gare ki ko 'yayanmu ba. Ya Abdallah lauya ne, Antin Zaria tana cikin kungiyar kare hakkin mata, ga su nan a zaune su ne shaidunki, na kuma gamsu idan ba su ga canji ba, su yi fatali da zumunci, su gurfanar da ni a gaban kuliya, idan har ban yarda na rabu da ke cikin mutunci ba. Fatana dai yanzu ki ba ni wata damar, ki yafe mini." Cikin rauni sosai ya karasa maganar. Ya Abdallah ya mi'ke ya ce, "Halimatu let gone be by gone, na rufe wannan maganar, ki yafe ta, na sake jaddada miki na kashe ta. Ubangiji ya kiyaye gaba. Anti ni kam na yi gaba sai kin fito." Suka mike ita ma tana jan kunnensa har da rantsuwar tabbas idan bai canja ba, wallahi da kanta za ta gurfanar da shi, tunda abin da yake yi tabbas cin zarafi ne. Sakina ce ta kasa yin magana saboda yadda take tsananin kaunarmu ni da Ya Sadik, shi yasa ba ta maraba da duk abin da zai ta'ba aurenmu, ta kuma lura a yanzu fishi nake yi da ita a dalilin ina ganin tamkar ta yi son kai ne a tsakanina da shi Suka tafi, ya bi su zuwa waje, bai wani jima ba ya dawo, ya sake zama a jikina sosai ya ce, "Tashi ki yi wanka, mu je ki rokar mini Antin Zariya ta bar mana su Amnah." Kafin na yi magana yaran sun shigo da gudu, ganin Babansu a kusa da ni yasa suka yi turus, Aman kawai ya 'karaso ya fa'da mana yana gwalan-gwalantunsa. Sanin da na yi yarana suna bu'katar jin dumina yasa na tashi na isa gare su, ai kuwa suka rungume ni, amma sun kasa yin wani kwakkwaran motsi saboda ganin Babansu. Na ja su muka yi dakina, suna ta ba ni labarin Abuja, da irin makarantar da suke zuwa. Fes suke cikin nutsuwa da walwala tabbacin suna samun kulawa ta musamman, kyaunsu ya matu'kar fitowa, kasancewar farare ne 'kal masu dogon gashi irin na fulanin Yola. Afra kam irin jikina ta yo rugugu sai ta zama tamkar 'Yar turawa saboda farinta da gashinta, buloras ke nan. Ya shigo yana ri'ke da Aman a kafadarsa, a darare suka ce "Daddy ina yini?" Ya kalle su yana jin takaicin nisan da ya haifar a tsakaninsa da 'ya'yan cikinsa. A hankali ya ajiye Aman ya buda hannuwansa ya ce, "Amnah, Afrah come to your daddy, why are you doing this to me, am I stranger?" Suka isa a sanyaye ya rungume su yana jin son su na sintiri a sassan jikinsa, hawaye ya goce masa sai fadin "Astagafirillah!" yake a hankali. Ya mi'ke ya fita da su, na bi su da ido, na kalli agogo, na ga biyar saura na yamma na kishingi'da ina labarto wa zuciyata wasu al'amura na tushenmu, wanda na sani, da wanda na ji labarinsu. # SURAYYA DEE ✍️ 2/8/23, 10:22 - Buhainat: 🌺 *SABO DA KAZA* 🌺 *NA* *SURAYYA DAHIRU* ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.``` ```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️ ____________(�?)______________ https://www.facebook.com/profile.php?id=100069755834980 •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·�? *Godiya ta tabbata ga Allah(S.W.T.). Tsira da aminci su tabba ga Annabin Rahama(S.A.W).* *SADAUKAWA GA IYAYENA GUDA HUDU* *ALHAJI MUHD TUKUR* *HAJ FATIMA LADI ALI* *ALHAJI DAHIRU ALI* *HAJ MARYAM HAMISU KANO* *ALLAH YA JI'KANKU DA RAHMA YA BAKU ALJANNAR FIRDAUSI*. *FATAN ALHERI GA MIJINA* *(M.I. NASHE)*. *JINJINA GA SHUGABAN KUNGIYAR LAFAZI WRITERS* *SADIK ABUBAKAR* *Na gode da kokarinka akan rubutuna*. *Assalamu alaikum sister's! Barkanmu da sake ha'duwa a cikin sabon littafina.* *Hakika na yabawa kaunar da kuka nuna mini akan littafin *Halin Yau*. *Ba abin da zance muku sai dai fatan Ubangiji ya saka muku da mafificin alheri*. *Ina fatan zaku bibiyi wannan labarin sannu a hankali dan jin da wanne sa'kon ya zo.* *Ina addu'ar Allah ya bani ikon rubuta dai dai, ya hana ni rubuta barna*. *JAN HANKALI* *GABA'DAYA WANNAN LABARIN 'KIR'KIRARRE NE (FICTION) BAI FARU BA. HAKAN NAN SUNA DA GARURUWAN DA SUKE CIKI BANA KOWA BANE, NA ZABE SU NE TA YADDA ZASU 'KAWATA LABARIN.* *IDAN KIN CI KARO DA ABIN DA YA YI KAMANCECENIYA DA RAYUWAR KI TO AKASI NE. MANUFAR LABARIN JAN KUNNE DA HANNUNKA MAI SANDA AKAN WANNAN RAYUWAR MAI CIKE DA RU'DANI. BA WAI SHAGUBE GA RAYUWAR WANI KO WATA BA*. 1&2. *Free page.* *Tushe* Asalin kakanmu Alhaji Zubairu Lawal Moriki, 'dan asalin 'kauyen Moriki ta cikin 'karamar hukumar Zurmin jahar Zamfara ne. Bahaushe ne, kuma Bafulatani, domin mahaifiyarsa Bafulatanar daji ce, kyakkawan dattijo fari tas. Ya taso cikin tsari da 'ka'idar tarbiyar Bahaushen Arewa mai tsananin ri'ko da dokokin shari'ar Islama. Fataucin dabbobi ne ya kawo shi garin Kano har ta zame masa tamkar gida. Domin kuwa sannu a hankali ya kwaso iyalinsa suka dawo kano gaba'daya. 'Ya'ya biyar mai dakinsa Maimuna (Adda) ta haifa masa, duk da sun binne wasu da dama a dalilin tana wabi. Hajiya Hafsatu ita ce babba (Yaya ta 'Kwalli) ba ta ta'ba haihuwa ba, sai dai kuma yan'uwan nata ba su ta'ba bari ta ga gurbin rashin haihuwa ba. Sai dai kawai motsawar da zuciya za ta yi idan sha'awar ganin jininka ta motsa. amma ba don kukan wani abu ba, domin 'ya'ya biyu 'yan uwanta suka bata ta goya, ta kuma aurar. Dukkan abin da ya shafi yaran kuwa yana hannunta. Ramla da Ashir. Mace mai zafi idan aka tabo ta, mai son dinke barakar zumunci, duk inda ta ga zumunci zai samu tawaya yanzunan za ta yi dukkan mai yiwuwa ta 'dinke shi. Sai Alhaji Abubakar Moriki (Abba) shi ne na biyu, dattijon arziki mai tsananin ri'ko da ka'idojin shari'a, masoyin zumunci da kyautata shi. Dukkan karatunsa ya yi ne a bangaren addini, a 'kasar Sudan ya yi digirinsa na farko a fannin sanin ilimin Hadisai. (Hadith Science) Daga nan ya wucewa 'kasar Masar ya sake zurfafa iliminsa a kan sanin a fannin Shari'a da rabon gado. Dukkan karatun tallafi ne na gwamnatin tarayyar Najeriya. Daga nan kuma sai ya fa'da harkar kasuwaancin safarar zobo da 'karo a tsakanin 'kasashen Africa. Sosai ya samu daukaka a harkar, ba 'karamin nasibi yake samu ba, domin idan ana lissafa attajirai, babu shakka za a saka Alhaji Abubakar Moriki. Matarsa 'daya Hajiya Saude (Umma). 'Yar asalin garin Yola ta jahar Adamawa ce. Kyakkawar mace fara 'kal mai cikakken diri, mai yalwataccen gashi, sai dai gajeriya ce. Mace ce mai izza da jin 'kai, ta tsani wani ya rabe su, kasancewar mijinta shi ne garkuwa a danginsa. 'Ya'ya shida Ubangiji ya azurta su, biyar 'din farko dukkansu mata ne kyawawan gaske domin dukkansu ita suka biyo, suka sami tsayin mahaifinsu duk da mijin nata ba baya ba ne wurin kyakkawar sifa, sai dai ko kusa ba a hada kyaun mace da namiji, sannan farinta da dogon gashinta baki sidik sun shahara, sai ta zamo tamkar Balarabiya. Haka 'ya'yanta suke farare dogaye, masu gashi, duk irin yadda Ubangiji Ya azurta ta da samun wa'dannan kyawawan yaran kuma masu lafiya, ita ba ta gode ba, domin ba abin da take so irin ta haifi namiji. Hafsat ce babba, wacce ya yi wa yayarsu magajiya, sai Maimuna (Ummu) mai sunan kakarmu, sai Juwairiya, Ramla, Sakina, sai autanta da ya ci sunan sahabin Ma'aiki Abubakar ake ce masa Sadik kasancewar sunan Abbban ke nan, ita kuma ta ce Gudale. Sai Hajiya Binta Moriki (Maman Kebbi) da take aure a Kebbi tana da 'ya'ya uku Shafa'atu, Adnan da Ashir. Sai Alhaji Ssni Moriki (Baban Gusau) da ya kasance dan kasauwa mai sayar da suturu, a cikin babbar kasuwar Gusau, a can kuma yake zaune da iyalinsa. Mutum mai tsauri da fe'de gaskiya, komai 'dacinta, marar daukar wargi. Matarsa 'daya da yara biyar, Fatima, Abubakar, Maimunatu (Ummj), Abbas, da Farisa. Abbas kuma yana tare da mu, tun daga karatun sakandire da ya yi a Science Dawakin Kudu da su Ya Sadik shike nan ya zama dan Kano, duk sa'anni ne da su Ya Al'amin, Kuma duk Gudale ne 'karaminsu. Mahaifina Alh Ibrahim Moriki (Baban Yara) shi ne autansu, kusan Alhaji Abubakar shi ya yi masa komai tunda ga kan hidimar makaranta, har ya zuwa aure. Ma'aikaci ne a hukumar ilimin bai 'Daya. Mahaifiyata Safiyya (Mama) 'yar Kano ce, ta fito daga unguwar Magashi, cikin babbar zuri'a, ina nufin masu haula da yawa ba wai ku'di ba. Matsakaicin kyau ne da ita, sannan tana da dan jiki, da manyan idanuwa dara-dara, sannan wankan tarwada ce, yayin da Baba ya kasance fari tas! Lokacin da aka auro Mamanmu, Umma tana goyon Ramla ne, sosai suke zaman lafiya, domin Mama tana gama gyara bangarenta, matu'kar mijinta ya fita to kuwa za ta rufe ta tafi wurin Umma saboda a gidansu na gado suke zaune wanda Abba ya fadada shi, ya zamanantar da shi, a cikin unguwar Hausawa 'Yan-Babura. Sosai Umma take jin da'din zama da Mama, saboda biyayyar da take yi mata, musamman yadda take hidima da 'ya'yanta, barin Ramla da barci ne kawai yake raba su. Mamanmu ba ta cika shekara a gidan ba ta haifi Abdallah, lamarin da bai yi wa Umma Da'di ba, ta ji babu dadi sai dai ba a samu canjin mua'amala ba. Kafin Mama ta cika shekaru hudu ta hada yara Uku duk maza Abdallah, Azzubair (Babangida) da kuma Ammar. A wannan lokacin kuma Umma ta fito da dukkan munanan dabi'unta, sosai ta dora karan tsana a kan Mama da ya'yanta, babban ba'kin cikinta yadda haihuwa ta tsaya mata cak ga kuma wata ta zo tana haifar maza duk shekara, nan gaba hasken da yake kofarsu zai koma kofar Safiya da Ibrahim. Ta fara hana 'ya'yanta zuwa bangaren kanin mahaifinsu, sannan kuma idan Maman ta zo, ba za ta ga fuska ba, 'dan abu 'kank'anin zai faru za ta fara habaicin har gobe mijinta shi ne garkuwarsu. Sosai Umma ta takura wa Mama har ta kai fargabar ta yi ba'ki take yi, saboda yadda take fuskantar tozarci. Hakurin Mama yasa ko Baba bai fahimci halin da suke ciki da Umma ba, sai da tafiya ta yi nisa. Shi ma rashin ganin su Ramla a gidansa ne, ya kuma lura Mama ta rage shiga wajen Umma. Kasancewar shi ma mai son zumuncin ne, sai ya yi kamar bai fahimci matsalar a wurin matar yayan nasa take ba, yana yi wa tasa matar wayo da dabara ta hanyar cewa ita ce 'karama, sannan ai ya lura ita ta janye daga jikinta, ya lura ba ta zuwa 'kofarta kamar da. Ana cikin haka Umma ta haihu, again dai mace ce, ko ka'dan ba ta yi farinciki a zuciyarta ba balle ta yi godiya. Aka yi sunan Sakina babu wani armashi, saboda ta riga ta dora rai a kan boy ne a dalilin ta yi scanning an tabbatar mata namiji ne, sai kuma ga kyawawar budurwa ta iso. Watan Sakina goma Mama ta sake haihuwar Al'amin, Wohoho! Ina wuta Umma ta jefa ta, a lokacin mahaifiyarmu ta fuskanci wani irin tashin hankali da matsatsi, domin an kai jallin da ko tsakar gidanta ya gagare ta fitowa, kullum tana 'daki, haka 'ya'yanta, sannan duk shedantar Umma ba ta yinta idan maigidanta Abba yana gida, musamman da yake mai yawan tafiye-tafiye ne sai abin nata ya sake bun'kasa. Tashin hankalinta yadda duk tafiya ba ya banbance tsakanin 'ya'yansa da na 'kaninsa, hatta keke da ya ce ba ya son 'ya'yansa mata su hau, duk ya saya wa su Abdallah kowa da nasa, haka indai yana gari to da Abdallah yake yawo ko'ina, daurin aure ne, ko ta'aziyya ko yawo haka, duk dinkin da zai yi tare yake yi da shi. Haka makaranta 'daya suke zuwa da 'yayansa shi ne kuma yake biya gaba'daya. Wannan ya sake ki'dima Umma tana ganin tamkar gazawarta ne yasa ta kasa haifar namiji duk kuwa da ko a fuska mijinta bai ta'ba nuna mata cewar 'ya'ya matan da take haifa masa ya gaji ko baya so ba, duk haihuwa sosai yake murna da hidima ya kuma zaba musu kyawawan suna. Cikin ikon ubangiji watan Al'amin goma. Umma ta haifi 'danta lafiyayye sak ita ya biyo shima, fari kal, mai gashi domin gashin har idonsa yake, tun yana jaririnsa dan tsurut ne babu nauyi, ma'ana ba jiki. Ga mamakin Umma Abba bai yi wani zumudinsa fiye da su Sakina ba, domin har zuciyarsa bai ji yaron ya 'dara Abdallah a wajensa ba, ke nan shi ba yanzu ya yi 'da ba. Wannan al'amarin ya sake tsananta kiyayyar Mamana a zuciyarta, ta gaskata asiri take yi don ta mallake su ga'badaya. Rainon Abubakar ya banbanta da duk 'ya'yan da Umma ta haifa, wani irin gata take nuna masa tamkar dai ba ta samu haihuwa gaba'daya ba sai da ta shekara talatin a dakin miji. Komai na yaron a wajenta mai girma ne, ba ta ha'da shi da komai, tun mijinta na yi mata fa'dan kar ta lalata shi, har ya ha'kura ya koma yi mata addu'a. Shekarar Sadik wanda Umma take'kiransa Gudale biyu aka aurar da Hafsatu 'yar wajen Umma ta farko aka kaita Zariya, saboda nan ne garin mijinta, kuma malami a Jami'ar Ahamadu Bello, daan boko na gaske, tun kafin auren ya sama mata gurbin karatu a Jami'ar inda za ta karanta Tsumi da Tanadi (Economics). Hakan yasa Umma ta 'ki haihuwa tuburan ta dakatar da ita da 'karfin tuwo a cewarta ta barwa Yara. Wani abin da ya damu Umma yadda Sadik ya bijire mata daga hana shi zuwa sashinmu, duk juyin da za ta yi sai ya zo wajen Al'amin, kullum cikin saya masa kayan wasan da za su dauke masa hankali take. Amma da zarar gari ya waye tofa zai tafi, ba zai yarda ya dawo ba, sai ya yi barci sannan Abdallah zai kawo shi. Watarana yana ta kukan zai tafi ta ri'ke shi ta hana, Abba ya gane dalilin kukansa aikuwa cin mutuncinta da ya yi ba ka'dan ba ne, ya ce matu'kar dansa ne to dole kuwa ya so jinin Ibrahim. Shike nan sai ya zama rabi-rabi, har ya fi zama wurin Mamanmu. Mama kuwa tun haihuwar Al'amin ta dinga 'bari, duk cikin da za ta samu sai ya bare, a haka har aka shafe shekaru tara da haihuwar Al'amin yayin da Sadik yake da takwas, shakuwa ce mai tsananin gaske a tsakaninsu, hakan nan sosai Ya Sadik ya shaku da Mamanmu. Na iso duniya ne cikin cire tsammanin haihuwa daga iyayena, sannan ba 'karamin wahalar gaske Mama ta sha wajen haihuwar ba, hakan ya zama sanadin da aka juya mata mahaifa gaba'daya. Idan mai karatu na biye da kyau, zai gane mu biyar ne 'ya'yan Ibarahim Moriki, ni ce kuma 'ya mace tilo da na biyo maza hudu, kamar yadda Ya Sadik ya biyo mata biyar ya zama namiji tilo. Na taso cikin gata iri-iri, ba daga iyayena ba, ba daga yayye ba, haka nan ba daga Abba da iyalinsa ba, kawai Umma ce ba ta sona, take adawa da duk abin da mijinta ko 'ya'yanta za su yi mini. Ta yi juyin duniya Sakina da Sadik su daina kula ni amma ina, domin duk miskililancin Gudale zai dauke ni, shi yasa mafi yawan hotunan muna yara ina hannunsa, ko ina kan cinyarsa, muna da hotuna ni da shi muna yara kala-kala. Wani ikon Allah yadda Ya Sadik ya fi zaman sashinmu, ni kuma na fi zaman sashinsu saboda Sakina, tunda aka yaye ni, na yi wayo kullum ina gurinta, duk zare idon Umma da muzurunta ba na fasa zuwa ko fasa zama, sai idan Sakina tana makaranta, domin duk inda za ta je tare da ni take zuwa. A lokacin an aurar da duka 'ya'yan Umma Sakina ce kawai ta rage. Sakina ita ka'dai ce mace domin tsararrakinta duk maza ne, Al'amin da Sadik. Don hakan shakuwa ce a tsakaninsu ba ka'dan ba. Sai dai ba zai yiwu ta dinga yawo tare da su ko kwana ba, sai ya zamana ta ja ni a jiki duk da karancin shekaruna, tunda shekaru goma ta ba ni cif, tare muke kwana, ita take mini wanka ta shirya ni. Wata irin shakuwa ce ta musamman a tsakaninmu, hakan ba 'karamin da'di yake yiwa Abba ba shi yasa ma ya dawo da ni bangaren gaba'daya. Umma ce take kyashi da hakan, take yawan hantarar Sakina a dalilin ita ta janyo ni. Da wayona da hankalina aka yi bikin Sakina, domin na shekara sha uku a duniya, saboda sai da ta yi karatun Nursing ta gama, a lokacin tana da shekaru ashirin da uku. Tunda aka yi bikin Sakina na kasa jin da'din zaman, saboda ka'daici da rashin samun fuskar yin walwala, na fara a-sha-ruwan-tsuntsaye, idan ba Abba ne a gari ba, ba na kaunar kwanan wurin Umma. A hakan dai rayuwar ta ci gaba da gudana ina kallon irin yadda mahaifiyata take rayuwa cikin zullumi da kaffa-kaffa, saboda takurar da Umma ta yi mata. Musamman da Abban ya sayi wani katon kango da yake jikin gidanmu, ya fasa kofa ta cikin gidan aka yi shuke-shuken su alaiyahu, shuwaka, lemon tsami, zogale da sauran tsirrai. To fa Mama ba ta isa zuwa ta tsinka ko ta aika a ciro mata ba. Na kammala aji uku na sakandire ba dadewa da bikin Sakina, kwatsam sai ga Abba da takardar makarantar kwana ta Sojin Sama ta garin Kaduna, (Air force Staff School Kaduna). Ko ka'dan ban yi murna ba, domin ban ta'ba sha'awar boarding ba, Aunty Ramla ce kawai ta yi boarding a gidanmu, sai su Ya Sadik. 'Karin 'bacin raina Kaduna ta yi mini nisa, da ma a cikin Kano ne da sauki. Hankalina ya tashi, na dinga kuka. Baba ko ya ce ba zai yiwu Abba ya yanke hukunci ya yi masa musu ba. Ya Sadik da ke tsakaninmu da tsakuwa sai murna yake yi yana fa'din, "Na gode wa Abba da ya samo miki boarding wata'kila idan aka yi sa'a kya zazzage wannan tebar da kika ajiye tamkar wata uwar mata, ke kam da wuri za ki tsufa." Wadannan kalaman su ne kullum a bakin Ya Sadik har ya sa na zama very guilty. Ina tunanin laifi ne don na kasance mai jiki. A tsaye nake cak ma'ana ina da tsayi, sannan ina da jiki sai na zama irin giant din nan da suke tafe da tsayinsu da jikinsu, ni din fara ce tas, sannan na yi sa'a ina da manyan idanu dara-dara, hanci ba wani dogo ba ne, amma kuma dai ba laifi akwai, sai dimples a dukkan kumatuna, ko abinci nake ci, suna lotsawa bare na yi murmushi ko dariya. Ina da gashi sosai, sai dai yawa ne da shi ba tsayi, har gaban goshina yake, har wani kamar saje ya yi mini, 'kirjina a cike suke kwarai da gaske, hakan ya janyo ana mini kallon na zarce shekaruna, haka 'kasana a bude yake, kusan ma kibar ta fi shahara daga kuguna. Bangaren halayya kuwa na kasance mai nacin kan abin da na saka a raina, sannan ina da kafiya, sai dai kuma ina da hakuri, da wahalar gaske aji ana fa'da da ni. Ni ko irin fitinar yarinta ban yi ba, ba ni da abokin fa'da sai Yaya Sadik shi ma shi ne mai tsokanar ta hanyar ce mini Yar sukuta, ko Sady bon bon, ko Guduyo, duk cikin sunayen na fi tsanar Guduyo, ban san manufar sunan ba, amma dai na fi zaton saboda ina da jiki ne. Ba yadda ban yi ya daina ba amma ya 'ki, sai na tsiri ce masa Gudale. A farkon abin ba kurarin da bai mini a kan na kiyayi ce masa wannan sunan domin ba sa'ana ba ne. Ban ji ba, don kuwa ban daina ba, tun yana kawo mini duka, har ya hakura. Ni dai tun tashina ban ga fitanannen a gidanmu irinsa ba, domin Umma ta riga ta sangarta shi, komai yake so sai ta yi masa koda kuwa ba daidai ba ne, yanzun nan zai gama yin iyashege amma da zarar ya bukaci abu to ba ta tuna laifukansa za ta yi masa son ransa jikinta na rawa. Kowa nan nan yake da shi, ba ga su Mama da Baba da yafi zaman wurinmu ba, ba ga Ummansa ba, ba ga su Ya Abdallah ba, barin ma Ya Al'amin da komai zai yi a duniya sai da Gudale, wata irin soyayya da shakuwa ce a tsakaninsu tamkar tagwaye, kammaninsu daya sai bannacin shi Al'amin baki ne, sannan mai sanyin hali ne, yayin da Sadik ya zama siriri fari tas, yanayinsa 'daya da Ramadan Both hatta gashin kansu kusan iri 'daya ne saboda ya dauko jinin fulanin Yola. Abba ne kawai ba ya ta Sadik saboda bai son giggiwar da yake yi, ba ya banbanta shi da yayyuna, kusan ma ya fi fifita Ya Abdallah domin ni dai ban taso na same shi a gidan ba, Abba ya kai shi 'kasar Oman yana karantar Law. Haka Yaya Babangida a Sudan ya yi digirinsa akan Arabiya, Ya Ammar kuwa a Jami'ar Nigeria (Nsukka) ya yi karatunsa na (Mass Communication). Dukkansu kuma Abba ne ya yi dawainiyarsu, hakan ba 'karamin damun Umma yake yi ba, sai dai kuma ba yadda za ta yi, tunda duk wani shigi da ficinta bai yi tasirin da ya hana Abba yi wa 'ya'yan 'dan uwansa hidima da zumunci ba. Babban abin da ya sake dagula lamarin Umma a kan mu, a lokacin da su Yaya Sadik suka kammala sakandire, sun riga sun sakankance America ko England za a kai shi karatu, tunda suna ganin ya kai wasu bare kuma tilon 'dansa. Sai dai fir Abba ya tire a kan ba inda zai tura Ya Sadik, a yanzu ma yake yin fitina kala-kala bare kuma ya sake tura shi kasashen da suke da 'yanci, don haka Ya Al'amin da Ya Sadik a Jami'ar Ahamad Bello suka samu gurbin karatu, inda Al'amin ya karanci Halayyar 'Dan Adam (Sociology). Shi kuma Sadik yake karantar Urban And Rural Development. (Tsara Cigaban Birane da Karkara). Yaya Abbas kuma ya samu (Geography). Ba irin rikicin da bai yi ba a kan ba zai yi karatun ba ga'badaya. Ya samu daurin gindin Umma, Abba kuwa ya ja ya kafe ba zai sauya ra'ayinsa ba, tunda ba ya so sai ya yi ta zama, haka ya dauki su Yaya Al'amin ya kai su Zariya, ya damka su a hannun mijin Anty Hafsatu, wacce muke 'kiran ta da Antin Zariya, shi ne Vice Chancellor na makarantar a lokacin. Kan dole Yaya Sadik ya tattara ya tafi Zariya shi ka'dai, ya fara karatunsa,da su Yaya Al'amin a gidan Anti suke da yake cikin kwatsas din makarantar. Yayin da Antin Zaria babbar Ma'aikaciya ce a ma'aikatar E.F.C.C. A lokacin da nake shirin shiga aji hudu na sakandire inda zan tafi makaranta a Kaduna, a wannan shekarar su Ya Sadik suka kammala digirinsu na farko, suka fito da sakamako mai kyau. Ganin a lokacin shekarunsu ba wani yawa suka yi ba, bayan sun kammala bautar kasa, Abba ya tura su digiri na biyu (Masters) a wannan karon ne suka rabu domin Yaya Al'amin a Jami'ar Bayero ya samu, yayin da Sadik da Abbas za su sake komawa Zariya. Yayin da Yaya Ashiru yake karantar pharmacy a B U K. Ba'kin ciki a zuciyar Umma tamkar ta halaka, sai neman tsari da zama tare da dangin miji gida 'daya take yi, domin gani take yi ai don Gudale ya taso a sa'anninsa da yawa yasa Abba bai kai shi karatu waje ba. Tunda Ashir ma a shekara 'daya suka kammala. A haka rayuwar ta ci gaba da gurgurawa, tunda na fara boarding ban sake ganin Ya Sadik ba, domin lokacin zan zo hutu, shi kuma ya tafi, ba mu hadu ba sai da ya kammala, a lokacin ni kuma ina shirin kammala sakandire. # One Love # Ana tare # Surayya Dee ✍️. 2/8/23, 10:22 - Buhainat: 🌺 *SABO DA KAZA* 🌺 *NA* *SURAYYA DAHIRU* ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.``` ```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️ ____________(�?)______________ https://www.facebook.com/profile.php?id=100069755834980 •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·�? *Gaisuwa da fatan alheri ga masu bibiyar labarin mussaman masu turo da ku'dinsu tun tafiyar bata yi nisa ba* *Iyah Basiru da Mutarin Baffa suna gaisheku da godiyar soayyar da kuke yi musu* *Jazakumullahu khaira*🤝 *Page* 3&4. Na dawo sanye cikin uniform dinmu tamkar na sojoji, a lokacin na zama budurwa musamman da nake da jiki, komai nawa ya bun'kasa, na dan rage 'kibar, amma 'kirjina da 'kuguna sun cika tam, fuskata ta zama ta 'yammata, haka nan hankali ya fara shiga ta. A harabar gidan muka yi kicibus da Ya Sadiq, ya bude baki yana mamamkin irin girman da na yi, saboda tsayinmu 'daya, shi bai samu irin tsayinmu ba, Allah ne ya so shi bai yi gajartar Umma ba. Yadda yake mini kallon na girma, ni kuma kallon mamakin yadda ya zama 'dan 'kyamo nake yi, sai dai fuskarsa ta zama matured, ya ajiye gemu da saje, wani irin siririn saurayi fari tas, ma'abocin gashi ba'ki, ga shi kuma ya zamo wani irin hadadden guy dan kwalisa, tun yana yaronsa komai sai mai tsada bare yanzu da ya girma. Idan har lissafina daidai ne, shekarunsa ashirin da biyar, yayin da nake goma sha shida, ina shirin shiga sha bakwai. Na bu'de baki da nufin yi masa magana sai na tuna bai ta'ba kai mini ziyara ba, don haka na dauke kaina, na yi tamkar ban gan shi ba, na shige shashinmu a guje. Ya biyo ni da sauri, ko ya tsaya ya karbi Baba da ya janyo mini jakar kayana. A falo na tarar da Mama na rungeme ta tana fadin "Kar ki kayar da ni, sai yaushe za ki daina mini irin wannan cakumar ne?" Kafin na ba ta amsa na jiyo muryar Ya Al'amin a kicin ai kuwa na sake bazama na yi kicin din, sai dai ina isa na ci burki ban san me yasa a wannan karon na kasa rungume shi ba, shi ma ya tsaya yana kallona, da murmushi a fuskarsa ya ce "Autar gidanmu ta girma, ta 'kara hankali". Na bu'de baki ke nan Ya Sadik ya shigo da saurinsa, sanin na yi masa abin da baya so, na gan shi na dauke kai, shi dai ya fi son na risina na gaishe shi tsabar son girma, alhalin shi ko antin Zariya sai ya ga dama zai gaishe ta a mutunce. A guje na 'buya a bayan Ya Al'amin ina cewa "Wayyo Mamana zo ki boye ni". Ai kuwa ya nufo ni gadan-gadan yana cewa "Ko bayan Abba kika je sai na hukunta ki wallahi". Haka kuwa sai da ya ba ni rankwashi masu zafi har uku, Mama kuwa fa'di take "Haba Ya Sadik daga dawowarta? Bar ta ta ci abinci ta huta sai ku 'dora daga inda kuka tsaya tunda dai dole sai kun tsokani juna." Ransa a 'bace ya ce "Ai daina shiga shirginta zan yi, wai ni ta kalla ta daukewa kai?" A tunzure na ce "A kan me ba zan dauke kai ba? Yau shekarata nawa a Kaduna, har ina shirin kammalawa kowa ya je mini ban da kai, na sani ko mantawa ka yi da ni, shi yasa ni ma na mantaka, gane ka ne ban yi ba, ba wai share ka na yi ba". Ya girgiza ya ce, "Ban zo din ba, ba kuma zan zo ba, kin zama wata gandardar da ke, ba hankali sai girma tamkar go'diya" Cikin takaici na ce, "Tubarkallah! Kuma in sha Allah sai matarka ta fi ni gandarewa, haka za ka yi ta zu'kewa kana zama 'dan tsurut, sai ka zo kana neman ka yi 'kibar ko don ka yi kwarjini amma ba za ka samu ba". Takaicina ya kama shi ya juya ya fice bai ce komai ba. Amma na san bai bar maganar ba. Kai tsaye shashinsu ya nufa ya tarar da Umma da Anti Maimuna, ya wuce ba tare da ya kalli Ramla ba, bare ta ci arzikin gaisuwa. Kaf yaran Umma ba mai halayyarta irin Maimuna don haka ita ma takun sa'ka take yi da mu, duk da tana gaisawa da mu, amma dai sama-sama. Ya fito zai shige bayan ya ce da uwarsu Baba ya aike su shi da Al'amin. A lalace Anty Maimuna ta ce, "Ka dai ji 'butur kana rawar 'kafa da 'yan uwan wasu amma naka ko kallo ba su ishe ka ba, da ma ka daina cusa kanka wurinsu domin da abu zai taso yanzun nan za su nuna maka kai ne bare ba ka da 'dan uwa namiji abokin ha'di, mu kuma da Ubangiji Ya ba ka ka raina mu, ba don iyashegenka ba da wa zai kai ka gata? Domin duk mai 'yan uwa mata ai ya wuce kaico." Da'di ya kama Umma tana cewa fa'da masa dai, "A ce wai ba dama na sarrafa Gudale, indai ina son zaman lafiya da shi, sai dai na bi ra'ayinsa, ya 'ki ba ni hadin kai ta yadda zai jagoranci dukiyar ubanku, ba abin da ya sani sai dai ya saka sutura mai tsada, ya kuma fesa turare, sa'a 'daya ya yarda ya yi karatun. Ki dubi yadda Abdallah ya yi kane-kane jikin Abbanku! Ki ga irin dukiyar da aka narkar a lokacin aurensa?" Maimuna ta tabe baki tana cewa "Addu'a za mu ci gaba da yi kawai, domin ba haka suka bar shi ba." Ya galla mata harara tare da cewa, "Ke kam kin sha haushi a ce ba ki da aiki sai 'batawa, ko kadan ba ki san gyara ba?". Sanin halinsa na rashin kunya da tijara yasa ta yi masa tsit. Ya fice yana ayyana shi bai ga laifi don su Al'amin sun mori Abbansu ba, asalima laifin Abban 'daya ne a wajensa ta yadda sam ba ya sakar masa mara, ya takura shi, ban don haka ba, ba ruwansa da duk wadda yake so ya yi wa alheri. A yanzu ma takaddama suke yi, a kan ya biya masa ya wuce Europe ya yi Ph.D 'dinsa amma Abban ya kafe ba zai kai shi waje da sunan karatu ba, a yanzu ma baya ganin kowa da gashi, bare kuma ya kai shi 'kasashen da suka riki 'yanci sama da addini da kuma zumunci. A Daren ranar dai ya shigo ya iske ni a falo na bude jakar kayana, da wadda na zubo tarkacen ragowar kayan shopping 'dina. Ya zauna bayan ya dauki remote ya canja zuwa channel O, na kalli allon talabijin 'din wata ce take rawa tamkar ba 'kashi a jikinta, wani abin mamaki kuma ba 'yar siririya ba ce, kusan yanayinmu 'daya ga tsayi, ga kuma jiki. Yaya Sadik ya ce, "Idan kika yi irin wannan rawar dubu ashirin zan baki." Na murgu'da baki na ce "Me aka yi dubu ashirin kuma? Ai na wuce ta, nan kuma ba club ba ne, sannan ba studio ka ha'da don ka yi mini 'kidan ba." Ya kafe ni da ido, ya kasa hadiye abin da ya zo masa wuya, ya ce, "Duk duniya ba mahalu'kin da ya mini rainin da kika mini, ina fatan na samu damar da zan biyar da ke." Na gurmu'da baki na ce "Har abada ba za ka samu wannan damar ba, idan kuwa ka samu to zan roki Ubangiji ya hana ka sakat idan ka tashi biyar da ni din. Ina kuma fatan na samu damar da zan juyaka tamkar waina a tanda". Gabansa ya fa'di, muka kalli juna a tare, ya kasa gane mene ne dalilin jin fa'duwar gaban da ya tsinci kansa a ciki, ya sake kallona. Wani irin abu ya dirar masa, rigar da take jikina ta yi matu'kar fito da surar 'kirjina. Ya tsinci kansa cikin wani irin yanayin da yake tsintar kansa idan ya kalli 'kirjina. Kafin mu sake magana Mama ta shigo ta ce, "Halan dai al'kawari na neman cika, yaushe rabon da na ganka a gidan nan a daidai irin wannan lokacin, ko dai Sady bon bon ta ci galaba a kanka zance ka zo?" Ya mi'ke a zabure ya ce, "Amma Mama kin gama da ni, ni kuwa me zan yi da wannan shirgin, 'kankanuwar yarinya amma ta zama gari guda, nan gaba kuma ai ba a san me za ta zama ba". Wani irin abu ya shige ni, na fara kokwanton ko yadda nake ganin kaina, ba haka saura mutane suke kallona ba, ko dai da gaske shirgi guda ce? Na hadiye wannan damuwar na ce, "Allah Ya sauwake mini me zan yi da kai, d'an tsurut da kai sai fitinar tsiya, da 'din ma da nake cewa sai kai yarinta ce". Ai kuwa ya tunkaro ni, na yun'kura na arce ko nauyin jikina ban ji ba. Na zauna bakin gado ina haki, ina ayyana kullum na ce zan daina kula Ya Sadik ba na iyawa ana jimawa idan na gan shi zan yi masa magana. Tun ina 'yar 'karama ta nake son Ya Sadik, domin kowa ya san shi ne saurayina, tun yana gwale ni har ya koma dukana, amma ban fasa cewar shi ne mijina ba, hatta su Abba sun sani, har tsokanar sa ake yi idan aka ji yana kushe ni, ana fa'din kada fa nan gaba wannan 'yar lukutar ta wahalar da kai, ya kuwa sha mur ya ce baya son irin wannan wasan. Hatta Ummansa ba ta k'aunar wannan maganar, a fili take fa'da tuni ta yi masa mata, 'yar aminiyarta za ta ba shi. 'Yar masu arziki irinsu, ba irina da muke rawa da bazarsu ba, tana neman tsari da hada iri da Safiyya. Ire ire wadannan maganganun ne yasa da na fara wayo na daina cewa shi ne mijin domin kuwa idan har Umma ta ji, to ba abin jin nauyi ba ne ta zagi Mamana a kan idona, haka Ya Al'amin bai son wannan wasan, ko da wasa bai ta'ba zolayar Sadik ba, haka nan bai ta'ba shiga sahun masu tsokana ta a kan son da nake yi wa Gudale ba, duk kuwa da matsanancin amincin da yake tsakaninsu. Ko 'dakinsu shi ya hana ni zuwa, ban san me ya cewa Mama ba, ta hana ni duk da bai fito ya fa'di dalilinsa ba, amma na da'de da fahimtar ko ka'dan ba ya son doguwar mua'amala tana ha'da mu. Ba na mantawa a lokacin da nake shekaru sha uku, zuwa sha hudu, a lokacin da kirjina ya fara bun'kasa ba abin da nake so irin na yi kwalliya na saka dinkin da zai nuna nima fa na zama mace, idan na yi kwalliyar kuma ba abin da nake matu'kar marari irin mu hadu da Ya Sadik, ba abin da yake sani farinciki irin na dinga zirga-zirga a gabansa, da zarar na ga Ya Al'amin ya fita to kuwa zan zari jiki na je dakin da zummar kai abinci ko yi musu shara. Tun a lokacin na fahimci irin yadda Yaya Sadik yake shagala da kallon kirjina, cikin dabara kuma zai dan shafe ni, ko ya zaunar da ni kusa da shi, ta yadda jikinmu zai dinga gogayya, ya biye mini ina ba shi labarai marasa kan gado. Wani lokacin tafin hannunmu yake hadewa ya dinga murzawa cikin wani irin yanayin da ban fahimta ba, ko kuma sai ya kunna mini waka wai na yi rawa ya gani ko na iya, shi yana son wacce ta iya rawa, haka zan dage na yi ta karairaya don kawai na burge shi. Kafin na gama zan ga yana ta faman matse cinyoyinsa, idonsa kuma ya canja, a haka har Al'amin ya fahimci barnar da take neman samun muhalli a cikin gidanmu. Sai ya fara hana ni zuwan, ni kuma sai na kwashe na fa'dawa Ya Sadik, sai da Mama ta sani a daki ta mini duka, ta hana ni kuka, sannan ta hana ni zuwan. Na nisa na ce, "Watau Yaya Sadik ya dauka har yau din nan kallon rashin hankali yake mini, anya kuwa ba ya afa 'kwaya? Ban da haka mene ne zai sa ya ce na yi rawa a gabansa a cikin falon gidanmu a gaban iyayenmu?" Na muskuta na sani har yanzu da nake shirin kammala sakandire ina jin son sa a raina, matu'kar kuma zan hararo mijina to babu shakka Gudale ne yake zuwa mini, sai dai ina cike da fargabar yadda ya ke kushe ni, yake ganin tamkar ban kai na shiga cikin zaratan mata na kece raini ba. Na mike na isa gaban madubi, na kalli kaina, kallo irin na tsanaki, duk da dai ban isa na jefa kaina cikin jerin matan da kyaunsu ya kai ya kawo ba, to amma kuma ba ni da makusa, musaman da na yi sa'a ina da tsayi, sannan fara ce ni tas, ga gashi sannan ga idanuwa, bayan haka ga dimples, tabbas ina da jiki, ta yadda k'irjina a cike suke dam, sannan daga kwankwasona ina da fa'di, wato dai a wannan lokacin da nake cikin shekarun budurci jikina yana da matu'kar daukar hankali duk kuwa da 'kibata. Na yi jim ina tunanin dalilin da yasa har yau 'din nan Gudale bai daina 'kure ni da kallo ba, musamman dai 'kirjina, shin shi ma ya fara son nawa ne ko kuwa sha'awa ce kawai tunda a yanzu na fara fahimtar so da kuma sha'awa. Ban fito daga dakin nan ba sai da na tabbatar ya fita, sannan na je na ci gaba da harha'da kayana. Washegari na shirya tafiya gidan uwar dakina Anti Sakina da har yau 'din wani iri zumunci muke yi ni da ita, sanin kowa ne, Sakina ta daukake ni fiye da su Ramla, balle kuma Sadik da ba wani shiri suke yi ba, ko da yake shi kam da wa yake shiri ne? Gara ma da Ya Al'amin shi ma a hakan don Al'amin 'din ba mai son hayaniya ba ne, da kullum sai an raba su, saboda wuyar zamansa. Na isa na tarar da ita a hadadden falonta tana yiwa yarta Nana kitso, tana manna mata sabulu a karshen jelar a dalilin tsantsin gashin Sakina ta 'debo. "Oyoyo Autarmu, zancenki nake yi yanzu ina cewa bari na zo na yi miki wainar fulawa na kai miki gida, ko kin dawo da gajiya." Na yi murmushi na zauna ina cewa, "Kullum cikin canja kaya kike, yanzu har kin sake gyara falon nan?" Ta murmusa ta ce, "To mene ne jin da'din duniyar, idan kana da hali ka more rayuwarka, ta hanyar cin abin da kake so, da kuma mallakar abin da ya ba ka sha'awa, ka yi kyauta, ka kyautata zumunci, ka yi sadaka, shike nan fa, da ka mutu taka ta 'kare". Na ce, "Haka ne!" ne da iyakacin gaskiyata. Domin na shaida hakan Sakina take mai kyale-kyale ce, musamman da mijinta ya kasance mai wadata, bayan hakan kuma ma'aikaciyar lafiya ce. Tana da yawan alheri tamkar mahaifinta Abba! Sannan ma'abociyar sadaka da kyautata zumunci ce, duk kayan kwalliya da dogayen riguna na mafi yawa ita ke saya mini, ita take saya mini mayukan da suke gyara mini fata, haka nan inner wears dina asalin designers take saya mini a cewarta su ne suka fi dacewa da ni ta yadda za su kama mini jiki sosai. Ta kalle ni da sakakkiyar fuska ta ce "Allah dai ya sa ki samu gatan da na samu, ki fara karatu kafin Abba ya bijiro da maganar aure, sai a yi ta miki kallon girma saboda yanayin jikinki". Na mike na yi kicin ina fadin "Ai ni sai na kammala degree kafin na yi aure duka-duka fa ko sha bakwai ban yi ba". Ta ce, "Allah ya sa dattijon namu ya yarda, ki ga ni ma fa da yadda aka yi na karatun, Abba ya daukaki aure, Baba ne ba ruwansa duk yadda ta fàdi sha ne, sai dai, shi ba ya cikin kwamitin zartarwa". Na isa kicin ina dariyar Sakina wai baya cikin kwamitin zartarwa, tamkar da wasu mahukuntar wata ma'aikatar take. Na dawo d'auke da ruwa da lemo na zauna ina cewa, "Su waye yan kwamitin zartarwar?" "Yaya da Abba mana!" Ta amsa mini a ta'kaice. Kafin na yi sallama sai ga Yaya Sadik ya shigo, ya yi sallama a 'kasan ma'koshi. Ya zauna yana karkada 'kafa 'daya kan 'daya "Na Moriki yau kuma abin ba ko sallama?" Sakina ta fa'da cikin kwantar da murya. Ya bu'de idonsa tamkar wadda ya tashi a barci ya ce, "Na yi fa, ba ki ji ba ne, ke kin ji?" Ya mini tambayar yana dawo da idonsa gare ni. Na girgiza kai ina cewa "Gaskiya Yaya Gudale ba ka yi ba." "To ban yi 'din ba 'katuwar banza marar tsoron Ubangiji." # Team Gudale # Team Guduyo # Surayya Dee ✍️ # Ana tare. 2/8/23, 10:22 - Buhainat: 🌺 *SABO DA KAZA* 🌺 *NA* *SURAYYA DAHIRU* ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.``` ```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️ ____________(�?)______________ https://www.facebook.com/profile.php?id=100069755834980 •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·�? *Fatan alheri ga marubuciya* *JAMILA JANAFTY* *BA WACCE TA KAI KI SON LABARIN SABO DA KAZA BALLE TA FIKI* *DAN HAKA GUDUYO NA MIKI SON SO FISABIDILLAHI*. Page 5&6. Sakina ta zuba masa ido tana hasashen 'kanin nata, tana son tuno yaushe rabon da ta gan shi a gidanta, ta kasa tuna when last da ya zo mata. Kaso mafi yawa ta fi zaton so na yake yi, sai dai rashin alkiblarsa ya sa ba za ta yi saurin gaskatawa ba. Amma a ranta addu'a ta shiga yi, Allah ya sa hakan ta kasance domin ta riga da ta fahimci ina son shi, da zarar ya furta da gudu zan amince, duk kuwa da rashin mutuncinsa. Ya katse tunanin Sakina da cewa, "Yanzu saboda Allah ruwa sai na ro'ka?" Na tashi ina cewa, "Bari a kawo maka Yaya Sadik!" Na dawo dauke da robar ruwa ta sona mai sanyi na ajiye masa ha'di da tumbler. A lalace ya kalle ni ya ce, "Ke kam ina tausayin mijinki wallahi wanda zai kwashe ki abin a yi masa jaje ne, kin wani taho sankamkam tamkar ra'kuma". Ba'kin cikin kalmar rakumar da ya jingina mini yasa na zauna a sanyaye, hawaye kuma ya kwace mini, abin mamaki sai ya jikinsa ya yi laushi, ina kallon yadda Sakina ta tsananta kallon mu musamman Yaya Sadik. Tsawon lokaci ina shar'be Sakina ta 'ki yin magana, ya ja tsaki ya ce, "Ki dubi Allah Sakina! Me na yi mata da za ta dinga yin irin wannan kukan?" Ta nisa ta ce, "Ta yi maka abin arziki, kai kuma ka zage ta?" "Sakina ban son 'karya! Gidan uwar wa na zage ta?" Kai tsaye ta ce, "Gidan uwarka". Ya yi kanta tamkar zai dake ta, ko gezau ba ta yi ba. Ya tsaya yana nuna mata yatsa cikin fishi ya ce, "Kar ki yi zaton don na zo gidanki shi ne za ki zage ni, ki kwashe 'kalau". Uffan ba ta ce masa ba, ta ci gaba da yi wa 'yarta kitso da take ta barci. Share shi da ta yi, yasa ya koma ya zauna. Cikin kara'di ya ce, "Guduyo kin sani ban son irin wannan iskancin, ta ya ya ke da kike yar lukuta da ya kamata ki nisanci za'ki, kin 'dauko lemo kina sha, ni kuma sai ki ba ni tsurar ruwa. Ban da rowa mene ne hakan? Na yi magana kin saka mini kuka, har wannan tana neman 'kulla munafuncin na zage ki, me na ce da yake nufin na zage ki?" A tunzure Sakina ta ce na fuskanci a tsiyace ka zo , sai dai kar ka shiga ru'du ba gidanku na je ba, bare ka tisa ni a gaba da cin mutunci, nan gidana ne don haka ka iya harshenka". Ya mi'ke yana cewa, "Idan ni 'dan halak ne a cikin Habu da Saude, ba za ki kuma gani na a gidanki ba, da'din abin namu gidan ba kango ko kufai ba ne". Ya kalle ni ya ce, "Zo mu wuce na rage miki hanya". Na galla masa harara na ce "Ina ce ba kai ka kawo ni ba?" Ya wuce yana cewa, "Me za a yi da shiga lamarin mata, daga wacce za ta yi maka sharri, sai wacce idan ka fa'di ainihin yadda take za ta ce ka ci fuskarta, yo mene ne don na ce miki ra'kuma? Alhalin dangantakar danjuma da 'danjummai ne a tsakaninki da ita." Muka bi shi da ido domin lamarin nasa tamkar a buge yake musamman yadda idaonsa suke tamkar mai jin barci ko wanda ya tashi a barcin. Sakina ta kalle ni ta ce, "Iyashegensa kullum 'kara tsananta yake yi, amma ba komai ba za mu gaza da yi masa addu'a ba har Ubangiji ya amsa mana". Na yi shiru ina jin tausayin Sakina saboda yadda take cikin bacin rai, a dalilin ba 'karamin so take yi wa 'dan uwan nata ba, amma shi ko ka'dan ba ya mata ragayya har gara ita ma a hakan a kan manyan yayun nasu. Bai zame masa abin kaico ya ci mutunci duk wacce ta nemi yi masa fa'da irin na gyara kayanka ba. Yana isa gida kai tsaye shashinsu ya nufa, ya samu Abba a falonsa. Ya shiga ya zauna, ya gaishe da mahaifin nasa ba sukuni a tare da shi. Ya amsa cikin kulawa. Ya numfasa ya ce, "Abba so nake na ji me ake ciki a kan tafiyar tawa". Abba ya ce, "Ba za ka je waje ba, idan karatun kake so ka nema a nan k'asar." Ransa ya kai 'kololuwar baci ya ce, "Abba wai ni kam ba ni da hakki a dukiyarka ne?" Abba ya harzuka ya ce, "Ilimin da na yi bai yi zurfin da zan gane kana da hakkin ko ba ka da shi ba, sai dai ka fahimtar da ni yanzu. Daga haihuwarka zuwa yau adadin dukiyata nawa ka lashe mini? Amma ban tsira daga ba'kin cikinka ba, shin ba ni da hakkin ka mini biyayya ne?" Sosai ya sake daure fuska ya ce, "Tsakanina da Allah Abba na fahimci ba ka ta tawa, a kullum adawa kake da duk wani 'kudirin da zan zo gabanka da shi da zummar ka lamince mini." "Akan me zan yi ta taka Sadik? Har yau din nan fa ban huta da yi maka hidima ba, amma ba ka gane irin kyautatawar da nake yi maka ba, yau kwana nawa ina cewa ka je ka rage wannan sumar da ka tara? Dubi wani irin gemun rashin mutunci da ka ajiye! Tamkar wani 'dan akuya". "Abba Sunnah ne fa!" Ya fa'da cike da iyashege. Ya masa da'kuwa ya ce, "Ungo naka! Wannan kam gemun raini ne ba na Sunna ba, ba za ka ji da'dina ba har sai ka yarda da ra'ayina ko da ba a ra'ayin ka ba ne, in ko ka ci gaba da yin fito na fito da ni, ni kuwa ba zan fasa nuna maka cewar ka zo duniyar nan ka same ni ne a cikin shekarun girmana, ma'ana ko da ban same ka ba, ba abin da zai shafi ni'imomin da Ubangiji ya yi mini. Uwarka ta cusa maka ra'ayin iska wai Gudale, to ina tabbatar maka a wajenta kake Gudale domin ba a kanka na samu haihuwar namiji ba, tuni da ma Ubangiji ya ba ni su da yawa, Ga su Abdallah, ga Ashir ban ta'ba kallon ka fisu ba, don haka ka ri'ke wannan". Takaici ya kama Umma da take gefe tana kallon su, haka ma Sadik din, don haka ya mike yana cewa, "A wannan era din dai babu na biyunka. Madalla da kai Abba! Mai fifita 'ya'yan dangi akan biological son d'insa, na hakura da karatun, digiri biyun da na yi ka daure ka saka mini albarka, sannan ka mini alfarmar samo mini aikin yi, domin a yau na fahimci ya kamata na fara tsayawa on my leg, domin dukiyarka ba tawa ba ce, bal ma 'ya'yan 'yan uwanka sun fi ni dama a cikinta". Tsoro ya kama Abba! Yana kallon Sadik yana nazartar sa, anya kuwa a she'dantarsa bai fara afa 'kwaya ba? Ya sani ba 'karamin tsoron sa yake ji ba, amma a watannin nan wani zubin yana iya zama a gabansa ya fa'di duk maganar da ta zo bakinsa babu fargaba, da za a jima kuma ko washegari sai ya ga wannan shakkar sa da yake yi ta dawo, tabbas ba zai yaudari kansa ba, tilon 'dan nasa yana shan wani abu da idan yana cikin wannan yanayin zai iya keta kowa. "Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un!" Abba yake ta fadi yayin da Sadik ya fice da sauri. A fili Abba ya nisa ya ce, "Allah ka kawo mini 'dauki, Allah ka shirya mini Sadik, ka sani ban ta'ba jin rashin da'di akan 'ya'ya matan da ka ba ni ba, ban taba zakuwar sai ka ba ni namiji ba, Allah ina tawasili da adalcin da na yi wa 'ya'yana mata ka shirya mini wannan yaron da kullum yake sake kangarewa". Umma ta yi wuki-wuki da ido domin ta ji a jikinta tamkar da ita mijin nata yake. Ta nisa ta ce, "Abban yara tsakani da Allah ya kamata ka ba shi damar tafiya karatun nan, irin haka yara suke shiga wani hali, kana da damar kai shi ko'ina a duniya, amma ka 'ki. Saboda Allah ka kai wasu ma bare shi, ai kamata ya yi mu gode masa da ya yarda ya yi karatun yake kuma son ya ci gaba". Takaicin ta mai tsananin gaske ya kama shi, ya nuna ta da yatsa ya ce, "Ina gargadin ki ki kiyayye ni, ki bar ni na ji da ba'kin cikin sangarta yaron nan da kika yi, an 'ki gode masan, da bai yarda ya yi karatun ba, wa ya yiwa asara? Kansa ya yiwa wallahi, domin ko ke uwarsa da arzikina kika same ni, kuma Ubangijina ya suturta ni ta yadda ba zan jira wani ya taimake ni ba. Ke dai da zuciyarki ta zarme akan sai 'da ya zo ya tallafa miki sai ki yi ta yi, da ikon Allah ni kam sai dai yaro ya mini abu don neman ya yi albarka, amma ba don ya tallafe ni ba". Sanin da ta yi ba ya kashedi sau biyu yasa ta mike sum-sum ta bar falon. Washegari da safe na fito daga shashen Umma inda nan nake kwana bisa umarnin Abba, domin tunda aka yi auren Sakina na gudu, a dalilin rashin samun fuska a wurin Umma, sai idan Abba yana gari. Amma a yanzu da girma ya cim masa bai cika ma yawace-yawace ba, sai Yaya Abdallah ne ya fi yin harkokin Abban shi yasa ma ba ya aikin gwamnati, amma Babban lauya ne mai zaman kansa. A hanyar da ta raba shashin Umma da na Mama muka yi kicibus da Yaya Sadik, na yi kamar ban gan shi ba, na wuce shi, ina ganin yadda ya tsaya ya bi ni da kallo, ba tare da ya ce mini uffan ba, na dai san ya 'kulu da dauke kan da na yi masa. A tunzure ya isa gurin Umma, tana kicin tana saka wa masu aikinta ido kan abincin da suke yi. Ganin da ta yi masa a tunzure yasa ta fice ta ri'ke hannunsa, sai da suka shiga 'dakinta ta zaunar da shi a bakin gado sannan ta dafa kafadarsa ta sassauta murya ta ce, "Mene ne kuma na bacin rai yanzu da sassafe nan?" A zafafe ya ce, "Wula'kanta ni da waccan 'katuwar yarinyar take yi a gidan nan ne yake mini ciwo". Gaban Umma ya buga, ta 'kare masa kallo ta ce, "Gudale mene ne abin damuwa akan Halimatu? Na fara jin tsoro fa". Sai ta fashe da kuka sosai! Ya ce, "Saboda Allah Umma kin so ki sake bata mini rai ne, mene ne abin kukan kuma?" Da hawaye face-face ta ce, "Ina jin tsoron kada Safiyya ta kwace mini kai, tamkar yadda 'ya'yanta suka kwace mini Abbanku, ina jin tsoron yawan damuwa da ka yi da lamarin yarinyar nan, mene ne da har za ka dinga 'bacin rai saboda ita? Anya Gudale ba son ta kake yi ba?" Ya mike da sauri zuciyarsa tana tsananin bugawa, bakinsa na rawa ya ce, "Wanne irin ba'kin hasashe ne wannan? Ni kike ganin zan so wannan yarinyar, to na yi yaya da ita? A yanzu haka ta fi ni girma, ta fi ni tudu to nan gaba kuma ai ban san me za ta zama ba, wallahi kin b'ata mini rai Umma! Shike nan sai ba zan yi zumunci da ita ba, ai tunda jini ya ha'da mu dole zan ji zafi idan ta gan ni ta bagarar". Cikin kara'di ta ce, "Ban son wannan damuwar da ka yi da ita, tunda har take bagarar da kai, mene ne kai ba za ka yi watsi da dukkan lamarinta ba?" Ya nisa ya ce, "Haka ne zan yi yadda kika ce". Ta goge fuskarta ta ce, "Na dade da gane duk kinibibin uwarta ta kwashe su tsaf, duk namijin da tsautsayi yasa ya kwashe ta ya shige su! Domin an yi ittifakin zuri'arsu ba sa barin namiji salin alin, ga tabbaci ma ina gani ba iya mijinta ta gama da shi ba, hatta kurwar Abbanku tana karkashin ikonta. Shi ne kuma ake son sai an ha'da da kai ka'dai da Ubangiji ya ba ni! Wallahi da hakan ta faru gara a ce ina kushewa". Ya ce, "Yanzu Umma a yadda nake din nan har ki yi tunanin zan so Guduyo? Ban da farar fata mene ne da ita ne, ai ni sam ba na son 'yan lukutayen mata, ba sa burge ni. Kawai dai ina son na samu damar da zan rika ganin surarta, domin tana matu'kar kidima ni". Ihu Umma ta fasa tana cewa "Shike nan ta faru ta 'kare, ashe da gaske kana shaye-shaye Gudale? Ni ka furtawa wannan 'kazamar kalmar?". Ya mike ba tare da ya ji wata fargabar komai ba ya ce, "Ni irin wannan abin naki ne yake ha'da ni da ke, to idan ban fa'da miki damuwata ba, wa zan fa'dawa ya fahimce ni? Ba na son ta, ban ta'ba raya zan so ta ba, amma idan ba zan rufe ki ba, da gaske ina son ganin ta, ai abin ki yi murna ne, Gudalenki ya zama man". Salati kawai Umma take yi tana 'karawa tana cewa, "Haka za ka yi mini?" Ya fice ya bar ta cikin bacin rai iri-iri. Shi kuma bai ga laifinsa ba, to idan mutum bai fa'dawa uwarsa damuwarsa ba wa zai fa'dawa a duniyarsa? Washagari da hantsi ya sake tarar da iyayen nasa. Kusa da Abba ya zauna a nutse tamkar gaske ya ce, "Abba fa'da mini don Allah kana da shekaru nawa ka auri Umma?". A matu'kar sanyaye Abban ya ce, "Ina da shekaru ashirin da biyar Mahaifina ya ce ya gaji da zamana haka, shi ne kuma ya za'ba mini ita, a dalilin ya saba da mahaifinta wajen saye da sayarwar dabbobi". Kai-tsaye Sadik ya ce, "Shekaruna ashirin da shida next month Abba!". Ido sosai dukkansu suka zuba masa, sun kasa gane me yake damun tilon 'dansu, ba a buge yake ba, amma kuma sun tabbatar ba a cikin hayyacinsa yake ba. Da mamaki Abba ya ce, "Aure kake so ke nan?" "Ya ka'da kafadarsa ya ce "No! Ina dai son na gane irin adalcin da tsohonka ya yi maka, mahaifinka yana da hangen nesa, ina yi maka ta'aziyyar rashinsa Allah ya jikan sa." "Amin summa amin." Abba ya tsinci kansa da furtawa cikin ru'du. Tsawon lokaci yana kallon Sadik sannan ya nisa ya ce, "Ka fara koyon sana'a, idan na gamsu ka mayar da hankalinka akan sana'ar sai a je ma nemo maka auren a inda ka ga yarinyar". A sanyaye Umma ta ce, "Abdallah da Babangida kai ka samo musu mata fa Abban Yara". Da sauri ya ce, "Su ma sai da na ba su damar su kawo zabinsu, sai da na ga ba su da niyyar kawowar ya sa na zabo musu da kaina, suka karba kuma babu musu. Har yau din nan ba wanda ya kunyata ni." "Shi ma ai ba zai kunyata ka ba". Ta fa'da a tunzure. "Allah Ya sa! Amma dai ya kawo wacce yake so da kansa, domin shi da su ba 'daya ba ne". Daga Umma har shi duk sun san magana ya fa'da musu shi yasa suka yi tsit. Sadik ya mi'ke yana cewa, "Ni dai ka samo mini aiki, ka riga ka san ni ba zan iya sana'a ba, tunda Allah ya sa na yi karatun". Ya sake cewa, "Ka samo mini matar, ba zan ba'da maka 'kasa a ido ba, amma dai Abba plz! Bari ka ji ra'ayina, ba gajeriya ba, sannan ba mai jiki ba. Yar shawalwala, doguwa, fara, mai dogon gashi, wacce ta kammala karatunta na jami'a. Bayan haka ta kasance yar attajiri ce, ba na son a kwaso mini 'yar talakawa su zo su cika mini gida tamkar yadda dangin Umma suke yi, idan za su zo. Babu lissafi sai su 'dungumo da yawansu tamkar gidadawa". Cikin wani irin yanayi Abba ya mi'ke. Sanin da Sadik ya yi duka za a kawo masa yasa shi kwasa a guje, ya fice. # Team Gudale # Team Guduyo # Surayya Dee✍️ # Ana tare 🤝. 2/8/23, 10:22 - Buhainat: 🌺 *SABO DA KAZA* 🌺 *NA* *SURAYYA DAHIRU* ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.``` ```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️ ____________(�?)______________ https://www.facebook.com/profile.php?id=100069755834980 •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·�? Page 7&8. Ya koma ya zauna cikin 'kunan rai mai yawa ya ce, "Ba zan fasa fa'da miki kin lalata rayuwar yaron nan saboda dalilinki na jahilci. Amma da'din abin ke ma ba jin dadinsa kike yi ba". Ta yi shiru tana wasi-wasin sakawa Gudalenta hannu aka yi, ai da baya mata irin wannan sha'kiyancin, sannan idan Abbansu na guri ko kwakkwaran motsi ba ya yi saboda shakkarsa da yake ji. Amma a kwanakin nan hatta Abban bai tsira ba. A fusace ya bar mata falon zuwa cikin 'dakinsa. Na fito harabar gidan na hango shi ya fito kusan a guje, a fili na ce, "Ko sai yaushe zai daina fitinar da Abba zai daina kai masa mahangur'ba?" Domin idan har na gan shi cikin hanzari sosai, ko gudu gudu ba shakka Abba ne ya kai masa wawura. Haka kawai sai na ji ina son tsokanarsa kamar yadda na saba. Na saka sauri, na rufa masa baya, har mashigar bangaren samarin gidan. Ganin zai 'kule ya saka na bude murya na ce "Yaya Sadik na dauko maka turmin ne?" Ya juyo a fusace ya ce mini, "Kan uwarki za ki dauko mini. Munafukar banza, kullum idonki na kaina, na rasa irin wannan mayata. Wallahi saboda ke zan fara shan Lahaula! Ashe 'dan uwanka ma yana bin diddiginka, yana burin ganinka a uku?" Na maze tamkar ban ji zafin furucinsa ba, na ce, "Na sani ko zai maka amfani idan zaka yi sana'ar da ka 'kware ta 'ketara katanga". Takaici ya kama shi, ya juyo da gudu, ni ma na kwasa a guje, da iyakacin 'karfina nake gudun domin kuwa idan na yi saken da ya cim mini abin da zai biyo baya ba mai sau'ki ba ne. Abba na tsaye fitowarsa ke nan ya hango muna tseren gudu, dalilin da ya sanya Yaya Sadik juyawa, ba tare da na lura ba. Dole ta gabansa zan wuce, na ci burki a gabansa cikin matsanancin haki, da kuma nutsuwar na tsira. Domin na sani iyashegen Gudale bai da tasiri matu'kar Abba na wajen, ilai kuwa da na tsugunna sai hango Yaya Sadik na yi ya juya cikin gudun fanfalaki zuwa wajensu. A matu'kar fusace Abba yake ce mini, "Ashe har yau 'din nan ba ki daina zuwa wajensu ba?" Jikina ya sabe da rawa, saboda sanin da na yi ya sha mini togaciya akan na kiyayi zuwa wajensu. Da kakkausar murya tamkar ba Abba ba, ya ce, "ki kiyayi Sadik, zai ji miki rauni, ba sa'anki ba ne, ba kuma shi da nutsuwar da zai ji nauyin wargaza miki rayuwarki, ki taya mu kulawa da tarbiyarki". Daga hakan ya wuce ya nufi 'kofar da za ta sada shi zuwa cikin tafkeken kongonsa da a yanzu gefe 'daya ya zama wani irin lambu, mai dauke da lemon tsami, na za'ki, goba, kashu, fasadabir, har da mangwaro, ga kuma su zogale da duk sauran ganyayyaki da su aka fara shukawa. A hakan kuma tamkar ba a yanki komai ba saboda tsananin girman wajen domin asali filaye biyu ne manya a ha'de. A sanyaye na mike na yi wajen Umma domin lokacin da suke gudanar da aikin abinci ya yi, kasancewa ta mai son koyon dabarun girki-girke ce ya sanya ni yin 'kawance da masu aikinta, musamman masu hidimar abinci. Duk da cewa ba ta sakar musu ragamar abincin gaba'daya. Duk da yadda nake ganin tana 'daure fuska idan na shiga kicin ba ya hana ni tsayawa na saka ido, har ma na kama wani abin, musamman idan na tabbatar Abba na nan, idan kuwa ba ya nan ba ta jin nauyin cewa na fita bavta son kinibibi da nunkufurci, shin me yasa ba zan koya a wajen uwata ba? Ba na fishi domin gobe ma zan sake shiga, a dalilin Ubangiji ya yi mata baiwar iya sarrafa girki, fiye da zato. Sannan kullum abinci kala uku take yi, biyu na rana, ga kuma na dare, na daren ne ma ban cika tsayawa ba, domin ta fi yin tuwo saboda Abba. Matu'kar ba miyar kuka za su yi ba, Baba Delu sai ta san yadda ta yi ta kira ni domin na ga yadda za a sarrafa nau'in miyar da za su yi. Saboda tana jin da'din girmama ta da nake yi, sannan tana son a ce an 'karu da ita, tana son ganin yarinyar da take da burun koyon girke-girke. Mafi yawa idan na koma wajenmu, sai na gwada abin da na koyo, shi yasa na yi sa'a na tara kalolin abinci masu yawa, da na iya sarrafa su, don ma boarding school nake yi ta cinye mini lokutana. *Kina bu'katar dukkan nau'in sutura masu kyau, zababbu kuma masu sau'kin farashi?* *Kina bukatar siyar da furnitures din ki?* *Kina bu'katar siyan furnitures din hannu da basu ji jki ba?* *Albishirinki A AMYAS NEWLY & FAIRLY USED.* *Zaki samu dukkan abin da kike so cikin farashi mai sau'ki.* *AMYAS NEWLY & FAIRLY* *komai da ruwanka ne domin hatta Talabijin da fridge, inji wanki, da dukkan dangin electronics zaku samu a wajensu. Sababbi ko tuwaris masu quality* *Dan haka ku tuntu'be su àkan wannan lambar dan tabbatar da nagartar kayansu. 08083909947* A hakan na cinye hutuna, na tattara na koma bisa rakiyar Yaya Al'amin da Yaya Sadik. Yaya Abbas ya tu'ka Abba zuwa wani daurin aure Dutse, domin ba wanda Abba yake yarda ya tuka shi, matu'kar ba Yaya Abdallah ba sai Ya Abbas domin a nutse yake yin tu'kinsa kai akan komai ma mai nutsuwa ne kwarai da gaske. A hanya sai takalar Autan Umma nake yi don dai na samu ya kula ni. Amma ya yi funfurus, tamkar ba da shi nake yi ba. Yaya Al'amin da ya kasance direba, ya tunzura ya ce, "Wai ke kam wacce irin yarinya ce ne? Tunda ga Kano kike yi masa magana amma har yanzu da muka iso Zariya bai ce miki kanzil ba. Hakan bai ishe ki isharar cewar ba ya cikin sukunin da zai kula ki ba? Ki 'kyale shi mana ya ji da damuwarsa". Yana rufe baki Ya Sadik ya juyo ya ce mini, "Ina jin ki, ai dai kin san laifi kika mini kan laifi! Amma ba ki san ki ba ni ha'kuri ba. Ranar nan Sakina ta nemi yin munafunci a tsakaninmu, yanzu kuma ga wani zai sake shiga, ki daina ba su damar shiga tsakanin zumuncinmu, saboda haka ma na yafe miki mun shirya. 'Yan ba'kin ciki sai su rungumi taransifoma". Yaya Al'amin ya ce, "Su waye 'yan ba'kin cikin?" Ba ja'inja Yaya Sadik ya ba shi amsa da cewa, "Kai da Sakina mana! Babban burinku ku ga mun sami matsala da Guduyo, to abin da ba ku sani ba, duk yadda kuke gadarar ku ne mafi kusa da ita, ni kuma zumuncina da ita ya fi 'karfin ku ce za ku shiga cikinsa, domin mutum kunyata zai yi". Sanin halinsa da Yaya Al'amin ya yi yasa shi fa'din, "Allah ya bar zumunci" A ta'kaice. Har muka isa Kaduna hira muke yi sosai, amma da zarar Ya Al'amin ya saka baki, ba kunya zai ce ya yi masa shiru! Tamkar dai shi ne Babba. Suka ajiye ni, muka rabu cikin alhini, Ya Sadik ya mini al'kawarin in sha Allah zai halarci bikin (Graduation Ceremony) da za mu yi. Na kalle su dukkansu na ce "Ba ku ba ni komai ba". Ya Al'amin ya juya ya shiga mota yana cewa, "Ke ro'ko ba ya miki nauyi ne?" Yayin da Ya Sadik ya zura hannu a aljihunsa ya fito da sabbin kudi masu yawa, ya zaro 'yan dari biyar guda hudu ya ce, "Ungo na sammiki, domin zance za ni shi yasa na samo sabbin ku'di kin san suna 'kara aji da kwarjini". Wannan maganar ta yi matu'kar razana ni, na yi nadamar ro'kon da na yi, da ya zama sanadin da na shiga wani irin tashin hankali da bugun zuciya. Ya lura da canjin da na samu, amma ya waske da fa'din, "Ki yi karatu sosai, ban da kawance da kawayen banza. Sannan ki kula da salla domin ita ce komai a rayuwar mumuni". Ya shige mota suka tafi, suka bar ni cikin zullumi da fargaba. Yaya Sadik kam duk tsiyarsa ba ya wasa da salla, wannan dabi'ar ce ta sanya yake samun sassauci a wajen Abba, yakan ce duk wanda ya ri'ke salla da sannu Ubangiji zai canja dabi'unsa zuwa kyawawan dabi'u. Na fi kwana uku ina cikin damuwar budurwarsa da ya ce mini zai je zance, haka siddan na ji na tsane ta tun ban gan ta ba. Na san ina sonsa, amma ban tabbatar ba sai a wannan lokacin da na ji zancen wata a bakinsa. Da 'kyar na cire wannan maganar a raina. Na fuskanci karatuna, don kuwa jarrabawar 'karshe zan rubuta, idan na samu tasgaro, ni ce nake da asara. Na tafi ba jimawa Yaya Sadik ya koma Jami'ar Bayero don yin Ph.D dinsa. Ya Al'amin kuma ya samu aiki da gidan Talabijin na 'kasa reshen jahar Kano (N.T.A KANO). Ya Abbas kam ya riga su samun aiki, ya jima yana aiki a Federal College of Education Kano(F.C.E). Yayin da Ashir take aiki a Asibitin Malam tunda Pharmacy ya karanta. Haka rayuwar ta ci gaba da gurgurawa har ranar bikin gama makarantar mu ta zo. Kusan kowa ya zo mini wannan bikin, hatta iyalan kawun Gusau sun zo, bare kuma Antin Zariya da muka fi kusanci. Sun ji da'din zuwan kuwa, domin na karbi kyautukan karramawa har guda uku. Na kar'bi na dalibar da tafi kowa 'da'a, na karbi na wacce ta fi kowa iya lissafi. Sannan na lashe kyautar dawowa makaranta akan ka'ida, ma'ana ba na 'karin hutu. Murnar da na gani akan fuskar ahalina ya matu'kar sa ni nisha'di da rawar kai. Ina fatan Allah Ya saka sakamakon jarabawa da muka kammala ya fi hakan sanya musu farinciki. Yaya Sadik ne kawai yake fadin "Akan me ban lashe Turanci da su Chemistry ba?" Wai ban yi kokarin a zo a gani ba. Kwana biyu tsakani muka kammala gaba'daya, direban Antin Zariya ya zo dauka ta a dalilin ta roki su Abba za ta dauko ni na yi kwanaki uku a gurinta sai mu taho tare, saboda za ta zo aiki na sati guda a ma'aikatarsu ta Kano. Sosai na ji da'din zama duk da ba zan iya tuna yaushe na zo mata ba, saboda ta fi zaman Abuja. Sannan ni kaina ban cika barin gida ba, idan kuwa har ba na gida to ba na wuce gidan Sakina. Ko gidan 'kanwar Mama da take zaune a 'Danladi Nasidi nan din ma ba sosai ba, na fi dai 'karfi a gidan Sakina." Ba wani jimawa WAEC ta fito, sosai sakamakona ya burge kowa, domin A1 guda uku ne a ciki sai B2 da B3 ko C babu, balle aje ga zancen D ko F. Haka result din JAMB ya yi kyau domin kuwa ya zarce 200. Wannan sakamakon shi yasa ba wahala na samu gurbin karatu a Jami'ar Bayero. Inda na tsinci kaina zan karanci (Human Anatomy) bangaren likitanci ne. Ba cece kucen da ba a yi ba, kafin na fara wannan karatun, saboda mafi yawa an fi son a aurar da ni, ni kuma na kafe a kan ba ni da saurayi, bisa hudubar Sakina. Kan dole Abba da Yaya suka shafa mini lafiya. Na fara karatun cikin dokokin masu yawa. Mafi yawa tare muke tafiya da Ya Sadik, idan kuma ba shi da lectures da safe idan yan mutuncinsa na kusa zai bar komai ya kai ni. Idan kuwa 'yan tsiyar suna kusa na kira layinsa sama da sau goma bai 'dauka ba. Ko kuma ya 'dauka ya balbale ni da sababi a kan shi ba direbana ba ne, ba kuma shi nake yiwa karatun ba. Haka zan kwantar da murya na ce, "In sha Allah za ka ci moriyar karatun nan, ka sake daurewa dai, ai na sani kana 'kokari". Wataran na yi sa'a ya fito ya kai ni, wani lokacin kuma ko nafi 'kuda naci zan ha'kura na 'kyale shi. A haka na kammala shekarar farko, karatun kuma yana tafiya yadda ya kamata, domin point 'dina ya yi nauyi. sosai. A wannan shekarar wani attajiri a gaban layinmu ka'dan ya nemi tayar mini da hankali wai so na yake yi, matarsa ce ta rasu ta bar shi da yara biyar, ba wani babba ba ne amma dai ya kai shekaru arba'in da biyar ko da shida. Kai tsaye Abba ya tunkura da maganar wai a ba shi izini tare da al'kawarin ba zai hana ni karatuna ba. Daga Abban har Baba sai murna suke yi wai mutumin kirki ne, kowa ya san shi, mai kokarin ri'ke iyali ne, ai ko na yi tsalle na dire na 'ki amincewa. Tun zuwan farko na fa'da masa gaskiyar magana ban amince ba, duk kuwa da bavshi da makusa, ba kuma wani tsufa a tare da shi. Kawai ina ganin yadda 'kawayena suka auri mai iyali suke artabu, kullum cikin fitina ba ga matar gida ba, ba ga yaran gidan ba, kullum sai an yi maka sanadin 'bacin rai, ko kuma a yi ta bin ka da bi-ta da 'kulli, duk wani alherinka ba za a gani ba, amma komin 'kankantar laifinka sai ya zama abin yayatawa, abin tattaunawa abin kaicon kuma har da sharri za a 'hada. Na sani wacce za ta ri'ke masa yara yake nema. Indai da adalci ai kamata ya yi ya nemi wata bazawara mai hankali, ko widow wadanda suka riga suka san matsalolin aure, suka kuma haifa su ma, amma rashin adalci ne zai sa a ce na amince, zaman aure zan yi ko rainon da babu godiya? Ba karamin takaici su Abba suka ji ba, da na 'ki amincewa, suka dinga fa'din sai na fito da wanda nake so domin ai da ma da sharadin ba sai na kammala karatun zan yi aure ba, aka bari na fara karatun. Haka na ba da ha'kuri a kan zan kawo. Yaya Sadik kuwa ya dinga fa'din "Ai kuwa kin yi wa kanki attajiri irin Alhaji Anas a ce yana son ki ki ce ba kya son sa? Bayan kyakkawan mutum ne ga nagarta?" Na bashi amsa da cewa, "Ba na son sa tunda dai ni zan zauna, ba wani ne zai zauna mini ba". Ya tabe baki ya ce, "kyakkawan da shi fiye da ke?" Na 'ki tankawa, domin so yake ya samu damar da zai yi mini cin mutunci. Daidai lokacin shi ma ya fara son wata Nusaiba Lawal Makole a gabanmu ka'dan suke Islamiyya 'daya muka yi. Babanta attajiri ne kwarai da gaske. Daliba ce a ECOSAT, tana karantar Lab Science. Siririya ce sosai, sannan doguwa fara. Ta dai dace da muradinsa. Kullum ni yake damun na samo masa lambar wayarta, mafi yawa a hanyarmu ta zuwa makaranta ko dawowa zancenta yake yi, ba ya la'akari da yanayina da yake canjawa matu'kar zai sako maganar Nusaiba. Haka kuma ba na ta'ba bari hirar ta yi tsayi, zan yanke ta, ko na bar shi ya yi ta abarsa shi ka'dai. # Team Sabo da kaza # Ana tare.🤝 # Surayya Dee ✍️. 2/8/23, 10:22 - Buhainat: 🌺 *SABO DA KAZA* 🌺 *NA* *SURAYYA DAHIRU* ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.``` ```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️ ____________(�?)______________ https://www.facebook.com/profile.php?id=100069755834980 •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·�? Page 9&10 *Fatan alheri ga marubuta Iyayen dakina masu wankakkiyar zuciya* *FADILA LAMI'DO* *BINTA ABBALE* *Na gode sosai da kokarinku kan rubutuna*. *Allah ya kara muku basira da daukaka*. Ranar Talata, a ranar da na kammala rubuta jarrabawar 'karshe ta zango na biyu ma'ana 'karshen aji biyu (Second Semester), tana cikin jerin ranakun da ba na mantawa. Ba don komai ba, sai don dalilai guda biyu. Na farko, wani irin al'amari ne ya faru da na kasa tatance shi. Domin jarrabawar 8-10 nake da ita. A ranar kuma Yaya Sadik ne kawai a gidan, daga Yaya Al'amin har Yaya Abbas sun yi je Moriki ta'aziyyar rashi da aka yi, har da Yaya Sadiq Abba ya ce su tafi amma ya 'ki ya ba da uzirin yana da test. Ba irin 'kiran da ban yi masa a waya ba, amma da yake 'yan tsiyar na kansa bai 'dauka ba, tunda ba shi da darasi a wannan lokacin. Na kalli agogo na ga kafin na fita na samu abin hawa zan iya makara, don haka na manta dokar hana ni zuwa shashensu. Da na duba harabar gidan na ga ba kowa, sai kawai na doshi gurin nasu. Na shiga da sallama na tarar da shi a kwance idonsa biyu. Amma ya yi la'kwas tamkar ruwa ya cinye shi. Daga bakin 'kofar na tsaya tunda a tsorace nake a dalilin karya dokar da na yi. Na marairaice na ce, "Ka rufa mini asiri Yaya Sadiq ka kai ni, na yi maka al'kawari daga yau ba zan sake matsa maka ba. Zan fa'da wa su Abba ko mai Adaidaita ne a daukar mini". Ya yi shiru tamkar ba da shi nake ba. Na bu'de baki da nufin sake ro'kon, ya 'daga mini hannu alamun na yi masa shiru. Na kame bakina tunda nema nake yi a gunsa. Cikin murya marar amo ya ce, "Kasala ke damuna, 'kafafuna ciwo, ke komai ma ciwo, ga sanyi nan sosai nake jin sa har cikin 'kashi. Zo ki mini tausar 'kafafuwana idan na ji dama-dama wata'kila na iya tu'kin". Ba tunanin komai na 'karasa na fara yi masa tausar, ban yi da yawa ba, ya dinga wani irin nishi, ya mi'ke. Ba zato kawai na ji ya 'kan'kame ni da 'karfin gaske. Yana wani irin abu, can kuma ya yi wani irin al'amari mai kama da gurnani, jikinsa ya saki sosai, ya sake ni. Ina bakin gadon ina fama da 'barin jiki da kuma tsoro, domin boxer 'din jikinsa bai iya hana abin *da ya feso shafa ta ba. Kafin na ce wani abu, sai jin sa na yi cikin tsawa ya ce, "Fitar mini a 'daki, ni kam ba an hana ki zuwa nan ba?" Jiki na rawa na 'dauki 'dankwalin da ya zame a hannu ban ma iya 'daurawa ba. Sai da na je bakin 'kofa na juyo, na gan shi ya mi'ke, ya doshi ban'dakin cikin 'dakin, na 'daga murya na ce, "Zacka zo ka kai ni 'din?" Kai kawai ya 'daga mini alamun e. Na dinga fa'din "Na gode sosai! Sai dai me? Haka na fita 'dankwali a hannu saboda tsananin ki'dima. Ina fita din kuma, Abba ya hango ni, ba kuma yadda zan yi na koma ko na 'buya. Saboda fili ne sosai ba wata ma'boya. Ya ja ya tsaya, ni ma na tsaya a inda nake, cikin rawar jiki na samu na 'daura 'dankwalin na gyara zaman Lab Coat din jikina. Na karasa gabansa na tsugunna ina gaishe shi cikin rawar murya irin ta rashin gaskiya. Fuska a 'daure ya ce "Me kika je yi can wajen?" "Abba makara zan yi shi ne na ro'ki Yaya Sadiq ya zo ya kai ni, jarabawa zan shiga ne". "Amma ban sha fa'da miki matu'kar ba shi da darasin safe, ki dinga tafiyarki ko kuma Al'amin ko Abbas wani ya kai ki ba?" "Ka fa'da Abba! Ka yi hakuri". Ya nisa ya ce "Sadiya! Na 'dago na kalle shi, da sauri na mayar da kaina 'kasa ba tare da na amsa 'kiran ba. Saboda yadda na ga tashin hankali a fuskarsa. "Na Sha fa'da miki ki daina zuwa wajensu, kin 'ki, na fa'da miki gaskiyar magana Sadik fa zai iya yin komai, domin ba shi da kunya bare ya ki nauyi". Yana rufe baki na ce "Addu'a za ka yi masa, bare ni ba ya mini rashin mutuncin". Ya jima yana kallona ya nisa ya ce, "Ke nan dai na yi 'karya?" Da sauri na hau rantsuwar ba hakan nake nufi ba. Ya nisa ya ce, "Ni na haifi Sadik ashe kuwa a ce ba na son sa, ko ba na yi masa kyakkawan zato, ko addu'ar shiriya bai taso ba. Amma hakan ba zai hana na fa'di gaskiyar lamari ba. Ina jin tsoron abin da zuwan ki wajensa zai haifar mana, yau ne karo na uku da nake ganin kin fito daga wajensu, idan har ba mantawa na yi ba, tun kina sakandire nake ta jan kunnenki akan ki kiyayi Sadik amma kin 'ki ko?" Na kasa bu'de baki na kare kaina, domin ni kaina a cikin ru'du nake a dalilin matsar da na sha a hannunsa, duk da dai iya rungumar ce kawai. Karon farko da na ji Abba ya ce shi ya haifi Yaya Sadik. Ya nisa ya sake cewa, "Ki fita harkarsa, sannan lallai ki turo mini wanda kika aminta da shi, hankalina ba zai kwanta ba, har sai na ga mun rabu salin alin da ke". Ya shige wajensa ya bar ni a wajen, na bi shi da ido ina raya daga tattakin da ya zame masa 'ka'ida ya dawo. Meeting sosai suka yi a kaina, Abba da Baba har Yayar 'Kwalli ta zo. Dukkansu bakinsu 'daya aure suke son yi mini kafin hutu ya 'kare. Tunda za mu yi dogon hutu. Na dinga jin kunyar Abba na sani wani irin kallo yake yi mini. Sannan na san ba zai bayyana musu ya gan ni na fito a wajen samari da sassafe kai babu kallabi ba. Cike da ladabi na ce, "Ni ban shirya da kowa ba, amma ku 'dan yi mini ha'kuri na 'dan lokaci 'kalilan". Yaya ta amsa da cewa "An ba ki lokacin Halima, sai dai ki sani ba mai yawa ba. Domin ba zai yiyu mu zuba miki ido da sunan karatu ba. Matu'kar ba ki turo wanda kike so ba, ba shakka Anas ne mijinki". Na 'daure fuska sosai don ta fahimci cewa ba na maraba da shi har cikin zuciyata. Haka na tattara na wuce gidan Sakina! Domin har yau 'din nan ba ni da inda nake zuwa na sake, na yi komai kaina tsaye irin gidanta, ko gidan Umman 'Danladi Nasidi ba na sakewa irin haka. Duk kuwa da mace ce mai son zumunci da inganta shi, komai yi mini take yi, idan har ina gidan matu'kar abu 'daya take da shi, to babu shakka sai dai ta hana Aziza 'diyarta ta ba ni, tana fa'din ai ita ce babba sai ta yi hakuri, duk kuwa da kwanaki ashirin ta ba ni kacal. Aziza na cikin mutanen da nake jin su har cikin raina, kusan a cousins 'dina na family din mahaifiyata na fi son Aziza haka na fi son mahaifiyarta a duk tarin 'yan-uwan mahaifiyata duk da yawansu kuwa, tunda 'ya'yan mahaifinsu yawa ne da su tamkar tsaki, iya wadanda na sani ma su ashirin da uku ne. Ban da wanda suka rasu, su goma kuma a gurin mahaifiyarsu, biyu sun rasu tun kafin a haife ni, yayin da 'daya ya yi hatsarin mota ya rasu a shekarar da na shiga sakandire. Saura su bakwai, mazansu uku, mata hudu, duk suna cikin Kano ban da guda 'daya da aure ya kaita jahar Ondo cikin garin Akure, Anti Kulsum kuma ita ce autarsu. Na isa gidan Sakina ban same ta ba, tana asibitin Malam inda take aiki, na shiga 'dakinta da a nan nake yin masauki na ajiye kayana, na fito na shiga kicin na hau bubb'de warmers 'din da suke kan drowers 'din kicin din. Na dauko plate na fara serving kaina babu 'keta domin ina cikin jerin mutanen da ba sa wasa da cikinsu musamman idan na samu kaza ko kifi. 'Yan aikinta guda biyu sai murnar zuwana suke yi, suna ta yi mini barka da zuwa cikin farin-ciki da girmamawa domin sun san zan 'dauke musu aikin abinci. Bayan karatuna ba abin da yake sanya ni nisha'di irin girki, ina son na yi girki, ba na gajiya da 'dorawa da saukewa. Shi yasa har su Nana yaran Sakina, murna suke da zuwana. Domin kuwa duk abin da suke son ci ba na gajiya wurin girka musu. Da yamma Sakina ta dawo ta tarar da ni. Ta ta'be baki ta ce "Ai ban sa rai za ki zo ba, tunda wancan hutun ba yadda ban yi da ke ba ki zo ba, kika shafa wa idonki toka. Saboda na Moriki ya hana ki." Na dinga dariya ina cewa, "Ba fa shi ba ne, Abba ne ya hana ya ce na zauna a gida kawai". Ta galla mini harara tare da cewa, "Ashe ba a gabanki ya ce duk yadda nake nuna isa a kanki zai nuna mini ban isa ba? Idan na ga 'kafarki a gidana a wancan lokacin to na isa 'din. Idan kuwa ban gan ki ba, to na kama kaina na tsaya a iya hurumina. 'Kiri da muzu kika kunyata ni, ai ni kuma kallon ki kawai nake yi". Na yi shiru a dalilin ta fi ni Gaskiya. Ta dinga cashe mini tana cewa "In dai na Moriki ne, ina zaune zan ji ku a rana, domin ba mai iya masa sai Mahallicinsa". A fili na ce, "kafatanin danginmu baibai kuke kallon Yaya Sadik. Amma idan akwai mutum mai da'din sha'ani ai shi ne". Wani irin kallo ta bi ni da shi mai matu'kar ratsa jiki, ta kasa hadiyewa ta ce, "Shin Halimatu mene ne tsakanin ki da na Moriki ne?" A sanyaye na ce, "Ba komai fa, sai zumunci da kika sani." A gigice ta zauna ta ce "Halimatu! Har sau biyu, plz ban da na Moriki, kar ki bari ki fa'da tarkonsa, ba za ki kwashe 'kalau ba. Zuciyarki mai taushi ce, mai hakuri ce, mai kuma sadaukarwa ce. Gudale 'kanina ne da na saki gora ya kama, ke nan nan duniya ba abin da zai yi na 'ki shi, ko na janye jinin da ya hada mu." Ta nisa sannan ta ce, "Amma wallahi bai fi ki a wajena ba, don haka zan fa'da miki gaskiyar magana irin su sai gogaggun mata, da suka san yau suka san gobe, suke tafiya kan 'yancin da turawa suka ba wa mace. Amma ke kam 'yar yarinya da ke, da yanzu ne kike cikin shekarun kuruciya, ina tabbatar miki wahalar da za ki sha ba ka'dan ba ce, domin son ki ya fi nasa yawa, har yau 'din nan ba ni da wani tabbacin yana son ki. Ko yana son naki shi kansa bai sani ba. Na san dai a duk lokacin da ya 'kyalla ido ya fahimci ba kya gida ya dinga bibiyar inda kike ke nan, amma hakan ba zai zama hujja na yana son ki ba. Tunda zai fa'da miki maganar da ta zo masa ba taunawa a gaban kowa. Ba ya jin damuwa ma idan ya saki kuka, ashe kuwa bai kamata ki bari ki makance , ki so shi har irin haka ba". Jin na yi mata shiru, ta zuba mini ido tana kallon yadda na tunbatsa da fishi. Ta nisa ta ce, "Halimatu akan Namoriki?" Na ce, "Ni ba na son irin haka gaskiya, ni ban ce miki ina son sa ba, kin zauna kina ta sukar lamarin, yo idan haka Allah ya tsara ya za a yi? Na dauka ko kowa zai kushe ke za ki 'kaunaci lamarin". Na zum'bura mata baki ainun. Ta yi matu'kar ka'duwa. Tsawon lokaci tana kokawa da numfashinta. Ta nisa ta ce, "Har haka al'amarin ya yi girmama? Namoriki akwai ja'irin bawa". Na 'ki tankawa, ta sake cewa ki musanya shi da Abbas, ya fi shi nagarta, ya fi shi hankali, sannan yana da abin yi, bayan haka kuma ba wani son sa kike yi ba, sosai za ki ji dadin zama da shi". Tana rufe baki na ce, "Wallahi ko a 'kafa aka daura mini shi sai na subuce na tsere. Ai ni din nan da kika gan ni ba na son namiji mai jiki, ba na son shiru-shiru, wanda zai ta gana maka azabar duniya ana 'karyataka. Idan ba ki sani ba, ki sani Aziza yake so, har na fa'da mata, sun fara magana kuma". Ta yi galala tana saurarona, a tunzure ta ce, "Ashe dai ya koya miki irin iyashegensa, ban da iskanci har ina wani jikin a-zo-a-gani a tare da Abbas? Kawai dai ki ce kin fi son 'dan 'kyamo ta yadda zai ma'kal'kale ki tamkar 'dan biri". Na dinga dariyar da ta 'kular da Sakina tamkar ta rufe ni da duka. Kafin mu yi magana muka ji ihun Nana da kaninta Na'im suna fa'din "Ga mai kama da anti Halimatu." Na kai idona kan talabijin 'din ina kallon yarinyar da suke fa'din muna kama fara ce sosai kuma 'yar duma-duma. Sai dai na fita bu'dewa ta 'kasa duk da ita ma na ga hawa take yi sosai. Sakina ta daka musu tsawar su yi mata shiru, ai kuwa nan da nan suka yi tsit da su. Maimakon ta bar maganar, sai ta sake cewa, "Ina son na ja hankali! Kar ki yi gan-gancin da Namoriki zai fahimci you are in love with him, domin kuwa ba 'karamin takaici zai cusa miki ba". Na 'daure fuska na ce "Ni fa ban ga dalilin tsananta wannan maganar ba Maman Nana! Domin dai ban ce miki komai ba, hasashe kike yi". Ta girgiza kai ta ce "Ai shike nan! Na san dai Namoriki dabi'unsa tamkar irin na *Sabo Da Kaza* ne da ba zai hana a yanka a cinye ta ba. Na fa'da miki gaskiya, na fita ha'kkin zumunci". Na mike ina guna-gunin ta bari ya furta yana so din mana kafin ta fara wannan jawabin mai kama da 'kafar ungulu. Ta bi ni da ido, mamakina tamkar ya kashe ta a zaune. Washegari da yamma sai ga shi a gidan Sakina tamkar jifa, wani iri na gan shi tamkar ba Gudale sarkin ado da ginshira ba. Ya yi 'kerere a kicin inda nake aikin yin dambu, na kalle shi na ce, "Kamar ba ka da lafiya?" Ya watsa mini kallo da idanuwansa da suka birkice, ya ce, "A'a asibitin Nasarawa ne a kaina 'yar rainin sense." Na ja bakina na tsuke. Na ci gaba da aikina. Ya kalle ni ya ce, "A tsaye za ki bar ni ne?" Na janyo wata irin kujera da suke zuwa ha'de da turmi na kai gabansa tare da cewa ga abin zama". Da saurinsa ya ja da baya tamkar ya ga wani mugun abu. *Alkalamin Surayya Dee*✍️ 2/8/23, 10:22 - Buhainat: 🌺 *SABO DA KAZA* 🌺 *NA* *SURAYYA DAHIRU* ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.``` ```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️ ____________(�?)______________ https://www.facebook.com/profile.php?id=100069755834980 •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·�? *Mai bu'katar karanta wannan labarin ya tura ku'din karatu 500 a wannan asusun.* *2384876855* *Surayya Ibrahim* *Zenith Bank.* *A tura shaidar biya ta wannan lambar 08032773332* *Note* *Shimfi'dar labarin shine farkon littafin! Dan haka wacce bata karanta shimfida ba ta koma ta Karanta*. *Page 11&12* Ya ce, "Ashe ke muguwa ce, kuma ma'ketaciya?" Mamakinsa ya kama ni ina son gane me na yi na 'keta da zalunci?" Na kalle shi na ga da gaske tsoron kujerar yake yi. Na ce, "me na yi maka da ka jingina mini wadancan siffofin?" Da kumfar baki ya ce mini "Wato so kike na yi ta haifar 'ya'ya mata ko?". Ya sake shayar da ni wani sabon mamakin fiye da na farko, na kasa yin ha'kurin maganar ta bi ruwa na ce "Zama a kan irin wannan kujerar ne sababin haifar 'ya'ya mata?" "E mana hakan na taso na ji ana fa'da shi yasa nake gudun kujerar tsugunno da kuke zama a kai, dan kar a zo a cika mini gidana da tarkacen mata". Na yi sukuri cikin kasala, amma kallon sa nake yi ina mamakin kalaminsa da babu azanci ko tauhidi a ciki. 'Karin ta'ajibin da na shiga shi ne babu jahilci a tare da shi, domin tun ba ni da wayo suka yi sau'kar al'kura'ani mai girma, ban da littafan addini daban-daban da suka samu sani a cikinsu. Sannan kuma ilimin zamanin ma a yanzu haka yana daf da kammala Doctoring degree 'dinsa. Ashe kuwa bai kamata ya yi amanna da irin wa'dannan maganganun da gidadawa, kuma jahilai suka kitsa su, wawaye suka aminta da su ba. Na nisa na ce "Ba a yi wa Allah dabara dai, shi ne Yake sarrafa komai, da ikonsa komai Yake gudana". "Allahu Akbar! Na fiki sanin hakan sai dai dole zan kiyaye duk abin da ya zo daidai da fahimtata na kuma gaskata shi". Na juya na ci gaba da abin da nake yi, ba tare da na sake tankawa ba. Tsawon mintuna ya katse shirun da ya ratsa kicin 'din ta hanyar cewa, "Kin bar ni a tsaye Guduyo". "Cike da rashin damuwa na ce "Na ba ka abin zama fa". Cikin rikici ya ce, "Ba na so! Ba zan zauna a kai ba, na kuma gaji da tsayuwar". "To ka koma falo ka zauna mana". Na fa'da don kaucewa rikicin gangan 'dinsa. "Ba ni da ala'ka da mai falon, ke nake nema, a inda na gan ki a nan zan tsaya". Na ajiye wu'kar hannuna na bude fanfon sink na wanke hannun na fita cikin fishi-fishi, murna-murna. Na dawo masa da stool din jikin mirror. Ya karba ya zauna, na bude fridged na zuba masa lemo da ruwa. Na zubo masa meat pie din da ban jima da kammala shi ba. Na kai gabansa, ban yi zaton zai ci ba. Amma ga mamakina sai gani na yi ya mi'ke ya wanke hannu. Ya dinga cin meat pie din nan tare da korawa da lemu. Da'di ya debi shi ya fara santi da cewa, "Har ga Allah na so kin amince da Comrade Anas, saboda a kusa kike ba zan dinga kewar kayan kwadayin da ba kya gandar yin su ba". Na bata rai na ce, "Kai kuma sai ka yi ta zaryar zuwa gidan kanwarka cin abinci?" Sai da ya hadiye na bakinsa ya ce, "Ai na san ni na daban ne a wajenki aiko mini za ki dinga yi". Na tabe baki na ce, "Idan mijin nawa ya amince ke nan?" Ya dago a razane ya ce, "Ashe nan gaba wani zai iya shiga tsakaninmu Guduyo?" "A to ai gaskiya ne, Yaya Gudale na san ko kai ba za ka amince kullum matarka ta dinga girki tana aika wa cousin ba". A sanyaye ya ce, "Ashe kawai cousin nake a wajen ki ko?" Ina jikin gas ban juyo ba na ce, "Idan ka so ai za ka iya 'kara wa kanka matsayin da ya zarta komai ma" Ya nisa ya ce "Ta ya ya?" Ni wallahii kaina daurewa yake yi". Na juyo da nufin canja akalar hirar tamu na tarar da ya cinye meat pie din nan tas. Na san da ma ma'abocin son snacks ne, domin kuwa ya fi son su fiye da abinci. Na kaikaice baki na ce "Yaya Gudale mai abin mamaki". Ya watso mini harara. Na waske na ce, "Ba ka magana da matar gidan amma ka zo kana cinye mata abinci, na taya ka jin kunya". Ya tashi da sauri yana ka'da 'yan yatsu alamun yin kashedi. Da bacin rai ya ce, "Kina shiga hancina Guduyo! Ina jiye miki ranar da zan fato ki". Na yi sukuri, sai kuma na ce, "Yi hakuri Yaya Sadik! Ni ai wasa nake yi maka, ba na son wannan harzukar da kake yi. Anty Sakina ta damu da kai, kai ma ka sani, daga maganar fatar baki, sai ka gindaya dutse a tsakaninku irin haka?" Ya zuba mini ido yana mini kallon takaici, amma hakan bai sa na karaya ba, na nisa a tsorace na ce, "Sakina mai son ka ce, mai 'kaunarka ce ba ta cancanci haka daga gare ka ba, saboda kawai ta yi maka fa'da irin na gyara kayanka". Kafin ya ce wani abu ta shigo kicin din. Mamakinsa ya kama ta, ta hadiye fishinta a kansa ta ce, "Na Moriki barka da lokaci." Ya dauke kai tamkar bai ji ba, bayan ni da na fi shi nesa da ita na ji ta. Ta sake 'daga murya ta ce, "Na ji da'din ganin ka, da ma fita zan yi amma motata ta yi faci taimake ni ka kai ni mana". Ido cikin ido ya ce, "Kar ki fara, don kuwa ba inda za ni, abin da yasa kika gan ni a gidan nan saboda maigidan 'dan abokin Abba ne na sani, ke ma kuma kin sani, ashe kuwa ina da dalilin shigowa, don haka kar ki yi zaton na kasa cika alwashin da na yi ne, kawai na gano ai ba gidanki ba ne." "Yanzu ba ka ji kunya ba? A gaban budurwarka kake fa'din irin wannan maganar ta sokwaye?" Ya tunzura ainun ya dinga nuna ta cikin rawar jiki ya ce, "Wallahi ke da Umma! Za ki san kin ce mini soko, za ki san kin mini 'kazafin ina da budurwa." Yana kallon ta ya nuna ni da yatsa ya ce, "Ni kika jinginawa waccan abar ko?" Ya girgiza kai cikin 'kunan rai mai tsanani. Ya fita fuu yana jaddada cewa ranar lahira sai Mai samaniya ya yi musu hukunci shi da Sakina. Sannan ta jira hukuncin duniya fishin Umma ke nan! Ya fice cikin shagwaba tamkar yaro 'dan 'karami. Haushi ya turnike ni, wai ni ce waccan abar tamkar wata abin 'kyama. Takaicinsa mai tsananin gaske ya sha'ke ni. Sakina ta juya tana azanci da fa'din, "*Sabo Da Kaza*". Ta sake dawowa kicin 'din tana 'kir'kirar wata guntuwar wa'karta da take cewa "Ruwa cikin cokali ya ishe mai hankali ya yi wanka, ka rungumi wadda yake son ka, ba wanda ka san 'koshin wahala kake yi ba, ko wanda bai san darajarka ko ta makusantanka ba". Na san da ni take, musamman da ita din ba ma'abociyar yin wake ba ce, hawaye ya 'balle mini. Na kashe gas, na bar kicin din ba tare da na kammala aikin ba. Na shige daki ina hawayen ba'kinciki. Tabbas da gaske son Yaya Sadik nake yi, irin son nan mai tsananin gaske. Na kuma san Sakina ba wai son ha'din ne ba ta yi ba. illa halin 'dan-uwanta take jiye mini, musamman da ba shi yake son ba. Ni kuma a yadda nake jin sa zan jure komai, ko da iyashegensa ya fi haka shahara. Gayunsa, kyaunsa, ginshirarsa, da komai nasa suke yi ruda ni, hatta rashin kunyarsa kuwa. Ba ni da wani lokacin da nake jin 'da'dinsa, na ji ni cikin shau'ki da farinciki irin idan ina tare da Gudale, ko da kuwa ba fararen lafazi zai mini ba. Na nisa ina jin takaicin waccan abar da ya 'kira ni da shi, na sani ba yau ya fara kira na da sunayen cin fuska ba, don kuwa hatta Guduyo din da ya kama bakinsa na sani don na yi ba'kin ciki ne ya sanya ya za'kulo wannan sunan da ban taba jinsa akan wata bil'adama ba. Sai dai abin mamaki ni kuma son sunan nake yi musamman da shi ne ya lan'kaya mini yake kuma fa'da mini. Na dinga jin ba zan sake kula shi ba, har sai ya gane ni ba waccan abar ba ce. Sai dai da kaina na dinga tambayar kaina ko zan iya wannan jarumtar? Domin duk abin da zai mini ana jimawa idan na gan shi zan hau masa magana, don 'karfin hali yana sha mini 'kamshi tamkar ba shi ya yi laifin ba. Haka na kammala kwanakin hutuna a gidan Sakina, na fara shirin komawa makaranta. Tirjiya na samu daga wurin Abba akan ba komawa makaranta har sai na tsayar da miji, da kyar ya bar ni bayan na yi al'kawari a cikin kwanakin zan tsayar. Na shiga ru'du sosai, to ni wa zan tsayar? Tabbas ba zan auri Alhaji Anas ba. Ina isa makaranta muka hadu da Munir, wani saurayi ne da yake nacin so na, ma'aikaci ne a kotun shari'ar musulunci. Ya 'dan manyata auren ne bai yi da wuri ba, masters yake a fannin Arabiya. Sam bai yi mini ba, saboda ustazu ne na 'karshe. Sai dai kuma ba shi da makusa, sannan so na yake tamkar ransa, kullum sai ya zo Old Side saboda ni, duk da ba wani kula shi nake yi ba. Muka gaisa a gajarce, ya dinga surutun na ba shi dama ya bayyana a gidanmu, a san da shi, idan Allah ya 'kaddara shi ne mijina zai yi farinciki, idan kuma bai 'kaddara ba zai ha'kura". Na yi murmushi na ce, "In sha Allah za ka ji ni". Muka rabu ina jin wani iri, a raina kam ba na jin son sa, amma kuma ba shi da wani kashin da za a 'ki son sa. Sai dai da na tsananta nazari sai na gane son Gudale ne yake hana ni kallon duk wani namiji balle har ya burge ni. A daddafe na yi sati ban nemi Yaya Sadik ba, shi ma kuma ya yi 'diban karan mahaukaciya da ni. Kan dole na gaji da fishinsa na dinga bibiyar sa har na samu ya huce yake kula ni. Bayan ya mini jidali iri-iri, wai don yana shiga shirgina ne yasa na raina shi, har nake ganin zan yi gaba da shi haka siddan. Na dinga mamakin yadda ya fusata, ashe ya san raini ne ka dauki gaba da mutum daga maganar fatar baki? Amma shi yake yi da duk wadda ya shiga gonarsa, ko da kuwa kuskure aka hango yana yi aka yi gyara masa. Da a ce Antin Zaria ba ta kammala sakandire aka yi mata aure ba, da ta haifi wanda ya fi shi, amma ba ya jin nauyin yi mata cin mutunci ko ya gan ta ido cikin ido ya dauke kansa. Haka anti Maimuna, ko 'dar ba ya ji wurin keta ta. Bare kuma Juwairiya da yake ganin tamkar ba 'yar gidansu ba ce a dalilin tun kafin a haife shi aka bawa Yayar Kwalli ita. Shi har ya fi mutuntata 'kananun yayyensa Ramla da Sakina. Duk da dai ba yadda za a yi su hadu da Sakina ba su yi fa'da ba, har yau fa'dan sa'ko da sa'ko ba su bar shi ba. A cikin fa'dan nasu za ka fahimci wani irin so suke yi wa juna mai wahalar samuwa a yau. Ni shaida ce ba 'karamar 'kauna Sakina take yi wa Gudale ba, kai dukkan sisters 'dinsa ma kawai wulakancinsa ne yasa suke kaffa-kaffa da shi. Kwana biyu a tsakani ya huce gaba'daya, ya yarda na shiga motarsa, muna dawowa a hanya ya ce, "Na samo lambar Nusy da kika 'ki samo mini". Zuciyata ta buga da tsananin gaske. Na ce "Na taya ka murna". "Ke ba kya murna na samo miki sister in-law?" Na yi ya'ke na ce "Na yi mana". Ya murmusa ya ce, "Muryarta me za'ki tamkar ta ki, kin san Ubangiji ya hore miki amo mai da'di, idan aka ji muryarki ta waya ba za a yi tunanin tu'ke'kiyar halitta aka bawa wannan muryar ba." Idona ya ciko da hawaye, wai har haka 'kibata ta munanta ne ko kuwa a idon Yaya Sadik ne ta 'kazanta? Na hakaito Nusaiba, siririya ce ta sosai tamkar Rahma Sadau a farkon shigowarta wasan kwaikwaiyo. Na dinga tunanin ni kuma da wacce jarumar zan kwatanta kaina? A lokacin na dan fi jarumar Izzar so da ka'dan musamman daga 'kasa, amma yanayin farinmu 'daya hatta idanuwanmu, haka tsayinmu zai zo 'daya, kawai dai jiki zan 'dan nuna mata, a dalilin na zarta ta cikar 'kirji, da fadin 'kugu. Sai dai ita ma daga baya ta zo tana kibar sosai. A fili na ce, "Hala dai kana mini kallon giwa saboda girma?" Ya ja gemunsa ya ce mini, "Nan kusa kafin a samu me jikinki ai za a jima, shekarunki ashirin fa kike da wannan jikin, idan kika kai shekaru talatin kuma ai sai addu'a". Wata irin karaya ta dinga shiga ta, hawaye ya goce mini, ina dauke su cikin dabara. Har muka isa gida ban sake magana ba. Na shiga ban'daki na ci kuka na koshi, kishin Nusaiba ya fi maganganunsa ciwo a zuciyata. Kwana biyu ban yarda mun tafi tare ba, na yi sa a ma tafiya ta same shi zuwa Enugu akan wani darasi. *Kina bu'katar canja kayan dakinki?* *Kina bu'katar abaya ta zamani?* *Kina bu'katar kayan kicin na alfarma?* *Kina bu'katar siyan ginannen gida?* *Kina bukatar samu gidan haya mai cike da tsaro?* *Kina bu'katar siyan filin da ba zaki shiga matsala ba?* *Tuntu'bi AMYAS NEW & FAIRLY USED* *CIKIN AMINCI DA SAUKAKKAN FARASHI* 08083909947. Bai dawo ba sai da ya shafe sati guda. Sosai na yi kewarsa, na dinga murnar dawowarsa na manta da komai. Ranar wata litinin tana cikin jerin ranakun da ba na mantawa da su saboda irin tozarci da na sha a wajen Gudale. Sanyin safiya muna tafiya zuwa B. U.K. mun zo daidai 'Danagundi danja ta tsayar da mu. Na zuba masa ido ina masa kallon tsaf! Wani irin al'amari ya dinga keta dukkan sassan jikina, kwalliyar da ya yi cikin tsadaddun kananun kaya sun matu'kar yi masa kyau, 'kuruciya sosai a tare da shi. A lokacin bai jima da yin birthday dinsa na shekaru 28 ba. Ya juyo muka hada ido, na waske na dauke kai. Bai yi magana ba, ganin ya daina kallona yasa na ci gaba da 'kare masa kallo ina tasbihi ga Ubangijin da ya kyautata halittar Yaya Sadik. Ban sani ba ko matsanancin son da nake yi masa yana da ala'ka da kyansa da nake gani sosai. Dan tsurut da shi sai 'daukar hankalin 'yammata musamman ma ni. Yanayinsa a wancan lokacin ya fi kama da Ramadan Both din shekarun baya. Kafin ya yi 'kiba. Mun zo daidai 'Kofar Famfo danja ta sake tsayar da mu. Na ci gaba da kallonsa, ba zato ya ce "Oh ni Guduyo saboda Allah wane irin kallo kike bi na da shi haka? Ba na so, ni gaskiya ki daina tsorata ni haka". Na nisa cikin borin kunya na ce, "Wane irin kallon ka kuma? Shin kai din tauraro ne ko me?" A kufule ya ce, "Ban son rainin wayo! Ina ce sau uku ina kama ki kin kafe ni da ido?" Cikin shau'ki da subutar baki na ce, "Kai mai kyau ne fiye da farin wata, bakinka ya dace da gemun nan da ka tsayar, ka iya zaben turare mai nutsar da zuciyar mai bege, komai naka cif tamkar kai ka za'ba". Ina rufe baki na ji ya dauki salati, idonsa ya canja sosai, saboda bacin rai ya ce, "Ashe ke 'din lalatacciya ce Guduyo? A gabana kike yabon kyaun halittar namiji? Kaicon ki! Zan fa'da miki da babbar murya, ni Saddi'ku 'kwalelenki, ba kya cikin jerin matan da zan nuna wa duniya su, asalima kunya zan ji a ce ke 'din matata ce. Amma zan fa'da wa su Abba gaskiya su yi gaggawar mi'ka ki 'dakin aure kafin a wayi gari a ga kinfi haka fitsara, Dan l ji tsoro ma Kika bani, Dan kuwa zaki iya shammatata ki danne ni". # Team Gudale # Team Guduyo # Surayya Dee # Ana tare🤝 2/8/23, 10:22 - Buhainat: 🌺 *SABO DA KAZA* 🌺 *NA* *SURAYYA DAHIRU* ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.``` ```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️ ____________(�?)______________ https://www.facebook.com/profile.php?id=100069755834980 •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·�? *Masu son karanta cikakken labarin babu yankewa ku biya 500 kudin karatu ta wannan asusun* *2384876855* *Surayya Ibrahim* *Zenith Bank.* *Sai a tura shaidar biya ta wannan lambar 08032773332*. *Tunasarwa* *Ina Jin koarafin cewar typing yana yin ka'dan.* *Ina bin umarnin kungiya ne na kada shafi ya wuce yawan allon comfuter biyu. A hakan kuma ina yi muku yawan allon comfuter uku ne.* *Amma in sha Allah za'a duba korafinku. Zuwa gaba* *Na gode sosai da yabawarku, da soyayyarku*🤝 *Page 13&14* Hawaye ya 'balle mini, wani irin takaicinsa ya mamaye mini 'kalbi. Cikin murya marar amo na ce, "Ni ka jefa da wannan 'kazaman kalmomi irin haka?" "A to 'kazafi na yi miki? Ban da lalata har kin san siffofin maza? Amma na gane ba ki da laifi, sakacina ne da nake bibiyarki nake zama sakarai a gabanki". Na kasa bu'de baki na ce masa uffan a dalilin bacin ran da yake raina mai girma ne. Har muka isa makaranta ya tsaya a inda ya saba ajiye motar ban ankara ba. Shirun da na ji ya yi yawa ne, ya sanya na 'dago fuskata jage-jage da hawaye amma na kasa furta kalma ko guda. Na yun'kura na 'dauki jakata na bu'de kofar amma na ji ta a rufe, na juya na kalle shi ya ha'de girar sama da ta 'kasa. Na san nufinsa, tunda ya sanya mini dokar da ta zame mini ka'ida kullum muka zo sai na yi masa godiya da fatan alheri don na gane shi ba direbana ba ne. Tun ina yi cikin iyashege da mamakin son girma irin nasa, har na dawo ina yi cikin farin-mciki da shagwa'ba. Amma a wannan ranar sai na ji sai dai komai zai faru ya faru din, amma ba zan gode masa ba, bayan ya gama tozarta ni. Fiye da shudewar awa guda muna zaune cikin motar, dukkanmu mun rasa darasin wannan lokacin. Ya hassalo sosai ya dube ni ya ce, "Ke ba na son iskanci kin ji! Za ki yi abin da ya kamace ki ko kuwa?" Yana rufe baki na ce "Ba zan yi ba". Ya sake harzuka ya ce, "Guduyo ki shiga hankalinki, bar ganin ki haka zan yi miki duka, zan karairaya ki na watsar da 'kasusuwanki a ruwan 'Bagwai". Na share shi ina jin yau dai kam bai isa na bi shi ba. Ya bu'de murya ya ce, "Idan na 'kirga uku ba ki yi dalilin da kika fitar mini daga mota na daina kallon ki ba, za ki yi mamakin abin da zai same ki". Ban san lokacin da tsaki ya subuce mini ba. Na ce "Allah yasa gadar Zurmi za ka kai 'kasusuwan nawa ka zubar. Ba na tsoron mutuwa, Ubangijin da ya 'kagi mutuwa ka'dai nake jin tsoro". Ya yi matu'kar ka'duwa ya kalle ni ya ce, "Ni Abubakar Sadik kika yi wa hakan?" Na dauke kaina ba tare da na tanka masa ba. Ya nisa ya ce, "Wallahi matu'kar ba ki yi godiya ba, za ki 'dan'dana kudarki a hannuna, sai hakan ya zame miki sanadin kuka mai yawa, don kuwa zai zama dalilin da ba zan sake yi miki sassauci ba. Kaf gidanmu ke ka'dai kike shiga hancina na dauke miki kai, amma tunda na gane ke din tabbatacciya ce zan gwada miki 'karshen tsageranci! Kumbusar banza kawai. Na fa'da miki da babbar murya duk jarabarki wallahi ni dai kam 'kwalelenki". Na daure na hadiye kukan da ya zo mini na ce, "Ko ina danne maza ai ka san dai kai sai dai na matse ka, domin ka yi mini ka'dan, yo ni maza irinku ma marasa zati mene ne abin burgewa a tare da ku ne?" Ya kuwa zabura ya dam'ke gashin kaina da ya sha dauri da ribbons da 'karfin gaske. Sosai na ji zafi amma na 'ki nunawa bare na karaya. Ya ce, "Ko a hanya kika nuna kin san ni sai na ci kazar ubanki. ya bugi 'kirjinsa ya ce, "Ni ne ba ni da zati ko Guduyo? Na rantse miki ba zan yarda ba, tunda na zo duniya ba wanda ya ci mini fuska irin ki". Cikin rashin tsoro na ce, "Ina fuskar da zan ci 'din? Ai idan na ce zan ci fuskarka ba za ta ragu ba, domin 'yar masayau ce ba afki". Ai kuwa ya dinga kawo mini duka ina karewa, ina sake cewa, "Wallahi yau na gane kai din mace ce da rigar maza! Domin duk namiji mai gwada 'kwanjinsa akan mace wallahi sakarai ne". Ina rufe baki ya sakar mini gashi, ya kifa kansa a jikin sitiyarin mota, tsawon lokaci sannan ya dago da fuskarsa da ta hade da zufa da hawaye duk da sanyin AC da ya cika motar. Yasa hannu ya zaro tissue a cikin kwalinta da take tsakanin kujerunmu. Ya dinga goge hawayen takaicina. Na sa ci kallon sa na ga gaba'daya ya birkice. Jijiyar kansa ta fito rada-rada idonsa ya yi jawur tabbacin ya kai 'koluluwar fusata. A raina ban ji 'dar ba, domin ya riga da ya kai ni 'karshe da bakaken maganganunsa, idan ma ni lalatacciyar ce ai shi ne ya lalata ni, domin duk wani abu na iskanci cikin dabara shi yake fara nuna mini shi. Na tuna da wayona da komai, ba a wani jima ba ma ya 'kankame ni ya mini tunbudin da ban san yadda ake yin sa ba sai a ranar. Soyayya ta hana ni ganin laifinsa, bare na nuna masa cin zarafi ya yi mini. Na sake tuno lokacin da ban yi hankali sosai ba, amma na fara girma yake jana dakinsu yasa ni rawa, ko ya zaunar da ni akan cinyarsa da nufin ganin hotuna a wayarsa. Na yi tsaki a fili, a zuciyata kuma na ce wai mai wannan ta'asar ne yake jifan wani da lalata. Amma laifina ne da na amince ban ta'ba nuna masa ba na so ba. Dole ya ce mini komai. Ba zato na ji ya danna mabudi, ni ma a gaggauce na bu'de motar na fice ina jin da na sake shiga motar nan gara na jingine karatun ga'badaya. Ina da hakuri akan komai amma na tsani a ta'ba mini mutunci. Zagayawa na yi na samu inda ba kowa na zauna a gefe na ci kuka sosai domin ba karamin dafa ni kalmominsa suka yi ba. Na tuna wai ni ce abin kunya a gare shi, ni ce ba zai iya nuna wa duniya ba a matsayin matarsa. Sannan kuma ni ce zan yi masa fyade. Duk yadda haushinsa yake nukurkusa ta ban ji na daina son sa ba, bai fita a raina na can ba. Sai dai kuma wata irin jarumta ta shige ni da nake jin zan iya auren Munir. Don haka ban 'bata lokaci ba, na zaro wayata karon farko da na 'kira Munir da kaina. Ya katse ya 'kira ni. Na dauka na yi masa sallama, ya amsa cike da zumudi mai yawa. "Ranki ya da'de! Ina fatan dai ba kuskuren kira na kika yi ba?" Na saki yar dariyar da babu nisha'di a cikinta na ce, "Ba kuskure ba ne kai din Ustaz na yi niyyar kira, ba kuma kiran kawai ba, zan sanar maka ka samu lokaci ka je wajen Abba". "Who am I today?" Ya fa'da cikin yanayi na farinciki. Na yi shiru ina sauraron maganganunsa na murna. Na katse shi ta hanyar fa'din "Zan shiga lakca". Na katse wayar ina jin dole na tattara na bar wa Gudale filin gidan tun bai tuso ni a gaba da bala'insa ba. Hawayen da ya yi ba zai zuba a banza ba, na sani akwai abin da zai shirya mini a gaba. Na kuma sani da gaske ni kawai yake 'dagawa kafa, amma ko antin Zaria ma ba ta tsira ba. Wannan karon kuwa na sani ba zancen sassaci tunda ya fa'da da bakinsa. *Kina neman kwararriya tela*? *Kina bu'katar kyawawan takalma da jaka irin na manyan Mata?*? *Kina bukatar samun zababbun suturu?* *Kawai tuntu'bi Umm Muhd collection* *Ina tabbatar miki zaki huce takaici* Washegari kuwa Munir da yamma ya je wajen Abba suka tattauna. Kwanaki uku a tsakani na je gai da shi da sassafe kafin na tafi makaranta. Har na mi'ke da nufin tafiya ya tsayar da ni. Ya ce, "Na yi binciken sirri akan wannan yaron domin na san ubansa duk da dai ba mua'amala muke yi ba. Sai dai bayanan da samu a kansa ba mai da'di ba ne. Ni ya ce mini ya ta'ba aure matar ce ta rasu tun ba su yi shekara guda ba. Yanzu kuma na sami bayanan da suke nuna mini tamkar shi din mai yin auren mutu'a ne. Tunda an tabbatar mini sau uku yana auren yana saki, duk aurarrakin nan kuma akwai rabo a tsakaninsu ma'ana yaransa uku daga uwaye mabanbanta." Na dinga jin wani irin tashin hankali na ratsa ni ashe Ustaz kura ne da fatar akuya! Ni zai yaudara? Kafin na ce wani abin Abba ya ce, "Don haka ina sanar da ke ki rabu da shi ba mijin aure ba ne, makaryaci ne mai auri saki". Ki nutsu sosai Ubangiji zai kawo miki wanda ya fi shi alheri tunda dai kin kafe ba kya son yaron kirki irin Anas". Na sunkuyar da kaina 'kasa ina jin wata irin damuwa na rasta ni ba don komai ba, sai don yadda babban mutum da ya kai shekaru talatin da biyar a duniya amma zai iya karkace baki ya shirga 'karya don kawai ya cim ma burinsa. Kaicon wannan halayyar tamu, kaicon son zuciyarmu da a kullum suke zama sandin shigar mu cikin 'kunci. Ko mene ne ribar da za ka samu idan ka yi 'karya don ka zalunci wani? Babu sai damalmalewar al'amura. "Tashi ki je, ki ci gaba d addu'a ni ma zan taya ki, amma ina jan hankalinki ki cire shi a ranki ba shi da nagartar da zamu ba shi aure. Ubangiji ya yi miki albarka, ya ba ki na gari". Na amsa da ameen tare da yin godiya da kuma yi masa fatan inganci a lafiyarsa. Na fita jikina babu 'kwari. Ina fita na hango Gudale yana shirin shiga motarsa na dauke kai, ina jin ko ya ce na zo na shiga ba zan shiga ba, bare na san shi ma ba zai dauke ni ba. Haka kwanaki suka shu'de ba tare da mun sake haduwa da Gudale ba, tsakaninmu sai daga nesa shi ma ba kasafai ba. A hankali sai na fara hucewa, kewarsa ta fara shiga ta, har na fara tunanin yadda za'a yi mu shirya. Ran nan sai ga Sakina ta zo gida, daga asibiti ma take. Muka yini cikin walwala a dalilin Umma ta je Yola. Matu'kar kuwa tana nan ba na samun fuskar da zan shiga cikinsu a yi hira da nishadi. Muna zaune a falon Umman muna cin shinkafa da wake da salak. Gudale ya shigo ba sallama, yana gani na ya hade fuska tamkar ya ga gawa. Ya zauna kusa da Sakina sosai ya jingina rabin jikinsa a jikinta, fuskarsa na kan kafadarta. Wani irin al'amari ya kama ni, shaukin kaunar su na diba na tamkar irin haka Yaya Al'amin yake so na. Kamarsu guda shi da Sakina, duk da kyan Gudale na tabbatar Sakina ta fi shi kyau. 'Ya'yan Umma kyawawan gaske ne matu'ka sai dai kyan Sakina ya zarce kwatance, tafi kowa kyau na ban mamaki. Duk iyashegensa 'kaunar da yake yi wa Sakina ba ta boyuwa, ita ce kawai za ta zage shi kanta tsaye bai rama ba. Sai dai ya gama hargagainsa amma ba zai zage ta ba, haka nan ita ce zai daina yi wa magana ya dawo ya fara yi mata ko ba ta neme shi ba. Da sauri ta ce, "Na Moriki jikinka zafi fa". A shagwabe ya ce, "Umma! Idan na shigo ban gan ta ba, sai na ji tamkar na yi ta rusa ihu, sai na je wajen Mama nake 'dan samun nutsuwa. Gaskiya zan hana ta tafiyar da ta wuce kwanaki biyu". Dariya ta yi ta ce, "Sai ka ce mai shan nono? To me za ta yi maka ne wadda ba za ka iya yi wa kanka ba, komai kake so Mama na yi maka, ga su Dala mai aikin abincin Umma, sannan ni ma komai ka ce kana so yi maka zan yi". Da wata irin murya mai rauni tamkar ba Gudale ba ya ce, "A'a Sakina ko ba za ta yi mini komai ba, na fi jin nutsuwa na shigo na gan ta a gidan nan, ina jin dadi idan ta gan ni ta bar komai ta tarairaye ni". Sakina ta murmusa ta ce, "Haka ne! To ka dinga jin maganarta ka daina sa ta bacin rai". Yana jikinta ya ce, "Ban son irin haka Sakina kin sani! Wai duka wata nawa kika ba ni ne?" Dariya ta yi ta ce, "Ai kai ne babba da shekaru sifili ka girme mini". Ta bu'de jakar hannunta ta mi'ko mini mukullin motarta ta ce, "Halimatu dauko mini wata farar leda ina zaton akwai maganin malaria a ciki". Na amsa na fice. Ban wani jima ba, na dawo dauke da ledar. Na mi'ka mata, ta bu'de ta duba ta fito da wanda ya kamata ya sha, sai da ta 'ballo masa, ta saka ni na 'bude ruwan roba na zuba masa a glass cup. Amma fir ya 'ki sha ya kafe lafiyarsa 'kalau kewar Umma ce kawai ta ke damunsa. Tsawon lokaci yana jingine jikinta, kafin ya yun'kura ya mi'ke, yana 'dan tangadi. Ina tsaye ya zo wucewa ta kusa da ni, na sassauta murya na ce "Sannu Yaya Gudale". Ba zato na ji saukar wan irin marin da ya katse mini ji da gani na wucin gadi. Na durkushe saboda ki'dima, na fashe da kuka sosai. A hanzarce Sakina ta iso kusa da mu tana tambayarsa ba'asin wannan uban marin da ya zabga mini. Bai kulata ba, illa ya bu'de murya yana fa'din "Ashe ba ki ji kashedin da na yi miki na kar ki sake nunawa kin san ni ba?" Ya yi hucin 'bacin rai, ya nisa! Ya ce "Bilhillazi idan kika sake yi mini magana sai kin ga tashin hankali! Na tsane ki, na tsani ko da jin muryar ki ne". Da 'kyar cikin rawar muryar kuka na ce "Na yi nadamar abin da na yi maka plz kar ka yanke zumunci da ni Yaya Gudale". "Tun ranar da kika ci mutuncina, kika tozarta ni, tun lokacin na tsane ki. Ina gargadin ki ki fita harkata if not you will be in trouble". Sakina ta yi sukuri tana nazartar mu, ta kalle ni ta ga na yi la'kwas hawaye na bin fuskata, na fahimci ta fi ni jin zafin marin da ya yi mini. Ta mayar da kallon ta gare shi ta ce, "Namoriki akan me za ka mare ta? Kasan haramun ne duka a fuska musamman ma ta mace baliga". Ya 'kan'kace manyan idanuwansa ya ce, "To ki fa'da mata ta kiyaye ni, na riga na cire ta a sahun 'yan-uwana! Matu'kar kuwa za ta mini magana wallahi sai na yi mata 'barin makauniya. Tunda na gane ba ta da kunya kuma ba ta da mutunci. Wai ni za ta kalli tsabar idona ta ce mini ba ni da zatin da cikakken namiji yake da shi, hakan bai ishe ta ba ta sake danganta ni da sakarai". Sakina ta nisa ta ce, "Namoriki tsakani da Allah bai kamata ka tsananta wannan maganar har haka ba. Ko ni ba zan iya lissafa adadin yadda kake kushe Halimatu ba, za ta yi maka abin arziki ma amma sai ka gwasale ta. Hatta Guduyon da kake kiran ta da shi, ta amsa har yau din nan ba wanda ya san ma'anarsa. Kai ne ke ce mata kumbusa, Sadi bon bon, 'Katuwa, Tu'ke'kiya, Ra'kuma da sauran sunaye na iyashege. Duk da hakan kuma jikinta na rawa take kyautata maka, ni na san ba haka kawai za ta fa'da maka abin da ka ce ta fa'da din ba". A tunzure ya ce, "Duk ina fa'da mata. Shin ni ban girme ta ba? Sannan duk sunayen dana ke fa'da din, fa'da mini guda 'daya wanda ba ta siffantu da shi ba". # Team Gudale # Team Gudiyo # Ana tare 🤝 # Surayya Dee ✍️. 2/8/23, 10:22 - Buhainat: 🌺 *SABO DA KAZA* 🌺 *NA* *SURAYYA DAHIRU* ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.``` ```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️ ____________(�?)______________ https://www.facebook.com/profile.php?id=100069755834980 •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·�? *Fatan alheri ga wadanan group din, mussaman wadanda suka bani support wajen sayan wannan littafin* *Takorites* *Janaftys* *Khaleesat palace* *Gwaram discussions* *High class women* *Da sauran groups daban daban*. *Na gode madallah Ubangiji ya albarkaci kasuwancinku da 'ya'yanku* *Gudale na jinjina muku, yana bu'katar addu'ar ku*😄 *Son so*🤝 *Ku'din karatu 500 ne. Biya ki karanta cikin nutsuwa da aminci* *2384876855* *Surayya Ibrahim* *Zenith Bank.* *Ki tura shaidar biya ta wannan lambar* *08032773332*. *Page 15-16* Sakina ta ce, "To ka sani ko ka siffantu da abin da ta ce 'din da gaske?" Ya kuwa sake hasala ya ce, "Haba ai ko makaho ya shafa zai san Ubangiji ya kyautata halittata. Baya ga hakan ta ina na zama sakarai?" Sakina ta dubi idonsa ta ce, "Ko ba sakarai ba ne kai, kana yin 'dabi'un sakarkaru domin kuwa babu shakka sakarai ne mai 'dabi'ar 'daga wa mace hannu. Ai namijin duniya ba a ganin 'kwanjinsa da sunan duka sai akan 'kato 'dan-uwansa amma ba mace mai rauni ba". Ya yi shiru a dalilin maganar Sakina ta yi kunnen doki da tawa maganar da na fa'da ta tunzura shi har da kukansa. Jin ya yi shiru, cikin muryar kuka na ce, "Dukana ya yi a ranar shi yasa na fa'da masa hakan, kuma Anti tunda na ba shi ha'kuri ai sai magana ta wuce. Zalina ya ci amma tuni na yafe masa, har ina yi masa magana saboda nasan illar gaba a shari'a". Tausayina ya yi matu'kar kama Sakina ta sunkuyar da kanta 'kasa saboda yadda idanuwanta suka ciko, a dalilin ta riga ta yi amannar na fa'da komar Gudale. Ta gane na gama mutuwa a kansa, irin son da ba jan kunnen da zai yi tasiri. Ta fahimci duk wulakancin da yake mini zuciyata ba ta 'kullatar sa na tsawon lokaci mai yawa. Ta nisa ta ce, "Tunda ta ba ka hakuri ai sai ka ha'kura, kai ma ka ba ta hakuri. Maganar ta wuce haka nan! Harshe da ha'kori ma ana sab'awa". Ya nuna ni da yatsa ya ce, "Munafukar banza, a gidan uwar wa kika ba ni ha'kuri? Ina ce nunawa kika yi kin wuce ki yi haka?" Sakina ta yi shiru tana ganin ikon Ubangiji. Ta kasa ha'kuri ta ce, "Yanzu ma ai ta ba ka hakuri Namoriki". Da sauri ya ce, "Ba na son haka Sakina, ya za a yi yarinya ta yi wa na gaba da ita rashin kunya, kuma ki dinga ba ta kariya? Wannan sam ba tarbiya ba ce, ba gata kike yi mata ba. Na kuma rantse, sai ta tuba kafin na dawo da ita cikin jerin dangina". Da sauri na ce, "Shike nan na tuba, Allah ya ba ka hakuri." Ya wani dau'ke kai ya ce, "Ki ci gaba da rashin kunyar idan abin yi ne". Sakina ta kalle shi ta ce, "Namoriki kai har za ka yi wa wani batun rashin kunya? Tabdi jam! Wannan shi ne wanzami baya son jarfa". A zafafe ya ce, "Sakina ki ci gaba da yi mini irin haka. Na rantse miki zan ba ki mamaki". Yana rufe baki ta ce, "Ai kullum sababbin mamaki ka ke shayar da ni". Ya shige cikin 'dakin Umma yana yin gunaguni. Yayin da Sakina ta 'dago ni daga durkuson da na yi. Ta dinga rarrashi na, ni kuma tuni na daina jin zogin marin saboda ya yarda za mu ci gaba da mu'amala. Hakuri ta dinga ba ni, tare da cewa, "Ki daina damuwa da lamarin Namoriki! Kin sani sarai manyan gidan ma ba hutawa suka yi da tsiyarsa ba. Ki kame daga kula shi". Na daure fuska sosai na ce, "Me kike nufi ne Maman Nana? Zumunci za ki gille?" Ta girgiza kai tare da cewa, "A'a wa zai raba zumunci, ko shiga cikin rikicin zumunta?" Kai tsaye na ba ta amsa da cewa, "Sai mai son ya kunyata, ya kuma tsinci kansa cikin marasa rabon rahma a ranar gobe". Ta zuba mini ido tana mini wani irin kallo mai tsanani. Ni kuma na waske na yi tamkar ban kula ba. Ta yi wani irin gauron numfashi ta ce, "Halimatu ba ki dace da fuskantar 'Kalubale mai gigitarwa ba. Ba wani tasku a gurin 'ya mace irin rashin samun nutsuwa a gidan aurenta. Yau na gaskata da gaske kina son wannan yaron, sai dai a karo na biyu zan maimaita miki ba ki dace da shi ba." Na 'daure fuska sosai tamkar hadari. Ta sassauta cikin rarrashi ta ce, "Ki yi amfani da iliminki, kar ki bari ki biye wa 'kawar zuciya, cizon yatsa ne zai biyo bayan hakan Sadiya". Cikin gajiyawa da maganganunta a tunzure na ce, "Don Allah Anti kin ji Yaya Sadik ya ce yana so na ne? Idan kuma kin fahimci irin jarabtar da aka mini a kansa ne kike mini haka, sai na ce miki ba ni da ikon daina son al'amarin da kike ganin aibu ne a wajenki". Da matu'kar mamaki ta ce, "Wato a idona ne aibu ko?" Ba ja-in-ja na ce mata, "E domin kuwa ni ban ga makusarsa ba, shi ba so na yake yi ba, bare ki dinga nuna mini ba kya son mu sake zama abu guda da ku". Na fa'da da rauni sosai. Sakina ta hau tattara kayanta musamman babbar ledar kayayyakin sayarwarta ne a ciki, tunda 'yar kasuwa ce ta sosai. Domin mijinta Dubai da China yake fita yana shigowa da kayayyaki daban-daban. Ta kalle ni ta ce, "Ni kika fa'dawa haka ko?" Na dauke kai na ce, " To akan me za ki dinga sanyaya mini guiwa?". Ta juya ta fita tana fadin, "Yi hakuri ba zan sake tsoma miki baki akan wannan matsalar ba." Na yi sakare ina jin rashin da'din fishin da na gani a fuskarta. Amma kuma ba na jin zan bi bayanta don na ba ta ha'kuri. Ina zaune shiru tsawon mintina uku, ina shirin mi'kewa Yaya Sadik ya fito daga dakin Umma, idonsa a 'dan birkice. Yana mi'ka tabbacin barci ne yake shirin kayar da shi. Shudin wando ne iya guiwa a jikinsa, ya sanya jar T-shirt an rubuta Gudale da babban ba'ki a bayan rigar. Kansa cike da suma ba'ka sidik irin ta fulanin Yola, ta sha gyara sai sheki take yi. Sosai ya yi kyau, kuruciya da 'karfi a tare da shi muraran. Ya zauna kujerar da take fuskantar wacce nake zaune. Ya 'dago muka hada ido, yana mini wani irin kallo mai sanya 'ya'ya mata diriricewa. Na dinga jin wani irin al'amari na ratsa ni, na dinga kame-kamen kunya. Da kyar na ce, "Don Allah na kawo maka abinci ka ci?" Ya harare ni sosai tare da cewa, "Kin ta'ba ganin na ci shinkafa da wake da yaji da mai?" Da sauri na ce, "To na yi maka indomie mana?" Ya yi shiru! Tamkar ba da shi nake yi ba. Sai da na maimaita har sau uku. Ya numfasa ya ce, "Je ki yi mini, amma idan kika da'de ba zan jira ba". Da sauri na mi'ke ina cewa, "Ba zan 'da'de ba In Sha Allah". Ina shiga kicin din Umma na jona ruwa a butar ruwan zafi, sannan na hau yanka albasa a zagaye (slice) sai da na yanka da yawa sosai, sannan na jajjaga atturuhu. Na kunna gas, daidai lokacin butar ta kashe kanta, tabbacin ya tafasa. Sai da na soya albasa da atturuhun sama-sama, sannna na zuba ruwan zafin, na zuba indomie din, na rufe. Na bude firij ina duba ko zanga wani abu. Ai kuwa na ga wani kwano shake da soyayyun kaji, da alamu suka nuna pepper chicken ne. Da kyar na banbaro, na zuba su a container da zata shiga microwave don dumamawa. Mintina ka'dan suka kammala. Jiki na rawa na shirya masa a tray tare da ruwan roba da dole shi yake sha, ha'di da lemon Lacasera, tamkar mai gida. Na dauka da rawar jiki na kai masa, na tarar da shi ya kishingi'da ya dora kafa daya kan 'daya, yana wayar da na tabbatar da mace ce. Na ajiye masa a kan side table din da yake kusa da shi. Na zauna ina sauraron yadda ya makale murya yana magana 'kasa-kasa tamkar ba Gudale ba, da kullum maganarsa a kausashe take. Haka kawai na ji raina ya baci, kishi mai tsananin gaske ya turnike ni. Ba yadda za a yi kuma na ce masa don me yake yin waya da wata? Na mi'ke da nufin bar masa wajen tun ban fara zunduma ihu mai gigitarwa ba. Har na je bakin kofar barin falon na ji ya bude murya sosai ya ce "Guduyo." Na juyo a hankali! Alamun dai shi nake sauraro. "Zo ki kwashi abincinki ba zan ci ba, ni za ki zo ki dangwararwa ki yi tafiyarki? Zo ki kwashe mini su, tun raina bai fi haka tafasa ba". Na dawo na zauna, cike da rawar murya na ce, "Ka yi hakuri to". "Ki fa tattare mini su tun ban watso miki ba". Na fara kuka ina cewa, "To ai na ba ka ha'kuri". Ya kafe ni da ido yana kallona sosai. Ya nisa ya ce, "Mene ne yasa ki kuka?" Na sunkuyar da kaina kasa ina shasshekar kuka sosai. Ya dinga fa'din, "Ba na son haka, tsakani da Allah ba na so, me na yi miki for God sake?" Ya hau bude plates din yana fa'din, "Dauko wani cokali mai yatsun ki taya ni ci". Na girgiza kai alamun ba zan ci ba. Ya mi'ke yana cewa, "To kwashe su ba zan ci ba, tunda ba ki san abin arziki ba ke sam". Cikin muryar kuka na ce, "Dazun nan fa ka ga ina cin abinci, na koshi ne". "Ba ruwana da koshinki". Ya fa'da kansa tsaye. Na mi'ke na yi kicin na dauko cokalin na zauna ina taya shi ci din, duk da ba wani ci nake yi ba. Ya cinye abincinsa. Ya sassauta ya ce, "A bangaren abinci ba ki da matsala Guduyo". Na daure fuska ba tare da na amsa ba. Ya kafe ni da ido ya ce, "Ban gane ba?" Cike da ta'bara na ce "Na gode to". Ya mi'ke yana cewa, "Wallahi kin same ni da yawa, ban san dalilin da idan kina wannan kumburar nake jin babu da'di ba, bayan duk wulakancin da kike mini." "Hmm! Allah ya ba ni ha'kuri Yaya Gudale da za ka zauna ka dinga yi wa wata macen 'yar murya akan kunnena." Ya yi shiru amma ya zura mini manyan idanuwansa masu kaifi. Ni ma na zuba masa nawa tsawon lokaci muna hakan. Ban san ya aka yi ba nawa idon ya fara zubar da hawayen da ban san manufarsa ba. Ya koma ya zauna ya ce, "Wai na tambaye ki mana. Shin kishina kike yi ne?" Cikin murya marar amo na ce, "Ba na son ka jajibo wacce za ta raba zumuncin da yake tsakanina da kai ne, musamman idan ta gane ni din ba Sakina ba ce a wajenka." Ya ce, "Wallahi Guduyo wani lokacin sai na ji tamkar kin zarta Sakina a gurina, idan mun yi fa'da fa ba na jin da'di, idan ba kya gidan nan sai na ji ya mini girma, idan na tuna aure zaki yi nan gaba sai na tsinci kaina cikin faduwar gaba mai tsananin gaske". Wani irin dadi ya kama ni, na murmusa na ce, "Fiye da hakan nake ji Yaya Sadik! Kawai ka daina kula kowacce mace, ni ma na daina kula kowanne namiji shike nan sai mu daina bacin rai da fargaba". Ya sake nutsuwa tamkar ba shi ba ya ce, "To ta yaya kin san dai dole za ki yi aure, su Abba ba za su bar ki ba". "Ai dai ba za a mini auren dole ba, sai na ce ba ni da saurayin da nake so". Kafin ya ba ni amsa Abba ya shigo falon ya gan mu, muka dinga 'kokarin gaishe shi. Ya kalle mu ya ce, "Ni ba Sadik ba ne ya ce mini na masa iyaka da Halimatu ba?" Ya shafa kansa ya ce, "Abba ai ta yi tuba, ta nemi gafara". Ya murmusa ya ce, "Ai na san tsakaninku shi yasa na ce babu ruwana a shirginku". Ya wuce fuskarsa da yalwataccen farinciki. Ya nisa ya ce, "Amma ina son Nusaiba Makole! Ina da hope a kanta, sannan zan fa'da mata ke ce favorite sistana". Na mike na hau kwashe plates din na kai su kicin, na dawo na dauki wayata a kusa da shi. Na juya na fice. Ina jin sa yana faman ambaton "Guduyo kar ki sake yin wani zunubin, ni za ki tashi ki bari ba excuse? Na rantse miki idan ba ki dawo na riga ki tashi ba, ba zan karbi tubanki ba". Na waske na 'ki dawowar. Washegari Juma'a na ro'ki iyayena akan zan je na yi weekend gidan Sakina. Saboda na nisanci Gudale sannan kuma na damu da fishinta, domin ba yadda za a yi Sakina ta iya yini zir ba ta neme ni ba. Amma gashi har kwana da yini ba ta mini waya ba, tabbacin na 'bata mata sosai. Ilai kuwa domin da na isa gidanta, na tarar da ita mijinta da yaransu duk suna falonsa, kasancewar tamkar yar gidan, haka nake a gidan Sakina, yasa na bisu falon. Abin mamaki mijinta da 'ya'yanta ne suka dinga mararin gani na. Ita sai ta mi'ke ta bar falon. Da kulawa minjinta ya kalle ni ya ce, "Halan kin yi wani gingimen laifi, domin duk rikicin Sakina ba ta yi da ke, amma na lura fishi take yi da ke mai yawa". Na dan yi 'yar dariya na tashi tsaye na ce, "shiryawa na zo mu yi" Na fice, ina jin sa yana fa'din "Zumunci irin na ku madalla da shi". Na shiga dakinta na tarar ta shirya da alamun ficewa za ta yi ta bar mini gidan, duk kuwa da ta kammala aikinta ta dawo gida. Na rungume ta ina cewa "Afuwan ya Ukti". Ta ture ni tana cewa, "Ba abin da za ki fa'da mini kuma, tunda akan gaskiya kika rufe ido kika zage ni". Na dago a razane na ce, "Ni na zage ki Maman Nana?" "Ban sani ba!" Ta fa'da a gajarce da alamun fishi. Na marairaice na ce, "Ba karyata ki zan yi ba, amma wallahi ni ban san na zage ki ba". "Halima! Wata maganar da za a fa'da maka ai tamkar zagi ne. Nuna mini kika yi son ki da Namoriki ne ba na yi. Shin a duniya akwai wacce zan so ya aura sama da ke? Babu wallahi sai dai duk da hakan gaskiya daya ce daga kin ta sai bata. Wai har ki bu'de baki ki nuna mini akwai bambanci a tsakaninki da mu. Ni kuwa na rantse miki ke da Sadik ba ku da maraba a wajena". Na dinga ba ta ha'kuri a dalilin ba karamin hasala ta yi da maganar tawa ba. Da 'kyar ta huce, sai dai ta ce, ba za ta kuma ce mini komai akan Gudale ba, ta riga ta fa'da mini gaskiyar magana, tunda ta ga ba yarda zan yi ba. Ta sakar mini 'kotar gatari na hadiya idan zai yiwu. # Team Gudale. # Team Guduyo. # Surayya Dee. # one love ana tare🤝. 2/8/23, 10:22 - Buhainat: 🌺 *SABO DA KAZA* 🌺 *NA* *SURAYYA DAHIRU Gwaram* ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.``` ```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️ ____________(�?)______________ https://www.facebook.com/profile.php?id=100069755834980 •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·�? *Gargadi* *Hakkin mallaka nawa ne ni ka'dai! Dan haka ina jan kunne kada ayi kuskuren ta'ba labarin nan.* *Ko karatan shi a kowacce kafar sadarwa ba tare da izinina ba*. *Biya ku'din karatunki ta wannan asusun* *2384876855* *Surayya Ibrahim* *Zenith Bank.* *Ki tura shaidar biya ta wannan lambar* *0803277332* *Second to the last free pages* *Page 17&18*. Na dinga ba ta ha'kuri, duk da dai ina nan kan bakata matu'kar Gudale ya furta, mini kalmar da nake fatan jin ta a bakinsa, to kuwa ba shakka ba zan tankwabar da ita ba. Da zarar mun yi aure zan saita abina, na mayar da shi irin yadda nake fatan ya zama. Muna cikin haka sai jin muryarsa muka yi yana cewa su Nana ina babarku? Sakina ta fita tana ce masa, "Kai yanzu Antin da za ka ce ne kake mini 'kyashi. Ka tsaya gaban 'ya'yanka kana cewa wai ina babarsu? Wacce irin magana ce wannan marar da'di haka?" Ya dauke kai ya ce, "sannu gyambo". Ya kalle ta ya ce "Ki cewa wannan katuwar yarinyar ta zo nan". Ta galla masa harara ta ce, "Ni za ka aika? Ka ji kunya wallahi, na rasa irin wannan bibikon da kake yi wa Sadiya! Da alamu dai duk yadda kake jin kanka din nan, kake kuma kushe ta, ka riga ka yi saken da ta zame maka tamkar fitila a rayuwarka idan babu haskenta sai ka kasa sakat. Amma don rashin kunya, sai ka bu'de baki ka yi ta kushe ta kana wulakanta ta, don kawai ka ga ita yarinya ce mai son zumunci da 'dinke shi". Takaicin Sakina ya kama shi ya nisa ya ce, "Allah ya yafe miki hakkina da kika dauka. Amma ina ba ki shawara ki gaggauta zubar da yawun bakinki na tabbatar yanzu a gurbace yake saboda kin ta'ba zuciyar Ummanki. Ina jiye miki tsoron fishinta Sakina!" Ya fa'da da muryar gargadi. Mijin Sakina ya yi dariya domin Gudale mutuminsa ne, ba ya gajiya wurin kallon diramarsa. Ya ce, "Gaskiya Sakina ya kamata ki sakar wa Namoriki mara ya yi fitsari, a hakan kike son ya dinga ce miki Antin?" Da sauri Yaya Sadik ya isa gabansa ya mi'ka masa hannu yana cewa, "Assalamu alaikum! Shi yasa ba na kaunar na zo gidanka ba ka nan, har zuciyata na san ka fi Sakina nufina da alheri". Baban Nana ya sake yin dariya ya ce, "To ai matsanancin son da take yi maka ne ya sanya ni ma nake taya ta son naka". A fili Yaya Sadik ya ce, "Ashe dai hatsabibiya ce Sakina? Namiji har namiji, amma yana yi wa mace fadanci?" Ya koma gefe yana cewa, "Allah ka dubi Gudalen Umma, Allah ka dora shi akan matarsa. Ubangiji namiji nake son zama a gidana". "Yawwa Namoriki taya ni jaje, ni kaina ina yawan tuhumar kaina akan lamarin Sakina". Ya fa'da cikin iyashege. A hasale Sakina ta ce, "Ai sai ku ta yi". Tsawon lokaci yana tare da Baban Nana suna hira, har sai da ya shirya ya fita sannan ya dawo wajen mu. Ya kafe akan zuwa ya yi ya dauke ni mu tafi gida. Sakina ta dage akan ba inda zan tafi, tunda kwanaki biyu zan yi, to kuwa ba dalilin da zai sa na tafi har sai ranar Lahadi. Shi ma ya kafe akan mutuwa ce kawai za ta dakatar da shi daga tafiya da ni. Sosai rikici ya kaure a tsakaninsu tamkar yara kananu. Ya kalle ni ya ce, "Sawunki a likkafa ki zo mu tafi, don wallahi ba za ki kwana ba, bijire wa ra'ayina yana nufin kin za'bi Sakina ne a kaina". Yana rufe baki ta ce mini, "Wallahi kika bi shi ina rantse miki da girman Ubangiji na yafe masa ke, ba ni ba ke, ba zan yi gaba da ke ba, amma Bilhillazi babu sauran aminci ko zumunci a tsakaninmu. Za'bi na gare ki". Na yi sukuri ina jin ina ma a ce mafarki nake yi. Ra'ayin wa zan girmama a tsakaninsu? Na yi imanin ba ni da 'yar-uwar data ke so na sama da Sakina! Ba ni da wacce ta zarce Sakina. Sakina na cikin jerin mutanen da suka 'daga darajata, ta hanyar zame mini tamkar sha'kikiyata, akan komai tana tsaya mini, har cikin zuciyata ban cika gane ba cikinmu 'daya ba. Asalima saboda soyayyar da take mini ne ya sanya Umma ba ta cika sakar mata fuska tamkar sauran 'yayanta ba, hakan kuma bai sa ta fasa jana a jiki ba. ita take kula da dukkan suturuna, domin mafi yawan tsadaddun dogayen rigunan da nake tu'amalli da su ita ce, haka nan duk wani gayun da zan yi ita ce, tunda ita akwai saka sutura ta garari, don haka kusan tare take yi mana sayayya ba wai kunce take ba ni ba. Wani lokacin kuma haka zata tisa Abba, Baba, Yaya Abdallah a gaba sai ta karbi kuda'de a hannunsu. Don kawai ta dinga saya mini suturu na alfarma, ban da wanda take yi da aljihunta. Shi yasa nake daukar ido, a idon Gudale kawai nake shan kushe. Na nisa ina jin matu'kar ba a dakin mahaifiyata nake ba, ba inda nake jina comfortable sai a 'dakin Sakina. A da ban damu da kwalliya ba, idan na yi wanka na shafa Vaseline na goga roll on to shike nan zan saka kayana, ko powder ba sosai ba. Na fi kauri a kicin, na fi jin nisha'di a girki sama da 'bata lokacina wajen yin kwalliya. Amma tasirin Sakina a rayuwata ya sanya ta cusa mini son yin kwalliya sosai, duk da ba na son mai nauyi, a kullum na fi son light make up. Ita ta koya mini shafa manyan mayuka masu fito mini asalin kalar fatata, duk da ni 'din fara ce tas, amma saboda fatar tawa ta ha'du da wacce take martaba ta sai na dawo tamkar ka taba jini ya fito, sannan ta yi taushi da sulbi. Na yarda da Sakina, na yarda mayuka da turarukan *Aisha Lame* Jakadiyar Oriflame da suka yi sabo da Sakina saboda nagartar kayanta da sauki, sannan ta 'kware wajen zaba wa mata man da zai yi daidai da fatarsu. A dalilina da Sakina Allah ka'dai ya san adadin matan da muka ha'da su da *Aisha Lame* saboda yadda fatarmu take daukar ido tamkar mun ha'da jinsi da Larabawan Saudiyya. Na dago ido na kalle shi na ga yana mini wani irin kallon da a ranar ya fara yi mini irinsa. Na sake diriricewa musamman da na saci kallon Sakina yadda ta 'dauke kanta tamkar ba ta san ina wajen ba. A hankali na wuce zuwa cikin 'dakin sosai, na kwanta akan gadon. Hakan ka'dai da na yi ya fahimci ba zan bi shi ba ke nan. Ya yi matu'kar ka'duwa da kunyata shi da na yi. Murya a dusashe ya ce, "Guduyo kin za'bi Sakina kin bar ni ko? Kin nuna mini duk abin da nake gani akan idonki da ayyukanki a kaina 'karya ce da yaudara muraran". Na runtse idona, na sake 'dora hannuna akan fuskar don na 'boye hawayen da yake zuba. Ya kalli Sakina ya ce, "Kin yi nasara! Sai dai kuma a wannan karon za ki gane ba na tsoron ki." Ya 'daga murya ya ce, "Guduyo da kin san asarar da kika tafka a dalilin wannan matakin da kika dauka da sai kin shimfida tabarma an miki jaje. Wata magana mafi soyuwa zan fa'da miki a hanya, wani albishir zan miki, amma na gode Allah da ya sanya na gane inda kika ajiye ni kafin na kai ga furtawa. Zan adana maganar tawa don na gane ba ke ya kamata ki ji ta ba". Na zabura na tashi zaune, na kalle shi na ga still dai wannan shu'umin kallon ya ke yi mini. Na mi'ke da nufin bin sa Sakina ta ce, "Kina fita ki tabbatar kin manta da ni wallahi". Kawai sai na zube na saka mata kuka sosai. Ta nuna shi da yatsa ta ce, "Wallahi yau za ka gane iyashegenka ka'dan ne Namoriki, duk sha'kiyancinka ba za ta bi ka ba, ja'iri annamimi kawai". Bai ce mata komai ba ya 'daga murya ya ce, mini "Gudidina! Za ki bi ni, ko kuwa kina tare da wannan kazallahar?" Na kasa magana, ya jima yana ta yi mini kalamin jan hankali, da al'kawarin dadda'dar magana za mu yi. Ganin ko motsi ban yi ba, yasa ya tunzura ya ce, "Shike nan na gode sosai". Ya nunata da yatsa ya ce, "Sakina ina rantse miki da girman Ubangiji sai na nuna miki iyakarki, sai kin gane ba na daukar wulakanci ko ka'dan, ya mi'ka mata dan yatsansa yana fa'din mu kunce, don kuwa yau din nan zan warware dukkan amincin da yake tsakaninmu". Ta share shi domin uffan ba ta ce masa ba. Bare ta ba shi yatsanta su kunce din. Cikin kara'di ya ce, "Tunda kika jingina mini anamimanci sai mun kunce ko za ki shi'de wallahi". Ta yi tsaki ta shige ban'daki. Ya sassauta murya sosai ya ce, "Yanzu Sadiyayye ni kika kunyata, kika tozarta a gaban masu yin mini hamayya? So kike na kwana cikin bacin rai ko?" Na girgiza masa kai. Ya sake kashe murya ya ce, "To taso mu yi tafiyarmu kawai, ina tabbatar miki na fi ta damuwa da ke, jiyan nan na gama fa'da miki idan ba kya nan, gidan girma yake mini". Daidai lokacin ta fito. Ta kalle ni ta ce, "Tashi ki shiga ki wanke fuskarki ki doro alwala, ki fara zikiri, yammacin Juma'a ba lokacin da zai tafi a surutai marasa kan gado ba ne, ki yawaita Istigifari duk taurin matsala sai ta warware miki. Ki dage wajen neman tsari da sharrin hatsabiban bayinsa masu hana mutane zaman lafiya da nutsuwa". Ya yi tsaki ya juya ya fice yana cewa, "Sara da sassaka baya hana gamji toho! Ban da dai kazallaharki ta wuce 'kima ina ruwanki da shiga shirgina da ita?" Sai da ta tabbatar ya ja motarsa ya bar gidan sannan ta kalle ni ta ce, "Shashar banza marar aji. Tunda kin kafe shi kike so, ashe ba za ki dinga kama kanki a gabansa ba? Wai ke wanne irin karatu kike yi ne da sam babu lissafi da azanci a cikinsa?" Na kasa ba ta amsa saboda na sani gaskiya ne, ba ni da aji ko ka'dan akan lamarin Gudale. Rashin bin sa da ban yi ba, shi ne ya sanya Sakina ta huce da ni sosai. Wayewar Asabar ya mini waya wai yana kofar gidan na fito na karbi sa'ko. A hankali na ce, "Ba za ta bar ni na fito ba". A masifance ya ce, "Ke ba na son maganar banza kin ji! Ina ce wanda kika kwaso mai dagaggen wando ma yana zuwa nan ya same ki, sai ni ne za ki ce ba zavta bar ki ba. Ban da dai ke hankalinki ragagge ne cewa za ki yi ni ne? Ki ce mata course mate 'dinki ne ya kawo miki handout dinki. Ina jiran ki yanzun nan". Ya kashe wayarsa ya bar ni da tunanin yadda zan ce wa Sakina zan fita kofar gida. Na fito na same ta tana wajen da ta ajiye injin wankinta! A sanyaye na fa'da mata zan leka waje na karbi sa'ko. Ta dago ta kalle ni sosai har na tsargu. Ta nisa ta ce mini "A kar'bar sakon ne har da sake gyara fuskarki?" Ta ja mayafinta tana cewa, "Mu je na raka ki". Gabana ya yanke ya fa'di na diririce. Hakan da ta gani yasa ta gane komai ta ce wato "Namoriki akwai fitinannen mutum". Kan dole muka fita! Yana zaune cikin motarsa ta alfarma. Ganin mu tare ya sanya ya sauke gilashin motar ya ce, "Na shiga uku ni Saddi'ku". Sakina ta daure fuska ta ce, "Duk tsiyarka ba inda za ta tafi, kuma wallahi sai na fa'da wa Abba wannan bibikon da kake yi, sam-sam ban yarda da kai ba". "A wulakance ya ce, "Yadda na shaida Allah daya ne haka na shaida ke din masharranciya ce, dadin abin ma abin da ya ha'da ki da Guduyo shi ya hada ni da ita bare ki nuna mini kin fi ni kusa da ita, mai shisshigi da cusa kai". "Ka kiyaye ni Namoriki" Sakina ta fa'da tana nuna masa yatsa. A kausashe ya ce, "Ai tun jiya na kiyaye ki Sakina! Tunda na gane jarumin namiji irin Yunus amma a hannunki yake ai dole a nemi tsari da tsiya mai wasali irin taki". Ta kalle ni ta ce, "Shige mu tafi munafukar banza marar kunya". Na shige na bar ta a tsaye. Na labe a jikin gate din. Na ji yo tana cewa, "Wallahi sai na yi maganin wannan girman kan naka, ba za ka ta'ba samun sassauci a wajena ba har sai ka fito a mutum, ka bayyana kyakkawar manufa akan Halimatu. Idan ba hakan ba kuwa, wallahi ka rubuta ka ajiye ba ka ga komai a irin tsiya da makircin da kake danganta mini su ba. Da ikon Ubangiji sai na kai ka 'kasa Namoriki". *Kina neman jakadiyar oriflame ta kwarai?* *Kina son mayuka da zasu face da launin fatarki a wannan lokacin na sanyi?* *Kina son 'kamshin na alfarma?* *Albishirinki indai harkar kayan kwalliya ne ma kece raini. Kina bu'katar ki zama Iya Basiru dawisu sarkim ado?* *Kawai tuntu'bi Aisha lame* *A wannan lambar 07036662633* A zafafe ya ce, "Da gaskiyar Umma da take fa'din an canja mata ke a asibiti, nononta da kika sha ne ya sanya kika rikide kika samu kammaninmu, amma kyakkawar siffar da aka yi miki, aka kuma yi miki mummunar zuciya irin ta kafiran Turawa masu ra'ayin ri'ko ya isa ya tabbatar mini ke din dangin su Ifiriti Minal Jinni ce amma ba jinin Malam Habu da Saude ba". Dariya ta kwace mini, na yi maza na rufe bakin nawa. Tsakin da Sakina ta ja mai 'karfi ne ya taimaka dariyar ta tsaya mini cak. Ta ce, "Komai za ka fa'da bai dame ni ba. All I know Halimatu ba za ta tafi ba sai gobe, kuma rashin kunyar da ka mini ba za ta ta fi a banza ba, sai ka gane ni ba su Antin Zaria ba ce". Da sauri na ruga na yi cikin gidan saboda na jiyo takunta. Yayin da haushinta ya mamaye zuciyarsa domin so ya yi ya ba'de ta da 'kurar tayar mota. Sai kuma ta riga shi barin wajen, abin da ya fi tsana ke nan ana cikin magana a tafi a bar shi. *AMYAS NEW & FAIRLY ITEMS* *komai da ruwanka ne su* *Ina amare yan kwalisa?* *Ina matan da suke son su yi canjin kayan daki?* *Ina matan da suke son kayan daki na hannu masu aminci?* *Kina son saida wayar hannunki, ko kuwa siya kike son yi?* *Kina neman electronics tuwaris, ko kuma ke ce zaki fitar da na ki?* *Kawai ki tuntu'be su ina tabbatar miki zaki samu komai daidai da bu'katar ki cikin rahusa* *08083909947.* Wannan al'amarin yana cikin abin da ba na mantawa domin a ranar yini muka yi Sakina na mini gorin rashin aji, tana habaicin mazan yanzu ma sun sha wahala kafin su aure ka amma suke wulakanci son ransu, ina kuma ga wanda ya gane son sa ake tamkar rai, alhalin shi bai ta'ba furta kalmar so ba? Na sani sarai da ni take, sai na yi sukuri, na kasa cewa komai. Iyaka dai na gane so take yi na ba ta ha'din kai, na daina nuna zakuwata akan lamarin Gudale. Na kuma gaskatata cewar bai fi ni a wajenta ba, domin kishina take yi muraran, so take yi na yi daraja a wajensa. Har yau din nan da nake ganin ta yi mini laifi na sani, ita din wata irin mace ce mai kyautata zumunci, ba abin da ba ta yi mini ba, duk wani kukan da na yi tare muke yin sa. Na tabbatar mahaifana biyu ne kawai suka mini abubuwan alheri da ya zarce wanda Sakina da mahaifinsu suka mini. Madalla da Abbahl! Madalla da Sakina! *** Na nisa na kalli agogo a dalilin na ji har an fara kiran sallar Maghrib, ashe na shafe lokaci ina tunanin rayuwata? Duk da dai har yanzu sharar fage ne, ban shiga cikin gundarin labarina ba, labarin rayuwar aurena, sunan wani littafin 'kanwata *(Ayusher Muhd)*. Rayuwa mai tarin kalubale, mai rikita-rikita da tashin hankali. Na mi'ke ina cewa, "Sai na sake samun zama zan ci gaba da yin waiwaye domin na auna kalubalen da na fuskanta, na sake jinjinawa kaina ba don komai ba sai don na san ni da kaina na yi jarumta, na jure al'amura masu nauyi, ta yadda za'a dinga ganin wauta da rashin kamun kaina. Ba kowa zai fahimci ne ba, ba kowa zai mini uzziri ba, haka nan ba kowa ne zai mini adalci ba. Sai masu fahimta, sai kuma matan da suka shiga irin al'amarin da na shiga. Sai an ji irin *Halin Yau* din da na fuskanta. Za'a gaskata azancin nan na *SABO DA KAZA* ba ya hana a yanka ta. Allah ya 'karawa mata ha'kuri da juriya a gidajen aurensu. Allah ya taimaki duk namijin da yake kyautata wa matansa, yake kokarin yin adalci, yake kuma sauke dukkan nauyin da yake kansa babu 'kwange, babu gajiya. Madalla da mazan da ba sa muzanta matan aurensu! Madalla da mazan da ba sa zaben jinsin da suke son a haifa musu. Madallah da maza masu sassauci da tausayin mace. *Ku hanzarta biyan ku'dinku dan kada a katse muku Jin wannan dambarwar* 🥰 # Team Gudale! # Team Guduyo! # Surayya Dee! # One love 🤝. 2/8/23, 10:22 - Buhainat: 🌺 *SABO DA KAZA* 🌺 *NA* *SURAYYA DAHIRU* ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.``` ```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️ ____________(�?)______________ https://www.facebook.com/profile.php?id=100069755834980 •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·�? *Assalamu alaikum sister's! Hakika na gode wa Ubangiji! Na kuma gode muku! Masu bibiyar wannan littafin ga'ba daya, mussaman wandada Suka saya da masu Shirin saya.* *Cikin yardar Allah free pages ya kammala a yau, bisa goyon bayanku da kuma horewar Mahallicinmu*. *Zan dakatar da posting na dan lokaci kalilan ina fatan zaku taimakawa kasuwa cina ta hanyar rufe kofar fitar mini da paid pages*. *Na gode sosai Ubangiji ya sanya na cika al'kawari, Allah ya sanya na gama muku lafiya, ina muku fatan a yi karatun lafiya cikin nisha'di.* *Gudale ya ce za'a yi fashin posting sau daya a sati. A da sau biyu za'a yi fashin, Amma soayyar da kuka nuna mini sai na 'Kara muku daya. Ina addu'ar Allah ya albarkace mu gaba'daya*🥰 *Biya 500 kudin karatu ta wannan asusun* *2384876855* *Surayya Ibrahim* *Zenith Bank.* *Sai a turo shaidar biya ta wannan lambar* *08032773332*. *Last free page* *Page 19&20* present. Na idar da sallah ina zaune a kan sallayar ina tunanin anya kuwa zan iya ha'kuri na yafe wa Gudale tamkar yadda ake so? Hawaye mai zafi ya 'balle mini. Tsakani da Allah ba abin da nake so irin ya fita a cikin rayuwata tun bai 'karasa kassara ni da ba'kin-cikinsa ba. A hakan ya shigo ya tarar da ni yana sa'be da Aman! A sanyaye ya zauna akan gado. Aman sai zillo yake na dauke shi amma na yi kememe na yi kamar ban gan shi ba. A sanyaye ya ce, "Halah! Kin ji Antin Zaria wai ba za ta ba mu su Amnah ba. Ta ri'ke su ke nan, ba za ta bayar ba sai idan ke ce kika ce sai ta ba ki 'ya'yanki! Don Allah ki daure ki tashi mu je ki nuna mata kina bu'katar su a tare da ke". Na dago idanuwana da suka kumbura na zuba masa. Na ce, "Akan me zan ce ta ba ni su alhalin na san a can ne za su samu gata da kulawa? Akan me zan dawo da su inda ake kallon su a marasa amfani? Har abada ba zan ta'ba iya wannan butulcin ba". Ya yi shiru, jikinsa ya sake yin sanyi. Tsawon lokaci dakin ya dauki ka'daici Sautin magana, sai motsin Aman da yake ta gwalantun da ba a fahimtar komai domin watansa goma sha biyar kacal. Cikin karfin hali ya ce, "Bari na watsa ruwa ki raka ni unguwa, don Allah ki shirya kafin na fito." Ya fa'da tare da miko mini Aman. Na yi funfurunfus na ki karbarsa. Ya sassauta murya ya ce, "Please my dear Halah! Wannan halayyar ba dabi'arki ba ce". Na galla masa harara na ce, "Akan me zan karbe shi alhalin ba ni ya kamata na zama uwarsa ba?" Ya yi turus yana kallona. Ya saki ajiyar zuciya ya ce, "Na sani ni mai laifi ne Guduyo! Amma na ce ki yi ha'kuri, ya kamata ki mini afuwa". Zuciya 'daya na ce, "Ka sawwake mini, domin idan ina kallon ka ba zan yafe maka ba". Amma da zarar ka sahale mini wannan kadaddararren zaman da babu komai a cikinsa sai ba'kin ciki, to kawai ka ji a ranka na yafe maka" . Ya hassalo ya ce, "Na rantse da Ubangiji sai na ci mutuncin Sakina, hatsabibiya marar mutunci! Na sani ita ce kanwa uwar ha'din wannan tashin hankalin da nake fuskanta, wato ba za ta daina tsoma mini baki a gidana ba?" A dake na ce, "Ahaf da ma na san kana nan da halinka, nan da kwanaki biyu za ka ci gaba da wula'kanta ni yadda ka saba. Akan idona kake zagin Sakina? Ina ce an riga an raba yar'uwata ce ba taka ba, kana cin mutuncin dangina, kuma kake tunanin zan yarda ka canja?" "Na ba ki hakuri dai, saboda na san ban kyautata miki ba. Amma tunda kin yarda da keken 'beran da take 'dora ki a kai ai shike nan. Sanin kowa ne Sakina ba ta nufina da alheri! Babban burinta ta kashe mini aure, ta 'dai'daita mini zaman lafiya a gidana, ta raba ni da kwanciyar hankali, ita dai ta gan ni a cikin tasku shi ne burinta". Ya fa'da yana haki saboda tsananin bacin rai. Na kalle shi ina mamakin da bai fahimci irin 'kaunar da Sakina take yi masa kwatankwacin irin son da take yi mini ne. Domin ni kaina ban yi zaton tana son sa har hakan ba, sai a yanzu da ta dawo da ni gidansa. Tunda nake da ita a wannan karon na ga laifinta har zuciyata. Saboda zarginta da son kai da ta nuna a tsakaninmu. Duk da dai zuciya ce da ba ta da 'kashi ta sa na yi wannan hasashen, domin ba abin da Sakina ba ta yi mini na alheri ba. Ta dauki ba'kin jini a cikin yan'uwanta, hatta mahaifiyarta sai da ta kusan sallama ta saboda ni. Amma hakan bai saka ta juya mini baya ba, ta tsaya mini, ta yi fito na fito da duk wanda yake son shatale ni. Take na ji kunyar yadda na nemi manta tarin alhairan da ta wanzu tana yi mini tun ina tsumman goyo. Har yau su Amnah ba su san cewa yayar Babansu ba ce, sun dauka yayata ce. Saboda tsananin kirkinta gare ni. Na kalle shi na ce, "Ba inda za ni, ina jin nauyin na fita da kai, a ce kai mijina ne, gaba'daya nawa kake da za ka zame mini miji?" Ba'kin cikin maganar da na yi ta kama shi. Ya tunzura ainun ya fice tare da buga kofar dakin da 'karfin gaske. Mintina ka'dan ya fito sanye cikin yadi mai tsada kalar shudin samaniya, ya 'dora hula shudiya sosai, ma'ana shudin ya ciza. Har yanzu da muka yi shekaru bakwai da aure, yana nan ba jiki, sai dai ya 'dan murje ka'dan, irin dai murjewar da Ramadan Both ya yi a yanzu. Ya yi kyau sosai! Sai 'kamshin tsadadden turaren maza na Cris Adam's yake tashi tamkar a dakin ya fesa. Ya sassauta murya sosai ya ce "Har na shirya amma kina zaune?" Na yi shiru na ki tankawa bare na ba shi amsa. Ya nisa ya ce "Wajen Baba zan je na yi tuba da neman afuwa, so nake mu je ki raka ni, ya gan mu tare don ya fahimci mun shirya kanmu". Yana rufe baki na ce, "Indai sai ya gan mu tare ne, zai gane mun shirya to kuwa ba zai taba ganewa ba". Ya tsaya cak, kallo mai tsanani yake yi mini. Na yi kamar ban ga yana kallona ba, na sake cewa "Kai yanzu sai ka iya zuwa gaban Baba da nufin gaisuwa ko wata magana?" Ba fargaba ya ce, "To ba Babana ba ne?" Ido cikin ido na ce, "Babana da Al'amin dai". "Tunda dai ya sanya an dawo mini da ke kam ai Babana ne, amma da ya ci gaba da zuba ido ana mini rashin mutunci da iko a gidana tabbas zan yi fiye abin da na yi din". Cikin 'daga murya na ce, "Ai na sani mrashin arzikinka ya kere tunanina. Ban da rashin kunya har ka iya zuwa gabansa, bayan duk cin zarafin da ka yi masa?" Ya fesar da zazzafar iskar bacin rai. Ya ce, "Ubangiji ka shaida na yafe wa Halah! Kar a kamata da laifin 'daga harshenta akan nawa". Ya fita da sanyin jiki. Har ya kai 'kofar fita daga falo, sai kuma ya dawo ya ce, "Na bar Aman yana barci a 'daki ki taimake ni, ki kula da shi". Yana rufe baki na ce, "Ba zan kula da shi din ba, domin ni ban siffantu da rainon yara maza ba". Ya sassauta murya sosai ya ce, "Abba ne fa". Na sunkuyar da kai kasa domin dai kam ban dauki lamarin duk abin da ya shafi Abba da sau'ki ba. Ni shaida ce ta yadda ya shafe rayuwarsa yana tiritiri da zumunci musamman ma alhalin gidanmu. Abba haifar mahaifinmu ne kawai bai yi ba, amma ba abin da da bai yi masa ba. Dukkan haihuwar da mahaifinmu ya yi, bai ta'ba sayan ragon suna ba. Bai ta'ba biyan ku'din makarantarmu ba, ko kayan abinci Babanmu bai san ya saya ba, domin tare Abba yake sauke musu da na gidansa, ko ashana katon guda za a kawo. Bai kuma ta'ba gajiya ko ya nuna alamun mulkin mallaka ga Babanmu ba, haka nan wani mahalu'kin bai ta'ba ji a bakinsa shi yake hidima da iyalin 'dan uwansa ba. Sannan nan Umma mai 'dakinsa za ta yi komai ta kwashe 'kalau, amma matu'kar za ta ta'ba ahalin mahaifinmu a nan take ganin taskunsa. Har igiyar aurenta guda ta ta'ba tsinkewa saboda izgilin da take yawan yi wa Mama. Hakan ya sake kambama kiyayyar da take yi mana. Ta kuma kafe akan asiri mahaifiyarmu take yi. Wadannan halayen girma na Abba da kyautatawarsa ya sanya nake girmama shi da dukkan zuciyata, ko mai irin sunansa na gani a hanya sai na girmama shi, ta hanyar cewa Babana. Idan kuma na ga mutumin mabukaci ne, sai na tallafa masa ko da idan na bayar din zan takura. A sanyaye na ce, "To zan duba maka shi kafin ka dawo". Ya marairaice ya ce, "So nake ki kula da shi muddin rai, ki kula da shi tamkar su Afrah". Da sauri na dinga girgiza kaina tabbacin ban amince ba. Na dora da cewa, "Ai ba 'daya suke ba, don haka ba za su samu kulawa iri 'daya ba, domin kai ma shaida ne ba su samu kulawarka, irin yadda ya samu ba". Ya rasa bakin magana, ya buge da cewa, "Shike nan hakan ma na gode" Ya juya ya fice. Kai tsaye cikin gida ya nufa, ya zarce shashinmu! Ya shiga ya gaisa da Mama a dakinta, ya wuce falon Baba. Sai da ya je gaban Baba sosai sannan ya durkusa, ya fara gaishe shi. Ya amsa ba yabo, ba fallasa. Tsawon lokaci yana gurfane, ya kasa magana domin sai da ya zo gaban Baban ya gane girman rashin mutuncin da ya yi masa. A sanyaye ya ce, "Baba ka dubi Allah ka yi mini ha'kuri. Ni kaina na san na yi maka ba daidai ba, wallahi tsananin tashin hankali da fargabar kar na rasa aurena ne ya sanya na yi abin da na yi din. Amma na yi nadama, don Allah ka yi hakuri ka yafe mini". Tsawon lokaci bai ji amsa ba, ya sani laifukansa sun tsananta, masu wahalar a yi afuwa cikin sau'ki ne. Ya sake sunkuyar da kai kasa yana cewa, "Baba daurewa zaka yi, ka karbi tubana indai ba so kake hakkinka ya sake damalmala mini lamaruna ba". Sai a lokacin Baban ya saki ajiyar zuciya mai nauyi ya ce "Idan ban yi ha'kuri ba na yi ya ya da kai? Ai duk abin da ka fa'da ko ka yi mini ai gaskiyar lamarin ke nan". Cikin nauyi sosai Gudale ya ce, "Ni dai Baba ka yi mini afuwa. Na yi tuba, a mini sassauci don Àllah". Ya nisa ya ce "Sadik ba abin da za ka yi mini a duniya da zai saka na fita daga al'amarinka! Kawai abu daya ne matu'kar ba ka yi ba, ni kuma ba ka isa na yi maka ba. Ba komai ba ne illa gaisuwa, indai har za ka gan ni ka dauke kai to ni kuwa ba ka isa na gaishe ka ba. Inka dauke wannan komai iyashegenka ai dole na yi hakuri tunda Ubangiji ne ya ba ni kai, kuma kamar yadda ka fa'da mini cewa mahaifinka ba abin da bai yi mini ba, tabbas haka ne ba na inkarin hakan, ban kuma ji zafin furucinka ba, domin ko mahaifinmu kawai ya haife ni ne, amma Alhaji shi ne komai nawa". Kunyar duniya ta kama Sadik yana tuno lokacin da ya tsaya a gaban 'kanin mahaifin nasa yana zazzaga masa dibar albarka. Ya dinga jin tamkar 'kasa ta tsage ya shige, tunda ba zai yiwu ya dawo da baya ya goge waccan ta'asar ba. "Ni dai ka yi ha'kuri Baba! Na sani ni mai laifi ne". Ya fa'di hakan cikin matsananciyar kunya. Ya zuba wa Sadik din da yake gurfane ido, yana jin tarin 'kaunarsa, yana sake jin alhinin rashin 'dan uwansa, ya tuna maganganun Abba da ya yi ta yi masa mafi yawa akan Sadik ne. Tabbas da a ce kowanne 'da halin mahaifinsa yake yi da ya bugi kirji ya ce Sadik sai ya fi kowa more kyawawan dabi'u. Sai dai kash, muna cikin wani irin zamanin da yara suke zama masu dabi'u irin na albasa. Ya nisa ya ce, "Tun tuni na yafe maka Sadik! Idan na ce ban ji zafin abin da ka yi ba na yi 'karya, idan na ce hankalina bai tashi ba, nan na yi munafunci. Sai dai na koma na auna maganganunka sai nake tuhumar kaina ko dai da gaske na yi son kai din? Na gaskata ka, tabbas da Alhaji ne ba zai daga ido ya yi magana akan ka ba, bare ya nuna an zalunce ka saboda tsananin kara da inganta zumunci." Daidai lokacin hawaye ya 'balle masa ya janyo tissue ya hau gogewa. Da rawar murya ya ce, "Har cikin zuciyata na yafe maka, ina fatan Ubangiji ya bude maka zuciya ka fahimci gaskiya, babbar damuwata da fargabar da nake ciki akan lamarinka guda 'daya ne. Yanzu Ubangiji ma ba zavka kiyayi ta'ba shi ba ? Ya maka baiwa kala-kala, ya ba ka rai, ya yi ka a Musulmi, ya ba ka lafiyar ji da gani. Sannan ya ba ka lafiyar cin duk nau'in abincin da kake so, ya ba ka damar zuwa bandaki da kanka ka yi lalurarka salin alin. Bugu da 'kari ya ba ka mace ta gari da take yi maka wani irin so da ko a wasan kwaikwaiyo yana wahalar samuwa. Ya azurta ka da lafiyayyen abin hawa, ya backa yalwataccen gida. Haka nan ya ba ka iyaye da dangi da kowa hankalinsa a kanka yake. Sannan ya ba ka haihuwa da wasu kullum a cikin kukan rashinta suke, wasu suna can, suna kashe ma'kudan kudade don neman maganin da zasu samu haihuwar". Ya yi shiru saboda yadda kuka ya sake zuwa masa. Tsawon lokaci Baban yana share hawaye, yayin da Uban gayyar idonsa ya cika taf da 'kwalla, jikinsa ya mutu murus, nadama ta sake kama shi. Da rawar murya Baba ya ce, "Sadik fa'da mini da bakinka me ya kamata ka yi wa Ubangijinka bisa wannan tarin falalar da ya yi maka? Don ya san kai bawa ne mai godiya". Cikin rauni sosai ya ce, "Kamata ya yi na kasance mai yawan godiya da tuba izuwa gare shi, sannan na kiyaye ka'idojin shari'a na girmama dokokin da aka gindaya, bayan haka na karbi duk abin da ya yi mini da hannu biyu ko da kuwa ba hakan nake so na ga ni ba". Baba ya ji dadi ya ce, "To mene ne ya hau kanka da kake yi wa Ubangijinka izgilin ba 'ya'ya mata kake so ba? Mene ne ya yi maka da'di wajen musgunawa matarka don kawai ta haifi mata, tunda na san kana son ta". Da sauri Sadik ya ce, "Alhamdulillah! Ubangijina yana mutunta ni Baba! Na gode masa da ya fahimtar da kai ina son Gudidina tamkar rai. Amma Sakina da Al'amin sun shigo mini cikin gida sun yi mini kane-kane sun hana ni damata ta mai gida. Da.ma bayan tuban da zan yi a gabanka, har da 'kararsu na kawo, ka fa'da musu su fita a harkar gidana idan kuwa ba haka ba Billahillazi kotu ce za ta raba ni da duk wanda ya sake shigar mini gida a cikinsu, munafukai azzalaumai yan ta'adda masu zuwa lahi..." Tsawar da Baba ya buga masa ce ta saka ya katse maganar ba don ya kammala ba. "Kai! Saurare ni mashiriricin banza marar kunyar wofi! A gabana kake wannan kalaman bayan ka ce tuba ka zo yi. Wanne irin tuba ne? Amma dai tuban muzuru ko?" Ya yi shiru ya kasa ba shi amsa. "Yanzu ashe ba duka ka ajiye makaman naka ba Sadik? Ina cikin fa'da maka irin rashin da'ar da ka yi wa Mahallicinka, sai ka katse ni ta hanyar kawo wata magana da babu komai a cikinta sai shiririta da rashin fahimta. Kasan irin son da Al'amin da Sakina suke maka kuwa?" Da sauri ya ce, "Na rantse Baba duk duniya su ne makiyana, ba su da buri irin su gan ni ina cikin ragaita da tagayyara. Na riga na shata jan layi da su. Ni kuwa mai za su mini a duniya? Wai su ne za su dauke mini mata, su boye ta, su koya mata yi mini tijara sannan a ce su masoyana ne? Ai kuwa Allah wadaran wannan son da suke yi mini da babu komai a cikinsa sai zalunci". "To yanzu dai na daina yi maka nasihar tunda ba shiga take yi ba ko?" Baba ya tambaye shi a raunane. "Ci gaba Baba ina jin ka! Ai tuni na yi wa Allah kuka a cikin sujjadda, na ro'ki shi gafara. Sannan ai na daina, da ma namijin nake kulafacin samu to an same shi, me ya rage ban da a yi godiya? Kuma Wallahi Baba nake fa'da maka, ba 'karamin son su Amna nake yi ba ashe? Ban fahimci hakan ba sai da waccan ta Zarian ta kwashe su, yanzu kuma don mulkin mallaka wai ba za ta dawo da su ba. Shin an ta'ba yin haka ne Baba? Ni ba yarda zan yi ba, kawai jira nake mu gama shiryota da Gudidina. Wallahi sai an ba ni 'ya'yana tunda ta ce ba za ta bayar ba sai ta ji a bakin uwarsu". Mamaki ya cika zuciyar Baba ya ce, "Waton da zarar ta huce za ka saka ta yi rashin mutunci kamar yadda ka saba ko? To na rantse maka da Allah umarni na ba ka kar ka kuskura ka yi wannan maganar idan kuwa ka yi babu shakka ban isa ba, ba ni kuma da mutunci ko ka'dan a idonka". "To shike nan na ha'kura saboda kai, ba zan yi magana ba Baba! Yanzu yaushe zan zo ka kai ni wajen Yayar Kwalli na ba ta ha'kuri?" Baba ya dan yi tari kadan ya ce, ,"To mu bar shi zuwa Juma'a daga Masallaci sai mu wuce. Sannan ina jan hankalinka ka sasanta da 'yan uwanka Al'amin da Sakina". Ya dinga godiya sosai, har ya mi'ke ya sake komawa ya gurfana. Ya kalli irin yadda ya sake gurfana tamkar zai kwanta masa. A ransa ya san wani al'amarin zai sake barowa. Ilai kuwa sai jin sa ya yi yana cewa, "Ka daure Baba ka je ka yi wa Guduyo nasiha yanzu fa gaba'daya ta bijire mini, yau dai kwanaki hudu ke nan da dawowarta amma har yanzu ba maganar arziki a tsakanin mu balle a je ga maganar gyara mini 'dakina". "Kunya ta kama Baban cike da nauyi ya ce, "Je ka zan kira ta a waya". Yana jin haka ya mike da azama yana cewa, "Na tafi to, ka kira fa kafin na isa, so nake ina shiga na gane ka yi magana". Da ido kawai ya bi bayansa yana ta faman yi masa addu'a a zuciyarsa. Domin ya gane akwai abubuwan da ba zai ta'ba dainawa ba. Bai zame ko ina ba sai bangarensu ya tarar da dukkan sisters dinsa suna nan, sun saka Umma a tsakiya a nata dabdala. Ya tsallake ya ratsa tsakiyarsu ya zauna jikin uwarsa. Cike da shagwa'ba ya ce, "Umma shi ne ake wannan dinner din babu ni?" Ba walwala ta ce, "To na sani ko za ta bar ka ka zo, tunda dai na gane ta yi galaba a kanka ta fi karfinka, sun kwace mini kai". Ta fa'da cike da rauni sosai. Cikin tarin soyayya ya ce, "Mai kwace Gudale a hannu Umma ai sai mutuwa, ba dai biladama ba. So nake yanzu ki yafe mini, ki kuma sanya Guduyo cikin jerin 'ya'yanki, matata ce kuma ita ce uwar su Amnah da Aman, ta ci albarkacinmu". Ta nisa ta ce, "To amma da sharadin za ka sake yin aure, har yau Fauziyya tana son ka". Gabansa ya yanke ya fa'di, ya zabura ya tashi a jikinta ya zauna sosai ya ce, "Gaskiya Umma ki yi ha'kuri ba zan sake jawo wa kaina masifa ba, waccan ma da na yi yaya na kwashe ne? Ki yi ha'kuri, a bar wannan maganar kawai don Allah". Sakina da take gefe ta kyalkyale da dariyar iyashege, yayin da su Antin Zaria suke fa'din yaro ya gane Jahar Borno a Arewacin 'kasarmu take". Ya hassalo musamman dariyar da Sakina take faman tintsirawa. Ya ce, "Umma ki ja wa Sakinatu kunne ta fita a harkata! Ba don ina gudun bacin ranki ba da tuni na saka an sakaye mini ita". Ai ko Umma ta hauta da fa'da tana cewa, "Yo Sakina za ta girma ne, tana gudun bacin rai na ne? Kai dai da ka damu da damuwata 'kara ha'kuri da ita kawai, idan ka hadu da dan-uwa mai wuyar zama ai sai dai ka yi ta ha'kuri kawai". Ya mi'ke ya saka hannuwa biyu ya dagata ya ce muje daki akwai abin da zan fa'da miki Umma! Ai kuwa ta bi shi suka bar su a falo. Sai da ya zaunar da ita a bakin gado, sannan ya tsugunna jikin kafafuwanta ya ce, "Na ro'ke ki Umma ki yi ha'kuri, ki sassautawa 'kaddarata! Ki yi hakuri ki karbi Guduyo a matsayin surakarki, ki yi mini alfarmar hakan Umma". Ta fara goge idanuwanta cikin kuka ta ce, "Na yarda zan sassauta mata, amma ka sani idan ka fifita ta a kaina zan janye sassaucin wallahi" Ya ru'ko hannunta ya ce, "Har abada ba ni da kamar ki, ba wata halitta da zan fifita sama da ke, ina ro'kon Ubangiji ya mini tsari da yin hakan". Cikin rarrashi ya ce zan kawo ta gabanki ta baki ha'kuri Umma! Na kuma jaddada mata cewar za ta iya bata mini rai na ha'kura, amma ta'ba ki na nufin fishina mai gigitarwa. Ke kuma sai ki saka mana albarka ki fa'da mata kin amince da zamanmu tare kina farinciki da hakan". Ta ce, "Sharadin haka ta sanya maka?" Da sauri zuciyarsa ta buga, ya aka yi ta harbo jirginsa da sauri? "A a Umma so nake dai kawai a yi afuwa a sassauta ko zuciyoyinmu sa nutsu, nan duniya ke ce cikon farincikina. Idan babu kyakkawar alaka tsakaninki da ita wallahi zan dauwama cikin kaico da nadama." Ya fa'di hakan cikin matsananciyar damuwa saosi. Karon farko da ta yarda za ta yi ha'kuri da Halimatu a matsayin surakarta ba don tana so ba, sai don hakan Gudalenta yake so. Ta nisa ta ce, "To shike nan na amince, amma ka sani yayarku ta ce ta ri'ke su Saudatu! Idan har na ji kun yi magana akan hakan, na san ita ce tunda kowa ya san yadda ta ma'kala su a ranta. Wallahi idan hakan ta faru har kai ma ba za ka ji da'dina ba, bare kuma ita". Da sauri ya ce, "Haba Umma ta isa ma ta fara wannan katobarar? Ke dai Allah ya kara miki lafiya na gode sosai Ubangiji ya shaida na yi godiya sosai Umman Saddi'ku". Suka dawo falo ya kalle su ya ce, "Kowacce ta tashi ta tafi gidanta kun zauna har takwas ta yi." Ya juya ya fice yana jiyo irin carin da suke yi masa. Ya dawo ya tarar da ni a falo ina kallon M.B.C 3 saboda yadda na saba da kallon Cartoons a dalilin su Amnah. Na amsa sallamar da ya yi na ci gaba da kallo na. Ya zauna kusa da ni ya ce, "Baba bai miki waya ba ke nan?" Ban kalle shi ba na ce, "Ya yi mini mana". Ya shige yana cewa, "Ki zo ki same ni, ina son mu tattauna wata muhimimiyar magana". Na tabe baki ina jin a raina kuma na san ba dai na taka dakinsa ba kam". Ina ganin ya shige na tashi na kashe komai na shige nawa dakin na rufe da mukulli. Ina jin sa ba irin sintirin da bai yi ba, ba kalar bugun kofar da bai yi ba, amma fir na ki. Waya kuwa kashe ta na yi. Washegari ya tarar da ni a Study Room! Fuskar nan a daure tam ya ce, "Kin kyauta da kike wulakanta mijin aurenki, ina bin ki ne saboda na san na yi miki laifi amma ke sam kin kafe, kin ci laya. To ki sani wallahi ba zan yarda ba, dole sai kin zo dakina wallahi". Na dago na watsa masa harara na ce, "Sai na ga dolen ai". Ya ce, "Kin gama abin karyawar ko kuwa?" Kai tsaye na ce, "Ba zan yi ba". Ya jijjiga kai ya koma." Ba a jima ba ya dawo cikin Shirin fita, Aman na hannunsa shi ma ya yi masa wanka, sun yi fes da su, kammaninsu guda har rashin jikin. Sai da suka fita sannan na gyra gidan na yi wanka. Ina zauane sai kawai na tsinci kaina da son ci gaba da hararo ba'dakalar da na shiga a baya. *LAIFIN DADI KAREWA* *Karshen Free pages ke nan na wannan kayataccen littafi mai suna _SABO DA KAZA..._ Zan dakatar da yin posting na dan lokaci ka'dan, da zarar kun karbi labarin ta hanyar sayan littafin zan ci gaba da sakar muku shi a Paid Group dina. Ku karanta cikin lumana da salama. Wanda ya yi noma dai ya huta da awo.* *Labarin Guduyo labari ne mai ta'ba zuciya, labarine da dole sai kin ci karo da irin kalar taki matsalar ko kaddarar. Ubangiji ya kara mana ha'kuri da juriya* *Duk wannan bayanin sharar fage ne. Ina tabbatar muku ba za ku yi nadamar saya ba, lallai kwalliya za ta biya kudin sabulu.* *Na san da yawa cikin masoyaba su ya kamata su fadi ba ni ba, to amma kasancewar an ce 'waka a bakin mai ita ta fi dadi.' Sannan kuma akwai sabbin masoya da ba su san littafina mai suna _HALIN YAU_ ba. Don haka ku hanzarta sayen wannan littafi don jin yadda aka haihu a ragaya!* *Bissalam! Sai na ji ku*. # Team Gudale. # Team Guduyo. # Surayya Dee. # One Love Ana Tare!🤝 2/8/23, 10:22 - Buhainat: *Wannan littafin na ku'di ne, biya 500 ku'din karatu ta wannan asusun* *2384876855* *Surayya Ibrahim* *Zenith Bank.* *A tura shaidar biya ta wannan lambar* *08032773332*. *SDK23&24* *Umma* Wata irin salama ta shige ta. Da murna sosai ta ce, "Ashe ya same ka da maganar yarinyar nan? Ni kuma har ina jan kunnensa kar ya zo da maganar gabanka, tunda ba lallai ka amince da ita ba". Ya numfasa ya ce, "Bai fa'da mini ba, amma na ji labarin 'yar wajen Alhaji Namakole yake so. Sai dai kuma kin sani ba zai yiwu ba, duk wanda yake unguwar nan ya sani, uban yarinyar ba shi da wanda yake 'ki iri na. Shi ne yake ya'dawa wai safarar miyagun kwayoyi nake yi, sannan ina kar'bar ku'din ruwa. Idan kuwa za a auna wannan maganganun a mizanin hankali ai kin ga ba zai so mu ha'da jini ba". Dake ita ma Umma ba son lamarin Nusaiba take yi ba, tafi son sa da Fauziya 'yar aminiyarta wanda hamsha'kan attajirai ne na garari, tun shekarun baya Allah ya yi wa mai gidan rasuwa, ke nan matar ce take sarrafa komai da tallafin manyan yaranta maza. Kawai don tana girmama ra'ayin Gudalenta sama da nata ra'ayin, shi yasa ba ta matsa masa sai ya auro Fauziya ba. A hankali ta ce "Haka ne, amma wace ce yarinyar? Domin akwai yar wajen marigayi Anbasada Jalo Jimeta. Da take son sa, na ga kuma za ta dace da ra'ayinsa da ya lissafa". A gajarce ya ce, "Madalla! Sai dai ni kuma ba ta dace da ra'ayina da tsarina ba. Sai ya ya ke nan?" Da sauri ta ce, "sai a bar shi, domin ta kula 'kankancinsa a kusa yake yanzun nan zai yarfata. *Shin kina bibiyar Faseelat kuwa?*. *Shin kina gyara kanki kuwa?* *Faseelat ta kware wajen zaba miki supplement din da zai dace da jikin ki* *Hakan ya sanya ta samu lambar yabo daga G.H.T*. *Tuntu'beta 0703929802* *Gudale dai ya ce zaki rabauta a sanadinta*😁 *SADIK* Da daddare Sadik ya je wajen Abba a dalilin tunda ya dawo da rana yake ta barcin gajiya. Bayan sun tattauna akan lamarin tafiyar da ya yi zuwa Nijer, sai kuma suka koma kan maganar ginin da ya dawo ya tarar ana daf da kammalawa. "Ai Abba ginin nan ya yi kyau duk da dai ban samu na shiga ba, amma ko daga nesa aka hango an san ya ginu, sannan wanda ya tsara ya cika fasihin magini. Murmushin jin da'di Abba ya yi tare da cewa, "Sai ka shiga ka gani za ka gaskata kwararren masanin abin ne ya yi aikin, sosai tsarin zai burge ka." Gudale ya yi mamakin yadda Abba ya sauko yake yi masa magana cikin sakin fuska, tun akan aikin da ya samo masa ya 'ki yi shike nan ya ninka watsi da lamarinsa. Amma abin mamaki yau har da dariya yake yi masa duk da ba tuba ya yi ba. A ran Sadik sai yake ganin ko don ya yi kwanaki baya nan ne. Hira sosai suka yi cikin nutsuwa. Tamkar ba Gudale da Abba ba. Ba su ankara ba har goman dare sannan suka yi sallama. Washegari sassafe Sadik ya nufi makaranta saboda kowanne 'dalibi zai gabatar da binciken da ya yi a Jamhuriyar Nijer. *Guduyo* A makaranta ina ganin sa da zai tafi gida, ya dauke kai ya wuce tamkar bai san ni ba. Don haka ni ma na yi 'karfin hali ban yi masa magana ba. Ina kallon sa ya shiga motarsa ya yi tafiyarsa ya bar ni, hakan ya tabbatar mini da gaske ya zafafa lamarin. Ban ji dadin hakan da ya yi mini ba duk da sai karfe shida zan kammala. A lokacin kuma sallar Azahar aka idar. Sukuku na karasa daukar darusan a dalilin fishin Gudale ya dame ni. Na iso harabar gidan na tarar da motar Yaya Sadik bayanta a burme sosai tabbacin wani ne ya buga masa ita. Na wuce ina fatan Allah ya sa iyakacin asarar ke nan, ba ta shafi lafiyarsa ba. Na shiga na tarar da shi tare da Yaya Al'amin a wajen Mama yana fa'da mata ikon Ubangiji ne ya sanya motar da ta debo bulo masu yawa ba ta ramutse shi ba. A ki'dime na ce, "Allah mun gode maka! Sannu Yaya Gudale' Ubangiji ya tsare ya mayar da alheri". Ya waske ya ki tanka mini. Na zauna ina ta jan maganar da nufin na samu ya kula ni. Mama ta ce " Haba Yaya Sadik ya kuma haka, yar 'kanwarka tana ta yi maka sannu amma ka 'ki amsawa?" Kai-tsaye ya ce, "Ai ba zan amsa mata ba Mama! Kuma ba 'kanwata ba ce na riga na yafe wa Sakina ita tuntuni su je su 'karaci 'kulle'kullen munafuncinsu da sunan zumunci ". Yaya Al'amin ya ce, "Wai kai sai yaushe za ka zama mutum sak? Ina ce 'dazun Ubangiji ya nuna maka 'kamshin mutuwa?" Cike da takaici Ya ce, "ba zan zama mutum ba sai ka daina shiga abin da bai shafe ka ba Al'amin". Mama ta mi'ke tana cewa "Ubangiji dai ya nuna mini kun girma, girman da babu shiririta". Yaya Al'amin ya ce, "Wannan addu'a tsakani da Allah da Sadik ta dace domin ni dai mutum ne sak Mama". A hassale ya dubi Al'amin ya ce, "Ni kuma a jinsin dabbobi nake ko kuwa jinsin Jinnu? Ka daina cin mutuncina". Cikin rashin damuwa Yaya Al'amin ya ce, "Na yi din Sadik da'din abin ma ba zan doku a hannunka ba". Da azama ya shiga kwadawa Mama Kira yana cewa "Mama zo ki ji abin da Aminu yake mini, gaskiya na gaji, tsakani da Allah sun takura mini shi da Sakina! Ki ja masa kunne, ya daina zalunta ta ta hanyar yi mini kutse akan abin da bai shafe shi ba". Da taushin murya Mama ta ce, "Rabu da shi ka ji tunda ya zama babban kwabo, yi ha'kuri ka yafe masa, dauki girman kawai Abubakar Sadik". Nan da nan kuwa fishin ya koma don na lura Yaya Sadik yana ba'kin cikin fikon da Yaya Al'amin ya yi masa. Abin da yake ba ni mamaki kuma shine Yaya Al'amin din ya fishi girman jiki bare a ce ko don ya fi shi girma ne. Tsawon lokaci suna zaune a falon kafin Yaya Al'amin ya ce, "Tokara ka tashi". Ya yi kamar bai ji shi ba. Sai da ya maimaita sannan ya ce "Atafau ba zai iya tafiya ba 'kafarsa da bayansa sun yi masa nauyi ainun sai lokacin na lura ashe 'kafarsa na'de take da bandeji irin wanda masu 'dori suke yi. Ashe wai targa'de ya yi a kafar ya kuma bugu a bayansa. Amma abin ya zo da sauki kwarai da gaske. Al'amin ya ce "Ai kuwa sai dai na dauko baro na saka a ciki, don na gaji da kinkimarka alhalin ban huta da rashin kunyar ka ba". Ba zato muka ji ya ware murya tamkar yaro karami yana cewa "Baba! Baba!" A gigice Baban ya fito sanye da jallabiya Yana tambayar jikin ne, ko dai asibiti za a koma? A shagwabe ya ce, "Cetona za ka yi a hannun Aminu cewa ya yi wai idan muka je dakinmu sai ya murtsuka ni tunda dai yau sai yadda ya yi da ni. Don haka ba inda za ni a nan zan kwanta, ko kuma ka taimaka ka kai ni wajen Umma tunda ya ce sai dai ya saka ni a baron kwasar shara" Ya gama maganar yana murtsuka idanuwansa a zuwan kuka yake yi. A take Baba ya rufe Yaya Al'amin da fa'da yana fa'din "Dan-uwanka ya ha'du da tsautsayi ba za ka tausaya masa ka taimake shi ba? Ban da ma da kwanansa a gaba ina ce da yanzu ba ka san irin ki'dimar da zaka shiga ba a dalilin rashinsa". Daga ni har Yaya Al'amin mun zuba wa Gudale ido tare da ta'ajjibin irin lauya zancen da ya yi tamkar a wasan kwaikwaiyo. Baba kuma ya hau kai ya zauna yana ta faman yiwa Yaya Al'amin sababi. Ni ban ta'ba ganin wanda yake fatan a dauke shi idan ba shi da lafiya ba irin Yaya Gudale. Kallon sa na yi na kalli 'kafar na gano ba ciwon gaske ya ji ba, 'yar buguwa ce sai kuma kujewa da 'kafar ta yi. Amma ya shagwargwabe ya lanjare saboda ya sani shi din 'dan gata ne ta ko ina. Duk gidan ba wanda yake gwada iyashegensa. Haka Yaya Al'amin ya ciccibe shi suka tafi. Zuwa dare dukkan ahalin 'yan 'dakinsu sun bayyana in ka dauke Antin Zaria da bata 'kasar. A bakin Sakina na ji cewar Umma ce ta 'kirasu cikin gigita ta sanar musu cewa Gudale ya hadu da tsautsayi. Sun cika masa falon da kayayyakin dubiya tamkar masu gasa a tsakaninsu. A wannan lokacin ba 'karamin wahalar da Yaya Al'amin ya yi ba, domin kuwa hatta alwallah sai ya yi masa wai ba zai iya ba. Bana mantawa da wannan jinyar tasa. Saboda na sha ganinsa yana tsalle idan ba kowa a tare da shi tabbacin bandejin karya ya na'de kafar da shi. Ya fake da ciwo yana zuba shagwaba son ransa, yana kuma ganawa Yaya Al'amin da Yaya Abbas azaba ta hanyar yi masa hidima. Tsawon sati yana jinyar iskanci, sannan ya ware bayan Abbas ya ci masa mutunci ta hanyar rantsuwar ba zai sake yi masa komai ba ko zai shi'de. Hakan ya yi matu'kar batawa Yaya Sadik rai, domin ya tsani a daga masa murya. Washegari kuwa sai ganinsa aka yi ya wartsake yana yin al'amuransa da kansa. A kuma ranar suka je tare da Abba da kuma Sakina sabon gidan da ake ginawa *Sakina* A dalilin Sakina na samau labarin irin kuranta ginin da Gudale ya yi. Tsarin ginin ya yi matu'kar burge shi, 'katon falo ne mai dauke da dakuna uku , kowanne da ban'dakinsa, biyu a jere daya kuma a can gefe. Kafar a benen maa falon take. Daga gefe kuma ga dinin area da kicin hadi da store. Sannan za'a iya shigowa ta cikin kicin din. Akwai kofar baya Wanda zaka fita waje sannan anan dinma akwai kafar bene, ma'ana zaka iya hawa saman ba tare da ka shiga falon ba. Saman kuwa dauke yake da falo da manyan dakuna biyu da kuma kicin. Tsarin ya tsaru sosai, sannan ya kawatu da mables da kuma wall papers hakanan fitilu da fentin dukkansu masu koluluwar tsada ne. Farin-cikin da Yaya Sadik ya nuna akan gidan ya sake karfafa wa mahaifinsa guiwar gabatar masa da kudirinsa. Sakina tana gefe sai ta ji Gudale na fa'din "Ai kuwa Abba wanann gidan ya fi da cewa da 'Dan kwalisa kamar ni". A hankali Abban ya ce "Wacce kwalisar kuma Sadik? bayan ba ka shirya nema na kanka ba, sai dai ka na'de kafar wando ka yi ya'ki da duk wanda ka ce kana bukatar abu bai yi maka ba. Alhalin guntun gatarinka yafi sari ka bani". "Ya marairaice ya ce "Abba! Ka sani duk mai suna Abubakar ba rago bane, ba mai kwange bane, sannan ba gajiyayye ba ne. Daure ka cigaba da yi mini Addu'a da sannu za ka yi alfahari da ni". Abba ya dara ya ce "Allah ya nuna mini wannan ranar, domin ina fatan! ka kwantata yi mini irin biyayyar da su Abdallah suke yi mini, Ni na za'ba masa matar aure ya karba babu nusu, kawo yau din nan da suka haifi yara biyu ba'a ta'ba jin kansu ba. Haka ma 'kaninsa Babangida. Madallah da Babanku Ibrahim da iyalinsa. Har yau din nan bai ta'ba mini kallon wa nake a wajensa ba, yana mini kallon uba ne mai cikakken iko akansa da dukkan Ahalinsa. Sakina ta ce mini dukkansu jikinsu ya yi sanyi da lafazin Abba, mussaman Gudale da yake jin tamkar *Dabaibayi*(Marigayayiyya Halima Amma Rip). Ko shagube Abba ya yi masa. Sun fito harabar gidan suka ga fulawowiyin da za'a dasa lodi guda a gefe, nan gaba ka'dan idan aka dasa su zasu sake 'kawata gidan. A fili Gudale ya ce, "Abba idan ka tashi yi mini gini irin wannan tsarin nake so Dan Allah. Sannan yadda wannan yake a tsakiyar filin haka nake bu'katar nawa saboda ka sani bana shiri da zafi, wannan kuwa za'a samu yalwatacciyar (ventilation) iska. Cikin rarrashi Abban ya ce, "Ai ni ba zan yi maka gini ba, ko su Abdallah da na yi musu, ai sai da na tabbatar suna fita suna nema, sannan na yi iko da su, suka nuna mini na isa. Shin Basu cancanci na yi musu komai ba?" "A sanyaye ya ce "Ni ma ina kammala karatun zan fara neman na kaina, sannan komai ka ce na yi , ko bana so zan yi dan kuwa ni nafi cacnanta na yi maka cikakkiyar biyayya." Da'din kalaman suka sanya Abba cikin ki'dima ya ce "Na shaida Ubangijina ba zai juyar da addu'ar da nake yi maka ba. Alhamdulillah! Ubangiji ya sake shirya mini kai. Saboda yadda ka kyautata harshenka ina tabbatar maka na mallaka maka wannan gidan." Sakina sai ganin Gudale ta yi akan guiwoyoyinsa yana faman godiya da fatan alheri ga mahaifin nasu. Dadi ya sake kama Abba ya ce, " Tashi abinka, idan Àllah ya kai mu gobe bayan na karya ka zo zan sake ba ka wata kyautar da tafi wannan gidan daraja da kima. Tunda yanzu ka san godiya, na tabbatar za ka yi farinciki fiye da wanda kake ciki a yanzu, na sani za ka yi mini godiya sosai". *Kina son canjin kayan daki, ko kina son renting din kayan amare?* *Kina son zababbun atamfofi ko leshina?*kina son kayan a *Kina son mallakar filin da Babu takaddama akansa?* *Ki tuntu'bi AMYAS NEW & FAIRLY ITEMS* *Komai kike so zaki samu* *Ina sake tunasar da ku suna sayan kaya Kamar yadda suke sayarwa* *08083909947* *Dare* *Abba* Bayan ya kammala shan shayi, suna falon suna kallon labaran karfe 9. Ya kalli Mai dakinsa ya ce, "Zan fa'da miki in sha Allah watan jibi da kwana biyu auren Sadik da Halimatu". A farko ba ta fahimci lamarin ba, sai ta dauka kawai had'awa za a yi a rana guda. Don Haka sai ta ce "Wai a ina ka samo masa yarinyar ne?". Ba wata fargabar komai ya ce "Yata Halimatu dai ta gidan nan ita ce matar". A zabure ta tashi domin kwarai da gaske ta ki'dima. Tsawon lokaci tana kokawa da numfashinta da 'kyar ta iya cewa, "Ni kam kana gwada mini iyakata akan 'ya'yan da ni na haife su cikin matsananciyar wahala kan wahala, ta ya ya za ka yi wannan ha'din? Indai ba don ka yi nufin na dawwama cikin ba'kin ciki ba ne. Gaba'daya 'ya'yan Safiyya maza ne, shike nan kuma yanzu Gudalen da na samu da 'kyar bayan shafe lokaci mai yawa ina addu'ar samunsa sai a sake bawa Safiyya dama a kansa?". Ta fashe da kuka tana fa'din dama mutuwa ta zo mata kafin ta ga wannan mugun lamarin. Ran maigidan nata idan ya kai dubu to kuwa ya baci. Da kakkausar harshe ya ce "Saudatu! Na riga da na yanke hukunci kuma Wallahi ba canji. Ko mutuwa kika yi ba zan fasa ba, haka zalika ko ni na mutu ba za'a fasa ba, domin na barwa mutanen kirki su cika mini wannan burin. Abin da za ki gane daya ne, wallahi idan har Sadik ya turje mini akan wannan auren tabbas ke da shi za ku bar mini gida, sai ki tafi can ki aura masa 'diyar da ta fi 'diyar Ibrahim a wajenki. Gobe zan sanar masa, ki shirya! matu'kar ya bijire mini, Wallahi ba wanda zai sa na sake zama da ku, domin ba zai yiwu na dinga sarrafa 'dan uwana da dukkan Ahalinsa ba, amma kuma ban isa, a cikin nawa Ahalin ba". # Team Gudale. # Team Guduyo. # Surayya Dee. # Ana tare 🤝. 2/8/23, 10:22 - Buhainat: *Wannan littafin na ku'di ne, biya 500 ku'din karatu ta wannan asusun* *2384876855* *Surayya Ibrahim* *Zenith Bank.* *A tura shaidar biya ta wannan lambar* *08032773332*. *Fitar da labarin nan laifine da yake dai dai da satar dukiya* *Gudale dai ya ce bai zaci za'a yi masa hakan ba* *Kuma yana hankalce da masu yin 'kafar ungulu a gidan cin kaza*😠. *SDK25&26*. *Umma* Lafazinsa ya sanya kukanta tsayawa cak. 'kiyayyar Safiyya tana sake girma a zuciyarta, a take kiyayyar ta sake yin reshe tana sake shafar Halimatu. Ita da kanta ta shaida ashe a da ba 'kin Sadiya take yi ba, domin a wannan ranar da aka zartar da hukuncin aurenta da Gudale sai ta gane a ranar ta ji tana yiwa Safiya da 'diyarta Sadiya tsana fiye da komai a doron 'kasa. Dalili 'daya ne ya hana ba zata tafi ta bar masa gida ba. Safiya ce dalilin! Domin idan har ta tafi ya tabbata ita ta yi nasara akanta. Duk wani bala'in da zai sameta a gidan aurenta ba shakka ta dalilin Safiyya ne ko 'ya'yanta, wacce irin fitina ce wannan? A ranta ta gasgata Safiyya irin zuri'ar kara da kiyashi ce daukar marar sani. masu raba 'da da mahaifi, masu raba soyayya, kazalika masu rabaka da jama'a saboda tsananin kissa da bariki. Cikin fishi ta tashi ta yi 'dakinta cikin matsanancin kuka. Tana kuka tana tunanin shikenan duk tanadin gatan da ta yiwa matar Gudale ya bi iska kenan? Domin matu'kar Halimatun Safiyya ce matarsa, ta tabbatar ko murmushinta ba zata samu ba, bare aje ga samun soyayyar da take yiwa surukurta ta'kidinta. Tabbas an cuceta iyakar cuta. Sai dai kuma ta lashi takobin yadda Safiyya ta hanata kwanciyar hankali, ta hana ta sakat itama yanzu zata sake takura mata, zata sake zafafa gabar da take tsakaninsu haka zalika zata hanata kwanciyar hankali ta hanyar saka autarta cikin uku. Tunda bata da ikon tankwabar da auren, to kuwa zata hana kwanciyar hankali da walwala a cikin rayuwar auren, matu'kar uwa tana da tasiri akan 'danta. *Umm Muhd collections* *Komai da ruwanka ce fa* *Ku tuntu'be ta ta* *Abba da Gudale* Washagarin ranar kuwa da misalin sha'daya na safe Gudale ya isa cikin gidan nasu, yana cikin wasi-wasin irin 'kyautar da za'a bashi da zai yi murna fiye da murnar da ya yi da aka bashi tsalelen gida ba tare da ya yi zato ba. To ko wata tsadaddiyar mota Abba zai bashi saboda tun ranar da ya yi hatsarin da bayan motar ya burma bai sake hawanta ba. Ya sani ko Abba bai canja masa ba, to kuwa lah shakka Umma da yayyensa zasu saya masa wacce tafi tasa da ta samu lahani daraja. Ya tarar da Abba shi ka'dai yana shan shayin moringa (zogale). Gefe kuma yana kallon tashar Africa TV 3, inda Abban ne yake gabatar da shiri akan rabon gado da hukunce-hunkuncesa. Da walwala sosai ya dinga marabtarsa, har shi da kansa Sadik ya tabbatar akwai babban al'amarin da mahaifin nasa zai 'dora masa. Wannan soyayyar, wannan haba-habar akwai abin da zai biyo bayansu mai matu'kar nauyi. Kusa da 'kafafuwan Abban ya zauna sosai daga kasa. Kofin shayin ya mi'ka masa tare da cewa, "Bismilla" Cikin tarin 'kaunar da mahaifi yake yi wa 'ya'yansa. Da azama ya kar'ba yana jin ba zai iya tuna rabon da Abba ya ba shi abin da yake ci ba. Bisa al'adarsa matu'kar ya ba ka sauran abin da yake ci to ba shakka tamkar ya sanya maka albarkasa ne. Sau tari a gabansa Abba zai ba wa Abdallah ko Al'amin abin da yake ci ko sha amma shi ya hana shi. Abin na matu'kar ci masa tuwo a kwarya. Ya tuna amsar da Abba ya ba shi lokacin da ya masa korafin ba ya masa irin yadda yake yi wa su Al'amin. Kai-tsaye Abban ya ce, "Su din sun yarda sun bar ra'ayinsu sun bi nawa, sun yarda na isa da su, sun kuma amince na fi su tunani da hangen nesa akan al'amarin rayuwa. Shin ba su cancanci soyayya da albarkata a kowanne bigire ba?" A wancan lokacin shiru kawai ya yi amma bai fahimci manufar mahaifin nasa ba, ya fi yarda son sa ne ba ya yi kawai. Don haka ya daina damuwa bare ya yi abin da suke yi na biyayya da kyautatawa. A yau Abubakar Sadik sai ya tsinci kansa cikin nutsuwa mai yawa, irin nutsuwar da sai wanda ya yi sa'a ya kuma yi gam-da-katar din samun mahaifin da yake haba-haba da yaransa zai fahimta. Ko zafin shayin bai ji ba, nan da nan ya kurbe tare da ajiye kofin tangaran mai dauke da sunan kamfanin Abba wato *Moriki & Brothers*. Gudale ya dinga tunanin shin mutane nawa ne masu tsananin son 'yan-uwansa irin mahaifinsa, hatta dukiyarsa yana jinginata tare da yan'uwansa ne. Rahamar Allah ta tabbata ga 'yanuwa masu son zumunci da sadaukawa irin Abba. Ya nutsu sosai yana sauraron albishir din da za a yi masa. Gyaran murya ya yi sannan ya ce, "Sadik a tsarina ba na so na yi maka aure ba tare da kana tsaye da kafafuwanka ba, ma'ana sai kana da aikin yi ko sana'a. Ba don komai ba sai nauyin da zai hau kanka ba ka'dan ba ne. Sai dai kuma duk yadda na so ba haka Ubangiji ya tsara ba. Ban zaci nan da ba'di ma zan amince a nemo maka aure ba, saboda ban yarda da nutsuwarka ba. Don haka ba zai yiwu a dauki yar mutane a ba ka ragamar kulawa da tarbiyarta ba". Zuciyar Gudale ta harba da tsananin gaske, bai yi zaton aure za a yi masa ba, shi yasa a canke-cankensa bai hakaito aure ba. Ya sake yin kasa da kansa yana jin faduwar gaba na sake tsananta a gare shi, shin wace ce yarinyar da aka zabo masa? 'Yar wane attajiri ne? Sannan ta yi daidai da taste dinsa? Yana cikin wannan yanayin ya ji Abba ya zarce da cewa, "Amma daga jiya na 'dan sami 'kwarin guiwar ba ka aure, da ma kuma na yi imanin lamuranka ba za su tabarbare gaba'daya ba. Tunda ka yi sa'a ka daina wasa da Sallah, tsawon shekaru biyar ke nan na gaskata ka akan salla komai tsananin yanayin sanyi ko na damina ba sa hanaka yin salla a jam'i musamman sallar Asuba. Annabi ya ce, "Salla tana daidaita sha'anin mumini, tana kange shi da aikata munana ayyuka da dabi'u. Gafarar Allah ta tabbata ga muminai masu jingine ababen shagala, da zarar sun ji liman ya ce, "Haiya alal Salah". Daga nan kuma sai Abban ya numfasa ya ce, "Ka saurare ni da kyau, ka kuma nutsu. A baya ka ce mini ka ba ni damar na samo maka mata kamar yadda na yi wa 'yan uwanka ko?" Kai kawai Gudale ya 'daga masa, saboda yadda yake cikin ki'dima da sanyin jiki. "Madalla!" Abba ya furta sannan ya zarce da cewa, "To idan Ubangiji ya kai mu 2 ga watan goma na wannan shekarar, nan da watanni biyu masu zuwa za ka zama ango. Zan sake yi maka albishir da cewa kwabonka ba zai yi ciwon kai ba. Komai ni zan yi maka har kudin kunshi da na kawayen amarya, fatana dai ka ri'ke mini ita da kyau. Idan ka yi mini hakan ni kuwa ba zan gaza wajen yi muku komai ba. Da kanka za ka gane ba abin da nake so tamkar kai da iyalinka". Murmushin jin da'di ya 'kwacewa Gudale. Hakan ya sake faranta ran Abba. Don haka ya yi 'kundubalar cewa, "Halimatus-Sa'adiya na za'ba maka ta zame maka mata kuma uwar ya'yanka. Na san za ta yi daidai da tsarin daka lissafa mini". Sosai kan Gudale ya daure ya kasa fahimtar wace ce Halimatu da aka ba shi ya aura. Rashin fahimtar da Abba ya gani a tare da Sadik din sai ya hutar da shi tsananta tunani ya ce, "Ina nufin 'yar uwarka *Guddi*." Wata irin dariya ta kama Gudale, ya dinga tintsirawa ba kakkautawa. Ba komai ya sa shi dariyar ba irin yadda Abba ya ce, *Guddi!* Ko mene ne abin wahalar fada a *Guduyo* tamkar mutum zai ce gudu sai kawai ya 'kara da yo shike nan fa. Can kuma ya nutsu ya ce, "A gafarce ni Abba! Yadda kake son fa'din sunan ne ya sanya ni dariya. Amma saboda Allah Abba ta ina Guduyo ta dace da wacce na siffanta maka?" Cikin rarrashi Abba ya ce, "Halima fara ce, doguwa, sannan tana da gashi". "E amma ba ta kammala karatunta ba, sannan ba 'yar attajiri ba ce". Abba ya nuna kansa ya ce, "Ka raina arzikina ke nan? Don kuwa ai ni ne ubanta ba wani ba." Ya fa'da a tunzure ka'dan. Ganin hakan ya sanya Gudale diriricewa yana cewa, "Amma dai a gaban Umma sai da na ce maka 'yar shawalwala nake so ba wai bunkusa ba. Sannan gaskiya ni ba ita ba ce zabin raina ba". "Ita ce zabin Allah a gunka, ka sanya hannu biyu ka karba, ban yi zaton za ka iya kunyata ni ba, su Abdallah ko tari ba su yi ba, suka karbi zabin da na yi musu cikin farinciki da godiya mai yawa. Shike nan tashi ka tafi zan musanya mata kai da Abbas ko Ashir tunda ita na isa da ita na sani ba za ta yi mini musu ba. Bare su kuma da nake da tabbacin ko wuta na ce su fa'da ba za su kunyata ni ba, za su na'de kafar wando ne kawai su fa'da. Ba abin da zan cewa 'ya'yan yan uwana sai fatan alheri. Tabbas ko ban haihu ba, na sani ba za su bar ni na koka ba, tunda suna yi mini biyayya fiye da ta 'dan da na haifa". Kuka kawai Gudale ya saka masa tamkar sanda yake yaro 'dan karami, sannan ya 'dora kansa a kan kafafuwan mahaifin nasa Sosai Abba yake nazarinsa yana kuma jin soyayyar 'dan nasa tana nema ta kasa sarrafuwa a lokacin. Tsawon mintuna sannan ya fahimci kukan shagwaba da iyashege kawai ya sanya shi a gaba yana yi masa, domin bai ji dumi a cikin hawayen nasa da yake diga a kan kafarsa ba, hakan ya sanya ya gane ba kukan ba'kin ciki yake yi ba. A tausashe ya ce, "Na ce ka tashi ka tafi tunda ba ka amince da hukuncina ba, shi ne za ka sanya mini kuka? Ban yi fishi ba ai, tunda Ashir yana nan, na tabbatar shi zai karba babu hamayya, kai kuma ka je ka nemo zabinka, damarka ce ba zan hana ka ba". Sai a lokacin Sadik ya 'dago kyakkawar fuskarsa hawaye yana tsere, shi da kansa bai san dalilin zubarsu ba amma ya yi amannar ba na bakin ciki bane, ba kuma na farinciki ba ne. A sanyaye ya ce, "Abba na ce maka ba zan karba ba ne da kake ta faman jingina wa Ashir matar da kake 'kirarin ka ba ni? Ka sani kuma babu jituwa a tsakanina da shi, tunda ya fahimci kana daukaka lamarinsu, shike nan sai yake neman wuce gona da iri, sau nawa Baba yana mana shari'a da Ashir? Duk lokacin da wani abu ya hada mu baya jin nauyin ya daga hannu ya zabga mini mari! Bayan da watanni kawai ya girme mini. Ko Al'amin da Abbas da muke gida daya ba sa yi mini wannan wulakancin, amma shi saboda gadarar Yayar 'Kwalli sai ya dinga tozarta ni alhalin na fishi karfi a gidan nan tunda shi 'dan mace ne." Kafin Abba ya yi magana Sadik ya sake zarcewa da fa'din, "Ka daina nuna mini sun fi ni a wajenka, ina jin haushin hakan, ka daina jingina wa Ashir Guduyo! Sosai abin ya yi mini ciwo a zuciyata, domin ba ta dace da mai mugun hali irinsa ba. Sannan har zuciyata na sake jin ba na son sa, ai na sani son ta yake yi, to ko don na tabbatar na yi masa kwalelenta, ba zan tankwabar da umarninka ba, mugu kawai, masu zuwa cin arziki amma sun zame wa halastattun 'yan gida 'karfen 'kafa". A nutse Abba ya ce, "Wato dai ba da kyakkawar manufa ka karbi auren ba, saboda kawai akwai yartsama a tsakaninka da Ashiru ne dalilin karbar?" Da sauri ya amsa da cewa "Saboda kai na karba Abba! Don ka ji a ranka ni ma ka isa da ni, ina fatan duk lokacin da na kawo zabina ni ma za a yi mini adalci albarkacin biyayyar da na yi, idan kuma ita ce ka'dai aka 'kaddara mini, shike nan". Sosai kalaman suka faranta ran mahaifin nasa, ya dinga sanya masa albarka, da nema masa tsari daga dukkan abin 'ki. Domin bai zaci zai amince cikin sau'ki ba, musamman da ya san halin 'dan nasa na gardama tamkar mutanen farko. Ya numfasa ya ce, "Na gode maka sosai Gudalena". Karon farko da ya ji mahaifinsa ya kira shi da wannan sunan, sannan har ya kara da fadin nasa. Da mamaki ya daga ido yana kallonsa. Murmushi Abban ya yi ya ce, "To ko ba nawan ba ne na Umma ne kawai?" Farincikin da Gudale ya tsinci kansa a ciki ba zai misaltu ba, har ya dinga jin anya ya taba shiga yanayin da ya saukar masa da farinciki bayan yana cikin rudani sosai. "A fili Abba ya ce, "Ba mahalu'kin da zai haifi 'da ya ce ba ya son sa sai dai ya guji halinsa, ko da kake ganin na fi son su Abdallah akanka ai ba hakan ba ne. Ubangiji da kansa bai daidaita 'dan cikinka da 'dan Dan-uwanka ba. Saboda yadda ya yi kasafin rabon gado da kansa, ta yadda ya nuna karfin jini. Sai dai kuma ayoyi daban-daban da hadisai masu yawa da suka yi ta nuna mana girman zumunci da kyautata shi, Ubangiji ya wajabta mana yin ibada, aure da kuma inganta zumunci. Amma muna cikin wani irin zamani da mutum bai san kowa ba sai 'ya'yansa, kadan ne suke daidaita 'ya'yansu da na yan'uwansu a fuskar mua'amala. An sani ba zai yiwu su zama 'daya ba amma ka ba su 'kofa da fuskar da za su ji a ransu cewar kaima Babansu ne, za su iya tunkararka da dukkan matsalolinsu, za su yi dariya a gabanka a yayin da suke cikin farinciki, haka nan za su yi kuka akan kafadarka a lokacin da suke cikin firgici ko 'bacin rai. Idan kuma Ubangiji ya azurtaka sama da su ka ji a ranka cewar ba iya kai da 'ya'yanka ne za ku ribaci wannan dukiyar ba, domin su ma suna da hakkin zumunci a cikinta. Allah Ya kan dauki mutum a cikin zuri'a ya bun'kasa arzikinsa da manufar ya zama bango a cikin wannan Ahalin. Mutane ka'dan sun fahimci manufar Ubangiji akan arziki da damar da ya basu ta rayuwa, sai su yi ta aikata alheri da kuma kyautata zumunci, yayin da wasu da yawa suke halaka ta hanyar daukan ra'ayin ri'kau na kowa ya tashi ya nema da kansa bayan kuma dole sai wani ya daga wani, kafin a kai ga gaci". Jikin Sadik ya yi sanyi ya 'dan fahimci mahaifin nasa ka'dan! Ya kuma rage jin haushin damar da ya bawa zumunci. Da Abba ya lura irin wa'dannan maganganun suna tasiri a zuciyar Sadik, fiye da fa'da, sai ya 'kudire zai dinga yi masa matashiyar su akai akai, har Ubangiji ya bude masa zuciyarsa ya fahimci rayuwa dai-dai ba yadda ya fahimceta a yanzu ba. Dan hakan sai ya datse wancan hanunka mai sanda da yake yi masa, ya dawo kan batun da yasan zai sanya shi farin-ciki. Da tarin soyayya ya ce "Ya ya labarin motarka kuwa? Baka ce mini komai ba tunda aka kaita wajen gyara". Kai-tsaye Gudale ya ce "Nifa bana sonta Abba dan haka ma ko tuntubar bakaniken ban sake yi ba". Cikin hikima ya ce "Ai Shikenan mai sunan Baban Nana Aisha(R.A.)! Ka yi nazarin wacce kake so, sai na yi maka oder, Ina fatan ta iso kafin lokacin bikinku. Waccar 'dinma ai bata fi wattanni biyar da saya maka ba, za'a gyarata sosai sai a barwa Halimatu saboda zuwa makaranta. Tunda kana daf da kammalawa, sannan aiki zaka fara ba da jimawa ba, baka da lokacin kaita da daukota, kuma ba zai yiwu iyalinka ta dinga jaurar hawan adaidaita ba tunda Ubangiji ya bada yadda za'ayi". Kan Gudale ya fasu saboda yadda Abba yake lalla'ba shi. Kafin ya yi magana ya ji murya Abba ya sake cewa "Ka nutsu sosai ka fa'da mini dukkan abin da kake so, komai yi maka zan yi dan ka gane ba ni da wanda ya kai ka balle ya fika. Abin da nake so da kai yanzu, ka 'dan fara samar da fahimta a tsakaninka da Halimatu duk da na sani kai da ita tsakaninku sai Allah! Amma zan so ka canja alakar shiriritar da take tsakaninku zuwa kyakkawar manufa mai cike da soyayya da mutuntawa". Gudale ya saki ajiyar zuciya mai nauyi ya ce "gaskiya ni Abba raina ni zata yi, bata da kunya, kawai ka fa'da mata da kanka, amma ka ja mata kunne ni wlh inta ce zata raina ni, ko yi mini yanga bubbugeta zan yi, sannan na ganar da ita rigarka kawai ta shiga". "Tunda ta shiga rigata, na gode maka, na sani kuma watarana zaka gode mini, ka kuma yi mini Addu'a akan zabin da na yi maka. Tashi ka je, Ubangiji ya yi maka alabarka". AMYAS NEW & FAIRLY ITEMS* *Masu bukatar siyan fili ko gida* *Masu bukatar gidan haya* *Masu bukatar siyar da kayansu Dan su yi canji duk ku tuntu'be su* *Sun shahara Akan kasuwancinsu saboda sauki da kuma kyakkawar alaka tsakaninsu da customers* *08083909947*. Ya mi'ke yana cewa "Na yi godiya sosai! Godiyar mota nake yi fa, zan je na duba wacce zata fi dacewa". Ya fice Uban yana binsa da addu'ar shiriya, yana fatan wataran ya zo ya tsugunna ya yi masa godiyar bashi Halimatu da ya yi. # Team Gudale. # Team Guduyo. # Surayya Dee. # Ana tare 🤝. 2/8/23, 10:22 - Buhainat: *Wannan littafin na ku'di ne, biya 500 ku'din karatu ta wannan asusun* *2384876855* *Surayya Ibrahim* *Zenith Bank.* *A tura shaidar biya ta wannan lambar* *08032773332*. *SDK27&28.* Barci sosai na sha tunda na idar da sallah na koma a dalilin bani da darasi sai karfe biyu. A makare na tashi na lalubo wayata na kalli agogo, da azama na tashi na shiga bayi na yi brush a gaggauce, hijabi kawai na zura, na doshi falon Abba, saboda nasan yana dab da komawa cikin dakinsa dan haramar fita tunda sha'daya ta wuce. A 'dan dogon coridon da ya raba falon Umma da na Abban muka yi kicibus da Yaya Sadik, ya fito daga falon. A fusace ya wuce ni, na 'dan daga murya na ce "Ina kwana?". Bai amsa ba. Da yake hankalina ya yi gaba sai ban sake maimatawa ba. Ina shiga falon, na tarar da Abba ya mi'ke yana shirin shigewa daki. Ganina ya sanya ya koma ya zauna. Ya amsa gaisuwata cike da kulawa kamar kullum, sai dai walwalar da na gani a tare da shi, ta sha banban mussaman da na ga Gudale daga wajensa ya fita. Sau tari indai ka shiga wajen Abba bayan fitar Gudale ba zaka samu walwala a tare da shi sosai ba, dan haka sai na dinga mamakin wannan annushuwar da yake ta faman yi mussaman yau da har ha'koronsa nake gani saboda murmushin da yake yi mai yawa ne. Na taya shi murmusawa amma kuma mamaki nake yi sosai. Da farin-ciki ya ce "Kinga Sadik yanzu?" Na 'daga kai tare da cewa "mun ha'du da shi zai fita, Ni kuma na shigo". Ya ce "Madallah! Maganar ki ya gama yi mini. Ba kunya, ba komai, ya ce mini na bashi ke ya aura, har na dinga mamakin da ban fahimci kun shirya kanku ba tuntuni". Na yi 'kasa da kaina, karon farko a rayuwata da na ji Abbah ya yi maganar da ban gasgata ba, domin na yi imani Gudale ba zai ce masa yana sona ba, tunda bai ta'ba furta mini ba, bai kuma fa'dawa Sakina da Yaya Al'amin ba. Kafin na ce "wani Abu sai jin muryarsa na yi yana cigaba da cewa "Na fa'da masa ya nemi amincewar ki, amma ya ce Na taimake shi na fa'da miki da kaina, domin idan a bakinsa ne zaki mayar da al'amarin wasa, bayan haka yana jin tsoron kada ki 'ki amincewa ki kuma raina shi". Take na sake yarda da zatona, wannan Shirin Abba ne dan kawai ya tabbatar da waccar maganar da na fa'da na ce dama ya za'ba mini Yaya Sadik. A hankali na ce "Abba ba ya sona gaskiya, da wasa yake yi". Ya zuba mini ido na tsawon lokaci kafin ya ce "Ashe auren ne ba kya so, shiyasa kowa ya zo sai kin bada uzziri. Ina ce anan kika ce ba kya son Abbas da Ashir? Gara Sadik da su, yanzu kuma Sadik din ya zo sai ki ce wani abu daban shin menene damuwar ki ne, fa'da mini matsalar ki Halimatu". Murya ba amo na ce bana son ka 'dora farin-cikina akan nasa ne, na sani Abba dukkan mu 'daya ne a wajenka. Amma ba zan so a yi masa dole ba". Ya nisa ya ce "Ba wani dole da zan yi masa, ya amince, kema kuma kin ce kin ji kin gani magana ta 'kare." Kai-tsaye na sake cewa "eh da gaske gara shi akan su Yaya Abbas". Na sani mamakina ne ya sake kama Abba dan haka sai ya buge da yin wani irin murmushi tare da cewa "je ki, zamu zauna da sauran iyayenku ina fatan nan da lokaci ka'dan ayi komai a kammala". Na fito, na shiga dakin Umma dan na gaisheta saboda ina son na tafi shahshinmu, domin na sake na yi murna son raina. Wai ni ce nake shirin zama Mrs Gudale sai nake ganin abin tamkar almara. Da sallamah na shiga cikin dakin na tarar da Gudale kinshige'de a bakin gadon Ummah. Yana ta danne danne a rantsatsiyar wayarsa, amma ko amsa sallamata bai yi ba. Na dan yi jim! Ina son na tambaye shi Umma Ina jin tsoron wulakancinsa. Na daure na ce Yaya Gudale! Ina kwana, ina Umma?" Ya ajiye wayar a gefensa ya tashi ya zauna sannan ya mini wani irin lalataccen kallo ya ce "Tana cikina! Daga yau idan na kuma jin kin ce mini Gudale sai na yi 'kasa kasa da ke, 'koshasshiya kawai". Kafin na ce komai Umma ta fito daga bayi da alamun alwallah ta yi dan yin walaha. Ganinmu tare ya sanya ta sake 'daure fuska tamkar an fa'da mata mugun abu. Na risina na gaisheta ta amsa a gajarce, tana shimfida abin sallah ta tayar ba tare da ta kalle ni ba. Jikina ya yi sanyi saboda wula'kancin da ta yi mini yafi na kullum. Na fita ina jin wani iri a raina, amma murnar da nake ciki sai ta sanya ban damu ba, bare na gane irin tasirin da Umma zata yi a gidan aurenna. *Kina fama da ulcer?* *Kina fama da bushewar ni'ima?* *Kina son fatarki ta yi kalar butter*? *Kinsan Sa'adan Mk bata amfani da kowanne irin supplement sai na manyan Mata kuma ingantacce* *Ki tuntu'bi Faseelat a lambar domin kuwa Iyah Basiru ta tabbatar kayanta amintattu ne, Shiyasa *G.H.T* suka karramata*. *07039269802*. *Dakin Umma*. Sai da ta idar sannan ta kalle shi ta ce "Menene kake ta faman huci tamkar marar lafiya". Cikin karaya ya ce "Abba ne! Ummah Abba ya kassara ni, wai aure zai yi mini, sannan ya rasa wacce zai bani sai wannan kumburar yarinyar dan kawai yana son sai na dauwama cikin firgici". Hawaye ya 'balle masa. Yayin da Umma ta fashe da kuka mai sauti. Sosai take kukan tunda ga 'kasan zuciyarta, ta jima tana yi, hakan ya sake kassara Gudalenta, nasa hawayen da yake yi ya tsaya cak. Ya rarrfo ya isa gareta, ya ru'ko hannuta ya dinga rarrashinta cikin tarin soyayyar da babu algus. Ta kalle shi ta zuba masa ido ta ce "Na jima ina yiwa matarka tanadin soyayya marar iyaka, na jima ina dakacen zuwan matarka domin ba zan yi surukunci da ita ba, zan mayar da ita tamkar su Ramla ne. Ashe ashe ba zanga hakan ba, Ashe wacce ba'kin cikinta zai dangana ni da kushewata zaka aura, Ashe dai da gaske Safiyya na haifarwa kai?" Ta 'karisa cikin kuka har da 'kwarewa. Shi kansa ba ya son auren, amma bai ji tashin hankali kamar wanda ya kula Umma na ciki ba, 'kasan ransa sai hasaso 'kirjin Guduyo yake yi, ya jima yana fatan ya samu damar da zai gansu a zahiri. Amma bai ta'ba hararo ta zamo matarsa ba, duk kuwa da yana damuwa da lamarinta, ya tsani ya laluba gidan bai ganta ba, ko da kuwa ba zasu yi maganar arziki ba. Da kansa yake tambayar kansa menene manufar hakan? Menene dalilin da yake Jin fargaba idan ya tuna zata yi aure? A hankali ya ce "Kin ta'ba ganin an 'kwacewa uwa 'danta Umma?" Da sauri ta ce "Na sha gani yafi sau dubu". Ya sake ri'ke hannunta sosai ya ce "In sha Allah! Ban da ni Ummah! kuma yanzu zuba ido zaki yi a kwace miki ni?" Cikin kuka ta ce "Ina ce Abbanku ma an kwace mini shi bare kuma kai da komai naka zai koma karkashin kulawarsu, ai ni kuma tawa ta 'kare. Sai dai na yi fatan Ubangiji ya baka ikon yi mini addu'a bayan na kwanta dama. Amma batun zan ji da'dinka ai na cire rai. Tunda ka ha'da kai da Ubanku zaka auri irin jaraba, irin raba zumunci, irin ja'iran bayi masu kwana a tafe, duk sammakon mutum sai dai ya tarar da haular su Safiyya sun riga shi". Duk ru'danin da yake ciki sai da ya ji tamkar ya yi dariya. Amma ya sani idan ya yi dariya yana nufin ta sake 'karfafa zarginta ne. Dan haka ya gintse ya ce "To ki yi duk abin da zaki yi dan auren nan ya sau'ka daga kaina, kin sani Ummah Yan lukatayen mata basa burge ni, bana son su. Ki fa'dawa Abba bana so, ya riga ya daure ni da jijiyoyin jikina ne. Saboda ya ce su Abdullahi basa ta'ba yi masa musu, sun yarda ya isa da su. Shiyasa na kasa yin bore mai yawa a gabansa. Amma a zahiri an 'kuntata mini iyaka". A fusace ta ce "Yo ai biyayyar yaudara ce da tuggu, biyayya ce irin ta bani manda na baka gishiri. Da ace bashi da arziki sai ya yi sati ma basu zo sun gaishe shi ba, bare kuma aje ga jallin zai zartar da hukunci a kansu ya zartu. Ta yi 'kwafa! Tare da cije yatsanta alamun dai tana cikin takaici mai tsananin gaske. A marairaice ya ce "ya zan yi ne Ummah? Bana sonta Wallahi". Ta nisa ta ce "Aure dole za'a yi shi, tunda ya ce idan har ka bijire masa ni ce. Dan haka zaka karbi aure! Amma idan har kana kishina kar ka sake ka shiga harkarta! Kar ka bari a zauna lafiya! Kar ka ta'bata, domin kuwa tabbas zata gado saurin haihuwa a wajen uwarta, tunda sun ga da maiko haka zata yi ta haihuwa ratata kamar da gayya dan kawai a tabbatar an gama da kai. Ka yi ta cusa mata ba'kin cikin da zata barka da kanta, daga nan sai kawai ka sallama musu ita, ta dawo gaban uwarta, mai tsautsayin daukar kara da kiyashi sai ya kwasheta shegiyar yarinya makira irin jaraba. Me za'a yi da zuri'ar gidan mai Ashafa, masu karyar malumta suna yin 'kulunboto. Har abada ba zan so ta ba tunda har cewa ya yi idan har na bada matsala sai dai mu bar masa gidan ni da kai. Idan komai ya lafa sai ka samo zabin ranka Yar shawalwala da zaku da'de bata tsufa ba, irin zuri'a da suke da yakana da adalci". Ya amsa da cewa "shikenan ki kwantar da hankalinki duk yadda kike so hakan zan yi miki, nan duniya ba abin da nake so irin ki, ina sane da tarin soyayyar da kike yi mini, na san irin tattalin farin-cikina da kike yi. Dan haka zan yi komai dan na sanya ki cikin nutsuwa ko da hakan na nufin bacin ran wasu ne". Wani irin Da'di ya mamayeta, ta hau murmushi tana cewa "Hankalina har ya kwanta, amma ka dage da addu'a sannan ina farin-cikin yadda ka yi fatali da ita a tsukun nan, ina fatan ka sake ninkawa". A hankali ya ce "Ni yanzu da ta shigo dakin nan ma ji na yi tamkar na yi mata 'kamshin mutuwa kawai tsabar takaici". Da sauri ta ce "A a Gudale banda shake wuya, kawai dai wulakanci da kankancin da aka san namiji da shi zaka fara nazarin su dan ka yi bitar su dallah dallah amma ban da duka. Masharanntan halittu ne, yanzun nan sai su burma mutum ya kwana a ciki". Ya nisa ya ce " To na ji! Amma ki kwantar da hankalin ki! Ta yadda nan gaba ba za'a zarge ki ba". Ta sake murmushi ta ce "Ashe dai Gudalen nawa akwai dabara! Zan ajiye komai, zan bar shi a zuciyata, duk da kuma ba zan iya nunawa lamarin soyayya ba". Da sauri ya ce "dama Ina nufin kar ki bari kiyayyar ki da lamarin ta bayyana a siffarki ko ayyukanki. Tsawon lokaci suna tare suna tattauna makomar auren. **** Murnar da nake ciki sai da ta bayyana kowa ya gane ina cikin yanayin da yayi mini da'di. Mama ta dinga tambayar menene ya sanya ni wannan nisha'din haka? Sai kawai na yi murmushi na ce "Ba komai". A daren aka yi rasuwa a Moriki matar Baba Yakubu 'dan-uwan su Baba ne da suke first cousins. Sassafe aka shiryawa Mama da Umma da kuma Yayar 'Kwalli tafiya yin TA'AZIYA, bisa jagoranci Yaya Al'amin yayin da jibi, Yaya Abbas zai kai su Abba. Baba ne baya Jin da'di shiyasa Abba ya ce matan suje. Bana manta wannan tafiyar saboda yadda ta yamutsa hazo. Bana wajen amma Mama ta bani labarin har na ji tamkar ina wajen. A hanya suna tafe ana hira, kusan dukkan hirar Umma gugar zana take yiwa Mama. Mafi yawa Mama kuma bata iya bu'de baki ta mayar mata da marta ni ba. A hanyar dawowar sune abin ya faru, tun tafiyar bata yii nisa ba Umma take ta faman cewa "Oh Allah ya ji'kan Rahamu! Yar gata da ita, uwar ya'ya mata, ki gansu reras sun cika 'dakin, ya'yanta mata shida aurararu ance har kansilan garin ma surukinta ne. Wanda Àllah ya bawa yaya mata ya karrama shi ba ka'dan ba. Tausayi da jin kai ai sai wajen mata, ga tarin falalar da zaka samu aljannah ta dalilin Yaya Mata uku bisa sharadin ka raine su, ka tarbiyantar da su cikin adalci da kamewa har zuwa aurensu. Annabi ya ce Aljannah ta tabbata ga wadannan iyaye. Amma ban taba jin falalar haihuwar 'ya'ya maza ba". Yaya tana budi baki sai ta ce "Ai kinsan tun a jahiliyya ba'a son haihuwar ya'ya mata saboda ana jingina musu rauni, ana ganin wahala kawai ake yi da su babu riba, domin ana aurar da su, shikenan wanine zai more su. Amma 'ya'ya maza fa? Garkuwa ne a ko ina, sannan duk runtsi dai suna nan a gida, za kuma suyi kowanne irin aiki dan su nemo". Da azama Umma ta ce "idan sun kasance jarumai ba, domin dai wasu ai gara matan da su tunda zuciyarsu a mace take. Mace imaninta yawa ne da shi, abin burgewa ta janyo maka surukuta da manyan mutane masu mulkin kasar". Duk da Mama ta san jirwaye take yi mata, bata sanya musu baki ba. Sai da aka koma hirar Yaya Al'amin da Yaya Sadik. Nan ma Yaya ce ta canja hirar saboda ta lura janye janye magana Ummah take yi. Dan Haka sai ta ce "Wai ya ake ciki kan maganar auren 'Ya'yan naki ne Safiyya?" Da mamaki Mama ta ce suwa kenan?" Abbas da Aziza mana?" Ta yi murmushi ta ce "Yaya ai Babanta ya ce zai bashi! Amma sai ba'di sannan zai kammala shirinsa, kinsan hidimar aure da yawa abin ka da masu 'karamin karfi dole a shirya a hankali". "Hakane kam domin kowa yana jin yau din nan" Yaya ta fa'da a gaggauce. Sai kuma ta sake cewa "wadannan mashiriritan nan Al'amin da Sadik, da alama sai an nemo musu dan ban ga alamar suna da 'yanmata ba. Jiya na gama yi da Ashir zan laluba na samo masa yarinyar kirki, ya dinga dariya yana fa'din kar na soma". Murmushi Mama ta yi tare da cewa "Ni bana biye ta wadannan, Ni ta auta nake yi." Yaya ta ce "Yo Halima ba ta tsaya ruwan ido ba, ai idan Abbansu ya gaji da bata dama sai da taji ya yi mata miji". Da sauri Mama ta ce "Da ya yi mini maganinta wallahi! Sadik da Al'amin ai ko zancen aure basa yi shekaranjiya da daddare fa da kin ji yadda suke musun wa zai zama shugaban kasa, wa zai zama gwamana a tsakaninsu sai ki zaci yara ne kananu. Sai da na gaji na ce da Al'amin tunda Kaine babba sai ka barshi ya fara za'ba. Sadik ko ya ce shi president zai zama, yayin da Al'amin ya hakura zai zama gwamanan. Na dinga dariyar su tamkar dai an tabbatar musu sune 'yan takara saboda yadda suka dage suna cece kuce. Na biye musu har ina hango kaina na zama uwar shugaban kasa, kuma uwar Gwamna". Yaya ta dinga dariya tare da cewa "kema shiriritar ki yawa ce da ita. Allah ya biya bakin ki to". Umma ta cika ta yi fam saboda zuciyarta ta kitsa mata ai da gayya safiyya ta yi wannan maganar domin tana son ta sanar da ita idan Gudale ya zama shugaban kasa ita kuma ta zama surukar president, sannan ga 'danta zai zama Gwamna. Wato izgili take yi mata. Hakan ya sake zafafa Kiyayyar auren a zuciyarta alhalin har lokacin Mama da Baba Basu san maganar auren ba, bare har ta yi mata Suna dawowa ta zaunar da Gudale ta ce "Ko na mutu ban yarda ka yi siyasa ba". Ya yi Dan murmushi ya ce me zan yi da siyasa? Allah na tuba". A kausashe ta ce "Safiyya ce ta mini habaicin zata zama surukur shugaban kasa, ni kuma idan ina raye ba zan so hakan ba, dan hakan kar ka yarda ka shiga harkar siyasa halaka ne, kar ka yarda ka dauki hakkin da ba zaka iya sau'ke shi ba. Domin mulki al'amari ne mai wahalar wa". A fili Gudale ya ce "Ki tsananta addu'a Ummah! Ki nemawa kanki tsari daga sharrin shaidan da na hassada. Mummunar dabi'a ce da take ruguza komai". Kuka sosai ta fara yi har da gunji, kuka na zallar bacin rai, yafi kama da kuka irin na kaicon yadda 'kaddara zata bawa Safiyya damar yin suruki da Gudalenta. Ya dinga lallashinta da cewa "Ban da abin ki Umma ina ce idan na zama shugaban kasar ke kuma kin zama uwar shugaba, sannan auren ai ba nisan kiwo zai yi ba. Bare ki yi ta bacin rai a banza". # Team Gudale. # Team Guduyo. # Surayya Dee. # Ana tare🤝. 2/8/23, 10:22 - Buhainat: *Wannan littafin na ku'di ne, biya 500 ku'din karatu ta wannan asusun* *2384876855* *Surayya Ibrahim* *Zenith Bank.* *A tura shaidar biya ta wannan lambar* *08032773332*. *Kun san za'kwa'kurar jakadiyar G.H.T.?* *Tana gyaran amare* *Tana da bada amintattun supplement din da yake dagargazar sanyi* *Tana da supplement din da yake zai-zaye kitse, ya ke fidda zahirin surar mace*. *Tana da wanda yake ha'de mace ko ta fara manyata kuwa.* *Fasilat tana da komai na wannan bangaren har da na ulcer da basir, Wanda basu da illah a lafiyarmu*. *Haka tana da wanda yake saukar da ni'ima da sanya 'dumi a jikin mace* 07039269802* *Gudale ya ce a nemo zakwa'kuran masu Gyaran amare su gyara masa Gudidi* *Na kuwa samo wanda na gamsu na kuma amince da kayayyakin su* *Dan haka kuma ku zo ayi muku naku gyaran domin kuwa Tested and trusted ne*🥰 *SDK29-30.* Da 'kyar ya lallaba ta ta yi shiru. Ya fita yana mamakin tsananin 'kiyayyar da take yiwa Mama. Tare da ta'ajjibin yadda mata ba sa raina 'dan karamin abu, su yi ta kambaba shi ta yadda zai zama 'katon laifin da zai yi sanadin damalmalewar al'amura masu yawa. Sai bayan su Abba sun je Moriki sun dawo. Sannan ya sanarwa Baba da Yaya ya yanke hukuncin aurena da Sadik nan da lokaci ka'dan. Dukkansu ba wanda ya yi inkarin hukuncin nasa, duk da sun san akwai na'kasu a tare da Sadik. Murna suka yi da fatan alheri, mussaman Babana. Yana dawowa gida ya tarar da ni tare da Mama muna kicin muna jefa 'Dan-wake. Daga bakin 'kofar ya tsaya ya ce "idan kun kammala ku zo akawai maganar da zamu yi". Muka kammala aikin cikin wasi-wasin maganar da za'a yi. A nutse ya ce "Alhaji ne ya zartar da hukuncin auren Halima da Sadik nan da wattanni biyu. Na sanar muku, dan ku sani, ku bi lamarin da addu'a". Wani irin farin ciki ya mamaye mini kalbi, yayin da Mama ta sunkuyar da kai 'kasa tana jin 'kunan rai. Ta dago idonta da ya cika da 'kwalla ta dubi Baba ta ce "Baban Ammar anya wannan lamarin zai yiwu kuwa? Ummansu ba zata so wannan ha'din ba. Ina jin tsoron abin da zai biyo baya, gaskiyar magana maganin kar ka ayi, kar a soma." Da 'bacin rai ya ce "wato kina son ki ce mini na nunawa Alhaji bashi da iko akan 'yar da na haifa? Kina son na nuna ina 'kyamar bawa tilon 'dansa aure alhalin duk matan duniya bai ga wacce ta dace da 'dansa ba sai tawa ' 'yar. Wato kina son ki ruguza mana zumunci? ita ai bata iya tarar gabansa ta nuna bata so ba, tunda ta sani yafi karfin ta. Amma ke da yake kin raina ni, kin tari gabana kin fa'da mini akan idona". Ya numfasa ya ce "Sai dai ki sani shure shure baya hana a yanka dabba, haka nan *sabo da kaza* baya hana a yanka a cinye. Wallahi akan wannan maganar zan sassaba miki fiye da zaton ki! Mutuwar Halima ko ta Sadik ne zai sa a dakatar da auren nan, amma ko ke ce kika mutu ina tabbatar miki ba za'a fasa ba". Na sake yin kasa da kaina, ina jin rashin da'din yadda Baba ya fusata yake ta fa'da ba sassautawa. Amma a 'kasan raina ina goyon bayansa na kar ya yarda ya bi maganarta ayi mini ta le'ko ta koma. Da rawar murya ta ce "Baka fahimce ni bane, amma ka yi hakuri. Akan me zan 'ki Sadik? Har zuciyata ina sonsa, uwarsa nake ji. Amma na barwa Allah ya zame mata jagora a hannunsu". Jikina ya yi sanyi, yayin da Abba ya ce 'yanzu kika yi magana". Da hakan na tashi na barsu. Sai da Baba ya fita, Mama ta shigo ta same ni a dakina ta zauna kusa da ni, ta ce mini "Kina ta rawar jiki, akan wannan ha'din. Ban yi zaton son da kike yiwa Sadik ya girmama haka ba. Tunda kika taso kike ganin tsana 'karara a idon uwarsa. Kullum a can kike kwana, amma abincin da zata baki ki karya yafi karfin ki sai idan akan idon Abbanku ne. Har yau da kike cikin shekaru ashirin ba zaki tuna me ta yi miki na kyautatawa ba, ba kuma komai kika yi mata ba, laifina ne ya shafe ki. Amma har kike murnar ki zamo surukarta, anya kinsan jidalin da mace take fuskanta idan ta ha'du da kiyayyar uwar miji?" Na yi 'kasa da kaina ina jin rauni, na kasa magana saboda gaba'daya na rasa me zan ce. Sai da ta yi waiwaye dan ta tabbatar ba wani a kusa da mu. Ta ri'ke hannnuna ta ce "ki fa'dawa Abbanku baku shirya da Sadik ba. Idan ya nemi Jin ta bakin ki, ina tabbatar miki baki dace da shi ba, nutsuwarsa ba mai yawa ba ce, ko ni da kika ga baya taya uwarsa yin gaba da ni, dan yana morata ne, da kuma shakuwa. Amma ai kinsan yadda ta tsananta sonsa, ta kuma dora dukkan buri akansa. Ba zata so ki ba, ba dan komai ba sai dan nice uwar ki. Shima kuma ba zai zabe ki ya bar uwarsa ba. Idan kika kafe sai shi, ina tabbatar miki zaki yi rayuwa ne mai tattare da takura da tsananinl, fiye da wacce nake fuskanta a wajen ta. Kina gani dai ba irin wahalar da ba na sha a hannunta har yau, Abin kaicon kuma bamu ha'da miji ba, ba kuma uwar miji ba ce. Amma har yau din nan ina rayuwa ne cikin zullumi saboda masifarta. Shin so kike abin ya yi mini yawa? Ga bacin ran da take cusa mini, sannan kuma na fara tararrabin damuwar da kike ciki". Na yi shiru! Tsawon lokaci ina tunanin mafita. Gaskiyar magana ban ji zan iya cewa na fasa ba, domin ni ka'dai nasan yadda nake jin Gudale a raina. Duk sallah kafin na ro'ki komai sai na ro'ki Allah ya sanya na zama matarsa, sai da addu'a ta amsu sai kuma na yi wasarere da cikar burina akan wani dalilin da bashi da tushe. Jin na yi shiru ya sanya ta fahimci ba zan yi abin da take so ba. Ta sake ri'ke hannnuna sosai ta ce "Halimatu ba zan so ki nace akan wannan auren ba, kar ki kafe, ina jiye miki tsoron fa'dawa tarkon da ba zaki iya subucewa ba". Nan ma na yi shiru! na 'ki yin magana. Ta mike ta ce "Na fa'da miki gaskiya tunda kin biyewa burin zuciya ai shikenan, ina miki fatan ki samu sassauci a dukkan abin da nake jiye miki tsoro". Sai a lokacin na ce "Ameen". Ta kafe ni da ido tana mini kallo mai tsananin gaske. Ta girgiza kai ta yi 'kwafa. Ta fice ta bar ni. Maimakon na yi nazarin maganganunta, na auna su, na gano girman soyayyar da take yi mini ta ninka wacce nake yiwa Gudale. Sai kawai na shiga hakaito kyaunsa, kwalliyarsa, hatta rashin kunyarsa burge ni take yi. Na hango 'dan tsurut din bakinsa mai dauke da fararen ha'kora tamkar kankara. Na sake ha'kaito sumarsa da take cike fam, gata 'baka wuluk, sannan ake gyarata tamkar sumar mace. A rayuwata ban ta'ba ganin namijin da shagwa'ba take yi masa kyau irin Gudale ba. Duk girmansa idan yana gaba Umma sai ka rantse yaro ne da bai da'de da yaye ba. Ita kuma bata fahimtar ya girma ta dinga lallaba shi kenan, sannan komai yake so sai ta yi masa. Har a lokacin bai wuce ya kwanta ya yi matashin kai da cinyarta ba, ba kuma zata motsa ba, dan kar ta tashe shi. Idan su Sakina na fa'dan ya bar musu uwa ta huta da hidimarsa haka nan. Ita ce take cewa "Ku bar mini autana ya yi yadda yake so. Duka duka nawa yake ne? ai ni idan ba gani na yi za'a aurar da 'dansa ba, ba zan gane ya girma ba." Shikenan sai suka koma zuba musu ido. **** Kwanci tashi har aka kwashi sati biyu da zartar da hukuncin aurenmu. Amma har lokacin ban ga sassauci daga wajen Yaya Sadik ba asalima na jima ban ganshi ba. Ranar litinin sassafe na fito dan tafiya makaranta, na ganshi tsaye shi da Yaya Al'amin. Na karasa kusa da su, na gaishe su. Yaya Al'amin ne kawai ya amsa, amma shi sai ya dauke kai. Hakan da yayi ya ta'ba Yaya Al'amin kwarai da gaske. Da daddare ya zo, ya shiga 'dakin mahaifiyarmu, sannan ya 'kira ni. Sai da ya rufe 'kofar sannan cikin murya kasa kasa ya ce "Halima! Da ke da Sadik 'daya ne, wallahi ba wanda ya fi wani a wajena, amma zan fa'da miki gaskiyar magana, ki samu Abba ki nuna masa ba Kya son wannan ha'din gara a mayar da auren ki kan Ashir. Ina tabbatar miki Abba adali ne ba zai kalubalence ki ba. A gabana Sadik yake nuna wa an yi masa dolen auren ki, ba ya jin kunyar idona". Idona ya ciko da hawaye, ina jin wani irin abu na taso mini. Cikin kuka na ce "Yana sona fa! Laifi na yi masa, kuma zamu shirya ne". Ya kalle ni sosai ya ce "shikenan Halima good luck". Ya fita da sauri. Na goge idona ina 'kunkunin ina son abina, ai ni zan zauna, ba wani ne zai yi mini zaman ba. Washagari na dawo daga makaranta muka yi kicibus da shi a harabar gidan. Na gaishe shi, ya bagarar tamkar yadda yake mini tun sanda ban yarda na biyo shi daga gidan Sakina ba. A hankali na ce "Yaya Gudale! Ya kamata ka huce hakanan, ai dai ka sani kafi Sakina a wajena, to menene na wannan doguwar gabar haka? Dan Allah mu shirya haka nan". Ya mini kallon wulakanci ya ce "ke kam kin ji jiki wallahi! Ashe ba zaki kame kanki ba? Wallahi na tsani mace marar aji". Ya yi tsaki ya wuce ya bar ni. Jikina ya yi sanyi sosai, na dinga auna maganarsa, maimakon na ji raina ya baci, sai na tsinci kaina da jin takaicin kaina na kama ni, me yasa ban zama mai aji ba? Tunda Yaya Sadik mai aji yake so. Na kudire duk inda aji yake zan nemo shi dan na burge shi. Amma matsalar a kansa ne bani da ajin kawai, shin zan iya kamewa akan lamarinsa? A wajen na 'daga hannu ina fa'din "Allah Yaya Sadik mai aji yake so, ina ro'kon a sanya na zama kamammiya a idonsa da zuciyarsa, Ubangiji a cika masa kirjinsa da soyayyata." Ranar jummaa Abba ya bukaci dukkan ahalin gidanmu su zo yana son ganin su. Bayan la'asar aka zauna. Ba bata lokaci ya sanar musu aurena da Sadik ya gabato. Aka yi addu'a da nasihohi, sannan ya sallami kowa bayan ya ce Al'amin da Ashir su maida hankali suma, tunda sun girmewa Sadik din, duk dai ba wani fiko ne mai yawa ba. Bana mantawa a cikin 'dakina na bangaren Ummah! Sakina ta zaunar da ni tana cewa "ki fa'dawa Abban ya canja miki Na Moriki da Ashir. Sadik fa ba zaki iya da shi ba Halimatu! Ina jiye miki tsoron kar ki shiga damuwa". Na zum'bura mata baki sosai, na kasa cewa komai saboda yadda nake Jin tamkar na rufe ta da duka. Dan kawai ita ta yi auren ku'di, mijinta bashi da wani kyau, duk da ita din ko a cikin kyawawan mata sai ance mai kyauce saboda yadda kyaunta ya shahara. To ni nafi son kyakkawan namiji, dan gaye, marar nauyi, sannan ma'abocin son cin da'di koba komai nima ai zan ci. Amma an tisa ni gaba ana ta cewa ban dace da shi ba, da sauran surutai marasa kan gado. Ta zuba mini ido ta ce "Ni Kika zum'burawa baki haka? Na dauke kai na ce "Ato ni na gaji da wannan maganar gaskiya, gashi nan kin janyo mini 'bacin ransa, tun abinda ya faru a gidanki har yau bai sake kula ni ba. Kuma ai nice zan yi zaman ba wani ne zai taya ni ba, kowa ya iya allonsa ya wanke kawai". Ta yi matu'kar razana ta ce "wato tun ba ki je hannunsa ba, kin fara yin koyi da rashin kunya da rashin mutuncinsa ko? Tabdi lallai kuwa! Ai shikenan ki wanke allon lafiya". Ta mike ta bar ni cikin bacin rai mai yawa. Ni kuma ina ganin idan ba hakan na yi mata ba, ba zata shafa mini lafiya ba. Na yarda da Yaya Gudale da yake cewa kazallaharta ta yi yawa. Shikenan Abba ya dinga shirin aurenmu tamkar dai ba'a ta'ba aurarwa ba sai akanmu. Sakina ya 'kira ya dam'kawa ma'kudan kuda'de akan ta shiryo mini lefe. Da sauran gyare gyraen amarya. Kan dole ta ajiye fishin da take yi da ni. Ta kira ni bamu zame ko ina ba sai gidan abokiyar karatunta fasilat hazikar jakadiyar *G.H.T*. Da murna *Anti Faseelat* ta 'karbe mu, ta kalle ni ta ce " ya naga Amarya ba kya glowing? duk kin yi duhu, har wasu 'kuraje nake ganin suna neman 'bata miki fuska?" Sakina ta ta'be baki ta ce "gata nan wata'kila streess din makaranta ne, sannan ta 'dorawa kanta damuwa, ba shawara ba komai ta canja mai din da take amafani da shi. Da murmushi Fasilat ta ce "kwantar da hankalinki Amaryarmu, bayan gyan jiki har mai zan baki ki matsa akan man na asali sai farar fatar ki ta dawo tamkar ta larabawan Jordan". Ni dai bance komai ba. Sai da muka sanyaya ma'koshinmu sannan ta yi mana iso zuwa dakin da kayayyakin suke ajiye. Ta kalle ni sosai ta ce "tunda fatarki fara ce sannan dry ce zan baki seti mai matu'kar kyau ki fara amafani da shi kafin bikin". Ta dauko wani kit din mayuka da tarkacensa, a ido ma ka'dai abin sha'awa ne. Ta sake za'kulo wani 'dan karami ta ce "ki ha'da da wannan, domin sai an hada da shi ake samun abin da ake bu'kata". Na kar'ba ina juyawa. A hankali na ce "Anti na gwada shi bai yi ba". Da sauri Fasilat ta ce "Ba wanda ya dace da fatarki aka baki ba, wata'kila na masu oily skin aka baki. Ki tambayi Sakina! Kayana masu kyau ne, sannan sai nasan ainihin kalarki kafin na baki shawarar wadanda zaki shafa". Na girgiza kai cike da gamsuwa. Sakina da ke haushina take ji, bata ce 'kala ba. Ta dai kalleta ta ce ki bata kwalli da jan baki har da powder". Ta hado dukkan abin da Sakina ta ce. Na sake nutsuwa ina duba wani supplement da yake yaki da kowanne irin sanyi da yake addar mata ba yanmata ba, ba matan aure ba. da kuma wanda amare zasu fara kafin auren. Ga wani irin lubricant mai kyau da daukar da nutsuwa Wanda ta ce sai anyi zan fara amfani da shi. Duka Sakina ta ce "Ta zuba su a leda. Yawan ku'din bai damu Sakina ba, saboda ta gasgata *Fasilat* da kayanta. Hatta basir din da ya sanya mijinta a gaba aka kasa samun maganinsa, wani maganin na *G.H.T.* ya sha ya dace. Ku tuntu'be ta a wannan lambar. *07039269802*. Siyan na gari aka ce maida ku'di gida. Na yi zurfi a tunanin yadda Anti Sakina tasan manyan mata da kasuwancinsu, shiyasa komai nata na daban ne, to baka samunsu barkatai a ko'ina, na kuma lura gogewar fatar Sakina tana 'damfare da yadda take tu'amalli da mayukan oriflame. Mussamna da yake ta hadu da wanda tasan sirrikan mayukan da zasu kar'bi kowacce launin fata, tana zaba mata wanda zasu yi daidai da ita. Wani Mai da *Aisha lame* ta za'ba wa Sakina a dalilin fatarta oily ce ba 'karamin fito da zahirin kalarta yake ba. Mussamna da yake ya dace da farare masu oily skin irinta. Ni da kaina na gamsu ban san wata jakadiyar oriflame da tasan kalolin mayunka da zata hada maka su gyrara ka tamkar Kawar Sakina ba. Duk Wanda ya yi mua'amala da ita zai so ya dauwama yana tu'amalli da kayanta. Tuntu'be ta kan wannan lambar dan samun mayukan da suka dace da fatarki. *07033662633.* Ranar biyan bukata rai ba'a bakin komai yake ba. Haka Sakina itama ta sayi nata kayayyakin gyaran auren a wajen jakadiyar *G.H.T Fasilat* ta yi mana sau'ki sosai. Ina jin Sakina tana ce mata, zata dawo ta siya mini wanda zan tare da su Da murmushi Fasilat ta ce "sannan ma dangin supplement din da zai daidaita ta, ya fiddo da zahirin shape dinta sun iso. Bayan bikin kuma sai mu duba yiyuwar yi miki rigista da su. Domin na shaida kin gane sirrin da ke cikin kayan *G.H.T*. Kin gane abu mai daraja farashinsa daban ne, haka nan aikinsa ma na daban ne". Sati 'daya kawai na yi, amma na yi matu'kar canjawa, kyaun fatata ya bayyana, zahirin farinta ya fito, ta yi laushi tu'bus. Ni da kaina bana gajiya da kallon kaina. Tafin hannuna ya yi laushi sosai saboda kullum hand lotion yana jakata. Hatta Mama sai da ta ce idan na san bleaching nake yi na kiyayi kaina. Na yi dariya na ce "Haba dai Mama duk yadda nake da farin nan sai na ha'da da Wanda zai lalata mini halittata? Kawai dai fatar ta samu mayukan da suka dace da ita ne, shiyasa take fitar da asalin kalar da Ubangiji ya yi ta. Ni da kaina bansan haka nake da kyau ba sai yanzu. Wani abin mamaki ni da kaina na ji dadin marata, wannnan farin ruwan da nake zubar mini lokaci zuwa lokaci ya kau, haka 'kai'kayin da nake 'dan ji from time to time ya tafi gaba'daya. Madallah da kayayyakin *G.H.T* mussaman wanda aka siya ta hannun jakadiyar da kamfanin ya gamsu da kokarinta da sau'kin kayanta. *Madallah da Faseelat 07039269802* *Madallah da jakadiyar G.H.T da bataq 'kwangen sayar da man da ba zai karbi fatar mutum ko kayan da baza 2su gyara zamantakewar auren mace ba*. *Lol Gudale ne ya ce a nemo zakkwakuran masu Gyaran mace in and out*🤪 *Ni kuma na Nemo wandanda suke tested and trusted*. # Team Gudale. # Team Guduyo. # Surayya Dee. # Ana tare 🤝. 2/8/23, 10:22 - Buhainat: *Wannan littafin na ku'di ne, biya 500 ku'din karatu ta wannan asusun* *2384876855* *Surayya Ibrahim* *Zenith Bank.* *A tura shaidar biya ta wannan lambar* *08032773332*. *SDK 31-32.* *Muna ha'da lefen Guduyo ne* *So zaku yi ta ganin shahararrun 'Yan kasuwa, da masu gyaran amare.* *Idan kuka bibiye su zaku tabbatar kayansu zabbabu ne, Kuna masu sauki ne*. *Kunsan dai supplements din da Iyah Basiru take amfani da su gangariya ne* *Shiyasa ta gamsu da Faseelat 07039269802 mai gangariyan kayan kamfanin G H.T.* Na fito sanye da shu'diyar shadda mai duhu doguwar riga, da aka 'kawata da duwatsu masu ruwan hoda. Na yafa mayafi kalar duwatsun. Na yi wani irin kyau saboda yadda nake she'ki da glowing. Jikina a cike rugu rugu da ni, komai ya cika dam, tamkar zai faso riga. Mama ta ce "Sakinan zuwa zata yi ta dauke ki?". A hankali na ce " ta ce Idan ta iso waya zata yi mini na fita, sai mun dawo zata shigo". Ai kuwa ina rufe baki wayata ta hau 'kara. Ina dubawa na ga ita ce. Na fita ina cewa Mama "sai mun dawo". Na shiga gaban motarta ta ja muka wuce. Bamu zame ko ina ba, sai sabon titi gidan 'kankara. Gidansu *Umm Muhd collection* na dinga mamakin yadda Sakina take sanya suturun da bana ganinsu a jikin kowa ashe ba a kasuwa take siyayyarta ba, a gurin matan da suke zana kayansu da kansu ne, su kuma yi oder su kaitsaye. Sanin kowa ne galibin matan da suke business da jarinsu da wahalar gaske ka ga irin kayansu a kasuwa. *Umm Muhd collection* tana cikin jerin irin wa'dannan yan kasuwar. A farko Sakina bata fahimci kayanta ba, Amma aminiyarta da suka hadu a dalilin karanta littafanta *Surayya Halin Yau* tana yi mata shunenta shikenan ta yarda da gaske kayayyakinta unique ne. Mussaman da ta jarraba ta gani. A yanzu haka Sakina tana cikin WhatsApp group dinta, tana ma karban kayayyakinta ta siyar mata tare da dogayen rigunnan da Sakinan take saidawa. Takalma na za'ba asalin Italians masu tsananin kyau. Haka jakunkuna ma qualatitives ne. Na gasgata, na kuma shaida kyau da sau'kin kayan Umm Muhd. Domin duk yadda *Sa'adan Mk* take da high tana siyayyar takalmi da jaka da kayayyakin kicin na alfarma kuma zababbu a wajen *Umm Muhd collection* *08063358662*. Bayan haka tela ce da ta shahara. Ba a dauki lokaci mai yawa ba Sakina ta kammala shirya mini lefe na garari. Siyayya ta Fisabidillahi ta yi. Ta kaiwa Abba ya gani, ya yaba mata kwarai da gaske. Ya umarceta da ta kai gidan Yayar Kwalli, ita kuma sai ta shirya yadda za'a kawo. Ya dinga sanyawa Sakina albarka, yana alfahari da ita cikin ya'yansa, a dalilin halin girma irin nata. Kwanaki kadan ta shiryo ita da jama'arta suka kawo kaya. Kayan da kowa ya kalla ya san an salwantar da dukiya mai yawa. Duk kayan cikin akwatin zababbu ne. Kuma masu daraja ne. Kayan costumes ka'dai ya isa a ha'da wani lefen, domin duka kayan oriflame ne, amma daga wajen jakadiyar su *Aisha lame* da ta goge a wajen sanin nau'in mayukan da zasu da ce da kowacce irin fata. Kai ka ce Damatology ce, ko kuma wacce ta yi digiri a custumalogy. Haka nan atamfofi da lesinan ciki selected ones ne, kowa yasan order mata ta sha ban ban da sauran gama gari. Mafi yawa a wajen *Amyas newly & fairly used* aka samo su. Idan kina bu'katar latest atamfofi da laces kawai tuntu'be ta a wannan layin na tabbatar zaki yaba ki kuma gode mini, duk da ita komai da ruwanka ce, ko kayan 'daki kike bu'katar canji duk tana da ruwa da tsaki a harkar, haka nan idan zaki siyi kayan daki sabbi ko na hannu masu kyau cikin rahusa duk ta shaharar a wannan fagen za kuma ki sameta da cika al'kawari kedai kawai tuntu'be ta. 08083909947. Har bikinmu ya zama saura sati uku babu jituwa ko ka'dan a tsakanina da Yaya Sadik! Ya rufe kofar sulhu, ya tsananta sosai. Ana haka Abbah ya ce masa ya dauke ni mu je mu yi test. Kai tsaye asibitin Malam muka je. Bamu 'bata lokaci soasai ba, aka kammala. Sakamakon gwajin jini na gynotype ya nuna ni A.A. ce yayin da Yaya Sadik ya kasance A.s. sai na Hiv da sakamakon mu ya nuna dukkan mu positive ne ma'ana bamu da 'kwayar cutar. Mun fito, muka hadu da Sakina, ta kalle mu ta watsar. Jikina na rawa na shiga gaisheta, a dalilin na matsu ta gama hucewa da ni. Yayin da Gudale ya yi gaba, ba tare da ya ce mata uffan ba. Muka fito tare tana duba results din namu. Ta miko mini tare da cewa "kun kai ga barka! baku da matsalar komai, ina yi muku fatan alheri". Na kasa amsawa, bansan kuma dalilin ba. Ta wuce da alama round take yi. Na bu'de murfin motar zan shiga, na ji kamar muryar Yaya Ashir ya ce "Sadiya". Na juya da sauri ai ko shine ba kama ba ce. Na amsa da sakakkiyar fuska. Na gaishe shi, ya amsa da walwala yana tambayar me na zo yi asibiti? Na kasa bashi amsa, ya m'iko hannu ya karbi file din hannuna. Ya dudduba ya mayar da su fuska ba walwala. Ya numfasa ya ce "fatan alheri! Tare kuke da Sadik kenan? I thought da Abbas kuke na ga motar Abba ce, nasan kuma Abbas kawai Abba yake bawa motarsa". Ya 'Dan rankwafa ka'dan ya ce "Sadik girma na shirin hawa kanka amma ba zaka gane rayuwa ba. Ina 'dan-uwanka kuma Yayanka amma ba zaka fito mu gaisa ba?". Kai-tsaye ya bashi amsa da cewa "Ai ba dan ni ka tsaya ba, tunda har ka bada tabbacin ka dauka Abbas ne. Ita dai da take kanwarka kuma masoyiyarka, sai ka sake na'de kafar wando ka yi ta zazzago mata kalaman 'kauna. Ni kuma ka yi ta watso mini na kuruciya da kiyayya". Ya kammala maganar tare da jan tsaki mai tsananin gaske. Ganin hakan ya sanya na shiga motar jiki a sanyaye saboda yadda naga dukkansu ransu ya kai 'kololuwar 'baci. Yaya Ashir ya ce "Na rantse maka ba dan a asibiti bane da kaga abin da zan yi maka, har kullum ina jaddada maka ni ba Al'amin ko Abbas bane da kake musu iskanci son ranka. Banda dai aure 'kaddara ne, me babbar mace irin Sadiya zata yi da kai? 'Dan mitsili da kai sai hancini da 'kifa'di". Yana rufe baki ya nausa cikin asibitin ya barmu a wajen. 'Kafafuwana har rawa suke yi, tsabar tsorata da halin da Yaya Gudale ya shiga. Sai numfarfashi yake ya rasa inda zai saka ransa. Ya jima kafin ya kalleni idonsa jawur tamkar gauta ya ce "A gaban ki Ashiru ya tozarta ni, amma kika kasa kare ni ko? To bari ki ji ina tabbatar miki sai dai a tsine mini amma sai dai auren ya koma kansa. Me za'a yi da matar da za'a ci mutuncin mijinta amma ta yi farin-ciki da hakan? Na gane dama soyayya kuke yi, to huta roro na bar masa, dama shi ya dace da kumbusa irin ki". Murya a dusashe na ce "Ka yi hakuri ka sani dai babu ruwana, ni kaina ji na yi tamkar na rufe shi da duka har sai ya karyata kansa. "Dallah rufe mini bakinki, makaryaciya kawai". Ya fa'da da kara'di. Na yi shuru! Na kame bakina a dalilin na ji haushin yadda ya daka mini tsawa. Bansan dalilin da ya sanya ya yi zagaye da mu ba, ina Hausawa ina asibitin Malam? Sai kawai ya bi ta gate din da yake Kan titin Zaria road, muka dinga tafiya, har muka isa round din tafiya Kaduna, sannan ya juyo. Na dinga mamakin hakan. Mun zo dai-dai gadar lado na ce "Yaya Gudale siya mini plantain chips ina son ci". Ya share! na sake maimatawa. A hassale ya ce "Ba zan siya ba, tun wuri ma ki daina wannan hamburin hayam din nan. Dan kuwa ba zan laminta ba, shiyasa kike ta hawa tamkar kina shan yist alhalin ciye ciye kawai kike yi ba control". Bansan ya aka yi ba sai kawai na tsinci kaina da cewa "ka fasa barwa Yaya Ashir din ne?". Ya dugunzuma ba ka'dan ba. Takaici ya shake masa makaoshi ya kasa cewa komai. Muna isa gidan ya karbi file ni kuma zan wuce wajenmu. Ya gallah mini harara tare da cewa "Tare zamu kai masa". Na bishi a baya. Muka tarar da Abba yana zaune a falo. Murnar ganin sakamakon gwajin ya dinga yi ta hanyar fa'din Alhamdulillah! Ya dinga sanya mana albarka. Ya rufe maganar da cewa motar Gudale tana hanya. Na fito na barsu. Ina shiga wajenmu na tarar da Mamah tana kuka irin hawayen nan na shar'be. Hankalina ya tashi matu'ka da gaske. Na dinga tambayar dalilin kukan, amma bata bude baki ta ce mini ta tafasa ba. Sai da aka jima bayan ta ga nima na fara kuka sosai. Murya ba amo ta ce "Umma ce ta fa'dawa Babanku wai ina yi mata shaguben na riga na sha gabanta a gidannan, sannan kuma Ina yi mata gadarar aurenki da Sadik har ina alfahari zai zama shugaban kasa. Da sauran maganganu na sharri". Na yi shiru! Raina ya baci, ita dai Umma kullum a cikin kirkirar matsala take. Yayin da Mama ta kasance mai damuwa da lamarinta. Yo Ni Allah na tuba idan ma na zama surukurta, komai zata yi ina ruwana da ita, ai kulawa ma yabace. A ganina Mama tana damuwa ne, shiyasa Umma take sake yi mata yadda ta ga dama. Na nisa na ce "ki yi hakuri Mama! Kayan lefe nan ne yake cinta, tunda aka kawo ta gansu ta sake birkicewa, hatta Sakina ma baki ga cin mutuncin da ta yi mata ba. Ta sani Ina dakina na sashinta amma ta daga murya tana yiwa Sakina tijarar yadda ta narka dukiya mai yawa a lefen. Amma sai na yi kamar ban ji ba. Dan Allah kema ki daina damuwa Mama! Ba yadda zata yi da ke sai kanadi". Ta zuba mini ido ta ce "Na lura ke ba Kya fargabar da nake jiye miki". Na saki ajiyar zuciya na ce "To ya zan yi tunda haka kaddara ta zaba mini". Ta mike tana cewa "Allah ya sani bana son auren nan, amma tunda kun dage ba zan yi jayayya da ikon Ubangiji ba. Ina fatan ko menene zai biyo baya ya kasance alheri ne, amma ki sani sai kin Kulla abota da hakuri da kuma juriya." **** Bayan kwanaki biyu. Ina zanue a falon Mama sanye nake cikin wata kyakkawan atamfa Yar Togo wacce na siya a wajen *Amyasa newly & Used* 08083909947. Koriya shar mai zanen yakuwa, da ro'di ro'din jah kadan Sosai ta karbi lallausar farar fatata. Mussaman yadda dinkin ya zauna a jikina, doguwar riga ce mai kwala. Ba zato na ji wayata ta hau kuwwa. Ina dubawa na ga sunan Yaya Gudale yana yawo akan allon wayar. Na dauka cike da matsanancin mamaki. "Ki fito ina wajen bukkar nan ina jiranki yanzun nan" Ya kashe wayarsa, ya barni ri'ke da tawa cikin matsanancin mamaki. Na dinga ayyana me ya faru da safiyar nan Gudale zai nemi ganina. Na mi'ke a sanyaye na shiga dakina, na dauko Jan mayafi, na tsinci kaina da sake goge fuskata da hodar da ta dace da nau'in fatata ta shararren kamfanin nan na oriflame, na tsinci kaina da shafa Jan baki ja. Na kalli kaina, na tsorata da yadda fatata ta zama. Wani irin sheki luwai luwai tamkar irin manyan mata yan kwalisa suke, haka na dawo. A zuciyata sai yabawa kawar Sakina nake yi, duk da kasuwanci take yi, na tabbatar zata samu ladan yadda take tsayawa kai da fata take gyarawa mata fatarsu cikin gaskiya da aminci. Na shafa turaren mai na Haramain Madina a hannuwanwana da wuyana ka'dan. Na fito, na isa zuwa kicin na cewa Mama "Na fita waje Yaya Sadik yana kira na". Ta kalle ni sosai ta kasa ha'diyewa ta ce "Da sassafe nan? Ashe shiyasa kika tashi kika shirya, tamkar zaki je wani gurin?" Ina dariya na ce "Wallahi ban san ma zai zo ba Mama". Na fita ina kallon lokaci a wayata da ya nuna 10:52 am. A fili na ce "Rana ta fara yi ai" Na murmusa na ce "idan mutum na zaune a gida ba ya gane lokaci ya tafi." Na ma'kala jan takalmina flat a dalilin tsayina ya ishe ni. A hankali nake tafiya, ina hango shi yana zaune a bukkar shi ka'dai yana ta faman latsa waya. *Sadik* Ba zato ya 'daga kansa ya hango ta a dalilin 'kamshin turaren da ta shafa ya kaiwa hancinsa caffa. Zuciyarsa ta buga saboda yadda yaga ta yi kyau na ban mamaki, dinkin ya fito da ainihin surar 'kirjinta daga kasa kuma ya bude. Take ya ji zumudin kwanakin da suka yi masa saura su zo da gaggawa. Domin yaga abin da ya jima yana harin ganinsu a zahiri. Bai san me yake ji akanta ba. Amma babu 'kiyayya, kawai dai shi yafi son yar siririya ne wacce zai ta cafewa babu nishi ko haki. Baya ga hakan, Yadda Ummansa take adawa da lamarinta yana rage masa tasirin yadda yake jin 'kaunarta wacce yake ganin dan jini ya ha'dasu ne da kuma yadda yake hango soyyayyarsa a idanuwanta. Na isa inda yake zaunen sai da na yi sallamah sau biyu sannan ya yi firgit alamun ya yi zurfi cikin tunanin. Na zauna na gaishe shi Ya amsa yana bina da kallon 'kurillah. Sanye yake cikin 'kananun kaya, jikin rigar an rubuta Gudale. Kusan duj rigunansa da handkerchief dinsa an rubuta hakan. Ya numfasa ya ce "Guduyo yaushe kika fara sanya janbaki saboda Allah?" Cike da iyashege na ce "baka lura bane dama ina saka wa from time to time". Ya 'daure fuska ya ce "Bana son karya kin ji! Fa'di dalilin da ya sanya kika saka kawai Malama". Na yi murmushi ina jin da'din yadda yake magana cike da rikici da wani irin abu da ban san yadda zan fasalta shi ba. Amma dai ya fara saukowa daga dogon fishin da ya yi. Na ce "To kawai a barshi na saka ne irin yadda yanmata suke yin kwalliya idan zasu fita, ko sun idan yi nisha'di". Ya bata fuska tare da zuba mini ido sosai ya ce "gyara kalaman ki. Basu yi mini ba, dan haka ban karbe su ba'. Na shagwabe fuska tare da cewa "Kai Yaya Gudale". Ya gallah mini harara tare da cewa"Ashe ban hana fa'dar wannan sunan ba?" Na sunkuyar da kaina kasa ina gunagunin ni ina son sunan, yana sanya ni nisha'di domin kuwa har cikin zuciyata nake jin shi din Gudale ne tamkar da dubu. Dan Haka ba ina nufin Gudalen da Umma take nufi ba. Ina nufin The only one I love. Ya girgiza "Wai shagwaba kike yi ne ko Ta'bara?" Kafin na yi magana ya ce "Ina jin ki, fa'da mini dalilin sanya wannan jan bakin?" Na yi kasa da kaina na ce "Ho Yaya Sadik! To mu barshi kai na sanyawa tunda zance ka zo". Ya wani zabura ya ce "Ka ji masharranciya! Wanne zance zan zo kuma?" Allah ya yafe miki hakkina da kika dauka kawai Guduyo". Ya fa'da yana gintse dariyar da take son bayar da shi. Ni kuma ganin sassauci a tare da shi na sanya na ce "Ya mini kyau kenan? Tunda ka tanka". Ya ci magani ya ce "Abba ne ya ce mu yi shawarar kalololin furniture's din da za'a zuba a gidan". Cikin son na kureshi na ce "wanne gidan kenan?" A raina kuma ina cewa ba zuwan kansa bane ke nan. Ya ce "Kin ga ki bini a hankali. Na riga da na za'bi wanda nake so a zuba mini a wajena, ba dan Abba ba, da ina zan bi ta kanki tunda na gane makiyana sune abokan huldar ki. Akan Ashir zan yi matu'kar baki mamaki Wallahi". Ganin zai birkice mini, ya sanya na yi gaggawar cewa "Na wajen nawa ma ka za'ba, ni ina da wani ra'ayin ne bayan naka?" Bai iya boye yadda maganar ta sanya shi farin-ciki ba a dalilin son girma irin nasa. Nan da nan ya sauko daga fishin ya ce "Na zabi Royal blue! Na wajen ki kuma kina son Coffey?" Da sauri na ce idan ya yi maka, nasan zai yi mini". Shikenan muka shiga hira cikin nutsuwa. Ya shaida mini Abba ya bashi ku'din siyayyar da zai yi, yaushe zan raka shi na taya shi zabe? Murna tamkar na zuba ruwa a 'kasa. Na ce "koda yaushe ma in ka cire Monday da Tuesday" Ya ce "shikenan". Na ce "kwanakin nan nafi zaman gidan Anti Sakina! Idan Ina can sai ka dauke ni a can din ko?" Na tambaya cikin sigar ro'ko. Ya ce "sai na mu je da ita ta taya mu zabe kinsan bayan 'kwarewarta a wajen kazallaha, tana da taste mai kyau. Ta iya zabe". Na yi dariya sosai, yayin da shi kuma ya 'kurawa saitin kirjina ido ya ce "kin fi dacewa da Guduyo" cikin wani irin yanayi. Sai kuma ya mi'ke yana fa'din daga yau din nan duk inda zaki je sai kin fa'da mini" Da'di ya kama ni a tunanina ya riga ya fa'da sona ne irin deep din nan. Cikin sigar tsokana na ce "An gama sir". Ya yi tafiyarsa babu waiwaye illah ni da na bishi da ido, ina addu'ar na samu damar shiga zuciyar sa fiye da yadda ya shiga tawa. # Team Gudale. # Team Guduyo. # Surayya Dee. # Ana tare 🤝. 2/8/23, 10:22 - Buhainat: *Wannan littafin na ku'di ne, biya 500 ku'din karatu ta wannan asusun* *2384876855* *Surayya Ibrahim* *Zenith Bank.* *A tura shaidar biya ta wannan lambar* *08032773332*. *SDK* *33-34.* Kwanaki ka'dan Mama da Umman Danladi Nasidi. Suka yi mini siyayyar kayan kicin za'bab'bu kuma na alfarma, na dinga mamakin yadda aka yi suka za'bo unique kaya suka dawo cikin kankanin lokaci, ba shan wahala, ko rana. Da na tsananta bincike sai na gano da Aziza suka fita inda ta kaisu wajen matasan Yan kasuwar da suke kasuwwancin da babu algus, suke bin 'karamar riba. Kayan su kuma mai aminci da tsananin kyau. *Amyas newly & fairly items* 08083909947. *Umm Muhd collections* 08063358662. Na dinga mamakin yadda Aziza ta sansu, amma dana tuna itama tana dan ta'ba business din tana shiga da kayan cikin makarantar da take zuwa North West, sai na janye mamakin. Sannan sau'kin kayansu da kyaunsu ya sanya manyan mata da yanmata 'yan kwalisa suke rubibin saya. Duk wacce take bu'katar kayan kicin ta tuntu'be su. Haka nan suturu na alfarma ba a barsu a baya ba. Kina so Sister kina bu'katar sai da kayan katako na 'dakin ki, ko layan daki na hannu ki kike bukata ko tuntu'bi *Amyas newly& fairly items* a wannan lambar 08083909947. Zaki samu dukkan nau'in kayan da kike bu'kata. Tare muka fita tunda asabar ce, Yaya Al'amin ne yake tu'ka su. Inda suka ajiye ni a gidan Yayar Kwalli. Daga nan kuma gidan Sakina zan wuce, zamu fita tare da ita da kuma Yaya Sadik duk da dai sai yamma ne fitae ta mu, ina son na je da wuri ne dan ta huce gaba'daya. Muka gaisa da Yaya! Ban jima ba ta bani kayayyaki a cikin babbar leda. Tana cewa da takardar yadda zaki yi amfani da su na ciki. Na yi godiya duk da yadda kunya ta kama ni dan na gane kayayyakin mata ne a ciki kala kala. Maman Kebbi ce ta aiko mini. Jim ka'dan na ce zan tafi. Ta tashi tana fadin bari idan Yayanki Ashir na nan sai ya kai ki, ki huta yawo da wannan kaya. Ta isa bakin 'kofar falon ke nan ya shigo. Ta ce "dama kiranka zan yi, ka zo ka Mayar da Halimatu gida daga nan ka karbo mini sakon a wajen Saude". Ya kalle ni muka gaisa ya ce "ba ni mintina goma na watsa ruwa, ba zan yarda na fita haka dukun dukun da ni ba, alhalin ke kin cakare tamkar mai zuwa gasar kyau". Na murmusa na ce "Yaya Ashir na baka minti ashirin ma". Yaya ta yi dariya ta ce idan ya so ya canja launin fatarsa ya kamo ki haske ba". Ya fita yana cewa "sai na fita Yaya! Wannan duk wata hikima ce da ake yiwa Amaren zamani, amma ai kowa yasan ba ta kai hakan ba." Ya fito sanye da yadin filtex ruwan toka, ya yi kyau sosai. Ni da kaina na dinga yaba haduwar Yaya Ashir. Ya fi Gudale cika ido. Amma bai kai shi kyau da fari ba. Amma batun haiba ya kere shi. Uwa uba ya fi shi nutsuwa da sassau'kan hali. Amma ni kuma zuciyata ba shi take so ba, ba shi yake burgeta ba, hakanan ba shi take sha'awa ba. Muka fito Yaya ta bimu da fatan alheri da kuma addu'ar mu gama lafiya. A hankali yake tu'kinsa tamkar ba ya so mu isa inda muka nufa. Na kosa ya kai ni unguwar Sallari inda Sakina take zaune. Amma sai tafiya yake tamkar irin tafiyar hawainiya. Ya sassauta murya ya ce "me kike so na siya miki dan ki gane dan kin za'bi Sadik kin bar ni ba zai zama dalilin gaba a tsakaninmu ba. Sai da maganar aurenku ta bayyana, na gane ashe 'Dan Bala ne ya yi miki kamun kazar kuku. Shiyasa kika dinga nuna mini baki fahimci halin da nake ciki akan ki ba". Na fashe da dariya a fili na ce "Anya akwai wanda ya kai Yaya Sadik yawan suna?" Domin kusan kowa da sunan da yake jingina masa. Yaya Ashir ya kirne fuska ya ce "Ato ai Sadik dan bala'in gaske ne, shiyasa nake ce masa 'Dan bala. Sai dai duk bala'insa na dama shi na shanye, Ni da shi kar tasan kar ne". Na sake yin dariyar domin na san gaskiya ya fa'da. Ban ta'ba ganin wanda ya tsarewa Gudalen Umma gaba irin Yaya Ashir ba. Ina tuno wani fa'dan da suka yi a gida daga cacar baki, Yaya Ashir ya ware iya karfinsa ba fargabar komai ya warware Gudale da wani irin gigitattcen mari. Dan kawai Gudalen ya ce masa ma'katulu shegen dangi". Ai kuwa kafin ya rufe baki ya ji saukar Marin da sai da jini y kwanta a gefen idonsa na hagu. Ya masa haka ya fi sau a 'kirga, shiyasa Yaya Ashir bai cika son zaman gidan mu ba. Saboda sun dinga tayarwa ahalin gidan hankali kenan, Sadik mai raini da wulakanci ne, yayin da Ashir yake da rashin daukan raini gashi kuma da saurin hasala fiye ma da Gudale. Sosai suke 'yar tsama, basa shiri ko ka'dan. Al'amin da Abbas ne maraina wayonsa, amma Ashir kam baya ta'ba shi ya kwashe kalau. Bansan dalili ba idan akwai abin da yake yiwa Gudale ciwo to bai wuce ko da wasa ace Ashir saurayina ne ba. Ya dinga kumfar baki ban dace da wanda zuciyarsa bata da alheri ba. Shi fa ko gani yayi mun yi magana da shi ya dinga fishi da ni yana fa'din bashi ba ni. Sai da Abba ya yi shari'ar cewa "Ashir Yayana ne kamar yadda yake jin shima Wa ne a gareni. Kai tsaye ya cewa Abba "Ni gidanmu 'daya da ita, shikuma nan ba gidansu bane , tunda ba Babansa bane 'Dan gidan, dan haka a fa'da masa ya daina tsallake iyaka". Abba ya rasa gane nufin Yaya Sadik! Ya dai lura 'yar tsamar da suke yi ne yasa yake yawan yi masa gorin ai shi 'dan mace ne dan hakan ba 'dan familinmu ba ne. "Ina zamu je ki za'bi abin da kike so?" Ya katse mini tunanin da nake faman yi. Na ce "ko ina ma Yaya Ashir". Kai tsaye wani hamsha'kin store ya kai ni. Ya ce na zabi komai nake so! Na gama ruwan idona, na zabi wani ba'kin dinner set mai kyau da tsada tun a lokacin ma kudinsa ya zarce dubu talatin bare yanzu. Ya ce ya yi ka'dan na kara da wani abin. Ina tunanin me zan dauka saboda komai an saya mini, idona ya kai kan dispenser sabuwar zuwa, dan da alama new moden ce. Bata da 'kan'kanta, kuma bata cika girma ba. Ya biya kudin aka saka mana a boot muka wuce. Har muka iso gidan Sakina hira muke yi, Kuma mafi yawa ta Gudale ce, a ranar na gane Yaya Ashir bai 'kullaci Gudale Kamar yadda shi ya kullace shi ba. Asalima kamar yana masa kallon hankali ne bai gama yi ba, amma nan gaba ai ba zai yi wani abin ba. Ya rufe maganarsa da cewa "Tunda ya yi sa'a ya same ki, ai Ubangiji ya cika masa niimomin duniya, duk wani abin da ya rasa na kyawawan dabi'u zamansa da ke zasu canja shi. Amma sai kin yi hakuri, kin yi juriya, kin yi addu'a mai yawa. Tunda kina sonsa na sani komai zai zo da sauki". Maganganun sun shige ni mussaman da ya ce Ina son Gudale. Na tausasa harshe na ce "Ina sonsa fa ka ce?" Ya gyada kai ya ce "kwarai kuwa! Domin na tàbbatar sonsa ne ya katange ni daga samun ki, sannan shi ya kasance dan gata ne mai kuma sa'a. Na sani Abba zai so ki kasance matar Sadik tunda kowa ya miki shaidar hakuri, duk yadda na shaidi Abba mutumin kirki ne, masoyin zumunci ne. Na sani zai fi son Sadik a kaina, sai dai kawai ya nuna 'duk daya muke a zahiri Saboda yadda Ubangiji ya cika kirjinsa da alheri. Dan hakan banga laifinsa da ya bashi auren ki ba". A sanyaye na kalle shi na ga yadda idanuwansa suka ka'da tabbacin yana cikin alhini mai yawa. Na ce "Yaya Ashir"! Ya amsa da "Na'am" murya a dakushe. Na ce "Ina son ka gane, Wallahi ina sonka, ba wai Yaya Sadik kawai nake so ba". Ya murmusa ya ce "Na gode! Ina tabbatar miki wannan maganar zata mini fitila a dukkan ragowan rayuwar da ta mini saura a cikin wannan duniyar. Ina miki fatan alheri. Ki dauke ni tamkar Al'amin. Duk sanda kike da matsala ki tuntu'be ni kaitsaye, bana fatan ma matsalar ta same ki, sai dai dole ta kan zo ta inda aka zata da ta inda ba a zace ta ba." Idona cike taf da 'kwalla na ce "Na gode". Ina tuna maganganun Sakina da ta ce na za'bi Ashir yafi Gudale nutsuwa da Sona. Na gasgata hakan domin kuwa ru'danin da na gani a tare da shi, yafi kama da yanayin da mutum yake tsintar kansa a ciki idan ya tafka asarar abu mai tsananin darajar gaske. Har muka isa gidan Sakina jikinmu a mace yake, na dinga jin wani iri. Na sani nafi jin Yaya Sadik a raina, na fi jin nisha'di idan ina tare da shi, hakanan shi nake fatan ya rungume ni a kirjinsa. Amma a wannan ranar na tabbatar ina son Yaya Ashir ma. Mussaman da ya kasance irin mazan nan da basu da girman kan da zasu fayyace wa mace yadda suke jin ta a zukatan su. Tare da shi muka shiga gidan, sai dai Bata nan, ta je gidan Aunty Maimuna. Yan aikinta kawai muka tarar. Ya ce "To mu je na kai ki gidan. Zuciyata 'daya na amince, dan nasan idan Gudaleya ji tare muke da Sakina zai iya zuwa gidan Anti Maimuna ya same mu, muka fito. Muna fitowa daga layin sai na ga tamkar Gudale a gaban wata motar. Sai ban amince shi din bane kasancewar 'dan gefen fuskar na gani sannan gilashin motar a zuge yake rif kamar yadda tamu take a zuge. Bugu da 'Kari bansan motar ko wanda ya mallake ta ba, bayan haka da kansa ya ce sai ya yi la'asar zai fito, yanzu kuwa ko azahar ba'a yi ba. Duk nisan da ke tsakanin Sallari zuwa Badawa lay out inda gidan Anti Maimuna yake, a ranar sai na ga tamkar 'kiftawa da Bismillah har mun isa duk kuwa da ba gudu yake yi ba. Da na laluba sai na gane nutsuwar da na samu a hira da Yaya Ashir ne ta hana na fahimci lokaci mai yawa muka shafe kafin mu isa. A tsaitsaye ya gaisa da su! ya barni tare da su, dama kuma na ce ya kai mini kayan da ya saya mini gida. Tunda zai karbowa Yaya sa'ko a wajen Umma. Na rako shi 'kofar gidan ina 'kara yi masa godiya, ya shiga motar ya tayar ke nan. Ni kuma ina tsaye, ina kallonsa. Fuskata 'dauke da wani irin murmushi da yake fitowa tunda ga 'kasan zuciyata. Kawai sai ga motar nan da na gani dazu. Kafin na gama tunanina. Horn din da Yaya Ashir ya yi alamun dai gaisuwa ga Gudale ne ya katse ni. Yayin da na daskare, na sani sai yayi mini tijarar ina sauraron ma'kiyinsa. Ya fito a motar yayin da abokin nasa ya ja motarsa ya yi gaba a abinsa. Sanye yake cikin gajeran wando 3 quarter fari 'kal, rigar kuma t shirt ce mai gajeran hannu kalar lemon green. Bayan Riga kamar koyaushe an rubuta *Gudale*. Kafarsa sanye da farin takalmin da ya dace da kayan jikinsa. 'Kamshinsa na turaren Chris Adams ya baibaiye wajen. Kallo 'daya na yi masa, na gane baya cikin sukunin zuciya, dan kuwa gaba'daya idanuwansa da suke ki'dama ni, a jirkice suke tamkar dai wanda ya tashi a barci, ko kuma wanda yake cikin 'karamin maye. Ya wuce ni tamkar bai ganni ba. Na bishi a baya ina jin tamkar ya tsaya mu yi hoto saboda yadda kwalliyar da yayi ta yi matu'kar burge ni. Duk kuwa da a zuciyata ina ganin bai kamata ya fito a hakan ba. Sai dai shi a wajensa wannan shigar is common. Kusan a tare muka shiga falon. Anti Maimuna sai ina ka saka take da shi. Ni kuwa dai a farko zuwan namu ta karbe ni babu yabo, ba fallasa. Sai dai bata iya ha'diye abin da ke ranta ba. Sai da ta ce "Ta tabbatar Sakina na biyo, bata ta'ba ganina a gidanta haka siddan ba. Dan haka ta riga da ta gane inda na ajiye ta. Na yi sukuri saboda yadda take maganar cikin fishi! Da kyar na ce "ki yi hakuri Anti ba hakan bane, makaranta ce take 'boye ni". "Amma ai bata 'boye ki daga zuwa wajen wadanda kika gamsu 'yan uwan ki bane ko?" Ta tambaye ni a 'kufule sosai. Na ji duk na muzanta saboda yadda Sakina ta bagarar da ni, sannan Gudale ya kishingi'da ya ri'ke kai tabbacin bashi da lokacin da zai kare ni kamar yadda yake yi idan 'yan mutuncinsa na kusa. Na kasa magana, hawaye ya cika mini ido 'kiris nake jira a dalilin dukkansu uku na ga fishi suke da ni muraran. Tsakani da Allah kuma duk na Sakina ya fi damuna, sannan na Gudale. A dalilin Anti Maimuna dama ba wani muhimimanci ne da ita a duniyata ba, asalima ban cika ko tuna ta a cikin jerin 'Yan uwana ba. Saboda tsananin izza da wulakancinta, da kuma yadda take taya Umma wula'kanta mana uwa. Shu'dewar mintina ka'dan muna zaune jigum jigum. Na mi'ke jiki a sanyaye na ce "Na tafi". Ai kuwa nan da nan Anti Maimuna ta sake hawa, tana fa'din maganganu wai ba dama a mini maganar gaskiya sai na 'dau fishi, saboda kawai mu 'yan gadara da isa ne, aiki ya samu mijina. Sai lokacin Sakina ta ce "Ya isa haka Anti dan Allah! Ke Halimatu koma ki zauna, tare zamu tafi". Na koma na zauna ina jin takaicin ke 'din da Sakina ta ce mini alhalin tasan bana son a ce mini ke. Komawar da na yi na zauna 'din bai yiwa Anti Maimuna ba sai da ta 'kara da fa'dawa Sakina cewa "Ai dama wajen ki ta zo, na tabbatar idan na rantse ba zan yi kaffara akan tasan kina nan ne, shiyasa ta zo mini". Ha'kuri dai Sakina ta bata da 'kyar ta bar maganar bayan ta ja kwafar da take isharar tana ciki da ni. Ta kalli Yaya Sadik ta ce "Gudalen Umma how far?" Da 'kyar ya bude idonsa da suka sake jirkicewa ya ce "Bana jin da'din yanayin ne, kuma kamar zazzabi nake ji." Ta tashi da sauri ta dauko masa ruwa da pracetamol, a baki ta bashi tsabar gata. Ni da Sakina muna kallonsu. A zuciyata kuma na sani hakan ba zai hana idan ta yi masa abu sa'banin ra'ayinsa ya nuna mata iyakarta ba. Sakina ta mi'ke da nufin shiga toilet. Yayin da Anti itama ta yi kicin ta mayar da tumbler din hannunta, sannan ta saka 'Yar aikinta ta shiryo mana abinci da kuma ruwa da lemo, da ta fito sai ta shige 'daki wajen Sakina. Kamar jira nake yi su bamu waje. Na muskuta na ce "Yaya Sadik sannu! da alamun kana jin zazzabin nan." Ya 'dago kansa da kyar cikin muryar gargadi ya ce "Kar ki sake bu'de bakinki da nufin yi mini magana! Na riga na barwa Ashiru ke, dama dole aka yi mini, yanzu kuwa ba zai yiwu na aure ki ba, alhalin na tabbatar kina tarayya da wani 'katon da zuciyarsa bata nufina da alheri. Ke ko zumuncin ma bana bu'katar yinsa da ke. Na yafe ki. Me za'a yi da wacce kullum sai ta jefa zuciyarka cikin 'bacin rai da firgici. Ba zai yiwu ace kina jefa ni cikin garari da jinya ba. Last warning! ki kiyaye Ni". Na manta kashedin da ya yi na kar na yi magana. Da sauri na ce "ka daina saurin hassala, ka daina yanke hukunci cikin zato Yaya Gudale! Gidansu na je shine Yaya ta ce ya dawo da ni gida fa. Kuma saboda Allah sai na ce ba..." Ai kuwa ban 'karasa ba, a dalilin yadda ya yi wani tsalle ya sha'ke mini wuya, da 'karfin gaske na dinga 'ko'karin 'kwatar kaina amma ina, 'karfin nasa tamkar na mashayin 'kwayar Tramol ne." Tun ina juriya har na gaza, na dinga wani irin 'ka'kari, shima na kasa a dalilin na fara galabaita. Sama sama nake jin yana cewa "Gara na kawar da ke, da gallaza mini da kike yi. Allah wadaran Ashiru! Allah ka gigita mini shi, fiye da yadda ya gallaza mini, yake 'kuntata mini". Kamar daga sama Anti Maimuna ta diro cikin falon, da azama ta iso, sai dai duk yadda ta so ya sake ni, bata samu dama ba. Yadda Anti take maganar ya sake ni cikin kara'di ya sanya Sakina ta fito a hanzarce. Bata yi yun'kurin saka hannu don ta 'kwace ni, kamar yadda Yayarsu take yi ba. Ranta a bace ta ce "Na Moriki saketa"! Ta sake maimatawa nan ma bai ji ba, yayin da ni kuma nake 'dan'dana ku'data. A kufule ta ce wa Anti "matsa. Da sauri ta matsa, tana cewa "Sosai ya sha'keta, Gudale kar ka yi kisan kai mun shiga uku". Sakina ta ri'ke hannunsa idonta cikin nasa ta ce "Yi ha'kuri ka saketa sai mu yi magana". Ga mamakina da Anti Maimuna sai kuwa ya sake ni, ta hanyar ingiza ni na fa'do daga kan kujerar. # Team Gudale. # Team Guduyo. # Surayya Dee. # Ana tare 🤝. 2/8/23, 10:23 - Buhainat: *Wannan littafin na ku'di ne, biya 500 ku'din karatu ta wannan asusun* *2384876855* *Surayya Ibrahim* *Zenith Bank.* *A tura shaidar biya ta wannan lambar* *08032773332*. *SDK* *35-36* Na dinga numfarfashin wahala da 'bacin rai. Na kifa kaina akan lallausar kafet din da yake shimfide ina kuka sosai. Kukan da ya ta'ba Sakina 'kwarai da gaske. Ta dago ni, ta zaunar da ni akan kujerar da ta yi nisa da wacce Gudale yake kai. A hankali ta ce "Me kika yi masa?" Na kasa bu'de baki na yi mata magana a dalilin yadda nake kuka sosai. Ta dinga lallashina, tare da shafar bayana, sai da ta ga na 'dan sami nutsuwa. Ta mike ta koma kusa da Gudale da shima yake faman haki saboda yadda yake cikin fishi. A hankali ta ce "Na Moriki! Annabi (S.A.W.). Ya yi ta jan kunnenmu kar mu zamo masu saurin fishi. Idan kuwa har mun yi fishin to mu kiyaye zartar da hukunci a sadda muke cikinsa. Na ro'ke ka! Ka daina biyewa zuciyarka a sanda kake cikin fishi, saboda Allah abin da kake yiwa Halimatu fa bai kamata ba. Kwanakin baya a gabana ka mareta. Yanzun kuma ka sha'keta ko matarka ce ita fa ka wuce iyaka, bare ba hakan bane, gaskiya wannan cin mutunci ne, na sani ba zaka so a ce wani ne yake yi mata hakan ba". Ya zuba mata ido cikin fitar hayyaci ya nuna ni ya ce "Indai bata kiyaye ni ba! Ina tabbatar miki watarana sai na sumar da ita. Na ce kar ta mini magana, amma saboda raini ya shiga tsakani na da ita, sai da ta yi". Ina kallon yadda Sakina ta tsananta kallonsa ta ce "wai har yau maganar ba ta wuce ba ne? Saura kwanaki ka'dan ku zama abu guda kai da ita, idan kana irin haka hankalin iyayenmu ba zai kwanta ba Na Moriki". Da sauri ya ce "Allah ya sauwa'ke na zama abu guda da wannan munafukar yarinyar, muguwa kuma ma'hainciya". Tsoro ya kama Sakina a dalilin furucin da yake yi a kaina. Ta kalle ni, ta ga na yi sururu ido duk ya ya ko'de. Ta mayar da kallonta gare shi, cike da son jin mai ya kawo wannan takaddamar. Ta ce "Saboda Allah me ta yi maka Na Moriki?". Kamar ba zai yi magana ba, sai kuma ya tunzura ya ce "Ba 'dazu na yi miki waya akan ke da ita zaku raka ni na sayi kayan da zan saka a biki ba? Tunda haka Abba yake son na yi, na amince har zuciyata, tare zamu je da ku. Na je jiya takanas na sanar mata, da kanta ta ce mini, zata zo gidan ki da wuri, sai mu yi amfani da motar ki, tunda weekend ne kina gida! Tun 'dazu nake buga mata waya. Amma ta 'ki 'dauka, ashe tana can tana yawon barba'da hadi da iskanci da Ashiru! Ni zata wulakanta? Sannan ta zo ta ce zata mini maganar banza". Ya karasa cikin matsanancin bacin rai tamkar ya rushe da kuka . Tsawon lokaci Sakina tana kallonmu duka. A ranar ta fahimci Gudale yana sona, amma bai fahimci yana son ba bare ya tattala soyayyar. Ta gane matsanancin kishina ne ya turnike shi. Ta dan samu sau'kin ru'danin da take ciki na zan auri wanda ba ya so na. Ta sassauta murya sosai ta ce "Ashir din ne kake wannan tashin hankalin dan ka gansu tare, shin ba 'dan-uwanta bane?". Da hanzari ya ce "Gara na ganta da Anas akan na ganta da shi. Ta sani Ashiru idan ya samu damar da zai 'batar da ni tsab zai aikata hakan saboda yadda yake tsananin adawa da ni". "Ka sassautawa kanka akan wannan kiyayyar da kake yiwa Ashir baka san ranar da zai yi maka ba". "Wallahi Sakina duk wani arzikin da zan same shi matu'kar sai ya biyo ta hannu ko hanyar Ashiru to na haramtawa kaina wannan arzikin". Ya ja tsaki sosai. Ya sake cewa har zuciyata bana sonsa, mutumin da ya zame mini cikas, sannan dake zuciyar sa 'baka ce, duk matan duniya bai ga wacce zata burge shi ba sai wannan abar" Yana nuna ni, yana 'kyabe baki, ido kuma sun kankance tsabar masifa. Ya sake zabura ya ce "Sakina In Sha Allah Ashiru ba zai yi albarka ba, ba zai rabauta ba, tunda juninsa nunkufurci ne da izgilanci". Sakina da ta fahimci Kishi ne yake yagalgala shi, sai ta takaita maganar ta hanyar cewa "To na kashe wannan maganar, amma Wallahi idan ka sake yi mata irin wannan sha'kar tabbas sai Abba ya ji, ai kishi ba hauka bane". Ya kuwa tunzura ya ce "Ummu" kina jinta ko?" Dake haka yake kiran Anti Maimuna Kamar yadda su Abba suke kiranta. Wanne kishi zan yi akan wannan yarinyar, ba sai da so ake kishi ba? Sanin kowa ne auren dole za'a yi mini, takura mini aka yi, yanzu kuwa zan na'de kafar wando na tan'kwabar da auren idan yaso a mini baki na dinga tsince tsince a kwararo kwararo. Allah barshi a dinga nuna Abba ana ga wanda ya tsinewa tilon 'dansa akan ya'ki yarda ya yi masa auren dole". Anti Maimuna ta ce "A a ba hakan za 'a yi ba, ka kwantar da hankalinka, ka bi umarnin Abba! Kana ganin wanda ba su kai ka a jikinsa ba ma yana kirarin ya isa da su. Tunda musulunci addinin adalci ne, ya baka damar auren mace sama da daya, daga baya sai ka auri zabin ranka". Tana direwa Sakina ta ce "Anti ki fa iya bakinki! Kar ki zo ki ji kunya" Yayin da nake gefe ina fama da 'bacin rai sosai a raina, na dinga jin tabbas idan har Gudale ya mi'ka kudirinsa na fasa kar'bar aurena gaban Abba. Ni kuwa zan taimaka masa dan Abba ya rushe maganar gaba'daya. Zan fadawa Abban nima na fasa, na yarda ya mayar da aurena kan Ashir! Na gaji da bala'in Sadik. Nan gaba idan ban yi sa'a ba, shine ajalina. Raina ya sosu 'kwarai da abin da ya yi mini, mussaman yadda yake ta nanata baya sona. "A hankali na ce "Nima ai dole aka yi mini! Amma saboda girman Abba ya zarce komai, shiyasa ban bude 'kofa ko guda da wani mahalu'kin zai fahimci hakan ba. Na yi maka al'kawarin matu'kar ka fa'da masa ka janye aurena, ni kuwa ba zan ji kunyar fa'da masa dama ba so nake yi ba. Ina tabbatar maka kuma a ranar da aka sanya ta aurenmu, ba fashi a ranar zan yi aure. Domin ina da masu sona da ko a ranar ka ce ka fasa, su kuma zasu kar'ba cikin murna da godiya mai yawa." Maganar ta buge shi ya mi'ke a harzuke Sakina ta ri'ke shi tana fa'din "Ba zaka sake ta'ba ta ba". Na sake hassala na ce "Bar shi ya doke ni, ya janyowa kansa fishin Yaya Ashir dan kuwa sai na fa'da masa, idan ka fi karfina, ai shi baka fi 'karfinsa ba." Hatta Sakina ta ka'du da kalamaina, bare Anti Maimuna da kuma Madugu uban tafiyar. Ni kuma shak'enin da ya yi ne, ya 'bata mini rai har nake jin zan iya fa'da masa komai. Ya dinga 'ko'karin isowa inda nake zaune, yayin da Sakina take ingiza shi. Ni kuwa Ina zaune ko gezau ban yi ba, Ina jin na shirya faruwar komai. Anti Maimuna ta ce "Tashi ki koma daki, kar ya zo ya miki abin da za'a ce bai kyauta ba alhalin kema tsiya ce fal cikinki". Haushin ta ya sake tunzura ni, na ce "Da yake anan ne, amma da a gidan Sakina ne na tabbatar ba zai ma fara ta'ba ni da sunan duka ba, bare har ya yi mini abin da zai zama kaico". Ta nuna ni da yatsa ta ce "ki shiga hankalin ki! Ni zaki yiwa rashin kunya?" Na yi 'kasa da kai ina gungunin ta yi hubbu ra'as tsakanina da Gudale ma'ana ta nuna son kai. Ta yi sororo tana mamakin abin da na yi mata wata'kila bata ta'ba zaton zan iya yi mata hakan ba. Ni kuma abin da bata sani bane na da'de ina son na sami dama akanta dan na nuna mata ku'di da mulkin mijinta bai ta'ba sawa na yi mata wani kallo na daban ba, da ya wuce gidanmu guda. Bana fatan na zo gaban ta da sunan ta yi mini kowacce irin alfarma tunda bata ganin darajar iyayena mussaman uwata. Ni kuwa ba abin da zai sa na ji nauyin yi mata iyashege idan ta shiga harka ta. Na sani yanzu gadara zata dinga yi mini a matsayin ta na yayar Gudale. Ni kuwa idan an 'kaddara ma ya zama mijin nawa, ita da Anti Juwairiya na sani baza su so ni ba, bare su mini karar ni kanwarsu ce ba wai matar kaninsu ba. Dan haka ba zan takura kaina sai sun so ni ba, bare na yi ta yi musu fadanci da biyayyar dole. Akan idona take fa'din bayan aurenmu ya nemo zabinsa ya aura. Na kalli Gudale yaddda ya rungume Sakina yana sakin ajiyar zuciya! Ba kuka yake ba, amma yana cikin matsanancin tashin hankali. Na da'de da gane duk da Sakina ba wani finsa da yawa ta yi ba, yafi sonta yafi raga mata. Da kyar ta lalla'ba shi ta sanya direban Antin ya kai shi, akan muma zamu zo yanzu. Tashin hankali sosai Gudale ya yi akan wannan maganar, tun ina ganin abin wasa ne, har na gane da gaske yake yi, domin yadda yasa abin a ransa sai da zazzabin takaici ya kwantar da shi. Har sai da iyaye suga shiga maganar domin kuwa kafewa ya yi, ya fasa auren. Ni ma kuma na kafe akan na fasa din bana so. Duk da a zuciyata ba hakan bane, domin har addu'a nake yi Àllah ya nuna ikonsa auren ya tabbata. Da kyar Abba da Baban Gusau suka daidaita lamarin. A tsukun motarsa ta iso. Saboda lalallaba shi da Abba yake yi, ya sake ha'da masa da sabuwar wayar da tafi kowacce daraja. Ya Kara masa yawan ku'din sayayyar da zai yi. Duk da hakan ba irin borin da bai yi akan a jawa Ashir kunne, ya kiyayi shiga lamuransa ba. Aka cigaba da shirye shiryen biki, babu wata fahimta ko shiri a tsakanin ango da Amarya. Kawai Abba ne yake ta kokarin daidata mu, domin nima an gyara mini waccan motar ta dawo tamkar sabuwa, to dama ba'a jima da sayanta ba, gata ya sanya mai ita ya ce ba ya sonta. Hatta waya nima Abba ya canja mini, amma bata kai darajar ta Gudale ba. Maimkon Yaya Sadik ya huce saboda wannan tagomashin da ya samu, sai ya sake gindaya gaba mai tsananin gaske a tsakaninmu. Saboda wai na ci amanarsa, na kuma yi masa rashin kunya, ashe wasa farin girki. Tanadin tsiyar da yake mini masu girma ne. Duk hidimar bikin ta bangaren Gudale Abbas ne yake yinta a dalilin Yaya Al'amin baya jin da'din ko in kula da Gudale yake nunawa auren, shiyasa shima ya ja ya dake, ya fake da hujjar tunda ni ce amaryar ba zai shiga harkar yara ba. Fa'din yadda aka shirya mana gidanmu bata baki ne. Domin yadda gidan ya tsaru, haka aka sake kawata shi da jere na alfarma. Tun sauran kwana goma masu shirya gida suka je suka shirya shi. Kwanaki ka'dan dangin Mama suka je, Suka jera mini kayan kicin da sauran tarkace irin su zannuwan gado, da su frames masu tsada. A bakinsu nake jin haduwar gidan, mussaman Aziza da ta jani 'daki. Tana cewa "Gidanki ko a birnin Santabul ya kai gida sis". Na dinga dariyar Aziza saboda iyashegenta. Tun a wannan rikicin na fara gane zuciyar Yaya Gudale mai 'kullaci ce, mai wahalar a gane inda ya dosa ne. Amma so ya sa idona ya rufe, na kasa yin jarumtar ha'kura da aurensa dan shine zai fi zama alheri. 2/10. Aka 'daura aurenmu a massalacin Dangi na Aliyu bin Abi Dalib. Daurin auren da ya samu dafifin al'umma. Hatta abokan kasuwanci da karatun Abba na 'kasashen k'etare sai da suka halarci 'daurin aurenmu. Zuwa wannan lokacin Sakina ta ware da ni, sosai take hidimar bikinmu ka'in da na'in. Kusan komai na hidimar bikin ita Abba ya 'dora, da taimakon Antin Zaria. Shiyasa Umma bata samu damar yiwa bikin rikon sakainar kashi ba. Abinci da nama tamkar wanda Abba ya yi shekaru masu dama yana tanadinsu, Raguna aka dinga yankawa sai a bankare su ana gasawa, kowa sai da ya yanki yadda yake so. Bare kaji da kifi. Ruwa da lemon kuwa wanka ne ba'a yi da su ba, hatta almajirai sun tabbatar bikinmu na ya'yan gata ne. A aurenmu ba batun a 'boye wani nau'in a abinci a bawa wasu isasshun mutane. Abincin da ake bawa manyan mutane, hakan ma talakawa suke zuwa su dibi da kansu. Mafi yawa mahalarta bikin sun fi kwatanta shi da bikin Tsohon Gwamnan jaharmu Mahmoud shinkafi da amaryarsa Takwarata Halima Babangida. Saboda ba karamin bajinta aka yi ba. Kowa sai da ya gamsu bikin na yan gata ne saboda yadda Abba ya kambaba shi. Haka Sakina kusan duk bayan awa biyu zata saka na canja kaya, ga mai kwalliya a gefe, mussaman da aka yi sa'a aka tanadar mini wasu irin mayuka da powder na garari masu 'kara kyau da taushin fata, sannan basa bari na yi gumi bare aje ga jallin kwalliya ta cabe. Kai madallah da kayan oriflame mussaman jakadiyarsu *Aisha lame *da zata nuna miki nau'in da suka dace da fatarki ga turaruka masu sanyin kamshi. *07036662633* Abin da ya yiwa auren cikas daya. Rashin walwalar ango, domin gaba'daya ya ki yarda ayi hidimar cikin walwala. Ko dinner din da aka yi daren jiya. Da 'kyar aka sanya ya halarta, haka ya zauna fuska babu annuri duk da yadda yake sanye da tufafi na kololuwar daraja, sai daukan ido muke yi, amma babu farin-ciki a kan fuskokinmu. Tun ranar alhamis ake biki. Ranar asabar din daurin auren da yamma Su Abba da Baban Gusau, da Yaya, da Maman Kebbi da kuma Babanmu. Suna zaune a falon Abba cikin matsanancin farin-ciki. Sadik suka sanya a gaba da nasiha iri iri. Akan ya zauna da ni lafiya cikin adalci. Ba'a jima ba Yaya ta iso dakinmu da muke zaune da 'kawayena mafi yawansu counsins 'dina ne da kuma Sakina da ta saje cikinmu, saboda bata da wani jiki duk da dai doguwace sambal. Na saka dankareren leshin da aka samo shi a *Amyas newly & fairly items*. Dinkin ya yi matu'kar zama a jikina mussaman dana kasance mai fafffadan kugu. Riga da zani ne, amma idan aka daura zani sai a rantse doguwar riga ce. Ankammala gyara mini daurin 'an kwali kenan Yaya ta iso cikin dakin ta ce "na ta so ". Da sauri Sakina ta ware wani hadadden mayafi tsadadde cikin order *Umm Muhd collection* Haka ma takalmi da jakar da na sanya a wajenta aka samo su. Wani irin kyau na yi ba 'dan ka'dan ba, sai walainiya nake yi. Komai ya yi fiye da yadda ma na zata. Sakina ta dauko turaren da ta zuba mini su a lefe. Ta fesa mini ka'dan, nan da nan 'daki ya kaure. Hatta Yaya sai da ta ce "Sakinatu wannan turaren na alfarma ne, da alama ya lashe ku'di masu nauyi, sai dai Kuma ya ci kudinsa, abin a saya ne". A hankali ta fa'di sunan turaren, ta san turarukan oriflame amma bata san wannan ba. Yaya ta ce fa'da mini sunansa Sakina! Zan fa'dawa Juwairiya ta saya mini ko Ashir". Da murmushi Sakina ta ce "Ni zan siya miki Yaya! Ai basu ka'dai ne yaranki ba". Da annushuwa Yaya take cewa "Sakinatu 'diyar Abba! Allah ya miki albarka, ya albarkaci zuri'ar ki". Cike da farin ciki ta amsa da "ameen". Amma dai Sakina fa'da mini sunan turaren ko Ashir zai daure ya sanya a lefensa". Da dariya Sakina ta ce "Ho Yaya! To ki kwantar da hankalinki da kaina zan siyo masa indai yana so. Ri'ke ni Yaya ta yi muka fita, har falon Abba! Kowa ya bu'de baki a cikinsu zai yi mini shaidar ha'kuri! Suka dinga nanata ha'kurin da nake da shi yanzu zai ninka na da ne. Tunda zaman aure ha'kuri shi yafi komai yawa a cikinsa. Shikuma mai girma Ango jan-kunnen da aka fi yi masa shine ya zama mai sassauci da afuwa. Ya yi mini adalci tunda dama kanwa nake a gare shi. Idan na yi masa kuskure kar ya 'dauki mataki a cikin fishi. Duk abin da ya taso mu yi kokarin magance shi a tsakaninmu, idan hakan ya ci tura sai mu saka wanda muka amince da nagartarsa. A take Baban Gusau ya mi'kawa Yaya sadakina tunda shine waliiyina, inda wani abokin Abba 'dan Sudan ya karbawa Yaya Sadik auren. Bisa al'adar gidan amarya ake bawa sadakinta a hannunta kafin a kaita dakinta. Ta miko mini tana cewa "karbi sadakinki da Bismillah Halimatu". Kaina a 'kasa cikin lullubi na karba din, ban duba ba, na mikawa Maman Kebbi! Ita kuma sai ta bayar a baka daga baya. Baba dai bai ce komai ba a dalilin duk shine karaminsu, illah albarka da ya sanyawa auren da kuma fatan alheri. A lokacin Abba ya ce "Yaya Idan kun yi sallar la'asar ku shirya ku kaita, ba sai duhu ya yi ba". Ai kuwa Yaya Sadik ya ce "Abba! Sai kuma ya yi 'kasa da kansa, ya kasa maganar. Cike da kulawa sosai Abba ya ce "me zaka ce Sadiki? Fa'di muna sauraron ka". Kansa a kasa, a hankali ya ce "Dan Allah Abba bana son gayyar nan da sunan rakiya plz". Cikin rashin fahimta Abba ya ce "rakiya kamar ya ya, wacce irin gayya Kuma?" Bai dago ba ya ce "Ni bana son wannan dafifin da sunan kai amarya". Da sauri Abba ya ce "Tunda al'ada ce kuma musulunci bai hana ba, ban ga aibun sa ba. Ina ce yau ne kawai, gobe zasu sake rakata ne?" Yaya Gudale ya yi kasa da kai ya 'ki tankawa dokin hukuncin bai yi masa dai-dai ba". Yayin da zuciyata take luguden fargaba wato so yake na tafi ni ka'dai ko yaya ne nufinsa? # Team Gudale. # Team Guduyo. # Surayya Dee✍️ # Ana tare🤝 2/8/23, 10:23 - Buhainat: *Wannan littafin na ku'di ne, biya 500 ku'din karatu ta wannan asusun* *2384876855* *Surayya Ibrahim* *Zenith Bank.* *A tura shaidar biya ta wannan lambar* *08032773332*. *AMYAS NEW & FAIRLY ITEMS* *Suna sayar da atamfofi da lesina da kuma dogayen rigun na alfarama* *Haka nan suna siyan kayan electronics idan kina bu'katar canji, ma'ana zasu kayan ki cikin daraja, sannan zasu sayar miki da nasu cikin farashi mai rahusa.* *Hatta kayan furnitures, suna siya, suna sayarwa* *Kina son siyan fili ko gida?* *kuna neman gidan haya?* *Kawai tuntu'bi mahukuntan a wannan lambar* *08083909947*. *SDK* *37-38.* Baban Gusau ya ce "Sadik kana son mutane 'kalilan su raka ta ne?" Ya kasa magana a dalilin kwarjini irin na Baban Gusau. Abba ya ce "shikenan Yaya da ke da Binta ku rakata duk mai son zuwa sai ya je daga baya". Jin hakan ya saka Gudale 'dagowa ya ce "Dan Allah Abba zan tafi da ita". Kafin kowa ya ce komai Abba da Baban Gusau sun ce "Madallah! Ko wani gidan za'a kaita ai zamu iya wakiltaka ka kaita dakinta, bare kuma dakinka zaka kaita da kanka, ai ba darajar da ta wuce hakan". Kawai sai ji na yi Baban Gusau ya riko kafa'data ya mi'kar da ni, bayan ya ru'ko hannun Sadik ya mike, ya kama hannuna ya dam'ka a nasa. Ya ce gata nan tafi ka kai ta! Amanarta na baka, nine Ubanku dukkan ku, sannan kuma nine wakilinta, ba wanda zan sassautawa a cikinku idan na same shi da laifin musgunawa 'dan-uwansa. Allah ya albarkaci aurenku, ya sanya albarka da farin ciki a gidanku". Hawaye ya balle mini, wanne irin abu ne haka Yaya Gudale ya yi? Ba kunya ya dinga ja na, maimakon ya fita da ni ta ta waje, saboda sau'kin jama'a. Sai ya bi da ni ta cikin gida, ta inda ake shiga garden. Aka dinga kallonmu. Muna shiga ya rufe 'kofar, sannan ya ja ni fii har ba'kin 'kofar mashigar falon. Ya sanya key ya bude. 'Kamshi ya bugi hancina. Muna shiga ya wancakalar da hannuna tare da cewa sai ki laluba dakinki, ko ki tabbata a nan" Ya isa bakin kofar ya tura ya rufe har da murza key. Ya wuce cikin sauri ya barni a tsaye tamkar gunki. Da kaina na tambayi kaina wacce irin amarya ce ni? Na jima a tsaye na rasa inda zan sanya kaina. Na dinga tuno 'kawayena da na halarci kai su dakin aurensu. Ta yadda ake zama da su a dakunan su, ana hira da farin ciki. Su kuma suna zaune a gefen gadonsu da ya sha lullubi na alfarma. A karshe iyaye su watse, su bar amarya da 'kawayenta ana ta hira cikin shakiyanci. Ba a barin amarya sai abokan ango, sun zo an sayi bakin amarya. Sannan a mayar da su gida bayan an yi musu alheri. Amma ni nawa kawayen ma suna can na barsu ko sallamah bamu yi da su ba. Gashi hannuna babu waya tana wajen Sakina. Kan dole na ja jiki na shiga dakin da Sakina ta ce mini shine dakina na kasa. Na tarar da anyi shimfida ta alfarma, akan dankareren gado. Na fa'di jagwab ina jin hawaye na goce mini. Ban taba ganin doguwar rana irin ranar da aka na shiga gidan aurena ba. Ba dan komai ba saboda yadda nake Jin tsananin takurar da na yi. Na da'de kafin na ji ana kiran sallar la'asar. Na tashi da 'kyar na doro alwallah, na kalli mayafin na tabbatar ba zai mini sallah ba. Na rasa yadda zan yi. Na bu'de drower na tarar da kayana na gida wanda nake sonsu da Sakina ta kawo su tun wanccan satin reras a jere. Na 'dauko hijabi na tada sallah. Na idar, ina kwance lamo. Ina jin wani bacin rai na saka'da ta, na rasa gane manufar Gudale ta yi mini irin wannan wulakanci, ya rabo ni da cikin jama'a, sannan ya zo ya rufe ni. Ya kasa marabta ta a matsayina na bakuwarsa a ranar farkonmu. Hawaye ya dinga gangaro mini, ina tunanin wacce rayuwa zan yi da mutumin da na kallafa shi a raina, alhalin shi bai san sassauci ko ragayya ba?. Biyar ta wuce na jiyo muryar Gudale a falo saboda ban rufe kofar dakin ba, sannan da 'karfi yake maganar. Da na kasa kunne sai na gano waya yake yi, kuma da Sakina. Ya 'daga murya sosai ya ce "Wallahi ba wacce zata zo mini gida a yau dai. Duk nacin ki, bazan bu'de ba, idan kayan ne da gaske ki bawa Abbas, idan na fito sallar maghrib zan karbar mata". Bansan me ta ce masa ba. Na ji yana cewa "Eh na ce gidan nawa, da na ki ne?" Ya katse wayarsa, ina jinsa har aka fara kiran sallar maghrib, sannan ya fita. Yana fita kuwa aka dauke wuta, na rasa inda zansa raina, zafi, da duhu suka yi mini 'kawanya. Ko bai rufe ni ba, ba iya fita zanyi ba, bare ya rufe ni ruf. Bai shigo gidan ba sai da aka idar da sallar isha da lokaci mai tazara. Ya dawo yana haska gidan da fitilar wayarsa. Yana janye da akwatin kayana. Har cikin dakin ya shigo ya ajiye akwatin a tsakiyar dakin. Sannan ya juya ya yi tafiyarsa, ba wani magana ba komai. Hawaye ya silalo mini, kafin na yun'kura na ga an dawo da wutar. Hakan ya bani damar ganin jakar hannuna a gefen akwatin, da kuma wata farar leda. Jikina na bari na janyo jakar, na bu'de na 'dauko wayata. Na sake dauko ledar na bu'de na ga lemo mai sanyi, da kuma ruwa, sai wata 'yan robobi guda biyu. 'Daya dauke da pepper chicken, 'dayar kuma wainar shinkafa ce, ga yajin kulikuli an nade shi cikin poil peper. Na manta ni amaryace, na dinga cusa wainar nan da ta yi mini da'di ba ka'dan ba. Ina ci, ina zare ido tabbacin yinin yunwa na yi. Na cinye, na ji ba inda ta je mini. Na koma kan aminiyata kaza, nan ma sai da na ci karfinta, sannan na ji ta ishe ni. Na kora da lemon fanta. Sannan na yi gyatsa, na yi Hamdala. Sai na tsinci kaina da yiwa duk wanda suke zama da yunwa a dalilin jinya ko talauci addu'ar samun sassauci. Yunwa masifa ce, mabudin aikata barna ce, Allah ka wadatamu da lafiya da kuma 'koshi. Na kishingi'da ina Jin sau'kin damuwar da nake ciki. Sakina ta fado mini, ina jinjina yadda ta damu da ni, na tabbattar Sakina tana mini so irin na wanda kuke same parents. 'Kwalla ta cika mini ido ina jin wani irin al'amari na shiga jikina akan halayyar Sakina. Ta aiko mini da abinci, saboda ta san na yini ban ci ba, ta kuma sani 'kaninta ba zai damu ya ciyar da ni ba, duk kuwa da hakkin akansa ya rataya. A fili na ce "Allah ka wanke mini zuciyata! Allah ka cika mini ita da alheri kamar yadda ka cika zuciyar Sakina da Abbanta Na shiga 'bandaki na wanko hannu da bakina. 'Kasan kafet din na kishingi'da ina duba wayata, ina kallon status 'din jama'a dauke da hotunan bikina suna mini fatan alheri. Ni da kaina mamakin kaina nake yi, saboda yadda na yi wani irin shu'umin kyau, kyaun fatata na matu'kar ki'dima ni. Madallah da mayuka da kayan gyara na *Aisha lame da Faseelat*. Ban 'bata lokaci sosai ba, na kashe datar na fito da caja na jona caji. A inda nake kwance barci mai nauyi ya yi awon gaba da ni. Ban farka ba, sai karfe shida na safiya. Na tashi ina istigifari, tare da tunanin wanne irin barci na yi haka, da ban ji 'Kiran sallah ba? A gurguje na 'doro alwallah! Na tada Sallah. Na idar, ina zaune ina zikirin safiya. Na kammala ina sake jin barci na 'diba na, ban yi mamakin yadda nake barci ba, saboda yadda na tara shi ba ka'dan ba. Na sake kwnaciya, ina mamakin yadda na iya kwanciya da kayan jikina. Ban sake gane inda nake ba sai takwas da rabi na safe. Na bu'de akwatina na fito da tawul da setin kayan wankan oriflame wanda suka dace da farar fatata, ya kuma dace da dry skin 'dina. Na shiga ban'daki, cikin Sa'a na kunna hita ba jimawa kuwa ruwan zafi ya iso famfon. Na sirka ruwan wanka mai dumi sosai dan na wartsake gajiyar da nake fama da ita. Na fito wankan daure da tawul, cikin nutsuwa na shirya, na yi matu'kar kyau cikin jan tattausan swisss material kirar kasar Dubai odaer din *Amyas newly & fairly items*. Sabon da na yi da siyayya a wajen *Amyas* na 'karyata batun da ake cewa kayan mata yafi tsada. Na dauko turare ina fesawa na dinga jiyo ana kwankwasa kofar falon, na yi kamar na fita na bu'de sai kuma na fasa, a dalilin fargabar ha'duwa nake yi da Gudale. Na zauna bakin gado ina sake jin kwankwasa kofar na sake tsananta. Kafin na yi wani abu, na ji wayata ta hau kuwwa, na tashi na dauko ta akan madubi. Ina dubawa na ga Yaya Sadik ne. Zuciyata ta harba da tsananin gaske. Na daure na amsa, na kanga a kunne. Cikin fa'da ya ce "Ba ki ji ana kwankwasa 'kofa bane?" Na ma'kal'kale murya na ce "Ban ji ba! Barci nake yi". Ya ja uban tsaki ya ce "Mai 'karya dai 'dan wuta, turaren uwar waye ya ke kawo mini ziyara har nan?" Na sani turaren da na sanya ne saboda yadda yake da kara'de waje cikin 'kan'kanin lokaci. Amma na waske na ce "Anya kuwa? Bansa turare ba fa". Ya ja tskai ya ce "Munafuncinku ya 'kare a kanku ke da Sakina". Na yi shiru ban amsa masa ba, illah iyaka na ji da'din yadda turarena ya isar mini da sa'ko a wajensa. Ya ce "Zaki fito ki bu'de ko kuwa?" Na shagwabe murya na ce "Fisabidillahi ina ba'kuwarka, kuma amarya ka ce na fita bu'de 'kofa da sassafen nan, sai ka ce Amaryar buzuzu?" Da sauri ya ce "Oh kin dauka kin kai ta buzuzu a wajena? To amaryar buzuzu ta kere ki, tun jiya ya kamata ace kin fahimci hakan". Na murmusa ka'dan na ce "Ina tausayinka ranar da zaka zama tamkar ango irin *Ayu*. Ni kuma a ranar zan baka raddin na wuce duk yadda kake tunanina." Da hanzari ya ce "Guduyo menene *Ayu* kuma?" Dariya ta so kwace mini saboda yadda ya yi tambayar a 'dan tsorace. Na ce wani halittar Allah ne mai tsananin son mace, mussaman matarsa". Ya nisa ya ce "A wanne jinsin yake?" Na ce "ba mutum bane, sannan ba jinnu bane" "Wato dabba ne ko?" Na yi shiru. Ya nisa ya ce "Ni kika kwatanta da dabba?" Jikina ya yi sanyi na ce ba fa dabba bane. Ya ja tsaki mai'karfi tare da cewa "Duk iyashegen da kike ji da shi, sai na sauke miki shi wallahi. Zan je na tambayo menene *Ayu* sai na gano ma'anarsa sannan zan dauki mataki". Na yi maza na ce "Amma dai idan ka tashi neman ma'anar kar ka saka sunana a ciki". Ya ce saboda kinsan al'amarin bana mutunci bane kenan?". Ya yi kwafa ya kashe wayarsa. Kan dole ya je ya bu'de kofar, ya tarar da Iman diyar Anti Ramla dauke da basket din kayan karin kumallo. Ta duka ta ce "Uncle ina kwana? Ga shi in ji Antin Zaria". Ya karba, ba tare da ya ce mata uffan ba. Ta juya ta tafi, a dalilin an ja kunnenta kar ta sake ta zauna. Ina daga daki ina jinsa yana karya wa, kamshin abincin ya shiga har dakin. Na kasa ha'kuri, na fita. Bance masa komai ba na dauki plate ina kokarin zuba wa kaina. Sai da na gama zuba ferfesun 'kafar sa da soyayyen dankali, ina 'ko'karin zuba shayi. Ya kaikaice ya ce "Amarya mai aji jira take akai mata abinci har daki, a lallabata, ta ci, yayin da ita kuma take nuna kunya da yauki". Maganar ta shige ni amma sai na waske na ce "Rai dai! Da sannu kunkuru zai je inda zomo ya je." Ya tabe baki ya ce amma kuwa sai an kosa bai isa ba". Na koma daki, ina kokarin mayar hawayen da yake yun'kurin zubo wa. Da yake bana wasa da cikina, tas na cinye, na kora da lafiyayyen shayin da ya sha kayan ha'di. Na dauki plates din, na je na kwashe wanda ya yi amfani da su, har basket din na kai kicin duk da bamu cinye ba. Tsaruwar falon da kicin din ba karamin burgeni suka yi ba. Hakika an narkar da dukiya mai yawa wajen kawata mana gida. Ubangiji ya saka dukkan iyaye da alheri. Na zo wucewa ina kallonsa yana kallon 'kirjina da 'dinkin kayana ya sake fito da su sosai. Na wuce a raina ina cewa "lallai kuwa kunkuru zai jima bai isa inda zomo yaje ba" Da na rasa me zan yi, na dauko tsintsitar kwakwa na share kafet din, haka na share tayals din da ita, saboda bansan inda aka jefa ta laushin ba. Na gangara na share falon, saboda na ga Gudale ya tashi. Na hada ruwa na yi moping. Kamshi ya cika gidan saboda a ko'ina na saka turaren masu mabanbanta kamshi, dan haka sai suke bada wani nau'in kamshi mai da'din sha'ka. Da na kammala na wanke hannuna, ja dauko ledar supplement dina na fitonda guda na hadiya. A raina ina karfafawa kaina guiwar na cigaba da tsuma kaina ta yadda duk sadda na tashi daga Amaryar buzuzin zai ki'dime a kaina. Ni da kaina na shaida ingancin maganin saboda yadda nake jin sauyi mai yawa a marata madallah da kayayyakin *Faseelat* *07039269802* Na zauna a falo ina kallon wata tasha da ake tseren motoci. Ban Jima da zaman ba ya fito sanye da farar shadda mai kyau sosai. Sai sheki yake, ga kamshi tamkar dai angon gaske. Bai cika saka kaya haka ba, kullum a cikin kananun kaya yake, shiyasa a kwanakin nan ya sake yi mini kyau a dalilin shigar manyan kayan da yake yi. Kallo daya ya mini ya dauke kai ya wuce bai ce 'kala ba. Na bi bayansa da ido, ina jin soyayyarsa na sake bin dukkan sassan jikina. Bayan azahar ba jimawa, sai ga tawagar mutanen gidan mu. Tunda ga kan Antin Zaria, har cousins din mu na Gusau da kebbi. Aka dinga hira cike da nishadi, gefe guda ana jimami gobe war hakan kowa yana daf da isa inda ya fito. Bikin aure da ha'da zumunci yake. Yammaci sosai duk yan'uwa sai jan kunne suke ta mini, tare da nanata mini hakuri shine mabudin dukkan nasara. Antin Zaria ta mi'ke tana cewa ragowan jama'ar ya kamata kuma su tafi. Kafin su tafin sai ga Abba, Baban Gusau da Yaya da kuma Maman Kebbi. Tare da Yaya Sadik da kuma su Yaya Al'amin da Abbas! Abin mamakai har da Yaya Ashir. Dukkanmu muna 'kasa a zaune, yayin da iyayenmu suke zaune Kan rantsatsiyar kujerar falon. Bayan an yi addu'a. Abba ya fara yi mana jawabi mai dauke da rauni da kashe jiki. Ya ha'da mu dukkanmu, ya dinga mana wasiyya da mu ri'ke zumunci, mu yi hakuri da duk wani kalubalen da yake cikinsa, Ubangiji da kansa ya wajabta yinsa, shiyasa yana cikin abubuwan da shaidan yake shiga cikinsa ya yi kane kane, ya jefa gaba da kiyayya a tsakanin 'yan-uwa. Ba dan komai ba, saboda ya sani zumunci ka'dai idan ya bari muka ri'ke shi, muka inganta shi, da sannu zai zame mana sanadin shiga aljannah. Shi kuma ba hakan yake so ba, abokan zama yake nema a wuta, shiyasa ba abin da yake sanya shi farin-ciki kamar idan ya yi galaba akan tarwatsa aure, da sanya bawa shirka, da kuma jefa kiyayya a cikin zumunta. Ya yi shiru tsawon lokaci, har kowa ya ji tamkar ko ya kammala ne. Ya nisa ya zarce da cewa "Bayan haka ina son na fa'da muku, mu yanzu ka'dan ne ya rage mana a cikin wannan duniyar, domin ko Autan mu ya kai shekaru sittin din da Annabi ya ce mafiya yawan al'ummarsa zasu rayu ne a tsakanin sittuna au saba'una, kalilan ne suke zarce hakan, yayin da yawa basa kai wannan shekarun ma. Dan haka ina sake jaddada muku ku yi ibada, ku yawaita istigifari, sannan ku zama bayi masu yawan godiya. Ina sake jan kunnenku ku zama masu sassauci, masu dauke kai ga wanda ya yi maka izgilanci da gangan, da sannu Ubangiji zai maka sakayya, ku zama adalai a cikin iyalinku". Ya sake dakatawa ya numfasa sannan ya cigaba da maganganu masu ta'ba zuciya domin da yawa duk kwalla ne a idanuwanmu. "Sadik! Sadik! Sadik". Sau uku ya 'kira shi yana amsawa. Ya kaurara murya ya ce "ka ji tsoron Ubangiji ka yiwa kanwarka kuma matarka adalci, ka sassauta mata, ka Kuma gane ita din mace ce, mace kuwa Ubangiji bai yi ta a mike ba. Annabi ya ce mana a karkace aka yi su, dan haka mu yi hakuri mai yawa da sha'anin su. Ka sani mun baka ita ne, ba dan mun gaji da ita, ko dan ka zauna da ita bisa alfarma ba. Cikin soyayya da adalci zaka ri'ke ta, ka yi mata sassauci a inda ta kuskure maka, ka yaba mata idan ta yi abin kyautatawa. Kar ka zalunceta, kar musguna mata, idan na kama da wannan laifin ka sani nima ba zan sassauta maka ba. Ina ro'kon Ubangiji ya sanya alkhairi mai yawa a aurenku, ya baku zuri'a mai albarka wacce zata yiwa musulunci da zumunci hidima". Dukkan falon suka amsa da "ameen". Haka su Baban Gusau, da Maman Kebbi suka sake tofa albarkacin bakinsu, kuma dai duk maganganun suna nuni damu zama masu ha'kuri da ladabi a duk inda zamu tsinci kanmu a rayuwa. Daidai nan Sakna ta nemi izinin zata shiga gida karban wani sako. Ta fita da sauri, ina kallon yadda Abba ya bita da kallon kauna, irin sahihiyar kaunar da Uban yake yiwa managarcin 'dansa. Ba jimawa kuwa ta dawo wasu mata uku, suna biye da ita da manyan tires an nade su da poil papper. Suka ajiye, suka gaisa da mu sannan suka tafi. Ta dauki tire daya ta bawa su Abba. Daya kuma ta bawa su Yaya Al'amin, yayin da dayan kuma namu na mata. Hadaddiyar fried rice ce da ta ji hanta sosai, ga kuma hadin ganye. Kowanne tray da cokulan roba a kalla guda bakwai a ciki. Ta kira Farisan Gusau suka yi kicin suka de'bo ruwa da lemo sai da suka rabawa kowa sannan suka zauna aka Fara cin abincin. Addu'ar albarka ba wacce iyayenmu basu yiwa Sakina ba. Hatta Antin Zaria sai da ta ce "wato dai Sakina idan ban yi da gaske ba, sai kin 'kwace girman nawa kamar yadda kika kwace mini fada a wajen su Baba da Yaya". Aka dinga dariyar maganar. Sosai Sakina ta mayar zaman ya zama wata irin walima mai da'di da sanya nisha'di da son a tabbata a cikin wannan yanayin na farin-ciki da kaunar juna. *Umm Muhd collections* *Tana sayar da hand bags da takalma na kece raini* *Tana dinkin manyan mata yan kwalisa* *Tana ha'da lefe* *Tana ha'da kayan haihuwa* *Tana da mayafai gangariya* *Tana da duk nau'in sutura* *Tana da zababbun kayan kicin*. *08063358662*. # Team Gudale# # Team Guduyo# # Surayya Dee ✍️ # Ana tare 🤝. 2/8/23, 10:23 - Buhainat: *Wannan littafin na ku'di ne, biya 500 ku'din karatu ta wannan asusun* *2384876855* *Surayya Ibrahim* *Zenith Bank.* *A tura shaidar biya ta wannan lambar* *08032773332*. *Umm Muhammad collections* *Sharrariyar mai sayar da dukkan kayan sutura da kuma takalma da jaka masu kyau da sau'kin farashi*. *Bayan haka tana ha'da lefe dai dai da aljihunku*. *Tana ha'da kayan haihuwa* *Sannnan kwararriyar tela ce da ake yayi* *08063358662*. *SDK* *39-40.* Zaman nan bai tashi ba, sai daf da maghrib! Bayan Antin Zaria ta dauko sauran kayan da ta rarraba a wajen dinner, ta bi duk Wanda yake wajen ta bashi hadaddiyar jaka mai dauke da kofin shayi na tangaran da tawul masu dauke da sunana da na Yaya Sadik a jiki. Su Abba kawai ta ce nasu na cikin gida. Suka dinga tafiya, suna barina, sai lokacin na ji kewa ta dirar mini. Da tuni ina cikinsu. Farisa ta gyara falon, ta wanke tires din yayin da aka zubar da cokulan. Ta kammala ta tafi ta barmu. Sakina ce kawai ta rage bata tafi ba. Ana idar da sallar sai ga Yaya Sadik ya dawo da sauri tamkar wanda ya yi mantuwa. Kai tsaye ya shigo dakin da muke zaune, mun idar da sallar tana ta fa'da mini abubuwan da zan dinga yi na janyo hankalinsa kaina. Ya na'de hannuwansa a 'kirji ya ce "Sakina! Na tambaye ki mana?" Ta kalle shi sosai ta ce "Ina jin ka". "Me yasa kike da kisisina ne? Bayan duk kazallahar da kika yi dazu kika sanya aka dinga kwarara miki addu'a ke ka'dai tamkar ke kawai suka haifa. Hakan ba ishe ki ba, sai kin zo kina koya mata makircin da zata kai ni 'kasa ko?" Ya fa'da cikin daurewar fuska. Ta sassauta ta ce "wato addu'ar da suka yi mana dukkan mu bata yi maka ba, wacce aka mini ne ta tsaya maka a rai?" Ya basar ya ce "To tashi ki tafi na sallame ki, daga nan har watanni shida kar ki zo, kin sani dai daga ni har ita 'kannenki ne ba yayyenki bane bare ki yi ta yi mana zarya". Ta murmusa ta ce "Na Moriki magidan ci". Ta dauki dankwalinta ta daura, tare da yafa mayafi. Ta kalleshi ta ce "Idan har ka yi halin girma ba zaka ganni a gidanka ba har sai ranar da Halimatu ta haifo little Sakina. Ina fata ba'di iyawar hakan". A tunzure ya ce "wa zai yi miki takwarar? Ga uwata, ga kuma Antin Zaria! Yo da na saka sunanki ba gara na sawa yarinya sunan rana ba. Haka kawai na je ta debo Halin ki na rasa yadda zan yi da ita. Matu'kar kuwa zan saka sunanki ki tabbatar lami ko Attine za'a ce mata tunda alhamis aka haife ki". Ta dinga dariya sosai tana cewa "To ita ai ba lallai ta zo alhamis din ba, indai an yanka mata rago da sunan Sakina, sannan a school zata amsa Sakina Sadik Moriki ai magana ta kare". Ya harareta ya ce "Dan me zaki batar da sunan Abba? Bayan yaran da zan haifa ne kawai zasu yi bearing da sunan sa kamar yadda Umma ta ke fa'da mini". Ta girgiza kai ta ce "*Sakina Sadik Abubakar*. Shike nan?" Ya daga kai tamkar dolo tare da cewa "shikenan sai dai ki sani ba a farko ba, domin so nake Abba da Baban Gusau su fara zuwa". Yana rufe baki ta mi'ka masa wata takarda da alamun risit ne. Domin ta kosa da wannan maganar ta shiririta. Ya karba ya duba, ya ce abincin da muka ci 'dazu ne ya lashe har dubunnai haka?" Ta ce "Eh na tura maka lambar asusuna ta what'sapp, sai ka tura mini ku'dina domin rufa maka asiri na yi. Bai kamata ace iyayenka da danginka na kusa sun zo babu komai a gidanka ba". Ya kuwa zabura ya ce "Kuturu! Ai kuwa kin ci uwar 'karya kin kwana da yunwa Sakina. Wato ni zaki yiwa bariki? Ki ciyo mini bashi, sannan ki nuna ke kika yi da aljihunki, ayi ta sanya miki albarka, sannan ki zagayo ki ce na biya ki ku'di?" "Eh mana ai dama haka Annabi ya koyar washagarin tariya idan da hali ango ya shirya 'yar walima. To kuma na ga an cika maka gidan saboda soyayya da gata. Sai kuma a bar mutane su tafi bakinsu a bushe alhalin Ubangiji ya bada damar da za'a yi fiye da hakan". "Sakina! Ya kira ta a tunzure ko ke ce 'kuda wajen naci ba zan baki ko kwabo ba. Ban saki ba, ban aike ki ba, ke ko maganar kika sake tayar wa sai na je gaban Abba da Baba na fa'da musu wannan wayon na ki, kinga sai su janye albarkar da suka saka miki tunda ba dan Allah kika yi ba. Ni dai kam ban san wata halitta mai tsananin bariki irin ki ba". Dariya ta kama mu, na maze ban yi ba, domin idan na yi din sai sai ta zamo mini wani abin daban. Yayin da Sakina ta kyale-kyale sosai. Ta ce "Kai yanzu akan kudin da bai gama rufa dubu arba'in ba kake wannan dagewar? To shikenan an bar maganar, amma ka sani bashi ne, bashi kuwa sai mai imani ne yake biya, ka shaida ban bar maka ba, zaka biya tilas". Haka ya tisa ta a gaba suka fita yana nuna mata dan'kareriyar motarsa da take filin gate an rufeta da tanfol. Daga rakiya bai dawo ba, sai da ya yi sallah. Yauma haka muka kwana ba tare da kowa ya san ma'kwancin 'dan-uwansa ba. Da safe da na tashi, na shiga madafi a dalilin na ga kicin 'din akwai komai na bu'kata. Dan Haka na fara shirin yin samosa da meat pie tunda hatta nikakken nama na gani a cikin madaidaicin freezer din. Na sani kuma duk hikimar Sakina ce tunda ta san bana gajiya da yin snacks. Kafin goma na safiya na kammala. Da yawa na yi. Na na'de shi cikin leda na saka a fridge na soya wanda nasan zamu karya da shi. Na tafasa shayi na zuba a cikin flask. Na kai su kan dining. Na gyara kicin din sannan na wuce zuwa 'daki, na kade gadon na share. Falon dai ban share ba saboda a yammacin jiya Farisa ta yi masa kyakkawar shara, kuma tun lokacin ba a sake zama a ciki ba. Dan Haka kawai na fesa air freshener bayan na jona burner na saka turaren wuta. Na yi wanka, na shirya cikin atamfa coffee sosai. Doguwar riga ce na kashe daurin dankwali na yi matu'kar kyau. Cikin 'dar 'dar na bu'de ragowan dakunan da suke cikin falon amma banga shi ba. Na tabbatar yana sama. Cikin dauriya na hau saman na tarar da kicin a farko sannan na shiga falon da aka shirya shi sosai. Na rasa wanne dakin zan shiga a cikin guda biyun. Na yi shahada na murda kofar dakin dake bangaren dama. Ai kuwa ina turawa na tarar da tafkeken daki tamkar nawa na 'kasa. Komai na dakin a shirye tamkar na mace. A jikin madubin na ganshi a tsaye yana taje sumarsa, ya shirya cikin kananun kayan da suka karbe shi. Duk da ya ji shigowata, hakan baisa ya Juyo ba. Na shiga ka'dan na sassauta murya sosai na ce "Ina kwana? Na kammala abinci, kai nake jira" Ya juyo ya ce "je ki fara cin abinki". Ban tanka ba, na fito, ba tare da na ji komai ba. Illah iyaka dai na 'daura damarar sauke nawa hakkin da ya rataya a kaina. Na zauna kan dinning table din na fara karyawa hankalina a kwance. Ina cin samosa ina korawa da shayi. Ba wani jimawa ya sauko, bai yi magana ba, ya ja kujerar nesa da ni, amma wacce zamu zama opposite. Na dinga rawar jikin zuba masa a plate da 'ko'karin ha'da masa shayi. Ya dakatar da ni tare da cewa "Ke bana son kinibibin banza ni kuturu ne ko kuwa yaro ne 'kan'kani?" Na tsame hannuna na ce "Ba ko 'daya yi hakuri". Da kansa ya yi komai, ya kammala ya mi'ke ya fice ba tare da ya ce mini uffan ba. Hawaye ya cika mini idona. Ina jin wacce irin amarya ce ni? Na zari tissue na goge ban bari ya zubo ba. Na hau saman na gyara masa, na wanke ban'dakin. Na bulbule masa wajen da turaruka daban daban. Na ga agogo sha'daya da kwata. Sai kawai na 'doro alwallah, na tada walaha. Na da'de ina rokon Ubangiji ya kara mini ha'kuri ya kuma sanya soyayya da tausayina a zuciyar mijina. A kan darduman barci ya sace ni, saboda tunda na tashi da asuba ban koma ba. Ban farka ba, sai da na ji ana 'Kiran sallah. Na yi salati ina ambaton istigifari. Ban ji yunwa ba sai wajen uku. Na shiga kicin na tsaya ina tunanin me zan yi ne? Sai kawai na ji waya, na fito da sauri na dauko. Cikin sa'a na ga Aziza ce take cewa tana harabar gidan. Da sauri na bu'de mata kofar. Muka rungume juna. Ta dire kayan hannunta sannan ta koma ta dauko kwandon da ta ajiye a bakin 'kofar. Shinkafa da miyar kaji Mama ta zubo mana. Ga kuma hadin salad, na ce aikuwa kamar kun san tashi na yi zan 'dora girki." Tare muka zuba, muka ci, ta dauko mana ruwa da lemo a kicin. Sosai na ji dadin zuwan Aziza. Sai da ta shiga ko'ina sannan muka adana kayayyakin da ta kawo mini. Karfe biyar ya dawo, dawowarsa ya sanya Aziza tafiya duk da shima ya ce mata ta yi zaman ta. Amma ta'ki, ta tafi. Yana zaune a kujera ya 'dora 'kafa daya kan 'daya. A hankali na ce "Na kawo maka abinci nan ko kuwa zaka je wajen cin abincin?" Ba tare da ya kalle ni ba ya ce "Wai ke kam dole sai kin yi mini magana ne? Abinci kawai na iya ci. Baki san ki yiwa mutum abin arziki ba, sai abinci? To abinci, ko ina na je ci zan yi, yanzu haka ma a 'koshe na ke". Na yi sororo na kasa gane wannan maganar tasa inda ta dosa. Na ce "me kake so na yi maka, ka fa'da mini, a shirye nake na yi maka komai matu'kar hakan zai sa ka gamsu ba abin da nake so irin ka daina wannan fishin. Ka daina nuna mini halin in kula". Ya sake 'daure fuska ya ce "Wallahi matu'kar baki fito mini da kayan da Ashiru ya siya miki ba, ba zaki taba gane kaina ba". Na yi shiru a hankali na ce. "Wannan dispenser 'din ce sai kuma wani dinner set yana kicin". Ya yi shiru tsawon lokaci sannan ya ce "Tashi ki dauko mini". Na tashi na dinga lalube a kicin har na ga inda aka saka, Àllah ya so ma ba'a bude ba. Na kasa 'dauka saboda nauyinsa, da 'kyar na dinga turo shi har na iso falo. Ina 'dan haki na ce "gashi." Ya yi mini lalataccen kallo ya ce "Sai ka ce wanda kika yi wani abin a zo a gani kike wannan haki". Na yi kasa da kaina ba tare da na ce uffan ba. Ga mamakina cak ya kinkimi kwalin ya fita da shi, sannan ya dawo ya dauki dispenser ya fice. Jimawa ka'dan ya dawo ban san yadda ya yi da su ba. A tunani na matsala ta kare a tsakanin mu. Ashe ban fara ganin matsaloli ba ma. Ya hau dinning ya ga shinkafa. Ai kuwa ya dinga sababi ba zai ci shinkafa da daddare ba. Jikina na rawa na ce "Yi hakuri bani minti na ka'dan na samo maka abin da zaka ci". Na shiga kicin na fito da meat pie guda uku na soya masa, na dafa shayin da ya ji citta da kaninfari. Na kai masa. Sanin da na yi idan ban zauna ya gama ci ya barni a wajen ba, na yi laifi. Kan dole na ja kujera na zauna ina kallonsa yana ci cikin yanga da basar wa. Yana kammalawa kuwa ya mi'ke ya haye sama ya bar ni. Na dinga mamakin wannan wulakanci na Gudale. Na kalli kaina na dinga jin ko dai ban kai mace bane da har ya iya kauda kai akai na irin haka, shin wula'kanci ne ko kuwa rashin so ne?. Da na ga tunanin zai yi mini yawa, sai kawai na je kicin na wanke yan plates din da muka bata. Na juye miya da shinkafar na sanya a fridge, na wanke kulolin. Na kashe fitilu da fanka. Na shige daki, wanka na yi, na fito da alwallah na yi sallah, na yi shafa'i da wutiri. Na dinga addu'a irin ta 'dazu, yanzu kuma na 'kara da ro'kon a sanya mini ha'kuri mai yawan akan lamarin Gudale. Na jima ina addu'ar sannan na tashi na dauko maina na kamfanin oriflame na shafe jikina. Na sanya rigar barci, na kwanta ba tare da na fesa turare ba, saboda yadda man da na shafa ya karade ni da kamshi mai da'di. Na yi barci mai da'di a dalilin mafarkin da na yi na haifawa Gudale kyawawan yara masu kama da shi. Da nisha'di sosai na tashi. Haka kwanaki suka dinga wucewa har na samu sati guda a gidan aurena. Wanda kwanaki bakwai din farko ma cikin ha'kuri na yi su. Domin bai saurare ni ba, bare mu fahimci juna, tun ina saka ran zamu shirya har na fara cirewa da naga na doshi sati biyu kullum al'amarin nasa na sake cabewa. Kullum sai Sakina ta yi mini waya, tana tambayar lafiya muke? Da walwala nake amsa mata lafiyar mu kalau. Domin ina jin kunyar na yi mata 'korafi akan Gudale. Domin ba karamin abin kunya bane na ce na fara fuskantar wula'kancin sa, zan yi dukkan juriya dan kada kunya ta a idon masu guje mini aurensa. Ranar Monday din da ta yi daidai da kwanaki na goma sha shida a gidan. Sassafe na tashi na shirya masa abin karyawa. Nima na karya, na yi shirin tafiya a asibiti, tunda yanzu asibiti zamu yi second semester din. Doguwar rigar shudin voile na sanya wanda jikinsa akwai jajayen stones. Ban 'daura dankwalinta ba sai na sanya. Wani Dan karamin hijabi iya kafada a dalilin labcoat zan sanya. Ban saka turare ba, illah na goga roll on din oriflame shima a wajen *Aisha lame 07036662633* muka samo shi. Kamshinsa kawai ya isheka har washagari. Na dauko hand bag 'dina wanda special order ce ta *Umm Muhd collection 08063358662*. Na saka duk abinda zan bu'kata, na rataya na fito bayan na sanya flat din takalmi mai stone jah, sannan kuma mai igiya ne. Mai da powder kawai na shafa, amma sai na yi wani irin kyau tamkar dai wata amarya mai karama. Na hau saman, bayan na saka labcoat din. Yana kwance cikin bargo, amma idonsa biyu. Daga bakin 'kofar na gaishe shi na ce "Zan je asibiti". Ya tashi zumbur ya na 'kare mini kallo. Cikin takaici ya ce "Tsakani da Allah an gama da ni, ban ta'ba sha'awar auren wacce bata kammala karatun ta ba. Amma kawai aka yi mini 'karfa 'karfa, wato ma sai da kika shirya zaki fa'da mini? To me ya hana ki yi tafiyar ki kawai?" Na danne 'bacin ran da ya taso mini na ce "I taught kana sane da two weeks suka bani, amma ka yi ha'kuri". Ya ce "kina nufin a haka za ki tafi? Kin ci kwalliya tamkar me zuwa party anya Guduyo kin san hukunce hukuncen Shari'a kuwa?" Na kasa cewa komai. Kai tsaye ya ce "je ki canja wannan kayan ba zaki fita da su ba". Ban ce komai ba na fita. Na sanyo riga da siket na atamfa, na koma. Tun kafin ya yi magana ya dinga girgiza kansa tabbacin ba su yi masa ba. Da yatsa ya ce "kin ga yadda siket din ya kama ki kuwa? Koma ki canjo wasu". Raina ya fara baci , amma na daure na ha'diye fishin nawa. Haka na sake komawa na sako wani yadi tamkar na rariya, an yi masa dinkin straight gown. Na 'dora labcoat din, sannan na sanya farin hijabi mai hula, ya sau'ko har kafadata. Na sake komawa yana zaune a tsakiyar gadon. Ya kalle ni ya ce "Asali fa harkar kiwon lafiya akwai munafunci a ciki, dan menene mace musulma ba zata saka hijabi har 'kasa ba?" Na sunkuyar da kai 'kasa ina addu'ar Allah ya sanya ya barni na tafi, Ni dai. Dan na lura jidali yake nema na da shi. "Yauwa na tuno! Menene Ayu din da kike mini fatan na zama, tunda kin ce kada an saka sunan ki a ciki, sai nake ta zullumin kada na yi tambaya a ga tamkar Kan nawa da motsi". Dariya ta kwace mini sosai saboda tsakaninsa da Allah ya yi maganar. Na ce "Na janye yi ha'kuri ni kaina ban san shi ba, a talabijin na ji an fa'da". Ya daure fuska ya ce "Ai idan kuna biye dramar yan wasan kwaikwayo da labarin novels kun dinga shiga cikin garari kenan, domin zama ake ana shiryawa dai-dai da ra'ayin da zai ja hankalin mutane.". Na ce "Ai kuwa Yaya Gudale suna debe kewa da cire takaici, kawai kowa da yadda yake kallon su ne, amma ai akwai masu fadarkawa da kuma darussa wanda babu son zuciya". Ya canja maganar da cewa "To kuma sai na tashi zan nema wa kaina abin da zan ci tunda shi ka'dai ne hakkin da kika gamsu ya zame miki wajibi ki yi mini?" Ya fa'da a tunzure ka'dan. Na kasa gane wannan jirwayen nasa. Amma sai na basar na ce "Na kammala tun tuni". "Me kika yi?" A hankali na ce "Irish na soya maka sai na yi maka miyar albasa" "To daga yau kar ki sake soya mini dankali ki saka a flask, na fi son sa a plate da zarar an kwashe shi daga mai". Da sauri na amsa da cewa "zan kiyaye". Ya kalli farin Tom's din da yake 'kafata. Ya mike da nufin ya shiga toilet. Da sauri na ce "sai na dawo". Bai juyo ba ya ce "ki jira ni Malama". Na sauko ina jin zuciyata na tafasa,na gane dai so yake sai na makara. Ba da'dewa ya fito, yana kallona ya wuce ya fice. Motar da ta zama mallakina ya yi amfani da ita ya kai ni har cikin asibitin Murtala. Da zan sauka ya zaro 'dari biyar biyu ya bani, yana cewa "kina gamawa ki hau adaidaita ki dawo, ban amince ki tsaya a ko'ina ba". Na kar'ba ina godiya, domin dai na ga alamun sassauci ka'dan duk da yadda ya sanya na hargitsa kayana. Ina tafiya ina tunanin menene ma'anar shaguben da yake yi mini na bansan komai a hakkinsa ba sai dafa abinci? Yana nufin ni zanje 'dakinsa da nufin wani al'amari ya shiga tsakanin mu ko kuwa? A fili na ce "Tabdi jam! Rashin ajin nawa bai yi tsananin hakan ba, zan dai cigaba da tattala kaina ta hanyar riko da kayayyakin Fasilat da ta zaba mini masu koluluwar amfniyda gyara mace. Tun yanzu nake jin sauyi da nisha'di sosai a tare da gangar jikina. Har na gasgata idan ka samu kwararriyar da hada kayan G.H.T. kamar na yadda Faseelat take yi, to kin yi bankwana da infection da dryness in sha Allah. *Faseelat G.H.T. *Tuntube ta a wannan layin domin ita din kwararriya akan sana'arta, kayan ta ingantatu ne sannan zata yi miki sauki kwasha kwasha ta yadda zaki gamsu ta zarce sauran* *07039269802*. # Team Gudale# # Team Guduyo# # Surayya Dee ✍️ # Ana tare 🤝. 2/8/23, 10:23 - Buhainat: *Wannan littafin na ku'di ne, biya 500 ku'din karatu ta wannan asusun* *2384876855* *Surayya Ibrahim* *Zenith Bank.* *A tura shaidar biya ta wannan lambar* *08032773332*. *Akwai harda copy na littafin *Kasaita* *Na marubuciya Maryam Kabir Mashi* *Mai so ta yi mini magana akwai shi a hannuna yanzu haka 1-3 ne*. *Faseelat mai gangariyan supplements din da suke karawa mace dandano da Kuma daidaita zahirin surar mace* *Shin kina fama da basir ko ulcer?* *Shin kina fama da tumbi?* *Shin kina fama da rashin ni'ima?* *Kina bu'katar mayuka masu gyara fata?* *Kwantar da hankalinki kukan ki ya zo karshe domin Faseelat karshe ne a wannan fagen ga ta da sau'kin farashi*. *Ki tuntube ta a wannan layin 07039269802*. *SDK* *41-42.* Present. Yauma 'kiran sallar azahar ne ya ankarar da ni, daga dogon tunanin da nake yi. Na tattara littafan da na tara a gabana, amma ban samu sukunin bibiyarsu ba, saboda yadda nake son na tariyo zamana da Gudale ya shiga zuciyata, tabbas sai na yi bita a nutse cikin adalci sannan na auna shi a ma'auni dan na yi hukunci na gaskiya. Sai da na sauke farillah, sannan na shiga kicin. Ina kicin 'din su Amna suka shigo, dake yanzu ta kofar kicin ake shigowa. Sanye suke cikin dogoyen riguna iri daya, cotton masu tsananin kyau, a yanzu da Kaya suka ta'azzara da tsada na sani ba 'karamin ku'di zasu lashe ba. Hatta hular kansu mai karshen tsada ce itama kuma iri 'daya kalar lemon green a dalilin flower rigar koriya mai haske ce. Kafafuwansu sanye cikin takalmi tamkar sandal amma an'kawata shi da stones masu 'daukar ido. Sai 'kamshin turaren *kidiz* suke yi. "Momy" Suka ha'da baki wajen kirana sannan dukkansu suka rungume ni. Na dinga jin farin-ciki na mamayata, ba abin da nake so sama da wa'dannan yara. Zan yi komai, haka zan bar komai dan rayuwarsu ta inganta. Zamansu a Abuja ya sanya na sake fahimtar wani darasi a rayuwa. Tabbas mahaifiya 'daya ce a fa'din duniya, amma idan mutum ya yarda zai yi uwaye 1000. Matu'kar zaka mutuntunta mutane, ka yi hakuri da cutarwarsu, ka tsananta addua. To da sannu Ubangiji zai daidaita maka lamurunka da su har ayi ta zaton tamkar ka asirce su ne. Antin Zaria ta wuce Yaya a gareni, ko kuma Yayar miji. Uwace ta sosai domin ta yi mini abin da uwa ce zata yi mini babu gajiyawa. Na sani 'ya'yan Gudale take hidima da su amma da ban yi hakuri da shi ba, da ban yi ha'kuri da cutarwar mahaifiyarsu ba, da ban girmamasu ba, da sun bar ni da ya'yana cikin halin wula'kancinsa. Da ban yi juriya ba, da ban samu gata da goyon baya a wajen Sakina ba. Tunda tun farko ba abin da fa'da mini dan ta kubutar da ni shiga matsalar da take hango mini idan har na kasance matar Gudale. Hakanan yaran da ban tsaya na nuna musu soyayyar da kowa yake fa'din na ma'kala su a raina ba, da ban hango tarin soyayyata a zuciyarsu ba, wata'kila da tafiyar nan da suka yi da basu yi kewata ba. Kamar yadda na tabbatar basa kewar mahaifinsu. Ni kuma ba zallar soyayya irin ta batanci nake gwada musu ba, soyayya ce mai cike da tarbiya da kuma tausayi, saboda ubansu ba su yake son a haifa masa ba. Ya'ya maza yake so wanda zasu zame masa garkuwa. Shiyasa ni kuma nake tsaye akan su dan kar su rasa soyayyar uba, su kuma rasa ta uwa. Na yi imanin wanda Ubangiji ya azurta shi da yara mata, ya masa arziki mai yawa. Domin kuwa tausayi da jin 'kai sai mata, matu'kar an musu kyakkawar tarbiya, An kuma yi sa'a sun tashi akan wannan tarbiyar. Shiyasa nake hana idona biyu da daddare nake yi musu addu'a da fatan Ubangiji ya shirya mini su, su zama masu albarka masu amfani, Ina fatan su zama tamkar su Antin Zaria. Na durkushe kan guiwoyina, na janyonsu, kowacce na gefen hannuna. Na kallesu da murmushi mai yawa. Amna ta ce "Ina yini Momy?" Afra ta ce "Momy ina kwana?" Na ce "sai yanzu kika tashi ne Afrah? Kina jin Ablah ta ce ina yini, ke kuma kika ce ina kwana, bayan yanzu ba morning bane Noon ne". Tasa daukkan hannu ta rufe fuskarta wai ita kunya. Muka yi dariya ni da Amna. Na ce "To me zan dafaa mana tunda ban riga da na 'dora abincin ba?". Amna da ta gaji Babanta wajen son snacks a matsayin abinci ta ce "Akwai meat pie a fridge?" Na ce "Gaskiya Babu Ablah". Afrah kuwa ni ta biyo daga siffa har dabi'u kawai dogon gashinta mai sulbi da kuma wasu daga kammanin Babanta , suka kara mata kyau sosai fiye da Ni. Amma da ke jikina ta debo Yar duma duma ya sanya take da farin jini kwarai da gaske. Ablah kuwa ba inda ta bar Sakina, duk yaran Sakina ba mai kama da ita tamkar Amnah. Ta ce "Momy to mu ci Indomie mana, amma ni dai a saka mini cinyar kaza". Na yi dariya, yayin da Amna ta ce "Ai shiyasa kullum kike zama fatt bon bon". Na ce "to kuje ku yi sallah kafin na gama mana". Har sun fita sai Afrah ta dawo ta ce "Momy ina 'kanin Ablah?" Na yi murmushi na ce "Yana tare da Dadi". Ta ce "yanzu idan muka zo wani hutun zan ga kin samo mini nawa 'kanin?" "Ho Afrah je ki yi sallah! Ai na dauka ma ba zaki koma Abujan ba". Ta ruga da gudu tana cewa "Zan koma Momi! Dadinmu na Abuja baya fa'da, baya dukan Mama. Baya zare ido, baya cewa sai mun zauna a waje 'daya, sannan yana yawo da mu a mota". Ina jin Amnah ta ce "kin manta Afrah damu yake zuwa shopping mu zabi abin da muke so. Sannan ya ce idan bamu koma ba, a Kano ba irin makarantar mu ta can mai 'dakin barci da na wasa". Ban ce musu komai ba, illah iyaka na da'de da fahimtar suna jin da'din zamansu a Abujan, sannan na gane mijin Antin Zaria na matu'kar kaunar su, yana nuna musu soyayyar da mahaifinsu bai muna musu ba. Duk kuwa da ya manyata, dan a matsayin jikokinsa suke. Na gama dafa mana indomin na samu madaidaicin tire mai circle mai dan zurfi na juye a ciki. Na daukar musu kananun lemon Ribena ni kuma na dauki pure water mai karancin sanyi, yayin da na daukar musu marar sanyin gaba'daya. A falo muka zauna bayan na shimfi'da mana ledar cin abinci. Sai da suka cire rigunansu suka zauna daga su sai best da pant dinsu mai kama da short nika. Muna ci suna bani labarin Kayan da'din da yake gidan Maman Abuja tunda su basu santa da Antin Zaria ba. A haka ya dawo ya same mu. Aman na rungume a jikinsa da alamun barci ya yi. Ya zauna yana kallonmu, yaran duk suka yi 'dif, suka zama a takure. Shi da kansa bai ji dadin yadda suka zama ba. Ya waske ya ce "Amnah wa Afrah ba gaisuwa?" Suka hau fadin"Dadi ina kwana" cikin rawar murya. Sun manta matashiyar da na yi wa Afrah dazu cewar yanzu ba safiya ba ce. To babu sabo ko shakuwa a tsakaninsu. Afrah da ba sosai take jin tsoronsa kamar Amnah ba, ta mike ta wanko hannunta, ta dawo ta isa kusa da shi tana leken fuskar Aman dake barci sosai akan cinyoyinsa. Ta mika hannu tana cewa "Kanin Abla ya kara girma Momy". Tana rufe baki ya ce " ke ba kaninki bane Afrah?" "Eh ai sunansu 'daya da Ablah! Da na yiwa Momi kuka shine ta ce idan ya girma, nima zata samo mini nawa 'kanin Baby boy mai kyau! Sai a sa masa Afreen. Ka ga Amnah wa Aman! Afrah wa Afreen". Ya zuba mata ido yana jinta har cikin ransa, yarinyar ruwa biyu ce, kammanin Guduyo da nasa duk ta ha'da sannan mai wayo ce sosai tamkar dai Yar tsofi. Ya janyo ta jikin sa karon farko da nufin nuna kulawa ba dan rashin lafiya ko dan ya hukuntata ba. Ta 'da'dare ta ce "Dadi am sorry! Na yarda 'kanina ne". Ta fa'da tana tunanin laifi ta yi masa. Cike da alhini ya ce "Fa'da miki zan yi, ki sake ro'kon Momi akan ta cika promise 'din samo miki na ki 'kanin domin ta ce mini ta fasa". Ta juyo ta zuba mini ido ta ce "Momi kin fasa wai?" Na girgiza kai na ce "ban fasa ba Afrah" Ta kyale-kyale da dariya sosai tare da cewa "Na sani Mominmu ba 'yar wuta ba ce, tunda Mama ta fa'da mana mai 'karya 'dan wuta ne". Dukkanmu muka zuba mata ido, kafin na ce wani abu. Amnah ta ce "Momi kuma promise kika yi mata, ba kyau rashin cika al'kawari". Mamakin yadda yaran suka 'kara wayo ya kama mu gaba'daya. Na bagarar da maganar da cewa Amnah "dauke tray din ki wanko hannun ki'. Ta tashi da sauri ta yi abin da na umarce ta. Na mayar wa da Afrah rigarta, yayin da Amnah ta saka tata da kanta. Rashin sabon da babu a tsakaninsu da shi ya sanya Amnah cewa "Afrah zo mu tafi wajen Maman Abuja, ta ce dama zamu fita unguwa". Da gudu suka fita, na bisu da kallo ina jin tamkar su dawo na cigaba da kallonsu. A sanyaye ya ce "Halah ba gaisuwa? Ba barka da zuwa, balle a bani ruwa na sanyaya ma'koshina". Na yi kamar ba da ni yake ba. Takaicin share shin da na yi, ya kama shi. Ya kwantar da Aman akan kujerar, ya yi dakinsa ya yi wanka ya canja kaya ya fito. Ya sake zama ya yi gyaran murya ya ce "Kawo mini abincin". Ban kalle shi ba na ce "Ban yi ba". Ransa ya baci ya ce "Duk hakurin da na baki? Duk yadda iyaye da yayu suka baki ha'kuri, amma kin kafe sai ka ce mai zuciyar dutse! A ina Kika samo wannan taurin kai da na zuciyar?" Na 'ki tankawa. Ya gaji ya ce "Nima dafa mini indomi, idan kuma kin yi snacks din ki soya mini ya ishe ni" A lalace na ce "Ban yi ba, babu nama". Ya dan tuzura ya ce "shekaranjiya na siyo nikakken naman na kawo, baki yi amafani da shi ba, ki ce ya kare?" Ba fargaba na ce "Abida ce na ji tana nema shine na bata". Ransa ya sake baci ya nuna kansa ya ce "wato yanzu ba ruwan ki da duk abin da zai bata mini rai ko? Har bu'katar Abida ce ta fi tawa?" Na murguda baki na ce "ina ce dai yar uwarka ce ba tawa ba". Ransa ya baci ha'kurinsa ya fara 'kwacewa ya ce "Kar ki fara yi mini rashin kunya, ranki zai baci, ki shiga hankalinki Halah" Cikin son na sake fusata shi na ce "Guduyo na ke ba wata *Halah* ba". Ya harzuka ya ce "Halima ki tashi ki dafa mini indomi ko abin da ya faru a 2020 ya sake faruwa a yanzu". Na tintsire da dariyar iyashege na ce "Ya faru sau uku dan Allah". Ya mike ya yi kicin yana fa'din "Billahillazi sai Baban Gusau ya zo gidan nan. Sai na 'kira miki Alaramma Malam mai jalalaini ya fahimtar da ke girman hakkina da yake kanki tunda kin mance". Na baki ha'kuri, har kuka na yi akan ki amma kin 'ki yafe mini. Sai ki fa'di me zan yi, a bar wannan maganar haka na gaji da ita matu'ka da gaske". Jim kadan ya dawo da lemo a hannunsa ha'di da biskit din pure Bliss. Ya zauna yana ci cikin bacin rai, da alamu yunwa yake ji ba 'yar ka'dan ba. Ya zauna yana tura biskit din nan, na lura a dole yake ci, shi yafi son abu mai gishiri akan mai za'ki akan dole yake cin wannan din, da alamu ko karyawa bai yi ba. Na sake kallonsa ta gefen idona, ina tuna ko sau nawa nake yin girki yana 'kin ci? Ko sau nawa na yi ta ro'konsa ya ci abincin da na 'bata lokaci na yi domin sa yana 'kunsa mini ba'kin ciki ta hanyar 'kin bude wa bare ya ci. Na nisa na ce "Duniya mai juyi juyi" Cikin rarrashi ya ce "Dan Allah Guduyo ki ji tausayina mu zauna lafiya, dan Allah let gone be by gone". Hawaye ya balle mini na ce "wato duk yadda ka wulakantani ta hanyar cewa Ni din tamkar 'kofar Dan-agundi haka ka ke jina. Hakan bai isheka ba, ka sake cewa zaman alfarma kake yi da ni, ka tabbatar mini bolar jakara ta fini a wajen ka. Sannan ka dauki kwanana ka kaiwa wacce kake so, ka tsaya gaban Mahaifina ka zage shi son ranka sannan yanzu ka yi tunanin zan yafe maka cikin sau'ki! Wata'kila dai kwayar da kake sha ta shafi wani bangare na tunaninka". Ya mi'ke ya ce "Ni ban zagi Baba ba! Allah shine shaidar ban zage shi ba, sannan idan ma na zage shi ai kaina na zaga, tunda a yanzun nima bani da uban da ya wuce shi. Kuma akan me zai zuba ido ya bari Sakina da Al'amin su shigo mini gida su cinye ni da yaki bai tsawatar ba?" Idonsa ya ka'da sosai ya ce "Me yasa kuke mini haka Guduyo? Ke da su Al'amin sam sam baku da kara ko kawaici, Yaya Abdallah ne kawai yake kwatanta yi mini alkunya. Amma ke da sauran brothers 'dinki ba kwa koyi da rayuwar Abba da su Sakina. Duk abin nan da muke ciki mafi yawan sisters 'dina a bayan ki suke, Amma ni kiri kiri su Al'amin suka nuna mini ke ce tasu". "A tunzure na ce "Maimuna da Juwairiya menene basu nuna mini ba su? Sannan ai cin mutuncin da kake yi ne ya wuce iyaka da ka'ida. Ni Wallahi ba abin da nake so irin ka 'karasa igiyar da ta yi saura a tsakaninmu. Kana zaman alfarma da ni ai kawai ka sauwake wa kanka zaman takura da alkunya. Dama ai ka sha fa'din Abba ya cuce ka da ya ha'da aurenmu". Na fara kuka sosai na ce " Ban san hirar saurayi da budurwa a tsakanin mu ba, bansan 'da'din hirar mata da miji ba, saboda kullum hantara da kyara ka fi amfani da su a kaina". Kuka nake har da shessheka na zarce da fa'din "Zamana da kai cutarwa ce, tunda indai ka 'kyalla ka ganni da cikin da yake naka ne, shikenan ni kuma watan shigata bala'i ya kama kenan. Kullum ina zaune da kai cikin zullumi da fargaba mai yawa. Ka sauwake mini ka auro taste 'dinka, wacce bata bu'de kamar kofar 'Dan-agundi ba. Wacce zaka dinga shillawa kana cafewa, wacce zata haifa maka yara maza reras a jere, Yar attajiri ba wacce ta shiga rigar arzikin Uban wasu ba". Hankalinsa ya yi koluluwar tashi, jiri ya debi shi ya zauna kan kujerar da karfi tabbacin bai shirya zama ba, fad'owa ya yi. Ido jawur, murya ba amo ya ce "Fear God Guduyo! Maganar da na ce Abba ya cuce ni, ai tsohuwar magana ce, tun farkon aurenmu ban sake katobarar fa'da ba, hukuncin da Abba ya dauka sai da na kusan salwanta wani sashen na jikina saboda kawai ma karyata kirarin da na yi, har yau kuma ban sake cewa an cuce ni ba. Amma dan son ki sake jefa ni cikin tasku shine kika dawo da maganar yanzu?" Na yi masa banza don na sani gaskiya ya fa'da. Ya numfasa ya ce "Na baki hakuri yafi cikin buhu. Ina miki albishir matu'kar kika yafe mini Ni kuwa duk abin da kike tunanin ban yi miiki ba, Wallahi sai na yi miki fiye da hakan, sau nawa zan fa'da tun kafin na aure ki nake jin ki cikin zuciyata, nake kishin ki?" Ido cike da hawaye na watsa masa harara na ce "Sau nawa zan ce maka ba gaskiya kake fa'da ba. Me yasa ka kasa nuna farin ciki da auren? Me yasa baka ta'ba zuwa zance ko sau 'daya dan ra'din kanka ba? Me yasa bayan auren ka kasa nuna mini kulawa a farkon kwanakina a gidanka? Me yasa ka gudu ka bar Ni? Amsar ita ce *Baka Sona*." Kuka sosai ya kwace mini na dinga yinsa sosai saboda yadda nake jin bacin rai na taso mini ba ka'dan ba. Amma a hakan na ce "Wanne zaka dawo da baya ka yi mini shi?" Da sauri ya matso gabana ya durkusa ya ce "Duka! Har zancen da ban zo ba yanzu zan zo miki. Zan baki kulawa sosai, yanzu ma farkon aure muke, yanzu nake fatan mu yi rayuwa mai cike da nutsuwa, ta baya cike take da kuruciya da wauta, ki bani dama kawai na tabbatar da sannu zan wanke duk ba'kin tambarin da na yiwa kaina a zuciyar ki". Na kalleshi ido cikin ido na ce to ai ni yanzu bana son ka". Maganar ta shige shi ainun ya ce "Ni ina son ki, son da nake miki ya isa mu zauna lafiya matu'kar dai zaki yiwa sharia biyayya". Ba shakkar komai na ce "idan ba zan yi biyayyar ba fa?" Ya zuba mini ido sosai nima na zuba masa, ina son na ji ko makauniyar soyayyar da nake yi masa zata ta so mini. Amma ban ji komai ba, tabbacin na riga na dahu da ba'kin cikinsa. Na janye idanuwana ina jan majina hadi da goge hawayen da ya ki yanke wa. A raunane ya ce "Sai na ha'du da jinya sannan zaki fahimci halin da nake ciki Guduyo?" Da kara'di na ce"sau nawa nake jinya sanadin ka? Amma sannu ma tana yi maka nauyin ka yi mini! Ka mutu ma 'karewar jinya bani da asara." A hankali ya ce "Tabbas ba ki da asara! Umma da su Amna ne zasu tafka asara, sai kuma su Sakina da zasu rasa tilon 'dan-uwansu tunda yanzu zumunci idan ba cikinku 'daya ba to babu wani kawaici ko kara". Ya mike yana tangadi tamkar wanda ya sha abar, nan kuwa tsabar ba'kin cikin yadda na bijire masa ne. Da wani zai zo gidan wanda bai san mu ba, bai san halin da na shiga a hannun sa ba, sai ya ga laifina, ya ce ina wula'kanta mijin aurena. Wanda kuma ya san mu sai ya ce "Mayya ce ni da na yarda nake zaune da shi. Shigar da ya yi ashe zazzabi ne ya rufe shi ina zaune ban sani ba. Har aka yi la'asar bai fito ba. Sai na yi kamar na leko shi, na ga dalilin da ya hana shi fita sallah sai na basar. Amma abin na mintsini na tunda Ubangiji ya sanya shi cikin bayi masu mutuntata sallah a jam'i. Na idar da tawa sallar ba jimawa Aman ya tashi, sanin da na yi Gudale ba lallai ya fito ba, ya sanya na rungume yaron, yayin da shima ya kwanta a jikina ya yi lamo tamkar dai ba daga barci ya tashi ba. Ban san ya aka yi ba, soyayyar yaron da na 'boye a cikin zuciyata ta dinga taso mini, na dinga jin tausayinsa na kama ni ta yadda na bari zuciya ta rinjaye ni, nake hukunta shi da laifin da ba nasa ba. Duk yadda bana daukar sa, duk yadda na tsige shi daga nono lokacinsa bai yi ba. Bai sanya ya guje ni, ko ya yi mini 'kiwa ba. Na mi'ke sabe da shi a kafa'da, na shiga kicin na dauko masa *Fan yoghurt* na saka stro na bu'de masa, ai kuwa nan da nan ya zuke. Na soya masa 'kwai, a kicin din na bashi ya cinye tas. Ya sha ruwa ya yi gyatsa. Na dauke shi, da nufin shiga dakin Gudale dan na kai masa 'dan sa! Sai kawai ganin shigowar Sakina na yi, a gigice ta nufi dakinsa ba tare da ce mini kanzil ba. # Tean Gudale# # Team Guduyo# # Surayya Dee ✍️ # Ana tare 🤝. 2/8/23, 10:23 - Buhainat: *Wannan littafin na ku'di ne, biya 500 ku'din karatu ta wannan asusun* *2384876855* *Surayya Ibrahim* *Zenith Bank.* *A tura shaidar biya ta wannan lambar* *08032773332*. *SDK* *43-44* Hakan da Sakina ta yi mini sai na zama very guilty. Domin kafatalin makusantan sa ba wacce nake jin nauyin ta irin Sakina. Shudewar mintina goma suka fito tana ri'ke da shi sosai. Na kallesu ina jinjina girman soyayyar dake tsakaninsu. Na tuna irin tijarar da yake yi mata. Na tuna irin rantsuwar da ta yi akan babu ita, babu shi. Har cewa ya yi idan ta sake zuwa masa gida sai yasa Yan ta'addah sun dauke ta kowa ya huta da wuyar zaman ta. Ita kuma ta kafe matu'kar ni ce matar gidan kuwa zata zo a duk sadda ta so. Amma idan wata daban yake aure, idan ya ganta a gidan sa ya tabbatar ba Sakina Abbansu ya ra'da mata ba. Amma a yau sai na gane soyayyar da ke tsakaninsu ta daban ce, duk wani cin alwashin da suke yi na babu su, babu juna iya lebensu ne, ko kan harshe bai hau ba, bare kuma zuciyoyinsu. Bansan me ya saka harshena ya yi mini nauyi ainun ba. Na kasa bu'de baki na yi musu magana, ko da kuwa iya sannu ne. Na koma na zauna a sanyaye! Aman ya kwanta a jikina tabbacin dai yana samun nutsuwa a jikin nawa. Mama na yiwa waya idan tuwo ta yi ta aikowa Aman! Kai tsaye ta ce bata yi girki ba, na san kuma dalilin da ya sanya ta hana ni. Har wajen takwas na dare ba su, babu labarin su. Ina zaune, ina ta faman tubka da warwara. Sai ga su sun dawo, ya 'dan ji sau'ki ba kamar lokacin da suka fita ba, tabbacin ruwa aka 'kara masa. A falo ya zauna. Yayin da Sakina ba ta zauna ba, ta ajiye masa ledar magungunansa, tare da cewa "Ka 'karantawa kanka damuwa, ka dai ji abin da likita ya fa'da maka". Ta juyo ta kalle ni ba walwala ta ce "jininsa ne ya yi 'kasa a dalilin baya samun barci da kuma wadataccen abinci. Shiyasa ulcer ta sake bada gudunmawa. Ki kula da abincinsa da maganinsa". Na ce "To" a hankali. Cikin rauni ya ce "Sakina kin ce zaki bata ha'kuri a madadina! Dan Allah kar ki tafi baki kawo 'karshen wannan dambarwar ba. Da gaske na ke yi bazan iya daukar abin da Guduyo ta dauka ba. Ta fini karfin zuciya, ki huce Sakina dan Allah". A hankali ta ce "Amma na ce ka kwantar da hankalinka ko?" "Ta ya ya hankalina zai kwanta kin zuba ido kina kallon yadda na zama a gidana, alhalin kina da damar da zaki kashe mini wannan wutar! Anti Sakina dan Allah ba zan iya ba". Ya fa'da cikin rauni sosai. Ta nisa ta ce "yanzu baka gamsu komai ya wuce ba?" Ya sake shagwabe mata ya ce "ki fa'da mata ta dinga dafa mana abinci, ta daina yi mini rashin kunya, sannan ta dinga zuwa 'dakina, ko kuma ta daina rufe mini 'kofar 'dakinta". Nauyin maganganunsa suka kama Sakina ta ce "To zan fa'da, za kuma ta gyara". Ya lumshe ido ya ce "Na gode Anti". A fili ta ce wannan "Antin dai ba har zuci bane". Ya sake cewa "Da gaske nake Antina ce ina da yar'uwar da ta zarce ki ne?" Ta murmusa ta ce "Sai Guduyo". Ya langwabe kai ya ce "Ita ai yanzu ta ture ni akan matsayina, ta 'ki yarda da dimbin soyayyar da nake yi mata. Shin an ta'ba yiwa wani 'dan-adam rashin uzziri iri na kuwa Sakina?". Ta ce "Ai kuwa uzzirin da ta yi maka ba kowa ake yi wa irinsa ba". Ya girgiza kansa ya ce "Na gamsu ta yi mini, amma yanzu ina rokon a sake yi mini. Pls Sakina! Ki yafe mini, na tabbatar idan kika huce gaba'daya Guduyo zata yafe mini. Ke ce ita, na sani". Ya fa'da yana ru'ko dukkan hannuwanta. Ta zuba masa ido sosai sannan ta ce "Tunda har na dawo maka da ita, ai kuwa ka san na yi ha'kuri". Ya sassauta murya ya ce "wannan na dole ne Sakina! Ki goge komai a zuciyar ki. Wallahi na canja, zan yi mata adalci, zama na Fisabidillahi zamu yi". Na lura jikin Sakina ya yi laushi tubus. Yayin da ni kuwa ban ji komai ba. Ta kalle ni fuskarta ba walwala ta ce "Tashi ki samo masa abin da zai ci kafin ya sha magani". A hankali na ce "Ban dafa komai ba". Ta zuba mini ido sosai ta ce "cewa na yi ai ki samo masa ba wai ki kawo ba". Girman Sakina ya sanya na mi'ke na doshi kicin din. A raina kuwa ba karamin takaici nake ji ba, domin na riga na ci alwashin ba zan sake 'dora tukunya saboda shi ba, ba zan sake dafa abinci na bashi dan ra'din kaina ba. Na sani bai son jollof din taliya tsurarta, wacce babu vegetables a ciki. Dan haka na dafa a hakan. Na zubo masa plate na Kai gabansa na ajiye. Na koma na dauko kifi a fride wanda na Riga na soya, na yi pepper fish. Na yi warming dinsa, na zuba mana taliyar a plate daya na dora kifin a kai saboda na sani Sakina masoyiyar kifi ce fiye da nama. Na saka fork guda biyu, na kai gabanta tare da cewa "ga abinci Maman Nana". Ta ce "Ya baki saka masa kifin ba shi? Na ce "Bai dame shi ba ne". Ina kallonsa yana ta juya abincin nan. Amma ga mamakina sai na ga yana ci a gaggauce tamkar dai ya samu abin da yake tsananin so. A zuciyata na ce "Ashe dama wulakanci ne, ba ci ne baka yi ba. Muka ci abincin mu da Sakina tana yi tana bawa Aman a baki. Muka kammala ta yi haramar tafiya, na rakata har harabar gate. Ta kalle ni ta sassauta murya ta ce "Ki dinga bashi abinci, sannan ki daina jan doguwar magana a tsakanin ku, komai ya ce kawai ki ce "To". Nan da nan na fara kuka na ce "Na gane dai yanzu so kike kawai ki koma bayan sa". Cikin rarrashi ta ce "Ai na sha fa'da miki ke da shi 'daya kuke a waje na, ba wanda ya fi wani. Kin sani a koyaushe ina bayan ki ne. Ba dan kin fi shi ba, sai dan kin fi shi gaskiya da ha'kuri. Sannan ba zai yiwu na zuba ido na bari ki wula'kanta ba, a ko'ina zan baki kariya. Hakan kuma ba shine dalilin da zan 'ki fa'da miki gaskiya ba." Ta yi shiru tana kallon yadda nake kuka 'kasa 'kasa. Ta sake sassauta murya ta ce "ki yi shiru! Ki ji me zance miki Sadiya". Na dan nutsu ka'dan. Ta yi waiwaye dan ta tabbatar babu kowa a kusa da mu. Ta numfasa ta ce "Ulcer ke damunsa. Ki kula da lafiyarsa ta hanyar bashi abinci mai kyau kuma marar yaji. Shin idan bai koshi ba, ta ina ma zai dinga kwadayin ki bare ki ja shi a kasa? Idan ba kya kwalliya ta ina zaki ki'dima shi ya rasa nutsuwa? Shin idan ba kya ta'kaita magana a tsakaninku yaushe zai damu da sai kin yi masa magana? Idan ya fita ki shiga ki gyara masa dakinsa. Na sani yanzu ya gane yana sonbki, amma so nake sai ya gane ke ce duniyarsa! kuma dole ne ya zauna dake cikin mutuntunta wa. Amma hakan ba zai faru ba sai kin iya takun ki." Hawaye ya 'balle mini na ce "kina nufin na dinga zuwa 'dakinsa kenan?" Da sauri ta ce "Idan ba ya gidan ki shiga ki gyara masa, amma ban ce ki je masa kwana ba. Ai na yi miki al'kawarin sai ya gane kuren sa akan furucinsa, sai ya 'karyata kansa da kansa." Bakina na rawa na ce "Na gode sosai". Mun jima a wajen sannan ta tafi. Na dawo na tarar basa falon. 'Dakina na shiga, ga mamakina sai ganinsa na yi, har ya yi wanka yana sanye da wata cotton 'din jallabiya marar nauyi maroon kala. Yana kwance akan gadona ya saka Aman a gabansa da yake barcinsa cikin nutsuwa, shima ya yi masa wankan. Ban ce masa 'kala ba, na shiga na yi wanka na kuma yi alwallah. Na shirya cikin lallausan kayan barci, riga mai dogon wando. Wanda order ne na mussaman cikin tarin odar *Umm Muhd collection* 08063358662. Har yanzu ban daina amfani da kayan Oriflame ba, tunda na yi sa'a na hadu da jakadiyar su da ta lakanci mayukan da suka dace da kowacce irin fata walau dry ko oily. Tun lokacin yanmattancina na gasgata mayukan oriflame da *Aisha lame* ta za'ba mini su, har yau kuma ban canja ba, domin kuwa duk tsiyar Gudale da kansa yake bani ku'din siyan mayukan Yana fa'din yana ganin amfanin su. Tuntu'be ta Dan samun naki nau'in man da zai dace da fatarki mussaman a wannan season 'din na hammattan. 07036662633. Na gasgata ta. Sai da na kammala komai, dakin ya kaure da kamshin kayan da na yi amfani da su. na fita kamar wacce zata je kicin sai kawai na shige dakin su Afrah na rufe na yi kwanciyata. Har barci ya fara 'dauka ta na dinga jin bugun kofar tare da 'kiran sunana. Na yi tsaki sosai na yi bakam. Da safe kuwa, da wuri na fito na shirya masa abin karin kummalo. Ya fito cikin shadda getzna fara 'kal. Kyau iya kyau ya yi, duk da fuskarsa a 'daure take, idonsa na gefen dama jini ya kwanta a ciki tabbacin yana cikin bacin rai mai tsananin gaske. Na yi kamar ban gane ba na ce "Ina kwana? an kammala abinci". Bai ko kalleni ba, bare ya amsa, ya fice da Aman. Na yi murmushi na ce "wanzami bai son jarfa. Kai tsaye wajen Umma ya nufa, ya same ta ta idar da walaha. Yayin da Amnah take kan gado tana barci, Afrah kuwa tana tare da Antin Zaria a 'daya dakin. Ta karbi Aman tana yi masa wasa. Ta shafa cikinsa ta ce "Da alamun cikin nan bai cika ba maigidana". Nan da nan ta 'kira Abida ta dauke shi tare da cewa "ki ha'da masa tea ya sha". Ta zuba masa ido sosai ta numfasa ta ce "Ya jikinka?" A hankali ya ce "Da sau'ki Umma! Dama zan fa'da miki ne zan je Gusau". Da azama ta ce "Yanzun?" Kai kawai ya daga mata. Ta zuba masa ido sosai tana nazartar sa. Cike da kulawa ta ce "A cikin halin da kake ciki na jinya zaka dauki mota ka tafi har Gusau? Idan baka damu da rayuwar ka ba ni na damu dan haka ba inda zaka je". Ya yi kasa da kansa ya ce "Ki yi hakuri ya zama dole ne, idan ba zuwa na yi ba, ba zan ta'ba samun nutsuwa ba." "Fa'da mini me zaka je yi" Ya yi shiru domin a yanzu ba zai ta'ba iya fa'din laifin Guduyo a gabanta ba. Dan haka sai ya ce "Zuwa zan yi na gaida Baban kawai". Ta ce "To sai ka samu lafiya sannan zaka je din". Ya yi shiru amma yana jin tamkar ya yi ta ihu, ba abin da yake so a yanzu irin ya samu kwanciyar hankali. Ya tabbatar kuma ba zai samu ba, sai ya samu aminci da Guduyonsa. Cikin rauni ya ce "Zan iya zuwa Umma". "Ba fa zaka je yau ba wallahi". Jin ta rantse ya sanya shi ha'kurin dole. Ya tashi yana cewa "To shikenan bari na koma na dan kwanta". Ta amsa da ambaton "Hakan ya fi". Ya shigo da sallamh ya tarar da na yi wanka na gyaran gidan tsab, ina zaune a falon ina karyawa cikin nutsuwa. Sanye nake cikin dankararen leshin da Kawata ta zana shi da kanta, ta yi oder, Ni kaina leshi ba karamin shiga raina ya yi ba, sannan ban ta'ba ganin wata da shi ba, saboda selected oder ne na manyan Mata. *Amyas newly & faily items* kenan. Murmushi na yi na yadda na samu hayar gida cikin sau'ki da rahusa a kuma area mai kyau da tsaro a hannusu. Na sake tuna sadda suka zo har guday suka sayi kujeruna cikin aminci da mutuntawa. Na tuna injin wanki na hannu mai kyau da na siyawa Aziza a hannusu tamkar sabo Kuma cikin farashi mai rahusa. Idan kuna neman komai da ruwanki to samu *Amyas newly & fairly used items* Komai na su cijin tsari da sauki da kuma.mutuntanta abokan huldarsu. O8083909947. Ya wuce wajen cin abinci ya zubo ya dawo falon ya zauna kusa da ni. Har ya kammala zaman kurame ne a tsakaninmu. Kallona kawai yake yi na sani kwalliyar da na yi ta ki'dima shi, sau tari yana yawan tambayar inda ake zabga mini dinkuna na garari. Da kansa ya nemi shagon telar Dan ya gasgata maganar da na fa'da masa cewa mace ce. Domin a farko ya dauka namiji ne yake auna ni saboda tsananin yadda idan aka mini dinki suke zama a cikina na yi cass, duk da ina da jiki. *Umm Muhd collection* kenan kwararriyar tela kuma shahararriyar yar kasuwar da bata saba al'kawari duk abin da kike so zata kawo miki har gida, dangin sutura, hatta kayan kicin, zababbu rantsattsu kuma a saukaka miki. Tabbas ni shaida ce. Wanda duk yake group dinta zai shada hakan 08063358662. Ya kasa ha'kuri ya dube ni ya ce *"Halah* fa'da mini matsayina a gidan nan". Ba ja in ja na ce "Mai gida mana". Yana kallon nawa dai ya ce "Amma saboda kin samu daurin gindi shine na zama banza, na zama abin wula'kantawa a wajen ki? Sau nawa zan baki ha'kuri? Me zan yi ki gane ina son ki? Me zan yi dan na samu zaman lafiya da ke? Kin hana ni nutsuwa, kin gigita mini zaman lafiya ta, ya ya kike so na yi ne?". Na yi shiru na 'ki tankawa. Ya sake cewa "Tunda kika dawo a cikin rarrashin ki nake amma kin kafe kamar Dutse. To gaskiya zan fa'da miki na gaji, *Haka ya isa(Fatima Aminu Baba).*" Nan ma na yi shiru bance komai ba. Da ya gaji da jiran amsa ta. Cikin bada umarni ya ce "ki tashi ki je ki gyara mini dakina". A gajarce na ce "Na gyara tuntuni! Shiga ka gani." Bai musa ba! Ya tashi ya nufi dakin. Ya ganshi a tsabtace. Komai a kintse, haka ban'dakin ga kuma kamshin turaren mutanan gabas na tashi. Ya kwada mini kira "Hal Mohammadah". Na zum'bura baki na amsa sannan na mi'ke na tsaya daga bakin kofar dakin. Na ce "Ga ni". Yana mini wani irin kallon da yake rikita ni, ya kashe murya ya ce "Gyara ya yi kyau! Na gode miki, Allah ya yi miki albarka". Na amsa da "amin" a kasan ma'koshina. Ya matso kusa da ni ya kamo hannuna ya ce "Shigo mana Guduyo ki ji abin da zan fa'da miki". Ya jani har tsakiyar dakin ya yi 'kasa da murya ya ce "Taya ni mana mu yamutsa shimfi'dar nan. Ba dan ni zaki yi ba, ki duba Ubangijin da ya wajaba miki yi mini biyayya." Na tsuke fuska sosai ba tare da na ce uffan ba, idona ya cika da 'kwalla na kasa magana. Ganin hakan ya saka ya fara kokarin rage tufafin jikina. Bakina na rawa na ce "Ba zan iya ba". Da sauri ya dinga fa'din "Zaki iya baby nah! Bari a fara 'din" Na fisge jikina na shammace shi na fito kusan a guje. Ya biyo ni muka fara kokawa, ganin da gaske zai kai ni 'kasa ya sa na fara kuka ina cewa "Na rantse sai na fa'dawa Baban Gusau baka daina wula'kanta ni a falo ba". Tamkar na watsa masa ruwan zafi haka ya sake ni a zabure. Murya a dashe ya ce "Ba anan nake nufin yi ba Wallahi! zo muje ki taimake ni dan girman Allah". Ya zura hannu a aljihunsa ya fito da key din motarsa ya dam'ka a hannuna. Ya ce "Na baki motata! Duk 'kasar da kike so zan kai ki, zan saya miki bangle din gold." Da karfi na ce "Bana so! Duk ka had'awa amaryarka, Ni kuma ka bar mini abina tunda kofar 'Dan-agundi ne". Ya tunzura ainun ya ce "Haka kike da kafiya? Ba kisan rarrashi da ban ha'kuri ba?" Na ce "A wajen ka na koya". Ya zauna ya dafe kansa, yana ambaton Innalillahi wa Inna ilaihir rajiun. A kausashe ya ce "fa'da mini me kike nufi da nine Halima? "Ina nufin ka sahale mini, na je na samu wanda zai so ni da dukkan na'kasuna. Tunda a wangale kake jina, 'yar slim kake so, ba Abuskutu irina ba. Na sani zaka sake samo wacce ta yi daidai da taste dinka. Uwar maza ba uwar 'ya'ya mata Irina ba. Don haka nima ka bani damar da zan samu wanda ya dace da ni". Ina rufe baki ya dinga fa'din "Innalillahi wa inna ilaihir raji'un" da 'karfin gaske. Shudewar mintina goma muna haka. Ya dago muka ha'da ido, duk jijiyoyin kansa ta fito ta yi ru'du ru'du. Na dauke idona daga kallonsa. "Ba zan iya rabuwa da ke ba, na baki ha'kuri, manyanmu sun baki. Me yasa zaki tsananta irin haka, me yasa ba zaki ha'kura ba?" Kai tsaye na ce "saboda ban san ha'kuri ba, ban kuma iya shi ba." A hankali ya ce "Ban san wata halitta a doron 'kasa da ta zarta ki ha'kuri da *Yakana(Takori)* ba." "Cikin ido na kalleshi na ce "A da ne! a lokacin da nake tsananin son ka, nake tsananin son na rayu da kai. Amma a yanzu babu sauran ha'kuri a tsakaninmu tunda na gane baka so na, bani da mutunci a idon ka. Na riga na fa'da maka, na ha'kura da komai. Na fa'da hawaye yana silalowa daga idona" Cikin rauni sosai ya ce "Don't do this to me Halimatu! Ina son ki, ina son na rayu da ke, ki taimake ni ki yi ha'kuri. Zan miki wani al'kawari da zan dauwama ina ro'kon Ubangiji ya bani ikon cika miki shi matu'kar kika yafe mini". Na gallah masa harara na ce "Ri'ke al'kawarinka idan ka auro Fauziya sai ka yi mata. Ni kam ba abin da nake so daga gareka irin ka sahale mini, ko na sha'ki iskar da babu takura a ciki. Sanin kanka ne akwai wadanda suka fika dacewa da ni, kamar yadda na fahimci ban dace da kai ba a yanzu". Ya zuba mini ido sosai yana jin wani irin tashin hankali na kekketa shi. Bakinsa na rawa ya ce "Ni kika fa'dawa hakan? Ni ko Guduyo?" Ba kunya na ce "Eh". Ya mi'ke ya sake fita. Ni kuwa ko ka'dan ban ji tsoron abin da zai biyo baya ba. Ban tashi a wajen ba, ya sake shigowa! Ya shige dakinsa. Yayin da tunanin da nake yi ya dinga kutso mini. Ba abin da nake bu'kata irin na samu lokaci irin haka na cigaba da hakaito al'amuran da na fuskanta. # Team Gudale# # Team Guduyo# # Surayya Dee✍️. # Ana tare 🤝. 2/8/23, 10:25 - Buhainat: *Wannan littafin na ku'di ne, biya 500 ku'din karatu ta wannan asusun* *2384876855* *Surayya Ibrahim* *Zenith Bank.* *A tura shaidar biya ta wannan lambar* *08032773332*. *SDK* *43-44* Hakan da Sakina ta yi mini sai na zama very guilty. Domin kafatalin makusantan sa ba wacce nake jin nauyin ta irin Sakina. Shudewar mintina goma suka fito tana ri'ke da shi sosai. Na kallesu ina jinjina girman soyayyar dake tsakaninsu. Na tuna irin tijarar da yake yi mata. Na tuna irin rantsuwar da ta yi akan babu ita, babu shi. Har cewa ya yi idan ta sake zuwa masa gida sai yasa Yan ta'addah sun dauke ta kowa ya huta da wuyar zaman ta. Ita kuma ta kafe matu'kar ni ce matar gidan kuwa zata zo a duk sadda ta so. Amma idan wata daban yake aure, idan ya ganta a gidan sa ya tabbatar ba Sakina Abbansu ya ra'da mata ba. Amma a yau sai na gane soyayyar da ke tsakaninsu ta daban ce, duk wani cin alwashin da suke yi na babu su, babu juna iya lebensu ne, ko kan harshe bai hau ba, bare kuma zuciyoyinsu. Bansan me ya saka harshena ya yi mini nauyi ainun ba. Na kasa bu'de baki na yi musu magana, ko da kuwa iya sannu ne. Na koma na zauna a sanyaye! Aman ya kwanta a jikina tabbacin dai yana samun nutsuwa a jikin nawa. Mama na yiwa waya idan tuwo ta yi ta aikowa Aman! Kai tsaye ta ce bata yi girki ba, na san kuma dalilin da ya sanya ta hana ni. Har wajen takwas na dare ba su, babu labarin su. Ina zaune, ina ta faman tubka da warwara. Sai ga su sun dawo, ya 'dan ji sau'ki ba kamar lokacin da suka fita ba, tabbacin ruwa aka 'kara masa. A falo ya zauna. Yayin da Sakina ba ta zauna ba, ta ajiye masa ledar magungunansa, tare da cewa "Ka 'karantawa kanka damuwa, ka dai ji abin da likita ya fa'da maka". Ta juyo ta kalle ni ba walwala ta ce "jininsa ne ya yi 'kasa a dalilin baya samun barci da kuma wadataccen abinci. Shiyasa ulcer ta sake bada gudunmawa. Ki kula da abincinsa da maganinsa". Na ce "To" a hankali. Cikin rauni ya ce "Sakina kin ce zaki bata ha'kuri a madadina! Dan Allah kar ki tafi baki kawo 'karshen wannan dambarwar ba. Da gaske na ke yi bazan iya daukar abin da Guduyo ta dauka ba. Ta fini karfin zuciya, ki huce Sakina dan Allah". A hankali ta ce "Amma na ce ka kwantar da hankalinka ko?" "Ta ya ya hankalina zai kwanta kin zuba ido kina kallon yadda na zama a gidana, alhalin kina da damar da zaki kashe mini wannan wutar! Anti Sakina dan Allah ba zan iya ba". Ya fa'da cikin rauni sosai. Ta nisa ta ce "yanzu baka gamsu komai ya wuce ba?" Ya sake shagwabe mata ya ce "ki fa'da mata ta dinga dafa mana abinci, ta daina yi mini rashin kunya, sannan ta dinga zuwa 'dakina, ko kuma ta daina rufe mini 'kofar 'dakinta". Nauyin maganganunsa suka kama Sakina ta ce "To zan fa'da, za kuma ta gyara". Ya lumshe ido ya ce "Na gode Anti". A fili ta ce wannan "Antin dai ba har zuci bane". Ya sake cewa "Da gaske nake Antina ce ina da yar'uwar da ta zarce ki ne?" Ta murmusa ta ce "Sai Guduyo". Ya langwabe kai ya ce "Ita ai yanzu ta ture ni akan matsayina, ta 'ki yarda da dimbin soyayyar da nake yi mata. Shin an ta'ba yiwa wani 'dan-adam rashin uzziri iri na kuwa Sakina?". Ta ce "Ai kuwa uzzirin da ta yi maka ba kowa ake yi wa irinsa ba". Ya girgiza kansa ya ce "Na gamsu ta yi mini, amma yanzu ina rokon a sake yi mini. Pls Sakina! Ki yafe mini, na tabbatar idan kika huce gaba'daya Guduyo zata yafe mini. Ke ce ita, na sani". Ya fa'da yana ru'ko dukkan hannuwanta. Ta zuba masa ido sosai sannan ta ce "Tunda har na dawo maka da ita, ai kuwa ka san na yi ha'kuri". Ya sassauta murya ya ce "wannan na dole ne Sakina! Ki goge komai a zuciyar ki. Wallahi na canja, zan yi mata adalci, zama na Fisabidillahi zamu yi". Na lura jikin Sakina ya yi laushi tubus. Yayin da ni kuwa ban ji komai ba. Ta kalle ni fuskarta ba walwala ta ce "Tashi ki samo masa abin da zai ci kafin ya sha magani". A hankali na ce "Ban dafa komai ba". Ta zuba mini ido sosai ta ce "cewa na yi ai ki samo masa ba wai ki kawo ba". Girman Sakina ya sanya na mi'ke na doshi kicin din. A raina kuwa ba karamin takaici nake ji ba, domin na riga na ci alwashin ba zan sake 'dora tukunya saboda shi ba, ba zan sake dafa abinci na bashi dan ra'din kaina ba. Na sani bai son jollof din taliya tsurarta, wacce babu vegetables a ciki. Dan haka na dafa a hakan. Na zubo masa plate na Kai gabansa na ajiye. Na koma na dauko kifi a fride wanda na Riga na soya, na yi pepper fish. Na yi warming dinsa, na zuba mana taliyar a plate daya na dora kifin a kai saboda na sani Sakina masoyiyar kifi ce fiye da nama. Na saka fork guda biyu, na kai gabanta tare da cewa "ga abinci Maman Nana". Ta ce "Ya baki saka masa kifin ba shi? Na ce "Bai dame shi ba ne". Ina kallonsa yana ta juya abincin nan. Amma ga mamakina sai na ga yana ci a gaggauce tamkar dai ya samu abin da yake tsananin so. A zuciyata na ce "Ashe dama wulakanci ne, ba ci ne baka yi ba. Muka ci abincin mu da Sakina tana yi tana bawa Aman a baki. Muka kammala ta yi haramar tafiya, na rakata har harabar gate. Ta kalle ni ta sassauta murya ta ce "Ki dinga bashi abinci, sannan ki daina jan doguwar magana a tsakanin ku, komai ya ce kawai ki ce "To". Nan da nan na fara kuka na ce "Na gane dai yanzu so kike kawai ki koma bayan sa". Cikin rarrashi ta ce "Ai na sha fa'da miki ke da shi 'daya kuke a waje na, ba wanda ya fi wani. Kin sani a koyaushe ina bayan ki ne. Ba dan kin fi shi ba, sai dan kin fi shi gaskiya da ha'kuri. Sannan ba zai yiwu na zuba ido na bari ki wula'kanta ba, a ko'ina zan baki kariya. Hakan kuma ba shine dalilin da zan 'ki fa'da miki gaskiya ba." Ta yi shiru tana kallon yadda nake kuka 'kasa 'kasa. Ta sake sassauta murya ta ce "ki yi shiru! Ki ji me zance miki Sadiya". Na dan nutsu ka'dan. Ta yi waiwaye dan ta tabbatar babu kowa a kusa da mu. Ta numfasa ta ce "Ulcer ke damunsa. Ki kula da lafiyarsa ta hanyar bashi abinci mai kyau kuma marar yaji. Shin idan bai koshi ba, ta ina ma zai dinga kwadayin ki bare ki ja shi a kasa? Idan ba kya kwalliya ta ina zaki ki'dima shi ya rasa nutsuwa? Shin idan ba kya ta'kaita magana a tsakaninku yaushe zai damu da sai kin yi masa magana? Idan ya fita ki shiga ki gyara masa dakinsa. Na sani yanzu ya gane yana sonbki, amma so nake sai ya gane ke ce duniyarsa! kuma dole ne ya zauna dake cikin mutuntunta wa. Amma hakan ba zai faru ba sai kin iya takun ki." Hawaye ya 'balle mini na ce "kina nufin na dinga zuwa 'dakinsa kenan?" Da sauri ta ce "Idan ba ya gidan ki shiga ki gyara masa, amma ban ce ki je masa kwana ba. Ai na yi miki al'kawarin sai ya gane kuren sa akan furucinsa, sai ya 'karyata kansa da kansa." Bakina na rawa na ce "Na gode sosai". Mun jima a wajen sannan ta tafi. Na dawo na tarar basa falon. 'Dakina na shiga, ga mamakina sai ganinsa na yi, har ya yi wanka yana sanye da wata cotton 'din jallabiya marar nauyi maroon kala. Yana kwance akan gadona ya saka Aman a gabansa da yake barcinsa cikin nutsuwa, shima ya yi masa wankan. Ban ce masa 'kala ba, na shiga na yi wanka na kuma yi alwallah. Na shirya cikin lallausan kayan barci, riga mai dogon wando. Wanda order ne na mussaman cikin tarin odar *Umm Muhd collection* 08063358662. Har yanzu ban daina amfani da kayan Oriflame ba, tunda na yi sa'a na hadu da jakadiyar su da ta lakanci mayukan da suka dace da kowacce irin fata walau dry ko oily. Tun lokacin yanmattancina na gasgata mayukan oriflame da *Aisha lame* ta za'ba mini su, har yau kuma ban canja ba, domin kuwa duk tsiyar Gudale da kansa yake bani ku'din siyan mayukan Yana fa'din yana ganin amfanin su. Tuntu'be ta Dan samun naki nau'in man da zai dace da fatarki mussaman a wannan season 'din na hammattan. 07036662633. Na gasgata ta. Sai da na kammala komai, dakin ya kaure da kamshin kayan da na yi amfani da su. na fita kamar wacce zata je kicin sai kawai na shige dakin su Afrah na rufe na yi kwanciyata. Har barci ya fara 'dauka ta na dinga jin bugun kofar tare da 'kiran sunana. Na yi tsaki sosai na yi bakam. Da safe kuwa, da wuri na fito na shirya masa abin karin kummalo. Ya fito cikin shadda getzna fara 'kal. Kyau iya kyau ya yi, duk da fuskarsa a 'daure take, idonsa na gefen dama jini ya kwanta a ciki tabbacin yana cikin bacin rai mai tsananin gaske. Na yi kamar ban gane ba na ce "Ina kwana? an kammala abinci". Bai ko kalleni ba, bare ya amsa, ya fice da Aman. Na yi murmushi na ce "wanzami bai son jarfa. Kai tsaye wajen Umma ya nufa, ya same ta ta idar da walaha. Yayin da Amnah take kan gado tana barci, Afrah kuwa tana tare da Antin Zaria a 'daya dakin. Ta karbi Aman tana yi masa wasa. Ta shafa cikinsa ta ce "Da alamun cikin nan bai cika ba maigidana". Nan da nan ta 'kira Abida ta dauke shi tare da cewa "ki ha'da masa tea ya sha". Ta zuba masa ido sosai ta numfasa ta ce "Ya jikinka?" A hankali ya ce "Da sau'ki Umma! Dama zan fa'da miki ne zan je Gusau". Da azama ta ce "Yanzun?" Kai kawai ya daga mata. Ta zuba masa ido sosai tana nazartar sa. Cike da kulawa ta ce "A cikin halin da kake ciki na jinya zaka dauki mota ka tafi har Gusau? Idan baka damu da rayuwar ka ba ni na damu dan haka ba inda zaka je". Ya yi kasa da kansa ya ce "Ki yi hakuri ya zama dole ne, idan ba zuwa na yi ba, ba zan ta'ba samun nutsuwa ba." "Fa'da mini me zaka je yi" Ya yi shiru domin a yanzu ba zai ta'ba iya fa'din laifin Guduyo a gabanta ba. Dan haka sai ya ce "Zuwa zan yi na gaida Baban kawai". Ta ce "To sai ka samu lafiya sannan zaka je din". Ya yi shiru amma yana jin tamkar ya yi ta ihu, ba abin da yake so a yanzu irin ya samu kwanciyar hankali. Ya tabbatar kuma ba zai samu ba, sai ya samu aminci da Guduyonsa. Cikin rauni ya ce "Zan iya zuwa Umma". "Ba fa zaka je yau ba wallahi". Jin ta rantse ya sanya shi ha'kurin dole. Ya tashi yana cewa "To shikenan bari na koma na dan kwanta". Ta amsa da ambaton "Hakan ya fi". Ya shigo da sallamh ya tarar da na yi wanka na gyaran gidan tsab, ina zaune a falon ina karyawa cikin nutsuwa. Sanye nake cikin dankararen leshin da Kawata ta zana shi da kanta, ta yi oder, Ni kaina leshi ba karamin shiga raina ya yi ba, sannan ban ta'ba ganin wata da shi ba, saboda selected oder ne na manyan Mata. *Amyas newly & faily items* kenan. Murmushi na yi na yadda na samu hayar gida cikin sau'ki da rahusa a kuma area mai kyau da tsaro a hannusu. Na sake tuna sadda suka zo har guday suka sayi kujeruna cikin aminci da mutuntawa. Na tuna injin wanki na hannu mai kyau da na siyawa Aziza a hannusu tamkar sabo Kuma cikin farashi mai rahusa. Idan kuna neman komai da ruwanki to samu *Amyas newly & fairly used items* Komai na su cijin tsari da sauki da kuma.mutuntanta abokan huldarsu. O8083909947. Ya wuce wajen cin abinci ya zubo ya dawo falon ya zauna kusa da ni. Har ya kammala zaman kurame ne a tsakaninmu. Kallona kawai yake yi na sani kwalliyar da na yi ta ki'dima shi, sau tari yana yawan tambayar inda ake zabga mini dinkuna na garari. Da kansa ya nemi shagon telar Dan ya gasgata maganar da na fa'da masa cewa mace ce. Domin a farko ya dauka namiji ne yake auna ni saboda tsananin yadda idan aka mini dinki suke zama a cikina na yi cass, duk da ina da jiki. *Umm Muhd collection* kenan kwararriyar tela kuma shahararriyar yar kasuwar da bata saba al'kawari duk abin da kike so zata kawo miki har gida, dangin sutura, hatta kayan kicin, zababbu rantsattsu kuma a saukaka miki. Tabbas ni shaida ce. Wanda duk yake group dinta zai shada hakan 08063358662. Ya kasa ha'kuri ya dube ni ya ce *"Halah* fa'da mini matsayina a gidan nan". Ba ja in ja na ce "Mai gida mana". Yana kallon nawa dai ya ce "Amma saboda kin samu daurin gindi shine na zama banza, na zama abin wula'kantawa a wajen ki? Sau nawa zan baki ha'kuri? Me zan yi ki gane ina son ki? Me zan yi dan na samu zaman lafiya da ke? Kin hana ni nutsuwa, kin gigita mini zaman lafiya ta, ya ya kike so na yi ne?". Na yi shiru na 'ki tankawa. Ya sake cewa "Tunda kika dawo a cikin rarrashin ki nake amma kin kafe kamar Dutse. To gaskiya zan fa'da miki na gaji, *Haka ya isa(Fatima Aminu Baba).*" Nan ma na yi shiru bance komai ba. Da ya gaji da jiran amsa ta. Cikin bada umarni ya ce "ki tashi ki je ki gyara mini dakina". A gajarce na ce "Na gyara tuntuni! Shiga ka gani." Bai musa ba! Ya tashi ya nufi dakin. Ya ganshi a tsabtace. Komai a kintse, haka ban'dakin ga kuma kamshin turaren mutanan gabas na tashi. Ya kwada mini kira "Hal Mohammadah". Na zum'bura baki na amsa sannan na mi'ke na tsaya daga bakin kofar dakin. Na ce "Ga ni". Yana mini wani irin kallon da yake rikita ni, ya kashe murya ya ce "Gyara ya yi kyau! Na gode miki, Allah ya yi miki albarka". Na amsa da "amin" a kasan ma'koshina. Ya matso kusa da ni ya kamo hannuna ya ce "Shigo mana Guduyo ki ji abin da zan fa'da miki". Ya jani har tsakiyar dakin ya yi 'kasa da murya ya ce "Taya ni mana mu yamutsa shimfi'dar nan. Ba dan ni zaki yi ba, ki duba Ubangijin da ya wajaba miki yi mini biyayya." Na tsuke fuska sosai ba tare da na ce uffan ba, idona ya cika da 'kwalla na kasa magana. Ganin hakan ya saka ya fara kokarin rage tufafin jikina. Bakina na rawa na ce "Ba zan iya ba". Da sauri ya dinga fa'din "Zaki iya baby nah! Bari a fara 'din" Na fisge jikina na shammace shi na fito kusan a guje. Ya biyo ni muka fara kokawa, ganin da gaske zai kai ni 'kasa ya sa na fara kuka ina cewa "Na rantse sai na fa'dawa Baban Gusau baka daina wula'kanta ni a falo ba". Tamkar na watsa masa ruwan zafi haka ya sake ni a zabure. Murya a dashe ya ce "Ba anan nake nufin yi ba Wallahi! zo muje ki taimake ni dan girman Allah". Ya zura hannu a aljihunsa ya fito da key din motarsa ya dam'ka a hannuna. Ya ce "Na baki motata! Duk 'kasar da kike so zan kai ki, zan saya miki bangle din gold." Da karfi na ce "Bana so! Duk ka had'awa amaryarka, Ni kuma ka bar mini abina tunda kofar 'Dan-agundi ne". Ya tunzura ainun ya ce "Haka kike da kafiya? Ba kisan rarrashi da ban ha'kuri ba?" Na ce "A wajen ka na koya". Ya zauna ya dafe kansa, yana ambaton Innalillahi wa Inna ilaihir rajiun. A kausashe ya ce "fa'da mini me kike nufi da nine Halima? "Ina nufin ka sahale mini, na je na samu wanda zai so ni da dukkan na'kasuna. Tunda a wangale kake jina, 'yar slim kake so, ba Abuskutu irina ba. Na sani zaka sake samo wacce ta yi daidai da taste dinka. Uwar maza ba uwar 'ya'ya mata Irina ba. Don haka nima ka bani damar da zan samu wanda ya dace da ni". Ina rufe baki ya dinga fa'din "Innalillahi wa inna ilaihir raji'un" da 'karfin gaske. Shudewar mintina goma muna haka. Ya dago muka ha'da ido, duk jijiyoyin kansa ta fito ta yi ru'du ru'du. Na dauke idona daga kallonsa. "Ba zan iya rabuwa da ke ba, na baki ha'kuri, manyanmu sun baki. Me yasa zaki tsananta irin haka, me yasa ba zaki ha'kura ba?" Kai tsaye na ce "saboda ban san ha'kuri ba, ban kuma iya shi ba." A hankali ya ce "Ban san wata halitta a doron 'kasa da ta zarta ki ha'kuri da *Yakana(Takori)* ba." "Cikin ido na kalleshi na ce "A da ne! a lokacin da nake tsananin son ka, nake tsananin son na rayu da kai. Amma a yanzu babu sauran ha'kuri a tsakaninmu tunda na gane baka so na, bani da mutunci a idon ka. Na riga na fa'da maka, na ha'kura da komai. Na fa'da hawaye yana silalowa daga idona" Cikin rauni sosai ya ce "Don't do this to me Halimatu! Ina son ki, ina son na rayu da ke, ki taimake ni ki yi ha'kuri. Zan miki wani al'kawari da zan dauwama ina ro'kon Ubangiji ya bani ikon cika miki shi matu'kar kika yafe mini". Na gallah masa harara na ce "Ri'ke al'kawarinka idan ka auro Fauziya sai ka yi mata. Ni kam ba abin da nake so daga gareka irin ka sahale mini, ko na sha'ki iskar da babu takura a ciki. Sanin kanka ne akwai wadanda suka fika dacewa da ni, kamar yadda na fahimci ban dace da kai ba a yanzu". Ya zuba mini ido sosai yana jin wani irin tashin hankali na kekketa shi. Bakinsa na rawa ya ce "Ni kika fa'dawa hakan? Ni ko Guduyo?" Ba kunya na ce "Eh". Ya mi'ke ya sake fita. Ni kuwa ko ka'dan ban ji tsoron abin da zai biyo baya ba. Ban tashi a wajen ba, ya sake shigowa! Ya shige dakinsa. Yayin da tunanin da nake yi ya dinga kutso mini. Ba abin da nake bu'kata irin na samu lokaci irin haka na cigaba da hakaito al'amuran da na fuskanta. # Team Gudale# # Team Guduyo# # Surayya Dee✍️. # Ana tare 🤝. 2/8/23, 10:25 - Buhainat: *Wannan littafin na ku'di ne, biya 500 ku'din karatu ta wannan asusun* *2384876855* *Surayya Ibrahim* *Zenith Bank.* *A tura shaidar biya ta wannan lambar* *08032773332*. *Na fa'da muku kuwa mai sirrin kayan *G.H.T. mai sau'kin farashi fiye da na sauran jakadun su?* *Faseelat ta kware wajen gyaran amare da nagartattun supplement marasa illah.* *Tana da supplement din dagargaza infection .* *Tana da maganin ulcer da na basir* *Haka nan tana da mayukan da suke gyaran fata.* *Tana da supplement masu narkar da kitse, masu daidaita shape din mace *. *Tuntu'be ta a wnanan lambar dan Karin bayani 07039269802*. *SDK* *45-46.* *Gudale* Kai tsaye gida ya koma, ya karya, sannan ya yi wanka ya rufe gidan ya doshi cikin gidansu. A falo ya tarar da Umma, tana karyawa. Ba wani walwala ta amsa gaisuwarsa. Cike da kulawa ya ce "Umma menene? Tun shekaranjiya nake ganin ki a haka". Kai ta girgiza alamun babu komai. Ya matsa kusa da ita sosai, ya ce "Dan Allah Umma bana son wannan yanayin da nake gani a tare ke" Ya fa'da cikin rauni sosai. A hankali ta ce "Gudale tun ba'a je ko ina ba ka fara canja mini? Sai ka kwana ka yini baka leko ka ganni na ganka ba! Idan na ce za'a karbe mini kai, ka ce mini ba hakan ba, amma a 'kasa da kwanaki ashirin ka fara mance uwarka. Wannan ne alwashin da ka yi mini? Na ce maka kar ka yi kuskuren ta'ba yarinyar nan, amma alamu sun nuna ba ka ji maganata ba". A hankali ya ce "Ina nan akan ra'ayina Umma! Ina tabbatar miki ba abin da ya faru, ina sake jaddada miki ba wanda zai sha gaban ki a wajena, balle har a sa na manta ki. Zan kuma tabbatar miki da gaskiyar maganganuna nan gaba ka'dan. Ki daina damuwa Ummah". A hakan Abba ya shigo ya same su. Ya zauna yana jin da'din yadda yake ganin nutsuwa tana ratsa Gudale. Ya dinga farin-ciki! A ransa yake raya da ya san aure zai sa ya nutsu haka da wuri ai da tuntuni ya yi masa. Ya mi'ka masa file, hannu biyu Gudale ya sanya ya karba. Abba ya ce "Jarrabawar daukan ma'aikata zaka je F.I.R.S. ranar laraba mai zuwa. Ya yi godiya, sannan ya ce "Akwai wata jarabawar ma da zan yi a Lagos satin sama, a sani cikin addu'a ba'a san inda za'a dace ba". Addu'ar kuwa duka iyayen nasa suka dinga jero masa. Tsawon lokaci suna tare kafin Abba ya fice ya barsu. Sai da Abba ya Jima da fitar, Gudale ya numfasa ya ce "ki kwantar da hankalinki Umma! kwanan nan zan tabbatar miki bana son Guduyo, ba kuma zan zauna da ita ba". Murmushin jin da'di ta yi! Sannan ta ce "Ni kuwa zan tsaya maka dan ka samu cikar burinka. Bana fatan ha'da iri da zuri'ar gidan mai Ashafa". Suka rabu cikin farin ciki. Ganin lokaci ya tafi ya sanya ya zarce massalaci dan gabatar da sallar azahar. Ana idarwa ya koma gidansa. Sai da ya kunna talabijin sannan ya kwanta a doguwar kujerar falon. Ya kalli agogo da ya nuna 1:33pm ya ja tsaki sosai ya furta "Ko sai yaushe zata dawo?" A ransa yake ayyana da ace tana gida da yanzu an kammala masa abincin da yake son ci. Amma yanzu, yana gida matarsa tana waje da sunan karatu. Wani irin abu ya tokare shi da ya tuna hijabin Guduyo bai hana aga tudun kirjinta ba. Abin da yake ki'dima shi a tare da ita. Yana son ya gansu a zahiri. Sannan ba abin da ya tsana tun fil'azal irin ace bata gida. Ko ba maganar arziki za su yi ba, yafi son ya ganta a gida. Balle kuma yanzu da take amsa sunan matarsa. Ya sake jan tsaki mai tsananin gaske tamkar yana tare da ita dan ta fahimci halin takaicin da yake ciki. Kamar daga sama ya ji an turo 'kofa ha'de da sallama. Ya yi bakam tamkar mai barci. Ganin hakan ya sanya na wuce dakina a hankali dan kar na tashe shi. Sallah kawai na yi, na fito zuwa kicin. Hidimar abinci na hau yi, ba jimawa gidan ya karade da 'kamshi. A nutse nake yin komai. Bansan ya tashi ya haye sama ba. Ina cikin shirya abincin akan dining na ga ya sauko da alwalarsa. Na bu'de murya na ce "Sannu da gida! Na dawo ai kana barci". A lalace ya ce "sannu da asibiti" Ya yi wucewar sa. Na yi sallah, na koma na hau aikin snacks tunda na fridge ya kare, shi kuma yafi son su akan abinci mussaman da daddare. Ban samu kaina ba sai wajen biyar. A gurguje na yi wanka, na shirya, sannan na zuba abinci na dawo falo. Ina ci ya shigo hannunsa da leda baka. Na karba tare da cewa "Sannu da dawowa". Ya zauna yana ta kumburin da ban san dalilinsa ba. Na cigaba da cin abincin. Ya gaji ya ce "tashi ki wanko mini! Banda dai ke yar wula'kanci ce na kawo abu, amma ki kasa budewa ki ga menene a ciki?" Na ajiye plate 'din hannuna na mi'ke, da ledar ina cewa "Yi ha'kuri". Na bu'de na ga yalo da 'data ne. Na wanko na zubo a bowl na ha'do da ruwa na kawo masa. Sai da na kammala cin abincin. Ya kalleni ya ce "Banga kin dauko yalon ba?" Na girgiza kai na ce "Basu dame ni ba". Ya kuwa tunzura ya ce "Dole su dame ki, domin suna rage kitse! Kin san kuwa ke cinsu ya kama". Na ce "Hakane" a gajarce. Na mi'ke da nufin barin falon. Ya ce "kar ki sake ki barni a zaune". Na koma na zauna, na kasa cewa komai. Ya 'kan'kace ido ya ce "fado mini hakkokin miji akan matarsa". Na yi shiru! Ya ja tsaki ya ce "sai ki fa'da mini me da me kika yi a Asibitin?" A hankali na ce "karatun da na je koya shi na yi kawai". Ya girgiza kai ya ce "kuma yanzu dan kawai Nasara asarar duniya sun yi galaba akan musulmai. Kika iya tsayawa gaban maza a haka, suna kallon surar 'kirjin ki cikin munafukin hijabin da bai hana komai bayyana ba. Alhalin ni da na biya sadaki bani da 'kimar da za'a nuna mini su. Ai wallahi 'karshen cuta an yi mini, sai dai fatan ta zame mini kaffara". Kaina ya daure, na zuba masa ido sosai sai na ga tamkar mai jin barci. Gaba'daya idonsa ya jirkice. Zuciyata ta dinga harbawa da sauri da sauri a dalilin zargin da ya tsananta a zuciyata. Ba komai make zato ba illah a buge yake domin maganar tasa tafi dace wa da wanda yake cikin maye. Ban da haka yaushe zai yi zaton ni ce zan nemi ya kalli wani abu a jikina mussaman 'kirjin da budurwa ta fi 'boyon sa a jikinta. Maimakon da ya ji na yi shiru, shima ya bar maganar sai kawai ya sake cewa "Tashi tsaye ki cire mini rigarki na ga yadda suke. Idan kuma zaki fa'da mini yadda suke da bakinki to". Na rasa inda zansa kaina. Na kasa tashi, haka na kasa ce masa uffan. Ya kalle ni ya ce "kin san Àllah sai kin za'bi daya! ko dai ki cire riga na gani da kaina, ko kuwa ki fa'di yadda suke da baki". Idona ya ciko da hawaye na ce "Bana son irin haka Yaya Sadik". "Idan ma Yaya Abubakar zaki ce Wallahi sai kin yi 'daya a cikin biyu". Na goge 'kwallar da take zuba. Na ce " ai ni bansan yadda zan kwantanta su ba." "Then sai ki cire mini rigar". Na fara kuka sosai. Ya tabe baki ya ce "ko bubburwa zaki yi sai kin bi umarnina Wallahi". Jin rantsuwar da ya yi ya sanya na ha'diye kukan na ce "Bani hasken yadda zan kwantanta su din". Ya numfasa ya ce "Ban da mugunta ki bu'de su to kawai mana". A hankali na ce "Ba zan iya ba". "Ooh to sai ki yi wanda zaki iya 'din". Ya fa'da a banza ce. Cikin daurewar fuska na ce "manya ne kamar kan jariri". Ya zungudo ya ce "wanne irin description ne wannan? Kinga Malama bayani sosai zaki yi mini, zubin mangwaro ne ko lemon za'ki, ko kuwa zubin kwakwa ne?". Na zum'bura baki na 'ki yin magana. Ya tunzura ya ce "To na ma fasa bayanin, ganinsu zan yi". Na yi kamar ban ji ba. "Kin ji" Ya fa'da da karfi. "Eh" na amsa masa a gajarce. "To Bismillah! Mi'ke domin ba a zaune nake bu'katar ganin ba". "Na mi'ke din amma a zuciyata na kudire idan har ni zan nuna masa, Wallahi ba zai gani ba. Duk maganar da ya yi baisa na bu'de ba. Ya hassalo ya ce "Anya kuwa Sadiya zaki yi albarka? Mijin da sai ya 'daga sawunsa zaki rabauta kike yi wa wannan gadddamar?" Cikin rawar murya na ce "ka ji tsoron Allah! Wacce irin amarya ka dauke ni ne?" Hawaye ya balle mini. Jikinsa ya dan yi sanyi ka'dan. Ya taso ya same ni inda nake tsaye. Ya ce "Da ga maganar fatar baki zaki dinga yi mini kuka? Kuma yanzu ya kike so na yi da rantsuwar da na yi akan sai na ga ni?" Na yi kasa da kaina na kasa bashi amsa. Ya sanya hannunwansa ya yi sama da rigar, da kyar ya samu ya fito da su, ya dago ya kalle ni ya ga na yi kicin kicin da fuska tamkar an fa'da mini sakon mutuwa. Ya koma ya zauna yana cewa "kar ki sauke rigar nan". Sai da ya gama kallonsa har ya gaji. Sannan ya numfasa cikin dakushasshiyar murya marar amo ya ce "you can sit down". Maimakon na zauna a falon sai kawai na juya zuwa dakina, ina tafe ina gyara rigata. Yayin da shikuma ya shiga wani irin al'amari mai wahalar gane wa. Washagari da safe sai da na kammala aikin gyara gidan sannan na soya Samomsa na dafa shayi. Na karya, na shiga wanka. A gurguje na shirya. Kamar jiya haka na nufi dakin oga Gudale". A zaune a tsakiyar gadon na same shi. Na gaishe shi, ya amsa ciki ciki. "Na kammala". Haka kawai na fa'da ya hayayyako mini. "Ke dai Guduyo hankalinki a sama yake wallahi. Ace wai baki iya komai ba, sai dafa abinci da fita sassafe! Baki san me zaki yiwa mijinki dan ki samu yardar mai duka ba?" Na yi jigum ina kallonsa da dukkan idanuwana cike da mamaki na ce "ka dai so ce mini bani da hankali ne kawai amma banda haka menene bana yi maka?" Ya girgiza kai ya ce "Yi tafiyar ki kawai" Na marairaice na ce "Kudin mota". Ya zuba mini ido ya ce "kina nufin ba ku'di a hannunki?" Kai tsaye na ce "Babu". Nam ma sai da ya gama hargagaginsa na an cuce shi. Ban tanka ba ya zaro 'dari biyar ya bani. Har na kai bakin 'kofa ya ce "idan kin dawo 'Danwake zaki yi mini". Na ce "Tom". Na fita ina ayyana yau ban samu arzikin rakiyar ba kenan. Ashe shi yana cikin halin son kasancewa da ni, amma ba damar hakan tunda bai yarda yana sona ba, bayan haka Umma bata son hakan ya kasance a tsakaninmu. Da na dawo na shirya masa 'danwaken, domin ina da dakken yaji mai da'din gaske. Ya ci iya cinsa, amma ya kasa yaba mini, bare ya ce thank you. Na tuna mijin Sakina komai ta girka masa sai ya ce Na gode. Bare kuma a ce shi ya zabi abin da za'a yi masa. Ya dinga yabawa tare da godiya. A haka muke gungurawa, zaman ba wani fahimta a cikinsa har muka cinye kwanaki wata. Ranar asabar bana mantawa ya sanar mini zai je Lagos jibi, zai yi kwanaki biyu zuwa uku. Duk da ba wani da'di muke yi ba, sai da na ji gabana ya fa'di, na tsinci kaina a cikin rashin Jin da'din tafiyarsa. Da ace na samu fuska a wajensa cewa zan yi zan bishi, to ina. Na yi masa addu'a. Abba kuwa ticket din jirgi ya siya masa. Farko so ya yi mu tafi tare, amma Gudale ya bada uzzirin zan samu gibi a karatuna tunda ba a weekend tafiyar ta Fado ba. Na yi masa cincin da dambun nama masu dama tamkar wanda zai kai wata. Da zamu yi sallama ya zuba mini ido sosai ya ce "Ubangiji da kansa ya shimfi'da dokokin aure. Dan haka har zuwa ranar da zaki gaji da zama a karkashin ikona wajibi ne ki yi mini biyayya, ki kuma kiyaye mini amana". Daga haka ya ja akwatinsa ya fice ba tare da ya bani damar cewa 'kala ba. Na bishi da Ido, a hankali na furta "Allah ya dawo da kai lafiya. Na koma daki ina jin hawaye na cika mini idona. Na kalli kudin da ya bani, ban 'kirga ba amma na sani zasu kai dubu goma. Tunda ya tafi ni dai bai Kira Ni ba. Ni kuma da na kira ma layin a kashe ban same shi ba. Ban kawo komai a raina ba, amma na matsu na ji muryarsa, na matsu na ji halin da yake ciki. Duk yadda ya nuna mini rashin soyayya, tawa zuciyar sonsa take kamar me. Addu'a nake ba kakkautawa Allah ya karkato mini da hankalinsa kaina, mu yi zama mai cike da soyayya da mutuntunta wa. Daga tafiyar kwana biyu ko uku sai gashi an shafe kwanaki goma an doshi sati biyu. Juma'a biyu kenan da tafiyarsa, sai Abba ya shigo ya duba ni da yamma. Ya tambaye Ni ko muna waya da Sadika. Na ce "Tunda ya tafi bamu gaisa ba". Ganin da Abba ya yi zan rikice ya sanya ya ce "lafiyarsa fa kalau, ya kira ni sau biyu, amma ba da layinsa ba." Na dan ji da'di ka'dan tunda lafiyarsa Lau. A hakan sai da aka shafe kusan wata biyu bai dawo ba, bai kuma neme ni ba. Ni kuma na gwada kiransa ya fi sau cikin buhu. Amma kwatakwata layin ba ya shiga. A wannan lokacin ne raunina ya fara bayyana, mussaman da na fara fahimtar kalamansa da ya ce har zuwa sanda zan gaji da auren sa. Kenan guduwa ya yi ya bar ni? Idan na gaji sai musan yadda zamu yi ni da Abba. Karatu da rashin nutsuwar da nake ciki suka sanya ni a gaba, na fara ramewa a tsaye. Dan ma na yi sa'a mayuka na zababbu ne ko a cikin oriflame 'din ma latest ne. Shiyasa ban yamushe ko 'bacin rai ya sanya na yi duhu ba. Bana gajiya wajen yiwa *Aisha lame* jinjina, a kullum bansan adadin matan da suke tambayar lambar wayarta ba dan fatarsu ta yi kyau da taushi irin tawa to. A wannan lokacin kowa ya ganni sai ya tanka ramar da na yi. Kowa sai ya tambayi anya lafiya nake kuwa? Amma sai ba'a wani damu ba, aka yi ta jingina mini ciki ne yake wahalar da ni. Wata juma'a da Abba ya zo gani na, na kasa boye damuwa ta na yi ta kuka mai ta'ba zuciya. Tsawon lokaci bai katse ni daga kukan ba. Sai da na yi shiru dan kaina. Sannan ya numfasa ya ce "kara ha'kuri Halimatu! Komai zai wuce ya zama tamkar ba'a yi ba. Hakan da Sadik ya yi ba ni ko ke ya tozarta ba. Da sannu zai gane kansa ya yi wa". Ya zarce da yi mini nasiha mai shiga zuciya, ya kuma sake jaddada mini ba wanda ya yi hakuri bai ci ribar rayuwar nan ba". A haka na cigaba da zama cikin ha'kuri da juriya, na kuma gane tabbas aurena ne baya so shiyasa, ya yi hakan saboda haka nima sai na mayar da akalar addu'ata wajen Allah ya yi mini za'bi. Duk da a 'kasan zuciyata nafi son ya sauko, ya karbi auren da dukkan zuciyarsa. *Ummma* A dakinta take tana gyara wardrobe dinta. Misalin 'karfe karfe uku na yammacin laraba. Kamar daga sama ta ji sallamarsa ya shigo mata daki. Ta zuba masa ido sosai. Yayin da shi kuma yake sosa kansa alamun kunya da rashin gaskiya a tare da shi. A hankali ta ce " Gudale" Kafin ya amsa ta zarce da cewa "ko wata uku baka gama rufawa ba har ka dawo? Haka muka yi da kai?" A hankali ya ce "Umma na kasa jurewa ne, kullum na kwanta mafarki nake yi marasa da'di, bani da nutsuwa ko ka'dan, ina jin tsoron hukuncin da Abba zai zartar". Ta yi kasake cikin son nazartar sa. A hankali ta ce "Kana nufin ka amince zaka zauna da kinababbiyar yarinyar nan? Kana nufin zaka ha'da mini jinina da haular gidan mai Ashafa?" A dunkule ya ce "To ya zan yi? hakan na cikin 'kaddarar da bazan iya kauce mata ba. Ki yi hakuri ni kai na a cikin takura nake, amma Fishin Abba nake guje Mana, mussaman matakin da zai iya dauka akan ki. Ina matu'kar kyamar na zame miki dan kuka mai janyo wa uwar sa jifa. Cikin rawar murya ta ce "Sun yi galaba! Su je sun samu, na sani a yanzu ma ba a hayyacin ka kake ba. Kiran ye suka yi maka. Oh ni Saude Ubangiji ka mini maganin abin da ba zan iya yiwa kaina ba. Allah ka mini maganin wadannan halittun masu mtofi a cikin kulle kulle, masu rubuce sunan namiji a allon karfe". 02-11-22. # Team Gudale# # Team Guduyo# # Surayya Dee ✍️ # Ana tare 🤝. 2/8/23, 10:25 - Buhainat: *Wannan littafin na ku'di ne, biya 500 ku'din karatu ta wanannan asusun* *2384876855* *Surayya Ibrahim* *Zenith Bank.* *A tura shaidar biya ta wannan lambar* *08032773332*. *SDK* *47-48.* Cikin rarrashi ya ce "A cikin nutsuwa nake Ummah! Ba abin da aka yi mini". "Yo dama ina zaka fahimci surkullen su? Kawai dai na barsu da Allah! Ban da haka ta ina ka dace da Halimatu? Yarinyar da ta tsotsi nonon makirci da shiga tsakanin tsaftacciyar soyayya, masiffafun mutane gadan jaraba". Ga mamakinsa sai ya ji kalaman Umma ba su yi masa da'di ba. Domin idan ya ce ba kewar ta ce ta dame shi ba ya yi 'karya. Hakanan dawo wa ya yi dan ya sauke abin da ya dame shi akan ta. Ya mi'ke yana cewa ki daina damuwa! Nan duniya ba abin da ya fiki daraja a waje na. Sannnan ba abin da zai shiga tsakaninmu". Cikin karaya da zallan bacin rai! Ta ce "Kayyah". "Abba yana gida ne?" Ya tambaya, nufin kauce wa maganganun ta. "Eh yana nan" Ta bashi amsa a gajarce. "Umma mu je ki raka ni, gaba'daya a tsorace nake! Sai yanzu nake ganin ban kyautata masa ba". Ta tabe baki ta ce "Ai shi kana jin tsoron fishinsa! Ka damu da bacin ransa. Amma ba ruwan ka da halin da zan shiga a dalilin rashin dace da suruka. Wai Halimatu zaka zauna da ita? Buskutar yarinya da nake fatan ta fadi ta ji ciwo a kashin kafarta ta yadda kafin likita ya samo 'kashinta ya yi mata dori ta na'kasa ta zama gurguwa." Ya mi'ke ya dafa kafadarta a hankali ya ce "Ina rantse miki da girman Ubangiji ba matar da zata wula'kanta ki na zauna da ita. Ba matar da zata zame miki barazana. Ban sallama ta ba, ki amince da Gudalenki Umma". Ta saki ranta ka'dan ta ce "je ka dai, yanzu sai ya ce "Da sani na ka 'ki dawowa da wuri, ba kuma ka kirashi a waya ba, tunda ya da'de yana mini shaguben ya san kana kira na". Kan dole ya nufi falon Abban. Ya same shi a zaune kasan kafet gabansa manyan littafai ne birjiki, da alamu suka nuna yana wani nazari ne. Ga mamakin Gudale da fara'a saosai Abba ya yake masa barka da zuwa tamkar dai ba laifi ya yi ba". Ya zama wani iri saboda yadda Abba ya kashe shi da kunya. Suka gaisa lafiya lau. Abba har tambayarsa da fatan ya samu Nasara a tafiyar da ya yi. A sanyaye Sadik yake amsa masa. Abba ya sake cewa "Har ina tunanin ya za'a yi da interview din da zaka yi a F.I.R.S. Sati mai zuwa ashe ka samu labarin". A hankali Gudale ya ce "ban ji ba, kawai na dawo ne, na ga zaman zai yi yawa". A gajarce Abba ya ce "Madallah". Da kyar ya mi'ke ya fita saboda jikinsa yana bashi Abba dungu ya yi masa. Ba laka a jikinsa ya yi sallama da mahaifin nasa ya nufi gidansa. ****** Ina kwance a kujera mai uku ya turo, ya shigo. A farkon na yi zaton gizo yake yi mini. Sai da ya shigo janye da akwatin kayansa na tabbatar ba gizo bane. Ko motsi ban yi ba, bare na tashi. Ya jima yana kallona, murya a bude ya ce "Baki gan ni bane?" Cike da rashin damuwa na ce "Na ganka mana! Sannu". Ya wuce janye da jakarsa sama. Sai da ya yi wanka, ya fito zuwa masallaci. Bai bata lokaci ba ya dawo. Ya jima a falo yayin da nake dakina kan sallayar da na idar da sallah, amma ban tashi ba. Ya shigo ya zauna a bakin gado. Karon farko da ya shigo dakina ya zauna tunda na je gidan. Na kammala na ninke su, na fice na bar shi a ciki. Ina zama a kujera ya karaso a fusace. Cikin fishi ya ce "Amma kin san bana son a tashi a barni ko?" Kai tsaye na ce "Na gama uzzirin da nake yi ne. Ban sani ba ko baka gama abin da ya kai ka 'dakin ba". Ya hassalo sosai, amma ban san dalilin da ya sanya, ya bar maganar ba. Ya zauna ya ce "Sammin ruwa na sha! Idan da abinci a taimake ni da shi". Ban ce komai ba na tashi na zubo masa jollof din Macaroni da soyayyar plantain a plate. Na ha'do da ruwa da lemo. Na nufi dinin area. Ya ce "kawo mini nan". Na 'dora masa akan center table din da yake kusa da shi. Na koma na zauna ina cigaba da kallona. Bansan me yasa ba, ban yi zumudin zuwansa ba, ban yi farin cikin dawowarsa ba ko ka'dan, duk da zuciyata cike take da son sa kuwa. Da kansa ya kai plate din kicin. Na yi mamakin hakan da ya yi amma ban tanka ba. Da ya dawo, sai ya zauna akan kujerar da nake kai wato 2 sitter. Ina kallonsa yana mini kallon kurillah, na yi kamar ban gani ba, na mayar da hankalina akan kallon da nake yi. Cikin wani irin yanayi ya 'kira ni "Guduyo" Ban amsa ba, na zuba masa ido tabbacin ina sauraron sa. "Fishi kike yi da ni?" Na janye idona na ce "me ka yi mini?" "Nima haka na ga ni" Ya fa'da cikin rashin damuwa. Ba zato na ji ya ru'ko hannuna ya ce "Ban cika damuwa da lalle ba, amma wannan ya mini kyau sosai. Kitson kan ki ma ya yi mini. Kwalliyar barka da zuwa aka yi mini?" Ban kalle shi ba na ce "Nasan zaka dawo ne? Bare har na yi maka wani shiri?" Ya yi shiru cikin rashin abin cewa. Ya yi karfin halin cewa "Ilhama aka cusa miki! Dan na same ki fes da ke". Takaicin sa ya kama ni. Da sauri na ce "Bikin couse mates dinmu muka yi, kwalliyar bikin ce". A razane ya ce "Biki?" Ba ja in ja na ce "eh" Nan da nan yanayin sa ya canja ya ce "Da iznin wa kika je gidan kunshi, wa ya lamin ce miki zuwa biki?" Kai-tsaye na ce "Da Sakina muka je 'kunshin, da zan je bikin kuma Abba na tambaya". Ina rufe baki ya ce "Sakina zata ha'du da fishina wallahi! Ni a duniya na tsani karambani da katsalandan. Amma ba laifin ta bane ai. Raina ni kika yi shiyasa kika fita ban sani ba." Na yi shiru ina sauraron sa cike da mamaki. Na saci kallon sa na ga ya yi kicin kicin da fuska tamkar an fa'da masa mummunar kalma. Tsawon lokaci muna hakan sai kuma abin ya sake ciyo shi ya ce "Da zan tafi ban ce miki asibiti ko makaranta kawai na yarda ki je ba?" Na kasa bu'de baki na ce masa komi saboda yadda ya bani dariya sosai ya dage yana sababi shi a dole ga Mai-gida. Sai da na shanye dariyata sannan na ce "Ai ban ji ka fa'di hakan ba, na dai ji ka ce idan na gaji da zaman auren na fita". Ya nuna ni da dan yatsan sa cikin fishi sosai "Ke kar ki kawo mini maganar banza kin ji". Na dauke kallo na daga gare shi tare da cewa "Ashe ban fahimci Yaya Gudale dai dai ba". Ga mamakina sai na ga ya ha'diye fishinsa, ya sassauta murya ya ce "Shikenan abar maganar haka nan, fa'da mini me ya faru da bana nan". Cikin rashin damuwa na ce "Ba abin da ya faru sai alheri. Na kammala zuwa asibiti, na koma makaranta" "Ba ki yi kewata ba?" Da azama na dinga girgiza kai tare da cewa "Ban yi ba ko ka'dan, dan kuwa na dauka sai ka shafe shekaru baka dawo ba". Ya tsananta kallo na ya nisa ya ce "fishi kika yi tabbas". Na murmusa na ce "matu'kar zaka yi mini adalci ai kasan shekarun baya ma da nake bording da baka shiga cikin ayarin masu kai mini ziyara ai idan na dawo bana kula ka, saboda ina mance duk wanda ya mance da ni ne, bare yanzu kuma da na sake yin hankali. Akan me zan yi fishi dan kawai ka yi hijirar watanni uku kacal? Na dauka zaka yi shekarun da zamu gaza ne ni da Abba har akai ga yi mini gaiba". Ya fusata ya ce "Ban son wannan zaro maganganun da kike yi, kar ki tunzura ni Guduyo. I come in peace". Na ta'be baki na ce "menene abin kada na fusata ka dan na fa'di gaskiya? Ai kasani dai idan muka gaza dole Abba ya saka alkali ya sahale mini, dan na samu wanda zai kwashe ni". Nan da nan idonsa ya juye, jijiyoyinsa suka bayyana. Murya a dakushe ya ce "kin ci mutuncin mijin da Allah ya za'bo miki, daga dawowa ta sai cin karo da bakaken maganganu?" Na sake yin fuska na ce "Daga fa'din gaskiyar magana? Dan Allah ko yanzu ka ce baka yi, baka ji a ranka akwai wanda zai fito ya na'de dukkan kunya ya dauke ni ba, ko da hakan kuwa zai ya mutsa hazo Dan m rikici?" Kafin na rufe baki ya kamo hannuna ya murde da iyakacin karfinsa, zafin ya gigita ni na fashe da kuka mai hade da hawaye. Yana huci ya ce "gaggauta tuba, ko na karairaya ki, sai ya dauke ki a nakashe". Azaba ta sanya ni cewa "na yi tuba". "Ban karbi wannan tuban ba." Da sauri na ce "Yi hakuri Yaya Sadik! Allah ya baka ha'kuri". Ya sake ni, ya koma kan kujera ya ce "Idan kika ce zaki dinga motsa mini kishina Billahillazi ke ce a wahala Guduyo, domin zan illata ki ne a banza. Sannan ki rufe mini bakin ki, nima yanzu zan yi miki smiling tabbacin na karbi tuban ki. Na kuma rufe maganar". Yana mini wani irin kallo da murmushi ya ce "Bari na je na duba motocin can! Ki shirya zamu fita". Yana rufe baki na girgiza kai tare da cewa "Bana jin da'di shiyasa ko School ban je ba yau". "Eh daure dai ki shirya din! Idan muna tare zaki warware, za kuma ki ji da'din". Ya fa'da yana hawa 'kafar bene dan dauko mukullin mota. Na bishi da kallon takaici, wato Yaya Gudale takaicin sa yawa ne da shi. Na murguda baki hadi da gatisne. A dole na bishi muka fita, kasan raina kuma haushinsa fal. A motata muka fita. Bamu zame ko ina ba sai filin koyon tu'ki. Ya dinga nuna mini yadda zan yi. Sama da awa guda muna zagaye, sai dai gaba'daya a takure nake a dalilin yadda ya matsa mini da shafata. Duk yadda zai yi jikinmu ya ha'du haka ya dinga yi tamkar dama so yake ya samu damar yin hakan. Kafin mu bar wajen sai da na yi zagaye uku da mu a filin. Cike da farin-ciki yake cewa "Da wuri hannunki zai fa'da Guduyo. Zan kai motar a saka miki *L* nan da lokaci kankani zaki fara fita da kan ki". Ya biya da mu Al-amir restaurant muka ci abinci ganin magahriba ta gabato sosai. Ga mamakina gidan Sakina ya zarce da mu. Sakina ta dinga ina ka saka da mu, ta yi dabarar jana daki muka bar Gudale da yaranta a falo. Maganganu masu nauyi ta yi mini a dunkule wanda suke nuni da cewa na yi kokarin dinke distance din dake tsakanin mu. Ta fahimci da sulhu ya dawo, na ja aji ka'dan na ha'kura tunda na sani a bau'de yake. Cikin 'kasa da mintina talatin sai da tasa ni na hadiye wasu irin supplement din Gangariyar Jakadiyar G.H.T. *Faseelat mai gyaran ciki da wajen Mata* *Kina fama da tumbi ko kurajen fuska?* *Kina fama da ulcer ko basir?* "Kina fama da dryness, to kukan ya Kare domin zan hadaki da wacce zata Baki ingantattun supplement din da babu kwange cikin farashi mai sau'ki* *Faseelat 07039269802*. Ta bani wanda bata bu'de ba, na tafi da shi. Muna fito wa ya kallemu ya ce "Haj Sakina an buga, an bar ki. Dafatan dai kin fahimci manufar gaisuwar da muka zo yi miki" Tana harar sa ta ce "Na san dai Halimatu ce zata zo ta gaishe ni, amma ba kai ba". Ya kalle ni ya ce "fa'da mata ba kisan zaki zo ba". Na 'ki tankawa, yayin da Sakina ta rakomu har waje tana yi masa tsiyar bai kawo mata tsarabar komai a fataucin da ya je Ikko ba, sai ya dauko ni ya kawo mata tamkar dai so yake ta fahimci zuciyarsa bata da karfin jurewa kudirinsa. Sanin da ya yi magana ta yi masa mai harshen damo ya sanya ya waske bai ja maganar ba. 'kunshin da ta kai ni ma ya so yin maganar kawai sharewa ya yi. Amma na sani zai yi maganar. A hanyar mu ta komawa ya dinga ja na da hira, har na dinga mamakin ashe ya dan iya magana cikin sakin fuska da taushin harshe? Ba abin da yake so irin na sake jiki da shi kamar da. Tun a gida Sakina sallar Isha ta same mu. Dan haka mun riga mun yi sallah. A falo muka yada zango. Ba kunya ya ce mini ban ta'ba kai masa ziyara dakin sa ba. Cikin son na nuna ban fahimce shi ba, na ce "Sau nawa ina zuwa kuwa?".. Ya girgiza kai ya ce "ke fa kina zuwa ne bayan kin shirya fita makaranta, ko idan bana nan ki je ki gyara, shikenan fa". Na yi murmushi na ce "Ashe kuwa ina zuwa". Muna kallo, yana rike da hannuna yana ta murza mini, duk ya sa jikina ya mutu, Ina jin wani irin al'amari na shiga ta da nake jin tamkar wanka ya kama ni, saboda yadda nake jin na zama wet. Ban sani ba ko tasirin maganin da Sakina ta dirka min ne. Uzziri ya kama shi, ya haye sama. Kafin ya dawo na kashe komai na shige dakina na rufe, na yi wanka, na yi kwanciyata bayan na rufe kofata da makulli. Domin na ci alwashin ni ba zan kai kaina dakinsa da kaina ba. Sai ya ajiye girman kai ya fa'da da bakinsa barobaro. Ba kuma zan sallama masa kaina da wuri ba, bayan wula'kancin da ya yi mini kala kala masu cin rai. Har da yi mini yawon 'ki. Da ya sauko, ya dinga buga mini kofa. Amma na yi funfurunfus. Ya yi iyakar kokarin sa akan na bu'de masa amma ban bude kofar ba. Tunda na idar da sallah ban koma ba, kai tsaye kicin na shiga, na hau aikin yin snacks. Na kammala agogo ya nuna mini karfe takwas har da kwata saboda na yi da yawa, tunda abin da da yafi son ci kenan. Ban soya wanda zamu ci ba, sai da na kammala gyara gidan fes. A nutse nake aiyyukana saboda sai sha biyu nake da lecture. Ina tsaye a kicin din sanye cikin cotton din rigar barci guiwa. Da takalminta take zuwa, da kuma band. Na kame gashina dake tsefe da band din. Na kunna gas kenan na ji shigowarsa. A Dan tsorace na gaishe shi. Bai amsa ba illah iyaka ya zuba mini ido yana kallona hannun sa na'de a 'kirjin sa. Yayin da kallon yake ratsa ni har cikin kaina. Murya a dashe na ce "Ina kwanaa?" Ya amsa a takaice. Ya numfasa ya ce "Na fuskanci kin matu'kar raina ni Guduyo". Kaina na kasa na ce "Da na yi maka me?" Da azama ya ce "kina nufin duk yadda na dinga buga miki kofa baki ji ba?" Na ci magani na ce ban ji ba". Ya make kafa'da ya ce "alright! Shikenan na yafe miki bacin ran da na kwana a cikin sa". Dariya ta kusa subuce mini. Da zan iya da na ce masa kar ya yafe din. Amma na san idan na fa'di hakan zamu kwashi 'yan kallo ne, dan haka sai na kame bance komai ba. Ba zato kawai na ji ya rungume ni ta baya, ya kwantar da kansa akan kafa'data yana shinshinata. Jikina ya amsa. Na fara kokarin zamewa, murya na rawa na ce "Ka bari dan Allah man da na dora zai kone kar ya janyo mana gobara". Ya sassauta rikon amma ba gaba'daya ba. A hakan na yi aikin. Duk inda na saka 'kafa nan yake mayar wa. Har cikin dakina yana biye da ni. Da zan shiga wanka ba irin ro'kon da ban yi masa ba, akan ya kyale ni na shiga toilet amma tuburan ya kafe sai dai mu shiga tare shima wankan zai yi. Alhalin sai da ya yi wankan sa ya fitto. Na kalli agogo na ga tara ta gota. A hankali na ce "Yaya Sadik ka yi wa Allah ka bar ni na yi wanka na karya, ina da abubuwan yi a gabana". Ya dauke kansa tamkar ba da shi nake yi ba, tabbacine kuma na ba zai kyale ni din ba. Har toilet din ya bini, na rasa inda zansa kaina. Kawai sai na yi brush, na yi kwaskarima na fito, domin ba zan iya tubewa a gabansa ba, kamar yadda yake fatan mu yi wankan tare. Hijab na sanya sannan na shirya a takure. Saboda yadda ya tasa ni a gaba da kallon 'kurillah. Sanin da na yi baya son na zuba masa abinci da kaina ya sanya ban yi gigin zuba masa ba. Ya zuba mini ido ina kai *fan cake* bakina. Ya ce "Ba zaki bani bane?" A hankali na ce "ga shi nan. Wa zai hana maigida abincin gidansa?" Da'di ya lullube shi har fuskarsa ta bayyana hakan. Kai ni kam bansan mai son girma irin Gudalen Ummah ba. Fuska a sake ya ce "To zuba mini mana, matu'kar kina kusa ai komai yi mini zaki yi". Na murmusa na ce "Na dauka sai kuturu ko yaro 'kan'kani ake yiwa irin wannan hidimar". Nan da nan ya ce "Ban son raini fa kin sani, ban son kananun maganganu". Na yi shiru na zuba masa ido, na kuma zuba masa abincin kamar yadda ya bu'kata. Na riga shi kammalawa. Na kalleshi na ce "Zan tashi". "Zuwa ina?" Na ce "makaranta! kada na yi latti". Ya zuba mini ido sosai ya ce "Na dawo jiya! Ki yi sammakon fita ki barni gadin gida, saboda kawai bani da wata daraja ko 'kima a idon ki". Na yi shiru, ina ganin ikon Allah. Kafin na ce wani Abu! ya ce "Yau alhamis ki ha'kura da makarantar nan, zuwa Monday tunda ba wani abu muhimmi zaku yi ba". Idona ya ciko da 'kwallah na ce "gaskiya muhimmin abu zanje yi, ban ta'ba ganin inda scientist suke fashi babu dalili ba". Hakan kawai na fada "ya ce "Na rantse miki da Allah babu inda zaki je yau. Idan kuma kika sa'ba mini akan haka wallahi zan iya dakatar da karatun gaba'daya, tunda na fahimci karatun yafi lahirarki muhimmanci". Hawaye ya balle mini na ce "A Ina na ce maka yafi lahirata?" Kai tsaye ya ce "Baki fa'da mini haka ba! Amma kin nuna mini ni ba komai bane a wajen ki, alhalin kuma nine lahirar ki". Takaici ya kama ni bansan yadda aka yi ba na tsinci kaina da cewa "Kai ne lahira ta, amma na sani ba zaka taimake ni wajen ganin na rabauta da samun dacewa a can ba, tunda ba sona kake yi ba". A hanzarce ya ce "Lallai Guduyo! Ashe mummunan zato kike mini irin haka? Bayan tunanin ki ne ya nemi kassara ni na dawo babu shiri". Na zuba masa ido sosai ina mamakin furucinsa. # Team Gudale # Team Guduyo # Surayya Dee ✍️ # Ana tare 🤝. 2/8/23, 10:25 - Buhainat: *Wannan littafin na ku'di ne, biya 500 ku'din karatu ta wanannan asusun* *2384876855* *Surayya Ibrahim* *Zenith Bank.* *A tura shaidar biya ta wannan lambar* *08032773332*. *AMYAS NEW & FAIRLY ITEMS* *KOMAI DA RUWANKA KENAN* *SUNA SIYEN KAYAN DAKI SECOND, SUNA KUMA SAYARWA* *SUNA SIYAN KAYAN ELECTRONICS, SUNA KUMA SAYARWA* *SUNA SAYAR DA KAYAN KICIN* *SUNA BADA HAYAR KAYAN AMARYA* *SUNA SIYAR DA SUTURU NA ALFARMA* *SUNA SAYAR DA FILI DA GIDAJE, SUNA BADA HAYAR GIDA*. *KU TUNTU'BE SU A WANNAN LAMBAR 08083909947*. *SDK* *49-50.* Da rawar murya na ce "Ba dai tunanina ba". "Waton 'karya na fa'da". Ya tambaya rai a 'dan bace. Na kasa bashi amsa. Na tashi na barshi a wajen, ya dinga kirana na wuce tamkar ba da ni yake yi ba. Ina shiga 'daki na haye gado na fashe da kuka sosai. Jim ka'dan ya shigo a fusace, kukan da ya ga ina yi sai ya sanyaya jikinsa. Murya a dashe ya ce "Bana son haka! Kar ki tayar mini da hankali haka siddan". Ban ce masa komai ba, haka nan ban daina kukan ba. Ya zauna a bakin gadon. A hankali ya ce "Shikenan bani da damar da zance ki yi kaza, ko ki bar kaza sai ya zama abin kuka da 'bacin rai a wajen ki? Har ni kike yiwa zaton ba zan baki damar da zaki rabauta ba?" Na yi shiru ina cigaba da kukana kasa 'kasa. Ya numfasa ya ce "Ke ce kike yiwa rabautar ki rikon sakainar kashi. Tunda kika zo gidan nan kin ta'ba zuwa 'dakina da nufin sauke hakkin da ya rataya a kan ki?" Kukana ya tsaya cak! Mamakinsa ya kama Ni! Ashe dai da gaske jira yake na kai masa kaina. Na rasa gane manufar Gudale. Bai ta'ba ganin alamun ina kule kulen maza ba, ko shima da nake sakar wa fuska har ya mini abin da bai kamata ba, amma dai bamu ta'ba yin lalata ba, bare ya yi tunanin nasan komai. Ba zan ji nauyin nemansa da kaina ba. Kafin na ce wani abu ya riga ni cewa "Na gama nazartar inda kika dosa, sai dai abin da baki sani ba shine. Matu'kar ba zaki sauke mini wannan hakkin ba Wallahi ba zaki rabauta ba. Dan ba zai yiwu ki yi ta wula'kanta ni, kina ci mini mutunci sannan ki ce zaki ga haske a al-amuran ki ba." Hawaye ya balle mini, da rawar murya na ce "Duk wula'kanta ni da ka yi tun farkon maganar auren nan har zuwa guduwar da ka yi ka barni ban ce komai ba sai kai? Dan Allah fa'da mini wula'kanci ko cin mutuncin da nake yi maka". "Gasu nan birjik! Ki fita ban sani ba, Ba zaki zo mini hira ba, sai dai kawai ki share mini daki, ki mini abinci, alhalin wannan hakkin zan iya daukar mai yi mini na biya". Murya na rawa na ce "Na gane bani da daraja! da gaske dai Ta buzuzun ma ta fini kima a idonka. Banda haka a ina aka ta'ba yin haka saboda Allah. Ko a wajen Allah bani da laifi tunda dai ban bijire maka ba. Kai ne baka nema ba, ni kuma ra'ayi ne bani da shi akan lamarin shiyasa ban nema ba". Ya nisa ya ce "Allah dai yana ganin komai, tun yaushe nake miki hannun ka mai sanda, kin gane sarai, amma kika nuna mini baki fahimta ba, akan me ba zaki taimake ni ba? Kinfi son sai na ajiye dukkan girmana. Shikenan kin ci riba! kuma na sani jiya kina ji na kika 'ki bu'de mini 'kofar nan". Na yi masa shiru tunda gaskiya ya fa'da. Ya mi'ke tsaye ya ce "Zan fita! Ba zan jima ba, ku'di zan samo mana na dawo, ki yi list din abin da bamu da shi, da kuma wanda kike bu'kata. Idan na dawo sai mu je mu yi shopping". 'kala ban ce ba! Har ya fara tafiya ya juyo ya ce "Na ce zan fita amma kin mini shiru? Haka kika ga ana yi wa miji? Anya Guduyo kin shigo gidan nan da nufin rabauta da aljannah kuwa?" Na nisa na ce "A dawo lafiya". Ya tafi yana cewa "Ameen" Na tashi na zauna ina rasa ajin da zan ajiye Gudale. Na lura yafi mahaukaci cusa takaici. *Gudale* Cikin gida ya shiga, sai da ya je ya gaida Baba da Mama. Sannan ya fito zuwa shashinsu. Ya tarar da iyayensa suna karya wa. Ya gaishe su, suka amsa fuska cike da kulawa mussaman Abba. Jikin Gudale ya yi kwari saboda ya gamsu Abba bai dauki zafi da shi akan tafiyar da ya yi ya jima, ba waya ba aike ba. Dan haka ya bararraje a gabansu tamkar yaro 'kan'kani. Abba ya gama nazartar sa ya ce "Ya ya ne Sadik?" Kafin ya yi magana wayar Umma da ta bari a falonta ta hau 'kara. Dan haka ta mi'ke da sauri. A shagwabe ya ce "Abba ba ni da ku'di a account dina, tafiyar nan ta cinye mini su. Ban son zama haka a gida". Da walwala Abba ya ce "Gidanka ai da abinci bana jin akwai abin da babu! Domin duk sati sai na yi mata aika, na kuma bata ku'di". Ya marairaice ya ce "Da so nake yi, na yi yadda ake yi Abba". "Me ake yi?" Abba ya tambaya a hanzarce. "Na kai ta ta yi shopping! Kuma na fara koya mata tu'ki! Zan dinga zuba mata mai a mota, sannan ku'di garkuwa ne Abba, ajiye su a daki ka'dai zasu taimake ni. Ba zan so ta bu'kaci wani abu na ce mata babu ba". Mamaki ya kama Abba matu'ka da gaske, ya nisa ya ce "Ban jin zata bu'kaci wani abin, hannunta da ku'di fa". Ya bata rai sosai ya ce "Abba ni ba ruwana da ku'din ta, so nake yi na dinga yi mata hidima ba wai ita ta yi mini ba. Ban son raini Abba". Murmushi sosai Abban ya yi har ha'koronsa suka bayyana ya ce "To ai tasan baka da aikin yi, komai naku yana karkashin kulawata ne. Kuma daga ni har ita ka fahimtar da mu baka son auren. Ka ga kuwa ni da nake son auren ai ba zan barta cikin kuncin rashin kudi ko kayan amfani ba, komai tana da shi inka dauke miji da soyayyar sa". Jikin Gudale ya mutu murus domin ya gano akwai wata a 'kasa a zuciyar mahaifin sa. A hankali ya ce "Abba! Ba'a cewa komai a sha'aniniji da mata fa". "Au haba?" Abban ya fa'da a tunzure. Nan da nan Gudale ya fara cewa "Ni dai ban ce bana son ta ba. Kuma yanzu da na dawo zan bata soyayyar da aka ce ta rasa, ba sai a taimake ni, a gode mini ba". "To bazan baka ku'dina ba, indai da gaske rainin ne baka so, ka fita ka yi kwadago, ko leburanci ka samo ku'din, sai ka yi mata hidimar yadda kake so". Ya rarrafa ya matsa jikin mahaifin nasa ya 'dora kansa a 'kafarsa yana cewa "Dan Allah ka bani Abba! Kar ka sani kuka bayan so nake na girma". Dariya ta so kwacewa masa, amma ya cije ya ce "Dan Allah Sadik yi ta kururuwa ba kuka ba. Idan ka so ka fasa girman ka koma jinjiri sai na ji dadin yi maka sabuwar tarbiya ma". Bai dago ba ya ce "Ha'kuri zaka 'kara yi Abba! Ubangiji zai mayar maka da ni yadda kake son ka ganni! Kada ka yi fishi dan Allah". Jikin uban ya yi sanyi sosai, soyayyar 'da da mahaifi ta taso masa. Ya shafa kansa ya ce "kana 'kona mini rai Sadik! Bana jin da'dinka sam, yan uwanka mata sun fiye mini kai, domin basa sani damuwa, basa tayar mini da hankali. Sun fika tausayina, sun fika giramama ni. Kai baka san komai ba, sai bu'katarka. Tausayinka nake ji Sadik shiyasa ban sallamaka ba, amma al'amarinka ya fara kai ni bango". Ya dago idanuwan sa sun ka'da a hankali ya ce "Na yi tuba Abba! Kar ka sallama ni, kai 'din Malami ne mai ta'kawa 'kara yi mini Addu'a da sannu Ubangiji zai karba". Tsawon lokaci falon ya yi shiru sai fama suke da sake saken zuciya. Sadik ne ya katse shirun ta hanyar cewa Abba "yanzu dai so kake na ri'ke maka 'yarka da soyayya mai sanyi da tsaya wa a zuciya ko?" Girgiza kai Abba ya yi ya kasa bashi amsa domin bai san gaba mai zai sake 'baro wa ba. "Abba ka yi shiru kuma". Da'kuwa ya yi masa tare da cewa "Tashi ka bani waje mashiriricin yaro kawai". Ya marairaice ya ce "Ka kubutar da ni kunya ta a idon yarinyar nan Abba! Na ce mata ta shirya zan kai ta shopping fa". "Zan baka! amma bashi". Da sauri ya ce "Na yarda! Amma Abba zan karba ne bisa sharadin sai na samu damar biya, bana son a deba mini lokaci, na kasa bayar wa a wannan lokacin. Sannan idan na mutu kafin na biya, ka yafe mini". Ga mamakin Abba sai jikinsa ya yi sanyi ya ce "To". Ya tashi ya dauko masa ku'di mai auki ya bashi yana cewa "Ubangiji ya shirya mini kai, ya baka ikon biyan bashi". Ya sunkuyar da kai yana godiya domin yawan ku'din ya matu'kar faranta ransa, bai yi zaton zai bashi masu nauyin haka ba". Suka yi sallama ya tafi, ko wajen Umma bai shiga ba, saboda yadda yake cikin zumudin komawa gidan sa. Ya fito kenan wayar abokinsa Faruk Bello ta shigo masa. Ya amsa da cewa "Ina Kano fa". Dariya sosai Faruk ya yi! Sannan ya ce "shegen sama lallai yarinyar nan ta yi wining. Ashe dai Halima yar lukutar zata ri'ke maka wuya". Nan da nan Sadik ya ji zuciyarsa ta motsa, akan me Faruk zai gatsa sunan matar sa? Bayan yasan tantirin dan-iska ne. Ya tuna abin da ya fa'da masa ranar dinner din bikinsu da ya ga Guduyo cikin kwalliyar Jan tufafi. Akan idonsa ya ce "Moriki wannan babban kayan kake yi wa bacin rai? Ko baka son ta ai zaka huta, na rantse maka da nasan da irin ta a gidanku da tuni na sure ta, dan kuwa zata kashe dukkan sha'awa, za kuma ta yi juriya". Tun wannan maganar ya sake jin haushin ta data sanya kayan da suka bayyana dukkan surarta. Faruk abokin Gudale ne tuntuni, mahaifinsa dan asalin jihar katsina ne, amma mazauna Kano. Masu ku'di ne na gaske, kuma gidansu suna rayuwa ne irin ta turai ma'ana kowa yana yin abin da yake so a sanda ya so. Bayan Al'amin da Abbaas Gudale bai da wanda ya wuce Faruk. Duk da abotar tasu akwai na'kasu a cikinta. A dalilin Faruk! Gudale ya fara shan shisha, har ila yau Faruk ne ya koya masa shan 'kwayoyin da suke saka mutum caji ya shiga cikin maye, sai dai da ke masu tsada suke afawa basa buguwa ainun, amma suna shiga yanayin da zasu iya keta kowanne 'Dan adam. Neman mata da nufin lalata ne kawai Gudale bai fa'da ba, wannan kam Ubangiji ya tsare shi, amma shegantaka sai wacce ya manta. Da sallamah ya shigo har cikin dakin, Ina kwance akan gadon ban motsa ba, na dai amsa sallamar a sanyaye. Ya dan yi jim yana kallona. Ya matso jikin gadon yana kallona. Ya kasa ha'kuri ya 'kira ni a kaurare "Guduyo".! Na amsa a gajarce. "Billahillazi lah ilaha ilallahuwa ba zan dauki wannan iskancin ba kin ji. Ya zan fita baki san ki ce mini a dawo lafiya ba, sai da na roka. Sannan na dawo ki kasa bu'de baki ki yi welcoming 'dina. Kina nufin sai na sake roka? Kin yi tsararo Wallahi". Ganin da gaske hautsine mini zai yi, dan haka kawai na ta'kaita maganar na ce "Gajen Hakuri ka yi, bana Jin da'di na fa'da maka. Sannu da dawowa Yaya Gudale". Bai amsa ba ya hawo gadon sosai ya janyo ni jikinsa yana ta'ba jikina. Ya kalli ido na ya ce "Amma jikinki babu zafi". Murya a dashe na ce "Eh kawai kasala nake ji da kuma ciwon kai, amma na ha'diyi Panadol". A hankali ya furta "sorry". Na kasa amsawa saboda yadda nake jin wani irin abu na ratsa ni, wanda na hakikan ce shauki ne. Ya dinga murtsika ni, yana saka baki yana sumbatar duk inda ya yi masa. Yayin da na yi lamo ina Jin da'din lamarin da nake jin tamkar mu tabbata a hakan. Mun jima yana ya mutsa ni, shi kansa jikinsa ya yi tubus da kyar ya sauka a gadon a dalilin 'kiran sallah da aka fara yi. Indomie kawai na dafa muka ci, na shirya cikin lallausan material da na siya a *Amyas* ya samu tsararren dinkin *Umm Muhd collection* Ya kalle ni sosai ya ce "zauna na tambaye ki wani abu Guduyo*. Na zauna ya ce "Tsakanin ki da Allah a ina Sakina take zabo wadannan suturun masu tsananin kyau da daukar ido ne. A hankali na ce *Amyas newly & fairly items* 08083909947. Da kuma ina?" ya tambaya da sauri. Na ce da "wajen kawarta *Umm Muhd collection*" Ya girgiza kai ya ce "wanene telanki?" Na ce "macece mai mini dinki ai" Ya ce "Alhamdulillah! Na dauka yadda aka miki dinki yana zama a jikinki wani katon ne ke gwada ki. Gaskiya ta iya dinki kwarai na yaba mata, kinsan duk telan da ya yiwa mai jiki dinki ya yi daidai ya zauna to lah shakka kwararren tela ne" Na nisa na ce " *Umm Muhd collection*ai kwararriyar tela ce cikin kwararru, Wanda suka ninka ni jiki ma yi musu dinki take su yi Cass da su." *08063358662.* Ya nisa ya ce Gaskiya ne na gamsu, domin ko hasidin iza hasad yasan dinkunan ki na garari ne, na yaba da su. Amma kinsan me?". Na girgiza kai ya ce "kin yi kyau sosai! Kamata ya yi ace wannan kwalliya dan ni kawai aka yi ta. Yanzu je ki cire ki sanya doguwar riga free size sai mu tafi, idan mun dawo sai ki mayar mini da wannan din". Ban ce komai ba na tashi domin tunda ya fa'di hakan, to kuwa dole na yi matu'kar dai ba so nake ya hargitse mini ba. Na canjo din, amma sai ya sake cewa "Fatar ki ka'dai abin a boye ce Guduyo. Sakina ta mayar da ke babbar mace. Na gode wa *Aisha lame* da ta yi miki zabin wadannan mayukan Ubangiji ya albarkaci kasuwancinta". Na ce "Ameen ai indai kayan oriflame ne, aka sameta to a yi burki kawai". *07036662633*. Daga haka muka fice, kasan zuciyata kuma farin-ciki fal a ciki, na kasa nuna masa takaicin gudun da ya yi ya bar ni da auren sa tsawon watanni kusan uku. Wajen koyan mota muka fara zuwa, muka shafe lokaci mai tsayi, kuma Ni nake tu'kin. Kawai shi saka ido da bada umarnin abin da zan yi ne aikinsa. Muka kammala yana sake jaddada mini idan muka sake dawowa ni zan mayar da mu gida da kaina. Daga nan muka wuce Ado Bayero mall wanda aka bu'de shi a wanann shekarar. Fa'din irin sayayyar da ya yi mini zai zama tamkar bata lokaci ne. Kawai abin da na sani ya kashe mini ku'di sosai, har raina na sani da biyu yake yin hakan. Ko dai dan ya goge laifin rashin nemana da bai yi ba tunda ya tafi, ko kuma dan ya samu ha'din kaina wanda ba a samunsa da tsiya tsiya. Daga shoprite Yahuza suya suport ya yi tunga. A mota ya barni ya fita, bai wani jima ba ya dawo dauke da ledoji a hannu. Har da ledar Habib yougort. Ya bude baya ya ajiye, sannan ya shigo muka tafi. Nan da nan 'kamshin kajin ya cika motar. Maimakon mu yi gida sai gidan Anti Ramla, dake farm centre. Ni na shiga gidan, yayin da shi ya nufi masallaci duk da dai an riga an idar tuntuni. Da murna ta karbe ni, amma na shige dakinta "Ina cewa wallahi ban yi sallah ba". Ta ce "ai kuwa gara ki yi har biyar ta wuce". Na Jima da idar wa amma ban iya tashi ba. Saboda yadda nake jin fargabar yadda zata kaya a tsakanina da Gudale a yau. Har 'dakin Iman ta kawo mini ruwa da lemo da kuma cincin. Ta zauna kusa da ni tana cewa Anti dan Allah idan anyi hutu ki cewa Mamanmu zan zo miki hutu". Ina murmushi na ce "Ba sai na fa'da mata ba ma zuwa zan yi da kaina na dauke ki". Itama ta murmusa ta ce "Na gode". Dai dai lokacin Antin ta shigo tana cewa wa Iman "ya kika tasa ta a taba da kallo haka, je ki ki 'karasa aikin ki, kinsan dai na rantse yau ke zaki yi abincin dare, baki iya komai ba sai kallo da barci". Ta fice tana kunkunin ita ta gaji. Muka gaisa a mutunce, tana ta tsokana ta da cewa "Autar gida amaryar Auta Gudale.". Na murmusa ban ce komai ba, saboda ina jin nauyin ta, tunda ita bata nuna mana kiyayyya kamar yadda yayyenta Maimuna da Juwairiya suke nuna mana. Ina kishingi'de sai kallona take yi, na sani kyaun fatata da ramar da na yi ne ya sanya take ganin tamkar ciki ne da ni. "Ramlatu" Gudale ya kira ta gatsal! Ta fita da sauri tana fadin " Ya ce ki zo ku tafi". Dan jim na yi ina mamakin yadda bai iya kara ko alkunya wajen saya sunan manyansa ba. A gaban 'yaranta da suka fara girma yana fa'din sunanta gatsal har da wani kaurarawa wai Ramlatu. Na mi'ke Ina ta jin kunyar wannan abin da ya yi. Na same su a tsaye, Yana cewa "zaki bani, ko ba zaki bayar ba?" Ita kuma cikin rarrashi ta ce "Zan baka mana Autan Umma! Amma dai hamsin zan turo maka, ba zaka samu yadda ka ce ba". Kai-tsaye ya ce "wallahi ba zan karbi hamsin ba, yau daya dan kin samu na mayar da ke mutum na bu'kaci abin ki, sai ya zama dogon turanci? Ba zaki bani kina mini godiyar na tsallake kan kowa na zo miki ba?" Ta ce "To na gode maka! Yanzu zan saka maka 50 din, next week sai na sake sako maka". Ko godiya bai yi ba, ya ce "Kar ya wuce goben if not ba zan karba ba". Sai lokacin ta bu'de masa murya ta ce "Dan Allah kar ka karba Sadik". Ya fice yana cewa "ki koma ki yi sallah an fara kirah. Ina idar wa kuwa kiran sa ya fado wayata, yana "fa'din fito mu taf" Muka fita da Iman har motar ta rako ni, sannan ta dora mini ledar da Mamanta ta bani spices din girki. Muna tafe a hanya ina ta zancen zuci, mun zo dai dai gadar lado ya ce "Amma kin sani sarai bana son ina tu'ki ki mini gum tamkar direba ke jan ki" Ban tanka ba. Ya kufula ya ce "Wallahi duk take taken ki na gano ki. To saurare ni da kyau! Kin san Allah yau dai idan kika mini sanadin bacin rai, baki kyauta mini ba. Ba kuma zan yarda ba, tun safe nake son na sanya farin ciki a fuskar ki, amma kina botsare wa? Abin da zan tunatar da ke shine matu'kar kika bari na yi fishi da ke a yau kin yi hannun riga tsakanin ki da rabauta a wajen Mahallicin ki. Haba! ina amfanin macen da ba zata fahimci komai ba, sai ta saka mutum ya yi bayani dallah dallah dan kawai ta ga iyakar sa. Guduyo iyashege a wajen ki yafi na tsohuwar motar diban itace". *Hajja Faseelat a matso a gyara mana Amaryar gobe*. *Na sani ingantattun supplement din ki zasu rikita Gudalen Umma* *Tamkar yadda suke gigita Malam Mk na Sa'a da Farida*🥰 *07039269802*. # Team Gudale# # Team Guduyo# # Surayya Dee# # Ana tare 🤝. 2/8/23, 10:25 - Buhainat: *51-52.* *Paid*. Na zuba masa ido ina jinjina girman 'karfin halinsa. A hankali na ce "me kake son na fahimta amma ban gane ba?" Ya dauke kai ya ha'de fuska ya ce "Ina nufin ki zubar da wannan halayyar banzar da kike son koyo wa. Wacce mace ce mai ilimi zata dinga yin abin da kike yi. Na rantse miki idan kika sake rufe mini kofa sai na kai ki gaban Abba sannan zan fa'da masa wula'kanta ni da kike yi. Dan kada na dauki mataki ace ni ba mai biyayya ba ne". Jikina ya yi sanyi, harshena ya yi nauyi, na kasa ko da motsi ne. Wato da ke yanzu yana da bu'kata dole na yi masa yadda yake so. Shi bai duba laifukan da ya yi ta yi mini ba. Kansa ya sani. Haka kuma mafi yawa dabi'ar maza take, indai suna da bu'kata to zasu yi komai dan kawar da wannan bukatar, amma idan basu da ita, ba ruwansu da duk halin da mace zata shiga. Allah sarki mata! Mace mai juriyar shanye dukkan takaicin namiji. Muna dawowa, Abba ma ya dawo, ganin hakan ya sanya Gudale parking a kofar gidan, muka fito, muka bi shi cikin GIDAN. A harabar gate din Abba ya dakata muka gaisa, farin-cikin dake shimfide a fuskarsa ba ka'dan bane, sai albarka yake sanya mana. Ya ce "mu tafi *GIDANMU(Janafty).,* Mu huta gajiya tunda yanzu muka dawo, ba sai mun shiga cikin gidan ba. Na so na leka na ga Mamana, amma na ha'kura na wuce wajenmu ta 'kofar lambu. Yayin da Yaya Sadik ya fita ta waje dan ya shigo da mota. Duk yadda yake cikin zumudi sai da ya yi alwallah ya tafi masallaci dan sallar isha. Ubangiji ya taimake shi a wannan bangaren, ba ya wasa da sallah a jam'i. Wanka na shiga, na fito dauke da alwala. Na feshe jikina da zababben body spray na kamfanin oriflame. Na goga roll on. Sannan na shafa mayukana da suma kamshi suke bayarwa na mussman. Na tsinci kaina da saka pant da bra. Abin da bana sakawa kenan idan zan kwanta brezia tunda na ji an ce tana sanadin kamuwa da ciwon sankarar mama. Amma yau na kakaba ta. Na dauko rigar barci mai laushi wacce ta zarce guiwa da ka'dan na saka. Na sake gyara gashina. Na jona burner na zuba turaren wuta. Bayan na feshe kayana da tsadadden turarena. Na dauko dogon hijabi gogagge na saka, na tada Sallah. Ina kan sallayar ya shigo. Ya kishingi'da akan gadon. Na shafa addu'a na yi masa sannu da dawowa, ya amsa idonsa a lumshe. Ya tashi ya ce "zo ki yi warming 'din kazar nan, ki ha'do mini da tea".Ganin tana da yawa ya sanya na saka a wata a fridge na dumama wadda zamu iya cinyewa. Tare muka fita. Ya haye sama, Ni kuma na shiga kicin. Na shirya komai a dining. Ya sauko! Cikin lallausar jallabiya sabuwa dal kalar ruwan madara, sai 'kamshin turarensa mai da'din gaske yake yi. Tare muka zauna wajen cin abincin. Ban yi sanya ko kunyar ci ba domin yunwa nake ji. Tun indomie din da na ci da zamu fita. Sai cincin da na ci ka'dan a gidan Anti Ramla, ni kuma wadannan abubuwan ban dauke su a abinci ba. Na kammala na zaro tissue na goge hannu da baki. Ya kalle ni ya ce "Guduyo kenan! 'Dazu zamu fita baki saka hijabi ba, amma yanzu daga ni sai ke a gida kin dauko burgujejen hijabi kin maka. Annabi ya ce "Madallah da macen da idan mijinta ya kalleta zata sanya shi farin ciki". A hankali na ce "Sallah na yi fah" "Eh haka ne! yanzun ma sallar kike yi yar rainin wayo, ki cigaba dai da wasa da ticket din shiga aljannar ki". Na yi shiru saboda na rasa me zan ce. Kicin na ga ya shiga ya fito da ledar Habib yougort din da ya siyo. Ya kalle ni fuska ba alamun sassauci ya ce "ki kashe komai ki zo 'dakina ina jiran ki, idan kika wuce 20 mintues ki sani ban yarda da ke ba. Kuma Annabi ya ce "Allah Yana yarda da mace ne idan mijinta ya yarda da ita". Ya haye abinsa, ya barni da binsa da ido. Brush na sake yi. Na ha'diyi supplement *G.H.T.* hadin amare da Faseelat ta yi min. Akan a dole na doshi saman nasa. Na shiga da sallamah, na tarar da shi yana zaune akan kafet din gaban gadon. Na zauna nima, ya bu'de robar yagourt din ya turo tare da cewa "Bismillah dauki ki sha". Na girgiza kai na ce "Na koshi sosai". Ina rufe baki ya ce "Ba ruwana da koshin ki! Maganar Annabi zan yiwa biyayya da ya ce a shayar da amare madara ko nono. Dan haka dauki ki shanye". A dole na sha yogurt din, duk da da'dinsa. Na shiga bayi na kuskure bakina. Na sake zama akan kafet din a takure. Ya kalle ni ya ce "Guduyo ban son irin wannan mood din a yau. Sannan ki tashi ki cire wannan hijabin tun raina bai fara baci ba". Na kasa cire wa. Ya gama shan youghrt din ya shiga toilet, ina jinsa yana brush. Ya fito ya dauki air freshener akan mirror ya feshe dakin. Ya matso inda nake ya saka hannu biyu ya ciccibe ni, na taimaka masa na mi'ke din. Ya cire hijabin ya yi wurgi da shi yana cewa "Wato halittar mace da 'kunbiya kunbiya take, wai ke a dole sai kin ja aji. A dole sai an miki irin yadda kuke jin labarin karya ko?" Dake a cikin ru'dani nake sai na kasa cewa uffan. Na zuba masa ido. Ya kalle ni from head to toe! Ya koma ta bayan ma. Ya dawo gabana ya ce "maimakon ki samo riga very transferent sai ki sako mini wannan cotton din? Bayan na sani Sakina zata cika miki akwati da irin wadannan rigunan dan kawai na zama *Jani talau*". Ba zato na ji ya rungume ni sosai, tsawon lokaci muna hakan, muna Jin bugun da zuciyoyinmu suke yi. Yayin da wannan rungumar ta sake zama sanadin soyayyar sa ta ninku a zuciyata. Na dinga jin sonsa ya tumbatsa ya cika zuciyar ya bi har raina da dukkan gangar jikina. Kisses ta ko ina yake sakar mini, na karshe wanda ya ki'dima ni shine wanda ya mini a kunnena. Komai na jikina sai da ya amsa wannan 'kiran nasa. Ya yi sama da rigar, ya cire itama ya wurgar da ita. Na yi saura daga ni sai pant da bra. A fili ya ce "wow *Funkaso babban girki! haka abin yake? Ashe dai da gaske Guduyon ce ta gaske. Bayan Guduyo kin sake zama Halah a gareni."* Kunya ta kama ni, na sanya dukkan hannuna na rufe fuskata. Ya gama kallonsa, da maganganunsa masu nauyi tamkar a ghetto area ya girma, wanda suka sake jefa ni cikin shau'kinsa. Ya yi iyakacin kokarinsa wajen cire bireziyar ya kasa. Cikin wata irin murya da ban yi zaton zai iya yinta ba ya ce "Ban son haka Gudidina taimake ni mana. Koya mini yadda ake yi, ta yadda nan gaba zan huta da cewa ki taya ni. Ganin na ki yin komai, ya sanya shi dauko almakashi ya yanka tsakiyar. Daga nan abin da ya biyo baya ba mai sau'kin fa'da bane. Domin dai kam da fitila a kunne ya yi komai, sannan duk wani lashe lashe ta tsostse ba wanda bai yi mini ba, shima kuma sai da ya sanya na yi masa. Bai bari na zama yar gari ba a harkar, a ranar ya koya mini komai, sannan ya mayar da ni cikakkiyar mace. Bayan ya nutsu ya ce "Oh yau dai burinki ya cika Halimatu kin cinyewa Umma 'danta kin raba shi da samarta ka". Duk da ina cikin yanayi mai nauyi! Ga 'kasana sai rad'ad'in gurzar da ya sha yake yi. Sai da daure a kunya ce na ce "Na yi sanadin mayar da Gudalen Ummah Man dai, girma ya zo. Sai fatan Allah ya sa ya gane ya girma din". Ya yi murmushi bai ce komai ba, ya je ya yi wanka ya fito da daure da tawul. Ina kwance ina kallonsa tunda har lokacin ya ki yarda ya kashe fitila. Na kalli agogo na ga sha biyu ta wuce, na tabbatar mun shafe lokaci mai yawa. Rawar jiki da sumbatu na sha ba adadi. Madallah da kayayyakin *Faaseelat* Dake iyashege a jininsa ne yana tsayen ya ce "Ba zaki tashi ki yi wanka ba? Duk yadda nake fama da ciwon cinyoyi na yun'kura na tashi ban langwabe ba. To kinsan dai ni ba mijin novel bane bare na yi 'karfin halin sunkutar ki ko da ina nishi ne, na kai ki toilet na wanke ki sannan na na'do ki a tawul tamkar jinjira". Dariya ya bani sosai na ce "zaka iya mana Gudale! Ina ce dai ban zan zarta nauyin dinner-set din nan da ka kinkima cak rannan?" Ya bu'de ido ya ce "Kina nufin dan kin ga girmana har kin jingine Yayan daga yau? Gudale gatsal? Haka dazu ma kika ce wai Gudalen Umma babu sakaye". Na gimtse dariyar ina tuna dazu da rana ya dinga gatsa sunan yayarsa, amma shi yanzu yana tuhumar an gatsa sunan sa. Na lallaba na tashi na yo wanka, bayan na kama ruwa da ruwan zafi sosai har sai da na ji dai dai sannan na fito na ganshi akan gado yana goge inda muka bata da tissue. Kunya ta sake kama ni, na dauke kai tamkar ban gani ba. Mansa na shafa, na fesa body spray na mayar da rigata. Na kalle shi ya yi 'dai'dai a gado, fuskarsa sai annuri take yi, da alamun gajiya a jikinsa. Na ce "a kashe fitilar?" A hankali ya ce "zo ki kwanta". Ban musa ba, illah iyaka na sani ba zan iya barci ba yau, tunda bana iya barci da haske a kaina. Da na kwanta, da kansa ya lulluba mini dubet sannan ya kashe fitilar ashe akwai makunna a kusa da jikin gadon. Ya kwanta ina jinsa yana karanto addu'ar barci. Hakan yasa nima na ankara na fara yi, muka gama, muka shafe jikinmu. Ya matso ya rungume ni sosai a hankali ya ce "Kin ri'ke tarbiyarki! Allah ya sanya albarka a dukkan rayuwar ki my *Halah*". Mamaki ya kama ni ashe dai Gudale ya iya abin arziki haka? Ya jiyar da ni da'di domin irin yadda ya biyar da ni ne ya hana na ji tsananin zafin da ake cewa ana ji. Sannan yanzu yana sanya mini albarka. Ya nisa ya ce "Zan fa'dawa Abba baki watsar da tarbiyarsu ba. Sannan nima ban lalata musu ke ba, sai da suka bani aurenki da kansu". A hankali na ce "Yama za'a yi ka ce haka?" Ya yi dariya ya ce "Ai na sani gani yake yi zan iya 'bata miki rayuwarki, alhalin ni ba zan iya cutar da ke ba". Daga haka muka bar maganar barci mai nauyi ya dauke mu. Duk da mun kwanta very late, amma Gudale ana kiran sallah ya tashi. Sai da ya yi alwallah ya tashe ni. Ya fice zuwa masallaci! Madallah da mutanan da suke katse barci ko wani aiki da zarar an kira sallah. Na ji shigworsa, amma shiru bai hawo saman ba. Kusan minitin ashirin sannan ya hawo. Ga mamakina sai ganinsa na yi da tray, Ya ajiye a gabana, na ga flask din tea da cups guda biyu da kuma sugar, sai kazar da na saka a fridge ya yi warming dinta. Ya shiga bayi ya wanke baki. Ya ce "akwai sabon brush a toilet din je ki yi, ki zo mu karya muna bukatar cin abu mai dumi kinsan dukkan mu virgins ne, dole sai mun kula da kan mu". Kunyar maganar ta kama ni, na kasa tashi. Ya ce "Ni dai na yi iya abin da zan iya yi. Ba zan ce sai na sabe ki na kai ki na miki brush ba, sannan na zo na dora ki a cinya ina baki a bakinki, ni na manta da kaina ba. Kai wasu marubutan ma da tsiya suke, haka siddan sun zo sun sakawa mata shubuha suna raina 'ko'karin mazansu na zahiri. To ki ji da wai marubuciya Ubangijin rubutun ta ne, ita zata ta shirya komai ta tsara, ta kashe wanda bata so, ta kuma raya wanda take so. Dan haka wasu suna yi rubutunsu tamkar gaske saboda yadda suke za'kulo matsaloli suna rubutun ta hanyar yin hannunka mai sanda dan ya zama iznah da gargadi. Yayin da wasu suke rubutun karya da batsa ta yadda tarbiya take kara shiga cikin garari. Yara suke ganinsu dai-dai da manya. A kuma cusa wa mata raina kokarin mazajensu a shimfida, ko a mua'amalar zaman yau da kullum." Na kifa kaina a jikin gadon ina dariya sosai! Kaina a kasa na ce "Wai kam ya aka yi ka san haka suke fa'da a littafin?". Ya ce "abokina Faruk budurwarsa tana yawan bashi labarin littafi, har tana tura masa wasu pages din. Sai yake tura mana. Wani shafi da na ga abin da mijin yake yi na ce "Amma wannan zasu cusa wa yanmata shubuha a ransu domin dai namijin bil-adam indai a cikin hankalinsa yake ai ba zai yi irin hakan ba. Sai dai a aljannah. Kuma fa ita bilhakki take ganin haka zai dinga yi mata." Dariya sosai ya bani na tashi na wanko bakin, na dawo ya ce "Bari na ha'da miki tea din da kaina Guduyo. Yau kin tabbata amarya mai aji". Na murmusa na ce "Da sannu kunkuru ya je inda zomo ya je any way na gode". Ya wani harare ni ya ce "Yau komin zungure zunguren maganar ki ba zan yi fa'da da ke ba *Hala*. Nasan alheri fa! Wato Sa'adu Bori da hikima yake da ya ce ashe mata wayo suke yi mana abin da'di na can..... Ashe dai reality yake fa'da?". Na yi dariya ban tanka ba. Illah iyaka na sani da dukkan zuciyarsa yake wannan shaukin. Sosai muka ci naman, yana ta fa'din dirty talks masu saukar da nauyi da kunya. Muna kammalawa na tattra na kai kwanukan kicin din dake saman na ajiye. Na dinga kewaya falon da ya sha�? kujerun alfarma tamkar falon kasa. Jina shiru ya le'ko ganin ina ta zagaye ya sanya shi murmushi ya ce "Kin kyauta! I thought guduwa kika yi ai". Da kansa ya ri'ke hannuna muka koma daki, barci sosai muka yi dan kuwa bamu farka ba sai shabiyu da rabi na Rana. A gurguje ya shiga wanka dan tafiya sallar juma'a, ni kuma na sauko 'kasa. Duk yadda na so na yi shara kasawa na yi a dalilin nauyin da jikina ya yi mini. Sa'ar da nayi babu datti, amma da na yi din da zai fi. Wanka na yi da ruwa mai zafi sosai, na shirya cikin wata coffee din abaya mai kyau da na sameta a *Amyas newly* na goga sabo janbakin oriflame. Na shiga kicin na fito da miya a fridge. Ganin zata isa har zuwa dare sai kawai na 'dora ruwa dan dafa farar shinkafa. Na hau aikin ha'da coslow. Kafin ya dawo na shirya komai na gyara kicin din sama sama. Na dauko robar yagourt din ta yi saura na sha, na ha'diyi Panadol, na kwanta. Ba jima wa ya dawo, na kalle shi, na ga yadda kayan suka yi masa kyau. Ya zauna yana ta'ba jikin nawa yana cewa "Wai jikin ne da gaske ko kuwa shagwaba ne?" Na ce "kawai nauyi ya yi mini, sai kuma kasala amma lafiyata kalau. Na shirya abinci a dining" Ya dago ni yana cewa "to taso mu ci, ai da akwai yunwa ma". Shi ya zuba mana a plate 'daya yana cewa "daga fita ta har kika yi wannan abincin?" Na ce "ai dama ina da miya". Ya cigaba da cin abincinsa bai ce komai ba. Ni Kuma so nake ya ce kin yi kokari, kuma abincin ya yi da'di. Tun ranar bai fita ko ina ba, sai dai zuwa masallaci, yana gida muna barzar amarci ba kakkautawa. Na gamsu hadin amare da *Faseelat* ta yi mini ya taka muhimmiyar rawa a rawar kan da Yaya Gudale yake yi a kaina. A raina na sake yarda Sakina babbar mace ce, duk wanda zata yi harkar saye da saryawa da su za ki samu kayansu zababbu kuma amintattu ne. Tunda na ga tana ha'diyarsu na tabbatar ta gamsu da nagartar kayan kamfanin *G.H.T* da jakadancin *Faseelart* ne tunda jamiar kiwon lafiya ce. Tuntu'be *Faseelart* a wannan lambar *07039269802.* dan ki samu naki supplement din da zai dace da ke. Cikin sassaukan farashi fiye da na sauran. Abu mai daraja shi ke sayar da kansa. Guduyo dai ta tabbatar tasted and trusted ne, domin ta sake samun sabon suna mai da'di sanadin yadda aka sameta zanzan *Hala*. Ga barin jiki da sanyayyar soyayya. Tamkar ba Gudalen Ummah sarkin son girma ba. Ranar Monday tun asuba na shiga kicin na kammala komai na abin karyawa, na gyara gidan ya yi fes. Karfe bakwai saura na fito a wanka, a gurguje na kurbi shayi. Na na'de meatpia a foil papper na dauki lemo na saka su a leda. Na hau sama na sanar masa zan fita. Ya zabura ya zauna ya ce "Yanzu ni ka'dai zaki bari a gidan? Kewar ki illah zata mini Halah". Wani Dadi ya ratsa ni. Na makale murya na ce "akan dole zan fita Yaya Gudale rabona da zuwa tun Tuesday kada na samu matsala" Ya ja numfashi ya ce "juya bayan ki na gani". Na juya din ya ce "gaskiya wannan kayan ba su mini ba. Ni kawai ya kamata na ga ni a jikin ki". Na kalli kayan ba wani illah a tare da su. Amma saboda masalaha na canjo wasu, kamar yadda ya ce din. Amma Ina dawowa a tunzure ya ce "Kin ga idan ba zaki saka hijabi har kasa ba sai ki fasa fitar". Jikina ya yi sanyi saboda yadda na ga ya yi kicin kicin, bana kaunar abin da zai ruguza tarairayar da yake yi mini. A hankali na ce "Tom bari na sako." Na sako dogon hijab har kasa na yadin toyobo da ya sha guga, kalar kunun kanwa. Ya kalle ni sosai ya ce "Ba wani Hijabin da bai kai wannan goguwa ba?" A Hankali na ce "akwai sai dai iya guiwa ne shi" Ya girgiza kai ya yi shiru. Na lura gaba'daya fitar ce baya so. Dan hakan nake ta lallabawa mu rabu kalau. Har cikin makarantar ya kai ni yana saka mini dokoki iri iri. Hatta glass din da ya tabbatar medicated ne sai da ya ce na cire shi, sai idan zan yin karatun zan saka. To kawai na ke cewa cikin ladabi da yardar zan kiyaye ka'idojin da ya sanya mini. Da zan sauka ya tambayi yaushe zan kammala. A hankali na ce "4". Ya nisa ya ce "alright" ya ciro gudar dubu ya bani tare da cewa "ga pocket money". Na kar'ba ina godiya sosai, domin nasan shi da son a gode masa. Na sauka cikin murna mai yawa. A wannan lokacin ba abin da nake so, yake kuma sanya ni farin ciki irin na ga walwala a fuskarsa. Ga mamakina 4 din a harabar makarantar ta yi masa. Kaina ya fasu, muna tafe ina ta yi masa barin jiki wajen jan doguwar hira a tsakaninmu. Ya kalle ni ya ce "yini na yi, ina zullumin lallen hannunki. Bana son sa Guduyo, dole abokan karatun ki maza su ga hannun ki. Wannan tunanin ya sababa mini kyamar lallen ki duk da yadda ya yi miki kyau". Na sassauta na ce "Ka yi hakuri zan kiyaye sosai, dan kuma ka samu nutsuwa ba zan sake yi ba, har sai ina cikin hutu mai dogon zango". Ya ce "Ko sai kin kammala karatun ma gaba'daya ba." "Na ce To". A wannan lokacin na sake sakankacewa akan tabbas fahimtar Yaya Gudale a baibai ake yi kawai. Domin yadda ya saukar da kai muke shan soyayyarmu abin tamkar almara. Wani lokacin idan ya yi abu na dinga kallon sa kenan domin ban zaci zai ajiye girman kansa a kaina irin hakan ba. Yayin da ni kuma na sake zama deep a cikin soyayyar sa. Har zuwa Friday lafiya lau, shi yake kai ni ya kuma dauko ni. Amma duk ranar Monday sai ya rikice mini. Ba karamin juriya nake yi ba, domin ya dinga sani canja kaya kenan. Na kasa gane wannan al'amarin. Bana samun kansa sosai sai a kwanakin week end. Satinsa uku da dawowa ya fara aiki da F I.R.S. Dan haka tare muke fita, kowa a motarsa, tunda ina iya zuwa makaranta da kaina yanzu. Har lokacin kuma Wata biyu da gyaruwar al'amura a tsakaninmu na kasa gane kaina, wani irin zazzabi nake yi cikin dare. Ga amai sai dai idan ban 'dora girki ba, sannan ina matu'kar kuntata idan ya nemi ya kusance ni. Kai tsaye na tabbatar da ina da shigar ciki da ya wuce kwanakin wata a dalilin karatuna na Anatomy tamkar na likitan ci ne. # Team Gudale # Team Guduyo # Surayya Dee ✍️ # Ana tare 🤝. 2/8/23, 10:25 - Buhainat: *53-54*. *SDK* Sosai nake shan wahala a dalilin komai na ci sai ya dawo, ga karatu da ya dauki zafi, saboda ina daf da fara jarrabawar zangon karatu na farko a aji hudu. Ba abin da nake ci ya zauna mini sai garin rogo. Duk na fyade jikina yayi laushi tubus. A hakan kuma nake kokarin rufe hancina na yi masa abinci. Sa'ar da na yi idan na yi snacks da yawa na saka fridge sai na dauki lokaci ban sake yin wani ba. Miya kuma Mama na kaiwa ta yi mini mai yawa itama na saka a fridge. Amma duk da hakan indai zan dafa shinkafa ko na 'dora miyar da nufi 'dumamawa ba zaman lafiya na dinga amai kenan. Ranar wata litinin da bana mantawa, da safe ina zaune a kicin domin kammala abinci yayin da Gudale yake falo, saboda zaman namu sama sama ne a dalilin daren jiya ya matsa na yarda da shi sai dai tafiyar bata yi nisa ba, na dinga kwarara masa amai shikenan ya tunzura ya ingiza ni yana fa'din ya fara gajiya da wannan iskancin da na tsira ba dama ya ta'ba ni zan gabatar da uzzirin bani da lafiya tamkar ni kawai aka tattara wa jinya. Haka na tashi na gyara masa wajen na zo zan kwanta ya ce Ata fau bai san wannan maganar ba, sai na fita na bar masa dakinsa tunda dai bani da wani amfanin da zan yi masa. Shine yake ta fishi, ya kuma rantse ba zan je makaranta ba sai na yi masa abin da zai ci. Tunda jinyar bata hana ni fita da sunan makaranta ba, to lah shakka sai na yi masa abin karyawa. Ina aikin ina nishi, ina toshe hancina, amma dankalin yana dauko soyuwa na fara kakarin amai, ba komai a cikin nawa ban da ruwaan Lipton. Na amayar da shi tas. Ina shirin wanke baki wani aman ya sake subuce mini dai dai lokacin ya shigo kicin din, ya ja ya tsaya a bakin kofar yana kallona cikin takaici. Ya bu'de murya ya ce "Wato hidima ta ce kawai take saka ki amai Guduyo? Bayan wula'kanta ni da kika yi jiya bai ishe ki ba, shine yanzu kike ta mini amaye amaye akan abin da zan ci? Sannan anjima ki ce zaki fita makaranta?" A hankali na ce "Da gaske ba ni da lafiya, ka kalle ni mana, ai kasan dai ba hakan nake yi maka ba. Ka kai ni asibiti ka tabbatar. Makarantar ma ba dan exam ne da ni ba, da ha'kura zan yi". Ya juya ya fice ban samu arzikin sannu ba. A daddafe na kammala na kai masa, ganin bakwai da mitina biyar ya sanya na sassauta murya na ce "Zaka daure ka ajiye ni ne? Ba zan iya tu'ki ba". Ya kafe ni da ido ya na kallon irin yadda na yi laushi. Ya ce "Tom". "Na gode" na furta da sauri. A gurguje na wanke jikina. Na zura doguwar riga, na dora hijab na fito, man zaitun kawai na shafa a dalilin kamshi ma ya gagare ni. Ya kalle ni ya ga ba abin da zai ce na canja domin a hargitse na ke. Har muka isa zaman kurame muke yi. Na dinga nazarin akan wannan shariyar da yake yi mini. Wato indai ba zai mori jikina ba, ba sauran walwala a tsakaninmu. Nan da nan na kore wannan zargin na yi masa uzziri. Domin ai bai san sababin ciwon nawa ba, wata'kila da ya fahimci yana shirin zama Dady ne da na samu kulawa da kuma ya ninka mini soyayya, hakanan zai mini uzziri ya gane ba da gangan nake gudunsa a shimfida ba. Ya mi'ka mini gudar dari biyar tare da cewa kin ce "11 zaki kammala?" Na ce "eh". "Gashi kina kammalawa ki hau adaidaita ki koma gida, ba zan samu zuwa ba". Na kar'ba ina godiya. Da muka kammala har 'kofar gida Aisha Sani abokiyar karatuna ta kawo ni. Na zauna a falo ina numfarfashi, ba abin da nake so irin na ci garin kwaki, da lemo mai sanyi. Daga nan na yi barci. Na 'kwada garin na ci, na kuma sha lemona. Na shige daki na kwanta a kasa kan kafet barci ya sure ni. Ban farka ba, sai azahar. Ina idarwa na fa'da kicin, na hau hidimar abincin Yaya Gudale. Yana dawowa cin abinci, ina kammala wa. Ya ci abinsa, ya koshi, ya tsare ni da ido ya ce "kin warke ne ko kuwa kin yi amaye amayen yayin da kike girki?". Na yi 'kasa da kaina ina jin hawaye yana shirin goce mini. Ba sannu, ba nuna kulawa sai tuhuma? Ya tunzura ya ce "Ban gane ba?" Sanin da na yi ba ya son ya yi mini magana na yi masa shiru, ya sanya cikin rawar murya na ce "Ban yi ba". "Guduyo me na yi miki?" Na girgiza kai na ce "Babu komai" amma hawaye sai tsere suke akan fuskata. Ya zuba mini ido ya ce "To kukan na mene ne?" Cikin kukan sosai na ce "Bani da lafiya Yaya Gudale! Jikina ciwo, komai ciwo yake mini, bana iya cin abinci, gashi ina jin yunwa saosai". Ya saki ajiyar zuciya ya ce "Allah ya baki lafiya. Gobe sai mu je ki ga likita". "Na gode" na furta ina goge hawayen idona. Da zai dawo ya siyo mini apple cikin ikon Allah da na ci ban yi aman ba. Washagari bani da exam. Dan haka ya je office ya gabatar da uzziri sannan ya dawo muka nufi asibitin Malam. Da taimakon Sakina na ga likta. Bayan gwaje gwaje aka tabbatar inda da ciki na watattani biyu ba sati daya. Har mota Sakina ta rakomu, tana ta farin-ciki da addu'ar Allah ya ingan ta. Ita ta siyi magungunan da aka rubuta mini, na karin jini da tsayawar amai. Tun a wajen na lura Sakina ta zarce uban gayyar murna da mararin samuwar cikin. Shi dai gashinan kadaran kadahar. Sai da muka isa gida na dauko apple a fridge na zauna a falon ina ci. Ya zuba mini ido sosai ya ce "Shikenan har an yi an gama? Saboda Allah daga yin aure har zamu haihu bamu mori amarci ba?" Na kalle shi na ce "mun zarce watanni biyar fa da aure. Ai bai yi wuri ba. Sa'anin aurenmu fa sun fara nauyi. Ya gallah mini harara ya ce "wattannin aurenmu zaki lissafa mini ko watannin fara yin auren? Shikenan daga dan ta'ba ki sai ki yi ciki ban gama gane komai ba. Gashi duk kin wani sake kin yi yaushi, sannan ba dama a more ki". A hankali na ce " Ai kuwa ba dan ta'bawa ka yi mini ba! Kai ma ka sani, sannan nan gaba in sha Allah zan ji sau'ki tunda ga magunguna an ba ni". Ya mi'ke ya fita yana fa'din shi kam wallahi an cuce shi, daga yin ciki na wani zama ragajab tamkar wacce ta haihu da yawa. Baya ga haka bai gama gane komai ba an fara masa amai daga nan kuma sai kashi da kukan jinjirai. Mamaki ya sanya na bishi da ido, na kasa bu'de baki na ce komai. Yana bu'de kofar falon Abba yana kokarin shigowa. Ya dawo da baya ya bashi hanya Yana cewa "Abba sannu da zuwa". Yanayin Abba ya nuna tamkar ya ji maganganun Gudale da yake yi, amma bai ce komai ba. Ya ce gaishe ni ya zo yi, ya ga fitarmu, sannan Sakina ta yi masa albishir din albarkar da ta sauka mana. Murnar da Abba ya yi ita ta wanke mini takaicin abin da mai cikin ya cusa mini. Ya dinga yi mana addu'a da fatan alheri. Gefe guda kuma jirwaye ya dinga yiwa Gudale akan muhimmanci gode wa ni'imomin Ubangiji. Ya tafi Gudale ya bishi a baya cikin sanyin jiki. Haka muka cigaba da mirgina wa, ban samu kan Gudale ba sai da cikina ya shiga wata uku da kwanaki. Amai ya tsaya mini, na daina zazzabin dare, sannan kasalar ta yi matu'kar raguwa, sai dan abin da ba za'a rasa ba. Sai ya zama kuma na koma kamshin turarensa nake matu'kar son na sha'ka, shiyasa kullum ina ma'kale da shi ba gajiya. Shi da kansa sai da ya ce "Ashe cikin ba zai hana mu komai ba?" Kaina na saman kirjinsa na ce "gajen ha'kuri ka yi dama". Shikenan sai zaman namu ya dawo normal mussman da bana nuna masa gazawa a shimfida. Na lura Gudale idan bai samu yadda yadda so a wannan fagen ba, to lah shakka babu zaman lafiya. Na sani ina matu'kar 'kuntata da jarabar sa har na fara fargabar dawowar sa, domin ko abinci ya dawo ci, sai ya kusance ni babu daga 'kafa. Idan na nuna ba haka ba sai ya zama sanadin da zai kwanaa ya yini bai ce mini 'kala ba. Ko ya yi ta habaicin duk hidimar da yake yi da ni, ba dama na yi masa abin da yake so, me za'a yi da sangartacciyar mace mai langwai. Ko ya yi ta fa'din 'kamshin aljannah a wannan yinin ko daren ya haramta a gare ni domin ban yi abin da ya yarda da ni ba. Yawan kusantar da yake yi ya haifar mini da wani irin ciwon mara mai tsananin gaske. Da zarar ya kammala idan na dinga magogo sai an 'dauki lokaci kafin na samu kaina. Tun yana ganin abin iskanci ne har ya gamsu da gaske nake yi. Ya dan rage yawan nema na amma dai kullum zai yi. Sai dai ba kamar da ba, ya rage ne kawai, a lokacin na gane mabu'kaci ne sosai sannan ya 'daura 'damarar sai ya mayar da ni mabukaciyar. Zaman dai ba yabo ba fallasa, har na shiga wata na hudu. Muna ta Shirin fara yin jarrabawar gwaji na second semester (Test) kawai Asuu ta tafi yajin aikin gargadi na wata 'daya. Dalibi baya son srike amma ni sai ya zo mini a dai-dai saboda yadda nake shan wahala. Tunda na samu cikin nan ban huta ba, sai dai karfin hali kawai, ga ciwon mara da ciki lafawa suke yi ba wai na daina ne gaba'daya ba. Da daddare ina kwance akan gadona ina charting da yan'uwa cikin *Moriki* family group din mu na WhatsApp. Kamar jifa sai Yaya Ashir ya shigo nan da nan group din ya cika. Ana ta hira cikin jin dadi mussaman da yake ana daukar lokaci ba'a hadu hakan ba a dalilin kowa tasa matsalar ta ishe shi amma yau kam har su Antin Zaria duk an hadu. Yaya Ashir ya yi tagging 'dina ya ce "Ke kam kina gari ne? Kin yi wahalar ga ni". Na tura emojin din dariya tare da cewa "Ina nan mana! Ai duk kallon kowa nake yi, ba wanda ya sake le'ko ni sai Anti Sakina". Nan da nan aka fara raddin wa nake 'kira ina gaisa wa da shi? Suma sun 'kyale ni da Sadik tunda ya mamaye kowa a wajena". Na sake yin dariya ina fa'din ba hakan bane, amma ai sune manya ya kamata su dinga 'kira suna jin lafiyata, a dinga turo mini goron juma'a". Sosai aka yi hira, har waya aka dinga buga wa wadanda basa online akan su shigo yau ana zumunci. Mutanan Gusau da Kebbi duk sun fito an yi da su. Gudale ne kawai ya makale bai ce komai ba amma ina ganinsa yana online din. Da Antin Zaria ta yi tagging dinsa tana cewa ya fito, sai ya gabatar da uzzirin yana cikin aiki ne ya gaida kowa kyauta. Sai goma aka rufe hirar aka yi bankwana, bayan Yaya Ashir ya sakawa duk wanda ya girma katin 500. Yayin da Yayyen nasa suka ce ai su ya kamata ya bawa ba mu ba. Shima ya kafe sai dai su bashi. Aka rabu cikin farin-ciki mai yawa. Na yi wanka na dauko sabon turaren Oriflame, na feshe kayana da shi, yayin da na goga roll on dinsa. Kai *Aisha lame* 07036672633. Madallah da kayanta da farashinsu. Na hau sama a hankali sai dai me? Ina zuwa na ji kofar a rufe, na dinga murda kofar amma shiru, na koma knocking nan ma shiru. Na koma kiransa a waya, amma sama da sau goma tana ringing bai dauka ba. Har na shiga daya dakin zan kwanta sai na ga sai na yi wahalar dauko bargo. Sai kawai na dawo kasa, idona taf da hawayen ba'kin ciki. Na dinga tunanin me na yi masa to? Nasan dai har ya dawo daga sallar isha, ya ci abinci kalau muke. Na dinga juyi, ina tunaninsa, na kasa jurewa na dauko wayata ña ga karfe dayan dare har da mintina uku. Na shiga doka masa 'kira, karshe sai ya kashe wayarsa ga'badaya. Ranar rabi da rabi na yi barci, har zuwa asuba. Ina idar wa, na fita falo na zauna, ya dawo ya ganni ya wuce. Na bishi da sauri ina cewa "Ina kwana?" Kamar ba zai amsa ba sai kuma ya amsa din a takaice. Muka isa har dakinsa ina tsaye ya haye godo ya lulluba har kansa tabbacin ba zai saurare ni ba. Na sassauta murya na ce "Me yake faruwa ne, me na yi maka? Ni bana son irin haka! Idan wani abin na yi da ya bata maka Allah ya baka ha'kuri, shike nan?" A gajarce ya ce "To je ki abin ki, ina bu'katar ka'daici ne". Na zauna a akan side durowa na fara yi masa kuka ina fa'din "Ni bana so, bana son haka gaskiya, ka daina yi mini fishi, jiya ko runtsawa ban yi ba, dan Allah ka barni na samu sukuni kasan dai bani da lafiya". Ya dago a tunzure ya nuna mini 'kofa ya ce "out" Na 'ki tashi, sannan ban daina kukan ba, sai ma volume da na 'kara tamkar wanda yake duka na. Ransa ya baci 'kwarai da gaske ya ce "Amma kuwa Sadiya zaki saka na miki duka sai ki yi kukan da dalili. Ban miki komai ba ki zo ki tasa ni gaba da kururu wa, wanne irin al'amari ne wannan? Shikenan! Bari ni na bar miki 'dakin tun baki janyo na miki dukan da dukkan *Moriki brothers* zasu mini ca akan ki ba. Tunda na gane a yanzu ma da kike dakin aure har da rabo, ba'a daina mini magana da ke babu shamaki ba. Ai wlh ba zan yarda ba". Na yi matu'kar ka'duwa da wannan furucin wato hirar jiya ce ta bata masa, me aka yi to? na yi shiru cikin bugawar zuciya. Murya a dashe tsabar al-ajabi na ce "Yanzu gaisuwar da aka yi cikin jama'a ne laifi? 'Yan uwana kuma 'yan uwanka sune abin bacin rai dan kawai mun gaisa?" Haka kawai na ce "ya sake hassala wai na yi masa rashin kunya. Yana kumfar baki ya ce "shin Ashiru Al'amin ne shi? Ko yanzu na fàdi na mutu ba abin da zai hana Ashiru shiga sahun zawarawanki tunda ba kunya ne da shi ba, bare ya yi mutunci. Saboda ke tabbattaciya ce shine kika wula'kanta ni, kika yi ro'ko, wai ki rasa wa zaki ro'ka sai Ashiru. Shikuma jiki yana rawa ya turo miki, amma da yake shedani ne yasan ya yi ta'addanci shine ya ha'da da su Farisa. Saboda yasan zan kalubalenci hakan. Wato ba ke kawai ya bawa ba, amma ai kowa ya san albarkcin ki suka ci kudinsa, tunda shi matsolo ne". Raina ya baci sosai, amma na ha'diye na ce "shikenan na yi kuskure ba zan sake yin magana ba, matu'kar ba da mata bane". Ya ta'be baki ya ce "Ina ce jiyan ma tagging dinki ya yi? Ke kuma shikenan kika balle da magana har da su ro'ko, ai tozarci kam kin yi mini, amma ki jira sakamakon da zai biyo baya". Duk yadda na so maganar ta wuce Gudale bai yarda ba. Domin gaba ya dauka da ni sosai. Abinci ya daina ci, ya daina dawowa cin abincin rana, da daddare kuwa duk naci na ba zan shiga masa dakin sa ba. Kwana uku muna haka, hankalina ya kai kololuwar tashi, ga rashin cikakkiyar lafiya, ga masifar fishin Gudale. Gaba'daya na birkice, na rasa inda zan tsoma raina. A wannan lokacin na 'kara gane wa ina cikin jarrabawar tsananin sonsa. Wani irin so nake yi masa da ya wuce ka'ida, shiyasa nake shiga tasku idan yana fishi. Ranar asabar da wuri na kammala yi masa samosa, ina addu'ar Allah ya sanya ya ci. Na gyara kicin da falon, sannan na yi wanka, na shirya cikin leshi dinkin bubu ne amma dinkin ya yi matu'kar tsaruwa. Anfi ganin iri irensu a mujallar ado da kwalliya. Madallah da dinkin *Umm Muhd collection* mai komai da ruwanka. Yo komai yi take yi indai na sana'a ne gashi kuma kayanta da sauki, kuma zababbu, na sha fa'da Ni shaida ce. Da wahalar gaske ka ga abu kana so ace ka jira. Komai available ne wajen *Ummu Muhd collection.08063358662*. Na fito falo hannuna dauke da tsinken turare irin dogayen nan. Na ma'kala na zauna ina kallon agogo goma na safe saura ka'dan, Ina ta tunanin jiya Abba juma'a Abba bai shigo mini ba, tunda yanzu ya sabar mini in dai ya dawo masallaci sai ya shigo mun gaisa Baba ne kawai bai fi sau uku ya zo mini ba. A Raina na ce "Da Gudale wani ne yau sai ya barni na shiga cikin gida nima na ji da'di tunda aka yi mini aure watanni kusan bakwai sau hu'du kawai na shiga. Ina tsaye ya fito cikin kwalliyar kananun kaya. Farar riga ce mai tsada samfurin Bvulgari sai shudin jeans ya gyara sumar nan sai she'ki take yi, kamshin turarensa yana karade ko ina. Na Sha gabansa ina cewa "YAU kwana uku kana punished dina, a ka'idar sharia kwanan uku ne karbabben fishi. Dan Allah ka huce hakanan, ko dan bebinka da yake cikina ya samu kuzari". Ya kalle ni ya watsar ya wuce ya nufi waje. Na bishi har muka isa kofar da zata sadamu da cikin gida. Na sake shan gabansa murya na rawa na ce "Dan Allah! Allah ya baka ha'kuri, bana iya cin abinci, ga'badaya bani da sukuni, alhalin kai ne ka zafafa lamarin nan, amma na yarda ban yi dai-dai ba, na baka ha'kuri ai sai ka ha'kura." Ya kankance ido ya ce "Tunda ba zan ha'kura ba ke ki ha'kura ki fita a harkata mana. *Kamar ni Sadik Abubakar Moriki* matar aurena zata dinga ro'kon wani majanunin bawan daya addabe ni, ya zame mini barazana a duniyata. Na rantse ba zan fasa fadar an cuce ni ba. Abba ya takaice ni wallahi! Haka kawai ya manna mini auren da babu yardata alhalin ra'ayina da naki is pararell. Na yi matu'kar ka'duwa, amma da ke so hana ganin laifi sai na ru'ko hannunsa ina hawaye na ce "Allah ne ya kaddara auren ba Abba ba! Ina son zama da kai, amma akan abu ka'dan sai ka rufe ido ka nuna mini dole aka yi maka ka aure ni, ko kuma kana zaune da ni akan tilas". Na lura jikinsa ya yi sanyi da kalamaina. A hankali na ce "Taimake ni mu je ka karya, samosa na yi maka. Ka yi hakuri". Na ru'ko hannunsa muka doshi falon dai dai lokacin Abba ya turo kofar da muka bar jikinta tamkar almara. A hankali ya ce "Sannu Halimatu ya jikin? Jiya ban samu shigowa ba, saboda na wuce ta'aaziya". Na zare hannuna na gaishe shi cikin girmama wa. Ya amsa yana ta mini sannu da sanya albarka. Haka Yaya Sadik ya gaishe shi ya masa masa babu yabo, babu fallasa. Ya juya yana cewa "Ba sai na shiga ba, tunda mun gaisa." Muka shiga falo, na zuba masa, ina ta rawar jikin ha'da masa shayi. Da haka na dinga lallaba shi, har ya huce. Dan rashin ta ido kuma shikenan ya fara nanukata, idan na yi magana akan ya bari na huta sai ya ce "kwanakin da ya dauka bai yi ba yake fanshe wa. Ba yadda na iya haka nake biye masa, na yi masa yadda yake so Ai kuwa sai ciwon ciki ya taso mini haikan na kwana na tashi da shi, rannan da yammaci sosai na je fitsari sai na ga jini jini hankalina ya yi matu'kar tashi. Na fito a gigice, na yi sa'a yana gida ya dawo daga wajen aiki. # Team Gudale # Team Guduyo # Surayya Dee ✍️ # Ana tare 🤝. 2/8/23, 10:25 - Buhainat: *Na ce ba kinsan wani hadi da ake yi wa asalin man ridi da kwakwa da wani man da ban kama sunansa ba, da ba'a samun original din su sai a wasu kebantaccun jahohi?* *kina fama da matsalar cinyewar gashi ko kuma rashin tsayinsa?*. *Kina neman ha'din da da zai sanya fatarki laushi da sulbi, kuma cikin saussaukan farashi? Tuntu'bi wannan lambar dan samun naki cikin sau'ki. Kaya mai inganci shi yake siyar da kansa.* *Sister Zainab 08039315577.* *SDK* *55-56.* A hanzarce ya nufi asibitin premier da ni, tunda shine mafi kusa. Gynecologist na ga Ni! aka kammala dube dube da gwaje gwaje aka gano cikin ne bai zauna dai-dai ba, sannan bakin mahaifar a bude take. Take suka kwantar da ni, aka fara shirin yi mini yar 'karamar tiyata. Suka gyara zaman cikin sannan aka daure bakin mahaifar. Kwana uku a asibitin, gatan da na gani a wajen danginmu ba ka'dan bane, na sani kuma ina sake samun soyayya dan kasancewata matar Gudale. Abba ji yake tamkar ya taya ni numfashi. Haka dukkan sisters dinsa kullum sai sun zo da kayayyakin ciye ciye. Mama ce a wajena. Haka brothers dina da iyalansu tamkar mai ciwo sosai haka aka dinga zarya da dawainiya akai na. Antin Zaria itama sai da ta zo a ranar ta koma. A lokacin na sake gane soyayyar da ake yiwa Gudale mai girma ce. Domin komai yi masa ake yi, duk wanda yake kusa aka kawo bill ko wani magani sai dai a biya ba wanda yake jiransa. Hatta Umma da ba wani sakar mini fuska take yi ba, sau biyu ta zo duba ni. Ranar da aka sallame ni Sakina tana asibitin da ke da daddare ne. Sai dai dokokin da aka sanya mini masu yawa ne, babu hawa bene, babu mua'amalar aure, babu daukar abu mai nauyi, babu garaje yayin tafiya ko wani al'amari, hatta shara duk an ce babu. Har zuwa lokacin da komai zai daidaita. Aka sanarwa mutanan gida an sallame ni zamu dawo ba sai sun zo ba. Take Abba ya kira Sakina a waya ya bada umarnin idan mun je gidan ba wajena za'a kai ni ba. Wajensa za'a kai ni, ya saka an gyara mini dakina da nake kwana kafin aurena. Nan da nan na ji babu da'di mussaman yadda na lura Gudale ya matsu a sallame ni, kullum sai ya tambayi likitan yaushe za'a sallame ni?. Sannan na sani tun fil'azal baya kaunar na tafi wani waje. Shi dai ko ba zai mini magana ba, ya dawo ya ganni a gida shine burinsa tun ban zama matarsa ba, na shaida wannan. Har cikin zuciyata ban so wannan hukuncin ba. Amma ban isa na bu'de baki na cewa Abba bazan bi hukuncinsa ba. A kofar gidan muka tarar da Gudale yanayinsa dai babu damuwa kuma babu walwala. Sakina ta taimaka mini na fito a motar, ta ri'ke ni muka shiga cikin gidan. Yayin da ya debo kayayyakina. A dakin da aka gyara mini muka zauna. Mama bata wani jima ta tafi wajenta bayan sun gaisa da Umma. Abba da kansa ya shigo har dakin ya mini sannu, ya kuma ce mini "Komai kike so ki ci, ko kike bu'kata ki fa'da, kin sani dama nan ne gidanku". Na amsa da "To" cikin girmamawa. Zamana gaban Umma ya sake fahimtar da ni da gaske bata sona amma abin mamaki ta damu da cikin jikina. Domin idan zan yi wanka 'Yan aikinta take turowa su taimaka mini ta hanyar surka ruwan, tunda ta ji ance jijjiga mai karfi tana iya sawa cikin ya fa'di shikenan komai sawa take ayi mini. Ni ce dai bata cika yiwa sannu, ko nuna tausaya wa ba. Hakan bai dame ni ba, mussaman da yake kullum Gudale a dakin nawa zai zo ya karya, hakan abincin rana, da daddare ne yake ci a wajenta. Indai yana gida to yafi zaman dakina. Mafi yawan hirarsa ta adadin kwanakin da zan yi na koma ne. Tun yana girman kan ya bayyana mini ya yi kewata har ta 'kure ya fara fa'da bayan na yi sati a gidan Abba. Wanda kwanakina goma rabona da gidansa kenan. Ranar litinin da ta yi dai-dai da 'daya ga watan October ranar hutu ce a gaba'daya fa'din tarayyar Nigeria. Saboda a irin wannan ranar aka 'yanta 'kasar daga hannun turawan Birtaniya. A ranar tun taran safe ya shigo ko wanka bai yi ba domin jallabiya ce a jikinsa idonsa a jirkice tabbacin ya afa 'kwayar. Na ce "Yaya Gudale amma ka ce mini ba zaka sake sha ba fa" Ya bagarar da maganata ta hanyar cewa "Wai baku fa'dawa Abban likitan ya ce zaki iya yin 'yan harkokinki cikin lura ba?" Na ce "An fa'da masa! Ya sani". Ya ce "To sai yaushe ya ce zaki dawo?" Na girgiza kai na ce "A a ban sani ba gaskiya". Ya jijjiga kai ya tashi bai ce komai ba. Da kansa ya shiga wajen Umma ya debo abinci ya dawo. Yana ci yana maganganun tsageranci. Wai shi ya gaji da wannan kasafin, haka kawai a dauko masa matarsa babu iznininsa, sannan ta samu sau'ki an ki mayar da ita, dan kawai gadarar auren ha'di ne. Ya tabbatar da 'yar wani wajen ne da ba'a yi masa hakan ba. Na yi shiru domin dai bani da bakin magana! Mussaman da nasan yana cikin yanayin da zai iya yin komai. Sai da ya tabbatar Abba ya kammala karya wa sannan ya fita. *Falon Abba* Bayan sun gaisa suka yi shiru na tsawon lokaci. Gudale ya katse shirun da cewa "Abba Halimatu ta samu sau'ki sosai". "Eh na sani Sadik" ya amsa masa a takaice. "Ya yi shiru. Can ya ce "To yaushe zata koma?" "Sai ta 'kara warwarewa" Daga hakan ya kame bakinsa ya tsuke. A sanyaye ya ce "To" ba dan ya so ba". Ya tashi ya fice ba tare da ya sake cewa uffan ba. Yayin da Abba ya bishi da ido yana ayyana abubuwa masu yawa a ransa. Abubuwan da ya ji da kunnensa Sadik din yana fa'da zai yi hukunci a kansu. *** A kasalance ya dawo dakina ya zauna gefen gadon yana ta 'kunci. Bai bu'da mini ba, nima kuma ban tambaya ba, domin na da'de da fahimtar idan yana cikin wannan yanayin, bai cika son ma na yi masa magana ba. Bare kuma yanzu ya ha'du da bacin rai. Ya gama zamansa tsawon lokaci ya fita ba tare da ya sake yin magana ba. Har karfe biyar ina ta zuba idon ganinsa amma shiru, sai dai na sani yana can yana barci tunda ya sha abun da dole sai ya yi wannan barcin na asara. Bai zo ba sai washagari. Wajen Umma ya karya a gurguje ya shigo muka gaisa a dalilin ya yi latti. Da daddare da ya shigo mini! Ya kaikai ce ido ya ce "Ki dinga 'kwarara jikinki ko dattijon nan zai gane kin warke". A hankali na ce "Ai yanzu kowa ya kalle ni yasan na samu lafiya tunda an kiyaye ka'idojin da aka gindaya mini a asibiti". Ya ce "To idan Abba yana gida ki dinga fita kina zagaya wa, dan gaskiya na gaji". Na yi shiru, na kasa cewa komai. Ya zuba mini ido sosai ya ce "Ban gane ba". A hankali na ce "Na ji". Ya ce "Amma dai kin sani bana so a mini shiru ko". Kai tsaye na ce "Yi ha'kuri dan Allah! Na ji zan yi". Kan dole na tsiri fita idan Abban na gidan, haka idan nasan ya fito zan je mu gaisa. Da kansa ya ce "ki dinga hutar da kanki Halima! Bar biye son zuciya, daure ki kula da lafiyarki, domin sai da ita kake da amfani". Kunya ta kama ni da na gane Abba ya fahimci manufar wannan shige da ficen nawa. A haka aka cinye sati, kafin nan kuma Yaya Sadik ya sake tuntu'bar Abba akan yaushe zan koma tunda na ji sau'ki sosai. Ya sake bashi amsar so yake na warware sosai. Rannan dai ta 'kure masa ya zo mini a sanyaye. Ya zuba mini ido tsawon lokaci har sai da kallon ya ratsa mini dukkan jikina, gane hakan da ya yi sai ya yi gyaran murya! Ya ce "Na gaji da zamanki a gidan nan ki fa'dawa Abba da bakinki cewar kin warware". Zuciyata ta harba na ce "Ba zan iya fa'da masa ba Yaya Sadik! Ka ga kwanaki ma ya gano zaryan da ka ce na dinga yi". Ya daure fuska sosai ya ce "Ba zaki iya ba kika ce?" A hankali na ce "Kunya! Da nauyi zan ji, ka fahimce ni dan Allah". Ya mi'ke tsaye ya ce "Ai shikenan! Tunda dai ban isa na baki umarni ki yi mini biyayya ba. Biyayyar miji kuma wajibi ne matu'kar ba zunubi zai sa ayi ba". Na kalle shi na ga ransa ya baci matu'ka da gaske. Da rawar murya na ce "kar ka yi fishi! Ka sani dai kullum farin cikinka shine kan gaba a wajena". Ya hassalo ya ce "makaryaciyar banza! Ta ina ne kike mutunta farin-cikin nawa? Ai da hakan ne ina ce miki ga yadda zaki yi. To kawai zaki ce mini, amma kin zauna ina fa'da, kina turje wa sannan ki ce mini yayyyen". Ya marairaice murya yana kwaikwaiyon abin da na ce din. Daga hakan ya fice ya buga mini 'kofa da tsananin gaske. Na yi sukuri ina mamakin wannan al'amarin, kawai Gudale ya so yi mini jidali ne. Banda haka ta Yaya zan iya cewa Abba zan koma gidan mijina? Bai jima da fita ba Sakina ta shigo, da alama daga asibiti ta zarto nan. Muka gaisa ta kalle ni ta ce "ko wani wajen na yi miki ciwo ne?" Na girgiza kai na ce "'Kalau nake". Ta jima tana nazarina ta nisa! Ta ce "ko ba kya jin da'din zaman ne? Na sani akwai takura". Nan ma na ce "Ni ban takura ba, komai yi mini ake yi". "To so kike ki koma wajen Na Moriki ya dinga jijjiga ki ko?" Kunya ta kama ni. Na fara yi mata kuka tare da cewa"Bana son haka Maman Nana". Ita kuwa ta zarce da cewa "Ai na ganshi a waje yana ta kumfar bakin ya gaji da ri'ke kin da ake yi! Ashe kema kin gajin kenan, bayan dan lafiyarki Abba ya tsare ki". Na ha'de fuska na ce "To ai ni na ji sau'ki, komai zan iya yi. Gara na koma kar damuwa ta yi masa yawa". Mamakina mai tsananin gaske ya kama Sakina ta rasa me zata ce mini. Ta mi'ke tana cewa "Ai sai ki fa'dawa Abba hakan". Na ru'ko hannunta na ce "Haka ma Yaya Gudale ya ce mini, amma kunya nake ji! Ko zaki taimake ni ki fa'da masa?" Ta fisge hannunta ta nuna ni da yatsa ta ce "shashar banza marar hankali! Ni kike fa'dawa hakan? Wlh Halimatu ki dawo hayyacinki wacce irin jarabta ki Gudale ya yi ne hakan? Duk wahalar da kika sha a sanadin rashin sassauta miki da ba ya yi, shine kike son sake komawa ya 'balle aikin da aka yi miki ko? Dama kin bi a hankali kin kula da lafiyarki domin idan baki da mamora jingine ki zai yi ya samo mai mamora". Hawaye ya balle mini Na ce "Fata dai na gari lamiri ne". Ta girgiza kai ta juya ta nufi 'kofar fita, ba tare da ta ce komai ba saboda ta fahimci na riga na bari soyayyar Gudale ta rinjayi komai a wajena ta yadda zan iya rufe ido na yi komai. Har ta bude handle din kofar sai kuma ta dawo. A sanyaye ta ce "Sadiya! Kar ki sake ki yarda da maganar Gudale da ya ce ki fa'dawa Abba zaki koma 'dakinki. Nima da na fa'da miki gatse ne. Kar ki yarda, ki yarda da hukuncin Abba! Komai zai yi babu son zuciya a lamarinsa. Kar ki yadda ki yi koyi da dabi'un Gudale na rashin kunya da rashin kawaici. Idan har zamansa da ke bai sa ya koyi ha'kurinki da sanyin halinki ba, ashe kuwa bai kamata ke ki yi koyi da munanan dabi'unsa ba". Jikina ya yi sanyi ina gasgata gaskiya Sakina ta fa'da. Amma babbar damuwata na tsani fishin Gudale! tayar mini da hankali yake yi. Sannan na tsani na ganshi a cikin damuwa, yanzun nan zan nemi nutsuwata na rasa. Ni da kaina na sani akwai nauyi sosai na tunkari Abba na ce zan koma dakina. Sai dai ko zan iya jarumtar jure fishin Autan Umma?. Na sani yanzu haka ma fishin da yake yi da hukuncin Abba ya fara shafa ta. Tunda shi matu'kar zai ce ga yadda za'a yi na ce ba hakan ba, to fa shikenan na ci mutuncinsa na raina shi. Na kalli Sakina ina hango tarin soyayyata da tausayina a idanuwanta. Na goge hawayen na ce "shikenan ba zan fa'da ba! Amma ki taya ni addu'a kada na kasa jurewar na fa'da din". Cikin lallashi ta ce "Banda ma baki da wayo, ai ba zai samu damar ce miki ki yi wannan 'danyen aikin ba. Shi ya je ya fa'da mana". Da sauri na ce "Tun yaushe ya fa'da masa? Kawai Abban ne mun rasa gane manufarsa". "To ke dai mace ce! Ba ruwan ki, ki zuba ido ki bar Gudale ya yi abin da yaga dama kada ki bashi tallafin ki". Na ce "To". Ta jima a dakin, tana ta hilata ta, tare da hannunka mai sandar idan mace ta bari soyayyarta ta rinjayi ta Namiji al'amarin da take fuskanta mai nauyi ne. Baya ga haka ya dinga yin iyashege kala kala kenan. Da na gaji na ce "Wato dai Maman Nana so kike na daina son Yaya Gudale?" A hankali ta ce "Ba nufina haka ba! Ina so dai ki danne shi a ranki, ki yi masa biyayya, ki sauke dukkan hakkinsa da ya rataya a kanki, amma matsananciyar soyayyar da kike masa barta a ranki! Yawaita addu'a kada ta zamo miki sanadin wahala a hannunsa". Na ce "Wato dai gani kike yi ni ne na mutu akansa, shi ba ya sona?" Nan da nan ta hauro ta hau zabga mini zagi, tana fadin "ki je ki biye masa tunda dai ke ba kya kishin kanki." Ni kuwa na zum'bura baki ainun duk da nasan bata son na yi mata hakan. Ta fita ta bar ni ina 'kunkunin ita ma ai tana son mijinta. Akan me zata ce kar na nuna wa mijina soyayya? Washagari da safe ina ta jiran shigowar Gudale amma shiru, sai jin fitarsa na yi, ba tare da ya shigo mini ba. Haka da rana bai dawo ba. Na yini cikin zullumi, ban sake shiga damuwa ba sai da daddare ya zo gidan ya ci abinci a wajen Ummansa ya gama abin da zai yi ya fice ba tare da ya neme ni ba. Duk da ina jin yadda ya dinga 'daga murya dan na ji ya zo gidan bu'katar ganina ne baya yi kawai. Ina jin ya fita hawaye ya balle mini. Na dauki wayata na dinga doka masa 'kira amma bai dauka ba, duk kuwa da na kira ya kai sau goma. 'karshe ma sai ya kashe wayarsa gaba'daya. Na kwana cikin damuwa. Washagari ban ji zuwansa ba, sai da zai fita ne na jiyo shi, shima na sani dan na gane ya zo ne, ya sanya ya yi abin da zan fahimci ya zo. Wayarsa na dinga 'kira ba 'kak'kautawa har na gaji dan kaina. Na dinga tambayar kaina me na yi da na cancanci ya yi mini dogon fishi irin haka?. Sai dare ya waiwaye ni, kafin lokacin kuwa duk na yi zuruzuru. Ya zauna yana kallona, na gaishe shi a sanyaye ya amsa yana cin magani. Tsawon dakika talatin kafin ya kalle ni ya ce "Na ga kina ta kiran wayata lafiya?" Na kasa bashi amsa domin ina bu'de baki kuka zan fashe da shi. Bansan me ya hana ya yi mini sababin shirun da na yi masa ba. Ya nisa ya ce "Idan kika kira sau daya, sau biyu, ba zaki gane ina cikin wani uzziri bane? Sai ki ta kirana rututu tamkar 'kina kiran yaroh?" Hawaye ya balle mini m. Jikinsa ya yi sanyi sosai. Ya ce "menene abin kuka Guduyo?" Ganin sosai nake kukan mai dauke da ajiyar zuciya, sai ya sassauta ya ce "goge hawayenki ki fa'da mini dalilin wannan kukan. Na jima kafin kukan ya tsaya mini. Na ce "Me na yi maka da zaka dinga zuwa gidan amma ba zaka dinga shigo wa kana duba lafiyata ba? Sannan na kira ka a waya ba zaka dauka ba, ba kuma zaka biyo ba?" Ya daure fuska ainun ya ce "Ai nasan kina lafiya ne! Ba zai yiwu na ce ga abin da nake so ki yi mini, ba ki ji nauyi ko kunya ba kika ce baza ki yi ba. Kinga kuwa kar ki saka ran kullum sai na zo ganin ki, tunda na gane ni ka'dai na damu da son kacenwarmu tare". Da sauri na ce "Amma dai Yaya Sadik kasan idan akwai abin da nake son na kasance da shi a doron 'kasa ai kai ne". Ya mele baki ya ce "Ni ban sani ba, tunda a baki ne. Da hakan ne har zuciyarki ai da ba sai na ce ki yi wa Abba magana ba. Da kan ki zaki nuna kin warware zaki koma dakinki ki cigaba da neman lahirarki. Amma saboda kin fi son zaman nan din , shiyasa ba kya fitar da na ce ki dinga yi idan Abba na kusa. Kuma shiyasa kika ce ba zaki iya fa'din kin ji sau'ki ba. Ni kuma abin da baki sani ba, na nemowa kaina mafita. Ba zan sake cewa ki koma ba, na zuba ido a cigaba da nuna mini iyaka akan hakkina. Sai dai ki sani ke za'a janyo wa. Kuma 'kin bani ha'din kai da kika yi da sunan kunya wallahi kwabar ki ce zata yi ruwa. Domin aure zan 'kara, ai idan a waje na nemo auren ba za'a mini abin da ake mini...". Kafin ya rufe baki na fashe masa da kuka sosai ina cewa "me na yi maka? " "Menene baki yi ba Guduyo? Yau kwana biyu na ce ki samu Abbanki ki ce kin ji garau, Kika bijire mini". Cikin kukan na ce "To zan fa'da masa shikenan?" Ya matso jikina sosai ya ru'ko dukkan hannuwanna ya ce "That's my *Hala*! Yanzu na ji da'di na kuma gane kin damu da damuwata. Yaushe zaki fa'da masa?" Na ce gobe da safe, tunda yanzu dare ya yi". "Yauwa na gode miki sosai! Yau zaki kwana cikin yardar Ubangiji tunda na yarda da ke." Cikin rauni sosai na ce "Ka fasa yin auren?" Ya sake ri'ke hannuna ya ce "To me zan yi da shi, dama ai zan yi ne dan na samu mai mini biyayya, tunda kin dawo hanya ai tuni na kore tunanin yinsa". Da'di ya yi matu'kar kama ni, na murmusa sosai. Yayin da ya yi amfani da hakan ya jagwalgala ni son ransa. Gaba'daya a cikin shau'ki muke, ko dan an dauki lokaci mai yawa ba'a hadu bane?. Da kyar muka rabu, yana ta mitar shi an tauye shi, shi ya ake so ya yi ne?. Washagari kuwa na murje duk kashedin da Sakina ta yi mini na kada na bawa Gudale tallafi akan hukuncin Abba. Na same shi da kaina a falonsa. Na yi sa'a Umma ta je ganin likita asibiti. Bayan mun gaisa sai kuma na kasa cewa komai. Da kansa ya gane ina da magana ya sassauta ya ce "fa'da mini damuwarki Halimatu na magance miki ita yanzu". Murya na rawa sosai na ce "Dama dama na warke sosai, kuma zan iya yan harkokina". Tsawon lokaci kafin Abba ya ce "Ai na sani Halimatu! Sai dai na yi mamaki da kika fi gamsuwa da ra'ayin mijinki akan na ubanki. Na tabbatar Sadik ne ya turo ki, ki yi mini wannan rashin kunyar, dan haka na yafe miki. Amma ki sanar masa cewa Ni da na cuce shi, na bashi ke akan dole ba dan yana so ba. Na fasa auren na ku, ma'ana bana so yaci gaba da wanzu wa, idan har ina da hakkin akan sa sai ya sakar mini ke". Ai kuwa na dage na fasa masa kuka ina cewa "Kar kashe mini aure Abba dan Allah". Ya yi shiru yana kallon irin yadda hawaye yake tsere a idona. Ya sassauta ya ce "Nutsu ki saurare ni da kyau! Sau biyu ina jinsa yana fa'da miki na cuce shi, da na bashi aurenki akan dole. Matu'kar ban karya masa wannan lagwan ba, ba zaki samu lafiya ba, duk sadda kika kuskure sai ya fa'da miki dole aka yi masa ba son ki yake yi ba. Kuma 'karya yake yi, idan kuma gaskiya yake fa'da shikenan zan yi adalci na gaskiya. Ki yi ha'kuri ki bani dama, sai Sadik ya fahimta zan bashi ke ne akan yana so, amma na gaji da zaman alfarmar da yake yi da ke". Cikin kuka na ce "Abba! Sai kukan ya sake kwace wa. Bai katse ni ba, sai da na yi mai isata na yi shiru dan kaina. Na ce "Abba idan ban koma ba aure zai yi". Na fa'da murya na rawa. A kufule ya ce "Ya jima bai yi ba, ya auro uku rana 'daya Halima! Ina ro'kon ki arziki, ko wannan ce biyayya ta karshe da zaki mini, kar ki bi bayansa ki kunyata ni, ki bari ya gane ke din kina da daraja, dole kuma ya kalli wannan darajar a yayin zaman aurenku. Ina nufin sai ya yarda ba dole na yi masa ba. Idan ba ya son ki, to ya dawo mini da ke salin alin. Ina da wandanda zan bawa su rike mini ke cikin soyayya da mutunci". Jikina ya yi sanyi 'kalau, kunyar Abba ta kama ni, na yadda ya tabbatar mini na yi masa rashin kunya. Ga kuma ro'kon da ya yi mini kada na kunya ta shi. Amma gaskiyar magana dukkan zuciyata na ga tunanin kada a matsawa Gudale, ya tunzura ya sake ni, na shiga uku. # Team Gudale # Team Guduyo # Surayya Dee ✍️ # Ana tare 🤝. 2/8/23, 10:25 - Buhainat: *Na ce ba kinsan wani hadi da ake yi wa asalin man ridi da kwakwa da ba'a samun original din su sai a wasu kebantaccun jahohi?* *kina fama da matsalar cinyewar gashi ko kuma rashin tsayinsa?*. *Kina neman ha'din da da zai sanya fatarki laushi da sulbi, kuma cikin saussaukan farashi? Tuntu'bi wannan lambar dan samun naki cikin sau'ki. Kaya mai inganci shi yake siyar da kansa.* *Sister Zainab 08039315577*. *SDK* *57-58*. Maganganu masu taushi da sanyaya zuciya Abba ya dabaibaye ni da su, har ya samu kaina na gamsu na amince zan yi biyayya na zauna tare da shi! Har zuwa lokacin da komai zai yi masa yadda yake so. Ya mi'ka hannu ya ce "ki fita harkarsa, ki daina daukar wayarsa bare ya hargitsa miki tunani, da sannu zan fahimtar da shi muhimmancin ki". Ba ja in ja na ce "zan kiyaye Abba". Ya ce "madallah da Halimatu ta shi ki yi, tafiyar ki, ki kwantar da hankalinki kina cikin aminci. Komai kike so kar ki 'kwari kanki". Na dawo dakina sukuku. Na kwanta akan gado hawaye na bin fuskata. Zuciyata ta yi nauyi ainun. Fargaba da zullumi fal a raina. Shin idan Abba ya kashe mini aure ya ya zan yi ne? Dai-dai lokacin cikina ya yi wani irin motsi mai karfi. Na saka hannu na dafe wajen da na ji ya motsa din. Rabon da ya yi mini irin wannan motsin tun ranar da aka daure mini bakin mahaifa, a ranar kam ya yi zillo sosai tabbacin ya 'kuntata. A fili na ce "Na sani kana taya ni ko kina taya ni faragabar dutsen da ake shirin gindaya tsakanina da farin cikina. A hankali na mi'ke na yi wanka na karya sama sama. Sai da na shirya tsaf, sannnan ya zo saboda week end ne. Kalaman Abba sun sanya mini kasala sosai. Shiyasa ya ganni ba kuzari. Ya tambayi ina lafiya kuwa? Na bashi amsa da "lafiya lau, yanayin ne babu da'di. Ya ce "Kin je wajen Abban kuwa?" A hankali na ce "Na je ban jima da dawowa ba." "To ya kuka Yi?" Ya tambaya cikin za'kuwa. Sai da na numfasa na bashi amsa da cewa " Ya ce ai ya fa'da maka sai na warware! Haka ya sake jaddada mini nima". Ya zabura ya mi'ke yana nuna ni da hannu cikin fishi ya ce "Haka muka yi? Ba na ce ki ce masa kin warware ba?" Na sassauta murya na ce "wallahi na fa'da masa. Baka ga fa'dan da ya mini ba, wai na raina shi tunda na tunkare shi da wannan maganar". Ya rasa yadda zai yi. Ya ce "Haka ya ce?" Na girgiza masa kai tabbacin eh. Ya fita yana cewa "Bari na je da kaina, na gaji da wannan kama karyar da ake mini". *Wajen Abba*. Kishingi'de ya same shi, yana karatun littafin Muwad'da Malik. Sai da ya kammala sannan ya ajiye ya fuskance shi. Cikin ladabi sosai Gudale ya ce "Barka da hantsi! Ya jiki jiki, ya kuma ha'kuri da rayuwar nan mai cike da hargitsi?" Mamaki ya kama Abba na wannan sabuwar nau'in gaisuwa da autansa ya yi masa. Murmushin da bai shirya yi ba ya subuce masa saboda yadda ya ga Sadik cikin nutsuwa tabbacin yana cikin neman taimakon sa. Ya amsa masa da Alhamdulillah a takaice. Ya dinga kame kame kafin ya yi kundubalar cewa "Abba Halimatu ta ji sau'ki sosai. Likita ya tabbatar da hakan kuma." "Na sani! Sakina ta fa'da mini bayanin likita" Abban ya fa'da hankalinsa na kan talabijin. Tsawon lokaci Gudale na fama da takaici, amma da yake nema yake yi sai ya ha'diye fishin ya ce "To Abba me take yi anan? Ya kamata ta koma dakinta duk abin da ba zata iya yi ba, zan yi mata uzziri tunda lalura ce". Sai lokacin Abba ya karkato da dukkan hankalinsa kan Gudale ya ce "Ka turo ta zo ta ce zata koma dakinta tunda zirga zirgar da ka sanya ta yi bai yi tasiri ba. Yanzu kuma ka zo da kanka a karo na uku". Kansa ya saukar 'kasa ba tare da ya cewa Abba komai ba. Tsawon dakika goma kafin Abba ya ce "To bari ka ji na fa'da maka dan ka saurara mini da wannan bibiyar da kake yi mini". Sai da ya numfasa sannan ya kaurara murya ya ce "waye ya baka auren Halimatu?" Zuciyarsa ta harba ka'dan. Cikin dauriya ya ce "Kai ne Abba". "Dama kuma dole na yi maka ko?" Wanann tambayar kam sai Gudale ya kasa amsa ta. Abba ya zarce da cewa "Abin da zan fa'da maka shine tunda ni na baka ita akan dole. Shine na ga bai kamata zaman na ku ya cigaba da wanzuwa ba. Har zuciyata ban kullace ka ba. Amma ka sani auren na ku ya ishe ni haka nan. Yadda na baka ita cikin girma da arziki. Ina baka umarni ka sakar mini ita a mutuntunce tun bamu rabu dutse a hannun riga ba." Wata irin fargaba ta shige shi mussaman da ya 'dago ya kalli fuskar Abba ya ga babu alamun wasa. Da rudani ya ce "Ta ce ina yi mata wani abin ne Abba?" "Ko daya wlh bata ce mini komai akan zamanku ba. Ita tana da ra'ayin kanta ne? Ai komai kake so hakan zata yi, tunda ita tana sonka, ba dole na yi mata take zaune da kai ba. Duk da cewa iko kawai na yi akanta na za'ba mata miji ta karba da hannu biyu take kuma mutuntata zaman". Kan Gudale ya daure. Shaguben na Abba ya buge shi kwarai da gaske. Ya numfasa ya ce "Da hannu biyu nima na karba Abba, gashi nan muna zaune 'kalau komai lafiya a tsakaninmu". "Hakane" Abba ya fa'da a gajarce. Tsawon lokaci ba Wanda ya sake magana a cikinsu. Gudale dai ya dorawa Halima laifi. Ya tsargu, gani yake wani abin ta fa'da. Takaici ya kama shi! Wanne irin aure yake yi da bashi da ikon zartar da hukuncin da yake so akan matarsa? Murya ba amo ya katse shirun da cewa "Abba fa'da mini ranar da zata koma dan na daina damunka". Kai-tsaye Abban ya ce "Ba zan ce ga rana ba. Amma da zarar ta warware da kaina zan saka ranar". Kan Gudale ya daure ainun! Ya rasa gane nufin Abban, ya kasa fahimtar warwarewar da Abba yake nufin Halimatu ta yi. Da fishi ya bar falon ba tare da ya ce uffan ba. Amma ya gaji da wannan mulkin mallakkan da ake yi masa. Indai haka ake yiwa mutum iko idan an yi masa aure to gara a bari ya yiwa kansa komai sai ya yi iko da iyalinsa. Ya gaji da wannan kama karyar. Ya kai gejin wajen ha'kuri da alkunya. Tabbas idan Abba ya cigaba da ri'ke masa mata zai gurfana a gabansa ya fa'da masa yana bukatar matarsa. Idan ya so ace ya yi rashin ta ido. Kwanaki biyu a tsakanin maganar sa da Abba ya zauna gaban Umma yana sakin maganganun ri'ke masa mata da aka yi. Ta kalle shi cikin kunan rai ta ce "waton dai so kake ka nuna mini kana son yarinyar nan ko?" Ba shakka bare nauyi ya ce "ko ba na sonta tunda akwai amfanin da take yi mini ai dole zan bu'kaci ta dawo dakinta". Jikinta ya yi sanyi. Ba dan komai ba sai dan yanayinsa ya tabbatar mata, baya cikin hayyacinsa. Kuma Gudalenta yana cikin soyayya mai zurfi. Sai dai kuma shi kansa bai fahimci irin deep din da ya yi akan soyayyar Guduyo ba. A fili ta ce "Allah ka shiga tsakanin duk mai son shiga tsakanin 'da da mahaifi. Allah ina nemawa Gudale tsari da kaidin mace da makircinta." Ya murmusa ya ce "Ameen Ummah! Ina son ki gane duk duniya ke ce farin-cikina. Ba abin da zan nema baki mini ba. Ina son ki taimake ni ki mini uzziri." Ga'ba daya ta 'dora hankalinta a kansa. Ya yi kasa da kansa ya ce "Ba da rashin kunya ba Umma! Ina bu'katar matata gaskiya. Dan haka ki gajarce mini wahalar nan ki sanar wa mijinki, na gaji da ri'ke mini ita da yake yi babu dalili. Akan ta aka fara jinya? Shin haka yake yiwa mazajen su Sakina? Ko dan ni bai dauke ni surukinsa ba? Alhalin yadda yake nunawa shine uban Guduyo ai kamata ya yi ya mayar da mua'amalata da shi irin yadda yake yi da surikansa". Umma da ba'kin cikin kalamansa suka turnike ta tamkar ta rushe da kuka. Murya na rawa ta ce "shi ka kasa cin mutuncinsa a gabansa, amma ni ka zo ka tasa ni a gaba kana tozarta ni. A gabana kake wannan tijarar akan Halimatu? Ashe dai zanga ranar da zaka so Kumbusar nan har haka? Ashe zaka iya fifita farin-cikinka akan nawa? " A sanyaye ya ce "Ba sonta nake yi ba Umma! Amma ita ce halal 'dina a halin yanzu. Kinsan nan duniya ba wanda nake so na yi sharing damuwata sama da ke. Saboda ba soyayyar da nake da garantin amintacciya ce sama da wacce kike yi mini. Ina 'kara yi miki alwashin babu mai shiga tsakanina da ke. Ki zuba ido zaki gane 'kaddara ce kawai ta ha'da ni da Guduyo". Ta saki ajiyar zuciyar samun nutsuwa. Ta ce "Zan fa'da masa, amma ka dage da addu'a, mutanan nan basu da tausayi bare su yi kawaici. Makirai ne na gaske, yan gadon kanainaye namiji ne". Ba damuwa tare da shi ya ce "Yo ni Umma idan aka ga an mallake ni ba 'karamin asiri ne zai kama ni ba. Domin kuwa ina addu'a sosai, sannan ni din masifaffe ne na gaske. Asiri yafi cin laku laku ai". Da haka ya lallabata suka bar maganar, suka shiga wata. Washagari ya zo ya same ni na yi wanka fes da ni duk da ban yi kwalliya ba. Ya tsaya bai zauna ba, yana mini irin kallo. A hankali na ce "sannu da zuwa ina kwana?" Bai amsa ba ya ce "Guduyo wato ke baki da matsalar zaman ki anan ko? Na gane kin mance da ni. Kin fi enjoying din gidan nan akan gidana. Menane bana yi miki ban da goyo?" Na murmusa na ce "shima idan ka daure din ai zaka iya, fafalo ce ba ni da nauyi sosai". Ya dan murmusa ya ce "kawai ki ce so kike na zama mijin novel". Na ce "A zahirin ma ana goyon fa". Kai tsaye ya ce "Yan shawalwalai ba". Daga haka na bar maganar. Ya ce "Na rantse na kusa na daina yi miki magana, na baki daga nan zuwa gobe ki san yadda zaki yi a dawo mini da ke. If not mun 'bata, kuma zan iya yin komai, har da budurwa zan yi". A raunane na ce "Ba yadda zan yi Yaya Gudale. Kar ka jingina mini laifi, ba zan iya watsa wa Abba k'asa a ido ba. Duk abin da yake yi saboda cigabanmu ne, Babinmu yake tattala mana". Ya hassalo ya ce "To ni watsa mini 'kasar tunda ya fini hakki akan ki. Wallahi idan baki yi a hankali ba, yau dai kam ba zaki rabauta ba, tunda kin gardame mini. Wai Babinmu yake tattala mana! Mai iyayyin tsiya, to mu ba zamu tattala shi ba da muka yi sanadin samuwarsa? Sai kaka ne zai yi wannan karambanin. To ki fa'da masa Uban Bebin ya ce zai tattala abinsa". Na yi shiru, amma zuciyata sai harba wa take yi a dalilin fusata da na ga ya yi. Murya na rawa na ce "kar ka ga laifina da gangan. Ni kaina na matsu na dawo". Ya kyabe baki ya ce "kal ka ga yaifina da yayyan". Na sauke kaina 'kasa dalilin dariyar yadda ya yi magana tamkar ta yaro dan karami, wai kuma nufinsa nine na yi hakan. Ya ce "idan fa kika wuce jibi a gidan nan, nasan inda kika ajiye ni" Ya fice ya bar ni da zullumi. Tsakani da Allah na tsani duk abin da zai jagula ran Gudale. Sonsa nake yi da dukkan zuciyata. Ina gudun bacin ransa fiye da komai. Babban farin-cikina na ganshi cikin walwala da sukuni. Bacin ransa kuma na nufin nawa bacin ran da zama cikin fargaba. Na rasa yadda zan yi na tunkari Abba. A ranar da ya diba mini idan ta wuce ban koma ba, zai dauki mataki Sakina ta zo. Yanayina ya tabbatar mata kiris nake jira na koma dakina da kaina. Na dinga yi mata kukan ta roki Abba na koma gidana. Gudale ya ce aure zai yi ya manta da ni. Cikin kuka na ce mata "Ni na gaji gaskiya, ni ban ce mijina ya mini laifi ba. Akan me za'a janyo mini rikici?" A sanyaye da dinbin mamaki take cewa "kar ki biye shi, kara ha'kuri. Abba ba zai bari a cutar da ke ba, bare shi ya yi miki sanadin cutarwar". Ta dinga lallaba ni, tana cewa na sassauta wannan zazzafar soyayyar, 'karya yake mini ba wata budurwar da zai yi. A daddafe na yi kwana biyu. Cikin dare ya 'kira ni a waya ya dinga fa'din "Na gode sosai Guduyo! Na gode da tozarci. Banda ina duba abu guda tak! Da na yi miki baki. Annabi ya ce da zai umarci wata halitta ta yiwa wata halittar sujjadda da ya ce mace ta yiwa mijinta saboda girman hakkinsa da yake kanta. Amma ke saboda gata kin yi watsi da sababin da zaki sami aljannah. Na gode sosai". A sanyaye na ce "Yaya Sadik kasan dai ina maka biyayya, ina kuma son ka". "A baki ba, ina soyayyar take? Banda musu da raini baki iya komai ba. Amma babu damuwa zan yi maganin wannan sha'kiyancin na ki. Billahillazi zan nemo wacce zata girmama ni, wacc zata bi ra'ayina koda ya ci karo da ra'ayinta". Nan da nan na fara yi masa kuka ina cewa "Ya zan yi ne? Abba fa! Babanmu ne dukkanmu" "To fa'da mini aljannarki a 'kafarsa take ko a 'kafata?" Na ce "a kafarka?" "Madallah! To indai hakane kina son na daga miki sawuna babu 'kwange, kawai ki je ki samu Abba ki ce zaki dawo dakinki. Idan kika yi hakan, to na gamsu kina sona, kina mini biyayya. Kuma in-dai miji na zamewa matarsa sababin shiga aljannah. To wajabat a gareki Yah Halah". Cikin kuka na ce"To". Yauwa Bebina ki kwanta ki yi barci, ki ji a ranki Yaya Gudalenki na son ki fiye da son da mijin bahaushe yake yiwa mai dakinsa" Wani irin Da'di ya kamani karon farko da ya bu'de baki ya ce yana sona. Tuni na manta komai, na dinga tunanin yadda zan yi na gamsar da Abba ina son komawa gidana. Washagari ta yi dai-dai da komawa asibiti. Umma Abba ya ce ta raka ni. Sanin da ya yi zai iya tare mu a waje ya a tafi da ni. Ya sanya ya wakilta Ashiru ya zo ya kai mu asibitin. Ashe kuwa Abba ya fahimci Yaya Gudale da kyau. Muna dawowa a kofar gidan muka tarar da shi. Sai dai ganin Ashir na tuka mota ya yi kicin kicin da fuska. Ya rasa inda zai tsoma ransa. Muna bakin gate kafin a bu'de gate ya le'ko ta windon da Umma take. Ya ce "sannunku Ummah." Ya kallo ni ya ce "Sauko ba sai kin shiga ba". Na saka hannu da nufin bude kofar, sai na ji Yaya Ashir ya yi locked dinta. A tunzure ya ce "Ashiru bude mata kofar". Bai ko kula shi ba, ya ja motar zuwa cikin gidan. Ina ganin yadda ta sake daure fuskarta. Bata son na koma gidan Gudale. Fata take yi auren ya balbalce a hakan. Amma kuma ta damu da damuwar da ta gani a fuskarsa a dalilin wulakancin da Yaya Ashir ya yi masa. Na sani kuma da Yaya Abbas ko Yaya Alamin ke tu'ka motar sai Gudale ya tafi da ni tunda ya raina su, su kuma basa tsananta fa'da da shi. Amma shi da Yaya Ashir kar tasan kar ne. Bugu da 'kari Yaya Ashir 'kashi daya ne da shi. Ma'ana irin karfafan mutanen nan ne. Idan suyi maka mahangurba sai ka je 'kasa. Hakan kuma yake zage dukkan 'karfinsa akan Gudale shiyasa yake kiyayarsa domin yasan baya cin riba a hannunsa kamar yadda yake yiwa su Yaya Al'amin. Yaya Ashir baya ba jin nauyin ya cakumi Gudale da fa'da matu'kar ya nemi yi masa iya shege ko isgilanci. Shiyasa har yanzu basa shiri da juna. Gane hakan da Abba ya yi shiyasa ya 'dora shi akan tafiyar, ya tabbatar Gudale bai isa 'daukata a gaban Yaya Ashir ba, duk tsagerancinsa kuwa. Dan kuwa ba zai zame wa Yaya Ashir komai ya na'de kafar wando su daku ba. Domin tamkar borkonon tsidugu haka yake wajen fa'da. Kuma abin mamaki Gudale kawai yake yiwa wannan bala'in. Su Yaya Abbas zasu zolaye shi su kwana 'kalau amma ban da Gudale. Ko dan Gudalen yana yi masa iyashegen shi 'dan mace ne? Shiyasa shi kuma yake nuna masa iyakarsa a cikin gidan da yake alfaharin nasu ne tunda shi 'dan namiji ne. Har gaban Abba ya kai ni. Ya damka masa mukallin motar tare da cewa "Gata nan na dawo da ita Abba! Zan koma, na bar aiki muhimmai a office. Ubangiji ya 'kara maka lafiya". Yaya Gudale na gefen falon a raku'be tunda ya biyo mu mun shigo tare, Umma ce ta shige wajenta. Abba ya riko hannunsa ya ce "madallah da jarumi irinka Ashir! A duk sadda na kalle ka na kan tuna sadda muke yara. Uwarka jarumace ta gaske. 'Kanwata ce ta nisa amma ta sha tara ku'dinta ta bani idan zan tafi makaranta Na sani daga siffa har jarumtar Binta ka dauke su tsaf, har jarumtar murkushe iyashegen mai iyashege duk ka dauko. Ina jinka a raina tamkar yadda nake jin ta. Na gaji da zaman ka hakan. Ka je gidan Babanku na Gusau ku daidaita da Farisa na baka ita". Ya koma 'kasa ya tsugunna ya ce "Na karba da hannu biyu Abba, dama ina son ta. Idan ina gaban ka na kan yi dakacen inama na fito ta tsatsonka? saboda tsananin karamcinka, wanda ka zamewa mahaifi tabbas masu sa'a ne, duk da ba lallai wani ya fahimci irin gam da katar din da ya yi ba. Bare ya yi koyi ya zama abin misali. Madallah da kai Abbah! Madallah da mutane irin ka. Allah ya shiryi masu halin albasa! Kar a gaji da addu'a, da sannu komai zai daidaita maka Abba". Albarka kan albarka Abba ya dinga sanya masa. Yana sake jinjina jarumtar Yaya Ashir har cikin zuciyarsa. Yana kuma gode masa yadda yake wanke masa Yaya Sadik. yake kuma hana shi kuzari indai yana wajen. Ya mi'ke ya fice da sauri bai ko kalli gefen da Gudale ya safare ba. Sai da ya fice Yaya Gude ya gaida Abba a raunane domin ya kai matu'kar ka'duwa da abin da suka yi masa shi da Ashir. "A fusace ya ce "Gata nan Abba ta warware! Zan tafi da ita". Kai tsaye Abba ya ce "Kai Sadik! Bude kunne ka ji ni da kyau. Komawa ne ba zata yi ba. Ai ni na baka ita, yanzu kuma tunda na gane cutar ka na yi, to na janye cutarwar". A matu'kar razane ya kallo ni ya ce "Daga yi miki wasa Guduyo shine kika zo, kika ha'da mini gurnet? Ai dai sau 'daya na fa'da, kuma kalmomin yabo nawa na fa'da miki?" Baki ma rawa na kalle shi na ce "Billahillazi ko point ban tofa a wannan maganar ba. Abba dan Allah na fa'da maka ina da damuwa da shi?" Ya girgiza kai ya ce "Baki fa'da mini ba. Sau biyu kunnena na jiyo mini sadda kake fa'din na cuce ka. Kuma indai ina da hakkin akan ka, ba zata koma ba". Hawaye ya balle mini, na rasa inda zan saka raina. Yayin da Yaya Sadik ya shiga wani irin yanayi mai wahalar wa. Cikin tsawa Abba ya ce mini "Tashi ki bani waje shasha da baki san ciwon kanki ba. Me zaki yi da namijin da zai kushe ki. Yana fa'da miki zaman alfarma yake yi da ke. Matu'kar ni din ubanku ne, na raba auren kenan". Jikina na rawa na tashi ina ha'da hanya, ina jin rabani da Gudale tamkar rabani da farin-ciki ne gaba'daya. A gado na kwanta ina wani irin kuka, mai cin rai. Ban dan yadda suka 'kare ba. Washagari dai ya kira ni a waya, yana mini sababin na ha'da masa munafurci, sai na yi murna tunda na shiga tsakaninsa da ubansa. Murya na rawa nake kare kaina. "Wallahi ban fa'da wa Abba komai ba, ka yarda da ni, ka ga fishin da kake yi da ni, ya jefa ni damuwa, jiya sai da likita ya ce jinina ya dan hau na rage damuwa. Dan Allah ka daina tayar mini da hankali, akan abin da kasan ba zan yi ba". Jikinsa ya dan yi sanyi ya ce "Ga ni nake yi baki damu da ni bane. Ni kawai na damu ki dawo gare ni". "Na damu fah Yaya Gudale! Ji nake yi kamar idan an kwanta na tsallako ta katanga". Ya ce "ko yar sirirya ce ke ai cikin jikinki ba zai bamu wannan damar ba. Kar ki fara tsallakowa, ban son ku ji ciwo. Amma idan kina son na yarda ba sa hannun ki, to ki shammace su ki taho zan bar kofar gadern a bu'de." Zuciya 'daya na ce "To". Wani abin almara. Abba sai ya fahimci kudirina. Sai ya rufe kofar garden da 'kwado. Sannan ya ja kunnen maigadi kar a bari na fita. Hakan ya sake firgita ni, mussaman yadda Yaya Sadik ya tsananta tayar mini da hankali. Rannan unexpected Abba ya karbe wayoyina. Kwanaki biyu baya samun wayata. * Wajen Baban Yara* Tun daga masallacim sallar asuba ya bi Baba ya ce "zasu yi magana. Sun zauna a falonsa tsawon lokaci, ya kasa cewa koami. "Sadik ka ce zamu yi magana! Kuma ka yi shiru". "Baba ka je ka samu Abba ya dawo mini da matata yau fiye da sati biyu yana ri'ke da ita. Ya ce sai na saketa" "Ashha amma ban sani ba! aka ce hutawa take yi sai jikinta ya yi 'kwari." "Ba wani hutawa Baba! Kawai yana son ya tozarta ni ne, an taba yin hakan? Ana zaune lafiya ace sai ka saki mace? Idan kuma da nine na yi hakan sai ace na yi wula'kanci, amma ni an rufe ido ana wula'kanta ni". "To kai ba abin da ka yi ya yanke wannan hukuncin, na sani Alhaji bashi da son zuciya". "Haba Baba! Saboda Allah ka bi bayana mana kawai, ina zaka tsaya bin ba'asin me na yi? Yo mi sai na yi laifi ne yake hukunta ni? Bansan me suke 'kullawa shi da ita ba, tunda ya zugeta ko wayarta ma bata shiga". Jikin Baba ya sanyi ya ce "To kwantar da hankalinka. Zan same shi zamu tattauna". "Yaushe zaka je?" Sadik ya tambaya a hanzarce. "Zuwa anjima" "A a Baba ni ba zan iya ha'kuri ba! Kawai ka je yanzu. Ni wallahi ban ta'ba shiga rudani irin haka ba. Bana iya barci, komai ya tsaya mini cak, hatta aikin office ban da Anti Rabi mai fahimta ce ai da komai ya cakalkale mini. Gaskiya a bani matata kawai". A take Baban ya mike ya ce "kwantar da hankalinka! Bari na je na dawo". Duk yadda Baban ya so su yi magana da Abba fir abin ya faskara domin Abban ya kafe sai Sadik ya kawo masa takardar Halimatu tunda cutarsa ya yi da ya bashi auren ta. Baba ya ce "Haba Alhaji! Ya za'a yi ka shiga sha'anin aure? Yara suna son junansu, ka rabu da su". "Oh Ibrahim fa'da mini yadda zan yi! Ina ce dana ha'da auren ban shawarce ka ba? Yanzu kuma da zan raba ne zan shawarce ka saboda kana ganin ka fini tsinkaye?" Nan da nan Baba ya dinga fa'din"Ba haka bane wallahi! Ka yi ha'kuri." Cikin fishi ya ce "ka fitar mini daga wannan maganar idan ba so kake na ci mutuncinka ba". Ya dinga bawa Yayan nasa ha'kuri. Ya tafi guiwa a sace". Yanayin Baba ka'dai ya tabbatar wa Sadik abin yafi karfinsa sannan al'amarin babba ne. Domin Baban cewa ya yi "ka je wajen Yayar 'Kwalli. Ni ba zai saurare ni ba". Da ga wajen Baba, ya doshi Kwalli ya je ya kinkimo Yayar takanas domin gaba'daya ya birkice. Dake gaba take da Abba sai bai bude mata wuta ba. Kamar yadda ya yiwa mahaifin Halimatu. Ta kuma bada umarnin ya bawa yaro matarsa bata son haka. Cikin ladabi ya ce "saurare ni Yaya! Cikin girma na bashi aure, kuma a gabana ya amsa zai ri'ke ta da amana. Amma kinsan kullum a cikin fa'din na cuce shi yake saboda na yi masa auren dole. Sannan Bayan auren ya wula'kanta ni, ya gudu ya barta tsawon wata biyu ba'a san inda yake ba, ba waya ba aike. Sannan bai gane gata na yi masa ba, sai yake nunawa alfarma yake yi mana ni da ita. Sai dai ki yi hakuri! Wallahi ba zan bashi ita ba, alhalin baya sonta a dole yake zaune da ita". Rantsuwar Abba ta kidima Gudale. Wani irin firgici ya shige shi. 'Kirjinsa ya yi nauyi dama ya sani guduwar nan da Umma ta ingiza shi ya sai ta zame masa sanadin baci rai mai tsananin gaske a wajen Abba. # Team Gudale # Team Guduyo # Surayya Dee✍️ # Ana tare 🤝. 2/8/23, 10:25 - Buhainat: *AMYAS NEW & FAIRLY ITEMS* *SUNA RENTING KAYAN AMARE* *SUNA SAYAR DA SUTTURUN MATA ZABBABU, NA ALFARMA, DA KAYAN KICIN*. *SUNA SIYAN KAYAN FURNITURES KO ELECTRONICS NA HANNU* *SUNA KUMA SAYARWA*. *SUNA SAYAR DA FILI DA GIDA*. *SUNA BADA HAYAR GIDA*. *KOMAI DA RUWANKA NE AMYAS GASU DA SANIN DARAJAR CUSTOMER. KAYANSU KUMA MASU INGANCI NE KUMA MASU RAHUSA NE*. *08083909947*. *SDK* *59-60*. Sai dai bai yi zaton kashe masa aure ne hukuncinsa ba. Zufa ta dinga karyo masa, duk da yanayin bana zafi bane. Murya na rawa ya ce "Indai akan rashin sonta ne ka rantse ba zaka dawo mini da ita ba, sai na ce Alhamdulillah. Domin kaffara bata hau kanka ba Abba. Na rantse da Ubangiji ina son ta, kuma wallahi 'karya na fa'da tsagwaronta da na ce ka cuce ni, gata ka yi mini na sani". Ya fa'da a hankali. Zuciyar mace mai rauni, nan da nan sai tausayin sa ya kama Yaya. Ta ce "Alhaji! Yi ha'kuri ka bashi matarsa, ai yanzu ya gane komai, gaba kuma ba zai sake ba". Abba ya numfasa ya ce "Ba zan bashi ba Yaya! Na gaji da auren ne fa gaba'daya. Wannan yaron bashi da mutunci ko ka'dan ya tisa yarinya da tijara iri iri, tsoronsa take ji kamar me". Yaya ta ce "To indai ba zaluntarta ya ke yi ba ina ruwanka? Ita ba ta ce ta gaji ba, sai kai ne zaka ce ta gaji? To tsakanin mace da miji sai Allah ba abin mamaki bane Halimatu ta yi maka tustu akan wannan maganar. Bashi matarsa kawai, ha'kuri zamu yi da Sadik ai, mu ci gaba da yi masa addu'a. Na kuma tabbatar karfin addu'ar ce ta sanya ya tsaya a iya hakan ma". Abba ya yi shiru alamun bai gamsu ba. Yayin da Gudale yake jin salama na shigarsa tunda Yaya bata zafafa ba dole Abba ya ha'kura. Sanin halin Abba da Yaya ta yi na kaifi daya ne ya sanya ta ce "Alhaji yi hakuri na sani ranka ya baci sosai, amma tunda har ya je ya dauko ni, ya gamsu na isa da kai, to yi masa afuwa ya shiga rigata". Sai lokacin Abba ya ce "Rabu da shi! Yanzun ma na sani ina bashi ita zai tisa ta a gaba da tijarar ta kawo kararsa, sannan nifa tunda cutarsa na yi na bashi ita, to lah shakka sai na janye cutarwar nan". Da azama Gudale ya ce "Na rantse Abba ba zan tada maganar ba. Ko uffan ba zan cewa Guduyo akan wannan maganar ba". Yaya ta nisa ta sauke ajiyar zuciya ta ce "Bana son na matsaka maka ne Alhaji! Saboda na sani duk abin da zaka yi babu son zuciya a ciki. Amma zan so ace ka ha'kura ni ce shaida idan ya kuma fa'din hakan ko ya yi abind da ya saba ka'ida ba zan shiga cikin hukuncinka ba. Amma yanzu ka bashi matarsa tunda yana son ta". Wata irin ajiyar zuciya ta kwacewa Gudale ta farin ciki. Amma sai ya ji Abba yana cewa "Ba zata koma ba, sai ya biya ni, komai da na yi masa a harkar auren, zan zauna na yi lissafi. Gida dai da mota na bar masa halak malak. Amma tunda ga kan lefe har hidimar abinci da sallamar amarya da kawayenta , da duk wata hidimar da na yi sai ya dawo mini da ku'dina. Idan ya dawo mini da su zan gamsu ba dole na yi masa ba, yana son ta. Sannan ba maganar na cuce shi. Yaya ta ce "Shikenan zai kawo abin da zai iya, amma kaima kasan irin kudin da ka narkar bai isa samunsu ba." Cikin fishi Abba ya ce "ai kuwa sai ya nemo su, ko zai shekara goma ne. Sannan na harmata masa ya yi bashi, ko ya je ya yi ro'ko, ko ya tisa Yan uwansa a gaba su bashi." Ya zuba masa ido sosai. Ya ce " Wallahi matu'kar wata ta tallafa maka a cikin su, ko ka yi bashi ba zan saurareka ba, idan kuma ka yi mini karya ko zamba Ubangiji zai ganar da ni". Tashin hankali sosai a tare da Gudalen Ummah. Ko iya ku'din lefe aka ce ya dawo da su ina zai iya samo wadannan milyoyin? Sannan uban shanu da raguna da aka dinga gasawa a aurensa kadai ina zai iya biyan ku'dinsu da albashinsa, bare a ha'do da sauran hidimomi? Zufar da ta daina keto masa, ta dawo tana yanko masa fiye da ta farko. Murya babu amo sosai ya ce "Abba ina zan samo wadannan kudaden saboda Allah? Gashi ka ce kada na tambayi kowa, ban da haka da ba za'a dauki lokaci mai yawa ba, zan kawo maka tunda 'kararrawa zan ka'da musu kowacce dole ta fito da ku'di da gwalagwalai ta bani". A lalace Abba ya ce "saboda kai ne Gudalensu ko? Matan dai sune madogararku daga kai har uwar taka. To Billahillazi duk wacce ka je ta baka ku'di ban yafe ba". Gudale ya fara fusata domin ya tsani ace Yan uwansa mata sun fi shi amfani. Ya kalli Yaya da ta yi sukuri ya ce "Yi hakuri Yaya! Ni na janyo miki wannan 'bacin ran. Ni nasan zafin da ake ji idan ka bawa na 'kasanka umarni ya bijire. Na kuma rayu a gidan nan ne cikin ba'kin cikin fikon da kowa ya yi mini. Guduyo kawai na girma! Komai za'a yi mini, duk gaskiyata Abba ya kan ce na yi ha'kuri ai ni ne 'karamin su. Hatta Ashiru na ki, zai zo har gidan nan ya ci mutuncina, amma 'koluluwar abin da Abba zai ce Yayanka ne ai. Dan haka dole ka yi hakuri da su tunda sun girme ka. Haka idan muna rikici da Sakina ita zai bawa gaskiya ya ce ita ce Babba dole na yi mata biyayya. Har na dauka wajibi ne na 'kasa ya yiwa na samansa biyayya". Abba ya ka'du da kalaman Sadik da 'karara yana yi ne dan ya tunzura Yaya ta ga bekensa, ta yi fishi da shi. Kafin ya yi magana ya ji Sadik din Ya sake cewa "zan ha'do iya abin da zan iya samu, tunda ni ban ce a yi mini biki irin na 'yan gata ba, alhalin ni ba gatan ne da ni ba." Ya mi'ke tare da sanya hannunsa ya 'daga Yaya cak. Ya ce "mu je na mayar da ke, ki yi ha'kuri, da wannan iyakar da aka nuna miki". Ai kuwa nan da nan Yaya ta fara share 'kwallah. Yayin da Abba ya harzuka ya mi'ke da nufin maka masa wani abin. Gudale ya fice da sauri ya na cewa "A to ai gaskiya ne, kullum sai ka ce ita din ba yayarku ba ce kawai, Uwace ta saosai. Amma an kasa bari na shiga rigarta." Abba ya dinga bawa Yaya ha'kuri yana cewa "Kar ki bari maganarsa ta shige ki, domin so yake ya hada mini rikici, ya mini sanadin rashin walwala tunda ya sani, ba abin da yake hana ni sukuni irin ace kina cikin damuwa ko matsala. Ba sai na ce miki komai ba akan fitinarsa. Idan ban dauki mataki ba. Zai cutar da yarinyar ne sosai, kin sani kuma ko kullum dukanta yake yi ubanta ba zai nuna ya sani ba, bare ya tanka. Amma yau da gobe ba abin da ba zata zo da shi ba. Ina jin tsoron kada ya hargitsa mana zumuncinmu da babu rikita rikitar zamani a cikinsa." Yaya ta gamsu sosai amma sai ta ce "To amma idan aka dan tura ka'dan ka bashi matarsa. Ba zai iya kawo wadannan kudaden ba." Abba ya ce "Na sani! So nake na fahimtar da shi irin alfarmomin da muka yi masa Ni da Halimatu. Ina son ya gane ba shi yake yi mana alfarma ba. Mune muka yi masa." Ya saka hannu ya mayar da ita ta zauna ya ce "zauna a kawo abin kari mu karya sai na kai ki da kaina". Sai da suka karya cikin nutsuwa da farin-cikin, suna ta hirarsu da ta shafe su, cikin hikimar mace kuma sai hannunka mai sanda take yiwa Abba akan yara masu dabi'ar Sadik ba abin da yake tasiri akan su irin addu'a. Abba yana tafiya kai Yaya gidanta. Gudale ya shigo gidan. Wajen Umma ya zauna, ya ce "Umma! Abba ya ce na biya shi duk ku'di da ya kashe a aurena. Ya kuma gindaya mini sharadin bai yarda na yi bashi, ko ro'ko ba. Ba kuma zai bani matata ba har sai na ha'do masa kudinsa." A lalace ta kalle shi ta ce "To ka sakar masa ita mana ka huta wa ranka." Ya bata rai ya ce "Ba yanzu ba Umma! Bana so idan na saketa na yi nadama. Ta yi tsuka ta ce "Na rasa gane wannan jarabar! Idan na ce kana sonta ka musa mini, banda haka, auren da muke neman sanadinsa me zai hana ba zaka sallama shi ba, tunda ga dalili an samu mai 'karfi. Ya fesar da zazzafar ajiyar zuciya ya ce "Umma so nake sai ta haihu tukun, bai kamata a saketa da 'karamin ciki ba, ko bana sonta ya kamata na yi mata adalci. Tsaki mai tsananin gaske ta ja tana jin takaicin Halimatu da uwarta na sake tsananta a zuciyarta, domin ta gane Gudalenta yana son Halima da gaske, wanda ta yi imanin ba soyayyar gaskiya ba ce. Tausayin kanta da Gudalenta ya yi matu'kar kamata. Tabbas wannan gayya Safiya ta yi mata da tilon danta. A hankali ta mike ta yi cikin bedroom dinta dan ta yi walaha, ta kuma bashi damar shiga dakin Halimatu tunda ta lura hankalinsa na can. Ai kuwa tamkar jira yake ta kauce ya nufi dakin da take da hanzarinsa. ***�? *Kina fama da infection mai naci?* *Kina fama da bushewsr rashin ni'ima?* *Kina fama da rikicin al'ada?* *Kuna fama da ulcer?* *Shin kin ta'ba jarraba maganin GHT?* *Shin kinsan suna da jakadu da yawa?* *Bari na fa'da miki jakadiyarsu da zata fa'da miki aikin kowanne magani, ba kuma zata baki Wanda ba zai karbe ki ba* *Sannan tana da saukakawa wajen farashi* *Tuntu'bi Faseelat a wannan lambar 07039269902 dan samun naki nau'in supplement din, Kinga dai yadda Iya Basiru ta yi tsaye a zuciyar Mk* *Idan kina da kyau ki Kara da wanka Haijya* Ina zaune a 'kasa, na jingina da gadon, Kamar jifa ya shigo. Farin ciki ya mamaye ni. Na debi rawar jiki da murya na ce "Sa sa sannu da zuwa Yaya Gudale! Kasan da 'kyar na iya hakuri har ka shigo, tamkar na fito na same ka". Ya watso mini wani lalataccen kallo. Ya ce "Makaryaciya kawai. Ai zaki san kin yaudare ni. Zan yi komai dan ki dawo gareni. Zaki san kin 'ki bin umarnina, zaki san kin amince da zaman nan, domin lissafin kwanakinki nake yi anan, wlh duk bashin da kike ci mini sai na fanshe su". Na tsinci kaina da yin murmushi da kuma murguda masa baki. Ai nan da nan ya iso gareni ya zauna a kasan shima, ya janyo ni jikinsa ya rungume sosai ya dinga sakin ajiyar zuciya. Ina kuma jin yadda zuciyarsa take harba wa. Tsawon lokaci muna hakan, muna samun nutsuwa a gangar jikinmu gaba'daya. Murya a dashe ya ce "I really need you Guduyo". Da'di ya kama ni, amma sai na waske da cewa "Nima hakan sai dai kuma dokar likita". Haka kawai na fa'da ya zabura ya sake ni ya ce "likita Allah ne? Ke dai kawai ki ce mini an hure miki kunne. Banda haka har zan ce ga yadda nake so ki kawo mini zance marar tushe? Ina ce dai likitan ba shi da ikon cewa ga abin da zai faru, domin sanin gaibu sai Allah.". Na kasa cewa komai. A dalilin al'amarin da Gudale yake neman yi a cikin gidansu ya firgita ni. Na ri'ke rigata na hana shi cire wa. Ya gallah mini harara. Ya ce "Zaki bijire mini ne? Ba ki ga 'ko'karina ba? Kin fi son na fita na nema a waje ko? Na girgiza kai domin idan har na bu'de baki kuka zan saka masa. Bai kula da kukana ba, bare ya fasa. Ya dinga ya mutsani, a ki'dime, yadda yake yi din ya tabbatar mini a matu'kar matse yake, sai dai ba zan bari ayi wannan rashin kunyar da ni ba. A gidan Abba da Umma bs. Ai kuwa cikin sa'a muka ji dawowar Abba. Nan da nan Gudale ya sake ni ya fara saisaita tunaninsa da rigar jikinsa. Yayin da ni kuma na janyo hijabi na saka, a dalilin na sani zai shigo ya gan ni. Murya a dakushe ya ce "Ina wayar ki?" Ba boye boye na ce "Tana wajen Abba" Ya girgiza kai ya ce "Zan siyo miki 'karama ki ri'ke a hannunki. Bana son na kira ki, na kasa samun ki sai na ji tamkar zan rusa ihu ne. A hankali na ce "Da ka barta kada Abba ya ce "Ina na samu waya?" Ya yi tsaki ya ce wai ke dal'kiyar ina ce? Ace babu sirri tsakaninki da mijinki? Guduyo ki kiyayi bata mini rai a cikin wannan halin da nake ciki". Na sassauta na ce "Allah ya baka ha'kuri". Dai dai nan Abba ya turo kofar dakin ya shigo. Ya yi turus ganin Gudale a zaune dirshan sannan yanayinsa ka'dai ya isa ya fahimtar da shi halin da yake ciki. Na shiga gaishe shi a Kunya ce. Ya amsa mini babu walwala kamar yadda ya saba yi mini a tsukun nan a dalilin na ki sakewa kamar yadda ya ke so. Ya kalli Gudale da ya ha'de girar sama da ta 'kasa. Shima ya sake daure fuska sosai ya ce "Sadik zo ka fice mini, na haramta maka shigo mini cikin gidan nan, har sai ka shirya. Ya mi'ke yana ha'da hanya na sani zuciyarsa tamkar ta yi bindiga. Yayin da ni kuma hawaye ya fara zubo mini. Yana ficewa Abba ya rufa masa baya ba tare da ya rufo mini kofar ba. Ina Jin Yaya Gudale yana cewa "Dan Allah Abba! Kar ka bari dukkan raunina ya bayyana, idan maganganun da na fa'da a gaban Yaya ne suka sake tunzura ka, dan Allah na yi tuba, na janye su, 'karya nake yi, a mini aikin gafara yadda aka saba. Ka hanata koma wa, yanzu kuma ka ce kar na shigo maka gida alhalin iyalina suna cikin gidan. Ni yanzu idan ban ji motsin yadda *Wakili* yake ba, tashin hankalin yawa zai yi mini". "Waye wakili kuma?" Abba ya tambaya cikin mamaki. "Wakilinka mana Abba! To abin cikin kwai dinka, ma'ana ajiyar dake cikin Guduyo". Abba ya rasa me zai ce masa sai kawai ya yi tsaki ya ce "To kuma idan Magajiya ce fa?" "Abba tabbas na sani uwa mai daraja ce amma a wannan sa'darar magajinka nake so ya fara iso wa. Ta yadda zan sanya masa sunanka. Domin so nake daga siffa har halayyarka ya yi wuf da su. Amma ba zan so idan an yi masa kuskure ya ce sai an dawo masa da abin da ya yi na alheri da neman yardar Mahallicci ba. Abba idan ba zan rufe ka ba. Wato Ubangiji ya maka baiwa da tarin falaloli. Kana da nagarta! Na yarda ban kyautata ba, amma ka wuce ka ce na biya ka hidimar da ka yi mini, Allah ya kewaye ka da ni'imomi daban daban. A duba Halin da nake ciki a yi mini sassauci, zan yiwa bakina linzami wa Billahillazi subutul kalam na yi". "Sai fa ka dawo mini da kuda'dena duk siyasarka, dai-dai da ku'din sadaki sai ka dawo mini da shi." Takaici ya ciyo Gudale ya ce "To shikenan Abba! Amma ka bani lambar wayar wanda ka bawa ya mini waliccin auren." Akan wanne dalilin? Me yasa baka tambayar lambar dan ka gaishe shi ba sai yanzu?" Ni kawia fa'da masa zan yi ya turo ku'din waliccin da ya yi mini, tunda zan biya9 sadakin aurena to kamata ya yi na na waklici kaina da kaina, dan haka sai ya turo mini ku'din da zan rage maka bashi. Abba ya zuba masa ido sosai ya kasa yin magana. Ya ce "kome zaka yi dai ka je ka yi, riba kuma ba zaka ci ta ba. Na kuma fa'da maka kada ka sake shigo mini gida wallahi! Matu'kar ba kudin nan ka samo ba, bana bu'katarka a cikinsa, idan kuma ka kafe zan dau mataki akan ka da wadda zata barka ka shigo mini gida". Ya fice cikin sauri yana cewa "Na dai roki arzikin a mini gafara. Amma dole sai an zubar mini da 'kimata ta namiji a idon matata". "Allah ya shirye ka Sadik" Abba ya furta cikin wani irin yanayi. Kwanaki biyar suka shude ba tare da mun ji ko da murya juna ni da Gudale ba. Idan na ce ba a cikin damuwa nake ba na yi 'karya, mussaman da ya kasance ko gaisuwata da kyar Umma take amsawa. Bani da matsalar komai amma babu sukunin zuciya, babu kuma walwala, tunda Abba ne kawai yake kula ni. Rannan sai ga Sakina kamar jifa. Ina ganinta na fara kuka, ita kuma ta dinga dariya tana cewa "Halimatu tattbara". Dariya ta kama ni, ina dariyar hawaye na zubar mini, ina kuma cewa "Ni wlh na gaji tafiya dakina zan yi" Ta make kafa'da alamun ko oho ta ce "Ai na gane ki kuma. Duk wani iyashegen mijinki kin kwashe su tsaf, ba wanda kike yiwa iskanci sai ni. Yanzu ma tashi ki tafi". Na zum'bura baki ina kunkunin ina cewa "Abar ni kawai". Kafin ta yi magana wayarta ta dauki kuwwa. Har ta katse bata dauka ba, sai da aka da aka 'kira sau uku sannan ta dauka a yangance ta kunna hands free ta ce "Na rantse maka Na Moriki ka uzzira mini haba". Ina Jin yadda ya marairaice ya ce haba Anti Sakina! Ina ce dai dazu ma sai da na yi ta ro'kon ki, dan Allah ki daina yi mini hakan bana jin da'di, kin san dai bani da kamar ki ko?". Ta yi murmushi ta ce "Haka fa! To fa'da mini ni da Guduyo wacece a gaba?" Sai kuma ya bu'de murya ya ce "wacce irin tambaya ce ne wannan? Kinsan dai kowa da matsayinsa. Ina ce yanzu d'a zata haifa miki Sakina? Kawai kowa da matsayinsa, dukkan ku jinina ne". Sosai dariya ta kwace wa Sakina ta ce "Na Moriki manyan duniya". Ya saki ajiyar zuciya ya ce "Sakina zaki mini taimakon nan, ko ba zaki yi mini ba?" Ta ce "Sakina ko?" "Anti Sakina na ce fa" ya fa'da a gajiye. "Zan bata mana yanzun haka ina gidan ma". Ya sake kaurara murya ya ce "Amma ba a dakinta kike ba yanzun?" "A a ina kicin ne" Yauwa Anti! Yadda na fa'da miki hakan zaki yi kin ji my dear sister. Kawai ki kira ni ki ce ga Guduyo ku gaisa, sai ki 'dan bamu space please and please Yayar auta". "Amma ka yi al'kawarin ka daina mini rashin kunya ko?" Da sauri ya ce "Dama kinsan ai ke ta daban ce a wajena kawai dai Allah ya sanya yadda muka makwabci juna a wajen haihuwa, Allah yasa a aljannah ma hakan ne". A sanyaye ta ce "Ameen Namorikina". Sai ta kashe wayar ina kallon yadda take wani irin farin ciki mai fitowa daga kasan zuciya. Ba'a dauki lokaci mai yawa ba, ta kira shi din, ta bani wayar. Ta fice zuwa wajen Ummah. Na sanya wayar a kunnena, na yi masa sallama. Ya amsa da wata irin murya da ni zan fahimci manufarta kawai. Ya lankwashe harshe ya ce "Guduyo tausayinki nake ji, bana son na yi miki sharing 'dina da wata, amma duk an rufe ido an ki gane halin da nake ciki. Kuma abin takaicin ma wai har da ke za'a ha'da kai, yanzun sai ki bada gudunmawar jefa ni a cikin tasku?" Murya na rawa na ce kasan dai abin ne yafi karfina. Nima ba yadda zan yi ne. Ba dan Abba bane a cikin maganar ai da sai dai a ga lefina a banza." Ya sake kashe murya ya dinga fado gunduma gunduman kalmomi masu nauyin bayyana wa, yayin da suke shiga jikina suna tasiri, soyayyarsa tana sake tunbatsa a zuciyata. Kewarsa ta kewaye mini gangar jikina. Na dinga murmushi ina shure shure akan gadon saboda yadda muryarsa da manyan kalamansa suka kidima ni, suka sanya ni cikin bege mai yawa. A kasalance ya ce "*Hala*" Tsigar jikin ta tashi, harshena ya yi mini nauyi na kasa amsa wa. Bai jira amsar tawa ba ya ce "Kar ki bada kofar da za'a sanya miki shubuha a kaina. Kin dai san da bana son na rayu da ke ba zan baki ajiyar Babina ba ko?" Da kyar na ce "Eh" Ya ce "To ki cigaba da kallona a matsayin da kika bani, kar ki yadda a shigo tsakaninmu. Ke din matata ce da Ubangiji ya saka aka bani ke da karfin tuwo ba dan ana so a bani ba. Sannan ke din Allah ya za'ba ki zamewa 'yayana uwa. Kinsan kuma na gode Allah ko?" Na yi shiru! Domin ban fahimce shi ba. Gane hakan da ya yi sai ya ce "Da ban gode wa Allah ba ai ba zan damu da ke ba, yanzu menene bana miki Guduyo? Har a cinya nake dora ki ko?" Na ce "Eh! "Yauwa to ko goyon ma da kike son na dinga yi miki idan kin haihu zan fara gwadawa kin ji. Sannan kuma ba ni, ba kallon yan mata. Ai na san ba kya so ko?" Da sauri na daga kai, sai kuma na ce "Eh" . Ya numfasa ya ce "To duk wanda zai ce miki bana son ki, ko kin fi sona, ba gaskiya ya fa'da ba, domin dai kinsan yadda nake lashe ki in and out, ai idan bana son ki ba zan iya yin hakan ba, tunda kinsan ina da 'kyan-kyami" Ai kuwa na saki baki na ce "Ai nasan kana sona sosai, na sani, shiyasa nake kallon Maman Nana a kife da ta dame ni da mitar son da nake maka yayi yawa kuma bani da aji akan ka, nan gaba zaka nuna mini halin maza. Yaya Al'amin ma jiya da ya shigo duba ni har da cewa idan ban yiwa Abba biyayya akan hukuncinsa ba, sadda zaka zo ka juya mini baya na kuka da kaina. Dan kuwa baza su sake barin Abba ya shiga shirgina ba". Ya fesar da ajiyar zuciya mai nauyi ya ce "Al'amin da Sakina sune barazana a rayuwata! Wai ace wadanda ka bawa so da yarda, sune suke cin dunduniyarka. Allahu ya yi musu irin abin da suke nufi da ni. Duk kuma kutunguilarsu sai dai su buga su barmu tare, azzalaumai masu yiwa soyayya illah". A sanyaye na ce "Amma dai ai suna son ka fa". Ya kuwa dako mini tsawa ya ce "A a 'kaunata suke yi, ba so ba. Ina so ga wanda yake son ya shiga gidanka ya kafa maka fandishon fitina da tashin hankali?" Na yi shiru na kasa bashi amsa. Ya nisa ya ce "Idan kina ri'ke maganganunsu watarana zaki wayi gari ne ki ga mun yiwa juna tazara mai yawa, domin idan suka cigaba da hure miki kunne zan koma gefe ne na bar ki da su, ni kuma na yi aurena, na samo wacce yan'uwanta baza su saka ta bijire mini ba, ina ce shikenan?" Nan da nan idona ya ciko da hawaye ina cewa "To na yarda da su ne? Ai ni kallon su kawai nake yi." "To shikenan ya isa" ya fa'da da sigar rarrashi. Ya cigaba da ratattabo maganganun da suke tasiri a zuciyar mace mussaman ace mijine yake wannan maganganun masu gigitar wa. Na dinga mamakin yadda ya iya fa'din irin wadannan kalmomin tamkar wanda ya yi ilimi a fannin. Bai bar ni ba, sai da ya tabbatar ya mini sabis din da zan iya yin fito na fito da duk wanda ya nemi shiga tsakaninmu. ****** *Asibitin Malam* Ashir na kewaye kawai sai ganin Sadik ya yi cikin sahun wadanda ake yiwa gwaji idan za'a ciri k'odarsu a ki'dime ya 'karasa wajensa yana tambayar ba'asi. Amma Sadik ya 'ki kula shi bare ya bashi amsa. Ashir na tsaye aka gama duk wani cike cike wani zabgegen Alhaji sai kaffa kaffa yake yi da Sadik din, alamun ririta shi yake yi. Sai da suka fito daga wajen sannan Ashir ya tari gabansu, ya tambayi Alhaji menene hadinsa da 'dan-uwansa. Sai lokacin Sadik ya bu'de baki ya ce " Ashiru bana shiga harkarka! Ka fita a tawa, ban sanka ba, bani da hadi da kai, akan me zaka nemi shiga al'amarina?" Alhaji ya kalli Ashir ya ce "ka san shi ne?" Da sauri ya ce "Wallahi kanina ne first cousins muke". Alhaji ya kalli Sadik ya ce "Garbati ka ce mini baka da kowa anan kai mutumin 'Kasar Kamaru ne?" Nan da nan ya diririce ya ce "eh hakane kuma gaskiyar kenan". Zufa ta dinga karyowa Ashir ya dinga hasashen wanne irin abu Sadik yake 'kullawa haka?" Nan da nan ya fito da waya ya kira Sakina, ya kwatanta mata inda suke tsaye, ya rufe maganar da cewa "ki gaggauta dan Allah". Aikuwa ba'a jima sosai ba ta iso cikin fargabar me zata ga ni. Ganinsa da Sadik sai ta samu nutsuwa ta sani dai fa'dansu ne da baya 'karewa. Ganinta kawai ya tabbatar wa Alhaji ita din jinin Garbati ce kamar yadda Gudale ya fa'da masa sunansa kenan. Nan da nan Gudale ya fara sababi kome za'a yi basu isa hana shi abin da yayi niyya ba, tunda an ri'ke masa mata duk sun zuba ido an ki a taimake shi. Ina zai samo uban milyoyin da aka ce sai ya kawo? Ya kalli Sakina cikin ido ya ce "Ni ina da imani, Ni mutumin kirki ne, Ni kuma mai tsoron kwanciyar kabari ne, kin san da wannan. Dan haka ba zan dauki makami na fara tare hanya, ko na fara sace Bani adam ba, dan haka na zabi na sayarwa mabu'kata kodata d'aya na karbo Guduyo. Wata'kila idan na yi hakan a daina nuna mini iko akan ikon da shari'a ta bani akan aurena" *Na ce ba kinsan wani hadi da ake yi wa asalin man ridi da kwakwa da ba'a samun original din su sai a wasu kebantaccun jahohi?* *kina fama da matsalar cinyewar gashi ko kuma rashin tsayinsa?*. *Kina neman ha'din da da zai sanya fatarki laushi da sulbi, kuma cikin saussaukan farashi? Tuntu'bi m lambar dan samun naki cikin sau'ki. Kaya mai inganci shi yake siyar da kansa.* *Sister Zainab 08039315577.* # Team Gudale # Team Guduyo # Surayya Dee✍️ # Ana tare. 🤝 2/8/23, 10:25 - Buhainat: *Ummu Muhammad collections* *Tana sayar da dukkan nau'in sutura masu kyau zababbu kuma masu sau'kin farashi* *Tana sayar da takalma da jaka masu kyau* *Tana ha'da lefe* *Tana ha'da kayan haihuwa* *Tana sayar da Data* *Tana yin adashe, Kuma fasihiyar Tela ce* *Tuntube ta a wannan lambar 08063358662* *Siyan na gari aka ce maida ku'di gida*. *SDK* *61-62* Jikin Sakina ya fara rawa, a ki'dime ta ce "Na shiga uku ni Sakinatu! Na Moriki wanne irin bahago ne kai? Abin da zaka yiwa Umma kenan? Ka zo ka sayar da 'kodarka? Sadik 'koda fa? Jikinsa ya yi sanyi ganin yadda Sakina ta rikice to Ummansa fa? Kunyar duniya ta rufar masa, bai yi tunanin ba shi ka'dai yake da hakkin kansa da kansa ba. Ya sani kuma matu'kar Umma ta sani ba zata bar shi ya sai da 'kodarsa ba. Ya tabbatar ko ita ce take bu'katar ayi mata dashen 'kodar ba zata so a ta'ba tasa ba, saboda tsananin yadda take sonsa, take kuma fatan ya rayu cikin farin-ciki da 'koshin lafiya. Yau ina zaisa kansa idan ta ji akan Guduyo zai sayar da kodarsa? Wai wanne irin abin ne ya same shi ne akan Guduyo? Shin sone ko kuwa da gaske gigita shi ake yi dan a nesanta shi da uwarsa? Kamar yadda take fa'da masa a kullum. Ya yi tsam a ransa tabbas ba yanzu ya fara jin abu akan Guduyo ba. Amma na yanzu ya fi karfi. Sai dai kuma bai ta'ba jin akwai wanda yafi Umma a duniyarsa ba, har Abba kuwa. Da ana yi masa wani abin ai da ya ji wannan son da matsayinta ya yi rauni. Ya fesar da ajiyar zuciya. Guiwarsa ta yi sanyi ganin Sakina tana share 'kwallah, yayin da idon Ashir ya ka'da sosai, ya hango soyayyarsa a cikin idon Ashir, amma yana tuna ai ya so Guduyo, da irin wula'kanta shi da yake sai ya dauke fuskarsa a kansa yana jin kishinsa na taso masa kwarai da gaske. Alhaji ya ce "su sami wuri su zauna ayi maganar a tsanake". Sakina ta ce "Ai gida zasu je ayi maganar a gaban mahaifinsu." Haka Ashir ya yi insisting sai an je gaban Abba. Yayin da Gudale ya nemi bijirewa shiga mota, ba zato ya ji Sakina ta dauke shi da mari. Ya zuba mata ido sosai yana dafe da fuskarsa, ransa in sun kai dubu sun baci. Kafin ya yi magana Ashir ya ce "ko ka shiga ka mutunta kanka, ko kuma Wallahi na shigar da kai a wula'kance, zabi na gareka". Kan dole ya shiga motar Alhaji suka dunguma. Basu zame ko ina ba sai falon Abba! Cikin ikon Allah duk suna falon daga Abban, har Yayar 'Kwalli da kuma Baba. Ba kuma komai ya ha'da su ba illah bikon Halimatu da suka je yiwa Gudale. Ganinsu a hargitse ga kuma bakuwar fuska a tare da su ya sanya suka shiga wasi-wasi. Amma cikin juriya Abba ya shiga marabtar Alhajin da ba bai gane shi ba. Cikin rawar murya Sakina ta ce "Ga Sadik nan Ashir ya gano aika-aikar da ya yi nufin yi. 'kodarsa ya sanya a kasuwa, shine wannan Alhajin zai siya ayi wa 'dansa dashe". Gaba'daya dakin ya dauki salati da hailala. Tsananin ki'dimar da Abba ya yi ya kasa cewa uffan. Cikin karfin hali Baba ya mayar da hankalinsa akan bakon. Ya ce "Alhaji ya aka yi ka yarda da wannan cinikin alhalin baka ga kowa nasa ba?" Ya numfasa ya ce "na bincike shi, tunda akwai inda sai magabatan mutum sun sanya hannu kafin ayi aikin mussaman iyaye ko matarsa. Sai ya ce mini shi din maraya ne, bashi da kowa kuma sunansa *Garbati Habu Shaho * zai bani dan Allah, dan kuma ya samu ku'din da zai dinga juyawa yana samun abin rufin asiri. Duk da hakan ban yarda ba, sai da muka je kotu, ya yi wannan maganar, sannan muka je wajen yan sanda aka yi statement dinsa, duk ba dan komai ba sai dan tsoron abin da zai je ya zo". Dakin ya yi tsit banda kukan Yaya da Umma ba abin da yake tashi a dalilin Sakina ta 'kira Umma dan ta ji ka sassabar da autanta ya yi akan matar da take fatan ya sake ta. Yayin da Gudale ya yi 'kasa da kansa yana jin kunyar mahaifiyarsa tana katantawa da shi. Da matu'kar rauni sosai Abba ya cewa Alhajin "nawa ka bashi?" Ya girgiza kai ya ce "Milyan arba'in muka yi zan bashi, ban kuma kai ga bashin ba. Dama gobe ne zan yi masa transfer, kawai dubu dari biyar na bashi dan ya dinga cin abinci mai kyau, da fruits ta yadda aikin zai tafi cikin Nasara". Kafin Abba ya yi magana Umma ta ce "Wallahi karya yake yi maka ba maraya bane, dan gata ne na bugawa a jarida. Ga ubansa nan, ga ni uwarsa, wadannan kuma duk iyayen sa ne, dan haka ciniki ba zai yiwu ba, bamu yarda ba, ba kuma zamu amince masa ba". Ta karasa cikin rishin kuka. Baba ya ce"Bani lambar asusun na dawo maka da 'kudinka, tunda aiki ba zai yiwu ba, ka karbi ku'din da ka bashi kawai". Alhaji ya ce "Na lura yana cikin damuwa ne yaron! Na ji dazu yana fa'din a ina zai samo milyoyin da aka ce sai ya kawo kafin a bashi Gunduma ce ko menene oho. Na dai fahimci tamkar matarsa aka ri'ke masa aka gindaya masa shara'di mai tsauri. Ina ro'konku tunda har tunaninsa ya bashi ya yi irin wannan akan yarinyar to ku saka hannu, ku tallafa masa a dawo masa da ita kawai. Idan kuma ku'din da zai biya bai wuce milyan biyar ba ni zan biya masa domin na gane ita ce nutsuwarsa, idan ba dawo wa hannunsa ta yi ba, wata'kila ya je ya jefa kansa a hanyar 'batan ci". Aka dinga yi masa godiya saboda fahimtar da ya yi da kuma yadda ya yarda aka rabu cikin mutuntuntawa tunda dubu dari biyar din da ya bawa Gudale ya ce ya bar masa halak malak. Baba ne ya raka Alhajin har wajen motarsa sannan suka yi musabaha suka rabu, Baba yana ta sake godiya, tare da yiwa 'dansa addu'ar samun lafiya. Fa'da tamkar a rufe Gudale da duka haka aka rufar masa kowa ya fa'di son ransa. Abin kaicon kuma har da Ashir a cikin masu fa'dan. A take Yaya ta zartar da hukuncin lallai Abba ya yi hakuri ya bashi matarsa kada a wayi gari kuma aji zai sa idonsa 'daya a kasuwa. Umma kuwa zuciyarta tamkar ta yi bindiga haka take ji. A ranar ta sake gane zahirin 'kiyayyar da take yi wa Safiyya domin ace a sanadin 'yarta Gudalenta zai salwantar da 'kodarsa ta tabbatar son da yake yiwa Guduyonsa ya wuce misali. Ya wuce ya tankwa'bu cikin ruwan sanyi, tabdi jam. Duk yadda yake jaddada mata aurensa da Halimatu ba rayayye bane. Ashe shaidanun mutanen nan sun shiga sun fita sun cusa masa soyayyar da tafi kama da sha-sha-shau! Tabbas nan gaba ka'dan zasu saka almakashin datse alaka su raba ta da shi, bata haufi akan hakan. Bakin cikin ya yunkoro mata, ta kasa sarrafa fishinta kawai sai ta barke da kuka mai tsananin gaske. Jikin kowa ya sake yin sanyi, domin su din shaidu ne na yadda bata ha'da al'amarin Gudale da komai a duniyarta. Sai gashi ya tafi zai yiwa kansa illah, ba tare da neman shawararta ba. Yayin da oga Gudale yake gefe yana Jin guiltiness yana kama shi. Kunyar Umma kawai ta hana shi motsa kwanjinsa, amma ba dan ita ba, da ba zai risina ba, zai tabbatar wa Abba zai iya yin komai ban da zubar da jinin mumini, dan ya samu kudin da zai fanshi Guduyo. Idan kuma ya dawo masa da kudadensa shi kuma ya kudire ba za'a sake shigar masa harkar gidansa ba. Akan me za'a nemi a dinga mulkar aurensa? Shi ba Baban Yara bane, da komai zai yi a gidansa sai abin da Abba ya ce ko ya zartar. So yake a barshi a mai cikakken iko a gidansa, tunda an gamsu ya isa aure, an yi masa, ga kuma matar da ciki ai kuwa an san ya girma, dan haka a barshi kawai da gidansa. Ba'a kula da cewa yanzun ya saba da mace ba, ba'a lura da cewa ko ba zai iya ri'ke kansa idan babu ita ba, sai kawai aka rufe ido ake tozarta shi, dan haka zai yi komai dan ya samo kudaden da Abba ya wula'kanta shi saboda su. Idan kuma ya dawo da su din to kuwa ba mahalukin da zai masa iko a gidansa tunda shi ya yi wa kansa komai. Idan kuma bai samu ku'din ba to zai na'de kafar wando ne kawai ya yi fatali da dokar Abba na haramata masa shiga gidansa, dan kuwa a dakin da Guduyo take zai dawo da kwana ko me za'a yi kuwa ba abin da zai fasa yi. Ko ya dinga kwana a dakin Abba a tsakiyarsu, tunda ana mua'amalantar sa tamkar yaro 'dan 'karami to kuwa zai koma tamkar mai shan nono, ba shikenan ba. Gyaran murya Abba ya yi ya ce "Yaya tunda kin karaya da iyashegensa zan bashi ita, saboda ke dan idan ta nine sai dai ya sayar ba damuwa ta ba ce. Amma kune shaidu Billahillazi duk ranar da ya kuma cewa "Na cuce shi da na bashi aurenta to lah shakka babu maganar ya cigaba da zama da ita." Yaya ta ce "Ba wannan maganar ai, domin yanzu ya gane komai, ya girma, gashi yana shirin zama uba." Da murya marar amo Gudale ya ce "Ni nasan na girma Yaya! Amma shi Abba so yake sai ta raina ni. So yake ta ga dukkan raunina, ta gane abin da ke kirjina ta yadda ba zan iya sarrafata ba. Baban Gusau ya fahimce ni, kwarai da gaske a kullum yana nuna mini miji ne yake da cikakken iko akan aurensa. Dan haka Baba ina baka wasiya idan mutuwa ta zo mini kafin zuwan *wakili* to na fa'da maka sunan Baban Gusau zai amsa. Karma a mayar masa da sunana a zaci sunan Abban Sakina ne". Sai lokacin Abba ya ce "Wai kai kana son fa'da mini ka fasa mini takwara ko? Yo masu sunana nawa ne? They're uncountable. Abdallah ya yi mini, su Hafsatu da Ramla kusan kowa yana da ni. Dama kuma Baban Gusau din shine Babanka ai, Madallah da wannan karamcin. Kuma ba zaka bar nan ba sai ka fa'da mini dalilin jigina mini *Shaho* a sunana da ka yi. Ko hakan ya zama sanadin rasa aurenka dungurungum, idan ya so ka je ka sayar da kanka gaba'daya". Nan da nan raunin Gudale ya bayyana domin tashin hankalinsa Abba ya ce zai raba masa aure. "A sanyaye ya ce "Ni fa Abba ba da kai nake ba. Nima sunan nawa Abubakar ai, sannan na jingina Shaho ne a matsayin sunan kauyen mu a Kamaru". Da'kuwa Abba ya yi masa ya ce "Gidanku". Ganin Abba zai sake murdewa Yaya ta katse Abba da cewa "Ya isa haka Alhaji. Salati goma ga Annnabi(S.A.W). Sai da aka yi addu'a sannan ta ce "Na rufe wannan maganar haka nan. Ya gane, ya kuma 'karyata kansa, kuma kowa ya gane yana son matarsa magana ta kare." Tamkar wanda aka zaburi Gudale ya ce "Yanzu Yaya har Guduyo an bari ta gane ina son ta har haka?" Zan roki arzikinku kada a fallashe ni, bana son tonon silili, kada zancen 'kodar nan ya fita waje domin ba dan ita zan sayar ba, zan yi ne dan na sauke nauyin da aka ce sai na biya. Ya kalli Sakina da Ashir ya ce "idan na ji maganar nan a waje a tsakaninku ne, kuma zan iya shata layi da mutum". Ashir ya hassalo ya ce "gyara kalamanka, domin dai da Sister Sakina kake amma ba da ni ba, don kuwa ka tabbatar sai na fa'dawa kowa wannan shashacin naka, na fahimtar da mutane su fahimci 'Kifadi ne kawai da kai amma babu jarumta. Idan ka so ka sanya dutse a tsakaninmu ba wai shata layi kawai ba". Ai kuwa ya hassalo ya kalli Yaya ya ce "Yaya kina jin Ashirunki ko? Na rasa masifa irin tasa, na ce bana son ya shiga harkata, idan ina 'kaunar ko kallona Ashiru ya yi shege nake bare kuma ya yi mini magana. Yayin da takaici ya shake Ashir. Wato ya lura da isgili Sadik yake ce masa Ashiru, tunda kowa Ashir yake fa'di idan aka cire Abba. "Yi ha'kuri ka rabu da shi ka ji". Cewar Yaya ta fa'da cikin rarrashi. Kafin Sadik din ya ce wani abu Ashir ya yi fit ya ce "daina bashi baki Yaya! Dan Allah Garbati kada ka ha'kura! Do your worst. Wanda zai sayar da kodarsa akan wacce baya so dan tsabar asaranci". Ba'kin ciki ya turnike Gudale. Murya na rawa ya ce "Ya Allah! Ga Sakina, wa Ashir wa Al'amin, Allah sun fitine ni, sun ha'da kai sun uzzara mini, suna neman kai ni k'asa a cikin al'amarin da bai shafe su ba, Ubangiji a mini maganinsu, a yi kishina". Umma da takaicinsa ya kai mata ma'kura sosai ta ce "Shasha kawai! Wanda bai san me ya kamace shi ba, idan ka kuma bu'de bakinka sai na ce maka kaico" Da 'kyar aka gama zaman bayan Yaya ta tabbatar ba zata bar gidan ba sai ta mayar masa da Halimatu gidansa. Baban Yara dai bai ce komai ba illah nasiha da yake ta faman yiwa Sadik dan ya gane ya zauna da yan'uwansa lafiya. Ya kuma zama mai biyayya da ha'kuri a akan sha'anin rayuwar duniya. ********** Ina zaune kan gadon Yaya ta shigo tamkar jifa ta ce "sauko Halimatu! Tashi na mayar da ke dakinki, ki yi ta ha'kuri da Sadik, kowanne Dan Adam da yadda yake da kuma yadda tsarinsa yake. Sadik na cikin karkatattun mutane da ba straight suke ba, duk yadda kake da su kuma zasu rufe ido su yi maka cin Kashi. Wato dai halayyarsu ta yi dai dai da dabi'armu ta yadda *Sabo da kaza* baya hana mu yanka mi cinye tas. 'kara hakuri da shi, kalar tasa soyayyar kenan". Murya na 'dan rawa na ce "Ni fa Yaya bai mini komai ba, lafiya muke zaune, amma Abba ya jingine ni, ki zama shaida ban ce yana mini wani abin ba. Haka kawai an janyo mini rikici bayan ban ce ina da matsalar komai ba". Ai kuwa jikin Yaya ya yi sanyi, nan da nan ta gyra bakinta ta ce "Ai shi Sadik fahimtar sa ne ba'a yi ba, amma rikicinsa sai an ta'ba shi". Ai kuwa na ce "Ashe kin gano Yaya! Dan haka Ni dai idan ban ce ga laifinsa ba a daina kirkirar mini matsala da shi". Ta zauna tana kallona ta ce "Wato aike na kika yi wajen Abbanku? Wato duk abin da bawan Allah nan ya yi dan ya nema miki 'kima a idonsa, a wajen ki laifi ne ashe? Na zum'bura baki na ce "Gaskiya laifi ne! Yanzu Allah ka'dai yasan halin da yake ciki. Ni nasan yana sona, dan haka ban damu da ake kallon ni nafi sonsa ba". Ta mike ta ce "To fito na mayar da ke tunda na fahimci kema babu arziki a tare da ke. Oh ni Hafsatu yau ina ganin yadda Tinkiya ta haifi Akuya. Ko da wasa ban zaci Abbanku zai haifi tijararre irin Sadik ba. Haka ban zaci Baban Yara zai haifo kafaffiya marar kawaici irin ki ba. Allah mun tuba! Àllah ya shiryeku". Na bata rai na hau tattara kayana, kasan raina kuwa fal farin ciki zan koma gidana, gidan da nake rayuwa da mutumin da nake sonsa fiye da komai. ***** Gudale yana durkuse a gaban mahaifiyarsa yayin da ita take zaune a bakin gado tana kuka har da shessheka. A matu'kar gajiye ya ce "Na yi tuba Ummah! A gafarce ni, ba yadda kike zato bane ba fa". Filo ta dauko tana maka masa tana yi kuma tana kuka. Karon farko da ta daga hannunta da sunan duka cikin bacin rai sosai. Dan haka sai ya sake ri'ke kafarta cikin rauni ya ke cewa "Ki mini komai matu'kar zaki huce Umma ke ce duniyata". Sai lokacin ta bu'de baki ta ce "Ai yanzu bani ce duniyarka ba, tunda har zaka iya mantawa da halin da zan shiga a sanadin rashin lafiyarka, ko ma rasa rayuwarka gaba'daya". Ta sake kecewa da kuka riris tana cewa"Safiyya ta ci galaba a kaina. Amma ka sani na tsani Halimatu! Tunda har al'amarinta ya yi tsananin da zaka sayar da 'kodarka dan ka rayu da ita. Ba zan yaudari kaina ba, kana tsananin sonta ta yadda idan na rabaku ma ni ce a ruwa. Dan haka ba zan sake cewa ka saketa ba, amma ka sani bana sonta, ba kuma zan so ta ba. Tsakanina da su sai a lahira, idan mun je sai mai rumfa ya yi alkalanci na gaskiya." "Umma dan Allah ki daina irin wannan kukan! Tabewa ne a gare ni. Sharrin Sakina da Ashiru ne, ba su fa'di maganar dai dai ba fa". Sosai ta hassalo ta ingiza shi ya Fa'di warwars ta ce "Na ha'kura da kai Sadik! Tunda na haife ka nake tattalaka, nake nuna maka gata da ya zarce na yan-uwanka. Amma kai kuma kai ne kake wahalar da ni, ka ke bijire mini, kake ha'da kai da abokan gaba ta. Ba komai ba zan yi maka baki ba, amma tabbas ban mori wahalar da na wanzu ina yi akan ka ba. Ka je komai zaka yi babu ruwana, na riga na sallamawa Safiyya kai. Àllah barshi a filin kiyama Ubangiji ya mini sakayyar abin da kuka yi mini. Tunda na sani ko asiri ne ai yana tarar da hali". Ta dinga goge hawayen idonta tana fa'din "Allah kar a kama shi da laifin kukan da nake yi, sharrin hatsabiban bayinka ya hadu da shi, Ubangiji idan akwai abin da yafi afuwa da yafiyar uwa na yi masa, Allah ka tsare shi daga fa'dawa makircin masu tofi a cikin kulle kulle". Wani irin hawayen tausayin uwarsa ya dinga tsere akan fuskarsa, ya kasa magana, ya kuma kasa tashi daga faduwar da ya yi. Cikin karfin hali ya rarrafa ya fa'da kan cinyarta murya na rawa ya ce "Na yi kuskure Ummah! Na kuma gamsu na na yi din. Amma ki yafe mini, ki yi hakuri". Ta zaro tissue a Geffen gadon ta face majina ta ce "Na yafe maka! Na sani ba yin kanka bane, gayyah ake son yi mini da kai ta yadda zan kunyata, na yi ba'kin ciki. Fatana dai ka dinga fahimtar nafi kowa hakki akan ka. Zan fi kowa ba'kin ciki idan ka na'kasa ko ka mutu ka barni. Safiyya tana da irinka reras hudu ne ko biyar, Ni kuwa fa? Kai ka'dai ne da ni. Duk yadda Yayarku ta haifi maza ai dai jikokine su." Baki na rawa yake fa'din "Na gode sosai Umma! Ki cigaba da yi mini Addu'a. In sha Allah ba abin da zai same ni. Ba zan fasa fa'da miki ba, ke ce duniyata, ki cigaba da yi mini uzziri, Guduyo kaddara ce ta bani ita, ki cigaba da yi mini Addu'a da sannu komai zai dai-dai ta mini". Dake shi din na mussaman ne a zuciyarta a lokacin ta yafe masa, ta dinga sanya masa albarka da neman kariya. Amma zuciyar ta yi mata nauyi ainun akan Halimatu. Tunda ga kasan zuciyarta take jin tsanar yarinyar, da kuma an cire wa Gudale 'koda ta sanadinta da sai dai Abba ya ha'diyi zuciya ya mutu amma tabbas sai ta yi shari'a da dukkan ahalin gidan su Halimatu, har mahaifinta kuwa. Sakina da take tsaye bakin kofar dakin tana sake jinjina girman soyayyar da ta ke tsakanin Umma da Gudalenta. Duk wannan laifin da ya yi, ta rufe ido ta ce ba yin kansa bane, asiri ne. Sannan ta yafe masa har tana yi masa addu'a ta mussaman. Ta sauke ajiyar zuciya ta ce "Allah ya 'kara rufa asiri." Ai kuwa Gudale ya dago fuskarsa da take kan cinyar Umma ya harareta ya ce "Duk abin da kike fatan ayi mini ba'a yi mini ba. Wato Sakina na kusa sallama ki wallahi. A duniya na tsani kazallaha, na tsani mai shiga sharo ba shanu". Ta'be baki ta yi ta ce "Ka da'de baka sallama ni ba. Wanda baisan komai ba, sai kansa". Karon farko da Umma ta bi bayan Sakina ta ce "Yi ha'kuri Sakinan Abba. Ya za'a yi da shi, ai sai ha'kuri a sake tsananta yi masa addu'a dan ni tsoro lamarinsa ya fara bani, amma dai na yafe masa". Ya jima kafin ya mi'ke ya tafi. Sai da ya shiga falon Abba ya tsugunna ya ce "A yi ha'kuri da ni Abba! Kar a gaji, a kuma sake yi mini alfarma kada a bari yarinyar nan ta gane raunina. Na jima ina fatan na zama namiji a gidana, a taimake ni burina ya cika". Nisa wa Abba ya yi tare da cewa "Ai matu'kar zaka dinga wula'kanta Sadiya tabbas ka kwana da sanin ni kake wula'kantawa. Fallasar da baka so, ai ka janyo wa kanka. Yanzu kowa ai ya gane cika baki ne, sonta kake yi fiye da yadda take son ka, tunda zaka iya salwantar da ranka akan ta." "Nifa Abba ba dan haka bane, dan kawai na sauke nauyin da ka ce sai na biya ne." Abba ya numfasa ya ce "To ai na ce idan baka biya ba, ka sallama mini ita, ai da sai ka sallama din kawai." "Haba Abba! haba Abba yanzu dai baka gode mini ba, dan na nuna kulawa ta akan Shalelenka?. Tunda ka ha'kura zata koma, ina maka albishir din wakili sunanka zai amsa, Baban Gusau ya biyo bayan ka tunda dama 'kaninka ne". Ya mi'ke ya ce "Bari na je na marabce ta, na sani tuni Yaya ta tafi da ita. Àllah dai ya kara maka lafiya *Ya Abati*". Ido kawai ya bi shi da shi domin kuwa al'amarin ya girmame shi. ***** Yaya tana fita shi kuma yana dawowa a gurguje ya tsaya ya yi mata godiya ya shigo ciki abinsa. Masu aikin Umma sai share gidan da moping suke yi kamar yadda Abba ya ce su zo su yi, tunda ansan gidan ya yi kura, duk da mai gidan a ciki yake kwana. Ina tsaye a tsakiyar dakina, sai kamshi turaren wuta yake tashi a dalilin an riga an kammalah gyransa. Ba sallama ya shigo, kaitsaye ya rungume ni yana shinshinata tare da sauke ajiyar zuciya. Murya ba amo ya ce "Really missed you my *Hala*. Farin-ciki ya dinga rasta ni. Na dinga jin inama zamu tabbata a haka. Tun kafin masu hidimar gyara gidan su tafi ya rufe dakin ya hau rawar jiki, bai samu nutsuwa ba sai da na biye shi, muka shayar da juna madarar kauna. Sai da muka nutsa ya kalle ni ya ce "Kin je kin yi mini hadin kitifo dan ki gane irin tasirin da kike da shi a zuciyata ko?" Na dinga rantsuwar ban san komai ba , ya yarda da ni. A farko tamkar zai botsare sai kuma ya janyo ni ya rungume yana cewa "komai Ashiru da Sakina zasu fa'da kada ki yarda da su. Domin idan kika ce zaki bijire mini, ko yin wasa da lamarina to komai yana iya faruwa a tsakaninmu". Murya na rawa na ce "Allah ya tsare ni, komai kake so hakan zan yi maka, koda zai bata rayukan jama'a da dama". Ya sake rungume ni sosai yana shfa cikina da ya fara tasawa yana cewa "Hey Magajin Abba barka da hutawa". Na dan yi murmushi na ce "Idan kuma magajiyar Umma ce fa?" Ya gimtse ka'dan ya ce "Na sani ai Mama zaki gado dan hakan Magajiyar Umma zata zo later". Lafiya lau muke zaune, mussaman da yanzu ba matsalar komai, ba ciwon ciki ko mara, hakan nan babu kasala da amai. A wannan tsukun Asuu ta janye strike din da take yi, na koma makaranta. Kaffa kaffa nake yi da abin da zai motsa ransa. A haka muke gungurawa har cikina ya shiga watan haihuwa. Siyayyar kayan da suka zama dole kawai muka yi, irin su riguna unisex da shawul da kuma towel sai su Pampers, amma duk ragowan ya ce sai an yi haihuwa. A satin da na kammala rubuta jarrabawar karshen zangon aji hudu aka kai ni asibiti, tunda tuni an gano ba zan iya haihuwar da kaina ba. Ranar *14 ga watan Janairu* aka ciro mini kyakkawan jaririyata mai cike da koshin lafiya. Na farfado na yi tozali da kyautar da Ubangiji ya yi mana wanda yawan dangi ko yawan ku'di basa sawa a samu. Kallon farko da na yiwa yarinyar ta shiga raina, soyayya irin ta uwa ta dinga kekketa dukkan jikina. Tun tana jaririya na tabbatar tafi kama da Gudale ba abin da ta dauko nawa. Amma koluluwar kama da Sakina ta ke yi. Na dinga kallon yarinyar ina jin dokin samuwarta, na sani Babanta ba ita yake harin samu ba. Amma ina da yakinin idan ya ga yadda ta dauko Sakinansa zai manta da waccan fatan nasa. Umman Danladi Nasidin ne a wajena. Amma kusan dukkan ahalin gidanmu a Asibitin suke yini. Hatta shi kansa Gudalen sau uku yake zuwa, dan haka ban fahimci halin da yake ciki ba, kawai dai baya daukar jaririyar sai dai ya kalle ta a cikin gadonta ko a hannuna ko hannun Umma wai bai iya daukar jarirai ba. *Na ce ba kinsan wani hadi da ake yi wa asalin man ridi da kwakwa da ba'a samun original din su sai a wasu kebantaccun jahohi?* *kina fama da matsalar cinyewar gashi ko kuma rashin tsayinsa?*. *Kina neman ha'din da da zai sanya fatarki laushi da sulbi, kuma cikin saussaukan farashi? Tuntu'bi wannan lambar dan samun naki cikin sau'ki. Kaya mai inganci shi yake siyar da kansa.* *Sister Zainab 08039315577.* # Team Gudale. # Team Guduyo. # Surayya Dee ✍️. # Ana tare 🤝. 2/8/23, 10:25 - Buhainat: *Wannan littafin na ku'di ne, biya 500 ku'din karatu ta wannan asusun* *2384876855* *Surayya Ibrahim* *Zenith Bank.* *A tura shaidar biya ta wannan lambar* *08032773332*. *63-64*. Ana gobe za'a sallame ni Mama da kanta ta nuna wa Yaya Gudale sha'awar idan an sallame ni na koma gabanta, ta kula da ni ko da na sati hudu ne. Kai tsaye ya ce "A a Mama kawai ki dawo gidana ki zauna amma ba zai yiwu ba, ni bana 'kaunar wannan al'adar bare ni da kiris ake jira ace ba zata dawo ba". Shiru kawai ta yi masa, amma a yadda na fahimta ba ta gamsu ba, mussaman yadda Umma ta sake tsananta gaba a tsakaninmu, ba zai yiwu ace kullum sai ta zo gidanmu ba. Haka nan ta sani duk wacce zata kawo ta zauna da ni, sai ya zama fitina tunda zuri'ar su Mama ne gaba'daya Umma bata 'kauna. Ashe da ta koma gida da kanta ta je gaban Abba ta ro'ki arzikin na dawo gabanta tunda bani da lafiya ga kuma jego. Take ya tabbatar mata idan an sallamo ni zai sa a kawo ni. Tana tafiya kuwa ya kira Yaya Gudale a lokacin muna tare. Umarni ya bashi na kai-tsaye akan cewa zan koma gida a kula da ni. Dan haka idan an yi sallama a wuce da ni kofar Baban Yara. Ya kara da cewa "Ban da Umman naku bata girma ina ce ita zan damka wa ragamar kulawa da Halimatu tunda ko ba matar ka bace 'ya ce a gunta ta sosai". Wani irin bacin rai ya taso wa Yaya Gudale. Ya kasa cewa Abban komai. Har sai da ya tambaye shi ya ji me ya ce? Ya amsa da ya ji. Yana katse wayar ya watsa mini wani irin kallon da ya tsorata ni. Na gigice, ya nuna ni da yatsansa ya ce "Wai ke wacce irin kafaffiyar mace ce ne? A gaban ki Mama ta tambaye ni akan ki koma gida na ce mata a a. Dake ita tasan girma da 'kimar aure sai ta hakura da hukuncina. Saboda ta san yadda Ubangiji ya karrama miji akan matarsa. Amma ke baki san komai ba sai kafirin taurin kai shine kika taurare kika kai maganar gaban Abba ko?". Na fara rawar baki ina fa'din "Wallahi ban san komai ba, ka yarda ni, ko Mama bansan zata yi maka magana ba". Ya sake yi mini wani lalataccen kallo ya mi'ke ya ce "Na rantse miki idan har kika tafi gida da sunan wanka, to ki tabbatar kin tafi kenan. Na ha'kura da ke, ba zan iya wannan auren da ban isa na zartar da hukuncina ba sai wanda kika tsara". Nan da nan na fara kuka ina cewa "Ka dinga fahimta ta mana, na rantse maka da girman Ubangiji ban san komai ba." Ya sassauta ka'dan ya ce "To na yarda baki san komai ba, to ina son yanzu ki fa'da wa Abba kin fi son a kawo miki wacce zata kula da ke, ki sami dai dabarar da zaki kubuce kawai. Idan kuma kin kafe ki sani ban yaudare ki ba. Dan kuwa sallama ki zan yi, na ha'kura Wallahii." Na sake fashewa da kuka na ce "komin kankantar abu sai ka ce "Zaka sallama ni, me yasa kake mini hakan? Kana son na gane, na kuma fahimci cewa kai baka sona, kuma bani da wani amfani a wajen ka matu'kar zan yi kuskure ko da kuwa a cikin rashin sani ne?" Ya mi'ke ya make kafa'da ya ce "komai kika gamsu da shi duk daya a waje na. Amma ina nan akan bakana matu'kar zaki tafi, to ki sani kin tafi kenan. Kuma da kaina zan shigo har cikin gidan na dauki wannan 'Yar taki da ba kya gajiya da kallon ta kina murmushi, tamkar wanda wakili ne ya fara iso wa. Duk tunanina Mama zaki biyo tunda ance galibin iyaye mata ake gado." Na kalle shi idona fal da hawaye ina ma zan iya ce masa tabbas gado ne, amma shine ya yi gadon tasa uwar. Sai dai na sani fa'din hakan zai zame mini sanadin bacin rai ne mai tsananin gaske. Banda bala'i daga haihuwa daya tak har ya yi raddi? Na kalle shi na ce "Allah ya sani ban sani ba, amma 'kira Abban na fa'da masa". Ya daure fuska ya ce "Ki 'kira shi a layin ki, ai na riga na gane so ake a sake wula'kanta ni, a ri'ke mini iyali, dan kawai ayi ta ganin raunina". A hankali na ce "kasan wayata tana gida". Ai kuwa ya 'kira Abban ya danna handsfree ya miko mini, ya koma gefe yana cin magani. Abba ya dauka na gaishe shi a raunane. Ya shiga tambayar ko lafiya nake? Na amsa da "lafiya 'kalau a matu'kar sanyaye". Ya ce "Ina sauraron ki". Cikin rawar murya irin ta jin tsoro da kuma rashin mafita na ce "Abba bana son tafiya gida! Na fi son a kawo mini mai zama". Karon farko da Abba ya bu'de mini wuta tamkar ba shi ba, tunda a kullum harshensa mai taushi ne sosai a kanmu. Amma a wannan ranar cikin fishi ya ce "kin ci ubanki Halimatu! Ni kika kira kina inkarin umarnin da na bayar? Na da'de da fahimtar baki da kunya ko ka'dan. Idan kin koma din me zaki iya yiwa kan ki? An yanka miki jiki, ba zaki bari a taimake ki, ki dan ji dama ba? Da ciwon zaki ji ko da raino ko kuwa da fitinar mijinki? Ba abin da zamu dora masa na dawainiya a dalilin kin dawo gida. Komai da aljihunmu zamu yi miki. Dan haka dole ki dawo ko na wata daya ne shasha da bata san ciwon kanta ba. Da kaina na zan zo na dauke ki, na ga wadda zai sake tunkara ta da maganar raini tsakanin ke da wanda yake saka ki wannan rashin mutuncin.". Daga haka ya kashe wayarsa ya bar ni cikin zullumi. Na kalli Yaya Gudale ya na'de hannu a kirjinsa ya cika ya batse tamkar zai fashe tsabar fishi. Zuciyata ta sake tsinkewa shin me zai biyo bayan aurena? A rarrabe na ce "Ya ya ka ji me ya ce ko?" Ya galla mini harara ya ce "Na ji da kyau! Sai dai ki sani ina nan kan bakana idan har aka tafi da ke to ba zaki dawo mini ba, na ha'kura kawai". Na fashe da wani irin kuka na tashin hankali, har wani shidewa nake yi. Ya yi tsaki ya ce "Baki fara kuka ba Wallahi". Take ya karbi wayarsa, ya kira Antin Zaria ya sake danna hands free suka gaisa cikin nutsuwa tamkar ba Gudale ba. Domin baya shiga shirginta ko ka'dan, baya ta'ba neman ta da kansa. Sai dai ita ta neme shi, duk yawan shekaru da mu'kaminta kuwa. Cike da farin-ciki ta ce "Gudalen Umma ya zama Dady! Gashi har girma na sosai ya fara kama shi. Ya bu'de murya ya ce sai yanzu ne na zama Dadi? Shin tun ina da shekaru nawa kika haifa mini 'ya'ya? Abba ya sha fa'da mini 'ya'yan da 'yan-uwanka suka haifa maka sune naka, domin sune zaka ga ni ranar tashin alkiyama. Ko kina nufin ni kawai yake yiwa wannan karatun kawai?" Nan da nan ta ce "Gaskiya ne Gudale ba kai kawai yake jaddada wa ba. Ka dade da manyan 'ya'ya tabbas, har kana Shirin daukar jikoki. Wannan 'ya tawa ce halak malak. Ban taba yaye ba saboda bani da lokaci, amma akan ta zan fara, Allah ya albarkaci rayuwarta gaba'daya". Ya sake kame wa ya ce "Sunanki ne da ita! Sannan na baki ita halak malak. Dan ki gane kina cikin mutanan da suke da 'kima a duniyata amma baki fahimta da wuri ba". Ai kuwa nan da nan muryarta ta fara rawa tabbacin kuka take yi na farin ciki. Cikin kuka ta ce "lallai kuwa ban fahimce ka ba Gudale! Ka bani kyautar 'ya macen da Ubangiji bai kaddara mini haihuwar ta ba? Tabbas Ubangiji baya juyar da addu'a! Ni ka'dai nasan yadda nake tashi cikin dare ina addu'ar Ubangiji ya bani 'ya mace ko guda daya ce. Har na ha'kura na fitar da rai. Ashe Kai ne zaka haifa mini, zan kuma tashi da ita a filin barka." Sai kawai ta fashe da kuka sosai, domin ba ta yi zaton Gudale yana tunawa da ita ba. Domin ko abu yake so ta yi masa, ba ta kai ya fa'da mata da kansa ba, sai dai Umma ta fa'da mata, ta kuma sanya dole ta yi masa. Godiyar da Antin Zaria ta ke yi cikin kuka shi ya tabbatar mini ba ta dauki al'amarin kyautar da sau'ki ba. Ni shaida ce yadda take tsananin son haihuwar ya'ya mata amma Ubangiji bai bata ba. Kwata kwata 'Ya'yanta ma uku ne da rak kuma dukkansu maza ne. Ya kaurara murya ya ce "Ki fara hidimar ta daga yau, dan kuwa ni ba zan taya ki ba". Da hanzari ta ce "yanzu kuwa! Bari na turo Maimuna yanzu, da sai jibi zan taho ganin baby da mamanta, amma yanzu gobe in sha Allah ina tafe bari na tura a siyo mini ticket 'din jirgin karfe bakwai na safe." Daga haka ya kashe wayar ya kalle ni, na yi sukuri, ido cike da hawaye. Ya ce "sunan yarinyata Hafsatu ba Saudatu ba. Abba ya saka mata sunan Ummah! To ni sunan Antin Zaria zan saka mata, ai shima 'Yar shi ta farko sunan Yayar 'Kwalli ta ci. To ko yi zan yi da shi, Umman ta zo daga baya". Na kasa cewa komai a dalilin fargabar da nake ciki sosai. Ya sake cewa "Na bada kyautar yarinyar kin ji da kunnenki. Dan haka kina tafiya gida shikenan, zan zo na karbi abata, na bawa sisterna. Ke kuma ki 'karata ke ka'dai sarkin masu gatan iyaye. Ai wlh mata irin ku idan mutum ya aureku bai more ba. Ace komai sai an nuna wa miji gazawar sa? Ba dama abar mutum ya yi yadda yake so da iyalinsa". Ya ja 'kwafa mai nuna bacin ran da yake ciki. Ilahirin jikina 'bari yake yi. Cikin 'karfin hali na ce "ka yi ha'kuri ba laifina bane, Dan Allah! Dan darajar Annabi ka janye wannan kudirin, zuciyata zata iya buga wa, ko ban ci arzikin komai ba, na ci albarkacin jinin da ya ha'da mu". Na fa'da cikin kuka sosai. Ban san ya aka yi ba tausayina ya kama shi ya ce "ke me ya hana na ci arzikin jinin a wajen ki? Me yasa kike yarda ake mini iko akan aurena? Ai kinsan wula'kanta ni za'a yi, shi yasa aka shirya wannan mana'kisar." "Wallahi ban sani ba Yaya Gudale ka yarda da ni". Ya shiru ya ce "alright na fahimce ki, na kuma yarda amma bisa sharadi daya tak. Billahillazi ba zaki yi ko sati uku ba. Yanzu ki fa'da mini da bakinki adadin kwanakin da zaki yi, idan kika saba to shikenan wanccan kudirin ya tabbata." Na sauke ajiyar zuciya ina goge hawaye na ce "Na gode sosai! Idan an sallame ni gobe, nasan su Anti zasu shirya walimar suna nan da sati guda to ka yi ha'kuri mu bar shi nan da 2weeks". Ya kuwa girgiza kai da sauri ya ce "A a ban gamsu ba, ba zan iya ba". Na ce "To kawai mu barshi nan da kwanaki goma sha biyu dan Allah". Ya numfasa ya ce "Idan fa ranar ta zo ba maganar wani uzziri ko ba zaki iya ba, zaki dawo ne salin alin ba wanda ya sani". Na daga kai. Ya ce "baki zaki bu'de ki yi magana Malama". A sanyaye na ce "Na amince". Hakan da muka yi ya saka ya sauko ya zauna a gefen gadon yana cewa "Na nuno masa fuskar yarinya mai karambani ta je ta kwaso Sakina sarkin kazallaha. Ina murna na gyara masa ita yadda zai ganta sosai. Ya dinga yi mata pics a wayarsa. Na ce me za'a dinga ce mata ne?" Ya ri'ke baki ya ce "ke Guduyo ki bari iyayenta su zaba mata mana, tunda dai ke kika haife ta ai magana ta kare. Yi kara ga iyayenta su zabi kowanne inkiya su fa'da mata." Na ce "To". Ina mamakin al'amarin Gudale. Yanzu ya gama fa'din ba zai bi ra'ayin Abba akan sunan yarinyar ba, amma kuma ya ce a bar su Sakina su zabi Nick name din da ya yi musu. Gudale sai Allah. Amma na fahimci yadda Abba yake yi akan lamarina ne yake matu'kar sosa masa rai. Muna hakan Umman Danladi Nasidi da likita suka shigo, dama ganinsa ya sanya ta fice, ganin shiru ya yi yawa ta shigo da taga likita zai shigo. Cikin ikon Ubangiji sai kawai ya bani sallamah. Bai fa'dawa kowa ba! Ya kammala komai ya debo mu da kansa ya kai ni har dakin Mama. Farin-cikin Mama ya kasa boyuwa ta dinga yi masa godiya, yayin da shi kuna ya maze babu yabo babu fallasa. Da daddare Abba da kansa har falon Baban Yara ya dinga mini nasiha cikin rarrashi da nuna kulawa. Ya dubi Baba ya ce "D'an ka dai ya same ni gar da gar ya ce sunan yarinya Hafsatu, yadda na yiwa Yayar Kwalli takwara da Antinsu ta Zaria shima haaka zai yi sunan Yayar tasu zai saka." Dariya saosai Baba ya yi ya ce "Sadik manya! Àllah dai ya kara shirya mana su". Washagari Antin Zaria ta iso. Da yamma kuwa ta fita ta jibgo siyayyar tamkar wanda a bishiya ta tsinko ku'din. Kaya masu koluluwar daraja ta narkowa yarinya, har da drower. Komai na siyayyar nan mother care ne, hatta setin robobin wanka. Abin koyon zama, na koyon tafiya, keken Yara, har da su lilo. Ga sarkar gold. Ni kuwa super da asalin leshi mai tsada bibbyu. Banda Wanda ta bayar a mini dinkin fitar suna. Dake Ina da kwararriyar tela a hannu sai ban damu da mishkilar da tela zai iya bayar wa ba. *Umm Muhd collections* kenan hazikar tela kuma shahararriyar yar kasuwa.kuma mai hada kayan haihuwa da na lefe. *08063358662*. Kwanaki uku masu zuwa za'a yi taron suna kamar yadda Antin Zaria ta shirya. An kara kwana biyu kenan. Hidima saosai Anti Zaria ta yi, domin taron sunan mai sunanta yafi kama da bikin Yar gata, domin kaza gida hudu ake raba ta. Harabar gate din gidan aka shirya aka kawata dake a lokacin ba'a fara kama hall dan yin taron suna ba. Alherin da na samu sanadin wannan yarinyar sai da na sayi fili a hannun kwararrun masu hadahadar gidaje da filaye *AMYAS NEW & FAIRLY ITEMS.* *08083909947*. Sai da Yaya Al'amin ya ga filin ya yadda, ya kuma gamsu da siye da siyarwar *AMYAS* din domin idan ka siyi gida ko fili a hannunsu ba ruwanki da zullumi ko fargaba sabanin wasu da zasu samu filin wani su siyarwa wani, kai Allah ya shirya mana dabi'u kawai. An ci, an sha an gyatse. Hatta Umma da tun case din 'kodar nan bata sake budi baki ta mini magana ba. Ko gaisheta na Yi matu'kar ba akan idon Abba ne ba, ba zata amsa ba. Amma sai da ta yi kwalliyar kece raini a taron sunan Hafsat. Antin Zaria da kanta ta saka mata *Amnah* Yayin da Sakina ta ce *Ablah* zau kira ta. Dan haka kowa yana fa'da mata wanda ya so. Kullum safiya ana yiwa yarinyar wanka Umma zata aiko mai aikinta ta dauke ta ba za'a dawo da ita ba sai azahar, domin goya ta take yi, abin da ba'a taba ganin ta yi ba goyon jiko ki. *Ummma* Tana goye da Amna ta lullube ta da shawul din ta. Zaune take a falon ta ita ka'dai tana cin dumamen tuwo. Gudale ya shigo da sallamah. Kusa da ita sosai ya zauna, ya kalle ta ya ce "Umma ba kya gajiya da goyon wannan yarinyar ne? Kada tasa miki ciwon baya fa". Ta murmusa ta ce "Yarinyar da ta biyo Sakina daga kama har siffa Ina zata yi nauyi? Da uwarta ta dauko ne zata dame ni". Ya dan yi dariya ya ce "Sai yanzu ma na ji haushi Umma da na nasan hakan zaki yi ta wahala da ita, da an bar mata sunan na ki". Ta zuba masa ido ta ce "Kana tunanin zan k'i jininka dan bana son zuri'ar su Safiyya? Kafin ya yi magana ta zarce da fa'din, "idan ina kallon yarinyar manta wa nake yi da uwarta, kawai ina kallon ta ne a jininka, na da'de ina yiwa matarka da ya'yanka tanadin soyayya mai yawa. Tunda ban samu damar da zan nuna wa matar ka zahirin kauna ba, to babu wani abu da kiyayyar da nake masa zai shafi jininka". Idonsa ya cika da kwallar tausayin uwarsa. Domin ya fara yarda yana son Guduyo. Rabuwa da ita kuma yana nufin tashin hankali a gare shi, domin nutsuwa zata yi masa tutsu. Kansa ya kulle kwarai da gaske. Da ya rasa abin cewa sai ya durkusa gabanta ya ri'ke hannunta ya ce "Na gode sosai Umma. Allah ya kara miki lafiya da nisan kwana." Daga haka sai ya mike ya fice da sauri domin sosai ya shiga rudani. Yayin da Umma ta bishi da kallo hawaye na bin kumatun ta. Bata tantamar gayya kawai Safiyya ta yi mata da Gudalenta. Tabbas ba dan Abba ba da ta nuna musu karshen gayya. Bata son su, bata kaunar ko hanya ta hada su, amma tunda karfin kaddara tasa jinin Gudalenta sai ya hadu da nasu, to zata yi iyakacin iyawarta bata bari kiyayyar da take yiwa ahalin ta shafi yaran Gudale ba. Amma ko yau ta samu damar da zata wula'kanta auren zata yi. Shiyasa take fatan Abba ya yi tafiya mai nisa ta yadda zata nuna wa Halimatu kuskuren auren danta da ta yi. Amma Abba baya tafiya mai tsayi. Ta sani kuma ta'ba auren Halima tamkar ta'ba nata auren ne. Ta saka tissue ta goge hawayen idonta a fili ta ce "Allah ka ara mini dama, Allah ka nuna mini lokacin da zan kunsa wa Safiya da ' yarta fiye da bakin cikin da suke kulla mini". **** Kwanaki suna ta shudewa tamkar walkiya, Kamar wasa har na kwashe kwanaki tara da zuwa gida. Ba karamin Jin da'din zama nake a gaban mahaifiyata ba, kulawa take bani ta yadda da hali numfashi ma yi mini zata yi. Ba abin da nake yi sai dai na shiga bandaki ta zo ta gasa mini jikina sosai, sannan abincin da nake ci ganye fa fruits ne mafi yawa saboda na samu sau'kin yin nishi. Ko hidimar Amna bana yi tunda idan aka Kai wa Umma ita tun safe sai azahar. Nono kawai zan bata Mama ta cigaba da rainon ta. Ko da daddare barci nake sosai bana sanin me Mama take ciki da jaririya sai rikicin nata ya tsananta ne zata tashe ni, da zarar ta koshi kuwa zata ce na kwanta na huta ta fice da ita. Bana aikin komai, a dalilin tausayina da take ji, gma dalilin lokacin haihuwa ta ba karamin wahalar tiyata ta sha ba, bata san c.s ba kamar operation bane. Zuwa lokacin kuma ciwon nawa ya ha'de sosai kiris ne bai warke ba, aikin ya yi kyau. Hutu da nutsuwar zuciyar da na samu ya sanya na yi wani irin kyau, na motse sosai, duk wani kumburin da na yi ya sace, kirjina ya sake cika. Ni da kaina na sani na murje na yi kyau. Mussaman da kullum Yaya Gudale zai shigo ya duba ni safe da dare, muyi hira cikin nutsuwa. Ga Kuma *Aisha lame* da baibaye ni da mayukan oriflame na alfarma da fata take sake zama ta kasaitattun mata. Har da wani hadadden seti na tsarki. Wanda ba karamin Jin da'din su nake yi ba. *07036662633*. Da daddare ya iske ni a dakina, na yi fes da ni, dakin sai kamshi turaren wuta yake yayin da nake kamshin turaren Al haramain Madina. Da walwala ya ce "Tana ina?" Na murmusa na ce "Wai Yaya Gudale kunyar fa'din sunanta kake yi ne? Na ce maka Amnah Antin Zaria ta sanya mata. Anti Sakina kuma ta ce Ablah, sai ka zabi wanda yafi kwanta maka." Ya yi murmushi ka'dan ya ce "kunyar 'yar fari nake yi, kada ace bani da kunya. Kinsan ban taba jin Umma ta fa'di sunan mai sunanta ba, haka Mama ban taba jin ta gatsa sunan Yaya Abdallah ba." Ya bani dariya sosai na ce "To ai su mata ne, ko baka ga su Abba suna fa'din sunayen su ba?" Ya ta'be baki ya ce "To ke ai ba kya kunyar, shiyasa ni nake yi. Kullum ki tasa ta a gaba kina kallon da baya kare wa nan gaba manta wa zaki yi da ni tunda kin samu 'ya. Na sake yin dariya na ce "Hoh Yaya Gudale". Ya yi kicin kicin da fuska alamun seriousness ya ce "Guduyo yau kwananki tara". Zuciyata ta tsinke a dalilin kwanakin da na diba zasu cika nan da kwanaki uku. Na kasa cewa komai amma na yi matu'kar razana. Ya jima yana nazarina ya numfasa ya ce "Yanayin ki ka'dai ya fahimtar da ni, kin shirya yaudara ta ne. Wato kin fi jin da'din zaman ki anan akan zama da ni?" Da sauri na girgiza kai na ce "Ba hakan bane Yaya Gudale! Ka fahimce ni dan Àllah. Ciwona bai kame gaba'daya ba, sannan duk wacce za'a kai mini ta zauna da ni, ba zata kai Mama kulawa ba. Ka yi hakuri na yi sati uku plz Abban Amnah". Na fa'da da sigar rarrashi da shagwaba. Ya mike tsaye ya kafe ni da kallon da yake ki'dima ni. Ya kankance ido ya ce "Uban Amna zaki ce, ba Abbanta ba. Na rantse miki da girman Ubangiji idan kika canja mini magana to tabbas nima kuwa zan zarta da kudirina. Ni zaki mayar dan iska Guduyo?" Na yi kasa da kaina na ce "Shikenan ka huce! zan dawo gatan". A fusace ya ce "Ba ni wasu daga cikin kayanki na fara yin gaba da su". Na ce "To". Na nuna masa wadanda bama amfani da su. Ya dauki bedsheets ya zuba ya daure. Ya sake zuba mini ido yana kuma murza yatsunsa alamun kashedi. Murya a kaurare sosai ya ce "Billahillazi Guduyo idan kika saba al'kawarinmu komai zai faru a tsakaninmu. Na fa'da miki gaskiyar magana kenan". Ya kinkimi uban kayan da ya daure su da kyar. Na kwanta na yi lamo. Abin duniya ya taru ya mini yawa. Ta yaya zan kalli idon Mamana na ce mata zan koma gidana? Wa zan fa'da wa ya fahimce ni. Wata zuciyar ta ce mini Abba. To idan Abba ya hana ni koma wa, ta hanyar tsawatar masa shin ya zan yi da hukuncin Gudale? Idan ma bai sallama ni ba, to babu shakka sai na hadu da kalolin fishinsa masu tayar da hankalina. Na sauke nannauyar ajiyar zuciya lah shakka zan yi komai dan na tsira da auren Gudale. A fili na ce "Allah ka kawo mini agaji". A haka barci ya kwashe ni. Da safe ya shigo muka gaisa kamar kullum. Ya kalli Amna a hannuna har ya dan yi mata wasa, sannan ya tafi wajensu. Haka na yini ina tufka da warwara. Da daddare sai gashi ya sake dawo da bedsheet din, ya sake jidar wasu kayan. Washagari kuwa yinin zullumi na yi ta yaya zan iya yin wannan danyen aikin a gobe? Shi kuwa ko a jikinsa domin a gaban Mama ya fita da wasu kayana da ya ya daure da zani. Da tambaye shi ina zashi da kaya ya ce wanki zai kai, sai ta gamsu, bata sake bi ta kai ba. Kafin wayewar gari duk na hargitse na susuce gaba'daya na zama wata iri abin tausayi. Da ya shigo cikin Shirin tafiya office, ya kalle ni ya ce "Zan dawo da rana na tarar kin koma ne, ko kuwa?" Na yi sororo na kasa bashi amsa. Ya sassauta ya ce "Na fa'dawa Abokiyar aikina ta yiwa mai kawo musu yan aiki magana ina so. Kin ga zata taya ki ayyukan gida da raino duk da dai jaririyar zata fi zama wajen Umma ne. Kuma yau din nan ta ce mini an samu yarinyar tana gidanta, shin na dauko miki ita yau ko sai gobe?" Baki na rawa na ce "ka barta kawai sai jibi. Sai da daddare zan koma idan Mama ta tafi kai wa Baba abinci". Ya daga kai cike da gamsu wa. Ya sunkuyo ya bani peck a dukkan chicks dina. Tare da cewa *"Thank you my Hala love".* Ya fice ya bar ni da tararrabin wannan rashin mutuncin da zai sa ni yi. Na sani cikin supplements din *Fasilat* da nake sha har da wanda yake daidaita jikin mace ta yadda kitse marar amafani yake zagwanyewa cikin gaggawa. Amma zullumin da nake ciki ya sake taimakawa wajen sake zubewata. *Shin kina gyara kanki kuwa?* *Shin kin jarraba kayan G.H.T?* *Idan kina fama da basir, infections, da ulcer ga magani ya zo miki cikin yardar Allah* *07039269802*. Har Bayan sallah isha na kasa tashi na tafi. Ina cikin wannan yanayin sai sallamar Abida na ji yar kanwar Umma ce ta zo daga Yola. Ba jima wa sosai ta shigo dakina ta ce "Wai na bada Amna in ji Ummah". A sanyaye na nuna mata karshen gado inda take kwance. Na sani kuma ba Umma ba ce ta aiko ta ba. Yaya Gudale ne. Basu fi mintina ashirin da fita ba, ya fara kiran wayata ba kakkauta wa. Na dauka, ga mamakina sai ya sassauta murya ya ce."Ran autar gidanmu ya dade kamar tuwo" Dariya ta subuce mini, na ce tare da naka Yaya Gudalen Umma da Sakina". Ya lankwashe harshe ya ce" "Muna ta jiran ki, ni da Bebinki fa. Ko na zo mu taho tare?" Na girgiza kai na ce "Ba sai ka zo ba, kawai ka jira ni a kofar garden." Ya ce "Tom " tare da katse wayar. Ina zaune ilahirin jikina bari yake yi mussaman kafafuwana, ga fargaba mai yawa. Duk sanyin da ake yi sai da jikina ya dauki dumi. Kusan awa guda ina zaune na kasa tashi, bare na tafi, gaba'daya kaina ya kulle. Bana son wannan tsarin, amma kuma cike nake da tsoron abin da zai biyo bayan bijire masa. Kafin na yi wani abu wayata ta hau kuwwa. Ganin shine sai da zuciyata ta sake tsinke wa. Na dauka na kasa magana a dalilin yadda harshe na ya yi mini nauyi. Cikin fishi ya ce "Kin ga Halima zaki dawo ne ko kuwa na koma cikin gida? Ya zaki jingine ni, sauro yana ta cizona sama da awa guda amma kin kasa fito wa". Murya na rawa na ce"Na kasa tashi ne, jikina rawa yake yi Yaya Sadik". Ya yi shiru domin ya sani idan har na ce masa Sadik to ina cikin yanayi mai nauyi da nake bu'katar uzziri ko sassauci. Ya nisa ya ce "me ya kawo miki barin jiki da wannan zullumin?" Da sauri na ce "kunyar su Mama da tsoron fishinka". Shi ma da sauri ya ce "Bar shi a kunyar dai domin na gamsu da hakan, amma ban gamsu kina tsoron fishina ba, da hakane da tuni kin da'de da dawo wa. Wallahi Halima! Kin ji rantsuwar dan musulmi ko? To yau a gidana zaki kwana matu'kar da aurena a kan ki. Bana magana biyu". *Na ce ba? Kinsan wani hadi da ake yi wa asalin man ridi da kwakwa da ba'a samun original din su sai a wasu kebantaccun jahohi?* *kina fama da matsalar cinyewar gashi ko kuma rashin tsayinsa?*. *Kina neman ha'din da da zai sanya fatarki laushi da sulbi, kuma cikin saussaukan farashi? Tuntu'bi wannan lambar dan samun naki cikin sau'ki. Kaya mai inganci shi yake siyar da kansa.* *Sister Zainab 08039315577.* # Team Gudale. # Team Guduyo. # Surayya Dee ✍️ # Ana tare 🤝. 2/8/23, 10:25 - Buhainat: Ina masu neman kasuwanci da zasu yi daga cikin gidan su?? Oriflame suna ba ma mutum damar tafiyar da kasuwanci a duk inda yake a fadin duniya Kungiyar mu ta The BBMs Goal Achievers za su gabatar da training ga wadanda suke da sha'awar fara kasuwanci su da Oriflame a kyauta Kyautar register da Oriflame daga daya zuwa bakwai ga watan Janairu (1-7) Oriflame na da kayayyakin kula da fata, kwalliya,turare da supplements, maganin infection da sauran su Abun da ake bukata shine iya jarin fara kasuwanci ki sai kuma zuciyar jajircewa da hakurin neman na kai Hanzarta kiyi magana ta nan 07036662633. *Cikin fuwacewar Ubangiji na samu na yi wannan, na gode da uzzirinku*. *SDK* *65&66* Jin hakan ya sanya na mi'ke na sanya hijabi na na fito na leka dakin Mama cikin sa'a tana bandaki tana wanka. Da sauri na fito ko rufe mata kofar ban yi ba. Na doshi hanyar waje cikin matsanancin Ina kofar garden din kuwa, yana tsaye tamkar gunki. Ina jin ajiyar zuciyar da ya dinga saki. Ya rike hannuna ya rufe kofar muka shiga cikin gidanmu. A falo muka yada zango. Na zauna hawaye ya goce mini. Ya kalle ni tsawon lokaci ya kasa cewa uffan tabbacin kukan da nake na sharbe ya ta'ba shi. Ya yi gyaran murya ya ce "Kina nufin ba'kin cikin dawowa gare ni har ya yi tsananin da zaki dinga irin wannan kukan mai dafa zuciya?" Na kasa cewa uffan, sannan hawayen ya ki tsaya wa. Ya sassauta ya ce "Ban yi miki hakan da nufin takura ko zalunci ba. Hakan shine kwanciyar hankalina, na tsani na shigo gidan na ga ba kya nan ko ban ji motsin ki ba. Ni ka'dai na san halin da nake ciki a dalilin rashin ji ko ganin motsin ki. Kema kuma shaida ce tun kafin mu yi aure bana son ki yi mini nisa. Yanzu Kuma cike nake da fargabar kada Abba ya sake ri'ke mini ke". Ganin ban daina kukan ba ya sanya ya matso gare ni sosai ya rungume ni yana bubbuga bayana ya ce "Ya isa hakan idan ba so kike na gamsu zama da ni ne ba kya marari ba. Zan fada miki gaskiya ko ba zamu yi magana ba, nafi son na gan ki a tare da ni, wulgawar ki ka'dai tana saukar mini da nutsuwa. Ban dawo da ke dan na musguna miki ko dan na yi miki sanadin bacin rai ba. Haka nan ban yi dan na ci mutuncin iyayenmu ba, na yi ne dan na samar wa kaina nutsuwa da aminci. Na kuma nuna wa kowa irin yadda nake son ki nake kuma da iko akan ki. Amma ke sai fama kike da kunci da bacin rai, shin gidan bariki na kira ki, ko kuwa gidan raya sunnar Ma'aki?" Ya yi shiru yayin da hawayena ya tsaya cak illah ajiyar zuciya da nake ta saki a jere. Ya sake ri'ke ni sosai ya ce "ki toshe kunnan ki, kome za'a ce kada ki damu, kin nuna mini soyayya, kin bi umarnina, na yaba, na kuma gode miki. Duk wanda ya tare ki da nufin yi miki raddin kin dawo da kan ki, ki fa'da musu umarnina kika bi, Allah kuma ya yaba miki domin shi ya wajab ta miki yi mini biyayya. Tashi ki wanko fuskarki, ki zo ki ci kazar da na siyo miki. Na kasa tashi, da kansa ya mikar da ni ya kai ni har ban'dakin ya tallafa mini, na dinga jin farin-cikin yadda ya ke tarairaya ta sai dai kuma zuciyata ta yi nauyi kwarai da gaske. Muka dawo falo, da kansa ya dauko plate, ya ha'do da flask din tea da duk abin da zan bu'kata dan ha'da shayin nan. Karon farko da naga yana mini abu na bauta ba dan yana bu'katar na yi masa wani abu in return ba. Ya zauna ya kalle ni ya ga idona cike da hawaye. Ya saki nannauyar ajiyar zuciya ya ce "oh my God! Wai menene matsalar ki? Waton kin fi jin tsoron cece-kucen mutane akan bacin raina?" Na girgiza kai na ce "kunyar Baba da Mama nake ji, na fito na dawo dakina basu sani ba, wanne irin kallo zasu yi mini, ya Abba zai kalle ni? Alhalin dama ya ce mini bani da kunya, yanzu ne zai tabbatar da rashin kunyata". Na fa'da ina rushe wa da kuka sosai. Kukan da na rusa ya yi sanadin tayar da Amna a bacci. Da sauri ya janyo ta, karon farko da ya dauke ta. Ya dora kafadarsa, sai dai kallo daya zaka yi ka gane bai iya daukar jarirai ba da gaske, saboda yadda ya damke ta tamkar za'a zo a warce ta. Ya dinga zagaya falon da ita. Amma fir ta ki yin shiru. Na bu'de baki na ce "kawo ta". Ya kuwa iso da sauri tabbacin dama so yake na karbe shi. Ina fara shayar da ita kuwa ta yi shiru, yayin da shi kuma ya dinga rarrashi na, har da sanya hannu ya goge mini hawaye. Cikin sigar rarrashi ya ce "Bari na je na wanke ki a wajen Mama da Baba ni kunyar ta kashe ni. Idan na yi hakan shikenan zaki daina mini wannan koke-koken?" Na daga kai da sauri. Ya mi'ke da azama ya fita. *Falon Baba* Kamar jifa haka Baban Yara ya ga Gudale ya shigo masa falo yana zaune yana kallon labaran tara a N.T.A . Ya kalle shi ya ce "Koma ka mini sallamah". Ya juya yana kunkunin a daina yi masa abu kamar har yanzu bai girma ba. A fili Baba ya ce "Allah dai ya shirya ka Sadik". Labule ya daga ya sake shigowa bayan ya ce "Assalamu alaikum" a hanzarce. Ai kuwa Baba ya ce "Ka sani ai matu'kar ba zaka tsaya na baka iznin shigo wa ba, ba zan saurareka ba, tunda na sani kana yin irin wannan iyashegen ne idan kana cikin gaggawa". Ya sake juya wa yana cewa "A gaskiya Baba kana sake tsananta wa, da dai baka yin haka, dabi'ar Abba ne yin hakan da baka yi koyi da shi ba. Assalamu alaikum ya Babati! Sadik ya shigo?" Ya fa'da da 'karfi. Sadik ya shigo" Baban ya fa'da cikin murmushi sosai. Har cikin zuciyarsa da jininsa yake jin Sadik. Sannan tabarar da yake yi masa tun yana yaro karami bai bari ba, ya dade da gane Sadik yana zama yaro kankani idan yana gabansa, sannan yafi sakewa a gabansa fiye da gaban mahaifinsa. Ya durkusa a gabansa sosai, ganin hakan da ya yi ya alamatar da Baba akwai babban al'amarin da zai gabatar masa. Kansan a kasa ya ce "Baba kasan dai Ni mutum ne da bana son ana takure ni. Amma shi Abba ya na'de kafar wando sai ya nuna wa Iyalina dukkan raunina akasu bayan tun ina karami nake addu'a na zama namijin duniya a cikin gidana." A makance Baba ya ce "Hakane". Ba dan ya fahimce shi ba. " To a gaskiya ni dama fa bana son wannan zaman da take yi a gidan nan da sunan jego, shiyasa..". Kafin ya karasa Mama ta shigo tana cewa "Har kun dawo daga asibitin ne, ina suke?" Nan da nan kwanyar Gudale ta hakaito masa ai rufin asini da Mama ta saba yi masa idan ya yi laifi ne yauma ta yi masa. A cikin mutanen da ya yarda karimai ne a rayuwarsa har da Mama halittar da Umman sa ta tsana tamkar ta shafe ta a doron 'kasa. Ya sauke ajiyar zuciya ya ce "mun dawo Mama amma na yanke hukuncin ba zata dawo ba, na mayar da su gida, shi Abba bai fahimce ni ba ko ka'dan shiyasa na zo inda za'a fahimce ni. Na tsani na bu'de ido na ganni ni ka'dai a cikin gidan." Mama ta yi sukuri tana kallonsa cikin rashin abin cewa. Domin ta sani shine ya zo ya tafi da Halimatu, ita kuma soyayya ta saka ta bishi babu shawara ba komai. Ashe kayan da ya yi ta fita da su da manufarsu, dama sun shirya sai dai a wayi gari a ga sun yi tafiyar su? Lallai sai kyale dan yau da rashin kunya da mutuncinsa, amma sanin da ta yi Sadik zai yi fiye da hakan yayin da Halimatu zata biye shi ta yi abin kunyar da ya zarce hakan saboda tsoron fishinsa sai ta hada su ta yi musu uzziri, amma ta kudire a ranta duk ranar da aka ce Halimatu ta zo gidan da nufin kwana a ranar zata gane bata wayo. Ya rarrafa ya je gaban Mama ya ru'ko hannunta ya ce "Allah dai ya kara miki lafiya Mamanmu! A duniya ina son mutum mai sirri bai rufa asirin wani, Allah ya rufa miki naki asirin. Ina matu'kar godiya sosai, sannan kar aga laifin Guduyo, laifina ne, ko kallon baki kyauta ba kada ayi mata, domin na baro ta tana ta kuka da bacin ran ya zata kalle ku. Na ce "Ta daina kuka zan zo na wanke ta". Baba ya ce "Ka wanke ta! Zo ka fice mini tunda dai kai kullum ba zaka bar ni na huta ba". Har ya je bakin kofar sai dawo ya ce "Saboda Allah me na yi Baba? Yaushe rabon da na kawo kara, ko a kawo maka tawa? Indai baka son na rame kawai ka samu Abba ka ce "Kai ka bani umarnin na tafi da matata, idan kuwa har ka bari ya yi mini fa'da. Àllah Baba a satin nan na dinga tsokanar fa'dan da sai ka gaji da sharia dan kuwa har mijin Juwairiya sai na tsokano, ta yadda zai koro muku ita". Baba ya daga hannu ya ce "Allah ga Sadik ka yafe masa , ka shirya mini shi". "Ameen ya adalin Uba! Ina godiya fa, na gode sosai. Ayi barci lafiya." Ya tafi babu waiwaye. Mama ta sauke ajiyar zuciya ta ce "Oh Sadik duniya! Shifa bilhakki yake al'amarinsa, Allah dai ya daidaita." Baba ya amsa da cewa"Amin". ** Ina falon ya dawo yana cewa "sai ki saki ranki na je na binne kunyar". Ya dauko ledar kazar ya kawo gabana. Ya shige ya debo ruwan wanke a hannu a faffadar roba, da kuma plate. Ya kalle ni ya ce "kwantar da ita ki sauko ki ci". Na kuwa shinfide ta akan kujerar na lullube ta da shawul dinta, ya murmusa ya ce "oh ni Garbati! Guduyo ta zama Mummy". Kunya ta kama ni na zum'bura masa baki. Yana mini wani irin kallo ya ce "Ba dan ciwon jiki ba, da bubbuge zan yi, ki yi ta zum'bura baki, sai an wayi gari an ga bakin ya zama tamkar na shantu". Kirki sosai ya yi mini a wannan daren domin hatta gashin da mama take yi mini na kwankwaso da cinyoyi zuwa kafafuwana shi ya mini, duk hannuwansa suka yi jawur. Muka zo kwanciya ya ce mu koma dakinsa na can gefe wanda yake kasa, shima sanyine ya koro shi daga sama. Mamakin da ya shayar da ni bai nemi komai ba. Kawai dai bai yarda yarinyar ta shiga tsakaninmu bane, a gadonta da ya kara siya mata ya saka a dakin ya ce na kwantar da ita. Na lullubeta sosai dama kuma Mama bata yarda ta kwanta a jikina sai ta sanya mana zani a tsakanina da ita. Kafin mu yi barci ya dan yi kissing dina sai dai bai yarda yaja wasannin da yawa ba. Kawai mamakin da ya bani da ya mayar da abincin Amna nasu su biyu. Na dinga mamakin baya jin karnin nono? Ashe da gaske ne matan da suke neman fatawar da mazansu suke zama tamkar jarirai idan suna shayarwa? Gudale na cikinsu. Don hakan ya 'kara mini yawan madarar da nake sha. Kullum kuma sai ya shigo mini da fresh milk yakance mutum biyu kike shayar wa dole a kula da cimar ki da kyau. Banda kaji da su kwai da yake lodosu kamar me, bayan wadda Abba yake aiko mana da su. Sati biyu ba wanda ya leko ni, nima kuma tattali da kulawar da nake samu irin wacce bai ta'ba gwada mini ba ya sanya na yi lakwas na manta da kowa kamar yadda yake so. Har kuma lokacin bai neme ni ba, duk kuwa da yaga na fara sallah tun kwanaki biyar. Lafiya lau muke zaune, kullum safiya na yiwa Amnah wanka idan zai fita office da kansa yake damke ta ya kai ta wajen Umma, ba za'a dawo da ita ba sai azahar. Suna fita kuwa Atika yarinyar da yake samo mini mai Taya ni aiki zata fito ta gyara ko ina, da alamu suka ta taba yin aiki a wani gidan ta iya aiki sosai, sannan tana iya fere dankali ta soya, ta kuma iya dafa indomi. Banda gyara kayan miya da sauran aikin girki masu sauki. Bai fara nuna zalamar sa ba sai da muka yi arba'in na dinga gode masa, domin ban yi zaton zai yi kawaici har haka ba. Ranar da komai ya faru ya kankame ni yana ta sakin maganganun masu nauyi yadda ya saba, ni kuma na lafe a jikinsa ina jin shau'kinsa na sake kekketa mini mussaman yadda ya yi komai very soft yana ririta lafiyata. Kwanaki biyar da yin arba'in din mu Amna ta fara wani irin kukan dare, idan shabiyun dare ta yi ta fara kuka ba zata yi shiru ba sai ukun dare tamkar mai lissafin lokaci. Tun yana dan yin kawaici yana taya ni, har ya fara kosa wa, domin kukan nata mai gigitarwa ne. Ni da kaina sai na koma dakina da barci, Sai dai yana dan lekowa ya mana sannu wanda a raina na kan dan ji babu da'di, nafi son ya bar barcinsa ya taya ni kamar yadda nake jin labarin wasu mazan na yi, ko irin mazan da nake karantawa a littafi suna karban yaran suce uwar taje ta kwanta ta huta. Na tuna haka mama take yi mini, komai Amna zata yi bata bani ita, sai ta ce na kwanta na huta matu'kar na bata nono ta sha. Kuma wai bayan ukun nan idan na samu ta yi barci sai ya lallabo ya jani dakinsa ya yi abin da zai yi, asuba kuma tana yi zan tashi na sallame shi, na kuma shirya ta, bana samun kaina sai wajen tara idan na yi wanka na shirya sannan nake dan samun barci kafin a dawo mini da ita. Kwanaki suka yi ta shudewa bata daina kukanta ba, sai dai yana dan raguwa, yanzu idan ta fara sha biyu to biyu saura take ha'kura. Shima kuma ba kasafai yake ma lekowar ba mussaman da a yanzu ba kukan gigita take yi ba. Ranar da ba na mantawa kwanaki biyu Amna bata yi kukan dare ba, ina ta murna, komai zai dai-dai mini domin rashin kwana a wajen Gudale ya sanya sama sama muke da shi yana ta yi mini shaguben na dauki son duniya na dorawa yarinya, akan me idan ta yi barci ba zan waiwaye shi ba, sai kawai na yi kwanciyata dan na nuna masa yanzu ina da wacce ta fi shi. Cikin kwantar da murya na ke cewa "Haba Yaya Gudale yaushe zata fika? Ha'kuri zaka kara sadda take yin shirun ni kuma barci ya ci idona, kuma a hakan fa ina zuwa maka ai". Ya ta'be baki ya ce "idan na zo na jaki da kaina ba". Wataran na yi shiru, watarana na yi karfin hali na ce "kamata yayi fa ka dinga tashi muna rainon tare". Ya ce "ai ke raina kulawar da nake baku kike yi mussaman ma na yarinyar nan, saboda kawai kin kwallafa ta a ran ki". Ana hakan rannan tun kafin shabiyu yarinyar take wani irin kuka na tashin hankali domin ba kakkautwa yi take yi da iyakacin iyawar ta. Har wani shidewa take yi. Har karfe biyu babu sauki. Atika kanta kasa barci ta yi ta dinga safa da marwa tana cewa "kawo ta Anti, bani na goye ta ki dan huta". Ni kuma ba zan iya bata ba , a dalilin kukan ya zarce na koyaushe gigitarwa. Na tabbatar mutanan cikin gida zasu iya jiyo ta. Amma Gudale ko leke. Wajen karfe biyu da abin ya tsananta nima kawai sai na fashe da kukan tana yi, ina yi, Atika ta rasa inda zata saka ranta. Murya na rawa ta ce "Ki yi ha'kuri Anti zata daina kuka, ko na je na kira miki Mama ko Umma halan bata da lafiya ne?" Wani irin kuka ya sake goce mini. Yarinya karama da bamu hada komai ba ta ji kuka ta fito ta damu, amma uban yarinya yana gidan yana shan barcinsa babu wata damuwa. Na goye ta ina cewa "Bari asuba ta yi Atika kada a tayar musu da hankali, zama uwa ai ba karamin al'amarine mai sau'ki ba." Ina ta jijjiga ta tare da kewaya falo zuwa daki, Atika na ta yi mini sannu a ranar son yarinyar ya shige ni, domin na ga tausayi karara a tare da ita duk kuwa da ba zata wuce shekaru sha hudu ba. Sai da kukan ya dan lafa na doshi dakin Gudale har lokacin tana yi duk da dai ya yi sauki da alamu barci ne zai dauke ta. Ina tura kofar na tarar da shi a tsakiyar gadon da waya a hannunsa, na yi turus raina ya yi koluluwar baci, murya na rawa tunda har lokacin da hawaye a idona na ce" "Idonka biyu Gudale? Yanzu duk wannan kwakwazon da ya cika gidan ashe kana ji? Wacce irin 'kiyayya kake gwada mini ne, har ta yi naso ta shafi abin da ka haifa a cikinka?" Ya dago a tunzure ya ce, "Allah Ya nuna mini ranar da za ki gode wa kokarina. Shin ha'kkina ne na fahimci matsalar jaririya ko kuwa hakkin uwa?" "Ba dama ki ga na runtsa sai kin addabe ni akan yarinyarki, wai a kanki aka fara haihuwa ne da kullum sai kin yi mini sanadin bacin rai akan ta? Baki da lokacin komai sai nata, ba ruwan ki da hakkina matu'kar yarinyar nan tana hannunki. To yanzu me kike so na yi miki? Nono zan bata ko goyon ta zan yi ne? Haba na gaji da wannan fallin naki na sabuwar uwa, shin jiya ta fara kuka ko yau? Ko kuwa jinya take yi, kin fa'da mini ban kawo magani ba?" Na juya na bar dakin zuciyata kamar ta fashe. Shikenan washagari ya dauki gaba da ni, ko tsayawa ya karya bai yi ba, bare ya kai ta wajen Umma. Mama da kanta ta shigo ta ce taji kukanta tana dubawa Ashe ciwon kunne take yi ruwa a kunnen sosai, abin tausayi. Mama ta dinga fa'dan ai da ban biye wa miji na gudo ba ai da duk na fahimci irin wa'dannan matsalolin. A take na buga wa Anti Sakina waya ta ce "Na kawo ta asibiti tana jiranmu. Muka fita tare da Mama ta yi kofarta yayin da ni da Atika muka shiga kofar Umma na gaisheta ta amsa Kamar akan dole, na sanar mata zan kai Amnah asibiti wajen Anti Sakina. A lalace ta ce "Wa zai kai ku?" Na ce "Adaidaita zamu hau". Ta kyabe baki ta ce "Allah ya bata lafiya". Na mike muka fito. Cikin Sa'a muka samu adaidaita na dauke shi drop har asibitin Malam. Dake Sakina a bangaren yara take nan da nan ta mana jagora har gaban babbar likitar yara ta asibitin gaba'daya *Dr Fatima Hanga*. Aka gama bincike ciwon kunne ne kawai. Aka goge ruwan aka hado ni da magunguna muka dawo gida. Ko abinci na ki yi, indomie kawai na dafa mana ni da Atika muka karya tunda bamu cu komai ba muka fice. Ganin barci sosai Amna take yi ya sanya nima na kwanta kusa da ita barci mai nauyi ya yi awon gaba da ni. Da rana bai dawo ba, nima na ji da'din hakan ina tashi na tarar da Atika ta yi karambanin dafa farar shinkafa ta yanka salad ta wanke ta barshi a colonder ta rufe da murfi. A falo na sameta tana kallo. Ta mini sannu, na shiga kicin ta biyo ni, na bu'de kula na ga shinkafa, har da karas a ciki ta yi kyaun dahuwa. Na kalle ta na ga alamun tsoro tsoro a tare da ita. Na murmusa na ce 'Madallah da Atika! ashe har haka kike da aiki?" mussaman yadda ta gyara kicin. Dadi ya kamata na yadda na yabe ta na kuma gode. A raina na ce wato dan adam yana da son a yabe shi, a kuma gode masa idan ya yi abin kirki. Atika yarinya da ita ta ji dadin yabawar da na yi mata duk da aikin ku'di take yi. Amma Yana matu'kar wahalar gaske Yaya Gudale ya yaba mini ko ya gode mini. Na saki hucin takaici na ce "To ya baki fito da miyar kin dumama kin ci ba?" Ta yi kasa da kanta ta ce "Ai ban fa'da miki ba, sannan ba zan iya zuba wa da kaina ba ina jin tsoro". Ban tambayi dalilin tsoron ba na ce mata "Daga yau idan kin girka abinci na miki laminin ki zuba wanda kika san zaki cinye, idan baki koshi ba ki 'kara, 'karya da gulma ne bana so kina ji, amma ki dinga zuba abincinki kina koshi. Na dumama miyar na dauko plate din da na ware mata na zuba mata sosai dan nasan ta da ci. Ni kuma cinta baya damuna tunda morarta nake yi ba ka'dan ba, kuma alhakin ciyarwarta yana kanmu, ta yini tana mana bauta an rabo ta daga gaban iyayen ta ba batun karatun arabi bare na boko, shin idan ba'a basu abinci sun koshi ba ina ake so su je su ci? Bayan suna mana hidimar da baza mu iya yiwa kan mu ba. Take tunanin saka ta a islamiyya ya zo mini, bai kamata na barta cikin jahilci kashi kashi ba. Tunda ta rasa na neman duniya wato boko, to gara ta je ta ji abin da zai taimake ta ta san Ubangiji ta yadda zata kyautata ibadarta, ta tsira da lahirarta. Tunda na fara disa mata maganin bata sake kuka ba, dama kuma likitan ta tabbatar mini tunda kurjin ya fashe to zata samu lafiya. Kwanaki biyu muna yar shariya a dalilin naje asibiti ban sanar da shi, ban kuma je na yi masa bayani ba. Kwana na uku na dinga jin kamar na yi masa magana, amma ina tuna yadda ya banzatar da mu shikenan sai na ji raina ya sake baci. A cikon kwana na hudu ya ha'kura ya sauko daga nasa fishin zai fita da sassafe ya shigo yana cewa "kin shirya ta ne na kai ta?" Na girgiza kai na ce "Je ka, kar a bata maka lokaci, ko riga ban sa mata ba, Atika zata kai ta". Ya zauna a bakin gadon yana son sai mun hada ido ya sakar mini kallon da yake susuta ni, ni kuma na share na ki yarda na kalle shi. Ya sassauta ya ce "Guduyo wai ki dinga wula'kanta ni akan yarinyar nan, yau da ba nine ubanta ba, tabbas sai dai a wayi gari aga na ha'diyi zuciya na mutu. Duk wani hakkina kin yi fatali da su, dan kawai kin haihu. Da haka duk mata suke yiwa mazajensu na rantse ba wanda zai yarda ayi masa haihuwa. Ba ruwan ki da zuwa wajena, yanzu ko tsafta ce mini shi kin daina. Ba ruwan ki da cikina, na ci abinci ko ban ci ba duk ba matsalar ki bane saboda na fa'di abin da bai miki da'di ba akan 'yar gold". Na numfasa na ce "plz mu bar maganar nan, tunda ka bu'kaci na gyara, zan gyara shikenan?". Da sauri ya ce "To yi gaggawa ki shirya ta na kaiwa Umma ita da kaina. Ta ji dumina, ba naki kawai ba Zan je office na dauko excuse ki shirya tarba ta, sosai na yi kewar ki Guduyo". Ya fa'da yana kanne mini ido. Na tsuke fuska na ce "Gaskiya ba sai ka dawo ba, dan barci zan yi". Ya sassauta ya ce "To Gudidina! Yadda kike so hakan za'a yi, ba zan dawo yanzu ba, ki kwanta ki yi barcinki ki huta. Amma zan dawo cin abinci da rana daga nan ba zan koma ba. Plz kar ki ce mini a a kinsan dai bana son ki zame mini tamkar doll a shimfida shiyasa nake son ayi cikin so da walwalarki. Me zan taho miki dashi, me kike sha'awa?" Na daure fuska na ce "Bana bu'katar komai". "Kash! Sadiyayye ana baki kina tankwabar wa. To ki shirya zamu fita idan na dawo". Na yi shiru na cigaba da shirya ta. Duk share shin da na yi sai da ya jira kuwa ya karbe ta suka tafi. Na yi zaune ina mamakinsa, dake yana da bu'kata ya ajiye fishin! Na sani kuma ba karamin aikinsa bane yana samun abin da yake so ya sake yi mini wani sabon iskancin, koma ya dora gabar a cigaba da yin ta. Ai kuwa da rana sai gashi sabe da Amnah tabbacin sai da ya fara shiga wajen Umma. *Ban ta'ba tunanin xan samu matsala a wannan tafiyar ba. Amma kasancewar Ubangiji ne yake sarrafa al'amura, abin ya juya ta inda ban ta'ba zati ba. Zan dan dakata zuwa lokacin da al'amura zasu dai-daita mini, bana fatan na dauki lokaci mai yawa.* *Allah ya sa za'a fahimci halin da nake ciki a kuma yi uzziri*. *Na gode sosai*. # Team Gudale. # Team Guduyo. # Surayya Dee ✍️. # Ana tare 🤝. 2/8/23, 10:25 - Buhainat: *Ummu Muhammad collections* *Tana sayar da dukkan nau'in sutura masu kyau zababbu kuma masu sau'kin farashi* *Tana sayar da takalma da jaka masu kyau* *Tana ha'da lefe* *Tana ha'da kayan haihuwa* *Tana sayar da Data* *Tana yin adashe, Kuma fasihiyar Tela ce* *Tuntube ta a wannan lambar 08063358662* *Siyan na gari aka ce maida ku'di gida" *SDK* *67&68.* Na hadiye fishina na gabatar masa da meat pie da lemo. Ya dinga jaye jayen magana, har ya tisa ni a gaba muka fita. A hanya ya kalle ni ya ce "zoben gold zan siya miki, kinsan ban siya miki komai ba as gift duk iyayen yarinyar ne suka yi komai. Farin ciki ya mamaye ni na murmusa ka'dan na ce "Thank you". Da kaina na zabi wanda nake so ya biya ku'din babu musu. Muka dawo ana shirin yin la'asar. Ya shiga da yarinyar wajen Umma ya wuce masallaci. Tunda ya dawo yake rawar jiki, ban samu kaina a hannunsa ba dai da yammaci ya yi sosai. Al'amarin Gudale na matu'kar takura ni domin rashin nauyinsa da cikakkiyar lafiyarsa na sake kara masa jarumta domin yana shafe lokaci mai yawa yana abu daya. Ya iya biyar da ni, yana murza ni yadda yake so ne, yana kuma sarrafa ni ta yadda zan dauwama a cikin sonsa da kulafacinsa, na kan manta duk wani kayan takaicinsa da zarar na shiga hannunsa. Sa'ar da na yi bashi da ha'kuri a wannan fagen, dana fahimci hakan sai nake iyakacin kokarina ina nuna kawaici da alkunya akan lamarin ta yadda nake samu na ja zarena a other room. Duk wulakancinsa matu'kar bu'katar abin ta ciwo shi sai ya tattaro duk wani siffar kamala da rarrashi da kuma wayo dan ya same ni yadda yake so. A haka rayuwar ta cigaba da gurgurwa yau fari gobe baki. Amma a gareni bakin yafi yawa domin ban huta a hannun Gudale ba ban huta da shagulatin bangaron da Umma take yi mini ba. Wani lokacin ma idan ta zaunar da shi ta karanta masa karya da gaskiya sai ya zama sanadin fada a tsakanina da shi, sai ya share ni. Wani lokacin na yi ta bibiko ina bashi ha'kuri a dalilin an jarrabi zuciyata da gudun bacin ransa. Wani lokacin kuma na daure na zuba masa ido. A haka har Amna ta cika shekara guda. Yarinya mai matu'kar kyau gashi tana samun kulawa, ga kuma suturu irin na 'ya'yan gata tsadaddun gaske. Ko ina yarinyar ta shiga daukar ido take yi. Antin Zaria bata dauki al'amarin Amnah da wasa ba. Daidai lokacin nima na kammala karatuna na fito da sakamako mai kyau. Na fara bautar kasa a asibitin Malam. A lokacin Amna ta yi shekara daya da rabi. Tuni Umma ta yayeta a dalilin mai sunanta tana kasar Jamus tana wani course na shekara daya tare suka tafi da mijinta. Saboda shi ya yi ritaya. Dai dai lokacin Yaya Gudale ya fara wani irin zazzabi, ba dama na fara dafa abinci zai fara amai. Ban isa na saka turare ba, bare shi ya saka da kansa. Ga yawu, duk wani laulayin ciki haka ya bayyana a tare da shi. Bai fita daga wanccan k'angin ba, wasu irin marurai suka fito masa har a hammata sosai ya ke jin jiki. Tsakaninsa da abinci sai farar taliyar hausa da manja. Ruwa sai an nemo masa na borehole mai zartsi. Tausayi yake bani domin shi ko pure water baya sha sai na roba, amma cikin lokaci kalilan rayuwa ta yi juyin waina da shi. Kowa ya tsorata aka dinga fargabar ko wani ciwo ne ya shige shi mai tayar da hankali. Yayin da ni kuma nake ta fari ina budewa, komai nawa ya cika, na yi wani irin kyau na ban mamaki. Tsawon lokaci yana fama da amai da zaben abinci. Bai samu kansa ba sai da ya shafe wata biyu. Amma maruru kam sauki suka yi, domin da wani ya warke, wani zai dawo. Duk wani gwaje an yi masa an ce lafiya lau. *Asibiti* Wani zuwa asibitin Gudale ya yi, wani likita da ya gaji da zaryar Gudale a asibiti ya ce "Anya ba Madam ce ta bar maka laulayin ciki ba? Wannan ciwon naka ina tantama idan ba laulayi kake yi ba." Da mamaki Gudale ya ce "Dama ana iya yin haka ne Dr?" "Yes of course wasu mazan idan matansu suna da ciki suna tsintar kansu a irin wananan yanayin amma ya banbanta da yadda kowa yake yin nasa. Sannan masu yi din basu da yawa. Jikin Gudale ya yi sanyi. Ya dawo gida cikin waswasi mai yawa. Ya fara sanya mini ido sosai. *** Ba zato washagari ya bini asibiti ya sanya aka mini test ai kuwa sakamakon ya nuna ina da ciki na wattani uku, a kuma lissafin jinyar Yaya Gudale ya fara ne tun cikin bai fi sati biyu ba. Muka dawo gida yana ta sababin ya gode da muguntar da na yi masa, me nake nufi da shi ne da zan turo masa ciwo ni kuma na yi ta yin kyau ina sake yin takama?". Na dinga rarrashi ina gintse dariyar da take neman subuce mini, ina tuna shekaranjiya ma sai da naga yana share kwalla yana fa'din ya Allah kasa ba ciwon hanta ne ya same ni ba. A hankali na ce "Allah ne mai ikon saka ciwo ko bayar da lafiya. Ka kuma sani da ina saka ciwo Yaya Gudale a cikin hayyacina da kai zan yiwa rowar sa, haka nam da ina da ikon cire maka wannan halin da kake ciki da tuni na yi. Ka yi hakuri". Hakan muke ta tafiya, sai da cikina ya shiga wata na biyar sannan ya samu ikon cin abinci, ya kuma daina yin marurai. Sai me? blBa sai kuraje a baki kuma suka baibaiye shi ba. Ko ruwa sai da dabara zai sha, kusan kurajen nan sun fi wahalar da shi akan jinyar domin komai ya saka a baki da azaba zai hadiya. Ya yi matu'kar zubewa. Rannan ya siyo youghrt amma yana sawa a baki ya mike tsaye. Tausayi ya kama ni. Na ce "Sannu Yaya Gudale na ga kuma babu yaji a ciki". Ba'kin ciki ya kama shi ya nuna ni da yatsa ya ce "ke kina da bakin yi mini magana? Muguwa kawai, ai na sani kulawar da na baki a cikin Amna kika raina, sau daya tak na ce miki mai langwai shine kika dinga tashi cikin dare kina buga mini Tabbati yada da Izaja'a ko? To ki je an karbi addu'arki sai dai ki sani kama tu dini tu danono zan miki. Ba zaki kuma ganin sassauci a waje na ba. Ke wannan da kina da dama wataran sai dai cikin dare ki daure ni. Na ji saukar bulalar lalle a jikina tsabar yadda kike da cikina. Kuma ki bi a sannu mugunta fitsarin fako ce." Gaba daya lamarin dariya yake bani kwarai da gaske, bansan ya aka yi ba dariyar ta kwace mini, na dinga yi ba kakkautawa. Ai kuwa ya fusata kwarai da gaske a wannan lokacin tashin hankalin dana fuskunta ba ka'dan bane. Domin ina ji ina gani ya haramta mini kunna gas. Ya je ya lodo mini gawayi. Ya kuma yi rantsuwar da shi zan dinga girki tunda ya gano ina da hannu wajen halin da yake ciki, ta baya son warin gas ba kuma zai mini uzziri ya cutu ba. Ya haramta shigo da ruwan sha ko da pure water ne kuwa. Tsakanina da pure water sai na je asibiti. Amma matu'kar a gidansa ne sai dai na sha wanda yake sha. Haka nan ko roll ya kwashe su ya haramta mini sakawa. Ranar da na dinga ro'kon ya bar ni na dinga saka roll saboda kada na dinga bashi, gashi ina shiga cikin jama'a. Ai abin da ya biyo baya ba mai sau'ki bane, wai wa nake da shi a waje da zance za'a ji ina tsami? Shine mijina shi kuma tsami tsamin yake sha'awa, yake muradi. Ya kalle ni ya ce "Ashe kirkina yawa ne dashi lokacin da kika dinga mini amaye amayen ba kya son turarena, haka na tattra na barshi. Har dakin na canja a sama wanda babu irin wannan kamshin amma baki gode mini ba. Da kika dawo kina son kamshin kuwa har fesa wa nake yi ya hau kaina duk dan na burge ki, ashe ke kina nan kina mini tanadin mugun nufi." Ya girgiza kai ya nuna kansa ya ce ni kika yiwa wannan iyashegen ko? Kuma dan munafunci da son zuciyar jama'a ayi ta faman cewa kina sona. Barin Sakina da har gorin soyayyar da kike yi mini take yi. To ki ki saurari hukuncin da zai biyo baya. Umma tana sake yi masa famfo, tana fa'da masa duk namijin da yake yiwa matarsa laulayin ciki to tabbas idan bai tashi tsaye ba ta gama da shi kenan, domin komai sai ta zartar irin wadannan matan sune matan jaraba, matar da zata saka namiji ya zagi uwarsa. Wannan cikin na shiga tsananin kunci kala kala domin ya gasgata maganganun Umma. Mussaman da take yawan ce masa zaka dinga jin idan baka tare da ita ka shiga kunci ko gidan ya yi maka fa'din gaske da kuma kunci, to tabbacin an rubuce ka a allon karfe ne. Kafin watan haihuwa ya tsaya na kumbura na yi sab'o sab'o ga haki tabbacin jinina ya hau. Wannan haihuwar ma aka tabbatar ba zan iya ba sai dai a sake yi mini c.s. Ku'din da ya bani na siyayya bai wani kai ya kawo ba. Ban yi korafi ba, domin fata nake na rabu da cikin lafiya. Komai zai biyo baya mai sau'ki ne. Ranar 21 ga watan July aka sake fito mini da kyakkawar jaririya ta, katuwar gaske tamkar bata san taskun da nake ciki ba. Gashinta sak irin na Gudale baki sidik har idonta dan sai da aka datse shi sannan take iya bude ido. Tun tana jaririya ake fadin ni ta iyo sai dai ta kwaso abubuwa da yawa na Babanta. Ban saka Gudale idona ba sai da na yi kwana uku da haihuwa a dalilin duk sadda zai zo ina barci. A ranar da muka hadu din bai iya boye abin da yake ransa ba. Ya tsaya a gabana ya ce mini "kin kyauta Guduyo bayan addu'ar jinya sai kika sake yin addu'ar ki yi ta jera mini mata, na sani kin ro'ki Allah hakan tunda lokacin haihuwar Amnah sai da kika tabbatar mini sai kin fara haifar mata. To kije ki karaci mugun yancinki, tunda na gane harshen ki da dikon baki nake jin tsoron kalamin bakinki domin komai kika fa'da sai ya zama wajabat". Na zuba masa ido ina mamakin wai menene matsalar Gudale ne? Ni shaida ce babu jahilci ko na digo a tare da shi. Sannan a birni aka haife shi, ya kuma girma a cikin birni. Ya girma a tsakiyar zakwakuran masu ilimi da azanci. amma idan ya yi wani kalaman sai ka yi zaton wani sabon tuba ne da bai san komai a addini ba. Haka nan sai ka yi zaton bai ta'ba shiga aji da nufin daukar kowanne irin ilimi ba. Kalaman sa idan yana cikin fishi ko abu ya zo masa ba yadda yake so ba, yafi dacewa da kalaman mutanan da basu taba shiga aji da nufin neman kowanne irin ilimi ba, mussaman wadanda suka rayu a karni na ashirin. Domin a wannan karnin na 21st century da duniya ta samu cigaba na ban mamaki ko mutum bai je makaranta ba, zai samu ilimin da zai fitar da shi a cikin duhun jahilci mussaman idan yana cudanya da masu ilimin. Amma gaba'daya Umma ta taka muhimmiyar rawa wajen gurbata tunaninsa da kalamansa. A hankali na ce "Har yau ba'a haifa maka 'ya'ya mata ba Yaya Sadik! Sai a gaba ma In sha Allah. Dan Allah ka nuna mini bolar yara mata. Ka dinga gode wa Allah wasu da yawa sunan suna neman haihuwar Ubangiji bai basu ba, ba dan ya manta da su ba, sai dan haka yake son ganinsu ya kuma gwada karfin imaninsu, domin Ubangiji baya kuskure. Amma kai ya baka, ya sake k'ara maka amma kana yi masa izgilin ba jinsin da kake so ya baka ba. To ni ina sonsu, ina fatan su zama tamkar su Antin Zaria matayen da sun zarta wasu mazan sau dubu, asalima da bazar su wani namiji yake taka rawa. Ya kafe ni da ido ya ce " cabdi jam! Allah ya jikan ki Umma ba dan kin mutu ba. Na gasgata ki da kike fa'din Halimatu ba matar arziki ba ce." Ya girgiza kai ya ce "Zaki san kin zage ni, zaki san kin ce mini mata sun fini anfani sune garkuwata. Yau duk zan tona miki asiri a gaban Umma! Zan fadi irin musguna mini da kike yi, zan fallasa irin tsananin ha'kuri da nake yi da muguntar ki". Tsakin da ban yi da niyya ba ya subuce mini mai karfin gaske. Ya ce "waton har Uwata ma baki bari ba? Kakar Amnah kika yiwa tsaki ko?" Hawaye ya balle mini na ce "Duk abin da kake mini Allah na kallon ka ai. Na tabbatar idan na mutu a yau kai ne ka kashe ni. Tun ina da ciki kake gana mini azabobi daban daban, yau kwana uku bamu ga juna ba, ka zo ba sannu, ba komai ka tisa ni a gaba da cin mutunci da wulakanci ba ruwan ka da halin da zan shiga. Ba komai da sanin Allah ai" Jikinsa ya dan yi sanyi ka'dan. Ya fice ba tare da ya ce mini kala ba. Yana fita Sakina ta shigo na dinga dabarar dauke hawayen idona. Ta dinga tambayar ba'asin kukan nawa. Na kasa bata amsa saboda har lokacin ina ganin ba karamin muzanci bane na fa'di halin da nake ciki da Gudale mussaman a gaban Sakina da ba irin togaciyar da bata yi mini ba. Ganin da ta yi na hadiye kukan na kuma boye damuwar da nake ciki sai itama ta bar maganar. Ashe tuntuni ya yiwa yarinya huduba da Saudat sunan Umma kenan. Tun ina asibiti Sakina ta lankaya mata Afrah. Goyon ciki da haihuwar Afrah yana cikin thought time din da bana manta wa domin wahala da wulakancin dana fuskanta a hannun Gudale. Har na gane ashe lokacin haihuwar Amnah da nake ganin bai yi wani zumudi ba, amma kuma yana dubata yana lekenta sannan da ta fara kwari yana daukarta duk kuwa da damketa yake yi. Ashe ba karamin kulawa da soyayya ta gani ba. Domin wannan yar ko kallon inda take ba ya yi. Na sani dan ya sake jefe mini takaici ne. Ya kuma ci riba domin akai akai nake share hawaye. Yayin da shima yake cike da takaicin na yi masa addu'a ya mini laulayi mai zafi, sannan na bishi da fatan na haifi mace to na je burina ya cika. Sai na yi rainon ta ni ka'dai. Ai ya yi tasa wahalar. Yanzu kuma sai na yi tawa. Dai-dai da pant bai kara akan kayan da na tsinto tun kafin haihuwar ba. Sai dai bani da matsalar kayanta tunda ina da sabbin kayan Amnah da bama ban bude ba saboda yadda take da kayan jarirai kamar na hauka. Haka wannan din ma yan'uwansa da nawa sun baibaiye mu da da rigunanta da duk abin da zan nema. Watan Afrah uku idan ka ganta sai ka zaci ta yi watanni biyar. Domin kuwa ta zama buleliya ga gashin Gudale ta debo yayin da shi kuma na Umma ya kwaso. Ta zama abin so da sha'awa har tafi Amnah sha'awa saboda ita wannan mai jiki ce. Shi da ya kudire ba zai nuna kulawa akanta ba, na sha ganinsa yana satar idona yana yi mata hotuna mussaman idan na shiryata na zaunar da ita cikin kekenta na koyon zama mai kyau. Matu'kar ina kicin ko daki ya dinga yi mata hoto kenan, ko ya kafe ta da ido yana murmushi, amma fa ba zai dauketa ba, ba kuma zai yarda ya yi akan idona ba. Amnah kuwa tafi zaman wajen Umma domin idan abin nasa na kusa kuskure kadan zata yi irin na yaro zai cire tausayi ya zaneta da tsinken tsintsiyar kwakwa. Na sani kuma da gayya yake yin hakan sai ni kuma nake daurewa ko a fuska bana nuna takaicin da nake ji bare na tofa wata magana ya ci mutuncina. Shiyasa ta fi son zama wajen Umma, tsoronsa take ji sosai. Yayin da Umma take ji da su tamkar tsoka a miya abin kamar almara, ita bata ji takaicin haihuwar matan da nake yi ba. Na taba jin tana fa'dawa kawarta ai Gudalena komai nawa ya debe shi, hatta haihuwar mata a farko, ga yaransa nan lafiyayyu kyawawa. Kuma abin burgewa jininsa yafi yawa a jikinsu. Ko wannan mai sunan nawa da ake ganin kamar uwar a jikinta ai dan dai tana da garin jiki ne, amma haka na yi goyon Yayar su ta Zaria katuwa tana rinjayata. Addu'ar da nake yi musu kada Allah ya sanya nono yayi tasiri akan su. Su gado nunkufurci da wuyar zama." Kawar tata dake itama hamshakiya ce ba wai yar fadanci ba ce, domin itama nata mijin ya tumbatsa da arziki. Kai tsaye ta ce " Ai kuwa tasirin nonon uwa a wajen danta dole ne. Kamar yadda kika yi tasiri akan ubansu haka suma tasu uwar zata yi. Kawai a cire son zuciya a masu kyakkawar tarbiya a barsu kuma suga girman uwarsu, domin duk wahalar da zaki yi dasu dai, ba ke ce uwarsu ba. Wataran ma sai su iya nuna miki waccan facalar ta ki, tafi kima a wajensu saboda tasirin nono. Kar ki shiga shirginta da ya'yanta domin har abada d'a mallakin uwarsa ne". A sanyaye Umma ta ce "Na jiki kuma zan kiyaye, sai dai nima har abada bana sonta, ba kuma zan so ta ba." "Kar kice haka domin baki san me gobe zata zo miki da shi ba. Ki daina damuwa k'awata". Jin motsin zasu fito ya sanya na yi azama na zagaya na bace dan kada ta ce ina yi mata labe. Tun a ranar na sake ganin girman Hajiya Bilki domin tun fil'azal bata yarda da son zuciyar Umma zata fa'da mata gaskiya sai dai ba kasafai take dauka ba. A wanna tsukun na samu offer aiki da asibitin Malam. Sosai na yi murna domin a yanzu ri'ke dubu daya wahala take yi mini. Gudale ya rufe bakin aljihunsa, komai na amfani ina da shi, amma fa babu kudi a hannu. Ko Abba ne ya bani ku'di ko Yaya Abdallah, ko kuma Baba ya bawa su Amnah kudi matu'kar ya kyalla ido ya gani, to kuwa sai ya san yadda yayi ya karbe su da sunan rance. Bansan meyasa ba yake ba'kin cikin ya ganni da ku'di. Tun Sakina tana mini fa'dan na daina bashi tunda duk wanda ya zo gidana ba zan iya bashi kyautar kudi ba. Sai dai ko kayan kwalliyata zan na diba na bayar, suma da suka k'are na koma cewa a gaida gida. Su Anti Maimuna suka fara raddin rowa ce da ni, su zo gidana da yara amma ba zan iya kyauta ko ta allura ba. Ai sun san ba hakan nake yiwa dangin uwata ba. Wadannan matsalolin da suka kewaye ni ya sanya na yi murnar aikin ba ka'dan ba. Nan da nan kuwa Gudale ya ci layar shifa ba zan yi aiki ba. Na kafe sai na yi, rikici har gaban Abba. Ya kuwa fatattake shi ya ce "Kana da son zuciya Sadik! Ina ce dukkan sisters dinka aiki suke yi. Ko Ummu da bata aiki kasuwanci take yi mai karfi, akan me zaka hanata bayan komin yaya kaima sai aikin ya taimake ka?" "Abba kowa da ra'ayinsa ni fa ko makarantar nan da kyar na ha'kura ta kammala. Ni fa tashin hankalina na dawo ban ganta ba. Ni gaskiya bana so. Menene bana ajiye mata? Bayan siyayyar da har yanzu kana yi mana duk watan duniya Abba. Nima Ina yi gata nan a zaune ka tambaye ta. Ni gaskiya nafi son ta zauna a gida ta yi aikin tarbiyar yara. Ni kuma na fita na nemo, amma ba zan iya wannan al'amarin ba." Abba ya murmusa ya ce "Sadik manya, wato na da'de banga yaro mai akidar rikau irin ka ba. Aikinta na ceton rai ne, shiyasa muka karfafa ta yi karatun dan ta taimaki al'umma mussaman yan uwanta mata. Yanzu kuma ka zo da wani maganar banza, na baka umarnin ka barta ta yi aikinta". Tunda ga lokacin muke cikin rashin nutsuwa domin ya ja kafe shi ba zan yi aiki ba, mussaman da yake zargin Yaya Ashir ya taimaka wajen samuwar aikin. Yayin da nima na kafe zan yi aikina tunda ina so, ina kuma da bu'kata. A wannan sadarar ya sake birkice mini abu ka'dan zai ha'da mu, zai zabga mini mari, ko a gaban su Amnah ne. Idan ta ga ya mareni din nan idan da safe ne ko rana idan ta ta fice to sai an yi kwanaki bata leko ba. Idan ta je ta dinga rawar jiki tana cewa Ummah "Daddy ne ya doki Mummy". Yayin da Umma take Jin da'din hakan tana sake samun nutsuwar ban fi karfin danta ba, ban halaka shi ba. Ba kuma ta ta'ba nuna masa ma ta sani ba, bare ta tsawatar masa. Sati biyu da fara zuwana aiki tashin hankalin da yake mini ya tsananta. Domin ya riga, ya kudire tunda an masa karfa karfa to lah shakka ba ni Jin da'dinsa. Wani mari da ya yi mini daga maganar fatar baki sai da jini ya kwanta a gefen idona ga yatsun hannunsa a ru'du ru'du a fuskata. Ya fice ya barni ina wani irin kukan da shi da kansa ya taba shi kwarai da gaske. Daga na ce masa ya daina fishi tunda ban yi masa komai ba, ya daina tayar mini da hankali haka nan. Shikenan ya mini wannan barin makauniyar tsananin gigitar da na shiga a wajen na zube na fashe da wani irin kuka ina fa'din "Allah na tuba, na sani musun da na yiwa Abba da Mahaifiyata ne. Allah a sassauta mini haka nan". Ai kuwa ya tsaya cak, tabbacin maganar ta shige shi ainun. A sanyaye ya bar gidan. Na jima ina kuka Afrah da take rarrafe ta rarrafo ta kwanta a jikina. Hakan da ta yi kuka ya sake goce mini. Na tuna dazu da na shiga wanka ta dinga tsala kuka amma ubanta yana jin ta yana ganin ta bai kula ba. Ko a zaune muke a falo duk wasan da zata yi ba zata taba rarrafa wa wajensa ba. Tausayina da nasu ya kama ni, na fara nadamar kafewar da na yi sai Gudale. Na dinga ganin wautata da na yi zaton zan iya sauya shi. Na jima ina kuka, sannan na sunkuci y'ata na shiga kicin da yafi kusa da ni. Na wanke fuskata na dawo falo na zauna ina shayar da ita, ina ta sakin ajiyar zuciya. A hakan Sakina ta turo kofa ta shigo. Ganin ta zuciyata ta nemi karye wa. Amma na tattaro dukkan jarumta na ha'diye kukan. Muka gaisa tana bina da kallo. Ta kasa hakuri ta ce "Yanzu Na Moriki ne ya miki wannan marin amma da yake ke jaka ce kika na'de kafar sake zama da shi, har kina shayar masa da yarinyar da baya gode miki hidimarta?" Idona ya ciko taf da k'walla ina jin bai kamata Sakina ta gane na kasa wanke allon nawa ba. Na ha'diye kukan na ce "Faduwa na yi na bugu a gefen idon ai sa'a ma na yi." Wani irin fishi na ga ni a tare da ita. Ta mike ta ce mini "kazar ubanki da wannan maganar Halimatu". Hawaye ya kwace mata ta ce "Zaki zauna ya kashe ki ne? Bayan hawan jinin da kike fama da shi, shine kike son sai ya manna miki ciwon zuciya? Ni zaki kallah ki ce mini faduwa kika yi? Shin wannan shatun yatsun na uban waye a fuskarki?" Na yi kasa da kaina na ce "zafin da ya gigita ni ne na mari kaina ban sani ba." Ai kafin na rufe baki kawai ta rufe ni da duka, tana yi tana danna mini ashariyoyi kala kala. Daga karshe kuma sai ta rungume ni tana fashe wa da kukan da ban ta'ba ganin ta yi irinsa ba. Hakan ya sanya nima nake kukan da na dade ina son yi a kafadarta ina boye wa dan kada na kunyata. Tsawon lokaci muna kukan ba Wanda ya rarrashi wani. Sai ita ta yi karfin halin tashi ta dauko mini hijabi, ta miko mini bayan ta dauke Afrah da ta yi barci. Ta ce "Tashi mu je Abba ya ga wannan dabbacin masoyin na ki". Na daure fuska sosai. Na ki yin ko da motsi. Juyin duniya na ki tashi, da ta bude mini wuta na ce mata "Ba inda zani sai na gama aikina. Ta ce "Ina Atika?" Na sake bata rai na ce ta tafi garinsu. Ganin yadda na ha'de rai, sai ta shige dakina ta shimfi'de yarinyar ta dawo ta ce "To tashi na taya ki aikin". Sai da muka kammala tas. Na yi wanka zuwa lokacin jini ya sake kwanciya sosai a idona. Ga mamakin Sakina da ta ce "Na tashi mu tafi". Na murtuke na ce" bansan wannan maganar ba, ni na riga na yafe masa". Ai kuwa ta mike jiki na rawa ta ce "Wannan kuwa shine karya Halimatu. Ni zaki yiwa irin wannan iyashegen? Ki sani aikin da ko a gidana bana yinsa dan kawai mu tafin, mun gama kin yi wanka sannan ki ce ke ba inda zaki je. Na rantse miki zan yi miki duka, ko kuma na kira Abban ya zo ya same ki anan tunda bai isa ki je masa da damuwarki ba, shi sai ya zo ai tunda baki da kunya da mutunci". # Team Gudale # Tewm Guduyo # Surayya Dee ✍️ # Ana tare 🤝. 2/8/23, 10:25 - Buhainat: *SDK* *69&70.* Jin hakan da ta ce "Na zube na rike mata kafa ina kuka ina cewa ta yi ha'kuri ta taimke ni. Idan Abba ya ji kashe mini aure zai yi". Wani irin matsanancin tausayina ya danneta ta zauna kan gadon ta sake fashe wa da kuka. Ta yi iyakacin yin ta. Ta tashi ta wanko idon ta a bandaki.Ta tsaya ta kalle ni ta ce "Ba zan ta'ba iya wannan ha'kurin na ki ba. Soyayyar da kike yi ta wuce ka'idojin hankali. Ha'kuri a irin wannan k'adamin cutar wa ne Halimatu". Ta daga kai ta numfasa ta ce "Allah ka sassauta mata wannan jarabtar, Ubangiji mun sauke nauyin zumunci, Allah ka kawo mata mafita." Hawaye ya balle mini, haka kawai nake jin Soyayyar Sakina tana bin dukkan jikina. Ina jin ta fiye da yadda nake jin Yaya Al'amin. Na goge idona da tissue ina fa'din "Na gode! Ki taimake ni kada ki fitar mini da wannan sirrin, dan Allah". Ta girgiza kai ta ce "To! Amma ban miki al'kawarin wataran ba zan fa'da ba." Tana shirin barin dakin ya shigo. Ya tsaya yana kallonmu kowanne da k'walla a idonsa, jikinsa ya sake mutuwa. A sanyaye ya ce "Sakina me ake tattauna wa ne, ke da yar dakin naki?" A banza ce ta ce masa takaici da bakin ciki". Yayin da ni kuma na ce "Sannu da dawo wa". Nan da nan ya samu kwarin guiwa ya ce "yauwa Gudidina ai ina ta kiran wayar ki, na ji me zan taho miki da shi, rashin daukar da baki yi ba, shine na dawo, na ga ko lafiya?". Na murmusa na ce "Da na je gyaran sama ne, na manta ta a can, ka yi ha'kuri ban ji ba ne". Sakina ta sandare, tana kallon ikon Allah. Ta juya ta tafi, amma tamkar ta shake ni. Sai da taje bakin kofa na ce "Anti Sakina na gode, sai mun yi waya. Bakin cikin abin da na yi ya sake turmushe Sakina, mussaman ha'kurin da na bashi, da kuma rashin biyo ta da nufin taka mata. Ina rufe baki ta dawo a hankali, tamkar ta yi mantuwa sai kawai ta shammace ni ta sakar mini rankwashi mai zafin gaske a tsakiyar kai, tare da dungure kan ta ce "Shasha kawai". Cikin kasala Yaya Gudale ya ce "A gabana Sakina? Ki fita a idona fa". Yanayin yadda yayi maganar ba karsashi ya tabbatar mata a tsorace yake. Ta nuna shi da yatsa ta ce "Na rantse Na Moriki idan ka sake kama sunana yanzun nan zan yi maka sanadin da zaka wula'kanta, ka ga iyakar iyashegenka. Idan kuma ka musa sake bu'de baki ka mini magana! Mugun bawa azzalumi kawai". Sanin idan ya tanka mata kwabarsa ce zata yi ruwa sai ya yi mukus, ya buge da fadin "Afrah barci take yi ne?". Abin da bai ta'ba tambaya ba kenan ni ban yi zaton ma ya rike inkiyar tata ba. Tsaki Sakina ta yi ta ce "munafiki, marar ragayya". Ta dan dakata ko zai yi magana, amma sai ta ji tsit. Ta girgiza kai ta tafi. Tana tafiya ya saki ajiyar zuciya mai karfi ya ce "kinsan bata nufina da alheri, na sani ko baki ce mata komai ba fuskarki ka'dai ta isa dalilin da zai sanya ta ya'ke ni, ta kuma kai ni kasa. Na sani tana son ki da dukkan zuciyarta. Amma ki sani bata kai ni a wajen ki ba. Sannan duk damuwar da zata yi da ke, na ninka ta, haka nan son da nake yi miki ya wuce misali, ya wuce irin wanda take yi miki. Ni da kaina ban ji dadin yadda marin ya shige ki ba, In sha Allah na daina dukan ki. Na gode da hakurin ki a kaina, na gode sosai da soyayyarki". Sai da ya lallaba ni, ya kusance ni, a haduwar kuma sai da ya tafi da kaso saba'in na bacin raina. Da muka nutsu, muka yi wanka kuma ya kwashe ni muka fice, bayan ya dauko ya Amnah. Ya din ga yi mana siyayya ba ji, ba ga ni. Afrah na sabe a jikinsa. Karon farko da ya dauketa, haka Amnah yana ri'ke da hannunta. Ya dinga nan da nan da ni, hakuri yake bani duk da dai bai furta ki yi ha'kurin kai tsaye ba. Amma komai nasa ya nuna nadama da neman afuwa. Bamu dawo ba sai dare domin sai da ya wuce da mu wani hadadden restaurant muka yi dinner sannan muka dawo. Ya gama parking kenan Sakina ta leko harabar gate din mu. Na fito daga mota na karasa wajenta ta ce "Kin je ya kalallame ki ko? Gobe ma zai sake yi miki, tunda ke ba zaki dauki mataki ba". Na dan bata fuska na ce "sai ya jiyo ki ya zaci kamar na fa'da miki wani abin ne?" Ta kame bakinta da sauri ta sandare tana kada kai a matu'kar razane. Ya yi wucewar sa bai ko kalli inda take ba. Yayin da Amnah ta yi wajenta tana cewa gun Umma zan biki". Itama ta yi tafiyarta bayan ta ri'ke Amnah tana cewa "Ni dai ban ta'ba ganin Halima sakarya ba sai akan ki. Mafi yawa masu suna Halima jarumai ne, masu mutuntata jama'a, sun kuma san ciwon kansu, basa yarda da wulakanci haka siddan. Amma ke kam sai na tashi tsaye akan ki, al'amarin naki akwai ban mamaki kwarai da gaske. **** Tun wannan marin da ya yi mini, da irin sassaucin da na yi masa, sai muka sami sau'kin rikici. Duk da dai wani lokacin zai iya kwanaki yana mini yar shariya, sama sama. Samun aikina ya zo mini da abubuwa guda biyu. Da farko matsalar rashin ku'di ta kau mini domin bai taba kallon ku'dina ba. Sai dai me? Bani da sukunin zuciya a dalilin rashin walwalar Yaya Gudale, domin ya matu'kar kyamaci aikin. Zamanmu ya koma wani iri, gaba'daya babu da'di a yanzu har wata jarumta ya koyo, ko kuma maganin barci yake sha oho? kullum dare karfe tara tana yi idan ya fara barci sai asuba. Idan ya karya ya fice sai dare zan ganshi tunda ni sai yamma nake dawo wa. Kwata kwata ya yanke duk wata hulda a tsakaninmu. Idan tura ta kai bango ne zai nemi hakkinsa. shima babu nisha'di irin na da. Duk wani styles da lashe lashen da yake ki'dima ni da su ya daina. Babu fa'da, amma kuma babu kwanciyar hankali, babu walwala ko ka'dan. Na fara ramewa a tsaye, na fara susuce wa. Hatta a asibiti an lura da rashin nutsuwar da nake ciki. Na dinga kewar zamanmu na watannin baya. Duk iyashegen da yake yi mini gara wanccan zaman akan wannan. Muna cikin haka na yaye Afrah. Har na yi zazzabi da ciwon nono na warke bai sani ba, bare ya mini sannu. Ba'a jima da yayen ba ya fara irin zazzabin da yayi a cikin Afrah. Marurai suka ce mu je zuwa. Rannan ya tubure mini idan nasan ciki ne da ni ba zai yarda ba, domin ba zai sake yarda ya sha azabar da ya sha wanccan karon ba. Tunda na riga na tabbatar masa ba'a fara haifa masa yara mata ba. Ya sani yanzun ma macen zan yi ta rokon na sake haifa tunda ya lura cikin ruwan sanyi nake yak'arsa. To wadannan din dana haifa sun ishe shi. Na yi shiru ina sauraron nishinsa. Bayan ya gama maganganunsa, da alamun kuma yana jin jiki ba ka'dan ba. Na rasa me zance sai kawai na zabi na fa'di gaskiyar magana. Na sassauta na ce "Ciki ne da ni Yaya Sadik shiyasa ma na yaye Afrah. Wata uku kenan." Ya yi shiru amma ya tunbatsa da fishi. Ya kasa magana. Ya girgiza kai ya ce "Kina musguna mini Guduyo! Amma babu damuwa, na zuba miki ido ki cigaba da bijire mini, saboda kawai Abba ya damka ragamar aurena a hannunki. Na ce bana son aikin da kike yi, amma anki a saurare ni. Yanzu kuma kin yi mini k'ofin duk sanda kike da ciki sai na shiga tasku mai yawa. Abin da na sani bazan sake d'aga miki hannu ba, tunda idan na dake kin ma, na fiki shiga tasku, amma zan dauki matakin wannan abin da kuke yi mini." Haka ya dinga jinya sosai a wannan karon har muryarsa sai da ta dashe. Bai samu kansa ba sai da cikin ya shiga wata shida. Watarana ya fito ya tarar da ni ina cin indomie da naman kaza Afrah tana gefena ina bata. Ya tsaya ya kare mu da kallo Ba'kin ciki ya shake shi a dalilin tunda na samu cikin kuma aka haramta masa cin kaza, duk da ya samu lafiya, amma shi da nama sai kallo. Ya sha rufe ido ya ci, yana gama wa kuwa zai yi ta sheka amai. Har aka kai jallin ko ganin ta ma ya ha'kura da yi. Ya nisa ya ce "Idan Ubangiji ya ha'da mutum da mace irin ki Guduyo tabbas nau'i ne na azabar duniya. Na da'de da gane ke din maketaciya ce ta gaske. Na ta'ba ganin wanda yake yiwa matarsa lififin ciki a duniya kuwa? Wallahi tunda uwata ta haife ni ban taba ko ji ba, bare na ga ni. Amma na gasgata Umma da ta ce "Kina neman kassara ni, ta yadda zan zaci duk mata hakan suke yiwa mazajensu wannan mugun fatan ta yadda zan tsorata da su. Amma ai an gama, ba sai na sake yarda kin yi cikin ba, bare ki yi ta gana mini azabobi iri iri". Ya fice na bishi kawai da ido. Bakin ciki da dariyar yadda ya susuce ya birkice ya sanya na dinga dariya ina k'yak'yatawa. Abin da sani na kuma kudire wa raina ko wanne bala'in zai yi ba zan yi tsarin iyali ba. Tunda Umma bata son na haihu da yawa, to kuwa idan zan samu dama duk shekara sai na dire mata jika har sai ta gamsu duk tijararta bata isa hana Allah zartar da ikon sa ba. Sannan ko ta yi nasarar raba ni da danta to na bar mata rundunar da a kullum yaumin sai ta tuna ni, ta ji ciwo a zuciyarta mai kullaci. **** Dakin Umma. A zaune ya tarar da ita akan kafet din gaban gadon Amnah na gefenta tana cin cheese. Tana ganinsa ta takure sosai, sai da ya zauna ta ce Dady "Ina kwana?" Ya amsa a takaice. Umma ta ce "Je ki wajen su Dala ki jira ni" Ai kuwa ta fice da sauri dama so take ta tashi, sai dai tun kwanaki da ta ganshi ta fice da gudu ai kuwa ya tafi da ita gida dan yasan Umma ba zata bari ya daketa ba. Shiyasa ya tafi da ita gaban uwarta ya saka tsinken zabori ya zane ta yana tambayar shi dodo ne ko kuwa cinnaka ne? Da zata ganshi ta gudu. Shiyasa bata sake gudu ba, sai dai ta takure gefe daya. Ya zauna ta kalle shi ta ce "Sannu da ibada ya jikin naka?" Lebe duk huciyar sanyi bakin nan duk ya yi wani iri tamkar bana Gudalen Umma dankwalinsa ba. Cikin rarrashi ta ce "Ya maganar yarinyar kana leka wa kuwa?" Ya ce "Ta ya ya zan dinga zuwa a hakan Umma? Dubi yadda na rame wuyana ya zama tamkar marikin lema. Ga lebena duk yayi babu kyan gani kamar na wani katon bagaujen kauye." Ta sake sassauta wa ta ce "Ai na ga ka fara warwarewa ne, amma dai kuna gaisawa a waya. Ya nisa ya ce "Muna waya sosai. Ni yadda ta matsa na tura ne ya fara damuna wanne irin al'amari ne hakan?". Ta sake kwantar da murya ta ce "Baban nata ne ya matsa mata ta fitar da miji, ko ya bata wani da bata son sa. Tunda kai take so, shiyasa suke son magabatanka su je, aure sai sadda ka shirya ko kuwa? Kasan dai tsakanina da uwarta alkunya ce". Ya ce "To amma dai sai na sake wartsake wa". Ta ce "To dai ka mayar da hankali, kuma na fa'da maka kada ka yi kuskuren fa'da mata, da zarar suka ji maganar bata riga da ta yi karfi ba, zasu shiga su fita, su lalata al'amarin. Baban Yara ya sha yun'kurin Karin aure sai abin ya lalace, kai karshe ma Abbanku aka sihirce ya hana shi, shikenan maganar sai tashin zance. To kaima hakan zasu yi maka. Kai ban da rabon wad'annan y'an matan da yake da zafi ta ina kamar ka, zai buge da auren wannan yarinya?. Rabo! Wato ba karamin al'amarine ba. Sai dai na gode wa Allah da ban hana ba, bare ya zama ajalina, ko su zo ta hanyar banza." Ya ce "sai yanzu na gamsu bamu dace ba Ummah! Muguwar yarinya ce ta gaske. Duk wani law da zata tabbatar da ni a cikin tasku ta san shi. Amma duk an hadu ana mini kallon azzalumi, wai dan uwanka ma baka fita a wajen sa ba. Ai *HALIN YAU* din nake ciki Àllah kawai zai fitar da ni". "Ta marairaice ta ce "Ai da idan ina fa'din mugun y'ancinsu baka yarda yanzu da ka zauna da su ai ka ga ni. Babbar godiyar da nake yi da basu samu galabar yi mini farraku da kai ba, saboda kullum na kai goshina a sujjuda sai na roka mana tsari da hatsabibancinsu". Ya numfasa ya ce "Umma kin tabbatar ta kammala karatunta ko?" Da sauri ta ce "Ta kammala digirinta na biyu ma. Kuma irin wacce kake so ce. Na tabbatar zata yi maka tunda ta yi mini. Sannan bata aiki, ta kuma yarda zata bi dukkan ra'ayinka. Kasan kai din Ubangiji ya kyautata maka halitta sannan kai ka'dai tilon namiji a wajen uwa da uba, wacce duk tasan ciwon kanta ai ririta ka zata yi, domin kai din kana da alfarmomi daban daban wata'kila ma ita ce uwar maza je". Ya murmusa ya ce "Allah ya sa Umma! Da kuwa Guduyo ta ga karyar yi mini Addu'a, tunda ta gane ita din mai zafin yawu ce shikenan ta kunshe ni take ta gana mini azaba ta hanyar rattaba mini mugayen addu'o'i." Ta saki tsaki ta ce "Wata'kila ma fa kambun baka ne da ita. Ni fa dama tun tana karamarta nake tsoron ta domin waddannan kwala kwalan idon ta nata yafi kama da na mayu ko masu kambun baka. Sannan matu'kar zata ce dama ayi kaza, to lah shakka abin nan zai faru ko ba yanzu yanzu ba. Sannnan na fa'da maka dama b'akin dake kan harshenta dafi ne, kada ka yarda ku yi fa'dan da zaka nuna mata kana son Amaryarka ta haifa maka maza, domin kuwa zata iya yi maka fatan itama tabi layinta tunda muguwa ce kuma azzaluma." Maganar ta shige shi ya juya ya ce "Amma kada ki yarda aji kin jingina mata maitar nan kinsan shari'ar bata karewa". Da sauri ta ce "Hakane, bare ni da basu ki na mace ba, tsabar yadda na tsare musu gaba. " Ya ce "Ba zaki mutu ba sai kin ga auren Amnah". Ta murmusa ta ce "Ai kuwa dai da har shampoo zan yi a kaina" Ya dan motsa kumatunsa alamun murmushi tunda kurajen bakinsa basa bari ya bude bakin sosai bare har ya kyakayata. Ya ce "To kuma yanzu ma ina cewa duk bayan sati biyu kike zuwa a miki shampoo din?" Ta girgiza kai ta ce "Ina nufin Tocin" Ya sake murmusawa ya ce "kurajen nan sun takura ni, ga dariya fal a cikina. To Umma kafin auren Amnah ai gashin na ki babu baki ko daya, tunda yanzu ma farin yafi yawa. Sannan gashinki tamkar kina shafa masa relaxer saboda bak'i da sulb'i. gashi nima haka nawa yake, abin da'di kuma har su Amnah duk kin sam musu." Ta yi dariya ta ce "Ai komai nawa sai haularka sun samu domin Ubangijin da yake kyautata halittar ya sani da ina da ikon tsara komai yayin halitta to naka yaran sai sun fi na kowa". Ya ce "na sani Umma! Na gode. Amma zan so, su fiki tsayi, sannan kada su dinga ajiye damuwowin mutane a ransu irin yadda kike yi". Ta nisa ta ce "Hm nima ai dole ne, ba wanda zai fahimci halin da nake ciki sai wadanda suka shiga takalmina. A zo a same ka da mijinka amma komai ayi muku tare. Alhalin ba mijinku daya ba. Sannan a fifita 'ya'yan wata akan naka ai kowa ya ga wannan lamarin an san kulunboto ne yake aiki ba wai zumunci ba. Na buga na ka'da amma ban samu makarin wannan al'amarin ba har yau. Kai Uban su Safiya ya nema musu duniya sai dai kuma a lahira su yi kallo, dan kuwa ko sun tsallake siradi sai dai su samu gidan haya domin shi yafi dace wa da su a dalilin musgunawa bayinsa da suka yi ta yi". Ya kame baki alamun mamaki ya ce "Umma wa ya fa'da miki akwai gidan haya a lahira?" "Ba wanda ya fa'da mini, amma hakan ne yafi dacewa da su". Ya girgiza kai ya ce "ki dai yi rikicin ki a duniya, amma a lahira kam wallahi walakiri bai san sanayya ba ko ka'dan". "Tun kafin ka zo nasan da hakan Gudale. Amma zaluncin da mutanan suka yi mini sai dai mai samaniya ya mini sakayya. Amma batun yafiya babu". Tsawon lokaci suna tare tana ta kushe Halimatu da uwarta da dukkan ahalinsu. Wata maganar ya kwabe ta, wata kuma ta shiga zuciyarsa, mussaman na k'arin auren da take ta haska masa wata'kila a jikin amarya yaran sa maza suke. **** Cikin abin da bana mantawa shine ranar wata Talata a lokacin cikina ya shiga wata na bakwai har ya yi nisa. Na kammala aikin gida, a ranar ban je aiki ba. Kawai na ji bayana ya kame, marata ta kulle wani irin ciwon da ban taba yin irinsa ba ya dabaibaye ni. Kafin wani lokaci da bashi da yawa na fita a hayyacina, na zube a tsakiyar falon ban sake sanin inda kaina yake ba. Sai bu'de ido na yi na gan ni a gadon asibiti, duk dangi suna kaina cirko cirko. Hannu na kai na shafa cikina na ji wayam, wani irin al'amari ya daki zuciyata. Hawaye ya balle mini. Yaya Al'amin da yafi kowa kusanci da jikin gadon ya matso yana fa'din "Maimakon ki ce Alhamdulillah sai kuma ki fara da kuka? Menene yake miki ciwo? Na girgiza kai na ce "Babu". Daga nan kowa ya matso ana mini sannu, Yaya Gudale aka babbake a gaban Yaya Al'amin tamkar me son ya fahimtar da shi karfin kusancin da yake tsakaninsa da ni, yafi wanda yake tsakanina da shi, shikuma Yaya Al'amin din ya je gefe ya bashi guri. A hankali na fahimci tiyata aka mini aka raba ni da cikin jikina, shin da rai ko babu rai?" Na rasa wa zan tambaya tunda ba wanda ya mini maganar. Da safe ba kowa sai Umman Danladi Nasidi, Gudale ya iso da abin karya wa. Umma ta yi dabara ta fice. Ina zaune akan gadon. Tuni Umma ta goge mini jikina, ina sanye da doguwar riga marar nauyi. Ya mini sannu, na amsa a hankali. Ya ce "Yanzu Guduyo menene matsalarki da har jininki ya yi mugun hawa haka? Kowa a family sai kallon uku saura yake mini, hatta Abba da kyar yake amsa mini gaisuwa, dan girman Allah me nake yi miki ne?". Na girgiza kai na ce "Babu komai". Ya numfasa ya ce "Allah ya baki lafiya" Na ce "Ameen". Muka dan yi shiru gaba'daya. Na kalle shi na ce "Ina Afra take?" Ya zuba mini ido ya ce "Tana wajen Sakina". Na sauke ajiyar zuciyar samun nutsuwa, domin yarinyar tana da kulafucina, ko Umma ba yarda take da ita bare kuma Mama. Amma tana yarda da Sakina, na sani kuma zata samu kulawa tamkar tana hannuna. Na sake cewa "Bebin fa ko ta koma ne?" Ya zuba mini ido sosai ya ce "waton kin hakkake dama mace ce a cikinki ko? Saboda baki fasa addu'a ba". Na dan ta'be baki na ce "Ba haka bane saboda kawai na hakikan ce haihuwar jinsi gadonta ake yi". Ya mi'ke ya ce "gado kamar Yaya?" Ba fargaba na ce "Yaya Al'amin matarsa namiji ta haifa ga shi nan har yana rarrafe, kuma Yaya Abdallah sai da ya haifi boys guda biyu a farko sannan ya samu matan daga baya. Ka sake duba gidan Yaya Babangida mace aka masa a farko amma maza uku suka biyo bayan macen. Yaya Ammar kuwa har yau macen yake fata bai samu ba. Kaga matayensu sun gado uwarsu ne. Dama kuma galibi anfi gadar uwar Mlmiji, shiyasa Antin Zaria bata haifi girl ko daya ba ba. Ga su Anti Sakina da Anti Ramla kowa mace daya ta haifa, boys dinsu sunfi yawa. Na gasgata wannan maganar yanzu saura uku kafin a samo maka boy, tunda mata biyar ka biyo rigis. Na gado tawa uwar mijin Ubangiji sarkin adalci". Ya nuna ni da dan yatsansa ya ce "Ni kika yi wa wannan cin mutuncin? Akan idona kika yiwa uwata gori? A gabana kika nuna mini Yan uwanki sun gado uwarku. Ni ma tawa uwar na gado?". Ban san me ya same ni ba, babu tsoronsa da nake ji na ce "Eh ko k'arya na yi?. Ai na fa'da maka haihuwar girls a gidanka yanzu aka fara". Idan na zauna da ke ko?" Na make kafa'da na ce "your choice". Ya girgiza kai ya ce "Anya allurar nan ta sake ki kuwa Guduyo? Ko kuma kin yi gamo da jinnil ashiq ne suke son su miki ingiza mai kantu?" Idona da hawaye na ce "Ai na sani ba'kin cikin da ka yi ta kunsa mini dan cikin ya zube ne burinka bai cika ba, shine ka zuba mini magani a lemo to ka ci riba ka yi kisan rai, tunda an riga an busa mata rai, Allah ya jikan little Sakina. Allah ya sa ta zamo me cetona". "Eh ai ke ka'dai kike da hakki a kanta, shiyasa zaki ce ta cece ki, sannan ni ba sunanta Sakina ba Wallahi, sunan yarinyata *Adama* sunan kanwar Umma ta Yola". Na kafe shi da ido, ina rasa me zan ce masa dan na raba mana takaicin da nake ji. Sai na murmusa na ce "Àllah ka jikan Umma Adama ka shaida na yafe mata, ka ajiye mini ita a makarantar *Annabi Ibrahim(A.S).* Ka kawo new Adama a kusa". Ya kufula ya ce "Duk masifarki kin gama yi mini haihuwa, wannan yarinyar tabbas kin zame mini kadangaren bakin tulu. Amma na bar ki da mai Rumfa. Ranar tashin alkiyama a mana hisabi, tunda kika mini kazafin kisan kai". Na murmusa na ce "ka dauki mataki tun yanzu kawai ka sauwakewa kanka zaman takura da zalunci". Ya ce "Allah ya baki lafiya. Na tabbatar ba a hayyacinki kike ba Billahillazi. Gaki da yawan azkar Guduyo! wa'danne irin kafiran shaidanune suke neman susuta ki haka?" Ya fice yana cewa "Kalu Innalillahi wa inna ilaihi Raji'un". Na murmusa na koma, na kwanta na ce "Allah ka saita tunanin wannan bawa naka". Sai da na shefe sati sannan aka sallame ni, tun lokacin kuma bai sake yarda mun kebe ba, bare wata sa in sa ta ha'da mu. Wata guda na warke, sai dan abin da ba'a rasa ba. Zaman mu ba yabo ba fallasa. Dama ya saba bani lokaci sosai idan na haihu tunda cs ake yi mini. Baya nemana sai na yi arba'in. Amma dai na sani a cike yake da ni a dalilin yana yawan cewa na ci mutuncinsa a akan idonsa tunda na yiwa uwarsa gori. To wallahi na jira sakamakon wannan katobarar dan kuwa ba zai bari ta bi ruwa ba. Ana haka Abba ya fara ciwo a tsaitsaye, tun yana ganin likita anan har ya fara jaurar zuwa Egypt asibiti. # Team Gudale # Team Guduyo # Surayya Dee ✍️ # Ana tare 🤝 2/8/23, 10:25 - Buhainat: *Na ce ba kinsan wani hadi da ake yi wa asalin man ridi da kwakwa da ba'a samun original din su sai a wasu kebantaccun jahohi?* *kina fama da matsalar cinyewar gashi ko kuma rashin tsayinsa?*. *Kina neman ha'din da da zai sanya fatarki laushi da sulbi, kuma cikin saussaukan farashi? Tuntu'bi wannan lambar dan samun naki cikin sau'ki. Kaya mai inganci shi yake siyar da kansa.* *Sister Zainab 08039315577.* *SDK* *71&72* Kowa yana cikin alhinin jinyar Abba! A dalilin an gano yana fama da ciwon mafitsara. Sosai yake shan wahala. Wani aiki da aka yi masa a Egypt ya dan samu sau'ki, har yana yan harkokinsa duk da dai baya fita, ya yi nisa. Ganin sau'kin da ya samu ya sanya Yaya Gudale ya zartar da kudirinsa na a nemo masa auren Munubiya Baffah K'unci. Y'a a wajen attajirin 'dan kasuwan da ya yi shura. Sannan uwarta kawar Umma ce ta sosai. Kusan ma ita ta yi masa shunenta. Na santa tabbas me kyau ce, kuma sirirya ce ta gaske. Sannan bata cika tsayi ba. Ta dai dace da y'ar shawalwala dai dai da tsarin Yaya Gudale. Gaban Baba ya fara kai maganar aje a nemo masa aure a gidan Alh Baffah Kunci. Ba ja in ja ya goya masa baya. Baba da kansa ya shirya komai, sai da komai ya kankama sannan ya sanar wa Abba. A matu'kar sanyaye Abba ya ce "Bana son wannan auren da zai yi. Babu nagarta a gidan da ya kwaso auren. Da a ce gidan tarbiya ne ai ba zamu hana shi abin da Ubangiji ya halasta masa ba. Saboda dalili na son zuciya". Baba ne ya dinga kawo misalai iri iri na bai kamata a soki lamarin aure ba. A bashi damarsa, abi lamarin da addu'a. A kan dole Abba ya ha'kura. Aka kai ku'din aure, aka saka ranar aure wata biyu masu zuwa. Baba ne kawai yake kan maganar kane kane, kuma wani ikon Allah bai fa'da wa Mama ba. Sai kuwa su Umma da mukarrabanta Anti Maimuna da Anti Juwairiya. Umma kuma ta hana kowa ya fa'da mini maganar a cikin yaranta. Hatta Sakina sai da Umma ta yi mata gargadi. Duk da ta sani, amma ta kasa fa'da mini a dalilin kiyaye maganar uwarsu. Sai dai gaba'daya a susuce nake ganinta. Karin abin da yasa ban samu labarin da wuri ba. Abba ya koma ganin likita kwanaki biyu da kai ku'din auren, suka tafi da Baba da kuma Yaya Gudale. A can suka tarar da Yaya Abdallah. Mama bata sani ba, bare na ji. Dan haka ina zaune cikina kwarkwaro. Umma da su Anti Maimuna suna ta shiri bikin kece raini, suna ta hada kayan lefe na alfarma. Sati hudu suka yi a Egypt, suka dawo. Sai lokacin na lura da kaffa kaffa da wayarsa da Gudale yake yi. Sannan da zarar ya dawo daga office zai tsala wanka ya fice. Tun ban damu ba har na fara kokwanto. Saura sati biyu biki. Na je duba Abba. Ya zaunar da ni yake ta yi mini nasiha mai ratsa jiki. Tabbas jikina ya yi sanyi duk da dai tunda jinyar nan ta ci karfinsa ya ninka yin nasiha akan girman ha'kuri da kuma riko da zumunci. Amma nasihar wannan ranar ta banbanta kwarai da gaske. Domin cewa ya yi "Na hore ki da yin ha'kuri Halimatu! Amma ban ce ki yi hakurin zalunci ba. Ko da na ce ban da kawo k'ara ai na fa'da miki ne dan na kubutar da ke auren Sadiki! Amma tunda Ubangiji ya kaddara mijinki ne kuma uban y'ay'anki ne ai sai da aka yi. Ina kuma gode miki sosai. Amma a yau zan tabbatar miki kada ki yadda da ha'kurin da kika san cutar wa ne a gare ki. Kada ki yarda ki dauki wula'kanci saboda ni, ko ki yi ta zaman takura saboda na ce babu kawo k'ara. Na janye miki wanccan takunkumin. Sannnan ina son ki kara ha'kuri, yadda baki tayar da hankalinki akan maganar aurensa ba, ya sanya na saka Abdallah ya canja miki mota, gobe kuma na sanar da Sakina ta zo kuje ki zabi duk kayan da kike so, sai a fitar da na wajen ki, ki bayar, ko ki yi sadaka da su. Na siyo miki sarka ma tana cikin kayana, bana son kowa ya ga ni. Shiyasa na boye miki ita. Sai ranar juma'a zan baki. Na yi sakare cikin rashin fahimta da zullumi mai tsananin gaske. Wai waye zai kara auren ne? Na gama lissafina, jikina ya dauki kyarma na dinga jin tashin hankali yana shiga ta. Duk yadda na so yin jarumtar hadiye tashin hankalin da ya ziyarce ni farat daya sai da na kasa. Na kifa kaina na dinga kuka a tafin hannuna. Kuka nake yi na kaico iri iri. Kuka nake yi na takaici, ina ma ace na ji maganar Abba! Ina ma na ji kashedin mahaifiyata, ina ma ace na ji shawarar Sakina. Wai aure Gudale zai yi? Amma ban cancanci ya zaunar da ni ya fa'da mini da bakinsa ba? Bani da wannan darajar, ba dan Abba ba wata'kila da sai saura wata kenan zan samu mai fada mini tunda kowa yana girmama ra'ayin Gudale ne. Kukan da nake yi, ya ta'ba Abba sosai ya kira ni a sanyaye cike kuma da soyayya da tausayi mai yawa. Ya ce "Halima kukan na menene ko dai akwai matsala ne?" Na girgiza kai na ce "Babu Abba! Tausayi kaina ne ya kama ni, da ace ka mutu da sai dai na ji ana shigo da amarya saboda bani da muhimmanci a wajen kowa. Dama ya'ya mata basu da daraja ne Abba sai dai a haifesu a rainesu, sai kuma a bada aurensu suma suje su yi ta haihuwa da raino. Idan suka yi rashin sa'a suna haifar ya'ya mata shikenan sun zama marasa daraja, tunda basu haifi wadanda zasu zama garkuwa a gida ba". Na karasa cikin kuka na tashin hankali. Ya yi shiru ya kasa magana, tsawon lokaci ina gunjin kuka bai ce kala ba. Sai da na nisa dan kaina ya ce "Yi salati Halimatu zuciyarki ta nutsu." Na dinga salatin kuwa, har na dan sami nutsuwar. Ya sassauta sosai ya ce "Ki bude zuciyarki da kunanki ki ji ni da kyau, wata'kila wannan ce maganar da zan fa'da miki ta karshe da zata jagoranci halin duk da zaki samu kanki a rayuwarki". "Haihuwar ya'ya mata daraja ce da ba kowa ke rabauta da samunta ba. Duk wanda kika an jera masa yara mata Ubangiji ya so shi da alheri mai yawa. Hadisin nan na Annabi(S.A.W.) ka'dai ya isa ya nutsar da zuciyar iyayen y'a'ya mata. Annabi ya ce Aljannah ta tabbata ga wanda ya haifi mata uku ya kula da tarbiyarsu har zuwa aurensu. Shin wacce daraja ce tafi wannan?" Bai jira ni ba, sai ya zarce da cewa "Bayan haka Halima halittar mace ta wuce ace bata da daraja domin duk namijin duniya an wajaba masa neman aljanna a kafar uwarsa. Shi kuma matarsa ta yi masa biyayya, bayan an dora masa nauyin cinta da suturarta, da maganinta, da kuma kare mutuncinta. Amma shi kuwa cikin kowanne bigire aka ce yabi uwa, yabi uwa. Duk kuma tumbatsa da kasaitar namiji da za'a ce wancan mutuimn bashi da aure sai kin ga darajarsa ta fa'di saboda babu mace a tare da shi." Ya nisa ya cigaba da cewa "Kada ki yarda a cusa wa zuciyarki dabi'u irin na jahiliya da har yanzu jama'ar da suka samu ilimummuka suke jahiltar lamarin. Duk wanda yake da ya'ya mata yana da arziki mai yawa. Na farko zuri'arsa zata yadu da wuri. Sannan ku a halittarku Ubangiji ya sanya muku jin kai da tausayi. Duk sadda kika kalli ya'yan da Allah ya baki sai ki hango ni." "Ai nima su ya bani, na kuma gode masa da dukkan zuciyata, shi kuma sai ya shirya mini su, ya daukaka su. Na yi imani ko ban tara arzikin da Ubangiji ya sanyawa albarka ba. Antinku ta Zaria ka'dai ta ishe ni jari. Sakina kadai idan na kalleta sai na tsinci kaina da cewa Ubangiji ka bani, ka sake k'ara mini na gode. Domin Sakina ita ka'dai tana daidai da wasu mazan ashirin. Har yau din nan Halimatu ba wanda ya san cewa tun shekaru goma da suka wuce duk abin da ake saukewa a gidan nan da kofar Baban Yara har ma da kofar mijinki da yake fankamar namiji ne cewar Antinku ce. Komai na bangaren kayan abinci da ake sauke wa babbar mota guda duk bayan wata uku, ita ce. Har yau din nan tunda Sakina take aiki ban kara siyan ruwan da nake sha ba, duk yawan ruwan robar da kike ga ni a gidan nan ko a wajen Baban Yara bamu muke siya da ku'dinmu ba." Mijin Ummu kuwa ba abin da baya yi. Duk da yasan mu din ba mabu'kata bane, sannan kwai da kajin da take sana'a kina ganin yadda ake shigo wa da su Kamar banza. Ga Juwairiya itama tana iya nata kokarin, sannan ko yara nawa zan bata takardunsu da nufin ta nemo musu gurbin karatu zata nemo koda kuwa ba a makarantar da take aiki ba. Ramla kuwa anan ta zo ta tsugunna ta ce "Ta dauke mini yiwa uwarsu sutura, tana yin kuma na alfarma, sannan tunda take aiki a NEPA ban sake biyan ku'din wuta ba. Gaki kema fara aikinki kullum naki abin arzikin a tafe yake. Dan haka duk abin da zaki yi, ki saka Allah! Ki yawaita istigifari, ki kuma tsananta yin godiya ga Allah. Idan kin tashi addu'a ki tsananta fa'din Ubangiji ka sanya albarka a cikin duk abin da ka bani, na dukiya ko na zuri'a. Baban Yara da Ubangiji ya bashi mazan a jere ai tare ya bamu, muka yi sa'a kuma ya shirya mana su, kowa yana ri'ke da kansa da iyalinsa, suna kuma iya kokarinsu na tallafin abin da zasu iya, sun kuma zame mana garkuwa, kuma abin ado, domin kuwa tabbas da namiji yakan zama garkuwa a gidansu amma idan ya zama a cikin nutsuwarsa. Dan haka ki yi ta haihuwar ya'ya mata cikin farin-ciki da godiya! Ga Sakinanki nan ta haifa miki mazan da na tabbatar zata saka su yi miki abin da zasu yi mata na alheri. Idan kuma ya kaddara kin samu namijin to kada ki yarda ki bashi wani matsayin da ya wuce na yan'uwansa domin dai d'a gaibu ne, kowa da irin baiwarsa. Muhimmi kawai ka yi wa kowa adalci ta hanyar yi musu tarbiya mai kyau, a basu dukkan nau'in ilimi, a kuma bisu da addu'ar shiriya. Amma nuna fifikon nan da galibin iyaye suke yi idan sun samu namij bayan an haifi mata da yawa yana matu'kar taka muhimmiyar rawa wajen damalmala tunanin yaron wanda galibi sai ki ga sun zama rudeness ta yadda su kansu basu amfani kansu ba, bare su amfani waninsu" Ya nuna kansa bayan ya numfasa ya ce "Nima victim ne Halimatu! Ba wani boye boye, amma Ubangiji ya sani na iyakacin kokarina akan Sadik! Amma uwarsa bata fahimta ba, tarbiya kuma ko ana so ko ana ki mafi yawa ta uwa ce. Tasirin uwa mai yawa ne akan danta. Sa'a daya da na yi, da Ubangiji ya tsare shi daga lalacewar zuciya, tunda yana sallah akan lokaci, sai nake da yakinin duk abin da yayi masa rauni da sannu Ubangiji zai daidaita masa. Sannan an yi sa'a yayi karatun da zai iya ri'ke kansa. Amma ai baya ciki bangon gidan nan. Sai dai kuma bis adalci shi yake saka mana katin waya tunda ya fara aiki. Sannan yakan siyo mini ice cream da yogurt tsabar shiririta". Ya murmusa ka'dan ya ce Wadannan misalan ya isa ya kwantar miki da hankali, ki fahimci gatan da Ubangiji zai yi miki a gaba. Domin idan kika yi musu tarbiya, suka sami ilimi ina tabbatar miki nan gaba kin huce takaici mussaman da yake Ubangiji ya cika galibin zuciyar y'ay'a mata da alheri da jin k'ai". Na samu nutsuwa sosai da kalamin Abba. Nauyin da kirjina ya yi a dalilin tsoro da firgici ya yi sauki. Amma kishi sai babbako mini yake ta inda duk ban yi zato ba. Na sauke ajiyar zuciya, amma hawaye na tsere na ce "Allah ya baka lafiya Abba! In sha Allah da sauran nasihohi da zaka mini a gaba masu yawa." Ya murmusa ya ce "Shekaru fa sun tafi Halima! Ko babu cuta ai ni kaina na sani nesa ta zo kusa. Duk wani ni'imomin duniya Ubangiji ya cika mini su." Ya nisa ya ce "babban burina shine na cika da imani. Ina muku fatan ku yi rayuwa cikin salama da tsantseni". Ya fito da waya ya kira Yaya Gudale da bai jima da fita ba. Ya ce "ka dawo yanzu nan". Ya kashe ya kira Baban Yara shima ya ce ya zo yanzu. Ba a dauki lokaci mai yawa ba suka shigo a tare, tunda dama tare suke. Suka zauna Abba ya dinga fa'da akan me yasa ba'a sanar da ni auren ba har zuwa yanzu alahalin ina da hakkin na sani. Dukkansu suka yi shiru. Domin sun tabbatar ba wanda ya sanar mini a cikinsu. Na dinga kallon su tamkar zautacciya Ubana da mijina sun boye mini za'a mini kishiya. Na sunkuyar da kai ina sake fashe wa da kuka. Sosai jikin Baban Yara ya yi laushi tubus, kukan nawa ya dinga taba shi, ya rasa karsashin da ya shigo da shi. Sosai kukan ya shige su Abba ne ya ce "Ashe kuma daga kai har d'an naka baku sanar mata maganar auren ba har zuwa yau da ya rage mako biyu". Baban Yara ya kasa magana. Yayin da Gudale ya ce "Na zabi na boye mata ne dan kada ta tashi hankalinta, ina son sai saura sati daya haka. Yanzun da ta ji baka gashi nan duk ta birkice ta ki'dima ba". Abba ya girgiza kai ya ce "hakane sai dai kuma za'a daga auren har sai nan da wata biyu idan ka fa'da wa matarka ka kuma kwantar mata da hankalinta sai a saka rana." Yaya Gudale ya yi shiru cikin bacin rai. Yayin da Baban Yara ya ce "Ha'kuri zaka yi! Ai bai kyautu a daga aure babu wani gamshasshen dalili ba. Ba girmanmu bane". Abba ya yi shiru yayin da Baba ya dinga bashi ha'kuri. Ya kalle ni ya ce ",Ki kwantar da hankalinki Halimatu! Karin aure halak ne matu'kar mutum yana da dama, kuma zai yi adalci. Sadik dan-uwanki ne na sani ba zai cutar da ke ba". Na kalli Baba kamar na ce cutar wa kuma na nawa? Sai kawai na daga kai na ce "Hakane Baba! Na gode Allah ya sanya alkhairi." Na juya na kalli Abba na ce "Na gode sosai Abba Ubangiji ya baka lafiya, na gode kwarai da gaske. Amma ka yi ha'kuri abar Baba da Yaya Sadik da ra'ayinsu" Na fa'da kuka na sake kwace mini. Tsawon lokaci kowa ya kasa cewa komai hatta Yaya Gudale kansa ya yi laushi sosai. Na nisa na ce "Abba zan tafi mu yini lafiya." Na tashi na tafi yana ta sanya mini albarka, yana kuma neman mini tsari daga dukkan abin ki. Na fito na dan labe ta bayan windo na ji yana ta fa'da akan abin da Gudale ya yi. Ya daga murya ya ce "Sadik idan ka cuci yarinyar nan alamuranka baza su daidaita ba. Anan kusa ban san yarinya mai yin soyayya dan Allah irin ta ba. Ban san mai ha'diyar ba'kin ciki irin nata ba. Sanin kowa ne zama da kai sai wanda ya shirya, sai mai ha'kuri kwarai da gaske." Tari ya sarke shi. Ya ce "Bana son auren amma Babanku ya mini fin karfi ya nemo maka, dan ya nuna mini ikon da yake da shi akan ka. Bude kunne ka jini Sadik, shine fa ya haifi Halimatu. Shine ubanta, ko na mutu idan ka ruguza mini zumunci ka tabbatar hakan na nufin rugujewar al'amarinka gaba'daya. Har yau ban haifi d'an da ya mini biyayyar da Babanku ya mini ba. Ina jan kunnenka Sadik ko bana raye biyayya biyu zaka yi masa, da wacce zaka yi mini da kuma tasa ta karan kansa." Baba ya ce "Ba zaka ma ka mutu ba Abba! Muna tare sai mun sake turawa." Abba ya nisa ya ce "bar ni dai na dinga fa'din abin da yake raina saboda yanzu mutuwa ko babu jinya yinta ake yi. Bare ni da take ta nuna mini alamu." Ya sake numfasa wa ya cewa Baba ka hado minl zamu tattauna in sha Allah" Baba ya amsa da "In sha Allah". Na wuce daga haka na barsu. Tafe nake ina jin wani irin zugi a zuciyata. Na doro alwallah na dinga sallar da ban san me nake fa'da ba. Wani irin azabben kishi mai saka ciwon kirji. Na dinga kuka a sujjuda na kasa cewa komai. Tsawon lokaci kafin na iya cewa Allah ka taimake ni, Allah ka sassauta mini, Allah kada ka saka ta sha gabana.". Na dago na tarar da shi a bakin gado ko shigowarsa ban ji ba. Dana sallame nake tashi na sake tayar da wata, karon farko a rayuwata da na fara jin ban son ga ni ko jin kalamin bakinsa. Yana zaune bai gaza ba, har ni na gaza na zauna. Ya saussata ya ce "Kin kai karata akan ban sanar miki zan yi aure ba. Ni kuma cikin adalcina da tausayina ne ya sanya ban fa'da din ba. Domin na sani zaki tayar da hankalinki ki zube a banza". Na zuba masa ido ina kallonsa cikin fitar hayyaci. Na rasa gane me nake ji gaba'daya. Ya sake cewa "Yarinyar bata da fitina haka take innocent kamar ke. Sannan ko kin girmeta ba zai wuce da one year ba. Kin san ni adali ne ba zai yiwu na bari sai kin tsufa sannan na dauko miki yarinyar da dole sai ta kere ki a shimfida saboda kuruciya ba. Amma yanzu competition zaku yi, idan kin fita hikima ma shikenan. Dan haka share hawayen ki. Kinsan kuma tunda aka miki aikin nan kusan wata biyu na barki ki dan gyagije. Amarci nake son na fara tun daga yau. Hawaye ya sauko mini. Na kasa cewa uffan. Ya sassauta ya ce "Ban son irin wannan kukan Guduyo! Kin sani bana so". Murya ba amo na ce "Nima bana so din, bani nake yi ba. Zuciyata ce take yi." Ya ce "To wanne irin abu take yi hakan? Akan me zata dinga wannan kukan bayan ta sani, na damu da ita, na kan shiga tasku idan tana cikin bacin rai?." Na zuba masa ido sosai har ya tsargu. Na dauke idona ba tare da na ce komai ba". Ya yi matu'kar tsargu wa ya sauko daga kan gadon ya ri'ke hannuna ya ce "Guduyo". Na kalle shi ba tare da na amsa ba. Ya ce "kar ki bari ki shiga wasi wasi a kaina kin sani dai ina son ki, kina da muhimmanci a rayuwata. Na dauke kai na ce "Hakane! Tunda kan Antin Zaria har Sakina. Babu mai kishiya sai ni. Tunda kan Yaya Abdallah har zuwa Yaya Al'amin babu mai mace biyu sai kai. Na sani su dukkansu sun sami son ransu, ni kuma ba type dinka ba ce . Dan haka dole ka samo taste d'inka kuma baka yi laifi ba." Ya sake tsananta ri'kon da yayi mini ya ce "kada ki fassara da hakan". Na cije na ce "Am sure haka ne! Ina yi maka fatan alheri, ina fatan ta kasance uwar mazaje dan ta da'de tana jan zarenta". Ya ce "Ameen Guduyo, kinsan addu'arki ana karba. Amma kema kina jan zarenki, kinsan dai I really love you. Karon farko da ya fa'da mini wannan kalmar babu zagaye zagaye. Sai dai bata mini da'di ko ka'dan ba, domin bata zo a sadda ta dace ba. Bata zo a mini a sad'arar da ta kamata ba, domin ya fa'da a dalilin na yi masa addu'ar da ta yi masa da'di ne. Ya kuma riga da ya yi imanin ina da zafin yawu. Na sake kallonsa na tabbatar wannan rarrashin da yake mini har da bu'katar kansa da yake son saukewa. Yayin da ni kuma kishi ya turnike ni. Na ji ko kadan bana sha'awar wannan al'amarin ya je na bar wa Munubiya. Na mi'ke, shima ya mike ya ce "Abba dai ya ce "Kada na musguna miki, na roke ki kema kada ki bari kishi ya saka ki zalunce ni." Murya na rawa na ce "Har abada ba zan iya zaluntakar ba Yaya Gudale. Amma na rokeka ka barni na samu nutsuwa, ka bar ni na yi fama da bakin cikin da yake nukurkusa ta". Na karisa kuka na goce mini. Ya yi shiru jikinsa ya mutu sosai. Ya ce "so kike kawai sai raunina ya bayyana Guduyo. Menene na wannan kukan saboda Allah? Gutsurata za'a yi ne, ko me? Saboda sanin ina da muhimmanci a wajenki shiyasa nima na yi miki adalci ban dauko miki yar karamar yarinya ba. Na fa'da miki fa warinki ce. Kin ga ai gogawa zaku yi. Sannan na rantse miki ita ba Guduyo ba ce, ba kuma jinina ba ce". Hawaye na zuba na ce "Amma ita zata haifa maka boys ko?" Ya ce "kema kafirin taurin kai ne da ke, ban da haka tunda kinsan kina cikin kebantattun halittun da ake amsa addu'arku me ya hana ki yi addu'a ki haifo mini boys din? Amma na lura kwata kwata baki damu ba". Na rausayar da kai na ce "Ban damu ba ko ka'dan! Idan na tuna Abbah da ahalinsa sai na ji ina alfaharin sawunsa dana tako." Ya hassalo ya ce "Bar ganin ina rarrashinki! Wallahi this wil be the last time da zaki sake tsayawa a gabana ki fa'da mini iyayena kika gado. Billahillazi sai na miki abin da zaki yi kuka na gaskiya. Domin wannan kukan duk na jin da'di kike yi fitannaniya tabattacciya kawai. Dama na fa'da miki gorin da kika yiwa Umma ba zai tafi a banza ba, to ta zabo mini wacce ba zata ta'ba yi mata gori ba, kuma na karba da dukkan zuciyata, domin ta dace da ra'ayina." Ya fice ya barni ina zubar da k'wallah. Wannan ranar tana cikin mafi tsaurin ranaku dana fuskanta a duniyata. Na ga tsayinta kwarai da gaske. Ana idar da sallar isha ya dawo, falo ya tarar da ni, domin zaman dakin ya gagare ni. Rabon da na ganshi a gida a irin wananan lokacin na manta. Kallo daya na yi masa na gane yana cikin matsuwa ne. Na ki yarda na kalle shi a dalilin ina cikin ba'kin ciki mai yawa. Dake yana neman hadin kai sai ya lankwashe harshe ya ce "Tunda na fita nake ta tunanin ki, takaicin kaina ya kama ni. Na ji ina ma ban daga miki harshe ba. Domin na hakikan ce kina cikin yanayin da kike bu'katar rarrashi da tarairaya daga gare ni, very sorry Gudidina". Maimakon na ji da'din kalamansa ko na sami sau'kin *HALIN YAU* din da nake ciki sai kawai na ji tamkar yana watsa mini garwashi ne. Kishi da kuma ganewar da na yi akwai abin da zai biyo bayan wannan kwantar da kan da ya yi, ba wai dan ya damu da halin da nake ciki bane. Ya turo mini ledar hannunsa gabana ya ce "gasashhiyar k'odar da kike so ce." Ban dago ba, bare na kalle shi ko na bude na ga ni. Ya mike ya na cewa bari na dauko miki fork da plate Maman Amnah". Bai jima ba, ya dawo da ya zauna daf da ni. Ya juyo mini ita gaba'daya. Bayan ya fito da fresh milk daga leda. Ya sani a jikinsa sosai. A da idan ya mini irin haka sai na jini tamkar sarauniya, zuciyata ta cika da shauki da bege. Amma a yau ban da suya babu abin da take yi mini. A baki ya yi nufin bani, amma na ki na karbi fork din, na fara ci da kaina. Sai dai sau biyu kawai na kai bakina na ajiye a dalilin bakin babu da'di tunda zuciya a cunkushe take. Ya zuba mini ido sosai ya ce "Duk wahalar da na sha dan na dada miki, ba zai sa ki ci dan na ji da'di ba? Haba Guduyona". A hankali na ce "Na gode! Shake mini wuya take yi." Ya bu'de fresh milk din ya ce "To ga mutumin sha ya sanyaya miki makoshi Sadiyayye. Da hausata da na ki fa'da miki ai. Amma ke da Abba baku fahimce ni dai-dai ba. Gashinan ai tun lokacin baki huta ba, ba ki barni na huta ba". Ban ce komai ba. Ya sake kwantar da ni a jikinsa ya ce "kin yi sallah ne?" Na daga masa kai tabbacin na yi. "To muje na taimaka miki ki yi wanka ki ji da'di a ranki, tun safe fa kike cikin wannan yanayin." Ya tara hannunsa a daidai bakina ya ce "zubo dukkan bacin ran da yake zuciyarki na je na wurga shi ruwan can na sallari". Hawaye ya balle mini a dalilin takaicin da yake sake cusa mini da sunan rarrashi. Abin da kuma yake yiwa kulafaci ba zai samu ba duk azinarsa kuwa". # Team Gudale. # Team Guduyo. # Surayya Dee ✍️. # Ana tare 🤝. 2/8/23, 10:25 - Buhainat: *Wannan littafin na ku'di ne, biya 500 ku'din karatu ta wanannan asusun* *2384876855* *Surayya Ibrahim* *Zenith Bank.* *A tura shaidar biya ta wannan lambar* *08032773332*. *SDK* *73&76* Duk rarrashinsa ban yarda na tashi ba, bare na shiga daki Kamar yadda ya so. Ya ha'kura ya tafi, ya kyale ni. Har tsakiyar dare ina falo kan sallaya. Sallah kawai nake yi ina kuka gaban Ubangijina. Wannan daren ya yi matu'kar tsauri a gare ni. Domin tsintar kaina na yi ina addu'ar a karbi raina na huta. Kamar yadda ban yi barci ba, haka shima bai yi ba. Domin sintiri ya yi ta yi tsakanin dakinsa zuwa falon. Ya zauna ina sallame wa ya ce "kada ki sake tayar da sallah Guduyo. Kin sani aikin da zaki yi mini yafi sallar nan da kike yi lada da kusanci wajen mahaliccinmu. Na miki iya laminin da zan iya yi miki". Na kalle shi na ce "Ba zan iya ba! Na roke ka, ka barni na samu sukuni". Ya hassalo sosai ya ce "kafaffiyar yarinya kawai! Dan ma kin samu ban ta'ba nuna miki komai ba. Nifa dama ba wai ina gamsuwa bane. Bare yau da kika sanya masifa a ranki duk kin wani zama ragajab". Na murmusa na ce "Allah ya yafe maka". Ya yi kwafa ya wuce Amma ba hakan ya so na yi ba. Na sani so ya yi na fashe da kuka ina tambayar ba'asin da gaske yake yi ko kuwa dan ya yi fishi ne?. Daga hakan kuma sai ya samu abin da yake so. Na tada Sallah na rabu da shi. Sai dai ina idar wa na kife ina gunjin kuka. Duk da na sani Gudale ya fa'da mini maganar dan na yi ba'kin cikine ta yadda zuciyata zata yi bindiga. Saboda na sani idan baya gamsuwa da ni ba zai dinga kidima idan mun kebe ba, ba zai dinga ajiye girman kansa dan ya samu yardata ba. Na tabbatar ko da bana zuwa wajen Faseelat dan samun nagartattun supplement din da suke kara mini daraja. Ina cikin sa'idan mata. Amma saboda zai yi aure ya rufe ido ya kalli tsabar idona ya ce mini baya gamsuwa da ni. A fili na ce "Tirkashi". Wani irin kishi mai dagargaza dukkan confidence ya dinga shiga ta. Na dinga kuka ina ambaton Innalillahi wa inna ilaihir Rajiun. Wajen k'arfe hudu ya sake dawowa ya tarar da ni akan sallayar ya ce "yanzun kin samu sukunin zuciyar ko kuwa?" Ba ja in ja na ce "Ubangiji ya saukaka mini Alhamdulillah". "To taso muje". Na yi yake na ce "Kai da baka gamsuwa menene na wannan bibiyar ne? Na ce bana so, bana ra'ayinka". Ya kuwa mike yana fa'din "Amma kin sani dai daga yanzu kina cikin tsinuwar malaiku dan kuwa ina cikin fishi mai tsananin gaske da ke". Na ce "Na tanadi katon carbi na yin istigifari mai yawa". "Guduyo laifin da kika yi cikin saninki shi zaki yiwa istigifari? Ai ni kika sabawa, kuma kin sani sarai Allah baya yafe laifin da ka yiwa wani". A hanzarce na ce "Indai kai na yiwa laifin dan Allah samu waje ka yi ta kwashe mini karama, dan kuwa indai sai na amince da kai to kuwa ba zan rabauta ba a yau dai" Ya juya yana cewa "Na barki Guduyo! Na bar miki abinki ki jika ki sha. Ni da nake shirin daukar sabo tsukakke ma". Na bishi da ido kawai, wani ikon Allah sai ban ji komai ba domin kuwa na san takaicin ban bashi bane ya sanya yake ta sakin maganganun daza su iya haifar da babbar matsala idan ba'a yi taka tsantsan ba. Maganganun sun shige ni, sun zauna a zuciyata. Washagari har ya fito cikin shirin fita ina zaune ba alamun gyangyandi. Ya zauna ya ce "Ina son mu tattauna maganar jere ta yadda zamu rufe maganar gaba'daya. Next week zasu zo jere. Na so na bata gidanta daban ta yadda zasu yi jerensu sosai, sai Umma ta nuna bata son hankalina ya rabu gara na ha'de iyalina waje guda. Yarinyar kuma ta amince. Yanzu ki za'ba sama kike so ko kasa?" Na sake yin yak'e na ce "Duk inda ka bani zan kar'ba ai kai ne maigidan". "To ki za'bi sama kin ga zaki dinga yin exercise, sannan ita ta roke ni, 3 bedroom take so". Na ce "hakan ya kamata tunda Yar babban gida ce. Ubanta da yan'uwanta masu fa'da aji ne". Ya yi sororo ya ce "magana kika fa'da mini Guduyo? Daga na tambaye ki dan kada ki sake kai k'arar ban baki zabi ba, shikenan sai ya zama bak'ar magana?" Na girgiza kai na ce "To me na fa'da wanda ba gaskiya ba? Ita ai ka ji ra'ayinta, ta amince ka ha'da mu, sannan kana son bata dakuna uku, tunda haka take bu'kata. To ni kuma ko garden ka kai ni ai zama zan yi kasani, tunda ni ba yar kowa ba ce". Ya mi'ke yana cewa "Allah ka'dai yasan adadin mugun halinki da nake ha'diye wa. Ace ba dama ka taro mace daga gabas, sai ta nausa ta yi yamma?" Ya koma daki ya dauko wayarsa. Har ya kai kofar fita. Na bu'de murya na ce "Daga asibiti zan wuce gidan Maman Nana" Da sauri ya ce "Capital No! Ban barki ba". "Gaskiya ina son zuwa Gudale". Ya juyo da mamakin yadda na ce Gudale gatsal. "Neman masifarki ya kare a kanki Guduyo. Duk sadda nake rarrashinki a lokacin kike botsare wa". Ya fice bayan ya ja tsaki mai tsananin gaske. Na kifa kaina a jikin kujera ina wani irin kuka mai dauke da shessheka. A gurguje na yi wanka na shirya. Kai tsaye wajen Abba na shiga, na tabbatar yanzu yana falo tunda har yanzu yana nan da dabi'ar jira a gama zuwa gaishe shi kafin ya shiga ya kwanta. Na tsugunna gabansa bayan na gaishe shi. Na kasa tashi. Cikin tarin 'kauna marar algus ya ce "menene matsalar ki Halimatu?" Cikin rishin kuka na ce "Abba zaka iya dakatar da auren, ka taimke ni ka hana shi, zan iya mutuwa a dalilin bugawar zuciya, ina sonsa, ina son na mallake shi ni ka'dai". Ya yafito ni, na rarrafa na isa daf da shi. Ya saka hannunsa a kaina. Ya ce "Yi salati Halimatu ki ji sanyi a kirjinki". Na dinga nanata salatin har na dan samu sau'kin suyar da kirjina yake Yi" Ya yi gyaran murya ya ce "Saurare ni da kyau Halimatu! Bu'de dukkan tunaninki, bu'de zuciyarki! Ubangiji ne ya halasta masa k'arin aure matu'kar yana da hali kuma yana da ra'ayin hakan. Idan na hana shi damar da Ubangiji ya bashi tabbas na yi son zuciya, na kuma yi wa shari'a katsalandan." Na fashe da wani irin kuka a dalilin isharar da maganar Abba ke yi mini cewa auren Gudale babu fashi. Bai hana ni ba, sai da na yi kuka sosai. Na dago na ce "Mutuwa nake son yi, ina zan saka kaina Abba?" Ya mi'ke kafafunsa ya ce "Saka kanki anan Halima ki yi kukanki son ranki". Na kifa kaina kuwa na dinga kuka hawaye na sauka kan kafafunsa. Cikin rawar murya ya ce "Ubangiji a sassauta mata kishin da yake neman kassara zuciyarta da tunaninta. Allah ka san dalilin da yasa aka k'ulla wannan auren idan an yi da mugun nufi ne. Na rok'e ka, ka tsare mini Halimatu, ka hana zaluncinsu yin tasiri a kanta. Idan kuma daga gareka ne, ka ha'da zuciyoyinsu, ka saka ta zama adala kuma jagora a gidan". Ya yi shiru yana jin yadda jikina yake bari. Ya sake sassauta wa ya ce "Ina ro'konka ya Allah ka wanke zuciyar Halimatu daga kishi mai sanya wa a halaka, kishin da zai sanya ta yi zalunci, da kishi mai sanya kunci, a sassauta mata ya Ubangiji". Wani ikon Allah sai na ji wani irin sauki da afuwa yana shigata. Na dako fuska jage jage da hawaye. Ga mamakina sai na ga shima kwallar yake yi. Cikin alhini da tausayi ya ce "Bu'de kunne ki ji ni sosai kada ki yarda dan mijinki ya k'ara aure ki yanke masa dukkan kauna da buri. Matu'kar bai wula'kanta ki ba, ba laifi bane k'arin aure. Kar kuma ki manta aljannarki zata fi samuwa ne idan kin yi masa biyayya. Kada ki kuskura ki bari fishin zuciya ya sanya ki zalunce shi. Kada ki bari ki bawa wata damar da zata karbe miki miji, duk abin da take da shi Ubangiji ya yi miki shi. Kada ki ji tsoron karawa da kowacce mace, domin Ubangiji ya halicci kowa cikin kyakkawar siffa. Babu mummuna, kowa mai kyau ne, Ubangiji baya kuskure, idan an fiki anan, sai kiga kema kin fi a wani fannin, babu kuma wanda yafi wani a wajensa sai wanda yafi tsoronsa yafi kyaun zuciya. Idan an fiki kyaun sifa yi kokari ki yi fintikau a kyaun zuciya." Na yi shiru ina sauraronsa da dukkan nutsuwata. Ya numfasa ya ce "Ki zama adalar uwargida Halimatu! Kada ki yarda ki yi kissar da mata suka fi kware wa ta tuggu. Fa'di magana anan, fesa a can sai kiga mace ita ka'dai ta cakalkala al'amura masu yawa. Kada ki yi kulunboton da miji zai zalunci wata matar saboda ke. Kada ki gallazawa abokiyar zamanki. Domin duk halittar da kika ga ni a doron kasa akwai manufar halittarsa. Ubangiji yana kishin bayinsa mussaman wadanda aka zalunta. Ki ji tsoron Allah! kada ki yi zaluncin da sakayya zata dawo miki ta inda baki yi zato ba. Duk matar da ta samu dama ta gallaza wa abokiyar zamanta ko y'ay'an da ba nata ba. Billahillazi Halimatu matar nan bata cin bulus. Ki nutsu ki yi duba na tsanake. Duk wacce ta uzzirawa wata lah shakka sai an uzzirawa nata yaran idan ta aurar da su. Mafi yawa kuma idan shekarun girma ya zo mata sai kiga komai ya kubuce mata, gidan ya yi mata kunci, hakanan a jarrabe ta da tashin hankali a cikin ya'yanta da lafiyarta." Tari ya sarke shi, sai da ya huta ya ce "ki sake duba duk wacce ta yi ha'kurin cutarwar miji, ko na kishiya a karshe sai kiga ta yi karfi a wannan gidan, domin Ubangiji ne yake bata kariya da kansa, ba kuma zata wula'kanta ba. Ina miki sha'awar kyakkawan karshe Halimatu. Sai dai bana son ki yi ha'kurin da yake na cuta ne, ko na rashin sanin ciwon kai. Idan kinga da cin mutunci to kawai ki ha'kura a maimakon ki shiga hanyar bata da sunan samun kan miji". Murya na rawa na ce ",Na gode! Na kuma ji duk abin da ka ce, zan kiyaye". Ya daga dukkan hannuwansa biyu sama ya ce "Allah ka saka Halima cikin bayinka da kake karba daga garesu, Ubangiji kasan yadda nake son aurenta ya dauwama! Ina rokonka ka hore mata mijinta, a cika zuciyarsa da soyayyarta mai tsayawa a rai, mai kuma naci, a baibaiye shi da tausayi mai hana zalunci, a sanya ta zama shugabar matansa har a aljannah". Na ru'ko hannunsa na ce "Ameen Abba! Ubangiji ya ji ka, madallah da kai". Ban San dalili ba sai kawai na sake kifa kaina a jikinsa ina kukan da bana ciwo bane, kuka ne mai shauki, ina ayyana ko mutane nawa ne irin Abba a wannan duniyar?" Daidai nan Baba ya shigo, ganinmu a hakan ya sanya ya yi turus. Ya samu gefe ya zauna. Ya ce "Kinsan dai bashi da cikakkiyar lafiya, amma sai ki zo ki tayar masa da hankali? Haka jiya kika yi, yau ma kin dawo, alhalin kinsan wannan koke koken zai iya sanya wa ya yanke hukunci na son rai. Ansan kishiya babu da'di to akan ki aka fara ne? Bana son rashin hakuri gaskiya". Abba ya ce "yi kukanki Halimatu ni kuma ina ta roka miki Ubangiji ya sanya wannan ne kuka mai tsanani da zaki yi a dukkan rayuwarki". Baba ya zauan a kasalance. Na dago na kalli Abba da tarin kauna irin wadda nake yi wa mahaifina. Ya mini wani irin murmushi da har yau bai bace mini ba. Ya ce "ki yawaita addu'a, ki yawaita istigifari". Na isa asibiti muka yi kicibus da Sakina sama sama muka gaisa ta zille a dalilin bata yarda mu yi doguwar magana saboda takunkunmin hana ta fa'da mini auren Gudale da aka yi. Kusan a tare muka tashi. Na bita muka tafi a motarta. A hanya na ce "oh Maman Nana har da ke a cikin masu boye mini Gudale zai yi aure?" Ta dan razana sai kuma ta ce "Na rasa yadda zan yi ne, ina jin tsoro ne, gani nake yi zuciyarki zata iya buga wa". Na dan yi yake na ce "Ba komai Maman Nana jiya Abba ya fa'da mini, zuciyata ta kusa tarwatsewa tabbbas! Domin ko runtsawa ban iya yi ba. Amma dazu da safe Abba ya sanyaya mini ita, ya kuma roka mini sassauci a wajen Ubangiji! Alhamdulillah na samu sukuni sai dai har yanzu kirjin ya yi nauyi sosai." Da karfi ta ce "Alhamdulillah! Allah ya a kara miki juriya, In sha Allah manufar da aka cusa masa auren ba zai samu ba, da ikon Rabbani". Nan da nan jikinta ya yi sanyi tabbacin bata so ta fa'di hakan ba. Ni kuma na waske tamkar ban fahimci komai ba. Na sani ko a gabana Umma ta yi mini rashin kyautata wa ba yadda zan yi da ita. Domin dai matar Abba ce! Matu'kar ba zan iya cin mutuncinsa ba, dole kuwa matarsa ta wuce cin mutuncina. Sannan ita ce ta haifi Antin Zaria, baiwar Allah da bata taba nuna mini banbanci tsakaninta da sister's dinta ba. Hakanan ita ce uwar Sakina. Ita ta haifar mini Gudale sannan kakar su Amnah ce. Kenan tana da tarin alfarmomi masu yawan da bazan iya yin fito na fito da ita ba. Duk yadda na kai da rashin ganin girmanta sai dai na barshi a raina, amma taci tudun da bazan iya keta ta ba. Na riga na gane k'addara ta yi mana wani irin dauri irin na huhun goro, tunda nima kullum a cikin takaicina take. Na numfasa na ce "Abba ya fahimtar da ni alamura masu yawa a yau din, na gasgata dari bisa dari babu son zuciya a tare da shi. Na kuma daura damarar bawa Yaya Gudale dukkan support din da mace ta gari zata bawa mijinta a yayin da zai kara aure. Ki taya ni addu'a na zama adalar uwargida". Jikinta ya mutu sosai ta ce "Na gode miki! Ni kuma idan har kika yi hakan na miki al'kawarin duk runtsi ina tare da ke. Abba ya ro'ke ni, na tsaya miki, kada na bari ki wula'kanta, na kuma tabbatar masa duk abin da zan yi dan ki gamsu kina da yar uwa mace zan yi. Zan kuma yi dukkan kokarina na ganin aurenki bai tabu ba. Da bakinsa ya tabbatar mini har aka daura aurenku baya so. Amma tunda kika haihu, ya tabbatar soyayyar da kike yiwa Namoriki mai girma ce. Ya tabbatar mini kullum sai ya ro'ki Ubangiji ya wanzar da aurenku muddin rai, ya baibaiye zaman naku da kwanciyar hankali da albarka Ya ro'ki ko bayan ransa kada na bari ki wula'kanta a hannun Namoriki'. Hawaye ya balle mini na tausayin Abba! Cikin wasiyyar da yake fa'da a bayyane, al'amarina ne akan gaba. Duk Wanda suka yi hira mai tsayi sai ya ce "kada a bar Sadik da iyawarsa a dinga saka masa ido, kada a kuma ayi fishi a yanke zumunta da shi, saboda halayyarsa. Sannan kada a bari Halimatu ta yi ha'kurin da yake na cuta ne. Har yau din nan ban san wani halitta da yafi Abba karamci da son dinke zumunci ba. Madallah da mutane da suke kokarin kyautata zumunci, madallah da mutane masu danne son zuciyarsu. Madallah da mutane masu sassauci da afuwa mussaman idan an zaluncesu. **** Muka isa gidanta na shige dakinta na kwnata ba jima wa barci ya yi gaba da ni. Barcin da ban yi ba shine yanzu ya gwada mini fin karfi. Sosai na yi barci domin sai kusan magariba na tashi, ina bude ido na ga Yaya Gudale yana tsaye tabbacin shi ya tashe ni. Ban ce komai na duro na shige bandaki. Ina fito wa na yi shimfida na tada Sallah, duk da na ganshi a zaune dirshan a bakin gadon. Na idar ya kalle ni ya ce "Na ce kada ki zo, amma saboda gardamarki sai da kika zo ko?" Ban kula shi ba illah iyaka na kafe shi da kallo mai tsananin gaske. "Tashi mu tafi". Ya fa'da da sigar umarni. Na mike shima ya mike. Ido cikin ido na ce "Ba inda zani kwana zan yi" "Kinsan Allah! Ba zaki kwana ba, akan me haka kawai ki baro dakinki ki ce zaki zo nan ki kwana?" "Ina da abin yi ne, kuka zan yi a jikinta, idan na kammala gobe zan dawo". "Saurara! Bana son shirmen banza kin ji". Dai dai nan Sakina ta shigo ta same mu a tsaye. Ta ce "A a ya haka kun yi cirko cirko tamkar zakaru". Ban amsa ta ba na ce masa "Idan zaka tafi yi tafiyarka, amma ba inda zani". Ya kalli Sakina ya ce "yanzu a gabanki take mini wannan wula'kancin amma kin kasa tsawatar mata?" Kafin ta bashi masa na yi fit na ce "Idan ta ce na bika tabbas zan bika sai dai da ikon Ubangiji sai ka ha'du da bacin rai a hanya". Nan da nan ya ce "Shikenan sai ki zauna ki kwanan amma ki sani tilas kika mini domin kuwa na sani tunda kika mini baki lah shakka sai na hadu da tsautsayi. Gobe zan dawo na dauke ki. Aniyar moda kuma tabi randa" Ya fice da sauri. Yayin da Sakina ta kyal-kyale da dariya tana cewa Guduyon Gudale sha mamaki. Ni kuma na daure fuska sosai. Ta zuba mini ido ta ce "Menene daliliinki na kin binsa? Bana son fa'dan rashin gaskiya". Nan da nan na fara hawayen takaicin Gudale. Ganin hakan jikinta ya yi sanyi, ta fice, sai ta yi dabarar turo mini Nana da kanneta Na'im da Haydar, da kuma Afrah da take lafe a jikina tunda suka dawo daga gidan Kakanin su Nana. Muna idar da sallah ta gabatar mana da abinci, ga mamakina sosai na ci abincin ko dan na tara yunwa ne, ko kuma dan ina tare da Sakina ne?. Cikin Sa'a mijinta baya kasar yana Dubai. Dan haka kwañan zaune muka yi. Ta dinga fahimtar da ni yadda zan kama kaina. "Ba ruwanki da matarsa, kar ki zalunceta, kaddara ce ta sanya gidanki itama shine gidanta. Ba kuma laifi ta yi ba. Babban abin da zaki yi shine kada ki yarda a raina ki, ki kame, ki masa biyayya da dukkan iyawarki, ki yi masa kawaici domin a yanzu sai kin yi ha'kuri a dalilin sai ya yi d'oki da zumudin samun sabon abu kamar yadda yake dabi'a ce. Zai ta yin abubuwan da zaki ga tamkar da gayya yake yinsu. Ba kuma da gangan din yake ba, ko dan ya musguna miki ba, yana yi ne saboda d'oki a lokacin ke kuma zuciyarki cike take da ciwo da kunci sai kiga kin sake tunzura. Kada ki bari ki dinga saka ido akansa ko matarsa, ki tattara ki jingine su, ki tallafi kanki, ki rungumi aikinki da y'ay'anki, har zuwa lokacin da zata zama yar gida ku zama d'aya". Na ce "To ki tsananta yi mini addu'a Maman Nana" Ta ru'ko dukkan hannuwana ta ce "Allah ya taimake ki, ya ninka miki hakuri da juriya, sannan ya baki azanci da hikimar zama. Kinsan fa gaba'daya zaman kishi azanci da hikima kawai yake bu'kata, ba munafunci da asirce asirce ba". Na girgiza kai na ce "ki dinga saka ni a hanya, har na fahimta". Ta ce "In sha Allah kuwa, duk dai ke din y'ar-iska ce, yanzun nan za'a fa'da miki yadda zaki yi, dan ki samu k'ima sai kawai ki je gabansa ki saki baki ai Maman Nana ta ce mini kaza da kaza, ai Yaya Al'amin ya ce kaza da kaza, Abba ma so yake ya rabamu, me za'a yi da halinki Halima?". Hawaye ya goce mini na ce "Billahillazi da ne! Ai yanzu na yi hankali". Ta saki kwafa ta ce "Da saura dai, idan za'a duba ta abin da kika yi ko kallonki ba zamu yi ba. Kiri kiri kin bak'antamu ni da Al'amin a wajen Namoriki. Alhalin duk dan kin yi mutunci muke yi miki komai, amma ke giyar soyayya ta bugar da ke hatta iyayenmu ma sai da kika nuna musu irin buguwar da kika yi a soyayyarsa". Kunyar kalamanta suka dirar mini na rasa me zan ce. Sai kawai na buge da cewa "ki yi hakuri dan Allah kada ki barni da kaina". Ta ce "Ya wuce ai Abba ma ya roka miki afuwa, ya ce ba yin kanki bane, maza irinsu Namoriki jarabta matansu suke yi". Washagari sai wajen goma muka tashi. Shima wayar Gudale ce ta tashe ni. Ina zaune ina mamakin barcin da na yi. Amma da na tuna bamu kwanta ba sai da aka yi sallar asuba sai na janye mamakin. Sakina ta sanya hijabi ta fita tana cewa "Ai tunda kina gidan nan kuma ba zai barni na sarara ba. Ta bud'e masa kofar falon tana yi masa sababin ba zai yi ha'kuri ba week muna dan runtsawa. Dake so yake ya samu tabi bayansa ina jin yadda ya lankwashe harshe ya ce "Goma fa! Da kuma tun takwas na zo fa? Kuma saboda na barku ku yi barci ku more ya sanya na bari sai yanzu, ashe ban yi gwaninta ba?" Ta wuce wajen yan aikinta Dan taga aikin da suke yi. Yana zaune a falo har ta dawo ya ce "Ina kwana?" "Ta dan murmusa ta ce "Yau kuma?" Ya waske da cewa "Ba dama na miki abin kyautata wa ki karba ki gode mini?" "Lafiya lau Namoriki shikenan?" Ya ce "Ina y'arki ina y'ay'ana?" Ina jiyo dariyar da ta saka tare da cewa "Yau kuma har da tambayar Yara? Allah ya yafe maka kawai". Ta wuce ta barshi. Ta le'ko ta ce shiga ki yi wanka ki fto mu karya". Ban musa mata ba. Na yi hakan. Na fito na tarar ta ajiye mini sabuwar doguwar riga free size, hade da inner wears sabbi. Na sanya na shirya fes tamkar bani da damuwa. Ina cikin fesa turare ta shigo ta ce "wow Autar gidanmu fa akwai taswirar kyau". Na murmusa dimples suka bayyana. Na ce na gode sosai! A ina kika samu inner wears size dina?" Ta waske ta ce "Ina dasu dama". Muna zuwa falo na ganshi suna cin abinci da su Nana. Ga Afrah akan cinyarsa tana fama da cinyar kaza. Ita kam tana son naman kaza, tamkar ni. Mamakinsa ya kama ni, na kasa tuna when last ya dauki Afrah. Yarinyar da bata samu kulawarsa ko ka'dan ba. Matu'kar zai dauketa to lah shakka ya kuntata mini ne, yake neman shiri, tunda ya riga ya gane yarinyar tana cikin weakness dina. Ba dan komai ba, sai saboda banzatar da ita da yake yi, gara Amnah ta samu kulawarsa sau dubu a kanta. Wani ikon Allah kuma Amnah ta fi jin tsoronsa ko dan yana zaneta da tsintsiya ne yayin da Afrah kuwa bai ta'ba dukanta ba. Muka karya cikin walwala sai saka ni yake yi a cikin maganarsa yayin da ni kuma nake sharewa. Ya ce "muje Guduyo! Zaki raka ni unguwa ne". Na girgiza kai na ce "Zamu fita tare da Maman Nana sai mun dawo tukun". Ransa ya baci ganin Sakina bata tanka ba. Ya mike ya ce "zo mana Sakina" Ta mike suka shiga dakinta. Dake kofar a bude take na kasa kunne ina jiyo su. "Sakina kin ga bana son haka! Ta ya ya zaki zuba mata ido tana mini wannan iskancin a gabanki? Haka kawai ta zo ta kwana baki hanata kin nuna mata daidai ba, na ha'kura na bar ta domin neman masalaha, yanzu na zo daukar ta, ta ce fita zaku yi still baki ce komai ba. Tsakaninki da Allah hakan dai-dai ne?" Ta ce "To ni ina nasan baka so ta kwana ba? Kuma yanzu Abba ne ya ce mu je ta za'bi furnitures din da take so, bisa adalci idan mun je ta za'ba sai na mayar da ita a maimakon gobe ta sake fito wa." A hankali ya ce "shikenan Sakina! Saboda Allah abin da ake mini ya dace, ke ya kamata a fa'dawa ko ni? Amma babu damuwa ku dawo lafiya". Ya fito a fusace ya tafi, wani iyashegen Afrah har da kukan zata bishi. Na dinga mamakin abin da ta yi, tana kallona amma wai shi take son bi. Muka zare jiki muka barsu da yan aikin Sakina muka fita. Irin kayana da Sakina ta zabar mini sai da na ce "Sun yi ku'di da yawa". Ta ce "Ku'di masu yawa Abba ya bayar ni kuma ba zan yi miki kyashi ko kwange ba" Hawaye ya balle mini na dinga jin kunyar da na cewa Gudale ni ba yar kowa ba ce, domin na yi imani sai an yi tsananin dace ne kayan Munubiya zasu kai nawa. Domin duk yadda aka siya mini kayan alfarma a farkon aurena, na yanzu sun keresu daraja. Hatta talabijin sai da aka dauko mini tafkekiya kuma new modern ban da kuloli na alfama. Haka kawai nake fakar idon Sakina nake dauke hawayen da yake ta kutso mini a dalilin karamcin irin na Abba da Sakina. A wajen muka bar kayan domin su zasu je su shirya komai. Muka je har gaban Abba ta bashi dukkan recit din siyayyar da aka yi, ya dinga sanya mana albarka, yana sake tausata, yana cewa komai kike so ki fa'da mini. Fatana kada ki bari a samu matsala ta bangaren ki, idan kika yi mini hakan kin biyani, ina tabbatar miki kuma ko na mutu ba ba zaki wula'kanta ba. Zan baza masu sa mini ido a cikin zaman aurenki". Murya na rawa na ce "Madallah da Abba! Na gode sosai, Ina fatan Ubangiji ya baka aljannar da ya tanada saboda masu zumunci". Sakina ta amsa da "amin". Daga nan na tashi na basu waje, na gaida Umma na wuce wajen Mamah. Ina ganinta na rungumeta tamkar yadda nake yi mata ina cikin shekarun kuruciya. Kukan da na hadiye ban yi a jikin Sakina ba, shine ita nake mata, a dalilin nasan nan gaba zan bu'kaci na sake yin kuka tunda dole nasan gwagwarmaya na gaba. Cikin kuka na ce "Mama har da ke ake boye mini abin da ya kamata ace na sani?" Ta ce "Nima sai shekaranjiya na ji. Sai ki k'ara, ha'kuri, kan ha'kuri tunda yanzu zai auro surukar da za'a so a nuna mata dukkan gata da soyayya." Na dinga kuka ita kuma bata hana ba, har sai da Yaya Al'amin ya shigo sa'be da dansa da ya yi wayo sosai. Ya ajiye shi ya sake hannu ya dago ni a jikin Mama ya sanya akan kafadarsa yana fa'din "Daure mana kinsan yadda kukanki yake dafa zuciyarta kuwa? Na sake barkewa da kuka, ina fa'din na gaza Yaya Al'amin" Ya ce "Baki gaza ba, har abada kuma ba zaki gaza ba. Karin auren namiji ba shine matarsa ta gaza ba. Ki yarda ibada ne domin Allah ne ya halatta. Ita kuwa ibada ana yi ne, ko ana so, ko ba a so. Ki k'ara ha'kuri, komai zai wuce, ki nutsu dan ki karfafa guiwar Abba. Ya damu da halin da yake ciki, ya kuma ce yana son mu fa'da miki ki yi hakuri, ki daure, komai zai daidaita miki." Haka Yaya Gudale ya shigo ya tarar da mu. Ya coge a bakin kofar falon. Mussaman da Mama tana kicin. Ya numfasa ya ce "Sakina ta gama nata famfom yanzu kuma kin dawo Al'amin yana d'ora wa. Ya shigo ya tsaya kusa da shi ya ce "Dan Allah dan darajar Annabi me na yi maka ne Al'amin? Bana nufinka da sharri, har yau har gobe kuma kana cikin muhimmai a duniyata. Amma sai ka dinga kokarin shatale ni, jibi yadda ka wani rungumeta tamkar yarinya yar k'aramar. Tsakanina da Allah ana mini ba dai-dai ba. Ai ni nafi kowa cancantatar na yi mata irin wannan rarrashin, amma kun zugeta tana guduna tamkar ajali. Bayan tun shekaranjiya da ta ji maganar auren nan ta tashi hankalinta, ta tashi nawa duk wani yun'kurin rarrashinta da nake yi ta tankwabar amma ta je wajen Sakina, yanzu ta dawo wajen ka alhalin na tabbatar ku duk gadar zare zaku shirya mana, tunda na gasgata bakwa nufina da alheri". Uffan Yaya Al'amin bai ce masa , domin ya riga ta hauro, idan kuwa ya bu'de baki ya sani sai sun yi rikicin da zai tashi hankalin iyayenmu. Dan haka ya sake ni, ya mike ya fice. Ya kalle ni ya ce "Zo mu tafi! Tun jiya kike gara ni, ina binki kina tozarta ni, wai ya kike son na yi ne?". Mama ta fito ta ce "Tashi ki bi mijinki ku tafi". Haka ya tasa ni a gaba muka tafi ina kuka sosai. Muna zuwa na yada zango a falo ina wani irin kuka mai cin rai. Ya zauna kusa da ni ya ru'ko ni, na zabura na fizge cikin kuka na ce "Kar ka kuma ta'ba ni, bana so, bana son ganinka." Ya yi shiru ya ce "Na sani zanga abin da yafi hakan, ba dai kin je an miki famfo ba?. Ba komai! Na gode. Ace wai Al'amin zai rungume ki ya rarrashe ki, amma ni bani da wannan damar. Kuma idan an tashi ace bani da kirki, ni murdadden mutum ne. Ina cikin tasku, ina cikin ba'kin ciki. Abba kullum na tsugunna gabansa da nufin na gaishe shi, mu dan yi hira da shi dan na ji da'di, amma ba zai yi mini hakan ba. Sai dai ya bige da magana akan ki, da ya bu'de baki zai ce kada na zalunce ki, kada na cutar da ke, kada na wula'kanta ki, amma ke an zuba ido kina cusa mini ba'ki cikin da yake neman kassara ni babu damuwa. Allah ya saka wannan shine kankarar zunubaina." Na share shi. Ya dinga son na bu'de baki na yi magana ni kuma na ki. Ya gaji ya mi'ke a matu'kar sanyaye ya ce "Shikenan! Shikenan Guduyo". Ko kallonsa ban yi ba. Sintiri ya yi shi yafi sau biyar. Har dare ban kula shi ba, bai gaji ba. Wajen goma na dare ya ce "Tashi mu shiga ki yi hakuri kin ji. Ina tabbatar miki ina jin kwatankwacin damuwar da kike ji. Ki yi hakuri tun sadda kike wannan tashin hankalin bani da sukuni. Ki ji tsoron Allah ki daina tayar mini da hankali haka nan. Kin je kin kwana lafiya lafiya a gidan Sakina. Amma kina dawowa kin dawo da masifa alhalin na barki ne dan ki samu nutsuwa. Ki yi ha'kuri, ki bani dama na yi biyayya Abba ya za'ba mini ke, na yi masa biyayya, yanzu kuma Umma sai ta ce bana mutunta ra'ayinta. Ni bani na ce ina sonta ba". Na katse shi ido tamkar garwashi na ce "Bani da hurumin kana so, ko baka so, ai nima ba sona kake yi ba aka baka. Itama kuma hakan ne saboda gata da ya kewaye ka. Wata'kila itama ka fa'da mata kumbusar matarka ba sonta kake yi ba, baka ita aka yi, akan tilas." Karon farko da naga ya shiga rudani dan na gasgata shi. Ya ru'ko hannuna ya ce "Billahillazi! Na rantse miki, ban taba maganar ki da ita ba. A farko na dauka kin fahimce ni saosai, saboda yadda kike sona da dukkan na'kasun da kowa yake mini kallon sun baibaiye ni. Ta Yaya zaki yi tunanin bana son ki, ta yaya zaki yi mini kallon zan ce bana son ki a gaban wata mace? Me yasa ba zaki kwantar mini da hankali a lokacin da nake cikin cankacakare ba? Me yasa Kika zabi ki bijire mini, ki gigita ni akan me Guduyo?" Ya dinga lallaba ni. Har na bu'de baki na ce "Shikenan na ha'kura. Ina fa'din haka ya ce "To taso mu je, ni nasan ba zaki ta'ba juya mini baya ba, domin na yi imanin son da kike mini garanti ne da babu algus". 2/8/23, 10:25 - Buhainat: *MURNAR ZAGAYOWAR RANAR HAIHUWATA* *14/01.* *Yau ne ranar birthday dina, a taya ni addu'a, Allah ya maimata mini, yasa na wanye ragowan kwanakin da suka yi mana saura cikin imani da kuma lafiyar da zan yi ibada da godiya bisa dinbin ni'imominsa gare ni* *Allah ya jiqan mahaifana mussaman uwa mahaifiya.* *Mama* *Ina ma kina raye na yi miki murna da barka ranar da kika tsallake siradin da Ubangiji da kansa ya ce wahala kan wahala ne.* *Na gode! Na gode!* *Allah ya jikanku, ya sanya kuna aljannah, da dukkan musulmin da suka rigaye mu*. *SDK* 77&78. Na kalle shi ido cikin ido na ce "wannan ne kuma ba zan iya ba. Na roke ka, dan Allah ka bar ni na samu sukuni". Ya kafe ni da ido na sani ba dan tsoron Abba ba da duka zai nada mini. Ya sauke ajiyar zuciya ya ce "zuwa yaushe zaki samu samu sukunin?" Na ce "Ban sani ba, ina dai bu'katar hutu da nutsuwar zuciya." Ya sassauta ya ce "Baki ga kamar haduwar tamu zata fi saurin saukaka miki damuwar da kike ciki ba? Kina lissafin adadin kwanakin da na dauka ina ha'kuri, ina tattala lafiyarki kuwa?" Na ja tsaki na ce "Kai da ba gamsuwa kake yi ba, kuma kana dakon tsukakke ba sai ka bar mini nawa ba?" Ya kufula ya ce "kin ce kin ha'kura me ya kawo wannan maganar? Ina lallaba ki ne saboda ki samu kwanciyar hankali". Na ce "Saboda ka samu dai! Idan kuma saboda ni ne, to barni na dauwama cikin damuwa da tashin hankali yadda ka saba sanya ni". Daga haka ya tashi ya koma daki ba tare da ya sake cewa komai ba. Washagari lahadi dukkan ahalin gidan muka hadu a gaban Abba inka dauke Antin Zaria. Hatta Yayar Kwalli ta halarci zaman. Yaya Abdallah ya bu'de taro da addu'a. Yayin da Abba ya yi nasiha mai shiga jiki, ya dinga nanata mu ri'ke Sallah, mu yawaita sadaka, mu kuma yi zumunci. Ba sai uwarku daya ubanku daya bane zaku yi zumunci. Ku sada zumunta da wanda ya yanke muku zumunci. Annabi ya yi ta wasiyya akan kada mu yi shirka, kada mu zubar da jinin mumini, kada mu tauye mudu, kada mu zalunci makwabatanmu, kada muci mutuncin junanmu. Ku yawaita istigifari domin mabudice na dukkan alheri. Ku sada zumunci, ku ji tausayin junanku, sannan ku zama masu afuwa da sassauci. Jikin kowa ya yi sanyi. Ya yi gyaran murya ya ce "Yaya kinsan wannan gidan asali na mahaifin mune, Ni da kanina Ibrahim muka gace shi. Duk da dai na fadada shi kwarai da gaske ta hanyar siyan gidajen da suke jikinsa. Dukkanku ku zama shaida kofar Ibrahim tasa ce halak malak. Yaya ta ce "me ya kawo wannan maganar Alhaji" ta fa'da murya na rawa. Yayin da Umma ta yi wuki wuki tasan ita yake kafawa hujja ba y'ay'ansa ba. A sanyaye ya ce "Ina jin tsoron shaidan a lokacin da babu hujja". Ya numfasa ya sake cewa "Auren Sadik kwanaki shida suka rage ga wanda Ubangiji ya kaddara masa ga ni. Ina son kowa ya saurare ni da kyau. "Na yi amfani da fa'din Allah da ya ce ya bawa namiji damar ya auri abin da ya yi masa da'di daga mataye bibbyu, uku, ko hurhudu, a karshe ya ce idan ba za'a iya ba ayi daya. "To shi ya ga zai iya, ya zabi ya yi kari, ni kuma ba zan matsa ba. Sai dai ina son ku zama shaida akan abin da zan fa'da domin ya zama an yiwa kowa adalci. "Sadik! Zaka kara aure amma ina son na rok'e ka idan har kasan a zuciyarka baka son Halima kada ka munafunci kanka ka magantu domin idan har ka yi aure kuma wula'kanci ya biyo baya ta kowacce fuska ba zan maka uzziri ba. Domin hakki ne akanka ka kiyaye mata mutuncinta a gaban danginka". Umma da Anti Maimuna suka yi wuki wuki domin dai shaguben Abba ya yi saurin ta'ba su. Ya zarce da cewa "Nine na baka aurenta, kuma tun wanccan lokacin na tabbatar maka nine ubanta. Kowa anan yasan halinka, yasan ba dan ita ce matarka ba da tuni an fara kirga maaka adadin matan da ka aura, ka saki. A ko'ina zan fadi gaskiya ko da hakan na nufin ta bata rayukan jama'a ne. Idan har zuwa yanzu da kuka shafe shekaru kusan biyar da aure kana ganin akwai na'kasu a cikin zamantakewarku to ka yanka duk abin da kake ganin ya yi maka daidai ni kuma zan fansheta. Domin ina matu'kar tsoron na mutu na barta a wulakantaccen hannu, ba ga kai ba, ba ga wadanda suke da tasiri akanka ba." Umma ta sake muzanta. Yayin da Yaya Sadik cikin rawar murya ya ce "Haba Abba! Haba Abba! A gabanta, a gaban Guduyo?" Muryarsa ta karye ya yi maza ya saka fuskarsa a dukkan hannuwansa tabbacin hawaye ne yake neman zubo masa. Dakin ya sake yin tsit kowa ya mayar da hankalinsa kan Uba da dansa. Sai da ya ha'diye kukan ya dago ya ce "A gafarce ni! Amma gaskiyar magana an tozarta ni a bainar nasi Abba? Kullum na zo gabanka da shaukin na zauna mu yi hira na ji da'di, baka duba hakan sai ka baibaiye ni da maganar Halima da girman hakkinta. Abubuwa da yawa da ake mini nake yin kawaici saboda kai, ba kowa ne za'a masa ya ha'kura ba. A duniya na tsani matata ta yi aiki, amma haka siddan. Sai ga Ashiru ya samo aiki ya kawo dan kawai y musguna mini. Na nuna bana so. Ba a duba uzzirina ba, aka bank'ara ni akan dole take aikin. Ni ka'dai nasan adadin ba'kin cikin da nake ha'diyewa a dalilin wannan aikin nata. Duk na danne na kai zuciya nesa saboda ina tsoron fidhinka, ina son zama da ita. Duk da hakan kuma sai a tara mini jama'a har da wadanda basa nufina da alheri, da wandanda idan na mutu baza su ji nauyin shiga gonata ba, ace wai za'a fanshi matar da ban ce bana sonta ko na gaji da ita ba a gabansu. Me na yi dana cancanci a mini irin wananan tozarcin dan manzan Allah?. Sai kawai ya fashe da kuka tamkar yaro 'kan'kani. Kuma kuka yake yi na tsantsar ba'kin ciki ba wai na iyashege ba. Yana yi, yana cewa "An ci mutuncina". Bansan ina matu'kar sonsa har lokacin ba. Domin ji na yi, na shiga wani irin tashin hankalin da bansan adadinsa ba ya sake rufar mini. Bansan ya aka yi ba, na ce "Kuka kuma Yaya Gudale?". Sakina da take gefena ta mintsine ni. Na yi maza, na kame bakina ina hirji ciki zuciyata. A ranar na ga zahirin kauna domin shi kansa Abba sai da kukan Gudale ya ta'ba shi. Ya dan diririce, sannan ya yi ta karfin halin cewa "To menene na kuka kuma tamkar Amnah?". Kowa na wajen sai da jikinsa ya sake yin laushi. Aka sake fahimtar jarumtar da Abba ya da'de yana yi akan al'amarin Gudale. Domin wani irin chemistry ne ya yi aiki mai matu'kar tsayawa a rai, da sha'awar karfin soyayyar da ke tsakanin Abba da Gudalensa amma zumunci da kawaici suka baibaiye shi yake ta boye wannan soyayyar, sannan yake ta jan kunnensa a kaina. Ni dai bana gajiya da jinjina wa Abba. He is my role model. Da rawar murya ya ce "Abba ai wallahi ban da dai ina da magauta a wajen nan da zasu iya yi mini vedio, da kuka zan yi irin wanda Amna ta dinga yi tana jinjira, dan ka gane tsananin ba'kin cikin da nake ciki". Girgiza kai Abba ya yi ya ce "Share hawayenka ka bu'de kunne ka saurare ni. Wallahi da gaske nake ba zan saurara maka ba, matu'kar ka ce zaka zalunci Halimatu ko bana raye idan ka cuceta akwai wadanda zasu kalubalenceka domin a hannun Ubangiji na damk'a amanarta, na kuma baza mutanen da Ubangiji ya cika zuciyarsu fa alheri su sanya mini ido a zamanku. Matu'kar kana son ka zama namiji a gidanka kamar yadda kake fata, to kuwa ka raba kanka da saka mata a harkar gidanka". "To na ji Abba! Amma ita Guduyon wacce irin nasiha kake yi mata a kaina? Ni bazan fa'di matsalata da ita a gaban Wanda basu ki yau ace bama tare ba. Zan dawo daga baya na fa'da maka duk irin wula'kanta ni da take yi dan ka dinga yin balance wajen jan kunnenmu gaba'daya. Na rantse ba karamin cutar da ni take yi ba. K'arfi da yaji ta mayar da ni bafade". Girgiza kai kawai Abba ya yi ya bar maganar tun kafin Gudale ya sake baro masa wata maganar da zata saka a kunyata ainun. Wannan maganganun na Abba sun sake zame mini dan zani a wajen Umma domin ba karamin kullata ta sake yi ba, mussaman yadda a gabanta aka bawa Gudale zabin ya sake ni, amma ya kasa karshe ya buge da kuka. Yaya da Baba suka tofa albarkacin bakinsu, su kuma sun fi jan kunnena, suna ta jaddada irin girman hakkin da miji yake da shi. Yayin da hakan ya yiwa Yaya Gudale da'di ya dinga fa'din "Na gode muku, ku fa'da dai yi mata matashiya domin gatan da ta samu ya saka ta manta." ***** Kwanaki biyu Gudale ya share ni, a dalilin Abba ya tozarta shi saboda ni a bayyanar nasi. Ni da shi kowa harkar gabansa yake yi. An kwashe komai na gidan, wasu na kaiwa Mama wasu kuma na sayarwa *AMYAS NEW & FAIRLY ITEMS* *08083909947*. Anyi sabon fenti. Ana gobe za'a zo jeren amarya. Sakina ta iso da masu shirya gida. Ba jimawa motar kaya ta iso. Gudale ma yana gidan. Suka gaisa, aka fara shigo da kaya ana ajiye wa. Gudale ya ce "Sama za'a hau da su". Sakina ta ce "Ban gane ba. Bafa kayan amarya bane na Halimatu ne". "Na sani ai, tuni mun gama magana da ita ta ce tana son saman". Nan da nan Sakina ta ci damara ta ce "Wannan shi ake kira gangan Namoriki. Tun fil'azal ai kasa na Guduyo ne. Sama naka, yanzu kuma da ka yi niyyar kara aure sai ka barwa Amaryarka samanka. Domin ina maka rantsuwa da zatin Allah komai kake nufin ya faru zai faru matu'kar ka nemi jan Wannan maganar". Maimakon ya bu'de mata wuta yadda ya saba. Sai ya sassauta ya ce "ke dadina da ke bakya fahimtar al'amura Sakina. Na fahimtar da Guduyo mun kammalah magana. Na fa'da a gidansu yarinyar cewar kasa ne nata, so kike na koma na karyata kaina haba Sakina". Ta make kafa'da ta ce "Wallahi ba zata dauki sama ba. Ko dai ka bawa Amaryarka sama ka koma ka karyata kanka, ko kuma ka samar mata wani waje. Ya kallo ni ya ce "Yanzu Guduyo ba zaki bude baki ki sanar mata ke kika zaba ba, sai ki bari ta mini kallon marar kirki?" Na dauke kai ba tare da na ce "kanzil ba, domin idan na ce zan kunyata Sakina tana iya nada mini duka sannan ta fita a dukkan sha'anina a yadda na ga ta tunzoro sosai. Ransa ya baci ya ce "Dama an fa'da mini yanzu zaki ko yi munafunci ta yadda zaki dinga boye alherina kina yada sharrina. Banda haka me yasa kika nuna mini kin amince?. Dama yadda nasan ni ka'dai ne namiji da ya kwanta a cikin Ummah, hakan na gasgata zuwan da kika yi gidan Sakina kulle kullen mugun abu kuka yi. Sakina b'ata tsaya b'ata yawun bakinta wajen fahimtar da shi ba ni ce na k'i ba, ita ce bata yarda ba. Yayin da nima ban kware mata baya ba. Ba'a dauki lokaci mai yawa ba, waje ya fara d'aukar harami domin tuni aka shirya falo. Har wani wajen karatu aka fitar mini. Zuwa yamma kuwa an kammala da ko ina, murna da daukin yadda aka gyara wajen ya yi matu'kar zangwaye kishin da nake jin tamkar na babbaka gidan. Na dinga yiwa Abba addu'ar gamawa lafiya. Kawai takaicin Gudale ne bai yi sassauci ba, mussaman yadda yake ta shirin yin biki cikin farin-ciki. Dan ya sake cusa mini takaici tunda ya ce nice na shiga tsakaninsa da ubansa. A gabana yake waya da Umma tana zayyana masa abubuwan da zai yi dan ya fita kunya a idon yarinyar da danginta, ya daina barin komai sai ita ta yi ko su Anti Maimuna. Baya Jin kunyar rarrashinta da cewa komai ina yi fa Umma, kawai yarinyar ce take raina kulawar da nake bata, alhalin kuma tasan ina sonta. Ni gaskiya Umma bansan ya zan yi ba fa, na fara gajiya". Yayin da ita kuma take cewa "A a ai hakan ma na samu, na kuma gode maka, an yi ban yi zaton ma za'a barka haka, ba tare da an sarrafeka ba. Ban da ina tsaye, ai da ko maganar aure ban isa na yi maka ba domin sai ka shafe kwanaki bakwai baka so ganina ba, tsabar yadda zuri'a gidan mai Ashafa zasu dinga rubuce ka a allon karfe, ko a tofe sunanka a ruwa ayi siddabarun da za'a ayi ta tafarfasa ka akan wuta. Ai masifar mutanen nan ba yar ka'dan ba ce." Wataran ya ce "Amma kin mini al'kawarin ba ruwanki da maganar mutanen nan. Wani lokacin kuma ya celNa fa'da miki asiri zai ci ni, amma ba zai yi tasiri ba Umma". Haka wadannan kwanakin masu tsauri suka dinga shudewa ba tare da na yarda da Yaya Gudale ba. Tun yana rarrashi da sauke duka girmansa, har ya fita harkata, tsakaninsa da ni sai bak'ar magana. Ranar da ya rage saura kwanaki biyu aurensa, da daddare ya same ni a falo inda na mayar makwancina. Ya sassauta ya ce "Yau kam tura ta kai bango. Zo ki ji Y'ar Abba". Na dauke kai na ce "Ina jin ka". "Abin da kike yi mini fa ya wuce ka'ida. Ki dubi uban ku'din da Abba ya narkar ya siya miki gadajen da zaki dinga lalube masa dansa da kyau amma fir kin rufe ido kin kasa gano manufar wannan alherin nasa". Na rasa yadda zan yi da takaicinsa, kawai sai na zabi na yi masa shiru. Ya ce "Ko kizo ki mini abinda zaki rabauta cikin farin-ciki da walwala ko kuma ki yi a dole kuma babu rabauta a tare da ke". Tsakin da ban yi niyya ba ya subuce mini. Ai kuwa babu zato kawai na ji ya buge mini baki. Zafi sosai na ji. Cikin ba'kin ciki da kishi na ce "Allah ya isana". Ai kuwa ya fusata ya ce "ni kika yiwa Allah ya isa Guduyo? Abin har ya kai da zagi? Na rantse miki ba zaki sake zagina ba, daga yau". Gaba'daya ya birkice ya shak'e ni, na saci kallonsa na ga idanuwansa a jirkice suke tabbacin yau ya tuna baya ya dan jefa k'wayarsa, abin da na jima banga ya yi ba. Tsoro ya kama ni, dana san a cake yake dan ban biye shi mun yi musayar yawu ba. Bare har na janyo wa kaina masifar da bansan inda zata tsaya ba. Wani irin murde ni ya yi tamkar ba dan tsurut ba. Ya sanya mini karfin da banyi zaton yana da shi har hakan ba. Wata irin mua'amala ya yi dani tamkar da baiwar da bata da k'ima ko ka'dan. Tun ina yun'kurin kwatar kaina har na fahimci ya da'de yana mini wannan tanadin. Dan haka na ha'kura na sallama ya yi iyakar abin da yake ganin ya hukunta ni. Tabbas na ji jiki, ya wahalar da ni, domin shi kansa tun yana yi dan ya samu nutsuwar da ya jima bai samu ba. Har ya koma yana yi dan kawai ya azabtar da ni. Tsawon lokaci sosai kafin ya tashi ya barni a wula'kance. Har asuba ina kwance, duk yadda na so na tashi na yi wanka kasawa na yi, dan tsananin ba'kin cikin halin da nake ciki. Ina kallonsa ya fito ya tafi masallaci. Da rarrafe na isa daki, na yi wanka da ruwan zafi sosai. Na dinga yin tsarki da ruwan zafi da kuma wani sabon cleansing cream na tsarki da Aisha lame jakadiyar Oriflame ta bani shawarar amfani da shi tunda na haihu. Kuma sosai nake Jin da'dinsa, har infections yake yaki da shi. Ina idar da sallah ya dawo. Ya kalle ni ya yi tsaki ya ce "ki ta wula'kanta ni saboda kawai ina miki kara ban ta'ba fito wa na fa'da miki ainihin yadda kike ba. Alhalin yadda kike bukekiya haka wajen yake". Na sandare, hawaye ya goce mini. Baki na rawa na ce "Ni Yaya Gudale?" Ya nuna ni da yatsa ya ce "Ke Halima! Domin kin tashi ma daga Guduyon tunda duk sun yi yaushi sun zama tamkar jarirai shida kika shayar". Ya yi shigewarsa ya barni da tsananin tashin hankali. Da wuri ya fice, a dalilin yau zasu yi dinner. Abba kuwa yana dawowa daga sallar juma'a sai gashi Yaya Abdallah ya rako shi har cikin falona. Duk yadda nake cikin damuwa hakan na daure na marabci Abba da murmushi da kanzagi. Yayin da shikuma ya ji da'di, ya yaba da kawatuwar wajena. A fili ya ce "Wato Halimatu ina son Sakina! Ina alfahari da ita, ki taya ni sonta, itama babu son zuciya a al'amuranta. Allah ka so Sakina, ka tsare ta, ka yafe mata". Na ce "Ameen Abba! Amma ni fa?" Ya murmusa ya ce "Ho autarmu! To ai ba sai na fa'da miki ba, domin ke din uwa ce, kinsan kuma yadda karamin d'a yake da shiga rai." Na yi murmushin da ya fito daga dukkan zuciyata, na ce "Ni da Yaya Abdallah wa kafi so to?" Ya tuntsire da dariyar da ban ta'ba ganin ya yi irin ta ba. Ya ce "Ashe kishi ne har haka da ke Sadiya?" Nima na yi dariyar na ce "Kawai ka fa'da Abba" Ya ce "shi na fi so. Kinsan shine babban d'ana". Na gimtse fuska na ce "To ni da maigidan nan fa". Ya ce "Kunnen doki kuke bansan wa yafi wani ba. Duk wanda yafi yiwa wani sassauci da afuwa a zamantakewarku to shi nafi so". Na yi dariya na ce "Allah ya baka aljannar daya tanada dan saddikai Abba" . Ya amsa da cewa "Ina ro'konsa ya sanya mu a rukuni daya da dukkan zuri'a, so nake mu makwabci juna a aljannar Halima". Ya miko mini dan karamin akwati mai daukar ido. Nasa hannu biyu na karba. Ina godiya sosai. Ya ce "Bu'de mana. Ina bu'de wa na ga wata irin dankareriyar sarka da zobe da kuma chain. Na zuba ido ina kiyasin mahaukatan ku'din da ta ci. Na yi kasa da kaina a dalilin raunin da ya shige ni. Na dago na ce "Sannu Abba! Madallah da Kai". Ya murmusa ya ce "ki yi farin-ciki, ki zauna a dakinki dan Allah. Amma idan akwai cutarwa kada ki yi hakuri. Allah ne shaidar yadda nake son aurenki ya yi k'arko, amma bana kaunar ki yi zaman kuttu. Kinsan halinsa Halima! Na sani kina juriya, addu'ar da nake yi miki na Ubangiji ya hore miki shi, In sha Allah ba za'a juyar da ita ba". Ya fita ba jimawa sai ga Yaya Al'amin da Yaya Ammar sun kawo mini katon fridge da injin wanki wai su suka siya mini. Ga akwatina uku kuma inji Baba wai kayar fa'dar kishiya ne ya fanshi Gudale. Basu wani jima ba suka tafi. Na zauna na yi tsam da raina na ga irin tarin dukiyar da aka tara mini duk dan a sanyaya mini zuciyata. Amma zuciyar kullum sake tafasa take yi mussaman da a yanzu Yaya Gudale ya sake murdewa. Na tuno motata da ta iso jiya. Na kalli tsadaddun frame da mahaifiyata ta siyo mini. Na sake kallon akwatinan da Baba ya mini dan ya wanke mini takaicin lefen da Umma bata bari an yi da ni ba. Akan kunnena ta cewa Sakina ko dankwali ba za'a siya mini ba. Tunda Abba ya kulle bakin aljihunsa saboda ni, komai ita take yi da taimkon su Anti Maimuna. Dan haka ba za'a mini komai ba, tunda ai nima an yi mini lokacin aurena. Motar da aka canja mini ba karamin kidimata taa yi ba. Mussaman da na barwa Yaya Ammar tawa ta da. Haka kayan dakin da aka sake mini, hatta Sakina sai da Umma ta ci mutuncinta. Domin so ta yi ta auro wacce zata kere mini a komai, sai kuma Abba ya fahimci manufarta, ya mayar da auren ya zame mini tamkar jari. Ya dinga nanata a kular masa da zamana ko bayan babu shi. Tabbas auren Yaya Gudale ya zo mini da tarin alfarmomi sai dai da yake an sanya mana k'yamar kishiya duk sai gatan da na samu bai wanke mini kishin ba, sai dai kuma na samu amincin kada a zo da sabbin kaya nawa sun tsufa. Karamcin Abba! Da yadda ya damu da farin-cikina, da yadda yake rokon na kwantar da hankalina na zauna lafiya da mijina sun matu'kar zangwaye haushin Gudale da ya damfaru a raina. Na k'udiri aniyar gyara kuskuren da nake yi, na gamsu k'arin auren da zai yi ba laifi bane. Ina zaune sai ga Amnah ta shigo a guje, Momi ki bani takalmin da Maman Abuja ta kawo mini inji Umma zamu tafi wajen bikin Dady". Na kalleta naga sai murna take yi. Na rausayar da kai na ce "To shiga ki dauko, yana dakinku ai". Da gudu ta yi study room din da aka kirkirar mini. Tana cewa "Momi shine ba ki ce na zo na ga yadda aka yi miki gyara ba?" Na ce "Ai yanzu kin ga ni". Ta shiga dakin da yake nasu ne . Ina jin tana ihun murna nasan kuma sabon gadonsu da fenti ne ya fa'da'da murnarta. Ta fito da takalmin a hannunta ya shiga dakina da yake makwabtaka da nasu. Jim ka'dan ta fito ta ce "Mummy gaskiya yau anan zan kwana. Ki cewa Maman Nana a dawo da Afrah." Na zare mata ido na ce "Maman Nana kika ce? Ke ba mamanki ba ce, Yayar tawa? Ta kame bakinta ta ce "very sorry Mummy. Maman sallari to". Na girgiza kai na ce "Ai bazan iya ba ". To ni na fa'da Mata?" Da sauri na ce" A a". Ta falfala tana cewa "Na tafi Ummah ta ce kada na da'de kar a tafi a barni". Na girgiza kai na dan yi murmushin da iya lebena ya tsaya. A fili kuma na ce "Umma duk nisanta ni da Amnah da kike yi dai ni na haifeta. Allah dai ya baki nisan kwanan da zaki ga sadda zata k'i saboda kin tsani uwarta". Ana idar da sallar la'asar ya shigo da leda a hannunsa. Bai ko kalle ni ba, ya fa'da dakinsa tunda yanzu ya tattaro ya dawo dakinsa na kasa tunda saman sun yi jere sun rufe abinsu. A kokarina na son dawo da mua'amala mai kyau a tsakaninmu na mike na bishi. Ina shiga na tarar wanka ya shiga. Na zauna na jira ya fito. Ya hau shirya wa cikin hanzari. Na isa gabansa na fara balle masa links, bai hana ba, bai kuma ce uffan ba. Muka kammala. Na kalle shi ya yi matu'kar yin kyau na dan murmusa na ce "Wannan amarya ta tsinci dami a kala. Autan Umma yafi tsada, tsada." Ya dauke kai. Na ce "Bai kamata ka bar ko wanne irin kunci a zuciyarka ba, kana shirin zama angon Yar shawalwala". Ya kafe ni da ido ya ce "Kin biyo ni nan din ma ki sake zagina ne?" Da sauri na ce "Haba dai rannan din ma subul da baka na yi. Ka yi hakuri". Ya ta'be baki ya ce "Ai ni ban iya hakuri ba, ke ni ban ma san shi ba". Ya dauki turare yana fesawa. Ni kuma na saka hannu na sake gyra masa zaman hularsa. Har bakin falo na yi masa rakiya. Na dawo na zauna ina ta hailala. Umma ce ta shirya kasaitacciyar mother's day a wani katafaren Hall. Na so zuwa amma Sakina ta hana ni ta hanyar cewa an baki gatin gayya ne?" Na ce "A a ". Ta ce "to yi zamanki kawai, ki yi ta salatin Annabi". Na ce "Tom". Duk yadda Umma ta ware Sakina a cikin hidimar sai da ta halarci wannan yinin wanda hakan ma bai fitar da ita a wajen Umma domin cewa ta yi tsurku ta je yi. Washagari asabar 7/01 aka daura auren Yaya Gudale da Munubiya. Auren da Umma ta so ta kuma girmama shi da dukkan zuciyarta. Yayin da Abba ya debi ido ya zuba a cikin sha'anin illah iyaka yana gefe yana addu'a kada Allah ya sa a kai ni k'asa. Sakina ta tabbatar mini zuciyarsa cike take da ba'kin cikin yadda aka raba masa gidan Sadik zuwa jami'iya biyu. Dan haka ta sake rokona na yi hakuri da duk abin da zan ga ni, domin hankalinsa ya kwnata, Lafiyarsa kuma ta inganta. Ita ma a daren ta kawo mini akwati biyu shake da kaya tamkar na lefe. Na yi murmushi da naga irin iner wears din a ciki ta bani wanda na saka dana kwana a gidanta. Dukkan yaran Umma na saman amarya inka dauke Antin Zaria da ta yi mirsisi ta k'i halarta bikin, duk kuwa da kusan rabin ku'din da Umma take wadaka da su daga aljihunta ne, sai kuma Anti Maimuna. Sakina ce kawai a wajena sai ka'dan daga cikin dangi, amma rabi da kwata suna sama domin kowa so yake ya samu shiga a wajen Umma. Amma nima dangin uwata da matan yayyena sun cika mini daki kowa yana kokarin sanyaya mini zuciya. 2/8/23, 10:25 - Buhainat: *SDK*. *79&80*. Zuwa goman dare kowa ya kama gabansa, gidan ya watse hatta kawayen su Yaya Al'amin sun mayar da su, sosai shi da Yaya Abbas suka shiga hidimar dan su huta gorin da Gudale yake yi musu na basu yi masa kara a lokacin aurenmu ba. Tunda shi a nasu bikin shine kirjin biki. A wannan karon sai suka wanke wancan laifin da yake ta kirarin sun yi masa duk da basu yi laifin ba. Tunda sun ce shine ya yiwa bikin rukon sakainar kashi. Sakina ce kawai ta rage a wajena, ta kasa, ta tsare kwana zata yi, duk kuwa da ta yiwa Umma sallama akan ta wuce gidanta. Muna zaune akan gado sai hawaye nake yi a dalilin gaba'daya kishi sai ya nemi dawo mini sabo fil. Yayin da Sakina take fa'din "Duk kokarin da kika yi, kuma sai ki dawo da hannun agogo baya?". Ban ce komai ba aka turo kofa, da sallamah ya shigo. Ganin Sakina ya yi turus. Da karfi ya ce "Oh oh waton Sakina na rantse kazallahar ki ta wuce min sherri. Kowa ya tafi ke kin zo kin tasa ta a gaba, kina sake koya mata dabarun kangarewa miji." Ta dauke kai bata tanka ba. Ya matso kusa da ni ya ce "Zo mu je ina son yin magana da ku". Na kalli Sakina na ga ta d'aure fuska. Dan haka na k'i tashi. Ya kalleta ya ce "Wai ke Sakina me kike ji da shi ne? Me kike nufi ne? Ni da gidana, da kuma matata amma maganarki tafi tawa muhimmanci?" Ita dai kawai kallonsa take yi, bata bu'de baki ta ce kanzil ba. Yasan kuma indai har ta zama irin haka to ta kai koluluwar fusata ne. Ganin hakan sai ya sassauta ya ce "Ni bana son irin haka gaskiya, to me na yi, kike mini irin wannan fishin?" Still kallonsa kawai take yi. Ya kalle ni ya ce "Ta so tana jiranmu". Sai lokacin ta ce "Tunda dangin amaryar basu kawo mata ita gabanta ba. To ita ma kuwa bata isa Halimatu ta je dakinta da kowacce irin manufa ba. Duk abin da aka dora ta akai zamu tabbatar mata, mun riga ta tashi". Nan da nan ya karaya ya ce "Sakina ke din cikinmu daya meyasa zaki bada gudunmawar ruguza gidana?" Da sauri ta ce "Cikinmu daya tabbas. Sai dai ni din yar'uwar Halimatu ce dan haka zan yi komai dan bata kaskanta a idon Amaryarka ba, ko da hakan na nufin tarwatsewar gidan ba wai ruguzarsa ba". Ya girgiza kai ya ce "kin zabi Halimatu kenan?" Ba ja ina ja ta ce "Eh". Ya yi kwafa ya ce "To yanzu fa'da mini yadda za'a yi?" Da sauri ta ce "Ka yi tafiyarka, gobe idan Allah ya kaimu sai ka daukota ku zo gabanta sai ka yi kowacce magana, na yi maka al'kawarin kuma zata saurareka". Ya juya yana cewa"yau ina ganin lukutar masifa, wai ni Sadik ake yiwa irin wannan tijara da ba'kin iko a gidana amma na kasa katabus. Tabdi jam! Annabi ya yi gaskiya da ya ce kaid'inku mai girma ne. Na tabbatar kin fi masifa tijara Sakina. Allah ya jikan mijnki ba dan ya mutu ba." Yana fita ta ce "tashi ki yi sallah har sadda zaki gaji, a maimakon ki zauna zuciya tai ta hakaito miki al'amuran da ba zaki iya hana faruwarsa ba, amma idan shaidan ya ga zaki ci riba sai ki ga ya bijiro miki da barci mai gushe dukkan damuwa. Dan haka ribaci daren, a maimakon ki zauna wasiwasi ya sake kidima ki". Hakan kuwa aka yi. Na yi sallah sosai na, har sai da gabbaina suka gaji. Akan sallayar na bingire. Sai da asuba ta tashe ni. Ina sallah ina kuka, ba dan komai ba, Sai dan kirkin Sakina ya shahara. Bamu koma barci ba, ita ta jagoranci aikin abin karyawa. Ni nawa ido ne, da nuna inda wani abu yake. Kafin taran safe ta shirya lafiyayyen abin karin kumallo. Muka yi wanka, muka kintsa. Wata irin kwalliya marar hayaniya ta tsantsara mini. Na sanya tsadaddiyar kamfala da ta samu shahararrren dinki. Ga kamshi tamkar ni ce amryar. Ta yi murmushi ta ce "Hakan nake son ganin ki. Uwargida sarautar mata, muka yi falo. Ta zubo mana abincin ni da ita a waje daya. Na zauna ina share hawaye. Ta ce "To kukan na menene?" Na girgiza kai na ce babu komai. "Ina so na ce miki na gode ne. Amma sai na ga kalmar ta yi kadan a ma'auni". Ta girgiza kai ta ce "To menene abin godiyar, idan za'a mini kishiya ba zaki zo mini dannar kirji ba kenan?" Na murmusa na ce "Ai ke Baban Nana ya same ki fiye da yadda yake hari". Sai kuma kukan ya subuce mini gaba'daya. Ta ce "da kuwa sai yamma zan tafi, amma na fasa ina kammala karya wa zan yi gaba tunda zaman nawa bashi da amfani". Na ru'ko hannunta na ce "ki yi hakuri dan Allah". Goma saura ya fito, ya yi wankansa ya shirya. Ya zauna kusa da Sakina yana cewa "Ran ki ya da'de kasaitacciyar mace". Ta yi kamar ba da ita yake ba. Ya kalle ni ya ce "babu gaisuwa ne?" Na yi yake na ce "Ina kwana, ya kwanan bakuwa?". Ya amsa da cewa "A safiyar nan kuka shirya wannan abin karin?" Na dan yi yake domin ganinsa da na yi har ya yi wanka ba karamin haushi na ji ba. Cikin karfin hali na mike na dauko masa na su da Sakina ta shirya musu cikin basket. Na ajiye a gabansa na ce "Ga naku". Ya kalli Sakina da ta yi kamar bata wajen, ya ce "kirkinki yawa ne da shi Sakina. Sannu na gode sosai. Kawai kallonsa ta yi. Sakina ce kawai take share Gudale ya damu, haka nan ita ce zai yiwa magana ta bagarar da shi, ya dinga bibiyar ta kula shi. Kusan ma daga ita sai Abba ne kawai Gudale ya damu da fishinsu, domin ko Umma ce, ita take fara saukowa ta neme shi, duk da ba kasafai ma take dogon fishi da shi ba, sai a dalilina ko a dalilin yana shigewa mahaifiyata ko yan-uwana. Ya dauki basket din yana "Madallah da kokarinku. Amma da Sakina zata bar ki, kamata ya yi ki kawo mana da kanki, dan ta ga girmanki, kin katse barci kin yi mata irin wannan alherin". Na kalli Sakina na ga ta d'aure fuska tamkar an fa'da mata mugun abu. Ganin hakan sai nima na kame, ya tafi yana cewa "Rakumi da akala". Ta girgiza kai ta ce "zai yi wahalar gaske ta yaba alherinki, kawai yi kokarin yin komai dan Allah domin kuwa dan Adam yana da dabi'ar manta alheri, da ri'ke kuskure. Sannan mafi yawanmu bamu cika yin uzziri a cikin mua'amalar yau da gobe ba. Dan haka duk da abin da zaki yi, kawai yi dan Allah, domin idan kika yi saboda shi to ko mutane basu yaba miki ba, baki da kaico. Domin wanda kika yi saboda shi zai yaba miki'. Na ce "To" da dukkan zuciyata. Sakina na gidan suka sauko tare. A falo muka zauna, na karbi amarya cikin karfin hali da juriya. Na dinga yake ina gabatar mata, da lemo, ruwa da cincin. A hankali ta gaida sakina. Yayin da Sakina ta amsa bayan ta mi'ke yi latse latse a wayarta ta ajiye ta a inda ta tashi. Na zauna a kujerar da take fuskantar mai uku wacce suke zaune. Cikin hikima nake kallonta. Tabbas kyakkawa ce, farace ta sosai, sannan mai gashi domin yadda ta nannade shi cikin ribon ta yadda daurin kallabinta ya zauna sosai. Baya ga haka kuma doguwa ce siririya daidai da ra'ayin Gudale. Sai dai tun a lokacin na fahimci ta girme mini. Domin a lokacin shekaruna asirin da biyar, yayin da ita ba zata yi kasa da ashirin takwas ba. Yadda nake satar kallonta, haka itama take satar kallona tana kare mini kallo. Tsawon lokaci yana cin cincin dinsa tare da kallo a allon talabijin. Kafin ya yi gyran murya ya fara yin addu'a. Ya zarce da cewa"Ina fatan ku zauna lafiya. Dukkanku ina sonku, ba kuma wacce zata saka na wula'kanta wata." Ya kalleta ya ce "Na san halin matata, nasan abin da zata yi, nasan wanda ba zata yi ba. Idan har kika ga baku zauna lafiya ba, to matsalar a gunki ce. Domin mai hakuri ce, matu'kar ta bude baki da nufin yin korafi to ta da'de tana yin hakuri da alkunya ne. Na auro ki ne, dan ina sonki, ina kuma da muradin yin hakan, amma ba dan ta gaza ko dan bana sonta ba". Dukkanmu kowa ya yi shiru yana kallo da saurarensa, gaba'daya mamakinsa ya rufe ni, ban yi zaton zai yi fatali da hudubar Umma na ya nuna mini iyakata idan ya yi aure a gaban matarsa ta yadda zan gajiya na bar gidan kowa ya huta. Ya juyo ya mayar da hankalinsa kaina. Ya ce "Guduyo! Kada ki aro halayyar da ban sanki da ita ba, domin ba zan yarda ba. Kin sani ko a wani gidan kike aure, ni din zan iya zuwa na ladabtar da ke matu'kar kika hana a zauna lafiya, bare kuma a hannuna kike, matsayinki yawa ne dashi a wajena, domin tun kafin aure ya hadamu, jini ya ha'damu, bayan haka ke ce uwarsu Amnah. Dan haka yadda kike da alfarmomi masu yawa a wajena, haka hukuncin da zan yi miki idan na same ki da laifi zai fi yawa. Domin kin fita sani na, yadda kika fahimce ni, ita bata fahimta ba. Komin kankantarki ke ce babba, dan haka ki ri'ke girman da Ubangiji ya baki, ki mini uzziri a inda na kuskure. Abin da nake son ki ri'ke shine ban yi aure dan na musguna miki ba, idan kuma ajizanci ya saka na musguna miki din kar ki ji cewar an sha gabanki ne a wajena, domin itama wataran zata ga abin da zan yi a kanki har ta yi zaton ban san komai ba sai soyayyarki." Na dinga kallonsa ina sake mamakinsa, ban yi zaton Yaya Gudale zai iya wannan jarumtar ba. Ban yi zaton a halin da muke ciki zai daura mini zani a kasuwa ba. Gaba'daya na fi zaton yadda yake kushe ni, yake gasa mini bakaken maganganun da suke gigita zaman lafiyata, hakan zai nuna wa amaryarsa dan ta raina ni, na sake shiga kunci. Sannan ashe yasan ta girme mini, amma ya dinga cewa sa'ata ce. Sai dai abin da yayi yanzu ya fahimtar da ni Gudale murdadden mutum ne, na bugawa a jarida. Fahimtar abin da yake zuciyarsa sai Ubangijinsa. Na sani yana sona, amma soyayyar bata hana ya mini iyashege. Kaso mai yawa na kishin da yake cina ya sake yin sauki a dalilin maganganunsa. Ya sake tsananta kallona ya ce "fa'di tsarin da zan yi muku wajen rabon kwana". Na sake yin yak'e a dalilin yadda zuciyata ta fara rawa, ba dan komai ba sai dan a yanzu zan dinga raba shi ne da wata. Kai ban da Ubangiji ne ya kaddara wannan al'amarin namiji ya mua'amalanci mace sama daya abin a kyamace shi ne kwarai da gaske. Cikin karfin hali mai yawa na ce "Na bar muku zabi duk abin da ya yi muku zan bi ra'ayinku da dukkan zuciyata." Ya kalli Munubiya ya ce "To ke fa'di tsarinki". Girgiza kai kawai ta yi ba tare da ta ce komai ba. Ya juyo gareni ya ce "To ku dinga yin kwana biyu". Na ce "To". "Sai maganar girki kowacce ta yi nata, hakan ya yi muku?". Nan ma ni na amsa da cewa "Ya yi". "Shikenan mai magana ta yi a Cikinku". Tsawon lokaci Munubiya bata ce komai ba. Ganin hakan ya sanya na ce "Kuna da sati guda da shariaa ta lamince ku yi kafin a raba kwana. Ni kuma na k'ara muku sati biyu. Kenan sai nan da sati uku za'a fara bin tsarin kwana bibbyun da ka ce". Munubiya ta 'dan murmusa ta ce "Na gode". Yayin da ya kafe ni da wani irin kallon bacin rai. Kallon da yake mini ya tabbatar mini ban yi masa gwaninta ba . Asalima tamkar na kunduma masa ashariya hakan ya yi. Sai dai da yake ido mashi ne sai idanuwan munubiya suka sanya ya ha'diye dukkan fishin da nake ganin yana kutsowa tun daga kasan zuciyarsa. Murya ba amo ya ce "Allah ya zaunar da mu lafiya". Ta mi'ke ta ce mini "mu yini lafiya. Yabi bayanta. Yayin da na bisu da kallon mamakin yau ni nake ganin Yaya Gudale da wata macen da muka yi kunnen doki a wajensa. Sai da ya rakata corridor din da kafar benen take ya ce "Ina zuwa bari, na ga Sakina". Ya dawo ya kalle ni ya ce "Su Guduyo iyayen gida, sarakan kankanba har da fece kwalliya haka, ke a dole sai an ga kema fa ba dama". Na murmusa tunda na sani zolaya ya yi mini. Ya shige daki wajen Sakina. Na bi bayansa. Ina shiga ya juyo ya ce "Koma inda kika fito domin sirri zamu yi". Sakina ta fit ta ce "Babu sirri a tsakanina da ita, komai ka fa'da mini zan fa'da mata, idan kuwa baka son ta ji to kawai ka rike maganarka." Ya girgiza kai ya ce "Sakina mu ture wasa kinsan dai ina da hakkin zumunci da ke. Tsakani da Allah ya kamata ki yiwa daya matar tawa ma adalci. Ba zan so tun yanzu ta fahimci bani da kima ko ka'dan a wajenki ba. Tana da hakkin ki yi mata a adalci a matsayin matar kaninki" Ta ce "Zan yi mata amma idan ka toshe kofofin da zata raina ni, ko ta raina Halimatu. Sannan ka fahimtar da ita cewa da akwai banbanci a tsakaninta da Halimatu a wajena, tunda uta wannan k'anwata ce kuma gidanmu guda. So karku yaudari kanku cewa zan mua'amalence ta yadda zan mua'amalanci Halimatu". Ya sake girgiza kai ya ce "Hakane! Amma dai ki kamanta Sakina. Kinsan dai yadda nake kambaba ki". Na yi sukuri ina mamakinsa yanzun nan ya gama daura mini zanin arziki a gaban matarsa, ya zo daki zai kunce mini ita kuma ya d'aura mata. Na yi murmushi domin dai ya wanke mini zuciyata, sannan gara ya mini hakan akan ya muzanta ni a waje ya ce zai kyautata mini a d'aki. Ta mike ta ce "Anjima ka'dan zan tafi, zamu leka muga dakin amarya. Amma ka saurare ni Namoriki! Ka zama adali a gidanka, kar ka sake ka muzanta Halima a gaban amaryarka da sunan zolaya. Koda wasa idan ka bada ita a gaban matarka, ka tabbatar zan jagoranci ta bayar da kai a idon duniya". Ya cukune ya ce "Sakina! Gaskiyar magana kankanbarki yawa ne da ita. Gaba'daya kin nuna mini mi bani da wani alfarma da zaki yi mini, komai Halimatu, duk alherinki ba kya nufar kowa da shi sai ita. To bari ki ji. Tafi son Al'amin akan ki, shima ya fi sonta a kaina, amma ke fir kin bantse mini, na kasa sarrafa ki cikin dadin rai, alhalin kinsan yadda kike a wajena". Nan da nan sai rauni ya shigeta. Ta sassauta ta ce "Ba haka bane, ai kaima ka sani bana ha'da al'amarinka da kowa. Sai dai kuma idan gaskiya zan fa'da ana fa'da maka abubuwan da yake gurbata mini tunanin dan-uwana. So nake Namorikina ya zama tsayayyen mutum mai ra'ayin kansa. Ya mutunta abin da zuciyarsa take so, ya kalli dunbin soyayyar da matarsa take yi masa, ya daina bari ana haska masa ita nagative. Sannan ya tsaya akan kafafunsa, kada ya yarda ayi masa ingiza mai kantu, domin lah shakka anzo kadamin da bazan yi maka uzziri akan al'amarinta ba. Kana sonta menene dalilin da ba zaka nutsu ka mutunta zamanku ba?".. Ya bata rai ya ce "Ai shikenan tunda kin gama bada ni a gabanta. Sakina kin sani ni mutum ne mai son sirri, mai son a girmama shi, akan me zaki mini hakan a gabanta. Yanzu kin bata lasisin da zata yi ta yin iyashege tunda ta sani an tsaya mata." Ya kalle ni ya ce "Ki je ki biya Malaminki. Kin kwace mini Abba da sakinata. Kina kuma shirin raba ni da Al'amin. Babu komai Allah ya bani ladan hakuri kawai." Ya juya ya fara tafiya da nufin barin dakin sai kuma ya dawo. Ya kalli Sakina ya ce "kun dame ni akan kada na muzanta ta a gaban Amaryarta, saboda kuna kishinta. Amma ni ta wula'kanta ni, ta nuna wa amarya am nothing to her.". Na zare ido na ce "Me na yi maka dan Allah?" Ya harare ni ya fita yana cewa "Ki je kin samu. Ki kuma jira abin da zai biyo baya domin tare zamu dandana wannan ba'kin cikin da kika kunsa mini". Sakina ta mini signal da Ido akan na rabu da shi. Sai da ya fita ta ce "Idan yana wannan dagewar, ai yi zaki yi, bakisan kin yi laifi ba, bare har ki damu." A hankali na ce "Tom". Domin gaba'daya jikina ya yi sanyi a dalilin yadda ya rikice cikin dakika ka'dan tamkar mai rauhanai. Da sauri Sakina ta fita falo a tunanina bayansa ta bi. Ashe wayarta ta dauko. Ta kishingi'da ta kunnata sai ga maganganun da muka tattauna bayan ta shigo daki suna fita tar tar. Ta dinga murmushi tabbacin Gudale ya yi abin da ya yi mata dadi. Ta kalle ni ta ce "Na Moriki yau ya yi bin a yaba masa." A sanyaye na ce "Me kika ji na fa'da da yake nufin na yi masa cin fuska?" Ta girgiza kai ta ce "Ba ki yi komai ba. Kawai tuntsirewa yake son yi. Kin yi jarumtar kara masa kwanakin amarci, sai dai na so jarumtar tafi haka, ina ma wata kika bashi, ta yadda zai gama doki da rawar kai kafin ya dawo miki". Na yi kasa da kaina tabbacin ba zan iya ba, satin biyun ma ba karamin karfin hali na gwada ba". Tare muka hau saman amarya da Sakina. Ta karbe mu da sakakkiyar fuska, ta kuma shiga da mu ko ina. Tabbas an shirya mata kayayyaki na alfarma, sai dai kuma basu kere nawa kayan ba. Muka zauna a falo ta bamu ruwa da lemo. Yayin da Gudale yake kishingi'de a kujera, a yanayinsa na fahimci baya cikin sukuni sosai. Yayin da duk motsin da zan yi said na ga Munubiya ni take kallo, wani irin kallon kurillah take yi mini da ya sanya na tsargu sosai. Bamu jima sosai ba muka dawo. Kwanakin amarcin nan ba k'aramin juriya na yi ba. Domin Umma ta zo ta ga dakin amarya, karon farko da ta shigo gidan Gudale, amma ta kasa yi mini kara ta shigo wajena. Ko da ace ta shigo din tabbas zan ji a raina ba dan ni ta zo ba, amma dai na ci albarkaci. Amma da suka hau saman amarya suka gama zamansu ba kunya ya ba kara suka yi tafiyarsu. Idan na ce ban ji haushi ba, na yi karya. Na dinga share hawaye ina ganin idan Umma tana ganin ni ba jininta ba ce, ba zata yiwa mijinta kara ba, to Anti Maimuna fa? Ace har zata ita zuwa ta shiga dakin Munubiya da basu hada komai ba illah matar kaninta. Amma Ni da jini ya ha'damu ta iya yi mini irin wannan wula'kancin? Yini na yi ina share kwalla. Komai ya nemi kwace mini a wannan kwanakin a dalilin shi kansa Gudalen wani irin fishi yake yi mini da bansan dalilin yinsa ba. A daddafe aka cinye wannan satin uku da na lamince su yi tare. A lissafin kwanaki tabbas sati uku ne, amma a wajena sun zarta watanni uku nisa da tsanani. Kusan kullum sai na yi kuka wala da rana, ko da safe, idan nasa kaina a filo da daddare kuwa wannan ya zama wajibin. Na yi zuru-zuru. Fuskata ta zama yar kuyas, ido ya sake fito wa. Bana samun sauki sai na fita wajen aiki, idan na dawo kuwa tamkar a kofar gidan nake ha'duwa da bacin rai. Kowa ya ganni yasan na fa'da amma ba wanda yake tambayar ba'asin ramar tunda ana ganin ina cikin yanayin da bai kamata a tambaye ni ba. Abba ne kawai duk sanda na shiga gaishe shi, sai ya ce "Kara hakuri, nasan ke din mai hakuri ce, amma a wannan lokacin da ake son sai kin gaza, Sai nake son kin ninka juriyarki, ki kuma tsananta addu'a. Madallah da ke Halimatu". Ire iren wadannan kalmomin na Abba su suke sanyaya mini zuciya, na samu k'warin guiwar ha'diye dukkan kalubalen da ake jifana da su. Domin na riga na fahimci ba abin da Abba yake so irin aurena ya tsira. Ranar da zan karbi girki, yini na yi cikin doki da farin-cikin zan samu yau na yi cikakken barcin da na jima ban yi ba. Na tanadi wannan ranar, mussaman Aisha lame ta shirya ni da products din oriflame da sai manyan mata ne suka san Martabarsa. Bare kuma kayayyakin *Faseelat* da kullu yaumin nake hadiyarsu. Cikin Sa'a ranar week end ce dan haka ina gida. Cikin karsashi nake yi masa snacks din duk da nasan yana sonsu. Ni da kaina mamakin yadda na zaku mu kebe nake yi, ban sani ba, ko dan tsawon lokaci mai yawa bamu hadu bane, domin dai haduwar da muka yi a falo ta tsiya tsyia ce ban gane komai ba sai wahala. Tun lokacin kuma ba'a sake ba. Itama kuma kafin ayi an dauki lokaci mai yawa tun kafin na haihu. Ko kuma supplement din da nake sha ne yake tasiri. Tun karfe biyar na yi wanka, na yi kwalliya tamkar me shirin zuwa gasar miss Nigeria. Da kaina na dinga gode wa Ubangijin da ya kyautata mini halitta. Sai dai me? Tunda ya dawo daga aiki na yi zaton zai shigo mini, amma sai jin takunsa na yi yana hawa sama. Nan da nan zuciyata ta fara baci, amma dai na sake na yi masa uzzirin ko zai dauko wani abu ne ko dai wani al'amari. Amma ga mamakina ya fito ya wuce sallar maghrib da ya dawo ma ko lekena bai yi ba, ya sake hawa sama abinsa. Daga lokacin na karaya komai ya kwance mini, a falo na zube ina wani irin kuka, tamkar kirjina zai fado. Wanne irin muzanci Gudale ya yi mini tanadi haka? Rana ta biyu da na yi kwanan zaune ba tare da barci ya sure ni ba. Na yi kuka fiye da kukan da na yi da na ji labarin karin aurensa. Tun a ranar kuma wani irin abu ya tsaya mini a cikin zuciyata. Washagari sassafe ya dawo daga motsa jiki ya shigo mini yana sanye da kayan motsa jikin, kafarsa sanye da boot an rubuta sport. Ina zaune a falo ido ya yi luhu luhu, tamkar matar mamaci. Karon farko da na gan shi na ji har cikin zuciyata bana son ganinsa. Ya zauna ya na mini tambayar da ta nemi sumar da ni. "Menene ya same ki haka Gudidina?" Na kalle shi hawaye na goce mini. Na kasa cewa komai. Na tuna a safiyar jiya asabar sai da muka yi maganar da yamma zan kar'bi girki, amma ya murtsike ya kaiwa wata hakkin da yake nawa ne. Har da yamma ma da na kammala snacks sai da na yi masa waya akan ya taho mini da youghrt sannan kuma kar ya tsaya a ko'ina na tanadar masa snacks kala-kala. Ashe kuwa babban wula'kanci ne ya tambayi ba'asin kukana ko ba'asin halin da nake ciki. Ya mike ya ce "Na dai tambaye ki, na fita hakkinki. Ya kalle ni, ina kuka! Ya ce "Dama zan fa'da miki ba sati biyu ya kamata ki bani ba, hudu zaki bani, kin ga ya zama sati biyar, a lissafin kwanaki kuma talatin da biyar. Jarumta ta shige ni ta ban mamaki, na zuba masa ido sosai na ce "Na baka shekaru hudu Yaya Sadik". Na mike na bar shi a wajen. Ya tunzura ya ce "Kika sake yi mini wula'kanci, ni zaki tashi ki bari? Waton kin wula'kanta ni, kin ci mutuncina a gaban wata ta hanyar neman kai da ni na sati biyu. shine yanzu kika yi na shekaru hudu?" Na ja tsaki na ce "Na gama magana kuma Sadik! Na baka shekaru hudu, dan Allah ka yi tozarcin da yafi na jiya tsanani". Yadda na kwana ban runtsa ba, haka na yini ban tsinana komai ba. Kuka da sallah kawai nake yi. Har dare ban saka ko ruwa a bakina ba, tashi guda na yi wata irin rama tamkar na shekara ina ciwo. Kwana biyu ina cikin wani irin tashin hankali, da bana fatan ko makiyata ta shiga irin wannan yanayin. Amma da na tsananta addu'a, na fara azumi, a dalilin abincin ba iya cinsa nake yi ba. Dan haka sai kawai nake yin azumi, nake nacin tsayuwar dare. Alhamdulillah kuma na samu sassauci. A kwana na uku na dawo daga asibiti ba jima wa. Munubiya ta shigo wajena ta ci kwalliya, kuma ta yi k'yau matuka da gaske. Hannunta dauke da babbar leda mai kyau da alamu suka nuna daga waje aka taho da ita. Duk da kishinta da yake cina, da hannu biyu na marabce ta. Ina ta yi mata yake bayan na baibaiye ta da ruwa da lemu, da snacks din da na bata lokaci na yiwa Gudale amma ya mini tofin Allah tsine. Da muryarta da gayu da ilimi suka ratsa ta ce "Maman Amnah bayan sati biyu da kika bani, sai kuma kika sake kara mini da wasu 2weeks?" Na sandare a zaun, na kasa cewa komai illah murmushi kawai na yi. Ta zarce da cewa "Na fa'da masa ban karba ba, wanccan dai da na karba, na yi godiya, na jinjina miki. Domin ni dai ba zan iya abin da kika yi ba. Dan haka nan da kwana hudu ki shirya karbar mijinki, Na gode sosai". Na yi jarumtar ha'diye komai na ce "Babu damuwa ai ni na baki, sannan mijina na yiwa alheri dan yasan na gode da adalcin da ya yi mini a zamanmu." Ta kai samosa bakinta ta ce "To dai ni ban karbi wannan k'arin ba." Muka yi shiru, muna kallon talabijin. Muna hakan iyalan gidansu suka zo mata. Ta ce su iso wajena. Na karbe su kuwa da girmama wa. Basu jima ba suka tafi wajenta yayin da na juyo musu cake din da na yi, ya zame mini na ba'kin ciki. Ta karba tana godiya, ta turo mini ledar gabanta ta ce "Gashi ". Na yi godiya, na rakata har kafar bene sannan na dawo wajena. Na zauna ina mamakin lamarin Gudale wato ce mata ya yi ni na kara masa kwanakin ba wai kwace mini ya yi ba. Na dan samu sau'ki amma ka'dan. Na duba ledar, kayan da na gani na alfarma sun bani mamaki domin hatta super wax guda biyu ce, da kuma dankararen leshi da mayafinsa. Ga kuma turaruka da sabulai masu tsada. Na kai cikin drower na adana, da nufin zan nuna wa Sakina. Haka ranar da ya cika sati bayan wancan kwanakin da aka yi cikin yardata, ya tattaro ya dawo dakinsa na wajena. Amma ko ta kaina bai bi ba. Asalima yana dawowa yake rufe dakinsa. Abin dana fahimta, ya k'udire sai ya rub'anya kwanakin da ya ce na yi neman kai da shi. Idan kwanakinta ya zo, yana rawar jiki, zai haye sama, idan ba dace na yi ba, ko gilmawarsa bana ga ni". Haka nake rayuwa, ba wanda na bu'de baki na ce ga halin da nake ciki Hatta mahaifina da bai cika saka baki akan al'amarina ba, sai da ya zaunar da ni a gaban mahaifiyata ya dinga yi mini nasiha da rarrashi akan na saukaka wa kaina kishin dana sanya a raina nake neman illata kaina. Yayin da Mama ta ce "Idan kika kashe kan ki, ko kika hadu da jinya, shi bashi da asara. Akan me zaki k'warzabi kan ki irin haka?". 2/8/23, 10:25 - Buhainat: *Wannan littafin na ku'di ne, biya 500 ku'din karatu ta wanannan asusun* *2384876855* *Surayya Ibrahim* *Zenith Bank.* *A tura shaidar biya ta wannan lambar* *08032773332*. *SDK* *81&82.* Na kasa bu'de baki na ce ga halin da nake ciki. A shekaruna na k'asa da talatin miji ya dauke mini kwana. Haka siddan, tsabar ya so wula'kanta ni. Na dinga kukan da ya ta'basu. Mama da yake mace ce sai ta taya ni, muka saka Baba a gaba muna yi masa kukan da ya ki'dima shi. Cikin karfin hali ya ce "Halimatu so kike yi na kasa yin jarumta a cikin zumuncina da dan-uwana? Abbanku duk maganarsa da tunaninsa akan ki ne, ki yi hakuri, kada ki kunyata shi." Na goge ido na ce "Na yi Baba". Na tashi na tafi, babu ko waiwaye. Haka Abba duk sadda zai gan ni, sai ya ce "Kin kasa yin jarumta ko Halimatu?" Na kan ce "A a Abba ai bani ma da matsala. Sai da na ga ya tsananta da tambayar sannan ce masa "Fama nake yi da zazzabin dare, ga ba cin abinci, sannan ga kasala, wata'kila dai sai na ga likita an yi mini test." Nan da nan, na ga ya samu k'warin guiwa har yana addu'ar Allah ya rabamu lafiya. Muka shafe kwanaki muna haka, bai waiwaye ni ba, nima kuma na hakura da shi, idan girkina ne, yana dakinsa a garkame, sassafe zai fice, idan ya dawo kuma ya shige ya rufe. Na tattra na zuba masa ido, amma abin yana cina, na kuma yi al'kawarin ba wanda zan fa'da wa wananan matsalar domin ina ganin ba karamar fallasa zan yiwa kaina ba. Ba irin rarrashi da hilar da Sakina ba ta yi mini ba, akan mecece matsalata nake wannan ramar da ta sanya na yi muni tunda asali ni mai garin jiki ce. Amma na yi juriya na ce bani da ita, kawai zazzabi nake yi da daddare. Umma kuwa ta dinga farin cikin yadda take ganina domin haka take so ta sanya ni, cikin tashin hankali ta yadda hankalin uwata zai tashi. Tabbas a wannan karon ta yi nasarar ganinmu cikin tasku domin Mamana ma ramar ta dinga yi a dalilin halin da take ganina a ciki duk da ban ta'ba bude baki na ce mata ga matsalata ba. Amma tana ganin yadda Umma take gayyato k'awayenta ganin Amaryar Gudale. Abin da ta'ba yi mini ba, ni asalima bata taba zuwa gidana ba. Haka nake rayuwa, ba wanda na cewa ga halin da nake ciki. Amma ramar da nake yi, ta yi matu'kar damun dukkan ahalina. Bai kula ni ba, sai da ya yi adadin kwanakin da ya kudire. Yayin da ni kuma na ki kula shi. Idan ya shigo dakina zan gaishe shi, amma bana ajiye masa abinci hakan nan ban yi gigin shigar masa daki ba, nima kuma bana bari ya zo nawa. Zaman ya yi tsauri a tsakaninmu kowa a hassale yake da dan-uwansa. A haka har amryarsa ta yi wata biyu, amma ni da shi abu kullum sake rikecewa yake domin na riga na taurare masa irin yadda bai yi zaton zan iya ba. Dai-dai lokacin kuma ya fara gazawa, ya fara gasgata ni shekaru hudu na bashi. Tun yana ganin bai kyautu ya neme ni ba, har ya ha'kura ya sauko ya fara neman shiri. Ni kuma Ubangiji ya sanya mini ha'kurin da ban yi zaton zan iya yinsa akan Gudale ba. Gaba'daya na tsike zuciyata, na kudire ba zan saurare shi ba, sai an yi shekaru hudu cif cif, idan muna da rai kuwa ranar da shekaru hudu suka cika a ranar zan bar aurensa, zan nuna masa zan rayu ko ba wanann mua'amalar, zan kuma tabbatar masa, na wuce irin wannan tozarcin da ya yi mini, mun riga mun yi zaman da ya fahimci alamurana ciki da bai, yasan abin da zanyi na gaskiya, da wanda zan yi da nufin tozarci. Dan haka rainin wayo ne kawai zai sa ya ce wai wula'kanta shi na yi da na k'ara masa kwanaki. Tun yana ganin abin wasa ne har ya sare. Ya dinga rarrashi da neman sulhu, amma ko a jikina. Rannan sai gashi ya dauko mini Sakina har cikin dakina. Ta kada ta raya na fa'di menene ya ha'damu na tubure akan babu komai. Shi kuma ya kafe akan fishi nake yi masa, akan laifin da bai sani ba ta bincike ni. Da Sakina ta tsananta sai na fa'di da dalilin rashin yi masa abubuwan da ya lissafa. Sai kawai na fashe mata da kuka. Ba'kin cikin ya turnike ni mai tsananin gaske. A dalilin yadda ya takarkare yana cewa Sakina."Ai sam sam na canja hali, tunda ya yi auren nan shikenan na dauki masifa na dora a raina". Na dinga mamakinsa na yadda ya lauya zance haka tamkar mace. Dan haka nima sai na ha'diye kukana na kalli Sakina na ce "tunda ya dauko ki ai kinsan bashi da gaskiya, amma na rufe wannan maganar tunda ya ce masifa na dora wa raina, ki yi tafiyarki, ki ta yi mini addu'a Àllah ya yaye mini masifar da ta dame ni." Ina rufe baki ya ce "Sakina ba haka za'a yi ba Wallahi! Kashe wannan dambarwar kawai zaki yi tunda ke tana ganin mutuncinki". Ta kalle shi, kallo mai tsananin gaske ta ce "Me ka yi mata Na Moriki?" Ya bata fuska ya ce "Idan ina kaunar irin hakan da kike yi mini shege nake, ta yaya zan dauko ki akan ki kashe mini fitinar da ta sako ni gaba kuma ki zo kina neman yi mini bita da kulli? Kawai ki zartar mata da hukuncin ta zauna lafiya da mijinta tunda ta gamsu ke din yayarta ce, amma sai ki bararraje kina neman jin ba'asin da bai shafe ki ba". Ta girgiza kai ta ce "Halima ki yi hakuri kin ji. Kara ha'kuri". Na kalleta na ce "Ko da idan na yi ha'kurin akwai cutar wa a ciki?" Ta zuba mini ido har sai da na ji a jikina ta ce "Ban ce ki yi hakuri na cutuwa ba, amma idan da yiyuwar zaki iya daurewa to ha'kurin shi ya fi." Na yi yak'e na ce "To shikenan Maman Nana, na yi ha'kuri". Sakina ta ce Na gode miki". Ta tafi ba tare da ta sake cewa komai ba. Yayin da ya bita ina jin yana yi mata korafin wannan ba kashe wuta ta yi ba. Ai kamata ya yi ta ce "Ni Sakina idan ina da mutunci a wajenki na kashe wannan maganar kar ki kuma tayar da ita. A yadda nasan tana girmama lamarinki shikenan zata sassauta ta dawo da walwalarta. Amma yanzu kin yi magan ba wani motsa kwanji babu jarumta". Ta bashi amsa da cewa "ba zan takura mata ba, domin bansan abin da kake k'unsa mata ba. Ai tunda har ka bari ta fara yi maka irin wannan tutsun to lah shakka zuwa gaba ba zaka ji dadinta ba. Ka gaggauta fahimtar al'amura a dai-dai Namoriki". "To ba dole ta taurare ta dinga yi mini iyashege a gaban bare ba, ta yadda itama amaryar zata samu kofar wula'kanta ni, tunda kun riga kun zugeta ta gane kun tsaya mata. Ai ni kam nan kusa bansan namijin da ake cusawa ba'kin ciki irina ba.". Daga hakan ban sake jin amsar da ta bashi ba. Tunda sun fice. Ya jima sosai kafin ya dawo, domin har na kammala abincin da na dora bayan fitarsu, miya ce kawai ta rage. Ina kicin ya shigo ta k'ofar kicin din, tunda yanzu anfi shigo wa ta k'ofar baya. Ya tsaya daf da ni yana ta son sai mun kalli juna. Na bata rai sosai ba tare dana tanka ba. ya ce "Babu kyua doguwar gaba mussaman ace mace ce take yi da miji". Na ce "Ai kuwa bana gaba Yaya Gudale domin kullum sai na gaishe ka, yanzu kuma gashi na dora tukunya saboda kai, dan ka gane tabbas Sakina uwata ce ba wai yayata ba". Yasa hannu ya murde gas din ya ce "To zo ki ji." Ya ru'ko hannuna. Na ce "Bari na wanke hannuna kaga yanzun nan na gama yanka albasa". Yana tsaye na wanke hannuna tas, na goge da tawul. Na bishi muka je har dakinsa. Ya dinga bare bare, yayin da na yi cak da ni. Dake a matu'kar bu'katar ya kasance da ni yake, hakan ya dinga yin komai a yunwace. Na dinga mamakin irin wannan rawar jikin tamkar baya samu yana sauke lalurarsa. Rabon da ya lalace mini a shimfida irin haka tun ban fara aiki ba, domin a wannan ranar duk wani nau'in da zai yi dan ya dada mini ya yi. Duk kokarinsa dan na mayar masa da martani kememe na k'i. Ni da kaina na dinga mamakin yadda aka yi na ji bana sha'awa ko enjoying din dukkan kokarinsa. Asalima ban amince dan ina so, ko dan na yi masa afuwa ba. Na amince masa ne dan ya tabbatar da gaske Sakina tana da mutunci a duniyata. Duk tsawon lokacin da ya dauka yana kid'ansa da rawarsa ban nuna gazawata ba. Yana kammalawa na tashi na zura rigata na yi dakina. Sai da na yi kuka sosai domin ji na yi gaba'daya ba'kin cikin tarayyar ta kama ni. Karon farko da na fara jin tsanar al'amarin gaba'daya. Na jima ina kuka sosai sannan na shiga wanka. Na fito na shirya tsab da ni. Na koma kicin na cigaba da karasa aikina. Ina shirya abincin a dining ya fito, sanye cikin kananun kaya da ya karbe shi. Kallo daya na yi masa na gane yana cikin damuwa mai yawa. Na dauke kai na ce "Ga abinci". A sanyaye ya ce "Yanzu Guduyo abin da kika yi kin kyauta? Na rantse da Allah gara ace baki amince ba gaba'daya akan wannan wula'kancin". Ya girgiza kai cikin rauni ya ce "shikenan! Babu damuwa". Na bata rai sosai na ce "Yo dama ai tunda ka samu irin wanda kake so ai komai na yi maka ban iya ba, komai zaka ce ba daidai ne ba". Ya tumbatsa tamkar zai fashe. Ya girgiza kai ba tare da ya ce komai ba. Ya zauna ya zuba abinci, sai dai cokali biyu kawai ya yi ya mike ya bar mini abina. Abin ya mini ciwo ba ka'dan ba. Yana fita kuwa hawaye ya goce mini. Bai sake dawowa ba sai dare. Ya tarar da ni a falo ya kaikace ya ce "Goben nan ki dawo mini da Afrah gidan nan, domin ai ba bayar da ita na yi ba, da za'a rike mini ita fiye da watanni uku, kina tashi daga asibitin da kike zarya kullum da sunan aiki ki wuce ki dauko mini yarinya if not daga ke har Sakinan zan gwada muku iyakacinku". Na murguda masa baki na ce "Yar da baka so ne kake wannan maganar akan ta yanzu ko kunya baka ji ba?" Ya shige daki yana cewa "ki bari goben ta yi ba'a dawo mini da ita ba, ki ga irin kwanjin da zan nuna, ko bana sonta ai dai ni ne ubanta, kuma ko laulayin da aka mini k'ofin na yi a cikinta ka'dai ya isa a girmama umarnina". Na kyale shi, illah iyaka na k'udiri aniyar ba zance wa Sakina ta bani Afrah ba, duk kuwa da nima na matsu ta dawo, domin yarinyar tana debe mini kewa saosai ta shiga raina fiye ma da Amnah. Washagari kuwa sai ga Sakina ta kawo Afrah da daddare tana cewa "Akan me ba zan ce ta bani ita ba zan tsaya zagaye zagaye?" Hawaye ya goce mini na kalleta cikin ido na ce "Billahillazi Maman Nana ban ce koami ba. Bani ce ba, kin dai san shi sarai". Ta ce "share hawayenki na yarda da ke, shima kuma na gode masa tunda har ya kasa zuwa ya daukota da kansa ai mutuntata ni ya yi, shiyasa ya goce ya ce kina son y'arki a gaban ki". Na kame baki na ce "oh Yaya Gudale zai iya ha'da yakin basasa Wallahi". Shikenan Afrah ta dawo na kuma gane hikimar Gudale ta dawo da yarinyar domin kuwa na samu sau'kin K'uncin da nake ciki. Na dinga kyakayata dariya kenan idan tana yin gwarancinta. Na daina zama shiru, domin idan tana kusa da ni. Ina biye ta muyi ta hira ina jin nishadi mai yawa. Yayin da shima zai yi ta kutso kansa a tsakaninmu. Na lura yana amfani da yarinyar ne dan ya sanya murmushi a zuciyata. Tabbas wani lokacin ina biye shi mu yi hira amma fa haka siddan bazan fara yi masa magana bà, matu'kar ba gaisuwa ba ce, ko kuma maganar abinci. Inka dauke wadannan to na dinke daga dukkan neman soyayyarsa. Zuciyata ta rinjayar mini Munubiya ce type dinsa, ita yake so, ita yake gamsuwa da ita to na bar mata, ba kuma zance ya sake ni ba, sai idan shine ya gaji dan kansa. Sannan zan bashi kaina domin sauke nauyin da Ubangiji ya wajabta mini, amma kuma bashi da alfarmar da zan biyar da shi cikin soyayya da nisha'di, tunda na bayan da na wanzu ina yi basu kubutar da ni daga tozarcinsa ba, to kuwa a yanzu da yake da wata da yake so, take yi masa irin amfanin da nake yi masa ba abin da zan yi masa na kubuta daga wula'kancinsa. Wata uku da yin auren na dauki hutun shekara. Kullum ina gida al'amarin kishin da ya takura ni, ya yi matu'kar yi mini sau'ki a zuciyata, domin na tattra su na watsar hatta lamarin Umma da a kullum yake sake tsananta a kaina ya daina damuna tunda na fahimci da gaske tafi son Munubiya a kaina shikenan nima na jingine ta da dukkan zuciyata, sai dai gaisuwa nake yi mata ta girma da arziki. Tsakanina da Gudale kuwa distance mai yawa ya shiga tsakaninmu domin har lokacin ban sauya masa a sabuwar mua'amalantar da na tsiro a tsakaninmu ba. Ya yi rarrashin amma na kasa sakewa, matu'kar zai bu'kace ni to kuwa lah shakka sai dai na zame masa tamkar gunki, duk abin da zai yi kuwa. Abin yana matu'kar damunsa. A kuma wannan lokacin halayyar kowa a tsakaninsa da Munubiya ta bayyana. Na farko ita bata son takurar da yake yi na rashin son fita. Ita kuwa matu'kar ta raya zata fita sai dai kawai ta sanar masa zata je waje kaza da sigar labari ba sigar naman izni ba. Wani lokacin ma indai yana wajena sai dai muji tashin motarta. Baya ga haka daga dukkan alamu bata iyawa da jarabarsa domin duk yadda nake masa wula'kanci ta hanyar zama masa tamkar gunki baya iya ha'kura ya barni da abina. A kuma matu'kar matse yake dawo mini. Sai dai bai ta'ba cewa ga matsalarsa da ita ba. Matsala ta biyu kuma matu'kar ita take girki indai har ya wuce taran dare a wajen Umma lah shakka ba zata bude masa kofa ba. Sai dai ya koma ya kwana a mota. Domin akwai ranar da ta yi masa hakan ya kira wayata akan na bu'de masa kofar wajena zai shiga dakinsa nima fir na ki tunda na ji irin knocking din da ya dinga yi mata amma baiwar Allah ya yi funfurunfus. Sai kuma matsalar da na kasa fahimtar ta nake kuma jin tsoron na nemi a wayar mini da kai. Munubiya wani irin kirki take yi mini, girmama ni take yi fiye da yadda take gimama Gudale. Ta ja Afrah a jikinta, tana kashe mata ku'di fiye da yadda ubanta yake mata. Duk inda zata Afrah na gaban motarta, ba dan karfin soyayyar da ke tsakaninmu da Afrah ba da sai yarinyar ta koma wajenta tsabar yadda take tattalinta, sai dai Afrah jele take yi tsakanin sama da kasa domin kuwa ba karamin kulafacina take yi ba. Ba dan haka ba ai da tuni ta bar ni domin irin kayan wasa na alfarmar da ta tara mata a sama, duk wanda zai fita wata kasar a cikin danginta sakon Afrah na mussaman ne. Daga haka kuma sai ta tsiri zaman wajena duk sadda na dawo daga aiki na huta to zata zo mini, ba kuma ta zuwa hannu Rabbana. Kullum da abin da zata kawo mini na ci, ko na amfani. Ni kuma na sake da ita, domin ban ga alamun cutarwa a tare da ita ba. Ko wajen Abba zani sai na jata mu tafi tare. Hakan kuma ya sake nutsar da zuciyar Abba ya dinga murna yana sanya mana albarka. Ya dinga gode mini, yana yaba mini. Amma da zamu shiga wajen Umm tare sai ta nuna banbanci, sai ta nuna ita ce tata, tun Munubiya bata fahimta ba har ta gane. Dan haka sai itama ta fara ja baya da Umma domin idan muka je bata yarda ta gaisa da Munubiya a falo sa ta kai za xza za z za za xzaz za a xzaz zax za za za zaz za zazz za xza za z z zaz z a xza z da za za xza zz zzzz zaxzaxz xza xza za zzazz z zz z xzaz zzzza zzz za zaz z zaz z zaz z zz xza zazzzazza xza zxa za xzsa zazz xzaa za za za z xza xza za xza za xzaz zaza xza z az z za xza zaz zx za xasxza xzazzza xzz😆😆 ta har uwardaki tana ta ina ka saka da ita. Ba kunya kuma ni ta bar ni a falo a wula'kance. Ta dinga tambayar Munubiya me take so, dafatan bata da matsala a gidan? Akan idona Umma ta sha fa'da mata "Ta sake ita ma matar gida ce, bayan hakan idan an sha gabanta a wajen Abba to ta sani ita din tata ce, zata kuma yi yaki da duk wanda zai musgunawa farin-cikinta. A duk sadda na tuna amsar da Munubiya ta kalli idon Umma ta fa'da mata sai na ji faduwar gaba dan tsananin mamaki, amma sai Umma ta waske ta yi kamar bata ji ta ba. Ba tsoro bare faragaba ta ce "Umma ai kuwa Abba uban kowa ne, domin idan muka je gabansa yana mua'amalantar mu eqaul da Maman Amnah, idan kuma abu zai bamu ni yake dankawa a hannu ba dan ya daidaita matsayinmu ba, sai dan na ji a jikina nima yarsa ce, amma duk sadda muka zo nan sai Maman Amnah ta muzanta domin ni ka'dai kike mua'amalanta da karamci. Na fara zargin kaina, domin ita bata hana Abbanta ya karrama ni ba Umma". Dake akan idona ne sai ta yi mukus. Yayin da ni kuma na mi'ke na ce na tafi saloon. Daga nan na wuce wajen mahaifiyata, tsananin ki'dimar da na shiga ya sanya na fara rarratabwa Mama katobarar da Munubiya ta yiwa Umma. Cikin son a bar maganar ta ce "Halima ba ruwanki, kada ki saka musu baki a shanninta da surukurta. Ban yarda ba, ban amince ki yi maganarsu da wani ba. Ita kanta kishiyar ta ki kada ki sake ki yi maganar Umma ko ta su Maimuna da ita bare randa munafunci zai fashe ya tashi da ke, ke dai kawai zuba musu ido kina gefe kina istigifari da hailala. Na ji da'din yadda kika ha'kura, gashi yanzu komai ya wuce." Na yi murmushi a zuciyata kuma na sani kawai sauki abin ya yi. Sai kuma matsalar Munu ta biyu da na kasa ganewa. Domin bayan waccan kirkin da take mini, sai take yawan son ta rungume ni, kullum ta zo sai ra rungume ni a zuwan oyoyo. Sai kuma abin ya zarce da bubbuga bayana cikin hikima. Ban gama fita a wanccan mamakin ba sai ta tsiri da bani peck a kunci tamkar dai gaisuwar larabawa. Dake mu anan bama irin wannan dabi'ar sai abin ya zame mini some how. Sannan a farkon zuwanta bata yin hakan. Sannu sannu kuma indai zamu zauna to ta dinga murza mini hannu tana yaba cikar hannuna. Tana fa'din na yawaita yin lalle domin ba karamin kyau zai yi mini ba. Kaina ya kulle na kasa fahimtar wannan abu na Munubiya. Shaidan sai hasaso mini abubuwa akan ta yake yi. Amma tunda bani da tabbas sai nake yi mata uzziri. Amma me? Sai abin yake sake tsananta har ta kai zata bar Gudale a sama ta taho wajena. Wani lokacin ya ha'kura wani lokacin ya biyota su tare mini. A fili kuma take fa'din gaskiya Ubangiji ya mini komai nawa a cike ga kuma murya mai fitar da amo. Randa ta fadi hakan a gaban Gudale ya tunzura ya ce "Ba ya so. Ta yi murmushi ta ce "zuwa yanzu ya kamata ace ka gama fahimtar ina yaba abin da yayi mini babu jin kunya. Ina kuma bagarar da abin da bai yi mini ba babu jin nauyi". Ya nuna ta da yatsa ya ce "Na fa'da miki da babbar murya bana so, amma idan baki yarda ba, ki cigaba, amma ki sani, ba zan miki hakurin da kullum nake yi akan ki ba, matu'kar kika tsiri yi mini irin wannan iyashegen akan Guduyo". Ta ta'be baki ta ce "Sadiki kenan, mamaki kuma na nawa? Ai sai yanzu nake ganin gaskiya kaddara ce ta zabo maka manyan matan da basu kamace ka ba. Mussaman Maman Amnah yadda take din nan Babban zaure". Ya cika, tamkar zai fashe amma ya kasa cewa komai ya mi'ke ya fice da alama wajen Umma ya nufa. Ta yi tsaki ta ce "Mummys boy". Yayin da ni kuma na sake tsorata da lamarinta, na kuma sake fahimtar zaman nasu ya fara tsami, amma shi da Umma suna ta boye wa. A hankali Umma ta fahimci Munubiya ba zata huce mata takaicina ba, domin zuwanta uku da bak'inta amma sai dai Munubiya ta karbe su a falona bata yarda ta tashi su tafi wajenta. Shikenan sai kuma teburin rikicin ya juya. Aka koma fa'da wa Gudale mun kai Munubiya an mallake mini ita. Ai farkon zuwanta ba hakan take yi ba. Amma yanzu tafi fifita al'amarina sama da na kowa hatta shi kansa uban gayyar. Abin duniya ya yiwa Umma zafi tun tafiya bata yi nisa ba, ta fahimci ba zata yi nasara ta hanyar Munubiya ba. Yayin da Gudale ya shiga wani irin tasku domin dai ya kasa daidaita wa da Munubiya a dalilin shima baudadden halinsa ya bayyana mata, yayin da ita kuma ya fahimci kwata kwata babu son auren a ranta, kawai dai ta yi aure ne dan shekarunta sun fara turawa amma ba dan ta dauke shi da muhimmanci ba. Ga kuma matsalar nima na ki sarrafuwa masa. Gaba'daya na cure na zama tamkar katako ya ka'da ya raya amma na ki canja wa. Wani dare bana mantawa yayi juyin duniya na yarda mu yi cikin dadin rai, har da cewa" iya na yau kawai zaki yi mini, sai sadda kika so kuma, dan Allah kin ji Guddin Abba". Na ture a ranar ma sai na ki yarda da wanda baya so din, domin a falo na yi kwanciyata. Tabbacin ba zan yi ba gaba'daya. Ya dinga rarrashi har ya tunzura ainun ya turmushe ni a wajen, kamar watannin baya. Yana gamawa ya ce akan wannan kofar d'an agundin kike yi mini irin wannan iyashegen. Na tabbatar ba haka kika barni ba Guduyo". Ai shikenan muka sake hawa dokin fishi, kowa na yiwa dan-uwansa kallon mugu azzalumi. Mun debi kwanaki, babu ko gaisuwa, tunda ni ce mai gaisuwar, na kuma daina, tunda ina fishin ya sake wula'kanta ni a falo, ya kuma yaba mini bakar magana. Dake a wannan bangaren bashi da hakuri sai kawai ya kai karata gaban Abba. Na dinga jinjina yadda ya kaikai ce ya fa'dawa Abba cewar ina gudunsa fiye da wata uku. Sannan ya kira Sakina dan ta yi sulhu amma ban ji ba, to ya kawo maganar gabansa ayi masa adalci. Ina durkushe gaban Abba kunya tamkar kasa ta tsage na shige. Yayin da shi kansa Abba ya Jima bai iya bude baki ya ce kanzil ba. Haka kawai ya rarrago ni, akan Abba yana nemanmu, ashe dan ya fa'di wannan babban al'amarin ne a gabana. Murya a dakushe Abba ya ce "Halimatu ina ta murna kin karbi girman da ya hau kanki da hannu biyu, ina farin-cikin kin kwantar da hankalinki, ina cikin murnar kina tsaye kan kafafunki ashe ke kin zubar da komai ne kin kama iska?" Nan da nan Gudale ya ce "Ai da bude maganar na yi sosai Abba wallahi da ka fahimci kwali kawai ta kama ba iska ba." Abba ya nuna shi da hannu ya ce rufe mini baki marar kunya kawai." Ya kame baki har da saka hannu ya ri'ke bakin yana cewa na yi tuba, amma dai a bi mini kadina dan darajar Annabi kada a dau maganar nan sakwa sakwa". Abba ya sassauta murya ya ce menene matsalarki Halima? Fa'da mini me ya miki?" Hawaye ya balle mini, cikin kuka na ce "Wula'kanta ni ya dinga yi, a farkon aurensa, ya dinga zaluntata shiyasa na bar mata shi, ni ban kullace shi ba, amma dai kam yaje ya rike wacce ya za'ba a kaina, Amaryarsa ba ruwana da ita tunda bata yi mini laifi ba. Shi da ya mini, shine ba ruwana da harkarsa, tunda dai bai ma yarda ya tozarta ni ba". Abba ya ce "Ai kuwa dai wannan shine hukunci na gaskiya ku tashi ku je." 2/8/23, 10:25 - Buhainat: *83-84.* Nan da nan Gudale ya ce "Amma dai Abba sai da na ce A mini adalci, ka yiwa alfarmar Malam Zubairu Rahimuhullah. Ka yiwa Guduyo irin fa'dan da zaka yiwa Sakina idan mijinta ya kawo maka karar tana cutar da shi". Jikin Abba ya yi matu'kar yin sanyi. Ya ce "yau har da Ubana ka nemi kafun k'afa da shi? To maganar ta kare kuwa". Ya kalle ni da tarin kauna ya ce "ki yi hakuri! Annabi ya ce Madallah da mutanan da suke yin afuwa idan an zaluncesu alhalin suna da ikon ramawa. Darajar miji yawa ne da ita, ina ta fa'da miki Annabi da kansa ya ce shine lauyanku ranar Gobe, ki tuna kuma dokokin dake cikin aure Allah ne ya shimfida da kansa dan haka biyayyr da aka wajabta muku ku yiwa miji, ba mijin zaku dinga kallo yayin biyayyar ba. Ubangijin da ya wajabta yin biyayyar zaku dinga kallo a farko." Na fara kuka ina cewa "Allah Abba ina ha'kuri sosai amma shi baya ga ni, sai ya yi ta kure ni. Kuma abin haushin sai ya nuna ma baisan ya yi laifi ba bare ya bada hakuri". "Ato idan bai gyara ba watarana zai zo gabar da zai kure kin ya rasa mai shawo masa kan matsalar ai". Nan da nan Gudale ya fara gyaran murya. Yana cewa "uhum uhum Abba dan Allah kar ka ce komai kawai a taimake ni dai a kashe wannan maganar a bata ha'kuri, amma kada a mini bakin da zan sake yin wani kuskuren, a kuma jarrabe ni da rasa wanda zai mini maganin matsalar". Na gallasa masa harara na ce "Wato Abba ne zai bada ha'kurin laifin da bai ji ba, bai ga ni ba." Ba kunya kuwa ya ce "Ato ba shi ya haife ni ba? Ina ce jiya har ce miki na yi na ci darajar Abba, amma kika yi funfurunfus to yanzu gashi nan a gabana a gabanki ya ce ki bini, ki yi ha'kuri da ni, da sannu Ubangiji zai hore miki ni". Na sandare tsabar ki'dimar da na shi na kalaman Gudale. Ya sake shayar da ni wani sabon mamakin ta hanyar cewa "Ai kin bani mamaki Wallahi! Yo wannan kallon ba shine zai sa na ki fa'din kin ki manta komai saboda alfaramar Abba ba". Na girgiza kai ina cewa "Allah abin godiya da baka zo a mace ba." Abba ya ce "Rabu da shi. Bai isa ya burma ni ba. Nima hakan ya ta'ba mini ai, a gabana ya nemi ha'da fitina tsakaninmu da Yaya ta Kwalli." Ya kuwa bata rai ya ce "Abba dole Guduyo ta dinga mini gashin kuma. A gabanta ake nuna mini kasawata. Zan tafi, ka bata umarni na karshe mai karfi akan ragaitar da nake yi a hannunta, tunda tasan kai din farin Uba ne." Abbaya girgiza kai ya ce "Ubangiji ya ganar da kai, ya shirya ka. Guddi tashi kuje! Nasan na isa da ke, shima tabbacin hakan ne ya sanya ya kawo mini wannan al'amarin gabana, to ya zanyi tunda na riski wannan zamanin?" Kunyar Abba ta rufar mini mussaman da na ga shima kunyar ce ta hana shi kuzari. Kaina na kasa na ce "Na ha'kura har zuciyata Abba! Ya ci darajarka". Na mike da sauri yayin da Gudale ya ce "Ina ganin tala jaurar duniya a wajen Guduyo ana son Uba da farin ciki, amma ba'a son dansa da kwanciyar hankali. To dai shine ya haife ni, gara na dinga fa'da miki dan ki dinga raga mini". Na tafi ban tsaya ba, amma ina jinjina girman iskancin Gudale. *Abba* Ya tattaro dukkan nutsuwarsa ya ce "Sadik sai na mutu zaka zama mutum sak?" A sanyaye Gudale ya ce "Na yi tuba Abba! Abin ne yafi karfina, a mini afuwa yadda aka saba". "Na yi maka Sadik Allah ya shirye ka. Sannan ina sake jan hankalinka akan yarinyar nan. Kar ka zalunceta da gangan. Idan ka ci amanarta in sha Allah kaima ba zaka ga da kyau ba. Ban da ma zuciya ba a ganinta bare a hukunta ta, ina salahar zuciyar Halima ina daukar tirka tirkarka? Har yau din nan ban ta'ba jin ta yi korafin rashin kirkin da uwarka take yi mata ba. Kana sonta, amma ka kasa sanya aminci a tskaninta da uwarka. Akan idona Saudatu take jagorantar a wula'kanta mini diyar Ibahim, yar wani, tafi yar jinina. Ai Wanda ya ce Allah ya huta. Sai kuma Ubangiji ya damk'e wa Halimatu kai, ya cusa maka sonta ta inda baku yi zato ba. Wallahi duk ranar da ka yi kuskuren sakin yarinyar nan daga kai har uwarka sai kun rasa sukunin zuciya da na gangar jiki. Idan kuma ka Cigaba da musguna mata da gayya, kaima ka dinga ganin sakayya ta inda baka yi zato ba kenan". "Abba kana son ka dinga yi mini baki dai". Gudale ya fa'da cikin rauni sosai. Ba baki bane gaskiya ne Sadik! Wataran sai ka yi bitar kalamaina. Wataran sai ka yi hawayen rashina, watarana sai ka duba ko ina baka ganni ba, bare har na fa'da maka gaskiya ka yi zaton na yi maka baki ne." Gudale ya sake yin kasa da kai ya ce "Allah ya kara maka lafiya da nisan kwana mai albarka, ina yi maka fatan aljanna Abba." A daki ya tarar da ni ya rungume ni, na dago ina hararsa na ce "Ka gama yin mini sharrin sannan ka yi zaton zan kula ka?" Ya kuwa ruga kamar yaro yana fa'din "Da zafi zafi ake dukan karfe ai yana falon bai koma ciki ba, bari na je na tabbatar masa ba karya na yi ba, bai isa na ci darajarsa ba." Sanin da na yi da gaske komawar zai yi, zai kuma iya yin rantsuwar da Abba zai gasgata shi, hakan ya sanya na bishi a guje mun fita kofar falon na cafko rigarsa "Ina cewa bana son haka, ka ga ka bari". Yayin da yake zillewa yana fa'din "Na rantse sai ya ji, ai kuma na gaji da kafiyarki". Na fara dariya dariya, kuka kuka ina fa'din "Dan Allah ka bari ka ga dai ba abokin wasanmu bane". Yana kokarin kwace wa ya ce "To yau sai ya zama abokin wasan, gobe sai ya koma Abban". "Na ce dan girman Ubangiji ka bari bana so". Ya zuba mini ido ya ce "Tom na fasa amma wallahi anjima kika yi mini wula'kancin da kika saba, ina tashi zan koma gabansa zan bude maganar sosai. Wallahi ba zan ji kunya ba". Na d'aga kai na ce "Shikenan na yarda." Dai dai nan Sakina ta shigo gate din namu ganina rike da shi, ya sanya ta ce "Oh lamarinku sai ku". Yayin da Gudale ya bata rai ya ce "Da y'an bani na iya sun gane sai su daina shiga tsakaninmu ko Guddin Abba?" Na cuno baki na ce "A a wallahi! Dole mutum ya yi kishin nasa ai". Ya wuce yana cewa "Allah sai kin yi tuba akan wannan bayar da ni da kika yi a gaban Sakina". Sakina ta tuntsire da dariya mai karfi tana fa'din su Namoriki an kamu da gaske". Ya k'i kulata a dalilin haushinta yake ji. Daren wannan ranar ya shiga cikin tarihi a rayuwar aurenmu, domin duk nau'in soyayya ba wacce Gudale bai mini ba. Hadin kan dana bayar ya sake armasa lamarin. Tsananin ki'dimar da ya shiga ya saka ya saki baki, cikin rawar murya yake fa'din "Ki daina mini waccan horon, komai zamu yi ki daina juya mini baya, ya kike son na yi ne?". Na ce "ba ga matarka can ba, mai tsukakke ba irin nawa k'ofar Dan... " Da sauri ya danne mini baki ya ce "Billahillazi haushin wula'kanta ni da kike yi ne, amma k'arya ne tsagwaronta. Da kina sona ba zaki kyautar da kwanakin da zan yi miki ba, na ce miki ina so ne? Abin ba karamin k'ona mini rai ya yi ba. Shiyasa nima na rama, amma saboda kinsan ni mayenki ne shine kika yi ta gasani na satittika masu yawa. Ina ro'konki arziki kada ki sake mini irin wannan gashin k'umar dan Wallahi zan iya zuwa gaban dukkan iyayenmu na fa'da musu azabar da kike gana mini." Cikin wata irin murya da ba zanci zan sake yiwa Gudale ba na ce "To ai baka gamsuwa kuma bani kake so ba". Jikinsa na rawa ya kamo kunnena ya rada mini "Wallahi ina sonki sosai Guduyona kema kin sani, aikin da kike fita kullum ne yake neman kassara ni." Ya fa'da muryarsa na karye wa alamun kuka ne ya nemi kwace masa. Jikina ya mutu, ya rungume ni hawayensa na diga a gadon bayana. Wannan kukan da ya yi mini sai ya zama tamkar an saka mini kyamar aikin. Na dinga rarrashi ina bashi ha'kuri tare da cewa "nan bada jimawa ba komai zai daidaita. Shikenan sai muka shirya na dinga tattala shi, ina kaffa kaffa da abin da zai ha'do mu. A wannan lokacin na ga sintirin da mata suke yi a gidan ya yi yawa, yammata da zawarawa. Ba abin da Munubiya take matu'kar so irin ta rungume ni, rannan na dawo daga aiki kawai ba zato a filin gate ta rungume ni ta shafo bayana har zuwa mazaunaina. Nan da nan jikina ya dauki rawa na zame ina kallonta. Ga mamakina bata nuna ta yi wani abin ba. Ta dinga yi mini barka da zuwa da wani irin kallon da bai kamata ta yi mini irinsa ba. Tun ranar sai na fara janye mata, na fara kaffa kaffa. Ita kuwa sai ta yi kamar bata gane ba, ta cigaba da zuwa wajena, tana sake jan Afrah a jikinta. Ga kyautar da take yawan yi mini na abubuwa masu daraja ta sake ninka wa. Abin da fahimta ba wani damuwa ta yi da Gudale ba, domin zata iya baro shi a samanta ta zo ta zaune mini, tana mini wani irin kallo da shagwaba shagwaba da suke matu'kar sanya ni a faragaba da zullumi. Idan na yi yun'kurin fa'dawa Gudale sai na fasa, domin dai bani da hujja gamshasshiya. A matu'kar tsorace nake da ita domin idan baka iya kama barawo ba, shi ya kama ka, sai dai na tsananta addu'ar Allah ya raba ni da sharrinta ya kawo mini mafita cikin ruwan sanyi. Ina cikin wannan zullumin jikin Abba ya tsananta. Aka kwantar da shi a Asibitin Malam. Duk wanda yaje wajensa sai ya yi hawaye domin duk yadda yake cikin ciwo sai ya ce "ku ri'ke zumunci, ku sadar da shi ko da kuwa ku an yanke muku. Idan ya kalli Babanmu sai ya ce "Ka yi hakuri da Sadik kada a bar shi da kansa, kuma kada halinsa ya sanya a yanke zumunta da shi. Kowa a family nan bashi da sukuni domin sosai Abba yake jin jiki. Haka kawai na dinga shiga fargaba mai yawa, domin na sani Abba ne jigo a zaman aurena. Yanzu idan ya mutu ya bar ni a wananan halin na gaba k'ura baya damisa ya zan yi ne? Umma bata sona, tana fatan ta samu hanyar wula'kanta ni fiye da wula'kancin da take yi mini a yanzu sannan ga kishiyar da alamunta suka nuna lesbian ce, kuma ta k'yasa ni. A wannan tsukun hawaye baya yanke wa a fuskata, a fili nake yin addu'a ina cewa "Allah ya tashi kafadunka Abba". Ranar juma'a 7 ga watan biyar da hantsi Abba ya amsa kiran Ubangiji. Mutuwar da ta yi mini wani irin mahangurba. Ina tsaye akan Abba ya cika, farin ciki daya da nake yi masa, ya yi salati yafi cikin carbi, sannan da zai cika ya samu damar cikawa da kalmar. Amma duk da hakan zubewa na yi na suma tsabar kidima. Na bude na ga ana shafa mini ruwa. Sakina tana kuka ta rike hannuna muka fice daga dakin, zuwa lokacin tuni an wuce da gawarsa domin a gaggauta shirya shi. Cikin Sa'a aka kammala ha'da shi aka fice da shi zuwa masallacin murtala idan an idar da sallar juma'a za'a sallace shi. Irin kuwwar gidan yake yi, ni sai nake ganin tamkar dukkan flowers da bishiyoyin gidan sun taya mu kuka da alhinin fita da gawar Abba. Domin gaba'daya gidan kaurewa ya yi, yayin da Ubangiji ya basu ikon busawa da karfi sosai. Idan na ce sai na fa'di irin dukan da mutuwar Abba ta yiwa ahalinmu to bata lokaci ne mai yawa. Amma dai kam ko ban ce komai ba kowa ya san an mini mutuwa ba ka'dan ba. Abba mutum ne har da rabi, ya wanzar da rayuwarsa gaba'daya a neman halak da kuma tiritiri da zumunci. Ina kuka Ina fa'din "Allah ka jikan Abba, ka bashi aljannar da ka tanada dan masu sada zumunta". Kowa a cikin dangi sai ya mini ta'aaziya ana fa'din sannu da rashi Halimatu, hakan kuma ba k'aramin karya mini zuciyata yake yi ba. Gudale idan na ganshi sai na ji tausayinsa yana kama ni domin kuka yake yi fiye da na yan'uwansa mata. Fuskarsa sanye da ba'kin glass amma hawaye sai dai aga yana zuba. Amma a hakan zai leko ya tasa ni a gaba ya ce sai na ci wani abu, hawaye bai yanke masa ba, cikin karfin hali yake fa'din "Sannu Guduyo, daure ki sha ko kunu ne, nasan yadda kike ji, to amma ya zamu yi ne?" Tsawon kwankin makoki kowa a ki'dime yake. Haka mahaifina a tsawon kwankin da na shafe a duniya ban ta'ba ganin sa cikin ki'dima irin a kwanakin mutuwar Abba ba. Haka Mama dan har ina rasa wanda yafi kuka a tsakaninta da Umma. Amma tunda mutuwa dole ce ba kuma yadda za'a yi mutum ya dawo, haka aka tattara aka ha'kura, muka bishi da addu'a. Sai dai kam ni da Gudale mun shafe kwanaki arba'in mutuwar tana yi mana wani irin bugu. Wani lokacin ma shi da kansa yake bani hakuri yana cewa "Na sani an miki mutuwa Guduyo amma ki yi hakuri in Sha Allah zan yi kokarin na maye miki gurbin Abba wajen kyautata wa, zan iyakacin kokarina na kiyaye amanarki da ya yi ta bani, da ikon Ubangiji ba zan yi abin da yake ta jin tsoro ba. Ro'kon da zan yi miki dan Allah idan na kuskure miki kada ki tsananta fishi, kinsan dai yadda Abba ya yi ta jaddada yadda yake son aurenmu ya wanzu. Nima na miki al'kawarin ba zan tsananta ba, a sadda kika kuskure mini". Na fashe da kuka yayin da ya Jani jikinsa idanuwansa jawur yana goge mini hawaye amma ya kasa sake bu'de baki tsabar yadda zuciyarsa take zabalbala. *Ina yi mana ta'aaziya*. *Ni kaina ina cikin alhini, ayi ha'kuri da wnanan.* 2/8/23, 10:25 - Buhainat: *AMYAS NEW & FAIRLY ITEMS* *SUNA RENTING KAYAN AMARE* *SUNA SAYAR DA SUTTURUN MATA ZABBABU, NA ALFARMA, DA KAYAN KICIN*. *SUNA SIYAN KAYAN FURNITURES KO ELECTRONICS NA HANNU* *SUNA KUMA SAYARWA*. *SUNA SAYAR DA FILI DA GIDA*. *SUNA BADA HAYAR GIDA*. *KOMAI DA RUWANKA NE AMYAS GASU DA SANIN DARAJAR CUSTOMER. KAYANSU KUMA MASU INGANCI NE KUMA MASU RAHUSA NE*. *08083909947*. *SDK* *85&86*. Kafin arba'in din Abba duk abin da ya mallaka an kamalla lissafinsa da taimkonsu mahaifina da kuma Baban Gusau. Yaya Abdallah da shine akan dukiyar komai ya ajiye shi har zuwa lokacin da za'a yi rabonta ga magada. Tabbas munsan Abba yana da arziki, mun sani kuma me alheri ne domin hatta ma'aikatan gidanmu sunsan irin kyauta da alherinsa, ban da aiyyukan alheri da yayi ta yi na fili dana boye, masallaci da islamiyoyi da kuma rijiyoyi da ya yi ta yiwa kansa tanadin gobensa. Don kuwa har ga ni muke yi yana yin alheri fiye da yadda arzikinsa yake. Amma sai bayan da ya mutu sai aka sake fahimtar wani darasi a rayuwar Abba. Na farko sai da ya mutu kowa ya fahimci irin tarin dukiyar da ya tara. Duk yadda ake tunanin Abba ya wuce nan. Ubangiji ya bashi wata irin dukiya amma sai bai nuna wata d'agawa ko alfahari ba, ko kuma ya yi ta hak'ilon sai an sanya shi sahun manyan attaijaran k'asa. Na biyu kuma abin da ya yi ya sake sanya kowa cikin jimami da hawayen da baya yanke wa. Littafi guda da ya da'de yana rubuta wasiyyar yadda za'a yi masa. Ya rubuta tun shekaru uku da suka wuce da aka ga ni a rubuce. Ya raba dukiyarsa gida uku da kansa. Kaso biyu na magadansa ne, ahalinsa kenan. Kaso d'ayar kuma da kansa ya rarraba a tskanin yan'uwansa da yasan ba zasu gaje shi ba. Wanda sanadin hakan kowa sai da ya mallaki dukiya me yawan gaske. Sai kuma wak'afi da ya yiwa kansa. Sai kuma Yaya Abdallah da ake ta akilon juya ku'din da shi. Irin abin da ya bashi a rubuce ko zai shekara goma bai fita da sunan neman ku'di ba, to lah shakka zai ci abinci zai sanya sutura zai kuma dauki nauyin iyalinsa. Sai kuma ya jaddada idan an raba gadonsa to lalle kada Gudale ya hada nasa kason dana yan'uwansa mata, kowa ya rike nasa gudun samun rikici akan dukiya. Sannan bai yarda ya jagoranci dukiyar da ta zama tasa ba, ya cigaba da aikinsa, Abdallah kuma ya kular masa da ita, domin idan akwai amintaccen da Abba ya gasgata Yaya Abdallah ne. Umma ba karamin kad'uwa ta yi da wannan lissafin da aka zaunar da su ana yi musu ba. Hakan kuwa Baban Gusau da manyan lauyoyi da Malamai suka yi rabon kamar yadda shari'a ta tanadar. Gudale ya ja dukiyar da ta mayar da shi wani irin hamshak'in attajiri na gaske, sai dai ko ka'dan bai yi murna, ko zumudi ba, haka nan ko kobo bai dauka ba, ya mi'kata kacokan ga Yaya Abdallah kamar yadda Abban ya ce shine zai cigaba da juya masa, sai dai komai an yi shi akan tsari da shaidu. A kafatalin Ya'yan Abba mutuwar tafi kidima Gudale, kuma shine wanda ya dade bai warware ba. Wani lokacin sai Sakina ta bar gidanta ta zo ta zauna da shi. *Watanni hudu* A hankali kuma har komai ya daidaita aka cigaba da harkoki. Sai dai kullum ta Allah Abba yana ranmu, yana samun adduoinmu babu kakkautawa. Yayin da Umma ta fita takaba sai kuma al'amuranta suka fara ta'azzara a dalilin Munubiya bata samu ciki ba, kullum sai ta zaunar da Gudale ta ce "Yaushe zasu barka ka haihu da wata, tunda uwarsu tasan kan dukiyarka da take hannun d'anta. Wai ace har bayan Abbanku yana kushewa ma sai da aka yi kulunboton da ya yi mini abin da kullum sai na yi hawaye? Ka shekara talatin har da d'oriya amma abar wasiyyar kada ka kula da abin da yake mallakinka ne, sai dai wani? Komai zaka yi sai an sani, kome kake so sai ka yi y'ar murya kuma akan abin da yake naka ne. Sannan ace kada ka ha'da dukiyarka da ta shakikanka amma kuma an damk'a ta a hannun wanda zai iya shatale cigabanka ta hanyar yin mugunta, tunda kullum idan ya so zai iyawa cewa asara ake tafkawa babu kuma mai kalubalantarsa". Da kunnena na ji wannan bitar da ta zaunar da shi take yi masa. Na kuma ji ya bata amsa da cewa "Umma Idan akwai Wanda na shaida babu son zuciya a lamarinsa to Abba ne, ya riga ya san ban iya kasuwancin ba, ya fahimce ni irin fahimtar da ke baki yi mini ba. Umma duk tarin dukiya matu'kar aka ce dauka za'a yi kullum, ba karuwa zata yi ba to la shakka wataran wayar gari za'a yi aga babu ita. Abba ya san dukkanmu kowa da iyalinsa, ya guje mana samun b'araka ne bayan babu shi akan abin duniya. Tunda ya sani kowacce tana da miji da y'ay'anta. Sannan su bai ce ga yadda zasu yi da nasu kason ba, kema bai ce ga yadda zaki yi da naki kason ba. Ni kuwa da yake ta tattala ni, har bayan babu shi to zan yi kokarin na ga na tsaya akan duk abin da ya ce ko da kuwa ya ci karo da ra'ayina". A hassale ta ce "Tunda baya nan, ai sai ka raba biyu ka bawa Antin Zaria ta siya maka hannun jari daban daban, Allah barshi rabin Abdallah sai ya dinga juya maka tunda dai sun zame mana kaska." Ya daure fuska ya ce "Umma dukiyar nan da kike ganin na sameta Wallahi bana sonta, na karba ne dan Ubangiji da kansa ya raba, ya kuma shirya ayi hakan. Wanda ya tara abarsa ya tafi ya barmu da ita, da ace zan rasa komai, Abba ya dawo zan fi son hakan. Amma tunda ba zai dawo ba, to ina tabbatar miki yadda ya ce na yi da dukiyar da ya yi ta tattalawa da taimkon Yaya Abdallah, har na gajeta to kuwa hakan zan yi. Ba zai zama na'kasu ba, idan na yiwa Yaya Abdallah yar murya tunda ai wahala yake yi mini, kuma yayana ne na sosai. Sannan ai yasan da Antin Zarian amma ya ambaci Abdallah. A fili Umma ta ce "Mai Ashafa bala'in duniya! In sha Allah sai mun tsaya ranar gobe k'iyama". Nan ma ba fargaba ya ce "Umma ina guje miki daukan alhakin da zaki je lahira idan an tsayar da ku din da kike fata ki kasa yin nasara domin dai baki da hujja akan tarin zarge zargen da kike yi masa. A yanzu ba abin da ya dace da ke irin ki rungumi istigifari don ki samu ki iske Abba cikin aminci ku cigaba da rayuwa a aljanna". Ta kuwa fashe da kuka tana cewa "In sha Allah! Sai dai ka tsananta addu'ar kada ayi mini kulunboton da a lahirar ma zan kasa ganinsa. Ai ni kam ina cikin masifar duniya." Ya ru'ko ta yana shafe mata hawaye, yana cewa "Ki yi shirun ki Umma! Gudale da duk abin da ya mallaka na ki ne, kuma har na daina numfashi zan ta yi miki addu'a, duk mai nufinki da sharri kansa zai koma". Na sulale na koma tunda dama zuwa na yi na gaishe ta, na ji wannan maganar dan hakan sai na koma wajena. Ba tare da na bari sun gan ni ba. Daki na shiga na kwanta zuciyata sai rawa take yi. Anya kuwa Umma ba zata yi nasarar kashe mini aure ba? Hawaye ya goce mini, ina fa'din Innalillahi lillahi wa inna ilaihir Rajiun. Wani ba'kin ciki ya tokare mini na yadda kusan kullum sai Umma ta zagi kakana bawan Allan da ya haifi wadanda suka fita. Abin kaico kuma ba akan komai ba sai zato da zargi. Yanzu kuma ta ce na hana Munubiya haihuwa. Duka duka auren da bai rufa shekara daya bane za'a fara lissafin na hana ta haihuwa? Na tuna rannan zamu fita tare da Munubiya ta'aaziyar Baban abokin Yaya Gudale da ya rasu, da muka dawo na ce muje mu gaida Umma kai tsaye ta ce ba zata je ba, ta yi wucewarta tabbacin da gaske take yi. Banda alhinin mutuwar Abba da ya karya dukkan zafin kan Yaya Gudale ai da tuni ya sallamata, tunda a yanzu idan zata fita bai isa ta nemi iznininsa ba. Har kuma yanzu bata shiga kicin da nufin yin girki, sai dai yan aikinta har biyu da ta Jere a saman. Duk masifar Gudale akan yan aikin sun matsa masa, a takure yake ya ha'kura ya zuba ido. Ba dan komai ba saboda Umma. A hakan dai muke rayuwa Umma ta shata layi sosai, a dole take gaisawa da yaran gidanmu, Babanmu kuwa yaki yarda da gabar da take son yi da shi, domin yadda duk safiyar duniya yake shiga ya gaida Abba, hakan ita ma kullum sai ya je ya gaishe ta ya duba ta. Sai dai ko ka'dan bata ganin karamcinsa, asalima ga ni take yi dan suna da ku'di ne, ta manta ko Abba bai bashi koami ba, yafi karfin abinci da sutura da bu'katar yau da kullum, bare kuma kason da ya samu ya kusan yin kankan da nata, ga kuma yaransa kowa ya kawo k'arfi, Antin Zaria kuma bata fasa alherin da take yi masa ba, asalima sai ta ha'da har kulawar da take yiwa Abba akansa. Abba ya yi watanni shida da rasuwa Yaya Gudale ya fara murde mini akan fita aiki, a farko da lallashi yake yi, yana cewa "kinsan dai ba abin da kika rasa, tunda na yi hakuri na yi biyayya, kema yanzu ki yi hakuri ki mini biyayya, ki ajiye aikin nan. Kin sani Guduyo bana so, bana kaunar na shigo wajenki ban ganki ba, ki ajiye aikin, idan komai ya kankama na business, zan fa'dawa Yaya Abdallah a yanka miki albashi, duk dai ba zai kai wanda Gwamnati take baki ba". Dariya kawai nake yi ina cewa "Aikina ba dan iya ku'di bane kawai, ceton rai ne, sannan idan baka wajena yana debe mini kewa da damuwa." Tun yana maganar jifa jifa har ya dawo kusan kullum sai ya yi, a dalilin Umma tana yawan nuna masa tunda baya ra'ayin matarsa ta yi aiki bai kamata ya yi hakuri ya cutu ba. Kuma Munubiya ma ta fa'da a gidansu a samo mata aiki tunda matarsa tana yi, ba zata yarda da digiri biyu a kanta ba amma tana gadin gida idan mun fice aiki. Wannan zugar ta Umma sai ta yi tasiri a zuciyarsa, ya fara murdewa, muka fara takun saka da shi, rabon da mu yi irin wannan zaman na doya da manja tun kafin rasuwar Abba. A dalilin nasihohinsa da mutuwarsa ta sanya nutsuwa da tausayina yin tasiri a zuciyar Gudale, amma tsohuwar nan sai da sake tunzura mini shi. Sanin da na yi aikin nawa ne bata so itama akaran kanta domin ina hucewa uwata takaici, sannan Munubiya bata kere ni ba, shine take son yin mini sanadin rasa wannan damar. Ni kuma sai na bijire na ki yarda na ajiye. Shikenan sai abubuwa suka fara yin tsami, babu fa'da a tsakaninmu, amma sam bana Jin da'dinsa. Sai ma ta gwada masa wata dabara ta fahimtar da shi ai mace mai aiki tana taimakon namiji tunda ai shima ya yi mata alfarma da ya barta take fita kullum tana cud'anya da maza. Dake tasan kishinsa da k'yamar aikina da ya yi, sai ta daina zagin Malam mai Ashafa tunda wataran yana taka mata burki, kuma maganar bata tasiri, tunda bai daina gaida Mama ba, bai daina mua'amalantar su Yaya Al'amin ba. Sannan aurena bai mutu ba. Bugu da kari ya sake ninka mua'amalarsa da Baba. Kullum a cikin fa'da masa take kayan kwalliya ya sauka akansa, hatta tufafi ma sai ya bushi iska, amma ita Munubiya ya yi kokari ya fitar da ita kunya, ya kuma k'ara kawaici akan ta tunda dai tana mutunta ra'ayinsa. A wannan lokacin kullum sai na yi kukan rashin Abba! Mussaman da Anti Maimuna da Anti Juwairiya suka bi ra'ayin uwarsu suke yakata da dukkan zuciyarsu. Bayan ra'ayin uwarsu sai na fahimci har da kyashinmu da suke yi suna ganin tamkar nan gaba zamu fi su k'arfi a family. Har ta kai jallin akan dole suke hulda da yan gidanmu, irin gaisuwar nan ta dole. Baba kawai suke gaisarwa shima bai isa su kai masa matsalarsu ko su shawarce shi akan wani lamarinsu ba. Anti Ramla ce ita tun filazal a tsakiya take, bata kyautata mini, amma kuma bata musguna mini, bata kuma bada goyon baya a musgunawar da ake yi mini, haka nan tana gaida iyayena cikin mutunci duk da bata jan doguwar hira yayin gaisuwar. Yayin da Antin Zaria da Sakina suke tare da mu dari bisa dari. Rashin samun goyon bayan wadannan mutane biyu shine sa'ar da Abba ya yi zumuncin da ya yi ta kashedin a ri'ke shi da girma bai ruguje tun bai jima a k'asa ba. Har yau, har gobe ina girmama Antin Zaria da Sakina mutane ne da suka gaji karmaci da arziki a wajen Ubansu. Mutane ne da idan Ubangiji ya albarkaci family da irinsu to yana wahalar gaske zumuncin wannan dangin ya rushe gaba'daya. Domin ko ka yi niyyar yin wani abu na tsiya idan ka tuno su, sai kawai ka ha'diye dukkan musgunawar da waninsu yake yi maka saboda nauyinsu. Ina cikin wannan yanayin na rashin da'din mu'amala da Gudale, Munubiya da ta fahimci hakan sai itama ta murde musu, ta ki basu goyan bayan su musguna mini. Anti Maimuna ta ka'da ta raya ta zama uwar dakinta amma sam ta ki haka Anti Juwairiya, ko bikin dan gidan Umma Adama ta Yola da zasu je, ba wanda ya fa'da mini sai Sakina. Umma kuma ta sanya Munubiya a gaba suka tafi tun saura kwanaki biyar bikin. Daga baya su Sakina suka bi bayansu bayan ta yi ta bani hakuri ta ce "Ko gobe idan na Moriki zai tafi kada ki yarda ki bishi, ki yi zamanki, ki koyi jarumtar barin inda ba'a son ganinki". Ido cike da k'walla na rike hannunta na ce "Madallah da Sakinan Abba". Ai kuwa suna dawowa Munubiya ta zo ta baje mini irin tsiyar da suka tafka da Anti Maimuna wai har da dambe suka yi. A tsorace na ce ai kuwa dai baki kyauta ba Yayar mijin naki?" Ta ta'be baki ta ce ato ina ruwana da ita, ai ina da ilimi ke da kike yar'uwarsu kuka rayu gida guda suka ki, suka juya Miki baya, suka zabi wata akan ki sai kuma na yi tunanin ni ba zasu yi mini fiye da hakan ba? Ta girgiza kai ta ce never ever in history. Kawai fa daga ta zuba mana abinci ta ce na sauko mu ci abinci, na ce mata Ni bana cin abinci da wata, wai shikenan na yi mata rashin kunya har tana cewa duk gatan da suke yi mini har zan ce mata wata, ashe bani da mutunci? Ni kuwa na ce mata a wajenta na koya". Na kame bakina na tsuke na ce "Allah ya rufa asiri" Ta amsa da amin. Bayan ta ce "kaf gidan nan akwai marar mutunci ne irinta? Da har zata ce wani bashi da shi?" Dai-dai lokacin kuma ta kwanto jikina tana cewa "Kamshinki da'di Maman Amnah! A hakan tamkar kin waye, amma idan na ga yadda kike barin jiki akan Dan-ummansa sai na yi ta mamaki. To menene wani abin burgewa ne a tare da shi da kika daukake shi har hakan?" Zuciyata ta tsinke mussaman da ta kai kanta yake shafar kirjina cikin hikima. Na mike dukkan jikina na bari na ce "Bana son irin hakan Munu! Kada ki bari na wanke amincin da zuciyata ta yi da ke". Ta kashe mini ido cikin rashin damuwa ta ce "Me na yi to Maman Amnah? Kinsan kin fi shi haduwa? Kin fi burge ni akansa?" Na dauki salati cikin firgici na ce "Allah ya shirye ki. Hawaye ya balle mini. Cikin kuka na ce "Wayyo Abba daga tafiyarka na fahimci bangon dana jingina ya zube, yau ga wata katuwar masifa tana tunkaro ni, ba wanda zai bani k'afarsa na yi kuka, ya kuma fahimce ni, bare a gasgata ni. Inna lillahi wa inna ilaihir Rajiun". Ta mike tana fa'din "calm down mana, da zaki nutsu ki yi tunani zaki ga ba abin da yafi hakan da'di, ba kuma zaki sake kwana da takaicinsa ba, to me zai dame ki, kina da ku'dinki, ba kya bu'katarsa fa'da mini inda iyashegensa zai yi tasiri. Kin ga ni yana mini gadara ko isa?" Ta girgiza kai ta ce "saboda yasan baya gabana, hatta uwar tasa ma ni bata gabana na yi aure ne kawai dan an matsa mini, amma mene ne a cikin auren ban da takaici da rashin y'ancin kai. Dama fata nake na haihu ko sau daya ne, Alhamdulillah na samu ko yanzu na ga damar kashe auren sai na zagi uwarsa". Zuciyata ta buga, ciki ne da Munubiya? Nan da nan na dinga a uziya da shaidanin da zai tunzura ni, tunda dai nasan Gudale na mua'amalantar ai kuwa idan da rabo ciki zai samu. Na kalli cikin idonta na ce "Bana ra'ayin hakan Munubiya! Bana so, kada ki janyo mu yi rikicin da za'a jimu". Ta mak'e kafa'da tare da cewa "Na gaji da zagaye zagaye Halima! Ina son ki sosai. Idan kuma kin k'i, to ban ki a jimu a gidan radio ba. Tunda na dora ido akan ki ban sake yi miki kallon kishiya ba sai abin kaunata. Zan yi komai dan na raba ki da lusarin mijinki Mumys boy, domin ke din kin wuce ace ana mulkar aurenki, kina da daraja kin wuce irin wannan kaskancin." Na koma na zauna ina ta ambaton Allah yayin da ita kuma ta wuce wajenta cikin kwanciyar hankali. A gigice na kira Sakina a waya na fa'da mata komai. Ta yi shiru domin ita ma ba karamin gigita ta yi da wannan maganar ba. Tsawon lokaci bata tanka ba, har sai da na ce "Kina jina kuwa?" A hankali ta ce "Ina jin ki Sadiya abin ne ya ki'dima ni, kaina ya kulle kwarai da gaske. Ki bari zan yi tunanin abin da zamu yi". Na ce "To". Washagari a asibiti Sakina ta dinga jinjina girman al'amarin, ta ce "Ba mutunci ne da yarinyar ba, zata iya burma ki, kawai shammatar ta zaki yi, ki dinga nadar maganganunta a waya saboda su zame miki shaida. Amma idan kika fito Kika fa'da za'a iya cewa sharri kika yi mata". Na yarda da shawarar Sakina. Amma na yi matu'kar janyewa Munubiya, duk da ita ta 'ki yarda ta yi fishi da ni irin yadda na yi da ita. Muna cikin wannan yanayin Munubiya ta fara wata irin jinya. Sosai take galabata, Gudale da daddare ya shigo mini, ba walwala ya ce "Gobe ki wuce da Munubiya asibiti ta ga babban likita". Na amsa da cewa "To Allah ya bata lafiya". Ni na jagoranci kai ta asibiti, na tsaya kuma ta ga likita, aka mata komai muka dawo. Ashe lokacin ma cikin ya shiga wata na biyar an kuma tabbatar mana yan biyu ne a cikinta kamar yadda scanning ya nuna. Tattali da gata ba wanda Umma bata nuna Mata ba, hatta Gudale da bai wani daukaki lamarinta ba, samun cikin Nan da yadda Umma ta sakankance maza zata haifo ya yi d'oki, ya ajiye abubuwa masu yawa yana nan nan da ita. Abin yana mintsini na. Duk sadda Umma take fa'din Munubiya ce zata haifo magajin Abba, sai na daga hannuna sama da nufin na yi addu'ar kada Allah ya sanya ta haifi namijin, sai kuma kunyar Ubangiji ta kama ni. Sai na fasa yin wannan addu'ar, sai kawai na ro'ki a cire mini damuwarsu a raina, ya kuma shirya mini yarana, ya tsare mini su. Tana warwarewa sai ga takardar samun aikinta da Ma'aikatar Human right, ashe anan mahaifiyarta take aiki sai dai na ji ana cewa tana daf da yin ritaya. Ga mamakina Gudale bai damu ba, amma kuma ni yak'i biyuwa mini ta da'din rai a dalilin aikina. Ya dauke wa kansa siya mini kayan kwalliya ko Undis, hatta gas idan ya kare kafin ya yi refeling sai na da'de ina fama, wani lokacin ya yi bayan ya gama wulakancinsa, wani lokacin ya jido mini gawayi, wani lokacin kuma ya bawa banza ajiya ta. Sai dai na yi da aljihuna. Makaranta da ya saka su Amnah ya kamata ace wacce tafi wannan ya saka su, amma duk ban ce komai ba, ban yi yun'kurin yin korafi ba, mussaman da aka yi dace makarantar suna da kwararrun Malamai, ta zama raina kama.Z A hakan kuma rannan mun shiga wajenta ni da shi da sassafe, ta kalle ni ina sanye da labcoat ta ce "Aikin ma'aikatan jinya ai sai dai kawai ayi shiru amma tsiyar da ake yi yafi na ko'ina. Barin ranar da za'a a kwana, ai lusarin mijine kawai zai dauki wannan kazantar. Nan da nan raina ya baci irin wanda bai ta'ba baci da Umma ba. Dake a cikin fishi nake sai ha'kurina ya kwace a kanta. Ba fargaba na ce "Allah dai ya tsaremu ni da Sakina, dake a waje daya muke ai". Ai kuwa wannan maganar ta girgiza Umma ta fashe da kuka tana fa'din na jefeta da bak'ar magana. "Amma ba laifina bane laifin Gudale ne da ya mayar da ita banza har na zageta akan idonsa. Sakina kuma ta ga karshen bijire mata da take yi a kaina. Gudale ya yi tsam ya kasa cewa komai amma ya tumbatsa da fishi. Na fito na barsu ina rayawa a raina ta saka ya sake ni. Duk gudun zuciyarta da nake yi bata ga ni, amma Munubiya da take fa'da mata kowacce magana gatsar ita take lallabawa. Tana ta danne cin kashin da take yi musu dan kada ta kunyata. Na wuce asibiti, a ranar bamu yi kwanan dadi ba, domin gaba'daya ya tunzura ainun. Ya dinga kumfar bakin tabbas na raina shi da na mayar wa Umma martani a gabansa. Yayin da ni kuma na ki tankawa, duk yadda nake jin zuciyata tamkar ta fashe a dalilin yadda ni yake bude mini wuta idan na kuskure amma bai isa ya yiwa Munu hakan ba. Har yau din nan basu yarda sun fito da maganar damben da ta yi da Anti Maimuna ba. Ya kalle ni ya ce"Kin mayar da ni mahaukaci ko Halimatu? To na rantse miki sai kin bar aikin nan kome kike ji da shi kuwa". Murya na rawa na ce "Ai kuwa ba zan bari ba Sadik! Ita wacvar matar da ke kana sonta kana tsoronta ai ta fara aikinta, ba kuma izninka amma baka ce komai ba". Ya murde mini kunne ya ce "Ko a Rivers State zata tafi kullum da sunan aiki ba zai dame ni ba, amma ke ko a kofar gidan nan zaki dinga yi ba zan yarda ba. Dama na yi hakuri ne, amma tunda baki fahimci ha'kurin da nake ta yi miki ba, kika mayar wa da Umma magana Wallahi magana ta kare, ai komai zata ce sai ki yi hakuri ki duba ita din uwata ce, amma tunda kika iya irin wannan wula'kancin to kuwa magana ta kare. Na dakatar da aikin ki" Na yi murmushi hawaye na zuba na ce "Bai dakatu ba, ba kuma zai dakatu ba Yaya Gudale." Washagari kuwa na yi ficewata, ina bakin A&E a tsaye sai ga Yaya Ashir, ya tsaya muka gaisa, muna cikin gaisawar suka zo shi da Umma ya kawota ganin likita. Hatta Ashir da ya gaida Umma bata amsa, bare kuma tawa gaisuwar. Shi kuwa Gudale ya kallemu ya watsar bayan ya sanya gilashinsa. Zuciyata ta tsinke na tabbatar abin da zai biyo baya ba mai sau'ki bane. *Hanyar komawarsu gida*. Umma sai fa'di take "To gashi dai ana maka hira da Mata har da kyakyacewa. Na fa'di gaskiya kuma ta zage ni ta hanyar nunawa y'ata ma hakan take, akan idonka kuma. Wallahi ban da nasan ba a barka haka siddan ba, to kuwa lah shakka da na sallamaka, ranar tashin kiyama sai Ubangiji ya yi mana hisabin wahalar da gatan da na rayu ina yi maka amma ka bijire mini, kake kuma zaune da matar da zata kalli idona ta mayar mini da magana a gabanka." Ta dinga goge hawaye da tissue. A hankali ya ce "Ki zuba ido Umma zan dauki mataki fah". Ta rakakkabe murya ta ce "Matu'kar baka tsaida aikinta ba. Billahillazi sai dai na sallamaka, zan fita daga dukkan sha'aninka Wallahi". Da yamma na dawo na tarar da shi a falona tunda dama a wajena yake. Idon nan nasa tamkar garwashi. Na wuce na yi dakina. Ya biyo ni yana fa'din "Hamshakiya ishasshiya! Yau zaki ga karshen kafiyarki". Ban kula shi ba. Ya sake hassala ya ce "Da uzinin uwar wa kika fita?" Sai lokacin na ce "Kada ka sake ka sako uwata a wannan maganar ". Ya kuwa fusata ya ce "Na sako uwar taki dan uwarki, Ina ce ni a akan idona kika yiwa tawa Uwar rashin kunyar?" Hawaye ya goce mini na ce "Bani da kaico Yaya Gudale dan ka zagi Mama, nasan zugo ka aka yi, kuma mai zugar ma bata tsira a wajenka ba, ashe kuwa dan ka zagi uwar wani ai ba abin na yi ba'kin ciki ba ne. Ai kuwa ya dauke ni da mari. Yana huci ya ce "Kin yi k'arya Wallahi! Halima ba zaki rabauta ba, na ce kada ki je aiki, kika take maganata, kika fice ko? Sannan kuma na je na tarar da ke da Ashiru kuna barbad'a Ashe Umma gaskiya ta fa'da. Amma kika rufe ido kika yi mata rashin kunya saboda kina ganin kin isa. To sai ki je, ki auri Ashiru domin ba zan iya cigaba da zama da ke, ba kya mini ragayya akan uwata ba, sannan ba zaki girmama ra'ayina ba. Na datse igiyar aurena d'aya akan ki". Bai jira komai ba ya fice. Bansan ya aka yi ba, na ji na fa'di akan gadona, k'irjina ya yi nauyi, ban yi zaton irin wannan hukuncin ne zai biyo baya ba". *Na ce ba kinsan wani hadi da ake yi wa asalin man ridi da kwakwa da ba'a samun original din su sai a wasu kebantaccun jahohi?* *kina fama da matsalar cinyewar gashi ko kuma rashin tsayinsa?*. *Kina neman ha'din da da zai sanya fatarki laushi da sulbi, kuma cikin saussaukan farashi? Tuntu'bi wannan lambar dan samun naki cikin sau'ki. Kaya mai inganci shi yake siyar da kansa.* *Sister Zainab 08039315577.* 2/8/23, 10:25 - Buhainat: *SDK* *87&88*. Idan na ce zan bayyana irin yadda sakin nan ya buge ni, na yi k'arya amma wacce mijin da take so ya saketa ba da hakkinta ba ita ce ka'dai zata fahimci irin dimuwar da nake ciki. Wani irin tashin hankalin da ban yi zaton zai ziyarce ni ba, ya mamaye ni. Na dinga jin ashe lokacin da Gudale zai kara kara aure ba tashin hanki na shiga ba. Yanzu ne nake cikin firgici mai yawa. Na kasa tashi har aka idar da sallar maghrib ban iya motsawa ba. Ina nan inda na zube har taran dare tamkar mutum mutumi. Ga Afrah bata nan, Amnah ta jata suna wajen Umma. Idona ya bushe a ranar na fahimci yin kuka ma ba karamin Rahma ba ne. Take na tuno Abba! Na dinga tuna yadda yake fatan aurenmu ya dauwama muddin rai, ashe hakan ba zai samu ba. A k'asa da shekara da mutuwarsa komai y subuce mini har da auren. Tunawar da na yi da Abba ne, wani irin kuka ya goce mini. Na dinga yi ina shesskar ajiyar zucy, ina jin inama na hadiye zuciya na mutu ko na huta da wananan masifar. Na dinga tuno togaciyar da Mamana ta yi mini kada na sake na zama surukar Umma domin ba zan huta a hannunta ba. Na gane wautar da na yi da nake ganin ba zan damu da matsalar Umma ba. Ashe kuwa ita ce matsalar, domin ita take jan kaso sab'a'in da biyar na matsalar aurena. Da k'yar na rarrafa na yo alwallah. A ranar kam ban san me na karanta a karatun sallah ba. Tsabar tashin hankali. Na idar, amma ba kasa tashi akan abin sallar. Kullum ta Allah na sani sai na yiwa Abba a addu'a a fili ko a boye. Amma a wannan daren kafin gari ya waye ban san adadin addu'ar da na dinga aika masa ba. Na idar da sallar asuba barci ya dan sure ni. Sai kawai na yi mafarin Abba da farin tufafi yana cewa "Alheri mai yawa ya tunkaro ki Halimatu! Daure ki mini alfarmar yin idda a dakinki, idan kuma ya nemi sulhu kada ki yi tutsu ba yin kansa bane, zuga ne da kuma sharrin zuciya, kada ki barshi a wannan halin, idan har kin kasa jure zama da shi, babu wacce zata zauna mini da shi, ni kuma so nake ki zame masa garkuwa har a aljannah". Daga haka ya dinga yin murmushi yana tafiya da baya da baya cikin murmusshi. Yayin dana dinga mi'ka masa hannu Ina cewa zan bika Abba! Ka tafi da ni". Bai ce komai ba amma ta girgiza kai alamun ba zan bishi ba. Koda na tashi ban manta mafarkin ba. Jikina ya sake sosai. Na kasa yin katabus, zufa sai karyo mini take yi tamkar ba sanyi ake yi ba. Har k'arfe takwas na safiya ina ta saken saken shin na tafi ne, ko kuwa na zauna na yi idda kamar yadda Abba ya ro'ke ni? Kaso mafi yawa na zuciyata yafi rinjayar mini na zauna. Dan hakan sai na zabi na zauna din, ina kuma fatan mu shirya domin bansan son Gudale bai yi rauni a zuciyata ba sai a ranar. Domin da na tuna ya sake ni sai zuciyata ta buga, zufa ta dinga karyo mini tamkar wanda na yi tseren gudu a lokacin zafi. Na kasa kunne na ga fitarsa amma har goma ta buga ban ji motsin ba, na leka ta windo amma na ga motocinmu duk suna nan tabbacin bai fita ba. Kuma ranar aiki ce. *Gudale*. Yana kwance a dakinsa abin duniya ya rufar masa, zuciyarsa ta ki kwanciya, mafarki ya yi Ashiru ya zo neman auren Guduyo. Ya ganta ta ci kwalliya tana zaune a yar bukkar da Abba ya gina a harabar gidan dan hutawarsu shi da Baban Yara. Sai murmushi take yi. Yayin da Ashiru yake fa'din "Ubangiji baya kuskure Halimatu! Bayan dogon lokaci dana dauka ina dakon soyayyarki, sai bayan da na cire rai da samun ki, sai Ubangiji ya juya al'amura, gashi zai cika mini buri. Zan yi komai dan na same ki, zan yi rikici da duk wanda ya nemi nuna mini ana barin halak dan kunya, a yanzu ke din ta mai rabo ce. Tunda wawan mijinki ya bar ki kika fito daga gidansa, ya sake yin wautar bari kika kammala iddarki to kuwa zan fafata da shi dan na tabbatar na yi masa kwalelenki kamar yadda ya yi mini a karon farko. Halimatu ta murmusa dimples suka lotsa. Abayar da take jikinta bata boye tudun kirjinta ba. Hannayenta dauke da lalle da ya sake kawata ta. Ta ce "Yaya Ashir kai me zabina, ka daina sako maganar Sadik domin tuni na rufe babinsa, dama kaddarar zan haifa masa su Amnah ne, ka daina bata ranka akan wannan sakaran". Dai dai nan ya farka. Fargaba me yawa ta kama shi, da ya tuno ya saki Guduyo fa da gaske. Nan da nan ya zabura ya duro daga kan gado yana cewa "Tabbas mafarki ba gaskiya bane, amma sau tari yana iya zama gaskiyar. Ashiru zaka yi abin da yafi haka shegantaka ma. Domin na tabbatar babu Allah a harshenka bare a zuciyarka, baka k'i na mutu ka zo zawarcin Guduyo ba". Ya dauki waya ya kira Sakina bugu biyu ta dauka. Kafin ta ce komai ya fit ya ce "Sakina maganar da Guduyo ta fa'da miki na janyeta, ki kira ki fa'da mata." Cikin rashin sanin manufarsa ta ce "Bamu yi waya da ita ba, rabona da ita tun jiya a asibiti, har yanzu kuma bamu yi waya ba, na kira duka layukanta a kashe, lafiya kuwa yau bata zo aiki ba?". Ya waske da cewa "shikenan sai anjima". "To ina ta tafi? Tunda bata fa'dawa Sakina ba ya tabbatar bata fada wa kowa ba. Wani irin al'amari ya dinga mamayarsa, amma idan ya tuna kukan da Umma take yi, ya sake hango yadda ya ganta tsaye da Ashiru babu fargaba ko nadamar ta karya dokar da ya saka mata, sai ya ji ransa ya kai koluluwar baci. *Dakin Guduyo*. Ina zaune hawaye yana ta zubo mini, sai kawai na ganshi a bakin kofar dakin ya yi turus wata'kila bai yi zaton zai gan ni a ciki ba, domin a hanzarce ya turo kofar. A sanyaye ya shigo dakin ya zauna akan front drower. Ya da'de yana kallona cikin rashin abin cewa. Yayin da na yi karfin halin ha'diye kukan da nake yi. Murya ba amo ya ce "Baki tafi ba guduyo?". Nima tawa muryar babu amo na ce "Ina nazarin inda zan tafi ne, tunda kasan ai Baba ba zai bar ni na zauna masa a gida ba, tunda kai kullum mai gaskiya ne a idonsa". A hankali ya ce "Ki ajiye aikinki Guduyo bana so, bana so, bana so." Murya na rawa na ce "Idan na ajiye so kake na dinga bin dangi ina yar murya ko? Ni ba aure ba, ni kuma ba ga abin da zan dogara da kaina ba." Ya sauko ya tsugunna a gabana ya ce "Kishinki nake ji mai yawa. Tabbas akwai Yar tsama a tsakaninmu da Ashiru, amma ban tsane shi ba, sai da ya bari na fahimci yana son ki, amma ke kin kasa gane iya gaisuwa kawai na amince ki yi da shi, na tsani doguwar hirar da babu hijabi a tsakaninku." Baki na rawa na ce "To ai yanzu tunda ka sake ni, ba ruwana da fa'da mini wannan maganganun, kai ma kuma babu ruwanka da aikina". Ya sassauta ya ce "Idan kin yarda ai shiryawa zamu yi Guduyo, ko barci fa ban yi ba, kalli yadda na sake kankance wa mana daga yammma zuwa yau". Wata irin salama ta shige ni, na tabbatar ko ban yi mafarki da Abba ba, ba zan iya yin turjiya mai yawa ba, kawai dai zan yi jarumtar da ba zan nemi sulhu da kaina ba. Hawaye ya goce mini, na kifa kaina akan guiwata na dinga yin kuka mai dauke da gunji saosai. Ya rikice yana cewa "Ki yi ha'kuri kin ji! Ki taimke ni, ki ajiye aikin nan, zan nemo miki wani, zan yanka miki albashi, kin sani Abba ya tara mana dukiya me yawa, so yake kuma na rayu da ke". Wannan maganar sai ta sake tsananta kukana. Cikin kuka sosai na ce "To ai kasan da hakan ka rufe ido ka sake ni, alhalin ban yi maka komai ba". "Nan da nan ya harzuko ya ce "Baki mini komai ba kika ce? Shin Ashiru wai matsayin su daya da Al'amin ne a wajenki? Ke nifa rungumar da Al'amin ya miki ma fa ha'kuri kawai na yi Billahillazi! tunda shari'a bata sanya takunkumi akan hakan ba, na kuma sani har duniya ta na'de babu aure a tsakaninku. Amma ina tabbatar miki Ashiru a yanzu haka bai ki na mutu ba". Na kasa cewa komai saboda yadda ya fitattike. Tsawon lokaci muka yi tsit, tamkar mutuwa ta gilma. Ya nisa ya ce "Ina son mu shirya yanzu Guduyo! Ki yiwa Allah ki ha'kura da aikin nan, na rantse miki ba zamu ta'ba samun zaman lafiya da ke ba matu'kar kina kan ra'ayinki". Ganin yana lallashina sai na dan ja zare ka'dan na ce "Ba dai ka rabu da ni ba? To kawai mu rufe maganar haka nan". Ya sassauta ya ce "Ni na riga da na huce Guduyo, kinga dai Abba da yanan ba zai ji da'di wannan bak'ar kaddarar da ta sauko mini na furta wannan kalmar ba. Mu rufe a tsakaninmu, ba sai kowa ya ji ba. Na zum'bura baki na yi shiru "Kawai ki ajiye musu aikin sai mu yi zamanmu lafiya, kuma tafiyar da baki yi kin bar ni ba, na yi matu'kar gode miki, na kuma sake girmamaki Allah ya yi miki albarka". Bansan meyasa ba, nake jin matu'kar Umma tana d'oron k'asa bazan ta'ba samun kwanciyar hankali da Gudale ba. Na yi imani da Allah ko kaffara ba zan yi ba, ita ce ta yi mini sanadin tsinkewar igiyar aurena ta hanyar sake tunzura shi. Hawaye ya goce mini, na kasa cewa komai. Ya ce "Zaki ajiye din?" Na tsinci kaina da cewa "Eh". Nan da nan ya rungume ni, yana cewa "Na gode sosai, Àllah ya kore shaidanin da yake tsakaninmu. Na janye, na mayar da ke". Na yi shiru illah hawayen da ya k'i yanke mini. Ya ce ", Amma dai kinsan bana son irin wannan kukan ko?" "Ai kuwa kuka ya same ni, akan abin da bai kai ya kawo ba kawai ka sake ni, idan kuwa haka ne ba za'a dauki lokaci mai yawa ba zaka haramta mana zaman gaba'daya". Jikinsa ya yi sanyi ya ce "ki daina yi mini mugun fata Guduyo! kaddara ce ta hau kaina da wani irin zazzafan kishi." Na kafe shi da ido na ce "menene matsalarka da Yaya Ashir ne? Yanzu gaisawa da shi sai ya zama sanadin mutuwar aure dan kawai darajar aure ta fa'di warwas, alhalin kuma shi din dan-uwana ne. Kawai dai an zugoka ne, an kuma saka ka datse mini aikina dan kawai ba'a son a ganni cikin walwala alhalin ba a kaina aka fara aikin ba". Ya zabura ya ture ni daga jikinsa, ya nuna ni da yatsa ya ce " Billahillazi zan yi miki dukan da ba zaki fahimci komai ba tsawon lokaci mai yawa. Baki da mutunci Guduyo! A gabana kike ta zagin Umma? To ta yi zugar tabbatacciya marar mutunci. Dama fa hakuri na yi, akan idona kika ce bana ganin mutuncinta, ina zaginta, to mu kaddara ma ina zagin nata amma ke kuma kin ci uwar karya kin kwana da yunwa ki zageta ki kwashe kalau a hannuna. Na mayar da ke tabbas, ko kina so, ko ba kya so kin maidu, kuma ki tashi ki shirya na raka ki, ki bata hakuri." Nan da nan na sake zum'bura baki, na juya fuskata tabbacin ba zan je ba kenan. Ya mike ya ce "Tun jiya nake cikin tashin hankali saboda ke, amma sam ke baki gane ba, kuma Wallahi ko zaki shide sai kin je." Ya fice ya bar ni da bacin rai mai yawa. Bai jima ba sai gashi ya dawo da belt. Na zabura na mike na ce "Na rantse idan ka dake ni da wannan abar zaka yi nadama." Ai sai kawai ya ce "Zan doke ki ne ba a matsayin miji ba, a matsayin yayanki da za'a tura gidan aurenki ya ladabtar da ke idan kika nemi zubar mana da tarbiyar gida". Na sha kune na ce "uhum uhum". Ya nuna kansa ya ce "Ban isa ba ko Guduyo? Babu wata alfarma da zaki iya yi mini ko? To bari laifin da kika yi mata ya zama sanadin da zata tsine mini, idan ya so na lalace na kasa yin albarka, idan kuma hakan ta faru ai ke ce a ciki, tunda ya'yanki ne zasu fi kowa yin asara". Na ce ba y'ay'ana kawai ba, na munu fa? Sannan ita meyasa ka barta take yin aikin?" Ba fargaba ya ce "Saboda ita ina sonta, ina kuma jin tsoronta, ke kuma bana son ki, na kuma fi karfinki ina ce shikenan?". Idona ya ciko da 'kwallah takaici tamkar na ha'diye zuciya na mutu. Haka ya tisa ni a gaba amma muna fitowa falo ya yar da belt din. Muna isa kofar shiga bangaren Umma zuciyata ta tsinke, saboda tuno Abba da na yi, sannan kuma zuciyata tana ganin bai cancanci na bata ha'kuri ba alhalin bata nufina da alheri. Mun zo daidai windon dakinta, na juya da sauri ai kuwa ya damko ni yana fa'din "Idan ba zaki yi saboda ki taimake ni ba, to ki girmamata saboda matar Abba ce, bata ha'kuri saboda shi" Shikenan na bishi muka shiga cikin gidan. Bamu zame koina ba sai ciki dakin Umma. Na zauna daga gefe a kasa yayin da Gudale ya zauna a bakin gadon. Na gaisheta ta amsa da k'yar a kuma wula'kance. Shima tasa ba walwala ta amsa masa. Tsawon lokaci ba wanda ya sake yin magana. Gudale sai kallona yake yi. Cikin karfin hali na ce "Umma ki yi hakuri akan abin da ya faru jiya, baki fahimce ni bane, kallon uwa nake yi miki, matu'kar ba zan fa'dawa uwata magana da nufin raini ko izgilanci ba, to kema kin wuce hakan, tunda ke din uwace mai girma a wajena". Ai kuwa a kufule ta ce "Bana son iyashege kin ji! Ta ina na zama uwarki? Inda ni uwace kya zage ni akan idona?" Gudale ya kyafta mini ido. Na daure na ce "Na yi kuskure ba zan sake ba, ki yafe ni Ummah". Ta kuwa dinga sakin maganganu masu ciwo, tana cewa "mu je mu biya Malaminmu aikinmu ya yi kyau, mun samu duniya yadda muke so, amma a lahira gidan haya ne ya kamace mu, domin duk mai yin surkullen da zai jarabta namiji, ko shiga tsakanin d'a da mahaifi shine talakan lahira". Na yi kasa da kaina, kuma abin mamaki sai ban ji bacin rai ba, bare na yi kuka ba dan komai ba illah yanayin Gudale da ya nuna yana cikin tsaka mai wuya. Kallo daya zaka masa ka gane ba karamin karfin hali yake na ha'diyar cin mutuncin da ta sanya ni a gaba tana yi mana ni da uwata ba. Amma da ke ta shiga rigar Abba, sai ban damu ba, asalima sai na gane ba karamin gigita zaman lafiyarts muka yi ba, ba dan komai ba sai dan ta kasa kaimu kasa, bata ganmu a taskun da take fatan ta ganmu ba". Sai da ya gama iyakar cin mutuncinta kaina na kasa, ban kara tankawa ba, har ta gajiya dan kanta. Na dago na kalleta, fuska da walwala na ce "Ki k'ara ha'kuri Umma! Ki kuma yafe mini". Daga haka na mike na ce "Allah ya kara lafiya". Ta ce "Ban da naci irin naki , wacce mace za'a yiwa irin haka amma a kasa ganin fishi a fuskarta, anya kuwa wannan kina da cikakken hankali?" Na dan sake fa'da'da walwalar fuskar na ce "To wa zai yi fishi ne da uwarsa Umma? Ai komai kika yi mini, kin kai ki yi, kin kuma cancanci hakan ne." Ta ja tsaki mai tsananin gaske. Yayin da Gudale ya biyo ni har bakin kofar fita ya ce "Na gode sosai, ki je ki jira ni. Ina nan zuwa yanzun." Ko kula shi ban yi ba, na fi kofar gadern na shige wajenmu. Na dauki na kira Sakina ma sanar mata komai. Tana bu'de baki sai cemin ta yi "Kin yi asarar hali Halimatu! Ya sake ki amma ki kwañan masa a gida? Gidan na uwarki ne ko na Ubanki?". Jikina ya sake na ce "Idan na tafin ma Baba dawowa da Ni zai yi, to ai gara ma na yi ha'kurin ba sai na raba bacin rai da su ba." Ta bani amsa da cewa "Hakane! Ni kuma kin raba bacin rai da ni ai. Amma kuwa duk nacinki sai na fa'di wannan maganar. Domin wajibi ne idan aure ya mutu a fa'da, hakanan idan an yi kome a fa'dawa shaidu saboda kafa hujja". Na bata rai tamkar tana ganina na ce "Ke ka'dai kin isa ki yi shaidar ai". Ta ce "Zaki ga wanda zan kafawa ja'irin mijinki hujja da shi". *Dakin Umma* Yana shiga ta ce "koma ka juya salamamme, akan idona kake wannan rawar kan akan wannan sundumar ko?" Ya bata rai ya ce"Umma fa'da mini me zan yi miki ki yaba mini ne akan Guduyo? Kina kallon irin kwanjin da nuna mata, har gabanki na kawota ta baki hakuri, amma Munu data Yi muku tijara a Yola ba wamda ta bawa hakuri asalima bata yarda ta yi muku laifin ba, illah tana ganin an danne mata hakkinta na Yar adam. Badan na bata baki ba da tuni ta gayyato muku yan Human right. Amma wannan da take ta lallaba ku, kuma Yar gidannan ce amma an k'i ta fir. Gaskiya Umma ki yi hakuri na rok'e ki." "Na rantse maka da kudirar Allah matu'kar tana son zama da kai sai ta ajiye aikin nan, dan ba zan yarda ta ka Yi ta cutuwa ba, tunda baka so to kuwa sai dai ta zauna ta zama cikakkiyar matar aure." "Shikenan na ji na yarda! Amma kema ki dan sassauta, ki rage zafin da kika dauka da ita". Bata kula she ba ta ce "Na gama maganata." A falo ya dawo ya same ni, ina ta share hawaye. Ya zauna daf da ni yana cewa "Yi hakuri kin ji Guddin Abba! Tashi ki shirya mu je shopping, duk abin da babu ko kike da bu'katarsa kawai ki rubuta. Kwanaki ma kin ce ya kamata na siyawa su Amnah dan kunnen gwal ko? To muje sarkoki ma zan siya musu tunda iyayensu ai sun siya musu dankunnen tuni." Haka ya dinga rarrashi, yana ta da'din baki a kokarinsa na wanke abin da yayi mini. Akan dole na bishi muka fice, Wanda hakan ma sai da ya tunzura Umma da muka dawo ita kuma ta shigo duba Munubiya, ta kalle shi ta ce "A haka kamar namiji, nan kuwa shangadawa ne. Wai macen da bata dauki al'amarin uwarka da girma bane kake yiwa irin wannan gudun zuciyar, ba dan tausayin maraici kada ya yi maka yawa ba, da na ce maka kaico. Amma tunda ba yin kanka bane, barka a hannun Allah ya tsare mini kai". Shikenan na ajiye aiki hakan ba karamin batawa mahaifiyata da Sakina rai ya yi ba, amma tunda na riga da na ajiye dole aka ha'kura aka zuba mini ido. Ranar wata asabar sai ga Baban Gusau ya zo takanas wajenmu no da Gudale, har falona ya shigo, ya dinga yiwa Gudale fa'da da nasiha, ya dinga tuno masa kalaman Abba akan aurenmu. Ya ce "Ranar da Sakina ta mini waya ta sanar da ni barnar da ka yi ban iya runtsawa ba, duk da ta ce mini ka janye." Kan Gudale a k'asa ya ce "A mini afuwa Babanmu. Tsautsayi ne da kaddara, In sha Allah hakan ba zai sake maimatuwa ba". Yayin da ni kuma ya dinga yaba mini akan ha'kurina, ya tabbatar mini nan kusa kafin a samu yarinya mai hakuri irina zai yi matu'kar wahalar gaske. Amma da sannu zan ga ribar ha'kurina. Addu'a sosai ya yi mana sannan ya ce "Duk abin da ya taso shine Babanmu gaba'daya. Na dinga kukan rashin Abba! Har ya yi zaton ko bacin ran da ya wuce ne ya dawo mini sabo. Ya mini al'kawarin zai dinga bibiyar zamanmu ba zai yarda da zaman k'wara ba, amma na yi ha'kuri for now. Sannan ya ja kunnen Gudale akan ban da k'auro tunda ya hana aiki, to lallai lallai kada ya sake ya ji labarin ban wadatu da komai ba. Ba a jima sosai ba munubiya ta haifi yan biyu duka mata, sai dai bakwaini ne. Dayar ma bata zo da rai ba, dayar kuma aka saka ta a kwalba. A wannan haihuwar ma Sai da Gudale ya kunsa mini ba'kin cikin ta hanyar cewa "Ya gode da addu'a, ai ya tuno tun lokacin aurensu na ce masa Yan biyu zata haifa, to ya ga ni, an haifi yan biyun kuma ya tabbatar da na so da na yi masa addu'a ko namiji daya a samu". Na kalle shi na ha'diye dariya da takaicinsa. Domin na riga dana gane duk nisan zamani Gudale ba zai canja gaba'daya ba. Maganar maitar da Umma take jifana da ita a wannan lokacin ta fito na ji har kunnena wai ni ce na yi sanadin haihuwar tun lokacin yin ta bai yi ba. Saboda tsananin ba'kin cikin da nake yi da cikin. To na je burina ya cika amma hakkin kisan rai ya rataya a kaina. Sosai abin ya so zama rikici domin mahaifiyata ta fara gazawa da wula'kancin da ake yi mini, amma Baban Yara ya danne maganar aka ha'kura akan dole. Haka rayuwar ta dinga tafiya, diyar Munubiya ta fito daga kwalba, sai dai ba'a jima ba, itama ta bi yar'uwarta. A lokacin kuma Yaya Gudale ya fara zazzabi da kuraje, ga amai lififi dai. Ya kalle ni ya ce "Duk kirkin da nake yi miki wananan karon ma sai kin yi mini bakin hali Guduyo?" Na. Ya yi dariya na kame bakina. Sai dai wanann karon bai fi sati biyu ba ya wartsake. Ba laifi bai yi mini tsiya sosai ba. Kuma komai nake so zai bani. Na fara cikowa, hankalina ya fara kwanciya. I Daidai lokacin kuma zalamar Munubiya kaina ta sake tsananta. *Dakin Munu* Zaune suke suna gado suna dan lashe lashe da tsotsensu ita da kawarta, sun yi nisa cikin sha'aninsu, kawai Umma ta tura kofar dakin a dalilin, ta Dade tana zaune a falon amma bata ji motsin mai d'akin ba. Kawai sai ya yanke hukuncin lekawa ta gani ko a kwance take tunda kullum Munubya cikin bada uzzirin nata da lafiya take. Ai kuwa ta yi mugun ga ni domin halin da ta gansu a ciki abin ya shallake hankali, ita a duniya bata ta'ba zaton da gaske mace zata nemi yar'uwarta mace ba. Kai wannan aikin ya munana Ubangiji ka shirye mu, ka tsare mana imaninmu. Salatin da Umma ta saka ne ya dawo da su a hankalinsu, wani abin mamaki sai basu nuna wani tashin hankali kamar yadda ita ta kadu ba. Kawar Munubiya wacce babbar mace ce da ta girme mata ta nisa ta kalle ta ta ce "Baby wannan fa?" Ta kawar da kai ta ce "Uwarsa ce" Ba kunya ta ce "Ai kuwa duk da ta tsufa ba za'a rasa mamora a jikinta ba, da ganinta lokacin da take cikin kuruciya an zuba mata halitta ta kerewa sa'a." Murmushi kawai Munubiya ta yi ta ce "Tsufanta ne ya hana na shigo da ita harkar ai, amma da ace mun yi zamani da ita me zai hana a moreta?". Sai kawai Umma ta fashe da kuka ta juya da nufin fita. Yayin da k'awar Munubiya da take kusan tsirara, ta yi wuf ta ru'ko Umma tana cewa "Ki kalli tsaraicina ki tafi salin alin, ai ban yi lalacewar hakan ba". Yayin da Munubiya ta mike itama babu kunya a yadda take ta rufe kofor ta rike Umma gam, yayin da waccar din ta dinga lalubar Umma tana ta dukan mazaunanta". Iya hakan dai suka yi mata sai dai na tsawon lokaci. Kuka ba irin wanda bata yi shi ba. Sai da suka gama tozarta ta, sannan Munubiya ta ce "Wallahi tallahi Umma idan na ji wannan maganar a bakin wani sai na yi k'ararki". Da azama d'ayar ta ce mata "Dauko mini jakata na shaka mata powder mu tub'eta tas ta yadda zamu dauki hotonta mu watsa sai mu ga k'aryar yadawar da zaki yi, idan kina son Allah ki fa'di wannan maganar, ki ga yadda zamu yi kaca kaca da mutuncinki." Munubiya ta ce "Bana Jin shakkar hukuncin da zaki saka tijarraen danki ya yi mini, domin a yanzu ba zamansa nake yi ba, zaman shawo hankalin surukarki da kika tsana nake yi, domin sonta nake, tana burge ni fiye da sangartaccen danki da yake abubawa tamkar wanda kika shayar da shi nonon tinkiya tsabar iskancinsa, dama a cike nake da ke ta yadda kike kishin danki, to yau dai kin tabbatar baya gabana. Tashi ki tafi idan kin k'aryatamu, kika fito da maganar wallahi sai na kai ki k'ungiya an kwana da ke. Mun kuma watsa hotonki ki barwa y'ay'a da jikoki tsarabar tarihin arziki". 2/8/23, 10:25 - Buhainat: *SDK*. *89&90.* *Ummah* Ta fi wata tana cikin razani da kad'uwa ta kuma kasa bu'de maganar gaba'daya ta tsorata da Munu, yayin da take tsananta saka ido a tsakanin Halimatu da Munubiya Tabbas ta yi nadamar zabowa Gudalenta Munubiya, sai dai kuma wasiwasi mai yawa take yi, domin gani take tamkar makircin Safiya ne ya sanya suka yiwa Munubiya wannan kulunboton ta yadda za'a kyamace ta, shikenan y'arta sai ta mallaki Gudalenta ita ka'dai. Ba'kin ciki kan ba'kin ciki ke nukurkusarta ba ka'dan ba, ta rasa yadda zata tsoma ranta. Gaba'daya ta susuce, ko barci ba sosai take samu ta yi ba, domin kuwa abin na cinta, barazanarsu ta hana ta fito ta fa'di masifar da ta gani. Bare ta samu sassauci. Ban san me ya samu Umma ba gaba'daya ta yi laushi, amma kuma ni ban samu sassauci ba, na kuma lura ta daina rawar kai akan Munubiya. Yayin da cikina ya cigaba da girma. Ba abin da Gudale yake fatan na ambata masa irin na ce na miji zan haifa, yayin da ni kuma na kame bakina ina ce masa "ka yi fatan ma na sauka lafiya mana." Ranar da na soma fa'da masa hakan bacin rai ya yi tamkar ya dauke ni wata bokanya. Saboda fitattike wa ya yi wai ai na ce masa sai an haifa masa girls guda biyar, yana sane bai manta mugun fatan da na yi masa ba. To ya tabbata ya haifi mata biyar reras, uku suna can suna jiransa ranar k'iyama su kama hannunsa suna Abi Abi har sai sun sada shi da aljannah". Na kyal-kyale da dariya na ce "Har da wanda basu ya hara a haifa masa ba ?" Ya sha kunu kuwa! Ya ce "Annabi ne dai ya ce "Wanda yaransa uku suka mutu suna k'anana, idan ya yi hakuri zasu ceshi shi, wani ya ce ko mai biyu? Annabi ya ce na'am. Sai wata ta ce har da mai guda daya? Annabi ya ce har da mai guda daya. Kinga ni kuwa zan samu albarkacin Little Adama da twins". Na murmusa domin yadda ya hakikance yana kiran little Sakina da sunan Adama wai shi a dole sai na ce ba sunan da nake so a saka mata ba kenan. Ya gyada kai ya ce "Allah ya yafe miki Guduyo! Kin mayar da ni abin dariya, sai kawai ya zaro tsinken tsintsiya ya miko mini. Na karba ya durkushe a gabana yana fa'din "sai na nuna masa abin dariya a jikinsa. Ai kuwa na tsunture da dariyar sosai. Ganin ya fitattike akan sai na yi pointing abin dariya a jikinsa ya Sanya na nuna kansa. Ya kuwa mike yana nuna kirjinsa yana cewa "Kaina da motsi kike nufi ko Guduyo?" Na kuwa sake kyakyacewa. Ya tunzura ya ce "ki gaggauta tuba tun ban kwashe miki karama kin kasa samun rabauta ba". Na sake yin dariyar na ce "Allah ya huci zuciyar Gwanki na Guduyo Baban Amnah". Shima dariyar ta kwace masa ya ce "Na rantse tunda kika ce kaina da motsi idan ba sai na koyo allura ba. Ta yadda zan dinga danne ki Ina yi miki alluran masu tabin kai idan yi so sai mu yi jinyar tare. Kuma ba Gwankinki bane na Munubiya ne. Addu'ar da zaki dinga yi mini ki samowa su Afrah brother shine kike yin kyashi, kai Guduyo zuciyarki da fa'di take Wallahi". Dariya ta sake kwace mini. A fili na ce "Allah ga Gudalen Abba ayi masa afuwa, ka san yadda ka sanya mini sonsa, Ubangiji a kintsa mini tunaninsa". Ya girgiza kai tare da cewa "Kin ci bashin kirana marar tunani. Tabbas baki barni haka siddan ba Guduyo". A kwana a tashi na shiga watan haihuwa, a wannan lokacin kuma Munubiya ta dauke hankalinta a kaina, sai dai bata fasa yi mini kirki ba, bata fasa yiwa su Amnah alheri ba. Ina gicciye Akan sallaya bayan na idar da sallah ina ta tunanin abin da zai biyo baya idan na haifi mace. Ga mamakina sai ban ji fargaba ta kama ni ba. Domin na riga da na fara tsikewa da halayyarsa, amma idan na tuna da idon Abba ma bai fasa yi mini iyashege ba, tun ina a asibiti, to ina kuma a yanzu?. Idan na yi yun'kurin na ro'ki Ubangiji ya sanya abin da yake cikina ya zama namiji ne, sai kunyar hakan ta kama ni, domin wasu ma su kawai su sami cikin ne matsalarsu, so suke su ga jininsu. Ni kuma ya bani amma na tsaya rokar kalar jinsin da nake so. Na sake tuno kissar da Àllah da kansa ya bamu a cikin kur'ani na Iyalan Imaran (Ali Imran). Mahaifiyar Nana Maryam irin yadda suka so su haifi namiji, har suka yi bakancen idan namiji ne zasu sanya ya zama mai yiwa masijdil akasa hidima. Amma da Ubangiji ya tashi ikonsa sai ya basu Nana Maryam, duk da basu so hakan ba, amma sai suka karba da godiya, suka yi mata addu'a, suka nema mata tsari daga shaidan suka kuma nema wa zuri'arta tsari gaba'daya. Hakan kuma suka yi mata tarbiyar yiwa masallacin hidima kamar yadda suke son namijin ya zama. To gashi har yau din nan da Ubangiji ya sanya albarka a sha'anininta, ya tsare ta, kusan shekaru dubu uku da faruwar al'amarin amma Ubangiji bai shafe tarihinta dana iyayenta ba. Sai ma ya zabeta ya saukar da babbar izina akanta da danta dan ta zama aya ga masu hankali. Idan ina tuna wannan ayar, ina kuma tuno sakayyar da Allah ya yiwa Abba da ya bashi yara mata, shi kuma ya zama bawa mai godiya, ya karbesu da farin-ciki, ya yi musu tarbiya cikin adalci da tausayi, ya kuma aurar da su a hannaye na gari. Ubangiji sai ya shirya masa su, ya daukaka su, ya kuma mayar masa su abin sha'awa a wajen kowa, domin ko Anti Maimuna da Anti Juwairiya ai ba wai basu da kirki bane gaba'daya, ra'ayin uwarsu suke girmamawa mussaman akai na. Kowanne irin jinsi aka baki yar'uwa yawaita godiya, kada kuma ki yarda ra'ayin namiji ko na danginsa ya sanya ki butulcewa Ubangijin da ya baki y'ay'a mata, yawaita yi musu addu'a, ki kuma tsaya ki basu tarbiyar da gobe za'a yi alfahari da su. Ya shigo ya same ni a hakan na kalle shi a jirgide na ga ya yi wanka ya shirya, ya yi kyau sosai. Kamshinsa na tsaddden turaren Chris adams ya cika mini dukkan kafofin hancina. Ya ce "Fita zamu yi da Munubiya, zan rakata mu dubo sister din Mum dinta da bata da lafiya, shekaranjiya waccar ta dawo daga Egypt." Ina daga yanda nake na ce "Ku gaishesu. Dan Allah kuma ka turawa Maman Nana ku'di a sake karo siyayyar kayan haihuwar nan. Kasan dai kayan da muka siya ba wasu masu yawa bane". Ya make kafa'da ya ce "Ba zan bata ba Wallahi. Ke nifa waccan Dubu Sittin din da na baki Billahillazi dan kada ki sanya ni a gaba da koke koke ne. Amma ban da hakan ace duk yawan yan'uwana dan zaki haihu sai na yi wata hidima? Wallahi ban da nasan halinki da koke koken banza da kafiya tamkar mutanen farko da ko wando ba zan siya ba, idan ya so idan anyi haihuwar su bada dankwali ko rigarsu a na'de musu y'arsu a ciki, ba nine da kunya ba. Ina ce ke na baki isassen ku'din da zaki sayi tufafin da zaki sanya da duk abin da zaki bu'kata?" Na ce "Eh cikin mamaki. "To kada ki sake yi mini maganar kayan Baby, domin ya fini, ko ta fini yawan iyaye wanda na bayar ma ai kara na yi musu, buga ki fa'da wa Yaya Abdallah ko Al'amin ko Abbas, ko kuma Ramlatu. Idan gaggawa kike yi marar kunya marar kawaici. Na yin sakare ina tu'ajjibin Yaya Gudale! Duk yadda nake ganin na karance shi, amma kullum yana sake fahimtar da ni, har yau ban kammala gane shi ba, bare na fahimce shi. Na ja gauron numfashi sosai. Na ce "Ai shikenan idan Abban ya zo a na'de shi a zanin ai". Ya murmusa ya ce "Hmmm maketaciya kawai, waton dai da gaske kike mata biyar zai biyo". Na kuwa tuntsire da dariya na ce "Ai hakan ne gaskiyar magana. Ka sani kai ko sai an yi maka bakwai kafin Wakilin ya iso ma". Ya mak'e kafa'da tare da cewa "Innalallaha ma'assabirin. Aniyar moda ta bi randa". Ya fice da sauri. Yayin da na daga murya na ce "A dawo lafiya". *Munubiya* Ta fito ta ci kwalliya kamar mai zuwa party ba dubiya ba. A hankali take takawa tamkar ta manta tsawon mintinan da ya kwashe yana zaman jiranta a mota. Da kansa ya dinga kallon agogon wayarsa, yana ta nazarin Guduyo bata ta'ba yi.masa irin wannan yaukin ba. Ya sake tuna wani zuwa da suka yi gidan Sakina, mintina biyu kawai ya yi yana jiranta, ya yi tafiyarsa ya barta. Sai dirban gidan ne ya dawo da ita. Ya kalli yanzu ya shafe minitna sama da talatin a zaune. Ta kuma fito babu wani alamun ta yi laifi, tamkar dai wani kaskantaccen direba. Kafin ta iso gare shi, Umma ya hango Umma ta fito. Gaisuwar da Munu ta yi mata ya yi matu'kar tsayawa Gudale a rai. Domin cewa "Umma barka da lokaci ya kike?" Wannan gaisuwar da mafi yawa matasa suke yinta gaskiya raine ne ba ka'dan ba. Shi a karan kansa baya son wanda ya girma ya ce masa ya kake? Bare kuma ace matar aurensa ta cewa uwarsa ya kike? Tabdi jam. Ransa ya baci sosai. Ya fito daga motar yayin da ita kuma ta tunkaro shi tana cewa "Har na fito, sai na tuna ban yiwa Maman Amnah sallamah, acan na shantake, kasan idan ina gabanta manta komai nake yi tsabar yadda take da kirki da shiga rai". Ai kuwa ha'kurinsa ya kare ya damk'e ta sosai yana fa'din "I hate you Munubiya." Ya girgiza ta sosai ya saketa. Ta hanyar tunkuda ta gefe guda. Ta kafe shi da ido ta ce "Zaka San ka ci zarafin jami'ar kare hakkin d'an Adam" Umma da take gefe ta ce "Ku bi a sannu dai". Takaicinsa ya sake girmama. Ya fito ya fice kofar gida. Yayin da Munu ta ja uban tsaki ta wuce ciki a fusace ainun. Bansan wainar da suke toya wa ba, a tsakanin Umma da surukurta da kuma Gudalenta, amma dai na fahimci akwai jikakkiya a tsakaninsu da suke ta faman nukunukunta. Ranar 25 ga wata December aka sake Ciro mini kyakkawan jaririna sai dai dan tsurut ne ba auki irin Babansa. Sosai Gudale ya yi murna. Sai dai duk yadda yake zumudi bai iya daukar yaron ba. Da gaske yake yi bai iya daukar jarirai ba. Da murmushi akan fuskarsa ya ce "Guduyo duniya! Waton dai yanzu kika yi niyya". Na murmusa bance komai ba. A take ya yi masa huduba da Abubakar sunan Abba, kuma sunansa". Karin farko da na yi jego Yaya Gudale bai bata mini Rai tun a asibiti ba. Haka nan kulawa da tattali mun samu tamkar ba Gudale ba. Dan kuwa bai yarda ya koma wajen Munu gaba'daya ba. Kwanaki biyun nan haka yake yi, idan ranar girkina ne, dakinsa zai shige ya yi kwanciyarsa. Da na yi masa magana, ya ce haka ya ke so, hakan kuma yaga dama. Da kansa ya zab'awa yaro inkiyar Aman. Wani irin gata da tattali yake yiwa yaron, amma ni ban ji ya dara su Amnah a zuciyata ba. Mussaman ma Afra da nake ganin ko yara nawa zan haifa zata cigaba da zama mowar y'ay'a. Duk da dai ban ta'ba bari hakan ya bayyana ba, ina kuma yawaita addu'a kada na fito da soyayyarta fili ta yadda zan janyo mata gaba a tsakanin yan'uwanta. Domin kalubalen da iyaye suke haifarwa a tsakanin y'ay'ansu ba ka'dan bane. Am sani dole akwai Wanda zaki fi so a cikin yaranki. Amma kada ki fifita shi akan yan'uwansa, kada ki daukaki lamarinsa sama da nasu, kada kuma ya zama su bakya shawara da su ta yadda kowa zai fahimci an kin fi son wance ko wane, abin kaicon kuma sai kiga ko haihuwa Suka fara yi anfi son Yayan wanda shine mowar. Wannan ba k'aramar fitina take haifarwa da kiyayya ba. Allah dai ya shiryemu ya sa mu fi karfin sake saken zuciya da kuma sharrin shaidan. Watan Aman uku ya yi kubibi da shi duk da dai ba wani girma ya yi ba, yanayinsu daya da Amnah domin itama haka take har yanzu sai dai doguwa ce har yau bata canja ba, komai na Sakina shine a jikinta, yayin da Aman ya ke kama da Gudale sosai. Afra ce ta yi ruwa biyu, idan muna tare ace kamata ta yi, idan tana tare da Gudale ace da shi tafi kama. Daidai lokacin ma fara.kosawa da jarabarsa akan Aman, domin duk ranar da na kuskura ya ganshi da rigar da ya sanshi da ita to ga ba lafiya, shi kullum sabuwar riga ake bude masa. Tun ina ganin zai gaji ya daina har na ha'kura na gasgata ba zai gaji ba. Da ya ji kukansa ko yana sama zan ganshi a sukwane. Idan ina yi masa mitar a goyon su Afrah bai yi wanann zumudin ba. Yana bani amsa da cewa "Ai shi ban sha wahalar laulayin cikinsa sosai ba, shiyasa nake taya ki raino, amma cikin Afrah ai ba karamin azaba kika roka mini ba. " Na ce "A a Yaya Gudale to ita kuma Amnah da baka yi laulayin ba gaba'daya fa?" Sai ya waske da fa'din "ai ita yar fari ce wannan kuwa Abba ne" Tun ina yi masa kawaici, ina biye masa a rainon Aman har na fara gundura, muka fara samun sabani sosai. Komai na yi ban iya ba. Ba dama yaron ya yi kuka zai fara rikecewa shima, yana fa'din da gayya na ki rarrashinsa so nake kawai na bata masa rai. Abin ya fara damuna domin na riga da na fahimci so yake ya lalata mini yaro kamar yadda tasa uwar ta yi masa gatan da babu kwaba a cikinsa. Ko Amnah na goyawa yaron idan ya gani babu lafiya ya dinga sababin za'a kayar masa da yaro, wanne shashanci ne hakan zan bawa yar tatsittsiyar yarinya goyon Abbansa? Jiki na rawa zai karbe shi, yana shafe shi, yana duddubawa ko an matse shi. Na fara gajiya domin na fara kai wa gejin ha'kurina. A daddafe yaron ya kai watanni takwas, gatan da yake ga ni a wajen Ubansa ya wuce duk tunanin me tunani. Domin kuwa komai na yaron mai girmane a wajensa. Har ta kai da kansa yake yi masa wanka bisa dalilin idan ni nake yi masa yana kuka, to ya fahimci sabulu nake shaka masa. Dan haka ya hutar da ni yi masa wanka. Bansan ya iya harkar raino ba sai akan Aman. Sai dai wani Ikon Allah duk yadda Gudale yake yi masa, shima kulaficina ne da shi. Daidai lokacin kuma Munubiya ta fara gazawa da rashin samun dama a wajena. Ta fara yi mini barazanar ko ta tsiya tsiya ce sai mun yi soyayya ita Bata tana son abu bata same shi ba, ta fahimci bansan alheri da rarrashi ba. Kuskuren farko da ya faru shine ban ta'ba fa'dawa Yaya Gudale matsalata da Munu da bakina ba, sai dai idan ta yi katobara akaina a gabansa ya taka mata burki. Amma ni ban ta'ba nuna masa akwai boyayyen abin da take nufina da shi ba. Al'amarin da ya fara rikita komai. Domin watan Aman goma Sha daya muka yi wani kazamin rikici. Da daddare wajen goma da rabi na dare. Ba zato na fito daga wanka daure da towel a lokacin kuma yana gida yana dakinsa na wajena. Kawai sai ganin Munubiya na yi ta fado dakina cikin wata irin rigar barci fan darinka tsirara. Ba wata wata ta shammace ni ta rungume ni tsam tsam. Na dinga kicin kicin k'watar kaina a dalilin ban son tawul din jikina ya subuce mini. Ilahirin jikina sai rawa yake yi, zuciyata sai bugawa take yi fiye da k'ima. Na fara kai mata mari ina zaginta. Amma ko dar ita sai kokarin kai wa sassan jikina cafka take yi, ni sai na ga tamkar a buge take. Kamar jifa sai gashi a bakin kofar dakin. Ya tsaya cak yana kallonmu, amma dukkan fishi da bala'in duniya duk ya tattaro ya yabawa fuskarsa. Yayin da Munu take fa'din kin fi shi komai. Kin fiye mini shi. *Ko kunsan hakan yana faruwa in reality?* *Ko kunsan ana lalata yanmata ta wannan hanyar mussaman a makaratu?* *Mu yawaita addu'a, mu yawaita istigifari*. *Allah ya tsare mu, ya tsare mana zuri'a*. 2/8/23, 10:25 - Buhainat: *Ummu Muhammad collections* *Tana sayar da dukkan nau'in sutura masu kyau zababbu kuma masu sau'kin farashi* *Tana sayar da takalma da jaka masu kyau* *Tana ha'da lefe* *Tana ha'da kayan haihuwa* *Tana sayar da Data* *Tana yin adashe, Kuma fasihiyar Tela ce* *Tuntube ta a wannan lambar 08063358662* *Siyan na gari aka ce maida ku'di gida" *SDK* *91&92* Tashin hankali ba'a saka masa rana. Domin wani irin shak'a Gudale ya yiwa Munu. Amma ita kuma tana ri'ke da ni gam gam. Dan haka ya ha'da mu tare ya dinga kai mana bugu ta ko ina. Ba k'aramin gigita ta ya yi ba kafin ta sake ni. Tawul d'ina ya fa'di, na yi tsirara. Sakwan kusan biyar ban iya sunkuyawa na dauko tawul din ba, tsabar yadda na muzanta. Tozarcin duniya ya lullube ni, wani irin kukan ba'kin ciki nake yi mai girgiza zuciya sosai. Na kalli yadda ya yiwa Munu jina-jina. Yayin da bakinta bai mutu ba. Fa'di take "matsalon wofi. Baka iya komai ba sai k'ifadi. Bana sonka, na fa'da matarka n nake so, kaddara ce ta baka ita, bata dace da d'an tsurut irin ka ba". Ni kaina ba k'aramar wahalar gaske na sha ba, bare ita da ya zage dukkan karfinsa ya jibge ta. A take kuma ya rangad'a mata saki. Duk yadda take jin jiki sai ta k'yal-k'yale da dariya ta ce "Saki daya na ragwaye ne. Ya tunzura ya ce "Na kara miki". Bakinta na jini ta ce "Ai idan baka cike ta ukun ba, ya tabbata raba mana kwana kake da uwarka, ai ni abin da nake yi yafi naku tsabta, ban ta'ba cin karo da uwar da take kishin d'anta irin taka ba". Ya kuwa sake yin kanta yana kai mata duka kan jiki, kan k'arfi da dukkan iyawarsa. Yana fa'din "Na cike Miki, tanbadaddiya tsinanniyar Allah da mala'ika Jibrilu". Da abin ya ta'azzara na ji tsoron kada ka ya yi kisan kai na kokarta na sanya riga, na saka dukkan karfina na ri'ke shi, yayin da nima ya dinga kai mini duka muryarsa a zafafe tamkar ya ha'diye zuciya yake cewa "Ni Kika yiwa hakan Guduyo?" Na hau barin baki, ai kuwa ya hankada ni, na kifa akan gado. Ya fita, na bishi da sauri domin na firgita da yanayinsa sosai. Wayar Sakina na kira, na fa'da komai da kuma halin da Munubiya take ciki. Na zauna a falo ina addu'ar Allah yasa kada Munu ta mutu mu shiga uku. Ba a Jima ba sai ga su Yaya Al'amin da Yaya Abbas, tare da Sakina. Cikin hikima ta gyara mata jiki. Duk jinin da ya bata mata da jiki, wanda kuma zai ja hankalin mutane sai da Sakina ta goge shi. Ta bata taimakon gaggawa ta farfado. Ta dinga sakin maganganu babu jin nauyi bar kunya. Tashin hankalin da muka ga ni ba dan ka'dan bane. Domin kuwa washagari sassafe sai ga jamian human Rights sun kawo sammaci. Abin takaici kuma har da Umma suka gaiyata. Muna kallo suka tafi da Umma da Gudalenta. Bamu san ahalin su Munubiya kara da kiyashi ne daukar marar sani. Domin kuwa duk amincin dake tsakanin Umma da Momi a wannan rikicin bai yi tasiri ba. Momi mahaifiayar Munu ta rufe ido ta manta duk sabo da kawancen da yake tsakaninsu. Suka daure su, domin sun riga sun shirya wa rikicin sosai, sannan sun saki makudan Ku'di Dan abi kadin cin zarafin da aka yiwa diyarta. Bata bada aurenta dan bata son yarta ko dan ta gaji da ita ba. Ba kuma inda aka ce a kama mace a daketa tamkar jaka. Hukumomi daban daban ta dinga gurfanar da Umma da Gudalenta. Har Amenesty sai da suka shiga case din. Duk yadda Umma take ganin suna da kudi, a wannan al'amarin bai yi tasiri ba. Wula'kanci sosai uwar munubiya ta jagoranci aka yiwa su Umma. Wannan shi aka cewa *SABO DA KAZA*. Kwanakinsu shida sannan aka sako su bayan Antin Zaria da Yaya Abdallah sun shiga sun fita, an kashe mahaukatan kuda'de. Kuka ba irin wanda Umma bata yi shi ba. Dan kuma rashin tsoron Allah sai cewa take yi "Ta tabbatar wannan abin aikin magauta ne". Shi kuma wata irin gaba ya dauka da ni mai tsananin gaske. Idan zan kwana ina yi masa magana ba zai ce mini kanzil ba. Gaba'daya ya firgice sai ramewa yake yi a tsaye. Mun kai wata a hakan na rasa inda zan tsoma raina domin hukuncin ya yi mini tsananin gaske. Da k'yar Sakina ta sasantamu, bayan ta shawo kansa ya fa'da mata ai nima na so ha'intarsa ne, tunda ban ta'ba fada masa tana mini hakan ba, bayan maganganun da bai yi zaton da gaske take yi ba. Da ta dinga fa'da a gabansa yana taka mata burki Tana tafiya ya kalli idona ya ce "Tun a wananan ranar na tsane ki. Idan na kalle ki, sai na tuna yadda na ganku ke da kawar shedanar taki. Wai da idona na ga wata tana kai wa abin da na girma da sonsu cafka? Ai na sani ba wannan ne karon farko da ta yi miki hakan ba. Me yasa baki fa'da mini ba?" Hawaye ya goce mini na ce "Baka gasgata ni ba kenan? Akan idonka na girma amma baka fahimci abin da zan yi da wanda ba zan iya yinsa ba?" Ya ce "Dan adam kuma akwai abin da ya kai shi saurin canjawa da butulci ne?" Haushi mai tsananin gaske ya turnike ni kwarai da gaske. Na mi'ke na ce "Allah ne shaidar komai". Na koma daki na zauna ina fashewa da kuka. Duk hakuri da kawaicin da na wanzu ina yiwa Yaya Gudale a zamantakewarmu ashe duk baya ga ni? Idan wani ne ya ce mini Yaya Gudale zai zarge ni zan karyata. Domin ko shi da nake ta zaman ha'kuri da shi, matu'kar ba ganinsa na yi turmi da tabarya ba, ba zan ta'ba zarginsa ba. Kome zan ga ni, kome za'a ce akansa kuwa. Tun a lokacin zuciyata ta yi wani nauyi, da rauni a dalilin gajiya da halayyarsa da kuma takaicin yadda ban aminta a idonsa ba. Gaba'daya zaman namu babu da'di a dalilin ya ja ya dake ba zai saurare ni ba. Na rasa gane inda ya ajiye ni. Domin dai ita Munubiya ya skaeta, amma Ni m bai sake ni ba sai faman gana mini azaba yake yi. Kwana biyu bani da gas, na fa'da ya kai sau uku. Amma ta tafasa bai ce ba. Idan da wutar NEPA zan yi maza maza na mana girki ni da yarana, domin na sha ajiyemasa ko kallon abinci ba ya yi bare ya bu'de. Idan kuwa babu sai dai na zuba ido. Sai da aka yi kwana biyar sannan ya yi refiling din. Aman kawai ya ke kulawa amma ni da Afrah tamkar ya Wurgar da mu. Rannan ya dawo ya tarar da Aman babu wando, Pampers na cire masa, yaron ya fito falo a guje tunda shekararsa guda kenan. Tun kuma Yana da watanni takwas ya fara tafiya, yanzu tafiyar ta yi kwari. Aikuwa sai ganinsa na yi sabe da shi a zuciye. Yana zuwa sai kawai ya dauke ni da wani irin mari! Afrah ta yi maza ta ce "Lah Ba kyau duka a face inji Islamic teacher din mu fa. Ta kalli yadda hawaye ya goce mini ta ce "Kawai ki fa'dawa Sister dinki ta zo ta rama miki. Tana nufin Sakina kenan. Domin duk a zatonsu yayata ce, ba tasa ba. Ya kuwa damk'ota itama ya faffala mata marin. Ya fice da shi a kafa'darsa. Tun a wananan ranar na kudire kuwa na yaye shi. Washagari kamar almara sai ga Sakina da kawarta, wai duba yaron abokiyar aikinsu Suka je bayan layinmu, shine ta biyota ta gaida Umma. Ta kasa samun nutsuwa da yadda ta gan ni. Bayan kawar ta tafi ta dawo ta tisa ni a gaba. Na kwashe komai ina kuka na fa'da mata. Ta jima bata ce komai ba. Kafin ta ce "Da zaki iya da kin bar wananan tak'adirin Halimatu. Farin cikinki bashi da yawa a gidansa. Ki yi ha'kuri, ki daina bari son zuciyarki yana rinjayar ki akan sha'aninsa." Hawaye ya balle mini. Ta mi'ke ta ce "ki tsananta addu'ar zabin Allah a zamanku. Duk yadda nake son taimakonki sai da hadin kanki na dari bisa dari. Amma ki sani fa har ku tsufa a hakan zaki kasance a hannunsa. Tunda ya riga ya fahimtar da ke shi din dabiunsa irin na *Sabo da kaza* ne ke kuma kin nuna masa *Damo* ce ke akan dabiun nasa". Ta mi'ke har ta kai bakin kofar dakin sai ta tsaya ta juyo ta ce "Ko zaki zo mu tafi?" Na girgiza kai na ce "Abba! Ya ce "Na yi ha'kuri". Ta dawo ta ci d'amara da mayafinta ta ce "Idan kika kuma sako mini maganar Abba akan al'amarinki sai na ci gidanku. Marar hankali! Shasha kawai. Ke bari ki ji Abba ba dan ya haife ni ba. Amma adali ne, da ace tun waccan marin kin bani ha'din kai da bai sake d'aga miki hannu ba. Amma dake kin mayar da kanki banza ina tabbatar miki Namoriki sai ya siyo dorina saboda ke." Ta tafi ta bar ni. Tun ranar na kasa samun lambobin Sakina idan zan kwana ina kira ba zan sameta ba. Da na duba ta a WhatsApp sai ma fahimci ta yi blocking dina ne. Bansan me ta cewa Antin Zaria ba, tunda har Afrah ta fa'da mata Dady ya mare ni jini ya fito a hancina. Sai kawai ganin Junaid muka yi ya iso Kano da sassafe tunda jirgin safe ya shigo. Shine babban d'an Antin Zaria, aure ma yake shirin yi a lokacin. Wai Mamanshi ta turo ya tafi mata da Amnah. Sakina kuma ta zo da kanta ta kwashi kayan Afrah ta ce a ha'da da ita. Domin tana ganin idan yarinyar bata tare da ni wata'kila na fi fahimtar jikina ma yana da hakki a kaina. Ina ji, ina gani aka tafi da su, na sani zasu fi samun nutsuwa da kwanciyar hankali a Abuja. Domin sanda aka yi case din Munu sai da Sakina ta tafi dasu asibiti ta duba su ta tabbatar ba'a b'ata su ba. Amma kullum cikin k'orafin makarantar da suke zuwa take yi. A farkon tafiyar Gudale ya turje akan ba inda zasu je. Sai da Antin Zaria ta bud'e masa wuta ta tuna masa ai ya riga ya bata Amnah, Afrah kuwa hutu zata yi, ta taya Amnah zama kafin ta warware. Ya hakikance da fa'din "Tunda baki dauketa a farkon ba, to sai ki bari a haifo wata". Ta lallaba shi da fa'din "Shikenan bar su su zo hutun yanzu." Shikenan suka tafi. Kwana biyu ciwon nono ya sanya ni a gaba ga zazzabi a dalilin yayen da na yi babu shiri. Ga kuma rashin Afrah sai komai ya tsaya mini cak. Duk na rafke na zube. Kukan Aman ya karu, idan Uban ya matsa na bashi nono a gabansa, yaro da ya ga yadda suka sake aune wa ga powder na shafa musu sai ya tsorota. Ya ki kama wa. Ya dauke shi suka fice. Sai gashi ya dawo a matu'kar tunzure ya ce Halimatu da izinin uwar wa kika yaye mini yaro d'an shekara guda tak?" Raina ya fara baci irin wanda bai ta'ba yi ba. Na zuba masa ido sosai karon farko da na ji tsanarsa tana nema samun muhalli a gefen zuciyata. Ido ya ciko da 'kwallah baki na rawa na ce "Kada ka yi kuskuren sake zagar mini uwa Sadik! Kasan waccan zagin ma ba wai na manta bane". "Na zage ki Makaryaciya mashararranciya. Ni da kika mayar wa uwata magana akan idona kuma a gabanta fa? Shine kike son sai kin ha'da ni gaba da Mama ko?. To duk mugun Halina da kuke fa'da ai ban ta'ba zaginta a gabanta ba." Na girgiza kai na ce "Ato dai na fa'da maka na rantse maka Na gaji, ba kuma zan sake yi maka uzziri ba." "Kar ki yi din dan uwarki". Na dago na kalle shi ido cikin ido na ce "ba dai uwata ba Wallahi." Ya ce "Sai tawa?" Na make kafa'da "ta wacce ya tsargu". Ya ajiye Aman ya ru'ko ni da nufin duka. Sai kawai na shammace shi na rungume shi na dartsa masa cizo a kunne da karfi na sosai. Ya yi iyakacin kokarinsa ya kwace ya kasa. Ban yarda na sake shi ba, sai da na tabbatar ya ji jiki, jini ya ya cika mini baki yayin da ya bata masa jikin rigarsa. Na koma gefe ina haki. Azaba ta kidima shi ya ce "Ashe ke mayyace da gaske Guduyo ni kika cinyewa kunne?" Ya rasa inda zai yi dan tsananin azaba. Ya jima bai dawo daidai ba. Bare ya iya yin magana. Sai da azabar ta yi sauki sannan ya ce "Zaki ga k'aryar iskanci Guduyo yau." Na zum'bura baki na ce "shege ka fasa." Ya ce "Na rantse miki da girman Ubangiji yaron nan bai yayu ba. Kafin na kirga uku kije ki wanko wannan abin da kika shafa yake firgita shi, ki zo ki shayar mini da shi". Yana rufe baki na ce "Na rantse da Allah matu'kar ni ce na haife shi, shi da shan nono sai dai na matarsa ko na saniya. Ko kuma ka kaiwa wacce ta ankarar da kai yaye shi na yi ta shayar da shi. Tunda ka mare ni akansa ka yi ka'dan na sake shayar da shi daga jikina". Ya mi'ke da nufin yin kaina sai kuma ya shafo kunnensa ya tsaya cak ya ce "ko ki zo ki dauke shi, ko na sake ki". Take na fusata irin fishin da ban ta'ba jin irinsa ba. Na ce "Har abada ni sakakkiyar ce domin na haramta wa kaina daukarsa bare na shayar da shi". Nan da nan ya ce "Amma ai ban kai ga sakin ba ko?" Ido cikin ido na ce "Wallahi na saku, idan juninka dabbanci ne Wallahi zaka ga aikin jakai. Tunda muka yi aure ban samu kwanciyar hankali ba. Ba nau'in wula'kanci da baka yi mini ba. Ba kalar tozarta ni da baka yi. Amma yau magana ta kare. Idan kana ganin ba zan iya rayuwa ba sai da kai to ka zuba ido ka yi kallo. A yau na yarda kaddara ce ta hada aurenmu. Na kuma kudiri aniyar sai na janyo kaddarar data ha'damu a ko'ina take na fatatattake ta. Yau ko ni ko kai a gidan nan". Ransa ya kai koluluwar baci mussaman da ya kasa dukana. Na yi tsaki na doshi kicin a dalilin kauri da nake jiyo wa ashe na dora indomie na manta. Na kashe gas din. Na dauke wuka a k'asa, ban kai ga ajiye wa ba kawai na ga wata katuwar tsaka ta fado mini ai kawai na kwasa a guje na yi falo. Shi kuma gani na a guje da wuka na doso shi, ai kawai sai ya suri Aman ya fice a guje tamkar mai gudun fanfalaki. Ganin yadda ya tsorata ainun sai na yasar da wukar nima na rufa musu baya a tunanina maciji shi kuma ya ga ni. "Ai muna fitowa harabar gidan muka ga Anti Maimuna da diyarta, ganin mu a guje gaba'dayanmu sai suma suka juya a guje. Anti Maimuna sai kabarbari da hailala take yi tana cewa "Wuta wuta". Ba kuma ta fasa gudun ba. Ban yarda na shiga sashin Umma ba. A harabar gate din namu gaba'daya na tsaya ina haki. Yayin da su Al'amin da Sakina suka iso suna cewa "Menene hakan?" Dake asabar din karshen wata ne duk a gidan ake yini. Yaya Gudale sai tsuma yake yana fa'din "Ban ta'ba shan maganin tauri ba Billahillazi! Wuka ta dauko zata caka mini". Yayin da Al'amin ya ja gefe ya na'de hannu a kirjinsa yana kallonmu sosai. Yaya Abbas ya ce "Me ka yi mata haka har ta iya jarumtar dauko wuka?" Ya kasa magana. Yayin da Sakina ta ce "Me ya ha'daku haka? Sai lokacin hawaye ya b'alle mini na ce "Akuya ya mayar da ni, ya sake ni ne kuma ya bini da duka". Yaya Al'amin ya fit ya ce "Again?". Sakina ma ta girgiza kai ta ce "Shine kuma kika za'bi ki saka kanki a uku? Saboda autan maza ya sake ki?" Ya tunzura ya nuna Sakina da hannu ya ce "To tozarta ni, ai kin ga yadda dan-uwanta ya koma gefe yana shirin kai mini duka, amma ke baki yi niyyar taimkona ba. Kuma ni ban saketa ba, ta sani, Allah ma ya sani". Tun a wajen rikici ya fara tsananta domin dai Al'amin da Sakina sun kafe ya sake ni, suna ta kokarin juya maganar ma akan ai biyu yayi. Ga wanccan dayan aure ya kare kenan. Yayin da ragowan jama'ar tun daga kan Abbas suka bi bayan Gudale bai sake ni ba, tunda ya musa. Kowa ya yi masa shaidar baya k'arya ya hakikan ce, barshi dai a zolaya ko son ya burma mutum idan ya ga abu zai kubuce masa ba. Yaya Abdallah ya mini wutah wuta na koma dakina. Amma ni nasan me na kudire a raina. Gaba'daya ya fice mini a kai. Tunda abin nan na Munubiya da ya faru fiye da wata bai saurare ni ba, wani irin zaman gaba yake da ni mai tsananin gaske. Yanzu kuma akan d'an cikina ya nemi ya wula'kanta ni ya tozarta ni. Ganin mun dawo gida sai kawai ya karkace ya cigaba da tijararsa har da fa'din tunda bana son Aman shima baya sona, dama shi tuni na fita akansa tunda har na iya cin amanarsa a cikin gidansa. Sakina ce mijina da zan ce na fa'da mata, kuma a yadda yasan munafuncinta ai ba zata fadi gaskiya ba. Gashi kuma yanzu kowa ya gane ita da Al'amin basa nufinsa da alheri, to Wallahi idan basu yi sa'a ba sai ya saka an dauke su an b'atar masa da su kowa ya huta da wuyar zamansu. Idan ina zaune sai nayi ta tuna sadda ya ce mini Dan uwarki. Ko kuma ki dauke shi ko na sake ki. Wato har na yi lalacewar da zai dinga yi mini barazana da saki?" Na shige dakina na shirya yar jakata tsab. Na ji a raina na ha'kura da shi, na ha'kura da duk abin da yake rikitani akansa. A yanzu na fahimci ba wai soyayya nake bu'kata ba. Mutuntawa da kwanciyar hankali nafi bu'kata. Washagari lahadi na tashi tamkar babu komai a raina, na yi yan hudimomina. Ganin hakan sai ya saki ransa. Washagari ya shirya, ya tafi wajen Aiki. Sai da na tabbatar ya kai awa guda da tafiya na kinkimi yar jakata na fice a dalilin ya fita da Aman nasan kuma wajen Umma ya kai shi. Kai tsaye asibitin Malam na nufa na samu Sakina na fa'da mata zan tafi Calabar wajen Anti Kulsum tunda yanzu tana can. Nan da nan ta ce "Kin shirya zama mace ne Halimatu? Idona ya ciko da k'wallah na ce "Eh". Ta ce "To ba Calabar zaki tafi ba. Jira ni na dauko excuse na fito." Na sallami mai adaidaita sahun da na yi niyyar ya kai ni har tasha. Sakina ta dauke ni a mota muka biya ta dauki Al'amin, mun jima muna tafiya . Sai da muka yi nisa sosai sannan ta samu waje. Suka bu'kaci na fa'da musu gaskiya shin ya sake saki na ko kuwa?" Kai-tsaye na fa'da musu gaskiyar abin da ya faru. Dukkansu sun gamsu bai sake ni ba. Amma zasu yi amfani da hakan su kawo mafita a cikin murdadden zamanmu da kowa yake cikin zulluminsa. Kuka ya goce mini ina cewa "Ni dai na gama. Na kuma gaji ba zan koma ba. Basu matsa mini ba, illah Sakina data mayar da abin tamkar wasa domin dariya ta yi mai yawa tana cewa "Yanzu Yaya Gudalen kike gudu Guduyo?" Yaya Alamin ya murmusa ya ce "Wata'kila da za'a jima sai ki ga ta lalubo wayarsa". Na fashe da kuka sosai har jijtinsu ya yi sanyi. A Ranar suka samo mini wani daki a cikin wani gida da wasu suka karba hayarsa amma mai gidan ya ce ban da wannan dakin. Ta hannun *AMYAS NEW & FAIRLY ITEMS* muka samu wannan d'akin. Daki ne madaidaici ya ji tayals da bandakinsa a ciki. Cikin unguwar Mariri kusa da gidan talabijin din da Yaya Al'amin yake aiki. Komai da zan bu'kata sai da suka zuba mini, hatta medium size din katifa. Ga shopping din kayan girki da karamin gas dina. Sai da suka tabbatar komai ya yi musu irin yadda suke so. Sannan suka bar ni cikin kwanciyar hankali tunda gidan da mutane duk da dai kabilu ne da basa ma jin hausa. Sakina ta karbi wayoyina. Ta bani wata karama mai sabon layi. Suka tafi, suka bar ni. *Gudale*. Ya dawo da yamma yana gaban Umma tana ta mitar idan ba Sa'a ta yi ba Halimatu ce ajalinsa. Tana kallona dinkin da aka yi masa a kunne duk kuwa da bai fa'di ita ta cije shi ba. Ya yi shiru. Ta zuciya ta ce "Matar da zata yaye maka d'a babu izininka kake zaune da ita, matar da zan fada ta fa'da, bayan sun shiga sun fita sun wargaza lamarin matarka. Oh ni Saude ina kallo". Ya mike yana cewa ki tsananta yi mini Addu'a. Ya sunkuya da nufin daukar Aman da yake ta barci. Ta ce "je ka abinka ka huta gajiya tunda ta riga ta washe shi, kuma k'arya take yi fuffuka kawai take yi saboda tasan yanzu ta gama da kai, yau da wata ce ta haifi wannan yaron da tuni ba'a zauna lafiya ba." Ya wuce ya barta tana faman yi masa addu'ar kada Allah ya sanya Halima da uwatata su kai shi k'asa. A kasalance ya shiga gidan. Dake a cikin fishi mai tsananin gaske yake bai ko nemi inda take ba. Tunda ya shige dakinsa bai fito ba, Sai sallar magahriba. Bai koma ba kuma sai da aka yi Isha. Sai lokacin shurun gidan ya masa yawa. Ya leka ko ina bata nan. Ya sauke girman kansa y shiga har dakinta nan ma shiru. Zuciyarsa ta fara harbawa da sauri da sauri. Ya dawo falo yana jin tashin hankali na ratsa shi. Kamar an tsikare shi ya mike ya yi bangaren Baban Yara. Ya tarar da su a falo. Suka gaisa Baban yana tambayar yasu Halimatu da dan-uwansa tunda amaren nasa sun yi masa nisa. Kan Gudale ya sake daure wa tabbas basu san bata nan ba, ba kuma ta gidan. Ya fice a gaggace babu ko sallama. Wajensa ya koma ya dauki mukullin mota. Ya nufi gidan Sakina. Yana ganinta a kicin ya shige cikin gidan yana ayyana ko ta karfin tsiya sai ta bar gidan. Ya gama dube dubensa bata nan. Ya hau tambayar su Nana ko Anti Halimatu tana ina?" Nana ta ce "Mun jima fa bamu ganta ba. Ya fice ba tare da ya cewa Sakina kanzil ba. Wasa-wasa an doshi sati biyu yana gararanbar nemanta. Har Abuja ya yi dirar mikiya a kokarinsa na gano ind take. Gidan Al'amin da Sakina ya je yafi sau cikin carbi. Haka gidan Abbas domin cousin dinta ce matarsa Azizan Umman Danladi Nasidi ce. Gidan Ashir ne a dangi kawai bai je ba. Wataran sai ya yi tamkar ya je, sai kuma ya fasa. A sati na uku ne da tura ta fara kai masa bango, ya je har gidan. Ashir da Farisa suka karbe shi cikin karamci. Jikinsa ya yi sanyi ganin yadda Ashir yake girmama Farisa ita kuma take masa biyayya kan jiki kan karfi. Ya tabbatar shi bai samar wa Guduyonsa irin wannan nutsuwar ba. Hankalinsa ya sake tashi ya tabbatar idan ta yi nasarar murkushe aurensa idan ta auri wani namijin da iya biyar da mace tsab zata manta da shi. Ga dai Ashir da ya karbi Farisa ba dan yana so ba ta wanke masa son kowacce mace a zuciyarsa. ** Hankalina a kwance nake zaune, domin kullum sai Yaya Al'amin ya zo ya duba ni safe da yamma. Sakina ce ba kullum ba, amma bata wuce kwanaki biyu. Sannan kullum sai mun yi waya da ita. Ba abin da ya dame ni. Sai tunanin mahaifana. Ko ya ya suke ciki a yanzu?. Kwanci tashi na kusa shafe kwanaki arba'in ba wanda yasan inda nake. *Gudale*. Zuwa wanann lokacin gaba'daya ya fita a hayyacinsa hatta uwarsa ta koma Jin tausayinsa duk da dai tana yawan ce masa "Yarinyar da ta biyo ka da wuka zata burma maka amma kake wannan tashin hankalin akan ta?" Da sauri ya ce "Duk wacce ta ce miki an ganta da wuka karya take yi miki". *Mama* Kanta ta kasa sukuni tun tana ganin cewar fishi Halimatu ta yi ta tafi inda zata samu sukunin zuciya, tunda tasan Baban Yara ba zai bata goyon bayan ta zauna a wajensu ba. Har ta fara sarewa. Gigitar da take ganin Sadik a ciki sai take ganin tamkar Umma ce ta kada mata yarinya uwa duniya. Hankula suka fara tashi. Kowa ya shiga damuwar rashin Halimatu. Yayin da Sakina da Al'amin suka yi kememe basu san inda take ba. Sau uku Gudale yana cewa Baban Yara ya matsa wa Sakina da Al'amin sun san inda take. Amma Baban bai dauki maganar serious ba. Cewa yake yi "Ba yadda za'a yi suyi hakan. Suma baka ga hankalinsu a tashe yake ba. Addu'a kawai zamu yi Àllah ya bayyana ta, Allah ya sa kada bacin ran da tafi da shi ya yi tasiri akan ta." Wannan maganar ta Baba ta hassala Gudale kwarai da gaske, ya zargi yabi bayan yarsa ne. Ban da haka yana kallon bala'in da ya shiga amma ya nuna masa ya zalunceta ne shiyasa ta barsu cikin bacin rai. Ya kwana yana nazarin hukuncin da zai dauka, domin ko sama da kasa zata ha'de ba zai rabu da ita ba. Sannan yanzu ya gano inda matsalar take. Sakina wa Al'amin sune a farko sai kuma samun daurin gindi a wajen Babansu. Ya girgiza kai a fili kuma ya ce "Zan yi maganinku gaba'daya". Sassafe dukkan sisters dinsa inka cire Antin Zaria da Sakina. A waya ya kira su ya fa'da musu Baban Yara ya ki tsawatarwa Al'amin da Sakina. Alhalin suna da saka hannu a batan matarsa Su taimake shi su yi masa kara su bashi gudunmawa kar su bar shi shi ka'dai. Ya sake rokansu su zo a hadu a gida ayi shawara. Ya riga kuma ya shata layi da Sakina banshi babu ita har a kiyama kuwa. Ai kuwa da yamma duk suka zo Kamar yadda ya so. Ya dinga ro'konsu su taya shi k'in gaida Baban Yara ko da na iya yau ne. Yasan hakan zai tayar masa da hankali sosai". Cikin sa'a kuwa sun fito sai ga Yayar Kwalli da Baban Yara sun fito da alamun damuwa a fuskokinsu. Duk suka risina suna fa'din "Yaya ina yini?" Kawai Ramla ce ta ce "Baba ina yini a gajar ce.. Hakan ya tayar da hakankalin Baba matu'ka da gaske. Yayin da Gudale ya yi fuska ko yayar ma bai gaishe ta ba. Yaya ta yiwa Juwairiya da'kuwa tana fa'din baku ga Babanku bane?" Suka dauke kai suna fa'din "Ya nuna mana banbanci ai. Ya nuna Halimatu ce mai uba, ya bar Sadik a maraya". Yaya ta yi kan Juwairiya da ke a hannunta ta girma. Yayin da Baba ya ce "Sadik zo mana ko kai ma ka gamsu baka da uban ne?" Fes ya ce "Kwarai kuwa domin ka nuna mini hubbul ra'as da ace Abba ne yake raye ba zai ta'ba nuna wa Halima banbanci ba, amma kai akan kununena ka nuna mini ita ce taka ina zaluntarta. Kiri kiri ka zuba ido ana mini wula'kanci ko ban ci arzikin komai ba, ai sai na ci na ubana da ya wanzar da rayuwarsa akan ka da iyalinka. Menene bai yi maka ba na gata? Shine yanzu zaka juya wa iyalinsa baya. Sai kawai ya fashe da kuka sosai. Yaya ta hauro ta ce "Ka ci uwarka Sadik!. Nan da nan ya ha'diye kukan ya ce "Daina zagin Umma" zagi Abba kawai". Ta dauki salati tana kuka tana cewa "Iyalin Alhaji ne suka saka mu a gaba haka da cin mutunci?" Ya kuwa zabura tamkar ya afa k'waya ya ce "Me zaki ce mini, me zaki fa'da mini Yaya? Kin riga kin nuna mini ke ido kike duba wa ba k'eya ba. Ban da hakan ina ce sadda Abba ya ri'ke mini Guduyo har kuka kika dinga yi da bai baki biko ba. Saboda yana da rai amma yanzu fa? Saboda ita Halima ubanta da ransa sai kika bi bayansu to ki je kwa hadu da Abba ranar k'iyama. Al'amin da bai jima da iso wa ba, shi da Yaya Abdallah ya yi kan Gudale yana cewa "Bari dai na sauke maka wannan tsagerancin na ka Sadik". 2/8/23, 10:25 - Buhainat: *Na ce ba kinsan wani hadi da ake yi wa asalin man ridi da kwakwa da ba'a samun original din su sai a wasu kebantaccun jahohi?* *kina fama da matsalar cinyewar gashi ko kuma rashin tsayinsa?*. *Kina neman ha'din da da zai sanya fatarki laushi da sulbi, kuma cikin saussaukan farashi? Tuntu'bi wannan lambar dan samun naki cikin sau'ki. Kaya mai inganci shi yake siyar da kansa.* *Sister Zainab 08039315577.* *Ina tallata muku Data mai rahusa.* *Ku tuntubi Marubuciya Aisha Dan Sabo lemu a wannan lambar* *08167768704* *SDK* *93&934* Kici kici suka fara kokawa tamkar suna cikin kuruciya. Duk kokarin Yaya Abdallah akan ya raba su abin ya ci tura. Domin dai Gudale ya zage dukkan k'arfinsa yana kai wa Al'amin naushi tabbacin jikakken tsumin bacin rai ya taso masa. Yayin da Al'amin din shima ya dage suna gwabzawa "Tare da cewa "akan idon iyayenmu zaka zage su?" Gudale kuma yana fa'din "sharrinka ya bika Aminu. A ina na zage su? Kuma da baku San inda take ba dukkanku da ban ganku a hakan ba, damuwarku ka'dan ce". Fa'da sosai kowa ya ji jiki. Sai da Abba ya daka tsawa Sannan Al'amin ya sake shi kowa na mayar da numfarfashi. Baba ya ce "Na gode maka Al'amin! Ina tsaye a waje zaka yi fada da dan-uwanka?". Kafin Al'amin ya magantu Gudale ya ce "Bai dauke ni dan-uwansa ba. Yar'uwarsa ya za'ba ya fifita a kaina. Duk kuma shiga sharo ba shanunka Wallahi sai ka kallemu ka barmu ni da Guduyo. In sha Allah ba zaku mutu ba, kai da Sakina sai kun kunyata, sai kun ga karshen shiga sha'anin aure." Yaya ta ce "Ba zaka yi shiru ba Sadik?" "Bar ni kawai Yaya na fa'di abin da yake zuciyata daga nan har gaban abada ba zan sassauta wa duk wanda ya nemi kassara mini zaman lafiyata ba. Ai ke ce babba amma kin kasa fa'da musu gaskiya, kin ki bada umarnin a fito mini da matata. Ubana mahaifi da ya rike mini Guduyo sai da na motsa kwanjina bare kuma wadannan azzaluman makirai. Ke da Baba kuma ko a lahira sai Abba ya ji irin juya mini bayan da kuka yi bayan ya shiga kushe wa." Ya zaro tissue a aljihunsa yana goge hawayen idonsa yana cewa "Allah ya jikan maza! Allahu ka karbi hidimar da Abba ya yiwa zumunci". Take Baban Yara shima ya fara hawaye, haka Yayar ma. Duk wajen sai kuka domin Abba ne kawai ya fado wa kowa. Yayin da Sadik yake cewa "Abba ka tafi ka bar ni na zama maraya. Ank'i yi mini kara, ank'i yi mini uzziri, ana shirin yanke mini zumunta da iyalina gaba'daya, an kwashe mini yarana, an dauke mini matata". Take Baban Yara ya cewa Abdallah ya ha'da masa dukkan ahalin gidan, har Antin Zaria bai dauke mata ba. Dake alhamis ne sai aka bar taron ranar asabar. Hatta Baban Gusau sai da ya zo a dalilin Gudale ana idar da sallar juma'a ya tafi ya durkushe gabansa yana hawayen Baban Yara ya zuba ido su Sakina suna wula'kanta masa aure. Baban Gusau ya bu'de masa wuta yana fa'din ai yasan komai shi ya cakalkala al'amuran aurensa da kansa. Tunda har yarinyar nan ta iya yin jarumtar barinka ka kure mata ne. Abin da kuma ba'a so namiji ya yi kenan. Da zarar aka kure ha'kurin mace to kuwa ba kasafai take sarrafuwa ta da'din rai ba. Gudale fa'di yake "Na yarda na yi kuskure Baba amma ka taimake ni kada ka zame mini baya, nan duniya bani da wanda ya fika, ka taya ni wannan fa'dan kowa ya juya mini baya." Fa'da Baban Gusau ta inda ya shiga bata nan yake shiga ba. Mussaman da ya fahimci idan ba'a tashi tsaye akan Gudale ba sai ya ha'da yakin basasa a family gaba'daya. Domin ya lura so yake ya jagoranci yan'uwansa su bijirewa Baban Yara, da Yayar Kwalli. Sanin da Gudale ya yi Baban Gusau mai zafi ne, mai kuma fed'e gaskiya ne ya sanya ya dinga hawaye yana cewa "Ka yi ha'kuri zan gyara komai. Na rantse da girman Ubangiji. Amma ka taimake ni ka bi bayana sun fi karfina. Abba ya yi ta fa'din kada a bar ni da kaina, kada a yanke mini zumunta. Ka saka baki a dawo mini da iyalina, yau fiye da wata biyu ana mini garkuwa da ita. Hatta y'ay'ana ma an kwashe mini su Baba. Ba kuma sharrin kowa bane illah Sakina da Al'amin. Baban Yara kuma ya basu dama, Yayar Kwalli kuma bata tsawatar ba. Duk an ha'de mini kai, kai ne kawai ka rage mini, dan Annabi Muhammadu Baba ka tsaya mini". Nan da nan zuciyar Baban ta karye ya ce "share hawayenka. Gobe da asuba zamu dauki hanya da ni za'a yi zaman da Ibrahim ya shirya. Amma ka mini al'kawarin ba zaka sake yi mata abin da ya tunzura ta ba, ka mini al'kawarin ba zaka kunya ta ni ba." Da sauri ya ce "Wallahi zaman lafiya zamu yi sosai, ai na ga aya na kuma fahimci ita ce duniyata". Kusan kowa ya halarci wannan zaman, in aka dauke Halimatu. Nasiha da jan hankalin Baban Yara ba karamin sanyaya jikinsu ta yi ba. Yayin da Yayar Kwalli da Baban Gusau suka yi shiru basu ce komai ba. Cikin muryar gargadi Baban Yara ya ce "Al'amin da Sakina". Suka amsa a hankali. Kai-tsaye ya ce "idan har kunsan inda Halimatu take to ku fito mini da y'ata domin duk cikinku babu wanda ya haifar mini ita. Idan kuma kuna da alaka da guduwarta kuka boye mini Ubangiji zan kai wa k'ararku ya bi mini kadin kukan da kuka sanya ni". Kan dole Sakina ta ce tana wajenta. Nan da nan Gudale ya ce "A to ai yanzu a yarda da maganata. Tsakanina da ku kuma sai a lahira". Baban Gusau ya daka masa tsawar da kowa sai da ya shiga taitatayinsa. Ya ce "Sakaran wofi idan ka kuma bu'de baki sai ranka ya baci. Ya kalli Maimuna ya ce "Ummu na fahimci ke ce kan gaba wajen wargaza mana zumunci, ki kiyayi kanki Wallahi! Ki rabu da son zuciya. Ace har ki zabi wata akan kanwarki diyaey Ibrahim? To Zan sassaba miki, zan wula'kanta ki Wallahi. Ta dinga kuka tana bada ha'kuri. Ya kalli Ramla ya ce "je ki kira mini iyayenku mata." Ba jima wa Mama ta iso, sai can kuma Umma ta iso cikin isar ita din matar wansa ce fa. Sosai Baban Gusau ya dinga yi musu nasiha, sannan ya ce "zaman lafiyar yaranku yana danfare ne da yadda kuka ha'da kanku kuke yi musu sassauci. Matu'kar babu soyayyarku da albarkarku a cikin lamarinsu to akwai mishkila." "Sakina Tashi yanzu ki dauko mini Halimatu". Baban Gusau ya fa'da cikin muryar umarni. Ba musu ta mi'ke yayin da Gudale ya yi k'wafa ya ce "oh wai ace kai da dan-uwanka babu jituwa? Bashi da burin da ya wuce ya samu damar da zai shatale ka?" Baban Gusau ya ce "Idan ka sake bu'de baki da nufin yiwa Sakina ko Al'amin rashin kunya sai na basu damar su cigaba da ajiyeta tunda baka ganin mutuncinsu". Nan da nan ya ce "Na yi shiru Baba". Takaicin duniya ya rufar wa Umma wai Gudalenta ne ya susuce ya hargitse akan Halimatu. Ta sani tun lokacin da Abbansa ya ri'ke masa ita, ta fahimci irin yadda yarinyar ta yi matu'kar yin tasiri a rayuwar danta. Mussaman da ya tafi siyar da k'odarsa. A yanzu kuma da wannan lamarin ya faru ta sake fahimtar idan babu Halima a tare da shi ba zai ta'ba zama mutum mai nutsuwa ba. Dan hakan ta ha'kura da kokarin kashe masa aure, amma dai ita bata sonta, zai yi wahalar gaske kuma ta so ta. Amma zata yi iyakacin kokarinta ta daina yin dalilin samun rikici a tsakaninsu. Sannan zata so ya k'ara aure nan ma ta kudire ba zata sake nemo masa da kanta ba. Kawai bata son ace Halima da y'ay'anta ne suke da alaka da dinbin dukiyarsa kawai. Domin dai ya tabbata Safiyya ce dai ta ci galaba akanta. Jikokinta ne magadan Gudale. ** Ina kwnace akan katifata sai ganin Sakina na yi, a hargitse tana cewa "Taso Halimatu! Baban Gusau ne ya bani umarnin na kai ki yanzu yanzu." "Ina jin haka na fashe da kuka sosai ina cewa "Ai kin ce sai na yi watanni shida kafin asan I da nake. Sannan sai ina so zan koma, idan bana so ba, zaki tsaya mini. Dama tun jiya da kike ta cewa Namoriki ya gigice, ya fita a hayyacinsa nasan akwai abin da zai biyo baya". Ta ce "Kin ga tashi mu tafi, ai damar a hannunki take. Sannan ki bu'de baki ki fa'di komai kike ciki da shi a gaban Baban Gusau. Kuma zan fa'da miki wata magana guda daya tak. Kada ki yarda har sai ya shawo kan mahaifiyarsa ta amince da ke a matsayin surukarta, domin ita din k'ashin baya ce a zamanku". Na sake fashe wa da kuka domin dai na riga na gane rashin Gudale a kusa da ni shine kwanciyar hankalina. Wadannan satittikan dana kwashe babu shi, babu jidalinsa sune kwanaki mafi da'di a gare ni tunda na kammala sakandire. Ba wanda yasan inda nake, ko mahaifiyarmu sai da Yaya Al'amin ya ga irin damuwar da take ciki ne, ya fa'da mata ina karkashin kulawarsa. Amma ta cigaba da nuna wa bata sani ba. Kan dole Sakina ta tisa ni a gaba ina rusa mata kuka tamkar wanda ta bubbuge ni. Ta tunzoro ta ce "Ki mini shiru Halimatu." Kuka nake bilhakki Ina cewa "Ba dan kin so na koma ba, ai da ba zaki fa'di inda nake ba Maman Nana". A kufule ta ce "Fiye da wata biyun nan da kika yi ashe baki gode mini ba? Kinsan hardship din dana tsallake saboda ke kuwa? To Umma saura kiris ta yi mini baki a dalilin Autanta ya fa'da mata nice barazana a rayuwarsa, yanzu haka bata karbar gaisuwata, Baban Gusau ne ya matsa mini sai na kawo ki, bayan Baban Yara ya ce ko mu fito da ke ko shima ya kai kararmu wajen mahaliccinmu. Shin ya ya kike son na yi ne?" Kuka ya sake goce mini domin ba karamin tashin hankali na tsinci kaina a ciki ba. Har cikin zuciyata na tsani Gudale, na na tsani ko zaman mota mu sake yi. Haka muka shiga gidan ina rusa kuka tamkar wanda aka sanar da ni mutuwar Mama. Muna isa falon da ake zaman. Gudale ya wani zabura ya yo wajena yana fa'din "Bana son kukan nan kin sani. Share idonki mu yi tafiyarmu gidanmu ki fa'da mini duk abubuwan da ba kya so daga gareni In sha Allah zan kiyaye". Ina kallon yadda Umma ta yi kicin kicin. Yayin da Baban Gusau ya ce "Sadik idan na sake magana Zanci mutuncinka. Wanne irin yaro ne kai haka da baka san kunya da kawaici ba?" Nan da nan ya kame bakinsa ya dinga cewa "Yi ha'kuri Baba! Kada ka yi fishi dan Annabi Musa". Baban Gusau ya ce "Dan wa ka ce Sadik?" Da sauri Gudale ya ce "Ina son na tuno maka irin girma da karamar Wanda ka ci sunansa ne. Abba ya ta'ba bani labarin Mahaifinku ya saka maka sunan ne saboda Girmama Annabi Musa (A.S). Allah ya k'ara maka lafiya da karama Baban Gusau. Gaba'daya Baban Gusau ya kasa cewa komai domin duk zafinsa sai da Gudale ya nemi birkita shi. Nasiha irin wacce Abba ya wanzu yana yi mana ita Baban Gusau ya dinga yi har kowa jikinsa ya yi sanyi wasun ma har da k'walla. Yayar Kwalli cikin kuka ta fa'di wula'kanta Baban Yara da Maimuna ta jagoranci kanneta da suka yi. Baban Gusau ya dauki salati ya dinga zaginta irin wanda bata taba zaton zai yi mata irinsa ba. Ya ce "Maimuna saurara na fahimci ce kece kike neman fita zakka, ke ce kike son ruguza dukkan ginin da Ubanku ya shafe lokacinsa yana ginawa. Wallahi hakkin Ibrahim zai iya damalmala miki lamarinki, ba irin biyayyar da bai yiwa Ubanku ba. Kun sani kuma ba haihuwarsa ya yi ba. Zamu saka kafar wando da ke, domin har yau din nan baki wuce hukuncina ba, shasha marar tunani. Haka ma Juwairiya ma ya wanketa, ya sanya suka tsuguunna har kasa suka bawa mahaifinmu ha'kuri. Ramla ce da ita a kullum take tsakiya, bata bayanmu, bata kuma bayam uwarta, a tsakiya take. Gudale har da ri'ke kafar Babanmu yana fa'din "Abba ya ce "Biyayya biyu zan yi maka. Ka dubi Àllah da manzonsa ka yafe mini. Har Gusau na je na dauko maka dan-uwanka dan ya baka ha'kuri. Ka daina zuba wa rikicina da su Al'amin ido. Sun riga sun ha'de mini kai Baba. Kamata ya yi kai ka ha'da kai da ni." Baban Gusau ya ce "Sadik rufe bakinka ko yanzun na saka Ashir ya lallasa mini kai. Soko kawai. Kullum kalaminka daya babu sauyi?" Ba'kin ciki ya turnike Gudale a gaban Ashiru za'a yi masa irin wannan yankar kaunar? Ya kalle ni ya ce "Yi hakuri Sadiya kin ji. Goge Idonki ki fa'da mini matsalarki, me yasa kika manta nine ubanki?" Ina kuka sosai na ce "Ba manta wa na yi ba, na ji tsoron kada ya zo gabanka ya lauya zance, ya kuma sanyaya maka jiki ta hanyar cewa shi maraya ne". Baban Gusau ya ce "Ai ni bai isa ya mini irin wannan iyashegen ba." Nan da nan Gudale ya ce "Ina neman alfarma Baba! Ka sallami kowa a bar mu da kai. Ina jin tsoron magauta su ji sirrin gidana, a mini wannan alfarmar darajar Manzon Allah (S.A.W). Baba ya mike ya ce "Mu biyo shi zuwa bukkar waje, su kuma su jiramu bai kammala ba. Ban ji nauyi ba, kaina na kasa na fayyace komai har wula'kancin da yake yi mini a falo, da kuma zagi da duka a gaban y'ay'ana. Baya ga haka tarbiyar da yake son yiwa Aman da ware shi da yake yana fifita shi. Da kuma matsalar Umma, da su Anti Maimuna ta yadda suka fifita bare a kaina, kuma duk yana kallo bai ta'ba taka burki ba. Baban Gusau ya dinga jinjina girman iskancin Gudale. Fa'da da yarfe ba irin wanda bai masa ba. Karshen karshe sai ya buge da bani ha'kuri, da falalar mai yafiya mussaman idan yana da ikon ramako, amma ya ha'kura ya mance komai. Ya kausasa murya ya ce "Sadik! Wallahi ka ji na rantse ko? Duk ranar da sake yi mata tozarcin nan a falo da kaina zan jagoranci raba aurenku. Balle kuma duka ko zagi, ka tabbatar ka daki aurenka". Baki na rawa ya ce "Na ji Baba! Zan kiyaye, ba zan sake ba". "To kin ji Ssdiya, nine alkalinki komai ya taso kar ki sake ki yin shiru, idan kuma ya cigaba da yin wannan dabi'ar ki bugo waya ki sanar da ni, amma yanzu na kashe wannan maganar, kibi mijinki ku koma gida a cigaba da ha'kurin zaman, amma ban da na cuta. Ba kunya na ce "Baba yi mini afuwa! Amma shawara kake bani na koma dakina ko kuwa umarni ne?" Ya kuwa ce "Shawara ce Sadiya!". Ba jin nauyi na ce "A sake yi mini afuwa, a gafarce ni Baba. Idan shawara ce ka yi ha'kuri ban karba ba Baba. Domin wacce duk kuka kuna bani ina bi da dukkan zuciyata amma bata yi tasiri a wajen wannan Dan halikin ba. Amma idan umarnine to zan yi maka biyayya da dukkan iyawata". Baba ya ce "Kalu Innalillahi wa inna ilaihir Rajiun". Wajen ya dauki shiru tsawon lokaci. Gudale ne ya fara gazawa da shirun ya ce "Dan Allah Baba ka yi wani abin. Kar ka bar ni da kaina. Na gamsu duk abin da ta fa'da ina yi, sai dai wani lokacin ita take tsokanata. Amma na yi al'kawarin ba zan sake ba, idan kuma na sake duk matakin da zaku dauka ba zan yi kuka da kowa ba sai da kaina. A mini ha'kuri ba dan halina ba". A sanyaye Baba ya ce "kin ji Sadiya". Na fara kuka mai tsananin gaske, na kasa bu'de baki na ce komai. Kukan da ya gigita su mussaman Gudale. Domin ya sani kuka ne na ba'kin ciki da kaico, ya kuma hango tawayar da soyayyarsa ta yi a zuciyata. Murya na rawa ya ke cewa "Allah ya baki hakuri. Dan son ki da Annabi ki sake yi mini uzziri ko da shine uzzirin karshe." Baba ya numfasa ya ce "Ki yi ha'kuri kin ji." Gudale a gigice ya ce "kin ji ya sake baki ha'kuri, komai kike so zan yi miki, na daina yi miki duk abin da zai sa ki yi ba'kin ciki da gangan". Tsawon lokaci ana ta turzawa amma na kafe ni dai na gaji da zaman. A karshen dai Baban Gusau ya yi ta maza ya ce "Ya bani umarnin na koma dakina. Na fashe da kuka na ce "Baba duk abin da yake so hakan za'a yi masa kenan? Na rantse maka ina koma wa zai cigaba da cin zarafina". Baki na rawa ya ce "Guduyo na ga aya ai. Wallahi Tallahi ba zan yi ba. Ai dai ga Babanmu nan shine alkalinki, shine shaidarki, kuma duk abin da ya shimfi'da mana akansa zamu zauna, ki yi ha'kuri kin ji Guddin Abba". Ya zarce da cewa "Tunda aka dauke ki har yau din nan na rantse miki da girman Ubangiji ban sake samun nutsuwa ba, an dauke mini su Amnah, kema bakya kusa ban fahimci kune duniyata ba sai yanzu. Baba ka zama shaida kome take so matu'kar bai karya ka'ida ba, zan yi mata, hakanan zan yi iyakacin kokarina na kiyaye cin mutuncinta ta kowacce fuska. Amma kuma ban yi al'kawarin ba zan bata mata rai ba, ban yi al'kawarin ba zamu samu sabani ba, amma na yi al'kawarin zan yi kokarin kiyaye hukunci cikin fishi. Zan kuma yi kokarin yi mata sassauci a sadda ta kuskure mini." Baba ya saki nannauyar ajiyar zuciya ya sake cewa kin ji ko Sadiya. Da ni ya kafawa kansa hujja". Hawaye ya goce mini na ce "Tunda ka bani umarnin komawa shikenan amma ba yanzu ba Baba. Ka tafi da ni Gusau nan da wata biyu ya turo Umma ta yi masa bikona a hannunka da sharadin tana son zamana da shi. Sannan yadda yake tisa ni a gaba na bata ha'kuri ko da ban yi mata laifi ba. To wajibi nima sai ya bada ha'kurin zagin da yake yiwa tawa uwar". Da sauri Gudale ya tsugunna guiwa bibbyu ya ce "Na janye, bacin rai ne, da sharrin zuciya. Mama uwa ce a wajena, aurena da ke kuma ya sake girmama lamarinta a idona. Ban ta'ba yi mata kallon raini ba, ko dan wannan mu bar maganar nan a tsakaninmu. Bata sani ba, ba a gabanta na zageta ba, da wanne idon kike son na je gabanta na tsugunna na ce ta yafe mini na zageta? Kada ki zubar da k'imar uban yayanki a idonta, ke zaki iya mantawa amma har abada ita ba zata manta ba. Ki yi ha'kuri." Baba ya ce "Tunda ke da shi kuka yi, ya ajiye dukkan girman kai ya durkushe a gabanki, to ki karbi tubansa". Na yi shiru tabbacin na yarda. Yana durkushen ya ce "Baba a sake mini lamini, wata biyu ya mini yawa Billahillazi ba zan iya ba, kema kin sani. Ba dan Abba ya ja kunnena kada na ajiye aikina ba. Da sai na ajiye na biki Gusau din. A yanzu hakan adalcin shugabannin ne ya saka ba'a kore ni ba. Tun batan ki bana iya yin komai. Ki ji tausayina Guduyo". Ana kuma Baba yaki tankawa. Amma akan tilas sai da Gudale ya sanya ya ro'ke ni na rage masa Tsananin nacin da ya sanya Baba a gaba ya sanya ya ce "Tunda na kafe, to ya barni na yi wata a wajensa na sake hucewa. Kuma tabbas ba zai bawa kowa ni ba sai mahaifiyarsa kamar yadda na bu'kata." Wannan hukuncin ya yiwa Gudale tsauri matu'ka gaya. Amma Baba ya ce "sai anyi hakan.". Mu koma falo aka cigaba da nasiha da ban ha'kuri. Gudale ya bawa Baba ha'kuri, tare da Yayar Kwalli. Washagari kuwa Baban Gusau ya tafi da ni bisa rakiyar Yaya Abbas. Ai sai Yaya Gudale ya mayar da Gusau tamkar unguwa. Ko tunanin aikinsa ba ya yi. Duk weekend acan zai yi duk kuwa da ba kulashi nake yi ba. Umma ta shiga tashin hankalin ganin Gudalenta a cikin tashin hankali gaba'daya ya birkice bashi da lokacin zama da ita. Iyakacinsa da ita ya leka a gurguje ya gaisheta. Kullum yana tafe a titi. Hatta Aman idan ya shigo baya bi takansa, wani lokacin yana kuka amma zai wuce ya bar shi. Kuka saosai Umma take yi tana gasgata an haukata mata Gudale ta yadda idan babu Halimatu a tare da shi ba zai amfani kansa ba, bare waninsa ya amfane shi. Hatta a wajen aikinsa an bashi quairy. Amma bai shiga taitatayinsa ba. Satina uku Baban Gusau ya tausaya masa kwarai da gaske, ya nemi na yi masa afuwa idonsa cike da k'walla akan na yarda na koma dakina hakanan dan Allah. Bashi Zan duba ba, na duba Allah na duba ubansa". Jikina ya yi sanyi na ce "Na ha'kura zan koma, amma ba dan na huce ba". Domin ni kaina mamakin kaina nake yi, na yadda aka cire mini ko da son ganin Gudale bare na zauna da shi. A ranar Baba ya tabbatar masa ko gobe Umma ta zo zata taho masa da ni. Jiki na rawa yake godiya. *Umma* "Dan Allah Umma, ki ji tausayina mana" Gudale ya fa'da idonsa cike taf da k'walla. Ta kufula ta ce "Duk wannan susucewar da ka yi ba zai sanya na tashi na tafi uwa duniya dan na dauko maka irin tsiya ba. Ashe duk iskancin da nake ganin a tare da yarinyar nan ka'dan ne? Ni zata yiwa hakan? Waton sai na kada billena zata zauna da kai, to dan kan uwarta kar ta zauna da kai, ina ce "kanta ta yiwa asara" Akan Guduyo! Gudale babu jarumta sai kawai ya fashe mata da kuka riris yana cewa "Allah a turo mini mala'ika Azara'ilu ya tafi da ni, dan darajar Annabinka. Uwata da matata sun ki yi mini uzziri. Zuciyata na ciwo, tunanina yana rikecewa, idona na zafi, yunwa tana neman kassara ni. Ubangiji a yanke mini wannan ukubar haka nan. Allah na tuba. Wayyo Mala'ika Azara'ilu ka zo ka kaini wajen Abbbana". Tsoro ya yi matu'kar kama Umma ganin yadda yake birgima a dakinta. Tausayi da rauni irin na uwa ya shigeta. Ta fashe da kuka ta ce "Allah ka yi wannan shari'ar da kanka. Wula'kanta da ake yi, ake bina da alkaba'i Ubangiji ka tausaya mini, ka shiga cikin al'amarin. Tashi ka daina wannan addu'ar, Gobe Direba ya kaimu tunda ka zabi wata a kaina, rashin Halimatu ne zai sanya ka nemi mutuwa ka bar ni. Na gode maka" Ya sake kece mata da kuka. Yana fa'din "Ba hakan bane Umma! Ki fahimce ni, bana ha'da ki da kowa Wallahi. Amma Guduyo a kusa da ni shine kwanciyar hankalina. Ki ji tausayina" Ta yi kwafa ta ce "Ai shikenan tana mika masa Aman tare da cewa "Karbe shi ya ji duminka kun taru kun mayar da shi maraya, me za'a yi da azzalumar yarinya irin Halimatu. Safiyya mai fa'da da ke ya ci riba ba dai mutum ba, sai bakaken aljanu. In Sha Allah sai kin tsokano fadan da za'a kai ki kasa tunda ni kin gama da Ni". Akan dole ta bi shi zuwa Gusau. Tun a mota yake ta ro'konta Allah da maaiki, ta yi magana mai nuna biko zata yi masa a gaban Baban Gusau. Ta taimaka ta samar masa kwanciyar hankali. Ta numfasa ta ce "Ban da dai an ga bamu da Abba ta yaya iyayenka zasu kasa yi maka biko sai ni uwa?" Ta goce da kuka tana fa'din "Baka share mini kukana ba Gudale. Duk gatan da nake yi maka,baka huce mini takaicin duniya ba tunda kake son jinin Safiyya har hakan. Makiyana kake so, sune farin cikinka. Wannan na cikin babbar jarawabata. Da ana mutuwa a dawo da Alhaji ya yi kallon yadda yan'uwansa suka bar ni da kai. Kuma da a gaban mahaifinta take Wallahi da sai dai ka ha'diye zuciya ka mutu da ba zan je ba, tunda su din butulu ne masu manta alkhairai.". Ha'kuri kan ha'kuri yake bata. ** Da hantsi suka iso. Sun jima ita da Baba a falo. Sannan aka kira ni. Na gaisheta ta amsa ba yabo ba fallasa. Baba ya sake bani ha'kuri, Yana ta fa'din na cigaba da ha'kuri, sannan wancan sharudan akansu zamu zauna, mu mutunta junanmu. Umma ta numfasa ta ce "Allah ya kiyaye gaba". Muka kamo hanya har muka iso Kano ba um ba um um a tsakaninmu. Da la'asar muka iso, maimakon ta raka ni k'ofarmu sai kawai ta yi shigewarta wajenta. Nima kuwa na bita, ina ayyana matu'kar bata raka ni da kanta ba, to kuwa bata shirya zamana da d'anta ba. Haka har dare ina dakina na wajenta. Gudale ya zo yafi sau a kirga ko kallonsa bana yi. Zuwan da ya yi da daddare Wanda a kiyasi zai yi daidai da shigowarsa dakin sau goma. A sanyaye matu'ka da gaske ya ce "Me kike nufi ne Guduyo? Ki yiwa Allah ki zo mu tafi gidanmu. Komai zaki yi mini, na fi son na ganki a dakinki, ki mini alfarmar hakan". Rai a bace na ce "Tunda na biyoka ai na yi maka sassauci. Amma na rantse ba zan bika ba. Ba kai ne zaka mayar da ni ba". Ya fita da sauri, sai gashi da Antin Zaria da ke tana hutun shekara. Har da su Amna ta zo sai dai suna gidan Anti Maimuna. Fadi yake bata ha'kuri Anti! Ki raka mini ita". Ta ru'ko ni jikinta tana cewa "Ya aka yi ne autarmu?" Ina hawaye na ce "Ni Umma ce zata raka ni". Ta mike tana fa'din "Je ka fa'dawa Mamanka abu mai sau'ki kenan. A gigice ya ce "Bata da lafiya fa Anti! Shin ba ke ce second Mum dina ba. Me yasa ba zaki dinga taimkona ba?" Ya fice a har gitse. Sassafe sai gashi da Yaya Abdallah. Akan ya ro'ke ni ya mayar da ni. Gaba'daya ya birkice ni sai nake ganin ya jima ko wanaka bai yi ba. Ya yi zuru zuru tabbacin baya cin abinci da gaske. Duk wani gayu da kwalisar nan babu. Gaba'daya babu jituwa tsakaninsa da Umma. Fishi take yi masa, ta hanyar yi masa zuru. Sai a lokacin na gane hatta Aman din da ya makalashi a ransa bashi da lokacinsa. Idan ya shigo dakin da nake, ya dinga cewa "So nake ki koma dakinki na dauko miki su Afrah ki ga yadda suka girma, suka koma tamakar y'ay'an larabawa." Uffan bana ce masa. Ya rasa yadda zai yi. Yayin da Umma ta ja ta kafe, tunda ta je har Gusau ta kada billenta to daga haka ba inda zata kuma zuwa. Ya fara wani irin zazzabin tashin hankali. Rannan sai ji na yi Umma tana waya da Sakina tana fa'din "sun zuba mini ido ita da yayarsu Antin Zaria kenan zan kassara mata zuciyar Gudale. Indai ita din uwarta ce ta zo ta mayar da ni ta huta da wannan jarabar tunda ita ce uwar dakina, kuma kanwa uwar gami. Ta k'are da fa'din "Wallahi Sakina ki yi kokari ki rabu da ni lafiya". Ban ji me take cewa ba ita Anti Sakinan. Ai kuwa tana dawowa daga aiki sai ganinta na yi. Tana shigowa dakina ta d'aure fuska tamkar bata ta'ba dariya ba. Ta ce "Tashi na mayar da ke, idan kin so ki cigaba da ri'ke mutuncin da aka taru aka nema miki, idan kuma kin ki kije ya kallalame ki, ki koma Yar gidan jiya. Kiyi masa biyayya, ki kyautata masa, amma kada ki yarda da cin mutunci ko da na magana ne bare zagi ko duka". Na fashe da kuka ina cewa "Kada ki mayar da ni." Nan da nan ta rantse da cewa "Yau kam indai na isa a dakinki zaki kwana, abin da zai biya baya kuma, na kara nemar wa kanki Karin daraja yana hannunki, ai ke ba yarinya ba ce." Haka ta tisa ni a gaba, ina kuka har cikin dakina. Tsabar yadda na tsani koma wa Gudale ya sanya na ji a zuciyata Sakina son kai ta nuna. Alhalin itama uwarsu ta matsa mata. Inda muka tarar da shi a falon, yana ganinmu da Sakina. Ya mike da kyar yana cewa "Na huce da Sakina. Na yafe miki." Ta ja tsaki ta ce "Dan Allah kada ka yafe mini. Ban da Umma ta roke ni arzikin na rako maka ita, kai ka isa ma ka ga k'afata a gidanka?" Ya kasa yin shiru ya ce "Tunda kin rakota ai magana ta kare. Yadda kike shiga al'amarin gidana ki hana ruwa gudu, na kai wannan k'arar gaban Mahaliccinmu. Amma ki sani idan wannan jinyar da nake yi, ta zama ajalina ke ce silah Sakina. Allah ne shaidar yadda nake tsananin son ki. ke kuma fir kin bantse mini, kin k'i ni, kin tattara kin watsar da ni. Ya karyar da murya ya ce "Ke da Abba wallahi! Ai ya ce kada a yanke mini zumunta". Ga mamakina sai na ga jikinta ya mutu murus. Ta kasa ce masa komai. Ta fita tana cewa "Allah ya sauwake ya tashi kafadunka." Duk nacinsa ya kasa samun hadin kaina. Ba irin da'din bakin da bai mini ba, amma ban saurareshi ba. Duk yadda ban kula shi ba,sia da ya samu sau'kin jikinsa tabbacin zulumi yafi yawa a jinyar. Washagari ya tarar da ni a dakina, ina ganinsa na fito na bar masa dakin. A sanyaye ya biyo ni harabar falon. *Assalamu alaikum*. *makaranta littafin Sabo da kaza barkanmu da yini.* *Ina Yaba muku, Ina kuma gode muku Ubangiji ya fini yabawa.* *Ina son ku koma ku karanta shimfi'dar labarin shafin farko kenan, daga nan sai ku karanta 19&20.* *Sai Kuma ku karanta 41&42 da Kuma 43&44.* *Sannan Ina jiran Jin ra'ayin ku ta yadda zan gina karshen duk kuwa da ba zan mika alkalamin a hannunku gaba'daya ba. Domin ina rubutu ne akan abin da yake faruwa ba wai abin da muke son ya faru ba.* *Zan dakata har zuwa sanda zan k'irga yawan ra'ayinku, dan nasan ta yadda zan bullo wa al'amarin*. *Ina cikin hidima mai yawa kanina dan-uwana zai yi aure a Wannan satin, ina neman addu'arku*. *Na gode sosai* *Surayya Dee ✍️* 2/8/23, 10:25 - Buhainat: *Shin kina bibiyar Faseelat kuwa?*. *Shin kina gyara kanki kuwa?* *Faseelat ta kware wajen zaba miki supplement din da zai dace da jikin ki* *Hakan ya sanya ta samu lambar yabo daga G.H.T*. *Tuntu'beta 0703929802* *Gudale dai ya ce zaki rabauta a sanadinta* *Fatana alheri ga* *Aliyu Dahiru (Abba)* *Da* *Safiyya Ahamad Sani* *(Malama)* *Allah ya sanya albarka a rayuwar aurenku*. *Ina godiya ga dukkan wadanda suka kira ni a waya/WhatsApp suka mini murnar auren kanina, da tambayar jikina.* *Na gode sosai Ubangiji ya saka muku da alheri* *SDK* *95&96* Ana kiran sallar azahar ina sauke doguwar ajiyar zuciya, saboda kammala hakaito badakalar da na shiga. Kafin na yi yun'kurin tashi. Ya fito cikin shirin fita masallaci ko kallon inda nake bai yi ba. Na bishi da kallon yadda yake ha'da ha'da hanya. Na idar da sallah Kenan na shiga kicin da nufin d'ora girki, ko su Afrah zasu shigo mini. Ina kicin din ya dawo. Murya kasa kasa na ji yana kirana. Na wanke hannuna na fito bayan na amsa. Ya kalle ni ya ce "Tunda kin kwashe kayanki a gaban ma'aikin Allah. Dauko mayafinki muje gaban Baban Yara. Ai na ro'ke shi ya baki ha'kuri. Tunda bai ro'ke ki ba, muje ya ro'ke ki a gabana. Na gaji, ina nufin koluluwar gajiya na yi Guduyo. Ina jiye miki tsoron kada ha'kurin da nake ta yi dan ki huce ya kwace mini." Na ja k'aramin tsaki na ce "Ya jima bai 'kwace ba". Ya girgiza kai ya ce "zo ki shige mu je". Yana rufe baki na ce "Wallahi ba inda zan je. Ai ni Baban Gusau ne babana". Nan da nan fishinsa ya sauka ya ce "Ma sha Allah! Tunda sarkin adalci ne Babanki maganar ta kare. Domin kuwa a gabanki zan kira na fa'da masa tsiyar da kike shuka mini duk da irin ha'kurin da ya yi ta baki." Na gallah masa harara na ce "Kai ko kunya baka ji, motsi ka'dan sai ka kai k'ara?" Ina rufe baki ya ce "To ya zan yi ne Guduyo? Ai tunda kika ha'da kai da Sakina na sani sai an mayar da ni tamkar yaron tumari. Me za'a yi da wuyar zama irin na Sakina? Gaba'daya babu tausayi bare imani a sha'aninta, na rantse bata siffantu da aikin jinya ba, tunda aiki ne na masu taushin zuciya da imani. Babu abin da ya kamace ta irin jami'ar tsaro, ta yadda halinta na ba sani ba sabo zai yi tasiri." Na bata rai na ce "lallai baka canja ba, ba kuma zaka canja ba, tunda kake yiwa Maman Nana irin wannan wula'kancin akan idona. Idan da gaske kana sona, ka kuma shirya daina cin mutuncina ai dole kuwa ka girmama dukkan ahalina. Sakina ai surukarka ce tunda kake aurena". Ya kame baki yana cewa "Subutul kalam ne. Ai kirkin Sakina yawa ne da shi. Ita ta dawo mini da ke, madallah da ita." Ganin da ya yi na biye shi muna magana sai ya bijiro da maganar da ta dame shi. Ya sassauta murya ya ce "Guduyo kina lissafin adadin watannin da na yi ni ka'dai kuwa? Wai ke ba kya kewata ne?" Na bata rai na ce "Bana yi! Har menene abu mai da'di a tare da kai da zan yi kewarsa?" Maganar ta yi matu'kar dukan zuciyarsa. Har hakan ya bayyana akan fuskarsa. Ya yi karfin halin cewa "Bani da abin arziki ko ka'dan a wajen ki ko?" Nan da nan na ce "Na tsiyar yafi yawa, ya kuma fi tsananta. Ka riga ka yiwa kanka illah a zuciyata". Ya juya ya tafi yana kunkunin shi ba zai yarda ya zama sauna a gidansa ba. Domin shi da Yunus din Sakina ba d'aya bane. Na bishi da ido ina tabbatar wa kaina akwai abubuwan da dole sai dai na yi ha'kuri amma ba zai ta'ba barinsu ba, barin zance da son girma na kan gaba. Na shirya abinci. Na leka na ce "Na gama abinci, na ajiye maka maganinka, sannan akwai supplement na GHT da Anti Sakina ta aiko maka na ulcer ne. Kamar ba zai amsa ba sai ya ce "Kin ji da'dinki Guddi. Ace wai har yau da kika shafe shekaru a dakin aure baki fahimci cewar a ko ina nake zan iya samun abinci ba? Baki fahimci kuma cewar duk abin da zan ci matu'kar bani da nutsuwa a zuciyata ba zai yi tasiri ba?" Na yi sakare ina kallonsa. Na nisa na ce "Jiyan nan na ji kana fa'dawa Sakina akan ta sani na dinga yi maka girki. Na yi din amma ban yi gwaninta ba?" Ya ta'be baki ya ce "Da hira kika zo mini dakin nan da nafi yaba miki, da na fi gode wa." Na fito Ina fa'din "Maman Nana dai ta ce kada ayi wasa da supplement din nan idan aka sha akan ka'ida za'a rabu da ulcer in sha Allah. Madallah da Faseelat 07039269802, da kayanta na GHT. Domin sau'kin kayanta da ingancinsu ne k'ashin bayan rubibinsu da ake yi. Ni kaina har murmushi na yi a dalilin har da nawa supplement din Sakina ta hado mini a wajen Faseelat. Ga kuma femwash na oriflame a wajen Aisha lame 07036662633. Da sauran kayan gyara na mussaman. Na yi tsam ina nazarin irin soyayyar da Sakina take yi mana ni da Gudale. Komai ta yi amfani da shi na gyaran jiki, sai ta siya mini ko sai ta saka na yi. A zahiri ni take gyarawa. A bad'ini kuma k'aninta take yiwa tanadin hutu da nutsuwa. Amma shi da yake kullum a karkace yake sai ya fi karkata a so take yi ta mayar da shi lusarin namiji a gidansa. Komai Zan yi masa matu'kar bai yi dai-dai da ra'ayinsa ba sai ya ce Sakina is behind everything am doing. Ya fito da kyar yana tafiya ya zauna a wajen cin abincin, ya kalle ni ya ce "Zuba wa miji abinci bauta ne, ko rashin yanci ne shima? Me zai hana kina ganin na fito ki zo ki yi serving dina? Allah dai ya yafe miki Guduyo". Ko kula shi ban yi ba, a dalilin na fahimci so yake ya shiriritar da fishin nawa. Bayan bai bani mukullin motar ba, bare ya siya mini bangle din gold din da kuma fita wajen da ya yi kirarin zai yi Kai ni. So nake kawai ya dauke ni mu barwa Umma gidan na dan wanai lokaci. "Ki shirya yanzu ki je gidan Sakina. Anjima zan zo." Na ce "To ba dan na fahimce shi ba, sai dan bana son doguwar magana a tsakaninmu sannan dama ina son zuwa gidanta. Ina gidan Sakina ta dawo daga aiki. Ba jima wa sai ga wayarsa yana cemin ya iso. Na ce "Ba zaka shigo bane?" Da sauri ya ce "Daga zuwan farko sai kawai na shigo gidan mutane?" Kaina ya daure. Na kasa cewa komai, fahimtar da ya yi ban fahimci manufarsa ba. Sai ya ce "Ki yi ha'kuri na zo ban sanar miki ba. Na kagu na zo na ji muryarki mai rikita kwanyar mai sauraronta". Na kashe wayar ina cewa "Ashe zance ka zo". Sakina da take zaune kusa da ni. Ta ce "daukar ki ya zo yi?" Na girgiza kai tare da cewa "Zance ya zo wai". Ta kyal-kyale da dariya tana cewa "Allah ka shirya mini autan Umma. Sai ki shigo da shi falon Baban Nana". Hakan kuwa ya shigo cikin kwalliya ta sosai, na kalle shi Ina ganin tamkar saurayin ne na gaske. Domin bashi da wani girma, mafi yawa gani ake Amnah kanwarsa ce tunda tsayi ne da ita. Na koma wajen Sakina tamkar zan dauko masa wani abu. Ya jima yana zaune yayin da ni kuma na biye Sakina muna dariyarsa. Mintina goma sha biyar sai ga kiransa ya sake shigowa wayata. Na dauka ya ce "Ranki ya da'de ina ta jiran ki, bani da jarumta akan al'amarinki fa." Na kashe wayar na fita. Na same shi ya harde kafa daya kan daya yana kallon talabijin. Na zauna nesa da shi sosai. Na gaishe shi da kyar. Shi kuma ya amsa da sakakkiyar fuska. Ya kaikaice zama ya ce "Kasaitar Ubangiji yawa ne da ita Guduyo. Kullum na zauna sai na yi ta lalubo dalilin da ya saka nake ganin girman gidanmu idan ba kya cikinsa. Bana fahimtar rashin kowa a gidan, amma ke ko zarce lokacin dawowa daga B.U.K. Kika yi sai na ji damuwa mai yawa. Ashe kin shiga zuciyata kin yi kane kane. Wani irin so nake yi miki mai wuyar samuwa ko a duniyar littafan tatsuniya". Na ta'be baki tabbacin ban gamsu ba. Ya mak'e kafa'da ya ce "kin san am always positive. Ba sai kin gasgata ni ba, domin ni na gamsu ke ce duniyata. Ina tashi daga nan ma wajen Baban Yara zanje na tsugunna na yi masa godiyar bani ke da aka yi. Abba ya so ya ganni a gurfane a gabansa ina yin godiyar bani ke da ya yi. To yanzu zanje na yi masa godiyar a gaban wakilinsa." Na tura baki gaba na ce "Baka tambayi izinina ba, ka dauko mini mota. Ina ce tun jiya ka bani kyautar ta?" Ina rufe baki ya zabura ya fita daga yanayin salamar da ya yab'a a fuskarsa. Ya dawo a Gudalen Umma. Ya nuna ni da yatsa ya ce "kin ci uwar k'arya kin kwana da yunwa Guduyo. Ina ce baki yarda kin yi mini abin da nake so ba? Ai cewa na yi idan kika yarda zan baki, kika k'i yarda din, sai kuma dan ke ce uwar son banza sai ki ce kin ci kyauta! To ki sake lale". Na mike na daure fuska na ce "To shikenan". Na fara tafiya da nufin barinsa. Da sauri ya ce "ki dawo Halah! Barina a wajen nan zai zama sanadin da ba zaki rabauta ba." Na dawo ina cin magani. Ya sassauta tamkar ba Tak'adiri Gudale ba. Ya ce "kin amince yau komai zai dai-daita, kin amince komai zai wuce, ya zama kamar ba'a yi ba?" Na ki tamka masa, ya iso kusa da ni ya ru'ko hannuna ya ce "pls mana Halah! Ki ji tausayin dan-uwanki. Nine fa Baban Afrah! Na ci arzikin kasancewata ubanta". Na ce "Kai da baka so ta ba, me yasa zaka nemi kamun k'afa da ita?" Ya ce "Hmm! Ba zaki gane bane, amma Wallahi yarinyar ta shiga raina, hotunan ta sun fi na kowa yawa a wayata. Ba zamu tsaya cecekuce da tone tone ba. A mini ha'kuri yanzu. Ki huce, na yi al'kawari a gaban Baban Gusau ba cin mutunci a tsakaninmu" Na yi shiru. Ya koma ya zauna yana lalubo wanccan yanayin, ya kashe murya ya ce "Zan tafi yan mata sai yaushe kuma?" Na kyal-kyale da dariya domin kwarai da gaske ya dage shi ala dole hira yake yi. Na ce "kana da mata ne?" Ya ce "Ina da mata da yara uku. Amma matu'kar kika bani hadin kai daga kanki na rufe kofa. Wannan al'kawari ne na yi miki shi, da zan dauwama ina rokon Allah ya bani ikon cika wa." Dadi ya ratsa ni, amma ban bari ya bayyana ba. Na ce " idan kana sona, ka je ka saketa sai ka zo mu fahimci juna". Ya zabura ya mike ya na cewa "wuyar sha'aninki ya kai k'urewa uwar Amnah. Ke an fasa zancen ma, zo mu tafi gida haba. Ina dalilin ina ta rarrashi kina sake nausa wa jeji?". Dariya ta so subuce mini. Na juya na yi wajen Sakina. Kememe ya ki shiga wajenta ya gaishe ta. Wai sai wani lokacin. Kuma a hakan yake so ta bani ha'kuri. Ya kuma za'bi gidanta amma ya kasa gaishe ta. Kai zuciyar Gudale sai Àllah. A hanya muna tafe sai cewa yake yi "Ba kyau ka bawa wasu damar daza su shigo matsalar gidanka. Ya sassauta ya ce "kinsan dai abin da kike yi mini haram ne ko? Zan miki albishir matu'kar kika mance komai mussaman a yau din nan to zaki rabauta domin duk bacin rai da kika saka ni, to kuwa na yafe miki. Sannan duk al'kawarin abubuwa da na ambata zan miki suma sun zama wajabat, har motar nan kuwa". Na cuno baki na ce "Bana so." "Nifa tunda ka mare ni akan yaron da na haife shi cikin wahala ka fita a raina. Tunda shi kake so, kake kuma muradi to ka je na bar maka shi. A hargitse ya ce "Na fara gajiya da gaske Guduyo. Ko dai ki ha'kura cikin girma da arziki, ko kuma ki ha'kura da tsiya tsiya tunda baki san rarrashi da ban ha'kuri ba. Na yi murmushi na ce "Zan ga yadda za'a yi kuwa". Ya hassalo ya ce "Guduyo me yasa sai kin kure ni ne? Idan ina kaunar ki ga raunina shega nake. Amma tunda kika hade da Sakina komai ma zaki saka na yi. Aman din da kike ta fishi akansa, Wallahi tunda kika gudu ban sake waiwaiyarsa ba. Komin kukansa bani da sukunin rarrashinsa. Nan duniya Umma ce kawai ta fiki a wajena." Na ce "Sakina fa?" Ya girgiza kai ya ce "so na kauna na jini tabbas bani da kamar Sakina, ta zarce komai da kowa a wajena. Kar ki yi mamakin kuma Al'amin ne zai biyo mata baya a wannan fagen sannan ku members ku biyo baya. Amma a so irin na bege, na burgewa, na jiyar da juna da'di, ba wacce zata kai ki, balle ta fiki". Murmushi ya subuce mini. Hakan da ya gani ya sanya ya ce "Dan Allah Guduyo mu kwanta tare kin ji?" "Ba zan kwanta da kai ba, idan na yi ciki kuma ka dawo da wula'kancinka, bare kuma ace na haifo mace?" Da sauri ya ce "Darajar kura'ani ba wannan maganar a zuciyata. Ni yanzu bawa ne mai godiya sosai. Na gamsu Ubangiji ya bani damammaki a rayuwa amma na kangare masa. Na shiga jirgin tuba da nutsuwa. Ina tabbatar miki a yanzu ba abin da nake so irin na ga na fara yi miki laulayin ciki. Na k'osa na gan ki da Baby." Na ce "Hakane! Amma ban yarda ba, kaga har yau Umma bata sona da kai, tunda k'ememe ta ki mayar da ni dakina. Ina kan bakana har sai ka kawota gabana ta roki arzikin na zauna da kai lafiya, ta kuma sanya albarka a zaman namu". Na dago na kalle shi yana mini wani irin lalataccen kallo ya tumbatsa tamkar zai fashe. Ya ce "Wallahi Tallahi kin yi ka'dan ki ce na kawo Ummah gabanki! Har abada tafi karfin hakan, ba kuma zata yi arahar da zata zama hakan ba. Kar ki yaudari kanki Guduyo. Umma uwata ce da ban ha'da darajarta da komai ba. Kar ki nemi wuce gona da iri kin ji. Kin ce sai ta je Gusau zaki dawo, ta je. Kin ce sai ita zata dawo mini da ke, ta bawa Sakina umarnin ta dawo da ke. Yanzu kuma ki ce sai ta zo gabanki ta ro'ki arzikin ki zauna lafiya da ni? Tabdi jam. Ashe kuwa baki fahimci rayuwar nan ba. Ba zata zo gabanki da nufin durkusawa ba, har abada Guduyo. Amma na yarda zamu je gabanta ta sanya mana albarka ki ji da kunnenki. Yau ne rana ta karshe da zaki kafa mini hujja da Umma. Ki bari, bana so, ba sa'ar ki ba ce, ba kuma zan dauki wannan iyashegen ba, if not zamu samu mummunan rikici" Ya fa'da a matu'kar kufule. Jikina ya yi sanyi a dalilin tsananin fishin da na gani a tare da shi. Tsawon lokacin mun yi jugum jugum tamkar masu zaman makoki. Shine ya fara hucewa ya ce "Ni na manta wannan maganar na shafe ta. Yayin da na daure fuska na turo baki sosai ina kunkinin ni ban shafe ta ba. Ya kasa daure wa da shiruna ya ce "Pls Guduyo ki manta komai, kinsan dai na yi k'ok'ari fa, gaba'daya na sauke komai, raunina ya gama bayyana a gabanki, to ki huce hakanan". Har muka isa gida rarrashi yake yi da campaign. Fadi yake "idan da abin da kike so ko sha'awa fa'da mini sai mu biya na siya miki." Yayin da na ce "Bana son komai." Na shammace shi na shige dakina na rufe kofa. Washagari da safe na fito da nufin yi masa karin kumallo. Ina cikin soya masa dankali, ya fito, ya tsaya a bakin kicin din. Wani irin kallo yake mini na takaici tsantsa. A hassale ya ce "Mandiya hamshak'iya, wai ke kafaffiyar yarinya ko? To ki je ki jika abinki ki sha. Bazan sake cewa ina so ba. Bare ki yi ta tozarta ni, komai mutum ya yi dan kansa. Zan zuba miki ido komai zaki yi, ki yi, amma Allah na ganin komai." Na juyo ba alamun damuwa a tare da ni. Dan na sake k'ular da shi sai na murmusa na ce "Na kammala abin karin kumallo kada ka fita baka karya ba". Ya kuwa tunzura ainun ya ce "Idan kika kuma bani abinci sai na kwashe miki karama Halimatu! Kinsan dai bakin miji tamkar na mahaifi ne. Ki bari yunwa ta kassara ni ai baki da asara". Ya juya fuu ya fice da sauri. Wajen Umma ya nufa ya tarar da ita zaune da Antin Zaria suna hira. Ya gaishe su a sanyaye, tare da cewa har kun tashi ne?" Anti Zaria ta bashi amsa da cewa "Ai da yau zamu wuce to an sami matsala bamu samu tickets ba. Sai jibi kuma." Umma ta kafe shi da ido tana nazarin irin ramewar da yake sake yi a kullum. Ta kasa ha'kuri ta ce "Wai menene matsalarka ne? Ina ce tunda ta dawo kuma shikenan sai ka sauke masifar da ka sanya wa zuciyarka hakanan." Ya numfasa cikin kunya da nauyi ya ce "Umma so nake ki bani dama na kawo ta gabanki, ki sanya mana albarka, ki nuna kina kaunar zaman ta cikin ahalinki, ki kuma sassauta kamar yadda muka yi da ke shekaranjiya." A hassale ta ce "Wato sai anyi hakan da ta kwantar maka da hankali? Wannan yarinyar ta zame mini kadangaren bakin tulu. Ban da kaddara me za'a yi da haularsu?" Ya marairaice ya ce "Ki yi ha'kuri Umma! Ina sake baki ha'kuri kaddara ce ta ha'damu, ita ce uwarsu Aman. Ki taimke ni ki sassauta, ki karbeta Ubangiji zai baki ladan masu ha'kuri. Ke din farar uwa ce Umma. Ba abin da baki yi mini ba, ba gatan da baki yi mini ba, duk ba wanda na manta." Ya durkushe gabanta guiwa biyu ya ce "Sake nuna mini soyayya ta hanyar yin ha'kuri da al'amarin Guduyo. Ina miki al'kawarin a tsaye nake akan k'afata, bata isa ta ta'ba mini ke na barta ba, bata isa ta wula'kanta ki ta kwashe k'alau a hannuna ba. Ta sani ke ce abu mafi daraja a wajena. Ina son ki mini adalci Umma ta hanyar yin hakuri da matar da Ubangiji ya za'ba mini, sake daure wa, ki mini wannan alfarmar". Ta share hawayen idonta ta shafa kansa ta ce "ka kawota zan yi hakan! Allah ya tsare mini kai. Allah ya kawar da dukkan abin da babu alheri a cikin rayuwarka. Aniya bi aniya In sha Allah". Antin Zaria da itama k'walla take yi ta hau fa'din "Ameen Umma! Ai kin gama yi masa dafa'i daina tsoron komai akan sa Ubangiji ba zai juyar da addu'arki ba". Ya dinga godiya sosai tare da al'kawarin duk runtsi ba zai bari a fi karfinsa a gidansa ba. Ba abin da Umma take kauna irin ta ce ya nemi Abida da take gabanta a yanzu. Amma da ta tuna irin tozarcin da Munubiya da uwarta suka yi mata sai ta tsorata. Ta kuma sani kanwarta Adama uwar Abida ita ce take ta fa'di tashin kawo mata taimakon yadda za'a yakice Baban Yara da iyalinsa a jikin Abba amma basu samu nasara ba. Ta sani kuma matu'kar ya auri Abida sai an mallake mata shi, ai hatta ita kanta sai ta koma karkashin ikon Adama. Kan dole ta ha'kura tana kukan zuci, tana hirji da nadamar yadda rayuwa bata zuwa mata yadda take so. Har yau da shekarun tsufa suka cimmata bata samu cikar burikanta ba. Bata ga Safiya a uku ba, bata ganta a kaico ba. Sai ma cigaba da a kullum take ganinta a ciki. Dukiyar mijinta da ta sanya ta d'agawa da kyashi, kusan rabinta ta Gudale ce. Yayin da ya kasance y'arta ce matarsa kuma uwar y'ay'ansa. Kuka ya goce mata sosai tana yi tana fa'din "Allah na yi tuba! Sai dai har abada babu aminci a tsakaninmu, na ajiye makaman fa'da da Safiya da ikon Ubangiji. Amma matu'kar da kulunboton da ta yi, to ba zata mutu ba sai ta hadu da sharrin bebayen aljanu darajar manzon Allah". Antin Zaria ta kasa jurewa ta fashe da dariya hawayen tausayin uwarsu kuma na gangarowa a fuskarta mai cike da kamala ta ce "Bebayen aljanu kuma Umma? Menene manufar hakan?" Cikin kuka Umma ta ce "Azaba zasu yi ta gana mata, duk juyin da za'a yi kuma baza su magantu ba. Kafin a ankare sai ta ji jiki fiye da yadda na ji". A wannan karon hatta Gudale sai da ya fashe da dariyar sosai. **** Ina zaune a falo wayata ta hau Kara ina dubawa na ga Yaya Gudale ne. Na dauka. Ga mamakina sai cewa ya yi anjima ka'dan zan shigo Allah ya sa kina gida?" Na dake na ce "Sai ka zo". Na kalli kaina tsab nake, cikin kwalliya. Ba jima wa kuwa ya iso. Shiru shiru bai shigo ba. Kafin na yi wani tunani sai kawai wayata ta hau kuwwa. Na dauka ganin shine sai cewa ya yi "Na iso ina wajen gate". Na dauki mayafi na fita, na tarar da shi zaune a mazaunin direba, ya sanya wa fuskarsa bakin glass da yake yawan sawa idan yana cikin rashin sukuni Na bu'de motar na zauna. Muka gaisa, ya zuba mini ido sosai. Ya numfasa ya ce "Sai yawo kike yi mini da hankali Halimatu! Zuwa yanzu ya kamata ki y'anta zuciyata daga zullumi, ki kuma hutar da gangar jikina daga kewa. Kinsan dai ni ban iya tsilla tsilla ba. Ina jiye miki tsoron kada na fa'da tarkon da zai zame mana fitina. Na gaji, ina bu'katar ki sosai". Na dauke kai na ce "Ai kaine har yanzu baka iya magana ba, da ka fara ma sai ka bantse". "To ba sai ki yi hakuri da ni a yadda nake ba. Ban iya karya ko munafunci ba. Dama kuma ban miki al'kawarin zan zama yadda kike so ba, na dai yi alwashin babu cin mutunci a tsakaninmu. Yanzu ki koma ciki ki ha'da mini ruwan wanka. Ki tanadar mini abinci yunwa nake ji. Sai ki shirya zaki raka ni unguwa". Na fita na fara tafiya, sai ji na yi yana cewa "Guduyo". Na dawo na tsaya. Ya miko mini leda mai dauke da tambarin Oriflame. Na karba na yi godiya sosai. Na shige na ajiye ledar a falo, na wuce dakinsa na shirya masa ruwan wanka kamar yadda ya bu'kata. Na dawo kicin na shirya masa abincin. Ina ta tunanin gara da na yi girkin ban biye shi da ya ce kada na sake bashi abincina ba. Na dawo falo na bu'de ledar ina ganin tsadaddun turaruka sai shower gel din da nake amfani da shi, da ya ji ina fa'da wa Sakina ya k'are. Ya shigo fuska a daure tamkar ba shi ba. Na yi masa sannu ya amsa. Ya wuce dakinsa. Ya fito sanye da jallabiya mai asalin kyau da tsada. Ya iso falo, ya zauna na ajiye ledar na ce "Nan zan kawo abincin?" Ya dauke kai ya ce "Eh. Na wuce ina mamakin wannan fishin da yake yi. Na kawo masa. Na zauna ina cigaba da ganin kayan. Ya kalle ni ya ce "Wa ya kawo miki wadannan turarukan masu daraja haka?" Na yi sakare ina tunanin me zance masa. Na dauke kai na ce "k'anin Sakina ne". Ya basar sai kuma ya ce "Allah dai ya sa kin fahimci manufar wannan alherin nasa". *Na gode sosai da ha'kurinku* *Na gode da fatan alherinku*. *Surayya Dee* ✍️ 2/8/23, 10:25 - Buhainat: *YABOWA DA JINJINA* *na matu'kar yabawa da jinjina ga SDK comments group, mussaman masu yin sharhi babu gajiyawa, bayan saka ku'dinku da kuka yi, wajen siyan ticket din karanta labarin, sai kuma kuke sake k'arfafa mini guiwa ta hanyar yin sharhi mai ma'ana.* *Na gode muku sosai! Ubangiji ya sanya albarka a dukkan sha'aninku* *SDK* *97&98*. Na waske ban ce komai ba. Muna zaune aka fara kiran maghrib ya mike ya fice tare da cewa "ki shirya ina dawo wa zamu fita". Bai jira amsata ba ya rufo k'ofar. Bai dawo ba sai da aka sallaci Isha. Yana dawowa ya tisa ni a gaba har wajen shashinmu ganin gaban Baban Yara zai kai ni sai na nemi turje wa tare da cewa "Ba inda zani ban yi niyyar shiga ba yau". Ya d'aure fuska ya ce "Billahillazi sai kin je". Na fara hawayen takaici na ce "ka daina mini wannan wula'kancin Yaya Sadik! Akan me zaka dinga zuwa gaban iyayenmu kana maganganu masu nauyi da rashin ta ido?" Ya mak'e kafa'da ya ce "kafiyar ki Guduyo. Kukanki kuma ba abin da zai hana. Na gaji da halinki, na gaji da neman yardar ki, na k'osa da wannan maganar, na gaji k'warai da gaske. Ke kuma baki shirya yin sassauci da afuwa ba. Da ace Abba na nan da tuni na sake gurfanar da ke a gabansa. Amma tunda baya nan sai na kawo ki gaban Baban Yara na kuma bu'de maganar k'arara." Na kalle shi ba alamun wasa ko zolaya a tare da shi. Hawaye ya goce mini na ce "Na rok'e ka kada ka mini hakan, dan girman Ubangiji". Ya kankance ido ya ce "Zan bar maganar ne ka'dai matu'kar zaki yarda komai ya wuce a tsakaninmu, zaki samar mini nutsuwar da nake bu'kata." Na daga kai na ce "Na yarda". Ya rike hannuna ya ce "To mu je, amma idan kika yaudare ni zaki ga karshen rashin kunya a gobe". Muka yi sashen Umma. Muka tarar daga ita sai Abida. Antin Zaria ta fita da su Amnah gidan kawarta Anty Sa'adan Mk. Suna ta shirin auren Junaid dinta. Muka zube a gabanta muna gaisuwa. Karon farko da ta amsa gaisuwa ta babu izgili, ko fishi a ciki. Abida ta mike sabe da Aman a kafadarta ta yi cikin daki, a dalilin bata ganin fuska a wajensa. Gudale ya numfasa ya ce "Ga mu a gabanki, muna neman afuwarki da albarkarki". Na yi shiru ina mamakinsa, ai fa'da mini abin da zamu je yi ba kenan. Ta numfasa ta ce "Na yafe muku! Sai dai zan ja kunnenku ko bayan raina kuka nuna wa Yayarku iko akan yaranku data ri'ke su Wallahi ba zaku ga da kyau ba. Y'ay'anku ne tabbas amma tunda ta ce zata ri'ke su to kuwa sun zama nata, zasu zauna a wajenta har zuwa sadda Ubangiji ya so. Idan kuwa ita ta dawo muku da su dan ra'din kanta shikenan, amma a bangarenku duk wanda ya yi magana tabbas ya nemi yin rikici da ni ne." Ta yi shiru! Can kuma murya ba amo ta ce "Allah ya muku albarka ya baku ha'kurin zama". Na saci kallon Gudale na ga wani irin farin ciki ya mamaye shi. Ya dinga fa'din "Mun gode sosai Ummah! Za'a kiyaye, Àllah ya k'ara miki lafiya da nisan kwana mai albarka". Ta amsa da "Amin". Nima dole na daure na hau godiya da yi mata addu'ar gama wa lafiyar. Muka mike Umma ta bude murya tana kiran Abida ta kawo Aman mu tafi da shi ya ji dumina. Nan da nan Gudale ya ce "Bar shi Ummah! Sai jibi ya zo, bata jin da'di". Muna tafe na ce "Me yasa baka karbo shi ba?" Kai-tsaye ya ce "Bana son a takura mini a wananan daren. Gobe asabar zan yi barci sosai da safe. Sannan na sani barina zaki yi da shi". Na yi shiru. A daddafe muka ci abinci, duk inda na saka kafata nan yake mayar wa. Ya ajiye dukkan girman kansa, ya zama tamkar bafade. Cewa yake yi "ki kwantar da hankalinki na miki al'kawarin Afrah zata dawo gabanki. Ai ban kyautar miki da ita ba. Amnah kawai na bata." Na kame bakina na ce "Amma dai ban ce komai ba. Ka ji dai kuma abin da Umma ta fa'da". Ya ce "na ji! Amma nan da wani lokaci ka'dan zan dawo da ita, yanzu dai na ha'kura saboda nasan akan ki laifin zai juye. Anti kuma mai fahimta ce. Baki da baki na fa'da mata Amnah kawai na bata, ita kuma ta ce Afrah ta raka ta kafin ta warware ta saba, dan haka duk zan tuna mata". Na ce "Bar ta kawai Anti ta wuce komai ai, ina laifin wanda ya so jininka?" Ya ce "kinsan Allah sai an dawo mini da ita, ai na sani k'arfin hali kike gwada wa na kuma gode miki. Ba kuma kowa ya ha'da wannan kitumurmurar ba sai Sakina. Ita ce a karambana ta zakalkale sai an tafi da Afrah dan kawai ta raba ni da komai ita ala dole sai na ki'dime na gigice. Tabbas sakonta ya buge ni, rashinku a tare da ni ya fahimtar da ni al'amura masu girma, ya saka na gane kune farin-cikina. Sai dai kuma bata san cewar Afrah ita ce mowar y'ay'a a wajen ki ba. Ta yadda rashinta a kusa da ke zai shafi farin cikinki". Da sauri na ce "Ba haka bane Yaya Gudale! Dukkansu daya ne a wajena, dan Allah kada ka fa'di hakan a gaban wasu, bana son a fahimci ko a zaci hakane zata yi ba'kin jini a tsakanin yan'uwanta. Shaidan baya raina kofar da zai shiga ya haddasa fitina da kyashi a tsakanin yan'uwantaka." Jikinsa ya yi sanyi ya ru'ko ni yana fa'din madallah da ke Guduyo! Kin fahimtar da ni abin da ban fahimta ba, a duk tsawon lokacin nan." Ya yi shiru zuciyarsa na ayyana masa ba dan Ubangiji ya cika zuciyar y'ay'a mata da alheri da tausayi ba, da tuni sun jefi shi a dalilin matsanancin banbancin da gyatumarsu take nuna wa a fili muraran a tsakaninsa da su. Ba dan addu'ar mahaifinsu ba da tuni ya zama tuburan tsabar gatan da ya taso a cikinsa na babu kyara ko kwaba. Komai yake so haka Umma take masa ko da kuwa ya ci karo da ra'ayinta. A kullum bata da ra'ayin kanta sai nasa. Ya tuno duk shawarar da zata yi da su Antin Zaria da ya zo ta zayyana masa. Matu'kar ya ce ba hakan za'a yi ba. Ba nauyi ba kunya zata bisu daya bayan daya a waya tana fa'da musu ta rushe waccar maganar. Ga sabuwar matsayarta. Ba kuma yadda zasu yi, dole ayi hakan. Ya tuna komai zasu bata matu'kar basu hado da wani abu nasa ba, baza su ga ta yi zumudi ko murna ba. A karshe ma sai dai ta bashi gaba'daya tana fa'din shi ya dauka. Ko Kuma ta ce "Mai son farin cikinta to ya faranta wa Gudale. Ya nisa ya tuna matsayi da shekarun Anti Zaria. Amma matu'kar a gaban Umma ne to bata ganinsu. Cewa take yi duk girman mace ai namiji ne jagoranta, Ubangiji ma bai daidaita tunanin namiji dana mace ba, sannan kuma namiji ne jagora a ko'ina. Karon farko da jikin Gudale ya yi sanyi, tausayin kansa, tausayin uwarsa da na sisters dinsa ya masa wani irin dirar ba zata. Ya tuna yadda Abba ya wanzu yana fa'dan illar banbanci da take nuna wa a zahiri babu fargaba babu damuwa. Ya sake tuno kalaman Abba a duk sadda ya ga tana wannan mummunar dabi'ar. Cewa yake yi "Àllah kada wannan ta'adar ya lalata al'amuran Sadik gaba'daya. Allah kada ka barshi da dabararsa. Ina kuma rokar masa a cika zuciyar yan'uwansa da soyayyarsa, a tsare mini zumuncinsu daga rudanin shaidan da hassada". Ya sauke ajiyar zuciya ya na gasgata addu'oin Abba ne kawai suka yi tasiri a kansa da yan'uwansa. Banda hakan da ya sani gaba ce mai tsananin gaske zata biyo baya. Domin har yau a fili Umma take sake nuna wa su Amnah sun fi y'ay'an su Sakina. Komai zata yi musu sai ta banbanta, bata kuma jin nauyin fa'din su din sune yan gida, su take da iko da su, sune zasu yi amfani da sunan Abba. A fili ya ce "Allah na tuba! Allah ka yafe mini, ka yafe wa Ummana, ka jikan Abba". Ya jima cikin sanyin jiki kafin ya kalle ni ya ce "Ina son ki Guddin Abba. Ina jin takaicin da har ya mutu ban tsugunna a gabansa na yi masa godiyar gatan da ya yi mini na bani aurenki ba. " Ya ru'ko hannuna sosai ya ce "Ina sake yi mana ta'aaziya Guduyo. Àllah ya jikansa. Kada kuma mu manta ba abin da yake so irin aurenmu ya wanzu muddin rai. Ki yi ha'kuri. Na yi kuskure kan kuskure. Amma zan kiyaye a gaba da dukkan iyawata. Ina sake miki al'kawarin ko y'ay'a mata goma zaki haifa mini a jere ina so, zan karbesu da farin ciki da godiya, zan kuma yi adalci a tsakaninsu. Zan dai-daita su da Aman! Allah ya shirya mana su gaba'daya". Na kalle shi, shima ya zuba mini ido, tsawon lokaci muna kallon juna cikin shauki da begen da ban yi zaton zan ji shi a kusa kusan nan akansa ba. Tsigar jikina har wani tashi take yi a dalilin kallon da yake mini girman al'amarin da ya kunsa ya kai kurewa. Daga haka ya mikar da ni, ya juya yana cewa "Hau na goya ki, na huta gorin ban ta'ba goyon ki ba." Na kuwa d'age rigata na d'ale shi. Ga mamakina bai durkushe ba, sai ma zunkuda ni da ya yi ta yadda na hau sosai. Ya dinga zagaya falon da ni. Na dinga mamakin karfin da Ubangiji ya bawa namiji, duk zatona ba zai iya saba ni a baya ba shiyasa yak'i ko da gwada wa ashe ba hakan bane. Na tabbatar ni kuma ban isa na goye shi na yi tafiya sak hakan ba, duk da bashi da wani girma. Na sake girmama lamarin Ubangiji. Mun jima a hakan na yi luf. Ya fara nishi ya ce "To sauko haka, gobe ma zan sake goya ki." Ai kuwa na ce "Ata fau ban san zance ba, sai ya hau sama da ni". Ya shige dakinsa da ni, yana fa'din "Wannan ne kuma ba zan iya ba, ina laifin wannan din da na yi, wato na hau sama da ke cinyoyina su rike na kasa katabus ko?" Kunya ta kama ni bayan ya wurgo ni kan gado ya biyo ni ya d'ora mini nauyinsa, sai numfarfashi yake yi. Na cuna baki na ce "Kawai dai sona da yake k'irjinka ne bai yi k'arfin da zaka mini hakan ba. Ban da haka menene a hawa saman? Ai na dauka ko Sallari na ce ka kai ni gidan Maman Nana zaka saba ni ka tafi babu musu". Ya galla mini harara bayan ya cire rigarsa ya ce "A a k'walli zan kai ki gidan Yaya. Ke ki raba kanki da soyayyar novel. da kallon Korean firms, to suma duk k'arya ne, zama ake a shirya yadda za'a yi. Amma ku sai ku ta yin hasashen hakan za'a dinga yi muku. Tun farko na fa'da miki hakan ba zai faru ba sai a aljannah. Yanzu kuwa tunda duk mintinan da kika shafe a bayana baki gode ba, baki yaba ba, to goben ma ba zan goye ki ba. Haba ku tausaya ku dinga gode wa kokarinmu. Mazan novel din nan fa babu su. Kema da a novel ne ba za ki zo a mai jiki ba, ba zan zama ina da cikakken iko akan ki ba. Da kin yi fishi shikenan zan bar ra'ayina na gaskiya na dawo na ki ra'ayin na son rai, komai zai tsaya mini ne cak har sai na ga murmushinki. Kai Allah dai ya shiryi mazan novels ragwaye ne na karshe. Gudalen Umma kuwa namiji ne da yake tsaye akan kafafunsa. Ina son ki amma ba zan yarda da iyashege ba. Kawai abin da yake damuna har nake ganin ina kama da mijin novel, idan na shigo gida ban ganki ba. To anan kam bani da jarumta, tun kafin na aure ki ma. Na bar hakan kuma a tasirin jini kawai." Karon farko tunda na dawo gidan na kyal-kyale da dariya har cikin zuciyata. Yayin da ya nufi bandaki yana fa'din "Ato ai gaskiya ne. Nima da a novel ne a wani ingarman namiji zan zo, mai k'irar zaki, miskili, yan mata na ta cuso kansu ina yarfa su. Ku'di kuwa ba zai zame mini matsala ba. Amma da ke a duniya mai cike da kalubale nake rayuwa ai kina ga ni dai kafin na karbi kudi mai auki sai karshen wata, idan kuwa ba hakan ba sai na sha tambayar ba'asin me zan yi da su a wajen Yaya Abdallah" Ya shige ya bar ni ina sake fashewa da dariya. Har Cikin zuciyata na ji ya wanke kaso mai yawa na bakinsa da nake ga ni. Nima dakina na nufa na shiga wanka. Wanka na yi sosai da kayan oriflame. Ga famewash na mussaman, ba abin da yake burgeni da shi irin yadda ko pant na saka sai ya yi kamshin famewash din nan. Bare kuma da Aisha ta sake nuna mini spray dinsa. Mussaman idan kika gama period kika yi amfani da shi a kasanki kin huce takaici, da kalubalen infections. Shiri na mussaman na yi. Na fito, na shirya bayan na dauko ledar kayan GHT na ha'diya. Kai nikam na dace da jakadun da suka san kayayyaki masu daraja. Gashi dai tunda Yaya Gudale ya fara shan maganin ulcer din GHT shikenan, haka supplement din GHT na basir ne ya warkar da mijin Sakina. Bare kuma ni da nake hadiyar na gyara mutuntakar mace, na tabbatar kayanta original ne. Madallah da jakadun kwarai. Kafin wani lokaci na dauki sheki duk da ko powder ban shafa ba. Na saka rigar barcina. Da kaina na tabbatar mun yi kewar juna, wannan ne karon farko da muka shafe watanni masu yawa ba'a hadu ba. Wata uku har da kwanaki. Sai kuma na kasa koma wa dakinsa. Kunya ta rufar mini tamkar sabon aure. Kwatsam sai jinsa na yi yana bude gate, ban gama mamakin inda zashi ba, na ji ya ja mota ya fice. Na kalli agogo na ga goma saura. A fili na furta "Ashe daren bai yi sosai ba." Bai wani jima ba, ya dawo, a falo ya yi burki ya dinga k'wada mini kira. Na fito bayan na sanya hijabi. Ya kalle ni ya watsar ya ce "Dauko plate". Na dauko na kawo masa. "Juye mana Guduyo, ya zaki ajiye mini ba tare da kin duba ledar ba, ashe ban hana na shigo da leda amma ki bar ta inda na ajiye ba?" Na ce "Allah ya baka ha'kuri". Tare da jan ledar ina bud'e wa. Gashasshiyyar koda ce da yougurt. Na juye a plate din. Na zauna. Ya kalle ni ya ce "Na ro'ke ki kada ki b'ata mini rai. Ina fork din dan Allah?" Na tashi na nufi kicin ina mamakin Yaya Gudale. Na kwaso na dawo. Ya karbi nasa ya fara ci, ba tare da na saka hannu ba. Ya kalle ni ya ce "Na fa roki kada ki b'ata mini rai?" Na zum'bura baki na ce "To ka ce na zo na ci ne?" Ya zuba mini ido, sai kuma murmushi ya kwace masa ya ce "To sauko na baki a baki ma. Duk jaye jayen fadanki, yau kam ba zan biye ki ba. Addu'a kawai nake ta yiwa Abba da ya bani ke, babu zancen na biye wa kuruciyarki mu yi fada." Na kafe shi da ido na ce "Hmm kai dai Yaya Gudale dila ma nan ta barka da wayo, shirya zance kuwa ko mace sai an tona wadda zata kai ka iya sarafa harshe da lauyewa. Komai yanzu zaka ce na rarrashi, gari na wayewa kuma zaka fara muzarai kana fa'din kai namiji ba za'a raina ka ba". Ya yi murmushi ka'dan ya ce "To ba namijin bane?" Na sake zum'bura baki tare da cewa"Namiji ai baya ja da baya a fagen daga, mu yi fa'dan kawai". Ya girgiza kai ya ce "Akan me zan yi fada da ke? Haram ba'idan! Jarumta ta akan namiji ne, amma ban da ke mace halitta mai rauni, kuma halittar da nake tsananin so. Ni da kika gan ni ba abin da nake so daga gare ki irin total submission. Ki yarda da Allah da manzonsa ki yarda da ni. Na canja, zan kuma tabbatar miki na canja din. Matso kusa da ni na dinga ba ki a baki kamar yadda kike ga ni darakta na bawa sharukhn umarni ya bawa kajol abu a baki". Akan dole sai da na yi dariya, a bakin kuma ya bani. Yana gama wa ya ce "Ba ki ce mini Thank you my love ba". Na fashe da dariya ya ce "A to kema gara na fara nuna miki yadda matan novel din suke yi." Daga haka ya jani daki, rawar jiki, sumbatu, kusan koma wa ya yi yana yin abubuwa out of control. Tausayinsa ya kama ni, domin Ni shaida ce shi din mabukaci ne na gaske, sannan kuma bai yarda da wayewar neman matan banza ba. Wannan daren na cikin jerin dararen da ba zasu gogu a tarihin aurenmu ba. Ba abin da bai fa'da mini na soyayya ba. Ba irin rawar jikin da bai yi mini ba. Ba kalar styles din da bai yi ba, kalmar ina son ki kuwa ya fa'da tamkar an goranta masa. Ha'kuri ya bani ya fi cikin carbi, al'kawarin ba zai sake duka ko zagina ba, ya yi su uncountable. Da kaina na gamsu son da yake mini yafi karfin kwatance. Ya sake jaddada mini Allah ya halatta masa mata uku bayan ni, amma shi ya haramtawa kansa. Na ishe shi rayuwa, zai dauwama yana rokon Ubangiji ya kaddara ya cika wannan al'kawarin. Amma kada hakan ya saka na yi wasa da al'amarimsa, ko na nemi takure shi, domin yana da hanyoyin da zai bai ya ladabtar da ni, ai na riga da nasan baya barin ta kwana. Na kiyaye bata masa rai da gangan ko bijiro da wani alamarin da zai kawo mana rud'ani. Ya sake rokon na k'ara ha'kuri da shi, na kara girmama Umma idan na yi masa hakan shi kuma zai dauwama yana yi mini sassauci. Har tsakiyar dare idonmu biyu. Jikina ya yi ligi ligi tsabar gurzar da na sha. A karse sai muka koma hawayen rashin Abba a dalilin maganganunsa da Gudale yake ta bitarsu. Fad'i yake Abba ya ce "Idan na cuce ki, ba zan ga da kyau ba. Abba yana son mu rayu tare. Abba ya ce kaza, Abba ya ce kaza. Karshe dai sai muka yi wanka muka hau nafila domin nema wa Abba gafarar Allah". Sai da muka yi sallah asuba sannan muka kwanta. Gudale na dawowa daga masallaci ya kankame ni muka yi kwanciyarmu. Barci sosai muka yi domin sai shabiyu muka farka. A daddafe muka karya. Sannan ya wuce masallaci. Yana dawowa ya shiga wanka. Ni kam sai da na yi wanka na shirya sannan na tada Sallah. Ban kai ga idarwa ba, ya shigo ya shyrya tsab da shi. Ya zauna bakin gado ya jira na idar ya kalle ni ya ce "Zan fita, zamu je gidan Yaya da Baban Yara, jiya bamu samu zuwa ba." Na kashe masa ido na ce "Adawo lafiya. Amma dai kada ka fitar mini da motata" Ya mi'ke ya na cewa "Wallahi ki cire hankalinki akan motar nan dan kuwa ba zan baki ba, na fasa fas". Na shagwabe fuska na ce "Amma.. Ya katseni da cewa "Maganin irinku da basa karbar rarrashi da wuri kenan. A lokacin da kin yarda Wallahi bar miki zan yi, idan ya so na tisa Yaya Abdallah a gaba sai an siyo mini wata. Amma tunda baki yarda a lokacin ba. Na fasa, ki dai yi addu'ar na samu na siya miki bangles din suna ba ni sha'awa sosai." Na sake kwakkabe fuska na ce "Kai Sweat heart". Ya kwashe da dariya Yana cewa "An marairaice murya za'a yiwa Gudale wayo. Allah dai ya yafe miki Guduyo. Adana wannan shagwabar sai mun je oza room zan kar'ba". Ya fice yana cewa "yau na zama sweating Guduyo! Allah ka jiqan Abba. Da yana nan ruga wa zan yi na fa'da masa sabon sunan da na samu." Na murmusa na ce "Abba ai ya san ina son ka! Ya sani sosai". Ya dawo ya rungume ni yana fa'din "Hakane! Na gode miki. Nima kuma na tabbatar masa Ina son ki tunda na nuna masa zan iya siyar da komai nawa dan na tsira da ke". Na kyal-kyale da dariya na ce "Da kanka kake fa'da mini? Kai da baka so na ji wannan maganar?" Ya murmusa ya ce "Na tabbatar sai Sakina ta fa'da miki ai. Kai Àllah ka yafewa Sakinata". Kai-tsaye wajen Baban Yara ya nufa. Ta cikin gidan ya shiga, ya gaida Mama ta amsa masa da sakakkiyar fuska tamkar komai bai faru ba. Ya zauna suka dan ta'ba hira, a dalilin ta zubo masa danwake. Yana ci suna hirarsu tamkar ba surukai ba. Ko da yake ita ganin Al'amin take yi masa, shima kuma kallon uwa yake mata fiye da suruka. Yana cikin ci Al'amin ya shigo, ganin Gudale ya saka bai zauna ba, ya gaisheta a tsaitsaiye ya juya zai fice. Mama ta ce "shigo ka zauna Al'amin." Bai musa ba, ya dawo ya zauna. Ta kalli Gudale ta ga yana cin abincinsa amma ya daure fuska tamkar bai ta'ba dariya ba. Ta ce "Baku gaisa ba Sadik". Ya sake ha'de rai ya ce "Na amsa sallamar da ya yi ai". "Mama ta sassauta ta ce "Ka amsa amma ko shi bai ji ba tunda a shake ka amsa din. Ni din ma dan ina cikin masu tsananin ji ne. Menene hakan kuke yi, na sani kullum kuka ha'du sai kun yi fa'da amma ba irin wannan ba. Ku ha'du a gabana babu mai cewa dan-uwansa kala-kanzil? Wanne irin abune hakan kuna girma kuna cin kasa? Al'amin da yafi Gudale sassauci ya ce "Kure ni ya yi Mama! A gabansu Yaya fa ya tsaya ya nemi zaginsu." Gudale ya mike ya ce "Aminu har gaban abada babu ni babu kai. Ina ce kai ne ka boye mini Guduyo? Da taimkonka Sakina ta shirya komai. To na riga na sallamaka na ha'kura da kai, da ikon Ubangiji kuma ba zaka ji na mutu a dalilin rashin dan-uwa namiji ba, Yaya Abdallah da su Yaya Ammar sun ishe ni. Ga Abbas nan ma. Bayan bita da kullin da kake yi mini a cikin gidana, hakan bai isheka ba sai ka mini sharrin na zagi su Baba. Allah ya so nima d'ansu ne. Nan da nan Gudale ya lauya zance murya ta fara rawa yana fa'din "Wato ni Ubana ya mutu shine ka zage zaka dake ni ko? Waton yanzu bani da wata alfarma a gidan nan tunda bani da dan-uwa namiji bani kuma da Abba ko? To Alhamdulillah shi Baban bai dauka a yadda ka dauka ba. Asalima yanzu zuwa na yi mu fita unguwa tare. Kai kuma ka je na sallamaka ai dan kana ganin na kwallafa raina akanka ne shiyasa kake mini iyashege. Hawaye ya zubo wa Gudale ya ce "Ka nuna mini Guduyo ce taka, ita kake kishi, ka je ranar tashin alkiyoma zamu tsaya gaban Ubangiji ya bi mini kadin soyayyar da na wanzu ina yi maka amma ka butulce mini, ka nuna mini wata kusan ta fi wata. Abin da Sakina da Antin Zaria basu iya ba kenan. Basu san banbanci a tsakaninmu da ku ba" Ya zaro tissue yana goge hawayen idonsa. Mama da Al'amin jiki ya yi matu'kar yin laushi. Ganin hakan da Gudale ya yi sai ya sake hakikance wa yana fa'din "Allah ya rufa mini asiri ina da Aman wataran shi zai zame mini dan-uwa. Ka riga ka shayar da ni mamaki Aminu". Mama ta goge k'walla ta ce "Gaskiya Al'amin kai ne da laifi, ya fika gaskiya." A sanyaye Al'amin ya ce "Ni fa Mama Anti Sakina ce ta saka ni a maganar nan, ban san komai ba, waya ta yi mini ta ce Na shiga lamarin tafi son ace akwai namiji a cikin maganar, hatta inda Guduyo ta zauna Wallahi Anti Sakina ta samo mata". Gudale ya sake fasuwa ya ce "kin yarda da maganata yafi son guduyo da ni? Ban da hakan da ya ga Sakina tana tare mata fa'da, nima ya tare mini mana? Kana tunanin Sakina bata sona ne ita? Baka ji a ranka cewar zata ji babu da'di a ranta ba? Ace duk yadda nake da kai ba zaka taimake ni ka rufa mini asiri ba? Na je gidanka yafi sau ashirin, har tsugunna maka na yi idan kasan inda matata take ka fa'da mini, amma ka yi funfurunfus. Sannan duk wannan ta'addancin da ka yi mini bai ishe ka ba, sai da ka sake nuna mini Baban Yara kai ya haifa zaka shiga tsakanina da shi. Domin Yayar Kwalli ai duk matsayinmu daya da kai a wajenta. Shiyasa nima na ware dukkan karfina ban yarda ka kai ni k'asa ba. Tun kuma a ranar na tabbatar bani da dan-uwa namiji, idan har kai da nake so zaka iya mini hakan to kuwa kowa ma zai tozarta ni. Dan haka na tattra na ha'kura da kai, haka Àllah yake son gani na, yan'uwa mata ya za'ba mini, na kuma gode masa. Idan Allah ya raya mini Aman ya wanke mini takaicin daka kunsa mini". Ya fa'da kuka na kwace masa na gaske. Al'amin da ke zuciyarsa mai taushi ce sai ya ki'dima ainun. Ya zabura ya isa kusa da Gudale ya ru'ko shi yana fa'din "Baka fahimce ni ba Sadik. Share hawayenka, dan Allah kada a shigo a zaci wani abin ne. Kasan idan Baba ya ganka a hakan hankalinsa tashi zai yi. Tunda baka fahimce ni ba, ka yi hakuri ni na manta komai". Gudale ya fizge yana cewa "Babu sauran aminci a tsakaninmu, gaisawa na yarda zamu gaisa daga hakan kuma kowa tasa ta fisse shi." Sai lokacin Mama ta ce "A a Sadik ba hakan za'a yi ba, tunda ya baka ha'kuri to ka huce magana ta mutu." Ya bata rai yana cewa "Kada ki shiga Mama dan kuwa ni na shafe shi a sahun dangina " Mama ta kalle shi ta ce "Ina baka ha'kuri kana sake turje wa? Sai yaushe zaka girma ne duk sadda kuka yi fada kai ne mai kafiya?" "Yo Mama ai shi yake tsokano ni, ni gaskiya kada ki shiga, ko Baba ma na fa'da masa babu ni babu shi da Sakina, na bar su aniyar moda ta bi randa. Guduyo kuma tana can mun shirya, ko yanzu na ce ban amince ta kula ku kai da Sakina ba zata yi mini biyayya, ba sai na ga karshen shiga sha'anin aure da kuka k'ware ba. Alfarmar d'akin ka'aba sai Gudidina ta nuna muku kune bare a tsakaninmu. Sai ta kunya ta ku". Mama ta ce "Ya baka ha'kuri fa! Nima na baka ashe babu wata alfarma da zaka yi mini Sadik?" Ya kumbura yana cewa "Haka kike mini fa tun fil'azal Mama! Idan na shata layi da Aminu Kan dole sai kinsa na goge." Ta sassauta ta ce "To ba ha'kuri ake yi ba. Kowa ka ga ni a duniya ha'kurin da yake yi yafi da'din da yake ji yawa. Al'amin miki masa hannu ku yi musabaha a kore shaidanin da ya shiga tsakaninku". Al'amin da kullum shi yake zama k'arami idan za'a yi musu sulhu, babu musu ya mi'ka hannunsa yayin da Gudale ya yi fuska ya mi'ka masa na hagu. Ganin hakan da Mama tayi sai suka tuna mata lokacin kuriciyarsu. Shaukin wanccan lokacin ya debeta, ta murmusa ta ce "Sadik hagu fa! Mai farawa da hagu kuwa ba shi da rabo mai yawa". Ya dauke kai shima sanin da ya yi ta yi magana ne irin yadda take yi masa yana yaro. Ya ce "Ba zan bashi hannuna na dama ba sai ya yi tuba Mama! Sai ya yi al'kawarin babu shi babu yi mini katsalandan a gidana. Sai ya yarda Ni da Guduyo daya ne tunda ya nuna mini ban fita a wajensa ba". Ya juyo a marairaice yana cewa "Mama yaushe ya samu Guduyo din da zai juya mini baya akanta? Ina ruwansa da duk abin da zan yiwa Baba! Shin ni ba Babana bane kenan? Ai da suka ga zan ta'ba su Yayar ba sun fito mini da Mata babu shiri ba? Maganin biri karen maguzawa, har yau kuma ina nan akan bakana wlh kai da Sakina idan baku kiyaye ni ba, sai na mayar da ku y'ay'an kuka". Al'amin ya fara hauro wa ya mayar da hannunsa jikinsa. Mama ta ce "Bana zai kara shiga tsakaninka da matarka ba alakwari ne wannan ni na yi maka shi. Amma dai kaima ka daina yi masa rashin kunya, shekara guda cir ya baka, ni uwarku na yi muku sulhiy, duk wanda ya tayar da maganar to ya nuna ban isa ba ku gaisa yanzun Nan. Sadik bashi hannunka. A wannan karon bai noke ba ya mi'ka masa dama tare da cewa "Assalamu alaikum". Al'amin ya amsa tare da mika nasa hannun yana cewa Wa'alaika Salam ya Aki". Shikenan sai Mama ta tashi ta karo musu danwaken tana fa'din to ku ci tare kuna hirarku kafin Baban naku ya fito." Ta fara tafiya Al'amin ya ce "Amma Baki ja masa kunne ba yau, ya daina ce mini Aminu". Ta kalli Gudale ta ce "ka ji baya so, ka bari kada shima ya fado maka naka wanda baya so. Nan da nan Gudale ya xey "Ai na huce da shi, kinsan kuma sai mun bata ne nake fa'da masa hakan. Ni duk wanda ya takura mini Ina fa'da masa asalin sunansa ne da ya dace da Yan gargajiya. Yanzu wa ya ta'ba jin na cewa Ashiru, Ashir? Har abada Ashiru zan ce masa, tunda baya ra'ayina baya nufina da alheri". Mama ta murmusa ta ce Allah ga Sadik nan ka yafe masa, ka so shi". Al'amin ya ce "Ni fa Mama?" Ta ce "Àllah ka so Al'amin ka yafe masa shikenan?" Gudale ya ce "kin yiwa kishiyarsa addu'a ina zai iya ha'kura bai tanka ba". Farin-cikin da Baba ya yi da ya gansu suna cin abinci a kwano daya ba dan ka'dan bane. Ya kasa boye murnarsa. Ya kalle su ya ce "Allah ya kore shaidanin da zai ruguza soyayyarku. Allah ya yi muku albarka". Ku gama ku zo mu tafi gaba'daya. Al'amin ka taya shi bawa Yaya ha'kurin katobarar da ya yi mata." Hakan kuwa tare ya zuba su a mota suka tafi. Ya dinga kallonsu cike da farin-ciki. Baba sai Hamdala yake yi ba dan komai ba sai dan yadda ya ga y'ay'an nasa a tsaye cak sun zama zaratan matasa. Tabbas y'ay'a maza abin ado me a wajen uba, garkuwa ne a cikin gida. Haka nan bango ne a wajen yanuwansu mata matu'kar an yi sa'a suna cikin nutsuwarsu. Ya tabbatar Al'amin da Gudale da suke sune kananu ma sun ishi su Sakina a matsayin iyayensu. Komin kankantar namiji ya kan zama uba a wajen mace. Ya kalle su ya ce "Ku taimaki Abdallah, ku taya shi kulawa da yan'uwanku mata, ku bibiye su, ku dinga kai misu ziyara, ku yawaita yi musu alheri. Domin har tsufan mace tana karkashin jagorancin namiji ne. Kada ku barsu su yi kukan rashinmu. Kada kuma kuyi abin da zai ta'ba darajarsu a gidan aurensu. Kada ku haifar da tazara a tsakaninku da su. Ta waya ka'dai zaku iya sanya farin-ciki a zukatansu. Mata da yawa basu da iyaye, a kullum suna kukan basu da wanda zasu tunkara da matsalolinsu, suna ha'kuri na dole saboda rashin iyaye. Amma idan aka yi sa'a tana da tsayayyen dan-uwa namiji sai ta samu sau'kin al'amuranta. Ku kula da yan'uwanku, komin ku'dinsu, komin shekarunsu suna bu'katar ku". Har suka isa gidan Yaya nasiha yake musu akan raunin da y'ay'a mata suke da shi, da kuma tarin kalubalen da suke fuskanta a wannan rayuwar. Shi yasa yake ta fito da maganar a bayyane dan su fahimta. Yaya ta marabce su da farin ciki, ta dinga godiya tare cewa tuni ta yafe ta manta komai. Amma ta sake jan hankalin Gudale ya zauna lafiya da matarsa, ya kuma yi mata adalci, ya yi ha'kuri da ita. Auren zumunci sarkakkiyarsa yawa ne da shi. Ta rufe maganarta da sanya musu albarka. Baba ya dinga yi mata godiya. Daga gidan Yaya yawo suka yi sosai. Sune ta'aaziya, sune dubiya a asibiti. Sune ziyarar gidajen su Anti Maimuna har kan Sakina. Sai yamma lis suka kammala. Suka dire a gidan Guduyo aka yi raha aka yi nasiha. Gudale ya daddage yana yi mata nasiha tunda ita kadai ce kanwarsa, sannan yadda ya mata nasihar tamkar ba shine mijinta ba. Fadi yake ri'ke mijinki gam, kada ki bari a shiga tsakaninku, ki kunyata duk mai kokarin shiga tsakanin ki da uban y'ay'anki". Baba ya dinga dariyar jin da'di yana fa'din you are always like that Sadik, u you will never ever change". Al'amin kuwa da yasan yarfe ne yafi yawa a nasihar, kuma da su ake sai kawai ya maze ya yi kamar bai gane ba. Da zasu tafi ya raka su har kofar gida sannan ya koma gidansa. 2/8/23, 10:28 - Buhainat: *GAISUWAR GIRMA Da JINJINA GA MANYAN MATA KUMA IYAYENA* *BA ZAI YIWU NA KAMMALA WANNAN LITTAFIN BAN MIKO GAISUWATA DA GODIYAR SOYAYYA DA K'WARIN GUIWAR DA KUKE MINI BA, KALMAR GODIYA HAKIKA TA YI MINI KA'DAN SAI DAI KAWAI NA CE UBANGIJI YA SANYA ALBARKA DA FARIN-CIKI A AL'AMURANKU FIYE DA YADDA KUKE MINI. KUN FAHIMTAR DA NI, NI DIN Y'AR GATA CE MAI UWAYE KARIMAI MASU TSAYUWA A CIKIN AL'AMARIN DIYARSU CIKIN KOWANNE BIGIRE*. *WALLAHI INA ALFAHARI DA KU, FIYE DA YADDA KUKE ALFAHARI DA RUBUTUN Y'ARKU*. *HAJIYA SALIHA ABUBAKAR ZARIA* *HAJ RABI SANI MADAKIN GINI* *HAJ HAFSATU C SODANGI*. *HAJIYA HALIMA D'ALHA SHEHU*. *HAJIYA HALIMATUS SA'ADIYA*. *GODIYA* *FANS DIN SURAYYA DEE* *HAKIKA DUK MARUBUCIYA DA MAKARANTA TAKE TAK'AMA*. *DUKKAN WACCE TA SAKA KU'DI TA SAYI RUBUTUNA HAKIKA NA GODE MATA, NA KUMA YABA MATA, INA FATAN UBANGIJI YA FINI YABAWA.* *INA FATAN UBANGIJI YA HORE MINI LAFIYA DA AZANCIN DA ZAN YI TA YI MUKU RUBUTUN DA ZAMU KARU GABA'DAYA* *MADALLAH DA KU! MADALLAH DA KARFAFA GUIWARKU. SURAYYA TANA GODIYA*. *INA KAMMALA MUKU WANNAN LITTAFIN CIKE DA ALHINI DA KEWARKU DA ZAN YI* *GUDALE YA YA JINJINA MUKU, YA KUMA CE MATU'KAR KUKA LAZIMCI ISTIGIFARI ZAKU RABAUTA* *ALHAMDULILLAH* *MARUBUTA* *TABBAS KUMA KUN TAKA MUHIMIYYAR RAWA A RUBUTUN SURAYYA* *DAN HAKA NA YABA NA KUMA GODE WA KOKARINKU, ALLAH YA CIGABA DA TSARE MANA ALKALAMANMU*. *AUNTY SUMAYYA TAKORI*. *JAMILA JANAFTY* *LUBNA SUFYAN* *ZAINAB MAZAWAJE* *AYUSHA MUHD* *SAFIYYA UMM ABDUL* *FADILA LAMI'DO* *BINTA ABBALE* *KULSUM BAFFA AZARE* *HASSANA DAN LARABAWA* *ZEEY KUMURYA* *SAKINA YAZID* *DONUT FAIRY* *DA DUKKAN MARUBUTAN LAFAZI WRITERS ASSOCIATION*. *GORON GAISUWA* *GA YAR'UWATA DA MUKA FARA GINA DABI'AR GUDALE TARE* *SISTER ASMA'U A3* *(MAMAN MAMA)*. *DA KUMA AMINIYATA* *HAUWA SAID YIDIE GOMBE* *(MAMAN MAMA)* *ALLAH YA BAR ZUMUNCI YA SHIRYA ZURIA*. *FATAN ALHERI GA* *DUKKAN DALIBAN UNITY KACHAKO GABA'DAYA KWATA, MUSSAMAN AJI NA 2008* *SON SON BISIBILLAHI*. *TUIKUICIN LITTAFIN GA* *SCHOOL DAUGHTERS DINA* *8 BABIES* *MUSSAMAN TA KARFEN* *HAFSAT RILWAN BELLO* *(BABY GIRL)*. *ALHERIN ALLAH YA ISKE KU HAR GADON BARCINKU*. *99&100*. *Prologue*. Ya dawo ya same ni a inda suka bar ni. Ya zauna sai farin ciki yake yi. Ya kasa yin shiru ya ce "Guduyo anya akwai farin-cikin da ya wuce cud'anya da jininka?" Na girgiza kai na ce "Babu". Ya saka hannu ya jani jikinsa ya ce "me ya sanyaya miki jiki haka? Alhalin kamata ya yi ki yi farin-ciki mai yawa". Na numfasa na ce "Tausayin Baba ne ya kama ni. Tunda Abba ya rasu gaba'daya wani irin tsufa ya yanko masa. Abubawa da yawa bai san ya yiwa kansa, bai san matsaloli da yawa ba, saboda Abba shine jagoransa, baya sanin duk wani rikicin da zai taso, amma tunda Abba ya kauce al'amura suka dabaibaye shi ba tare da yasan yadda zai dinga warwaresu ba. A yanzu da ya tisa ku a gaba yana yawo da ku sai na fahimci yana son ya koya muku juriyar daukar nauyi ne. Ya sani idan baku saba ba zaku sha wahala kamar yanzu da nauyin ya koma kansa yake shan wahalar gaske. Allah ya jikan Abba". A sanyaye Gudale ya ce "Ameen Gudidina! Kin sake fahimtar da ni manufar Baba wanda duk ban kawo hakan ba. Àllah ya bamu ikon daukar nauyin da zai hau kan mu". Na amsa da "Ameen Abban Amnah". Ya murmusa ya ce "kinsan dai tun farko ina yin kawaici akan Amnah tunda yar fari ce, bare kuma yanzu da na bayar da ita. Dadin Afrah zaki dinga ce mini tunda na fahimci an kara mini matsayi, na tashi daga Yaya Gudale. Na koma sweaty da kuma alkunya da Yaranmu". Na murmusa ban ce komai ba. Tun daga lokacin muke rayuwa cikin farin-ciki da mutunta juna. Ina iyakacin bakin kokarina na kiyaye abin da zai ha'do mu rikici. Kullum a cikin gyaran kaina da gidana nake. Sai dai duk da hakan idan ya so rikici, kan abu kalilan sai ya botsare mini. A hakan dai muke ta lallabawa. Ba zato kawai ya sanar da ni satin sama zamu wuce Umrah ni da shi da Afrah da Aman da kuma Ummah. Na dinga tunanin yaushe ya dauki passport dina? Tunda ina da shi a dalilin shekaru uku da suka wuce Abba ya biya mini na sauke farali. Sai da ya kammala komai sannan ya fa'da. Har zuciyar Umma ta ji babu da'di amma ta ha'kura akan dole, mussaman da ta ji da ita za'a yi tafiyar. A babban hotel muka sauka. Ni da Gudale dakinmu daya, yayin da Umma da su Afrah suke daki daya. Mun yi ibada, mun kuma sha soyayya. Na dinga kokarin k'ulla kyakkawar alaka mai karfi da Umma. Amma ta ki bada damar hakan. Sai na ha'kura tunda dai ta sauko sosai bata cika aibata ni ba, to na gode da hakan ma. Bangles din da ya yi al'kawarin siya mini ya siya, warwaro guda biyu. Da kuma wani murtukukeken bangle guda daya. Jikina ya yi sanyi da irin ku'din da suka lashe. Gold yana zuba tsada, haka ya siyawa Afrah, babbar sarka da zata jima bata saku a wuyanta ba. Ya ce "Nasan Antin Zaria ta da'de da siyawa y'arta, gara kema na daure na siyawa taki y'ar". Na dinga goge k'wallar farin ciki, hakika na gamsu da soyayyarsa, ni da shi ban san wanda yafi wani son dan-uwansa ba. Wannan tafiyar shine mafarin dawowar Afra! Domin tunda muka dawo ya shafawa idonsa toka ya ri'ke ta. Hakan kuma ya zo akan gabar su Antin Zaria zasu sake komawa kasar Germany zata yi shekaru biyu. Aikuwa ta ce tare da Amnah zasu tafi shikenan baki alaikum ba'a samu bacin rai ba. Sai dai zasu zo nan da watanni takwas ayi bikin Junaid. Bamu jima da dawowa daga Saudiya ba, Yaya Gudale ya fara wani ciwon ido azababben gaske. Ido na warke wa hakori ya harbu Na tabbatar a Saudi na samo ciki. Kusan sati uku yana magogo. Kowa ya ganshi sai ya tausaya. Umma kuwa fa'di take "cikine da matarsa. Ai shikuma indai za'a yi masa haihuwa fa babu shi babu sukuni. Ban da dai yadda Allah ya tsara, hakan za'a yi ta yaya za'a zuba mini ido ina yi masa wannan tanadin tsiyar. Shi kuma a yanzu da baya kaunar ta shiga shirginmu fa'di yake "Umma mutum yana da ikon sakawa wani ciwo ne? Bani ka'dai bane, da akwai maza da suke yin laulayi. Na sani kuma da zabi za'a bawa Guduyo ba zata yarda na dinga wahalar da nake yi ba. Ki dinga yi mana addu'ar na samu lafiya, ita kuma ta sauka lafiya". Idan ta ji hakan sai ta yi gum. Tana jin takaicina kamar ta shak'e ni. Cikin sa'a bai dauki lokaci mai yawa ba, ya warware. Komai kuma yana ci babu zabe. Ban ta'ba jin dadin aure ba sai a wannan lokacin. Ba wai baya bata mini ba, ba wai da'di nake ciki a kullum ba. Amma akwai mutuntata wa a tsakaninmu. Sannan bani da matsalar komai, duk abin amfani bani da matsalarsa. Haka nan bangaren sutura ma babu laifi. Abu mafi da'di sassaucin da Umma ta yi. Ta rage yi masa famfo a kaina, tunda shima ba ya yarda ya tattauna matsalata da ita. Dan haka ba kasafai muke samun sabani ba. Ya canja wa Afrah makaranta. Ya daidaita ta da Aman. Komai tare yake yi musu, ko fita zai yi matu'kar ba wajen aiki bane to tare zai fice da su. Hankalina ya kwanta sosai. Ban damu da saurin fishinsa ba, tunda na yi sa'a indai na yi tuba zai ha'kura. A hakan har watan haihuwa ya tsaya aka ciro mini kyakkawan jaririna mai kama da Aman. Komai na Gudale ne a jikin yaron. Murna kan murna Gudale ya yi fadi yake "Baban Gusau ne wannan. Sauran ki Baban Yara ". Na murmusa na ce "Maman Kebbi fah? Tunda na lura so kake yi sai ka jera sunayen yan gidansu Abba". Ya murmusa ya ce ai kuwa domin so nake nima nawa autan ya zama Baban Yara ne". Na ce "Gashi kuma na gama. Haihuwa biyar duka c.s abin a jinjina a tausaya mini ne". Ya yi dariya ya ce "Ke kya fara? Baki haifo mini Sakinata ba?" Na ce "Sakinarka ko tawa?" Ya ce "Karfin hali fa take gwadawa nan duniya Sakina ba wanda take so kamar ni har ya'yanta kuwa". Yana rufe baki ta shigo da murmushi a fuskarta. Nan da nan kuma sai ya waske yana fa'din "Wa zai yiwa Sakina takwara kuma ana zaune kalau? Haka siddan yarinyar ta kwaso halinta. Tunda dai na haifo photo copy dinta ai ya isa ta gode mini. Jiya da naga hoton Amnah a status din Antin Zaria har tsorata na yi da yadda kullum take sake juyewa tana komawa tamkar Sakinan Guduyo sarkin shiga tsakanin soyayya". Na jima ina kallonsa, ina mamakin yadda ya murde tamkar ba shi ya gama kwarzanta ta ba, yana fatan na haifo masa baby girl ya sanya sunanta. Amma tana shigowa ya waske shi a dole bai damu da ita ba. Ta sake murmusawa ta ce "Autan Umma ina ce mun shirya?" Ya ha'de rai ya ce "Ni fa duk wanda ya fifita wani a kaina babu aminci a tsakaninmu. Idan kina son na yafe miki to ki daina kwashe soyayyar da kike mini kina bawa Guduyo". Ta kyal-kyale da dariya tana fa'din "Gudale ka samu duniya Allah yasa lahira tafi hakan. Ni na taba ganin mai kishi da matarsa irin ka? Ka ce Al'amin ba zai sota sama da kai ba, hakan kuma aka yi, kan dole ya zabe ka ya bar ta, yanzu kuma ka ce nima ba zan fi sonta akan ka ba? Wannan adalci ne?" Ya matsa kusa da ita ya mika mata yaron ya jingina barin jikinsa a kafadarta ya ce "Saboda duk cikin yan'uwana na fi sonku. Dan haka zan ji ba'kin ciki mai yawa idan kuka fi son wani a a kaina. Tare muka ta so ke ce babbarmu akan me wata da ta zo daga sama ta kwace mini ku, kuma ayi zaton an so zaman lafiya da ni?" Daga ni har Sakina muka yi dariya. Na ce "To fa'da masa ya bar ni na yi zumunci da Farisa, nima ita ce kawata kuma yar'uwata amma sam baya barina na je gidanta, Yaya Ashir ai dan-uwana ne, kuma ni ban ta'ba sonsa ba tun da. Bare yanzu da bana ganin kowa a gabana sai Dadin Afrah." Ya murmusa ya ce"shikenan ku yi zumuncinku, Ashiru ma na yafe masa zaluntata da ya dinga yi muna yara. Al'kawari na yi babu ni babu shi, amma jiya Baban Yara ya saka na yafe masa na dawo da zumuntar da na yanke da shi". A wannan karon Sakina ce ta yi dariyar tana cewa "Idan baka yafe masa ba, me zai rage shi?" Hidima sosai Yaya Gudale ya mini, wannan ce haihuwar da aka yi masa ya yarda shi aka yiwa ya yi dukkan hidima, dan ko haihuwar Aman da ya samu namijin da yake kulafaci cewa ya yi indai iyayen yaron ba zasu yi hidimar ba na d'aure musu shi a d'ankwali. Amma wannan kam kan jiki kan k'arfi yake yin komai. Tuni kuma ya yiwa yaro huduba da Musa. Da kansa kuma ya ce Arif za'a dinga kiransa. Baban Gusau ya yi murna sosai. Ya taho takanas ya kawo raguna biyu da kayayyaki masu yawa. Iyalinsa ma sai da suka zo ganin mai sunan mijinsu. Bare kuma Farisa da take gari. Hankalina ya kwanta sosai. Ba abin da yake damuna. Sai matsalar Yaya Gudale na saurin hasala, ban isa ya ce yana da bu'kata na bijire ba, idan kuwa na bijire ya dinga kunci kenan da tashin hankalin ai dan ya fa'da mini sirrin zuciyarsa ne na ba zai sake yin aure ba shine nake tak'ama. Ina laifin ya yi ha'kuri, na yi har sati biyar? Ban samu kwanciyar hankali ba sai da na koma kwana a dakinsa. Na riga da na gane shi komin shirina da shi, komin kyautata masa da zan yi matu'kar zan yi nesa da shi a shimfida to kuwa zai shafe idonsa ya manta komai na alherina. Shi dai babban alherin da zan yi masa da zarar ya zo da bu'katarsa na bar komai na tarairayaye shi. Shikenan na mutuntata shi, ina kuma son shi. Akasin hakan kuma zai zama dalilin da zai ce na raina shi, ban damu da shi ba. Shikenan sai ya zama sanadin da zai sa ya yi mini fishi sosai. Ni kuma an jarrabe ni da k'yamar ganin fishinsa. Idan ya botsare mini gigicewa nake yi har sai na shawo kansa sannan nake nutsuwa. Ban Jima da haihuwa ba. Auren Junaid da y'ar tsohon Gwamnan Kano ya taso. Shirin biki ake yi na attajirai kuma yan boko. Irin tanadin da ake yiwa bikin ka'dai ya isa a gane bikin manya ne kuma yan boko. Anyi shagali irin wadda ba zai yiwu na fa'da ba. Antin Zaria da mijinta Kano suka dawo tunda duk danginsu suna na dan haka anan za'a yi bikin. Tunda ga kan bikin dangin amaryar dana ango anyi shine cikin farin-ciki da wadata. An bawa kowa damar ya shiga dakin taro, babu shamaki. An kashe dukiya sai fatan alheri kawai. An kai amarya jiya, sai kuma kwarya kwaryar liyafa da mai d'akin Gwamna mai ci ta shirya a gidan gwamnati, wannan kam an takaice adadin mutane saboda yanayi na tsaro. Muna sashen Umma ana ta aiki. Sai ga Anti Maimuna ta shigo da hadaddiyar envelopes a hannunta Ashe Katina ne guda shida a ciki. Gudale ya shigo, muka yi magana ya karbi mukullin gida wai ya manta nasa a office. Har ya fita sai kuma ya dawo ya shige ciki wajensu Umma. Bai wani jima ba nima na shiga dan kwantar da Arif da yake bayana. Ai kuwa sai tashin hayaniya nake jiyo wa daga dakin Umma. Muryar Anti Maimuna sai rawa take yi, tana fa'din 'Umma ta saka baki Gudale ya bata katin ya zata yi da kawarta data yi mata waya ta shirya ta zo ta ajiye mata katin?" Yayin da shi kuma ya rantse ba zai bayar ba. Umma ta ce katin guda nawa ne shin?" A raunane ta ce "shida ne, amma tun acan Antin Zaria ta cire daya ta rubuta matar Abdallah. Dan haka saura biyar Ni, Juwairiya, Ramla, Sakina, shine dayan zan bawa k'awata. (matar d'an majalisa ne ita ma). Ya zo ya dauke ya ce na matarsa ne. Tunda matar Abdallah zata je ai ta wakilci yan kofarsu, idan aka bata ita ka'dai, to Farisa fa?ai duk matsayinsu daya a gidan". Ya hassalo sosai ya ce "Tabbas matsayinsu d'aya. Amma ke kuma na fiki matsayi ko? Tunda kika raba muku a tsakaninku kin gamsu su Ramla ya zama dole su je, to ni kuma fa? Nawa na dauka, bani kuma da ra'ayin zuwa dan haka matata ce zata je mini". Rikici ya kaure ta fara kuka tana fa'din "Umma ta saka baki mana". Umma ta yi k'undubalar cewa "Gudale bata ka ji, kubutar da ita jin kunya". Nan da nan ya ce "Umma a wula'kanta ni, ta hanyar cire ni a jerin yaran gida sannan ki bi bayanta? Inda ka'ida za'a bi ai kamata ya yi na samu biyu, amma d'ayan ma sai a hana ni saboda ba ni da k'ima, ko saboda bani da alaka da gidan? Wallahi tunda ta dai-daita mini mata da wata a cikin gidan nan to bazan bata ba, ko gaban Antin zamu je ai na sani ta lissafa da Guduyo, amma ita tunda bata son ta shiyasa zata kyautar da nata a kawarta. To Wallahi sai Guduyo ta je bikin nan, sai dai ita ta ha'kura ta bada nata, ko kuma ta tozarta ba matsalata bace." Anti Maimuna ta fashe da kuka tana cewa "Ya wula'kanta ta saboda ni". Yayin da shima yake cewa "ita ta wula'kanta shi tunda kawarta ta fi matarsa. Umma kuwa da ke har gobe bata son fishinsa ta kasa yi masa fa'da. Suna ji suna ga ni ya fito da katin nan. Ni kuma tuni na fice na shiga ana cigaba da aiki da ni. Ya fito ya kira ni. Ba sukuni ya ce "Anjima ka'dan ki dawo ki shirya zan kai ki govt house." Na ce "To". Ya tafi ya bar ni, da sake saken zuciya. Damuwa ta d'aya yadda Anti Maimuna zata sake tsananta mini. Dama yaya lafiyar kura? Dole Anti Maimuna ta bawa kawarta ha'kuri. Ba karamin da'din halarta bikin nan na yi ba a dalilin ganin Anti Sa'adan Mk. Ita ce a gaba a kawayen uwar ango. Bata halarci ragowan events din ba, a dalilin sai jiya ta dawo daga Egypt raka Hajiyar Bichi ganin likita. Na kallesu suna high Table ita da Antin Zaria. Sun yi matu'kar kyau, ba wanda zai ce sun zarce shekaru arba'in. Ilimi da gayu ya samu muhalli. A yanzu haka Sa'a ita ce shugaba a kungiyar kare hakkin mata da yara. Sannan tana da gidauniyar lauyoyi mai zaman kanta wacce ita ce take jagoranta. Na dinga kallonsu ina fatan Nima na zama kamarsu. Manyan mata sun kewaye Antin Zaria. Ba abin da yafi ilimi Dadi. Ga Amnah na gefenta bata yarda ta barta a ko'ina. Kowa gani yake autar ta ce tunda duk kama suke yi. A wannan lokacin na ji sha'awar na koma na yi masters dina ya kama ni. Ko ba zan yi aikin ba, zurfafa ilimi abu ne mai matu'kar amfani. Ga dai Anti Sa'a, na tuno sadda Yaya Gudale ya hana ni aiki, har misali da ita Antin Zaria ta yi mini, ta ce itama mijinta hana ta aiki ya yi, amma ta yi ta zurfafa iliminta. Dan haka nima zan yi kokarin zurfafa ilimina duk da dai na sani sai na jure jidalin Gudale a dalilin baya kaunar ya shigo gida bai gan ni ba tamkar yaro mai shan nono. Gashi bata aikin har yau amma tana da hanyoyin samun ku'di daban daban, ga kuma kungiyoyin tallafawa mata da marayu da take jagoranta. Haka aka gudanar da walimar nan cikin ilimi da nutsuwa. Haj Sa'adah Mk ita ta yi bayani a madadin uwar ango. Duk yadda ake kwarzanta dadin muryata na tabbatar ta Anti Sa'a ta kere tawa. Gashi a gayance cikin gogewa da ilimummuka daban daban take maganar. Nasiharta ta fi karkata a yiwa Amarya nasiha da kuma gujewa sharrin kawaye. Bayan haka sai gode wa kokarin miji. Ta kuma ja hankalin angon akan ya zama adali mai yin sassauci akan amaryarsa domin ta bar kowa nata tana zaune da shi." Kowa ya dinga murmushi a dalilin jawaban nata babu son zuciya, ba kuma ta ja shi ba. A takaice ta yi shi bai gunduri kowa ba. Tana kammala wa dakin ya dauki tafi raf raf. Duk yadda dakin ya ha'da zakwakuran manyan mata sai da kwalliyar Iyah Basiru ta yi matu'kar birge kowa. Ta zama big madam abin alfaharin miji da y'a'ya. Mussaman da a yanzu burin Baban d'anta Jawad yake daf da cika domin ana tsakiyar shirye shiryen kaddamar da jirgin da ya siya mata, ya kuma sanya masa D'an iya airlines. Ban sake tsinkewa da lamarin Antin Sa'a ba sai da mijinta ya zo daukarta. Muna harabar gidan gwamnati dankareriyar motar ta shigo. Shi yake tukin da kansa. Ya fito duk da shekarun girma sun hau shi yana nan a tsaye da karfinsa da lafiyarsa. Mussaman da yake rayuwar ta yi albarka, an cimma dukkan buri. Matashin saurayi ne ya fito a gaban motar. Ina jiyo Anti Sa'a tana fa'din yanzu Malam baka taho mini da twins ba?" Ya murmusa ya ce "Na fa'da miki ba zan koma gida ba." Amir ya ce "Mami dan Allah ki zo mu tafi, tun safe Malam yana ta yawo da ni, na gaji, ina son kuma na je naga ko Mamana ta sha maganinta". Sa'a ta kalli yaron da tarin kauna duk da har yau bata ta'ba fa'da masa ita ce Uwarsa ba. Ta ce "To Amir, bani mintina uku mu yi sallama da uwar bikin". Ina kusa da Antin Zaria ta iso suka dan rungume juna suna yin sallama da fatan alheri. Tana cewa Anti ta yi kokarin zuwa kafin ta wuce domin zasu yi bikin kaddamar da Dan iya airline da kuma katafariyar jami'ar da Mk ya kwashe shekaru goma yana gininta. Anti Zaria ta ce "zan zo In sha Allah? Oh burin Jawad dai ya cika, jirgin nan na cikin ransa. Àllah ya sanya albarka. Sannan ki fa'da wa oga a bani vacancy na mutum biyu dan su yi aikin koyar wa. Sa'a na dariya ta ce "Duk da dai kinsan har yau din nan ra'ayinsa shine akan gaba, amma bana jin zai tankwabar da bukatarki". Ta rakata har gaban Mk, ya yi mata murna, ita ma ta yi godiyar ta ga sakonsa. Sannan ta yi masa murnar Cigaban da ya zo musu, ta kuma gabatar da bukatarta. Cikin yakana ya ce" daga yanzu zuwa ko yaushe duk tsayin zamani kina da alfarama a makarantata. Kada ki ji komai." Ta yi godiya ta ce "A gaida Farida". Ya bata fuska ya ce "Ai baki gayyace ta wannan bikin ba, bayan duk kokarin da ta yi, duk wadancan events din ta zo tunda k'awarki bata nan, amma saboda son kai a wannan sai kuka ware mini ita". Dariya saosai Antin Zaria ta yi ta dinga fa'din Afuwan ". Yayin da Sa'adah ke gefe bata ce komai ba. Ta kalli Amir ta ce "ka gaida Mamanka da kyau". Ya amsa da "zata ji Anti". Suka shiga mota, Mk na tu'ki, Sa'a na gaba, Amir kuma na baya a zaune. Charting yake da Jawad. Zuwa yanzu ya san Sa'a ce ta haife shi, amma bai nuna ya sani ba tunda daga ita har Mk ba wanda ya zaunar da shi ya fa'da masa. Farida kuma har yau din nan soyayya take nuna masa gangariya fiye da Amira. Dan haka shima yake tare da ita, yake son Amirah fiye da su Jawad ko dan sun sha nono guda ne? Amma baya iya danne kaunar Sa'adah matu'kar suna tare, ya dinga yin abubuwa na soyayyar jini, ita kuma tana lallaba shi. Amma komai nasa da dukkan al'amarinsa bata shiga. Farida ce uwarsa har gobe. Ha'kuri da juriyarta ya sanya ta cigaba da zama tauraruwar Mk. Har kuma yanzu idan ta murde masa rasa sukuni yake yi, shiyasa yake kaffa kaffa da abin da zai sa ta tunzura. Duk da yana motsa mata kwanji idan zata zo masa da son rai, wani zubin kuwa kan dole yake ha'kuri ya bar ta domin rikici a jininta ne, bare kuma ya hadu da kishi. Shi kuma sonta da tsoron fishinta a ransa ne, ba zai canju ba. A hanya ya ce "Burinki ya cika, Jawad ya siya miki jirgi" Ta kyal-kyale da dariya ta ce" ya ce fa tare ya siya mana." "Ya kyabe baki ya ce "Wannan shine yaudara. Tun yana kankani kika kitsa masa maganar da ya gimamata a zuciyarsa. Ai kallonku nake yi ke da shi kawai. Kuma wai har kuna iya kalubantar nafi son su Amir". Ta waiwaiya ta ga voice note yake yiwa Jawad, hankalinsa baya tare da su, ta dawo da hankalinta kan Mk. Ta ce "Malam! Mu bar maganar nan sai mun je gida kada ya ji me kake cewa yaje ya fa'dawa uwarsa ta zaci kamar sun dame ni ne, dan yanzu idan ta ji wannan maganar idan ta tisa ni a gaba da tsokana cikin dabara sai gidan ya yi mini zafi. Tunda a fili zaka nuna ni ce Babba. Ha'kuri kawai zaka ce na yi". Ya murmusa ya ce "Akan me ba zan baki ha'kuri ba, kin shige zuciyar mijinta kin yi kane kane kin bar ta a sakade ai dole ki yi ha'kuri da ita kema. Ba zai yiwu a mata duka biyu ba". Sa'a ta fashe da dariya tana cewa "Allah ya so gidan kowa daban, da ina nan tana mini kisan mummuke, kai kishi da irinsu Farida sai an shirya matu'ka gaya. Allah ya so ni, ya hore mini kai". Shima ya fashe da dariya ya ce "kinsan kuwa zanci gaba da nuna ban fahimci ita matsokaniya ba ce". "Eh ai Amarya ce da bata laifi a wajenka". "Ke kuma uwargidana kuma zuciyata gaba'daya ba". Amir da yake jinsu ya ce "ita kuma Mamana hantarka ce ko?" Suka fashe da dariya dukkansu uku. A haka har suka isa gida suna hira cikin nisha'di. *Madallah da Mk da ahalinsa* Fatan alheri ga ahalin *HALIN YAU*. Yadda ya kawo ni da kansa haka ya dawo ya dauke ni. Afrah da Aman na gaban motarsa suna ta cin inibi. Ina fito wa ya ce su koma baya su zauna. Da kansa ya fito ya bu'de mini motar, ya karbi Arif sai da na zauna sosai sannan ya miko mini shi sannan ya rufo mini kofar. Muna tafe cikin farin-ciki, duk Wanda ya ganmu sai ya yi sha'awarmu. Duk macen da ta gan ni a hakan ga miji ga y'ay'a reras ha kuma wadata sai ta yi sha'awata ta yi fatan Ina ma itama ta samu hakan ba tare da tunanin irin kalubalen da na tsallake, nake kuma fuskanta ba. Tunda dai har a yanzun da muke zaune kalau ha'kuri nake yi kan ha'kuri. Sau'ki kawai na samu. Sati daya da bikin Antin Zaria da mijinta da Amnah suka koma Germany. Yayin da Abba mai bin ango tuni ya koma kasar Turkey inda yake Masters dinsa. Autanta Ja'afar ne ka'dai aka bari shima jibi Yaya Gudale zai mayar da shi makarantar Nigerian Turkish da take Abuja, yana ajin karshe S.s.3. *Shekaru biyu a gaba*. A kwana a tashi babu wahala, tuni na yaye Arif. Na koma jami'ar Bayero ina masters degree. Wanda da kyat da sudin goshi ya bari. Ina karatun ne dan ina so amma da tuni na ha'kura. Domin tun hudun dare Zan tashi, sai na gama da hidimarsa. Duk yadda nake da yan aiki har biyu to ba zai yarda ya ci abincinsu ba. Dama kuma sai da ya kafa hujjar karatuna ba zai sa ya samu gibi a kulawata ba. Ya dai yarda zai ajiye mini yan aiki su taya ni gyaran guda da kula da Yara. Amma hidimarsa kwaya daya ba zai rage mini ba. Na yarda da hakan tunda karatun nake so. A wannan lokay a yi matu'kar zubewa, amma fatata ta yi k'yau tabbacin mayukan Oriflame na Aisha suna tasiri, ga kuma lafiyayyen abinci. Kawai jarabar Gudale da rashin samun hutu ne damuwata, kullum ina makaranta, idan na dawo gida kuma hidimarsa ba yar ka'dan ko mai sau'ki ba ce. Domin dai dai ruwa idan zai sha sai na zuba masa. Idan yan tsiyar suna kusa ma Sai na shirya tsab zan tafi sai ya ce "Na koma na yi shigar yaku bayi. Ko kuma ya ce "Na tafi da Arif ai ba mai rikici bane. A hakan dai nake lallabawa har na samu na kammala. Ranar wata asabar ina zaune a gefensa. Rarrashi nake yi tamkar wanda na yi masa laifi. Cikin kwantar da murya na ce "Daurewa zaka yi na je makarantar nan." Ya ha'da rai ya ce "Asabar din da zan samu mu yini tare ma sai kin fita, nifa kina kwarata Guduyo, tsakani da Allah kina cutata". A sanyaye na ce ",Na yi tuba Dadin Afrah! Kara ha'kuri watanni suka rage mini". Ya yi shiru can ya ce "Karfe nawa zaki je?" Da sauri na ce "sha'daya zan fita zuwa azahar in sha Allah Ina hanyar dawowa". Ya kalli agogo ya ga Tara da rabi. Ya nisa ya ce "Tunda kin sa mun karya da wuri. Zo ki mini tausa kafin lokacin fitar ya yi." Gabana ya yanke ya fa'di domin nasan ba iya tausar zan yi ba. Na tuna daren jiya bai tsallake ba, haka da asuba ma, yanzu ma idan ba sa'a na yi ba, ba zan tsallake ba. Ya kallo ni ya ce "Tausar da zaki yin ne yasa kika wani zabura?" Na kasa magana illah ido da na zuba masa. Ya girgiza kai ya ce "Tashi ki je! Allah ya bani ladan hakuri. Allah ya bani iko na yi ta kyautata miki. Ya bani ha'kurin rakinki. Ba dama na ta'ba ki, ko na ce ki yi mini kaza sai kin nuna na fitine ki. Amma da yake duniya ne a gaban ki, ai bakya k'osawa da zirga zirga a titi da sunan makaranta, duk sanyi, duk damina". Kullum kina study room kina nazari. Amma da zance ki shigo d'akina shikenan duk wani rauninki zai bayyana". Murya na rawa na ce "Ba hakan bane Dadin Afrah ka yi ha'kuri". Ya girgiza kai ya ce "ke ce da ha'kuri Guduyo. Amma kar kiji da wai, matu'kar kina mini irin hakan Wallahi zan warware al'kawarin da na yi miki, na bazan k'ara aure ba. Dan kuwa ba zan yarda ki jefa ni a halaka ba, gara na saba alk'awari zai fi mini sau'ki". Nan da nan hawaye ya b'alle mini na ce "Ba fa na yi maka musu Yaya Gudale. Ina yin kokari kai ma ka sani, amma kullum baka yaba mini, kuma yanzun na ce ba zan yi bane?" Ya ce "Baki ce ba, amma yanayin ka'dai ya nuna mini ba zaki saki ranki yadda zan samu farin cikin da nake bu'kata ba. Yana rufe baki na fa'da masa na ha'de bakinmu. Ban samu kaina a hannunsa ba sai goma da kusan rabi, a gaurguje na yi wanka na shirya. Dake y'an kirkin na kusa ya dauki Arif muka tafi tare, tunda Afrah da Aman suna islmamiya. A mota ya jira ni na kammala muka dawo, yana sake jaddada mini al'kawari yana nan, ba zai karya ba, sai idan ni na so. Muna isa gida ya ce wajen Baban Yara zai je, idan zan je Bismillah. Na bishi sanin ban masa laifin da zai kai k'arar da zai kunyata ni ba. Muna isa k'ofar falon ya durkushe ya fara rararfe tamkar Arif. Baba sai fa'di yake "Assha Sadik yau ba azo an yi moping ba, zaka na'de k'ura a jikinka." Bai tashi ba kuwa har ya isa gaban Baban ya durkusa guiwa biyu. Cikin rauni sosai ya ce "Yauma godiyar nake son na sake yiwa Abba kuma baya nan?" Baban Yara ya ce "sau nawa zaka yi godiya ne Sadik?" Ba kunya ya ce "Ina Jin da'din zama da ita ne Abba. Na gode sosai Abba! Allah ya jikanka". Baba ya biye masa ya ce "Dama na fa'da maka ko ina kwance zaka gode mini". Baba da taya bera bari ya kalloni ya ce "Kara kwantar masa da hankali Halimatu! Sake yiwa aure biyayya, kin sani bani da burin na ga aurenku ya dire har a aljannah. Allah yayi miki albarka da zuri'arku gaba'daya". Ya mayar da hankalinsa kan Gudale ya ce "Madallah da Sadik! Na sani Ubangiji zai mayar mini da kai yadda nake fata". Daga hakan kuma sai ganin Gudale na yi ya koma ya zauna ya nutsu ya ce "Baba barka da yini ya jikin?" Na kyal-kyale da dariya domin sai yanzu na gane waccar gaisuwar da ya yi ta Abba ce, ta yanzu ce ta Baba. Ho diramar Gudale idan kana gani ba ruwanka da kallon tv, yak'i yarda ya girma. Har yanzu bai bar kowa ba. Kuma ya koyawa Baba diramar shima. Ya hareri na ya ce "Na rantse muka koma gida sai na baki tsinke kin nuna mini abin dariya a jikina. A gabana, a gaban Baban Yara kike wannan dariyar anya kina son karamarki ta dire Guduyo?" Na gimtse dariyar. Baba kuwa uffan bai ce ba. Na zauna na gaishe shi, sai kuma muka dinga hira har Mama ta shigo ta same mu. ** Mun kammala karatun sai jele muke yi a gaban profs dan.mi samu mu karbi result din mu. Abokiyar karatuna Sajida. Har gida ta kawo mini super wax da wani uban laxe cikin wani kawataccen kwali tamkar box. An rubuta Rabiu & Sajida. Na dainga yi mata murnar auren da ya zo mata. Tunda sa'anni muke shekaru talatin kenan. Amma sai da na yi Mata dan bikin ko da wasa bata Nina ba sai da Abu ya kankama. Ta yi murmushi ta ce shine ya bu'kaci hakan tsohone mai iyalifa. Wata'kila matar ce baya so ta sani tunda ya yi ta yun'kurin auren baya yiwuwa, wata'kila kuma sirri yake so. Na yi murmushi na ce "Allah ya ka'dai fitina ya sanya alheri. Ko tsoho ne ai namiji ne sannan ya tara ai. Tunda k'awaye ma ya narkar da kuda'de ya bamu wadannan kaya haka." Muka yini da ita, har Yaya Gudale ya same ta, suka gaisa sama sama ya haye sama. Ta kalli ni ta ce "Mijinki bashinda sabo". Na ce "Haka yake, baya sakewa da kowacce mace inba ni ba. Kada ki dauka wula'kanci ne". Muka yi sallama na rakata na dawo. Na ha'da ruwa da lemo da meatpie na nufi dakinsa. Kallonsa kawai na yi na gane yauma ya tuna baya, ya afa abar. Hankalina ya yi matu'kar tashi ainun. Na ajiye masa na zauna na kalle shi idon nan ya ciko da k'wallah tsabar cajin da take yi masa. Ba'kin ciki mai yawa ya rufe ni. A fusace na ce "Tabdi jam! Ashe baka bar wannan dabi'ar ba Yaya Gudale? Ina ka biya haka?" Kallona kawai yake ba tare da ya iya bu'de baki ya amsa mini ba. Na fusata na ce "Idan baka ji tausayin mu yan'uwanka mata ba, ai sai ka ji tausayin manyan ya'yanka mata ne. Haka zasu taso su dinga ganinka lokaci zuwa lokaci kana cikin rashin nutsuwa ka dawo mahaukaci, haka kake son Aman ya dinga ga ni daga gareka? A hakan zai zame maka aboki kuma garkuwa?" Jikinsa ya yi sanyi ainun. Na mike na nuna shi da hannu na ce "Kunya dai kam ka ji ta Wallahi". Nan da nan ya zabura ya mi'ke ya ce "Na rantse kika zage ni sai jikinki ya fa'da miki, ance miki na sha da yawa ne ta yadda zan kasa fahimtar komai? Gajiya na yi, shiyasa na sha dan na wartsake." Idona ya ciko na ce "Ba dan ka wula'kanta kanka ba har na iya daga maka murya Yaya Gudale? Sai dai kada ka shiga ru'du na rantse maka ko zagina ka yi idan na saka kafa na fita ba zaka kuma ganina da sunan matarka ba". Ina rufe baki ya koma ya zauna ya yi lakwas a hankali ya furta "I come in peace". Tausayinsa ya yi matu'kar kama ni. Na fice na samu gefe na yi kuka na gaji. Na sauka k'asa na shiga cikin yara muna ta hidima duk kuwa da bani da sukuni. Ana kiran sallar maghrib ya sauko ya yi wanka amma idon nan ya ka'da sosai sannan da kyar yake tafiya. Ya kalli Aman da tuni ya yi alwallah yana jiransa ni kuma ina ta wasiwasin ko zai iya fitowa ma. Amma da yake Ubangiji ya sanya shi a cikin bayi masu son sallah sai gashi ya fito. Ya rike hannun Aman suka fice. Ni da Afrah da Arif muka yi a gida. Ranar ko dakinsa ban je ba, ba zan iya tuna yaushe rabon da na yi masa hakan ba. Muna cikin haka ranar bikin Sajida ta zo. Dake na share shi, kwanaki biyu bana ko bu'de baki na yi masa magana, duk ya rikice da son mu shirya. Da kansa ya kai ni har wajen bikin. Wani shahararrren Hall. Ya zauna ya jira ni a mota. A hanyar mu ta koma wa sai neman magana yake yi, ni kuma na kame bakina na k'i kula shi. Har muka iso gida bai ha'kura da nacin magana ba, ni kuma ban kula ba. Washagari juma'a da yamma ba sai tashin hankali ba. Wai Anti Maimuna ce ta dawo gida. Da kuma wani irin ihu ta shigo, hatta ni da bangarena yake da tazara da cikin gida sai da na ji kururuwarta. A ki'dime Gudale ya fice dama dawowarsa kenan parking kawai ya yi. Ina son fita amma dai na ha'kura tunda abin a kofar Umma ne bana son tashin hankali, tunda dai lallaba wa nake yi. Ashe wai aure mijinta ya daura dazu da aka idar da sallar juma'a. Bai fa'da mata ba sai bayan ya dawo daga daurin auren. Shine ta kasa ha'kuri ta fito ta bar masa gidan. Tashin hankalin da ta shiga ba ka'dan bane. Hatta su Sakina sai da suka taya ta jin ciwo, ko ni nan na ji babu da'di domin ko yaya aka taba naka sai ka ji ciwo. Kan dole Baban Yara ya mayar da ita da daddare bayan ya yi mata wuta wuta. Umma sai kuka take tana cewa duk yadda take da Hajiya Laraba uwarsa amma ta yi mata hakan? Sai lokacin na tuna irin abin da Umma da Maimuna suka so yi mini kenan lokacin auren Munubiya. Amma da yake ni din yar gata ce ina da Abba sai burinsu bai cika ba. Irin alherin da na samu a sanadin auren ba dan kishi ba, da sai na ce ya yi ta yin auren duk shekara. A karshe kuma auren ya watse babu albarka, babu kuma mutunci. Sai gashi da na yi ha'kuri, ina zaune Ubangiji ya saka an yiwa Anti Maimuna abin da ta jagoranci ayi mini. Tana cikin wannan tashin hankalin ya dauki amaryarsa suka wuce London. Wani abin mamaki ashe Sajida ce amaryar. Na ki'dima da buwayar Ubangiji. Idan na so nima yanzu sai na je gidan na k'i zuwa part dinta tamkar yadda ta dinga yi mini akan Munubiya, kai wato ba k'aramin bakin ciki na hadiya ba. Amma ba zan iya hakan ba domin saka alheri da sharri babban jihadi ne da yake kawo zaman lafiya a zamantake wa mussaman a sha'anin zumunci. Sannan ita din diyar Abba ce, ko ba komai ta ci arzikin ubanta. Kwanaki hudu kenan ina fishi da Gudale. Gaba'daya bashi da nutsuwa, ba abin da yake so irin na kula shi. Dana zauna na yi tsam da raina sai na gane addu'ar da Abba ya yi mini yana hawaye ne Ubangiji ya kar'ba. Ya roka mini Ubangiji ya hore mini Gudale sau ba adadi. Ya roka mini a cika masa zuciya da soyayyata mai naci, da tausayi mai hana zalunci. Tabbas Ubangiji ya kar'ba domin duk iyashegensa idan yaga ina kuka to fa shikenan dukkan rauninsa zai bayyana. Idan kuwa har ya yi mini laifin da na yi fishi da shi to bashi babu nutsuwa. Har sai ya samu aminci daga gare ni. Hawaye ya goce mini a fili na ce "ko irin su Abba guda nawa ne suka yi saura a wannan duniyar?" Na daga hannuna na ce Allah ka jiqan Abba". Da daddare ina zaune ni ka'dai a dalilin ya kwashe yara sun fita bayan ya yi juyin duniya na bisu na k'i. Suka dawo da ledoji niki niki a hannunsu Afrah da Aman da kyar suke jansu. Yayin da shi ya shigo daga 'karshe sabe da Arif da yayi barci. Ya tsaya yana kallona ya ce "Maman Amnah kin ga Arif ya yi barci". Na dauke kai na ce "Na ga ni, kwantar da shi". Haka kawai na ce "ya juya yana cewa "To" cikin murna domin kuwa duk maganar da zai yi bana cewa ko uffan". Ya dawo falo ya dauki babbar leda shake da dogayen riguna da takalma ya turo mini gabana yana cewa "ga naki" A hankali na ce "Na gode." Yayin da su Afrah suke ta gwada na su. Ya yi jim yana kallona ya ce "Amma dai bana son na kawo abu ba'a bude ba ko?" Na tura baki na ce "Ai zan bu'de ne, ba dai nawa bane". A sanyaye ya tashi, ya yi dakinsa. Sai kuma tausayin yadda ya kwantar da kansa ya yi matu'kar kama ni. Kwanaki biyar ai nasan ba karamin ragaita yake ciki ba. Cikin dare kuwa ya kasa ha'kuri ya zo ya jani. Jikinsa na rawa yake cewa "ki taimake ni, na yarda na yi kuskure ai ba zan sake ba. Yanzu ma tsautsayi ne, nafi shekara ban sha ba. Kuma idan zan sha din bana sha ta bugar da ni" Na watsa masa kallo na ce "Àllah zaka yiwa wayo Yaya Gudale?" Ya girgiza kai ya ce "Astagafirullah! Na yi tuba bazan sake ba, ki yarda da ni, idan na ce na daina abu ina kokarin kiyayyewa. Tunda na yi al'kawarin bazan sake zagi ko dukanki ba, na karya al'kawarin?" Na girgiza kai. Ya ce "To bare kuma laifin da Allah nake yiwa. Kinsan nafi sonsa, nafi tsoronsa da ke ko?" Na daga kai da sauri na rungume shi ina cewa "Madallah da Gudalen Umma" Shikuma ya kankame ni yana ta sakin ajiyar zuciya. Can ya dago ni ya ce "Guduyo idan kinsan kina biye Sakina kuna rubuta sunana a cikin kulle kulle ku ji tausayina ku bari. Nifa burina na zama namiji a gidana. " Na yi murmushi na ce "Ai dan kasan ka yi laifi ne, amma waya Kai ka fishi kan abu ka'dan ma. Kwanakin baya ka manta kalar fishin da ka yi mini akan kawai na yi lalle ba tare da anyi hutun school ba". Ya dauke kai yana murmushi ka'dan ya ce "Ato na dai roki a mini a wannan laminin. " Shikenan muka shirya. Sai dai duk sallar farillah ko ta nafila sai na roka masa shiriya, sai na roka masa lafiya da habakar arziki, hakanan kullum sai na roki Ubangiji ya cigaba da hore mini shi, ya kuma cika zuciyarsa da soyayyata da tausayina. *Shekaru goma a gaba*. Zuwa wannan lokacin almura sun daidutu, hankali da girma sun ratsa mu. Yanzu haka yara biyar ne a gabana bayan Afra, Aman, Arif, sai na yi Afreen mai sunan Sakina. Sai kuma autana Aryan mai sunan Baban Yara". Amnah ce dai har yau tana wajen Antin Zaria a yanzu haka ta fara karatun medicine a kasar Sweden. Afrah kuwa tana shekarar karshe a secondary gaba'daya iu juye ni sak. Duk cikin su ita ka'dai ce mai kama da ni kwabo da kwabo har garin jiki, ita har ta fini gashi da fari ma, tunda sun yi sa'a Umma ta sam musu. Ragowan yaran kama suke da Gudale da Sakina. Komai na tafiya daidai sai dai ha'kuri da kullum a cikin yinsa nake. Har yau din nan Gudale bai canja halayyarsa ba. Yanzun na zai tuntsure ko ya lauya zance kuma dole ka sauko domin sai ka ji tamkar ka zalunce shine. Umma tana nan tsufa ya cimmata ainun. Babu soyayya a tsakaninmu har gobe sai dai kuma ta sassauta kiyayar da take yi mana. Mussaman da har gobe taimakekeniya ne a tsakanin yan k'ofarmu da tasu. Mune bangonsu, suma sune namu. Kowa kuma yana cikin rufin asirinsa. Kullum sai Mama ta je ta dubo ta, ta zauna da ita bisa umarnin Baban Yara, tunda Maman ta fita dan k'wari, ita take taimaka mata wajen wanka da hidiida yan aiki ba zai yiwu suyi mata ba. Muna zaune a falo daga ni sai shi yana mitar aikin da Antin Zaria ta samo mini na lakcarin a jami'ar tsohon ministan ilimi Prof. Mk Bichi. Da yake tana da hanya kuma jamia ce mai zaman kanta sau uku kawai zan fita a sati. Sakina ta shigo mana a yanzu ta zama babbar mace sosai. Ta kalle shi ta ce "gemai gemai da kai ba zaka bar kishi da fitina ba Namoriki?" Ya girgiza kai ya ce "Nafi son na ganta kullum a tare da ni". Ta ce "Yi ha'kuri ka barta ta je ta koyar da ilimi, karatunta mai daraja ne barta ta yad'a shi a tsakanin alumma." Ya durkushe a gabanta ya ce "To yayata, yadda kika ce hakan za'a yi. Na amince saboda ke, amma idan kulawar da nake samu daga gareta ta yi rauni tabbas zan janye, zata dawo ta zauna ta kula da iyalinta, ki zama shaida." Sakina ta murmusa ta ce "Autan Umma baban soyayya! Ina yinka over". Ya murmusa ya ce "Bayan Umma ke da Guduyo ne mafi soyuwa a zuciyata Sakina. Na gode sosai. In sha Allah har a filin barka sai Abba ya jinjina miki." Na durkushe tamkar yadda ya yi a gabanta na ce "Madallah da Sakinan Abba. Madallah da yar'uwa irin ki, madallah da zumunci irin na ki Na gode Ubangiji ya sanya albarka a dukiyarki da ya'yanki". Hawaye ya zubo mata ta ce "Nima kune mafi soyuwa a dukkan yan'uwana. Àllah ka shaida na cika wasiyyar Abba! Àllah ya sanya albarka da alhairi a dukkan rayuwarku da ahalinku, ya dauwamar da aurenku har a aljannah". Gudale cikin rauni ya ce "Ameen Ameen ya Ukti wa iya ki". Karshe. Alhamdulillah! Sai mun ha'du a sabon littafi na gaba.