[3/3, 16:54] Sis Nerja'art👰🏻: https://www.facebook.com/105966804349754/posts/105967661016335/?sfnsn=mo *......FANSAR RAI.......* _*STORY AND WRITTEN BY SIS NERJA'ART✍🏻*_ *INTELLIGENT WRITERS ASSO....®* [On Ward Together] _*DEDICATED TO ZM CHUBA'DO*_ *PAGE ONE* Kotun cike take mak'il da jama'a kowa ya nutsu ana sauraren shara'ar da akeyi ana jinjina ma hukuncin da alk'ali yake yankewa, wata shari'ar tabaka tausayi wata kuma tabaka haushi, saidai babu yadda zakayi, me karanta k'ara ne yacigaba da karantawa inda yace shara'a ta biyar wadda take ta karshe a wannan ranar itace shara'ar jawahir wadda ake zargi da laifin kisa ta kashe mutane d'aid'aya har bakwai tsawon watanni goma da suka shud'e inda dangin wad'anda takashe suke k'ararta sukeso abi masu rayukan 'yan uwansu, ana ta zaman k'arar ammah har yau ba'a samu aka kammala ba idan Jawahir tana kusa anaso a gurfanar da ita a gaban kotu. Wasu yan sanda ne guda biyu suka tafo da wata yarinya wadda bazaka gaza shekaru ashirin da biyu ba hannunta da kafafunta duk an d'auresu da kaca, dakyar take tafiya suna biye da ita a baya har aka isa da ita a daidai wajen da aka tanadar mata dan tatsaya, Alk'ali d'agowa yayi daga rubutun da yake yakalli yar matashiyar yarinyar yaduk'a yacigaba da rubutun. Me karanto k'ara ne yace kotu tana buk'atar ganin lauyan wadda ake k'ara da lauyan masu k'ara. D'aya daga cikin lauyoyin da suke zaune kujerar gaba ne yamik'e yajuya yakalli Alk'ali yace ya megirma me shara'a sunana Barr Musa Bello (MB) nine lauyan 'yan uwan wad'anda aka kashe. Jinjina kai Alk'ali yayi nan me gabatar da k'ara yace kotu tana buk'atar ganin lauyan wadda ake k'ara. Shuru Kotun yayi nan aka sake maimaitawa sai chan d'aya daga cikin lauyoyin yamik'e yace Allah yagafarta malam lauyan wadda ake k'ara Allah ya yi mashi cikawa wata biyu kenan da suka wuce. Gabad'aya kotun surutu tad'auka nan Alk'ali yad'ago yace ya rasu? Me karanto k'ara ne cike da rud'ewa yace Allah yagafarta malam Barr Muhsin ne kuma wanchan Lauya d'in da yafara tsaya mata idan ban manceba shima mutuwa yayi toh ya akayi duka lauyoyin nata har biyu suka rasu? Shuru Alk'ali yayi sai chan yace wannan baya cikin hurumin mu tunda bamu isa muhana mutum tafiya ba idan lokacinshi ya yi, saidai kotu tana so taga wanda zai tsaya ma wadda ake k'ara inkuma bata da lauya toh hukunci zai hau kanta kamar yadda kotu tazartas zata mata d'aurin rai da rai ko akasheta, inkuma ita zata iya kare kanta toh kotu naso tafito tayi mata bayani yadda akayi mutane dai d'aya har bakwai suka rasa rayuwarsu ta hanya d'aya. Yarinyar duk'ewa tayi k'asa cike da tashin hankali tafara rusa kuka inda gabad'aya kotun takacame da surutu, Alk'ali teburin da yake a gabanshi yabuga nan kotu tayi tsit. Yan rubuce rubuce yayi sannan yad'ago yace wadda ake k'ara tana da abinda zata ce, ko zata iya kare kanta? D'agowa tayi daga duk'iyar da tayi tana mecigaba da kuka. Yan sandan da suke tsaye kusa da ita ne suka daka mata tsawa sukace tayi ma mutane shuru. K'ok'arin had'iye kukanta tayi nan me karanto shara'a yasake cewa wadda ake k'ara ko zaki iya kare kanki? Jikinta gabad'aya rawa yake nan tasa hannu tadafe kanta lokaci guda tasulale k'asa a sume. Me karanta k'ara ne yace Subhanallahi ta suma, Alk'ali d'agowa yayi yakalleta sannan yace zamu d'aga wannan k'arar zuwa sati biyu masu zuwa lokacin muna sa ran wadda ake k'ara ta dawo cikin hayyacinta yanzu aje da ita abata kulawar da tadace sannan za a cigaba da tsaronta a gidan yari (prison) kamar yadda akeyi,, bubbuga table yayi nan wasu yan sanda ukku mata sukazo suka d'auketa suka fita da ita. Tunda aka fara shara'ar gabad'aya hankalinshi yatattara yana kallon yadda komai yake tafiya musamman ma shara'ar yarinyar da ake zargi da kisan mutane har bakwai,,bubbuga table da Alk'ali yayi yasa duk suka mik'e gabad'aya nan alk'ali yatafi, mutumin dake sanye da riga irin ta lauyoyi komawa yayi yazauna tare da kallon nakusa da shi yace Barrister junaid me kake tunani agame da wannan shara'ar da ake ta wannan yarinyar kana tunanin itace tayi wannan kisan? Murmushi Wanda aka kira da barrister junaid yayi yace inba ita ba wa kake tunani ai itace Barrister. Girgiza kai yayi yace sam batamin kama da wadda zata iya aikatawa ba. Da mamaki yake kallonshi yace me kake nufi da hakan? Cikin nuna rashin damuwa yace inaso intsaya mata a matsayin lauyanta. Zumbur Barr Junaid yamik'e tsaye yace Barrister Faruk ka san abinda kake fad'a kuwa? Na tabbata dan kana sabon Lauya a court d'innan bakasan halin da ake cikiba game da wannan shara'ar wannan yarinyar da kake gani itace takashe mutane bakwai sannan lauyoyinta biyu da suka tsaya mata duk ta kashesu, daga ciki har da Barr Muhsin da aka maidoka madadinshi itace tayi silar barinshi duniya dan haka kar kasaka kanka aciki domin shara'arta me had'ari ce, Shuru yayi kamar me tunani sai chan yajuyo yakalli Barr Junaid yace bazan gasgatar da hakaba har sai na gane ma idanu na. Jinjina kai Barr Junaid yayi yace gane ma idanunka daidai yake da rasa rayuwarka kamar yadda su Barr Muhsin suka rasa tasu rayuwar a dalilin nema suceceta dan wannan yarinyar bana tunani mutum ce hatta cikin gidan yari d'in duk wanda yasaki yata6a lafiyarta to bai kwana da rai dan sau biyu ana fiddo mata biyu da suke a rufe sun mutu a binciken da akayi angane cewa sun tak'uleta fad'a ne a ranar washe gari ba'a tashi dasuba saisa yanzu aka ware mata d'akinta ita kad'ai, shawarar da zan baka kar kajawo ma kanka abinda zai hanaka kwanciyar hankali kabarta kawai akasheta. Barr Faruk murmushi yayi yace har yanzu banji wata kwakkwarar hujjaba da zata sa ingazaba dan haka ina nan akan bakana. Mik'ewa Barr junaid yayi yace har yanzu na lura baka fahimci inda zance na yanufa ba. Barr Faruk ma mik'ewa yayi yana murmushi yace na fahimceka kar kadamu zamu iya tafiya. D'aukar kayansu sukayi suka juya suka fita daga court d'in lokacin babu kowa ciki sai su biyu suka rage. Barr Faruk bayan ya koma office d'inshi zama yayi yana so yayi aiki saidai shara'ar yarinyar nan ta tsaya mashi a rai kasa aiwatar da komai yayi cikin ranshi yace taya za'ace yarinya k'arama ce take kisa? Anya kuwa ba sharri aka ja mataba? Mik'ewa yayi tsaye yace wannan yarinyar kwata-kwata batayi kama da wadda zatayi wannan aika aikan ba dan fuskarta kawai zaka kalla kagane hakan,,,wayarshi yad'auko yayi kira daga chan 6angaren ana d'agawa ko sallama baiyiba yace kazo office d'ina yanzu kasameni,,yana fad'in haka kashe wayar yayi tare da komawa yazauna yana juyawa bisa kujerar da yake zaune. Ba'afi minti goma ba nan aka fara knocking, umurni yabada aka bud'e k'ofar. Wani mutun ne sanye da rigarshi ta lauyers yashigo d'an gajerene baida tsawo sosai tsayawa yayi daga wajen yace Barrister gani. Barr Faruk nuni yayi mashi da kujerar da take opposite d'inshi alamun yazo yazauna. Bai musaba yazo yazauna yana kallon Barr Faruk dan jin abinda zaice. Shima kallonshi yayi nad'an lokaci sannan Ahankali cikin muryarshi me sanyi yace Barr Bilal wani taimako nakeso kayi min. Wanda aka kira da barr bilal murmushi yayi yace toh Oga wane irin taimako ko aiki ne kakeso inyi maka. Shuru yayi na d'an lokaci sannan yace so nake kaje kasamo min duk wani information game da yarinyar nan da ake shara'a da ita a court. Cikin rashin fahimta yace Oga wace yarinya kenan? Barr Faruk d'an yatsine fuska yayi sannan yace wadda ake zargi da laifin kisa. Zumbur Barr Bilal yamik'e tsaye a tsorace yake kallon Barr Faruk yace Oga kar kafara haka na tabbata dan baka dad'e da zuwaba saisa bakasan halin da ake cikiba duk lauyan da yayi k'ok'arin tsaya mata zai iya rasa rayuwarshi karufa ma kanka asiri kar kajefa kanka cikin abinda zai zame maka matsala. Cikin nuna rashin damuwa yace ban damu da hakan ba dan inaso inyi bincike sosai akan haka Indai har nagane batada laifi a ciki ni zan tsaya mata a shara'ar nan ban damu da inrayu ko inmutu ba fatana shine inkasance a bayan gaskiya akowane lokaci. Cikin kid'ima yace ammah Oga gaskiya.....Katseshi Barr Faruk yayi yace ba shi natambayeka ba kaje kawai kayi abinda nasanya ka. Cikin sanyin jiki yace toh zanyi insha Allahu zuwa gobe zanzo maka da duk wasu bayanan da suka dace. 'D'aga kai yayi alamun toh, sannan yace zaka iya tafiya. juyawa Barr Bilal yayi cikin sanyin jiki yafita. Barr Faruk duba agogon hannunshi yayi sannan yamik'e yad'auki suit d'inshi yasaka yadad'e idanunshi da bak'in glass sannan yad'auki key d'in motarshi yafita cike da tak'ama yake taku Wani lauyer ne yabiyo bayanshi da wasu takardu a hannunshi yana cewa 'Dallabai ga rohoton da muka samu game da case d'in Alhaji Salisu da yake so katsaya mashi akan k'arar da yashigar a court akan wani gida dayake so ak'watar mashi na wani matashi da yace ya siyar mashi da gidan ammah bai tashi daga gidan ba,,,,tafiya yake yana binshi yana kora mashi bayani har saida yakai aya sannan Barr Faruk yajuyo yakalleshi ta cikin glass d'inshi yace kaje kafad'a mashi yacanza lauyer dan ni bazan iya d'aure ma k'arya gindi ba na gama bincike akan case d'inshi banga wani k'amshin gaskiya akan cewa gidan mallakinshi bane,,,yana fad'in haka yajuya yashige motarshi yabar court d'in. A nutse yake tuk'i inda kid'i me dad'i yake tashi a cikin motar ahaka har ya isa G.R.A a gaban wani tank'amemen gida yayi horn, megadi dasauri yazo yabud'e mashi gate yacinna kan motarshi a wajen da aka tanada dan ajiye motoci yaje yai parking sannan yafito hannunshi rik'e da briefcase d'inshi yashiga cikin babban gidan hayaniyar da yajiyo ne a main parlor yasa direct yawuce part d'inshi, Yana shiga ajiye yar briefcase d'inshi yayi yacire kayanshi yafad'a toilet dan yayo wanka. Bayan ya fito ya shirya kwanciya yayi saman makeken gadon dake cikin d'akin tare da maida idanunshi yalumshe. Ta haka ne nasamu damar k'are mashi kallo Barr Faruk dogo ne yana da haske sosai saidai bazaka kirashi fari ba fuskarshi doguwace med'auke da dogon hanci bakinshi d'an madaidaici ne, idanuwanshi manya ne sosai sannan yana da saje sirri a fuskarshi wanda yataimaka wajen k'ara ma fuskar kyau, gashin kanshi kawai zaka kalla kagane cewa shi bafullatani ne na usul, saidai yanayinshi da ka gani zaka gane ba mutum bane me yawan son hayaniya ba, saurayine wanda shekarunshi bazasu gaza 29yrs ba. Turo k'ofar da akayine yasa yabud'e lumsassun idanunshi ahankali yasafkesu a k'ofar wata mata ce tashigo cikin shiga ta alfarma tana kama da saurayin sosai saidai ita fara ce matar bazata wuce shekaru arba'in da bakwai ba, fuskarta d'auke da murmushi ta isa bakin gadon daga gefenshi tazauna tace Son ashe ka dawo? Dan guntun murmushi yayi yace Eh Momcy ban dad'e da dawowa ba. Shafa kanshi tayi tace kuma shine kakwanta? katashi muje kayi lunch nasan ka kwaso yunwa. D'agowa yayi yakalleta yace Mom... sai kuma yayi shuru. Murmushi tayi a karo nabiyu tace oh sorry su Hajiya Maijidda ce sukazo ita da Nasiba ya kamata ma kazo kugaisa. Marairaicewa yayi cike da Shagwa6a yace Mom ina buk'atar hutu yanzu please kisa akawo min lunch d'ina a nan bana son hayaniya. Matar tace shikenan Son yadda kakeso haka za'ayi bari inkawo maka ma dakaina. Murmushi yayi yace thanks mom. Tashi matar tayi tafita chan sai gata d'auke da tray tazo ta ajiye saman wani d'an center table tace son katashi kaci bari inturo Nasiba takawo maka drinks. Saurin cewa yayi a'a Momcy please kar kituro min ita yau banason yawan surutu kuma kinsan da ta zo damuna zatayi. Shikenan Son bari ni inje inkawo maka da kaina. Baice komai ba yatashi yanufi inda ta ajiye mashi abincin yazauna yafara ci. Bayan ya gama yad'auko System d'inshi yazauna yafara research aciki wayoyinshi ne da aka dinga kira yasa yad'auko su yakashe ganin zasu hanashi yin abinda yake son yi. *WASHE GARI* Tunda yaje wajen aiki files d'in da yagani kusan ukku a office d'inshi yasa ko kallonsu baiyiba yawuce yazauna ko minti goma da zama baiyiba secratry yashigo gaisheshi yayi sannan yawuce wajen da files d'in suke yad'auko yakawo mashi yace ranka yadad'e wannan daga gidan Alhaji k'asim ne suna gaiyatarka a matsayin lauyan da sukeso yatsaya masu akan gadonsu da dangin mamacin sukeso su cinye, sannan wannan kuma Alhaji Mamman ne ya aiko ya ce ya yi maka bayani duk wani abu da ake buk'ata suna ciki sannan wannan kuma na Alhaji Bashir ne ya..... D'aga mashi hannu da Barr Faruk yayi ne yasa yai shuru bai ida bayani ba. Hannu yamik'a mashi yace bani na gidan Alhaji k'asim bai musaba yamik'a mashi yace Oga sauran fa? Cike da k'osawa da maganar yace amaida masu ace na ce su samu wani lauyan. Juyawa sectary yayi yafita da files d'in Barr Faruk bud'e files d'in da ya amsa yayi yafara dubawa knocking d'in da akayi ne yasa yad'ago kai tare da cewa yes come in. Barr Bilal ne yashigo hannunshi rik'e da wani file zuwa yayi yazauna yace sannu Oga. Murmushi Barr Faruk yayi yace Yauwa Barrister ina fata dai ka samo min duk wani detail din da yadace. Eh toh ansamu abinda yasauwak'a mik'a mashi file d'in yayi yace saidai duk k'ok'arin da nayi ban samu full information ba wajen masu kula da prison d'in. Bud'e file d'in yayi yaduba yace Jawahir Muhammad Maikudi shine cikakken sunanta? Eh shine sunanta d'iyar wani hamshak'in me kud'i ce saidai a yanzu mahaifin nata baya raye, ana zarginta da kashe mutane kusan bakwai ko ma sama da haka ta hanyoyi daban daban. Jinjina kai yayi yace shikenan iyakar abinda kasamo game da ita? Gyara zamanshi yayi yace sannan abinda nak'ara sani shine itace tai silar mutuwar Barr Mubarak alokacin da yake k'ok'arin ganin ya tsaya mata kasancewar shi lauyan abokin mahaifinta ne sai yanemi yataimaka mata wajen fitar da ita ta hanyar k'aryata k'arar, a daren ranar da zai rasu ya je prison d'in ya gana da ita lokacin da yashiga ba'asan abinda yahad'a suba andai jiyo ta fasa k'ara nan ma'aikatan gidan yarin suka yi saurin zuwa dan gane ma idanunsu abinda yake faruwa ammah abinda yabasu mamaki shine ansameta ta shak'e mashi wuya tana kuka inda shi kuma yake k'ok'arin k'wace kanshi daga rik'on da tayi mashi dakyar aka samu aka 6an6areshi daga hannunta nan ma'aikatan suka fara bugunta inda shikuma aka fitar da shi ranshi duk a 6ace abinda aka kasa ganewa shine a matsayinshi na lauyanta minene yahad'a su fad'a? Tafiyar da yayi washe gari sai jin labarin mutuwarshi akayi wanda aka rasa dalilin haka saidai an sameshi cikin jini. Barr Faruk idanu yazuba mashi yana kallonshi. Barr Bilal cigaba yayi da cewa tun daga lokacin aka dinga surutu ana cewa ko dai aljanace ko kuma wani yabud'e mata tafita taje takashe shi, koda dai ba'a tabbatar da hakan ba aduk binciken da akayi babu wata hujja da tanuna haka sai kuma Barr Muhsin babban lauya kuma lauyan da yakasance lauyan mahaifinta wanda bayan rasuwarshi aka kawoka a matsayin madadinshi........ _Wannan littafin na kud'i ne ga duk me buk'ata zai biya d'ari biyu N200 Kacal zai turo MTN card ta wannan number d'in 09035938246 ko katuro 200 ta account number d'innan 5330055604 FIDELITY BANK, idan katura ka aiko da screen shot na transaction ta wannan number d'in 09035938246_ _Ga mutanen Niger zasu tura 300f ta wannan number d'in +22794775574_ _Gareku masoyan gaskiya_ _*GARA B'ASA! GARA B'ASA!! GARA B'ASA!!!* wannan gara'basa anyi tane kad'ai ga duk wanda keson karanta littafin *FANSAR RAI* da *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shaharariyar marubuciyar nan watau *AMINA ABBA UMAR* ga duk mai bukatar karanta duka novel's d'in biyu zai biya *N300* kadai domin samun damar karantasu cikin aminci, gareku masoyan gaskiya muna jiran ku nuna mana k'aunarku ta hanyar biyan *N300* kad'ai, idan duka biyun kakeso zaka turo kud'i ta wannan account number d'in 3092292135 FIRST BANK, ko kuma katin waya Mtn na d'aya daga cikin Numbers d'in nan 09035938246 ko kuma 07030792790, ko 07036073670, sai ka aiko da shedar biya ta d'aya daga cikin numbers d'in, sai munji daga gareku masoyanmu_ _Sis Nerja'art✍🏻_ [3/4, 16:05] Sis Nerja'art👰🏻: https://www.facebook.com/105966804349754/posts/105967661016335/?sfnsn=mo *......FANSAR RAI.......* _*STORY AND WRITTEN BY SIS NERJA'ART✍🏻*_ *INTELLIGENT WRITERS ASSO....®* [On Ward Together] _*DEDICATED TO ZM CHUBA'DO*_ *PAGE TWO* Barr Bilal cigaba yayi da cewa a lokacin da za'a yanke mata hukuncin kisa ne saboda batada lauya shine shikuma Barr Muhsin yafito yatsaya mata a matsayin lauyanta haka aka fara gabatar da shara'a sau biyu aka zauna kotu wannan zaman da za'ayi jiya shine zai kama na ukku toh shine wata biyu da suka wuce aka tsinci gawarshi a chan wani daji saidai ba'asan wanda yakashe shi ba. Barr Faruk ajiye biron da take hannunshi yayi yace kuma ba'ayi bincike aka gano wanda yayi kisan ba? Duk binciken da yadace anyi ammah ba'a samu komai ba agame da mutuwarshi, nidai gaskiya hankalina bai kwantaba akan yarinyar chan dan nima kaina ina tantama akan shara'arta kar kajefa kanka cikin halaka kabari kawai kotu tayanke mata hukuncin kisa kowa yahuta. Girgiza kai yayi yace bazan bari ayanke mata hukuncin kisa ba har sai na tabbatar da itace me laifin dan gaskiya a irin shekarunta bana tunani zata iya irin wannan aika aikan. Cikin sanyin jiki yace a'a Barrister kar kace haka. Shuru Barr Faruk yayi yacigaba da duba file d'in da aka kawo nata sai chan yarufe yajuyo yakalli Barr Bilal yace Barr Bilal ina nan akan batuna na son intaimaka mata dan haka zanje inyi magana da Alk'ali kome kenan gobe bayan azuhur zan zo muje karakani a chan prison d'in...tun kan yarufe baki Barr Bilal yai zumbur yamik'e tsaye yace ni kuma Oga? Kallonshi Barrister yayi yace Eh saboda inason samun wasu bayanai daga wajenta. Barr Bilal kamar zaiyi kuka yace shikenan Allah yakaimu zanyi yadda kace. Murmushi Barr Faruk yayi yace nagode sosai Barrister. Batare da ya ce komai ba yajuya yafita. Barr Faruk cigaba yayi da nazari akan file d'in Jawahir kafin daga bisani yatashi yabar office d'in. A chan gidan yari duk inda kakalla matane suke ta faman aiki a gefe d'aya nahango Jawahir duk'e gaban wasu mata masu kula da su hannunsu rik'e da bulali magana suke mata akan tatashi tayi aiki ammah tak'i ko motsawa batayiba bare asa ran zata tashi. D'aya daga cikin matan ne tad'aga bulala tashaud'a mata cikin fushi tace ke wace irin macece kullum ayi ta fama da ke akan kitashi kiyi aiki ammah kik'i. Kokad'an jawahir bata motsaba bare asa ran zata tashi. Su dukansu d'aga bulalen hannunsu sukayi suka dinga shaud'a mata ta ko'ina suke dukanta ammah ko kad'an bata motsaba kanta yana sunkuye k'asa ta runtse idanunta gam bugunta suke kamar sun samu jakka lokaci guda tasulale k'asa tafad'i saida suka ga bata iya motsi sannan suka barta nan mutum biyu yakamata suka tafi da ita d'akinta ana zuwa aka wurgata suka rufe k'ofar nan wajen tayi kwance idanuwanta a rufe gashin kanta duk ya baje mata fuska ahankali tad'ago hannunta tadafe kanta daga haka bacci me nauyi yayi awon gaba da ita. Ruwan sanyin da aka makaka mata a jiki ne yasa tayi saurin bud'e idanuwanta d'aya daga cikin masu tsaronsu ce abinci ta ajiye mata cikin wani d'an k'aramin kwano duka abincin bai wuce ayi loma biyar yak'are ba, a wulak'ance tace ga abincinki nan. Tashi tayi zaune tana kallonta da idanuwanta da suke lumshewa saboda wahala har matar tajuya tatafi. Maimakon taci abincin sai ma rarrafawa da tayi dakyar taje chan k'arshen ginin d'akin tad'age wani dutsi dan babba babba dayake ajiye cikin d'akin nata tad'auko wani d'an k'aramin littafi duk ya cumimiye me kama da diary tabud'e hannunta yana rawa tad'auko wata biro still dai hannunta yana rawa tafara rubutu chan kuma tarufe tamaida inda tad'auko tatashi tana tafiya tana rangaji takoma chan wajen da abincin yake tazauna d'aukowa tayi zata ci wata irin iska me karfi tataso a cikin d'akin k'ara jawahir tasaki nan tasulale tasume. Barr Faruk zuwa yayi yasamu Alk'ali sukayi magana Alk'ali Jinjina ma maganar tashi yayi yace anya barrister zaka iya wannan aikin? Nifa yarinyar chan hankalina bai kwanta da itaba. Murmushi Barr Faruk yayi yace Allah yagafarta malam hankalina ne bai kwanta da abinda ake zarginta akaiba nafiso inyi bincike intabbatar da gaskiya idan dai har nagano akwai sa hannunta a ciki toh zan janye daga tsaya mata. Alk'ali yace toh shikenan tunda ka ce haka Allah ubangiji yataimaka. Barr Faruk yace Ameen zanje insamu registrar muyi magana inyaso kafin azauna court a karo nagama ingama bincike akanta. Jinjina kai Alk'ali yayi yace hakane. Barr Faruk yana komawa gida a harabar gate d'in gidansu yaga wata irin dank'areriyar mota ko kallon motar baiyiba yazo zai wuce nan driver yai saurin fitowa yaje yalek'a ta window d'in motar daidai da Barr Faruk yayi horn dan abud'e mashi gate. Juyowa yayi yakalli driver d'in da yace ranka yadad'e d'alla'bai ne yake son magana da kai. 'Bata fuska yayi yace wanene kuma haka? Bud'e motar da akayi aka fitone yasa yajuya yakalli wanda yafito daga cikin motar Alhaji Mani yagani nan yak'ara had'e fuska har ya iso wajen daga saitin motar yatsaya sannu Barrister. Batare da ya juyoba ya amsa da yauwa. Alhaji Mani yace ina fata kaga sak'o na jiya dan ina ta Kiran wayarka inji daga gareka ammah baka d'auka. Cikin nuna rashin damuwa yace Eh nagani kawai dai bazan iya tsaya makaba so yakamata kasamo wani lauyan. Cikin d'aga murya yace haba Faruk meyasa zakayi min haka? Toh tsaya fad'i kud'in da kakeso inbiyaka kasan dai banda matsalar kud'i. Wani irin kallo Barr Faruk yayi mashi kafin daga baya yaja motarshi yashige cikin gate d'in da megadi tuni ya bud'e mashi. Alhaji Mani tsaye yayi yana bin motar da kallo cike da bak'in ciki da takaici Jinjina kai yayi tare da cize le6e yace tabbas bakasan wanene niba ammah zan fahimtar da kai,,,,juyawa yayi cikin 6acin rai yanufi wajen motarshi inda driver yai saurin binshi yaje yabud'e mashi k'ofa yashiga. Washe gari bayan azuhur Barr Faruk yakira Bilal a waya yace yana son ganinshi a office d'inshi. Bayan ya zo ne Barr Faruk yace yana so yarakashi gidan yari dan yagana da Jawahir. Hankalin Bilal ba k'aramin tashi yayiba gabad'aya yanemi nutsuwarshi yarasa ji yake kamar yace bazaijeba saidai baya iya yi ma Ogan nashi musu dan haka saida yahad'e wani wahalallen miyau sannan ya amsa da toh. Barr Faruk saida yagama wani aiki da yake sannan yakira shugaban gidan yarin sukayi magana akan zuwan da zaiyi yagana da Jawahir a matsayin shi na lauyanta meson kareta. Bayan sun gama wayar yamik'e yace ma Bilal suje. A cikin motar shi suka shiga suka kama hanyar prison na mata su dukansu shuru sukayi babu me magana kasancewar shi dama Barr Faruk ba me yawan magana bane, shi ko Bilal tsoro ne yataru yai mashi yawa ahaka har suka isa. Suna isa daidai zasu shiga k'ofar Barr Faruk bai ko tsaya yi ma masu gadi magana ba yanemi yawuce su dukansu tasowa sukayi suna cewa malam Lafiya ina zakaje? Wa kake nema? Batare da ya basu amsar tambayoyinsu ba yad'ago ID card d'inshi yanuna masu cikin sauri duk sukaja baya yawuce matan da suke zaune suna aiki nan duk suka zuba masu idanu suna kallonsu duk inda suka gifta binsu suke da ido wad'anda suke cikin Ceil ma haka suka dinga lek'osu k'ofa k'ofa suka dinga shiga duk inda aka nemi a tsaidasu Barr Faruk ID Card kawai yake nuna masu baya tsayawa dogon bayani da su, wasu ko basu tsaida su kasancewar sun san Barr Bilal ahaka har suka kai wajen wani d'aki inda me gadi na musamman akasa yana tsaron k'ofar inda daga gefen d'akinta d'akin wasu mata ne su ukku a ciki, Barr Bilal cike da tsoro yajuyo yakalli Barr Faruk yace Oga nan ne take. Cikin nuna rashin damuwa yace toh muje girgiza kai yayi yace a'a zan jiraka a daidai nan kaje kadawo ganin yadda yatsorata yasa yace shikenan nan yawuce zai tafi megadin d'akin yayi saurin mik'ewa yanufo wajenshi yace malam wa kake nema? ID Card din hannunshi yanuna mashi nan yai saurin bud'e mashi yana shirin shiga Megadin yace saidai ranka yadad'e...sai kuma yayi shuru Barr Faruk yana jin haka yaciro wayoyinshi daga cikin suit d'inshi yamik'a ma megadin sannan yawuce yashiga, tsaye yayi bakin karfunan k'ofar yana bin cikin da kallo wani d'an k'aramin kurkuku ne baida girma sosai kuma babu wadataccen haske a ciki Juyowa yayi yakalli me gadin yace ina buk'atar haske. Megadi zuwa yayi yad'auko wata torch light me haske sosai yahaska d'akin nan Haske yagauraya a d'akin wucewa Barr Faruk yayi yashiga tsakiyar d'akin yahangeta zaune kanta sadde a k'asa inda gashi yabaje mata fuska tsaye yayi yana kallonta kafin daga bisani yataka ya isa wajen da take tsugunnawa yayi gabanta ganin har lokacin bata d'ago ba yasa yace Jawahir . Shuru tayi tak'yaleshi kokad'an bata motsaba sake kiran sunanta yayi ahankali tad'ago kai takalleshi ta cikin gashinta da yake baje a fuskarta idanuwanta yakalla da sukayi jajir kamar garwashi inda fuskarta take a tamke babu fara'a ko kad'an wani irin kallo takeyi mashi, Barr Faruk tsugunne yayi shima yana binta da kallo a karo na ukku yakira sunanta. Cikin wata irin murya cike da k'araji tace kabar nan wajen!! tana fad'in haka ta sadda kanta k'asa inda gashin ya ida baje mata fuska. Mik'ewa Barrister yayi cikin sanyin jiki yawuce zai fita dan tabbas baiga alamun zai samu abinda yake son samuba daga gareta saidai me yake faruwa da ita da gabad'aya tacanza anya kuwa mutum ce ita? Sake juyawa yayi yakalleta yaga still dai kanta yana sunkuye dan haka yawuce yafita, tsaye yayi a daidai k'ofar d'akin yana kallonta ta jikin k'arfunan. Megadin wajen ne yazo yarufe k'ofar sannan yatsaya gefen Barrister Faruk yace 'Dallab'ai daman nasan mawuyacine a wannan irin lokacin ta iya yi maka magana dan lokutta da dama tana shiga cikin wannan yanayin. Juyowa Barr Faruk yayi yakalleshi yace in ba damuwa inason samun wasu bayanai daga gareka game da ita. Barr Bilal da yake mak'ale gefe d'aya yace a'a Oga da dai ka hak'ura kawai mun tafi. Shareshi Barr Faruk yayi yacigaba da cewa duk abinda kasani a game da ita nakeson ji daga gareka. Jinjina kai megadin yayi sannan yawuce yakoma wajen zamanshi nan Barr Faruk yabi bayanshi kujera yanuna mashi yazauna nan suka fara juyo sautin kukanta Barr Faruk har zai mik'e nan megadin yace a'a Barrister kar kaje dan kusan kullum sai tayi wannan kukan. Cike da mamaki yake kallonshi yace toh minene dalilinta na kukan? Girgiza kai yayi yace wannan ne dai ban saniba abinda dai kawai nasani a game da ita shine.... Wannan littafin na kud'i ne ga duk me buk'ata zai biya d'ari biyu N200 Kacal zai turo MTN card ta wannan number d'in 09035938246 ko katuro 200 ta account number d'innan 5330055604 FIDELITY BANK, idan katura ka aiko da screen shot na transaction ta wannan number d'in 09035938246_ _Ga mutanen Niger zasu tura 300f ta wannan number d'in +22794775574_ _Gareku masoyan gaskiya_ _*GARA B'ASA! GARA B'ASA!! GARA B'ASA!!!* wannan gara'basa anyi tane kad'ai ga duk wanda keson karanta littafin *FANSAR RAI* da *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shaharariyar marubuciyar nan watau *AMINA ABBA UMAR* ga duk mai bukatar karanta duka novel's d'in biyu zai biya *N300* kadai domin samun damar karantasu cikin aminci, gareku masoyan gaskiya muna jiran ku nuna mana k'aunarku ta hanyar biyan *N300* kad'ai, idan duka biyun kakeso zaka turo kud'i ta wannan account number d'in 3092292135 FIRST BANK, ko kuma katin waya Mtn na d'aya daga cikin Numbers d'in nan 09035938246 ko kuma 07030792790, ko 07036073670, sai ka aiko da shedar biya ta d'aya daga cikin numbers d'in, sai munji daga gareku masoyanmu_ _Sis Nerja'art✍🏻_ [3/5, 15:59] Sis Nerja'art👰🏻: https://www.facebook.com/105966804349754/posts/105967661016335/?sfnsn=mo *......FANSAN RAI.......* _*STORY AND WRITTEN BY SIS NERJA'ART✍🏻*_ *INTELLIGENT WRITERS ASSO....®* [On Ward Together] _*DEDICATED TO ZM CHUBA'DO*_ *PAGE THREE* Tun lokacin da aka kawo ta nan aka rufe a lokacin akwai wasu mata guda biyu masu irin laifinta na kisa an ke'bance su nan su kad'ai aka had'e su d'aki d'aya kasancewar duk wadda zakaga ankawo nan toh ta aikata babban laifi ne wanda za'ayi mata d'aurin rai da rai dan ba'a had'asu da k'ananun masu laifi, tun da aka kawota ban ta6a jin tayi magana da sauran matan biyun da aka had'esu ba dan ina lura da su sosai saidai ita take'be kanta ita kad'ai taraku'be wani lokacin tadinga kuka sosai abinda yafi bani mamaki shine idan dare yayi duk baccin da zanyi infarka sai na ganta zaune idanuwanta suna kallon wacchan yar k'aramar tagar da ke cikin d'akin kafin kaga ta kwanta bacci dawuya, yawanci zakaga ta baza gashin kanta ya rufe mata fuska kamar yadda kashiga kaganta. sauran matan biyu ganin bata biye masu yasa suka dinga tsangwamarta ammah bata biyesu idan ma aka kawo masu abinci saidai sudauka sucinye subarta bata ta'ba d'aga kai takallesu ba nikuma ganin haka yasa nafad'a ma masu kawo abincin saboda haka ne aka dinga fitar mata da nata daban, akwai wani lokaci da aka kawo masu abinci nan abokan zaman suka cinye nasu daidai ita kuma ta d'auko nata zata ci kawai suka taso suka zo zasu janye Kwanon abincin nata sai tarik'e batare da ta kallesuba ganin haka yasa suka kalli juna suka kwashe da dariya babbar wadda daga ganinta ba alamun imani atare da ita ne tanemi tafizge kwanon da k'arfi ammah sai takasa abun ya basu mamaki ganin da hannu d'aya tarik'e kwanon ammah ta kasa k'wacewa kanta dai yana sunkuye a k'asa a fusace babbar tawanka mata mari. Ba shiri tad'ago takalleta batare da ta saki kwanon ba ganin batada niyar saki yasa gudar tazo nan suka rufeta da duka suna bugunta ta ko'ina saida mukazo muka janyeta nan aka yi masu bulala akan laifin bugunta da sukayi saidai me wannan bulalar bata shigesuba dan sunji haushin bugun da akayi masu akanta dan haka da dare ma suka k'ara dukanta kafin su kwanta bacci kwanciyar nan da sukayi washe gari ba'a tashi dasuba koda akazo za'a fitar da su wajen aiki me tsanani da ake sakasu nan aka samesu kwance sun mutu ita kuma tana chan zaune k'arshen bango ta had'e kai da gwiwa kowa ya yi mamakin mutuwarsu nan aka fara zargin ko tana da hannu a ciki aka dinga dukanta ana tambayarta tafad'i yadda akayi suka mutu cikin k'araji tace ni ban kashesu ba, cigaba akayi da dukanta saida akayi mata jinajina sannan aka fitar da ita aka yankar mata wani k'aton fili akace tashare ko awa d'aya batayi ana zuwa aka samu wajen fes nan aka bata wanki dayawa akace tayi shima bata d'au lokaci ba aka samu ta gama saboda haka akayi tunanin ko wasu ke tayata dan haka aka tafi da ita kitchen aka bata nik'an markaden da za'a girki tunda tarik'e tafara juya kayan miyar bata tsayaba saida suka nuk'u duk mutanen wajen sukaita mamakin ganin ko alamar gajiya babu tare da ita bayan ak'alla duk rana mutum biyu akesawa sunuka ammah itako ita kadai tayi. Haka aka dinga bata aiki iri-iri duk dan tafad'i yadda akayi suka mutu ammah tak'i akayi duk binciken da yadace ammah ba'a gane dalilin dayasa suka mutuba kuma babu kwakkwarar shedar da tanuna itace tayi kisan dan haka aka kyaleta, kasan abinda yafi bani mamaki wani lokacin ko da ankawo mata abincin yadda aka ajiyeshi haka ake zuwa a d'auka bata ta'bashi ba kuma anrasa me takeci ni kaina nasha inyi la'be ko naga abincin da takeci ammah ban gani gashi duk yadda zakaso tayi magana batayi inma tayi toh ba wata me tsawo bace, Akwai wani lokaci da aka fita da ita za'a kaita wajen da zata gana da lauyanta Barr Mubarak ana fita tashak'e wata 'Yar aikin gidan nan da take matsa mata sosai dakyar aka samu aka k'waceta duk kacar da aka d'aureta da ita ammah nema tayi tagudu saboda haka ne aka hana fitowa da ita daga cikin d'akinta akace adinga barinta ko da lauyanta ya zo saidai yashiga yagana da ita a ciki, inba court za'ajeba ba'a fitowa da ita sai yau da naga anfito da ita ankaita ta yi aiki bansan dalilin hakan ba, ammah na fi tunanin dan ma'aikatan suna jin haushin yadda ita ake barinta bata aiki. Ko kad'an baka ta'ba jin maganarta dan hatta lauyoyinta ma haka zasuzo suyi ta faman mata tambayoyi ammah bata basu amsa daga k'arshe ma duk sai rasasu akayi saboda hakane nafara tunanin anya mutum ce. Ajiyar zuciya Barr Faruk yasafke tare da juyawa yakalli Ceil din da Jawahir take ciki sannan yamik'e yace nagode sosai Baba kuma ni insha Allahu zanyi k'ok'ari wajen ganin ta bani duk wata amsar da tadace. A'a Barrister kabi ahankali dan akwai had'ari acikin rayuwarta. Murmushi yayi yace kar kadamu Nan yajuya suka tafi Barr Bilal yana biye da shi yace barrister ka dai ji Komai da kunnenka ina fata yanzu zaka janye kudurinka nason ganin ka taimaka mata. Girgiza kai yayi yace ina nan akan bakana zan taimaka mata. Zaro ido yayi yace zaka taimaka mata? Toh nidai ba da niba dan ba abinda zaisa inshiga rayuwarta. Tsayawa Barr Faruk yayi yajuyo yakalleshi yace ni zan shiga rayuwarta kuma kaima dole kashiga yana fad'in haka yajuya yawuce yanufi chan wajen motarsu. Tsaye Barr Bilal yayi yabishi da kallo kafin daga baya yabi bayanshi suka shiga mota suna shirin tafiya wani ma'aikacin gidan yazo suka gaisa da su Barr Faruk yace Oga ya sanar da ni zuwanku ina ta jira ashe har kunzo. 'Dan guntun murmushi Barr Faruk yayi yace Eh munzo ai daman ya fad'a min baya nan toh kuma na kira wayarka ban samuba saidai shi ya yi ma sauran ma'aikatan bayanin zuwana saisa ban samu matsala ba. Yace Eh ai sun san da zuwanka da abinda zai kawoka dafatan dai ka gama? Eh toh kusan haka ammah zan dawo dan ban samu abinsa nake son samuba. "Toh shikenan idan ka dawo sai kata'bo ni, godiya barr faruk yayi mashi nan sukayi sallama yaja motar sukabar gidan yarin. Tunda yakoma gida tunanin labarin da megadi yabashi da yanayin da yaga jawahir a ciki yake tabbas har cikin ranshi yana da niyar taimakonta saidai me shima ya fara tantama akan hakan. Wayarshi yad'auko yakira shugaban me kula da gidan yarin yace gobe zai dawo zai tattauna da Jawahir dan yanason more information game da case d'inta sannan asa agyarata asa tayi wanka wannan gashin nata agyara mata shi. Dariya Mahadi yayi yace toh Barrister angama ammah wannan gashin nata ko angyara shi dakanta take yamitse abunta ammah shikenan za'ayi. Bayan sun gama wayar fitowa yayi yasamu Hajiya Nuratu a parlor tana waya zuwa yayi yazauna a gefenta har tagama wayar takalleshi tana murmushi tace Son ka fito? Murmushi yayi yace Eh Momcy d'azu ai na shigo lokacin kina sallah Ohk ina fatan dai ka ci abinci. Yatsina fuska yayi yace Eh Momcy na ci. Ba dan ta yarda da maganarshiba tace Allah dai yasa dagaske kake dan nasanka bakason cin abinci. Allah first love na ci. "Toh shikenan na yarda d'azu mukayi waya da Nasiba ta ce kwana biyu baka je wajentaba meyasa? Dan guntun murmushi yayi yace Momcy aiki ne yaimin yawa wata shara'a ce tasha min kai sosai saisa ma yanzu kikaga kullum ina gida ammah zan kirata a waya. Gyad'a kai tayi tace toh shikenan Allah dai yataimaka yashige mana gaba. Barr Faruk yace Ameen Momcy Daddy ya dawo ne? "A'a ya dai ce min yau zai dawo idan tafiyar ta samu inko bata samuba sai jibi" Allah yamaidoshi lafiya Momcy bari inje ina wani aikine in d'an ida. Toh Son badamuwa Allah yataimaka. Ameen Momcy. Washe gari wajen k'arfe sha d'aya kasancewar weekend ne yashirya yaje gidan yari dan yagana da Jawahir a office d'in shugaban yasafka kasancewar abonki shi ne sosai bayan sun gaisa ne Mahadi yace Barrister wai dagaske zaka tsaya ma Jawahir maikudi a wannan shara'ar tata? Murmushi yayi yace Eh insha Allahu ina da burin haka. Shuru yayi sai chan yace kuma kana gani babu wata matsala. Ta'be baki yayi yace bana tunanin haka. Shikenan bari insa akawo maka ita nan,,,wayarshi yad'auko yakira wata ma'aikaciyarsu suna gama wayar yakalli Barr Faruk yace abokina gatanan za'a kawota bari ind'an fita ana jirana a waje zan turo ma'aikacinmu ko akwai abinda kake buk'ata kafin intafi? Murmushi yayi yace bana buk'atar komai maybe kafin kadawo na gama abinda nake na tafi. Mahadi yace Eh gaskiya ina tunanin haka dan zan dad'e ammah kakula. Hannu yamik'a mashi sukayi musabaha yatafi. Barr Faruk wayarshi yashiga latsawa chan yajiyo yanayin tafiya kamar ana jan mutum d'ago kai yayi yakalli k'ofar wasu matane biyu jaye da wata yarinya andaureta da kaca hannuwa da k'afafuwa dakyar take tafiya har suka shigo da ita, ido Barr Faruk yazuba mata yana kallonta cikin ranshi yace wacece wannan? Matan ne sukace 'Dallabai gata Oga yace akawota. Kallon matan yayi yace wacece wannan? Jawahir fa nace akawo min? wannan ai itace jawahir din",,cewar d'aya daga cikin matan. Kallonshi yamaida ga yarinyar da aka shigo da ita take tsaye kanta sunkuye a kasa doguwa ce kalarta farace ko ma ace me haske sosai daga gani wahala ce tadisar da ita fuskarta me round ce hancinta dogo ne ba chan ba bakinta madaidaici koda tana cikin yanayi na wahala ammah hakan bai hana agane kyaunta, Jinjina kai yayi yace shikenan zaku iya bamu waje. Tsawa suka daka mata sukace bazaki tsugunna ba? Ahankali tazame k'asa ta tsugunna still dai kanta na sunkuye a kasa bata d'agoba, juyawa matan sukayi suka fita Inda wani ma'aikaci yatsaya daga bakin k'ofar yadda yana hangensu. Barr Faruk zuba mata idanu yayi yana kallonta tana kallon ankwar da take hannunta Ahankali yakira sunanta. D'ago kai tayi tana mashi kallon mamaki batare da ta amsaba. Numfasawa yayi yace Jawahir sunana Barr Faruk Sani Maishadda. Wani irin kallo tayi mashi cikin dasashiyar murya tamaimaita Sani Maishadda! Da mamaki yake kallonta yace kin sanshi ne? Wani irin murmushi tayi mai wuyar fassarawa sannan tace menene yakawo ka wajena? Ta6e baki yayi yace ba komai bane yakawo ni sai dan inaso intaimaka maki idan kika bani duk wani bayani da yadace zanyi k'ok'ari wajen ganin na fitar da ke daga cikin gidan nan. Lokaci guda fuskarta tacanza takoma kwata-kwata babu annuri tace bana buk'atar taimakon ka, Baki buk'atar taimako na saboda wane dalili nifa so nake intaimaka maki kifita daga gidan nan ammah idan har kika ban damar haka. Idanu tak'ura mashi tana kallonshi sai kuma chan tajuyar da kanta gefe d'aya tace bazaka iya taimaka min ba kabarni kawai ink'arasa rayuwata ahaka kar kajefa rayuwarka cikin hatsari dan shiga rayuwata daidai yake da ruguza duk wani farin cikin rayuwarka. No Jawahir kidaina cewa haka akowane lokaci ni me tsayawa ne bayan gaskiya kuma nasan ke bakida hannu a cikin kisan nan. Fashewa tayi da wani irin firgitaccen kuka tace wannan ba gaskiya bane Barrister kar kasaki kayi gigin shiga rayuwata gudun kar kayi silar rasa taka rayuwarka. Mik'ewa yayi tsaye yamatso kusa da ita yace ban damu da rayuwataba Indai akan gaskiya zanyi aikina. Cikin wata irin razanannar murya tace tabbas zaka aikata babban kuskure idan har kanemi kataimaka min zaka iya rasa rayuwarka kamar yadda lauyoyi biyu suka rasa tasu rayuwar. Cike da mamaki yake kallonta ganin yadda lokaci guda tahargitse yace jawahir kodai kina da hannu acikin mutuwar su Barr muhsin? K'ara sautin kukanta tayi tace ina gargad'inka kar kayi gigin shiga rayuwata katafi kawai. Matso da kujerarshi yayi yazauna a gabanta yace na ji zan tafi ammah inaso kifad'a min gaskiyar lamari akan kisan da akayi shin kina da hannu a ciki? Hannuwanta biyu masu d'aure da ankwana tasa tadafe kanta da su dataji ya fara sara mata k'ara tafasa da dukkan k'arfinta wanda yasa saida gabad'aya d'akin ya amshi shi kanshi Barr Faruk saida yada d'e kunnuwanshi har tagama k'arar idanuwanta yaga lokaci guda sun juye sun canza ta yi wata kala da ita. Barr Faruk d'auko wata Newspaper yayi ya ajiye a gabanta yace me zakice a nan? Ido tazuba ma hoton da yake manne jikin newspaper d'in kafin daga baya tajanye idanunta daga kallonta. Barr Faruk yace shin gaskiya ne wannan bayanin da akayi na hotonki da aka buga akan kin kashe mutane bakwai ciki har da nakusa da ke? Zumbur Jawahir tamik'e tsaye tare da ja baya kad'an tace ina sake gargad'inka kar kayi gigin shiga rayuwata kabari kawai ayanke min hukuncin kisa domin hakan shine kawai zai kasance *FANSAR RAI* kagaugauta zare hannunka acikin lamurra na banso kaima kajefa kanka cikin wahalalliyar rayuwa, dan taimakona daidai yake da barazana da rayuwarka,,,saurin dafe kanta tayi da taji ya sara mata. Daidai lokacin matan suka shigo sukace 'Dallabai 20 minutes d'in da aka baku ta cika. D'aga kai yayi cikin sanyin jiki yace kutafi da ita. D'ago kai Jawahir tayi takalleshi sannan tajuya suka riketa suka tafi. Ajiyar zuciya Barr Faruk yasafke tare da mik'ewa tsaye yafara zagaye d'akin maganganunta suka dinga tariyo mashi a k'walwa cikin ranshi yace kenan tana nufin da hannunta acikin kisan nan duk da akayi? Saidai taya hakan zai kasance bayan ita me k'ananun shekaru ce? Tunowa yayi da irin kallon da tayi mashi lokacin da za'a tafi da ita sai yaga gabad'aya idanuwanta sun canza sunyo waje, ahankali yace anya yarinyar nan mutum ce? Wayarshi ce da tafara ringing takatseshi daga tunanin da yakeyi dan haka yad'auki key d'in motarshi yaficce cikin sauri saboda wannan Kiran ya san cewa Alk'ali ne yake nemanshi a court. _Wannan littafin na kud'i ne ga duk me buk'ata zai biya d'ari biyu N200 Kacal zai turo MTN card ta wannan number d'in 09035938246 ko katuro 200 ta account number d'innan 5330055604 FIDELITY BANK, idan katura ka aiko da screen shot na transaction ta wannan number d'in 09035938246_ _Ga mutanen Niger zasu tura 300f ta wannan number d'in +22794775574_ _Gareku masoyan gaskiya_ _*GARA B'ASA! GARA B'ASA!! GARA B'ASA!!!* wannan gara'basa anyi tane kad'ai ga duk wanda keson karanta littafin *FANSAR RAI* da *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shaharariyar marubuciyar nan watau *AMINA ABBA UMAR* ga duk mai bukatar karanta duka novel's d'in biyu zai biya *N300* kadai domin samun damar karantasu cikin aminci, gareku masoyan gaskiya muna jiran ku nuna mana k'aunarku ta hanyar biyan *N300* kad'ai, idan duka biyun kakeso zaka turo kud'i ta wannan account number d'in 3092292135 FIRST BANK, ko kuma katin waya Mtn na d'aya daga cikin Numbers d'in nan 09035938246 ko kuma 07030792790, ko 07036073670, sai ka aiko da shedar biya ta d'aya daga cikin numbers d'in, sai munji daga gareku masoyanmu_ _Sis Nerja'art✍🏻_ [3/6, 15:07] Sis Nerja'art👰🏻: https://www.facebook.com/105966804349754/posts/105967661016335/?sfnsn=mo *......FANSAN RAI.......* _*STORY AND WRITTEN BY SIS NERJA'ART✍🏻*_ *INTELLIGENT WRITERS ASSO....®* [On Ward Together] *DEDICATED TO ZM CHUBA'DO* *PAGE FOUR* Suna janye da jawahir suka maida ta d'akinta suka wullar da ita ciki suka maida k'ofar suka gark'ame, Jawahir had'e kai da gwiwa tayi tafara fitar da kuka Marar sauti wata irin k'ara tafara ji me kama da kukan hadari saurin mik'ewa tsaye tayi tafara waige waige jin k'arar daga saman d'aki take yasa tayi saurin d'aga kanta sama wata irin razanannar k'ara tasaki tare da sulalewa k'asa tafad'i a sume. Barr Faruk bayan ya je wajen Alk'ali sun sake tattaunawa akan case d'in Jawahir nan ya amshi file d'inta yaduba akan dai laifin kisan ake zarginta list d'in mutanen da takashe yabi. Yana gama dubawa wasu information yad'auka akan mutanen sannan yatashi yatafi koda yakoma office d'in shi kiran Barr Bilal yayi a waya yace yanaso yaje yasamo mashi hotunan wad'anda ake zargin Jawahir ta kashe, Jim Barr Bilal yayi cikin ranshi ko baisoba dan a rayuwarshi bayason abinda zaisa yashiga Case d'in Jawahir, ba dan ya soba ya amsa mashi da toh zaiyi k'ok'arin hakan. Barr Faruk yace yatabbatar koma me ake kar yawuce zuwa gobe da safe. Barr Bilal ya amsa da insha Allahu. Suna gama wayar yatashi yakama hanyar gida yana isa a parlour yasamu Hajiya Nuratu zaune a main parlor tana ganinshi tayi murmushi tare da cewa sannu da dawowa Son Shima murmushin yayi yamatso yabata peck a goshi yace yauwa first love dafatan na dawo na sameki lafiya? Lafiya lau ya aikin? Alhamdulillah Momcy muna ta fama. "ai na gani Son dan yanzu kullum busy kake Allah ubangiji dai yataimaka" Barr Faruk yace Ameen First love Wai son ka je gidansu Nasiba kuwa? Murmushi yayi yace a'a Momcy yau dai nakeson zuwa. Shikenan son ya dai kamata kaje dan Allah kadaina wannan zurfin cikin naka kana son Nasiba ammah sai kadinga basarwa kadinga bata kulawarka ta hakane zata gane kana sonta. Murmushi yayi yace Toh Momxy insha Allah zanci gaba da k'ok'arin hakan. Allah yayarda dan wallahi idan har kayi wasa da damarka karasa Nasiba babu ruwana. Dariya yayi yace insha Allahu ma bazan rasataba Momcy kema nasan ai bazaki bari inrasata ba. Toh ya zanyi tunda kana ta ja mata aji ai sai inzare hannuna aciki. Marairaicewa yayi yace kai momcy keda zakiyi min fatan insameta yanzu ma bari inshiga ciki inshirya inzo inyi lunch zuwa anjima sai inje ingano Masoyiyata. Momcy cikin jin dad'i tace toh shikenan Son idan zakaje sai kayi min magana zan baka sak'o kakai mata Barr Faruk ya amsa da toh momcy nan wuce yanufi hanyar part d'inshi da kallo Hajiya Nuratu tabi d'an nata cike da so kafin daga bisani tamik'e itama tanufi part d'inta. Barr Faruk bayan ya shiga part d'inshi wanka yayi yashirya yafito yayi lunch bayan sallar la'asar ne yad'auki key d'in motarshi yabiya part d'in Momcy yafad'a mata zai tafi gidansu Nasiba wata Leda tad'auko dank'are da kaya tabashi tace yakaimata. Murmushi yayi ya amsa yace toh momcy mun gode Allah yak'ara girma da bud'i. Itama murmushin tayi cikin jin dad'i tace Ameen son. Yana fita motarshi yabud'e yasaka kayan a bayan mota sannan yabud'e mazaunin megadi yashiga yaja motar driver yahangeme mashi gate yabar gidan dagudu. Cikin k'ank'anin lokaci ya isa Malali Quarters a daidai k'ofar gidan Alhaji Sufyan Mai Nasara yayi horn nan megadi yataso cikin sauri yalek'o ganin motarshi yasa yai saurin hangame mashi tankamemen gate d'in gidan yashiga. A daidai inda ake parking d'in motocin gidan yai parking yad'auko wayarshi yayi dialing d'in wata number, saida takusan tsinkewa sannan akayi picking tare da yin sallama akace Hello Lovely. Lumshe idanunshi yayi dan sosai yakejin dad'in sunan da take kiranshi da shi yace Sweetheart kifito ganinan nazo. Daga chan 6angaren Nasiba tace ohk ina zuwa. Katse wayar yayi tare da Jingine kanshi jikin kujerar yana jiranta tafito. Tayi kusan minti biyar sannan tafito tana tafiya tana yauk'i, Nasiba chocolate colour ce bak'inta mekyau ne batada tsawo sosai saidai yar duma duma ce idan tana tafiya jikinta gabad'aya yake motsawa koda take bak'a ammah tana da kyaunta daidai ita idanuwanta dara dara ne, a nutse take takowa sanye cikin gown din material red da bak'in veil har ta iso wajenshi baisan ta zoba knocking tayi ma glass d'in motarshi nan yabud'e idanunshi tare da bud'e mata gaba fuskarta d'auke da murmushi tashigo tare da yin sallama. Shima murmushin yayi yana binta da kallo dan sosai tayi mashi kyau. Kallonshi tayi cike da shauk'in so tace lovely kallon fa? Lumshe idanunshi yayi yabud'e yace Sweetheart kinyi kyau sosai. Uhm nagode ammah fa fushi nake da kai. Zaro ido yayi yace da nayi maki mi? Juyawa tayi takalli window tace Komai ma kayi yau kusan kwana ukku baka kirani a wayaba kuma rannan munje gidan shine ko kafito mugaisa. Cikin kwantar da murya yace Ayya sorry sweetheart kinsan yanayin aikin namu yanzu kullum busy nake fara aikin nan da nayi a High Court natarar da aiki dayawa yana jirana yanzu haka shara'ar da na amsa zan tsaya ma mutane sun kai goma banda ma wad'anda namaida nace bazanyi ba saisa kusan kullum banda lokacin kaina cikin research nake. 6ata fuska tayi tace gaskiya lovely tun bakayi nisa da aikin nan ba ya fara fita a raina dan ko munyi aure nasan sai ka fi ba aikinka muhimmanci akaina. Girgiza kai yayi yace wannan ba hujja bace Nasiba shi aiki daban haka shima aure daban yake ina sonki Kamar yadda nasan kema kina sona kar kidinga sa damuwa a ranki akan haka koda bayan aurenmu ni nasan yadda zan kula da ke batare da nashiga hak'k'in kiba. Ajiyar zuciya tasafke tace hakane lovely saisa a kullum nake k'ara jinka acikin raina dan Allah kar karabu da ni komin daren dad'ewa. Murmushi yayi yace kar kidamu insha Allahu muna tare babu abinda zaya rabamu. Allah yasa, bismillah kazo mushiga cikin gida. Girgiza kai yayi yace a'a muyi hirarmu a nan. Kai lovely narasa meyasa bakason shigowa cikin gida kai wai kunyar Ummi ita babu ruwanta tana d'akinta ma. Ni bazan fa shigaba sweetheart nan dai nakeso muyi hirarmu. Shikenan lovely duk yadda kakeso haka za'ayi. Nan suka zauna suka dinga hira cike da k'aunar juna kafin daga bisani sukayi sallama kamar kar su rabu sukeji yad'auko kayan da Mom tabada yabata yamik'a mata nan tayi mashi godiya takoma cikin gida shikuma yafizgi mota yakama hanyar gida tuk'i yake a nutse yana tafiya nan yafara jin motsi a bayan motarshi ta mirror yakalla ammah baiga kowaba ji yayi kamar anwane glass d'in bayan motar dan haka yayi saurin waigawa ganin ba kowa yasa yajuyo k'iiiiittttt yataka burki cikin sauri yatsayar da motar a lokacin da yaga wata tsohuwa tukuf rik'e da sanda ta zo ta gifta mashi ta gaban motar ajiyar zuciya yasafke ganin saura kad'an yabigeta Allah yataimakeshi yatsayar da motar da idanu yabita yana kallonta d'ago kai tayi takalleshi saida gabanshi yafad'i wanda yasa baisan dalilin fad'uwar gaban ba cikin sauri yajanye idanunshi daga kallonta dan idanuwanta sun tsorata shi wasu ficificin idanu ne k'wayar Idanun blue ce ba kalar ta mutane ba saddar da kanta tayi tana rik'e da yar sandarta tawuce batare da ya sake kallon inda takeba yaja motarshi yatafi cikin ranshi yana cewa Allah ya taimakeni da na bugeta,,,tuk'i yake ammah gabad'aya kamannin tsohuwar suke fad'o mashi a rai ahaka har ya isa gida. Da dare bayan ya dawo daga masallaci sallar isha'i dinner d'inshi yaci sannan yaima momcy sallama yatafi part d'inshi system d'inshi yad'auko yafara searching kamar yadda yasabayi kusan kullum kafin yakwanta bacci, sai wajen k'arfe goma yagama yaje yai wanka yayi shirin kwanciya saida yakwanta yakira Nasiba a waya sukasha hirarsu har wajen 12 sannan sukayi sallama suka kwanta bacci. Baccinshi yake a nutse hankali kwance ahankali yafara jin taku a cikin d'akinshi ana k'was k'was k'was k'ara gyara kwanciyarshi yayi cike da jin dad'in baccinshi wani irin iska yaji fuuuuuu ta gefen kanshi ta wuce firgit yafarka daga baccin tare da tashi zaune yalalubo makunnin fitila yakunna yana bin d'akin da kallo ammah baiga komai ba kallon agogo yayi yaga k'arfe biyu da rabi na dare dan haka yad'auka acikin mafarkine yaji hakan nan yakoma yakwanta tare da kashe fitilar d'akin. Washe gari wajen k'arfe goma yagama shirinshi na zuwa wajen aiki yafito part d'in Momcy yaje ganin har lokacin bacci take yasa yawuce dining yayi breakfast d'inshi sama sama ganin yana shirin yin late yasa yawuce yanufi wajen aiki yana shiga secretary yashigo yakawo mashi wasu files yace inji Oga yabada yace abashi. Amsa yayi yafara dubawa nan yabud'e system d'inshi yafara aiki a ciki. Barr Bilal ne yaturo k'ofar yashigo Barr Faruk yana ganinshi yajanye files d'in da suke gabanshi tare da rufe system d'inshi. Hannu Barr Bilal yamik'a mashi sukayi musabaha sannan yazauna yana kallon files d'in da Barr Faruk yajanye yace Barrister wad'annan fa? Murmushi Barr Faruk yayi yace ina wani aiki ne agame da shara'ar da zamu zauna ta gidan marayun nan da ake son k'wacewa. Ayya Allah sarki gaskiya Barrister kana k'ok'ari sosai samun irinka a yanzu sai antona dan bakowa bane za'a iya kawo ma mak'udan kud'in da Alhaji Mani yakawo maka ba yak'i kar6a dan kawai yad'aure ma k'arya gindi. Murmushi Barr Faruk yayi yace ya maganar hotunan ina fata dai ansamo min? Murmushi shima yayi yace Eh na samo wajen registrar saidai me abin da mamaki yanayin da aka d'auko hotunan. Mamaki kuma? Barr Bilal bud'e briefcase d'inshi yayi yafiddo wani d'an envelop yamik'a ma Barr Faruk batare da ya yi maganaba shima yakar6a yabud'e yafara dubawa hotunan mutane bakwai ne yagani dukkansu hotunan anja masu layi da jini cike da mamaki yake kallon hotunan dukansu duk na manyan mutane ne biyu daga cikinsu ma suna da mulki acikin garin katsina, Barr Bilal ne yace kaga wannan jinin da ake sawa a hoton shine dalilin da yasa akace itace tayi kisan saboda ko lokacin da aka kashe babban me kud'in nan Alhaji Nalaraba shima anyi amfani da jinin a hotonshi sannan duk mutanen nan da aka kashe tana da alak'a da su wasu dan duk abokan mahaifinta ne. Ajiyar zuciya Barr Faruk yasafke yace ta wace hanya tabi tayi kisan shin da wuk'a aka kashesu ko da bindiga? Girgiza kai yayi yace babu d'aya daga ciki saidai ta hanyar rataya aka kashe wasu wasu kuma anshak'e masu wuya. Hotunan mutum ukku yaware waje guda yace wad'annan da kake gani mahaifi ne da 'ya'yanshi saidai bamusan dalilinta na kashesu ba. Kar6an hotunan yayi yana dubawa kafin daga bisani yace nagode sosai Barr Bilal da wannan k'ok'arin da kayi min Zanyi k'ok'arin zuwa inji daga gareta kafin inje ga dangin mamatan. Barr Bilal mik'ewa yayi tsaye yace ba damuwa Barrister saidai kakula da kanka. Kar kadamu a kowane lokaci natashi neman wani taimakon zan nemeka ina fata hakan ba matsala. Murmushi Barr Bilal yayi yace Eh babu matsala sai naji daga gareka,,Shima mik'ewa yayi yamik'a mashi hannu sukayi musabaha sannan barrister Bilal yatafi. Yana barin office d'in komawa Barr Faruk yayi yazauna bisa kujerarshi tare da d'auko hotunan yana sake dubawa kowane d'aya anyi mashi mark da jini, kwashewa yayi yasaka cikin envelop d'in sannan yamik'e yad'auki suit d'inshi yasaka sannan yawuce yafita. Motarshi yashiga yabar Kotun yanufi gidan yari tun a mota yak'ara Shugaban prison din yasanar da shi zuwanshi dan haka yana isa wani ma'aikacin gidan yatarbeshi yayi mashi jagora zuwa d'akin da Jawahir take a rufe, suna gaisawa da megadin da yake kula da gate din da su Jawahir suke nan yatashi yabude masu k'ofar d'an kurkukun da take ciki ana budewa yawuce yashiga d'akin duhu gareshi kasancewar tagar da take ciki yar k'arama ce dan hasken da ke akwai babu yawa ammah duk da haka zaka iya ganin wanda yake ciki, ganinta yayi chan k'arshen bango ta takure duk ta baje gashinta a fuskarta ta juya baya, daga bakin k'ofar me aiki prison d'in yatsaya inda Barr Faruk yashiga ciki fara takawa yayi ahankali ya isa wajen da take zaune ta sadda kanta a k'asa gashinta baya bari aga fuskarta..... _Wannan littafin na kud'i ne ga duk me buk'ata zai biya d'ari biyu N200 Kacal zai turo MTN card ta wannan number d'in 09035938246 ko katuro 200 ta account number d'innan 5330055604 *NANA HALLIRU* FIDELITY BANK, idan katura ka aiko da screen shot na transaction ta wannan number d'in 09035938246_ _Ga mutanen Niger zasu tura 300f ta wannan number d'in +22794775574_ _Gareku masoyan gaskiya_ _*GARA B'ASA! GARA B'ASA!! GARA B'ASA!!!* wannan gara'basa anyi tane kad'ai ga duk wanda keson karanta littafin *FANSAR RAI* da *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shaharariyar marubuciyar nan watau *AMINA ABBA UMAR* ga duk mai bukatar karanta duka novel's d'in biyu zai biya *N300* kadai domin samun damar karantasu cikin aminci, gareku masoyan gaskiya muna jiran ku nuna mana k'aunarku ta hanyar biyan *N300* kad'ai, idan duka biyun kakeso zaka turo kud'i ta wannan account number d'in 3092292135 FIRST BANK, ko kuma katin waya Mtn na d'aya daga cikin Numbers d'in nan 09035938246 ko kuma 07030792790, ko 07036073670, sai ka aiko da shedar biya ta d'aya daga cikin numbers d'in, sai munji daga gareku masoyanmu_ _Sis Nerja'art✍🏻_ [3/7, 20:57] Sis Nerja'art👰🏻: https://www.facebook.com/105966804349754/posts/105967661016335/?sfnsn=mo *......FANSAN RAI.......* _*STORY AND WRITTEN BY SIS NERJA'ART✍🏻*_ *INTELLIGENT WRITERS ASSO....®* [On Ward Together] *DEDICATED TO ZM CHUBA'DO* *PAGE FIVE* Tsaye yayi yana kallonta nan yabud'e baki zaiyi magana sai ji yayi cikin wata irin murya ta ce minene yamaidoka wajena? Bance kafita daga harkata ba, ko kaima ka zo ne dan ka gaji da rayuwarka kamar yadda su Barr Muhsin suka gaji da tasu rayuwar? Ko turoka akayi wajena kaima? Lokaci guda duk tajero mashi wad'annan tambayoyin idanu Barr Faruk yazuba ma gashinta da yabaje mata fuska kafin daga bisani yace jawahir ni banzo da niyar komai ba wajenki sai dan intaimaka maki kifita daga kurkukun nan fatana ki amsa min tambayoyin da zanyi maki. Cikin murya me amo tace su ma ai da haka suka zo min, babu amsar da zaka samu daga wajena idan har kana son rayuwarka katafi kabar wajen nan. Barr Faruk d'auko hotunan yayi yatsugunna a gabanta ya ajiyesu yace ina son kifad'a min gaskiyar al'amari akan kisan wad'annan mutanen. Jawahir ta cikin gashin takalli hotunan da yabajesu a gabanta d'aya bayan d'aya tadinga kallonsu chan sai tafasa wata irin k'ara tare da fashewa da kuka cikin sauri takai hannunta yana rawa tad'auko d'aya daga cikin hotunan tamanna a k'irjinta tare da dagewa da dukkan k'arfinta tafasa wata irin razanannar k'ara wadda saida tasa gabad'aya d'akin ya amsa shi kanshi ma'aikacin prison d'in da me gadi cikin sauri suka matso wajen d'akin dan sugane ma idanunsu me yake faruwa,,cikin wani irin murya wadda ba irin ta dazu ba tace ku kasheni inhuta rayuwata bata da sauran amfani nice nakashe su nima kukashe ni,,yanayin yadda take maganar zaka gane bata cikin hayyacinta tana rungume da hoton tamik'e tsaye cikin k'araji tace na ce kukasheni na gaji da rayuwar me kuke jira da bazaku kasheni ba, Barr Faruk mik'ewa yayi yanufi inda take tsaye cikin sauri taja da baya tare da d'aga mashi hannu tace kar kayi gigin Matsowa kusa da ni jin haka yasa yaja yatsaya. Jawahir zuwa tayi chan gefe tazauna tare da zuba ma hoton ido tana kallo tana me cigaba da kuka me shiga rai. Me aiki gidan da yashigo shima tsaye yayi yana kallonta yace ma Barr Faruk anya kuwa babu wani abu a k'asa akan hoton nan da tarik'e. Idanun Barr Faruk akanta yace nima ina tunanin haka ammah koma me kenan zanji daga gareta, tsaida kukan da take tayi idanuwanta suna a kan hoton kamar ba itace tagama kukaba tace kufita daga wajen nan. Tsaye sukayi cirko-cirko suna kallonta. D'ago kai tayi takallesu idanuwanta sunyo waje tazaresu duk jini ya kwanta cikin hargagi tace na ce kufita!!! Megadi ne yai saurin zuwa yakwashe sauran hotunan da suke baje yace ma su Barr Faruk muje. Tsaye Barr Faruk yayi yana kallonta nan tagalla mashi wata irin uwar harara tace me kake kallo katafi! Bai musaba yajuya yafita yana fita megadi yamaida k'ofar yarufe tare da mik'a mashi hotunan yace Barrister yakamata kafita daga harkar yarinyar nan, Zaidu me aikin prison yace ka ji da kanta ta furta cewa itace tayi kisan kabari kawai akasheta. Juyowa Barr Faruk yayi yakallesu yace ban tabbatar da hakan ba dole sai naji daga gareta kar kudamu zan barta yanzu tahuta saboda naga ganin hoton chan ya sa tashiga cikin wani irin yanayi,,,,yafad'a tare da kallon cikin Ceil din da jawahir take ciki ta kwanta a k'asa rungume da hoton tana me cigaba da kuka. Shima megadin kallonta yayi cikin sanyin jiki yace shikenan Allah yakaimu goben. Ameen yace tare da kar6ar hotunan yai masu sallama yajuya yatafi yana tunanin maganganunta musamman da tace shima anturoshi kamar yadda aka turo sauran lauyoyin cikin ranshi yace me take nufi da hakan? Su wane irin lauyoyi ne?Dole insamo amsar wannan tambayar. Yana komawa court direct office d'in Barr junaid yawuce yasameshi zaune yana aiki waje Barr Junaid yabashi yazauna tare da mik'a mashi hannu suka gaisa sannan yace ya dai Barrister naganka haka? Murmushi Barr Faruk yayi yace Barr Junaid inaso insan wanene Barr Muhsin inaso insan yanayin aikinshi da shida Barr Mubarak. Juyawa Barr Junaid yayi a kujerar da yake zaune sannan yace su ma manyan lauyoyi ne kamar ka. Girgiza kai yayi yace ba wannan nakeson ji ba inaso kafad'a min yanayin aikinsu sannan inaso insan ya akayi suka tsaya ma Jawahir a matsayin lauyoyinta shin wani ne yasasu ko su suka sa kansu kamar yadda nima nasa kaina?. Shuru Barr Junaid yayi sai chan yace nidai abinda nasani akan Barr Mubarak shi babban lauya ne kuma abokin mahaifinta gaskiya banda masaniya idan wani yasashi ko shi yasa kanshi a matsayinshi na abokin mahaifinta lokacin da yake raye. Ido Barr Faruk yazuba mashi yana kallonshi nan Barr Junaid yacigaba da cewa shikuma Barr Muhsin babban lauya ne kuma lauyan mahaifinta duk wani abu da mahaifinta zaiyi ko kwangila ko zai siya gida ko wani abu to barr Muhsin ne yakeda shaida akan haka dan shine lauyanshi bayan rasuwar Barr Mubarak ana shirin yanke mata hukuncin kisa nan shima yafito a matsayinshi na lauyan mahaifinta zai tsaya mata ammah bai samu nasarar hakan ba yarasu dan daga cikinsu babu wanda yasamu tattaunawa da ita dan Barr Muhsin ma ne yad'an samu wasu bayanai agareta har sun fara zama biyu a kotu ba'ayi zama na ukku ba yarasu. Shiko Barr Mubarak koda sau d'aya bai samu wani bayani agaretaba a iya saniba saidai ban saniba a ranar da yayi zuwa nak'arshe a wajenta har tashakeshi ko yasamu wasu bayan daga gareta,,,wannan shine abinda nasani agame da wad'annan lauyoyin. Murmushi Barr Faruk yayi yace nagode sosai abokina ni zan tafi idan wani taimakon yatashi zanzo innema. Cikin sauri yace Karufan asiri wallahi ni ban gaji da rayuwataba kaida dai kasa kanka kayi ranka yadad'e. Murmushi Barr Faruk yayi a karo nabiyu sannan yajuya yakoma office d'inshi yana shiga yamaida yarufe dan kar ma azo atakura mashi, kunna laptop d'inshi yayi yafara yan danne danne, chan kuma yad'ago yajingine kanshi a jikin kujerar da yake zaune idanunshi suna akan system d'in yana kallo kamar yana nazarin wani abu Ahankali yace yaushe zan samu wasu bayanai a wajen Jawahir har inyi bincike kafin kwanakin zama kotu suyi? Ajiyar zuciya yasafke yad'auko wayarshi yakira Barr Bilal yana yin picking ko sallama baiyi mashiba yace Barr Bilal inaso inbaka wani aiki. Barr Bilal daga chan 6angaren yace ba damuwa barrister. Mik'ewa Barrister Faruk yayi yace kabude datarka akwai abinda zan turo maka ina buk'atar asamo min ta kowane hali. Daga chan 6angaren Barr Bilal yace ba damuwa bari inbud'e. Kashe wayar yayi yakoma yazauna nan yatura mashi ta system d'inshi. Jawahir da ke kwance rungume da hoto tana kuka lokaci guda d'akin yafara girgiza cikin sauri tatashi zaune tana ja da baya ahankali ahankali tana girgiza kai hoton yana manne a k'irjinta gam har tajingine jikin bangon d'akin baki tabud'e tanaso tayi magana ammah takasa sai rawa da bakinta yakeyi wata irin guguwa ce a nad'e tanufo inda take lokaci guda tayi sama da ita tafara juyata a saman iska k'ara Jawahir take da k'arfi ammah muryarta bata fita bare tayi tunanin za'aji, ji tayi iskar tana nema tafizge hoton nan tak'ara matseshi a jikinta gashinta taji anja da k'arfi, wuntsila k'afafu tashiga yi tana kware baki tayi k'ara ammah still muryar bata fita tun daga nan aka sakota tafad'o k'asa tabuge goshi lokaci guda taga guguwar ta 6ace dakyar ta iya maida idanunta tarufe hoton dai yana manne a jikinta. Chan bayan sallar azuhur wata ma'aikaciyar wajen me suna Asabe tazo rik'e da d'an kwanon abinci a hannunta har lokacin jawahir tana nan wajen da take tana shigowa ajiye kwanon tayi tare da warware dorunar da take hannunta tashad'a ma Jawahir, dakyar ta iya bud'e idanunta cike da wahala takalleta babu alamar fara'a a fuskarta tace tashi zaune watau ke bacci kikeyi ko? K'ara shad'a mata bulalar tayi tace ance maki hutu ake a gidan yari idan akazo ke me laifi ce babu ke babu hutawa kitashi kici abinci za'a baki wani aiki. Jawahir idanu tazuba mata tana a kwancen batare da ta tashi zaune ba,,a fusace tasake d'aga bulalar tak'ara shad'a mata cikin tsawa tace kitashi nace!!! Jawahir dakyar ta iya tashi zaune tana rungume da hoton a k'irjinta. Zaro ido matar tayi tace menene wannan nake gani a hannunki Kamar hoto? Waye yabaki shi? Shuru Jawahir tayi tana cigaba da kallonta da rinannun idanunta. Hannu matar tamik'a mata tace mik'o min shi nan. Jawahir k'ara matseshi tayi a k'irjinta batare da tayi maganaba. A fusace matar tad'aga bulalar tacigaba da zuba mata tana cewa na ce kibani ke daman bakida kunya sai anayi maki magana kidinga ma mutane shuru nice daidai dake dole ki ladabtu a cikin gidan nan,,ganin yadda take bugunta ammah ta k'i tamiko hoton yasa matar takai hannu da tsiya tana nema takwace shi jawahir ganin yana shirin 6arkewa yasa tasakar ma matar, matar harara tabanka mata tana nishi tace da baki sakiba da yau kinga yadda zanyi dake, nan tajuyo da hoton tana kallo tayi murmushi tace dakyau wannan had'ed'en guy d'in kike kallo ko shima kasheshin zakiyi? Shuru Jawahir tayi tare da duk'ar da kanta k'asa. Murmushi matar tayi a karo na biyu tace koma minene a cikin ranki kicireshi babu ke babu fita daga nan. Ahankali jawahir tabud'e baki tace kibani hoton. Harara matar tawurga mata tace bazan bayarba zuwa zanyi ink'onashi dan haka na baki minti biyar kici abincin kafin indawo infita da ke wajen aiki,,,tana fad'in haka tajuya zata fita. Bata ji alamun tashin jawahir ba kawai sai ganinta tayi a tsaye a gabanta fuska a murtuk'e cikin k'araji tace na ce kiban hoton. Matar ta tsorata da yanayin da taganta ammah tadake bata nuna ba tace bazan bayarba bari ma kiga ketashi zanyi tana d'ago hoton zata keta jawahir takai mata wata irin cacuma tahad'eta da jikin bango. Da dukkan k'arfinta tashake mata wuya idanuwanta sukayo waje muryarta tana rawa tace idan har kikayi gigin 'barka hoton nan sai na kasheki, k'arshen tsorata Kande ta tsorata nan tayi saurin sakin hoton gabad'aya jikinta 6ari yakeyi, jawahir na ganin ta saki hoton tayi wurgi da ita gefe tafad'i, mik'ewa Kande tayi dagudu taficce a tsorace ko tsayawa rufe k'ofar batayiba saidai megadi yazo yarufe dan yana ta tambayarta lafiya ammah inaa bata tsaya saurareshiba bare tabashi amsa. Jawahir ko d'aukar hoton tayi tana takawa dakyar ta isa wajen wannan dutsin da yake cikin d'akin tad'aga tad'auko dan cimimiyayyen littafinta tasaka hoton ciki tamaida ta ajiye ma'ajiyinta da bakowa yasan da shiba, tana ajiyewa tayi kwanciyarta a wajen tadage kanta sama tana kallon rufin d'akin. Barr Faruk cigaba yayi da bincikenshi inda a gefe d'aya yake tunanin anya kuwa yarinyar nan tana da lafiya? Toh kodai mahaukaciya ce? Ammah meyasa maganganunta basuyi Kama da na marassa hankali ba? Ganin baida amsar tambayoyinshi yasa yayi tsaki cike da takaici sannan yacigaba da aikinshi har wajen k'arfe ukku sannan yatashi yatafi gida. Bayan sallar la'asar yana kwance a d'akinshi yana dannar waya Mom taturo k'ofa tashigo yana ganinta ajiye wayar yayi tare da yin murmushi. Zuwa tayi tazauna bakin gadon tace son kana nan ashe ai na d'auka ka fita? Eh Mom ina nan wallahi na gaji ne saisa ban fitaba. Cike da jin tausayin d'an nata tace Allah sarki Son ai kana ma k'ok'ari da aikin nan Allah ubangiji dai yacigaba da rufa asiri. Cikin jin dad'i yace Ameen Momcy. Yauwa daman zuwa nayi inyi maka albishir da cewa Daddynka yana nan dawowa gobe. Cike da jin dad'i yatashi zaune yace Momcy dagaske gobe Daddy zai dawo? Murmushi tayi tace Eh haka yace min. Kai Alhamdulillah gaskiya naji dad'i bari inkirashi intuna mashi da tsarabar da nace yasiyo min. Momcy tace ai ya ma fad'a min ya siyo maka kaima kasan bazai iya mancewa da shalelenshi ba, ni yanzu burina idan yadawo atsaida maganar aurenku da Nasiba dan nidai na k'agara inga bikkinku. Shafa kai yayi cike da jin kunya. Ganin haka yasa momcy tamik'e tace bari inje in ida aikin da nake daman zuwa nayi in isar da sak'on da yabani yace infad'a maka dan ya kira wayoyinka d'azu bai samuba. Murmushi yayi yace Allah sarki Daddyna aiko na gode bari ma yanzu zan kirashi waya. Momcy tace hakan dai yakamata,,nan tawuce tafita Barr Faruk wayarshi yad'auko cike da jin dad'i yakira Daddynshi. _Free Page_ _Wannan littafin na kud'i ne ga duk me buk'ata zai biya d'ari biyu N200 Kacal zai turo MTN card ta wannan number d'in 09035938246 ko katuro 200 ta account number d'innan 5330055604 FIDELITY BANK, idan katura ka aiko da screen shot na transaction ta wannan number d'in 09035938246_ _Ga mutanen Niger zasu tura 300f ta wannan number d'in +22794775574_ _Gareku masoyan gaskiya_ _*GARA B'ASA! GARA B'ASA!! GARA B'ASA!!!* wannan gara'basa anyi tane kad'ai ga duk wanda keson karanta littafin *FANSAR RAI* da *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shaharariyar marubuciyar nan watau *AMINA ABBA UMAR* ga duk mai bukatar karanta duka novel's d'in biyu zai biya *N300* kadai domin samun damar karantasu cikin aminci, gareku masoyan gaskiya muna jiran ku nuna mana k'aunarku ta hanyar biyan *N300* kad'ai, idan duka biyun kakeso zaka turo kud'i ta wannan account number d'in 3092292135 FIRST BANK, ko kuma katin waya Mtn na d'aya daga cikin Numbers d'in nan 09035938246 ko kuma 07030792790, ko 07036073670, sai ka aiko da shedar biya ta d'aya daga cikin numbers d'in, sai munji daga gareku masoyanmu_ _Sis Nerja'art✍🏻_ [3/8, 19:10] Sis Nerja'art👰🏻: https://www.facebook.com/105966804349754/posts/105967347683033/?substory_index=0&sfnsn=mo *......FANSAR RAI.......* _*STORY AND WRITTEN BY SIS NERJA'ART✍🏻*_ *INTELLIGENT WRITERS ASSO....®* [On Ward Together] *DEDICATED TO ZM CHUBA'DO* *PAGE SIX* Washe gari Barr Faruk bayan ya tashi cikin sauri yafara shiri dan 11 flight d'in su Daddy zai safka gashi har 10 ta yi, yana gama shirin yafito yasamu Momcy ta taimaka ma yan aikin gidan angyara ko'ina sai k'amshi yake tashi ga kwalliya da taca6a kasancewar ita macece me son gayu sosai, cikin jin dad'i Faruk ya k'arasa wajenta yana cewa momcy duk shirin tarbar Dad ne? Murmushi tayi tace sosai ma kusan wata d'aya megida bai nan ai dole Shima murmushin yayi yace Hakane momcy nan yagaisheta ta amsa tace muje kayi breakfast gashinan a dining, kallon agogon da take manne a tsintsiyar hannunshi yayi yace momcy zanje d'auko Dad fa. Itama juyawa tayi takalli agogon da take manne a bangon d'akin tace ai dasauran lokaci kaje dai ko yayane kad'an yi dan nasan da yadawo bazaka zauna wani breakfast ba. Faruk bai musaba yawuce yanufi dining Momcy tabishi tahad'a mashi nan yazauna yana yi, ya d'anci ba laifi yamik'e nan yace ma momcy zai tafi dan a lokacin baifi 10 minutes jirgin su Dad yasafka ba. D'aya daga cikin maka-makan motocin da suke harabar gidan yashiga saida yakama hanyar airport sannan yakira a wajen aiki yasanar da su bazai samu damar shigowaba yau. Yana isa daidai lokacin jirgin yasafka dan haka yafito yatsaya yana jira afara fitowa. Idanu yazuba ma masu safkowa daga saman matattakalar har saida kusan rabinsu suka safka sannan yahango Dad d'inshi, cikin sauri yawuce yaje yatarboshi cike da farin ciki. Shima kanshi Alhaji Sani Maishadda cikin jin dad'i yarungume d'an nashi d'aya tilo cike da jin sonshi a ranshi Faruk ne yace sannu da dawowa Daddyna ina farin ciki sosai da dawowarka. Shafa kanshi yayi yace nima ina farin ciki da nadawo nasamu shalelena lafiya. Murmushi Faruk yayi yace nagode Daddyna, muje ga motar chan, Faruk taya Dad d'aukar kayan sukayi suka nufi wajen motar da yazo da ita. Tunda suka shigo mota suka kama hanyar gida hira kawai suke cike da farin cikin ganin juna ahaka har suka isa, a harabar gidan suka samu momcy tsaye tana jiran dawowar mijinta ai yana fitowa daga mota taje tarungumeshi bata damu da Faruk da yake tsaye a wajenba, shiko d'aukar babbar jakkar yayi yashiga da ita gida yabarsu nan tsaye suna Murnar ganin juna. Yana ajiye jakkar yaje yad'auko sauran kayan lokacin su mommy har sun haye sama zata taimaka ma mijin nata yakimtsa. Barr Faruk a nan parlor yazauna saman kujera yad'auki wayarshi yakira Barr Bilal yana yin picking yace ya dai Barr Bilal ansamu kuwa? Daga chan 6angaren murmushi Barr Bilal yayi yace har yanzu dai saidai ina k'ok'arin ganin na samu saidai bari inturo maka wasu bayanan da nasamo. Ohk ba damuwa katuro bari ind'auko system d'in,,kashe wayar yayi yamik'e yanufi part d'inshi yana shiga yajiyo shower akunne ruwa na ta tsiyaya wucewa yayi yanufi toilet din dan yakashe yana kashewa juyowar da zaiyi yaga kamar giftawar mutum cikin sauri yafito ammah baiga kowaba cikin ranshi yace maybe idanunshi ne sukayi mashi gizo dan haka yaje yad'auki laptop d'inshi yafita yakoma parlor har lokacin su momcy basu fitoba dan haka yazauna yacigaba da aikinshi. Yana cikin yi su Dad suka fito suka sameshi Dad yace Shalele ana ta fama da aiki ko? Murmushi yayi yace Eh Dad,,,nan yature system d'in yak'ara yi ma Dad din nashi sannu da hanya. Zama Dad yayi gefen d'anshi yace son ina fata babu wata matsala ko? Girgiza kai yayi yace babu. Momcy ce tace kasan ma idan akwai bazaice maka akwaiba ni abinda yake bani mamaki da aikin nan kullum cikin aiki ake ba hutu. Dad ne yace ai daman aikin lauya ya gaji haka saidai hak'uri fatanmu dai Allah ubangiji yataimaka mashi acikin aikinshi. Nan suka amsa da Ameen. Momcy zuwa tayi takawo ma Dad girkin da tasa aka shirya mashi nan yazauna yana ci Barr Faruk yana gama aikinshi janye laptop d'in yayi suka cigaba da hira da iyayenshi cike da nishad'i, Dad tsarabar da yayo yad'auko yaba kowa nashi hatta ma'aikatan gidan sannan yafitar da wata tsarabar yace ma Faruk ta Nasiba ba. Cike da jin kunya ya amsa yace toh Dad mungode. Sai wajen azuhur sannan suka tashi sukayi alwallah shi da Dad d'inshi suka tafi masallaci bayan sunyo sallah ne a hanyarsu ta dawoba Dad yace Son meyasa kak'i accepting d'in Alhaji Mani da yanemi kakasance lauyanshi da zai tsaya mashi ya amshi gidanshi? Kallon Dad din yayi cike da mamaki yace Dad wa yafad'a maka? Murmushi yayi yace ai kasan yayan abokina ne muna gaisawa da shi sosai gaskiya bazanji dad'iba idan har baka tsaya mashiba. B'ata fuska Faruk yayi yace Dad kasan bazan iya bin bayan rashin gaskiya ba, kuma shi Alhaji Mani baida gaskiya, gidan wasu marayu ne yakeso intsaya mashi ya amsa. A'a Son ban tunanin haka baka saniba ko gidanshi ne. Allah Dad dagaske nayi bincike ba nashi bane, na bashi hak'uri dan ni aikina babu Magud'i a ciki gaskiya kawai nake goya ma baya, marairaicewa yayi yace please Dad katayani da addu'a Allah yashige min gaba akan wannan aikin nawa banda buri a rayuwata da yawuce intaimaka ma masu gaskiya wajen ganin na kwato masu hak'k'insu dan daman wannan dalilin ne yasa naje nakaranci law. Cikin sanyin jiki Dad yace Hakane Son insha Allahu zan ci gaba da tayaka addu'a kamar yadda nakeyi a kullum. cikin jin dad'i yace nagode sosai Daddyna. Suna shiga gida direct part d'inshi yawuce a saman kujera 3 seater yakwanta tare da d'age kanshi sama tunaninshi d'aya yadda shara'a kusan biyar suka tasoshi a gaba acikin wata biyu ko'ina k'ok'ari yake wajen samun bayanan da suka dace saidai shara'ar jawahir itace kad'ai matsalar shi har yau baisamu jin komai daga wajenta ba. *BARRISTER UMAR FARUK.* Alhaji Sani Maishadda da Hajiya Nuratu haifaffun garin Daura ne dake cikin jihar katsina sun fito daga family d'aya na wani babban Alk'ali Nasir mai shadda, 'ya 'yanshi ukku a duniya Alhaji Abdul'aziz ne babba sai Alhaji Umar sannan autarsu Hajiya Kilima, Hajiya Nuratu diyace ga Alhaji Umar shikuma Alhaji Sani Maishadda d'a ne ga Alhaji Abdul'aziz su biyu iyayenshi suka haifa shi da k'anenshi kasancewar iyayensu masu son junansu ne yasa suka had'a ya'yansu auren zumunci, shi da d'iyar k'anen babanshi Hajiya Nuratu bayan bikkinsu ne Allah yayi ma mahaifinta rasuwa yarage daga kakanninta sai yan uwan babanta biyu suka rage mata dan dama mahaifiyarta wajen haihuwarta Allah yayi mata cikawa. Alhaji Sani Maishadda babban d'an kasuwa ne yana da manyan shagunan shi a cikin garin katsina da plaza wannan dalilin ne yasa bai zauna a Daura garin iyayenshi ba yazauna a cikin garin katsina. Hajiya Kilima a chan garinsu take auren wani kansilan garin tana da yaranta biyar Shekararsu Alhaji Sani Maishadda hud'u da aure sannan Allah yabasu haihuwa suka haifi Umar Faruk sunan Mahaifin Mom da yarasu aka sa mashi, bayan shi sun haifi ya'ya biyu ammah duk sun rasu tun daga nan kuma basu sake haihuwa ba, duk son duniya suka d'auka suka d'aura ma d'annan nasu tilo, ya yi primary da secondary school a makarantu masu tsada a cikin garin katsina inda daga gefe d'aya ya samu iliminshi na islamiyya bakin gwalgwado, koda Faruk yake d'an masu kud'i wanda yakeda gata gaba da baya ammah hakan baisa yatashi sargataccen yaroba yana da hankali da tausayi sosai dan tun yana k'arami Indai yaga almajiri to duk kud'in da suke hannunshi sai ya bashi inma babu to wajen mahaifinshi yake zuwa ya amso yabada. Wata rana lokacin yana ajin k'arshe a secondary school yana kallon wani film yaga yadda ake shara'a ana fafatawa sai abun yaburgeshi sosai yaji yana son aikin dan haka yaje gidan wani makwabcinsu abokin Daddynshi dayake lauya ne yamatsa mashi saida yaje da shi kotu yaga anyi shara'a a gabanshi wata taburgeshi wata kuma batayi mashi dad'iba ganin yadda wasu da gaskiyarsu ammah ake masu fin k'arfi dan haka ne yace shiko baida karatun da zaiyi sai na law. Iyayenshi ma suka amince da hakan dan duk abinda yakeso su ma shi suke so. Yana gama secondary school d'inshi suka tura shi chan USA a chan yayi karatun Law d'inshi tsawon shekaru shidda yazama babban Lauya yadawo, lokacin da yadawo ana gwagwata wata Shari'a wanda makwabcinsu ne yake yinta kusan shekara d'aya nan yadamk'a mashi ita kuma yai nasarar lashewa, haka yatsaya da wani justice Samir suka kara a wata Shari'a nan ma yalashe, hatta shi kanshi Barr Muhsin sunyi wata shara'a da shi. Nan Dadynshi yafara cukucukun sama mashi aiki dayake abu ga masu kud'i aka bashi a Shari'a court. Barr Faruk baya tsaya ma duk Wanda bai da gaskiya ko da bai saniba yatsaya maka daga inda yagano kaine ba akan gaskiya ba zai barka yace kacanza lauya, ahaka yafara yin suna yana a cikin wata na takwas da fara aikinshi Barr Muhsin yarasu nan aka d'aukoshi aka maida shi a High court aka bashi muk'amin shi, a ranar da yafara zuwa court d'in ya amshi Shari'a guda biyu da Barr muhsin yafara bai idaba na wasu bayin Allah, Watanshi biyu a court d'in yazo sukayi wata shara'a bayan sun gama tasu ne a ranar akazo akayi ta jawahir yaganta tabashi tausayi yaji yana da gurin tsaya mata. Nasiba d'iya ce ga wani chairman nagarin katsina Alhaji Sufyan abokin Dad d'inshi ne itama maminta k'awar mommynshi ce, bayan gama karatunshi ne da yadawo suka had'u da ita ta zo gidan, sannan shima momcy tana aikenshi a gidansu wajen Hajiyarta, momcy ce tayi mashi sha'awar ya auri Nasiba shima dayake ya lura da nutsuwarta sai ya amince suka fara soyayya har zuwa yanzu da ake shirin tsaida maganar aurensu degree d'inta kawai ake jira ta ida had'awa. **** **** Wayarshi ce da tafara ringing yasa yatashi zaune daga kwancen da yake yad'auko wayar ganin Nasiba ce yasa yayi murmushi tare da yin picking yace sahibata y kk? Daga chan 6angaren amsawa tayi da lafiya kaima dafatan haka Habibyna. Nima Lafiya nake saidai....shuru yayi Saidai me??? Cewar Nasiba. Ahankali yace saidai tunaninki da nake yawan yi. Dariya tayi cikin jin dad'i tace wallahi nima haka nake fama da tunaninka wai bazakayi ma su Daddy magana ba suzo sunema maka aurena nifa hankalina ba zai kwantaba indai banga anyi aurenmu ba dan ina tsoron yan matan nan nasan suna sa maka ido saisa na kasa samun nutsuwa. Dariya Barr Faruk yayi sosai yace lallai Nasiba da alama zakiyi kishi. Ta6e baki tayi kamar tana a gabanshi tace inma kaji ance kishi to kad'an kenan dan hauka ma zan iya yi akanka. Cikin jin dad'i yace nagode sosai My wife to be insha Allah. Lumshe idanunta tayi tace kaifa me zaka iya yi akaina idan akace wani yana sona. Murmushi yayi cike da k'asaita yace bana ma tunanin akwai wanda zai iya jayayya da soyayyar da nikeyi maki dan nasan na riga da na mallake zuciyarki. Uhm Allah lovely hakane fa nidai fatana kakasance tare da ni har abada. "wannan ba matsala bane sweetheart dan nima fatan da nake kenan a rayuwata,,,kallon agogon bango yayi ganin biyar tayi yasa yace Sweety zan kiraki da anjima yanzu zan fita wani d'an aiki da zanyi. 'Bata fuska tayi tace nifa wallahi aikin nan ya fara isata duk shi yake cinye min lokaci na. Murmushi yayi yace kar kidamu zamuyi waya kikular min da kanki. Ahankali tace Uhm hmm,, nan sukayi sallama yakashe wayar, mik'ewa yayi yad'auko key d'in motarshi yafito yabar gidan. Hanyar unguwar yari yakama yana zuwa saida yabiya wajen Ogan prison d'in suka gaisa yafad'a mashi zai he yaga Jawahir nan yakira wani ma'aikacin gidan suka tafi tare suna shiga saidai suka gaisa da megadi nan yabud'e masu wajen Jawahir daga bakin k'ofa ma'aikacin yatsaya inda Barr Faruk yashiga ciki yasameta tsaye wajen yar k'aramar tagar da take a d'akin ta juya baya, matsawa yayi ahankali, muryar Jawahir yaji cikin sanyinta tace akowane lokaci gargad'i nikeyi maka akan kanisantar da kanka daga gareni ammah akowane lokaci k'ara kusanto kanka kakeyi shin wai ka gaji da rayuwarka ne? Dan guntun murmushi yayi yace kusan haka Indai akan aikinane toh ban damu da rayuwartaba, jawahir ya kamata ki fahimceni nifa banzo da niyar incutar da rayuwarkiba. Cikin muryar kuka tace haka su ma sauran suka fad'a, nidai shawarar da zan baka shine kafita hanyata kabarni inmutu dan mutuwar itace tadace da rayuwata. Cike da mamaki yace meyasa kikace haka jawahir? Batare da ta juyoba tace saboda itace sakamakon abinda na aikata. Girgiza kai yayi yace bazan yarda da maganarkiba jawahir dan bakiyi kama da wadda tayi kisan ba, nidai dama nakeso kibani intaimakeki tahanyar fad'a min dukkan abinda yafaru ta hakane kawai zan iya taimaka maki. Girgiza kai tayi batare da ta juyoba tace babu abinda zaka iya sani a game da ni, ina k'ara baka shawara kayi baya da ni inko ba hakaba zakayi da kasani a rayuwarka dan kaima baza'a ta'ba barinkaba. Matsowa yayi yace jawahir suwanene bazasu ta'ba barina ba? Juyowa tayi taimashi wani irin kallo sannan tajuya takoma tazauna. Biyota Barr Faruk yayi yace Jawahir kinyi shuru kiban amsa. Maimakon tayi magana sai ma had'e kai da gwiwa datayi tacigaba da kuka. Barr Faruk ya yi juyin duniyar nan tayi magana ammah tak'i kan dole yajuya yatafi yabarta cike da jin haushin rashin maganar da takeyi mashi. _*Free Page*_ _Wannan littafin na kud'i ne ga duk me buk'ata zai biya d'ari biyu N200 Kacal zai turo MTN card ta wannan number d'in 09035938246 ko katuro 200 ta account number d'innan 5330055604, *NANA HALLIRU* FIDELITY BANK, idan katura ka aiko da screen shot na transaction ta wannan number 09035938246_ _Ga mutanen Niger zasu tura 300f ta wannan number d'in +22794775574_ _Gareku masoyan gaskiya_ _*GARA B'ASA! GARA B'ASA!! GARA B'ASA!!!* wannan gara'basa anyi tane kad'ai ga duk wanda keson karanta littafin *FANSAR RAI* da *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shaharariyar marubuciyar nan watau *AMINA ABBA UMAR* ga duk mai bukatar karanta duka novel's d'in biyu zai biya *N300* kadai domin samun damar karantasu cikin aminci, gareku masoyan gaskiya muna jiran ku nuna mana k'aunarku ta hanyar biyan *N300* kad'ai, idan duka biyun kakeso zaka turo kud'i ta wannan account number d'in 3092292135 FIRST BANK, ko kuma katin waya Mtn na d'aya daga cikin Numbers d'in nan 09035938246 ko kuma 07030792790, ko 07036073670, sai ka aiko da shedar biya ta d'aya daga cikin numbers d'in, sai munji daga gareku masoyanmu_ _Sis Nerja'art✍🏻_ [3/9, 14:43] Sis Nerja'art👰🏻: https://www.facebook.com/105966804349754/posts/105967347683033/?substory_index=0&sfnsn=mo *......FANSAR RAI.......* _*STORY AND WRITTEN BY SIS NERJA'ART✍🏻*_ *INTELLIGENT WRITERS ASSO....®* [On Ward Together] *DEDICATED TO ZM CHUBA'DO* *PAGE SEVEN* Gudu yake sosai yana neman ma6oye cike da tashin hankali yawaiga yakalli wata tsohuwa tukuf saman iska tana biye da shi gashin kanta me tsawo sosai wuta tana kamawa ta bisa shi wata yar bukka ce da yahango cikin sauri yanufi wajen bukkar dan yasamu mafaka k'ark'ashin wasu tulin ciyawu yashiga yaboye zufa take kwarara a jikinshi ta ko'ina, yana kallon matar tashigo tatsaya tana kalle kalle chan kuma sai yaga ta fara nad'ewa siffar jikinta tana komawa ta macizzai, wani irin k'aton maciji takoma wanda saboda girmanshi sai ahad'a kusan mutane k'attai ukku sannan ayi fad'in macijin ahankali yake tafowa yanufo wajen ciyawar, k'arshen tashin hankali ya shigeshi dan ya san yau kwananshi sun k'are duk yadda yaso yatashi yagudu ammah yakasa dan ya san ko da ya tashi baida wajen tsira,,,,k'arar fad'uwar wani abu ne yasa yafarka firgit daga baccin da yake gabad'aya ya yi zufa jikinshi sai 6ari yake waige waige yafara yi a d'akin tare da kunna makunnin fitila ajiyar zuciya yasafke tare da furta Alhamdulillah da yaga ba dagaske bane mafarki yayi, glass cup ne yagani a tsakiyar d'akin afashe tabbas k'ararshi ne yatadashi daga baccin da yake yi, mamaki yafara taya cup d'in yashigo d'akin shi har yafashe, kallon agogo yayi ganin k'arfe d'ayan dare yasa cikin sanyin jiki yakoma yakwanta batare da ya kashe bedside lamp d'inba kasa komawa bacci yayi dan mafarkin da yayi ya bashi tsoro sosai dan ko a film bai ta6a ganin maciji mai girman wanda yagani a mafarkin ba, saidai tsohuwar da yagani tana binshi tabbas ya ta6a ganin fuskarta ammah kuma a ina? Tunowa yayi da tsohuwar da yagani ya kusa bugewa lokacin yana tuk'in mota, Zumbur yatashi zaune yana k'ara tuno fuskarta tabbas itace to kodai ba mutum bace? Girgiza kai yayi yace wannan nasan sharrin mafarki ne ba komai ba nan yakoma yakwanta tare da sake yin wata addu'a har wajen k'arfe ukku idanunshi biyu yana tunanin mafarkin da yayi kafin daga bisani bacci yad'aukeshi. Har yatashi dasafe jikinshi babu k'wari tun daga ranar kusan kullum sai ya yi mafarki da tsohuwar nan kowace rana da irin mafarkin da zaiyi na tsoro akanta, kwana ukku bai samu yaje wajen Jawahir ba saboda wata Shari'a da suka shiga tsawon kwanakin a chan garin Kano saida sukayi nasara sannan yadawo gida saidai duk da haka jawahir tana a ranshi ya ce Barr Bilal yadinga kwatanta zuwa wajenta ko a dace shi tafad'a mashi wani abu akanta ammah kullum sukayi waya Barr Bilal cewa yake bata ma kallonshi bare tayi mashi magana, shidai Barr Faruk ba dan ya yardaba dan yasan dakyar ne idan yana zuwa saboda ya lura kamar tsoronta yakeji. Ranar da yadawo ganin dare ya yi yasa baijeba yai zamanshi gida dan yahuta amsa waya ko har yagaji da masu kira suna tayasu murnar nasarar da sukayi. Washe gari koda yaje aiki yalek'a yan ayyukan da suka dace yayi sannan yatashi yana shirin fita Barr Bilal yashigo office d'inshi kallonshi yayi yace barrister fita ma zakayi ko? Eh zanje Chan priso. Barr Bilal yace Allah kau Barrister da zaka bi ta shawarata da ka kyale yarinyar nan k'ila ma ba mutum bace. Kaidai kasani matsoracin kawai nidai sai na je daman koda kace min ka je ban yarda da kaiba. Murmushi Barr Bilal yayi yace k'ara da kagane hakan dan tabbas banjeba. Wucewa Barr Faruk yayi yace ni kaga tafiyata kar ka6ata min lokaci, nan yawuce yafita yashiga motarshi yatafi. Yana shiga zaune yasameta ta Jingine kanta a jikin bango tana kallon sama, tsayawa yayi daga gefenta yace Jawahir lokaci yana k'urewa duka fa yanzu kwana hud'u yarage azauna kotu banda wata kwakkwarar hujja da zan kareki da ita, murmushi tayi batare da tad'ago kantaba tace Barrister ya kamata ace abubuwan da kake gani a mafarkinka ya sa ka janye daga tsaya min da kakeso kayi bazan gaji da fad'a maka kafita daga rayuwata ba, Cike da mamaki yake kallonta yace mafarki kuma? Wane irin mafarki kike magana inayi? Batare da ta kalleshiba tace na san ka sani tun daga tsohuwar da kagani ta gifta maka ta gaban mota zuwa ga mafarken da kakeyi da ita, shawarar da zan baka kawai itace kazare hannunka daga cikin wannan shara'ar. Mamaki ne ya ida kashe Barr Faruk yace jawahir ya akayi kikasan tsohuwar da mafarkan da nakeyi? Waye yafad'a maki bayan nasan babu wanda yasani inba niba kuma ban fad'a ma kowaba anya kuwa zargin da akeyi ba gaskiya bane ke ba mutum bace? 'Dan guntun murmushi tayi lokaci guda kuma hawaye suka gangaro mata tace wannan amsar ce nima nakasa ganewa a yanzu saisa nafi buk'atar mutuwa akan rayuwata. Idanu yazuba mata yana kallonta ba k'aramin firgita yayi da maganartaba nan yafara tunani akan matum ko aljan ce? Bai ida tabbatarwa ba saida yaji ta ce nasan dole kayi tunani akan hakan ammah ni abinda nasani shine ni mutum ce kamar kowa. Girgiza kai yayi yace ban yadda da hakan ba, idan ke mutum ce ya akayi kikasan tsohuwar da nakusa bugewa har da mafarken da nikeyi. Had'e kanta tayi da gwiwa tafara rusa kuka tace Barrister bakada hali irin na su Barr Muhsin bazan gaji da cemaka kazare hannunka ba dan banso kashiga wahalalliyar rayuwa. Cikin sanyin jiki yace na ji haka ammah idan kinsan banda hali irin nasu toh me zai hana kifad'a min tarihinki, sannan su Barr muhsin wane irin haline garesu? Shuru tayi nan yasake maimaita mata Numfashin da yaji ta fara safkewa ne yasa yai saurin k'ara matsawa kusa da ita da mamakinshi sai yaga har ta yi bacci, cikin sauri yaja da baya yace anya kuwa yarinyar nan mutum ce? Juyawa yayi yafita yaje yasamu megadi zaune a wajen da yake zama tare da ma'aikacin prison d'in da sukazo tare da shi, cikin sanyin jiki yace Baba inaso inmaka tambaya akan jawahir in bazaka damuba. Murmushi megadi yayi yace nikuma insha Allahu zan fad'a maka abinda nasani. Zama yayi daga gefen megadin yace Baba inaso kafad'a min a iya saninka shin jawahir tana wasu abubuwa na mamaki masu kama da na aljannu? Murmushi yayi yace tabbas nima kaina abinda nakeso insani kenan dan wasu lokuttan inji tana wasu irin surutai tana kuka, a da duk ayyukan da ake fitar da ita tanayi ammah hannunta babu kanta ko kad'an da zaka gani kace tana cikin wahala ko aikin aka fita da ita baka ganin alamar gajiya atare da ita,,kai abubuwa da dama dai inkaga tayi sai ka dasa alamar tambaya saidai gaskiya nafi tunanin mutum ce saboda akwaita da kula da addini dan da lokacin sallah ya yi zakaga tayi alwallah tayi Sallah inma babu ruwa zata rok'eni insanmata ruwa tayi alwallah ammah nima fa ina yawan kokwanto akanta har yau na kasa gane gaskiya akanta. Ajiyar zuciya Barr Faruk yasafke yace shikenan baba Nagode sosai da bayaninka. Yana fita a mota tafiya kawai yakeyi ammah tunaninshi yana ga jawahir duk ya rasa ya ma zaiyi dan yakasa gane kanta. Yana isa court direct office d'in Barr Bilal yawuce Barr Bilal yana ganinshi yace Allah yasa ba maganar jawahir kazo min da itaba dan wallahi da na ganka gabana har fad'uwa yakeyi. Murmushi Barr Faruk yayi tare da zama yace kaidai ka cika tsoro ni ba wannan yakawoni ba nazo inmaka tambaya agame da aikin su Barr muhsin. Idanu Barr Bilal yazuba mashi yana kallonshi nan Barr Faruk yacigaba da cewa inaso kafad'a min agame da aikinsu waye yasasu suka tsaya ma jawahir? Dan d'azu take wata irin magana tace min wai taga ni ba irin su Barr Muhsin bane banda irin halayyarsu. Girgiza kai yayi yace kamar yadda nafad'a maka banda masaniya akai saidai gaskiya Barr Muhsin yana kar6ar cin hanci Indai har zai tsaya ma mutum a matsayin lauya sannan akwai wata rana da nazo zan kawo mashi wasu files lokacin yana tsaye a gaban office d'inshi da alama bud'ewa zaiyi aka kirashi a waya na ji yana magana yana cewa kar sudamu shi zai kar6i k'arar yatsaya mata sannan za'a turo mashi 5 millons abarmashi aikin a hannunshi shi ya san yadda zaiyi komai, koda yajuyo yaganni duk sai yacanza fuska alamun baiji dad'iba nan yace ma Wanda suke wayan yabari zai kirashi su ida magana,,,tun daga lokacin da naga ya tsaya a matsayin lauyan jawahir yasa raina yaban tabbas akanta ake maganar kuma ya amshi cin hanci dan yatsaya mata saidai shi ma Barr Mubarak a yadda naji ance sai wane da wane yake tsaya mawa wannan ne kawai iya abinda nasani akan aikinsu. Murmushi Barr Faruk yayi yace nagode sosai da bayaninka. Shima murmushin yayi yace bakomai. Bayan ya koma gida ma haka yawuni baida tunani sai na maganar jawahir akan mafarkinshi da tsohuwar da yakusa bankewa da mota, shin wai taya jawahir tasan duk wannan, yarasa meyasa har yanzu ta k'i tayi mashi wani kwakkwaran bayani ta barshi sai wahala yake,,wani irin haushi yaji yace anya bazan zare hannunaba akan shara'ar yarinyar nan inbari akashe ta ba? Saurin girgiza kai yayi yace hakan bai daceba yakamata inbari infara jin ta bakinta sai idan na tabbatar da tana da laifi sannan inzare hannuna. Wasa wasa har kwana biyu yana zuwa yana ta fama da jawahir tayi mashi bayani ammah ta k'i ko kad'an ma bata damuba da hukuncin da za'a yanke mata na kisa, Daren da zasu shiga court yazo yasameta ana shirin fita da ita za'a kaita wajen horo kallon ma'aikatan wajen yayi yace yanaso abarta zaiyi magana da ita dan haka suka kyaleta saboda sun san matsayinshi da kuma yadda yake a wajen shugaban gidan yarin. Komawa tayi tazauna tare da kallonshi da mamakinshi sai yaga tayi mashi murmushi ta ce Barrister kaidai na lura baka gajiya kana da burin taimaka ma wadda rayuwarta batada sauran amfani. Shima murmushin yayi yace kokad'an ba haka bane jawahir ina da burin taimaka makine dan bana tunani kina da hannu a kisan nan saboda bakiyi kama da muguwa ba. Lokaci guda fara'ar fuskarta tagushe tace idan kuma ya kama ni me fuska biyu ce fa? Murmushi yayi me k'ara ma fuskarshi kyau yace da ace haka ne da zan iya fahimta. Girgiza kai tayi tace babu abinda zaka iya fahimta akaina barrister. Haka dai kikace saidai kinsan gobe ne zamu zauna kotu ammah har yau bansamu kowane irin bayani akanki ba bansan me zanceba, ya kamata *KIYARDA DANI* bazan ta'ba cutar da rayuwarki ba inma wani abu su Barrister Muhsin sukayi maki Toh ni banzo da niyar cuta agareki ba. Tun kan yarufe baki tace nasan da hakan dan da ace ba hakaba da bazaka ta'ba kai wannan lokacin ba kaima. Cike da mamaki yace kenan zaki kasheni? Shuru tayi tare da kauda kanta k'asa. Barr Faruk yace shin dagaske ne akan zargin da akeyi na cewa kina da hannu akan mutuwar su Barr Muhsin? Mik'ewa tayi tsaye tare da takawa tamatsa chan wajen yar tagar tatsaya d'an guntun murmushi tayi wanda yafi kuka ciwo yace Barr Mubarak shine abokin mahaifina ya yi shirin taimaka min saboda wani guri nashi shine kad'ai abinda nasani ammah bansan game da mutuwarshi ba sannan Barr Muhsin lauyan mahaifina ne ya yi shirin taimaka min shima saboda wani dalili nashi nadaban ba wai dan ya ku'butar da ni ba, shin wai miye amfanin rayuwar mutanen da babu komai a ransu sai zalunci? Laifi ne mutuwarsu? Taya kake tunani zanso rayuwa bayan na rasa duk wani farin ciki nawa na rayuwa,,,,fashewa tayi da kuka tace rayuwarsu batada sauran amfani a duniya bana nadama akan mutuwar kowa a yanzu hatta ni kaina idan namutu bazan ta'ba nadama ba akan haka,,,, juyowa tayi takalleshi tahad'e hannuwanta biyu tace na rok'eka kataima kar kaje kotu gobe kabari kawai akasheni dan mutuwar ta fiye min rayuwata. Barr Faruk bakinshi mutuwa yayi yarasa me ma zaice mata jin anfara kiran sallah ne yasa tawuce tashige wani d'an k'aramin kewaye da yake cikin Ceil din wanda girmanshi bai fi tak'i hud'u ba. Ajiyar zuciya yasafke sannan shima yafita dan yaje yayi sallah, bayan ya dawo ne yasameta har ta kwanta tayi bacci dan haka yatafi yana mamakin yadda da ranta ya 'baci toh sai tayi bacci. _*Free Page*_ _Wannan littafin na kud'i ne ga duk me buk'ata zai biya d'ari biyu N200 Kacal zai turo MTN card ta wannan number d'in 09035938246 ko katuro 200 ta account number d'innan 5330055604, *NANA HALLIRU* FIDELITY BANK, idan katura ka aiko da screen shot na transaction ta wannan number 09035938246_ _Ga mutanen Niger zasu tura 300f ta wannan number d'in +22794775574_ _Gareku masoyan gaskiya_ _*GARA B'ASA! GARA B'ASA!! GARA B'ASA!!!* wannan gara'basa anyi tane kad'ai ga duk wanda keson karanta littafin *FANSAR RAI* da *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shaharariyar marubuciyar nan watau *AMINA ABBA UMAR* ga duk mai bukatar karanta duka novel's d'in biyu zai biya *N300* kadai domin samun damar karantasu cikin aminci, gareku masoyan gaskiya muna jiran ku nuna mana k'aunarku ta hanyar biyan *N300* kad'ai, idan duka biyun kakeso zaka turo kud'i ta wannan account number d'in 3092292135 FIRST BANK, ko kuma katin waya Mtn na d'aya daga cikin Numbers d'in nan 09035938246 ko kuma 07030792790, ko 07036073670, sai ka aiko da shedar biya ta d'aya daga cikin numbers d'in, sai munji daga gareku masoyanmu_ _Sis Nerja'art✍🏻_ [3/10, 20:03] Sis Nerja'art👰🏻: *......FANSAR RAI.......* _*STORY AND WRITTEN BY SIS NERJA'ART✍🏻*_ *INTELLIGENT WRITERS ASSO....®* [On Ward Together] *DEDICATED TO ZM CHUBA'DO* *PAGE EIGHT* Barr Faruk daga nan direct gidan Barr MB yawuce wanda yakasance lauya ne me kare masu k'ara babban lauya ne tun a Shari'ah court yasanshi da yafara aiki a chan kafin ayi mashi transfer amaidoshi High Court yana isa gidan a cikin mota yazauna yad'auko waya yakirashi yana yin picking yayi mashi sallama, bayan ya amsa ne yace dan Allah Barrister idan kana gida kafito gani a k'ofar gidanka. Barr MB yace k'ofar gidana kuma Barr Faruk? ina fata dai babu wata matsala. Murmushi yayi yace babu. Ohk shikenan bari infito ganinan. Amsawa yayi da toh sannan yakashe wayar. Yana nan zaune ba'a fi minti biyar ba Barr MB yafito nan Barr Faruk yabud'e mashi gidan gaba dan yashigo cikin motar suyi magana bai kawo komai a ranshiba yazo yashiga tare da mik'a mashi hannu suka gaisa fuskarshi d'auke da murmushi yace ai da rabon ma zaka sameni dan ban dad'e da dawowa ba daga gidan wani Alhaji Mansur akan maganar kotu da zamu zauna gobe. Murmushi Barr Faruk yayi yace Allah sarki akan shara'ar jawahir ko? Barr MB yace Eh wallahi wannan shed'aniyar yarinyar idan kaganta baka ta6a cewa zata iya kisa. Da mamaki yake kallonshi yace kai yanzu har ka yadda da ta yi kisan. Kallonshi yayi yace a'a me zai hana in k'i yadda bayan mutanen da takashe hatta lauyoyinta ma bata barsuba saida takashesu mun fa dad'e muna fafatawa akan wannan shari'ar kusan wata goma kenan, na tabbata dan baka ta'ba zuwaba kaga shara'ar da kaima abun sai ya baka mamaki ai gobe nasan dole ayanke mata hukuncin kisa saboda batada lauyan da zai tsaya mata inma akwai to tabbas babu abinda zai iya yi. Murmushi Barr Faruk yayi cike da jin dad'i dan yasan tabbas Barr MB baisan shine lauyan da zai tsaya mata ba, gyara zama yayi cike da jin dad'in bayanin da yake kora mashi yace ammah Barrister taya akayi ita yarinyar tabi manyan mutanen takashe su kuma har suka iya tsayawa? Dariya Barr MB yayi yace toh nima dai abinda ban saniba kenan dan nidai anbiya ni kud'in aiki ankuma fad'a min itace tayi kisan tadinga binsu d'aya bayan d'aya tana kashewa kuma abinda zai baka mamaki daga danginta sai abokan mahaifinta takashe. Barr Faruk idanu yazuba mashi yana kallonshi yace toh wanene yashigar da k'arar? Shuru yayi sai chan yace mutane ukku ne kuma duk abokan mahaifinta ne d'aya daga cikinsu ya je gidan yatarar da ta yi kisa nan take gargad'inshi da shima yashirya tana nan zuwa gareshi shine yakira police aka kamata bayan ya koma gida daga nan yashigar da k'ara a kotu Jinjina kai Barr Faruk yayi yace saidai har yanzu ban gamsu da hakan ba. Murmushi Barr MB yayi a karo na biyu yace koma menene ni ban damuba tunda an lale min kud'ina yanzu jira nike agama shara'ar a ida cika min kud'ina. Girgiza kai Barr Faruk yayi yace ammah hakan ba daidai bane. Barr MB har ya bud'e baki zaiyi magana kome yatuno sai kuma yafasa yace ina saurarenka minene yake tafe da kai kayi min Kiran gaugawa haka. 'Dan yatsina fuska Barr Faruk yayi yace daman zuwa nayi mugaisa dan kwana dayawa rabon da muhad'u tunda nabar aiki a court d'inku. Barr MB ba dan ya yardaba yace toh shikenan Nagode kasan yanayin aikin ne namu sai ahankali. Hakane Allah ubangiji yataimaka mana. Ya Amsa da Ameen nan sukayi sallama yafita daga motar shikuma yaja motarshi yatafi Yana isa gida bai lura da su Dad da suke parlour zaune ba har zai haura saman step sai jin muryar Dad yayi ya ce Shalele. Tsayawa yayi tare da juyawa yadawo yana murmushi yazauna yace Dad ashe kuna nan ban lura da ku ba. Momcy ce tace taya zaka lura da mu ka shigo wani a birkice da kai. Sosa k'eya yayi yace wallahi momcy gajiya ce nayi. Uhm daman inba gajiya ba minene acikin aikin lauya aini da ka bi ta tawa da bakayi aikinba. Daddy yace a'a Nuratu kidaina wannan maganar dan bata daceba albarka kawai yakamata musa mashi acikin aikinshi dan yana bakin k'ok'arin shi kuma ni abun alfahari na ne inga d'ana ya kasance jajirtacce. Momcy cikn sanyin jiki tace hakane Alhaji. Daddy yace yauwa,,sannan yamaida kallonshi ga Faruk da yasunkuyar da kanshi k'asa yace Son daman akan maganar sa ranar aurenka da Nasiba wata nawa kakeso asa? 'Dago kai yayi yakalleshi cike da jin dad'i yace Daddy ranar aurenmu za'a tsaida? Murmushi Daddy yayi yace Eh haka nake buri Son dan yanzu auren ne yadace da kai tunda ka samu aiki sannan shi Alhaji Sufyan shi yakirani waya yace mufito atsaida ranar aurenku. Sunkuyar da kai yayi cike da jin kunya yace Daddy duk lokacin da kuka tsaida ya yi min. Momcy tace shegen gora ji yadda ya marairaice kamar duka ammah tunda yace haka kawai Alhaji asa shekara guda. Saurin d'agowa yayi yace shekara kuma momcy? Momcy da Daddy ko me zasuyi inba dariya ba, Faruk mik'ewa yayi cikin sauri yabar wajen. Koda yashiga part d'inshi sosai yanuna farin cikin shi akan ranar aurensu da za'a tsaida nan yakira Nasiba yafad'a mata itama tayi ta murna. Suna gama wayar tashi yayi yashiga wanka yana cikin wankan yaji kamar giftawar mutum ta wajen toilet din saurin waigawa yayi ammah baiga kowaba dan haka yad'auko towel yad'aura yafito yadudduba ba kowa cikin d'akin dan shi daman ya san dakanshi yarufe k'ofar da key nan yakoma ya ida wankanshi yafito yashirya yasafko parlorn k'asa yayi lunch d'inshi sannan yakoma part d'inshi yakashe wayoyinshi dan yasamu yayi aikinshi cikin nutsuwa. File d'in jawahir da aka bashi yad'auko yasake dubawa tare da duba bayanan da yatattara akanta daga k'arshe yabud'e laptop d'inshi yacigaba da bincike sallah ce kawai take tadashi daga inda yake har k'arfe sha biyun dare yayi bai san tayiba yana nan yana aiki, momcy ma da taga bai fitoba saidai takawo mashi dinner d'inshi a nan d'aki. Har wajen k'arfe d'aya yana nan yana aiki, hamma da yafara ne yasa ya ayyana a ranshi zai tashi yaje yakwanta ahankali yafara jiyo taku a chan k'asan bene kamar ana hawa step k'arar takalma masu tsini ana k'was k'was, shuru yayi yana saurare sai jin k'arar yake ta k'i k'arewa daga karshe yaji kamar anyo wajen d'akinshi cike da rashin tsoro yamik'e yaje yabud'e k'ofa sai ji yayi tsit k'arar ta daina lek'awa yayi baiga kowaba dan haka yamaida d'akin yarufe yazo yakashe laptop d'inshi yashige bedroom alwallah yayi yai sallah raka'a biyu sannan yahaye saman gadonshi saida yatofe jikinshi da addu'a sannan yakwanta bai dad'e da kwanciya ba bacci yakwashe shi. Washe gari wajen k'arfe tara yagama shirinshi dan da k'arfe goma za'a fara gabatar da shara'a sama sama yayi breakfast nan iyayenshi sukayi mashi addu'ar samun nasara sannan yatafi lokacin da ya isa kotu ta cika makil Alk'ali kawai ake jira ya iso daga chan gaba yaje wajen da Barr Bilal yakama mashi yazauna nan suka gaisa da sauran lauyoyin suna a haka alk'ali ya iso nan kowa yamik'e tsaye har saida yaje yazauna sannan su ma suka koma suka zauna. Me karanta k'ara ne yatashi yafara yin sallama sannan yace a yau 2 ga watan marich wanda yai daidai da 6 ga watan rajab... Shara'ar farko da zamu fara gabatarwa itace shara'ar indo wadda ake zargi da kashe d'an kishirta dan haka kotu tana buk'atar indo tabayyana a gabanta, wata mata ce tafito idanuwanta kumbure saboda tsananin kuka me gabatar da k'ara juyawa yayi yakalli Alk'ali yace Allah yagafarta malam wannan itace indo. D'ago kai Alk'ali yayi yakalli wadda aka kira da indo sannan yasadda kai yayi yan rubuce rubuce yace kotu tanaso indo tabayyana mata yadda akayi takashe d'an kishiryata...... Haka aka gama shara'ar indo aka yanke mata hukuncin da yadace nan aka sake kiran wata shara'ar wani da yake zargin abokinshi da shigowa gidanshi cikin dare yayi mashi sata, and'auki lokaci ana tattaunawa kowa lauyanshi yana k'ok'arin kareshi inda daga k'arshe aka gane makwabcinshi ne yashiga yayi mashi satar. Ana gama yanke hukunci nan me gabatar da k'ara yamik'e yace sai shara'a ta gaba wadda itace ta k'arshe a yau itace shara'ar Jawahir wadda ake zargi da kisan mutane bakwai, wadda iyalan mamatan suka shigar da k'ara wata goma da suka wuce. Alk'ali d'ago kai yayi yace kotu tana buk'atar ganin wadda ake k'ara. Me karanto k'ara ne yasake maimaita abinda Alk'ali yace. Ma'aikatan gidan yari ne mata biyu suka tafo suna janye da ita har wajen da aka tanadar mata dan tatsaya. Me karanto k'ara yace ga jawahir wadda ake k'ara nan ta bayyana. Alk'ali yace kotu tana buk'atar ganin lauyan masu k'ara da na wadda ake k'ara. Barr MB ne yamik'e yace Assaalamu Alaikum nine Barr Mahamud Bello lauyan da yake tsaya ma masu k'ara. Jinjina kai Alk'ali yayi yaduk'a yayi yan rubuce rubuce nan Barr MB yazauna, me karanto k'ara yace kotu tana buk'atar ganin lauyan wadda ake k'ara idan akwai. Shuru kotu tayi ana jira aga wane me kasada ne wanda yagaji da rayuwarshi yatsaya ma jawahir. Jawahir da take tsaye duk'ar da kanta tayi idanuwanta sun cika taf da k'wallah. Barr Bilal ne yad'an ta6o Barr Faruk da yafad'a duniyar tunani daidai lokacin da aka sake maimaita ana buk'atar ganin lauyan wadda ake k'ara, ahankali yamik'e tsaye yayi sallama yace nine Barr Faruk Sani Maishadda lauyan da yake kare wadda ake k'ara, gabad'aya kotun d'auka tayi da surutu, jawahir dakyar ta iya d'aga kai takalleshi lokacin shima ita yake kallo ko kad'an bataso hakaba taso ace ya bari anyanke mata hukunci, 'yan sanda ne suka shiga nutsar da mutanen da suke kallon shara'a, Barr MB da mamaki yake kallonshi yai mashi irin kallon nan na haka kayi min? Alk'ali jinjina kai yayi nan Barr Faruk yakoma yazauna. Alk'ali d'agowa yayi yace kotu ta ba lauyoyi dama idan da mai kwakkwarar shaida yatashi yagabatar da ita inkuma wadda ake tuhuma tana da abinda zata kare kanta akan tuhumar da akeyi mata na kisan kai akaro na hud'u da akayi zaman kotu toh bismillah Shuru jawahir tayi still dai kanta yana sunkuye a k'asa. Mai karanta k'ara ne yasake karanta abinda Alk'ali yace nan tayi shuru . Mik'ewa Barr MB yayi yace ya me girma me shara'a inaso kotu taban dama inma Jawahir wasu yan tambayoyi. Alk'ali yace kotu ta baka dama. Dan rissinawa yayi yace nagode sannan yataka ya isa inda jawahir take tsaye yace Malama jawahir shin ko zaki iya sanar da kotu dalilinki na kashe wad'annan bayin Allahn da kikayi? D'ago kai tayi takalleshi da Idanuwanta da sukayi jajir tana so tabud'e baki tayi magana ammah ta kasa bakin nata taji kamar anrike mata shi. K'ara maimaita mata tambayar yayi ammah shuru saidai kallonshi da takeyi. Murmushi yayi yace idan wannan tambayar batada amsa toh ga tambaya ta biyu a lokacin da Alhaji Tanimu yashigo yasameki kinyi kisa kinyi mashi barazanar zaki kasheshi shima haka ne ko ba hakaba? Still dai shuru jawahir tayi saidai hawayen da suke gangaro mata. Murmushin mugunta yayi yajuya yakalli Alk'ali yace ya megirma me shara'a yakamata kotu tagaugauta yanke ma jawahir kisa daidai da laifinta da tayi na kisa saboda batada amsar da zata iya badawa a wannan tambayoyin da nayi mata yakamata kotu tayadda da cewa jawahir itace wadda tayi kisa tayi amfani da mark ajikin hotunan wad'anda takashe, d'auko hotunan yayi yamik'a aka mik'a ma Alk'ali. Duba hotunan Alk'ali yayi nan Barr MB yacigaba da cewa tabbas Jawahir ta shek'a wad'annan bayin Allahn lahira batare da ansan dalilinta na aikata hakan ba wanda daga k'arshe tahad'a da lauyoyin da suka kasance suna nema sukare ta. Jawahir runtse idanunta tayi nan wasu sabbin hawaye suka gangaro mata. Barr Faruk ne yai saurin mik'ewa tsaye yace ya me girma me shara'a ya kamata kotu tagargadi Barr Mahmud Bello akan munanan maganganun da yake jifar wadda ake k'ara da su. Jinjina kai Alk'ali yayi yace kotu ta amshi k'orafinka dan haka kai barrister kagyara kalamanta. Dan rissinawa Barr MB yayi yace nagode ya me girma me shara'a ina Neman afuwa Sannan yajuya yakalli jawahir yace ko zaki iya kare kanki akan wannan laifin? Shuru jawahir tayi tana mecigaba da kallonshi. Juyawa yayi yakalli Alk'ali yace ya megirma me shara'a inaso kotu tagaugauta yanke ma Jawahir hukunci dan batada amsar da zata iya kare kanta da ita. Mik'ewa Barr Faruk yayi yace ina da ja ya me girma me shara'a ina so kotu taban dama zan d'anyi wasu tambayoyi ga iyalan mamata. 'Yan rubuce rubuce yayi sannan yad'ago yace kotu ta baka dama. 'Dan rissinawa yayi yace nagode sannan yafito yatsaya nan Barr MB yakoma yazauna cike da jin haushi dan ba haka yasoba. Me karanta k'ara ne yamik'e yace kotu tanason ganin iyalan masu k'ara sugurfana a gabanta. Daga chan cikin jama'ar da suke zaune kallon shara'a wasu mutane goma suka fito sukazo gaba wajen da aka tanadar suka tsaya, matsowa Barr Faruk yayi kusa da su yace ku ne iyalan wad'anda suka rasu? Dukansu d'aga kai sukayi alamun Eh. Murmushi yayi yace ko zaku iya ma kotu bayani akan mutuwar mamatan shin akwai wanda yaga lokacin da jawahir tazo gidan takashe su? Kame Kame suka fara suka rasa tayadda zasuyi bayani . Barr Faruk sake jefo masu tambaya yayi yace munaso kuyi mana bayani yadda akayi kukasan itace tayi kisan nan ma sukayi shuru suna kallon gefe d'aya juyawa yayi yakalli Alk'ali yace ya megirma me shara'a inaso kotu tawanke jawahir daga laifin da ake zarginta da shi dan babu wanda zai iya bada shedar cewa Jawahir ce tayi kisan, saurin mik'ewa Barr MB yayi yace ya me girma me shara'a yakamata kotu tasa Barr Faruk yagyara kalamanshi dan yana nema yazargi wani na daban bayan kuma kowa ya san itace tayi kisan tun daga mark d'in da ke jikin wad'anda aka kashe. Jinjina kai Alk'ali yayi, Barr Faruk juyawa yayi yace ina neman afuwa ya me girma me shara'a saidai ni ina ganin har yanzu basu bada kwakkwarar shaida da tanuna jawahir ce tayi kisan ba, Alk'ali yace miye hujjarka na cewa haka? Barr Faruk yace saboda ko lokacin da su Barr muhsin suka rasu and'aura zargi akan wannan baiwar Allahn alhali lokacin tana nan gidan yari ana tsaronta taya zata fita har tayi kisa tadawo. Barr MB a fusace yace ammah ai kowa yasan itace tayi. Juyawa Barr Faruk yayi wajenshi yace shin a matsayinka na lauyan masu k'ara tunda su sunkasa yin magana munaso kafad'a mana a lokacin da jawahir tashiga gidajen mamatan ance wasu da dare takashesu shin ta wace hanya tashiga gidan alhali gidan rufe yake ko su basu rufe gidajen su? Juyawa Barr MB yayi yakalli Alk'ali yace ya megirma me shara'a tambayoyin Barr Faruk sunyi ma masu shigar da k'ara tsauri saisa suka kasa bashi amsa sannan jawahir ana zarginta da yin layar zana ta wannan hanyar ne take zuwa tayi kisan, ya me girma me shara'a yakamata kotu taduba bayanina da yadda akayi jawahir takasa kare kanta a lokacin da nayi mata tambaya. Alk'ali duk'awa yayi yai yan rubuce rubuce yad'ago yakalli jawahir yace shin ko zaki iya kare kanki akan tuhumar da akeyi maki? Barr Faruk kallon jawahir yayi da take ta hawaye ta kasa cewa komai kowa ya zuba mata idanu yana jiran tayi magana chan dai tagirgiza kai, Barr Faruk maida kallonshi yayi ga Alk'ali yace ya megirma me shara'a muna nema kotu tataimaka mana tad'age k'arar nan zuwa zama na gaba domin akwai binciken da muke wanda bamu idaba a matsayina na lauyan wadda ake k'ara kuma saboda k'arancin lokacin zuwana bai sa nasamu na ida bincike na ba ina neman wannan alfarmar kotu taduba min. Murmushin nasara Barr MB yayi yace ya me girma me shara'a yakamata kotu tayi watsi da wannan alfarmar da barristern wadda ake k'ara yanema domin baida wata kwakkwarar shaida da zai iya kare wadda ake k'ara da ita, munaso kotu ta gaggauta yanke ma wadda ake k'ara hukuncin da yadace da ita. Shuru Kotun tayi har saida alk'ali yagama rubuce rubucenshi yad'ago yace barrister Faruk kotu ta amshi uzurinka a matsayin lauyan wadda ake k'ara wanda bai dad'eba da tsaya mata dan haka kotu ta baka dama kaje kakawo mata kwakkwaran shaidar da kace ba ita tayi kisan ba, zamu d'age wannan k'arar zuwa 2 ga wata nagaba watau wata d'aya me zuwa insha Allahu shi muke fata yakasance zama na k'arshe,,,,yana fad'in haka yabubbuga table. Barr Faruk wani irin dad'i yaji a ranshi dan yasan wannan hanyar kawai zaibi yaku6utar da jawahir saboda baida hujjar da zai iya kareta, inda shikuma Barr MB yaji kamar yabuge kowa saboda haushi. Jawahir fashewa tayi da kuka dan ba haka tasoba haka matan suka riketa suka tafi da ita prison. Haka aka tashi Shari'a masu murna sunayi masu bak'in ciki suna yi. _*Free page*_ _Wannan littafin na kud'i ne ga duk me buk'ata zai biya d'ari biyu N200 Kacal zai turo MTN card ta wannan number d'in 09035938246 ko katuro 200 ta account number d'innan 5330055604, *NANA HALLIRU* FIDELITY BANK, idan katura ka aiko da screen shot na transaction ta wannan number 09035938246_ _Ga mutanen Niger zasu tura 300f ta wannan number d'in +22794775574_ _Gareku masoyan gaskiya_ _*GARA B'ASA! GARA B'ASA!! GARA B'ASA!!!* wannan gara'basa anyi tane kad'ai ga duk wanda keson karanta littafin *FANSAR RAI* da *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shaharariyar marubuciyar nan watau *AMINA ABBA UMAR* ga duk mai bukatar karanta duka novel's d'in biyu zai biya *N300* kadai domin samun damar karantasu cikin aminci, gareku masoyan gaskiya muna jiran ku nuna mana k'aunarku ta hanyar biyan *N300* kad'ai, idan duka biyun kakeso zaka turo kud'i ta wannan account number d'in 3092292135 FIRST BANK, ko kuma katin waya Mtn na d'aya daga cikin Numbers d'in nan 09035938246 ko kuma 07030792790, ko 07036073670, sai ka aiko da shedar biya ta d'aya daga cikin numbers d'in, sai munji daga gareku masoyanmu_ _Sis Nerja'art✍🏻_ [3/11, 21:25] Sis Nerja'art👰🏻: *......FANSAR RAI.......* _*STORY AND WRITTEN BY SIS NERJA'ART✍🏻*_ *INTELLIGENT WRITERS ASSO....®* [On Ward Together] *DEDICATED TO ZM CHUBA'DO* *PAGE NINE* Barr MB suna fita yanufi wajen Barr Faruk da yake shirin shiga motarshi yana zuwa murmushi yayi yace Barrister kenan wane tsotsai yakaika tsaya ma Jawahir ina ce ko ka gaji da rayuwarka ne saisa?. Shima murmushin yayi yace kusan haka dan daman ita mutuwa akowane lokaci zuwa takeyi. Tab'e baki yayi yace hakane daman ashe kaine lauyanta shine kazo kabugi ta cikina kaji sirrina? Cikin rashin damuwa yace wannan ai ba wani abu bane tunda duk cikin aikinmu ne. "Na san da haka saidai kai na san bakasan komai ba akan case d'in jawahir dan haka Kataimaka ma kanka kajanye daga tsaya mata". Kar kadamu barrister kai shaida ne bana bayan k'arya akowane lokaci bayan gaskiya nakebi dan haka kai zan ba shawara kajanye kar kad'aure ma k'arya gindi inma kud'i aka baka kamaida masu abinsu. Barr MB Katseshi yayi yace kai kana ganin kaine akan gaskiya nima haka nake gani dan haka muhad'e kawai wata me kamawa idan Allah ya sa rayuwarka ta kai. Dariya Barr Faruk yayi yace toh Allah yakaimu nan yabud'e motarshi yashiga yabar Barr MB duk haushi ya cikashi. Barr Faruk yana komawa gida wanka yayi yashirya yafita parlour dan yayi lunch momcy ce tafito tana fara'a tace Son har andawo? Zama yayi saman cushion cike da nuna gajiya yace Eh Momcy. Itama zama tayi gefenshi cikin nuna tausayawarta tace sannu son da alama ka gaji dayawa ina fata dai anyi nasara? Murmushi yayi yafad'a ma momcy yadda akayi,,,ta tausaya ma jawahir sosai koda bai fad'a mata ainahin abinda akayiba ya 6oye mata dan kar tatada hankalinta tanuna bata yadda ba yasa yace mata kawai zarginta akeyi da laifin kisa kuma baya tunanin ita tayi saboda yarinya ce k'arama. Addu'a tayi akan Allah yataimaka yaku6utar da ita idan har batada laifi aciki. Ya amsa mata da Ameen. Fitowar Daddy ne yasa suka gaisa shima yayi mashi sannu da dawowa sannan suka d'unguma zuwa dining area dan suyi lunch, suna cikin yi Dad yakalleshi yace Son gobe fa za'ayi baikonka da Nasiba. Murmushi yayi me nuna jin dad'i yace toh Daddy na gode sosai, wata nawa za'a tsaida bikkin? Shuru Daddy yayi sai chan yace ina tunanin bazai wuce wata ukku ba dan Dad d'inta ya ce bayaso aja lokaci dayawa kuma mu ma bamuda matsala mun gama shirinmu tunda hatta gida kana da shi. Momcy tace hakane Alhaji nima kaina bansan aja lokaci dayawa saisa nanuna farin cikina da akace baza'a fi wata ukku ba. Faruk yana jinsu saidai yayi murmushi yacigaba da cin dinner d'inshi. Bayan sallar la'asar yana dawowa daga masallaci ko gida bai shigaba yashiga motarshi yabar gidan yakama hanyar prison. Jawahir tunda aka maidata a cikin d'an kurkukun d'akinta bajewa tayi a k'asa tana wani irin kuka me cike da k'ara, duk tacika wajen da kuka wasu ma'aikatan gidan ne sukazo da manyan bulalai suka sameta nan suka kwatsa mata tsawa sukace tayi masu shuru dakyar ta iya danne kukan nata saidai hawaye da take idanuwanta duk suka k'ank'ance maida idanuwanta tayi tarufe bata sake bud'e suba saida Barr Faruk yazo batare da ta bud'e idanunba tana jin abud'e k'ofar anshigo cikin muryar kuka tace bance maka kar ka kuskura kashiga acikin wannan maganar ba? Sau nawa nafad'a maka mutuwata tafi rayuwata amfani, Miyasa bazaka ji maganar da mutane suke fad'a ba akaina, dakyar tabud'e idanunta tace barina in rayuwa a doron k'asa tamkar kashe d'an maciji ne ba'a sare kanshiba, shawara zan baka kabi maganar da sauran mutane suka fada maka karabu da ni gudun kar matsalata ta shafeka. Matsowa yayi kusa da ita cikin sanyin jiki yace jawahir ban damuba kowace irin matsala tasameni dan ni na riga da nasa ma raina ina da burin taimakonki komai zan iya yi dan ganin kin fita daga gidan nan saboda zama nan baidace dakeba. Wasu sabbin hawaye ne suka gangaro mata tace Barrister Kaine kake ganin haka ammah ni rayuwata a cikin d'akin nan ta fiye min kwanciyar hankali akan bala'in da nake ciki wanda barina gidan nan zai iya shafar kowa. Cike da mamaki Barr Faruk yace wane irin bala'i ne kike ciki haka? Shin ko zani iya saninshi? Tashi tayi zaune tace saninshi zai iya sa kaima yashafeka bazan gaji da fad'a makaba kanisantar da kanka daga gareni. Jawahir nayi maki alk'awalin zan taimaka maki da dukkan k'arfina. 'Dan guntun murmushi tayi tare da janye kanta gefe. Barr Faruk yace nasan ba lallai ne kiyarda daniba dan kina min kallon kamar halayyata iri d'aya ce da tasu barrister muhsin saidai ni ba haka nakeba kiyarda da ni. Girgiza kai tayi tace ba na ji akwai wanda zan iya yarda da shi a wannan lokacin har zuwa k'arshen rayuwata. Jawahir ya kamata kifahimceni banzo da niyar cuta agarekiba kitaimaka kiban had'in kai dan inwanke ki daga zargin da duniya takeyi maki. Wani irin kallo tayi mashi tace zargi kuma? Wanene yafad'a maka zargi ne? Koma minene Jawahir ina da burin taimaka ma rayuwarki, shuru tayi na d'an lokaci kamar tana nazarin wani abu sai chan tayi murmushi tare da goge hawayenta kamar ba ita bace tagama kuka tace shikenan tunda ka ce zaka taimaka min saidai duk matsalar da kashiga kar kayi kuka da kowa sai kanka. Cikin nuna rashin damuwa yace na amince da haka, dan haka inaso kiban tarihin rayuwarki. Mik'ewa tayi tsaye tana tafiya dakyar har ta isa wajen yar k'aramar tagar da take yawan tsayawa wajenta,,ganin kamar bataji abinda yaceba yasa Barr Faruk yasake maimaita mata. 'Dan guntun murmushi tayi batare da ta juyoba tace na amince zan fad'a maka tarihin rayuwata ammah ba anan ba saidai idan zaka fitar da ni daga kurkukun nan muje wani waje dan Indai a nan ne na tabbata zamu shiga matsala daga ni har kai dan matsalata zata iya shafarka, bazata ta'ba barinkaba. Shuru Barr Faruk yayi kamar yana nazarin maganarta sai chan yace wace irin matsala zata shafeni? Kowace irin matsala zata iya shafarka Indai har kanason jin tarihina saidai kayi yadda nace maka. Ajiyar zuciya yasafke yace shikenan Jawahir zan kwatanta hakan zanje in nemi amincewar shugaban gidan nan in ya amince sai mu fita muje wani wajen zuwa gobe. Baya baya tafara ja lokaci guda muryarta tafara rawa tace kayi gaugawan barin wajen nan yanzu. Da mamaki yake kallonta yace saboda me? Juyowa tayi fuskarta cike da tashin hankali cikin d'aga murya tace na ce kabar wajen nan katashi kafita! Ganin yadda lokaci guda tabirkice yasa yamik'e yawuce yafita cike da mamaki, bayanshi Jawahir tabi cikin sauri tajanyo k'ofar tarufe tare da ja da baya ahankali taje chan wajen kusurwar d'akin tatsaya jikinta gaba d'aya rawa yake nan tayi saurin zama tare da dunk'ule jikinta waje guda tadafe kanta da dukkan hannuwanta. Barr Faruk yana tsaye yana kallonta ta 'yan hudojin k'ofar yana jiyo sautin kukanta ahankali da magana wadda bazaice ga abinda take cewaba chan kuma sai yaji ta shuru. Ji yayi kamar yashiga d'akin dan yagane ma idanunshi abinda yake faruwa da ita sai kuma yafasa yawuce suka tafi. Yana fita direct office d'in shugaban gidan yarin yawuce yana zuwa yashiga lokacin wasu files ne hannun Alhaji mahadi yana dubawa yana ganinshi Murmushi yayi yace ya dai abokina har ka gama? kujera faruk yaja yazauna yace abokina dan Allah wata alfarma nazo nema a wajenka. Alhaji Mahadi yace haba alfarma kuma? Ina jinka Numfasa yayi yace Jawahir nakeso ataimaka a ara min ita zuwa gobe zan fita da ita saboda zan d'auko wani bayani ne wanda itace zata taimaka min wajen d'aukoshi a matsayina na lauyanta. Zaro ido mahadi yayi yace fita fa kace zakayi da ita daga gidan yarin nan? Cikin nuna rashin damuwa yace Eh kuma insha Allahu da nagama abinda zanyi zan maidota. Girgiza kai mahadi yayi yace kayi hak'uri Barrister gaskiya hakan bazai yuwuba kafita da ita dan tana cikin tsaro me tsanani fita da ita laifi ne a k'a'idar aikin nan ba'a fita da me laifi indai ba asibiti ko court za'aje ba. Na san da haka abokina taimaka min zakayi insha Allahu zan maido ta bazan dad'eba ina gama d'aukar bayanan da zan d'auka zan gurfanar da ita a wajenku, nayi maka alk'awalin haka kataimaka min ko dan amincin da ke tsakaninmu muyi abun mugama batare da sanin kowaba. Iska yafuzgar yace gaskiya dan dai Kaine saisa zan amince ammah katabbatar ka maidota dawuri gudun kar wata matsala tafaru banaso kowa yasan kun fita. Cikin jin dad'i Barr Faruk yace kar kadamu abokina insha Allahu zanyi k'ok'arin haka. Toh shikenan Allah yakaimu Cikin jin dad'i yace Ameen Nagode sosai sai goben idan na zo. Nan yamik'a mashi hannu sukayi sallama yatafi. Tafiya yake a cikin motarshi a hankali ba wani gudun kirki yakeba kallon mirror da zaiyi sai gani yayi kamar wannan tsohuwar ce zaune a bayan sit d'in motar saurin waigawa yayi yakalla sai baiga kowaba yak'ara kallon mirror yaga gatanan dai zaune kanta sadde a k'asa wani irin burki yaja yatsaya ba dan Allah ya taimakeshiba da ya fad'a ma motar da take gabanshi, juyowa yayi gabad'aya yakalli bayan sit din ammah baiga kowaba yak'ara kallon mirror nan ma baigantaba a wannan lokacin ajiyar zuciya yasafke tare da Jingine kanshi a jikin kujerar cikin ranshi yace idanuwanshi ne sukayi mashi gizo dan tana ranshi ne, saidai me miyasa jawahir tasan da maganar tsohuwar kodai itama jawahir ba mutum bace,,,kwankwasa mashi glass akayi yai saurin bud'e idanunshi sai gani yayi fiitt wani abu ya wuce ammah baiga ko menene ba fitowa yayi daga motarshi yana dubawa babu kowa sai yan motocin da suke wucewa jefi jefi dan haka ne yakoma cikin motar yatada yatafi ammah yana ta mamaki wanene yakwankwasa mashi glass d'in mota. Yana cikin tuk'i Nasiba takirashi a waya yana yin picking yai sallama bayan sun gaisa ne tafara yi mashi tsegumin rashin zuwa murmushi yayi yace Sweetheart ganinan yanzu hope dai kina gida? Cike da jin dad'i tace Eh ina gida lovely sai ka iso. Yace ohk kiban minti biyar insha Allahu na iso. Toh Allah yakawo min kai Allah. Ameen sweetheart. Yana gama wayar ya ajiyeta yacigaba da tuk'in shi a nutse har ya isa gidansu Nasiba yana yin parking a harabar wajen da ake ajiye motoci kiranta yayi a waya yace tafito gashi. Suna gama wayar yanufi wajen wasu plastic chair yazauna chan sai ga Nasiba ta fito tana yafiyarta me jan hankali idanu yazuba mata yana kallonta cike da shauk'in sonta dan har cikin ranshi yake jin son Nasiba shi a tsarin rayuwarshi bai damu da kyakkyawar maceba shidai nutsatstsa me hankali kawai yakeso me addini ahaka har ta iso bai saniba yana ta tunani saida tahura mashi iska a fuska sannan yadawo cikin hankalinshi yasakar mata Murmushi. Zama tayi itama tana murmushin tace Lovely tunanin me kakeyi haka? Lumshe idanunshi yayi yabud'e sannan yace tunanin sweetheart d'ina nake. Murmushin jin dad'i tayi tace nagode sosai lovely ammah sai inga kamar yanzu ka rage damuwa da ni, dan kwananka biyu bakazo mukaga junaba saidai muyi waya. Girgiza kai yayi yace kod'aya Sweetheart a kowane lokaci kina a cikin raina kawai dai kwana biyu shara'a tasani a gaba. Cikin sanyin jiki tace to shikenan ammah dan Allah kadinga zuwa ina ganinka ko zan samu sauk'i a raina. Toh shikenan sweetheart zan dinga zuwa ko dan saboda nima ganinki yana sa min nutsuwa inrage yawan tunaninki. Wata dank'areriyar mota ce tashigo a gate d'in gidan nan duk suka zuba ma motar idanu Barr Faruk yace Allah yasa ba Dad bane yadawo. Murmushi Nasiba tayi dan ta sanshi sarai bayaso suna had'uwa da Dad wai kunyarshi yakeji tace aiko bashi bane ammah yana nan cikin gida. Yana shirin bud'e baki yayi tambaya nan driver d'in motar yayi saurin fitowa yazo yabud'e bayan motar wanda yafito ne yasa Barr Faruk yagirgiza saida mamaki yabayyana a idanunshi, shima mutumin kallonshi yake yana murmushi har ya iso ta wajen Barr Faruk bai saniba saida yaji Nasiba tana gaisheshi sannan yadawo cikin hayyacinshi yad'an rissinar da kanshi ya gaisheshi amsawa yayi fuska a sake sannan yawuce yanufi cikin gidan Barr Faruk da kallo yabishi inda shima mutumin yajuyo yakalleshi yana mashi murmushi sannan yajuya yashige. Yana shigewa yayi saurin juyowa yakalli Nasiba da itama take kallonshi yace Sweetheart wanene wannan? Murmushi tayi tace aminin Dad d'ina ne nasan zuwa yayi suyi magana akan ranar aurenmu da za'a tsaida dan duk yadda yace haka za'ayi saboda Dad gabad'aya shi yamik'a ma ragamar komai. Damuwa ce tabayya k'arara a fuskar Faruk ammah yayi k'ok'arin boyeta tabbas shine mutumin da yasameshi bayan sun fito daga kotu yana tafiya a hanya zai koma gida yazo yashigar da motarshi a gaban tashi yatare mashi hanya kan dole yatsaya yafito cike da jin haushi yajingina da motarshi yana jira yaga wanene yai mashi haka. Anyi kusan minti ukku sannan driver d'in yabud'e mota yafito yazagaya yabud'e bayan motar wani Alhaji ne yafito yana tafiya cikin isa ya iso wajen Barr Faruk da mamakin Barr Faruk sai ji yayi ya kira sunanshi batare da ya amsaba yazuba mashi idanu yana kallonshi murmushi mutumin yayi yace nasan zakayi mamakin ganina dan baka sanniba saidai ni na sanka. Cigaba yayi da kallonshi batare da ya ce komai ba. Mutumin yacigaba da cewa sunana Alhaji Mansur Mai harka da dollars, Cikin rashin damuwa Barr Faruk yace me kake buk'ata a wajena da kazo katare min hanya? Murmushi yayi a karo nagaba yace babu abinda nake buk'ata saidai ina so inmaka gargad'i akan kajanye maganar tsayawa yarinyar nan da muke k'ara akan kisan da tayi dan muna bin jinin 'yan uwanmu munaso akasheta kamar yadda itama takashe ba wai gwaninta bane dan ka tsaya mata kaima kanka baka wuce takashekaba kamar yadda takashe sauran lauyoyin ta. Murmushi yayi cikin nuna rashin damuwa yace nagode da shawararka nan yajuya zai tafi mutumin yace ammah naga kamar baka d'au shawarar ba ko? Juyawa Barr Faruk yayi yace kusan haka. Jinjina kai mutumin yayi yace haka nagani saidai ya zama dole kad'au shawarar dan babu wanda ya isa yatsaya mata kamar yadda takashesu Itama ya zama dole ad'au *FANSAR RAI* akanta. Murmushi Barr Faruk yayi a karo na biyu yace baizama dole hakan yakasance ba sai kabari sai antabbatar da itace d'in sannan kace haka. Ko da ban tabbatar ba nasan itace, kai na lura bakasan matsayina ba agarin nan saisa nake fad'a kana fad'a. Wani irin kallo Barr Faruk yayi mashi yace ban damu da matsayinka ba dan ni ina akan aikina,,,yana fad'in haka yabud'e motarshi yashiga yaja dabaya yacanza hanya,,,ta'ba hannu da Nasiba tayi yasa yai firgit yad'ago yakalleta. Lafiya lovely naga duk ka canza wai ma tunanin me kakeyi? Dan guntun murmushi yayi yace bakomai Wani irin kallo tayi mashi tace ban yardaba kaidai kafad'a min damuwarka. Dagaske sweetheart babu komai ina fata kina farin ciki sosai akan sa ranar aurenmu da za'ayi gobe? Hannu biyu tasa tarufe fuskarta sannan tad'aga mashi kai alamun Eh. Murmushi Barr Faruk yayi yace nima haka sweetheart, duba agogon da take manne a tsintsiyar hannunshi yayi yace Sweety bari intashi intafi kinga magrib ta gabato. Bud'e fuska tayi cikin shagwaba tace kai lovely tun yanzu? Duka yaushe kazo da har zaka tafi. Cike da kulawa yace kiyi hak'uri Sweety wallahi nima naso inshigo da wuri dan dai wani aiki da najene ammah gobe au jibi ashe gobe gidan cike yake jama'a. Dariya tayi tace toh bazaka zo da dare ba? "Eh toh zan duba ingani. Marairaicewa tayi tace dan Allah kashigo. Mik'ewa tsaye yayi yace shikenan Sweety insha Allahu zan shigo. Cikin jin dad'i itama tamik'e tace yauwa lovely zanyi farin ciki sosai idan kazo,,, Kallonta yayi yace me zaki ajiye min? Juya idanu tayi tace abu me dad'i. Murmushi yayi yace Toh shikenan sai na shigo,,,,rakashi tayi har wajen mota saida yashiga yatafi sannan takoma cikin gida. Alhaji mansur dake zaune a setting room d'in aminin nashi kallonshi yayi yana murmushi bayan sun gama gaisawa yace abokina wai wanda nagani tare da Nasiba a nan waje ko shine wanda zata aura? Oh Faruk Eh shine. Jinjina kai yayi yace Dakyau ashe ta kwana gidan sauk'i. Cikin nuna rashin fahimta yace ban fahimta ba minene yakwana gidan sauk'i? Murmushi yayi nan yakwashe duk yadda sukayi da Barr Faruk yafad'a mashi. Baki Alhaji Sufyan yasaki yana kallonshi yace yanzu Faruk d'inne yace haka? Ya akayi ma har yatsaya mata a matsayin lauya? Hmm kaidai bari abokina nima dai ban saniba ai yaron nan baida kunya. Jinjina kai yayi yace kabarshi mun san ta inda zamu 6ullo mashi. Hannu yabashi suka kashe suna dariya... *Free Page* _Wannan littafin na kud'i ne ga duk me buk'ata zai biya d'ari biyu N200 Kacal zai turo MTN card ta wannan number d'in 09035938246 ko katuro 200 ta account number d'innan 5330055604, *NANA HALLIRU* FIDELITY BANK, idan katura ka aiko da screen shot na transaction ta wannan number 09035938246_ _Ga mutanen Niger zasu tura 300f ta wannan number d'in +22794775574_ _Gareku masoyan gaskiya_ _*GARA B'ASA! GARA B'ASA!! GARA B'ASA!!!* wannan gara'basa anyi tane kad'ai ga duk wanda keson karanta littafin *FANSAR RAI* da *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shaharariyar marubuciyar nan watau *AMINA ABBA UMAR* ga duk mai bukatar karanta duka novel's d'in biyu zai biya *N300* kadai domin samun damar karantasu cikin aminci, gareku masoyan gaskiya muna jiran ku nuna mana k'aunarku ta hanyar biyan *N300* kad'ai, idan duka biyun kakeso zaka turo kud'i ta wannan account number d'in 3092292135 FIRST BANK, ko kuma katin waya Mtn na d'aya daga cikin Numbers d'in nan 09035938246 ko kuma 07030792790, ko 07036073670, sai ka aiko da shedar biya ta d'aya daga cikin numbers d'in, sai munji daga gareku masoyanmu_ _Sis Nerja'art✍🏻_ [3/12, 19:43] Sis Nerja'art👰🏻: *......FANSAR RAI.......* _*STORY AND WRITTEN BY SIS NERJA'ART✍🏻*_ *INTELLIGENT WRITERS ASSO....®* [On Ward Together] *DEDICATED TO ZM CHUBA'DO* *PAGE TEN* Barr Faruk bayan ya koma gida da ka ganshi kasan yana cikin tashin hankali bakomai ne yad'aga mashi hankali ba sai dan yasan kallon da Alhaji Mansur yayi mashi akwai alamar tambaya a ciki, fatan shi dai kar yazame mashi matsala a cikin maganar aurenshi. Haka yakasance gabad'aya yakasa sukuni har dare wajen k'arfe tara yakira Nasiba a waya har suka gama hirarsu bata nuna mashi akwai wata matsala ba saboda haka yad'an saki ranshi. Wajen k'arfe d'ayan dare farkawa yayi daga baccin da yake a razane saboda mummunan mafarkin da yayi na wannan tsohuwar da yasaba mafarki da ita ce tazo mashi a saman iska tana rik'e da wata zandamemiyar wuk'a wadda tsawonta baya misultuwa sai shek'i wuk'ar takeyi ta nufo shi shikuma yana ta gudu har takusa taddoshi nan yayi tuntu6e yafad'i gabad'aya tatafo da dukkan k'arfinta zata caka mashi sai ganin wata matashiyar yarinya yayi ta zo ta rik'e wuk'ar gashinta duk ya baje mata fuska tana cewa yatashi yaruga,,,yana zuwa daidai nan yafarka daga baccin nashi gumi kawai yake had'awa, ya dad'e a zaune yana k'ara tariyo mafarkin a cikin ranshi kafin daga bisani yamik'e yaje yayi alwallah yai sallah raka'a biyu yayi addu'a yakoma yakwanta dakyar yakoma baccin nashi. Washe gari koda yatashi yashirya fitowa yayi parlor yasamu su momcy suna breakfast, Daddy ne yace son ka fito?murmushi yayi yace Eh Daddy nan yagaishesu sannan yaja kujera yazauna momcy dakanta tahad'a mashi nashi breakfast d'inshi nan shima yazauna yayi, ya d'an ci ba laifi yamik'e momcy tace ba dai har ka k'oshi ba? Murmushi yayi yace wallahi momcy cikina ya cika. "Hmm daman ai haka kake bakason cin abinci saisa gakanan sai k'arewa kakeyi. Daddy ajiye cup d'in tea d'in da yake a hannunshi yayi yace Son kasan dai banaso kana fita da yunwa. Marairaicewa yayi yace Allah Daddy na k'oshi kaga fa naci sosai. Daddy yace toh shikenan yanzu zuwa anjima zan kira Alhaji Sufyan muji yadda za'ayi akan baikon ku da za'ayi subamu lokacin da zamuje dan munyi magana da abokaina su Alhaji Salisu da Alhaji Abu. Cikin nuna jin kunya yace toh Daddy. Momcy ce tace ina ruwan son nasan dai kana murna da ranar nan dan tunda kafito baki ya k'i rufuwa. Cike da jin kunya Faruk yawuce yabarsu. Yana jiyosu suna mashi dariya, bayan tafiyarshi daddy yace ma momcy Hajiya munyi magana da malam ya nuna farin cikin shi sosai dan shima daman ya damu Faruk yayi aure dan da cewa yayi yaje cikin 'ya'yan gwaggonshi yaza6a dan ya gaji da ganinshi babu aure saida nace mashi ai ya samu mata sannan. Dariya momcy tayi tace ina ruwan malam ai yanaso yaga auren Faruk, Itama Gwaggo Harira da nafad'a mata bakaga yadda tanuna farin cikiba da tace zatazo sai nace mata ai mazane zasu sa bikkin ba mataba. Daddy yace Allah sarki, Allah dai yanuna mana ranar bikkin nan dan kowa murna yake. Ameen dai,,cewar momcy. Barr Faruk yana komawa part d'inshi key d'in motarshi yad'auko da dukkan wayoyinshi sai system d'in aikinshi yafito d'aya daga cikin motocin da suke a harabar gidan yashiga Secretary yakira a waya yafad'a mashi bazai samu shigowa ba yau yasanar da su dan akwai aikin da zaije yi. Bayan sun gama wayar tada motar yayi dagudu yabar gidan cikin k'ank'anin lokaci ya isa prison, yana isa office d'in shugaban yasafka nan suka gaisa sannan yace ya zo akan maganar fitarsu da jawahir. Shuru shugaban yayi sai chan yace toh shikenan barrister ammah bari ahad'aku da 'yan sanda suyi maku rakiya. A'a ba sai ka had'ani da wasu yan sanda ba naga hankalinka ya d'an tashi toh kakwantar da shi zan maido maku jawahir lafiya kamar yadda kuka ban ita. Ajiyar zuciya yasafke yace shikenan barrister ammah dan Allah Kakula kasan yarinyar nan tana da hatsari. Yar dariya yayi yace ku dai kuka san haka insha Allahu kamar yadda dai nayi maka alk'awali zan maidota. Alhaji Mahadi wayarshi yad'auko yakira wata mata yace sukawo mashi jawahir yanzu. Aiko suna gama wayar ko minti ishirin ba'ayiba sai ga jawahir ankawo, kallon Barr Faruk tayi da shima yake kallonta nan matan suka k'watsa mata tsawa sukace bazata tsugunna ba. A maimakon tatsugunna sai ma dai zama da tayi a k'asa tare da sunkuyar da kanta tagaishesu nan duk suka amsa mata. Alhaji Mahadi nuna Barr Faruk yayi yace nasan dai kinsan wannan lauya d'in wanda yake k'ok'arin tsaya maki toh gashinan yanaso kufita na amince mashi saboda matsayinshi ammah da badan hakaba bazaki ta'ba barin gidan nan ba har sai angama shara'a, sannan zan ja kunnenki idan kuka fita kar kisaki kiyi tunanin guduwa domin duk inda kikaje sai munsa ankamoki, ina fata kinji ni? D'aga kai kawai jawahir tayi alamun toh batare da ta kalleshiba sawa yayi aka cire mata ankwar da take a hannunta da kafafunta. Mik'ewa Barr Faruk yayi yace toh Alhaji bari muje. Shikenan barrister dan Allah kakula Murmushi yayi yace babu matsala insha Allahu. Wucewa yayi a gaba matan suka bishi suna rik'e da jawahir ahaka har suka fito sukaje wajen motarshi bayan mota matan suka bud'e mata tashiga Barr Faruk baidamu da hakan ba yabud'e mazaunin driver yashiga, matan ne sukaje suka fad'a ma masu gadi akan oga ne yace afita da Jawahir sannan suka bud'e mashi gate. Tunda yafara tuk'i yana kallonta ta cikin mirror tana kallon window babu wanda yatanka ma wani har suka hau titi saida sukayi nisa a tafiyar sannan Barr Faruk yace ina yakamata muje ko inkaiki gidana? Girgiza kai kawai tayi alamun a'a. Jin haka yasa Shima yayi shuru baisake cewa komai ba, a daidai wani shagon kaya yayi parking d'in motarshi yace minti biyu nan yafito yashiga bai dad'eba yadawo da wata Leda yabud'e gaban mota yasaka sannan yazaya yashiga yatada, ta mirror yakalleta yaga ta jingine kanta a jikin kan sit d'in da take zaune ta lumshe idanunta haka yacigaba da tafiya chan jawahir tace muje hotel. Kallonta yayi yaga still idanuwanta suna a lumshe dan haka yakama hanyar wani babban hotel dake cikin garin katsina wanda sai d'an wane da wane yake zuwa suna isa wajen da ake parking d'in motoci yaje yai parking d'in tashi sannan yajuyo yakalli jawahir da har lokacin idanunta suna a lumshe yace kifito mushiga, ahankali tabud'e idanunta da sukayi jawur yanayinta zaka kalla kagane cewa ba wai bacci tayiba dakyar tabud'e murfin motar tafita nan shima yabud'e yafita tare da zagayawa yad'auko ledar sannan yawuce a gaba tana bayanshi har suka isa cikin hotel d'in suka tsaya a reception d'aki Barr Faruk yakama masu mai kyau da tsada na kwana d'aya koda wuni zasuyi ammah kud'in kwana d'aya yabiya sannan ya amshi key d'in d'akin. Kallon jawahir yayi yace muje, wucewa tayi gaba yana binta a baya suka haura step sukaje wasu manyan d'akuna wad'anda suka fi na k'asan kyau room 5 yabud'e jawahir tsaye tayi tak'i shiga saida yace bismillah kishiga man sannan tashiga, a parlour tatsaya tana kallon makeken parlorn daidai lokacin da shima yashigo yarufe d'akin yawuce bedroom yabud'e shima komai fes Fitowa yayi yasamu jawahir a wajen da yabarta a tsaye ledar da yashigo da ita yamik'a mata yace ga wannan rigace kishiga ciki kiyi wanka kisaka sai kikawo wad'annan kayan naki abada awanke maki kafin mutashi tafita sun bushe, bata musaba takar6i ledar tawuce bedroom d'in cikin sauri tana shiga tamurza key sannan tafara zagaya d'akin tana binshi da kallo lokaci guda hawaye suka fara fita daga idanunta saurin goge hawayen tayi tai saurin fad'awa bathroom, ruwa tahad'a masu gumi tayi wanka saida tatisa wanka ya kai sau biyar tawanke kanta tas hatta kayan da tacire dakanta tawanke ita kanta saida taji wani iri da taga yadda sukayi, bayan ta gama a cikin toilet d'in tashanyasu tafito, wani irin sanyi ne taji yana ratsata da tayi wankan ledar da Barr Faruk yabata tabud'e taga jallabiya ce me gyale a ciki nan tad'auka tasaka saida tagyara kanta sannan tayi sallah bayan ta gama zuwa tayi tabud'e k'ofar takoma saman gado takwanta tare da runtse idanunta jinta take duk wata iri. Barr Faruk da bayan shigarta zama yayi a parlorn har saida yaji anfara kiran sallar azuhur sannan yatashi yarufe d'akin da key yaje masallaci bayan ya dawo kiran waya yayi yasa akawo masu abinci koda aka kawo nan yazauna yaci nashi yabar ma jawahir nata idan tafito taci ammah har yagama bata fitoba dan haka yad'auka yanufi bedroom d'in knocking yayi da mamaki yaji k'ofar a bud'e turawa yayi a hankali yashiga sai ganinta yayi kwance saman gado tayi rufa da blanket kanta ne kawai a waje, kallo d'aya yayi mata yad'auke kai yaje saman bedside ya ajiye mata abincinta yawuce zai tafi har ya juya sai jin muryarta yayi ta ce bana buk'atar abincin, juyowa yayi yakalleta still dai idanuwanta a rufe yace kina nufin haka zaki zauna da yunwa bazaki ci komai ba. 'Dan guntun murmushi tayi tace kar kadamu da cina kaje kawai kaci idan ka gama sai kazo inbaka tarihin nawa. Cike da zumud'i yace ni na gama Indai kin shirya toh sai mufara,,zuwa yayi yazauna bisa wata 1 seater dake opposite d'in gadon, shuru jawahir tayi tak'i bud'e idanunta bare yasa ran zata tashi tafara,,cikin ranshi yace anya kuwa zata fara yanzu? Bai gama tunanin ba yaji ta ce ka k'osa infara ko? Da mamaki yake kallonta kamar tasan abinda yake cikin ranshi. Bud'e idanunta tayi tasafkesu akanshi tace dafatan ka shirya yanzu infara maka. D'auko jakkar laptop d'inshi yayi yafiddota a ciki yakunna sannan yace na shirya. 'Dan guntun murmushi tayi tare da d'aga kanta tana kallon ceiling tace dafarko dai kamar yadda kaji ko kasani mahaifina ba 6oyayya bane a garin nan nasan kana jin sunanshi Alhaji Muhammad Maikudi,,, Alhaji Muhammad mai kud'i dan asalin garin funtua ne dake cikin nan k'aramar hukumar katsina, Malam Sani da Malama Ramatu sune iyayensu, 'ya'ya biyu ubangiji yabasu a duniya daga Mu'azu shine babba sai k'anenshi Muhammad watau mahaifina. Mahaifinsu Malam Sani yana da rufin asirinshi ba laifi dan d'an kasuwa ne yana da d'an shagonshi da yake siyar da yan kayan miya Alhamdulillah yana samu sosai dan zan iya cewa duk yawancin yan ungunwarsu wajen malam Sani me kayan miya suke siya har ma da yan k'etaren unguwar dan kayan miyarshi suna da sauk'i ga kyau, Tun tashin Muhammad yakasance mai son karatun arabi da na zamani inda kuma d'an uwanshi yakasance akasin haka baison karatu, mahaifinsu malam Sani kullum cikin nasiha yakeyi mashi akan yadaure yayi karatu kamar yadda d'an uwanshi yakeyi, ba dan ya soba ya amince yashiga makaranta suka kasance aji d'aya da k'anenshi saidai hakan baisa yadinga karatun ba dan duk gwajin da za'ayi masu baya wani ci sosai sa6anin k'anenshi da yake maida hankali dan dama shi yana da burin karatun a ranshi duk wata kyauta da za'a bada Tun daga primary har secondary yana cikin wad'anda za'a ba saboda k'ok'arinshi da maida hankali a karatunshi saboda haka ne yasa yayanshi yatsaneshi kiri Kiri yake nuna mashi bak'in ciki a fili shikuma dayake Allah ya yi shi mai hak'uri da son d'an uwan nashi dan haka cikin kyautukan da yake samu yadinga bashi wasu ko yaraba rabi yabashi duk dan azauna lafiya. Bayan sun gama secondary school takardun Muhammadu sunyi kyau sosai inda shikuma Mu'azu nashi zaiyi gyara mahaifinsu ya nuna bak'in cikinshi da rashin cin d'an nashi Mu'azu ammah da yake shi mutum ne mai yadda da k'addara dan haka yace zai sake biya mashi yagyara shiko yace inaa bazaiyi ba babu wani karatu da zai k'ara yi yanzu dan shi ya gama nashi kasuwanci yake da burin yi dan haka malam Sani yasama mashi shagon haya acikin kasuwa yazuba mashi yan provision inda shikuma Muhammadu yanuna karatu yakeson cigaba dan haka mahaifinsu yasama mashi admission na Degree a A.B.U Zariya yaje chan yana karatunshi hankali kwance. Mu'azu ko ya maida hankalinshi da Sana'ar shi har yasamu budurwa wadda yakeso yace ma Mahaifin nasu shi aure yakeson yi, da fari da Mahaifin ya ce yabari yak'ara tara yan kud'i sannan yayi maganar aure ammah fafur yanuna a'a dan haka Mahaifinnasu ya amince akaje akayi magana gidansu Fatima aka tsayar da ranar aure. Shiko Malam Sani baida buri akowane lokaci sai na son aika ma danshi Muhammad kud'i da ya d'an tara dan saboda ya san bazai ta'ba zuwa yanema ba dan shi yana da zurfin ciki ko da yana son abu toh zai barshi bazai nuna ba saidai idan ya ga yazama dole ne makaranta ake buk'ata sannan zaiyi ma Mahaifin nashi magana yatura mashi. Ahaka har yaje aji biyu a karatunshi inda shikuma Mu'azu akasha shagalin bikkinsu amaryarshi tatare a wani gidan haya da yakama masu, Muhammad lokacin ya so yazo bikkin nashi saidai suna exams ne dan haka yahak'ura saida suka gama yadawo gida. Yana aji ukku ne Allah yayi ma Alhaji Sani rasuwa ta dalilin hadarin mota da sukayi akan hanyarshi tadawowa daga k'aramar hukumar ajiwa lokacin ya je dubiyar wani abokin kasuwancinshi da baida lafiya sukayi accident saidai aka maido gawarshi gida, ba k'aramin tashin hankali iyalanshi suka shiga ba dan ita Inna Ramatu har suma saida tayi, shiko Muhammad gani yake ya fi kowa shiga damuwa da burinshi bai cikaba mutuwa tarabashi da mahaifinshi dan ya ci burin yagama karatu yasamu aiki iyayenshi suci moriyar wahalar da suke sha wajen karatunshi. Tunda yadawo gida saida akayi arba'in lokacin mutuwar ta lafa sannan Inna Ramatu tamatsa mashi yakoma makaranta da zai tafi tatura shi gidan yayan nashi yafad'a mashi zai koma ammah Mu'azu babu abinda yabashi saidai cewa da yayi Allah yakiyaye. Yan kud'in da Inna Ramatu tahad'a mashi dasu yakoma makaranta, basu je mashi ko inaba suka k'are dan ko da siyan handout akabar mutum ya wahala, Koda yakoma makaranta baifi wata d'aya ba 'yan kud'in da yaje da su suka k'are ganin yanayin da suke ciki shi da mahaifiyarshi na rashi yasa kawai yafara shiga kasuwar garin duk ranar da take ci yana zuwa yayi dako yasamu d'an abinda zai rufa ma kanshi asiri saida yahad'a da tsaron shagon wani idan sun tashi lecturer yake zuwa ahaka har yasamu da cukucuku ya had'a degree d'inshi dan yayanshi bai taimaka mashi da ko kud'in mota inma Inna Ramatu tamatsa mashi yatambayeshi ko ya tambaya saidai yace baida kud'i da dai ace ya yi mashi magana dawuri da ya bashi yanzu hidima tayi yawa. Haka sukaitayi har yagama karatunshi bai ta6a d'aukar Naira d'aya yabashiba kuma shima bai ta6a damuwa ba. Bayan ya gama Mahaifiyarsu ta so yafara neman aikin gwamnati ammah yace a'a sai ya yi masters d'inshi, Yaya Mu'azu fad'a yadinga yi yace haka zai k'are wajen bauta ma boko Maimakon yakama aiki yayi aure dan shi a lokacin har matarshi ta haihu d'anta namijii ya ci suna Umar,,,wasu siraran hawaye ne suka gangaro daga idanun jawahir tasa hannu tagoge sannan tacigaba da cewa Saida Muhammad yadinga lalla'ba mahaifiyarsu sannan ta amince yaje chan Kaduna yayi masters d'inshi duka kud'in gadonshi ya amsa yayi amfani da su wajen karatunshi da taimakon Mahaifin wani abokinshi Salmanu da yake kaduna yasamu yagama masters d'inshi dan yana tausaya mashi sosai musamman yadda yaga yana fafucikar neman yan kud'in da yake karatun da su, da dad'i ba dad'i ahaka yagama masters d'inshi. Bayan ya gama ne Mahaifin Salmanu yasamo masu aiki tare d'an shi a wani company da yake cikin garin Kaduna. Murna ba a magana wajen Muhammad da mahaifiyarshi shiko Mu'azu haushi yadinga ji yana cewa ina ma amfanin irin wannan aikin ai haram kawai za'aci da zuwa yayi yakama Sana'a ita zata fisheshi shidai Muhammad bai ta6a kulashi ba. Dakyar yasamu inna Ramatu ta amince yafara aiki a nan kaduna gidansu abokin nashi yazauna kasancewar baida amini kamarshi, albashinshi nafarko Inna Ramatu da dan uwanshi ya aiko mawa nan sukaita sa mashi albarka. Intak'aice maka acikin shekara biyu Muhammad ya tara kud'i sosai a lokacin ne Inna Ramatu tabud'e mashi wuta akan yadawo katsina yabar kaduna shima hakan duk hadda zigin yayanshi Mu'azu dan haka yasanar ma baban nashi halin da ake ciki dayake mutum ne mai kirki nan yace kar yadamu zai nema mashi transfer yakoma katsina da aiki. Haka ko akayi yakoma cikin garin katsina ba dan ta soba tahak'ura tace ai k'ara nan ya d'anfi kusa akan kaduna nan kuma suka tisoshi a gaba akan maganar aure nan yaimata alk'awalin insha Allahu zaiyi ammah sai ya fara gini nan ta amince da hakan, kud'in da yake samu na albashinshi biyu yake rabawa ya aika masu da rabi shikuma yayi amfani da rabi dayake mutum ne me gaskiya baifi shekara ba aka k'ara mashi matsayi a wajen aikin, Gini babba yafara yi batare da sanin mahaifiyarshi ba cikin wata shidda yagina dank'areren gidanshi a cikin garin katsina sai bayan ya yi ginin ne yad'auko su sukazo suka gani daga nan yafara shirye shiryen aure yasamu wata bafullatana yar cikin kebbi ya aura shima lokacin sunje wani workshop ne a chan garin suka had'u da Khausar har sukayi aure bikkin da akayi shagali sosai Inna Ramatu tana son khausar sosai dan babu ruwanta ga hak'uri, shekararsu d'aya da aure yamaido su Inna Ramatu da Baba Mu'azu a gidanshi part yafitar masu da shi yace ya fi son suzauna kusa da shi lokacin Baba Mu'azu yaranshi biyu Umar shine babba sai Aliyu. Khausar sosai take girmama mahaifiyar mijin nata da d'an uwanshi hatta matarshi khausar tana girmamata sosai, ganin haka yasa Fatima tadinga d'aukar kanta watace dan wata rana ita take bada umurnin d'in abinda za'ayi a gidan. Muhammad ganin tunda yayanshi yadawo gidan bai aikin komai sai zaman gida duk sai yaji ba dad'i yabarshi ahaka koda dama shi yad'auke mashi nauyin komai wata rana Shima Mu'azu yaje yasamu k'anen nashi yace shi fa ya gaji da zaman gida taya zai dinga zama babu aiki kamar mace. Jin haka yasa Muhammad yace kayi hak'uri yaya nima k'ok'arin sama maka nake dan nima banjin dad'in ganinka haka. Mu'azu yace a'a toh hakan dai yakamata. A cikin yan kwanakin Muhammad yabud'e mashi babban shago na kaya a kasuwa yazuba mashi komai yabashi ammah wannan abun da yayi mashi maimakon yagode sai ma yaraina yaje yasamu inna Ramatu yafad'a mata yace wai a matsayinshi na yayanshi maimakon yasama mashi aiki a company da yake aiki shine yabud'e mashi shago shi ga sarkin kasuwanci ko. baki tarik'e tace anya kuwa Mu'azu kana da hankali yanzu duk k'ok'arin da bawan Allahn nan yakeyi akanmu baka gani kaduba fa kaga d'anka ya sakashi makaranta shi yake d'aukar nauyin karatunshi mu kanmu babu abinda muke nema murasa a gidan nan daga shi har matarshi a tsaye suke a kanmu. Hakan baiyi ma Mu'azu dad'iba ammah babu yadda ya iya tunda mahaifiyarsu bata goyi bayanshi ba saidai yaje wajen matarshi sudinga kitstsima gulmarsu shi da ita. _Free Page_ _Wannan littafin na kud'i ne ga duk me buk'ata zai biya d'ari biyu N200 Kacal zai turo MTN card ta wannan number d'in 09035938246 ko katuro 200 ta account number d'innan 5330055604, *NANA HALLIRU* FIDELITY BANK, idan katura ka aiko da screen shot na transaction ta wannan number 09035938246_ _Ga mutanen Niger zasu tura 300f ta wannan number d'in +22794775574_ _Gareku masoyan gaskiya_ _*GARA B'ASA! GARA B'ASA!! GARA B'ASA!!!* wannan gara'basa anyi tane kad'ai ga duk wanda keson karanta littafin *FANSAR RAI* da *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shaharariyar marubuciyar nan watau *AMINA ABBA UMAR* ga duk mai bukatar karanta duka novel's d'in biyu zai biya *N300* kadai domin samun damar karantasu cikin aminci, gareku masoyan gaskiya muna jiran ku nuna mana k'aunarku ta hanyar biyan *N300* kad'ai, idan duka biyun kakeso zaka turo kud'i ta wannan account number d'in 3092292135 FIRST BANK, ko kuma katin waya Mtn na d'aya daga cikin Numbers d'in nan 09035938246 ko kuma 07030792790, ko 07036073670, sai ka aiko da shedar biya ta d'aya daga cikin numbers d'in, sai munji daga gareku masoyanmu_ _Sis Nerja'art✍🏻_ [3/13, 20:23] Sis Nerja'art👰🏻: *......FANSAR RAI.......* _*STORY AND WRITTEN BY SIS NERJA'ART✍🏻*_ *INTELLIGENT WRITERS ASSO....®* [On Ward Together] *DEDICATED TO ZM CHUBA'DO* _Wannan littafin na kud'i ne ga duk me buk'ata zai biya d'ari biyu N200 Kacal zai turo MTN card ta wannan number d'in 09035938246 ko katuro 200 ta account number d'innan 5330055604, *NANA HALLIRU* FIDELITY BANK, idan katura ka aiko da screen shot na transaction ta wannan number 09035938246_ _Ga mutanen Niger zasu tura 300f ta wannan number d'in +22794775574_ _Gareku masoyan gaskiya_ _*GARA B'ASA! GARA B'ASA!! GARA B'ASA!!!* wannan gara'basa anyi tane kad'ai ga duk wanda keson karanta littafin *FANSAR RAI* da *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shaharariyar marubuciyar nan watau *AMINA ABBA UMAR* ga duk mai bukatar karanta duka novel's d'in biyu zai biya *N300* kadai domin samun damar karantasu cikin aminci, gareku masoyan gaskiya muna jiran ku nuna mana k'aunarku ta hanyar biyan *N300* kad'ai, idan duka biyun kakeso zaka turo kud'i ta wannan account number d'in 3092292135 FIRST BANK, ko kuma katin waya Mtn na d'aya daga cikin Numbers d'in nan 09035938246 ko kuma 07030792790, ko 07036073670, sai ka aiko da shedar biya ta d'aya daga cikin numbers d'in, sai munji daga gareku masoyanmu_ _Free Page_ *PAGE ELEVEN* Muhammad dayake ba zaunanne bane yau baya wannan gari gobe baya wanchan gari dan haka gida yadawo kamar hannun yayanshi Mu'azu sai yadda yace hatta Khausar ita da yake gidan mijinta sai yadda akayi da ita, duk da haka bata ta'ba bud'e baki tafad'a ma mijinta ba, itadai burinta suyi zaman lafiya saboda k'arfin hali irin na Fatima habaici tadinga yada mata wai juya saidai aci ayi kashi ba haihuwa dan lokacin Khausar Shekararsu ukku da aure saidai tashige d'aki tasha kukanta tagode ma Allah. Saida suka shekara hud'u da aure sannan Allah yabata ciki kar kuso kuga murna wajen Muhammad da mahaifiyarshi shiko Mu'azu bak'in ciki yacikashi dan baiso Khausar tasamu cikiba ya so ace shi zai gaje dukiyar d'an uwanshi, Fatima ma a fili tadinga nuna bak'in cikinta itadai khausar bata taba kulataba. Cikin khausar na shiga wata tara tahaifi zangadediyar d'iyarta mai kama da mahaifinta sak, Muhammad kasa tsaye da zaune yayi yadinga fitar da kud'i yana siyayya abinda zai baka mamaki koda akayi haihuwar d'an uwan nashi baiyi mashi barka ba bai ma zo inda diyartake ba dan haka yad'auka dakanshi yakaimashi har part d'inshi sannan ya amshi d'iyar yakalla yamik'a mashi. Ranar suna yarinya taci suna jawahir, Muhammad ba k'ananun kud'i yakashe ba dan kud'i sunyi kuka sosai, hakan ma ya k'ara b'ata ma Mu'azu rai har yaje yasamu k'anen nashi yai mashi magana dan mi zai dinga 'barnar kud'i haka wannan ai almubazzaranci ne, murmushi Muhammad yayi yace insha Allahu yaya zan kiyaye. Tunda aka haifeni Umar shine me k'ok'arin zuwa yad'aukar ma Ummana ni dan tunda yak'yalka ido yaganni nashiga ranshi musamman ma tun barka da mutane suka dinga cewa ina Kama da shi kuma hakane muna yanayi sosai. Son duniya iyayena suka d'auka suka d'aura min hatta kakata kullum sai tasa ankawo mata ni ta ganni. Abun yana ma Mu'azu da matarshi ciwo sosai har wani lokacin yakasa boye bak'in cikinshi yaje yasamu inna Ramatu yace wai dan Muhammad yana da kud'i saisa tafi son d'iyarshi akan ya'yanshi, inna Ramatu nan zata dinga yin fad'a tace ita duka natane kar yasake irin wad'annan maganganun, dan haka saidai suyita kulle kullenshi shi da matarshi. Lokacin da nacika shekara d'aya a duniya Abba yabiya mana umara da ni da ummana sai Inna Ramatu sannan shi mukaje a tare, yace shikuma yayanshi sai wata tafiyar sannan yaje da iyalanshi Wayyooo kar kuso kuga bak'in ciki a wajen Mu'azu dan har gaba yayi da Abbu har suka dawo daga umara yana fushi da shi duk tulin tsarabar da yayi mashi ammah hakan baisa yasafko ba saida yabiya mashi shi da matarshi sukaje sannan hankalinshi yakwanta. Haka rayuwar gidan mu tacigaba da tafiya da dad'i ba dad'i dan shima Abbu ko bai fad'aba kasan baya jin dad'in zama da d'an uwan nashi hak'uri kawai yake da shi. Ina da shekara biyar aka sani school lokacin Yaya Umar yana SS1 inda Yaya Aliyu kuma yana JSS2 dan dama sun girme min dan ko yaya Aliyu ya bani kusan shekaru takwas. Gatan duniyar nan babu irin wanda ban samu wajen iyayena da kakata itako Matar Abba Mu'azu tsakanina da ita saidai hantara saboda hakane ma ban cika zuwa inda takeba daman Yaya Umar ne me d'an kulani dayake shi ba Maison hayaniya bane sosai saisa bai cika shiga shirmenaba yaya Aliyu ko kad'an kad'an ya mangareni ko yadukeni inkoma inta ma iyayena kuka saidai suyita lallashi. Ina da shekara goma Allah yayi ma Inna Ramatu rasuwa munyi kukan rashi sosai dan tsohuwar nan ta yi yaya Umar har da suma dan duk ya fimu sabawa da ita saboda rabin rayuwarshi a wajenta yakeyinta. Bayan rasuwarta Abba Mu'azu kullum baida aiki sai kar'bar kud'i wajen Abbu kuma baida ikon yace babu nan zai fara fad'a har sai ya bashi. Lokacin da Yaya Umar yagama secondary school d'inshi Abbu admission yasamo mashi a chan Egypt yafita karatu. Nayi kuka sosai da tafiyarshi dan dama dashi ne nake shiri Dan shi Yaya Aliyu tsakanina da shi sai hantara dan zan iya cewa shine yakwaso halin iyayenshi. Arzik'i Abbu akowane lokaci k'ara bunk'asa yake dan haka ne ma yabud'e companynshi yazuba ma'aikata suna kular mashi da shi abun ya yi ma Abba Mu'azu ciwo dan shi yaso ace ya sa yakula da companyn ba wasuba. Ana ahaka har nashiga jss 1 lokacin su Ummi da Abbu suka koma aikin hajji suka barni wajen Ummah Fatima na sha wahala sosai dan komawa nayi kamar baiwarta, hatta idan zanyi bacci saidai inkwanta k'asa duk sanyin tiles d'innan dan cewa take bana hawan mata gado, ga tsangwamar Yaya Aliyu da nakesha wani lokacin inta ji ina ma ace shine aka fitar dashi waje yayi karatu ba yaya Umar ba ammah shi a nan Abbu yabarshi yace shi yayi karatun a cikin garinsu dan baiso duk sukwashe abar gidan bakowa hakan baiyi mashi dad'iba dan ya K'wallaci Abbu sosai a ranshi akan hakan. Wahalar da nasha a hannun bayin Allahn nan bata fad'uwa dan wata rana ko makaranta ban samun zuwa dukan da nake sha ko ba'a magana dan duk rana sai nasha dukan Umma Fatima, yadda kasan d'iyar almajira haka nakoma duk gatana ammah suka barni bana samun ko wanki. sai daren da su Ammi zasu dawo sannan tasa aka wanke min kayana tas kuma tabarni nakwanta saman gadonta. Koda su Ammi suka dawo sun lura da canzawar da nayi ammah basu nunaba nan suka cikasu da tsaraba babu kunya suka amshe, nice ma nake fad'a ma Ammi irin abinda aka dinga yi min saidai tace ai laifinane tasan bana jin magana koda a cikin zuciyarta ba hakaba ko kad'an bataji dad'iba kawai bata nuna bane. Bayan shekara d'aya ranar wata laraba Abbu ya dawo daga wata tafiya da yayi a chan Dubai suna zaune a setting room d'inshi shi da Ammi suna hira nan Abba Mu'azu yashigo Indai ka ga yazo wajen Abbu Toh akwai abinda yake nema wajenshi waje yasamu yazauna nan suka gaisa, bayan sun gaisa yanemi kud'i wajen Abbu nan Abbu yaje yad'auko yabashi batare da ya musaba har ya mik'e zai tafi Abbu yace yauwa Yaya daman inaso muyi wata magana da kai. Komawa yayi yazauna yace ina saurarenka, Ammi har ta mik'e zata basu waje Abbu yace tazauna nan takoma tazauna wasu files ne guda biyu yad'auko yace daman akan maganar gidana na goruba road da aka kammala ginawa ne. Abba Mu'azu yana jin haka yawashe baki yace toh toh nagane wannan babban gidan mekyau kenan. Murmushi Abbu yayi yace Eh shine nakeso kashaida na mallaka ma Khausar shi daman ita nagina mawa. Lokaci guda fuskar Abba Mu'azu tacanza zuwa wani irin yanayi Abbu cigaba yayi da cewa sai wannan filin nawa na mallaka ma Jawahir hatta companyna komai naciki na maida da sunanta,,saurin Katseshi Abba Mu'azu yayi yace wannan wane irin zancen banza ne kakeyi watau Khausar ta shanyeka ko? Cike da mamaki yake kallon yayannashi yace Subhanallahi yaya wannan wace irin magana ce haka kakeyi? Cikin 6acin rai yace Eh d'in na fad'a wannan munafukar matar shanyeka tayi inba hakaba taya zaka d'auki wannan makeken gidan kamallaka mata dan gulma kamaida sunan companynka yazama na 'yar k'aramar yarinyar chan, watau ni da Ya'yana kake bak'in cikin mumoreka ko, toh ko kak'i ko kaso mune dai naka dan bamu canzuwa ammah mata ko ana canzata. Subhanallahi Yaya wannan wace irin magana ce kakeyi? Ammi cikin sanyin jiki tace kayi hak'uri yaya shima dawasa yakeyi maka ba gaske bane. Wane irin kallo Abba yayi mata yace au ni kika maida yaronki da zakice wasa yakeyi min? Ke rabani da wannan munafuncin naki duk abinda kike k'ullawa minene ban saniba. Ammi shuru tayi tare da sunkuyar da kanta k'asa tana jin ba dad'i a ranta. Abbu da yaga abun yayan nashi ba me k'arewa bane yace yaya ammah ai hakan da nayi ba laifi bane dan na kyautata ma iyalina. Eh ba wani abun bane Ammah wallahi bazan iya bari kamallaka mata gidan nan ba. Kasan me hak'uri bai iya b'acin rai ba nan ran Abbu ya'baci yace saidai hak'uri yaya dan na riga da na mallaka mata ni duk abinda zanyi nafiso inyi adalci a rayuwata bakin gwalgwado kaima ina kyautata maka da iyalinka banta'ba bari kuka nemi wani abu kuka rasaba duk abinda kakeso inayi maka kuma wannan baiwar Allah bata ta'ba tankawaba toh akanme zakaji zafinta. Jinjina kai Abba Mu'azu yayi yace Eh dole kayi min gori banga laifinkaba watau dan kana bani shine yau zakayi min gori saboda matarka shikenan nagode nima Allah yahore min kaga idan zan k'ara kallon abun hannunka yana fad'in haka yajuya yawuce yafita cikin fushi. Ammi cike da damuwa tace Alhaji meyasa kayi haka d'an uwanka nefa ai da ka barshi ni na yafe ba sai ka bani gidan ba. Abbu girgiza kai yayi yace ra'ayi nane Khausar kuma ba laifi bane dan na baki tunda ke matatace sannan ke shedace bakin gwalgwado ina k'ok'arin kyautata ma bawan Allahn nan ammah baya gani nidai Allah ya sani ina bakin k'ok'arina sannan idan nafasa baki gidan banyi ma kaina da ke kanki adalci ba sannan tun lokacin da aka fara ginin companyna daman dasunan na d'iyata ne, kibari kawai zai safko. Ammi cikin sanyin jiki tace to shikenan Alhaji nagode sosai Allah ubangiji yasaka da alkhairi yak'ara bud'i. Abbu ya amsa da Ameen. Ummah Fatima tana tsakar gida Abba yashigo part d'insu cikin b'acin rai yawuce yanufi room d'inshi saurin binshi tayi taje tasameshi a tsaye yana zagaye d'akin tsayawa itama tayi tace Alhaji Lafiya? Cize le6e yayi yace Fatima ina fa lafiya yau ni Muhammad yaci ma mutunci akan matarshi. Da mamaki take kallonshi tace wane irin cin mutunci muhammad d'in dakanshi? Hmm kedai bari,,,nan yakwashe duk yadda sukayi yafad'a mata. Salallami tafara yi tace yanzu shi Ahmad zai fifita matarshi akanka bayan kai d'an uwanshine kuma dan cin fuska a gaban idanunka yace ya mallaka mata wannan dank'areren gidan wai company ya ba d'iyarshi watau mu haka yakeso mudauwaba mu da bakomai nashiba. K'wafa Mu'azu yayi yace kibarni da shi nasan abinda zanyi dan dama baisan ya kaini wuya ba tuni. Ai wallahi Alhaji k'ara kad'auki mataki tun kan yarabe masu dukiyarshi muna nan zaune. "ai wannan dole ne ind'auka dan wallahi bazan ta6a bari yarabe masuba ni yabarni nan baki a sake ina hamma,,,yana fad'in haka yawuce yafita. Abbu bayan angama wannan fita yayi yaje yasamu lauya d'inshi yafad'a mashi komai yabashi copy d'aya daga cikin takardun inda yaje yasamu abokanshi biyu yadamk'a masu copy d'aid'aya dan suzama shaida ya mallaka ma matarshi gidan da yagina sai companynshi ya mallaka ma d'iyarshi. Da dare suna shirin bacci Ammi cike da damuwa tace Alhaji dan Allah kataimaka kasasanta tsakaninka da d'an uwanka kar hakan ya'bata maku zumunci. Murmushi yayi yace kar kidamu babu abinda zai ta6a zumuncinmu yanzu haka akwai wani gida da nikeso insiya inmallaka mashi kinga shikenan haka ya yi ko? Murmushi Ammi tayi tace Eh Alhaji yayi Allah yasaka da alkhairi. Intak'aice maka tun daga wannan ranar Abba Mu'azu bai sake yi ma d'an uwanshi magana ba koda shi ya yi mashi shiko d'auke kai yake baima Amsawa ahaka har sukaci wata d'aya. Wata ranar lahadi Abbu yaje yasamu abba Mu'azu yaso suzauna sutattauna akan fushin da yake da shi ammah yak'i yace Indai har yanaso suzauna toh dole sai ya janye kyautar da yayi ma matarshi da d'iyarshi shikuma Abbu yace gaskiya bazai iyaba shima akwai wani gida da yasa aka gyara suje yagani zai mallaka mashi shi. Abba yace baisan da wannan ba dan yasan bazai kai na Ammi kyauba saidai ayi musanya yabata nashi shi kuma yabashi nata. Abba yace gaskiya bazai iyaba. Abun ya yi ma Abba Mu'azu ciwo sosai. A daren ranar Abbu duk damuwa tadameshi har sun kwanta bacci yafad'a ma Ammi abinda yake faruwa tace dan Allah yabashi gidan Indai har hakan zaisa asamu zaman lafiya, Abbu yace toh shikenan bari sai zuwa safe sai muga yadda za'ayi. Ashe Abbu nah bazai kai safen ba cikin dare suna bacci wasu Katti ukku suka shigo cikin gidan babu wanda yasan shigowarsu wajen k'arfe biyun dare sai ji su Abbu sukayi ana buga masu k'ofa da k'arfi a firgice duk suka farka Abbu yatambaya wanene? Muryar wani k'ato sukaji ya ce kazo Kabud'e mana ko mubud'e dakanka. Abbu salati kawai yake inda Ammi take kuka tana salati. Cikin tsawa mutanen sukace bazakazo Kabud'e ba sai mun bud'e dakanmu? Mik'ewa Abbu yayi zaije yabud'e Ammi tayi saurin rik'eshi tace dan Allah Alhaji kar kaje. Yana shirin yin magana suka harbe k'ofar da bindiga suka shigo su duka fuskokinsu da face Max d'aya yake rik'e da bindiga d'aya kuma shar'be'biyar wuk'a d'ayanko bai rik'e da komai. A ranar su Ammi sunga tashin hankali dan sasu sukayi sukai kneeldown karon farko takardun gidan Ammi da na company suka tambaya Abbu yace shi baida wani company kuma wannan shi kad'ai ne gidanshi. Kan bindiga suka buga mashi Ammi tasaki wata irin k'ara, har saida wajen yafashe sukace kabamu mukace yace ni na fad'a maku banda su. Sukace zaka rasa rayuwarka idan har kayi mana gardama dan munsan akwai. Abbu nacewa yayi akan babu nan d'aya daga ciki yad'aga wuk'a biyun suka rirrike Abbu itako Ammi zuwa tayi tarikesu tana kuka tace dan Allah kar sukashe mata miji zata basu duk abinda sukeso. Wurgi sukayi da ita gefe kafin tataso anyi ma Abbu yankar rago sai jini da yafara tsartuwa,,,,jawahir fashewa tayi da wani irin kuka tace sun kashe min Abbu nah a lokacin ni ina chan d'akina ina bacci koda lokacin ban wuce shekaru sha biyar ba a duniya, goge hawayen tayi tace Ammi wata irin razanannar k'ara tasaki daidai lokacin mutane biyu suka cire Max d'insu suna goge hannuwansu da suka 'baci da jini nan ita kuma tasulale k'asa a sume. Ashe d'aure megadin gidanmu sukayi yana ta yunk'urin yakwance ammah yakasa sai bayan tafiyarsu yasamu yakwance dakyar sannan yashigo yagane ma idanunshi abinda yafaru su ma masu aikin gidanmu tsoro ne yahanasu fitowa sai bayan tafiyarsu nan akaje aka sanar da Abba Mu'azu yazo yadinga kuka kowa wajen kuka yake, me gadi ne yakira police inda aka yayyafa ma Ammi ruwa tafarfad'o hatta ni da nake k'arama nayi kuka sosai da naga cin mutuncin da akayi ma Abbu nah. Kafin safe gidanmu ya cika da mutane inda yan sanda suke ta binciken gidan suna so sudauki report aka dinga ma Ammi tambayoyi tana fad'in abinda yafaru har wajen k'arfe tara sannan akayi ma Abbu wanka da za'aje kaishi Abba Mu'azu yashiga d'akin da aka sitirta gawar yana kuka yana ma d'an uwan nashi addu'a nan aka barshi dan yayi mashi addu'a akaba Ammi dama itama taje tayi ammah takasa. Ahaka aka tafi da Abbu gidanshi na gaskiya nan aka fara zaman makoki ammah abinda zai baka mamaki ba wani bincike da aka cigaba da yi dan gane wad'anda sukayi aika aikar Ammi saidai tagaji tasamu Abba Mu'azu tayi mashi maganar yace ai yan sanda suna chan suna bakin k'ok'arinsu suna ta bincike. A rana ta biyu da rasuwar yaya Umar yazo k'asar nan shima yayi kuka sosai har saida akayi arba'in sannan yakoma school, Ammi damuwa tad'auka ta aza ma kanta nima haka kusan kullum sai na ce akaini wajen Abbu nah daga ni har Ammi idan kaganmu sai ka tausaya mana dan duk mun fita hayyacinmu. Anayin arba'in su Abba Mu'azu suka dawo cikin gidanmu ya amshi key d'in part d'in Abbi yace nan zai zauna shi da matarshi inda d'akina yakoma na yaya Aliyu saidai nakoma d'akin Ammi nazauna aiko nan su Abba Mu'azu suka dinga zuba mulki a gidan Ammina takoma abun tausayi dan Ummah Fatima matsa mata tadinga yi a cikin gidan ma ba ko'ina take da ikon zuwaba ita da gidan mijinta ammah aka sa mata dokoki, hatta shi kanshi Yaya Aliyu taka Ammina yake son ranshi wani lokacin saidai muyi zamanmu a d'aki Ammi tayita kuka ina tayata, Abinci ma kanshi sai angama dama abamu saidai 'yan aikin gidan suke fakar Idanun su Ummah Fatima sukawo mana a d'aki idan Ammi tayi masu magana akan sudaina sai suce a'a koda ace zasu rasa aikinsu sai sun taimaka mata dan su kansu sunsan sun mori matar nan sosai abun hannunta baya tsone mata idanu tana da kyauta. Haka rayuwarmu tacigaba da tafiya a gidan namu da yazama kamar dodonmu duk motocin Abbina suka koma su Abba yake shiga motar da Abbu yasiya ma Ammi ita Abba ya amshe yaba ummah, Wata rana muna zaune a d'aki Ammi tana min k'arin karatun islamiyya nan Ummah Fatima tashigo direct wajen wardrobe d'in Ammi tawuce batare da ta tanka ma Ammi ba tana zuwa tafara fitar da kayan Ammi daga cikin wardrobe d'in. Ammi ce tace lafiya Hajiya kika zazzago min kaya? Juyowa tayi tagalla mata Harara tace lafiyar kenan zan d'auki kayan da naga basu dace da kisaba dan a yanzu ba a matsayin komai kikeba. Ammi tana kallo tazazzage mata kaya takwashe rabi da kwata hatta k'addarorin Ammi saida takwashe, babu yadda Ammi ta iya dole tahak'ura, yan aikin gidan gabad'aya korasu tayi lokacin da tagane suna kaima Ammi abinci saida tayi bala'i sosai sannan takoresu tace bazata iya zama da munafukai ba. Tun daga ranar duk wani aikin gidan yakoma wajen Ammi, munga rayuwa sosai dan hatta karatuna saida yanemi yatsaya dan kud'in da za'a biyamin babu saboda makarantar tana da tsada sosai saida Ammi tasiyar da wasu gwalagwalenta wad'anda taboye sannan tabiya min nacigaba da makaranta ta har nayi JSCE. Dawowa gidan da nayi yasa nacigaba da taimaka ma Ammi da ayyukan gida, dan rashin imanin su Abba abincin da suke bamu baifi mutum d'aya yaciba wani lokacin ma rabin plate. Bayan shekara d'aya da Ammi taji shurun ya yi yawa ba'a ce komai ba akan maganar mutuwar mijinta da maganar gadonsu yasa tashirya taje gidan wani Aminin dadynshi tafad'a mashi tanaso araba masu gadon su. Ya amince da toh zaizo suyi magana da Abba Mu'azu. Koda yazo sukayi magana baice ma Ammi komai ba yatafi saima Alhaji Mu'azu da yazo yadinga fad'a dan mi zataje takai k'ararshi tace wai araba masu gado, a ranar wulak'anci yayi ma Ammi sosai har yakirata da matsiyaciya d'iyar talakawa. Kwana d'aya biyu bataji Alhaji Lurwan ya zo ya yi maganaba dan haka tasake d'aukar k'afa taje gidanshi yace tayi hak'uri ana ta k'ok'ari anaso ahad'a dukiyar Alhaji Muhammad sannan araba masu gado. Duk atunaninta dagaske ne dan haka takoma gida ammah har sati biyu bataji wata maganaba dan haka tabarshi tasake zuwa wajen wani abokin Abbu me suna Alhaji Surajo shima dai ba bayani, saida taje wajen aminnan Abbu hud'u ammah da sun shiga maganar ana kwana biyu zata watse. Nan hankalin Ammi yatashi sosai taje tasamu lauya d'in Abbu watau Barr Muhsin tafad'a mashi. Abinda yabata mamaki shima baiyi wani yunk'urin taimakonta ba dan ganin gadonta ya fito, dan haka tafitar da kayan d'akinta tasiyar taje tashigar da k'ara kotu, duk wannan abun fa Ammi tana yine dan kawai nawa hak'k'in ba ma nataba saidai abinda ita bata saniba shine wannan k'arar da tashigar zata zame mata matsala a rayuwa. _*Remain 1 page mugama free Page's😍*_ _Sis Nerja'art✍🏻_ [3/14, 21:42] Sis Nerja'art👰🏻: *......FANSAN RAI.......* _*STORY AND WRITTEN BY SIS NERJA'ART✍🏻*_ *INTELLIGENT WRITERS ASSO....®* [On Ward Together] *DEDICATED TO ZM CHUBA'DO* _Wannan littafin na kud'i ne ga duk me buk'ata zai biya d'ari biyu N200 Kacal zai turo MTN card ta wannan number d'in 09035938246 ko katuro 200 ta account number d'innan 5330055604, *NANA HALLIRU* FIDELITY BANK, idan katura ka aiko da screen shot na transaction ta wannan number 09035938246_ _Ga mutanen Niger zasu tura 300f ta wannan number d'in +22794775574_ _Gareku masoyan gaskiya_ _*GARA B'ASA! GARA B'ASA!! GARA B'ASA!!!* wannan gara'basa anyi tane kad'ai ga duk wanda keson karanta littafin *FANSAR RAI* da *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shaharariyar marubuciyar nan watau *AMINA ABBA UMAR* ga duk mai bukatar karanta duka novel's d'in biyu zai biya *N300* kadai domin samun damar karantasu cikin aminci, gareku masoyan gaskiya muna jiran ku nuna mana k'aunarku ta hanyar biyan *N300* kad'ai, idan duka biyun kakeso zaka turo kud'i ta wannan account number d'in 3092292135 FIRST BANK, ko kuma katin waya Mtn na d'aya daga cikin Numbers d'in nan 09035938246 ko kuma 07030792790, ko 07036073670, sai ka aiko da shedar biya ta d'aya daga cikin numbers d'in, sai munji daga gareku masoyanmu_ _Last Free Page_ *PAGE TWELVE* Wasu siraran hawaye ne suka gangaro ma Jawahir masu d'umi saurin runtse idanunta tayi tacigaba da cewa Ammi tana shigar da k'ara a Shara'a Court suka aiko ma Abba da takardar shammaci na ana gaiyatarshi a court akan k'arar da Ammi tashigar nashi dan wani tsohon alkali Makobcinmu yasama mata lauyan da zai tsaya mata, Abbu na jin haka hankalinshi yatashi yaje yasamu Barr Muhsin yafad'a mashi nan sukazo suna lallab'ata akan taje tajanye k'arar ammah tak'i dan haka Barr Muhsin yace zai tsaya yakare wanda ake k'ara, ana saura sati d'aya azauna kotu Abba Mu'azu yazo yasamu Ammi a d'akinta yace shi ya yarda zai bada duk wata dukiyar Abbu araba idan ta amince takawo duk wasu takardu nashi da suke hannunta shima zaisa atattaro sauran, Ammi tace bata yadda ba bazata bayarba abin ya 'bata ma Abba Mu'azu rai sosai da yaje yana fad'a ma matarshi ne Yaya Aliyu yaji nan ranshi ya'baci yace yanzu Abba wacchan matar har ta isa takaika k'ara akan kud'in dan uwanka? Wallahi bata isaba sai na nuna mata batada wayau, wacece ita,,,cike da jin dad'in kalamanshi Abba yace kabarta kawai Aliyu nasan ta inda zan biyo mata dan bata isa tatozarta ni a Idanun jama'a ba. Wallahi Abba batada amfani acikin gidan nan kawai akorata takoma garinsu tunda wanda ya aurota ya mutu ya bar duniyar. Murmushin mugunta Abba yayi yace Son kai ma kake fad'a ana ji, katayani tunanin hanyar da zamubi mukoreta tatafi tabar mana garin. Uhm shikenan Abba zan samo mana mafita. Bayan kwana ukku da yin abun Ammi tana kwance tana bacci da rana nikuma ina gefenta inayin homework d'ina dan a lokacin na cigaba da zuwa school ina SS 2 kamar an mintsireta sai ganin Ammi nayi ta tashi a firgice da mamaki nake kallonta nace Ammi Lafiya? Bin d'akin tashiga yi da kallo sai chan tace Jawahir kebbi nakeson zuwa hankalina ya yi gida. Zaro ido jawahir tayi tace Ammi kebbi kuma? Murmushi tayi tace Eh jawahir inason zuwa dan ina ji a raina bazan kai wani lokaci ba,,hawaye ne suka gangaro mata tace ganinsu shine kwanciyar hankalina zanje kawai. Fashewa jawahir tayi da kuka tace nima zan biki Ammi. A'a Jawahir bazanje dakeba kizauna kawai insha Allahu zuwa jibi zan dawo,,,Ammi na fad'in haka tafara had'a kayanta cikin wata yar k'aramar jakka tazuba kaya kala ukku da takardun gidanta da Abbu yabata take ta faman boyesu tana gama had'awa tasaka hijab tajuyo takalli jawahir da ke tafaman kuka tace kiyi hak'uri jawahir idan da rabo zan dawo gareki. Rik'ota jawahir tayi tace dan Allah Ammina kar kitafi kibarni. Cikin sanyin jiki Ammi tak'wace jikinta tace jawahir kikula da kanki,,,tana fad'in haka tajuya cikin sauri tafita daidai zata fita Aliyu yashigo gidan tsayawa yayi yana kallonta a wulak'ance saida taganshi tatuna batayi sallama da su Ummah ba dan gabad'aya jin jikinta take wani iri,,tsayawa tayi tace Aliyu kafad'a ma ummanku na tafi kebbi. Yatsina fuska yayi yace toh menene namu a ciki kiyi ta tafiya mana. Ammi batace komai ba tajuya tafita dan indasabo ta saba da rashin kunyar Aliyu, malam Idi driver tagani wajen megadi suna hira nan ta isa wajensu suka gaisa sannan tace mashi kebbi takeso yakaita. Da mamaki suke kallonta sukace Hajiya Lafiya zakije kebbi a wannan lokacin? Murmushi tayi tace buk'atar hakan ne yataso min. Malam idi yace toh Hajiya muje,,,megadi ne yataso yabud'e mata mota tare da yi mata Allah yakiyaye tana shiga motar idi na shirin tadawa sai ga Alhaji Mu'azu ya shigo gidan kallon malam idi yayi yace ina zakaje da ita? Jikin malam idi yana b'ari yace daman kebbi tace inkaita. Abba Mu'azu kallon Ammi yayi sannan yawuce yashige gida, Ammi runtse idanunta tayi wasu hawaye masu zafi suka gangaro mata ahaka suka kama hanya. Tunda suka Kama hanya Ammi sharar hawaye kawai take ahaka sukayi tafiyar kusan awa biyu suna shiga wani d'an kauye dake mararrabar katsina nan suka fara ganin wasu motoci biyu suna bin bayansu ammah basu kawo komai a ransuba sai malam idi da yaga sunk'i wucewa sai yarage speed dan suzo suwuce su ammah da mamakinshi sai yaga su ma sunrage yace Hajiya wad'an chan motocin sai bin bayanmu sukeyi, Ammi ta cikin mirror takallesu tace k'ila su ma hanyarmu sukayi ko gari d'aya zamuje. Malam idi yace hakane dan haka yacigaba da tafiyarshi normal ta wata boyayyar hanya suka ratsa sukabi dan suyi saurin isa kebbi da mamaki sai ganin motocin sukayi sun biyo bayansu lokaci guda d'aya daga cikin motar tak'ara gudu tazo ta wucesu tana wucewa tasha gabansu cikin sauri malam idi yaja wani irin burki dan kar yafad'a ma motar nan motar bayansu itama tatsaya, motar da take gabansu ce aka bud'e wasu karti biyar suka fito k'osassu rikicewa Malam idi yayi yafara salati tare da k'ok'arin so yatada motar ammah kafin yayi wani yunk'uri har mutanen sun iso ta window suka Fisge key d'in motar tare da bud'e k'ofar suka fiddoshi yafad'o k'asa, Ammi fasa k'ara tayi tare da furta innalillahi wa'inna ilaihiraji'un nashiga ukku. Zagayawa sukayi suka bud'e mata sukace tafito, jikinta yana rawa tafito tace dan Allah kuyi hak'uri kufad'a min abinda kukeso. Dariya suka kwashe da ita gabad'ayansu sun dad'e suna yi kafin daga bisani sukayi shuru d'aya daga cikinsu ne yace bamu buk'atar komai a wajenki face ranki kawai da mukeso. Ammi na jin haka ta ida rikicewa malam idi yace dan Allah kuyi hak'uri kar kukashemu. Tsawa suka kwatsa mashi sukace yayi masu shuru nan wani k'ato bak'i k'irin yayo wajen Ammi da shar'be'biyar wuk'a baya tafara ja a tsorace tana cewa dan Allah kar kakasheni mi nayi maku da kukeson rabani da raina? Waige waige tadinga yi tahango wata yar hanya aiko nan tabaza aguje nan suka bita dukansu, gudu take iya k'arfinta duk k'ayoyin da suke cikin dajin ta taka ammah bata ma san tana takawaba saboda bala'in da take gani, ka san ba'a had'a gudun mace da namiji ganin sun kusa taddota yasa tak'ara gudu tana ambaton sunan Allah bata ankaraba sai ji tayi wani ya tad'e mata k'afa ta fad'i daidai wajen wani suri, ja tadinga yi da baya tana kuka tana cewa dan Allah kuyi min hak'uri, wani ne yazo yazare mata hijab tare da damk'ar gashin kanta yajuya yakalli sauran yace gaskiya tana da kyau da son samune ace yanzu na d'an huta da ita kafin akasheta. Nan sukasa dariya sukace ai kana hutawa da ita muma sai mun huta da ita. Ammi Khausar tana jin haka tabud'e baki dakyar tace babu wanda ya isa yata'ba min jiki saidai kukashe ni. Daidai lokacin Malam idi ya iso wajen cikin sauri yaduk'a gaban wanda yake rik'e da Ammi yana rok'onshi kar yakasheta. Shuru yayi yana kallonshi nan wani yatafo daga bayanshi batare da sanin malam idi ba saidai yaji anda'ba mashi wuk'a dakyar ya iya yin salati nan yafad'i k'asa yana shure shure jini yana ta malala har yamace. Wata irin k'ara Ammi Khausar tasaki cike da tashin hankali nan wanda yake rik'e da ita yabuga mata kanta ajikin icce,dinga buga mata kan yayi a iccen da dukkan k'arfinshi jini yadinga fita ta kan, kumbura yayi sosai tun tana motsi har tamace saida yatabbatar da mutuwarta sannan yasaketa tafad'i k'asa ya amshi wuk'a yaluma mata sannan suka wuce cikin sauri suka bar wajen. 'Daid'aikun mutanen da suke wucewane a saman abin hawa suka ga motar a gefen titin a bud'e suka kira police sukazo sukayi bincike har aka gano gawarwakin aka bincika motar aka d'auko jakkar Ammi Khausar aciki aka samu duk wani address d'inta. Aka d'auki gawarwakinsu aka kai gida. Jawahir wani irin kuka tadinga yi mai shiga rai tana jin kamar yanzu ne abun yafaru kasa cigaba da labarin tayi saboda kukan da takeyi Barr Faruk jikinshi sanyi yayi sosai d'ago kai yayi yakalleta yace jawahir kiyi hak'uri Allah ubangiji yajik'an su Abbu da Ammi. Goge hawayenta tayi tace Ameen sannan tacigaba da cewa.... A ranar naga tashin hankali sosai a lokacin da nacikaro da gawar Ammina a tsakar gidanmu an kawo kanta ya yi suntum kamar zai fashe bansan lokacin da nasulale nasuma ba saidai gani na nayi a gadon asibiti wata mata tana jiyyata ashe har nayi sati bansan lokacin da aka kai Ammi gidanta nagaskiya ba saida na'kara kwana d'aya nan namatsa saida aka sallameni nakoma gida lokacin har anyi sadakar sati d'aya, kuka nadinga yi sosai saida wani malamin mu da yazo min gaisuwa yayi min wa'azi sannan nadaina, damuwa nad'auka nasa ma raina duk na fita hayyacina saida nayi wata d'aya nadawo daidai, na d'auka mutuwar Ammi zaisa su Abba Mu'azu sucanza ashe abun ba haka bane Ammi tana wata d'aya da rasuwa nan aka tasoni a gaba duk wani aikin gida yadawo kaina, nakoma kamar wata baiwa tun ba'aje ko'ina ba na ida fita hayyacina abinci sai anso ake bani inci, dakyar nasamu nagama SS2 rashin kud'in da zasusa incigaba da karatuna yasa karatun yatsaya dan Abba Mu'azu cewa yayi bazai biya min ba....... Tana kawowa nan Barr Faruk yaji ta yi shuru d'ago kai yayi yakalleta da mamakinshi sai yaga tana bacci. Saurin mik'ewa yayi ya isa bakin gadon yaga dagaske ko baccinta takeyi cikin ranshi yace ikon Allah tunda nake ban ta'ba ganin mutum irin wannan ba, d'aukar laptop d'inshi da wayoyinshi yayi yakoma parlor yazauna yana cigaba da aikinshi. Tayi awa d'aya tana bacci ahankali tafara juya kanta tana girgizawa tanaso tabud'e idanunta ammah ta kasa wata irin k'ara tasaki tare da bud'e idanunta a firgice ta tashi zaune lokacin da taga jini duk a hannuwanta bin hannuwan tayi da kallo tare da girgiza kai tace a'a meyasa hakan tafaru? Hoton da yake kusa da ita tayi saurin d'aukowa taduba hoton Alhaji Sa'idu tagani tabbas shine wanda tayi mafarki dashi d'aukar hoton tayi tayaga gutsin gutsin tasaka cikin dosbin dakyar take tafiya tana jan k'afa har tashiga toilet wanke hannuwanta tayi cikin sauri tacire jallabiyar tasaka kayanta da tazo da su dasauri tafito daga bedroom d'in, barr Faruk d'agowa yayi yakalleta yace lafiya jawahir me yake faruwa? Muryarta tana rawa tace Barrister tashi muje kamaidani zama na a nan akwai had'ari, daman ba na fad'a makaba cigaba da rayuwata a doron k'asa hadarine, muje kamaidani kafin tazo inba hakaba kaima rayuwarka zata iya salwanta. Mik'ewa yayi cikin rashin fahimtar maganarta yace jawahir wacece zatazo? Lokaci guda jawahir tarikid'e Idanuwan nan sukayi jajir cikin d'aga murya tace na ce muje kamaida ni! Barr Faruk bai musaba yad'auki system da wayoyinshi yawuce gaba jawahir tana dafe da kanta ahaka take binshi har suka fito yarufe d'akin yaje yabasu key d'insu sannan suka wuce wajen motarshi. Suna shiga tura kanta tayi tsakanin cinyiyonta wani irin sautin kuka takeyi, gabad'aya kan Barr Faruk ya d'aure yarasa dalilin damuwarta a lokaci guda ahaka har suka isa gidan yarin suna isa tana shirin bud'e mota tafita yakira sunanta juyowa tayi takalleshi yace sai yaushe zaki ida min labarin? Girgiza kai tayi tace bazan iyaba Barrister akwai had'ari sosai acikin rayuwata, Barr Faruk yace duk da haka jawahir ya kamata kidaure. Bud'e motar tayi tafita shima nan yabud'e yafito nan yawuce gaba wasu 'yan sanda sukazo suka rik'eta wata irin tafiya takeyi tana rangaji har office d'in shugabansu. Da mamaki yake kallonsu yace Barrister lafiya? Murmushi Barr Faruk yayi yace lafiya lau na maidota kamar yadda nayi Alk'awali. Murmushi yayi yace aiko ka kyauta dan ina nan hankalina a tashe na kasa zaune da tsaye saboda gangancin barinka da nayi kuka fita da ita dan na karya dokat aikina, ammah kamar ta yi kuka ko? Kallonta Barr Faruk yayi yaga yadda idanunta sukayi jajir. Alhaji Mahadi sawa yayi 'yan sanda sumaidata d'akinta dakyar take tafiya tana yin baya kamar zata fad'i. Bayan tafiyarsu Barr Faruk yace kasan duk wanda yake cikin gidan nan yatuna rayuwarshi tabaya dole yaji wani iri. Hakane ammah in kayi rayuwa mekyau ba. Murmushi yayi yana shirin yin magana wayarshi tafara ringing d'aukowa yayi yai picking tare da yin sallama yace Daddy. Daga chan 'bangaren dady yace Faruk kazo gida yanzu zakaje Daura. Daura kuma Daddy? A wannan lokacin? Daddy tsinke wayarshi yayi Barr Faruk yayi murmushi yace Alhaji Mahadi bari intashi intafi ana nemana a gida ammah kafin intafi zan d'anyi magana da jawahir. Alhaji Mahadi shuru yayi sai chan yace shikenan Barrister babu damuwa bari insa arakaka. 'Daya daga cikin ma'aikatan gidan yakira nan Barr Faruk yamike suka tafi suna zuwa yasamu jawahir kwance a k'asa idanuwanta a rufe daga gefenta yatsugunna yace jawahir. Zumbur tatashi zaune hawaye na fita daga idanunta bakinta yana rawa tace Faruk kabar wajen nan kawuce katafi kar taganka. Da mamaki yace wai jawahir wacece zata ganni? Kukan me kike haka? Wai me yake faruwa da rayuwarki? Cikin kuka tace Faruk kaje kawai, Faruk yace babu inda zanje jawahir sai kin fad'a min abinda yake faruwa. Juyawa tayi cikin sauri tafara waige waige sai kuma chan tamik'e tsaye dakyar tana kyangasa k'afa tanufi wajen da dutsin nan yake ajiye tana zuwa tad'agashi dakyar tajawo d'an k'aramin littafinta jinginewa tayi jikin bango cikin sauri Barr Faruk yataso yazo inda take a tsaye yace lafiya jawahir? Kallonshi tayi da idanuwanta da suka fara lunshewa cikin jigata tace Barrister ga wannan duk wani bayani da kake nema zaka samu a ciki, katafi. Amsa yayi yarik'e, yace jawahir yakamata akaiki asibiti ko bakida lafiya. Girgiza kai tayi tace kaidai katafi. Barr Faruk har ya bud'e baki zaiyi magana tace dan Allah kar kace komai katafi kawai. Juyawa yayi cikin sanyin jiki yafita. Yana fita jawahir tafad'i k'asa a sume. Tausayinta duk yacika Barr Faruk haka yawuce yatafi cikin sauri dan amsa kiran Dadynshi. Yana isa a parlour yasamu Daddy yana jiranshi ko zama baiyiba Daddy yace Faruk d'azu Malam ya kirani ya ce yana ta Kiran wayarka bai samuba lafiya dai ko? Zama yayi sannan yace Daddy ina tunanin network ne. Toh shikenan yanzu kaje kashirya kaje Daura ya ce yau yau d'innan yana son ganinka. Yau kuma Daddy me yake faruwa? Nima ban saniba Faruk kaidai kaje kashirya inkaje sai kaji dan tun d'azu yake kirana a waya yana tambayata ka tafo. Mik'ewa Barr Faruk yayi yace shikenan Daddy bari inje inyi wanka inyi sallar la'asar sai intafi. Daddy yace toh shikenan haka yakamata. Har yagama shiri yana tunanin dalilin kiran gaugawa da kakan nashi yakeyi mashi koda zai tafi Daddy tsaraba yabashi sosai yace yakaima Mahaifin nashi, bayan ya yi sallama da iyayenshi yakama hanyar Daura gudu yake sosai. Bayan tafiyar Barr Faruk da minti talatin aka kira Alhaji Mahadi shugaban prison a waya yana yin picking daga chan 'bangaren akace masu kula da bincike ne. Alhaji Mahadi yace toh Lafiya dai ko? "Eh toh kana da labarin mutuwar babban d'an kasuwar nan Alhaji Saidu Nepa? Da mamaki Alhaji Mahadi yace banda labari yaushe yarasu? Daga chan 6angaren akace baifi awa d'aya da rasuwa ba shine muke bincike akan mutuwarshi mun tsinci hoto irin Wanda aka kashe su Alhaji Saminu shine mukeso muji shin wannan yarinyar jawahir tana prison d'innan? Eh Eh tana nan a rufe,,,,cewar Alhaji Mahadi. Daga chan 'bangaren akace babu inda taje yau? Ba aje da ita ko kotu ko asibiti ba? Shuru yayi sai chan yace am a'a d'azu Barr Faruk ya fita da ita ya yi bincike akan aikinshi. Wanene kuma Barr Faruk? Lauyanta da yake kareta ammah sun dawo tun d'azu. Shikenan zamu nemeshi. Cikin 50 minutes Barr Faruk ya isa daura saboda gudun da yake da motar yana isa a k'ofar gidan kakannin nashi yaga malam zaune yana ba wasu darasi dan haka yatsugunna yagaishesu bayan sun gaisa yashiga cikin gida yasamu yar tsohuwar tashi suka gaisa nan takawo mashi hura damamma yana sha suna hira yana janta ahaka har yagama yace bari yaje yaga ko malam ya gama dan lokacin biyar da rabi tayi tace Eh gaskiya zuwa yanzu ya gama. Yana fita yasameshi zaune yana jan carbi daga gefen d'an buzunshi yazauna suka sake gaisawa yatambayeshi mutanen gida yace kowa yana lafiya, Malam yace ai mahaifinka ya kirani d'azu ya ce wai iyayen yarinyar da zaka aura sunce ad'aga sa ranar sai zuwa jibi ayi baikon. Faruk yana shirin yin magana nan wayarshi tafara ringing fiddowa yayi yai picking tare da yin sallama. Daga chan 6angaren akace Barr Faruk muna buk'atar ganinka a yanzu dan samun cikakkun bayanai daga wajenka saboda munsan kana da labari awa biyu da suka wuce ankashe babban dan kasuwa Alhaji Saidu nepa, da mamaki yake saurarenshi yace ankashe shi kuma? Eh saisa mukeso muji daga gareka dan antabbatar mana ka fita da jawahir daga prison yau. Cikin sanyin jiki yace ammah koda nafita da ita ai babu inda taje hotel kawai muka safka. Barrister koma menene inkazo sai muyi magana dan yanzu haka muna a cikin bincike. Barr Faruk yace shikenan sai na shigo, yana gama wayar kallon malam yayi da yatsareshi da idanu yace wacece jawahir kuma? Barr Faruk yace wata baiwar Allah ce da nake tsaya mawa a shara'arta shine wai suke zarginta da kisa. Jinjina kai Malam yayi yace kusan abinda yasa nace kazo kenan akan yawan mugun mafarkin da nake akanka. Mafarkina kuma? Yafad'a cike da mamaki. Eh mafarkinka kuma duk akan wannan aikin naka ne, Faruk ya kamata ka ajiyeshi dan ina tsoron wani abu yafaru da rayuwarka. Gabanshi wani irin mummunan fad'uwa yayi yace ajiye aiki kuma malam? Kar kayi duba da abinda kagani acikin mafarki dan duk wannan sharrin mafarki ne. Eh Faruk zai iya zama haka ammah ni ina tsoron abinda zai faru da rayuwarka ko ga wani naka...... _Shin wane irin mafarkine Malam yayi da har yakeso Barr Faruk ya ajiye aikinshi?_ _Shin Barr Faruk yana da yadda zaiyi yakare jawahir akan zargin kisa da akeyi mata?_ _Anya kuwa ba jawahir bace take kisan nan ba? inko ba ita bace toh wanene?_ _Wane dalili ne yasa aka d'aga baikon Barr Faruk kodai akwai wata k'ullaliya a k'asa da akeson yi?_ _Shin minene cikin wannan littafin (diary) da jawahir taba Barr Faruk?_ _Tofa laifin dad'i k'arewa, wad'annan amsoshin naku duk suna acikin cigaban *FANSAR RAI* kar kumance har yanzu bamuyi komai ba acikin labarin d'and'ana labarin kawai mukayi_ _Ga duk me buk'atar cigaba da karantawa cikin aminci zai biya d'ari biyu (200) dan kasancewa da SIS NERJA'ART_ _Akowane lokaci muna maraba da masoya nagaskiya Sis Nerja'art takuce_ _Sis Nerja'art✍🏻_ [7/24, 11:09 PM] Sis Nerja'art 2: *......FANSAR RAI......* *INTELLIGENT WRITER'S ASSO....®* [On Award Together] _Follow me on Wattpad: *Sis-Nerja*_ _Wannan Littafin na kud'i ne domin karantawa cikin aminci da yarda ga duk me buk'ata zai turo katin Mtn na d'ari biyu N200 kacal ta wannan number d'in 09035938246, ko ta account number 5330055604, Idan katura ka aiko da screen shot na transaction a wannan number d'in 09035938246_ _Akwai gara'basar *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shahararriyar marubuciyar nan *AMEENA ABBA UMAR* tare da novel d'in *FANSAR RAI* akan farashin N300 kacal, ko da kud'in ka sai da rabonka_ PART TWO _~GORON SALLAH~_ *PAGE 1* Kwance yake saman makeken gadonshi yad'age kanshi sama yana kallon Ceiling tare da lumshe idanunshi kamar me bacci ammah azahiri tunani yake rayuwar jawahir kawai yake tunani akan irin gwagwarmayar da tasha, tambayar kanshi yafara yi daman ashe tana da aure? Toh ina mijin nata? Meyasa bai ta'ba ganinshi ya je wajenta ba??tambayoyin da suka dinga mashi yawo kenan a k'walwa saidai me a gefe d'aya Allah Allah yake yi gari ya ida wayewa yayi wanka yatafi gidan kaso na mata dan yagana da ita dan ya fi so ya ida samun full details kafin yafara aikinshi,,,, yana cikin wannan tunani bacci 'barawo yasace shi. Wajen k'arfe bakwai kiran da yashigo wayarshi ne yatashe shi dakyar yabud'e idanunshi da sukayi mashi nauyi saboda rashin samun isashen bacci, d'auko wayar yayi yaduba yana ganin me kiranshi sai ma yamaida ta silent sannan yamik'e yashiga wanka. Bayan ya fito ya shirya cikin shirinshi na tafiya aiki jikkar laptop d'inshi da wayoyinshi yad'auko yafito parlor daidai da Momcy ta shigo parlorn d'auke da plask tsayawa tayi tana kallonshi. Murmishi Faruk yasakar mata tare da gaisheta. Amsawa tayi sannan tace Son ka dai san babu inda zakaje sai ka yi breakfast ko? 'Bata fuska yayi yace Momcy bana jin yunwa. Batace mashi komai ba tawuce dining area. Ajiye kayan da suke hannunshi yayi yabi bayanta yana zuwa yaja kujera yazauna, fara serving d'inshi tayi sannan tace d'azu Nasiba ta kirani a waya ta ce tana ta kiran wayarka baka d'auka ba. Yi yayi kamar baiji ba yafara breakfast d'inshi. Kallonshi Momcy tayi tace Faruk magana fa nake maka ka min shuru. 'Dagowa yayi yakalleta yasakar mata murmushi sannan yace momcy time d'in bacci nake kuma ko da natashi ban bi ta kan wayarba saboda naga zanyi late ban tafi aiki ba. Momcy kallonshi kawai tayi tawuce tatafi cikin ranta tana mamakin halin d'an nata. Sama sama yayi breakfast d'in yamik'e yad'auki kayanshi yaficce yabar gidan. Yana cikin mota yana tuk'inshi a nutse nan wayarshi tafara ringing kallon wayar yayi ganin sunan da yabayyana a jikin screen d'in wayar yasa yai saurin yin picking tare da yin sallama,,, yanayin yadda yake maganar kawai zaka gani kagane cewa akan wajen aiki ne suke tattaunawa sun dad'e suna wayar kafin daga bisani suyi sallama. Suna gama wayar d'an guntun tsaki yaja tare da canza hanya yanufi wajen aikinsu. Yana isa yai parking a daidai inda yasaba yin parking yad'auko bakin space d'inshi yadad'e fuskarshi sannan yafito daga cikin motar yazagaya yabud'e mazaunin me zaman banza yad'auko jakkar laptop d'inshi. Tafiya yake cikin takunshi me burgewa duk inda yagifta sai mutane sun mashi barka da safiya saidai kawai yad'aga masu hannu, wad'anda suka yi mashi farin sani ne kawai zasuce daman haka yake dan Barr Faruk ba mutum bane me yawan son hayani. Yana zaune a office d'inshi akayi mashi knocking izini yabada ashigo nan aka turo k'ofa. 'Daga kai yayi yakalli me shigowa sai kuma yamaida kallonshi ga system d'in shi. Sacratery takowa yayi ya iso wajen Barr Faruk daga gaban table d'inshi yatsaya yace Barrister barka da aiki. Batare da ya d'agoba yace yauwa barka. File d'in da yake hannunshi yamik'a mashi yace gashi oga yace akawo maka. Ohk ajiye nan. Ajiyewa yayi saman table d'in yace atashi lafiya sannan yajuya yafita. Barr Faruk d'auko file d'in yayi yabud'e yafara dubawa chan sai yamik'e tare da d'aukar file d'in da key d'in motarshi yafita. Saida yafara biyawa a office d'in ogansu suka tattauna sannan yatafi. Yana barin nan direct gidan yari yawuce yana isa kamar yadda yasaba office d'in abokin nashi yafara safka bayan sun gaisa ne yanuna yanaso yaje yagana da jawahir. Alhaji Nasibi yanuna ba matsala nan yakira wani ma'aikacin gidan kamar yadda yasaba yahad'a shi da Barr Faruk suka je. Suna zuwa suka sameta zaune ta had'e kai da gwiwa, daga bakin k'ofa ma'aikacin yatsaya inda shi kuma Barr Faruk yashiga ciki ko kad'an bata motsa ba daga inda take da alama kamar bata ma san da shigowarshi ba. Barr Faruk matsawa yayi yatsugunna a gabanta tare da kiran sunanta ahankali. Bud'e rinannun idanuwanta tayi tare da d'ago kanta tasafke idanunta a fuskarshi inda fuskarta take a d'aure. Cike da jin tausayinta yake binta da kallo inda itama take kallonshi babu ko k'yaftawa. Ajiyar zuciya yasafke yace jawahir insha Allahu zan taimaka maki zan wanke ki daga zargin da akeyi maki. Lokaci guda tamik'e tsaye tare da sakar mashi murmushi sannan tawuce tafara taku d'aya biyu sai taja tatsaya batare da ta juyo ta kalleshi ba cikin dashewar murya tace zargi kuma? Wanene yafad'a maka zargina akeyi? Duk abinda kaji ance na aikata to dagaske ne. Mik'ewa yayi daga inda yake yatsaya yace idan har abinda kika rubuta a kan labarinki gaskiya ne toh tabbas zanyi k'ok'ari wajen wanke ki. Murmushi tayi a karo na biyu tare da sake jefa mashi tambaya tace labarina kuma? 'Dan matsowa yayi kad'an yace Eh saidai inaso insan k'arshen shi dan samun cikakkar hujja. Shuru tayi kamar bataji abinda yaceba ganin haka yasa Barr Faruk yace shin ina Umar? Lokaci guda tajuyo takalleshi cikin sauri tatako ta iso wajen da yake tsaye tare da cacimo wuyar rigarshi muryarta tana rawa tace wanene yafad'a maka shi? Ina kasan yaya umar d'ina?,, tafad'a tare da fashewa da kuka. K'wacewa yayi daga rik'on da tayi mashi yad'an ja baya kad'an yace ban san umar ba saidai na karanta acikin labarin da kika rubuta. Hannu tamik'a mashi muryarta tana rawa tace ina diary na. Cikin nuna rashin damuwa yace yana wajena zanyi wani aiki ne akanshi ammah jawahir ya kamata kisanar da ni ina umar da su Abba shin suna raye? Sulalewa tayi a lokaci guda tazauna k'asa tare da rushewa da kuka tace nima ban saniba bansan me yasa babu wani wanda yazo gareniba meyasa zasuyi min haka? Takowa yayi yamatso wajen da take yace kenan suna a raye jawahir? Wani irin kallo tayi mashi har ta bud'e baki zatayi magana sai kuma tafasa. Ganin haka yasa yacigaba da cewa jawahir dole sai kin daure kin sanar da ni komai domin ta haka ne zamu samu mafita wad'annan mutanen da suka kashe maki iyaye, sannan ita wannan aljanar ta wace hanya takebi tana d'aukar maki fansa akansu, kuma idan har itace take yin kisan ai inaga bai dace ace ankama ki akan laifin da bake kika aikata ba ammah me yasa tun lokacin da akayi abun baki sanar da hukuma ba? Inaga da ace kin sanar da......wata irin k'ara jawahir tayi tare da toshe kunnuwanta cikin d'aga murya tace ya isa haka barrister! ya isaaa!!! Hawaye ne suka cigaba da fita daga idanunta tace taya kake tunanin hukuma zata taimaka min bayan Ammina ita kanta ta je ma hukuma ammah babu wanda yakulata bare har yataimaka mata, wannan dalilin ne yasa nad'auki fansa dakaina ban damu da abinda zai faru da niba bana buk'atar cigaba da rayuwata ina so akasheni saidai kafin nan nafiso incika burina a rayuwa sai na ida kashe wad'anda suke da hannu a mutuwar iyayena daga nan nima zanyi farin ciki sosai idan na mutu dan daman mutuwar itace nafi buk'ata,,,,, juyawa tayi takalli gefe guda sannan tace rayuwata batada sauran amfani ban ta'ba bak'in ciki ba akan zaman da nayi a nan na tsawon wata goma zanyi farin ciki ace daga nan gidan sai k'abarina zan shiga..... Katseta Barr Faruk yayi yace jawahir wannan wace irin magana ce kikeyi kidaina cewa haka insha Allahu zaki rayu ni zan taimaka maki kifita daga gidan nan saidai ta ina zan fara bi, shin ya za'ayi in iya sanar da kotu cewa aljanah ce take wannan kisan? "Wannan ba gaskiya bane nice nan nayi kisan Barrister kar kasaka kanka acikin lamurra na domin gudun kar kajefa rayuwarka acikin had'ari, duk wanda yanemi yajawo jikinshi agareni yana shiga matsala yakamata kafahimci hakan. Kallonta yake gabad'aya ta hargitse yace ban damu da wannan ba jawahir kawai dai akwai wasu tambayoyi da nakeso inyi maki shin ina lauyan mahaifinki wanene shi? Sannan dagaske kina da hannu acikin mutuwar Alhaji.... Bata bari yak'arasaba takatseshi tace ya isa haka barrister na fad'a maka babu abinda zaka samu daga gareni wannan duk ba gaskiya bane,,,, tana fad'in haka tamik'e taje chan wajen 'yar k'aramar tagar nan da tasaba tsayawa wajenta tatsaya tajuya mashi baya ahankali tace wannan duk shirina ne ya kamata katashi katafi. Idanu Faruk yazuba mata yana kallonta har ya bud'e baki zaiyi magana tatari numfashinshi tace banason jin komai daga gareka dan Allah kabarni haka bansan ya zanyi ba tambayoyinka sun min yawa!. Mik'ewa Barr Faruk yayi yace shikenan jawahir zan tafi ammah inaso kisani zan dawo agareki bamuda isashen lokaci ya kamata kisan haka sai anjima,,,, yana fad'in haka yajuya zai tafi sai jin muryarta yayi ta ce katabbatar ka maido min diary d'ina. 'Dan guntun murmushi yayi yajuya yafita. yana fita yajiyota ta fashe da kuka d'an ja yayi yatsaya sai kuma chan yawuce yatafi. Saida yabiya ta office d'in Alhaji Mahadi sukayi sallama sannan yawuce yatafi yana a mota DPO yakira shi a waya yace suna son ganinshi yanzu, amsa masu yayi da toh gashinan zuwa sannan yakashe wayar. Lokacin da ya isa station d'in direct office d'in DPO yawuce lokacin yana ciki suna ganawa da wani dan haka yajira sugama. Kusan minti shidda sai ga mutumin ya fito juyowar da Barr Faruk zaiyi nan sukayi ido hud'u da Alhaji Mansur wani shu'umin murmushi Alhaji Mansur yasakar mashi tare da cewa Barr Faruk barka da rana. Kallo d'aya Barr Faruk yayi mashi batare da ya tanka shi ba yawuce zai shige sai jiyo muryarshi yayi daga baya yana cewa har yanzu kana da damar da zaka mallaki Nasiba but in kana da buk'atar hakan. Ja yayi yatsaya har ya bud'e baki zaiyi magana sai kuma yafasa yawuce yashige. Dariya Alhaji Mansur yayi yace nasan dai zaka amince da hakan. Yana shiga hannu yamik'a ma DPO suka gaisa nan yanuna mashi kujera yazauna, tambayarshi yayi ya aiki ya amsa da Alhamdulillah. DPO jujjuyawa yayi a kujerar da yake zaune sannan yace Barrister Faruk ba komai yasa na kiraka ba sai akan case d'in jawahir akan kisan Alhaji Sa'idu wanda a yanzu mun k'ara samun k'wak'k'warar hujjar da tanuna mana tana da hannu a cikin kisan shi zamu mik'a case d'in a kotu dan ya kamata kotu tayi gaugawar d'aukar mataki saboda abu sai k'ara cigaba yake. Shuru Faruk yayi yazuba mashi idanu yana kallonshi har yakai aya sannan yace DPO na ji bayaninka saidai inaso kasan cewa wannan zancen duk ba gaskiya bane jawahir bata da hannu acikin mutuwar Alhaji Sa'idu Nepa yakamata kudaina zarginta saboda kun duba CCTV Camera a daidai lokacin da akayi kisan muna a hotel kaga babu hujjar da zatasa ace itace takasheshi. 'Dan guntun murmushi DPO yayi yace Eh munga haka ammah wannan bai isa yazama k'wak'warar shaida ba, inaso kasan wani abu duk mutuwar wad'anda ake zarginta akansu kusan haka yafaru kuma muna tunani tana amfani da layar zana ne tana 'bacewa taje takashesu sannan su kansu lauyoyinta bata barsu ba tana acikin gidan yari takashesu. Na ji wannan saidai ban gamsu da hujjarka ba. Cikin d'aga murya DPO yace Barrister nasan aikina sannan ina k'ok'ari wajen ganin na kawo cikakkun hujjoji da dole za'a yadda cewa itace takashesu kamar yadda tun yanzu na fara samu dan mun samu hoto kamar yadda muka samu an aje a mutuwar sauran mutanen shin wannan ba hujja bane? Murmushi Barr Faruk yayi yace kusan haka saidai inaso kasani nima zanyi bakin k'ok'arina a matsayina na lauyanta. Jinjina kai DPO yayi yace dakyau Barr Faruk. Mik'ewa yayi tare da mik'a mashi hannu sukayi musabaha sannan yace na barka lafiya. Ta'be baki DPO yayi yace ba damuwa a duk lokacin da buk'atar nemanka yataso zakaji kirana. Ohk ba damuwa inspector sai na ji ka. Tunda yakama hanya ba abinda yatsaya mashi a rai sai maganganun da jawahir tafad'a mashi kenan har hukuma sun sanar da su akan kisan da akayi ma mahaifinta ammah ba'a d'au wani mataki ba? Indai hakane to da wannan damar sukayi amfani wajen d'aukar fansar kisan da akayi ma iyayenta saidai taya zan samu cikakkun hujjojin da zan iya kareta da su? taya zan wanketa gaban kotu? A fili yace ya zama dole jawahir kiyi min magana indai har kinason barin gidan kason nan ammah ita fa wannan aljanar...bai rufe bakiba sai gani yayi ta mirrir d'in motarshi kamar wannan tsohuwar ce zaune tana kallonshi da k'walak'walan idanunta saurin jan burki yayi yatsaya tare da waiwayawa baya ammah baiga kowa ba, ajiyar zuciya yasafke tare da jingine kanshi a jikin kujera kusan minti ukku sannan yatada motarshi yanufi gida. Yana isa wanka yayi yashirya sannan yafito parlor yasamu iyayenshi Momcy tazubo mashi lunch yazauna yayi suka d'an ta'ba hira yatashi yakoma d'akinshi wayoyinshi gabad'aya yakashe dan kar atakura mashi yad'auko laptop d'inshi tare da diary d'in jawahir yazauna yana aiki saida yaji k'walwarshi ta d'auki caji tana buk'atar hutu sannan ya ajiye tare da kwantawa saman gadonshi bai dad'e da kwanciya ba bacci yai awon gaba da shi daman abu ga wanda bai samu yaruntsa ba. Ba shine yafarka daga baccin da yake ba sai wajen biyar a gurguje yai wanka sannan yad'auro alwallah. Bayan ya gama duk shirinshi yad'auki laptop d'inshi da key d'in motarshi yafita dan yaje chan gidanshi da yake gani zaifi samun kwanciyar hankali yayi aikinshi yana fita daidai lokacin motar nasiba ta cinno kai cikin gate d'in gidan..... _Sis Nerja'art✍🏻_ [7/24, 11:09 PM] Sis Nerja'art 2: *......FANSAR RAI......* *INTELLIGENT WRITER'S ASSO....®* [On Award Together] _Wannan Littafin na kud'i ne domin karantawa cikin aminci da yarda ga duk me buk'ata zai biya d'ari biyu N200 kacal ta wannan number d'in 09035938246, ko ta account number 5330055604, Idan katura ka aiko da screen shot na transaction ta wannan number d'in 09035938246_ _Akwai gara'basar *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shahararriyar marubuciyar nan *AMEENA ABBA UMAR* tare da novel d'in *FANSAR RAI* akan N300 kacal, ko da kud'in ka sai da rabonka_ PART TWO _~GORON SALLAH~_ *PAGE 2* Kallon motarta yayi yad'auke kai sannan yawuce yanufi parking space wajen motarshi, wani irin parking tayi yana ji lokacin da taja burki dak'arfi, tabud'e motar tafito cikin sauri tanufi wajen da yake tafiya tare da kiran sunan shi. Ja yayi yatsaya batare da ya juyoba har ta iso, gabanshi tatsaya tana kallonshi damuwa k'arara ta bayyana a fuskarta cikin karyayyar zuciya tace haba Faruk yanzu har ni zaka gani na zo ammah kashareni baka ma da lokacina. Faruk sai a lokacin yakalleta yace ba haka bane Nasiba taya kike tunanin zan shareki. Ba ga shinan ba ka yi, bansan menayi maka ba har zaka yanke hukunci irin haka faruk, wane irin laifi nayi maka da har zaka k'i amincewa da aurena, ko sona ne kadaina yi,,,, tafad'a hawaye suna fita daga idanunta. Hankalin faruk ya tashi sosai ammah bai nuna mataba yace ko d'aya Nasiba ba haka bane ke kanki shaida ce ina sonki kuma ba wai na fasa aurenki bane mahaifinki ne kawai yakeso yabada matsala a cikin maganar aurenmu. Katseshi tayi tace koma dai minene faruk bai dace saboda aikinka kak'ini ba, meyasa kake son fifita aikinka akaina? Kana nuna min kamar aikinka ya fini matsayi a wajenka. 'Dan guntun murmushi yayi yace Nasiba kidaina cewa haka ko d'aya ba haka bane huruminki daban na aikina daban banaji zan iya had'a soyayyarki da komai saidai me bazan ta'ba bari sonki yashafi aikina ba bansan dalilin da yasa mahaifinki yakeso yashiga cikin aikina ba idan har baiyi niyar bani aurenki ba kawai sai yafito yafad'a min ba wai sai ya sa min dokar da bata shafi aurenmu ba. Fashewa da matsanancin kuka tayi tace Faruk ban ta'ba tunanin haka daga gareka ba koma menene na d'auka zaka iya sadaukar da shi akan soyayyarmu, me zai hana kahak'ura da koma menene muyi aure. Zuba mata idanu yayi yana kallon yadda take kuka bilhak'i duk sai yaji tausayinta ammah yana tunowa da yadda sukayi da mahaifinta sai yagirgiza kai yace bazan iya haka ba, kamar yadda wani uzuri na aikina bazai hanani aurenki ba toh haka shima aurenki bazai shiga hurumin aikina ba duk son da nake maki zan iya hak'ura har zuwa lokacin da mahaifinki zai amince muyi aure dan haka kar kiga laifina a ciki kiyi hak'uri,,, Yana fad'in haka yawuce yanufi wajen motarshi yabud'e,, cikin kuka Nasiba tafara k'wala mashi kira ammah yashareta yashiga yamaida yarufe yatada motar yabar gidan, ta window yana kallon yadda take kuka tana bin motar da kallo, duk sai yaji babu dad'i wani irin abu ya tsaya mashi a rai, yana fita daga gate d'in gidan taka burki yayi yatsaya tare da kife kanshi a jikin steering yana jin wani irin tausayinta da soyayyarta sun mamaye mashi zuciya, shi kanshi ya san yayi k'ok'ari sosai wajen danne sonta, girgiza kai yayi ahankali yace Nasiba mahaifinki ne yasaka mu cikin wannan halin ammah ni ina sonki. Ya dad'e a wajen sannan yaja motarshi yatafi, tuk'i kawai yake ammah yana jin babu dad'i a ranshi har ya isa gidanshi da yaci buri sutare shi da amaryarshi Nasiba. Nasiba ganin yadda yaficce bai ko tsaya saurarentaba yasa tacigaba da kukanta tare da juyawa cikin sauri tashiga cikin gidan, Momcy da shigowarta parlor kenan sai ganin Nasiba tayi kamar anjefota. Cike da mamaki tamatso wajen tana cewa lafiya Nasiba me yake faruwa? Kasa yi ma Mom bayani tayi sai ma cigaba da kukan da take nan hankalin Mom ya ida tashi taruk'ota sukaje saman kujera suka zauna sannan tace dan Allah Nasiba kidaina kukan haka kiyi min bayani me yake faruwa? Cikin sheshek'ar kuka tace Mom Faruk ne. Ajiyar zuciya Mom tasafke tace me yafaru da Faruk d'in wani abu yayi maki? Cigaba da kukanta tayi dan batasan abinda zatace ma Mom ba. Ganin haka yasa Mom tace shikenan kidaina kukan kibarni da shi zai zo yasameni. Tsagaitawa tayi daga kukan tace baimin komai ba cewa yayi bazai aureniba. Zaro idanu Mom tayi tace shi Faruk d'in da kanshi yace haka? Sadda kanta tayi k'asa tace ba wai hakaba ya ce min aikinshi ya fiye mashi ni. Jinjina kai tayi cikin ranta tace watau kenan k'arya yayi masu da yace yayi magana da Daddyn Nasiba akan kar ayi baikonsu sai ta gama karatunta, to me yake nufi da hakan, koma menene zaya dawo gidan yasameni,,, dafa Nasiba tayi tace kinga kidaina 'bata hawayenki insha Allahu babu abinda zai hana aurenku da Faruk kibarni da shi. Wata irin kunya ce takama Nasiba tace Mom ba wai haka ba kawai dai....sai kuma tayi shuru. Murmushi Mom tayi tace koma menene kar kidamu kinji? 'Daga kai tayi alamun toh sannan tamik'e tace Mom bari intafi gida. A'a Nasiba tun yanzu? Ko ruwa fa baki sha ba. Kanta sadde k'asa tace Allah Mom nagode daman sauri nake Hajiya ta aikeni. Toh shikenan Nasiba kikwantar da hankalinki babu abinda zai hana aurenku da Faruk kibarshi zai dawo gidan yasameni, kigaishe da Hajiyarku kinji. Cikin jin dad'i tace toh Mom zataji sosai. Tunda tashiga mota inba goge hawaye ba babu abinda take maganganun Faruk sun tsaya mata a rai sosai dan bata ta'ba tunanin hakan daga gareshiba musamman yadda yake nuna mata so ta d'auka ba wani case ba hatta aikinshi zai iya hak'ura da shi saboda ita sai gashi taga ba hakaba, ammah meyasa su Daddy sukace dole sai ya janye ya tsame hannunshi daga case d'in sannan zasu amince subashi ita? Miye had'in aurensu da aikinshi?,,, buga steering d'in motar tayi tare da girgiza kai a fili tace sam hakan bai daceba. Wajen k'arfe biyar motocin police ukku suka tsaya a harabar gidan yarin inda police d'in suka fito wasu suka tsaya a nan wasu kuma suka shiga ciki tare da ogansu direct office d'in shugaban gidan suka je inda DPO yashiga ciki su kuma suka ja suka tsaya bakin k'ofa. Bayan sun gaisa da Alhaji Mahadi ne DPO yake ce mashi mun dai dawo akan case d'in yarinyar chan. 'Dan guntun yawu Alhaji Mahadi yagad'e yace toh 'yallabai dafatan dai ba wani abu yasake faruwa ba? No bakomai saidai akan kisan Alhaji Sa'idu Nepa wallahi ka yi sakaci da kayarje aka fita da ita alhali ka san hakan baya daga cikin aikinku abar me laifi lauyanshi yafita da shi koma za'a fita ai kyau a had'a da su da police bare ma wannan yarinyar da take da had'ari. Cikin sanyin jiki yace hakane d'alla'bai nima sai daga baya naga rashin dacewar hakan ammah Barr Faruk mutum ne me amana na sanshi sosai wannan yana daga cikin dalilin da yasa na amince mashi. Shuru DPO yayi na d'an lokaci sai chan yace ai bata a nan duk yadda kad'auki mutum bai zama dole hakaba, inma haka ne taya zasu iya fita su kad'ai ai zata ma iya guduwa kaima kanka ka san iya dad'ewarmu muna bincike akan case d'innan kafin mugane itace take kisan, shikenan dai kakiyaye yanzu bari inje inganta dan akwai wasu tambayoyi da nakeso inyi maka. Alhaji Mahadi yace toh shikenan babu damuwa, nan yad'auko wayarshi yakira wani ma'aikaci yazo yayi ma su DPO jagora har d'akin da aka gark'ame jawahir. Suna isa suka sameta zaune ta jingine kanta da bango tana kallon gefe d'aya har suka shiga bata d'aga kai takallesu ba. DPO ne yamatsa kusa da ita tare da d'an tsugunnawa a gabanta yace sannu ko jawahir. 'Dago kai tayi takalleshi sai kuma tamaida kallonta a gefe d'aya. Jinjina kai yayi sannan yace nasan ko ban fad'a ba kinsan abinda yakawoni inaso ki amsa laifinki na kashe Alhaji Sa'idu Nepa kamar yadda kika kashe sauran. Ahankali tabud'e baki tace banda masaniya akan mutuwarshi. 'Dan guntun murmushi yayi yace ko kina da hujjar da zaki iya kare kanki da ita bayan bincikenmu ya nuna mana kece? Shin abun tambaya ko kina layar zana ko wani siddabaru ne?. Shuru tayi kamar bataji abinda yaceba. Juyawa yayi yakalli wata police mace yace tambayar min ita. Cikin sauri tazo wajen jawahir sai ji tayi anja mata gashi dak'arfi wanda hakan yasa saida tasaki 'yar k'ara, muryar macen taji ta ce bazaki amsa tambayar da akayi maki ba. Runtse idanunta tayi tare da kai hannunta zata rik'e hannun police d'in sai ji tayi ta sa mata wani abu me kamar k'arfe a wuyanta wanda yataimaka wajen d'ago kanta sama, ji tayi abun ya shak'eta sosai muryar police d'in taji ta ce bazaki amsa tambayar da akayi makiba. Dak'yar tabud'e baki muryarta tana rawa tace ni bansan komai akan hakaba. Taya zamu yadda da hakan bayan jiya kun fita tare da Barr Faruk. Tsananin azabar da takeji ne yasa tafara safke numfashi kad'an kad'an dak'yar tace na fad'a maku bani ba....k'ara matse mata wuya da akayi da k'arfen yasa takasa k'arasa fad'in abinda yake bakinta nan idanuwanta sukayo waje. Ganin haja yasa DPO yace ak'yaleta. Ana janye mata k'arfen daga wuyanta nan taduk'e tana tari tare da rik'e wuyanta. Muryar DPO taji yana cewa jawahir idan har kika cigaba da 'boye min gaskiya fiye da wannan zansa ayi maki, inaso kifad'a min gaskiya game da mutuwar Alhaji Sa'idu ko shima bazaki amsa laifinba kamar yadda kika k'i amsa na sauran? 'Dago kai tayi a galabaice takalleshi tana nishi tace bai zama dole in iya amsa abinda banda masaniya a kai. Murmushi yayi yace matsalata da ke taurin kai ammah da sannu zan safke maki shi, zanje incigaba da bincike idan har na ida tabbatar da kece kikayi kisan to nayi maki alk'awalin zaki fuskanci hukunci me tsauri akan k'aryar da kikayi min, yana fad'in haka yamik'e tsaye yace a kowane lokaci zaki iya ganina na dawo gareki a duk lokacin da kika ganni to ki tabbata asirinki ya gama tonuwa kuma zaki fuskanci hukuncin daidai da abinda kika aikata,,, yana fad'in haka yajuya yatafi inda sauran police suka take mashi ba. Jawahir da idanu tabishi hannunta yana rik'e da wuyanta har lokacin numfashinta bai ida komawa daidai ba dan idanuwanta ko gabad'aya suka birkice, kwanciya tayi a wajen tana safke numfashi sama sama kafin daga bisani tafara motsa bakinta ahankali kamar me karanto wani abu chan sai ga wani haske ya bayyana a chan k'arshen bangon d'akin jawahir tashi tayi zaune tana tari sama sama nan tayi yunk'urin mik'ewa tsaye ammah takasa lokaci guda takoma takwanta tare da runtse idanunta ahankali hasken yabayyana a wajen da take yashiga jikinta,,, nan bacci yayi awon gaba da ita. Alhaji Sufyan da Hajiya maijidda daidai lokacin da suka fito daga d'aki zata raka mijinta da zai fita suka jiyo k'ara a d'akin Nasiba cikin sauri su dukansu suka nufi d'akin, suna zuwa suka tura k'ofar suka shiga, su dukansu ja sukayi suka tsaya lokacin da suka ganta tana watse d'akin duk kayan kwalliyar da suke saman mirror ta zubar da su tana kuka, cikin sauri Hajiya Maijidda tanufi wajenta tarik'eta tana cewa lafiya Nasiba me yake faruwa? Fad'awa tayi jikin mahaifiyartata tare da fashewa da sabon kuka tana cewa Mummy meyasa su Daddy zasuyi min haka bayan sun san inason Faruk, miye had'in aurenmu da aikinshi? meyasa zasuce dole sai ya yanje daga wani case sannan zasu bashi ni? Hakan da sukayi sun kyauta mana kenan? Hajiya Maijidda juyawa tayi takalli mijin nata da yake tsaye sannan tamaida kallonta ga d'iyarta da take rungume jikinta tace yanzu Nasiba akan haka ne kike nema kimaida kanki mahaukaciya?. Cikin kuka tace fiye da haka ma zanyi mummy indai akan son Faruk ne, saboda haka ya daina kulani d'azu na je gidansu ya shareni. Alhaji Sufyan takowa yayi yamatso wajen da suke tsaye yace haba Nasiba minene abun damuwa ni fa taimakonki nayi domin naji labarin cewa case d'in da faruk yad'aukar ma kanshi yana da had'ari sosai dan yarinyar kisa tayi ba mutum d'aya ba ta kashe mutane dadama ke hatta lauyoyinta bata bariba, tana abu saikace ba mutum ba duk wanda yanemi yara'beta sai taga bayanshi, shi kanshi Faruk ya san da haka ammah bansan dalilin da yasa yanace sai ya tsaya mataba taya kike gani zan d'auki 'yata inba lauya irin faruk. Cikin kuka tace Daddy,,, sai kuma tayi shuru. Cigaba yayi da cewa ki kwantar da hankalinki indai har Faruk dagaske yake sonki na tabbata zai janye game da wannan case d'in sannan zai zo yanemi aurenki, ina jin tsoro kar wani abu yashafeki game da case d'in nan Nasiba kiyi tunani a kai ni mahaifinki ne me son farin cikinki. Janyewa tayi daga cikin Hajiya maijidda tawuce dagudu tafita tabar d'akin tana cigaba da kukanta. Su duka da idanu suka bita sai chan Hajiya Maijidda tace kar kadamu Alhaji katafi kawai kabarni da ita zan fahimtar da ita yadda zata gane. Ajiyar zuciya yasafke yace to shikenan maijidda dan Allah kiyi k'ok'arin hakan. Toh Alhaji insha Allahu, sai ka dawo. Toh Allah yasa nan yawuce yatafi ita kuma tanufi part d'inta dan tasan chan ne kawai Nasiba zataje. _Sis Nerja'art✍🏻_ [7/24, 11:09 PM] Sis Nerja'art 2: *......FANSAR RAI......* *INTELLIGENT WRITER'S ASSO....®* [On Award Together] _Wannan Littafin na kud'i ne domin karantawa cikin aminci da yarda ga duk me buk'ata zai turo katin Mtn na d'ari biyu N200 kacal ta wannan number d'in 09035938246, ko ta account number 5330055604, Idan katura ka aiko da screen shot na transaction a wannan number d'in 09035938246_ _Akwai gara'basar *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shahararriyar marubuciyar nan *AMEENA ABBA UMAR* tare da novel d'in *FANSAR RAI* akan N300 kacal, ko da kud'in ka sai da rabonka_ _~GORON SALLAH Last page~_ *PAGE 3* Wajen k'arfe taran dare Barr Faruk yabaro gidanshi tunda yafito daga cikin gidan zai shiga mota yadinga ji kamar ana bin bayanshi sai ya waiga sai yaga ba kowa cikin ranshi yace inma aljannu ne to na fi k'arfinsu. Mota yashiga yabar gidan tuk'inshi yake a nutse har ya isa gida, direct part d'inshi yawuce yai wanka yashirya, yana cikin saka kaya Dad yakirashi a waya yace yasameshi a parlor, amsawa yayi da toh. Saida yagama shirinshi sannan yafita yasamesu zaune shi da Mom. Gaishe da iyayenshi yayi sannan yazauna yace Dad gani. Dad yace na ganka Faruk tambayarka nakeso inyi mi yahad'a ka da Nasiba? 'Dago kai yayi yakalleshi yace Dad wani abu tace na yi mata? Mom harararshi tayi tace ba a saniba ana tambayarka kana tambayar mutane. Kwantar da murya yayi yace ba haka bane Mom kiyi hak'uri. "Kaine dai zaka ba kanka hak'uri, wallahi Faruk baka kyauta ba d'azu yarinyar nan tashigo tana kuka kuma nasan fitarka da kuka had'u kayi mata wani abun, kawai dan kaga tana sonka shine zaka dinga wulak'antata, wai ma me tayi maka? Ganin yadda Mom take fad'a yasa jikinshi yayi sanyi yace Mom kuyi hak'uri babu abinda nayi mata. Dad yace anya kuwa Faruk, toh menene dalilinka na k'in amincewa ayi baikonku bayan iyayenta sun amince da hakan, faruk ko dai so kake kawatsa mana k'asa a idanu kasa muji kunya. Kallon Dad d'in nashi yayi cikin sanyin jiki yace ko d'aya ba haka bane Dad nima kaina ina son Nasiba saidai kawai saboda mahaifinta da yakeso yamaida min soyayya kamar kasuwanci, yadda nakeson Nasiba haka ma aikina ina sonshi. Su dukansu idanu suka zuba mashi cikin rashin fahimtar maganarshi Dad yace me kake nufi da hakan? Watau kana nufin ba wai saboda karatunta kak'i amincewa ba kana da wani dalili naka? " Eh Dad nasan koda ban fad'a makuba dole wata rana kusani, akan wani case ne shine mahaifinta da abokinshi suka nuna bazasu bani itaba har sai na janye nikuma naga ba zan iyaba dan baidace ace maganar aurenmu ta shafi aikina ba" Tsaki Mom taja tace toh menene ba sai ka amince kajanye ba. A'a Mom kod'aya yin hakan bai daceba domin wannan shara'ar itace tafiye min komai a rayuwata ban da burin da yawuce inga ina taimaka ma mutane musamman ma wad'anda aka zalunta aka tauye ma hak'k'insu, idan har shi mahaifin Nasiba bai kasance wanda zai iya taimaka ma wanda aka zalunta ba toh bai dace yahana wani yataimaka ba, janyewata a shara'ar nan daidai yake da salwantar rayuwar jawahir wanda hakan zai iya sa akasheta. Dad da Mom lokaci guda sukace Jawahir kuma? Wacece hakan? Shuru Faruk yayi saida Mom tace tambayarka muke sannan yajuyo yakalleta yace Mom ta kasance yarinya ce wadda aka salwantar da ran iyayenta dan aci dukiyar da mahaifinta yatara wannan duk bai isaba saida akayi silar zuwanta gidan yari,, ganin yadda jikin iyayenshi yayi sanyi yasa yace dan Allah na rok'eku kar ku hanani yin wannan taimakon indai akan aurena da Nasiba ne na hak'ura ko da ace sonta zai kasheni dan bazan iya kasuwanci da soyayyata ba idan har mahaifinta zai iya bani ita ahaka to inkuma bazai iyaba shikenan na hak'ura ammah kugafarce ni idan har maganata ta 'bata maku rai iyayena hak'ik'a ban fad'i haka ba dan in 'bata maku,,, yana fad'in haka yamik'e cikin sauri yawuce yanufi part d'inshi. Su dukansu da kallo suka bi shi suna jin wani iri a cikin ransu musamman ma Mom da tasan halin d'anta ta tabbata tunda har d'anta yafurta haka to zai iya hak'ura ko da ace zai rasa rayuwarshi akan soyayyar Nasiba. Dad ne yajuyo yakalleta yace Nuratu kinji abinda Faruk yace. Cikin sanyin jiki tace babu yadda zamuyi tunda har yafurta ammah me zai hana kasamu shi mahaifin Nasiba kafahimtar da shi wannan shara'ar da Faruk zaiyi ai batada wani aibu tunda akan gaskiya zaiyi ta inyaso sai yajanye k'udurunshi ya amince yabashi auren Nasiba. Shuru Dad yayi yana nazarin maganarta na d'an wani lokaci sannan yace shikenan zan kwatanta hakan kikwantar da hankalinki. Murmushi tayi tace bakomai Alhaji nagode, yanzu muje mukwanta dare ya yi. Kallon agogo yayi yace hakane sannan yamik'e suka nufi part d'insu. Faruk yana shiga part d'inshi fridge gabud'e yad'auko ruwa yatsiyaya acikin cup yad'aga kai yashanye sannan yawuce yanufi wajen kujera yazauna tare da d'auko wayarshi chan kuma yayi wurgi da ita yadafe kanshi da dukkan hannuwanshi, ahankali yafara jiyo k'ara kamar ruwa yana zuba a toilet lokaci guda yamik'e yanufi bedroom yana shiga yawuce toilet yamurd'a k'ofar yashiga fanfo ne yagani a bud'e ruwa suna ta tsiyaya, wajen fanfon yaje yad'ibi ruwan yazuba ma fuskarshi bud'e idanun da zaiyi tare da d'ago kai ta cikin madubi yaga kamar wannan tsohuwar tsaye a bayanshi gashin nan ya baje mata fuska saurin waigawa yayi ammah baiga kowaba yasake juyowa yakalli madubi nan ma ba kowa ajiyar zuciya yasafke tare da kashe famfon yafito yarufe toilet d'in yawuce yanufi gadonshi yazauna saida yayi addu'a sannan yakashe haske yakwanta Duk yadda yaso yayi bacci ammah ya kasa babu abinda yake tunani sai labarin da yake cikin diary d'in jawahir, ammah toh wacece wannan aljannar miye had'inta da jawahir? Taya za'a ce mahaifiyarta ce tayi fatalwa bayan bai ta'ba jin haka ba saidai aljannu sudinga siffa irin ta mutane, Ba ma wannan ba ina k'anen babanta da mijinta Umar meyasa bai ta'ba ganin sun zo dubata ba koda akayi zama a kotu baigansu ba? Shin meyasa bazatayi min bayani yadda zan fahimta ba? Runtse idanunshi yayi ahankali yace Jawahir ya kamata kice wani abu,,, Juyawa yayi d'ayan 'barin yakwanta yana ta tunane tunanenshi ahaka har bacci yai awon gaba da shi. Washe gari yana wajen aiki wajen k'arfe sha d'aya yana ta fama da ayyukanshi na kwana biyu da bai samu yazauna ba ga wata shara'a da zasu zauna a jibi duk abin ya taru ya yi mashi yawa, knocking d'in k'ofa yaji anyi tun kan yabada izini aka turo k'ofar aka shigo. 'Dago kai yayi dan ganin wanene yashigo batare da izininshi ba sai ido hud'u sukayi da Nasiba, ajiyar zuciya yasafke tare da jingine kanshi a jikin kujerar da yake zaune. Takowa tayi ta iso taja kujera tazauna tana me kallonshi. Jin shuru yasa yad'ago kai yakalleta nan suka had'a ido a karo na biyu, d'an guntun murmushi yayi yace Nasiba kece da kanki maimakon kiyo min waya? Ajiye jakkarta tayi a saman table d'in tazare bak'in space d'in da yake manne a idanunta, ganin idanunta yayi sunyi ja alamun ta ci kuka har zaiyi magana nan tatari numfashinshi tace babu abinda zakace min Faruk ni kawulak'anta narasa me kake nufi da hakan ashe bazaka iya salwantar da komai ba akaina. Kinga Nasiba ba haka bane kawai dai....... Kawai dai me? Wai ma shin wacece wannan yarinyar da saboda ita kasalwantar da soyayyarmu wacece ita a wajenka?,,, tafad'a tare da fashewa da kuka. Faruk duk sai yaji wani iri ganin Nasiba tana kuka duk sai yama rasa me zaiyi, chan yayi k'arfin hali yace Nasiba duk yadda kike tunani ba haka bane ke kanki shedace banda wata wadda nakeso bayanki kawai dai abinda mahaifinki yazo min da shi ne naji kwatakwata bazan iyaba idan har sun amince zasu bani aurenki a haka ashirye nake muyi aure ammah bazan ta'ba yin baya akan case d'in Jawahir ba domin ya zama dole intaimaka mata. 'Dagowa tayi takalleshi tare da rage sautin kukanta tace ammah ai ka san rayuwarta tana da had'ari wannan dalilin ne yasa su Daddy sukeso kajanye dan kar wani abu yashafemu, na ji labari ta kashe mutane dadama daga ciki har da lauyoyin da suka nemi sutsaya mata ammah Faruk ahaka kake ik'irarin zaka tsaya mata? Toh nifa soyayyata kana nufin ka hak'ura da ni? Shuru Faruk yayi tare da rintse idanunshi yana jin wani iri a ranshi wanda yakasa misulta hakan. Mik'ewa Nasiba tayi tace tunda bana da amsa shikenan nagode Faruk ni zan tafi. Saurin bud'e idanunshi yayi yakalleta nan tad'auki jakkarta tajuya zata tafi ahankali yakira sunanta. Tsayawa tayi batare da ta juyoba tace bana son jin komai daga wajenka Faruk indai har baka janye k'udurunka ba zan tafi zanyi jinyar zuciyata akan tabon da kayi mata saidai ban saniba ko zata iya warkewa,,, tana fad'in haka tawuce cikin sauri zata fita. Saurin mik'ewa tsaye yayi yace Nasiba dan Allah kitsaya kisaurareni,,, bata ko tsayaba taficce tare da rufe mashi k'ofa. Buga table d'in da yake gabanshi yayi sannan yakoma yazauna tare da dafe kanshi cikin ranshi yace meyasa zaki min haka Nasiba? Duk yadda yaso yacigaba da aikin da yake kasawa yayi nan yai zaune zugum abubuwa sun taru sunyi mashi yawa. Daga k'arshe yai shirin tashi sai ga Barr Bilal ya shigo dan haka yafasa suka zauna suka cigaba da aiki tare har wajen k'arfe d'aya sannan suka tashi sukaje masallaci daga chan barr faruk yaimashi bankwana yawuce gida. Tunda yakoma gida bai sake fitaba nan yazauna yacigaba da aikinshi yana ji wayoyinshi suna ta ruri ammah yashare su bai d'aga kiran kowaba daga k'arshe ma yakashe wayoyin. Alhaji Sufyan kallon Abokin nashi yayi yace Alhaji kaga har yanzu babu wani bayani daga yaron chan ya faye taurin kai ban saniba ko hakan yana nufin ya hak'ura da auren Nasiba. Shuru Alhaji Mansur yayi yana nazarin maganar sai chan yace gaskiya ne nima na fahimci hakan, watau yana nufin abinda yasa gaba sai ya cimmashi bai saniba shi zai kwana a ciki domin bana tunanin yarinyar chan tana barin duk wanda yara'beta wallahi ina bak'in cikin barinta a raye da akayi har zuwa wannan lokacin batare da an d'auki fansar rayukan da takashe ba, taya za'ayi ace wanda yai kisa irin haka anbarshi har tsawon wannan lokacin a raye, miye amfanin hakan bayan kowa ya shaida itace,,, yafad'a cike da nuna damuwa. Jinjina kai Alhaji Sufyan yayi yace hakane shi kanshi Faruk bansan dalilin tsaya mata da yayi ba kodai akwai wanda yabashi cin hanci? Ohon mashi koma me kenan insha Allahu bai isa yahana hukunci zartuwaba akanta ya zama dole yadda takashe itama akasheta. Hakane Alhaji Allah dai yashige mana gaba. Ameen. *BAYAN SATI 'DAYA* Jawahir tana zaune d'an kurkukun d'akinta ita kad'ai kanta sadde a k'asa hannunta rik'e da wani d'an tsinke tana rubutu a k'asa koda rubutun ba fitowa yakeba ammah ahaka takeyi tana zubar da hawaye, kawai sai ji tayi an bud'e k'ofa anshigo saurin runtse idanunta tayi tare da tsayawa da abinda takeyi. Barr Faruk ne yatsaya yana kallonta sai kuma chan yatako ya iso inda take, saurin mik'ewa tsaye tayi tare da matsawa gaba tajuya mashi baya cikin dashewar murya tace menene dalilinka nadawo wa wajena shin ba na ce kadaina zuwa ba? Wani irin haushi ne yakama Faruk yana ji kamar yajuya yai tafiyarshi sai kuma yadake yace ammah ai kinsan bamuda isashen lokaci ya kamata ki fahimci hakan jawahir. Cikin muryar kuka tace ban damu da hakan ba. Jinjina kai yayi yace hakane ammah dai ya kamata ki k'arashe min labarinki,, Shuru tayi tak'yaleshi kamar bataji abinda yace ba dan hakane Faruk yamatso kusa da ita yace Jawahir shin wai ina mijinki Umar meyasa ban ta'ba ganinshi ya zo nan ba? Tun kan yarufe baki tafashe da kuka, dafe k'irjinta tayi da hannunta cikin kuka tace Yaya Umar d'ina? Taya zaizo inda nake alhali kowa yana fushi da ni, ko kad'an banyi nadamar abinda na aikata ba,, juyowa tayi takalleshi fuska sha'be sha'be da hawaye tace shin zaka taimaka min in ida cika burina inyaso akashe ni daga baya? Kallonta yake cike da mamaki, d'an guntun murmushi tayi tace ban damu da cigaba da rayuwa ba domin rayuwata batada sauran amfani saidai ina burin inje inda iyayena sukaje. Saurin katseta yayi yace ba haka ba jawahir yakamata ki ida min labarinki domin musan ta yadda zamu 'bullo ma lamarin ko da ace kina so in taimaka maki ki cika burinki dole ne in ida sanin komai shin kina da hannu a cikin mutuwar su Barr Muhsin? Shin dagaske ku ne kuka kashe Alhaji Sa'idu Nepa? Murmushi tayi cikin nuna rashin damuwa kamar ba itace take kuka ba tace ni kaina bansan abinda zan iya cewa ba, saidai abu guda nasani Alhaji Sa'idu nice nakasheshi da hannuna. Saurin ja da baya yayi cike da mamakk yake kallonta yace kece kika kashe shi? Garin ya bayan muna tare a hotel kuma baki fitaba? Girgiza kai tayi tace ba wai dole sai na fitaba sannan nake samun damar kisa na san ka karanta diary na yakamata ace ka fahimci komai akan haka, taya zan iya barin wanda yake da gurin rabani da rayuwata batare da na cika nawa gurin ba. Matsowa yayi kusa da ita yace kenan jawahir kina nufin yana cikin mutanen da suka kashe iyayenki? Girgiza kai tayi a karo na biyu sannan tace baya ciki kawai dai d'an uwanshi ne yaturoshi daga chan Europe yazo yaga bayana kafin yadawo k'asar nikuma naga idan nabarshi zai iya samun galaba akaina, shi d'in abokin Abba ne shima saidai d'an uwane na jini ga Alhaji Tanimu sunaso suga bayana ammah kuma bansan me yasa hakaba. Jawahir wannan ba wani abu bane da ace zaki min cikakken bayani da na taimaka miki na maki alk'awali zan tura ma Alhaji Tanimu takardar gaiyata domin muzauna kotu da shi da ma sauran duk wanda yake da hannu akan kisan iyayenki yakamata ki fahimci bana da burin da yawuce inwanke ki daga zargin da ake maki. Ahankali tace zargi kuma? Wanene yace maka zargi ne na fad'a maka gaskiya ne nice nake kisan da taimakon wadda takasance masoyiya a gareni. Shuru Faruk yayi cikin ranshi yace yarinyar nan ta cika taurin kai dayawa,,, muryarta yaji tana cewa iyayena sun sha suce ina da taurin kai tun ina k'arama musamman ma Ammina a duk lokacin da tayi min wanka tad'auko min kaya zan saka sai in nuna bana son su duk yadda zata so insa bana yarda har sai ta canza min wasu wannan dalilin ne yasa take cemin jawahir kin cika taurin kai,, d'an guntun murmushi tayi tare da kallonshi tace ammah wannan ba shine dalilin da yasa nake da taurin kai ba wani lokacin ina duba ne da abinda yadace da rayuwata. Mamakine yacika Faruk ganin a zuci yayi magana ammah har ta san abinda yace cikin ranshi yace anya itama ba aljanar bace, ajiyar zuciya yasafke sannan yace hakane jawahir kin faye taurin kai nima kaina kiduba tsawon lokacin da nad'auka ina bibiyarki akan kifad'a min komai game da rayuwarki ammah kin k'i... Katseshi tayi tace ba wai haka ba kawai dai banaso had'arin da yake tare da ni yashafeka dan baka cancanci hakan ba. Jawahir kar kiyi duba da hakan insha Allahu babu abinda zai sameni dan Allah na rok'eki ki ida sanar da ni komai a game da rayuwarki, shin a lokacin da Abba yazo da malamin nan me yafaru da lokacin da Umar yagano kina da hannu a cikin kisan da akeyi? Dafe kanta tayi da yasara mata lokaci guda tayi tace a'a bazan ce ga abinda yafaru ba nima kaina kawai dai duk abinda yafaru yana cikin.....bata k'arasa fad'in abinda yake bakinta ba sai gani yayi kamar an fizgeta da k'arfin ta je ta bugi bango, wata irin razanannar k'ara tasaki tare da sulalewa k'asa a sume. _Sis Nerja'art✍🏻_ [7/24, 11:10 PM] Sis Nerja'art 2: *......FANSAR RAI......* *INTELLIGENT WRITER'S ASSO....®* [On Award Together] _Wannan Littafin na kud'i ne domin karantawa cikin aminci da yarda ga duk me buk'ata zai biya d'ari biyu N200 kacal ta wannan number d'in 09035938246, ko ta account number 5330055604, Idan katura ka aiko da screen shot na transaction ta wannan number d'in 09035938246_ _Akwai gara'basar *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shahararriyar marubuciyar nan *AMEENA ABBA UMAR* tare da novel d'in *FANSAR RAI* akan N300 kacal, ko da kud'in ka sai da rabonka_ *PAGE 4* Mummyn Nasiba ce tashiga d'akin d'iyarta ta tasameta zaune ta buga tagumi girgiza kai tayi sannan taje gefenta tazauna cike da jin tausayinta tace Nasiba ya kamata kikwantar da hankalinki kidaina saka damuwa a ranki kiduba kiga a 'yan kwanakin nan yadda duk kika bi kika rame. 'Dago kai tayi takalli mahaifiyarta idanunta cike da hawaye tace bazan iyaba mummy bansan me yasa Faruk zaiyi min haka ba duk son da nake mashi ammah shine zai saka min da haka, shin wai ma wacece wannan yarinyar da yafifitata akan soyayyata. Shafa kan d'iyartata tayi cike da jin tausayinta tace Nasiba saisa nace maki Faruk baida kirki kicire tunaninshi a ranki dan shi dama kike tunaninshi baisan kina yi ba da ace ya damu dake da bai fifita aikinshi akankiba. Mik'ewa tayi tsaye tare da fashewa da kuka tace Mummy duk su Daddyne suka ja min hakan da ace sun barshi da aikinshi ai da bazai za'bi aikin akaina ba, koma menene yasamemu ai daga ubangiji ne ni inason faruk a hakan. Yi shuru Nasiba kar insake jin haka kinsan dai kowane iyaye bazasu so 'ya'yansu susha wahala ba, taya kike tunani zamu amince ki auri Faruk a wannan yanayin ko ma ince akan wannan bala'in da yaratumo ma kanshi, ya kamata kigane cewa mahaifinki gatane yayi maki domin bayason duk abinda zai ta'ba lafiyarki. Komawa tayi takwanta saman gadonta tajuma ma mahaifiyartata baya tare da fashewa da wani sabon kukan. Hajiya Maijidda nan tadinga lallashinta tare da k'ok'arin kwatanta mata har tasamu tasafko daga fushin tadaina kukan. Washe gari Faruk bai samu yakoma wajen jawahir ba saboda shara'ar da zasu shiga haka sukaje suna ta fafatawa har Allah yabasu nasara suka gama. Bayan kwana biyu koda yaje gidan kaso bai samu ganawa da jawahir ba dan lokacin tana bacci koda yatambayi me gadi yashaida mashi tun baccin da takwanta shekaran jiya ne ammah tana yi tana d'an farkawa tayi sallah sai kuma idan ankawo mata abinci shine ake tashinta, haka yajuya yatafi batare da ya samu yadda yakeso ba abun ya d'aure mashi kai sosai dan bai ta'ba ganin irin haka ba. A rana ta biyu ce da yakoma yasamu su DPO sunje wajenta sun tsareta da tambayoyi abun ya bashi mamaki sosai dan duk atunaninshi angama case d'in hakanan, DPO yana ganinshi yace Barr Faruk mun sake had'ewa kenan. Murmushi Faruk yayi yace ai na d'auka tuni angama da wannan case d'in. Taya za'a gama bayan ta k'i ta amsa laifinta, tana da taurin kai sosai. Ta'be baki Faruk yayi yace bai zama dole mutum ya amsa laifin da bai aikata ba, yakamata ace ka gamsu da ba ita tayi kisan ba tunda bakada k'wak'warar shaidar da tanuna maka ita duk binciken da zakayi ka yi ammah baka samu ba, da ace ka yi wani tunanin watak'il zaka samu wani nadaban da yayi kisan. Mik'ewa DPO yayi yamatso kusa da inda Barr Faruk yake tsaye yace har ni zaka fad'a ma haka bayan nasan itace tayi wannan kisan? Ni ko nake da k'wak'warar shaida ko da ace a yanzu nayi niyar kamata akan wannan laifin sai ta kamu saboda duk alamomi sun nuna itace, ya kamata kasan abinda kake fad'a musamman ga babban d'an sanda wanda yasan makamar aikinshi, juyawa yayi yakalli jawahir da kanta yake sadde k'asa yace tana da k'arancin shekaru sannan tana da fuska biyu zan iya amfani da damata insa ta amsa laifin nan ta k'arfin tsiya tunda ta k'i amsawa ta lalama. 'Dan guntun murmushi Barr Faruk yayi yace d'allabai tabbas kana da wannan damar a matsayinka na DPO sannan nima ina da tawa damar da zan iya kareta a matsayina na lauyanta, ba ma wannan ba idan naso zan iya shigar da k'arar duk wanda ya zargeta muyi zama na musamman da shi a kotu, kaga kai kana da damar kamata ni kuma ina da damar kareta. 'Daga mashi hannu DPO yayi yace ya isa haka ya kamata kadinga sanin abinda kake fad'a katsaya a matsayinka kawai na lauyanta mai bata kariya, idan har kace zaka shiga hurumina kai kanka zan iya sa a d'aureka ba lauya ba koda ace alk'ali ne, da sannu zan tabbatar maku da cewa itace tayi wannan kisan, kallon jawahir yayi yace kekuma kisaurare ni zan dawo a gareki,,, yana fad'in haka yajuya zai tafi sai jin muryar Faruk yayi ya ce ni kuma dasannu zan wanketa akan duk wani laifin da ake zarginta. Jinjina kai yayi tare da yin murmushi sannan yawuce yafita, yana fita direct office d'in Alhaji Mahadi yawuce. Bayan ya zauna ne yace wai wanene wanchan Barrister d'in. Wane kenan d'alla'bai? Shuru yad'anyi na d'an lokaci sannan yace lauyan da yake kare wannan yarinyar wadda tayi kisa. Oh barister faruk kake nufi na gane shi. DPO yace eh shi, ya cika zak'ale min akan aikina wai har ni yakece ma zaiyi k'arata akan wacchan yarinyar, Da mamaki Alhaji Mahadi yake kallonshi yace Barr Faruk d'in? Ko dai baisan ko wanene kai ba? Ta'be baki yayi yace me zai hanashi sani bayan kayan da nake sanye da su sun isa sununa bashi matsayina kuma ya je station ya gani kawai dai na lura kamar yanaso yanuna min shi wani ne, shin wai ma wanene mahaifinshi a garin nan? Alhaji Sani Meshadda shine mahaifinshi,, cewar Alhji mahadu Jinjina kai DPO yayi yace dakyau da wannan damar yake amfani yana d'aukar kanshi wanine saboda matsayin mahaifinshi koda shima d'in na ga ba k'aramin lauya bane ammah ya kamata yadaina shiga hurumina akan case d'ina da yarinyar chan. Alhaji Mahadi yace kayi hak'uri d'alla'bai zan fahintar da shi domin Faruk abokina ne ba wai haka yakeba bansan dalilinshi na yin haka ba saboda ba mutum bane mai shiga sabgar da bata shafeshi ba. A'a kabarshi kar kayi mashi magana kakyaleni da shi kawai dan bai sanni ba saisa yake min haka ammah dasannu zai sanni,,, yana fad'in haka yamik'e. Faruk kallon jawahir yayi da take zaune ta zuba ma gefe d'aya idanunta da sukayi jajir, matsowa yayi gefenta yad'auko diary d'inta daga cikin suit d'inshi yamik'a mata yace gashi na maido maki. Saurin juyowa tayi takalleshi sannan ta amsa muryarta tana rawa tace nagode. 'Daga kai yayi sannan yace duk abinda yake ciki na gani saidai babu inda zai kaini ga ha'bar zaren, shin ko zaki fad'a min inda zan had'u da su Umar domin mugana? Wani irin kallo tayi mashi wanda shi kanshi baisan ma'anarshi ba saidai ya fi danganta shi da harara. Ta'be baki yayi yace duk ba wannan ba yakamata kisan cewa bamuda wani isashen lokaci sannan kar wai kidamu da maganganun DPO bare har sutsorata ki, ammah yakamata kudaina kisan nan da kuke kumik'o min case d'in ni zan tsaya maki wajen ganin na k'wato maki hak'inki kamar yadda nayi maki alk'awali, sannan wannan matar meyasa take wahalar da ke alhali ta nuna taimakonki zatayi. Cikin k'araji tace ya isa haka barrister ya isa! Maganganunka suna min yawa, taya zakace inmik'a case d'ina agareka bayan lokaci ya k'ure? Hawaye ne suka gangaro mata ahankali tace tun farko yakamata ace Ammina ta samu wanda zai iya tsaya mata yak'watar mata hak'inta ammah hakan ya gagara daga k'arshe ma aka ga bayanta, ni kaina wace hanya ce banbi ba dan ganin ank'wato min hak'ina ammah hakan bai samuba saboda azzalumai sunyi yawa,, shuru tayi nad'an lokaci sannan tacigaba da cewa sai yanzu da tadawo dan tad'auki fansa sai hakan yazama laifi? Ban damu da duk abinda zai faruba ni ina bayanta sannan zan cigaba da taimaka mata wajen ganin ta d'auki fansa, na tabbata kai ba irinsu Barr Muhsin bane dan haka ya kamata karabu da ni kar kajefa kanka acikin had'ari a dalilin son kataimaka ma wacce rayuwarta bata da sauran amfani, fashewa tayi da kuka tace duk wani farin ciki nawa anraba ni da shi hatta mijina da nake gani shine kad'ai nake jin dad'i ta 'bangarenshi ammah daga baya ya tsaneni yana ganin laifina akan abinda na aikata,, d'aga murya tayi dak'arfi tace meyasa haka yaya umar? Meyasa Ammi tayi min haka!!! cimimiyo gashinta tayi dak'arfi tare da fashewa da matsanancin kuka. Barr Faruk mutuwar tsaye yayi yana kallonta duk sai yaji wani iri a ranshi ganin yadda take kuka bil hak'i. Tsugunnawa yayi a gabanta yace jawahir kidaina cewa haka ni nayi maki alk'awali zan taimaka maki yakamata kifahimci hakan. 'Dago manyan idanunta tayi da suka rine saboda kuka tasafke su akan fuskarshi cikin sheshek'ar kuka tace katafi kawai barrister kadaina wahalar da kanka ban damu da duk abinda mutane zasu fad'a ba akaina saidai abu d'aya nasani duk abinda nasa a gaba sai na yi shi, shin ko zaka taimaka min akan d'aukar fansar da nake? Inhar zaka taimaka min akan haka shine kad'ai taimakon da nakeso daga gareka. Shuru yayi yana kallonta yama rasa abinda zaice mata sai chan yabud'e baki zaiyi magana tayi saurin tarar numfashinshi tace nasan bazaka ta'ba taimaka min ba katafi kawai kabarni ni da Ammina zamu cigaba da ganin bayansu, ba kowane zaiso rayuwarsa takasance me had'ari irin tawa ba. Barr Faruk girgiza kai yayi yace jawahir yakamata kifahimci abinda nake nufi. Saurin mik'ewa tsaye tayi tace babu wanda zan fahimta kamar yadda nima babu me fahimtata, katashi katafi kawai. Har ya bud'e baki zaiyi magana tai saurin tarar numfashinshi tace na rok'eka katashi katafi zanji da abinda yadameni,, hannu tasa tayi saurin dafe kanta da yasara mata tare da runtse idanunta dan duk lokacin da zaizo yayi mata maganar nan sai ta ji kanta kamar zai cire saboda tsananin ciwo. Mik'ewa yayi tsaye yace lafiya jawahir me yake faruwa? Ahankali tabud'e idanunta tace a'a babu komai katafi kawai. Ammah kamar kanki yana ciwo. Wucewa tayi takoma chan k'arshen bango tazauna tace babu abinda yake damuna na rok'eka katafi ina buk'atar hutawa. Jinjina kai yayi tare da juyawa yatafi batare da ya sake cemata komai ba, da kallo tabishi har yafita sannan takife kanta da gwiwa tashiga rera kuka me shiga rai.. Koda yakoma gida kwanciya yayi jikinshi duk ya yi sanyi sosai, ga wani irin haushi da yakeji akan yadda jawahir take mashi dan de kawai yai alk'awalin tsaya mata da badan hakaba da tuni ya rabu da ita, saboda bai ta'ba ganin irin haka ace kwatakwata bata damu da rayuwarta ba, saidai ya fi tunanin haka akan rashin samun farin cikinta, ammah kuma me yafaru bayan a yadda yaga ta rubuta a diary d'inta tana samun kwanciyar hankali a wajen umar, ahankali a fili yace to wai ma ina umar? Ajiyar zuciya yasafke tare da gyara kwanciyarshi yana me cigaba akan tunanin haka saidai gefe d'aya na zuciyarshi soyayyar masoyiyarshi abun k'aunarshi tana fizgarshi ammah baya iya nuna hakan saboda hali irin na faruk duk yadda yakeson abu daga lokacin da aka nemi aimashi iko da shi toh zai iya ja baya dashi komi irin k'aunar da yakeyi mashi kusan hakan ne yake tunani zai faru da soyayyarshi da Nasiba. Daga k'arshe da yaga tunanin yana nema yadameshi yamik'e yad'auko laptop d'inshi yacigaba da aiki. ________washe gari Zaune yake wajen aiki yana tura wani sak'o ta laptop gabad'aya ya maida hankalinshi da aikin da yake, knocking d'in k'ofa akayi nan yabada izini ashigo, Barr junaid ne yaturo k'ofar yashigo. Faruk yana ganinshi yai murmushi yace kamar ka san kana a raina. Zuwa yayi yaja kujera yazauna yace wallahi kau barrister nima ganin kwana biyu bamu had'u bane yasa nace bari inshigo office d'in mutumin nawa inga ko yana nan. Ture system d'in yayi gefe bayan sak'on da yake turawa ya gama shiga sannan yace ina nan abubuwa ne sunsha min kai. Ga kuma case d'in jawahir,,, cewar Barr Junaid. Murmushi Faruk yayi yace kusan haka ammah har yanzu na rasa samun k'wak'k'warar sheda. Shima junaid murmushi yayi yace bana tunanin zaka samu indai akan case d'in yarinyar chan ne, yauwa Barrister wai intambayeka ya maganar baikon ka? Na ji kamar ance ba'ayi ba. Kallonshi yayi da mamaki yace wanene yafad'a maka haka? Kaga Faruk baidace ka'boye min komai ba ni abokinka ne sannan ina ganin kamar ba daidai bane kayi watsi da soyayyarka saboda kawai wannan case d'in ya kamata kafahimci haka. Ta'be baki Barr Faruk yayi yace hakane saidai inaso kasani zan iya hak'ura da komai indai har za'a yi min wasa da hankali, ban damu da irin son da nake ma Nasiba ba koda ace zan rasa raina idan har mahaifinta bazai iya bani ita ahaka ba, bazan ta'ba janyewa daga case d'in jawahir ba har sai naga abinda zai ture ma buzu nad'i. Haba Faruk wace irin magana ce haka kakeyi yakamata kagane cewa ita fa Jawahir mai laifi ce kar kayi wasa da damarka karasa soyayyarka. Duba agogon hannunshi yayi cike da k'osawa da maganar Junaid kamar ba zai ce komai ba sai kuma chan yad'ago yakalleshi yace a yanzu ba kowa bane zai iya fahimta ammah inaso kasani da sannu zan wanke jawahir daga zargin da akeyi mata. 'Yar dariya Barr Junaid yayi yace ka jika da wata irin magana da sannu dai asirinta zai tonu, wallahi Faruk ina baka shawara kafita daga harkar case d'in yarinyar nan dan kar kaji kunya.. Katseshi yayi ta hanyar cewa Junaid idan ka gama abinda yakawoka zaka iya tafiya domin ina aiki me muhimmanci. Mik'ewa tsaye junaid yayi yace yi hak'uri oga yanzun nan ko, atashi lafiya. 'Daga kai kawai Faruk yayi batare da ya ce komai ba yajawo syatem d'inshi ganin haka yasa Junaid yawuce yafita yabar office d'in. Wajen k'arfe biyar Faruk yagama shiri yafito zai fita a parlor yacikaro da Momcy tana zaune ta buga uban tagumi, zuwa yayi daga gefenta yazauna tare da rik'o mata hannu. 'Dago kai tayi takalleshi saida tasafke ajiyar zuciya sannan tace Faruk. Marairaicewa yayi yace dan Allah Momcy kidaina tagumi. Murmushi tayi tace ai dole inyi Faruk d'azu Hajiya Maijidda takirani tana min maganar Nasiba tana chan ta tashi hankalinta sosai, Faruk ya kamata kagane cewa Nasiba tana sonka sosai koma menene bata cancanci irin haka daga gareka ba. Kwantar da kanshi yayi saman kafad'arta yace Momcy laifin mahaifinta ne ni banda matsala ko da a yanzu zai janye k'udurinshi ni kuma zan auri Nasiba. Girgiza kai tayi tace Faruk ka fiye taurin kai watau kana nufin kai bazaka iya janye naka ba. 'Dago kanshi yayi yakalleta cikin sanyin jiki yace a'a Mom nawa bazai ta'ba janyuwa ba idan har nace zan janye toh tabbas banyi adalci ba domin Jawahir tana buk'atar taimako taya za'a zalunci mutum sannan akamashi a rufe, ta rasa me tsaya mata yak'wato mata hak'inta na tabbata daga inda najanye za'a iya kasheta inko nayi haka ban kasance me adalci ba akan aikina. Cike da tausayin d'an nata take kallonshi tace hakane Faruk Allah ubangii yataimaka insha Allahu zaka auri Nasiba dayardar Allah ita rabonka ce. Cikin jin dad'in kalaman mahaifiyar tashi yace nagode sosai Momcy. Shafa kanshi tayi tace bakomai Babana. Mik'ewa yayi yace Momcy bari inje akwai wani aiki da zanyi yanzu. Toh shikenan Allah ubangiji yataimaka sai ka dawo. Ameen Momcy. Wajen k'arfe biyar da rabi ya isa gidan kaso direct office d'in Alhaji Mahadi yafara zuwa kamar yadda yasaba bayan sun gaisa ne mahadi yakalleshi yace wai Faruk minene yahad'aka da DPO ne? Ta'be baki Faruk yayi yace me fa? Wani abu yace maka ya faru? A'a ba wai haka ba. 'Dan guntun murmushi Barr Faruk yayi yace kabarni da shi kawai yanzu dai bari inje inga jawahir wallahi yarinyar nan ta k'i tabani had'in kai yadda yakamata. Jinjina kai Alhaji Mahadi yayi yace kama gode ma Allah da bata shek'aka lahira ba. Uhm kaidai kasani malam ni bari intashi inje. Dariya Alhaji Mahadi yayi yace toh shikenan ba damuwa abokina bari insa arakaka. Lokacin da suka isa tsaye yasameta wajen 'yar k'aramar tagar nan idanunta suna ga d'an hasken da yake shigowa tsaye yayi daga bakin k'ofar yana kallonta inda ma'aikacin gidan yake tsaye a waje yana jiranshi takowa yayi yamatso kusa da ita bai ankara ba sai jiyo muryarta yayi ta ce shin zaka taimaka min in cika burina? Ajiyar zuciya yasafke yace jawahir ya kamata kifahimta lokaci yana k'ure mana kidaure ki ida bani hujjojin da zasu taimaka wajen ganin na tseratar da ke daga gidan nan. Cikin muryar kuka tace meyasa kafi damuwa da fitata akan d'aukar fansar abinda akayi min? Wa yafad'a maka na damu da incigaba da rayuwa? Nidai abu d'aya nakeso shine inga bayan duk wanda yarabani da iyayena. Cikin sanyin jiki yace jawahir nasan haka kifahimceni idan har kika ban dama nayi aikina yadda yadace toh dole ne ingurfanar da su agaban hukuma ni zan taimaka maki da hakan. Ahankali tace hukuma kuma? Ni bana buk'atar hukuma a ciki nafiso kowane d'a yad'and'ani irin rad'ad'in da naji a lokacin da narasa iyayena, nasan bazaka ta'ba taimaka min ba ammah ni zanyi komai dakaina. Tsaye Barr Faruk yayi yana kallonta cikin ranshi yace meyasa jawahir take haka ko har yanzu bata yarda dani ba? Juyowa tayi ahankali takalleshi idanun nan nata sunyi jajir kamar garwashin wuta duk sun k'ank'ance d'an guntun murmushi tayi tace kar kadamu ahakan ma nagode. Amm jawahir ya kamata kifahimci kwana goma sha biyar fa yarage mana lokaci bazai ishemu ba kidaure muyi abinda yadace. Dafe kanta tayi da hannu d'aya ahankali tace wannan shine abinda yadace Barrister a gobe zan kasance cikin farin ciki saboda akwai aikin da zan aiwatar wanda shine zai rage min rad'ad'in abinda nakeji. Tun kan tarufe baki yace jawahir kisa zakiyi? Takawa tayi dak'yar tana k'yangashi taje tazauna tare da jingine kai da bango sannan tace abinda yadace da rayuwata zanyi. Matsowa yayi kusa da inda take zaune yatsaya yace jawahir na rok'eki ki taimaka kiban k'wak'warar hujja ni zan taimaka maki akan dukkan abinda yadace nayi maki wannan alk'awaline duk wanda yake da hannu akan mutuwar mahaifinki bazan ta'ba barinshi ba koma wanene shi. Ahankali tamaimaita kalmar da yace koma wanene shi? sannan tad'anyi guntun murmushi tace kana nufin koda ace kana da dangantaka da shi idan har kagane yana da hannu a ciki zaka taimaka min? Shuru Barr Faruk yayi sai chan yace ban damu da kusanci na da shi ba domin ina akan aikina ne zanyi k'ok'arin haka kiyarda da ni jawahir. Hawaye ne suka gangaro mata tace bana so kajefa kanka acikin had'ari Barrister domin rayuwata babu komai a cikinta sai had'ari idan har kacigaba da bibiyata ahaka komai zai iya faruwa da kai wannan dalilin ne yasa nakeso kacire hannunka a ciki sannan saboda haka ne nakasa fad'a maka komai akan rayuwata. Kidaina cewa haka jawahir ban damu da duk yanayin da zan shiga ba indai ina akan aikina nidai kawai taimako d'aya nakeso kiyi min. Idanu tazuba mashi batare da tayi magana ba ganin haka yasa yace shin ina labarin su umar da d'an uwan mahaifinki? Ko zaki fad'a min inda suke saboda ina da tarin tambayoyi akansu sannan ya zama dole Abbanku yagurfana a gaban kotu. Hawaye ne suka cigaba da fita daga idanunta d'aya bayan d'aya chan tafara shashek'ar kuka lokaci guda tafashe da kuka tace bansan me zan ce maka ba barrister bansan ya akayi haka ba...hamma ce tafara yi chan kuma tayi murmushi cikin murya me kama da ta masu jin bacci tace koma menene zaka sani zanyi k'ok'arin haka ammah ya kamata yanzu katafi sai mun had'u a karo na gaba zan sanar da kai komai. Sai a lokacin yalura da yadda gari yafara duhu yace kar kidamu jawahir ba wani abu bane zan iya zama a nan har lokacin da naso in fita. 'Dan guntun murmushi tayi tace saboda shugaban gidan ya kasance abokinka? Da mamaki yake kallonta yace wanene yafad'a maki haka? Janye idanunta tayi daga kallonshi. Mik'ewa yayi yace zan tafi gobe dasafe zan dawo agareki. Saurin cewa tayi a'a kar kadawo a lokacin saboda ina da aiki me muhimmacu da zanyi da k'arfe goma. Aiki kuma? Wai wane irin aiki ne haka kike magana akai ban fahimceki ba?,, yafad'a fuskarshi d'auke da mamaki. Cikin nuna rashin damuwa tace ba lallai ne kafahimci hakan ba katafi kawai. Ta'be baki yayi yace shikenan zan tafi ammah goben dai zan dawo yakamata ki ida sanar da ni komai akanki. A'a bazai yuwu ba saidai zuwa jibi. Kallonta Barrister Faruk yayi nad'an lokaci sannan yace kin amince jibin zaki ida sanar da ni komai akan rayuwarki? Saurin juya baya tayi cikin rawar murya tace ban saniba ko hakan zai yuwuba ya kamata kakula akan haka zaka iya jefa rayuwarka cikin matsala kafahimci hakan. Kinga jawahir yanzu ba lokacin jayayya bane koma menene kishirya lokacin da duk nadawo zaki ida sanar da ni komai lokaci ya k'ure mana ammah kin kasa gane hakan, ni zan tafi. Ko juyowa batayi takalleshi ba bare yasa ran zatayi mashi magana dan haka yawuce yayi tafiyarshi. Tana jin an rufe d'akin hawaye suka gangaro mata tayi saurin runtse idanunta wata irin mahaukaciyar dariya da taji ne yasa tayi saurin bud'e idanun. A saman iska taga matar zaune cikin mummunan siffa fuskarta fari tas babu alamun jini bakinta duk ya tsatstsage hak'ora sunyo waje, idanuwanta a d'inke suke da farin zare babu alamun k'waya a ciki gashin kan nan nata ya yi tsaitsaye saman iska sai juyawa yake, dariya tacigaba da yi cikin sauri jawahir tad'an ja baya tana cigaba da kallonta muryarta tana rawa tace me yamaidoki wajena? Muryar matar taji kamar tartsatsin tsawa ta ce jawahir ya zama dole kiyi nadamar maganar da kika fad'a min idan dai har kina son ki tseratar da rayuwarki sannan baki isa kisanar da barrister komai ba. Cikin d'aga murya tace bazan ta'ba nadama ba ban damuba ink'arashe rayuwata a nan cikin gidan nan daman rayuwar tawa batada sauran amfani a duk lokacin da kikaso zaki iya kasheni. Matsowa matar tayi kusa da ita tana me cigaba da dariya sai kuma chan tatsagaita dariyar da take tace ke matsalarki d'aya kin cika taurin kai duk wahalar da nake baki ammah hakan ya kasa sawa ki aje makaman da suke saman kanki koma menene dai shikenan nasan dai kina sane da aikin da yake gabanmu gobe. Wani irin kallo jawahir tayi mata tare da jan tsaki tajuya zata tafi, wani farin abu ne yafito daga cikin idanun matar jawahir bata ankara ba sai ji tayi an fizgeta da k'arfi anbuga da bango nan tasulale tafad'i a sume, matar na ganin haka tabushe da wata irin dariya nan ta isa wajen da jawahir take kwance a sume, wani irin abu tadinga karantawa wanda ba kowane zai gane abinda take cewa ba saboda yaren da take, wata 'yar kwalba ce tabayyana a hannunta k'arama tabud'e ta takarkata a wajen fuskar jawahir sai ga wani abu kamar jini yana zubowa har saida yak'are sannan tagirgiza ta'bace.... _Sis Nerja'art✍🏻_ [7/24, 11:10 PM] Sis Nerja'art 2: *......FANSAR RAI......* *INTELLIGENT WRITER'S ASSO....®* [On Award Together] _Wannan Littafin na kud'i ne domin karantawa cikin aminci da yarda ga duk me buk'ata zai biya d'ari biyu N200 kacal ta wannan number d'in 09035938246, ko ta account number 5330055604, Idan katura ka aiko da screen shot na transaction ta wannan number d'in 09035938246_ _Akwai gara'basar *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shahararriyar marubuciyar nan *AMEENA ABBA UMAR* tare da novel d'in *FANSAR RAI* akan N300 kacal, ko da kud'in ka sai da rabonka_ *PAGE 5* Sai bayan sallar isha'i sannan Barr Faruk yakoma gida saida sukayi dinner da iyayenshi sannan yawuce d'akin shi yayi wanka yai shirin bacci yana hawa saman gadonshi zai kwanta nan haske yad'auke gabad'aya duhu yabayyana a d'akin, tsaki yaja tare da mik'a hannunshi saman bedside zai d'auko wayarshi sai ji yayi wayam babu komai lalubawa yashigaa yi cike da mamaki ganin a sama ya ajiyeta ammah bai gantaba, ahankali yaji ana bud'e mashi k'ofar d'aki nan yai zaune yana jira yaji wanene yashigo, tafiya yafara ji anayi a tsakiyar d'akin, cikin rashin tsoro yace wanene? Momcy?. Shuru yaji ba amsa sai ma k'arar tafiyar da aka cigaba da yi cikin d'aga murya yace koma wanene yayi magana man? Nan ma shuru sai jin wata irin k'ara yayi shuuuuuu chan kuma yaji an datse d'akin daidai lokacin haske yadawo. Mamaki yakamashi sosai yana juyawa yaga wayarshi ajiye inda ya aje ammah kuma duk ya laluba d'azu bai ji taba, ahankali yace watau wani yad'aukar min waya shine yanzu yamaido, mik'ewa yayi cikin sauri yafita yabar d'akin duddubawa yadinga yi ko zai ga wani ammah baiga kowaba har yasafko parlor su Dad ne yagani zaune shi da Mom suna ganinshi sukace ya dai Faruk lafiya kake ta sauri haka? Murmushi yayi yatsaya daga saman step yace bakomai Dad ku ne kuka shigo d'akina? Cike da mamaki sukace mu kuma? Daman na ji an shigone lokacin da aka d'auke wuta kuma ina ta magana na ji shuru. Dad kallon Mom yayi itama takalleshi sannan suka maida kallonsu ga Faruk sukace yaushe kuma aka d'auke nepa ba dai yanzu ba? Da mamaki yake kallonsu yace bakuga an d'auke ba? Yanzu fa aka maidota. Dad yace a'a Faruk akwai nepa gaskiya ba'a d'aukeba. Cikin ranshi yace toh ya akayi haka? Me hakan yake nufi,,, ganin yadda iyayen nashi suke kallonshi yasa yai murmushi yace ina ji wutar d'akina ce tad'auke tadawo bari inje inkwanta. Mom tace toh ammah kace ka ji kamar anshigo d'akin kuma bamuga kowa ya zo ya wuceba. Cikin nuna rashin damuwa yace ina ji k'ofar ce tayi k'ara bari inje inkwanta sai dasafenku. Basu kawo komai aransu ba sukace toh shikenan sai dasafe. Juyawa yayi yakoma d'akin shi cikin ranshi yana tunanin toh kodai aljannu ne suke bibiyarshi? Addu'a yayi yahau gadonshi yakwanta bai kawo komai a ranshi ba, bai dad'e da kwanciya ba bacci yai awon gaba da shi. Da asuba saida Dad yazo yatasheshi sannan yasamu yaje masallaci yasamu sallah cikin lokaci dan haka koda yadawo baccinshi yakoma..... Wajen k'arfe tara yafarka daga baccin da yake a firgice yatashi saboda mummunan mafarkin da yayi dafe kai yayi tare da furta Alhamdulillah da yaga mafarki ne yake ba gaskiya bane dan mafarkin sosai yatsorata shi. "Wata k'atuwar macijiya ce yagani tana binshi da gudu shi kuma yana ta gudu da dukkan k'arfinshi dan yasamu yatsira, a duk lokacin da zai waiga sai ya ga tana gab da taddoshi ga bakinta tana bud'ewa alamun zatayi mashi tsartuwa, k'ara gudu yake yana neman mafaka ahaka har ya iso wajen wani k'aton gida, wani irin dad'i yaji lokacin da akaron farko yayi tozali da gidan dan haka yana isa baiyi wata wata ba yashiga, daidai da ya shiga k'ofar gidan tamaida kanta tarufe sai gani yayi gidan ya koma mashi wani k'aton fili duk itace ne kawai a ciki, tsaye yayi yana bin filin da kallo chan yafara jiyo kuka ahankali yana tashi, waiwayawa yadinga yi yanaso yajiyo inda yakejin sautin kukan wata 'yar siririyar hanya ce yagani dan haka yabita yana tafiya chan bayan wani icce yahango mutum zaune, cikin sauri ya isa wajen sai ganin jawahir yayi tana ganinshi tabushe da dariya tare da mik'ewa tsaye nan take tayi girgiza sai komawa tayi wannan k'atuwar macijiyar. Saurin ja da baya yafara kafin daga bisani yajuya yacigaba da gudu nan ko macijiyar tacigaba da binshi, daga nesa da shi yahango wasu d'ungozon mutane tsaye wani irin farin ciki yaji nan yai saurin isa wajensu yana cewa kutaimaka min ammah babu wanda yakalleshi har yashiga tsakiyarsu lokaci guda yaja yatsaya lokacin da yayi tozali da mutum kwance a k'asa alamun ya mutu murya yajiyo daga bayanshi an bushe da dariya wadda takusan rikita mashi dodon kunne saida yai saurin toshe kunnuwanshi da hannuwanshi har saida dariyar talafa sannan yajanye, kunnuwanshi ne suka jiyo ana cewa wannan shine aikin da zan yi a yau d'in nan! saurin juyawa yayi sai baiga kowa ba dan haka ya ida isa wajen mutumin da yake kwance a k'asa har ya kai hannu zai janye abinda aka rufe mashi fuska da shi yaji wata irin murya ta yi mashi magana da k'arfi me kama da gargad'i ance kar kakuskura abud'e!!!! daidai nan yafarka daga baccin. Sosai mafarkin yatsorata shi saidai abun ya tsaya mashi rai sosai wai jawahir ce take bibiyarshi tana son taga bayanshi ammah kuma ba wannan ba toh shi mutumin da yagani kwance wanene shi? Tunowa yayi da muryar da take dariya tace wannan shine aikin da zanyi yau,,, sai kuma jawahir tafad'o mashi a rai jiya da take fad'a mashi gobe akwai aikin da zatayi, ahankali yace toh me hakan yake nufi? Kenan tana nufin kisa zatayi? Ture blanket d'in da yayi rufa da shi yayi cikin sauri yamik'e yafad'a toilet. Bayan ya yo wanka a gurguje yashirya ko breakfast bai tsayaba ganin momcy bata fitoba yasa yaficce yabar gidan. Motarshi yafizga cikin k'ank'anin lokaci ya isa gidan kaso, bai biya ta wajen Alhaji Mahadi ba shugaban gidan saidai yakirashi a waya yashaida mashi zuwanshi da son ganin jawahir da yake cikin sauri dan haka ya amince mashi yaturo wani ma'aikaci sukaje tare. Suna isa cikin sauri yashiga d'akin kwance yasameta gashin nan duk ya baje mata fuska da alama bacci take, ajiyar zuciya yasafke cikin ranshi yace wannan duk yaye yayen mafarki ne, juyawa yayi zai tafi sai kuma yaja yatsaya ahankali yajuyo tare da tsugunnawa a gabanta wani farin abu yagani kamar Alli anyi rubutu da shi k'ananu a kusa da inda take kwance k'ura idanunshi yayi akan rubutun sai gani yayi ansa sunan Alhaji Tanimu Nepa 10:30am, gaban Faruk saida yafad'i a fili yasake maimaita sunan sannan yace me zatayi da sunanshi ko shima ta kasheshi? Ammah kuma me lokacin yake nufi 10:30am, tsugunne yayi wajen yana tunani chan yatuno da yashiga mota ya ji a redio ana sanarwa a yau babban d'an kasuwa Alhaji Tanimu Nepa zai zo gaisuwar rasuwar d'an uwanshi da k'arfe goma jirginshi zai safka. Saurin girgiza kai yayi yace a'a bai dace ba hakan, kiran sunan jawahir yafara yi ammah shuru bata ko motsa ba batada banbanci da matacce, ganin haka yasa yaduba agogon hannunshi sai gani yayi k'arfe goma da minti biyar, ahankali yace ya kamata inyi wani abu a yanzun nan, mik'ewa yayi cikin sauri yawuce yafita ko bankwana bai tsaya yi da megadi ba kamar yadda yasaba. Motarshi yashiga yajata dagudu yabar gidan yarin, gudu yake sosai cike da tashin hankali yana cewa meyasa haka jawahir? Meyasa bazaki bari hukuma tad'auki mataki ba idan har yana da hannu a cikin mutuwar iyayenki, bazan bari kikasheshi ba yazama dole intseratar da shi dan ina son samun bayanai daga wajenshi, gudu yake sosai kamar wanda zai bar garin daidai da round d'in da zai sadashi da airport aka had'a wani irin go slow da yai sanadiyar tsaida duk wani abun hawa da yake wajen. Hankalin Barr Faruk ba k'aramin tashi yayiba tsaki kawai yakeja yana duba agogo ji yake kamar yafito yabar motar yataka k'asa ya ida isa da k'afafunshi. K'arfe goma daidai lokacin jirgin sama yasafka wanda ya iso daga k'asar Europe a filin jirgi mutane ne suke fitowa daga cikin shi chan sai ga Alhaji Tanimu ya fito cikin sauri driver d'inshi yaje ya amshi kayanshi yasaka a mota inda security suka take mashi baya dan yi mashi rakiya zuwa gidanshi kamar yadda yabuk'aci hakan dan akula da lafiyarshi, bud'e mashi mota akayi yashiga motoci biyar ne a gaban wadda yake ciki sai biyar a bayanta duk na masu kula da shi, yana zaune a gidan baya ya kame nan wayarshi tafara ringing. 'Daukota yayi yai picking fuskarshi d'auke da murmushi yake wayar yana cewa nan da mintuna kad'an zan iso gida kujirani, wani irin burki da aka ja ne yakatseshi daga wayar da yakeyi cikin 'bacin rai yakalli driver d'in yace bakada hankali? Ko bakasan aikinka ba da zaka wani ja burki haka? Ahankali yace kayi hak'uri megida nan yaja motar suka cigaba da tafiya. Camera d'in wayarshi yabud'o dan yad'auki kanshi hoto dan yatura ma iyalanshi kamar yadda suka buk'ata nan yak'yalla juyo da wayar yayi dan yaga hoton da yayi abinda yagani ne acikin wayar yai mummunan d'aga mashi hankali nan take yafara zufa cikin d'aga murya yace ma driver tsayar da motar nan!!! K'iiittttt driver yaja mota yatsaya, security na ganin haka su ma duk suka tsayar da motocinsu, Alhaji Tanimu yana jin mota ta tsaya baijira aka bud'e mashi ba yabud'e dakanshi cikin sauri yafita yatsaya tsakiyar security yana mazurai. Tambayarshi sukayi ko lafiya. Hoton da yad'auki kanshi yanuna masu yace kuduba kugani wallahi aljanah ta biyoni har ta shigar min a hoto Amsar wayar sukayi cikin sauri suka duba sai kuma suka mik'a mashi sukace basuga komai ba. Amsa yayi yasake kallo shima baiga komai ba nan yasaki ajiyar zuciya. Driver d'inshi ne yace ranka yadad'e k'ila idanunka ne sukayi maka gizo kaga kamar aljanah ammah ni dai banga komai ba. Katseshi yayi yace dallah malam rufe ma mutane baki, yanzu kowa yashiga mota mucigaba da tafiya Kowa komawa yayi yashiga mota nan aka cigaba da tafiya. Alhaji Tanimu zaune yayi yai shuru duk a tsorace yake dan shi macemacen nan sun d'aga mashi hankali sosai musamman ma ta k'anenshi ya zama dole da ya yi masu gaisa zuwa gobe zai tattara iyalansa sukoma chan Europe da zama dan chan yafiye mashi kwanciyar hankali. Yana cikin tunanin wayarshi tafara ringing dubawar da zaiyi da mamaki sai ganin number d'in Malam Salahu driver d'inshi yayi mamaki duk yakamashi yace wannan kiran fa bayan gashinan yana tuk'i shine kuma yake kiranshi. Sharewa yayi har ta tsinke a karo na biyu wani kiran yasake shigowa da wata sabuwar number, tsaki yaja sannan yai picking daga chan 'bangaren yaji muryar driver d'inshi ya ce 'Dallabai gani na iso Airport d'in banganka ba kuma antabbatar min cewa jirginku ya safka. Cikin Alhaji Tanimu murd'awa yayi sai ji kayi wani abu k'ululululuuu lokaci guda tsoro yad'arsu a ranshi yace Salahu kana nufin ba kai bane kazo d'aukata? Daga chan 'bangaren cikin rashin fahimtar maganar megidan nashi yace 'Dallabai ai cemin kayi sai goma da ishirin saisa ban zo ba sai yanzu, Alhaji tanimu sakin wayar yayi a tsorace yalek'a mazaunin driver dan ganin wanene zaune sai gani yayi wayam motar babu kowa ita kad'ai take tafiya. K'ara yasaki da dukkan k'arfinshi baisan lokacin da fitsari yakubce mashi ba nan yakai hannu zai bud'e murfin motar yafad'a waje dan bai damu da ko yaji ciwoba indai zai fita yatseratar da rayuwarshi sai ji yayi k'ofar a rufe take, bubbuga glass yashiga yi yana k'walah ma security kira a tunaninshi ta hakan zasu jiyoshi ammah babu ma wanda yasan yana yi, k'ara kallon mazaunin driver yayi yaga ba kowa still dai motar ita kad'ai take tafiya sai shi da yake zaune a cikinta, nan take yasume a inda yake zaune......... _Sis Nerja'art✍🏻_[7/24, 11:11 PM] Sis Nerja'art 2: *......FANSAR RAI......* *INTELLIGENT WRITER'S ASSO....®* [On Award Together] _Wannan Littafin na kud'i ne domin karantawa cikin aminci da yarda ga duk me buk'ata zai biya d'ari biyu N200 kacal ta wannan number d'in 09035938246, ko ta account number 5330055604, Idan katura ka aiko da screen shot na transaction ta wannan number d'in 09035938246_ _Akwai gara'basar *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shahararriyar marubuciyar nan *AMEENA ABBA UMAR* tare da novel d'in *FANSAR RAI* akan N300 kacal, ko da kud'in ka sai da rabonka_ *PAGE 6* ....Kamar an tadashi haka yafarfad'o daga suman da yayi nan yafara tunani Allah yasa mafarkine ba gaske ba abinda yagani, k'ara lek'awa yayi yaga motar dai ita kad'ai ce take tuk'a kanta nan gabanshi yacigaba da dukan ukku ukku, motsin da yajine a kusa da shi yasa yai zumbur yawaiga, wata mata ce yagani zaune gefenshi sanye cikin shiga ta alfarma ta dad'e fuskarta da bak'in glass ta juya baya tana kallon tagar mota. Saurin ja da baya yayi tare da jinginewa a jikin murfin mota kan kace mi zufa ta wanke mashi fuska dak'yar yabud'e bakinshi yana rawa yace dan Allah kiyi hak'uri kitafi ku kuke ganinmu ba mu muke ganinku ba. Juyowa tayi tare da bushewa da wata irin mahaukaciyar dariya, ahankali glass d'in fuskarta yacire kanshi nan take kyakkyawar fuskarta takoma wata irin mumunan halitta wadda ta ida firgitashi, har saida yakusan sake wani sumar yaji an wanka mashi wani gigitaccen mari ba shiri yafarfad'o, wata irin k'ara yasaki a tsorace tare da kai hannu zai bud'e k'ofar motar sai ji yayi an rik'e mashi hannu gam har saida yasake sakin k'ara. Wata irin mummunan murya marar dad'in saurarece tafara fitowa daga bakin matar muryar da tasa gabad'aya motar saida ta amsa....Alhaji Tanimu bazan ta'ba barinka ba yadda kayi silar mutuwar mijina kaima ya zama dole kamutu!!! Cikin Alhaji Tanimu katsawa yayi baisan lokacin da yafara zawo ba, cikin rawar murya yace kiyi hak'uri wallahi bansan komai ba, babu wanda nakashe dan Allah kibarni da raina. Bushewa tayi da wata mahaukaciyar dariya tace bai kamata ace ka mance zunubin da ka aikata ba na kashe Alhaji Muhammad. A firgice yamaimaita sunan yace Alhaji muhanmad? Maimakon tabashi amsa sai cewa tayi kaduba kaga motocin da suke zagaye da kai gaba da baya saidai duk da wannan tsaron ya zama dole kamutu domin na dad'e ina jiran wannan ranar bayan kun raba mijina da ranshi ni kaina baku barni ba saida kuka ga bayana sannan dukiyar d'iyata kun cinyeta saboda zalunci irin naku. Had'e hannuwa yayi waje guda jikinshi yana rawa yace dan Allah kiyi min rai wallahi bansan komai ba akai indai dukiya ce nayi maki alk'awali zan mallaka maki dukan abinda namallaka kar kikashe ni. Cikin k'araji tace mutuwarka ta zama dole Tanimu rayuwarka batada sauran amfani domin maha'inci irinka baidace yacigaba da rayuwa ba, duba agogo kaga daidai lokacin da yadace kamutu ya yi nasan bakada wata wasiyya da zaka bayar tunda babu ma wanda zaka ba a kusa. Alhaji Tanimu yana yin yunk'urin yin magana sai ganin hannun matar nan yayi ya cafki wuyanshi, numfashinshi d'aukewa yafara yi nan yacigaba da yunk'urin magana ammah yakasa, dariyar mugunta tashiga k'yalk'yatawa, nan idanuwanshi duk sukayo waje saboda tsananin shak'a, jijiyoyin kanshi duk suka mimmik'e hannu yasa zai k'wace kanshi daga mak'arar da tayi mashi ammah baida k'arfin haka dan gabad'aya k'arfinshi ya tafi nan yafara shure shuren mutuwa, saida taga jikinshi ya saki alamun ya mutu sannan tak'yaleshi tabushe da wata irin mahaukaciyar dariya daidai lokacin motar tafara kauce layi tana tafiya tana karkacewa lokaci guda tatsaya a saman titi nan duk sauran motocin suka tsaya ana tunanin lafiya motar Alhaji tai irin wannan tsayawar cikin sauri duk suka fito suka nufi wajen motar suna zuwa suka k'wank'wasa glass ammah shuru, sun dad'e tsaye a wajen ganin suna neman had'a go slow yasa d'aya daga cikinsu yafasa glass d'in da mamaki sai ganin Alhaji sukayi a kwance shi kad'ai cikin motar babu driver cikin sauri suka bud'e motar ganin kokad'an baya numfashi yasa suka d'aukeshi cikin sauri suka nufi asibiti inda wasu suka tsaya suka kira jami'an tsaro nan da nan titi yacika da mutane ana ta kora jawabi saidai abinda yafi d'aure masu kai babu driver kuma tunda suke tafiyar basuga lokacin da mota tatsayaba har driver yafita suna cikin wannan halin ne wayar Alhaji Tanimu tafara ringing d'aya daga cikin jami'an tsaro ne yad'auko wayar ganin driver d'in Alhaji ne yake kira yasa yai picking batare da ya yi magana ba, daga chan 'bangaren akace Alhaji ga dai ninan airport d'in ina ta jira ko jirgin da yasafka ba naku bane? Jami'in tsaro ne yace kana magana da jami'an tsaro muna buk'atar ganinka a yanzu. Wani wahalallen yawu yahad'e yace 'yalla'bai lafiya? Me yake faruwa? Ina Alhaji? Bai bashi amsaba saidai yafad'a mashi inda zaizo yasamesu. Cikin dak'ik'a kad'an ya iso wajen cikin d'aya daga cikin motocin Alhaji nan fa kowa mamaki yakamashi DPO yakalli security's yace wannan shine kuke nufi? Sukace eh Ogah shine mune dai zai raina ma hankali yafita bayan ya kashe Alhaji yaje yad'auko wata motar. Cikin rashin fashimtar maganarsu driver yace d'alla'bai me yake faruwa ne? Ina Alhajin? DPO yace koma menene muje station yanzu a chan sai kayi bayanin komai. Bayani kuma? Wani abune yafaru d'alla'bai? Maimakon yabashi amsa sai ma ankwa da yasaka mashi nan suka tafi da shi station. Koda aka kai Alhaji Tanimu asibiti nan aka tabbatar da mutuwarshi dan haka aka d'auki gawarshi aka kai gida hankalin iyalenshi ya tashi sosai nan sukaita kuka. DPO ne yafad'a masu wanda ake suspecting da yin kisan nan fa kowa yaita mamaki. Barr Faruk ya shiga damuwa sosai lokacin da yaga wannan go slow da aka had'a na abubuwan hawa ba adadi ya yi tsaki ya fi ak'irga musamman da yaga babbar mota ce tahad'a wannan go slow d'in, lokacin da yasamu damar wucewa yana isa airport yatarar jirgi tuni ya safka dan haka yafara tunani ina ma zaiyi shin wajen jawahir zai koma ko kuma zai je gidan Alhaji Tanimu nepa? Daga k'arshe yayanke shawara da yaje gidan Alhaji Tanimu nepa kasancewarshi babba yasa gidanshi yakasance ba 'boyayye bane dan haka yaja mota cikin sauri yanufi hanyar gidan. Lokacin da ya isa daidai lokacin aka kawo gawarshi daga asibiti a gaban idanunshi iyalenshi suka dinga kuka suna zubewa, hankalin Barr Faruk ba k'aramin tashi yayi ba cikin ranshi yace wannan aikin jawahir ne, buga motarshi yayi da k'arfi a fili yace jawahir bansan irinki ba kin cika taurin kai, ganin yadda dangin mamacin suka tashi hankalinsu duk sai abun yabashi tausayi dan haka yashiga motarshi yabar gidan. Koda aka tafi da driver chargi office tambayarshi aka yi akan mutuwar Alhaji Tanimu yanace akan baisan komai ba akai nan fa aka dinga dukanshi ammah yanacd da cewa shi dai ba shi yazo d'aukar Alhaji Tanimu ba dan a lokacin ma bai fito daga gida ba kuma koda sukayi wayar farko da Alhaji yafad'a mashi lokacin da zaizo d'aukarshi sai kuma daga baya yakirashi yace yabari sai goma da rabi lokacin jirginsu zai safka saisa ma baizo ba a lokacin sai wajen k'arfe goma da rabi, cikin galabaita yace ammah wallahi ba nine nazo d'aukar Alhaji ba. Tsayawa DPO yayi yana kallonshi yanayin yadda yai maganar babu alamun k'arya a cikinta, jinjina kai yayi yace taya zamu tabbatar da hakan bayan motar Alhaji ce wacchan ma toh wanene yad'aukota bayan kowa kai yagani. Cikin kuka yace wallahi iyakar gaskiya ta ce nafad'a maku bani bane ni lokacin ina gidana. DPO kallon police d'in da yake tsaye wajen yayi yai mashi nuni alamun yazo zasuyi magana dan haka yabiyoshi suka fita. Bayan sun fitane DPO yakalleshi yace gaskiya wannan lamarin akwai d'aurin kai a ciki banga alamar mutumin nan shine yai kisan nan ba. Yace Eh gaskiya nima na lura da haka dan jiya da mukaje gidan mukayi tambaya megadi ya ce mana yaga anfita da mota kasancewar glass d'in motar bak'ine yasa bai gane wanda yake cikiba ammah ko a lokacin ya san Driver yana cikin Quarters d'in gidan saisa baikawo komai a ranshi ba dan ya san shine kad'ai yake fita da motar toh bayan wasu mintuna kuma ya ga driver ya fito da wata motar har suka gaisa yace Alhaji zai je yad'auko airport ya san yanzu jirginsu yana gab da safka nan megadi yayi mashi adawo lafiya iya abinda yasani kenan bai kawo komai a ranshi ba game da fitar wacchan motar ta farko kuma akwai tazarar kusan rabin awa tsakanin fitar wacchan motar da wadda driver yafita da ita, babu alamun da yanuna na cewa ya ga dawowar driver bayan fitar motar farko. Fuzgar da iska DPO yayi yace tabbas hakane dan daga airport zuwa inda aka kashe Alhaji Tanimu tafiya ce me d'an nisa ammah ya akayi haka bayan kowa ya ce shine yagani a cikin motar sannan a lokacin da aka kashe Alhaji Tanimu ba'a ga tsayawar motar ba bare ace anga fitar wani toh wai duk ya hakan tafaru? Shuru officer yayi yana nazarin maganar DPO chan DPO yace saidai idan har wanda yai kisan layar zana yayi yafita daga motar toh ammah taya hakan?,,, ahankali yace jawahir fa? Juyowa yayi yakalli officer yace ina tunanin wani abu akan haka yanzu kuyi sauri kuje kubincika min motar da aka kashe Alhaji kuga ba wani hoto da aka ajiye a ciki. Ohk Sir angama. Barr Faruk koda yakoma gidan kaso samun Jawahir yayi zaune ta zuba ma gefe d'aya idanu yana isa cikin d'aga murya yace menene haka kika aikata? Tabbas nasan kece kika kashe Alhaji Tanimu miye amfanin shara'ar da ake da har bazaki iya hak'ura kotu tak'watar maki hak'k'inki ba. Mik'ewa tayi tsaye tana kallonshi ido cikin ido cikin murya me kama da ta kuka tace bana son kotu tak'watar min hak'ina nafiso ink'wata dakaina shin ni a lokacin da suka kashe min nawa iyayen wanene yak'watar min nawa hak'in? Hawaye ne suka fara gangaro mata a idanunta tace babu wanda yai k'ok'arin taimakona haka aka banzatar da maganar mutuwar iyayena sai kace ankashe dabba, shin kuna tunanin hakan baimin ciwo ba? Ko kuna tunanin 'ya'yansu zasu shiga damuwa kamar yadda nashiga? Ko kad'an bazasu shiga damuwa kamar ni ba saboda su mahaifi kawai suka rasa ni kuma har da mahaifiyata narasa. tsaye yayi yana binta da kallo matsawa tayi gaba kad'an tajuya mashi baya sannan tacigaba da cewa na rasa duk wani farin cikin rayuwata tun bayan rasuwar mahaifiyata a da ina ganin kamar bayan ran mahaifina ina da sauran gata tunda ga mahaifiyata ashe ba haka bane ita kanta saida suka rabani da ita, ban sake kwatanta shiga farin cikiba sai da yaya umar yashiga rayuwata ashe wannan ma nad'an lokaci ne, duk saboda dukiya suka rabani da kowa nawa sannan sukayi amfani da dukiyata duk wannan bai ishesu ba ina a cikin gidan nan sun je sun kwashe files d'in filayen da suke mallakina shin ni me na'aikata wanda ba daidai ba a nan? Juyowa tayi takalleshi tace dan kawai na rama abinda akayi min shikenan na aikata kuskure? Zalunta ta fa akayi ammah ba wanda yataimaka min sai yanzu da nasamu wacce take taimaka min sannan za'a ce banyi daidai ba? Barr Faruk jikinshi sanyi yayi sosai cikin sanyin murya yace ba wai haka ba jawahir ni ina tare da ke zan taimaka maki nafiso sugurfana a gaban kotu dan su wankeki daga laifin da ake zarginki da shi. Cikin muryar kuka tace ba wai zargi bane dagaske ne duk na kashesu kuma ban ta'ba nadamar hakan ba ina da burin in ida kashe sauran inyaso nima kotu tayanke min hukuncin kisa zanfi farin ciki da hakan. Jawahir duk kibar wannan kiyi yadda nace maki na maki alk'awali zan taimaka maki na ganin an hukunta duk wani me laifi ko da ace d'an uwanane ko wani makusancina yake da hannu a ciki na maki alk'awalin sai na gurfanar da shi a gaban kotu, abu guda kawai zakayi shine kisanar da ni sauran suwanene? Sannan ina kawunki da umar? Girgiza kai tashiga yi tace wannan ne ban saniba abinda dai nasani shine na kashesu, na kashe yaya umar da hannu wannan shine nadamar da nayi a rayuwata,,,, ta k'arashe fad'a tare da fashewa da kuka. Mutuwar tsaye barr faruk yayi yace dagaske kin kashesu? Ban san ya akayiba ta rabani da rabin raina dan kawai bata k'aunar aurenmu da shi bansan dalilin kasheshi ba kawai dai abinda nasani....tana zuwa nan sai kuma taja bakinta tayi shuru. Ganin haka yasa Faruk yace jawahir kikwantar da hankalinki kiyi min bayanin komai nayi maki alk'awali zan taimaka maki. Cikin sanyin jiki tace bansan me zan ce ba barrister ammah duk wani bayani yana cikin memory card d'in yaya umar. Taya zan samu memory card d'in? Girgiza kai tayi tace bana tunanin samunshi zai kasance acikin sauk'i. Cikin rashin fahimtar maganarta yace meyasa bazai kasance acikin sauk'i ba, kar kidamu kifad'a min inda zan samoshi. Shuru tayi na d'an lokaci sannan tace banaso wani abu yasameka saboda ni na tabbata bazata ta'ba barinka kaje kad'auko ba. Kinga jawahir kicire komai a ranki kifad'a min insha Allahu ni zan je ind'akko shi. Wucewa tayi wajen 'yar tagar nan tatsaya sannan tace yana a chan cikin gidanmu ina tunani a babban parlor saidai nemanshi ba abune me sauk'i ba a k'asa nayada shi nima kaina ban iya cewa ga inda yake ammah wani lokaci zan kwatanta tuna inda yake. Jinjina kai Barr Faruk yayi yace shikenan ni zan je ind'auko shi kikwantar da hankalinki. 'Daga kai kawai tayi alamun toh sannan takoma tazauna tare da had'e kai da gwiwa tana jin wani irin ciwo a ranta dan ya ta'bo mata inda yake mata k'aik'ayi. Ganin haka yasa Barr Faruk yajuya yafita. Ko da police suka je suka bincika motar basu samu wani hoto ba dan haka suka koma suka sanar da DPO duk da haka saida yakira Alhaji Mahadi yatambayeshi jawahir yashaida mashi tana nan cikin gidan yarin ba'a fita da ita ko'ina ba. Saida Drivern Alhaji Tanimu yayi kwana ukku a wajensu suka tabbatar da badai shi d'in bane yai kisa sannan suka sakeshi kisan ya d'aure ma kowa kai nan jama'a suka dinga tunanin aljannu ne inda DPO yafi tunanin da sa hannun jawahir a ciki saidai baida shaidar da zai iya zarginta ya dai bar abun a ranshi. _Sis Nerja'art✍🏻_ [7/24, 11:11 PM] Sis Nerja'art 2: *......FANSAR RAI......* *INTELLIGENT WRITER'S ASSO....®* [On Award Together] _Wannan Littafin na kud'i ne domin karantawa cikin aminci da yarda ga duk me buk'ata zai biya d'ari biyu N200 kacal ta wannan number d'in 09035938246, ko ta account number 5330055604, Idan katura ka aiko da screen shot na transaction ta wannan number d'in 09035938246_ _Akwai gara'basar *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shahararriyar marubuciyar nan *AMEENA ABBA UMAR* tare da novel d'in *FANSAR RAI* akan N300 kacal, ko da kud'in ka sai da rabonka_ *PAGE 7* Bayan ya bar gidan yarin tun a mota yakira Barr Bilal a waya yatambayeshi inda zai sameshi yafad'a mashi yana gida dan haka direct yawuce gidan Barr Bilal yana isa yakirashi a waya yafito bayan sun gaisa ne yace Barr Bilal wani taimako ne nake nema a wajenka. Barr Bilal yace toh Barrister Allah dai yasa ba akan case d'in jawahir bane. Murmushi yayi sannan yace kaidai ka cika tsoro kuma anyi sa'a akanshi ne. "Toh fa ka ji irinta nidai gaskiya Barrister kayi hak'uri wallahi ina tsoron case d'in yarinyar chan ban shirya mutuwa yanzu ba". Dariya Barr Faruk yayi yace toh ai mutuwa tana kan kowa kaga kakwantar da hankalinka yanzu bari muyi maganar da takawo ni. Barr Bilal cikin sanyin jiki yace toh shikenan oga ai dole abi abinda kakeso. Jingine jikinshi yayi a motarshi sannan yace Barr Bilal shin ko zaka iya rakani gidan su jawahir? Sannan idan akwai wani abu da kasani agame da 'yan gidansu inaso kasanar da ni. Shuru yayi nad'an lokaci sannan yace toh gidansu dai na sanshi saidai a rufe yake a yanzu sannan mutanen gidansu a yadda naji duk sun mutu ko ma ince suna cikin wad'anda takashe. Da mamaki Barr Faruk yake kallonshi yace dagaske ta kashesu har da Umar? Cikin rashin fahimtar abinda yake nufi yace wanene kuma shi? Shuru Barr Faruk yayi cikin ranshi yace Jawahit mi yasa kika aikata wannan kuskuren? Chan kuma yaja numfashi yace shikenan zanje muyi magana da Alk'ali zan san yadda zanyi in samo makullin gidansu muje dan akwai abinda nakeson d'aukowa zuwa gobe. Toh nidai zan dai rakaka intsaya nesa da gidan ammah babu abinda zaisa inshiga dan inason raina. Murmushi Barr Faruk yayi yace toh shikenan babu damuwa hakan ma nagode yanzu bari inje inga Alk'ali. Barr Bilal yace toh Barrister koma me kenan sai kata'boni a waya. Toh shikenan sai ka ji ni suna yin sallama yashiga motarshi yatafi. Ya yi niyar zuwa wajen alk'ali sai kuma yayi tunani key d'in wajen DPO kawai zai iya samunshi dan haka daga nan yawuce chan station wajen DPO yai mashi bayanin abinda yakeso, tambayarshi DPO yayi me zaya d'auko a cikin gidan?. Barr Faruk yace akwai bincike me muhimmanci ne da yakeson yi a cikin gidan. Wannan ba hujja bace babu abinda zaka samu akan bincikenka kadai tsaya bincikenka akan jawahir. Murmushi Barr Faruk yayi yace ammah ai ina akan aikina ne kuma aikina ya bani dama zan iya kowane irin bincike a matsayina na lauya. Jinjina kai DPO yayi yace shikenan idan har aikinka ya baka dama sai kayi yadda kaga ya dace ammah ni bazan bada key d'in gidanba saboda bai dace ashigaba tunda ba kowa a ciki. Shuru Barr Faruk yayi bai sake cewa komai ba dan ya san DPO ya fad'i hakane dan kawai yana jin haushinshi akan 'yar tsamar da sukayi, daga k'arshe ma yatashi yatafi yana tunanin yadda za'a yi yasamu key d'in gidansu jawahir. Haka dai yakoma gida har sukayi lunch yana tunanin mafita Momcy ko ta yi mashi tambayoyi ba adadi akan ganin yadda yake ta tunane tunane tun da suka zauna yin lunch saidai yace mata bakomai daga k'arshe yace gajiya ce bacci kawai yakeson yi, yana gamawa tace yatafi yahuta dan haka yatafi part d'inshi a parlor yakwanta yana tunanin yadda zai 'bullo ma lamarin yana a haka bacci yayi awon gaba da shi. Baifi baccin minti talatin ba yafarka saboda mafarkin da yayi saurin tashi zaune yayi cikin ranshi yana addu'a Allah yasa mafarkin shi yakasance gaskiya kallon agogo yayi yaga k'arfe hud'u ta gota dan haka yatashi yawatsa ruwa sannan yayi sallah yana gamawa yazari key d'in motarshi yaficce yabar gidan. A karo na biyu yakoma gidan kaso nan yanemi buk'atar sake ganin Jawahir aka amince mashi yana shiga yasameta kwance tana ta bacci nan yatsaya yana tunanin ko yatasheta yatambayeta saidai kuma bayason tashinta, ya yi kusan minti goma a tsaye yana tunanin yadda zaiyi, gefe d'aya kuma yana tunanin mafarkin da yayi cikin ranshi yace wannan ai mafarkine bai zama dole yakasance gaskiya ba jawahir da take nan ciki a ina zata samu key d'in gidansu? Chan kuma yayi wani tunanin dan haka yawuce wajen dutsin nan nacikin d'akin yana dubawa bayanshi da mamaki sai ganin keys yayi guda biyu nan yad'auko mamaki duk ya ida cika shi cikin ranshi yace tabbas yarinyar nan akwai abubuwa masu rikitarwa a tare da ita taya za'a ce tana cikin gidan nan me tsaro ammah a tare da ita akwai wasu abubuwa batare da sanin kowa ba, toh ammah kodai aljanarta take kawo mata? Inko hakane mezaisa bazatayi k'ok'arin fitar da ita daga gidan ba? Ganin ta motsa ne yasa yakatse tunaninshi yawuce yabar d'akin, k'arar rufe k'ofar da megadi yayi ne yasa tafarka daga baccin da take ahankali tabud'e idanunta tashi tayi zaune tajingine kanta a jikin bango kan kace mi hawaye sun fara wanke mata fuska wanda ita kad'ai tasan dalilin yin haka chan kuma sai tamik'e tanufi wajen 'yar k'aramar tagarnan da haske yake shigo mata ta nan tatsaya wata tsuntsuwa ce guda d'aya take ta shawagi a wajen nan jawahir tazuba mata idanu tana kallonta tana murmushi chan sai ganin tsuntsuwar tayi ta haye saman wani icce dake bayan d'akin ta girgiza ta zama k'aton maciji, tsaye jawahir tayi tana kallonshi nan taga ya tunkaro inda take ahankali tace Ammi. Yana isowa wajen tagar tayi saurin ja da baya nan macijin yashigo dogo ne sosai dan saida yanannad'e jikinshi saboda tsawon d'akin bazai iya d'aukar ko rabinshi ba ahankali tace Ammi mi kikeso agareni? Wani irin haske tagani ya fito daga bakin macijin sai gani tayi hasken ya kauraye d'akin lokaci guda macijin yazama siffar wannan tsohuwar, matsowa tayi a dudduk'e tatsaya gefen jawahir cikin shak'ak'ar murya wadda bata fita sosai tace kina ta aikata kuskure a karo na ba adadi jawahir kin cika taurin kai. Kallon tsohuwar take chan kuma sai ta janye idanunta tace Ammi taya kike tunanin zaki cigaba da samuna cikin ruwan sanyi bayan laifin da kika aikata min? Bushewa da dariya tsohuwar tayi tace a wajenki ne hakan yakasance laifi ammah ni a wajena ba haka bane. Cikin d'aga murya tace saboda kin tsaneshi saisa kike ganin haka kinyi amfani da damarki kin rabani da farin cikina alhalin bai........maganar me gadi ce tajiyo yana cewa ke kuma dawa kike surutu haka? Kallon Ammi tayi da take tsaye tana kallonta sannan tajuya takalli megadi batare da tayi maganaba dan ta san baiga Ammi ba. Cikin fad'a yace ke baki iya nusuwa kamar yadda sauran sukeyi sai kullum kidinga damun mutane da surutu kar kibari insake jin bakinki. Har yagama maganar yajuya yatafi jawahir batace mashi komai ba tamaida kallonta ga tsohuwar da take cigaba da kallonta har ta bud'e baki zatayi magana tsohuwar tatari numfashinta tace jawahir taurin kanki ne yasa kike cigaba da zama nan da ace zaki ajiyeshi da ni zan fitar da ke daga nan ammah wanchan barristern yana so yashiga sha'ani na kuma gab nake da inyi maganinshi... Tun kan tarufe baki jawahir tace shin shima zaki kasheshi ne kamar yadda kika kashe sauran? Wane laifine ya aikata maki? Bushewa tayi da dariya tace jawahir duk abinda naso shi nake aikatawa. Cikin fad'a jawahir tace a wannan karon bazan ta'ba bari ki aikata abinda kika so ba. Cigaba da dariya tsohuwar tayi nan jawahir tawuce takoma tazauna tana kallo tsohuwar ta'bace, tura hannuwanta duka biyun tayi cikin gashin kanta. Bayan sallar isha'i yana kwance a d'akinshi ya d'age kanshi sama yana kallon ceiling Momcy tashigo d'akin baiji shigowarta ba sai ji yayi ana shafa mashi kai, lumshe idanunshi yayi tare da yin murmushi. Faruk meyasa kake yawan damun kanka da tunani baka tsoron wani abu yasameka. Tashi yayi zaune yana cigaba da murmushi yace momcy ba tunani nake ba. Zama tayi gefenshi tace Faruk ni mahaifiyarka ce nafi kowa sanin halinka na san kana son Nasiba saidai zuciyarka bazata barka ba, naso ace ka yi masu yadda sukeso dan subaka aurenta. Rik'o hannun mahaifiyar tashi yayi yace momcy kiyi hak'uri indai har Nasiba rabona ce zan sameta kicigaba da tayani da addu'a kawai, cikin sanyin jiki tace shikenan faruk insha Allahu zan cigaba, wata leda tamik'a mashi tace ga wannan Malam ya aiko maka dashi d'azu. Amsa yayi yace nagode zan kirashi zuwa gobe tunda yanzu dare yayi. Momcy tace toh shikenan bari intashi intafi Daddynka na chan na baro shi kad'ai. Murmushi yayi yace toh Mom sai dasafe. Allah yakaimu Son. Washe gari wajen 11am barr faruk yakira Barr Bilal yafad'a mashi zai zo yarakashi gidansu Jawahir nan Barr bilal yace yanzu zasu shiga kotu ne saidai da anjima dan haka Barr Faruk yace shikenan zuwa anjiman sai muje. Bayan sallar la'asar ne Barr Bilal dakanshi yazo gidan yad'auki Barr Faruk suka kama hanya tunda suka fara tafiya kowa shuru yayi chan Barr Faruk yaga shurun ya yi yawa duk surutun Bilal ammah yau ya yi shuru dan haka yajuyo yakalleshi yace ya dai Barr Bilal lafiya yau naga ka yi shuru? Ta'be baki yayi yace taya kake tunanin zan iya magana bayan zaka kaini inda zan mutu wallahi Barrister da ace ba kai bane babu wanda zaice inje gidan in amince inje dan ina tsoron gidan kamar yadda nake tsoron yarinyar chan. Murmushi Barr Faruk yayi yace kaifa ka ji matsalar ka tsoro wani abu ne akace ke akwai acikin gidan? Ni ban saniba ammah tunda har yarinyar tafito daga gidan ai dole yakasance abun tsoro, kabarni incigaba da lazumina kawai. Shuru Barr Faruk yayi cikin ranshi dariya yake ma Barr Bilal akan tsoron shi da yayi yawa ahaka har suka isa sai ji yayi ya ja mota ya tsaya a gaban wani gida. Kallon gidan Barr Faruk yayi yace wannan shine gidan? Girgiza kai yayi yace ga gidan chan gaba. Da mamaki Barr Faruk yake kallon dank'areren gidan da Barr Bilal yanuna mashi wanda a cikin layin babu gida me girmanshi da kyaunshi koda gidajen wajen suna da kyau sosai yace kana nufin wanchan shine gidan? Murmushi yayi yace eh ai ba abun mamaki bane ga wanda yasan kud'in megidan nidai ina daga nan bazan k'ara matsawa ko ina ba sai kafita ka ida takawa. Murmushi Barr Faruk yayi yace shikenan ba damuwa daman nima banaso ka isa har k'ofar gidan saboda na fad'a maka ba da sanin hukuma nazo ba banaso asan na zo kajirani bari inshiga infito. Cikin sanyin jiki yace toh shikenan Allah yasa kafito lafiya ammah dai kadinga addu'a. Baice mashi komai ba yawuce yatunkari gidan fitowa Barr Faruk yayi daga cikin motar rik'e da 'yar brief case d'in Faruk dan ya yi tunanin zai tafi da ita sai kuma yaga ba haka ba dan haka yatsaya yana kallonshi cikin ranshi yana mamakin rashin tsoron Barr Faruk. Yana zuwa k'ofar gidan tsayawa yayi saida yaga babu kowa gaba da baya sannan yad'auko makullen nan yabud'e k'ofar yashiga k'aton fili ne yafara cin karo da shi duk ganyaye suna ta yawo a tsakiyar filin hango k'ofar da zata sadaka cikin gidan yayi yaga rufe take nan yataka ya isa yana zuwa yasa gudan key d'in yabud'e duk ya'nah ce da k'ura shiga yayi yana bin part parts d'in gidan da kallo yana tunanin wane part yakamata yashiga tunowa yayi da mafarkin da yayi d'akin da yagani tabbas kamar parlor ne koda babu kaya a cikinshi toh ammah wane parlorn daga ciki? Tsaye yayi yarasa wanda zai shiga ya yi kusan minti biyar tsaye a wajen shi kad'ai sai chan yafara tunanin labarin jawahir a k'arshen inda tatsaya mashi murmushi yayi yace babban parlor zan shiga cikin sauri yanufi wajen parlorn yana zuwa yatura k'ofar yajita a rufe makullen da suke hannunshi yasa zai bud'e ammah yak'i bud'uwa daga chan gefe yajiyo k'ara kamar ansa key anbud'e wani d'aki waiwayawa yayi baiga kowaba dan haka yaje yafara tura k'ofofin d'akunan saidai dukkansu a rufe suke ta k'arshence yana turawa yaji a bud'e ajiyar zuciya yasafke tare da kallon k'ofar d'akin tabbas k'ofar ce yagani acikin mafarkinshi ahankali yafurta Alhamdulillah! Tura k'ofar d'akin yayi yashiga ya'na ce tafara yi mashi sallama a fuska yayi saurin cireta nan yaja yana bin d'akin da kallo k'ura ce sosai aciki kasancewar gidan ya dad'e babu kowa a cikinshi tsaye yayi yana tunanin ta ina zai fara neman Memory Card d'in da zai taimaka mashi wajen samun k'wak'warar shedar da yake nema kuma tabbas yana cikin d'akin, saidai baisan ta inda zai faraba bayan duk tulin k'urar dake cikin d'akin runtse idanunshi yayi yana ji kamar yajuya yakoma baya saidai tabbas yasan sai ya samo Mcard d'in sannan zai iya samun abinda yake nema. Maganar jawahir ce ta cikin mafarki tafara dawo mashi lokacin da yaga ta jawoshi ta shigo da shi cikin gidan ta nuna mashi wani d'aki mai jan k'ofa tace kashiga nan a nan cikine kawai zaka iya samun memory d'in daga farkon d'akin zuwa tsakiyar d'akin kar kawuce nan zaka sameshi tana fad'in haka ta'bace. Bud'e idanunshi yayi cike da k'warin gwiwa yaduk'a yafara lalube a cikin tulin k'urar dake k'asan dakin a nutse yake lalube daga yad'auko dutsi sai yad'auko wasu abubuwan ahaka har saida yazo tsakiyar d'akin har zai cigaba sai yatsaya ganin ya zo tsakiyar d'akin dan haka yacigaba da lalube sannan yaji ya ta6o wani d'an abu k'arami cikin sauri yadauko goge shi yashiga yi chan yayi murmushi tare da furta Alhamdulillah tabbas shine cikin sauri yamik'e tsaye kawai sai ji yayi k'ofa ta maida kanta ta rufe dak'arfi, juyawa yayi yakalli k'ofar daga bayanshi yaji wata plastic chair da tasha k'ura tana motsi nan ma yayi saurin juyawa ammah baiga kowa samanta ba sai gani yayi kamar anjata tazo dagudu ta wuce fit tagabanshi A karo nafarko da yaji gabanshi ya fad'i ammah cikin dakewa yace wanene? Fitilun dake cikin d'akin ne suka fara d'aukewa suna kawowa nan yayi saurin juyawa zaije wajen k'ofa sai gani yayi hasken d'akin ya d'auke koda da rana ne ammah wani irin duhu yabayyana har baya ganin abinda yake gabanshi Memory Card din yayi saurin zurawa acikin aljihunshi yad'auko wayarshi dan yahaska sai ji yayi anfizge wayar ta fad'i k'asa wata irin dariya yaji anfara cikin wani irin amon murya gabad'aya d'akin yana amsawa, nan yai saurin runtse idanunshi yafara karanta duk addu'ar da tazo a bakinshi. Murya me k'arfi ce yaji tana tashi tana cewa baka isa kashiga gonata ba bazan ta'ba barinka ba idan har kafita da wannan abun da kad'auka ni na ajiye shi ni nake tsaronshi babu wanda ya isa yad'aukeshi batare da izini na ba. Hannu yasa cikin sauri yatoshe kunnuwanshi da yakeji kamar dodon kunnenshi zaiyi zillo yafad'o saboda k'arfin muryar cigaba yayi da karanto addu'o'i daga bakinshi wata irin k'ara yadinga ji yai saurin bud'e idanunshi sai ganin wani k'aton dutsi yayi wanda yahaske d'akin ya yo saitin inda yake tsaye cikin sauri yamatsa gefe guda ta gefenshi dutsin yawuce yafad'i rijim a bayanshin nan k'ura tabaje d'akin, tari yafarayi yana son yashak'i numfashi ammah babu ta inda zai ji iska saboda k'urar da tacika a d'akin, duk ya fita hayyacinshi ammah duk da haka bai daina addu'ar da yakeyi ba chan yaji wata irin iska me k'arfi ta taso chan kuma sai yaji iskar ta lafa nan haske yabayyana a d'akin, d'aukar wayarshi yayi da take k'asa yayi saurin fitowa daga cikin d'akin yana tari jawo k'ofar yayi yarufe. A chan 'bangaren Barrister Bilal dake tsaye waje jikin mota a tsorace yana jiran fitowar Barr Faruk nan yahango wani irin duhu ya bayyana a gidan kallon inda yake yayi yaga haske ammah cikin gidan duhu ne zufa ce tafara kwararo mashi tsoro duk yabayyana a fuskarshi k'afafuwanshi rawa suka fara briefcase din dayake rik'e da ita hannunshi yasaki, bakinshi yana rawa yafara karanta wa'innahu sulaimana wa innahu bismillahirrahmanur rahim ssaids fitsari yakusa yakubce mashi saboda tsoro tunani yayi yashiga mota yagudu kawai dan baya tunanin Barrister Faruk zai fito da rai bare ma yasamu nasarar d'auko abinda yakaishi cikin gidan yana cikin tunanin yaga hasken gidan ya dawo, bud'e motar yayi zai shiga sai ganin Barr Faruk yayi ya fito yana atishawa da tari jikinshi duk ya yi farin k'ura cikin sauri yanufi wajenshi yana isa yace lafiya Barrister ya akayi naganka haka? Mik'a mashi key d'in yayi alamun yarufe gidan, amsa yayi yarufe sannan yarik'eshi suka nufi wajen mota yana mashi sannu yana cewa saida nace kar kashiga gidan nan ammah kashiga. Dafe k'irjinshi yayi da yake mashi zafi ahankali yace kawuce da ni gidana. Amsawa yayi da toh nan yakama hanyar gidan Barr Faruk. _Sis Nerja'art✍🏻_ [7/24, 11:11 PM] Sis Nerja'art 2: *......FANSAR RAI......* *INTELLIGENT WRITER'S ASSO....®* [On Award Together] _Follow me on Wattpad: *Sis-nerja*_ _Wannan Littafin na kud'i ne domin karantawa cikin aminci da yarda ga duk me buk'ata zai turo katin Mtn na d'ari biyu N200 kacal ta wannan number d'in 09035938246, ko ta account number 5330055604, Idan katura ka aiko da screen shot na transaction a wannan number d'in 09035938246_ _Akwai gara'basar *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shahararriyar marubuciyar nan *AMEENA ABBA UMAR* tare da novel d'in *FANSAR RAI* akan farashin N300 kacal, ko da kud'in ka sai da rabonka_ *PAGE 8* Suna isa gidanshi a tare suka shiga ciki Barr Faruk bai tsaya sauraren surutun da Bilal yakeyi mashi ba yawuce toilet yana shiga yamaida k'ofa yarufe nan yatsaya a bakin k'ofa yana tunanin abinda yafaru da shi tabbas a yanzu ya ida gasgata maganar Jawahir akan aljanar nan, ya dad'e tsaye kafin daga bisani yasamu yayi wanka yafito, shiryawa yayi cikin kayan shi da yake da su a gidan sannan yafito parlor yasamu Barr Bilal zaune yana shan lemu, yana ganinshi murmushi yayi yace Barrister yanzu har ka fito fes ba kamar lokacin da muka zo ba wai me yafaru da kai? Zama yayi saman kujera yai shuru kamar bai ji abinda yace ba sai chan har Barr Bilal ya fitar da rai da samun amsar shi sai ji yayi ya ce babu komai kawai dai gidan ne ya yi k'ura sosai saisa kaga na fito duk k'ura jikina. Barr Bilal ba dan ya yarda ba yace ammah Barrister na hango gidan ya yi duhu babu haske wallahi na tsorata sosai da guduwa zanyi. Murmushi Barr Faruk yayi yace ni banga hakan ba kaga tashi muje masallaci gashichan anfara kiran sallar magrib. Mik'ewa sukayi sukayo alwallah suka kama hanyar masallacin da yake a cikin anguwar. Bayan sun dawo Barr Bilal yayi mashi sallama yakoma gida shi kuma Barr Faruk yayi zaman shi nan dan yasamu yayi aikinshi a nutse, bayan sallar isha'i kiran Dad yayi yace kar atsaya jiranshi bazai dawo gida ba zai kwana a gidan shi saboda akwai aikin da yake a yanzu Dad ya amsa mashi da toh tare da yi mashi addu'ar fatan nasara. Wajen k'arfe goman dare d'auko laptop d'inshi yayi da yajona charge sannan yad'auko memory d'in yasaka a cikin wayarshi yana kunna wayar wata irin k'ara tayi me kama da tsawa dan har saida yatsorata. Cikin recording yashiga yaga guda d'aya ne nan yakai hannu zai kunna kamar an fizgi wayar sai ganinta yayi ta k'wace daga hannunshi ta fad'i k'asa mik'ewar da yayi zai d'auko nan haske yad'auke gabad'aya gidan duhu yabayyana duk'awa yayi yafara laluben wayarshi har ya lalubota zai d'auka sai ji yayi anjata ta matsa, tsayawa yayi mamaki duk ya cikashi lokaci guda yaji k'arar bud'e k'ofar bedroom d'in kuma yaga hasken wayar ya kunnu ta d'an haska d'akin hannu yakai a karo na biyu zai d'auka sai gani yayi tawuce ta yi hanyar waje dagudu mik'ewa yayi yana cewa wanene yake ja min waya? Wai wanene? Shuru yaji dan haka yabi wayar tashi ana cigaba da janta a k'asa shi kuma yana bi har saida sukazo daidai wani d'aki wanda babu komai a cikinshi suna zuwa k'ofa tabud'e ja yayi yatsaya cikin ranshi yana karanta addu'o'i dan lamarin ya fara bashi tsoro yana nan tsaye wayar tashige d'akin baiyi niyar shigaba yana tsaye a cikin bak'in duhun nan yajiyo ringing d'in wayar sai jin muryar Nasiba ta cikin wayar yayi tana cewa Hello Faruk ban ta'ba tunanin zaka iya rabuwa da ni ba Faruk ka san ina sonka dan Allah kadawo gareni,,, tana fad'in haka tafashe da kuka, cike da mamaki yace Nasiba kuma? Kirana tayi a wayar? Jin sautin kukanta yasa yayi saurin shiga d'akin yana shiga k'ofa tamaida kanta da k'arfi tarufe nan hasken wayar yad'auke d'akin yayi dund'um da duhu wata irin sautin murya yaji me kama da kukan hadari ta bushe da dariya duk d'akin ya amsa, Faruk nan fa gabanshi yafad'i ammah kokad'an bai nuna alamun tsoroba yana cigaba da addu'a a cikin zuciyarshi jin yadda ake cigaba da dariyar babu k'ak'k'autawa yasa cikin dakewa yad'aga murya yace wai wanene nan? Bai rufe bakiba yaji anjawoshi da k'arfi anbuga kanshi da bango wani irin zogi yaji yai saurin sulalewa k'asa yazauna tare da rik'e kan da yakeji tamkar ya fashe, murya yafara jiyowa me k'arfi cikin gurnani ana cewa ka yi kuskure Faruk da har kashiga rayuwata na gargad'eka kar kafito da memory d'innan ammah saida kafito da shi, toh bazan ta'ba barinka ba yau d'in nan sai naga bayanka. Sai a lokacin yafahimci kowacece tabbas aljanar nan ce ta gidansu jawahir bud'e baki yayi cikin juriya yace baki isa kiga bayana ba saidai ni inga naki bayan. Sake bushewa tayi da dariya a karo na biyu sannan tace ka yi k'arya kaga bayana zan iya rabaka da ranka a duk lokacin da naso. A harzuk'e yamik'e tsaye koda babu haske a d'akin cikin d'aga murya yace bazaki iya kasheni ba ammah ni zan iya rabaki da rayuwarki ta hanyar karanta maki ayoyin ubangiji, bai jira jin abinda zata ce ba yafara karanta wasu ayoyi daga cikin alk'ur'ani, wata irin k'ara tafara yi wadda taso tatada 'yar k'aramar girgizar k'asa a d'akin, saurin toshe kunnuwanshi yayi dan yasan k'arar zata iya yi mashi lahani a kunne sannan yana cigaba da addu'ar k'ofar d'akin ce tashiga bud'ewa da rufe kanta dak'arfi chan kuma sai yaji an daina k'arar d'akin ya d'auki tsit daidai lokacin hasken gidan yadawo, ajiyar zuciya yasafke tare da kallon wayarshi da take a k'asa tsakiyar d'akin, zuwa yayi yad'auka hannunshi d'aya yana dafe da kanshi yafita daga d'akin, dudduba saura d'akunan yayi yaji babu wata alama da aljanar za'ace ta shiga dan haka yakoma bedroom d'in duk wannan abun baisa yatsorata ba dan dama Faruk ba dai kafiya ba indai yasa kanshi yin abu babu abinda zai hanashi yana komawa yayi joining d'in wayar da laptop d'inshi yatura recording d'in acikin laptop d'in sannan yakunna wata irin k'ara yajiyo shuuuuu kamar iska dan haka yad'auko wayarshi yakunna karatun alk'ur'ani yasa volume sannan yad'auko earpeace yasaka yakunna recording d'in acikin laptop d'in... Muryoyine yafara ji suna tashi a ciki hakan yasa yagane cewa cigaban inda tatsaya da rubutun tane acikin diary d'in: *CIGABAN LABARI* Jawahir cigaba da kallon Malamin tayi tana nishi inda shima yake kallonta kamar irin zakin nan da yake neman abinci ido rufe, ganin batada niyar shigowa yasa yad'ebo wani abu yawatsa mata wata irin k'ara tasaki tare da ida shigowa d'akin taja tatsaya a gaban malamin, Ummah jikinta rawa kawai yake tana jin kamar tasaki fitsari a nan inda take tsaye, Umar ko wani irin haushi da takaici suka cikashi lokaci guda yafara jin tsanarta cikin ranshi yana cewa tabbas a yanzu na ida gasgatarwa itace tarabani da d'an uwana, Abba ko zufa yafara yi shi kanshi ya tsorata dan bai ta'ba kawo ma ranshi itace take kisan ba. Malamin kallon su Abba yayi yace kun ganta daman na fad'a maku fatalwa ce take cikin gidan nan. Su duka sukace fatalwa kuma? Wannan ai jawahir ce kuma bata mutu ba. Hannu yamik'a yana karanto wani abu me kama da yare sai gata ta tsugunna a gabanshi nan yadafa kanta yana cigaba da karatun nan tafara k'ara chan yasaki kanta yakalli su Abba yace tabbas akwai fatalwa a tare da yarinyar nan kuma itace take tsorata ku. Umar mik'ewa yayi a fusace yace ba wai fatalwa kad'ai ba jawahir ce take amfani da damarta tana kisa itace takashe su Aliyu, zumbur Ummah tamik'e tace jawahir d'in takashe min d'a? Fashewa tayi da kuka tace akan wane dalili zatayi min haka me d'ana yatsare mata? Mik'a mata hotunan hannunshi yayi yace gasu a wajenta nagansu tare da wannan wuk'ar kuma ina tunanin next target d'inta Abba ne. Zuface tacigaba da kwararo ma Abba lokaci guda yajik'e sharkaf kamar wanda aka watsa ma ruwa saurin mik'ewa yayi ya amshi hotunan yana kallo tabbas hoton Aliyu ne da na Abokinshi kuma irin hotunan da aka dinga tsinta ne lokacin da aka kashe su Alhaji Jamilu Cikin wata irin firgitattar murya tabushe da dariya wadda tasa saida baki d'ayansu suka juya suka kalleta mik'ewa tsaye tanemi tayi nan malamin yasake watsa mata wani abu me kamar gari nan tafasa k'ara tare da komawa tazauna, a karo na biyu tasake yunk'urin mik'ewa yad'ebo abun zai watsa mata tayi saurin sa hannu takare nan wata irin iska tataso maganin yazube, yunk'urin d'ebo wani yayi nan tabushe da dariya tare da mik'ewa tsaye cikin sauri, muryarta ta rikid'e ta zama kamar irin kukan mafad'acin dokin nan bud'e baki tayi tafara magana wadda tasa gabad'aya d'akin ya amsa sunan Alhaji Mu'az takira sannan tacigaba da ce baikamata wannan yasa kashiga damuwa ba idan har zaka iya tunawa da abinda ka aikata ma d'an uwanka kaine kasa aka kasheshi sannan nima karabani da raina tabbas nasan wannan bokan ne yayi maku aiki akaina bazan ta'ba barin duk wanda yake da hannu ba akan mutuwata sai naga bayanshi, a yau d'innan zan rabaka da rayuwarka a gaban iyalanka kafara k'irga dak'ik'un mutuwarka daga yanzu.....bata rufe baki ba taji an shak'eta da wani abu me kama da igiya k'ara tasaki tana yunk'urin k'wacewa ammah takasa malamin ne yashak'eta da wani abu me kama da igiya na tsafi nan yashiga karanta wasu d'alasimai yana zagayeta kuka tafara yi ahankali chan kuma tafasa k'ara daganan bata sake cewa komai ba. Abba jin kalamanta da yayi ba k'aramin tsorata yayi ba dan har fitsari yasaki bai saniba, ummah ko bata da banbanci da wanda yasuma dan d'if wuta tad'auke mata tun lokacin da taga jawahir ta taso kusan bata ma san abinda take cewa ba. Umar ranshi ba k'aramin 'baci yayi ba yace watau yarinyar nan gani take ma su Abba suka kashe mata mahaifi saisa take son raina ma mutane wayo har tana ik'irarin rabashi da rayuwarshi... Muryar malamin suka ji yana cewa wannan ba wani abu bane tabbas a lokacin da aka saka mata laya a cikin baki anyi ganganci domin akusa da iccen suri aka saka saisa fatalwarta tatashi, kukwantar da hankalinku ni zan kamata yanzun nan in tafi da ita. Abba saurin matsowa yayi wajen shi jikinshi yana rawa yace dan Allah malam kataimaka mana wallahi indai baka tafi da ita ba kasheni zatayi kamar yadda takashe abokaina zan baka ko nawa kakeso na yi maka alk'awali dan Allah kataimaka min. Malam yace kar kadamu zanyi bakin k'ok'arina kakwantar da hankalinka dan ta riga ta zo hannu daga yanzu zata zama tarihi dan kun gama ganinta. Umar kallon mahaifin nashi yayi yace Abba indai har kana da hannu akan mutuwar Abbu to baka kyauta ba, saurin juyowa yayi yakalleshi yace kai banza ne wanene yafad'a maka dagaske ne kawai dai so take taga ta kasheni saisa tayi wannan k'aryar ni bansan komai ba akan mutuwar d'an uwana, taya ma zan iya kashe shak'ik'ina bayan halarcin da yayi min a rayuwa idan har akace na kasheshi toh tabbas na zama butulu. Cikin fushi yace toh shikenan saidai ni kuma ya zama dole inbi ran d'an uwana dan sai na d'auki *FANSAR RAI* kamar yadda takasheshi itama zan kasheta ban damu da aljannun k'aryarta ba! Abba saurin girgiza kai yayi yace a'a Umar kar kayi haka kabar ma malam komai shi ya san yadda zaiyi da ita. Malam zuwa yayi yabud'e jakkarshi yad'auko wata kwalba da wani abu cikin wata 'yar roba yanufo wajen da jawahir take a d'aure, bud'e idanunta tayi dakyar tana kallonsu a galabaice ahankali tabud'e baki tace me yasa zakuyi min haka, Abba nice dan Allah kukwance ni ummah, Abba murmushi yayi yace munafuka ai yau kema dole kimutu kamar yadda kikaso kikashe mu. Ahankali tace kisa kuma? Da yaushe nace zan kasheku? Kallon umar tayi da yake ta huci tace yaya umar dan Allah kace susakeni kar sukasheni. Tsanarta ce tagani k'arara a idanunshi ranshi a 'bace yace idan har su basu kasheki ba ni zan kasheki dan d'aukar ma d'an uwana fansa tabbas ke butulu ce jawahir duk halarcin da nayi maki a rayuwa baki ganiba. Hawaye ne suka gangaro mata tace Yaya Umar bai dace kace hakaba wannan ba shine butulci ba, shin laifi ne dan na d'auki fansar ran iyayena? Tsawa yakwatsa mata yace ya isheki haka! wanene yakashe iyayen naki kina nufin Aliyu? Juyawa tayi takalli malam da yaruntse idanunshi yadage yana ta karanto wasu d'alasimai a cikin wani abu me kamar mai cikin roba, wata irin razanannar k'ara tasaki nan kamanninta suka fara sauyawa k'iba tafara k'arawa lokaci guda sukaga ta rikid'e ta koma wani k'aton biri malam saurin bud'e idanunshi yayi kafin yayi yunk'urin yin wani abu tuni ta fisge igiyar tsafin da yad'aureta da ita wani irin tartsatsin wuta yatashi tasa hannu takare fuskarta. Ummah saman kujera tayi saurin fad'awa tare da fasa k'ara tace mun shiga ukku wayyo jama'a kutaimaka min, Abba ko saurin ja da baya yayi yatsaya bayan Umar da yake rik'e sa wuk'a yana nunata alamun idan har ta iso zai caka mata, bushewa tayi da wata irin mahaukaciyar dariya sannan tace bazan ta'ba fasa abinda nayi niya ba. 'Debo maganin malam yayi dasauri zai watsa matayi tayi saurin gocewa ya sake d'ebowa a karo na biyu nan ma tagoce, zai sake d'ebowa tasa dogon hannunta tak'wa'be robar nan yazube. Girgiza tayi tadawo siffar Khausar Ammin jawahir gashin nan nata ya mimmik'e saman iska juyawa tayi takalli Abba nan tanuna shi da hannunta sai gashi ya yi saman iska, wuntsila wuntsila yafara yi da k'afafu saitin da fanka take wanawa tanufa da shi nan yafara ihu, cikin sauri malam yanufi wajen 'yar jakkarshi nan tayi saurin juyawa tanuna jakkar da yatsa sai ga hayak'i yana fita cikinta k'ara malam yasaki cikin sauri yad'auko jakkarshi da mamaki yake kallon khausar da tunda yake itace aljanar da tata'ba ja da shi ganin yadda hayak'i yake fita daga cikin jakkarshi yasa yayi layar zana ya'bace cikin sauri dan kar ta'ba mata tsafi. Umar na ganin haka yayi sauri yanufi inda mahaifinshi yake kafin ya isa gashin khausar wani siriri guda ya shak'o wuyan Alhaji Mu'azu sai gashi a jikin fanka ta d'aureshi, ummah saurin mik'ewa tayi takoma bayan kujera ta'boye. Umar saita khausar yayi da wuk'ar hannunshi cikin sauri yanufo inda take zai caka mata hannunta tanuna shi da shi sai ga wani irin haske ya fito yanufi wajenshi sakin wuk'ar hannunshi yayi yasa hannuwanshi duka biyun yashak'e wuyanshi karkata kanta tayi tana k'yalk'yala dariya nan shima yakarkata kanshi yana so yajanye hannunshi daga wuyanshi ammah ya kasa saboda tsananin mak'arar da tasa yayi, chan sai tayi wurgi da shi yafad'a k'asa yana nishi ummah da take tsaye bayan kujera tana kuka cikin sauri ta iso wajenshi tana zuwa tarik'eshi tana cigaba da kuka. Khausar kallon Abba tayi da yake saman iska saitin fanka nan wani haske yafito daga idanunta sai ga gashinta ya sargafe akan fankar k'ara Abba yafara yi yana neman agaji, dariya tacigaba da k'yalk'yalawa tace mu'azu nice ajalinka kamar yadda karaba ni da mijina da rayuwarmu har kanaso kaga bayan 'yata a yau buri na zai cika zan kasheka kaima kamar yadda nakashe sauran mugayen abokanka dan haka dak'ik'un mutuwarka sun kusa cika, bud'e baki yayi a galabaice yana so yayi magana ammah ya kasa sai nishi da yakeyi sama sama duk jijiyoyin kanshi sun mik'e, idanuwanshi sunyo waje, ja tad'anyi da baya nan fanka tacigaba da juyawa da Abba yana ta wuntsila k'afafu saboda tsananin azaba har wuyanshi yakare ranshi yarabu da jikinshi. Ummah ko tana zaune a gaban idanunta Abba yamutu kuka kawai takeyi tana kiran sunan Alhaji. Faruk hankalinshi yana fara dawowa jikinshi ganin yadda tayi ma mahaifinshi yasa yasake yunk'urin mik'ewa dak'yar yajawo wuk'ar yanufi wajenta zai caka mata a karo na biyu, juyowa tayi tanuna shi da hannunta sai ga wani haske ya bayyana me kama da shocking yana shiga jikin umar nan yafara k'ara, murmushi tayi tace na so in k'yaleka ammah ka nema ma kanka mutuwa dan haka dole kaima kamutu, fad'uwa yayi k'asa yana tirje tirje Ummah mik'ewa tayi dak'yar tana kuka tafara takowa muryarta tana shak'ewa tana kiran sunan umar chan sai tayanke jiki tafad'i k'asa. Nuna Abba tayi da hannu sai gashi ya fad'o k'asa a mace, ja tayi da baya tare da tsagaitawa daga dariyar da take nan wani haske yafara fita daga jikinta sai ga suffar jawahir kamanninta ya dawo saurin bud'e idanunta tayi, akan Abba tasafkesu da yake kwance k'asa abinda yafaru ne yafara dawo mata a k'walwa har zata nufi inda Alhaji Mu'azu yake kamar ance tajuya tana waigawa sai ganin umar tayi kwance yana ta shure shure. Cikin sauri ta isa wajenshi jikinta yana rawa ta tallabo kanshi tad'aura saman cinyarta tare da fashewa da kuka tace Yaya Umar dan Allah katashi muje asibiti, kallonta yake yana motsa baki yana so yayi magana ammah ya kasa, ganin haka yasa jawahir tak'ara sautin kukanta tana cigaba da kallon masoyin nata, chan taji muryarshi chan k'asa a hankali ya ce na tsaneki jawahir, tsagaitawa tayi daga kukan da take cike da mamaki take kallonshi tace Yaya umar meyasa zaka tsaneni ba laifina bane. Juyar da kanshi yayi yana kallon ceiling ahankali yake motsa baki kamar me karanta wani abu chan kuma sai taga ya ja numfashi da k'arfi ya rufe idanunshi. girgiza shi tafara yi tana cewa dan Allah Yaya Umar katashi kar katafi kabarni, duk yadda take girgizashi ammah ko motsi bayayi ganin haka yasa tafasa wata irin k'ara wadda tasa gabad'aya gidan saida ya amsa, rungumeshi tayi jikinta tana cigaba da kuka tana cewa dan Allah katashi ina sonka ina son cigaba da rayuwa da kai, Yaya Umar kaine gatana idan kabarni ban san halin da zan shiga ba, kaga taso muje ga abinci chan na girka inzuba maka kaci yau ranar farin ciki ce agaremu ranar zagayowar shekarar aurenmu ina sonka sosai Yaya Umar, sumbatu tadinga yi kamar zararra, ganin har lokacin bai motsa ba yasa tasake fasa wata k'ara tace Ammi meyasa kikayi min haka kin rabani da rabin rai na wallahi na tsaneki bana k'aunarki ke azzaluma ce. Bata rufe bakinta ba sai ga Ammi ta bayyana cikin wata irin mummunan halitta zaune saman iska ta kishingid'a kamar wadda take zaune saman kujera, cikin muryarta marar dad'in saurare tace shin laifi ne dan na taimaka maki na rabaki da wanda yayi yunk'urin kasheki? Cikin kuka jawahir tace k'arya kike Umar bai chan chanci hakaba bazai ta'ba kasheni ba tabbas a yanzu na yadda da maganarki da kika ta'ba cewa sai kin rabani da shi toh a yau kin rabani da shi hankalinki ya kwanta saidai ina so kisani na tsaneki fiye da yadda natsani su Abba a rayuwata. Bushewa tayi da wata irin mahaukaciyar dariya tace yau kece kike ik'irarin cewa kin tsani mahaifiyarki wadda tafi kowa k'aunarki saboda soyayyar wani? Matsowa tafara yi kusa da jawahir Janye Umar tayi cikin sauri tare da d'auko wuk'ar da ke gefenta tamik'e tsaye tace eh na fad'a na tsaneki kika saki kika matso kusa da ni sai na kasheki. Rage sautin dariyarta tayi tace daman ni ai matatta ce banda sauran rayuwa saidai ina so kijanye kalmar tsanar da kikayi min, kiduba kiga bayanki babban mak'iyinki ne kwance a mace, runtse idanu jawahir tayi hawaye suna zubo mata, ta'ba hannu aljanar tayi sai ga hotuna guda ukku sun bayyana a hannunta ajiyesu tayi a k'asa gaban jawaahir tace duba hotunan nan na san zakiyi farin ciki idan kika ga guda daga cikinsu, ahankali tabud'e idanuwanta da suka fara kumbura tasafkesu akan hotunan guda na Abba ne sai na Yaya Umar a kan na k'arshen tatsaida idanunta tare da fashewa da kuka hoton ta ne ita da iyayenta suna rungume da ita, saurin duk'awa tayi tad'auki hotonsu ita da iyayenta sannan tamaida kallonta ga Aljanar d'an guntun murmushi tayi sai kuma tahad'e fuska lokaci guda sannan tace na tsaneki ke ba Ammina bace. Bushewa tayi da dariya a karo na ba adadi saida tayi me isarta sannan tace kidaina furta kalmar tsana agareni ya zama dole kidinga min biyayya. Cikin d'aga murya jawahir tace baza'ayi maki biyayya ba daga yanzu ina so kifita daga rayuwata babu ke babu ni idan har kika sake shiga rayuwata zan kasheki! Wata irin k'ara aljanar tasaki tace wannan kuskure ne kike aikatawa jawahir. A fusace jawahir tanufi wajenta da gudu rik'e da wannan wuk'ar tun kan ta isa Aljanar tanuna ta da yatsanta me kama da sanda sai ga wata iska ta taso tana zuwa sai d'aukar jawahir tayi tai wurgi da ita sai gata chan gefe ta fad'a ta baya dak'arfi. Kwance tayi k'asa tana jin wani irin zafi a bayanta, chan kuma tayi yunk'uri tatashi zaune. Matsowa Aljanar tayi kusa da ita tamik'a mata hannu alamun tamik'o hannunta. Hawaye ne suka cigaba da fita daga idanun jawahir ba tare da ta mik'a hannunta ba tace na tsaneki Ammi kikasheni kawai kamar yadda kika kashe Yaya Umar inko baki kasheni ba ni zan ga bayanki bana k'aunarki. Muryar Aljanar ce tafara fita bibiyu tace wannan kuskure ne kike aikatawa na gargad'eki akan kidaina cewa kin tsaneni ammah kin k'i to dasannu zani azabtar da ke yadda baki tunani kisaurareni. Alhaji Tanimu koda ya iso gidan a k'ofar da zata sadaka da cikin gidan yatsaya yakira wayar Alhaji Mu'azu ammah har ta k'arashi ringing bai d'agaba kusan missed call biyar yayi mashi yana shirin yin na shidda ne yajiyo anfasa k'ara a cikin gidan dan haka cikin sauri yanifi cikin gidan yana shiga yai sallama yaji shuru a parlor yafara jiyo kuka ahankali yana tashi dan haka yanufi parlorn yana d'aga labule da gawar Alhaji Mu'azu yafara cin karo..... _Sis Nerja'art✍🏻_ [7/24, 11:11 PM] Sis Nerja'art 2: *......FANSAR RAI......* *INTELLIGENT WRITER'S ASSO....®* [On Award Together] _Follow me on Wattpad: *Sis-nerja*_ _Wannan Littafin na kud'i ne domin karantawa cikin aminci da yarda ga duk me buk'ata zai turo katin Mtn na d'ari biyu N200 kacal ta wannan number d'in 09035938246, ko ta account number 5330055604, Idan katura ka aiko da screen shot na transaction a wannan number d'in 09035938246_ _Akwai gara'basar *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shahararriyar marubuciyar nan *AMEENA ABBA UMAR* tare da novel d'in *FANSAR RAI* akan farashin N300 kacal, ko da kud'in ka sai da rabonka_ *PAGE 9* Cikin sauri yashiga parlorn yanufi wajen gawar tashi yatsaya cike da firgita yace Alhaji Mu'azu lafiya? Kwanciyar me kakeyi nan ko bakada lafiya ne? Jin sautin kukan jawahir yasa yajuya sai a lokacin yakula da ummah da ke shimfid'e k'asa itama babu alamun numfashi atare da ita gefe guda kuma jawahir ce wajen gawar Umar tana jijjigashi tana kuka, tsorata yayi sosai cikin sauri ya isa wajen jawahir yana zuwa akid'ime yace ke me yasamesu ya akayi suke a nan ba dai mutuwa sukayi ba dai ko? Ko d'agowa batayi takalleshi ba bare yasa ran samun amsar tambayarshi ganin haka yasa yace tambayarki nake me yafaru da su? Nan ma shuru wuk'ar da yagani gefenta ne yasa a fusace yace bazaki bani amsar tambayar da nake maki ba? Sai a lokacin tajuyo takalleshi da rinannun idanuwanta da suka fara firgicewa kallo d'aya tayi mashi tad'auke kai shi kanshi saida yasha jinin jikinshi ammah hakan baisa yayi shuru ba jinjina kai yayi yace wannan mutuwa sukayi kuma nasan kece kika kashesu, mi yasa zaki kashesu? Me suka aikata maki? Wallahi bazan ta'ba barinki ba ya zama dole hukuma tasani kema akasheki. Mik'ewa tayi tsaye bai ankaraba kawai sai ganinta yayi gabanshi baisan lokacin da ta isoba har saida yad'an tsorata, kallonshi tatsaya yi bata ko k'yaftawa ganin haka yasa yad'an ja da baya dan yanayin kallon da takeyi mashi na tuhuma ne cikin dakewa yace ke lafiya ko nima kasheni zakiyi kamar yadda kika kashe sauran? Wallahi sai na sanar da hukuma. Sai a lokacin tabud'e baki dak'yar cikin dashewar murya tace Alhaji Tanimu Nepa ka zo ne dan ka amshe sauran dukiyata a wajen Abba ko? Gabanshi wani irin mummunan fad'uwa yayi dak'yar yahad'iye wani yawu dake mak'ale cikin bakin shi nan yafara inda inda yace ni ni kuma? A'a ni ni ziyara nakawo mashi. 'Dan guntun murmushi tayi tace na san komai,, matsowa tafara yi wajenshi yayi saurin ja dabaya yace k'aryane ni bansan komai ba akan dukiyarki wai ma wacece ke? Binshi tafara yi yanda cigaba da yin baya baya tace tabbas nasan haka kuma nasan kana da hannu akan mutuwar mahaifina kaima. Tsorata yayi sosai da jin maganar da tayi cikin ranshi yace wanene yasanar da ita mune muka kashe iyayenta bayan lokacin da mukayi maganar a d'aki muka yita mu takwas ne acikin gidan babu wani mahaluki a ciki toh ammah kuma....muryarta yaji ta ce wannan haka yake na san kana da hannu a ciki. Hanyar k'ofa yanufa yana cewa a'a bansan komai ba akan mutuwarsu. Tsaye jawahir tayi tana kallonshi chan sai tafad'a saman kujera tazauna tare da dafe kanta ganin haka yasa yayi saurin juyawa zai bar d'akin sai jin muryarta yayi ta ce idan har kasanar da wani abinda yafaru sai na kasheka! Da gudu ya ida fita ko motarshi bai tsaya shiga ba dan kar ma ya'bata lokaci yabar gidan. Wani irin kuka tadinga yi a nan inda take zaune k'arar wayar da taji kusa da itane yasa tajuya sai ganin wayar Umar tayi tana d'aukowa taga recording ne yayi saving cikin sauri takunna tana saurare taji duk abinda yafaru ne akayi recording a tsorace ta ajiye wayar tana tunanin wanene yayi recording d'in...... Faruk yana gama saurare ajiyar zuciya yasafke ahankali yace watau abinda yafaru kenan dukkansu ta kashe har da Umar? Toh ammah banji.....k'arar buga gida yafara jiyowa ana knocking nan yakalli agogo yaga duka k'arfe d'ayan dare cike da mamaki yace to wanene yake buga gida a wannan lokacin ko dai megadi ne Mik'ewa yayi sai ji yayi andaina bugawa har zai je yabud'e sai kuma yafasa yakoma yazauna. Dariya ce yafara jiyowa tana tashi daga wajen tagar d'akinshi dan haka yak'ara sautin karatun alk'ur'ani sannan yacigaba da aikinshi har wajen k'arfe biyun dare sannan yakwanta bacci. Wajen k'arfe sha d'aya yaje gidan kaso yana isa yasamu jawahir tsaye a wajen da tasaba tsayuwa, tsayawa yayi daga bayanta har ya bud'e baki zaiyi magana sai jin muryarta yayi cikin sheshek'ar kuka ta ce ka yi k'ok'ari sosai da har ka iya ku'buta daga hannun Ammin saidai ina baka shawara kacigaba da addu'a dan itace zata cigaba da tseratar da kai daga sharrinta dan daga baya na gane ba taimako kawai Ammi ta ke ba har da zalunci take tunda har ta iya kashe wanda baida hak'k'i acikin mutuwar Abbu............. A lokacin da nagama sauraren recording d'in na yi mamaki sosai kuma na tabbatar Yaya Umar ne yayi shi tabbas a ranar na san dole sai police sun zo tunda har nayi sakacin barin Alhaji Tanimu a raye yafita saidai ban yi nadamar abinda Ammi ta aikata ba saidai rad'ad'in mutuwar Mijina da nakeji, cikin sauri nad'auko wayar dan inaso tazama sheda akan abinda na aikata dan akasheni nima sai ji nayi an fizge wayar daga hannuna sai gani nayi ta fad'i k'asa safkowa nayi daga saman kujera zan d'auko wayar sai gani nayi anjata tayi hanyar k'ofa tsayawa nayi ina kallonta sai jin muryar Ammi nayi ta ce bazan ta'ba bari kid'auki wayar nan ba babu wanda ya isa yad'auketa har yasaurari abinda yafaru. Juyawa jawahir tayi tana waige ammah bata gantaba dan haka tafara takawa saida tad'auki diary d'inta da Umar yashigo da shi parlorn, sannan tanufi wajen k'ofar sai wayar tacigaba da tafiya tafita daga cikin d'akin motsin da takeji a bayantane yasa tagane Ammi tana bayanta dan haka tacigaba da tafiya har saida takai wajen wani bokitin k'arfe da tafiddo d'azu zata d'ibi ruwan mopping tagoge kitchen dan a lokacin da akayi abin 'yar aikinsu ta je gidansu zata kwana biyu, rarimo bokitin tayi cikin sauri tajuya daidai lokacin da Ammi take bayyana cikin zafin nama tabuga mata shi a kai, sannan tayi wurgi da shi da sauri tad'auki wayar dagudu tanufi d'akin 'yar aikinsu da bakomai a cikinshi tana shiga tazauna k'asa jikinta yana rawa tabud'e wayar taciro Memory card d'in, dariya tafara ji gabad'aya d'akin yana amsawa da ita cikin wata irin kakkausar murya taji muryar Ammi tana cewa kin aikata kuskure jawahir bazaki ta'ba yin nasara ba akan abinda kike son samu. Rik'e memory d'in tayi gam a hannunta cikin rawar murya tace k'arya kike Ammi baki isa kihana ni samun abinda nakeso ba, na fad'a maki kifita daga rayuwata bana sonki na tsaneki. Wata irin k'ara taji anfasa sannan cikin muryar fushi taji Amminta tana cewa ina gargad'inki da furta kalmar tsana agareni jawahir domin hakan zai iya jawo maki shiga cikin wani irin mawuyacin hali a rayuwarki. Cikin kuka tace taya zan daina tsanarki bayan kinyi amfani da jikina da hannuna wajen kashe mijina? na tsaneki Ammi, tana fad'in haka tahad'e kai da gwiwa tacigaba da rusa kuka. Bayan fitar Alhaji Tanimu wayarshi yad'auko yakira DPO yashaida mashi abinda yafaru nan DPO yace yajirasu gasunan zuwa. Jawahir tana cikin kukan tajiyo jiniyar motoci ammah hakan bai sa tad'ago ba dan tasan daman tabbas sai hakan ya faru, tana jiyosu suna shigowa cikin gidan inda wasu duk suka zagaye gidan parlor suka fara shiga inda suka ga su Alhaji Mu'azu kwance, tsaye sukayi a wajen gawarwakin suna dubawa DPO hana kowa yayi yata'ba gawarwakin yace aje azo mashi da duk wani mahaluki da yake cikin gidan sannan yakira likita a waya. Tana jiyo police suna bud'e sauran d'akuna ammah bata motsaba har suka shigo cikin d'akin da take zaune tsawa suka daka mata sukace me take a nan bata ko d'ago kai ba bare har tatanka masu dan haka biyu daga cikinsu suka shugo suka kamata memory d'in ne yakubce daga hannunta yafad'i tana so tayi magana ammah takasa babu wanda yalura da shi daga cikinsu saidai suka d'auko wayar Umar suka fita da ita a parlor suka kaita suka zaunar da ita k'asa inda tatadda megadinsu shima a zaune yayi zugum yana kallon gawarwakin iyayen gidanshi. DPO kallonta yayi sannan yamaida kallonshi ga Alhaji Tanimu dake tsaye wajen gawar Abba yace wannan ce Alhaji?. Kallonta Alhaji Tanimu yayi sannan yace Eh itace tabbas ita takashesu. Daidai lokacin likita ya iso yana duba Abba da Yaya Umar yace ai sun mutu ammah ummah suma tayi dan haka aka tafi da ita asibiti. Matsowa DPO yayi yatsugunna gabanta yana k'are mata kallo har lokacin kanta sunkuye k'asa tana hawaye jinjina kai yayi yace me zakice a game da mutuwar mutanen nan? Shuru tayi bata amsa mashi ba, damk'o gashinta yayi tayi saurin runtse idanunta yace tambayarki nake shin kece kika kashesu? A nan ma ban bashi amsar tambayar da yayi min ba muna a haka aka kawo mashi hoton Yaya Umar da na Abba wanda Ammi ta ajiye min ansa maker an yi masu tick koda yaduba yaga exactly irin wanda duk yatsinta ne lokacin da aka kashe su Alhaji Jamilu dan haka yasa aka kamani aka tafi da ni policestation aka rufe ni tsawon kwana biyu yana bincike inda yatabbatar da nice nayi kisan daga nan yamakani a kotu, kwana biyun nan da nayi kusan kullum sai Alhaji Tanimu ya zo ya dubani abinda yake bashi mamaki bana tare da wata damuwa atare da ni kuma har lokacin ban bud'e baki nayi magana ba, duk zuwan da Alhaji Tanimu yakeyi so kawai yake imbud'e baki in amsa ma police nice nayi kisan ammah nak'i a ranar da aka mik'a case d'ina kotu koda yazo yake tambayata shin ko akwai hanyar da zanbi inkare kaina a kotu? 'Dan guntun murmushi nayi ganin shi kad'ai ne a wajen yasa nace kar kadamu da wannan saidai ina so kaje kafara shiri dan kaine mutum na gaba da zaka bak'unci lahira. Dariyar mugunta yayi yace taya kike tunanin zaki kasheni bayan ke hukuncin kisa ne za'a yanke maki bazan ta'ba bari kibar gidan ba koda kin bari a gidan kaso rayuwarki zata k'are, , sannan duk wasu takardu da suke mallakinki na samu nasarar d'auko su a cikin gidan ku zan mallake dukkan dukiyarki hatta ta cikin account d'inki zanyi k'ok'arin ganin na mallaketa. Murmushi tayi a karo na biyu tace wannan ba matsala bane saidai inaso kasani daga kai har wad'anda kake tare d su babu wanda zai iya tsere wa daga hannuna dole sai kun mutu kamar yadda sauran suka mutu. Dariya Alhaji Tanimu yadinga yi har saida aka zo aka koma da jawahir d'akin da take a rufeta. Ranar litinin aka zo aka d'auketa cikin motar 'yansanda aka tafi da ita kotu koda aka je batace uffan ba tana ganin lauyoyi biyu suna ta fafatawa da wani lauya da taso taganeshi ammah takasa wanda yake a matsayin shi yake kareta har aka gama shara'ar bata fahimci komai ba tana ji ana ta mata tambayoyi saidai tabisu da idanu. Ganin bata amsa cewa itace tayi kisan ba yasa Alk'ali yayanke mata hukuncin zama gidan yari na tsawon sati biyu kafin adawo zama na biyu, daga nan kotu aka wuce da ita gidan mata inda aka had'eta d'aki guda da wasu mata biyu masu irin laifinta na kisa,, saidai su kallo d'aya zakayi masu kaga babu alamun imani atare da su mugaye ne nan fa suka fara mata gani gani tare da nema surainata. Saidai duk wannan baisa jawahir takula su ba saidai tayi zaune waje d'aya tayi shuru tana jinsu suna ta hira ammah bata kulasu ko kad'an bataga alamar damuwa a tare da su akan zaman da suke a cikin gidan kason nan ba, inda ita kuma saboda rashin sabo yasa takasa sakewa tana ji gabad'aya rayuwar ta canza mata saidai ko kad'an batayi nadamar abinda ta aikata ba, kusan kullum sai anzo anfita da su an kaisu sunyi aiki me wahala, a duk lokacin da suka fita dan yin aikin jawahir bata k'ara sanin inda hankalinta yake har sai anmaidasu d'an kurkukun d'akinsu. Bayan sati d'aya lauya me kareta yazo aka fiddota aka kaita wajen da aka tanada dan ganawa da me laifi idan aka zo ziyartar shi musamman ma lauyoyi idan har lauyan ya buk'aci haka, koda tazo taga shine wanda taga yana kareta a kotu tsayawa tayi tana kallonshi murmushi yayi yace sannu jawahir na san dai kin sanni a matsayina na abokin mahaifinki yakamata kikwantar da hankalinki kinutsu ki amsa min duk tambayoyin da zanyi maki ni zan taimaka maki kifita daga gidan nan. Tunda yafara magana idanu tazuba mashi tana kallonshi har yakai aya sai a lokacin tayi murmushi tace Barr Mubarak ko? Shima murmushin yayi yace Eh haka ashe kin gane ni ai na d'auka bazaki iya tunani ba tunda tun bakida wayau sosai narabu da zuwa gidanku, nayi mamaki sosai da yakasance d'iyar abokina ce take rayuwa a nan gidan kaso har ake yayata labarinta a gari akan cewa ta yi kisa wannan dalilin ne yasa nazo inwanke ki akan zargin da akeyi maki. Tarar numfashinshi tayi tace ba wai zargi ba Barrister bana buk'atar taimako irin naka domin baka dace kataimaka min ba katafi kawai. Murmushi yayi yace baidace kice haka ba ga wanda yakeson taimaka maki. Itama murmushin tayi cikin alamun nuna rashin damuwa tace fiye ma da hakan zan ce gareka barrister katafi kawai kanuna tausayawarka ga wani na daban ba wai wacce takasance abokiyar gabanku ba. Da mamaki yake kallonta yace abokiyar gabanmu fa kikace? Wacece abokiyar gabanmu kuma ni da wa? Ta'be baki tayi tace na san ka san komai, koma me kenan da sannu zan fahimtar da kai. Haka suka rabu Barr Mubarak bai samu had'in kan jawahir ba a rana ta biyu koda yadawo nan ma bai samu yadda yakeso ba har suka zauna zama na biyu a kotu nan ma bata amsa laifinta ba akan zargin da akeyi mata dan haka akace ak'ara mata wata d'aya a gidan kaso sannan adinga sata aiki me tsanani. Saida tayi sati biyu tana faman wahala duk wani aiki me wuya ana sata saidai abinda zai baka mamaki jikinta bai ta'ba nunawa ba, a lokacin da take sati na ukku ne Barr Mubarak yazo dan yagana da ita koda aka fiddota wajen da zasu gana kallonta yayi yai murmushi yace sannu malama jawahir Idanu tazuba mashi batare da ta ce komai ba ganin haka yasa yacigaba da cewa jawahir taurin kanki ya yi yawa kin sanni kuma kinsan taimaka maki zanyi kisamu kifita da gidan nan dan baidace da ke ba a matsayinki na d'iyar babban mutum irin Alhaji Muhammad kibani had'in kai intaimaka maki. Idanu tazuba mashi batare da ta ce komai ba ganin bata da niyar yin magana yasa yad'auko wasu takardu yamik'a mata yace amshi wannan signing kawai nakeso kiyi min idan har kikayi ni kuma na yi maki alk'awalin zan taimaka maki wajen ganin kin bar gidan nan. Kallon takardun tayi sai taga na filaye ne guda biyu ga sunan Mahaifinta nan a jikin takardun, d'an guntun murmushi tayi sannan tace ba wai ka zo da niyar taimako na ba kawai dai kace ka zo da niyar cin dukiyata kaima, a matsayinka na abokin Abbuna baka kasance mutumin kirki irinshi ba. Kinga ba wannan natambayeki ba indai har kinason barin gidan nan ya zama dole kiyi abinda nakeso inko ba haka ba kina ji kina gani za'a kasheki. Matsowa tayi kusa da shi tace toh menene dan na je inda iyayena sukaje! Ko ance maka bansan lokacin da kaje katsaya ma Abba ba wajen ganin kun k'wace ma Ammina hak'inta ta k'arfi da yaji ba? Kasan komai akan dukiyar mahaifina ammah son zuciya yahana kafad'i gaskiya, kuma tabbas nasan su Alhaji Tanimu ne suka turoka wajena, tir da hali irin naka. Dariya Barr Mubarak yayi yace dakyau na ji dad'i da kika gane hakan a yanzu tunda kinsan halina ya kamata ki cika wad'annan takardun dan samun ku'butar ki daga gidan nan inko ba haka ba a banza zaki mutu sannan dukiyar da take mallakinki zata dawo k'ark'ashinmu hatta companyn mahaifinki kinga shikenan zuri'ar Muhammad me shadda ta zama tarih.....bai gama rufe baki ba tayi kukan kura tayo kanshi kafin yayi wani yunk'uri ta shak'e mashi wuya da dukkan k'arfinta, k'ok'arin k'wacewa yafara ammah yakasa dan k'arfin ba na mutum d'aya bane, buga table yafara yi dak'arfi sai ga masu kula da ita sun shigo dan dama suna bakin k'ofa nan fa aka fara k'ok'arin k'waceshi, kuka jawahir tadinga yi cikin d'aga murya tana cewa bazan ta'ba bari hakan yafaru ba bazan barka ba barrister, saida kusan maza biyar suka taru sannan suka samu suka 'ban'bare hannunta daga wuyan barrister mubarak tari yafara yi, bugunta suka fara yi a wajen saida suka bugeta sosai har tasuma sannan aka jata aka maidata d'akinta. Barr Mubarak ya dad'e a wajen tsaye rik'e da wuyanshi yana tari idanuwanshi sunyi jajir kafin daga baya yad'auki takardunshi yafita. Yana barin nan wani makeken gida yaje a parlorn gidan yasamu su Alhaji Tanimu su ukku zaune suna ganinshi suka fara murmushi wani da yake zaune kusa da Alhaji Tanimu ne yace ya dai barrister muna fata dai angama komai. Zama yayi tare da tsiyaya wani swan water da yake saman center table yasha saida yashanye kofi guda sannan ya ajiye kofin yace hmm ina fa hakan yasamu yarinyar chan saura kad'an takasheni.. Su duka idanu suka zuba mashi sukace garin ya? Ajiyar zuciya yasafke yace yarinyar chan ina tunani aljannu gareta. Dariya Alhaji Tanimu yayi yace muma ai Aljannun kanmu ne akan kud'i haba Barrister ya kamata kayi wani abu man kar fa kamance da mak'udan kud'ad'en da mukayi maka alk'awalin su kaga idan har kataimaka mana tayi signing shikenan zaka iya zare hannunka akan case d'in inyaso ma akasheta babu ruwan wani. Shuru Barrister Mubarak yayi kamar me nazarin wani abu ya d'auki mintuna sosai yana nazari sai chan yace kubarni da ita na san yadda zanyi tasa hannu yau d'innan zanje wajen likitana yataimaka min da wata allura ce da na caka mata ita zata fita daga hayyacinta na san a lokacin zata amince tayi signing d'in batare da ta saniba. Su dukansu dariya sukasa sukace lallai barister ashe k'walwarka tana ja sosai. Dariya shima yayi yace yoh ba dole tajaba ai bazan ta'ba mancewa da rashin mutuncin da Alhaji Muhammad yayi min ba lokacin da nanemi yataimaka min da wasu kud'i zan biya bashi yace min baidasu bayan gabana aka kawo mashi wata leda cike da kud'i sai cewa yayi wai ba na shi bane na ajiya ne aka kawo mashi, saidai dubu d'ari yabani ni da nake neman million guda, koma menene kukasance cikin shiri gobe dan zan kawo maku takardun nan da signing d'in yarinyar chan. Shewa suka dinga yi a wajen suna cigaba da tattaunawa sun d'au lokaci sosai suna tattaunawa kafin su rabu akan gobe zasu sake had'uwa. Barr Mubarak bayan ya bar nan kamar yadda yayi alk'awali saida yabiya wajen wani likita amininshi yasamo allurar sannan yawuce gidanshi lokacin da yakoma iyalanshi duk basu nan yana shiga d'akinshi wanka yayi yafito parlor yana magana shi kad'ai yana cewa wato har wannan lokacin su madam basu dawoba su da nace kar suyi marece tsaki yaja tare da zama bisa 3 seater yad'auko remote yana canza channel sallama aka yi aka shigo ciki ciki ya amsa nan wata babbar mata tashigo da tray d'auke da abinci da lemu ta ajiye a gaban Barr Mubarak tace 'Dalla'bai ga abincinka Hajiya tace akawo maka idan ka dawo, tana fad'in haka tatashi cikin sauri tafita tabar d'akin, saida tafita sannan yajuyo yakalli tray d'in, a karo na biyu aka sake sallama matar ce yaga ta dawo kallo d'aya yayi mata yad'auke kai dan shi ya tsani 'yan aiki suna shigo mashi d'aki, zuwa tayi ta ajiye wani jug da tashigo da shi tatsiyaya mashi kunun aya tamik'a mashi tace Alhaji ga shi. Juyowa yayi a wulak'ance yakalleta yace ni nasaki kizuba min? Girgiza kai tayi tace a'a. Toh bar nan wajen A saman table d'in da yake gabanshi ta ajiye sannan tamik'e tafita. Tsaki yaja tare da kallon cup d'in ganin had'ed'en lemun kankana ne yasa yad'auka yafara sha dan yana son shi sosai, saida yasha kusan kofi biyu sannan yabarshi. Bayan magrib yana zaune yafara jin cikinshi ya fara ciwo tun yana d'aukar abun wasa sai gashi ya kwanta har akayi sallar isha'i yana murd'e murd'e matarshi koda tadawo taganshi a wannan halin hankalinta ya tashi sosai dan haka taje tad'auko wayarta dan takira family doctor d'insu tana fita yana kwance yana ta murd'e murd'e sai ganin wata irin mata me mummunan halitta yayi ta bayyana a gabanshi tana tsaye tana kallonshi koda yana cikin halin ciwo saida yatsorata yunk'urawa yayi zai tashi ammah yakasa, murmushi tayi wanda yasa hak'oranta suka bayyana waje, Cikin zafin ciwo yace wacece ke? Me kikazo yi a nan. Rikid'a tayi takoma siffar kamannin Jawahir, yunk'urin mik'ewa yayi nan tanuna shi da hannunta sai gashi ya koma ya kwanta a nan take duk kasala tarufeshi. Zagaye gadon da yake kwance tayi tana dariya saida tayi me isarta sannan tace bazan baka damar magana ba saboda bana buk'atar jin komai daga bakinka tambayar da kayi min itace maganarka ta k'arshe a duniya, kamar yadda nayi alk'awali bazan ta'ba barinka ba bare har kasamu damar cutar da ni dan haka kafin ka kasheni ni zan fara shafe babin rayuwarka, idanu Barr Mubarak yazuba mata yana kallonta ko hannunshi yakasa motsawa, cigaba tayi da cewa kun zalunceni kun cuci abokantaka da kuka yaudari mahaifina kuka kasance me fuska biyu a wajenshi saboda dukiyarshi har saida kukayi silar barinshi duniya sannan wannan bai ishekuba kunaso kushafe duk wani tarihi na rayuwarshi toh inaso kasan cewa nasan lokacin da kaje wajen likita ka amso allurar nan nikuma nayi amfani da damata nakawo maka lemu me guba kasha na tabbata ko minti goma bazaka k'araba yanzu zaka mutu, zaka rigani zuwa inda kakeso kakaini dan haka na barka lafiya.....k'arar k'ofar da tajine alamun za'a bud'e yasa tayi saurin 'bacewa. Barr Mubarak hawaye ne suka fara fita daga idanunshi yana kallon matarshi tana ta faman yi mashi sannu tana shaida mashi likita yana nan tafe zai dubashi, a lokacin ne yafara yunk'urin amai ammah yakasa tashi nan inda yake kwance yafara aman jini yana jin ciwon cikin yana k'ara tsananta a nan take yamutu kafin isowar likita dan lokacin da ya iso tuni ya bar duniya. Hankalin mutane ya tashi sosai akan mutuwar Barr Mubarak musamman ma da likita yatabbatar da guba aka bashi yaci saidai anduba ba'a ga alamun ya ci wani abu me guba ba acikin abincin da aka kawo mashi ba nan aka rasa inda yasamo guba yaci. Mutuwarshi tasa su Alhaji Tanimu suka shiga damuwa sosai inda suka fara tunanin jawahir tana da hannu akan mutuwarshi sune suka fara yad'a abun nan aka d'auka ana cewa itace tayi layar zana daga gidan yari taje takasheshi saidai hakan bai zama k'wak'warar sheda ba saidai duk da haka ana zarginta ammah babu wanda zai iya bada shedar cewa itace tayi kisan. Mutuwarshi ta tada hankalin Alhaji Tanimu sosai saboda haka ne asatin da yamutu yatattara yagudu Europe dan ya tsorata sosai akan kisan da aka yi ma nakusa da shi...... Jawahir na kawowa nan juyowa tayi takalli Barr Faruk tace wannan dalilin ne yasa ake cewa na kashe lauyana me son kareni saidai mutane basu san cewa shi d'in me fuska biyu ne ni a wajena fuskar azzalumi gareshi,,, hawaye ne tafara yi nan takoma wajen zamanta tazauna. Barr Faruk kasa cewa komai yayi ganin yadda take hawaye yasa yaje yalek'a waje yace ma ma'aikacin gidan yana buk'atar ruwan sha nan yatafi dan ya samo mashi. Dawowa yayi yakalleta yace Tabbas Alhaji Tanimu ya kasance shed'ani ne idan har abinda kika fad'a akanshi gaskiya ne, ammah shi Barr Muhsin fa, ya akayi yatsaya maki kuma kina nufin shima yana da hannu a ciki saisa kika kasheshi? Shuru tayi tazuba ma gefe d'aya idanu tana kallo, daidai lokacin ma'aikacin gidan yakawo mashi purewater me sanyi saman tray yad'auro cup a sama, amsa Barr Faruk yayi yai mashi godiya bayan ya fita ya basu waje ne yatsiyaya a cup d'in yamik'a ma jawahir. Tsayawa tayi tana Kallon cup d'in sai kuma chan ta amsa tare da yin murmushi tace nagode, nan takafa cup d'in a bakinta saida tashanye sannan tatsaya tana kallon cup d'in tana murmushi. Shima kallonta yake ahankali yace ya burgeki ne cup d'in? Girgiza kai tayi tare da mik'a mashi bayan ya amsa ne tace wannan cup d'in ankawo shi ne saboda kai ne zaka sha ruwan kuma kai mutum ne me daraja a wajensu mu ko k'ask'antattu ne a ko'ina. Tarar numfashinta yayi yace a'a jawahir kidaina cewa haka kema mutum ce me daraja kuma insha Allahu zaki bar gidan nan rayuwarki zata koma irin wadda kikayi a da zaki cigaba da kasancewa a cikin farin ciki komai zai zama tarihi. Murmushi tayi har saida hak'oranta suka bayyana sannan tagirgiza kai tace kaine kake tunanin haka barrister. Shima murmushin yayi sannan yace ina saurarenki ya kamata ki ida sanar da ni abinda yafaru bayan mutuwar Barr Mubarak. Ajiyar zuciya tasafke sannan tacigaba da cewa........... _Sis Nerja'art✍🏻_ [7/24, 11:11 PM] Sis Nerja'art 2: *......FANSAR RAI......* *INTELLIGENT WRITER'S ASSO....®* [On Award Together] _Follow me on Wattpad: *Sis-nerja*_ _Wannan Littafin na kud'i ne domin karantawa cikin aminci da yarda ga duk me buk'ata zai turo katin Mtn na d'ari biyu N200 kacal ta wannan number d'in 09035938246, ko ta account number 5330055604, Idan katura ka aiko da screen shot na transaction a wannan number d'in 09035938246_ _Akwai gara'basar *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shahararriyar marubuciyar nan *AMEENA ABBA UMAR* tare da novel d'in *FANSAR RAI* akan farashin N300 kacal, ko da kud'in ka sai da rabonka_ *PAGE 10* ....Har lokacin zaman mu kotu yayi mukazo babu lauyan da zai tsaya min ana ta surutu akan na kashe lauyana, duk yadda akaso in amsa laifin kisan nan ammah nak'i amsawa saboda haka ne alk'ali yasake d'aga shara'ar nan da wata ukku masu zuwa inda yabada umurni da acigaba da sani aiki me tsanani a gidan yari. Duk tsawon lokacin da nad'auka a gidan kaso muna zaune d'aki d'aya da wad'annan matan biyu watau Raliya da Rufaida har lokacin magana bata ta'ba had'ani da su ba koda daman suna nuna min tsana duk lokacin da za'a kawo mana abinci saidai sucinye har nawa, ahaka wata rana mukayi fad'a akan abincina da aka kawo min koda wannan fad'an ma Ammi ce sukayi da ita a lokacin tana jikina wanda yakaisu har suka dakeni a k'arshe ma suka yanke shawarar kasheni a cikin dare, ita kuma Ammi ganin haka yasa takashesu da daren dasafe aka tashi basu da rai,,wannan dalilin ne yasa aka maido ni wannan d'akin ni kad'ai ina cigaba da rayuwata, ana azabtar da ni aka hana adinga fita da ni aiki saidai batare da sanin shugaban gidan ba suke fita da ni suna sakani dan a ganinsu bazasu iya barina incigaba da zama haka ba kamar anmin gata ne. Ana saura wata d'aya musake komawa kotu a lokacin ne Barr Muhsin yazo a matsayin lauyan da zai kareni ko kad'an banyi mamaki da ganinshi ba dan daman na sanshi a matsayinshi na lauyan mahaifina wanda yasan duk wani sirrin duniyarshi ta ciki da waje, tunda yazo ban ta'ba ce mashi uffan ba ya yi juyin duniya inyi mashi magana ammah na k'i har lokacin komawarmu kotu yayi muka koma haka aka gabatar da shara'a suka fafata shida Barr MB, yana k'ok'arin kareni saidai kawai inbisu da idanu har akayi aka gama inda aka k'ara d'aga shara'ar tamu zuwa wasu watanni biyu masu zuwa, nan aka maidoni gidan yari da alokacin yazame min gida idan da sabo na saba saidai duk lokacin da za'a fita da ni zuwa kotu ina jin wani irin yanayi a duk lokacin da muka fara tafiya cikin mota ina kallon mutane masu wucewa. Haka dai Barr Muhsin yayi ta bina ammah bai samu yadda yakeso ba har aka sake wani zaman da yakasance na biyun k'arshe dan har lokacin baida k'wak'warar hujjar da zai kareni, a nan ma sake d'aga shara'ar akayi zuwa wasu watannin biyu masu zuwa a lokacin ne Barr Muhsin da aka maido ni gidan yari yazo yasameni kallona yake cike da mamaki yace Jawahir narasa meyasa kwatakwata kin kasa sakin jiki da ni nifa ba da niyar cutarwa nazo makiba taimakonki nakeson yi ammah kin kasa gane haka. Murmushi nayi nace gane hakan abu ne mewuya domin mutane abun tsoro ne. A cikin idanunshi naga mamaki k'arara koda mamakin bai nuna akan maganata ta farko da nayi agareshi ba saidai hakan ya faru ne saboda maganar da nayi bai zaci hakan ba, jinjina kai yayi yace hakane ammah jawahir ai kin sanni kinsan bazan zo da niyar cutar da ke ba. Matsowa tayi kusa da shi sannan ahankali tace cutarwa ta nawa kuma? Shin ka mance lokacin da katsaya ma Abba akan kunaso kuk'wace kamfani na ta k'arfin tsiya? Ko baku bane kuka bugo jabun takardu akan kamfanin dan kawai kuga kun rabamu da su, hatta gidan Ammina kaine katsaya ma Abba wajen ganin ya k'waceshi ta karfin tsiya, idan ko haka ne cutarwa ta nawa zakayi min!.... Da mamaki yake kallonta har takai aya sannan yace jawahir duk wa yafad'a miki wannan? Wallahi ba gaskiya bane ko kad'an ban ta'ba tunanin cutar da ku ba. Murmushi jawahir tayi a karo na biyu sannan tace ba ma wannan kad'ai ba hatta abinda kake da niyar aikatawa na sani. Kasa cemata komai yayi yana binta da kallo kafin daga bisani yawuce yatafi. Tun wannan zuwan bai sake dawowa ba sai bayan kwana ukku, koda yazo aka fiddo mashi ita dan sugana kallonshi tayi tace ashe zaka k'ara dawowa da ace zaka taimaka ma kanka da ka hak'ura da zuwa wajena dan bana buk'atar taimakonka. Cikin ran Barr Muhsin yace wannan na rasa wace irin yarinya ce anya zata amince musamu abinda mukeso cikin ruwan sanyi? Chan kuma a fili yace zuwana shine daidai idan har ban taimaka makiba tabbas zan kasance acikin masu butulci mutanen gari zasu zageni a matsayina na lauyan mahaifinki ace na kasa kareki. Cikin d'aga murya tace kaje kanuna tausayawarka ga wasu ba dai ga ni ba domin ni bana buk'atar hakan. Jinjina kai yayi cike da mamakin maganganunta cikin ranshi yace lallai yarinyar nan da ace babu abinda nake nema a gareta da bazan ta'ba tsayawa tana min wannan wulak'ancin ba.... Jawahir tana zuwa nan a labarinta kallon Barr Faruk tayi da har lokacin yake tsaye ya tsareta da idanu d'an guntun murmushi tayi tace Barr muhsin tun bayan rasuwar Ammina baya k'asar zan iya cewa sai ma bayan mutuwar Barr Mubarak ne sannan yadawo kuma su Alh Tanimu ne suka turoshi ko ma ince Alhaji Tanimu ne yahad'a shi da sauran mutanen da sukeso suga sun mallake dukiyata koda yagane nice sukeson yin aiki a kaina ya yi farin ciki sosai domin shima akwai abinda yake buk'ata a wajena. Wannan abun da mukayi da Barr Muhsin yasa sai bayan sati d'aya yasake dawowa bayan anfiddoni yad'auko wani Atm yanuna min yace wannan mallakin mahaifinkine yana da kud'ad'e a cikinshi kuma gab ake da arufe account d'in saboda ya kwana biyu ba'ayi amfani da shi ba kuma ba kowane yasan yana da wannan account d'inba tunda ya fi amfani da wanchan gudan, wannan ya bud'e shi ne saboda masu biyanshi bashi idan ya basu koda duk yarjejeniyar da suke akan bada bashi yana sanar da ni a matsayina na lauyanshi dan mahaifinki baya abu sai ya samu mesheda, wannan dalilin ne yasa nasan komai akan wannan Atm d'in da sabon account d'inshi. Ta'be baki tayi tace nasan haka saidai bakasan Pin d'in da zaka ciro kud'in ba wannan dalilin ne yasa kasanar da ni? Yanayin yadda take magana har mamaki take bashi dan tana da saurin fahimtar abu saidai bai nuna mata mamakinshi ba yace hakane inda zaki amince kisanar da ni da naje ancire kud'ad'en kafin arufe account d'in. Kallonshi tayi a wulak'ance tace wannan ne bazai yuwu ba Barrister zanfi farin ciki ace sun rufe account d'in da dai ace kaine zaka ciro kud'in nan dan nasan kai zasu amfana. Maganata ta 'bata mashi rai sosai ahaka yatafi yabarni. Ya fad'a ma abokan nashi na k'i amincewa dan ina da wayo sosai koda k'arancin shekaru na, wanda yake jagoran su bayan tafiyar Alhaji Tanimu ne yazauna yatsara masu wata dubara inda suka samu wani k'wararre a wajen rubutu wanda yake da baiwa duk rubutun da yagani zai iya yin irinshi haka suka bashi irin rubutun mahaifina yayi masu, yarjejeniya ce suka rubuta akan wannan filayen da suke kawo min files d'insu insa hannu nak'i, sun kashe kud'ad'e sosai akan aikin inda Barr Muhsin yataimaka masu suka zauna har kotu akan cewa mahaifina ya siyar ma da Alhaji Tanimu filin kasancewar ansan Barr Muhsin shine lauyan mahaifina kuma ga sheda angani ta rubutu da komai yasa aka basu filayen sunyi farin ciki sosai da wannan nasarar da suka samu nan suka sanar da Alhaji Tanimu ta waya shi kuma yabasu dama da su saida ma gwamnati filayen biyu daman itace tabuk'aci hakan saboda filayen yana da girma sosai dan duk cikin filayen mahaifina babu me girmansu nan aka basu mak'udan kud'i sukaje suka raba a tsakaninsu. Dalilin mutuwar Barr Muhsin kuma ganin bai ci nasarar samun Pin d'in a wajena ba yasa yashirya yaje wajen boka yai mashi bayanin duk abinda yakeso nan bokan yabashi wani kwalli yace da ya shafa yazo wajena duk abinda yakeso zanyi mashi nan yayi ta murna har yayanke shawarar hatta babban account d'in Abbu sai yasa nayi mashi signing ya fitar da kud'i, toh akan hanyar shine tadawowa Ammi takasheshi acikin motarshi aka tsinci gawarshi, shine dalilin da yasa ake cewa shima ni nakasheshi dan kawai ya tsaya min.....tana zuwa nan a labarin sai ganin wata irin guguwa sukayi me k'arfi tana shigowa cikin d'an kurkukun d'akin ta k'aramar tagar nan cikin sauri jawahir tamik'e tatsaya gaban Barr Faruk, su dukansu idanu suka zuba ma guguwar har tagama shigowa nan tahad'e waje guda sai ga wannan tsohuwar ta bayyana, tana bayyana tabushe da dariya. Barr Faruk da mamaki yake kallonta tabbas itace wannan tsohuwar da yata'ba gani kuma itace yake yawan gani a mafarkin shi, muryar jawahir ce yaji ta ce Ammi menene dalilinki na zuwa nan a wannan lokacin? Ci gaba tayi da dariyarta marar dad'in saurare me kama da haniniyar doki saida tayi me isarta sannan tadogara sandarta tafara takowa ahankali inda suke tsaye jawahir saurin cewa tayi a'a kar kimatso nan kitsaya nan! Bata musaba taja tatsaya tana me kallon Barr Faruk da yake tsaye bayan Jawahir kamar wanda ruwa yacinunashi tayi da yatsa cikin shak'ak'k'ar murya da bata fita sosai tace kai kai kana shiga hurumina dayawa, ina gargad'inka da kadaina inko ba haka ba rayuwarka zata zama tarihi. Saurin tarar numfashinta jawahir tayi tace baidace kisake aikata kuskure ba a karo na biyu Ammi, shin shi kinga ya yi maki kama da mugayen mutane ne? Meyasa kin cika son kanki dayawa? Bushewa tayi da dariya akaro na biyu sannan tace tunda har ya iya zuwa yad'auko memory d'innan tabbas ya aikata kuskure sannan nice kad'ai nake da ikon iya fitar da ke daga gidan nan ammah sai kinyi nadamar maganarki. Cikin d'aga murya tace wannan ne kuma bazai ta'ba faruwa ba Ammi kece dai yakamata kiyi nadamar kashe yaya umar da kikayi!! Bushewa tasake yi da dariyar mugunta sannan tace kisanar da shi yayi gaugawar maida Memory Card d'innan dan wannan shine umurni na. Fitowa Barr Faruk yayi daga bayan Jawahir har ya bud'e baki zaiyi magana nan jawahir tayi mashi nuni da yayi shuru bai musaba yaja bakinshi yayi shuru, nan tsohuwar ta d'age kanta sama nan wani farin haske yabayyana wanda daga jawahir har Faruk idanunsu suka kasa jure kallon hasken dan kar yayi masu illa, su dukansu sukayi saurin runtse idanunsu har saida jawahir taji alamun bacewarta sannan tabud'e idanunta ajiyar zuciya tasafke tare da juyawa takalli Faruk da yabud'e idanunshi a daidai wannan lokacin tace yanzu aiki ya ganka sai ka yi da gaske sannan zaka iya tseratar da kanka daga Ammi daman wannan dalilin ne yasa tun farko nakasa fad'a maka komai dan nasan Ammi bazata ta'ba barinka cikin kwanciyar hankali ba ni kaina ba barina takeba kullum cikin azabtar da ni take. Faruk da yazuba mata idanu sai a lokacin yayi magana yace ammah jawahir meyasa take cutar da ke bayan da fari tana taimakonki, miyasa tabari har aka kawo ki nan gidan kaso kina rayuwa marar 'yanci bayan ta san duk itace me laifi ba ke ba? Juyawa tayi takalli gefe d'aya tare da yin guntun murmushi sannan tace dalili d'aya ne yasa duk take min haka ba wai komai bane sai dan kawai na furta mata kalmar tsana sannan nanuna inaso tarabu da ni ammah a maimakon tarabu da ni shine take wahalar da ni, nikuma hankalina baya kwanciya idan har tana cigaba da kasancewa tare da ni domin gani nake duk wanda yara'beni sai ta ga bayanshi, haka taso taga bayan wata ma'aikaciyar gidan nan akan matsa ma rayuwata da tayi saida nayi mata dagaske nanuna zan kashe kaina idan har tayi mata wani abu sannan tafasa saidai duk da haka saida tatsorata ta, taimako guda ne kawai nake buk'ata daga Ammina shine kad'ai yasa nake buk'atar kasancewarta tare da ni, ina jin dad'in d'aukar fansar da take tayani bana nadamar wannan domin shine hukuncin da yadace da azzalumai irinsu Alhaji Tanimu, ko a yanzu haka aka kasheni bazan ta'ba nadama ba dan na cika burina saidai abinda ba a rasaba ammah in da so samune ace na cika gabad'aya burin nawa,,, rintse idanunta tayi wasu siraran hawaye suka gangaro mata. Faruk rasa abinda zaice mata yayi sunyi kusan minti biyar a haka sannan yace Jawahir kikwantar da hankalinki kamar yadda nayi maki alk'awali insha Allahu zan taimaka maki yanzu dai abu d'aya yarage kisanar da ni suwanene sauran mutanen da suke da hannu a mutuwar su Abbu insha Allahu ni kuma zanyi abinda yadace, sannan zanyi k'ok'arin had'a duk wata sheda waje guda kafin lokacin zaman k'arshe yayi a kotu ammah kafin nan ina zan samu Ummah? Sannan Megadin gidanku shima ina zan sameshi? Ahankali tabud'e idanunta tasafkesu akan fuskarshi sannan tace Ummah tana chan asibiti kwance saboda tashin hankalin da tashiga jininta ya hau sosai sannan ga mutuwar 'barin jikin dama da takamu da shi (paralyse), na ji ance har yanzu batasan inda hankalinta yakeba bata magana da kowa saidai tabi mutane da kallo. "Ammah toh wane asibiti ne aka kaita?" Girgiza kai tayi tace nima ban saniba kawai dai abinda nasani ina nan gidan kaso wani lokaci Ammi da tazo wajena nan take nuna min abinda yafaru na ga komai a cikin tafin hannunta Ummah tana kwance bata iya komai likitoci suna ta k'ok'ari akanta saidai har tsawon wannan lokacin bata san inda kanta yakeba, saidai duk wannan abun da nagani ban gane wane asibiti bane, sannan megadin gidan mu buzu ne ainafin shi d'an k'asar Nijar ne bayan faruwar haka yagudu yakoma gida bamu san inda yake zaune ba a chan, Alk'ali ma saida yanemi akawoshi kotu dan amsa wasu tambayoyi saidai akazo aka fad'a mashi ya gudu kuma hakan ya faru ne saboda tsananin tsoratar da yayi akan kisan da akayi ma mutanen gidan kar shima abun yashafeshi. Barr Faruk yace shikenan jawahir kikwantar da hankalinki ni na san yadda zanyi, zanje intattara duk wani bayanai da suke wajena saidai abu d'aya da ace zan sake samun wani abu da zai k'ara taimaka min da zanfi buk'atar hakan. Shuru jawahir tayi kamar me tunanin wani abu sai kuma chan tace akwai abu d'aya da zaka iya samu saidai samunshi kamar ba abune me sauk'i ba. Barr Faruk yace kar kidamu fad'a min shi koma menene zanyi bakin k'ok'ari kamar yadda na iya d'auko memory d'innan. Cikin sanyin jiki tace ba wai a wajen Ammi zaka same shi ba, wannan yana a gidan Alhaji Tanimu da ace kana da damar da zaka iya shiga gidan har d'akinshi da ka samo wayar Abba da take hannunshi dan a lokacin da aka kamani sunyi amfani da wani key da suka sata sun shiga gidanmu sun yaye duk dukiyar Abba da k'addarorin shi, hatta wayarshi ma tana wajen Alhaji Tanimu saboda duk wayar da Abba zaiyi da mutum tana recording din maganar da sukayi tsawon wani lokaci kafin voice d'in yagoge indai har ba shi Abba yagoge ba toh yana cikin wayar, har sai and'an kwana biyu sannan maganar take gogewa , sannan wayar da yake kiransu da itace a wajen Alhaji Tanimu, ahakane nake gani zaka iya samun duk wasu bayanai da kake nema saboda maganganun da sukayi yana ciki wannan dalilin ne yasa yad'auke wayar ya adanata a cikin gidanshi batare da sanin kowa ba wannan itace kad'ai zata taimaka maka kagane sauran mutanen da Abba yake tare da su. "Ammah jawahir wannan zai yi wuya gaskiya dan bana tunanin abu ne me sauk'i shiga cikin gidanshi har inje d'akinshi inyi bincike inma zan sanar da hukuma na tabbata babu wanda zai bani goyon bayan hakan gaskiya saidai kawai muyi hak'uri da wayar nan, toh ammah idan har sai cikinta zamu samu abinda muke buk'ata taya zamu iya hak'ura da ita?,,, kanshi ne yayi ma tambayar sai kuma yasafke ajiyar zuciya tare da kallon jawahir da tatsareshi da idanu yace bansan ta yadda zan iya shiga gidanba, ya kike gani ya dace? " Nima bansan yadda za'ayi ba saidai kawai ahak'ura" "A'a jawahir baza'a hak'ura ba zan je inyi tunani inga hanyar da yadace inbi dan inaso ingane ko suwanene suke da hannu a ciki kafin Amminki takashesu, bari intafi koma menene zaki ji ni zanyi k'ok'ari wajen ganin na samo mafita a cikin kwana biyu bazan dawo wajenki ba har sai na samo wayar na gane suwanene suke da hannu a ciki, saidai to wayar wace iri ce yadda zan ganeta?. Tsayawa tayi tana tunani sai chan tace fara ce zaka ganta a cikin wardrope d'inshi ta gefen dama daga chan k'asan kayanshi nan zaka ganta. Da mamaki yake kallontwa yace Jawahir duk ya akayi kika san wannan bayan ke kina nan cikin gidan kaso? Ko kema ba mutum bace! Murmushi tayi har saida hak'oranta suka bayyana sannan tace zan sanar da kai ammah ba yanzu ba, sannan ni mutum ce kamar kowa, kaje kawai ina maka fatan samun nasara. Juyawa yayi yatafi cikin sanyi jiki, daga nan office d'in Alhaji Mahadi yawuce yasameshi zaune ankawo mashi wasu mata sabbin zuwa guda biyu wad'anda suke da case na kashe mijinsu ganin Barr Faruk ya shigo yasa yace ma mataimakiyarshi atafi da su asasu cikin kurkukun d'akin nan k'arami wanda wasu mata ukku suke a cikin shi amsawa tayi nan taba wasu ma'aikata biyu umurni aka tafi da su. Bayan suk sun fita Alhaji Mahadi yace bismillah Barrister kazauna. Bai musaba yaja kujera yazauna. Kallonshi Alhaji Mahadi yayi yana murmushi yace ya dai barrister na ga duk ka yi sanyi dayawa ko duk case d'in jawahir d'inne yake gwagwata ka? Ajiyar zuciya yasafke yace ba ma haka ba abokina wani taimako nakeso DPO yayi min ammah ban san yanayin kirkin shi ba ko zai fahimci abinda nakeso. Indai akan Jawahir ne bazai ta'ba fahimta ba dan ka san laifin da aka kamata da shi, kuma indai DPO ne bana tunani zai amince maka koma menene dan yana da tsatstsauran ra'ayi da ganin shi wani ne, musamman ma da yaga yadda kuke 'yar tsama akan case d'in yarinyar nan. Ta'be baki Barr Faruk yayi yace koma menene dasannu zan wanke Jawahir daga zargin da ake mata. Toh Allah dai yataimaka. Ameen. _________ Abban Nasiba ne yashigo yasameta Zaune ta tisa waya a gaba tana kallo ta shagala da kallon wayar bata ji shigowar mahaifinta ba, Alhaji Sufyan matsowa yayi idanuwanshi akan wayarta suka safka, girgiza kai yayi yace Nasiba har yanzu dai kina nan akan bakanki bazaki iya daina tunanin Faruk ba, inbakayi wasa ba sai na k'wace wayar nan tunda hotunanshi kike kallo a cikinta. Saurin janye wayar tayi takifata a jikinta sannan tatashi zaune tare da sadda kanta k'asa. Cigaba yayi da cewa kikwantar da hankalinki indai Faruk rabonki ne zaki sameshi kidaina sa damuwa a ranki kar kija ma kanki wani ciwon shi yana chan baima san kina yi ba. 'Dagowa tayi takalleshi tace toh Daddy insha Allahu zan kiyaye. Amsawa yayi da yauwa 'yar lele haka nake son ji, tashi kije kikira min Hajiyarki sannan kije dining ga icecream chan na sawo maki dan nasan kina sonshi sosai. Murmushi tayi tace toh Daddy nan tamik'e tatafi. Bin ta yayi da kallo tare da girgiza kai yazauna saman kujera sannan yace Allah yakyauta. _Sis Nerja'art✍🏻_[7/24, 11:13 PM] Sis Nerja'art 2: *......FANSAR RAI......* *INTELLIGENT WRITER'S ASSO....®* [On Award Together] _Follow me on Wattpad: *Sis-nerja*_ _Wannan Littafin na kud'i ne domin karantawa cikin aminci da yarda ga duk me buk'ata zai turo katin Mtn na d'ari biyu N200 kacal ta wannan number d'in 09035938246, ko ta account number 5330055604, Idan katura ka aiko da screen shot na transaction a wannan number d'in 09035938246_ _Akwai gara'basar *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shahararriyar marubuciyar nan *AMEENA ABBA UMAR* tare da novel d'in *FANSAR RAI* akan farashin N300 kacal, ko da kud'in ka sai da rabonka_ *PAGE 11* Tsawon kwana biyu Barr Faruk yad'auka yana tunanin hanyar da zaibi yashiga gidan Alhaji Tanimu har yasamu damar zuwa d'akinshi yad'auko wayar saidai babu hanyar da yaga zata 'bule mashi dan ranar sadakar ukku ma saida yaje gidan da sunan gaisuwa yaje masu hatta parlorn Alhaji Tanimi ya shiga yai ma 'yan uwanshi gaisuwa dan a cikin parlorn wasunsu suka zauna saidai hankalinshi ba k'aramin tashi yayi ba nan yasare yasan hakan saidai a mafarki zai iya faruwa. A gefe d'aya ga Ammin Jawahir da tatakura mashi dan kusan kullum sai ya yi mafarki da ita ko kuma cikin dare tatasheshi daga bacci ayi ta tsorata shi. Yau ma bayan ya gama had'a bayanenshi wajen k'arfe sha biyun dare ya gama shirin kwanciyarshi har ya kwanta nan ya fara jiyo motsi kamar ana hawan step, ana kiran sunanshi tashi yayi zaune cikin ranshi yace tabbas nasan itace , jiyayi ana cigaba da hawa babu k'ak'k'autawa yanayin yadda ake taka benen kamar irin ansa takalmi masu tsini, sai ji yayi anfara k'wank'wasa mashi k'ofa, magana yafara jiyowa kamar ta mahaifinshi yana tambaya wanene nan? Cikin sauri Faruk yamik'e yaje yabud'e ammah baiga kowaba dan haka yafita sai ganin Dad d'inshi yayi tsaye a chan wajen part d'insu gaban Faruk saida yafad'i ahankali yace ba dai tado su Dad tayi ba, muryar Dad yaji yana cewa Faruk wanene yake k'wank'wasa k'ofa na fito zan d'auki ruwa marassa sanyi dan na cikin freezer d'in part d'ina duk sunyi sanyi shine naji kamar ana knocking d'in k'ofa. "Dad babu kowa nima ruwan nafito ind'auka ammah banji k'arar k'omai ba",, Cewar Faruk. Tsayawa Dad yayi yana kallonshi yace yanzu kai baka ji ba? Ni na jiyo ana kwank'wasawa kamar ma ta part d'inka. Murmushi Yayi yace Dad ka fara tsufa ne saisa kaji haka nidai da nake sabon jini ban jiyowa. Girgiza kai Dad yayi yana murmushi yace kai ko faruk shikenan dai yanzu koma kakwanta k'arfe d'aya ta yi. " Toh Dad kaje kakwanta bari inje ind'auko ruwan ammah dan Allah kadaina fitowa a wannan lokacin kaga darene". Shikenan Faruk zan daina nima dai saboda k'ishin da nakeji yasa nafito ammah zan daina, je kad'auko ruwan bari intafi sai dasafe. Yauwa Dad Allah yakaimu. Saida yaga shigewar Dad sannan yafara safka daga saman step d'in ahankali yana lek'awa yaga ko zaiganta ammah baiga kowaba har yaje wajen fridge sai kuma yafara jiyo motsi achan tsakar gida har zai je yabud'e k'ofa yafita sai kuma yafasa dan ya san da ya bud'e sai su Dad sun jiyo kuma sai sun fito dan haka kawai yajuya zai koma part d'inshi sai jin k'ara yayi wajen kunnenshi wani irin shuuuuu kamar wucewar iska anbi ta bayanshi. Juyawa yayi saurin yi tare da cewa wanene? Koma waye yabayya kanshi!! Shurun da yaji anyi yasa yajuya yacigaba da tafiyarshi. Yana zuwa part d'inshi shiga yayi batare da ya murza key ba yawuce yanufi bedroom tun kan yashiga sai ji yayi k'ofar parlor d'in da yarufe ta bud'e kanta da k'arfi, juyawa yayi cikin 'bacin rai yace koma wanene yabayyana kanshi mana, shuru yaji dan haka yaje yayi bismillah yarufe k'ofar sannan yaje yashiga bedroom d'inshi, yana shiga hasken d'akin yad'auke daidai da ya rufe k'ofa, jingine jikinshi yayi da k'ofar ahankali yafara karanto addu'o'i, muryace yafara jiyowa daga wajen gadon shi tana tashi da k'arfi ana cewa barka da wannan lokacin Barr Faruk. Cikin dakiya da nuna rashin tsoro yace koma wacece na ce ya kamata tabayyana kanta. Dariya yaji an bushe da ita kamar irin haniniyar dokin nan saboda k'arfin dariyar har saida yayi saurin toshe kunnuwanshi saida yatabbatar da dariyar ta lafa sannan yasaki kunnuwan tare da cewa wannan alama ce ta matsoraci duk jarumi bayyana kanshi yakeyi, na san kece Ammin Jawahir shin menene yakawoki wajena ko nima d'in kinzo ne dan kiga bayana? Tun kan yarufe baki yaji wata irin murya me tsoratarwa cikin k'araji tana cewa da ace kana da hannu a ciki da sai na ga bayanka a yanzun nan, sannan ni ce kad'ai yakamata intaimaka ma jawahir tabar gidan nan aduk lokacin da naso, ikona ne wannan ba naka ba saidai jawahir tana da taurin kai sosai ta kasa yin nadama akan kalmar tsanar da tajefeni da ita, kai d'in kuma baka burgeni koda kana k'ok'ari wajen ganin ka taimaki d'iyata dan haka ina gargad'inka da kayi baya daga case d'in nan, wannan shine kad'ai abinda yakawoni wajenka,,, tana fad'in haka sai ji yayi shuru nan hasken d'akin yadawo. Murmushi yayi ahankali yace wannan ne kuma bazai yuwu ba dan ni nasa kaina kuma babu wanda ya isa yasani injanye ban damu da koma wacece ke ba dan baki gabana da mutane irina nake da lokacin jayayya,,, wucewa yayi yadudduba ko'ina bai gantaba dan haka yaje yahau gado tare da yin addu'o'i yakwanta ko kad'an tsoro bai d'arsu cikin ranshi ba dan ya san addu'a itace takobin mumini, saidai tunda yakwanta bai samu yarintsa ba kamar kullum yana ta tunanin mafita har wajen k'arfe hud'u sannan yad'an samu bacci kafin daga bisani yatashi lokacin sallar asuba. Hankalinshi k'in kwanciya yayi ganin kwanaki goma ne kawai suka rage mashi wata dabara ce tafad'o mashi dan haka bayan ya yi breakfast yakira wani abokinshi Barr Nas a waya tare suka yi karatu har wajen aikinsu d'aya lokacin da yake aiki a SHARI'A COURT abokai ne sosai dan koda a yanzu ba wajen aikinsu d'aya ba suna tare, bayan sun gaisa ne yatambayeshi inda zai sameshi yafad'a mashi kasancewar weekend ne babu aiki, shiryawa yayi yad'auki system d'inshi da komai wanda zai buk'ata yashiga motar shi yanufi gidan Barr Nas yana isa daidai lokacin shima yashawo kwana Barr Faruk tsayawa yayi har saida ya iso da motarshi nan yafito yanufo wajen Faruk yana murmushi yace Barrister kace dai dagaske kake zaka zo. Hmm dole kace haka tunda ka san baka gidan kaja nazo ashe da saidai inkoma. "A'a Wallahi ban dad'e da fitaba na kai Madam gidane ina safketa najuyo dan kar kazo ban nan, yanzu dai mushiga da mota ciki. Barr Faruk ba tare da ya ce komai ba yatada motar shi, saida Barr Nas yashiga tashi motar yayi horn megadi yabud'e masu gate sannan suka shiga da motocin, bayan sunyi parking ne suka nufi parlorn gidan Barr Nas yana cewa yau dai kamar a mafarki sai gaka a gidana ina ji rabon da kazo tun bikkina. "Toh ka dai san yanayin aikin mu bamuda lokacin zama bare har inzo gidanka, yanzu ma haka akan aikine yasa kaganni" Hmm nasan haka kai kullum da aiki kake fakewa, malam muma fa duk aikin nan muke irin naka ammah a haka muna samun lokacin ziyara kai ko kullum saidai kabada wani uzuri, ko dai Nasiba ce take 'boye mana kai tun ba'ayi bikkin ba? Murmushi yayi jin an ambaci sunan abun son shi saidai a ranshi yana tunowa da wani abu yasafke ajiyar zuciya yace Nasir muyi maganar da takawoni wajen ka. Toh shikenan Barr ina saurarenka. Barr Faruk yace daman wani taimako ne nakeso kayi min dan nasan kaine kad'ai zaka iya yimin yadda nakeso, Gyara zamanshi yayi yace wani irin taimako ne wannan koma wane iri ne kafad'a zanyi maka indai baifi k'arfina ba koda ma ya fi zansan yadda zanyi intaimakeka. Murmushi yayi sannan yace ranar sadakar ukku watau jiya na ga motarka ka fita daga gidan marigayi Alhaji Tanimu Nepa ni kuma lokacin nashiga gidan zanyi masu gaisuwa, shine nakeso inji ya kake da shi daman ka sanshi? Allah Sarki ai Alhaji Tanimu Mahaifin abokina ne Nazir tare mukayi secondary school da shi muna mutunci sosai da shi, shi naje ma gaisuwa dan kusan tun ranar da akayi rasuwar kullum sai na je. Wani irin sanyi Faruk yaji a ranshi har saida farin ciki yabayyana a fuskarshi Alhankili yafurta Alhamdulillah. Da mamaki Barr Nas yake kallonshi yace lafiya Barrister me yafaru naga kana fara'a? Lafiya lau Nasir na ji dad'i sosai da jin bayananka a yanzu ina da k'warin gwiwar samun abinda nakeso watau wani case ne me zafi mukeyi shine nake son kataimaka min a ciki kayi min jagorar zuwa gidanshi. Cike da mamaki yace case kuma? Wane irin case ne haka? Ko akan kisan da ake zargin anyi mashi dan naji anata jitajitar kasheshi akayi saidai anrasa wanda yayi kisan dan ajiya ma aka sako driver d'inshi an wankeshi daga zargin da ake mashi, saidai har yau anrasa wanda yayi kisan ana tadai bincike ankasa samun k'wak'k'warar shaida za'a iya kama wanda yayi laifin. Tsayawa yayi yana saurarenshi har yakai aya nan yarasa me zaice tunani yafara yi yasanar da shi komai akan case d'in jawahir ko kuma yayi shuru abunshi,, Muryarshi yace yaji ya ce ya dai Barrister ka yi shuru lafiya dai ko? Girgiza kai yayi yace babu komai saidai kawai.....shuru yayi batare da ya k'arasa fad'in kalmar da take bakinshi ba. Ganin haka ya Barr Nas yatashi yakoma kusa da Barr Faruk bisa 2 seater d'in da yake zaune sannan yace Faruk kayi min bayanin koma menene zan fahimceka kuma zan taimaka maka saboda ka cancanci haka. Har cikin ranshi ya ji dad'in bayanin abokin nashi sosai kuma ya san tunda har yafurta toh zai taimaka mashi dan tun a makaranta baya da aboki kamarshi da Barr Junaid dan duk tare sukayi karatu har gama makarantar su sannan wajen aiki d'aya saidai Barr Junaid ne kawai a lokacin baiyi zurfin karatu kamar nasuba dan shi daga HND yatsaya su kuma har masters sunyi saisa sukafi shak'uwa da Barr Nasir sai daga baya ne dayakoma a kotun da Barr Junaid yake aikine abotarsu tak'ara k'arfi,,, jijjigashi Barr Nas yayi yace wai lafiyarka Faruk sai wasu tunane tunane kakeyi ya kamata kanutsu kafad'a min koma menene. Shikenan Nasir zan sanar da kai komai yanzu nasan zaka taimaka min, bayan na baro court d'inku anmaidoni a nan HIGH COURT shine natarar ana wani case wanda bayan rasuwar lauyan da yake jagorantar case d'in yake kare wadda ake k'ara shine ni kuma na amshi case d'in yadawo hannu na dan kare wadda ake k'arar a lokacin da na lura tana buk'atar taimako ana nema atauye mata hak'k'i mutane da dama sun nemi su fahimtar da ni had'arin da yake cikin case d'in ammah ni duk wannan bai dameniba burina d'aya shine inwanke wadda ake k'arar a idanun duniya........ Kwashe komai yayi akan case d'in Jawahir yafad'a mashi saidai ya 'boye mashi gaskiya a game da Fatalwar da ke tare da jawahir har tsorata shi da ake babu abinda yafad'a mashi. Hankalin Barr Nas ya tashi sosai da yaji labarin saidai bai katseshi ba har saida yagama fad'a mashi komai sannan yace tabbas naji labarin case d'innan ko ba ita bace Jawahir Muhammad? wadda tayi kisa har takashe lauyoyinta saidai na ji labarin ya d'an sha banban da wanda kabani ammah tabbas ina tunanin itace. Eh itace saidai abinda aka fad'a ba gaskiya bane Nasir ni kaina ina neman hujjojin da zan tabbatar ma mutane da haka saisa a yanzu haka nakeso kayi min jagora zuwa gidan Alhaji Tanimu dan akwai abinda nakeso ind'auko. Tun kan yarufe baki cikin sauri Barr Nasir yamik'e tsaye yace ka san abinda kake fad'a kuwa Barrister? Taya kake tunanin zamu iya shiga gidan Alhaji Tanimu har wai kad'auko wani abu a d'akinshi batare da sanin kowa ba, ka san dai za'a iya kamamu idan har kuma hakan yafaru har kotu za'a banka mu sannan kisan da ake cewa anyi mashi mu za'a ce mun kasheshi gaskiya hakan bazai yuwuba kama daina wannan tunanin. Shima mik'ewa yayi cikin sanyin jiki yace Nasir kar kadamu insha Allahu babu abinda zai faru zanyi k'ok'ari wajen ganin na yi komai batare da angane mu ba. Cikin karaya Barr Nasir yace Faruk anya hakan zai yuwu da dai ka hak'ura kawai. "Nasir kadaina cewa haka na yi maka alk'awari babu abinda zai sameka koma menene yafaru bazan ta'ba bari asakaka cikiba laifin gabad'aya nawa ne wannan alk'awarine nayi maka. Ganin yadda yanace yasa Nasir ya amince sutafi, nan suka zauna yana cigaba da tayashi aikin da yake a nan sukayi azuhur yaba megadin shi kud'i yayo masu takeaway suka ci dan matarshi sai marece zata dawo. Bayan sunyi sallar la'asar ne suka kama hanyar gidan Alhaji Tanimu inda gabad'ayansu zuciyoyinsu babu dad'i jikinsu ya yi sanyi sosai saboda basusan abinda zasu tarar ba idan sukaje, Barr Nas yake driving inda Barr Faruk yake zaune gefenshi yana ta sak'e-sak'e cikin ranshi har suka isa gidan suna zuwa aka hangame masu tankamemen gate d'in gidan suka cinna kan motar su a ciki, Motocine sosai a parking space dan haka suka samu waje su ma suka ajiye tasu motar. Barr Nas juyowa yayi yakalli Faruk yace Barrister wallahi ina jin tsoro sosai taya kake ganin shiga d'akin Alhaji tanimu zai yi mana sauk'i bayan akwai mutane sosai a cikin gidan. Ajiyar zuciya yasafke yace nima ina tunanin haka Nasir saidai banda yadda zanyi tunda tun farko ni nayi ma yarinyar alk'awari zan taimaka mata kuma dole sai na samo wayar itace zata taimaka min nan da kwana goma inku'butar da jawahir dan da kwanaki goman nan sun shud'e na tabba za'a yanke mata hukuncin kisa dan wannan zaman shine zama na k'arshe da za'ayi, mushiga kawai in gwada sa'a ta. Ammah ta ya kake tunanin zamu iya shiga cikin gidanshi har d'akin shi? "Kar kadamu da wannan ni zan shiga ba kai ba bazan sakaka cikiba Nasir koma menene zai faru saidai yafaru da ni kad'ai yanzu fito mushiga ciki muyi masu gaisuwa dan inga yanayin mutanen da suke ciki. Ajere suka tafi suna tsayawa suna gaisawa da jama'ar da suke zaune saman tabarma har suka shiga setting room d'in gidan inda dangin mamacin suke zaune suna amsar gaisuwa bayan sun gaisa sunyi masu gaisuwa Nasir yaduk'o da kanshi saitin fuskar Faruk ahankali yace banga Nazir ba ina tunani baya nan ammah bari intambaya, matsawa yayi kusa da k'anen Nazir da yake zaune chan k'arshen bango yatambayeshi inda Nazir yake yace mashi yana cikin gida dan haka suka tashi suka shiga koda matane a ciki ammah ahaka sukayi ta ratsawa suna gaishesu har suka shiga babban parlor inda suka samu matan mamacin zaune da mutanensu, gaishesu sukayi sannan Nasir yatambayi mahaifiyar Nazir inda Nazir yake tace yana chan part d'in Abbansu ya yi wasu bak'i kuje chan kusameshi kuce na ce ina jiranshi yakawo min keys d'in part d'in. Barr Faruk kallon Nasir Yayi yai murmushi irin na da alama zamuyi nasara, girgiza kai Nasir yayi alamun a'a sannan suka mik'e suka nufi part d'in da yake mallakin megidan. Tun da suka tunkari hanyar part d'in suka fara jiyo hayani alamun ana labari haka suka isa suna shiga suka tarar da su tsaisaye alamun tafiya zasuyi Nazir yana ganinsu yace A'a Barrister sannunku da zuwa. Hannu suka mik'a masu duk aka gaisa sannan suka k'ara yi mashi gaisuwa. Mutane ukkun nan da suke tsaye ne sukace mu zamu wuce Allah yajik'anshi yace toh nagode muje inrakaku, kallon su Barr Faruk yayi yace dan Allah kuzauna ina zuwa bari indawo. abu daman ga wad'anda suke nema dan haka suka zauna haka yafita da abokanshi dan yarakasu. Barr Faruk kallon Nas yayi cikin sanyin jiki yace ban san ta inda zan faraba barrister ammah bari infara ta'ba bedroom d'in inji idan bud'e yake, Barr Nas da yanuna alamun tsorata yace a'a Barrister kar fa ashigo aganka. Batare da ya ce komai ba yamik'e cikin sauri yanufi hanyar da zata sadaka da bedroom d'in yana zuwa yamurd'a k'ofar yaji datse take gam nan fa duk yaji ba dad'i yadawo yazauna tare da dafe kai yace hakan bazai ta'ba yuwuwa ba nasan bazan yi nasara ba Nasir. Ajiyar zuciya Nas yasafke yace kakwantar da hankalinka Faruk ko ma ba ta wannan hanyar ba insha Allahu zaka samu k'wak'warar shedar da zaka bayar. Yana bud'e baki zaiyi magana suka jiyo taku alamun an nufo d'akin dan haka sukayi shuru sai ga Nazir ya shigo fuskarshi d'auke da murmushi yace kuyi hak'uri na barku ku kad'ai, wallahi abokaina ne da mukayi karatu da su a London Sukace Allah sarki a'a babu komai, zama yayi yana kallon Barr Faruk yace kaima Barrister d'inne irin Nas ko?. Murmushi yayi yace a'a shi dai ne lauya. "Ayyah Allah sarki aini tun farko mancewa nayi da abokina babban lauya ne da shi zan saka acikin case d'in kisan da akayi ma mahaifina dan ak'wato mana hak'k'inmu. Barr Faruk kallon Barr Nas yayi da shima yake kallonshi su dukansu sukayi shuru aka rasa wanda zaiyi magana daidai lokacin akayi sallama aka shigo su dukansu suka juya suka kalli k'ofa tare da amsawa wata dattijuwa ce tashigo nan duk suka gaisheta bayan ta amsa ne tace Nazir ina key d'in bedroom d'in Abbanku zamu d'auko sauran lemuna a ciki. Aunty Amina kinsan dai anhana bud'ewa nima kaina dak'yar nasamu Ummah tabani key d'in nashigo parlor. Harararshi tayi tace kai ni dallah bani ind'auko abinda zan d'auko sai inmaido maka kayi ta tseguminka saikace wata uwa abu zan d'auka a ciki. Ganin yadda tafara d'aga murya tana fad'a yasa yaciro keys d'in acikin aljihu yamik'a mata amsawa tayi taje tabud'e tashiga. Barr Faruk kallon kallo suka fara da Barr Nas sai kuma suka maida hankalinsu ga k'ofar bedroom d'in da tabud'e, Faruk ji yake kamar yayi tsalle yashige saidai hakan bazai ta'ba yuwuwa suna kallo tagama d'auko lemunan tarufe d'akin tamik'o ma Nazir key d'in, sannan tafara jidar lemunan tana fita da su. Nazir a gefen da yake zaune ya d'age wani throw pillow ya ajiye Keys d'in a wajen yace muma ai yanzu zamu fita tun kan azo afara yi mana surutu tace da dai ya fi maku. Faruk yana kallo nan ya ida sarewa yatabbatar bazai samu yadda yake so ba. Bayan ta fita nan Barr Nas da Nazir suka fara hira inda shi kuma Barr Faruk yayi shuru abin duniya duk ya isheshi, Nazir bai damu da shurun da yayi ba dan yana ganin yanayinshi yagane shi d'in ba mutum bane me son hayaniya sosai ba, suna cikin hirar nan wayar Nazir tafara ringing d'aukowa yayi yai picking tare da yin sallama, basuji abinda akace mashi ba saidai ji sukayi yana cewa toh shikenan Kawu ganinan zuwa ai dama ina cikin gidan bari infito, kashe wayar yayi yakallesu yace bari ind'anje indawo wasu abokan Abba sukazo mana gaisuwa daga Kaduna, ajiyar zuciya Barr Faruk yasafke kafin Nas yayi magana shi yayi saurin cewa Allah Sarki toh shikenan babu damuwa sai ka dawo. Nas dai murmushi yayi dan ya san dalilin Faruk na cewa haka. Mik'ewa Nazir yayi yafita lokacin da aka sake kiranshi waya, yana barin d'akin cikin sauri Faruk yamik'e yanufi wajen kujerar da yazauna yana zuwa yahankad'e pillow yad'auko keys d'in wani irin farin ciki yaji a ranshi yajuya yakalli Nas da yakeyi mashi kallon mamaki ganin babu wani alamun tsoro a tare da shi har ya iya d'aukar key d'in, murmushi yasakar mashi tare da cewa ina zuwa bari inyi sauri inje ind'auko bazan 'bata lokaci ba. Cikin sanyin jiki yace a'a Faruk ina jin tsoro. Batare da ya tanka shi ba yawuce yanufi hanyar Bedroom d'in yana zuwa yasa key d'in da yaga Nazir ya nuna ma matar nan, yana murzawa sai ga k'ofa ta bud'e juyowa yayi yakalli Barr Nas da yagama tsorata sannan yazare key d'in yashiga cikin bedroom d'in yamaida k'ofa yarufe, tsaye yayi a bakin k'ofar yana bin d'akin da kallo komai na ciki ya ji sosai za'a iya cewa aljannar duniya kenan, ta'be baki Faruk yayi sannan cikin sauri yanufi wajen wardrobe d'in yana zuwa baiyi wata wata ba yabud'e yafara bincike cikin sauri dubawa yadinga yi ammah baiji wayar ba saida yaduba kusan sau ukku baiga komai ba nan hankalinshi yafara tashi yace shikenan and'auketa daga wajen toh ammah tana ina? Ko dai Jawahir batasan inda takeba daman haka nan tace min tana cikin wardrobe d'inshi?. Tsaye yayi wajen, jikinshi duk ya yi sanyi sosai chan kuma yatuna da irin matsalar da zai shiga dan haka yajuyo cikin sauri zai fito yabar d'akin. Nas da yake zaune tsoro duk ya gama cikashi Allah Allah kawai yake Faruk yafito kafin dawowar Nazir yana cikin haka kawai sai jiyo muryar Nazir yayi ya tunkaro d'akin yana waya yana cewa shikenan Ummah ganinan yamzu zan kawo maki keys d'in daman sun tafi yanzu ina tare da su Nas ne kuma shi dai d'an gidane babu damuwa sai mufito mukoma setting room..... _Sis Nerja'art✍🏻_ [7/24, 11:13 PM] Sis Nerja'art 2: *......FANSAR RAI......* *INTELLIGENT WRITER'S ASSO....®* [On Award Together] _Follow me on Wattpad: *Sis-nerja*_ _Wannan Littafin na kud'i ne domin karantawa cikin aminci da yarda ga duk me buk'ata zai turo katin Mtn na d'ari biyu N200 kacal ta wannan number d'in 09035938246, ko ta account number 5330055604, Idan katura ka aiko da screen shot na transaction a wannan number d'in 09035938246_ _Akwai gara'basar *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shahararriyar marubuciyar nan *AMEENA ABBA UMAR* tare da novel d'in *FANSAR RAI* akan farashin N300 kacal, ko da kud'in ka sai da rabonka_ *PAGE 12* Barr Nas da yake zaune tsoro duk ya gama cikashi Allah Allah kawai yake Faruk yafito kafin dawowar Nazir yana cikin haka kawai sai jiyo muryar Nazir yayi ya tunkaro d'akin yana waya yana cewa shikenan Ummah ganinan yanzu zan kawo maki keys d'in daman sun tafi yanzu ina tare da su Nas ne kuma shi dai d'an gidane babu damuwa sai mukoma setting room. Wayyoooo kar kuso kuga Nas a lokacin zufa ce tafara kwarara daga jikinshi yana jin kamar yanutse cikin kujera, tsoro da fargaba duk suka d'arsu a cikin zuciyarshi, Nazir na gama wayar ya ida shigowa cikin d'akin yana shigowa yakalleshi yace ya naga kana zufa? Sorry bari ak'ara Ac d'in daman d'azu muka rageta. Shi dai da idanu yabishi kawai cikin ranshi yana cewa shikenan Faruk ya ja min, muryar Nazir yajiyo yana cewa ina abokin naka ba dai ya tafi ba? Dabarbarcewa yayi yarasa abinda zaice sai chan cikin rawan murya yace am ya je waje zai amsa waya ne. Toh shikenan bari mujira yadawo sai mukoma chan setting room ko kuma mutafi muhad'e da shi dan Ummah ta fara fad'a wai inkawo mata key d'in d'akin Abba saboda ba'a so ana shigowa yanzu za'a fara surutu. 'Yan cikin Nas saida suka kad'a yarasa abinda zaice ma Nazir sai chan cikin dauriya yace Nazir ko zaka taimaka min da ruwa insha kafin yadawo kaga kar mufita yadawo kuma bamu nan baisan inda muka nufa ba. Mik'ewa Nazir yayi yace hakane kuma bari inje inkawo maka ruwan dan na nan ciki basuda sanyi inyaso in nagamu da shi sai infad'a mashi. 'Daga kai kawai yayi dan baya ji a yanzu zai iya magana saboda tsananin tsoron da yashiga juyawa Nazir yayi yafita dan samo ma abokin nashi ruwa. Yana fita Nas yana son yamik'e ammah yakasa jikinshi ssi rawa yake yana nan zaune sai ga Faruk ya fito yana fitowa cikin sauri yarufe d'alkin, jin motsin tafiya yasa yawurgo ma Nas key d'in yayi saurin juyawa tare da kanga wayarshi a kunne kamar yana waya. Nas tura key d'in yayi a k'ark'ashin throw pillow d'in da Nazir ya ajiye key d'in daidai lokacin Nazir yashigo yana cewa na sa yanzu za'a kawo maka. Ajiyar zuciya Nas yasafke ganin asirinsu bai tonuba. Nazir kallon Faruk yayi da yajuya yana waya yace ashe ya dawo ai da nafita ban ganshiba. Murmushi Nas yayi yace Eh kana fita yadawo kuma aka sake kiranshi waya shine yamatsa chan yana yi. Nazir yace Allah sarki yanzu kuzo mukoma setting room na san sun ragu gashi fitarnan da nayi andameni infito inrufo d'akin. Murmushi Nas yayi yace haba ba damuwa ai mu ba bak'i bane, daidai lokacin Faruk yajuyo yana murmushi yace bakomai ai yanzu ma zamu tafi dan daga wajen aiki ake min neman gaggawa. Nazir yace tun yanzu maimakon kubari sai anjima. Kar kadamu muma munso mubari sai da anjima dan dai kiran gaggawar da akayi min ammah zamu dawo wani lokacin. 'Dauko key d'in Nazir yayi yace toh shikenan sai mufita gabad'aya in mik'a masu key d'in inhuta. Faruk yana lura da Nas da yake ta yi mashi kallon tuhuma ammah yak'i kulashi ahaka har suka fita. Saida suka jirashi yafara mik'a key d'in wa Ummanshi sannan suka tafi yarakasu har wajen mota yayi masu godiya suka shiga suka tafi, suna fara tafiya Nas yajuyo yakalleshi yace wai ya dai Faruk sai alama nake ta tambaya kuma ka gane nufina ammah kashareni wallahi hankalina ya tashi sosai Allah ya taimaka guy d'in nan bai gane komai ba. Murmushi Faruk yayi yace daman ya gane da kai zaka fi kwana ciki tunda abokinka ne. Au haka ma kace ko? "Toh me kakeso ince? Yanzu dai fad'a min shin ka d'auko wayar ko kuwa hakanan kafito baka gantaba? Murmushi yayi yace Eh toh banga wayar ba. Kana nufin baka gantaba hakanan kafito?,, Nas yatambayeshi cike da mamaki. Juyawa yayi yakalli taga sannan yace ina nufin ban gantaba a inda jawahir ta fad'a min saidai na ganta a wani wajen na daban. Ajiyar zuciya Barr Nas yasafke yace Alhamdulillah na ji dad'in haka gaskiya Barrister kai d'in nadaban ne saisa ko a school nake jinjina maka dan k'walwarka tana ja sosai. Juyowa Faruk yayi yakalleshi tare da fiddo wayar daga cikin aljihunshi yana murmushi yace tabbas ina farin ciki Nas ko ba komai wayar nan zata taimaka min wajen samun duk wani abu da nakeso, yanzu dai mu wuce gidana kasafkeni dan ko motsta bazan d'auko gidanka ba. Kallonshi Nas yayi yace ban gane insafkeka ba malam, muje dai ind'auko su Madam inmaidasu gida inyaso kaga sai muwuce gidan naka ko ba haka ba? Hakan ya yi abokina ai duk yadda kakeso haka za'ayi dan yau ba k'aramin taimako kayi min ba. " yoh ba dolena intaimakeka ba tunda nima ka taimaka min wajen samo soyayyar madam a school" Su dukansu dariya sukasa nan Faruk yagirgiza kai tare da juyawa yana cigaba da kallon taga. Bayan sunyi sallar magrib a cikin anguwarsu Faruk sannan suka wuce gidanshi a parlor suka zauna Faruk yaso yakunna wayar ammah yajita a kashe alamun ba charge dan haka yatashi yajonata sunayin sallar isha'i Barr Nas yace shi zai wuce gida koma menene inyaso gobe zasu had'u. Barr Faruk yace babu damuwa nan yarakashi har wajen mota yana tsokanarshi tashin hankalin da yaga ya shiga lokacin da yafito cikin d'akin. Barr Nas yana dariya yace ka ma yi sa'a da bakaga na saki zawo ba dan wallahi har na hango makomata gaskiya na yi kasada dayawa Allah dai ne yacecemu. Hakane Nas ni fa daman kai nafi ji ba kainaba dan banaso inja maka wani abu yasameka. Hmm toh yanzu ya za'ayi idan zaka maida wayar? Barr Faruk yace a'a bazan maidata ba tunda shima ba tashi bace idan nagama bincikena zansan yadda zanyi da ita. Toh shikenan Barrister Allah dai yataimaka sai dai goben idan na shigo. Toh Allah yakaimu. Bayan tafiyarshi Faruk wanka yayi yashirya wajen k'arfe tara yacire wayar daga charge yafara bincika abubuwan da suke cikinta ya samu shaidu sosai dan hatta recordings ya samu na wayar da akayi har da wanda alamu yanuna anyi recording antura ma wani ya saurara, wata murya da yaji anyi waya da me ita saida yaji kamar ya san muryar ammah yakasa tantanceta. Cikin contacts yashiga yafara binciken numbobin ciki nan yaci karo da number d'in da tad'aga mashi hankali saurin d'auko wayarshi yayi yasaka number d'in yayi dialing a nan ya ida tabbatarwa da tabbas number d'ince hankalinshi ba k'aramin tashi yayi ba, ajiye wayar yayi tare da dafe kanshi ji yayi komai ya tsaya mashi, chan kuma yamik'e yafara zagaye d'akin yana zuwa yana dawowa hannuwanshi suna a bayanshi ya rik'esu tunowa yafara yi da lokacin da jawahir take ce mashi zaka taimaka min kana nufin komai kusancinka da mutum idan har yana da hannu a ciki bazaka ta'ba barinshi ba? Cize le'be yayi a hankali sannan yakoma yazauna yak'ara d'auko number yasake dubawa tabbas idanunshi ba gizo sukeyi mashi ba toh ammah me hakan yake nufi kenan shima akwai hannuwanshi acikin mutuwar mahaifan Jawahir? A'a kodai abokinshi ne kawai ammah baida hannu acikin mutuwarsu, toh ammah call recording d'in da naji fa tabbas akwai na muryarshi ya ji shi, sake kunno recording d'in yayi yasaurara muryarce yaji tana cewa Hello kana jina ya kamata kayi k'ok'ari wajen ganin ka samo mana file d'in filin nan dan da alama zaiyi kud'i sosai ni na san yadda za'ayi asiyar da shi batare da kowa ya ganeba dan nima kaga wannan filin da kabarmin gwamnati nasiyar mawa kuma ta siya da kud'ad'e masu tsoka. Toh shikenan Alhaji koma me kenan nasan hanyar da zanbi insamo dan dama maganar da muka gama yi da Alhaji tanimu kenan dan shine jagoran komai, da ace akwai hanyar da zanbi da a yau d'innan sai naga bayan yarinyar nan kowa yahuta dan na san idan har tamutu dole abarmin gadonta gabad'aya tunda ni kad'ai ne d'an uwan mahaifinta,,, Cewar Alhaji Mu'azu. Daga chan 'bangaren dariya akayi akace kaidai kabi komai a hankali ko da baka kasheta ba zaka iya yin amfani da damarka wajen ganin mun samo dukiyar Alhaji Muhammad, inyaso idan har mun gama samun yadda mukeso zaka iya kasheta saidai kuma idan har zaka rufe ma mutane baki dan kar ayi zargin wani abu kamar yadda mukayi bayan munsa ankashe Alhaji Muhammad da matarshi. Dariya Alhaji Mu'azu yayi yace ai fiye da hakan ma zan iya sa wa ayi mata dan ni ban had'a komai da kud'iba abokina, yanzu dai zuwa anjima zan kiraka idan har nagama tattara bayanan filin inyaso sai muje musiyar da shi. Yauwa mutumina kayi k'ok'arin haka sai na ji daga gareka. Ana zuwa nan recording d'in yak'are. Wani kuma yasake kunnowa nan ma yaji muryar mutumin yana cewa, Hello Alhaji Mu'azu ina jinka d'azu ka kirani bana kusa. Eh Wallahi abokina cewa nayi ta samu fa a yanzu ga wani gida nan na Alhaji Muhammad da nagano yana da shi batare da sanin kowaba sai yanzu naga takardun gidan na je na ganshi kuma antabbatar min da nashine. Daga chan 'bangaren dariya akayi akace lallai Alhaji Muhammadu wayonshi ya yi yawa watau yana da gida batare da sanin ka ba, toh bari zan zo inje muga gidan idan har yana da girma sosai ni zan sayeshi dan dama inaso mutashi da iyalina daga nan, kace abu ya zo gidan sauk'i ai wallahi mutuwar nan tashi dad'i tayi min dan ko bakomai munsan muma mun mori dukiyarshi. Alhaji Mu'azu ma dariya yayi yace kaidai bari a yanzu gashinan ina ta facaka da kud'i yadda nakeso ba kamar lokacin da yake raye ba, ka san mutuwarshi ko kad'an bata d'aga min hankali ba sai waje d'aya lokacin da kabani layarnan insaka mashi a baki toh a nan ne nad'an tsorata dan ko da su Alhaji Mannir suka shigo gidan zasu kasheshi ban wani d'aga hankaliba dan na san zamuyi nasara. Katseshi yayi yace a'a Alhaji Mu'azu kayi shuru kar ajiyo ka asirinmu yatonu agane mune muka kasheshi abar maganar kawai zan zo yanzun nan muje inga gidan dan ka san bana wasa da kud'i,,, su dukansu dariya sukayi. Hakayayi ta kunno recording d'in me muryar yana saurare ________Yana gama sauraren recording d'in ajiyar zuciya yasafke tare da kwantar da kanshi saman gadon inda k'afafuwanshi suna a k'asa ahankali yace tabbas biri ya yi kama da mutum toh ammah ta wace hanya zanbi wajen ganin na kamasu da laifin da nake zarginsu, dan shi kad'ai ne yagane muryarshi bai gane muryoyin sauran da yaji ba saidai ya gane ta mutane biyar saboda sunansu da Alhaji Mu'azu yake ambata a cikin wayar saidai mutum biyu ne bai ganeba toh ammah su wanene? Shin suna raye ko su ma ankashesu? Kanshi ne yajefa ma tambayoyin. Kasa runtsawa yayi dan kwatakwata daman bai sa ma ranshi yin bacci a lokacin ba nan yayi kwance yana ta 'yan tunane tunane tare da neman hanyar da zai 'bullo wajen ganin ya kamashi da laifin da yake zarginshi da shi, tashi yayi yad'auko wayarshi yana tura duk recording d'in da yake so masu alak'a da case d'in ya dad'e yana turawa dan suna da yawa sosai saida yaza'bi iya wanda yakeso, a cikin kunnuwanshi akayi kiran sallar asuba. Wajen k'arfe goma yagama shirin shi yaje wajen aiki kasancewar litinin ce yana zaune yana aikinshi nan aka kirashi a waya dubawa yayi ganin private number ne yasa yashare baiyi picking ba wani kiran yasake shigowa a karo na biyu, tsaki yayi sannan yad'auko wayar zai kashe ta gabad'aya dan kar tahanashi yin aikinshi sai kuma yafasa yayi picking batare da yayi magana ba. Daga chan 'bangaren akace Hello kana ji? Shuru yayi yana sauraren muryar kamar ya ta'ba jinta k'ara jefo mashi tambaya akayi "wai ko ba Barr Faruk bane" Saurin d'ago wayar yayi daga kunnenshi yadanna inda zatayi mashi recording d'in maganar sannan yace Hello ina ji. Au daman kana ji shine zakayi shuru watau har rainin hankalinka ya kai ga haka,,, tsaki yaji anja sannan aka kashe wayar. Bai damu da hakan ba ya ajiye wayar yacigaba da aikinshi. Saida yatashi daga aiki sannan yaje yasamu Jawahir tana ganinshi murmushi tasakar mashi tace ina tayaka murna. Shima murmushin yayi yace murnar me kenan? "yanayinka da nagani ya sa na gane ka samo wayar" Matsowa yayi kusa da ita yace Eh hakane na samo kuma duk na saurara saidai mafi yawansu sun mutu dan naji maganarsu da sunan su da aka kira acikin recording d'in. Fara'ar da take fuskarta ce tagushe tace tabbas hakane duk sun mutu dan dama mutane takwas ne kuma a yanzu shidda daga cikinsu sun mutu, Yaya Aliyu baya cikinsu kawai dai Ammi ta d'auki fansar kasheta da yake da hannu a ciki da kuma niyarshi ta ganin bayana, Mijina Umar ma baya da hannu a ciki, su Abba da abokanshi ne. Jinjina kai yayi yace na fahimci haka Jawahir saidai akwai wani taimako da nakeso kiyi min. Taimako kuma? Wane irin taimako ne?,, tajefa mashi tambaya. "Kar kidamu yanzu zan sanar da ke koma menene..... _____________ Bayan kwana biyu Faruk yana kwance a d'akinshi Mom tashigo tasameshi zama tayi daga gefenshi tace ya dai Faruk ba dai tunani kake ba? Murmushi yayi tare da tashi zaune yace No Momcy bacci natashi ne. Ohk, ina fatan babu wata matsala. Kallon Mom d'in tashi yayi cike da k'aunarta dan ya san bata son ganinshi cikin kowace irin matsala, girgiza kai yayi yace babu komai Momcy. Yauwa haka nakeson ji da anjima idan zaka fita zan baka sak'o kabiya kakaima Hajiya Maijidda. Da mamaki yake kallonta yace Hajiya Maijidda kuma? Cikin nuna rashin damuwa tace Eh ita tunda kai bakayi da 'yarta wannan ba zai sa mu mudaina zumunci ba dan ka san matsayinta a wajena. Murmushi yayi yace toh Ammi babu damuwa ai yanzu ma zan watsa ruwa infita sai ma kawai infara zuwa gidan. Hmm ka ji da shi kana so kana kaiwa kasuwa nasan dai kana son ganin Nasiba ne. Kallon mahaifiyar tashi kawai yake batare d ya ce komai ba. Nan tamik'e tace idan kafito sai kasameni a part d'ina ka amshi sak'on. Toh Mom. Wajen k'arfe biyar ya isa gidansu Nasiba yana shigar da motarshi cikin gate d'in gidan daidai lokacin Nasiba tacinno kan tata motar, da mamaki take kallon motar Faruk cikin ranta taji wani irin sanyi har ta ayyana ko ya dawo gareta, murmushi tayi tace inko hakane zanyi farin ciki sosai, duba fuskarta tayi ta cikin mirror d'in motar taga fes take sannan tabud'e tafita. Faruk yana yin parking zaune yayi cikin motar sai a lokacin yafara tunanin ta yadda zai iya shiga yakai ma Hajiyar Nasiba sak'o da tun chan baya baiyi tunanin haka ba ko da ya san hakan yana da nasaba da son ganin sanyin idaniyarshi da yakwana biyu baisakata a idanunshi ba, zaune yayi yana kallonta har tafito daga motar tajingine a jikin motar tana kallon tashi motar. Ganin haka yasa yabud'e yafito hannunshi rik'e da sak'on Mom, tsayawa yayi yana kallonta shima da manyan idanuwanshi su dukansu kowa yana ayyana abu acikin zuciyarshi chan sai Faruk yataka yanufi wajen da take. Har ya isa bata daina kallonshi ba, sallama yayi mata sai a lokacin tajanye idanunta daga kallonshi tasadda kanta k'asa sannan ta amsa mashi ahankali. Murmushi yayi yana jin wani irin dad'i a ranshi, muryarta yaji ta gaisheshi, nan ya amsa, daga haka kuma duk sukayi shuru still dai idanunshi suna a kanta gani yayi ta d'an rame, ya shagala da kallonta ita kuma jira kawai take yafad'a mata ya dawo gareta bakinta d'auke da murmushi jin shuru har lokacin bai ce mata komai ba yasa tad'an d'ago tasaci kallonshi karaf suka had'a idanu. Dabarbarcewa yayi yace am Nasiba daman Mom ce tabani sak'o inkawo ma Hajiya ban saniba ko tana ciki. Saurin ida d'ago kai tayi takalleshi nan k'wallah tacika idanun cikin ranta tace ashe daman ba dawowa yayi gareni ba, ahakali tabud'e baki cikin murya me kama da ta kuka tace kashiga tana ciki. Tsaye yayi yana kallonta shi kanshi baiji dad'in hakan ba ko bakomai ai ya kamata ace sun gaisa, cikin k'arfin hali yace Nasiba ina fatan kina lafiya? 'Daga mashi kai tayi alamun Eh. Ajiyar zuciya yasafke yace ammah na ga kin d'an rame saisa nayi tunanin ko bakida lafiya. Hawayen da suka taru cikin idanunta ne suka zubo, cikin zuciyarta tace lallai ma Faruk watau tambaya yake ko banda lafiya bayan ciwon da yabar min acikin zuciyata, girgiza kai tayi tace a'a kawai dai...sai kuma tayi shuru. Kawai dai me? Memakon tabashi amsa sai cewa tayi kaima naga ka d'an rame ko duk aikin ne? K'ayataccen murmushin shi me tsada yasakar mata sannan yace ko d'aya lafiya ta lau saidai kece kad'ai damuwata. Ji tayi kamar a mafarki yafad'a mata haka shi kanshi saida yaga tsantsan mamaki a tattare da fuskarta, saurin sa hannu tayi tagoge hawayen da suke fita tace anya Faruk hakane ba kawai ka fad'a min bane? Na tabbata da ace kana sona da bazaka ta'ba banzatar da ni ba. No Nasiba ko d'aya ban banzatar da ke ba kawai dai banda yadda zanyi ne saboda Daddynki ammah ni ko a yanzu yajanye k'udurinshi.. Tarar numfashinshi tayi tace ammah dai Faruk wannan bai dace yazama hujjar da zaka iya hak'ura da ni ba kaidai kawai kace min ka daina sona, bayan ka dasa min ciwon da har yanzu ya kasa warkewa a cikin zuciyata. K'ara matsowa yayi saitin fuskarta yace Nasiba da sannu zani dawo gareki kikwantar da hankalinki. 'Dan guntun murmushi tayi sannan tace wane lokaci ne wannan ko har sai na bar duniya? Please kidaina wannan maganar bazaki mutu ba insha Allahu nan da 'yan kwanaki kad'an zan dawo gareki, kallon k'ofar gidansu yayi sannan yace kinga amsa inbaki kishigar ma Mummy da shi. Wani irin dad'i taji akan maganarshi ko bakomai yanzu ta tabbatar Faruk zai dawo gareta, kasa 'boye farin cikinta tayi har saida yabayyana, tace dagaske kake Faruk? Maido kallonshi yayi akan fuskarta sannan yace insha Allahu Nasiba dan bana ji zan iya cigaba da rayuwa batare da ke ba, nasan Daddynki yana nan bazan shiga gidan ku ba dan banso muhad'u dan Allah ki amsa kikai mata. Kallon motocin da suke wajen tayi taga dukkansu suna nan dan haka ta san tabbas Daddy yana gida, bata musaba ta amshi ledar. Murmushi yayi yace yauwa na gode, nan yajuya zai tafi, bud'e baki tayi kamar zatayi magana sai kuma tafasa. Ja yayi yatsaya tare da juyowa yakalleta yace please Nasiba akwai wani d'an taimakon da nakeso kiyi min. Murmushi tayi tace toh ba damuwa, menene kakeso ko ma menene kafad'a zanyi maka. Rasa yadda zai ce mata yayi dan bayaso tazargi wani abu, ganin ya yi shuru yasa tace kai nake sauraro. Am daman dan Allah Number d'in Alhaji Mansur nakeso kisamo min a wajen Daddynki ammah dan Allah kar kibari yagane ni zaki ba. Murmushi tayi tace indai wannan ne kar kadamu zan samo maka. Shima murmushin yasakar mata yace Nagode sosai My Wife to be sai na jiki. Wayyo farin ciki tsantsa Nasiba tashiga batasan lokacin da tamaimaita kalmar ba, nan yajuya yafara tafiya, ji take kamar tatsaidashi ammah takasa. Shi kanshi wani irin dad'i yake ji ko bakomai ya ba idanunshi abincin shi, ko da ya san ya yi k'ok'ari sosai wajen controlling kanshi bai nuna mata irin yadda yadamu sosai d'innan ba, ko da ya san k'asan zuciyarshi shi kanshi ciwone da baida magani indai ba ya ga anmallaka mashi Sanyin idaniyar shi ba. Yana isa wajen motarshi har ya bud'e zai shiga yajuyo yakalleta yasakar mata lallausan murmushi itama maida mashi martani tayi sannan tanufi cikin gida. Tana shiga dagudu tanufi hanyar part d'in Mummy tana k'wala mata kira, ja tayi tatsaya a parlor lokacin da tagansu zaune ita da Daddynta, Daddyne yace Nasiba wannan irin kira haka me yafaru? Ko ta samu ne? Murmushi tayi tace bakomai Daddy. Yace ke dai fad'amin shalele ko ansamo mana wani sabon siriki? Kunya ce takamata tayi saurin mik'a ma Hajiya Maijidda ledar da Faruk yabata tace Hajiyata ga sak'onki sannan tajuya dagudu tanufi part d'inta. Ba Daddy ba hatta Hajiya maijidda saida tadara, duba ledar tayi ganin sak'on Hajiyar Faruk ne yasa tayi murmushi tace watau yau ta had'u da abin k'aunarta saisa tashiga farin ciki, har ta bud'e baki zata sanar da mijin nata dalilin farin cikin d'iyar tasu nan wayarshi tafara ruri, mik'ewa yayi yafita yana cewa ganinan zuwa. Nasiba tana shiga d'akinta saman gadonta tafad'a tare da jawo pillow tarungume a k'irjinta fuskarta tana d'auke da k'ayataccen murmishin da tunda taga Faruk take fitar da shi, ahankali tace nagode faruk tabbas a yanzu na tabbatar zaka dawo gareni, lumshe idanunta tayi tare da k'ara matse pillown a k'irjinta tana jin farin cikin da rabon da taji irinshi tun lokacin da aka fasa baikonsu da Faruk... _Sis Nerja'art✍🏻_ [7/24, 11:14 PM] Sis Nerja'art 2: *......FANSAR RAI......* *INTELLIGENT WRITER'S ASSO....®* [On Ward Together] _Follow me on Wattpad: *Sis-nerja*_ _Wannan Littafin na kud'i ne domin karantawa cikin aminci da yarda ga duk me buk'ata zai turo katin Mtn na d'ari biyu N200 kacal ta wannan number d'in 09035938246, ko ta account number 5330055604, Idan katura ka aiko da screen shot na transaction a wannan number d'in 09035938246_ _Akwai gara'basar *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shahararriyar marubuciyar nan *AMEENA ABBA UMAR* tare da novel d'in *FANSAR RAI* akan farashin N300 kacal, ko da kud'in ka sai da rabonka_ *PAGE 13* ...Nasiba ce zaune a parlon Daddynta da dare ita da iyayen nata suna kallo ammah ita duk hankalinta ba a wajen kallon yakeba tunani kawai take tana neman hanyar da zatabi tasamo number d'in Alhaji Mansur batare da Daddynta ya ganeba, a gefe d'aya kuma tambayar kanta take shin me yasa Faruk yake son tasamo mashi number d'in? Chan kuma a fili tace ko dai akan maganar aurenmu ne yakeso suyi magana. Muryar Hajiyarta ce taji ta ce lafiya Nasiba kike magana ke kad'ai? Murmushi tayi dan batasan maganar ta fito fili ba dan ma Allah ya taimaketa ahankali tayita, girgiza kai tayi tace a'a ba magana nakeba Mummy, juyawa tayi takalli Daddynta da hankalinshi yake a kan news d'in da yake kallo gyaran murya tayi tace am Daddy dan Allah ka ara min wayarka. Juyowa yayi yakalleta yace Nasiba me zakiyi da ita ba dai wayarki babu credit ciki ba? Girgiza kai tayi tana murmushi tace a'a Daddy Number d'in Yaya Maryam zan d'auka na yi loosing d'in contact d'inta. Mummy ce tace ai dama sauk'i tunda number ce kikayi loosing ba taki wayar ba. Turo baki tayi tace kai Mummy ni yaushe rabon da inyada waya anfi shekara biyu. Daddy ne yamik'a mata wayarshi yace amsa rabu da ita shalele anfad'a mata da da yanzu d'aya ne bataga da bambanci ba. Amsa Nasiba tayi tana dariya tace Allah Daddy ita Mummy da abu ya wuce sai tadinga tuno ma mutum Kibarta Shalele na ma kusan canza maki sabuwar waya. Mummy murmushi tayi tace oho dai na baku zuwa gobe ai sai anji ku indai Nasiba ce. Fakar idanun iyayenta tayi tashiga cikin contact d'in Daddy tad'auki number d'in Alhaji Mansur sannan tamik'a ma mahaifin nata wayarshi. Zama tayi na kusan mintuna biyar sanna tayi masu sallama tatashi takoma part d'inta cike da farin ciki, saida tahau saman gado sannan talalubo number d'in Faruk. A chan 'bangaren Faruk bayan ya gama shirin shi na bacci yana kwance saman gadonshi yana tunanin abar k'aunarshi yana jin wani irin dad'i a ranshi akan had'uwarshi da ita, shi kanshi ya san yana son Nasiba sosai ya yi k'ok'ari sosai da har ya iya danne son nata a yau bai nuna mata ya yi missing d'inta ba, murmushi ne yasu'buce mashi lokacin da yatuno yadda suke nuna ma juna soyayya kafin wannan abun yafaru, lumshe idanunshi yayi ahankali sannan yace Nasiba kina raina a kowane lokaci, yadda kike missing d'ina nima haka nake naki, ina fata akwai lokacin da komai zai zo k'arshe muyi aure.....yana cikin haka wayarshi tafara ringing tashi yayi zaune tare da d'aukota saman bedside ganin Nasiba ce yasa yai murmushi tare da yin picking, daga chan 'bangaren tayi mashi sallama ya amsa nan kuma duk sukayi shuru sai chan kuma takauda shurun ta hanyar cewa ina fata ka koma gida lafiya? Lafiya lau Nasiba. Wani irin haushi taji ganin a yanzu wai Faruk ne yake kiranta da sunanta ko dai ya daina sonta ne? Wasu siraran hawaye ne suka gangaro mata cikin sanyin murya tace am daman na kira ne infad'a maka na samo number d'in. Kai masha Allah na ji dad'i sosai Baby ina fata dai baki bari Daddy yagane ba? 'Dan guntun murmushi tayi cikin ranta tace wai kuma Baby dan na samo mashi abinda yake so, sai kuma chan tace uhm uhm bai gane ba. Toh shikenan kituro min kinji? Shuru tayi batace mashi komai ba, sake maimaita mata yayi nan ma shuru. Ajiyar zuciya yasafke yace Nasiba kiyi hak'uri duk yadda kikeji nima kaina ina ji ba wai na daina sonki bane wallahi ina k'aunarki sosai saidai banda wani za'bi da zan iya hak'ura da case d'innan bayan alk'awali nayi akanshi kuma kema kinsan girman alk'awali. Fashewa tayi da kuka tace ammah Faruk ka san ina sonka shine karabu da ni.. Katseta yayi yace kidaina cewa haka Nasiba wallahi ko d'aya ban rabu da ke akan son raina ba kuma har yanzu ina nan akan bakana zan dawo gareki a duk lokacin da muka gama shara'ar nan kikwantar da hankalinki kin ji ko? Rage sautin kukanta tayi tace shikenan Faruk ina nan ina jiranka dan Allah kar kabarni. Murmushi yayi yace kar kidamu da sannu zan baki mamaki dan banaso aja lokacin bikkin mu, nidai fatana kidaure kicire duk wata damuwa a ranki kikwantar da hankalinki sannan kidaina kirana a waya kar parents d'inki sugane har yanzu muna tare ransu ya'bace kibari mubi komai a sannu Nasiba. Cikin jin dad'in kalamanshi tace toh shikenan Hearty duk yadda kakeso haka za'ayi. Lumshe idanunshi yayi tare da sakin murmushi sannan chan k'asan mak'oshinshi yace kece rayuwata zan kasance da ke akowane lokaci acikin zuciyata, kikwanta kiyi bacci. Ita kanta lumshe idanunta tayi tana fitar da murmushi me sauti "Nagode sosai Hearty hak'ik'a nayi farin ciki da jin kalmar nan a yau zanyi baccin da rabon da inyi irinshi tun muna tare shikenan sai dasafe. Sallama sukayi suka kashe wayar kusan a tare suka manna wayoyinsu a bisa k'irjinsu suna murmushin farin ciki, kowa na jin soyayyar d'an uwanshi tana fizgarshi. Chan Faruk yaji shigowar text yad'aga wayar yana dubawa sai ganin number d'in Alhaji Mansur yayi ta turo mashi. Murmushin jin dad'i yayi cikin ranshi yace kin gama min komai My Life, nan yatura mata " Thanks my wife to be insha Allah, Good Nyt, kiyi bacci me dad'i. A karo na biyu tasake lumshe idanunta cikin jin dad'i tace Night too My Everlasting,,, tana manne da wayar a k'irjinta a haka tayi bacci. Achan 'bangaren Faruk tashi yayi yagama duk abinda zaiyi sannan yakoma yakwanta. Washe gari yana zaune a parlorn d'akinshi yana kallon kwallo inda a saman d'an teburin da yake gaban kujerar da yake zaune fruit salad ne yana sha, sai wajen k'arfe sha d'aya yagama kallon yamik'e yad'auko wayarshi da yajona charge yakoma inda yake zaune kasancewar ranar bazaije wajen aiki ba, Number d'in Alhaji Mansur yalalubo yakira, har saida takusan tsinkewa sannan akayi picking, sallama yayi daga chan 'bangaren Alhaji mansur ya amsa a dak'ile tare da tambayar wanene. Faruk bai damu da yanayin da ya amsa shi ba yace am Barr Faruk ne daman na kira ne intambayeka dan Allah in ba damuwa ina zan sameka dan akwai magana me muhimmanci da zamuyi. Tun kan yarufe baki yaji muryar Alhaji Mansur cikin fad'a yana cewa babu wata magana me muhimmanci indai ba janyewa kayiba kabari aka kashe yarinyar chan kamar yadda takashe wasu. Murmushi Faruk yayi dan yanayin yadda yayi maganar ta so tabashi dariya ammah yadanne sannan yace koma menene kaban dama muhad'u sai mutattauna. Toh shikenan zan turo maka adress d'in Guest House d'ina sai kazo kasameni. Cikin jin dad'i Barr Faruk yace toh shikenan sai na jika,,, bai jira jin abinda zai ce ba yakashe wayar tare da saving d'in recording d'in da yayi, gudar wayarshi yad'auko yakunna muryar da yake tunani ta Alhaji Mansur ce yasake saurare tabbas ya ida gasgatarwa da tashin ce, yana nan zaune sai ga message ya shigo wayarshi yana dubawa yaga Alhaji Mansur ne, murmushi yayi yace dakyau haka nakeso nan yamik'e yashige bedroom d'inshi bai dad'eba yafito hannunshi rik'e da key d'in motarshi fuskarnan ya dad'eta da bak'in glass d'aukar wayoyinshi yayi yafita yabar gidan. Yana isa k'ofar gate d'in gidan duk security's suka taso suka nufo wajen motarshi ganin haka yasa yagane bazasu barshi yashiga ba nan suka fara tambayarshi me yazo yi? batare da ya basu amsaba yad'auko wayarshi yakira Alhaji Mansur yana yin picking yace gani a k'ofar gidanka wad'annan k'attin da katara sun hanani shigowa. Ba su da akace ma k'atti ba hatta shi kanshi Alhaji Mansur ya ji ciwon abun dan de kawai yana so yasan abinda yakawoshi saisa yadanne fushinshi yace basu waya muyi magana. Mik'ama d'aya daga cikinsu wayar yayi yace oganku yana son magana da ku. Amsa yayi yakanga a kunne nan sukaji yana cewa ohk sir angama, mik'a ma Barr Faruk wayar yayi sannan yabada umurni aka hangame mashi tank'amemen gate d'in yashigar da motarshi parking yayi yafito nan d'aya daga cikinsu yayi mashi jagora zuwa cikin gidan, Faruk ko kanshi d'aurewa yayi ganin makeken Guest House d'in Alhaji Mansur ahaka har suka isa wani tank'amemen parlor inda Alhaji Mansur d'in yake zaune ya kame sai hura hanci yake. Sucurity d'in komawa yayi inda Barr Faruk yayi sallama yashiga, amsawar ma cikin tak'ama aka yi mashi, murmushi kawai Faruk yayi yaje yazauna saman kujerar da take opp d'in wadda Alhaji Mansur yake zaune cikin tak'ama yazauna tare da d'aura k'afa d'aya saman d'aya, koda Alhaji Mansur yakalleshi saida yaga ya yi mashi k'warjini, zare glass d'in da yake fuskarshi yayi sannan yace sannu Alhaji. Cikin isa ya amsa da yauwa ka ce kana son ganina ko? Murmushi yayi yace Eh saboda inaso ka amsa min wasu tarin tambayoyi da ke gareni. Da mamaki yake kallonshi yace wane irin tambayoyine haka? Ta'be baki yayi yace ba wasu tambaboyi bane masu wuya kawai dai akan case d'in mutuwar su Alhaji Muhammad Mai kud'i ne. Gaban Alhaji Mansur wani irin mummunan fad'uwa yayi yai saurin gyara zaman shi tare da kallon Faruk yace ban fahimceka ba me kake nufi? Murmushi yayi yace daman bazaka fahimceni ba saidai yanayin yadda kafirgita ya sa na gane ka d'an fahimci wani abu, ammah dai kar kadamu da wannan na san dai Alhaji Muhammad abokinka ne kai da su Alhaji Tanimu toh abin mamakin bayan mutuwarshi kuka koma kuka k'ulla abota da yayanshi Alhaji Mu'azu, saidai hakan baisa kuyi tunanin ko za'a iya zarginku da wani abu ba? Ko ma ace akwai wani abu da kuka shirya ku d'in? Zumbur Alhaji Mansur yamik'e tsaye cikin fushi yace ban ganeba me kake nufi, wannan ai zancen banza ne ka zo ne daman dan karaina min hankali? Murmushi yayi a karo na biyu sannan yace kaga Alhaji da ka zauna munyi magana cikin kwanciyar hankali ba sai an jiyo abinda muke tattaunawa ba. 'Daga murya yayi yace kowa yajiyo man ina ruwana, watau ni kake zargi ko kenan? Shima mik'ewar yayi yace ni ba zarginka nakeba tambayoyi suka kawoni wajenka kuma ya kamata ka amsa min su, shin ya labarin kud'ad'e, gidaje, filayen marigayi Alhaji Muhammad da suke hannunku ko kun ajiyesu ne sai d'iyarshi ta fito daga gidan kaso sannan kumallaka su a wajenta tunda kawunta wanda kuke tayawa ajiyewa ya rasu? Alhaji Mansur mutuwar tsaye yayi yana kallon Faruk da tsantsan mamaki jin kalaman da suka fito bakinshi bayan babu wanda yasan wannan sirrin sai su kad'ai toh ina yaji hakan? Yana cikin tunanin yaji muryar Faruk ya cigaba da cewa sannan takardun kamfanin yarinyar chan ya kamata ace kun damk'a mata abunta, filayen da gomnati tasiya ma a wajenku ko tana da alak'a da su? A fusace cikin d'aga murya yace ya isheka haka Barrister! ya isa!!! Watau ni zakazo kaci ma mutunci dan kawai mahaifin Nasiba ya hanaka auren d'iyarshi ni zaka ja ma sharri? Toh wallahi ya zama dole indamk'a ka a hannun hukuma dan bazan lamunci hakan ba da girmana a gari kanemi kazubar min da shi, duka dukiyar muhammad nawa take da har zamu so mucita kaduba girman Guest house d'ina wanda ko rabin girman gidana bai kai ba shin wannan bai isa yazama shaidaba akan cewa na fishi dukiya? Bazan barkaba dole kotu tashiga ciki,,, wayarshi yad'auko yana shirin lalubo number. Murmushi Barr Faruk yayi yace kiran wayar da zakayi daidai yake da tona ma kanka asiri, shin zaka iya tuna wata mota sabuwa fil da Alhaji Muhammad yasiya wadda kaci burin kamallaketa Wadda cikin motocinka babu kamar ta? Ko zaka iya tuna wayar da kukayi da Alhaji Mu'azu akan son mallakar dukiyar jawahir da take cikin account d'in mahaifinta?.. Wayar da take hannunshi ce tasu'buce tafad'i nan yafara zufa 'yan cikinshi saida suka kad'a, wuta tad'auke mashi d'if saida yayi kusan minti biyar suna kallon kallo da Barr Faruk sannan yayi k'ok'arin saita kanshi sannan cikin inda-inda yace ina kaji wannan? wanene yafad'a maka hakan? Tsayawa Barr Faruk yayi yana kallonshi ganin haka yasa Alhaji Mansur yanufoshi a harzuk'e yana cewa tambayarka nake kabani amsa! Ja yayi da baya yace ka ga kar kamatso min nan ni tambayarka nayi kuma amsa nakeso. Idanuwan Alhaji Mansur jajir sukayi saboda 'bacin rai cikin fushi yanuna mashi hanya yace fitar min daga gida tun kan insa afitar da kai ta k'arfi, wannan cin fuska ya yi yawa ace katako har cikin gidana kaci min fuska, kai wanene a garin nan da har zakayi min haka? Ta'be baki yayi cikin nuna rashin damuwa yace na ji zan fita kuma ni ba kowa bane saidai inaso kasani na san abubuwa da dama agame da duk abinda kuka aikata, sannan kashirya zan k'ara dawowa gareka dan neman amsar wad'annan tambayoyin kai har ma da wasu na daban, murmushin gefen baki yayi sannan yace na barka lafiya,,, yana fad'in haka yajuya yafita. Alhaji Mansur tsaye yayi yakasa ta'buka komai mamaki duk ya gama cikashi nan kuma yafara zagaye d'akin yaje yadawo haka yaitayi cikin ranshi yana tunanin wanene yasanar da Barrister duk wannan to kodai yarinyar chan ce? Toh ammah ita kanta batasan abinda duk muka shiryaba, saidai ya kamata inyi wani abu a nan, komawa yayi yazauna yad'auko wayarshi yalalubo wata number bata dad'e tana ringing ba akayi picking ko sallama bai tsaya yi ba yace Alhaji da matsala. Daga chan 'bangaren akace matsala kuma? Wace iri kenan? "Lauyan wannan yarinyar ya zo ya sameni ya tisani a gaba yana min wasu tambayoyin da suka nemi surikita min k'walwa wanda bansan amsoshinsu ba ammah ba ma wannan ba tambayar a nan itace duk ina yasan wad'annan abubuwan? Daga chan 'bangaren dariya aka fara kyalkyatawa har saida Alhaji Mansur yafusata ganin dariyar batada niyar k'arewa yasa yace watau kai dariya ma kakeyi ko? Dole inyi dariya Alhaji Mansur wannan abun bai kamata yad'aga maka hankaliba. Ajiyar zuciya yasafke yace hakane ammah ya zama dole inyi wani abu akan yaron nan kafin yanemi tozartani koda na san hakan ba zai ta'ba yuwuwa ba ammah dole inga bayanshi, ya kamata muhad'u da kai zuwa anjima domin musan ta inda zamu 'bullo mashi. Toh shikenan babu damuwa zan shigo. Kashe wayar yayi tare da mik'ewa yana cigaba da zagaye d'akin still dai wayarshi tana a hannunshi, ya dad'e a tsaye yana kaiwa da kawowa daga k'arshe yatsaya waje guda tare da duba wayarshi yakira wata number ana yin picking batare da ya yi sallama ba yace Barrister ina son muhad'u da kai yanzun nan kazo gidana kasameni. Ohk ba damuwa sai ka zo ina nan ina jiranka. Yana gama wayar komawa yayi yazauna tare da cije le'be yana jinjina kai yace tabbas ya zama dole inyi maganinka Barrister ba ma kai ba duk wanda yace zai shiga rayuwata sai naga bayanshi dan haka muje zuwa. Bayan ya bar gidan Alhaji Mansur direct gidan kaso yawuce yana isa yasamu jawahir zaune jingine da bango ta d'age kanta sama tana kallon rufin d'akin inda hawaye suka fara wanke mata fuska, daga gefenta yatsaya yana mata kallon mamaki. Ahankali tajuyo takalleshi tare da goge hawayen fuskarta sannan tasadda kanta k'asa tace Barrister ina jin tsoro dan Allah kazare hannunka daga cikin wannan case d'in kar wani abu yasamu rayuwarka. Jikinshi sanyi yayi nan yatsugunna gabanta yace jawahir meyasa kikace haka? Kikwantar da hankalinki babu abinda zai faru zanyi k'ok'ari sosai wajen ganin na fitar da ke a cikin gidan kason nan ke yakamata kibani k'warin gwiwa domin wannan shine zama na k'arshe da za'ayi ya kamata mucigaba da addu'a insha Allahu mune da nasara. Girgiza kai tayi tace baka fahimceni ba Barrister. Na fahimceki man indai akan su Alhaji Mansur ne kicire duk wata damuwa a ranki daidai nake da su sannan basu isa suyi abinda ubangiji baiyi ba. Cikin sanyin jiki tace hakane. Toh kikwantar da hankalinki kinga daga nan ma wajen DPO nakeson wucewa dan yasanar da ni asibitin da aka kwantar da matar Alhaji Mu'azu dan haka koma mekenan zan sanar da ke kikwantar da hankalinki komai zai zo cikin sauk'i. 'Daga kai kawai tayi alamun toh. Nan yayi mata sallama yatashi yatafi. Yana isa station number d'in DPO yakira yasanar da shi zuwanshi nan yabada izini da ashigo da shi office d'inshi. Faruk yana shiga yasameshi yana waya dan haka yaja kujera yazauna har saida yagama sannan yamik'a mashi hannu suka gaisa. Bayan sun gaisa ne DPO yace ina saurarenka me ke tafe da kai? Murmushi yayi sannan yace ba komai bane yake tafe da ni sai akan dai case d'in jawahir kamar yadda a binciken da nakeyi nagano cewa matar Alhaji Mu'azu tana nan a raye ana jinyarta a wani asibiti shine nakeso asanar da ni asibitin dan inason ganawa da it. Da mamaki DPO yake kallonshi dan ya san in ba shi da su Alhaji Mansur ba babu wanda yasan tana asibiti, Faruk kamar ya san abinda yake tunani yace baidace ace kun 'boye ma kotu tana raye ba domin duk a cikin k'undin case d'in jawahir da naduba banga inda aka fad'i matarshi tana raye ko ta mutu ba. Jikin DPO sanyi yayi yace tabbas tana raye kuma wannan ba laifina bane polices d'in da suka bada sheda ne basu rubuta ba ammah shikenan zan sanar da kai asibitin saidai ko ka je babu abinda zaka samu daga wajenta dan har yanzu batasan inda kanta yake ba. Jinjina kai Barr Faruk yayi yace babu damuwa. Nan DPO yasanar da shi. Sallama yayi mashi yatafi shi kanshi cikin ranshi ya yi mamakin yadda yau DPO bai mashi rainin wayo ba haka yashiga motarshi yawuce private hospital d'in, yana isa baisha wahalar gane room d'in da takeba dan haka yawuce, yana shiga yasameta a kwance tsaye yayi yana kallonta tana kwance bata ko motsi, wata dattijuwa ce tajuyo takalleshi tace sannu da zuwa. Murmushi yayi sannan yayi sallama tare da ida shiga d'akin. Bayan ta amsa gaisawa sukayi yatambayeta ya me jiki? Cikin sanyin jiki tace toh Alhamdulillah za'a ce. Kallonshi yamaida ga Ummah da akasa ma drip idanuwanta a rufe kamar me bacci yace bacci ma takeyi ko? Uhm wane bacci yaro ko ma idanonta biyu ba'a ganewa dan har yanzu kusan shekara d'aya kenan babu uhm bare uhm uhm saidai kallon mutane kawai da take. Mamaki ne yakama Barr Faruk yace Allah yasauk'e Allah yabata lafiya ko zan iya sanin Doctor d'in da yake dubata. Goge hawayen da suka zubo mata tayi tace Eh Dr Aminu ne. Ohk Allah yabada lafiya. ___________ Washe gari da marece yanufi gidan su Nasiba yana isa megadi yasanar da shi bata nan murmushi yayi sannan yace toh babu damuwa Alhaji fa? Eh toh Alhaji yana ciki. Toh ko zan iya ganinshi? Wani yaron gidan ne megadi yatura yace yaje yace ana sallama da Alhaji, sannan yabud'e ma Barr Faruk gate yashiga da motarshi yana yin parking yafito yajingina a jikin motar sai ga yaron ya fito ya ce ance wai wa ke nemanshi? Kace mashi Faruk ne. Toh yace nan yakoma yashaida mashi. Barr Faruk ya yi kusan mintuna goma a wajen tsaye kafin Alhaji Sufyan yafito. Fuska a murtuk'e yanufo wajen da Faruk yake tun kan ya ida isowa yace lafiya me yakawo ka gidana? Ko ka zone kashaida min ka janye daga case d'in. 'Dan rissinawa Faruk yayi yagaisheshi a maimakon ya amsa sai ma k'ara jefo mashi tambaya yayi yace ina fata ba'a kan aurenku da d'iyata kazoba ko, dan bazan ta'ba amincewa ba har sai ka janye k'udurinka. 'Dagowa Faruk yayi yakalleshi sannan yace ko d'aya Alhaji ba wannan ne dalilin zuwana ba. Toh menene dalilin zuwan naka? Shuru Faruk yayi. Nan Alhaji Sufyan ya ida harzuk'a yace ba tambayarka nake ba!..... _Sis Nerja'art✍🏻_ [7/24, 11:14 PM] Sis Nerja'art 2: *......FANSAR RAI......* *INTELLIGENT WRITER'S ASSO....®* [On Ward Together] _Follow me on Wattpad: *Sis-nerja*_ _Wannan Littafin na kud'i ne domin karantawa cikin aminci da yarda ga duk me buk'ata zai turo katin Mtn na d'ari biyu N200 kacal ta wannan number d'in 09035938246, ko ta account number 5330055604, Idan katura ka aiko da screen shot na transaction a wannan number d'in 09035938246_ _Akwai gara'basar *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shahararriyar marubuciyar nan *AMEENA ABBA UMAR* tare da novel d'in *FANSAR RAI* akan farashin N300 kacal, ko da kud'in ka sai da rabonka_ *PAGE 14* Ganin yadda yaharzuk'a yasa Faruk yayi murmushi yace kakwantar da hankalinka ba wai dalilin d'iyarka yasa nazoba na zone akan aikina. Cikin nuna rashin fahimtar inda zancen yadosa yace ban fahimceka ba wane irin aikin kenan? Juyawa yayi yakalli gefe d'aya sannan yace a matsayina na barrister ko ma ince akan case d'in jawahir na zone dan ind'an maka wasu tambayoyi wad'anda suka shige min duhu. Wani irin kallo Alhaji Sufyan yayi mashi mai wuyar fassarawa koda Barr Faruk bai san ya yi ba saboda ba shi yake kallo ba, ida harzuk'a Alhaji Sufyan yayi yanuna kanshi yace ni ni zakazo kayi ma tambaboyin banza akan wacchan yarinyar? Miye had'ina da ita da har zakazo kace zaka tambayeni, inma kana yi ne saboda na hakana ka auren d'iyata toh bari kaji kayi duk abinda kaga dama ammah Nasiba ta fi k'arfinka dan haka kabar gidan nan yanzu tun kan insa'ba maka,,, yana fad'in haka yajuya a harzuk'e zai koma gida. Sai a lokacin Faruk yajuyo yakalleshi yace shin me zaka iya cewa akan kisan da akayi ma Alhaji Muhammad Mai kud'i? Chak Alhaji Sufyan yaja yatsaya batare da ya juyoba ganin haka yasa Faruk yacigaba da cewa sannan dukiyar yarinyar chan da take hannunku shin kun ajiye mata ne da sunan idan ta fito zaku mallaka mata ita? Sannan dukiyarta da kuka amsa hannun Alhaji Mu'azu da sunan zakuyi business shin ya maganar business d'in? Jikin Alhaji Sufyan sanyi yayi yai saurin juyowa yakalleshi cikin 'bacin rai yace ban fahimceka ba kana nufin dukiyarta tana wajenmu ko kuma kana nufin muna da hannu a cikin mutuwar shi? Faruk kana da hankali kuwa? Murmushi yayi cikin nuna rashin damuwa yace ba wai haka ba Alhaji kowa ya san kusancinku da Alhaji Muhammad sannan bayan mutuwarshi kuka koma abota da d'an uwanshi wanda yake da gurin ganin ya mallake dukiyarshi sannan sanin kanku ne Alhaji Muhammad ya bar duniya yana binku bashi kuma kun ci guri sosai akan wasu abubuwa nashi hatta.......katseshi yayi yace ya isa haka Faruk wannan tatsinniyoyin naka duk kasan wanda zakayi masu ba wai niba kowa ya san cewa Alhaji Muhammad abokin alk'alla ta ne ba wai abokina bane akan wane dalili zan so mallakar wani abu nashi bayan dukiya nima ina da ita tun daga tsarin gidana da matsayina ya kamata kafahimci hakan. 'Daga kai Faruk yayi yana kallon gidan sannan cikin nuna rashin damuwa yace ammah toh idan yakasance wannan gidan mallakinshi ne fa mezaka iya cewa? Kai!!! Banason shashancin banza me kake nufi da maganarka gidan nawa ne mallakin wani? Inji wane mak'aryacin yafad'i haka? Fad'amin! Girgiza kai Faruk yayi yace babu wani mak'aryaci da yafad'i hakan saidai ka sayi gidan a hannun Alhaji Mu'azu a kan farashi me sauk'i bayan kuma kun san gidan ba mallakinshi bane. Tsawa yadaka mashi yace Faruk na gaji da jin wad'annan k'aryayyakin naka na banza wanda me hankali bazai ta'ba d'aukarsu ba tun muna mu biyu kafita kabar min gida! Har Faruk ya bud'e baki zaiyi magana yayi saurin tarar numfashinshi cikin d'aga murya yace na ce kafita kabar min gida ko bakaji abinda nace ba!? Ganin yadda yad'au zafi sosai yasa Faruk yace shikenan na ji zan tafi ammah..... Kar kasaki kafad'i wani abu a wajen nan katafi nace!!! Gyad'a kai yayi yajuya yabud'e motarshi yashiga yana jin Alhaji Sufyan yana ta fad'a haka yatada motar, yana fitar da motarshi daga gate d'in gidan Nasiba tana 'bullowa da tata motar wani irin dad'i taji a ranta dan ta d'auka wajenta yazo saidai abinda yabata mamaki ya ganta ammah yashare yayi tafiyarshi, duk sai taji babu dad'i cikin ranta tace ko lafiyarshi shi kuma? Girgiza kai tayi tashigar da motarta cikin gidan hango Daddynta tayi yana ta kaiwa da kawowa a wajen ranshi duk a 'bace, mamakine yacikata tayi saurin yin parking d'in motar tafito tanufi wajen mahaifin nata tana cewa Daddy lafiya? Me yafaru? Juyowa yayi yai mata wani irin kallo cikin 'bacin rai sannan yajuya yashige gida. Mutuwar tsaye Nasiba tayi tace ikon Allah me yafaru? Ko dai dan Faruk ya zo gidan ne yasa ranshi ya'baci kuma fa na ga shima Faruk ya tafi ranshi a 'bace toh me yafaru? Ajiyar zuciya tasafke sannan itama tabi bayan Daddynta tashiga cikin gidan a parlor tasameshi tsaye Hajiya Maijidda tana tambayarshi abinda yafaru. Hucci kawai yake dan ranshi ba k'aramin 'baci yayi ba chan yajuyo yakalli Nasiba sannan yamaida kallonshi ga matarshi cikin d'aga murya yace wai ni ni Faruk zai zo yaci ma mutunci har cikin gidana. Kusan a tare sukace cin mutun kuma? Cize le'be yayi sannan yace eh man duka nawa yaron nan yake da har zai kalli tsabar idona yatuhumeni akan mutuwar Alhaji Muhammad har yana ik'irarin cewa wai muncinye ma d'iyar shi dukiya, gidan nan ma da nake ciki cewa yayi na yarinyar ne. Nasiba a kid'ime tace Daddy, nan tasa hannu tatoshe bakinta tare da fashewa da kuka ahankali tace Faruk meyasa kayi haka. Hajiya Maijidda cike da mamaki tace Faruk d'in yace haka Alhaji? Toh in ba shiba wanene? murmushi yayi mai ciwo sannan yace duka yaron nan nawa yake wallahi da ace bani mutunci da mahaifinshi da yau yau d'innan sai na sa an d'aureshi a garin nan! Baya baya Nasiba tafara ja sannan taruga dagudu tanufi d'akinta tare da fashewa da wani irin kuka me shiga rai tana shiga saman gadonta tafad'a tana me cigaba da kukan, wani irin haushin Faruk ne taji cikin ranta tace wai shine yaci mutuncin mahaifina daman ya san abinda zai aikata saisa yace insamo mashi number d'in Alhaji Mansur,, , kuka tacigaba da yi sosai. Hajiya Maijidda kallon mijin nata tayi da ranshi yayi matuk'ar 'baci tace Alhaji baidace ka'bata ranka saboda wannan yaron ba ina tunanin ya yi hakane kawai dan ka hanashi auren d'iyarka ammah ko indai dan hakane baida mutunci. K'wafa yayi yace kibarni Hajiya baisan wanene ni ba wallahi idan baibi a sannuba sai na sa and'aureshi a garin nan inga ubanda yatsaya mashi babu ruwana da mutuncin da muke da mahaifinshi tunda shi haka yake, ba barister ba ko alk'aline babu ruwana. A'a Alhaji kayi hak'uri abi komai a sannu kawai dai kaje kayi ma mahaifinshi magana dan yagargad'i d'anshi yafita daga harkar ka idan har bai daina ba toh shine kake da damar yi mashi kowane irin hukunci. Jinjina kai Alhaji Sufyan yayi yace kibarni da shi kawai Hajiya zai san da ni yake, je kid'auko min key d'in motata. Amsawa tayi da toh, taje tad'auko mashi har tadawo yana nan tsaye inda yake mik'a mashi tayi ya amsa yawuce yafita cemashi tayi Allah yakiyaye ammah bai amsataba saboda yanayin da yake na 'bacin rai. Rik'e baki tayi tace oh ni Maijidda wannan yaro ammah dai baida mutunci da ace mahaifinshi shima ba mai kud'i bane da nace bak'in ciki yake da dukiyarmu,,, tunowa tayi da Nasiba dan haka cikin sauri tanufi part d'inta tana isa tasameta a bedroom kwance sai faman rusar kuka take daga gefen gadon tazauna tare da kiran sunanta nan Nasiba tayi shuru. Ganin haka yasa tace kindai ji abinda Faruk yayi ma mahaifinki yaron nan ashe baida mutunci bai gaji arzik'iba. Tashi tayi zaune tare da tsaida kukanta tace wallahi Mummy da ace banga fitar Faruk daga gidan nan ba da bazan ta'ba yarda da cewa shine ya aikata ba yanzu dan rashin mutunci yakalli tsabar idanun mahaifina yafad'a mashi haka? Kenan soyayyar da yakeyi min duk ta k'aryace. Ta'be baki tayi tace toh ai yanzu gashinan dai kin gani da idanunki. Fashewa tayi da wani sabon kukan tace wallahi indai har Faruk ya yi min haka dan yatozarta mu toh yaje ya yi ma kanshi ni kuma zanyi k'ok'ari wajen ganin na cireshi a raina dan iyayena sun fiye min komai ba'ayi wanda zai zo yaci musu fuska har ransu ya'baci ba. Jin kalaman da tayi yasa Mummynta tajawota jikinta kamar jira take tafad'a tare da rungume mahaifiyartata tana cigaba da rusa kuka. Lallashinta Hajiya Maijidda tashiga yi dak'yar tasamu tashawo kanta har tahak'ura tadaina kukan. ________ A chan wani k'urmin daji dake wajen garin katsina tsakanin wasu k'auyuka biyu, dajin yana da duhu da yawan itatuwa sosai, iska kawai yake kad'awa a cikinshi baka jin motsin komai sai kukan tsuntsaye kawai babu mahalukin da yake shigarshi saboda ansan had'arin da ke cikinshi dan a tsakiyar dajin wasu 'yan fashi su biyar da suke rayuwa a cikinshi a duk lokacin da sukaso suna fita suyi fashi a gari ko kuma agayyacesu wani wajen suje suyi kisa saboda k'auran sunan da sukayi yasa mutane suke tsoron dajin. 'Yan fashin zaune suke suna zuk'ar shisha inda iskan da ke cikin dajin yake kad'asu, daga chan gaba da su kad'an ogansune zaune a bisa kujera hannunshi rik'e da k'walbar giya ya kame yana sha, su dukansu sun duk'ufa suna sharholiyarsu nan suka fara jiyo k'arar tafiya kamar ana tun karo wajen da suke, saurin ajiye shishir sukayi kowa yad'auko makaminshi yarik'e a hannu, inda ogansu yanuna ko inkula hankalinshi kwance yana ta shan giyarshi, suna nan a tsaye suna ta mazurai suna jira suga wane me k'arancin kwananne zai kawo kanshi, sun dad'e tsaye a haka sai ganin 'bullowar wata kyakkyawar budurwa sukayi basusan lokacin da suka saki baki suna kallonta ba, sanye take cikin wata gown wadda takama jikinta sosai inda gashin kanta yake baje a tsakiyar bayanta kyakkyawar fuskarnan tata ta sha makeup tafiya take ta jan hankali tatunkarosu tana masu murmushi me jan hankali su dukansu sun shagala suna kallonta har saida takusa isowa wajen da suke sannan sukayi saurin nunata da bindiga sukace kitsaya nan idan har kika matso zamu harbeki. Cikin nuna rashin damuwa taja tatsaya tare da waigawa takallo ogansu da yake zaune har lokacin yana shan giya, fuskannan tata d'auke da murmushi tabud'e baki cikin siririyar murya me dad'in saurare tace idan ba damuwa inaso kubani dama inyi magana da oganku. Juyawa sukayi suka kalli ogan suna shirin yin magana sai jin muryarshi sukayi ya ce kubarta ta iso muji da me tazo. Saurin matsawa sukayi suka bata hanya tawuce tana karairaya duk suka bita da kallo suna lasar le'be, tana isa gabanshi taja tatsaya idanu yazuba mata yana kallonta daga sama har k'asa ganin haka yasa tajuya baya sannan tajuyo, ajiye kwalbar giyar yayi cikin muryar maye yace wacece ke? Me yake tafe da ke wajena? Maimakon tabashi amsa sai fad'awa da tayi jikinshi tazauna tana cigaba da yi mashi murmushin nan nata me saurin rikita mutun. Ganin haka yasa yabushe da dariya yace da alama wannan 'yar hannu ce tamuce. Ganin haka yasa su ma suka bushe da dariya sannan suka koma suka zauna, hannu yakai yafara shafa gashin kanta yace gaskiya kina da kyau sosai, Fari tayi mashi da idanu tace nagode. Ajiyar zuciya yasafke yace lallai ke d'in ta dabance, hannunshi yad'aura bisa wuyanta tayi saurin janye wuyanta, gashinta yadamk'o dak'arfi yana shirin tura fuskarshi a wuyanta tureshi tayi da dukkan k'arfinta tamik'e tsaye tana jifanshi da wani mugun kallo. Kyalkyacewa yayi da wata muguwar dariya yace tunda har kika kawo kanki ya zama dole kiyi abinda nakeso, hannu yakai zaya jawo ta tayi saurin yin baya tare da girgiza kai. Gyatsa yayi sannan yajuya yakalli yaranshi da suke tsaye cirko cirko cikin muryar maye yace kukaimin ita cikin bukkata, su dukansu suka kwashe da dariya sukace angama oga ashe har muma yau zamu yagi rabonmu daman mun kwana biyu bamu samu namaba, juyawa tayi takallesu taga sun nufota gadan gadan nan tanuna su da hannunta sai ga wata irin iska ta tashi me kama da guguwa su dukansu saida suka tsorata sukayi saurin sa hannu suka rufe idanunsu dan kar ta shiga, bud'e baki tayi tasaki wata irin razanannar k'ara wadda tasa gabad'ayansu saida suka firgita suka juya zasu bar wajen sai ganin wani haske sukayi a gabansu dan haka suka had'e waje guda kowa yana raba idanu, ogansu kuma yunk'urin tashi yayi daga kujerar da yake zaune nan iska tajashi da k'arfi sai gashi a kusa da sauran 'yan uwanshi 'yan fashi, Nuni tayi da hannunta a sama tafara karanto wasu irin d'alasimai sai ga wata k'atuwar macijiya ta bayyana a wajen su dukansu saida suka tsorata suka san yau sun gamu da gamonsu, bushewa tasakeyi da dariya nan tayi girgiza tazama wata k'atuwar dodanniya, murya suka fara jiyowa wadda tasa gabad'aya dajin yadinga amsawa ji sukayi ana cewa kuuuu azzalumai ban zo wajenku domin komai ba sai dan d'aukar *FANSAR RAI* zan kasheku kamar yadda kukaga bayana ku d'in azzalumai ne bazan ta'ba barinku ba. Su dukansu tsaye suke sunaso suyi magana ammah tsoro ya hana babu wanda bai saki zawoba a wajen da suke tsaye, macijiyar ce sukaga tana tunkaro inda suke tsaye dukkansu yunk'urin guduwa sukayi ammah sai ji sukayi kasala ta safkar masu har macijiyar ta iso wajensu tana zuwa tasakar masu tsartuwa nan duk suka zube k'asa kowa yana jijjiga suna safke numfashi. Ganin haka yasa tasake bushewa da wata razanannar dariya me kama da kukan hadari, sannan tanunasu da hannunta sai ga wasu k'ananun macizzai sun fito daga bakin wannan babbar macijiyar suna fitowa suka nufi wajen da mutanen nan suke kwance suna zuwa suka fara sarinsu, nan 'yanfashin suka fara ihu hayak'i yana fita daga jikinsu, sun dad'e a haka kafin daga bisani duk suka mace, saida tatabbatar da babu me motsi a cikinsu sannan lokaci guda ta'bace ita da macizzan. ***** ***** Barr Faruk tunda yabaro gidan Alhaji Sufyan cikin 'bacin rai ya isa gida saidai duk da haka baiyi nadamar hakan ba saboda akowane lokaci ashirye yake dan ganin ya tafiyar da aikinshi yadda yakamata, yana isa a k'ofar gate gidansu sai ganin motar Barr MB yayi anfaka ta, tsayar da motarshi yayi tare da fitowa yajingina a jikinta yana jira yaji da me yazo. Ganin haka yasa Barr MB yafito yanufo wajen da Faruk yake tsaye yana murmushi yace ashe na zo a daidai yanzu nake shirin kiran wayarka sai gaka. Shima murmushin yayi yace gaskiya ka taki sa'a. Hannu Barr Mahamud Bello yamik'a mashi sukayi musabaha sannan yace ya aiki? Murmushi yayi yace Alhamdulillah gashinan muna ta tayi. Ajiyar zuciya yasafke yace hakane saidai nasan ka yi mamakin zuwana wajenka ko? Ta'be baki Faruk yayi yace ko d'aya dan nasan zuwanka yana da nasaba da Alhaji Mansur a matsayinka na lauyanshi da wad'anda suke k'ara. Jinjina kai yayi yace tabbas hakane ammah Barrister ka bani mamaki ace wai kaine da kanka kake zarginsu abun kunyanma har da surukinka dan kawai sun hanaka auren d'iyarsu, hakan bai dace da kai ba dan duk garin nan inzaka kewaye babu wanda bai san arzik'in nan nasu bane ko da Alhaji Muhammad yana da kud'i ammah bayada kud'in da zasu nemi suci dukiyarshi ya kamata kasan irin abinda yake fitowa daga bakinka a matsayinka na lauyan wadda ake k'ara. Murmushi ne yabayyana a fuskar Barr Faruk yazuba mashi idanu yana kallo har saida yakai aya sannan yace dakyau Barrister aikinka yana kyau, saidai maganar da kayi akwai gyara a cikinta dan ko da ace kowa zai yarda da cewa dukiyarsu ce toh ni bazan ta'ba yarda da hakan ba dan nasan ba dukanta bace dukiyarsu, kaidai kawai katsaya a matsayinka baka san komai ba akai kabarni da su kawai dan duk abinda zaka fad'a ba zan ta'ba yarda ba dan ni nasan abinda baka saniba, am ina da abunyi idan babu sauran abinda yakawoka zaka iya tafiya saidai ince sai munhad'u a kotu. Murmushi Barr Mahamud Bello yayi yace toh shikenan tunda ka ce haka ammah Barrister ya kamata kabi a sannu akan su Alhaji Mansur gudun kar wani abu yafaru. Jinjina kai kawai yayi yabud'e motarshi yashiga sannan yayi horn megadi yazo yahangeme mashi gate d'in gidansu yacinna motarshi a ciki inda Barr Mb yashiga tashi motar yakama gabanshi...... _Sis Nerja'art✍🏻_ [7/24, 11:14 PM] Sis Nerja'art 2: *......FANSAR RAI......* *INTELLIGENT WRITER'S ASSO....®* [On Ward Together] _Follow me on Wattpad: *Sis-nerja*_ _Wannan Littafin na kud'i ne domin karantawa cikin aminci da yarda ga duk me buk'ata zai turo katin Mtn na d'ari biyu N200 kacal ta wannan number d'in 09035938246, ko ta account number 5330055604, Idan katura ka aiko da screen shot na transaction a wannan number d'in 09035938246_ _Akwai gara'basar *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shahararriyar marubuciyar nan *AMEENA ABBA UMAR* tare da novel d'in *FANSAR RAI* akan farashin N300 kacal, ko da kud'in ka sai da rabonka_ *PAGE 15* Alhaji Mansur da yake manne da waya a kunnenshi duk ya saurari komai su Barr Faruk suka tattauna kasancewar sa Barr MB yayi yakirashi a waya yadda zai saurari hirar tasu, yana gama saurare wurgi yayi da wayar tare da komawa yazauna yace lallai yaron chan ya cika taurin kai idan har bai janye k'udurinshi ba ya zama dole inyi wani abu akanshi dan bai isa ya'bata min duk wani shirye shirye na ba. Toh ammah ta ya yakamata in'bullo mashi? Shuru yayi yana tunani sai kuma chan yayi murmushi yace idan ka san wata bakasan wata ba nan yatashi yad'auko wayarshi. Washe gari yana office d'inshi zaune ya d'age kanshi sama yana kallon ceiling a ka ga yanayinhi ka san tunani yake, yana nan a haka sai ji yayi anturo k'ofar d'akin anshigo. 'Dago kai yayi dan ganin wanene yashigo batare da annemi iziniba karaf suka had'a idanu da Nasiba yanayin yadda tashigo babu alamun fara'a a fuskarta yasa yagane akwai wata a k'asa, zaune yayi yana kallonta har ta iso wajen table d'in da yake gabanshi, kujera yanuna mata yace bismillah kizauna. Zare glass d'in da yake fuskarta tayi tare da yatsina fuska tace ba wannan yakawoni wajenka ba Faruk. Murmushi yayi cikin ranshi yace na san za'a rina,,, ajiye jakkarta tayi saman table d'in sannan tace na zo ne inyi maka godiya akan abinda kayi ma mahaifina Faruk tabbas kai butulu ne ban ta'ba sanin haka ba sai a yanzu, na yi da nasani da har na amince namallaka maka zuciyata, ina maka kallon mutumin kirki wanda nakeso yakasance abokin rayuwata ashe har akwai ranar da zakaje kakalli tsabar idanun mahaifina kaci mashi mutunci har kazargeshi akan kisan wani. Dafe kanshi yayi da hannuwanshi duka biyu jin tana neman tak'ara mashi wani zafin da yake saman kanshi, muryarta yaji ta fashe da kuka dan haka yad'ago kanshi cikin sanyin murya yace haba Nasiba meyasa zakice haka bayan ke bakisan abinda yake faruwaba. Cikin d'aga murya tace taya zan san abinda yake faruwa bayan ka ci mana mutunci tabbas kai butulu ne Faruk kuma insha Allahu kamar yadda kaso katozarta mahaifina ubangiji bazai ta'ba baka daman haka ba, na yi nadamar saninka a rayuwata Faruk. Saurin mik'ewa yayi tsaye yace wai wace irin maganace kikeyi haka Nasiba baidace kice hakaba ni fa akan aikina nake ba wai tozarta mahaifinki nakeson yi ba. Koma me zakace kafad'a Faruk nima kaina ban wuce matsayin da zaka tozartani ba, ashe wannan dalilin ne yasa kace insamo maka number d'in Alhaji Mansur dan kawai sun hanaka aurena shine zaka 'bullo masu ta wannan hanyar har kana ik'irarin cewa gidan mahaifina ba nashi bane, wai me yake damunka ne haka faruk!? Ajiyar zuciya yasafke yace Nasiba yakamata kifamceni duk yadda kike tunani ba haka bane. 'Daga mashi hannu tayi fuskarta sha'be sha'be da hawaye tace babu abinda zanji daga gareka bayan wanda kayi ahakan ma nagode Faruk a yanzu na ida tabbatarwa kai d'in ba masoyina bane mutum ne meson tozarta ni, ashe nikad'ai nake haukana na d'auki soyayyata na baka da zuciya d'aya kaikuma a wajenka ba hakaba nagode sosai Faruk na tayaka murna da kayi silar zubar da hawayena sannan kayi yadda kakeso rayuwace ubangiji yana sane da duk abinda kake aikatawa, na barka lafiya, jakkarta tad'auka cikin sauri tajuya tafita tabar d'akin. Dunk'ule hannuwanshi yayi yabuga a jikin table d'in da yake gabanshi yace meyasa haka Nasiba? Meyasa bazaki saurareni ba? Hannu yasa yashafa kanshi tare da wucewa cike da tashin hankali yakoma bayan kujerarshi yatsaya nan yafuzgar da wata irin iska me zafi daga bakinshi kan kace mi ya fara zufa, wayarshi ce tafara ringing ammah ko kallon wajen da take ajiye baiyi ba, komawa yayi yazauna tare da dafe kanshi da dukkan hannuwanshi biyu cikin d'aga murya yace daman nasan ba kowane zai fahimceni ba tabbas wannan shine matsalar da jawahir take ji min tsoron inshiga, na rasa masoyiyata adalilin case d'inta ammah ya zama dole inyi abinda yadace dasannu zan maido da martabar soyayyata, nasiba bazan ta'ba bari inrasaki ba zanyi k'ok'ari sosai wajen ganin kowa ya fahimceni, ya fi awa d'aya a nan zaune yana ta 'yan tunane tunane kafin daga baya yadanna k'ararrawa masinja yashigo wasu files ne yad'auko yamik'a mashi yace wad'annan kakaisu office d'in Director sannan yamik'e yahad'a duk abinda yake buk'ata yafita, tunda yafito daga office d'in yanufi harabar da motocinsu suke wata bak'ar mota ce Jeep yaga a kusa da tashi motar saboda glass d'in bak'ine yasa bai lura da mutanen da suke cikiba saidai bai ta'ba ganin wani ma'aikacinsu a cikin motar ba, ganin ta d'an tare mashi hanya yasa yanufi wajen zaiyi knocking d'in glass dan amatsa yafitar da tashi motar, tun kan ya isa sai gani yayi anja motar antafi dan haka shima yashiga tashi yakama gabanshi. Yana cikin tuk'i Daddynshi yakirashi a waya yace kazo gida kasameni yanzu murmushi yayi yace toh Daddy ganinan zuwa ina hanya. Bayan sun gama wayar cikin ranshi yace Allah yasa dai lafiya. Yana isa yasameshi a parlornshi zaune ganinshi yasa yanuna mashi waje alamun yazo yazauna. Fuskarshi d'auke da murmushi yace toh Dad, kallon drink d'in da yake saman table yayi ganin haka yasa Dad yad'auko cup yatsiyaya yamik'a mashi, amsa yayi tare da yin godiya sannan yafara sha. Gyaran murya Alhaji Sani yayi sannan yace Faruk me yahad'aka da Alhaji Sufyan. Saurin janye kofin yayi daga bakinshi yace na'am Dad. 'Daga kai yayi yace na san ka ji abinda nace. Shuru yayi cikin ranshi yace watau har ya sanar da Dad,, muryar Dad yaji ya ce kai nake saurare. 'Dagowa yayi yakalli mahaifin nashi yace babu komai Dad. A'a bazakace babu komai ba kaga Faruk banson rigima kafita harkar Alhaji Sufyan dan shi ba abokin yinka bane nayi mamaki sosai da naji wai kaine kaje har gida kaci mashi mutunci har kana fad'a mashi cewa wai gidanshi ba mallakinshi bane, wa ya aikeka ko ma ince ina kaji hakan? Jikin shi sanyi yayi sosai yace kayi hak'uri Dad ina akan aikina ne. "Dakata banason irin haka kar insake ji ka shiga harkarshi dan shi d'an siyasa ne ka san yana da kud'in da zai mallaki fiye da wannan gidan, sannan katsaya iya aikinka babu ruwanka da duk abinda bai shafeka ba. Har ya bud'e baki zaiyi magana sai kuma yafasa dan ya san ba lallai ne Dad yafahimci abinda zai fad'a ba, Dad yace ka yi shuru. Toh Dad insha Allahu. Yauwa haka nakeson ji Son. Murmushi yayi yace toh Dad. Kallon agogo Dad yayi yace bari intashi daman fita zanyi natsaya jiranka. Shikenan Dad sai ka dawo. Zaune yayi wajen har mahaifin nashi yatashi yatafi sai kuma chan shima yamik'e yakoma part d'inshi, yana jin babu dad'i a cikin ranshi. ______Da dare yana kwance yana ta tunanin yadda zai 'bullo ma lamarin dan hankalinshi ya tashi sosai da aka saka mahaifinshi a ciki saboda indai dan shine kar mahaifansa susan komai a game da wannan case d'in, yana nan kwance bai saniba har k'arfe d'aya tagota, dariya ce yafara jiyowa a falon d'akinshi tana tashi, saurin tashi yayi zaune cikin ranshi yace wannan dariyar fa? Ji yayi ancigaba da yi babu k'ak'k'autawa dan haka yakunna fitila tare da mik'ewa tsaye yanufi hanyar fita, yana bud'e k'ofar bedroom d'in sai yaji kamar takun mutum ana tafiya a chan babban parlor sautin dariyar yana cigaba da tashi kasancewar da k'arfi akeyinta, ji yayi kamar yajuya yakoma bedroom d'inshi sai kuma yafasa dan yanaso yaga me yin dariyar dan haka yabud'e k'ofa yafita daga saman matattakalar bene yatsaya yaji ana cigaba da taku na tafiya ammah baiga kowaba dan haka yagane Ammin jawahir ce har ya bud'e baki zaiyi magana sai kuma yafasa saboda kar su Dad sujiyo dan haka yajuya yakoma part d'inshi, yana shiga bedroom yamaida yarufe juyowar da zaiyi sai ganinta yayi a tsaye bayanshi cikin siffar da tasaba bayyana saidai wannan karon gashin nan nata farine kal har yana ta'ba k'asa saboda tsawonshi tana tsaye da 'yar sandarta tana kallonshi da k'wala k'walan idanunta wanda girmansu sun kai na goruba saurin jingine jikinshi yayi a jikin k'ofa cikin dakiya yace mi yakawo ki wajena? Bushewa tayi da dariya wadda tasa gabad'aya d'akin saida ya amsa, saida tayi me isarta sannan tabud'e baki cikin kakkausar murya tace aduk lokacin da naso ganin mutum ina bayyana a gareshi kuma kaima ka san haka, bana neman umurni bare har abani izini,,, dogara sandarta tayi tana tafiya a dudduk'e har saida taje tsakiyar d'akin sannan tatsaya tare da juyowa takalleshi yana nan tsaye a inda yake, sake bushewa tayi da wata dariyar tayi wadda ta wannan karon ta sha bambam da ta farko da wannan jinta yayi kamar kukan jaki saboda rashin dad'inta saida tayi me isarta sannan tace babu abinda zaka iya yi akan case d'in su Alhaji Mansur domin wuk'a da nama duk suna a hannu na sai na kashesu kamar yadda sukayi silar barina duniya ni da mijina sannan zan tseratar da d'iyata daga gidan kaso da kaina. Cikin nuna rashin tsoro yace wannan ne bazaki iyaba domin tun farko yakamata kitseratar da ita ammah kika kasa, sannan maganar su Alhaji Mansur na riga na maido case d'in a hannuna ni yadace inwanke jawahir a idanun duniya sannan inyi silar da zaisa arufesu a gidan yari ayi masu d'aurin rai da rai. Sake bushewa tayi da dariya sannan tace bakada iko a wannan hurumin domin nice me power, ina sake gargad'inka akan kajanye hannunka a cikin case d'in nan domin tseratar da kanta daga bala'o'in da suke tunkarar rayuwarka, su Alhaji Mansur bazasu ta'ba barinka ba zasuyi k'ok'arin ganin sunga bayanka ammah idan har ka za'bi mutuwarka akan komai toh shikenan saidai duk wannan abun da kake bai ta'ba burgeni ba dan nasan wuk'a da nama suna a hannuna. Nunata yayi da yatsaya yace ke d'in azzalluma ce bawai kina taimakon jawahir bane kawai dai kina cutar da rayuwarta ne gashinan ta dalilinki kowa guje mata yake. Wata irin razanannar k'ara tasaki wadda tasa har saida akayi k'aramar girgizar k'asa a cikin d'akin. Saurin toshe kunnuwanshi yayi har saida k'arar talafa sannan yasakesu. Nunashi tayi da yatsanta cikin 'bacin rai tace idan har kacigaba da jifata da munanan kalamai zan d'and'ana maka azabata. Bud'e baki yayi zaiyi magana sai ji yayi kamar anrik'e bakin nashi, juyawa tayi baya tace bana buk'atar jin komai daga gareka, nan tafara takawa tink'is tink'is tanufi wajen da ya ajiye briefcase d'inshi ganin haka yasa Faruk cikin sauri yanufi wajen da take, juyowa tayi ahankali tare da nunashi da hannunta nan wata irin iska tataso sai ji yayi and'aukeshi anyi wurgi da shi gefe d'aya ya fad'i kanshi ya bugu da k'asa. Jawahir da take k'wance a cikin d'an kurkukun d'akinta tana bacci cikin daren nan, lokaci guda tafarka tare da fasa k'ara da dukkan k'arfinta wadda tasa saida duk mutanen da suke kusa da d'akin da take suka farka, hatta shi kanshi megadin saida yafarka rik'e kanta tayi tare da jan gashinta da dukkan k'arfinta ahankali tace a'a Ammi kar ki aikata haka ya kamata kibar Barr Faruk kar kiyi mashi komai bai chanchanci hakan daga garekiba, bazan ta'ba bari kiyi mashi wani abu ba, 'Daga murya tayi tace a'a Ammi na ce kar kiyiiiii!! waige waige tafara yi chan kuma tamik'e cikin sauri tanufi wajen bango tana zuwa tabuga kanta da k'arfi, wani irin zafi ne taji ammah ahaka tasake bugawa nan take jini yawanke mata fuska tasulale k'asa a hankali tare da furta sunan Amminta. Daidai lokacin maigadi ya iso d'akin yadallota da fitila ganinta a kwance shame shame yasa yayi saurin bud'e k'ofar yashiga. Ammi ko da komai yafaru a cikin kunnenta ta jiyo sautin d'iyartata tsayawa tayi chak a inda take tsaye tare da fasa k'arar da tasa saida Faruk yafarfad'o daga suman da yayi, cikin d'aga murya tace a'a jawahir bazan ta'ba bari wani abu yasameki ba, nan take tayi girgiza ta'bace. Yunk'urin tashi yayi daga inda yake kwance ammah yakasa jin jikinshi yayi duk yana yi mashi ciwo saboda buguwar da yayi, dafe kanshi yayi da hannunshi sai a lokacin yasamu damar fara karanto addu'o'i sannan yasamu yamik'e dak'yar yanufi toilet, ruwan zafi yahad'a yagasa jikinshi bayan ya fito ne yanufi wajen briefcase d'inshi yabud'e ajiyar zuciya yasafke ganin bata ta'ba mashi komai ba saidai me ya jiyo lokacin da tafurta sunan jawahir to me yafaru da ita? Jin k'arar bugawar agogo alamun k'arfe ukku yasa yakwanta yana jin jikinshi duk yana mashi ciwo ahaka yasamu yayi bacci. ____ Megadi yana shiga d'akin tsaye yayi a wajen kan jawahir cike da mamaki ganin ko kad'an bata motsi ga jini yana fita daga goshinta hakan yasa yayi saurin fita yad'auko wayarshi yakira shugaban su yasanar da shi halin da ake ciki, nan da nan aka kira First Aid Member na prison d'in sukazo suka fara mata dressing ammah jinin bai tsayaba, ruwa aka d'ebo aka watsa mata bata farfad'o ba daga suman da tayi sunyi kusan minti talatin akanta ganin har lokacin bata farfad'oba yasa suka kira shugaban suka sanar da shi yace to suyi k'ok'ari sutsayar da jinin da yake zuban kafin zuwa safe idan har bata farfad'oba sai akaita asibiti. Haka ko akayi har asuba bata farfad'oba dan haka ana yin sallah aka d'auketa aka saka cikin mota aka nufi asibiti da ita inda motocin 'yansanda biyu suka rakasu har babban asibiti da ke cikin garin, a emergency unit aka wuce da ita a lokacin cike yake babu gado dan haka aka kama mata d'aki a aminity aka kwantar da ita nan likitoci suka yo kanta ganin daga gidan yari akazo da ita, dubata sukayi sannan suka nad'e mata kai da bandage bayan sunyi mata dressing sannan suka sa mata drip, daga k'ofar d'akinta 'yansanda biyar ne tsaye suna kaiwa da kawowa. Sai wajen k'arfe goma sha biyu sannan tafarfad'o daga suman da tayi. Tana bud'e idanunta taganta kwance a wani wajen na daban mamakine yakamata tace ina ne nake nan? Yunk'urin tashi tayi sai kuma takasa, hannu tasa tafizge drip d'in da aka sa mata tatashi zaune tare da dafe kanta da taji kamar zai cire saboda tsananin ciwon da yakeyi mata, daidai lokacin doctor yashigo yana ganinta yayi saurin nufo inda take yace lafiya me yafaru? Runtse idanunta tayi tana ji kamar zai fad'o nan yazo yarik'eta takoma takwanta yamaida mata drip d'in sannan yafita yarubuta wata allura yace aje asamo yanzu zaiyi mata ita. Ba a dad'eba aka kawo allurar yayi mata sannan yafita yace kar wanda yashiga abarta tana buk'atar samun hutu tsawon awanni bakwai, nan suka amsa da toh sannan yawuce, d'aya daga cikin police d'inne yabud'e d'akin yalek'a ganinta a kwance yasa yamaida k'ofar yarufe..... _Sis Nerja'art✍🏻_ [7/24, 11:14 PM] Sis Nerja'art 2: *......FANSAR RAI......* *INTELLIGENT WRITER'S ASSO....®* [On Ward Together] _Follow me on Wattpad: *Sis-nerja*_ _Wannan Littafin na kud'i ne domin karantawa cikin aminci da yarda ga duk me buk'ata zai turo katin Mtn na d'ari biyu N200 kacal ta wannan number d'in 09035938246, ko ta account number 5330055604, Idan katura ka aiko da screen shot na transaction a wannan number d'in 09035938246_ _Akwai gara'basar *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shahararriyar marubuciyar nan *AMEENA ABBA UMAR* tare da novel d'in *FANSAR RAI* akan farashin N300 kacal, ko da kud'in ka sai da rabonka_ *PAGE 16* ...Yana gama shirin shi ko wajen aiki bai biyaba yau yawuce gidan kaso dan yana so yaga halin da jawahir take ciki yana isa yasamu labarin abinda yafaru dan haka daga nan yawuce asibitin, yana isa likita yana fitowa daga d'akin yatabbatar masu da har lokacin bacci take. Awanta biyar tana baccin lokaci guda tabud'e idanunta tafara waresu a cikin d'akin ganin babu kowa yasa tatashi zaune hannunta takalla wanda aka sa ma kanula tasa gudan hannun tafizgeta sannan tayi saurin safkowa daga saman gadon, fara takawa tayi ahankali tanufi wajen taga, d'an d'age labule tayi talek'a ganinsu tayi tsaye wasu zazzauna a k'ofar d'akin, ganin wani yana shirin kallon tagar yasa tayi saurin sakin labulen tare da komawa takwanta tana ji suka bud'e d'akin suka lek'ota sannan suka maida suka rufe, tana jin sun rufe tatashi zaune tana bin d'akin da kallo kamar me neman wani abu sai kuma chan tamik'e wasu kaya tahango ajiye saman 'yar k'aramar drowar da take cikin d'akin cikin sauri taje tad'auka tashiga toilet nan tatsaya tana bin toilet d'in da kallo, 'yar tagar da tagani ne yasa tayi murmushi ajiye kayan tayi sannan tataka drum talek'a tagar, ganin wajene bayan d'akin yasa tasafko tad'auki kayan tasaka nan tafara tunanin ta yadda zata iya fita, juyowa tayi taje tarufe k'ofar toilet d'in ahankali sannan tataka drum d'in taja ragar (net) d'in tagar da k'arfi ammah tak'i 'balluwa dan haka tasa bakinta tafara ciccirewa da hak'oranta abinda zai baka mamaki kamar ba hak'oran mutum ba yanayin yadda take cire ragar da su saida tafara cire na 'bari guda sannan tasa hannunta taja dak'arfi sai gashi ta 'ba'b'bakota gabad'aya, koda tagar ba wani girma gareta ba ammah ahaka tatura kanta tafitar da shi saida taga babu motsin kowa a wajen sannan ta ida fidda jikinta dakyar tadira bayan ginin, gyalen kayanta tasa tarufe fuskarta da shi sannan cikin sauri tawuce zata zagaya tana 'bullowa sai ganin 'yansandar tayi tsaye a gaban d'akin suna kaiwa da kawowa dan haka sai tak'ara jan mayafinta a fuskarta sannan tacanza hanya cikin sauri tafita tabar asibitin tana fita tasamu me napep tatsaida tafad'a mata anguwar da zai kaita cikin sauri tashiga tace suje dan haka yajata suka tafi, tana yi tana kallon agogon da ke manne a gaban napep d'in har suka isa inda tace yakaita, suna isa tafita daga napep d'in tajuya zata tafi me keke napep d'in yace Hajiya kud'ina. Tsayawa tayi cak tare da juyowa dan ita ta ma mance da zata biya wasu kud'i gashi batada su, k'ara maimaita mata yayi. Ahankali tace kud'i? A'a kayi hak'uri banda su. Harara yawurga mata yace da kinsan bakida kud'in shine zaki shigo min napep. Ganin wani mutum ya nufo wajen yasa tad'aga murya tace dan Allah kayi hak'uri wallahi a rud'e nake saisa ban tsaya d'auko kud'i ba, fitowa yayi daga cikin napep d'in yace wallahi babu inda zakije sai kin biyani kud'ina. Ganin haka yasa mutumin yanufo wajen yana cewa lafiya me yafaru? Cikin fushi me napep d'in yace wannan yarinyar ce dan rainin wayo zata shigo min napep bayan na kawota inda takeso sai tace min batada kud'i. Kallonta mutumin yayi yace haka akayi? 'Daga kai tayi alamun Eh. Toh shikenan ni zan biya nawa ne kud'in naka? Jawahir tana jin haka sai tayi murmushi tace nagode sosai sannan tajuya tatafi cikin sauri, tana zuwa k'ofar gate d'in gidan taja tatsaya kamar tayi knocking sai kuma tafasa, tura k'ofar gidan tayi ahankali sai jin motsi tayi a toilet na wajen k'ofar alamun megadin yana ciki dan haka tatura tashiga tamaida tarufe sannan tafara takawa sad'af sad'af ahaka tanufi hanyar cikin gidan tana shiga nan ma shuru batare da wani tsoro ba tafara taka matattakalar benen ahaka tahau sannan tamurd'a k'ofar wani d'aki jinta a bud'e yasa tad'an bud'e ahankali sai gani tayi babu kowa a ciki, k'arar shower tajiyo a toilet dan haka tabud'e d'akin ahankali tashiga tana lalla'bawa dan kar ajiyo k'arar takun ta, daga tsakiyar d'akin tatsaya tana binshi da kallo sai kuma chan tanufi wajen bedside tana zuwa tajawo drower k'asa tajita a datse dan haka tabud'e ta saman taji ita kuma a bud'e, lalubawa tafara yi sai ga key ta gani tafiddo cikin sauri tabud'e ta k'asar tana jawowa sai ga wasu files a ciki fiddosu tayi gabad'aya tafara dubawa daidai lokacin taji anrage k'arfin shower d'in, bubbud'ewa tayi cikin sauri tana dubawa tad'auko wasu files guda biyu tamaida sauran tarufe drower sannan tad'auka, jiyo murya tayi a cikin toilet d'in ana cewa Hajiya ke ce ganinan ina wanka, mik'o min towel. Kallon k'ofar toilet d'in tayi sannan tawuce cikin sauri tafita tarufe d'akin, dagudu tasfka daga saman benen, hayaniya tafara jiyowa a gudan d'akin na mutanen gidan dan haka cikin sauri tafita, a filin gidan tasamu megadi tsaye saita nutsuwarta tayi sannan tawuce zata fita, kallonta yayi ammah ita ko bata kalli inda yakeba tana ji yace sannu Hajiya dan ya d'auka ko k'awar d'iyar gidan ce, amsawa tayi sannan yabud'e mata k'ofa taficce. Tana fita ajiyar zuciya tasafke dan ita kanta ta san ba k'aramin namijin k'ok'ari tayiba da har tayi kasadar shiga cikin gidan, takawa tafara yi har tasamu napep tashiga sannan tafad'a mashi inda zai kaita ranta fal da farin ciki ta yi nasarar samo abinda takeso, ahaka har suka isa asibitin, suna isa talaluba dan tabashi kud'i sai taji wayam ba jakka ajiyar zuciya tasafke cikin ranta tace da da yanzu ba d'aya bane, muryar dattijon taji ya ce d'iyata munzo. Cikin sanyin jiki tace kayi hak'uri baba ina tunanin kud'in da zan biyaka ne ashe babu kud'i atare da ni. Juyowa yayi yakalleta yace kamar ya bakida kud'i ai bakiyi kama da marassa kud'iba d'iyata. Cikin sanyin jiki tace dagaske nake Baba wallahi banda su. Gyad'a kai yayi yace toh shikenan jeki kawai na yafe. Godiya tayi mashi cikin jin dad'i sannan tafita, tafiya tafara yi bata ankaraba sai gata ta gaban 'yansandan nan cikin sauri tajawo gyalen tasake rufe fuskarta, murya Barr Faruk tajuyo da bai dad'e da dawowa asibitin ba alamun yana waya dan haka tadake tawuce tazagaya baya babu wanda yaganeta daga cikinsu, tsayawa tayi saida taga wasu mutane sun wuce sannan tataka dakali tawurga files d'in ta cikin tagar sannan itama tasamu tahau tadira aciki, tana dirawa tayi saurin cire kayan jikinta ta ajiye a nan cikin toilet d'in tad'auko unifoam d'inta na gidan yari tasaka sannan tad'auko files d'in, saida tad'an kanga kunnenta a wajen k'ofa jin ba motsin kowa yasa tabud'e ahankali tashiga, saurin jawo 'yar k'aramar drower da take ajiye cikin room d'in tayi wadda aka ajiye saboda ajiye ma patient kaya, tasaka files d'in. Doctor ne yatafo yana cewa bari inshiga yanzu lokacin farkawarta ya yi idan har mukaga ta farka babu wani ciwo atare da ita sai mu sallameku, d'aya daga cikin masu kula da gidan yarin ne yace tabbas hakan yakamata Doctor dan yarinyar chan tana da had'ari zamanta a gidan yari shine kwanciyar hankalinmu, shidai bai fahimci abinda yake nufiba saidai yayi murmushi yabud'e k'ofar yashiga. Kwance yasameta ta lulle'be har fuskarta yana isa yajanye mayafin ahankali tabud'e idanunta, murmushi yayi yace ashe kin farka ai na d'auka yanzu ne yakamata ace allurar ta sakeki, shuru tayi tana binshi da kallo, kallon hannunta yayi yaga ba kanula yace ya akayi kika cire? Kallon hannun nata tayi sannan tace am daman daman na ji yana min zafi ne. Ohk, akwai inda yake maki ciwo yanzu? Girgiza kai tayi, nan yasake dubata yace saidai na san har yanzu kina jin ciwon kan ammah zasu dinga maki dressing d'in ciwon naki. Batace komai ba saima kallonshi da takeyi ganin haka yasa yarubuta mata sallama tare da magungunan da za'a siya mata bayan ya gama yafita yasanar da su dan haka wasu police mata biyu suka shigo tana a nan inda take kwance suka saka mata ankwa a hannu, kallon hannuwanta tayi sannan tatashi suka izata a gaba suka fita da ita d'akin nan duk 'yansandar suka rufa masu baya, juyawa tayi takalli Faruk da yake waya har lokacin shima ya juyo yana kallonta, motsa baki tayi alamun tana son yin magana sai kuma tafasa sai tayi mashi nuni da idanu alamun yazo yaji. Kashe wayar yayi yatako wajen yana zuwa yatsaya yace har an sallameta sukace eh, Bakinta takai saitin kunnenshi tarad'a mashi wani abu wanda babu wanda yaji abinda tace sannan tawuce aka tafi da ita. Tsayawa yayi a wajen har suka wuce sannan yaje yashiga d'akin yaduba drower yafiddo files d'in, tsaye yayi yana kallon files d'in mamaki duk ya cikashi cikin ranshi yace ita kuma ina tasamosu ko dai ta fita daga gidan kason nan? Kallon d'akin yayi yace ammah kuma ai ba hanyar da zata fita batare da ansaniba, wayarshi ce da tafara ringing yasa yayi saurin fita daga d'akin tare da kanga wayar a kunnenshi yanufi wajen motarshi. Yana komawa gida zama yayi yabud'e files d'in yana dubawa cikin ranshi duk mamaki ya gama cikashi ganin yadda akayi tasamesu, chan kuma yayi murmushi yace wannan aikin naki ya yi sosai Jawahir, toh ammah idan yazama Amminta ce tad'auko su fa? Girgiza kai yayi yace wannan ne kuma bansaniba ko ma ya akayi na ji dad'in samunsu sosai. Wayarshi yad'auko yad'auki files d'in hoto sannan ya ajiye yashiga shigar da su acikin laptop d'inshi bayan ya gama ne yakira Barr Nas a waya suka tattauna daga nan kuma yatashi yafara shirin fita. A chan 'bangaren Alhaji Mansur hankalinshi a tashe yake sosai akan yadda Barr Faruk yakeson ganin ya tona masu asirin da yake binne babu wanda yasan da shi dan haka yafara tunanin yadda zai 'bullo mashi. Ranar wata talata Barr Faruk yana gida da marece Alhaji Mansur yakirashi a waya, ya yi mamakin ganin kiran nashi sosai kamar ba zai d'agaba har tatsinke yana tunanin kiran me yakeyi mashi chan sai wani kiran yasake shigowa dan haka yayi picking batare da yayi magana ba. Jin anyi picking yasa Alhaji Mansur yakalli nakusa da shi yayi murmushi sannan yace Barrister ina fatan kana jina? Daga chan 'bangaren Faruk yace Eh ina ji. Mik'ewa yayi tsaye sannan yace idan babu damuwa inaso yanzu muhad'u da kai a gida akwai maganar da nakeso muyi. Shuru Faruk yayi baice komai ba. Ganin haka yasa Alhaji Mansur yayi tunanin ko bai yarda da shi ba dan haka yace inma bazaka zo ba toh kafad'i inda yadace muhad'u. Cikin gadara da nuna isa yace idan zaka iya zamu had'u a chan Rahama Restuarent. Toh shikenan nan da rabin awa zaka sameni a chan. Batare da ya amsaba yakashe wayar. Tsaki Alhaji Mansur yayi yace yaron nan ya cika jin kan tsiya shi gani yake kamar shi wanine ammah bakomai zan safke mashi girman kan nan nashi bari inje inshirya intafi duk yadda mukayi da shi zaka ji. Suna gama wayar yatashi yashiga wanka yashirya yafita. Yana isa Rahama Restuarent babu mutane sosai a ciki yaja kujera yazauna nan yabada umurni akawo mashi coffee yana cikin sha ne Alhaji Mansur ya iso yafara ware idanu yana tunanin inda zai zauna kafin Faruk ya iso da mamakinshi sai hangoshi yayi zaune, murmushi yayi sannan yanufi wajen yaja kujera yazauna yace ashe har ka iso. Batare da ya kalleshiba yace Eh, me kake buk'ata akawo maka? Yatsina fuska yayi yace bana buk'atar komai. Batare da ya ce komai ba yacigaba da shan cofee d'inshi, Alhaji mansur hannu yasa a aljihu yazaro cheque ya ajiye mashi a gabanshi yana murmushi yace gashi Batare da ya kalli cheque d'inba yace menene wannan? 'Yar dariya yayi sannan yace abokan rayuwa ne mana kakalla kagani. Kallon cheque d'in yayi yai murmushi sannan yacigaba da shan coffeen shi. Ganin haka yasa Alhaji Mansur yayi tunanin ya yi nasara yace wannan gabad'aya na mallaka maka su kaje kacire inma basu ishekaba kayi min magana ink'ara maka wasu. Sai a lokacin ya ajiye coffeen yad'auko cheque d'in yaduba murmushi yayi yace 5billions, me kakeso inyi maka ne? Bushewa Alhaji Mansur yayi da dariya yace dakyau haka akeso kud'i masu canza kowa, gyara zamanshi yayi yace yauwa ka yi tambaya mekyau abu d'aya nakeso kayi shine kajanye daga case d'in yarinyar chan, idan har kayi haka ni kuma zan k'ara maka linkin wad'annan kud'in. Jinjina kai Faruk yayi yana murmushi yace wannan ne daman dalilin kiran da kayi min. Eh shine kaga sai mutaru murufa ma juna asiri kai kaci dukiya ita kuma akasheta, kai kowane lokaci ma kaji kana son kud'i kakirani ni kuma zan aiko maka da su batare da 'bata lokaci ba. K'ara duba cheque d'in yayi gaba da baya sannan yayageshi yawurga mashi. Baki Alhaji Mansur yasaki yana kallonshi cike da mamaki yace kai kana da hankali kuwa? Ka san abinda ka aikata? Mik'ewa yayi tsaye lokaci guda fara'ar da take fuskarshi tagushe cikin d'aga murya yace ni ko nasan abinda na aikata dan ni ba irin sakarkarun lauyoyin da ake siya bane, idan har kanaso kaga 'bacin raina toh kace zaka siyeni da kud'i, ka kalli kanka kai ba abun kunya bane kakalli kamata kace zaka siyeni da kud'i? Ko ka mance wannan Barr Faruk Sani Maishadda ne lauyan gaskiya? K'ut Alhaji Mansur yahad'iye wani wahalallen yawu duk idanu suka raina fata dan bai d'auka zai ga haka daga wajen Faruk ba. Girgiza kai yayi yace bazaka ta'ba samun hakan daga gareniba dan ni aikina gaskiya nake karewa bana d'aure ma k'arya gindi dan haka kawai kasaurari nan da kwana biyar zamanmu a kotu, yana fad'in haka yajuya a fusace zai tafi sai jin muryar Alhaji Mansur yayi ya ce Faruk kar ka aikata wannan kuskuren dama ce guda d'aya nabaka kaje kayi tunani cikin kwana biyu idan har baka canza tunaninka ba toh komai zai iya faruwa. Ja yayi yatsaya har yagama sauraren maganar tashi sannan yawuce yayi tafiyarshi. Buga teburin Alhaji Mansur yayi tare da furta shiittt!! sannan yamik'e ranshi a 'bace yatafi... *BAYAN KWANA BIYU* Daddyn Faruk ne zaune a parlornshi hannunshi rik'e da Jarida yana dubawa inda gefenshi matarshi ce zaune tana dannar waya, wayarshi da take gefenshi ce tafara ruri nan yad'auko ganin number ce ba suna yasa yace ko wanene yake kirana da wannan number d'in? Hajiya Nuratu murmushi tayi tace kad'aga kaji ko wanene Alhaji. Bai musaba yayi picking tare da yin sallama. Wata irin murya yaji wadda babu alamun mutunci a cikinta akace ina fata ina magana da Alhaji Sani Maishadda? Kallon Haj Nuratu yayi da itama take kallonshi sannan yace Eh shine da wa nake magana? Sanin da wanda kake magana ba dole bane dan ba shine dalilin da yasa nakiraka ba saidai ina so kabud'e kunnuwanka kasaurareni dakyau, kaja ma d'anka kunne yafita daga harkarmu inko ba haka ba zaya gane cewa ya ta'bo tsuliyar dodo dan zamu farauci rayuwarshi. A kid'ime Dad yamik'e tsaye cike da tashin hankali yace Hello ina ji dan Allah me d'an nawa yayi maku? Bushewa akayi da dariya sannan akace bakaga komai ba daga cikin tashin hankali indai har bai zare hannuwanshi daga case d'in Jawahir ba dan indai har yace zai cigaba da kareta zamu kasheshi. Dad ida rud'ewa yayi cikin rawar murya yace dan Allah kuyi hak'uri kar kukashe shi wallahi shi kad'ai namallaka na yi maku alk'awali zai janye. Kar ma yajanye mudai mun fad'a maku kugargad'eshi dan yaron nan naku ya cika taurin kai saidai ba irinmu ake ma taurin kai ba dan zamu iya rabashi da rayuwarshi....ana fad'in haka aka tsinke kiran, Daddy nan yafara cewa hello hello ammah yaji shuru sai lokacin yagane cewa ankashe wayar, wurgi yayi da wayarshi saman kujerar tashin hankali k'arara yabayyana, Hajiya Nuratu da take tsaye gefenshi itama hankalinta a tashe ganin yadda mijin nata hankalinshi yatashi sosai tace Alhaji lafiya me yafaru. Alhaji Sani da yafara kwarara zufa kallonta yayi sannan yakoma yazauna nan itama tazauna gefenshi tace dan Allah kayi min bayani menene yafaru. Girgiza kai yayi yace Nuratu muna cikin matsala dan anfara farautar rayuwar Faruk akan aikinshi. Saurin dafe k'irji tayi cike da tashin hankali tace me? Rayuwar d'ana ake farauta? Me yatsare masu? Ajiyar zuciya Dad yasafke sannan yace akan wai case d'in Jawahir sukace idan har bai janyeba sai sun kasheshi. Fashewa da kuka Haj Nuratu tayi tace na shiga ukku d'an nawa zasu kashe? Inko har hakana ya zama dole ya ajiye aikin nan gabad'aya dan wallahi inason d'ana banason inrabu da shi. Cikin sanyin jiki Alhaji Sani yace wannan dolene Hajiya mik'o min wayata yanzu inkirashi. Mik'ewa tayi cikin sauri tad'auko mashi wayarshi tamik'a mashi tana cigaba da kuka cike da tashin hankali gabanta yana dukan ukku ukku akan kalmar kisa da aka furta za'a yi ma tilon d'anta..... _Sis Nerja'art✍🏻_ [7/24, 11:14 PM] Sis Nerja'art 2: *......FANSAR RAI......* *INTELLIGENT WRITER'S ASSO....®* [On Ward Together] _Follow me on Wattpad: *Sis-nerja*_ _Wannan Littafin na kud'i ne domin karantawa cikin aminci da yarda ga duk me buk'ata zai turo katin Mtn na d'ari biyu N200 kacal ta wannan number d'in 09035938246, ko ta account number 5330055604, Idan katura ka aiko da screen shot na transaction a wannan number d'in 09035938246_ _Akwai gara'basar *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shahararriyar marubuciyar nan *AMEENA ABBA UMAR* tare da novel d'in *FANSAR RAI* akan farashin N300 kacal, ko da kud'in ka sai da rabonka_ *PAGE 17* ....Lalubo number d'in Faruk Daddy yayi yakira ammah har tatsinke ba'ayi picking ba, dan haka yasake kira, saida yayi mashi 5 missed bai d'aga ba, lokacin Faruk yana gidan kaso wajen Jawahir ya bar wayarshi a cikin mota dan bai shiga da ita yanzu saboda a tsarin dokar gidan ba'a bari ashiga da waya shine ma ake d'aga mawa yana shiga da ita saboda kusancinshi da shugaban gidan saisa. Kallon Jawahir yayi da tunda yazo take zaune ta yi shuru jikinta ya yi sanyi sosai yace wai jawahir me yake faruwa da ke ne haka na d'auka abin farin cikine tunda kwanaki ukku kawai suka rage mana. Girgiza kai tayi tare da yin d'an guntun murmushi sannan tace Barrister bazaka fahimta bane ina tsoron halin su Alhaji Mansur su d'in mugaye ne sannan ina bak'in cikin abinda yafaru da kai da budurwarka duk a kaina. Murmushi yayi yace indan wannan ne kikwantar da hankalinki insha Allahu babu matsala sannan maganar Nasiba kibarta kawai na san fushi take da ni ammah da sannu zata safko dan muna son junanmu sosai. Gefe d'aya takalla tana murmushi ahankali tace Yaya Umar d'ina sai kuma tafashe da kuka. Hankalin Faruk tashi yayi yace Jawahir lafiya kukan me kikeyi haka? Girgiza kai tayi tace nima ban saniba saidai kawai ina son Yaya Umar tabbas Ammi ta cutar da rayuwata taya zan iya yafe mata wannan laifin da tayi min na rabani da rabin rayuwata? Shin ita batasan mecece soyayya ba? Shin ta mance yanayin da tashiga a lokacin da tarasa Abbuna?,,, mik'ewa tayi tsaye cikin muryar kuka tace na san bata mance hakan ba kawai dai ta yi amfani da son zuciyartane wajen rabani da masoyina. Mik'ewa shima yayi yace Jawahir kidaina tuna abinda yawuce. Taya zan daina tunawa bayan ta dasa min ciwon da bazai ta'ba warkewa a cikin zuciyataba, saurin sa hannu tayi tagoge hawayen fuskarta sannan tajuyo takalleshi tana murmushi tace ka ga katashi katafi azahar ta yi. Kallon agogon da take manne a tsintsiyar hannunshi yayi yace hakane bari intafi ammah bazan dawoba yau. Murmushi tayi tace ba damuwa Barrister hakan ma nagode a kowane lokaci ina maka fatan alkhairi a cikin rayuwarka, musamman akan jajircewarka a lokacin da kuka had'u da Alhaji Mansur ba kowane za'a ba wad'annan mak'udan kud'in ya iya barinsu ba. Da mamaki yake kallonta yace ya akayi kikasan hakan? Murmusai tayi a karo na biyu sannan tace wannan ba abun mamaki bane, yanzu dai katafi kar karasa jam'i. Jinjina kai yayi sannan yawuce yatafi. A nan cikin masallacin gidan kaso yayi sallah sannan yashiga motarshi bayan ya fita daga gidan ne yad'auko wayarshi sai ganin 5 missed call yayi yana dubawa yaga Dad ne mamaki yakamashi yace lafiya kuwa Dad yayi min wannan missed call? Dialing d'in number d'in Dad yayi, lokacin Dad yana tsaye yana kaiwa da kawowa hankalinshi a tashe yana add'ua Allah yasa ba wani abu yasamu d'an nashiba itako Mom zaune take tana fitar da sautin kuka ahankali adaidai lokacin wayarshi da take hannunshi tafara ringing, jikinshi yana rawa yaduba sai ganin Faruk yayi ajiyar zuciya yasafke sannan yad'auka ko sallama baiyi ba yace Faruk kana ina? Daga chan 'bangaren yace ganinan a mota Dad zan dawo gida lafiya dai ko? Muryar mom yajiyo tana cewa kace mashi yayi sauri yadawo gida yanzun nan, nan Dad yafad'a mashi. Amsawa yayi da toh duk sai jikinshi yaji ya yi sanyi ganin hankalin iyayenshi yadda yatashi dan haka yagane akwai dai wani abu, duk da yanaso yawuce gida saidai kuma yaji ya fiso yafara yin abinda zaiyi kafin yaje gida dan haka ya yalalubo wata number yakira yana gama wayar yak'ara ma motarshi gudu cikin k'ank'anin lokaci ya isa inda zaije. Baifi minti sha biyar ba yafito yatafi gida yana isa a parlor yasamesu cirko cirko suna ta kaiwa da kawowa ja yayi yatsaya yace Dad Mom lafiya naganku haka? Mom ce tayi saurin isowa wajenshi tare da fashewa da kuka, nan hankalinshi yatashi yace me yafaru Mom? Muryar Dad d'inshi yajiyo yana cewa dole katambayi me yafaru Faruk ka ja and'aga mana hankali toh wallahi bazamu iyaba ya zama dole ka ajiye aikin nan naka. Cikin rashin fahimtar abinda yafaru yace Dad me yasa? Me yafaru da har zakayi wannan furucin? Jinjina kai yayi yace Faruk komai ma ya faru akan aikin nan ake barazana da rayuwarka har ake kiranmu waya ana gargad'inmu idan har baka janye daga wani case ba za'a kasheka. Murmushi yayi yace haba Dad wai dan wannan ne kukwantar da hankalinku babu abinda zasuyi min kawai dai sun fad'a ne dan sutsorata ku. Mom ce tadaka mashi tsawar da bata ta'ba yi mashi irinta ba tace kai shashashan ina ne? Ina kata'ba jin anyi irin wannan? toh wallahi baka isaba Faruk ya zama dole ka ajiye aikin nan akan wani banzan case ka rasa matar da zaka aura ka 'bata da surukinka sannan kuma a yanzu wasu suna barazana da rayuwarka ai ba dole sai ka yi aikinba. Girgiza kai yayi yace a'a Mom dan Allah kar kuyi min haka. Muryar Dad ce takatseshi yace Faruk bamu shirya kwana zaune ba ka san dai bamuda wani d'a bayanka dan haka ya zama dole ka ajiye aikin nan gabad'aya dan gudun had'arin da yake cikinshi. Gaban Faruk saida yafad'i ahankali yace na shiga ukku menene yake faruwa da ni? Su wanene suka kira iyayena, tabbas nasan bai wuce mutane biyu,,, matsawa yayi wajen mahaifin nashi yace dan Allah Dad kuyi hak'uri kar kurabani da aikina wallahi sunyi hakane kawai dan injanye daga case d'in jawahir suna so sutauye mata hak'k'inta kuma janyewata daidai yake da rasa rayuwarta gashi na yi mata alk'awalin zan taimaketa kukwantar da hankalinku babu abinda zai faru da ni ina akan gaskiyata ubangiji yana tare da ni basu isa suyi min abinda Allah baiyi min ba su d'in azzalumai ne barinsu a doron k'asa daidai yake da cigaba da yad'uwar zaluncin su sannan.....wani irin gigitaccen mari Dad yad'aukeshi da shi wanda yasa saida yai saurin ja da baya tare da dafe kuncinshi yana kallon mahaifin nashi. Mom ce tace ka min daidai Alhaji. Cikin fad'a Dad yace kai wane irin shashasha ne wanda baisan abinda yakeba watau mu zakayi ma wa'azi ko? Toh bari kaji indai har mune iyayenka ya zama dole ka ajiye aikin nan yau yau d'innan. Inkuma ba haka ba saidai yaza'ba ko mu ko aikin,,, cewar mom cikin 'bacin rai. Runtse idanunshi yayi da suka kad'a sukayi jajir sannan yasulale yazauna k'asa dirshen ahankali yafara furta innalillahi wa'inna ilaihiraji'un, sannan yabud'e idanunshi yasafkesu akan iyayenshi muryarshi tana rawa yace Dad dan Allah kuyi hak'uri kutaimaka min kunsan girman alk'awali....mom ce takatseshi tace wallahi Faruk kasake magana sai na k'ara maka wani marin, aikine mun hana shi kuma idan har kai ka isa da mu kaje kayi yadda kakeso,,, tana fad'in haka tawuce a harzuk'e tabar wajen. Dad ma bayanta yabi suka bar Faruk nan zaune dirshen a k'asa, duka hannunshi yasa yadafe kanshi yace wannan wace irin *K'ADDARA CE* menene yake shirin faruwa da ni? Me yasa su Alhaji Mansur basubar abun a tsakaninmu ba saida suka saka iyayena a ciki? Ya jawahir zataji idan har taji labarin na janye? Wasu siraran hawaye ne suka gangaro mashi yace Mom Dad meyasa kuka kasa fahimtata? Wayarshi ce tafara ringing yashare kamar bazai d'agaba sai kuma yad'auko yana dubawa sai ganin number d'in Alhaji Mansur yayi dan haka yayi picking cikin 'bacin rai. Dariya ce tafara tashi sannan akace ya kaji salon namu Barrister? Ina fatan dai a yanzu ka janye gudun kar wani abu yasameka dan nasan iyayenka bazasu ta'ba jure ma rashinka ba. Murmushi yayi cike da takaici sannan yace hakan bazai ta'ba sawa injanyeba ina nan akan bakana, tabbas a yanzu na tabbatar ku d'in matsorata ne da har kukeson janyewata, ba jarumta bace ace kun biyo ta 'bangaren iyayena nine nan daidai da ku dani yakamata kukara. Daga chan 'bangaren akace kana nufin bazaka janyeba kenan? Eh ina nan aka bankana sai na kunyataku a idanun duniya idan har ina da numfashi kowa sai ya san ku d'in azzalumai ne. Dakyau Barrister kai d'in ka cika taurin kai ammah dasannu zamu saitaka muzuba mugani. Tsaki yaja sannan yakashe wayar ranshi duk a 'bace, wajen yayi zaune dirshen yana tunanin ina ma ace iyayenshi zasu fahimceshi ammah yanayin da yagansu ya san bazasu ta'ba fahimtarshi ba musamman Dad da yake kaifi d'aya, yana nan zaune yana neman mafita aka fara kiran sallar la'asar Dad yafito yawuce masallaci ko kalllon inda yake baiyi ba dan haka shima yatashi cikin sanyin jiki yanufi part d'inshi cikin sauri yawatsa ruwa sannan yad'auro alwallah yana fitowa yasaka kaya yad'auki wayarshi cikin sauri yanufi masallaci dan har antada sallah a lokacin. Saida yarasa raka'a biyu, bayan ya gama sallah zaune yayi a masallacin duk yana jinshi wani iri saidai yana kallon hakan akan abinda yafaru tsakaninshi da iyayenshi, saida yaga za'a fara sharar masallaci wajen k'arfe hud'u da rabi sannan yafito cikin sanyin jiki yataka yanufi gida, yana cikin tafiya sai ganin wata jeep yayi ta faka a gabanshi anbud'e k'ofar baya ko kallonta baiyiba yawuce zai tafi sai ji yayi ance dan Allah malam muna da tambaya. Juyowar da zaiyi nan aka watsa mashi wani farin abu a fuska, runtse idanunshi yayi nan yanemi yaruga suka jawoshi da k'arfin tsiya suka saka a mota daga nan bai sake sanin inda kanshi yake ba. Ahankali yafara bud'e idanunshi yana maidawa yalumshe, jijjagashi da akayine yasa yabud'e idanunshi nan yafara ganin mutanen da suke tsaye bibiyu, runtsewa yayi yasake bud'ewa sai ganinshi yayi cikin wani d'aki tsakiyar wasu mutane su biyar kowanensu d'auke da makami, yunk'urin tashi yayi sai a lokacin yajishi d'aure tamau, kallon kujerar da yake zaune samanta yayi ta roba and'aure mashi hannuwa da k'afafuwa, abinda yafaru da shine yafad'o mashi a rai yakalli mutanen da suke zagaye da shi dukkansu babu wanda fuskarshi take da kalar imani, d'aga murya yayi yace suwanene ku? Meyasa kuka kawoni nan? Su duka shuru sukayi suna kallonshi. Ganin haka yasa yakwatsa masu tsawa yace bakuji ina tambayarku nace wanene yakawoni nan wajen? Ko ku kurmaye ne? Daidai lokacin aka bud'e k'ofa aka shigo da mamaki yake kallon wanda yashigo ahankali yace Alhaji Mansur? Murmushi yayi yace tabbas nine barrister ashe ka farka ai tun jiya muke nan tare da kai kana ta bacci lallai da alama baccin ya yi maka dad'i. Gabanshi wani irin mummunan fad'uwa yayi yace kana nufin tun jiya nake nan wajen? Dariya Alhaji Mansur yayi yace sosai ma ai ba abun mamaki bane. Innalillahi wa'inna ilaihiraji'un Alhaji Mansur me yasa ka aikata min haka, ashe daman kaine kasa aka d'auko ni? Kujerar da take kallon inda Faruk yake zaune yajawo yazauna sannan yace toh ya ka iya tunda taurin kanka ne yaja maka, kaga yanzu cikin ruwan sanyi na satoka yanzu kana nan tare da mu jibi bazamu shiga kotu da kaiba. Shuru Faruk yayi yana tunanin halin da iyayenshi zasu shiga idan suka nemeshi basu ganshiba, cikin karaya yace Alhaji Mansur hakan da kayi bai dace ba domin ina akan aikina ne ba wai ina yin hakan dan in tozartaku ba. Bushewa da dariya yayi yace ashe zakayi saurin karaya haka ban yi zaton haka ba saidai ka makaro Faruk, tunda har nagargad'eka baka jiba toh a nan zaka cigaba da rayuwarka da mutanena. 'Dagowa Faruk yayi yakalli mutanen d'aya bayan d'aya sannan yayi murmushi yace ban damu da duk abinda zakayi min ba Alhaji Mansur tunda ina akan gaskiyata sannan ko da ba ni ba ita yarinyar bazata ta'ba barinku ba sai ta kasheku kamar yadda takashe sauran abokan naku dasannu ku ma zaku bak'unci lahira, Mik'ewa yayi a fusace yawanka mashi mari. Saurin runtse idanunshi yayi saboda wani irin zafi da yaji ya ziyarci kuncinshi, d'agowa yayi yakalli Alhaji Mansur cike da mamaki bakinshi yamutu yakasa cemashi komai. Nunashi da yatsa Alhaji Mansur yayi yace kasan abinda bakinka yake fad'a domin ni d'innan ba kanwar lasa bane na tabbata har yanzu baka ida sanin wanene ni ba, ba kowa bane zai takani yazauna lafiya. Murmushi Faruk yayi yace wannan marin da kayi min bashi ne kad'auka karubuta ka ajiye wannan. Alhaji Mansur har ya bud'e baki zaiyi magana nan wayarshi da take hannunshi tafara ringing dubawa yayi sannan yai picking basu ji abinda ake ce mashi ba saidai sukaji yana cewa Eh gashinan ya farka ai yanzu bamuda damuwa abokina kakwantar da hankalinka yana nan wajen a nan zai ci gaba da zama har sai lokacin da yasaduda yadawo hanya inko ba haka ba saidai yakasance tare da mu, dariya yafara kyalkyatawa sai kuma chan yace toh shikenan sai anjima sai mun had'e ai na d'auka zakazo kaga mutumin namu duk wannan jin kan nashi babu shi atare da shi yau, ai kabarshi ina nan da kai sai ya safke girman kan nan nashi,,, suna saurarenshi yagama wayar sannan yakalli Faruk yace toh Barrister daga yanzu ka ga gidanka nan a nan zaka cigaba da rayuwa babu kai babu fita,, sannan ku kuma yanuna wad'annan k'attin biyar yace kucigaba da kula da shi ban yadda ko tsakar gida abarshi yafito ba hatta toilet gashinan cikin d'aki. Gabad'aya sukace angama oga. Murmushi yayi sannan yawuce yafita. Da idanu Barrister Faruk yabishi yana jin wani irin k'unci a cikin ranshi ba komai yad'aga mashi hankaliba sai iyayenshi da baisan halin da suke ciki ba, muryar d'aya daga cikin k'attin yaji wanda da alama shine ogansu ya ce ku zauna nan da shi bari inje indawo. Amsawa sukayi da toh nan suka wuce suka zauna suna kallon Faruk nan yajingine kanshi a jikin kujerar tare da runtse idanunshi. A chan 'bangaren iyayen Faruk ganin har dare bai dawoba kuma ga motocinshi duk suna gida dan haka suka fara tunanin ina yaje ko abokinshi yazo suka fita a mota, hankalinsu bai ida tashiba saida dare yayi baidawoba har k'arfe sha biyun dare sannan suka kira wayarshi suka ji ta akashe, atak'aice dai haka suka kwana rabi a zaune ammah bai dawoba. Wasa wasa washe gari har azuhur bai dawoba dan haka Dad yadinga kiran abokan Faruk da yasani yana tambayarsu sukace basu ganshiba, nan hankalinsu ya ida tashi sukayi tunanin ko mutanen nan suka saceshi, Momcy kuka tadinga yi sosai akan rashin ganin d'an nata haka tashiga mota tadinga zuwa gidajen da tasan yana d'an zuwa ammah babu labarinshi. Har dare haka suka ci nemanshi ammah babu 'bar'bashinshi ba su ba hatta duk wanda yake kusa da su saida yashiga tashin hankali akan rashin ganin Barrister inda daga k'arshe aka kai cigiyarshi gidajen television da na redio. Nasiba suna zaune ita da iyayenta a parlor suna kallon news inda ita hankalinta yake akan waya tana chart a nan ne iyayenta sukaga hoton Barr Faruk an dallo ana cigiyarshi, jin sunan wanda ake cigiyane yasa tayi saurin d'ago kai tamaida kallonta ga TV gabanta wani irin mummanan fad'uwa yayi tace na shiga ukku Daddy Mummy kuduba min wallahi Faruk ne ake cigiya me yafaru da shi?. Murmushi Alhaji Sufyan yayi yace tabbas wannan Faruk ne ikon Allah ko ya akayi haka, yanzu haka wajen iya yin shi ne yayi ma wad'anda suka kasa hak'uri suka d'aukeshi ko kuma wannan yarinyar takasheshi. Hajiya Maijidda rik'e baki tayi tace na shiga ukku yanzu Faruk d'inne ya'bata tun shekaran jiya? Nasiba da tayi mutuwar zaune hankalinta ya tashi sosai kasa cema iyayen nata komai tayi tana ta kallon hotunanshi da ake dallawa a TV ana cigiya chan sai ga hawaye sun fara fita nan tasa ma iyayenta kuka. Su dukansu kallonta sukayi cike da mamaki sukace ke kuma kukan me kikeyi? Cikin kuka tace Daddy Faruk d'ina ba'a ganshi ba ya 'bace . Daddynka fusata yayi yadaka mata tsawa yace ke bana son shashancin banza ai ba ubanki bane ya'bace da zaki ma mutane kuka kuma yaushe Faruk d'in yazama naki wannan azzalumin maci amana, inma banda abinki miye abun tada hankali kan 'bacewar wanchan butulun? Cikin sheshek'ar kuka tace wallahi Daddy Faruk ba mugu bane mutumin kirkine bana son wani abu yasameshi dan Allah muje nemanshi. Mummynta ce takai hannu tabuge mata maki tace ke dai shashasha ce miye abun tada hankali ga 'bacewar wanda yaso yatozarta mahaifinki yanzu haka rashin mutuncin yayi ma wasu sukaji basu iya hak'uri, K'ara sautin kukanta tayi tana jin wani irin haushi akan maganar da iyayenta suke marar dad'i akan Faruk dan ita ta san har yanzu tana jinshi a ranta. Mahaifinta ne yace kibarta kawai Hajiya sai tayi ta yi tunda ita batasan ciwon kanta ba bata kishina duk cin zarafin da yake mana bata gani ni wallahi dad'i ma naji yanzu ai iyayenshi zasu gane abinda muke fad'a masu akan abubuwan da d'an nasu yakeyi tunda su basu iya hanasu. Mik'ewa Nasiba tayi cikin sauri tajuya tafita daga parlorn tana cigaba da kuka. Mummynta ce tace oh ni yau naga ikon Allah watau Alhaji yarinyar chan dai da alama bata hak'ura da yaron chan ba. Cikin 'bacin rai yace kibarta ko kukan jini zatayi bazata ta'ba auren Faruk ba ko da ace yana nan bare ma baya nan dan bazan ta'ba ba irinshi auren d'iyataba. Shuru Mummyn Nasiba tayi dan ita babu abinda tatsana sama da 'bacin ran d'iyartata dan ma ba hali da ta je ta lallasheta. Nasiba kuka tadinga yi kamar wadda aka aiko ma da sak'on mutuwa wani irin tausayin Faruk ne taji ya d'arsu a zuciyarta, wayarta tad'auko takira numbers d'inshi dukansu a kashe nan tacigaba da rusa kuka daga k'arshe tatashi tad'auko mayafinta tazari key d'in motarta tabi ta k'ofar baya taficce batare da sanin iyayenta ba. Tuk'i take ammah kuka takeyi ahaka har ta isa gidansu Faruk, tana isa ko tsayawa rufe motar batayi ba tashiga gidan da gudu, duk mutane ne zazzaune anyi cirko cirko kowa yana jimamin 'bacewarshi tsawon kwana biyu, a parlor tasamu Mom zaune tana ta matsar hawaye ana lallashinta tana zuwa tafad'a jikinta tare da fashewa da wani irin kuka me ban tausayi, cikin kuka tadinga cewa Mom dan Allah ina Faruk? Dagaske ne ya 'bace? Dan Allah Mom kice min Faruk d'ina yana d'akinshi wallahi ina sonshi bana so inrasa shi. Mom kamar jira take nan itama d'in tafashe da kuka, k'ok'arin k'wace Nasiba akayi daga jikin Mom ammah tarik'eta gam. Dakyar aka samu aka 'ban'bareta nan takwanta a k'asa tana cigaba da rusa kuka, aka rasa wanda za'a lallasa ita da Mom. Alhaji Sani Maishadda da abokan Faruk ne suka dinga k'ok'arin zuwa wajaje nemanshi inda a chan garin daura kakanshi yasa aka dinga safkar alk'ur'ani ana sadaka.... _Sis Nerja'art✍🏻_ [7/24, 11:14 PM] Sis Nerja'art 2: *......FANSAR RAI......* *INTELLIGENT WRITER'S ASSO....®* [On Award Together] _Follow me on Wattpad: *Sis-nerja*_ _Wannan Littafin na kud'i ne domin karantawa cikin aminci da yarda ga duk me buk'ata zai turo katin Mtn na d'ari biyu N200 kacal ta wannan number d'in 09035938246, ko ta account number 5330055604, Idan katura ka aiko da screen shot na transaction a wannan number d'in 09035938246_ _Akwai gara'basar *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shahararriyar marubuciyar nan *AMEENA ABBA UMAR* tare da novel d'in *FANSAR RAI* akan farashin N300 kacal, ko da kud'in ka sai da rabonka_ *PAGE 18* Mummyn Nasiba saida tafaki idanun mijin nata sannan tanufi d'akin d'iyartata dan talallashi abunta sai gani tayi wayam babu ita nemanta tafara yi tana dubawa a parking space taga babu motarta dan haka tasan ta fita dawowa tayi tasamu mijin nata tace oh ni Alhaji watau yarinyar chan fita tayi daga gidan nan. Da mamaki yake kallonta yace kina nufin bata nan? Eh na duba d'akinta kuma naga motarta bata nan. K'wafa yayi yace watau gidansu Faruk taje dan bata jin magana kibarni da ita zata dawo gidan tasameni. Har dare Nasiba tana gidansu Faruk hawayen idanunta sun kasa tsayawa fuskarnan duk ta kumbura saboda tsananin kukan da tasha tana zaune gefen Mom koda aka kawo masu abinci daga ita har Mom k'in ci sukayi saida akayi da gaske sannan suka d'an ci, suna nan a haka Barr Junaid da Nas suka shigo saurin mik'ewa tayi tanufi wajen da yake tun kan yayi magana tatari numfashinshi tace Junaid anga Faruk d'ina ko? Junaid kallon Nas yayi su dukansu jikinsu ya yi sanyi sannan yakalli Nasiba tare da girgiza mata kai. Ja tafara yi da baya nan wasu hawayen suka wanke mata fuska tace shikenan tunda ku bazaku iya ganoshi ba ni zan je innemeshi da kaina, ni zan iya dawowa da shi. Barr Nas ne yayi k'arfin halin cewa kiyi hak'uri Nasiba muna bakin k'ok'arinmu ammah har yanzu Allah baisa andaceba insha Allahu zamu gano Faruk kikwantar da hankalinki. Wajen Mom takoma tatsugunna kusa da kujerar da take zaune tace Mom kin gani ko basu ganoshi ba kidaina kuka ni zanje in nemeshi. Ganin yadda take magana kamar zararra yasa mom ta girgiza kai tace a'a Nasiba babu inda zakije insha Allahu zasu gano mana shi. Fashewa tayi da kuka tace Mom har sai yaushe? Kwantar mata da kanta saman cinyarta tayi nan tafara lallashinta dan batasan abinda zatace mata ba. Kuka tadinga yi sosai har saida Dad yadawo nan yasamu yalallasheta tadaina kukan ganin har tara ta yi yasa yace tatashi tatafi gida, da fari ta ce babu inda zataje har sai Faruk ya dawo saida Dad yadinga lalla'bata sannan tahak'ura tatashi tatafi. Tana isa gida a parlor tasamu iyayen nata mahaifinta sai kaiwa da kawowa yake tana shigowa yace daga ina kike? Batare da ta damu da yanayin da taganshi ba tace daga gidan su Faruk nake...bata rufe baki ba taji ya wanka mata bari. Saurin dafe kuncinta tayi tare da kallon mahaifin nata cike da mamaki dan wannan shine karo na farko a rayuwarta da yata'ba marinta. Nunata yayu da yatsaya yace ke har kin isa kitsallake maganata? Da izininwa kika fita daga gidan nan? Shuru tayi tare da sadda kanta k'asa tana hawaye kanta yayo zai rufeta da duka Hajiya Maijidda tayi saurin shan gabanshi tace a'a Alhaji dan Allah kar kabugeta yarinya ce Nasiba batasan komai ba sai andinga kwatanta mata. Wata uwar harara yawurga mata yace Nasibar ce yarinya? Shuru tayi tana kallonshi. Cigaba yayi da cewa toh wallahi duk lokacin da tak'ara barin gidan nan sai na mugun sa'ba mata ban yarda ko nan da waje tasake fitaba. Wucewa Nasiba tayi sumi sumi tanufi d'akinta tana ji yana cewa ka ga 'yar iskar yarinya ni zaki maida banza watau ke ga shugabar soyayya ko? Mummyn Nasiba ce tace Alhaji ayi hak'uri. Tsaki yaja sannan yawuce a fusace yakoma d'akinshi. Bayan d'iyartata tabi tana zuwa tasameta zaune saman gado ta dafe kuncinta tana ta kuka, zuwa tayi tazauna kusa da ita tace haba Nasiba meyasa bakiji yanzu gashinan kinja ya doke ki. 'Dago kai tayi takalli mahaifiyartata cikin sheshekar kuka tace Mummy fad'a min menene laifina a ciki? Dan kawai ina son Faruk, ai bani nadasa ma kaina son nashi ba meyasa ake ganin laifina? Matsowa Mummy tayi kusa da ita tare da dafata tace haba Nasiba kidaina cewa haka kinga kema baki kyautaba ya kamata zuwa yanzu ace kin cireshi a ranki ko dan saboda tozarcin da yaso yayi ma mahaifinki kinga a yanzu mahaifinki yana fushi da ke saboda abinda kikayi baki kyautaba. Girgiza kai tashiga yi cikin kuka tace Mummy kune zakuga rashin kyautawa ta ammah ni zuciyata gani take hakan shine daidai dan saboda tana son Faruk, indai har abinda nayi a wajenku ba daidai bane to kuyafe min na ji ni me laifi ce saidai bazan ta'ba iya cire son shi ba ammah ina fatan inyi k'ok'arin cireshi a raina ko da ace hakan zai zama sanadiyar mutuwata indai har hakan zaisa infaranta maku. Rungumeta jikinta Hajiya Maijidda tayi tace a'a Nasiba kidaina cewa haka dan bamuso murasaki munason ki sosai. 'Dagowa tayi takalleta tare da yin murmushi wanda yafi kuka ciwo sannan tace indai har kuna so na to ya kamata kubarni incigaba da kasancewa da soyayyar Faruk dan zuciyata tana sonshi hakan kawai zakuyi min ingane cewa kuna k'aunata. Da mamaki take kallon d'iyartata da soyayya ta gama rufe mata idanu cikin sanyin jiki tace Nasiba kinsan dai duk duniyar nan babu wanda yakaimu k'aunarki saboda mu mune iyayenki saidai mahaifinki nakeji kinsan idan har yafad'i magana to baya canzata. Ruk'o hannuwan mahaifiyartata tayi tana kallonta da idanuwanta da suka kumbura saboda tsananin kuka tace Mommy dan Allah ke kikasance da ni domin ke uwace na tabbata ke kad'ai zaki iya fahimtata. Rungumeta tayi tare da shafa bayanta tace ina tare da ke d'iyata tabbas nice kad'ai yafi dacewa infara fahimtarki, kidaina kukan mucigaba da addu'a insha Allahu Faruk zai bayyana. Ajiyar zuciya tasafke tace nagode sosai Mummyna. Bakomai d'iyata yanzu dai kidaina kukan nan bari inje inkawo maki abinci kici kiwatsa ruwa kikwanta ko? Goge hawayenta tayi tare da yin murmushi tace nagode mummyna. ***** ***** A chan 'bangaren Faruk yana chan da mutanen nan a cikin d'akin a d'aure dan a yanzu ma ya samu ansafkeshi daga saman kujerar a saman gado aka d'aureshi indai har zaiyi wata buk'atar kusan mutum ukku suke rakashi wajen toilet yashiga yagama abinda zaiyi sannan sumaidoshi sud'aure Alhaji Mansur kusan kullum sau ukku yake zuwa yadubasu yakawo masu abinci koda shi a wulak'ance ake bashi abinci kuma ba ci yakeyi ba sai yaga yunwa ta cishi sosai sannan yaci, wulak'anci da cin mutunci kala-kala yake sha a wajensu Alhaji Mansur da mutanenshi saidai shi duk wannan bai dameshiba abu d'aya ne yake d'aga mashi hankali halin da iyayenshi suka shiga sai kuma case d'in jawahir baisan yadda zai kasanceba ita kanta ya san sai ta zargi wani abu kar ma tad'auka yaudararta yayi. A yau ma yana zaune a inda aka d'aureshi hankalinshi a tashe yana tunanin kotun da za'a zauna gobe sai gani yayi anwurgo mashi takeaway a saman jikinshi, kallo d'aya yayi mashi yad'auke kai, d'aya daga cikinsu ne yataso yana cewa watau sai ma kad'auke kai idan bazaka ci abincin ba sai kayi magana ba sai na kwanceka ba. Shuru yayi kamar baiji abinda yace ba. Cikin 'bacin rai yace kai wai wane irin banzan mutum ne ayita maka magana kayi shuru kak'yale mutane ka san kabi a sannu inba hakaba zan nakasaka a wajen nan nace zaka ci abincin ko ka k'oshi. Nan ma shuru yayi yaba bango ajiyarshi. A fusace yad'aga bindigar da take hannunshi yabuga mashi a kai, Faruk saida yasaki k'ara saboda zafin bugun. 'Dago mashi kai yayi dak'arfi yace idan har kacigaba da mana taurin kai sai mun azabtar da kai a gidan nan, kalleka dan Allah a yanzu gakanan a wulak'ance a wajenmu duk wannan jin kan nan da tak'ama babu su. Wani daga cikin sauran da suke zaune ne yace cinnaka ni ko naga ba jin kai kaga fa yadda yake taka k'asa kamar irin baya so d'innan shi a dole ga me kud'i barrister sai ga rayuwar barrister ta k'are a hannunmu ya koma wani k'ask'antacce. Su dukansu dariya sukasa suna cewa dan Allah jibarshi, duk ina dukiyar yanzu. Bud'e baki Faruk yayi ahankali yace koma me zakuce bazan ta'ba damuwa ba saidai inaso kusani a duk ranar da nayi nasarar barin gidan nan gabad'ayanku sai na sa and'aureku. Kan bindiga wanda aka kira da cinnaka yasake buga mashi a fuska har saida jini yafito daga hancinshi, runtse idanu yayi dak'arfi yana jin rad'ad'in bugun. 'Daya daga cikin wad'anda suke zaune ne yace a'a Cinnaka kadaina dukanshi ka ga Alhaji bai ce mubugeshi ba kabari abani izini sannan mucasashi tunda shi har yana ma tunanin zaya fita daga nan har yasa ad'auremu, wayyoo Allah har ma na d'an tsorata dan Allah kutaimaka min zasu kamani wallahi tsoron zaman gidan kaso nakeji......su dukansu kwashewa sukayi da dariya, wani kuma yace ahaka wai shashashan yake gani zamu barshi yafita lallai da sauranka. Haka sukaita tsokanarshi shi dai yayi shuru bai sake cewa komai ba saboda rad'ad'in da yakeji a fuskarshi. Yana ji Cinnaka yakoma yazauna batare da ya kwance mashi hannuwa ba koda daman shima ba yunwar yake ji ba inma yana ji sai ta cishi sannan yake cin abincin da suke bashi. Jawahir da take zaune a d'an kurkukun d'akinta tun bata damu da rashin zuwan Barrister ba har abun yazo yafara damunta dan bai ta'ba d'aukar wannan lokacin bai zoba gashi ma abun tashin hankalin gobe ne zama na k'arshe da zasuyi a kotu,,, mik'ewa tayi tsaye tare da jingine jikinta a jikin bango ahankali tace ko dai Barrister ya janye ne shima bazai iya taimakona ba? Girgiza kai tayi tace ah'ah ko kuma wani abu yafaru da shi? Hannu tasa tatoshe bakinta nan k'wallah ta cika mata idanu tace na shiga ukku ba dai akaina wani abu yafaru da shi ba, idan ko hakane ya zanyi, nice sila,,, Tana nan tsaye a haka akazo aka bud'e d'akin juyowa tayi dan ganin wanda zai shigo sai taga ma'aikaciyar gidan ce, ajiyar zuciya tasafke Kallonta matar tayi a wulak'ance tace ke zo muje ana son ganinki. Nuna kanta tayi tace ni? Harararta tayi tace akwai wani ne cikin d'akin? Batare da ta bata amsaba tad'auko kallabinta tad'aure kanta sannan tabi bayanta suka fita, da mamaki take kallon inda suka nufa tabbas wajen da ake kaisune idan wani ya zo ganawa da su. Suna zuwa sai jin matar tayi ta ce kawo hannunki, mik'awa tayi nan taga ansa mata ankwa sannan matar tace kishiga ciki d'allabai yana ciki. Tambayar kanta tayi tace Faruk kenan yazo ganawa da ni ammah kuma yau bai shigo wajenaba sai nan....Daka mata tsawa matar tayi tace me kika tsaya jira? Shiga tayi d'akin da mamaki take kallon wanda yake tsaye. Murmushi yasakar mata yace sannu d'iyata ina fata kina lafiya? Wannan dai mahaifin bai kyautaba da baya zuwa ganin d'iyarnan tashi. 'Daure fuska tayu tace menene dalilinka na zuwa wajena? Matsowa yayi kusa da ita yana murmushi yace kikwantar da hankalinki na zo ne kawai duba lafiyarki sannan injajanta maki 'bacewar da akace Barrister Farukya yi tsawon kwana ukku. Zaro idanu tayi waje da mamaki take kallonshi tace kana nufin Barrister ya 'bace? Alhaji Mansur dariya yasake yi yace ya naga kin tsorata, nima dai haka naji ban saniba ko akan wani case aka saceshi gashi mu kuma gobe ce ranar shara'a ta k'arshe. Idanu tazuba mashi tana kallonshi cikin ranta tace ko dai akan case d'ina ne? Ya kikayi shuru ko kina tsoron makomarki ta gobe? Sai a lokacin tayi murmushi tace ban damu da makomata ba saidai na san duk abinda yafaru da Faruk ku ne sila, shin ko shima kun kasheshi kamar yadda kuka kashe iyayena? Tarar numfashinta yayi yace ko kuma kin kasheshi kamar yadda kika kashe sauran lauyoyinki, shin taya ma gobe za'a barki bayan kin kashe lauyoyi ukku. 'Daga murya tayi tace idan har kuka bari wani abu yafaru da Barrister bazan ta'ba barinku ba da duk wanda yake da hannu a ciki sai naga bayanshi, kukyaleshi yayi rayuwarshi domin shi baida laifi a ciki nice me laifin kuma idan har saboda ni kuka kamashi kusakeshi ni na amince akasheni ammah kar ku kashe wanda baisan komai ba a kai. "Jawahir mu bamu kamashi ba dan baya hannunmu kece ma nayi tunanin kin kasheshi ammah dai shikenan ke kad'ai kikasan wannan sirrin dan nasan daman ba fad'a min gaskiya zakiyiba nima daman jaje nazo maki, ni zan tafi ko ma mekenan sai munhad'e a kotu gobe ina fata zaki kasance cikin bak'in ciki kasancewar yau itace ranarki ta k'arshe gobe kamar yanzu kina cikin k'abarinki, na barki lafiya. Hawaye ne suka gangaro mata a kuncinta ganin ya juya zai tafi yasa cikin d'aga murya tace na fad'a maka kar kabari wani abu yafaru da rayuwar Barrister wallahi idan har kakasheshi nima sai naga bayanka kafin nima akasheni. Bai tsaya bata amsaba yawuce yatafi. Dafe kanta tayi da hannuwanta da suke da ankwa, matar ce tazo tatisata gaba tamaidata chan d'akinta tamaida tarufe. Tana shiga sulalewa tayi k'asa tazauna tare da fashewa da wani irin matsanancin kuka, cikin kuka tadinga cewa Ammi kizo gareni ina buk'atar taimakonki ko da ace wannan shine taimako na k'arshe da zakiyi min a duniya dan Allah kizo gareni......bata rufe baki ba sai ga wani farin haske ya bayyana a gabanta, saurin mik'ewa tayi tana kallon haskenan nan yafara komawa siffar mutum kafin k'iftawar idanu sai ga tsohuwarnan ta bayyana. Bud'e baki tayi zatayi magana tatari numfashinta tace tabbas Barrister yana cikin mawuyacin hali dan yana hannunsu sun kamashi saidai bazan ta'ba taimaka mashi ba. Saurin zamewa tayi k'asa tatsugunna tare da had'e hannuwanta biyu waje guda cikin muryar kuka tace dan Allah Ammi kitaimaka min kitseratar da shi domin rayuwarshi tana da muhimmanci sosai bai dace ace wani abu ya sameshi ba a dalilina ni k'wara akasheni dan tawa rayuwar batada sauran amfani. Dariya matar tayi sannan tace Jawahir yau gaki a gabana tsugunne kina rok'ona bayan da baki ta'ba hakan ba, saidai tsanar da kikayi min ammah yau kece a haka dubeki. Fashewa tayi da kuka tace tabbas ni k'ask'antatta ce kar kiyi duba da abinda yafaru dan Allah kiceci wannan bawan Allahn banaso sukasheshi. Zureren hannunta tad'ago tace kiyi duba zuwa nan jawahir. Saurin d'ago kanta tayi tadubi hannun Barrister Faruk ne tagani zaune an d'aureshi idanunshi a rufe. Wasu sabbin hawayen ne suka gangaro mata nan tsohuwar tajanye hannunta sannan tace wannan itace k'addararshi bazan ta'ba iya zuwa inceceshi ba, ke kuma ya kamata kafin gobe kiyi nadamar maganar da kika fad'a min idan har kinason cigaban rayuwarki inko ba haka ba kema kanki zaki mutu. Matsowa tayi kusa da matar tana me cigaba da kuka tace bazan ta'ba nadama ba indai a kan kainane saidai zan iya Nadama indai har zaki ceci Faruk kije kiku'butar da shi. Bushewa tsohuwar tayi da dariya sannan tace dakyau jawahir hakan ya yi miki kyau, saidai ni bazan ta'ba taimaka ma wanda kikeso intaimaka ba saboda ni bana taimako abu guda kawai nake kuma shi na iya shine *'DAUKAR FANSA* Jawahir kasa cemata komai tayi nan taduk'ar da kanta tana me cigaba da kuka cike da tashin hankali..... ______ Gidan su Faruk mutane zuwa suke suna yi ma iyayenshi jaje dan gidan komawa yayi kamar gidan gaisuwa mutane sai shiga da ficce sukeyi inda suke addu'a Allah yabayyanar da shi. Hatta limamin unguwar kullum sai ya zo anyi safka sannan ayi abincin sadaka a raba. Iyayenshi duk sun fita hayyacinshi saboda tashin hankalin da suka shiga. A ranar yau da takasance kwanan Faruk ukku baya gida, Dad d'inshi yana zaune a setting room shi kad'ai ya buga tagumi Barr Nas yazo gidan duk sallamar da yayi Dad baijiba saida yad'an buga k'ofa sannan yad'ago yakalleshi yace bismillah Nasir kashigo man. Shiga yayi yazauna a k'asa suka gaisa bayan sun gaisa ne Dad yace Nasir kuna ta k'ok'ari gaskiya mungode sosai, a yanzu mudaina wahalar da kanmu wajen yawon nemanshi mucigaba da addu'a indai har yana raye Allah zai bayyana mana shi, saidai abinda nake zargi mutanen da suka ta'ba kirana waya sukace ingargad'eshi yacire hannunshi daga wani case ina tunanin sune suka sace min shi dan a ranar da akayi maganar a ranar ya'bata. Cikin sanyin jiki Barr Nas yace Dad wane mutane ne? Me sukace maka? Kwashe komai yayi yafad'a ma Barr Nas. Mamaki yacikashi yace tabbas wad'annan mutanen akan case d'in Jawahir ne. Eh tabbas hakan sukace wai yajanye akan case d'inta ammah wacece ita? Meyasa zasuyi min haka da sunbi ta lalama ai da na sashi ya janye. Shuru Nasir yayi sai chan yace tabbas case d'in akwai rikitarwa a cikinshi saidai ita yarinyar tana a kan gaskiyarta wannan dalilin ne yasa Faruk yakeso yawanketa a idanun duniya daga zargin da akeyi mata, saidai a yanzu lokaci ya k'ure na tabbata a gobe idan har babu lauyan da zai tsaya mata kasheta za'ayi gashi Barr Faruk shine kad'ai zai iya tsaya mata. Jinjina kai Dad yayi yace Allah yakyauta, Allah dai yabayyanar da shi a duk inda yake. Barr Nas ya amsa da Ameen sannan yayi mashi sallama yatafi. Nasiba saboda tashin hankalin da tashiga ko baccin kirki bata iyawa abinci ko ba'a magana sai Mummynta ta yi dagaske sannan take samu tana d'anci kullum cikin kuka take, Daddynta ko shareta yayi yafita batunta. Yau ma kamar kullum Hajiya Maijidda ce tashigo da azuhur tasameta zaune saman darduma da alama sallah tagama saidai ta jingine jikinta a jikin gado tana hawaye, tsayawa Hajiya Maijidda tayi tana kallonta sai kuma chan tataka ta isa wajenta a saman gadon tazauna cikin lallashi tace haba Nasiba wai meyasa kikesa ma ranki damuwa addu'a fa yakamata kiyi mashi duk inda yake Allah zai bayyana mana shi. Goge hawayen fuskarta tayi tare da gyara zamanta ta fuskanci mahaifiyartata sannan tace Mummy dan Allah taimako d'aya nakeso kiyi min. Toh ina jinki wane irin taimako ne? Saida takalli k'ofa sannan tace dan Allah kitaimaka min kibarni inje gidansu Faruk ingano Mom d'inshi na tabbata tana chan hankalinta a tashe, nima zuwana zai sa ind'anji sauk'in rad'ad'in da nakeji a raina. Jimm tayi sannan tace Nasiba kinsan mahaifinki baya so ranshi 'baci zaiyi. Kamar jira take tafashe da kuka tace Mummy kitaimaka min wajenki ne kawai nake jin dad'i kin san yadda nakeson Faruk hankalina bazai ta'ba kwanciya ba idan banje naji halin da ake cikiba yanzu. Cikin sanyin jiki tace shikenan Nasiba tashi kije ammah kar kidad'e saboda kar Daddynki yadawo bakinan kinsan ba ke ba hatta ni kaina sai raina ya 'baci. Murmushin jin dad'i tayi tace nagode sosai mummyna. Shafa kanta tayi tace bakomai dota idan kinje kigaishe min da Hajiya Nuratu. Toh insha Allahu zataji Mummy, nan tamik'e tashirya tafita tana Allah Allah kar suhad'u da Daddynta a lokacin da zata fitar da motarta sai gashi cikin ikon Allah har tatafi bai dawo ba..... _Sis Nerja'art✍🏻_ [7/24, 11:14 PM] Sis Nerja'art 2: *......FANSAR RAI......* *INTELLIGENT WRITER'S ASSO....®* [On Award Together] _Follow me on Wattpad: *Sis-nerja*_ _Wannan Littafin na kud'i ne domin karantawa cikin aminci da yarda ga duk me buk'ata zai turo katin Mtn na d'ari biyu N200 kacal ta wannan number d'in 09035938246, ko ta account number 5330055604, Idan katura ka aiko da screen shot na transaction a wannan number d'in 09035938246_ _Akwai gara'basar *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shahararriyar marubuciyar nan *AMEENA ABBA UMAR* tare da novel d'in *FANSAR RAI* akan farashin N300 kacal, ko da kud'in ka sai da rabonka_ *PAGE 19* Washe gari ya kama ranar litinin tun da safe a gidan kaso akasa duk wani wanda za'aje kotu da shi yayi wanka yashirya, jawahir tunda tashirya zaune tayi tana tunanin halin da Faruk yashiga akanta ko kad'an fuskarta babu alamun fara'a dan jiya ko rintsawa bata samu tayiba, abinda zai ba mutum mamaki ita hankalinta bai tashi akan zaman kotun da za'ayi ba, bah wai kuma dan tana da tabbacin zata tsira ba dan tasa ma ranta dole cikin biyu ayi d'aya ko rayuwa ko mutuwa ko da ta ma fi bama ranta mutuwar dan tasan itace kawai makomarta. Kamar yadda aka saba a duk ranar da za'a shiga kotu akan case d'in jawahir ana yin sanarwa a gidajen yad'a labarai saboda za'a iya cewa mafi yawa daga cikin mutanen da suke garin katsina sun san da case d'inta dan abinda ba'a ta'ba jin an aikata bane sai akanta, musamman ma da akasan manyan mutane ne masu hannu da shuni ake zarginta da kisansu, wannan dalilin ne yasa duk ranar da za'a shiga kotu akan case d'inta mutane dadama suke zuwa acika kotun mak'il, wasu ko ba komai yake kawosu ba sai dan suzo sugane ma idanunsu yarinyar da akace tana da k'arancin shekaru takeyin kisan. Dad d'in Faruk da a yanzu ko baccin kirki baya samu yayi saboda 'bacewar d'anshi, yau ma tunda yadawo sallar asuba bai koma bacci ba Redionshi yajawo yakunna yana daga kwance saman doguwar kujera dan a yanzu ya fi sauraren Redio ko dan saboda yana tunanin a nan zai iya samun bayyanar d'anshi indai ma ansameshi a wani wajen, yana cikin sauraren labaran safiyar yau akan abubuwan da suka farune yaji ana sanarwa "Gwamnatin jihar katsina zata bada tallafi ga wad'anda 'yan ta'adda suka shiga garuruwansu suka kashe masu 'yan uwa sannan suka kora masu dabbobi suka tafi da su, inda me girma gwamna yayi sanarwa zai taimaka masu da tallafi. Sannan a cikin labaran na mu zakuji cewa a yau ne za'a yi zama na k'arshe a kotu akan case d'in Jawahir Muhammad Maikud'i wadda ake zargi da kashe kawunta da 'ya'yanshi wanda daga baya hukuma tagano hadda mijinta aciki sannan tasambad'a abokan mahaifinta suka ziyarci lahira inda dangin mamatan suke k'ararta akan suna so abi masu hak'k'in rayuwar 'yan uwansu, ko me ya jawo ma yarinyar yin kinsan? Wannan ne bamu saniba dan har yanzu ba'a samu wata k'wak'kwarar hujjaba guda d'aya da me laifin tabayar saidai jitajitan da mutane sukeyi, koma me kenan kukasance da mu da anjima acikin labaran mu dan jin yadda shari'ar ta kasance.. Haka kuma a cikin labaran namu zakuji cewa... Dad tsaki yaja tare da kashe redion yakunna TV dan yakalli News tunda yakunna TV d'in kallo kawai yake ammah hankalinshi ba a wajen yakeba abinda yatsaya mashi a rai case d'in yarinyar da yaji ansanar musamman ma sunan da aka ambata Jawahir Muhammad Maikud'i tabbas zai iya cewa 'ya ce ga Marigayi Alhaji Muhammad Maikud'i inko ba haka ba toh sunan ya zo iri d'aya da nashi toh ammah shima ya san yana da d'iya guda d'aya bazai iya cewa ga sunanta ba, anya kuwa itace ba wata bace ta daban ba? Toh ko dai itace Jawahir d'in da Faruk yatsaya mawa wadda saboda case d'in ake barazana a rayuwarshi, tabbas ko zaya iya zama itace dan zai iya tuna labarin da Faruk yabasu akan case d'in ya ce ana zarginta akan kisa. Jinjina kai yayi yace tabbas itace wannan saboda ita aka d'auke min d'ana....haka yayi ta tunane tunane inda daga k'arshe yakasa kallon News d'in yakashe TV d'in yayi kwance yana tunanin halin da d'anshi yake ciki a yanzu ko da rai ko kuma babu rai. _______ A chan 'bangaren Faruk yana kwance a saman gado ko runtsawa bai samu yayiba saboda tashin hankalin da yake ciki musamman akan shara'ar da za'a gabatar a yau ta jawahir, ko da daman ba samun wani baccin kirki yakeba saboda halin da yake ciki ga d'aurin da akayi mashi wai dan kar yagudu ahaka yake kwanciya. Hatta sallah sai ya yi dagaske sannan suke barinshi yayi shima sai kusan mutum ukku sun tsareshi sannan. ****** Wajen k'arfe Taran safe aka fiddo wad'anda za'a yi shara'a akan case d'insu aka saka cikin mota aka nufi kotu inda motocin 'yansanda suka kasance gaba da bayan motarsu, tunda suka fara tafiya matan suka dinga bin titi da kallo masu farin ciki sunayi masu bak'in ciki nayi akan case d'insu dan kowa ya san makomarshi, jawahir ko jingine jikinta tayi a inda take zaune yanayinta kawai zaka kalla kagane tana cikin tashin hankali saidai abinda zai baka mamaki ba wai akan case d'inta tashiga tashin hankalinba ta shiga ne saboda halin da Barrister yashiga akanta, wasu siraran hawaye ne suka gangaro mata tayi saurin sa hannu tagoge, a cikin zuciyarta tana addu'a Allah yasa ko bayan ranta Faruk yaku'buta daga sharrin mutanen nan, ahaka har suka isa HIGH COURT bata saniba saida aka bud'e aka fara fita sannan takusa da ita tata'bota tafito..... ******** Nasiba bayan ta gama sallar asuba da azkhar d'inta gari yana fara haske fitowa tayi dan tagaishe da iyayenta kamar yadda tasaba saidai da ka kalli fuskarta zakaga alamar bata runtsaba, hanyar part d'in mahaifinta tanufa tana isa a parlor taji muryarshi yana waya har zata d'age labulen tashiga sai kuma tafasa taja tatsaya dan yagama wayar abinda taji yana fad'a ne a wayar yad'aga mata hankali sosai saurin sa hannu tayi tatoshe bakinta tare da zaro idanu gabanta wani irin mummunan fad'uwa yayi tayi saurin ja da baya lokacin da taji yana cewa "Haba Alhaji Mansur ai kar kadamu tunda dai Faruk yana hannunmu nasan yarinyar nan ta shiga damuwa sosai saboda ba lauyanta,,, dariya yayi sannan yace ai ya kamata muma muje High court d'innan ayi shara'ar a gabanmu akasheta kowa yahuta kaga shikenan sai mucinye sauran dukiyar hankalinmu kwance. Eh daman ka fad'a min kunyi magana da Barr M.B jiya toh shikenan koma menene sai mun had'u a kotun". Saurin juyawa tayi dagudu tabar wajen tare da fashewa da kuka tana isa parlor taci karo da mahaifiyarta da tafito daga part d'inta, kallonta tayi tace lafiya Nasiba. Jikinta tafad'a tare da k'ara sautin kukanta. Kingani ko kedai bakijin magana yanzu haka wani laifin kikayi ma Daddyn naki ko? Na fad'a maki kicigaba da addu'a indai Faruk yana raye zaya dawo. Cikin sheshek'ar kuka tabud'e baki tace Mummy...sai kuma tayi shuru. Rik'ota Hajiya Maijidda tayi tace shikenan kiyi hak'uri muje inrakaki d'akinki kikwanta kafin agama had'a breakfast insa akawo maki. Tana a jikin Mummyntata a haka sukaje tarakata har bedroom d'inta saida talallasheta tadaina kukan sannan tatafi. Nasiba tana ganin ta fita mik'ewa tayi taje tarufe d'akinta tacigaba da kukan maganganun da taji mahaifinta yana yi a waya suna dawo mata, kanta tafara tambaya tana cewa kenan su Daddy sun san inda Faruk yake? Ammah akan me suke magana dukiyar wa zasu cinye? Ko dai akwai gaskiya akan maganar da Faruk yafad'a akan Daddynta? Saurin girgiza kai tayi tace a'a Daddyna ba haka yakeba kawai dai suna magana akan wani abun nadaman ammah kuma.....komawa tayi takwanta tare da dafe kanta da taji ya fara sara mata nan hawaye suka cigaba da ambaliya a fuskarta.... __________ Tunda aka shiga kotun waje aka samar masu su kusan hud'u ne suka zauna, mutane ne sosai a cikin kotun, ahankali ahankali ake zuwa lokaci guda kotun tacika mak'il da jama'a ana jiran k'arasowar alk'ali inda gabad'aya ciki da wajen kotun zagaye take da police, a gaba kuma lauyoyin masu k'ara da wad'anda ake k'ara ne zazzaune, goma saura minti biyar alk'ali yafito nan gabad'aya mutanen suka mik'e har saida yazauna sannan kowa yazauna. Court Reporter ne yamik'e yayi sallama tare da yin addu'a bayan anshafa ne sannan yace a yau 2 ga watan Afurili (April) wanda yayi daidai da 7 ga watan Rajab......Shara'a ta farko da zata kasance a yau itacs Shari'ar Maimuna Ahmad wadda ake zargi da zuba ma mijinta guba a cikin abinci yaci yamutu daga k'arshe dangin mijin sukayi k'ararta bayan antabbatar masu da guba ce takasheshi, juyawa yayi yakalli Alk'ali yace Allah yagafarta malam wannan itace shari'ar tamu ta farko, jinjina kai Alk'ali yayi nan court reporter yaje yamik'a ma alk'ali file d'inta. Dattijon Alk'alin gyara zaman farin glass d'inshi yayi a saman fuskarshi sannan yaduba file d'in ya d'au kusan minti biyar a duk'e sannan yad'ago kai yace kotu tana buk'atar ganin Maimuna ta bayyana a gabanta. Jawahir da tunda taji za'a fara karanto k'ara taruntse idanunta dan a tunaninta shari'ar ta ce za'a fara'a bata bud'eba sai da taji ta kusa da ita ta fara kuka ahankali sannan tabud'e takalleta da alama itace Maimuna nan wasu police mata guda biyu sukazo suka jata suka tafi da ita wajen da aka tanadar ma me k'ara da wanda ake k'ara dan sutsaya. Alk'ali d'agowa yayi yakalleta sannan yaduk'a yafara 'yan rubuce rubuce sai kuma yad'ago yace kotu tana buk'atar ganin lauyan me k'ara da na wadda ake k'ara. 'Daya daga cikin lauyoyin da suke zaune ne a layin gaba yamik'e yayi sallama sannan yace sunana Barr Mu'ammar nine lauyan da yake kare wadda ake k'ara sannan yakoma yazauna, Barr Junaid da yake zaune ya yi zugum bai ma san abinda ake tattaunawa ba saboda hankalinshi yana wajen abokinshi da ya'bata tsawon kwanaki hud'u, Barr Bilal ne yad'an zunguroshi da biron hannunshi sannan yadawo hayyacinshi saurin mik'ewa yayi yai sallama sannan yace sunana Barr Junaid nine lauyan da yake kare mek'ara. 'Dago kai Alk'ali yayi yakalleshi sannan yaduk'a yayi 'yan rubuce rubucenshi. Yad'ago kai yace kotu tana so maimuna tabayyana mata gaskiya a game da kisan da ake zargin ta yi ma mijinta ta hanyar ciyar da shi guba. Sheshek'ar kuka tafara yi saida megabatar da k'ara yamik'e yasake maimaita mata jawabin alk'ali sannan cikin inda inda tace bani bace nakashe shi dan lokacin da yamutu bana gidan. Alk'ali ganin ta yi shuru bata sake cewa komai ba yasa yaduk'a yayi 'yan rubuce rubuce sannan yad'ago yace shin ko Lauyan wad'anda suke k'ara yana da shedar da zai bayyana ma kotu wadda zatasa tagamsu da cewa maimuna ce tayi kisan bayan a yanzu maimuna ta nuna ba itace tayi kisan ba. Mik'ewa Barr Junaid yayi yace tabbas ina da ja ya maigirma mai shara'a inaso kotu taban dama ind'an yi wasu tambaboyi ga maimuna. Kotu ta baka dama,,, cewar alk'ali. Fitowa Barr Junaid yayi yanufi wajen da take tsaye yace malama maimuna shin ko zaki iya sanar da mu kina ina a lokacin da mijinki yamutu? Inda inda tafara yi tace na je gidan 'yar uwata ranar ban gida nima saidai nadawo natarar da gawarshi. Murmushi Barr Junaid yayi yace shikenan abinda kika sani? 'Daga kai tayi alamun eh. Juyawa yayi yakalli alk'ali yace ya megirma me shara'a maimuna bata amsa laifinta ba saidai duk na kusa da ita sunsan cewa itace tayi kisan. Lauyan wadda ake k'ara ce yayi saurin mik'ewa yace ya me girma me shara'a ya kamata a tsawatarwa lauyan wanda suke k'ara yagyara jawabanshi dan sunyi muni ga wadda ake k'ara. 'Dagowa Alk'ali yayi yakalli Barr Junaid yace kagyara bayaninka. 'Dan duk'ar da kai yayi cikin girmamawa yace na gode, sannan yad'ago yace ya megirma me shara'a inaso kotu taban dama ingabatar da shedu. Kotu ta baka dama. Godiya yayi yace malam zubairu me gadi da Talatu me aikin gidan sune sheda. Alk'ali ne yace kotu tana buk'atar ganin Malam Zubairu me gadi gidan Sadik'u da Talatu me aiki sun gurfana a gabanta. Su dukansu suka fito nan aka sa su sukayi rantsuwa akan zasu fad'i gaskiya sannan aka tambayesu suka bada shedar cewa babu inda taje a ranar tana gida inda 'yar aikin gidan tak'ara da cewa a gabanta ta ga me d'akintata ta fiddo wani abu cikin leda ta zuba a cikin abincin wanda yaci yamutu. Maimuna na jin haka tafashe da kuka tace talatu sharri zaki ja min Allah ya isa ban yafeba, police d'in da suke bayanta tsaye ne suka daka mata tsawa tayi shuru, Barr Junaid cewa yayi sukoma suzauna sannan yamaida kallonshi ga alk'ali yace ya megirma me shara'a bayan wannan shedar ina da shedar report d'in da likita yabada na mutuwar mamacin inda ya rubuta ya ci guba sannan an d'auko abincin da yaci anduba anga akwai guba a ciki. Alk'ali ajiye biron hannunshi yayi yace ina sheda? Barr Junaid d'auko wata farar takardar yayi yaje yamik'a ma alk'ali yace ya me girma me shara'a wannan itace shedata sannan a cikin file d'in mamacin ma akwai shedar hakan, nan yaje yad'auko file d'in yakawo ma alk'ali yace jiya na amsoshi a asibiti. Dubawa alk'ali yayi sannan yad'ago yakalli wadda ake k'ara yace shin ko kina da ja akan wannan shedun da aka samo? Shuru tayi tana cigaba da kuka ganin haka yasa lauyanta yamik'e yace ina da ja ya megirma me shara'a abinda lauyan masu k'ara yafad'a ba gaskiya bane. Cikin kuka tace tabbas hakane nice nakasheshi saboda bana sonshi iyayena ne suka aura min shi, wallahi nice nakashe shi. Alk'ali yace kin tabbata kece? 'Daga kai tayi alamun Eh. Duk'awa yayi yai 'yan rubuce rubuce sannan yad'ago yace Alhamdulillah kin amsa laifinki bayan duk bayanai sun nuna hakan dama, dan haka kotu zata yanke maki hukuncin zaman gidan kaso har k'arshen rayuwarki domin laifin da kika aikata na kashe mijinki wannan shine adalcin kawai da zamuyi. Kuka tacigaba da yi cike da tashin hankali nan aka tafi da ita. Jawahir wani irin tausayinta taji ganin yadda take kuka saidai me matar itace me laifi babu yadda za'ayi. Haka me gabatar da k'ara yamik'e yasake bayani akan k'ara ta biyu aka fito aka fara yin shara'a. Jawahir tana nan tsaye saida akayi ma mutane hud'u inda wasu aka yanke masu hukuncin kisa wasu kuma aka maidasu gidan yari, ita d'in kanta ta san dole cikin biyu za'ayi guda ko kisa ko yanke hukuncin k'arashe rayuwa a gidan kaso, wasu siraran hawaye ne suka gangaro mata cikin zuciyarta tace Barr Faruk rayuwarka kawai nakeji ba wai abinda zai faru da ni ba, ina ma ace Ammi zata taimaka taku'butar da kai. Ana gama wad'annan shari'o'in megabatar da k'ara yamik'e yace sai shari'ar da takasance ta k'arshe a wannan ranar itace shari'ar Jawahir Muhammad Maikud'i wadda ake zargi da yin kisa na mutane d'aid'aya har mutum bakwai, inda dangin mamatan suka shigar da k'ara,, sannan yaje yamik'a ma alk'ali file d'in, kotun kacamewa tayi da surutu saida alk'ali yad'an buga tebirinshi sannan akayi tsit, Duk'awa yayi yafara duba file d'in ya d'auki lokaci yana dubawa sannan yad'ago yace kotu tana buk'atar ganin Jawahir wadda ake k'ara ta bayyana a gabanta. Police d'in matan nan ne guda biyu suka fito da ita tatsaya a wajen da ake tsayawa, me karanta k'ara yace ya me girma me shari'a wannan itace Jawahir. 'Dago kai alk'ali yayi yakalleta nan yashaidata sannan yacigaba da cewa kotu tana son ganin lauyan masu k'ara da na wadda ake k'ara. Barr MB ne yamik'e yayi sallama sannan yace sunana Barr Mahamud Bello nine lauyan masu k'ara,, sannan yakoma yazauna. Shuru babu wanda yasake mik'ewa daga cikin lauyoyin, Barr Junaid dafe kanshi yayi tare da runtse idanunshi saboda tsananin tashin hankalin rashin abokinshi dan shi kanshi shara'ar da sukayi ta maimuna ya san ya yi k'ok'ari sosai a yadda ya iya yinta saboda tashin hankalin da yake ciki. Me gabatar da k'ara ganin babu wanda yamik'e daga cikinsu yasa yak'ara cewa kotu tana son ganin lauyan wadda ake k'ara. Jawahir idanu tazuba ma lauyoyin lokaci guda tasafke idanunta k'asa dan ta san babu lauyanta a ciki. Me gabatar da k'ara ne yasake maimaitawa nan Barr MB yamik'e yakalli alk'ali yace ya me girma ne shara'a lauyan wadda ake k'ara ya gudu saboda baida bayanan da zai kare wadda ake k'ara da su. Karaf a kunnuwan Barr Junaid lokaci guda yamik'e a harzuk'e yace k'arya ne ya me girma me shara'a lauyanta ba guduwa yayi ba akwai dalili me k'arfi da yahana bayyanarshi, kallon Barr Mb yayi yace ya kamata kadinga gyara kalamanka sannan yakoma yazauna. Barr MB d'an rissinawa yayi sannan yakoma shima yazauna. Alk'ali da yake kallonsu bayan sun zauna ne yace shin ko akwai wanda lauyan wadda ake k'ara yawakilta a cikinku? Su duka shuru sukayi nan yasake cewa ko akwai wanda zai kare wadda ake k'ara? Nan ma shuru. Dan haka yaduk'a yayi 'yan rubuce rubucenshi sannan yad'ago yakalli jawahir yace Malama Jawahir kamar dai yadda shari'ar tamu ta baya takasance tsawon shekara d'aya har yau kin kasa amsa laifukanki akan zargin da akeyi maki shin ko a yau zaki iya kare kanki kafin kotu tazartas da hukunci na k'arshe? 'Dago kanta tayi takalli alk'ali sannan tamaida idanunta ga d'unbin jama'ar da suke zaune wajen kowa idanunshi akanta suna jira suji abinda zata fad'a, karaf idanunta suka safka akan mutum biyu. Alhaji Mansur da Alhaji Sufyan murmushin mugunta suka sakar mata. Idanu tazuba masu bata ko k'yaftawa musamman ma Alhaji Sufyan nan hawaye suka fara gangarowa daga cikin idanunta, tana ji kamar taje tashak'esu Alk'ali sake maimaita mata tambayar yayi ammah bata ma san yana yi ba, saida police d'in wajen suka d'an ta'bota sannan tadawo hayyacinta. Ganin bata ce komai ba yasa alk'ali yace shin ko Lauyan masu k'ara yana da k'wak'k'warar shaidar da zata ida bayyanar ma kotu cewa jawahir ce tayi kisan? Mik'ewa Barr MB yayi yace tabbas ina da ita ya me girma me shara'a inaso kotu taban dama ind'anyi ma jawahir wasu 'yan tambayoyi. Dama alk'ali yabashi nan yawuce yanufi inda jawahir take tsaye.... _____****______ Barr Faruk hankalinshi atashe yake a ranar duk k'ok'arin da yayi dan yakwance kanshi kasawa yayi yana nan zaune inda aka d'aureshi idanunshi suna a kan agogo har k'arfe tara da rabi tabuga, kallonsu yayi yaga suna zaune su biyu dan sauran ukkun basunan sun fita tare da ogansu gashi wad'anda sukafi rashin mutuncin ne suke zaune babu damar yarok'esu, runtse idanunshi yayi ahankali yace kiyi hak'uri Jawahir banda yadda zanyi in ceceki wannan itace k'addararki saidai ina maki fatan Allah yatseratar da ke,,, bud'e k'ofar da akayine yasa yai saurin bud'e idanunshi sai ganin d'aya daga cikinsune yashigo d'auke da takeaway, sauran yaji sunce ya dai bahbah wani abu aka kawo mana? Zuwa yayi ya ajiye masu kowa takeaway guda yace wani aiki ne mukayi da oga yau mun samu kud'i sosai cikin kud'in ne yace ink'ara siyo mana breakfast tunda bamu k'oshiba, su dukansu dariya sukasa sukace dakyau, nan yakoma yazauna kusa da su, su kuma suka d'auka suka fara ci, Barr Faruk yana kallonsu suka ci abincinsu shi ko ba'ayi mashi ko tayi ba. Faruk wasu irin hawaye ne masu gumi suka gangaro mashi saboda tsananin tausayin halin da Jawahir zata shiga yau, runtse idanunshi yayi yana cigaba da yi mata addu'a a cikin zuciyarshi. Jin su yayi shuru dan haka yabud'e idanunshi sai gani yayi mutane biyu daga cikinsu sun hankad'e kai saman kujera suna bacci inda d'ayan yake zaune yana kallonshi. Mamakine yakamashi cikin ranshi yace daga gama cin abinci sai bacci. Bai ankaraba kawai sai gani yayi babu mutumin a wajen, mamakine ya ida kamashi yace ikon Allah ina mutumin nan yayi? Murya ce yajiyo a bayanshi me firgitarwa wadda sautinta tacika d'akin gabad'aya yaji ance "barka da wannan lokacin Barr Faruk" Yunk'urin waigawa yayi dan yaga me magana ammah yakasa saboda d'aurin da akayi mashi. Ji yayi anbushe da wata irin mahaukaciyar dariya wadda tasa saida yad'an firgita, muryarce yaji tana cewa wannan aikina ne Barrister. Dakewa yayi yace wanene nan? Ko ma wanene yabayyana min kanshi!! Shuru yaji nan yasake maimaitawa nan ma shuru dan haka yatabbatar da babu kowa d'akin. Runtse idanunshi yayi tare da safke ajiyar zuciya. **** ***** Barr MB kallonta yayi yace Malama Jawahir a iya binciken da mukayi mun gane cewa kin kashe Alhaji Mu'azu da 'ya'yanshi biyu wanda d'aya daga cikinsu mijine a gareki kinyi kisan ba dan komai ba sai dan kawai kina so kigaje dukiyar da ke gareshi. Da mamaki tajuyo takalli Barr MB, bai damu da mamaki da yagani a fuskarta ba yacigaba da cewa, a lokacin da aka tuntu'bi Megadin ku ya bada shedar cewa daman kin dad'e kina yunk'urin kashe yayan mahaifin naki da shi da iyalanshi wannan dalilin ne yasa itama me aikin gidanku tagudu takoma garinsu saboda tsoron gargad'in da kika ta'ba yi masu a lokacin da suka ta'ba ganinki kin nufi d'akin kawun naki da wuk'a a hannunki lokacin yana bacci zaki kasheshi sai gashi 'yar aikin ta shigo ta ganki, a dalilin haka tatsorata takoma gidansu sannan shima megadinku bayan ankamaki da muka samu wannan bayanin daga wajenshi mun sake nemanshi dan musamu k'arin bayani ammah ya tsorata ya gudu ya koma garinsu chan Marad'i, shin ko zaki k'aryata wannan? Baki tasaki tana kallonshi ganin yadda yake ta zubo mata k'arya. Ganin batace komai ba yasa yacigaba da cewa sannan su kuma abokan mahaifinki kin kashesu ne saboda dalilin kun siyar masu da companynku wanda saboda karayar arzik'i yasa kuka rabu da shi shine daga baya kika dinga kashesu saboda kisamu kimaido companyn a hannunki, wannan bayanin mun sameshi a wajen sauran wad'anda suke da hannu wajen sayen companyn..... Wata irin k'ara jawahir tasaki takai hannu cikin zafin nama tashak'e mashi wuya tace wallahi k'arya kake min, meyasa zakayi min k'arya. Idanuwanshi waje sukayi saboda zafin mak'ara nan yafara neman yak'wace kanshi, police ne suka 'ban'bareshi daga hannunta alk'ali yace yakamata kisan a inda kike nan kotu ne ya zama dole kidinga ladabi. Barr MB mik'a ma alk'ali takardun hannunshi yayi nan ya amsa yaduba sannan yad'ago yakalleta yace ga shaidar siyar da company da kukayi wanda a yanzu yake mallakin mutum biyu sannan ga duk bayani akan kisan da kikayi ko zaki iya kare kanki a gaban kotu me adalci? Wasu sabbin hawaye ne suka gangaro mata tayi saurin runtse idanunta, Alk'ali sake maimaita mata yayi, ahankali tagirgiza kai alamun a'a. Buga table Alk'ali yayi yace tunda bakida shedar da zaki kare kanki kotu ta yanke maki hukuncin.....tun kan alk'ali ya ida fad'a Jawahir tasulale tazauna k'asa d'irshen tare da fashewa da kuka dan ta san kisane kawai zai biyo baya gashi bata cika burinta ba....... _Sis Nerja'art✍🏻_ [7/24, 11:15 PM] Sis Nerja'art 2: *......FANSAR RAI......* *INTELLIGENT WRITER'S ASSO....®* [On Ward Together] _Follow me on Wattpad: *Sis-nerja*_ _Wannan Littafin na kud'i ne domin karantawa cikin aminci da yarda ga duk me buk'ata zai turo katin Mtn na d'ari biyu N200 kacal ta wannan number d'in 09035938246, ko ta account number 5330055604, Idan katura ka aiko da screen shot na transaction a wannan number d'in 09035938246_ _Akwai gara'basar *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shahararriyar marubuciyar nan *AMEENA ABBA UMAR* tare da novel d'in *FANSAR RAI* akan farashin N300 kacal, ko da kud'in ka sai da rabonka_ *PAGE 20* K'ofar Kotun ce aka turo da k'arfi aka shigo wanda hakan yaja hankalin duk mutanen da suke cikin kotun suka juya dan ganin wanda zai shigo, shima kanshi Alk'ali bai ida fad'in hukuncin da yayanke ma Jawhir ba, wanda yabud'e k'ofar ne yashigo inda daga bayanshi sukaji murya ana cewa Ya Megirma me shara'a kar ayanke mata hukunci na zo da hujjoji masu k'arfi da zan bayyana ma kotu wanda zaisa agane batada laifi acikin kisan da akayi. Jawahir na jin muryarshi saurin d'ago kai tayi tana kallonshi cike da mamaki, sanye yake cikin kayan aiki shi da nakusa da shi watau Barr Nas. Alhaji Mansur da Alhaji Sufyan saurin mik'ewa sukayi tsaye mamaki duk ya bayyana a fuskarsu k'arara sukace kai daga ina kake ya akayi kazo nan? Kallonsu Barr Faruk yayi yai murmushi sannan yataka yanufi wajen alk'ali yana cewa agafarceni ya me girma me shari'a. Alk'ali gyara zaman farin glass d'inshi yayi sannan yace watau sai yanzu kaga damar zuwa, kotu zakayi ma wasa da hankali bayan a farko baka zo ba saida kotu zata zartas da hukunci sannan. Matsowa yayi yace agafarceni ya me girma me shara'a babban daliline yahanani zuwa wanda idan kabani dama nagabatar da hujjata zan sanar da kotu dalilin. Jinjina kai Alk'ali yayi yace kotu ta baka dama, kowa yakoma yazauna. Nan duk aka zauna, Jawahir mik'ewa tayi tsaye daga duk'en da take tana kallonshi, shima kallonta yayi sannan yamaida kallonshi ga Alk'ali yace Allah yagafarta malam nagode sosai, a yau zan gabatar da shedun da natattara akan zargin da akeyi ma Jawahir ammah kafin nan inaso kotu tafara bani dama infara tattaunawa da wadda ake k'ara. Alk'ali yace ta baka dama. Juyawa yayi ga jawahir sannan yace shin malama jawahir ko zaki taimaka kifad'a ma kotu yadda kike da Alhaji Mu'azu da su Alhaji Tanimu? Shuru tayi tana kallonshi, nuni yayi mata alamun tayi magana sannan tace Eh Alhaji Mu'azu yayan mahaifina ne su kuma abokan mahaifina ne bayan rasuwarshi suka koma tare da yayan mahaifin nawa. Jinjina kai yayi yace dakyau sannan yajuya ga alk'ali yace Allah yagafarta malam hujjata ta farko da zan fara gabatarwa itace Marigayi Alhaji Mu'azu da Abokan mahaifinta su takwas kenan sunyi amfani da damarsu sun kashe mahaifinta da mahaifiyarta dan sugaje dukiyarshi ban fad'i hakan ba saida natabbatar da shedata. Kotun ce tafara kacamewa da hayaniya jin abinda yafito daga bakin Barr Faruk, saida aka nutsar da mutane sukayi shuru. Juyawa Faruk yayi yakalli k'ofa yace kushigo. Wani buzu ne yashigo nad'e da rawani a kanshi sai wata dattijuwa tana tura wata mata a saman wheelchair, jawahir idanu tazuba ma matar ahankali tace Ummah, matar ma kallonta tayi nan hawaye suka gangaro mata. Barr Faruk ne yanuna buzun yace wannan shine megadin gidan Alhaji Mu'azu wannan kuma uwar d'akinshi ce. Alk'ali d'agowa yayi yakallesu sannan yace ma megadin kotu tanaso kafad'a mata gaskiya akan abinda kasani a game da gidan Alhaji Mu'azu. 'Dage kanshi sama yayi yace eh zan fad'i gaskiya ni nine megadin shi kuma wannan yarinya tun bayan mutuwar iyayenta Alhaji yake azabtar da ita yana cin dukiyarta shi da abokanshi, akwai wata rana ina zaune a wajen gate ina sauraren radio Alhaji yafito zai shiga mota yafita nan naji yana waya yana cewa zai san hanyar da zaibi yafito da ita suje banki yasa taciro mashi kud'i daga account d'in mahaifinta, toh bayan nan na ta'ba jin suna magana da wani abokinshi yana cewa zai siyar mashi da wani gida da yagano k'anen nashi yana da shi baisan da gidan ba sai bayan mutuwar d'an uwan nashi, sannan a game da mutuwar d'an uwan nashi a ranar da aka shigo aka kasheshi Alhaji Mu'azu najiyo yana magana da wasu a waje ban dai ji abinda yake cewa ba saidai na ji ya ce masu ga makullin gidan nan, toh kuma da makullin aka bud'e gidan aka shigo aka kasheshi, d'aga hannunshi yayi sama yace wallahi wannan shine abinda nasani banyi maku k'arya ba. Alk'ali jinjina kai yayi sannan yaduk'a yacigaba da rubuce rubucenshi yace Barrister muna saurarenka. Faruk juyawa yayi ga Ummah yace Hajiya munaso kifad'a ma kotu matsayinki a wajen Alhaji Mu'azu da duk abinda kika sani akan kisanshi. Goge hawayen fuskarta tayi tare da motsa 'bari d'ayan jikinta da yake da lafiya sannan murya chan k'asa tafara magana ganin haka yasa aka d'auko mata lasifika aka kanga wajen bakinta fara jawabi tayi tace nice matar Alhaji Mu'azu kamar yadda kotu taso zan fad'a mata gaskiya maganar gaskiya tabbas ni da mijina mun cutawa yarinyar nan kuma ya ci dukiyarta wannan shine abinda nasani sannan itace takasheshi da 'ya'yana biyuuuuu, kyarma tafara yi tana jijjiga nan wasu nurse guda biyu sukayo saurin zuwa wajenta dan dama tare da su sukazo, alk'ali yabada izini afita da ita amaidata asibiti nan suka tafi da ita. Barr MB me yamik'e a fusace yace ya megirma me shari'a ya kamata kotu tagaggauta hukunta lauyan wadda ake k'ara akan zuwa da yayi har asibiti yazo da marar lafiya wanda a halin yanzu ya ja ta shiga wani hali, wannan ba daidai bane. Alk'ali d'agowa yayi yace Barr MB yace koma kazauna, komawa yayi cikin sanyin jiki yazauna Barr Faruk cigaba yayi da cewa shedata ta gaba da zan bada itace Marigayi Alhaji Mu'azu da Abokan mahaifinta su takwas sunyi amfani da damarsu sun kashe mahaifinta da mahaifiyarta dan sugaje dukiyarshi ban fad'i hakan ba saida natabbatar da shedata, wayarshi yad'auko yakunno recording d'in duk maganganun da yatura na wayar da su Alhaji Mu'azu yayi da abokanshi d'aya bayan d'aya yakunna ma alk'ali yasaurara, gabad'aya kotun tayi tsit ana saurare, akan lokacin da suke had'a plan zasu kashe Alhaji muhammad da kuma kisan da sukayi ma mahaifiyar jawahir sannan wajen ciro kud'i dan su mallaki dukiyarta duk ya saurara Alhaji Mansur ne yayi saurin mik'ewa yace wannan k'arya ne sharrinshi ne kawai. Kallonshi alk'ali yayi yace kotu tana gargad'inka kar kasake sa mana baki in ba hakaba zaka fuskanci hukunci. Komawa yayi cikin sanyin jiki yazauna sannan alk'ali yaduk'a yafara 'yan rubuce rubuce, nan Barr Faruk yacigaba da cewa wannan bayanin duk na sameshi a cikin wayar Alhaji Mu'azu saboda wayarshi tana saving d'in call recording, ga ma wayar ta shi nan yamik'a ma alk'ali yadudduba cikin wayar nan yajinjina kai, yace cigaba da bayaninka. Cigaba yayi da cewa sannan duk ga bayanai nan akan dukiyarta da suka mallaka da takardun jabu da suka dinga bugowa shaidar sun sayi fili da gidaje daga hannun mahaifinta, ita kuma ta shigar da k'ara kotu ammah anyi watsi da k'arar wannan dalilin ne yasa tadinga d'aukar mataki da hannuwanta saidai batayi niyar kashe d'an uwan mahaifin nataba shine yafara neman kasheta sannan ita kuma dan takare kanta takasheshi, kamar dai yadda matarshi tayi bayani. Alk'ali yace shin ko zamu iya samun bayanai agame da dukiyar Alhaji Muhammad d'in? Eh Allah yagafarta malam ammah kafin nan inaso kotu taban dama inyi ma mutane biyu wasu tambayoyi wad'anda tambayoyin ne zasu taimaka wajen samun cikakkar sheda. Alk'ali kotu ta baka dama su wanene mutane biyun? Juyawa yayi yakalli Alhaji Mansur da Alhaji Sufyan da suke zaune suna zare idanu sunyi sharkaf da zufa, Sannan yace Alhaji Mansur Maiharka da dollar sai Alhaji Sufyan me nasara. Alk'ali ne yasake maimaita sunan yace kotu tana son ganinsu sun hallara a gabanta. Su dukansu kusan tare suka mik'e cikin sanyin jiki suka fito suka tsaya. Barr Faruk matsawa yayi kusa da su yace Alhaji Mansur da Alhaji Sufyan wasu 'yan tambayoyine zanyi maku ammah kafin nan ya kamata kufara sanar da kotu matsayinku a wajen Alhaji Muhammad. Su dukansu sukace Na'am Yace eh kar dai kumanta a kotu kuke ya kamata duk abinda zaku fad'a kufad'i gaskiya. Gyaran murya Alhaji Mansur yayi sannan yakalli Alk'ali yace ni abokin kasuwancin Alhaji Muhammad ne a lokacin da yake raye bayan rasuwarshi ne muka koma kasuwanci da d'an uwanshi, wannan shine dalilin sanin da nayi mashi. Murmushi Barr Faruk yayi sannan yakalli Alhaji Sufyan yace kaikuma fa me zakace? Eh toh nima dai kamar yadda Alhaji Mansur yace nima haka nake da su. Kana nufin kaima abokan kasuwancinka ne? Eh haka. Dakyau ammah a iya binciken da nayi na gane cewa ba wai abokin kasuwanci kawai bane akwai aminta a tsakaninku da su, ammah ba ma wannan ba na san kun san komai a game da mutuwar Alhaji Muhammad da me d'akinshi Khausar ko akwai abinda zaku iya cewa? Alhaji Mansur ne cikin 'bacin rai yace kai banason zancen banza me kake nufi? Sharri zaka ja mana? Barr MB mik'ewa yayi yace ya megirma me shara'a ya kamata kotu tagargad'i lauyan wadda ake k'ara akan irin tambayoyin da yakeyi ma su Alhaji Mansur domin suna muni agaresu. Alk'ali kallon Barr Faruk yayi yace kagyara yanayin tambayarka. 'Dan rissina kai yayi yace nagode sannan yajuya garesu yace, kafin mutuwar Alhaji Muhammad kun ta'ba taruwa ku takwas a chan wani d'aki kukayi magana inda kowa yafurta abinda yakeso yamallaka na Alhaji Muhammad a k'ark'ashin jagorancin d'an uwanshi, ko zaku iya tuna haka? Su dukansu shuru sukayi suna kallon kallo sai chan Alhaji Mansur yagirgiza kai yace bansan anyi haka ba. Shuru faruk yayi sai kuma yajuya yakalli Alk'ali yace ya megirma me shara'a tabbas su Alhaji Mansur da Alhaji Sufyan suna cikin mutanen da suke da hannu akan mutuwar Alhaji Muhammad dan a nan cikin wayar da namik'o duk akwai muryoyinsu da maganganun sirrin da sukayi a tsakaninsu sannan ga k'arin shedar da ke gareni ta k'arshe, juyawa yayi yakallesu sannan yabud'e file d'in da yake hannunshi yad'ago masu yace shin cikinku akwai wanda yagane takardun da suke cikin file d'innan? Zaro idanu sukayi gabad'aya nan take cikin Alhaji Sufyan yakad'a yace ina kasamo wad'annan?. Murmushi yayi sannan yace takardar farko original ce ta companyn Alhaji Muhammad inda ta biyu takasance jabu ce kun bugotane dan ku samu ku mallake companyn ga signing d'inku nan da komai. Mai gabatar da k'ara ne yazo ya amsa yakai ma alk'ali, wasu takardun yafiddo yanuna masu yace wannan fa me zakuce akanta? Shuru sukayi suna kallonshi sai Alhaji Mansur yayi k'arfin halin cewa wannan ai kai za'a tambaya dan kai kasan sharrin da kake shirin k'ullawa. Girgiza kai yayi yace wannan ba sharri bane sannan yajuya yakalli Alk'ali yace ya megirma me shara'a wannan takardun motocin Alhaji Muhammad ne da suka samo a cikin gidanshi bayan mutuwarshi sunyi amfani da wani ya yi masu yarjejeniya akan kowane d'aya daga cikinsu Alhaji Muhammad ya siyar mashi da motocinshi biyu ga signing nan irin nashi anje anyi, zuwa yayi yamik'a ma Alk'ali nan yaduba, sannan yace ya megirma me shara'a na tabbata da za'a tuhumesu da zasu fad'i gaskiyar cewa suna da hannu a cikin mutuwarshi da kuma irin k'ulle k'ullen da suka dinga shiryawa akan dukiyarshi wadda sunci fiye da rabin dukiyar dan Alhaji Sufyan shi yashirya masu yadda zasuyi susamo dukiyar da take cikin account d'in jawahir inda su Alhaji Mansur da Alhaji Tanimu sukaje suka shirya ma kawunta k'arya a matsayinshi na bagidaje sukace yasamo masu kud'in zasu yi kasuwanci wanda zai dinga kawo masu kud'i sosai shine yayi amfani da damarshi yatafi da jawahir a banki yasa tayi mashi signing d'in rabin dukiyarta aka fiddo daga acount d'in koda yakawo masu ba wai business sukayi ba sunje sun raba kud'in a tsakaninsu ne. Alhaji Sufyan ne yayi saurin katseshi yace ya megirma me shara'a wannan k'arya ne sharri kawai yake son ja mana dan ya'bata mana suna bamusan komai ba akan abinda ake zarginmu da shi ba dan bamu aikata ba kawai dai yana da wani nufi akanmu ne dan kawai na hanashi auren d'iyata saisa yakeso ya'bata mana suna. Faruk kallon Alk'ali yayi yace ko d'aya ba sharri bane Allah yagafarta malam duk sun aikata dan ga shedu nan na tara ga muryoyinsu nan a cikin wayata. sake kunno recording d'aya daga cikin su yayi nan murya tafara tashi ana cewa "Hello kana jina ya kamata kayi k'ok'ari wajen ganin ka samo mana file d'in filin nan dan da alama zaiyi kud'i sosai ni na san yadda za'ayi asiyar da shi batare da kowa ya ganeba dan nima kaga wannan filin da kabarmin gwamnati nasiyar mawa kuma ta siya da kud'ad'e masu tsoka. Toh shikenan Alhaji koma me kenan nasan hanyar da zanbi insamo dan dama maganar da muka gama yi da Alhaji tanimu kenan dan shine jagoran komai, da ace akwai hanyar da zanbi da a yau d'innan sai naga bayan yarinyar nan kowa yahuta dan na san idan har tamutu dole abarmin gadonta gabad'aya tunda ni kad'ai ne d'an uwan mahaifinta,,, Cewar Alhaji Mu'azu. Daga chan 'bangaren dariya akayi akace kaidai kabi komai a hankali ko da baka kasheta ba zaka iya yin amfani da damarka wajen ganin mun samo dukiyar Alhaji Muhammad, inyaso idan har mun gama samun yadda mukeso zaka iya kasheta saidai kuma idan har zaka rufe ma mutane baki dan kar ayi zargin wani abu kamar yadda mukayi bayan munsa ankashe Alhaji Muhammad da matarshi. Dariya Alhaji Mu'azu yayi yace ai fiye da hakan ma zan iya sa wa ayi mata dan ni ban had'a komai da kud'iba abokina, yanzu dai zuwa anjima zan kiraka idan har nagama tattara bayanan filin inyaso sai muje musiyar da shi. Yauwa mutumina kayi k'ok'arin haka sai na ji daga gareka". Yana k'arewa wani kuma yasake kunnowa me irin muryar sukaji yana cewa, Hello Alhaji Mu'azu ina jinka d'azu ka kirani bana kusa. Eh Wallahi abokina cewa nayi ta samu fa a yanzu ga wani gida nan na Alhaji Muhammad da nagano yana da shi batare da sanin kowaba sai yanzu naga takardun gidan na je na ganshi kuma antabbatar min da nashine. Daga chan 'bangaren dariya akayi akace lallai Alhaji Muhammadu wayonshi ya yi yawa watau yana da gida batare da sanin ka ba, toh bari zan zo inje muga gidan idan har yana da girma sosai ni zan sayeshi dan dama inaso mutashi da iyalina daga nan, kace abu ya zo gidan sauk'i ai wallahi mutuwar nan tashi dad'i tayi min dan ko bakomai munsan muma mun mori dukiyarshi. Alhaji Mu'azu ma dariya yayi yace kaidai bari a yanzu gashinan ina ta facaka da kud'i yadda nakeso ba kamar lokacin da yake raye ba, ka san mutuwarshi ko kad'an bata d'aga min hankali ba sai waje d'aya lokacin da kabani layarnan insaka mashi a baki toh a nan ne nad'an tsorata dan ko da su Alhaji Mannir suka shigo gidan zasu kasheshi ban wani d'aga hankaliba dan na san zamuyi nasara. Katseshi yayi yace a'a Alhaji Mu'azu kayi shuru kar ajiyo ka asirinmu yatonu agane mune muka kasheshi abar maganar kawai zan zo yanzun nan muje inga gidan dan ka san bana wasa da kud'i,,, su dukansu dariya sukayi.... Suna gama saurare yace shin wannan ba muryarka bace Alhaji Sufyan ko itama sharri akayi maka? Fara raba idanu yayi yakalli Alk'ali cikin alamar rashin gaskiya yace ni bansan komai ba akai sharri yake son ja min wallahi. Alk'ali baice komai ba yana dai cigaba da kallonshi sai kuma yad'auko takardun gidan yasake dubawa. Barr Faruk cigaba yayi da cewa sannan akwai lokacin da Alhaji Mansur yakirani muka had'u yagargad'eni akan injaye daga shari'ar Jawahir har yad'auko mak'udan kud'i yabani ammah ban amsaba dan haka ne yasa aka kamani aka rufe a wani gida dan kar inzo inbada sheda a kotu wannan ne dalilin da yasa ban halarci kotu da wuri ba yau dan sai a yau nasamu natsero daga gidan Cikin d'aga murya Alhaji Mansur yace k'arya yake wallahi sharri kawai yake ja min ba ni bane. Kallonshi Faruk yayi yace ina da sheda da zata bayyanar da haka dan lokacin da muka had'u na yi recording d'in duk maganar da mukayi batare da ka saniba, nan yakunno recording d'in yakunna ma Alk'ali sannan yace bayan wannan akwai wata shedar, kallon Barr Nas yayi yace kace sushigo, nan yamik'e yafita duka mutanen cikin kotun juyawa sukayi dan ganin wanda zai shigo, police ne suka shigo da wasu mutane biyar a d'aure , Alhaji Mansur yana ganinsu zabura yayi nan yafara kalle kalle yana neman hanyar gudu yarasa, Barr Faruk kallon Alk'ali yayi yace wad'annan sune mutanen da yasa suka satoni suka tsareni Alk'ali kallonsu yayi yace kufad'a ma kotu tsakaninku ga Allah abinda kuka sani inkukayi k'arya kotu zata hukuntaku. Babban sune yayi k'arfin halin cewa wallahi wad'annan mutanen sune suka kiramu suka bamu kud'i sukace musato Barrister mutsareshi shine suka bamu gidan da muka zauna da shi, wallahi sune suka sa mu. Alk'ali kallonsu Alhaji Mansur yayi da gabad'ayansu idanu sun raina fata yace toh kunji duk shaidar da aka samu akanku ya kamata kufad'a ma kotu gaskiya inko ba hakaba kotu zatasa atambayeku. Shuru sukayi suna mazurai chan alk'ali yad'akko waya yakira ba'a yi minti biyar ba sai ga wasu k'atti su hud'u sun fito kowane d'aya hannunshi rik'e da shar'be'biyar bulala, Alhaji Sufyan yana ganinsu yayi saurin cewa wallahi zan fad'i gaskiya duk abinda yafaru mun aikata tabbas mu takwas ne muka shirya komai shidda daga ciki duk sun mutu, munci dukiyar Alhaji Muhammad sannan duk takardun nan mu mukasa aka had'a mana jabu muka siyar ma da gwamnati filayenshi guda biyu ko Alhaji Mansur? Fashewa da kuka Alhaji Mansur yayi yace tabbas hakane mun aikata kuma sharrin shaid'anne dan Allah munaso kotu ta yafe mana insha Allahu bazamu sake aikata irin haka ba. Alk'ali ajiyar zuciya yasafke yace Alhamdulillah kun amsa laifinku da kanku dan haka kotu zata yanke maku hukunci daidai da yadda shari'a tace, dan haka za'a yi maku hukunci guda biyu na farko dai bayan kun biya wannan baiwar Allahr dukiyarta da kukaci ku da kuke raye zakuyi zaman shekara guda a gidan kaso, na biyu kuma wannafsi binafsi dan haka ya zama dole za'a kasheku kamar yadda kuka kashe wasu. Sannan kotu ta wanke Jawahir muhammad mekud'i daga zargin da akeyi mata dan haka kotu ta saketa zata koma tacigaba da rayuwarta sannan za'a damk'a mata dukkan dukiyarta da wad'annan 'barayin sukaci. Su Alhaji Mansur duk'awa sukayi k'asa suna kuka suna cewa dan Allah Alk'ali ataimaka mana wallahi hukuncin nan ya yi mana tsauri ataimaka a safsafta mana tunda mun amsa laifinmu sannan kud'in da suka rage hannunmu basu kai wanda muka ci mata ba. Girgiza kai Alk'ali yayi yace wannan ne kuma bazai yuwu ba dole ayi maku hukunci daidai da na kowa, kubar ma ta wannan sai kun biyata kud'in da kukaja aka rufeta tsawon shekara guda batare da hak'k'inta ba. Mutanen da ke zaune cikin kotun salati suka farayi suna Allah wadai da halin su Alhaji Mansur. Jawahir da take tsaye tun d'azu inba hawaye ba babu abinda take, hannu tad'aga tafara yi ma Allah godiya sai kuma chan cikin kuka tace tunda dai har gaskiya ta bayyana na ji dad'i bana buk'atar komai daga wajensu subar kud'in na yafe kawai dai akashesu su ma shine zan fi jin dad'i. Alk'ali yace ba maganar yafewa a cikin hukuncin da kotu tazartas ya zama dole subiya wad'annan kud'in, kallon police yayi yace atafi da su subiya kud'in ga list nan na kud'inta da sukaci idan kud'ad'ensu basu isaba kusiyar da duk wata k'addara da suka mallaka. Su kuma wad'annan (yanuna wad'anda suka sace Faruf yace) atafi da su gidan yari zasuyi bauta tsawon shekara guda sannan asakesu, yana fad'in haka yabuga table d'in gabanshi. Nan take aka saka ma su Alhaji Sufyan da Alhaji Mansur ankwa aka fita da su. Nasiba da take tsaye wajen motarta ita da mahaifiyarta suna kuka nan suka nufi wajen da mahaifin nata yake kafin su isa 'yan jarida har sun rufeshi sun fara mashi tambayoyi a matsayinshi na d'an siyasa, kutsawa sukayi suka isa wajen, yana ganinsu yayi saurin sadda kanshi k'asa...... _Sis Nerja'art✍🏻_[7/24, 11:21 PM] Sis Nerja'art 2: *......FANSAR RAI......* *INTELLIGENT WRITER'S ASSO....®* [On Ward Together] _Follow me on Wattpad: *Sis-nerja*_ _Wannan Littafin na kud'i ne domin karantawa cikin aminci da yarda ga duk me buk'ata zai turo katin Mtn na d'ari biyu N200 kacal ta wannan number d'in 09035938246, ko ta account number 5330055604, Idan katura ka aiko da screen shot na transaction a wannan number d'in 09035938246_ _Akwai gara'basar *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shahararriyar marubuciyar nan *AMEENA ABBA UMAR* tare da novel d'in *FANSAR RAI* akan farashin N300 kacal, ko da kud'in ka sai da rabonka_ *PAGE 21* Nasiba cikin sheshek'ar kuka tace Daddy kalli abun kunyar da kajawo mana yanzu hakan da kayi daidai ne? Kaduba kaga halin da kajefa kanka da mu a ciki a idanun duniya, meyasa kabi son zuciya ka aikata hakan? Ba ka tunanin yadda rayuwarmu zata kasance, taya kake tunanin laifin nan da ka aikata zai goge a idanun mutane? Ya kakeso muyi da rashin ka? Meyasa haka Daddy, meyasa?,,, kukan da yaci k'arfinta ne yasa tayi saurin juyawa, har lokacin kan Alhaji Sufyan yana sadde a k'asa ji yake kamar a mafarki abin yafaru hawaye ne suka fara fita daga idanunshi, muryar matarshi yaji cikin muryar kuka tana cewa Alhaji ban ta'ba tunanin haka daga garekaba wallahi ka ban kunya ka zubar mana mutunci da k'ima daga ni har 'ya'yanka tirr da wannan halin naka, daman Nasiba ta fad'a min akwai abinda yake faruwa a kotu muzo mugane ma idanunmu ashe daman abinda zamuzo mugani kenan? Meyasa haka Alhaji!,, Nasiba ce tajuyo cikin sauri tarungume mahaifiyartata sai a lokacin yad'ago kai yakalleta. Police tisashi sukayi a gaba aka wuce da shi dan dama tuni antafi da Alhaji Mansur mota, 'yan jaridar da suke ta mashi tambayoyi bai samu ya amsa ma kowaba saboda halin nadama da yashiga. Suna jin tashin motar nan su Nasiba suka k'ara sautin kukan da suke dan sunsan tabbas a yanzu ya yi masu nisa daga rayuwarsu. Ana gama shari'ar Barr MB ne farkon wanda yafara mik'ewa yaba Barr Faruk hannu suka gaisa sannan yatayashi murna, Barr Junaid ko dasauri yazo yarungume abokin nashi yana cewa Faruk ka dawo, nagode ma Allah da mutanen nan basu samu damar cutar da kai ba, muna ta wahalar nemanka ashe kana hannun azzaluman chan. Murmushi Faruk yayi yace Junaid kaidai ko, Sai a lokacin yajuya yakalli inda jawahir take tsaye tana kuka har ya taka zai tafi sai ji yayi anrungumoshi tare da fashewa da kuka, dubawar da zaiyi sai ganin mahaifiyarshi yayi cikin sauri yarungumeta yace Mom d'ina. Cikin kuka tace nagode ma Allah da yamaido man kai Faruk wallahi na shiga damuwa sosai akan rashinka ashe zan sake sakaka a cikin idanuna, mutanen chan sun zalunceni ban yafe masuba da suka rabani da kai, ina sonka sosai d'a na. K'ara rungumeta yayi jikinshi cike da jin tausayin mahaifiyartashi yace nima haka mummyna ina k'aunarki sosai, a yanzu babu wanda zai sake rabamu muna tare. Dad da ya iso a lokacin dafashi yayi yace d'ana Faruk, k'wallah ce tacika mashi idanu yace ashe zamu sake ganinka nagode ma Allah da basu rabani da kai ba. 'Dan guntun murmushi yayi yace Daddyna nima ina farin cikin sake ganinku. Farin ciki suka dinga yi sosai a wajen duk wani me k'aunar Barr Faruk saida yazo yatashi murna duk da haka hankalinshi yana wajen jawahir samu yayi yajanye Mom daga jikinshi yace yana zuwa nan yanufi inda take, yana zuwa yabud'e baki zaiyi magana sai tarigashi tace nagode sosai Faruk da namijin k'ok'arin da kayi akaina tabbas ka cika mutumin kirki ka taimakeni a daidai lokacin da nake buk'atar taimako ka wankeni daga zargi a idanun jama'a, koda akaina ka fuskanci matsalar rayuwa ammah hakan bai sa kabarni ba nagode, nagode, nagode sosai Faruk. Cike da jin tausayinta yace jawahir kidaina cewa haka domin wannan ba komai bane kin cancanci hakan ko ma ba keba hak'k'inane intaimaka ma duk wani wanda yake buk'atar taimako irin wannan hatta rayuwata zan iya bayarwa akan aikina. Da mamaki take kallonshi cikin ranta tana jinjina ma k'wazo irin na Faruk da son taimakonshi, wasu sabbin hawayen ne suka gangaro mata tace ina ma ace Ammina tana raye taga irin wannan ranar, ina ma ace zanga irin farin cikin da zata shiga, ina ma ace Yaya Umar yana raye,,,, kukan da yaci k'arfinta ne yasa tayi saurin juya mashi baya. Faruk har ya bud'e baki zaiyi magana sai ganin Nasiba yayi gabanshi tsaye tana kuka, idanu yazuba mata ganin yadda take kuka bilhak'k'i, cikin sheshek'ar kuka tace Faruk dan Allah kayi hak'uri da abinda yafaru tabbas na yi kuskure da nakasa fahimtarka, mahaifina baiyi mana adalciba dan duk shine yajefamu a cikin wannan halin nayi nadamar kasancewarshi a matsayin uba agareni dan bai cancanci hakan ba, Allah wadai da mahaifi me hali irin nashi. Tarar numfashinta yayi yace a'a Nasiba kidaina cewa haka ko ba komai shi ubane. K'ok'arin rage sautin kukanta tayi sannan tace tabbas shi ubane ammah ba irin uban da yadace ayi alfahari da shi ba domin ya 'bata mana suna a idanun duniya wallahi na yi nadamar rayuwata ina ma ace inmutu inhuta da wannan rayuwar Faruk ban ta'ba tunanin haka daga mahaifina ba ashe daman shine yasaceka, hannuwanta tahad'e waje guda tace dan Allah Faruk kar kakamani da laifin da bani na aikata ba, tabbas nayi maka mummunan fahimta a lokacin da kaso kafahimtar da ni komai saidai duk hakan daman ubangiji ya k'addara hakan zai faru dan Allah kayafe min ba dan halina ba. Wani irin tausayinta ne yaji ya d'arsu a cikin ranshi yace Nasiba wallahi bakiyi min komai ba inma kinyi na yafe maki dan baki cancanci inrik'eki acikin raina akan wani laifi da ba nakiba. Fashewa tayi da kuka tace nagode sosai Faruk nagode, sai a lokacin tajuya inda jawahir take tsaye ta juya baya matsawa tayi tatsaya gabanta tace na tabbata kowanene akayi ma irin abinda akayi maki sai ya ji ba dad'i a ranshi dan an zalunceki anci amanarki dan Allah ina neman afuwarki akan abinda mahaifina ya aikata maki. 'Dago kai jawahir tayi tana kallonta. Ganin haka yasa Nasiba tace ba wai ina neman afuwa bane akan asaki mahaifina saidai ina neman afuwa akan kasancewata 'yarshi mukaci da hak'k'inki dan Allah kiyafe min. 'Daga mata kai kawai Jawahir tayi batare da tayi magana ba. Nasiba kallon Faruk tayi tace dan Allah Faruk kar wannan abun da yafaru yasa kabarni dan Allah kar kakalleni da halin mahaifina inaso kacigaba da kasancewa tare da ni. Juyawa yayi yakalli iyayenshi da aketa tayawa murnar dawowar d'ansu sannan yace Nasiba yanzu ba lokacin wannan maganar bace, kallon jawahir yayi yace muje kugaisa da iyayena. Bata musaba tajuyo tabi bayanshi suka tafi suka bar Nasiba nan tsaye tana kuka, daidai lokacin mahaifiyarta tazo nan tafad'a jikinta tana cewa Mummy na rasa Faruk ya daina sona, meyasa? Girgiza kai Hajiya Maijidda tayi tace a'a Nasiba kizo muje gida kawai. Haka tabi mahaifiyartata suka tafi. Faruk nuna ma iyayenshi Jawahir yayi nan suka gaisa suka yi mata jaje sannan suka tayata murnar ku'butar da tayi daga gidan kaso. Mom dai tana manne da d'an nata chan tace Faruk wai ya akayi kaku'buta daga hannun wad'anchan azzaluman? Murmushi yayi yace Mom muje gida sai insanar da ku komai. Dad ne yace Alhamdulillah kinga zuwan da mukayi kotu ya yi amfani daman raina ya bani zamu ga Faruk saisa nace maki muzo, yanzu kuzo muje gidan. Gabad'ayansu suka d'unguma suka nufi gida dan da fari har Jawahir ta k'i binsu ta ce ita dai subarta a nan zata tafi gidansu saidai Dad yace shin mu ba iyayenki bane Jawahir? Ko bakomai nima matsayin uba nake a wajenki saboda matsayin mahaifinki a wajena. Da mamaki suke kallonshi tace daman ka san Abbu? Murmushi yayi yace sosai ma muje gida zan sanar da ke inda nasanshi, bata musaba sannan tabisu suka nufi gidansu Faruk gabad'ayansu har da su Barr Nas da Barr Junaid. Suna zuwa Mom d'akinta taja Jawahir tahad'a mata ruwan wanka tayi bayan ta fito tad'akko mata wata jallabiya tabata tasaka saida sukayi sallah sannan suka fito parlor Jawahir dai ta kasa sakin jiki dan ita rayuwarta ba mai saurin yadda da mutane bace tunda tataso haka take, suna nan zaune su Dad da su Faruk suka fito kusan lokaci guda bayan sun dawo daga masallaci, koda suka zauna Dad cewa yayi afara kawo abinci aci kafin afara wata magana dan haka Mom taje tasanar da masu aiki, nan da nan aka fara shigo masu da abinci iri iri kowa yafara serving d'in kanshi ammah banda jawahir ganin ta k'i sakin jiki yasa mom ta d'ibi abincin tajata sukaje d'akinta tace Jawahir kisaki jikinki nan ma gidane kiyi abinda kikeso mu bamuda matsala kinji. Murmushi tayi tace nagode Mom. Duk yadda Mom taso taci abincin k'i tayi dak'yar tad'anci kad'an tabarshi dan haka tak'yaleta. Bayan kowa ya kimtsa cikinshi suka had'u a parlor. Dad ne yafara cewa toh Alhamdllh a yanzu sai kasanar da mu yadda akayi kaku'buta. Faruk murmushi yayi sannan yakwashe yadda akayi aka saceshi yafad'a masu da yadda yadinga shan wahala a wajensu har zuwa shigowar d'an uwan nasu da takeaway yakawo ma sauran. Su duka idanu suka zuba mashi suna kallonshi cike da mamaki dan Mom ko hawaye tafara ganin haka yasa Faruk yacigaba da cewa "duk a tunanina wannan me dariyar ya tafi jin shurun da yayi sai chan naga bayyanar wata tsohuwa a gabana dudduk'e tafiyarta dakyar dakyar " kallon jawahir yayi yace ke dai na san kin gane ko wacece, d'aga kai tayi alamun Eh, cigaba yayi da cewa tana bayyana kallona tatsaya yi sai chan tace Barrister daman ban fad'a maka ba nice kad'ai nake da ikon taimaka ma Jawahir? Wani irin kallo nayi mata cikin nuna rashin tsoro nace taimako na ubangiji ne shikad'ai yake iya taimaka ma bawansa. Bushewa tayi da dariya tace bazanyi maka jayayya ba saidai ina farin ciki guda a yau Jawahir ta yi nadamar da dadad'ewa nake jira tayita ammah saboda taurin kanta batayiba a yanzun ma abun bak'in cikin ta yi ne ba dan komai ba sai dan tana neman intaimaka maka. Kallonta faruk yadinga yi cikin nuna rashin fahimtar maganarta. 'Dan dogaro sandarta tayi tamatso kusa da shi sannan tacigaba da cewa a lokacin da za'a fito da su akaisu kotu hankalinta a tashe yake ganin haka yasa nabayyana a gareta natambayeta ko tana buk'atar taimakona? Girgiza kai tayi tace bana buk'atar taimakonki. Bushewa da dariya tsohuwar tayi tace cikin ke da Faruk dole sai wani ya riga wani shek'awa lahira. A rikice jawahir tace ban fahimta ba me zai faru da faruk d'in? Sake bushewa tayi da dariya saida tayi me isarta sannan tace zasu kasheshi a bayan an yanke maki hukunci a kotu saboda kar susakeshi yatona masu asiri. Fashewa Jawahir tayi da kuka cikin sauri taduk'a k'asa tace Ammi na rok'eki dan Allah kitaimakeshi kar kibari sukasheshi bai cancanci hakan ba. Girgiza kai tayi tace bakida ikon neman taimakona batare da yin nadama ba. 'Dago kai tayi fuska sha'be sha'be da hawaye tace indai har akan Faruk ne na amince saida taruntse idanunta cike da takaici sannan tace na yi nadamar kalmar da nafad'a maki kiyi hak'uri insha Allahu bazan sakeba, ina sonki Ammina....dariyar da taji ana kyalkyalawane yasa tayi saurin bud'e idanunta dan gabad'aya d'akin yake amsaba dubawa tayi taga babu Ammin tata saidai muryar dariyar taji tana fita, tana nan duk'e a haka akazo aka fita da su aka tafi da su kotu. Tana kawowa nan a bayanin nata tanuna inda Faruk yake zaune da sandarta sai gani yayi d'aurin da akayi mashi ya kwance, cikin muryarta me ban tsoro tace zaka iya fita ga k'ofa chan a bud'e nan da minti takwas zata iya rufe kanta, jin haka yasa Faruk yayi saurin mik'ewa duk sai yajishi wani iri dakyar yafara takawa dan a lokacin matar har ta 'bace, bin gidan yadinga yi da kallo bai san inda yakeba da karambani yagano k'ofa yana fita k'ofar tana maida kanta tadatse tsayawa yayi yak'are ma gidan kallo saida yagane anguwar sannan yasamu abun hawa yahau yanufi gidan Barr Nas, ya yi sa'a ya sameshi a gida nan yayi ta murnar dawowarshi wanka yayi yashirya cikin sauri, sannan yace ma Nasir yad'auko mashi ajiyar da yakawo mashi ranar da za'a kamashi dan dama jikinshi ne yadinga bashi kamar akwai abinda zai iya faruwa da shi wannan dalilin ne yasa yad'auki dukkan shedun da yatara yakai ma Barr Nas ya ajiye mashi wajenshi hatta wayarshi da yafi amfani da ita saida yakashe yabashi dan ya san a cikinta ya ajiye abubuwa dadama masu muhimmanci,daga nan suka fito cikin sauri suka nufi kotu dan a lokacin sun makara dan sunsan dole cikin biyu ayi d'aya ko angama shari'ar Jawahir ko kuma ana cikin yi....yana kawowa nan a labarin yace wannan shine abinda yafaru da ni. Hankalinsu gabad'aya saida yatashi sosai Dad yace tabbas Alhaji Sufyan ya kasance maha'inci ban ta'ba tunanin haka daga gareshiba ace da sa hannunshi aka sace min d'a duk kusancin da ke tsakaninmu ina mashi kallon abokina na k'warai ashe ba haka ba. Jawahir sai a lokacin tad'ago takalleshi tace ya akayi kasamo Ummah katafo da ita? Murmushi yayi yace lokacin da naje asibitin naga halin da take ciki nan nanemi taimakon likitocin suka taimaka suka ban ita nacanza mata asibiti inda zata fi samun kulawa dan asibitin da su Alhaji Mansur suka kaita wata k'aramar asibiti ce wadda basuda wadatattun kayan aiki kuma sunyi hakane dan kawai suna so tamutu itama, toh cikin ikon Allah ina maidata chan suka dinga bata kulawa sosai har tafara samun sauk'i, dan tana iya motsa 'bare d'aya na jikinta saisa ma nace atafo da ita tunda tana magana. Shi kuma megadinku buzu wannan aikinki ne dan kece kika samar mana taimako Amminki tasanar da mu inda yake. Jinjina kai su Dad suka dinga yi mamaki duk ya cikasu. Barr Junaid yace lallai sharrin su Alhaji Mansur ya fi tunanin duk wani me tunani ashe duk wannan k'ulla k'ullan su sukayi shi sukaja aka kama baiwar Allahr nan. Dad girgiza kai yayi yace wasu mutanen macen zuciya garesu babu abinda sukasa gaba sai son kansu, kallon jawahir yayi yace tabbas na san mahaifinki dan abokin kasuwancina ne a lokacin da yake raye kamfanina da nashi kusan tare suke tafiya dan ma baza'a had'a ba nashi kamfanin ya fi nawa d'aukaka saboda wasu kayan ya fini saidai shi ba mutum bane me bak'in ciki yana son cigaban mutane nan yasa muka had'a hannu tsakanin kamfanina da nashi muna shigo da kaya tare wani lokacin idan kamfaninshi yana buk'atar rancen kud'i a nawa kamfanin yake zuwa yana ranta nima haka akan wannan ne yasa muka k'ulla abota sosai akan kasuwancinmu dan kowa yana son cigaban d'an uwanshi bamufi wata takwas a haka ba nanemi rancen wasu kud'i saboda wasu kayan aikin injin da nakeso inje Dubai insiyo yad'auki kud'in yabani, koda naje Dubai saida nayi kusan wata ukku sannan nasamu yadda nakeso naturo da kayan ni ban dawoba a wata na biyar ne naturo mashi da kud'inshi daga chan saidai 1 million da tarage ban bashiba, ak'alla saida nayi wata goma sannan nadawo k'asar nan bayan na dawo ne nasamu labarin rasuwarshi nan hankalina yatashi sosai haka nad'auko million d'aya d'in nan naje gidanshi nayi sallama nasa aka kira man matarshi koda tafito nayi mata gaisuwa sannan nabata cheque d'in kud'in, tun bayan rasuwarshi na so mucigaba da kasuwanci tsakanin kamfanina da nashi ammah d'an uwanshi yak'i dan haka nabarshi lokaci guda kamfanin yadaina kawo kud'i yadda yakamata nawa yazo yafi shahara, a haka nak'ara nema muhad'a hannu da Alhaji Mu'azu mumaido ma kamfanin tattalin arzik'inshi ammah yak'i dan gani yake kamar wani cutarshi nakeson yi wannan dalilin ne yasa nafita harkar kamfanin. Jawahir fashewa tayi da kuka tace tabbas kaine Alhaji Sanin da yazo gida yakawo ma Ammina cheque akan kud'in ne aka nemi a salwantar da rayuwarta Su duka kallonta suke cike da mamaki Barr Nas yace kamar ya? Kwashe komai tayi tasanar da su akan mutuwar Amminta nan duk jikinsu yayi sanyi sukayi ma iyayen nata addu'a. Mom ce tarungumota jikinta tana lallashinta dakyar aka samu tayi shuru sannan Dad yace Jawahir kikwantar da hankalinki mu zamu zauna da ke zamu kula da ke duk abinda kikeso zamuyi maki kid'aukemu a matsayin iyayenki. 'Dago kai tayi takalleshi tayi murmushi tace nagode sosai Dad da wannan karamcin da kukayi min saidai ina so inkoma wajen dangin mahaifiyata zan je incigaba da rayuwata da su tunda suna raye, bazan iya cigaba da zama cikin garin nan ba. Haba Jawahir mu ma fa zamu zauna da ke tsakani ga Allah bazamu ta'ba cutar da ke ba,,, cewar Faruk Girgiza kai tayi tace a'a Faruk su ma suna buk'atata na sani kawai dai halin Abba ne yasa suka daina zuwa garin nan, na san ku d'in mutanen kirki ne saidai zamana a nan bazai yuwu ba. Dad yace shikenan Jawahir mun fahimceki ammah kibari kikwana biyu a nan sannan kitafi. Kallon agogo tayi tace a yau nakeson tafiya. Faruk ne yayi saurin cewa a'a ba yau ba please kid'an mana kwana biyu kamar yadda Dad yace. Shuru tayi batace komai ba. Sallamar mutane da suka jiyo ne yasa gabad'aya suka tashi suka fita suka bar Mom da Jawahir a nan Mom tana k'ara lallashinta. Mutane ne dayawa sukayo gungu guda sukazo tayasu murnar dawowar Faruk, a setting room d'in Dad suka zauna. Nan da nan gida yafara cika har mata suka dinga zuwa, Jawahir tashi tayi takoma part d'in Mom tana zuwa takwanta nan da nan tafara baccin gajiya. A ranar gidan Alhaji Mansur da Alhaji Sufyan akaje aka tattara duk dukiyoyinsu da duk abinda suka mallaka hatta gidajensu. Su Nasiba ba k'aramin tashin hankali suka shiga ba sunyi kuka sosai dan gidan da suke ciki ma amsheshi akayi akace za'a maida ma jawahir abunta dan haka suka koma wani madaidaicin gida na mahaifiyarta, yayyenta biyu masu aure saida sukazo suka ci kukansu har suka gode ma Allah, a gidajen sada labarai aka dinga yayata abinda yafaru hatta gidajen talabijin saida aka dinga nuna su Alhaji Sufyan ana fad'in abinda sukayi wannan abun ya yi ma iyalansu ciwo sosai. A ranar aka had'a duk abinda suka mallaka aka fidda ma jawahir hak'ik'k'inta sauran dukiyar kuma aka damk'ata ga iyalansu. Da dare aka kira Faruk aka sanar da shi dan washe gari yaje da jawahir adamk'a mata dukiyarta ya amsa da toh. Mom nan nan take ta yi da Jawahir ammah ita ko ta k'i sakewa da ita magana ma sai tadaina yi masu dan tunda tatashi daga bacci tacanza koda Faruk yaga yanayinta yace subarta kawai wannan ba ita bace dan haka aka k'yaleta ita kad'ai tak'unshe kanta a d'akin Mom, abinci ma akayi akayi da ita taci ammah tak'i yadda aka ajiye mata haka akazo aka d'auka. Ganin haka yasa Faruk yafara tunanin yadda zaiyi yarabata da Aljanar nan. Washe gari koda suka tashi nemanta akayi aka rasa a cikin gidan nan hankalinsu yatashi sosai dan ba'a san lokacin da tabar gidan ba, wajen k'arfe goma Malam Nasir (Kakan Faruk) ya iso garin nan yasamesu suna shirin fita nemanta yace sudawo suzauna, bayan sun zauna an gaisa ne yakalli Alhaji Sani yace Faruk ya shaida min komai ta waya wannan dalilin ne yasa nazo dan intaimaka ma yarinyar na san saboda haka ne yasa tabar gidan dan tabbas aljanarta zata san komai akai, jiya ban samu naruntsa ba ina ta aiki akan yadda zan tunkareta kuma Alhamdulillah ina tunanin zamuyi nasara. Su dukansu amsawa sukayi da masha Allah, Allah Ubangiji dai yasa adace, Dad yace ammah Malam ba a nan gizo yake sak'a ba ai ba'a san inda yarinyar take ba yanzu. Jim Malam yayi sai chan yace tana da sauran dangi a garin nan? Faruk yace a'a. Tunani yafara yi sai chan yace toh gidansu fa akwai wani a ciki? Nan ma Faruk yace a'a. Jin haka yasa Malam yace tabbas babu inda zataje sai gidansu a chan ne kad'ai aljanar zata kaita tunda babu kowa a gidan, kallon Faruk yayi yace yi sauri katashi muje chan gidan nasu, kad'auko min wacchan ledar da nazo da ita. Cikin sauri suka tashi suka fita a cikin motar Faruk suka shiga har da Dad suka tafi aka bar Mom a gida. Gudu Faruk yadinga yi da motar har suka isa gidan suna zuwa suka tarar da gate d'in a bud'e dan haka a gaban gidan sukayi parking d'in motarsu suka fito Faruk yace nan ne gidan mushiga, har ya wuce zai shiga malam yayi saurin rik'oshi yace a'a kar kushiga kujira, nan suka ja suka tsaya, addu'a yayi sannan yace sushiga suna shiga filin gidan itacene suke ta kad'awa ga ganyaye a k'asa duk sun bushe, su dukansu bakinsu d'auke da addu'a suka nufi hanyar da zata sadaka da cikin gidan suna shiga tsakar gidan wata irin k'ara sukaji me had'e da iska, nan suka ja suka tsaya kallon d'akunan sukayi sukaga kowane rufe yake, dariya ce sukaji ta fara tashi a d'aya daga cikin d'akunan dan haka cikin sauri suka nufi d'akin kafin su isa k'ofar d'akin ta bud'e kanta sai duhu sukaga ya bayyana a ciki, malam ne yace masu kowa yacigaba da addu'a kar yadaina dan haka suka nufi d'akin, Faruk wayarshi yad'auko yakunna touch sannan suka shiga, a k'arshen bango suka ganta tsaye bisa iska k'afafuwanta sun nannad'e gashin kan nan ya mik'e tsaye ga bakin nan na jirkice, idanuwanta k'ara fitowa sukayi waje k'wayar kamar ba zaune take a cikin idanun ba, gabad'aya halittarta ta canza, kallonta suka tsaya suna yi cike da mamaki, Faruk ne yayi k'arfin halin cewa Jawahir ya akayi kikazo nan? Wata irin murya sukaji me kama da gurnanin zaki ana cewa taya zan zauna bayan kunaso kurabani da rayuwata bazan ta'ba barin duk wanda yaso yarabani da duniyarnan ba. Malam nuni yayi ma Faruk alamun yayi shuru sannan shi yace ya zama dole kirabu da yarinyar nan kidaina wahalar da ita hakanan. Bushewa tayi da dariya tare da matsowa bisa iska har lokacin bata safka k'asa ba tace hakan ba zai ta'ba yuwuwa ba babu wanda zai rabani da d'iyata ko wanene yaso haka sai na ga bayanshi. Malam na jin haka ya amshi ledar da take hannun Faruk yabud'e yad'auko wata roba k'arama wadda take d'auke da wani ruwa a ciki, sannan yad'auko wata leda me d'auke da wani farin abu kamar gari, bud'e ledar yayi yad'ebo farin abun yayi bismillah yawatsa mata, wata irin k'ara tasaki sai gata ta fad'o tim k'asa, hasken d'akin ya dawo. cikin sauri yabud'e robar yawatsa mata ruwan, nan tasake sakin wata k'ara me k'arfi wadda tasa saida suka toshe kunnuwansu saboda kar k'arar ta lahanta masu dodon kunne, cikin k'araji tace kar kakuskura kasake watsa min ruwan nan banaso kadaina, wanene kai???? Malam kallonsu Faruk da Dad yayi yace kuje kurik'e man ita, su duka suka nufi wajen da take kafin su isa hannu tad'aga tanunasu sai gasu kamar anyi wurgi da su su biyun sun fad'a chan gefe. Ganin haka yasa malam yafara karanta ayoyin Allah dak'arfi sannan yafara zagaye d'akin yana d'ibar ruwan yana watsawa nan tadinga ihu tare da yunk'urin ja da baya, Faruk ne yafara mik'ewa dakyar yanufi inda take malam wurgo mashi garin maganin yayi yace yawatsa mata a saman kanta nan ya amsa ya watsa mata tasake sakin wata k'arar sannan tasulale k'asa asume, ganin haka yasa malam yai saurin isa wajenta yace ma Faruk yabud'e mashi bakinta, nan yafara k'ok'arin bud'ewa dak'yar yasamu yabud'e mata nan Malam yazuba mata ruwan maganin a ciki, yagoga mata na garin a fuska, bud'e idanunta tayi tare da k'wala k'ara tature Faruk da ke rik'e da ita nan tabank'are jikinta tare da bud'e bakinta gabad'aya nan wani irin farin hayak'i ne yadinga fita daga bakin, idanuwanta duk sukayo waje, hayak'in yana gama fita kallonsu tayi d'aya bayan d'aya sai kuma tamaida idanunta tarufe tadaina ko da motsi. Faruk yace Malam me yafaru da ita bata motsi ko ta suma? Malam da yake kallonta girgiza kai yayi sannan yakalli su Faruk yace ba suma tayi ba tana raye bazata ta'ba tashiba har sai anyi abu d'aya. Cikin rashin fahimtar maganarshi sukace bamu ganeba Malam Jinjina kai yayi yace tabbas layar da aka sa ma gawar ne a kusa da iccen suri aljannun da suke cikin iccen ne suka tado fatalwarta kuma tana rayuwa ne a cikin hak'ark'arin jawahir wannan dalilin ne yasa take amfani da jikinta da ruhinta, sannan wannan fitar da tayi zata iya dawowa nan da 'yan awanni kad'an idan har ba'ayi saurin zuwa k'abarinta aka tono wannan layar ba dan a yanzu haka layar tana nan cikin k'abarin da antone aka k'one shikenan fatalwar zata koma bazata sake bayyanaba. Saurin mik'ewa Faruk yayi yace ni zan je intone k'abarin kujirani bari inje ind'auko megadinsu yarakani mak'abartar. Malam yace toh kutafi da ashana da kun tono ku k'oneta kar kubaro wajen baku k'onetaba Faruk ya amsa da toh nan yawuce cikin sauri yatafi..... _Sis Nerja'art✍🏻_ [7/24, 11:21 PM] Sis Nerja'art 2: *......FANSAR RAI......* *INTELLIGENT WRITER'S ASSO....®* [On Ward Together] _Follow me on Wattpad: *Sis-nerja*_ _Wannan Littafin na kud'i ne domin karantawa cikin aminci da yarda ga duk me buk'ata zai turo katin Mtn na d'ari biyu N200 kacal ta wannan number d'in 09035938246, ko ta account number 5330055604, Idan katura ka aiko da screen shot na transaction a wannan number d'in 09035938246_ _Akwai gara'basar *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shahararriyar marubuciyar nan *AMEENA ABBA UMAR* tare da novel d'in *FANSAR RAI* akan farashin N300 kacal, ko da kud'in ka sai da rabonka_ *PAGE 22* Yana barin gidan chan gidan da yasafke buzu megadi lokacin da yad'akkoshi daga Marad'i dan yazo yabada sheda yawuce ya yi sa'a daidai lokacin yafito daga cikin gidan, ganin motar Faruk yasa yanufo wajen cikin hausar shi da bata fita sosai yace hannu da zuwa Alhaji hannu. Murmushi Faruk yayi yace yauwa buzu megadi ashe na yi sa'a da fita ma zakayi. Washe baki yayi yace eh na d'an fitone zanga gari kafin gobe inkoma garinmu. Allah sarki, yanzu shigo mota inmaka wata tambaya. Bai musaba yabud'e motar yashiga yace toh Alhaji ai dun yanda kashe haka za'ayi. Yanayin maganarshi tana ba Faruk dariya har saida yayi murmushi sannan yace yauwa tambayar da zanyi maka itace: dan Allah kana iya tuna mak'abartar da aka binne Hajiya Khausar bayan ta rasu? Yatsa yasa yadafe kanshi irin yana tunanin nan sai chan yace Eh aradu har k'abarinta na sani kusa da wani iccen giginyane akwai tudu a wajen ban mancewa har lokacin nayi tuntu'be a wajen nafad'i bayan mun rufota har yanzu akwai tabon gurjewar da nayi a gwiwata bari ma kaganshi. A'a kabarshi ba sai na ganiba yanzu fad'a min mak'abartar muje dan inason ganin k'abarinta. Angama oga nan yafad'a mashi Faruk yaja motar dagudu yanufi anguwar da mak'abartar take suna zuwa suka samu waje daga chan k'etare sukayi parking d'in motarsu suka tsallako, megadin mak'abartar suka samu suka gaisa nan Faruk yafayyace mashi komai akan abinda yakawoshi, da fari megadin be yarda ba dan ya yi tunani wani abu sukeson yi ne kawai. Ganin haka yasa Faruk yace na san baka yarda da maganataba saboda duniyar nan ta yanzu ta 'baci matsafa sunyi yawa suna amfani da wani sashe na jikin gawa suna tsafi da shi, wallahi ni ba wannan yakawoni ba idan baka yarda ba muje tare ayi komai a gabanka. Jin haka yasa megadin ya amince suka je tare buzu megadi tsaye yayi yana tunanin inda zai gane k'abarin saboda tsawon shekaru ukku kenan da binneta, gefe gefen mak'abarta yafara bi dan ya san tabbas daga gefe yake, megadi ganin haka yasa yace da hak'ura kukayi dan kusan shekara ukku ai babu abinda zaku samu saboda bayan ita mutum dubu nawa aka binne a wajen. Jikin Faruk sanyi yayi dan ya san gaskiya megadi yafad'a. Daidai wani iccen giginya dake kusa da wani d'an rami buzu megadi yatsaya yace alk'ur'an nan ne wajen ga ma k'abarin nan kusa da giginyar nan. Megadin mak'abartar ne yace ka tabbata nan ne dan gaskiya an kwana biyu ba'a binne mutane a wajen ba dan duk gawar da aka binne saidai washe gari azo atadda k'abarin a bud'e ko ansake rufewa haka yake faruwa wannan dalilin ne yasa gabad'aya aka daina binne gawa a wajen. Sake kallon wajen yayi yace wallahi nan ne ban manceba. Jin haka yasa Faruk yace tunda ya tabbata da nan d'inne toh mutone wajen mugani ta yuwu aga gawar. Megadin mak'abartar amincewa yayi nan suka duk'a suka fara tonen k'abarin babu komai a cikinshi sai k'asa haka sukaita tonawa daga k'arshe ma sai farin yashi suka fara gani, ganin haka yasa Faruk yaduk'a yasaka hannunshi yafara lalubawa cikin yashin yana cewa indai har wajen nan ne toh tabbas zamuga layar, cigaba yayi da lalube ganin baiji komai yasa yasa suka cigaba da tone ramin har said sukayi mashi zurfi sosai sannan suka kwashe k'asar ciki, suna cikin kwasar k'asar ne buzu megadi yakwaso da wani abu bak'i nan yanuna ma su faruk. Me gadin mak'abarta ne yad'auko abun yana dubawa nannad'e yake da zare yace to menene wannan ko dai layar ce? Buzu yace anya kuwa ai laya ba bak'a bace. Wurgi yayi da shi yace wani dai abun ne daban kunga ahak'ura kawai k'ila ma ba nan bane tunda kusan shekara ukku ai ya isa amance. Faruk ne yayi saurin zuwa yad'auko abun yace tabbas raina ya bani wannan ce layar bakuga an nad'e da zare ba, bari inbud'a muga abinda yake ciki, nan yafara warware zaren saida yawarware tas yaga da fata aka had'a an d'inketa nan suka warware d'inkin sai ga wani siririn gashi guda d'aya a ciki, cire gashin sukayi suka bud'e layar nan wani bak'in hayak'i yafito daga ciki, sunan Khausar ne tun daga sama har k'asan layar, faruk yace kungani ko wallahi itace aljihunshi yafara lalube zai d'auko ashana nan sukaga wata irin isaka ta taso me k'arfi wadda tasa gabad'aya iccinan da suke cikin mak'abartar suka fara kad'awa su kansu iskar saida taso tayi masu yawa. Faruk saurin fiddo ashanar yayi yafara kyastawa saidai saboda iska da ya kyasta sai tamutu, saida yakyasta ashana kusan guda goma tana mutuwa ganin haka yasa megadi yace saidai muhad'e waje guda mukare yadda iska bazata shigaba da wannan shawarar sukayi amfani nan suka had'e wata irin k'ara suka dinga ji tana tashi a wajen ahaka suka kyasta ashanar, muryace suka juyo ana cewa kar kak'ona kabari zan tafi bazan sake dawowa ba kabarni ina gargad'inka kar kak'onata!!! Saurin cinna wutar yayi a jikin layar tafara ci, k'abarin khausar saida yad'an girgiza nan wani bak'in hayak'i yafito daga ciki, layar na kusa cinyewa a hannunshi yayardata a k'asa daidai lokacin iskar da take wajen tadaina kad'awa komai yatsaya chak, jinjina kai megadin mak'abarta yayi yace lallai Annabi ya yi gaskiya tsafi gaskiya ne yana kama mutum yanzu daman da abinda aka k'ulla ma wannan baiwar Allah saisa tun bayan ita babu wanda aka sake rufewa a cikin k'abarin nan dan ko anrufe mutum wahala za'asha sai ma ancanza mashi waje. Buzu megadi yace wallahi da gaskiyarka haka abun yake, kallon faruk yayi yace yanzu shikenan bazata sake kashe kowaba Jawahir ta dawo daidai Hamdala faruk yayi nan suka maida k'asar ramin suka rufe sannan suka wuce godiya sukayi ma megadi sosai sannan suka tafi. Biyawa yayi yasafke buzu megadi gidan da yake nan yatambayeshi gobe da k'arfe nawa zai wuce yace da asuba, kud'i yafiddo sosai yabashi yace yayi kud'in mota da tsaraba nan buzu yayi ta mashi godiya har da fita daga cikin mota yaduk'a yana godiya. Faruk yace bakomai shine da godiya da yayarda yabiyoshi suka zo katsina. A chan 'bangaren Jawahir Malam addu'o'i kawai yake yi mata, har a lokacin bata motsi sai wata irin zufa da take kwarara daga fuskarta jikinta zafi yayi sosai kamar me zazza'bi dan hucin zafin har su suna jinshi, daidai lokacin da Faruk ya k'ona layar taja dogon numfashi nan tafara atishawa, saida tayi ta fi goma. Dawowar Faruk gidan ne tafarka tatashi zaune tana binsu da kallo daga k'arshe tasafke idanunta akan faruk da yashigo a daidai lokacin ahankali tabud'e baki tace me yake faruwa da ni? Kun rabani da Ammina ko? A'a Jawahir ba rabaki mukayi da ita ba. 'Dan guntun murmushi ne tayi sannan tamik'e dak'yar tafito tsakar gidan duk su ma suka fito, wani part ne taje tabud'e tashiga taja tatsaya a tsakiyar parlorn lokaci guda tafara hawaye tajuyo takalli Faruk tace nan shine part d'inmu ni da Yaya Umar d'ina a nan muke rayuwarmu ammah Ammi tazo tarabamu wannan dalilin ne yasa nakasa cigaba da sonta, na sani kun rabani da ita bazan ta'ba damuwaba, kallonta tamaida ga Malam tace nagode sosai Malam. Faruk cikin sanyin jiki yace Jawahir kakana ne wannan. Murmushi tayi ahankali tasake cewa nagode. Saurin goge hawayen da suke kwarara a fuskarta tayi sannan tafito daga d'akin tace ya kamata inje Kebbi inason ganin dangina wad'anda su kad'ai suka rage min dangi a duniya. Dad yace a'a jawahir kibari sai kin samu sauk'i sannan kitafi, mu zamu rakaki wajen danginki. Malam yace tabbas hakan yakamata dan nima kaina akwai wasu magunguna da zan d'aurata akansu na tsawon kwana biyu. Faruk yace to kinji abinda yace dan Allah kizo mukoma gidanmu na tabbata mom zata kula da ke sosai. Ita kanta ta san jikinta yana mata ciwo dan haka ta amince, ammah saida tafara shiga part d'in Abba taduba duk wasu file babu su, kallon Faruk tayi tai murmushi tace su Abba sun mutu ni kuma antafi da ni prison ummah tana asibiti sunyi amfani da duk wannan damar sun zo sun kwashe duk wani abu me amfani, saidai wannan ba shine a gabana ba, a yanzu na fi farin ciki da natabbatar su ma zasu mutu. Faruk yace haka ne ina tayaki murnar samun 'yancin kanki jawahir. Murmushi tasake yi a karo na biyu tace nagode. A cikin motar da sukazo duk suka shiga suka koma gida, nan Malam yakawo maganin da yazo da shi yabata yace tadinga sha kullum sau ukku a rana na tsawon kwana biyu ne, godiya tayi mashi tare da su Dad, nan mom tadinga nan nan da ita. Da marece Faruk yasanar da ita neman da akeyi mata akan dukiyarta tace bazata iya zuwa ba yau saidai zuwa gobe shima d'in yayarda da hakan dan saboda batada lafiya. Bacci tadinga yi a ranar sallah kad'ai take tadata da kuma ta yi sai takoma. Malam yace abarta duk na gajiya ne da kuma yanayin da take ciki. Nan yakawo tsarabar da yakawo masu yabasu yayi masu nasiha da wa'azi dan duk zuwan da zaiyi ko idan sukaje sai ya yi masu nasiha akan suji tsoron Allah ga dukkan al'amurransu, sannan yakoma Daura. Faruk shi kanshi wani irin dad'i yaji a ranshi a yanzu ji yayi kamar an cire mashi wata k'aya a jikinshi hankalinshi ya kwanta akan ku'butar jawahir saidai chan k'asan zuciyarshi kuma akwai abinda yake damunshi wanda yake da muhimmanci a rayuwarshi, kwance yayi d'akinshi yana tunani chan kuma yamaida idanunshi yalumshe. Washe gari wajen k'arfe goma jawahir tafarka daga baccin da takoma bayan ta yi sallar asuba, Mom ce tahad'a mata ruwan wanka taje tayi bayan ta fito tasamu riga gown saman gadonta an ajiye mata, murmushi tayi tad'auki rigar taduba ta yi mata kyau sosai wasu siraran hawaye ne suka gangaro mata tana cikin kallon rigar Mom taturo k'ofa tashigo hannunta rik'e da tray, ganin Jawahir tana hawaye yasa tayi saurin ajiye tray d'in ta iso wajen tana cewa jawahir lafiya? Me yafaru? Batare da ta janye idanunta akan rigar ba tace akowane lokaci Ammi taje kasuwa tana siya min irin wad'annan rigunan saboda ta san d'iyarta tana sonsu sosai bazan ta'ba sanin ta siyo min ba saidai da na fito daga wanka inga ta d'aura min a saman gado wannan ne natuna a lokacin da naga rigar nan, a yanzu babu Ammi na rasa komai. Matsowa Mom tayi tace duk uwa tana sanin abinda d'iyarta take so tabbas Amminki tana nan baki rasataba, saurin juyowa takalli mom tayi, Mom tace nice Amminki jawahir d'ana guda d'aya a duniya ko zaki iya kirana da Mummy. Cikin sauri jawahir tafad'a jikin Mom tare da fashewa da kuka tace nagode sosai Mom nagode tabbas ke Mom d'ina ce nagode da wannan matsayin da kika bani zan cigaba da kiranki da mom har k'arshen rayuwata. Wani irin sanyi Mom taji a cikin ranta cikin jin dad'i tace nagoe sosai Jawahir. Faruk da yake tsaye a k'ofar d'akin zai shigo dan yasanar da Jawahir fitar da zasuyi jin abinda suke tattaunawa yasa yatsaya yana saurarensu, jingine kanshi yayi da bango yana murmushi sai kuma chan yawuce yabar wajen. Mom taimaka mata tayi tashirya sannan tasata taci abinci bayan ta gama taruk'ota suka fito parlour takunna mata kallo tana yi suna d'an ta'ba hira Faruk da Dad ne suka shigo suka gansu Dad yace lallai uwa da 'yarta suna nan suna ta kallo mu sunma mance da mu. Murmushi Mom tayi tace to ya kuka iya kunsan dai babu me shiga tsakanin uwa da 'ya. Faruk ya ji dad'in furucin Mom sosai yace toh tsakanin uwa da d'a fa? Su dukansu dariya sukayi Mom tace kana kishi ne? Jawahir zamowa tayi daga saman kujerar tagaishesu cikin girmamawa suka amsa mata nan su ma suka zauna suna ta hira ita dai murmushi kawai take yanayin family d'in yana burgeta. Faruk ne yace to ke d'iyar Mom bazakice komai ba sai murmushi kawai kike yi. Mom tace ina ruwanka sarkin sa ido. Kallon Dad yayi yace kana ji ko Dad yanzu Mom ta daina ji dani ashe daman duk jin da ake da ni na rashin d'iyartane yanzu tunda ta zo ni anjefani a kwandon shara. Yanayin yadda yayi maganar har Jawahir saida tayi dariya. Mik'ewa yayi yace bari ma inyi tafiyata tunda abun haka yake tun kan Dad ma yajuya min ba, Dad yace a'a Son kayi hak'uri wa ne ni injuya maka baya. Kallon agogon hannunshi yayi yace Allah Dad su Barr Nas suna jirana bari inje, kallon jawahir yayi yace da anjima idan nadawo zamu fita. Amsawa tayi da toh. Nan iyayen nashi sukayi mashi Allah yakiyaye. Jawahir dai saidai kallonshi tayi batace komai ba. Wajen k'arfe ukku suka fita da Jawahir sukajr kotu aka mallaka mata komai da yake hak'k'inta na hannunsu Alhaji Mansur da Alhaji Sufyan sannan na wajen marigayi Abba ma da aka tattara aka mallaka mata matarshi bata tashi da komai ba saboda mallakin jawahir ne. Filaye kusan biyar da gidaje hud'u sai motoci biyar tatashi da su sai mak'udan kud'in da aka saka mata a account d'inta aka bata takardun kamfaninta da komai, banda kuma gidansu da suke zaune da a yanzu yazama shima mallakinta. Nan tayi godiya suka shiga mota suna cikin tafiya kallon Faruk tayi tace dan Allah ko zaka rakani gidan da su Nasiba suke zaune? Shuru yayi kamar baiji abinda taceba saida tasake maimaita mashi sannan ya amince suka je daga nesa da gidan yayi parking yace taje kar tadad'e, yana kallo tad'ibi wasu file tafita da su baice mata komai ba dan baisan abinda zatayiba, da idanu yabita har tashiga cikin gidan. Tana shiga tasamesu zaune a parlor su dukansu Mummy da yaranta ukku sunyi jugum dan mutane d'aid'aiya ne suke zuwan masu jaje basu ganetaba saboda sau d'aya suka ta'ba ganinta, yanayin yadda suka tarbeta ne yasa tagane haka. Gaishesu tayi tace sunana Jawahir mekud'i. Su dukansu jikinsu sanyi yayi dan a yanzu sun ganeta. File d'in hannunta tamik'a masu tace ga wannan takardun gidanku ne namaido maku kukoma kuzauna kucigaba da rayuwa na mallaka maku shi halak malak, domin ko bakomai baku cancanci hakan daga gareniba bakuda laifi a ciki baidace arabaku da gidanku ba. Hajiya maijidda ce kayi k'arfin halin cewa a'a jawahir ai mallakinki ne. Biro tafiddo cikin jakkarta tayi signing tamik'a mata tace gashinan kusa hannu wallahi na baku halak malak kukoma kucigaba da rayuwarku bazan ta'ba amsa ba bai dace inkasance me son kainaba ku ma mutane ne kuna buk'atar raayuwar 'yanci na tabbata zakufi jin dad'in zaman chan dan Allah na rok'eku ku amsa, kuyi hak'uri da abinda yafaru na tabbata kunji babu dad'i a ranku. Yaya sadiya ce tayi k'arfin halin amsa nan taduba su dukansu kuka suka fashe da shi sunayi mata godiya. Nasiba da idanunta suke kumbure tace tabbas ke d'iyar mutinci ce jawahir baki dace ace iyayenki aka ci ma mutunci hakaba nayi nadamar kasancewar Dad a matsayin uba agareni domin shi mutum ne meson kanshi da yawa, na yi ma kaina alk'awali bazan ta'ba taka inda Daddy yakeba saboda abinda ya aikata me muni wanda yaja mana mutane suke kallonmu da abin, ya ja munrasa komai har da k'imarmu da ace ya hak'ura baibi son zuciya ba koda ace acikin k'aramin gida muke rayuwa zamu hak'ura muzauna domin ubangiji shi yanufemu da haka, kibar gidanki jawahir hak'k'inki ne kece kad'ai yadace kigajeshi. Jawahir da tafara hawaye saboda tausayi girgiza kai tayi tace a'a Nasiba wallahi bazan amsaba na baku kyauta kuje kucigaba da zama kawai domin na tabbata da ace a lokacin ya nuna yanaso Abbu zai bashi kuma da ace Abbu yana raye bazai ta'ba bari kubar gidan ba, dan Allah na rok'eku kuzauna. Su duka shuru sukayi suna mamakin irin halin jawahir ita aka zalunta ammah ita take binsu tana rok'onsu sukoma gidan. Su duka har da mahaifiyarsu suka safko k'asa sunayi mata godiya bataji dad'in hakan ba tace sudaina nan tasa Nasiba tabata account number d'inta tayi mata transfer d'in 2millions, bayin Allahn nan suna kuka suna mata godiya ganin haka yasa tayi masu sallama su duka suka tashi dan su rakata tace a'a subarshi dan ta san Faruk bayaso suhad'u haka tafito tana goge k'wallah ta isa wajen motar Faruk da yake zaune yana waya ganinta yasa yakashe wayar tare da cewa wani abu sukayi maki? Saida tashigo tarufe motar sannan tace a'a basuyi min komai ba. Ammah me kikayi a gidan?. Juyawa tayi takalli taga sannan tace na yi abinda yadace ne, sannan tajuyo tace dan Allah saura gidan Alhaji Mansur. Da mamki yake kallonta yace wai me kike aikatawa mi kikayi da file d'in da kika fita da shi?. Hawaye ne suka gangaro mata tace Yaya Umar sai kuma tayi shuru na d'an lokaci a karo na biyu tace Barrister tun ina k'arama Abbu yana kwatanta min akan taimakon nak'asa da kai musamman wanda yashiga cikin wani hali, ya sha yace min kar inbari wani yayi kuka a dalilina kar inbari wani yayi kuka ni kuma inyi dariya inkasance mutum me adalci a rayuwata. Ajiyar zuciya yasafke dan tabbas ya gane file d'in mallaka ma su Nasiba shi tayi, rok'onshi tasake yi akan yataimaka yakaita gidan Alhaji Mansur yakaita kud'i da fili taba iyalanshi tare da maida masu motar da kotu ta amsa tashi nan suma sukayi ta mata godiya. Faruk mamakin halayyar jawahir kawai yake tabbas a yanzu ya fahimci ita mutum ce me adalci wadda abun duniya bai rufe mata idanu ba inko hakane to tabbas halin iyayenta ne tagado Koda suka koma gida Mom da Dad suka samu zaune a parlor suna jiransu, bayan sun zauna ne Jwahir tatattaro duka files d'in tamik'a ma Faruk banda guda d'aya daga ciki amsa yayi yana tambayar me zai mata da su, zataje ganin gidajen da filayen ne? Batare da ta bashi amsaba taje tamik'a ma Dad gudan tare da zama k'asa gefen k'afarshi tace Dad wannan na kamfani ne na mallaka maka shi a hannunka domin nasan kaine kad'ai zaka iya kula da shi kamar yadda zaka kula da naka. Jinjina kai Dad yayi yace shikenan jawahir na amshi wannan amanar zan kular maki da shi yadda yadace insha Allahu zan maido maki darajar kamfaninki kamar lokacin da mahaifinki yana raye. Fashewa tayi da kuka tace nagode sosai Dad sai kuma kud'in da ke account d'ina zan turo maka sai ayi amfani da su wajen ha'b'bako kamfanin. A'a jawahir banason kud'inki ni zanyi maki komai da aljihuna domin ko bakomai akwai amana tsakanina da mahaifinki. Duk da haka Dad na fi so ayi da dukiyar nan domin hankalina zaifi kwanciya,. Katseta Dad yayi yace dangin mahaifiyarki suna buk'atar wani abu daga gareki. Dad zan basu zan raba dukiyar ukku inbasu kashi guda sauran sai ayi amfani da ita. A'a jawahir tunda dai kin nace zan amshi kashi d'aya kibasu d'aya, sauran kuma kiyi amfani da ita. Ganin bataso tacigaba da yi mashi gardama amatsinyishi na babba yasa ta amince da hakan. Kallonta tamaida ga Faruk da yake jiran jin abinda zatace akan files d'in da tabashi, murmushi tayi tace wannan kuma kaza'bi gida d'aya da fili guda duk na mallaka maka sannan Dad yad'auki mota guda Mom kuma abata fili d'aya, na san kunfi k'arfin hakan ammah nima na baku ne saboda Allah dan ni kaina na san banda abinda zan iya biyanku da shi saidai addu'a Su duka sukace a'a bazasu d'auki komai ba tayi amfani da abunta duk yadda taso sud'auka ammah suka k'i dan haka tafitar da gida da mota tace zata mallaka su ga Ummah dan ko bakomai uwace gareta. Nan suka amince da hakan indai har ita zata ba babu matsala saboda ta cancanta saboda matsayinta. Bayan sun gama tattaunawane take sanar da su gobe takeso tawuce Kebbi nan suka nuna basu yarda ba, nacewa tayi da hakan saboda garin ji take duk ya gundureta komai ji take babu dad'i tunda tafito daga gidan yarin ba dan komai ba sai dan rashin wani makusancinta a cikin garin, wannan dalilin ne yasa tanace. daga k'arshe dai suka amince ba dan sun so ba sukace Allah yakaimu, sai kowa yakasance cikin shiri gobe sai muje Kebbi ammah ta flight zamu bi, inyaso sai insa driver yatafi da motar da kikeso atafin maki da ita chan, kai kuma Faruk a yau kaje kayi mana booking d'in jirgi. Toh Dad insha Allahu. Jawahir godiya tayi masu sosai har da k'wallarta nan Mom talallasheta sukace tadaina kuka. Da marece tare da Mom suka shiga kitchen tatayata girkin dare, Mom jin son yarinyar take a cikin ranta ji take ina ma ace d'iyarta ce dan a rayuwarta tana son 'ya'ya mata saidai ubangiji bai bataba sai d'a d'aya tilo. Wajen k'arfe tara Jawahir tana kwance a chan part d'in mummy kallon agogo tayi nan tamik'e tad'auko hijab d'inta tasaka tafito a main parlor, tana safkowa tasamu Faruk zaune yana dannar waya, Murmushi tayi tataka ta isa wajen da yake tayi sallama. Sai a lokacin yalura da ita nan ya amsa yace daman bakiyi bacci ba? Zama tayi tace Eh na kasa baccin ne. Idanu yazuba mata yace meyasa kika kasa? ina tunani sai zuwa anjima,,, tabashi amsa. Ajiyar zuciya yasafke yace ammah Jawahir bazaki hak'ura da tafiyar nan ba sai zuwa jibi, kinga gobe na so kije kiga filayenki da gidajen sannan gidanku ya kamata afitar da duk kayan da suke ciki. Duk'ar da kanta tayi k'asa tace ba damuwa Yaya Umar kai zaka iya.....saurin d'ago kai tayi tace am yi hak'uri wlh na saba cewa yaya umar ne. Murmushi yayi yace ba damuwa nima ai Umar d'inne ko kin mance? Murmushin itama tayi tace kaima yayanane ammah saidai ince Yaya Faruk. A karo na biyu yayi murmushi yace nagode sosai jawahir da wannan matsayin da kika bani daman kinga ban da kowa ni kad'ai ne wajen iyayena sai 'ya'yan k'anwar iyayena. Jawahir tace Allah sarki, ashe bakasan dad'in k'anneba. Tarar numfashinta yayi yace au ke kin sani ashe? Dariya tayi har saida hak'oranta suka bayyana tace ina fa nasani, ni dai gobe zan tafi Kebbi. Hmmm kedai kin k'agara kitafi kamar wani abu muke maki to wai ma kin san inda suke zaune? Eh Man a cikin garin Fanah a lantarki, ko da ba lallaine ingane gidan ba ammah gidan ba wani me wuyar ganewa bane da ance gidan Malam me salati duk an sanshi acikin lantarki. Toh shikenan goben sai muje ammah naso kije kigano gidajen, ko zaki shirya tun da wuri mufara zuwa. Girgiza kai tayi tace a'a Yaya Faruk bazan iyaba ni fa duk sun fita raina banason ganin gidajen da filayen, K'wallar da yaga sun cika mata idanu ne yasa yace shikenan Jawahir ya kikeso ayi maki da su a aje maki har sai ranar da kikazo katsina?. Shuru tayi sai chan tace cikin gidajen aba Ummah guda sannan duk kayan da suke cikin gidanmu na mallaka mata su tasa akwashe sannan abata mota guda sai kuma kud'i zan turo a account wanda za'a basu na maganinta. Faruk jinjina ma jawahir yayi sosai irin tausayinta da son taimako tabbas ba kowa ne zai iya irin haka ba, yace toh shikenan jawahir zanyi duk yadda kikeso. Nan yafiddo wayarshi yace bari kiga wani abu, gidaje ne guda hud'u da filaye ukku sai motoci ukku duk yagwada mata taduba tace wad'annan fa?. Kallonta yayi yace d'azu naje nagano su shine nad'auko maki su hoto dan na san wannam zumud'in na son zuwa kebbi bazai barki kije ganosuba kuma sai gashi hakan. Dariya tayi tace kai dai ko Barrister. Idanu yazuba mata yace nidai me? Girgiza kai tayi tace bakomai sannan takalli agogo tace bari inje inkwanta dare ya yi fa. Faruk yace toh shikenan sai Allah ya kaimu nima yanzu zanje inkwanta. Har ta juya zata tafi yace am baki ji ba. Juyowa tayi tace na'am. Murmushi yayi yace kije kawai ba komai. Itama murmushin tayi tajuya takoma part d'in Mom cike da farin cikin gobe zata je Kebbi..... _Sis Nerja'art✍🏻_ [7/24, 11:21 PM] Sis Nerja'art 2: *......FANSAR RAI......* *INTELLIGENT WRITER'S ASSO....®* [On Ward Together] _Follow me on Wattpad: *Sis-nerja*_ _Wannan Littafin na kud'i ne domin karantawa cikin aminci da yarda ga duk me buk'ata zai turo katin Mtn na d'ari biyu N200 kacal ta wannan number d'in 09035938246, ko ta account number 5330055604, Idan katura ka aiko da screen shot na transaction a wannan number d'in 09035938246_ _Akwai gara'basar *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shahararriyar marubuciyar nan *AMEENA ABBA UMAR* tare da novel d'in *FANSAR RAI* akan farashin N300 kacal, ko da kud'in ka sai da rabonka_ *PAGE 23* Washe gari tun da safe suka tashi suka fara shirin tafiya dan jirgin k'arfe goma zasu bi, tun wajen k'arfe tara driver yakama hanyar kebbi da mota inda aka zuba duk wata tsaraba da akwatin kayan jawahir da aka saka wanda bata san da shi ba, dan mamaki ma taba Faruk sam bata yi tunanin tatanadi kayan sawa ba. Wajen k'arfe goma saura Barr Nas yakaisu airport, goma daidai tana yi jirginsu yad'aga zuwa KEBBI STATE tunda suka baro gida jawahir shuru tayi duk kuma sai taji wani iri sai a lokacin tayi tunanin shin ko har yanzu dangin mahaifiyartata suna a nan cikin garin Kebbi, gabanta saida yafad'i tace Allah yasa dai suna nan. Suna safka suka samu mota suka yi shata suka kama hanyar FANAH jawahir dai titi kawai take kallo yanayin garin yana burgeta dan zata iya tunawa tun tana k'arama rabonta da garin a lokacin da Amminta taci burin k'ara zuwa da ita a lokacin tarasu, saurin goge jawayen da suka gangaro mata tayi Faruk ne kawai yalura da su ammah bai ce komai. Sun d'an d'auki lokaci suna tafiya har suka isa garin a lantarki wani dattijo suka tambaya gidan Malam me salati dan ita bazata iya ganewaba saboda da jimawa rabonta da garin nan yayi masu kwatance me mota ya ida isa da su har k'ofar gidan suka biyashi kud'inshi suka fita. Wani gida ne babba wanda da kagani ka san family house ne, daga gaban gidan akwai icce a k'ark'ashin iccen wani tsoho ne da wasu manya biyu zaune hannun tsohon rik'e da carbi yana masu magana, ganinshi yasa Jawahir taganeshi tace tabbas wanchan ne kakana na ganeshi, cikin sauri tanufi wajen da yake tace Baba Malam, daga shi har mutanen d'ago kai sukayi suka kalleta lokaci guda sukace Jawahir yau kece a garin namu? Jikin tsohon tafad'a tare da fashewa da kuka tace Baba Malam meyasa kukayi min haka kuka daina sona. Su dukansu jikinsu yayi sanyi dan basuda bakin magana, tsohon ne yayi k'arfin halin cewa bamu daina sonki ba jawahir muna k'aunarki wallahi ba laifinmu ba. 'Dagowa tayi cikin muryar kuka tace koma menene Baba malam baidace laifin wasu yashafeni ba ku duka dangin mahaifiyata kun yadani babu me k'aunata sai wad'anchan, tanuna su Faruk da suke tsaye. Juyawa su duka sukayi suka kalli su Faruk sukace bismillah sannunku da zuwa. Amsawa sukayi da yauwa nan suka zo zasu zauna d'aya daga cikin mutanen ne yace a'a kuzo mushiga gida ya za'ayi mubarku waje bismillah mushiga ciki. Gabad'aya suka mik'e suka nufi cikin gidan inda suka nufi 'bangaren Baba Malam dan gidan irin family house d'innan ne suna shiga da sallama wata 'yar dattijuya tafito daga cikin wani d'aki tana gyara zane, Baba Malam ne yace Mairo kawo mana tabarma muna da manyan bak'i yau. Cikin fara'a tace masha Allah marhabanbikum bak'inmu muna maku barka da zuwa, amsawa sukayi da yauwa. Babbar tabarma tad'auko tashimfid'a nan duk suka zauna suka fara gaisawa tsohuwar ce tazuba ma Jawahir idanu tace oh ni Mairo wannan d'iya kamar 'yar wajen khausar. Baba Malam yace itace man baki ganeta ba. Saurin rik'o jawahir tayi tace oh ni 'yar nan kece? Ashe kina nan shine baki ko lek'o mu ko dan mahaifiyarki ai ya kamata kidinga zuwa wajenmu. Jawahir kallonta tayi cikin muryar kuka tace ku ne dai baku nemana dan kunga iyayena basu raye. Baba Malam ne yace a'a jawahir ba haka bane kiyi hak'uri wallahi bamuda laifi a ciki d'an uwan babanki ne bayaso muna zuwa gidanku ga su Musa nan kitambayesu kiji irin wulak'ancin da yake mana idan munje, ko bayan rasuwar mahaifiyarki saida mukaso yabamu ke mudawo da ke hannunmu ammah yak'i yaci mana mutunci yace kar yasake ganinmu gidanshi idan har ba zuciyar kare garemuba, Musa ko ba haka yace mana ba? Wanda aka kira da Musa ne yace tabbas hakane Baba ni kaina raina ya 'baci da cin mutuncin da yayi mana ko bakomai khausar 'yar uwarmu ce baidace yahanamu zuwa ganin d'iyartaba Dad ne yace gaskiya bai kyauta ba cin mutunci baida dad'i, ba adalci bane ace ya rabata da danginta ba. Gyad'a kai Baba Malam yayi yace kaima dai ka fad'a bawan Allah raina ya 'baci sosai a duniyar nan yara hud'u namallaka ukku maza sai khausar ita kad'ai ce mace dole hankalina yatashi domin ita kad'ai ce talula wani gari tayi aure na san batada matsala da mijinta dan mutumin kirki ne saidai d'an uwanshi, wallahi tun bayan rasuwarta ban ta'ba kwana ba tare da na tuna jawahir a raina ba dan ina tausaya mata halin da zata shiga a hannun wannan mutumin. Dad jinjina kai yayi yace gaskiya ne ai Alhaji Mu'azu baida kirki, kallon jawahir yayi da take ta kuka yace Jawahir kinji dai abinda sukace ya kamata kiyi masu uzuri, tunda basuda laifi a ciki. Kallon Dad tayi tace hakane Dad na san duk Abba ne yaja min, babu komai na yafe. Su duka sun nuna farin cikinsu nan Baba Malam yatambayeta ina su Abba ya akayi yabarta tazo, Shuru tayi nan yayi murmushi cike da talaici yace wallahi Alhaji Mu'azu baida kirki wai har yayi maki aure batare da ya fad'a manaba saboda bai d'aukemu da darajaba saidai muji labari a wajen wasu, nuna Faruk yayi yace wannan ne mijin naki? Girgiza kai tayi tace a'a ba shi bane. Toh wanene? Baba Musa yajefo mata tambayar. Shuru tayi tarasa abinda zata ce masu ganin haka yasa Faruk yace Jawahir ya kamata kisanar da su komai. Fashewa tayi da kuka tace ban san abinda zan ce masu ba me zan fad'a masu? Infad'a masu duk na kashesu? Su duka a zabure sukace kin kashesu kuma? Faruk ne yace a'a Jawahir kidaina cewa haka. Cikin kuka tace toh ai ko bance ba haka yake, Baba Malam bari insanar da ku komai, gyara zamanta tayi tare da k'ok'arin tsaida kukan da take sannan takwashe komai tafad'a masu tun daga mutuwar mahaifinta da mahaifiyarta har aurenta da Umar da kisan da suka dinga yi, hatta zamanta a gidan yari da taimakon da Faruk yayi mata babu abinda ta'boye masu. Ba Baba Malam ba hatta 'yan uwan mahaifiyartata da kakarta saida suka yi kuka saboda tsananin tausayi, sukaita jimamin abun nan suka dinga yi ma su Faruk da iyayenshi godiya sukace bakomai. Baba Musa yaje yasanar da iyalanshi bak'in da sukayi yace ashirya masu abinci inda shima Baba Bello ma haka sannan yakira k'anensu Baba Nura yasanar da shi zuwan d'iyar autarsu khausar nan da nan yabaro gona yazo gida. Suna nan Driver ya iso garin ta waya akayi mashi kwatancen inda zaizo dan dama ya san garin sosai ahaka ya iso da motar. Matan su Baba Musa da yaransu ne suka zo dan sugaisa da bak'i nan Baba Musa yagwada masu Jawahir inda suma yagabatar da su a wajenta, mata biyu yanuna mata da yara bakwai yace matanshi ne da yaranshi akwai wasu yaran nashi biyar suna gidan mazajensu, sannan yanun wasu matan biyu da yara goma yace na maibi mashi ne Baba Bello, sannan mata d'aya da yara biyar yace na Baba Nura ne, nan sukaita farin cikin ganin 'yar uwartasu inda itama tanuna mafarin cikin ganin dangin mahaifiyartata. Hira aka dinga yi tsakanin su Baba Malam da su Dad inda Faruk yabi Baba Nura suka shiga gari yana nuna mashi garin nasu. Saida sukayi sallar azuhur nan suka zauna a babban tsakar gida aka baje tabarma abinci aka dinga shigowa da shi daga cikin gida had'ad'd'en dambu ne wanda yasha zogale da Tuwon dawa miyar ku'bewa d'anya gefe d'aya kuma Fura ce wadda tasha zuma sai kaji soyayyu da madarar shanu da aka dafa masu haka suka zauna suka kwashi girki abincin sosai yayi ma su Dad dad'i dan sun ci shi sosai. Bayan sun gama ne wajen k'arfe ukku Dad yace ma Faruk ya kamata yaje yayi masu booking d'in jirgin da zasu koma, Baba Malam yace ina bazai yuwuba sukoma yau saidai sukwana suka nuna a'a dan gobe akwai aiki kan dole yahak'ura yabarsu, Baba Nura ne yaraka Faruk yaje yayi booking d"in jirgin k'arfe shiddan marece sannan suka dawo. Wajen k'arfe biyar Faruk yana waje shi da Baba Nura suna hira nan Baba Nura yamik'e yace bari yad'an shiga gida yafito Faruk yace toh ba damuwa yana shiga nan Faruk yakira Jawahir a waya dan a lokaci tana cikin danginta suna ta nan nan da ita kamar sumaidata ciki, ganin Faruk ne yake kiranta yasa tayi saurin yin picking. Yana ji ta d'aga yace kifito waje Jawahir akwai maganar da nakeso muyi. Amsawa tayi da toh nan tamik'e tafito tasameshi shi kad'ai, Faruk murmushi yayi yace watau anga dangi har anmance da mu. Itama murmushin tayi tace a'a Barrister ni na isa inmance da ku bana ma fatan haka. Ajiyar zuciya yasafke yace toh Allah yasa, kiran sunanta yayi ta amsa sannan yace na so ace kin amince kizauna da mu dan Mom zatayi farin ciki da hakan ammah kin k'i, duk da banga laifin hakan ba dan kema zakifi jin dad'in zama da danginki. Cikin sanyin jiki tace hakane Barrister na za'bi zama da dangina ba wai dan bazan iya zama da ku ba kod'aya kun cancanci hakan saidai kawai sune kad'ai dangina da suka rage min a duniya zan zauna da su inyi alfahari da hakan ko da nasan da banbanci irin zaman da zanyi a nan da kuma wanda nayi a gidanmu nan gidan jama'a ne ni kuma ba mace bace da tasaba zama cikin mutane saidai a haka na san zan koyi wani darasin a cikin rayuwa. Tausayinta ne yakamata Faruk yace hakane Jawahir na san ma zaki ji dad'in zamanki da su dan su d'in dangine na gari mutanen kirki, saidai kina da dukiya a katsina bansan yadda za'ayi da gidaje da filayenki ba. Murmushi tayi tace kabar wannan a hannunka kawai. Toh shikenan zan ajiye maki ammah a duk lokacin da kika samo yadda zakiyi da su sai kisanar da ni yauwa kinga ga motar nan ya kawo maki sannan kiduba akwai akwatin kayan sawa a ciki. Da mamaki take kallonshi tace kayan sakawa kuma? Wa yabani bayan na san banda su? Ni na had'a maki dan naga bakida su kuma baki nema ba, Jawahir idan kinason wani abu kidinga fad'a min, na ce maki kid'aukeni a matsayin yaya kamar yadda kika d'auki Umar ina neman wannan alfarmar a wajenki jawahir. K'walla ce tacika mata idanu tace na d'aukeka tamkar Yaya Umar shin ka amince indinga kiranka da sunan Yaya Umar? Murmushi Faruk yayi cike da farin ciki yace na amince jawahir, nagode da wannan matsayin da nasamu a wajenki. Itama murmushin tayi tace nice da godiya akan karamcin da kuka nuna min. A'a kidaina godiya domin kin fi k'arfin hakan,,, Suna nan a haka Baba Nura yadawo nan suka zauna suna hira. Wajen k'arfe biyar da rabi su Dad suka fito nan duk mutanen gidan suka rakosu a cikin motar Baba Musa suka shiga aka kaisu Airport, jawahir kasa fitowa tayi suyi bankwana a d'akin Inna Mairo tazauna taci kukanta dan duk sai taji ba dad'i tafiyar da zasuyi daga k'arshe ko da Baba Nura yashigo yace tafito suyi bankwana da su Faruk cewa tayi ace tana masu Allah yakiyaye bayi zata shiga yanzu. Haka yaje yafad'a masu sak'onta, Dad yace Jawahir ko dai kuka take dan na ga koda zamu fito kamar zatayi kuka. Baba Nura yace nima naga tana kukan ammah ta shiga toilet yanzu. Su dukansu duk sai sukaji babu dad'i haka suka shiga mota suka tafi. Tsaraba nik'i nik'i aka had'a masu cikin ledar Viva guda biyu saboda tafiyar jirgi ce, k'arfe shidda daidai jirginsu yad'aga suka kama hanyar katsina. Tunda suka dawo gida duk sai suka ji ba dad'i da ba jawahir dan d'an kwana biyun da tayi sun saba sosai kamar ta yi wata, Bayan sallar isha'i duk takirasu tayi masu barka da safka tare da masu godiya akan taimakon da sukayi mata. Zamanta a cikin danginta ya yi mata dad'i sosai dan suna nuna mata so saisa nan da nan tasake sukaita hira, yayyen mahaifiyarta kowa ya so tazauna a 'bangarenshi ammah Baba Malam yace a'a a wajensu zata zauna dan haka suka hak'ura suka barta wajen iyayen nasu. *BAYAN KWANA BIYU* Su Nasiba sun koma a gidansu da Jawahir tamaido masu inda suka cigaba da zama ita da mahaifiyartata koda ba dad'in zaman suke ji ba saboda rashin Alhaji Sufyan ko ma ace tashin hankalin abinda yafaru, yayyen Nasiba kusan kullum sai sunzo gidan saboda mahaifiyarsu da tafi kowa sa damuwa a ranta dan har jininta saida yahau kwana biyu tad'an kwanta ciwo. Nasiba ko abu goma da ishirin suka taru sukayi mata yawa bayan tashin hankalin da tashiga ta rashin mahaifi ga kuma soyayyar Faruk da take d'awainiya da ita saidai a yanzu tana tunanin kamar bazai sake saurarenta ba. Yau ma dai tana zaune a d'akinta ita kad'ai ta buga tagumi tana tunanin masoyin nata, Aunty Sadiya ce tashigo tana mata magana ammah Nasiba bata ma san tana yi ba har saida tad'an ta'bata sannan tadawo hayyacinta saurin goge k'wallan da suka cika mata idanu tayi tace Yaya Sadiya yaushe kika shigo? Zama tayi gefenta cike da jin tausayinta tace haba Nasiba wane irin abune kike haka kina ganin hankalin kowa ba'a kwance yakeba duk muna k'ok'arin danne damuwarmu saboda mahaifiyarmu yanzu da ace ta shigo ta ganki me kike tunani kinsan dai dole hankalinta yasake tashi, kinsan dai ciwonta. Girgiza kai tayi tace Yaya Sadiya bazaku fahimceni ba, ba wai ina kuka akan Daddy bane a'a kawai ina kuka akan Faruk da nariga namallaka ma gabad'aya zuciyata wallahi yaya sadiya ina mashi son da ni kaina bazan iya misulta shi ba, ammah a yanzu Faruk ya tsaneni na san bazai ta'ba aurena ba saboda abinda mahaifina ya aikata wannan wace irin jaraba ce ya zanyi? Kifad'a min Yaya Sadiya ya zanyi Faruk yasoni? Hannunta tajanyo tad'aura saman k'irjinta tace ji kiji yadda zuciyata take bugawa akan sonshi. Tausayinta ne yakama Sadiya tajanye hannunta tare da zuba ma k'anwartata idanu da soyayya take nema tazautata. Ganin haka yasa Nasiba tafashe da kuka tace kice wani abu Yaya Sadiya dan Allah kifahimceni na san Mummy ce kawai tasan irin halin da nake ciki gashi batada isassar lafiya bare yanzu intunkareta da maganar. Dafata Sadiya tayi tace kikwantar da hankalinki Nasiba zan taimakeki nima na fahimceki kibani hankalinki gabad'aya zan fad'a maki yadda zakiyi kisamu Faruk. Saurin goge hawayenta tayi tare da tattara hankalinta gaba'aya ga yayartata dan jin abinda zata fad'a mata. _______ Mom ce zaune a Parlor tana kallo nan tafara jin sallama a wajen k'ofa. Amsawa tayi tare da bada izinin shigowa. Nasiba ce tashigo cikin ado kanta sadde a k'asa cike da jin kunya. Mom na ganinta nan cikin fara'a tace a'ah wai Nasiba ce bismillah kishigo man. Shigowa tayi a nutse taduk'a k'asa Mom tace miye haka zaki zauna k'asa kihau kujera man. Girgiza kai tayi tace a'a Mom nan ma ya yi, ina wuni? Amsawa Mom tayi sannan tatambayeta Mummynta tace tana nan lafiya lau. Daga nan kuma duk sukayi shuru Nasiba duk tarasa me ma zatace ita kuma Mom duk sai taji ba dad'i da bata jajanta masu abinda yafaru ba koda ta san Alhaji Sufyan ya yi masu laifi. Mom mik'ewa tayi tace bari inkawo maki ruwa kitashi kikoma saman kujera Nasiba. Har ta bud'e baki zatayi magana sai muryar Faruk tajiyo yana waya saurin d'ago kai tayi takalli hanyar part d'inshi da tajuyo muryar daidai lokacin da yake safkowa saman step karaf suka had'a idanu tsaye Faruk yayi a wajen yana kallonta cike da mamakin ganinta, inda itama Nasiba tazuba mashi idanu lokaci guda k'wallah suka cika mata ido, Mom tsaye tayi tana kallonsu sai chan tace Faruk ka fito ne? Jin muryar Mom yasa yayi saurin d'auke idanunshi daga kan Nasiba tare da ida safkowa yanufi wajen Mom yana cewa Eh Mom yanzu zan d'an fita ne. Ganin yadda yabasar yasa tace ga Nasiba baku gaisaba ko baka ganta ba? Batare da ya kalli inda take ba yace sannu Nasiba ya gida? Wani irin k'ululun bak'in ciki ne yatsaya mata a mak'ogoro cikin ranta tace lallai ma Faruk watau dagaske yanzu ya daina sona. Mom tace jirani Faruk inkawo ma Nasiba ruwa zan d'akko maka sak'o. Bai musaba yatsaya batare da ya ce komai ba, maida kallonta tayi ga Nasiba tace ina zuwa sannan tawuce tafita. Kamar jira suke tana fita nan duk suka zuba ma juna idanu, Nasiba saurin mik'ewa tayi tsaye tamatso inda yake cikin muryar kuka tace dan Allah Faruk kar ka azabtar da zuciyata bazan iya jure rashinka ba abubuwa biyu sun taru sun min yawa dan Allah kasafsafta min kayi hak'uri kar ka kamani da laifin da ba nawa ba. Har lokacin idanunshi suna a kanta duk ta d'an fad'a da kaga yanayinta ka san tana cikin damuwa, kauda idanunshi yayi gefe yace Nasiba ni me nayi maki? Ina ce kece da kanki kikace baki sona toh minene nawa a ciki ko ance maki ni marar zuciya ne da zanta bibiyarki. Tun kan yarufe baki tafashe da kuka tace Faruk wallahi rashin fahimta ne yasa nafad'i haka dan duk tunanina kana so katozarta mahaifina ashe ba haka bane daga baya na fahimci haka, tabbas su Dad sun kasance azzalumai da har suka aikata haka ga abokinsu saboda dukiyarshi, ni kaina ina da na sani akan kasancewata d'iya ga Alhaji Sufyan domin bai cancanci kasancewa uba agareni ba, dan Allah Faruk kayi hak'uri da abinda su Daddy suka aikata maka sannan kuma na gane kuskurena dan Allah kayi hak'uri kayafe min Faruk. Murmushi yayi cikin nuna rashin damuwa yace koma me kikayi daidai ne Nasiba ni ban rik'eki ba akan abinda yafaru kije kawai. Tun kan yarufe baki tace ammah kana nufin ka daina sona? Ta'be baki yayi yace tun lokacin da kika nemi indaina sonki ni kuma nadaina dan haka a yanzu babu sonki a raina. Saurin ja da baya tafara yi tare da k'ara sautin kukanta tace shikenan Faruk nagode ashe har zaka iya daina sona a lokaci guda? Meyasa haka Faruk? Miyasa bazaka fahimceni ba? Shuru yayi yak'yaleta jin motsin Mom yasa tayi saurin tsaida kukanta tare da sa hannu tagoge fuskarta kallon Faruk tayi da yake kallon gefe sannan tajuya cikin sauri tafita daidai lokacin da Mom zata shigo da tray a hannunta tsayawa tayi tana kallon Nasiba tace ah-ah Nasiba ina kuma zakije? Duk'ar da kanta tayi k'asa tace Mom zanje gidane. Ammah ai da kin bari kinsha ko ruwane nan fa ba bak'on waje bane Nasiba gida ne. Ahankali tace kiyi hak'uri Mom wani lokacin zan sha yanzu sauri nake su Yaya Sadiya suna jirana nagode sosai Mom,,, tana fad'in haka tawuce cikin sauri tafita. Mom mamakine yacikata tayi saurin shiga parlorn tasamu Faruk a tsaye yana dannar waya cikin 'bacin rai tace Faruk me kayi ma Nasiba? 'Dagowa yayi yakalli Mahaifiyartashi yace ni kuma Mom? Banyi mata komai ba. Ajiye tray d'in hannunta tayi tace na tabbata akwai abinda kayi mata tunda har tafita tana kuka, haba Faruk bai dace kakasance butulu ba ko bakomai Nasiba ba ita tayi maka laifi ba mahaifinta ne dan su basusan ma ya yi ba, duk wannan zaman jajen da mukayi duk da ita mukayi shi ta shiga tashin hankali sosai dan ko abinci bata iya ci sannan bata barin gidan nan sai dare shima sai su Dad d'inka sun sa ta tatafi gida, shin wannan ba k'auna bace? wallahi Faruk ba baki zan maka ba ammah na tabbata mawuyacine kasamu me sonka kamar Nasiba domin ita da zuciyata d'aya take k'aunarka. Shuru yayi duk sai yaji jikinshi ya yi sanyi dan tabbas ya san Nasiba tana k'aunarshi shima kanshi yana sonta ya yi mata haka ne kawai saboda abinda tayi mashi. Mom cigaba tayi da cewa Faruk baka isa kacanza ma zuciyarka abinda take k'auna ba a lokaci guda ammah shikenan kayi abinda kake gani daidai ne a wajenka, tana fad'in haka tawuce tabarshi wajen tsaye, runtse idanunshi yayi ahankali yace inko hakane banyi ma Nasiba adalci ba, saurin zama yayi tare da dafe kanshi yana tunanin yanayin da Nasiba tafita lokaci guda yayi saurin mik'ewa yad'auki wayarshi yafita cikin zuciyarshi yana addu'a Allah yasa Nasiba ta isa gida lafiya. Mom direct d'akin Dad ta isa tasameshi zaune yana karanta Newspaper ganin yadda tashigo yasa yace lafiya Hajiya naga duk ranki a 'bace? Zama tayi gefenshi tace dole raina ya'baci Alhaji wallahi Faruk baya kyautawa wai menene laifin Nasiba a ciki da har zai rabu da ita? Nuratu wani abun yafaru? Kwashe komai tayi game da zuwan Nasiba tasanar da shi, girgiza kai Dad yayi yace Faruk kenan kirabu da shi Hajiya ni nasan yana son Nasiba kawai dai yana dannewane, kinsan halin d'an naki ammah ina nan da ke dakanshi zai koma wajenta. Cikin sanyin jiki tace Allah yasa haka Alhaji. Ameen Nuratu kar ma kisa damuwa a ranki, yauwa daman ke naje jira ad'an kawo min coffee d'innan me dad'i wanda kika saba had'a min. Mik'ewa tayi tana murmushi tace toh Alhaji yanzu ko. Nasiba da taimakon Allah ta samu ta isa gida lafiya tana shiga a parlor tasamu mahaifiyarta da 'yan uwanta zaune k'ok'arin 'boye damuwarta tayi tamatsa kusa da Mummynta tace sannu Mummy ya jikin naki? Hajiya Maijidda ajiye ruwan da tasha magani da shi tayi idanunta suna akan d'iyartata tace Nasiba lafiya naganki haka me yafaru dan idanunki sun nuna kinyi kuka? Saurin duk'ar da kanta tayi tace bakomai Mummy ba kuka nayi ba. Haj Maijidda kallon Yaya Sadiya tayi tace wannan k'anwartaku bansan irinta ba ita akowane lokaci tana son 'boye damuwarta. Yaya Sadiya tace hakane Mummy saidai k'ila kuma ko wani abun tatuna yasata kuka. Murmushi Haj Maijidda tayi tace na san d'iyata babu abinda tatuna kawai dai soyayyar Faruk ce take d'awainiya da ita saidai Faruk bana tunanin zai cigaba da sonta saboda abinda mahaifinta ya aikata ya kamata kubata shawara tahak'ura da shi. Wasu hawaye ne masu zafi suka gangaro mata cikin sauri tajuya tashige d'akinta tamaida tarufe saman gado tafad'a nan tashiga rusa kuka da k'arfi. Su Yaya Sadiya da Yaya Na'ima sunyi juyin duniya akan tabud'e k'ofar ammah tak'i kan dole suka rabu da ita. Saida tayi kuka me isarta sannan tayi shuru idanunta duk sun kumbura kanta taji ya fara mata ciwo nan tamaida idanunta taruntse. Faruk motarshi yashiga yakife kanshi a kan steering yana jin babu dad'i akan abinda yayi ma Nasiba, sun had'a mata tension biyu ga nashi ga na mahaifinta ya san dole ta shiga damuwa sosai ba abinda yafi tada mashi hankali sai fitar da tayi cikin 'bacin rai baisan yanayin da zata isa gida ba, saurin d'ago kai yayi yad'auko wayarshi yakirata ammah har tagama ringing ba'a d'agaba sake kiran yayi nan ma ba'a d'aga ba dan haka yatada motarshi yatafi cikin ranshi yana addu'a Allah yasa ta isa gida lafiya. Nasiba ko tana kwance lokacin da yayi mata 2 missed tana ji ammah takasa bud'e idanunta taduba me kiran dan gabad'aya taji komai ma ya fita ranta batason jin muryar kowa a yanayin da take ciki. Bayan kamar minti goma wani kiran yasake shigowa a wayarki tsaki taja tare da bud'e idanunta tajawo wayar zata kashe nan idanunta suka safka ga sunan me kiranta wasu sabbin hawaye ne suka gangaro mata tamaida wayar ta aje har tatsinke wani kiran yasake shigowa ji tayi bazata iya k'in d'agawaba dan haka tayi picking tare da mannawa a kunnenta, muryar Faruk taji ya ce please Nasiba kifito gani a waje ina jiranki, ahankali ta amsa da toh sannan takashe wayar. Su Yaya Sadiya suna zaune sukaga ta fito sanye da hijab, mummy ce tace ina kuma zakije? Batare da ta juyoba tace ina nan waje sannan cikin sauri tawuce tatafi. Yaya Na'ima tace oh ni lallai Nasiba soyayya ta rufe mata idanu lallai tana son guy d'innan sosai. Hmmm kece daman baki saniba ammah Nasiba k'aunar da take ma Faruk ni har mamaki take bani daman zata taimaka tacireshi a ranta dan bana tunanin zai aureta. Mummy da take saurarensu tace a'a kudaina cewa haka ku dai kutayata da addu'a Allah yaza'ba mata abinda zaifi zama alkhairi. Su duka suka amsa da Ameen. Kanta sunkuye a k'asa tafito a harabar gidansu taganshi tsaye a jikin motarshi ammah ko da sau d'aya bata d'ago takalleshi ba har ta iso wajen, shi ko idanu yakafeta da su yana kallon yadda take tafiya a nutse dan Nasiba ba bayaba wajen nutsuwa, har ta iso wajen idanunshi suna a kanta. Tana zuwa ja tayi tatsaya sai a lokacin tad'ago idanunta da sukayi ja saboda kuka tace gani. Cikin idanunta yakalle cike da nuna damuwa yace yanzu Hearty duk akaina aka zubar da wad'annan hawayen?. Harara tawurga mashi tace kaga kafad'a min abinda yakawoka inma biyoni kayi kaimin wani wulak'ancin toh babu damuwa bismillah kayi zan iya jurewa saboda duk abinda yafaru laifina ne nice namallaka zuciyata ga wanda bai damu da ita ba, zan iya hak'ura Faruk ko da ace zan rasa rayuwata bazan sake matsa maka ba domin na san bakada laifi a ciki duk abinda yafaru na san mahaifinane yaja min. Jikin Faruk sanyi yayi sosai yace Nasiba ko d'aya banzo dan inci mutuncinki ba saidai na zone dan inbaki hak'uri sannan inmaido martabar soyayyata. Da mamaki take kallonshi tana so tayi magana ammah takasa. Ganin haka yasa Faruk yayi murmushi yace inbanda abun Nasiba taya za'ayi tayi tunanin Faruk zai iya daina sonta bayan ya riga da ya mallaka mata zuciyarshi, Nasiba ina sonki da zuciya d'aya kamar yadda kike sona wallahi nayi maki hakane dan kema kid'and'ani bak'in cikin da kika d'and'ana min a lokacin da kika nisantar da kanki agareni, bana ji zan iya daina sonki Nasiba domin kece Rayuwata. Wasu irin hawaye ne suka gangaro a fuskarta muryarta tana rawa tace dagaske kake Faruk? Dagaske kana sona zaka aureni? 'Daga kai yayi yace sosai ma indai ba kece kika daina sona ba, ammah a yanzu haka a shirye nake idan kikace inturo sai inturo ayi maganar aurenmu. 'Daga hannunta tayi sama tace Allah nagode maka da kamaido min masoyina, kallonta tamaida ga Faruk tace wallahi bazan iya daina sonka ba Faruk na riga na gama mallaka maka zuciyata idan nabarka taya zan iya son wani. Ajiyar zuciya yasafke tare da furta Alhamdulillah na yi farin ciki da jin haka daga gareki Nasiba, nima bazan iya son wata ba dan kin riga kin mamaye gabad'aya zuciyata, yanzu dai ina fatan za'a yafe min sannan acigaba da bani kulawa kamar da, komai yawuce mucigaba da nuna ma juna soyayya har zuwa aurenmu. Murmushi tayi cikin jin dad'in maganarshi tace insha Allahu Faruk na yi maka alk'awalin haka zan cigaba da baka kulawa har k'arshen rayuwata wallahi bakaji farin cikin da kasaka ni ba a yau ji nake kamar a mafarki kadawo gareni. Su duka dariya sukayi Faruk yace duk farin cikin da zaki shiga na fiki Nasiba yanzu dai kiyi min iso wajen Mummy inshiga mugaisa yau dai zan cire kunya in nemi aurenki dakaina inyaso idan nakoma gida sai insanar da su Dad su kuma su ida nasu. Wayyoo kar kuso kuga farin ciki wajen Nasiba rasa inda zata sa kanta tayi, haka tanufi hanyar cikin gida tana shiga da gudu ta isa parlor tana k'wala ma Mummy kira, su duka suka d'ago suna kallonta. Kusa da mummy tazauna cike da farin ciki tace Mummy Faruk ne yazo ya ce zai shigo yanzu kugaisa. Su duka farin ciki suka nuna nan Mummy tace taje tace yashigo. Mik'ewa tayi tafita cikin sauri suka bita da idanu, mummy tace kungani ko ai nasan suna k'aunar junansu sosai shima bazai iya barinta ba sai ya biyota. Su Aunty Sadiya sukace lallai kam ga alama nan mungani. Tana fita tasanar da shi sak'on Mummy sannan tafad'a mashi batada lafiya, a tare suka jero suka shigo gidan bakinshi d'auke da sallama yashiga parlorn suka amsa mashi har zai zauna a k'asa Mummy tace a'a kar yasaki yazauna yahau kujera dan haka yazauna saman kujera d'an zamowa yayi yagaisheta ta amsa nan yayi mata ya jiki sannan suka gaisa da su Yaya Sadiya da suke zaune gefenta. Nasiba ko baki k'in rufuwa yayi haka tafita tafara had'a mashi kayan motsa baki. Mummy ce cikin k'arfin hali tace dan Allah Faruk kayi hak'uri da abinda yafaru wallahi ba da saninmu bane Alhaji yake aikata wad'annan mugayen halayyar daga ni har 'ya'yana babu wanda yasan haka sai daga baya ashe su ne suka saceka dan Allah kayi hak'uri kar kadubemu da laifin da bamu muka aikata ba. 'Dago kai yayi yakalleta cike da girmamawa yace kod'aya Mummy bana kalkonku da laifin da ba naku bane ai laifin wani baya ta'ba shafar wani nima kaina banyi hakan dan in tozartasu ba saidai nayi ne dan intseratar da yarinyar da aka zalunta sannan daga baya ake shirin ganin anrabata da rayuwarta. Mummy tace hakane na san haka Faruk wannan dalilin ne yasa na k'ara son Nasiba takasance mata ga miji irinka domin ka cancanci asoka ko dan saboda gaskiyarka. Su yaya Sadiya sukace hakane muma muna k'ara bada hak'uri Faruk. Murmushin jin dad'i yayi yace bakomai nagode sosai, daidai lokacin Nasiba tashigo d'auke da k'aton tray ta ajiye gabanshi nan duk suka mik'e zasu bar wajen yace Mummy daman magana nakeso muyi da ke. Toh Faruk kagama sannan sai muyi maganar. Kanshi sadde k'asa yace wallahi mummy Alhamdulillah daga gida nake. Komawa tayi tazauna tace nan ma gidan ne ban yarda ba sai ka ci. Kallon Nasiba yayi da tatsiyaya mashi lemu a cup tamik'o mashi nan ya amsa tare da sakar mata lallausan murmushi itama tamaida mashi da martani. Kur'ba yayi ya ajiye sannan yaduk'ar da kanshi k'asa yace daman Mummy akan maganar auren Nasiba ne idan anban dama sai insanar da su Dad inyaso cikin satin nan atsaida rana. Mummy kallon Nasiba tayi nan Nasiba tamik'e cikin jin kunya tawuce sumi sumi tabar wajen tana ji kamar tanutse saboda kunya. Murmushi Mummy tayi tace haba Faruk wannan ai abun farin ciki ne agaremu ba damuwa kasanar da su Alhaji kawai akowane lokaci mu ai ashirye muke. Godiya yayi mata tace bakomai Faruk ai mune da godiya dan kai d'in mutum ne wallahi, dan Allah katayamu godiya a wajen Jawahir akan taimakon da tayi mana kaduba kaga yadda tamaido mana gidan da yake mallakinta da dukiya. Murmushi yayi yace ai cancanta ce tasa haka mummy kuma ku ai bakuda laifi a ciki saisa itama ta ga dacewar maido maku kayanku. Jinjina kai tayi tace Allah dai yasaka da alkgairi. Amsawa yayi da Ameen sannan yamik'e yace Mummy bari inwuce. Tun yanzu? Baka dai ci komai ba. Allah mummy a k'oshe nake ne. Toh shikenan Faruk mungode sosai Allah yasaka da alkhairi dan Allah kagaishe min da Hajiya Nuratu kafin ink'ara samun k'arfin jiki inshigo. Toh Mummy insha Allahu zata ji. Yana fita tak'wala ma Nasiba kira nan tafito tabishi a wajen mota tasameshi nan sukayi bankwana kasancewar magrib ta yi nan yaimata alk'awalin kiranta da dare. Haka suka rabu kowa zuciyarshi fal da farin ciki........ _Sis Nerja'art✍🏻_ [7/24, 11:21 PM] Sis Nerja'art 2: *......FANSAR RAI......* *INTELLIGENT WRITER'S ASSO....®* [On Ward Together] _Follow me on Wattpad: *Sis-nerja*_ _Wannan Littafin na kud'i ne domin karantawa cikin aminci da yarda ga duk me buk'ata zai turo katin Mtn na d'ari biyu N200 kacal ta wannan number d'in 09035938246, ko ta account number 5330055604, Idan katura ka aiko da screen shot na transaction a wannan number d'in 09035938246_ _Akwai gara'basar *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shahararriyar marubuciyar nan *AMEENA ABBA UMAR* tare da novel d'in *FANSAR RAI* akan farashin N300 kacal, ko da kud'in ka sai da rabonka_ *PAGE 24* A ranar farin ciki ne fal acikin ran Faruk da dare tunda suka zauna yin dinner Mom da Dad suna lura da shi da bakinshi yak'i rufuwa saboda farin ciki, su dukansu shuru sukayi suna jira suji ya fad'a masu dalilin farin cikin da yake yi. Bayan sun gama dinner ne yakalli iyayen nashi yace Dad Mom daman akwai maganar da nakeso muyi da ku. Su duka sukace toh muna saurarenka. Sosa kai yayi cikin jin kunya sannan yace daman Mummynsu Nasiba ce tace inturo ayi maganar aurenmu. Dad kallon Mom yayi takalleshi suka bushe da dariya yace Daman Nuratu ban fad'a makiba kurabu da shi dakanshi zai koma sushirya kansu. Murmushi Mom tayi tace ai gashinan yanzun na gani daman ban tsaya 'bata lokacina ba wajen yi mashi fad'a. Toh ai yanzu gashinan dai kin gani dan nasan wannan soyayyar tasu ta riga ta gama bin jinin jikinsu dan ma dai d'an nan naki ya cika taurin kai, ammah dai yanzu shikenan Faruk fad'i yaushe kakeso aje nema maka auren? 'Dago kai yayi cikin jin kunya yace ni Dad? Uhm hum muna saurarenka. Duk'ar da kanshi yayi ahankali yace cikin satin nan. Su dukansu sunji dad'in hakan da yace sukace toh shikenan babu damuwa insha Allah nan da kwana biyu zasu tura a tsaida ranar aure kawai. Cike da farin ciki yace nagode sosai Mom and Dad Allah yasaka da alkhairi, Allah yak'ara girma. Sukace Ameen. A karo na biyu suka tambayeshi ko wata nawa yakeso asa bikkin. Mik'ewa yayi tsaye saida yafara tafiya sannan yace kar yawuce wata biyu please,,, yana fad'in haka yawuce cikin sauri yanufi part d'inshi, muryar Dad ce yajiyo yana cewa kar kasamu damuwa yadda kakeso haka za'ayi Son. Yana shiga d'akinshi wanka yayi yai shirin kwanciya sannan yakira Nasiba a waya da itama tun bayan tafiyarshi bakinta yak'i rufuwa saboda farin ciki nan hankalin mahaifiyarta da 'yan uwanta yakwanta dan a yanzu sun gane duk Faruk ne dalilin damuwarta ba wai rashin mahaifinsu kawai ba. Hira suka sha sosai a waya a nan ne yake sanar da ita yadda sukayi da su Dad nan itama tayi ta murna, soyayya suka sha sosai sai da dare yaraba tsaka sannan sukayi bankwana suka kwanta tare da yi ma juna alk'awalin had'uwa gobe. Bayan kwana biyu Dad yasanar da su Malam da Su Aunty Kilima nan abokan Dad su ukku da d'an uwanshi sukaje suka nema ma Faruk auren Nasiba a wajen wani k'anen mahaifinta Malam sulaiman mutumin kirkine sosai nan ya amince aka tsaida rana nan da wata biyu masu zuwa. Haka aka koma aka fara shirye shiryen aure inda Faruk yak'ara gyara gidanshi da zai tare da amaryarshi nan da wata biyu. A chan 'bangaren Jawahir hankalinta ya kwanta sosai zamanta a wajen dangin mahaifiyarta dan tana samun kulawa yadda yadace gabad'ayansu kowa nan nan yake da ita dan haka tasaki ranta kud'ad'e tafiddo daga account d'inta dayawa taraba biyu taba kakanninta rabi sauran rabin kuma taraba ma yayyen mahaifiyartata sukaita mata godiya inda motar tabarta da sunan duk wanda zai fita yana iya d'auka yafita da ita ammah yayyen mahaifiyartata basu amimce da hakan ba su dakansu suka koya mata mota dan tadinga tuk'awa dakanta. Khausar d'iyar Baba Musa itace tsararta dan haka suka k'ulla abota sosai Jawahir tana sonta saboda sunan mahaifiyarta gareta islamiyyarsu aka sata nan tafara karatu hankali kwance inda a cikin zuciyarta taci burin cigaba da karatunta na high institution. A 'bangare guda kuma suna waya da Faruk da su Mom dan kusan kullum sai sun gaisa, a wajen Mom ne take jin labarin sa ranar auren Faruk nan tayi Allah yasa alkhairi, abun ya tsaya mata a rai sosai koda suka gama waya da Mom kiran Faruk tayi lokacin yana wajen aiki ya yi busy dayawa bai d'agaba saida yagama aikinshi sannan yakirata a waya, lokacin tana kwance suna kallo ganin me kiran yasa tatashi zaune tare da yin picking tayi sallama. Amsa mata Faruk yayi yace k'anwata ina fata kina lafiya. K'walla ce tacika mata idanu tace Yaya Faruk shine har akayi maka baiko tsawon sati biyu ammah baka fad'a min ba hakan da kayi ka kyauta ma k'anwarka? Ayya k'anwata yi hak'uri wallahi ba haka bane ina ta so infad'a maki mancewa nakeyi. "Ammah ai kusan kullum muna yin waya kawai dai bakaso kafad'a min ba sai gashi ita Mom ta fad'a min" Kiyi hak'uri Jawahir ba haka bane ai zan zo. "Uhm Allah yasa alkhairi kayi zamanka kawai,,, tana fad'in haka takashe wayarta. Faruk sake kira yayi ammah batayi picking ba murmushi yayi yace lallai ana fushi da ni Jawahir kasa samun sukuni tayi a ranar ba dan komai ba sai dan abinda Faruk yayi mata su Innah damunta sukayi da tambaya akan abinda yake damunta tace bakomai. Tun daga ranar indai Faruk zai kirata a waya bata d'agawa koda itama bata jin dad'in hakan da takeyi mashi saidai tana fushi da shi akan abinda yayi mata. ++++++++++++ A 'bangaren Hajiya Maijidda kud'i tafitar sannan tasiyar da k'addarorinta tayo ma d'iyartata order d'in kayan d'aki na gani na fad'a set biyu sannan tasiya mata kayan kitchen dan itace uwa da uba har a lokacin babu wanda yalek'a Alhaji Sufyan daga cikinsu bare susan halin da yake ciki dan su kansu kunyar tunkarar gidan yari suke da sunan sune iyalanshi. ______Wasa wasa haka aka ci wata guda ana saura wata guda bikki Mom taje itada Aunty kilima k'anwar mahaifinsu Mom suka had'o lefe na gani na fad'a akwati goma sha biyu akayi mata anzuba duk wani abu da yadace sannan aka kai lefe. Su Mummy da danginsu Nasiba sun yaba sosai da irin kayan da aka zubo mata nan suka bada tukaici me tsoka su ma. * * * Faruk ganin har lokacin Jawahir bata kulashi ba yasa yashirya ranar wata asabar yaje Kebbi batare da ya sanar da ita ba. Yana isa yakira Baba Nura yaje yad'auko shi suka nufi gidan. A waje suka gaisa da Baba Malam sannan suka shiga ciki suka gaisa da Innah a d'akinta yazauna nan takawo mashi fura me sanyi yasha, su Baba Musa duk zuwa sukayi suka gaisa nan aka cika mashi gabanshi da abinci da balango, furar yanark'a sosai dan ta yi mashi dad'i. Hira sukayi sosai da su Baba Malam da su Baba Nura duk wannan bidirin jawahir tana cikin gida wajen su Khausar batasan abinda ake ba har saida su Faruk sukayo sallar la'asar sannan Baba Nura yashiga cikin gida yasamesu zaune suna hira kallon Jawahir yayi yace kizo kugaisa da bak'o gashichan ya zo tun d'azu. Bak'o kuma?,,, jawahir tatambaya. Eh kishiga yana chan 'bangaren su Innah. Amsawa tayi da toh nan tamik'e tajawo hijab d'inta tasaka, Khausar tace wai wanene yazo? Oho nima ina sani Baba Nura bai fad'a min ba saidai kitaso muje mugani. Dariya Khausar tayi tace babu inda zanje dan wannan bak'on da alama na musamman ne lallai garinmu ya amsheki nan da nan anyi mana sabon kamu eyyen ba. Harara Jawahir tadoka mata tace kinga Khausar kidaina wannan maganar ko kin mance ni matar aure ce. Ta'be baki khausar tayi tace wallahi ba mecewa haka idan ba ke kika fad'a ba kuma ma auren da babu shi yanzu. Tsaki Jawahir taja tawuce tatafi batare da ta bata amsaba tana jiyota tana cewa agaishe man da surukin namu ammah tayi shuru. Tana shiga part d'in inna fuskarta kicin kicin tawuce tanufi inda inna take zaune tace wai inna wanene yazo? Kishiga ciki man sai kigane ma idanunki. Jawahir tsayawa tayi cikin ranta tace wallahi indai har wajena akazo zan wulak'anta mutum dan ni samari basu gabana, muryar Inna taji ta ce bazaki shigaba sannan tawuce tashiga. Tana d'age labule bakinta d'auke da sallama nan sukayi ido biyu da Faruk batasan lokacin da murmushi yasu'buce mataba cikin sauri ta ida shiga d'akin tace lah yaya Faruk kaine kazo ashe shine baka fad'a min ba? Murmushi yayi yace taya zan fad'a maki bayan k'anwartawa fushi take da yayan nata saisa nazo dan in goge laifina. Waje tasamu tazauna nan tagaisheshi ya amsa tatambayeshi su Mom yace duk suna lafiya lau. Amaryar fa ko ma ince Auntyna? Murmushi yayi yace tana nan lafiya lau itama tana gaisheki, nidai yanzu ayi hak'uri adaina fushin nan da akeyi da ni na amsa laifina insha Allahu bazan sake ba. Turo baki tayi batare da ta ce komai ba. Ahankali yace please my k'anwa kiyi hak'uri wallahi na shafa'a ne. Juyawa tayi gefe guda sannan tace shikenan na hak'ura. Yauwa kokefa har na ji dad'i ina fata babu wata matsala? Girgiza kai tayi tace babu. Ajiyar zuciya yasafke yace toh yanzu yaushe zakizo katsina? Ya kamata kizo kafin bikki dan wata d'aya kinga yarage. Kicin kicin tayi da fuska tace zan zo sai mun gama exams islamiyya dan next week zamu fara. Toh menene na had'e fuska? na ji ba damuwa idan kun gama sai azo kinga ayi hidimar bikki k'anwar ango tana kusa. Murmushi tayi tace hakane yayana. Faruk janta yayi da hira sukaita yi har wajen k'arfe biyar sannan sukayi sallama kud'i yafiddo sosai yabata yace ta sayi abinda takeso tunda baiyo tsara ba, da dafari har ta k'i amsa tace akwai kud'i a wajenta shareta yayi yabar mata su nan sannan yaje sukayi sallama da su inna da Baba Malam su ma ya ajiye masu kud'i sosai su Yaya Nura ne suka kaishi airport yabi jirgin k'arfe biyar da rabi yakoma katsina. Jawahir ta yi farin ciki sosai da zuwanshi haka taje talabarta ma khausar zuwan yayan nata da kud'in da yabata dan su Baba Malam taba su k'in amsa sukayi, a wajensu taga invitation d'in Faruk na d'aurin aure nan tayi Allah yasa alkhairi dan daman ya fad'a mata ba'a kaida bugo IV na 'yanmata ba lokacin da yazo saisa bai tafo mata da nata ba, batama yi tunanin anbugo na d'aurin aureba saida taganshi. *BAYAN SATI UKKU* Gidajen biyu aka fara hidima sosai inda kud'ad'e aka dinga ruwanu dan ma amarya ta ce ba wani program d'in da zatayi saboda yanayin da suke ciki saidai wa'azi kawai ta amince ayi. Amarya Nasiba ta sha gyara ta yi gwanin kyau sai salk'i take da kaganta kaga amarya saboda kyaun da tayi na amare. Ana saura kwana ukku bikki suna zaune a harabar gidansu suna hira da Faruk tace Lovely wai dan Allah Jawahir ta zo garin nan ne? Girgiza kai yayi yace a'a. Cike da mamaki take kallonshi tace meyasa toh sai yaushe zata zo? Zata dai halarci bikkinmu ko? Toh wannan ne ban dai saniba dan ance min suna exams a islamiyya kinga kenan ba damar tazo. Cikin nuna tausayi tace Allah sarki Jawahir baiwar Allah wallahi yarinyar nan tana bani tausayi gata mutuniyar kirki,, k'walla ce tacika mata idanu tace duk su Daddy sune silar jefata cikin wannan yanayin ta rasa kowa nata wace irin rayuwace wannan, taya zata kasance cikin farin ciki? Ganin yadda tafara hawaye yasa cikin sanyin jiki yace Nasiba duk abinda kikaga ya samu bawa to daga ubangiji ne babu wanda ya isa yatsallake k'addararshi, kuma a yanzu Jawahir tana rayuwa me dad'i a wajen dangin mahaifiyarta. Duk da haka Lovely ta yi rashi. Kinga Nasiba kidaina sa damuwa a ranki Jawahir batada matsalar komai, mubar wannan maganar yanzu kud'in da naturo maki sun isa ko kuna buk'atar k'ari. Girgiza kai tayi tace bana buk'atar k'ari na wajena sun isheni dan ni ba wani taron da zanyi. Shikenan rabin ran duk yadda kikeso haka za'ayi. Murmushi tayi tace nagode sosai Lovely. Hirarsu suka cigaba da yi cike da shauk'i da k'aunar juna har saida aka fara kiran sallar magrib sannan sukayi sallama yatafi gida. Ranar alhamis aka gabatar da wa'azi wanda mutane d'aid'ayane suka halarta sakamakon rashin gayyar da amarya tayi ko ma ace ita da danginta sukayi duka abokanta mutum ukku tagayyata sai 'yan uwa, amarya ta yi kyau sosai anyi wa'azi me ratsa jiki inda aka ci aka sha. Ranar juma'a kuma akayi ma amarya lalle, inda ranar asabar aka d'aura auren faruk Sani Maishadda da amaryarshi Nasiba Sufyan Mai Nasara akan sadaki mafi daraja wanda dubban mutane suka halarci d'aurin auren kasancewarsu 'ya'yan manya yasa aurensu yazagaye cikin garin katsina da gidajen yad'a labarai ko da rabi da kwatan mutanen duk na 'bangaren ango ne dan amarya basu wani yi gayyaba saidai dangi, abokan mahaifinta ma wasu sun halarci d'aurin auren, ango baki k'in rufuwa yayi saboda farin ciki ga jama'a da suka dinga mashi Allah yasa alkhairi su Barr Nas da Barr Junaid manyan abokan ango sin sha babbar riga sune suka dinga haba haba da jama'a. Gidajen biyu cike suke da jama'a ana ta hidima abunka da bikkin masu kud'i haka aka dinga fiddo naira. Mutanen Kebbi tun ranar juma'a suka iso Katsina ammah banda su Jawahir da suke jarabawa a islamiyya itama ta so zuwa saidai Exams d'in tahana dan an d'aga masu ita ne da tuni sun gama a lokacin baifi guda hud'u sugama ba, Mom bataji dad'iba koda sukayi waya tace tazauna tayi jarabawarta inyaso idan sun gama sai tazo tayi masu hutu da hakan Jawahir ta mince, saidai takira ango tayi mashi Allah yasa alkhairi. A 'bangaren Nasiba ta sha kyau har ta gaji dan gyarane ta sha shi saidai da kaganta ka san tana cikin damuwa wanda ba komai yaja hakanba sai tunanin rabuwa da gida da zatayi tafuskanci sabuwar rayuwa, Nasiha iri iri tasha a wajen mahaifiyarta da dangin iyayenta. Da marece angwaye suka zo da motoci aka d'auki amarya aka kaita a chan gidan angonta da ke chan Goruba Road, gida ne na gani na fad'a dan tun daga tsarin ginin zuwa kayan da aka zuba mashi komai ya ji, shi kanshi Faruk part d'inshi iyayenshi sun tsara mashi sosai dan duk kayan da suke ciki saida aka kwashe aka canza mashi sabbi abunka da d'an gata. 'Yan kawo amarya sunyi santin gidan da tsarinshi inda wasu daga cikinsu suka dinga ma gidan vedio, Nasiba dai tana zaune a tsakiyar royal bed d'inta k'udundune cikin mayafinta inba hawaye ba babu abinda take. Bayan sallar magrib jama'a suka fara watsewa yarage daga amarya sai yayyenta da k'awarta d'aya me suna Amrah, Amrah aminiyar Nasiba ce tun tashinsu hatta karatunsu tare sukayi a school guda babanta wani hamshak'in me kud'i ne zama a iya cewa yana cikin mak'arraban gwamnati, su suka sake gyara mata gida tas aka kunna turaren wuta. Sai wajen k'arfe tara su angwaye sukazo tun kafin su shigo su Aunty Sadiya suka sa'be suka tafi aka barta tadinga kuka hatta Amrah tafiya tayi saboda kiran da aka dinga mata a gida. Nasiba kuka tadinga yi har angwaye suka shigo duk surutan da suka dinga bata ma san abinda suke cewa ba dan hankalinta baya wajensu, Faruk ko rawar jiki yadinga yi yanaso sutafi subar mashi amaryarshi ammah suka k'i saida yaja Barr Nas gefe yace ya kamata yace sutafi hakanan dare yakeyi, shi ko Barr Nas mi zaiyi inba dariya ba koda suka dawo yakalli su Barr Junaid yace toh ku sai kuzo mutafi tun kan ango yabiyomu da ta'barya su dukansu dariya sukayi Barr Junaid yace ai naga alama angon nan ya k'agara mutafi dan ina lura da irin kallon da yake mana, toh arufe mana taro da addu'a kafin muwatse tunda mun rako ango gidanshi lafiya. Faruk shuru yayi yak'yalesu suka dinga mashi shak'iyanci. Cikin abokansu ne d'aya daga ciki yayi masu addu'ar zaman lafiya sannan sukayi masu sallama suka tafi Faruk yarakasu saida suka bar gidan sannan yarufe yadawo yasamu amaryarshi a inda yabarta har lokacin k'udundune take cikin mayafi tana sheshek'ar kuka. Daga gefenta yazauna tare da yin sallama ahankali, jin shuru yasa yakai hannu yayaye mayafin nan tayi saurin runtse idanunta yace haba Hearty miye abun kuka a ciki yau fa ranar farin ciki ce agaremu godiyarmu yakamata mununa ma ubangiji akan wannan ranar da yanuna mana. Shuru tayi nan yad'ago fuskarta yana goge mata hawaye saida yatabbatar ta daina kukan sannan yasata taje tayi alwallah sukayi sallah bayan sun gama sunyi duk abinda yadace daga nan yafita yakoma part d'inshi dan haka Nasiba tasamu damar yin wanka koda d'ar d'ar kawai take gabanta yana ta fad'uwa tana fitowa tashirya cikin sauri tagama duk abinda zatayi tahaye gadonta takwanta bata dad'e da kwanciya ba taji Faruk ya bud'e k'ofa ya shigo saurin runtse idanu tayi kamar me bacci tana ji yahau gadon yakwanta gefenta muryarshi taji saitin kunnenta yana cewa Hearty ba dai kinyi bacci ba?. Shuru tayi nan yai murmushi tare da janyota jikinshi yana cewa ban yarda ayi wannan baccinba dan yau ranar farin ciki ne agaremu ya kamata mununa ma juna irin son da muke fad'a muna yi ma juna, shafata yafara yi Saurin tura kanta tayi cikin k'irjinshi nan yai murmushi tare da kai hannu yakashe bedside lamp daga nan wasa yacanza..... Washe gari Faruk lalla'bata yadinga yi nan tadinga narke mashi tana zuba shagwa'ba, breakfast daga gidansu Faruk aka aiko masu da shi tun kan sutashi bacci, tare sukayi wanka suka shirya sannan suka fito sukayi breakfast Nasiba tana ta narkewa shi ko sai rawar jiki yakeyi akanta. A ranar bai lek'a ko k'ofar gida ba yana nan manne da matarshi indai ba masallaci zai je ba, sai magrib sannan yafita nan Nasiba tasamu damar shirya kayanta. Bayan sallar isha'i Faruk yadawo gida nan sukayi wanka suka yi dinner sannan suka zauna a parlornshi suna kallo, Nasiba manne mashi tayi a jiki inda shi kuma idanunshi suke a lumshe kamar me bacci gabad'ayansu babu ma meyin kallon, fuskarshi taji ya tura cikin gashin kanta tare da k'ara matseta a jikinshi nan itama tak'ara narke mashi, muryarshi taji ahankali kamar me jin bacci yana cewa Hearty ina k'aunarki da dukkan zuciyata tabbas sonki a cikin jinin jikina yake ji nake kamar a mafarki yau nine tare da wadda nafi k'auna a matsayin mata agareni. 'Dago kanta tayi takalleshi tana murmushin jin dad'i tace tabbas nima ina cikin farin ciki sosai da ubangiji yamallaka min kai a matsayin miji agareni ina ji a raina na fi kowace mace dace da samun miji irinka, shima idanu yazuba mata yana mata wani shu'umin kallo. Saurin maida kanta tayi takwantar a k'irjinshi nan yashafa bayanta yace Nasiba indai har zaki kula da ni toh ni kuma zan nuna maki cewa babu wata mace a cikin duniyar zuciyar Faruk indai ba ke ba. Wani irin dad'ine taji sosai dan kalamanshi sun ratsata, ahankali tace inko hakane zan baka kulawa wadda babu namijin da yata'ba samun irinshi, fiye da yadda uwa take son d'anta, zan nuna maka tattalin so da k'auna zallah dan Allah Faruk karik'eni amana. Bakida damuwa da wannan matata yanzu sai kitashi muje anuna min son da ake min wanda yafi wanda uwa take ma d'anta. Tun kan yarufe baki tayi saurin d'ago kai ta kalleshi, d'aga mata kira yayi nan taturo baki tace nidai a'a. Kallon agogo yayi yace tunda dai har kika fad'a ya zama dole in gani a ido domin gani ya kori ji kinga ma yanzu dare ya yi muje kawai malama. K'walla ce tacika mata idanu tace dan Allah kayi hak'uri kaga fa ban warkeba. Cak yad'auketa yace ai aikin lada ne zakiyi muje kawai amaryata. Nasiba ji take kamar tafashe da kuka dan ita kad'ai tasan irin wahalar da tasha hannunshi jiya, a bedroom d'inshi yawuce da ita saidai ji tayi ya safketa saman gadonshi nan shima yahau, cike da tsoro kamar zatayi kuka tace dan Allah kar kayi min komai Allah ciwo nake ji. Shareta yayi yakashe bedside lamp sannan yajanyota jikinshi yarungume, ahankali cikin kunnenta yarad'a mata cewa kikwantar da hankalinki hearty babu abinda zanyi maki bacci kawai zamuyi dan nima ina tausayinki Allah dai yayi maki albarka domin kin faranta min. Murmushin jin dad'i tayi nan hankalinta yakwanta tagyara kwanciyarta a cikin kunnenta taji yana rad'a mata kalamai masu ratsa gangar jiki ahaka har bacci yayi awon gaba da ita. ____________ Khausar kallon Jawahir tayi da take kwance ta d'age kai sama tana kallon ceiling tace wai ke sister tunanin me kike tun d'azu. 'Dagowa jawahir tayi takalleta tace ni ba tunani nakeba kawai dai ina tunanin rayuwane. Uhm ko kuma kina tunanin zuwa Katsina dan na ji kince ma Mom da anyi hutun islamiyya zakije masu hutu. Cikin sanyin jiki tace Khausar bazanje katsina ba a nan zanyi hutuna tunda hutun sati biyu ne aka bamu. Kai Sister ammah dai da baki kyauta ba kinga ko bikkin Barrister bakije ba muna jarabawa lokacin, kuma yanzu sai kik'i zuwa kiyi masu Allah yasa alkhairi ko d'an man shanu musha, dan ma naga Barrister yanzu tunda yayi aure tsawon kwana biyu baku gaisaba ko fushi yake da rashin zuwanki bikkinshi. Jawahir runtse idanunta tayi dan itama kanta abun yana damunta ta yi tunanin dalilin dai rashin zuwanta ne yasa tun ranar d'aurin aure da takirashi tayi mashi Allah yasa alkhairi basu sake wayaba, toh ko dai yana fushin da ni dagaske? Muryar Khausar taji tana cewa yoh wa yasanar maki sai kikira kitambayeshi. Shuru tayi bata sake cewa komai ba dan bata d'auka a fili tayi maganar ba. A ranar da marece tana cikin game da wayarta kiran Faruk yashigo tsayawa tayi tana kallon wayar cike da mamaki cikin ranta tace yau kuma antuna da ni kenan. Har saida takusan tsinkewa sannan tayi picking tare da yin sallama, daga chan 'bangaren Faruk da yake kwance saman cinyar Nasiba amsa mata yayi tare da cewa k'anwata fushi nake da ke. Murmushi Jawahir tayi tace kayi hak'uri yayana na san na yi laifi kuma na baka uzurina. 'Dago kai yayi yakalli Nasiba da itama take kallonshi nan suka sakar ma juna murmushi sannan yace anya kuwa uzurin nan naki zai kar'bu bayan bakizo kika ga amaryata ba. Daga chan 'bangaren Jawahir murmushi tayi tace Allah sarki ni, dan Allah Yayana ayi min hak'uri zan zo. Nasiba ce tace bazan hak'uraba k'anwata har sai kinzo kin goge laifinki. Murmushi Jawahir tayi dan ta jiyo abinda tace, Faruk ne yace kindai ji abinda tace ko? Bari ma inbaki ita kuyi magana. Cikin jin kunya tace a'a Yaya Faruk Allah kunyarta nakeji. Dariya yayi yace nidai babu ruwana gatanan sai k'anwar lauya tasan yadda zata kare kanta,,, wayar yamik'a Nasiba da take ta dariya. Itama Jawahir 'yar dariyar tayi jin Nasiba ta yi sallama yasa ta amsa tare da cewa Auntyna ina wuni? "Uhm bazan amsaba fushi nake" Marairaicewa tayi tace dan Allah kiyi hak'uri wallahi ina son zuwa lokacin exams muke a islamiyya ammah zan zo. Toh shikenan k'anwata na kar'bi uzurinki ya dai kamata kizo idan kun gama dan ga d'aki nan mun ware nakine kinga sai kiyi mana hutun nan kafin akoma. Dariya Jawahir tayi tace d'aki kuma Auntyna. Eh man mu dai muna jiranki. Faruk ne yace kibarta hearty idan tayi wasa dakanmu zamuje har chan KEBBI mud'aukota. Jawahir rage fara'ar fuskarta tayi tace zan zo insha Allahu Yayana ayi hak'uri. Toh shikenan Jawahir sai kinzo muna godiya sosai. Bakomai Auntyna nima nagode nan sukayi sallama takashe wayar, ta'be baki tayi ta ajiye wayar sannan tamik'e tafito tsakar gida tasamu Inna Mairo zaune tana cin k'uriga nan itama tazauna gefenta tad'iba tafara ci. Faruk kallon Nasiba yayi da take rik'e da wayarshi yace k'anwarnan tawa gudun garin nan take na lura da ita bata son zuwa. Cikin sanyin jiki Nasiba tace wallahi Lovely banga laifinta ba saboda abinda su Daddy sukayi mata basu kyautaba sun cutar da rayuwarta sun rabata da duk wani farin cikinta ni wallahi har kunyarta nakeji,,, k'walla ce tacika mata idanu ganin haka yasa Faruk yace Nasiba haka ubangiji yak'addara babu wanda ya isa yacanza k'addararshi. Cikin muryar kuka tace kaduba kagani lovely duka yarinyar nan nawa take ammah ace jawarci take. Kinga Nasiba banaso kiyi min 'barnar hawayenki komai yasamu bawa daga ubangiji ne banason kina shiga damuwa Goge hawayenta tayi nan Faruk yafara lalla'bata yana lallashinta cikin dabara yasamu yarabata daga damuwar da tashiga. ___∆∆∆∆∆____ Dad kud'ad'e yafitar akayo order d'in duk kayan aikin da ake buk'ata inda yazuba ma'aikata sosai a cikin companyn Jawahir aka fara gudanar da aiki nan da nan company yafara ha'b'bakowa dan shi Dad mutum ne mekula sosai da sanin makamar aiki. A cikin gidan Kaso su Alhaji Mansur da Alhaji Sufyan aiki ake saka su sosai ana wahalar da su babu wanda zai ce ga matsayinsu a da, sunyi nadamar abinda suka aikata sosai dan basusan rayuwa zata juye masu hakaba gashi gabad'ayansu babu wanda iyalanshi yazo dubashi, sunyi bak'k'i sun rame duk sun fita hayyacinsu kullum cikin aibata junansu suke da da sun sani kuka ko ba'a magana musamman idan suka tuna akwai ranar da ma za'a rabasu da rayuwarsu gabad'ayanta. ****** ******* Jawahir bayan ta dawo daga gidan kitso ganin Baba Malam tayi zaune shi kad'ai a bisa 'yar kujerarshi a k'ofar gida yana sauraren radio, wajenshi tanufa tatsugunna tagaisheshi yace Jawahir har an dawo?. Eh Baba Malam. Toh sannunki. Yauwa Baba. Ganin yadda tayi yasa yagane akwai magana a bakinta dan haka yace Jawahir kisanar da ni duk abinda yake cikin ranki kar kidamu zan fahimceki. Ahankali tace am daman Baba wata 'yar alfarmar nake nema a wajenku. Toh ina saurarenki. Shuru tayi sai kuma chan tace dan Allah idan ba zan takura maku ba inaso ataimaka asamo min makaranta incigaba da karatuna. Shuru yayi yana saurarenta ganin daga nan bata sake cewa komai ba yasa yace toh jawahir bazank'i ta takiba ammah da son samune zan fi so ace aure kikayi tunda kinga wanchan mijin naki ya rasu aure shine mutuncinki ammah zaki iya fara karatun kafin Allah yakawo mijin inyaso sai ki ida karatun a gidanki dan ni kinga gaskiya babu d'iyar da nake bari tayi karatu a gidan nan saidai tafara ta ida a gidan mijinta, yanzu haka kinga Khausar da Rashida an tsaida ranar aurensu watanni ukku suka rage ayi bikkin, idan hakan ya yi maki ba matsala. Jikinta sanyi yayi cikin ranta tace chakwakiya kenan ni ina naga wani manemin aure ni da babu ma aure agabana yanzu na fi son inyi karatu inyaso daga baya idan da rabo zanyi aure. Ganin ta yi shuru yasa yace Jawahir rayuwarki ta fi had'ari tunda kin ta'ba aure saisa nafison kiyi aure saidai komai lokacine idan Allah ya kawo maki mijin sai ayi auren. Cike da ladabi tace toh Baba Malam nagode sosai insha Allahu zan kasance me biyayya agareku. Cikin jin dad'i yace yauwa Jawahir Allah yayi maki albarka. Amsawa tayi da Ameen tace atashi lafiya sannan tamik'e cikin sanyin jiki tashiga cikin gida, 'bangarensu Khausar tawuce tasameta kwance tana bacci dan haka tafito takoma 'bangarensu. Tunda tazauna tunanin maganar Baba Malam kawai take wai ya fi son tayi aure ita kuma a yanzu bata shirya ma aureba a tsarin rayuwarta ta fi so tayi karatu tazama wani abu wadda za'ayi alfahari da ita, ammah yanzu taya ma zata iya fara yarda tayi soyayya koda ta san d'an zamanta a garin mutanen da suka dinga zuwa wajenta da sunan so suna da yawa. Wasu siraran hawaye ne suka gangaro mata ahankali tace Abba kun cuceni duk kune kuka ja min da ace kun barni na cigaba da karatuna da duk hakan bai faru ba, goge hawayen tayi tare da cewa na mik'a ma ubangiji lamurrana domin shi ya fi kowa sanin halin da nake ciki Allah kaza'ba min abinda zaifi zama alkhairi a rayuwata. ******* ******** Faruk da Nasiba soyayyarsu kawai suke sha suna kula da junansu sosai ko da ace Faruk yana wajen aiki tana k'ok'arin kiranshi ko shi yakirata dan kawai suji lafiyar juna. Faruk yana k'ok'arin zuwa dubo Ummah a asibitin da ake jinyarta har tafara samun sauk'i saidai duk k'ok'arin da suke akanta 'barin jikinta guda ya shanye bata iya komai daga k'arshe ma suka nemi susallameta takoma gida zasu d'aurata akan magani dan bazata ta'ba komawa daidai ba. Faruk amincewa yayi da hakan nan yasa aka kwashe duk kujeru da kayan d'akin da suje gidansu Jawahir aka kaisu a gidan da taba ummah, gidane madaidaici me d'auke da d'akuna ukku kowane ciki da parlor. A ranar da aka sallameta gidan yawuce da su itada masu jiyyarta su biyu inda d'aya daga cikinsu yayartace tana aure a chan funtua dan haka suka dawo gidan itada mijinta dan cigaba da kula da 'yar uwartata da a yanzu sai anyi mata komai kamar yadda Faruk yabata shawara. Ummah kuka tayi sosai lokacin da Faruk yasanar da ita kyautar da Jawahir tayi mata na gidan da mota sai kuma kud'ad'en da tabada abata. Kuka tadingayi tana cewa kaicona ina ma ace ban zalunci wannan yarinyar ba ko da sau d'aya ban ta'ba kyautata mataba daga ita har mahaifiyarta, yanzu ga shinan yadda rayuwata takoma dan Allah ina zanganta in nemi gafararta. Faruk yace kar kidamu duk abinda Jawahir tayi maki cancantane yasa hakan sannan zuciyar jawahir mekyau ce akowane lokaci tana da burin kyautata ma mutane kidaina sa damuwa a ranki kinji dai abinda likita yace kafin kubaro asibiti. Motsa 'barin jikinta me lafiya tayi tace dole inyi kuka Faruk dan na cutar da yarinyar nan fiye da tunanin wani me tunani sai gashi rayuwa ta juya min na rasa komai nawa a yanzu itace take taimakona dan tarufa min asiri. Lallashinta suka dinga yi tayi shuru nan Faruk yadamk'a masu komai sannan yasa aka kawo masu kayan abinci sosai wanda yafitar da kud'inshi yasiyesu dan kawai saboda su. Haka suka dinga yi mashi godiya suna shi mashi albarka har yatafi. *BAYAN WATA UKKU* Nasiba ce tafito daga kitchen d'auke da Cup a hannunta jikinta sanye cikin kayan bacci tanufi d'akin Faruk, tana shiga zaune yake ya d'aura laptop a saman cinyarshi yana wani aiki, daga gefenshi tazauna tace wash sannu lovely. Batare da ya kalletaba yace kema sannunki hearty. Hmm kaine da sannu kaida tun d'azu kake faman aiki yauwa lovely dan Allah akwai maganar da nakeso muyi da kai. Janye laptop d'in yayi tare da janyota yad'aura bisa cinyarshi sannan yace ina saurarenki hearty wace magana kikeson muyi? Murmushi tayi tamik'a mashi cup d'in da tashigo da shi tace toh kasha wannan kajik'a mak'oshinka sannan muyi maganar. Amsa yayi bai musaba yasha saida yashanye kunun ayar da takawo mashi tas sannan yace toh ina saurarenki. Kwantar da kanta tayi a k'irjinshi sannan cikin sanyin murya tace dan Allah Lovely kataimaka muje Kebbi wajen Jawahir muganota ko da wuni guda ne tunda ita har yau bata lek'o mu ba. Jan hancinta yayi yace kedai baki gajiya, toh ai ita yakamata tazo taganki. 'Bata fuska tayi kamar zatayi kuka tace dan Allah Lovely kataimaka muje mu ai sai mukwashe ladar zumuncin. Hmm tunda kince haka shikenan kibari sai weekend sannan muje wuni guda mudawo. Rungumeshi tayi tace nagode sosai Lovely Allah yasaka da alkhairi, ai kam saidai kawai mubata mamaki dan bama zata san zamuje ba. Hamma yafara yace kinga tashi muje mukwanta dan ni nan na gaji aikin ma bazan ida shi ba sai zuwa gobe. Shagwa'be fuska tayi tace toh saidai kad'aukeni muje. Cicci'barta yayi yace toh ya zanyi ai dole inyi yadda kikeso amaryata. Dariya tayi tace a'a ni yanzu ba amarya bace ai na kwana biyu. Baice mata komai ba saida yadireta saman gado sannan yace toh ke micece? Maimakon tabashi amsa sai ma juyawa da tayi tana murmushi dan haka shima yakwanta daga bayanta tare da kashe masu haske..... _Sis Nerja'art✍🏻_ [7/24, 11:21 PM] Sis Nerja'art 2: *......FANSAR RAI......* *INTELLIGENT WRITER'S ASSO....®* [On Ward Together] _Follow me on Wattpad: *Sis-nerja*_ _Wannan Littafin na kud'i ne domin karantawa cikin aminci da yarda ga duk me buk'ata zai turo katin Mtn na d'ari biyu N200 kacal ta wannan number d'in 09035938246, ko ta account number 5330055604, Idan katura ka aiko da screen shot na transaction a wannan number d'in 09035938246_ _Akwai gara'basar *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shahararriyar marubuciyar nan *AMEENA ABBA UMAR* tare da novel d'in *FANSAR RAI* akan farashin N300 kacal, ko da kud'in ka sai da rabonka_ *PAGE 25* Ana saura kwana ukku suje Kebbi Nasiba tamatsa mashi suka je gidan su Dad, sunyi farin ciki da zuwansu nan Mom tadinga nan nan da ita dan tana son Nasiba sosai, a chan suka wuni sai dare sannan Faruk yaje zai d'akkota. Suna a parlor zaune suna hira ita da Mom nan Faruk yakalleta yace sutafi dare ya yi. Amsawa tayi da toh sannan tace Ammah kafin mutafi ina son zamuyi wata magana da su Mom daman tun d'azu naso yinta sai kuma naga Dad ya fita. Muryarshi sukaji ya ce toh gani na dawo me za'a fad'a min Su duka juyawa sukayi suka kalleshi sukai murmushi Mom tace ashe kana kusa. Shima murmushin yayi yace Eh wallahi wani meeting ne yatsaida ni saisa kuka ji ni shuru har wannan lokacin ban dawo ba. Sannu da zuwa sukayi mashi nan yashigo yazauna yana cewa wace magana ce d'iyartawa takeson yi da mu? Faruk kallonta yayi yai murmushi sannan yamaida kallonshi ga iyayenshi yace wai maganar zuwan da zamuyi Kebbi zata fad'a maku batasan munyi maganar ba. Eh toh kusan itace ammah ba ita bace. Mom tace toh shikenan d'iyata fad'a mana fatana dai ba matsala bace kuka fara samu da mijin naki? Duk'ar da kanta tayi cikin nutsuwa tace Mom Dad dan Allah alfarma nake nema wadda na san wajenku ne kawai zan iya nemanta. Da mamaki suke kallonta sukace wace irin alfarma ce Nasiba kifad'i kowace irice insha Allahu zaki sameta. Shuru tayi na d'an lokaci sai kuma chan tace dan Allah so nike kurok'ar man Faruk ya auri Jawahir. Su duka idanu suka zuba mata mamaki k'arara a fuskarsu, Faruk ne yayi k'arfin halin cewa Nasiba wannan wace irin magana ce kikeyi kinsan abinda kike fad'a kuwa? 'Dagowa tayi takalleshi idanu cike da k'walla tace tabbas na san abinda nake fad'a Faruk ina son kataimaka ka auri Jawahir domin ko bakomai ta cancanci hakan ya kamata muyi duba da rayuwarta ita d'in yarinya ce me k'arancin shekaru tana buk'atar auren miji wanda zai bata kulawa sosai wanda zatayi farin cikin kasancewa da shi a matsayinta na marainiya na tabbata kaine kad'ai zata iya aura tasamu wannan gatan domin kai ka san halin da take ciki zaka tausaya ma rayuwarta. Mom ce tayi k'arfin halin cewa keko Nasiba miyasa kikayi wannan maganar har kikeso mijinki yak'ara aure? Hawaye ne suka gangaro daga idanunta tace Mom banaso inkasance mace me son kanta dayawa na san ina son Faruk kuma ina da kishi saidai ina ji a raina kamar idan Jawahir bata auri Faruk ba banyi ma kaina adalci ba domin shine kad'ai namijin da yadace ya aureta. Wani irin kallo yawurga mata yace kar kisake wannan maganar kitashi mutafi gida tunda bani nace maki ina buk'atar k'ara aureba kuma duka wata nawa da yin bikkinmu har zaki wani ce ink'ara aure sannan Jawahir da kike gani matsayin k'anwa take a wajena ba wai sonta nake ba. Had'e hannuwanta tayi waje guda alamun rok'o tace dan Allah Faruk kar kak'i amincewa da auren Jawahir wallahi na amince zan zauna da ita da zuciya d'aya domin ita d'in zuciyarta mekyau ce, shin ni idan nice zan so ace wani nawa ya fad'a irin halin da Jawahir take ciki? Ya kamata kayi tunani rayuwarta tana buk'atar tallafi duk yadda zataji dad'in zama a wajen kakanninta bazai ta'ba kai zaman da zakayi da ita ba domin na tabbata zaka bata duk kulawar da tadace, na maka alk'awali zamuyi zaman lafiya da ita zamu kasance abun koyi ga duk sauran mata har ayi alfahari da mu,, Kasa cemata komai yayi saidai kallon mamaki da yakeyi mata. Juyawa tayi takalli Mom da Dad tace dan Allah ina rok'onku kusa baki a ciki Dad na san ku zaku fahimci abinda nake nufi wannan dalilin ne yasa ban ta'ba mashi maganar ba sai yau da muke zaune a gabanku wallahi tun kan muyi aure da Faruk nasa ma raina ba zan ta'ba zama ni kad'ai da shi ba zai kasance mijinmu ni da Jawahir domin wannan shine adalcin rayuwa ko bakomai mahaifina yana cikin mutanen da suka ruguza mata duk wani farin ciki nata, dan Allah Dad kutaimaka kufahimci abinda nake nufi. Jinjina kai Dad yayi yace tabbas Nasiba ke mace ce me adalci kinsan abinda yakamata, banyi niyar shiga cikin maganar nan ba na fiso kuje kuyi shawara a tsakaninku idan shi ya amince zai aureta to mu bamuda matsala yadda duk kuka tsara daidai ne ko Hajiya?. Mom da take kallon Nasiba cike da mamaki d'aga kai tayi tace hakane Alhaji suyi shawara a tsakaninsu kawai zai fi. Fashewa da kuka Nasiba tayi tace dan Allah Dad kutaimaka kusa baki a ciki na tabbata kune kad'ai zakuyi mashi magana yasaurareku wallahi idan har bai auri Jawahir ba banyi ma rayuwata adalci ba ta rasa mijinta a lokacin da take buk'atar shi kuma duk ta silar su mahaifina dan Allah na rok'eku Mom kuce wani abu. Ganin yadda take kuka yasa su dukansu suka ji tausayinta Dad yace kidaina kuka hakanan Nasiba, sannan yamaida kallonshi ga Faruk da yahad'e fuska idanunshi suna a kan waya yana dannawa kamar baisan abinda ake tattaunawaba Dad yace toh kai Faruk ka ji abinda matarka tace tana neman wannan alfarmar. 'Dagowa yayi yakalli mahaifin nashi yace Dad ni fa ban da burin auren mata biyu. Duk da haka Faruk tunda matarka ce tanemi kayi auren sai kataimaka kayi bare ko bakomai Jawahir ta cancanci ka aureta. Ammah Dad duka aurenmu fa wata ukku da yinshi. Toh ai ba matsala bane. Faruk juyawa yayi yakalli mahaifiyarshi da jikinta yayi sanyi sosai nan tad'aga mashi kai alamun Eh. Duk'ar da kanshi yayi k'asa yama rasa abida zaice ganin iyayen nashi duk sun goya ma maganar Nasiba baya. Nasiba idanu tazuba mashi tana jira taji abinda zai ce har lokacin hawaye basu daina fita daga idanunta ba. Jin ya yi shuru yasa Dad yace kai muke saurare Faruk. Sai da yayi kusan minti ukku sannan yace shikenan na amince. Saurin rik'oshi Nasiba tayi tace dagaske ka amince zaka aureta? Harararta yayi yace tunda kun nuna kuna son hakan. Janye hannunta tayi daga rik'on da tayi mashi cikin sanyin jiki tace dan Allah kar kayi duba da abinda mukeso kataimaka kaima kaso auren a cikin ranka insha Allahu zakayi alfahari da mu. Toh wai Nasiba ita d'in Jawahir tace maki batada wanda take so? Jim tayi sannan tace na tabbata insha Allahu bata da shi. Jinjina kai yayi yace shikenan ammah da sharad'i guda idan dai har tana da wanda takeso dole mubarta ta aureshi,,, Cewar Faruk. Tace toh shikenan na yarda da wannan. Dad da Mom dai idanu suka zuba masu suna kallonsu cikin ransu suna jinjina ma k'ok'arin Nasiba dakanta take neman mijinta yak'ara aure wanda itama d'in basu dad'e da yin auren ba. Nasiba godiya tayi mashi sannan tajuya tayi ma su Mom su ma godiya. Addu'a su Dad suka dinga yi mata dan tabbas sunsan d'an nasu ya yi dacen mata dan samun irinsu Nasiba a yanzu sai an tona, mik'ewa Faruk yayi yai ma su Dad sallama sannan yace kisameni waje ina jiranki. Itama mik'ewar tayi tai masu sallama sannan tabi bayan Faruk da tuni ya yi gaba. Suna fita Mom kallon Dad tayi tace oh Alhaji kaga ikon Allah wallahi Nasiba yarinyar kirki ce ta san abinda yakamata. Jinjina kai Dad yayi yace ai kedai bari gaskiya Nasiba ta yi kuma nima kaina na ji dad'in hakan da tayi dan tuni nayi ma Faruk sha'awar auren Jawahir dan nasan zasu dace kuma ko bakomai shi zai kula da maraicinta. Ammah Alhaji yanzu kana ganin shi Faruk d'in zai aureta kalli fa yadda yanuna baya sonta. Murmushi Dad yayi yace Hajiya kibarni da shi kawai. Mom tace toh shikenan Alhaji Allah dai yatabbatar mana da alkhairi. Amsawa yayi da Ameen. Tunda suka shiga mota suka kama hanyar gida Faruk shuru yayi Nasiba ko ganin yadda yad'auke kai yasa tayi shuru dan ta san fushi yake da ita. Suna isa gida d'akinta tawuce, zama tayi bakin gado tadafe kanta nan wasu siraran hawaye suka gangaro mata saurin gogesu tayi tamik'e taje tayi wanka tai shirin kwanciya sannan tafito tanufi part d'in Faruk. Tana shiga tasameshi kwance murmushi tayi tace Lovely har ka kwanta kenan? Shuru yayi nan tataka ta isa wajen gadon takwanta daga bayanshi tana kwanciya yakai hannu yakashe hasken d'akin. Matsowa tayi kusa da shi cikin sanyin murya tace Lovely dan Allah kayi hak'uri idan har abinda nayi ya 'bata maka rai wallahi banyi hakan da wata manufaba nayi ne saboda hakan shine dacewa. Muryarshi taji ya ce Nasiba a wajenki ne hakan yake dacewa watau shine zaki d'auki maganar da kika tsara kije kifad'a ma iyayena koda ace ni bana da ra'ayin hakan ke tunda kinaso dole kenan inyi ke awajenki hakan kin min adalci. Fashewa tayi da kukan da tun tuni yake cinta ammah tadanne shi sai a lokacin tasamu damar yin shi, cikin kuka tace dan Allah Faruk kayi hak'uri banyi hakan saboda son zuciya ba, nayi ne kawai saboda ina tsoron alhakin abinda mahaifina yayi mata yahau kanmu banda kwanciyar hankali a duk lokacin da natuna mahaifinmu ya bamu munci da hak'in wata ya suturtamu da hak'in wata ya salwantar da ran wasu, dan Allah Faruk kataimaka ka auri Jawahir ba dan halinaba na san kai mutumin kirki ne kuma me fahimta zaka fahimci abinda nake nufi dan Allah kayi min wannan taimakon ko da ace shine taimako na k'arshe da zakayi min a duniya, na maka alk'awali zamu zauna lafiya tamkar 'yan uwan juna please Faruk kataima min,,, nan tasake fashewa da wani sabon kukan. Wani irin tausayinta ne yad'arsu a ran Faruk, juyowa yayi yafuskanci inda take tare da rungumota jikinshi cikin lallashi yace Nasiba kidaina kukan nan bana so kinsan dai banason jin kukanki, shikenan na amince zan aureta ammah da sharad'i d'aya. Saurin d'agowa tayi takalleshi tace wane irin sharad'ine dan Allah kafad'a min insha Allahu zan kiyaye. Idanu yazuba mata yana kallon cikin idanuwanta sannan yace sharad'in shine idan har Jawahir tana da wanda takeso dole kijanye daga k'udurin nan dan bazan ta'ba amince ma aurenta ba idan tana son wani na daban domin gudun kar incutar da ita. 'Daga kai tayi tace ba damuwa na amince da wannan sharad'in. Gyara mata kwanciya yayi a jikinshi yace toh shikenan yanzu muyi bacci dan ni bacci nake ji. Toh nagode sosai Lovely Allah yasaka da alkhairi Allah yabarmu tare. Amsawa yayi da Ameen daga nan kuma babu wanda yak'ara cewa komai daga cikinsu kowa da abinda yake tunani a cikin ranshi. *********** Ranar juma'a Faruk yakira Baba Nura yasanar sa shi zuwan da zasuyi da amaryarshi dan dama suna gaisawa sosai ko bayan bikki saida Baba Nura yazo yaga amarya yai masu wuni guda, a ranar Faruk yaje yayi masu booking d'in jirgi. Washe gari jirgin k'arfe goma sha d'aya suka bi suka je Kebbi wajen sha biyu sun isa Baba Nura yaje yad'aukosu daga airport. Suna isa gidan tarba me kyau akayi masu musamman Nasiba a 'bangaren su Inna Mairo tazauna matan 'yan uwan maman Jawahir suka zo aka dinga gaisawa cikin mutunci da sakin fuska ana mata Allah yasa alkhairi na aurensu. Nasiba haka tadinga gaisawa da mutanen gidan cikin sakin fuska dan a lokacin da sukazo su jawahir basu gidan sai wajen k'arfe d'aya suka dawo daga islamiyya saboda suna tsayawa tahafiz, su ukku suka jero suka nufo gidan ita da su Khausar da Na'ima lokacin su Baba Musa da su Faruk suna zaune a waje, Khausar ce tahangoshi tace lahh Jawahir wanchan kamar Barrister ne yazo. Batare da ta d'ago kanta da ke duk'e k'asa ba tace uhm kedai bakida aiki sai hango mutane ko ma ince sa ido toh bashi bane. Tsaki Khausar tayi tace kokuma kece bakida aiki sai afad'a maki magana kik'i yarda bayan baki d'ago kika ga kowanene ba, toh nidai na ce wallahi shine kuma kid'ago kigani. Jin ta rantse yasa Jawahir tad'ago dan tagane ma idanunta aiko d'agowar da tayi ya yi daidai da kallosu da Faruk yayi nan suka had'a ido. Saurin safke idanunta tayi k'asa tare da yin murmushi cikin ranta tace ashe dai shine wani irin dad'i taji ya d'arsu a ranta suna zuwa shiga gidan duk suka gaishesu sannan suka wuce zasu shige Baba Malam ne yace Jawahir bakiga Faruk ba ne? Tsayawa tayi nan su Khausar suka shige. 'Dago kai tayi takalleshi tana murmushi tace lah Yaya Faruk ashe kaine sannu da zuwa ina wuni? Murmushi yayi cikin ranshi yace lallai yarinyar nan har tad'ago takalleni muhad'a idanu shine yanzu zata wayance bata ganeni ba, basarwa yayi yace yauwa jawahir andawo islamiyyar ko? Eh Yaya Faruk ya su Mom da Dad? Hmm suna chan fushi suke da ke. Marairaicewa tayi tace Allah sarki ni wallahi inaso inje hutun ne ba'a bamu shi dayawaba lokacin ammah insha Allahu kwanan nan zan je inyo maku sati biyu, ina Auntyn tawa? Murmushi yayi yace kedai kije da dad'in bakinki kullum maganar kenan zakije ammah har yau shuru bakije ba ai Auntyn taki tana nan ciki sai kije kikaranta mata dad'in bakin naki k'ila ta yarda da ke. Cike da jin dad'i tace dagaske tare kukazo da ita? Eh tare mukazo zatayi maku wuni. Saurin juyawa tayi tace bari inje ingaisa da Auntyna wallahi na ji dad'i sosai. Su dukansu murmushi sukayi Baba Malam yace ina ruwan Jawahir. Cikin sauri tashiga 'bangaren Inna a parlor tajuyo muryarsu suna hira, d'age labule tayi tana cewa oyoyooo ga Auntyna. Nasiba na ganin ta shigo d'auke kai tayi tare da juyawa tace ni ba ruwana da ke fushi nake. Saurin matsawa gabanta jawahir tayi tatsugunna tace dan Allah Auntyna kiyi hak'uri wallahi ina so inzo Allah ne bai nufa ba. Inna Mairo ce tace kokuma bakiyi niyar zuwa ba Kai Inna bafa haka bane kinsan komai sai Allah ya yi, marairaicewa tayi tace dan Allah ba dan halina ba Aunty Nasiba kiyi hak'uri wallahi nima kaina na san ban kyauta ba. Sai a lokacin Nasiba tajuyo tace shikenan tunda kema kin gane baki kyauta ba na hak'ura ammah inji yaushe za'a zo mana. Murmushi tayi tace nagode sosai Auntyna insha Allahu ina nan tafe dan idan nazo sai na dad'e a wajenku. Hmm toh Allah yasa. Ameen Auntyna, nan suka gaisa tatambayeta gida da su hajitarta tace duk suna lafiya lau. Hira suka zauna suka dinga yi kamar daman irin sun san juna sosai har su khausar suka shigo suka gaisa. Bayan sunyi azuhur ne sunci abinci Inna Mairo tafito tsakar gida tana dafa madarar shanu, d'akin yarage daga Jawahir sai Nasiba dan su Khausar tunda suka shiga cikin gida basu dawo ba, kallonta Nasiba tayi tace dan Allah Jawahir ina k'ara baki hak'uri akan abinda mahaifinmu ya aikata maki wallahi bamusan komai ba akai. Kai Aunty Nasiba dan Allah kibar tuna abinda yawuce. K'walla ce tacika mata idanu tace dole intuna jawahir domin ko kema har kikoma ma mahaliccinki bazaki ta'ba mance hakan ba, kar kiyi k'arya a fili alhalin azuciyarki ba haka bane. Hawaye ne suka gangaro ma Jawahir tace tabbas nasan *DA CIWO A RAYUWATA* ammah babu yadda na iya komai muk'addarine dama chan Allah ya k'addara ba zan k'are rayuwata tare da iyayenaba *K'ADDARA CE* ta rabamu dan Allah mubar maganar Aunty Nasiba banaso tunawa domin inajin wani iri a duk lokacin da natariyo rayuwar da nayi a baya saidai ina jin d'an sanyi idan natuna da d'aukar *FANSAR RAI* na iyayena da nayi. Murmushi Nasiba tayi tace hakane Allah yajik'ansu yasa sun huta. Jawahir Amsawa tayi da Ameen daga nan kuma duk suka yi shuru. Inna Mairo ce tashigo da wani galan a hannunta tamik'a ma Jawahir tace jeki gidan Ladidi ki amso min Man Shanun da nabata ta dafa min d'azu. Amsa jawahir tayi tace toh nan tatashi tafita. Tana fita Baba Nura yashigo yace amarya kina nan anbarki ke kad'ai ko? Murmushi tayi tace a'a basu dad'e da fita ba ma yauwa dan Allah Malam Nura ko zaka taimaka kayi min magana da su Baba dan akwai magana me muhimanci da nakeso zamuyi da su. Baba Nura yace toh shikenan bari inje insanar da su. Fita yayi yaje yafad'a ma su Baba Malam sak'on Nasiba dan har lokacin suna zaune a k'ark'ashin bishiyar da yake zama saman tabarma dan a nan ma suka ci abinci, Faruk yana jin sak'on Nasiba yagane maganar da takeso tayi masu duk sai yaji wani iri. Haka suka tashi suka shiga cikin gida a tsakar gida aka shimfid'a tabarma Baba Malam, Baba Musa, Baba Jamilu, Baba Nura, Faruk sai Inna Mairo suka zauna daga chan gefe Nasiba tafito tazauna. Baba Malam ne yayi gyaran murya yace ance kina son magana da mu Allah dai yasa lafiya. Duk'ar da kai tayi cike da ladabi tace lafiya lau Baba daman wata alfarma ce nake nema a wajenku bansaniba ko zan sameta. Wace irin alfarma ce wannan?,,, baba malam yatambayeta. Kallon Faruk tayi sannan tace mijina nake son nema ma auren Jawahir. Su duka da mamaki suke kallonta, Baba Musa yayi k'arfin halin cewa keko wace irin magana kike ni na d'auka wata magana ce me muhimmanci taya zakice mijinki ya auri Jawahir bayan ba'a dad'e da bikkinku ba. Cikin sanyin jiki tace wannan maganar ma tana da muhimmanci dan Allah kutaimaka mana idan har hakan zai yuwu wallahi ni babu matsala na amince zan zauna da ita da zuciya d'aya ko bakomai rayuwar Jawahir yaci ace antausaya mata. Faruk ne cikin kwantar da murya yace zan auri Jawahir idan har kuka ban dama na yi maku alk'awali zan kula da ita bazan ta'ba bari tazubar da hawayeba tayi da tasani akan aurena ba amincewarku mukeso idan har batada wanda zata aura inkuma tana da shi shikenan sai in hak'ura domin komai nufine na ubangiji. Jinjina kai sukayi gabad'ayansu Baba Malam yace wannan gaskiya ne Faruk tunda dai har kaida matarka kun amince zaku zauna da ita tsakani ga Allah shikenan muma mun amince ka aureta domin ko bakomai ka cancanci hakan idan har muka ce zamu hanaka jawahir toh mun zama butulu dan ko halarcin da kayi mata ya ci ace mun amince, na yarda da kai 100% nasan zaka kula da ita da dukiyarta indai har ina da iko da Jawahir toh na mallaka maka ita. Su Baba Musa ne sukace wannan gaskiya ne muma mun amince da hakan. Inna Mairo ita kanta ta yi farin ciki sosai ko bakomai ta san Faruk zai kular mata da jikarta jinjina ma k'arfin halin Nasiba tayi ganin wai dakanta take nema ma mijinta aure. Faruk da Nasiba godiya sukayi masu. Su ko farin ciki baki har yak'i rufuwa dan daman sunaso Jawahir tasamu miji wanda zai kula da maraicinta, nan sukaita shi masu albarka, kowa farin ciki fal a ranshi dan sunsan indai ta auri Faruk ta more miji. Nasiba ce tace kar afad'a ma Jawahir abari su zssu fad'a mata da kansu. Su Baba Malam suka amince da hakan. Wajen k'arfe ukku Jawahir tadawo takawo ma Inna Mairo sak'onta tace kiyi hak'uri inna sai yanzu tagama dafawa ashe bata soyaba sai da naje. Murmushi Inna tayi tace bakomai ai daman na yi tunanin haka daman ina ta Allah Allah tasoya kafin sutashi tafiya. Murmushin itama Jawahir tayi tace ai nan zasu kwana gaskiya bamu yarda sutafi yau ba. Nasiba da take cikin d'aki tana jiyota saidai tayi murmushi kawai. Shigowa Jawahir tayi tace gaskiya babu inda zakuje yau Aunty Nasiba bari ma inma Yaya Faruk magana. Au keda baki ma lek'a inda mukeba kike da bakin cewa haka. Dariya Jawahir tayi tace dole ma inyi zuciya inzo ko dan inhuta da gorin da ake min. Ai da dai ya fi maki, yauwa Jawahir akwai magana me muhimmanci da nakeso muyi. Wace magana kenan Aunty?. Ina zuwa,,, wayarta tad'auko takira Faruk tace yashigo dan Allah suyi magana, ya amsa da toh. Bayan ya shigo ne ya zauna takalli Jawahir da tayi shuru tana jira taji abinda zasuce sannan Nasiba tace dan Allah Jawhir wata 'yar alfarma ce muke nema a wajenki. Alfarma kuma?,,, tatambaya cike da mamaki. Janye kai Nasiba tayi gefe guda sannan tace dan Allah ina so ki auri Faruk. Zumbur tamik'e tsaye tace ni kuma? Aunty Nasiba kinsan abinda kike fad'a kuwa? 'Daga kai tayi tace Eh na sani cewa nayi kitaimaka ki aureshi. Jawahif juyawa tayi takalli Faruk da yajingine kanshi a jikin kujera idanuwanshi suna a lumshe yana saurarensu, d'auke kai tayi tace gaskiya ba zan iya auren mijinki ba ni kawai matsayin Yaya yake a wajena. Saurin bud'e idanu Faruk yayi yakalleta. K'walla ce ta cika ma Nasiba idanu tace kar kice haka Jawahir dan Allah kitaimaka ki aureshi na maki alk'awalin zamu zauna da ke lafiya, bazamu ta'ba cutar da rayuwarki ba, idan har baki auri Faruk ba hankalina bazai ta'ba kwanciya ba, dan Allah kitaimaka ki auri Faruk na tabbata zai kula da ke fiye da yadda Umar yakula da ke. Zama Jawahir tayi tare da juyawa tana kallon gefe guda nan hawaye suka fara fita daga idanunta. Faruk ganin yadda take hawaye yasa jikinshi yayi sanyi nan yayi ma Nasiba nuni alamun tabasu waje, mik'ewa Nasiba tayi tafita cikin sanyin jiki, Nan yamaida kallonshi ga Jawahir ahankali yakira sunanta tajuyo takalleshi cikin muryar kuka tace Yaya Faruk dan Allah kace min maganar da Aunty tayi da wasa take ba da gaske ba. Murmushi yayi yace Jawahir dagaske take ina sonki kuma zan aureki idan har kin amince. Saurin tarar numfashin shi tayi tace ban amince ba bazan ta'ba aurenka ba domin kai Yayana ne. Wani irin haushi Faruk yaji ammah yadanne yace idan har kin d'aukeni a matsayin Umar zaki iya aurena Jawahir tunda shima kin aureshi ko kin mance lokacin da muke bankwana zaki dawo nan kikace infad'i duk abinda nake so kiyi min nace bana buk'atar komai sai abu guda, kikace menene nace zan sanar da ke ba yanzu ba, inzaki tuna cewa kikayi Allah yakaimu lokacin insha Allahu komenene zan nema zaki mallaka min shi, idan ko haka ne Jawahir aurenki nakeson yi dan Allah ki amince min. Kallonshi tayi fuska sha'be sha'be da hawaye tace taya zan iya aurenka Yaya Faruk? Taya zan auri mijin Aunty Nasiba idan har nayi haka ban mata adalciba ga mahaifinta anrufe sanoda ni sai kuma in auri mijinta dan Allah kacanza wani abun ammah bazan iya aurenka ba. 'Dan guntun murmushi yayi yace wannan alfarmar ita kad'ai nake nema a wajenki idan kuma har baki amince ba shikenan zan hak'ura Jawahir saidai na san kisan girman alk'awali da hukincin rashin cikashi. Cikin kuka tace ni ba wai alk'awalin bane bazan iya cikawa ba kawai dai aurenka ne bazan iyaba kai fa matsayin Yayana kake kuma Aunty Nasiba ban mata adalci ba idan na auri mijinta nidai kayi hak'uri bazan iyaba Barrister...tun kan tarufe baki sai jin muryar Inna Mairo sukayi ta ce Jawahir indai kika k'i amincewa da aurenshi tabbas kin zama butulu domin duk halarcin da mutanen nan sukayi maki baidace kice haka ba. Cikin kuka tad'ago takalli Inna Mairo sai kuma tajuya cikin sauri tashige uwar d'aka tamaida k'ofa tarufe. Inna Mairo kallon Faruk tayi tace kar kadamu Faruk zamu fahimtar da ita. Nasiba ce tashigo ganin yadda sukayi cirko cirko yasa tagane Jawahir bata amince ba, dan haka tace Inna dan Allah kulallasheta ta amince da auren nan zamu zauna lafiya bazan ta'ba cutar da itaba insha Allahu zatayi alfahari da auren nan da zatayi. Murmushi inna mairo tayi tace kubarta kawai Nasiba zata amince, muma ai abun farin cikine agaremu ko bakomai munsan zata rage yawan shiga damuwa da tunane tunanen da take. Faruk dai baice komai ba dan ya san daman mawuyacine ta amince ta aureshi saidai shima a yanzu yana da burin aurenta dan yacanza mata rayuwa yamaido mata farin cikin da tarasa a rayuwarta. Har sakayi sallar la'asar bata fitoba dan haka Baba Malam yaje yabuga mata k'ofa lokacin tana kwance har lokacin tana kuka dan jin abun take wani iri wai itace Nasiba take rok'o ta auri mijinta, jin muryar Baba Malam yasa tayi saurin tsaida kukan tare da tashi cikin sauri tabud'e k'ofar takoma tazauna tana sheshek'ar kuka. Baba Malam ne da Inna Mairo suka shigo suka samu waje suka zauna nan Baba Malam yakalleta yace Jawahir idan har kikayi ma mutanen nan haka baki kyauta ba, kar kimance halarcin da Faruk yayi maki a rayuwa kar ki kasance me manta alkhairi, kar kisaka kanki cikin mutane marassa godiya, tunda su suka nemi ki aureshi ba ke ce kika nema ba Jawahir na tabbata idan har kika auri Faruk bazaki ta'ba yin da kin saniba dan shi d'in mutumin kirki ne. Girgiza kai tayi cikin muryar kuka tace ni ba wai na k'i bane kawai dai hakan ba adalci bane in auri mijinta nidai sutaimaka subarni ink'are rayuwata a haka dan Allah na rok'eku. Baba Malam ne yace shikenan Jawahir mu bazamuyi maki dole ba zamu hak'ura da abinda mukeso dan bamu muka haifekiba dole mubari kiyi abinda zai faranta maki rai. Inna Mairo ce tace tabbas haka ne Alhaji domin mu mahaifiyarta muka haifa itace zata kasance me biyayya da duk abinda mukeso Allah sarki rayuwa mutuwa bata barin wani dan wani yaji dad'i, ina ma ace Khausar tana raye. Jawahir tana jin haka k'ara sautin kukanta tayi tare da zamowa k'asa cikin kuka tace dan Allah Inna da Baba kuyi hak'uri wallahi nima mai biyayya ce zanyi maku biyayya ga duk abinda kukeso na amince zan auri Faruk dan Allah kusa ma rayuwata albarka. Suna jin haka duk sai wani irin farin ciki yalullu'besu nan sukaita shimata albarka, gefe d'aya kuma tausayinta suke ji. Jawahir kasa cewa komai tayi saidai cigaba da kukanta da tayi. Fitowa sukayi suka samu su Baba Musa da su Faruk zaune sunyi shuru suna jira sufito suji yadda sukayi da ita dan Faruk tsintar kanshi yayi da jin wani iri akan nunawa da Jawahir tayi bata sonshi, yana ganin su Baba Malam sun fito saida gabanshi yafad'i wanda yarasa dalilin fad'uwar gaban, idanu yazuba masu yana kallonsu, Nasiba ce tayi k'arfin halin cewa Baba ya kukayi da ita ta amince? Murmushi su Baba Malam sukayi sukace Eh ta amince. Gabad'ayansu hamdala sukayi Faruk ko ajiyar zuciya yasafke yaji wani irin sanyi ya ziyarceshi. Nan shi da Nasiba sukayi masu godiya. Nasiba jikkarta tad'auko tafiddo dubu d'ari taje tatsugunna gaban Baba Malam tace Baba ga wannan kud'in neman aurene ni nad'auki nauyin biyansu, sannan insha Allahu su Dad zasu zo atsaida ranar aure mudai muna rok'on ataimaka mana kar asa rana dayawa dan munfiso ayi bikkin batare da anja lokaci ba. Su dukansu mamaki yakamasu ganin yadda ko kad'an bata nuna damuwa ba saima murna da take. Inna Mairo ce takasa daurewa tace tabbas wannan mata zuciyarki me kyau ce tunda nake a tarihin rayuwata da idanuna kece macen da nata'ba ganin ta yi hakan, Allah ubangiji yasaka da alkhairi, Allah yabiyaki da gidan aljanna. Murmushi Nasiba tayi tace babu komai Inna ai Jawahir 'yar uwatace kuma duk musulmi na k'warai zaiso ma d'an uwanshi abinda yake so ma kanshi, ko bakomai Jawahir ta cancanci fiye da hakan a wajena dan itama ta taimaka mani a lokacin da nake buk'atar taimako taya zan kasance me manta alkhairi. Maganar da tayi ta shigesu sosai nan sukaita mata godiya, Faruk ko saidai idanu yazuba mata cikin zuciyarshi yana gode ma ubangiji da yamallaka mashi Nasiba a matsayin mata dan tabbas ita d'in macece ta gari. A chan 'bangaren Jawahir tana ganin su Baba Malam sun fita komawa tayi takwanta nan tafara rera sabon kuka, dan dole ta amince da za'bin su saboda a yanzu batada na sama da su suna k'ok'arin yi mata duk abinda take buk'ata, alk'awaline tayi ma kanta bazasu ta'ba kuka da itaba babu abinda zasu nema a wajenta surasa itace zata koma madadin mahaifiyarta a wajensu, wannan dalilin ne yasa tayi saurin amincewa da auren Faruk. Har wajen k'arfe biyar Jawahir bata fitoba dan haka wajen biyar da rabi suka bar Kebbi sunso suyi bankwana da Jawahir ammah tak'i fitowa dan koda Inna Mairo tashiga dan tafad'a mata tafiyar da zasuyi samunta tayi tana bacci ko da ma ba baccin gaske takeba dan bataso tasake had'a idanu da mutanen ne saisa tatsiri baccin k'arya zuciyarta a tunkushe. Nasiba Alk'awali tayi masu insha Allahu da sunje zasu sanar da su Dad azo ayi maganar auren, Faruk ko saidai yabita da idanu ta k'ara daraja sosai a cikin idanunshi. K'aramin galan d'in kindirmo da man shanu aka basu da k'ananun tsarabobi suka tafi da su har airport su baba musa suka rakasu saida jirginsu yatashi sannan suka baro airport d'in. Suna komawa gida Nasiba part d'inta tawuce Faruk kamar jira yake yabi bayanta fara cire kaya tayi sai gashi ya shigo kallonshi tayi tai murmushi tace ya dai ango bazaka d'an watsa ruwaba kafin magrib?. Matsowa yayi kusa da ita yace yanzu saboda Allah Nasiba hakan da kikayi kin kyauta?. Murmushi tayi tace me nayi, dan kawai na nema maka auren Jawahir sai yazama laifi, kaima fa kana sonta malam kafiddo farin cikinka a fili kawai ba sai ka 'boye min ba. Rik'o ta yayi yana mata kallon mamaki yace Nasiba wa yafad'a maki ina son Jawahir? Cikin idanunshi takalla tace soyayyarta nagani a cikin idanunka ko zaka iya rantsewa kace baka sonta. Jan hancinta yayi yace ni bance ina sonta ba. Janye hancinta tayi tace wash da zafi fa Lovely, ni dai nasan kana sonta kawai dai kana basarwa ne,,, tana fad'in haka tajuya tana k'ok'arin cire skirt d'inta, rik'o hannunta yayi yace ya akayi kikasan haka?. Batare da ta juyo ba tayi murmushi tace tun daga yanayin yadda kake waya da ita da yadda kake yawan min labarinta kai tunma kafin nan zan iya cewa tun a kotu nafara ganin alamar hakan. Faruk kasa cewa komai yayi nan yaja yai tsaye yana kallonta cike da mamaki. Juyowa tayi takalleshi fuskarta d'auke da murmushi tace ko zakayi wanka muje muyi kar magrib yayi kaga na gaji sosai yau. Batare da ya ce komai ba yafara cire kayanshi dan rasa abinda zaice mata yayi. ------*****------- A daren Nasiba takira su Dad da Mom tafad'a masu yadda sukayi da su Baba Malam, washe gari Faruk yaje gida nan yasake fad'a masu komai har da irin k'ok'arin da Nasiba tayi wajen nema mashi auren Jawahir. Daga Dad har Mom sun jinjina mata nan sukaji ta k'ara shiga ransu sukayi Allah yasa alkhairi. Dad yasa mom takira Nasiba a waya tatambayeta wata nawa yadace asa bikkin nan Nasiba tace kar yawuce wata biyu kamar yadda akasa nata suka amince da haka. A cikin satin ne su Dad da abokinshi sukaje Kebbi suka nema ma Faruk auren Jawahir wajen Baba Malam yace ai Nasiba ta nema mashi auren saidai ayi baiko, haka ko akayi akasa bikki wata biyu masu zuwa, dan a lokacin bikkinsu Khausar sati bakwai yarage nan aka ce za'a k'ara sati guda ayi tare da na su Jawahir jin haka yasa su Dad sukace a'a kar ak'ara kawai arage sati guda daga cikin wata biyun da akasa sai ayi bikkin tare nan da sati bakwai nan su Baba Malam suka amince su Dad dayake a mota sukazo suka fiddo kayan sa bikkin da suka ciko boot da su suka bada sannan suka juya saboda tafiyar mota ce basuso suyi dare dan ma driver yakawo su. _________Jawahir ko tun ranar da su Faruk sukazo sukayi maganar aurenta tad'auki damuwa tasa a ranta saida Inna Mairo tadinga mata nasiha tare da bata shawara tabar ma ubangiji za'bi acikin rayuwarta sannan tarage sa damuwa tadinga tashi kullum cikin dare tana kaima ubangiji kukanta tare d neman za'binshi a cikin rayuwarta. Su khausar ko murna suka dinga yi suna tsokanarta dan cewa suke daman chan sun ga alamar faruk yana sonta yanayin yadda yake kallonta, Rashida tace yoh itama d'in bakiga yadda take d'oki idan yazoba tana sonshi gulma ce kawai mudai munji dad'i. Shuru jawahir tayi tak'yaleshi nan magana tazagaye gida akaita murna tare da yin Allah yasa alkhairi. Lokacin da akasa bikki ko jawahir kasa fitowa tayi a d'aki ta'boye tadinga kuka. Sauran mutanen gida aka dinga murna musamman da akaji tare da nasu Khausar za'a had'e ayi ...... _Sis Nerja'art✍🏻_[7/24, 11:22 PM] Sis Nerja'art 2: *......FANSAR RAI......* *INTELLIGENT WRITER'S ASSO....®* [On Ward Together] _Follow me on Wattpad: *Sis-nerja*_ _Wannan Littafin na kud'i ne domin karantawa cikin aminci da yarda ga duk me buk'ata zai turo katin Mtn na d'ari biyu N200 kacal ta wannan number d'in 09035938246, ko ta account number 5330055604, Idan katura ka aiko da screen shot na transaction a wannan number d'in 09035938246_ _Akwai gara'basar *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shahararriyar marubuciyar nan *AMEENA ABBA UMAR* tare da novel d'in *FANSAR RAI* akan farashin N300 kacal, ko da kud'in ka sai da rabonka_ *PAGE 26* Tunda su Dad suka dawo suka fad'a masu Nasiba maganar baikon da akayi murna tadinga yi abun har yaba Faruk mamaki ganin yadda bata nuna damuwa ba, lokacin suna zaune a parlor nan tafara tsara yadda bikkin zai kasance, batare da ya ce mata komai ba yamik'e yashige bedroom d'inshi. Da idanu tabishi nan tayi d'an guntun murmushi wanda baikai zuci ba sannan tamik'e tabi bayanshi, tana shiga tasameshi kwance a saman gado kanshi yana kallon ceiling. Zuwa tayi takwanta a k'irjinshi cikin shagwa'ba tace shine muna magana sai kataso katafowarka kabaroni ko? Batare da ya kalletaba yace Nasiba wai anya kina sona? Da mamaki take kallonshi tace me kagani? kaga wani abu ya canza ne daga soyayyar da nake nuna maka? Kusan haka dan da ace kina sona da sai kinyi kishina. K'wallah ce tanemi tafito daga idanunta tayi saurin maidata tace Faruk kaima ka san ina sonka soyayyar da nake makace yasa nakeson ka auri Jawahir dan Allah kadaina irin wannan tunanin indai ba so kake kad'aga min hankali ba. Sai a lokacin yad'ago yakalleta murmushi yasakar mata yace shikenan hearty insha Allahu na daina, nagode sosai da irin k'aunar da kike nuna min. Itama murmushin tayi tace kadaina godiya agareni Lovely, yauwa ammah dan Allah nan gidan Jawahir zata zauna ko? Dan wallahi nafiso muzauna tare kaga mun dinga hira tunda kai ficcewa kake wajen aiki kabarni ni kad'ai. Toh Hearty duk yadda kikeso haka za'ayi tunda ga gudan part d'in chan sai tazauna a ciki. Cikin jin dad'i tace nagode sosai Lovely, sai kuma tamarairaice tace dan Allah inaso idan kabani dama gobe inje ingano Mummy. Shafa bayanta yayi yace toh Allah yakaimu goben idan nadawo wajen aiki sai inkaiki. Godiya tayi mashi cikin jin dad'i. _______**______ Nasiba ce zaune a gidansu tare da mahaifiyarta da 'yan uwanta da suka zo su ma, suna cikin hira ne take sanar da su maganar auren da Faruk zaiyi, su dukansu hucking sukayi sukace aure kuma? Wane Faruk d'in wai ma?,,, cike da mamaki suke tambayarta Murmushi tayi tace nawa man. Yaya Sadiya ce tace ban gane nakiba duka yaushe akayi bikkin naku da har zai k'ara aure? Cikin nuna rashin damuwa tace Yaya Sadiya ai ba wani abu bane dan ya k'ara aure nice ma nanema mashi auren. Daga Mummy har su Yaya Sadiya rik'e baki sukayi suna kallonta cike da mamaki. Bata damu da irin kallon da suke mataba tace ba wani abun mamaki bane dan na ce haka. Nasiba anya kina cikin hayyacinki kuwa? Ke ana gudun kishiya ke kuma kina jawo ma kanki ita. K'walla ce tacika mata idanu tace toh ya zanyi wallahi ina tausayin Jawahir sosai kuduba kuga mahaifinmu ne yajefata halin da take ciki na rashin duk wani makusanci nata hatta mijinta, ya zanyi idan bance ta auri Faruk ba, bamusan halin da take ciki ba koda ace bata nuna a fili ba ansan akwai damuwa acikin ranta, sannan duk abinda mahaifinmu yayi mata hakan baisa tak'i mu ba dan tasan ba mu mukayi ba, wallahi duk irin k'aunar da nakeyi ma Faruk zan iya hak'ura ya auri Jawahir domin ita d'in mutuniyar kirki ce, nidai dan Allah kusa albarka a cikin auren nan kar kusakar min da gwiwata a lokacin da nake sanar da ku aikin ladan da zanyi. Su dukansu jikinsu sanyi yayi nan sukayi masu Allah yasa alkhairi, Mummy ta jinjina ma halin d'iyartata dan bata ta'ba tunanin hakan ba saboda Nasiba tana da kishi sosai. Nan tayi masu wuni sai dare Faruk yazo d'aukarta suka koma gida. Bayan sati biyu da sa bikkin Nasiba ta amshi kud'ad'e wajen Faruk taje da kanta tafara had'a ma Jawahir lefe kaya na gani nafad'a masu tsada tahad'a mata komai da zuciya d'aya batare da tasa mugunta ba akwatuna takwas Faruk yace tahad'o mata, wasu kayan duk irin nata ne taza'bo mata hakan da tayi ya k'ara mata k'ima da daraja a idanun mijinta da surikkanta nan Faruk yabata kud'ad'e sosai yace tayi hidima da su itama. Godiya tayi mashi sosai. A chan 'bangaren su Jawahir ko duk wani shirye shirye da ake yi ma Khausar da Rashida yanzu anhad'a har da ita akeyi tun ana saura wata guda bikki aka fara masu gyara musamman ma ita da akasan ta ta'ba aure, yaunzu gabad'aya ta mik'a lamurranta ga Allah kullum addu'arta d'aya Allah yatabbatar mata da alkhairi a cikin rayuwarta, gefe guda kuma ta sha ta'boye kanta taci kuka batare da sanin kowaba, ga wata irin kunyar su Mom da takeji yanzu indai ba su suka kirata aka gaisaba bata kira shima bakamar da ba yanzu bata sakewa suyi hira. Faruk ko ya kira bata d'agawa saidai idan message yaturo mata sannan tamaida mashi reply hakan yana ba Faruk mamaki sosai dan hakane yashirya yaje Kebbi a motarshi a waya yasanar da ita zai zo dan haka Jawahir tafara shirin tarbarshi, Baba Nura tafad'a mawa shi kuma yasanar da su Baba Malam sukace Allah yakawoshi lafiya. Ranar asabar tun da safe da tatashi tashiga kitchen tafara girki Khausar ce tazo tana tayata fried rice suka shirya mashi wadda tasha had'i sannan sukayi mashi pep chicken da kunun aya . Wajen k'arfe d'aya sun gama nan taje tayi wanka tun tana girkin hankalinta yana wajen Faruk tana so takirashi taji yanayin tafiyar tashi bare da yasanar da ita a mota zai zo, har waya tad'auko zata kirashi sai kuma tafasa. Cikin kayan da yayi mata da zata dawo kebbi tad'auko wata shadda gown brown tasaka wadda tasha aiki da pink d'in zare, ita tazauna tayi kwalliyarta. Tana zaune saman darduma bayan ta gama sallar azuhur sai ga kiran Faruk ya shigo. Saurin d'auko wayar tayi tazuba mata idanu tana kallo har saida takusan tsinkewa sannan tayi picking tare da yin sallama. Amsa mata yayi sannan yace kifito ganinan na iso. Har zatace mashi yashigo nan yakashe wayar dan haka tamik'e tad'auke darduma saida tak'ara gyara fuskarta tad'akko pink d'in gyale tayafa sannan tafito tanaso tashiga 'bangaren su Khaisar tace tafito tarakata sai tajiyo hayaniya a cikin gidan alamun kowa yana nan ita kuma ga kunya bataso tahad'u da 'yan cikin gida dan haka tasamu Inna Mairo tafad'a mata ya iso. Inna Mairo tace toh taje tashigo da shi kanta sunkuye a k'asa tafita. Faruk da ke zaune cikin mota ya zuba ma k'ofar gidan idanu dan ganin ta inda zata fito dan a lokacin su Baba Malam basu nan ba kowa a wajen, idanunshi a kanta tafito har ta iso wajen motar ta shi taja tatsaya tare da yin sallama. Amsawa yayi tare da bud'e mata k'ofar gaba yace tazagayo tazauna. Sai a lokacin tad'ago takalleshi sanye yake cikin manyan kaya ya yi kyau sosai da har zatace mashi a'a ganin yadda yatsareta da idanu yasa bata musaba tazagaya taje tashiga tabar k'ofar a bud'e, gaishe shi tayi maimakon ya amsa sai cewa yayi shine ko kikirani kiji yanayin tafiyar tunda natafo ko. Shuru tayi dan ita kanta ta san bata da gaskiya. Ta cikin mirror yake kallonta ganin batada niyar d'ago kanta bare tayi magana yasa yace Jawahir nuna rashin kulawar da kike min bana jin dad'inshi idan kina haka sai inga kamar baki sona, tilasta maki akayi sai kin aureni ko? Shuru tayi nan ma tana wasa da yatsun hannunta. Juyowa yayi yakalleta yace indai har baki sona kifad'a min Jawahir wallahi sai inhak'ura ba wani abu bane sai inbarki ki auri wanda kikeso dan nima kaina bazanso kiyi auren da bakiso ba. Sai a lokacin tad'ago kai takalleshi idanu cike da k'walla tace Yaya Faruk ba wai bana sonka bane ka cancanci insoka ko dan saboda alkhairin da kayi min da taimaka man da kayi a lokacin da nake buk'atar taimako bazan ta'ba kasancewa butulu agareka ba ko da ace wanine na daban kakawo kace in aura ni me biyayya ce agareka bazan ta'ba baka kunya ba, kawai dai banason zama da Aunty Nasiba a matsayin kishiyarta ne sai inga kamar banyi mata adalciba kamar na so kaina dayawa, wannan dalilin ne yasa kaga na kasa sakewa hankalina ya k'i kwanciya. Wani irin sanyi yaji a ranshi nan yasafke ajiyar zuciya sannan yace Jawahir idan dai har kina sona to dan Allah kidaina shareni kisaki jikinki da ni Nasiba kuma batada matsala wallahi itace ma tagoya min baya in aureki na tabbata zata zauna da ke lafiya domin ita d'in mutuniyar kirkice ba irin mahaifinta ba, ina sonki jawahir ina fatan kema zaki taimaka kisoni. Murmushi ne yasu'buce mata ahankali tace nagode Yaya Faruk. Idanu yazuba mata yace bakice komai ba zaki so ni ko? Saurin fita tayi daga cikin motar tace kashigo kagaisa da Inna Mairo kafin su Baba Malam sudawo daga wajen jana'izar wani abokinshi da ke nan bayan layinmu sunce bazasu dad'eba. Murmushi Faruk yayi batare da ya ce komai ba yabud'e motar yafito nan tawuce gaba yana biye da ita a baya suka shiga cikin gida. Gaisawa sukayi da Inna Mairo cikin girmamawa daga nan Jawahir tawuce kitchen takawo mashi abinda tatanadar mashi, tana gama ajiyewa tazuba mashi yace saidai tazauna suci tare indai ba haka ba bazai ciba. Marairaicewa tayi tace dan Allah Yaya Faruk kaci ni na k'oshi. 'Dauke kanshi yayi yace shima bazai ciba duk yunwar da yakeji zai hak'ura sai ya koma gida sannan zai ci. Tana jin haka tazauna k'asa tare da jawo plate tana zubawa yana kallonta tana turo baki ahaka tad'an zuba rabin plate. Murmushi yayi sannan yasafko k'asa shima nan yafara cin wanda tazuba mashi, lumshe idanu yayi yace ashe amaryar tawa itama ba bayaba wajen iya girki. Murmushi tayi sannan tafara cin wanda tazuba ma kanta. Suna cikin ci sukaji sallamar su Baba Malam Jawahir d'aukar plate d'inta tayi cikin sauri tanufi bedroom dan kar sushigo suganta. Faruk dariya yayi nan suka shigo suka gaisa da shi sannan suka bashi waje yakimtsa cikinshi. Bayan ya gama ne yafita suka sake gaisawa sannan yafiddo tsarabar da yazo da ita cikin boot yasa aka shiga da ita cikin gida. Har sukayi sallar la'asar baiga fitowar Jawahir ba dan haka yakirata a waya yace tafito suyi bankwana tafiya zaiyi. Kiran Khausar tayi a waya dan tafito sugaisa da shi dan ta san halin Khausar indai har yatafi basu gaisaba sai ta sha tsegumi wajenta. Tare suka fito da Khausar suka sameshi tsaye wajen motarshi nan suka iso Khausar tagaisheshi. Amsawa yayi cikin sakin fuska yace ya gida khausar? Lafiya Lau Yaya Faruk, ya su Mom? Duk suna lafiya lau, kallon Jawahir yayi sannan yace ina fata dai kina kula min da matata. Saurin d'agowa Jawahir tayi takalleshi nan yad'aga mata gira. Dariya Khausar tayi tace ina kula da ita sosai angonmu, dan bana barin kowa yakalleta bare yasamu damar yi mata magana. Murmushi yayi yace gaskiya na ji dad'in jin haka daga gareki nagode sosai Khausar bari inbada tukuici, nan yasa hannu a aljihu yad'auko bandir d'in 'yan 500 yamik'a mata. Amsa tayi cikin jin dad'i tayi godiya sannan takoma gida tabasu waje dan suyi bankwana. Tana wucewa Faruk yace Jawahir ya kamata kisake kidaina wannan kunyar taki dan gaskiya tana cutar da ni kwatakwata baki bani kulawa ko waya baki bari muyi hakan baya min dad'i. Batare da ta d'ago ta kalleshi ba tace toh zan gyara. Yauwa kokefa, mota yabud'e yafiddo wata leda wadda duk kud'i ne a ciknta yamik'a mata yace ga wannan kinyi hidima da su. Girgiza kai tayi tace a'a kabarsu akwai kud'i a account d'ina. Ban damu da kud'inki ba wannan ni nabaki, kinsan dai bana son gardama. Amsa tayi taimashi godiya. Yace bakomai yanzu dai bari inwuce kar inyi dare. Toh Yaya Faruk nagode agaishe da su Mom da Su Aunty Nasiba. Insha Allahu zasuji idan na isa zan kiraki waya salan kik'i d'auka kamar yadda kika saba min, Allah had'aki zanyi da Baba Malam. Ahankali tace kayi hak'uri zan d'auka. Shiga motar yayi yace Allah yasa. Bakuyi bankwana da su Baba Malam ba,,, cewar jawahir da take kallonshi. Duba agogo yayi yace munyi bankwana suna tafiya ma kika fito daga cikin gida, yauwa ban tambayeki Event d'in da zakiyi ba dan idan za'a kawo lefe nakeso in aiko maki da Invitation Card d'inki saboda zan d'anyi tafiya workshop kwana biyu. Girgiza kai tayi tace babu abinda zanyi walima ce kawai zanyi itama a makaranta. Murmushi yayi cikin ranshi ya ji dad'in hakan dan shi daman ba mutum bane meson party saisa koda Nasiba ma batayi ba ya ji dad'i, yace shikenan zan sa abugo maki ko inturo kud'i Baba Nura yabugo a nan garin. Amsawa tayi da toh nan tayi mashi godiya. Kallon cikin idanunta yayi yace baza'a fad'a min magana me dad'i ba wadda zata tayani hira acikin mota tunda ni kad'ai ne. Janye idanunta tayi cikin jin kunya tace Allah yakiyaye hanya Allah yamaida mana kai gida lafiya. Amsawa yayi da Ameen sannan yace baki fad'a min kina sona ba. Saurin juyawa tayi cikin jin kunya tashige gida. Dariya yayi sannan yatada mota yakama hanyar Katsina. Gudu yadinga yi da motar sosai ba shi ya isa ba sai dare. ________ Tun daga lokacin yake samun damar yin waya da Jawahir dan yanzu tana d'aga wayarshi idan yakirata cikin dabara yasamu tasake suka dinga hira sosai dan a kullum sai yakirata kusan sau ukku a rana ammah baya kira agaban Nasiba, a gefe guda kuma yana ba matarshi kulawa sosai babu abinda zata nema tarasa a wajen mijinta wannan dalilin ne yasa Nasiba tak'ra kwantar da hankalinta. Ana saura sati ukku bikki aka kai lefen Jawahir inda Dad yad'auki nauyin kayan d'akinta yace shi zaiyi dan alk'awali yayi ma kanshi ko da ace ba Faruk zata aura ba shi zaiyi mata kayan d'aki saboda zaman mutuci da amana da yayi da mahaifinta zai iya cewa shine silar d'aukakar kamfaninshi, ya dai barsu da kayan kitchen d'inta. Nan su Baba Malam sukaita mashi godiya tare da addu'a itama Jawahir ta ji dad'in hakan sosai nan tasake saka ma ranta zata zauna da d'ansu da matarshi lafiya ko dan irin soyayyar da mutanen nan suke nuna mata. Barr Faruk ya je workshop a Abuja saida sukayi sati biyu sannan suka dawo tare da matarshi yaje suka safka a hotel. Ana saura sati d'aya bikki suka dawo lokacin Dad har ya zuba ma Jawahir kayan d'akinta a part d'inta da zata zauna, set biyu yayi mata na bedroom sai na parlor set d'aya ya kashe kud'i sosai kamar yadda zaiyi ma 'yar cikinshi. *BAYAN SATI 'DAYA* Su Baba Malam sunyi k'ok'ari sosai wajen saya ma su Khausar da Rashida kayan d'aki set guda guda sai kayan kitchen. Inda ita kuma Jawahir akayi mata kayan kitchen nagani na fad'a saboda ita ba'a siya mata kayan d'akiba saisa nata duk sukafi kyau da tsada. Baba Nura ne yabugo masu invitation card me d'auke da sunayen amaren su duka ukku wanda suka dinga gayya da shi walima ne kawai zasuyi a islamiyyarsu sai kuma yinin bikki da za'ayi daga nan kowace amarya atafi da ita gidanta. 'Yan uwa da abokan arzik'i duk sunzo dan gudanar da bikki nan Baba Malam yaware shanu biyu aka yanka dan ayi hidima da su, amare suna shan gyara sosai nan da nan suka canza dan ita kanta Inna Mairo ba'a barta a bayaba wajen gyara 'yan jikokin nata gyara tayi masu irin nasu na 'yan zamfara. Yau ma bayan ta gama tsuma Jawahir tana kwance saman gado inda tabar su Khausar suka fita dan suje suyo masu abubuwan da zasu raba wajen walima gobe, wayartace a hannunta tana chart da Faruk nan Inna Mairo tashigo da wata leda tazauna bisa gadon sannan tad'akko wata gumba a ciki tamik'a mata tace tashi kici wannan. Kallon gumbar tayi ta'bata rai tace ni fa Inna na gaji da 'yan ciye ciyen nan. Rik'e baki inna tayi tace yau Allah ya had'ani da shashashar yarinya ke ana so agyaraki miji yajiki zam ammah ke bakiso ko mancewa kike da gidan kishiya zakije? Tashi Jawahir tayi ta amshi gumbar tana turo baki nan tafara ci, ji tayi da dad'i dan haka tacigaba da ci saida taci kusan rabi sannan Inna Mairo ta amsa tace tabarta haka. Komawa tayi takwanta tana cigaba da chart d'inta. A account d'inta Faruk yaturo mata kud'i yace tak'ara dan yasan wad'anda yaturo mata bazasu isheta ba godiya tayi mashi. A chan Katsina ko ba wata hidima akeyi sosai ba dan wannan karan ba sosai sukayi gayya ba saboda a ganinsu kamar za'a takura mutane tunda duka yanzu baifi wata shidda da yin wanchan bikkin ba, Malam ne yabada shawarar hakan saisa. Mummyn Nasiba da su Yaya Sadiya sunje har gida sunyi ma su Mom Allah yasa alkhairi. Itako uwar gayyar ba'a magana dan ita tabugo IV taba Barr Nass yagayyaci abokansu, gefe guda kuma tabada aka d'inka ma ango kayan da zaisa na d'aurin aure. Ran asabar wajen k'arfe goma su Dad da abokanshi biyar sai Faruk da abokanshi da Malam suka shiga jirgi suka je Kebbi dan da k'arfe sha d'aya za'a d'aura aure. Amare sun sha kyau sosai su dukansu da ka kalli fuskarsu zakaga a kumbure duk sun sha kuka Khausar ce me d'an dama dama daga cikinsu. Wajen k'arfe sha d'aya aka d'aura auren Faruk Sani Maishadda da amaryarshi Jawahir Muhammad Maikud'i, Sai Khausar Musa Maisalati da Mansur Abba sannan Rashida Jamilu Maisalati da angonta Aminu Umar. Jama'a da dama sun samu halartar d'aurin auren tun daga mutanen Kebbi da ma wad'anda ba na kebbi ba. Ana d'aura aure su Faruk suka koma masaukin da aka safkesu shi da abokanshi biyu inda su Dad da sauran abokan suka koma Katsina. Jawahir ganin yadda gidan yacika yasa tasulale takoma cikin bedroom d'in Inna tayi zamanta ita kad'ai dan hayaniyar taji bata so. Tana zaune ta buga tagumi nan Faruk yakirata waya, kallon wayar tayi kamar bazata d'auka ba sai kuma chan tad'auka batare da ta ce komai ba. Daga chan 'bangaren Faruk yayi sallama yace ya dai amaryata ina fatan kina lafiya?. Cikin muryarta da tadashe saboda kuka tace lafiya lau. Runtse idanunshi yayi cikin nuna damuwa yace oh my god jawahir ba dai kuka kike ba? Shuru tayi nan yasafke ajiyar zuciya yace dan Allah kidaina 'bannatar min da hawayenki My Jawa kinga yau ranar murna ce agaremu kicire kowace damuwa acikin ranki kinga and'aura aure yanzu andamk'a min amanarki insha Allahu zan baki duk wata kulawa da tadace dan zan nuna maki ni d'in me k'aunarki ne zan mantar da ke duk wata damuwa da kike cikinta dan Allah Jawahir kisama min gurbi acikin zuciyarki ko yayane. Runtse idanunta tayi nan hawaye suka fara gangaro mata tana jin maganganunshi har cikin kwanyar kanta. Jin ta yi shuru yasa yace shikenan Jawahir bari inbarki kar incika ki da surutu ni zan nema ma kaina matsugunni a cikin zuciyarki da sannu zan koya maki sona, kihuta lafiya. Tana ji ya kashe wayar janye wayarta tayi tad'aura saman k'irjinta batare da ta bud'e idanunta ba nan hawaye suka cigaba da fita. Tana cikin haka Inna Mairo tashigo tasameta a gefenta tazauna tafara lallashinta har tasamu tayi shuru sannan tad'auko wani tsumi tabata tace ga wannan kisha Wani irin haushi Jawahir taji dan har ta fara gajiya da abubuwan da Inna Mairo take d'irka mata babu yadda ta iya ta amshi tsumin tafara sha jinshi tayi da dad'i ba kamar sauran ba dan haka tad'age kai tashanye shi tas. Nan inna tabata wata gumba ta amsa tafara ci wani irin gard'i taji ba kamar ta jiyaba wannan tafi dad'i dan kwakwa da zuma ne a jikinta haka tacita sosai. Wajen k'arfe ukku aka had'a mata ruwan wanka tayi bayan ta gama aka shiryata cikin lace me tsada saida sukayi sallar la'asar sannan su Baba Malam suka shigo haka aka fito da amare aka kaisu d'akinshi yayi masu nasiha sosai. Nan sukaita kuka. Su Khausar aka d'auka a motoci aka tafi da su gidajen mazajensu inda Jawahir kuma sai k'arfe biyar sannan aka rakata filin jirgi ita da mijinta da abokanshi suka shiga jirgin. Dakyar aka 'bam'bareta daga jikin Inna Mairo da zasu tafi. Tunda suka shiga jirgin tahad'e kanta da gwiwa tadinga rusa kuka. Duk yadda Faruk yaso yalallasheta kasawa yayi dan kuka tadinga yi sosai. Suna isa Katsina suka tarar da motoci biyu su Aunty Kilima k'anwar Malam sunzo tararsu nan Aunty Kilima da wata k'awar Mom suka shiga mota d'aya da amarya inda gudar motar da driver yazo da ita su Faruk da Barr Nas suka shigeta. Jawahir tana k'udundune cikin gyale har lokacin hawaye take ahaka suka isa gidan iyayen Faruk, d'akin Mom aka wuce da ita ganin har lokacin da sauran mutane a gidan. Aunty kilima ce tazauna da ita a d'akin saboda kunya Jawahir takasa bud'e lullu'bin haka su Mom suka shigo suka gaisa suka sake mata nasiha bayan sallar isha'i aka tattarata aka kaita gidan mijinta Aunty Kilima da Hajiya Maimuna k'awar Mom ne kad'ai suka kaita direct part d'in Nasiba suka wuce da ita lokacin gidan ba kowa sai ita kad'ai tana ganinsu cikin sauri tazo tataresu tarungume Jawahir da ke lullu'be tana mata sannu da zuwa. Su Hajiya Kilima sunji dad'in yadda Nasiba tanuna kulawa nan suka zaunar da su suka yi masu nasiha daga nan aka wuce da Jawahir part d'inta da yasha gyara sosai. A saman gado suka zaunar da ita suka sake mata nasiha sannan sukai mata bankwana suka tafi. Saida taji ba motsin kowa sannan tayaye mayafinta tana bin d'akin da kallo. Wajen k'arfe tara Faruk yadawo gidan Nasiba ce tatareshi tarakashi part d'inshi yayi wanka yashirya ledojin da yashigo da su guda biyu tad'auki guda tace mashi suje. Da mamaki yake kallonta yace ina zamuje? Murmushi tayi tace wajen amarya man. Cikin wasa yaharareta yace kamar irin kin gaji da ni kike nema kibada ni. Dariya tayi tace eh d'in na ji bakomai nidai muje malam inrakaka dan bacci nakeji. Haka suka fito tare sukaje part d'in Jawahir a parlor Nasiba tazauna yashiga ciki yasameta zaune dan tunda taji shigowarsu tamaida lullu'binta daga gefenta yazauna yana murmushi yace amarya ta ango kinsha k'amshi. Shuru tayi nan yakai hannu zai yaye lullu'bin tayi saurin fad'awa jikinshi Murmushi yayi a karo na biyu tare da rungumeta yace hanani ganin kyakkyawar fuskar za'ayi? Ko sai na siya?. Shuru tayi nan yajanyeta tare da mik'ewa yace bakomai zan siya yanzu muje ga Nasiba chan a parlor tana jiranmu. Mik'ewa tayi tabi bayanshi ta cikin gyalenta me shara shara take ganin hanya har suka fito parlor inda Nasiba take, a kujerar da take zaune yazauna inda Jawahir tazauna a 1 seater nan yayi masu nasiha. Nasiba yafara tambaya ko tana da abinda zatace saidai tayi murmushi tace babu saidai abu guda shine yayi adalci atsakaninsu yarik'esu amana. Murmushi Faruk yayi yace insha Allahu zanyi bakin k'ok'arina wajen ganin na yi adalci, kallon Jawahir yayi yace kefa akwai abinda zakice? Girgiza kai tayi alamun a'a. Nan yayi masu addu'ar zaman lafiya. Mik'ewa Nasiba tayi tace toh Amarya da Ango sai ince mukwana lafiya. Kallonta Faruk yayi yace Hearty tun yanzun? Murmushi tayi tace wallahi na gaji sosai ga bacci ina ji. Mik'ewa yayi yace toh bari inrakaki. Saurin wucewa tayi gaba tana cewa a'a kabarshi nagode amaryarmu ga amanar miji nan na damk'a maki mukwana lafiya. Tana fita taja masu k'ofa cikin sauri takoma part d'inta tana shiga tafashe da kuka tare da fad'awa saman gado wani irin kishine tadinga ji ganin yau mijinta ne zai kwana da wata ba itaba, kuka tadinga yi sosai kamar k'irjinta zai fito duk yadda taso tayi controlling d'in kukanta kasawa tayi saida tayi me isarta, har wajen k'arfe d'aya tana kwance zugum zuciyarta tadinga ayyana mata wasu abubuwa akan Faruk da Jawahir daga k'arshe takori shaid'an tamik'e taje tad'auro alwallah, sallah tayi raka'a biyu sannan tazauna karatun alk'ur'ani dan ji tayi kwatakwata bata ma jin baccin. Sai wajen k'arfe ukku sannan tasamu taruntsa. A chan 'bangaren su Faruk bayan fitar Nasiba komawa yayi gefen Jawahir yazauna tare da yaye mata malullu'binta saurin sadda kanta tayi k'asa. Idanu yazuba mata yana k'are mata kallo duk sai taji ta tsargu nan gabanta yafara fad'uwa. Saida yayi kusan minti biyar yana kallonta sannan yasa taje tad'auro alwallah sukayi sallah a nan parlor bayan sun gama ne yakama kanta yayi mata addu'a sannan yad'akko masu ledar da Nasiba ta ajiye masu dakanshi yatashi yaje kitchen yad'akko plate da cups. Kaza yafara bata da fari ta k'i amsa saida yafara lalla'bata sannan tayarda taci cike da jin kunya take amsa, saida yatabbatar ta k'oshi sannan shima yafara cin nashi. Mik'ewa jawahir tayi tashige bedroom d'inta toilet tafad'a tawanke hannu da bakinta sannan tazo tahaye gadonta ko kaya bata cireba gabanta yana dukan ukku ukku ita abun har mamaki yake bata ganin wannan ba shine aurenta na farko ba ammah duk tsoro ya kamata. Tana nan kwance Faruk yashigo hawa yayi saman gadon tare da kallonta ganin yadda take wuk'i wuk'i da idanu yace Rabin ran ya kamata kicire kayan nan bazakiji dad'in bacci da su ba. Cikin rawar murya tace a'a zan iya. Murmushi yayi yace toh ai ni zasu takura man ammah bakomai tunda kince haka bari inrage maki su dakaina Saurin tashi tayi zaune cike da tsoro tace bari inje incanza dakaina. Rik'ota yayi yamatsa gab da ita nan yazuba mata manyan idanunshi saurin sadda kanta tayi k'asa tare da cewa bari inje incire....bata rufe bakiba taji hannunshi a bayanta yana neman yazage mata zip d'in riga saurin d'ago kai tayi takalleshi wanda hakan ya yi daidai da zage Zip d'in da yayi. Tureshi tanemi tayi saima yarungumeta jikinshi tare da zame mata doguwar rigar nan hannunshi yafara yawo acikin jikinta. Yadda gabanta yake fad'uwa Faruk yana ji dan har lokacin tana manne a jikinshi, cike da tsoro tace dan Allah Yaya Faruk kadaina. Cikin kunnenta yarad'a mata Habibti yau fa ranar farin ciki ce agaremu dan Allah kibarni inyi. Runtse idanunta tayi jin ya kirata da sunan da Umar yake kiranta da shi, jin ta yi shuru yasa yakwantar da ita ahankali nan yazuba mata idanu yana k'are mata kallo, ahankali tabud'e idanunta takalleshi ganin yadda yatsareta da mayun idanunshi sai a lokacin yakashe masu fitila. Jawahir koda take ba sabuwar shiga ba ammah ta gurzu a hannun Faruk dan har kuka saida tayi saboda wahalar da tasha, Faruk ko za'a iya cewa fita yayi hayyacinshi, saida yasamu nutsuwa sannan yabarta. 'Daukarta yayi sukayi wanka tare sannan suka dawo suka kwanta yana manne da ita a jikinshi. Washe gari bayan sunyi sallar asuba komawa sukayi bacci ba sune suka tashi ba sai wajen k'arfe tara da rabi, Faruk nema yayi suyi wanka tare da Jawahir tak'i dan kasa had'a idanu tayi da shi saboda kunya daga k'arshe yad'auketa yashiga da ita toilet tana ta nuk'u nuk'u da jiki yashareta yawanketa tas sannan shima yayi wanka. Bayan sun fito ne suka shirya sannan yajata suka nufi babban parlor. Suna zuwa suka samu Nasiba zaune ta sha gayu tana jira sufito. Tana ganinsu murmushi tasaki tare da tashi cikin sauri tanufi inda suke tana zuwa tarik'e Jawahir da kanta yake sadde k'asa tace amarya sannunku da fitowa. Maimakon ta amsa saima duk'awa da tayi tagaisheta amsawa tayi tare da rik'o hannunta tamik'e tace ina fata dai kina lafiya. 'Daga Kai tayi cike da jin kunya. Kallon Faruk tayi da yake ta faman murmushi nan itama tayi murmushi sannan tagaisheshi, jawota yayi yarungume ahankali cikin kunnenta yarad'a mata kin mance irin gaisuwar da kikeyi min?. Murmushi tayi itama ahankali tace yanzu ai bamu kad'ai bane Lovely dole mucanza,,, tana fad'in haka tazare jikinta tare da rik'o hannun Jawahir gudan hannun tarik'o nashi tace muje kuyi breakfast kar mubar amarya da yunwa. Dining suka wuce tayi serving d'in kowa nan suka fara ci Jawahir ba wani ci take sosai ba Faruk yana lura da ita ji yake kamar yayi mata d'ure dan de kawai Nasiba da ke wajen. Nasiba tana gama ci tatashi takoma d'akinta dan tabasu waje Faruk ko kamar jira yake nan yafara feeding d'in Jawahir saida yatabbatar ta k'oshi sannan yabarta. Waya aka kirashi dan haka tatashi takoma part d'inta tagyara abunta sannan tazauna takira su Baba Malam a waya suka gaisa. Tana cikin wayar Faruk yashigo daga gefenta yazauna har saida tagama sannan ya amshi wayar ya ajiye yace habibty shine kika gudo kika barni ko? Murmushi tayi tace ba gudowa nayi ba. Rungumeta yayi sannan yace toh me kikayi?. Shuru tayi nan yasafke ajiyar zuciya sannan yace dan Allah Habibty ataimaka a ajiye kunyar nan dan ina buk'atar kulawarki sosai. 'Dagowa tayi takalleshi har ta bud'e baki zatayi magana sai kuma tafasa ganin haka yasa yakwantar da ita sannan shima yakwanta gefenta yadinga janta da hira tana d'an biye mashi. Wajen azuhur sukayi wanka sannan yatafi masallaci ita kuma tayi sallarta a gida bayan ya dawo Nasiba tazo takirata sukayi lunch. Da marece yafita dan haka suka samu damar zama ita da Nasiba suka sha hira sosai dayake Nasiba akwaita da son mutane nan da nan tasa Jawahir tasake da dare tare suka shiga kitchen sukayi girki duk yadda taso Jawahir tabarshi ammah tak'i saida takama mata sukayi. Tun daga ranar tare suke girki breakfast ne kawai bata samun damar fitowa suhad'a tare saboda Faruk baya bari ahaka har suka cinye kwana ukkunsu a ranar da zai koma wajen Nasiba nan tace ta k'ara masu sucike sati guda dan a lokacin bata jin dad'in jikinta kawai dai bata nuna masu ba dan kar sutada hankalinsu, koda Faruk ya ji dad'in hakan ammah bai nuna mataba, a fili yanuna bai yarda ba saida tadinga lalla'bashi sannan ya amince yakoma suka ida sati gudansu yakoma hannun uwargidanshi inda yanuna ya yi missing d'inta sosai, ta ji dad'in ganin yadda yanuna mata ya yi missing d'inta. ***** Zaman lafiya sukeyi sosai idan kaga Nasiba da Jawahir baka ta'ba cewa kishiyoyine dan suna k'aunar junansu suna mutunta juna, Faruk ko ya zage wajen kula da matanshi ko da sau d'aya baya yarda a fuska yanuna ga wadda yafi so saidai idan ya ke'be da matanshi ne yake nuna masu yadda yake k'aunarsu nan kowace hankalinta yakwanta ganin ta ciri tuta a wajen mijinta *BAYAN WATA 'DAYA* Kasancewar lokacin Hajji ne daman tuni ya biya masu batare da saninsu ba nan yad'auki matanshi sukaje aikin hajji. Tunda sukaje Nasiba batada cikakkar lafiya ahaka tayi hajjinta saidai jawahir take kula da ita da mijinsu. Sai da suka gama hajji sunje umrah sannan taga likita a chan ne yake sanar da su tana da shigar ciki na wata biyu nan su Faruk da Jawahir sukaita murna. Bayan sun dawo ne suka cigaba da kula da ita dan Jawahir bata bari ko cokali tad'auke inda a 'bangaren goga Faruk ma haka duk motsin da zatayi sai sun tambayeta abinda yake damunta hatta abinci sai ta fad'i irin wanda za'a dafa. Tana jin dad'in irin kulawar da suke bata da cikinta. Watansu d'aya da dawowa suka shirya suka je kebbi lokacin cikin Nasiba yana wata ukku kwanansu biyu suka dawo gida. Jawahir kanta ta samu nutsuwa sosai dan har k'iba ta yi koda su Baba Malam suka ga yadda take cikin kwanciyar hankali sai hankalinsu yakwanta, sunje gidan Khausar dan ita Rashida ta dawo gida saboda laulayin da takeyi. Ranar wata litinin Jawahir tashigo parlor tasamu Nasiba zaune tana cin yalo gefenta Faruk ne zaune, zuwa tayi tazauna tana cewa Auntyna me kuma ake ci? Murmushi Nasiba tayi tace kinganni nan wallahi yalo naji inaso shine oga yasiyo min. 'Daukar guda tayi tace bari inci wannan dan gaskiya ya biya raina. Dariya Nasiba tayi tatura mata robar yalon tace kici iya cinki sister ni har ya fara isata tun d'azu nake ci. Murmushi Jawahir tayi nan tace nagode Auntyna sannan tafara ci, kallon Faruk tayi tace Lovely (dayake itama sunan da take kiranshi da shi kenan) maimakon kasiyo har da d'ata ? Murmushi shima yayi yace toh ai bakice asiyo makiba habibty Auntyn taki yalo kawai tace asiyo. Ajiye yalon tayi tace ni d'ata nakeso Allah ban iya cin yalon. Faruk kallon Nasiba yayi itama takalleshi sukai murmushi sannan tace 'yar k'anwata ko dai kin kamu ne kema? Turo baki tayi tace ban kamu da komai ba Aunty kawai dai d'ata nakeso. Murmushi Faruk yayi yace toh shikenan bari insa asamo maki ai duk zan iya da ku nan yad'akko wayarshi yakira megadi yafad'a mashi. Mik'ewa tayi taje kitchen tad'aura masu girki daurewa kawai take dan kwana biyun nan itama ba isassar lafiya gareta ba...... _Sis Nerja'art✍🏻_ [7/24, 11:22 PM] Sis Nerja'art 2: *......FANSAR RAI......* *INTELLIGENT WRITER'S ASSO....®* [On Ward Together] _Follow me on Wattpad: *Sis-nerja*_ _Wannan Littafin na kud'i ne domin karantawa cikin aminci da yarda ga duk me buk'ata zai turo katin Mtn na d'ari biyu N200 kacal ta wannan number d'in 09035938246, ko ta account number 5330055604, Idan katura ka aiko da screen shot na transaction a wannan number d'in 09035938246_ _Akwai gara'basar *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shahararriyar marubuciyar nan *AMEENA ABBA UMAR* tare da novel d'in *FANSAR RAI* akan farashin N300 kacal, ko da kud'in ka sai da rabonka_ *PAGE 27* Cikin Nasiba yana da wata hud'u lokacin aka fiddo da su Alhaji Sufyan daga gidan yari za'a ratayesu dan a lokacin shekararsu guda cif a gidan kaso, duk sunyi bak'i sun rame, a mota aka kaisu gidajensu dan suyi bankwana da iyalansu, Mummyn Nasiba a waya takirata dan taje ammah tace babu inda zata batason sake sakashi a cikin idanunta, nan tazauna tadinga kuka, Jawahir ganin yadda Nasiba take kuka yasa duk sai jikinta yayi sanyi duk'awa tayi gabanta tana hawaye tace dan Allah Aunty Nasiba kiyi hak'uri nasan ni najamaki da badan haka ba da duk haka bata faruba dan Allah kiyafe min. 'Dago kai Nasiba tayi takalleta cikin kuka tace wallahi ba laifinki bane Jawahir bakida laifin komai a ciki *SON ZUCIYA* ne da kwad'ayi suka ja ma Daddy ina nadamar kasancewarshi mahaifi agareni yanzu gashinan abinda yaja ma kanshi, ba wai ina kuka akan abinda za'ayi mashi bane kawai dai ina kuka akan mutuncinmu da yazubar mana yanzu shikenan kowa zai dinga kallonmu da abinda mahaifinmu ya aikata na tabbata yau dai ta kasance *RANAR NADAMA* agareshi ranar da bai ta'ba tunanin zata zo mashi ba saidai nadamar bazata ta'ba kasancewa mai amfani agareshi ba. Jawahir ma fashewa tayi da kuka nan aka rasa me rarrashin wani saida sukayi me isarsu sannan sukayi shuru dan lokacin Faruk baya gida. Su Alhaji Sufyan da Alhaji Mansur bayan ankaisu sunyi bankwana da iyalansu nan aka wuce da su wajen da za'a ratayesu su dukansu kuka suke sha'be sha'be kamar k'ananun yara, d'aura su akayi saman wani dogon gini aka rufe masu fuska sannan aka sa igiya aka rataye masu kai sasu akayi sukayi kalmar shahada sannan aka saki igiyar sukayo k'aya, ji kake k'yat alamun karyewar wuya nan sukaita wuntsila wuntsila da k'afafu har saida ransu yarabu da jikinsu. ________ Jawahir tunda tatashi yau dakyar tayi sallar asuba nan saman darduma tayi kwance dan ranar Faruk ba a d'akinta yakeba, wajen k'arfe shidda yashigo yasameta kwance ta k'udundune tana ta kwasar bacci wajen da take yanufo yana cewa Habibiti ba dai har yanzu bacci kike ba, ta'bata yayi yaji jikinta da zafi. Rud'ewa yayi yace subhanallahi ba dai bakida lafiya ba. Maganarshi ce tatasheta daga baccin da take nan tabud'e idanu dak'yar k'amshin turarenshi ne yadoki hancinta tayi saurin tureshi tamik'e tashiga toilet tafara kwarara amai. Hankalin Faruk ya tashi sosai ganin yadda take amai kamar zata amaye 'yan hanjin cikinta gabad'aya ta galabaita tana gama aman taimaka mata yayi tai wanka tashirya sannan yafito da ita yace ma Nasiba zasuje asibiti Jawahir bata da lafiya hankalin Nasiba ya tashi sosai tace saidai suje tare. Haka ko akayi atare sukaje wajen family doctor d'insu da yace susameshi a asibiti nan yadubata yaimata tambayoyi tabashi amsa sannan yarubuta mata tests yace taje ayi mata a lab. Bayan sunyo sun kawo sakamako nan yake tabbatar masu da tana d'auke da ciki tsawon wata ukku, murna wajen Faruk da Nasiba ba'a magana dan ita ko uwar gayyar kunya ce takamata. Haka suka dawo gida suna ta murna Faruk ko baki har kunne yana ta godiya ga ubangiji ganin matanshi dukansu ciki garesu Nasiba nata wata hud'u Jawahir kuma wata ukku. Zuwa yayi yasanar da su Mom su ma sukaita murna nan tasamo masu wata mata tazo gidan tazauna tana masu girki da gyaran gida. 'Dakunansu da na mijinsune kawai basu bari agyara masu su suke abunsu. Faruk ko indai yana gida toh yana manne da matanshi yana basu kulawa sosai duk abinda sukeso sai ya samo masu shi, kusan tare suke rainon cikin da shi. Dan ma Jawahir nata ba mai laulayi bane sosai saisa take samun damar yin wasu ayyukan indai bai gida tare da ita ake girkin abinci. Faruk d'aukarsu yayi yakaisu gidan Ummah suka ganta nan Ummah tayi ta kuka da taga jawahir tana rok'onta gafara Jawahir ta tausaya ma halin da taga ummah dan har lokacin 'barin jikinta d'aya shanye yake komai sai anyi mata har kuka jawahir tayi saboda tausayi tace ta yafe mata tad'auko kud'i masu yawa tabata. *BAYAN WATA SHIDDA* Cikinsu ya tsufa sosai dan a lokacin Nasiba nata yana cikin wata na goma ana sa ran haihuwa yau ko gobe inda Jawahir nata yake wata na tara. Mummyn Nasiba ta so amaido mata Nasiba tahaihu a gida ganin abubuwan zasuyi mashi yawa mata biyu duk tsohon ciki garesu ammah Faruk yace a'a abarsu zai iya saidai Inna Mairo da tazo daga Kebbi tazauna tana kula da su gabad'aya dan cewa tayi da Nasiba da Jawahir dukansu d'aya ne a wajenta. Yau tun da Nasiba tatashi take fama da ciwon mara haka suka fito zasuyi breakfast daurewa kawai takeyi bata bari sun ganeba kasa cin komai tayi chan da taji cikinta ya wani irin juya mata nan tafara cize le'be. Ganin haka yasa duk hankalinsu yatashi Faruk yayi saurin yo inda take yana tambayarta lafiya. Jawahir ma saurin mik'ewa tayi tanufi wajenta cikin tashin hankali tana cewa Aunty me yake damunki ko jikin ne? Girgiza kai tafara yi cike da juriya tace wayyoo cikina. Faruk rasa yadda zaiyi yayi nan yakwala ma Inna Mairo kira cikin sauri tazo ganin halin da Nasiba take ciki yasa tace haihuwa ce yayi maza yakaita asibiti. 'Daukarta yayi chak yafita da ita jawahir da take ta faman kuka zuwa tayi tad'akko jikkar kayan haihuwar da aka tanada lokacin da tafita Faruk har yasakata cikin mota nan ya amshi jakkar yace takoma gida. Cikin kuka tace ita dai saidai suje tare bazata zauna ba. Kallon inna Mairo yayi yace takula da ita bari suje nan yashiga mota yajata dagudu yanufi asibiti da Nsiba da take kwance tana ta salati. Yana isa Hajiyar Nasiba ta isa a daidai lokacin nan aka wuce da ita labour room Nasiba duk ta fita hayyacinta sai zufa takeyi. Nan su Faruk da Hajiyar Nasiba sukayi cirko cirko suna jira. Jawahir ko tunda suka koma cikin gida kasa tsaye da zaune tayi dan hankalinta ya tashi sosai akan halin da taga Nasiba a ciki, inna mairo lalla'bata tadinga yi dan takwantar da hankalinta saboda tsohon cikinta ammah tak'i kiran Faruk tadinga yi a waya tana tambayarshi halin da Nasiba take ciki ko ta haihu saidai yace a'a sudai cigaba da mata addu'a. Sai wajen k'arfe d'aya sannan Nasiba tahaifo shantalelen d'anta jajir da shi sak Faruk nan su Faruk da Mummyn Nasiba suka dinga murya har da su Yaya Sadiya da su ma sunzo asibitin. Faruk kiran jawahir yayi a waya yafad'a mata nan tadinga murna sannan yakira su Mom yasanar da su. Wajen k'arfe biyu aka sallamesu bayan antabbatar da lafiyar me jego da ta baby. Mummyn Nasiba ta so tawuce da ita gida ammah Faruk yace a'a dan haka tayarda suka koma gidanshi. Suna isa Jawahir ce tafara zuwa dagudu ta amshi yaron tarungume tana murna sannan tayi ma Auntynta ta barka. Nasiba d'akinta tawuce takwanta kafin ruwan zafin da su Inna Mairo suka d'aura yadafu. Duk wanda yazo saidai yakalli baby a hannun Jawahir dan kamashi tayi tarik'e yaron ya shiga ranta sosai, su Inna Mairo saidai suka dinga mata tsiya suna cewa itama ai sai takawo masu kamarshi tunda haihuwartata yau ko gobe ne. Su Mom duk sunzo barka a ranar gidan cika yayi da jama'a. Wajen k'arfe biyar Jawahir tazame kanta takoma d'akinta dan daman tun da aka tafi da Nasiba asibiti tafara jin ciwon mara kawai dai tana daurewane ammah a lokacin taji abun ya k'aru a k'asan kafe tazauna nan tafara murk'ususu tayi kusan minti talatin a nan Inna Mairo tashigo tasameta a wannan halin duk ta jik'e sharkaf da zufa, hankalin inna mairo ya tashi sosai tatambayeta abinda yake damunta ammah jawahir takasa cemata komai saidai gefen mararta da take nuna mata nan Inna Mairo tagane nak'uda ce takeyi cikin sauri tafita taje part d'un Faruk tasanar dashi. Nan yafito a rud'e yazo yad'auketa da inna mairo sukaje asibiti duk wannan abun su Nasiba basu saniba suna chan part d'inta da jama'a 'yan zuwa barka. Suna isa asibiti aka kar'beta aka shiga da ita labour room ana gama sallar magrib tahaifo shantalelen d'anta, nurses suka fito suka sanar da su Faruk nan yad'aga hannu yaita godiya ga ubangiji akan kyautar da yayi mashi ta 'ya'ya biyu a rana guda, kawo mashi d'an akayi shima kyakkyawa da shi yana kamashi da shi waya yad'akko yakira Nasiba yafad'a mata. Da fari bata yarda ba saida yarantse mata nan ita da 'yan barka akaita mamakin haihuwar jawahir, su mom yakira basu d'au lokaci ba suka iso asibitin. Faruk jin abun yake kamar a mafarki wai shine da yara biyu a rana guda. Sai bayan sallar isha'i aka sallamesu suka koma gida nan ma aka kafa wata sabuwar murnar. 'Yan barka santin yaran suka dinga yi ganin kamanninsu guda da yanayin jikinsu duk na mahaifinsu ne idan ba amfad'a makaba sai kace 'yan biyu ne mutum d'aya yahaifesu. Dad da Mom ma sunyi farin ciki sosai ganin rana guda sun samu jikoki har biyu. Faruk ko da ka kalleshi kasan yana cikin farin ciki kasa zaune da tsaye yayi, Inna Mairo ce tagyara maijego sannan tasata taci tuwon da aka girka masu. Gida kullum cike yake da mutane 'yan barka kowa yana farin cikin k'aruwar da aka samu, Dad kud'i yafitar sosai yaba Mom taje dubai tasiyo ma yara kaya duk iri d'aya sannan aka siya ma masu jego kaya kowa akwati biyu. Ranar suna Faruk ya yi bajinta dan kud'i yafitar sosai akayi hidimar suna da su, inna mairo ita takeyi ma jarirrai da masu jego wanka, shiga iri d'aya Jawahr da Nasiba sukeyi a zaman barka hatta jarirran ma haka. Ranar daren suna Faruk yakira matan nashi a part d'inshi yatambayesu sunan da suke so asa ma yaran, Nasiba ce tayi saurin cewa tana so asa ma nata sunan mahaifin Jawahir. Jawahir saboda mamaki kasa cemata komai tayi saidai hawaye da suke fita daga idanunta daga k'arshe tasafko k'asa tadurk'usa tare da rik'o hannun Nasiba tana mata godiya. Nasiba tace bakomai ta cancanci fiye da hakan a wajenta. Shi kanshi Faruk ya ji dad'in hakan da Nasiba tayi nan yatambayi Jawahir sunan da ita takeso asa ma nata. Itama tace sunan mahaifin Nasiba, nan Nasiba tace bata yarda da hakan ba bataso asa sunan mahaifinta dan bai cancanci hakan daga jawahir ba nan tanemi alfarma da jawahir tabarta taza'ba mashi suna Jawahir amincewa tayi Nasiba taza'ba mashi sunan Dad. Faruk ya ji dad'in haka yai masu godiya sannan yad'akko makullan mota yadamk'a masu kowa da tashi suma sukayi godiya. Baba Malam shanu biyu ya aiko masu da su inda Dad yasiyo manyan raguna biyu ya aiko da su. Ranar suna yara suka ci suna Muhammad da Sani inda Muhammad ake kiranshi da Affan, Sani kuma suna kiranshi da Ameer, anyi shagali sosai ankashe kud'i abun sai sambarka dan shiga iri d'aya masu jegon suka dinga yi yaran nasu ma haka mutane dadama sunyi sha'awar yadda kishiyoyin biyu suke tafiyar da rayuwarsu da k'aunar da suke nuna ma junansu. Faruk ko ji yake kamar ya fi kowane namiji sa'ar samun mata. Bayan angama hidimar suna anwatse nan Inna mairo tacigaba da kula da masu jego da yaransu, gyara tadinga yi masu na mutunci yadda zatayi ma Jawahir haka takeyi ma Nasiba bata barinsu suke'be da mijinsu har saida suka yi arba'in sannan tatattara takoma garinsu tare da sha tara na arzik'i da tasamu daga wajen Faruk da matanshi hatta mummyn Nasiba da su Mom saida sukayi mata kyauta me tsoka. Faruk hankalinshi kwance yana kula da matanshi sosai gefe guda ga yaransu da suke ta girma sun taso da ka gansu ka ga tagwaye dan komai iri d'aya akeyi masu kamanninsu sai k'ara komawa take sak ta mahaifinsu. **** ****** Dad yana kula da companynshi da na jawahir sosai nan sukaita k'ara ha'bbaka kud'ad'e suna shigowa yadda yakamata, tura ma jawahir kud'inta yake ta account d'inta baya cin ko naira d'aya ko da tana cewa yadinga d'ibar kasonshi ammah yace a'a baida kaso a ciki na companynshi ya isheshi dan haka tadinga tura ma su Baba Malam tatura ma Baba Musa kud'ad'e sosai yasa aka gyara masu gidansu. Cikin kud'in tafidda wani kaso da fili tadamk'a ma Nasiba nan Nasiba tayita mata godiya har da kuka. Sannan tasa aka gina masu wani k'aton boutique wanda akayo masu order kaya a chan dubai duk wasu kaya na gani na fad'a anzuba su a tantsamemen boutique d'in da yaci suna *FANAJ BOUTIQUE* wanda aikin Jawahir ne nan su Nasiba da Faruk sukaita jin dad'i. *BAYAN SHEKARA 'DAYA DA WATA BIYU* Nasiba ce zaune a babban parlornsu inda gefenta Ameer da Affan ne suna ta wasa da kayan wasan da aka baje masu, duba lokaci kawai take kasancewar darene, Jawahir ce tashigo parlorn babu ko sallama sanye da hijab da alama daga anguwa suke, zama tayi saman kujera batare da ta ce ma Nasiba komai ba ganin haka yasa Nasiba hankalinta yatashi tace lafiya Sis me yake faru tun d'azu ina nan ina jiranku kudawo daga asibitin ko jikin ne? Hawaye ne suka gangaro ma Jawahir. Mik'ewa Nasiba tayi takomo kusa da ita tana cewa lafiya Jawahir kifad'a min abinda yafaru kinga hankalina ya tashi. Tun kan tayi magana su Ameer suka nufo wajen dagudu suka fad'a jikin Jawahir cikin maganarsu da bata fita sosai suka ce Ammi kin siyo mana chocolate d'in? Nasiba ce tarik'osu ganin suna neman haye Jawahir tace kunga Ammi batada lafiya kubarta. Affan ne yaturo baki yace uhm uhm Ummi. Murmushi Nasiba tayi tace ni bari inbaku chocolate d'in, nan tajasu taje tad'akko masu a part d'inta sannan suka zauna suna sha suna wasa. Kusa da Jawahir takoma tana cewa kiyi min bayanin abinda yafaru Sister. Shigowar Faruk ne yasa duk suka juya suka kalleshi Nasiba tace yauwa gaka wai me yake faruwa ne dan Allah me likita yace yana damunta. Murmushi Faruk yayi tare da mik'a mata takardar hannunshi yace k'aruwa muka samu. Saurin amsa tayi tana dubawa tayi saurin rungume jawahir tana cewa Alhamdulilah Sis ashe mun samu baby har na tsawon wata biyu wayyo dad'i. Fashewa da kuka Jawahir tayi cikin kuka tace wallahi ba'a kyauta min ba duka yaushe na haifi Affan ko yayeshi banyi ba sai ace ina da wani cikin. Nasiba kallon Faruk tayi sukai murmushi sannan tace toh menene Sister ai ba wani abu bane. Wallahi wani abune Aunty Nasiba duka nawa nake da za'a ce ina da ciki na biyu kuma kema ai da sai yayi maki inda ta tsakani ga Allah yabi. Faruk da Nasiba dariya ce take cinsu, yadanne tashi yace toh ai itama yi mata zanyi kikwantar da hankalinki. Mik'ewa tayi tana turo baki tace ai da yi mata zakayi kamar yadda muka haihu tare wannan karon ma sai kayi mata,,, tana fad'in haka tawuce fuuu tanufi part d'inta. Nasiba da Faruk ko me zasuyi inba dariya ba Nasiba tace ina ruwan Jawahir da wauta. Tsagaitawa yayi da dariyar da yake yace toh kin dai ji abinda tace kema inyi maki kusake haihuwa tare. Zaro idanu Nasiba tayi waje tace karufa man asiri Lovely idan nima nayi cikin wa zai kular mana da su Affan? Juyawa tayi takallesu taga har sunyi bacci a saman carpet d'in tace kaga tashi muje katayani d'aukarsu inkaisu d'aki inyaso sai kaje chan kayi ta lallashi dan ka yi laifi. Mik'ewa yayi yace kedai bari hearty akwai aiki agabana. Dariya tayi tad'auki Affan shi kuma yad'auki Ameer suka nufi part d'inta, saida tawanke masu hannu sannan takwantar da su a saman gado dan dama tuni ta yi masu shirin bacci tazauna jiran dawowarsu Faruk, itama tahau takwanta, daga gefenta Faruk yazauna yace hearty ba dai bacci zakiyi tun yanzu ba duka fa yanzu tara tayi. Hamma tayi tace wallahi Lovely yau d'in ne jina nake duk wata iri kamar banda lafiya. Kwantar da kanshi yayi a saman k'irjinta yace Hearty ko dai kema kin kamu? Zaro idanu tayi waje tace karufa min asiri ni banda komai. Murmushi yayi yace toh inma akwai ya kuka iya tunda kuna tare da lafiyayyen miji ni ai abun farin ciki ne agareni kuyi ta haifa min 'yan tagwaye. Turo baki tayi tace nidai a'a. Bakinshi yasa yaciji le'benta ahankali yace kedai Eh Hearty, Kallon agogo tayi tace dan Allah katashi kaje kaji da 'yar uwata ka barota ita kad'ai. Tallabo fuskarta yayi yace wai da ingama ji da ke kafin inje,,yafad'a yana kashe mata ido guda. Tureshi tayi daga jikinta tatashi zaune tace dan Allah lovely katafi ka ga ka barta ita kad'ai gashi batada lafiya. Shafa cikinta yayi yace kema d'in ai bakida lafiya. Uhm uhm ni lafiya ta lau,, tafad'a tana ture mashi hannu. Tallabo fuskarta yayi yamanna mata kiss a baki, nan takoma takwanta, shafa kanta yayi yace zan tafi Hearty sai dasafe. Murmushi tayi tace Allah yakaimu masoyina abun alfaharin mu,, tana fad'in haka tayi saurin juya mashi baya dan tasan idan ba haka tayiba bazai barta ba, tana jinshi yabata peck a kumatu tare da cewa ina sonki sosai matata kikular min da kanki. Murmushi kawai tayi batare da ta ce komai ba nan yakalli yaran nashi da suke ta bacci sannan yakashe masu fitala yafita yabar d'akin. Part d'inshi yawuce yafara yin wanka saida yashirya cikin shirin bacci sannan yafito yanufi part d'in Jawahir yana zuwa yasameta kwance saman gado ta lumshe idanunta ammah daga ganin yanayinta ba bacci take ba, zama yayi a gefen gadon yakai hannu yashafa fuskarta sannan yace taya masoyiya zatayi fushi da masoyinta dan kawai Allah ya basu kyautar da ba wanda zai iya basu ita idan ba shi ba, Ahankali tabud'e idanunta takalleshi sai kuma tajanye fuskarta gefe. Ajiyar zuciya yasafke yace Habibty kinsan dai banason ganinki a wannan yanayin dan Allah kifad'a min menene laifina a ciki. Turo baki tayi cikin shagwa'ba tace toh ba kaine kayi min ciki ni kad'ai ba bayan wanchan karon tare da Aunty Nasiba muka haihu. Dariya ce take cinshi ammah yadanne dan kar yayi wani laifin sannan yace toh ai kece kin fita zalama saisa kika rigata samun ciki. Kallon rashin fahimtar inda maganarshi tadosa tayi mashi tace me kake nufi da hakan? Wane irin zalama nafita?. Ganin bata ganeba yasa yace babu komai itama ai tana da nata cikin ba wai ke kad'ai nayi mawa ba. Saurin tashi zaune tayi cike da jin dad'i tace dan Allah dagaske kake lovely. 'Daga mata gira yayi nan tafad'a jikinshi tare da rungumeshi tace na ji dad'i sosai Lovely. Shima rungumeta yayi yace dan Allah Habibty kuyi hak'uri da yanayina ina son 'ya'ya sosai in son samune kuyi ta haifa min su dayawa. Ajiyar zuciya tasafke tace kayi hak'uri lovely nasan ban kyauta maka ba da fushin da nayi akan kyautar da ubangiji yabamu dan Allah kayafe min 'Dago kanta yayi yakalli cikin idanunta sannan yace babu komai Habibty ai ku d'in baku laifi ina k'aunarku fiye da tunaninku nidai fatana kucigaba da nuna min k'auna da tarairaya. Zaka samu fiye da hakan ma Lovely, ina sonka so na gaskiya wanda ni kaina bazan iya misulta shi ba bana ji zan iya son wani kamar yadda nake sonka. Tun kan tarufe baki yace kina nufin har Umar? Murmushi tayi tare da komawa takwanta tace tabbas nasan na so Yaya Umar saidai son da nakeyi maka ya lunka wanda nayi mashi saboda kai da gabad'aya rayuwata nake k'aunarka shi kuma da zuciyata, na mallaka maka gabad'aya soyayyata. Wani irin farin cikine yalullu'be Faruk yai saurin rungumeta yace nagode sosai Jawahir da irin wannan matsayin da nasamu awajenki, nagode ma Allah da yamallaka min ke amatsayin mata na soki tun lokacin da banyi tunanin zan sameki ba ashe ke d'in rabona ce. Lumshe idanunta tayi tare da tura hannuwanta cikin sumar kanshi tana shafawa tana jin sonshi yana k'ara mamaye mata duk ga'b'ban jiki. Lamo yayi a jikinta sai kuma chan yad'ago yakalleta itama bud'e idanunta tayi suka sakar ma juna lallausan murmushi tace ya dai Lovely? Mik'a yayi sannan yace ya kamata aji da ni yanzun nan gaskiya. Hararshi tayi cikin wasa sannan tace bayan cikin da kayi min sai kuma kace wani inji da kai. Toh ya kika iya tunda kina auren lafiyayyen miji ko ana nufin baza'a baniba. Saurin jawoshi tayi yafad'o jikinta tace ni wacece da zan hana mijina shi da kayanshi akoda yaushe ashirye nake domin kar'barka. Murmushi Faruk yayi yakai hannu yakashe masu fitila tare da jawo bargo yalullu'besu. _Ina ganin haka nayi saurin tattaro takarduna da alk'alamina nafito daga d'akin tare da jawo masu k'ofa nace asuba tagari Mr nd Mrs *FANAJ*_ *BISSALAM* _Alhamdulillah anan muka kawo k'arshen wannan littafin me suna *FANSAR RAI* kurakuren da suke ciki Allah yayafe mana_ _*Nagode sosai da irin k'aunar da kuka nunamin da lokacinku da kuka bani Allah ubangiji yabar zumunci Allah yak'ara dank'on zumunci*_ _Ina maku albishir da sabon novel d'ina me suna *KUWWA DA KUWWA* (bata korar buzu)_ _Labari ne wanda yak'unshi abubuwa da dama wanda sai mutum ya karanta sannan zai fahimci hakan ga kad'an daga cikin labarin_ ~~~~~~ _*KUWWA DA KUWWA.....*_ _(Bata korar buzu)_ Kwance take saman makeken gadonta tana bacci inda dogon gashinta yabaje mata a fuska, yanayin yadda take baccin kawai zaka kalla kagane cewa a nutse takeyin shi, lokaci guda tatashi zaune zumbur tare da saurin sa hannunta takare fuskarta, wani irin farin haskene yadaki tafin hannunta ji kake wata irin k'ara k'attt. Janye hannunta tayi tare da sa gudan hannun tagyara gashinta da yake baje a fuskarta nan kyakkyawar fuskarta tabayyana, ajiyar zuciya tasafke tare da mik'ewa tsaye tanufi wajen makeken mirror da yake manne a bangon d'akin tatsaya tana duba fuskarta, komawa tayi tazauna tare da dafe kanta da hannu biyu cikin siririyar muryarta me dad'in saurare tace *Najma* meyasa kike kai ma fuskata hari meyasa kikeso ki'bata min fuska? sauri janye hannunta tayi takalli zobenta da yake manne a dogon yatsan hannunta na tsaka sai kuma tamik'e tanufo k'ofa tun kan ta iso k'ofar dakanta ta bud'e, tana fita parlor nan wasu mata kusan su goma da suke sanye da kaya iri d'aya suka zube k'asa suna kwasar gaisuwa, batare da ta amsa masuba taje bisa lumtsumemiyar kujerarta tazauna sannan da hannu tayi masu nuni da subar wajen. Cikin sauri duk suka tashi suka fita tare da jawo mata k'ofa. Duk wannan abun da yake faruwa tana gani a cikin wani d'an k'aramin madubi dake hannunta, wurgi tayi da madubin ganin batayi nasara ba tamik'e cikin fushi tana cewa ko da ba yau ba *Najla* sai na cika burina, sai na 'bata maki wannan kyakkyawar fuskar da kike tak'ama da ita bazan ta'ba barinki ba.... ** ** ** ** Tunda suka shigo cikin garin kallon mutane kawai suke abun yana burgesu ganin yadda suke ta rayuwarsu, itako shugabar tasu yatsina fuska kawai take dan abun sam bai burgeta ba, suna tafiya a wajen titi wata mata tagifta ta gabansu nan d'aya daga cikinsu tafara lasar baki saurin shak'o wuyanta gimbiya najma tayi tace kar kikuskura kilashi wani a cikin garin nan domin garin nan yana da had'ari sosai duk mayen da suka kama basu barinshi a raye,,, tana fad'in haka tatureta gefe nan tayi saurin duk'awa cike da girmamawa tace kigafarceni ya shugabata. Batare da ta amsa mataba tawuce gaba suna biye da ita a baya suna cikin tafiya a wajen kasuwa tana kallon wani shago da yad'auke mata hankali saboda cikowar mutanen da suke cikinsh nan wani tsoho yatafo da 'yar sandarshi yana dogarawa bai kulaba yad'an bugeta. A fusace tajuyo takalleshi tare da shak'oshi cikin fushi tace kai wane irin dabba ne da zaka bugeni, bakasan wacece ni ba?. Jikin tsohon yana karkarwa yace kiyi hak'uri bana gani sosai ne. Batare da ta sakeshi ba tace bana yafiya a duk lokacin da akayi man laifi sai na d'auki fansa dan haka bazan ta'ba barinka ba, dogon harshenta tafara fiddowa daga cikin bakinta tana shirin lashe fuskar tsohon, daga bayanta taji andaka mata tsawa saurin maida harshen tayi tasaki tsohon tajuyo dan ganin wanda yayi tsawar Wasu mutane ne tagani tsaye a bayan wani kyakkyawan saurayi yana sanye da kaya na sarauta duk sun fito daga cikin motocinsu, saurayin ne cikin 'bacin rai yace ke wace irin macece bakida hankali zaki shak'e tsoho ko iyayenki basuyi maki tarbiya ba?. Tsayawa tayi tana kallonshi cike da mamaki jin kalaman da yake fad'a mata wanda tunda take a rayuwarta ba'a ta'ba fad'a mata irinsu ba sai yau da tashigo k'asar nan yawon bud'e ido. Kallon tsohon saurayin yayi yaga yana ta kyarma sannan yakalli nakusa da shi yace aje arakashi gida. 'Dan russunawa yayi yace angama ranka yadad'e nan biyu daga cikin mutanen suka yi saurin nufar inda tsohon yake suka ruk'oshi suka sa cikin mota suka tafi da shi. Kallon kallo suka dinga yi shi da Gimbiya Najma yana mata kallon tsana, inda ita kuma take jifanshi da mugun kallo, sai kuma chan yajuya aka bud'e mashi mota cikin k'asaita yashiga aka rufe nan sauran mutanen nashi kowa yashiga mota suka bad'a ma su Najma k'ura suka tafi. Cikin 'bacin rai tace wanene wannan? Wanene shi da har zai d'aga min murya? Ya zama dole kubishi kugano min inda yake da kuma matsayinshi a garin nan dan bazan ta'ba barinshi ba!!! Mata ukku ne suka 'bace lokaci guda. Nan Najma takalli sauran tana hucci sai kuma tarufe idanunta tana motsa baki ahankali nan ita da sauran matan suka 'bace 'bat. ___kuyanginta ne zaune kusa da ita suna ta mata hidima inda ita kuma take ta murza zoben da yake hannunta, k'wank'wasa k'ofa akayi nan masu tsaron k'ofar sukayi saurin bud'ewa. Wata farar macece tashigo fuskarnan fara fat. 'Dago kai Najla tayi takalleta tace Hasisa ina kika shiga yau tun d'azu ina ta nemanki. Saurin duk'awa tayi tace kigafarceni ya shugabata hak'ik'a na zo maki da wani labari da zai sakaki cikin farin ciki. Idanu Gimbiya Najla tazuba mata hakan yaba Kuyangar damar cigaba da maganarta dan tasan shugabar tasu ba me yawan hayaniya bace... Yau 'yar uwarki tafita da bak'ak'en kuyanginta yawon bud'e ido inda ni kuma nayi amfani da tsafina nabisu batare da na bari ta ganni ba, wata k'asa ce me suna Miraj mukaje inda mutane ne suke rayuwa a k'asar suna rayuwa ta 'yanci sannan suna da arzik'i sosai k'asar tana cikin k'asashe da ake ji da su wajen dukiya sannan sarkinsu ya kasance me adalci saidai abinda zai baki mamaki su d'in suna bin wani addini sannan su mutane ne ba irin muba, kowane maye yana tsoron zuwa k'asar miraj saboda basu yarda da maita ba duk lokacin da suka kama maye basu barinshi suna had'a wuta me zafi suk'oneshi wannan dalilin ne yasa muke tsoron tunkarar k'asar tun shekaru d'ari biyu a chan baya, saidai wasu daga cikinmu sunsha suyi k'ok'arin zuwa k'asar sukama mutanen ciki wasu suna samun nasarar dawowa da ransu wasu kuma ana kamasu akashe. Gimbiya Najla idanu tazuba mata tana saurarenta, cigaba tayi da cewa saidai abun mamaki da ban tsoro a yau d'innan wani mutum me shiga ta alfarma yanayinshi kawai zaki kalla kigane shi d'in jinin sarauta ne ya harzuk'a Gimbiya Najma da kalamanshi da yayi mata wanda taci alwashin d'aukar fansa bazata ta'ba barinshi ba dan a yanzu haka ta tura bak'ak'en kuyanginta dan sugano mata asalin mutumin...... ____*****_____ ....A yanzu nice shugabarku nice shugaba a k'asar Nairan ya zama dole kowane mahaluk'i yayi min mubaya'a fararen mayu da bak'ak'en mayu duk wanda yak'i haka zan kasheshi a yanzun nan,,, tana fad'in haka tazauna saman kujerar mulki... Tsugunne take a gaban gawar tana ta rusa kuka nan wata kuyanga tashigo cikin sauri tamaida k'ofar tarufe cike da girmamawa tace ya shugabata ya kamata kitashi kibar masarautar nan dan a yanzu 'yar uwarki ta aiko azo akawo mata ke, jama'arta suna nan dayawa sun nufo d'akinki. 'Dago fuskarta tayi da tayi jajir saboda tsananin kuka takalli kuyangartata har ta bud'e baki zatayi magana sukaji anfara buga k'ofa dak'arfi, kuyangarce cikin sauri tanufo inda take tataimaka mata tamik'e tsaye.......... +++++++++++ ...Ranka yadad'e ya kamata kaduba maganata baidace ace kamar kai ba a matsayinka na babban sarki ace d'anka yarima yana zaune babu aure bayan duk wata dukiya yana da ita shin idan baiyi aure yanzu ba sai yaushe zaiyi ko sai bayan mutuwarmu kaduba kaga 'yar uwarshi yadda take k'aunarshi tana binshi ammah ko kad'an baya kulata shin hakan da yakeyi ya dace kenan.....bud'e k'ofar da akayi aka shigone yasa taja bakinta tayi shuru saboda yanayin takun tafiyar da tajiyo yasa tagane Yarima ne, sai a lokacin sarki yad'ago kai yakalleta sannan yamaida kallonshi ga yarima d'an da yad'auki son duniya yad'aura mashi..... _____ ..Ya kamata ace Gimbiya ta fito a wannan ranar anyi girkin masarautar nan da ita kar kumance hakan shine al'adar masaraurar nan duk amaryar da aka auro acikinta dole ne bayan sati biyu tafito tashiga kitchen dakanta tagirka abincin da Yarima, sarki da sarauniya zasu ci a ranar nan wannan sak'one aje afad'a ma gimbiya!!! Wata kuyanga ce cikin sauri tamik'e tafita dan ta isar da sak'on uwargijiyarta. Wadda tagama bayanin juyawa tayi takalli Sarauniya mahaifiyar yarima da itama take kallonta nan tasakar mata murmushi mai cike da ma'anoni sannan tawuce gaba inda sauran kuyanginta suka take mata baya. A lokacin da sak'on ya iso agareta tsaye tayi tarasa ta inda zata fara, k'arar k'araurawa tajiyo daga waje nan tafara jiyo muryar jakadiya tana cewa a yau ranar murnar ce agaremu auren yarima da gimbiyarshi ya cika sati biyu a yanzu haka muna jiran fitowar gimbiya zatazo tagirka ma yarima da iyayenshi abinci me dad'i wanda zasuci dan nuna farin cikin wannan ranar. Kallon agogo tayi da daidai lokacin k'arfe sha d'aya daidai tabuga saurin matsawa tayi tad'age labule nan taga yanayin gidan ko akwai rana sosai. Ja tafara yi da baya cike da tashin hankali tana tunanin ta yadda zata iya fita a wannan lokacin dan ta san ba irin wannan lokacin bane lokacin fitarta..... *_KUWWA DA KUWWA....._* (Bata korar buzu) Labarin ya sha banban da wanda kuka saba karantawa. shima ga duk me buk'ata zai sameshi akan farashi naira d'ari biyu (200), saidai bazan fara sakinshi ba har sai na gama typing d'in part 1. Kar kubari abaku labari Kukasance da ni acikin sabon free novel d'ina wanda yake tafe gajeren labari me suna *NADAMAR RAI* _Taku har kullum sis Nerja'art✍🏻_ [7/24, 11:09 PM] Sis Nerja'art 2: *......FANSAR RAI......* *INTELLIGENT WRITER'S ASSO....®* [On Award Together] _Follow me on Wattpad: *Sis-Nerja*_ _Wannan Littafin na kud'i ne domin karantawa cikin aminci da yarda ga duk me buk'ata zai turo katin Mtn na d'ari biyu N200 kacal ta wannan number d'in 09035938246, ko ta account number 5330055604, Idan katura ka aiko da screen shot na transaction a wannan number d'in 09035938246_ _Akwai gara'basar *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shahararriyar marubuciyar nan *AMEENA ABBA UMAR* tare da novel d'in *FANSAR RAI* akan farashin N300 kacal, ko da kud'in ka sai da rabonka_ PART TWO _~GORON SALLAH~_ *PAGE 1* Kwance yake saman makeken gadonshi yad'age kanshi sama yana kallon Ceiling tare da lumshe idanunshi kamar me bacci ammah azahiri tunani yake rayuwar jawahir kawai yake tunani akan irin gwagwarmayar da tasha, tambayar kanshi yafara yi daman ashe tana da aure? Toh ina mijin nata? Meyasa bai ta'ba ganinshi ya je wajenta ba??tambayoyin da suka dinga mashi yawo kenan a k'walwa saidai me a gefe d'aya Allah Allah yake yi gari ya ida wayewa yayi wanka yatafi gidan kaso na mata dan yagana da ita dan ya fi so ya ida samun full details kafin yafara aikinshi,,,, yana cikin wannan tunani bacci 'barawo yasace shi. Wajen k'arfe bakwai kiran da yashigo wayarshi ne yatashe shi dakyar yabud'e idanunshi da sukayi mashi nauyi saboda rashin samun isashen bacci, d'auko wayar yayi yaduba yana ganin me kiranshi sai ma yamaida ta silent sannan yamik'e yashiga wanka. Bayan ya fito ya shirya cikin shirinshi na tafiya aiki jikkar laptop d'inshi da wayoyinshi yad'auko yafito parlor daidai da Momcy ta shigo parlorn d'auke da plask tsayawa tayi tana kallonshi. Murmishi Faruk yasakar mata tare da gaisheta. Amsawa tayi sannan tace Son ka dai san babu inda zakaje sai ka yi breakfast ko? 'Bata fuska yayi yace Momcy bana jin yunwa. Batace mashi komai ba tawuce dining area. Ajiye kayan da suke hannunshi yayi yabi bayanta yana zuwa yaja kujera yazauna, fara serving d'inshi tayi sannan tace d'azu Nasiba ta kirani a waya ta ce tana ta kiran wayarka baka d'auka ba. Yi yayi kamar baiji ba yafara breakfast d'inshi. Kallonshi Momcy tayi tace Faruk magana fa nake maka ka min shuru. 'Dagowa yayi yakalleta yasakar mata murmushi sannan yace momcy time d'in bacci nake kuma ko da natashi ban bi ta kan wayarba saboda naga zanyi late ban tafi aiki ba. Momcy kallonshi kawai tayi tawuce tatafi cikin ranta tana mamakin halin d'an nata. Sama sama yayi breakfast d'in yamik'e yad'auki kayanshi yaficce yabar gidan. Yana cikin mota yana tuk'inshi a nutse nan wayarshi tafara ringing kallon wayar yayi ganin sunan da yabayyana a jikin screen d'in wayar yasa yai saurin yin picking tare da yin sallama,,, yanayin yadda yake maganar kawai zaka gani kagane cewa akan wajen aiki ne suke tattaunawa sun dad'e suna wayar kafin daga bisani suyi sallama. Suna gama wayar d'an guntun tsaki yaja tare da canza hanya yanufi wajen aikinsu. Yana isa yai parking a daidai inda yasaba yin parking yad'auko bakin space d'inshi yadad'e fuskarshi sannan yafito daga cikin motar yazagaya yabud'e mazaunin me zaman banza yad'auko jakkar laptop d'inshi. Tafiya yake cikin takunshi me burgewa duk inda yagifta sai mutane sun mashi barka da safiya saidai kawai yad'aga masu hannu, wad'anda suka yi mashi farin sani ne kawai zasuce daman haka yake dan Barr Faruk ba mutum bane me yawan son hayani. Yana zaune a office d'inshi akayi mashi knocking izini yabada ashigo nan aka turo k'ofa. 'Daga kai yayi yakalli me shigowa sai kuma yamaida kallonshi ga system d'in shi. Sacratery takowa yayi ya iso wajen Barr Faruk daga gaban table d'inshi yatsaya yace Barrister barka da aiki. Batare da ya d'agoba yace yauwa barka. File d'in da yake hannunshi yamik'a mashi yace gashi oga yace akawo maka. Ohk ajiye nan. Ajiyewa yayi saman table d'in yace atashi lafiya sannan yajuya yafita. Barr Faruk d'auko file d'in yayi yabud'e yafara dubawa chan sai yamik'e tare da d'aukar file d'in da key d'in motarshi yafita. Saida yafara biyawa a office d'in ogansu suka tattauna sannan yatafi. Yana barin nan direct gidan yari yawuce yana isa kamar yadda yasaba office d'in abokin nashi yafara safka bayan sun gaisa ne yanuna yanaso yaje yagana da jawahir. Alhaji Nasibi yanuna ba matsala nan yakira wani ma'aikacin gidan kamar yadda yasaba yahad'a shi da Barr Faruk suka je. Suna zuwa suka sameta zaune ta had'e kai da gwiwa, daga bakin k'ofa ma'aikacin yatsaya inda shi kuma Barr Faruk yashiga ciki ko kad'an bata motsa ba daga inda take da alama kamar bata ma san da shigowarshi ba. Barr Faruk matsawa yayi yatsugunna a gabanta tare da kiran sunanta ahankali. Bud'e rinannun idanuwanta tayi tare da d'ago kanta tasafke idanunta a fuskarshi inda fuskarta take a d'aure. Cike da jin tausayinta yake binta da kallo inda itama take kallonshi babu ko k'yaftawa. Ajiyar zuciya yasafke yace jawahir insha Allahu zan taimaka maki zan wanke ki daga zargin da akeyi maki. Lokaci guda tamik'e tsaye tare da sakar mashi murmushi sannan tawuce tafara taku d'aya biyu sai taja tatsaya batare da ta juyo ta kalleshi ba cikin dashewar murya tace zargi kuma? Wanene yafad'a maka zargina akeyi? Duk abinda kaji ance na aikata to dagaske ne. Mik'ewa yayi daga inda yake yatsaya yace idan har abinda kika rubuta a kan labarinki gaskiya ne toh tabbas zanyi k'ok'ari wajen wanke ki. Murmushi tayi a karo na biyu tare da sake jefa mashi tambaya tace labarina kuma? 'Dan matsowa yayi kad'an yace Eh saidai inaso insan k'arshen shi dan samun cikakkar hujja. Shuru tayi kamar bataji abinda yaceba ganin haka yasa Barr Faruk yace shin ina Umar? Lokaci guda tajuyo takalleshi cikin sauri tatako ta iso wajen da yake tsaye tare da cacimo wuyar rigarshi muryarta tana rawa tace wanene yafad'a maka shi? Ina kasan yaya umar d'ina?,, tafad'a tare da fashewa da kuka. K'wacewa yayi daga rik'on da tayi mashi yad'an ja baya kad'an yace ban san umar ba saidai na karanta acikin labarin da kika rubuta. Hannu tamik'a mashi muryarta tana rawa tace ina diary na. Cikin nuna rashin damuwa yace yana wajena zanyi wani aiki ne akanshi ammah jawahir ya kamata kisanar da ni ina umar da su Abba shin suna raye? Sulalewa tayi a lokaci guda tazauna k'asa tare da rushewa da kuka tace nima ban saniba bansan me yasa babu wani wanda yazo gareniba meyasa zasuyi min haka? Takowa yayi yamatso wajen da take yace kenan suna a raye jawahir? Wani irin kallo tayi mashi har ta bud'e baki zatayi magana sai kuma tafasa. Ganin haka yasa yacigaba da cewa jawahir dole sai kin daure kin sanar da ni komai domin ta haka ne zamu samu mafita wad'annan mutanen da suka kashe maki iyaye, sannan ita wannan aljanar ta wace hanya takebi tana d'aukar maki fansa akansu, kuma idan har itace take yin kisan ai inaga bai dace ace ankama ki akan laifin da bake kika aikata ba ammah me yasa tun lokacin da akayi abun baki sanar da hukuma ba? Inaga da ace kin sanar da......wata irin k'ara jawahir tayi tare da toshe kunnuwanta cikin d'aga murya tace ya isa haka barrister! ya isaaa!!! Hawaye ne suka cigaba da fita daga idanunta tace taya kake tunanin hukuma zata taimaka min bayan Ammina ita kanta ta je ma hukuma ammah babu wanda yakulata bare har yataimaka mata, wannan dalilin ne yasa nad'auki fansa dakaina ban damu da abinda zai faru da niba bana buk'atar cigaba da rayuwata ina so akasheni saidai kafin nan nafiso incika burina a rayuwa sai na ida kashe wad'anda suke da hannu a mutuwar iyayena daga nan nima zanyi farin ciki sosai idan na mutu dan daman mutuwar itace nafi buk'ata,,,,, juyawa tayi takalli gefe guda sannan tace rayuwata batada sauran amfani ban ta'ba bak'in ciki ba akan zaman da nayi a nan na tsawon wata goma zanyi farin ciki ace daga nan gidan sai k'abarina zan shiga..... Katseta Barr Faruk yayi yace jawahir wannan wace irin magana ce kikeyi kidaina cewa haka insha Allahu zaki rayu ni zan taimaka maki kifita daga gidan nan saidai ta ina zan fara bi, shin ya za'ayi in iya sanar da kotu cewa aljanah ce take wannan kisan? "Wannan ba gaskiya bane nice nan nayi kisan Barrister kar kasaka kanka acikin lamurra na domin gudun kar kajefa rayuwarka acikin had'ari, duk wanda yanemi yajawo jikinshi agareni yana shiga matsala yakamata kafahimci hakan. Kallonta yake gabad'aya ta hargitse yace ban damu da wannan ba jawahir kawai dai akwai wasu tambayoyi da nakeso inyi maki shin ina lauyan mahaifinki wanene shi? Sannan dagaske kina da hannu acikin mutuwar Alhaji.... Bata bari yak'arasaba takatseshi tace ya isa haka barrister na fad'a maka babu abinda zaka samu daga gareni wannan duk ba gaskiya bane,,,, tana fad'in haka tamik'e taje chan wajen 'yar k'aramar tagar nan da tasaba tsayawa wajenta tatsaya tajuya mashi baya ahankali tace wannan duk shirina ne ya kamata katashi katafi. Idanu Faruk yazuba mata yana kallonta har ya bud'e baki zaiyi magana tatari numfashinshi tace banason jin komai daga gareka dan Allah kabarni haka bansan ya zanyi ba tambayoyinka sun min yawa!. Mik'ewa Barr Faruk yayi yace shikenan jawahir zan tafi ammah inaso kisani zan dawo agareki bamuda isashen lokaci ya kamata kisan haka sai anjima,,,, yana fad'in haka yajuya zai tafi sai jin muryarta yayi ta ce katabbatar ka maido min diary d'ina. 'Dan guntun murmushi yayi yajuya yafita. yana fita yajiyota ta fashe da kuka d'an ja yayi yatsaya sai kuma chan yawuce yatafi. Saida yabiya ta office d'in Alhaji Mahadi sukayi sallama sannan yawuce yatafi yana a mota DPO yakira shi a waya yace suna son ganinshi yanzu, amsa masu yayi da toh gashinan zuwa sannan yakashe wayar. Lokacin da ya isa station d'in direct office d'in DPO yawuce lokacin yana ciki suna ganawa da wani dan haka yajira sugama. Kusan minti shidda sai ga mutumin ya fito juyowar da Barr Faruk zaiyi nan sukayi ido hud'u da Alhaji Mansur wani shu'umin murmushi Alhaji Mansur yasakar mashi tare da cewa Barr Faruk barka da rana. Kallo d'aya Barr Faruk yayi mashi batare da ya tanka shi ba yawuce zai shige sai jiyo muryarshi yayi daga baya yana cewa har yanzu kana da damar da zaka mallaki Nasiba but in kana da buk'atar hakan. Ja yayi yatsaya har ya bud'e baki zaiyi magana sai kuma yafasa yawuce yashige. Dariya Alhaji Mansur yayi yace nasan dai zaka amince da hakan. Yana shiga hannu yamik'a ma DPO suka gaisa nan yanuna mashi kujera yazauna, tambayarshi yayi ya aiki ya amsa da Alhamdulillah. DPO jujjuyawa yayi a kujerar da yake zaune sannan yace Barrister Faruk ba komai yasa na kiraka ba sai akan case d'in jawahir akan kisan Alhaji Sa'idu wanda a yanzu mun k'ara samun k'wak'k'warar hujjar da tanuna mana tana da hannu a cikin kisan shi zamu mik'a case d'in a kotu dan ya kamata kotu tayi gaugawar d'aukar mataki saboda abu sai k'ara cigaba yake. Shuru Faruk yayi yazuba mashi idanu yana kallonshi har yakai aya sannan yace DPO na ji bayaninka saidai inaso kasan cewa wannan zancen duk ba gaskiya bane jawahir bata da hannu acikin mutuwar Alhaji Sa'idu Nepa yakamata kudaina zarginta saboda kun duba CCTV Camera a daidai lokacin da akayi kisan muna a hotel kaga babu hujjar da zatasa ace itace takasheshi. 'Dan guntun murmushi DPO yayi yace Eh munga haka ammah wannan bai isa yazama k'wak'warar shaida ba, inaso kasan wani abu duk mutuwar wad'anda ake zarginta akansu kusan haka yafaru kuma muna tunani tana amfani da layar zana ne tana 'bacewa taje takashesu sannan su kansu lauyoyinta bata barsu ba tana acikin gidan yari takashesu. Na ji wannan saidai ban gamsu da hujjarka ba. Cikin d'aga murya DPO yace Barrister nasan aikina sannan ina k'ok'ari wajen ganin na kawo cikakkun hujjoji da dole za'a yadda cewa itace takashesu kamar yadda tun yanzu na fara samu dan mun samu hoto kamar yadda muka samu an aje a mutuwar sauran mutanen shin wannan ba hujja bane? Murmushi Barr Faruk yayi yace kusan haka saidai inaso kasani nima zanyi bakin k'ok'arina a matsayina na lauyanta. Jinjina kai DPO yayi yace dakyau Barr Faruk. Mik'ewa yayi tare da mik'a mashi hannu sukayi musabaha sannan yace na barka lafiya. Ta'be baki DPO yayi yace ba damuwa a duk lokacin da buk'atar nemanka yataso zakaji kirana. Ohk ba damuwa inspector sai na ji ka. Tunda yakama hanya ba abinda yatsaya mashi a rai sai maganganun da jawahir tafad'a mashi kenan har hukuma sun sanar da su akan kisan da akayi ma mahaifinta ammah ba'a d'au wani mataki ba? Indai hakane to da wannan damar sukayi amfani wajen d'aukar fansar kisan da akayi ma iyayenta saidai taya zan samu cikakkun hujjojin da zan iya kareta da su? taya zan wanketa gaban kotu? A fili yace ya zama dole jawahir kiyi min magana indai har kinason barin gidan kason nan ammah ita fa wannan aljanar...bai rufe bakiba sai gani yayi ta mirrir d'in motarshi kamar wannan tsohuwar ce zaune tana kallonshi da k'walak'walan idanunta saurin jan burki yayi yatsaya tare da waiwayawa baya ammah baiga kowa ba, ajiyar zuciya yasafke tare da jingine kanshi a jikin kujera kusan minti ukku sannan yatada motarshi yanufi gida. Yana isa wanka yayi yashirya sannan yafito parlor yasamu iyayenshi Momcy tazubo mashi lunch yazauna yayi suka d'an ta'ba hira yatashi yakoma d'akinshi wayoyinshi gabad'aya yakashe dan kar atakura mashi yad'auko laptop d'inshi tare da diary d'in jawahir yazauna yana aiki saida yaji k'walwarshi ta d'auki caji tana buk'atar hutu sannan ya ajiye tare da kwantawa saman gadonshi bai dad'e da kwanciya ba bacci yai awon gaba da shi daman abu ga wanda bai samu yaruntsa ba. Ba shine yafarka daga baccin da yake ba sai wajen biyar a gurguje yai wanka sannan yad'auro alwallah. Bayan ya gama duk shirinshi yad'auki laptop d'inshi da key d'in motarshi yafita dan yaje chan gidanshi da yake gani zaifi samun kwanciyar hankali yayi aikinshi yana fita daidai lokacin motar nasiba ta cinno kai cikin gate d'in gidan..... _Sis Nerja'art✍🏻_ [7/24, 11:09 PM] Sis Nerja'art 2: *......FANSAR RAI......* *INTELLIGENT WRITER'S ASSO....®* [On Award Together] _Wannan Littafin na kud'i ne domin karantawa cikin aminci da yarda ga duk me buk'ata zai biya d'ari biyu N200 kacal ta wannan number d'in 09035938246, ko ta account number 5330055604, Idan katura ka aiko da screen shot na transaction ta wannan number d'in 09035938246_ _Akwai gara'basar *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shahararriyar marubuciyar nan *AMEENA ABBA UMAR* tare da novel d'in *FANSAR RAI* akan N300 kacal, ko da kud'in ka sai da rabonka_ PART TWO _~GORON SALLAH~_ *PAGE 2* Kallon motarta yayi yad'auke kai sannan yawuce yanufi parking space wajen motarshi, wani irin parking tayi yana ji lokacin da taja burki dak'arfi, tabud'e motar tafito cikin sauri tanufi wajen da yake tafiya tare da kiran sunan shi. Ja yayi yatsaya batare da ya juyoba har ta iso, gabanshi tatsaya tana kallonshi damuwa k'arara ta bayyana a fuskarta cikin karyayyar zuciya tace haba Faruk yanzu har ni zaka gani na zo ammah kashareni baka ma da lokacina. Faruk sai a lokacin yakalleta yace ba haka bane Nasiba taya kike tunanin zan shareki. Ba ga shinan ba ka yi, bansan menayi maka ba har zaka yanke hukunci irin haka faruk, wane irin laifi nayi maka da har zaka k'i amincewa da aurena, ko sona ne kadaina yi,,,, tafad'a hawaye suna fita daga idanunta. Hankalin faruk ya tashi sosai ammah bai nuna mataba yace ko d'aya Nasiba ba haka bane ke kanki shaida ce ina sonki kuma ba wai na fasa aurenki bane mahaifinki ne kawai yakeso yabada matsala a cikin maganar aurenmu. Katseshi tayi tace koma dai minene faruk bai dace saboda aikinka kak'ini ba, meyasa kake son fifita aikinka akaina? Kana nuna min kamar aikinka ya fini matsayi a wajenka. 'Dan guntun murmushi yayi yace Nasiba kidaina cewa haka ko d'aya ba haka bane huruminki daban na aikina daban banaji zan iya had'a soyayyarki da komai saidai me bazan ta'ba bari sonki yashafi aikina ba bansan dalilin da yasa mahaifinki yakeso yashiga cikin aikina ba idan har baiyi niyar bani aurenki ba kawai sai yafito yafad'a min ba wai sai ya sa min dokar da bata shafi aurenmu ba. Fashewa da matsanancin kuka tayi tace Faruk ban ta'ba tunanin haka daga gareka ba koma menene na d'auka zaka iya sadaukar da shi akan soyayyarmu, me zai hana kahak'ura da koma menene muyi aure. Zuba mata idanu yayi yana kallon yadda take kuka bilhak'i duk sai yaji tausayinta ammah yana tunowa da yadda sukayi da mahaifinta sai yagirgiza kai yace bazan iya haka ba, kamar yadda wani uzuri na aikina bazai hanani aurenki ba toh haka shima aurenki bazai shiga hurumin aikina ba duk son da nake maki zan iya hak'ura har zuwa lokacin da mahaifinki zai amince muyi aure dan haka kar kiga laifina a ciki kiyi hak'uri,,, Yana fad'in haka yawuce yanufi wajen motarshi yabud'e,, cikin kuka Nasiba tafara k'wala mashi kira ammah yashareta yashiga yamaida yarufe yatada motar yabar gidan, ta window yana kallon yadda take kuka tana bin motar da kallo, duk sai yaji babu dad'i wani irin abu ya tsaya mashi a rai, yana fita daga gate d'in gidan taka burki yayi yatsaya tare da kife kanshi a jikin steering yana jin wani irin tausayinta da soyayyarta sun mamaye mashi zuciya, shi kanshi ya san yayi k'ok'ari sosai wajen danne sonta, girgiza kai yayi ahankali yace Nasiba mahaifinki ne yasaka mu cikin wannan halin ammah ni ina sonki. Ya dad'e a wajen sannan yaja motarshi yatafi, tuk'i kawai yake ammah yana jin babu dad'i a ranshi har ya isa gidanshi da yaci buri sutare shi da amaryarshi Nasiba. Nasiba ganin yadda yaficce bai ko tsaya saurarentaba yasa tacigaba da kukanta tare da juyawa cikin sauri tashiga cikin gidan, Momcy da shigowarta parlor kenan sai ganin Nasiba tayi kamar anjefota. Cike da mamaki tamatso wajen tana cewa lafiya Nasiba me yake faruwa? Kasa yi ma Mom bayani tayi sai ma cigaba da kukan da take nan hankalin Mom ya ida tashi taruk'ota sukaje saman kujera suka zauna sannan tace dan Allah Nasiba kidaina kukan haka kiyi min bayani me yake faruwa? Cikin sheshek'ar kuka tace Mom Faruk ne. Ajiyar zuciya Mom tasafke tace me yafaru da Faruk d'in wani abu yayi maki? Cigaba da kukanta tayi dan batasan abinda zatace ma Mom ba. Ganin haka yasa Mom tace shikenan kidaina kukan kibarni da shi zai zo yasameni. Tsagaitawa tayi daga kukan tace baimin komai ba cewa yayi bazai aureniba. Zaro idanu Mom tayi tace shi Faruk d'in da kanshi yace haka? Sadda kanta tayi k'asa tace ba wai hakaba ya ce min aikinshi ya fiye mashi ni. Jinjina kai tayi cikin ranta tace watau kenan k'arya yayi masu da yace yayi magana da Daddyn Nasiba akan kar ayi baikonsu sai ta gama karatunta, to me yake nufi da hakan, koma menene zaya dawo gidan yasameni,,, dafa Nasiba tayi tace kinga kidaina 'bata hawayenki insha Allahu babu abinda zai hana aurenku da Faruk kibarni da shi. Wata irin kunya ce takama Nasiba tace Mom ba wai haka ba kawai dai....sai kuma tayi shuru. Murmushi Mom tayi tace koma menene kar kidamu kinji? 'Daga kai tayi alamun toh sannan tamik'e tace Mom bari intafi gida. A'a Nasiba tun yanzu? Ko ruwa fa baki sha ba. Kanta sadde k'asa tace Allah Mom nagode daman sauri nake Hajiya ta aikeni. Toh shikenan Nasiba kikwantar da hankalinki babu abinda zai hana aurenku da Faruk kibarshi zai dawo gidan yasameni, kigaishe da Hajiyarku kinji. Cikin jin dad'i tace toh Mom zataji sosai. Tunda tashiga mota inba goge hawaye ba babu abinda take maganganun Faruk sun tsaya mata a rai sosai dan bata ta'ba tunanin hakan daga gareshiba musamman yadda yake nuna mata so ta d'auka ba wani case ba hatta aikinshi zai iya hak'ura da shi saboda ita sai gashi taga ba hakaba, ammah meyasa su Daddy sukace dole sai ya janye ya tsame hannunshi daga case d'in sannan zasu amince subashi ita? Miye had'in aurensu da aikinshi?,,, buga steering d'in motar tayi tare da girgiza kai a fili tace sam hakan bai daceba. Wajen k'arfe biyar motocin police ukku suka tsaya a harabar gidan yarin inda police d'in suka fito wasu suka tsaya a nan wasu kuma suka shiga ciki tare da ogansu direct office d'in shugaban gidan suka je inda DPO yashiga ciki su kuma suka ja suka tsaya bakin k'ofa. Bayan sun gaisa da Alhaji Mahadi ne DPO yake ce mashi mun dai dawo akan case d'in yarinyar chan. 'Dan guntun yawu Alhaji Mahadi yagad'e yace toh 'yallabai dafatan dai ba wani abu yasake faruwa ba? No bakomai saidai akan kisan Alhaji Sa'idu Nepa wallahi ka yi sakaci da kayarje aka fita da ita alhali ka san hakan baya daga cikin aikinku abar me laifi lauyanshi yafita da shi koma za'a fita ai kyau a had'a da su da police bare ma wannan yarinyar da take da had'ari. Cikin sanyin jiki yace hakane d'alla'bai nima sai daga baya naga rashin dacewar hakan ammah Barr Faruk mutum ne me amana na sanshi sosai wannan yana daga cikin dalilin da yasa na amince mashi. Shuru DPO yayi na d'an lokaci sai chan yace ai bata a nan duk yadda kad'auki mutum bai zama dole hakaba, inma haka ne taya zasu iya fita su kad'ai ai zata ma iya guduwa kaima kanka ka san iya dad'ewarmu muna bincike akan case d'innan kafin mugane itace take kisan, shikenan dai kakiyaye yanzu bari inje inganta dan akwai wasu tambayoyi da nakeso inyi maka. Alhaji Mahadi yace toh shikenan babu damuwa, nan yad'auko wayarshi yakira wani ma'aikaci yazo yayi ma su DPO jagora har d'akin da aka gark'ame jawahir. Suna isa suka sameta zaune ta jingine kanta da bango tana kallon gefe d'aya har suka shiga bata d'aga kai takallesu ba. DPO ne yamatsa kusa da ita tare da d'an tsugunnawa a gabanta yace sannu ko jawahir. 'Dago kai tayi takalleshi sai kuma tamaida kallonta a gefe d'aya. Jinjina kai yayi sannan yace nasan ko ban fad'a ba kinsan abinda yakawoni inaso ki amsa laifinki na kashe Alhaji Sa'idu Nepa kamar yadda kika kashe sauran. Ahankali tabud'e baki tace banda masaniya akan mutuwarshi. 'Dan guntun murmushi yayi yace ko kina da hujjar da zaki iya kare kanki da ita bayan bincikenmu ya nuna mana kece? Shin abun tambaya ko kina layar zana ko wani siddabaru ne?. Shuru tayi kamar bataji abinda yaceba. Juyawa yayi yakalli wata police mace yace tambayar min ita. Cikin sauri tazo wajen jawahir sai ji tayi anja mata gashi dak'arfi wanda hakan yasa saida tasaki 'yar k'ara, muryar macen taji ta ce bazaki amsa tambayar da akayi maki ba. Runtse idanunta tayi tare da kai hannunta zata rik'e hannun police d'in sai ji tayi ta sa mata wani abu me kamar k'arfe a wuyanta wanda yataimaka wajen d'ago kanta sama, ji tayi abun ya shak'eta sosai muryar police d'in taji ta ce bazaki amsa tambayar da akayi makiba. Dak'yar tabud'e baki muryarta tana rawa tace ni bansan komai akan hakaba. Taya zamu yadda da hakan bayan jiya kun fita tare da Barr Faruk. Tsananin azabar da takeji ne yasa tafara safke numfashi kad'an kad'an dak'yar tace na fad'a maku bani ba....k'ara matse mata wuya da akayi da k'arfen yasa takasa k'arasa fad'in abinda yake bakinta nan idanuwanta sukayo waje. Ganin haja yasa DPO yace ak'yaleta. Ana janye mata k'arfen daga wuyanta nan taduk'e tana tari tare da rik'e wuyanta. Muryar DPO taji yana cewa jawahir idan har kika cigaba da 'boye min gaskiya fiye da wannan zansa ayi maki, inaso kifad'a min gaskiya game da mutuwar Alhaji Sa'idu ko shima bazaki amsa laifinba kamar yadda kika k'i amsa na sauran? 'Dago kai tayi a galabaice takalleshi tana nishi tace bai zama dole in iya amsa abinda banda masaniya a kai. Murmushi yayi yace matsalata da ke taurin kai ammah da sannu zan safke maki shi, zanje incigaba da bincike idan har na ida tabbatar da kece kikayi kisan to nayi maki alk'awalin zaki fuskanci hukunci me tsauri akan k'aryar da kikayi min, yana fad'in haka yamik'e tsaye yace a kowane lokaci zaki iya ganina na dawo gareki a duk lokacin da kika ganni to ki tabbata asirinki ya gama tonuwa kuma zaki fuskanci hukuncin daidai da abinda kika aikata,,, yana fad'in haka yajuya yatafi inda sauran police suka take mashi ba. Jawahir da idanu tabishi hannunta yana rik'e da wuyanta har lokacin numfashinta bai ida komawa daidai ba dan idanuwanta ko gabad'aya suka birkice, kwanciya tayi a wajen tana safke numfashi sama sama kafin daga bisani tafara motsa bakinta ahankali kamar me karanto wani abu chan sai ga wani haske ya bayyana a chan k'arshen bangon d'akin jawahir tashi tayi zaune tana tari sama sama nan tayi yunk'urin mik'ewa tsaye ammah takasa lokaci guda takoma takwanta tare da runtse idanunta ahankali hasken yabayyana a wajen da take yashiga jikinta,,, nan bacci yayi awon gaba da ita. Alhaji Sufyan da Hajiya maijidda daidai lokacin da suka fito daga d'aki zata raka mijinta da zai fita suka jiyo k'ara a d'akin Nasiba cikin sauri su dukansu suka nufi d'akin, suna zuwa suka tura k'ofar suka shiga, su dukansu ja sukayi suka tsaya lokacin da suka ganta tana watse d'akin duk kayan kwalliyar da suke saman mirror ta zubar da su tana kuka, cikin sauri Hajiya Maijidda tanufi wajenta tarik'eta tana cewa lafiya Nasiba me yake faruwa? Fad'awa tayi jikin mahaifiyartata tare da fashewa da sabon kuka tana cewa Mummy meyasa su Daddy zasuyi min haka bayan sun san inason Faruk, miye had'in aurenmu da aikinshi? meyasa zasuce dole sai ya yanje daga wani case sannan zasu bashi ni? Hakan da sukayi sun kyauta mana kenan? Hajiya Maijidda juyawa tayi takalli mijin nata da yake tsaye sannan tamaida kallonta ga d'iyarta da take rungume jikinta tace yanzu Nasiba akan haka ne kike nema kimaida kanki mahaukaciya?. Cikin kuka tace fiye da haka ma zanyi mummy indai akan son Faruk ne, saboda haka ya daina kulani d'azu na je gidansu ya shareni. Alhaji Sufyan takowa yayi yamatso wajen da suke tsaye yace haba Nasiba minene abun damuwa ni fa taimakonki nayi domin naji labarin cewa case d'in da faruk yad'aukar ma kanshi yana da had'ari sosai dan yarinyar kisa tayi ba mutum d'aya ba ta kashe mutane dadama ke hatta lauyoyinta bata bariba, tana abu saikace ba mutum ba duk wanda yanemi yara'beta sai taga bayanshi, shi kanshi Faruk ya san da haka ammah bansan dalilin da yasa yanace sai ya tsaya mataba taya kike gani zan d'auki 'yata inba lauya irin faruk. Cikin kuka tace Daddy,,, sai kuma tayi shuru. Cigaba yayi da cewa ki kwantar da hankalinki indai har Faruk dagaske yake sonki na tabbata zai janye game da wannan case d'in sannan zai zo yanemi aurenki, ina jin tsoro kar wani abu yashafeki game da case d'in nan Nasiba kiyi tunani a kai ni mahaifinki ne me son farin cikinki. Janyewa tayi daga cikin Hajiya maijidda tawuce dagudu tafita tabar d'akin tana cigaba da kukanta. Su duka da idanu suka bita sai chan Hajiya Maijidda tace kar kadamu Alhaji katafi kawai kabarni da ita zan fahimtar da ita yadda zata gane. Ajiyar zuciya yasafke yace to shikenan maijidda dan Allah kiyi k'ok'arin hakan. Toh Alhaji insha Allahu, sai ka dawo. Toh Allah yasa nan yawuce yatafi ita kuma tanufi part d'inta dan tasan chan ne kawai Nasiba zataje. _Sis Nerja'art✍🏻_ [7/24, 11:09 PM] Sis Nerja'art 2: *......FANSAR RAI......* *INTELLIGENT WRITER'S ASSO....®* [On Award Together] _Wannan Littafin na kud'i ne domin karantawa cikin aminci da yarda ga duk me buk'ata zai turo katin Mtn na d'ari biyu N200 kacal ta wannan number d'in 09035938246, ko ta account number 5330055604, Idan katura ka aiko da screen shot na transaction a wannan number d'in 09035938246_ _Akwai gara'basar *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shahararriyar marubuciyar nan *AMEENA ABBA UMAR* tare da novel d'in *FANSAR RAI* akan N300 kacal, ko da kud'in ka sai da rabonka_ _~GORON SALLAH Last page~_ *PAGE 3* Wajen k'arfe taran dare Barr Faruk yabaro gidanshi tunda yafito daga cikin gidan zai shiga mota yadinga ji kamar ana bin bayanshi sai ya waiga sai yaga ba kowa cikin ranshi yace inma aljannu ne to na fi k'arfinsu. Mota yashiga yabar gidan tuk'inshi yake a nutse har ya isa gida, direct part d'inshi yawuce yai wanka yashirya, yana cikin saka kaya Dad yakirashi a waya yace yasameshi a parlor, amsawa yayi da toh. Saida yagama shirinshi sannan yafita yasamesu zaune shi da Mom. Gaishe da iyayenshi yayi sannan yazauna yace Dad gani. Dad yace na ganka Faruk tambayarka nakeso inyi mi yahad'a ka da Nasiba? 'Dago kai yayi yakalleshi yace Dad wani abu tace na yi mata? Mom harararshi tayi tace ba a saniba ana tambayarka kana tambayar mutane. Kwantar da murya yayi yace ba haka bane Mom kiyi hak'uri. "Kaine dai zaka ba kanka hak'uri, wallahi Faruk baka kyauta ba d'azu yarinyar nan tashigo tana kuka kuma nasan fitarka da kuka had'u kayi mata wani abun, kawai dan kaga tana sonka shine zaka dinga wulak'antata, wai ma me tayi maka? Ganin yadda Mom take fad'a yasa jikinshi yayi sanyi yace Mom kuyi hak'uri babu abinda nayi mata. Dad yace anya kuwa Faruk, toh menene dalilinka na k'in amincewa ayi baikonku bayan iyayenta sun amince da hakan, faruk ko dai so kake kawatsa mana k'asa a idanu kasa muji kunya. Kallon Dad d'in nashi yayi cikin sanyin jiki yace ko d'aya ba haka bane Dad nima kaina ina son Nasiba saidai kawai saboda mahaifinta da yakeso yamaida min soyayya kamar kasuwanci, yadda nakeson Nasiba haka ma aikina ina sonshi. Su dukansu idanu suka zuba mashi cikin rashin fahimtar maganarshi Dad yace me kake nufi da hakan? Watau kana nufin ba wai saboda karatunta kak'i amincewa ba kana da wani dalili naka? " Eh Dad nasan koda ban fad'a makuba dole wata rana kusani, akan wani case ne shine mahaifinta da abokinshi suka nuna bazasu bani itaba har sai na janye nikuma naga ba zan iyaba dan baidace ace maganar aurenmu ta shafi aikina ba" Tsaki Mom taja tace toh menene ba sai ka amince kajanye ba. A'a Mom kod'aya yin hakan bai daceba domin wannan shara'ar itace tafiye min komai a rayuwata ban da burin da yawuce inga ina taimaka ma mutane musamman ma wad'anda aka zalunta aka tauye ma hak'k'insu, idan har shi mahaifin Nasiba bai kasance wanda zai iya taimaka ma wanda aka zalunta ba toh bai dace yahana wani yataimaka ba, janyewata a shara'ar nan daidai yake da salwantar rayuwar jawahir wanda hakan zai iya sa akasheta. Dad da Mom lokaci guda sukace Jawahir kuma? Wacece hakan? Shuru Faruk yayi saida Mom tace tambayarka muke sannan yajuyo yakalleta yace Mom ta kasance yarinya ce wadda aka salwantar da ran iyayenta dan aci dukiyar da mahaifinta yatara wannan duk bai isaba saida akayi silar zuwanta gidan yari,, ganin yadda jikin iyayenshi yayi sanyi yasa yace dan Allah na rok'eku kar ku hanani yin wannan taimakon indai akan aurena da Nasiba ne na hak'ura ko da ace sonta zai kasheni dan bazan iya kasuwanci da soyayyata ba idan har mahaifinta zai iya bani ita ahaka to inkuma bazai iyaba shikenan na hak'ura ammah kugafarce ni idan har maganata ta 'bata maku rai iyayena hak'ik'a ban fad'i haka ba dan in 'bata maku,,, yana fad'in haka yamik'e cikin sauri yawuce yanufi part d'inshi. Su dukansu da kallo suka bi shi suna jin wani iri a cikin ransu musamman ma Mom da tasan halin d'anta ta tabbata tunda har d'anta yafurta haka to zai iya hak'ura ko da ace zai rasa rayuwarshi akan soyayyar Nasiba. Dad ne yajuyo yakalleta yace Nuratu kinji abinda Faruk yace. Cikin sanyin jiki tace babu yadda zamuyi tunda har yafurta ammah me zai hana kasamu shi mahaifin Nasiba kafahimtar da shi wannan shara'ar da Faruk zaiyi ai batada wani aibu tunda akan gaskiya zaiyi ta inyaso sai yajanye k'udurunshi ya amince yabashi auren Nasiba. Shuru Dad yayi yana nazarin maganarta na d'an wani lokaci sannan yace shikenan zan kwatanta hakan kikwantar da hankalinki. Murmushi tayi tace bakomai Alhaji nagode, yanzu muje mukwanta dare ya yi. Kallon agogo yayi yace hakane sannan yamik'e suka nufi part d'insu. Faruk yana shiga part d'inshi fridge gabud'e yad'auko ruwa yatsiyaya acikin cup yad'aga kai yashanye sannan yawuce yanufi wajen kujera yazauna tare da d'auko wayarshi chan kuma yayi wurgi da ita yadafe kanshi da dukkan hannuwanshi, ahankali yafara jiyo k'ara kamar ruwa yana zuba a toilet lokaci guda yamik'e yanufi bedroom yana shiga yawuce toilet yamurd'a k'ofar yashiga fanfo ne yagani a bud'e ruwa suna ta tsiyaya, wajen fanfon yaje yad'ibi ruwan yazuba ma fuskarshi bud'e idanun da zaiyi tare da d'ago kai ta cikin madubi yaga kamar wannan tsohuwar tsaye a bayanshi gashin nan ya baje mata fuska saurin waigawa yayi ammah baiga kowaba yasake juyowa yakalli madubi nan ma ba kowa ajiyar zuciya yasafke tare da kashe famfon yafito yarufe toilet d'in yawuce yanufi gadonshi yazauna saida yayi addu'a sannan yakashe haske yakwanta Duk yadda yaso yayi bacci ammah ya kasa babu abinda yake tunani sai labarin da yake cikin diary d'in jawahir, ammah toh wacece wannan aljannar miye had'inta da jawahir? Taya za'a ce mahaifiyarta ce tayi fatalwa bayan bai ta'ba jin haka ba saidai aljannu sudinga siffa irin ta mutane, Ba ma wannan ba ina k'anen babanta da mijinta Umar meyasa bai ta'ba ganin sun zo dubata ba koda akayi zama a kotu baigansu ba? Shin meyasa bazatayi min bayani yadda zan fahimta ba? Runtse idanunshi yayi ahankali yace Jawahir ya kamata kice wani abu,,, Juyawa yayi d'ayan 'barin yakwanta yana ta tunane tunanenshi ahaka har bacci yai awon gaba da shi. Washe gari yana wajen aiki wajen k'arfe sha d'aya yana ta fama da ayyukanshi na kwana biyu da bai samu yazauna ba ga wata shara'a da zasu zauna a jibi duk abin ya taru ya yi mashi yawa, knocking d'in k'ofa yaji anyi tun kan yabada izini aka turo k'ofar aka shigo. 'Dago kai yayi dan ganin wanene yashigo batare da izininshi ba sai ido hud'u sukayi da Nasiba, ajiyar zuciya yasafke tare da jingine kanshi a jikin kujerar da yake zaune. Takowa tayi ta iso taja kujera tazauna tana me kallonshi. Jin shuru yasa yad'ago kai yakalleta nan suka had'a ido a karo na biyu, d'an guntun murmushi yayi yace Nasiba kece da kanki maimakon kiyo min waya? Ajiye jakkarta tayi a saman table d'in tazare bak'in space d'in da yake manne a idanunta, ganin idanunta yayi sunyi ja alamun ta ci kuka har zaiyi magana nan tatari numfashinshi tace babu abinda zakace min Faruk ni kawulak'anta narasa me kake nufi da hakan ashe bazaka iya salwantar da komai ba akaina. Kinga Nasiba ba haka bane kawai dai....... Kawai dai me? Wai ma shin wacece wannan yarinyar da saboda ita kasalwantar da soyayyarmu wacece ita a wajenka?,,, tafad'a tare da fashewa da kuka. Faruk duk sai yaji wani iri ganin Nasiba tana kuka duk sai yama rasa me zaiyi, chan yayi k'arfin hali yace Nasiba duk yadda kike tunani ba haka bane ke kanki shedace banda wata wadda nakeso bayanki kawai dai abinda mahaifinki yazo min da shi ne naji kwatakwata bazan iyaba idan har sun amince zasu bani aurenki a haka ashirye nake muyi aure ammah bazan ta'ba yin baya akan case d'in Jawahir ba domin ya zama dole intaimaka mata. 'Dagowa tayi takalleshi tare da rage sautin kukanta tace ammah ai ka san rayuwarta tana da had'ari wannan dalilin ne yasa su Daddy sukeso kajanye dan kar wani abu yashafemu, na ji labari ta kashe mutane dadama daga ciki har da lauyoyin da suka nemi sutsaya mata ammah Faruk ahaka kake ik'irarin zaka tsaya mata? Toh nifa soyayyata kana nufin ka hak'ura da ni? Shuru Faruk yayi tare da rintse idanunshi yana jin wani iri a ranshi wanda yakasa misulta hakan. Mik'ewa Nasiba tayi tace tunda bana da amsa shikenan nagode Faruk ni zan tafi. Saurin bud'e idanunshi yayi yakalleta nan tad'auki jakkarta tajuya zata tafi ahankali yakira sunanta. Tsayawa tayi batare da ta juyoba tace bana son jin komai daga wajenka Faruk indai har baka janye k'udurunka ba zan tafi zanyi jinyar zuciyata akan tabon da kayi mata saidai ban saniba ko zata iya warkewa,,, tana fad'in haka tawuce cikin sauri zata fita. Saurin mik'ewa tsaye yayi yace Nasiba dan Allah kitsaya kisaurareni,,, bata ko tsayaba taficce tare da rufe mashi k'ofa. Buga table d'in da yake gabanshi yayi sannan yakoma yazauna tare da dafe kanshi cikin ranshi yace meyasa zaki min haka Nasiba? Duk yadda yaso yacigaba da aikin da yake kasawa yayi nan yai zaune zugum abubuwa sun taru sunyi mashi yawa. Daga k'arshe yai shirin tashi sai ga Barr Bilal ya shigo dan haka yafasa suka zauna suka cigaba da aiki tare har wajen k'arfe d'aya sannan suka tashi sukaje masallaci daga chan barr faruk yaimashi bankwana yawuce gida. Tunda yakoma gida bai sake fitaba nan yazauna yacigaba da aikinshi yana ji wayoyinshi suna ta ruri ammah yashare su bai d'aga kiran kowaba daga k'arshe ma yakashe wayoyin. Alhaji Sufyan kallon Abokin nashi yayi yace Alhaji kaga har yanzu babu wani bayani daga yaron chan ya faye taurin kai ban saniba ko hakan yana nufin ya hak'ura da auren Nasiba. Shuru Alhaji Mansur yayi yana nazarin maganar sai chan yace gaskiya ne nima na fahimci hakan, watau yana nufin abinda yasa gaba sai ya cimmashi bai saniba shi zai kwana a ciki domin bana tunanin yarinyar chan tana barin duk wanda yara'beta wallahi ina bak'in cikin barinta a raye da akayi har zuwa wannan lokacin batare da an d'auki fansar rayukan da takashe ba, taya za'ayi ace wanda yai kisa irin haka anbarshi har tsawon wannan lokacin a raye, miye amfanin hakan bayan kowa ya shaida itace,,, yafad'a cike da nuna damuwa. Jinjina kai Alhaji Sufyan yayi yace hakane shi kanshi Faruk bansan dalilin tsaya mata da yayi ba kodai akwai wanda yabashi cin hanci? Ohon mashi koma me kenan insha Allahu bai isa yahana hukunci zartuwaba akanta ya zama dole yadda takashe itama akasheta. Hakane Alhaji Allah dai yashige mana gaba. Ameen. *BAYAN SATI 'DAYA* Jawahir tana zaune d'an kurkukun d'akinta ita kad'ai kanta sadde a k'asa hannunta rik'e da wani d'an tsinke tana rubutu a k'asa koda rubutun ba fitowa yakeba ammah ahaka takeyi tana zubar da hawaye, kawai sai ji tayi an bud'e k'ofa anshigo saurin runtse idanunta tayi tare da tsayawa da abinda takeyi. Barr Faruk ne yatsaya yana kallonta sai kuma chan yatako ya iso inda take, saurin mik'ewa tsaye tayi tare da matsawa gaba tajuya mashi baya cikin dashewar murya tace menene dalilinka nadawo wa wajena shin ba na ce kadaina zuwa ba? Wani irin haushi ne yakama Faruk yana ji kamar yajuya yai tafiyarshi sai kuma yadake yace ammah ai kinsan bamuda isashen lokaci ya kamata ki fahimci hakan jawahir. Cikin muryar kuka tace ban damu da hakan ba. Jinjina kai yayi yace hakane ammah dai ya kamata ki k'arashe min labarinki,, Shuru tayi tak'yaleshi kamar bataji abinda yace ba dan hakane Faruk yamatso kusa da ita yace Jawahir shin wai ina mijinki Umar meyasa ban ta'ba ganinshi ya zo nan ba? Tun kan yarufe baki tafashe da kuka, dafe k'irjinta tayi da hannunta cikin kuka tace Yaya Umar d'ina? Taya zaizo inda nake alhali kowa yana fushi da ni, ko kad'an banyi nadamar abinda na aikata ba,, juyowa tayi takalleshi fuska sha'be sha'be da hawaye tace shin zaka taimaka min in ida cika burina inyaso akashe ni daga baya? Kallonta yake cike da mamaki, d'an guntun murmushi tayi tace ban damu da cigaba da rayuwa ba domin rayuwata batada sauran amfani saidai ina burin inje inda iyayena sukaje. Saurin katseta yayi yace ba haka ba jawahir yakamata ki ida min labarinki domin musan ta yadda zamu 'bullo ma lamarin ko da ace kina so in taimaka maki ki cika burinki dole ne in ida sanin komai shin kina da hannu a cikin mutuwar su Barr Muhsin? Shin dagaske ku ne kuka kashe Alhaji Sa'idu Nepa? Murmushi tayi cikin nuna rashin damuwa kamar ba itace take kuka ba tace ni kaina bansan abinda zan iya cewa ba, saidai abu guda nasani Alhaji Sa'idu nice nakasheshi da hannuna. Saurin ja da baya yayi cike da mamakk yake kallonta yace kece kika kashe shi? Garin ya bayan muna tare a hotel kuma baki fitaba? Girgiza kai tayi tace ba wai dole sai na fitaba sannan nake samun damar kisa na san ka karanta diary na yakamata ace ka fahimci komai akan haka, taya zan iya barin wanda yake da gurin rabani da rayuwata batare da na cika nawa gurin ba. Matsowa yayi kusa da ita yace kenan jawahir kina nufin yana cikin mutanen da suka kashe iyayenki? Girgiza kai tayi a karo na biyu sannan tace baya ciki kawai dai d'an uwanshi ne yaturoshi daga chan Europe yazo yaga bayana kafin yadawo k'asar nikuma naga idan nabarshi zai iya samun galaba akaina, shi d'in abokin Abba ne shima saidai d'an uwane na jini ga Alhaji Tanimu sunaso suga bayana ammah kuma bansan me yasa hakaba. Jawahir wannan ba wani abu bane da ace zaki min cikakken bayani da na taimaka miki na maki alk'awali zan tura ma Alhaji Tanimu takardar gaiyata domin muzauna kotu da shi da ma sauran duk wanda yake da hannu akan kisan iyayenki yakamata ki fahimci bana da burin da yawuce inwanke ki daga zargin da ake maki. Ahankali tace zargi kuma? Wanene yace maka zargi ne na fad'a maka gaskiya ne nice nake kisan da taimakon wadda takasance masoyiya a gareni. Shuru Faruk yayi cikin ranshi yace yarinyar nan ta cika taurin kai dayawa,,, muryarta yaji tana cewa iyayena sun sha suce ina da taurin kai tun ina k'arama musamman ma Ammina a duk lokacin da tayi min wanka tad'auko min kaya zan saka sai in nuna bana son su duk yadda zata so insa bana yarda har sai ta canza min wasu wannan dalilin ne yasa take cemin jawahir kin cika taurin kai,, d'an guntun murmushi tayi tare da kallonshi tace ammah wannan ba shine dalilin da yasa nake da taurin kai ba wani lokacin ina duba ne da abinda yadace da rayuwata. Mamakine yacika Faruk ganin a zuci yayi magana ammah har ta san abinda yace cikin ranshi yace anya itama ba aljanar bace, ajiyar zuciya yasafke sannan yace hakane jawahir kin faye taurin kai nima kaina kiduba tsawon lokacin da nad'auka ina bibiyarki akan kifad'a min komai game da rayuwarki ammah kin k'i... Katseshi tayi tace ba wai haka ba kawai dai banaso had'arin da yake tare da ni yashafeka dan baka cancanci hakan ba. Jawahir kar kiyi duba da hakan insha Allahu babu abinda zai sameni dan Allah na rok'eki ki ida sanar da ni komai a game da rayuwarki, shin a lokacin da Abba yazo da malamin nan me yafaru da lokacin da Umar yagano kina da hannu a cikin kisan da akeyi? Dafe kanta tayi da yasara mata lokaci guda tayi tace a'a bazan ce ga abinda yafaru ba nima kaina kawai dai duk abinda yafaru yana cikin.....bata k'arasa fad'in abinda yake bakinta ba sai gani yayi kamar an fizgeta da k'arfin ta je ta bugi bango, wata irin razanannar k'ara tasaki tare da sulalewa k'asa a sume. _Sis Nerja'art✍🏻_ [7/24, 11:10 PM] Sis Nerja'art 2: *......FANSAR RAI......* *INTELLIGENT WRITER'S ASSO....®* [On Award Together] _Wannan Littafin na kud'i ne domin karantawa cikin aminci da yarda ga duk me buk'ata zai biya d'ari biyu N200 kacal ta wannan number d'in 09035938246, ko ta account number 5330055604, Idan katura ka aiko da screen shot na transaction ta wannan number d'in 09035938246_ _Akwai gara'basar *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shahararriyar marubuciyar nan *AMEENA ABBA UMAR* tare da novel d'in *FANSAR RAI* akan N300 kacal, ko da kud'in ka sai da rabonka_ *PAGE 4* Mummyn Nasiba ce tashiga d'akin d'iyarta ta tasameta zaune ta buga tagumi girgiza kai tayi sannan taje gefenta tazauna cike da jin tausayinta tace Nasiba ya kamata kikwantar da hankalinki kidaina saka damuwa a ranki kiduba kiga a 'yan kwanakin nan yadda duk kika bi kika rame. 'Dago kai tayi takalli mahaifiyarta idanunta cike da hawaye tace bazan iyaba mummy bansan me yasa Faruk zaiyi min haka ba duk son da nake mashi ammah shine zai saka min da haka, shin wai ma wacece wannan yarinyar da yafifitata akan soyayyata. Shafa kan d'iyartata tayi cike da jin tausayinta tace Nasiba saisa nace maki Faruk baida kirki kicire tunaninshi a ranki dan shi dama kike tunaninshi baisan kina yi ba da ace ya damu dake da bai fifita aikinshi akankiba. Mik'ewa tayi tsaye tare da fashewa da kuka tace Mummy duk su Daddyne suka ja min hakan da ace sun barshi da aikinshi ai da bazai za'bi aikin akaina ba, koma menene yasamemu ai daga ubangiji ne ni inason faruk a hakan. Yi shuru Nasiba kar insake jin haka kinsan dai kowane iyaye bazasu so 'ya'yansu susha wahala ba, taya kike tunani zamu amince ki auri Faruk a wannan yanayin ko ma ince akan wannan bala'in da yaratumo ma kanshi, ya kamata kigane cewa mahaifinki gatane yayi maki domin bayason duk abinda zai ta'ba lafiyarki. Komawa tayi takwanta saman gadonta tajuma ma mahaifiyartata baya tare da fashewa da wani sabon kukan. Hajiya Maijidda nan tadinga lallashinta tare da k'ok'arin kwatanta mata har tasamu tasafko daga fushin tadaina kukan. Washe gari Faruk bai samu yakoma wajen jawahir ba saboda shara'ar da zasu shiga haka sukaje suna ta fafatawa har Allah yabasu nasara suka gama. Bayan kwana biyu koda yaje gidan kaso bai samu ganawa da jawahir ba dan lokacin tana bacci koda yatambayi me gadi yashaida mashi tun baccin da takwanta shekaran jiya ne ammah tana yi tana d'an farkawa tayi sallah sai kuma idan ankawo mata abinci shine ake tashinta, haka yajuya yatafi batare da ya samu yadda yakeso ba abun ya d'aure mashi kai sosai dan bai ta'ba ganin irin haka ba. A rana ta biyu ce da yakoma yasamu su DPO sunje wajenta sun tsareta da tambayoyi abun ya bashi mamaki sosai dan duk atunaninshi angama case d'in hakanan, DPO yana ganinshi yace Barr Faruk mun sake had'ewa kenan. Murmushi Faruk yayi yace ai na d'auka tuni angama da wannan case d'in. Taya za'a gama bayan ta k'i ta amsa laifinta, tana da taurin kai sosai. Ta'be baki Faruk yayi yace bai zama dole mutum ya amsa laifin da bai aikata ba, yakamata ace ka gamsu da ba ita tayi kisan ba tunda bakada k'wak'warar shaidar da tanuna maka ita duk binciken da zakayi ka yi ammah baka samu ba, da ace ka yi wani tunanin watak'il zaka samu wani nadaban da yayi kisan. Mik'ewa DPO yayi yamatso kusa da inda Barr Faruk yake tsaye yace har ni zaka fad'a ma haka bayan nasan itace tayi wannan kisan? Ni ko nake da k'wak'warar shaida ko da ace a yanzu nayi niyar kamata akan wannan laifin sai ta kamu saboda duk alamomi sun nuna itace, ya kamata kasan abinda kake fad'a musamman ga babban d'an sanda wanda yasan makamar aikinshi, juyawa yayi yakalli jawahir da kanta yake sadde k'asa yace tana da k'arancin shekaru sannan tana da fuska biyu zan iya amfani da damata insa ta amsa laifin nan ta k'arfin tsiya tunda ta k'i amsawa ta lalama. 'Dan guntun murmushi Barr Faruk yayi yace d'allabai tabbas kana da wannan damar a matsayinka na DPO sannan nima ina da tawa damar da zan iya kareta a matsayina na lauyanta, ba ma wannan ba idan naso zan iya shigar da k'arar duk wanda ya zargeta muyi zama na musamman da shi a kotu, kaga kai kana da damar kamata ni kuma ina da damar kareta. 'Daga mashi hannu DPO yayi yace ya isa haka ya kamata kadinga sanin abinda kake fad'a katsaya a matsayinka kawai na lauyanta mai bata kariya, idan har kace zaka shiga hurumina kai kanka zan iya sa a d'aureka ba lauya ba koda ace alk'ali ne, da sannu zan tabbatar maku da cewa itace tayi wannan kisan, kallon jawahir yayi yace kekuma kisaurare ni zan dawo a gareki,,, yana fad'in haka yajuya zai tafi sai jin muryar Faruk yayi ya ce ni kuma dasannu zan wanketa akan duk wani laifin da ake zarginta. Jinjina kai yayi tare da yin murmushi sannan yawuce yafita, yana fita direct office d'in Alhaji Mahadi yawuce. Bayan ya zauna ne yace wai wanene wanchan Barrister d'in. Wane kenan d'alla'bai? Shuru yad'anyi na d'an lokaci sannan yace lauyan da yake kare wannan yarinyar wadda tayi kisa. Oh barister faruk kake nufi na gane shi. DPO yace eh shi, ya cika zak'ale min akan aikina wai har ni yakece ma zaiyi k'arata akan wacchan yarinyar, Da mamaki Alhaji Mahadi yake kallonshi yace Barr Faruk d'in? Ko dai baisan ko wanene kai ba? Ta'be baki yayi yace me zai hanashi sani bayan kayan da nake sanye da su sun isa sununa bashi matsayina kuma ya je station ya gani kawai dai na lura kamar yanaso yanuna min shi wani ne, shin wai ma wanene mahaifinshi a garin nan? Alhaji Sani Meshadda shine mahaifinshi,, cewar Alhji mahadu Jinjina kai DPO yayi yace dakyau da wannan damar yake amfani yana d'aukar kanshi wanine saboda matsayin mahaifinshi koda shima d'in na ga ba k'aramin lauya bane ammah ya kamata yadaina shiga hurumina akan case d'ina da yarinyar chan. Alhaji Mahadi yace kayi hak'uri d'alla'bai zan fahintar da shi domin Faruk abokina ne ba wai haka yakeba bansan dalilinshi na yin haka ba saboda ba mutum bane mai shiga sabgar da bata shafeshi ba. A'a kabarshi kar kayi mashi magana kakyaleni da shi kawai dan bai sanni ba saisa yake min haka ammah dasannu zai sanni,,, yana fad'in haka yamik'e. Faruk kallon jawahir yayi da take zaune ta zuba ma gefe d'aya idanunta da sukayi jajir, matsowa yayi gefenta yad'auko diary d'inta daga cikin suit d'inshi yamik'a mata yace gashi na maido maki. Saurin juyowa tayi takalleshi sannan ta amsa muryarta tana rawa tace nagode. 'Daga kai yayi sannan yace duk abinda yake ciki na gani saidai babu inda zai kaini ga ha'bar zaren, shin ko zaki fad'a min inda zan had'u da su Umar domin mugana? Wani irin kallo tayi mashi wanda shi kanshi baisan ma'anarshi ba saidai ya fi danganta shi da harara. Ta'be baki yayi yace duk ba wannan ba yakamata kisan cewa bamuda wani isashen lokaci sannan kar wai kidamu da maganganun DPO bare har sutsorata ki, ammah yakamata kudaina kisan nan da kuke kumik'o min case d'in ni zan tsaya maki wajen ganin na k'wato maki hak'inki kamar yadda nayi maki alk'awali, sannan wannan matar meyasa take wahalar da ke alhali ta nuna taimakonki zatayi. Cikin k'araji tace ya isa haka barrister ya isa! Maganganunka suna min yawa, taya zakace inmik'a case d'ina agareka bayan lokaci ya k'ure? Hawaye ne suka gangaro mata ahankali tace tun farko yakamata ace Ammina ta samu wanda zai iya tsaya mata yak'watar mata hak'inta ammah hakan ya gagara daga k'arshe ma aka ga bayanta, ni kaina wace hanya ce banbi ba dan ganin ank'wato min hak'ina ammah hakan bai samuba saboda azzalumai sunyi yawa,, shuru tayi nad'an lokaci sannan tacigaba da cewa sai yanzu da tadawo dan tad'auki fansa sai hakan yazama laifi? Ban damu da duk abinda zai faruba ni ina bayanta sannan zan cigaba da taimaka mata wajen ganin ta d'auki fansa, na tabbata kai ba irinsu Barr Muhsin bane dan haka ya kamata karabu da ni kar kajefa kanka acikin had'ari a dalilin son kataimaka ma wacce rayuwarta bata da sauran amfani, fashewa tayi da kuka tace duk wani farin ciki nawa anraba ni da shi hatta mijina da nake gani shine kad'ai nake jin dad'i ta 'bangarenshi ammah daga baya ya tsaneni yana ganin laifina akan abinda na aikata,, d'aga murya tayi dak'arfi tace meyasa haka yaya umar? Meyasa Ammi tayi min haka!!! cimimiyo gashinta tayi dak'arfi tare da fashewa da matsanancin kuka. Barr Faruk mutuwar tsaye yayi yana kallonta duk sai yaji wani iri a ranshi ganin yadda take kuka bil hak'i. Tsugunnawa yayi a gabanta yace jawahir kidaina cewa haka ni nayi maki alk'awali zan taimaka maki yakamata kifahimci hakan. 'Dago manyan idanunta tayi da suka rine saboda kuka tasafke su akan fuskarshi cikin sheshek'ar kuka tace katafi kawai barrister kadaina wahalar da kanka ban damu da duk abinda mutane zasu fad'a ba akaina saidai abu d'aya nasani duk abinda nasa a gaba sai na yi shi, shin ko zaka taimaka min akan d'aukar fansar da nake? Inhar zaka taimaka min akan haka shine kad'ai taimakon da nakeso daga gareka. Shuru yayi yana kallonta yama rasa abinda zaice mata sai chan yabud'e baki zaiyi magana tayi saurin tarar numfashinshi tace nasan bazaka ta'ba taimaka min ba katafi kawai kabarni ni da Ammina zamu cigaba da ganin bayansu, ba kowane zaiso rayuwarsa takasance me had'ari irin tawa ba. Barr Faruk girgiza kai yayi yace jawahir yakamata kifahimci abinda nake nufi. Saurin mik'ewa tsaye tayi tace babu wanda zan fahimta kamar yadda nima babu me fahimtata, katashi katafi kawai. Har ya bud'e baki zaiyi magana tai saurin tarar numfashinshi tace na rok'eka katashi katafi zanji da abinda yadameni,, hannu tasa tayi saurin dafe kanta da yasara mata tare da runtse idanunta dan duk lokacin da zaizo yayi mata maganar nan sai ta ji kanta kamar zai cire saboda tsananin ciwo. Mik'ewa yayi tsaye yace lafiya jawahir me yake faruwa? Ahankali tabud'e idanunta tace a'a babu komai katafi kawai. Ammah kamar kanki yana ciwo. Wucewa tayi takoma chan k'arshen bango tazauna tace babu abinda yake damuna na rok'eka katafi ina buk'atar hutawa. Jinjina kai yayi tare da juyawa yatafi batare da ya sake cemata komai ba, da kallo tabishi har yafita sannan takife kanta da gwiwa tashiga rera kuka me shiga rai.. Koda yakoma gida kwanciya yayi jikinshi duk ya yi sanyi sosai, ga wani irin haushi da yakeji akan yadda jawahir take mashi dan de kawai yai alk'awalin tsaya mata da badan hakaba da tuni ya rabu da ita, saboda bai ta'ba ganin irin haka ace kwatakwata bata damu da rayuwarta ba, saidai ya fi tunanin haka akan rashin samun farin cikinta, ammah kuma me yafaru bayan a yadda yaga ta rubuta a diary d'inta tana samun kwanciyar hankali a wajen umar, ahankali a fili yace to wai ma ina umar? Ajiyar zuciya yasafke tare da gyara kwanciyarshi yana me cigaba akan tunanin haka saidai gefe d'aya na zuciyarshi soyayyar masoyiyarshi abun k'aunarshi tana fizgarshi ammah baya iya nuna hakan saboda hali irin na faruk duk yadda yakeson abu daga lokacin da aka nemi aimashi iko da shi toh zai iya ja baya dashi komi irin k'aunar da yakeyi mashi kusan hakan ne yake tunani zai faru da soyayyarshi da Nasiba. Daga k'arshe da yaga tunanin yana nema yadameshi yamik'e yad'auko laptop d'inshi yacigaba da aiki. ________washe gari Zaune yake wajen aiki yana tura wani sak'o ta laptop gabad'aya ya maida hankalinshi da aikin da yake, knocking d'in k'ofa akayi nan yabada izini ashigo, Barr junaid ne yaturo k'ofar yashigo. Faruk yana ganinshi yai murmushi yace kamar ka san kana a raina. Zuwa yayi yaja kujera yazauna yace wallahi kau barrister nima ganin kwana biyu bamu had'u bane yasa nace bari inshigo office d'in mutumin nawa inga ko yana nan. Ture system d'in yayi gefe bayan sak'on da yake turawa ya gama shiga sannan yace ina nan abubuwa ne sunsha min kai. Ga kuma case d'in jawahir,,, cewar Barr Junaid. Murmushi Faruk yayi yace kusan haka ammah har yanzu na rasa samun k'wak'k'warar sheda. Shima junaid murmushi yayi yace bana tunanin zaka samu indai akan case d'in yarinyar chan ne, yauwa Barrister wai intambayeka ya maganar baikon ka? Na ji kamar ance ba'ayi ba. Kallonshi yayi da mamaki yace wanene yafad'a maka haka? Kaga Faruk baidace ka'boye min komai ba ni abokinka ne sannan ina ganin kamar ba daidai bane kayi watsi da soyayyarka saboda kawai wannan case d'in ya kamata kafahimci haka. Ta'be baki Barr Faruk yayi yace hakane saidai inaso kasani zan iya hak'ura da komai indai har za'a yi min wasa da hankali, ban damu da irin son da nake ma Nasiba ba koda ace zan rasa raina idan har mahaifinta bazai iya bani ita ahaka ba, bazan ta'ba janyewa daga case d'in jawahir ba har sai naga abinda zai ture ma buzu nad'i. Haba Faruk wace irin magana ce haka kakeyi yakamata kagane cewa ita fa Jawahir mai laifi ce kar kayi wasa da damarka karasa soyayyarka. Duba agogon hannunshi yayi cike da k'osawa da maganar Junaid kamar ba zai ce komai ba sai kuma chan yad'ago yakalleshi yace a yanzu ba kowa bane zai iya fahimta ammah inaso kasani da sannu zan wanke jawahir daga zargin da akeyi mata. 'Yar dariya Barr Junaid yayi yace ka jika da wata irin magana da sannu dai asirinta zai tonu, wallahi Faruk ina baka shawara kafita daga harkar case d'in yarinyar nan dan kar kaji kunya.. Katseshi yayi ta hanyar cewa Junaid idan ka gama abinda yakawoka zaka iya tafiya domin ina aiki me muhimmanci. Mik'ewa tsaye junaid yayi yace yi hak'uri oga yanzun nan ko, atashi lafiya. 'Daga kai kawai Faruk yayi batare da ya ce komai ba yajawo syatem d'inshi ganin haka yasa Junaid yawuce yafita yabar office d'in. Wajen k'arfe biyar Faruk yagama shiri yafito zai fita a parlor yacikaro da Momcy tana zaune ta buga uban tagumi, zuwa yayi daga gefenta yazauna tare da rik'o mata hannu. 'Dago kai tayi takalleshi saida tasafke ajiyar zuciya sannan tace Faruk. Marairaicewa yayi yace dan Allah Momcy kidaina tagumi. Murmushi tayi tace ai dole inyi Faruk d'azu Hajiya Maijidda takirani tana min maganar Nasiba tana chan ta tashi hankalinta sosai, Faruk ya kamata kagane cewa Nasiba tana sonka sosai koma menene bata cancanci irin haka daga gareka ba. Kwantar da kanshi yayi saman kafad'arta yace Momcy laifin mahaifinta ne ni banda matsala ko da a yanzu zai janye k'udurinshi ni kuma zan auri Nasiba. Girgiza kai tayi tace Faruk ka fiye taurin kai watau kana nufin kai bazaka iya janye naka ba. 'Dago kanshi yayi yakalleta cikin sanyin jiki yace a'a Mom nawa bazai ta'ba janyuwa ba idan har nace zan janye toh tabbas banyi adalci ba domin Jawahir tana buk'atar taimako taya za'a zalunci mutum sannan akamashi a rufe, ta rasa me tsaya mata yak'wato mata hak'inta na tabbata daga inda najanye za'a iya kasheta inko nayi haka ban kasance me adalci ba akan aikina. Cike da tausayin d'an nata take kallonshi tace hakane Faruk Allah ubangii yataimaka insha Allahu zaka auri Nasiba dayardar Allah ita rabonka ce. Cikin jin dad'in kalaman mahaifiyar tashi yace nagode sosai Momcy. Shafa kanshi tayi tace bakomai Babana. Mik'ewa yayi yace Momcy bari inje akwai wani aiki da zanyi yanzu. Toh shikenan Allah ubangiji yataimaka sai ka dawo. Ameen Momcy. Wajen k'arfe biyar da rabi ya isa gidan kaso direct office d'in Alhaji Mahadi yafara zuwa kamar yadda yasaba bayan sun gaisa ne mahadi yakalleshi yace wai Faruk minene yahad'aka da DPO ne? Ta'be baki Faruk yayi yace me fa? Wani abu yace maka ya faru? A'a ba wai haka ba. 'Dan guntun murmushi Barr Faruk yayi yace kabarni da shi kawai yanzu dai bari inje inga jawahir wallahi yarinyar nan ta k'i tabani had'in kai yadda yakamata. Jinjina kai Alhaji Mahadi yayi yace kama gode ma Allah da bata shek'aka lahira ba. Uhm kaidai kasani malam ni bari intashi inje. Dariya Alhaji Mahadi yayi yace toh shikenan ba damuwa abokina bari insa arakaka. Lokacin da suka isa tsaye yasameta wajen 'yar k'aramar tagar nan idanunta suna ga d'an hasken da yake shigowa tsaye yayi daga bakin k'ofar yana kallonta inda ma'aikacin gidan yake tsaye a waje yana jiranshi takowa yayi yamatso kusa da ita bai ankara ba sai jiyo muryarta yayi ta ce shin zaka taimaka min in cika burina? Ajiyar zuciya yasafke yace jawahir ya kamata kifahimta lokaci yana k'ure mana kidaure ki ida bani hujjojin da zasu taimaka wajen ganin na tseratar da ke daga gidan nan. Cikin muryar kuka tace meyasa kafi damuwa da fitata akan d'aukar fansar abinda akayi min? Wa yafad'a maka na damu da incigaba da rayuwa? Nidai abu d'aya nakeso shine inga bayan duk wanda yarabani da iyayena. Cikin sanyin jiki yace jawahir nasan haka kifahimceni idan har kika ban dama nayi aikina yadda yadace toh dole ne ingurfanar da su agaban hukuma ni zan taimaka maki da hakan. Ahankali tace hukuma kuma? Ni bana buk'atar hukuma a ciki nafiso kowane d'a yad'and'ani irin rad'ad'in da naji a lokacin da narasa iyayena, nasan bazaka ta'ba taimaka min ba ammah ni zanyi komai dakaina. Tsaye Barr Faruk yayi yana kallonta cikin ranshi yace meyasa jawahir take haka ko har yanzu bata yarda dani ba? Juyowa tayi ahankali takalleshi idanun nan nata sunyi jajir kamar garwashin wuta duk sun k'ank'ance d'an guntun murmushi tayi tace kar kadamu ahakan ma nagode. Amm jawahir ya kamata kifahimci kwana goma sha biyar fa yarage mana lokaci bazai ishemu ba kidaure muyi abinda yadace. Dafe kanta tayi da hannu d'aya ahankali tace wannan shine abinda yadace Barrister a gobe zan kasance cikin farin ciki saboda akwai aikin da zan aiwatar wanda shine zai rage min rad'ad'in abinda nakeji. Tun kan tarufe baki yace jawahir kisa zakiyi? Takawa tayi dak'yar tana k'yangashi taje tazauna tare da jingine kai da bango sannan tace abinda yadace da rayuwata zanyi. Matsowa yayi kusa da inda take zaune yatsaya yace jawahir na rok'eki ki taimaka kiban k'wak'warar hujja ni zan taimaka maki akan dukkan abinda yadace nayi maki wannan alk'awaline duk wanda yake da hannu akan mutuwar mahaifinki bazan ta'ba barinshi ba koma wanene shi. Ahankali tamaimaita kalmar da yace koma wanene shi? sannan tad'anyi guntun murmushi tace kana nufin koda ace kana da dangantaka da shi idan har kagane yana da hannu a ciki zaka taimaka min? Shuru Barr Faruk yayi sai chan yace ban damu da kusanci na da shi ba domin ina akan aikina ne zanyi k'ok'arin haka kiyarda da ni jawahir. Hawaye ne suka gangaro mata tace bana so kajefa kanka acikin had'ari Barrister domin rayuwata babu komai a cikinta sai had'ari idan har kacigaba da bibiyata ahaka komai zai iya faruwa da kai wannan dalilin ne yasa nakeso kacire hannunka a ciki sannan saboda haka ne nakasa fad'a maka komai akan rayuwata. Kidaina cewa haka jawahir ban damu da duk yanayin da zan shiga ba indai ina akan aikina nidai kawai taimako d'aya nakeso kiyi min. Idanu tazuba mashi batare da tayi magana ba ganin haka yasa yace shin ina labarin su umar da d'an uwan mahaifinki? Ko zaki fad'a min inda suke saboda ina da tarin tambayoyi akansu sannan ya zama dole Abbanku yagurfana a gaban kotu. Hawaye ne suka cigaba da fita daga idanunta d'aya bayan d'aya chan tafara shashek'ar kuka lokaci guda tafashe da kuka tace bansan me zan ce maka ba barrister bansan ya akayi haka ba...hamma ce tafara yi chan kuma tayi murmushi cikin murya me kama da ta masu jin bacci tace koma menene zaka sani zanyi k'ok'arin haka ammah ya kamata yanzu katafi sai mun had'u a karo na gaba zan sanar da kai komai. Sai a lokacin yalura da yadda gari yafara duhu yace kar kidamu jawahir ba wani abu bane zan iya zama a nan har lokacin da naso in fita. 'Dan guntun murmushi tayi tace saboda shugaban gidan ya kasance abokinka? Da mamaki yake kallonta yace wanene yafad'a maki haka? Janye idanunta tayi daga kallonshi. Mik'ewa yayi yace zan tafi gobe dasafe zan dawo agareki. Saurin cewa tayi a'a kar kadawo a lokacin saboda ina da aiki me muhimmacu da zanyi da k'arfe goma. Aiki kuma? Wai wane irin aiki ne haka kike magana akai ban fahimceki ba?,, yafad'a fuskarshi d'auke da mamaki. Cikin nuna rashin damuwa tace ba lallai ne kafahimci hakan ba katafi kawai. Ta'be baki yayi yace shikenan zan tafi ammah goben dai zan dawo yakamata ki ida sanar da ni komai akanki. A'a bazai yuwu ba saidai zuwa jibi. Kallonta Barrister Faruk yayi nad'an lokaci sannan yace kin amince jibin zaki ida sanar da ni komai akan rayuwarki? Saurin juya baya tayi cikin rawar murya tace ban saniba ko hakan zai yuwuba ya kamata kakula akan haka zaka iya jefa rayuwarka cikin matsala kafahimci hakan. Kinga jawahir yanzu ba lokacin jayayya bane koma menene kishirya lokacin da duk nadawo zaki ida sanar da ni komai lokaci ya k'ure mana ammah kin kasa gane hakan, ni zan tafi. Ko juyowa batayi takalleshi ba bare yasa ran zatayi mashi magana dan haka yawuce yayi tafiyarshi. Tana jin an rufe d'akin hawaye suka gangaro mata tayi saurin runtse idanunta wata irin mahaukaciyar dariya da taji ne yasa tayi saurin bud'e idanun. A saman iska taga matar zaune cikin mummunan siffa fuskarta fari tas babu alamun jini bakinta duk ya tsatstsage hak'ora sunyo waje, idanuwanta a d'inke suke da farin zare babu alamun k'waya a ciki gashin kan nan nata ya yi tsaitsaye saman iska sai juyawa yake, dariya tacigaba da yi cikin sauri jawahir tad'an ja baya tana cigaba da kallonta muryarta tana rawa tace me yamaidoki wajena? Muryar matar taji kamar tartsatsin tsawa ta ce jawahir ya zama dole kiyi nadamar maganar da kika fad'a min idan dai har kina son ki tseratar da rayuwarki sannan baki isa kisanar da barrister komai ba. Cikin d'aga murya tace bazan ta'ba nadama ba ban damuba ink'arashe rayuwata a nan cikin gidan nan daman rayuwar tawa batada sauran amfani a duk lokacin da kikaso zaki iya kasheni. Matsowa matar tayi kusa da ita tana me cigaba da dariya sai kuma chan tatsagaita dariyar da take tace ke matsalarki d'aya kin cika taurin kai duk wahalar da nake baki ammah hakan ya kasa sawa ki aje makaman da suke saman kanki koma menene dai shikenan nasan dai kina sane da aikin da yake gabanmu gobe. Wani irin kallo jawahir tayi mata tare da jan tsaki tajuya zata tafi, wani farin abu ne yafito daga cikin idanun matar jawahir bata ankara ba sai ji tayi an fizgeta da k'arfi anbuga da bango nan tasulale tafad'i a sume, matar na ganin haka tabushe da wata irin dariya nan ta isa wajen da jawahir take kwance a sume, wani irin abu tadinga karantawa wanda ba kowane zai gane abinda take cewa ba saboda yaren da take, wata 'yar kwalba ce tabayyana a hannunta k'arama tabud'e ta takarkata a wajen fuskar jawahir sai ga wani abu kamar jini yana zubowa har saida yak'are sannan tagirgiza ta'bace.... _Sis Nerja'art✍🏻_ [7/24, 11:10 PM] Sis Nerja'art 2: *......FANSAR RAI......* *INTELLIGENT WRITER'S ASSO....®* [On Award Together] _Wannan Littafin na kud'i ne domin karantawa cikin aminci da yarda ga duk me buk'ata zai biya d'ari biyu N200 kacal ta wannan number d'in 09035938246, ko ta account number 5330055604, Idan katura ka aiko da screen shot na transaction ta wannan number d'in 09035938246_ _Akwai gara'basar *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shahararriyar marubuciyar nan *AMEENA ABBA UMAR* tare da novel d'in *FANSAR RAI* akan N300 kacal, ko da kud'in ka sai da rabonka_ *PAGE 5* Sai bayan sallar isha'i sannan Barr Faruk yakoma gida saida sukayi dinner da iyayenshi sannan yawuce d'akin shi yayi wanka yai shirin bacci yana hawa saman gadonshi zai kwanta nan haske yad'auke gabad'aya duhu yabayyana a d'akin, tsaki yaja tare da mik'a hannunshi saman bedside zai d'auko wayarshi sai ji yayi wayam babu komai lalubawa yashigaa yi cike da mamaki ganin a sama ya ajiyeta ammah bai gantaba, ahankali yaji ana bud'e mashi k'ofar d'aki nan yai zaune yana jira yaji wanene yashigo, tafiya yafara ji anayi a tsakiyar d'akin, cikin rashin tsoro yace wanene? Momcy?. Shuru yaji ba amsa sai ma k'arar tafiyar da aka cigaba da yi cikin d'aga murya yace koma wanene yayi magana man? Nan ma shuru sai jin wata irin k'ara yayi shuuuuuu chan kuma yaji an datse d'akin daidai lokacin haske yadawo. Mamaki yakamashi sosai yana juyawa yaga wayarshi ajiye inda ya aje ammah kuma duk ya laluba d'azu bai ji taba, ahankali yace watau wani yad'aukar min waya shine yanzu yamaido, mik'ewa yayi cikin sauri yafita yabar d'akin duddubawa yadinga yi ko zai ga wani ammah baiga kowaba har yasafko parlor su Dad ne yagani zaune shi da Mom suna ganinshi sukace ya dai Faruk lafiya kake ta sauri haka? Murmushi yayi yatsaya daga saman step yace bakomai Dad ku ne kuka shigo d'akina? Cike da mamaki sukace mu kuma? Daman na ji an shigone lokacin da aka d'auke wuta kuma ina ta magana na ji shuru. Dad kallon Mom yayi itama takalleshi sannan suka maida kallonsu ga Faruk sukace yaushe kuma aka d'auke nepa ba dai yanzu ba? Da mamaki yake kallonsu yace bakuga an d'auke ba? Yanzu fa aka maidota. Dad yace a'a Faruk akwai nepa gaskiya ba'a d'aukeba. Cikin ranshi yace toh ya akayi haka? Me hakan yake nufi,,, ganin yadda iyayen nashi suke kallonshi yasa yai murmushi yace ina ji wutar d'akina ce tad'auke tadawo bari inje inkwanta. Mom tace toh ammah kace ka ji kamar anshigo d'akin kuma bamuga kowa ya zo ya wuceba. Cikin nuna rashin damuwa yace ina ji k'ofar ce tayi k'ara bari inje inkwanta sai dasafenku. Basu kawo komai aransu ba sukace toh shikenan sai dasafe. Juyawa yayi yakoma d'akin shi cikin ranshi yana tunanin toh kodai aljannu ne suke bibiyarshi? Addu'a yayi yahau gadonshi yakwanta bai kawo komai a ranshi ba, bai dad'e da kwanciya ba bacci yai awon gaba da shi. Da asuba saida Dad yazo yatasheshi sannan yasamu yaje masallaci yasamu sallah cikin lokaci dan haka koda yadawo baccinshi yakoma..... Wajen k'arfe tara yafarka daga baccin da yake a firgice yatashi saboda mummunan mafarkin da yayi dafe kai yayi tare da furta Alhamdulillah da yaga mafarki ne yake ba gaskiya bane dan mafarkin sosai yatsorata shi. "Wata k'atuwar macijiya ce yagani tana binshi da gudu shi kuma yana ta gudu da dukkan k'arfinshi dan yasamu yatsira, a duk lokacin da zai waiga sai ya ga tana gab da taddoshi ga bakinta tana bud'ewa alamun zatayi mashi tsartuwa, k'ara gudu yake yana neman mafaka ahaka har ya iso wajen wani k'aton gida, wani irin dad'i yaji lokacin da akaron farko yayi tozali da gidan dan haka yana isa baiyi wata wata ba yashiga, daidai da ya shiga k'ofar gidan tamaida kanta tarufe sai gani yayi gidan ya koma mashi wani k'aton fili duk itace ne kawai a ciki, tsaye yayi yana bin filin da kallo chan yafara jiyo kuka ahankali yana tashi, waiwayawa yadinga yi yanaso yajiyo inda yakejin sautin kukan wata 'yar siririyar hanya ce yagani dan haka yabita yana tafiya chan bayan wani icce yahango mutum zaune, cikin sauri ya isa wajen sai ganin jawahir yayi tana ganinshi tabushe da dariya tare da mik'ewa tsaye nan take tayi girgiza sai komawa tayi wannan k'atuwar macijiyar. Saurin ja da baya yafara kafin daga bisani yajuya yacigaba da gudu nan ko macijiyar tacigaba da binshi, daga nesa da shi yahango wasu d'ungozon mutane tsaye wani irin farin ciki yaji nan yai saurin isa wajensu yana cewa kutaimaka min ammah babu wanda yakalleshi har yashiga tsakiyarsu lokaci guda yaja yatsaya lokacin da yayi tozali da mutum kwance a k'asa alamun ya mutu murya yajiyo daga bayanshi an bushe da dariya wadda takusan rikita mashi dodon kunne saida yai saurin toshe kunnuwanshi da hannuwanshi har saida dariyar talafa sannan yajanye, kunnuwanshi ne suka jiyo ana cewa wannan shine aikin da zan yi a yau d'in nan! saurin juyawa yayi sai baiga kowa ba dan haka ya ida isa wajen mutumin da yake kwance a k'asa har ya kai hannu zai janye abinda aka rufe mashi fuska da shi yaji wata irin murya ta yi mashi magana da k'arfi me kama da gargad'i ance kar kakuskura abud'e!!!! daidai nan yafarka daga baccin. Sosai mafarkin yatsorata shi saidai abun ya tsaya mashi rai sosai wai jawahir ce take bibiyarshi tana son taga bayanshi ammah kuma ba wannan ba toh shi mutumin da yagani kwance wanene shi? Tunowa yayi da muryar da take dariya tace wannan shine aikin da zanyi yau,,, sai kuma jawahir tafad'o mashi a rai jiya da take fad'a mashi gobe akwai aikin da zatayi, ahankali yace toh me hakan yake nufi? Kenan tana nufin kisa zatayi? Ture blanket d'in da yayi rufa da shi yayi cikin sauri yamik'e yafad'a toilet. Bayan ya yo wanka a gurguje yashirya ko breakfast bai tsayaba ganin momcy bata fitoba yasa yaficce yabar gidan. Motarshi yafizga cikin k'ank'anin lokaci ya isa gidan kaso, bai biya ta wajen Alhaji Mahadi ba shugaban gidan saidai yakirashi a waya yashaida mashi zuwanshi da son ganin jawahir da yake cikin sauri dan haka ya amince mashi yaturo wani ma'aikaci sukaje tare. Suna isa cikin sauri yashiga d'akin kwance yasameta gashin nan duk ya baje mata fuska da alama bacci take, ajiyar zuciya yasafke cikin ranshi yace wannan duk yaye yayen mafarki ne, juyawa yayi zai tafi sai kuma yaja yatsaya ahankali yajuyo tare da tsugunnawa a gabanta wani farin abu yagani kamar Alli anyi rubutu da shi k'ananu a kusa da inda take kwance k'ura idanunshi yayi akan rubutun sai gani yayi ansa sunan Alhaji Tanimu Nepa 10:30am, gaban Faruk saida yafad'i a fili yasake maimaita sunan sannan yace me zatayi da sunanshi ko shima ta kasheshi? Ammah kuma me lokacin yake nufi 10:30am, tsugunne yayi wajen yana tunani chan yatuno da yashiga mota ya ji a redio ana sanarwa a yau babban d'an kasuwa Alhaji Tanimu Nepa zai zo gaisuwar rasuwar d'an uwanshi da k'arfe goma jirginshi zai safka. Saurin girgiza kai yayi yace a'a bai dace ba hakan, kiran sunan jawahir yafara yi ammah shuru bata ko motsa ba batada banbanci da matacce, ganin haka yasa yaduba agogon hannunshi sai gani yayi k'arfe goma da minti biyar, ahankali yace ya kamata inyi wani abu a yanzun nan, mik'ewa yayi cikin sauri yawuce yafita ko bankwana bai tsaya yi da megadi ba kamar yadda yasaba. Motarshi yashiga yajata dagudu yabar gidan yarin, gudu yake sosai cike da tashin hankali yana cewa meyasa haka jawahir? Meyasa bazaki bari hukuma tad'auki mataki ba idan har yana da hannu a cikin mutuwar iyayenki, bazan bari kikasheshi ba yazama dole intseratar da shi dan ina son samun bayanai daga wajenshi, gudu yake sosai kamar wanda zai bar garin daidai da round d'in da zai sadashi da airport aka had'a wani irin go slow da yai sanadiyar tsaida duk wani abun hawa da yake wajen. Hankalin Barr Faruk ba k'aramin tashi yayiba tsaki kawai yakeja yana duba agogo ji yake kamar yafito yabar motar yataka k'asa ya ida isa da k'afafunshi. K'arfe goma daidai lokacin jirgin sama yasafka wanda ya iso daga k'asar Europe a filin jirgi mutane ne suke fitowa daga cikin shi chan sai ga Alhaji Tanimu ya fito cikin sauri driver d'inshi yaje ya amshi kayanshi yasaka a mota inda security suka take mashi baya dan yi mashi rakiya zuwa gidanshi kamar yadda yabuk'aci hakan dan akula da lafiyarshi, bud'e mashi mota akayi yashiga motoci biyar ne a gaban wadda yake ciki sai biyar a bayanta duk na masu kula da shi, yana zaune a gidan baya ya kame nan wayarshi tafara ringing. 'Daukota yayi yai picking fuskarshi d'auke da murmushi yake wayar yana cewa nan da mintuna kad'an zan iso gida kujirani, wani irin burki da aka ja ne yakatseshi daga wayar da yakeyi cikin 'bacin rai yakalli driver d'in yace bakada hankali? Ko bakasan aikinka ba da zaka wani ja burki haka? Ahankali yace kayi hak'uri megida nan yaja motar suka cigaba da tafiya. Camera d'in wayarshi yabud'o dan yad'auki kanshi hoto dan yatura ma iyalanshi kamar yadda suka buk'ata nan yak'yalla juyo da wayar yayi dan yaga hoton da yayi abinda yagani ne acikin wayar yai mummunan d'aga mashi hankali nan take yafara zufa cikin d'aga murya yace ma driver tsayar da motar nan!!! K'iiittttt driver yaja mota yatsaya, security na ganin haka su ma duk suka tsayar da motocinsu, Alhaji Tanimu yana jin mota ta tsaya baijira aka bud'e mashi ba yabud'e dakanshi cikin sauri yafita yatsaya tsakiyar security yana mazurai. Tambayarshi sukayi ko lafiya. Hoton da yad'auki kanshi yanuna masu yace kuduba kugani wallahi aljanah ta biyoni har ta shigar min a hoto Amsar wayar sukayi cikin sauri suka duba sai kuma suka mik'a mashi sukace basuga komai ba. Amsa yayi yasake kallo shima baiga komai ba nan yasaki ajiyar zuciya. Driver d'inshi ne yace ranka yadad'e k'ila idanunka ne sukayi maka gizo kaga kamar aljanah ammah ni dai banga komai ba. Katseshi yayi yace dallah malam rufe ma mutane baki, yanzu kowa yashiga mota mucigaba da tafiya Kowa komawa yayi yashiga mota nan aka cigaba da tafiya. Alhaji Tanimu zaune yayi yai shuru duk a tsorace yake dan shi macemacen nan sun d'aga mashi hankali sosai musamman ma ta k'anenshi ya zama dole da ya yi masu gaisa zuwa gobe zai tattara iyalansa sukoma chan Europe da zama dan chan yafiye mashi kwanciyar hankali. Yana cikin tunanin wayarshi tafara ringing dubawar da zaiyi da mamaki sai ganin number d'in Malam Salahu driver d'inshi yayi mamaki duk yakamashi yace wannan kiran fa bayan gashinan yana tuk'i shine kuma yake kiranshi. Sharewa yayi har ta tsinke a karo na biyu wani kiran yasake shigowa da wata sabuwar number, tsaki yaja sannan yai picking daga chan 'bangaren yaji muryar driver d'inshi ya ce 'Dallabai gani na iso Airport d'in banganka ba kuma antabbatar min cewa jirginku ya safka. Cikin Alhaji Tanimu murd'awa yayi sai ji kayi wani abu k'ululululuuu lokaci guda tsoro yad'arsu a ranshi yace Salahu kana nufin ba kai bane kazo d'aukata? Daga chan 'bangaren cikin rashin fahimtar maganar megidan nashi yace 'Dallabai ai cemin kayi sai goma da ishirin saisa ban zo ba sai yanzu, Alhaji tanimu sakin wayar yayi a tsorace yalek'a mazaunin driver dan ganin wanene zaune sai gani yayi wayam motar babu kowa ita kad'ai take tafiya. K'ara yasaki da dukkan k'arfinshi baisan lokacin da fitsari yakubce mashi ba nan yakai hannu zai bud'e murfin motar yafad'a waje dan bai damu da ko yaji ciwoba indai zai fita yatseratar da rayuwarshi sai ji yayi k'ofar a rufe take, bubbuga glass yashiga yi yana k'walah ma security kira a tunaninshi ta hakan zasu jiyoshi ammah babu ma wanda yasan yana yi, k'ara kallon mazaunin driver yayi yaga ba kowa still dai motar ita kad'ai take tafiya sai shi da yake zaune a cikinta, nan take yasume a inda yake zaune......... _Sis Nerja'art✍🏻_[7/24, 11:11 PM] Sis Nerja'art 2: *......FANSAR RAI......* *INTELLIGENT WRITER'S ASSO....®* [On Award Together] _Wannan Littafin na kud'i ne domin karantawa cikin aminci da yarda ga duk me buk'ata zai biya d'ari biyu N200 kacal ta wannan number d'in 09035938246, ko ta account number 5330055604, Idan katura ka aiko da screen shot na transaction ta wannan number d'in 09035938246_ _Akwai gara'basar *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shahararriyar marubuciyar nan *AMEENA ABBA UMAR* tare da novel d'in *FANSAR RAI* akan N300 kacal, ko da kud'in ka sai da rabonka_ *PAGE 6* ....Kamar an tadashi haka yafarfad'o daga suman da yayi nan yafara tunani Allah yasa mafarkine ba gaske ba abinda yagani, k'ara lek'awa yayi yaga motar dai ita kad'ai ce take tuk'a kanta nan gabanshi yacigaba da dukan ukku ukku, motsin da yajine a kusa da shi yasa yai zumbur yawaiga, wata mata ce yagani zaune gefenshi sanye cikin shiga ta alfarma ta dad'e fuskarta da bak'in glass ta juya baya tana kallon tagar mota. Saurin ja da baya yayi tare da jinginewa a jikin murfin mota kan kace mi zufa ta wanke mashi fuska dak'yar yabud'e bakinshi yana rawa yace dan Allah kiyi hak'uri kitafi ku kuke ganinmu ba mu muke ganinku ba. Juyowa tayi tare da bushewa da wata irin mahaukaciyar dariya, ahankali glass d'in fuskarta yacire kanshi nan take kyakkyawar fuskarta takoma wata irin mumunan halitta wadda ta ida firgitashi, har saida yakusan sake wani sumar yaji an wanka mashi wani gigitaccen mari ba shiri yafarfad'o, wata irin k'ara yasaki a tsorace tare da kai hannu zai bud'e k'ofar motar sai ji yayi an rik'e mashi hannu gam har saida yasake sakin k'ara. Wata irin mummunan murya marar dad'in saurarece tafara fitowa daga bakin matar muryar da tasa gabad'aya motar saida ta amsa....Alhaji Tanimu bazan ta'ba barinka ba yadda kayi silar mutuwar mijina kaima ya zama dole kamutu!!! Cikin Alhaji Tanimu katsawa yayi baisan lokacin da yafara zawo ba, cikin rawar murya yace kiyi hak'uri wallahi bansan komai ba, babu wanda nakashe dan Allah kibarni da raina. Bushewa tayi da wata mahaukaciyar dariya tace bai kamata ace ka mance zunubin da ka aikata ba na kashe Alhaji Muhammad. A firgice yamaimaita sunan yace Alhaji muhanmad? Maimakon tabashi amsa sai cewa tayi kaduba kaga motocin da suke zagaye da kai gaba da baya saidai duk da wannan tsaron ya zama dole kamutu domin na dad'e ina jiran wannan ranar bayan kun raba mijina da ranshi ni kaina baku barni ba saida kuka ga bayana sannan dukiyar d'iyata kun cinyeta saboda zalunci irin naku. Had'e hannuwa yayi waje guda jikinshi yana rawa yace dan Allah kiyi min rai wallahi bansan komai ba akai indai dukiya ce nayi maki alk'awali zan mallaka maki dukan abinda namallaka kar kikashe ni. Cikin k'araji tace mutuwarka ta zama dole Tanimu rayuwarka batada sauran amfani domin maha'inci irinka baidace yacigaba da rayuwa ba, duba agogo kaga daidai lokacin da yadace kamutu ya yi nasan bakada wata wasiyya da zaka bayar tunda babu ma wanda zaka ba a kusa. Alhaji Tanimu yana yin yunk'urin yin magana sai ganin hannun matar nan yayi ya cafki wuyanshi, numfashinshi d'aukewa yafara yi nan yacigaba da yunk'urin magana ammah yakasa, dariyar mugunta tashiga k'yalk'yatawa, nan idanuwanshi duk sukayo waje saboda tsananin shak'a, jijiyoyin kanshi duk suka mimmik'e hannu yasa zai k'wace kanshi daga mak'arar da tayi mashi ammah baida k'arfin haka dan gabad'aya k'arfinshi ya tafi nan yafara shure shuren mutuwa, saida taga jikinshi ya saki alamun ya mutu sannan tak'yaleshi tabushe da wata irin mahaukaciyar dariya daidai lokacin motar tafara kauce layi tana tafiya tana karkacewa lokaci guda tatsaya a saman titi nan duk sauran motocin suka tsaya ana tunanin lafiya motar Alhaji tai irin wannan tsayawar cikin sauri duk suka fito suka nufi wajen motar suna zuwa suka k'wank'wasa glass ammah shuru, sun dad'e tsaye a wajen ganin suna neman had'a go slow yasa d'aya daga cikinsu yafasa glass d'in da mamaki sai ganin Alhaji sukayi a kwance shi kad'ai cikin motar babu driver cikin sauri suka bud'e motar ganin kokad'an baya numfashi yasa suka d'aukeshi cikin sauri suka nufi asibiti inda wasu suka tsaya suka kira jami'an tsaro nan da nan titi yacika da mutane ana ta kora jawabi saidai abinda yafi d'aure masu kai babu driver kuma tunda suke tafiyar basuga lokacin da mota tatsayaba har driver yafita suna cikin wannan halin ne wayar Alhaji Tanimu tafara ringing d'aya daga cikin jami'an tsaro ne yad'auko wayar ganin driver d'in Alhaji ne yake kira yasa yai picking batare da ya yi magana ba, daga chan 'bangaren akace Alhaji ga dai ninan airport d'in ina ta jira ko jirgin da yasafka ba naku bane? Jami'in tsaro ne yace kana magana da jami'an tsaro muna buk'atar ganinka a yanzu. Wani wahalallen yawu yahad'e yace 'yalla'bai lafiya? Me yake faruwa? Ina Alhaji? Bai bashi amsaba saidai yafad'a mashi inda zaizo yasamesu. Cikin dak'ik'a kad'an ya iso wajen cikin d'aya daga cikin motocin Alhaji nan fa kowa mamaki yakamashi DPO yakalli security's yace wannan shine kuke nufi? Sukace eh Ogah shine mune dai zai raina ma hankali yafita bayan ya kashe Alhaji yaje yad'auko wata motar. Cikin rashin fashimtar maganarsu driver yace d'alla'bai me yake faruwa ne? Ina Alhajin? DPO yace koma menene muje station yanzu a chan sai kayi bayanin komai. Bayani kuma? Wani abune yafaru d'alla'bai? Maimakon yabashi amsa sai ma ankwa da yasaka mashi nan suka tafi da shi station. Koda aka kai Alhaji Tanimu asibiti nan aka tabbatar da mutuwarshi dan haka aka d'auki gawarshi aka kai gida hankalin iyalenshi ya tashi sosai nan sukaita kuka. DPO ne yafad'a masu wanda ake suspecting da yin kisan nan fa kowa yaita mamaki. Barr Faruk ya shiga damuwa sosai lokacin da yaga wannan go slow da aka had'a na abubuwan hawa ba adadi ya yi tsaki ya fi ak'irga musamman da yaga babbar mota ce tahad'a wannan go slow d'in, lokacin da yasamu damar wucewa yana isa airport yatarar jirgi tuni ya safka dan haka yafara tunani ina ma zaiyi shin wajen jawahir zai koma ko kuma zai je gidan Alhaji Tanimu nepa? Daga k'arshe yayanke shawara da yaje gidan Alhaji Tanimu nepa kasancewarshi babba yasa gidanshi yakasance ba 'boyayye bane dan haka yaja mota cikin sauri yanufi hanyar gidan. Lokacin da ya isa daidai lokacin aka kawo gawarshi daga asibiti a gaban idanunshi iyalenshi suka dinga kuka suna zubewa, hankalin Barr Faruk ba k'aramin tashi yayi ba cikin ranshi yace wannan aikin jawahir ne, buga motarshi yayi da k'arfi a fili yace jawahir bansan irinki ba kin cika taurin kai, ganin yadda dangin mamacin suka tashi hankalinsu duk sai abun yabashi tausayi dan haka yashiga motarshi yabar gidan. Koda aka tafi da driver chargi office tambayarshi aka yi akan mutuwar Alhaji Tanimu yanace akan baisan komai ba akai nan fa aka dinga dukanshi ammah yanacd da cewa shi dai ba shi yazo d'aukar Alhaji Tanimu ba dan a lokacin ma bai fito daga gida ba kuma koda sukayi wayar farko da Alhaji yafad'a mashi lokacin da zaizo d'aukarshi sai kuma daga baya yakirashi yace yabari sai goma da rabi lokacin jirginsu zai safka saisa ma baizo ba a lokacin sai wajen k'arfe goma da rabi, cikin galabaita yace ammah wallahi ba nine nazo d'aukar Alhaji ba. Tsayawa DPO yayi yana kallonshi yanayin yadda yai maganar babu alamun k'arya a cikinta, jinjina kai yayi yace taya zamu tabbatar da hakan bayan motar Alhaji ce wacchan ma toh wanene yad'aukota bayan kowa kai yagani. Cikin kuka yace wallahi iyakar gaskiya ta ce nafad'a maku bani bane ni lokacin ina gidana. DPO kallon police d'in da yake tsaye wajen yayi yai mashi nuni alamun yazo zasuyi magana dan haka yabiyoshi suka fita. Bayan sun fitane DPO yakalleshi yace gaskiya wannan lamarin akwai d'aurin kai a ciki banga alamar mutumin nan shine yai kisan nan ba. Yace Eh gaskiya nima na lura da haka dan jiya da mukaje gidan mukayi tambaya megadi ya ce mana yaga anfita da mota kasancewar glass d'in motar bak'ine yasa bai gane wanda yake cikiba ammah ko a lokacin ya san Driver yana cikin Quarters d'in gidan saisa baikawo komai a ranshi ba dan ya san shine kad'ai yake fita da motar toh bayan wasu mintuna kuma ya ga driver ya fito da wata motar har suka gaisa yace Alhaji zai je yad'auko airport ya san yanzu jirginsu yana gab da safka nan megadi yayi mashi adawo lafiya iya abinda yasani kenan bai kawo komai a ranshi ba game da fitar wacchan motar ta farko kuma akwai tazarar kusan rabin awa tsakanin fitar wacchan motar da wadda driver yafita da ita, babu alamun da yanuna na cewa ya ga dawowar driver bayan fitar motar farko. Fuzgar da iska DPO yayi yace tabbas hakane dan daga airport zuwa inda aka kashe Alhaji Tanimu tafiya ce me d'an nisa ammah ya akayi haka bayan kowa ya ce shine yagani a cikin motar sannan a lokacin da aka kashe Alhaji Tanimu ba'a ga tsayawar motar ba bare ace anga fitar wani toh wai duk ya hakan tafaru? Shuru officer yayi yana nazarin maganar DPO chan DPO yace saidai idan har wanda yai kisan layar zana yayi yafita daga motar toh ammah taya hakan?,,, ahankali yace jawahir fa? Juyowa yayi yakalli officer yace ina tunanin wani abu akan haka yanzu kuyi sauri kuje kubincika min motar da aka kashe Alhaji kuga ba wani hoto da aka ajiye a ciki. Ohk Sir angama. Barr Faruk koda yakoma gidan kaso samun Jawahir yayi zaune ta zuba ma gefe d'aya idanu yana isa cikin d'aga murya yace menene haka kika aikata? Tabbas nasan kece kika kashe Alhaji Tanimu miye amfanin shara'ar da ake da har bazaki iya hak'ura kotu tak'watar maki hak'k'inki ba. Mik'ewa tayi tsaye tana kallonshi ido cikin ido cikin murya me kama da ta kuka tace bana son kotu tak'watar min hak'ina nafiso ink'wata dakaina shin ni a lokacin da suka kashe min nawa iyayen wanene yak'watar min nawa hak'in? Hawaye ne suka fara gangaro mata a idanunta tace babu wanda yai k'ok'arin taimakona haka aka banzatar da maganar mutuwar iyayena sai kace ankashe dabba, shin kuna tunanin hakan baimin ciwo ba? Ko kuna tunanin 'ya'yansu zasu shiga damuwa kamar yadda nashiga? Ko kad'an bazasu shiga damuwa kamar ni ba saboda su mahaifi kawai suka rasa ni kuma har da mahaifiyata narasa. tsaye yayi yana binta da kallo matsawa tayi gaba kad'an tajuya mashi baya sannan tacigaba da cewa na rasa duk wani farin cikin rayuwata tun bayan rasuwar mahaifiyata a da ina ganin kamar bayan ran mahaifina ina da sauran gata tunda ga mahaifiyata ashe ba haka bane ita kanta saida suka rabani da ita, ban sake kwatanta shiga farin cikiba sai da yaya umar yashiga rayuwata ashe wannan ma nad'an lokaci ne, duk saboda dukiya suka rabani da kowa nawa sannan sukayi amfani da dukiyata duk wannan bai ishesu ba ina a cikin gidan nan sun je sun kwashe files d'in filayen da suke mallakina shin ni me na'aikata wanda ba daidai ba a nan? Juyowa tayi takalleshi tace dan kawai na rama abinda akayi min shikenan na aikata kuskure? Zalunta ta fa akayi ammah ba wanda yataimaka min sai yanzu da nasamu wacce take taimaka min sannan za'a ce banyi daidai ba? Barr Faruk jikinshi sanyi yayi sosai cikin sanyin murya yace ba wai haka ba jawahir ni ina tare da ke zan taimaka maki nafiso sugurfana a gaban kotu dan su wankeki daga laifin da ake zarginki da shi. Cikin muryar kuka tace ba wai zargi bane dagaske ne duk na kashesu kuma ban ta'ba nadamar hakan ba ina da burin in ida kashe sauran inyaso nima kotu tayanke min hukuncin kisa zanfi farin ciki da hakan. Jawahir duk kibar wannan kiyi yadda nace maki na maki alk'awali zan taimaka maki na ganin an hukunta duk wani me laifi ko da ace d'an uwanane ko wani makusancina yake da hannu a ciki na maki alk'awalin sai na gurfanar da shi a gaban kotu, abu guda kawai zakayi shine kisanar da ni sauran suwanene? Sannan ina kawunki da umar? Girgiza kai tashiga yi tace wannan ne ban saniba abinda dai nasani shine na kashesu, na kashe yaya umar da hannu wannan shine nadamar da nayi a rayuwata,,,, ta k'arashe fad'a tare da fashewa da kuka. Mutuwar tsaye barr faruk yayi yace dagaske kin kashesu? Ban san ya akayiba ta rabani da rabin raina dan kawai bata k'aunar aurenmu da shi bansan dalilin kasheshi ba kawai dai abinda nasani....tana zuwa nan sai kuma taja bakinta tayi shuru. Ganin haka yasa Faruk yace jawahir kikwantar da hankalinki kiyi min bayanin komai nayi maki alk'awali zan taimaka maki. Cikin sanyin jiki tace bansan me zan ce ba barrister ammah duk wani bayani yana cikin memory card d'in yaya umar. Taya zan samu memory card d'in? Girgiza kai tayi tace bana tunanin samunshi zai kasance acikin sauk'i. Cikin rashin fahimtar maganarta yace meyasa bazai kasance acikin sauk'i ba, kar kidamu kifad'a min inda zan samoshi. Shuru tayi na d'an lokaci sannan tace banaso wani abu yasameka saboda ni na tabbata bazata ta'ba barinka kaje kad'auko ba. Kinga jawahir kicire komai a ranki kifad'a min insha Allahu ni zan je ind'akko shi. Wucewa tayi wajen 'yar tagar nan tatsaya sannan tace yana a chan cikin gidanmu ina tunani a babban parlor saidai nemanshi ba abune me sauk'i ba a k'asa nayada shi nima kaina ban iya cewa ga inda yake ammah wani lokaci zan kwatanta tuna inda yake. Jinjina kai Barr Faruk yayi yace shikenan ni zan je ind'auko shi kikwantar da hankalinki. 'Daga kai kawai tayi alamun toh sannan takoma tazauna tare da had'e kai da gwiwa tana jin wani irin ciwo a ranta dan ya ta'bo mata inda yake mata k'aik'ayi. Ganin haka yasa Barr Faruk yajuya yafita. Ko da police suka je suka bincika motar basu samu wani hoto ba dan haka suka koma suka sanar da DPO duk da haka saida yakira Alhaji Mahadi yatambayeshi jawahir yashaida mashi tana nan cikin gidan yarin ba'a fita da ita ko'ina ba. Saida Drivern Alhaji Tanimu yayi kwana ukku a wajensu suka tabbatar da badai shi d'in bane yai kisa sannan suka sakeshi kisan ya d'aure ma kowa kai nan jama'a suka dinga tunanin aljannu ne inda DPO yafi tunanin da sa hannun jawahir a ciki saidai baida shaidar da zai iya zarginta ya dai bar abun a ranshi. _Sis Nerja'art✍🏻_ [7/24, 11:11 PM] Sis Nerja'art 2: *......FANSAR RAI......* *INTELLIGENT WRITER'S ASSO....®* [On Award Together] _Wannan Littafin na kud'i ne domin karantawa cikin aminci da yarda ga duk me buk'ata zai biya d'ari biyu N200 kacal ta wannan number d'in 09035938246, ko ta account number 5330055604, Idan katura ka aiko da screen shot na transaction ta wannan number d'in 09035938246_ _Akwai gara'basar *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shahararriyar marubuciyar nan *AMEENA ABBA UMAR* tare da novel d'in *FANSAR RAI* akan N300 kacal, ko da kud'in ka sai da rabonka_ *PAGE 7* Bayan ya bar gidan yarin tun a mota yakira Barr Bilal a waya yatambayeshi inda zai sameshi yafad'a mashi yana gida dan haka direct yawuce gidan Barr Bilal yana isa yakirashi a waya yafito bayan sun gaisa ne yace Barr Bilal wani taimako ne nake nema a wajenka. Barr Bilal yace toh Barrister Allah dai yasa ba akan case d'in jawahir bane. Murmushi yayi sannan yace kaidai ka cika tsoro kuma anyi sa'a akanshi ne. "Toh fa ka ji irinta nidai gaskiya Barrister kayi hak'uri wallahi ina tsoron case d'in yarinyar chan ban shirya mutuwa yanzu ba". Dariya Barr Faruk yayi yace toh ai mutuwa tana kan kowa kaga kakwantar da hankalinka yanzu bari muyi maganar da takawo ni. Barr Bilal cikin sanyin jiki yace toh shikenan oga ai dole abi abinda kakeso. Jingine jikinshi yayi a motarshi sannan yace Barr Bilal shin ko zaka iya rakani gidan su jawahir? Sannan idan akwai wani abu da kasani agame da 'yan gidansu inaso kasanar da ni. Shuru yayi nad'an lokaci sannan yace toh gidansu dai na sanshi saidai a rufe yake a yanzu sannan mutanen gidansu a yadda naji duk sun mutu ko ma ince suna cikin wad'anda takashe. Da mamaki Barr Faruk yake kallonshi yace dagaske ta kashesu har da Umar? Cikin rashin fahimtar abinda yake nufi yace wanene kuma shi? Shuru Barr Faruk yayi cikin ranshi yace Jawahit mi yasa kika aikata wannan kuskuren? Chan kuma yaja numfashi yace shikenan zanje muyi magana da Alk'ali zan san yadda zanyi in samo makullin gidansu muje dan akwai abinda nakeson d'aukowa zuwa gobe. Toh nidai zan dai rakaka intsaya nesa da gidan ammah babu abinda zaisa inshiga dan inason raina. Murmushi Barr Faruk yayi yace toh shikenan babu damuwa hakan ma nagode yanzu bari inje inga Alk'ali. Barr Bilal yace toh Barrister koma me kenan sai kata'boni a waya. Toh shikenan sai ka ji ni suna yin sallama yashiga motarshi yatafi. Ya yi niyar zuwa wajen alk'ali sai kuma yayi tunani key d'in wajen DPO kawai zai iya samunshi dan haka daga nan yawuce chan station wajen DPO yai mashi bayanin abinda yakeso, tambayarshi DPO yayi me zaya d'auko a cikin gidan?. Barr Faruk yace akwai bincike me muhimmanci ne da yakeson yi a cikin gidan. Wannan ba hujja bace babu abinda zaka samu akan bincikenka kadai tsaya bincikenka akan jawahir. Murmushi Barr Faruk yayi yace ammah ai ina akan aikina ne kuma aikina ya bani dama zan iya kowane irin bincike a matsayina na lauya. Jinjina kai DPO yayi yace shikenan idan har aikinka ya baka dama sai kayi yadda kaga ya dace ammah ni bazan bada key d'in gidanba saboda bai dace ashigaba tunda ba kowa a ciki. Shuru Barr Faruk yayi bai sake cewa komai ba dan ya san DPO ya fad'i hakane dan kawai yana jin haushinshi akan 'yar tsamar da sukayi, daga k'arshe ma yatashi yatafi yana tunanin yadda za'a yi yasamu key d'in gidansu jawahir. Haka dai yakoma gida har sukayi lunch yana tunanin mafita Momcy ko ta yi mashi tambayoyi ba adadi akan ganin yadda yake ta tunane tunane tun da suka zauna yin lunch saidai yace mata bakomai daga k'arshe yace gajiya ce bacci kawai yakeson yi, yana gamawa tace yatafi yahuta dan haka yatafi part d'inshi a parlor yakwanta yana tunanin yadda zai 'bullo ma lamarin yana a haka bacci yayi awon gaba da shi. Baifi baccin minti talatin ba yafarka saboda mafarkin da yayi saurin tashi zaune yayi cikin ranshi yana addu'a Allah yasa mafarkin shi yakasance gaskiya kallon agogo yayi yaga k'arfe hud'u ta gota dan haka yatashi yawatsa ruwa sannan yayi sallah yana gamawa yazari key d'in motarshi yaficce yabar gidan. A karo na biyu yakoma gidan kaso nan yanemi buk'atar sake ganin Jawahir aka amince mashi yana shiga yasameta kwance tana ta bacci nan yatsaya yana tunanin ko yatasheta yatambayeta saidai kuma bayason tashinta, ya yi kusan minti goma a tsaye yana tunanin yadda zaiyi, gefe d'aya kuma yana tunanin mafarkin da yayi cikin ranshi yace wannan ai mafarkine bai zama dole yakasance gaskiya ba jawahir da take nan ciki a ina zata samu key d'in gidansu? Chan kuma yayi wani tunanin dan haka yawuce wajen dutsin nan nacikin d'akin yana dubawa bayanshi da mamaki sai ganin keys yayi guda biyu nan yad'auko mamaki duk ya ida cika shi cikin ranshi yace tabbas yarinyar nan akwai abubuwa masu rikitarwa a tare da ita taya za'a ce tana cikin gidan nan me tsaro ammah a tare da ita akwai wasu abubuwa batare da sanin kowa ba, toh ammah kodai aljanarta take kawo mata? Inko hakane mezaisa bazatayi k'ok'arin fitar da ita daga gidan ba? Ganin ta motsa ne yasa yakatse tunaninshi yawuce yabar d'akin, k'arar rufe k'ofar da megadi yayi ne yasa tafarka daga baccin da take ahankali tabud'e idanunta tashi tayi zaune tajingine kanta a jikin bango kan kace mi hawaye sun fara wanke mata fuska wanda ita kad'ai tasan dalilin yin haka chan kuma sai tamik'e tanufi wajen 'yar k'aramar tagarnan da haske yake shigo mata ta nan tatsaya wata tsuntsuwa ce guda d'aya take ta shawagi a wajen nan jawahir tazuba mata idanu tana kallonta tana murmushi chan sai ganin tsuntsuwar tayi ta haye saman wani icce dake bayan d'akin ta girgiza ta zama k'aton maciji, tsaye jawahir tayi tana kallonshi nan taga ya tunkaro inda take ahankali tace Ammi. Yana isowa wajen tagar tayi saurin ja da baya nan macijin yashigo dogo ne sosai dan saida yanannad'e jikinshi saboda tsawon d'akin bazai iya d'aukar ko rabinshi ba ahankali tace Ammi mi kikeso agareni? Wani irin haske tagani ya fito daga bakin macijin sai gani tayi hasken ya kauraye d'akin lokaci guda macijin yazama siffar wannan tsohuwar, matsowa tayi a dudduk'e tatsaya gefen jawahir cikin shak'ak'ar murya wadda bata fita sosai tace kina ta aikata kuskure a karo na ba adadi jawahir kin cika taurin kai. Kallon tsohuwar take chan kuma sai ta janye idanunta tace Ammi taya kike tunanin zaki cigaba da samuna cikin ruwan sanyi bayan laifin da kika aikata min? Bushewa da dariya tsohuwar tayi tace a wajenki ne hakan yakasance laifi ammah ni a wajena ba haka bane. Cikin d'aga murya tace saboda kin tsaneshi saisa kike ganin haka kinyi amfani da damarki kin rabani da farin cikina alhalin bai........maganar me gadi ce tajiyo yana cewa ke kuma dawa kike surutu haka? Kallon Ammi tayi da take tsaye tana kallonta sannan tajuya takalli megadi batare da tayi maganaba dan ta san baiga Ammi ba. Cikin fad'a yace ke baki iya nusuwa kamar yadda sauran sukeyi sai kullum kidinga damun mutane da surutu kar kibari insake jin bakinki. Har yagama maganar yajuya yatafi jawahir batace mashi komai ba tamaida kallonta ga tsohuwar da take cigaba da kallonta har ta bud'e baki zatayi magana tsohuwar tatari numfashinta tace jawahir taurin kanki ne yasa kike cigaba da zama nan da ace zaki ajiyeshi da ni zan fitar da ke daga nan ammah wanchan barristern yana so yashiga sha'ani na kuma gab nake da inyi maganinshi... Tun kan tarufe baki jawahir tace shin shima zaki kasheshi ne kamar yadda kika kashe sauran? Wane laifine ya aikata maki? Bushewa tayi da dariya tace jawahir duk abinda naso shi nake aikatawa. Cikin fad'a jawahir tace a wannan karon bazan ta'ba bari ki aikata abinda kika so ba. Cigaba da dariya tsohuwar tayi nan jawahir tawuce takoma tazauna tana kallo tsohuwar ta'bace, tura hannuwanta duka biyun tayi cikin gashin kanta. Bayan sallar isha'i yana kwance a d'akinshi ya d'age kanshi sama yana kallon ceiling Momcy tashigo d'akin baiji shigowarta ba sai ji yayi ana shafa mashi kai, lumshe idanunshi yayi tare da yin murmushi. Faruk meyasa kake yawan damun kanka da tunani baka tsoron wani abu yasameka. Tashi yayi zaune yana cigaba da murmushi yace momcy ba tunani nake ba. Zama tayi gefenshi tace Faruk ni mahaifiyarka ce nafi kowa sanin halinka na san kana son Nasiba saidai zuciyarka bazata barka ba, naso ace ka yi masu yadda sukeso dan subaka aurenta. Rik'o hannun mahaifiyar tashi yayi yace momcy kiyi hak'uri indai har Nasiba rabona ce zan sameta kicigaba da tayani da addu'a kawai, cikin sanyin jiki tace shikenan faruk insha Allahu zan cigaba, wata leda tamik'a mashi tace ga wannan Malam ya aiko maka dashi d'azu. Amsa yayi yace nagode zan kirashi zuwa gobe tunda yanzu dare yayi. Momcy tace toh shikenan bari intashi intafi Daddynka na chan na baro shi kad'ai. Murmushi yayi yace toh Mom sai dasafe. Allah yakaimu Son. Washe gari wajen 11am barr faruk yakira Barr Bilal yafad'a mashi zai zo yarakashi gidansu Jawahir nan Barr bilal yace yanzu zasu shiga kotu ne saidai da anjima dan haka Barr Faruk yace shikenan zuwa anjiman sai muje. Bayan sallar la'asar ne Barr Bilal dakanshi yazo gidan yad'auki Barr Faruk suka kama hanya tunda suka fara tafiya kowa shuru yayi chan Barr Faruk yaga shurun ya yi yawa duk surutun Bilal ammah yau ya yi shuru dan haka yajuyo yakalleshi yace ya dai Barr Bilal lafiya yau naga ka yi shuru? Ta'be baki yayi yace taya kake tunanin zan iya magana bayan zaka kaini inda zan mutu wallahi Barrister da ace ba kai bane babu wanda zaice inje gidan in amince inje dan ina tsoron gidan kamar yadda nake tsoron yarinyar chan. Murmushi Barr Faruk yayi yace kaifa ka ji matsalar ka tsoro wani abu ne akace ke akwai acikin gidan? Ni ban saniba ammah tunda har yarinyar tafito daga gidan ai dole yakasance abun tsoro, kabarni incigaba da lazumina kawai. Shuru Barr Faruk yayi cikin ranshi dariya yake ma Barr Bilal akan tsoron shi da yayi yawa ahaka har suka isa sai ji yayi ya ja mota ya tsaya a gaban wani gida. Kallon gidan Barr Faruk yayi yace wannan shine gidan? Girgiza kai yayi yace ga gidan chan gaba. Da mamaki Barr Faruk yake kallon dank'areren gidan da Barr Bilal yanuna mashi wanda a cikin layin babu gida me girmanshi da kyaunshi koda gidajen wajen suna da kyau sosai yace kana nufin wanchan shine gidan? Murmushi yayi yace eh ai ba abun mamaki bane ga wanda yasan kud'in megidan nidai ina daga nan bazan k'ara matsawa ko ina ba sai kafita ka ida takawa. Murmushi Barr Faruk yayi yace shikenan ba damuwa daman nima banaso ka isa har k'ofar gidan saboda na fad'a maka ba da sanin hukuma nazo ba banaso asan na zo kajirani bari inshiga infito. Cikin sanyin jiki yace toh shikenan Allah yasa kafito lafiya ammah dai kadinga addu'a. Baice mashi komai ba yawuce yatunkari gidan fitowa Barr Faruk yayi daga cikin motar rik'e da 'yar brief case d'in Faruk dan ya yi tunanin zai tafi da ita sai kuma yaga ba haka ba dan haka yatsaya yana kallonshi cikin ranshi yana mamakin rashin tsoron Barr Faruk. Yana zuwa k'ofar gidan tsayawa yayi saida yaga babu kowa gaba da baya sannan yad'auko makullen nan yabud'e k'ofar yashiga k'aton fili ne yafara cin karo da shi duk ganyaye suna ta yawo a tsakiyar filin hango k'ofar da zata sadaka cikin gidan yayi yaga rufe take nan yataka ya isa yana zuwa yasa gudan key d'in yabud'e duk ya'nah ce da k'ura shiga yayi yana bin part parts d'in gidan da kallo yana tunanin wane part yakamata yashiga tunowa yayi da mafarkin da yayi d'akin da yagani tabbas kamar parlor ne koda babu kaya a cikinshi toh ammah wane parlorn daga ciki? Tsaye yayi yarasa wanda zai shiga ya yi kusan minti biyar tsaye a wajen shi kad'ai sai chan yafara tunanin labarin jawahir a k'arshen inda tatsaya mashi murmushi yayi yace babban parlor zan shiga cikin sauri yanufi wajen parlorn yana zuwa yatura k'ofar yajita a rufe makullen da suke hannunshi yasa zai bud'e ammah yak'i bud'uwa daga chan gefe yajiyo k'ara kamar ansa key anbud'e wani d'aki waiwayawa yayi baiga kowaba dan haka yaje yafara tura k'ofofin d'akunan saidai dukkansu a rufe suke ta k'arshence yana turawa yaji a bud'e ajiyar zuciya yasafke tare da kallon k'ofar d'akin tabbas k'ofar ce yagani acikin mafarkinshi ahankali yafurta Alhamdulillah! Tura k'ofar d'akin yayi yashiga ya'na ce tafara yi mashi sallama a fuska yayi saurin cireta nan yaja yana bin d'akin da kallo k'ura ce sosai aciki kasancewar gidan ya dad'e babu kowa a cikinshi tsaye yayi yana tunanin ta ina zai fara neman Memory Card d'in da zai taimaka mashi wajen samun k'wak'warar shedar da yake nema kuma tabbas yana cikin d'akin, saidai baisan ta inda zai faraba bayan duk tulin k'urar dake cikin d'akin runtse idanunshi yayi yana ji kamar yajuya yakoma baya saidai tabbas yasan sai ya samo Mcard d'in sannan zai iya samun abinda yake nema. Maganar jawahir ce ta cikin mafarki tafara dawo mashi lokacin da yaga ta jawoshi ta shigo da shi cikin gidan ta nuna mashi wani d'aki mai jan k'ofa tace kashiga nan a nan cikine kawai zaka iya samun memory d'in daga farkon d'akin zuwa tsakiyar d'akin kar kawuce nan zaka sameshi tana fad'in haka ta'bace. Bud'e idanunshi yayi cike da k'warin gwiwa yaduk'a yafara lalube a cikin tulin k'urar dake k'asan dakin a nutse yake lalube daga yad'auko dutsi sai yad'auko wasu abubuwan ahaka har saida yazo tsakiyar d'akin har zai cigaba sai yatsaya ganin ya zo tsakiyar d'akin dan haka yacigaba da lalube sannan yaji ya ta6o wani d'an abu k'arami cikin sauri yadauko goge shi yashiga yi chan yayi murmushi tare da furta Alhamdulillah tabbas shine cikin sauri yamik'e tsaye kawai sai ji yayi k'ofa ta maida kanta ta rufe dak'arfi, juyawa yayi yakalli k'ofar daga bayanshi yaji wata plastic chair da tasha k'ura tana motsi nan ma yayi saurin juyawa ammah baiga kowa samanta ba sai gani yayi kamar anjata tazo dagudu ta wuce fit tagabanshi A karo nafarko da yaji gabanshi ya fad'i ammah cikin dakewa yace wanene? Fitilun dake cikin d'akin ne suka fara d'aukewa suna kawowa nan yayi saurin juyawa zaije wajen k'ofa sai gani yayi hasken d'akin ya d'auke koda da rana ne ammah wani irin duhu yabayyana har baya ganin abinda yake gabanshi Memory Card din yayi saurin zurawa acikin aljihunshi yad'auko wayarshi dan yahaska sai ji yayi anfizge wayar ta fad'i k'asa wata irin dariya yaji anfara cikin wani irin amon murya gabad'aya d'akin yana amsawa, nan yai saurin runtse idanunshi yafara karanta duk addu'ar da tazo a bakinshi. Murya me k'arfi ce yaji tana tashi tana cewa baka isa kashiga gonata ba bazan ta'ba barinka ba idan har kafita da wannan abun da kad'auka ni na ajiye shi ni nake tsaronshi babu wanda ya isa yad'aukeshi batare da izini na ba. Hannu yasa cikin sauri yatoshe kunnuwanshi da yakeji kamar dodon kunnenshi zaiyi zillo yafad'o saboda k'arfin muryar cigaba yayi da karanto addu'o'i daga bakinshi wata irin k'ara yadinga ji yai saurin bud'e idanunshi sai ganin wani k'aton dutsi yayi wanda yahaske d'akin ya yo saitin inda yake tsaye cikin sauri yamatsa gefe guda ta gefenshi dutsin yawuce yafad'i rijim a bayanshin nan k'ura tabaje d'akin, tari yafarayi yana son yashak'i numfashi ammah babu ta inda zai ji iska saboda k'urar da tacika a d'akin, duk ya fita hayyacinshi ammah duk da haka bai daina addu'ar da yakeyi ba chan yaji wata irin iska me k'arfi ta taso chan kuma sai yaji iskar ta lafa nan haske yabayyana a d'akin, d'aukar wayarshi yayi da take k'asa yayi saurin fitowa daga cikin d'akin yana tari jawo k'ofar yayi yarufe. A chan 'bangaren Barrister Bilal dake tsaye waje jikin mota a tsorace yana jiran fitowar Barr Faruk nan yahango wani irin duhu ya bayyana a gidan kallon inda yake yayi yaga haske ammah cikin gidan duhu ne zufa ce tafara kwararo mashi tsoro duk yabayyana a fuskarshi k'afafuwanshi rawa suka fara briefcase din dayake rik'e da ita hannunshi yasaki, bakinshi yana rawa yafara karanta wa'innahu sulaimana wa innahu bismillahirrahmanur rahim ssaids fitsari yakusa yakubce mashi saboda tsoro tunani yayi yashiga mota yagudu kawai dan baya tunanin Barrister Faruk zai fito da rai bare ma yasamu nasarar d'auko abinda yakaishi cikin gidan yana cikin tunanin yaga hasken gidan ya dawo, bud'e motar yayi zai shiga sai ganin Barr Faruk yayi ya fito yana atishawa da tari jikinshi duk ya yi farin k'ura cikin sauri yanufi wajenshi yana isa yace lafiya Barrister ya akayi naganka haka? Mik'a mashi key d'in yayi alamun yarufe gidan, amsa yayi yarufe sannan yarik'eshi suka nufi wajen mota yana mashi sannu yana cewa saida nace kar kashiga gidan nan ammah kashiga. Dafe k'irjinshi yayi da yake mashi zafi ahankali yace kawuce da ni gidana. Amsawa yayi da toh nan yakama hanyar gidan Barr Faruk. _Sis Nerja'art✍🏻_ [7/24, 11:11 PM] Sis Nerja'art 2: *......FANSAR RAI......* *INTELLIGENT WRITER'S ASSO....®* [On Award Together] _Follow me on Wattpad: *Sis-nerja*_ _Wannan Littafin na kud'i ne domin karantawa cikin aminci da yarda ga duk me buk'ata zai turo katin Mtn na d'ari biyu N200 kacal ta wannan number d'in 09035938246, ko ta account number 5330055604, Idan katura ka aiko da screen shot na transaction a wannan number d'in 09035938246_ _Akwai gara'basar *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shahararriyar marubuciyar nan *AMEENA ABBA UMAR* tare da novel d'in *FANSAR RAI* akan farashin N300 kacal, ko da kud'in ka sai da rabonka_ *PAGE 8* Suna isa gidanshi a tare suka shiga ciki Barr Faruk bai tsaya sauraren surutun da Bilal yakeyi mashi ba yawuce toilet yana shiga yamaida k'ofa yarufe nan yatsaya a bakin k'ofa yana tunanin abinda yafaru da shi tabbas a yanzu ya ida gasgata maganar Jawahir akan aljanar nan, ya dad'e tsaye kafin daga bisani yasamu yayi wanka yafito, shiryawa yayi cikin kayan shi da yake da su a gidan sannan yafito parlor yasamu Barr Bilal zaune yana shan lemu, yana ganinshi murmushi yayi yace Barrister yanzu har ka fito fes ba kamar lokacin da muka zo ba wai me yafaru da kai? Zama yayi saman kujera yai shuru kamar bai ji abinda yace ba sai chan har Barr Bilal ya fitar da rai da samun amsar shi sai ji yayi ya ce babu komai kawai dai gidan ne ya yi k'ura sosai saisa kaga na fito duk k'ura jikina. Barr Bilal ba dan ya yarda ba yace ammah Barrister na hango gidan ya yi duhu babu haske wallahi na tsorata sosai da guduwa zanyi. Murmushi Barr Faruk yayi yace ni banga hakan ba kaga tashi muje masallaci gashichan anfara kiran sallar magrib. Mik'ewa sukayi sukayo alwallah suka kama hanyar masallacin da yake a cikin anguwar. Bayan sun dawo Barr Bilal yayi mashi sallama yakoma gida shi kuma Barr Faruk yayi zaman shi nan dan yasamu yayi aikinshi a nutse, bayan sallar isha'i kiran Dad yayi yace kar atsaya jiranshi bazai dawo gida ba zai kwana a gidan shi saboda akwai aikin da yake a yanzu Dad ya amsa mashi da toh tare da yi mashi addu'ar fatan nasara. Wajen k'arfe goman dare d'auko laptop d'inshi yayi da yajona charge sannan yad'auko memory d'in yasaka a cikin wayarshi yana kunna wayar wata irin k'ara tayi me kama da tsawa dan har saida yatsorata. Cikin recording yashiga yaga guda d'aya ne nan yakai hannu zai kunna kamar an fizgi wayar sai ganinta yayi ta k'wace daga hannunshi ta fad'i k'asa mik'ewar da yayi zai d'auko nan haske yad'auke gabad'aya gidan duhu yabayyana duk'awa yayi yafara laluben wayarshi har ya lalubota zai d'auka sai ji yayi anjata ta matsa, tsayawa yayi mamaki duk ya cikashi lokaci guda yaji k'arar bud'e k'ofar bedroom d'in kuma yaga hasken wayar ya kunnu ta d'an haska d'akin hannu yakai a karo na biyu zai d'auka sai gani yayi tawuce ta yi hanyar waje dagudu mik'ewa yayi yana cewa wanene yake ja min waya? Wai wanene? Shuru yaji dan haka yabi wayar tashi ana cigaba da janta a k'asa shi kuma yana bi har saida sukazo daidai wani d'aki wanda babu komai a cikinshi suna zuwa k'ofa tabud'e ja yayi yatsaya cikin ranshi yana karanta addu'o'i dan lamarin ya fara bashi tsoro yana nan tsaye wayar tashige d'akin baiyi niyar shigaba yana tsaye a cikin bak'in duhun nan yajiyo ringing d'in wayar sai jin muryar Nasiba ta cikin wayar yayi tana cewa Hello Faruk ban ta'ba tunanin zaka iya rabuwa da ni ba Faruk ka san ina sonka dan Allah kadawo gareni,,, tana fad'in haka tafashe da kuka, cike da mamaki yace Nasiba kuma? Kirana tayi a wayar? Jin sautin kukanta yasa yayi saurin shiga d'akin yana shiga k'ofa tamaida kanta da k'arfi tarufe nan hasken wayar yad'auke d'akin yayi dund'um da duhu wata irin sautin murya yaji me kama da kukan hadari ta bushe da dariya duk d'akin ya amsa, Faruk nan fa gabanshi yafad'i ammah kokad'an bai nuna alamun tsoroba yana cigaba da addu'a a cikin zuciyarshi jin yadda ake cigaba da dariyar babu k'ak'k'autawa yasa cikin dakewa yad'aga murya yace wai wanene nan? Bai rufe bakiba yaji anjawoshi da k'arfi anbuga kanshi da bango wani irin zogi yaji yai saurin sulalewa k'asa yazauna tare da rik'e kan da yakeji tamkar ya fashe, murya yafara jiyowa me k'arfi cikin gurnani ana cewa ka yi kuskure Faruk da har kashiga rayuwata na gargad'eka kar kafito da memory d'innan ammah saida kafito da shi, toh bazan ta'ba barinka ba yau d'in nan sai naga bayanka. Sai a lokacin yafahimci kowacece tabbas aljanar nan ce ta gidansu jawahir bud'e baki yayi cikin juriya yace baki isa kiga bayana ba saidai ni inga naki bayan. Sake bushewa tayi da dariya a karo na biyu sannan tace ka yi k'arya kaga bayana zan iya rabaka da ranka a duk lokacin da naso. A harzuk'e yamik'e tsaye koda babu haske a d'akin cikin d'aga murya yace bazaki iya kasheni ba ammah ni zan iya rabaki da rayuwarki ta hanyar karanta maki ayoyin ubangiji, bai jira jin abinda zata ce ba yafara karanta wasu ayoyi daga cikin alk'ur'ani, wata irin k'ara tafara yi wadda taso tatada 'yar k'aramar girgizar k'asa a d'akin, saurin toshe kunnuwanshi yayi dan yasan k'arar zata iya yi mashi lahani a kunne sannan yana cigaba da addu'ar k'ofar d'akin ce tashiga bud'ewa da rufe kanta dak'arfi chan kuma sai yaji an daina k'arar d'akin ya d'auki tsit daidai lokacin hasken gidan yadawo, ajiyar zuciya yasafke tare da kallon wayarshi da take a k'asa tsakiyar d'akin, zuwa yayi yad'auka hannunshi d'aya yana dafe da kanshi yafita daga d'akin, dudduba saura d'akunan yayi yaji babu wata alama da aljanar za'ace ta shiga dan haka yakoma bedroom d'in duk wannan abun baisa yatsorata ba dan dama Faruk ba dai kafiya ba indai yasa kanshi yin abu babu abinda zai hanashi yana komawa yayi joining d'in wayar da laptop d'inshi yatura recording d'in acikin laptop d'in sannan yakunna wata irin k'ara yajiyo shuuuuu kamar iska dan haka yad'auko wayarshi yakunna karatun alk'ur'ani yasa volume sannan yad'auko earpeace yasaka yakunna recording d'in acikin laptop d'in... Muryoyine yafara ji suna tashi a ciki hakan yasa yagane cewa cigaban inda tatsaya da rubutun tane acikin diary d'in: *CIGABAN LABARI* Jawahir cigaba da kallon Malamin tayi tana nishi inda shima yake kallonta kamar irin zakin nan da yake neman abinci ido rufe, ganin batada niyar shigowa yasa yad'ebo wani abu yawatsa mata wata irin k'ara tasaki tare da ida shigowa d'akin taja tatsaya a gaban malamin, Ummah jikinta rawa kawai yake tana jin kamar tasaki fitsari a nan inda take tsaye, Umar ko wani irin haushi da takaici suka cikashi lokaci guda yafara jin tsanarta cikin ranshi yana cewa tabbas a yanzu na ida gasgatarwa itace tarabani da d'an uwana, Abba ko zufa yafara yi shi kanshi ya tsorata dan bai ta'ba kawo ma ranshi itace take kisan ba. Malamin kallon su Abba yayi yace kun ganta daman na fad'a maku fatalwa ce take cikin gidan nan. Su duka sukace fatalwa kuma? Wannan ai jawahir ce kuma bata mutu ba. Hannu yamik'a yana karanto wani abu me kama da yare sai gata ta tsugunna a gabanshi nan yadafa kanta yana cigaba da karatun nan tafara k'ara chan yasaki kanta yakalli su Abba yace tabbas akwai fatalwa a tare da yarinyar nan kuma itace take tsorata ku. Umar mik'ewa yayi a fusace yace ba wai fatalwa kad'ai ba jawahir ce take amfani da damarta tana kisa itace takashe su Aliyu, zumbur Ummah tamik'e tace jawahir d'in takashe min d'a? Fashewa tayi da kuka tace akan wane dalili zatayi min haka me d'ana yatsare mata? Mik'a mata hotunan hannunshi yayi yace gasu a wajenta nagansu tare da wannan wuk'ar kuma ina tunanin next target d'inta Abba ne. Zuface tacigaba da kwararo ma Abba lokaci guda yajik'e sharkaf kamar wanda aka watsa ma ruwa saurin mik'ewa yayi ya amshi hotunan yana kallo tabbas hoton Aliyu ne da na Abokinshi kuma irin hotunan da aka dinga tsinta ne lokacin da aka kashe su Alhaji Jamilu Cikin wata irin firgitattar murya tabushe da dariya wadda tasa saida baki d'ayansu suka juya suka kalleta mik'ewa tsaye tanemi tayi nan malamin yasake watsa mata wani abu me kamar gari nan tafasa k'ara tare da komawa tazauna, a karo na biyu tasake yunk'urin mik'ewa yad'ebo abun zai watsa mata tayi saurin sa hannu takare nan wata irin iska tataso maganin yazube, yunk'urin d'ebo wani yayi nan tabushe da dariya tare da mik'ewa tsaye cikin sauri, muryarta ta rikid'e ta zama kamar irin kukan mafad'acin dokin nan bud'e baki tayi tafara magana wadda tasa gabad'aya d'akin ya amsa sunan Alhaji Mu'az takira sannan tacigaba da ce baikamata wannan yasa kashiga damuwa ba idan har zaka iya tunawa da abinda ka aikata ma d'an uwanka kaine kasa aka kasheshi sannan nima karabani da raina tabbas nasan wannan bokan ne yayi maku aiki akaina bazan ta'ba barin duk wanda yake da hannu ba akan mutuwata sai naga bayanshi, a yau d'innan zan rabaka da rayuwarka a gaban iyalanka kafara k'irga dak'ik'un mutuwarka daga yanzu.....bata rufe baki ba taji an shak'eta da wani abu me kama da igiya k'ara tasaki tana yunk'urin k'wacewa ammah takasa malamin ne yashak'eta da wani abu me kama da igiya na tsafi nan yashiga karanta wasu d'alasimai yana zagayeta kuka tafara yi ahankali chan kuma tafasa k'ara daganan bata sake cewa komai ba. Abba jin kalamanta da yayi ba k'aramin tsorata yayi ba dan har fitsari yasaki bai saniba, ummah ko bata da banbanci da wanda yasuma dan d'if wuta tad'auke mata tun lokacin da taga jawahir ta taso kusan bata ma san abinda take cewa ba. Umar ranshi ba k'aramin 'baci yayi ba yace watau yarinyar nan gani take ma su Abba suka kashe mata mahaifi saisa take son raina ma mutane wayo har tana ik'irarin rabashi da rayuwarshi... Muryar malamin suka ji yana cewa wannan ba wani abu bane tabbas a lokacin da aka saka mata laya a cikin baki anyi ganganci domin akusa da iccen suri aka saka saisa fatalwarta tatashi, kukwantar da hankalinku ni zan kamata yanzun nan in tafi da ita. Abba saurin matsowa yayi wajen shi jikinshi yana rawa yace dan Allah malam kataimaka mana wallahi indai baka tafi da ita ba kasheni zatayi kamar yadda takashe abokaina zan baka ko nawa kakeso na yi maka alk'awali dan Allah kataimaka min. Malam yace kar kadamu zanyi bakin k'ok'arina kakwantar da hankalinka dan ta riga ta zo hannu daga yanzu zata zama tarihi dan kun gama ganinta. Umar kallon mahaifin nashi yayi yace Abba indai har kana da hannu akan mutuwar Abbu to baka kyauta ba, saurin juyowa yayi yakalleshi yace kai banza ne wanene yafad'a maka dagaske ne kawai dai so take taga ta kasheni saisa tayi wannan k'aryar ni bansan komai ba akan mutuwar d'an uwana, taya ma zan iya kashe shak'ik'ina bayan halarcin da yayi min a rayuwa idan har akace na kasheshi toh tabbas na zama butulu. Cikin fushi yace toh shikenan saidai ni kuma ya zama dole inbi ran d'an uwana dan sai na d'auki *FANSAR RAI* kamar yadda takasheshi itama zan kasheta ban damu da aljannun k'aryarta ba! Abba saurin girgiza kai yayi yace a'a Umar kar kayi haka kabar ma malam komai shi ya san yadda zaiyi da ita. Malam zuwa yayi yabud'e jakkarshi yad'auko wata kwalba da wani abu cikin wata 'yar roba yanufo wajen da jawahir take a d'aure, bud'e idanunta tayi dakyar tana kallonsu a galabaice ahankali tabud'e baki tace me yasa zakuyi min haka, Abba nice dan Allah kukwance ni ummah, Abba murmushi yayi yace munafuka ai yau kema dole kimutu kamar yadda kikaso kikashe mu. Ahankali tace kisa kuma? Da yaushe nace zan kasheku? Kallon umar tayi da yake ta huci tace yaya umar dan Allah kace susakeni kar sukasheni. Tsanarta ce tagani k'arara a idanunshi ranshi a 'bace yace idan har su basu kasheki ba ni zan kasheki dan d'aukar ma d'an uwana fansa tabbas ke butulu ce jawahir duk halarcin da nayi maki a rayuwa baki ganiba. Hawaye ne suka gangaro mata tace Yaya Umar bai dace kace hakaba wannan ba shine butulci ba, shin laifi ne dan na d'auki fansar ran iyayena? Tsawa yakwatsa mata yace ya isheki haka! wanene yakashe iyayen naki kina nufin Aliyu? Juyawa tayi takalli malam da yaruntse idanunshi yadage yana ta karanto wasu d'alasimai a cikin wani abu me kamar mai cikin roba, wata irin razanannar k'ara tasaki nan kamanninta suka fara sauyawa k'iba tafara k'arawa lokaci guda sukaga ta rikid'e ta koma wani k'aton biri malam saurin bud'e idanunshi yayi kafin yayi yunk'urin yin wani abu tuni ta fisge igiyar tsafin da yad'aureta da ita wani irin tartsatsin wuta yatashi tasa hannu takare fuskarta. Ummah saman kujera tayi saurin fad'awa tare da fasa k'ara tace mun shiga ukku wayyo jama'a kutaimaka min, Abba ko saurin ja da baya yayi yatsaya bayan Umar da yake rik'e sa wuk'a yana nunata alamun idan har ta iso zai caka mata, bushewa tayi da wata irin mahaukaciyar dariya sannan tace bazan ta'ba fasa abinda nayi niya ba. 'Debo maganin malam yayi dasauri zai watsa matayi tayi saurin gocewa ya sake d'ebowa a karo na biyu nan ma tagoce, zai sake d'ebowa tasa dogon hannunta tak'wa'be robar nan yazube. Girgiza tayi tadawo siffar Khausar Ammin jawahir gashin nan nata ya mimmik'e saman iska juyawa tayi takalli Abba nan tanuna shi da hannunta sai gashi ya yi saman iska, wuntsila wuntsila yafara yi da k'afafu saitin da fanka take wanawa tanufa da shi nan yafara ihu, cikin sauri malam yanufi wajen 'yar jakkarshi nan tayi saurin juyawa tanuna jakkar da yatsa sai ga hayak'i yana fita cikinta k'ara malam yasaki cikin sauri yad'auko jakkarshi da mamaki yake kallon khausar da tunda yake itace aljanar da tata'ba ja da shi ganin yadda hayak'i yake fita daga cikin jakkarshi yasa yayi layar zana ya'bace cikin sauri dan kar ta'ba mata tsafi. Umar na ganin haka yayi sauri yanufi inda mahaifinshi yake kafin ya isa gashin khausar wani siriri guda ya shak'o wuyan Alhaji Mu'azu sai gashi a jikin fanka ta d'aureshi, ummah saurin mik'ewa tayi takoma bayan kujera ta'boye. Umar saita khausar yayi da wuk'ar hannunshi cikin sauri yanufo inda take zai caka mata hannunta tanuna shi da shi sai ga wani irin haske ya fito yanufi wajenshi sakin wuk'ar hannunshi yayi yasa hannuwanshi duka biyun yashak'e wuyanshi karkata kanta tayi tana k'yalk'yala dariya nan shima yakarkata kanshi yana so yajanye hannunshi daga wuyanshi ammah ya kasa saboda tsananin mak'arar da tasa yayi, chan sai tayi wurgi da shi yafad'a k'asa yana nishi ummah da take tsaye bayan kujera tana kuka cikin sauri ta iso wajenshi tana zuwa tarik'eshi tana cigaba da kuka. Khausar kallon Abba tayi da yake saman iska saitin fanka nan wani haske yafito daga idanunta sai ga gashinta ya sargafe akan fankar k'ara Abba yafara yi yana neman agaji, dariya tacigaba da k'yalk'yalawa tace mu'azu nice ajalinka kamar yadda karaba ni da mijina da rayuwarmu har kanaso kaga bayan 'yata a yau buri na zai cika zan kasheka kaima kamar yadda nakashe sauran mugayen abokanka dan haka dak'ik'un mutuwarka sun kusa cika, bud'e baki yayi a galabaice yana so yayi magana ammah ya kasa sai nishi da yakeyi sama sama duk jijiyoyin kanshi sun mik'e, idanuwanshi sunyo waje, ja tad'anyi da baya nan fanka tacigaba da juyawa da Abba yana ta wuntsila k'afafu saboda tsananin azaba har wuyanshi yakare ranshi yarabu da jikinshi. Ummah ko tana zaune a gaban idanunta Abba yamutu kuka kawai takeyi tana kiran sunan Alhaji. Faruk hankalinshi yana fara dawowa jikinshi ganin yadda tayi ma mahaifinshi yasa yasake yunk'urin mik'ewa dak'yar yajawo wuk'ar yanufi wajenta zai caka mata a karo na biyu, juyowa tayi tanuna shi da hannunta sai ga wani haske ya bayyana me kama da shocking yana shiga jikin umar nan yafara k'ara, murmushi tayi tace na so in k'yaleka ammah ka nema ma kanka mutuwa dan haka dole kaima kamutu, fad'uwa yayi k'asa yana tirje tirje Ummah mik'ewa tayi dak'yar tana kuka tafara takowa muryarta tana shak'ewa tana kiran sunan umar chan sai tayanke jiki tafad'i k'asa. Nuna Abba tayi da hannu sai gashi ya fad'o k'asa a mace, ja tayi da baya tare da tsagaitawa daga dariyar da take nan wani haske yafara fita daga jikinta sai ga suffar jawahir kamanninta ya dawo saurin bud'e idanunta tayi, akan Abba tasafkesu da yake kwance k'asa abinda yafaru ne yafara dawo mata a k'walwa har zata nufi inda Alhaji Mu'azu yake kamar ance tajuya tana waigawa sai ganin umar tayi kwance yana ta shure shure. Cikin sauri ta isa wajenshi jikinta yana rawa ta tallabo kanshi tad'aura saman cinyarta tare da fashewa da kuka tace Yaya Umar dan Allah katashi muje asibiti, kallonta yake yana motsa baki yana so yayi magana ammah ya kasa, ganin haka yasa jawahir tak'ara sautin kukanta tana cigaba da kallon masoyin nata, chan taji muryarshi chan k'asa a hankali ya ce na tsaneki jawahir, tsagaitawa tayi daga kukan da take cike da mamaki take kallonshi tace Yaya umar meyasa zaka tsaneni ba laifina bane. Juyar da kanshi yayi yana kallon ceiling ahankali yake motsa baki kamar me karanta wani abu chan kuma sai taga ya ja numfashi da k'arfi ya rufe idanunshi. girgiza shi tafara yi tana cewa dan Allah Yaya Umar katashi kar katafi kabarni, duk yadda take girgizashi ammah ko motsi bayayi ganin haka yasa tafasa wata irin k'ara wadda tasa gabad'aya gidan saida ya amsa, rungumeshi tayi jikinta tana cigaba da kuka tana cewa dan Allah katashi ina sonka ina son cigaba da rayuwa da kai, Yaya Umar kaine gatana idan kabarni ban san halin da zan shiga ba, kaga taso muje ga abinci chan na girka inzuba maka kaci yau ranar farin ciki ce agaremu ranar zagayowar shekarar aurenmu ina sonka sosai Yaya Umar, sumbatu tadinga yi kamar zararra, ganin har lokacin bai motsa ba yasa tasake fasa wata k'ara tace Ammi meyasa kikayi min haka kin rabani da rabin rai na wallahi na tsaneki bana k'aunarki ke azzaluma ce. Bata rufe bakinta ba sai ga Ammi ta bayyana cikin wata irin mummunan halitta zaune saman iska ta kishingid'a kamar wadda take zaune saman kujera, cikin muryarta marar dad'in saurare tace shin laifi ne dan na taimaka maki na rabaki da wanda yayi yunk'urin kasheki? Cikin kuka jawahir tace k'arya kike Umar bai chan chanci hakaba bazai ta'ba kasheni ba tabbas a yanzu na yadda da maganarki da kika ta'ba cewa sai kin rabani da shi toh a yau kin rabani da shi hankalinki ya kwanta saidai ina so kisani na tsaneki fiye da yadda natsani su Abba a rayuwata. Bushewa tayi da wata irin mahaukaciyar dariya tace yau kece kike ik'irarin cewa kin tsani mahaifiyarki wadda tafi kowa k'aunarki saboda soyayyar wani? Matsowa tafara yi kusa da jawahir Janye Umar tayi cikin sauri tare da d'auko wuk'ar da ke gefenta tamik'e tsaye tace eh na fad'a na tsaneki kika saki kika matso kusa da ni sai na kasheki. Rage sautin dariyarta tayi tace daman ni ai matatta ce banda sauran rayuwa saidai ina so kijanye kalmar tsanar da kikayi min, kiduba kiga bayanki babban mak'iyinki ne kwance a mace, runtse idanu jawahir tayi hawaye suna zubo mata, ta'ba hannu aljanar tayi sai ga hotuna guda ukku sun bayyana a hannunta ajiyesu tayi a k'asa gaban jawaahir tace duba hotunan nan na san zakiyi farin ciki idan kika ga guda daga cikinsu, ahankali tabud'e idanuwanta da suka fara kumbura tasafkesu akan hotunan guda na Abba ne sai na Yaya Umar a kan na k'arshen tatsaida idanunta tare da fashewa da kuka hoton ta ne ita da iyayenta suna rungume da ita, saurin duk'awa tayi tad'auki hotonsu ita da iyayenta sannan tamaida kallonta ga Aljanar d'an guntun murmushi tayi sai kuma tahad'e fuska lokaci guda sannan tace na tsaneki ke ba Ammina bace. Bushewa tayi da dariya a karo na ba adadi saida tayi me isarta sannan tace kidaina furta kalmar tsana agareni ya zama dole kidinga min biyayya. Cikin d'aga murya jawahir tace baza'ayi maki biyayya ba daga yanzu ina so kifita daga rayuwata babu ke babu ni idan har kika sake shiga rayuwata zan kasheki! Wata irin k'ara aljanar tasaki tace wannan kuskure ne kike aikatawa jawahir. A fusace jawahir tanufi wajenta da gudu rik'e da wannan wuk'ar tun kan ta isa Aljanar tanuna ta da yatsanta me kama da sanda sai ga wata iska ta taso tana zuwa sai d'aukar jawahir tayi tai wurgi da ita sai gata chan gefe ta fad'a ta baya dak'arfi. Kwance tayi k'asa tana jin wani irin zafi a bayanta, chan kuma tayi yunk'uri tatashi zaune. Matsowa Aljanar tayi kusa da ita tamik'a mata hannu alamun tamik'o hannunta. Hawaye ne suka cigaba da fita daga idanun jawahir ba tare da ta mik'a hannunta ba tace na tsaneki Ammi kikasheni kawai kamar yadda kika kashe Yaya Umar inko baki kasheni ba ni zan ga bayanki bana k'aunarki. Muryar Aljanar ce tafara fita bibiyu tace wannan kuskure ne kike aikatawa na gargad'eki akan kidaina cewa kin tsaneni ammah kin k'i to dasannu zani azabtar da ke yadda baki tunani kisaurareni. Alhaji Tanimu koda ya iso gidan a k'ofar da zata sadaka da cikin gidan yatsaya yakira wayar Alhaji Mu'azu ammah har ta k'arashi ringing bai d'agaba kusan missed call biyar yayi mashi yana shirin yin na shidda ne yajiyo anfasa k'ara a cikin gidan dan haka cikin sauri yanifi cikin gidan yana shiga yai sallama yaji shuru a parlor yafara jiyo kuka ahankali yana tashi dan haka yanufi parlorn yana d'aga labule da gawar Alhaji Mu'azu yafara cin karo..... _Sis Nerja'art✍🏻_ [7/24, 11:11 PM] Sis Nerja'art 2: *......FANSAR RAI......* *INTELLIGENT WRITER'S ASSO....®* [On Award Together] _Follow me on Wattpad: *Sis-nerja*_ _Wannan Littafin na kud'i ne domin karantawa cikin aminci da yarda ga duk me buk'ata zai turo katin Mtn na d'ari biyu N200 kacal ta wannan number d'in 09035938246, ko ta account number 5330055604, Idan katura ka aiko da screen shot na transaction a wannan number d'in 09035938246_ _Akwai gara'basar *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shahararriyar marubuciyar nan *AMEENA ABBA UMAR* tare da novel d'in *FANSAR RAI* akan farashin N300 kacal, ko da kud'in ka sai da rabonka_ *PAGE 9* Cikin sauri yashiga parlorn yanufi wajen gawar tashi yatsaya cike da firgita yace Alhaji Mu'azu lafiya? Kwanciyar me kakeyi nan ko bakada lafiya ne? Jin sautin kukan jawahir yasa yajuya sai a lokacin yakula da ummah da ke shimfid'e k'asa itama babu alamun numfashi atare da ita gefe guda kuma jawahir ce wajen gawar Umar tana jijjigashi tana kuka, tsorata yayi sosai cikin sauri ya isa wajen jawahir yana zuwa akid'ime yace ke me yasamesu ya akayi suke a nan ba dai mutuwa sukayi ba dai ko? Ko d'agowa batayi takalleshi ba bare yasa ran samun amsar tambayarshi ganin haka yasa yace tambayarki nake me yafaru da su? Nan ma shuru wuk'ar da yagani gefenta ne yasa a fusace yace bazaki bani amsar tambayar da nake maki ba? Sai a lokacin tajuyo takalleshi da rinannun idanuwanta da suka fara firgicewa kallo d'aya tayi mashi tad'auke kai shi kanshi saida yasha jinin jikinshi ammah hakan baisa yayi shuru ba jinjina kai yayi yace wannan mutuwa sukayi kuma nasan kece kika kashesu, mi yasa zaki kashesu? Me suka aikata maki? Wallahi bazan ta'ba barinki ba ya zama dole hukuma tasani kema akasheki. Mik'ewa tayi tsaye bai ankaraba kawai sai ganinta yayi gabanshi baisan lokacin da ta isoba har saida yad'an tsorata, kallonshi tatsaya yi bata ko k'yaftawa ganin haka yasa yad'an ja da baya dan yanayin kallon da takeyi mashi na tuhuma ne cikin dakewa yace ke lafiya ko nima kasheni zakiyi kamar yadda kika kashe sauran? Wallahi sai na sanar da hukuma. Sai a lokacin tabud'e baki dak'yar cikin dashewar murya tace Alhaji Tanimu Nepa ka zo ne dan ka amshe sauran dukiyata a wajen Abba ko? Gabanshi wani irin mummunan fad'uwa yayi dak'yar yahad'iye wani yawu dake mak'ale cikin bakin shi nan yafara inda inda yace ni ni kuma? A'a ni ni ziyara nakawo mashi. 'Dan guntun murmushi tayi tace na san komai,, matsowa tafara yi wajenshi yayi saurin ja dabaya yace k'aryane ni bansan komai ba akan dukiyarki wai ma wacece ke? Binshi tafara yi yanda cigaba da yin baya baya tace tabbas nasan haka kuma nasan kana da hannu akan mutuwar mahaifina kaima. Tsorata yayi sosai da jin maganar da tayi cikin ranshi yace wanene yasanar da ita mune muka kashe iyayenta bayan lokacin da mukayi maganar a d'aki muka yita mu takwas ne acikin gidan babu wani mahaluki a ciki toh ammah kuma....muryarta yaji ta ce wannan haka yake na san kana da hannu a ciki. Hanyar k'ofa yanufa yana cewa a'a bansan komai ba akan mutuwarsu. Tsaye jawahir tayi tana kallonshi chan sai tafad'a saman kujera tazauna tare da dafe kanta ganin haka yasa yayi saurin juyawa zai bar d'akin sai jin muryarta yayi ta ce idan har kasanar da wani abinda yafaru sai na kasheka! Da gudu ya ida fita ko motarshi bai tsaya shiga ba dan kar ma ya'bata lokaci yabar gidan. Wani irin kuka tadinga yi a nan inda take zaune k'arar wayar da taji kusa da itane yasa tajuya sai ganin wayar Umar tayi tana d'aukowa taga recording ne yayi saving cikin sauri takunna tana saurare taji duk abinda yafaru ne akayi recording a tsorace ta ajiye wayar tana tunanin wanene yayi recording d'in...... Faruk yana gama saurare ajiyar zuciya yasafke ahankali yace watau abinda yafaru kenan dukkansu ta kashe har da Umar? Toh ammah banji.....k'arar buga gida yafara jiyowa ana knocking nan yakalli agogo yaga duka k'arfe d'ayan dare cike da mamaki yace to wanene yake buga gida a wannan lokacin ko dai megadi ne Mik'ewa yayi sai ji yayi andaina bugawa har zai je yabud'e sai kuma yafasa yakoma yazauna. Dariya ce yafara jiyowa tana tashi daga wajen tagar d'akinshi dan haka yak'ara sautin karatun alk'ur'ani sannan yacigaba da aikinshi har wajen k'arfe biyun dare sannan yakwanta bacci. Wajen k'arfe sha d'aya yaje gidan kaso yana isa yasamu jawahir tsaye a wajen da tasaba tsayuwa, tsayawa yayi daga bayanta har ya bud'e baki zaiyi magana sai jin muryarta yayi cikin sheshek'ar kuka ta ce ka yi k'ok'ari sosai da har ka iya ku'buta daga hannun Ammin saidai ina baka shawara kacigaba da addu'a dan itace zata cigaba da tseratar da kai daga sharrinta dan daga baya na gane ba taimako kawai Ammi ta ke ba har da zalunci take tunda har ta iya kashe wanda baida hak'k'i acikin mutuwar Abbu............. A lokacin da nagama sauraren recording d'in na yi mamaki sosai kuma na tabbatar Yaya Umar ne yayi shi tabbas a ranar na san dole sai police sun zo tunda har nayi sakacin barin Alhaji Tanimu a raye yafita saidai ban yi nadamar abinda Ammi ta aikata ba saidai rad'ad'in mutuwar Mijina da nakeji, cikin sauri nad'auko wayar dan inaso tazama sheda akan abinda na aikata dan akasheni nima sai ji nayi an fizge wayar daga hannuna sai gani nayi ta fad'i k'asa safkowa nayi daga saman kujera zan d'auko wayar sai gani nayi anjata tayi hanyar k'ofa tsayawa nayi ina kallonta sai jin muryar Ammi nayi ta ce bazan ta'ba bari kid'auki wayar nan ba babu wanda ya isa yad'auketa har yasaurari abinda yafaru. Juyawa jawahir tayi tana waige ammah bata gantaba dan haka tafara takawa saida tad'auki diary d'inta da Umar yashigo da shi parlorn, sannan tanufi wajen k'ofar sai wayar tacigaba da tafiya tafita daga cikin d'akin motsin da takeji a bayantane yasa tagane Ammi tana bayanta dan haka tacigaba da tafiya har saida takai wajen wani bokitin k'arfe da tafiddo d'azu zata d'ibi ruwan mopping tagoge kitchen dan a lokacin da akayi abin 'yar aikinsu ta je gidansu zata kwana biyu, rarimo bokitin tayi cikin sauri tajuya daidai lokacin da Ammi take bayyana cikin zafin nama tabuga mata shi a kai, sannan tayi wurgi da shi da sauri tad'auki wayar dagudu tanufi d'akin 'yar aikinsu da bakomai a cikinshi tana shiga tazauna k'asa jikinta yana rawa tabud'e wayar taciro Memory card d'in, dariya tafara ji gabad'aya d'akin yana amsawa da ita cikin wata irin kakkausar murya taji muryar Ammi tana cewa kin aikata kuskure jawahir bazaki ta'ba yin nasara ba akan abinda kike son samu. Rik'e memory d'in tayi gam a hannunta cikin rawar murya tace k'arya kike Ammi baki isa kihana ni samun abinda nakeso ba, na fad'a maki kifita daga rayuwata bana sonki na tsaneki. Wata irin k'ara taji anfasa sannan cikin muryar fushi taji Amminta tana cewa ina gargad'inki da furta kalmar tsana agareni jawahir domin hakan zai iya jawo maki shiga cikin wani irin mawuyacin hali a rayuwarki. Cikin kuka tace taya zan daina tsanarki bayan kinyi amfani da jikina da hannuna wajen kashe mijina? na tsaneki Ammi, tana fad'in haka tahad'e kai da gwiwa tacigaba da rusa kuka. Bayan fitar Alhaji Tanimu wayarshi yad'auko yakira DPO yashaida mashi abinda yafaru nan DPO yace yajirasu gasunan zuwa. Jawahir tana cikin kukan tajiyo jiniyar motoci ammah hakan bai sa tad'ago ba dan tasan daman tabbas sai hakan ya faru, tana jiyosu suna shigowa cikin gidan inda wasu duk suka zagaye gidan parlor suka fara shiga inda suka ga su Alhaji Mu'azu kwance, tsaye sukayi a wajen gawarwakin suna dubawa DPO hana kowa yayi yata'ba gawarwakin yace aje azo mashi da duk wani mahaluki da yake cikin gidan sannan yakira likita a waya. Tana jiyo police suna bud'e sauran d'akuna ammah bata motsaba har suka shigo cikin d'akin da take zaune tsawa suka daka mata sukace me take a nan bata ko d'ago kai ba bare har tatanka masu dan haka biyu daga cikinsu suka shugo suka kamata memory d'in ne yakubce daga hannunta yafad'i tana so tayi magana ammah takasa babu wanda yalura da shi daga cikinsu saidai suka d'auko wayar Umar suka fita da ita a parlor suka kaita suka zaunar da ita k'asa inda tatadda megadinsu shima a zaune yayi zugum yana kallon gawarwakin iyayen gidanshi. DPO kallonta yayi sannan yamaida kallonshi ga Alhaji Tanimu dake tsaye wajen gawar Abba yace wannan ce Alhaji?. Kallonta Alhaji Tanimu yayi sannan yace Eh itace tabbas ita takashesu. Daidai lokacin likita ya iso yana duba Abba da Yaya Umar yace ai sun mutu ammah ummah suma tayi dan haka aka tafi da ita asibiti. Matsowa DPO yayi yatsugunna gabanta yana k'are mata kallo har lokacin kanta sunkuye k'asa tana hawaye jinjina kai yayi yace me zakice a game da mutuwar mutanen nan? Shuru tayi bata amsa mashi ba, damk'o gashinta yayi tayi saurin runtse idanunta yace tambayarki nake shin kece kika kashesu? A nan ma ban bashi amsar tambayar da yayi min ba muna a haka aka kawo mashi hoton Yaya Umar da na Abba wanda Ammi ta ajiye min ansa maker an yi masu tick koda yaduba yaga exactly irin wanda duk yatsinta ne lokacin da aka kashe su Alhaji Jamilu dan haka yasa aka kamani aka tafi da ni policestation aka rufe ni tsawon kwana biyu yana bincike inda yatabbatar da nice nayi kisan daga nan yamakani a kotu, kwana biyun nan da nayi kusan kullum sai Alhaji Tanimu ya zo ya dubani abinda yake bashi mamaki bana tare da wata damuwa atare da ni kuma har lokacin ban bud'e baki nayi magana ba, duk zuwan da Alhaji Tanimu yakeyi so kawai yake imbud'e baki in amsa ma police nice nayi kisan ammah nak'i a ranar da aka mik'a case d'ina kotu koda yazo yake tambayata shin ko akwai hanyar da zanbi inkare kaina a kotu? 'Dan guntun murmushi nayi ganin shi kad'ai ne a wajen yasa nace kar kadamu da wannan saidai ina so kaje kafara shiri dan kaine mutum na gaba da zaka bak'unci lahira. Dariyar mugunta yayi yace taya kike tunanin zaki kasheni bayan ke hukuncin kisa ne za'a yanke maki bazan ta'ba bari kibar gidan ba koda kin bari a gidan kaso rayuwarki zata k'are, , sannan duk wasu takardu da suke mallakinki na samu nasarar d'auko su a cikin gidan ku zan mallake dukkan dukiyarki hatta ta cikin account d'inki zanyi k'ok'arin ganin na mallaketa. Murmushi tayi a karo na biyu tace wannan ba matsala bane saidai inaso kasani daga kai har wad'anda kake tare d su babu wanda zai iya tsere wa daga hannuna dole sai kun mutu kamar yadda sauran suka mutu. Dariya Alhaji Tanimu yadinga yi har saida aka zo aka koma da jawahir d'akin da take a rufeta. Ranar litinin aka zo aka d'auketa cikin motar 'yansanda aka tafi da ita kotu koda aka je batace uffan ba tana ganin lauyoyi biyu suna ta fafatawa da wani lauya da taso taganeshi ammah takasa wanda yake a matsayin shi yake kareta har aka gama shara'ar bata fahimci komai ba tana ji ana ta mata tambayoyi saidai tabisu da idanu. Ganin bata amsa cewa itace tayi kisan ba yasa Alk'ali yayanke mata hukuncin zama gidan yari na tsawon sati biyu kafin adawo zama na biyu, daga nan kotu aka wuce da ita gidan mata inda aka had'eta d'aki guda da wasu mata biyu masu irin laifinta na kisa,, saidai su kallo d'aya zakayi masu kaga babu alamun imani atare da su mugaye ne nan fa suka fara mata gani gani tare da nema surainata. Saidai duk wannan baisa jawahir takula su ba saidai tayi zaune waje d'aya tayi shuru tana jinsu suna ta hira ammah bata kulasu ko kad'an bataga alamar damuwa a tare da su akan zaman da suke a cikin gidan kason nan ba, inda ita kuma saboda rashin sabo yasa takasa sakewa tana ji gabad'aya rayuwar ta canza mata saidai ko kad'an batayi nadamar abinda ta aikata ba, kusan kullum sai anzo anfita da su an kaisu sunyi aiki me wahala, a duk lokacin da suka fita dan yin aikin jawahir bata k'ara sanin inda hankalinta yake har sai anmaidasu d'an kurkukun d'akinsu. Bayan sati d'aya lauya me kareta yazo aka fiddota aka kaita wajen da aka tanada dan ganawa da me laifi idan aka zo ziyartar shi musamman ma lauyoyi idan har lauyan ya buk'aci haka, koda tazo taga shine wanda taga yana kareta a kotu tsayawa tayi tana kallonshi murmushi yayi yace sannu jawahir na san dai kin sanni a matsayina na abokin mahaifinki yakamata kikwantar da hankalinki kinutsu ki amsa min duk tambayoyin da zanyi maki ni zan taimaka maki kifita daga gidan nan. Tunda yafara magana idanu tazuba mashi tana kallonshi har yakai aya sai a lokacin tayi murmushi tace Barr Mubarak ko? Shima murmushin yayi yace Eh haka ashe kin gane ni ai na d'auka bazaki iya tunani ba tunda tun bakida wayau sosai narabu da zuwa gidanku, nayi mamaki sosai da yakasance d'iyar abokina ce take rayuwa a nan gidan kaso har ake yayata labarinta a gari akan cewa ta yi kisa wannan dalilin ne yasa nazo inwanke ki akan zargin da akeyi maki. Tarar numfashinshi tayi tace ba wai zargi ba Barrister bana buk'atar taimako irin naka domin baka dace kataimaka min ba katafi kawai. Murmushi yayi yace baidace kice haka ba ga wanda yakeson taimaka maki. Itama murmushin tayi cikin alamun nuna rashin damuwa tace fiye ma da hakan zan ce gareka barrister katafi kawai kanuna tausayawarka ga wani na daban ba wai wacce takasance abokiyar gabanku ba. Da mamaki yake kallonta yace abokiyar gabanmu fa kikace? Wacece abokiyar gabanmu kuma ni da wa? Ta'be baki tayi tace na san ka san komai, koma me kenan da sannu zan fahimtar da kai. Haka suka rabu Barr Mubarak bai samu had'in kan jawahir ba a rana ta biyu koda yadawo nan ma bai samu yadda yakeso ba har suka zauna zama na biyu a kotu nan ma bata amsa laifinta ba akan zargin da akeyi mata dan haka akace ak'ara mata wata d'aya a gidan kaso sannan adinga sata aiki me tsanani. Saida tayi sati biyu tana faman wahala duk wani aiki me wuya ana sata saidai abinda zai baka mamaki jikinta bai ta'ba nunawa ba, a lokacin da take sati na ukku ne Barr Mubarak yazo dan yagana da ita koda aka fiddota wajen da zasu gana kallonta yayi yai murmushi yace sannu malama jawahir Idanu tazuba mashi batare da ta ce komai ba ganin haka yasa yacigaba da cewa jawahir taurin kanki ya yi yawa kin sanni kuma kinsan taimaka maki zanyi kisamu kifita da gidan nan dan baidace da ke ba a matsayinki na d'iyar babban mutum irin Alhaji Muhammad kibani had'in kai intaimaka maki. Idanu tazuba mashi batare da ta ce komai ba ganin bata da niyar yin magana yasa yad'auko wasu takardu yamik'a mata yace amshi wannan signing kawai nakeso kiyi min idan har kikayi ni kuma na yi maki alk'awalin zan taimaka maki wajen ganin kin bar gidan nan. Kallon takardun tayi sai taga na filaye ne guda biyu ga sunan Mahaifinta nan a jikin takardun, d'an guntun murmushi tayi sannan tace ba wai ka zo da niyar taimako na ba kawai dai kace ka zo da niyar cin dukiyata kaima, a matsayinka na abokin Abbuna baka kasance mutumin kirki irinshi ba. Kinga ba wannan natambayeki ba indai har kinason barin gidan nan ya zama dole kiyi abinda nakeso inko ba haka ba kina ji kina gani za'a kasheki. Matsowa tayi kusa da shi tace toh menene dan na je inda iyayena sukaje! Ko ance maka bansan lokacin da kaje katsaya ma Abba ba wajen ganin kun k'wace ma Ammina hak'inta ta k'arfi da yaji ba? Kasan komai akan dukiyar mahaifina ammah son zuciya yahana kafad'i gaskiya, kuma tabbas nasan su Alhaji Tanimu ne suka turoka wajena, tir da hali irin naka. Dariya Barr Mubarak yayi yace dakyau na ji dad'i da kika gane hakan a yanzu tunda kinsan halina ya kamata ki cika wad'annan takardun dan samun ku'butar ki daga gidan nan inko ba haka ba a banza zaki mutu sannan dukiyar da take mallakinki zata dawo k'ark'ashinmu hatta companyn mahaifinki kinga shikenan zuri'ar Muhammad me shadda ta zama tarih.....bai gama rufe baki ba tayi kukan kura tayo kanshi kafin yayi wani yunk'uri ta shak'e mashi wuya da dukkan k'arfinta, k'ok'arin k'wacewa yafara ammah yakasa dan k'arfin ba na mutum d'aya bane, buga table yafara yi dak'arfi sai ga masu kula da ita sun shigo dan dama suna bakin k'ofa nan fa aka fara k'ok'arin k'waceshi, kuka jawahir tadinga yi cikin d'aga murya tana cewa bazan ta'ba bari hakan yafaru ba bazan barka ba barrister, saida kusan maza biyar suka taru sannan suka samu suka 'ban'bare hannunta daga wuyan barrister mubarak tari yafara yi, bugunta suka fara yi a wajen saida suka bugeta sosai har tasuma sannan aka jata aka maidata d'akinta. Barr Mubarak ya dad'e a wajen tsaye rik'e da wuyanshi yana tari idanuwanshi sunyi jajir kafin daga baya yad'auki takardunshi yafita. Yana barin nan wani makeken gida yaje a parlorn gidan yasamu su Alhaji Tanimu su ukku zaune suna ganinshi suka fara murmushi wani da yake zaune kusa da Alhaji Tanimu ne yace ya dai barrister muna fata dai angama komai. Zama yayi tare da tsiyaya wani swan water da yake saman center table yasha saida yashanye kofi guda sannan ya ajiye kofin yace hmm ina fa hakan yasamu yarinyar chan saura kad'an takasheni.. Su duka idanu suka zuba mashi sukace garin ya? Ajiyar zuciya yasafke yace yarinyar chan ina tunani aljannu gareta. Dariya Alhaji Tanimu yayi yace muma ai Aljannun kanmu ne akan kud'i haba Barrister ya kamata kayi wani abu man kar fa kamance da mak'udan kud'ad'en da mukayi maka alk'awalin su kaga idan har kataimaka mana tayi signing shikenan zaka iya zare hannunka akan case d'in inyaso ma akasheta babu ruwan wani. Shuru Barrister Mubarak yayi kamar me nazarin wani abu ya d'auki mintuna sosai yana nazari sai chan yace kubarni da ita na san yadda zanyi tasa hannu yau d'innan zanje wajen likitana yataimaka min da wata allura ce da na caka mata ita zata fita daga hayyacinta na san a lokacin zata amince tayi signing d'in batare da ta saniba. Su dukansu dariya sukasa sukace lallai barister ashe k'walwarka tana ja sosai. Dariya shima yayi yace yoh ba dole tajaba ai bazan ta'ba mancewa da rashin mutuncin da Alhaji Muhammad yayi min ba lokacin da nanemi yataimaka min da wasu kud'i zan biya bashi yace min baidasu bayan gabana aka kawo mashi wata leda cike da kud'i sai cewa yayi wai ba na shi bane na ajiya ne aka kawo mashi, saidai dubu d'ari yabani ni da nake neman million guda, koma menene kukasance cikin shiri gobe dan zan kawo maku takardun nan da signing d'in yarinyar chan. Shewa suka dinga yi a wajen suna cigaba da tattaunawa sun d'au lokaci sosai suna tattaunawa kafin su rabu akan gobe zasu sake had'uwa. Barr Mubarak bayan ya bar nan kamar yadda yayi alk'awali saida yabiya wajen wani likita amininshi yasamo allurar sannan yawuce gidanshi lokacin da yakoma iyalanshi duk basu nan yana shiga d'akinshi wanka yayi yafito parlor yana magana shi kad'ai yana cewa wato har wannan lokacin su madam basu dawoba su da nace kar suyi marece tsaki yaja tare da zama bisa 3 seater yad'auko remote yana canza channel sallama aka yi aka shigo ciki ciki ya amsa nan wata babbar mata tashigo da tray d'auke da abinci da lemu ta ajiye a gaban Barr Mubarak tace 'Dalla'bai ga abincinka Hajiya tace akawo maka idan ka dawo, tana fad'in haka tatashi cikin sauri tafita tabar d'akin, saida tafita sannan yajuyo yakalli tray d'in, a karo na biyu aka sake sallama matar ce yaga ta dawo kallo d'aya yayi mata yad'auke kai dan shi ya tsani 'yan aiki suna shigo mashi d'aki, zuwa tayi ta ajiye wani jug da tashigo da shi tatsiyaya mashi kunun aya tamik'a mashi tace Alhaji ga shi. Juyowa yayi a wulak'ance yakalleta yace ni nasaki kizuba min? Girgiza kai tayi tace a'a. Toh bar nan wajen A saman table d'in da yake gabanshi ta ajiye sannan tamik'e tafita. Tsaki yaja tare da kallon cup d'in ganin had'ed'en lemun kankana ne yasa yad'auka yafara sha dan yana son shi sosai, saida yasha kusan kofi biyu sannan yabarshi. Bayan magrib yana zaune yafara jin cikinshi ya fara ciwo tun yana d'aukar abun wasa sai gashi ya kwanta har akayi sallar isha'i yana murd'e murd'e matarshi koda tadawo taganshi a wannan halin hankalinta ya tashi sosai dan haka taje tad'auko wayarta dan takira family doctor d'insu tana fita yana kwance yana ta murd'e murd'e sai ganin wata irin mata me mummunan halitta yayi ta bayyana a gabanshi tana tsaye tana kallonshi koda yana cikin halin ciwo saida yatsorata yunk'urawa yayi zai tashi ammah yakasa, murmushi tayi wanda yasa hak'oranta suka bayyana waje, Cikin zafin ciwo yace wacece ke? Me kikazo yi a nan. Rikid'a tayi takoma siffar kamannin Jawahir, yunk'urin mik'ewa yayi nan tanuna shi da hannunta sai gashi ya koma ya kwanta a nan take duk kasala tarufeshi. Zagaye gadon da yake kwance tayi tana dariya saida tayi me isarta sannan tace bazan baka damar magana ba saboda bana buk'atar jin komai daga bakinka tambayar da kayi min itace maganarka ta k'arshe a duniya, kamar yadda nayi alk'awali bazan ta'ba barinka ba bare har kasamu damar cutar da ni dan haka kafin ka kasheni ni zan fara shafe babin rayuwarka, idanu Barr Mubarak yazuba mata yana kallonta ko hannunshi yakasa motsawa, cigaba tayi da cewa kun zalunceni kun cuci abokantaka da kuka yaudari mahaifina kuka kasance me fuska biyu a wajenshi saboda dukiyarshi har saida kukayi silar barinshi duniya sannan wannan bai ishekuba kunaso kushafe duk wani tarihi na rayuwarshi toh inaso kasan cewa nasan lokacin da kaje wajen likita ka amso allurar nan nikuma nayi amfani da damata nakawo maka lemu me guba kasha na tabbata ko minti goma bazaka k'araba yanzu zaka mutu, zaka rigani zuwa inda kakeso kakaini dan haka na barka lafiya.....k'arar k'ofar da tajine alamun za'a bud'e yasa tayi saurin 'bacewa. Barr Mubarak hawaye ne suka fara fita daga idanunshi yana kallon matarshi tana ta faman yi mashi sannu tana shaida mashi likita yana nan tafe zai dubashi, a lokacin ne yafara yunk'urin amai ammah yakasa tashi nan inda yake kwance yafara aman jini yana jin ciwon cikin yana k'ara tsananta a nan take yamutu kafin isowar likita dan lokacin da ya iso tuni ya bar duniya. Hankalin mutane ya tashi sosai akan mutuwar Barr Mubarak musamman ma da likita yatabbatar da guba aka bashi yaci saidai anduba ba'a ga alamun ya ci wani abu me guba ba acikin abincin da aka kawo mashi ba nan aka rasa inda yasamo guba yaci. Mutuwarshi tasa su Alhaji Tanimu suka shiga damuwa sosai inda suka fara tunanin jawahir tana da hannu akan mutuwarshi sune suka fara yad'a abun nan aka d'auka ana cewa itace tayi layar zana daga gidan yari taje takasheshi saidai hakan bai zama k'wak'warar sheda ba saidai duk da haka ana zarginta ammah babu wanda zai iya bada shedar cewa itace tayi kisan. Mutuwarshi ta tada hankalin Alhaji Tanimu sosai saboda haka ne asatin da yamutu yatattara yagudu Europe dan ya tsorata sosai akan kisan da aka yi ma nakusa da shi...... Jawahir na kawowa nan juyowa tayi takalli Barr Faruk tace wannan dalilin ne yasa ake cewa na kashe lauyana me son kareni saidai mutane basu san cewa shi d'in me fuska biyu ne ni a wajena fuskar azzalumi gareshi,,, hawaye ne tafara yi nan takoma wajen zamanta tazauna. Barr Faruk kasa cewa komai yayi ganin yadda take hawaye yasa yaje yalek'a waje yace ma ma'aikacin gidan yana buk'atar ruwan sha nan yatafi dan ya samo mashi. Dawowa yayi yakalleta yace Tabbas Alhaji Tanimu ya kasance shed'ani ne idan har abinda kika fad'a akanshi gaskiya ne, ammah shi Barr Muhsin fa, ya akayi yatsaya maki kuma kina nufin shima yana da hannu a ciki saisa kika kasheshi? Shuru tayi tazuba ma gefe d'aya idanu tana kallo, daidai lokacin ma'aikacin gidan yakawo mashi purewater me sanyi saman tray yad'auro cup a sama, amsa Barr Faruk yayi yai mashi godiya bayan ya fita ya basu waje ne yatsiyaya a cup d'in yamik'a ma jawahir. Tsayawa tayi tana Kallon cup d'in sai kuma chan ta amsa tare da yin murmushi tace nagode, nan takafa cup d'in a bakinta saida tashanye sannan tatsaya tana kallon cup d'in tana murmushi. Shima kallonta yake ahankali yace ya burgeki ne cup d'in? Girgiza kai tayi tare da mik'a mashi bayan ya amsa ne tace wannan cup d'in ankawo shi ne saboda kai ne zaka sha ruwan kuma kai mutum ne me daraja a wajensu mu ko k'ask'antattu ne a ko'ina. Tarar numfashinta yayi yace a'a jawahir kidaina cewa haka kema mutum ce me daraja kuma insha Allahu zaki bar gidan nan rayuwarki zata koma irin wadda kikayi a da zaki cigaba da kasancewa a cikin farin ciki komai zai zama tarihi. Murmushi tayi har saida hak'oranta suka bayyana sannan tagirgiza kai tace kaine kake tunanin haka barrister. Shima murmushin yayi sannan yace ina saurarenki ya kamata ki ida sanar da ni abinda yafaru bayan mutuwar Barr Mubarak. Ajiyar zuciya tasafke sannan tacigaba da cewa........... _Sis Nerja'art✍🏻_ [7/24, 11:11 PM] Sis Nerja'art 2: *......FANSAR RAI......* *INTELLIGENT WRITER'S ASSO....®* [On Award Together] _Follow me on Wattpad: *Sis-nerja*_ _Wannan Littafin na kud'i ne domin karantawa cikin aminci da yarda ga duk me buk'ata zai turo katin Mtn na d'ari biyu N200 kacal ta wannan number d'in 09035938246, ko ta account number 5330055604, Idan katura ka aiko da screen shot na transaction a wannan number d'in 09035938246_ _Akwai gara'basar *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shahararriyar marubuciyar nan *AMEENA ABBA UMAR* tare da novel d'in *FANSAR RAI* akan farashin N300 kacal, ko da kud'in ka sai da rabonka_ *PAGE 10* ....Har lokacin zaman mu kotu yayi mukazo babu lauyan da zai tsaya min ana ta surutu akan na kashe lauyana, duk yadda akaso in amsa laifin kisan nan ammah nak'i amsawa saboda haka ne alk'ali yasake d'aga shara'ar nan da wata ukku masu zuwa inda yabada umurni da acigaba da sani aiki me tsanani a gidan yari. Duk tsawon lokacin da nad'auka a gidan kaso muna zaune d'aki d'aya da wad'annan matan biyu watau Raliya da Rufaida har lokacin magana bata ta'ba had'ani da su ba koda daman suna nuna min tsana duk lokacin da za'a kawo mana abinci saidai sucinye har nawa, ahaka wata rana mukayi fad'a akan abincina da aka kawo min koda wannan fad'an ma Ammi ce sukayi da ita a lokacin tana jikina wanda yakaisu har suka dakeni a k'arshe ma suka yanke shawarar kasheni a cikin dare, ita kuma Ammi ganin haka yasa takashesu da daren dasafe aka tashi basu da rai,,wannan dalilin ne yasa aka maido ni wannan d'akin ni kad'ai ina cigaba da rayuwata, ana azabtar da ni aka hana adinga fita da ni aiki saidai batare da sanin shugaban gidan ba suke fita da ni suna sakani dan a ganinsu bazasu iya barina incigaba da zama haka ba kamar anmin gata ne. Ana saura wata d'aya musake komawa kotu a lokacin ne Barr Muhsin yazo a matsayin lauyan da zai kareni ko kad'an banyi mamaki da ganinshi ba dan daman na sanshi a matsayinshi na lauyan mahaifina wanda yasan duk wani sirrin duniyarshi ta ciki da waje, tunda yazo ban ta'ba ce mashi uffan ba ya yi juyin duniya inyi mashi magana ammah na k'i har lokacin komawarmu kotu yayi muka koma haka aka gabatar da shara'a suka fafata shida Barr MB, yana k'ok'arin kareni saidai kawai inbisu da idanu har akayi aka gama inda aka k'ara d'aga shara'ar tamu zuwa wasu watanni biyu masu zuwa, nan aka maidoni gidan yari da alokacin yazame min gida idan da sabo na saba saidai duk lokacin da za'a fita da ni zuwa kotu ina jin wani irin yanayi a duk lokacin da muka fara tafiya cikin mota ina kallon mutane masu wucewa. Haka dai Barr Muhsin yayi ta bina ammah bai samu yadda yakeso ba har aka sake wani zaman da yakasance na biyun k'arshe dan har lokacin baida k'wak'warar hujjar da zai kareni, a nan ma sake d'aga shara'ar akayi zuwa wasu watannin biyu masu zuwa a lokacin ne Barr Muhsin da aka maido ni gidan yari yazo yasameni kallona yake cike da mamaki yace Jawahir narasa meyasa kwatakwata kin kasa sakin jiki da ni nifa ba da niyar cutarwa nazo makiba taimakonki nakeson yi ammah kin kasa gane haka. Murmushi nayi nace gane hakan abu ne mewuya domin mutane abun tsoro ne. A cikin idanunshi naga mamaki k'arara koda mamakin bai nuna akan maganata ta farko da nayi agareshi ba saidai hakan ya faru ne saboda maganar da nayi bai zaci hakan ba, jinjina kai yayi yace hakane ammah jawahir ai kin sanni kinsan bazan zo da niyar cutar da ke ba. Matsowa tayi kusa da shi sannan ahankali tace cutarwa ta nawa kuma? Shin ka mance lokacin da katsaya ma Abba akan kunaso kuk'wace kamfani na ta k'arfin tsiya? Ko baku bane kuka bugo jabun takardu akan kamfanin dan kawai kuga kun rabamu da su, hatta gidan Ammina kaine katsaya ma Abba wajen ganin ya k'waceshi ta karfin tsiya, idan ko haka ne cutarwa ta nawa zakayi min!.... Da mamaki yake kallonta har takai aya sannan yace jawahir duk wa yafad'a miki wannan? Wallahi ba gaskiya bane ko kad'an ban ta'ba tunanin cutar da ku ba. Murmushi jawahir tayi a karo na biyu sannan tace ba ma wannan kad'ai ba hatta abinda kake da niyar aikatawa na sani. Kasa cemata komai yayi yana binta da kallo kafin daga bisani yawuce yatafi. Tun wannan zuwan bai sake dawowa ba sai bayan kwana ukku, koda yazo aka fiddo mashi ita dan sugana kallonshi tayi tace ashe zaka k'ara dawowa da ace zaka taimaka ma kanka da ka hak'ura da zuwa wajena dan bana buk'atar taimakonka. Cikin ran Barr Muhsin yace wannan na rasa wace irin yarinya ce anya zata amince musamu abinda mukeso cikin ruwan sanyi? Chan kuma a fili yace zuwana shine daidai idan har ban taimaka makiba tabbas zan kasance acikin masu butulci mutanen gari zasu zageni a matsayina na lauyan mahaifinki ace na kasa kareki. Cikin d'aga murya tace kaje kanuna tausayawarka ga wasu ba dai ga ni ba domin ni bana buk'atar hakan. Jinjina kai yayi cike da mamakin maganganunta cikin ranshi yace lallai yarinyar nan da ace babu abinda nake nema a gareta da bazan ta'ba tsayawa tana min wannan wulak'ancin ba.... Jawahir tana zuwa nan a labarinta kallon Barr Faruk tayi da har lokacin yake tsaye ya tsareta da idanu d'an guntun murmushi tayi tace Barr muhsin tun bayan rasuwar Ammina baya k'asar zan iya cewa sai ma bayan mutuwar Barr Mubarak ne sannan yadawo kuma su Alh Tanimu ne suka turoshi ko ma ince Alhaji Tanimu ne yahad'a shi da sauran mutanen da sukeso suga sun mallake dukiyata koda yagane nice sukeson yin aiki a kaina ya yi farin ciki sosai domin shima akwai abinda yake buk'ata a wajena. Wannan abun da mukayi da Barr Muhsin yasa sai bayan sati d'aya yasake dawowa bayan anfiddoni yad'auko wani Atm yanuna min yace wannan mallakin mahaifinkine yana da kud'ad'e a cikinshi kuma gab ake da arufe account d'in saboda ya kwana biyu ba'ayi amfani da shi ba kuma ba kowane yasan yana da wannan account d'inba tunda ya fi amfani da wanchan gudan, wannan ya bud'e shi ne saboda masu biyanshi bashi idan ya basu koda duk yarjejeniyar da suke akan bada bashi yana sanar da ni a matsayina na lauyanshi dan mahaifinki baya abu sai ya samu mesheda, wannan dalilin ne yasa nasan komai akan wannan Atm d'in da sabon account d'inshi. Ta'be baki tayi tace nasan haka saidai bakasan Pin d'in da zaka ciro kud'in ba wannan dalilin ne yasa kasanar da ni? Yanayin yadda take magana har mamaki take bashi dan tana da saurin fahimtar abu saidai bai nuna mata mamakinshi ba yace hakane inda zaki amince kisanar da ni da naje ancire kud'ad'en kafin arufe account d'in. Kallonshi tayi a wulak'ance tace wannan ne bazai yuwu ba Barrister zanfi farin ciki ace sun rufe account d'in da dai ace kaine zaka ciro kud'in nan dan nasan kai zasu amfana. Maganata ta 'bata mashi rai sosai ahaka yatafi yabarni. Ya fad'a ma abokan nashi na k'i amincewa dan ina da wayo sosai koda k'arancin shekaru na, wanda yake jagoran su bayan tafiyar Alhaji Tanimu ne yazauna yatsara masu wata dubara inda suka samu wani k'wararre a wajen rubutu wanda yake da baiwa duk rubutun da yagani zai iya yin irinshi haka suka bashi irin rubutun mahaifina yayi masu, yarjejeniya ce suka rubuta akan wannan filayen da suke kawo min files d'insu insa hannu nak'i, sun kashe kud'ad'e sosai akan aikin inda Barr Muhsin yataimaka masu suka zauna har kotu akan cewa mahaifina ya siyar ma da Alhaji Tanimu filin kasancewar ansan Barr Muhsin shine lauyan mahaifina kuma ga sheda angani ta rubutu da komai yasa aka basu filayen sunyi farin ciki sosai da wannan nasarar da suka samu nan suka sanar da Alhaji Tanimu ta waya shi kuma yabasu dama da su saida ma gwamnati filayen biyu daman itace tabuk'aci hakan saboda filayen yana da girma sosai dan duk cikin filayen mahaifina babu me girmansu nan aka basu mak'udan kud'i sukaje suka raba a tsakaninsu. Dalilin mutuwar Barr Muhsin kuma ganin bai ci nasarar samun Pin d'in a wajena ba yasa yashirya yaje wajen boka yai mashi bayanin duk abinda yakeso nan bokan yabashi wani kwalli yace da ya shafa yazo wajena duk abinda yakeso zanyi mashi nan yayi ta murna har yayanke shawarar hatta babban account d'in Abbu sai yasa nayi mashi signing ya fitar da kud'i, toh akan hanyar shine tadawowa Ammi takasheshi acikin motarshi aka tsinci gawarshi, shine dalilin da yasa ake cewa shima ni nakasheshi dan kawai ya tsaya min.....tana zuwa nan a labarin sai ganin wata irin guguwa sukayi me k'arfi tana shigowa cikin d'an kurkukun d'akin ta k'aramar tagar nan cikin sauri jawahir tamik'e tatsaya gaban Barr Faruk, su dukansu idanu suka zuba ma guguwar har tagama shigowa nan tahad'e waje guda sai ga wannan tsohuwar ta bayyana, tana bayyana tabushe da dariya. Barr Faruk da mamaki yake kallonta tabbas itace wannan tsohuwar da yata'ba gani kuma itace yake yawan gani a mafarkin shi, muryar jawahir ce yaji ta ce Ammi menene dalilinki na zuwa nan a wannan lokacin? Ci gaba tayi da dariyarta marar dad'in saurare me kama da haniniyar doki saida tayi me isarta sannan tadogara sandarta tafara takowa ahankali inda suke tsaye jawahir saurin cewa tayi a'a kar kimatso nan kitsaya nan! Bata musaba taja tatsaya tana me kallon Barr Faruk da yake tsaye bayan Jawahir kamar wanda ruwa yacinunashi tayi da yatsa cikin shak'ak'k'ar murya da bata fita sosai tace kai kai kana shiga hurumina dayawa, ina gargad'inka da kadaina inko ba haka ba rayuwarka zata zama tarihi. Saurin tarar numfashinta jawahir tayi tace baidace kisake aikata kuskure ba a karo na biyu Ammi, shin shi kinga ya yi maki kama da mugayen mutane ne? Meyasa kin cika son kanki dayawa? Bushewa tayi da dariya akaro na biyu sannan tace tunda har ya iya zuwa yad'auko memory d'innan tabbas ya aikata kuskure sannan nice kad'ai nake da ikon iya fitar da ke daga gidan nan ammah sai kinyi nadamar maganarki. Cikin d'aga murya tace wannan ne kuma bazai ta'ba faruwa ba Ammi kece dai yakamata kiyi nadamar kashe yaya umar da kikayi!! Bushewa tasake yi da dariyar mugunta sannan tace kisanar da shi yayi gaugawar maida Memory Card d'innan dan wannan shine umurni na. Fitowa Barr Faruk yayi daga bayan Jawahir har ya bud'e baki zaiyi magana nan jawahir tayi mashi nuni da yayi shuru bai musaba yaja bakinshi yayi shuru, nan tsohuwar ta d'age kanta sama nan wani farin haske yabayyana wanda daga jawahir har Faruk idanunsu suka kasa jure kallon hasken dan kar yayi masu illa, su dukansu sukayi saurin runtse idanunsu har saida jawahir taji alamun bacewarta sannan tabud'e idanunta ajiyar zuciya tasafke tare da juyawa takalli Faruk da yabud'e idanunshi a daidai wannan lokacin tace yanzu aiki ya ganka sai ka yi da gaske sannan zaka iya tseratar da kanka daga Ammi daman wannan dalilin ne yasa tun farko nakasa fad'a maka komai dan nasan Ammi bazata ta'ba barinka cikin kwanciyar hankali ba ni kaina ba barina takeba kullum cikin azabtar da ni take. Faruk da yazuba mata idanu sai a lokacin yayi magana yace ammah jawahir meyasa take cutar da ke bayan da fari tana taimakonki, miyasa tabari har aka kawo ki nan gidan kaso kina rayuwa marar 'yanci bayan ta san duk itace me laifi ba ke ba? Juyawa tayi takalli gefe d'aya tare da yin guntun murmushi sannan tace dalili d'aya ne yasa duk take min haka ba wai komai bane sai dan kawai na furta mata kalmar tsana sannan nanuna inaso tarabu da ni ammah a maimakon tarabu da ni shine take wahalar da ni, nikuma hankalina baya kwanciya idan har tana cigaba da kasancewa tare da ni domin gani nake duk wanda yara'beni sai ta ga bayanshi, haka taso taga bayan wata ma'aikaciyar gidan nan akan matsa ma rayuwata da tayi saida nayi mata dagaske nanuna zan kashe kaina idan har tayi mata wani abu sannan tafasa saidai duk da haka saida tatsorata ta, taimako guda ne kawai nake buk'ata daga Ammina shine kad'ai yasa nake buk'atar kasancewarta tare da ni, ina jin dad'in d'aukar fansar da take tayani bana nadamar wannan domin shine hukuncin da yadace da azzalumai irinsu Alhaji Tanimu, ko a yanzu haka aka kasheni bazan ta'ba nadama ba dan na cika burina saidai abinda ba a rasaba ammah in da so samune ace na cika gabad'aya burin nawa,,, rintse idanunta tayi wasu siraran hawaye suka gangaro mata. Faruk rasa abinda zaice mata yayi sunyi kusan minti biyar a haka sannan yace Jawahir kikwantar da hankalinki kamar yadda nayi maki alk'awali insha Allahu zan taimaka maki yanzu dai abu d'aya yarage kisanar da ni suwanene sauran mutanen da suke da hannu a mutuwar su Abbu insha Allahu ni kuma zanyi abinda yadace, sannan zanyi k'ok'arin had'a duk wata sheda waje guda kafin lokacin zaman k'arshe yayi a kotu ammah kafin nan ina zan samu Ummah? Sannan Megadin gidanku shima ina zan sameshi? Ahankali tabud'e idanunta tasafkesu akan fuskarshi sannan tace Ummah tana chan asibiti kwance saboda tashin hankalin da tashiga jininta ya hau sosai sannan ga mutuwar 'barin jikin dama da takamu da shi (paralyse), na ji ance har yanzu batasan inda hankalinta yakeba bata magana da kowa saidai tabi mutane da kallo. "Ammah toh wane asibiti ne aka kaita?" Girgiza kai tayi tace nima ban saniba kawai dai abinda nasani ina nan gidan kaso wani lokaci Ammi da tazo wajena nan take nuna min abinda yafaru na ga komai a cikin tafin hannunta Ummah tana kwance bata iya komai likitoci suna ta k'ok'ari akanta saidai har tsawon wannan lokacin bata san inda kanta yakeba, saidai duk wannan abun da nagani ban gane wane asibiti bane, sannan megadin gidan mu buzu ne ainafin shi d'an k'asar Nijar ne bayan faruwar haka yagudu yakoma gida bamu san inda yake zaune ba a chan, Alk'ali ma saida yanemi akawoshi kotu dan amsa wasu tambayoyi saidai akazo aka fad'a mashi ya gudu kuma hakan ya faru ne saboda tsananin tsoratar da yayi akan kisan da akayi ma mutanen gidan kar shima abun yashafeshi. Barr Faruk yace shikenan jawahir kikwantar da hankalinki ni na san yadda zanyi, zanje intattara duk wani bayanai da suke wajena saidai abu d'aya da ace zan sake samun wani abu da zai k'ara taimaka min da zanfi buk'atar hakan. Shuru jawahir tayi kamar me tunanin wani abu sai kuma chan tace akwai abu d'aya da zaka iya samu saidai samunshi kamar ba abune me sauk'i ba. Barr Faruk yace kar kidamu fad'a min shi koma menene zanyi bakin k'ok'ari kamar yadda na iya d'auko memory d'innan. Cikin sanyin jiki tace ba wai a wajen Ammi zaka same shi ba, wannan yana a gidan Alhaji Tanimu da ace kana da damar da zaka iya shiga gidan har d'akinshi da ka samo wayar Abba da take hannunshi dan a lokacin da aka kamani sunyi amfani da wani key da suka sata sun shiga gidanmu sun yaye duk dukiyar Abba da k'addarorin shi, hatta wayarshi ma tana wajen Alhaji Tanimu saboda duk wayar da Abba zaiyi da mutum tana recording din maganar da sukayi tsawon wani lokaci kafin voice d'in yagoge indai har ba shi Abba yagoge ba toh yana cikin wayar, har sai and'an kwana biyu sannan maganar take gogewa , sannan wayar da yake kiransu da itace a wajen Alhaji Tanimu, ahakane nake gani zaka iya samun duk wasu bayanai da kake nema saboda maganganun da sukayi yana ciki wannan dalilin ne yasa yad'auke wayar ya adanata a cikin gidanshi batare da sanin kowa ba wannan itace kad'ai zata taimaka maka kagane sauran mutanen da Abba yake tare da su. "Ammah jawahir wannan zai yi wuya gaskiya dan bana tunanin abu ne me sauk'i shiga cikin gidanshi har inje d'akinshi inyi bincike inma zan sanar da hukuma na tabbata babu wanda zai bani goyon bayan hakan gaskiya saidai kawai muyi hak'uri da wayar nan, toh ammah idan har sai cikinta zamu samu abinda muke buk'ata taya zamu iya hak'ura da ita?,,, kanshi ne yayi ma tambayar sai kuma yasafke ajiyar zuciya tare da kallon jawahir da tatsareshi da idanu yace bansan ta yadda zan iya shiga gidanba, ya kike gani ya dace? " Nima bansan yadda za'ayi ba saidai kawai ahak'ura" "A'a jawahir baza'a hak'ura ba zan je inyi tunani inga hanyar da yadace inbi dan inaso ingane ko suwanene suke da hannu a ciki kafin Amminki takashesu, bari intafi koma menene zaki ji ni zanyi k'ok'ari wajen ganin na samo mafita a cikin kwana biyu bazan dawo wajenki ba har sai na samo wayar na gane suwanene suke da hannu a ciki, saidai to wayar wace iri ce yadda zan ganeta?. Tsayawa tayi tana tunani sai chan tace fara ce zaka ganta a cikin wardrope d'inshi ta gefen dama daga chan k'asan kayanshi nan zaka ganta. Da mamaki yake kallontwa yace Jawahir duk ya akayi kika san wannan bayan ke kina nan cikin gidan kaso? Ko kema ba mutum bace! Murmushi tayi har saida hak'oranta suka bayyana sannan tace zan sanar da kai ammah ba yanzu ba, sannan ni mutum ce kamar kowa, kaje kawai ina maka fatan samun nasara. Juyawa yayi yatafi cikin sanyi jiki, daga nan office d'in Alhaji Mahadi yawuce yasameshi zaune ankawo mashi wasu mata sabbin zuwa guda biyu wad'anda suke da case na kashe mijinsu ganin Barr Faruk ya shigo yasa yace ma mataimakiyarshi atafi da su asasu cikin kurkukun d'akin nan k'arami wanda wasu mata ukku suke a cikin shi amsawa tayi nan taba wasu ma'aikata biyu umurni aka tafi da su. Bayan suk sun fita Alhaji Mahadi yace bismillah Barrister kazauna. Bai musaba yaja kujera yazauna. Kallonshi Alhaji Mahadi yayi yana murmushi yace ya dai barrister na ga duk ka yi sanyi dayawa ko duk case d'in jawahir d'inne yake gwagwata ka? Ajiyar zuciya yasafke yace ba ma haka ba abokina wani taimako nakeso DPO yayi min ammah ban san yanayin kirkin shi ba ko zai fahimci abinda nakeso. Indai akan Jawahir ne bazai ta'ba fahimta ba dan ka san laifin da aka kamata da shi, kuma indai DPO ne bana tunani zai amince maka koma menene dan yana da tsatstsauran ra'ayi da ganin shi wani ne, musamman ma da yaga yadda kuke 'yar tsama akan case d'in yarinyar nan. Ta'be baki Barr Faruk yayi yace koma menene dasannu zan wanke Jawahir daga zargin da ake mata. Toh Allah dai yataimaka. Ameen. _________ Abban Nasiba ne yashigo yasameta Zaune ta tisa waya a gaba tana kallo ta shagala da kallon wayar bata ji shigowar mahaifinta ba, Alhaji Sufyan matsowa yayi idanuwanshi akan wayarta suka safka, girgiza kai yayi yace Nasiba har yanzu dai kina nan akan bakanki bazaki iya daina tunanin Faruk ba, inbakayi wasa ba sai na k'wace wayar nan tunda hotunanshi kike kallo a cikinta. Saurin janye wayar tayi takifata a jikinta sannan tatashi zaune tare da sadda kanta k'asa. Cigaba yayi da cewa kikwantar da hankalinki indai Faruk rabonki ne zaki sameshi kidaina sa damuwa a ranki kar kija ma kanki wani ciwon shi yana chan baima san kina yi ba. 'Dagowa tayi takalleshi tace toh Daddy insha Allahu zan kiyaye. Amsawa yayi da yauwa 'yar lele haka nake son ji, tashi kije kikira min Hajiyarki sannan kije dining ga icecream chan na sawo maki dan nasan kina sonshi sosai. Murmushi tayi tace toh Daddy nan tamik'e tatafi. Bin ta yayi da kallo tare da girgiza kai yazauna saman kujera sannan yace Allah yakyauta. _Sis Nerja'art✍🏻_[7/24, 11:13 PM] Sis Nerja'art 2: *......FANSAR RAI......* *INTELLIGENT WRITER'S ASSO....®* [On Award Together] _Follow me on Wattpad: *Sis-nerja*_ _Wannan Littafin na kud'i ne domin karantawa cikin aminci da yarda ga duk me buk'ata zai turo katin Mtn na d'ari biyu N200 kacal ta wannan number d'in 09035938246, ko ta account number 5330055604, Idan katura ka aiko da screen shot na transaction a wannan number d'in 09035938246_ _Akwai gara'basar *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shahararriyar marubuciyar nan *AMEENA ABBA UMAR* tare da novel d'in *FANSAR RAI* akan farashin N300 kacal, ko da kud'in ka sai da rabonka_ *PAGE 11* Tsawon kwana biyu Barr Faruk yad'auka yana tunanin hanyar da zaibi yashiga gidan Alhaji Tanimu har yasamu damar zuwa d'akinshi yad'auko wayar saidai babu hanyar da yaga zata 'bule mashi dan ranar sadakar ukku ma saida yaje gidan da sunan gaisuwa yaje masu hatta parlorn Alhaji Tanimi ya shiga yai ma 'yan uwanshi gaisuwa dan a cikin parlorn wasunsu suka zauna saidai hankalinshi ba k'aramin tashi yayi ba nan yasare yasan hakan saidai a mafarki zai iya faruwa. A gefe d'aya ga Ammin Jawahir da tatakura mashi dan kusan kullum sai ya yi mafarki da ita ko kuma cikin dare tatasheshi daga bacci ayi ta tsorata shi. Yau ma bayan ya gama had'a bayanenshi wajen k'arfe sha biyun dare ya gama shirin kwanciyarshi har ya kwanta nan ya fara jiyo motsi kamar ana hawan step, ana kiran sunanshi tashi yayi zaune cikin ranshi yace tabbas nasan itace , jiyayi ana cigaba da hawa babu k'ak'k'autawa yanayin yadda ake taka benen kamar irin ansa takalmi masu tsini, sai ji yayi anfara k'wank'wasa mashi k'ofa, magana yafara jiyowa kamar ta mahaifinshi yana tambaya wanene nan? Cikin sauri Faruk yamik'e yaje yabud'e ammah baiga kowaba dan haka yafita sai ganin Dad d'inshi yayi tsaye a chan wajen part d'insu gaban Faruk saida yafad'i ahankali yace ba dai tado su Dad tayi ba, muryar Dad yaji yana cewa Faruk wanene yake k'wank'wasa k'ofa na fito zan d'auki ruwa marassa sanyi dan na cikin freezer d'in part d'ina duk sunyi sanyi shine naji kamar ana knocking d'in k'ofa. "Dad babu kowa nima ruwan nafito ind'auka ammah banji k'arar k'omai ba",, Cewar Faruk. Tsayawa Dad yayi yana kallonshi yace yanzu kai baka ji ba? Ni na jiyo ana kwank'wasawa kamar ma ta part d'inka. Murmushi Yayi yace Dad ka fara tsufa ne saisa kaji haka nidai da nake sabon jini ban jiyowa. Girgiza kai Dad yayi yana murmushi yace kai ko faruk shikenan dai yanzu koma kakwanta k'arfe d'aya ta yi. " Toh Dad kaje kakwanta bari inje ind'auko ruwan ammah dan Allah kadaina fitowa a wannan lokacin kaga darene". Shikenan Faruk zan daina nima dai saboda k'ishin da nakeji yasa nafito ammah zan daina, je kad'auko ruwan bari intafi sai dasafe. Yauwa Dad Allah yakaimu. Saida yaga shigewar Dad sannan yafara safka daga saman step d'in ahankali yana lek'awa yaga ko zaiganta ammah baiga kowaba har yaje wajen fridge sai kuma yafara jiyo motsi achan tsakar gida har zai je yabud'e k'ofa yafita sai kuma yafasa dan ya san da ya bud'e sai su Dad sun jiyo kuma sai sun fito dan haka kawai yajuya zai koma part d'inshi sai jin k'ara yayi wajen kunnenshi wani irin shuuuuu kamar wucewar iska anbi ta bayanshi. Juyawa yayi saurin yi tare da cewa wanene? Koma waye yabayya kanshi!! Shurun da yaji anyi yasa yajuya yacigaba da tafiyarshi. Yana zuwa part d'inshi shiga yayi batare da ya murza key ba yawuce yanufi bedroom tun kan yashiga sai ji yayi k'ofar parlor d'in da yarufe ta bud'e kanta da k'arfi, juyawa yayi cikin 'bacin rai yace koma wanene yabayyana kanshi mana, shuru yaji dan haka yaje yayi bismillah yarufe k'ofar sannan yaje yashiga bedroom d'inshi, yana shiga hasken d'akin yad'auke daidai da ya rufe k'ofa, jingine jikinshi yayi da k'ofar ahankali yafara karanto addu'o'i, muryace yafara jiyowa daga wajen gadon shi tana tashi da k'arfi ana cewa barka da wannan lokacin Barr Faruk. Cikin dakiya da nuna rashin tsoro yace koma wacece na ce ya kamata tabayyana kanta. Dariya yaji an bushe da ita kamar irin haniniyar dokin nan saboda k'arfin dariyar har saida yayi saurin toshe kunnuwanshi saida yatabbatar da dariyar ta lafa sannan yasaki kunnuwan tare da cewa wannan alama ce ta matsoraci duk jarumi bayyana kanshi yakeyi, na san kece Ammin Jawahir shin menene yakawoki wajena ko nima d'in kinzo ne dan kiga bayana? Tun kan yarufe baki yaji wata irin murya me tsoratarwa cikin k'araji tana cewa da ace kana da hannu a ciki da sai na ga bayanka a yanzun nan, sannan ni ce kad'ai yakamata intaimaka ma jawahir tabar gidan nan aduk lokacin da naso, ikona ne wannan ba naka ba saidai jawahir tana da taurin kai sosai ta kasa yin nadama akan kalmar tsanar da tajefeni da ita, kai d'in kuma baka burgeni koda kana k'ok'ari wajen ganin ka taimaki d'iyata dan haka ina gargad'inka da kayi baya daga case d'in nan, wannan shine kad'ai abinda yakawoni wajenka,,, tana fad'in haka sai ji yayi shuru nan hasken d'akin yadawo. Murmushi yayi ahankali yace wannan ne kuma bazai yuwu ba dan ni nasa kaina kuma babu wanda ya isa yasani injanye ban damu da koma wacece ke ba dan baki gabana da mutane irina nake da lokacin jayayya,,, wucewa yayi yadudduba ko'ina bai gantaba dan haka yaje yahau gado tare da yin addu'o'i yakwanta ko kad'an tsoro bai d'arsu cikin ranshi ba dan ya san addu'a itace takobin mumini, saidai tunda yakwanta bai samu yarintsa ba kamar kullum yana ta tunanin mafita har wajen k'arfe hud'u sannan yad'an samu bacci kafin daga bisani yatashi lokacin sallar asuba. Hankalinshi k'in kwanciya yayi ganin kwanaki goma ne kawai suka rage mashi wata dabara ce tafad'o mashi dan haka bayan ya yi breakfast yakira wani abokinshi Barr Nas a waya tare suka yi karatu har wajen aikinsu d'aya lokacin da yake aiki a SHARI'A COURT abokai ne sosai dan koda a yanzu ba wajen aikinsu d'aya ba suna tare, bayan sun gaisa ne yatambayeshi inda zai sameshi yafad'a mashi kasancewar weekend ne babu aiki, shiryawa yayi yad'auki system d'inshi da komai wanda zai buk'ata yashiga motar shi yanufi gidan Barr Nas yana isa daidai lokacin shima yashawo kwana Barr Faruk tsayawa yayi har saida ya iso da motarshi nan yafito yanufo wajen Faruk yana murmushi yace Barrister kace dai dagaske kake zaka zo. Hmm dole kace haka tunda ka san baka gidan kaja nazo ashe da saidai inkoma. "A'a Wallahi ban dad'e da fitaba na kai Madam gidane ina safketa najuyo dan kar kazo ban nan, yanzu dai mushiga da mota ciki. Barr Faruk ba tare da ya ce komai ba yatada motar shi, saida Barr Nas yashiga tashi motar yayi horn megadi yabud'e masu gate sannan suka shiga da motocin, bayan sunyi parking ne suka nufi parlorn gidan Barr Nas yana cewa yau dai kamar a mafarki sai gaka a gidana ina ji rabon da kazo tun bikkina. "Toh ka dai san yanayin aikin mu bamuda lokacin zama bare har inzo gidanka, yanzu ma haka akan aikine yasa kaganni" Hmm nasan haka kai kullum da aiki kake fakewa, malam muma fa duk aikin nan muke irin naka ammah a haka muna samun lokacin ziyara kai ko kullum saidai kabada wani uzuri, ko dai Nasiba ce take 'boye mana kai tun ba'ayi bikkin ba? Murmushi yayi jin an ambaci sunan abun son shi saidai a ranshi yana tunowa da wani abu yasafke ajiyar zuciya yace Nasir muyi maganar da takawoni wajen ka. Toh shikenan Barr ina saurarenka. Barr Faruk yace daman wani taimako ne nakeso kayi min dan nasan kaine kad'ai zaka iya yimin yadda nakeso, Gyara zamanshi yayi yace wani irin taimako ne wannan koma wane iri ne kafad'a zanyi maka indai baifi k'arfina ba koda ma ya fi zansan yadda zanyi intaimakeka. Murmushi yayi sannan yace ranar sadakar ukku watau jiya na ga motarka ka fita daga gidan marigayi Alhaji Tanimu Nepa ni kuma lokacin nashiga gidan zanyi masu gaisuwa, shine nakeso inji ya kake da shi daman ka sanshi? Allah Sarki ai Alhaji Tanimu Mahaifin abokina ne Nazir tare mukayi secondary school da shi muna mutunci sosai da shi, shi naje ma gaisuwa dan kusan tun ranar da akayi rasuwar kullum sai na je. Wani irin sanyi Faruk yaji a ranshi har saida farin ciki yabayyana a fuskarshi Alhankili yafurta Alhamdulillah. Da mamaki Barr Nas yake kallonshi yace lafiya Barrister me yafaru naga kana fara'a? Lafiya lau Nasir na ji dad'i sosai da jin bayananka a yanzu ina da k'warin gwiwar samun abinda nakeso watau wani case ne me zafi mukeyi shine nake son kataimaka min a ciki kayi min jagorar zuwa gidanshi. Cike da mamaki yace case kuma? Wane irin case ne haka? Ko akan kisan da ake zargin anyi mashi dan naji anata jitajitar kasheshi akayi saidai anrasa wanda yayi kisan dan ajiya ma aka sako driver d'inshi an wankeshi daga zargin da ake mashi, saidai har yau anrasa wanda yayi kisan ana tadai bincike ankasa samun k'wak'k'warar shaida za'a iya kama wanda yayi laifin. Tsayawa yayi yana saurarenshi har yakai aya nan yarasa me zaice tunani yafara yi yasanar da shi komai akan case d'in jawahir ko kuma yayi shuru abunshi,, Muryarshi yace yaji ya ce ya dai Barrister ka yi shuru lafiya dai ko? Girgiza kai yayi yace babu komai saidai kawai.....shuru yayi batare da ya k'arasa fad'in kalmar da take bakinshi ba. Ganin haka ya Barr Nas yatashi yakoma kusa da Barr Faruk bisa 2 seater d'in da yake zaune sannan yace Faruk kayi min bayanin koma menene zan fahimceka kuma zan taimaka maka saboda ka cancanci haka. Har cikin ranshi ya ji dad'in bayanin abokin nashi sosai kuma ya san tunda har yafurta toh zai taimaka mashi dan tun a makaranta baya da aboki kamarshi da Barr Junaid dan duk tare sukayi karatu har gama makarantar su sannan wajen aiki d'aya saidai Barr Junaid ne kawai a lokacin baiyi zurfin karatu kamar nasuba dan shi daga HND yatsaya su kuma har masters sunyi saisa sukafi shak'uwa da Barr Nasir sai daga baya ne dayakoma a kotun da Barr Junaid yake aikine abotarsu tak'ara k'arfi,,, jijjigashi Barr Nas yayi yace wai lafiyarka Faruk sai wasu tunane tunane kakeyi ya kamata kanutsu kafad'a min koma menene. Shikenan Nasir zan sanar da kai komai yanzu nasan zaka taimaka min, bayan na baro court d'inku anmaidoni a nan HIGH COURT shine natarar ana wani case wanda bayan rasuwar lauyan da yake jagorantar case d'in yake kare wadda ake k'ara shine ni kuma na amshi case d'in yadawo hannu na dan kare wadda ake k'arar a lokacin da na lura tana buk'atar taimako ana nema atauye mata hak'k'i mutane da dama sun nemi su fahimtar da ni had'arin da yake cikin case d'in ammah ni duk wannan bai dameniba burina d'aya shine inwanke wadda ake k'arar a idanun duniya........ Kwashe komai yayi akan case d'in Jawahir yafad'a mashi saidai ya 'boye mashi gaskiya a game da Fatalwar da ke tare da jawahir har tsorata shi da ake babu abinda yafad'a mashi. Hankalin Barr Nas ya tashi sosai da yaji labarin saidai bai katseshi ba har saida yagama fad'a mashi komai sannan yace tabbas naji labarin case d'innan ko ba ita bace Jawahir Muhammad? wadda tayi kisa har takashe lauyoyinta saidai na ji labarin ya d'an sha banban da wanda kabani ammah tabbas ina tunanin itace. Eh itace saidai abinda aka fad'a ba gaskiya bane Nasir ni kaina ina neman hujjojin da zan tabbatar ma mutane da haka saisa a yanzu haka nakeso kayi min jagora zuwa gidan Alhaji Tanimu dan akwai abinda nakeso ind'auko. Tun kan yarufe baki cikin sauri Barr Nasir yamik'e tsaye yace ka san abinda kake fad'a kuwa Barrister? Taya kake tunanin zamu iya shiga gidan Alhaji Tanimu har wai kad'auko wani abu a d'akinshi batare da sanin kowa ba, ka san dai za'a iya kamamu idan har kuma hakan yafaru har kotu za'a banka mu sannan kisan da ake cewa anyi mashi mu za'a ce mun kasheshi gaskiya hakan bazai yuwuba kama daina wannan tunanin. Shima mik'ewa yayi cikin sanyin jiki yace Nasir kar kadamu insha Allahu babu abinda zai faru zanyi k'ok'ari wajen ganin na yi komai batare da angane mu ba. Cikin karaya Barr Nasir yace Faruk anya hakan zai yuwu da dai ka hak'ura kawai. "Nasir kadaina cewa haka na yi maka alk'awari babu abinda zai sameka koma menene yafaru bazan ta'ba bari asakaka cikiba laifin gabad'aya nawa ne wannan alk'awarine nayi maka. Ganin yadda yanace yasa Nasir ya amince sutafi, nan suka zauna yana cigaba da tayashi aikin da yake a nan sukayi azuhur yaba megadin shi kud'i yayo masu takeaway suka ci dan matarshi sai marece zata dawo. Bayan sunyi sallar la'asar ne suka kama hanyar gidan Alhaji Tanimu inda gabad'ayansu zuciyoyinsu babu dad'i jikinsu ya yi sanyi sosai saboda basusan abinda zasu tarar ba idan sukaje, Barr Nas yake driving inda Barr Faruk yake zaune gefenshi yana ta sak'e-sak'e cikin ranshi har suka isa gidan suna zuwa aka hangame masu tankamemen gate d'in gidan suka cinna kan motar su a ciki, Motocine sosai a parking space dan haka suka samu waje su ma suka ajiye tasu motar. Barr Nas juyowa yayi yakalli Faruk yace Barrister wallahi ina jin tsoro sosai taya kake ganin shiga d'akin Alhaji tanimu zai yi mana sauk'i bayan akwai mutane sosai a cikin gidan. Ajiyar zuciya yasafke yace nima ina tunanin haka Nasir saidai banda yadda zanyi tunda tun farko ni nayi ma yarinyar alk'awari zan taimaka mata kuma dole sai na samo wayar itace zata taimaka min nan da kwana goma inku'butar da jawahir dan da kwanaki goman nan sun shud'e na tabba za'a yanke mata hukuncin kisa dan wannan zaman shine zama na k'arshe da za'ayi, mushiga kawai in gwada sa'a ta. Ammah ta ya kake tunanin zamu iya shiga cikin gidanshi har d'akin shi? "Kar kadamu da wannan ni zan shiga ba kai ba bazan sakaka cikiba Nasir koma menene zai faru saidai yafaru da ni kad'ai yanzu fito mushiga ciki muyi masu gaisuwa dan inga yanayin mutanen da suke ciki. Ajere suka tafi suna tsayawa suna gaisawa da jama'ar da suke zaune saman tabarma har suka shiga setting room d'in gidan inda dangin mamacin suke zaune suna amsar gaisuwa bayan sun gaisa sunyi masu gaisuwa Nasir yaduk'o da kanshi saitin fuskar Faruk ahankali yace banga Nazir ba ina tunani baya nan ammah bari intambaya, matsawa yayi kusa da k'anen Nazir da yake zaune chan k'arshen bango yatambayeshi inda Nazir yake yace mashi yana cikin gida dan haka suka tashi suka shiga koda matane a ciki ammah ahaka sukayi ta ratsawa suna gaishesu har suka shiga babban parlor inda suka samu matan mamacin zaune da mutanensu, gaishesu sukayi sannan Nasir yatambayi mahaifiyar Nazir inda Nazir yake tace yana chan part d'in Abbansu ya yi wasu bak'i kuje chan kusameshi kuce na ce ina jiranshi yakawo min keys d'in part d'in. Barr Faruk kallon Nasir Yayi yai murmushi irin na da alama zamuyi nasara, girgiza kai Nasir yayi alamun a'a sannan suka mik'e suka nufi part d'in da yake mallakin megidan. Tun da suka tunkari hanyar part d'in suka fara jiyo hayani alamun ana labari haka suka isa suna shiga suka tarar da su tsaisaye alamun tafiya zasuyi Nazir yana ganinsu yace A'a Barrister sannunku da zuwa. Hannu suka mik'a masu duk aka gaisa sannan suka k'ara yi mashi gaisuwa. Mutane ukkun nan da suke tsaye ne sukace mu zamu wuce Allah yajik'anshi yace toh nagode muje inrakaku, kallon su Barr Faruk yayi yace dan Allah kuzauna ina zuwa bari indawo. abu daman ga wad'anda suke nema dan haka suka zauna haka yafita da abokanshi dan yarakasu. Barr Faruk kallon Nas yayi cikin sanyin jiki yace ban san ta inda zan faraba barrister ammah bari infara ta'ba bedroom d'in inji idan bud'e yake, Barr Nas da yanuna alamun tsorata yace a'a Barrister kar fa ashigo aganka. Batare da ya ce komai ba yamik'e cikin sauri yanufi hanyar da zata sadaka da bedroom d'in yana zuwa yamurd'a k'ofar yaji datse take gam nan fa duk yaji ba dad'i yadawo yazauna tare da dafe kai yace hakan bazai ta'ba yuwuwa ba nasan bazan yi nasara ba Nasir. Ajiyar zuciya Nas yasafke yace kakwantar da hankalinka Faruk ko ma ba ta wannan hanyar ba insha Allahu zaka samu k'wak'warar shedar da zaka bayar. Yana bud'e baki zaiyi magana suka jiyo taku alamun an nufo d'akin dan haka sukayi shuru sai ga Nazir ya shigo fuskarshi d'auke da murmushi yace kuyi hak'uri na barku ku kad'ai, wallahi abokaina ne da mukayi karatu da su a London Sukace Allah sarki a'a babu komai, zama yayi yana kallon Barr Faruk yace kaima Barrister d'inne irin Nas ko?. Murmushi yayi yace a'a shi dai ne lauya. "Ayyah Allah sarki aini tun farko mancewa nayi da abokina babban lauya ne da shi zan saka acikin case d'in kisan da akayi ma mahaifina dan ak'wato mana hak'k'inmu. Barr Faruk kallon Barr Nas yayi da shima yake kallonshi su dukansu sukayi shuru aka rasa wanda zaiyi magana daidai lokacin akayi sallama aka shigo su dukansu suka juya suka kalli k'ofa tare da amsawa wata dattijuwa ce tashigo nan duk suka gaisheta bayan ta amsa ne tace Nazir ina key d'in bedroom d'in Abbanku zamu d'auko sauran lemuna a ciki. Aunty Amina kinsan dai anhana bud'ewa nima kaina dak'yar nasamu Ummah tabani key d'in nashigo parlor. Harararshi tayi tace kai ni dallah bani ind'auko abinda zan d'auko sai inmaido maka kayi ta tseguminka saikace wata uwa abu zan d'auka a ciki. Ganin yadda tafara d'aga murya tana fad'a yasa yaciro keys d'in acikin aljihu yamik'a mata amsawa tayi taje tabud'e tashiga. Barr Faruk kallon kallo suka fara da Barr Nas sai kuma suka maida hankalinsu ga k'ofar bedroom d'in da tabud'e, Faruk ji yake kamar yayi tsalle yashige saidai hakan bazai ta'ba yuwuwa suna kallo tagama d'auko lemunan tarufe d'akin tamik'o ma Nazir key d'in, sannan tafara jidar lemunan tana fita da su. Nazir a gefen da yake zaune ya d'age wani throw pillow ya ajiye Keys d'in a wajen yace muma ai yanzu zamu fita tun kan azo afara yi mana surutu tace da dai ya fi maku. Faruk yana kallo nan ya ida sarewa yatabbatar bazai samu yadda yake so ba. Bayan ta fita nan Barr Nas da Nazir suka fara hira inda shi kuma Barr Faruk yayi shuru abin duniya duk ya isheshi, Nazir bai damu da shurun da yayi ba dan yana ganin yanayinshi yagane shi d'in ba mutum bane me son hayaniya sosai ba, suna cikin hirar nan wayar Nazir tafara ringing d'aukowa yayi yai picking tare da yin sallama, basuji abinda akace mashi ba saidai ji sukayi yana cewa toh shikenan Kawu ganinan zuwa ai dama ina cikin gidan bari infito, kashe wayar yayi yakallesu yace bari ind'anje indawo wasu abokan Abba sukazo mana gaisuwa daga Kaduna, ajiyar zuciya Barr Faruk yasafke kafin Nas yayi magana shi yayi saurin cewa Allah Sarki toh shikenan babu damuwa sai ka dawo. Nas dai murmushi yayi dan ya san dalilin Faruk na cewa haka. Mik'ewa Nazir yayi yafita lokacin da aka sake kiranshi waya, yana barin d'akin cikin sauri Faruk yamik'e yanufi wajen kujerar da yazauna yana zuwa yahankad'e pillow yad'auko keys d'in wani irin farin ciki yaji a ranshi yajuya yakalli Nas da yakeyi mashi kallon mamaki ganin babu wani alamun tsoro a tare da shi har ya iya d'aukar key d'in, murmushi yasakar mashi tare da cewa ina zuwa bari inyi sauri inje ind'auko bazan 'bata lokaci ba. Cikin sanyin jiki yace a'a Faruk ina jin tsoro. Batare da ya tanka shi ba yawuce yanufi hanyar Bedroom d'in yana zuwa yasa key d'in da yaga Nazir ya nuna ma matar nan, yana murzawa sai ga k'ofa ta bud'e juyowa yayi yakalli Barr Nas da yagama tsorata sannan yazare key d'in yashiga cikin bedroom d'in yamaida k'ofa yarufe, tsaye yayi a bakin k'ofar yana bin d'akin da kallo komai na ciki ya ji sosai za'a iya cewa aljannar duniya kenan, ta'be baki Faruk yayi sannan cikin sauri yanufi wajen wardrobe d'in yana zuwa baiyi wata wata ba yabud'e yafara bincike cikin sauri dubawa yadinga yi ammah baiji wayar ba saida yaduba kusan sau ukku baiga komai ba nan hankalinshi yafara tashi yace shikenan and'auketa daga wajen toh ammah tana ina? Ko dai Jawahir batasan inda takeba daman haka nan tace min tana cikin wardrobe d'inshi?. Tsaye yayi wajen, jikinshi duk ya yi sanyi sosai chan kuma yatuna da irin matsalar da zai shiga dan haka yajuyo cikin sauri zai fito yabar d'akin. Nas da yake zaune tsoro duk ya gama cikashi Allah Allah kawai yake Faruk yafito kafin dawowar Nazir yana cikin haka kawai sai jiyo muryar Nazir yayi ya tunkaro d'akin yana waya yana cewa shikenan Ummah ganinan yamzu zan kawo maki keys d'in daman sun tafi yanzu ina tare da su Nas ne kuma shi dai d'an gidane babu damuwa sai mufito mukoma setting room..... _Sis Nerja'art✍🏻_ [7/24, 11:13 PM] Sis Nerja'art 2: *......FANSAR RAI......* *INTELLIGENT WRITER'S ASSO....®* [On Award Together] _Follow me on Wattpad: *Sis-nerja*_ _Wannan Littafin na kud'i ne domin karantawa cikin aminci da yarda ga duk me buk'ata zai turo katin Mtn na d'ari biyu N200 kacal ta wannan number d'in 09035938246, ko ta account number 5330055604, Idan katura ka aiko da screen shot na transaction a wannan number d'in 09035938246_ _Akwai gara'basar *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shahararriyar marubuciyar nan *AMEENA ABBA UMAR* tare da novel d'in *FANSAR RAI* akan farashin N300 kacal, ko da kud'in ka sai da rabonka_ *PAGE 12* Barr Nas da yake zaune tsoro duk ya gama cikashi Allah Allah kawai yake Faruk yafito kafin dawowar Nazir yana cikin haka kawai sai jiyo muryar Nazir yayi ya tunkaro d'akin yana waya yana cewa shikenan Ummah ganinan yanzu zan kawo maki keys d'in daman sun tafi yanzu ina tare da su Nas ne kuma shi dai d'an gidane babu damuwa sai mukoma setting room. Wayyoooo kar kuso kuga Nas a lokacin zufa ce tafara kwarara daga jikinshi yana jin kamar yanutse cikin kujera, tsoro da fargaba duk suka d'arsu a cikin zuciyarshi, Nazir na gama wayar ya ida shigowa cikin d'akin yana shigowa yakalleshi yace ya naga kana zufa? Sorry bari ak'ara Ac d'in daman d'azu muka rageta. Shi dai da idanu yabishi kawai cikin ranshi yana cewa shikenan Faruk ya ja min, muryar Nazir yajiyo yana cewa ina abokin naka ba dai ya tafi ba? Dabarbarcewa yayi yarasa abinda zaice sai chan cikin rawan murya yace am ya je waje zai amsa waya ne. Toh shikenan bari mujira yadawo sai mukoma chan setting room ko kuma mutafi muhad'e da shi dan Ummah ta fara fad'a wai inkawo mata key d'in d'akin Abba saboda ba'a so ana shigowa yanzu za'a fara surutu. 'Yan cikin Nas saida suka kad'a yarasa abinda zaice ma Nazir sai chan cikin dauriya yace Nazir ko zaka taimaka min da ruwa insha kafin yadawo kaga kar mufita yadawo kuma bamu nan baisan inda muka nufa ba. Mik'ewa Nazir yayi yace hakane kuma bari inje inkawo maka ruwan dan na nan ciki basuda sanyi inyaso in nagamu da shi sai infad'a mashi. 'Daga kai kawai yayi dan baya ji a yanzu zai iya magana saboda tsananin tsoron da yashiga juyawa Nazir yayi yafita dan samo ma abokin nashi ruwa. Yana fita Nas yana son yamik'e ammah yakasa jikinshi ssi rawa yake yana nan zaune sai ga Faruk ya fito yana fitowa cikin sauri yarufe d'alkin, jin motsin tafiya yasa yawurgo ma Nas key d'in yayi saurin juyawa tare da kanga wayarshi a kunne kamar yana waya. Nas tura key d'in yayi a k'ark'ashin throw pillow d'in da Nazir ya ajiye key d'in daidai lokacin Nazir yashigo yana cewa na sa yanzu za'a kawo maka. Ajiyar zuciya Nas yasafke ganin asirinsu bai tonuba. Nazir kallon Faruk yayi da yajuya yana waya yace ashe ya dawo ai da nafita ban ganshiba. Murmushi Nas yayi yace Eh kana fita yadawo kuma aka sake kiranshi waya shine yamatsa chan yana yi. Nazir yace Allah sarki yanzu kuzo mukoma setting room na san sun ragu gashi fitarnan da nayi andameni infito inrufo d'akin. Murmushi Nas yayi yace haba ba damuwa ai mu ba bak'i bane, daidai lokacin Faruk yajuyo yana murmushi yace bakomai ai yanzu ma zamu tafi dan daga wajen aiki ake min neman gaggawa. Nazir yace tun yanzu maimakon kubari sai anjima. Kar kadamu muma munso mubari sai da anjima dan dai kiran gaggawar da akayi min ammah zamu dawo wani lokacin. 'Dauko key d'in Nazir yayi yace toh shikenan sai mufita gabad'aya in mik'a masu key d'in inhuta. Faruk yana lura da Nas da yake ta yi mashi kallon tuhuma ammah yak'i kulashi ahaka har suka fita. Saida suka jirashi yafara mik'a key d'in wa Ummanshi sannan suka tafi yarakasu har wajen mota yayi masu godiya suka shiga suka tafi, suna fara tafiya Nas yajuyo yakalleshi yace wai ya dai Faruk sai alama nake ta tambaya kuma ka gane nufina ammah kashareni wallahi hankalina ya tashi sosai Allah ya taimaka guy d'in nan bai gane komai ba. Murmushi Faruk yayi yace daman ya gane da kai zaka fi kwana ciki tunda abokinka ne. Au haka ma kace ko? "Toh me kakeso ince? Yanzu dai fad'a min shin ka d'auko wayar ko kuwa hakanan kafito baka gantaba? Murmushi yayi yace Eh toh banga wayar ba. Kana nufin baka gantaba hakanan kafito?,, Nas yatambayeshi cike da mamaki. Juyawa yayi yakalli taga sannan yace ina nufin ban gantaba a inda jawahir ta fad'a min saidai na ganta a wani wajen na daban. Ajiyar zuciya Barr Nas yasafke yace Alhamdulillah na ji dad'in haka gaskiya Barrister kai d'in nadaban ne saisa ko a school nake jinjina maka dan k'walwarka tana ja sosai. Juyowa Faruk yayi yakalleshi tare da fiddo wayar daga cikin aljihunshi yana murmushi yace tabbas ina farin ciki Nas ko ba komai wayar nan zata taimaka min wajen samun duk wani abu da nakeso, yanzu dai mu wuce gidana kasafkeni dan ko motsta bazan d'auko gidanka ba. Kallonshi Nas yayi yace ban gane insafkeka ba malam, muje dai ind'auko su Madam inmaidasu gida inyaso kaga sai muwuce gidan naka ko ba haka ba? Hakan ya yi abokina ai duk yadda kakeso haka za'ayi dan yau ba k'aramin taimako kayi min ba. " yoh ba dolena intaimakeka ba tunda nima ka taimaka min wajen samo soyayyar madam a school" Su dukansu dariya sukasa nan Faruk yagirgiza kai tare da juyawa yana cigaba da kallon taga. Bayan sunyi sallar magrib a cikin anguwarsu Faruk sannan suka wuce gidanshi a parlor suka zauna Faruk yaso yakunna wayar ammah yajita a kashe alamun ba charge dan haka yatashi yajonata sunayin sallar isha'i Barr Nas yace shi zai wuce gida koma menene inyaso gobe zasu had'u. Barr Faruk yace babu damuwa nan yarakashi har wajen mota yana tsokanarshi tashin hankalin da yaga ya shiga lokacin da yafito cikin d'akin. Barr Nas yana dariya yace ka ma yi sa'a da bakaga na saki zawo ba dan wallahi har na hango makomata gaskiya na yi kasada dayawa Allah dai ne yacecemu. Hakane Nas ni fa daman kai nafi ji ba kainaba dan banaso inja maka wani abu yasameka. Hmm toh yanzu ya za'ayi idan zaka maida wayar? Barr Faruk yace a'a bazan maidata ba tunda shima ba tashi bace idan nagama bincikena zansan yadda zanyi da ita. Toh shikenan Barrister Allah dai yataimaka sai dai goben idan na shigo. Toh Allah yakaimu. Bayan tafiyarshi Faruk wanka yayi yashirya wajen k'arfe tara yacire wayar daga charge yafara bincika abubuwan da suke cikinta ya samu shaidu sosai dan hatta recordings ya samu na wayar da akayi har da wanda alamu yanuna anyi recording antura ma wani ya saurara, wata murya da yaji anyi waya da me ita saida yaji kamar ya san muryar ammah yakasa tantanceta. Cikin contacts yashiga yafara binciken numbobin ciki nan yaci karo da number d'in da tad'aga mashi hankali saurin d'auko wayarshi yayi yasaka number d'in yayi dialing a nan ya ida tabbatarwa da tabbas number d'ince hankalinshi ba k'aramin tashi yayi ba, ajiye wayar yayi tare da dafe kanshi ji yayi komai ya tsaya mashi, chan kuma yamik'e yafara zagaye d'akin yana zuwa yana dawowa hannuwanshi suna a bayanshi ya rik'esu tunowa yafara yi da lokacin da jawahir take ce mashi zaka taimaka min kana nufin komai kusancinka da mutum idan har yana da hannu a ciki bazaka ta'ba barinshi ba? Cize le'be yayi a hankali sannan yakoma yazauna yak'ara d'auko number yasake dubawa tabbas idanunshi ba gizo sukeyi mashi ba toh ammah me hakan yake nufi kenan shima akwai hannuwanshi acikin mutuwar mahaifan Jawahir? A'a kodai abokinshi ne kawai ammah baida hannu acikin mutuwarsu, toh ammah call recording d'in da naji fa tabbas akwai na muryarshi ya ji shi, sake kunno recording d'in yayi yasaurara muryarce yaji tana cewa Hello kana jina ya kamata kayi k'ok'ari wajen ganin ka samo mana file d'in filin nan dan da alama zaiyi kud'i sosai ni na san yadda za'ayi asiyar da shi batare da kowa ya ganeba dan nima kaga wannan filin da kabarmin gwamnati nasiyar mawa kuma ta siya da kud'ad'e masu tsoka. Toh shikenan Alhaji koma me kenan nasan hanyar da zanbi insamo dan dama maganar da muka gama yi da Alhaji tanimu kenan dan shine jagoran komai, da ace akwai hanyar da zanbi da a yau d'innan sai naga bayan yarinyar nan kowa yahuta dan na san idan har tamutu dole abarmin gadonta gabad'aya tunda ni kad'ai ne d'an uwan mahaifinta,,, Cewar Alhaji Mu'azu. Daga chan 'bangaren dariya akayi akace kaidai kabi komai a hankali ko da baka kasheta ba zaka iya yin amfani da damarka wajen ganin mun samo dukiyar Alhaji Muhammad, inyaso idan har mun gama samun yadda mukeso zaka iya kasheta saidai kuma idan har zaka rufe ma mutane baki dan kar ayi zargin wani abu kamar yadda mukayi bayan munsa ankashe Alhaji Muhammad da matarshi. Dariya Alhaji Mu'azu yayi yace ai fiye da hakan ma zan iya sa wa ayi mata dan ni ban had'a komai da kud'iba abokina, yanzu dai zuwa anjima zan kiraka idan har nagama tattara bayanan filin inyaso sai muje musiyar da shi. Yauwa mutumina kayi k'ok'arin haka sai na ji daga gareka. Ana zuwa nan recording d'in yak'are. Wani kuma yasake kunnowa nan ma yaji muryar mutumin yana cewa, Hello Alhaji Mu'azu ina jinka d'azu ka kirani bana kusa. Eh Wallahi abokina cewa nayi ta samu fa a yanzu ga wani gida nan na Alhaji Muhammad da nagano yana da shi batare da sanin kowaba sai yanzu naga takardun gidan na je na ganshi kuma antabbatar min da nashine. Daga chan 'bangaren dariya akayi akace lallai Alhaji Muhammadu wayonshi ya yi yawa watau yana da gida batare da sanin ka ba, toh bari zan zo inje muga gidan idan har yana da girma sosai ni zan sayeshi dan dama inaso mutashi da iyalina daga nan, kace abu ya zo gidan sauk'i ai wallahi mutuwar nan tashi dad'i tayi min dan ko bakomai munsan muma mun mori dukiyarshi. Alhaji Mu'azu ma dariya yayi yace kaidai bari a yanzu gashinan ina ta facaka da kud'i yadda nakeso ba kamar lokacin da yake raye ba, ka san mutuwarshi ko kad'an bata d'aga min hankali ba sai waje d'aya lokacin da kabani layarnan insaka mashi a baki toh a nan ne nad'an tsorata dan ko da su Alhaji Mannir suka shigo gidan zasu kasheshi ban wani d'aga hankaliba dan na san zamuyi nasara. Katseshi yayi yace a'a Alhaji Mu'azu kayi shuru kar ajiyo ka asirinmu yatonu agane mune muka kasheshi abar maganar kawai zan zo yanzun nan muje inga gidan dan ka san bana wasa da kud'i,,, su dukansu dariya sukayi. Hakayayi ta kunno recording d'in me muryar yana saurare ________Yana gama sauraren recording d'in ajiyar zuciya yasafke tare da kwantar da kanshi saman gadon inda k'afafuwanshi suna a k'asa ahankali yace tabbas biri ya yi kama da mutum toh ammah ta wace hanya zanbi wajen ganin na kamasu da laifin da nake zarginsu, dan shi kad'ai ne yagane muryarshi bai gane muryoyin sauran da yaji ba saidai ya gane ta mutane biyar saboda sunansu da Alhaji Mu'azu yake ambata a cikin wayar saidai mutum biyu ne bai ganeba toh ammah su wanene? Shin suna raye ko su ma ankashesu? Kanshi ne yajefa ma tambayoyin. Kasa runtsawa yayi dan kwatakwata daman bai sa ma ranshi yin bacci a lokacin ba nan yayi kwance yana ta 'yan tunane tunane tare da neman hanyar da zai 'bullo wajen ganin ya kamashi da laifin da yake zarginshi da shi, tashi yayi yad'auko wayarshi yana tura duk recording d'in da yake so masu alak'a da case d'in ya dad'e yana turawa dan suna da yawa sosai saida yaza'bi iya wanda yakeso, a cikin kunnuwanshi akayi kiran sallar asuba. Wajen k'arfe goma yagama shirin shi yaje wajen aiki kasancewar litinin ce yana zaune yana aikinshi nan aka kirashi a waya dubawa yayi ganin private number ne yasa yashare baiyi picking ba wani kiran yasake shigowa a karo na biyu, tsaki yayi sannan yad'auko wayar zai kashe ta gabad'aya dan kar tahanashi yin aikinshi sai kuma yafasa yayi picking batare da yayi magana ba. Daga chan 'bangaren akace Hello kana ji? Shuru yayi yana sauraren muryar kamar ya ta'ba jinta k'ara jefo mashi tambaya akayi "wai ko ba Barr Faruk bane" Saurin d'ago wayar yayi daga kunnenshi yadanna inda zatayi mashi recording d'in maganar sannan yace Hello ina ji. Au daman kana ji shine zakayi shuru watau har rainin hankalinka ya kai ga haka,,, tsaki yaji anja sannan aka kashe wayar. Bai damu da hakan ba ya ajiye wayar yacigaba da aikinshi. Saida yatashi daga aiki sannan yaje yasamu Jawahir tana ganinshi murmushi tasakar mashi tace ina tayaka murna. Shima murmushin yayi yace murnar me kenan? "yanayinka da nagani ya sa na gane ka samo wayar" Matsowa yayi kusa da ita yace Eh hakane na samo kuma duk na saurara saidai mafi yawansu sun mutu dan naji maganarsu da sunan su da aka kira acikin recording d'in. Fara'ar da take fuskarta ce tagushe tace tabbas hakane duk sun mutu dan dama mutane takwas ne kuma a yanzu shidda daga cikinsu sun mutu, Yaya Aliyu baya cikinsu kawai dai Ammi ta d'auki fansar kasheta da yake da hannu a ciki da kuma niyarshi ta ganin bayana, Mijina Umar ma baya da hannu a ciki, su Abba da abokanshi ne. Jinjina kai yayi yace na fahimci haka Jawahir saidai akwai wani taimako da nakeso kiyi min. Taimako kuma? Wane irin taimako ne?,, tajefa mashi tambaya. "Kar kidamu yanzu zan sanar da ke koma menene..... _____________ Bayan kwana biyu Faruk yana kwance a d'akinshi Mom tashigo tasameshi zama tayi daga gefenshi tace ya dai Faruk ba dai tunani kake ba? Murmushi yayi tare da tashi zaune yace No Momcy bacci natashi ne. Ohk, ina fatan babu wata matsala. Kallon Mom d'in tashi yayi cike da k'aunarta dan ya san bata son ganinshi cikin kowace irin matsala, girgiza kai yayi yace babu komai Momcy. Yauwa haka nakeson ji da anjima idan zaka fita zan baka sak'o kabiya kakaima Hajiya Maijidda. Da mamaki yake kallonta yace Hajiya Maijidda kuma? Cikin nuna rashin damuwa tace Eh ita tunda kai bakayi da 'yarta wannan ba zai sa mu mudaina zumunci ba dan ka san matsayinta a wajena. Murmushi yayi yace toh Ammi babu damuwa ai yanzu ma zan watsa ruwa infita sai ma kawai infara zuwa gidan. Hmm ka ji da shi kana so kana kaiwa kasuwa nasan dai kana son ganin Nasiba ne. Kallon mahaifiyar tashi kawai yake batare d ya ce komai ba. Nan tamik'e tace idan kafito sai kasameni a part d'ina ka amshi sak'on. Toh Mom. Wajen k'arfe biyar ya isa gidansu Nasiba yana shigar da motarshi cikin gate d'in gidan daidai lokacin Nasiba tacinno kan tata motar, da mamaki take kallon motar Faruk cikin ranta taji wani irin sanyi har ta ayyana ko ya dawo gareta, murmushi tayi tace inko hakane zanyi farin ciki sosai, duba fuskarta tayi ta cikin mirror d'in motar taga fes take sannan tabud'e tafita. Faruk yana yin parking zaune yayi cikin motar sai a lokacin yafara tunanin ta yadda zai iya shiga yakai ma Hajiyar Nasiba sak'o da tun chan baya baiyi tunanin haka ba ko da ya san hakan yana da nasaba da son ganin sanyin idaniyarshi da yakwana biyu baisakata a idanunshi ba, zaune yayi yana kallonta har tafito daga motar tajingine a jikin motar tana kallon tashi motar. Ganin haka yasa yabud'e yafito hannunshi rik'e da sak'on Mom, tsayawa yayi yana kallonta shima da manyan idanuwanshi su dukansu kowa yana ayyana abu acikin zuciyarshi chan sai Faruk yataka yanufi wajen da take. Har ya isa bata daina kallonshi ba, sallama yayi mata sai a lokacin tajanye idanunta daga kallonshi tasadda kanta k'asa sannan ta amsa mashi ahankali. Murmushi yayi yana jin wani irin dad'i a ranshi, muryarta yaji ta gaisheshi, nan ya amsa, daga haka kuma duk sukayi shuru still dai idanunshi suna a kanta gani yayi ta d'an rame, ya shagala da kallonta ita kuma jira kawai take yafad'a mata ya dawo gareta bakinta d'auke da murmushi jin shuru har lokacin bai ce mata komai ba yasa tad'an d'ago tasaci kallonshi karaf suka had'a idanu. Dabarbarcewa yayi yace am Nasiba daman Mom ce tabani sak'o inkawo ma Hajiya ban saniba ko tana ciki. Saurin ida d'ago kai tayi takalleshi nan k'wallah tacika idanun cikin ranta tace ashe daman ba dawowa yayi gareni ba, ahakali tabud'e baki cikin murya me kama da ta kuka tace kashiga tana ciki. Tsaye yayi yana kallonta shi kanshi baiji dad'in hakan ba ko bakomai ai ya kamata ace sun gaisa, cikin k'arfin hali yace Nasiba ina fatan kina lafiya? 'Daga mashi kai tayi alamun Eh. Ajiyar zuciya yasafke yace ammah na ga kin d'an rame saisa nayi tunanin ko bakida lafiya. Hawayen da suka taru cikin idanunta ne suka zubo, cikin zuciyarta tace lallai ma Faruk watau tambaya yake ko banda lafiya bayan ciwon da yabar min acikin zuciyata, girgiza kai tayi tace a'a kawai dai...sai kuma tayi shuru. Kawai dai me? Memakon tabashi amsa sai cewa tayi kaima naga ka d'an rame ko duk aikin ne? K'ayataccen murmushin shi me tsada yasakar mata sannan yace ko d'aya lafiya ta lau saidai kece kad'ai damuwata. Ji tayi kamar a mafarki yafad'a mata haka shi kanshi saida yaga tsantsan mamaki a tattare da fuskarta, saurin sa hannu tayi tagoge hawayen da suke fita tace anya Faruk hakane ba kawai ka fad'a min bane? Na tabbata da ace kana sona da bazaka ta'ba banzatar da ni ba. No Nasiba ko d'aya ban banzatar da ke ba kawai dai banda yadda zanyi ne saboda Daddynki ammah ni ko a yanzu yajanye k'udurinshi.. Tarar numfashinshi tayi tace ammah dai Faruk wannan bai dace yazama hujjar da zaka iya hak'ura da ni ba kaidai kawai kace min ka daina sona, bayan ka dasa min ciwon da har yanzu ya kasa warkewa a cikin zuciyata. K'ara matsowa yayi saitin fuskarta yace Nasiba da sannu zani dawo gareki kikwantar da hankalinki. 'Dan guntun murmushi tayi sannan tace wane lokaci ne wannan ko har sai na bar duniya? Please kidaina wannan maganar bazaki mutu ba insha Allahu nan da 'yan kwanaki kad'an zan dawo gareki, kallon k'ofar gidansu yayi sannan yace kinga amsa inbaki kishigar ma Mummy da shi. Wani irin dad'i taji akan maganarshi ko bakomai yanzu ta tabbatar Faruk zai dawo gareta, kasa 'boye farin cikinta tayi har saida yabayyana, tace dagaske kake Faruk? Maido kallonshi yayi akan fuskarta sannan yace insha Allahu Nasiba dan bana ji zan iya cigaba da rayuwa batare da ke ba, nasan Daddynki yana nan bazan shiga gidan ku ba dan banso muhad'u dan Allah ki amsa kikai mata. Kallon motocin da suke wajen tayi taga dukkansu suna nan dan haka ta san tabbas Daddy yana gida, bata musaba ta amshi ledar. Murmushi yayi yace yauwa na gode, nan yajuya zai tafi, bud'e baki tayi kamar zatayi magana sai kuma tafasa. Ja yayi yatsaya tare da juyowa yakalleta yace please Nasiba akwai wani d'an taimakon da nakeso kiyi min. Murmushi tayi tace toh ba damuwa, menene kakeso ko ma menene kafad'a zanyi maka. Rasa yadda zai ce mata yayi dan bayaso tazargi wani abu, ganin ya yi shuru yasa tace kai nake sauraro. Am daman dan Allah Number d'in Alhaji Mansur nakeso kisamo min a wajen Daddynki ammah dan Allah kar kibari yagane ni zaki ba. Murmushi tayi tace indai wannan ne kar kadamu zan samo maka. Shima murmushin yasakar mata yace Nagode sosai My Wife to be sai na jiki. Wayyo farin ciki tsantsa Nasiba tashiga batasan lokacin da tamaimaita kalmar ba, nan yajuya yafara tafiya, ji take kamar tatsaidashi ammah takasa. Shi kanshi wani irin dad'i yake ji ko bakomai ya ba idanunshi abincin shi, ko da ya san ya yi k'ok'ari sosai wajen controlling kanshi bai nuna mata irin yadda yadamu sosai d'innan ba, ko da ya san k'asan zuciyarshi shi kanshi ciwone da baida magani indai ba ya ga anmallaka mashi Sanyin idaniyar shi ba. Yana isa wajen motarshi har ya bud'e zai shiga yajuyo yakalleta yasakar mata lallausan murmushi itama maida mashi martani tayi sannan tanufi cikin gida. Tana shiga dagudu tanufi hanyar part d'in Mummy tana k'wala mata kira, ja tayi tatsaya a parlor lokacin da tagansu zaune ita da Daddynta, Daddyne yace Nasiba wannan irin kira haka me yafaru? Ko ta samu ne? Murmushi tayi tace bakomai Daddy. Yace ke dai fad'amin shalele ko ansamo mana wani sabon siriki? Kunya ce takamata tayi saurin mik'a ma Hajiya Maijidda ledar da Faruk yabata tace Hajiyata ga sak'onki sannan tajuya dagudu tanufi part d'inta. Ba Daddy ba hatta Hajiya maijidda saida tadara, duba ledar tayi ganin sak'on Hajiyar Faruk ne yasa tayi murmushi tace watau yau ta had'u da abin k'aunarta saisa tashiga farin ciki, har ta bud'e baki zata sanar da mijin nata dalilin farin cikin d'iyar tasu nan wayarshi tafara ruri, mik'ewa yayi yafita yana cewa ganinan zuwa. Nasiba tana shiga d'akinta saman gadonta tafad'a tare da jawo pillow tarungume a k'irjinta fuskarta tana d'auke da k'ayataccen murmishin da tunda taga Faruk take fitar da shi, ahankali tace nagode faruk tabbas a yanzu na tabbatar zaka dawo gareni, lumshe idanunta tayi tare da k'ara matse pillown a k'irjinta tana jin farin cikin da rabon da taji irinshi tun lokacin da aka fasa baikonsu da Faruk... _Sis Nerja'art✍🏻_ [7/24, 11:14 PM] Sis Nerja'art 2: *......FANSAR RAI......* *INTELLIGENT WRITER'S ASSO....®* [On Ward Together] _Follow me on Wattpad: *Sis-nerja*_ _Wannan Littafin na kud'i ne domin karantawa cikin aminci da yarda ga duk me buk'ata zai turo katin Mtn na d'ari biyu N200 kacal ta wannan number d'in 09035938246, ko ta account number 5330055604, Idan katura ka aiko da screen shot na transaction a wannan number d'in 09035938246_ _Akwai gara'basar *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shahararriyar marubuciyar nan *AMEENA ABBA UMAR* tare da novel d'in *FANSAR RAI* akan farashin N300 kacal, ko da kud'in ka sai da rabonka_ *PAGE 13* ...Nasiba ce zaune a parlon Daddynta da dare ita da iyayen nata suna kallo ammah ita duk hankalinta ba a wajen kallon yakeba tunani kawai take tana neman hanyar da zatabi tasamo number d'in Alhaji Mansur batare da Daddynta ya ganeba, a gefe d'aya kuma tambayar kanta take shin me yasa Faruk yake son tasamo mashi number d'in? Chan kuma a fili tace ko dai akan maganar aurenmu ne yakeso suyi magana. Muryar Hajiyarta ce taji ta ce lafiya Nasiba kike magana ke kad'ai? Murmushi tayi dan batasan maganar ta fito fili ba dan ma Allah ya taimaketa ahankali tayita, girgiza kai tayi tace a'a ba magana nakeba Mummy, juyawa tayi takalli Daddynta da hankalinshi yake a kan news d'in da yake kallo gyaran murya tayi tace am Daddy dan Allah ka ara min wayarka. Juyowa yayi yakalleta yace Nasiba me zakiyi da ita ba dai wayarki babu credit ciki ba? Girgiza kai tayi tana murmushi tace a'a Daddy Number d'in Yaya Maryam zan d'auka na yi loosing d'in contact d'inta. Mummy ce tace ai dama sauk'i tunda number ce kikayi loosing ba taki wayar ba. Turo baki tayi tace kai Mummy ni yaushe rabon da inyada waya anfi shekara biyu. Daddy ne yamik'a mata wayarshi yace amsa rabu da ita shalele anfad'a mata da da yanzu d'aya ne bataga da bambanci ba. Amsa Nasiba tayi tana dariya tace Allah Daddy ita Mummy da abu ya wuce sai tadinga tuno ma mutum Kibarta Shalele na ma kusan canza maki sabuwar waya. Mummy murmushi tayi tace oho dai na baku zuwa gobe ai sai anji ku indai Nasiba ce. Fakar idanun iyayenta tayi tashiga cikin contact d'in Daddy tad'auki number d'in Alhaji Mansur sannan tamik'a ma mahaifin nata wayarshi. Zama tayi na kusan mintuna biyar sanna tayi masu sallama tatashi takoma part d'inta cike da farin ciki, saida tahau saman gado sannan talalubo number d'in Faruk. A chan 'bangaren Faruk bayan ya gama shirin shi na bacci yana kwance saman gadonshi yana tunanin abar k'aunarshi yana jin wani irin dad'i a ranshi akan had'uwarshi da ita, shi kanshi ya san yana son Nasiba sosai ya yi k'ok'ari sosai da har ya iya danne son nata a yau bai nuna mata ya yi missing d'inta ba, murmushi ne yasu'buce mashi lokacin da yatuno yadda suke nuna ma juna soyayya kafin wannan abun yafaru, lumshe idanunshi yayi ahankali sannan yace Nasiba kina raina a kowane lokaci, yadda kike missing d'ina nima haka nake naki, ina fata akwai lokacin da komai zai zo k'arshe muyi aure.....yana cikin haka wayarshi tafara ringing tashi yayi zaune tare da d'aukota saman bedside ganin Nasiba ce yasa yai murmushi tare da yin picking, daga chan 'bangaren tayi mashi sallama ya amsa nan kuma duk sukayi shuru sai chan kuma takauda shurun ta hanyar cewa ina fata ka koma gida lafiya? Lafiya lau Nasiba. Wani irin haushi taji ganin a yanzu wai Faruk ne yake kiranta da sunanta ko dai ya daina sonta ne? Wasu siraran hawaye ne suka gangaro mata cikin sanyin murya tace am daman na kira ne infad'a maka na samo number d'in. Kai masha Allah na ji dad'i sosai Baby ina fata dai baki bari Daddy yagane ba? 'Dan guntun murmushi tayi cikin ranta tace wai kuma Baby dan na samo mashi abinda yake so, sai kuma chan tace uhm uhm bai gane ba. Toh shikenan kituro min kinji? Shuru tayi batace mashi komai ba, sake maimaita mata yayi nan ma shuru. Ajiyar zuciya yasafke yace Nasiba kiyi hak'uri duk yadda kikeji nima kaina ina ji ba wai na daina sonki bane wallahi ina k'aunarki sosai saidai banda wani za'bi da zan iya hak'ura da case d'innan bayan alk'awali nayi akanshi kuma kema kinsan girman alk'awali. Fashewa tayi da kuka tace ammah Faruk ka san ina sonka shine karabu da ni.. Katseta yayi yace kidaina cewa haka Nasiba wallahi ko d'aya ban rabu da ke akan son raina ba kuma har yanzu ina nan akan bakana zan dawo gareki a duk lokacin da muka gama shara'ar nan kikwantar da hankalinki kin ji ko? Rage sautin kukanta tayi tace shikenan Faruk ina nan ina jiranka dan Allah kar kabarni. Murmushi yayi yace kar kidamu da sannu zan baki mamaki dan banaso aja lokacin bikkin mu, nidai fatana kidaure kicire duk wata damuwa a ranki kikwantar da hankalinki sannan kidaina kirana a waya kar parents d'inki sugane har yanzu muna tare ransu ya'bace kibari mubi komai a sannu Nasiba. Cikin jin dad'in kalamanshi tace toh shikenan Hearty duk yadda kakeso haka za'ayi. Lumshe idanunshi yayi tare da sakin murmushi sannan chan k'asan mak'oshinshi yace kece rayuwata zan kasance da ke akowane lokaci acikin zuciyata, kikwanta kiyi bacci. Ita kanta lumshe idanunta tayi tana fitar da murmushi me sauti "Nagode sosai Hearty hak'ik'a nayi farin ciki da jin kalmar nan a yau zanyi baccin da rabon da inyi irinshi tun muna tare shikenan sai dasafe. Sallama sukayi suka kashe wayar kusan a tare suka manna wayoyinsu a bisa k'irjinsu suna murmushin farin ciki, kowa na jin soyayyar d'an uwanshi tana fizgarshi. Chan Faruk yaji shigowar text yad'aga wayar yana dubawa sai ganin number d'in Alhaji Mansur yayi ta turo mashi. Murmushin jin dad'i yayi cikin ranshi yace kin gama min komai My Life, nan yatura mata " Thanks my wife to be insha Allah, Good Nyt, kiyi bacci me dad'i. A karo na biyu tasake lumshe idanunta cikin jin dad'i tace Night too My Everlasting,,, tana manne da wayar a k'irjinta a haka tayi bacci. Achan 'bangaren Faruk tashi yayi yagama duk abinda zaiyi sannan yakoma yakwanta. Washe gari yana zaune a parlorn d'akinshi yana kallon kwallo inda a saman d'an teburin da yake gaban kujerar da yake zaune fruit salad ne yana sha, sai wajen k'arfe sha d'aya yagama kallon yamik'e yad'auko wayarshi da yajona charge yakoma inda yake zaune kasancewar ranar bazaije wajen aiki ba, Number d'in Alhaji Mansur yalalubo yakira, har saida takusan tsinkewa sannan akayi picking, sallama yayi daga chan 'bangaren Alhaji mansur ya amsa a dak'ile tare da tambayar wanene. Faruk bai damu da yanayin da ya amsa shi ba yace am Barr Faruk ne daman na kira ne intambayeka dan Allah in ba damuwa ina zan sameka dan akwai magana me muhimmanci da zamuyi. Tun kan yarufe baki yaji muryar Alhaji Mansur cikin fad'a yana cewa babu wata magana me muhimmanci indai ba janyewa kayiba kabari aka kashe yarinyar chan kamar yadda takashe wasu. Murmushi Faruk yayi dan yanayin yadda yayi maganar ta so tabashi dariya ammah yadanne sannan yace koma menene kaban dama muhad'u sai mutattauna. Toh shikenan zan turo maka adress d'in Guest House d'ina sai kazo kasameni. Cikin jin dad'i Barr Faruk yace toh shikenan sai na jika,,, bai jira jin abinda zai ce ba yakashe wayar tare da saving d'in recording d'in da yayi, gudar wayarshi yad'auko yakunna muryar da yake tunani ta Alhaji Mansur ce yasake saurare tabbas ya ida gasgatarwa da tashin ce, yana nan zaune sai ga message ya shigo wayarshi yana dubawa yaga Alhaji Mansur ne, murmushi yayi yace dakyau haka nakeso nan yamik'e yashige bedroom d'inshi bai dad'eba yafito hannunshi rik'e da key d'in motarshi fuskarnan ya dad'eta da bak'in glass d'aukar wayoyinshi yayi yafita yabar gidan. Yana isa k'ofar gate d'in gidan duk security's suka taso suka nufo wajen motarshi ganin haka yasa yagane bazasu barshi yashiga ba nan suka fara tambayarshi me yazo yi? batare da ya basu amsaba yad'auko wayarshi yakira Alhaji Mansur yana yin picking yace gani a k'ofar gidanka wad'annan k'attin da katara sun hanani shigowa. Ba su da akace ma k'atti ba hatta shi kanshi Alhaji Mansur ya ji ciwon abun dan de kawai yana so yasan abinda yakawoshi saisa yadanne fushinshi yace basu waya muyi magana. Mik'ama d'aya daga cikinsu wayar yayi yace oganku yana son magana da ku. Amsa yayi yakanga a kunne nan sukaji yana cewa ohk sir angama, mik'a ma Barr Faruk wayar yayi sannan yabada umurni aka hangame mashi tank'amemen gate d'in yashigar da motarshi parking yayi yafito nan d'aya daga cikinsu yayi mashi jagora zuwa cikin gidan, Faruk ko kanshi d'aurewa yayi ganin makeken Guest House d'in Alhaji Mansur ahaka har suka isa wani tank'amemen parlor inda Alhaji Mansur d'in yake zaune ya kame sai hura hanci yake. Sucurity d'in komawa yayi inda Barr Faruk yayi sallama yashiga, amsawar ma cikin tak'ama aka yi mashi, murmushi kawai Faruk yayi yaje yazauna saman kujerar da take opp d'in wadda Alhaji Mansur yake zaune cikin tak'ama yazauna tare da d'aura k'afa d'aya saman d'aya, koda Alhaji Mansur yakalleshi saida yaga ya yi mashi k'warjini, zare glass d'in da yake fuskarshi yayi sannan yace sannu Alhaji. Cikin isa ya amsa da yauwa ka ce kana son ganina ko? Murmushi yayi yace Eh saboda inaso ka amsa min wasu tarin tambayoyi da ke gareni. Da mamaki yake kallonshi yace wane irin tambayoyine haka? Ta'be baki yayi yace ba wasu tambaboyi bane masu wuya kawai dai akan case d'in mutuwar su Alhaji Muhammad Mai kud'i ne. Gaban Alhaji Mansur wani irin mummunan fad'uwa yayi yai saurin gyara zaman shi tare da kallon Faruk yace ban fahimceka ba me kake nufi? Murmushi yayi yace daman bazaka fahimceni ba saidai yanayin yadda kafirgita ya sa na gane ka d'an fahimci wani abu, ammah dai kar kadamu da wannan na san dai Alhaji Muhammad abokinka ne kai da su Alhaji Tanimu toh abin mamakin bayan mutuwarshi kuka koma kuka k'ulla abota da yayanshi Alhaji Mu'azu, saidai hakan baisa kuyi tunanin ko za'a iya zarginku da wani abu ba? Ko ma ace akwai wani abu da kuka shirya ku d'in? Zumbur Alhaji Mansur yamik'e tsaye cikin fushi yace ban ganeba me kake nufi, wannan ai zancen banza ne ka zo ne daman dan karaina min hankali? Murmushi yayi a karo na biyu sannan yace kaga Alhaji da ka zauna munyi magana cikin kwanciyar hankali ba sai an jiyo abinda muke tattaunawa ba. 'Daga murya yayi yace kowa yajiyo man ina ruwana, watau ni kake zargi ko kenan? Shima mik'ewar yayi yace ni ba zarginka nakeba tambayoyi suka kawoni wajenka kuma ya kamata ka amsa min su, shin ya labarin kud'ad'e, gidaje, filayen marigayi Alhaji Muhammad da suke hannunku ko kun ajiyesu ne sai d'iyarshi ta fito daga gidan kaso sannan kumallaka su a wajenta tunda kawunta wanda kuke tayawa ajiyewa ya rasu? Alhaji Mansur mutuwar tsaye yayi yana kallon Faruk da tsantsan mamaki jin kalaman da suka fito bakinshi bayan babu wanda yasan wannan sirrin sai su kad'ai toh ina yaji hakan? Yana cikin tunanin yaji muryar Faruk ya cigaba da cewa sannan takardun kamfanin yarinyar chan ya kamata ace kun damk'a mata abunta, filayen da gomnati tasiya ma a wajenku ko tana da alak'a da su? A fusace cikin d'aga murya yace ya isheka haka Barrister! ya isa!!! Watau ni zakazo kaci ma mutunci dan kawai mahaifin Nasiba ya hanaka auren d'iyarshi ni zaka ja ma sharri? Toh wallahi ya zama dole indamk'a ka a hannun hukuma dan bazan lamunci hakan ba da girmana a gari kanemi kazubar min da shi, duka dukiyar muhammad nawa take da har zamu so mucita kaduba girman Guest house d'ina wanda ko rabin girman gidana bai kai ba shin wannan bai isa yazama shaidaba akan cewa na fishi dukiya? Bazan barkaba dole kotu tashiga ciki,,, wayarshi yad'auko yana shirin lalubo number. Murmushi Barr Faruk yayi yace kiran wayar da zakayi daidai yake da tona ma kanka asiri, shin zaka iya tuna wata mota sabuwa fil da Alhaji Muhammad yasiya wadda kaci burin kamallaketa Wadda cikin motocinka babu kamar ta? Ko zaka iya tuna wayar da kukayi da Alhaji Mu'azu akan son mallakar dukiyar jawahir da take cikin account d'in mahaifinta?.. Wayar da take hannunshi ce tasu'buce tafad'i nan yafara zufa 'yan cikinshi saida suka kad'a, wuta tad'auke mashi d'if saida yayi kusan minti biyar suna kallon kallo da Barr Faruk sannan yayi k'ok'arin saita kanshi sannan cikin inda-inda yace ina kaji wannan? wanene yafad'a maka hakan? Tsayawa Barr Faruk yayi yana kallonshi ganin haka yasa Alhaji Mansur yanufoshi a harzuk'e yana cewa tambayarka nake kabani amsa! Ja yayi da baya yace ka ga kar kamatso min nan ni tambayarka nayi kuma amsa nakeso. Idanuwan Alhaji Mansur jajir sukayi saboda 'bacin rai cikin fushi yanuna mashi hanya yace fitar min daga gida tun kan insa afitar da kai ta k'arfi, wannan cin fuska ya yi yawa ace katako har cikin gidana kaci min fuska, kai wanene a garin nan da har zakayi min haka? Ta'be baki yayi cikin nuna rashin damuwa yace na ji zan fita kuma ni ba kowa bane saidai inaso kasani na san abubuwa da dama agame da duk abinda kuka aikata, sannan kashirya zan k'ara dawowa gareka dan neman amsar wad'annan tambayoyin kai har ma da wasu na daban, murmushin gefen baki yayi sannan yace na barka lafiya,,, yana fad'in haka yajuya yafita. Alhaji Mansur tsaye yayi yakasa ta'buka komai mamaki duk ya gama cikashi nan kuma yafara zagaye d'akin yaje yadawo haka yaitayi cikin ranshi yana tunanin wanene yasanar da Barrister duk wannan to kodai yarinyar chan ce? Toh ammah ita kanta batasan abinda duk muka shiryaba, saidai ya kamata inyi wani abu a nan, komawa yayi yazauna yad'auko wayarshi yalalubo wata number bata dad'e tana ringing ba akayi picking ko sallama bai tsaya yi ba yace Alhaji da matsala. Daga chan 'bangaren akace matsala kuma? Wace iri kenan? "Lauyan wannan yarinyar ya zo ya sameni ya tisani a gaba yana min wasu tambayoyin da suka nemi surikita min k'walwa wanda bansan amsoshinsu ba ammah ba ma wannan ba tambayar a nan itace duk ina yasan wad'annan abubuwan? Daga chan 'bangaren dariya aka fara kyalkyatawa har saida Alhaji Mansur yafusata ganin dariyar batada niyar k'arewa yasa yace watau kai dariya ma kakeyi ko? Dole inyi dariya Alhaji Mansur wannan abun bai kamata yad'aga maka hankaliba. Ajiyar zuciya yasafke yace hakane ammah ya zama dole inyi wani abu akan yaron nan kafin yanemi tozartani koda na san hakan ba zai ta'ba yuwuwa ba ammah dole inga bayanshi, ya kamata muhad'u da kai zuwa anjima domin musan ta inda zamu 'bullo mashi. Toh shikenan babu damuwa zan shigo. Kashe wayar yayi tare da mik'ewa yana cigaba da zagaye d'akin still dai wayarshi tana a hannunshi, ya dad'e a tsaye yana kaiwa da kawowa daga k'arshe yatsaya waje guda tare da duba wayarshi yakira wata number ana yin picking batare da ya yi sallama ba yace Barrister ina son muhad'u da kai yanzun nan kazo gidana kasameni. Ohk ba damuwa sai ka zo ina nan ina jiranka. Yana gama wayar komawa yayi yazauna tare da cije le'be yana jinjina kai yace tabbas ya zama dole inyi maganinka Barrister ba ma kai ba duk wanda yace zai shiga rayuwata sai naga bayanshi dan haka muje zuwa. Bayan ya bar gidan Alhaji Mansur direct gidan kaso yawuce yana isa yasamu jawahir zaune jingine da bango ta d'age kanta sama tana kallon rufin d'akin inda hawaye suka fara wanke mata fuska, daga gefenta yatsaya yana mata kallon mamaki. Ahankali tajuyo takalleshi tare da goge hawayen fuskarta sannan tasadda kanta k'asa tace Barrister ina jin tsoro dan Allah kazare hannunka daga cikin wannan case d'in kar wani abu yasamu rayuwarka. Jikinshi sanyi yayi nan yatsugunna gabanta yace jawahir meyasa kikace haka? Kikwantar da hankalinki babu abinda zai faru zanyi k'ok'ari sosai wajen ganin na fitar da ke a cikin gidan kason nan ke yakamata kibani k'warin gwiwa domin wannan shine zama na k'arshe da za'ayi ya kamata mucigaba da addu'a insha Allahu mune da nasara. Girgiza kai tayi tace baka fahimceni ba Barrister. Na fahimceki man indai akan su Alhaji Mansur ne kicire duk wata damuwa a ranki daidai nake da su sannan basu isa suyi abinda ubangiji baiyi ba. Cikin sanyin jiki tace hakane. Toh kikwantar da hankalinki kinga daga nan ma wajen DPO nakeson wucewa dan yasanar da ni asibitin da aka kwantar da matar Alhaji Mu'azu dan haka koma mekenan zan sanar da ke kikwantar da hankalinki komai zai zo cikin sauk'i. 'Daga kai kawai tayi alamun toh. Nan yayi mata sallama yatashi yatafi. Yana isa station number d'in DPO yakira yasanar da shi zuwanshi nan yabada izini da ashigo da shi office d'inshi. Faruk yana shiga yasameshi yana waya dan haka yaja kujera yazauna har saida yagama sannan yamik'a mashi hannu suka gaisa. Bayan sun gaisa ne DPO yace ina saurarenka me ke tafe da kai? Murmushi yayi sannan yace ba komai bane yake tafe da ni sai akan dai case d'in jawahir kamar yadda a binciken da nakeyi nagano cewa matar Alhaji Mu'azu tana nan a raye ana jinyarta a wani asibiti shine nakeso asanar da ni asibitin dan inason ganawa da it. Da mamaki DPO yake kallonshi dan ya san in ba shi da su Alhaji Mansur ba babu wanda yasan tana asibiti, Faruk kamar ya san abinda yake tunani yace baidace ace kun 'boye ma kotu tana raye ba domin duk a cikin k'undin case d'in jawahir da naduba banga inda aka fad'i matarshi tana raye ko ta mutu ba. Jikin DPO sanyi yayi yace tabbas tana raye kuma wannan ba laifina bane polices d'in da suka bada sheda ne basu rubuta ba ammah shikenan zan sanar da kai asibitin saidai ko ka je babu abinda zaka samu daga wajenta dan har yanzu batasan inda kanta yake ba. Jinjina kai Barr Faruk yayi yace babu damuwa. Nan DPO yasanar da shi. Sallama yayi mashi yatafi shi kanshi cikin ranshi ya yi mamakin yadda yau DPO bai mashi rainin wayo ba haka yashiga motarshi yawuce private hospital d'in, yana isa baisha wahalar gane room d'in da takeba dan haka yawuce, yana shiga yasameta a kwance tsaye yayi yana kallonta tana kwance bata ko motsi, wata dattijuwa ce tajuyo takalleshi tace sannu da zuwa. Murmushi yayi sannan yayi sallama tare da ida shiga d'akin. Bayan ta amsa gaisawa sukayi yatambayeta ya me jiki? Cikin sanyin jiki tace toh Alhamdulillah za'a ce. Kallonshi yamaida ga Ummah da akasa ma drip idanuwanta a rufe kamar me bacci yace bacci ma takeyi ko? Uhm wane bacci yaro ko ma idanonta biyu ba'a ganewa dan har yanzu kusan shekara d'aya kenan babu uhm bare uhm uhm saidai kallon mutane kawai da take. Mamaki ne yakama Barr Faruk yace Allah yasauk'e Allah yabata lafiya ko zan iya sanin Doctor d'in da yake dubata. Goge hawayen da suka zubo mata tayi tace Eh Dr Aminu ne. Ohk Allah yabada lafiya. ___________ Washe gari da marece yanufi gidan su Nasiba yana isa megadi yasanar da shi bata nan murmushi yayi sannan yace toh babu damuwa Alhaji fa? Eh toh Alhaji yana ciki. Toh ko zan iya ganinshi? Wani yaron gidan ne megadi yatura yace yaje yace ana sallama da Alhaji, sannan yabud'e ma Barr Faruk gate yashiga da motarshi yana yin parking yafito yajingina a jikin motar sai ga yaron ya fito ya ce ance wai wa ke nemanshi? Kace mashi Faruk ne. Toh yace nan yakoma yashaida mashi. Barr Faruk ya yi kusan mintuna goma a wajen tsaye kafin Alhaji Sufyan yafito. Fuska a murtuk'e yanufo wajen da Faruk yake tun kan ya ida isowa yace lafiya me yakawo ka gidana? Ko ka zone kashaida min ka janye daga case d'in. 'Dan rissinawa Faruk yayi yagaisheshi a maimakon ya amsa sai ma k'ara jefo mashi tambaya yayi yace ina fata ba'a kan aurenku da d'iyata kazoba ko, dan bazan ta'ba amincewa ba har sai ka janye k'udurinka. 'Dagowa Faruk yayi yakalleshi sannan yace ko d'aya Alhaji ba wannan ne dalilin zuwana ba. Toh menene dalilin zuwan naka? Shuru Faruk yayi. Nan Alhaji Sufyan ya ida harzuk'a yace ba tambayarka nake ba!..... _Sis Nerja'art✍🏻_ [7/24, 11:14 PM] Sis Nerja'art 2: *......FANSAR RAI......* *INTELLIGENT WRITER'S ASSO....®* [On Ward Together] _Follow me on Wattpad: *Sis-nerja*_ _Wannan Littafin na kud'i ne domin karantawa cikin aminci da yarda ga duk me buk'ata zai turo katin Mtn na d'ari biyu N200 kacal ta wannan number d'in 09035938246, ko ta account number 5330055604, Idan katura ka aiko da screen shot na transaction a wannan number d'in 09035938246_ _Akwai gara'basar *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shahararriyar marubuciyar nan *AMEENA ABBA UMAR* tare da novel d'in *FANSAR RAI* akan farashin N300 kacal, ko da kud'in ka sai da rabonka_ *PAGE 14* Ganin yadda yaharzuk'a yasa Faruk yayi murmushi yace kakwantar da hankalinka ba wai dalilin d'iyarka yasa nazoba na zone akan aikina. Cikin nuna rashin fahimtar inda zancen yadosa yace ban fahimceka ba wane irin aikin kenan? Juyawa yayi yakalli gefe d'aya sannan yace a matsayina na barrister ko ma ince akan case d'in jawahir na zone dan ind'an maka wasu tambayoyi wad'anda suka shige min duhu. Wani irin kallo Alhaji Sufyan yayi mashi mai wuyar fassarawa koda Barr Faruk bai san ya yi ba saboda ba shi yake kallo ba, ida harzuk'a Alhaji Sufyan yayi yanuna kanshi yace ni ni zakazo kayi ma tambaboyin banza akan wacchan yarinyar? Miye had'ina da ita da har zakazo kace zaka tambayeni, inma kana yi ne saboda na hakana ka auren d'iyata toh bari kaji kayi duk abinda kaga dama ammah Nasiba ta fi k'arfinka dan haka kabar gidan nan yanzu tun kan insa'ba maka,,, yana fad'in haka yajuya a harzuk'e zai koma gida. Sai a lokacin Faruk yajuyo yakalleshi yace shin me zaka iya cewa akan kisan da akayi ma Alhaji Muhammad Mai kud'i? Chak Alhaji Sufyan yaja yatsaya batare da ya juyoba ganin haka yasa Faruk yacigaba da cewa sannan dukiyar yarinyar chan da take hannunku shin kun ajiye mata ne da sunan idan ta fito zaku mallaka mata ita? Sannan dukiyarta da kuka amsa hannun Alhaji Mu'azu da sunan zakuyi business shin ya maganar business d'in? Jikin Alhaji Sufyan sanyi yayi yai saurin juyowa yakalleshi cikin 'bacin rai yace ban fahimceka ba kana nufin dukiyarta tana wajenmu ko kuma kana nufin muna da hannu a cikin mutuwar shi? Faruk kana da hankali kuwa? Murmushi yayi cikin nuna rashin damuwa yace ba wai haka ba Alhaji kowa ya san kusancinku da Alhaji Muhammad sannan bayan mutuwarshi kuka koma abota da d'an uwanshi wanda yake da gurin ganin ya mallake dukiyarshi sannan sanin kanku ne Alhaji Muhammad ya bar duniya yana binku bashi kuma kun ci guri sosai akan wasu abubuwa nashi hatta.......katseshi yayi yace ya isa haka Faruk wannan tatsinniyoyin naka duk kasan wanda zakayi masu ba wai niba kowa ya san cewa Alhaji Muhammad abokin alk'alla ta ne ba wai abokina bane akan wane dalili zan so mallakar wani abu nashi bayan dukiya nima ina da ita tun daga tsarin gidana da matsayina ya kamata kafahimci hakan. 'Daga kai Faruk yayi yana kallon gidan sannan cikin nuna rashin damuwa yace ammah toh idan yakasance wannan gidan mallakinshi ne fa mezaka iya cewa? Kai!!! Banason shashancin banza me kake nufi da maganarka gidan nawa ne mallakin wani? Inji wane mak'aryacin yafad'i haka? Fad'amin! Girgiza kai Faruk yayi yace babu wani mak'aryaci da yafad'i hakan saidai ka sayi gidan a hannun Alhaji Mu'azu a kan farashi me sauk'i bayan kuma kun san gidan ba mallakinshi bane. Tsawa yadaka mashi yace Faruk na gaji da jin wad'annan k'aryayyakin naka na banza wanda me hankali bazai ta'ba d'aukarsu ba tun muna mu biyu kafita kabar min gida! Har Faruk ya bud'e baki zaiyi magana yayi saurin tarar numfashinshi cikin d'aga murya yace na ce kafita kabar min gida ko bakaji abinda nace ba!? Ganin yadda yad'au zafi sosai yasa Faruk yace shikenan na ji zan tafi ammah..... Kar kasaki kafad'i wani abu a wajen nan katafi nace!!! Gyad'a kai yayi yajuya yabud'e motarshi yashiga yana jin Alhaji Sufyan yana ta fad'a haka yatada motar, yana fitar da motarshi daga gate d'in gidan Nasiba tana 'bullowa da tata motar wani irin dad'i taji a ranta dan ta d'auka wajenta yazo saidai abinda yabata mamaki ya ganta ammah yashare yayi tafiyarshi, duk sai taji babu dad'i cikin ranta tace ko lafiyarshi shi kuma? Girgiza kai tayi tashigar da motarta cikin gidan hango Daddynta tayi yana ta kaiwa da kawowa a wajen ranshi duk a 'bace, mamakine yacikata tayi saurin yin parking d'in motar tafito tanufi wajen mahaifin nata tana cewa Daddy lafiya? Me yafaru? Juyowa yayi yai mata wani irin kallo cikin 'bacin rai sannan yajuya yashige gida. Mutuwar tsaye Nasiba tayi tace ikon Allah me yafaru? Ko dai dan Faruk ya zo gidan ne yasa ranshi ya'baci kuma fa na ga shima Faruk ya tafi ranshi a 'bace toh me yafaru? Ajiyar zuciya tasafke sannan itama tabi bayan Daddynta tashiga cikin gidan a parlor tasameshi tsaye Hajiya Maijidda tana tambayarshi abinda yafaru. Hucci kawai yake dan ranshi ba k'aramin 'baci yayi ba chan yajuyo yakalli Nasiba sannan yamaida kallonshi ga matarshi cikin d'aga murya yace wai ni ni Faruk zai zo yaci ma mutunci har cikin gidana. Kusan a tare sukace cin mutun kuma? Cize le'be yayi sannan yace eh man duka nawa yaron nan yake da har zai kalli tsabar idona yatuhumeni akan mutuwar Alhaji Muhammad har yana ik'irarin cewa wai muncinye ma d'iyar shi dukiya, gidan nan ma da nake ciki cewa yayi na yarinyar ne. Nasiba a kid'ime tace Daddy, nan tasa hannu tatoshe bakinta tare da fashewa da kuka ahankali tace Faruk meyasa kayi haka. Hajiya Maijidda cike da mamaki tace Faruk d'in yace haka Alhaji? Toh in ba shiba wanene? murmushi yayi mai ciwo sannan yace duka yaron nan nawa yake wallahi da ace bani mutunci da mahaifinshi da yau yau d'innan sai na sa an d'aureshi a garin nan! Baya baya Nasiba tafara ja sannan taruga dagudu tanufi d'akinta tare da fashewa da wani irin kuka me shiga rai tana shiga saman gadonta tafad'a tana me cigaba da kukan, wani irin haushin Faruk ne taji cikin ranta tace wai shine yaci mutuncin mahaifina daman ya san abinda zai aikata saisa yace insamo mashi number d'in Alhaji Mansur,, , kuka tacigaba da yi sosai. Hajiya Maijidda kallon mijin nata tayi da ranshi yayi matuk'ar 'baci tace Alhaji baidace ka'bata ranka saboda wannan yaron ba ina tunanin ya yi hakane kawai dan ka hanashi auren d'iyarka ammah ko indai dan hakane baida mutunci. K'wafa yayi yace kibarni Hajiya baisan wanene ni ba wallahi idan baibi a sannuba sai na sa and'aureshi a garin nan inga ubanda yatsaya mashi babu ruwana da mutuncin da muke da mahaifinshi tunda shi haka yake, ba barister ba ko alk'aline babu ruwana. A'a Alhaji kayi hak'uri abi komai a sannu kawai dai kaje kayi ma mahaifinshi magana dan yagargad'i d'anshi yafita daga harkar ka idan har bai daina ba toh shine kake da damar yi mashi kowane irin hukunci. Jinjina kai Alhaji Sufyan yayi yace kibarni da shi kawai Hajiya zai san da ni yake, je kid'auko min key d'in motata. Amsawa tayi da toh, taje tad'auko mashi har tadawo yana nan tsaye inda yake mik'a mashi tayi ya amsa yawuce yafita cemashi tayi Allah yakiyaye ammah bai amsataba saboda yanayin da yake na 'bacin rai. Rik'e baki tayi tace oh ni Maijidda wannan yaro ammah dai baida mutunci da ace mahaifinshi shima ba mai kud'i bane da nace bak'in ciki yake da dukiyarmu,,, tunowa tayi da Nasiba dan haka cikin sauri tanufi part d'inta tana isa tasameta a bedroom kwance sai faman rusar kuka take daga gefen gadon tazauna tare da kiran sunanta nan Nasiba tayi shuru. Ganin haka yasa tace kindai ji abinda Faruk yayi ma mahaifinki yaron nan ashe baida mutunci bai gaji arzik'iba. Tashi tayi zaune tare da tsaida kukanta tace wallahi Mummy da ace banga fitar Faruk daga gidan nan ba da bazan ta'ba yarda da cewa shine ya aikata ba yanzu dan rashin mutunci yakalli tsabar idanun mahaifina yafad'a mashi haka? Kenan soyayyar da yakeyi min duk ta k'aryace. Ta'be baki tayi tace toh ai yanzu gashinan dai kin gani da idanunki. Fashewa tayi da wani sabon kukan tace wallahi indai har Faruk ya yi min haka dan yatozarta mu toh yaje ya yi ma kanshi ni kuma zanyi k'ok'ari wajen ganin na cireshi a raina dan iyayena sun fiye min komai ba'ayi wanda zai zo yaci musu fuska har ransu ya'baci ba. Jin kalaman da tayi yasa Mummynta tajawota jikinta kamar jira take tafad'a tare da rungume mahaifiyartata tana cigaba da rusa kuka. Lallashinta Hajiya Maijidda tashiga yi dak'yar tasamu tashawo kanta har tahak'ura tadaina kukan. ________ A chan wani k'urmin daji dake wajen garin katsina tsakanin wasu k'auyuka biyu, dajin yana da duhu da yawan itatuwa sosai, iska kawai yake kad'awa a cikinshi baka jin motsin komai sai kukan tsuntsaye kawai babu mahalukin da yake shigarshi saboda ansan had'arin da ke cikinshi dan a tsakiyar dajin wasu 'yan fashi su biyar da suke rayuwa a cikinshi a duk lokacin da sukaso suna fita suyi fashi a gari ko kuma agayyacesu wani wajen suje suyi kisa saboda k'auran sunan da sukayi yasa mutane suke tsoron dajin. 'Yan fashin zaune suke suna zuk'ar shisha inda iskan da ke cikin dajin yake kad'asu, daga chan gaba da su kad'an ogansune zaune a bisa kujera hannunshi rik'e da k'walbar giya ya kame yana sha, su dukansu sun duk'ufa suna sharholiyarsu nan suka fara jiyo k'arar tafiya kamar ana tun karo wajen da suke, saurin ajiye shishir sukayi kowa yad'auko makaminshi yarik'e a hannu, inda ogansu yanuna ko inkula hankalinshi kwance yana ta shan giyarshi, suna nan a tsaye suna ta mazurai suna jira suga wane me k'arancin kwananne zai kawo kanshi, sun dad'e tsaye a haka sai ganin 'bullowar wata kyakkyawar budurwa sukayi basusan lokacin da suka saki baki suna kallonta ba, sanye take cikin wata gown wadda takama jikinta sosai inda gashin kanta yake baje a tsakiyar bayanta kyakkyawar fuskarnan tata ta sha makeup tafiya take ta jan hankali tatunkarosu tana masu murmushi me jan hankali su dukansu sun shagala suna kallonta har saida takusa isowa wajen da suke sannan sukayi saurin nunata da bindiga sukace kitsaya nan idan har kika matso zamu harbeki. Cikin nuna rashin damuwa taja tatsaya tare da waigawa takallo ogansu da yake zaune har lokacin yana shan giya, fuskannan tata d'auke da murmushi tabud'e baki cikin siririyar murya me dad'in saurare tace idan ba damuwa inaso kubani dama inyi magana da oganku. Juyawa sukayi suka kalli ogan suna shirin yin magana sai jin muryarshi sukayi ya ce kubarta ta iso muji da me tazo. Saurin matsawa sukayi suka bata hanya tawuce tana karairaya duk suka bita da kallo suna lasar le'be, tana isa gabanshi taja tatsaya idanu yazuba mata yana kallonta daga sama har k'asa ganin haka yasa tajuya baya sannan tajuyo, ajiye kwalbar giyar yayi cikin muryar maye yace wacece ke? Me yake tafe da ke wajena? Maimakon tabashi amsa sai fad'awa da tayi jikinshi tazauna tana cigaba da yi mashi murmushin nan nata me saurin rikita mutun. Ganin haka yasa yabushe da dariya yace da alama wannan 'yar hannu ce tamuce. Ganin haka yasa su ma suka bushe da dariya sannan suka koma suka zauna, hannu yakai yafara shafa gashin kanta yace gaskiya kina da kyau sosai, Fari tayi mashi da idanu tace nagode. Ajiyar zuciya yasafke yace lallai ke d'in ta dabance, hannunshi yad'aura bisa wuyanta tayi saurin janye wuyanta, gashinta yadamk'o dak'arfi yana shirin tura fuskarshi a wuyanta tureshi tayi da dukkan k'arfinta tamik'e tsaye tana jifanshi da wani mugun kallo. Kyalkyacewa yayi da wata muguwar dariya yace tunda har kika kawo kanki ya zama dole kiyi abinda nakeso, hannu yakai zaya jawo ta tayi saurin yin baya tare da girgiza kai. Gyatsa yayi sannan yajuya yakalli yaranshi da suke tsaye cirko cirko cikin muryar maye yace kukaimin ita cikin bukkata, su dukansu suka kwashe da dariya sukace angama oga ashe har muma yau zamu yagi rabonmu daman mun kwana biyu bamu samu namaba, juyawa tayi takallesu taga sun nufota gadan gadan nan tanuna su da hannunta sai ga wata irin iska ta tashi me kama da guguwa su dukansu saida suka tsorata sukayi saurin sa hannu suka rufe idanunsu dan kar ta shiga, bud'e baki tayi tasaki wata irin razanannar k'ara wadda tasa gabad'ayansu saida suka firgita suka juya zasu bar wajen sai ganin wani haske sukayi a gabansu dan haka suka had'e waje guda kowa yana raba idanu, ogansu kuma yunk'urin tashi yayi daga kujerar da yake zaune nan iska tajashi da k'arfi sai gashi a kusa da sauran 'yan uwanshi 'yan fashi, Nuni tayi da hannunta a sama tafara karanto wasu irin d'alasimai sai ga wata k'atuwar macijiya ta bayyana a wajen su dukansu saida suka tsorata suka san yau sun gamu da gamonsu, bushewa tasakeyi da dariya nan tayi girgiza tazama wata k'atuwar dodanniya, murya suka fara jiyowa wadda tasa gabad'aya dajin yadinga amsawa ji sukayi ana cewa kuuuu azzalumai ban zo wajenku domin komai ba sai dan d'aukar *FANSAR RAI* zan kasheku kamar yadda kukaga bayana ku d'in azzalumai ne bazan ta'ba barinku ba. Su dukansu tsaye suke sunaso suyi magana ammah tsoro ya hana babu wanda bai saki zawoba a wajen da suke tsaye, macijiyar ce sukaga tana tunkaro inda suke tsaye dukkansu yunk'urin guduwa sukayi ammah sai ji sukayi kasala ta safkar masu har macijiyar ta iso wajensu tana zuwa tasakar masu tsartuwa nan duk suka zube k'asa kowa yana jijjiga suna safke numfashi. Ganin haka yasa tasake bushewa da wata razanannar dariya me kama da kukan hadari, sannan tanunasu da hannunta sai ga wasu k'ananun macizzai sun fito daga bakin wannan babbar macijiyar suna fitowa suka nufi wajen da mutanen nan suke kwance suna zuwa suka fara sarinsu, nan 'yanfashin suka fara ihu hayak'i yana fita daga jikinsu, sun dad'e a haka kafin daga bisani duk suka mace, saida tatabbatar da babu me motsi a cikinsu sannan lokaci guda ta'bace ita da macizzan. ***** ***** Barr Faruk tunda yabaro gidan Alhaji Sufyan cikin 'bacin rai ya isa gida saidai duk da haka baiyi nadamar hakan ba saboda akowane lokaci ashirye yake dan ganin ya tafiyar da aikinshi yadda yakamata, yana isa a k'ofar gate gidansu sai ganin motar Barr MB yayi anfaka ta, tsayar da motarshi yayi tare da fitowa yajingina a jikinta yana jira yaji da me yazo. Ganin haka yasa Barr MB yafito yanufo wajen da Faruk yake tsaye yana murmushi yace ashe na zo a daidai yanzu nake shirin kiran wayarka sai gaka. Shima murmushin yayi yace gaskiya ka taki sa'a. Hannu Barr Mahamud Bello yamik'a mashi sukayi musabaha sannan yace ya aiki? Murmushi yayi yace Alhamdulillah gashinan muna ta tayi. Ajiyar zuciya yasafke yace hakane saidai nasan ka yi mamakin zuwana wajenka ko? Ta'be baki Faruk yayi yace ko d'aya dan nasan zuwanka yana da nasaba da Alhaji Mansur a matsayinka na lauyanshi da wad'anda suke k'ara. Jinjina kai yayi yace tabbas hakane ammah Barrister ka bani mamaki ace wai kaine da kanka kake zarginsu abun kunyanma har da surukinka dan kawai sun hanaka auren d'iyarsu, hakan bai dace da kai ba dan duk garin nan inzaka kewaye babu wanda bai san arzik'in nan nasu bane ko da Alhaji Muhammad yana da kud'i ammah bayada kud'in da zasu nemi suci dukiyarshi ya kamata kasan irin abinda yake fitowa daga bakinka a matsayinka na lauyan wadda ake k'ara. Murmushi ne yabayyana a fuskar Barr Faruk yazuba mashi idanu yana kallo har saida yakai aya sannan yace dakyau Barrister aikinka yana kyau, saidai maganar da kayi akwai gyara a cikinta dan ko da ace kowa zai yarda da cewa dukiyarsu ce toh ni bazan ta'ba yarda da hakan ba dan nasan ba dukanta bace dukiyarsu, kaidai kawai katsaya a matsayinka baka san komai ba akai kabarni da su kawai dan duk abinda zaka fad'a ba zan ta'ba yarda ba dan ni nasan abinda baka saniba, am ina da abunyi idan babu sauran abinda yakawoka zaka iya tafiya saidai ince sai munhad'u a kotu. Murmushi Barr Mahamud Bello yayi yace toh shikenan tunda ka ce haka ammah Barrister ya kamata kabi a sannu akan su Alhaji Mansur gudun kar wani abu yafaru. Jinjina kai kawai yayi yabud'e motarshi yashiga sannan yayi horn megadi yazo yahangeme mashi gate d'in gidansu yacinna motarshi a ciki inda Barr Mb yashiga tashi motar yakama gabanshi...... _Sis Nerja'art✍🏻_ [7/24, 11:14 PM] Sis Nerja'art 2: *......FANSAR RAI......* *INTELLIGENT WRITER'S ASSO....®* [On Ward Together] _Follow me on Wattpad: *Sis-nerja*_ _Wannan Littafin na kud'i ne domin karantawa cikin aminci da yarda ga duk me buk'ata zai turo katin Mtn na d'ari biyu N200 kacal ta wannan number d'in 09035938246, ko ta account number 5330055604, Idan katura ka aiko da screen shot na transaction a wannan number d'in 09035938246_ _Akwai gara'basar *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shahararriyar marubuciyar nan *AMEENA ABBA UMAR* tare da novel d'in *FANSAR RAI* akan farashin N300 kacal, ko da kud'in ka sai da rabonka_ *PAGE 15* Alhaji Mansur da yake manne da waya a kunnenshi duk ya saurari komai su Barr Faruk suka tattauna kasancewar sa Barr MB yayi yakirashi a waya yadda zai saurari hirar tasu, yana gama saurare wurgi yayi da wayar tare da komawa yazauna yace lallai yaron chan ya cika taurin kai idan har bai janye k'udurinshi ba ya zama dole inyi wani abu akanshi dan bai isa ya'bata min duk wani shirye shirye na ba. Toh ammah ta ya yakamata in'bullo mashi? Shuru yayi yana tunani sai kuma chan yayi murmushi yace idan ka san wata bakasan wata ba nan yatashi yad'auko wayarshi. Washe gari yana office d'inshi zaune ya d'age kanshi sama yana kallon ceiling a ka ga yanayinhi ka san tunani yake, yana nan a haka sai ji yayi anturo k'ofar d'akin anshigo. 'Dago kai yayi dan ganin wanene yashigo batare da annemi iziniba karaf suka had'a idanu da Nasiba yanayin yadda tashigo babu alamun fara'a a fuskarta yasa yagane akwai wata a k'asa, zaune yayi yana kallonta har ta iso wajen table d'in da yake gabanshi, kujera yanuna mata yace bismillah kizauna. Zare glass d'in da yake fuskarta tayi tare da yatsina fuska tace ba wannan yakawoni wajenka ba Faruk. Murmushi yayi cikin ranshi yace na san za'a rina,,, ajiye jakkarta tayi saman table d'in sannan tace na zo ne inyi maka godiya akan abinda kayi ma mahaifina Faruk tabbas kai butulu ne ban ta'ba sanin haka ba sai a yanzu, na yi da nasani da har na amince namallaka maka zuciyata, ina maka kallon mutumin kirki wanda nakeso yakasance abokin rayuwata ashe har akwai ranar da zakaje kakalli tsabar idanun mahaifina kaci mashi mutunci har kazargeshi akan kisan wani. Dafe kanshi yayi da hannuwanshi duka biyu jin tana neman tak'ara mashi wani zafin da yake saman kanshi, muryarta yaji ta fashe da kuka dan haka yad'ago kanshi cikin sanyin murya yace haba Nasiba meyasa zakice haka bayan ke bakisan abinda yake faruwaba. Cikin d'aga murya tace taya zan san abinda yake faruwa bayan ka ci mana mutunci tabbas kai butulu ne Faruk kuma insha Allahu kamar yadda kaso katozarta mahaifina ubangiji bazai ta'ba baka daman haka ba, na yi nadamar saninka a rayuwata Faruk. Saurin mik'ewa yayi tsaye yace wai wace irin maganace kikeyi haka Nasiba baidace kice hakaba ni fa akan aikina nake ba wai tozarta mahaifinki nakeson yi ba. Koma me zakace kafad'a Faruk nima kaina ban wuce matsayin da zaka tozartani ba, ashe wannan dalilin ne yasa kace insamo maka number d'in Alhaji Mansur dan kawai sun hanaka aurena shine zaka 'bullo masu ta wannan hanyar har kana ik'irarin cewa gidan mahaifina ba nashi bane, wai me yake damunka ne haka faruk!? Ajiyar zuciya yasafke yace Nasiba yakamata kifamceni duk yadda kike tunani ba haka bane. 'Daga mashi hannu tayi fuskarta sha'be sha'be da hawaye tace babu abinda zanji daga gareka bayan wanda kayi ahakan ma nagode Faruk a yanzu na ida tabbatarwa kai d'in ba masoyina bane mutum ne meson tozarta ni, ashe nikad'ai nake haukana na d'auki soyayyata na baka da zuciya d'aya kaikuma a wajenka ba hakaba nagode sosai Faruk na tayaka murna da kayi silar zubar da hawayena sannan kayi yadda kakeso rayuwace ubangiji yana sane da duk abinda kake aikatawa, na barka lafiya, jakkarta tad'auka cikin sauri tajuya tafita tabar d'akin. Dunk'ule hannuwanshi yayi yabuga a jikin table d'in da yake gabanshi yace meyasa haka Nasiba? Meyasa bazaki saurareni ba? Hannu yasa yashafa kanshi tare da wucewa cike da tashin hankali yakoma bayan kujerarshi yatsaya nan yafuzgar da wata irin iska me zafi daga bakinshi kan kace mi ya fara zufa, wayarshi ce tafara ringing ammah ko kallon wajen da take ajiye baiyi ba, komawa yayi yazauna tare da dafe kanshi da dukkan hannuwanshi biyu cikin d'aga murya yace daman nasan ba kowane zai fahimceni ba tabbas wannan shine matsalar da jawahir take ji min tsoron inshiga, na rasa masoyiyata adalilin case d'inta ammah ya zama dole inyi abinda yadace dasannu zan maido da martabar soyayyata, nasiba bazan ta'ba bari inrasaki ba zanyi k'ok'ari sosai wajen ganin kowa ya fahimceni, ya fi awa d'aya a nan zaune yana ta 'yan tunane tunane kafin daga baya yadanna k'ararrawa masinja yashigo wasu files ne yad'auko yamik'a mashi yace wad'annan kakaisu office d'in Director sannan yamik'e yahad'a duk abinda yake buk'ata yafita, tunda yafito daga office d'in yanufi harabar da motocinsu suke wata bak'ar mota ce Jeep yaga a kusa da tashi motar saboda glass d'in bak'ine yasa bai lura da mutanen da suke cikiba saidai bai ta'ba ganin wani ma'aikacinsu a cikin motar ba, ganin ta d'an tare mashi hanya yasa yanufi wajen zaiyi knocking d'in glass dan amatsa yafitar da tashi motar, tun kan ya isa sai gani yayi anja motar antafi dan haka shima yashiga tashi yakama gabanshi. Yana cikin tuk'i Daddynshi yakirashi a waya yace kazo gida kasameni yanzu murmushi yayi yace toh Daddy ganinan zuwa ina hanya. Bayan sun gama wayar cikin ranshi yace Allah yasa dai lafiya. Yana isa yasameshi a parlornshi zaune ganinshi yasa yanuna mashi waje alamun yazo yazauna. Fuskarshi d'auke da murmushi yace toh Dad, kallon drink d'in da yake saman table yayi ganin haka yasa Dad yad'auko cup yatsiyaya yamik'a mashi, amsa yayi tare da yin godiya sannan yafara sha. Gyaran murya Alhaji Sani yayi sannan yace Faruk me yahad'aka da Alhaji Sufyan. Saurin janye kofin yayi daga bakinshi yace na'am Dad. 'Daga kai yayi yace na san ka ji abinda nace. Shuru yayi cikin ranshi yace watau har ya sanar da Dad,, muryar Dad yaji ya ce kai nake saurare. 'Dagowa yayi yakalli mahaifin nashi yace babu komai Dad. A'a bazakace babu komai ba kaga Faruk banson rigima kafita harkar Alhaji Sufyan dan shi ba abokin yinka bane nayi mamaki sosai da naji wai kaine kaje har gida kaci mashi mutunci har kana fad'a mashi cewa wai gidanshi ba mallakinshi bane, wa ya aikeka ko ma ince ina kaji hakan? Jikin shi sanyi yayi sosai yace kayi hak'uri Dad ina akan aikina ne. "Dakata banason irin haka kar insake ji ka shiga harkarshi dan shi d'an siyasa ne ka san yana da kud'in da zai mallaki fiye da wannan gidan, sannan katsaya iya aikinka babu ruwanka da duk abinda bai shafeka ba. Har ya bud'e baki zaiyi magana sai kuma yafasa dan ya san ba lallai ne Dad yafahimci abinda zai fad'a ba, Dad yace ka yi shuru. Toh Dad insha Allahu. Yauwa haka nakeson ji Son. Murmushi yayi yace toh Dad. Kallon agogo Dad yayi yace bari intashi daman fita zanyi natsaya jiranka. Shikenan Dad sai ka dawo. Zaune yayi wajen har mahaifin nashi yatashi yatafi sai kuma chan shima yamik'e yakoma part d'inshi, yana jin babu dad'i a cikin ranshi. ______Da dare yana kwance yana ta tunanin yadda zai 'bullo ma lamarin dan hankalinshi ya tashi sosai da aka saka mahaifinshi a ciki saboda indai dan shine kar mahaifansa susan komai a game da wannan case d'in, yana nan kwance bai saniba har k'arfe d'aya tagota, dariya ce yafara jiyowa a falon d'akinshi tana tashi, saurin tashi yayi zaune cikin ranshi yace wannan dariyar fa? Ji yayi ancigaba da yi babu k'ak'k'autawa dan haka yakunna fitila tare da mik'ewa tsaye yanufi hanyar fita, yana bud'e k'ofar bedroom d'in sai yaji kamar takun mutum ana tafiya a chan babban parlor sautin dariyar yana cigaba da tashi kasancewar da k'arfi akeyinta, ji yayi kamar yajuya yakoma bedroom d'inshi sai kuma yafasa dan yanaso yaga me yin dariyar dan haka yabud'e k'ofa yafita daga saman matattakalar bene yatsaya yaji ana cigaba da taku na tafiya ammah baiga kowaba dan haka yagane Ammin jawahir ce har ya bud'e baki zaiyi magana sai kuma yafasa saboda kar su Dad sujiyo dan haka yajuya yakoma part d'inshi, yana shiga bedroom yamaida yarufe juyowar da zaiyi sai ganinta yayi a tsaye bayanshi cikin siffar da tasaba bayyana saidai wannan karon gashin nan nata farine kal har yana ta'ba k'asa saboda tsawonshi tana tsaye da 'yar sandarta tana kallonshi da k'wala k'walan idanunta wanda girmansu sun kai na goruba saurin jingine jikinshi yayi a jikin k'ofa cikin dakiya yace mi yakawo ki wajena? Bushewa tayi da dariya wadda tasa gabad'aya d'akin saida ya amsa, saida tayi me isarta sannan tabud'e baki cikin kakkausar murya tace aduk lokacin da naso ganin mutum ina bayyana a gareshi kuma kaima ka san haka, bana neman umurni bare har abani izini,,, dogara sandarta tayi tana tafiya a dudduk'e har saida taje tsakiyar d'akin sannan tatsaya tare da juyowa takalleshi yana nan tsaye a inda yake, sake bushewa tayi da wata dariyar tayi wadda ta wannan karon ta sha bambam da ta farko da wannan jinta yayi kamar kukan jaki saboda rashin dad'inta saida tayi me isarta sannan tace babu abinda zaka iya yi akan case d'in su Alhaji Mansur domin wuk'a da nama duk suna a hannu na sai na kashesu kamar yadda sukayi silar barina duniya ni da mijina sannan zan tseratar da d'iyata daga gidan kaso da kaina. Cikin nuna rashin tsoro yace wannan ne bazaki iyaba domin tun farko yakamata kitseratar da ita ammah kika kasa, sannan maganar su Alhaji Mansur na riga na maido case d'in a hannuna ni yadace inwanke jawahir a idanun duniya sannan inyi silar da zaisa arufesu a gidan yari ayi masu d'aurin rai da rai. Sake bushewa tayi da dariya sannan tace bakada iko a wannan hurumin domin nice me power, ina sake gargad'inka akan kajanye hannunka a cikin case d'in nan domin tseratar da kanta daga bala'o'in da suke tunkarar rayuwarka, su Alhaji Mansur bazasu ta'ba barinka ba zasuyi k'ok'arin ganin sunga bayanka ammah idan har ka za'bi mutuwarka akan komai toh shikenan saidai duk wannan abun da kake bai ta'ba burgeni ba dan nasan wuk'a da nama suna a hannuna. Nunata yayi da yatsaya yace ke d'in azzalluma ce bawai kina taimakon jawahir bane kawai dai kina cutar da rayuwarta ne gashinan ta dalilinki kowa guje mata yake. Wata irin razanannar k'ara tasaki wadda tasa har saida akayi k'aramar girgizar k'asa a cikin d'akin. Saurin toshe kunnuwanshi yayi har saida k'arar talafa sannan yasakesu. Nunashi tayi da yatsanta cikin 'bacin rai tace idan har kacigaba da jifata da munanan kalamai zan d'and'ana maka azabata. Bud'e baki yayi zaiyi magana sai ji yayi kamar anrik'e bakin nashi, juyawa tayi baya tace bana buk'atar jin komai daga gareka, nan tafara takawa tink'is tink'is tanufi wajen da ya ajiye briefcase d'inshi ganin haka yasa Faruk cikin sauri yanufi wajen da take, juyowa tayi ahankali tare da nunashi da hannunta nan wata irin iska tataso sai ji yayi and'aukeshi anyi wurgi da shi gefe d'aya ya fad'i kanshi ya bugu da k'asa. Jawahir da take k'wance a cikin d'an kurkukun d'akinta tana bacci cikin daren nan, lokaci guda tafarka tare da fasa k'ara da dukkan k'arfinta wadda tasa saida duk mutanen da suke kusa da d'akin da take suka farka, hatta shi kanshi megadin saida yafarka rik'e kanta tayi tare da jan gashinta da dukkan k'arfinta ahankali tace a'a Ammi kar ki aikata haka ya kamata kibar Barr Faruk kar kiyi mashi komai bai chanchanci hakan daga garekiba, bazan ta'ba bari kiyi mashi wani abu ba, 'Daga murya tayi tace a'a Ammi na ce kar kiyiiiii!! waige waige tafara yi chan kuma tamik'e cikin sauri tanufi wajen bango tana zuwa tabuga kanta da k'arfi, wani irin zafi ne taji ammah ahaka tasake bugawa nan take jini yawanke mata fuska tasulale k'asa a hankali tare da furta sunan Amminta. Daidai lokacin maigadi ya iso d'akin yadallota da fitila ganinta a kwance shame shame yasa yayi saurin bud'e k'ofar yashiga. Ammi ko da komai yafaru a cikin kunnenta ta jiyo sautin d'iyartata tsayawa tayi chak a inda take tsaye tare da fasa k'arar da tasa saida Faruk yafarfad'o daga suman da yayi, cikin d'aga murya tace a'a jawahir bazan ta'ba bari wani abu yasameki ba, nan take tayi girgiza ta'bace. Yunk'urin tashi yayi daga inda yake kwance ammah yakasa jin jikinshi yayi duk yana yi mashi ciwo saboda buguwar da yayi, dafe kanshi yayi da hannunshi sai a lokacin yasamu damar fara karanto addu'o'i sannan yasamu yamik'e dak'yar yanufi toilet, ruwan zafi yahad'a yagasa jikinshi bayan ya fito ne yanufi wajen briefcase d'inshi yabud'e ajiyar zuciya yasafke ganin bata ta'ba mashi komai ba saidai me ya jiyo lokacin da tafurta sunan jawahir to me yafaru da ita? Jin k'arar bugawar agogo alamun k'arfe ukku yasa yakwanta yana jin jikinshi duk yana mashi ciwo ahaka yasamu yayi bacci. ____ Megadi yana shiga d'akin tsaye yayi a wajen kan jawahir cike da mamaki ganin ko kad'an bata motsi ga jini yana fita daga goshinta hakan yasa yayi saurin fita yad'auko wayarshi yakira shugaban su yasanar da shi halin da ake ciki, nan da nan aka kira First Aid Member na prison d'in sukazo suka fara mata dressing ammah jinin bai tsayaba, ruwa aka d'ebo aka watsa mata bata farfad'o ba daga suman da tayi sunyi kusan minti talatin akanta ganin har lokacin bata farfad'oba yasa suka kira shugaban suka sanar da shi yace to suyi k'ok'ari sutsayar da jinin da yake zuban kafin zuwa safe idan har bata farfad'oba sai akaita asibiti. Haka ko akayi har asuba bata farfad'oba dan haka ana yin sallah aka d'auketa aka saka cikin mota aka nufi asibiti da ita inda motocin 'yansanda biyu suka rakasu har babban asibiti da ke cikin garin, a emergency unit aka wuce da ita a lokacin cike yake babu gado dan haka aka kama mata d'aki a aminity aka kwantar da ita nan likitoci suka yo kanta ganin daga gidan yari akazo da ita, dubata sukayi sannan suka nad'e mata kai da bandage bayan sunyi mata dressing sannan suka sa mata drip, daga k'ofar d'akinta 'yansanda biyar ne tsaye suna kaiwa da kawowa. Sai wajen k'arfe goma sha biyu sannan tafarfad'o daga suman da tayi. Tana bud'e idanunta taganta kwance a wani wajen na daban mamakine yakamata tace ina ne nake nan? Yunk'urin tashi tayi sai kuma takasa, hannu tasa tafizge drip d'in da aka sa mata tatashi zaune tare da dafe kanta da taji kamar zai cire saboda tsananin ciwon da yakeyi mata, daidai lokacin doctor yashigo yana ganinta yayi saurin nufo inda take yace lafiya me yafaru? Runtse idanunta tayi tana ji kamar zai fad'o nan yazo yarik'eta takoma takwanta yamaida mata drip d'in sannan yafita yarubuta wata allura yace aje asamo yanzu zaiyi mata ita. Ba a dad'eba aka kawo allurar yayi mata sannan yafita yace kar wanda yashiga abarta tana buk'atar samun hutu tsawon awanni bakwai, nan suka amsa da toh sannan yawuce, d'aya daga cikin police d'inne yabud'e d'akin yalek'a ganinta a kwance yasa yamaida k'ofar yarufe..... _Sis Nerja'art✍🏻_ [7/24, 11:14 PM] Sis Nerja'art 2: *......FANSAR RAI......* *INTELLIGENT WRITER'S ASSO....®* [On Ward Together] _Follow me on Wattpad: *Sis-nerja*_ _Wannan Littafin na kud'i ne domin karantawa cikin aminci da yarda ga duk me buk'ata zai turo katin Mtn na d'ari biyu N200 kacal ta wannan number d'in 09035938246, ko ta account number 5330055604, Idan katura ka aiko da screen shot na transaction a wannan number d'in 09035938246_ _Akwai gara'basar *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shahararriyar marubuciyar nan *AMEENA ABBA UMAR* tare da novel d'in *FANSAR RAI* akan farashin N300 kacal, ko da kud'in ka sai da rabonka_ *PAGE 16* ...Yana gama shirin shi ko wajen aiki bai biyaba yau yawuce gidan kaso dan yana so yaga halin da jawahir take ciki yana isa yasamu labarin abinda yafaru dan haka daga nan yawuce asibitin, yana isa likita yana fitowa daga d'akin yatabbatar masu da har lokacin bacci take. Awanta biyar tana baccin lokaci guda tabud'e idanunta tafara waresu a cikin d'akin ganin babu kowa yasa tatashi zaune hannunta takalla wanda aka sa ma kanula tasa gudan hannun tafizgeta sannan tayi saurin safkowa daga saman gadon, fara takawa tayi ahankali tanufi wajen taga, d'an d'age labule tayi talek'a ganinsu tayi tsaye wasu zazzauna a k'ofar d'akin, ganin wani yana shirin kallon tagar yasa tayi saurin sakin labulen tare da komawa takwanta tana ji suka bud'e d'akin suka lek'ota sannan suka maida suka rufe, tana jin sun rufe tatashi zaune tana bin d'akin da kallo kamar me neman wani abu sai kuma chan tamik'e wasu kaya tahango ajiye saman 'yar k'aramar drowar da take cikin d'akin cikin sauri taje tad'auka tashiga toilet nan tatsaya tana bin toilet d'in da kallo, 'yar tagar da tagani ne yasa tayi murmushi ajiye kayan tayi sannan tataka drum talek'a tagar, ganin wajene bayan d'akin yasa tasafko tad'auki kayan tasaka nan tafara tunanin ta yadda zata iya fita, juyowa tayi taje tarufe k'ofar toilet d'in ahankali sannan tataka drum d'in taja ragar (net) d'in tagar da k'arfi ammah tak'i 'balluwa dan haka tasa bakinta tafara ciccirewa da hak'oranta abinda zai baka mamaki kamar ba hak'oran mutum ba yanayin yadda take cire ragar da su saida tafara cire na 'bari guda sannan tasa hannunta taja dak'arfi sai gashi ta 'ba'b'bakota gabad'aya, koda tagar ba wani girma gareta ba ammah ahaka tatura kanta tafitar da shi saida taga babu motsin kowa a wajen sannan ta ida fidda jikinta dakyar tadira bayan ginin, gyalen kayanta tasa tarufe fuskarta da shi sannan cikin sauri tawuce zata zagaya tana 'bullowa sai ganin 'yansandar tayi tsaye a gaban d'akin suna kaiwa da kawowa dan haka sai tak'ara jan mayafinta a fuskarta sannan tacanza hanya cikin sauri tafita tabar asibitin tana fita tasamu me napep tatsaida tafad'a mata anguwar da zai kaita cikin sauri tashiga tace suje dan haka yajata suka tafi, tana yi tana kallon agogon da ke manne a gaban napep d'in har suka isa inda tace yakaita, suna isa tafita daga napep d'in tajuya zata tafi me keke napep d'in yace Hajiya kud'ina. Tsayawa tayi cak tare da juyowa dan ita ta ma mance da zata biya wasu kud'i gashi batada su, k'ara maimaita mata yayi. Ahankali tace kud'i? A'a kayi hak'uri banda su. Harara yawurga mata yace da kinsan bakida kud'in shine zaki shigo min napep. Ganin wani mutum ya nufo wajen yasa tad'aga murya tace dan Allah kayi hak'uri wallahi a rud'e nake saisa ban tsaya d'auko kud'i ba, fitowa yayi daga cikin napep d'in yace wallahi babu inda zakije sai kin biyani kud'ina. Ganin haka yasa mutumin yanufo wajen yana cewa lafiya me yafaru? Cikin fushi me napep d'in yace wannan yarinyar ce dan rainin wayo zata shigo min napep bayan na kawota inda takeso sai tace min batada kud'i. Kallonta mutumin yayi yace haka akayi? 'Daga kai tayi alamun Eh. Toh shikenan ni zan biya nawa ne kud'in naka? Jawahir tana jin haka sai tayi murmushi tace nagode sosai sannan tajuya tatafi cikin sauri, tana zuwa k'ofar gate d'in gidan taja tatsaya kamar tayi knocking sai kuma tafasa, tura k'ofar gidan tayi ahankali sai jin motsi tayi a toilet na wajen k'ofar alamun megadin yana ciki dan haka tatura tashiga tamaida tarufe sannan tafara takawa sad'af sad'af ahaka tanufi hanyar cikin gidan tana shiga nan ma shuru batare da wani tsoro ba tafara taka matattakalar benen ahaka tahau sannan tamurd'a k'ofar wani d'aki jinta a bud'e yasa tad'an bud'e ahankali sai gani tayi babu kowa a ciki, k'arar shower tajiyo a toilet dan haka tabud'e d'akin ahankali tashiga tana lalla'bawa dan kar ajiyo k'arar takun ta, daga tsakiyar d'akin tatsaya tana binshi da kallo sai kuma chan tanufi wajen bedside tana zuwa tajawo drower k'asa tajita a datse dan haka tabud'e ta saman taji ita kuma a bud'e, lalubawa tafara yi sai ga key ta gani tafiddo cikin sauri tabud'e ta k'asar tana jawowa sai ga wasu files a ciki fiddosu tayi gabad'aya tafara dubawa daidai lokacin taji anrage k'arfin shower d'in, bubbud'ewa tayi cikin sauri tana dubawa tad'auko wasu files guda biyu tamaida sauran tarufe drower sannan tad'auka, jiyo murya tayi a cikin toilet d'in ana cewa Hajiya ke ce ganinan ina wanka, mik'o min towel. Kallon k'ofar toilet d'in tayi sannan tawuce cikin sauri tafita tarufe d'akin, dagudu tasfka daga saman benen, hayaniya tafara jiyowa a gudan d'akin na mutanen gidan dan haka cikin sauri tafita, a filin gidan tasamu megadi tsaye saita nutsuwarta tayi sannan tawuce zata fita, kallonta yayi ammah ita ko bata kalli inda yakeba tana ji yace sannu Hajiya dan ya d'auka ko k'awar d'iyar gidan ce, amsawa tayi sannan yabud'e mata k'ofa taficce. Tana fita ajiyar zuciya tasafke dan ita kanta ta san ba k'aramin namijin k'ok'ari tayiba da har tayi kasadar shiga cikin gidan, takawa tafara yi har tasamu napep tashiga sannan tafad'a mashi inda zai kaita ranta fal da farin ciki ta yi nasarar samo abinda takeso, ahaka har suka isa asibitin, suna isa talaluba dan tabashi kud'i sai taji wayam ba jakka ajiyar zuciya tasafke cikin ranta tace da da yanzu ba d'aya bane, muryar dattijon taji ya ce d'iyata munzo. Cikin sanyin jiki tace kayi hak'uri baba ina tunanin kud'in da zan biyaka ne ashe babu kud'i atare da ni. Juyowa yayi yakalleta yace kamar ya bakida kud'i ai bakiyi kama da marassa kud'iba d'iyata. Cikin sanyin jiki tace dagaske nake Baba wallahi banda su. Gyad'a kai yayi yace toh shikenan jeki kawai na yafe. Godiya tayi mashi cikin jin dad'i sannan tafita, tafiya tafara yi bata ankaraba sai gata ta gaban 'yansandan nan cikin sauri tajawo gyalen tasake rufe fuskarta, murya Barr Faruk tajuyo da bai dad'e da dawowa asibitin ba alamun yana waya dan haka tadake tawuce tazagaya baya babu wanda yaganeta daga cikinsu, tsayawa tayi saida taga wasu mutane sun wuce sannan tataka dakali tawurga files d'in ta cikin tagar sannan itama tasamu tahau tadira aciki, tana dirawa tayi saurin cire kayan jikinta ta ajiye a nan cikin toilet d'in tad'auko unifoam d'inta na gidan yari tasaka sannan tad'auko files d'in, saida tad'an kanga kunnenta a wajen k'ofa jin ba motsin kowa yasa tabud'e ahankali tashiga, saurin jawo 'yar k'aramar drower da take ajiye cikin room d'in tayi wadda aka ajiye saboda ajiye ma patient kaya, tasaka files d'in. Doctor ne yatafo yana cewa bari inshiga yanzu lokacin farkawarta ya yi idan har mukaga ta farka babu wani ciwo atare da ita sai mu sallameku, d'aya daga cikin masu kula da gidan yarin ne yace tabbas hakan yakamata Doctor dan yarinyar chan tana da had'ari zamanta a gidan yari shine kwanciyar hankalinmu, shidai bai fahimci abinda yake nufiba saidai yayi murmushi yabud'e k'ofar yashiga. Kwance yasameta ta lulle'be har fuskarta yana isa yajanye mayafin ahankali tabud'e idanunta, murmushi yayi yace ashe kin farka ai na d'auka yanzu ne yakamata ace allurar ta sakeki, shuru tayi tana binshi da kallo, kallon hannunta yayi yaga ba kanula yace ya akayi kika cire? Kallon hannun nata tayi sannan tace am daman daman na ji yana min zafi ne. Ohk, akwai inda yake maki ciwo yanzu? Girgiza kai tayi, nan yasake dubata yace saidai na san har yanzu kina jin ciwon kan ammah zasu dinga maki dressing d'in ciwon naki. Batace komai ba saima kallonshi da takeyi ganin haka yasa yarubuta mata sallama tare da magungunan da za'a siya mata bayan ya gama yafita yasanar da su dan haka wasu police mata biyu suka shigo tana a nan inda take kwance suka saka mata ankwa a hannu, kallon hannuwanta tayi sannan tatashi suka izata a gaba suka fita da ita d'akin nan duk 'yansandar suka rufa masu baya, juyawa tayi takalli Faruk da yake waya har lokacin shima ya juyo yana kallonta, motsa baki tayi alamun tana son yin magana sai kuma tafasa sai tayi mashi nuni da idanu alamun yazo yaji. Kashe wayar yayi yatako wajen yana zuwa yatsaya yace har an sallameta sukace eh, Bakinta takai saitin kunnenshi tarad'a mashi wani abu wanda babu wanda yaji abinda tace sannan tawuce aka tafi da ita. Tsayawa yayi a wajen har suka wuce sannan yaje yashiga d'akin yaduba drower yafiddo files d'in, tsaye yayi yana kallon files d'in mamaki duk ya cikashi cikin ranshi yace ita kuma ina tasamosu ko dai ta fita daga gidan kason nan? Kallon d'akin yayi yace ammah kuma ai ba hanyar da zata fita batare da ansaniba, wayarshi ce da tafara ringing yasa yayi saurin fita daga d'akin tare da kanga wayar a kunnenshi yanufi wajen motarshi. Yana komawa gida zama yayi yabud'e files d'in yana dubawa cikin ranshi duk mamaki ya gama cikashi ganin yadda akayi tasamesu, chan kuma yayi murmushi yace wannan aikin naki ya yi sosai Jawahir, toh ammah idan yazama Amminta ce tad'auko su fa? Girgiza kai yayi yace wannan ne kuma bansaniba ko ma ya akayi na ji dad'in samunsu sosai. Wayarshi yad'auko yad'auki files d'in hoto sannan ya ajiye yashiga shigar da su acikin laptop d'inshi bayan ya gama ne yakira Barr Nas a waya suka tattauna daga nan kuma yatashi yafara shirin fita. A chan 'bangaren Alhaji Mansur hankalinshi a tashe yake sosai akan yadda Barr Faruk yakeson ganin ya tona masu asirin da yake binne babu wanda yasan da shi dan haka yafara tunanin yadda zai 'bullo mashi. Ranar wata talata Barr Faruk yana gida da marece Alhaji Mansur yakirashi a waya, ya yi mamakin ganin kiran nashi sosai kamar ba zai d'agaba har tatsinke yana tunanin kiran me yakeyi mashi chan sai wani kiran yasake shigowa dan haka yayi picking batare da yayi magana ba. Jin anyi picking yasa Alhaji Mansur yakalli nakusa da shi yayi murmushi sannan yace Barrister ina fatan kana jina? Daga chan 'bangaren Faruk yace Eh ina ji. Mik'ewa yayi tsaye sannan yace idan babu damuwa inaso yanzu muhad'u da kai a gida akwai maganar da nakeso muyi. Shuru Faruk yayi baice komai ba. Ganin haka yasa Alhaji Mansur yayi tunanin ko bai yarda da shi ba dan haka yace inma bazaka zo ba toh kafad'i inda yadace muhad'u. Cikin gadara da nuna isa yace idan zaka iya zamu had'u a chan Rahama Restuarent. Toh shikenan nan da rabin awa zaka sameni a chan. Batare da ya amsaba yakashe wayar. Tsaki Alhaji Mansur yayi yace yaron nan ya cika jin kan tsiya shi gani yake kamar shi wanine ammah bakomai zan safke mashi girman kan nan nashi bari inje inshirya intafi duk yadda mukayi da shi zaka ji. Suna gama wayar yatashi yashiga wanka yashirya yafita. Yana isa Rahama Restuarent babu mutane sosai a ciki yaja kujera yazauna nan yabada umurni akawo mashi coffee yana cikin sha ne Alhaji Mansur ya iso yafara ware idanu yana tunanin inda zai zauna kafin Faruk ya iso da mamakinshi sai hangoshi yayi zaune, murmushi yayi sannan yanufi wajen yaja kujera yazauna yace ashe har ka iso. Batare da ya kalleshiba yace Eh, me kake buk'ata akawo maka? Yatsina fuska yayi yace bana buk'atar komai. Batare da ya ce komai ba yacigaba da shan cofee d'inshi, Alhaji mansur hannu yasa a aljihu yazaro cheque ya ajiye mashi a gabanshi yana murmushi yace gashi Batare da ya kalli cheque d'inba yace menene wannan? 'Yar dariya yayi sannan yace abokan rayuwa ne mana kakalla kagani. Kallon cheque d'in yayi yai murmushi sannan yacigaba da shan coffeen shi. Ganin haka yasa Alhaji Mansur yayi tunanin ya yi nasara yace wannan gabad'aya na mallaka maka su kaje kacire inma basu ishekaba kayi min magana ink'ara maka wasu. Sai a lokacin ya ajiye coffeen yad'auko cheque d'in yaduba murmushi yayi yace 5billions, me kakeso inyi maka ne? Bushewa Alhaji Mansur yayi da dariya yace dakyau haka akeso kud'i masu canza kowa, gyara zamanshi yayi yace yauwa ka yi tambaya mekyau abu d'aya nakeso kayi shine kajanye daga case d'in yarinyar chan, idan har kayi haka ni kuma zan k'ara maka linkin wad'annan kud'in. Jinjina kai Faruk yayi yana murmushi yace wannan ne daman dalilin kiran da kayi min. Eh shine kaga sai mutaru murufa ma juna asiri kai kaci dukiya ita kuma akasheta, kai kowane lokaci ma kaji kana son kud'i kakirani ni kuma zan aiko maka da su batare da 'bata lokaci ba. K'ara duba cheque d'in yayi gaba da baya sannan yayageshi yawurga mashi. Baki Alhaji Mansur yasaki yana kallonshi cike da mamaki yace kai kana da hankali kuwa? Ka san abinda ka aikata? Mik'ewa yayi tsaye lokaci guda fara'ar da take fuskarshi tagushe cikin d'aga murya yace ni ko nasan abinda na aikata dan ni ba irin sakarkarun lauyoyin da ake siya bane, idan har kanaso kaga 'bacin raina toh kace zaka siyeni da kud'i, ka kalli kanka kai ba abun kunya bane kakalli kamata kace zaka siyeni da kud'i? Ko ka mance wannan Barr Faruk Sani Maishadda ne lauyan gaskiya? K'ut Alhaji Mansur yahad'iye wani wahalallen yawu duk idanu suka raina fata dan bai d'auka zai ga haka daga wajen Faruk ba. Girgiza kai yayi yace bazaka ta'ba samun hakan daga gareniba dan ni aikina gaskiya nake karewa bana d'aure ma k'arya gindi dan haka kawai kasaurari nan da kwana biyar zamanmu a kotu, yana fad'in haka yajuya a fusace zai tafi sai jin muryar Alhaji Mansur yayi ya ce Faruk kar ka aikata wannan kuskuren dama ce guda d'aya nabaka kaje kayi tunani cikin kwana biyu idan har baka canza tunaninka ba toh komai zai iya faruwa. Ja yayi yatsaya har yagama sauraren maganar tashi sannan yawuce yayi tafiyarshi. Buga teburin Alhaji Mansur yayi tare da furta shiittt!! sannan yamik'e ranshi a 'bace yatafi... *BAYAN KWANA BIYU* Daddyn Faruk ne zaune a parlornshi hannunshi rik'e da Jarida yana dubawa inda gefenshi matarshi ce zaune tana dannar waya, wayarshi da take gefenshi ce tafara ruri nan yad'auko ganin number ce ba suna yasa yace ko wanene yake kirana da wannan number d'in? Hajiya Nuratu murmushi tayi tace kad'aga kaji ko wanene Alhaji. Bai musaba yayi picking tare da yin sallama. Wata irin murya yaji wadda babu alamun mutunci a cikinta akace ina fata ina magana da Alhaji Sani Maishadda? Kallon Haj Nuratu yayi da itama take kallonshi sannan yace Eh shine da wa nake magana? Sanin da wanda kake magana ba dole bane dan ba shine dalilin da yasa nakiraka ba saidai ina so kabud'e kunnuwanka kasaurareni dakyau, kaja ma d'anka kunne yafita daga harkarmu inko ba haka ba zaya gane cewa ya ta'bo tsuliyar dodo dan zamu farauci rayuwarshi. A kid'ime Dad yamik'e tsaye cike da tashin hankali yace Hello ina ji dan Allah me d'an nawa yayi maku? Bushewa akayi da dariya sannan akace bakaga komai ba daga cikin tashin hankali indai har bai zare hannuwanshi daga case d'in Jawahir ba dan indai har yace zai cigaba da kareta zamu kasheshi. Dad ida rud'ewa yayi cikin rawar murya yace dan Allah kuyi hak'uri kar kukashe shi wallahi shi kad'ai namallaka na yi maku alk'awali zai janye. Kar ma yajanye mudai mun fad'a maku kugargad'eshi dan yaron nan naku ya cika taurin kai saidai ba irinmu ake ma taurin kai ba dan zamu iya rabashi da rayuwarshi....ana fad'in haka aka tsinke kiran, Daddy nan yafara cewa hello hello ammah yaji shuru sai lokacin yagane cewa ankashe wayar, wurgi yayi da wayarshi saman kujerar tashin hankali k'arara yabayyana, Hajiya Nuratu da take tsaye gefenshi itama hankalinta a tashe ganin yadda mijin nata hankalinshi yatashi sosai tace Alhaji lafiya me yafaru. Alhaji Sani da yafara kwarara zufa kallonta yayi sannan yakoma yazauna nan itama tazauna gefenshi tace dan Allah kayi min bayani menene yafaru. Girgiza kai yayi yace Nuratu muna cikin matsala dan anfara farautar rayuwar Faruk akan aikinshi. Saurin dafe k'irji tayi cike da tashin hankali tace me? Rayuwar d'ana ake farauta? Me yatsare masu? Ajiyar zuciya Dad yasafke sannan yace akan wai case d'in Jawahir sukace idan har bai janyeba sai sun kasheshi. Fashewa da kuka Haj Nuratu tayi tace na shiga ukku d'an nawa zasu kashe? Inko har hakana ya zama dole ya ajiye aikin nan gabad'aya dan wallahi inason d'ana banason inrabu da shi. Cikin sanyin jiki Alhaji Sani yace wannan dolene Hajiya mik'o min wayata yanzu inkirashi. Mik'ewa tayi cikin sauri tad'auko mashi wayarshi tamik'a mashi tana cigaba da kuka cike da tashin hankali gabanta yana dukan ukku ukku akan kalmar kisa da aka furta za'a yi ma tilon d'anta..... _Sis Nerja'art✍🏻_ [7/24, 11:14 PM] Sis Nerja'art 2: *......FANSAR RAI......* *INTELLIGENT WRITER'S ASSO....®* [On Ward Together] _Follow me on Wattpad: *Sis-nerja*_ _Wannan Littafin na kud'i ne domin karantawa cikin aminci da yarda ga duk me buk'ata zai turo katin Mtn na d'ari biyu N200 kacal ta wannan number d'in 09035938246, ko ta account number 5330055604, Idan katura ka aiko da screen shot na transaction a wannan number d'in 09035938246_ _Akwai gara'basar *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shahararriyar marubuciyar nan *AMEENA ABBA UMAR* tare da novel d'in *FANSAR RAI* akan farashin N300 kacal, ko da kud'in ka sai da rabonka_ *PAGE 17* ....Lalubo number d'in Faruk Daddy yayi yakira ammah har tatsinke ba'ayi picking ba, dan haka yasake kira, saida yayi mashi 5 missed bai d'aga ba, lokacin Faruk yana gidan kaso wajen Jawahir ya bar wayarshi a cikin mota dan bai shiga da ita yanzu saboda a tsarin dokar gidan ba'a bari ashiga da waya shine ma ake d'aga mawa yana shiga da ita saboda kusancinshi da shugaban gidan saisa. Kallon Jawahir yayi da tunda yazo take zaune ta yi shuru jikinta ya yi sanyi sosai yace wai jawahir me yake faruwa da ke ne haka na d'auka abin farin cikine tunda kwanaki ukku kawai suka rage mana. Girgiza kai tayi tare da yin d'an guntun murmushi sannan tace Barrister bazaka fahimta bane ina tsoron halin su Alhaji Mansur su d'in mugaye ne sannan ina bak'in cikin abinda yafaru da kai da budurwarka duk a kaina. Murmushi yayi yace indan wannan ne kikwantar da hankalinki insha Allahu babu matsala sannan maganar Nasiba kibarta kawai na san fushi take da ni ammah da sannu zata safko dan muna son junanmu sosai. Gefe d'aya takalla tana murmushi ahankali tace Yaya Umar d'ina sai kuma tafashe da kuka. Hankalin Faruk tashi yayi yace Jawahir lafiya kukan me kikeyi haka? Girgiza kai tayi tace nima ban saniba saidai kawai ina son Yaya Umar tabbas Ammi ta cutar da rayuwata taya zan iya yafe mata wannan laifin da tayi min na rabani da rabin rayuwata? Shin ita batasan mecece soyayya ba? Shin ta mance yanayin da tashiga a lokacin da tarasa Abbuna?,,, mik'ewa tayi tsaye cikin muryar kuka tace na san bata mance hakan ba kawai dai ta yi amfani da son zuciyartane wajen rabani da masoyina. Mik'ewa shima yayi yace Jawahir kidaina tuna abinda yawuce. Taya zan daina tunawa bayan ta dasa min ciwon da bazai ta'ba warkewa a cikin zuciyataba, saurin sa hannu tayi tagoge hawayen fuskarta sannan tajuyo takalleshi tana murmushi tace ka ga katashi katafi azahar ta yi. Kallon agogon da take manne a tsintsiyar hannunshi yayi yace hakane bari intafi ammah bazan dawoba yau. Murmushi tayi tace ba damuwa Barrister hakan ma nagode a kowane lokaci ina maka fatan alkhairi a cikin rayuwarka, musamman akan jajircewarka a lokacin da kuka had'u da Alhaji Mansur ba kowane za'a ba wad'annan mak'udan kud'in ya iya barinsu ba. Da mamaki yake kallonta yace ya akayi kikasan hakan? Murmusai tayi a karo na biyu sannan tace wannan ba abun mamaki bane, yanzu dai katafi kar karasa jam'i. Jinjina kai yayi sannan yawuce yatafi. A nan cikin masallacin gidan kaso yayi sallah sannan yashiga motarshi bayan ya fita daga gidan ne yad'auko wayarshi sai ganin 5 missed call yayi yana dubawa yaga Dad ne mamaki yakamashi yace lafiya kuwa Dad yayi min wannan missed call? Dialing d'in number d'in Dad yayi, lokacin Dad yana tsaye yana kaiwa da kawowa hankalinshi a tashe yana add'ua Allah yasa ba wani abu yasamu d'an nashiba itako Mom zaune take tana fitar da sautin kuka ahankali adaidai lokacin wayarshi da take hannunshi tafara ringing, jikinshi yana rawa yaduba sai ganin Faruk yayi ajiyar zuciya yasafke sannan yad'auka ko sallama baiyi ba yace Faruk kana ina? Daga chan 'bangaren yace ganinan a mota Dad zan dawo gida lafiya dai ko? Muryar mom yajiyo tana cewa kace mashi yayi sauri yadawo gida yanzun nan, nan Dad yafad'a mashi. Amsawa yayi da toh duk sai jikinshi yaji ya yi sanyi ganin hankalin iyayenshi yadda yatashi dan haka yagane akwai dai wani abu, duk da yanaso yawuce gida saidai kuma yaji ya fiso yafara yin abinda zaiyi kafin yaje gida dan haka ya yalalubo wata number yakira yana gama wayar yak'ara ma motarshi gudu cikin k'ank'anin lokaci ya isa inda zaije. Baifi minti sha biyar ba yafito yatafi gida yana isa a parlor yasamesu cirko cirko suna ta kaiwa da kawowa ja yayi yatsaya yace Dad Mom lafiya naganku haka? Mom ce tayi saurin isowa wajenshi tare da fashewa da kuka, nan hankalinshi yatashi yace me yafaru Mom? Muryar Dad d'inshi yajiyo yana cewa dole katambayi me yafaru Faruk ka ja and'aga mana hankali toh wallahi bazamu iyaba ya zama dole ka ajiye aikin nan naka. Cikin rashin fahimtar abinda yafaru yace Dad me yasa? Me yafaru da har zakayi wannan furucin? Jinjina kai yayi yace Faruk komai ma ya faru akan aikin nan ake barazana da rayuwarka har ake kiranmu waya ana gargad'inmu idan har baka janye daga wani case ba za'a kasheka. Murmushi yayi yace haba Dad wai dan wannan ne kukwantar da hankalinku babu abinda zasuyi min kawai dai sun fad'a ne dan sutsorata ku. Mom ce tadaka mashi tsawar da bata ta'ba yi mashi irinta ba tace kai shashashan ina ne? Ina kata'ba jin anyi irin wannan? toh wallahi baka isaba Faruk ya zama dole ka ajiye aikin nan akan wani banzan case ka rasa matar da zaka aura ka 'bata da surukinka sannan kuma a yanzu wasu suna barazana da rayuwarka ai ba dole sai ka yi aikinba. Girgiza kai yayi yace a'a Mom dan Allah kar kuyi min haka. Muryar Dad ce takatseshi yace Faruk bamu shirya kwana zaune ba ka san dai bamuda wani d'a bayanka dan haka ya zama dole ka ajiye aikin nan gabad'aya dan gudun had'arin da yake cikinshi. Gaban Faruk saida yafad'i ahankali yace na shiga ukku menene yake faruwa da ni? Su wanene suka kira iyayena, tabbas nasan bai wuce mutane biyu,,, matsawa yayi wajen mahaifin nashi yace dan Allah Dad kuyi hak'uri kar kurabani da aikina wallahi sunyi hakane kawai dan injanye daga case d'in jawahir suna so sutauye mata hak'k'inta kuma janyewata daidai yake da rasa rayuwarta gashi na yi mata alk'awalin zan taimaketa kukwantar da hankalinku babu abinda zai faru da ni ina akan gaskiyata ubangiji yana tare da ni basu isa suyi min abinda Allah baiyi min ba su d'in azzalumai ne barinsu a doron k'asa daidai yake da cigaba da yad'uwar zaluncin su sannan.....wani irin gigitaccen mari Dad yad'aukeshi da shi wanda yasa saida yai saurin ja da baya tare da dafe kuncinshi yana kallon mahaifin nashi. Mom ce tace ka min daidai Alhaji. Cikin fad'a Dad yace kai wane irin shashasha ne wanda baisan abinda yakeba watau mu zakayi ma wa'azi ko? Toh bari kaji indai har mune iyayenka ya zama dole ka ajiye aikin nan yau yau d'innan. Inkuma ba haka ba saidai yaza'ba ko mu ko aikin,,, cewar mom cikin 'bacin rai. Runtse idanunshi yayi da suka kad'a sukayi jajir sannan yasulale yazauna k'asa dirshen ahankali yafara furta innalillahi wa'inna ilaihiraji'un, sannan yabud'e idanunshi yasafkesu akan iyayenshi muryarshi tana rawa yace Dad dan Allah kuyi hak'uri kutaimaka min kunsan girman alk'awali....mom ce takatseshi tace wallahi Faruk kasake magana sai na k'ara maka wani marin, aikine mun hana shi kuma idan har kai ka isa da mu kaje kayi yadda kakeso,,, tana fad'in haka tawuce a harzuk'e tabar wajen. Dad ma bayanta yabi suka bar Faruk nan zaune dirshen a k'asa, duka hannunshi yasa yadafe kanshi yace wannan wace irin *K'ADDARA CE* menene yake shirin faruwa da ni? Me yasa su Alhaji Mansur basubar abun a tsakaninmu ba saida suka saka iyayena a ciki? Ya jawahir zataji idan har taji labarin na janye? Wasu siraran hawaye ne suka gangaro mashi yace Mom Dad meyasa kuka kasa fahimtata? Wayarshi ce tafara ringing yashare kamar bazai d'agaba sai kuma yad'auko yana dubawa sai ganin number d'in Alhaji Mansur yayi dan haka yayi picking cikin 'bacin rai. Dariya ce tafara tashi sannan akace ya kaji salon namu Barrister? Ina fatan dai a yanzu ka janye gudun kar wani abu yasameka dan nasan iyayenka bazasu ta'ba jure ma rashinka ba. Murmushi yayi cike da takaici sannan yace hakan bazai ta'ba sawa injanyeba ina nan akan bakana, tabbas a yanzu na tabbatar ku d'in matsorata ne da har kukeson janyewata, ba jarumta bace ace kun biyo ta 'bangaren iyayena nine nan daidai da ku dani yakamata kukara. Daga chan 'bangaren akace kana nufin bazaka janyeba kenan? Eh ina nan aka bankana sai na kunyataku a idanun duniya idan har ina da numfashi kowa sai ya san ku d'in azzalumai ne. Dakyau Barrister kai d'in ka cika taurin kai ammah dasannu zamu saitaka muzuba mugani. Tsaki yaja sannan yakashe wayar ranshi duk a 'bace, wajen yayi zaune dirshen yana tunanin ina ma ace iyayenshi zasu fahimceshi ammah yanayin da yagansu ya san bazasu ta'ba fahimtarshi ba musamman Dad da yake kaifi d'aya, yana nan zaune yana neman mafita aka fara kiran sallar la'asar Dad yafito yawuce masallaci ko kalllon inda yake baiyi ba dan haka shima yatashi cikin sanyin jiki yanufi part d'inshi cikin sauri yawatsa ruwa sannan yad'auro alwallah yana fitowa yasaka kaya yad'auki wayarshi cikin sauri yanufi masallaci dan har antada sallah a lokacin. Saida yarasa raka'a biyu, bayan ya gama sallah zaune yayi a masallacin duk yana jinshi wani iri saidai yana kallon hakan akan abinda yafaru tsakaninshi da iyayenshi, saida yaga za'a fara sharar masallaci wajen k'arfe hud'u da rabi sannan yafito cikin sanyin jiki yataka yanufi gida, yana cikin tafiya sai ganin wata jeep yayi ta faka a gabanshi anbud'e k'ofar baya ko kallonta baiyiba yawuce zai tafi sai ji yayi ance dan Allah malam muna da tambaya. Juyowar da zaiyi nan aka watsa mashi wani farin abu a fuska, runtse idanunshi yayi nan yanemi yaruga suka jawoshi da k'arfin tsiya suka saka a mota daga nan bai sake sanin inda kanshi yake ba. Ahankali yafara bud'e idanunshi yana maidawa yalumshe, jijjagashi da akayine yasa yabud'e idanunshi nan yafara ganin mutanen da suke tsaye bibiyu, runtsewa yayi yasake bud'ewa sai ganinshi yayi cikin wani d'aki tsakiyar wasu mutane su biyar kowanensu d'auke da makami, yunk'urin tashi yayi sai a lokacin yajishi d'aure tamau, kallon kujerar da yake zaune samanta yayi ta roba and'aure mashi hannuwa da k'afafuwa, abinda yafaru da shine yafad'o mashi a rai yakalli mutanen da suke zagaye da shi dukkansu babu wanda fuskarshi take da kalar imani, d'aga murya yayi yace suwanene ku? Meyasa kuka kawoni nan? Su duka shuru sukayi suna kallonshi. Ganin haka yasa yakwatsa masu tsawa yace bakuji ina tambayarku nace wanene yakawoni nan wajen? Ko ku kurmaye ne? Daidai lokacin aka bud'e k'ofa aka shigo da mamaki yake kallon wanda yashigo ahankali yace Alhaji Mansur? Murmushi yayi yace tabbas nine barrister ashe ka farka ai tun jiya muke nan tare da kai kana ta bacci lallai da alama baccin ya yi maka dad'i. Gabanshi wani irin mummunan fad'uwa yayi yace kana nufin tun jiya nake nan wajen? Dariya Alhaji Mansur yayi yace sosai ma ai ba abun mamaki bane. Innalillahi wa'inna ilaihiraji'un Alhaji Mansur me yasa ka aikata min haka, ashe daman kaine kasa aka d'auko ni? Kujerar da take kallon inda Faruk yake zaune yajawo yazauna sannan yace toh ya ka iya tunda taurin kanka ne yaja maka, kaga yanzu cikin ruwan sanyi na satoka yanzu kana nan tare da mu jibi bazamu shiga kotu da kaiba. Shuru Faruk yayi yana tunanin halin da iyayenshi zasu shiga idan suka nemeshi basu ganshiba, cikin karaya yace Alhaji Mansur hakan da kayi bai dace ba domin ina akan aikina ne ba wai ina yin hakan dan in tozartaku ba. Bushewa da dariya yayi yace ashe zakayi saurin karaya haka ban yi zaton haka ba saidai ka makaro Faruk, tunda har nagargad'eka baka jiba toh a nan zaka cigaba da rayuwarka da mutanena. 'Dagowa Faruk yayi yakalli mutanen d'aya bayan d'aya sannan yayi murmushi yace ban damu da duk abinda zakayi min ba Alhaji Mansur tunda ina akan gaskiyata sannan ko da ba ni ba ita yarinyar bazata ta'ba barinku ba sai ta kasheku kamar yadda takashe sauran abokan naku dasannu ku ma zaku bak'unci lahira, Mik'ewa yayi a fusace yawanka mashi mari. Saurin runtse idanunshi yayi saboda wani irin zafi da yaji ya ziyarci kuncinshi, d'agowa yayi yakalli Alhaji Mansur cike da mamaki bakinshi yamutu yakasa cemashi komai. Nunashi da yatsa Alhaji Mansur yayi yace kasan abinda bakinka yake fad'a domin ni d'innan ba kanwar lasa bane na tabbata har yanzu baka ida sanin wanene ni ba, ba kowa bane zai takani yazauna lafiya. Murmushi Faruk yayi yace wannan marin da kayi min bashi ne kad'auka karubuta ka ajiye wannan. Alhaji Mansur har ya bud'e baki zaiyi magana nan wayarshi da take hannunshi tafara ringing dubawa yayi sannan yai picking basu ji abinda ake ce mashi ba saidai sukaji yana cewa Eh gashinan ya farka ai yanzu bamuda damuwa abokina kakwantar da hankalinka yana nan wajen a nan zai ci gaba da zama har sai lokacin da yasaduda yadawo hanya inko ba haka ba saidai yakasance tare da mu, dariya yafara kyalkyatawa sai kuma chan yace toh shikenan sai anjima sai mun had'e ai na d'auka zakazo kaga mutumin namu duk wannan jin kan nashi babu shi atare da shi yau, ai kabarshi ina nan da kai sai ya safke girman kan nan nashi,,, suna saurarenshi yagama wayar sannan yakalli Faruk yace toh Barrister daga yanzu ka ga gidanka nan a nan zaka cigaba da rayuwa babu kai babu fita,, sannan ku kuma yanuna wad'annan k'attin biyar yace kucigaba da kula da shi ban yadda ko tsakar gida abarshi yafito ba hatta toilet gashinan cikin d'aki. Gabad'aya sukace angama oga. Murmushi yayi sannan yawuce yafita. Da idanu Barrister Faruk yabishi yana jin wani irin k'unci a cikin ranshi ba komai yad'aga mashi hankaliba sai iyayenshi da baisan halin da suke ciki ba, muryar d'aya daga cikin k'attin yaji wanda da alama shine ogansu ya ce ku zauna nan da shi bari inje indawo. Amsawa sukayi da toh nan suka wuce suka zauna suna kallon Faruk nan yajingine kanshi a jikin kujerar tare da runtse idanunshi. A chan 'bangaren iyayen Faruk ganin har dare bai dawoba kuma ga motocinshi duk suna gida dan haka suka fara tunanin ina yaje ko abokinshi yazo suka fita a mota, hankalinsu bai ida tashiba saida dare yayi baidawoba har k'arfe sha biyun dare sannan suka kira wayarshi suka ji ta akashe, atak'aice dai haka suka kwana rabi a zaune ammah bai dawoba. Wasa wasa washe gari har azuhur bai dawoba dan haka Dad yadinga kiran abokan Faruk da yasani yana tambayarsu sukace basu ganshiba, nan hankalinsu ya ida tashi sukayi tunanin ko mutanen nan suka saceshi, Momcy kuka tadinga yi sosai akan rashin ganin d'an nata haka tashiga mota tadinga zuwa gidajen da tasan yana d'an zuwa ammah babu labarinshi. Har dare haka suka ci nemanshi ammah babu 'bar'bashinshi ba su ba hatta duk wanda yake kusa da su saida yashiga tashin hankali akan rashin ganin Barrister inda daga k'arshe aka kai cigiyarshi gidajen television da na redio. Nasiba suna zaune ita da iyayenta a parlor suna kallon news inda ita hankalinta yake akan waya tana chart a nan ne iyayenta sukaga hoton Barr Faruk an dallo ana cigiyarshi, jin sunan wanda ake cigiyane yasa tayi saurin d'ago kai tamaida kallonta ga TV gabanta wani irin mummanan fad'uwa yayi tace na shiga ukku Daddy Mummy kuduba min wallahi Faruk ne ake cigiya me yafaru da shi?. Murmushi Alhaji Sufyan yayi yace tabbas wannan Faruk ne ikon Allah ko ya akayi haka, yanzu haka wajen iya yin shi ne yayi ma wad'anda suka kasa hak'uri suka d'aukeshi ko kuma wannan yarinyar takasheshi. Hajiya Maijidda rik'e baki tayi tace na shiga ukku yanzu Faruk d'inne ya'bata tun shekaran jiya? Nasiba da tayi mutuwar zaune hankalinta ya tashi sosai kasa cema iyayen nata komai tayi tana ta kallon hotunanshi da ake dallawa a TV ana cigiya chan sai ga hawaye sun fara fita nan tasa ma iyayenta kuka. Su dukansu kallonta sukayi cike da mamaki sukace ke kuma kukan me kikeyi? Cikin kuka tace Daddy Faruk d'ina ba'a ganshi ba ya 'bace . Daddynka fusata yayi yadaka mata tsawa yace ke bana son shashancin banza ai ba ubanki bane ya'bace da zaki ma mutane kuka kuma yaushe Faruk d'in yazama naki wannan azzalumin maci amana, inma banda abinki miye abun tada hankali kan 'bacewar wanchan butulun? Cikin sheshek'ar kuka tace wallahi Daddy Faruk ba mugu bane mutumin kirkine bana son wani abu yasameshi dan Allah muje nemanshi. Mummynta ce takai hannu tabuge mata maki tace ke dai shashasha ce miye abun tada hankali ga 'bacewar wanda yaso yatozarta mahaifinki yanzu haka rashin mutuncin yayi ma wasu sukaji basu iya hak'uri, K'ara sautin kukanta tayi tana jin wani irin haushi akan maganar da iyayenta suke marar dad'i akan Faruk dan ita ta san har yanzu tana jinshi a ranta. Mahaifinta ne yace kibarta kawai Hajiya sai tayi ta yi tunda ita batasan ciwon kanta ba bata kishina duk cin zarafin da yake mana bata gani ni wallahi dad'i ma naji yanzu ai iyayenshi zasu gane abinda muke fad'a masu akan abubuwan da d'an nasu yakeyi tunda su basu iya hanasu. Mik'ewa Nasiba tayi cikin sauri tajuya tafita daga parlorn tana cigaba da kuka. Mummynta ce tace oh ni yau naga ikon Allah watau Alhaji yarinyar chan dai da alama bata hak'ura da yaron chan ba. Cikin 'bacin rai yace kibarta ko kukan jini zatayi bazata ta'ba auren Faruk ba ko da ace yana nan bare ma baya nan dan bazan ta'ba ba irinshi auren d'iyataba. Shuru Mummyn Nasiba tayi dan ita babu abinda tatsana sama da 'bacin ran d'iyartata dan ma ba hali da ta je ta lallasheta. Nasiba kuka tadinga yi kamar wadda aka aiko ma da sak'on mutuwa wani irin tausayin Faruk ne taji ya d'arsu a zuciyarta, wayarta tad'auko takira numbers d'inshi dukansu a kashe nan tacigaba da rusa kuka daga k'arshe tatashi tad'auko mayafinta tazari key d'in motarta tabi ta k'ofar baya taficce batare da sanin iyayenta ba. Tuk'i take ammah kuka takeyi ahaka har ta isa gidansu Faruk, tana isa ko tsayawa rufe motar batayi ba tashiga gidan da gudu, duk mutane ne zazzaune anyi cirko cirko kowa yana jimamin 'bacewarshi tsawon kwana biyu, a parlor tasamu Mom zaune tana ta matsar hawaye ana lallashinta tana zuwa tafad'a jikinta tare da fashewa da wani irin kuka me ban tausayi, cikin kuka tadinga cewa Mom dan Allah ina Faruk? Dagaske ne ya 'bace? Dan Allah Mom kice min Faruk d'ina yana d'akinshi wallahi ina sonshi bana so inrasa shi. Mom kamar jira take nan itama d'in tafashe da kuka, k'ok'arin k'wace Nasiba akayi daga jikin Mom ammah tarik'eta gam. Dakyar aka samu aka 'ban'bareta nan takwanta a k'asa tana cigaba da rusa kuka, aka rasa wanda za'a lallasa ita da Mom. Alhaji Sani Maishadda da abokan Faruk ne suka dinga k'ok'arin zuwa wajaje nemanshi inda a chan garin daura kakanshi yasa aka dinga safkar alk'ur'ani ana sadaka.... _Sis Nerja'art✍🏻_ [7/24, 11:14 PM] Sis Nerja'art 2: *......FANSAR RAI......* *INTELLIGENT WRITER'S ASSO....®* [On Award Together] _Follow me on Wattpad: *Sis-nerja*_ _Wannan Littafin na kud'i ne domin karantawa cikin aminci da yarda ga duk me buk'ata zai turo katin Mtn na d'ari biyu N200 kacal ta wannan number d'in 09035938246, ko ta account number 5330055604, Idan katura ka aiko da screen shot na transaction a wannan number d'in 09035938246_ _Akwai gara'basar *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shahararriyar marubuciyar nan *AMEENA ABBA UMAR* tare da novel d'in *FANSAR RAI* akan farashin N300 kacal, ko da kud'in ka sai da rabonka_ *PAGE 18* Mummyn Nasiba saida tafaki idanun mijin nata sannan tanufi d'akin d'iyartata dan talallashi abunta sai gani tayi wayam babu ita nemanta tafara yi tana dubawa a parking space taga babu motarta dan haka tasan ta fita dawowa tayi tasamu mijin nata tace oh ni Alhaji watau yarinyar chan fita tayi daga gidan nan. Da mamaki yake kallonta yace kina nufin bata nan? Eh na duba d'akinta kuma naga motarta bata nan. K'wafa yayi yace watau gidansu Faruk taje dan bata jin magana kibarni da ita zata dawo gidan tasameni. Har dare Nasiba tana gidansu Faruk hawayen idanunta sun kasa tsayawa fuskarnan duk ta kumbura saboda tsananin kukan da tasha tana zaune gefen Mom koda aka kawo masu abinci daga ita har Mom k'in ci sukayi saida akayi da gaske sannan suka d'an ci, suna nan a haka Barr Junaid da Nas suka shigo saurin mik'ewa tayi tanufi wajen da yake tun kan yayi magana tatari numfashinshi tace Junaid anga Faruk d'ina ko? Junaid kallon Nas yayi su dukansu jikinsu ya yi sanyi sannan yakalli Nasiba tare da girgiza mata kai. Ja tafara yi da baya nan wasu hawayen suka wanke mata fuska tace shikenan tunda ku bazaku iya ganoshi ba ni zan je innemeshi da kaina, ni zan iya dawowa da shi. Barr Nas ne yayi k'arfin halin cewa kiyi hak'uri Nasiba muna bakin k'ok'arinmu ammah har yanzu Allah baisa andaceba insha Allahu zamu gano Faruk kikwantar da hankalinki. Wajen Mom takoma tatsugunna kusa da kujerar da take zaune tace Mom kin gani ko basu ganoshi ba kidaina kuka ni zanje in nemeshi. Ganin yadda take magana kamar zararra yasa mom ta girgiza kai tace a'a Nasiba babu inda zakije insha Allahu zasu gano mana shi. Fashewa tayi da kuka tace Mom har sai yaushe? Kwantar mata da kanta saman cinyarta tayi nan tafara lallashinta dan batasan abinda zatace mata ba. Kuka tadinga yi sosai har saida Dad yadawo nan yasamu yalallasheta tadaina kukan ganin har tara ta yi yasa yace tatashi tatafi gida, da fari ta ce babu inda zataje har sai Faruk ya dawo saida Dad yadinga lalla'bata sannan tahak'ura tatashi tatafi. Tana isa gida a parlor tasamu iyayen nata mahaifinta sai kaiwa da kawowa yake tana shigowa yace daga ina kike? Batare da ta damu da yanayin da taganshi ba tace daga gidan su Faruk nake...bata rufe baki ba taji ya wanka mata bari. Saurin dafe kuncinta tayi tare da kallon mahaifin nata cike da mamaki dan wannan shine karo na farko a rayuwarta da yata'ba marinta. Nunata yayu da yatsaya yace ke har kin isa kitsallake maganata? Da izininwa kika fita daga gidan nan? Shuru tayi tare da sadda kanta k'asa tana hawaye kanta yayo zai rufeta da duka Hajiya Maijidda tayi saurin shan gabanshi tace a'a Alhaji dan Allah kar kabugeta yarinya ce Nasiba batasan komai ba sai andinga kwatanta mata. Wata uwar harara yawurga mata yace Nasibar ce yarinya? Shuru tayi tana kallonshi. Cigaba yayi da cewa toh wallahi duk lokacin da tak'ara barin gidan nan sai na mugun sa'ba mata ban yarda ko nan da waje tasake fitaba. Wucewa Nasiba tayi sumi sumi tanufi d'akinta tana ji yana cewa ka ga 'yar iskar yarinya ni zaki maida banza watau ke ga shugabar soyayya ko? Mummyn Nasiba ce tace Alhaji ayi hak'uri. Tsaki yaja sannan yawuce a fusace yakoma d'akinshi. Bayan d'iyartata tabi tana zuwa tasameta zaune saman gado ta dafe kuncinta tana ta kuka, zuwa tayi tazauna kusa da ita tace haba Nasiba meyasa bakiji yanzu gashinan kinja ya doke ki. 'Dago kai tayi takalli mahaifiyartata cikin sheshekar kuka tace Mummy fad'a min menene laifina a ciki? Dan kawai ina son Faruk, ai bani nadasa ma kaina son nashi ba meyasa ake ganin laifina? Matsowa Mummy tayi kusa da ita tare da dafata tace haba Nasiba kidaina cewa haka kinga kema baki kyautaba ya kamata zuwa yanzu ace kin cireshi a ranki ko dan saboda tozarcin da yaso yayi ma mahaifinki kinga a yanzu mahaifinki yana fushi da ke saboda abinda kikayi baki kyautaba. Girgiza kai tashiga yi cikin kuka tace Mummy kune zakuga rashin kyautawa ta ammah ni zuciyata gani take hakan shine daidai dan saboda tana son Faruk, indai har abinda nayi a wajenku ba daidai bane to kuyafe min na ji ni me laifi ce saidai bazan ta'ba iya cire son shi ba ammah ina fatan inyi k'ok'arin cireshi a raina ko da ace hakan zai zama sanadiyar mutuwata indai har hakan zaisa infaranta maku. Rungumeta jikinta Hajiya Maijidda tayi tace a'a Nasiba kidaina cewa haka dan bamuso murasaki munason ki sosai. 'Dagowa tayi takalleta tare da yin murmushi wanda yafi kuka ciwo sannan tace indai har kuna so na to ya kamata kubarni incigaba da kasancewa da soyayyar Faruk dan zuciyata tana sonshi hakan kawai zakuyi min ingane cewa kuna k'aunata. Da mamaki take kallon d'iyartata da soyayya ta gama rufe mata idanu cikin sanyin jiki tace Nasiba kinsan dai duk duniyar nan babu wanda yakaimu k'aunarki saboda mu mune iyayenki saidai mahaifinki nakeji kinsan idan har yafad'i magana to baya canzata. Ruk'o hannuwan mahaifiyartata tayi tana kallonta da idanuwanta da suka kumbura saboda tsananin kuka tace Mommy dan Allah ke kikasance da ni domin ke uwace na tabbata ke kad'ai zaki iya fahimtata. Rungumeta tayi tare da shafa bayanta tace ina tare da ke d'iyata tabbas nice kad'ai yafi dacewa infara fahimtarki, kidaina kukan mucigaba da addu'a insha Allahu Faruk zai bayyana. Ajiyar zuciya tasafke tace nagode sosai Mummyna. Bakomai d'iyata yanzu dai kidaina kukan nan bari inje inkawo maki abinci kici kiwatsa ruwa kikwanta ko? Goge hawayenta tayi tare da yin murmushi tace nagode mummyna. ***** ***** A chan 'bangaren Faruk yana chan da mutanen nan a cikin d'akin a d'aure dan a yanzu ma ya samu ansafkeshi daga saman kujerar a saman gado aka d'aureshi indai har zaiyi wata buk'atar kusan mutum ukku suke rakashi wajen toilet yashiga yagama abinda zaiyi sannan sumaidoshi sud'aure Alhaji Mansur kusan kullum sau ukku yake zuwa yadubasu yakawo masu abinci koda shi a wulak'ance ake bashi abinci kuma ba ci yakeyi ba sai yaga yunwa ta cishi sosai sannan yaci, wulak'anci da cin mutunci kala-kala yake sha a wajensu Alhaji Mansur da mutanenshi saidai shi duk wannan bai dameshiba abu d'aya ne yake d'aga mashi hankali halin da iyayenshi suka shiga sai kuma case d'in jawahir baisan yadda zai kasanceba ita kanta ya san sai ta zargi wani abu kar ma tad'auka yaudararta yayi. A yau ma yana zaune a inda aka d'aureshi hankalinshi a tashe yana tunanin kotun da za'a zauna gobe sai gani yayi anwurgo mashi takeaway a saman jikinshi, kallo d'aya yayi mashi yad'auke kai, d'aya daga cikinsu ne yataso yana cewa watau sai ma kad'auke kai idan bazaka ci abincin ba sai kayi magana ba sai na kwanceka ba. Shuru yayi kamar baiji abinda yace ba. Cikin 'bacin rai yace kai wai wane irin banzan mutum ne ayita maka magana kayi shuru kak'yale mutane ka san kabi a sannu inba hakaba zan nakasaka a wajen nan nace zaka ci abincin ko ka k'oshi. Nan ma shuru yayi yaba bango ajiyarshi. A fusace yad'aga bindigar da take hannunshi yabuga mashi a kai, Faruk saida yasaki k'ara saboda zafin bugun. 'Dago mashi kai yayi dak'arfi yace idan har kacigaba da mana taurin kai sai mun azabtar da kai a gidan nan, kalleka dan Allah a yanzu gakanan a wulak'ance a wajenmu duk wannan jin kan nan da tak'ama babu su. Wani daga cikin sauran da suke zaune ne yace cinnaka ni ko naga ba jin kai kaga fa yadda yake taka k'asa kamar irin baya so d'innan shi a dole ga me kud'i barrister sai ga rayuwar barrister ta k'are a hannunmu ya koma wani k'ask'antacce. Su dukansu dariya sukasa suna cewa dan Allah jibarshi, duk ina dukiyar yanzu. Bud'e baki Faruk yayi ahankali yace koma me zakuce bazan ta'ba damuwa ba saidai inaso kusani a duk ranar da nayi nasarar barin gidan nan gabad'ayanku sai na sa and'aureku. Kan bindiga wanda aka kira da cinnaka yasake buga mashi a fuska har saida jini yafito daga hancinshi, runtse idanu yayi dak'arfi yana jin rad'ad'in bugun. 'Daya daga cikin wad'anda suke zaune ne yace a'a Cinnaka kadaina dukanshi ka ga Alhaji bai ce mubugeshi ba kabari abani izini sannan mucasashi tunda shi har yana ma tunanin zaya fita daga nan har yasa ad'auremu, wayyoo Allah har ma na d'an tsorata dan Allah kutaimaka min zasu kamani wallahi tsoron zaman gidan kaso nakeji......su dukansu kwashewa sukayi da dariya, wani kuma yace ahaka wai shashashan yake gani zamu barshi yafita lallai da sauranka. Haka sukaita tsokanarshi shi dai yayi shuru bai sake cewa komai ba saboda rad'ad'in da yakeji a fuskarshi. Yana ji Cinnaka yakoma yazauna batare da ya kwance mashi hannuwa ba koda daman shima ba yunwar yake ji ba inma yana ji sai ta cishi sannan yake cin abincin da suke bashi. Jawahir da take zaune a d'an kurkukun d'akinta tun bata damu da rashin zuwan Barrister ba har abun yazo yafara damunta dan bai ta'ba d'aukar wannan lokacin bai zoba gashi ma abun tashin hankalin gobe ne zama na k'arshe da zasuyi a kotu,,, mik'ewa tayi tsaye tare da jingine jikinta a jikin bango ahankali tace ko dai Barrister ya janye ne shima bazai iya taimakona ba? Girgiza kai tayi tace ah'ah ko kuma wani abu yafaru da shi? Hannu tasa tatoshe bakinta nan k'wallah ta cika mata idanu tace na shiga ukku ba dai akaina wani abu yafaru da shi ba, idan ko hakane ya zanyi, nice sila,,, Tana nan tsaye a haka akazo aka bud'e d'akin juyowa tayi dan ganin wanda zai shigo sai taga ma'aikaciyar gidan ce, ajiyar zuciya tasafke Kallonta matar tayi a wulak'ance tace ke zo muje ana son ganinki. Nuna kanta tayi tace ni? Harararta tayi tace akwai wani ne cikin d'akin? Batare da ta bata amsaba tad'auko kallabinta tad'aure kanta sannan tabi bayanta suka fita, da mamaki take kallon inda suka nufa tabbas wajen da ake kaisune idan wani ya zo ganawa da su. Suna zuwa sai jin matar tayi ta ce kawo hannunki, mik'awa tayi nan taga ansa mata ankwa sannan matar tace kishiga ciki d'allabai yana ciki. Tambayar kanta tayi tace Faruk kenan yazo ganawa da ni ammah kuma yau bai shigo wajenaba sai nan....Daka mata tsawa matar tayi tace me kika tsaya jira? Shiga tayi d'akin da mamaki take kallon wanda yake tsaye. Murmushi yasakar mata yace sannu d'iyata ina fata kina lafiya? Wannan dai mahaifin bai kyautaba da baya zuwa ganin d'iyarnan tashi. 'Daure fuska tayu tace menene dalilinka na zuwa wajena? Matsowa yayi kusa da ita yana murmushi yace kikwantar da hankalinki na zo ne kawai duba lafiyarki sannan injajanta maki 'bacewar da akace Barrister Farukya yi tsawon kwana ukku. Zaro idanu tayi waje da mamaki take kallonshi tace kana nufin Barrister ya 'bace? Alhaji Mansur dariya yasake yi yace ya naga kin tsorata, nima dai haka naji ban saniba ko akan wani case aka saceshi gashi mu kuma gobe ce ranar shara'a ta k'arshe. Idanu tazuba mashi tana kallonshi cikin ranta tace ko dai akan case d'ina ne? Ya kikayi shuru ko kina tsoron makomarki ta gobe? Sai a lokacin tayi murmushi tace ban damu da makomata ba saidai na san duk abinda yafaru da Faruk ku ne sila, shin ko shima kun kasheshi kamar yadda kuka kashe iyayena? Tarar numfashinta yayi yace ko kuma kin kasheshi kamar yadda kika kashe sauran lauyoyinki, shin taya ma gobe za'a barki bayan kin kashe lauyoyi ukku. 'Daga murya tayi tace idan har kuka bari wani abu yafaru da Barrister bazan ta'ba barinku ba da duk wanda yake da hannu a ciki sai naga bayanshi, kukyaleshi yayi rayuwarshi domin shi baida laifi a ciki nice me laifin kuma idan har saboda ni kuka kamashi kusakeshi ni na amince akasheni ammah kar ku kashe wanda baisan komai ba a kai. "Jawahir mu bamu kamashi ba dan baya hannunmu kece ma nayi tunanin kin kasheshi ammah dai shikenan ke kad'ai kikasan wannan sirrin dan nasan daman ba fad'a min gaskiya zakiyiba nima daman jaje nazo maki, ni zan tafi ko ma mekenan sai munhad'e a kotu gobe ina fata zaki kasance cikin bak'in ciki kasancewar yau itace ranarki ta k'arshe gobe kamar yanzu kina cikin k'abarinki, na barki lafiya. Hawaye ne suka gangaro mata a kuncinta ganin ya juya zai tafi yasa cikin d'aga murya tace na fad'a maka kar kabari wani abu yafaru da rayuwar Barrister wallahi idan har kakasheshi nima sai naga bayanka kafin nima akasheni. Bai tsaya bata amsaba yawuce yatafi. Dafe kanta tayi da hannuwanta da suke da ankwa, matar ce tazo tatisata gaba tamaidata chan d'akinta tamaida tarufe. Tana shiga sulalewa tayi k'asa tazauna tare da fashewa da wani irin matsanancin kuka, cikin kuka tadinga cewa Ammi kizo gareni ina buk'atar taimakonki ko da ace wannan shine taimako na k'arshe da zakiyi min a duniya dan Allah kizo gareni......bata rufe baki ba sai ga wani farin haske ya bayyana a gabanta, saurin mik'ewa tayi tana kallon haskenan nan yafara komawa siffar mutum kafin k'iftawar idanu sai ga tsohuwarnan ta bayyana. Bud'e baki tayi zatayi magana tatari numfashinta tace tabbas Barrister yana cikin mawuyacin hali dan yana hannunsu sun kamashi saidai bazan ta'ba taimaka mashi ba. Saurin zamewa tayi k'asa tatsugunna tare da had'e hannuwanta biyu waje guda cikin muryar kuka tace dan Allah Ammi kitaimaka min kitseratar da shi domin rayuwarshi tana da muhimmanci sosai bai dace ace wani abu ya sameshi ba a dalilina ni k'wara akasheni dan tawa rayuwar batada sauran amfani. Dariya matar tayi sannan tace Jawahir yau gaki a gabana tsugunne kina rok'ona bayan da baki ta'ba hakan ba, saidai tsanar da kikayi min ammah yau kece a haka dubeki. Fashewa tayi da kuka tace tabbas ni k'ask'antatta ce kar kiyi duba da abinda yafaru dan Allah kiceci wannan bawan Allahn banaso sukasheshi. Zureren hannunta tad'ago tace kiyi duba zuwa nan jawahir. Saurin d'ago kanta tayi tadubi hannun Barrister Faruk ne tagani zaune an d'aureshi idanunshi a rufe. Wasu sabbin hawayen ne suka gangaro mata nan tsohuwar tajanye hannunta sannan tace wannan itace k'addararshi bazan ta'ba iya zuwa inceceshi ba, ke kuma ya kamata kafin gobe kiyi nadamar maganar da kika fad'a min idan har kinason cigaban rayuwarki inko ba haka ba kema kanki zaki mutu. Matsowa tayi kusa da matar tana me cigaba da kuka tace bazan ta'ba nadama ba indai a kan kainane saidai zan iya Nadama indai har zaki ceci Faruk kije kiku'butar da shi. Bushewa tsohuwar tayi da dariya sannan tace dakyau jawahir hakan ya yi miki kyau, saidai ni bazan ta'ba taimaka ma wanda kikeso intaimaka ba saboda ni bana taimako abu guda kawai nake kuma shi na iya shine *'DAUKAR FANSA* Jawahir kasa cemata komai tayi nan taduk'ar da kanta tana me cigaba da kuka cike da tashin hankali..... ______ Gidan su Faruk mutane zuwa suke suna yi ma iyayenshi jaje dan gidan komawa yayi kamar gidan gaisuwa mutane sai shiga da ficce sukeyi inda suke addu'a Allah yabayyanar da shi. Hatta limamin unguwar kullum sai ya zo anyi safka sannan ayi abincin sadaka a raba. Iyayenshi duk sun fita hayyacinshi saboda tashin hankalin da suka shiga. A ranar yau da takasance kwanan Faruk ukku baya gida, Dad d'inshi yana zaune a setting room shi kad'ai ya buga tagumi Barr Nas yazo gidan duk sallamar da yayi Dad baijiba saida yad'an buga k'ofa sannan yad'ago yakalleshi yace bismillah Nasir kashigo man. Shiga yayi yazauna a k'asa suka gaisa bayan sun gaisa ne Dad yace Nasir kuna ta k'ok'ari gaskiya mungode sosai, a yanzu mudaina wahalar da kanmu wajen yawon nemanshi mucigaba da addu'a indai har yana raye Allah zai bayyana mana shi, saidai abinda nake zargi mutanen da suka ta'ba kirana waya sukace ingargad'eshi yacire hannunshi daga wani case ina tunanin sune suka sace min shi dan a ranar da akayi maganar a ranar ya'bata. Cikin sanyin jiki Barr Nas yace Dad wane mutane ne? Me sukace maka? Kwashe komai yayi yafad'a ma Barr Nas. Mamaki yacikashi yace tabbas wad'annan mutanen akan case d'in Jawahir ne. Eh tabbas hakan sukace wai yajanye akan case d'inta ammah wacece ita? Meyasa zasuyi min haka da sunbi ta lalama ai da na sashi ya janye. Shuru Nasir yayi sai chan yace tabbas case d'in akwai rikitarwa a cikinshi saidai ita yarinyar tana a kan gaskiyarta wannan dalilin ne yasa Faruk yakeso yawanketa a idanun duniya daga zargin da akeyi mata, saidai a yanzu lokaci ya k'ure na tabbata a gobe idan har babu lauyan da zai tsaya mata kasheta za'ayi gashi Barr Faruk shine kad'ai zai iya tsaya mata. Jinjina kai Dad yayi yace Allah yakyauta, Allah dai yabayyanar da shi a duk inda yake. Barr Nas ya amsa da Ameen sannan yayi mashi sallama yatafi. Nasiba saboda tashin hankalin da tashiga ko baccin kirki bata iyawa abinci ko ba'a magana sai Mummynta ta yi dagaske sannan take samu tana d'anci kullum cikin kuka take, Daddynta ko shareta yayi yafita batunta. Yau ma kamar kullum Hajiya Maijidda ce tashigo da azuhur tasameta zaune saman darduma da alama sallah tagama saidai ta jingine jikinta a jikin gado tana hawaye, tsayawa Hajiya Maijidda tayi tana kallonta sai kuma chan tataka ta isa wajenta a saman gadon tazauna cikin lallashi tace haba Nasiba wai meyasa kikesa ma ranki damuwa addu'a fa yakamata kiyi mashi duk inda yake Allah zai bayyana mana shi. Goge hawayen fuskarta tayi tare da gyara zamanta ta fuskanci mahaifiyartata sannan tace Mummy dan Allah taimako d'aya nakeso kiyi min. Toh ina jinki wane irin taimako ne? Saida takalli k'ofa sannan tace dan Allah kitaimaka min kibarni inje gidansu Faruk ingano Mom d'inshi na tabbata tana chan hankalinta a tashe, nima zuwana zai sa ind'anji sauk'in rad'ad'in da nakeji a raina. Jimm tayi sannan tace Nasiba kinsan mahaifinki baya so ranshi 'baci zaiyi. Kamar jira take tafashe da kuka tace Mummy kitaimaka min wajenki ne kawai nake jin dad'i kin san yadda nakeson Faruk hankalina bazai ta'ba kwanciya ba idan banje naji halin da ake cikiba yanzu. Cikin sanyin jiki tace shikenan Nasiba tashi kije ammah kar kidad'e saboda kar Daddynki yadawo bakinan kinsan ba ke ba hatta ni kaina sai raina ya 'baci. Murmushin jin dad'i tayi tace nagode sosai mummyna. Shafa kanta tayi tace bakomai dota idan kinje kigaishe min da Hajiya Nuratu. Toh insha Allahu zataji Mummy, nan tamik'e tashirya tafita tana Allah Allah kar suhad'u da Daddynta a lokacin da zata fitar da motarta sai gashi cikin ikon Allah har tatafi bai dawo ba..... _Sis Nerja'art✍🏻_ [7/24, 11:14 PM] Sis Nerja'art 2: *......FANSAR RAI......* *INTELLIGENT WRITER'S ASSO....®* [On Award Together] _Follow me on Wattpad: *Sis-nerja*_ _Wannan Littafin na kud'i ne domin karantawa cikin aminci da yarda ga duk me buk'ata zai turo katin Mtn na d'ari biyu N200 kacal ta wannan number d'in 09035938246, ko ta account number 5330055604, Idan katura ka aiko da screen shot na transaction a wannan number d'in 09035938246_ _Akwai gara'basar *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shahararriyar marubuciyar nan *AMEENA ABBA UMAR* tare da novel d'in *FANSAR RAI* akan farashin N300 kacal, ko da kud'in ka sai da rabonka_ *PAGE 19* Washe gari ya kama ranar litinin tun da safe a gidan kaso akasa duk wani wanda za'aje kotu da shi yayi wanka yashirya, jawahir tunda tashirya zaune tayi tana tunanin halin da Faruk yashiga akanta ko kad'an fuskarta babu alamun fara'a dan jiya ko rintsawa bata samu tayiba, abinda zai ba mutum mamaki ita hankalinta bai tashi akan zaman kotun da za'ayi ba, bah wai kuma dan tana da tabbacin zata tsira ba dan tasa ma ranta dole cikin biyu ayi d'aya ko rayuwa ko mutuwa ko da ta ma fi bama ranta mutuwar dan tasan itace kawai makomarta. Kamar yadda aka saba a duk ranar da za'a shiga kotu akan case d'in jawahir ana yin sanarwa a gidajen yad'a labarai saboda za'a iya cewa mafi yawa daga cikin mutanen da suke garin katsina sun san da case d'inta dan abinda ba'a ta'ba jin an aikata bane sai akanta, musamman ma da akasan manyan mutane ne masu hannu da shuni ake zarginta da kisansu, wannan dalilin ne yasa duk ranar da za'a shiga kotu akan case d'inta mutane dadama suke zuwa acika kotun mak'il, wasu ko ba komai yake kawosu ba sai dan suzo sugane ma idanunsu yarinyar da akace tana da k'arancin shekaru takeyin kisan. Dad d'in Faruk da a yanzu ko baccin kirki baya samu yayi saboda 'bacewar d'anshi, yau ma tunda yadawo sallar asuba bai koma bacci ba Redionshi yajawo yakunna yana daga kwance saman doguwar kujera dan a yanzu ya fi sauraren Redio ko dan saboda yana tunanin a nan zai iya samun bayyanar d'anshi indai ma ansameshi a wani wajen, yana cikin sauraren labaran safiyar yau akan abubuwan da suka farune yaji ana sanarwa "Gwamnatin jihar katsina zata bada tallafi ga wad'anda 'yan ta'adda suka shiga garuruwansu suka kashe masu 'yan uwa sannan suka kora masu dabbobi suka tafi da su, inda me girma gwamna yayi sanarwa zai taimaka masu da tallafi. Sannan a cikin labaran na mu zakuji cewa a yau ne za'a yi zama na k'arshe a kotu akan case d'in Jawahir Muhammad Maikud'i wadda ake zargi da kashe kawunta da 'ya'yanshi wanda daga baya hukuma tagano hadda mijinta aciki sannan tasambad'a abokan mahaifinta suka ziyarci lahira inda dangin mamatan suke k'ararta akan suna so abi masu hak'k'in rayuwar 'yan uwansu, ko me ya jawo ma yarinyar yin kinsan? Wannan ne bamu saniba dan har yanzu ba'a samu wata k'wak'kwarar hujjaba guda d'aya da me laifin tabayar saidai jitajitan da mutane sukeyi, koma me kenan kukasance da mu da anjima acikin labaran mu dan jin yadda shari'ar ta kasance.. Haka kuma a cikin labaran namu zakuji cewa... Dad tsaki yaja tare da kashe redion yakunna TV dan yakalli News tunda yakunna TV d'in kallo kawai yake ammah hankalinshi ba a wajen yakeba abinda yatsaya mashi a rai case d'in yarinyar da yaji ansanar musamman ma sunan da aka ambata Jawahir Muhammad Maikud'i tabbas zai iya cewa 'ya ce ga Marigayi Alhaji Muhammad Maikud'i inko ba haka ba toh sunan ya zo iri d'aya da nashi toh ammah shima ya san yana da d'iya guda d'aya bazai iya cewa ga sunanta ba, anya kuwa itace ba wata bace ta daban ba? Toh ko dai itace Jawahir d'in da Faruk yatsaya mawa wadda saboda case d'in ake barazana a rayuwarshi, tabbas ko zaya iya zama itace dan zai iya tuna labarin da Faruk yabasu akan case d'in ya ce ana zarginta akan kisa. Jinjina kai yayi yace tabbas itace wannan saboda ita aka d'auke min d'ana....haka yayi ta tunane tunane inda daga k'arshe yakasa kallon News d'in yakashe TV d'in yayi kwance yana tunanin halin da d'anshi yake ciki a yanzu ko da rai ko kuma babu rai. _______ A chan 'bangaren Faruk yana kwance a saman gado ko runtsawa bai samu yayiba saboda tashin hankalin da yake ciki musamman akan shara'ar da za'a gabatar a yau ta jawahir, ko da daman ba samun wani baccin kirki yakeba saboda halin da yake ciki ga d'aurin da akayi mashi wai dan kar yagudu ahaka yake kwanciya. Hatta sallah sai ya yi dagaske sannan suke barinshi yayi shima sai kusan mutum ukku sun tsareshi sannan. ****** Wajen k'arfe Taran safe aka fiddo wad'anda za'a yi shara'a akan case d'insu aka saka cikin mota aka nufi kotu inda motocin 'yansanda suka kasance gaba da bayan motarsu, tunda suka fara tafiya matan suka dinga bin titi da kallo masu farin ciki sunayi masu bak'in ciki nayi akan case d'insu dan kowa ya san makomarshi, jawahir ko jingine jikinta tayi a inda take zaune yanayinta kawai zaka kalla kagane tana cikin tashin hankali saidai abinda zai baka mamaki ba wai akan case d'inta tashiga tashin hankalinba ta shiga ne saboda halin da Barrister yashiga akanta, wasu siraran hawaye ne suka gangaro mata tayi saurin sa hannu tagoge, a cikin zuciyarta tana addu'a Allah yasa ko bayan ranta Faruk yaku'buta daga sharrin mutanen nan, ahaka har suka isa HIGH COURT bata saniba saida aka bud'e aka fara fita sannan takusa da ita tata'bota tafito..... ******** Nasiba bayan ta gama sallar asuba da azkhar d'inta gari yana fara haske fitowa tayi dan tagaishe da iyayenta kamar yadda tasaba saidai da ka kalli fuskarta zakaga alamar bata runtsaba, hanyar part d'in mahaifinta tanufa tana isa a parlor taji muryarshi yana waya har zata d'age labulen tashiga sai kuma tafasa taja tatsaya dan yagama wayar abinda taji yana fad'a ne a wayar yad'aga mata hankali sosai saurin sa hannu tayi tatoshe bakinta tare da zaro idanu gabanta wani irin mummunan fad'uwa yayi tayi saurin ja da baya lokacin da taji yana cewa "Haba Alhaji Mansur ai kar kadamu tunda dai Faruk yana hannunmu nasan yarinyar nan ta shiga damuwa sosai saboda ba lauyanta,,, dariya yayi sannan yace ai ya kamata muma muje High court d'innan ayi shara'ar a gabanmu akasheta kowa yahuta kaga shikenan sai mucinye sauran dukiyar hankalinmu kwance. Eh daman ka fad'a min kunyi magana da Barr M.B jiya toh shikenan koma menene sai mun had'u a kotun". Saurin juyawa tayi dagudu tabar wajen tare da fashewa da kuka tana isa parlor taci karo da mahaifiyarta da tafito daga part d'inta, kallonta tayi tace lafiya Nasiba. Jikinta tafad'a tare da k'ara sautin kukanta. Kingani ko kedai bakijin magana yanzu haka wani laifin kikayi ma Daddyn naki ko? Na fad'a maki kicigaba da addu'a indai Faruk yana raye zaya dawo. Cikin sheshek'ar kuka tabud'e baki tace Mummy...sai kuma tayi shuru. Rik'ota Hajiya Maijidda tayi tace shikenan kiyi hak'uri muje inrakaki d'akinki kikwanta kafin agama had'a breakfast insa akawo maki. Tana a jikin Mummyntata a haka sukaje tarakata har bedroom d'inta saida talallasheta tadaina kukan sannan tatafi. Nasiba tana ganin ta fita mik'ewa tayi taje tarufe d'akinta tacigaba da kukan maganganun da taji mahaifinta yana yi a waya suna dawo mata, kanta tafara tambaya tana cewa kenan su Daddy sun san inda Faruk yake? Ammah akan me suke magana dukiyar wa zasu cinye? Ko dai akwai gaskiya akan maganar da Faruk yafad'a akan Daddynta? Saurin girgiza kai tayi tace a'a Daddyna ba haka yakeba kawai dai suna magana akan wani abun nadaman ammah kuma.....komawa tayi takwanta tare da dafe kanta da taji ya fara sara mata nan hawaye suka cigaba da ambaliya a fuskarta.... __________ Tunda aka shiga kotun waje aka samar masu su kusan hud'u ne suka zauna, mutane ne sosai a cikin kotun, ahankali ahankali ake zuwa lokaci guda kotun tacika mak'il da jama'a ana jiran k'arasowar alk'ali inda gabad'aya ciki da wajen kotun zagaye take da police, a gaba kuma lauyoyin masu k'ara da wad'anda ake k'ara ne zazzaune, goma saura minti biyar alk'ali yafito nan gabad'aya mutanen suka mik'e har saida yazauna sannan kowa yazauna. Court Reporter ne yamik'e yayi sallama tare da yin addu'a bayan anshafa ne sannan yace a yau 2 ga watan Afurili (April) wanda yayi daidai da 7 ga watan Rajab......Shara'a ta farko da zata kasance a yau itacs Shari'ar Maimuna Ahmad wadda ake zargi da zuba ma mijinta guba a cikin abinci yaci yamutu daga k'arshe dangin mijin sukayi k'ararta bayan antabbatar masu da guba ce takasheshi, juyawa yayi yakalli Alk'ali yace Allah yagafarta malam wannan itace shari'ar tamu ta farko, jinjina kai Alk'ali yayi nan court reporter yaje yamik'a ma alk'ali file d'inta. Dattijon Alk'alin gyara zaman farin glass d'inshi yayi a saman fuskarshi sannan yaduba file d'in ya d'au kusan minti biyar a duk'e sannan yad'ago kai yace kotu tana buk'atar ganin Maimuna ta bayyana a gabanta. Jawahir da tunda taji za'a fara karanto k'ara taruntse idanunta dan a tunaninta shari'ar ta ce za'a fara'a bata bud'eba sai da taji ta kusa da ita ta fara kuka ahankali sannan tabud'e takalleta da alama itace Maimuna nan wasu police mata guda biyu sukazo suka jata suka tafi da ita wajen da aka tanadar ma me k'ara da wanda ake k'ara dan sutsaya. Alk'ali d'agowa yayi yakalleta sannan yaduk'a yafara 'yan rubuce rubuce sai kuma yad'ago yace kotu tana buk'atar ganin lauyan me k'ara da na wadda ake k'ara. 'Daya daga cikin lauyoyin da suke zaune ne a layin gaba yamik'e yayi sallama sannan yace sunana Barr Mu'ammar nine lauyan da yake kare wadda ake k'ara sannan yakoma yazauna, Barr Junaid da yake zaune ya yi zugum bai ma san abinda ake tattaunawa ba saboda hankalinshi yana wajen abokinshi da ya'bata tsawon kwanaki hud'u, Barr Bilal ne yad'an zunguroshi da biron hannunshi sannan yadawo hayyacinshi saurin mik'ewa yayi yai sallama sannan yace sunana Barr Junaid nine lauyan da yake kare mek'ara. 'Dago kai Alk'ali yayi yakalleshi sannan yaduk'a yayi 'yan rubuce rubucenshi. Yad'ago kai yace kotu tana so maimuna tabayyana mata gaskiya a game da kisan da ake zargin ta yi ma mijinta ta hanyar ciyar da shi guba. Sheshek'ar kuka tafara yi saida megabatar da k'ara yamik'e yasake maimaita mata jawabin alk'ali sannan cikin inda inda tace bani bace nakashe shi dan lokacin da yamutu bana gidan. Alk'ali ganin ta yi shuru bata sake cewa komai ba yasa yaduk'a yayi 'yan rubuce rubuce sannan yad'ago yace shin ko Lauyan wad'anda suke k'ara yana da shedar da zai bayyana ma kotu wadda zatasa tagamsu da cewa maimuna ce tayi kisan bayan a yanzu maimuna ta nuna ba itace tayi kisan ba. Mik'ewa Barr Junaid yayi yace tabbas ina da ja ya maigirma mai shara'a inaso kotu taban dama ind'an yi wasu tambaboyi ga maimuna. Kotu ta baka dama,,, cewar alk'ali. Fitowa Barr Junaid yayi yanufi wajen da take tsaye yace malama maimuna shin ko zaki iya sanar da mu kina ina a lokacin da mijinki yamutu? Inda inda tafara yi tace na je gidan 'yar uwata ranar ban gida nima saidai nadawo natarar da gawarshi. Murmushi Barr Junaid yayi yace shikenan abinda kika sani? 'Daga kai tayi alamun eh. Juyawa yayi yakalli alk'ali yace ya megirma me shara'a maimuna bata amsa laifinta ba saidai duk na kusa da ita sunsan cewa itace tayi kisan. Lauyan wadda ake k'ara ce yayi saurin mik'ewa yace ya me girma me shara'a ya kamata a tsawatarwa lauyan wanda suke k'ara yagyara jawabanshi dan sunyi muni ga wadda ake k'ara. 'Dagowa Alk'ali yayi yakalli Barr Junaid yace kagyara bayaninka. 'Dan duk'ar da kai yayi cikin girmamawa yace na gode, sannan yad'ago yace ya megirma me shara'a inaso kotu taban dama ingabatar da shedu. Kotu ta baka dama. Godiya yayi yace malam zubairu me gadi da Talatu me aikin gidan sune sheda. Alk'ali ne yace kotu tana buk'atar ganin Malam Zubairu me gadi gidan Sadik'u da Talatu me aiki sun gurfana a gabanta. Su dukansu suka fito nan aka sa su sukayi rantsuwa akan zasu fad'i gaskiya sannan aka tambayesu suka bada shedar cewa babu inda taje a ranar tana gida inda 'yar aikin gidan tak'ara da cewa a gabanta ta ga me d'akintata ta fiddo wani abu cikin leda ta zuba a cikin abincin wanda yaci yamutu. Maimuna na jin haka tafashe da kuka tace talatu sharri zaki ja min Allah ya isa ban yafeba, police d'in da suke bayanta tsaye ne suka daka mata tsawa tayi shuru, Barr Junaid cewa yayi sukoma suzauna sannan yamaida kallonshi ga alk'ali yace ya megirma me shara'a bayan wannan shedar ina da shedar report d'in da likita yabada na mutuwar mamacin inda ya rubuta ya ci guba sannan an d'auko abincin da yaci anduba anga akwai guba a ciki. Alk'ali ajiye biron hannunshi yayi yace ina sheda? Barr Junaid d'auko wata farar takardar yayi yaje yamik'a ma alk'ali yace ya me girma me shara'a wannan itace shedata sannan a cikin file d'in mamacin ma akwai shedar hakan, nan yaje yad'auko file d'in yakawo ma alk'ali yace jiya na amsoshi a asibiti. Dubawa alk'ali yayi sannan yad'ago yakalli wadda ake k'ara yace shin ko kina da ja akan wannan shedun da aka samo? Shuru tayi tana cigaba da kuka ganin haka yasa lauyanta yamik'e yace ina da ja ya megirma me shara'a abinda lauyan masu k'ara yafad'a ba gaskiya bane. Cikin kuka tace tabbas hakane nice nakasheshi saboda bana sonshi iyayena ne suka aura min shi, wallahi nice nakashe shi. Alk'ali yace kin tabbata kece? 'Daga kai tayi alamun Eh. Duk'awa yayi yai 'yan rubuce rubuce sannan yad'ago yace Alhamdulillah kin amsa laifinki bayan duk bayanai sun nuna hakan dama, dan haka kotu zata yanke maki hukuncin zaman gidan kaso har k'arshen rayuwarki domin laifin da kika aikata na kashe mijinki wannan shine adalcin kawai da zamuyi. Kuka tacigaba da yi cike da tashin hankali nan aka tafi da ita. Jawahir wani irin tausayinta taji ganin yadda take kuka saidai me matar itace me laifi babu yadda za'ayi. Haka me gabatar da k'ara yamik'e yasake bayani akan k'ara ta biyu aka fito aka fara yin shara'a. Jawahir tana nan tsaye saida akayi ma mutane hud'u inda wasu aka yanke masu hukuncin kisa wasu kuma aka maidasu gidan yari, ita d'in kanta ta san dole cikin biyu za'ayi guda ko kisa ko yanke hukuncin k'arashe rayuwa a gidan kaso, wasu siraran hawaye ne suka gangaro mata cikin zuciyarta tace Barr Faruk rayuwarka kawai nakeji ba wai abinda zai faru da ni ba, ina ma ace Ammi zata taimaka taku'butar da kai. Ana gama wad'annan shari'o'in megabatar da k'ara yamik'e yace sai shari'ar da takasance ta k'arshe a wannan ranar itace shari'ar Jawahir Muhammad Maikud'i wadda ake zargi da yin kisa na mutane d'aid'aya har mutum bakwai, inda dangin mamatan suka shigar da k'ara,, sannan yaje yamik'a ma alk'ali file d'in, kotun kacamewa tayi da surutu saida alk'ali yad'an buga tebirinshi sannan akayi tsit, Duk'awa yayi yafara duba file d'in ya d'auki lokaci yana dubawa sannan yad'ago yace kotu tana buk'atar ganin Jawahir wadda ake k'ara ta bayyana a gabanta. Police d'in matan nan ne guda biyu suka fito da ita tatsaya a wajen da ake tsayawa, me karanta k'ara yace ya me girma me shari'a wannan itace Jawahir. 'Dago kai alk'ali yayi yakalleta nan yashaidata sannan yacigaba da cewa kotu tana son ganin lauyan masu k'ara da na wadda ake k'ara. Barr MB ne yamik'e yayi sallama sannan yace sunana Barr Mahamud Bello nine lauyan masu k'ara,, sannan yakoma yazauna. Shuru babu wanda yasake mik'ewa daga cikin lauyoyin, Barr Junaid dafe kanshi yayi tare da runtse idanunshi saboda tsananin tashin hankalin rashin abokinshi dan shi kanshi shara'ar da sukayi ta maimuna ya san ya yi k'ok'ari sosai a yadda ya iya yinta saboda tashin hankalin da yake ciki. Me gabatar da k'ara ganin babu wanda yamik'e daga cikinsu yasa yak'ara cewa kotu tana son ganin lauyan wadda ake k'ara. Jawahir idanu tazuba ma lauyoyin lokaci guda tasafke idanunta k'asa dan ta san babu lauyanta a ciki. Me gabatar da k'ara ne yasake maimaitawa nan Barr MB yamik'e yakalli alk'ali yace ya me girma ne shara'a lauyan wadda ake k'ara ya gudu saboda baida bayanan da zai kare wadda ake k'ara da su. Karaf a kunnuwan Barr Junaid lokaci guda yamik'e a harzuk'e yace k'arya ne ya me girma me shara'a lauyanta ba guduwa yayi ba akwai dalili me k'arfi da yahana bayyanarshi, kallon Barr Mb yayi yace ya kamata kadinga gyara kalamanka sannan yakoma yazauna. Barr MB d'an rissinawa yayi sannan yakoma shima yazauna. Alk'ali da yake kallonsu bayan sun zauna ne yace shin ko akwai wanda lauyan wadda ake k'ara yawakilta a cikinku? Su duka shuru sukayi nan yasake cewa ko akwai wanda zai kare wadda ake k'ara? Nan ma shuru. Dan haka yaduk'a yayi 'yan rubuce rubucenshi sannan yad'ago yakalli jawahir yace Malama Jawahir kamar dai yadda shari'ar tamu ta baya takasance tsawon shekara d'aya har yau kin kasa amsa laifukanki akan zargin da akeyi maki shin ko a yau zaki iya kare kanki kafin kotu tazartas da hukunci na k'arshe? 'Dago kanta tayi takalli alk'ali sannan tamaida idanunta ga d'unbin jama'ar da suke zaune wajen kowa idanunshi akanta suna jira suji abinda zata fad'a, karaf idanunta suka safka akan mutum biyu. Alhaji Mansur da Alhaji Sufyan murmushin mugunta suka sakar mata. Idanu tazuba masu bata ko k'yaftawa musamman ma Alhaji Sufyan nan hawaye suka fara gangarowa daga cikin idanunta, tana ji kamar taje tashak'esu Alk'ali sake maimaita mata tambayar yayi ammah bata ma san yana yi ba, saida police d'in wajen suka d'an ta'bota sannan tadawo hayyacinta. Ganin bata ce komai ba yasa alk'ali yace shin ko Lauyan masu k'ara yana da k'wak'k'warar shaidar da zata ida bayyanar ma kotu cewa jawahir ce tayi kisan? Mik'ewa Barr MB yayi yace tabbas ina da ita ya me girma me shara'a inaso kotu taban dama ind'anyi ma jawahir wasu 'yan tambayoyi. Dama alk'ali yabashi nan yawuce yanufi inda jawahir take tsaye.... _____****______ Barr Faruk hankalinshi atashe yake a ranar duk k'ok'arin da yayi dan yakwance kanshi kasawa yayi yana nan zaune inda aka d'aureshi idanunshi suna a kan agogo har k'arfe tara da rabi tabuga, kallonsu yayi yaga suna zaune su biyu dan sauran ukkun basunan sun fita tare da ogansu gashi wad'anda sukafi rashin mutuncin ne suke zaune babu damar yarok'esu, runtse idanunshi yayi ahankali yace kiyi hak'uri Jawahir banda yadda zanyi in ceceki wannan itace k'addararki saidai ina maki fatan Allah yatseratar da ke,,, bud'e k'ofar da akayine yasa yai saurin bud'e idanunshi sai ganin d'aya daga cikinsune yashigo d'auke da takeaway, sauran yaji sunce ya dai bahbah wani abu aka kawo mana? Zuwa yayi ya ajiye masu kowa takeaway guda yace wani aiki ne mukayi da oga yau mun samu kud'i sosai cikin kud'in ne yace ink'ara siyo mana breakfast tunda bamu k'oshiba, su dukansu dariya sukasa sukace dakyau, nan yakoma yazauna kusa da su, su kuma suka d'auka suka fara ci, Barr Faruk yana kallonsu suka ci abincinsu shi ko ba'ayi mashi ko tayi ba. Faruk wasu irin hawaye ne masu gumi suka gangaro mashi saboda tsananin tausayin halin da Jawahir zata shiga yau, runtse idanunshi yayi yana cigaba da yi mata addu'a a cikin zuciyarshi. Jin su yayi shuru dan haka yabud'e idanunshi sai gani yayi mutane biyu daga cikinsu sun hankad'e kai saman kujera suna bacci inda d'ayan yake zaune yana kallonshi. Mamakine yakamashi cikin ranshi yace daga gama cin abinci sai bacci. Bai ankaraba kawai sai gani yayi babu mutumin a wajen, mamakine ya ida kamashi yace ikon Allah ina mutumin nan yayi? Murya ce yajiyo a bayanshi me firgitarwa wadda sautinta tacika d'akin gabad'aya yaji ance "barka da wannan lokacin Barr Faruk" Yunk'urin waigawa yayi dan yaga me magana ammah yakasa saboda d'aurin da akayi mashi. Ji yayi anbushe da wata irin mahaukaciyar dariya wadda tasa saida yad'an firgita, muryarce yaji tana cewa wannan aikina ne Barrister. Dakewa yayi yace wanene nan? Ko ma wanene yabayyana min kanshi!! Shuru yaji nan yasake maimaitawa nan ma shuru dan haka yatabbatar da babu kowa d'akin. Runtse idanunshi yayi tare da safke ajiyar zuciya. **** ***** Barr MB kallonta yayi yace Malama Jawahir a iya binciken da mukayi mun gane cewa kin kashe Alhaji Mu'azu da 'ya'yanshi biyu wanda d'aya daga cikinsu mijine a gareki kinyi kisan ba dan komai ba sai dan kawai kina so kigaje dukiyar da ke gareshi. Da mamaki tajuyo takalli Barr MB, bai damu da mamaki da yagani a fuskarta ba yacigaba da cewa, a lokacin da aka tuntu'bi Megadin ku ya bada shedar cewa daman kin dad'e kina yunk'urin kashe yayan mahaifin naki da shi da iyalanshi wannan dalilin ne yasa itama me aikin gidanku tagudu takoma garinsu saboda tsoron gargad'in da kika ta'ba yi masu a lokacin da suka ta'ba ganinki kin nufi d'akin kawun naki da wuk'a a hannunki lokacin yana bacci zaki kasheshi sai gashi 'yar aikin ta shigo ta ganki, a dalilin haka tatsorata takoma gidansu sannan shima megadinku bayan ankamaki da muka samu wannan bayanin daga wajenshi mun sake nemanshi dan musamu k'arin bayani ammah ya tsorata ya gudu ya koma garinsu chan Marad'i, shin ko zaki k'aryata wannan? Baki tasaki tana kallonshi ganin yadda yake ta zubo mata k'arya. Ganin batace komai ba yasa yacigaba da cewa sannan su kuma abokan mahaifinki kin kashesu ne saboda dalilin kun siyar masu da companynku wanda saboda karayar arzik'i yasa kuka rabu da shi shine daga baya kika dinga kashesu saboda kisamu kimaido companyn a hannunki, wannan bayanin mun sameshi a wajen sauran wad'anda suke da hannu wajen sayen companyn..... Wata irin k'ara jawahir tasaki takai hannu cikin zafin nama tashak'e mashi wuya tace wallahi k'arya kake min, meyasa zakayi min k'arya. Idanuwanshi waje sukayi saboda zafin mak'ara nan yafara neman yak'wace kanshi, police ne suka 'ban'bareshi daga hannunta alk'ali yace yakamata kisan a inda kike nan kotu ne ya zama dole kidinga ladabi. Barr MB mik'a ma alk'ali takardun hannunshi yayi nan ya amsa yaduba sannan yad'ago yakalleta yace ga shaidar siyar da company da kukayi wanda a yanzu yake mallakin mutum biyu sannan ga duk bayani akan kisan da kikayi ko zaki iya kare kanki a gaban kotu me adalci? Wasu sabbin hawaye ne suka gangaro mata tayi saurin runtse idanunta, Alk'ali sake maimaita mata yayi, ahankali tagirgiza kai alamun a'a. Buga table Alk'ali yayi yace tunda bakida shedar da zaki kare kanki kotu ta yanke maki hukuncin.....tun kan alk'ali ya ida fad'a Jawahir tasulale tazauna k'asa d'irshen tare da fashewa da kuka dan ta san kisane kawai zai biyo baya gashi bata cika burinta ba....... _Sis Nerja'art✍🏻_ [7/24, 11:15 PM] Sis Nerja'art 2: *......FANSAR RAI......* *INTELLIGENT WRITER'S ASSO....®* [On Ward Together] _Follow me on Wattpad: *Sis-nerja*_ _Wannan Littafin na kud'i ne domin karantawa cikin aminci da yarda ga duk me buk'ata zai turo katin Mtn na d'ari biyu N200 kacal ta wannan number d'in 09035938246, ko ta account number 5330055604, Idan katura ka aiko da screen shot na transaction a wannan number d'in 09035938246_ _Akwai gara'basar *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shahararriyar marubuciyar nan *AMEENA ABBA UMAR* tare da novel d'in *FANSAR RAI* akan farashin N300 kacal, ko da kud'in ka sai da rabonka_ *PAGE 20* K'ofar Kotun ce aka turo da k'arfi aka shigo wanda hakan yaja hankalin duk mutanen da suke cikin kotun suka juya dan ganin wanda zai shigo, shima kanshi Alk'ali bai ida fad'in hukuncin da yayanke ma Jawhir ba, wanda yabud'e k'ofar ne yashigo inda daga bayanshi sukaji murya ana cewa Ya Megirma me shara'a kar ayanke mata hukunci na zo da hujjoji masu k'arfi da zan bayyana ma kotu wanda zaisa agane batada laifi acikin kisan da akayi. Jawahir na jin muryarshi saurin d'ago kai tayi tana kallonshi cike da mamaki, sanye yake cikin kayan aiki shi da nakusa da shi watau Barr Nas. Alhaji Mansur da Alhaji Sufyan saurin mik'ewa sukayi tsaye mamaki duk ya bayyana a fuskarsu k'arara sukace kai daga ina kake ya akayi kazo nan? Kallonsu Barr Faruk yayi yai murmushi sannan yataka yanufi wajen alk'ali yana cewa agafarceni ya me girma me shari'a. Alk'ali gyara zaman farin glass d'inshi yayi sannan yace watau sai yanzu kaga damar zuwa, kotu zakayi ma wasa da hankali bayan a farko baka zo ba saida kotu zata zartas da hukunci sannan. Matsowa yayi yace agafarceni ya me girma me shara'a babban daliline yahanani zuwa wanda idan kabani dama nagabatar da hujjata zan sanar da kotu dalilin. Jinjina kai Alk'ali yayi yace kotu ta baka dama, kowa yakoma yazauna. Nan duk aka zauna, Jawahir mik'ewa tayi tsaye daga duk'en da take tana kallonshi, shima kallonta yayi sannan yamaida kallonshi ga Alk'ali yace Allah yagafarta malam nagode sosai, a yau zan gabatar da shedun da natattara akan zargin da akeyi ma Jawahir ammah kafin nan inaso kotu tafara bani dama infara tattaunawa da wadda ake k'ara. Alk'ali yace ta baka dama. Juyawa yayi ga jawahir sannan yace shin malama jawahir ko zaki taimaka kifad'a ma kotu yadda kike da Alhaji Mu'azu da su Alhaji Tanimu? Shuru tayi tana kallonshi, nuni yayi mata alamun tayi magana sannan tace Eh Alhaji Mu'azu yayan mahaifina ne su kuma abokan mahaifina ne bayan rasuwarshi suka koma tare da yayan mahaifin nawa. Jinjina kai yayi yace dakyau sannan yajuya ga alk'ali yace Allah yagafarta malam hujjata ta farko da zan fara gabatarwa itace Marigayi Alhaji Mu'azu da Abokan mahaifinta su takwas kenan sunyi amfani da damarsu sun kashe mahaifinta da mahaifiyarta dan sugaje dukiyarshi ban fad'i hakan ba saida natabbatar da shedata. Kotun ce tafara kacamewa da hayaniya jin abinda yafito daga bakin Barr Faruk, saida aka nutsar da mutane sukayi shuru. Juyawa Faruk yayi yakalli k'ofa yace kushigo. Wani buzu ne yashigo nad'e da rawani a kanshi sai wata dattijuwa tana tura wata mata a saman wheelchair, jawahir idanu tazuba ma matar ahankali tace Ummah, matar ma kallonta tayi nan hawaye suka gangaro mata. Barr Faruk ne yanuna buzun yace wannan shine megadin gidan Alhaji Mu'azu wannan kuma uwar d'akinshi ce. Alk'ali d'agowa yayi yakallesu sannan yace ma megadin kotu tanaso kafad'a mata gaskiya akan abinda kasani a game da gidan Alhaji Mu'azu. 'Dage kanshi sama yayi yace eh zan fad'i gaskiya ni nine megadin shi kuma wannan yarinya tun bayan mutuwar iyayenta Alhaji yake azabtar da ita yana cin dukiyarta shi da abokanshi, akwai wata rana ina zaune a wajen gate ina sauraren radio Alhaji yafito zai shiga mota yafita nan naji yana waya yana cewa zai san hanyar da zaibi yafito da ita suje banki yasa taciro mashi kud'i daga account d'in mahaifinta, toh bayan nan na ta'ba jin suna magana da wani abokinshi yana cewa zai siyar mashi da wani gida da yagano k'anen nashi yana da shi baisan da gidan ba sai bayan mutuwar d'an uwan nashi, sannan a game da mutuwar d'an uwan nashi a ranar da aka shigo aka kasheshi Alhaji Mu'azu najiyo yana magana da wasu a waje ban dai ji abinda yake cewa ba saidai na ji ya ce masu ga makullin gidan nan, toh kuma da makullin aka bud'e gidan aka shigo aka kasheshi, d'aga hannunshi yayi sama yace wallahi wannan shine abinda nasani banyi maku k'arya ba. Alk'ali jinjina kai yayi sannan yaduk'a yacigaba da rubuce rubucenshi yace Barrister muna saurarenka. Faruk juyawa yayi ga Ummah yace Hajiya munaso kifad'a ma kotu matsayinki a wajen Alhaji Mu'azu da duk abinda kika sani akan kisanshi. Goge hawayen fuskarta tayi tare da motsa 'bari d'ayan jikinta da yake da lafiya sannan murya chan k'asa tafara magana ganin haka yasa aka d'auko mata lasifika aka kanga wajen bakinta fara jawabi tayi tace nice matar Alhaji Mu'azu kamar yadda kotu taso zan fad'a mata gaskiya maganar gaskiya tabbas ni da mijina mun cutawa yarinyar nan kuma ya ci dukiyarta wannan shine abinda nasani sannan itace takasheshi da 'ya'yana biyuuuuu, kyarma tafara yi tana jijjiga nan wasu nurse guda biyu sukayo saurin zuwa wajenta dan dama tare da su sukazo, alk'ali yabada izini afita da ita amaidata asibiti nan suka tafi da ita. Barr MB me yamik'e a fusace yace ya megirma me shari'a ya kamata kotu tagaggauta hukunta lauyan wadda ake k'ara akan zuwa da yayi har asibiti yazo da marar lafiya wanda a halin yanzu ya ja ta shiga wani hali, wannan ba daidai bane. Alk'ali d'agowa yayi yace Barr MB yace koma kazauna, komawa yayi cikin sanyin jiki yazauna Barr Faruk cigaba yayi da cewa shedata ta gaba da zan bada itace Marigayi Alhaji Mu'azu da Abokan mahaifinta su takwas sunyi amfani da damarsu sun kashe mahaifinta da mahaifiyarta dan sugaje dukiyarshi ban fad'i hakan ba saida natabbatar da shedata, wayarshi yad'auko yakunno recording d'in duk maganganun da yatura na wayar da su Alhaji Mu'azu yayi da abokanshi d'aya bayan d'aya yakunna ma alk'ali yasaurara, gabad'aya kotun tayi tsit ana saurare, akan lokacin da suke had'a plan zasu kashe Alhaji muhammad da kuma kisan da sukayi ma mahaifiyar jawahir sannan wajen ciro kud'i dan su mallaki dukiyarta duk ya saurara Alhaji Mansur ne yayi saurin mik'ewa yace wannan k'arya ne sharrinshi ne kawai. Kallonshi alk'ali yayi yace kotu tana gargad'inka kar kasake sa mana baki in ba hakaba zaka fuskanci hukunci. Komawa yayi cikin sanyin jiki yazauna sannan alk'ali yaduk'a yafara 'yan rubuce rubuce, nan Barr Faruk yacigaba da cewa wannan bayanin duk na sameshi a cikin wayar Alhaji Mu'azu saboda wayarshi tana saving d'in call recording, ga ma wayar ta shi nan yamik'a ma alk'ali yadudduba cikin wayar nan yajinjina kai, yace cigaba da bayaninka. Cigaba yayi da cewa sannan duk ga bayanai nan akan dukiyarta da suka mallaka da takardun jabu da suka dinga bugowa shaidar sun sayi fili da gidaje daga hannun mahaifinta, ita kuma ta shigar da k'ara kotu ammah anyi watsi da k'arar wannan dalilin ne yasa tadinga d'aukar mataki da hannuwanta saidai batayi niyar kashe d'an uwan mahaifin nataba shine yafara neman kasheta sannan ita kuma dan takare kanta takasheshi, kamar dai yadda matarshi tayi bayani. Alk'ali yace shin ko zamu iya samun bayanai agame da dukiyar Alhaji Muhammad d'in? Eh Allah yagafarta malam ammah kafin nan inaso kotu taban dama inyi ma mutane biyu wasu tambayoyi wad'anda tambayoyin ne zasu taimaka wajen samun cikakkar sheda. Alk'ali kotu ta baka dama su wanene mutane biyun? Juyawa yayi yakalli Alhaji Mansur da Alhaji Sufyan da suke zaune suna zare idanu sunyi sharkaf da zufa, Sannan yace Alhaji Mansur Maiharka da dollar sai Alhaji Sufyan me nasara. Alk'ali ne yasake maimaita sunan yace kotu tana son ganinsu sun hallara a gabanta. Su dukansu kusan tare suka mik'e cikin sanyin jiki suka fito suka tsaya. Barr Faruk matsawa yayi kusa da su yace Alhaji Mansur da Alhaji Sufyan wasu 'yan tambayoyine zanyi maku ammah kafin nan ya kamata kufara sanar da kotu matsayinku a wajen Alhaji Muhammad. Su dukansu sukace Na'am Yace eh kar dai kumanta a kotu kuke ya kamata duk abinda zaku fad'a kufad'i gaskiya. Gyaran murya Alhaji Mansur yayi sannan yakalli Alk'ali yace ni abokin kasuwancin Alhaji Muhammad ne a lokacin da yake raye bayan rasuwarshi ne muka koma kasuwanci da d'an uwanshi, wannan shine dalilin sanin da nayi mashi. Murmushi Barr Faruk yayi sannan yakalli Alhaji Sufyan yace kaikuma fa me zakace? Eh toh nima dai kamar yadda Alhaji Mansur yace nima haka nake da su. Kana nufin kaima abokan kasuwancinka ne? Eh haka. Dakyau ammah a iya binciken da nayi na gane cewa ba wai abokin kasuwanci kawai bane akwai aminta a tsakaninku da su, ammah ba ma wannan ba na san kun san komai a game da mutuwar Alhaji Muhammad da me d'akinshi Khausar ko akwai abinda zaku iya cewa? Alhaji Mansur ne cikin 'bacin rai yace kai banason zancen banza me kake nufi? Sharri zaka ja mana? Barr MB mik'ewa yayi yace ya megirma me shara'a ya kamata kotu tagargad'i lauyan wadda ake k'ara akan irin tambayoyin da yakeyi ma su Alhaji Mansur domin suna muni agaresu. Alk'ali kallon Barr Faruk yayi yace kagyara yanayin tambayarka. 'Dan rissina kai yayi yace nagode sannan yajuya garesu yace, kafin mutuwar Alhaji Muhammad kun ta'ba taruwa ku takwas a chan wani d'aki kukayi magana inda kowa yafurta abinda yakeso yamallaka na Alhaji Muhammad a k'ark'ashin jagorancin d'an uwanshi, ko zaku iya tuna haka? Su dukansu shuru sukayi suna kallon kallo sai chan Alhaji Mansur yagirgiza kai yace bansan anyi haka ba. Shuru faruk yayi sai kuma yajuya yakalli Alk'ali yace ya megirma me shara'a tabbas su Alhaji Mansur da Alhaji Sufyan suna cikin mutanen da suke da hannu akan mutuwar Alhaji Muhammad dan a nan cikin wayar da namik'o duk akwai muryoyinsu da maganganun sirrin da sukayi a tsakaninsu sannan ga k'arin shedar da ke gareni ta k'arshe, juyawa yayi yakallesu sannan yabud'e file d'in da yake hannunshi yad'ago masu yace shin cikinku akwai wanda yagane takardun da suke cikin file d'innan? Zaro idanu sukayi gabad'aya nan take cikin Alhaji Sufyan yakad'a yace ina kasamo wad'annan?. Murmushi yayi sannan yace takardar farko original ce ta companyn Alhaji Muhammad inda ta biyu takasance jabu ce kun bugotane dan ku samu ku mallake companyn ga signing d'inku nan da komai. Mai gabatar da k'ara ne yazo ya amsa yakai ma alk'ali, wasu takardun yafiddo yanuna masu yace wannan fa me zakuce akanta? Shuru sukayi suna kallonshi sai Alhaji Mansur yayi k'arfin halin cewa wannan ai kai za'a tambaya dan kai kasan sharrin da kake shirin k'ullawa. Girgiza kai yayi yace wannan ba sharri bane sannan yajuya yakalli Alk'ali yace ya megirma me shara'a wannan takardun motocin Alhaji Muhammad ne da suka samo a cikin gidanshi bayan mutuwarshi sunyi amfani da wani ya yi masu yarjejeniya akan kowane d'aya daga cikinsu Alhaji Muhammad ya siyar mashi da motocinshi biyu ga signing nan irin nashi anje anyi, zuwa yayi yamik'a ma Alk'ali nan yaduba, sannan yace ya megirma me shara'a na tabbata da za'a tuhumesu da zasu fad'i gaskiyar cewa suna da hannu a cikin mutuwarshi da kuma irin k'ulle k'ullen da suka dinga shiryawa akan dukiyarshi wadda sunci fiye da rabin dukiyar dan Alhaji Sufyan shi yashirya masu yadda zasuyi susamo dukiyar da take cikin account d'in jawahir inda su Alhaji Mansur da Alhaji Tanimu sukaje suka shirya ma kawunta k'arya a matsayinshi na bagidaje sukace yasamo masu kud'in zasu yi kasuwanci wanda zai dinga kawo masu kud'i sosai shine yayi amfani da damarshi yatafi da jawahir a banki yasa tayi mashi signing d'in rabin dukiyarta aka fiddo daga acount d'in koda yakawo masu ba wai business sukayi ba sunje sun raba kud'in a tsakaninsu ne. Alhaji Sufyan ne yayi saurin katseshi yace ya megirma me shara'a wannan k'arya ne sharri kawai yake son ja mana dan ya'bata mana suna bamusan komai ba akan abinda ake zarginmu da shi ba dan bamu aikata ba kawai dai yana da wani nufi akanmu ne dan kawai na hanashi auren d'iyata saisa yakeso ya'bata mana suna. Faruk kallon Alk'ali yayi yace ko d'aya ba sharri bane Allah yagafarta malam duk sun aikata dan ga shedu nan na tara ga muryoyinsu nan a cikin wayata. sake kunno recording d'aya daga cikin su yayi nan murya tafara tashi ana cewa "Hello kana jina ya kamata kayi k'ok'ari wajen ganin ka samo mana file d'in filin nan dan da alama zaiyi kud'i sosai ni na san yadda za'ayi asiyar da shi batare da kowa ya ganeba dan nima kaga wannan filin da kabarmin gwamnati nasiyar mawa kuma ta siya da kud'ad'e masu tsoka. Toh shikenan Alhaji koma me kenan nasan hanyar da zanbi insamo dan dama maganar da muka gama yi da Alhaji tanimu kenan dan shine jagoran komai, da ace akwai hanyar da zanbi da a yau d'innan sai naga bayan yarinyar nan kowa yahuta dan na san idan har tamutu dole abarmin gadonta gabad'aya tunda ni kad'ai ne d'an uwan mahaifinta,,, Cewar Alhaji Mu'azu. Daga chan 'bangaren dariya akayi akace kaidai kabi komai a hankali ko da baka kasheta ba zaka iya yin amfani da damarka wajen ganin mun samo dukiyar Alhaji Muhammad, inyaso idan har mun gama samun yadda mukeso zaka iya kasheta saidai kuma idan har zaka rufe ma mutane baki dan kar ayi zargin wani abu kamar yadda mukayi bayan munsa ankashe Alhaji Muhammad da matarshi. Dariya Alhaji Mu'azu yayi yace ai fiye da hakan ma zan iya sa wa ayi mata dan ni ban had'a komai da kud'iba abokina, yanzu dai zuwa anjima zan kiraka idan har nagama tattara bayanan filin inyaso sai muje musiyar da shi. Yauwa mutumina kayi k'ok'arin haka sai na ji daga gareka". Yana k'arewa wani kuma yasake kunnowa me irin muryar sukaji yana cewa, Hello Alhaji Mu'azu ina jinka d'azu ka kirani bana kusa. Eh Wallahi abokina cewa nayi ta samu fa a yanzu ga wani gida nan na Alhaji Muhammad da nagano yana da shi batare da sanin kowaba sai yanzu naga takardun gidan na je na ganshi kuma antabbatar min da nashine. Daga chan 'bangaren dariya akayi akace lallai Alhaji Muhammadu wayonshi ya yi yawa watau yana da gida batare da sanin ka ba, toh bari zan zo inje muga gidan idan har yana da girma sosai ni zan sayeshi dan dama inaso mutashi da iyalina daga nan, kace abu ya zo gidan sauk'i ai wallahi mutuwar nan tashi dad'i tayi min dan ko bakomai munsan muma mun mori dukiyarshi. Alhaji Mu'azu ma dariya yayi yace kaidai bari a yanzu gashinan ina ta facaka da kud'i yadda nakeso ba kamar lokacin da yake raye ba, ka san mutuwarshi ko kad'an bata d'aga min hankali ba sai waje d'aya lokacin da kabani layarnan insaka mashi a baki toh a nan ne nad'an tsorata dan ko da su Alhaji Mannir suka shigo gidan zasu kasheshi ban wani d'aga hankaliba dan na san zamuyi nasara. Katseshi yayi yace a'a Alhaji Mu'azu kayi shuru kar ajiyo ka asirinmu yatonu agane mune muka kasheshi abar maganar kawai zan zo yanzun nan muje inga gidan dan ka san bana wasa da kud'i,,, su dukansu dariya sukayi.... Suna gama saurare yace shin wannan ba muryarka bace Alhaji Sufyan ko itama sharri akayi maka? Fara raba idanu yayi yakalli Alk'ali cikin alamar rashin gaskiya yace ni bansan komai ba akai sharri yake son ja min wallahi. Alk'ali baice komai ba yana dai cigaba da kallonshi sai kuma yad'auko takardun gidan yasake dubawa. Barr Faruk cigaba yayi da cewa sannan akwai lokacin da Alhaji Mansur yakirani muka had'u yagargad'eni akan injaye daga shari'ar Jawahir har yad'auko mak'udan kud'i yabani ammah ban amsaba dan haka ne yasa aka kamani aka rufe a wani gida dan kar inzo inbada sheda a kotu wannan ne dalilin da yasa ban halarci kotu da wuri ba yau dan sai a yau nasamu natsero daga gidan Cikin d'aga murya Alhaji Mansur yace k'arya yake wallahi sharri kawai yake ja min ba ni bane. Kallonshi Faruk yayi yace ina da sheda da zata bayyanar da haka dan lokacin da muka had'u na yi recording d'in duk maganar da mukayi batare da ka saniba, nan yakunno recording d'in yakunna ma Alk'ali sannan yace bayan wannan akwai wata shedar, kallon Barr Nas yayi yace kace sushigo, nan yamik'e yafita duka mutanen cikin kotun juyawa sukayi dan ganin wanda zai shigo, police ne suka shigo da wasu mutane biyar a d'aure , Alhaji Mansur yana ganinsu zabura yayi nan yafara kalle kalle yana neman hanyar gudu yarasa, Barr Faruk kallon Alk'ali yayi yace wad'annan sune mutanen da yasa suka satoni suka tsareni Alk'ali kallonsu yayi yace kufad'a ma kotu tsakaninku ga Allah abinda kuka sani inkukayi k'arya kotu zata hukuntaku. Babban sune yayi k'arfin halin cewa wallahi wad'annan mutanen sune suka kiramu suka bamu kud'i sukace musato Barrister mutsareshi shine suka bamu gidan da muka zauna da shi, wallahi sune suka sa mu. Alk'ali kallonsu Alhaji Mansur yayi da gabad'ayansu idanu sun raina fata yace toh kunji duk shaidar da aka samu akanku ya kamata kufad'a ma kotu gaskiya inko ba hakaba kotu zatasa atambayeku. Shuru sukayi suna mazurai chan alk'ali yad'akko waya yakira ba'a yi minti biyar ba sai ga wasu k'atti su hud'u sun fito kowane d'aya hannunshi rik'e da shar'be'biyar bulala, Alhaji Sufyan yana ganinsu yayi saurin cewa wallahi zan fad'i gaskiya duk abinda yafaru mun aikata tabbas mu takwas ne muka shirya komai shidda daga ciki duk sun mutu, munci dukiyar Alhaji Muhammad sannan duk takardun nan mu mukasa aka had'a mana jabu muka siyar ma da gwamnati filayenshi guda biyu ko Alhaji Mansur? Fashewa da kuka Alhaji Mansur yayi yace tabbas hakane mun aikata kuma sharrin shaid'anne dan Allah munaso kotu ta yafe mana insha Allahu bazamu sake aikata irin haka ba. Alk'ali ajiyar zuciya yasafke yace Alhamdulillah kun amsa laifinku da kanku dan haka kotu zata yanke maku hukunci daidai da yadda shari'a tace, dan haka za'a yi maku hukunci guda biyu na farko dai bayan kun biya wannan baiwar Allahr dukiyarta da kukaci ku da kuke raye zakuyi zaman shekara guda a gidan kaso, na biyu kuma wannafsi binafsi dan haka ya zama dole za'a kasheku kamar yadda kuka kashe wasu. Sannan kotu ta wanke Jawahir muhammad mekud'i daga zargin da akeyi mata dan haka kotu ta saketa zata koma tacigaba da rayuwarta sannan za'a damk'a mata dukkan dukiyarta da wad'annan 'barayin sukaci. Su Alhaji Mansur duk'awa sukayi k'asa suna kuka suna cewa dan Allah Alk'ali ataimaka mana wallahi hukuncin nan ya yi mana tsauri ataimaka a safsafta mana tunda mun amsa laifinmu sannan kud'in da suka rage hannunmu basu kai wanda muka ci mata ba. Girgiza kai Alk'ali yayi yace wannan ne kuma bazai yuwu ba dole ayi maku hukunci daidai da na kowa, kubar ma ta wannan sai kun biyata kud'in da kukaja aka rufeta tsawon shekara guda batare da hak'k'inta ba. Mutanen da ke zaune cikin kotun salati suka farayi suna Allah wadai da halin su Alhaji Mansur. Jawahir da take tsaye tun d'azu inba hawaye ba babu abinda take, hannu tad'aga tafara yi ma Allah godiya sai kuma chan cikin kuka tace tunda dai har gaskiya ta bayyana na ji dad'i bana buk'atar komai daga wajensu subar kud'in na yafe kawai dai akashesu su ma shine zan fi jin dad'i. Alk'ali yace ba maganar yafewa a cikin hukuncin da kotu tazartas ya zama dole subiya wad'annan kud'in, kallon police yayi yace atafi da su subiya kud'in ga list nan na kud'inta da sukaci idan kud'ad'ensu basu isaba kusiyar da duk wata k'addara da suka mallaka. Su kuma wad'annan (yanuna wad'anda suka sace Faruf yace) atafi da su gidan yari zasuyi bauta tsawon shekara guda sannan asakesu, yana fad'in haka yabuga table d'in gabanshi. Nan take aka saka ma su Alhaji Sufyan da Alhaji Mansur ankwa aka fita da su. Nasiba da take tsaye wajen motarta ita da mahaifiyarta suna kuka nan suka nufi wajen da mahaifin nata yake kafin su isa 'yan jarida har sun rufeshi sun fara mashi tambayoyi a matsayinshi na d'an siyasa, kutsawa sukayi suka isa wajen, yana ganinsu yayi saurin sadda kanshi k'asa...... _Sis Nerja'art✍🏻_[7/24, 11:21 PM] Sis Nerja'art 2: *......FANSAR RAI......* *INTELLIGENT WRITER'S ASSO....®* [On Ward Together] _Follow me on Wattpad: *Sis-nerja*_ _Wannan Littafin na kud'i ne domin karantawa cikin aminci da yarda ga duk me buk'ata zai turo katin Mtn na d'ari biyu N200 kacal ta wannan number d'in 09035938246, ko ta account number 5330055604, Idan katura ka aiko da screen shot na transaction a wannan number d'in 09035938246_ _Akwai gara'basar *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shahararriyar marubuciyar nan *AMEENA ABBA UMAR* tare da novel d'in *FANSAR RAI* akan farashin N300 kacal, ko da kud'in ka sai da rabonka_ *PAGE 21* Nasiba cikin sheshek'ar kuka tace Daddy kalli abun kunyar da kajawo mana yanzu hakan da kayi daidai ne? Kaduba kaga halin da kajefa kanka da mu a ciki a idanun duniya, meyasa kabi son zuciya ka aikata hakan? Ba ka tunanin yadda rayuwarmu zata kasance, taya kake tunanin laifin nan da ka aikata zai goge a idanun mutane? Ya kakeso muyi da rashin ka? Meyasa haka Daddy, meyasa?,,, kukan da yaci k'arfinta ne yasa tayi saurin juyawa, har lokacin kan Alhaji Sufyan yana sadde a k'asa ji yake kamar a mafarki abin yafaru hawaye ne suka fara fita daga idanunshi, muryar matarshi yaji cikin muryar kuka tana cewa Alhaji ban ta'ba tunanin haka daga garekaba wallahi ka ban kunya ka zubar mana mutunci da k'ima daga ni har 'ya'yanka tirr da wannan halin naka, daman Nasiba ta fad'a min akwai abinda yake faruwa a kotu muzo mugane ma idanunmu ashe daman abinda zamuzo mugani kenan? Meyasa haka Alhaji!,, Nasiba ce tajuyo cikin sauri tarungume mahaifiyartata sai a lokacin yad'ago kai yakalleta. Police tisashi sukayi a gaba aka wuce da shi dan dama tuni antafi da Alhaji Mansur mota, 'yan jaridar da suke ta mashi tambayoyi bai samu ya amsa ma kowaba saboda halin nadama da yashiga. Suna jin tashin motar nan su Nasiba suka k'ara sautin kukan da suke dan sunsan tabbas a yanzu ya yi masu nisa daga rayuwarsu. Ana gama shari'ar Barr MB ne farkon wanda yafara mik'ewa yaba Barr Faruk hannu suka gaisa sannan yatayashi murna, Barr Junaid ko dasauri yazo yarungume abokin nashi yana cewa Faruk ka dawo, nagode ma Allah da mutanen nan basu samu damar cutar da kai ba, muna ta wahalar nemanka ashe kana hannun azzaluman chan. Murmushi Faruk yayi yace Junaid kaidai ko, Sai a lokacin yajuya yakalli inda jawahir take tsaye tana kuka har ya taka zai tafi sai ji yayi anrungumoshi tare da fashewa da kuka, dubawar da zaiyi sai ganin mahaifiyarshi yayi cikin sauri yarungumeta yace Mom d'ina. Cikin kuka tace nagode ma Allah da yamaido man kai Faruk wallahi na shiga damuwa sosai akan rashinka ashe zan sake sakaka a cikin idanuna, mutanen chan sun zalunceni ban yafe masuba da suka rabani da kai, ina sonka sosai d'a na. K'ara rungumeta yayi jikinshi cike da jin tausayin mahaifiyartashi yace nima haka mummyna ina k'aunarki sosai, a yanzu babu wanda zai sake rabamu muna tare. Dad da ya iso a lokacin dafashi yayi yace d'ana Faruk, k'wallah ce tacika mashi idanu yace ashe zamu sake ganinka nagode ma Allah da basu rabani da kai ba. 'Dan guntun murmushi yayi yace Daddyna nima ina farin cikin sake ganinku. Farin ciki suka dinga yi sosai a wajen duk wani me k'aunar Barr Faruk saida yazo yatashi murna duk da haka hankalinshi yana wajen jawahir samu yayi yajanye Mom daga jikinshi yace yana zuwa nan yanufi inda take, yana zuwa yabud'e baki zaiyi magana sai tarigashi tace nagode sosai Faruk da namijin k'ok'arin da kayi akaina tabbas ka cika mutumin kirki ka taimakeni a daidai lokacin da nake buk'atar taimako ka wankeni daga zargi a idanun jama'a, koda akaina ka fuskanci matsalar rayuwa ammah hakan bai sa kabarni ba nagode, nagode, nagode sosai Faruk. Cike da jin tausayinta yace jawahir kidaina cewa haka domin wannan ba komai bane kin cancanci hakan ko ma ba keba hak'k'inane intaimaka ma duk wani wanda yake buk'atar taimako irin wannan hatta rayuwata zan iya bayarwa akan aikina. Da mamaki take kallonshi cikin ranta tana jinjina ma k'wazo irin na Faruk da son taimakonshi, wasu sabbin hawayen ne suka gangaro mata tace ina ma ace Ammina tana raye taga irin wannan ranar, ina ma ace zanga irin farin cikin da zata shiga, ina ma ace Yaya Umar yana raye,,,, kukan da yaci k'arfinta ne yasa tayi saurin juya mashi baya. Faruk har ya bud'e baki zaiyi magana sai ganin Nasiba yayi gabanshi tsaye tana kuka, idanu yazuba mata ganin yadda take kuka bilhak'k'i, cikin sheshek'ar kuka tace Faruk dan Allah kayi hak'uri da abinda yafaru tabbas na yi kuskure da nakasa fahimtarka, mahaifina baiyi mana adalciba dan duk shine yajefamu a cikin wannan halin nayi nadamar kasancewarshi a matsayin uba agareni dan bai cancanci hakan ba, Allah wadai da mahaifi me hali irin nashi. Tarar numfashinta yayi yace a'a Nasiba kidaina cewa haka ko ba komai shi ubane. K'ok'arin rage sautin kukanta tayi sannan tace tabbas shi ubane ammah ba irin uban da yadace ayi alfahari da shi ba domin ya 'bata mana suna a idanun duniya wallahi na yi nadamar rayuwata ina ma ace inmutu inhuta da wannan rayuwar Faruk ban ta'ba tunanin haka daga mahaifina ba ashe daman shine yasaceka, hannuwanta tahad'e waje guda tace dan Allah Faruk kar kakamani da laifin da bani na aikata ba, tabbas nayi maka mummunan fahimta a lokacin da kaso kafahimtar da ni komai saidai duk hakan daman ubangiji ya k'addara hakan zai faru dan Allah kayafe min ba dan halina ba. Wani irin tausayinta ne yaji ya d'arsu a cikin ranshi yace Nasiba wallahi bakiyi min komai ba inma kinyi na yafe maki dan baki cancanci inrik'eki acikin raina akan wani laifi da ba nakiba. Fashewa tayi da kuka tace nagode sosai Faruk nagode, sai a lokacin tajuya inda jawahir take tsaye ta juya baya matsawa tayi tatsaya gabanta tace na tabbata kowanene akayi ma irin abinda akayi maki sai ya ji ba dad'i a ranshi dan an zalunceki anci amanarki dan Allah ina neman afuwarki akan abinda mahaifina ya aikata maki. 'Dago kai jawahir tayi tana kallonta. Ganin haka yasa Nasiba tace ba wai ina neman afuwa bane akan asaki mahaifina saidai ina neman afuwa akan kasancewata 'yarshi mukaci da hak'k'inki dan Allah kiyafe min. 'Daga mata kai kawai Jawahir tayi batare da tayi magana ba. Nasiba kallon Faruk tayi tace dan Allah Faruk kar wannan abun da yafaru yasa kabarni dan Allah kar kakalleni da halin mahaifina inaso kacigaba da kasancewa tare da ni. Juyawa yayi yakalli iyayenshi da aketa tayawa murnar dawowar d'ansu sannan yace Nasiba yanzu ba lokacin wannan maganar bace, kallon jawahir yayi yace muje kugaisa da iyayena. Bata musaba tajuyo tabi bayanshi suka tafi suka bar Nasiba nan tsaye tana kuka, daidai lokacin mahaifiyarta tazo nan tafad'a jikinta tana cewa Mummy na rasa Faruk ya daina sona, meyasa? Girgiza kai Hajiya Maijidda tayi tace a'a Nasiba kizo muje gida kawai. Haka tabi mahaifiyartata suka tafi. Faruk nuna ma iyayenshi Jawahir yayi nan suka gaisa suka yi mata jaje sannan suka tayata murnar ku'butar da tayi daga gidan kaso. Mom dai tana manne da d'an nata chan tace Faruk wai ya akayi kaku'buta daga hannun wad'anchan azzaluman? Murmushi yayi yace Mom muje gida sai insanar da ku komai. Dad ne yace Alhamdulillah kinga zuwan da mukayi kotu ya yi amfani daman raina ya bani zamu ga Faruk saisa nace maki muzo, yanzu kuzo muje gidan. Gabad'ayansu suka d'unguma suka nufi gida dan da fari har Jawahir ta k'i binsu ta ce ita dai subarta a nan zata tafi gidansu saidai Dad yace shin mu ba iyayenki bane Jawahir? Ko bakomai nima matsayin uba nake a wajenki saboda matsayin mahaifinki a wajena. Da mamaki suke kallonshi tace daman ka san Abbu? Murmushi yayi yace sosai ma muje gida zan sanar da ke inda nasanshi, bata musaba sannan tabisu suka nufi gidansu Faruk gabad'ayansu har da su Barr Nas da Barr Junaid. Suna zuwa Mom d'akinta taja Jawahir tahad'a mata ruwan wanka tayi bayan ta fito tad'akko mata wata jallabiya tabata tasaka saida sukayi sallah sannan suka fito parlor Jawahir dai ta kasa sakin jiki dan ita rayuwarta ba mai saurin yadda da mutane bace tunda tataso haka take, suna nan zaune su Dad da su Faruk suka fito kusan lokaci guda bayan sun dawo daga masallaci, koda suka zauna Dad cewa yayi afara kawo abinci aci kafin afara wata magana dan haka Mom taje tasanar da masu aiki, nan da nan aka fara shigo masu da abinci iri iri kowa yafara serving d'in kanshi ammah banda jawahir ganin ta k'i sakin jiki yasa mom ta d'ibi abincin tajata sukaje d'akinta tace Jawahir kisaki jikinki nan ma gidane kiyi abinda kikeso mu bamuda matsala kinji. Murmushi tayi tace nagode Mom. Duk yadda Mom taso taci abincin k'i tayi dak'yar tad'anci kad'an tabarshi dan haka tak'yaleta. Bayan kowa ya kimtsa cikinshi suka had'u a parlor. Dad ne yafara cewa toh Alhamdllh a yanzu sai kasanar da mu yadda akayi kaku'buta. Faruk murmushi yayi sannan yakwashe yadda akayi aka saceshi yafad'a masu da yadda yadinga shan wahala a wajensu har zuwa shigowar d'an uwan nasu da takeaway yakawo ma sauran. Su duka idanu suka zuba mashi suna kallonshi cike da mamaki dan Mom ko hawaye tafara ganin haka yasa Faruk yacigaba da cewa "duk a tunanina wannan me dariyar ya tafi jin shurun da yayi sai chan naga bayyanar wata tsohuwa a gabana dudduk'e tafiyarta dakyar dakyar " kallon jawahir yayi yace ke dai na san kin gane ko wacece, d'aga kai tayi alamun Eh, cigaba yayi da cewa tana bayyana kallona tatsaya yi sai chan tace Barrister daman ban fad'a maka ba nice kad'ai nake da ikon taimaka ma Jawahir? Wani irin kallo nayi mata cikin nuna rashin tsoro nace taimako na ubangiji ne shikad'ai yake iya taimaka ma bawansa. Bushewa tayi da dariya tace bazanyi maka jayayya ba saidai ina farin ciki guda a yau Jawahir ta yi nadamar da dadad'ewa nake jira tayita ammah saboda taurin kanta batayiba a yanzun ma abun bak'in cikin ta yi ne ba dan komai ba sai dan tana neman intaimaka maka. Kallonta faruk yadinga yi cikin nuna rashin fahimtar maganarta. 'Dan dogaro sandarta tayi tamatso kusa da shi sannan tacigaba da cewa a lokacin da za'a fito da su akaisu kotu hankalinta a tashe yake ganin haka yasa nabayyana a gareta natambayeta ko tana buk'atar taimakona? Girgiza kai tayi tace bana buk'atar taimakonki. Bushewa da dariya tsohuwar tayi tace cikin ke da Faruk dole sai wani ya riga wani shek'awa lahira. A rikice jawahir tace ban fahimta ba me zai faru da faruk d'in? Sake bushewa tayi da dariya saida tayi me isarta sannan tace zasu kasheshi a bayan an yanke maki hukunci a kotu saboda kar susakeshi yatona masu asiri. Fashewa Jawahir tayi da kuka cikin sauri taduk'a k'asa tace Ammi na rok'eki dan Allah kitaimakeshi kar kibari sukasheshi bai cancanci hakan ba. Girgiza kai tayi tace bakida ikon neman taimakona batare da yin nadama ba. 'Dago kai tayi fuska sha'be sha'be da hawaye tace indai har akan Faruk ne na amince saida taruntse idanunta cike da takaici sannan tace na yi nadamar kalmar da nafad'a maki kiyi hak'uri insha Allahu bazan sakeba, ina sonki Ammina....dariyar da taji ana kyalkyalawane yasa tayi saurin bud'e idanunta dan gabad'aya d'akin yake amsaba dubawa tayi taga babu Ammin tata saidai muryar dariyar taji tana fita, tana nan duk'e a haka akazo aka fita da su aka tafi da su kotu. Tana kawowa nan a bayanin nata tanuna inda Faruk yake zaune da sandarta sai gani yayi d'aurin da akayi mashi ya kwance, cikin muryarta me ban tsoro tace zaka iya fita ga k'ofa chan a bud'e nan da minti takwas zata iya rufe kanta, jin haka yasa Faruk yayi saurin mik'ewa duk sai yajishi wani iri dakyar yafara takawa dan a lokacin matar har ta 'bace, bin gidan yadinga yi da kallo bai san inda yakeba da karambani yagano k'ofa yana fita k'ofar tana maida kanta tadatse tsayawa yayi yak'are ma gidan kallo saida yagane anguwar sannan yasamu abun hawa yahau yanufi gidan Barr Nas, ya yi sa'a ya sameshi a gida nan yayi ta murnar dawowarshi wanka yayi yashirya cikin sauri, sannan yace ma Nasir yad'auko mashi ajiyar da yakawo mashi ranar da za'a kamashi dan dama jikinshi ne yadinga bashi kamar akwai abinda zai iya faruwa da shi wannan dalilin ne yasa yad'auki dukkan shedun da yatara yakai ma Barr Nas ya ajiye mashi wajenshi hatta wayarshi da yafi amfani da ita saida yakashe yabashi dan ya san a cikinta ya ajiye abubuwa dadama masu muhimmanci,daga nan suka fito cikin sauri suka nufi kotu dan a lokacin sun makara dan sunsan dole cikin biyu ayi d'aya ko angama shari'ar Jawahir ko kuma ana cikin yi....yana kawowa nan a labarin yace wannan shine abinda yafaru da ni. Hankalinsu gabad'aya saida yatashi sosai Dad yace tabbas Alhaji Sufyan ya kasance maha'inci ban ta'ba tunanin haka daga gareshiba ace da sa hannunshi aka sace min d'a duk kusancin da ke tsakaninmu ina mashi kallon abokina na k'warai ashe ba haka ba. Jawahir sai a lokacin tad'ago takalleshi tace ya akayi kasamo Ummah katafo da ita? Murmushi yayi yace lokacin da naje asibitin naga halin da take ciki nan nanemi taimakon likitocin suka taimaka suka ban ita nacanza mata asibiti inda zata fi samun kulawa dan asibitin da su Alhaji Mansur suka kaita wata k'aramar asibiti ce wadda basuda wadatattun kayan aiki kuma sunyi hakane dan kawai suna so tamutu itama, toh cikin ikon Allah ina maidata chan suka dinga bata kulawa sosai har tafara samun sauk'i, dan tana iya motsa 'bare d'aya na jikinta saisa ma nace atafo da ita tunda tana magana. Shi kuma megadinku buzu wannan aikinki ne dan kece kika samar mana taimako Amminki tasanar da mu inda yake. Jinjina kai su Dad suka dinga yi mamaki duk ya cikasu. Barr Junaid yace lallai sharrin su Alhaji Mansur ya fi tunanin duk wani me tunani ashe duk wannan k'ulla k'ullan su sukayi shi sukaja aka kama baiwar Allahr nan. Dad girgiza kai yayi yace wasu mutanen macen zuciya garesu babu abinda sukasa gaba sai son kansu, kallon jawahir yayi yace tabbas na san mahaifinki dan abokin kasuwancina ne a lokacin da yake raye kamfanina da nashi kusan tare suke tafiya dan ma baza'a had'a ba nashi kamfanin ya fi nawa d'aukaka saboda wasu kayan ya fini saidai shi ba mutum bane me bak'in ciki yana son cigaban mutane nan yasa muka had'a hannu tsakanin kamfanina da nashi muna shigo da kaya tare wani lokacin idan kamfaninshi yana buk'atar rancen kud'i a nawa kamfanin yake zuwa yana ranta nima haka akan wannan ne yasa muka k'ulla abota sosai akan kasuwancinmu dan kowa yana son cigaban d'an uwanshi bamufi wata takwas a haka ba nanemi rancen wasu kud'i saboda wasu kayan aikin injin da nakeso inje Dubai insiyo yad'auki kud'in yabani, koda naje Dubai saida nayi kusan wata ukku sannan nasamu yadda nakeso naturo da kayan ni ban dawoba a wata na biyar ne naturo mashi da kud'inshi daga chan saidai 1 million da tarage ban bashiba, ak'alla saida nayi wata goma sannan nadawo k'asar nan bayan na dawo ne nasamu labarin rasuwarshi nan hankalina yatashi sosai haka nad'auko million d'aya d'in nan naje gidanshi nayi sallama nasa aka kira man matarshi koda tafito nayi mata gaisuwa sannan nabata cheque d'in kud'in, tun bayan rasuwarshi na so mucigaba da kasuwanci tsakanin kamfanina da nashi ammah d'an uwanshi yak'i dan haka nabarshi lokaci guda kamfanin yadaina kawo kud'i yadda yakamata nawa yazo yafi shahara, a haka nak'ara nema muhad'a hannu da Alhaji Mu'azu mumaido ma kamfanin tattalin arzik'inshi ammah yak'i dan gani yake kamar wani cutarshi nakeson yi wannan dalilin ne yasa nafita harkar kamfanin. Jawahir fashewa tayi da kuka tace tabbas kaine Alhaji Sanin da yazo gida yakawo ma Ammina cheque akan kud'in ne aka nemi a salwantar da rayuwarta Su duka kallonta suke cike da mamaki Barr Nas yace kamar ya? Kwashe komai tayi tasanar da su akan mutuwar Amminta nan duk jikinsu yayi sanyi sukayi ma iyayen nata addu'a. Mom ce tarungumota jikinta tana lallashinta dakyar aka samu tayi shuru sannan Dad yace Jawahir kikwantar da hankalinki mu zamu zauna da ke zamu kula da ke duk abinda kikeso zamuyi maki kid'aukemu a matsayin iyayenki. 'Dago kai tayi takalleshi tayi murmushi tace nagode sosai Dad da wannan karamcin da kukayi min saidai ina so inkoma wajen dangin mahaifiyata zan je incigaba da rayuwata da su tunda suna raye, bazan iya cigaba da zama cikin garin nan ba. Haba Jawahir mu ma fa zamu zauna da ke tsakani ga Allah bazamu ta'ba cutar da ke ba,,, cewar Faruk Girgiza kai tayi tace a'a Faruk su ma suna buk'atata na sani kawai dai halin Abba ne yasa suka daina zuwa garin nan, na san ku d'in mutanen kirki ne saidai zamana a nan bazai yuwu ba. Dad yace shikenan Jawahir mun fahimceki ammah kibari kikwana biyu a nan sannan kitafi. Kallon agogo tayi tace a yau nakeson tafiya. Faruk ne yayi saurin cewa a'a ba yau ba please kid'an mana kwana biyu kamar yadda Dad yace. Shuru tayi batace komai ba. Sallamar mutane da suka jiyo ne yasa gabad'aya suka tashi suka fita suka bar Mom da Jawahir a nan Mom tana k'ara lallashinta. Mutane ne dayawa sukayo gungu guda sukazo tayasu murnar dawowar Faruk, a setting room d'in Dad suka zauna. Nan da nan gida yafara cika har mata suka dinga zuwa, Jawahir tashi tayi takoma part d'in Mom tana zuwa takwanta nan da nan tafara baccin gajiya. A ranar gidan Alhaji Mansur da Alhaji Sufyan akaje aka tattara duk dukiyoyinsu da duk abinda suka mallaka hatta gidajensu. Su Nasiba ba k'aramin tashin hankali suka shiga ba sunyi kuka sosai dan gidan da suke ciki ma amsheshi akayi akace za'a maida ma jawahir abunta dan haka suka koma wani madaidaicin gida na mahaifiyarta, yayyenta biyu masu aure saida sukazo suka ci kukansu har suka gode ma Allah, a gidajen sada labarai aka dinga yayata abinda yafaru hatta gidajen talabijin saida aka dinga nuna su Alhaji Sufyan ana fad'in abinda sukayi wannan abun ya yi ma iyalansu ciwo sosai. A ranar aka had'a duk abinda suka mallaka aka fidda ma jawahir hak'ik'k'inta sauran dukiyar kuma aka damk'ata ga iyalansu. Da dare aka kira Faruk aka sanar da shi dan washe gari yaje da jawahir adamk'a mata dukiyarta ya amsa da toh. Mom nan nan take ta yi da Jawahir ammah ita ko ta k'i sakewa da ita magana ma sai tadaina yi masu dan tunda tatashi daga bacci tacanza koda Faruk yaga yanayinta yace subarta kawai wannan ba ita bace dan haka aka k'yaleta ita kad'ai tak'unshe kanta a d'akin Mom, abinci ma akayi akayi da ita taci ammah tak'i yadda aka ajiye mata haka akazo aka d'auka. Ganin haka yasa Faruk yafara tunanin yadda zaiyi yarabata da Aljanar nan. Washe gari koda suka tashi nemanta akayi aka rasa a cikin gidan nan hankalinsu yatashi sosai dan ba'a san lokacin da tabar gidan ba, wajen k'arfe goma Malam Nasir (Kakan Faruk) ya iso garin nan yasamesu suna shirin fita nemanta yace sudawo suzauna, bayan sun zauna an gaisa ne yakalli Alhaji Sani yace Faruk ya shaida min komai ta waya wannan dalilin ne yasa nazo dan intaimaka ma yarinyar na san saboda haka ne yasa tabar gidan dan tabbas aljanarta zata san komai akai, jiya ban samu naruntsa ba ina ta aiki akan yadda zan tunkareta kuma Alhamdulillah ina tunanin zamuyi nasara. Su dukansu amsawa sukayi da masha Allah, Allah Ubangiji dai yasa adace, Dad yace ammah Malam ba a nan gizo yake sak'a ba ai ba'a san inda yarinyar take ba yanzu. Jim Malam yayi sai chan yace tana da sauran dangi a garin nan? Faruk yace a'a. Tunani yafara yi sai chan yace toh gidansu fa akwai wani a ciki? Nan ma Faruk yace a'a. Jin haka yasa Malam yace tabbas babu inda zataje sai gidansu a chan ne kad'ai aljanar zata kaita tunda babu kowa a gidan, kallon Faruk yayi yace yi sauri katashi muje chan gidan nasu, kad'auko min wacchan ledar da nazo da ita. Cikin sauri suka tashi suka fita a cikin motar Faruk suka shiga har da Dad suka tafi aka bar Mom a gida. Gudu Faruk yadinga yi da motar har suka isa gidan suna zuwa suka tarar da gate d'in a bud'e dan haka a gaban gidan sukayi parking d'in motarsu suka fito Faruk yace nan ne gidan mushiga, har ya wuce zai shiga malam yayi saurin rik'oshi yace a'a kar kushiga kujira, nan suka ja suka tsaya, addu'a yayi sannan yace sushiga suna shiga filin gidan itacene suke ta kad'awa ga ganyaye a k'asa duk sun bushe, su dukansu bakinsu d'auke da addu'a suka nufi hanyar da zata sadaka da cikin gidan suna shiga tsakar gidan wata irin k'ara sukaji me had'e da iska, nan suka ja suka tsaya kallon d'akunan sukayi sukaga kowane rufe yake, dariya ce sukaji ta fara tashi a d'aya daga cikin d'akunan dan haka cikin sauri suka nufi d'akin kafin su isa k'ofar d'akin ta bud'e kanta sai duhu sukaga ya bayyana a ciki, malam ne yace masu kowa yacigaba da addu'a kar yadaina dan haka suka nufi d'akin, Faruk wayarshi yad'auko yakunna touch sannan suka shiga, a k'arshen bango suka ganta tsaye bisa iska k'afafuwanta sun nannad'e gashin kan nan ya mik'e tsaye ga bakin nan na jirkice, idanuwanta k'ara fitowa sukayi waje k'wayar kamar ba zaune take a cikin idanun ba, gabad'aya halittarta ta canza, kallonta suka tsaya suna yi cike da mamaki, Faruk ne yayi k'arfin halin cewa Jawahir ya akayi kikazo nan? Wata irin murya sukaji me kama da gurnanin zaki ana cewa taya zan zauna bayan kunaso kurabani da rayuwata bazan ta'ba barin duk wanda yaso yarabani da duniyarnan ba. Malam nuni yayi ma Faruk alamun yayi shuru sannan shi yace ya zama dole kirabu da yarinyar nan kidaina wahalar da ita hakanan. Bushewa tayi da dariya tare da matsowa bisa iska har lokacin bata safka k'asa ba tace hakan ba zai ta'ba yuwuwa ba babu wanda zai rabani da d'iyata ko wanene yaso haka sai na ga bayanshi. Malam na jin haka ya amshi ledar da take hannun Faruk yabud'e yad'auko wata roba k'arama wadda take d'auke da wani ruwa a ciki, sannan yad'auko wata leda me d'auke da wani farin abu kamar gari, bud'e ledar yayi yad'ebo farin abun yayi bismillah yawatsa mata, wata irin k'ara tasaki sai gata ta fad'o tim k'asa, hasken d'akin ya dawo. cikin sauri yabud'e robar yawatsa mata ruwan, nan tasake sakin wata k'ara me k'arfi wadda tasa saida suka toshe kunnuwansu saboda kar k'arar ta lahanta masu dodon kunne, cikin k'araji tace kar kakuskura kasake watsa min ruwan nan banaso kadaina, wanene kai???? Malam kallonsu Faruk da Dad yayi yace kuje kurik'e man ita, su duka suka nufi wajen da take kafin su isa hannu tad'aga tanunasu sai gasu kamar anyi wurgi da su su biyun sun fad'a chan gefe. Ganin haka yasa malam yafara karanta ayoyin Allah dak'arfi sannan yafara zagaye d'akin yana d'ibar ruwan yana watsawa nan tadinga ihu tare da yunk'urin ja da baya, Faruk ne yafara mik'ewa dakyar yanufi inda take malam wurgo mashi garin maganin yayi yace yawatsa mata a saman kanta nan ya amsa ya watsa mata tasake sakin wata k'arar sannan tasulale k'asa asume, ganin haka yasa malam yai saurin isa wajenta yace ma Faruk yabud'e mashi bakinta, nan yafara k'ok'arin bud'ewa dak'yar yasamu yabud'e mata nan Malam yazuba mata ruwan maganin a ciki, yagoga mata na garin a fuska, bud'e idanunta tayi tare da k'wala k'ara tature Faruk da ke rik'e da ita nan tabank'are jikinta tare da bud'e bakinta gabad'aya nan wani irin farin hayak'i ne yadinga fita daga bakin, idanuwanta duk sukayo waje, hayak'in yana gama fita kallonsu tayi d'aya bayan d'aya sai kuma tamaida idanunta tarufe tadaina ko da motsi. Faruk yace Malam me yafaru da ita bata motsi ko ta suma? Malam da yake kallonta girgiza kai yayi sannan yakalli su Faruk yace ba suma tayi ba tana raye bazata ta'ba tashiba har sai anyi abu d'aya. Cikin rashin fahimtar maganarshi sukace bamu ganeba Malam Jinjina kai yayi yace tabbas layar da aka sa ma gawar ne a kusa da iccen suri aljannun da suke cikin iccen ne suka tado fatalwarta kuma tana rayuwa ne a cikin hak'ark'arin jawahir wannan dalilin ne yasa take amfani da jikinta da ruhinta, sannan wannan fitar da tayi zata iya dawowa nan da 'yan awanni kad'an idan har ba'ayi saurin zuwa k'abarinta aka tono wannan layar ba dan a yanzu haka layar tana nan cikin k'abarin da antone aka k'one shikenan fatalwar zata koma bazata sake bayyanaba. Saurin mik'ewa Faruk yayi yace ni zan je intone k'abarin kujirani bari inje ind'auko megadinsu yarakani mak'abartar. Malam yace toh kutafi da ashana da kun tono ku k'oneta kar kubaro wajen baku k'onetaba Faruk ya amsa da toh nan yawuce cikin sauri yatafi..... _Sis Nerja'art✍🏻_ [7/24, 11:21 PM] Sis Nerja'art 2: *......FANSAR RAI......* *INTELLIGENT WRITER'S ASSO....®* [On Ward Together] _Follow me on Wattpad: *Sis-nerja*_ _Wannan Littafin na kud'i ne domin karantawa cikin aminci da yarda ga duk me buk'ata zai turo katin Mtn na d'ari biyu N200 kacal ta wannan number d'in 09035938246, ko ta account number 5330055604, Idan katura ka aiko da screen shot na transaction a wannan number d'in 09035938246_ _Akwai gara'basar *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shahararriyar marubuciyar nan *AMEENA ABBA UMAR* tare da novel d'in *FANSAR RAI* akan farashin N300 kacal, ko da kud'in ka sai da rabonka_ *PAGE 22* Yana barin gidan chan gidan da yasafke buzu megadi lokacin da yad'akkoshi daga Marad'i dan yazo yabada sheda yawuce ya yi sa'a daidai lokacin yafito daga cikin gidan, ganin motar Faruk yasa yanufo wajen cikin hausar shi da bata fita sosai yace hannu da zuwa Alhaji hannu. Murmushi Faruk yayi yace yauwa buzu megadi ashe na yi sa'a da fita ma zakayi. Washe baki yayi yace eh na d'an fitone zanga gari kafin gobe inkoma garinmu. Allah sarki, yanzu shigo mota inmaka wata tambaya. Bai musaba yabud'e motar yashiga yace toh Alhaji ai dun yanda kashe haka za'ayi. Yanayin maganarshi tana ba Faruk dariya har saida yayi murmushi sannan yace yauwa tambayar da zanyi maka itace: dan Allah kana iya tuna mak'abartar da aka binne Hajiya Khausar bayan ta rasu? Yatsa yasa yadafe kanshi irin yana tunanin nan sai chan yace Eh aradu har k'abarinta na sani kusa da wani iccen giginyane akwai tudu a wajen ban mancewa har lokacin nayi tuntu'be a wajen nafad'i bayan mun rufota har yanzu akwai tabon gurjewar da nayi a gwiwata bari ma kaganshi. A'a kabarshi ba sai na ganiba yanzu fad'a min mak'abartar muje dan inason ganin k'abarinta. Angama oga nan yafad'a mashi Faruk yaja motar dagudu yanufi anguwar da mak'abartar take suna zuwa suka samu waje daga chan k'etare sukayi parking d'in motarsu suka tsallako, megadin mak'abartar suka samu suka gaisa nan Faruk yafayyace mashi komai akan abinda yakawoshi, da fari megadin be yarda ba dan ya yi tunani wani abu sukeson yi ne kawai. Ganin haka yasa Faruk yace na san baka yarda da maganataba saboda duniyar nan ta yanzu ta 'baci matsafa sunyi yawa suna amfani da wani sashe na jikin gawa suna tsafi da shi, wallahi ni ba wannan yakawoni ba idan baka yarda ba muje tare ayi komai a gabanka. Jin haka yasa megadin ya amince suka je tare buzu megadi tsaye yayi yana tunanin inda zai gane k'abarin saboda tsawon shekaru ukku kenan da binneta, gefe gefen mak'abarta yafara bi dan ya san tabbas daga gefe yake, megadi ganin haka yasa yace da hak'ura kukayi dan kusan shekara ukku ai babu abinda zaku samu saboda bayan ita mutum dubu nawa aka binne a wajen. Jikin Faruk sanyi yayi dan ya san gaskiya megadi yafad'a. Daidai wani iccen giginya dake kusa da wani d'an rami buzu megadi yatsaya yace alk'ur'an nan ne wajen ga ma k'abarin nan kusa da giginyar nan. Megadin mak'abartar ne yace ka tabbata nan ne dan gaskiya an kwana biyu ba'a binne mutane a wajen ba dan duk gawar da aka binne saidai washe gari azo atadda k'abarin a bud'e ko ansake rufewa haka yake faruwa wannan dalilin ne yasa gabad'aya aka daina binne gawa a wajen. Sake kallon wajen yayi yace wallahi nan ne ban manceba. Jin haka yasa Faruk yace tunda ya tabbata da nan d'inne toh mutone wajen mugani ta yuwu aga gawar. Megadin mak'abartar amincewa yayi nan suka duk'a suka fara tonen k'abarin babu komai a cikinshi sai k'asa haka sukaita tonawa daga k'arshe ma sai farin yashi suka fara gani, ganin haka yasa Faruk yaduk'a yasaka hannunshi yafara lalubawa cikin yashin yana cewa indai har wajen nan ne toh tabbas zamuga layar, cigaba yayi da lalube ganin baiji komai yasa yasa suka cigaba da tone ramin har said sukayi mashi zurfi sosai sannan suka kwashe k'asar ciki, suna cikin kwasar k'asar ne buzu megadi yakwaso da wani abu bak'i nan yanuna ma su faruk. Me gadin mak'abarta ne yad'auko abun yana dubawa nannad'e yake da zare yace to menene wannan ko dai layar ce? Buzu yace anya kuwa ai laya ba bak'a bace. Wurgi yayi da shi yace wani dai abun ne daban kunga ahak'ura kawai k'ila ma ba nan bane tunda kusan shekara ukku ai ya isa amance. Faruk ne yayi saurin zuwa yad'auko abun yace tabbas raina ya bani wannan ce layar bakuga an nad'e da zare ba, bari inbud'a muga abinda yake ciki, nan yafara warware zaren saida yawarware tas yaga da fata aka had'a an d'inketa nan suka warware d'inkin sai ga wani siririn gashi guda d'aya a ciki, cire gashin sukayi suka bud'e layar nan wani bak'in hayak'i yafito daga ciki, sunan Khausar ne tun daga sama har k'asan layar, faruk yace kungani ko wallahi itace aljihunshi yafara lalube zai d'auko ashana nan sukaga wata irin isaka ta taso me k'arfi wadda tasa gabad'aya iccinan da suke cikin mak'abartar suka fara kad'awa su kansu iskar saida taso tayi masu yawa. Faruk saurin fiddo ashanar yayi yafara kyastawa saidai saboda iska da ya kyasta sai tamutu, saida yakyasta ashana kusan guda goma tana mutuwa ganin haka yasa megadi yace saidai muhad'e waje guda mukare yadda iska bazata shigaba da wannan shawarar sukayi amfani nan suka had'e wata irin k'ara suka dinga ji tana tashi a wajen ahaka suka kyasta ashanar, muryace suka juyo ana cewa kar kak'ona kabari zan tafi bazan sake dawowa ba kabarni ina gargad'inka kar kak'onata!!! Saurin cinna wutar yayi a jikin layar tafara ci, k'abarin khausar saida yad'an girgiza nan wani bak'in hayak'i yafito daga ciki, layar na kusa cinyewa a hannunshi yayardata a k'asa daidai lokacin iskar da take wajen tadaina kad'awa komai yatsaya chak, jinjina kai megadin mak'abarta yayi yace lallai Annabi ya yi gaskiya tsafi gaskiya ne yana kama mutum yanzu daman da abinda aka k'ulla ma wannan baiwar Allah saisa tun bayan ita babu wanda aka sake rufewa a cikin k'abarin nan dan ko anrufe mutum wahala za'asha sai ma ancanza mashi waje. Buzu megadi yace wallahi da gaskiyarka haka abun yake, kallon faruk yayi yace yanzu shikenan bazata sake kashe kowaba Jawahir ta dawo daidai Hamdala faruk yayi nan suka maida k'asar ramin suka rufe sannan suka wuce godiya sukayi ma megadi sosai sannan suka tafi. Biyawa yayi yasafke buzu megadi gidan da yake nan yatambayeshi gobe da k'arfe nawa zai wuce yace da asuba, kud'i yafiddo sosai yabashi yace yayi kud'in mota da tsaraba nan buzu yayi ta mashi godiya har da fita daga cikin mota yaduk'a yana godiya. Faruk yace bakomai shine da godiya da yayarda yabiyoshi suka zo katsina. A chan 'bangaren Jawahir Malam addu'o'i kawai yake yi mata, har a lokacin bata motsi sai wata irin zufa da take kwarara daga fuskarta jikinta zafi yayi sosai kamar me zazza'bi dan hucin zafin har su suna jinshi, daidai lokacin da Faruk ya k'ona layar taja dogon numfashi nan tafara atishawa, saida tayi ta fi goma. Dawowar Faruk gidan ne tafarka tatashi zaune tana binsu da kallo daga k'arshe tasafke idanunta akan faruk da yashigo a daidai lokacin ahankali tabud'e baki tace me yake faruwa da ni? Kun rabani da Ammina ko? A'a Jawahir ba rabaki mukayi da ita ba. 'Dan guntun murmushi ne tayi sannan tamik'e dak'yar tafito tsakar gidan duk su ma suka fito, wani part ne taje tabud'e tashiga taja tatsaya a tsakiyar parlorn lokaci guda tafara hawaye tajuyo takalli Faruk tace nan shine part d'inmu ni da Yaya Umar d'ina a nan muke rayuwarmu ammah Ammi tazo tarabamu wannan dalilin ne yasa nakasa cigaba da sonta, na sani kun rabani da ita bazan ta'ba damuwaba, kallonta tamaida ga Malam tace nagode sosai Malam. Faruk cikin sanyin jiki yace Jawahir kakana ne wannan. Murmushi tayi ahankali tasake cewa nagode. Saurin goge hawayen da suke kwarara a fuskarta tayi sannan tafito daga d'akin tace ya kamata inje Kebbi inason ganin dangina wad'anda su kad'ai suka rage min dangi a duniya. Dad yace a'a jawahir kibari sai kin samu sauk'i sannan kitafi, mu zamu rakaki wajen danginki. Malam yace tabbas hakan yakamata dan nima kaina akwai wasu magunguna da zan d'aurata akansu na tsawon kwana biyu. Faruk yace to kinji abinda yace dan Allah kizo mukoma gidanmu na tabbata mom zata kula da ke sosai. Ita kanta ta san jikinta yana mata ciwo dan haka ta amince, ammah saida tafara shiga part d'in Abba taduba duk wasu file babu su, kallon Faruk tayi tai murmushi tace su Abba sun mutu ni kuma antafi da ni prison ummah tana asibiti sunyi amfani da duk wannan damar sun zo sun kwashe duk wani abu me amfani, saidai wannan ba shine a gabana ba, a yanzu na fi farin ciki da natabbatar su ma zasu mutu. Faruk yace haka ne ina tayaki murnar samun 'yancin kanki jawahir. Murmushi tasake yi a karo na biyu tace nagode. A cikin motar da sukazo duk suka shiga suka koma gida, nan Malam yakawo maganin da yazo da shi yabata yace tadinga sha kullum sau ukku a rana na tsawon kwana biyu ne, godiya tayi mashi tare da su Dad, nan mom tadinga nan nan da ita. Da marece Faruk yasanar da ita neman da akeyi mata akan dukiyarta tace bazata iya zuwa ba yau saidai zuwa gobe shima d'in yayarda da hakan dan saboda batada lafiya. Bacci tadinga yi a ranar sallah kad'ai take tadata da kuma ta yi sai takoma. Malam yace abarta duk na gajiya ne da kuma yanayin da take ciki. Nan yakawo tsarabar da yakawo masu yabasu yayi masu nasiha da wa'azi dan duk zuwan da zaiyi ko idan sukaje sai ya yi masu nasiha akan suji tsoron Allah ga dukkan al'amurransu, sannan yakoma Daura. Faruk shi kanshi wani irin dad'i yaji a ranshi a yanzu ji yayi kamar an cire mashi wata k'aya a jikinshi hankalinshi ya kwanta akan ku'butar jawahir saidai chan k'asan zuciyarshi kuma akwai abinda yake damunshi wanda yake da muhimmanci a rayuwarshi, kwance yayi d'akinshi yana tunani chan kuma yamaida idanunshi yalumshe. Washe gari wajen k'arfe goma jawahir tafarka daga baccin da takoma bayan ta yi sallar asuba, Mom ce tahad'a mata ruwan wanka taje tayi bayan ta fito tasamu riga gown saman gadonta an ajiye mata, murmushi tayi tad'auki rigar taduba ta yi mata kyau sosai wasu siraran hawaye ne suka gangaro mata tana cikin kallon rigar Mom taturo k'ofa tashigo hannunta rik'e da tray, ganin Jawahir tana hawaye yasa tayi saurin ajiye tray d'in ta iso wajen tana cewa jawahir lafiya? Me yafaru? Batare da ta janye idanunta akan rigar ba tace akowane lokaci Ammi taje kasuwa tana siya min irin wad'annan rigunan saboda ta san d'iyarta tana sonsu sosai bazan ta'ba sanin ta siyo min ba saidai da na fito daga wanka inga ta d'aura min a saman gado wannan ne natuna a lokacin da naga rigar nan, a yanzu babu Ammi na rasa komai. Matsowa Mom tayi tace duk uwa tana sanin abinda d'iyarta take so tabbas Amminki tana nan baki rasataba, saurin juyowa takalli mom tayi, Mom tace nice Amminki jawahir d'ana guda d'aya a duniya ko zaki iya kirana da Mummy. Cikin sauri jawahir tafad'a jikin Mom tare da fashewa da kuka tace nagode sosai Mom nagode tabbas ke Mom d'ina ce nagode da wannan matsayin da kika bani zan cigaba da kiranki da mom har k'arshen rayuwata. Wani irin sanyi Mom taji a cikin ranta cikin jin dad'i tace nagoe sosai Jawahir. Faruk da yake tsaye a k'ofar d'akin zai shigo dan yasanar da Jawahir fitar da zasuyi jin abinda suke tattaunawa yasa yatsaya yana saurarensu, jingine kanshi yayi da bango yana murmushi sai kuma chan yawuce yabar wajen. Mom taimaka mata tayi tashirya sannan tasata taci abinci bayan ta gama taruk'ota suka fito parlour takunna mata kallo tana yi suna d'an ta'ba hira Faruk da Dad ne suka shigo suka gansu Dad yace lallai uwa da 'yarta suna nan suna ta kallo mu sunma mance da mu. Murmushi Mom tayi tace to ya kuka iya kunsan dai babu me shiga tsakanin uwa da 'ya. Faruk ya ji dad'in furucin Mom sosai yace toh tsakanin uwa da d'a fa? Su dukansu dariya sukayi Mom tace kana kishi ne? Jawahir zamowa tayi daga saman kujerar tagaishesu cikin girmamawa suka amsa mata nan su ma suka zauna suna ta hira ita dai murmushi kawai take yanayin family d'in yana burgeta. Faruk ne yace to ke d'iyar Mom bazakice komai ba sai murmushi kawai kike yi. Mom tace ina ruwanka sarkin sa ido. Kallon Dad yayi yace kana ji ko Dad yanzu Mom ta daina ji dani ashe daman duk jin da ake da ni na rashin d'iyartane yanzu tunda ta zo ni anjefani a kwandon shara. Yanayin yadda yayi maganar har Jawahir saida tayi dariya. Mik'ewa yayi yace bari ma inyi tafiyata tunda abun haka yake tun kan Dad ma yajuya min ba, Dad yace a'a Son kayi hak'uri wa ne ni injuya maka baya. Kallon agogon hannunshi yayi yace Allah Dad su Barr Nas suna jirana bari inje, kallon jawahir yayi yace da anjima idan nadawo zamu fita. Amsawa tayi da toh. Nan iyayen nashi sukayi mashi Allah yakiyaye. Jawahir dai saidai kallonshi tayi batace komai ba. Wajen k'arfe ukku suka fita da Jawahir sukajr kotu aka mallaka mata komai da yake hak'k'inta na hannunsu Alhaji Mansur da Alhaji Sufyan sannan na wajen marigayi Abba ma da aka tattara aka mallaka mata matarshi bata tashi da komai ba saboda mallakin jawahir ne. Filaye kusan biyar da gidaje hud'u sai motoci biyar tatashi da su sai mak'udan kud'in da aka saka mata a account d'inta aka bata takardun kamfaninta da komai, banda kuma gidansu da suke zaune da a yanzu yazama shima mallakinta. Nan tayi godiya suka shiga mota suna cikin tafiya kallon Faruk tayi tace dan Allah ko zaka rakani gidan da su Nasiba suke zaune? Shuru yayi kamar baiji abinda taceba saida tasake maimaita mashi sannan ya amince suka je daga nesa da gidan yayi parking yace taje kar tadad'e, yana kallo tad'ibi wasu file tafita da su baice mata komai ba dan baisan abinda zatayiba, da idanu yabita har tashiga cikin gidan. Tana shiga tasamesu zaune a parlor su dukansu Mummy da yaranta ukku sunyi jugum dan mutane d'aid'aiya ne suke zuwan masu jaje basu ganetaba saboda sau d'aya suka ta'ba ganinta, yanayin yadda suka tarbeta ne yasa tagane haka. Gaishesu tayi tace sunana Jawahir mekud'i. Su dukansu jikinsu sanyi yayi dan a yanzu sun ganeta. File d'in hannunta tamik'a masu tace ga wannan takardun gidanku ne namaido maku kukoma kuzauna kucigaba da rayuwa na mallaka maku shi halak malak, domin ko bakomai baku cancanci hakan daga gareniba bakuda laifi a ciki baidace arabaku da gidanku ba. Hajiya maijidda ce kayi k'arfin halin cewa a'a jawahir ai mallakinki ne. Biro tafiddo cikin jakkarta tayi signing tamik'a mata tace gashinan kusa hannu wallahi na baku halak malak kukoma kucigaba da rayuwarku bazan ta'ba amsa ba bai dace inkasance me son kainaba ku ma mutane ne kuna buk'atar raayuwar 'yanci na tabbata zakufi jin dad'in zaman chan dan Allah na rok'eku ku amsa, kuyi hak'uri da abinda yafaru na tabbata kunji babu dad'i a ranku. Yaya sadiya ce tayi k'arfin halin amsa nan taduba su dukansu kuka suka fashe da shi sunayi mata godiya. Nasiba da idanunta suke kumbure tace tabbas ke d'iyar mutinci ce jawahir baki dace ace iyayenki aka ci ma mutunci hakaba nayi nadamar kasancewar Dad a matsayin uba agareni domin shi mutum ne meson kanshi da yawa, na yi ma kaina alk'awali bazan ta'ba taka inda Daddy yakeba saboda abinda ya aikata me muni wanda yaja mana mutane suke kallonmu da abin, ya ja munrasa komai har da k'imarmu da ace ya hak'ura baibi son zuciya ba koda ace acikin k'aramin gida muke rayuwa zamu hak'ura muzauna domin ubangiji shi yanufemu da haka, kibar gidanki jawahir hak'k'inki ne kece kad'ai yadace kigajeshi. Jawahir da tafara hawaye saboda tausayi girgiza kai tayi tace a'a Nasiba wallahi bazan amsaba na baku kyauta kuje kucigaba da zama kawai domin na tabbata da ace a lokacin ya nuna yanaso Abbu zai bashi kuma da ace Abbu yana raye bazai ta'ba bari kubar gidan ba, dan Allah na rok'eku kuzauna. Su duka shuru sukayi suna mamakin irin halin jawahir ita aka zalunta ammah ita take binsu tana rok'onsu sukoma gidan. Su duka har da mahaifiyarsu suka safko k'asa sunayi mata godiya bataji dad'in hakan ba tace sudaina nan tasa Nasiba tabata account number d'inta tayi mata transfer d'in 2millions, bayin Allahn nan suna kuka suna mata godiya ganin haka yasa tayi masu sallama su duka suka tashi dan su rakata tace a'a subarshi dan ta san Faruk bayaso suhad'u haka tafito tana goge k'wallah ta isa wajen motar Faruk da yake zaune yana waya ganinta yasa yakashe wayar tare da cewa wani abu sukayi maki? Saida tashigo tarufe motar sannan tace a'a basuyi min komai ba. Ammah me kikayi a gidan?. Juyawa tayi takalli taga sannan tace na yi abinda yadace ne, sannan tajuyo tace dan Allah saura gidan Alhaji Mansur. Da mamki yake kallonta yace wai me kike aikatawa mi kikayi da file d'in da kika fita da shi?. Hawaye ne suka gangaro mata tace Yaya Umar sai kuma tayi shuru na d'an lokaci a karo na biyu tace Barrister tun ina k'arama Abbu yana kwatanta min akan taimakon nak'asa da kai musamman wanda yashiga cikin wani hali, ya sha yace min kar inbari wani yayi kuka a dalilina kar inbari wani yayi kuka ni kuma inyi dariya inkasance mutum me adalci a rayuwata. Ajiyar zuciya yasafke dan tabbas ya gane file d'in mallaka ma su Nasiba shi tayi, rok'onshi tasake yi akan yataimaka yakaita gidan Alhaji Mansur yakaita kud'i da fili taba iyalanshi tare da maida masu motar da kotu ta amsa tashi nan suma sukayi ta mata godiya. Faruk mamakin halayyar jawahir kawai yake tabbas a yanzu ya fahimci ita mutum ce me adalci wadda abun duniya bai rufe mata idanu ba inko hakane to tabbas halin iyayenta ne tagado Koda suka koma gida Mom da Dad suka samu zaune a parlor suna jiransu, bayan sun zauna ne Jwahir tatattaro duka files d'in tamik'a ma Faruk banda guda d'aya daga ciki amsa yayi yana tambayar me zai mata da su, zataje ganin gidajen da filayen ne? Batare da ta bashi amsaba taje tamik'a ma Dad gudan tare da zama k'asa gefen k'afarshi tace Dad wannan na kamfani ne na mallaka maka shi a hannunka domin nasan kaine kad'ai zaka iya kula da shi kamar yadda zaka kula da naka. Jinjina kai Dad yayi yace shikenan jawahir na amshi wannan amanar zan kular maki da shi yadda yadace insha Allahu zan maido maki darajar kamfaninki kamar lokacin da mahaifinki yana raye. Fashewa tayi da kuka tace nagode sosai Dad sai kuma kud'in da ke account d'ina zan turo maka sai ayi amfani da su wajen ha'b'bako kamfanin. A'a jawahir banason kud'inki ni zanyi maki komai da aljihuna domin ko bakomai akwai amana tsakanina da mahaifinki. Duk da haka Dad na fi so ayi da dukiyar nan domin hankalina zaifi kwanciya,. Katseta Dad yayi yace dangin mahaifiyarki suna buk'atar wani abu daga gareki. Dad zan basu zan raba dukiyar ukku inbasu kashi guda sauran sai ayi amfani da ita. A'a jawahir tunda dai kin nace zan amshi kashi d'aya kibasu d'aya, sauran kuma kiyi amfani da ita. Ganin bataso tacigaba da yi mashi gardama amatsinyishi na babba yasa ta amince da hakan. Kallonta tamaida ga Faruk da yake jiran jin abinda zatace akan files d'in da tabashi, murmushi tayi tace wannan kuma kaza'bi gida d'aya da fili guda duk na mallaka maka sannan Dad yad'auki mota guda Mom kuma abata fili d'aya, na san kunfi k'arfin hakan ammah nima na baku ne saboda Allah dan ni kaina na san banda abinda zan iya biyanku da shi saidai addu'a Su duka sukace a'a bazasu d'auki komai ba tayi amfani da abunta duk yadda taso sud'auka ammah suka k'i dan haka tafitar da gida da mota tace zata mallaka su ga Ummah dan ko bakomai uwace gareta. Nan suka amince da hakan indai har ita zata ba babu matsala saboda ta cancanta saboda matsayinta. Bayan sun gama tattaunawane take sanar da su gobe takeso tawuce Kebbi nan suka nuna basu yarda ba, nacewa tayi da hakan saboda garin ji take duk ya gundureta komai ji take babu dad'i tunda tafito daga gidan yarin ba dan komai ba sai dan rashin wani makusancinta a cikin garin, wannan dalilin ne yasa tanace. daga k'arshe dai suka amince ba dan sun so ba sukace Allah yakaimu, sai kowa yakasance cikin shiri gobe sai muje Kebbi ammah ta flight zamu bi, inyaso sai insa driver yatafi da motar da kikeso atafin maki da ita chan, kai kuma Faruk a yau kaje kayi mana booking d'in jirgi. Toh Dad insha Allahu. Jawahir godiya tayi masu sosai har da k'wallarta nan Mom talallasheta sukace tadaina kuka. Da marece tare da Mom suka shiga kitchen tatayata girkin dare, Mom jin son yarinyar take a cikin ranta ji take ina ma ace d'iyarta ce dan a rayuwarta tana son 'ya'ya mata saidai ubangiji bai bataba sai d'a d'aya tilo. Wajen k'arfe tara Jawahir tana kwance a chan part d'in mummy kallon agogo tayi nan tamik'e tad'auko hijab d'inta tasaka tafito a main parlor, tana safkowa tasamu Faruk zaune yana dannar waya, Murmushi tayi tataka ta isa wajen da yake tayi sallama. Sai a lokacin yalura da ita nan ya amsa yace daman bakiyi bacci ba? Zama tayi tace Eh na kasa baccin ne. Idanu yazuba mata yace meyasa kika kasa? ina tunani sai zuwa anjima,,, tabashi amsa. Ajiyar zuciya yasafke yace ammah Jawahir bazaki hak'ura da tafiyar nan ba sai zuwa jibi, kinga gobe na so kije kiga filayenki da gidajen sannan gidanku ya kamata afitar da duk kayan da suke ciki. Duk'ar da kanta tayi k'asa tace ba damuwa Yaya Umar kai zaka iya.....saurin d'ago kai tayi tace am yi hak'uri wlh na saba cewa yaya umar ne. Murmushi yayi yace ba damuwa nima ai Umar d'inne ko kin mance? Murmushin itama tayi tace kaima yayanane ammah saidai ince Yaya Faruk. A karo na biyu yayi murmushi yace nagode sosai jawahir da wannan matsayin da kika bani daman kinga ban da kowa ni kad'ai ne wajen iyayena sai 'ya'yan k'anwar iyayena. Jawahir tace Allah sarki, ashe bakasan dad'in k'anneba. Tarar numfashinta yayi yace au ke kin sani ashe? Dariya tayi har saida hak'oranta suka bayyana tace ina fa nasani, ni dai gobe zan tafi Kebbi. Hmmm kedai kin k'agara kitafi kamar wani abu muke maki to wai ma kin san inda suke zaune? Eh Man a cikin garin Fanah a lantarki, ko da ba lallaine ingane gidan ba ammah gidan ba wani me wuyar ganewa bane da ance gidan Malam me salati duk an sanshi acikin lantarki. Toh shikenan goben sai muje ammah naso kije kigano gidajen, ko zaki shirya tun da wuri mufara zuwa. Girgiza kai tayi tace a'a Yaya Faruk bazan iyaba ni fa duk sun fita raina banason ganin gidajen da filayen, K'wallar da yaga sun cika mata idanu ne yasa yace shikenan Jawahir ya kikeso ayi maki da su a aje maki har sai ranar da kikazo katsina?. Shuru tayi sai chan tace cikin gidajen aba Ummah guda sannan duk kayan da suke cikin gidanmu na mallaka mata su tasa akwashe sannan abata mota guda sai kuma kud'i zan turo a account wanda za'a basu na maganinta. Faruk jinjina ma jawahir yayi sosai irin tausayinta da son taimako tabbas ba kowa ne zai iya irin haka ba, yace toh shikenan jawahir zanyi duk yadda kikeso. Nan yafiddo wayarshi yace bari kiga wani abu, gidaje ne guda hud'u da filaye ukku sai motoci ukku duk yagwada mata taduba tace wad'annan fa?. Kallonta yayi yace d'azu naje nagano su shine nad'auko maki su hoto dan na san wannam zumud'in na son zuwa kebbi bazai barki kije ganosuba kuma sai gashi hakan. Dariya tayi tace kai dai ko Barrister. Idanu yazuba mata yace nidai me? Girgiza kai tayi tace bakomai sannan takalli agogo tace bari inje inkwanta dare ya yi fa. Faruk yace toh shikenan sai Allah ya kaimu nima yanzu zanje inkwanta. Har ta juya zata tafi yace am baki ji ba. Juyowa tayi tace na'am. Murmushi yayi yace kije kawai ba komai. Itama murmushin tayi tajuya takoma part d'in Mom cike da farin cikin gobe zata je Kebbi..... _Sis Nerja'art✍🏻_ [7/24, 11:21 PM] Sis Nerja'art 2: *......FANSAR RAI......* *INTELLIGENT WRITER'S ASSO....®* [On Ward Together] _Follow me on Wattpad: *Sis-nerja*_ _Wannan Littafin na kud'i ne domin karantawa cikin aminci da yarda ga duk me buk'ata zai turo katin Mtn na d'ari biyu N200 kacal ta wannan number d'in 09035938246, ko ta account number 5330055604, Idan katura ka aiko da screen shot na transaction a wannan number d'in 09035938246_ _Akwai gara'basar *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shahararriyar marubuciyar nan *AMEENA ABBA UMAR* tare da novel d'in *FANSAR RAI* akan farashin N300 kacal, ko da kud'in ka sai da rabonka_ *PAGE 23* Washe gari tun da safe suka tashi suka fara shirin tafiya dan jirgin k'arfe goma zasu bi, tun wajen k'arfe tara driver yakama hanyar kebbi da mota inda aka zuba duk wata tsaraba da akwatin kayan jawahir da aka saka wanda bata san da shi ba, dan mamaki ma taba Faruk sam bata yi tunanin tatanadi kayan sawa ba. Wajen k'arfe goma saura Barr Nas yakaisu airport, goma daidai tana yi jirginsu yad'aga zuwa KEBBI STATE tunda suka baro gida jawahir shuru tayi duk kuma sai taji wani iri sai a lokacin tayi tunanin shin ko har yanzu dangin mahaifiyartata suna a nan cikin garin Kebbi, gabanta saida yafad'i tace Allah yasa dai suna nan. Suna safka suka samu mota suka yi shata suka kama hanyar FANAH jawahir dai titi kawai take kallo yanayin garin yana burgeta dan zata iya tunawa tun tana k'arama rabonta da garin a lokacin da Amminta taci burin k'ara zuwa da ita a lokacin tarasu, saurin goge jawayen da suka gangaro mata tayi Faruk ne kawai yalura da su ammah bai ce komai. Sun d'an d'auki lokaci suna tafiya har suka isa garin a lantarki wani dattijo suka tambaya gidan Malam me salati dan ita bazata iya ganewaba saboda da jimawa rabonta da garin nan yayi masu kwatance me mota ya ida isa da su har k'ofar gidan suka biyashi kud'inshi suka fita. Wani gida ne babba wanda da kagani ka san family house ne, daga gaban gidan akwai icce a k'ark'ashin iccen wani tsoho ne da wasu manya biyu zaune hannun tsohon rik'e da carbi yana masu magana, ganinshi yasa Jawahir taganeshi tace tabbas wanchan ne kakana na ganeshi, cikin sauri tanufi wajen da yake tace Baba Malam, daga shi har mutanen d'ago kai sukayi suka kalleta lokaci guda sukace Jawahir yau kece a garin namu? Jikin tsohon tafad'a tare da fashewa da kuka tace Baba Malam meyasa kukayi min haka kuka daina sona. Su dukansu jikinsu yayi sanyi dan basuda bakin magana, tsohon ne yayi k'arfin halin cewa bamu daina sonki ba jawahir muna k'aunarki wallahi ba laifinmu ba. 'Dagowa tayi cikin muryar kuka tace koma menene Baba malam baidace laifin wasu yashafeni ba ku duka dangin mahaifiyata kun yadani babu me k'aunata sai wad'anchan, tanuna su Faruk da suke tsaye. Juyawa su duka sukayi suka kalli su Faruk sukace bismillah sannunku da zuwa. Amsawa sukayi da yauwa nan suka zo zasu zauna d'aya daga cikin mutanen ne yace a'a kuzo mushiga gida ya za'ayi mubarku waje bismillah mushiga ciki. Gabad'aya suka mik'e suka nufi cikin gidan inda suka nufi 'bangaren Baba Malam dan gidan irin family house d'innan ne suna shiga da sallama wata 'yar dattijuya tafito daga cikin wani d'aki tana gyara zane, Baba Malam ne yace Mairo kawo mana tabarma muna da manyan bak'i yau. Cikin fara'a tace masha Allah marhabanbikum bak'inmu muna maku barka da zuwa, amsawa sukayi da yauwa. Babbar tabarma tad'auko tashimfid'a nan duk suka zauna suka fara gaisawa tsohuwar ce tazuba ma Jawahir idanu tace oh ni Mairo wannan d'iya kamar 'yar wajen khausar. Baba Malam yace itace man baki ganeta ba. Saurin rik'o jawahir tayi tace oh ni 'yar nan kece? Ashe kina nan shine baki ko lek'o mu ko dan mahaifiyarki ai ya kamata kidinga zuwa wajenmu. Jawahir kallonta tayi cikin muryar kuka tace ku ne dai baku nemana dan kunga iyayena basu raye. Baba Malam ne yace a'a jawahir ba haka bane kiyi hak'uri wallahi bamuda laifi a ciki d'an uwan babanki ne bayaso muna zuwa gidanku ga su Musa nan kitambayesu kiji irin wulak'ancin da yake mana idan munje, ko bayan rasuwar mahaifiyarki saida mukaso yabamu ke mudawo da ke hannunmu ammah yak'i yaci mana mutunci yace kar yasake ganinmu gidanshi idan har ba zuciyar kare garemuba, Musa ko ba haka yace mana ba? Wanda aka kira da Musa ne yace tabbas hakane Baba ni kaina raina ya 'baci da cin mutuncin da yayi mana ko bakomai khausar 'yar uwarmu ce baidace yahanamu zuwa ganin d'iyartaba Dad ne yace gaskiya bai kyauta ba cin mutunci baida dad'i, ba adalci bane ace ya rabata da danginta ba. Gyad'a kai Baba Malam yayi yace kaima dai ka fad'a bawan Allah raina ya 'baci sosai a duniyar nan yara hud'u namallaka ukku maza sai khausar ita kad'ai ce mace dole hankalina yatashi domin ita kad'ai ce talula wani gari tayi aure na san batada matsala da mijinta dan mutumin kirki ne saidai d'an uwanshi, wallahi tun bayan rasuwarta ban ta'ba kwana ba tare da na tuna jawahir a raina ba dan ina tausaya mata halin da zata shiga a hannun wannan mutumin. Dad jinjina kai yayi yace gaskiya ne ai Alhaji Mu'azu baida kirki, kallon jawahir yayi da take ta kuka yace Jawahir kinji dai abinda sukace ya kamata kiyi masu uzuri, tunda basuda laifi a ciki. Kallon Dad tayi tace hakane Dad na san duk Abba ne yaja min, babu komai na yafe. Su duka sun nuna farin cikinsu nan Baba Malam yatambayeta ina su Abba ya akayi yabarta tazo, Shuru tayi nan yayi murmushi cike da talaici yace wallahi Alhaji Mu'azu baida kirki wai har yayi maki aure batare da ya fad'a manaba saboda bai d'aukemu da darajaba saidai muji labari a wajen wasu, nuna Faruk yayi yace wannan ne mijin naki? Girgiza kai tayi tace a'a ba shi bane. Toh wanene? Baba Musa yajefo mata tambayar. Shuru tayi tarasa abinda zata ce masu ganin haka yasa Faruk yace Jawahir ya kamata kisanar da su komai. Fashewa tayi da kuka tace ban san abinda zan ce masu ba me zan fad'a masu? Infad'a masu duk na kashesu? Su duka a zabure sukace kin kashesu kuma? Faruk ne yace a'a Jawahir kidaina cewa haka. Cikin kuka tace toh ai ko bance ba haka yake, Baba Malam bari insanar da ku komai, gyara zamanta tayi tare da k'ok'arin tsaida kukan da take sannan takwashe komai tafad'a masu tun daga mutuwar mahaifinta da mahaifiyarta har aurenta da Umar da kisan da suka dinga yi, hatta zamanta a gidan yari da taimakon da Faruk yayi mata babu abinda ta'boye masu. Ba Baba Malam ba hatta 'yan uwan mahaifiyartata da kakarta saida suka yi kuka saboda tsananin tausayi, sukaita jimamin abun nan suka dinga yi ma su Faruk da iyayenshi godiya sukace bakomai. Baba Musa yaje yasanar da iyalanshi bak'in da sukayi yace ashirya masu abinci inda shima Baba Bello ma haka sannan yakira k'anensu Baba Nura yasanar da shi zuwan d'iyar autarsu khausar nan da nan yabaro gona yazo gida. Suna nan Driver ya iso garin ta waya akayi mashi kwatancen inda zaizo dan dama ya san garin sosai ahaka ya iso da motar. Matan su Baba Musa da yaransu ne suka zo dan sugaisa da bak'i nan Baba Musa yagwada masu Jawahir inda suma yagabatar da su a wajenta, mata biyu yanuna mata da yara bakwai yace matanshi ne da yaranshi akwai wasu yaran nashi biyar suna gidan mazajensu, sannan yanun wasu matan biyu da yara goma yace na maibi mashi ne Baba Bello, sannan mata d'aya da yara biyar yace na Baba Nura ne, nan sukaita farin cikin ganin 'yar uwartasu inda itama tanuna mafarin cikin ganin dangin mahaifiyartata. Hira aka dinga yi tsakanin su Baba Malam da su Dad inda Faruk yabi Baba Nura suka shiga gari yana nuna mashi garin nasu. Saida sukayi sallar azuhur nan suka zauna a babban tsakar gida aka baje tabarma abinci aka dinga shigowa da shi daga cikin gida had'ad'd'en dambu ne wanda yasha zogale da Tuwon dawa miyar ku'bewa d'anya gefe d'aya kuma Fura ce wadda tasha zuma sai kaji soyayyu da madarar shanu da aka dafa masu haka suka zauna suka kwashi girki abincin sosai yayi ma su Dad dad'i dan sun ci shi sosai. Bayan sun gama ne wajen k'arfe ukku Dad yace ma Faruk ya kamata yaje yayi masu booking d'in jirgin da zasu koma, Baba Malam yace ina bazai yuwuba sukoma yau saidai sukwana suka nuna a'a dan gobe akwai aiki kan dole yahak'ura yabarsu, Baba Nura ne yaraka Faruk yaje yayi booking d"in jirgin k'arfe shiddan marece sannan suka dawo. Wajen k'arfe biyar Faruk yana waje shi da Baba Nura suna hira nan Baba Nura yamik'e yace bari yad'an shiga gida yafito Faruk yace toh ba damuwa yana shiga nan Faruk yakira Jawahir a waya dan a lokaci tana cikin danginta suna ta nan nan da ita kamar sumaidata ciki, ganin Faruk ne yake kiranta yasa tayi saurin yin picking. Yana ji ta d'aga yace kifito waje Jawahir akwai maganar da nakeso muyi. Amsawa tayi da toh nan tamik'e tafito tasameshi shi kad'ai, Faruk murmushi yayi yace watau anga dangi har anmance da mu. Itama murmushin tayi tace a'a Barrister ni na isa inmance da ku bana ma fatan haka. Ajiyar zuciya yasafke yace toh Allah yasa, kiran sunanta yayi ta amsa sannan yace na so ace kin amince kizauna da mu dan Mom zatayi farin ciki da hakan ammah kin k'i, duk da banga laifin hakan ba dan kema zakifi jin dad'in zama da danginki. Cikin sanyin jiki tace hakane Barrister na za'bi zama da dangina ba wai dan bazan iya zama da ku ba kod'aya kun cancanci hakan saidai kawai sune kad'ai dangina da suka rage min a duniya zan zauna da su inyi alfahari da hakan ko da nasan da banbanci irin zaman da zanyi a nan da kuma wanda nayi a gidanmu nan gidan jama'a ne ni kuma ba mace bace da tasaba zama cikin mutane saidai a haka na san zan koyi wani darasin a cikin rayuwa. Tausayinta ne yakamata Faruk yace hakane Jawahir na san ma zaki ji dad'in zamanki da su dan su d'in dangine na gari mutanen kirki, saidai kina da dukiya a katsina bansan yadda za'ayi da gidaje da filayenki ba. Murmushi tayi tace kabar wannan a hannunka kawai. Toh shikenan zan ajiye maki ammah a duk lokacin da kika samo yadda zakiyi da su sai kisanar da ni yauwa kinga ga motar nan ya kawo maki sannan kiduba akwai akwatin kayan sawa a ciki. Da mamaki take kallonshi tace kayan sakawa kuma? Wa yabani bayan na san banda su? Ni na had'a maki dan naga bakida su kuma baki nema ba, Jawahir idan kinason wani abu kidinga fad'a min, na ce maki kid'aukeni a matsayin yaya kamar yadda kika d'auki Umar ina neman wannan alfarmar a wajenki jawahir. K'walla ce tacika mata idanu tace na d'aukeka tamkar Yaya Umar shin ka amince indinga kiranka da sunan Yaya Umar? Murmushi Faruk yayi cike da farin ciki yace na amince jawahir, nagode da wannan matsayin da nasamu a wajenki. Itama murmushin tayi tace nice da godiya akan karamcin da kuka nuna min. A'a kidaina godiya domin kin fi k'arfin hakan,,, Suna nan a haka Baba Nura yadawo nan suka zauna suna hira. Wajen k'arfe biyar da rabi su Dad suka fito nan duk mutanen gidan suka rakosu a cikin motar Baba Musa suka shiga aka kaisu Airport, jawahir kasa fitowa tayi suyi bankwana a d'akin Inna Mairo tazauna taci kukanta dan duk sai taji ba dad'i tafiyar da zasuyi daga k'arshe ko da Baba Nura yashigo yace tafito suyi bankwana da su Faruk cewa tayi ace tana masu Allah yakiyaye bayi zata shiga yanzu. Haka yaje yafad'a masu sak'onta, Dad yace Jawahir ko dai kuka take dan na ga koda zamu fito kamar zatayi kuka. Baba Nura yace nima naga tana kukan ammah ta shiga toilet yanzu. Su dukansu duk sai sukaji babu dad'i haka suka shiga mota suka tafi. Tsaraba nik'i nik'i aka had'a masu cikin ledar Viva guda biyu saboda tafiyar jirgi ce, k'arfe shidda daidai jirginsu yad'aga suka kama hanyar katsina. Tunda suka dawo gida duk sai suka ji ba dad'i da ba jawahir dan d'an kwana biyun da tayi sun saba sosai kamar ta yi wata, Bayan sallar isha'i duk takirasu tayi masu barka da safka tare da masu godiya akan taimakon da sukayi mata. Zamanta a cikin danginta ya yi mata dad'i sosai dan suna nuna mata so saisa nan da nan tasake sukaita hira, yayyen mahaifiyarta kowa ya so tazauna a 'bangarenshi ammah Baba Malam yace a'a a wajensu zata zauna dan haka suka hak'ura suka barta wajen iyayen nasu. *BAYAN KWANA BIYU* Su Nasiba sun koma a gidansu da Jawahir tamaido masu inda suka cigaba da zama ita da mahaifiyartata koda ba dad'in zaman suke ji ba saboda rashin Alhaji Sufyan ko ma ace tashin hankalin abinda yafaru, yayyen Nasiba kusan kullum sai sunzo gidan saboda mahaifiyarsu da tafi kowa sa damuwa a ranta dan har jininta saida yahau kwana biyu tad'an kwanta ciwo. Nasiba ko abu goma da ishirin suka taru sukayi mata yawa bayan tashin hankalin da tashiga ta rashin mahaifi ga kuma soyayyar Faruk da take d'awainiya da ita saidai a yanzu tana tunanin kamar bazai sake saurarenta ba. Yau ma dai tana zaune a d'akinta ita kad'ai ta buga tagumi tana tunanin masoyin nata, Aunty Sadiya ce tashigo tana mata magana ammah Nasiba bata ma san tana yi ba har saida tad'an ta'bata sannan tadawo hayyacinta saurin goge k'wallan da suka cika mata idanu tayi tace Yaya Sadiya yaushe kika shigo? Zama tayi gefenta cike da jin tausayinta tace haba Nasiba wane irin abune kike haka kina ganin hankalin kowa ba'a kwance yakeba duk muna k'ok'arin danne damuwarmu saboda mahaifiyarmu yanzu da ace ta shigo ta ganki me kike tunani kinsan dai dole hankalinta yasake tashi, kinsan dai ciwonta. Girgiza kai tayi tace Yaya Sadiya bazaku fahimceni ba, ba wai ina kuka akan Daddy bane a'a kawai ina kuka akan Faruk da nariga namallaka ma gabad'aya zuciyata wallahi yaya sadiya ina mashi son da ni kaina bazan iya misulta shi ba, ammah a yanzu Faruk ya tsaneni na san bazai ta'ba aurena ba saboda abinda mahaifina ya aikata wannan wace irin jaraba ce ya zanyi? Kifad'a min Yaya Sadiya ya zanyi Faruk yasoni? Hannunta tajanyo tad'aura saman k'irjinta tace ji kiji yadda zuciyata take bugawa akan sonshi. Tausayinta ne yakama Sadiya tajanye hannunta tare da zuba ma k'anwartata idanu da soyayya take nema tazautata. Ganin haka yasa Nasiba tafashe da kuka tace kice wani abu Yaya Sadiya dan Allah kifahimceni na san Mummy ce kawai tasan irin halin da nake ciki gashi batada isassar lafiya bare yanzu intunkareta da maganar. Dafata Sadiya tayi tace kikwantar da hankalinki Nasiba zan taimakeki nima na fahimceki kibani hankalinki gabad'aya zan fad'a maki yadda zakiyi kisamu Faruk. Saurin goge hawayenta tayi tare da tattara hankalinta gaba'aya ga yayartata dan jin abinda zata fad'a mata. _______ Mom ce zaune a Parlor tana kallo nan tafara jin sallama a wajen k'ofa. Amsawa tayi tare da bada izinin shigowa. Nasiba ce tashigo cikin ado kanta sadde a k'asa cike da jin kunya. Mom na ganinta nan cikin fara'a tace a'ah wai Nasiba ce bismillah kishigo man. Shigowa tayi a nutse taduk'a k'asa Mom tace miye haka zaki zauna k'asa kihau kujera man. Girgiza kai tayi tace a'a Mom nan ma ya yi, ina wuni? Amsawa Mom tayi sannan tatambayeta Mummynta tace tana nan lafiya lau. Daga nan kuma duk sukayi shuru Nasiba duk tarasa me ma zatace ita kuma Mom duk sai taji ba dad'i da bata jajanta masu abinda yafaru ba koda ta san Alhaji Sufyan ya yi masu laifi. Mom mik'ewa tayi tace bari inkawo maki ruwa kitashi kikoma saman kujera Nasiba. Har ta bud'e baki zatayi magana sai muryar Faruk tajiyo yana waya saurin d'ago kai tayi takalli hanyar part d'inshi da tajuyo muryar daidai lokacin da yake safkowa saman step karaf suka had'a idanu tsaye Faruk yayi a wajen yana kallonta cike da mamakin ganinta, inda itama Nasiba tazuba mashi idanu lokaci guda k'wallah suka cika mata ido, Mom tsaye tayi tana kallonsu sai chan tace Faruk ka fito ne? Jin muryar Mom yasa yayi saurin d'auke idanunshi daga kan Nasiba tare da ida safkowa yanufi wajen Mom yana cewa Eh Mom yanzu zan d'an fita ne. Ganin yadda yabasar yasa tace ga Nasiba baku gaisaba ko baka ganta ba? Batare da ya kalli inda take ba yace sannu Nasiba ya gida? Wani irin k'ululun bak'in ciki ne yatsaya mata a mak'ogoro cikin ranta tace lallai ma Faruk watau dagaske yanzu ya daina sona. Mom tace jirani Faruk inkawo ma Nasiba ruwa zan d'akko maka sak'o. Bai musaba yatsaya batare da ya ce komai ba, maida kallonta tayi ga Nasiba tace ina zuwa sannan tawuce tafita. Kamar jira suke tana fita nan duk suka zuba ma juna idanu, Nasiba saurin mik'ewa tayi tsaye tamatso inda yake cikin muryar kuka tace dan Allah Faruk kar ka azabtar da zuciyata bazan iya jure rashinka ba abubuwa biyu sun taru sun min yawa dan Allah kasafsafta min kayi hak'uri kar ka kamani da laifin da ba nawa ba. Har lokacin idanunshi suna a kanta duk ta d'an fad'a da kaga yanayinta ka san tana cikin damuwa, kauda idanunshi yayi gefe yace Nasiba ni me nayi maki? Ina ce kece da kanki kikace baki sona toh minene nawa a ciki ko ance maki ni marar zuciya ne da zanta bibiyarki. Tun kan yarufe baki tafashe da kuka tace Faruk wallahi rashin fahimta ne yasa nafad'i haka dan duk tunanina kana so katozarta mahaifina ashe ba haka bane daga baya na fahimci haka, tabbas su Dad sun kasance azzalumai da har suka aikata haka ga abokinsu saboda dukiyarshi, ni kaina ina da na sani akan kasancewata d'iya ga Alhaji Sufyan domin bai cancanci kasancewa uba agareni ba, dan Allah Faruk kayi hak'uri da abinda su Daddy suka aikata maka sannan kuma na gane kuskurena dan Allah kayi hak'uri kayafe min Faruk. Murmushi yayi cikin nuna rashin damuwa yace koma me kikayi daidai ne Nasiba ni ban rik'eki ba akan abinda yafaru kije kawai. Tun kan yarufe baki tace ammah kana nufin ka daina sona? Ta'be baki yayi yace tun lokacin da kika nemi indaina sonki ni kuma nadaina dan haka a yanzu babu sonki a raina. Saurin ja da baya tafara yi tare da k'ara sautin kukanta tace shikenan Faruk nagode ashe har zaka iya daina sona a lokaci guda? Meyasa haka Faruk? Miyasa bazaka fahimceni ba? Shuru yayi yak'yaleta jin motsin Mom yasa tayi saurin tsaida kukanta tare da sa hannu tagoge fuskarta kallon Faruk tayi da yake kallon gefe sannan tajuya cikin sauri tafita daidai lokacin da Mom zata shigo da tray a hannunta tsayawa tayi tana kallon Nasiba tace ah-ah Nasiba ina kuma zakije? Duk'ar da kanta tayi k'asa tace Mom zanje gidane. Ammah ai da kin bari kinsha ko ruwane nan fa ba bak'on waje bane Nasiba gida ne. Ahankali tace kiyi hak'uri Mom wani lokacin zan sha yanzu sauri nake su Yaya Sadiya suna jirana nagode sosai Mom,,, tana fad'in haka tawuce cikin sauri tafita. Mom mamakine yacikata tayi saurin shiga parlorn tasamu Faruk a tsaye yana dannar waya cikin 'bacin rai tace Faruk me kayi ma Nasiba? 'Dagowa yayi yakalli Mahaifiyartashi yace ni kuma Mom? Banyi mata komai ba. Ajiye tray d'in hannunta tayi tace na tabbata akwai abinda kayi mata tunda har tafita tana kuka, haba Faruk bai dace kakasance butulu ba ko bakomai Nasiba ba ita tayi maka laifi ba mahaifinta ne dan su basusan ma ya yi ba, duk wannan zaman jajen da mukayi duk da ita mukayi shi ta shiga tashin hankali sosai dan ko abinci bata iya ci sannan bata barin gidan nan sai dare shima sai su Dad d'inka sun sa ta tatafi gida, shin wannan ba k'auna bace? wallahi Faruk ba baki zan maka ba ammah na tabbata mawuyacine kasamu me sonka kamar Nasiba domin ita da zuciyata d'aya take k'aunarka. Shuru yayi duk sai yaji jikinshi ya yi sanyi dan tabbas ya san Nasiba tana k'aunarshi shima kanshi yana sonta ya yi mata haka ne kawai saboda abinda tayi mashi. Mom cigaba tayi da cewa Faruk baka isa kacanza ma zuciyarka abinda take k'auna ba a lokaci guda ammah shikenan kayi abinda kake gani daidai ne a wajenka, tana fad'in haka tawuce tabarshi wajen tsaye, runtse idanunshi yayi ahankali yace inko hakane banyi ma Nasiba adalci ba, saurin zama yayi tare da dafe kanshi yana tunanin yanayin da Nasiba tafita lokaci guda yayi saurin mik'ewa yad'auki wayarshi yafita cikin zuciyarshi yana addu'a Allah yasa Nasiba ta isa gida lafiya. Mom direct d'akin Dad ta isa tasameshi zaune yana karanta Newspaper ganin yadda tashigo yasa yace lafiya Hajiya naga duk ranki a 'bace? Zama tayi gefenshi tace dole raina ya'baci Alhaji wallahi Faruk baya kyautawa wai menene laifin Nasiba a ciki da har zai rabu da ita? Nuratu wani abun yafaru? Kwashe komai tayi game da zuwan Nasiba tasanar da shi, girgiza kai Dad yayi yace Faruk kenan kirabu da shi Hajiya ni nasan yana son Nasiba kawai dai yana dannewane, kinsan halin d'an naki ammah ina nan da ke dakanshi zai koma wajenta. Cikin sanyin jiki tace Allah yasa haka Alhaji. Ameen Nuratu kar ma kisa damuwa a ranki, yauwa daman ke naje jira ad'an kawo min coffee d'innan me dad'i wanda kika saba had'a min. Mik'ewa tayi tana murmushi tace toh Alhaji yanzu ko. Nasiba da taimakon Allah ta samu ta isa gida lafiya tana shiga a parlor tasamu mahaifiyarta da 'yan uwanta zaune k'ok'arin 'boye damuwarta tayi tamatsa kusa da Mummynta tace sannu Mummy ya jikin naki? Hajiya Maijidda ajiye ruwan da tasha magani da shi tayi idanunta suna akan d'iyartata tace Nasiba lafiya naganki haka me yafaru dan idanunki sun nuna kinyi kuka? Saurin duk'ar da kanta tayi tace bakomai Mummy ba kuka nayi ba. Haj Maijidda kallon Yaya Sadiya tayi tace wannan k'anwartaku bansan irinta ba ita akowane lokaci tana son 'boye damuwarta. Yaya Sadiya tace hakane Mummy saidai k'ila kuma ko wani abun tatuna yasata kuka. Murmushi Haj Maijidda tayi tace na san d'iyata babu abinda tatuna kawai dai soyayyar Faruk ce take d'awainiya da ita saidai Faruk bana tunanin zai cigaba da sonta saboda abinda mahaifinta ya aikata ya kamata kubata shawara tahak'ura da shi. Wasu hawaye ne masu zafi suka gangaro mata cikin sauri tajuya tashige d'akinta tamaida tarufe saman gado tafad'a nan tashiga rusa kuka da k'arfi. Su Yaya Sadiya da Yaya Na'ima sunyi juyin duniya akan tabud'e k'ofar ammah tak'i kan dole suka rabu da ita. Saida tayi kuka me isarta sannan tayi shuru idanunta duk sun kumbura kanta taji ya fara mata ciwo nan tamaida idanunta taruntse. Faruk motarshi yashiga yakife kanshi a kan steering yana jin babu dad'i akan abinda yayi ma Nasiba, sun had'a mata tension biyu ga nashi ga na mahaifinta ya san dole ta shiga damuwa sosai ba abinda yafi tada mashi hankali sai fitar da tayi cikin 'bacin rai baisan yanayin da zata isa gida ba, saurin d'ago kai yayi yad'auko wayarshi yakirata ammah har tagama ringing ba'a d'agaba sake kiran yayi nan ma ba'a d'aga ba dan haka yatada motarshi yatafi cikin ranshi yana addu'a Allah yasa ta isa gida lafiya. Nasiba ko tana kwance lokacin da yayi mata 2 missed tana ji ammah takasa bud'e idanunta taduba me kiran dan gabad'aya taji komai ma ya fita ranta batason jin muryar kowa a yanayin da take ciki. Bayan kamar minti goma wani kiran yasake shigowa a wayarki tsaki taja tare da bud'e idanunta tajawo wayar zata kashe nan idanunta suka safka ga sunan me kiranta wasu sabbin hawaye ne suka gangaro mata tamaida wayar ta aje har tatsinke wani kiran yasake shigowa ji tayi bazata iya k'in d'agawaba dan haka tayi picking tare da mannawa a kunnenta, muryar Faruk taji ya ce please Nasiba kifito gani a waje ina jiranki, ahankali ta amsa da toh sannan takashe wayar. Su Yaya Sadiya suna zaune sukaga ta fito sanye da hijab, mummy ce tace ina kuma zakije? Batare da ta juyoba tace ina nan waje sannan cikin sauri tawuce tatafi. Yaya Na'ima tace oh ni lallai Nasiba soyayya ta rufe mata idanu lallai tana son guy d'innan sosai. Hmmm kece daman baki saniba ammah Nasiba k'aunar da take ma Faruk ni har mamaki take bani daman zata taimaka tacireshi a ranta dan bana tunanin zai aureta. Mummy da take saurarensu tace a'a kudaina cewa haka ku dai kutayata da addu'a Allah yaza'ba mata abinda zaifi zama alkhairi. Su duka suka amsa da Ameen. Kanta sunkuye a k'asa tafito a harabar gidansu taganshi tsaye a jikin motarshi ammah ko da sau d'aya bata d'ago takalleshi ba har ta iso wajen, shi ko idanu yakafeta da su yana kallon yadda take tafiya a nutse dan Nasiba ba bayaba wajen nutsuwa, har ta iso wajen idanunshi suna a kanta. Tana zuwa ja tayi tatsaya sai a lokacin tad'ago idanunta da sukayi ja saboda kuka tace gani. Cikin idanunta yakalle cike da nuna damuwa yace yanzu Hearty duk akaina aka zubar da wad'annan hawayen?. Harara tawurga mashi tace kaga kafad'a min abinda yakawoka inma biyoni kayi kaimin wani wulak'ancin toh babu damuwa bismillah kayi zan iya jurewa saboda duk abinda yafaru laifina ne nice namallaka zuciyata ga wanda bai damu da ita ba, zan iya hak'ura Faruk ko da ace zan rasa rayuwata bazan sake matsa maka ba domin na san bakada laifi a ciki duk abinda yafaru na san mahaifinane yaja min. Jikin Faruk sanyi yayi sosai yace Nasiba ko d'aya banzo dan inci mutuncinki ba saidai na zone dan inbaki hak'uri sannan inmaido martabar soyayyata. Da mamaki take kallonshi tana so tayi magana ammah takasa. Ganin haka yasa Faruk yayi murmushi yace inbanda abun Nasiba taya za'ayi tayi tunanin Faruk zai iya daina sonta bayan ya riga da ya mallaka mata zuciyarshi, Nasiba ina sonki da zuciya d'aya kamar yadda kike sona wallahi nayi maki hakane dan kema kid'and'ani bak'in cikin da kika d'and'ana min a lokacin da kika nisantar da kanki agareni, bana ji zan iya daina sonki Nasiba domin kece Rayuwata. Wasu irin hawaye ne suka gangaro a fuskarta muryarta tana rawa tace dagaske kake Faruk? Dagaske kana sona zaka aureni? 'Daga kai yayi yace sosai ma indai ba kece kika daina sona ba, ammah a yanzu haka a shirye nake idan kikace inturo sai inturo ayi maganar aurenmu. 'Daga hannunta tayi sama tace Allah nagode maka da kamaido min masoyina, kallonta tamaida ga Faruk tace wallahi bazan iya daina sonka ba Faruk na riga na gama mallaka maka zuciyata idan nabarka taya zan iya son wani. Ajiyar zuciya yasafke tare da furta Alhamdulillah na yi farin ciki da jin haka daga gareki Nasiba, nima bazan iya son wata ba dan kin riga kin mamaye gabad'aya zuciyata, yanzu dai ina fatan za'a yafe min sannan acigaba da bani kulawa kamar da, komai yawuce mucigaba da nuna ma juna soyayya har zuwa aurenmu. Murmushi tayi cikin jin dad'in maganarshi tace insha Allahu Faruk na yi maka alk'awalin haka zan cigaba da baka kulawa har k'arshen rayuwata wallahi bakaji farin cikin da kasaka ni ba a yau ji nake kamar a mafarki kadawo gareni. Su duka dariya sukayi Faruk yace duk farin cikin da zaki shiga na fiki Nasiba yanzu dai kiyi min iso wajen Mummy inshiga mugaisa yau dai zan cire kunya in nemi aurenki dakaina inyaso idan nakoma gida sai insanar da su Dad su kuma su ida nasu. Wayyoo kar kuso kuga farin ciki wajen Nasiba rasa inda zata sa kanta tayi, haka tanufi hanyar cikin gida tana shiga da gudu ta isa parlor tana k'wala ma Mummy kira, su duka suka d'ago suna kallonta. Kusa da mummy tazauna cike da farin ciki tace Mummy Faruk ne yazo ya ce zai shigo yanzu kugaisa. Su duka farin ciki suka nuna nan Mummy tace taje tace yashigo. Mik'ewa tayi tafita cikin sauri suka bita da idanu, mummy tace kungani ko ai nasan suna k'aunar junansu sosai shima bazai iya barinta ba sai ya biyota. Su Aunty Sadiya sukace lallai kam ga alama nan mungani. Tana fita tasanar da shi sak'on Mummy sannan tafad'a mashi batada lafiya, a tare suka jero suka shigo gidan bakinshi d'auke da sallama yashiga parlorn suka amsa mashi har zai zauna a k'asa Mummy tace a'a kar yasaki yazauna yahau kujera dan haka yazauna saman kujera d'an zamowa yayi yagaisheta ta amsa nan yayi mata ya jiki sannan suka gaisa da su Yaya Sadiya da suke zaune gefenta. Nasiba ko baki k'in rufuwa yayi haka tafita tafara had'a mashi kayan motsa baki. Mummy ce cikin k'arfin hali tace dan Allah Faruk kayi hak'uri da abinda yafaru wallahi ba da saninmu bane Alhaji yake aikata wad'annan mugayen halayyar daga ni har 'ya'yana babu wanda yasan haka sai daga baya ashe su ne suka saceka dan Allah kayi hak'uri kar kadubemu da laifin da bamu muka aikata ba. 'Dago kai yayi yakalleta cike da girmamawa yace kod'aya Mummy bana kalkonku da laifin da ba naku bane ai laifin wani baya ta'ba shafar wani nima kaina banyi hakan dan in tozartasu ba saidai nayi ne dan intseratar da yarinyar da aka zalunta sannan daga baya ake shirin ganin anrabata da rayuwarta. Mummy tace hakane na san haka Faruk wannan dalilin ne yasa na k'ara son Nasiba takasance mata ga miji irinka domin ka cancanci asoka ko dan saboda gaskiyarka. Su yaya Sadiya sukace hakane muma muna k'ara bada hak'uri Faruk. Murmushin jin dad'i yayi yace bakomai nagode sosai, daidai lokacin Nasiba tashigo d'auke da k'aton tray ta ajiye gabanshi nan duk suka mik'e zasu bar wajen yace Mummy daman magana nakeso muyi da ke. Toh Faruk kagama sannan sai muyi maganar. Kanshi sadde k'asa yace wallahi mummy Alhamdulillah daga gida nake. Komawa tayi tazauna tace nan ma gidan ne ban yarda ba sai ka ci. Kallon Nasiba yayi da tatsiyaya mashi lemu a cup tamik'o mashi nan ya amsa tare da sakar mata lallausan murmushi itama tamaida mashi da martani. Kur'ba yayi ya ajiye sannan yaduk'ar da kanshi k'asa yace daman Mummy akan maganar auren Nasiba ne idan anban dama sai insanar da su Dad inyaso cikin satin nan atsaida rana. Mummy kallon Nasiba tayi nan Nasiba tamik'e cikin jin kunya tawuce sumi sumi tabar wajen tana ji kamar tanutse saboda kunya. Murmushi Mummy tayi tace haba Faruk wannan ai abun farin ciki ne agaremu ba damuwa kasanar da su Alhaji kawai akowane lokaci mu ai ashirye muke. Godiya yayi mata tace bakomai Faruk ai mune da godiya dan kai d'in mutum ne wallahi, dan Allah katayamu godiya a wajen Jawahir akan taimakon da tayi mana kaduba kaga yadda tamaido mana gidan da yake mallakinta da dukiya. Murmushi yayi yace ai cancanta ce tasa haka mummy kuma ku ai bakuda laifi a ciki saisa itama ta ga dacewar maido maku kayanku. Jinjina kai tayi tace Allah dai yasaka da alkgairi. Amsawa yayi da Ameen sannan yamik'e yace Mummy bari inwuce. Tun yanzu? Baka dai ci komai ba. Allah mummy a k'oshe nake ne. Toh shikenan Faruk mungode sosai Allah yasaka da alkhairi dan Allah kagaishe min da Hajiya Nuratu kafin ink'ara samun k'arfin jiki inshigo. Toh Mummy insha Allahu zata ji. Yana fita tak'wala ma Nasiba kira nan tafito tabishi a wajen mota tasameshi nan sukayi bankwana kasancewar magrib ta yi nan yaimata alk'awalin kiranta da dare. Haka suka rabu kowa zuciyarshi fal da farin ciki........ _Sis Nerja'art✍🏻_ [7/24, 11:21 PM] Sis Nerja'art 2: *......FANSAR RAI......* *INTELLIGENT WRITER'S ASSO....®* [On Ward Together] _Follow me on Wattpad: *Sis-nerja*_ _Wannan Littafin na kud'i ne domin karantawa cikin aminci da yarda ga duk me buk'ata zai turo katin Mtn na d'ari biyu N200 kacal ta wannan number d'in 09035938246, ko ta account number 5330055604, Idan katura ka aiko da screen shot na transaction a wannan number d'in 09035938246_ _Akwai gara'basar *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shahararriyar marubuciyar nan *AMEENA ABBA UMAR* tare da novel d'in *FANSAR RAI* akan farashin N300 kacal, ko da kud'in ka sai da rabonka_ *PAGE 24* A ranar farin ciki ne fal acikin ran Faruk da dare tunda suka zauna yin dinner Mom da Dad suna lura da shi da bakinshi yak'i rufuwa saboda farin ciki, su dukansu shuru sukayi suna jira suji ya fad'a masu dalilin farin cikin da yake yi. Bayan sun gama dinner ne yakalli iyayen nashi yace Dad Mom daman akwai maganar da nakeso muyi da ku. Su duka sukace toh muna saurarenka. Sosa kai yayi cikin jin kunya sannan yace daman Mummynsu Nasiba ce tace inturo ayi maganar aurenmu. Dad kallon Mom yayi takalleshi suka bushe da dariya yace Daman Nuratu ban fad'a makiba kurabu da shi dakanshi zai koma sushirya kansu. Murmushi Mom tayi tace ai gashinan yanzun na gani daman ban tsaya 'bata lokacina ba wajen yi mashi fad'a. Toh ai yanzu gashinan dai kin gani dan nasan wannan soyayyar tasu ta riga ta gama bin jinin jikinsu dan ma dai d'an nan naki ya cika taurin kai, ammah dai yanzu shikenan Faruk fad'i yaushe kakeso aje nema maka auren? 'Dago kai yayi cikin jin kunya yace ni Dad? Uhm hum muna saurarenka. Duk'ar da kanshi yayi ahankali yace cikin satin nan. Su dukansu sunji dad'in hakan da yace sukace toh shikenan babu damuwa insha Allah nan da kwana biyu zasu tura a tsaida ranar aure kawai. Cike da farin ciki yace nagode sosai Mom and Dad Allah yasaka da alkhairi, Allah yak'ara girma. Sukace Ameen. A karo na biyu suka tambayeshi ko wata nawa yakeso asa bikkin. Mik'ewa yayi tsaye saida yafara tafiya sannan yace kar yawuce wata biyu please,,, yana fad'in haka yawuce cikin sauri yanufi part d'inshi, muryar Dad ce yajiyo yana cewa kar kasamu damuwa yadda kakeso haka za'ayi Son. Yana shiga d'akinshi wanka yayi yai shirin kwanciya sannan yakira Nasiba a waya da itama tun bayan tafiyarshi bakinta yak'i rufuwa saboda farin ciki nan hankalin mahaifiyarta da 'yan uwanta yakwanta dan a yanzu sun gane duk Faruk ne dalilin damuwarta ba wai rashin mahaifinsu kawai ba. Hira suka sha sosai a waya a nan ne yake sanar da ita yadda sukayi da su Dad nan itama tayi ta murna, soyayya suka sha sosai sai da dare yaraba tsaka sannan sukayi bankwana suka kwanta tare da yi ma juna alk'awalin had'uwa gobe. Bayan kwana biyu Dad yasanar da su Malam da Su Aunty Kilima nan abokan Dad su ukku da d'an uwanshi sukaje suka nema ma Faruk auren Nasiba a wajen wani k'anen mahaifinta Malam sulaiman mutumin kirkine sosai nan ya amince aka tsaida rana nan da wata biyu masu zuwa. Haka aka koma aka fara shirye shiryen aure inda Faruk yak'ara gyara gidanshi da zai tare da amaryarshi nan da wata biyu. A chan 'bangaren Jawahir hankalinta ya kwanta sosai zamanta a wajen dangin mahaifiyarta dan tana samun kulawa yadda yadace gabad'ayansu kowa nan nan yake da ita dan haka tasaki ranta kud'ad'e tafiddo daga account d'inta dayawa taraba biyu taba kakanninta rabi sauran rabin kuma taraba ma yayyen mahaifiyartata sukaita mata godiya inda motar tabarta da sunan duk wanda zai fita yana iya d'auka yafita da ita ammah yayyen mahaifiyartata basu amimce da hakan ba su dakansu suka koya mata mota dan tadinga tuk'awa dakanta. Khausar d'iyar Baba Musa itace tsararta dan haka suka k'ulla abota sosai Jawahir tana sonta saboda sunan mahaifiyarta gareta islamiyyarsu aka sata nan tafara karatu hankali kwance inda a cikin zuciyarta taci burin cigaba da karatunta na high institution. A 'bangare guda kuma suna waya da Faruk da su Mom dan kusan kullum sai sun gaisa, a wajen Mom ne take jin labarin sa ranar auren Faruk nan tayi Allah yasa alkhairi, abun ya tsaya mata a rai sosai koda suka gama waya da Mom kiran Faruk tayi lokacin yana wajen aiki ya yi busy dayawa bai d'agaba saida yagama aikinshi sannan yakirata a waya, lokacin tana kwance suna kallo ganin me kiran yasa tatashi zaune tare da yin picking tayi sallama. Amsa mata Faruk yayi yace k'anwata ina fata kina lafiya. K'walla ce tacika mata idanu tace Yaya Faruk shine har akayi maka baiko tsawon sati biyu ammah baka fad'a min ba hakan da kayi ka kyauta ma k'anwarka? Ayya k'anwata yi hak'uri wallahi ba haka bane ina ta so infad'a maki mancewa nakeyi. "Ammah ai kusan kullum muna yin waya kawai dai bakaso kafad'a min ba sai gashi ita Mom ta fad'a min" Kiyi hak'uri Jawahir ba haka bane ai zan zo. "Uhm Allah yasa alkhairi kayi zamanka kawai,,, tana fad'in haka takashe wayarta. Faruk sake kira yayi ammah batayi picking ba murmushi yayi yace lallai ana fushi da ni Jawahir kasa samun sukuni tayi a ranar ba dan komai ba sai dan abinda Faruk yayi mata su Innah damunta sukayi da tambaya akan abinda yake damunta tace bakomai. Tun daga ranar indai Faruk zai kirata a waya bata d'agawa koda itama bata jin dad'in hakan da takeyi mashi saidai tana fushi da shi akan abinda yayi mata. ++++++++++++ A 'bangaren Hajiya Maijidda kud'i tafitar sannan tasiyar da k'addarorinta tayo ma d'iyartata order d'in kayan d'aki na gani na fad'a set biyu sannan tasiya mata kayan kitchen dan itace uwa da uba har a lokacin babu wanda yalek'a Alhaji Sufyan daga cikinsu bare susan halin da yake ciki dan su kansu kunyar tunkarar gidan yari suke da sunan sune iyalanshi. ______Wasa wasa haka aka ci wata guda ana saura wata guda bikki Mom taje itada Aunty kilima k'anwar mahaifinsu Mom suka had'o lefe na gani na fad'a akwati goma sha biyu akayi mata anzuba duk wani abu da yadace sannan aka kai lefe. Su Mummy da danginsu Nasiba sun yaba sosai da irin kayan da aka zubo mata nan suka bada tukaici me tsoka su ma. * * * Faruk ganin har lokacin Jawahir bata kulashi ba yasa yashirya ranar wata asabar yaje Kebbi batare da ya sanar da ita ba. Yana isa yakira Baba Nura yaje yad'auko shi suka nufi gidan. A waje suka gaisa da Baba Malam sannan suka shiga ciki suka gaisa da Innah a d'akinta yazauna nan takawo mashi fura me sanyi yasha, su Baba Musa duk zuwa sukayi suka gaisa nan aka cika mashi gabanshi da abinci da balango, furar yanark'a sosai dan ta yi mashi dad'i. Hira sukayi sosai da su Baba Malam da su Baba Nura duk wannan bidirin jawahir tana cikin gida wajen su Khausar batasan abinda ake ba har saida su Faruk sukayo sallar la'asar sannan Baba Nura yashiga cikin gida yasamesu zaune suna hira kallon Jawahir yayi yace kizo kugaisa da bak'o gashichan ya zo tun d'azu. Bak'o kuma?,,, jawahir tatambaya. Eh kishiga yana chan 'bangaren su Innah. Amsawa tayi da toh nan tamik'e tajawo hijab d'inta tasaka, Khausar tace wai wanene yazo? Oho nima ina sani Baba Nura bai fad'a min ba saidai kitaso muje mugani. Dariya Khausar tayi tace babu inda zanje dan wannan bak'on da alama na musamman ne lallai garinmu ya amsheki nan da nan anyi mana sabon kamu eyyen ba. Harara Jawahir tadoka mata tace kinga Khausar kidaina wannan maganar ko kin mance ni matar aure ce. Ta'be baki khausar tayi tace wallahi ba mecewa haka idan ba ke kika fad'a ba kuma ma auren da babu shi yanzu. Tsaki Jawahir taja tawuce tatafi batare da ta bata amsaba tana jiyota tana cewa agaishe man da surukin namu ammah tayi shuru. Tana shiga part d'in inna fuskarta kicin kicin tawuce tanufi inda inna take zaune tace wai inna wanene yazo? Kishiga ciki man sai kigane ma idanunki. Jawahir tsayawa tayi cikin ranta tace wallahi indai har wajena akazo zan wulak'anta mutum dan ni samari basu gabana, muryar Inna taji ta ce bazaki shigaba sannan tawuce tashiga. Tana d'age labule bakinta d'auke da sallama nan sukayi ido biyu da Faruk batasan lokacin da murmushi yasu'buce mataba cikin sauri ta ida shiga d'akin tace lah yaya Faruk kaine kazo ashe shine baka fad'a min ba? Murmushi yayi yace taya zan fad'a maki bayan k'anwartawa fushi take da yayan nata saisa nazo dan in goge laifina. Waje tasamu tazauna nan tagaisheshi ya amsa tatambayeshi su Mom yace duk suna lafiya lau. Amaryar fa ko ma ince Auntyna? Murmushi yayi yace tana nan lafiya lau itama tana gaisheki, nidai yanzu ayi hak'uri adaina fushin nan da akeyi da ni na amsa laifina insha Allahu bazan sake ba. Turo baki tayi batare da ta ce komai ba. Ahankali yace please my k'anwa kiyi hak'uri wallahi na shafa'a ne. Juyawa tayi gefe guda sannan tace shikenan na hak'ura. Yauwa kokefa har na ji dad'i ina fata babu wata matsala? Girgiza kai tayi tace babu. Ajiyar zuciya yasafke yace toh yanzu yaushe zakizo katsina? Ya kamata kizo kafin bikki dan wata d'aya kinga yarage. Kicin kicin tayi da fuska tace zan zo sai mun gama exams islamiyya dan next week zamu fara. Toh menene na had'e fuska? na ji ba damuwa idan kun gama sai azo kinga ayi hidimar bikki k'anwar ango tana kusa. Murmushi tayi tace hakane yayana. Faruk janta yayi da hira sukaita yi har wajen k'arfe biyar sannan sukayi sallama kud'i yafiddo sosai yabata yace ta sayi abinda takeso tunda baiyo tsara ba, da dafari har ta k'i amsa tace akwai kud'i a wajenta shareta yayi yabar mata su nan sannan yaje sukayi sallama da su inna da Baba Malam su ma ya ajiye masu kud'i sosai su Yaya Nura ne suka kaishi airport yabi jirgin k'arfe biyar da rabi yakoma katsina. Jawahir ta yi farin ciki sosai da zuwanshi haka taje talabarta ma khausar zuwan yayan nata da kud'in da yabata dan su Baba Malam taba su k'in amsa sukayi, a wajensu taga invitation d'in Faruk na d'aurin aure nan tayi Allah yasa alkhairi dan daman ya fad'a mata ba'a kaida bugo IV na 'yanmata ba lokacin da yazo saisa bai tafo mata da nata ba, batama yi tunanin anbugo na d'aurin aureba saida taganshi. *BAYAN SATI UKKU* Gidajen biyu aka fara hidima sosai inda kud'ad'e aka dinga ruwanu dan ma amarya ta ce ba wani program d'in da zatayi saboda yanayin da suke ciki saidai wa'azi kawai ta amince ayi. Amarya Nasiba ta sha gyara ta yi gwanin kyau sai salk'i take da kaganta kaga amarya saboda kyaun da tayi na amare. Ana saura kwana ukku bikki suna zaune a harabar gidansu suna hira da Faruk tace Lovely wai dan Allah Jawahir ta zo garin nan ne? Girgiza kai yayi yace a'a. Cike da mamaki take kallonshi tace meyasa toh sai yaushe zata zo? Zata dai halarci bikkinmu ko? Toh wannan ne ban dai saniba dan ance min suna exams a islamiyya kinga kenan ba damar tazo. Cikin nuna tausayi tace Allah sarki Jawahir baiwar Allah wallahi yarinyar nan tana bani tausayi gata mutuniyar kirki,, k'walla ce tacika mata idanu tace duk su Daddy sune silar jefata cikin wannan yanayin ta rasa kowa nata wace irin rayuwace wannan, taya zata kasance cikin farin ciki? Ganin yadda tafara hawaye yasa cikin sanyin jiki yace Nasiba duk abinda kikaga ya samu bawa to daga ubangiji ne babu wanda ya isa yatsallake k'addararshi, kuma a yanzu Jawahir tana rayuwa me dad'i a wajen dangin mahaifiyarta. Duk da haka Lovely ta yi rashi. Kinga Nasiba kidaina sa damuwa a ranki Jawahir batada matsalar komai, mubar wannan maganar yanzu kud'in da naturo maki sun isa ko kuna buk'atar k'ari. Girgiza kai tayi tace bana buk'atar k'ari na wajena sun isheni dan ni ba wani taron da zanyi. Shikenan rabin ran duk yadda kikeso haka za'ayi. Murmushi tayi tace nagode sosai Lovely. Hirarsu suka cigaba da yi cike da shauk'i da k'aunar juna har saida aka fara kiran sallar magrib sannan sukayi sallama yatafi gida. Ranar alhamis aka gabatar da wa'azi wanda mutane d'aid'ayane suka halarta sakamakon rashin gayyar da amarya tayi ko ma ace ita da danginta sukayi duka abokanta mutum ukku tagayyata sai 'yan uwa, amarya ta yi kyau sosai anyi wa'azi me ratsa jiki inda aka ci aka sha. Ranar juma'a kuma akayi ma amarya lalle, inda ranar asabar aka d'aura auren faruk Sani Maishadda da amaryarshi Nasiba Sufyan Mai Nasara akan sadaki mafi daraja wanda dubban mutane suka halarci d'aurin auren kasancewarsu 'ya'yan manya yasa aurensu yazagaye cikin garin katsina da gidajen yad'a labarai ko da rabi da kwatan mutanen duk na 'bangaren ango ne dan amarya basu wani yi gayyaba saidai dangi, abokan mahaifinta ma wasu sun halarci d'aurin auren, ango baki k'in rufuwa yayi saboda farin ciki ga jama'a da suka dinga mashi Allah yasa alkhairi su Barr Nas da Barr Junaid manyan abokan ango sin sha babbar riga sune suka dinga haba haba da jama'a. Gidajen biyu cike suke da jama'a ana ta hidima abunka da bikkin masu kud'i haka aka dinga fiddo naira. Mutanen Kebbi tun ranar juma'a suka iso Katsina ammah banda su Jawahir da suke jarabawa a islamiyya itama ta so zuwa saidai Exams d'in tahana dan an d'aga masu ita ne da tuni sun gama a lokacin baifi guda hud'u sugama ba, Mom bataji dad'iba koda sukayi waya tace tazauna tayi jarabawarta inyaso idan sun gama sai tazo tayi masu hutu da hakan Jawahir ta mince, saidai takira ango tayi mashi Allah yasa alkhairi. A 'bangaren Nasiba ta sha kyau har ta gaji dan gyarane ta sha shi saidai da kaganta ka san tana cikin damuwa wanda ba komai yaja hakanba sai tunanin rabuwa da gida da zatayi tafuskanci sabuwar rayuwa, Nasiha iri iri tasha a wajen mahaifiyarta da dangin iyayenta. Da marece angwaye suka zo da motoci aka d'auki amarya aka kaita a chan gidan angonta da ke chan Goruba Road, gida ne na gani na fad'a dan tun daga tsarin ginin zuwa kayan da aka zuba mashi komai ya ji, shi kanshi Faruk part d'inshi iyayenshi sun tsara mashi sosai dan duk kayan da suke ciki saida aka kwashe aka canza mashi sabbi abunka da d'an gata. 'Yan kawo amarya sunyi santin gidan da tsarinshi inda wasu daga cikinsu suka dinga ma gidan vedio, Nasiba dai tana zaune a tsakiyar royal bed d'inta k'udundune cikin mayafinta inba hawaye ba babu abinda take. Bayan sallar magrib jama'a suka fara watsewa yarage daga amarya sai yayyenta da k'awarta d'aya me suna Amrah, Amrah aminiyar Nasiba ce tun tashinsu hatta karatunsu tare sukayi a school guda babanta wani hamshak'in me kud'i ne zama a iya cewa yana cikin mak'arraban gwamnati, su suka sake gyara mata gida tas aka kunna turaren wuta. Sai wajen k'arfe tara su angwaye sukazo tun kafin su shigo su Aunty Sadiya suka sa'be suka tafi aka barta tadinga kuka hatta Amrah tafiya tayi saboda kiran da aka dinga mata a gida. Nasiba kuka tadinga yi har angwaye suka shigo duk surutan da suka dinga bata ma san abinda suke cewa ba dan hankalinta baya wajensu, Faruk ko rawar jiki yadinga yi yanaso sutafi subar mashi amaryarshi ammah suka k'i saida yaja Barr Nas gefe yace ya kamata yace sutafi hakanan dare yakeyi, shi ko Barr Nas mi zaiyi inba dariya ba koda suka dawo yakalli su Barr Junaid yace toh ku sai kuzo mutafi tun kan ango yabiyomu da ta'barya su dukansu dariya sukayi Barr Junaid yace ai naga alama angon nan ya k'agara mutafi dan ina lura da irin kallon da yake mana, toh arufe mana taro da addu'a kafin muwatse tunda mun rako ango gidanshi lafiya. Faruk shuru yayi yak'yalesu suka dinga mashi shak'iyanci. Cikin abokansu ne d'aya daga ciki yayi masu addu'ar zaman lafiya sannan sukayi masu sallama suka tafi Faruk yarakasu saida suka bar gidan sannan yarufe yadawo yasamu amaryarshi a inda yabarta har lokacin k'udundune take cikin mayafi tana sheshek'ar kuka. Daga gefenta yazauna tare da yin sallama ahankali, jin shuru yasa yakai hannu yayaye mayafin nan tayi saurin runtse idanunta yace haba Hearty miye abun kuka a ciki yau fa ranar farin ciki ce agaremu godiyarmu yakamata mununa ma ubangiji akan wannan ranar da yanuna mana. Shuru tayi nan yad'ago fuskarta yana goge mata hawaye saida yatabbatar ta daina kukan sannan yasata taje tayi alwallah sukayi sallah bayan sun gama sunyi duk abinda yadace daga nan yafita yakoma part d'inshi dan haka Nasiba tasamu damar yin wanka koda d'ar d'ar kawai take gabanta yana ta fad'uwa tana fitowa tashirya cikin sauri tagama duk abinda zatayi tahaye gadonta takwanta bata dad'e da kwanciya ba taji Faruk ya bud'e k'ofa ya shigo saurin runtse idanu tayi kamar me bacci tana ji yahau gadon yakwanta gefenta muryarshi taji saitin kunnenta yana cewa Hearty ba dai kinyi bacci ba?. Shuru tayi nan yai murmushi tare da janyota jikinshi yana cewa ban yarda ayi wannan baccinba dan yau ranar farin ciki ne agaremu ya kamata mununa ma juna irin son da muke fad'a muna yi ma juna, shafata yafara yi Saurin tura kanta tayi cikin k'irjinshi nan yai murmushi tare da kai hannu yakashe bedside lamp daga nan wasa yacanza..... Washe gari Faruk lalla'bata yadinga yi nan tadinga narke mashi tana zuba shagwa'ba, breakfast daga gidansu Faruk aka aiko masu da shi tun kan sutashi bacci, tare sukayi wanka suka shirya sannan suka fito sukayi breakfast Nasiba tana ta narkewa shi ko sai rawar jiki yakeyi akanta. A ranar bai lek'a ko k'ofar gida ba yana nan manne da matarshi indai ba masallaci zai je ba, sai magrib sannan yafita nan Nasiba tasamu damar shirya kayanta. Bayan sallar isha'i Faruk yadawo gida nan sukayi wanka suka yi dinner sannan suka zauna a parlornshi suna kallo, Nasiba manne mashi tayi a jiki inda shi kuma idanunshi suke a lumshe kamar me bacci gabad'ayansu babu ma meyin kallon, fuskarshi taji ya tura cikin gashin kanta tare da k'ara matseta a jikinshi nan itama tak'ara narke mashi, muryarshi taji ahankali kamar me jin bacci yana cewa Hearty ina k'aunarki da dukkan zuciyata tabbas sonki a cikin jinin jikina yake ji nake kamar a mafarki yau nine tare da wadda nafi k'auna a matsayin mata agareni. 'Dago kanta tayi takalleshi tana murmushin jin dad'i tace tabbas nima ina cikin farin ciki sosai da ubangiji yamallaka min kai a matsayin miji agareni ina ji a raina na fi kowace mace dace da samun miji irinka, shima idanu yazuba mata yana mata wani shu'umin kallo. Saurin maida kanta tayi takwantar a k'irjinshi nan yashafa bayanta yace Nasiba indai har zaki kula da ni toh ni kuma zan nuna maki cewa babu wata mace a cikin duniyar zuciyar Faruk indai ba ke ba. Wani irin dad'ine taji sosai dan kalamanshi sun ratsata, ahankali tace inko hakane zan baka kulawa wadda babu namijin da yata'ba samun irinshi, fiye da yadda uwa take son d'anta, zan nuna maka tattalin so da k'auna zallah dan Allah Faruk karik'eni amana. Bakida damuwa da wannan matata yanzu sai kitashi muje anuna min son da ake min wanda yafi wanda uwa take ma d'anta. Tun kan yarufe baki tayi saurin d'ago kai ta kalleshi, d'aga mata kira yayi nan taturo baki tace nidai a'a. Kallon agogo yayi yace tunda dai har kika fad'a ya zama dole in gani a ido domin gani ya kori ji kinga ma yanzu dare ya yi muje kawai malama. K'walla ce tacika mata idanu tace dan Allah kayi hak'uri kaga fa ban warkeba. Cak yad'auketa yace ai aikin lada ne zakiyi muje kawai amaryata. Nasiba ji take kamar tafashe da kuka dan ita kad'ai tasan irin wahalar da tasha hannunshi jiya, a bedroom d'inshi yawuce da ita saidai ji tayi ya safketa saman gadonshi nan shima yahau, cike da tsoro kamar zatayi kuka tace dan Allah kar kayi min komai Allah ciwo nake ji. Shareta yayi yakashe bedside lamp sannan yajanyota jikinshi yarungume, ahankali cikin kunnenta yarad'a mata cewa kikwantar da hankalinki hearty babu abinda zanyi maki bacci kawai zamuyi dan nima ina tausayinki Allah dai yayi maki albarka domin kin faranta min. Murmushin jin dad'i tayi nan hankalinta yakwanta tagyara kwanciyarta a cikin kunnenta taji yana rad'a mata kalamai masu ratsa gangar jiki ahaka har bacci yayi awon gaba da ita. ____________ Khausar kallon Jawahir tayi da take kwance ta d'age kai sama tana kallon ceiling tace wai ke sister tunanin me kike tun d'azu. 'Dagowa jawahir tayi takalleta tace ni ba tunani nakeba kawai dai ina tunanin rayuwane. Uhm ko kuma kina tunanin zuwa Katsina dan na ji kince ma Mom da anyi hutun islamiyya zakije masu hutu. Cikin sanyin jiki tace Khausar bazanje katsina ba a nan zanyi hutuna tunda hutun sati biyu ne aka bamu. Kai Sister ammah dai da baki kyauta ba kinga ko bikkin Barrister bakije ba muna jarabawa lokacin, kuma yanzu sai kik'i zuwa kiyi masu Allah yasa alkhairi ko d'an man shanu musha, dan ma naga Barrister yanzu tunda yayi aure tsawon kwana biyu baku gaisaba ko fushi yake da rashin zuwanki bikkinshi. Jawahir runtse idanunta tayi dan itama kanta abun yana damunta ta yi tunanin dalilin dai rashin zuwanta ne yasa tun ranar d'aurin aure da takirashi tayi mashi Allah yasa alkhairi basu sake wayaba, toh ko dai yana fushin da ni dagaske? Muryar Khausar taji tana cewa yoh wa yasanar maki sai kikira kitambayeshi. Shuru tayi bata sake cewa komai ba dan bata d'auka a fili tayi maganar ba. A ranar da marece tana cikin game da wayarta kiran Faruk yashigo tsayawa tayi tana kallon wayar cike da mamaki cikin ranta tace yau kuma antuna da ni kenan. Har saida takusan tsinkewa sannan tayi picking tare da yin sallama, daga chan 'bangaren Faruk da yake kwance saman cinyar Nasiba amsa mata yayi tare da cewa k'anwata fushi nake da ke. Murmushi Jawahir tayi tace kayi hak'uri yayana na san na yi laifi kuma na baka uzurina. 'Dago kai yayi yakalli Nasiba da itama take kallonshi nan suka sakar ma juna murmushi sannan yace anya kuwa uzurin nan naki zai kar'bu bayan bakizo kika ga amaryata ba. Daga chan 'bangaren Jawahir murmushi tayi tace Allah sarki ni, dan Allah Yayana ayi min hak'uri zan zo. Nasiba ce tace bazan hak'uraba k'anwata har sai kinzo kin goge laifinki. Murmushi Jawahir tayi dan ta jiyo abinda tace, Faruk ne yace kindai ji abinda tace ko? Bari ma inbaki ita kuyi magana. Cikin jin kunya tace a'a Yaya Faruk Allah kunyarta nakeji. Dariya yayi yace nidai babu ruwana gatanan sai k'anwar lauya tasan yadda zata kare kanta,,, wayar yamik'a Nasiba da take ta dariya. Itama Jawahir 'yar dariyar tayi jin Nasiba ta yi sallama yasa ta amsa tare da cewa Auntyna ina wuni? "Uhm bazan amsaba fushi nake" Marairaicewa tayi tace dan Allah kiyi hak'uri wallahi ina son zuwa lokacin exams muke a islamiyya ammah zan zo. Toh shikenan k'anwata na kar'bi uzurinki ya dai kamata kizo idan kun gama dan ga d'aki nan mun ware nakine kinga sai kiyi mana hutun nan kafin akoma. Dariya Jawahir tayi tace d'aki kuma Auntyna. Eh man mu dai muna jiranki. Faruk ne yace kibarta hearty idan tayi wasa dakanmu zamuje har chan KEBBI mud'aukota. Jawahir rage fara'ar fuskarta tayi tace zan zo insha Allahu Yayana ayi hak'uri. Toh shikenan Jawahir sai kinzo muna godiya sosai. Bakomai Auntyna nima nagode nan sukayi sallama takashe wayar, ta'be baki tayi ta ajiye wayar sannan tamik'e tafito tsakar gida tasamu Inna Mairo zaune tana cin k'uriga nan itama tazauna gefenta tad'iba tafara ci. Faruk kallon Nasiba yayi da take rik'e da wayarshi yace k'anwarnan tawa gudun garin nan take na lura da ita bata son zuwa. Cikin sanyin jiki Nasiba tace wallahi Lovely banga laifinta ba saboda abinda su Daddy sukayi mata basu kyautaba sun cutar da rayuwarta sun rabata da duk wani farin cikinta ni wallahi har kunyarta nakeji,,, k'walla ce tacika mata idanu ganin haka yasa Faruk yace Nasiba haka ubangiji yak'addara babu wanda ya isa yacanza k'addararshi. Cikin muryar kuka tace kaduba kagani lovely duka yarinyar nan nawa take ammah ace jawarci take. Kinga Nasiba banaso kiyi min 'barnar hawayenki komai yasamu bawa daga ubangiji ne banason kina shiga damuwa Goge hawayenta tayi nan Faruk yafara lalla'bata yana lallashinta cikin dabara yasamu yarabata daga damuwar da tashiga. ___∆∆∆∆∆____ Dad kud'ad'e yafitar akayo order d'in duk kayan aikin da ake buk'ata inda yazuba ma'aikata sosai a cikin companyn Jawahir aka fara gudanar da aiki nan da nan company yafara ha'b'bakowa dan shi Dad mutum ne mekula sosai da sanin makamar aiki. A cikin gidan Kaso su Alhaji Mansur da Alhaji Sufyan aiki ake saka su sosai ana wahalar da su babu wanda zai ce ga matsayinsu a da, sunyi nadamar abinda suka aikata sosai dan basusan rayuwa zata juye masu hakaba gashi gabad'ayansu babu wanda iyalanshi yazo dubashi, sunyi bak'k'i sun rame duk sun fita hayyacinsu kullum cikin aibata junansu suke da da sun sani kuka ko ba'a magana musamman idan suka tuna akwai ranar da ma za'a rabasu da rayuwarsu gabad'ayanta. ****** ******* Jawahir bayan ta dawo daga gidan kitso ganin Baba Malam tayi zaune shi kad'ai a bisa 'yar kujerarshi a k'ofar gida yana sauraren radio, wajenshi tanufa tatsugunna tagaisheshi yace Jawahir har an dawo?. Eh Baba Malam. Toh sannunki. Yauwa Baba. Ganin yadda tayi yasa yagane akwai magana a bakinta dan haka yace Jawahir kisanar da ni duk abinda yake cikin ranki kar kidamu zan fahimceki. Ahankali tace am daman Baba wata 'yar alfarmar nake nema a wajenku. Toh ina saurarenki. Shuru tayi sai kuma chan tace dan Allah idan ba zan takura maku ba inaso ataimaka asamo min makaranta incigaba da karatuna. Shuru yayi yana saurarenta ganin daga nan bata sake cewa komai ba yasa yace toh jawahir bazank'i ta takiba ammah da son samune zan fi so ace aure kikayi tunda kinga wanchan mijin naki ya rasu aure shine mutuncinki ammah zaki iya fara karatun kafin Allah yakawo mijin inyaso sai ki ida karatun a gidanki dan ni kinga gaskiya babu d'iyar da nake bari tayi karatu a gidan nan saidai tafara ta ida a gidan mijinta, yanzu haka kinga Khausar da Rashida an tsaida ranar aurensu watanni ukku suka rage ayi bikkin, idan hakan ya yi maki ba matsala. Jikinta sanyi yayi cikin ranta tace chakwakiya kenan ni ina naga wani manemin aure ni da babu ma aure agabana yanzu na fi son inyi karatu inyaso daga baya idan da rabo zanyi aure. Ganin ta yi shuru yasa yace Jawahir rayuwarki ta fi had'ari tunda kin ta'ba aure saisa nafison kiyi aure saidai komai lokacine idan Allah ya kawo maki mijin sai ayi auren. Cike da ladabi tace toh Baba Malam nagode sosai insha Allahu zan kasance me biyayya agareku. Cikin jin dad'i yace yauwa Jawahir Allah yayi maki albarka. Amsawa tayi da Ameen tace atashi lafiya sannan tamik'e cikin sanyin jiki tashiga cikin gida, 'bangarensu Khausar tawuce tasameta kwance tana bacci dan haka tafito takoma 'bangarensu. Tunda tazauna tunanin maganar Baba Malam kawai take wai ya fi son tayi aure ita kuma a yanzu bata shirya ma aureba a tsarin rayuwarta ta fi so tayi karatu tazama wani abu wadda za'ayi alfahari da ita, ammah yanzu taya ma zata iya fara yarda tayi soyayya koda ta san d'an zamanta a garin mutanen da suka dinga zuwa wajenta da sunan so suna da yawa. Wasu siraran hawaye ne suka gangaro mata ahankali tace Abba kun cuceni duk kune kuka ja min da ace kun barni na cigaba da karatuna da duk hakan bai faru ba, goge hawayen tayi tare da cewa na mik'a ma ubangiji lamurrana domin shi ya fi kowa sanin halin da nake ciki Allah kaza'ba min abinda zaifi zama alkhairi a rayuwata. ******* ******** Faruk da Nasiba soyayyarsu kawai suke sha suna kula da junansu sosai ko da ace Faruk yana wajen aiki tana k'ok'arin kiranshi ko shi yakirata dan kawai suji lafiyar juna. Faruk yana k'ok'arin zuwa dubo Ummah a asibitin da ake jinyarta har tafara samun sauk'i saidai duk k'ok'arin da suke akanta 'barin jikinta guda ya shanye bata iya komai daga k'arshe ma suka nemi susallameta takoma gida zasu d'aurata akan magani dan bazata ta'ba komawa daidai ba. Faruk amincewa yayi da hakan nan yasa aka kwashe duk kujeru da kayan d'akin da suje gidansu Jawahir aka kaisu a gidan da taba ummah, gidane madaidaici me d'auke da d'akuna ukku kowane ciki da parlor. A ranar da aka sallameta gidan yawuce da su itada masu jiyyarta su biyu inda d'aya daga cikinsu yayartace tana aure a chan funtua dan haka suka dawo gidan itada mijinta dan cigaba da kula da 'yar uwartata da a yanzu sai anyi mata komai kamar yadda Faruk yabata shawara. Ummah kuka tayi sosai lokacin da Faruk yasanar da ita kyautar da Jawahir tayi mata na gidan da mota sai kuma kud'ad'en da tabada abata. Kuka tadingayi tana cewa kaicona ina ma ace ban zalunci wannan yarinyar ba ko da sau d'aya ban ta'ba kyautata mataba daga ita har mahaifiyarta, yanzu ga shinan yadda rayuwata takoma dan Allah ina zanganta in nemi gafararta. Faruk yace kar kidamu duk abinda Jawahir tayi maki cancantane yasa hakan sannan zuciyar jawahir mekyau ce akowane lokaci tana da burin kyautata ma mutane kidaina sa damuwa a ranki kinji dai abinda likita yace kafin kubaro asibiti. Motsa 'barin jikinta me lafiya tayi tace dole inyi kuka Faruk dan na cutar da yarinyar nan fiye da tunanin wani me tunani sai gashi rayuwa ta juya min na rasa komai nawa a yanzu itace take taimakona dan tarufa min asiri. Lallashinta suka dinga yi tayi shuru nan Faruk yadamk'a masu komai sannan yasa aka kawo masu kayan abinci sosai wanda yafitar da kud'inshi yasiyesu dan kawai saboda su. Haka suka dinga yi mashi godiya suna shi mashi albarka har yatafi. *BAYAN WATA UKKU* Nasiba ce tafito daga kitchen d'auke da Cup a hannunta jikinta sanye cikin kayan bacci tanufi d'akin Faruk, tana shiga zaune yake ya d'aura laptop a saman cinyarshi yana wani aiki, daga gefenshi tazauna tace wash sannu lovely. Batare da ya kalletaba yace kema sannunki hearty. Hmm kaine da sannu kaida tun d'azu kake faman aiki yauwa lovely dan Allah akwai maganar da nakeso muyi da kai. Janye laptop d'in yayi tare da janyota yad'aura bisa cinyarshi sannan yace ina saurarenki hearty wace magana kikeson muyi? Murmushi tayi tamik'a mashi cup d'in da tashigo da shi tace toh kasha wannan kajik'a mak'oshinka sannan muyi maganar. Amsa yayi bai musaba yasha saida yashanye kunun ayar da takawo mashi tas sannan yace toh ina saurarenki. Kwantar da kanta tayi a k'irjinshi sannan cikin sanyin murya tace dan Allah Lovely kataimaka muje Kebbi wajen Jawahir muganota ko da wuni guda ne tunda ita har yau bata lek'o mu ba. Jan hancinta yayi yace kedai baki gajiya, toh ai ita yakamata tazo taganki. 'Bata fuska tayi kamar zatayi kuka tace dan Allah Lovely kataimaka muje mu ai sai mukwashe ladar zumuncin. Hmm tunda kince haka shikenan kibari sai weekend sannan muje wuni guda mudawo. Rungumeshi tayi tace nagode sosai Lovely Allah yasaka da alkhairi, ai kam saidai kawai mubata mamaki dan bama zata san zamuje ba. Hamma yafara yace kinga tashi muje mukwanta dan ni nan na gaji aikin ma bazan ida shi ba sai zuwa gobe. Shagwa'be fuska tayi tace toh saidai kad'aukeni muje. Cicci'barta yayi yace toh ya zanyi ai dole inyi yadda kikeso amaryata. Dariya tayi tace a'a ni yanzu ba amarya bace ai na kwana biyu. Baice mata komai ba saida yadireta saman gado sannan yace toh ke micece? Maimakon tabashi amsa sai ma juyawa da tayi tana murmushi dan haka shima yakwanta daga bayanta tare da kashe masu haske..... _Sis Nerja'art✍🏻_ [7/24, 11:21 PM] Sis Nerja'art 2: *......FANSAR RAI......* *INTELLIGENT WRITER'S ASSO....®* [On Ward Together] _Follow me on Wattpad: *Sis-nerja*_ _Wannan Littafin na kud'i ne domin karantawa cikin aminci da yarda ga duk me buk'ata zai turo katin Mtn na d'ari biyu N200 kacal ta wannan number d'in 09035938246, ko ta account number 5330055604, Idan katura ka aiko da screen shot na transaction a wannan number d'in 09035938246_ _Akwai gara'basar *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shahararriyar marubuciyar nan *AMEENA ABBA UMAR* tare da novel d'in *FANSAR RAI* akan farashin N300 kacal, ko da kud'in ka sai da rabonka_ *PAGE 25* Ana saura kwana ukku suje Kebbi Nasiba tamatsa mashi suka je gidan su Dad, sunyi farin ciki da zuwansu nan Mom tadinga nan nan da ita dan tana son Nasiba sosai, a chan suka wuni sai dare sannan Faruk yaje zai d'akkota. Suna a parlor zaune suna hira ita da Mom nan Faruk yakalleta yace sutafi dare ya yi. Amsawa tayi da toh sannan tace Ammah kafin mutafi ina son zamuyi wata magana da su Mom daman tun d'azu naso yinta sai kuma naga Dad ya fita. Muryarshi sukaji ya ce toh gani na dawo me za'a fad'a min Su duka juyawa sukayi suka kalleshi sukai murmushi Mom tace ashe kana kusa. Shima murmushin yayi yace Eh wallahi wani meeting ne yatsaida ni saisa kuka ji ni shuru har wannan lokacin ban dawo ba. Sannu da zuwa sukayi mashi nan yashigo yazauna yana cewa wace magana ce d'iyartawa takeson yi da mu? Faruk kallonta yayi yai murmushi sannan yamaida kallonshi ga iyayenshi yace wai maganar zuwan da zamuyi Kebbi zata fad'a maku batasan munyi maganar ba. Eh toh kusan itace ammah ba ita bace. Mom tace toh shikenan d'iyata fad'a mana fatana dai ba matsala bace kuka fara samu da mijin naki? Duk'ar da kanta tayi cikin nutsuwa tace Mom Dad dan Allah alfarma nake nema wadda na san wajenku ne kawai zan iya nemanta. Da mamaki suke kallonta sukace wace irin alfarma ce Nasiba kifad'i kowace irice insha Allahu zaki sameta. Shuru tayi na d'an lokaci sai kuma chan tace dan Allah so nike kurok'ar man Faruk ya auri Jawahir. Su duka idanu suka zuba mata mamaki k'arara a fuskarsu, Faruk ne yayi k'arfin halin cewa Nasiba wannan wace irin magana ce kikeyi kinsan abinda kike fad'a kuwa? 'Dagowa tayi takalleshi idanu cike da k'walla tace tabbas na san abinda nake fad'a Faruk ina son kataimaka ka auri Jawahir domin ko bakomai ta cancanci hakan ya kamata muyi duba da rayuwarta ita d'in yarinya ce me k'arancin shekaru tana buk'atar auren miji wanda zai bata kulawa sosai wanda zatayi farin cikin kasancewa da shi a matsayinta na marainiya na tabbata kaine kad'ai zata iya aura tasamu wannan gatan domin kai ka san halin da take ciki zaka tausaya ma rayuwarta. Mom ce tayi k'arfin halin cewa keko Nasiba miyasa kikayi wannan maganar har kikeso mijinki yak'ara aure? Hawaye ne suka gangaro daga idanunta tace Mom banaso inkasance mace me son kanta dayawa na san ina son Faruk kuma ina da kishi saidai ina ji a raina kamar idan Jawahir bata auri Faruk ba banyi ma kaina adalci ba domin shine kad'ai namijin da yadace ya aureta. Wani irin kallo yawurga mata yace kar kisake wannan maganar kitashi mutafi gida tunda bani nace maki ina buk'atar k'ara aureba kuma duka wata nawa da yin bikkinmu har zaki wani ce ink'ara aure sannan Jawahir da kike gani matsayin k'anwa take a wajena ba wai sonta nake ba. Had'e hannuwanta tayi waje guda alamun rok'o tace dan Allah Faruk kar kak'i amincewa da auren Jawahir wallahi na amince zan zauna da ita da zuciya d'aya domin ita d'in zuciyarta mekyau ce, shin ni idan nice zan so ace wani nawa ya fad'a irin halin da Jawahir take ciki? Ya kamata kayi tunani rayuwarta tana buk'atar tallafi duk yadda zataji dad'in zama a wajen kakanninta bazai ta'ba kai zaman da zakayi da ita ba domin na tabbata zaka bata duk kulawar da tadace, na maka alk'awali zamuyi zaman lafiya da ita zamu kasance abun koyi ga duk sauran mata har ayi alfahari da mu,, Kasa cemata komai yayi saidai kallon mamaki da yakeyi mata. Juyawa tayi takalli Mom da Dad tace dan Allah ina rok'onku kusa baki a ciki Dad na san ku zaku fahimci abinda nake nufi wannan dalilin ne yasa ban ta'ba mashi maganar ba sai yau da muke zaune a gabanku wallahi tun kan muyi aure da Faruk nasa ma raina ba zan ta'ba zama ni kad'ai da shi ba zai kasance mijinmu ni da Jawahir domin wannan shine adalcin rayuwa ko bakomai mahaifina yana cikin mutanen da suka ruguza mata duk wani farin ciki nata, dan Allah Dad kutaimaka kufahimci abinda nake nufi. Jinjina kai Dad yayi yace tabbas Nasiba ke mace ce me adalci kinsan abinda yakamata, banyi niyar shiga cikin maganar nan ba na fiso kuje kuyi shawara a tsakaninku idan shi ya amince zai aureta to mu bamuda matsala yadda duk kuka tsara daidai ne ko Hajiya?. Mom da take kallon Nasiba cike da mamaki d'aga kai tayi tace hakane Alhaji suyi shawara a tsakaninsu kawai zai fi. Fashewa da kuka Nasiba tayi tace dan Allah Dad kutaimaka kusa baki a ciki na tabbata kune kad'ai zakuyi mashi magana yasaurareku wallahi idan har bai auri Jawahir ba banyi ma rayuwata adalci ba ta rasa mijinta a lokacin da take buk'atar shi kuma duk ta silar su mahaifina dan Allah na rok'eku Mom kuce wani abu. Ganin yadda take kuka yasa su dukansu suka ji tausayinta Dad yace kidaina kuka hakanan Nasiba, sannan yamaida kallonshi ga Faruk da yahad'e fuska idanunshi suna a kan waya yana dannawa kamar baisan abinda ake tattaunawaba Dad yace toh kai Faruk ka ji abinda matarka tace tana neman wannan alfarmar. 'Dagowa yayi yakalli mahaifin nashi yace Dad ni fa ban da burin auren mata biyu. Duk da haka Faruk tunda matarka ce tanemi kayi auren sai kataimaka kayi bare ko bakomai Jawahir ta cancanci ka aureta. Ammah Dad duka aurenmu fa wata ukku da yinshi. Toh ai ba matsala bane. Faruk juyawa yayi yakalli mahaifiyarshi da jikinta yayi sanyi sosai nan tad'aga mashi kai alamun Eh. Duk'ar da kanshi yayi k'asa yama rasa abida zaice ganin iyayen nashi duk sun goya ma maganar Nasiba baya. Nasiba idanu tazuba mashi tana jira taji abinda zai ce har lokacin hawaye basu daina fita daga idanunta ba. Jin ya yi shuru yasa Dad yace kai muke saurare Faruk. Sai da yayi kusan minti ukku sannan yace shikenan na amince. Saurin rik'oshi Nasiba tayi tace dagaske ka amince zaka aureta? Harararta yayi yace tunda kun nuna kuna son hakan. Janye hannunta tayi daga rik'on da tayi mashi cikin sanyin jiki tace dan Allah kar kayi duba da abinda mukeso kataimaka kaima kaso auren a cikin ranka insha Allahu zakayi alfahari da mu. Toh wai Nasiba ita d'in Jawahir tace maki batada wanda take so? Jim tayi sannan tace na tabbata insha Allahu bata da shi. Jinjina kai yayi yace shikenan ammah da sharad'i guda idan dai har tana da wanda takeso dole mubarta ta aureshi,,, Cewar Faruk. Tace toh shikenan na yarda da wannan. Dad da Mom dai idanu suka zuba masu suna kallonsu cikin ransu suna jinjina ma k'ok'arin Nasiba dakanta take neman mijinta yak'ara aure wanda itama d'in basu dad'e da yin auren ba. Nasiba godiya tayi mashi sannan tajuya tayi ma su Mom su ma godiya. Addu'a su Dad suka dinga yi mata dan tabbas sunsan d'an nasu ya yi dacen mata dan samun irinsu Nasiba a yanzu sai an tona, mik'ewa Faruk yayi yai ma su Dad sallama sannan yace kisameni waje ina jiranki. Itama mik'ewar tayi tai masu sallama sannan tabi bayan Faruk da tuni ya yi gaba. Suna fita Mom kallon Dad tayi tace oh Alhaji kaga ikon Allah wallahi Nasiba yarinyar kirki ce ta san abinda yakamata. Jinjina kai Dad yayi yace ai kedai bari gaskiya Nasiba ta yi kuma nima kaina na ji dad'in hakan da tayi dan tuni nayi ma Faruk sha'awar auren Jawahir dan nasan zasu dace kuma ko bakomai shi zai kula da maraicinta. Ammah Alhaji yanzu kana ganin shi Faruk d'in zai aureta kalli fa yadda yanuna baya sonta. Murmushi Dad yayi yace Hajiya kibarni da shi kawai. Mom tace toh shikenan Alhaji Allah dai yatabbatar mana da alkhairi. Amsawa yayi da Ameen. Tunda suka shiga mota suka kama hanyar gida Faruk shuru yayi Nasiba ko ganin yadda yad'auke kai yasa tayi shuru dan ta san fushi yake da ita. Suna isa gida d'akinta tawuce, zama tayi bakin gado tadafe kanta nan wasu siraran hawaye suka gangaro mata saurin gogesu tayi tamik'e taje tayi wanka tai shirin kwanciya sannan tafito tanufi part d'in Faruk. Tana shiga tasameshi kwance murmushi tayi tace Lovely har ka kwanta kenan? Shuru yayi nan tataka ta isa wajen gadon takwanta daga bayanshi tana kwanciya yakai hannu yakashe hasken d'akin. Matsowa tayi kusa da shi cikin sanyin murya tace Lovely dan Allah kayi hak'uri idan har abinda nayi ya 'bata maka rai wallahi banyi hakan da wata manufaba nayi ne saboda hakan shine dacewa. Muryarshi taji ya ce Nasiba a wajenki ne hakan yake dacewa watau shine zaki d'auki maganar da kika tsara kije kifad'a ma iyayena koda ace ni bana da ra'ayin hakan ke tunda kinaso dole kenan inyi ke awajenki hakan kin min adalci. Fashewa tayi da kukan da tun tuni yake cinta ammah tadanne shi sai a lokacin tasamu damar yin shi, cikin kuka tace dan Allah Faruk kayi hak'uri banyi hakan saboda son zuciya ba, nayi ne kawai saboda ina tsoron alhakin abinda mahaifina yayi mata yahau kanmu banda kwanciyar hankali a duk lokacin da natuna mahaifinmu ya bamu munci da hak'in wata ya suturtamu da hak'in wata ya salwantar da ran wasu, dan Allah Faruk kataimaka ka auri Jawahir ba dan halinaba na san kai mutumin kirki ne kuma me fahimta zaka fahimci abinda nake nufi dan Allah kayi min wannan taimakon ko da ace shine taimako na k'arshe da zakayi min a duniya, na maka alk'awali zamu zauna lafiya tamkar 'yan uwan juna please Faruk kataima min,,, nan tasake fashewa da wani sabon kukan. Wani irin tausayinta ne yad'arsu a ran Faruk, juyowa yayi yafuskanci inda take tare da rungumota jikinshi cikin lallashi yace Nasiba kidaina kukan nan bana so kinsan dai banason jin kukanki, shikenan na amince zan aureta ammah da sharad'i d'aya. Saurin d'agowa tayi takalleshi tace wane irin sharad'ine dan Allah kafad'a min insha Allahu zan kiyaye. Idanu yazuba mata yana kallon cikin idanuwanta sannan yace sharad'in shine idan har Jawahir tana da wanda takeso dole kijanye daga k'udurin nan dan bazan ta'ba amince ma aurenta ba idan tana son wani na daban domin gudun kar incutar da ita. 'Daga kai tayi tace ba damuwa na amince da wannan sharad'in. Gyara mata kwanciya yayi a jikinshi yace toh shikenan yanzu muyi bacci dan ni bacci nake ji. Toh nagode sosai Lovely Allah yasaka da alkhairi Allah yabarmu tare. Amsawa yayi da Ameen daga nan kuma babu wanda yak'ara cewa komai daga cikinsu kowa da abinda yake tunani a cikin ranshi. *********** Ranar juma'a Faruk yakira Baba Nura yasanar sa shi zuwan da zasuyi da amaryarshi dan dama suna gaisawa sosai ko bayan bikki saida Baba Nura yazo yaga amarya yai masu wuni guda, a ranar Faruk yaje yayi masu booking d'in jirgi. Washe gari jirgin k'arfe goma sha d'aya suka bi suka je Kebbi wajen sha biyu sun isa Baba Nura yaje yad'aukosu daga airport. Suna isa gidan tarba me kyau akayi masu musamman Nasiba a 'bangaren su Inna Mairo tazauna matan 'yan uwan maman Jawahir suka zo aka dinga gaisawa cikin mutunci da sakin fuska ana mata Allah yasa alkhairi na aurensu. Nasiba haka tadinga gaisawa da mutanen gidan cikin sakin fuska dan a lokacin da sukazo su jawahir basu gidan sai wajen k'arfe d'aya suka dawo daga islamiyya saboda suna tsayawa tahafiz, su ukku suka jero suka nufo gidan ita da su Khausar da Na'ima lokacin su Baba Musa da su Faruk suna zaune a waje, Khausar ce tahangoshi tace lahh Jawahir wanchan kamar Barrister ne yazo. Batare da ta d'ago kanta da ke duk'e k'asa ba tace uhm kedai bakida aiki sai hango mutane ko ma ince sa ido toh bashi bane. Tsaki Khausar tayi tace kokuma kece bakida aiki sai afad'a maki magana kik'i yarda bayan baki d'ago kika ga kowanene ba, toh nidai na ce wallahi shine kuma kid'ago kigani. Jin ta rantse yasa Jawahir tad'ago dan tagane ma idanunta aiko d'agowar da tayi ya yi daidai da kallosu da Faruk yayi nan suka had'a ido. Saurin safke idanunta tayi k'asa tare da yin murmushi cikin ranta tace ashe dai shine wani irin dad'i taji ya d'arsu a ranta suna zuwa shiga gidan duk suka gaishesu sannan suka wuce zasu shige Baba Malam ne yace Jawahir bakiga Faruk ba ne? Tsayawa tayi nan su Khausar suka shige. 'Dago kai tayi takalleshi tana murmushi tace lah Yaya Faruk ashe kaine sannu da zuwa ina wuni? Murmushi yayi cikin ranshi yace lallai yarinyar nan har tad'ago takalleni muhad'a idanu shine yanzu zata wayance bata ganeni ba, basarwa yayi yace yauwa jawahir andawo islamiyyar ko? Eh Yaya Faruk ya su Mom da Dad? Hmm suna chan fushi suke da ke. Marairaicewa tayi tace Allah sarki ni wallahi inaso inje hutun ne ba'a bamu shi dayawaba lokacin ammah insha Allahu kwanan nan zan je inyo maku sati biyu, ina Auntyn tawa? Murmushi yayi yace kedai kije da dad'in bakinki kullum maganar kenan zakije ammah har yau shuru bakije ba ai Auntyn taki tana nan ciki sai kije kikaranta mata dad'in bakin naki k'ila ta yarda da ke. Cike da jin dad'i tace dagaske tare kukazo da ita? Eh tare mukazo zatayi maku wuni. Saurin juyawa tayi tace bari inje ingaisa da Auntyna wallahi na ji dad'i sosai. Su dukansu murmushi sukayi Baba Malam yace ina ruwan Jawahir. Cikin sauri tashiga 'bangaren Inna a parlor tajuyo muryarsu suna hira, d'age labule tayi tana cewa oyoyooo ga Auntyna. Nasiba na ganin ta shigo d'auke kai tayi tare da juyawa tace ni ba ruwana da ke fushi nake. Saurin matsawa gabanta jawahir tayi tatsugunna tace dan Allah Auntyna kiyi hak'uri wallahi ina so inzo Allah ne bai nufa ba. Inna Mairo ce tace kokuma bakiyi niyar zuwa ba Kai Inna bafa haka bane kinsan komai sai Allah ya yi, marairaicewa tayi tace dan Allah ba dan halina ba Aunty Nasiba kiyi hak'uri wallahi nima kaina na san ban kyauta ba. Sai a lokacin Nasiba tajuyo tace shikenan tunda kema kin gane baki kyauta ba na hak'ura ammah inji yaushe za'a zo mana. Murmushi tayi tace nagode sosai Auntyna insha Allahu ina nan tafe dan idan nazo sai na dad'e a wajenku. Hmm toh Allah yasa. Ameen Auntyna, nan suka gaisa tatambayeta gida da su hajitarta tace duk suna lafiya lau. Hira suka zauna suka dinga yi kamar daman irin sun san juna sosai har su khausar suka shigo suka gaisa. Bayan sunyi azuhur ne sunci abinci Inna Mairo tafito tsakar gida tana dafa madarar shanu, d'akin yarage daga Jawahir sai Nasiba dan su Khausar tunda suka shiga cikin gida basu dawo ba, kallonta Nasiba tayi tace dan Allah Jawahir ina k'ara baki hak'uri akan abinda mahaifinmu ya aikata maki wallahi bamusan komai ba akai. Kai Aunty Nasiba dan Allah kibar tuna abinda yawuce. K'walla ce tacika mata idanu tace dole intuna jawahir domin ko kema har kikoma ma mahaliccinki bazaki ta'ba mance hakan ba, kar kiyi k'arya a fili alhalin azuciyarki ba haka bane. Hawaye ne suka gangaro ma Jawahir tace tabbas nasan *DA CIWO A RAYUWATA* ammah babu yadda na iya komai muk'addarine dama chan Allah ya k'addara ba zan k'are rayuwata tare da iyayenaba *K'ADDARA CE* ta rabamu dan Allah mubar maganar Aunty Nasiba banaso tunawa domin inajin wani iri a duk lokacin da natariyo rayuwar da nayi a baya saidai ina jin d'an sanyi idan natuna da d'aukar *FANSAR RAI* na iyayena da nayi. Murmushi Nasiba tayi tace hakane Allah yajik'ansu yasa sun huta. Jawahir Amsawa tayi da Ameen daga nan kuma duk suka yi shuru. Inna Mairo ce tashigo da wani galan a hannunta tamik'a ma Jawahir tace jeki gidan Ladidi ki amso min Man Shanun da nabata ta dafa min d'azu. Amsa jawahir tayi tace toh nan tatashi tafita. Tana fita Baba Nura yashigo yace amarya kina nan anbarki ke kad'ai ko? Murmushi tayi tace a'a basu dad'e da fita ba ma yauwa dan Allah Malam Nura ko zaka taimaka kayi min magana da su Baba dan akwai magana me muhimanci da nakeso zamuyi da su. Baba Nura yace toh shikenan bari inje insanar da su. Fita yayi yaje yafad'a ma su Baba Malam sak'on Nasiba dan har lokacin suna zaune a k'ark'ashin bishiyar da yake zama saman tabarma dan a nan ma suka ci abinci, Faruk yana jin sak'on Nasiba yagane maganar da takeso tayi masu duk sai yaji wani iri. Haka suka tashi suka shiga cikin gida a tsakar gida aka shimfid'a tabarma Baba Malam, Baba Musa, Baba Jamilu, Baba Nura, Faruk sai Inna Mairo suka zauna daga chan gefe Nasiba tafito tazauna. Baba Malam ne yayi gyaran murya yace ance kina son magana da mu Allah dai yasa lafiya. Duk'ar da kai tayi cike da ladabi tace lafiya lau Baba daman wata alfarma ce nake nema a wajenku bansaniba ko zan sameta. Wace irin alfarma ce wannan?,,, baba malam yatambayeta. Kallon Faruk tayi sannan tace mijina nake son nema ma auren Jawahir. Su duka da mamaki suke kallonta, Baba Musa yayi k'arfin halin cewa keko wace irin magana kike ni na d'auka wata magana ce me muhimmanci taya zakice mijinki ya auri Jawahir bayan ba'a dad'e da bikkinku ba. Cikin sanyin jiki tace wannan maganar ma tana da muhimmanci dan Allah kutaimaka mana idan har hakan zai yuwu wallahi ni babu matsala na amince zan zauna da ita da zuciya d'aya ko bakomai rayuwar Jawahir yaci ace antausaya mata. Faruk ne cikin kwantar da murya yace zan auri Jawahir idan har kuka ban dama na yi maku alk'awali zan kula da ita bazan ta'ba bari tazubar da hawayeba tayi da tasani akan aurena ba amincewarku mukeso idan har batada wanda zata aura inkuma tana da shi shikenan sai in hak'ura domin komai nufine na ubangiji. Jinjina kai sukayi gabad'ayansu Baba Malam yace wannan gaskiya ne Faruk tunda dai har kaida matarka kun amince zaku zauna da ita tsakani ga Allah shikenan muma mun amince ka aureta domin ko bakomai ka cancanci hakan idan har muka ce zamu hanaka jawahir toh mun zama butulu dan ko halarcin da kayi mata ya ci ace mun amince, na yarda da kai 100% nasan zaka kula da ita da dukiyarta indai har ina da iko da Jawahir toh na mallaka maka ita. Su Baba Musa ne sukace wannan gaskiya ne muma mun amince da hakan. Inna Mairo ita kanta ta yi farin ciki sosai ko bakomai ta san Faruk zai kular mata da jikarta jinjina ma k'arfin halin Nasiba tayi ganin wai dakanta take nema ma mijinta aure. Faruk da Nasiba godiya sukayi masu. Su ko farin ciki baki har yak'i rufuwa dan daman sunaso Jawahir tasamu miji wanda zai kula da maraicinta, nan sukaita shi masu albarka, kowa farin ciki fal a ranshi dan sunsan indai ta auri Faruk ta more miji. Nasiba ce tace kar afad'a ma Jawahir abari su zssu fad'a mata da kansu. Su Baba Malam suka amince da hakan. Wajen k'arfe ukku Jawahir tadawo takawo ma Inna Mairo sak'onta tace kiyi hak'uri inna sai yanzu tagama dafawa ashe bata soyaba sai da naje. Murmushi Inna tayi tace bakomai ai daman na yi tunanin haka daman ina ta Allah Allah tasoya kafin sutashi tafiya. Murmushin itama Jawahir tayi tace ai nan zasu kwana gaskiya bamu yarda sutafi yau ba. Nasiba da take cikin d'aki tana jiyota saidai tayi murmushi kawai. Shigowa Jawahir tayi tace gaskiya babu inda zakuje yau Aunty Nasiba bari ma inma Yaya Faruk magana. Au keda baki ma lek'a inda mukeba kike da bakin cewa haka. Dariya Jawahir tayi tace dole ma inyi zuciya inzo ko dan inhuta da gorin da ake min. Ai da dai ya fi maki, yauwa Jawahir akwai magana me muhimmanci da nakeso muyi. Wace magana kenan Aunty?. Ina zuwa,,, wayarta tad'auko takira Faruk tace yashigo dan Allah suyi magana, ya amsa da toh. Bayan ya shigo ne ya zauna takalli Jawahir da tayi shuru tana jira taji abinda zasuce sannan Nasiba tace dan Allah Jawhir wata 'yar alfarma ce muke nema a wajenki. Alfarma kuma?,,, tatambaya cike da mamaki. Janye kai Nasiba tayi gefe guda sannan tace dan Allah ina so ki auri Faruk. Zumbur tamik'e tsaye tace ni kuma? Aunty Nasiba kinsan abinda kike fad'a kuwa? 'Daga kai tayi tace Eh na sani cewa nayi kitaimaka ki aureshi. Jawahif juyawa tayi takalli Faruk da yajingine kanshi a jikin kujera idanuwanshi suna a lumshe yana saurarensu, d'auke kai tayi tace gaskiya ba zan iya auren mijinki ba ni kawai matsayin Yaya yake a wajena. Saurin bud'e idanu Faruk yayi yakalleta. K'walla ce ta cika ma Nasiba idanu tace kar kice haka Jawahir dan Allah kitaimaka ki aureshi na maki alk'awalin zamu zauna da ke lafiya, bazamu ta'ba cutar da rayuwarki ba, idan har baki auri Faruk ba hankalina bazai ta'ba kwanciya ba, dan Allah kitaimaka ki auri Faruk na tabbata zai kula da ke fiye da yadda Umar yakula da ke. Zama Jawahir tayi tare da juyawa tana kallon gefe guda nan hawaye suka fara fita daga idanunta. Faruk ganin yadda take hawaye yasa jikinshi yayi sanyi nan yayi ma Nasiba nuni alamun tabasu waje, mik'ewa Nasiba tayi tafita cikin sanyin jiki, Nan yamaida kallonshi ga Jawahir ahankali yakira sunanta tajuyo takalleshi cikin muryar kuka tace Yaya Faruk dan Allah kace min maganar da Aunty tayi da wasa take ba da gaske ba. Murmushi yayi yace Jawahir dagaske take ina sonki kuma zan aureki idan har kin amince. Saurin tarar numfashin shi tayi tace ban amince ba bazan ta'ba aurenka ba domin kai Yayana ne. Wani irin haushi Faruk yaji ammah yadanne yace idan har kin d'aukeni a matsayin Umar zaki iya aurena Jawahir tunda shima kin aureshi ko kin mance lokacin da muke bankwana zaki dawo nan kikace infad'i duk abinda nake so kiyi min nace bana buk'atar komai sai abu guda, kikace menene nace zan sanar da ke ba yanzu ba, inzaki tuna cewa kikayi Allah yakaimu lokacin insha Allahu komenene zan nema zaki mallaka min shi, idan ko haka ne Jawahir aurenki nakeson yi dan Allah ki amince min. Kallonshi tayi fuska sha'be sha'be da hawaye tace taya zan iya aurenka Yaya Faruk? Taya zan auri mijin Aunty Nasiba idan har nayi haka ban mata adalciba ga mahaifinta anrufe sanoda ni sai kuma in auri mijinta dan Allah kacanza wani abun ammah bazan iya aurenka ba. 'Dan guntun murmushi yayi yace wannan alfarmar ita kad'ai nake nema a wajenki idan kuma har baki amince ba shikenan zan hak'ura Jawahir saidai na san kisan girman alk'awali da hukincin rashin cikashi. Cikin kuka tace ni ba wai alk'awalin bane bazan iya cikawa ba kawai dai aurenka ne bazan iyaba kai fa matsayin Yayana kake kuma Aunty Nasiba ban mata adalci ba idan na auri mijinta nidai kayi hak'uri bazan iyaba Barrister...tun kan tarufe baki sai jin muryar Inna Mairo sukayi ta ce Jawahir indai kika k'i amincewa da aurenshi tabbas kin zama butulu domin duk halarcin da mutanen nan sukayi maki baidace kice haka ba. Cikin kuka tad'ago takalli Inna Mairo sai kuma tajuya cikin sauri tashige uwar d'aka tamaida k'ofa tarufe. Inna Mairo kallon Faruk tayi tace kar kadamu Faruk zamu fahimtar da ita. Nasiba ce tashigo ganin yadda sukayi cirko cirko yasa tagane Jawahir bata amince ba, dan haka tace Inna dan Allah kulallasheta ta amince da auren nan zamu zauna lafiya bazan ta'ba cutar da itaba insha Allahu zatayi alfahari da auren nan da zatayi. Murmushi inna mairo tayi tace kubarta kawai Nasiba zata amince, muma ai abun farin cikine agaremu ko bakomai munsan zata rage yawan shiga damuwa da tunane tunanen da take. Faruk dai baice komai ba dan ya san daman mawuyacine ta amince ta aureshi saidai shima a yanzu yana da burin aurenta dan yacanza mata rayuwa yamaido mata farin cikin da tarasa a rayuwarta. Har sakayi sallar la'asar bata fitoba dan haka Baba Malam yaje yabuga mata k'ofa lokacin tana kwance har lokacin tana kuka dan jin abun take wani iri wai itace Nasiba take rok'o ta auri mijinta, jin muryar Baba Malam yasa tayi saurin tsaida kukan tare da tashi cikin sauri tabud'e k'ofar takoma tazauna tana sheshek'ar kuka. Baba Malam ne da Inna Mairo suka shigo suka samu waje suka zauna nan Baba Malam yakalleta yace Jawahir idan har kikayi ma mutanen nan haka baki kyauta ba, kar kimance halarcin da Faruk yayi maki a rayuwa kar ki kasance me manta alkhairi, kar kisaka kanki cikin mutane marassa godiya, tunda su suka nemi ki aureshi ba ke ce kika nema ba Jawahir na tabbata idan har kika auri Faruk bazaki ta'ba yin da kin saniba dan shi d'in mutumin kirki ne. Girgiza kai tayi cikin muryar kuka tace ni ba wai na k'i bane kawai dai hakan ba adalci bane in auri mijinta nidai sutaimaka subarni ink'are rayuwata a haka dan Allah na rok'eku. Baba Malam ne yace shikenan Jawahir mu bazamuyi maki dole ba zamu hak'ura da abinda mukeso dan bamu muka haifekiba dole mubari kiyi abinda zai faranta maki rai. Inna Mairo ce tace tabbas haka ne Alhaji domin mu mahaifiyarta muka haifa itace zata kasance me biyayya da duk abinda mukeso Allah sarki rayuwa mutuwa bata barin wani dan wani yaji dad'i, ina ma ace Khausar tana raye. Jawahir tana jin haka k'ara sautin kukanta tayi tare da zamowa k'asa cikin kuka tace dan Allah Inna da Baba kuyi hak'uri wallahi nima mai biyayya ce zanyi maku biyayya ga duk abinda kukeso na amince zan auri Faruk dan Allah kusa ma rayuwata albarka. Suna jin haka duk sai wani irin farin ciki yalullu'besu nan sukaita shimata albarka, gefe d'aya kuma tausayinta suke ji. Jawahir kasa cewa komai tayi saidai cigaba da kukanta da tayi. Fitowa sukayi suka samu su Baba Musa da su Faruk zaune sunyi shuru suna jira sufito suji yadda sukayi da ita dan Faruk tsintar kanshi yayi da jin wani iri akan nunawa da Jawahir tayi bata sonshi, yana ganin su Baba Malam sun fito saida gabanshi yafad'i wanda yarasa dalilin fad'uwar gaban, idanu yazuba masu yana kallonsu, Nasiba ce tayi k'arfin halin cewa Baba ya kukayi da ita ta amince? Murmushi su Baba Malam sukayi sukace Eh ta amince. Gabad'ayansu hamdala sukayi Faruk ko ajiyar zuciya yasafke yaji wani irin sanyi ya ziyarceshi. Nan shi da Nasiba sukayi masu godiya. Nasiba jikkarta tad'auko tafiddo dubu d'ari taje tatsugunna gaban Baba Malam tace Baba ga wannan kud'in neman aurene ni nad'auki nauyin biyansu, sannan insha Allahu su Dad zasu zo atsaida ranar aure mudai muna rok'on ataimaka mana kar asa rana dayawa dan munfiso ayi bikkin batare da anja lokaci ba. Su dukansu mamaki yakamasu ganin yadda ko kad'an bata nuna damuwa ba saima murna da take. Inna Mairo ce takasa daurewa tace tabbas wannan mata zuciyarki me kyau ce tunda nake a tarihin rayuwata da idanuna kece macen da nata'ba ganin ta yi hakan, Allah ubangiji yasaka da alkhairi, Allah yabiyaki da gidan aljanna. Murmushi Nasiba tayi tace babu komai Inna ai Jawahir 'yar uwatace kuma duk musulmi na k'warai zaiso ma d'an uwanshi abinda yake so ma kanshi, ko bakomai Jawahir ta cancanci fiye da hakan a wajena dan itama ta taimaka mani a lokacin da nake buk'atar taimako taya zan kasance me manta alkhairi. Maganar da tayi ta shigesu sosai nan sukaita mata godiya, Faruk ko saidai idanu yazuba mata cikin zuciyarshi yana gode ma ubangiji da yamallaka mashi Nasiba a matsayin mata dan tabbas ita d'in macece ta gari. A chan 'bangaren Jawahir tana ganin su Baba Malam sun fita komawa tayi takwanta nan tafara rera sabon kuka, dan dole ta amince da za'bin su saboda a yanzu batada na sama da su suna k'ok'arin yi mata duk abinda take buk'ata, alk'awaline tayi ma kanta bazasu ta'ba kuka da itaba babu abinda zasu nema a wajenta surasa itace zata koma madadin mahaifiyarta a wajensu, wannan dalilin ne yasa tayi saurin amincewa da auren Faruk. Har wajen k'arfe biyar Jawahir bata fitoba dan haka wajen biyar da rabi suka bar Kebbi sunso suyi bankwana da Jawahir ammah tak'i fitowa dan koda Inna Mairo tashiga dan tafad'a mata tafiyar da zasuyi samunta tayi tana bacci ko da ma ba baccin gaske takeba dan bataso tasake had'a idanu da mutanen ne saisa tatsiri baccin k'arya zuciyarta a tunkushe. Nasiba Alk'awali tayi masu insha Allahu da sunje zasu sanar da su Dad azo ayi maganar auren, Faruk ko saidai yabita da idanu ta k'ara daraja sosai a cikin idanunshi. K'aramin galan d'in kindirmo da man shanu aka basu da k'ananun tsarabobi suka tafi da su har airport su baba musa suka rakasu saida jirginsu yatashi sannan suka baro airport d'in. Suna komawa gida Nasiba part d'inta tawuce Faruk kamar jira yake yabi bayanta fara cire kaya tayi sai gashi ya shigo kallonshi tayi tai murmushi tace ya dai ango bazaka d'an watsa ruwaba kafin magrib?. Matsowa yayi kusa da ita yace yanzu saboda Allah Nasiba hakan da kikayi kin kyauta?. Murmushi tayi tace me nayi, dan kawai na nema maka auren Jawahir sai yazama laifi, kaima fa kana sonta malam kafiddo farin cikinka a fili kawai ba sai ka 'boye min ba. Rik'o ta yayi yana mata kallon mamaki yace Nasiba wa yafad'a maki ina son Jawahir? Cikin idanunshi takalla tace soyayyarta nagani a cikin idanunka ko zaka iya rantsewa kace baka sonta. Jan hancinta yayi yace ni bance ina sonta ba. Janye hancinta tayi tace wash da zafi fa Lovely, ni dai nasan kana sonta kawai dai kana basarwa ne,,, tana fad'in haka tajuya tana k'ok'arin cire skirt d'inta, rik'o hannunta yayi yace ya akayi kikasan haka?. Batare da ta juyo ba tayi murmushi tace tun daga yanayin yadda kake waya da ita da yadda kake yawan min labarinta kai tunma kafin nan zan iya cewa tun a kotu nafara ganin alamar hakan. Faruk kasa cewa komai yayi nan yaja yai tsaye yana kallonta cike da mamaki. Juyowa tayi takalleshi fuskarta d'auke da murmushi tace ko zakayi wanka muje muyi kar magrib yayi kaga na gaji sosai yau. Batare da ya ce komai ba yafara cire kayanshi dan rasa abinda zaice mata yayi. ------*****------- A daren Nasiba takira su Dad da Mom tafad'a masu yadda sukayi da su Baba Malam, washe gari Faruk yaje gida nan yasake fad'a masu komai har da irin k'ok'arin da Nasiba tayi wajen nema mashi auren Jawahir. Daga Dad har Mom sun jinjina mata nan sukaji ta k'ara shiga ransu sukayi Allah yasa alkhairi. Dad yasa mom takira Nasiba a waya tatambayeta wata nawa yadace asa bikkin nan Nasiba tace kar yawuce wata biyu kamar yadda akasa nata suka amince da haka. A cikin satin ne su Dad da abokinshi sukaje Kebbi suka nema ma Faruk auren Jawahir wajen Baba Malam yace ai Nasiba ta nema mashi auren saidai ayi baiko, haka ko akayi akasa bikki wata biyu masu zuwa, dan a lokacin bikkinsu Khausar sati bakwai yarage nan aka ce za'a k'ara sati guda ayi tare da na su Jawahir jin haka yasa su Dad sukace a'a kar ak'ara kawai arage sati guda daga cikin wata biyun da akasa sai ayi bikkin tare nan da sati bakwai nan su Baba Malam suka amince su Dad dayake a mota sukazo suka fiddo kayan sa bikkin da suka ciko boot da su suka bada sannan suka juya saboda tafiyar mota ce basuso suyi dare dan ma driver yakawo su. _________Jawahir ko tun ranar da su Faruk sukazo sukayi maganar aurenta tad'auki damuwa tasa a ranta saida Inna Mairo tadinga mata nasiha tare da bata shawara tabar ma ubangiji za'bi acikin rayuwarta sannan tarage sa damuwa tadinga tashi kullum cikin dare tana kaima ubangiji kukanta tare d neman za'binshi a cikin rayuwarta. Su khausar ko murna suka dinga yi suna tsokanarta dan cewa suke daman chan sun ga alamar faruk yana sonta yanayin yadda yake kallonta, Rashida tace yoh itama d'in bakiga yadda take d'oki idan yazoba tana sonshi gulma ce kawai mudai munji dad'i. Shuru jawahir tayi tak'yaleshi nan magana tazagaye gida akaita murna tare da yin Allah yasa alkhairi. Lokacin da akasa bikki ko jawahir kasa fitowa tayi a d'aki ta'boye tadinga kuka. Sauran mutanen gida aka dinga murna musamman da akaji tare da nasu Khausar za'a had'e ayi ...... _Sis Nerja'art✍🏻_[7/24, 11:22 PM] Sis Nerja'art 2: *......FANSAR RAI......* *INTELLIGENT WRITER'S ASSO....®* [On Ward Together] _Follow me on Wattpad: *Sis-nerja*_ _Wannan Littafin na kud'i ne domin karantawa cikin aminci da yarda ga duk me buk'ata zai turo katin Mtn na d'ari biyu N200 kacal ta wannan number d'in 09035938246, ko ta account number 5330055604, Idan katura ka aiko da screen shot na transaction a wannan number d'in 09035938246_ _Akwai gara'basar *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shahararriyar marubuciyar nan *AMEENA ABBA UMAR* tare da novel d'in *FANSAR RAI* akan farashin N300 kacal, ko da kud'in ka sai da rabonka_ *PAGE 26* Tunda su Dad suka dawo suka fad'a masu Nasiba maganar baikon da akayi murna tadinga yi abun har yaba Faruk mamaki ganin yadda bata nuna damuwa ba, lokacin suna zaune a parlor nan tafara tsara yadda bikkin zai kasance, batare da ya ce mata komai ba yamik'e yashige bedroom d'inshi. Da idanu tabishi nan tayi d'an guntun murmushi wanda baikai zuci ba sannan tamik'e tabi bayanshi, tana shiga tasameshi kwance a saman gado kanshi yana kallon ceiling. Zuwa tayi takwanta a k'irjinshi cikin shagwa'ba tace shine muna magana sai kataso katafowarka kabaroni ko? Batare da ya kalletaba yace Nasiba wai anya kina sona? Da mamaki take kallonshi tace me kagani? kaga wani abu ya canza ne daga soyayyar da nake nuna maka? Kusan haka dan da ace kina sona da sai kinyi kishina. K'wallah ce tanemi tafito daga idanunta tayi saurin maidata tace Faruk kaima ka san ina sonka soyayyar da nake makace yasa nakeson ka auri Jawahir dan Allah kadaina irin wannan tunanin indai ba so kake kad'aga min hankali ba. Sai a lokacin yad'ago yakalleta murmushi yasakar mata yace shikenan hearty insha Allahu na daina, nagode sosai da irin k'aunar da kike nuna min. Itama murmushin tayi tace kadaina godiya agareni Lovely, yauwa ammah dan Allah nan gidan Jawahir zata zauna ko? Dan wallahi nafiso muzauna tare kaga mun dinga hira tunda kai ficcewa kake wajen aiki kabarni ni kad'ai. Toh Hearty duk yadda kikeso haka za'ayi tunda ga gudan part d'in chan sai tazauna a ciki. Cikin jin dad'i tace nagode sosai Lovely, sai kuma tamarairaice tace dan Allah inaso idan kabani dama gobe inje ingano Mummy. Shafa bayanta yayi yace toh Allah yakaimu goben idan nadawo wajen aiki sai inkaiki. Godiya tayi mashi cikin jin dad'i. _______**______ Nasiba ce zaune a gidansu tare da mahaifiyarta da 'yan uwanta da suka zo su ma, suna cikin hira ne take sanar da su maganar auren da Faruk zaiyi, su dukansu hucking sukayi sukace aure kuma? Wane Faruk d'in wai ma?,,, cike da mamaki suke tambayarta Murmushi tayi tace nawa man. Yaya Sadiya ce tace ban gane nakiba duka yaushe akayi bikkin naku da har zai k'ara aure? Cikin nuna rashin damuwa tace Yaya Sadiya ai ba wani abu bane dan ya k'ara aure nice ma nanema mashi auren. Daga Mummy har su Yaya Sadiya rik'e baki sukayi suna kallonta cike da mamaki. Bata damu da irin kallon da suke mataba tace ba wani abun mamaki bane dan na ce haka. Nasiba anya kina cikin hayyacinki kuwa? Ke ana gudun kishiya ke kuma kina jawo ma kanki ita. K'walla ce tacika mata idanu tace toh ya zanyi wallahi ina tausayin Jawahir sosai kuduba kuga mahaifinmu ne yajefata halin da take ciki na rashin duk wani makusanci nata hatta mijinta, ya zanyi idan bance ta auri Faruk ba, bamusan halin da take ciki ba koda ace bata nuna a fili ba ansan akwai damuwa acikin ranta, sannan duk abinda mahaifinmu yayi mata hakan baisa tak'i mu ba dan tasan ba mu mukayi ba, wallahi duk irin k'aunar da nakeyi ma Faruk zan iya hak'ura ya auri Jawahir domin ita d'in mutuniyar kirki ce, nidai dan Allah kusa albarka a cikin auren nan kar kusakar min da gwiwata a lokacin da nake sanar da ku aikin ladan da zanyi. Su dukansu jikinsu sanyi yayi nan sukayi masu Allah yasa alkhairi, Mummy ta jinjina ma halin d'iyartata dan bata ta'ba tunanin hakan ba saboda Nasiba tana da kishi sosai. Nan tayi masu wuni sai dare Faruk yazo d'aukarta suka koma gida. Bayan sati biyu da sa bikkin Nasiba ta amshi kud'ad'e wajen Faruk taje da kanta tafara had'a ma Jawahir lefe kaya na gani nafad'a masu tsada tahad'a mata komai da zuciya d'aya batare da tasa mugunta ba akwatuna takwas Faruk yace tahad'o mata, wasu kayan duk irin nata ne taza'bo mata hakan da tayi ya k'ara mata k'ima da daraja a idanun mijinta da surikkanta nan Faruk yabata kud'ad'e sosai yace tayi hidima da su itama. Godiya tayi mashi sosai. A chan 'bangaren su Jawahir ko duk wani shirye shirye da ake yi ma Khausar da Rashida yanzu anhad'a har da ita akeyi tun ana saura wata guda bikki aka fara masu gyara musamman ma ita da akasan ta ta'ba aure, yaunzu gabad'aya ta mik'a lamurranta ga Allah kullum addu'arta d'aya Allah yatabbatar mata da alkhairi a cikin rayuwarta, gefe guda kuma ta sha ta'boye kanta taci kuka batare da sanin kowaba, ga wata irin kunyar su Mom da takeji yanzu indai ba su suka kirata aka gaisaba bata kira shima bakamar da ba yanzu bata sakewa suyi hira. Faruk ko ya kira bata d'agawa saidai idan message yaturo mata sannan tamaida mashi reply hakan yana ba Faruk mamaki sosai dan hakane yashirya yaje Kebbi a motarshi a waya yasanar da ita zai zo dan haka Jawahir tafara shirin tarbarshi, Baba Nura tafad'a mawa shi kuma yasanar da su Baba Malam sukace Allah yakawoshi lafiya. Ranar asabar tun da safe da tatashi tashiga kitchen tafara girki Khausar ce tazo tana tayata fried rice suka shirya mashi wadda tasha had'i sannan sukayi mashi pep chicken da kunun aya . Wajen k'arfe d'aya sun gama nan taje tayi wanka tun tana girkin hankalinta yana wajen Faruk tana so takirashi taji yanayin tafiyar tashi bare da yasanar da ita a mota zai zo, har waya tad'auko zata kirashi sai kuma tafasa. Cikin kayan da yayi mata da zata dawo kebbi tad'auko wata shadda gown brown tasaka wadda tasha aiki da pink d'in zare, ita tazauna tayi kwalliyarta. Tana zaune saman darduma bayan ta gama sallar azuhur sai ga kiran Faruk ya shigo. Saurin d'auko wayar tayi tazuba mata idanu tana kallo har saida takusan tsinkewa sannan tayi picking tare da yin sallama. Amsa mata yayi sannan yace kifito ganinan na iso. Har zatace mashi yashigo nan yakashe wayar dan haka tamik'e tad'auke darduma saida tak'ara gyara fuskarta tad'akko pink d'in gyale tayafa sannan tafito tanaso tashiga 'bangaren su Khaisar tace tafito tarakata sai tajiyo hayaniya a cikin gidan alamun kowa yana nan ita kuma ga kunya bataso tahad'u da 'yan cikin gida dan haka tasamu Inna Mairo tafad'a mata ya iso. Inna Mairo tace toh taje tashigo da shi kanta sunkuye a k'asa tafita. Faruk da ke zaune cikin mota ya zuba ma k'ofar gidan idanu dan ganin ta inda zata fito dan a lokacin su Baba Malam basu nan ba kowa a wajen, idanunshi a kanta tafito har ta iso wajen motar ta shi taja tatsaya tare da yin sallama. Amsawa yayi tare da bud'e mata k'ofar gaba yace tazagayo tazauna. Sai a lokacin tad'ago takalleshi sanye yake cikin manyan kaya ya yi kyau sosai da har zatace mashi a'a ganin yadda yatsareta da idanu yasa bata musaba tazagaya taje tashiga tabar k'ofar a bud'e, gaishe shi tayi maimakon ya amsa sai cewa yayi shine ko kikirani kiji yanayin tafiyar tunda natafo ko. Shuru tayi dan ita kanta ta san bata da gaskiya. Ta cikin mirror yake kallonta ganin batada niyar d'ago kanta bare tayi magana yasa yace Jawahir nuna rashin kulawar da kike min bana jin dad'inshi idan kina haka sai inga kamar baki sona, tilasta maki akayi sai kin aureni ko? Shuru tayi nan ma tana wasa da yatsun hannunta. Juyowa yayi yakalleta yace indai har baki sona kifad'a min Jawahir wallahi sai inhak'ura ba wani abu bane sai inbarki ki auri wanda kikeso dan nima kaina bazanso kiyi auren da bakiso ba. Sai a lokacin tad'ago kai takalleshi idanu cike da k'walla tace Yaya Faruk ba wai bana sonka bane ka cancanci insoka ko dan saboda alkhairin da kayi min da taimaka man da kayi a lokacin da nake buk'atar taimako bazan ta'ba kasancewa butulu agareka ba ko da ace wanine na daban kakawo kace in aura ni me biyayya ce agareka bazan ta'ba baka kunya ba, kawai dai banason zama da Aunty Nasiba a matsayin kishiyarta ne sai inga kamar banyi mata adalciba kamar na so kaina dayawa, wannan dalilin ne yasa kaga na kasa sakewa hankalina ya k'i kwanciya. Wani irin sanyi yaji a ranshi nan yasafke ajiyar zuciya sannan yace Jawahir idan dai har kina sona to dan Allah kidaina shareni kisaki jikinki da ni Nasiba kuma batada matsala wallahi itace ma tagoya min baya in aureki na tabbata zata zauna da ke lafiya domin ita d'in mutuniyar kirkice ba irin mahaifinta ba, ina sonki jawahir ina fatan kema zaki taimaka kisoni. Murmushi ne yasu'buce mata ahankali tace nagode Yaya Faruk. Idanu yazuba mata yace bakice komai ba zaki so ni ko? Saurin fita tayi daga cikin motar tace kashigo kagaisa da Inna Mairo kafin su Baba Malam sudawo daga wajen jana'izar wani abokinshi da ke nan bayan layinmu sunce bazasu dad'eba. Murmushi Faruk yayi batare da ya ce komai ba yabud'e motar yafito nan tawuce gaba yana biye da ita a baya suka shiga cikin gida. Gaisawa sukayi da Inna Mairo cikin girmamawa daga nan Jawahir tawuce kitchen takawo mashi abinda tatanadar mashi, tana gama ajiyewa tazuba mashi yace saidai tazauna suci tare indai ba haka ba bazai ciba. Marairaicewa tayi tace dan Allah Yaya Faruk kaci ni na k'oshi. 'Dauke kanshi yayi yace shima bazai ciba duk yunwar da yakeji zai hak'ura sai ya koma gida sannan zai ci. Tana jin haka tazauna k'asa tare da jawo plate tana zubawa yana kallonta tana turo baki ahaka tad'an zuba rabin plate. Murmushi yayi sannan yasafko k'asa shima nan yafara cin wanda tazuba mashi, lumshe idanu yayi yace ashe amaryar tawa itama ba bayaba wajen iya girki. Murmushi tayi sannan tafara cin wanda tazuba ma kanta. Suna cikin ci sukaji sallamar su Baba Malam Jawahir d'aukar plate d'inta tayi cikin sauri tanufi bedroom dan kar sushigo suganta. Faruk dariya yayi nan suka shigo suka gaisa da shi sannan suka bashi waje yakimtsa cikinshi. Bayan ya gama ne yafita suka sake gaisawa sannan yafiddo tsarabar da yazo da ita cikin boot yasa aka shiga da ita cikin gida. Har sukayi sallar la'asar baiga fitowar Jawahir ba dan haka yakirata a waya yace tafito suyi bankwana tafiya zaiyi. Kiran Khausar tayi a waya dan tafito sugaisa da shi dan ta san halin Khausar indai har yatafi basu gaisaba sai ta sha tsegumi wajenta. Tare suka fito da Khausar suka sameshi tsaye wajen motarshi nan suka iso Khausar tagaisheshi. Amsawa yayi cikin sakin fuska yace ya gida khausar? Lafiya Lau Yaya Faruk, ya su Mom? Duk suna lafiya lau, kallon Jawahir yayi sannan yace ina fata dai kina kula min da matata. Saurin d'agowa Jawahir tayi takalleshi nan yad'aga mata gira. Dariya Khausar tayi tace ina kula da ita sosai angonmu, dan bana barin kowa yakalleta bare yasamu damar yi mata magana. Murmushi yayi yace gaskiya na ji dad'in jin haka daga gareki nagode sosai Khausar bari inbada tukuici, nan yasa hannu a aljihu yad'auko bandir d'in 'yan 500 yamik'a mata. Amsa tayi cikin jin dad'i tayi godiya sannan takoma gida tabasu waje dan suyi bankwana. Tana wucewa Faruk yace Jawahir ya kamata kisake kidaina wannan kunyar taki dan gaskiya tana cutar da ni kwatakwata baki bani kulawa ko waya baki bari muyi hakan baya min dad'i. Batare da ta d'ago ta kalleshi ba tace toh zan gyara. Yauwa kokefa, mota yabud'e yafiddo wata leda wadda duk kud'i ne a ciknta yamik'a mata yace ga wannan kinyi hidima da su. Girgiza kai tayi tace a'a kabarsu akwai kud'i a account d'ina. Ban damu da kud'inki ba wannan ni nabaki, kinsan dai bana son gardama. Amsa tayi taimashi godiya. Yace bakomai yanzu dai bari inwuce kar inyi dare. Toh Yaya Faruk nagode agaishe da su Mom da Su Aunty Nasiba. Insha Allahu zasuji idan na isa zan kiraki waya salan kik'i d'auka kamar yadda kika saba min, Allah had'aki zanyi da Baba Malam. Ahankali tace kayi hak'uri zan d'auka. Shiga motar yayi yace Allah yasa. Bakuyi bankwana da su Baba Malam ba,,, cewar jawahir da take kallonshi. Duba agogo yayi yace munyi bankwana suna tafiya ma kika fito daga cikin gida, yauwa ban tambayeki Event d'in da zakiyi ba dan idan za'a kawo lefe nakeso in aiko maki da Invitation Card d'inki saboda zan d'anyi tafiya workshop kwana biyu. Girgiza kai tayi tace babu abinda zanyi walima ce kawai zanyi itama a makaranta. Murmushi yayi cikin ranshi ya ji dad'in hakan dan shi daman ba mutum bane meson party saisa koda Nasiba ma batayi ba ya ji dad'i, yace shikenan zan sa abugo maki ko inturo kud'i Baba Nura yabugo a nan garin. Amsawa tayi da toh nan tayi mashi godiya. Kallon cikin idanunta yayi yace baza'a fad'a min magana me dad'i ba wadda zata tayani hira acikin mota tunda ni kad'ai ne. Janye idanunta tayi cikin jin kunya tace Allah yakiyaye hanya Allah yamaida mana kai gida lafiya. Amsawa yayi da Ameen sannan yace baki fad'a min kina sona ba. Saurin juyawa tayi cikin jin kunya tashige gida. Dariya yayi sannan yatada mota yakama hanyar Katsina. Gudu yadinga yi da motar sosai ba shi ya isa ba sai dare. ________ Tun daga lokacin yake samun damar yin waya da Jawahir dan yanzu tana d'aga wayarshi idan yakirata cikin dabara yasamu tasake suka dinga hira sosai dan a kullum sai yakirata kusan sau ukku a rana ammah baya kira agaban Nasiba, a gefe guda kuma yana ba matarshi kulawa sosai babu abinda zata nema tarasa a wajen mijinta wannan dalilin ne yasa Nasiba tak'ra kwantar da hankalinta. Ana saura sati ukku bikki aka kai lefen Jawahir inda Dad yad'auki nauyin kayan d'akinta yace shi zaiyi dan alk'awali yayi ma kanshi ko da ace ba Faruk zata aura ba shi zaiyi mata kayan d'aki saboda zaman mutuci da amana da yayi da mahaifinta zai iya cewa shine silar d'aukakar kamfaninshi, ya dai barsu da kayan kitchen d'inta. Nan su Baba Malam sukaita mashi godiya tare da addu'a itama Jawahir ta ji dad'in hakan sosai nan tasake saka ma ranta zata zauna da d'ansu da matarshi lafiya ko dan irin soyayyar da mutanen nan suke nuna mata. Barr Faruk ya je workshop a Abuja saida sukayi sati biyu sannan suka dawo tare da matarshi yaje suka safka a hotel. Ana saura sati d'aya bikki suka dawo lokacin Dad har ya zuba ma Jawahir kayan d'akinta a part d'inta da zata zauna, set biyu yayi mata na bedroom sai na parlor set d'aya ya kashe kud'i sosai kamar yadda zaiyi ma 'yar cikinshi. *BAYAN SATI 'DAYA* Su Baba Malam sunyi k'ok'ari sosai wajen saya ma su Khausar da Rashida kayan d'aki set guda guda sai kayan kitchen. Inda ita kuma Jawahir akayi mata kayan kitchen nagani na fad'a saboda ita ba'a siya mata kayan d'akiba saisa nata duk sukafi kyau da tsada. Baba Nura ne yabugo masu invitation card me d'auke da sunayen amaren su duka ukku wanda suka dinga gayya da shi walima ne kawai zasuyi a islamiyyarsu sai kuma yinin bikki da za'ayi daga nan kowace amarya atafi da ita gidanta. 'Yan uwa da abokan arzik'i duk sunzo dan gudanar da bikki nan Baba Malam yaware shanu biyu aka yanka dan ayi hidima da su, amare suna shan gyara sosai nan da nan suka canza dan ita kanta Inna Mairo ba'a barta a bayaba wajen gyara 'yan jikokin nata gyara tayi masu irin nasu na 'yan zamfara. Yau ma bayan ta gama tsuma Jawahir tana kwance saman gado inda tabar su Khausar suka fita dan suje suyo masu abubuwan da zasu raba wajen walima gobe, wayartace a hannunta tana chart da Faruk nan Inna Mairo tashigo da wata leda tazauna bisa gadon sannan tad'akko wata gumba a ciki tamik'a mata tace tashi kici wannan. Kallon gumbar tayi ta'bata rai tace ni fa Inna na gaji da 'yan ciye ciyen nan. Rik'e baki inna tayi tace yau Allah ya had'ani da shashashar yarinya ke ana so agyaraki miji yajiki zam ammah ke bakiso ko mancewa kike da gidan kishiya zakije? Tashi Jawahir tayi ta amshi gumbar tana turo baki nan tafara ci, ji tayi da dad'i dan haka tacigaba da ci saida taci kusan rabi sannan Inna Mairo ta amsa tace tabarta haka. Komawa tayi takwanta tana cigaba da chart d'inta. A account d'inta Faruk yaturo mata kud'i yace tak'ara dan yasan wad'anda yaturo mata bazasu isheta ba godiya tayi mashi. A chan Katsina ko ba wata hidima akeyi sosai ba dan wannan karan ba sosai sukayi gayya ba saboda a ganinsu kamar za'a takura mutane tunda duka yanzu baifi wata shidda da yin wanchan bikkin ba, Malam ne yabada shawarar hakan saisa. Mummyn Nasiba da su Yaya Sadiya sunje har gida sunyi ma su Mom Allah yasa alkhairi. Itako uwar gayyar ba'a magana dan ita tabugo IV taba Barr Nass yagayyaci abokansu, gefe guda kuma tabada aka d'inka ma ango kayan da zaisa na d'aurin aure. Ran asabar wajen k'arfe goma su Dad da abokanshi biyar sai Faruk da abokanshi da Malam suka shiga jirgi suka je Kebbi dan da k'arfe sha d'aya za'a d'aura aure. Amare sun sha kyau sosai su dukansu da ka kalli fuskarsu zakaga a kumbure duk sun sha kuka Khausar ce me d'an dama dama daga cikinsu. Wajen k'arfe sha d'aya aka d'aura auren Faruk Sani Maishadda da amaryarshi Jawahir Muhammad Maikud'i, Sai Khausar Musa Maisalati da Mansur Abba sannan Rashida Jamilu Maisalati da angonta Aminu Umar. Jama'a da dama sun samu halartar d'aurin auren tun daga mutanen Kebbi da ma wad'anda ba na kebbi ba. Ana d'aura aure su Faruk suka koma masaukin da aka safkesu shi da abokanshi biyu inda su Dad da sauran abokan suka koma Katsina. Jawahir ganin yadda gidan yacika yasa tasulale takoma cikin bedroom d'in Inna tayi zamanta ita kad'ai dan hayaniyar taji bata so. Tana zaune ta buga tagumi nan Faruk yakirata waya, kallon wayar tayi kamar bazata d'auka ba sai kuma chan tad'auka batare da ta ce komai ba. Daga chan 'bangaren Faruk yayi sallama yace ya dai amaryata ina fatan kina lafiya?. Cikin muryarta da tadashe saboda kuka tace lafiya lau. Runtse idanunshi yayi cikin nuna damuwa yace oh my god jawahir ba dai kuka kike ba? Shuru tayi nan yasafke ajiyar zuciya yace dan Allah kidaina 'bannatar min da hawayenki My Jawa kinga yau ranar murna ce agaremu kicire kowace damuwa acikin ranki kinga and'aura aure yanzu andamk'a min amanarki insha Allahu zan baki duk wata kulawa da tadace dan zan nuna maki ni d'in me k'aunarki ne zan mantar da ke duk wata damuwa da kike cikinta dan Allah Jawahir kisama min gurbi acikin zuciyarki ko yayane. Runtse idanunta tayi nan hawaye suka fara gangaro mata tana jin maganganunshi har cikin kwanyar kanta. Jin ta yi shuru yasa yace shikenan Jawahir bari inbarki kar incika ki da surutu ni zan nema ma kaina matsugunni a cikin zuciyarki da sannu zan koya maki sona, kihuta lafiya. Tana ji ya kashe wayar janye wayarta tayi tad'aura saman k'irjinta batare da ta bud'e idanunta ba nan hawaye suka cigaba da fita. Tana cikin haka Inna Mairo tashigo tasameta a gefenta tazauna tafara lallashinta har tasamu tayi shuru sannan tad'auko wani tsumi tabata tace ga wannan kisha Wani irin haushi Jawahir taji dan har ta fara gajiya da abubuwan da Inna Mairo take d'irka mata babu yadda ta iya ta amshi tsumin tafara sha jinshi tayi da dad'i ba kamar sauran ba dan haka tad'age kai tashanye shi tas. Nan inna tabata wata gumba ta amsa tafara ci wani irin gard'i taji ba kamar ta jiyaba wannan tafi dad'i dan kwakwa da zuma ne a jikinta haka tacita sosai. Wajen k'arfe ukku aka had'a mata ruwan wanka tayi bayan ta gama aka shiryata cikin lace me tsada saida sukayi sallar la'asar sannan su Baba Malam suka shigo haka aka fito da amare aka kaisu d'akinshi yayi masu nasiha sosai. Nan sukaita kuka. Su Khausar aka d'auka a motoci aka tafi da su gidajen mazajensu inda Jawahir kuma sai k'arfe biyar sannan aka rakata filin jirgi ita da mijinta da abokanshi suka shiga jirgin. Dakyar aka 'bam'bareta daga jikin Inna Mairo da zasu tafi. Tunda suka shiga jirgin tahad'e kanta da gwiwa tadinga rusa kuka. Duk yadda Faruk yaso yalallasheta kasawa yayi dan kuka tadinga yi sosai. Suna isa Katsina suka tarar da motoci biyu su Aunty Kilima k'anwar Malam sunzo tararsu nan Aunty Kilima da wata k'awar Mom suka shiga mota d'aya da amarya inda gudar motar da driver yazo da ita su Faruk da Barr Nas suka shigeta. Jawahir tana k'udundune cikin gyale har lokacin hawaye take ahaka suka isa gidan iyayen Faruk, d'akin Mom aka wuce da ita ganin har lokacin da sauran mutane a gidan. Aunty kilima ce tazauna da ita a d'akin saboda kunya Jawahir takasa bud'e lullu'bin haka su Mom suka shigo suka gaisa suka sake mata nasiha bayan sallar isha'i aka tattarata aka kaita gidan mijinta Aunty Kilima da Hajiya Maimuna k'awar Mom ne kad'ai suka kaita direct part d'in Nasiba suka wuce da ita lokacin gidan ba kowa sai ita kad'ai tana ganinsu cikin sauri tazo tataresu tarungume Jawahir da ke lullu'be tana mata sannu da zuwa. Su Hajiya Kilima sunji dad'in yadda Nasiba tanuna kulawa nan suka zaunar da su suka yi masu nasiha daga nan aka wuce da Jawahir part d'inta da yasha gyara sosai. A saman gado suka zaunar da ita suka sake mata nasiha sannan sukai mata bankwana suka tafi. Saida taji ba motsin kowa sannan tayaye mayafinta tana bin d'akin da kallo. Wajen k'arfe tara Faruk yadawo gidan Nasiba ce tatareshi tarakashi part d'inshi yayi wanka yashirya ledojin da yashigo da su guda biyu tad'auki guda tace mashi suje. Da mamaki yake kallonta yace ina zamuje? Murmushi tayi tace wajen amarya man. Cikin wasa yaharareta yace kamar irin kin gaji da ni kike nema kibada ni. Dariya tayi tace eh d'in na ji bakomai nidai muje malam inrakaka dan bacci nakeji. Haka suka fito tare sukaje part d'in Jawahir a parlor Nasiba tazauna yashiga ciki yasameta zaune dan tunda taji shigowarsu tamaida lullu'binta daga gefenta yazauna yana murmushi yace amarya ta ango kinsha k'amshi. Shuru tayi nan yakai hannu zai yaye lullu'bin tayi saurin fad'awa jikinshi Murmushi yayi a karo na biyu tare da rungumeta yace hanani ganin kyakkyawar fuskar za'ayi? Ko sai na siya?. Shuru tayi nan yajanyeta tare da mik'ewa yace bakomai zan siya yanzu muje ga Nasiba chan a parlor tana jiranmu. Mik'ewa tayi tabi bayanshi ta cikin gyalenta me shara shara take ganin hanya har suka fito parlor inda Nasiba take, a kujerar da take zaune yazauna inda Jawahir tazauna a 1 seater nan yayi masu nasiha. Nasiba yafara tambaya ko tana da abinda zatace saidai tayi murmushi tace babu saidai abu guda shine yayi adalci atsakaninsu yarik'esu amana. Murmushi Faruk yayi yace insha Allahu zanyi bakin k'ok'arina wajen ganin na yi adalci, kallon Jawahir yayi yace kefa akwai abinda zakice? Girgiza kai tayi alamun a'a. Nan yayi masu addu'ar zaman lafiya. Mik'ewa Nasiba tayi tace toh Amarya da Ango sai ince mukwana lafiya. Kallonta Faruk yayi yace Hearty tun yanzun? Murmushi tayi tace wallahi na gaji sosai ga bacci ina ji. Mik'ewa yayi yace toh bari inrakaki. Saurin wucewa tayi gaba tana cewa a'a kabarshi nagode amaryarmu ga amanar miji nan na damk'a maki mukwana lafiya. Tana fita taja masu k'ofa cikin sauri takoma part d'inta tana shiga tafashe da kuka tare da fad'awa saman gado wani irin kishine tadinga ji ganin yau mijinta ne zai kwana da wata ba itaba, kuka tadinga yi sosai kamar k'irjinta zai fito duk yadda taso tayi controlling d'in kukanta kasawa tayi saida tayi me isarta, har wajen k'arfe d'aya tana kwance zugum zuciyarta tadinga ayyana mata wasu abubuwa akan Faruk da Jawahir daga k'arshe takori shaid'an tamik'e taje tad'auro alwallah, sallah tayi raka'a biyu sannan tazauna karatun alk'ur'ani dan ji tayi kwatakwata bata ma jin baccin. Sai wajen k'arfe ukku sannan tasamu taruntsa. A chan 'bangaren su Faruk bayan fitar Nasiba komawa yayi gefen Jawahir yazauna tare da yaye mata malullu'binta saurin sadda kanta tayi k'asa. Idanu yazuba mata yana k'are mata kallo duk sai taji ta tsargu nan gabanta yafara fad'uwa. Saida yayi kusan minti biyar yana kallonta sannan yasa taje tad'auro alwallah sukayi sallah a nan parlor bayan sun gama ne yakama kanta yayi mata addu'a sannan yad'akko masu ledar da Nasiba ta ajiye masu dakanshi yatashi yaje kitchen yad'akko plate da cups. Kaza yafara bata da fari ta k'i amsa saida yafara lalla'bata sannan tayarda taci cike da jin kunya take amsa, saida yatabbatar ta k'oshi sannan shima yafara cin nashi. Mik'ewa jawahir tayi tashige bedroom d'inta toilet tafad'a tawanke hannu da bakinta sannan tazo tahaye gadonta ko kaya bata cireba gabanta yana dukan ukku ukku ita abun har mamaki yake bata ganin wannan ba shine aurenta na farko ba ammah duk tsoro ya kamata. Tana nan kwance Faruk yashigo hawa yayi saman gadon tare da kallonta ganin yadda take wuk'i wuk'i da idanu yace Rabin ran ya kamata kicire kayan nan bazakiji dad'in bacci da su ba. Cikin rawar murya tace a'a zan iya. Murmushi yayi yace toh ai ni zasu takura man ammah bakomai tunda kince haka bari inrage maki su dakaina Saurin tashi tayi zaune cike da tsoro tace bari inje incanza dakaina. Rik'ota yayi yamatsa gab da ita nan yazuba mata manyan idanunshi saurin sadda kanta tayi k'asa tare da cewa bari inje incire....bata rufe bakiba taji hannunshi a bayanta yana neman yazage mata zip d'in riga saurin d'ago kai tayi takalleshi wanda hakan ya yi daidai da zage Zip d'in da yayi. Tureshi tanemi tayi saima yarungumeta jikinshi tare da zame mata doguwar rigar nan hannunshi yafara yawo acikin jikinta. Yadda gabanta yake fad'uwa Faruk yana ji dan har lokacin tana manne a jikinshi, cike da tsoro tace dan Allah Yaya Faruk kadaina. Cikin kunnenta yarad'a mata Habibti yau fa ranar farin ciki ce agaremu dan Allah kibarni inyi. Runtse idanunta tayi jin ya kirata da sunan da Umar yake kiranta da shi, jin ta yi shuru yasa yakwantar da ita ahankali nan yazuba mata idanu yana k'are mata kallo, ahankali tabud'e idanunta takalleshi ganin yadda yatsareta da mayun idanunshi sai a lokacin yakashe masu fitila. Jawahir koda take ba sabuwar shiga ba ammah ta gurzu a hannun Faruk dan har kuka saida tayi saboda wahalar da tasha, Faruk ko za'a iya cewa fita yayi hayyacinshi, saida yasamu nutsuwa sannan yabarta. 'Daukarta yayi sukayi wanka tare sannan suka dawo suka kwanta yana manne da ita a jikinshi. Washe gari bayan sunyi sallar asuba komawa sukayi bacci ba sune suka tashi ba sai wajen k'arfe tara da rabi, Faruk nema yayi suyi wanka tare da Jawahir tak'i dan kasa had'a idanu tayi da shi saboda kunya daga k'arshe yad'auketa yashiga da ita toilet tana ta nuk'u nuk'u da jiki yashareta yawanketa tas sannan shima yayi wanka. Bayan sun fito ne suka shirya sannan yajata suka nufi babban parlor. Suna zuwa suka samu Nasiba zaune ta sha gayu tana jira sufito. Tana ganinsu murmushi tasaki tare da tashi cikin sauri tanufi inda suke tana zuwa tarik'e Jawahir da kanta yake sadde k'asa tace amarya sannunku da fitowa. Maimakon ta amsa saima duk'awa da tayi tagaisheta amsawa tayi tare da rik'o hannunta tamik'e tace ina fata dai kina lafiya. 'Daga Kai tayi cike da jin kunya. Kallon Faruk tayi da yake ta faman murmushi nan itama tayi murmushi sannan tagaisheshi, jawota yayi yarungume ahankali cikin kunnenta yarad'a mata kin mance irin gaisuwar da kikeyi min?. Murmushi tayi itama ahankali tace yanzu ai bamu kad'ai bane Lovely dole mucanza,,, tana fad'in haka tazare jikinta tare da rik'o hannun Jawahir gudan hannun tarik'o nashi tace muje kuyi breakfast kar mubar amarya da yunwa. Dining suka wuce tayi serving d'in kowa nan suka fara ci Jawahir ba wani ci take sosai ba Faruk yana lura da ita ji yake kamar yayi mata d'ure dan de kawai Nasiba da ke wajen. Nasiba tana gama ci tatashi takoma d'akinta dan tabasu waje Faruk ko kamar jira yake nan yafara feeding d'in Jawahir saida yatabbatar ta k'oshi sannan yabarta. Waya aka kirashi dan haka tatashi takoma part d'inta tagyara abunta sannan tazauna takira su Baba Malam a waya suka gaisa. Tana cikin wayar Faruk yashigo daga gefenta yazauna har saida tagama sannan ya amshi wayar ya ajiye yace habibty shine kika gudo kika barni ko? Murmushi tayi tace ba gudowa nayi ba. Rungumeta yayi sannan yace toh me kikayi?. Shuru tayi nan yasafke ajiyar zuciya sannan yace dan Allah Habibty ataimaka a ajiye kunyar nan dan ina buk'atar kulawarki sosai. 'Dagowa tayi takalleshi har ta bud'e baki zatayi magana sai kuma tafasa ganin haka yasa yakwantar da ita sannan shima yakwanta gefenta yadinga janta da hira tana d'an biye mashi. Wajen azuhur sukayi wanka sannan yatafi masallaci ita kuma tayi sallarta a gida bayan ya dawo Nasiba tazo takirata sukayi lunch. Da marece yafita dan haka suka samu damar zama ita da Nasiba suka sha hira sosai dayake Nasiba akwaita da son mutane nan da nan tasa Jawahir tasake da dare tare suka shiga kitchen sukayi girki duk yadda taso Jawahir tabarshi ammah tak'i saida takama mata sukayi. Tun daga ranar tare suke girki breakfast ne kawai bata samun damar fitowa suhad'a tare saboda Faruk baya bari ahaka har suka cinye kwana ukkunsu a ranar da zai koma wajen Nasiba nan tace ta k'ara masu sucike sati guda dan a lokacin bata jin dad'in jikinta kawai dai bata nuna masu ba dan kar sutada hankalinsu, koda Faruk ya ji dad'in hakan ammah bai nuna mataba, a fili yanuna bai yarda ba saida tadinga lalla'bashi sannan ya amince yakoma suka ida sati gudansu yakoma hannun uwargidanshi inda yanuna ya yi missing d'inta sosai, ta ji dad'in ganin yadda yanuna mata ya yi missing d'inta. ***** Zaman lafiya sukeyi sosai idan kaga Nasiba da Jawahir baka ta'ba cewa kishiyoyine dan suna k'aunar junansu suna mutunta juna, Faruk ko ya zage wajen kula da matanshi ko da sau d'aya baya yarda a fuska yanuna ga wadda yafi so saidai idan ya ke'be da matanshi ne yake nuna masu yadda yake k'aunarsu nan kowace hankalinta yakwanta ganin ta ciri tuta a wajen mijinta *BAYAN WATA 'DAYA* Kasancewar lokacin Hajji ne daman tuni ya biya masu batare da saninsu ba nan yad'auki matanshi sukaje aikin hajji. Tunda sukaje Nasiba batada cikakkar lafiya ahaka tayi hajjinta saidai jawahir take kula da ita da mijinsu. Sai da suka gama hajji sunje umrah sannan taga likita a chan ne yake sanar da su tana da shigar ciki na wata biyu nan su Faruk da Jawahir sukaita murna. Bayan sun dawo ne suka cigaba da kula da ita dan Jawahir bata bari ko cokali tad'auke inda a 'bangaren goga Faruk ma haka duk motsin da zatayi sai sun tambayeta abinda yake damunta hatta abinci sai ta fad'i irin wanda za'a dafa. Tana jin dad'in irin kulawar da suke bata da cikinta. Watansu d'aya da dawowa suka shirya suka je kebbi lokacin cikin Nasiba yana wata ukku kwanansu biyu suka dawo gida. Jawahir kanta ta samu nutsuwa sosai dan har k'iba ta yi koda su Baba Malam suka ga yadda take cikin kwanciyar hankali sai hankalinsu yakwanta, sunje gidan Khausar dan ita Rashida ta dawo gida saboda laulayin da takeyi. Ranar wata litinin Jawahir tashigo parlor tasamu Nasiba zaune tana cin yalo gefenta Faruk ne zaune, zuwa tayi tazauna tana cewa Auntyna me kuma ake ci? Murmushi Nasiba tayi tace kinganni nan wallahi yalo naji inaso shine oga yasiyo min. 'Daukar guda tayi tace bari inci wannan dan gaskiya ya biya raina. Dariya Nasiba tayi tatura mata robar yalon tace kici iya cinki sister ni har ya fara isata tun d'azu nake ci. Murmushi Jawahir tayi nan tace nagode Auntyna sannan tafara ci, kallon Faruk tayi tace Lovely (dayake itama sunan da take kiranshi da shi kenan) maimakon kasiyo har da d'ata ? Murmushi shima yayi yace toh ai bakice asiyo makiba habibty Auntyn taki yalo kawai tace asiyo. Ajiye yalon tayi tace ni d'ata nakeso Allah ban iya cin yalon. Faruk kallon Nasiba yayi itama takalleshi sukai murmushi sannan tace 'yar k'anwata ko dai kin kamu ne kema? Turo baki tayi tace ban kamu da komai ba Aunty kawai dai d'ata nakeso. Murmushi Faruk yayi yace toh shikenan bari insa asamo maki ai duk zan iya da ku nan yad'akko wayarshi yakira megadi yafad'a mashi. Mik'ewa tayi taje kitchen tad'aura masu girki daurewa kawai take dan kwana biyun nan itama ba isassar lafiya gareta ba...... _Sis Nerja'art✍🏻_ [7/24, 11:22 PM] Sis Nerja'art 2: *......FANSAR RAI......* *INTELLIGENT WRITER'S ASSO....®* [On Ward Together] _Follow me on Wattpad: *Sis-nerja*_ _Wannan Littafin na kud'i ne domin karantawa cikin aminci da yarda ga duk me buk'ata zai turo katin Mtn na d'ari biyu N200 kacal ta wannan number d'in 09035938246, ko ta account number 5330055604, Idan katura ka aiko da screen shot na transaction a wannan number d'in 09035938246_ _Akwai gara'basar *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shahararriyar marubuciyar nan *AMEENA ABBA UMAR* tare da novel d'in *FANSAR RAI* akan farashin N300 kacal, ko da kud'in ka sai da rabonka_ *PAGE 27* Cikin Nasiba yana da wata hud'u lokacin aka fiddo da su Alhaji Sufyan daga gidan yari za'a ratayesu dan a lokacin shekararsu guda cif a gidan kaso, duk sunyi bak'i sun rame, a mota aka kaisu gidajensu dan suyi bankwana da iyalansu, Mummyn Nasiba a waya takirata dan taje ammah tace babu inda zata batason sake sakashi a cikin idanunta, nan tazauna tadinga kuka, Jawahir ganin yadda Nasiba take kuka yasa duk sai jikinta yayi sanyi duk'awa tayi gabanta tana hawaye tace dan Allah Aunty Nasiba kiyi hak'uri nasan ni najamaki da badan haka ba da duk haka bata faruba dan Allah kiyafe min. 'Dago kai Nasiba tayi takalleta cikin kuka tace wallahi ba laifinki bane Jawahir bakida laifin komai a ciki *SON ZUCIYA* ne da kwad'ayi suka ja ma Daddy ina nadamar kasancewarshi mahaifi agareni yanzu gashinan abinda yaja ma kanshi, ba wai ina kuka akan abinda za'ayi mashi bane kawai dai ina kuka akan mutuncinmu da yazubar mana yanzu shikenan kowa zai dinga kallonmu da abinda mahaifinmu ya aikata na tabbata yau dai ta kasance *RANAR NADAMA* agareshi ranar da bai ta'ba tunanin zata zo mashi ba saidai nadamar bazata ta'ba kasancewa mai amfani agareshi ba. Jawahir ma fashewa tayi da kuka nan aka rasa me rarrashin wani saida sukayi me isarsu sannan sukayi shuru dan lokacin Faruk baya gida. Su Alhaji Sufyan da Alhaji Mansur bayan ankaisu sunyi bankwana da iyalansu nan aka wuce da su wajen da za'a ratayesu su dukansu kuka suke sha'be sha'be kamar k'ananun yara, d'aura su akayi saman wani dogon gini aka rufe masu fuska sannan aka sa igiya aka rataye masu kai sasu akayi sukayi kalmar shahada sannan aka saki igiyar sukayo k'aya, ji kake k'yat alamun karyewar wuya nan sukaita wuntsila wuntsila da k'afafu har saida ransu yarabu da jikinsu. ________ Jawahir tunda tatashi yau dakyar tayi sallar asuba nan saman darduma tayi kwance dan ranar Faruk ba a d'akinta yakeba, wajen k'arfe shidda yashigo yasameta kwance ta k'udundune tana ta kwasar bacci wajen da take yanufo yana cewa Habibiti ba dai har yanzu bacci kike ba, ta'bata yayi yaji jikinta da zafi. Rud'ewa yayi yace subhanallahi ba dai bakida lafiya ba. Maganarshi ce tatasheta daga baccin da take nan tabud'e idanu dak'yar k'amshin turarenshi ne yadoki hancinta tayi saurin tureshi tamik'e tashiga toilet tafara kwarara amai. Hankalin Faruk ya tashi sosai ganin yadda take amai kamar zata amaye 'yan hanjin cikinta gabad'aya ta galabaita tana gama aman taimaka mata yayi tai wanka tashirya sannan yafito da ita yace ma Nasiba zasuje asibiti Jawahir bata da lafiya hankalin Nasiba ya tashi sosai tace saidai suje tare. Haka ko akayi atare sukaje wajen family doctor d'insu da yace susameshi a asibiti nan yadubata yaimata tambayoyi tabashi amsa sannan yarubuta mata tests yace taje ayi mata a lab. Bayan sunyo sun kawo sakamako nan yake tabbatar masu da tana d'auke da ciki tsawon wata ukku, murna wajen Faruk da Nasiba ba'a magana dan ita ko uwar gayyar kunya ce takamata. Haka suka dawo gida suna ta murna Faruk ko baki har kunne yana ta godiya ga ubangiji ganin matanshi dukansu ciki garesu Nasiba nata wata hud'u Jawahir kuma wata ukku. Zuwa yayi yasanar da su Mom su ma sukaita murna nan tasamo masu wata mata tazo gidan tazauna tana masu girki da gyaran gida. 'Dakunansu da na mijinsune kawai basu bari agyara masu su suke abunsu. Faruk ko indai yana gida toh yana manne da matanshi yana basu kulawa sosai duk abinda sukeso sai ya samo masu shi, kusan tare suke rainon cikin da shi. Dan ma Jawahir nata ba mai laulayi bane sosai saisa take samun damar yin wasu ayyukan indai bai gida tare da ita ake girkin abinci. Faruk d'aukarsu yayi yakaisu gidan Ummah suka ganta nan Ummah tayi ta kuka da taga jawahir tana rok'onta gafara Jawahir ta tausaya ma halin da taga ummah dan har lokacin 'barin jikinta d'aya shanye yake komai sai anyi mata har kuka jawahir tayi saboda tausayi tace ta yafe mata tad'auko kud'i masu yawa tabata. *BAYAN WATA SHIDDA* Cikinsu ya tsufa sosai dan a lokacin Nasiba nata yana cikin wata na goma ana sa ran haihuwa yau ko gobe inda Jawahir nata yake wata na tara. Mummyn Nasiba ta so amaido mata Nasiba tahaihu a gida ganin abubuwan zasuyi mashi yawa mata biyu duk tsohon ciki garesu ammah Faruk yace a'a abarsu zai iya saidai Inna Mairo da tazo daga Kebbi tazauna tana kula da su gabad'aya dan cewa tayi da Nasiba da Jawahir dukansu d'aya ne a wajenta. Yau tun da Nasiba tatashi take fama da ciwon mara haka suka fito zasuyi breakfast daurewa kawai takeyi bata bari sun ganeba kasa cin komai tayi chan da taji cikinta ya wani irin juya mata nan tafara cize le'be. Ganin haka yasa duk hankalinsu yatashi Faruk yayi saurin yo inda take yana tambayarta lafiya. Jawahir ma saurin mik'ewa tayi tanufi wajenta cikin tashin hankali tana cewa Aunty me yake damunki ko jikin ne? Girgiza kai tafara yi cike da juriya tace wayyoo cikina. Faruk rasa yadda zaiyi yayi nan yakwala ma Inna Mairo kira cikin sauri tazo ganin halin da Nasiba take ciki yasa tace haihuwa ce yayi maza yakaita asibiti. 'Daukarta yayi chak yafita da ita jawahir da take ta faman kuka zuwa tayi tad'akko jikkar kayan haihuwar da aka tanada lokacin da tafita Faruk har yasakata cikin mota nan ya amshi jakkar yace takoma gida. Cikin kuka tace ita dai saidai suje tare bazata zauna ba. Kallon inna Mairo yayi yace takula da ita bari suje nan yashiga mota yajata dagudu yanufi asibiti da Nsiba da take kwance tana ta salati. Yana isa Hajiyar Nasiba ta isa a daidai lokacin nan aka wuce da ita labour room Nasiba duk ta fita hayyacinta sai zufa takeyi. Nan su Faruk da Hajiyar Nasiba sukayi cirko cirko suna jira. Jawahir ko tunda suka koma cikin gida kasa tsaye da zaune tayi dan hankalinta ya tashi sosai akan halin da taga Nasiba a ciki, inna mairo lalla'bata tadinga yi dan takwantar da hankalinta saboda tsohon cikinta ammah tak'i kiran Faruk tadinga yi a waya tana tambayarshi halin da Nasiba take ciki ko ta haihu saidai yace a'a sudai cigaba da mata addu'a. Sai wajen k'arfe d'aya sannan Nasiba tahaifo shantalelen d'anta jajir da shi sak Faruk nan su Faruk da Mummyn Nasiba suka dinga murya har da su Yaya Sadiya da su ma sunzo asibitin. Faruk kiran jawahir yayi a waya yafad'a mata nan tadinga murna sannan yakira su Mom yasanar da su. Wajen k'arfe biyu aka sallamesu bayan antabbatar da lafiyar me jego da ta baby. Mummyn Nasiba ta so tawuce da ita gida ammah Faruk yace a'a dan haka tayarda suka koma gidanshi. Suna isa Jawahir ce tafara zuwa dagudu ta amshi yaron tarungume tana murna sannan tayi ma Auntynta ta barka. Nasiba d'akinta tawuce takwanta kafin ruwan zafin da su Inna Mairo suka d'aura yadafu. Duk wanda yazo saidai yakalli baby a hannun Jawahir dan kamashi tayi tarik'e yaron ya shiga ranta sosai, su Inna Mairo saidai suka dinga mata tsiya suna cewa itama ai sai takawo masu kamarshi tunda haihuwartata yau ko gobe ne. Su Mom duk sunzo barka a ranar gidan cika yayi da jama'a. Wajen k'arfe biyar Jawahir tazame kanta takoma d'akinta dan daman tun da aka tafi da Nasiba asibiti tafara jin ciwon mara kawai dai tana daurewane ammah a lokacin taji abun ya k'aru a k'asan kafe tazauna nan tafara murk'ususu tayi kusan minti talatin a nan Inna Mairo tashigo tasameta a wannan halin duk ta jik'e sharkaf da zufa, hankalin inna mairo ya tashi sosai tatambayeta abinda yake damunta ammah jawahir takasa cemata komai saidai gefen mararta da take nuna mata nan Inna Mairo tagane nak'uda ce takeyi cikin sauri tafita taje part d'un Faruk tasanar dashi. Nan yafito a rud'e yazo yad'auketa da inna mairo sukaje asibiti duk wannan abun su Nasiba basu saniba suna chan part d'inta da jama'a 'yan zuwa barka. Suna isa asibiti aka kar'beta aka shiga da ita labour room ana gama sallar magrib tahaifo shantalelen d'anta, nurses suka fito suka sanar da su Faruk nan yad'aga hannu yaita godiya ga ubangiji akan kyautar da yayi mashi ta 'ya'ya biyu a rana guda, kawo mashi d'an akayi shima kyakkyawa da shi yana kamashi da shi waya yad'akko yakira Nasiba yafad'a mata. Da fari bata yarda ba saida yarantse mata nan ita da 'yan barka akaita mamakin haihuwar jawahir, su mom yakira basu d'au lokaci ba suka iso asibitin. Faruk jin abun yake kamar a mafarki wai shine da yara biyu a rana guda. Sai bayan sallar isha'i aka sallamesu suka koma gida nan ma aka kafa wata sabuwar murnar. 'Yan barka santin yaran suka dinga yi ganin kamanninsu guda da yanayin jikinsu duk na mahaifinsu ne idan ba amfad'a makaba sai kace 'yan biyu ne mutum d'aya yahaifesu. Dad da Mom ma sunyi farin ciki sosai ganin rana guda sun samu jikoki har biyu. Faruk ko da ka kalleshi kasan yana cikin farin ciki kasa zaune da tsaye yayi, Inna Mairo ce tagyara maijego sannan tasata taci tuwon da aka girka masu. Gida kullum cike yake da mutane 'yan barka kowa yana farin cikin k'aruwar da aka samu, Dad kud'i yafitar sosai yaba Mom taje dubai tasiyo ma yara kaya duk iri d'aya sannan aka siya ma masu jego kaya kowa akwati biyu. Ranar suna Faruk ya yi bajinta dan kud'i yafitar sosai akayi hidimar suna da su, inna mairo ita takeyi ma jarirrai da masu jego wanka, shiga iri d'aya Jawahr da Nasiba sukeyi a zaman barka hatta jarirran ma haka. Ranar daren suna Faruk yakira matan nashi a part d'inshi yatambayesu sunan da suke so asa ma yaran, Nasiba ce tayi saurin cewa tana so asa ma nata sunan mahaifin Jawahir. Jawahir saboda mamaki kasa cemata komai tayi saidai hawaye da suke fita daga idanunta daga k'arshe tasafko k'asa tadurk'usa tare da rik'o hannun Nasiba tana mata godiya. Nasiba tace bakomai ta cancanci fiye da hakan a wajenta. Shi kanshi Faruk ya ji dad'in hakan da Nasiba tayi nan yatambayi Jawahir sunan da ita takeso asa ma nata. Itama tace sunan mahaifin Nasiba, nan Nasiba tace bata yarda da hakan ba bataso asa sunan mahaifinta dan bai cancanci hakan daga jawahir ba nan tanemi alfarma da jawahir tabarta taza'ba mashi suna Jawahir amincewa tayi Nasiba taza'ba mashi sunan Dad. Faruk ya ji dad'in haka yai masu godiya sannan yad'akko makullan mota yadamk'a masu kowa da tashi suma sukayi godiya. Baba Malam shanu biyu ya aiko masu da su inda Dad yasiyo manyan raguna biyu ya aiko da su. Ranar suna yara suka ci suna Muhammad da Sani inda Muhammad ake kiranshi da Affan, Sani kuma suna kiranshi da Ameer, anyi shagali sosai ankashe kud'i abun sai sambarka dan shiga iri d'aya masu jegon suka dinga yi yaran nasu ma haka mutane dadama sunyi sha'awar yadda kishiyoyin biyu suke tafiyar da rayuwarsu da k'aunar da suke nuna ma junansu. Faruk ko ji yake kamar ya fi kowane namiji sa'ar samun mata. Bayan angama hidimar suna anwatse nan Inna mairo tacigaba da kula da masu jego da yaransu, gyara tadinga yi masu na mutunci yadda zatayi ma Jawahir haka takeyi ma Nasiba bata barinsu suke'be da mijinsu har saida suka yi arba'in sannan tatattara takoma garinsu tare da sha tara na arzik'i da tasamu daga wajen Faruk da matanshi hatta mummyn Nasiba da su Mom saida sukayi mata kyauta me tsoka. Faruk hankalinshi kwance yana kula da matanshi sosai gefe guda ga yaransu da suke ta girma sun taso da ka gansu ka ga tagwaye dan komai iri d'aya akeyi masu kamanninsu sai k'ara komawa take sak ta mahaifinsu. **** ****** Dad yana kula da companynshi da na jawahir sosai nan sukaita k'ara ha'bbaka kud'ad'e suna shigowa yadda yakamata, tura ma jawahir kud'inta yake ta account d'inta baya cin ko naira d'aya ko da tana cewa yadinga d'ibar kasonshi ammah yace a'a baida kaso a ciki na companynshi ya isheshi dan haka tadinga tura ma su Baba Malam tatura ma Baba Musa kud'ad'e sosai yasa aka gyara masu gidansu. Cikin kud'in tafidda wani kaso da fili tadamk'a ma Nasiba nan Nasiba tayita mata godiya har da kuka. Sannan tasa aka gina masu wani k'aton boutique wanda akayo masu order kaya a chan dubai duk wasu kaya na gani na fad'a anzuba su a tantsamemen boutique d'in da yaci suna *FANAJ BOUTIQUE* wanda aikin Jawahir ne nan su Nasiba da Faruk sukaita jin dad'i. *BAYAN SHEKARA 'DAYA DA WATA BIYU* Nasiba ce zaune a babban parlornsu inda gefenta Ameer da Affan ne suna ta wasa da kayan wasan da aka baje masu, duba lokaci kawai take kasancewar darene, Jawahir ce tashigo parlorn babu ko sallama sanye da hijab da alama daga anguwa suke, zama tayi saman kujera batare da ta ce ma Nasiba komai ba ganin haka yasa Nasiba hankalinta yatashi tace lafiya Sis me yake faru tun d'azu ina nan ina jiranku kudawo daga asibitin ko jikin ne? Hawaye ne suka gangaro ma Jawahir. Mik'ewa Nasiba tayi takomo kusa da ita tana cewa lafiya Jawahir kifad'a min abinda yafaru kinga hankalina ya tashi. Tun kan tayi magana su Ameer suka nufo wajen dagudu suka fad'a jikin Jawahir cikin maganarsu da bata fita sosai suka ce Ammi kin siyo mana chocolate d'in? Nasiba ce tarik'osu ganin suna neman haye Jawahir tace kunga Ammi batada lafiya kubarta. Affan ne yaturo baki yace uhm uhm Ummi. Murmushi Nasiba tayi tace ni bari inbaku chocolate d'in, nan tajasu taje tad'akko masu a part d'inta sannan suka zauna suna sha suna wasa. Kusa da Jawahir takoma tana cewa kiyi min bayanin abinda yafaru Sister. Shigowar Faruk ne yasa duk suka juya suka kalleshi Nasiba tace yauwa gaka wai me yake faruwa ne dan Allah me likita yace yana damunta. Murmushi Faruk yayi tare da mik'a mata takardar hannunshi yace k'aruwa muka samu. Saurin amsa tayi tana dubawa tayi saurin rungume jawahir tana cewa Alhamdulilah Sis ashe mun samu baby har na tsawon wata biyu wayyo dad'i. Fashewa da kuka Jawahir tayi cikin kuka tace wallahi ba'a kyauta min ba duka yaushe na haifi Affan ko yayeshi banyi ba sai ace ina da wani cikin. Nasiba kallon Faruk tayi sukai murmushi sannan tace toh menene Sister ai ba wani abu bane. Wallahi wani abune Aunty Nasiba duka nawa nake da za'a ce ina da ciki na biyu kuma kema ai da sai yayi maki inda ta tsakani ga Allah yabi. Faruk da Nasiba dariya ce take cinsu, yadanne tashi yace toh ai itama yi mata zanyi kikwantar da hankalinki. Mik'ewa tayi tana turo baki tace ai da yi mata zakayi kamar yadda muka haihu tare wannan karon ma sai kayi mata,,, tana fad'in haka tawuce fuuu tanufi part d'inta. Nasiba da Faruk ko me zasuyi inba dariya ba Nasiba tace ina ruwan Jawahir da wauta. Tsagaitawa yayi da dariyar da yake yace toh kin dai ji abinda tace kema inyi maki kusake haihuwa tare. Zaro idanu Nasiba tayi waje tace karufa man asiri Lovely idan nima nayi cikin wa zai kular mana da su Affan? Juyawa tayi takallesu taga har sunyi bacci a saman carpet d'in tace kaga tashi muje katayani d'aukarsu inkaisu d'aki inyaso sai kaje chan kayi ta lallashi dan ka yi laifi. Mik'ewa yayi yace kedai bari hearty akwai aiki agabana. Dariya tayi tad'auki Affan shi kuma yad'auki Ameer suka nufi part d'inta, saida tawanke masu hannu sannan takwantar da su a saman gado dan dama tuni ta yi masu shirin bacci tazauna jiran dawowarsu Faruk, itama tahau takwanta, daga gefenta Faruk yazauna yace hearty ba dai bacci zakiyi tun yanzu ba duka fa yanzu tara tayi. Hamma tayi tace wallahi Lovely yau d'in ne jina nake duk wata iri kamar banda lafiya. Kwantar da kanshi yayi a saman k'irjinta yace Hearty ko dai kema kin kamu? Zaro idanu tayi waje tace karufa min asiri ni banda komai. Murmushi yayi yace toh inma akwai ya kuka iya tunda kuna tare da lafiyayyen miji ni ai abun farin ciki ne agareni kuyi ta haifa min 'yan tagwaye. Turo baki tayi tace nidai a'a. Bakinshi yasa yaciji le'benta ahankali yace kedai Eh Hearty, Kallon agogo tayi tace dan Allah katashi kaje kaji da 'yar uwata ka barota ita kad'ai. Tallabo fuskarta yayi yace wai da ingama ji da ke kafin inje,,yafad'a yana kashe mata ido guda. Tureshi tayi daga jikinta tatashi zaune tace dan Allah lovely katafi ka ga ka barta ita kad'ai gashi batada lafiya. Shafa cikinta yayi yace kema d'in ai bakida lafiya. Uhm uhm ni lafiya ta lau,, tafad'a tana ture mashi hannu. Tallabo fuskarta yayi yamanna mata kiss a baki, nan takoma takwanta, shafa kanta yayi yace zan tafi Hearty sai dasafe. Murmushi tayi tace Allah yakaimu masoyina abun alfaharin mu,, tana fad'in haka tayi saurin juya mashi baya dan tasan idan ba haka tayiba bazai barta ba, tana jinshi yabata peck a kumatu tare da cewa ina sonki sosai matata kikular min da kanki. Murmushi kawai tayi batare da ta ce komai ba nan yakalli yaran nashi da suke ta bacci sannan yakashe masu fitala yafita yabar d'akin. Part d'inshi yawuce yafara yin wanka saida yashirya cikin shirin bacci sannan yafito yanufi part d'in Jawahir yana zuwa yasameta kwance saman gado ta lumshe idanunta ammah daga ganin yanayinta ba bacci take ba, zama yayi a gefen gadon yakai hannu yashafa fuskarta sannan yace taya masoyiya zatayi fushi da masoyinta dan kawai Allah ya basu kyautar da ba wanda zai iya basu ita idan ba shi ba, Ahankali tabud'e idanunta takalleshi sai kuma tajanye fuskarta gefe. Ajiyar zuciya yasafke yace Habibty kinsan dai banason ganinki a wannan yanayin dan Allah kifad'a min menene laifina a ciki. Turo baki tayi cikin shagwa'ba tace toh ba kaine kayi min ciki ni kad'ai ba bayan wanchan karon tare da Aunty Nasiba muka haihu. Dariya ce take cinshi ammah yadanne dan kar yayi wani laifin sannan yace toh ai kece kin fita zalama saisa kika rigata samun ciki. Kallon rashin fahimtar inda maganarshi tadosa tayi mashi tace me kake nufi da hakan? Wane irin zalama nafita?. Ganin bata ganeba yasa yace babu komai itama ai tana da nata cikin ba wai ke kad'ai nayi mawa ba. Saurin tashi zaune tayi cike da jin dad'i tace dan Allah dagaske kake lovely. 'Daga mata gira yayi nan tafad'a jikinshi tare da rungumeshi tace na ji dad'i sosai Lovely. Shima rungumeta yayi yace dan Allah Habibty kuyi hak'uri da yanayina ina son 'ya'ya sosai in son samune kuyi ta haifa min su dayawa. Ajiyar zuciya tasafke tace kayi hak'uri lovely nasan ban kyauta maka ba da fushin da nayi akan kyautar da ubangiji yabamu dan Allah kayafe min 'Dago kanta yayi yakalli cikin idanunta sannan yace babu komai Habibty ai ku d'in baku laifi ina k'aunarku fiye da tunaninku nidai fatana kucigaba da nuna min k'auna da tarairaya. Zaka samu fiye da hakan ma Lovely, ina sonka so na gaskiya wanda ni kaina bazan iya misulta shi ba bana ji zan iya son wani kamar yadda nake sonka. Tun kan tarufe baki yace kina nufin har Umar? Murmushi tayi tare da komawa takwanta tace tabbas nasan na so Yaya Umar saidai son da nakeyi maka ya lunka wanda nayi mashi saboda kai da gabad'aya rayuwata nake k'aunarka shi kuma da zuciyata, na mallaka maka gabad'aya soyayyata. Wani irin farin cikine yalullu'be Faruk yai saurin rungumeta yace nagode sosai Jawahir da irin wannan matsayin da nasamu awajenki, nagode ma Allah da yamallaka min ke amatsayin mata na soki tun lokacin da banyi tunanin zan sameki ba ashe ke d'in rabona ce. Lumshe idanunta tayi tare da tura hannuwanta cikin sumar kanshi tana shafawa tana jin sonshi yana k'ara mamaye mata duk ga'b'ban jiki. Lamo yayi a jikinta sai kuma chan yad'ago yakalleta itama bud'e idanunta tayi suka sakar ma juna lallausan murmushi tace ya dai Lovely? Mik'a yayi sannan yace ya kamata aji da ni yanzun nan gaskiya. Hararshi tayi cikin wasa sannan tace bayan cikin da kayi min sai kuma kace wani inji da kai. Toh ya kika iya tunda kina auren lafiyayyen miji ko ana nufin baza'a baniba. Saurin jawoshi tayi yafad'o jikinta tace ni wacece da zan hana mijina shi da kayanshi akoda yaushe ashirye nake domin kar'barka. Murmushi Faruk yayi yakai hannu yakashe masu fitila tare da jawo bargo yalullu'besu. _Ina ganin haka nayi saurin tattaro takarduna da alk'alamina nafito daga d'akin tare da jawo masu k'ofa nace asuba tagari Mr nd Mrs *FANAJ*_ *BISSALAM* _Alhamdulillah anan muka kawo k'arshen wannan littafin me suna *FANSAR RAI* kurakuren da suke ciki Allah yayafe mana_ _*Nagode sosai da irin k'aunar da kuka nunamin da lokacinku da kuka bani Allah ubangiji yabar zumunci Allah yak'ara dank'on zumunci*_ _Ina maku albishir da sabon novel d'ina me suna *KUWWA DA KUWWA* (bata korar buzu)_ _Labari ne wanda yak'unshi abubuwa da dama wanda sai mutum ya karanta sannan zai fahimci hakan ga kad'an daga cikin labarin_ ~~~~~~ _*KUWWA DA KUWWA.....*_ _(Bata korar buzu)_ Kwance take saman makeken gadonta tana bacci inda dogon gashinta yabaje mata a fuska, yanayin yadda take baccin kawai zaka kalla kagane cewa a nutse takeyin shi, lokaci guda tatashi zaune zumbur tare da saurin sa hannunta takare fuskarta, wani irin farin haskene yadaki tafin hannunta ji kake wata irin k'ara k'attt. Janye hannunta tayi tare da sa gudan hannun tagyara gashinta da yake baje a fuskarta nan kyakkyawar fuskarta tabayyana, ajiyar zuciya tasafke tare da mik'ewa tsaye tanufi wajen makeken mirror da yake manne a bangon d'akin tatsaya tana duba fuskarta, komawa tayi tazauna tare da dafe kanta da hannu biyu cikin siririyar muryarta me dad'in saurare tace *Najma* meyasa kike kai ma fuskata hari meyasa kikeso ki'bata min fuska? sauri janye hannunta tayi takalli zobenta da yake manne a dogon yatsan hannunta na tsaka sai kuma tamik'e tanufo k'ofa tun kan ta iso k'ofar dakanta ta bud'e, tana fita parlor nan wasu mata kusan su goma da suke sanye da kaya iri d'aya suka zube k'asa suna kwasar gaisuwa, batare da ta amsa masuba taje bisa lumtsumemiyar kujerarta tazauna sannan da hannu tayi masu nuni da subar wajen. Cikin sauri duk suka tashi suka fita tare da jawo mata k'ofa. Duk wannan abun da yake faruwa tana gani a cikin wani d'an k'aramin madubi dake hannunta, wurgi tayi da madubin ganin batayi nasara ba tamik'e cikin fushi tana cewa ko da ba yau ba *Najla* sai na cika burina, sai na 'bata maki wannan kyakkyawar fuskar da kike tak'ama da ita bazan ta'ba barinki ba.... ** ** ** ** Tunda suka shigo cikin garin kallon mutane kawai suke abun yana burgesu ganin yadda suke ta rayuwarsu, itako shugabar tasu yatsina fuska kawai take dan abun sam bai burgeta ba, suna tafiya a wajen titi wata mata tagifta ta gabansu nan d'aya daga cikinsu tafara lasar baki saurin shak'o wuyanta gimbiya najma tayi tace kar kikuskura kilashi wani a cikin garin nan domin garin nan yana da had'ari sosai duk mayen da suka kama basu barinshi a raye,,, tana fad'in haka tatureta gefe nan tayi saurin duk'awa cike da girmamawa tace kigafarceni ya shugabata. Batare da ta amsa mataba tawuce gaba suna biye da ita a baya suna cikin tafiya a wajen kasuwa tana kallon wani shago da yad'auke mata hankali saboda cikowar mutanen da suke cikinsh nan wani tsoho yatafo da 'yar sandarshi yana dogarawa bai kulaba yad'an bugeta. A fusace tajuyo takalleshi tare da shak'oshi cikin fushi tace kai wane irin dabba ne da zaka bugeni, bakasan wacece ni ba?. Jikin tsohon yana karkarwa yace kiyi hak'uri bana gani sosai ne. Batare da ta sakeshi ba tace bana yafiya a duk lokacin da akayi man laifi sai na d'auki fansa dan haka bazan ta'ba barinka ba, dogon harshenta tafara fiddowa daga cikin bakinta tana shirin lashe fuskar tsohon, daga bayanta taji andaka mata tsawa saurin maida harshen tayi tasaki tsohon tajuyo dan ganin wanda yayi tsawar Wasu mutane ne tagani tsaye a bayan wani kyakkyawan saurayi yana sanye da kaya na sarauta duk sun fito daga cikin motocinsu, saurayin ne cikin 'bacin rai yace ke wace irin macece bakida hankali zaki shak'e tsoho ko iyayenki basuyi maki tarbiya ba?. Tsayawa tayi tana kallonshi cike da mamaki jin kalaman da yake fad'a mata wanda tunda take a rayuwarta ba'a ta'ba fad'a mata irinsu ba sai yau da tashigo k'asar nan yawon bud'e ido. Kallon tsohon saurayin yayi yaga yana ta kyarma sannan yakalli nakusa da shi yace aje arakashi gida. 'Dan russunawa yayi yace angama ranka yadad'e nan biyu daga cikin mutanen suka yi saurin nufar inda tsohon yake suka ruk'oshi suka sa cikin mota suka tafi da shi. Kallon kallo suka dinga yi shi da Gimbiya Najma yana mata kallon tsana, inda ita kuma take jifanshi da mugun kallo, sai kuma chan yajuya aka bud'e mashi mota cikin k'asaita yashiga aka rufe nan sauran mutanen nashi kowa yashiga mota suka bad'a ma su Najma k'ura suka tafi. Cikin 'bacin rai tace wanene wannan? Wanene shi da har zai d'aga min murya? Ya zama dole kubishi kugano min inda yake da kuma matsayinshi a garin nan dan bazan ta'ba barinshi ba!!! Mata ukku ne suka 'bace lokaci guda. Nan Najma takalli sauran tana hucci sai kuma tarufe idanunta tana motsa baki ahankali nan ita da sauran matan suka 'bace 'bat. ___kuyanginta ne zaune kusa da ita suna ta mata hidima inda ita kuma take ta murza zoben da yake hannunta, k'wank'wasa k'ofa akayi nan masu tsaron k'ofar sukayi saurin bud'ewa. Wata farar macece tashigo fuskarnan fara fat. 'Dago kai Najla tayi takalleta tace Hasisa ina kika shiga yau tun d'azu ina ta nemanki. Saurin duk'awa tayi tace kigafarceni ya shugabata hak'ik'a na zo maki da wani labari da zai sakaki cikin farin ciki. Idanu Gimbiya Najla tazuba mata hakan yaba Kuyangar damar cigaba da maganarta dan tasan shugabar tasu ba me yawan hayaniya bace... Yau 'yar uwarki tafita da bak'ak'en kuyanginta yawon bud'e ido inda ni kuma nayi amfani da tsafina nabisu batare da na bari ta ganni ba, wata k'asa ce me suna Miraj mukaje inda mutane ne suke rayuwa a k'asar suna rayuwa ta 'yanci sannan suna da arzik'i sosai k'asar tana cikin k'asashe da ake ji da su wajen dukiya sannan sarkinsu ya kasance me adalci saidai abinda zai baki mamaki su d'in suna bin wani addini sannan su mutane ne ba irin muba, kowane maye yana tsoron zuwa k'asar miraj saboda basu yarda da maita ba duk lokacin da suka kama maye basu barinshi suna had'a wuta me zafi suk'oneshi wannan dalilin ne yasa muke tsoron tunkarar k'asar tun shekaru d'ari biyu a chan baya, saidai wasu daga cikinmu sunsha suyi k'ok'arin zuwa k'asar sukama mutanen ciki wasu suna samun nasarar dawowa da ransu wasu kuma ana kamasu akashe. Gimbiya Najla idanu tazuba mata tana saurarenta, cigaba tayi da cewa saidai abun mamaki da ban tsoro a yau d'innan wani mutum me shiga ta alfarma yanayinshi kawai zaki kalla kigane shi d'in jinin sarauta ne ya harzuk'a Gimbiya Najma da kalamanshi da yayi mata wanda taci alwashin d'aukar fansa bazata ta'ba barinshi ba dan a yanzu haka ta tura bak'ak'en kuyanginta dan sugano mata asalin mutumin...... ____*****_____ ....A yanzu nice shugabarku nice shugaba a k'asar Nairan ya zama dole kowane mahaluk'i yayi min mubaya'a fararen mayu da bak'ak'en mayu duk wanda yak'i haka zan kasheshi a yanzun nan,,, tana fad'in haka tazauna saman kujerar mulki... Tsugunne take a gaban gawar tana ta rusa kuka nan wata kuyanga tashigo cikin sauri tamaida k'ofar tarufe cike da girmamawa tace ya shugabata ya kamata kitashi kibar masarautar nan dan a yanzu 'yar uwarki ta aiko azo akawo mata ke, jama'arta suna nan dayawa sun nufo d'akinki. 'Dago fuskarta tayi da tayi jajir saboda tsananin kuka takalli kuyangartata har ta bud'e baki zatayi magana sukaji anfara buga k'ofa dak'arfi, kuyangarce cikin sauri tanufo inda take tataimaka mata tamik'e tsaye.......... +++++++++++ ...Ranka yadad'e ya kamata kaduba maganata baidace ace kamar kai ba a matsayinka na babban sarki ace d'anka yarima yana zaune babu aure bayan duk wata dukiya yana da ita shin idan baiyi aure yanzu ba sai yaushe zaiyi ko sai bayan mutuwarmu kaduba kaga 'yar uwarshi yadda take k'aunarshi tana binshi ammah ko kad'an baya kulata shin hakan da yakeyi ya dace kenan.....bud'e k'ofar da akayi aka shigone yasa taja bakinta tayi shuru saboda yanayin takun tafiyar da tajiyo yasa tagane Yarima ne, sai a lokacin sarki yad'ago kai yakalleta sannan yamaida kallonshi ga yarima d'an da yad'auki son duniya yad'aura mashi..... _____ ..Ya kamata ace Gimbiya ta fito a wannan ranar anyi girkin masarautar nan da ita kar kumance hakan shine al'adar masaraurar nan duk amaryar da aka auro acikinta dole ne bayan sati biyu tafito tashiga kitchen dakanta tagirka abincin da Yarima, sarki da sarauniya zasu ci a ranar nan wannan sak'one aje afad'a ma gimbiya!!! Wata kuyanga ce cikin sauri tamik'e tafita dan ta isar da sak'on uwargijiyarta. Wadda tagama bayanin juyawa tayi takalli Sarauniya mahaifiyar yarima da itama take kallonta nan tasakar mata murmushi mai cike da ma'anoni sannan tawuce gaba inda sauran kuyanginta suka take mata baya. A lokacin da sak'on ya iso agareta tsaye tayi tarasa ta inda zata fara, k'arar k'araurawa tajiyo daga waje nan tafara jiyo muryar jakadiya tana cewa a yau ranar murnar ce agaremu auren yarima da gimbiyarshi ya cika sati biyu a yanzu haka muna jiran fitowar gimbiya zatazo tagirka ma yarima da iyayenshi abinci me dad'i wanda zasuci dan nuna farin cikin wannan ranar. Kallon agogo tayi da daidai lokacin k'arfe sha d'aya daidai tabuga saurin matsawa tayi tad'age labule nan taga yanayin gidan ko akwai rana sosai. Ja tafara yi da baya cike da tashin hankali tana tunanin ta yadda zata iya fita a wannan lokacin dan ta san ba irin wannan lokacin bane lokacin fitarta..... *_KUWWA DA KUWWA....._* (Bata korar buzu) Labarin ya sha banban da wanda kuka saba karantawa. shima ga duk me buk'ata zai sameshi akan farashi naira d'ari biyu (200), saidai bazan fara sakinshi ba har sai na gama typing d'in part 1. Kar kubari abaku labari Kukasance da ni acikin sabon free novel d'ina wanda yake tafe gajeren labari me suna *NADAMAR RAI* _Taku har kullum sis Nerja'art✍🏻_ v