Ayshacool "Ba ta damu ba, ta rintse ido ta ci gaba da faɗin ""Ka rabu da ni, ka ƙyale ni na yi rayuwata, ka bi kakanin" "nawa kabari ku ƙarata, ni meye nawa da zaka din ga cutar da mutanen da suke tare da ni, ina ruwanka" "da rayuwata? Sai dai shiru, bai bayyana ba, kuma ba ta ji sanyi yana ratsata da yake alamta mata yana guri ba." "Watso litattafan gurin ta fara ƙoƙarin yi, cikin damuwa da kuka, amma suka ƙi faɗowa, tamkar gina su" aka yi a gurin. Sai ma ƙara jin ciwo da ta yi a hannunta. "Babu tsammani, wani littafi guda ɗaya tal ya faɗo ƙasa. Ta ƙurawa littafin ido, sai kuma cikin azama ta" "ƙarasa ta ɗauki littafin, na kwanaki ne da ta fara karantawa Ƙaisarya ƙwace." "Sai dai ta buɗe littafin, ta ga sai farar takarda babu komai a ciki, ta zazzage shi ta sake buɗewa amma" babu komai a jiki. "Sai kuma a hankali ta lura da gurin da jininta ya taɓa, rubutu ya fara bayyana a jiki." "A hankali rubutu ya ci gaba da bayyana, tun yana dishi-dishi har ya yi clear." "Ko da ta fara karanta wannan shafin, sai ta ga tamkar ba ci gabn gurin da ta tsaya ne, a wancan karon ba," "amma saboda tsananin son jin ƙwaƙwaf, da gudun kar ya kuma ƙwace littafin, kawai ta ci gaba da" karantawa a haka. "Shekaru masu yawa da suka gabata, ƙauyen Buda da ke cikin ƙaramar hukumar Garkon jihar Kano." "Sannu a hankali mutane sun raya gurin, su na gudanar da rayuwarsu cikin kwanciyar hankali, da su da" "dabbobin su, ba tare da wata damuwa ba." "Bayan shafe tsawon shekaru, ba tare da zuriyar wannan aljani sun kuma waiwayar mutanen gurin," "domin ɗaukar fansa ba, kwatsam! Rana ɗaya mutanen garin suka tashi da fari. An yi noma ana jiran ayi girbi, kawai suka je gonakin su, suka tarar da shukokin su sun ƙone ƙurmus. Su ka shiga tashin hankali mara misaltuwa, domin noma yana ɗaya daga cikin abin da suka dogara da shi, domin rayuwa. Ba su gama wannan alhinin ba, dabbobin su suka din ga kamuwa da ciwo, ga yunwa da rashin wadattacen" abinci. "Tsuntsayen su, suka din ga kamuwa da mura su na mutuwa su ma." "Hankalinsu ya yi mummunan tashi, suka rasa menene mafita, sai mutumin da yake jagorantar wannan" "ƙauye, ya yi tafiya domin bincikawa, ko za a samu magani, da kuma neman maƙwabtan ƙauyuka, su" tallafa musu saboda abin da ya same su. "A ɗaya daga maƙwabtan ƙauyukan, ake gaya masa sun yi sake, da suka zauna haka babu wani boka, da" "zai iya yi musu binciken abin da ka iya faruwa, da kuma gaya musu maganin matsalolinsu." "A nan take aka haɗo shi da wani boka, suka taho garin tare." "Bokan ya ce a ba shi kwanaki uku, zai dawo musu da bayani. Ya tafi kan wani dutse da jakar kayansa, sai" "bayan kwanaki uku, ya saukko ya koma gurin mai gari." """Ba ni labari, me yake faruwa da wannan gari, muke ta afkawa cikin bala'i a jejjere haka?""" "Bokan ya dube shi ya ce ""Ba komai ya haddasa wannan abubuwan ba, face ɗaukar fansar da wasu daga" "cikin aljanu zuriyar Dirsham suke yi, a kan abin da ainihin wanda suka fara zama a cikin ƙauyen nan suka" "yi musu."" Nan ya ba su labarin abin da ya faru, duk da dama wani sun sani." """To yanzu mene ne abin yi?""" """Zan yi muku aiki, amma na ɗan lokaci ne, domin kuwa za su kuma dawowa dan ba sa yafiya, abu ɗaya" "za ku yi wanda nake ganin shi ne mafita""" "Cikin zaƙuwa mai gari ya ce ""Mene ne wannan abin?""" """Yauwwa, za ku bada mutum ɗaya, ko biyu da za a yi wa girkar aljani, yadda zai din ga yi muku bayanin" "abin da ka iya faruwa wanda ba ku sani ba, sai dai za ku din ga yi wa aljanin hidima, da yi masa duk abin da yake so, shi kuma abu kafin ya faru ya sanar muku. Idan da wani mataki da za a ɗauka, duk zai din ga" "gaya muku""." "Mai gari ya ɗan yi shiru sannan ya ce ""To wai mene ne girkar?""" "Bokan ya gyara zamansa, ya ƙara tattara hankalinsa a kan mai gari ya ce ""Girka na nufin a zaunar da" "aljani ko kuma aljanu a jikin mutum, ta yadda za su iya zuwa kansa a duk lokacin da ya kira su. Idan aka yi haka za ku iya magana da su ma ta bakin wanda aka yi wa girkar, idan ma wani bayanin ne su yi muku""" "Mai gari ya ce ""Taɓɗijan, Aljanu kuma? Ba na tunanin akwai wanda zai amince ya yarda ayi masa wannan" "abun, mu dai ka yi abin da ya kamata ka taimake mu""" Ayshacool "Ya ce ""To shikenan, babu laifi sai dai maganin ba mai ɗorewa ba ne ba, ku sake bani kwana biyu kafin" "hudowar alfijir na ranar Alhamis zan yi aikin""" "Haka kuwa aka yi, bayan kwana biyu, kafin hudowar alfijir, boka ya kawo wani ƙaho, da aka naɗe shi da" "farin zare, aka rataya masa wasu layoyi ya ce a za a binne a tsakiyar garin." "Ya saka aka gina wata ƙatuwar tukunya, aka haƙa rami aka sakata, ya zuba tarkacen tsaface-tsaface da" "lauyoyi, da wannan ƙahon aka binne ta a tsakiyar garin." "Sun yi imani, kuma sun yarda da wannan abu da boka ya yi musu, dan haka suka zauna lafiya a garin. Sai" "dai ɗaya daga makusantan mai gari, ya ce masa ya dace a tara mutane a samu ko mutum ɗaya, a yi masa girka saboda gudun abin da ka iya faruwa a gaba." "Ya amince da wannan shawarar, aka tara mutane aka yi musu bayani. sarkin aska ya yi farat ya ce shi ya" "yarda ya amince a yi masa girkar, saboda wani abu da ya ƙulle a ransa." "Haka aka yi shiri, aka haɗa shi da 'yan rakiya, zuwa ɗaya ƙauyen gurin bokan nan domin yi masa girkar" Aljanu. "Sai dai da boka ya bashi zaɓin kalar aljanun da yake so ayi masa girkar da su, sai ya zaɓi baƙaƙen aljanu!" Maimakon farare. "Aka yi masa girka, ya koma Buda, su na murna za su ƙara samun afuwa da kariya daga sharrin zuriyar" "aljani Dirsham Jaddul jinn, sai dai kash! Rashin sani ya fi dare duhu, Sarkin aska ya yi amfani da wannan damar gurin mayar da mutanen garin tamkar bayinsa, babu wanda yake ja da shi, abin da ya faɗa tilas ayi ko ba a so saboda kar aljani ya hukunta mutum. Ya sanya wa mutane tsananin tsoronsa, hatta mai" gari sai abin da sarkin aska yake so shi ake yi. "Kullum mutanen garin, cikin sintirin kai dabbobinsu suke yi, domin sadaukarwa aljani duna da aka yi" "masa girka da shi, domin ya kare su ya kare ƙauyen daga bala'i. Ya din ga janyo wasu daga cikin aljanun da mutanen Buda suka yi wa laifi, yana canza tsarin jinsinsu, ta hanyar sadaukar musu da jini, da yi musu alkawarin taimaka musu, gurin ɗaukar fansa a kan mutanen garin." "Sarkin baka na garin Buda, ya kasance cikin mutanen da suke bayar da magani, idan mutum ba shi da" "lafiya. 'yar sa guda ɗaya tal a duniya mai suna Lanti, duk in da za shi yawonsa da ita yake tafiya. Sarkin aska abokinsa ne, amma tun da aka yi masa girka ya canza halaye suka raba hanya." "Kwatsam! Sarin aska ya ce Aljani duna ya ce kar wanda ya sake bayar da magani a garin, idan ba shi ba," kuma garin babu wani wanda yake bayarwa dama bayan sarkin baka. "Sarkin baka ya ce Uban dunan ma ya yi kaɗan, balle shi kansa dunan, babu wanda ya isa ya hana shi" bayar da magani. "Sarkin aska ya ce akwai gagarumin bala'i, muddin ya ci gaba da bayar da magani, sarkin baka ya ce" bala'in ya daɗe bai afku ba. Nan rashin jituwa ya ɓarke a tsakaninsu. "Mutanen gari, duk da su na jin tsoron sarkin aska, amma sai aka rabu biyu, wasu suna bayan sarkin baka," wasu kuma sarkin aska. "Kwatsam! Aka tsinci gawar sarkin baka a daji, jikinsa babu ko ƙwarzane balle a ce dabbobin daji ne suka" kashe shi. "Lanti ta shiga tashin hankali, ta yi kuka sosai da sosai, dan daga ita sai kakaninta sai shi ta sani, babarta ta" "daɗe da rasuwa, shi ne yake yi mata komai." "Sarkin aska ya samu dama ya ci gaba da tsula tsiyarsa, sai da ya talauta da yawa jama'ar garin, saboda" tsoron sa da ya sanya musu. "Bayan wasu shekaru, Lanti ta yi aure har ta haifi 'ya mace, mutsnen Buda suka sake tashi da wata" "annobar, a lokacin sarkin aska ya yi bulaguro da shi da yaronsa." "Aka wayi gari ƙafafuwan yaran garin yana shanyewa, ga wani irin tari da ƙuraje da suka din ga fesowa" mutane. "Aka rasa yadda za ayi, ga Sarkin aska baya nan, tun da mahaifin lanti ya mutu, ba ta yi gigin cigaba da" "sana'ar sa ba, amma ganin halin da mutane suke ciki, ya sanya ta fara ba su ɗan abin da ta sani na" "magani, a matsayin taimakon gaggawa. Saboda alaƙar su da sarkin aska ta ƙara yin tsami, bayan da ɗansa ya nuna ya na son ta taƙi amincewa." Ayshacool "Ko da sarkin aska ya dawo ya tarar da abin da yake faruwa, ya yi ta bala'i a kan dan me Lanti ta bayar da" "magani, idan ba ta yi wasa ba Duna ya yi fushi da ita, abin da ya samu babanta ne zai same ta. Abin ya tsayewa Lanti, ta daɗe da tunanin sarkin aska yana da sanya hannu a cikin mutuwar mahaifinta." "Mijinta ya ce ta yi haƙuri kar ta tanka. Kawai aka wayi gari, 'yar gurin Lanti ba ta iya tafiya ƙafafuwanta" "sun shanye, ita ma ta kamu da wannan larurar""" "Nana ta juya shafin gaba, amma ta ga wayam babu rubutun komai. Ta dudduba duk rubutun ya goge," "har na baya da ta karanta. Raunin hannunta take ƙoƙarin matso jini ta kuma shafawa a kai, ta ci gaba da karantawa, ta ji wata iska mai ƙarfi na ƙoƙarin ƙwace littafin daga hannunta." "Iya ƙarfinta ta saka, ta riƙe littafin, amma iskar ta haɗa da ita, ta yi sama ta fizge littafin ya shiga inda ya" "faɗo, Nana kuma ta dawo ƙasa tim!" """Wash!"" Ta faɗa jin yadda ta ji ƙashin bayanta tamkar ya buɗe." Guguwar ta rikiɗe ƙaisar ya bayyana. """Idan ba ki yi wasa ba, taurin kai zai yi ajalinki kamar yadda ya yi na kakannin kakaninki, kodayake idan" "ba ki yi haka ba ai ba za a ce daga zuriyar su ki ka fito ba. Saboda ke na ɓatar da rubutun jikin littafi," "amma saboda baƙar jaraba, ki ka gano jinin ki ne zai bayyana rubutun. Sai kuwa kin yi jinyar jinin ki da ki" "ka yi amfani da shi ki ka buɗe rubutun""." """To waye ya ce ka kirawo ni ina zaman zamana?""" """Ai kuma na fasa faɗar abin da ya sanya na kirawo ki, fita ki ban guri""" "Nana ta ce ""Ta ina zan bi?""" """Ta kaina""" "Tsaki Nana ta ja ta ce ""Ai ba ni na kawo kaina ba"" ta yi maganar tana juyi." """Wash Allah!"" Ta faɗa cikin marairaicewa saboda ciwon da bayanta yake yi." """Nana, an yi salla fa""" "Tashi ta yi zaune tana kallo Nasiru, da yake a tsaye a bakin ƙofa, ta ɗan yamutsa fuska ta ce ""Na gode" "Nasiru""" "Ta yi juyi ta ji bayanta ya ƙara riƙewa, da ƙyar ta iya tashi ta lallaɓa ta fita ta yi alwala, ta dawo ta yi salla." "A wannan karon tiryan-tiryan abin da ta karanta a littafin Ƙaisar ya din ga dawowa kanta, ba ta manta" "komai ba, saɓanin sauran mafarkan da take manta komai." """Sarkin baka, sarkin aska, Garba ga baka ga aska, kenan sarkin baka yana da alaƙa da labarin mutanen" "ƙauyen Buda?' 'A'a ba zai yiwu ba kawai dai labari ne ya zo a haka. Amma ya Lanti ta yi da 'yar ta mai ciwo, kuma za ta yarda sarkin aska ya ba su magani. Mtsew ƙaisar bai yi ba. Amma da nake danganta sarkin baka da wannan labarin, wataƙila ƙaryarsa ce kawai yake rubutawa ba wai faruwa ya yi a gaske ba." "Ba ta yi aune ba, ta ga lokaci ya kusa ƙure mata, ta tashi ta fara shiri a gaggauce, ta jiyo hargowar Baba," yana ta bala'i tare da jaddada ta nemo kuɗin da za a mayar wa su Saleh kafin sati ɗaya. "Ita dai ba ta ce uffan ba, ta gama kintsawa ta nufi gidan aikinta. Ba ta tashi tuna abin da ya faru ba jiya" sai yanzu da ta nufi gidan. Gaba ɗaya pressure Baba ta sanya ta manta da abin da ya faru jiya a gidan Alhaji Zailani. "Yau gidan a buɗe yake, tana zuwa tura ƙofar kawai ta yi ta shiga. Yana kallonta har ta wuce ta shiga cikin" gidan. "Shukura ta tarar a falo, ta gaisheta ta amsa mata a yatsine ta ce ""Yau Hajiya ba ta nan, sun fita da" "Jummai tun sassafe, Haidar yana gurin Daddy, idan da wani abu ki shiga kitchen ki duba ki dafa muku, ni na tafi""" "Saroro ta yi jin ta ce wai Haidar yana sashen mai gidan, Shukura ba ta jira me Nana za ta ce ba kawai ta" fice ta tafi. "Nana ta shiga kitchen, ta dafa abin da za ta bawa Haidar, da wanda za ta samu ta ci ita ma, sai dai shiru" babu Haidar babu alamarsa. "Ta din ga kallon agogo, ta ga yakamata ace zuwa yanzu an wanke masa baki, an yi masa wanka ya karya" "amma bai fito daga sashen Alhaji Zailani ba, duk da ma bai fiye yin dogon bacci ba idan gari ya waye." "Abu kamar wasa har ƙarfe sha ɗaya da mintuna na rana, Haidar ɗin bai fito ba, sai ta ji ta damu ƙwarai" da gaske. "Ta nemi guri ta zauna, tana tunanin ko tarko ya yi mata, amma wata zuciyar ta ce ya za ayi ya haɗa baki" da 'yar sa ya yi miki tarko? Tun da dama yana wasa da Haidar sosai. "Kamar a cikin tunani, ta din ga jin kukan Haidar, yana ce mata yunwa yake ji." Ayshacool "Firgigit ta tashi, kamar wadda aka mintsina, ta nufi sashin Alhaji Zailani." "A ƙofar falonsa ta din ga kwaɗa sallama amma shiru, ba a amsa ba. Ta zira kai ta shiga falon amma babu" kowa a falon. Sai kuma jiri ya fara ɗibarta garin ya din ga jujjuya mata. "Ƙaton frame ɗin da yake ɗauke da hoton Alhaji Zailani, a hankali ya juye Alhaji Fatuhu ya bayyana a jiki," idanunsa na zubar da hawayen jini. """Innalillahi wa innalillahi raji'un, Innalillahi wa innalillahi raji'un"" Nana ta din ga maimaitawa." "Fitilun ɗakin ne suka ɗauke, wata iska ta din ga buga tagogin da ƙarfi." "Muryar Alhaji Fatuhu ta ci gaba da ji yana sheshsheƙar kuka, sai kuma ta fara jin muryar Muhsin yana" "kiranta ""Anty Nana, Anty Nana"" sautun muryar Haidar ma ya fara amsa kuwwa a kunnenta ""Anty yunwa nake ji""" """Ƙaisar wai meye haka ne? Dole sai ka tozarta ni a gaban mutane, meye haka ka ke yi mini?"" Nana ta yi" maganar cikin ɗaga murya. "A take ta ga komai ya koma yadda yake, sai Alhaji Zailani a gabanta." """Lafiya dai?"" Ya yi maganar yana mata kallon tuhuma. Duk ta haɗa gumi sai ajiyar zuciya take yi." """Haidar zan ɗauka na ba shi abinci, lokacin cin abincin safen sa ya wuce""" "Alhaji Zailani ya yi murmushi ya ce ""Kin damu da ba ɗan da ke ki ka haife shi ba a kan kuɗi ƙalilan, ni a" "kan kuɗi masu yawa nake buƙatar ki ara mini dama, amma kin ƙi. Kuɗi zan baki ba ƙanana wanda ke da" "talauci har abada""." """Ka ce ""Har abada? Kai wa ya baka wannan tabbacin? Dan Allah kar ka sake tunkarata da wannan" "maganar, ka rabu da ni ba na so""." """Daɗina da ɗan talaka girman kai, ke ga talauci ga girman kai""" """Na ji, dan Allah ka bani yaron nan na ba shi abinci""" "Ya yi dariya ya ce ""A tunaninki, zan zuba miki ido ne, na rasa damata wallahi ko za ki mutu sai na yi" "amfani da ke na cimma muradina, ba zan sake lallaɓa ki ba, ta ƙarfin tsiya sai na samu abin da nake so""" "Jikin Nana ya hau rawa, sai ta marairaice ""Dan zatin Allah ka yi haƙuri, ka rufa mini asiri bayan Allah da" "manzonsa mutuncina ne kawai ya rage mini dan Allah ka yi haƙuri""" "Shima ya kwantar da murya ya ce ""A'a Asma'u, mutuncinka kuɗinka, idan kina da kuɗi miji sai wanda ki" "ka zaɓa. Auren ma bai zama dole ki yi ba, na ishe ki komai. Kin ga yau ne ranar sa'ar aikin nan, dan Allah ki kwantar da hankalinki, ba dogon lokaci za a ɗauka ba""" "Dif! Dif! Dif haka zuciyarta ta ƙara ƙaimin bugawa, maimakon tsoro ya shigeta sai wata irin rawa da" jikinta yake yi. """Ka bani hanya na wuce, idan ba haka ba wallahi sai na kashe ka, ka je a duba maka taurarin Shukura," "wataƙila na ta sun fi nawa haske. Ka bani hanya kafin na yi ajalinka""" "Ganin ya ƙame kamar gunki yana kallonta, ya sanya ta hankaɗe shi, ta buɗe ƙofa ta fita. Tana fita daga" "ɗakin ta ƙara jin ta burkice, kamar hankalinta zai gushe." "Biyo bayanta ya yi, tana gaba yana bin ta a baya yana kiran sunanta." "Tun kafin ta ƙarasa gate, ta gan shi zaune a kan benci shikaɗai, addu'a ta din ga yi Allah ya sa a buɗe gate" "ɗin yake ta fice, domin in dai wannan ne ba kulata zai yi ba ya buɗe ƙofar. Kullum fuskarsa cikin rawani." "Sai da Alhaji Zailani ya yi mamaki, domin hatta masu gadi ya aike su, duk da ga babban yaronsa mai zuwa" aike a gidan. "Ga mamakin Nana, kafin ta ƙaraso gurin gate ɗin, ya miƙe tsaye ya nufo su, taku biyar ya yi ya tsaya ya" kafe Alhaji Zailani da ido. Ji ya yi tamkar an yi masa wani irin mugun dabaibayi ya kasa ɗaga ƙafarsa. "A hankali ya juya ya nufi Nana da take ta jijjiga gate ɗin, tana neman hanyar fita." "Bai ce mata uffan ba, ya buɗe mata gate ɗin ta fita ko takalmi babu a ƙafarta." Ayshercool 08081012143 Ayshacool P22 "A hankali Alhaji Zailani ya buɗe idanunsa, ya gan shi a kan gadonsa a kwance. Shiru ya yi yana ƙoƙarin" tariyo abin da ya faru. "Fes komai ya dawo kansa, amma daga iya lokacin da ya biyo Nana, suka yi ido huɗu da wannan Buzun," ya kasa tuna komai. "Ya tashi zaune yana ƙoƙarin saukkowa daga kan gadon, sai ga Hajiya Amina ta shigo ɗakin, hannunta" ɗauke da kofin tea. """Sannu Alhaji ka tashi?""" """Yaushe ki ka dawo?""" """Tun la'asar, nan muka tarar da kai a sume, Haidar na ta kuka na ce Nanan ba ta zo ba ne? Amma doctor" "Sharif ya zo ya ce ba sai an kai ka asibiti ba, ya yi maka abin da zai yi maka, ya ce jininka ne ya ɗan hau""" Ya yi shiru yana tunanin to meya same shi haka? Amma ya kasa tuna komai. **** "Nana kuwa tana shiga gidansu, gaba ɗaya suka mayar da hankalinsu kanta, saboda a yadda ta shigo" "gidan, idonta a rufe, ƙafafuwanta babu ko takalmi." "Suwaiba ta ce ""Jaraba""" "Kukan tsuntsaye ne ya gauraye ilahirin dajin, sai kuma ƙaton tafki mai ɗauke da ruwa shuɗi, sai rugugi" "yake yi, yana tambal-tambal." "Tana tsaye tana kallon ruwan, ƙaisar ya bayyana a kan ruwan, yana shawagi yana kaɗa ruwan." """Wallahi ba ka da wani amfani a rayuwata, kana kallon za a ci mini mutunci, amma ba ka yi komai ba, ba" "ka da aiki sai ƙoƙarin haukata ni."" Ta yi maganar a hasale." "Bai yi magana ba, sai ƙara girgiza ruwan da yake yi, ruwan ya watso har sai da ya jiƙa ta, sannan ya ce" """Allah ne zai tsare ki ba ni ba""" "Cikin kuka ta ce ""Ai dama ban ce kai zaka tsare ni ba, idan ma gatse ka ke yi mini ba zan taɓa neman" "taimakon ka ba, amma na meye za ka din ga razana ni a gaban mutane, sai na fita hayyacina na aikata abin da zai saka a ce ba hayyacina nake ba?""" """Abin da ki ka gani haka yake ko a zahiri, ba yi na yi dan na tsorata ki ba kawai"" ya yi maganar yana" "fitowa daga cikin ruwan, da wani baƙin mayafi a jikinsa, yana jan ƙasa tare da ɗigar da ruwa." """Biyo ni"" ya yi maganr yana yin gaba. Bin bayansa ta yi, suka ƙarasa gaban wani dutse, ba ta san ya aka yi" "ba, ta gan su a cikin libraryn sa." "Ya ce ""Wannan mutumin da ki ka gani yana kuka da hawayen jini, yana daf da faɗawa mawuyacin hali, a" "saboda abin da abokinsa zai yi masa. Abu ɗaya yake damunsa da yasa za a iya galaba a kansa, ba shi da riƙo da ibada sosai, sai baƙar aƙida da ra'ayin riƙau. Kuma ni ba na zama a guri mai ƙazanta, ko gurin da ake ta'amalli da jini, mussaman na bil'dama, ta yaya zan zo inda ki ke, alhalin inda ki ke zuwa ana" ta'amalli da jinin bil'adama? "Jininku ya fi jinin kowace halitta ƙarni mara daɗi, amma ya fi kowanne zaƙi da daɗi idan aka sha. Shi yasa" "masu aiki da jininsin aljnun da suke ta'amalli da jini, da an ba su jinin bil'adama, suke aiki cikin gaggawa," "domin babu jinin da ya kai na su zaƙi da daɗi in ji masu sha""." "Mudubin da yake gurin ya nuna mata, ya ce ""Kalli"" cikin tsoro da razani, ta kalli mudubin." "Alhaji Zailani ta gani tsirara, ana kwarara masa jini a jikinsa, yana buɗe baki tare da ziro harshensa waje," jikinsa yana karkarwa. "Wata irin razana ta yi ta buɗe idonta, karaf ya sauka a cikin na Baba." """Uban me ya dawo da ke gida yanzu? Ko suma kin yi musu wani abun sun kore ki?""" Ta girgiza kai alamar a'a. """To me ya dawo da ke gida yanzu?""" """Kaina ne yake ciwo""" """Ki sha magani ki koma, idan ma korar ki suka yi, ki san abin yi, dan wallahi ban san ina zan nemo kuɗin" "nan na biya ba""" "Ya gama faɗansa, ya bar ƙofar ɗakin, tana nan zaune ta ji sallamar Inna a tsakar gida." "Ta amsa daga ɗaki, tare da bata damar ta shiga." """Nana ya na ganki a haka? Ba ki da lafiya ne?""" """A'a me ki ka gani?""" """Idonki ya yi jawur sosai fa""" "Nana ta yi murmushi ta ce ""Lafiya ƙalau bacci na yi """ "Inna ta ce ""Bacci kuma? Ina gurin aikin?""" """Daga can nake"" ta bata amsa" """Wallahi da can gidan aikin zan je, kawai na fara zuwa nan""." "Nana ta karanto damuwa a fuskar Inna, ta ce ""Meyafaru?""" """Muhsin fa ya rasu yau ne uku""" "Wata irin zabura Nana ta yi, ta ja da baya tana bin ƙwayar idon Inna da kallo, domin ta gazagata abin da" yake fitowa daga bakin Innan. """Ba Muhsin Fatuhu ba amma ko?"" Nana ta yi maganar cikin tashin hankali, da ya gaza ɓoyuwa a kan" fuskarta. Ayshacool "Cikin damuwa Inna ta ce ""Shi mana, idan ba kya komai ki tashi mu je ki yi musu gaisuwa, an gano" "gidansu mun je ma daga makaranta""." "Tamkar an tsinkewa Nana laka, haka jikinta ya mutu laƙwas, fatan ta a ce bacci take yi kawai mafarki ne." Can kuma sai mafarkin da ta yi da Muhsin ɗin ya dawo mata fes. "Zabura ta yi tai waje, Inna ta bi bayanta, tana kiran sunan ta." "Baba da yake tsakar gida ya ce ""Lafiya ina za ki haka?""" "Inna ta ce ""Ɗaya daga cikin ɗalibanta ne ya rasu za mu je gaisuwa"" gaban Baba ya faɗi cikin tsoro, ya fara" fargabar kar dai ta tabbata iskokan Nana ke kashe wanda take mu'amala da su?. """To Allah ya jiƙan sa""" Inna ce ta amsa ta bi bayan Nana. "Inna ta tare musu abin hawa, suka hau suka tafi. Sam Nana ba ta gane abubuwan da Inna take faɗa," fatanta kawai ya zamana mafarki ne ba gaskiya ba. Saboda akwai kyakkyawar shaƙuwa a tsakaninta da "Muhsin, saboda lokacin da aka kawo shi ma, bai kai a ɗauke shi ba, saboda ƙanƙantarsa, har goya shi Nana take yi, Allah ya sa mata ƙaunar yaron a zuciyarta." "Sosai ake zaman makoki a gidan Alhaji Fatuhu, ɗan sa bai taɓa mutuwa ba, sai a kan Muhsin, shi ne" ƙarami amma ya shiga ransa. "Rumfuna aka kafa a cikin gidan, inda yake karbar gaisuwa, cikin gidan kuma mata ne suke karɓa gaisuwa." "Gida ne katafaren gaske, ga girma ya sha kayan alatu." "Alhaji Fatuhu yana tsaye yana gaisawa da wasu, ya ga wucewar Nana da Inna." "Jikinsa ne ya yi sanyi, ganin yanayin tashin hankalin da yake kwance a kan fuskar Nana." "Inna har falon ta raka Nana, don yi wa babar Muhsin gaisuwa." "A gigice Nana ta shiga falon, kamar mai neman wani abu, ta tsaya tana rarraba ido ba tare da ta cewa" kowa komai ba. "Inna ta taɓa ta ta ce ""Ga mahaifiyarsa ki yi mata gaisuwa""" "Nana ta kalli matashiyar matar da ba ta wuce shekara ashirin da huɗu ba, idanunta jawur." "Nana ta ƙarasa gabanta ta risuna ta ce ""Baiwar Allah wai dan Allah Muhsin ya rasu?""" "Alhaji Fatuhu ne ya yi sallama a falon, suka amsa Nana ta waiwaya tana kallonsa ya ce ""Nana kin samu" "labarin mutuwar ɗan ki ko?"" Sai mahaifiyar Muhsin ta zabura ta ce ""Ke ce Nanan dama? Muhsin har ya rasu kafin ya daina magana sunan ki yake kira, yana cewa a kai shi gurinki"" sai a lokacin Nana ta ji kuka" "ya ƙwace mata, Inna take ba su labarin Nana ta je makaranta ganin Muhsin lokacin ba shi da lafiya ba ya" zuwa makaranta. "Cikin kuka maman ta ce ""Na gode sosai da sosai, ƙaunar da ki ka nuna masa ce ta sanya, duk wanda ya" "san shi, zai san sunan ki a bakinsa""" "A wannan karon ta yarda da zancen mutane, ta fara lura da duk wanda ya shiga ranta take son shi, sai ya" rasa rayuwar sa. """Wai ke ba za ki daina kukan nan ba, kamar a kan ki aka fara rashin ɗa? Wannan ai rashin tawakalli ne?""" "Nana ta waiwaya ta kalli mai maganar suka yi ido huɗu. Matar ta ce ""Ahh wannan ba Nana ba ce, yayar" "Jamila""" "Alhaji Fatuhu ya ce ""Kin santa ne? Antyn su Muhsin ce a Young talented academy""" "Hajiya sa'a ta ce ""Na santa, ba ki gane ni ba ne?"" Nana ta girgiza mata kai alamar a'a." """Ba da ke mu ka haɗu kwanaki a gidan maman khairat ba?"" Nana ta sake ɗaga ido ta kalle ta, a take ta so" ta nemi nutsuwarta ta rasa. "Wani abu mai muhimmancin gaske take son tunawa, amma abu ya gagara sai ma wani irin sarawa da" kanta ya yi. "Hajiya Sa'a ta nemi ta rasa nutsuwar ta, ganin fuskar Nana tana canzawa kamar ba ta mutum ba, tana" "wani irin ja tamkar an shafa mata jar kala. Neman guri ta yi ta zauna da sauri, jin jiri zai ɗebe ta." "A hankali Nana ta ɗauke kanta, daga kallon hajiya Sa'a, ta yi musu gaisuwa, ta tashi jiki a sanyaye ta ce" tafiya za ta yi. "Mahaifiyar Muhsin ta ce ""Bari mu je ki yi wa kakarsa gaisuwa dan ita ma ta sanki a bakinsa." "Haka Nana ta din ga yi musu gaisuwa, tana jin tamkar su ma suna zargin ita ta kashe musu ɗa," mussaman da aka ce yana ta kiran sunanta. "Ta rako Nana har harabar gidan, tana ci gaba da yi mata godiya. Alhaji Fatuhu ya ƙaraso ya ce ""To Nana" "Allah ya ƙara mana haƙurin rashin Muhsin""" "Ta jinjina kai amma ta kasa magana. Ya kalli maman Muhsin ya ce ""Yanzu Alhaji Zailani ya kira ni, yake" "bani haƙuri bai shigo ba yau, ba shi da lafiya ne wai""" Ayshacool """Ai ɗazu Hajiya Amina ta zo da safe tare da mai aikinta sun kuma yi mana gaisuwa ai ba komai sun yi" "ƙoƙari mun gode sosai""" "Gaban Nana ya yi mummunar faɗuwa, ba dai Alhaji Zailanin dai da ta sani ba, tuno abin da ta gani a" "falonsa ɗazu ta yi. Sai dai ta rasa me ma za ta ce, wataƙila ma ƙaisar ne kawai yake wasa da hankalinta." Haka suka kama hanyar komawa gida. "Nana na komawa gida la'asar, kasancewar ba ta salla, sai ta shiga ta yi wanka ta kintsa jikinta." "Wani abu mai ɗaci ya tsaye mata a wuyanta, har ya fara ƙoƙarin hana ta numfashi." "Ba ta ko iya gani saboda azabar jiri da ciwon kai, ta kwanta ta yi shiru ta rufe idanunta, ta din ga tuna" mutanen duk da suka rasa rayukansu da yanzu ita ma take kyautata zaton saboda ita ne. "Ta fashe da kuka, tana ""Wannan wace irin rayuwa ce, gaba ɗaya na kasa tantance ni mece ce ma gaba" "ɗaya. Allah ya tsinewa tsohuwar da ta gada mini wannan masifar wallahi ba zan yafe ba""." * "Malam Gambo mai allon ƙasa ne zaune a kan buzunsa, ya nutsu yana sauraren Alhaji Zailani." """Ni dai abin nan ya firgita ni malam, ni ban taɓa abu makamancin haka ba, yanayin kamar ɗimuwa ko" "gushewar hankali""" "Malam Gambo ya numfasa ya ce ""Me yasa ka yi gaggawa? Wutar ciki ce da kai Alhajin Allah, ai a sannu" "za ka bi ta, ba kowacce yarinya za ka yi wa irin wannan tayin kai tsaye ba, mussaman idan ba ta saba ba, duk lalacewar zamani akwai na Allah""" """Wallahi kuwa yarinyar ta bani mamaki, akwai taurin kai na tsiya""" """Yanzu ba wannan ba, matsalar da nake gaya maka akwai, ita na duƙufa bincike a kai, kwanaki ba akwai" "wani wuridi da na yi maka ba, na kira wani aljani ya yi mana aiki ba ya ƙi?""" "Da sauri Alhaji Zailani ya ce ""Eh an yi haka""" """To wannan aljanin shi ne a kanta, goɗiyarsa ce""" "Alhaji Zailani ya waro ido ya ce ""Haba, ni fa na ce, wallahi da ta buge ni ta wuce, kamar wani ingarman" "doki ne ya hankaɗe ni""" """To ya zame maka dole ka kula ka yi taka tsantsan, ka bi a sannu burinka ya cika idan ka ci gaba da far" "mata zai iya ajalinka!""" """Ajalina fa ka ce?""" """Ƙwarai da gaske, hatsabibin matashin saurayin aljani ne, ba ya neman rigima da kowa amma idan aka" "taɓa shi faɗa da shi ba ya ƙarewa har abada""" "Alhaji Zailani ya jinjina kai cike da gamsuwa, dan kuwa a rayuwarsa babu babban abin da yake tsoro" "sama da mutuwa, ko zancenta ba ya so gani yake, yana da cikakkiyar lafiya da ba za ta tunkaro shi a daidai wannan lokacin ba." "Sai da Nana ta shafe kwanaki uku, babu lafiya ga wani irin zazzafan zazzaɓi da take fama. A kwana na" huɗu ta lallaɓa ta koma gidan Alhaji Zailani. "Hajiya Amina na ganinta cikin damuwa ta ce ""Nana kwana biyu lafiya kuwa?""" """Wallahi Hajiya ba ni da lafiya ne""" """Allah sarki, ga shi ke ba waya balle a ji halin da ki ke ciki, Haidar duk ya damu yana ta tambayar ki.""" "Tana rufe bakinta sai ga Haidar ya fito da gudu, ya ɗane jikin Nana. Sai ta tuno da Muhsin, take wata" "fargaba ta shige ta, kar shi ma abin da ya samu Muhsin ya same shi, saboda sun shaƙu sosai. Jiki a" sanyaye ta rungume Haidar. """Nana anya kin warware kuwa, bari na kira Doctor Sharif ya zo ya duba ki, duk kin yi zuru-zuru""." "Ita dai Nana ba ta ce komai ba, har mamakin kirkin Hajiya Amina take yi." "Har gida doctor Sharif ya zo, ya duba Nana, ya bata magunguna da allurai, ya saka mata ruwa a gidan." "Ganin Nana a kwance duk sai Haidar ya damu, ya koma kusa da ita ya kwanta shima." "Nana cike da ƙaunar yaron take kallonsa, tana tuna Haidar, ta din ga addu'a Allah ya kare shi ya kiyaye" "shi, kar abin da ya samu Muhsin shi ma ya same shi." "Kafin yamma Nana ta ɗan ji ƙwarin jikinta, har ta din ga ɗaga Haidar tana yi masa wasa, saboda yadda" "duk ya damu, da ganinta a kwance." "Hajiya Amina ta fito falon ta miƙowa Nana waya, Nana ta saka hannu ta karɓa tana kallonta." "Ta ce ""Tun da shi sirikin nawa, bai kawo miki waya ba, ni ga shi na baki, ki lallaɓa da ita, bai kamata a ce" "budurwa kamar ki ba ta da waya ba. Ga dubu uku, idan kin fita ki tsaya ki sai layi a yi miki rijista ki saka a ciki, in sha Allah nan da kwana uku za a biya duk ma'aikatan gidan nan albashin su. Ko wani abun ne ya" "faru kya din ga bugo waya ki sanar""" Ayshacool "Nana ta juya wayar, da gani ba wani amfani aka yi da ita ba, sai ƙyalli take yi, har da charger." """Yanzu Hajiya wannan tawa ce?""" """Eh mana Nana, ko ba ta yi miki ba?""" "Nana ta girgiza kai ta yi murmushi ta ce ""Wallahi ban taɓa zaton zan riƙe waya mai kyau da tsada har" "haka ba. Allah ya faranta miki, ya kula miki da zuriyar ki, ya dauwwamar muku da farin ciki na gode sosai da sosai""" "Hajiya Amina ta yi murmushi ta ce ""Nima na gode sosai, ina jin daɗin yadda ki ke kula da Haidar da" "zuciya ɗaya, na ga kina da yawan ibada da azumi, dan Allah ki yi mini Addu'a idan ina da rabo Allah ya bani haihuwa"" Turus Nana ta yi tana kallonta, a wannan shekarun nata me za ta yi da wata haihuwa?." "Ta yi murmushi ta ce ""Kin yi mamaki ko? Ai ban taɓa haihuwa ba, ki roƙa mini, idan kuma ba ni da rabo," "Allah ya ƙara mini dangana""" "Nana a ƙasan zuciyarta murna ta taya Hajiya Amina, na rashin haɗa zuriya da wannan majanunin mijin" "nata mara addini. Amma a zahiri ta ce ""Ki yi haƙuri Hajiya, kin san komai rabo ne, kuma Allah ya fi mu sanin abin da ya dace da mu. Ko kin bar duniya in dai ɗan Adam zai rama halacci ire-irena da yaran da ki ka riƙe, za su yi miki addu'a. Kar ki manta ba ke kaɗai ba ce uwar mumunai Allah ya ƙara mata yarda, ba ta samu haihuwa ba amma uwa ce ga dukkanin muminai, a rashin samun haihuwar nan, ke ba ki san me Allah ya tanadar miki ba, wanda bai bawa waɗanda suka haihu ba"" kai tsaye kalaman Nana suka din ga shiga zuciyar Hajiya Amina, da sai da hawaye ya cika mata ido. Ta ji daɗin kalaman Nana, na ƙwarin" "gwiwa, ta yi mamakin yadda Nana ta iya tsara maganganu cikin hikima." """Na gode sosai Nana, kin ƙara sawa na ji nutsuwa, Allah ya ba ki zuriya ta gari. Ka da Allah ya jarrabe ki" "da ƙaddarar rashin haihuwa. Duk ta tawakallinka, akwai gaɓar da mutane mussaman 'yan uwanka mata sun saka ka ji tamkar ba ka da amfani.""" """Amin na gode sosai Hajiya. Amma ta ki jarrabawar ki ka sani, da wata jarrabawar gara rashin haihuwa" "sau dubun dubu"" haka su ka din ga hira da Hajiya Amina, har lokacin tafiyar ta ya yi." "Tana shirin tafiya, Shukura ta dawo, Haidar yana kallonta, amma bai damu ya je gurinta ba, ya rirriƙe" "Nana yana cewa zai bi ta ta tafi da shi ba. Da ƙyar ta lallaɓa shi, ta fita." "Habu na ganinta ya taso zai buɗe mata gate, ya ce ""Malama har kin taso?""" "Nana ta ce ""Eh malam Habu, shekaranjiya na zo zan fita, duk ba kwa nan""" """Eh wallahi mai gidan nan ne ya aike mu""" "Ta ce ""Allah sarki, yauwwa dan Allah ina wannan ɗan uwan naku?""" "Habu ya ce ""Wanne daga ciki?""" """Wannan ɗin nan""" """Ya sunan shi?""" "Nana ta girgiza kai ta ce ""Ban san sunansa ba, ɗaya ɗan uwan naku dai Sule ya ce mini ba shi da" "cikakkiyar lafiya, kurman nan"" Habu ya kwashe da dariya ya ce ""Kayya ba kurma ba ne ba yana magana""" "Ta ce""To ai shi kullum baya magana, fuska a rufe kamar amarya. Shi ya buɗe mini ƙofar ranar na fita""" """Allah sarki, yana gane komai, kawai da larura ce a ƙwaƙwalwarsa, ba kuma wai hauka yake yi tuburan" "ba, wasu lokutan ma sai ya shafe sati bai ce uffan ba, yana kwance ma ba lafiya""" "Cikin tausayawa Nana ta ce ""Allah ya sauwwaƙe, na tafi sai da safe""" """To sauka lafiya, Allah ya tsare"" ta amsa da Amin ta tafi." "Ɓoye wayarta ta yi, saboda ta san tsaf Baba zai ƙwace wayar nan, mussaman yanzu da yake neman kuɗi" ido rufe. "Bayan Nana ta koma gida, Jamila take tambayarta ashe sun haɗu da Hajiya Sa'a a gidan rasuwa, amma ta" ce ba ta santa ba. "Nana ta ce ""Ina cikin jimami da alhinin mutuwar yaron ne, shiyasa na kasa gane ta""" "Jamila ta ce ""Allah sarki, ashe yaron ma sunanki ya yi ta kira kafin ya rasu""" "Nana ta kalli Jamila daga sama zuwa ƙasa ta ce ""Wannan karon ma ni na kashe shi ko?"" Ta yi magana" tana tsare Jamila da ido. "Jamila ta ce ""A'a ni ban ce ba, kawai labari fa take bayarwa""" "Nana ta gyaɗa kai cikin gargaɗi ta ce ""Jamila ina son hawainiyar matar nan ta kiyayi rama ta, idan ta ci" "gaba da ƙoƙarin cin iyaka ta, za ta faɗo cikin wutar da za ta ƙona ta da ita da amfanin gonarta, wannan saƙona ne a gare ta."" Saroro Jamila ta yi cikin tsoro, jin yadda Nana take magana kamar an shaƙe ta." Ayshacool "Kamar kuma wadda ta razana a cikin bacci, jikin Nana ya ɗan yi girgiza sannan ta ce ""Jamila yau wainar" "fulawa nake sha'awa, zan sai fulawa ki sai mana manja, mu soya mana"" da yake sun saba yin haka." Jamila kawai ta jinjina mata cikin tsoro. Da daddare Jamila ta samu Nana tana shirin kwanciya bacci ta ce """Nana wai Hajiya Sa'an wani abun ta yi miki ne, ki ke cewa na yi mata kashedi?""" "Cikin rashin fahimta Nana ta ce ""Wace ce Hajiya Sa'a?""" """Wadda ku ka haɗu a gidan rasuwa""" "Nana ta ce ""A'a wani abin ta ce na yi mata?""" """A'a to ai ke ce ki ke cewa na ce ta kiyaye ki, kuma babbar mace kamar wannan shi yasa na tambaye ki""" "Nana ta waro ido ta ce ""Ni babu abin da ta yi mini, ni fa ko magana ban yi mata ba, me ta yi mini zan ce" "ta kiyaye ni?"" Sai a lokacin Jamila ta fahimci kamar Nana ba ta san ta yi maganar ba sai ta ƙyale ta." "Ranar da aka bawa Nana albashi, kamar ta taka rawa, ganin ta mallaki dubu ashirin ta ta, ta kanta. Ga" "dubu ashirin da Alhaji Zailani ya ce a bata, baban Haidar kuma ya ce a bata dubu goma, sai da ta tashi da dubu hamsin. Iya salarynta ta yi murna da shi, wanda aka ce Alhaji Zailani ya bata kuwa, ji ta yi tana ƙyanƙyamin su." "Da murna ta nufo gida, tana tunanin wace bajintar yakamata ta yi a gida, yadda kowa zai amfana." "Amma tana zuwa Baba ya turke ta da bala'i ""Wai Asma'u ba za ki ƙuƙuta a samu komai a hannunki ba?" "Ƙanin uban yaron nan ya kira ni a waya, yana idan ba zan dawo da kuɗin ba, hukuma ce za ta raba mu, ba ki da asara ko a jikin ki ko?""" "Nana ta saka hannu a aljihun rigarta, kasancewar kuɗin dubu goma goma ne, ta ciro uku ta bawa Baba ta" "ce ""Baba wannan ne kawai a hannuna, nima yau aka biya ni albashi""." """Yauwwa ko ke fa, ba zan taɓa su ba kiran su zan yi su zo su karɓi abin su, duk da koma me aka yi mini ke" "ce sila, da kin haƙura kin kwantar da hankalinki shikenan, amma mugun halinki ya sanya ki ke ta yi wa yaron nan wulaƙanci, yanzu kalli halin da ki ka jefa mu"" Nana ta daina mamakin ƙarfin hali da son kai irin na Baba, sai dai ta yi shiru ya gama surutansa ta tashi ta tafi." "Abu kamar wasa, ƙaramar magana ta juye zuwa ga babba, domin kuwa Saleh cewa ya yi ba zai karɓi" "dubu talatin ba, dan ko kwatan abin da ya kashe ba a ba shi ba. Dan haka ya kai Baba police station." "Haka aka turo jami'an tsaro, suka tisa ƙeyar Baba zuwa gurin 'yan sanda. Sai Gaddafi aka nemo, ya bi" bayan su. "Gaddafi ya kalli Saleh, ya ce ""Yanzu kai Saleh saboda rashin ta ido, ka rasa wanda za ka kawo gurin 'yan" "sanda sai mahaifina, saboda rashin kara, ko dan zaman amanar da muka yi a ikko, ga yayanka na auren" "ƙanwata.""" "Saleh ya ce ""Ka ga malam, a batun kuɗi babu wata kara, yarinyar nan ba ƙaunata take yi ba, har tana" "neman hallaka ni, ban aure ta ba zan bar muku kuɗina ne?""" "Duk yadda a ka yi da Saleh a yi sulhu, amma ya ƙi yarda, sai da aka yi yarjejeniya, cewar nan da kwanaki" "uku za su kawo kuɗinsa gaba ɗaya a ba shi""." "Ranar yau na ɗaya daga cikin ranakun da Nana, ba za ta iya mantawa da su ba, domin bayan dawowarta" "gida, Baba ya din ga yi mata bala'i tamkar zai tsine mata, har da cewar ya yi dana sanin haihuwar su da" "ɗan uwanta, ya yi dana sanin haɗuwa da mahaifiyar su har ya aureta ta haife su""." "Gaddafi ya ce ""Dan Allah Baba ka yi haƙuri ka yi shiru haka mana, sai ɗaga murya ka ke yi duk maƙwabta" "su na jin ka, kuma ka na ta cewa ta nemo kuɗi a biya, ka san dai ba wata sana'a take yi ba, idan kuma ba hanyar banza ka ke son ta shiga ba""" "Cikin takaici Baba ya ce ""Ka bar ni Gaddafi, ban taɓa haifar ɗan da yake neman ya yi ajalina ba kamar" "Nana, da me zan ji ne? Ba ta tausayina ko kaɗan duk wata hanya da zan bi na aurar da ita, ta nutsu nima na nutsu ta ƙi, a dalilinta a ka kai ni station a ke nema a rufe ni. Lokacin da aka haife ki babu farin cikin da ban yi ba, na so ki, amma kina neman ki kashe ni. To wallahi idan kuɗin nan ba su samu ba a ka rufe ni, sai kin bar gidan nan, kuma kwana ki bakwai na baki ki fito da wani mijin, ko ki koma gurin uwarki ki bar" "mini gida""" Ayshercool 08081012143 Ayshacool *AUNTY ZEE MOM MUJAHID KATSINA 08162859027* *INGANTACCEN MAGANIN SANYI MAI WANKO DUK WANI DATTIN MARA SANYI MAI HANA HAIHUWA SA WARIN GABA RASHIN NI IMA JIN ZAFI YAYIN MU AMALAR AURATAYYA FITAR FARIN RUWA MAI WARI KAIKAYIN GABA TUSAR GABA KURAJEN GABA TUSAR GABA BUDEWAR GABA CIWON JIKI RASHIN GAMSUWA* *Maganin sanyi 5k* *Maganin sanyi* *5k* *Maganin ciwon Qoda 10k* *Maganin HepatitisB ASHA NA TSAWON WATA DAYA MUNBADA ANWARKE DA YARDAR ALLAH 40k* *MAGANIN MATA KALOLI DABAN DABAN INGANTATTU MASU LAFIYA DA KARA KUZARI AKWAI NA MATA AKWAI NA MAZA UWARGIDA DA AMARE KU GARZAYO WURIN AUNTY ZEE MOM MUJAHID KATSINA* *INGANTACCEN MAGANIN GYARAN NONO MAI TADA KOMADAR NONO DA DUK WATA TAMOWA TA NONO ZAI CIKO DA TUWON NONO YA TADA KOMATSEWARSU BANCE ZASU TASHI BA ZADAI SU CIKO SUYI KYAU* *Maganin gyaran Nono 8k* *MAGANIN RAGE TUMBI KODA YAKAI GIRMAN CIKIN YAN BIYU INSHA ALLAH KI GWADA MAGANIN AUNTY ZEE DA YARDAR ALLAH ZAKI GODE* *Maganin Rage Tumbi 7k* *MAGANIN BASUR KODA YAKAI GA YIN TSIRO INSHA ALLAH AGWADA ZA ADACE* *Maganin Basur 5k* *MAGANIN CIWON SUGAR CIKIN IKON ALLAH MUNBADA ANRABU DASHI* *Maganin ciwon Sugar 10k* *08162859027* *09070027627* *Location*KATSINA STATE* *ACCOUNT NUMBER* *8162859027* *ZAINAB SHU AIBU* *OPAY* *OR* *3968303018* *FCMB* *ZAINAB SHU AIBU* *DAN ALLAH IN KINSAN BAKI SHIRYA BA KARKI YI MAGANA DAN ALLAH KIBARI KI SHIRYA AUNTY ZEE MOM MUJAHID KATSINA TAKUCE SAI KUNZO* CHAPTER 23 "Cikin maɗaukakin sauti Nana take kuka ""Baba ka kashe ni ka huta, idan ma ba ka kashe ni ba, ni zan" "kashe kaina wai ya ake so na yi ne?""" "Gane nufin Nana da Gaddafi ya yi, yadda take harin rijiyar gidan da take buɗe, cikin tsananin zafin nama" "ya rigata isa gaban rijiyar, ya rufe ta, tana ƙarsowa ta yi karo da Gaddafi ta faɗi ƙasa." "Ya kalli Baba ya ce ""Yakamata ka din ga haƙuri, ka din ga tausasa lafuzanka, ka san ba ta da cikakkiyar" "lafiya idan ta kashe kanta, kai fa abin zai dama fiye da kowa. Kuma maganar kuɗin nan, ka bar komai a" "hannuna ko ba duka ba za a samo wasu, a ba shi ka daina cewa ta fita ta nemo kuɗi a biya. Ka daina biye shawarar da ake baka ta banza, mai baka shawarar ba za ta bari ka yi wa yaranta haka ba""" "Ya durƙusa ya ɗaga Nana, kawai ya ji tausayinta ya kama shi. Matsaloli sun yi wa rayuwar ta yawa." "Duk da uban nauyin da ta yi, tamkar ta haɗiyi dutse, haka ya ɗaga ta ya kai ta ɗakin su, ya kwantar da ita." "Har ya yinƙura zai tashi, Nana ta danƙo rigarsa, ya kalle ta, idanunta a rufe, sai ruwan hawaye da yake" zuba ta gefen idonta. """Ka ƙarawa ja wa tsohon nan kunne, idan ba haka ba nan gaba kan sa nan zan cilla a rijiya, ya iya" "bakinsa""" "Gaddafi ya ce ""Wane tsohon? Baban ka ke nufi?""" "Ta tashi zaune, ba tare da ta buɗe idonta ba ta riƙe hannayensa. A take ya ji kamar an jona masa" "shocking, jikinsa tamkar za a fizge naman jikinsa, ga shi ya kasa motsi, ya kuma kasa magana." "Ta yi murmushi ta ce ""Ina fatan yanzu ka gane mai baka saƙon? Ina ƙyale ku ne saboda ku ne abu ma fi" "soyuwa ga uwar gijiyata, amma aka ci gaba da matsa mata zan yi gagarumar ɓarna.""" A hankali ta saki Gaddafi ta silale a gurin ta koma ta kwanta. Tamkar korarrare Gaddafi ya fita cikin "tashin hankali, babu wanda ya tsaya yi wa magana ya fice daga gidan. Tun da Gaddafi yake bai taɓa shiga" "bala'i irin wannan ba. Har a lokacin da ya fita, da ƙyar yake iya sarrafa jikinsa tamkar zai fita hayyacinsa." "Washegari da safe tamkar babu abin da ya faru, Nana ta shirya ta gaida Baba za ta fita amma ya yi mata" "banza, jikinta babu ƙwari ta tafi gidan Alhaji Zailani." "Inda Allah ya taimake ta, tun da wannan abin ya faru, bai ƙara yinƙurin far mata ba." "A hankali take bubbuga gate ɗin, duk da ba ta da tabbacin ma, ana iya jin bugun nata. A yadda take jin" "duniyar ta yi mata zafi, ji take tamkar ta nemi guri ta kwanta a nan ƙofar gidan." Ayshacool "Aka buɗe gate ɗin, tana ɗaga kai suka yi ido huɗu. Dumm! Gabanta ya yi mummunar faɗuwa, babu shiri" "ta sunkuyar da kanta, ita ba ta shiga ba, ita kuma ba ta koma ba." "Kawai ya mayar da ƙofar zai rufe, babu shiri ta tura ta shiga, ta kalle shi tana son ta yi magana, amma ya" "yi mata wani irin kwarjini da babu wani ɗan Adam da ya taɓa yi mata. Ƙoƙarin gane kamaninsa take yi," amma babu dama rawaninsa ya rufe ko ina na fuskarsa sai idanunsa kawai. "Ta kama hanya ta nufi cikin gidan, sai da ta je tsakiyar harabar gidan, sai ga wasu irin murguza-murguzan" "karnuka da ba 'yan Nigeria ba, tun da ta zo gidan, ba ta taɓa ganin su ba sai dai ta jiyo haushin su. Sai da daddare ake sakin su, da safe kuma a mayar da su keji. Da guda ɗaya ne karen aka ƙaro biyu. Yau kuma" Sule bai samu ya mayar da su da wuri ba har ta zo. "A gigice ta kurma wani irin gigitaccen ihu, ta watsar da takalmanta ta zura da gudu ta yo baya, aikuwa" karnukan suka rufa mata baya su na wani irin haushi da zubar da yawu mai ban tsoro. Yana tsaye yana "kallonsu, kafin ta ƙaraso gurin da yake har ta fara fita daga hayyacinta." "Cukuikuye shi ta yi tana ihu, ta daina ganin komai, sai su biyu a cikin sahara, sai kuma jin sautin haushin" karnukan. "Ƙaisar ne ya bayyana, ya yi wata irin girgiza, ya zama wani irin narkeken kare shi ma, haushi ɗaya ya yi sai" "da gurin ya yi amsa kuwwa a take karnukan suka gudu, kamar barewar da ta ji kukan zaki." "Ya girgiza jikinsa ya koma yadda yake, ya miƙa wa Buzun hannu ya ce ""Ko da wasa, idan ka sake yinƙurin" "razana ta, ko wani abu na cutarwa a gare ta, zan shafe tarihinka a duniya""." "Nana ta buɗe idanunta da kyar, ta kalli yadda buzun nan, ya rikiɗe ya koma tsohon nan mai kama da" ƙaisar. Sai dai ko motsi ta kasa. "Wata irin dariya tsohon ya din ga ɓaɓɓakawa, gurin ya din ga amsa kuwwa da hargowa." """Kai ɗan samari, ka sake nazarin kalaman da ka faɗa, bayan tsawon shekaru mun sake haɗuwa, mun" "kuma haɗu a gaɓar da ta dace Ƙaisar"" ya yi maganar yana ci gaba da dariya." "A hankali ya ɗago Nana daga jikinsa da ta riga ta suma, ya kalli harabar gidan duk wannan kururwar da ta" "yi, babu wanda ya fito." "Ya sanya yatsunsa biyu, manuniya da na kusa da shi ya daki goshin Nana sau uku." "A hankali ta motsa ta ɗaga kanta, a falon cikin gidan ta ganta. Hajiya Amina ta ce ""Ohh sannu Nana, haka" "ki ke tsoron kare? Laifin masu gadi ne da ba su mayar da su sun rufe ba, sannu ba ki ji ciwo ba ko?""" "Nana ta jinjina kai hawaye na zubowa daga idanunta. Alhaji Zailani ya fito falo, sai baza ƙamshi yake cikin" dakkakiyar shadda. "Ya tsaya a falon ya kalli inda Nana take ya ce ""Lafiya kuma take kuka?""" """Wallahi karnuka aka bari ba a kulle ba, suka biyo ta shi ne har da kakunta, yanzu suka shigo tare da" "Yusuf""" "Ya girgiza kai ya ce ""Laifin masu gadi ne ai, bari na fita sai na dawo""" "Nana ta ƙura masa ido, tana son tuna wani abu a kansa, amma ta kasa, ta ci gaba da kallonsa har ya fice." "Da ƙyar ta iya jan ƙafafunta, ta tafi ɗakin Haidar. Ta shiga banɗaki domin wanke fuskarta, ta tsaya ta" zuba wa fuskarta ido a jikin mudubi. "Ta yi shiru tana tuna tun daga tashinta daga bacci yau da safe, zuwa yadda ta zo gidan nan, daga lokacin" "da karnukan nan suka biyo ta, tunanin ta ya hargitse gaba ɗaya, ta kasa bambance mene ne ya faru a zahiri, menene ya faru ba a zahiri ba, kuma Hajiya Amina ta ce mata, tare suka shigo da Yusuf to ta yaya?" "Ɓangaren kanta ɗaya ya sara, da sai da ta dafe kan nata. ""Wai ko ni ma dai ba mutum ba ce ba? Ko kuma" "dai ƙaisar ya fara nasarar raba ni da hankalina ne?"" Ta furta a hankali cikin tsoro da sheshsheƙar kuka." "Jin ana bubbuga ƙofar banɗakin, ya sanya ta sauri ta wanke fuskarta ta fito. Haidar ta gani a tsaye yana" "mutsutsuka idanunsa. Ta kama shi ta wanke masa baki, ta yi masa wanka." * "Alhaji Zailani ne a zaune a cikin motarsa, gefensa kuma doctor Sharif ne a ciki a zaune." """Sharif""" """Na'am Alhaji"" ya yi maganar cikin girmamawa." """A wannan karon ma, taimakon da ka saba nake so ka yi mini""" "Doctor Sharif ya ce ""Babu abin da zaka nema, na kasa yi maka shi, ka faɗi ko mene ne""" """Yaushe ne EDD ɗin Shukura?""" Ayshacool "Mama kuwa tun da Baba ya zo mata da maganar nan, ta kasa zaune ta kasa tsaye, ta rasa abun da yake" "yi mata daɗi. Wani abu mai masifar zafi ya tsaya mata tun daga ƙirjinta zuwa bakinta. Tana ganin ya za ayi a ce, ga su Jamila a zaune, Nana ta samu hamshaƙin mai kuɗi haka." "Ana yin sallar magariba Baba ya fita masallaci, ita ma ta yafa mayafinta ta fice." * "Jamila ce a zaune a gaban Hajiya Sa'a, fuskar ta ɗauke da matsanancin tsoro take kallonta." "Ta dafa kafaɗar Jamila ta ce ""Kin tabatta ta sha maganin da aka ba ta a kunun ayar?""" """Ta ce mini ta sha, amma ba a gabana ta sha ba""" """Shikenan kar ki damu, ki kwantar da hankalinki. Za mu ci gaba da ƙoƙari har zuwa lokacin da zamu samu" "abin da muke so. Abin da nake so da ke shi ne ki zamo mai riƙe mana sirri, za ki samu kuɗi Jamila, irin wanda ba ki taɓa zaton riƙe su, ba za ki yi rayuwar ƙunci da talauci irin na gidanku ba. Nana ita kawai muke buƙata idan ba haka ba, ba zaki zama abin da nake hangen ki zama ba"" ta yi maganar cikin bawa" Jamila ƙwarin gwiwa. "Mama ce zaune a cikin wata rumfa, tare da wani mutum, ta tattara masa hankalinta gaba ɗaya." """Ai na gaya miki Rabi, muddin ba ki yi da gaske ba, wallahi ki na ji kina gani, sai dai ke da yaranki ku yi" "mata biyayya. Tasirin taurarinta ba za su bari na yaranki su haska ba.""" "Cikin damuwa ta ce ""Ai na ga alama, 'yar shegiya kwatsam mutum ya fito wai aurenta zai yi, a zuwa ɗaya" "ba ka ga uban kuɗin da ya bawa ubanta ba, bai gaya mini nawa ba ne ba, amma wallahi na san da yawa. Kalli aikin raino take yi, amma albashin dubu talatin aka bata, ta bawa ubanta. Wallahi ko buɗe ido ba na ƙaunar na yi na ganta. Ni dai dan Allah ka wargaza maganar nan, kar a yi auren nan. Duk da na ji tana" "cewa uban ba ta so""" "Ya yi murmushi ya ce ""Ta kwana gidan sauƙi, yau zan kwana aikin, da ni da almajiraina, za a yi farraƙu" "mai zafi. Ki zube kuɗi kawai abin da yake hannunki a fara""" "Haka ta buɗe jakarta, ta ciro kuɗi ta ajiye masa." **** "Tinkis-tinkis yake tafiya, kamar wani bujimin sa, ya nufi motar da zai hau ya fita, sai dai yana ƙarasawa" Nana ta miƙe tsaye. Sai da ya ɗan tsorata da ganinta. "Ya ce ""Lafiya dai ko?""" "Ta miƙe tsaye ta ce ""Wani dalilin ne ya sanya ka je ka samu mahaifina, ka ce masa zaka aure ni?""" "Yayi dariya tare da shafa tumbinsa ya ce ""Dalilin da yasa ki ka ƙi amincewa da buƙata ta, ya sanya na biyo" "ta in da dolen ki ki yarda. Amma na yi mamakin yadda ƙwaƙwalwar ki take aiki da har ki ka yi saurin gano ni ne. Sai daga baya na gane ba iya taurarinki nake buƙata ba. Ina buƙatar aljanin da yake tare da ke ma. Kuma wannan ƙwaƙwalwar ta ki ma ina buƙatar ta""" "Cike da ƙwarin gwiwa Nana ta ce ""Ni na yi maka kala da wadda za ta auri fasiƙi ne? Mazinaci baya auren" "kowa face 'yar uwassa mazinaciya, ni ba irin ka ba ce ba, kuma Ubangiji mai adalci ne, ba zai yi mini wannan jarrabawar ba""" "Ya sake yin dariya ya ce ""Akwai abin da ba a kuskurewa ƙaddara. Nima zinar da nake yi ta neman duniya" "ce, kafin na mutu zan tuba. Kuma tun da baban ki uban kwaɗayi ne da son abin duniya, zan ta ba shi abin" "da yake so, domin buƙata ta biya. Tun da ke ba ki da wayo, ba ki san inda duniyar ta sanya a gaba ba."" Ya" "buɗe motarsa ya shiga ya zauna, Nana ta bi shi da kallo cikin ɗacin rai." "Ya sauke gilashin motar ya kalle ta ya ce ""Ki kwantar da hankalinki, na ga kina da abubuwan da zan iya" "mora da yawa a jikinki, dan haka ko na aure ki zan iya zama da ke na ɗan lokaci amaryata"" ya fara jan motarsa ya baro parking space ɗin." "Ƙaisar ta gani ya bayyana, ya sha gaban motar, yana kallon motar, babu tsammani sai ga wannan tsohon" "da take gani, mai kama da shi, ya keto ƙasa ya fito ya yi jifa da ƙaisar gefe." "Gabanta ne ya faɗi, sai da ta dafe ƙirjinta ta ja da baya, ta ɗaga kanta ta ga har Alhaji Zailani ya bar" "harabar gidan, sai dai idanunta suka sauka a cikin na Buzun nan da ya ƙure ta da ido ko ƙiftawa ba ya yi." Kamar wadda ya yi wa dabaibayi ta kasa motsi. """Antyn Haidar, yau ma karen ne, na ganki a nan a tsaye"" kamar wadda ta tashi daga bacci, ta kalli Yusuf" "ta ƙaƙalo murmushi ta ce ""A'a ba karen bane, yanzu zan shiga ciki""" Ayshacool *AUNTY ZEE MOM MUJAHID KATSINA 08162859027* *INGANTACCEN MAGANIN SANYI MAI WANKO DUK WANI DATTIN MARA SANYI MAI HANA HAIHUWA SA WARIN GABA RASHIN NI IMA JIN ZAFI YAYIN MU AMALAR AURATAYYA FITAR FARIN RUWA MAI WARI KAIKAYIN GABA TUSAR GABA KURAJEN GABA TUSAR GABA BUDEWAR GABA CIWON JIKI RASHIN GAMSUWA* *Maganin sanyi 5k* *Maganin sanyi* *5k* *Maganin ciwon Qoda 10k* *Maganin HepatitisB ASHA NA TSAWON WATA DAYA MUNBADA ANWARKE DA YARDAR ALLAH 40k* *MAGANIN MATA KALOLI DABAN DABAN INGANTATTU MASU LAFIYA DA KARA KUZARI AKWAI NA MATA AKWAI NA MAZA UWARGIDA DA AMARE KU GARZAYO WURIN AUNTY ZEE MOM MUJAHID KATSINA* *INGANTACCEN MAGANIN GYARAN NONO MAI TADA KOMADAR NONO DA DUK WATA TAMOWA TA NONO ZAI CIKO DA TUWON NONO YA TADA KOMATSEWARSU BANCE ZASU TASHI BA ZADAI SU CIKO SUYI KYAU* *Maganin gyaran Nono 8k* *MAGANIN RAGE TUMBI KODA YAKAI GIRMAN CIKIN YAN BIYU INSHA ALLAH KI GWADA MAGANIN AUNTY ZEE DA YARDAR ALLAH ZAKI GODE* *Maganin Rage Tumbi 7k* *MAGANIN BASUR KODA YAKAI GA YIN TSIRO INSHA ALLAH AGWADA ZA ADACE* *Maganin Basur 5k* *MAGANIN CIWON SUGAR CIKIN IKON ALLAH MUNBADA ANRABU DASHI* *Maganin ciwon Sugar 10k* *08162859027* *09070027627* *Location*KATSINA STATE* *ACCOUNT NUMBER* *8162859027* *ZAINAB SHU AIBU* *OPAY* *OR* *3968303018* *FCMB* *ZAINAB SHU AIBU* *DAN ALLAH IN KINSAN BAKI SHIRYA BA KARKI YI MAGANA DAN ALLAH KIBARI KI SHIRYA AUNTY ZEE MOM MUJAHID KATSINA TAKUCE SAI KUNZO* Page 24 """Baba dan zatin Allah, ka duba lamarin nan, wallahi ba na son mutumin nan, ba shi da kirki dan Allah" "Baba ka yi mini rai""" """Nana duk rashin kirkinsa, bai kai talauci rashin mutunci ba, idan ki ka ga ba a yi auren nan ba, to sai dai" "idan wani mijin ki ka kawo, ke ko wani ki ka kawo ɗin wallahi ga dai mai rufin asiri ba zan bawa wani ke" "ba, gara ma ki yi haƙuri, ki tattara komatsan ki""" """Ya Allah, Ya Allah Astagfirullah"" ta faɗa duk a jejjere.""" """Mahaifinki ba zai taɓa canza hali ba, sam ta kansa kawai yake yi""" "Nana ta ɗaga kai a karo na biyu, da ta sake ganinta a gurin ƙaisar ta ce ""Koma mene ne kai ne sila, kana" "ɗaya daga cikin dalilan da ya sanya Baba son rabuwa da ni ko ta halin ƙaƙa.""" "Ƙaisar ya ce ""Kar ki ga laifina, tun da na baki zaɓi tuntuni, ki ka tsaya wahalar da kan ki"" ya yi maganar" yana rubutu da hannunsa ɗaya mara ciwon. "Ya ɗora da cewa ""Matar babanku ta je gurin Malamin da ya zane ki rannan, a kan a wargaza maganar" "auren nan, dama ya kan yi mata aiki ire-iren waɗannan, idan Allah ya taimake ki aikin ya ci, sai ki ga an fasa, kalli abin da aka yi"" mudubin da ya saba nuna mata, ya nuna mata." "An raba wata 'yar tsana gida biyu, an rubuta sunan Nana a jikin ɓari ɗaya, ɓari ɗaya kuma Alhaji Zailani," ana ta wani surkulle. "Ya ɗora da cewa ""Abin da ba su sani ba su duka su ne, shi wannan mutumin ya kai matakin ƙololuwa a" "ƙungiyar asiri, to wani asiri ne kuma zai kama shi?""" "Nana cikin kuka ta ce ""Wannan malamin shi ne ya zane ni rannan""" "Ƙaisar ya kwashe da dariya, ya ci gaba da rubutun sa." "Cikin kuka ta ce ""Kuma duk saboda kai, Allah ne gatana, kowa nice ba ya so kawai"" ta yi magana tana" ƙarewa malam Ɗayyabu kallo a jikin mudubin. "Sai kuma ta daina ganin malam Ɗayyabu, sai Jamila tare da Hajiya Sa'a da kuma maman khairat." "Da sauri ta kalli Ƙaisar ta ce ""Wannan matar ba ita ka ce mini ta bayar da jinin Muhsin a ƙungiyar asiri ba?" "Amma me yasa da na tashi na manta, na ganta na kasa tunawa?""" """Ashe kin san ainihin abin da ya faru, ki ke cewa na kashe wanda ki ke ƙauna?"" Ta yi shiru tana satar" kallonsa. """Shi ma wannan yaron na yanzu, idan ba ki yi wasa ba, ana daf da shafe tarihinsa a duniya, akwai" "yiwuwar 'yan ƙungiya su nemi a ba su jininsa""" "Cikin matsanancin tsoro Nana ta kalli Ƙaisar ta ce ""A'a kar mu yi haka da kai Ƙaisar, dan Allah yaro ne fa" "bai san komai ba.""" "Ya ce ""Ni babu abin da zan yi da shi, kawai dai na gaya miki ne. Hatta ɗan da babarsa za ta haifa a nan" "gaba kaɗan, an gama shirya yadda za a yi da shi"" A razane Nana ta tashi tsaye, amma sai ta ganta a tsakar ɗakinsu. Gigicewa ta yi ta nufo tsakar gida, ta ga tsakar gidan baƙi ƙirin, dare ya tsala." Ayshacool "Sai kuma ta fara ƙoƙarin tuna abin da ya razanata, har ta fito tsakar gida, amma ta kasa tuna komai." "Ta koma ta zauna jikinta yana tsuma, ta rasa ma wace addu'a za ta yi. Zuwa yanzu idan da sabo ta saba" da matsanancin bugun zuciya saboda yawan razana da take yi. "Ta haɗa kanta da gwiwarta, ta rasa ma wani tunanin za ta yi, kasancewar bacci ɓarawo ne, ya sanya ya yi" nasarar yin awon gaba da ita. "Sai dai ta din ga ganin Haidar, yana ta kuka tana ƙoƙarin rarrashin sa, amma ya ƙi yin shiru sai tsala ihu" "take yi. A wani ɓangaren kuma na mafarkin, ta ga Shukura a dokar daji, tana ta uban gudu da tsohon cikin nan, jikinta babu suturar kirki, duk jikinta raunika, kanta babu ko ɗan kwali, ga hannunta riƙe da Haidar sai gudu take tana kururuwa. Bayanta wani mutum ne ya rufe fuskarsa da baƙin ƙyalle yake bin ta," hannunsa riƙe da wuƙa ga jikinsa sai ɗigar da jini yake yi. "Kukan Hidar sai amsa kuwwa yake yi, yana kiran sunan Nana." "A wannan karon ma a razane ta tashi, da ""Innalillahi wa innalillahi raji'un"" daidai lokacin aka tayar da" sallar asuba a masallaci. "Gudu-gudu sauri-sauri, ta fita ta yi alwala, ta gabatar da raka'atanul fajar, sanan ta yi sallar asuba. Ta" "zauna tana tasbihi ta din ga tunanin 'yan kwanakin nan ba ta iya karanta Alqur'ani. Azkar ɗin ma sai ta shafe kwanaki ba ta yi ba, ganin ko ta yi babu abin da yake canzawa. Sai kuma ta tafi tunani, wataran a islamiyya da ta farka ta ga malam Auwal a kanta, yana ta raira karatun Alqur'ani, hakan ya tabattar mata" da ƙaisar ya ziyarceta. "Bayan ya sanya ta tashi, ta yi alwala ta dawo ta zauna, ya dube ta ya ce ""Nana idan kin je gida kina azkar" "kuwa? Kuma kina karanta Alqur'ani?"" Ta girgiza masa kai alamar a'a." """To me yasa?""" "Cikin rauni da karaya ta ce ""Ko na yi Allah ba ya kare ni, na fi shan wahala ma idan na yi"" da sauri ya tari" "numfashinta ya ce ""A'uzbillahi, waye ya gaya miki Allah ba ya kare ki? Da ba ya kare ki da Allah kaɗai ya san abin da zai faru da ke. Addu'oin da ki ke yi, da larurar da ki ke fama da ita, ba ya nufin karatun Alqur'ani da azkar da ki ke yi ba sa yi miki amfani, jarrabawa ce, daga Allah. Ke kina ganin Aljani na bibiyar marasa ji? Sun fi bibiyar nutsatsu masu addini, hakan na nufin jarrabawa ce, mai imani ba a barin shi haka babu jarrabawa. Kuma burinsu kenan ki daina ibada, su sake samu su miƙe ƙafa a jikinki, su ci" "gaba da azabtar da ke. Musulma ce ke, ki zama mai kyautatawa Allah zato""." "Ko da ta zo nan a tunaninta, sai ta ce ""Astagfirullah, wa a tubu ilaihi""" "Ƙarfe tara da rabi na safe, Baba ya fito tsakar gida yana neman Nana. Mama ta ce ""Ba fa ta nan""" """Ban gane ba ta nan ba, ina ta tafi? Ba na kafa mata dokar kar ta sake fita ba, ana daf da ɗaura mata" "aure?""" """To ka isa da ita ne? Ai ba ka isa ka gaya mata ta ji ba, ka yi kaɗan""" "Ƙwafa ya yi ya ce ""Za ta dawo ta same ni, zan ci ubanta a cikin gidan nan wallahi"" Bayan ya gama" "bambaminsa ya fita, Mama ta koma ɗakinta ta ɗauki wayarta ta kira Malam ɗayyabu." "Sai da ta kusa tsinkewa ya ɗaga, ""Malam yaya a ke ciki? An gama aikin ne?""" """Eh a kan aikin muka kwana jiya""" """To shikkenan, na gode sosai da sosai, baban nata fa ka yi aikin a kansa?""." "Ya ce ""Kar ki damu, ba wanda ban yi ba fa""" "Ta ajiye wayar, tana kuma tunanin me yakamata ta yi." "Kafin azahar ɗan aiken Alhaji Zailani ya zo, ya kawo uban kayan abinci kamar za a buɗe ƙaramin shagon" "sayar da kayan abinci. Bakin Baba ya ƙi rufuwa, sai shiga yake yana fita yana washe baki, yana ƙiyasata" irin abin da zai yi wa Nana muddin ta bijirewa auren Alhaji Zailani. "Yaron nasa ya sanar da Baba cewar, tafiyar gaggawa ta kama Alhaji Zailani, washegari zai dawo, amma" "ko baya nan bai dawo a goben ba, za a ɗaura auren nan ranar Juma'a, kuma ba ya buƙatar taron jama'a," waliyyai kawai sun isa. "Baba yana tsuma ya tabattarwa da yaron Alhaji Zailani, mai suna Sani cewa ya tabattarwa da Alhaji" Zailani ba za a samu wata matsala ba. "Nana kuwa gaba ɗaya ji ta yi jikinta ya ƙara sanyi, tun da garin Allah ya waye, komai ba ya yi mata daɗi," tamkar ta mutu ta huta. "Duk mutanen gidan sun koma baccin safe, ta shirya ta fice daga gidan." Ayshacool "A hanya gari ya ƙarasa wayewa Nana, ta je ta din ga bubbuga gate ɗin, aka zare sakata aka buɗe. Sai dai" "maimakon ya ba ta hanya, sai ya zura mata idanunsa yana kallonta. Hankaɗa ƙofar ta yi ta shiga a fusace," "ta tsani wannan ɗan iskan kallon da yake yi mata, shi kuma kullun fuska a rufe, ba a ganin fuskarsa sai dai ya yi ta kallon mutane." "Burki ta ja ta tsaya, tana kallon yadda ƙosassun karnukan nan, suke safa da marwa a harabar gidan. Ta" "waiwayo ta kalle shi, ya kawar da kansa kamar bai gan ta ba, ya mayar da gate ɗin ya rufe ya saka mukulli, ya nufi ɗakinsu na masu gadi." "Karnukan suka yi cirko-cirko suna kallon Nana, su na haushi." """Dan Allah ka raka ni bakin ƙofar shiga"" ta yi maganar a marairaice. Bai kulata ba ya cigaba da tafiya." """Dan Allah idan ba za ka raka ni ba ka buɗe mini ƙofa na koma"". Ganin da gaske ba zai rakata ba, kuma" "ba zai buɗe mata ba, ga karnuka su na nufo ta, kawai ta rufa masa baya da gudu. Ya tsaya ya waiwayo ya kalleta. Ta ja ta tsaya cikin tsananin tsoro." "Sule ne ya fito yana miƙa da alama a lokacin ya tashi, ya kalle su ya ce ""Nana lafiya na ganki da sassafen" "nan? Kuma ya na ganku a tsaye haka lafiya dai?""" """Tsoro nake ji, na ce ya raka ni yaƙi, kuma ya kalle ƙofa ya ƙi buɗe mini na koma gida, kuma so suke su" "biyo ni su cije ni"" ta yi maganar idanunta na cika da hawaye saboda tsoro." "Sule ya yi dariya ya ce ""yi haƙuri, ni ban san dalilin da ya sanya ku ke yawan samun saɓani da Buzu ba." "Jira ni na ɗaure karnukan sai ki wuce""" "Ta goge hawayen ta ce ""To na gode sosai"" Shi kuwa tuni ya shige ɗakin su, ya bar ta da Sule." "Ko da Nana ta shiga cikin gidan, ɗakin Haidar ta nufa kai tsaye, yana kwance yana ta baccinsa. Ajiyar" "zuciya ta din ga saukewa, ta durƙusa a gabansa ta dafa kansa, tana karanto masa addu'oin da suka sauwwaƙa a bakinta. Tana ɗan tofa masa. Wata irin razana ya yi a baccin, har da ɗan ihunsa, Nana ta" "rungume shi, ya ƙanƙameta ta cigaba da yi masa addu'a." "Yau Shukura ta na gida, sun yi hutun makaranta. Har mamaki take yi yadda Nana ba ta gajiya da abin da" Haidar yake yi mata na hayyata irin ta su ta yara. "Duk motsin da ya yi, ta san me yake nufi, zuwan Nana gidan ya yi ƙiba ya zama ƙato saboda yadda yake" "cin abinci. Ga kuma karatu da take koya masa, har da addu'oi." "Nana ta ce ""Shukura"" karon farko da ta taɓa kiran sunanta, Shukura ta kalli Nana da mamakin tsaurin" idon da ta yi. """Na san ba zan dauwwama ina kula da Haidar ba, amma dan Allah ina son ko yaya ki ajiye aƙidar boko, ki" "din ga jansa a jiki, kuma ki tsayawa azkar ɗin sa da kula da yi masa addu'a. Ke kanki ki ƙara ƙaimin addu'a" "sosai da sosai, ka na da ido ne kawai amma ba na ganin gari ba, abin da Allah ya so kawai shi muke gani""" """To da na ce miki ba na addu'a ne, da za ki buɗe ƙazamin bakin ki, kina kiran sunana haka kai tsaye ni" "sarki ce?""" "Nana ta kalli Shukura ido cikin ido ta ce ""Ni ki ke cewa mai ƙazamin baki! To kar ki yi abin da na ce, idan" "kin ƙi ji ai ba za ki ƙi gani ba""" "Babban abin da ya bawa Shukura mamaki, bai wuce yadda ta ji tamkar an saka mukulli an rufe mata baki" "ba, bayan sun haɗa ido da Nana ba, ta yi gum ta kasa cewa komai." "Gaba ɗaya Nana ta manta da wani sharaɗi da Baba ya kafa mata ma, hatta batun auren Alhaji Zailani ma" "sai ta daina jin ya dame ta, mummunan mafarkin da ta yi da su Shukura ne kawai yake damunta. Sai kuma wata irin fargaba da ta rasa ko ta mece ce." "Domin ragewa kanta damuwa, tare suka yi girkin dare da Jummai. Hajiya Amina ce ta ce ""Nana ki zo ki" "tafi, na ga alamun hadari a garin nan, kuma tun da ba abin da ki ke yi""" """A'a kar ki tafi"" Haidar ya yi maganar yana riƙe rigar Nana." "Nana ta kalle shi da murmushi a fuskarta ta ce ""Idan na zauna zaka goya ni?""" """Eh zan goya ki, ki yi bacci"" ya yi maganar cike da shirirtar su ta yara." "Da ƙyar a ka yi masa wayo, Hajiya Amina ta ɗauke shi, Nana har za ta fita, Jummai ta biyo ta da kular" "abinci ta ce ""Dan Allah Nana ki ajiyewa masu gadi, na san yanzu su na can waje shan wannan shayin nasu na ibada, ba za su dawo ba sai cikin dare. ki ɗan tura ɗakinsu ki ajiye musu, idan ba su san an ajiye ba, karnuka ne suke zubar musu." Ayshacool "Jiya da na ajiye musu a waje ba su sani ba, su ka kwance karnuka, aikuwa su na sako su, suka je in da aka" "ajiye abincin suka kifar, suka hau ci"" Nana ta ɗan yi Jimm sannan ta karɓa ta fita." "Kamar yadda Jummai ta faɗa kuwa, Nana tun kafin ta ƙarasa bakin gate ɗin, take jiyo hayaniyar buzayen" "a ƙofar gida, alamun duk su na waje a ƙarƙashin bishiyar da suke zama da yamma su sha shayi, su yi" wasan takobuna. "Amma duk da haka sai ta tsaya a ƙofar ɗakin nasu tana sallama, ko za ta ji an amsa, amma ta ji shiru. Sai" "ta ɗan tura ƙofar ɗakin, wani irin ƙamshin turare ya kawo wa hancinta ziyara." "Ta zura flask ɗin abincin, ta yinƙura za ta tashi, kawai ta ji kukan Haidar a cikin ɗakin yana kiran sunanta." """Anty Nana, ki zo)" "Ba ta yi nazarin komai ba, balle tunanin ta baro Haidar ɗin a cikin gida ba, kawai sai ta ɗimauce ta" hankaɗa ƙofar ɗakin ta shiga. "Cak ya tsaya ya waiwayo ya kalli inda take tsaye. Daga shi sai dogon wando, hannunsa riƙe da mataji," "yana taje dogon gashinsa da ya kwanta a kan kafaɗarsa zuwa dokin wuyansa. Gefensa butar shayi ce, take ta dahuwa a kan wuta, kuma da alama a cikin wutar aka zuba turaren wutar da yake tashi." "Cikin matsanancin tashin hankali tsoro da razani, ta yi yinƙurin juyawa ta fita, amma ƙofar ɗakin da" "tagogi suka kulle, sautin wata irin guguwa ya karaɗe ɗakin. A take ya rikiɗe daga kamaninsa zuwa wannan tsohon mai kama da Ƙaisar, ya bayyana cikin suffa mai matuƙar ban tsoro, ya buɗe ƙaton bakinsa mai kama da bakin tsohuwar rijiya, ya fara fito da wata irin wuta Jawur tana wani irin hayaƙi," lamar gobarar tankar mai. "Iya ƙarfinta ta dafe kanta, ta ƙwala ihu ta faɗi a gurin sumammiya. Jin ihunta ya sanya ya sake" "waiwayawa ya kalle ta, ya ganta a ƙasa ba ta ko motsi. Ya ƙarewa ɗakin kallo domin ya ga abin da ya razanata amma bai gani ba." "Ya mayar da hankali ya ƙarasa taje gashinsa, ya tufke abinsa, ya zira rigarsa, ya shafa turare sannan ya" "kawo rawaninsa ya naɗa. Ya zauna a gaban shayinsa, ya fara tsiyayowa yana kurɓa a hankali tamkar shikaɗai ne a cikin ɗakin babu wata halitta kuma." "Gidansu Nana tun da aka yi sallar magariba, Nasiru ya shigo gida yake tambayar ko Nana ta dawo." "Suwaiba ta ce ""wai kai Nasiru Nanan nan uwarka ce ne?""" """Ban sani ba, idan ma uwar ta wa ce ina ruwan ki?""" "Cikin hasala ta ce ""Idan na kama ka wallahi sai na gwara kanka""" """Ba ki da wannan ƙarfin wallahi"" ya yi maganar yana fita. Ya zauna a ƙofar gida yana kallon hanya, amma" "babu Nana babu alamar ta. Tsoro ne ya fara kama shi, kar ya je ko ta sake ɓata aljanun nata sun kai ta wani gurin." "Yana zaune ya hango Baba ya nufo gida, hannunsa riƙe da manyan ledoji." Nasiru ya tashi ya karɓo masa kayan suka shiga gida. "Su na shiga Nana ya fara tambayar Mama, amma ta ce ba ta dawo ba. A take hankalin Baba ya tashi, ya" fara tunanin ko dai ta gudun ne? "Sai a lokacin ya fara binciken ina ne gidan da Nana take aiki, tun da take zuwa bai taɓa bibiyar ina take" zuwa aikin ba. "Gaddafi baya nan, dan haka ya ɗauki Nasiru, suka fita neman Nana." "Gurin ƙarfe tara na dare, Gaddafi ya dawo gida, ya shigo cikin gida zai wanke kayansa, yana neman" "Nasiru zai aike shi. Suwaiba ta gaya masa halin da ake ciki. Ya yi saroro ya ce ""Yanzu har ƙarafe tara ba a" "san inda take ba? Kuma babu wanda ya san gidan aikin nata?""" "Jamila ta ce ""Ni dai ta taɓa kwatanta mini, can wajen quarters ɗin markaz ne, wai gidan Alhaji Zailani""" """Sako hijjabin ki mu je, mu duba""" "Mama ta ce ""Ku je ina? Babu inda za ta je""" "Ya haɗe rai ya kalli Jamila ya ce ""Ba magana nake yi miki ba, sai na taka wuyanki tukuna?"" Ba Jamila ba" "ita kanta Mama sai tsuke bakinta ta yi, dan iya ashariyar Gaddafi ta ishe su." "Sam ba su sha wahalar gano gidan ba, kasancewar Alhaji Zailani sanannen mutum, saboda yawan" kyautar da yake yi da taimakon al'umma. "A tsatstsaye suka tarar da mutane a ƙofar gidan, buzaye sai magana suke yi da yaren su." "Kai tsaye Gaddafi ya kutsa suka shiga cikin gidan, mutane ne a tsaye a ƙofar ɗakin masu gadi, ga matar" gidan a tsaye fuskarta ɗauke da damuwa. Ayshacool "Gaddafi ya nufe ta, suka gaisa ya ce ""Dan Allah ni yayan yarinyar da take yi muku aiki ne, Nana tun da ta" "fita tun safe bamu ganta ba, shi ne muka zo nan ko ta zo?""" "Hajiya Amina ta ce ""Alhamdilillah mu na ta tunanin yadda za a yi, tun bayan la'asar muka yi sallama, ta" "tafi gida. yanzun nan yarona ya shigo yana gaya mini wai masu gadi sun ganta a ɗakinsu a sume, su suna waje, mutum ɗaya suka bari a ɗakin, shi kuma ba shi da lafiyar ƙwaƙwalwa, ya ƙi magana an rasa wanda zai taɓa ta ma. Yanzu nake tunanin ya za a yi a samo wani daga gidansu, dan ni ban san gidansu ba""" "Gaddafi ya ce ""Ɗakin masu gadi kuma?"" Ya juya ya nufi ɗakin." "Nana na sume a tsakar ɗakin, gefe guda shi kuma yana zaune yana kaɗa ƙafafuwan sa, tamkar ba ya jin" hayaniyar da ake yi. "Gaddafi ya nufi Nana da sauri, ya ɗago ta, yatsun hannunta da na ƙafarta duk sun ƙandare kamar wadda" "ta daɗe da mutuwa, ga jikinta sanyi ƙalau." "Ya ɗaga kai ya kalli Buzun nan da duk abin da ake yi, sabgar gabansa kawai yake yi, ya kalli Nana. Duk da" "ba shiri suke yi da ita ba, amma ya san Nana ba ta cikin jerin yara marasa ji, amma me ya kawo ta ɗakin masu gadi?." Hajiya Amina ce ta saka Yusuf ya ɗauki su Gaddafi ya tafi kai su gida. "Cikin damuwa Habu yake dubansa ya ce ""Buzu, ya aka yi yarinyar nan ta shigo ɗakinmu, me ya same ta?" "Me yasa kuma ba ka kira wani daga cikinmu ba?"" Ɗaga idanunsa ya yi ya kalli Habu, a dole Habu ya ja" "bakinsa ya tsuke, duk da tarin tambayoyin da suke bakinsa." "Cike da takaici, da matsananciyar tsana da damuwa, Baba yake kallon Nana yake maimaita a ɗakin masu" "gadi ka gano Nana?""" """Idan an yi magana a ce aljanu ne suka hanata aure, ga haƙiƙanin abin da ya hanata aure nan ai"" Mama" "ta din ga faɗar maganganu. Jamila ta ce ""Mama ba lallai abin da ki ke tunani ba ne ba, kin san ba ta da cikakkiyar lafiya""" """Eh ban sani ba sai yanzu da ki ke gaya mini, rashin lafiya ne za a ganta a ɗakin masu gadi da wani?""" """To ai an ce mahaukaci ne, har fa muka taho yana kallon dandazon mutane, bai yi magana ba, kuma bai" "fito ba"" cewar Jamila, dan ta ƙi yarda zuciyarta ta bata wani mugun abin Nana take aikatawa." "Kawai Baba ya tafi ɗaki, Mama ta bishi tana faɗin ""Yanzu baban Jamila, baka gudun a zo a ji kunya?" "Wallahi tun da ta fara haka, ko an yi auren nan ba za ta zauna ba, kunyata ka za ta yi, tun da ta furta maka ba ta son auren nan, take ta wannan iskancin. Maza nawa ta ce ba ta so? ko dai ka san abin yi ko" "kuma abin da za ta yi a gaba sai ya fi na yanzu muni""" "Wata irin tafasa zuciyar Baba ta din ga yi, tafasar da tun da yake bai taɓa jin zuciyarsa ta yi ba, wata irin" matsananciyar tsanar Nana ta mamaye zuciyarsa. Kamar mahaukaci haka ya fito fiuu ya yi waje. Ayshercool 08081012143 Ayshacool *AUNTY ZEE MOM MUJAHID KATSINA 08162859027* *INGANTACCEN MAGANIN SANYI MAI WANKO DUK WANI DATTIN MARA SANYI MAI HANA HAIHUWA SA WARIN GABA RASHIN NI IMA JIN ZAFI YAYIN MU AMALAR AURATAYYA FITAR FARIN RUWA MAI WARI KAIKAYIN GABA TUSAR GABA KURAJEN GABA TUSAR GABA BUDEWAR GABA CIWON JIKI RASHIN GAMSUWA* *Maganin sanyi 5k* *Maganin sanyi* *5k* *Maganin ciwon Qoda 10k* *Maganin HepatitisB ASHA NA TSAWON WATA DAYA MUNBADA ANWARKE DA YARDAR ALLAH 40k* *MAGANIN MATA KALOLI DABAN DABAN INGANTATTU MASU LAFIYA DA KARA KUZARI AKWAI NA MATA AKWAI NA MAZA UWARGIDA DA AMARE KU GARZAYO WURIN AUNTY ZEE MOM MUJAHID KATSINA* *INGANTACCEN MAGANIN GYARAN NONO MAI TADA KOMADAR NONO DA DUK WATA TAMOWA TA NONO ZAI CIKO DA TUWON NONO YA TADA KOMATSEWARSU BANCE ZASU TASHI BA ZADAI SU CIKO SUYI KYAU* *Maganin gyaran Nono 8k* *MAGANIN RAGE TUMBI KODA YAKAI GIRMAN CIKIN YAN BIYU INSHA ALLAH KI GWADA MAGANIN AUNTY ZEE DA YARDAR ALLAH ZAKI GODE* *Maganin Rage Tumbi 7k* *MAGANIN BASUR KODA YAKAI GA YIN TSIRO INSHA ALLAH AGWADA ZA ADACE* *Maganin Basur 5k* *MAGANIN CIWON SUGAR CIKIN IKON ALLAH MUNBADA ANRABU DASHI* *Maganin ciwon Sugar 10k* *08162859027* *09070027627* *Location*KATSINA STATE* *ACCOUNT NUMBER* *8162859027* *ZAINAB SHU AIBU* *OPAY* *OR* *3968303018* *FCMB* *ZAINAB SHU AIBU* *DAN ALLAH IN KINSAN BAKI SHIRYA BA KARKI YI MAGANA DAN ALLAH KIBARI KI SHIRYA AUNTY ZEE MOM MUJAHID KATSINA TAKUCE SAI KUNZO* Page 25 "Ko da Baba ya fita Gaddafi ya nemo, a gurin masu shayi." "Gaddafi ya ce ""lafiya kuwa?""" """Ofishin 'yan bijilanti zaka raka ni""" """Amma a daren nan? Me ya faru?""" """Mu je za ka gani""" Gaddafi ya bi Baba zuwa gurin 'yan bijilanti. "Baba ya shigar da ƙorafi, a kan zargin yin lalata da yarinyar sa." "Gaddafi ya ce ""Baba, babu tabbacin abin da ka ke faɗa fa?""" """Babu tabbaci, aka same ta a ɗaki tare da shi sama da awanni?""" "Gaddafi ya ce ""Amma ai ka san ba cikakkiyar lafiya ce da ita ba""" """Ka rufe mini baki Gaddafi"" Gaddafi ya yi shiru, 'yan bijilanti suka bayar da mutum biyu, tare da Gaddafi" aka tafi taho da Buzu. "Hankalin Habu ya yi mummunan tashi, ganin wai an zo a tafi da ɗan uwansu gurin hukuma. Cikin" "damuwa ya ce ""Wallahi ina da tabbacin babu abin da ya yi mata, ba shi da cikakkiyar lafiya ƙwaƙwalwa" "ne, amma ba wani abin ya yi mata ba, ai mutane sun ga a yadda muka tarar da su""" "Jami'in bijilanti ya ce ""To ka ɗaukko takardar shaidar ba shi da hankalin, ka haɗo da ita mu tafi, ko ce" "maka aka yi mahaukaci ba zai iya wani abun ba"" sauran buzayen ma duk hankalinsu a tashe." "Haka aka tasa Buzu da Habu, da wasu daga cikin buzayen, suka tafi ofishin 'yan bijilanti." "Shugaban gurin ya ce ""Waye daga cikin su, aka tarar da su a ɗakin? Ina kuma ita yarinyar?""" "Baba ya ce ""Tana gida a sume""" """A sume kuma? Shekararta nawa?""" """Shekara ashirin da ɗaya""" """Ikon Allah, to waye a cikin su?"" Gaddafi ya nuna Buzu." """Kai malam ya aka yi aka tarar da kai daga kai ita a ɗaki, tsawon awanni, sauke rawanin nan na fuskarka" "ina magana kana kallona""" "Habu ya ce ""Yallaɓai ba shi da cikakkiyar lafiya fa, wallahi taɓin hankali ne da shi, ina da tabbacin babu" "abin da ya haɗa shi da yarinyar nan""" "Sule ya ce ""Ba ma sa shiri da ita, wallahi rashin fahimta aka samu, na ga kwanon abinci a ɗakin, ina" "kyautata zaton ma abinci ta kai mana, akwai dai abin da ya faru tabbas""" """Ba da ku nake magana ba, ka buɗe baki ka yi mana bayani, ko kurma ne?"" Shugaban bijilanti ya yi" "maganar yana kallon Buzu. Amma bai ko motsa ba, balle ya yi magana." "Ya sake tsuke fuska ya ce ""Sauke rawanin nan kafin na saka a sauke maka shi yanzun nan, ka ƙunshe" "fuska kamar ɗan taliban"" ƙura masa ido ya yi bai yi magana ba." "Habu ya ce ""Ka cire rawanin dan Allah, ka yi maganar abin da ya faru""" "Sule ne ya kai hannu zai sauke masa rawanin, amma ya riƙe masa hannu." """Dattijo, alamu sun nuna fa mutumin nan da gaske mahaukaci ne""" "Baba ya ce ""Wallahi ko dawanau ce a kansa sai an bi mini hakkina, dama 'yan kwanakin nan shi ne yake" "hure mata kunne, sai ta kai bayan magariba a waje ba ta dawo ba. Ta ƙi aure fafur kowa ya zo ba ta so""" Ayshacool """To kai Baba ya ka ke so a yi? Kana gani ya ƙi magana, ita yarinyar ba ku zo da ita ba, ni wannan case a" "bari gobe in Allah ya kaimu ku tafi gurin 'yan sanda""." "Baba ya ce ""Duk fa wata shaida da ake nema, ta tabatta tun da abin da suke yi kenan, sai ya aure ta ya je" "su ƙarata"" gaba ɗaya suka kalli Baba. Cikin tashin hankali Habu ya ce ""Dan Allah dattijo ka yi haƙuri, wallahi ba su saba yin komai ba, wannan karon ma rashin fahimta ne, Nana mutuniyar kirki ce, shi kuma ba shi da cikakkiyar lafiyar ƙwaƙwalwa, dan Allah ka yi haƙuri""" """Wallahi ba zan haƙura ba, daga nan har kotun ƙoli mu je, a karɓa mini hakkina na ci mini mutunci ta" "hanyar yin lalata da 'ya ta, ana daf da ɗaura mata aure"" Gaddafi dai ya yi shiru yana kallon ikon Allah, bai ta taɓa tunanin Baba zai ɗauki irin wannan matakin ba." """Dan Allah ka yi haƙuri, ka ga nan ba ƙasarmu ba ce ba, idan aka kai mu gaban shari'a wahalar da mu za a" "yi, dan Allah ka yi haƙuri"" Sule ya yi maganar cikin magiya. Baba ya fututtuke ya din ga bala'i, buzayen" nan su na ba shi haƙuri. """Payer la dot"" ya furta cikin harshen faransanci yana kallon Habu. Habu ya waro ido, shi ma ya juye" "harshe, suka koma magana da french." "Jiki a sanyaye Habu ya kalli Baba ya ce ""Nawa ne sadakin?""" "Gaddafi ya ce ""Baba wai da gaske aura masan ita za ka yi?""" """Eh mana, tun da haka ta zaɓa. Ai wallahi ba za ta zubar mini mutunci a idon duniya ba, dan na san tun" "da Rabi ta san maganar nan babu wanda ba zai ji a ciki da wajen unguwar nan ba, har a dangi sai ta yi ta yamaɗiɗi, tun da haka ta zaɓa ta samu""" "Baba ya mayar da idonsa kan Habu ya ce ""Ko ma nawa ne, ku bayar da sadaki da safe ya zo ya ɗauke ta""." "Habu ya sake kallon Buzu, cike da damuwa ko zai canza magana, amma ya ga babu alamar hakan." "Hatta 'yan bijilantin, sai da su ka ba shi haƙuri, da rarrashi amma fafur Baba ya ƙi yarda kamar wanda ake" ƙara zugawa. "Habu ya ce kuɗin hannunsa ba su da yawa, bari ya kira waya a kawo kuɗi." "Shugaban bijilanti ya ce ba za ɗaura auren nan a ofishin bijilanti ba, sai dai a tafi gidan mai unguwa, a yi a" gaban jagororin unguwa. "Haka kuwa a ka yi, abin da Baba bai sani ba, da kansa ya ƙara tagayyara Nana, da yayata maganar." "Naira dubu ɗari biyu Habu ya bayar, a matsayin sadakin auren Nana Asma'u ƙarfe sha biyu saura na dare." "Gaddafi dai Baba ya ƙure masa mamaki, duk da ya san har da ziga a cikin lamarin na Baba." "Sai dai kuma Gaddafi ya yi mamakin yadda buzaye, masu gadi suka iya biyan har Naira dubu ɗari biyu a" take matsayin sadaki. Nawa ake ba su kuɗin gadin da har su ka ci suka tayar da kan biyan wannan kuɗin haka?. "Can gida kuwa Nasiru ne yake ta tattaɓa Nana cikin tsoro, saboda sanyin da jikinta ya yi, kamar gawa." Sai can wajen ƙarfe goma na dare ta farka. Ta saka Nasiru ya kawo mata ruwa ƙofar ɗaki. Da rarrafe ta "fito bakin ƙofar ta yi alwala. Ko yinƙurawa ba ta iya yi balle ta tashi, saboda wani irin jiri da take yi. Da" jikin kaya ta jingina daga zaune ta yi salla. Ta idar ta sake kwanciya. "Nasiru ya ce ""Nana ba za ki ci abinci ba? Ga awara na sayo miki mai zafi"" amma ya ji shiru. Ya duba sai ya" "ga ta koma yadda take da farko, hannunta zuwa ƙafafuwan ta duk sun ƙandare sun lanƙwashe." "Sha biyu da rabi Baba suka nufo gida, Gaddafi ya ce ""Amma Baba ba a yi ganganci ba kuwa? Kawai ka" "aura mata mutunen da baka san ma wani iri ba ne ba, dubu ɗari biyu fa suka bayar na sadaki ba ka tunanin ma ko wasu marasa gaskiyar ne?""" """Gaddafi wannan abin da na yi shi ne kawai maganin abin da yarinyar nan take aikatawa. Sau nawa ana" "yinƙurin aurenta tana ƙi? Mutumin nan da ya fito fa cewa ta yi za ta gudu, ko kuma ta kashe kanta a kan" "auren, amma ta san ta je ɗaki gurin namiji. Wannan ne kawai hanyar da zan bi na aurar da ita. Muddin za a din ga saka lokaci ba za ta taɓa bari a yi ba""." "Gaddafi ya numfasa ya ce ""Haka ne, amma ba na tunanin za ta bi maza ko makamancin haka.""" """Ba a shaidar ɗan yau Gaddafi. Allah ya zaunar da ita lafiya""" "Gaddafi yana son sake yin magana, amma ya fasa ya yi shiru." Ayshacool "Mama tamkar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha, haka ta ji bayan da Baba ya yi mata bayanin abin da ya faru." """Wallahi ka yi dabara baban Jamila, wallahi da haka za ta ci gaba da zubar mana da mutunci a idon duniya, kuma auren ba za ta yi shi ba, duk wanda ya zo haka za ta ci gaba da korarsa. Kuma shi kansa Alhajin idan ya ji abin da ya faru ba zai yarda ya aure ta ba, ba ma ita kaɗai ba, duk wanda ya ji maganar nan ba zai yadda ya aure ta ba, amma tun da aka yi haka ka ga an yi maganin kowa ma. Kuma asiri ya" "rufu, tun da ta yi iƙrarin kashe kanta, ko guduwa muddin aka yi mata wannan auren""." """Ai yanzu sai ta yi duk abin da ta ga dama, na yi wa tufkar hanci. Har Gaddafi yana wani cewa ba za ta" "aikata ba, ba zata aika ta ba uban me ya kaita ɗakin masu gadi? Ƙila ma Allah ne ya tashi tona mata asiri" "hakan ta faru""" "Mama ta ce ""To Allah dai ya kyauta""" "Jamila kuwa jikinta ya yi sanyi sosai, sam ba ta taɓa tunanin Baba zai ɗauki wannan matakin ba. A" "yanayin yadda suka tarar da Nana, bai yi kama da wadda ta aikata wani rashin gaskiya ba." **** "Cikin matsanancin ɓacin rai sule yake magana, ""Habu yanzu da ka yarda aka yi wannan auren ya zamu yi" "da su gaba ɗaya?""" "Habu ya ce ""Amma ai ka na ji, da kansa ya ce a biya sadakin ko?""" """A'a ni ya za ayi na sani, tun da ba iya faransanci na yi ba, kuma da ya ce ka biya masa sadakin sai ka biye" "masa? Mutumin da ba hankali ne da shi ba, kai yanzu idan aka saka maka takobi a wuya, za ka iya nuna danginsa ko ahalinsa ne? Daga taimako sai jajubo mana wahala? Aure ai ɗawainiya ne, shekarata nawa a Nigeria iyalina su na can sahara, ban kawo su nan ba, yanzu ya ka ke so mu yi?""" "Habu ya kwantar da murya ya ce ""Dan Allah Souley ka yi haƙuri, duk ba abin ɗaga hankali ba ne ba, idan" "aka samo wani gidan gadin, sai ya fara aikin gafin kafin a san abin yi""" "Tamkar ya gaurawa Habu mari ya ce ""A haka zai yi gadin? Mutumin da sai ya yi sati bai ce uffan ba, aikin" "gadi fa ba buɗewa da rufe ƙofa ba ne kawai""" """Ai ba hauka yake tuburan ba, kuma ko a nan ai mu na tafiya mu bar shi, kuma ya yi gadin, dan Allah ka" "yi haƙuri ka daina ɗaga muryar nan, zamu san abin yi da yardar Allah""" """Ni wallahi har mamaki ka ke bani Habou, daga tsintar mutum sai wahala ka ke da shi, kamar wani" "tsohonka, na ga yadda za ayi ai da wannan badaƙalar""" "Habu ya dafa kafaɗar Sule ya yi murmushi ya ce ""Babu abin da zai faru sai alkhairi in sha Allah, kuma" "Allah ya na gani taimako muka yi, ba zamu wulaƙanta ba"". Da ƙyar Habu ya samu ya shawo kan Sule." * "Nana ba ta sake tashi ba, sai washegari ƙarfe bakwai na safe, shi ma Nasiru ne ya tashe ta, kamar jiya a" "bakin ƙofar ɗakin su ta yi alwala, ta yi sallar asuba a zaune. Yana zaune ta idar, tana idarwa ya ce ""Nana kar ki kwanta, ga kokona ki sha ki daina wannan baccin, jikin ki fa sanyi yake yi""" "Ta girgiza kai ta ce ""Na ƙoshi Nasiru, jikina babu ƙwari nima ji nake kamar mutuwa zan yi""" "Da sauri ya ce ""Ba mutuwa za ki yi ba, yunwa ki ke ji, ki sha kaɗan"" ganin yadda ya damu sosai da sosai," "ya sanya ta karɓa ta sha kaɗan, ta ajiye ta fara ƙoƙarin kwanciya." "Suwaiba ce ta shigo ɗakin, tare da rangaɗa guɗa ta ce ""Amaryar tsakar dare, mai doki ya koma kuturi, ba" "a auri mai gida ba an auri mai gadi, to Allah ya sanya alkhairi""." "Nana ta ɗaga jajayen idanunta ta kalli Suwaiba, ta mayar da idonta kan Nasiru ta ce ""Nasiru mafarki ne" "wai?""" "Ya girgiza kai ya ce ""A'a a zahiri ne""" """To me Suwaiba take cewa ne?""" "Cike da ƙuruciya ya ce ""Wai jiya da daddare aka yi auren ki""" """Aurena kuma? Kamar yaya?""" "Ya ce ""Wallahi nima ban sani ba"" Suwaiba ta cigaba da dariya, tana ɗaukar jakar kayan kwalliyar ta." "Baba ne ya shigo ɗakin, ya tarar da Nana a zaune, ga Nasiru a gabanta da kofin koko." """Yauwwa kin tashi kenan? To ki buɗe kunnen ki da kyau, ki saurare ni""" "Ta zubawa Baba manyan idanunta, da suka yi kama da na Japanese sai dai nata manya ne." Ayshacool **** """Jamila"" Nana ta furta da ƙyar, saboda yadda take jin tamkar an ɗora mata wani ƙaton dutse a kanta." """Na'am""" """Da gaske Baba yake yi, an ɗaura mini aure, ko kuwa mafarki ne?""" "Jamila ta ɗan taɓe baki ta ce ""Da gaske ne mana, zai yi miki ƙarya ne?""" "Ta sake cewa ""Kuma da buzayen nan?""" """Eh fa""" """Waye a cikin su?""" "Jamila da ta fara ƙosawa da tambayoyin Nana ta ce ""Ni fa ban sani ba, tun da ba taɓa zuwa na yi ba balle" "na san su. Ke ma Nana me ya yi miki zafi, da za ki je ɗakin masu gadi me ki ke yi a ciki? Dama ana iƙrarin kin ƙi yin aure, yanzu ga abin da ki ka ja wa kanki nan""" "Sanin ko ta yi bayani ba fita za ta yi ba, ya sanya ta jan bakinta ta tsuke. Ta ci gaba da sauke numfashi da" "ƙyar. Tiryan-tiryan ta shiga tuno abin da ya faru, sai dai tunaninta ya tsaya cak a daidai lokacin da ta ga wannan mutumin a cikin ɗakin, har ta razana ta ƙwala ihu." "Cike da dana sani take raya, da lokacin da ta firgitan nan addu'a ta yi, da wata ƙila hakan ba ta faru ba." "Ta ɗaga kai a hankali, ta ƙurawa ƙofar da Jamila ta fita ido. Wani irin huci haɗi da nishi ta din ga ji, ba" tare da ta san daga ina yake fitowa ba. "Wata irin narkekiyar macijiaya ce, ta fito daga cikin roofing ɗin ɗakin, tana tsartuwa ta yo kan Nana." "Tamkar an ɗaure ta, ta kasa motsi, kuma ta kasa magana kawai ta zubawa sarautar Allah ido." "Ta ci gaba da nufo ta tana tsartuwa, sai kuma Nana ta ga macijiyar ta ƙame a guri guda, tana ta wutsul-" "wutsul tana fasa kai, tana neman hanyar guduwa." "Wani dogon hannu ta ga an zuro ta taga, an danƙi kan macijiyar, an janye ta, sai da aka janye ta, sannan" "Nana ta razana ta iya tashi zaune tana maimaita ""Innalillahi wa innalillahi raji'un""" "Tagar ɗakin ta kalla, ta ga ƙaisar a tsaye, ya tattare macijiyar, ya zura ta a cikin wata 'yar mitsitsiyar" kwalba. Har yanzu hannunsa ɗaya da rauni. "Ya dubi Nana ya ce ""Wannan ma 'yar aike ce, aka kuma aikota jininki ake so ko ta halin ƙaƙa, kuma 'yar" "uwakki aka bawa abin da ta zo ta ajiye a ɗakin nan, da zai bayar da damar samo jinin naki. Sai dai waccan jakar ce ta hana macijiyar ƙarasowa inda ki ke"" ya ƙarasa maganar yana nuna wa Nana, jakar da sarkin baka ya bata." """Duk ba wannan ce ma ta saka na zo da kaina gurin ki, rana tsaka ba. Ina mai tabattar miki da wannan" "auren da mahaifin ki ya yi miki, ya jefa rayuwar ki a cikin sabon babin ƙaddara da ƙalubalen rayuwa, ba kuma ke kaɗai ya jefa ba har da ni. Sai dai na yi alwashin ba zamu wahala muka ɗai ba, sai na yi masa mafi munin azabtarwa a kansa da kuma iyalansa, duk wani farinciki da yake tunanin samu a duniyar nan, sai ya yi hannun riga da shi, ke kuma ki shirya tsaf dan wanda aka aura miki ko dai ya yi ajalina ko na yi" ajalinsa! Ayshercool 08081012143 Ayshacool *AUNTY ZEE MOM MUJAHID KATSINA 08162859027* *INGANTACCEN MAGANIN SANYI MAI WANKO DUK WANI DATTIN MARA SANYI MAI HANA HAIHUWA SA WARIN GABA RASHIN NI IMA JIN ZAFI YAYIN MU AMALAR AURATAYYA FITAR FARIN RUWA MAI WARI KAIKAYIN GABA TUSAR GABA KURAJEN GABA TUSAR GABA BUDEWAR GABA CIWON JIKI RASHIN GAMSUWA* *Maganin sanyi 5k* *Maganin sanyi* *5k* *Maganin ciwon Qoda 10k* *Maganin HepatitisB ASHA NA TSAWON WATA DAYA MUNBADA ANWARKE DA YARDAR ALLAH 40k* *MAGANIN MATA KALOLI DABAN DABAN INGANTATTU MASU LAFIYA DA KARA KUZARI AKWAI NA MATA AKWAI NA MAZA UWARGIDA DA AMARE KU GARZAYO WURIN AUNTY ZEE MOM MUJAHID KATSINA* *INGANTACCEN MAGANIN GYARAN NONO MAI TADA KOMADAR NONO DA DUK WATA TAMOWA TA NONO ZAI CIKO DA TUWON NONO YA TADA KOMATSEWARSU BANCE ZASU TASHI BA ZADAI SU CIKO SUYI KYAU* *Maganin gyaran Nono 8k* *MAGANIN RAGE TUMBI KODA YAKAI GIRMAN CIKIN YAN BIYU INSHA ALLAH KI GWADA MAGANIN AUNTY ZEE DA YARDAR ALLAH ZAKI GODE* *Maganin Rage Tumbi 7k* *MAGANIN BASUR KODA YAKAI GA YIN TSIRO INSHA ALLAH AGWADA ZA ADACE* *Maganin Basur 5k* *MAGANIN CIWON SUGAR CIKIN IKON ALLAH MUNBADA ANRABU DASHI* *Maganin ciwon Sugar 10k* *08162859027* *09070027627* *Location*KATSINA STATE* *ACCOUNT NUMBER* *8162859027* *ZAINAB SHU AIBU* *OPAY* *OR* *3968303018* *FCMB* *ZAINAB SHU AIBU* *DAN ALLAH IN KINSAN BAKI SHIRYA BA KARKI YI MAGANA DAN ALLAH KIBARI KI SHIRYA AUNTY ZEE MOM MUJAHID KATSINA TAKUCE SAI KUNZO* Page 26 "Jin abin Nana ta din ga yi tamkar tunani, kuma tamkar mafarki, domin da ta tashi zaune, ba ta ga ƙaisar" "ɗin ba, kuma ba ta ga macijiyar ba." "Muryar Yaya Atine ta jiyo a tsakar gida tana faɗin ""Wanda ya ƙi ji ai ba ya ƙi gani ba, sam ban ga laifin Isa" "ba abin da ya yi, wannan hukuncin shi ne ya dace da ita, babu irin rarrashi da ban bakin da ba a yi wa" "yarinyar nan, amma kowa ya zo sai ta yi burus fafur ta ƙi yarda da maganar aure, hankalinta ba ya" "kwanciya sai maganar ta lalace, idan wani abin da aljan wani abin tsagwaron iskanci ne kawai, dan a iya adadin yawon nema mata magani da aka yi, ai ya ci a ce ta warke""" "Mama kuwa tamkar ta taka rawa dan murna, duk yadda take ƙoƙarin ɓoyewa, sai da farincikin ta ya kasa" ɓuya. "Ta yi caraf da maganar Yaya Atine ta ce ""To ai yanzu an yi mai ɗungurugum, haihuwa da hanji, ko in ce" "mai doki ya koma kuturi, tun da babban mutum ne mai rufin asiri ya fito yana sonta, amma fafur ta ƙi, har tana iƙirarin za ta gudu, ko ta kashe kanta, ashe ita gurin wasu take zuwa lalacewa"" saurin katse" "maganar ta yi, bayan da suka yi ido huɗu da Nana a tsaye a ƙofar ɗakin su." """Rabi, duk abin da za ki ce na yi, ba zai dame ni ba, dan na riga na saba da duk wani ƙazafi da cin mutunci" "da ki ke yi mini, har ƙazafin maita kin yi mini duk abi dame ni ba, kuskure ma fi girma da za ki yi shi ne, yi mini ƙazafin zina, babu wanda ya kama ni ra'ayil aini, ina yi kar ki ƙara danganta ni da zina""" "Jamila ta zaburo ta ce ""Nana, Maman ki ke gaya wa haka? Ki ke kiran sunanta gatsal haka?""" """Ba ita kaɗai ba, kafataninku nake yi wa kashedi, kar wanda ya sake gangancin danganta ni da zina," "amma idan kun ƙi ji ba za ku ƙi gani ba""" "Ta nufi banɗaki, tana jin Yaya Atine tana kiran ta, amma ta yi mata banza, ta shiga ta yi alwala ta koma" "ɗaki ta tayar da sallar azahar. Tana zaune a bigiren da ta yi salla, ta kasa addu'a ko lazumin ta kasa, haka" "zalika ta kasa kukan ma, ta rasa me ma za ta ce. Kawai ta haɗa kanta da gwiwarta ta yi shiru. Har yanzu ji take tamkar kawai barazana ake yi mata, amma ba da gaske ne wai an yi mata aure ba." "Ga yunwa tana ji, ga jikinta a mace babu ƙwari, ga damuwa gaba ɗaya ji take kamar ma ba ita ba ce ba." "Can ɓangaren Hajiya Amina kasa zaune ta yi ta kasa tsaye, ta din ga mita tana faɗa, har da cewa sai ta kai" Baban Nana Human rights. "Shukura ta ce ""Mummy ki na da ɗorawa kai, mutumin ya yi wa 'yar sa aure, kuma ki ce za ki kai shi" "human rights?""" Ayshacool """To Shukura na rasa abun da zan yi zuciyata ta yi mini sanyi ne, gaba ɗaya tausayin yarinyar nake ji. Ba" "na tunanin an tsaya an ji ta bakin ta. Ke ba kya gurin lokacin da aka kira ni, aka ce an ganta a ɗakin masu gadi. Gaba ɗaya ba ta hayyacinta, ba ki ga a yadda aka fito da ita ba. Kuma shi ma a buzayen wannan wanda ba ya maganar ne fa, har aka yi ta balahirar nan aka gama bai yi magana ba. Ke wait kamar fa" "yarinyar nan ita ma tana da mental issues""" "Shukura ta ce ""Au ke sai yanzu ki ka gane? Ni na daɗe da fuskantar hakan, shi yasa wasu lokutan ba na" "sakewa da ita, ko na ganta da Haidar""" "Cike da damuwa ta sake cewa kuma babanta ya san mutumin da ya aura matan, yana da mental issues?""" """Mummy ina zan sani ina nan?""" """Oh my God"" Mummy ta faɗa tana zama." "Ta ci gaba da cewa ""Wannan mutanen da ba sa iya zama guri ɗaya, yanzu suna nan anjima su na can," "yanzu haka za su yi ta yawo da ita, ko kuma can ƙasar ta su zai kaita oho. Dan Allah Shukura, ki ɗan haɗo" "ɗan abin da ya sauwwaƙa mu haɗa a kai mata, ko ma mene ne ya same ta, duk a dalilin mu ne""" "Shukura ta ce ""A'a ba a dalilinmu ba ne, ki daina ɗora mana laifi Mummy, zan haɗa abin da ya samu, ni" "yadda za mu yi da Haidar kawai nake ji wallahi, dan yadda yake ƙaunar ta ba ya ƙaunata haka. Inda Allah" "zai taimake ni babansa cikin satin nan zai dawo, da ban san yadda zan yi ba""" "Mummy ta yi murmushi ta ce ""Ina jin sa fa tun safe yake bin Jummai, yana ce mata ina Anty. Tana" "tsokanarsa tana cewa antynta ce ba ta sa ba, har da kukansa ya zo yana gaya mini, in cewa Jummai Anty Nanansa ce ba ta ta ba""" """Ai sun shaƙu sosai ne, zan ga abin da zan yi a kai"". Shukura ta yi maganar tana ɗaukar remote." **** "Cikin ƙanƙanin lokaci labarin aure Nana, ya karaɗe dangi da unguwa baki ɗaya, Mama na ta nanata ai" "cikin dare aka ɗaura auren a gidan mai unguwa, jin hakan ya sanya sai mutane su tambayi ba'asin dalilin yin hakan, saboda ba abu ne da aka saba da shi ba, mussaman auren budurwa, a ce an ɗaura shi cikin" dare kamar yaƙi. "Sai Mama ta ce ""Hmm ku dai a yi sha'ani, labarin ne babu daɗin ji""" "Yaya Atine ce ta bi Nana da kwanon abinci har ɗaki ta tsaya a kanta ta ce ""Ki tashi ki saka wani abu a" "cikin ki, kina ta kwanciya kin wuni ba ki ci komai ba"" Nana ta yi mata banza ko ƙwaƙwƙwaran motsi ba ta" yi ba. "A hasale Yaya Atine ta ce ""Shikkenan kin yi wa kanki"" Nasiru kuwa ya kasa zaune ya kasa tsaye, idan ya" "fita ya zagaya sai ya dawo ya leƙa Nana, har aka yi sallar magariba salla ce kawai take fito da Nana, babu" wanda ta tankawa a gidan. "Saura ƙiris Alhaji Zailani ya furzo abincin da yake ci, bayan da Hajiya Amina ta kammala yi masa bayanin" "abin da ya faru. Ji ya yi tamkar ta zuba masa wuta a zuciyarsa. Wannan shi ake cewa ga ƙoshi ga kwanan yunwa. A zuciyarsa ya ce amma wannan an yi la'anannen tsoho, mu gama yarjejeniyar zai ba ni aurenta burina na daf da cika, kawai sai ya aurawa wani, saboda hauka. A fili kuwa cikin ƙwarewa da iya duniyanci, ya nuna halin ko in kula ya ce Allah ya kyauta. Bayan ya kammala cin abinci ya cewa Hajiya" "Amina ta zauna a sashenta kawai, zai ɗan fita." """Amma na ga yaushe ka dawo, da har zaka sake fita koma mene ne ka bari sai da safe mana?""" """Yaushe ki ka fara kafa mini dokoki a gidana?"" Yayi maganar yana tsare ga ido, babu shiri ta ce ""Allah ya" "baka haƙuri""" "Kamar zai haukace, haka ya ɗauki mota ya fita, yana tafe yana ta ɗure-ɗuren ashariya a cikin mota, yana" zage-zage. "Gidan malam Gambo ya nufa, gurin sha ɗaya na dare, haka ya kira shi a waya ya fito." """Alhajin Allah, lafiya kuwa ka zo a daren nan, ba yau ka dawo daga tafiya ba?""" "Cikin damuwa ya ce ""Babu lafiya, dan kuwa an yanka ta tashi""" """Too ikon Allah, me ya faru?""" """Yarinyar nan, da za a ɗaura mana aure, babanta ya yarda zai bani aurenta, ina murna muradina zai cika," "kawai yau na dawo na tarar wai ya aurawa ɗaya daga masu gadin gidana, saboda an ganta a ɗakinsu, wai ko yana zarginta ne oho masa, ni ko inda yake ban je ba, dan Allah meye abin yi? Ni fa ina iya saka a" "kashe ko ma uban wa aka aura mata, muddin muradina zai cika""" Ayshacool """Idan ma kin kashe kanki, ƙaddara ta riga fata, dole ki tashi ki ƙwarara jikinki, ki ci abinci ki ware. Ko dai" "mu yi gaba da gaba da ƙalubalen da yake tunkaro mu, ko kuma ki amince na ɗauke ki baki ɗaya, idan ba haka ba ba zan iya cewa ga abin da zai faru ba""" "Nana ta ɗaga ido ta kalli inda yake zaune, ta yi masa shiru ba ta ce masa komai ba." "Ya miƙe tsam ya rufe littafin, ya miƙa hannunsa can saman wani guri, ya ɗaukko wata kwalba, ya zo" "gabanta ya zauna, ya ƙura mata ido, take ta ji tamkar an zare mata kuzarinta." "Ya watsa mata wani koren abu a fuska, babu shiri Nana ta yinƙura ta tashi zaune tana tari." Ummi ta gani a ɗakin da take a asibiti. """Zan sha ruwa"" Nana furta a wahale. Aka kawo mata ruwa, ta sha sosai sannan ta koma ta kwanta. Sai" "da Nana ta kwana a asibiti sannan aka sallame ta, wata irin azababbiyar yunwa da ta sako ta gaba, haka ta din ga cin abinci." "Sun koma gida babu daɗewa sai ga Hajiya Amina, tare da Haidar. Yana ganin Nana ya je ya maƙalƙale" mata yana murna. Ita kanta Nana ta yi murnar ganin Hajiya Amina da Haidar. """Nana, duk da ni ba na zargin ki, kuma ba zan takura miki da tambayar jin abin da ya faru ba, amma ki yi" "haƙuri da abin da ya faru, amma idan ba kya son auren nan ki yi mini magana, a shigar da ƙara a" "hukumance a raba auren, kalli duk yadda ki ka rame""" "Jiki a sanyaye Nana ta ce ""Na gode sosai da sosai Hajiya, Allah ya saka da alkhairi ina fatan Allah ya sanya" "haka shi ne mafi alkhairi, ni ba auren ne damuwata ba, zargin da ake yi mini.. ta kasa ci gaba saboda" yadda kuka ya ƙwace mata. "Ta dafa bayan Nana ta din ga rarrashinta. Kaya ta kawowa Nana, har da bedsheets sabo da tsofaffi" "amma masu kyau, ga 'yan kayan kitchen da ta kawo mata, da Shukura ta bayar a kawo mata. Ta yi ta godiya, ta tashi za ta tafi, Nana ta ce za ta raka ta, ta ce ""A'a ai ke yanzu matar aure ce, ki yi zaman ki" "Allah ya sanya alkhairi"" ta ƙarasa maganar tana danƙawa Nana kuɗi a hannu." "Maƙwabta na ta zuwa Allah ya sanya alkhairi, da biyu domin su ga halin da Nana take ciki, har da 'yan" "islamiyyar su, da tun da ta bar makarantar babu wanda ya bibiye ta, balle a ji dalilin daina zuwan ta." "Baba sai kaiwa yake yi, yana komowa yana nanatawa Nana ta haɗa kayanta cif, ta fara shiri. Yanayin" "yadda take ganin duniya ta juya mata baya, ta ji ina ma ba a haife ta ba, kuma duk wannan abin babu wanda ya kira mahaifiyarta ya gaya mata halin da ake ciki. To me ye ma amfanin gaya mata, tun da ba wani abin za ta amfana miki ba, kuma kin san ba zuwa za ta yi ba. Wata zuciyar ta tunatar da ita." "Da daddare gari ya yi tsit, Nana tana ta juyayi da tunanin wa ma aka aura mata a cikin buzayen, tun da su" na da yawa. "Babu tsammanni bacci ya yi awon gaba da ita, sai dai ta din ga jin ta tamkar a zahiri ba mafarki ba. Da" "wata irin murya mara daɗin ji, cikin maɗaukakin sauti mai matuƙar razani da kiɗima zuciya ake yi mata magana." """Ko kin san wa ki ka aura? Mutumin da shi kansa bai tantance waye shi ba, bai san mene ne jinsa ba," "mutum ne shi ko aljan. Rayuwa da shi na iya sadar da ke da ajalin ki. Lokaci ya yi da za ki biya abin da kakannin ki suka aikata, da kuma abin da ya faru a silar ki ke ce tabbas ke za ki biya wannan bashin. Ki tsira da ranki ki bar gida, ki yi nesa da gida, ko kuma ki fuskanci rayuwa mafi muni da hatsari"" A gigice Nana ta tashi, ta fita tsakar gida da gudu tana haki, jan burki ta yi duk da zuciyarta na raya mata ta zare sakata ta ruga da gudu. Wani irin zafi take ji da matsanancin tashin hankali, ji take kawai ta buɗe ƙofa ta" fita shi ne za ta samu nutsuwa. "Juyawa ta yi da nufin ta fice ta bar gidan, amma ta ji kamar ta na ƙwaƙƙwaran motsi, zuciyarta za ta yi" bindiga saboda bugun da take yi. """Ki na ƙara ɗaga ƙafarki, zuciyar ki za ta tsaya da aiki. Sai da na gaya miki, babu irin kashedin da ban yi" "miki ba, ki ka yi kunnen uwar shegu da ni, wallahi da kin sake kin buɗe ƙofa kin fita, haukacewa za ki yi. Yanzu dabara ta rage ga mai shiga rijiya"" A wannan karon ta gane muryar ƙaisar ce, amma ta farkon ba" ta san muryar waye ba. Ayshacool "Zumbur ta tashi zaune, tana kallon ɗakinsu, a iya saninta dare ne ta kwanta tana bacci, amma yanzu ta" ga azahar ce. "Yaya Atine ta shigo ɗakin tana faɗin ""Kin gama shure-shuren da ihun, kin ga dama kin tashi kenan?" "Wallahi tun wuri ki ajiye wannan haukan aljanun naki, ki kama kanki, ba kowa ne zai zauna kina masa wannan shirmen banzar ba, idan kin ga dama ki tashi ki wuce ki yi wanka ki zo ki ci abinci"" Nana ba ta" "motsa ba, tana tunanin ko ta yi sallar asuba?." "Ummi ta shigo ɗakin da jaka fuskarta ɗauke da mamaki ta ce ""Nana"" Nana ta ɗaga kai ta kalle ta." """Kin ga yanzu daga fita ta, na haɗu da wasu buzaye, wai 'yan uwan mijin ki ne, suka ba ni wannan kayan" "wai a ba ki, sun ce , a ce ki yi haƙuri abin ya zo babu shiri, kuma ba su da isassun kuɗi. Kin ga dubu hamsin, wai a baki ki yi wani abin ga kuma kaya""" "Yaya Atine ta waro ido ta ce ""Buzayen?""" """Wallahi kuwa""" """Kirawo Rabi maza a yi a gabanta"" aka kirawo Mama, aka buɗe zip ɗin jakar." "Danƙareriyar shadda bazin ce a farko, fara ƙal an yi mata aiki irin na buzaye, har da awarwaraye da ɗan" "kunne, da sarƙa." "Kaya dai Atamfa set biyar, sai takalma guda biyu da turare har da na wuta." "Ummi ta ce ""To ke Nana ki na ta wani buntsire-buntsire da alama wannan za su kula da ke. Kalli a yadda" "aka yi auren fa, amma har suka yi miki wannan kayan haka."" Ita kanta Mama abin ya ba ta mamaki ya tsaye mata a rai ta za ta Nana za ta tozarta fiye da haka." "Ummi ta ce sai An yi wa Nana gyaran jiki an yi mata lalle da gyaran gashi, tun da har sun ƙoƙarta sun" kawo wannan kayan. "Da aka gaya wa Baba nuna wa ya yi ko a jikinsa, duk da cikin ransa ya ji daɗin kayan da suka kawo mata," damuwarsa kar ma a fara yi masa zancen kayan ɗaki. Dan sadakin ma naira dubu hamsin ya ware zai ba ta. **** "A tsanake yake ƙare masa kallo, tun daga kansa, har zuwa kan yatsunsa da suke ɗauke da manyan" "zobunan azurfa. Duk da fuskarsa a rufe take, sai idanunsa kawai ake iya gani, yatsun hannunsa su ka fallasa asirin kalar farar fatarsa." """Ko za ka sauke rawanin naka mu yi magana?"" A hankali ya juya ƙwayar idonsa, yana kallonsa amma bai" yi magana ba. """Magana nake, ka sauke rawanin fuskarka mu yi magana"" still bai sauke ba, kuma bai yi magana ba, sai" "ma yinƙurawa da ya yi, ya juya zai fita"" cikin azama ya tashi ya sha gabansa ya ce ""Ya mu na magana za" "ka tashi ka tafi?""" """Me yasa ka kira ni?"" Ya yi maganar yana tsare shi da ido." """Buƙata ce""" """Ta me?""" """Ina so ka gaya mini ko nawa ka ke buƙata, ka saki yarinyar nan Nana da babanta ya aura maka""" "Ya gyara tsayuwarsa sosai yana kallon cikin idanun Alhaji Zailani, ya ce ""Je devrais divorcer?"" Alhaji" "Zailani ya yi ƙuri da ido yana kallonsa, dan bai gane me ya ce ba." "Ya taka a hankali ya je gaban Alhaji Zailani ya tsaya, sannan ya ce ""Me yasa ka ke so na sake ta?""" """Saboda na fi ka buƙatar ta""" "Ya sauke ajiyar zuciya ya ce ""Ka ce ka fi ni buƙatar ta?"" Kafin Alhaji Zailani ya ba shi amsa, kawai ya gansu" a tsakiyar dokar daji. "Ya saka hannu, ya sauke rawanin fuskarsa, kyakyawar fuskarsa ta bayyana ya ce ""Ka ce ka fini buƙtarta?" "Har ka manta da abin da na yi maka a wancan lokacin?, shi ne ka sake biyo ni da wannan maganar?""" "Ya saka hannunsa a wuyan Alhaji Zailani, wasu irin dogwayen farata suka tsiro a yatsunsa, a hankali" "kamaninsa suka gushe, fuskar wani tsoho tukuf ta bayyana." "Ya ƙara tsananta shaƙe Alhaji Zailani ya ce ""Ni na fika buƙatar ta, fansa ta zan ɗauka a kanta. Mallakina" "ce, fansa zan ɗauka, dan haka na fika buƙatar ta!!" "Jin numfashin sa ya yi, ya dawo iya ƙirjinsa, jini ya fara zubowa daga gurin da ya huda shi da faratansa." Ayshercool 08081012143 Ayshacool **** "Gidan su Nana kuwa, ranar ta kasance ranar da za a kaita, sai dai babu wanda ya san ina za a kai ta," "kuma ko katifa Baba bai saya ba. Da Ummi ta yi masa magana sai cewa ya yi ba shi da kuɗi, ita ta yi mata. Abin ya ɓata mata rai, babu wanda ya san wani irin guri za a kaita, idan babu labule da katifa a ƙasa za ta zauna? Ga kuɗin sadakin Nanan har dubu ɗari biyu a hannunsa." "Nana kuwa kawai dai ga ta nan ne, hankalinta ya kasu kashi-kashi, tana tunanin maganganun da ta ji da" "wannan muryar, ga kuma abin da ƙaisar ya gaya mata. Duk da wani ɓangaren na zuciyarta na gargaɗinta da yadda da maganganun Aljanu, wataƙila kawai wasa suke yi mata da hankali. Tana jiyo Mama tana ɓaɓɓaka dariya tana cewa yanzu idan buzayen su ka ƙi zuwa, su nuna in da za a kai Nana, ko kuma suka" gudu shikenan Nana ta zama bazawara. "Maganar ta sosawa Nana rai nesa ba kusa ba, wato duk bayan abubuwan da ta yi mata a baya, har ma" "tunani take yi, ta yi zawarci. A take Nana ta yi wa kanta alwashin ko bangon duniya wanda aka aura mata, zai ɗauke ta ya kai ta, za ta bi shi ko da kuwa zai din ga azabtar da ita ne, ta gwammace hakan da ta sake dawowa gidan nan da sunan zawarci tun da dai ibada take yi." "Abubuwan da suke damunta kuwa, ta fauwwalawa Allah, ta dake ta je ta yi wanka. Ta yi kwalliya da" "wannan shaddar, da kayan da aka kawo mata." "Kasancewar Nana tana da fata mai kyau, 'yan kayan da Ummi ta haɗo ta yi mata gyaran jiki na kwana" "biyu, ta yi kyau fatar ta ƙara haske. Ga zanen lalle an yi mata. Gashin kanta ma ya yi kyau, komai kyau ne" da shi idan ya sha gyara. "Sai da Mama ta yi saroro, da Nana ta fito cikin kayan nan, tamkar matar wani hamshaƙin mai kuɗi. Duk" "da ta rame sosai, amma kayan sun zauna a jikinta, tamkar tela ya gwada ta. Fuskarta babu yabo babu fallasa ta fito tana gaisawa da 'yan uwa da abokan arziki." "Nan gida ya ɗauki guɗa, aka din ga yi mata fatan alkhairi. Duk da ga a yadda auren ya zo mata, kuma har" "a lokacin ba ta tantance waye ma mijin nata ba. Amma ganin mutanen da suke ta shiga su na fita, ana" "cin abinci, a dalilinta. Kawai ta durƙusa ta yi sujudu shukur, ko ba komai wannan wata rana ce da kowace" "mace da ta san ciwon kanta, take fatan gani a rayuwarta." """Allah ga Nana, Allah ga baiwar ka. Ina godiya da tarin ni'imomin ka a gare ta"" ta ɗago fuskarta duk" "hawaye. Suwaiba ta ce ""Ji wata gulma, har da sujjada kamar auren gaske, wai a dole sai an raina wa mutane hankali. Mu dai a hanzarta a yi a bar mana ɗaki""" "Nana ta kalle ta ta ce ""Suby kenan, ai duk ci gaba ci gaba ne, ba ɗaki ba gidan zan bar muku baki ɗaya ku" "sake, ina fatan aniyar kowa ta bi shi""" "Suwaiba ta ce ""Aniyar kowa ta bi shi kamar yaya, me ki ke nufi?""" "Ta girgiza kai ta ce ""A'a ba zan biye miki ba, ni yau ina cikin farin ciki ne a gare ni, ba zan biye miki ki" "lalata mini ita ba"" Suwaiba ta ci gaba da faɗar maganganu. Nana kuma ta fice ta bar mata ɗakin." "A hakan an sassamu wanda suka bayar da gudummawa sosai da sosai, domin kowa yana yabon Nana da" "halaye na gari, dan duk 'ya'yan malam Isa babu mai haƙurinta da biyayya, duk da wasu lokutan ita ma" "tana da faɗa, amma akwai ladabi. Ummi ta kasa ta tsare tana karɓar kaya da kuɗin gudunmawar da kanta," "Ta kuma din ga ƙoƙarin, duk wani yinƙurin kawo hargitsi da Mama take ƙoƙarin yi a gurin taron ta hana." "Nana ta samu kayan kitchen, da kuɗaɗe daga hannun jama'a da dangi." "Da yamma sai ga Yusuf da mota, tare da Sule, Hajiya Amina ta ce a ɗauki Nana a ciki." "Yaya Atine ta ce a fara zuwa su ga gurin, su san abin da za su saya, amma Yusuf ya ce babu buƙatar" "hakan, amarya za su ɗauka." "Gaba ɗaya jikin Nana a sanyaye yake, su Yaya Atine suka saka ta sake wanka, Ummi ta bata wata lafaya" "da ta saya mata, ta saka ta feshe ta da turare." "Ana ta rangaɗa guɗa, aka kai Nana gurin Mama wai ta yi mata nasiha." "Mama ta ce ""A'a ni me zan ce, ai ta san komai ba abin da ba ta sani ba, a sauka lafiya""" "Nana a ranta ta ce ""Ko ba ki faɗa ba lafiya zan sauka, kuma sai Allah ya kunya ta ki""." "Baba yana ƙofar gida, aka kai masa Nana ya yi mata nasiha." Ayshacool "Ya ƙare mata kallo ya ce ""Yanzu kin ga abin da ki ka janyo wa kan ki ko Asma'u? To ki buɗe kunne ki" "saurare ni, babu zawarci a gidana, duk ɗan da zan aurar kin san ina jaddada wannan, ba zawarci babu" "yaji a gidana. Allah ya rufa miki asiri da miji na gari, amma fafur ki ka ƙi. Je ki Allah ya ba da sa'a ya baku" "zaman lafiya"" Nana ta daskare a gurin ta kasa motsi balle ta tashi." """Na ce ki je Allah ya sanya alkhairi"" ya maimaita mata." "Ta ɗago idanunta a hankali ta ce ""Baba... Sai kuma maganar ta maƙale ta ƙi ƙarasa fitowa, saboda kuka" da wani abu mai nauyi da ya danne mata maƙoshinta. "Ta yinƙura ta tashi, har sun kai bakin motar, ta waiwaya, kawai ta ga Baban ya zubo mata ido, idanunsa" cike da hawaye. Kawai ta yi bismillah ta shiga motar. "Ba Nana ce yarinya ta farko da Baba ya aurar ba, amma har cikin zuciyarsa ya ji rabuwa da ita, duk da" "tarin haushinta da yake ji. Wani sashen na zuciyarsa kuma ya fara tunatar da shi, da jin kamar bai kyauta ba abin da ya aikata." "Kasancewar mota ɗaya tak aka kawo, daga Yaya Atine, Anty Sa'a sai Ummi suka tafi raka Nana." "Su na tafe a hanya su na ta hirar su, Nana kuwa zubar da hawaye kawai take yi." "Sosai Yusuf ya ji tausayin Nana, shi kansa ya jinjina girman wauta da rashin sanin ciwon kai da mahaifin" Nana ya yi. """Kai wannan wace irin unguwa ce duk babu mutane, wannan ai sai a yanka mutum a binne ba a sani ba""" "Ai kuwa babu shiri Nana ta ɗago, tabbas haka ne, unguwar manyan gidaje ne sosai awon gwamanti, sai" dai babu alamar akwai jama'a da yawa a unguwar. "Gaban wani gida suka yi parking, mai ɗauke da doguwar katanga." "Ko da suka fito, Yaya Atine ta ce ""Aka ce mai gadi ne, ya na ga katafaren gida haka?""" "Sule ya ce ""Eh gidan da zai yi aikin gadin ne, a ɗakin masu gadi za su zauna""" "Ta ce ""To ikon Allah"" ya buɗe gate ɗin suka shiga." "Akwai ƙatuwar haraba a gidan, ta ko ina shuke-shuke ne, main gidan kuma yana can nesa da gate ɗin" gidan. Daga nan kusa da gate ɗin kuma wani wani ƙaramin gini ne. "Sule ya buɗe ɗakin ya ce su shiga. Ɗaki ne babba falle ɗaya, sai banɗaki sai ƙamshin sabon fenti da kuma" turaren wuta yake tashi. "Sabuwar katifa ce gal babba a ɗakin, ga labulaye da wardrobe mai guda biyu da mudubi ƙarami, ga kuma" carfet a tsakiyar ɗakin. "Yaya Atine ta ce ""Yanzu a sati ɗayan ku ka yi wannan shirin?""" "Sule ya ce ""Eh, wani mu muka yi, wani kuma Hajiyar da muke yi wa aiki ce, ita ta sai labulaye da abin" "shimfiɗar nan, da kayan ɗakin ma, abubuwa kaɗan mu ka ƙarasa""" """Lallai tana da kirki sosai, bayan kayan da ta je ta kai mata gida. Amma Ummi babanku ya tafasa" "makaronin asara ko cokali fa bai saya wa Nanan ba""" "Ummi ta tsuke fuska ta ce ""Babu kitchen kenan? A ina za mu ajiye mata kayan kitchen ɗin""" "Sule ya ce ""Ai abu ne na maleji, sai dai a ajie mata a nan ɗin, tun da yana da girma sosai""" "Anty Saude ta ce ""Bawan Allah kuma cikin gidan da mutane?""" "Ya jinjina kai ya ce ""Eh akwai, sai dai ba ma zauna bane ba""" "Ya Atine ta shiga banɗaki, ta kunna famfo ta ga ruwa na zuwa, ga shi har da wearing ɗin nepa da sola na" gidan a ɗakin. """To yanzu ina angon, mu fa ko sau ɗaya ba mu gan shi ba""" "Sule ya ce ""Yana nan tafe, sai an jima za a rako shi, idan kuma za ku jira ne to shikenan""" "Yaya Atine ta waro ido ta ce ""A ina ɗin? Wannan unguwar duk kangwaye, ku wuce mu tafi ke Nana Allah" "ya baku zaman lafiya""" "Ummi ta riƙe hannun Nana ta ce ""Nana kin dai ji abin da Baba ya gaya miki, ki yi haƙuri da abin da" "ƙaddara ta zaɓa miki, ki yi zaman ki, ke kin san wannan gidan namu, ba gurin da idan ka bar shi zaka so koma masa bane. Ki zama mai tuna wace ce ke, kuma daga ina ki ke, sharrin da ake yi miki kawai a gidan" "ya ishe ki. Allah ya baku zaman lafiya ya baku zuri'a ɗayyiba. Na karɓi kuɗin sadakin ki a hannunsa, da" "kyar ya bayar da dubu hamsin, wai sauran da su aka yi hidimar biki. Ina son ɗan sayo miki kayan kwallita," "da underwears idan kin amince, idan ba ki amince ba na baki kuɗin ki""" "A hankali Nana ta ce ""Duk yadda ki ka yi na amince""" Ayshacool """To shikenan, ga wata dubu ashirin ki riƙe a hannunki, a irin kuɗin gudunmawar bikin ki ce, ko za ki yi" "amfani da su, a sha amarci lafiya"" Nana tana ji suka tafi suka bar ta ita kaɗai ƙwal." "Shiru garin, ko ƙwaƙƙwaran motsin wani abin ba ta ji, ta ɗaga kai tana kallon ɗakin." "A zuciyarta ta din ga addu'a, tana roƙon Allah ya shiga lamarinta. Yawan gane-gane da Nana take yi, ya" "sanya zuciyar Nana fara ƙeƙashewa. Ta bayan ɗakin take jin hayaniya, ana surutai da dake-dake ana hira, tamkar a irin gidan yawan nan." "Kiran sallar magariba ta ji, ta tashi tsam, ta shiga banɗakin ta ɗauro alwala, ta dawo ɗakin ta yi sallar" magariba. "Bayan ta idar duhun magariba ya ƙara yi, sai dai ɗakin akwai hasken fitilar solar." "A hankali kuma tsoro ya fara shigar Nana, ta daina jin hayaniyar da take jiyowa, ko ina ya yi tsit." "Daga bisani kuma ta din ga jin bugun zuciyarta yana ƙaruwa, sai kuma hasken fitilar ɗakin ya ɗauke baki" "ɗaya. Ta kifa kanta a kan ƙafarta, jikinta ya fara tsuma." "A hankali ta ɗago kanta, ta ganta a cikin sahara a zaune, sai sautin iska da yake kaɗa yashin saharar. A" "wannan karon ma yana tsaye, hannunsa riƙe da akalar raƙuminsa. Tashin sautin kaɗe-kaɗe ta din ga ji, ba tare da ta ga daga inda kiɗan yake tashi ba, ga wata zazzaƙar murya da take ta rangaɗa guɗa, muryar na amsa kuwwa a dajin. Ya taka a hankali ya je gabanta, ya miƙa mata hannu. Ta ɗago a hankali ta kalle shi, ta ɗaga hannunta za ta miƙa masa. Ta ji an yi sallama firgigit ta buɗe idonta tana kallon mai yin" sallamar. Ayshercool 08081012143 Ayshacool Page 28 "Da Sule suka yi ido huɗu, ya shigo wasu buzayen suka biyo bayansa, hannunsu riƙe da kaya." "Ya kalli Nana ya ce ""Afuwan mun tsorata ki ko? Ki yi haƙuri ba mu zo da wuri ba, mun tsaya mun yi salla" isha'i ne. "Ita dai Nana ba ta ce komai ba, aka din ga jere cartons na ruwa a ɗakin." Ita dai ta yi shiru ta sunkuyar da kanta ƙasa. "A hankali ta din ga jin tamkar numfashinta zai ɗauke, wani irin bugu zuciyarta take yi, sanyi yana ratsa ta." "Ta ɗago kanta domin shaƙar wadatacciyar iska, kar numfashinta ya ɗauke." "Fararen kaya ne a jikinsa, irin na buzaye, ya yi rawani da shuɗin yadi, ga wata ɗamara da ya yi da wani" "shuɗin yadin, gefen ƙugunsa kuma soke da takobi a cikin kubenta, wuyansa yana sanye da wani abu, na fata wanda ya ɗara laya girma, kuma bai kai girman jaka ba. Yatsunsa sanhe da zobunan azurfa, ga kuma ƙarfen tagulla a tsintsiyar hannunsa, ya dafe gefen cikinsa, shigar ta buzaye ce, kuma ta wata fuskar" kamar ta larabawa. "Yana gaba Habu yana bayansa, shi ma ya sha kwalliya cikin shigar buzayen. Wani irin daddaɗan ƙamshin" "turare," "ya karaɗe ilahirin ɗakin, Nana ba ta taɓa jin turare mai tsananin ƙamshi kamar wannan ba." "Sai kuma sauran buzayen aƙalla su biyar, duk sun sha kwalliya." "Dadduma suka shimfiɗa masa ya zauna. Gaba ɗaya suka zauna a gefe, suka yi shiru. Habu ya ce ""Mu yi" "addu'a"" aka fara Addu'a." "Nana ba ta san a tsakaninsu waye mijin nata ba, sai dai tana ƙoƙarin satar kallonsa, duk da kamar kullum" "kamar yadda ta saba ganinsa, fuskarsa a rufe take da rawani." "Ba ta san me aka karanta a addu'ar ba, saboda ta lula tunani, sai muryar Habu da ta ji ya kama sunanta." """Nana""" "Ta ce ""Na'am""" """Da farko dai ina mai ba ki haƙuri a kan abin da ya faru, kin san komai Allah ne yake ƙ'addarawa. Jikina ya" "yi matuƙar sanyi da abin da ya faru. Na gane dalilin wannan auren ne ya sanya muka baro gida. Ki yi haƙuri bawa ba ya tsallake ƙaddararsa. Ina yi muku fatan alkhairi da fatan Allah ya baku zaman lafiya. Na san abubuwan da mu ka ba ki na aure, be kai abin da ake kashe muku na aure ba, amma ki yi haƙuri a hankali za mu duba a yi miki, kin san masu ƙaramin ƙarfi ne mu. Dama ɗan kuɗin gadin tarawa muke yi, za mu tura gida wannan abu ya bijiro, kuma kuɗin hannunmu duk ya ƙare. Dan Allah ki yi haƙuri da abin" "da Allah ya ƙaddara miki.""" "Nana dai ba ta ce komai ba, ya sake nuna mata kayan da suka zo da su ya ce ""Ga sayayya nan, abin" "wanka ne da kayan wanke baki, da ɗan abin da ba a rasa ba na kayan tsafta. Yanzu mu na sauri mu koma," "ba wanda zai kula da ƙofa dole mu koma da wuri, amma zamu dawo da yardar Allah"" su ka ƙara yi musu" fatan alkhairi. "Shi kuwa tun da ya zauna, ƙwaƙwƙwaran motsi ma bai yi ba, balle ya tofa wani abu ba." "Sai da Nana ta ga sun miƙe baki ɗaya shi yana zaune, sannan ta fara zazzaro ido." "Gaba ɗaya sai suka juya yare, su na yi masa magana, har suka gama maganar, shi dai bai ce uffan ba." "Ɗaya bayan ɗaya suka fice, hakan ya ƙara tabattar mata da shi ne mijin nata. A take ta tuna Sule ya taɓa" gaya mata ba shi da cikakkiyar lafiyar ƙwaƙwalwa. 'kenan mahaukaci Baba ya aura mini?' ta tambayi kanta. "Ƙoƙarin tuna wasu abubuwan take yi a kansa, amma abu ya gagara, ta ji gaba ɗaya kanta ya toshe." "Ta yinƙura ta tashi, ta tafi banɗaki domin ta yi alwala ta yi sallar isha'i." "Sai dai bayan ta yi alwala da ƙyar ta baro banɗakin, saboda duk taku sai ta ji tamkar zuciyarta za ta fashe." "Ƙafafuwan ta su ka gaza ɗaukar ta, a dole ta zauna ta kalli gabas, ta tayar da salla. A zaunen ma jiri take" "yi, da haka ta yi salla." "Shi dai bai kula ta ba, bai kuma tashi daga gurin da yake a zaune ba, kamar gunkin budda." "Ta idar da sallar, ta koma jikin bango ta matse jikinta, ta rasa abin da yake yi mata daɗi, ji take kamar ta" "kurma ihu, ga sanyin nan da take ji ƙaruwa yake yi, tsigar jikinta sai tashi take yi." """Allah ka dube ni, dan Allah ƙaisar kar mu yi haka da kai, ni hauka shi hauka ta ya ya za a yi wannan" "zaman"" ta furta hakan a hankali." Ayshacool "Sun shafe dogon lokaci, kamar babu halitta mai motsi da ta wanzu a gurin, Nana tana ta tufka da" "warwara a zuciyarta, kawai ta ga ya tashi tsaye. Zuciyarta ta ƙara tsinkewa da tsoro da razani, tare da hakaito mata miyagun abubuwa, yanzu idan ya yankata a gurin nan ya gudu fa? Mussaman wannan takobin da take gani." "A hankali yake tafiya, ya tafi gefen wardrobe ɗin ɗakin, da aka kafe abin rataye kaya. Ya cire takobin ya" "rataye ta. Ba tare da ya waiwayo ba, ya fara kwance rawaninsa. Kasancewar ya juya mata baya, ya sanya" "ta zuba masa ido ko ƙiftawa ba ta yi. Ya kwance rawanin gaba ɗaya, ya ninke Nana ta zuba wa sarautar Allah ido, ganin kansa ɗauke da gashi baƙi wuluk, ya tufke shi tamkar an yi wa kan bahauhishiya saloon." "Ya saka hannu ya zare rigar jikinsa, da sauri ta sunkuyar da kanta, tana kallon gefe, kamar mara gaskiya." "A hankali ta ƙara ɗagowa, ta ganshi da dogon wando, da shirt, ya ninke rigar da rawaninsa, ya buɗe" wardrobe ɗin ya saka kayan a ciki. "Ba ta san ya aka yi ba, kawai sai gani ta yi sun haɗa ido. A take ta tuno ganin da ta yi masa, har ta suma a" ɗakin su. "Da wata irin azama ta tashi, duk da bugun zuciyar da take ji da kuma jiri, ta ja da baya ta tsaya cikin tsoro" da razani. "Ya ci gaba da kallonta, ba tare da ko ƙifta ido ba." "Kawai Nana ta fashe da kuka, ba tare da sanin dalilin da ya sanya ta kukan ba." "Gani ta yi ɗakin yana juya mata, ya kawar da kansa daga kallonta, ya fice daga ɗakin. Fitarsa ke da wuya" ta silale a gurin ta faɗi. "A hankali ta fara juyi tana tari, a cikin kunnuwanta take jin bugun zuciyarta, ta ja jikinta ta tashi da ƙyar." "Ta karkaɗe hannunta saboda ƙura, ƙaisar ta gano sanye baƙar riga tana jan ƙasa, yana shirya litattafan sa," yana goge su. "Da ƙyar tarin ya ɗan lafa mata ta ce ""Ƙaisar""" """Ya aka yi?"" Ya amsa ba tare da ya kalle ta ba." """Tsoro nake ji, ji nake yi kamar zan mutu. Ba ka ji yadda zuciyata take bugawa ba""" """Ina jin yadda take bugawa mana, ai mutuwar ma za ki yi idan ba ki yi wasa ba, tun da ke dai kin ƙware a" "taurin kai. Wannan mutumin ƙila shi zai yi ajalin ki. Ki kan ji bugun zuciya da sanyi ne, idan ina guri to me" "yasa ba na gurin daga ke sai shi ki ke jin bugun zuciyar?"" Ya jefo mata tambayar." "Nana ta ɗan yi shiru, sai kuma ta ware ido, amma ta kasa magana. Ya ce ""Eh, ai na gaya miki ba ki da" "tabbacin abin da ki ka aura, mutum ne ko kuma jinsinmu"" yana gama maganar ya yi gaba. A rikice Nana ta bi shi tana faɗin ""Dan Allah ka tsaya ka saurare ni, yanzu ya zan yi dan Allah?""" "Ya waiwayo ya kalle ta ya ce ""Au tambayata ma ki ke yi ya ya za ki yi? Shirka fa ki ke ƙoƙarin ko kin" "manta?""" "Nana cikin kuka ta ce ""Ba haka nake nufi ba, amma wallahi tsoro nake ji idan na ci gaba da rayuwa da shi," "zan iya mutuwa""" "Ƙaisar ya ce ""Ai da da na gaya miki ba ki yadda ba"" ya juya zai tafi, ta riƙo rigarsa""" """Zan watsa ki ta waje, idan ki ka kuma bi na""" "Za ta yi magana ya ce ""Sai kuma ki yi"" kawai ya ɓacewa ganinta." Kawai ta koma gefe ta tsaya tare da fashewa da kuka. "Yana zaune a gefen ɗakin nasu, ya na shan hantsi, sai ga Sule ya zo da kwandon kayan abinci." """Ango har ka tashi? Ya mariée ɗin ?""" "Ya nuna masa ɗakin, alamar tana ciki. Gaba gaɗi Sule ya nufi ɗakin da kwandon Abincin cikin hanzari" Buzu ya miƙe ya tsaya a ƙofar ɗakin. "Sule ya ce ""Au yi haƙuri, bari na zauna daga nan"" ya nemi guri ya zauna a gefensa." "Nana kuma ta buɗe idonta, ta ganta kwance a kan katifar, jikinta babu naɗin lafayar da aka kawo ta da" "shi, sai riga da skirt ɗin ta na ciki, kanta ko ɗan kwali babu. A razane ta dubi jikinta tana tambayar kanta, ko ya yi mata wani abin ne?. Ta kalli gefen katifar ta ga lafayar a ninke a ajiye. Da azama ta yinƙura ta faɗa banɗaki, amma ba ta ga alamar an yi mata wani abu ba." "Ta yi tsarki, ta yi alwala tana ta istigfari ta yi sallar asuba, cike da jin kunyar Ubangiji, yadda lokaci ya ja" gari ya yi haske ba ta yi salla ba. "Bayan ta idar tana jiyo Sule yana ta zuba da yaren su, shi dai ba ta ji maganar sa ba. Ta yi mamakin abin" da ya sanya Sule kasa yin zuciya ya ci gaba da surutu ba tare da ana kula shi ba. Ayshacool "Babu tsammani ya shigo ɗakin, ba tare da ko sallama ba. Aikuwa ta zabura ta ja da baya tana kallonsa." "Kai tsaye ya nufo ta, ya ajiye mata kwandon Abincin a gabanta. Ya nemi guri ya zauna ya zuba mata ido," da kwandon kayan abincin a tsakiyar su. "Nana ta sunkuyar da kanta, sanyi na ratsa ta." """Zan ci abinci"" ta ji muryarsa kamar daga sama, ɗaga kai ta yi ta kalle shi, ji ta yi kamar ta ce masa to ya" "ci mana, sai kuma ta tuna ashe fa wai yanzu mijinta ne. Mamaki ne ma ya kamata, dan har a lokacin tana mamakin idan ba kurma ba ne ba." "Ta janyo kwandon ta sassuke abincin, ta fara ƙoƙarin zuba masa, kawai ta ga ya tashi ya fita. Sai ga shi ya" "dawo da abin da suke hura wutar dafa shayi, har da butar shayin ma, da alama abin da suke yi a wajen tun ɗazu kenan, shan shayin." "Ya buɗe cikin kayansa, ya ɗaukko turaren wuta, ya zuba a kan sauran garwashin. Take ɗakin ya karaɗe" "da ƙamshi mai daɗin gaske. Ya samu guri ya zauna, ya karɓi abincin, ya koma gefe ya sauke takunkumin rawaninsa ya hau ci." "Nana kuwa kasa cin abincin ta yi, ta yi tsuru sai satar kallonsa da take yi, ya gama ci ya ɗauki kwanukan" "da ya ci, ya fita waje ya wanke ya dawo ya ajiye mata. Ya tsiyayi sauran shayinsa na butar, ya shanye abin sa." "Ya kewaye ta, ya ɗauki pillow ya koma can gefe ya ajiye ya kwanta. An shafe tsawon lokaci, na zaune ba" "tare da sanin abin yi ba. Jin yunwa ta uzzura mata ya sanya ta ɗan zuba abincin ta fara ci. Tun tana cakala har ta saki jiki, ta ci gaba da zurawa kawai suka yi ido huɗu, tana ta loma. Sai kuma ta yi sak, ta ci gaba da" "ci ta kasa kamar wadda ta aikata rashin gaskiya, kuma ya ƙi daina kallonta. Ƙarshe sai haƙura ta yi da cin" "abincin, kallon da yake yi mata duk ya sanya ta damu." * "Gidan su Nana tun a ranar kowa ya watse, dan baba faɗa ya yi ta yi, yana cewa duk wanda ya kwana sai" "dai ya nemi abin da zai ci, shi ba shi da abin da zai sake bayarwa a bawa mutane." "Suwaiba ta ƙarewa ɗakin su kallo ta ce ""Ohhh abin tsiya, ko tsinke ba ta bari ba, duk ta kwashe komai" "balle mu gada.""" "Mama ta ce ""Au ke har wata tsiyar ki ke saka ran gada a gurinta? Me za ki gada banda gayyar masifa, ai" "gara da tarkata komai ta tafi, ma sake mu miƙe ƙafa mu huta mu ma""" "Jamila da ta shirya tsaf za ta fita ta ce ""Aikuwa dai""" """To kafin hankali ya dawo kan ku, Ubangiji Allah ya kawo muku mazaje na gari 'yan uban uban su, wanda" "kowa sai ya koka a tashi kan munafukan unguwa da na family""" Suwaiba har da tsalle ta ce Amin Mamanmu maganin kukanmu. "Jamila ta yi murmushi ta ce ""Ni dai sai anjiman ku""" "Mama ta ce ""To a sauka lafiya""" * "A tsanake take kallon yadda mai gidan nata, yake ɗan yamutsa fuska bayan ya kammala cin abinci." "A hankali ta ce ""Daddy""" """Na'am baby""" """Ya dai? Jikin ne ko garin? Na ganka so silent""" "Ya ɗan yi miƙa ya ce ""Pressure ce ta ɗan yi mini yawa wallahi, ina shirin tafka asara ne, kwana biyun da" "ban je kasuwa ba, har an yi mini ɓarna wallahi. Ga kaya sun iso Nigeria na gama clearance amma" "coustom sun ƙi sakar mini kayan""" """Subhnallah, in sha Allah ba za ka yi asarar ko naira biyar ba. Allah zai warware komai, bari mu duƙufa da" "addu'a in sha Allah ba wani abu""" "Ya yi murmushi ya ce ""Sweetheart, Allah ya amsa mana, ɗan duba mini paracetamol idan ki na da shi," "kaina yana ciwo, ina so na je asibiti ma a duba ni ko bp na ne ya hau""" "Cikin damuwa ta ce ""In sha Allah ba shi ba ne ba ya hau, dan Allah ka kwantar da hankalinka, mu na" "buƙar lafiyarka just recently fa kai ne ka ke yi mini nasiha a kan yadda da ƙaddara""" "Ya girgiza kai ya ce ""A'a ba ma damuwar na saka a raina ba, kawai jikina ne babu daɗi""" "Ta tashi ta ce ""Bari na ɗaukko maka"" ta nufi bedroom ɗin ta." * "Alhaji Zailani ne zaune a gaban malam Gambo, sai gumi yake yi kamar ya yi wa sarki ƙarya." """Na rasa gane abin da ya faru gaba ɗaya, ni dai na san mun yi da kai za mu yi magana da wanda ta aura" "ɗin, na ba shi kuɗi ya sake ta, sai dai ban san meyafaru ba na kira shi ɗin a zahiri, ban kira shi ba na kasa" "tunawa, ni dai kawai na ganshi a mafarki ban ma san meyafaru ba kawai na farka na ji tamkar an shaƙe ni, da ƙyar nake numfashi""" Ayshacool "Ta tashi ta kwance kayan da Ummi, ta yi mata sayayyar su." "Ɗan kayan shafe-shafe ne, da turaruka sai under wears, duk da masu arha ne Nana ta ji daɗi sosai da" sosai. "Duk da tana jin haushinta, amma ta san idan ba Ummin ba, babu wanda zai tsaya tsayin daka ya yi mata" "wannan abin. Ta haɗa da na gurin Hajiya Amina, duk ta jere. Ta janyo drower mudubin, ta ga burshes ne da comb a ciki. Ta mayar ta rufe." "Ta janyo jakar kayanta, ta buɗe wardrobe ɗin, ta ga ɓangare ɗaya shaƙe da kayansa, sai da abin ya bawa" Nana mamaki. "Ɓangare ɗaya ta jere kayanta, ta tsaya tana kallon kayan, duk da galibi wanda hajiya Amina ta ba ta ne," "ba ta san lokacin da murmushi ya suɓuce mata ba. Ta daɗe tana burin ganin kayanta a cikin wardrobe. Dan a gida, a wata tsohuwar adakar kakar su take zuba su, ƙarewa wataran talauci ya ishi Baba ya ce ta zazzage kayanta, ta ba shi. Haka ta ba shi ya sayarwa 'yan gwangwan ya sayo mata viva ya bata wai ta zuba kayan a ciki, tun da tsummokaran nata ba su da yawa. Daga baya ta koma zubawa a kwalaye, daga ƙarshe dai Jamila ce ta samo mata ghana must go ta bata, take saka kayan ta a ciki. Amma yau ga kayanta a wardrobe, kuma kaya kusan set goma sha uku, sababbi da tsofaffi, ga atamfofinta uku da ba a" kai ga ɗinkawa ba. "Ta ninke bargonta, da bedsheets da Shukura ta bayar a bata, ta saka su a saman wardrobe ɗin." "Drower ƙasan wardrobe ɗin kuma, ta saka takalmanta guda biyu, da jakar gidan sarkin baka, da pad ɗin" "ta. Ta gyara kan katifar ta ɗame ta da bedsheets. Ta tashi tsaye tana kallon katifar, ita ma tsawon rayuwarta a kan wani tsohon bargon Baba take kwana, shi ma dai na kakar ta ta ne, bargon nan tamkar" "ya koma audigarsa saboda tsufa, amma yau albarkacin aure, ga ta da ƙatuwar katifa." "Wani murmushin ne ya sake suɓuce mata, ta juyo kawai ta yi karo da shi a tsaye a bayanta." "Ba ta san lokacin da ta ƙwala ihu ba, dan sam ba ta ji alamun mutum a bayanta ba." "Kuma kasancewar ta ƙure da jikin katifar, razanar da ta yi, sai ta faɗa kan katifar." "Taku ɗaya ya ƙara, ya tsaya a kanta yana kallonta." Ayshercool 08081012143 Ayshacool 29 "Ƙara rikicewa ta yi, ta kasa tantance abin da take gani daga cikin idanunsa." "Ya sauke rawaninsa, ya saka hannu a aljihunsa, ya ɗaukko wayarta ya ajiye mata a gefen ta. Tashi ta yi" "zaune tana kallon wayar, gaba ɗaya ta manta ma tana da wata waya, a ina ya samu wayata? Ta tambayi kanta." "Ta bi wayar da kallo, ta kasa taɓa ta. Ya sake zura hannunsa a cikin aljihunsa ya ciro wata roba, ya ajiye" "mata, ya juya ya fita. Sai da ya fita ta ɗan samu ta nutsu, ta kai hannunta ta ɗauki wayar ta duba ta ga a" "kashe take, sai ƙamshi take yi. Ta kalli robar da ya ajiye mata, dabino ne fal a cikin robar lubiya." "Gefe kuma ga kwanukan abinci, fulasan kawai ta kalla ta san daga gidan Hajiya Amina suke." "Tana cikin tunani, ta ji sallamar mace. Ta amsa tare da kallon ƙofar ɗakin. Wata mata ce ta shigo, Nana ta" "yi mata maraba, ta shimfiɗa mata sallaya ta zauna." "Bayan sun gaisa Nana ta ce ""Ban gane ki ba""" """Eh ai ba ki sanni ba, a nan baya muke, aka ce ai an kawo amarya na ce bari na zo mu gaisa""" "Nana ta ce ""Allah sarki, dama da mutane a nan haka? Shiru nake jin unguwar duk da jiya na zo""" "Matar ta ce ""Eh, ai a nan baya nake, sunana na Haulat, amma kin je kun gaisa da mutanen gidan""" "Nana ta girgiza kai ta ce ""Ai ban san da mutane a gidan ba""" "Haula ta ce ""Ai ba su fiye zama bane ba, kullum cikin yawo suke, amma yau ko gobe za su dawo.""" "Zuwan Haulat sai ya ɗebe wa Nana kewa, su ka yi ta hira." "Sun daɗe su na hirar, sannan ta yi wa Nana sallama, ta rako ta har bakin ƙofar ɗakin ta ce ""Idan na fara" "fita, nima zan kawo miki ziyara""" """To shikenan, ai a nan baya muke""" "Nana ta ce ""Kuma da gidaje a gurin? Na ga duk kangwaye ne?""" "Haula ta ce ""Gamu kuwa, akwai gidaje a gurin""" """Allah sarki, to na gode sosai ki gaida gida""" "Yana zaune a kan benci, yana shan shayi a cikin ɗan ƙaramin kofin nan nasu, Nana ta jima tana mamakin" "kofin da suke shan shayin nan, tamkar wasan yara. A ganinta sai mutum ya sha goma bai ƙoshi ba." "Tana hango shi su na fitowa da Haulat, ya rufe fuskarsa." "Ta zo za ta fita ta tsaya tana gaishe shi, amma ya yi shiru, kuma bai ɗaga kai ya kalle ta ba, ta fita." "Sai da Nana ta ji babu daɗi, haryanzu ita ba ta ga wata alama ta hauka a tare da shi ba, kuma jiya ya yi" "magana ba kurma bane ba, tsagwaron wulaƙanci ne ya sanya sai a yi masa magana amma ya yi shiru." "Da daddare ma, zuwa ya yi ya saka ta a gaba, yana kallonta yana kallon kwanukan abincin da ba ta san" "waye ya kawo ba, ta san dai na gidan Hajiya Amina ne." "Haka ta zuba masa ya ja gefe ya sauke rawaninsa ya ci abinsa, sai dai da ya gama ci, yake ɗaukar kwanon" "da ya ci abinci ya fita ya wanko ya zo ya ajiye. Abin da ta lura da shi, shine mutum ne mai tsafta sosai." "Ita dai tana gefe sai dai ta saci kallonsa, sai dai ƙasan zuciyarta tana mamakin yadda yau ba ta jin bugun" "zuciyar, sai dai sanyi da take ji." "Bayan ya ajiye kwanukan, ya tashi ya kwance rawanin sa, duk da wayarta take ɗan dannawa, sai da ta" "saci kallon gashin kansa, kawai ta ji tana son ya ware shi, ta ga adadin tsawonsa." "Ya rage kayan jikinsa, ya ɗauki radion sa, da kayan shayinsa ya fice daga ɗakin." "Yana fita ta ja ajiyar zuciya, ta tashi ta shiga banɗaki, ta yi wanka ta wanke bakinta, tayi alwala, ta fito ta" shirya ta kwanta. "A iya saninta, wayarta take ɗan duddubawa tana tunanin yadda aka yi ya samu wayarta." """Amarya ba kya laifi, ko kin kashe mai gida?""" """Meye haka wai?""" """A ina?""" """Ni fa yanzu matar aure ce, ya zaka din ga kawo ni nan, duk lokacin da ka ga dama?""" "Ya ajiye littafin hannunsa ya ce ""Ina ruwana da auren ki? Auren jeka na yi ka? Auren da haryanzu ba ki da" "tabbas a kansa? Haryanzu ba fa ki san me ki ka aura ba, kuma kamar an ce ma mahaukaci ne ko?""" "A ƙule Nana ta ce ""Ko ma dai mene ne ina ruwan ka? Zan gano da kaina, koma wane ne, idan ma mutum" "ɗin ne ko akasin haka""" "Ƙaisar ya ce ""Jiya fa ki ka zo nan ki na yi mini kuka, ki dai san iya abin da yakamata ki yi, da inda yakamata" "ki tsaya kar allura ta tono garma""" """Eh, haushi ka ke ji na yi aure, ba tare da tsammaninka ba, balle ka sake hanawa""" Ayshacool "Kawai ƙaisar ya bushe da wata irin dariya, da sai da ta tsorata ya ce ""Ke haryanzu ba ki san ina ki ka dosa" "ba, ni ba jinnil ashiƙ bane da zan hana ki aure, na baya ma mazan naki ne ba su yi mini ba, duk da" "wannan ma da na farga da wuri sai na ruguza shi, sai dai idan na matsa za ki iya rasa rayuwar ki baki ɗaya, shi yasa na ƙyale""" "Nana ta ce ""Saboda me?""" """Kawai"" ya bata amsa." """Amma wai da gaske aljani yana auren mutum?""" """Eh""" """To ku ina naku matan ku ke auren na mutum?""" "Ya ce ""To ai ni ba aljanin soyayya ba ne ba da za ki tambaye ni.""" "Nana ta ce ""Amma ka hana ni aure? Me yasa ka saka Saleh ciwon ciki?""" """Ke ko duk matan bil'adama sun ƙare zan auri masifaffiya ne mai azabar taurin kai kamar ke ne?""" """Eh abin nan ne, da ake cewa makaho ga ido, ya ce wari yake, na fi ƙarfin ka ne kawai""" "Ya ce ""Ko?""" """Eh mana, dan Allah ka gaya mini ya ake yi ku ke auren bil adama""" """Ni ma ban sani ba, sai dai zan baki wani littafi ki karanta, soyayyar Aljani Ridwan, da bil adama"" Nana ta" "zabura ta ce ""Dan Allah, ya sarkin baka, a wane hali yake yanzu? Kuma ni ba littafin soyayya nake so ba," "wannan littafin na Jaddul jinn nake so ka bani na ƙarasa karantawa""" """Ba zan bayar ba, kuma ba wannan ne ya sanya na kira ki ba, duba jikin mudubi, ki zo ki gaya mini abin" "da ki ka gani""" "Nana ta ce ""Wallahi ba zan kalla ba, masifa da bala'i kawai ka ke nuna mini a cikin mudubin nan, Allah ya" sa ya tarwatse... """Wallahi sai kin kalla, wataƙila zuciyar ki ta saduda, ki yi abin da ya dace""" "Kawai ta ganta a gaban mudubin, Jamila ta gani a kwance tsirara, Hajiya Sa'a na ta tsira mata allurar nan." "Tsigar jikin Nana ta tashi, ta rintse idanunta ta ce ""Dan Allah me take yi mata? Jamila ce fa""" """Ƙwarai ita ce, Matar ta umarceta ta kawo mata jininki, ta ce ba za ta iya ba, shi ne ta bi ta bayan gida," "yanzu haka ta gama mallake ta, duk abin da ta ce ta yi shi za ta din ga yi, ba za ta taɓa kaucewa maganar ta ba""" """Innalillahi wa innalillahi raji'un, yanzu ya zan yi, kar ta cutar da Jamila, shiyasa ni tun farko ba na son" "yawon maƙwabtan nan da take yi. Wannan matar ba ita ta bayar da Muhsin ba?""" "Ƙaisar ya ce ""ƙwarai ita ce, kuma ba wannan ba, bayan cin moriyar ganga, yada ƙwauron ta za ta yi. Ba" "wannan ba bayan ɗalibin ki da ki ka rasa, babansa ma an sako shi gaba, wataƙila nan kusa ko nesa kaɗan ya bi ɗan nasa""." """A'a ba gaskiya ba ne ba Ƙaisar, hakan ba zai taɓa yiwuwa ba""" """Dama ai ba gaya miki nake yi domin ki yadda ba""" "Ta ɗan yi shiru cikin jimami da tashin hankali, ta ce ""Yanzu meye abin yi, ba na son Jamila ta faɗa ga" "halaka"" ta yi magana cikin kuka." """Kin fi ni sanin abin yi ai Nana Asma'u""" """A'a ban da wannan, wannan ba mafita ba ce ba, na gaya maka ba zan yi wannan ba""" "Ya ce ""To shikenan, sai ki zura ido mutane na cutuwa alhalin ki na da yadda za ki yi, ki taimaka musu""" """A'a ƙasair"" kawai ta ga tamkar ya wurgota waje." "Ihu ta saka ganin tana faɗowa daga sama, za ta faɗa cikin ruwa. A razane ta tashi tana faɗin ""Ya Allah"" ta" dafe saitin zuciyarta tana haki. "Ita kaɗai ce a cikin ɗakin, ta janyo wayarta ta duba lokaci, ta ga uku da rabi na dare. Ta yi shiru domin" "tuna abin da ya razanata daga baccin, amma ta kasa, kawai faɗowarta daga dogon tsaunin da libararyn" Ƙaisar zuwa ƙasan ruwa ta iya tunawa. "Ta kalli ɗakin, fitila a kunne, amma ba ya ciki." "Ta tashi a hankali, ta nufi ƙofar ɗakin, ta leƙa harabar gidan." "Yana kwance a kan benci, yana bacci ya tada kansa da hannunsa. Gabansa ɗan murhun dafa shayinsa ya" "mutu, ga butar shayin da kofinsa." "Wasi-wasi ta shiga yi, a kan ko tashin sa za ta yi. Wutar gurin ce ta ɗauke gaba ɗaya, gurin ya gauraye da" "duhu, aka yi wata irin walƙiya mai hasken gaske, kawai ta ga wannan tsohon a tsaye a kansa." "Tamkar an dasa ta, ta kasa motsi ta kasa gaba ta kasa baya, aka sake walƙiyar nan, ta sake ganin tsohon" "nan a tsaye a kansa, sai dai wannan karon ya feso wani irin tartsatsin wuta da ya tilasta mata yin baya cikin matsanancin tsoro." Ayshacool "A hankali ta buɗe idonta, kawai ta ganshi a tsaye yana kallonta, kamar taɓaɓiyya haka ta zura da gudu," "ta koma kan katifa ta kifa kanta tana haki, saboda tsoro da razani. Maganganun Ƙaisar suna nema su fara zama gaskiya a kan mutumin nan. Tabbas ta fara tantamar kasancewar sa mutum. Duk da ta san ba ta da cikakkiyar lafiya ƙaisar ya saba tsorata ta, amma ya za a yi a ce mutumin da ta hango yana bacci, cikin" "abin da bai fi ƙifta ido sau biyu ba, ta gan shi a gabanta." "A ɓangaren sa shi ma mamaki yake yi, me take yi a tsaye a bayan labule a wannan tsohon dare haka?." * "Hajiya Sa'a ce take kallon Jamila, tana wani irin mugun murmushi ta ce ""To jamsy me ki ka ce yanzu?""" "Jamila ta ce ""Ta yaya zan samo miki jinin nata?""" """Yauwwa Jamila, ba wani abu ne mai wahala ba, magani zan baki a abinci, ki kai mata ta ci, sai kuma abin" "da za ki ajiye mata a ɗaki""" "Jamila ta ce ""To shikenan, babu damuwa an gama""" """Kin tabattar za ki iya?""" """Eh mana, me zai hana?""" "Hajiya Sa'a da Maman Khairat suka kalli juna, suka sheƙe da dariya, Hajiya Sa'a ta ce ""Yauwwa jamcy, zan" "gaya miki duk yadda za a yi "" Jamila ta gama wuninta a gidan, sannan ta tafi gida. Sai dai gaba ɗaya ta din ga jin ta wani iri, tamkar akwai wani abu da ba dai-dai ba a tattare da ita." **** "Tamkar bakin mama ya taɓo ƙeyarta, haka take washe baki, a gaban malaminta. Ta ce ""Anya ka taɓa yi" "mini aiki mai zafin wannan? Komai ya tafi yadda ake so, wallahi yadda na tsara masa komai haka ya bi," "dama abin yana cin sa a rai ƙiri-ƙiri mai kuɗi ya zo ta ce ba ta so""" "Ya yi dariya ya ce ""Mu ɗin na wasa ne? Gangaran ne ni fa, ai duk taurin buƙata muka ɗauki allo muka hau" "kan buzu mun gama da ita""" "Mama ta ce ""Ai kuwa na ga zahiri, malam saura na 'yan matana, a bamu na farin jini. Wallahi duk" "samarin nasu ba na arziki sai tarkace babu wata mamora a tattare da samarin nasu, ni kuma masu maiƙo" "nake so, inda zamu jingina mu huta, ka san rayuwar ce sai a hankali, ba zan so mu dauwwama a talauci ba, su yi gadon masifa ba""" "Yayi murmushi ya ce""Tabbas wahala abar gudu ce, za a san abin yi, ki bayar da kuɗi, za a sai binta sudan," "da ma'u wardi, sai farin goro zan yi musu wani aiki""" """To kamar nawa ka ke ganin zai isa?""" "Ya ɗan yi shiru ya ce ""Ba da dubu goma sha biyar, akwai turarukan da zan haɗa da su ma, da wasu" "saiwoyi."" Ganin buƙatar ta ta biya a baya, ya sanya babu fargabar komai ta amince ta ɗebo kuɗi ta ajiye masa, ta yi masa sallama ta tafi." **** "Bayan sallar asuba kallonsa Nana take yi, tana tuna abin da ya faru jiya da daddare." "Fuskarsa daina zahiri ba ta yi kama da ta miyagu ba, ta kalle shi daga sama har ƙasa, babu wata alama da" "take nuna ba mutum bane, a suffar sa ta zahiri." "Amma dole tana buƙatar tabattar da waye shi, ta kalli inda yake zaune yana ta fama da radio. Akwai" "aikin jin radio, sai dai magana ce aiki a gurinsa." """Ina kwana?"" Ya ji muryar Nana babu tsammani. Ya ɗago ya kalle ta domin ya tabbatar idan da shi take." "Ta sake cewa ""Ina kwana?"" Ɗaga mata hannu kawai ya yi, tare da jinjina kai." "Takaici ya kama Nana, maganar ce dai ba zai yi ba." "Kawai ta ga ya tashi ya ɗauki ɗan kurfotin dafa shayinsa, ya zuba ruwa a cikin butarsa. Ya ɗauki wata" "baƙar leda ya tashi zai bar mata ɗakin. Cikin sauri ta tashi ta ce ""Kawo na dafa maka"" ya kalle ta ya girgiza mata kai." "Ta miƙa hannu za ta karɓi butar, ya janye ya ce ""A'a""" "Ya juya zai fita, kawai ya ji ta biyo bayansa. Ya tsaya ya waiwayo, tana ƙoƙarin tsare shi da ido, amma ta" kasa. Ya kuma yin gaba ta sake bin sa. "Sai ya fasa fitar, ya dawo ɗakin, ita ma ta biyo shi ta dawo." "Ya samu guri ya zauna, yana kallon butar shayinsa yana kallon Nana, da ta maze." Bayan wani ɗan lokaci ya tashi ya fara shirin shiga wanka. Nana ta maze ta ɗauki wayarta tana dannawa. "Sai da ya shiga banɗakin, ta bi bayansa da kallo." "Hajiya Amina ta kira a waya, cikin ikon Allah kuwa bugu biyu ta ɗaga tana ""Amarya kin sha ƙamshi""" "Cikin jin nauyinta Nana ta ce ""Hajiya ina kwana?""" """Lafiya ƙalau Nana, ya ki ke fatan kina lafiya? Ina ta kiran wayar ki a kashe""" Ayshacool "A nan Habu ma ya karya, ya zauna su ka yi hira da Nana, shi kuwa da ya gama cin abincin sa, ya koma" gefe ya yi musu shiru. "Shi ma bai wani jima sosai ba, ya tafi. Gaba ɗaya zaman shiru ya ishi Nana, shi ba kula ta yake yi ba, sai" "dai ta wuni a ɗaki shiru, shi kuma yana waje, yana jin radio da aikin dafa shayi kamar ibada, ko hutawa ba ya yi, har mamaki take yi idan yana gane abin da ake yi a radion." "Bayan azahar yana kwance, a ɗakin, radion ta cika wa Nana kunne, ta dube shi ta ce ""Dan Allah zan shiga" "cikin gidan nan, na yi musu sallama, tun da na ga alamar akwai mutane a cikin gidan"" ya gyaɗa mata kai kawai." "Ta ɗumama ruwa a kan gas, ta shiga ta yi wanka ta fito, sanye da dogon hijjabi. Ta ɗauki kayan da za ta" "saka, ta koma banɗaki ta canza ta fito. Doguwar riga ta sako, hannunta riƙe mayafin rigar. Ta cire hular" "kanta, ta tsaya a gaban mudubi tana shafa mai. Abin ka da mace, kuma amarya, sai ta tsaya a gaban" mudubin tana gyara fuskarta. "Ta tsiyayo humra ta shashshafa a jikinta. Ta janyo drower mudubin, inda yake ajiya kayansa ta buɗe a" "hankali, ta waiwaya ta kalle shi, ta ga idonsa a rufe, ta ɗauki turaren sa, ta tsiyaya a hannunta, ta shafa a wuyanta." "Yana daga kwance yana kallonta, ta ƙasan idonsa. Sai da ta gama tsaf, za ta fita kawai ya yi gyaran murya." Ta tsaya ta waiwayo tana kallonsa. "Ya yinƙura ya tashi, ya nufe ta, ta tsaya ƙyam tana kallonsa. Gani ta yi tamkar zai shige cikin ta, babu shiri" "ta fara ja da baya, sai da ta dangana da jikin bango." Ayshercool 08081012143 Ayshacool Page 30 "Zazzaro ido Nana take yi, numfashin ta na neman sarƙewa, saboda tsoro da fargaba." "Ya saka hannunsa ya kamo hannunta cikin nasa, wani irin sanyi ya ratso ta, tun daga tafukan hannayenta" har zuwa ƙafafuwan ta. Ya kama gefen rigarsa ya goge in da ta shashshafa turare a hannunta. Ya saka "hannunsa a gefen wuyanta, nan ma ya goge wanda ta shafa a nan." "Na saman rigarta yake kallo, sannan ya kalli idonta. Ta yi tsuru-tsuru a ranta ta ce ""Daga ɗan shafa" "turaren sa, shi ne yake mini wannan tijarar haka""" "Idonta ta saka kwalli, bakinta kuma ta saka man leɓe mai kala, sai girarta da ta gyara. Ba ta gama zancen" "zucin ba, ya saka hannunsa ya fara goge man da ta saka a leɓenta." "Riƙe hannunsa ta yi za ta yi magana, amma ya yi mata wani irin kallo da ta rasa na mene ne, babu shiri ta" "yi tsit. Ya goge leɓenta tsaf. Ya kalli idanunta da suka sha kwalli, ya mayar da hannun sa kan girarta, ya hargitse gashin girarta." "Ya zare mayafin rigar da ta ɗora a kanta, ya ciro hijjabin da ta shiga wanka da shi, ya hau saka mata." "Kamar ta rusa ihu ta ce ""wanka fa na yi da shi, ba ka ga duk danshin ruwa a jiki ba?"" Bai amsa mata ba," "ya jefa mayafin rigar a kan katifa, ya koma gurin da yake zaune ya zauna. Wani irin takaici ya tokare" "Nana, kamar ta kurma ihu, saura ƙiris ta ce ta fasa fitar, amma ta tuna zaman shiru za ta zauna ta yi a ɗakin, ko ma shi ya fice ya bar ta. Ta ja takalmanta ta fice daga ɗakin tana haɗe fuska." "Fasalin gidan ya yi mata kyau sosai da sosai, sai da ta zagaya ta bayan wata baranda, sannan ta gano" ƙofar shiga. Tun daga barandar take ɗan jiyo hayaniya sama-sama. "Ta buɗe ta shiga da sallama. Samari ne su kusan biyar a falon, su na kallon ball su na ta hayaniya." "Sallamar ta ce ya sanya su yin shiru, suka amsa mata." """Sannunku, dan Allah matar gidan nake nema""" "Ɗaya daga cikin su mai riƙe da remote a hannunsa ya ce ""Tana sama"" ya yi maganar yana nuna mata" upstairs. "A falon saman benen ta tarar da matar, babba ce mai jiki fara tas da ita, tana shan lemo a kofi tana" danna remote. "Ta amsa sallamar Nana, tana yi mata kallon rashin sani." """Ina wuni?""" "Matar fuskarta babu yabo babu fallasa ta ce ""Lafiya ƙalau, zauna mana ga kujera nan"" Nana ta zauna, ta" "kalle ta ta ce ""Dama ni ce matar mai gadinku, da muka tare, na ga tun da muka zo ba kwa nan, sai jiya na ji motsin mota a gidan, shi ne na ce bari na zo mu gaisa""" """Allah sarki, sannu ko? Da maigidan ya ce mini buzaye ne""" "Nana ta ce ""Maigidana ne buzun, ni bahaushiya ce""" """Ohh Allah sarki, ya sunan ki ne?""" """Nana""" "Ta ce ""Ma sha Allah, sannun ki""" "Nana ta ce ""Yauwwa, idan akwai wani aiki ma, idan ki na buƙata, idan bai fi ƙarfina ba, a yi mini magana" "zan yi in sha Allah""" "Matar ta jinjina kai ta ce ""To shikenan na gode sosai"" Matar ta ɗan yi shiru tana kallon Nana. Ta yi" "mamakin yadda yarinyar mace kamar Nana, ta auri Buzu har yake yawon gadi da ita." "Sanin da Nana ta na idan ta koma, zaman tsuru-tsuru za ta yi da wannan kurman mutumin, ya sanya ta ja" "ta yi zamanta, ta ci gaba da kallon Tv. Matar kuma ba ta ce mata uffan ba. Can Nana ta ce ""Hajiya ba ki da 'yan aiki?""" """Ina da su, ba na zama ne sosai a ƙasar, duk sun watse mun ma dai samu saɓani ne""" """Ke ki ke aikin da kan ki?""" """Ni da yara muke yi""" "Nana ta ce ""Allah sarki, idan kina buƙatar aikin ma, zan din ga zuwa ina yi miki""" "Duk da tana basar da Nana, sai da ta yi murmushi ta ce ""To in sha Allah"" sai da Nana ta gama kallon," sannan ta tashi ta yi wa matar da ko sunanta ba ta sani ba sallama. "Ta sauka ta fita, sai dai tana fita ta yi kiciɓis da shi, sai da ta tsorata, yana tsaye a bakin ƙofar shiga cikin" "falon gidan, yana jiran ta" """Lafiya? Ya na ganka a nan?"" Yana ganin ta fito kawai ya yi gaba ya bar ta a gurin. Ba ƙaramin ƙuluwa" take yi da wannan dunkun-dunkun ɗin da yake yi ba na rashin magana. * "Babbar mace ce a ƙalla za ta yi shekara talatin da bakwai zuwa da takwas, hannunta riƙe da waya take" "kaiwa tana komowa a ɗakin, ta sake kai wayar kunnenta." """Hello Yaya kina ji na? Dan Allah maganar nan da gaske ki ke?""" Ayshacool "Daga ɗaya ɓangaren matar ta ce ""Oho ban tabattar ba, amma kin san babu lallai a yi jita-jita da irin" "wannan maganar, amma abu mafi sauƙi ki saka lokaci mu je mu tabattar""" """Yanzu Yaya idan maganar nan ta tabatta, baban su Imaran ya kyauta mini? A yi auren yarinya ta amma" "a kasa gaya mini an yi mini adalci a haka? Ba fa shikaɗai yake da hakki a kan yarinyar nan ba""" """To yaya za ki yi maijidda? Kawai mu shirya mu je shi ya fi sauƙi""" "Gyaran muryarsa da ta ji ya sanya ta kashe wayar babu shiri, tana faɗin sannu da zuwa." "Ya ƙura mata ido ya ce ""Meye haka na ganki wani iri?"" Ta so ta jure zuwa ya samu nutsuwa su yi magana" "ta fahimta, amma ta kasa. Cikin damuwa ta ce ""Labari na ji wai an yi wa Nana aure, shi ne nake son in tabattar""" Nan da nan ya haɗe fuska tamkar tasowar hadari lokacin marka-marka. """Wato ba zaki fasa kiran tsohon mijinki ba ko Maijidda, ni fa na gaji ba zan lamunci wannan iskancin naki" "ba na shekara da shekaru""" "Cikin ƙoƙarin kare kanta ta ce ""Ka yi haƙuri, wallahi ba kiransa nake yi ba. Da Yaya nake waya wallahi""" """Bani wayar nan""" "Ta ɓoye wayar a bayanta ta ce ""Wallahi ba da shi nake waya ba, Yaya ce"" za ki bani ko sai na ɓata miki rai." "Ta miƙa masa wayar tana kuka ta ce ""Dan Allah baban su Walida, ka bani wayar nan, hankalina ba zai" "kwanta ba sai na tabattar da gaskiyar maganar nan""" "Ya tsaya cak yana kallonta ya ce ""Allah wadaran halinki, ko kunyar Ubangiji ba kya ji, babu wata Nana da" "aka yi wa aure, tsohon mijinki ne ki ke bibiya, tirr da halinki"" fashewa ta yi da kuka, tana sheshsheƙa mai cike da ƙunar rai." * """Zan yi wanka"" ya yi maganar yana tsare ta da ido." "Nana ta ɗaga kai ta kalle shi, ta ce ""To ka yi mana""" "Ta yi magana tana ɓata rai, tare da mayar da hankalinta kan wayarta, da ta gano tarin fina-finai a ciki." "Tun bayan da Hajiya Amina ta bata wayar, ta nunawa Nasiru, ya karɓi wayar ya fita da ita gurin abokan sa aka yi turi, ba ta taɓa sanin da su a wayar ba." "Shiru ya yi yana kallon Nana, ganin ba ta gane abin da yake nufi ba. Kawai ya shiga banɗakin." "Ƙofar banɗakin ta bi da kallo, gaba ɗaya ta kasa gane kansa, babu yadda za ayi ace mutumin da yake da" "taɓin hankali, ya din ga gudanar da al'amuransa cikin nutsuwa. Sai dai kuma wannan shirun nasa ma," "yana ƙara tabattar da taɓin hankalin nasa. Duk da ma ba wannan ba, hankalinta ya fi karkata ga son sanin ainihin waye shi." "Ya shafe tsawon lokaci a banɗakin, dan sai da Nana ta manta da shi ma, sannan ya fito. Jikinsa sai tsuma" yake yi. "Ya nufo kan katifar da Nana take kai tsaye, bai ce mata uffan ba, ya zazzageta ya janye bedsheets ɗin da" yake shimfiɗe a kan katifar ya duƙunƙune a ciki. Galala ta saki baki tana kallonsa. "Lallai babu alamar hankali a nan"" ta faɗa a zuciyarta. Sai dai ta lura da yadda jikinsa yake ta tsuma da" rawar sanyi. "Ga garin babu sanyi sam, ita gumi ma take yi, amma ta ga yana ta tsuma. Ya jima sosai a haka, daga" "bisani ya tashi tsaye, ya nannaɗe bedsheet ɗin ya ya jefe mata a ka, ya wuce gaban mudubin." """Ya haka, me yasa ka jefo mini?""" "Waiwayo wa ya yi mata wani mugun kallo, ya juya ya ci gaba da abin da yake yi." "Taɓe baki ta yi, ta tashi ta ɗaukko wani zanin, ta shimfiɗa ta zauna. Hannunsa ɗauke da robar mai, ya" nufo ta. "Ya ajiye man a gefenta, ya zauna ya juya mata bayansa." "Ƙuri ta yi wa bayansa da ido, daga bisani ta ce ""Me za a yi ne?""" "Ya ɗauki robar man, ya saka mata a hannunta, ya nuna mata bayansa da hannunsa." "A ɗan tsorace ta ce ""Wai taɓa ka zan yi?""" Ya juyo gaba ɗayansa ya zuba mata ido. "Nana ba ta taɓa ƙare masa kallo ba, sai yanzu. A hankali ta fara jin sanyi yana ratsata, bugun zuciyar ta" ya fara ƙaruwa. "Cikin sauri ta ce ""To juya"" ya juya mata. Ta ɗaga robar man ta na kallo, duk rubutun jiki da french ne, ba" ta iya gane komai ba. "Ta tsiyayo man, sai ƙamshi yake yi, hannun ta har rawa yake yi, ta kai hannunta bayansa. Sai dai tana" "ɗora hannunta ta ji tsigar jikinta ta tashi, sanyi na ƙara ratsa ta." Ayshacool "Ta ture gashinsa gefe, ta fara shafa man a bayansa, sai dai tana shafa masa, yanayinta yana canzawa" "zuwa wani abu, da ta kasa tantance mene ne." "Tsayar da hannunta ta yi a guri ɗaya, ta ƙi gaba ta ƙi baya, jin zuciyarta na rayo mata wani abu a game da" "shi. Haushin kanta ne ya kama ta, kawai ta ja da baya ta haɗe rai. Ya sake waiwayo wa ya kalle ta. Kamar wanda aka yi wa dole ya ce ""Sanyi nake ji""" "Murguɗa baki ta yi, ta ja jikinta lungun katifa, ta yi masa shiru. Ganin ba ta da niyyar sake taɓa shi, ya" sanya ya tashi ya nemi guri ya kwanta a ƙasa. "Shiru ta yi tana zancen zuci, iya tsawon rayuwarta, ita ba ta taɓa kai hannunta jikin wani namiji tana sane" "ba. Kuma ba ta taɓa jin abu makamancin irin haka ba, a tattare da wani ba." "'ki shiga hankalinki Nana, kar wannan farar fatar ta ruɗe ki"" wata zuciyar ta gargaɗe ta." "Guntun tsaki ta yi, ba tare da ta shirya ba." """Ya dai?"" Muryar Ƙaisar ta dawo da ita tunaninta." "Ta kalle shi, yana ta haɗa wasu abubuwa a cikin kwalabe." """Kai ne ko?"" Ta yi maganar a ɗan ƙule." """Na yi me?"" Ya yi maganar ba tare da ya kalle ta ba." """Ka fi ni sani ai""" "Ƙaisar ya girgiza kai ya ce ""Sanin gaibu sai Allah ai, ban san me na yi miki ba""" "Nana ta ce ""Ka sani""" "Ya ɗan kalle ta, kawai ya bushe da dariya ya tashi tsaye yana faɗin ""Kar ki damu, yanayi ne da bil adama" "su kan kasance a ciki, ai ba ki yi wani abu ba, ba abin damuwa ba ne ba. Kuma ni bani da hannu a wannan lamarin. Sai dai ina tunatar da ke, kafin ki yi aika-aika ki tabattar da wane ne shi""" "Banza ta yi masa, ta nufi wata ƙofa da take buɗe." "A hankali ta buɗe idonta, tana kwance a kan katifarta, ta kalli gurin da yake kwance, yana nan kamar" "yadda ya kwanta. Ya dunƙule jikinsa guri guda, jikinsa ko riga babu. Ta shafa jikinta ta ji gumi take yi," amma shi alamu suka nuna sanyi yake ji. "Ta yinƙura da ƙyar ta tashi, ta ɗaukko bargonta a saman wardrobe, ta nufe shi." """Ka tashi ga bargo ka rufa""" "A hankali ya buɗe idonsa, ya kalle ta, kawai ya mayar ya lumshe. Ba ta haƙura ba ta sake cewa ga shi ka" "rufa tun da sanyi ka ke ji. Ta yi maganar tana ajiye masa bargon. Hankaɗe bargon ya yi gefe a zuciye," yana ƙoƙarin gyara kwanciyarsa. """Me ya sa zaka jefar mini da abu, idan ba ka so sai ka jefar mini, haka ɗazu ma ka jefa mini bedsheet a" "kaina, ni ka daina yi mini haka. Kawai ya tashi zaune. Me Nana za ta gani, kamaninsa sun koma na tsohon" nan da take gani a tare da shi. Ihu ta kurma da ƙarfi ta suma a gurin. * "Sanye take da doguwar rigar bacci shara-shara blue black, ta yi mata kyau sosai, ga tsohon cikinta, tana" gefen gado tana shan abu a cikin kofi. "Da sallama ya shigo ɗakin, ta amsa masa, ya zauna a kusa da ita. Ta ce ""Ya yi baccin?""" "Ya ce ""Ya yi da kyar, ban da labarin Anty Nana, babu abin da yake yi mini, yana ta biya mini abin da take" "koya masa. Babu yadda za a yi ta dawo gidan nan ne ta ci gaba da kula da shi?""" "Ta kwaɓe baki ta ce ""Ta ina? Na gaya maka an yi mata aure da buzayen da suke gadin gidanmu""" "Ya ce ""Ikon Allah, to dama buzaye na auren wasu wanda ba irin su ba ne?""" "Shukura ta ce ""Waye ya san musu ma? Abin ne dai ga shi nan""" """Allah ya kyauta, ni dai Haidar nake ji, da alama sun shaƙu, wai me ki ke sha a cikin kofin nan ne?"" Ya yi" magana yana karɓar kofin. "Magani ya gani a ciki, ya tsuke fuska ya ce ""Wai me yasa ba kya ji ne? Na hana ki shan wannan" "abubuwan, ya za a yi ki na da tsohon ciki ki din ga shan wannan abubuwan? Sai kin yi wa kan ki illa?""" "Shukura ta ɓata fuska ta ce ""Ba fa da yawa na sha ba, kuma ai duk dan kai nake yi""" """Kuma ni na ce miki ina bukatar wannan abin? Fruit bai ishe ki ba me ki ke nema kuma? Kawai sai kin" "illata mini yaro? Wallahi na kuma ganin kina shan wannan abubuwan sai ranki ya ɓaci"" ya tashi ya fice ya bar mata ɗakin." "Haushi ne ya ishe ta, kawai ta nemi guri ta kwanta." "Girma da nauyin cikin jikinta, bai hanata yin gudun ceton ranta ba, tana gudun tana waiwaye, ga" "numfashinta na neman barin huhunta, saboda tsananin gajiya." "Karo ta yi da wani mutum sanye da farar riga, miƙa masa hannu take yi, tana faɗin ""Dan Allah ka taimake" "ni""" Ayshacool "Lokaci ɗaya abin da yake cikinta, ya yi wani irin dunƙulewa, ya na danno ta. Cikin gigita ta tsaya tare da" "durƙusawa a kan gwiwoyinta, tana jin nishi." "Mutumin da yake bin ta ya ƙaraso gabanta, ya saka hannu ya cire abin da ya rufe fuskarsa da shi." "Cikin tashin hankali ta ce ""Daddy""" """Ki yi haƙuri Shukura, ni za ki taimaka, ki sadaukar mini da abin da yake cikin ki""" "Jan jikinta ta fara yi, tana girgiza kanta, cikin kuka da azabar naƙuda take faɗin ""A'a Daddy, dan Allah ka" "bar mini jaririna, na baka tawa rayuwar amma ka bar mini jaririna dan Allah""" "Ya girgiza kai ya ce ""Ba na buƙatar rayuwar ki Shukura, yaron nan kawai nake buƙata""" "Mutumin nan mai farar riga, ya buɗe fuskarsa, sai ta ga doctor Sharif ne. Cikin kuka take ce masa ""Dan" "Allah Doctor ka taimake ni, ka ba shi haƙuri""." "Bai saurare ta ba, ya durƙusa ya yi mata wata allura, take ta yi wani irin nishi, jaririn ya faɗo." "Ya ɗauke shi har mabiyiyar, ya miƙa wa Alhaji Zailani." "Alhaji Zailani ya ciro wata 'yar wuƙa, ya ɗaga jaririn kansa a ƙasa, ƙafafuwan sa a sama." "Ihu take iya ƙarfin ta, tana yi masa magiya, amma ya ɗaga wuƙar nan zai caka wa jaririn, bai kai ga caka" "masa ba, ta ji an kira sunanta. Tana ɗaga kai ta ga Nana." "Nana ta jefa mata wata sharɓeɓiyar wuƙa, a rikice Alhaj Zailani ya yi kan Shukura, cikin sa'a ta caka masa" wuƙar da Nana ta jefo mata. """Shukura lafiya? Me ya same ki? Me ya samu jaririn naki?"" Ta buɗe idonta a hankali ta kalli fuskar mijinta" da ke ɗauke da matsananciyar damuwa. """Meya faru?"" Ya sake tambayarta." "Jikinta ne kawai yake karkarwa, tana zare ido cike da matsanancin tsoro da tashin hankali." "Ba ta iya yi masa magana ba, sai godiya da ta din ga yi wa Allah a zuciyarta, da ya zamana mafarki ne ba" gaskiya ba. * "Da safe Nana na ta karkaɗe ɗaki tana gyarawa, ko gaishe shi ba ta yi ba, dama ba amsawa yake yi ba idan" "ta gaishe shi. Sai dai fes take tuna abin da ya faru jiya da daddare, yadda fuskarsa ta canza baki ɗaya. Sai" "dai haryanzu tana ji a ranta, sharrin Ƙaisar ne ya sanya take ganin wannan abubuwan a tattare da shi." """Zan yi wanka"" ta ji muryarsa tana tsaka da gyara ɗakin." "Ta kalle shi ta ce ""To banɗakin zan biyo ka ko ya za a yi?"" Ta yi maganar cikin tsiwa." "Bakinta ya bi da kallo, rasa me zai ce mata ya yi, a wannan karon ma, ba ta gane abin da yake nufi ba," kawai ya wuce banɗakin. Yana shiga ta dira mitar abin da yake yi mata. """Wai zai yi wanka, ko bin sa zan yi na yi masa wankan, ni ban gane ba""" "Ta ci gaba da aikinta, yana fitowa bai tsaya wata-wata ba, ya sake yaye bedsheet ɗin da ta gama" shimfiɗawa ya rufa yana rawar sanyi. "A hanzarce ta ɗago a ƙule ta ce ""Lafiya, meye haka wai?"" Ta yi maganar kamar ta fashe da kuka, saboda" a lokacin ta gama sanya zanin gadon. "Jin ta tsaya masa a ka, saboda ya ɗauki bedsheet ya sanya ya miƙe, ya watsar mata da shi a gurin." "Ya ɗauki kayan da zai saka ya shiga toilet ya canza, ya fito ya bar mata ɗakin. Cikin hantsi ya fita ya zauna" "ya takure jikinsa, ɗumin ranar yana taɓa shi." Nana ta ci gaba da mita tana ƙara gyarawa. "Muryar Habu ta jiyo, ta leƙa ta taga, ta gan su tare a zaune. Yadda Habu ya yi shiru ya nutsu ne, ya sanya" "ta gane mijinta magana yake yi, amma muryarsa ƙasa-ƙasa, ba a jin tasa sai dai ta Habu ake iya ji." "Ta saki labulen ta nemi guri ta zauna, Habu ya yi sallama a ƙofar ɗakin. Ta amsa masa. Ya ce ""Na shigo?""" """Eh bismillah"" sai ta ga ya shigo shikaɗai." "Nana ta ce ""Ina kwana?""" """Lafiya ƙalau Alhamdilillah. Ya rayuwar?""" "Nana ta yi murmushi, haryanzu hausar su wasu lokutan sai a hankali, ta ce ""Lafiya ƙalau""" """Ga wannan"" ya yi maganar yana ba ta leda." "Jiki a sanyaye ta ce ""Malam Habu, abin da ya faru Allah ne ya ƙaddara, wannan ɗawainiyar ta isa haka," "kullum sai kun kawo mana Abinci, ga ɗawainiya da ku ke ta yi. Zan fara girki in sha Allah""" "Ya yi murmushi ya ce ""Kar ki damu, ai dolen mu ne mu kula da ke. Kayan miya ne a ciki da sauran kayan" "amfani. Duk abin da babu, akwai lambata a rubuce a gurin mijin naki, sai ku kira ni"" Nana ta jinjina masa kai." Ayshacool "Sai kuma Habu ya yi murmushi ya ce ""Amm amarya, mutumin fa ya kawo mini ƙarar ki, ya ce ki na yi" "masa rashin kunya, ki na ɗaga masa murya. Dan Allah kamar yadda na gaya miki ki yi haƙuri da shi dan" "Allah. A hankali za ki fuskanci yadda za ki zauna da shi, na san abin zai yi miki wahala amma dan Allah ki" "yi haƙuri hakan tamkar jihadi ne, ke ma Allah ya kawo ki mu yi tare""" "Nana ta haɗiye maganganu da tambayoyi da ta so yi wa Habu, ta daure ta ce ""Hmm ƙara ta ma ya kawo" "ko? To shikenan na daina""" """Ki yi haƙuri amma, yanayin ciwon nasa ne ba ya son hayaniya, shi yasa""" "Nana ta ce ""Babu damuwa in sha Allah, ina son ma na yi maka wasu tambayoyi, amma sai ka kuma" "dawowa""" "Gyaran muryar sa su ka ji, Habu ya miƙe. Buzu ya juya yare ya yi masa magana, Habu ya jinjina kai." "Ya zo ya wuce ya buɗe wardrobe, ya ɗebo kayansa masu datti, da ya nannaɗe ya bawa Habu." "Habu ya karɓa, ya yi musu sallama, ya tafi." "Nana ta din ga kallonsa, bakinta fal magana, amma ya ƙi kallonta." """Shi ne ka ce ina yi maka rashin kunya ko? To me na yi maka na rashin kunya? Dama ashe ka na magana" "ni ce ba ka kulawa ko?"" Ya lumshe idanunsa yana kaɗa ƙafar sa." """Idan ba ka yi mini magana, ba zan san na yi maka laifi ba, ko na san abin da ka ke so ba, da wanda ba ka" "so"" ta gama surutunta, ganin ba shi da niyyar tanka mata ya sanya ta kama wani abin." "Kayan miyar da Habu ya kawo, ta zauna ta gyara tsaf, ta yi greating ɗin su. Ta ɗora a kan gas. Tana jin" "yadda yake tari, saboda zafin attaruhu. Ta dafa taliya da miya." "Ya din ga bin ta da ido, har ta gama." "Ta zuba masa ta ajiye masa komai, ta tashi ta je ta yi alwala, ta dawo ta tayar da sallar azahar." "Ta idar ta yi azkar, ta ninke dadduma, ta gan shi ya haɗa gumi, yana cakalar abincin, fuskarsa ta yi jawur," sai gumi ne yake tsatstsafo masa. """Lafiya ya na ga ka na gumi, abincin babu daɗi ne?"" Ya ja numfashi ya kalle ta, hannunsa riƙe da cokali" mai yatsu. "Babu irin tambayar da ba ta yi masa ba, amma bai ba ta amsa ba, har ta gaji ta rabu da shi. A haka ya" cinye abincin. Nana ta rasa abin da ya sanya shi haɗa wannan uban gumin. Idonta ne ya sauka a kan wayarta. A take tunanin mahaifiyarta ya ƙara faɗo mata. Jiki a sanyaye ta ƙarasa ta ɗauki wayar tana kallon screen ɗin. "Jiki a sanyaye ta buɗe wayar, ta shiga gurin kira, ta shigar da lambobin kamar yadda ta haddace su, cike" da fatan Allah ya sa wayar ta shiga. "Babu zato babu tsammani, ta ji wayar ta shiga. Gyara zamanta ta yi tana fatan Allah ya sa ta ji abin da" "take tsammanni. Sai dai akasin haka ta ji muryar namiji, muryar mutumin da ta tsana a rayuwarta." "Cikin dakiya ta ce ""Baba ina wuni?""" """Lafiya kalau wace ce?""" "Cikin sanyin murya ta ce ""Dan Allah me wayar nake nema""" "Ya ce ""To wace ce ke ɗin?""" "Ta yi ajiyar zuciya ta ce ""Baba Nana ce, mamana nake nema"" ta yi maganar cikin rawar murya, idanunta" na cika da hawaye. """Ai dama na sani, wallahi na sani, na san ba ta fasa bibiyar tsohon mijinta ba, wallahi zan gauraya da ita""" "A ruɗe Nana ta ce ""Dan Allah Baba ka tsaya ka ji, wallahi ba sa waya da Babanmu, lamba ta ce, dan Allah" "ka haɗa ni da ita ko muryarta na ji, dan Allah.. ƙit ya kashe wayar ba tare da ta gama faɗar abin da za ta faɗa ba." "Wata irin tafasa zuciyarta ta din ga yi, cike da ɓacin rai da tashin hankali. Wasu irin hawaye masu raɗaɗi" suka fara biyo fuskar ta. "Ta ɗauki wayar ta yi jifa da ita, caraf ya cafke wayar." Ya kalli yadda hawaye yake fita daga idanunta. "Kawai ya ga ta taso za ta fita daga ɗakin, jikinta yana rawa." "Har za ta gota shi, ya danƙo hannunta ya yo baya da ita, yana ƙarewa Ƙaisar kallo da ya bayyana a" gefenta yana huci!. Ayshercool 08081012143 Ayshacool Page 31 "Bai kula Ƙaisar ba, ya ja Nana zuwa kan katifa, ya zaunar da ita, idanunta a lumshe, har a lokacin kuma" "fitar da hawaye suke yi, babu ƙaƙƙautawa. Ya taɓa tafukan hannayenta, ya ji sanyi ƙalau kamar an ciro ta daga ƙanƙara." "Ya ƙura mata ido yana nazarin ta, a take ya tuno ranar da ta shiga ɗakinsu, tana kiran Haidar, su na haɗa" ido ta ja da baya ta ƙwala ihu ta faɗi. "Haka jikinta ya ƙandare, ta din ga karkarwa, ya ga wani narkeken baƙin muzuru ya bayyana a ɗakin, yana" ta zagaye ta. "Ya sauke numfashi, ya sanya yatsunsa biyu, ya danna bayan kunnenta. Ya miƙe ya bar kusa da ita. A" "hankali jikinta ya daina rawar, ta buɗe idonta, sai dai tun da ta buɗe idon, ba ta tashi daga gurin ba balle ta ci abinci." "Ya din ga satar kallonta, amma ba ta tashi daga in da take ba, balle ta ci abinci. Yana son ya yi magana" amma ya rasa me zai ce mata. "Ta tashi zaune da ƙyar, ta haɗa kai da gwiwa, ta yi kuka mai isar ta. Sai da aka kira la'asar sannan ta tashi" "ta yi alwala, ta tayar da salla." "Bayan ta idar tana zaune ta yi shiru, ya dawo ɗakin, ya duba gurin da ta gama girkin, babu alamar ta ci" abinci. """Ba za a ci abinci ba?"" Ta ji maganar sa babu tsammani." "Ta ɗaga kai ta kalle shi, kamar mai jiran ƙiris, kawai ta sake fashewa da kuka. Ya yi zuru da ido yana bin ta" "da kallo, bai ce ta yi shiru ba, har ta yi mai isar ta yi shiru." "Duk ya damu ganin ba ta ci abinci ba, ya rasa me zai ce mata, ga shi yanayinta ya fahimci rigimammiya ce." "Jin motsi a waje ana taɓa gate, ya sanya ya tashi ya rufe fuskar sa, ya fita ya duba waye." "Tsayawa ya yi yana kallon su, mata ne su uku, da ƙanan yara sai wani ɗan matashin saurayi." """Sannu malam, ko kai ne mijin Nanan?"" Ya tsaya tsuru yana kallon su." """Gurin Nana mu ka zo tana nan?"" ya nuna musu ɗakin su." "Suka wuce, Ummi tana cewa ""Na yi ƙoƙari fa da na iya kawo mu gidan nan""" "Bayan Jamila ya bi da kallo, jikinsa na ba shi wani abu a game da ita." "Wata irin zabura Nana ta yi ta rungume Ummi, ba ta taɓa tsammanin ganin su ba. Ta rungume Jamila" "cikin farin ciki ta ce ""Dama za ku zo ba ku gaya mini ba?""" "Ummi ta ce ""Mu ki bamu guri mu zauna""" "Nasiru ya ce ""Hajiya Anty Nana amarya"" daƙuwa ta yi masa ta ce ""Gidanku""" "Ya yi dariya ya ce ""Na yi missing ɗin ki sosai""" "Take ta manta da damuwar da take ciki, ta ware suka hau hira. Ta juye musu sauran abincin da ba ta ci" "ba, ta ce za ta ɗora musu wani." "Ummi ta ce ""Ke a ƙoshe muke, ga shi wannan miya ce na ɗan yi miki, tun bayan kawo ki da kwana biyu," "na so yi miki, bana jin daɗi ne. Ga ɗan cin-cin da dubulan na yi miki. Ga kuma turarukan wuta da wata" "maƙwanciyar ku, ta bayar a kawo miki ga humra ma. Sai kuma kaya da na ɗan ƙara sayo miki""" "Nana ta ce ""Allah sarki, na gode sosai da sosai Anty Ummi, Allah ya saka da mafificin alkhairi. Jamcy ya" "garin ne?""" "Jamila ta ce ""Uhumm mamaki nake yi, kamar ba ke ce ki ka gama uban kuka ba, an aura miki buzu," "amma kalli yadda ki ka ware yanzu""" "Nana ta yi murmushi ta ce ""To ba dole na ware ba, lafiyayyen ɗaki, ga wardrobe, ga katifata ga" "banɗakina nikaɗai ba takura ga wuta 2hrs ba yankewa""" "Suwaiba ta ce ""Katifa ko abin da ake yi a kan katifar?""" "Nana ta ce ""Duka ɗan sunna ai ba zai ƙi sunna ba Jamila, tun da dan haka ake auren""" "Ummi ta ce ""Dan uban ku da yara a gurin ku ke yi mana batsa""" "Nana ta yi murmushi ta ce ""Ya Baba, ina mama su ba za su zo ba?""" "Ummi ta ce ""Za su zo ne, Baba babu lafiya ƙafarsa ce take ciwo""" "Nana ta ce ""Ciwon ƙafa kuma?""" """Wallahi kuwa, ba za ki kira mijin naki mu gaisa ba""" "Nana ta ɗan kwaɓe baki ta ce ""Ba kula ku zai yi ba, Nasiru ya makaranta"" ta karkatar da zancen ga" "Nasiru. ""Makaranta lafiya ƙalau Alhamdilillah""" "A ƙofar ɗakin ya yi gyaran murya ya tsaya, Nana ta yinƙura ta tashi, ta ɗaga labulen. Babu hijjabi a jikinta," sai doguwar rigar atamfa. "Ya miƙo mata leda, ta saka hannu biyu ta karɓa, bai ce mata komai ba, ya juya ya koma bakin gate." "Fura da Nono ne kaya guda, abin sai da ya bawa Nana mamaki, ba ta san a ina ya samo su ba. Ta ajiye" "musu suka dama, suka sha." Ayshacool "Jamila ta miƙa wa Nana ɗan ƙaramin flask ta ce ""Nana ga mutuniyar ki na yi miki wainar fulawa"" Nana ta" "haɗiyi yawu cikin murna ta din ga yi wa Jamila godiya. Ta ce ""Wannan sai dare zan dafa shayi na ci da ita""" "Suwaiba ta ce ""Ashe fa buzu ki ke aure, ba za a gaya miki shayi ba yanzu""" "Nana ta ce ""Kamar kin sani, ni yanzu shayi ai sai dai na koya wasu, kwana muke mu wuni shan shayi" "babu ƙaƙƙautawa"" suka yi dariya." "Har magariba su na gidan, sai da suka yi sallar magariba, Nana ta fito har bakin gate ta rako su, sai dai" baya nan. "Ummi ta ce ""Kin ga har zamu tafi, bamu haɗu mun gaisa ba""" "Nana ta ce ""Ina ga yana masallaci""" "Suka yi sallama, suka tafi Nana ta koma ɗaki. Har cikin ranta ta ji daɗin zuwan su." "Ta yi wanke-wanke ta gyara ɗakin fes. Ta ɗaukko flask ɗin wainar fulawar, ta saka a gaba ta fara ci. Ba ta" "ci da yawa ba, Haula ta yi sallama." "Nana ta amsa cikin sakin fuska, duk da ta yi mamakin ganinta a daidai wannan lokacin." """Anty Haula ba ki yi fushi ba? Haryanzu ban fara fita ba, shi yasa ban shigo miki ba""" "Haula ta ce ""Allah sarki, kar ki damu wallahi, ashe baƙi ki ka yi?""" "Ba tare da Nana ta yi tunanin komai ba, ta ce ""Eh, 'yan gidanmu ne su ka zo, bismillah matso mu ci" "abinci"" Aikuwa Haula ta gyara zama ta zura hannu a kwano, ta fara cin abincin. Kafin Nana ta yi loma" "ɗaya ta yi huɗu da rabi, kafin wani lokaci Nana sai filin kwanon ta gani, Haula na ta suɗar baki saboda yajin wainar." "Sai da ran Nana ya sosu, dan kuwa ta so cin wainar nan ta ƙoshi." "Labulen ɗakin kawai ya ɗaga ya shigo, Haula ta tashi zumbur. Ta kalli Nana ta ce ""Na gode sosai sai" "anjima"" sai da Haula ta fice sannan ya shigo ɗakin." "Ya zauna a gurin da ya saba zama, Nana ta ɗaukko ta sa furar da ta ajiye masa, da cin-cin da dubulan a" "plate, ta nufe shi." """Sannu da zuwa"" ya jinjina mata kai." """ 'yan gidanmu ne fa suka zo"" ta yi maganar fuskarta na bayyanar da annashuwa. Ya gyaɗa mata kai." """Na gode sosai da sosai, da karamcin da ka yi mini, ga taka furar ga kuma wannan"" ta yi magana tana" tura masa plate ɗin dubulan. "Ya saka hannu biyu ya karɓi kofin furar, Nana ta zauna a gefensa, a tsanake yake sha, ya ɗauki cin-cin ya" "saka a bakinsa, maimakon ya tauna yadda yakamata, amma ya din ga tauna shi a hankali kamar mai tsoron tauna dutse." """Da daɗi?"" Ya jinjina mata kai alamar eh." "Nana ta ɗan yi ƙasa da murya ta ce ""Dan Allah ka din ga yi mini magana mana. Haryanzu ban san" "sunanka ba"" ya kalle ta yana ci gaba da tauna cin-cin ɗin sa." """Ka gaya mini sunan ka"" ya ajiye kofin hannunsa yana hamma, ya jingina da jikin bango yana lumshe" idanunsa. "Ta gaji ta ƙyale shi, ta fara shirin kwanciya, ta shiga banɗaki domin kama ruwa ta yi alwalar kwanciya" bacci. "A sukwane ya miƙe, duk da bacci ya fara ɗaukarsa, kwanon da Nana ta ci wainar nan ya ɗauka, ya jujjuya" kwanon ya ga babu komai a ciki. "Ya ajiye kwanon, ya koma gurin da yake kwanciya, ya zauna ya yi shiru." "Nana kuwa tana saka ƙafarta a banɗakin, ta ganta a cikin wani gida, mai dogon gini, mai ɗauke da ƙofofi" "daban-daban. Ɗaya daga cikin kofofin ta bi, tana neman hanyar fita, amma da ta shiga sai ta ga ta koma" ainihin gurin da take da farko. "Tana cikin laluben ƙofar, kawai ta ci karo da Baba, ƙafarsa ɗaya an nannaɗe ta da sarƙa, an ɗaure ta" tamau. "Da sauri Nana ta nufe shi, cikin tashin hankali ta ce ""Baba lafiya kuwa? Me ya same ka haka?""" """Ni ma ban sani ba Nana, dan Allah ki kwance mini sarƙar nan, ina jin ƙafata kamar za ta cire, ba na iya" "bacci""" "Cikin damuwa ta ce ""Ka kwantar da hankalinka, bari na gani idan zan iya kwance maka"" Ta durƙusa ta" "fara ƙoƙarin kwance masa sarƙar, sai dai ta rasa ina ne ainihin gurin da aka ƙulle ƙafar." """Idan ki ka kuskura ki ka kwance masa, ba zai sake taka ƙafarsa ba har abada"" Nana ta ɗago tana kallon" Ƙaisar. """Dan me za ka ce kar na kwance masa? Ba ka ga halin da yake ciki ba, ko iya taka ƙafar baya yi ba?""" "Ƙaisar ya ce ""Ban gaya miki sai na hukunta shi ba? Har yanzu ba ki yadda mu na cikin mummunan haɗari" "daga ni har ke ba, a dalilin wannan auren. Dan haka dole shi ma ya ɗanɗana kuɗarsa""" Ayshacool "Cikin ɗaga murya ta ce ""Ƙaisar baban nawa? Ka kwance masa ƙafarsa"" kawai tana waiwayewa ta daina" ganin Baba. """Idan duniya za ta taru, babu wanda ya isa ya kwance masa ƙafar nan, idan bai yi wasa ba sai ta yi" "ajalinsa"" yayi maganar cikin ɗaga murya." "Tamkar mai shirin haukacewa ta ce ""Ba zai yiwu ba, wallahi sai ka kwance shi, wai kai wane irin halitta ne" "da babu ɗigon imani, a zuciyar ka?""" "Ƙaisar ya ce ""Ko ma dai mene ne, abu ɗaya za ki yi ki kwance masa ƙafar nan, wanda kin san mene ne, ba" "sai na gaya miki ba. Mu ajiye wannan a gefe tukuna, ban san iya adadin lokacin da za a ɗauka kafin ki san ciwon kanki ba, ki daina wasa da rayuwar ki ba. A wannan karon ma an baki abu kin ci, za kuwa ki" "ɗanɗana kuɗar ki, a nan na nuna miki an tsaface ƙanwar ki, amma ta kawo abu ta baki ki ka ci""" "Nana ta ce ""Idan ma ka nuna mini, da na tashi nake manta komai, kuma ba zan taɓa yarda da" "maganganun ka ba, yaudarata kawai ka ke so ka yi, domin na amince da mugun nufin ka, kuma har abada ba zan amince ba, ko da ba ma jituwa da su, na san ba za su cutar da ni ba""" "Ya ce ""Shikenan, zamu gani""" "A hankali ta yi kokarin yin juyi a kan katifar, amma ta ji wani irin azababben fitsari, tamkar mararta za ta" "yi bindiga, ga wata irin ƙullewa da mararta ta yi har cikin bayanta da ƙafafuwanta. Da ƙyar da dabara, ta" "tashi ta tafi banɗaki. A zaton ta da ta yi fitsarin shikenan, za ta ji marar ta saki, amma babu abin da ya canza." "Da bin bango ta fito ,ta dawo kan katifar ta kwanta. Bacci ne a kanta, amma wani irin azababben ciwon" mara ya turnuƙe ta. "Yana kwance yana jin nishinta sama-sama, tun farkawar ta da shigarta Banɗaki, duk a kan idanunsa." "Murƙususu ta din ga yi a kan katifar, tana numfarfashi. Rabonta da ciwon mara mai irin wannan azabar," tun farko-farkon fara period ɗin ta. Da idan ta fara sai an kai ta chemist an yi mata allurai. "Daga baya abin ya ragu sosai, amma na yau kam, ba ta taɓa makamancin irin sa ba, ji take tamkar ba za" ta wayi gari ba. "Ko na minti ɗaya ciwon baya lafawa, ga shi ya haɗe mata da ciwon ciki, da na ƙirji kamar za ta bar duniya." A duƙe ta sake komawa banɗaki ta saka pad. "A haka ta wayi gari, cikin mawuyacin hali, ta yi kukan ta gaji. Ta saukko daga kan katifar ta kwanta a ƙasa" "amma babu afuwa. Ko sau ɗaya bai ce mata sannu ba, da gari ya yi haske ma bar mata ɗakin ya yi, saboda yadda kukanta ya cika masa kunne." "Tamkar za ta haihu, haka ta fita daga hayyacinta, gaba ɗaya ta manta da batun ba itakaɗai ce a ɗakin ba," "ta cire kayan jikinta, ta bar vest da underwear. Rashin tanka matan da ya yi ba ƙaramin ƙona mata rai ya" yi ba. "Can amai ya din ga taso mata, ga wata irin gudawa ta azaba da fitar ta kawai, yake ƙara gigita ta saboda" "sai cikin ya haɗu ya ƙule da marar sannan take yin ta. Ga fitarta tamkar tana zawon wuta haka take ji, ta ga duniyar tana juya mata, ta din ga salati tana ambaton Allah. Tun tana iya zuwa banɗakin a duƙe, ta koma rarrafe." "Ta din ga wani irin amai, mai wari da ƙarni. Idanunta suka yi zuru-zuru, kamar ta yi wata da watanni tana" rashin lafiya. "Ta kwanta ta yi rub da ciki, ta lumshe idonta. Ta ji an ɗagota. Sosai ya ɗago ta ya haɗa ta da ƙirjinsa." "Babu rawani a kansa, ya kwance gashin kansa, ya sauka a kan kafaɗarsa. Suna haɗa ido, ta sake fashewa da kuka, saboda ta ji zafin rashin kula ta da ya yi balle ya yi mata sannu." Ya kai dogwayen yatsunsa ya share hawayen da yake fitowa daga idonta. Ta saka hannu ta ture "hannunsa, da yake share mata hawayen." "Ya kama bayan hannunta ya kai bakinsa ya sumbuta, ya ɗago ya ƙura mata ido, yana matsa hannunta a" "hankali. Zuba masa ido Nana ta yi, sai ta ga kamar ba shi ba. Ya sake kai bakinsa goshinta ya sumbaci goshin nata." "Ta sake fashewa da kuka, ya haɗa goshinsa da nata ya ce ""Shhhhh""" "Gabanta ya faɗi, sai da ta razana jin ya ɗora hannunsa a kan marar ta." "A hankali ta fara jin releif, daga wannan matsanancin ciwon da take ji." "Bai ɗauke goshinsa daga nata ba, numfashin sa da yake shiga nata, jikinta ne ya saki ya mutu murus, ta" kasa ko ƙwaƙwƙwaran motsi. A hankali ta fara jin bacci yana ɗaukar ta. Ayshacool "Su Jamila kuwa bayan sun dawo daga gidan Nana, Baba ya tambaye su ya suka baro ta." "Suwaiba ta ce ""Tana nan lafiya kalau, ta ce a gaishe ka""" """Ina amsawa, ya gidan nata akwai abinci kuwa?""" "Nasiru ya yi farat ya ce ""Baba ɗaki dai, a ɗaki ɗaya take da banɗaki, amma akwai abinci a ɗakin. Har" "mijinta ya kawo mana fura da Nono""." "Baba ya ce ""Ko ma dai a rami suke ba ɗaki ɗaya ba, ai ita ta jiyo, tun da Allah ya nufi ya rufa mata asiri," "ya bata miji na gari na rufin asiri ta zaɓi ta tonawa kanta asiri, yanzu ta ƙare a tantalbatete""" "Jamila dai kawai fatan ta, Allah ya sa ta yi nasara a kan Nana." "Babu kunya Mama ta saka Nasiru a gaba, tana yi masa tambayar ƙawaƙwaf da son sanin halin da Nana" take ciki na daɗi ko akasin haka. **** "Bangaren Shukura, duk da ta kan yi mafarkai na ban tsoro barkatai, amma bai fiye damunta ba, wasu" "lokutan da ta farka ma shikenan, mussaman idan tana da ciki ta fi irin wannan mafarkan. Amma a wannan karon ta kasa mantawa da wannan mafarkin da ta yi, a cikin jikinta take jin tsoro da fargaba a kan mafarkin." "Duk da ba ta iya gaya wa Sagir abin da ta gani a mafarki ba, kawai ta ce masa mummunan mafarki ne, ya" "yi ta kwantar mata da hankali, da tabattar mata da mafarki ba gaskiya ba ne ba." "Sai dai jin abin take yi, tamkar ma ya riga ya faru ne, ko kuma yana daf da faruwa, haka kurum sai ta ji" gabanta ya faɗi ta razana. **** "Tare da su Habu ta hange shi zaune kan wani ƙaton carfet fari tas, a cikin sahara , suna ta shan shayi su" "na hira cikin nishaɗi, gaban su dabino kala-kala a cikin tasoshi, yana cikin su ba ya magana sai murmushi." Ƙyam ta tsaya tana ƙare masa kallo. Karaf ya ɗago kai suka yi ido huɗu. Ya yinƙura ya nufo ta yana murmushi. Ta kawar da kanta gefe ta haɗe rai. "Bai ce mata uffan ba, ya rungume ta yana ci gaba da murmushi ya ce ""Ya aka yi ne?""" """Ni rabu da ni, bayan ka ƙi yi mini sannu"" ta yi magana cikin shagwaɓa." """Tuna dai, na yi miki fa, to yanzu ya jikin naki, me ki ke ji?""" """Ba komai""" """Kin tabatta?"" Ta ɗaga masa kai alamar eh." "Ya zagayo da hannunsa, ya ɗora a kan mararta, ya sunkoyo daidai kunnenta ya ce ""Hmm haka ne, na ji" "da sauƙi, na yi uzuri a wannan karon, amma idan aka ƙara zan ɗauki mataki""" "Nana ta ce ""Me aka yi da zaka ɗauki mataki?""" """Komai ma""" "Ta yi murmushi ta ɗaga kai ta kalle shi ta ce ""Har yanzu ba ka gaya mini sunan ka ba""" "Ya yi dariyar da ta ƙara masa kyau, ya ce ""Sunana ki ke son sani?"" Ta jinjina masa kai alamar eh." "Cikin raɗa ya ce mata ""BUZU""" """Buzu"" ta maimaita a hankali tana buɗe idonta." "Shiru ta yi tana jin mafarkin da ta yi a ƙwaƙwalwarta, sai kuma abun da ya faru da ya rungume ta ɗazu," "ya fara dawo mata. Ta nutsu sosai ta ga shi ma a mafarki abin ya faru. Ta ƙarewa ɗakin kallo, babu kowa a cikin sa sai ita kaɗai." "Sai dai ta ji mararta ta daina ciwon, ta tashi ta ɗora ruwa ta yi wanka, ta gyara jikin ta, ta rasa abin da" "yake yi mata daɗi, ga shi ta kasa cin abincin. Dabinon da ya taɓa bata ta ɗaukko ta hau ci." "Bayan sallar magariba, ya shigo ɗakin da leda, kai tsaye ya tafi kusa da ita ya zauna." "Ko kallon gurin da yake ta ƙi yi, saboda ta ji haushin yadda ya kasa kula ta duk wannan azabar wahalar da" ta sha. """Ki ci"" ya yi maganar yana ajiye mata ledar." "Murguɗa baki ta yi ta ce ""Ba na ci"" ya yi shiru yana kallon ta." Ta kawar da kanta gefe tana ci gaba da ƙunƙuni. Ƙarshe ma ta tashi ta koma can gefe ta yi zamanta. "Ta ɗago ta ce ""Ka ci ni na ƙoshi, ba zan iya girki ba, ba na son ƙamshin abinci"" kawai ya yi shiru bai ce" komai ba. "Ta kunna kallo a wayarta, tana yi tana cin dabinonta." """Salamu Alaikum"" suka ji ana sallama a wajen ɗakin." """Wa'alaikum salam warahmatullah. Viens"" ta ji ya amsa, ganin abin ta yi banbarakwai. Habu ne ya shigo" da sallama fuskarsa ɗauke da damuwa. "Ya yi ajiyar zuciya ya ce ""Hankalina duk a tashe, ya kira ni ya ce ba ki da lafiya, ba ki ci abinci ba tun safe""" "Nana ta waiwaya ta kalle shi, ya maze abin sa." """Ta ina ya gaya maka?""" """Ta waya"" Habu ya amsa mata." "Ta ɗan kwaɓe baki ta ce ""Abin da ma bai ce mini sannu ba, kuma yana kallo na kusa mutuwa""" Ayshacool "Habu ya yi murmushi ya ce ""Amma ya damu sosai ai, tun da ya kira ni kuma ya saka na tafi neman abin" "da za ki ci."" Ya ajiye mata ledar ya ce ""Ga abin da ya ce na sayo miki""" "Ta ce ""Ni idan bai ce mini sannu ba, ba zan ci ba""" "Habu ya kalle shi yana murmushi, ya yi masa magana da french." "Ba tare da ya kalli Nana ba ya ce ""Na faɗa ɗazu""" """Da yaushe?""" """Ki na bacci""" "Mamaki ne ya cika ta, jin ya yi doguwar magana, dan haka ta yi yinƙurin jan maganar." """Dama mutum ya san abin da ake yi ne, idan yana bacci, ni na ƙoshi""" """Sannu"" ya faɗa a taƙaice." "Habu ya ce ""Lallai abin mamaki, abin ya burge ni, ga kayansa nan an wanke an goge, tun da jikin naki da" "sauƙi, Alhamdilillah ni zan tafi""" "Nana ta ce ""Mun gode sosai, ka gaida gida""" """Allah ya sauwwaƙe ya ƙara lafiya"" bayan tafiyarsa Nana ta ci gaba da kallo, ba tare da ta taɓa ledar da" "Habu ya kawo ba, balle wadda ya shigo da ita." "Babu tsammani ta ji an fizge wayar hannunta, sai da ta tsorata, a fusace yake kallonta." """Ki ci abinci"" ya faɗa a hasale. Murmushi ne ya so kufce mata, amma a zahiri sai ta kwaɓe fuska kamar za" ta yi kuka. "Ya janyo ledar da ya fara shigowa da ita, ya buɗe ta kankana ce a ciki. Sai dai ta sha mamaki da ya buɗe" "ledar da Habu ya kawo ta ga gasashshiyar kaza. Ita dai ta san tsakiyar wata ne, a ina suke samo kuɗin da" "suke wadaƙa haka?""" """Ci"" ta kuma jin muryarsa." "Sai kuma ta yi tsuru-tsuru ganin yadda ya yi mata kwarjini, saboda ya kafe ta da ido. Kamo hannunta ya" "yi ya ɗora a kan kankanar ya ce ""Ci"" kamar mara gaskiya ta ɗauka ta kai bakinta." "Duk da gefe guda hankalinta na kan kazar nan, har da haɗiyar yawu, saboda sai tururi take yi ga ƙamshi." "Ya tashi ya ɗauki kofi, ya tsiyayo shayi, a cikin butar shayinsa, ya zo ya ajiye a gefen sa." """Ki ci"" ya kuma maganar yana zaro mata ido." "Ba shiri ta tattarata nutsuwarta, duk santa da kazar, kasa sakin jiki ta yi ta ci, saboda tsoron yadda ya" "tsare ta da ido, sai dai tana iya hango tausayi da damuwa a cikin idanun nasa." """Na ƙoshi"" ta faɗa a ɗan tsorace." "Ya ɗauki ɗan ƙaramin kofin da ya zuba shayi, ya miƙa mata, a zaton ta shayi ne, sai dai tana sha, ta ji" tamkar ta haɗiyi wuta. A take yanayinta ya sauya ta ji duniyar ta fara juya mata! Ayshercool 08081012143 Ayshacool https://chat.whatsapp.com/FMI9ln54k8E3VhCaqgRAZq Page 32 "Gani ya yi ta rintse idanunta, jikinta ya fara karkarwa, mamaki ne ya kama shi, ya duba cikin kofin ya ga" "shayi ne a ciki. Ya kai bakinsa ya sha, shi bai ji komai ba." "Murƙususu take yi, a galabaice tana jin tamkar ana yayyanka kayan cikinta, ta yi wani yinƙuri sai ta fara" "aman jini mai yauƙi. Ta ɗauki lokaci tana yi. Ta ɗaga kai da ƙyar, ta ga Buzu a tsaye a kanta, kafin daga bisani ya rikiɗe mata zuwa wannan tsohon. A razane ta fara ja da baya. Ya ja da baya ya buɗe bakinsa, zai fara feso mata wuta, Ƙaisar ya bayyana yana wani irin huci." "Tsohon ya buɗe bakinsa yana dariya mai razanarwa, hayaƙi na fitowa daga bakinsa, ya ce ""Na sani, na" "san za a rina, ta wannan hanyar ce kaɗai zan hukunta ka Ƙaisar""" "Cikin tsawa Ƙaisar ya ce ""Kuskure mafi girma da zaka aikata, shi ne cutar da yarinyar nan, cutar da uwar" "gijiyata tamkar cutar da ni ne, dan haka ni da kai muke wannan rigimar babu ruwanta, domin babu ta yadda za a yi ta biya bashin da ba ita ta ci shi ba""" """Ƙarya ne, sai ta biya shi, ita ce za ta biya ka sanya wannan a ranka. Ka fi kowa sanin ba ma yafiya, ba ma" "yafe bashin gaba, sai ta biya wannan bashin"" ya ɗaga sandarsa ya nuna Nana da ita, amma cikin zafin nama, ta ji an yi sama da ita an watsar a guri ɗaya." "A hankali ta ja jikinta tana tari, ƙaisar ya bayyana a gabanta, cikin ɓacin rai ya ce ""Ki sanya a ranki ba a yi" "komai ba, ƙalubale da tarkuna marasa adadi mun din ga faɗa musu kenan, idan mun tsallake wani, wani sai mun faɗa masa""" "Nana ta ɗago kanta a galabaice ta kalli Ƙaisar ta ce ""Wai dan Allah waye wannan tsohon? Me na yi masa," "Ko shi ne na aura a suffar mutum ne?""" """Sanin waye shi, ba shi da wani amfani a gare ki. Ki yi ta kanki da rayuwar ki kawai. Ko dai ki bar wannan" "auren mu tsira baki ɗaya, ko kuma yanzu mu ka fara wahala""." "Nana ta girgiza kai ta ce ""Sanin waye shi yana da amfani a gare ni, waye shi? Meye alaƙa ta da shi da" "yake tsorata ni, laifin me na aikata masa yake iƙirarin sai na biya? Da wace hujjar zan kashe auren nan? Ko har ka manta irin ƙalubalen da na keto?""" "Shiru Ƙaisar ya yi mata yana karkaɗe rigarsa, har ta buɗa baki za ta yi magana, ta jiyo sautin wata ƙara a" "bayan wata ƙofa, kuma ta ji tamkar ta san muryar da ta yi ƙarar." """Ihun me nake ji haka?""" """Je ki duba mana"" ya bata amsa yana yin gaba, ya nufi kofar da sautin ƙarar yake. Yana shiga Nana ta" "rufa masa baya, sai dai ta yi turus da ta ga Jamila a ɗaure a jikin wani itace, jikinta babu kaya, fatarta" "tamkar ta ƙone, ga wasu zarurruka da aka saka, aka ɗaɗɗaure ta da su." "Hankali tashe Nana ta ce ""Kai Jamila, me ta yi maka? Meya same ta haka?""" "Ƙaisar ya ce ""Me ta yi mini ki ke tambaya? Me ya faru bayan kin ci abincin da ta kawo miki? Idan Alhaji" "Zailani zai kassara yaran da ya haifa a cikin sa, saboda duniya ke me yasa ki ke tunanin dan kun haɗa uba" "ɗaya da ita ba za ta cuce ki ba? Dole ta karɓi hukuncin abin da ta aikata, ko da kuwa ya kama na kashe ta ne." Nana za ta yi magana ta ji ana taɓa fulon da take kai. "Ta buɗe idonta ta ga wani irin matsanancin duhu, babu alamar haske ta ko ina. Ta yinƙura ta tashi zaune," tana faɗin hasbunallahu wani'imal wakil. "Ta miƙe tsaye tana laluben hanya, ganin duhun na ƙara tsananta. Walƙiya aka yi mai tsananin haske, da" "ya gauraye ɗakin, ya bayyana tsaye da sandarsa yana kallon Nana. Rikicewa ta yi ta saka ihu. ta zabura za ta kasa da gudu. Tun da ta tashi tsaye a kan katifarta yake kallonta. Sai da ta yi ihun nan, ta nufi hanyar" "waje, ya miƙe da azama ya riƙe ta." Fizge-fizge ta hau yi cikin matsanancin tsoro da razani. """Me ya faru ne?"" Ya yi magana cikin nutsuwa da kamala." "Fashewa ta yi da kuka, cikin rawar murya ta ce ""Tsoro nake ji, dan Allah ka daina tsorata ni""" """Me na yi miki?"" Ya yi maganar fuskarsa ɗauke da damuwa." "Ta ɗaga kai ta kalli kamilalliyar fuskar sa, ya lumshe idanunsa ya buɗe a kanta. Ta sunkuyar da kanta tana" "jin yadda sanyi yake ratsa ta, zuciyarta take bugawa, jikinta sai tsuma yake yi." Ayshacool * "Da safe babu kowa a ɗaki sai Nana, ta shiga banɗaki ta yi wanka, ta gama ta buɗe ƙofar ta fito, ta ganshi" "yana gyara mata shimfiɗarta, ya karkaɗe mata. Ya ɗauki tsintsiya ya fara share ɗakin." "Ya ɗago suka haɗa ido, ya kawar da kansa ya ci gaba da shararsa. Saboda daga ita sai zanin wankanta ta" "fito, dan ba ta san yana ɗakin ba." "Nana ta ƙaraso ta ce ""Ka bari, zan share ɗakin, bari na shirya""" """Ba komai, ki huta ba kya jin daɗi"" ta ɗan ware ido, jin ya yi magana." "Ta numfasa ta ce ""Ina kwana""" """Wane kwanan?""" """Gaishe ka na yi fa"" ya ɗago ya kalle ta ya mayar da kansa ya cigaba da shararsa, ya gama ya kwashe ya" je ya zubar. "Ta shirya yana gefe yana aikin shan shayi, yana haɗawa da dabino yana ci." "Ta bubbuɗe kazar da Habu ya kawo, ta ɗumama, ta ɗibi miya ta haɗa su ta ƙara dafawa, ta zuba ta ajiye" a gabansa. "Ya girgiza kai ya ce ""Naki ne, ki ci""" "Ta ce ""Ai na ci, kai ba ka ci ba""" "Ya girgiza kai ya ce ""Na ƙoshi""" "Nana ta sake tura masa kwanon ta ce ""A'a ba ka ƙoshi ba, dan Allah ka ci"" ta yi maganar tana saka masa" cokali a kan kwanon. "Ya kama cokalin, ya ɗan yagi kaɗan zai kai bakinsa ya ce ""Bismillah"" Nana ta ɗaga kai ta kalle shi da" mamaki. "Jiki a sanyaye ta ce ""Na san wataƙila ina yin wasu abubuwa, da za ka kasa gane kaina, kamar ba ni da" "hankali wasu lokutan. Na san babu lallai an yi maka bayani, ina fama da rashin lafiya ne"" ta yi maganar tana wasa da yatsun hannunta." "Ya ce ""Aa yau ba ki yi rashin lafiya ba, kin warke ai tun jiya"" sai ta ga kamar bai fuskanci abin da take nufi" ba. "Ta tsura masa ido, tabbas ma sha Allah, kyakyawan ne, fari ne mai dogon hanci sosai da ɗan siririn sajen" "sa, kuma a nutse yake. Babu babban abin da yake ɗaukar hankalinta game da shi, bayan nutsuwar sa, sai wannan kyakyawan dogon gashin da yake da shi, tamkar mace. Duk da ta kasa tantance abubuwa da" "dama a kansa, amma zuciyarta na ɗauke da tarin tambayoyin da take fatan bakinta ya furta." "Ya ɗago shi ma ya tsare ta da nasa idanun, yana tauna a hankali. Ta sauke nata idanun ta ce ""Amm ban" "san sunanka ba haryanzu ba fa""" "Kamar ba zai yi magana ba ya ce ""Zan sha ruwa"" tana mamakin dalilin da ya sanya yake kaucewa wannan" "tambayar har sau biyu, sai ta ƙyale shi, ta ɗaukko ruwan ta ba shi." """To ka bani wayata, na yi kallo""" """A'a"" ya furta yana tashi tsaye. ya tafi gaban mudubi, ya fara shiri. Yana tsaka taje gashin nasa, ya hango" "Nana ta cikin mudubin, tana kallonsa. Ya ɗaukko comb ɗin ya nufo Nana, da sauri ta sunkuyar da kai." "Ya zo gabanta ya miƙa mata comb ɗin, ta tsaya tana kallon sa, ya ƙara miƙa mata. Ta saka hannu ta karɓa," "ya gyara zamansa ya juya mata baya, ya ɗan yo baya da kansa. Ta yi shiru tana kallon kan nasa." """Ki taɓa, na ga ki na so"" wata irin kunya ta kama Nana, haushin kanta ya kama ta, yadda ta bari har ya iya" gane gashin kansa yana burge ta. "Ta dafa kafaɗarsa, da nufin ta tashi, kawai ta gansu a wani ƙasaitaccen ɗaki na alfarma, maimakon ɗakin" su. "Ta kalli jikinta, ta ganta sanye da wasu kayan na daban. Hannunta dai riƙe da comb ɗin. Duk yadda ta yi" ƙoƙarin yin magana ta kasa. "Ta saka hannu, ta fara taje lallausan gashin nasa, ta gama ta tufke masa kamar yadda yake yi. Ya miƙe" "tsaye ya juyo ya kalle ta, ya kama hannunta ya sumbata ya ce ""Allah ya yi miki albarka""" "Kamar wadda aka jonawa shocking ta zabura, ta ga ɗakin ba kowa, ga dai kwanukan da ya ci abinci, ya" "wanke ya ajiye mata. Ta tashi tsam ta je ta leƙa ta taga, ta hango shi a zaune a kan kujera, a gefen gate" "ya kara radio a kunnensa, gefe ga butar shayin sa." "Ta dafa bango ta jingina a hankali, hawaye ya fara ziraro mata, a hankali ta ce ""Ka yi nasara ƙaisar, ka" "burkita mini ƙwaƙwalwata fiye da baya. Na fara hauka, ba na iya tantance zahiri, tunani da mafarki. Ka cutar da ni"" ta ƙarasa maganar tana sheshsheƙar kuka." "Muryar Ƙaisar ta ji tana amsa kuwwa a ɗakin. ""Ba ni ba ne, ko zan saka ki hauka ba yanzu ba, da sauran" "lokaci, ina ƙara baki lokaci ne. Abin da na yi ta yi miki gargaɗi a kai ne""" """Allah yana tare da ni, ba zan bayar da magani ba Ƙaisar, ba na buƙata ka ƙyale ni na yi rayuwata dan" "Allah"" ta ƙarasa maganar wani kukan yana kufce mata." Ayshacool """Nana"" ta ji muryarsa a bazata. Da sauri ya sauke rawaninsa a kiɗime ya ce ""Meya faru?"" Kasa magana ta" "yi, ta ci gaba da kuka." "Cikin damuwa yake kallonta, ya rasa abin da zai ce mata, ga shi da gaske kukan take mai tsuma zuciya." """Na yi wani abu ne?"" Ya furta yana kallonta. Ta girgiza masa kai alamar a'a." "Ya sake cewa ""Ba lafiya ne?""" "Ta sake girgiza masa kai. Ya saka hannu ya dafa kafaɗarta, a take wani irin sanyi ya shige ta, har" ƙafafuwanta. "Babu tsammani ya haɗa ta da ƙirjinsa, duk da tana jin yadda zuciyarta take harabawa da sauri, amma ta" "yi shiru ba ta motsa ba, ba ta tunanin a rayuwarta, akwai wanda ya taɓa ba ta wannan damar. Maimakon ta daina kukan, sai ta sake fashewa da sabon kuka, sababbi da tsofaffin damuwoyinta duk suka taso mata. A hankali ta ji ya zura hannunsa a cikin nata ya riƙe." "Duk da a ƙasan zuciyarta, tana jin mafarki ne, amma ta ji daɗin samun damar zubar da hawayen nan da" ta samu. * "Tamkar zai tashi sama, haka yake bala'i yana kumfar baki." """Ai dama na sani, wallahi haryanzu tana son tsohon mijinta, kuma tana magana da shi ta waya, ina da" "cikakkiyar shaida a kan hakan""" "Wata babbar mace da fuskarta ke ɗauke da damuwa ta ce ""A'a Iliyasu, ba na tunanin Mai jidda za ta yi" "haka""" """Au goya mata baya za ayi ma kenan? Ina da cikakkiyar shaida, ba na son mutuncinta ya zube ne kawai" "saboda 'ya'yana""" """A'a ba goya mata baya zan yi ba, amma ka yi haƙuri dan Allah""" """A'a a yi magana a buɗe, idan tsohon mijinta take so, to ta koma gurinsa ba dole""" "Maijidda na gefe tana ta sharɓar kuka, tamkar ranta zai fita, ya gama bambamin masifarsa ya fice daga" gidan. "Matar ta dawo da hankalinta kan Maijidda ta ce ""Wai maijidda abin da Iliyasu ya faɗa gaskiya ne? Ana" "idar da sallar asuba fa ya kira ni a waya ya ce lallai na zo na ji abin da ki ka aikata""" "Cikin kuka ta ce ""Wallahi Adda ba a yi haka ba, roƙonsa kawai na yi ya bani dama na je na ga halin da" "yarinyata take ciki, an ce mini an yi aurenta, amma ban sani ba, ko ba komai Nana da Imaran su ma" "yarana ne, na rasa irin wannan abu ƙiri-ƙiri an raba ni da yarana""" "Adda ta ce ""To ke mai jidda ban da abinki, ba a gurin babansu suke ba? Ko a kan yara biyu sai ki" "salwantar da aurenki, da yaran nan shida saboda guda biyu ne?""" "Ta ɗago jajayen idanunta ta ce ""Adda su ma biyun ni na haife su, ba su da kama ta, su na buƙata ta," "shekara goma sha ina tattalin wannan auren, duk da ƙiyayyar da yake nuna wa 'ya'yana amma wallahi" "zuciyata na Kano tare da Nana da ɗan uwanta""" """Aikuwa sai ki yi haƙuri, Allah ya ƙaddara abin da zai riga ya faru. Yanzu ki bari zan shirya da kaina, ki" "kawo abin da ki ke da shi da ki ka ajiye saboda aurenta, mu haɗa a kai mata ke dai ki yi haƙuri da zuwa," "zuwa lokacin da zai saukko. Bari na kira shi a waya""" "Adda ta kira Iliyasu, sai da ta ta tsinke ta sake kira, sannan ya ɗaga." """Dan Allah malam Iliya ka yi haƙuri, ita ma ta ce a baka haƙuri, ba za ta sake ba""" """A'a ai na daɗe ina fuskantar take-takenta ne, kuma wallahi ba za ta sake riƙe waya ba, kuma wallahi ta" "sake ta taka zuwa ƙafarta zuwa garin Kano, ta fake da yaranta ta haɗu da tsohon mijinta, a bakin aurenta tun da ni na ɗan iska ba ne""" """Ai ba ma za ta sake ba, ta tuba ta daina ka yi haƙuri ka yafe mata"" ya gama bala'insa, Maijidda na jin sa" ba abin da take yi sai kuka. """Maijidda ki yi haƙuri, idan ki ka kashe auren nan saboda yara biyu ya za ki yi da na gaban ki? Duk abu" "gidan nan akwai ci akwai sha. Idan ki ka koma gidan Gwaggo ma, ita ba cikakkiyar lafiya ba, ga babu guri" "gara ki yi haƙuri. Ita yanzu tun da ta yi aure ta samu ta zo inda ki ke"" Adda ta gama maganganunta," Maijidda ba ta sake tofawa ba. **** "Habu ne a tsaye a ƙofar ɗakin, yana kwaɗa sallama, ya amsa masa." "Ya ɗaga labulen ya shiga, kawai ya tarar da su a zaune a gefen katifa, Buzu yana fifita mata shayi a kofi," "gabanta kuma ga ledar ƙosai ga kankana. Tana tauna ƙosan a hankali, fuskarta duk busasshen hawaye." Ayshacool "Cikin damuwa ya ce ""Amarya, meya faru ne? Ya kira ni hankali a tashe ya ce kina kuka, ko wani abin ya yi" "miki ne da ba kya so?"" Ta ɗaga kai ta kalle shi, sai kuma ta ji tausayin sa ya kama ta, daga shi har Habun." "Ta ce ""Ba abin da ya yi mini fa""" "Habu ya ce ""Kar ki ji komai, gaya mini idan wani abun ya yi miki ma?""" """Bai yi mini komai ba""" """Subhnallah, amma hankalinsa ya tashi sosai da sosai fa ya kira ni ya gaya mini, ki na kuka bai san" "meyafaru ba. Ko ba kya son sa ne?""" "Nana ta ɗaga kai ta kalle shi, aikuwa ya tsare ta da ido, da alama jiran amsar sa take yi. Ta kawar da" kanta gefe tana murguɗa baki. "Habu ya yi shiru yana murmushi, buzu ya miƙa mata kofin shayin, ta karɓa, sai dai ta tuna wancan karon" "da ya ba ta abu ta sha, hankalinta gushewa ya yi, dan haka ta ci gaba da riƙe kofin a hannunta." "Ganin babu wata matsala ya sanya Habu ya ce ""To ni bari na tafi, amma dan Allah a daina yi masa rigima," "ni bari na tafi""" "Suka yi magana da french, Habu ya yi musu sallama, ya tafi." "Yana tafe a hanya, hana murmushi yana yi musu fatan alkhairi, domin ya ji daɗin yadda ya gan su." """To kai ma ka ci ƙosan mana"" ta yi magana tana ɗaukkowa ta miƙa masa." "Ya saka hannu ya karɓa, ya saka a bakinsa." "Nana ta numfasa ta ce ""Daga yanzu idan ina yin kuka, ko bani da lafiya, ka daina gaya musu, ka ga an" "saka shi yana ta zuwa, kuma da nisa daga can zuwa nan""" "Ya dube ta ya ce ""To ki daina""" """To, amma dama wai ka na magana haka, amma sai ka din ga yi mini shiru? Ba na jin daɗin hakan" "gaskiya"" ya ɗan yi murmushi ya ce ""Ɗaukewa take yi""" """Me?""" """Maganar "" ya bata amsa." "Cikin mamaki ta ce ""To ta yaya maganar mutum take ɗaukewa, kamar wutar nepa?""" "Ya ce ""Ban sani ba, wataran ma yaren naku, ɗaukewa yake yi, na manta duka""" "Kawai ta ɗauki kalaman nasa, a matsayin zolaya, sai ma suka bata dariya." """To ni dai ka gaya mini sunanka""" """Buzu""." "Ta ce ""Ai Buzu ba suna bane ba, sunanka na gaskiya""" """Shi na faɗa""" """To ai Buzu ba suna ba ne ba, kamar sunan ƙabila ne""" "Horn ɗin mota suka ji, a bakin gate, dan haka ya tashi ya fita ya je ya buɗe, bayan ya buɗe, ya ƙi dawowa" ɗakin ya yi zamansa a waje. "Sai bayan sallar isha'i ya dawo, ya ci abinci ya nemi guri ya ɗaukko wayarta, ya kunna film ɗin Indiya" fassarar hausa yana kallo. "Ta ƙura masa ido, duba yadda ya tattara nutsuwar sa a kan screen ɗin wayar." """Wai zuwa yaushe za ka bani wayata ne? Ina son kiran su Anty Ummi, tun da suka tafi ban kira na ji yaya" "suka je gida ba"" ya yi mata shiru, ya ci gaba da kallon." "Zaman shirun ya dame ta, ga wayarta a hannunsa, ga babu abokin hira. Ta kwanta bacci da wuri ko za ta" "yi bacci, amma ta kasa." Da ƙyar bacci ya ɗauke ta. "Daf da kiran sallar asuba ta tashi, ta shiga banɗaki ta duba, ta ga ta samu tsarki, ta yi wanka ta yi alwala" "ta fito. Ta kunna fitilar ɗakin, haske ya gauraye ɗakin, ba ya cikin ɗakin. Duk da wasu lokutan idan ta kwanta bacci ba ta iya tantance mafarki ko kuma zahiri, amma ba ta tunanin da idonta ta taɓa ganin ya kwana ɗakin. Ko dai ya kwanta a farkon dare, tsakiyar dare ta neme shi ta rasa, ko farkon dare baya nan," cikin dare ta ganshi kafin asuba ta neme shi ta rasa. "Har ta doshi ƙofar ɗakin, da niyyar ta ɗaga labule ta duba, ta gani ko yana waje, amma ta fasa da tuna" "abin da ta gani a wancan karon. Babu tsammani iska ta kaɗa labulen, ta hango shi a kan benci a kwance ya takure, yana bacci." Sai ta ji tausayin da ya kama ta. "Ta tayar da salla, ta yi nafila raka'a biyu, ta zauna ta din ga istigfari da salatin annabi Sallallahu alaihi" Wasallam. Bayan ta gama ta ɗaga hannayenta ta din ga tasbihi duk wanda ya zo bakinta yi take yi. La'ilahaillalahul azimul halim La'ilahaillalahul jalilul jabbar La'ilahaillalahul kabirul mut'al La'ilahaillalahu muɗɗali'i sittar La'ilahaillalahul khaliƙul laili wa nahar. "Allahu Allahu rabbi, la ushriku bi hi shai'an." Ayshacool "Allahumma inni as'aluka bi anni, ashhadu annaka antal ahadussamadu lazi lam yalid wa lam yulad, wa" lam yakun lahu kufwan ahad. "Sai da ta gama tasbihin kaf, sai kuma ta rasa abin da za ta roƙa. Ta sauke hannunta a hankali ta yi shiru," "kawai daga bisani ta rufe da sayyidul istigfar, dai-dai lokacin an kira sallar asuba." "Ƙarar zubar ruwan famfo ta ji, ta dake ta je ta leƙa, ta hango shi a durƙushe yyana alwala. Ya idar ya zare" sakatar gate ya fice. """Abin mamaki, mutum mai taɓin hankali ya san salla, ya san addini anma kuma a ce ba shi da lafiyar" "ƙwaƙwalwa anya kuwa?"" Ta tambayi kanta." """Zan ci gaba da tunzura ka, da ƙoƙarin ƙure haƙurinka, har sai na tantance ainihin jinsin ka, sai na gano" "ko kai waye!"" Ji ta yi an bushe da dariya mara daɗin ji, gaba ɗaya ɗakin ya ɗauki sautin." AYSHERCOOL 08081012143 Ayshacool Page 33 "Ƙoƙarin dai-daita nutsuwarta ta yi, ta tattara hankalinta guri guda." "Ta fara jin sanyi yana ratsa ta, ta din ga nanata Innalillahi wa innalillahi raji'un. Sai kuma ɗif tamkar an yi" "ruwa an ɗauke, ta daina jin sautin dariyar." "Ta tafi banɗaki, ta sake yin alwala, ta zo ta yi raka'atanul fajari, sannan ta yi sallar asuba." "Ta zauna a kan daddumar, tana kallon wardrobe, tana son ta je ta ɗaukko Alqur'ani, amma ta kasa tashi." "Ta yi ƙoƙarin yin karatun Alqur'anin da ka, ta karanta abin da ta sani, amma ta ji tamkar an tattare komai" daga cikin kanta an kwashe bar mata fanko. "Ba ta san me ya ci gaba da wakana ba, ta ji an taɓa hannunta. Ta buɗe idonta ta ɗaga kanta ta kalle shi." "Ta ganta zaune a kan daddumar, sai dai gari ya yi haske sosai, da alama takwas ma ta wuce." "Ya nuna mata ledar hannunsa ya ce ""A zo a karya, ga abinci"" ƙamshin soyayyen ƙosan ya daki hancin" Nana yawunta ya tsinke. Duk son ta da ƙosai ta girgiza masa kai. "Ya ce ""Me yasa?""" """Azumi na ɗauka""" """Da izinin wa?"" da fari shirin tashi take yi, babu shiri ta koma ta zauna, tana bin sa da ido. Mamaki take yi" har ya san sai da izninsa za ta yi azumi?. "Ya kamo hannunta, ya juyo cikin tafukan hannun ya ce ""Kalli, kin zubar da jini sosai, ta ya ya za ki ɗauki" "azumi? Ki ci abinci""" "Ta noƙe kafaɗarta ta ce ""Ni ba zan karya ba, na riga na yi niyya, ka bari daga wannan idan zan kuma yi" "zan gaya maka in sha Allah""" "A fuskarsa ta ga alamar ya ji haushi, saboda yadda y tsuke fuskar, kawai ya gyaɗa kai ya ce ""sai ki yi na" "gani"" ya tashi daga gabanta. Ta bi bayansa da kallo, yana tashi ita ma ta tashi, ta haye katifarta saboda bacci kanta har wani nauyi ya yi mata." * "Jamila fatar jikinta, ta warke, amma da ƙyar take tafiya tamkar tsohuwa. Hatta banɗaki sai an kai ta," komai a duƙe take yin sa. "Babu shiri Mama ta ɗauki Jamila, ta kira ƙanwarta ta raka ta zuwa gurin wani mai magani, tana ta bala'in" "daga zuwa gidan Nana wannan masifar ta afka mata. Ta din ga faɗan ba yadda ba ta yi da su ba, a kan kar su je gidan Nanan, tun da dai alkhairi babya bibiyar ta, amma suka nace su ka tafi." "Ko da suka je gurin mai maganin, ya ƙare wa Jamila kallo ya ce ""Gaskiya wannan ya fi ƙarfina, sai dai na" "nemo Ibrahima wakilin rafi, ya duba ta. Idan da wani abu ma duk zai yi muku bayani""" "Mama ta ce ""Waye hakan? Kuma a ina yake?""" "Ya ce ""Kar ki damu, yanzu za ki gani, ba a nesa yake ba, yana nan kusa""" "Mama ta ce ""To madalla, mun gode sosai da sosai """ "Mutumin ya tashi, ya din ga tattara shirgi a ɗakin, da tsummokara ya cika gurin da su, kamar ɗakin" "mahaukaci. Sannan ya buɗe wasu manyan randuna a shaƙe da ruwa, ya barbaɗa wani magani a ciki. Ya buɗa wata jaka, ya kwaso wasu tarkace, ya ɗaura wani guru a damtsensa, sannan ya saka yaronsa ya kawo masa, garwashi a cikin kasko, ya turare ɗakin da wani irin hayaƙi mai warin gaske, sannan ya nemi" guri ya zauna a tsakiyar shirgin nan da ya baje. "Ya sunkuyar da kansa, ya din ga karanto wasu abubuwa da ba a iya gane me yake cewa, saboda ba yaren" "hausa ba ne, yana yi yana kaɗa kansa." Can bayan wani lokaci ya ɗago kansa a hankali. "Gaba ɗaya kamaninsa sun sauya, fuskarsa duk ta wani tattare tamkar tsoho, jikinsa kuma sai karkarwa" "yake yi, kamaninsa sun canza." "Ba Mama ba hatta Jamila, a tsaroce suka ja da baya, su na rarraba ido." "Ya ƙure Jamila da ido sannan ya ce ""Wannan ai wani aljani ne yake jinya a jikinta"" Ba Jamila hatta Mama" "cikin bala'in kiɗima da tashin hankali, ta kalli mai maganin ta ce ""Aljani yake jinya a jikinta kuma, na shiga uku na lalace, ta yaya?""" """A'a ba ki shiga uku ba, uban duƙusa su ka yi wa laifi da alama, ya hukunta su ne, su duka daga ita har shi" "a haka""" "Cikin rashin fahimta ta ce ""Wa kenan?""" """Wani aljani ne shi ma""" "Cikin damuwa ta ce ""Ya za a yi Jamila ta ga aljani ta yi masa wani laifi?""" """To wannan kuma wani abu ne daban, ba na son dai yin doguwar magana, balle dogon jawabi, amma" "idan ta nutsa ita ta san ta yi laifin. Yanzu dai zan baku magani, na sha da shafawa, sai kuma wanda za ta" din ga sheƙa kafin ta kwanta bacci. Ayshacool "Daga nan sai kuma a samu ƙosai mai zafi, a yi sadakarsa bayan la'asar. Amma iya ƙanan yara wanda ba" "su kai shekaru goma ba, su za a bawa. Za ta miƙe gaba ɗaya, ta warke. Sai kuma a nemi saurayin zakara, a yanka a fige shi a sulala, da almuru idan an gama rabawa yaran ƙosan, a tona rami a binne zakaran. Zai bar jikinta ya yi jinya a wani guri. Wanda kuma su ka ba ta aikin. ta yi musu su za su ɗauki ragamar ba wa uban duƙusa haƙuri. Ni ba ma shi nake ji ba, an riga an nakasta aljanin har abada. Ya ƙone sosai daga feshin wutar da aka yi masa. Wata ƙila ya yafe mata gaba ɗaya, wataƙila kuma shi ma ya ce sai ya rama," "duk da babu lallai ya samu damar hakan ƙungiya ba za ta ba shi wannan damar ba""" "Cikin tashin hankali ta ce ""Ni fa duk ban fahimta ba, ka na maganar ƙungiya, bayar da haƙuri, duk me ya" "kawo wannan zancen?""" "Ya ce ""Ki bar shi a haka kawai yadda na gaya miki """ "Cikin damuwa ""Ni dai malam ka taimake ni dan Allah, ka da yarinyar nan ta nakasa ita ma. Yayarta ta nan" "haka take ta fama da aljanun nan, da ƙyar ta yi aure tamkar za ta haukace, daga zuwa gidanta ta gamu" "da wannan masifar""" """Kar ki damu, ba wani abu"" Ya ɗaga hannunsa sama, ya dunƙule ya watsowa Mama wani ƙulli guda uku," "ya ce ""A je a yi mata wanka da shi, za ta ware, na baƙar takarda shi ne na shan, sai na shaƙar""" Bayan ya basu maganin ya sallame su. **** "Haɗuwa da kuma ƙasaitar ɗakin, ya sanya Nana sakin baki tana ƙarewa ɗakin kallo, tare da tunanin yau" kuma a ina take?. "Sai dai yanayin adon da aka yi wa ɗakin, ba wai ado ne irin na wannan zamanin da muke ciki ba. Ta ɗaga" "kai ta kalli rufin ɗakin, sai dai ga mamakinta, sai ta kasa tantance wani irin rufi ne, gini ne dogo mai matuƙar tsawon gaske. Sai da ta kalli wani sashi na jikin ɗakin, sai ta ga ya yi kama da cikin dutse,, ba wai gini ne na bulo ko ƙasa ba." "Wani irin ƙamshi ya karaɗe ilahirin ɗakin, amma shi ma ƙamshin sai ta ji bai dace da wannan zamanin ba." "A hankali ta kalli gadon da take kai a zane, ta shafa saman gadon, wani irin laushi na ban mamaki," "bayanta ga fululluka a ajiye. Jin motsi ya sanya ta zabura ta waiwaya zuwa inda take jin motsin. Sai a yanzu ta hango wani sashi da ta sani a gurin. Gurin da ta gan ta jiya tana taje masa gashin kansa ne. Gadon ya tunkaro da kofin shayi a hannunsa yana takawa a hankali, jikinsa sanye da wata doguwar riga" fara ƙal. "Sai da ya zo gaban gadon sannan ya ajiye kofin a gefe, ya taka wani abu ya hawo gadon." "Kallonta yake yi yana wani irin murmushi mai ƙayatarwa, ya sumbaci bakinta ya ce ""que se passe-t-il?""" """Ban iya ba"" ta bashi amsa tana kallonsa ta ƙasan idonta." "Ya yi dariya yana rungume ta a jikinsa ya ce ""Me ya faru na ce"" ya yi maganar yana shafa gefen fuskarta." "Ta ɗan tura baki ta ce ""Ni sanyi nake ji"" ta yi maganar kamar za ta yi masa kuka." "Ya ɗan girgiza kai ya ce ""Ai ina kusa da ke, kwantar da hankalinki yanzu zan ba ki ɗumin da ya dace da" "yanayin jikinki, wanda ba zai cutar mini da une ame(Soul/ruhinki ba). Ni ma ki bani wanda ya dace da ni," "ni sanyin nake buƙata"". Ya yi maganar yana rungumeta a jikinsa, cike da shauƙi." "Tamkar almara haka Nana take ganin abubuwan da suke faruwa a tsakanin ta da shi, Kasa saita kanta ta" "yi a dalilin yadda jikinta yake wata irin tsumar da tun da aka haife ta, ko a duniyarta ta zahiri ba ta taɓa tsintar kanta a makamancin wannan yanayin ba. Ita duk yadda take tsintar kanta a mabanbantan yanayi, da gurare ba ta taɓa mafarki makamancin wannan a rayuwarta ba. Ga shi ya fi kama da zahiri ba mafarki" ba. "Amma duk da haka, ta bar wa zuciyarta mafarki ne, babu tunanin komai take biye masa, tamkar" "masoyan da suka shafe tsawon lokaci, cikin matsananciyar soyayya da ƙaunar juna." "Bayan wani lokaci a hankali ya buɗe idonsa, ya ƙura mata ido idanunta a lumshe. Ta buɗe nata suka yi" ido huɗu. "Ta ɗan zaro masa ido, tare da murguɗa masa baki ta ce ""Meye?""" Ayshacool "Ya yi murmushi ya ce ""Komai ma, je suis heureux (Ina cikin farin ciki) na samu farin ciki amma ba cancan" "ba saura sex... Hannu ta saka ta toshe masa baki tana hararsa. ""Kai ba ka jin kunya ne? Ka ke faɗar irin wannan maganat?""" "Dariya ya yi, yana ƙoƙarin cizon hannun nata. Ya ce ""Yanzu ma ai ba mu ji kunyar ba, tun da..." "Ba ta bari ya ƙarasa ba, ta yinƙura ta kama kafaɗarsa, za ta cije shi, ya mirgina ta yana dariya." """Haryanzu ka ƙi ka gaya mini sunanka"" ta yi maganar tana lumshe idonta" """Ƙasair"" ya furta a taƙaice." """Ƙaisar kuma?"" Ta furta a zahiri bayan da ta buɗe ido, ta ga yadda take ƙanƙame da pillow." "Juyowa ya yi daga inda yake zaune, da wani ɗan ƙaramin littafi a hannunsa, suka yi ido huɗu. Kawai ya yi" wani irin murmushi yana ɗan kaɗa kai ya ci gaba da kallon ɗan ƙaramin littafin. "Ta tashi tana ƙarewa kanta kallo, tana jin abin da ya faru a tsakanin su a jikinta, dan hatta ƙamshin" "turaren da yake yi, shi take ji haryanzu." "Ita dai ba gwanar nannauyan bacci ba, balle ta ce ko abin ya faru a zahiri tana bacci. Ko da tana gurin" "ƙaisar da an taɓa ta take tashi. Wasu lokutan ko tsayuwa aka yi a kanta, sai ta farka." "Sai dai ba ta gama razana ba, sai da ta ji ta ba a daidai ba gaba ɗaya. Da sauri ta tashi ta tafi banɗaki," "cikin damuwa. Sai dai ko da ta duba, ta sha mamakin abin da ta tarar. Abin da ya faru a mafarki ta gan shi a zahiri, azumin ya karye ɗungurungum, kamar yadda ya gaya mata." "Ta jingina da bangon banɗakin, al'amuran sun fara ba ta tsoro, ta yaya mutum zai biyo ta cikin mafarki," "har ya aiwatar da abin da ya ce? Yaya aka yi ta iya biye masa haka, babu kunya babu jin nauyin sa, duk" "al'amarin baƙi ne a gare ta, kuma ta farka sun haɗa ido yana murmushi, kamar dai ya san abin da ya faru." "Maganganun Ƙaisar su na ta ƙara tabatta ba ta tunanin ɗan Adam ne Buzun nan. Jiki a matuƙar sanyaye," ta yi wanka. "Ko da ta fito ba ya ɗakin, ba ta ko yi yinƙurin gyaran ɗakin ba, ta zauna zaman jiransa." * "Mama ce take zaune a ɗaki, tana ba wa Suwaiba labarin yadda aka yi a gurin malamin nan." """Ni anya ma kuwa Suwaiba, idan Jamila ta warke, ba gurinsa za mu koma ba, ya haɗa muku maganin" "farin jini, tun da wannan karon na ga kamar maganin malam Ɗayyabu bai yi ba""." "Suwaiba ta ce ""To mama, a bari dai a fara ganin yanayin jikin nata, amma na yi mamaki da aka ce wai" "aljani ta yi wa laifi. Ni na fara zargin Nana wallahi""." """Ai idan na faɗa wasu lokutan haushi ku ke ji, a zo a sayo mini waken da zan soya a yi sadakar nan," "anjima kaɗan na je na sayo zakaran nan. Kar rana ta take an ce ƙosan da zafinsa ake so a bayar""" "Nasiru ya ce ""Mama shi ƙosan ne zai ba ta lafiya? Allah kawai za.." """Rufe mini baki kafin na ragargaje ka a gurin, dama yadda ka ke shishshige mata kafin ta tafi, duk ka ko yi" "miyagun halayen ta""." **** "Nana ko karyawa ba ta yi ba, ba kuma ta da niyyar ɗora komai, ta zauna zaman jiran dawowar sa." "Ba a yi mintuna talatin ba ya shigo, hannunsa riƙe da ledar buredi." "Ya ajiye mata a gabanta, bai yi magana ba zai juya, ta riƙo rigarsa ta tashi tsaye." """Ina son na san waye kai? Me na aura? Na kasa fahimtar abubuwan da suke faruwa ka yi mini bayani"" ta" yi maganar numfashinta na fita sama-sama. """Waye ni?"" Ya yi maganar cike da mamaki, yana kallonta." "Ta ce ""Eh shi nake son sani, ba na gane abubuwan da suke faruwa, ka yi mini bayanin waye kai? Daga ina" "ka ke? A ina danginka suke? Saboda na samu nutsuwar zuciya da kwanciyar hankali ka gaya mini""" """je ne sais pas (ban sani ba) ni ma haryanzu ban san waye ni ba""" "Ta buɗe baki za ta yi magana ya riga ta ta hanyar cewa ""Ki yi mini magana cikin girmamawa, ki daina" "ɗaga mini murya""" """Ni ba ni da nufin ɗaga maka murya, amma ka yi mini bayani, ba na gane kan yadda al'amura suke" "faruwa, ta yaya za ka din ga bi na cikin mafarki kuma... Sai kuma ta yi shiru, ganin yana sauraren ta da mamaki a fuskar sa." """Kuma me?""" """Ka din ga tsorata ni"" ta ƙarasa a sanyaye." Ayshacool """Ni kuma? Ta yaya zan bi ki mafarki? Mafarki ba gaske bane ai, kuma wani ba ya shiga baccin wani. Kuma" "me na yi na.."" sai kuma ya yi shiru, ya kasa ci gaba maganganun da yake son yi, suka tsaya a iya ƙirjinsa da maƙogwaronsa." "A ƙoƙarin sa na ya yi maganar, kawai sai ya fara tari, ba tare da maganar ta fito ba. Sai kuma Nana ta" "rikice ta fara dana sanin abubuwan da ta gaya masa. A take Ƙaisar ya faɗo mata. Ta san babu abin da ba zai iya aikatawa ba, duk domin ta amince da abin da yake so." """Sannu, ko na baka ruwa?"" Ya girgiza mata kai ya fita." "Kawai ta zauna ta tattara hannunta, ta zabga uban tagumi ta ma rasa mene ne abin yi, a tsakanin shi da" Ƙaisar waye yake raina mata hankali. "Tun da take ta taso, ta fara ganin Ƙaisar a siffofi daban-daban, bai taɓa yinƙurin yin makamanciyar" "wannan alaƙar da ita ba, ko a farke ko kuma a bacci. Ita hasalima idan ana irin wannan zantukan har mamaki take yi, ba ta taɓa jin wani abu mai kama da feelings ba, sai da aka yi mata wannan auren, ta fara rayuwa inuwa ɗaya da wannan Buzun." "Sai dai yadda mafarkin nata ya kasance, tamkar zahiri ba mafarki ba, tun da har ta farka ta tarar" sakamakon abin da ya kwana a zahiri. "Guntun tsaki ta ja, ta tashi da ƙyar ta fara gyaran ɗakin." "Da ta gama ta shirya cikin hijjabi ta fito harabar gidan ba ta gan shi ba, kawai ta yi shigewar ta cikin gidan." "A falon gidan ta tarar da matar, tana mopping, Nana ta gaisheta. Ta ɗan saki fuska ta amsa ta ce ""Kwana" "biyu ba ki shigo ba""" "Nana ta ce ""Ba ni da lafiya ne, kawo na yi miki""" """A'a ba komai, kar ki damu zan goge"" Nana ta ƙarasa ta karɓa ta ce ""Bani zan goge. Masu aikin naki ba su" "dawo bane?""" """Wallahi tsoron su nake ji ne, tun da suka yi mini sata ne, su ka gudu sarƙoƙinmu na gold kaf suka sace." "Shi yasa yanzu nake ƙoƙarin mu yi komai da kanmu falon ma sai a yi sati ba shara, tun da ba yara""" "Nana ta karɓi mopping, ta goge ɗakin tsaf, sai dai ta din ga jin jikinta wani iri babu daɗi." "Har su Tv duk Nana ta karkaɗe ta goge mata, bayan ta gama sai ga wani saurayi mai kama da matar ya" "shigo, da gayyar abokansa." "Bayan Nana ta gama da falon ƙasan, matar ta ce ""Dan Allah taimaka ki karkaɗe mini falon saman ma""" "Nana ta ce ""Babu damuwa"" ta hau saman benen, sai dai hawanta ke da wuya, ta ƙara jin jikinta babu" "daɗi, kamar za ta fita hayyacinta. Sai ta fara sauri ta yi ta kammala, ta kammala kafin wani abin ya faru." "Ga mamakinta ta ga wata matashiyar budurwa, za ta ɗan girme mata, ta fito daga wani sashi na ɗakunan" "saman benen, tsiga-tsigal da siraran ƙafafuwanta ta saka mini skirt sai vest a jikinta." "Nana ta kalle ta ta ce ""Sannu ina kwana"" Sai a lokacin ta kula da Nana ta ce ""Yauwwa"" ta nufi wata ƙofa." """Siyama"" matar ta kira sunanta. Cak ta tsaya ta waiwayo ta ce ""Na'am""" """Wai Yusra ba za ta fito ta karya ba ne?""" "Siyama ta ɗan ɗage kafaɗa ta ce ""I don't know""" "Matar ta ɗauki wayar ta, ta danna sannan ta kara a kunnenta." """Ki fito falo, ina son ganin ki"" ta ajiye wayar, tana mita ƙasa-ƙasa. Nana a ranta ta din ga mamakin, da" "mata kamar wannan a gida, amma a ce saboda babu mai aiki an yi sati ba a yi shara ba." "Nana ta nemi guri ta yi zamanta a kan carfet, tana kallon t.v. sai dai har ta shafe lokaci a zaune, ba ta ga" wadda aka kira ɗin ta fito ba. "Aƙalla Nana ta kai awa biyu, tana kallon film a MBC2 na divergent. Sai da aka gama ta yinƙura ta tashi ta" "ce ""Na tafi""" "Matar ta ce ""Har za ki tafi? Duba dining akwai ragowar bredi, ina ga har da sauran dankali ma ko za ku yi" "amfani da shi""" "Nana ta yi murmushi ta ce ""A'a Hajiya na gode sosai, idan na tafi da shi sai dai na ajiye, a ƙoshe muke sai" "anjima"" ba ta ma jira mai Hajiyar za ta ce ba, ta yi waje abin ta, tana jinjina rainin hankalin matar, dan" wulaƙanci ma ita za a bawa ragowar buredi. "A harabar gidan ta hango shi yana ta kaiwa yana komowa, ita tun da ta samu kallo ma har ta manta da" "shi. Wani irin kallo ya yi mata da sai da ta ɗan tsorata. A hankali take takawa tana satar kallonsa, har ta wuce bai kula ta ba, bai kuma bi ta ɗakin ba." *Ayshacool "Alhaji Fatuhu ne yake zaune yana kallo, ya ɗan kalli matarsa Fadila ya ce ""Kin an yi wa malamr su Muhsin" "aure kuwa?""" "Ta ce ""Haba dai?""" """Ƙarya na yi kenan?"" Ta dafe bakinta da sauri ta ce ""Afuwan""" "Ya ce ""Haka na ji a bakin Yaya Sa'a, ashe wai ta santa""" "Fadila ta ce ""Haka na ji ranar da ta zo gaisuwa, amma ba ta kyauta ba, abin babu gayyata""" """Ni tun kwanaki ta ce mini za ta yi auren ai, na ma zata tuni an yi fa, ashe sai kwanan nan aka yi, amma" "duk da haka zan bayar da wani abun a bata""" """Gaskiya yakamata, ni ma zan bayar, ina fatan Allah ya kawo rabo, ta yi yaronta takwara""" Ya ɗan yi murmushi yana tuna yaron nasa. "Ta ce ""Yauwwa Daddy, ya ciwon kan kuwa?""" "Ya ɗan ɓata fuska ya ce ""Ke dai a yi sha'ani kawai, daurewa nake yi amma duk da haka Alhamdilillah""" """To sannu Allah ya ƙara afuwa""" """Amin babyna"" ta yi murmushi tana ɗan yi masa fari da ido." * "Yunwa ce ta ishi Nana, ita ba azumin ba, amma ba ta ci komai ba, ta ɗora girki, sai dai fafur ya ƙi shigowa" ɗakin. "Muryar Habu ta ji yana ta kwaɗa sallama, ta saka hijjabi ta leƙa, ta ga Buzu ba ya gurin. Ta amsa sallamar" ta ce ya shiga. "Ya shiga yana sake sallama, ta amsa masa ta ce ""Ina ga ya ɗan fita ne""" "Cikin damuwa ya ce ""Ya fita kuma, ina yaje?""" "Nana ta ce ""Nima ban sani ba, amma ai dama yana fita""" """Duk da haka, kar ya din ga nisa, ki din ga hana shi fitar, kin san ba shi da cikakkiyar lafiya""" "Nana ta ce ""Ta yaya zan hana shi fita, ni ka zo gaɓar da nake son a zo. Ni fa mutumin nan tun da aka yi" "auren nan, ko sunansa ban sani ba, kullum na tambaye shi sai ya ce mini sunan shi Buzu. Yakamata na san waye shi, a ina ku ke a ƙasar ku? Kuma yaushe za mu je na ga danginku. Tun da a haka tawa ƙaddarar ta zo.""" "Habu ya numfasa ya ce ""Kin yi gaskiya Amarya, shi yasa na yi ta ce miki ki yi haƙuri, ki karɓi ƙaddara, sai a" yanzu na ƙara tabattar da wannan ƙaddarar ce ta haɗo mu baki ɗaya. "Magana ta gaskiya, ban san waye Buzu ba, a sahara na tsince shi cikin mawuyacin hali, mai kama da" "gushewar hankali da ɗimuwa. Yanayin kamaninsa ya sanya na san ɗan uwa ne buzu, kuma buzyen ma kala-kala ne, na ji yana iya hausa ya kuma iya French, shi yasa na tabattar da Buzun Nijar ne. Na yi yinƙurin tafiya da shi Nijar, saboda idan na bar shi a saharar nan, zai iya rasa ransa, ban kuma san da wa zai haɗu ba, dan haka na yi nufin tafiya da shi Nijar, domin neman ahalinsa. Sai dai da na yi yinƙurin nufin komawa Nijar da shi, sai guguwar sahara ta taso, ta rufe hanyar baki ɗaya. Dole na canza hanya na nufo Nigeria, jikina ya bani akwai wani abu, domin duk wata hanya da zan bi mu koma Nijar na kasa" samun ta. "Ina da wasu abokai a Nigeria, su na kira suka karɓe ni, da niyyar a taimaka mini, a samo masa magani." "Saboda duk abin da na tambaye shi game da shi bai sani ba, sunansa, waye shi, daga ina yake, ina za shi" "duk bai sani ba. Wasu lokutan zai yi miki abu lafiya kalau na cikakken mai hankali, sai dai ba zai taɓa iya" "ce miki waye shi ba. Wasu sai ya burkice, ba magana yana ma iya daina gane mutane gaba ɗaya. Ba ya son magana ko da yana normal, sannan wasu lokutan ya kan burkice ya din ga jijjiga. Duk gurin mai maganin da muka je a Nigeria sai a ce ba za a iya ba shi magani ba. Shi yasa tun da aka yi auren nan, za ki ga kusan kullum ina zuwa, ina kawo muku abin amfani, wallahi ina matuƙar tausayinsa ne. Ba shikaɗai ba" "har da ke ma""" "Jikin Nana ya mutu murus, ta ce ""Yanzu shikenan ba ku san kowa na shi ba? Me na aura kenan?""" "Cikin kwantar da hankali Habu ya ce ""Akwai dalilin da Allah ya sanya ya haɗa ku, da babu wanda ya sani" "sai shi. Ni kaina na fuskanci ƙalubale baro ahalina na taho Nigeria nema wa wanda ban sani ba magani. Idan ki ka saka hannu ki ka dafa mini a kan wannan jihadin, Allah ne kawai zai biya mu. Idan ba ki amince ba kuma shikenan babu dole, sai na wuce gaba a raba auren, dama mahaifinki ne ya matsa ya sanya aka" "yi auren dole""." "Ba su ankara ba kawai su ka gan shi a cikin ɗakin, ya ajiye abin dafa shayinsa, da kayan dafa shayin, ya" juya zai bar ɗakin. "Habu ya tashi da sauri yana faɗin ""Tun ɗazu na zo ai, ba ka nan ga kayan dahuwar shayin nan na kawo" "maka""" Ayshacool 34 "Habu bai yi zuciya ba, ya sake bin bayan Buzu, ya juya yare, ya tsaya yana yi masa magana, ya din ga" zuba babu ƙaƙƙautawa. "Nana kuma mamaki ne ya ishe ta, ganin Yadda Habu ha rikice gaba ɗaya, kuma ita ba ta ga abin da ya yi" "na ba daidai ba, da zai yi wannan rikicewar kamar mara gaskiya ba." "Ita wasu lokutan har mamaki yake bata, kamar tsoron buzun yake ji, shi da yake taimakonsa amma ba ya" ƙaunar ya ga ɓacin ransa ko kaɗan. "Nana ko a jikinta, ba ta ma san yadda suka ƙarke ba." Sai dai ta yi ta jujjuya maganganun da Habu ya gaya mata. Yanzu shikenan haka za ta ci gaba da rayuwa "da mutumin da ba a ma san suwaye danginsa ba? Ko a daɗe ko a jima dole tana buƙatar sanin waye shi," kuma suwaye ahalinsa. "Ba ta taɓa jin lallai tana son ganin Ƙaisar ba sai a wannan lokacin. Ba shiri ta kwanta ta hau bacci, ko za ta" "gan shi, amma ba ta ga komai ba, har ta gama baccin ta tashi." "Bayan farkawarta ta ga wayarta a gefenta, a lokacin yamma ta yi sosai da sosai. Da sauri ta ɗauki wayar," "ta kira lambar Ummi, dan tun da suka zo, ba ta ji ya suka je gida ba." "Sai da ta kusa katsewa, sannan Ummi ta ɗaga." "Nana ta yi sallama, Ummi ta amsa ta ce ""Kai, Nana a ina ki ka samu waya?""" "Nana ta ce ""Dama ina da ita, kin san lambar ki na haddceta, saboda ke ce line 911 ɗi na""" "Ummi ta yi murmushi ta ce ""Eh lallai kam, ya ki ke ya mai gidan?""" """Alhamdilillah, ya ku ka je gida, ban samu na kira ku ba, bayan tafiyar ku na ɗan yi rashin lafiya ne""" "Ummi ta ce ""Alhamdilillah, mun je gida ƙalau. Kai Nana daga zuwa sai rashin lafiya, a dai ciki ba ne ko?""" "Nana ta kwashe da dariya ta ce ""Dan azaba auren kwanaki sai ciki?""" """Eh mana, tun da ina jin fitsarar da ki ke yi, ranar da mu ka zo""" "Nana ta ce ""Wallahi kawai cika baki ne, ji na yi za su raina mini hankali ne. Kuma ba na fatan ko alama, a" "ga ɓaraka a tattare da aurena""" "Ummi ta ce ""Allah sarki Nana, in sha Allah auren nan, sai ya baki kwanciyar hankalin da ba ki taɓa" "tsammani ba. Ke Jamila fa babu lafiya fa""" "Nana ta dafe ƙirjinta ta ce ""Babu lafiya kuma? Me ya same ta?""" """Oho, ni mun yi waya da maman, ban gama gane kan zancen ba. Wai tun da mu ka baro gurin ki," "washegari ta tashi ba ta iya tsayuwa, wani abu duk ya feso mata a jikinta""." "Nana ta girgiza kai ta ce ""Hmm na san cewa aka yi ni ce ko?""" """A'a wai sun je gurin wani mai magani, aljani ne yake hawa kansa ya bayar da magani, ya ce musu wai" "wani aljani suka yi wa laifi"" Kan Nana ya sara, ta yi shiru tana son tuna wani abu, amma ta gagara tuna komai." "Ummi ta ci gaba da cewa ""Shi ne ya basu magani, wai ya sha sannan a yi sadakar ƙosai mai zafi da" "la'asar""" "Nana ta ce ""Ita sadakar ƙosan ta mece ce, sharaɗin mene ne? Kin ga Mama ba za ta din ga kiyaye irin" "wannan yawace-yawacen ba ko? Wane irin sadakar ƙosai mai zafi da la'asar?""" """A'a ni ina zan sani, tun da ba ni na ba su maganin ba, ina gefe labari aka bani""" "Nana ta numfasa ta ce ""Sadaka mahaɗin Addu'a ce, amma wannan sharuɗɗan da ake sakawa ne, ni ba" "na gane kansu""" """To ni ya za ni tsitsiye ni, labari kawai na ji, ban ma je na duba ta ba""" "Jikin Nana a sanyaye ta yi ajiyar zuciya ta ce ""Shikenan, Allah ya sauwwaƙe ya jikin Baban?""" """To da sauƙi, ni rabona da gidan tun biki, amma sun ce yana jin jiki, ƙafar nan tana yi masa ciwo sosai""" "Nana ta ce ""To shikkenan, zan samu na je na duba su baki ɗaya, in sha Allah, amma jikina ya yi sanyi, na" "san ciwon Jamila cewa za a yi nice""" """Ke rabu da su dan Allah, ni wallahi na jiye miki daɗin auren nan, Allah ya sanya shi ne mafi alkhairi," "amma da zaman wannan gidan namu, ba gara auren ba, kullum cikin bala'i. Ko banza ɗakin ki a cike yake da kayan abinci""" "Nana ta ɗan yi shiru, kamar ta gaya wa Ummi halin da ake ciki, na rashin sanin dangin mijinta, amma ta" "basar. Ta ce ""To Allah ya sa mu dace""" "na gode sosai ki gaida yaran""" "Suka yi sallama, Nana ta tashi ta ɗan yi gyare-gyaren ta, ta ɗauki magic coal ɗin sa da yake haɗawa da" "gawayi, ya kunna wutar dafa shayi, ta kunna turaren wuta. Ta ɗauki wayarta ta kunna karatun Alqur'ani." "Fafur ya ƙi shigowa ɗakin, sai bayan isha'i." Ayshacool "Ya shigo da 'yar ledarsa, ya ɗauki kwano ya zazzage fruit, ya je ya wanko abin sa, ya dawo ya zauna a" "gurin zamansa, ya fara ci a hankali." "Nana ta na kallon sa, zuciyarta ɗauke da tunani daban-daban." "Ta dake zuciyarta, ta tashi ta tafi kusa da shi ta zauna." "Bai ko ɗaga kansa ba, balle ya nuna ya san tana zaune a gurin." """Ba za ka ci abincina ba ne, ka je ka sayo fruit ka ke ci?"" Sannu a hankali yake tauna apple ɗin bakinsa," bai kula ta ba. """Ni mamaki ma nake yi, idan ka je da yaya ka ke sayayyar, magana ka ke yi musu, ko kuma ni ce kawai ba" "ka kulawa?""" "Ya ɓare ayaba zai kai bakinsa, ta riƙe hannun, ta sauke shi ƙasa a hankali. Ya ɗago idanunsa yana kallon" "ta. Ta yi saurin sauke nata ta yi murmushi ta ce ""Na san na yi maka laifi, bai kamata abubuwan da na gaya maka ba, ka yi haƙuri ina cikin damuwa ne, amma ka yi mini afuwa ba zan sake ba"" ya sunkuyar da kansa ya yi shiru." """Ka yi magana mana"" ta yi maganar a raunane." "Ture ta ya yi daga kusa da shi, ya tashi ya bar mata ɗakin. Abin ya yi wa Nana ciwo, sai dai ta tuna" "bayanin Habu daki-daki, tabbas wasu abubuwan da yake za ka san ba normal yake ba." "Ta tashi zuciyar ta cike da damuwa, sai dai a zuciyarta ta ƙuduri aniyar jure kowane irin ƙalubale, tun da" "ba duka yake ba, ba kuma zagi yake yi ba, gara zamanta a nan da shi sau dubu, a kan ta koma gidan su." "Ta kunna gas ta ɗora ruwa, domin ta yi wanka kafin ta kwanta, garin akwai yanayin hadari, dan haka" akwai sanyi. "Tana ɗan dube-dube, da goge kan mududinta, ta ga ɗan littafin da yake yawo da shi, ko ta ga yana" "karantawa, da biro a cikin drower mudubi." "Ta ɗauka ta buɗe, ta ga kyakyawan rubutunsa, wani da French, wani da hausa." """A ba ni kankana, da ayaba na dubu biyu. A bani buredi mai kyau babba guda ɗaya. Ina son wannan jan" "abin, na kuɗin da na bayar"" sai da Nana ta yi dariya, wato duk a rubuce yake sayen abin da yake zuwa da shi. Tana shirin buɗe wani shafin, ta ji wutar gas ɗin na fita da yawan gaske, tukunyar kai na wata irin" tafasa kamar ta diro daga kan gas ɗin. "A gigice ta nufi gas ɗin ta sauke, abin ya ba ta mamaki, dan ko mintuna biyar a yi da ɗora ruwan ba, yake" wannan tafasar. "Ta juye ruwan a flask, ta sake ɗora wani." "Yana tafasowa ta haɗa ruwan ta shiga wanka, sai dai bayan ta shiga banɗakin, ta ji ruwan ya yi mata zafi" "sosai, maimakon ta kunna famfo, ta ƙara sirkawa, sai ta jingina da bango tana jiran ya huce. Shiru ta yi" tana ta tunani daban-daban a zuciyarta. "Ɓangaren buzu bayan ya dawo ɗakin, ye nemi Nana ya rasa, ya ga littafin sa a kan mudubi. Ya ɗan yi" jimm ko zai ji motsinta amma shiru. "Kusan mintuna goma bai ji ko zubar ruwan famfo ba, balle ya yi tunanin tana banɗaki." "Gaba ɗaya hankalinsa ya tashi, kamar yadda ya tashi ɗazu, da ya dawo ya tarar ba ta nan ashe tana cikin" gidan nan ba ta gaya masa ba. Kasa jurewa ya yi ya nufi banɗakin kawai ya buɗe ƙofar. "Zabura Nana ta yi, ta saki ƙara, domin ƙoƙarin cire zanin jikinta take yi ta yi wanka." "Cak ya tsaya yana kallonta, ta saka hannu ta riƙe zanin da hannu ɗaya, hannu ɗaya kuma ta kare ƙirjinta" da shi. "Sannu a hankali take jin sanyi, ƙirjinta kuma ya fara bugawa." "Ta sake ɗaga ido, suka haɗa ido, ko a jikinsa ya ci gaba da tsare ta da ido. Ta yinƙura da niyyar magana," "amma ta ji ta kasa furta komai, ta sake sunkuyar da kanta ƙasa." "A hankali ta ji ya rufe ƙofar toilet ɗin, wata irin ajiyar zuciya ta yi, jiki a sanyaye ta yi wanka, sai dai ta" kasa fitowa saboda kunya. "Da kyar ta iya fitowa, amma ta ga baya ɗakin, cikin hanzari take shiri, domin kwanta, kafin ya sake" shigowa. "Gari sai walƙiya ake yi, da wata irin tsawa hadari yana tasowa." "Tana gama zura rigar ta ya shigo, bai ce komai ba, ya rufe taga sai dai yana juyowa gaba ɗaya kamaninsa" "sun sauya, ya koma wannan tsohon." "Kallon kallo suka yi da ita, ta tsaya tana yi masa wani irin kallo, mai cike da tsoro da razani, a take fitilar" "ɗakin ta ɗauke, ɗakin ya gauraye da wani irin matsanancin duhu, ƙofa da tagar ɗakin su ka din ga" bugawa da ƙarfin gaske. Ayshacool "Wata irin walƙiyya ta haska ɗakin, ta ganshi sanye cikin wannan fararen kayan da take ganinsa da su," "hannunsa riƙe da sandar sa, idanunsa baƙi ƙirin wani baƙin hayaƙi na fitowa daga cikin su." "Ya hangame bakinsa, ya fara fito da wuta." """Allahumma ajirni fil musibati, wa aklifni kharin min ha"" ta yi maganar tana sanya hannunta, ta ɗora a" kanta. """Meyafaru?"" Ta ji muryarsa. Ta buɗe idonta ta kalle shi a hankali. Fuskarsa ɗauke da damuwa yake" tambayarta. Da sauri ta ja da baya tana girgiza masa kai. """Kar ka sake zuwa kusa da ni, ka yi mini duk abin da za ka yi mini, na gaji me na yi maka ne?"" Ta yi" maganar cikin kuka. "Cikin mamaki yake bin ta da kallo, yana tunanin me ya yi mata take wannan kururwar." "Ya taka ya ƙara matsawa kusa da ita, amma ta din ga ja da baya, tana maimaita ""kar ka matso kusa da ni," "ba na buƙatar ka, kar ka zo inda nake""." """Kalli ni mutum ne ba abin tsoro ba, babu abin da na yi miki, le regard kalli"" ya yi maganar yana nuna" mata hannunsa domin ta taɓa ta tabattar. "Cikin fita hayyaci Nana ta ce ""Ka fita ba na son ganinka, ba za ka haukata ni a banza ba, ka fita ba na son" "ganin ka"" ta yi maganar jikinta na tsuma da karkarwa. Cikin sauri ya nufi ƙofar fita yana waiwayen ta." Yana fita ta silale ta faɗi a gurin. "Fitar sa ke da wuya, ruwan sama mai ƙarfin gaske ya sauka." **** "Dare ya tsala, Fadila na zaune bacci ya gagari idonta, ta kalli kusa da ita, mijinta Sagir yana ta baccinsa" "hankali a kwance, ita kuwa duk dare fargabar kwanciya bacci take yi, saboda miyagun mafarke-mafarken da take yi. Tun Sagir na damuwa har ya gaji ya rabu da ita." "Ta yi niyyar yin alwala ta yi nafila ko raka'a biyu ce, amma kasala ta danne ta, ga wani irin tsoro da take ji." "Dama ko normal sallar farilla a zaune take yin ta, saboda yadda cikin ya tsufa sosai da sosai ga shi da" "girma. Ga exams tana facing, ba ta iya karatun sam." "Ta dafe goshinta tana wani irin gumi, duk da sanyin A.C da ya sanyaya ɗakin." "Tana jiyo surutan Haidar a cikin bacci, yana ta kiran sunan Nana." Kawai ta zuba uban tagumi hannu bibbiyu ba tare da sanin abin yi ba. **** "Ko da Nana ta buɗe idanunta, da hasken fitilar ƙwan ɗakin, ta fara karo." "Ta juyo da kanta, da ya yi mata nauyi tamkar zai tarwatse, kawai ta hange shi a bakin ƙofar banɗaki, yana" "ta sanɗa yana cire kayan jikinsa a hankali, da suke ta ɗigar da ruwa, jikinsa yana ta wata irin karkarwa. Aka yi walƙiya ta hangi yadda ruwa yake zuba ta taga. A take ta tuna abin da ya faru, da azama ta tashi zaune, ta yinƙura ta tashi, ta nufe shi. Sai a lokacin ya farga da ta tashi. Sai da ya tsorata ya tsaya cak," yana tsoron kar ta sake rikicewa ta ce ba ta son ganinsa. """Me yasa ka fita ruwa ya dake ka har haka? Subhanallah"" ta yi maganar tana karɓar rigar hannunsa." "Babban abin da ya tsorata ta, bai wuce yadda jikinsa yake karkarwa ba, haƙoransa suke haɗuwa da juna, su na bayar da wani irin sauti." "Ta buɗe wardrobe ta ɗaukko zaninta, ta fara goge masa ruwan jikinsa. Cikin damuwa ta ce ""Me yasa ka" "tsaya ruwa ya dake ka haka?"" Kawai ya kalle ta." "Ta ajiye zanin, ta ɗaukko flask ɗin da ta zuba ruwan zafi, ta shiga banɗakin ta zuba a bokiti, ta haɗa masa" ruwa mai zafi. """Ka shiga ka yi wanka da shi, za ka rage jin sanyin"" bai musa ba ya shiga banɗakin, ta ɗauko wando ta" "rataye masa a jikin ƙofar, ta rufe masa ƙofar." "Ta ɗaukko bargonta, ta ajiye a kan katifar, ta duba kayanta, ta samo man zafi ta ajiye. Ta tsaya tana" "jiransa. Ba a jima ba ya fito, sai dai jikinsa na ta ci gaba da tsuma, yana karkarwa." "Mamaki take yi, yadda dukan ruwa ya saka shi haka, ita ba ta san adadin dukan da ruwa ya yi mata ba," ko ciwon kai bai taɓa saka ta ba. "Ta ɗaukko riga, ta miƙa masa, amma ya ture ta, ya nufi gurin da yake kwanciya." "Ta riƙo hannunsa ta ce ""Zauna a nan"" ta nuna masa gefen katifar. Ya zauna a hankali yana rintse" idanunsa. "Ta ɗauki man zafi tana shafa masa a jikinsa, sai dai jikinsa ya ɗauki zafi rauuu." """In baka rigar ka saka?"" Ya girgiza mata kai alamar a'a." "Ta gyara masa fulo ta ce ""To kwanta"" ya ja jikinsa a hankali ya kwanta, ta lulluɓe shi da bargo." Ayshacool "Ta yi shiru cikin matsananciyar damuwa, ita kanta ba ta san ya aka yi yau ta gigice har haka ba. Ba ta san" "yadda aka yi ta rasa nutsuwar ta har hankalinta ya gushe ba, duk da abubuwa irin haka na faruwa da ita, wasu lokutan kuma ta na iya sarrafa kanta." "Ji ta yi yana wani irin nishi, jikinsa tamkar ana girgiza shi. Ta ɗaga bargon cikin damuwa, ta ga yana jijjiga." "Ta rikice ta fashe da kuka ta ce ""Dan Allah ka yi haƙuri, tsoro ka ke bani ne, ba ina nufin ka fita ruwa ya" "dake ba ne ba.""" "Tana kuka ta ɗaukko ɗan kwalinta, ta jiƙo shi da ruwa, ta ci gaba shafa masa. Amma ta ga leɓensa har ya" "fashe saboda karkarwa. Ta kalli gari yadda ake ta lafta ruwa, balle ta ce a taimaka mata a kai shi asibiti." "Ya yi mata alama da hannunsa ta matsa kusa da shi, ta matsa sosai a hankali ya ce ""Zafi, ana ƙona ni," "ƙonewa nake yi""" "Cikin kuka ta ce ""A'a babu wanda yake ƙona ka, zazzaɓi ne ka yi haƙuri""" """A'a, ƙona ni ake yi, sanyi nake so""" "Cikin rashin fahimta ta ce ""Sanyi kuma?""" """Eh, saboda ƙonewa nake yi yanzu"" yayi maganar haƙoransa na ƙara karo da juna." "Cikin damuwa ta ce ""To mu koma bakin ƙofar ɗakin?""" "Ya girgiza kai ya ce ""Sanyin da ki ke ji nake so""" """Sanyin da nake ji kuma? Ai ba na jin sanyi""" """A'a ki na ji, ki taimaka mini dan Allah, sanyin da ki ke ji nake so""" """To ta yaya zan baka?""" """Jikinki za ki bani, shi nake buƙata ko zan daina jin zafin wutar nan"" duk da jikinsa yana rawa, amma tana" fahimtar abin da yake faɗa. """To ai ni ban san ta yaya zan baka ba""" Ta yi maganar a sanyaye dan ba ta san ya yake nufi ba. """Kin yarda za ki bani?"" Ya yi maganar yana buɗe idonsa da suka kaɗa su ka yi jawur ya kalle ta." "Ta jinjina masa kai alamar eh, cikin tsoro dan ba ta san ya yake nufi ba." "Ya buɗe mata cikin bargon, ya saka hannunsa ɗaya ya janyo ta, ya mayar da bargon ya rufe., ya mirgina" ta gefensa ya saka hannayensa ya ƙanƙame ta. """Wash Allah! Zafi zan ƙone"" ta yi maganar a gigice, saboda wani irin zafi da yake fitowa daga jikinsa," "yana ratsa fatarta, duk da akwai rigar bacci a jikinta." "Ta yinƙura za ta tashi, sai dai ta kasa, saboda ya danne ta, ta kowane ɓangare." """Yi hakuri, ba za ki ƙone ba, za ki daina ji""" "Nana ta fashe da kuka tana girgiza kanta, shi da zafin yake fitowa daga jikinsa ya yake ji kenan?." "A hankali yake shafa gashin kanta, zuwa bayanta, yana sauke numfashi a wahale. Cike da ƙarfin hali yake" "cewa ""Yi haƙuri, na san ba zaki ƙone ba, nikaɗai nake ƙonewa"" ya din ga hura mata iska a kunnenta." "A hankali ta daina jin zafin, temperature jikinsa, ta fara komawa normal, ta ji ya daina wannan" "tsumar, numfashin ma da yake ta saukewa ya daina. Sai ta ɗan zabura a rikice ta ɗago, ta kai hannu" "hancinsa. Bai buɗe idonsa ba ya ce ""Ban mutu ba, ina numfashi"" ajiyar zuciya ta sauke tare da gode wa Allah ganin yana raye ya kuma dawo daidai." """Sannu ka daina jin zafi?"" Ya jinjina kai alamar eh." """Dan Allah ka yi haƙuri ka yafe mini, tsorata ni ka ke yi ne, ba ina sane na yi maka ba""" """Ni ma ki na tsorata ni wasu lokutan""" "Cikin mamaki ta ce ""Ta yaya?""" """An gama ruwan ko?"" Ya yi maganar yana basar da wadda ya yi." """Eh an daina, amma dama ka na doguwar magana haka sosai?""" """Eh""" """Amma na yi ta magana ɗazu ka ƙyale ni"" ta yi maganar da shagwaɓar da ita kanta ba ta san ta iya ta ba." "Dariya ta ji yana yi, ya ƙara riƙe ta gam." """Yanzu wai da gaske ba ka iya tuna komai game da kan ka?""" "Ya ɗan yi shiru sannan ya numfasa ya ce ""Haka ne, ina iya tuna abubuwa na yau da kullum, wasu lokutan" "kuma ba na iya tuna komai ma. Tun da farka a cikin wannan duniyar da nake jin ta tamkar mafarki, nake iya ƙoƙarina na tuna waye ni, saboda na fuskanci babu wanda yake rayuwa shikaɗai kowa yana da ahali. Amma a duk lokacin da na yi ƙoƙarin hakan, na takura ƙwaƙwalwata, sai na ji wani duhu ya ƙara ninkuwa a cikin kaina, na ji kamar kan zai tarwatse. Kuma a ƙarshe sai na yi rashin lafiya, ko dai na ji wannan zafin tamkar ana babbaka mini wuta, ko kuma na sake manta wasu muhimman abubuwan. Amma yanzu ke ce" "ahalina""" """Kenan ba dalilin dukan ruwan nan ne ya saka jijjiga ba?""" """Ba zan iya ganewa ba, abubuwan suke saka ni hakan da yawa""" Ayshacool 35 "Nana ta motsa, ta ji taushin katifar da suke kai, ta fi ta ɗakinsu. Ga ƙamshin turaren da ya sauya, ya" "sanya Nana sakankancewa a kan a wannan karon ma, irin wancan mafarkin ne." "Gaba ɗaya jikinta rawa yake yi, a wannan karon ma ta kasa sarrafa kanta da nutsuwar ta." Sai dai a wannan karon al'amarin ya banbanta da na farko. """Kai ka rabu da ni"" Ta faɗa da ƙarfi, tana ƙoƙarin ture shi." """A'a"" ya faɗa ƙasa-ƙasa." "Tabbas ba mafarki ba ne ba, bayan Buzun mijin nata ya dangana da ita, wani bugire mai girman gaske," bugiren da ba ta taɓa kawo faruwar sa a tsakanin su ba. Ita a tunaninta tun da ba shi da cikakkiyar lafiyar "ƙwaƙwalwa ba ya jin komai, hakan ne ya sanya take yawonta ma babu hijjabi a ɗakin, sai ta ga ya dame ta da kallo, ta rufe jikinta." "Cikin kuka ta ce ""Dan Allah ka ƙyale ni""" """je suis désolé (ki yi haƙuri)"" ya yi maganar muryarsa ƙasa-ƙasa." "Bayan wani lokaci da Nana ba ta iya tantance adadinsa ba, domin ta daɗe da daina gane komai." """Ma femme. (Matata)"" Ya yi maganar yana ɗan murza ya tsunta. Ta buɗe idonta da ya yi jawur, da ƙyar" tana kallon sa. A wannan karon fitilar ɗakin a kunne take. Sai dai fatarsa ta yi jawur. Ta sunkuyar da kanta daga kallonsa. "Ya saka hannu ya share hawayen da ke fuskarta, sai dai kuma ya kasa magana." "Ya kai bakinsa ya sumbaci goshinta, ya kamo hannunta ma ya sumbata. Ta lumshe idanunta tana" numfashi a hankali. """Merci (Na gode)"" shiru ta yi tana ƙara sunkuyar da kanta." "Ya saka hannunsa ya ɗago fuskarta, amma ta lumshe idanunta, ta ƙi buɗewa." """Kalle ni mana""" "Kwaɓe baki ta yi, ta ci gaba da kuka. Ya saki murmushi yana goge mata hawayen fuskarta ya ce ""A yi" "haƙuri""" "Ya ci gaba da wasa da yatsun hannunta, daga baya ya tashi a hankali yana kallonta, sai dai ya rasa abin" gaba ɗaya. "Nana ta yinƙura da ƙyar, ta tashi zaune, ta ja bargon ta rufe jikinta." "Su na haɗa ido ta sunkuyar da kai ƙasa, fuskarta a haɗe, hawaye na biyo fuskarta." """Yi haƙuri"" ya yi maganar yana kallon ta." "Kawai ta sake fashewa da kuka, har da sheshsheƙa." "Shafa bayanta ya ci gaba da yi, cikin sigar rarrashi, amma ta maze ta din ga kuka." "Ya ce ""Ki yi shiru""" "Ba ta kula shi ba, ta janyo rigarta, ta saka ta yinƙura ta tashi da ƙyar, ta nufi gas ɗin ta." "Ta dafa ruwa ta shiga banɗaki, ta jima sannan ta fito, a ƙofar banɗakin ta tarar da shi a tsaye." "Sai da ta ɗan tsorata, ta na ƙoƙarin raɓa shi ta wuce, ya ce ""Ni fa?"" Ta kalle shi." "Ya ce ""Zan yi wanka""" "Ta ba shi hanyar shiga banɗakin, ya kalli hanyar ya ce ""Ruwan sanyi? A a ina jin sanyi""" """Bari na dafa"" ya koma gefe ya zauna, ta ɗora masa ruwan, ta kalli agogon ɗakin, huɗu da rabi, ta san" idan ta kwanta yanzu ba bu lallai ta samu sallar asuba. "Ta shimfiɗa sallaya, ta ajiye wayarta a kai, ta ajiye hijjabinta." "Yana gefenta, sai bin ta yake yi da ido." "Ta kai ruwan banɗaki, ta na haɗa masa, sai a yanzu ta tuna lokacin da ya ce mata zai yi wanka, ashe" ruwan sanyi ne ba ya so. "Ta kashe famfon kenan, ta yinƙura ya shigo banɗakin. Ta tashi tsaye tsam tana rarraba ido." "Ya mayar da ƙofar ya rufe, ta ɗago da sauri ta ce ""Amm ga ruwan nan, idan zafin bai yi ba, sai ka kunna" "famfo ka ƙara sirkawa""." """Na kasa tuna yadda ake wankan, sai kin tuna mini""" """A'a wallahi nima ban iya ba"" ta yi maganar idanunta a waje dan tsoro." """Amma ke ki ka yi? Ko wankan kwanciya bacci ki ka yi?""" "Gaba ɗaya mamaki ya cika Nana, mutumin da magana take yi masa wahala, shi ne ya ritsa ta da wannan" maganganun kamar ana karanta masa. """Dan Allah ka yi haƙuri, ni ban iya ba""" """Astagfirullah ba kyau ƙarya"" ya yi maganar yana taɓa ruwan." * "Doctor Sharif ne da wani likita a kan Shukura, su na gwada bp ɗin ta. Duk ta kumbura sosai da sosai." "Jininta ya hau sosai da sosai, ba zai yiwu a yi mata tiyata a wannan ƙadamin a cire jaririn ba, saboda" hawan da jininta ya yi. Ga shi lokacin haihuwar ta bai yi ba. "Sakamakon da ya fito daga lab kuma, still ya nuna jininta ya yi ƙasa." Ayshacool "Doctor Sharif ya fito cikin damuwa, ya dubi Hajiya Amina da Yusuf, da kuma mijinta Sagir ya ce ""Wai me" "yake damun Shukura har haka. Normal teses ɗin suke tuk daga farkon cikin nata, amma lokaci ɗaya a ce jininta ya yi wannan mugun hawan ta kumbura har haka?""" "Sagir ya ce ""Wallahi doctor na rasa gane kan ta, tun bai fi kwana uku da dawowa ta ba, duk ta canza. Ba" "ta cin abinci, bacci ma ba ta iya yi. Kullum na farka cikin dare tana zaune, na yi, na yi na tambaye ta mene ne,ta ce mini ba komai, Mummy ai har ke na gaya wa ko za ki tambayeta abin da yake damun ta." "Hajiya Amina ta ce ""Rigima ce kawai irin ta Shukura, duk ta ɗaga hankalinta, wai tana ji a jikinta wannan" "cikin mutuwa za ta yi. Ina ta rarrashinta ina ba ta haƙuri, amma ta addabi kanta kuma wallahi farkon" "cikin duk ba haka ta yi ba.""" "Cikin damuwa Yusuf ya ce ""Yanzu doctor mene ne abin yi?""" """Zamu ajiye ta a nan, a samu jinin ya sauka, idan babu matsala za a iya barin cikin ya cika watannin" "haihuwar fine, idan kuma akwai matsala za a tiyata a cire cikin""" "Hajiya Amina ta ce ""Allah ya zaɓa abin da ya fi alkhairi""" "Doctor ya amsa da ""Amin, dan Allah a kula, hajiya ke kaɗai za ki zauna a gurin ta, babu 'yan dubiya" "Please, kar a bari kowa ya je inda take, yanzu dai ta samu bacci Alhamdilillah""" """To shikenan in sha Allah, za a kiyaye""" "Kiran Alhaji Zailani ne ya shigo wayarsa, dan haka ya bar gurin ya yi gaba ya ɗaga." """Sharif""" """Na'am ranka ya daɗe""" """Yaya ake ciki, Amina ta gaya mini su na asibitin ku Shukura babu lafiya, haihuwar ce ko yaya?""" """A'a tukuna dai ranka ya daɗe, jininta ya yi hawan da ba zai yiwu mu yi tiyata yanzu ba, mu na dai" "ƙoƙarin dai-daita jinin nata ne""." """To ko ma dai mene ne, kar ka manta da maganar mu""" """Ban manta ba, ina sane ranka ya daɗe""" """Yauwwa ya yi"" ya katse wayar." * "Jamila ce zaune fuskarta duk hawaye, a gaban Hajiya Sa'a. Hajiya sa'a ta riƙo hannunta ta ce ""Kar ki" "damu Jamila, na san kin yi iya ƙoƙarin ki, za mu canza fasalin aikin namu, Sannan za ki samu lafiya za ki" "warke gaba ɗaya ma""" Jamila ta jinjina kai ba tare da ta ce komai ba. """Akwai wata tafiya da nake son na yi Abuja, idan babu damuwa ina son za ki raka ni, amma sammako za" "mu yi, mu je mu dawo?""" "Ta ɗan yi shiru sannan ta ce ""Mama za ta bar ni, Baba ne babu lallai ya yadda, amma na san za ta saka" "baki ya bar ni, zan ma iya tahowa bai sani ba""" """Yauwwa Jamsy, kar ki damu ki kwantar da hankalinki, in dai mu na tare, kuma za ki din ga yi mini" "biyayya babu abin da ba zan yi miki ba, kin ji yarinyar kirki?"" Jamila ta jinjina kai tana ɗan sakin fuskarta." "Ta numfasa ta ce ""Hajiya bari na je gida""" """Ban ce ki daina ce mini Hajiya ba?""" """Yi haƙuri Mummy""" """Good, sai kin dawo yarinyar kirki, ki gaida gida, zan saka miki kuɗin, kayan kwalliya a account ɗin ki""" "Ta saki murmushi ta ce ""Tom Na gode sosai da sosai, Allah ya saka da alkhairi""" "Ta juya ta bar falon, tana jin wani irin nishaɗi, duk da wata irin fargaba na ratsa ta, daga ƙarƙashin" "zuciyarta, da ba ta san ta mece ce ba." "Karo ta yi da wani matashin saurayi, yana ƙoƙarin shiga gidan." """Sannu ina wuni?""" """Lafiya ƙalau ya ki ke?""" """Lafiya ƙalau"" ta amsa tana niyyar raɓa shi ta wuce." """Gurin Mummy ki ka zo ne?""" "Jamila ta ce ""Eh gurinta na zo""" "Ya ce ""Ok shikenan, ki gaida gida""" """Gida zai ji na gode sosai da sosai"" ta nufi gate ɗin ta fice." **** "Da ƙyar Nana ta iya sallar asuba, saboda gajiya ga bacci da take ji, da ta idar da sallar ma, a kan sallaya ta" jingina tana gyangyaɗi ta kasa azkar ɗin. "Hannunta ya ɗan shafa, ta buɗe idonta da kyar ta kalle shi." """Bacci ne?"" Ta ɗaga masa tana lumshe idonta." "Ya kama hannunta, ya ɗaga ta tsaye, ya ja ta zuwa kan katifa. Ta tsaya tana ƙoƙarin cire hijjabin, ya" "ƙarasa cire mata ta kwanta. Ta hau katifa ta buɗe bargo ta kwanta, kawai ta ji shi ma ya bankaɗo bargon ya shigo. Zumbur ta tashi zaune tana kallon sa. A ranta ta ce ""Lallai ji mutum da samun guri"" za ta yi" magana ta fasa ta tsaya tana kallon sa. Ayshacool "Shi kuwa ya yi kwanciyarsa, ya lumshe idanunsa, ya bar ta a zaune tana hamma. Sai da bacci ya ci" ƙarfinta sannan ta kwanta. Sai da ya ji ta kwanta sannan ya buɗe idonsa. Ya juya sosai yana kallonta. "Zai iya cewa tun da ya tsinci kansa a cikin wannan duniyar da yake a yanzu, wadda yake kamantawa da" "duniyar mafarki, bai taɓa tsintar kansa cikin nishaɗi da farincikin yau ba." "Ya kasance cikin damuwa, da tsananin ɓacin ran rashin sanin waye shi, daga ina yake? Ina zai dosa?" "Rashin sanin amsoshin nan, na dugunzuma hankalinsa da haifar da wani irin nauyi a ƙirjinsa, wani irin duhu ya mamaye shi, bai taɓa jin daɗin komai, ko farinciki da komai ba. Duk da dai-dai gwargwado Habu da sauran wanda suke tare su na ƙoƙari a kansa, amma sam babu abin da yake raguwa na duhu da" damuwa a tare da shi. Sai bayan da ya fara kasancewa da Nana a ɗaki guda. "Ganin gilmawarta kawai, yana kallon ta, yana jin daɗi. Ya kan ji kamar ya yi mata magana amma sai ya" "kasa, ya rasa mai zai ce mata. A wannan duniyar da ya yi wa laƙabi da duniyar mafarki, ya ga mutane na" "bawa ahali muhimmanci, amma shi ba shi da su, kuma ba a duba rashin ahalin nasa ba, aka aura mata shi, hakan ya kan saka ya ji tausayinta." "Yanzu a wannan duniyar yana kallon Nana a matsayin ahalinsa. Duk da ba ya son hayaniya, amma" "muryarta mai sanyi da daɗin sauraro, ba kamar su Habu ba, sai yana cikin damuwa ko rashin lafiya, ya din ga jin muryoyin su a sama kamar kwarankwatsa ba." "Ya kan ji babu daɗi idan ya ji ta shiru, yana matuƙar son ya ga tana kallon sa, idan su ka haɗa ido ta" "murguɗa baki tana magana ƙasa-ƙasa, komai na ta a sanyaye." "Ya ƙura mata ido, yadda ta yi nisa a baccinta, ya sumbaci goshinta, ya mayar da bakinsa wuyanta ya" "sumbata. Ta buɗe ido ta juyo ta kalle shi, idanun na ƙoƙarin sake rufewa. Ya kwantar da kanta a kan ƙirjinsa. Ba ta yi musu ba, sai ma jikinta da ya saki. Murmushi ya yi jin yadda numfashinta yake shiga nasa," ya ji tamkar su dauwwama a haka saboda yadda yanayin ya yi masa daɗi. """Ke ce Ahalina""" "Nana ce ta raɓe a gefen ƙofa, tana hango ƙaisar yana rubutu, sai dai wannan karon ba a cikin Library" "bane ba, gurin da yake haɗa magunguna ne. Ga tarkacen kwalaban magunguna ko ina a cikin gurin." """Ya dai?"" Ya tambaye ta." """Ba komai"" ta faɗa a hankali, tana sinne kai." "Ya ce ""Na ga kwana biyu kina nema na, ba mu haɗu ba, akwai matsala ne, ko kina buƙatar wani abin" "ne?"" Ta girgiza kai tana sinnewa." """Wai meyafaru ne na ga kin canza yau gaba ɗaya, kamar ba ke ba? Kin wani nutsu"" Still taa yi shiru tana" ƙifta ido. "Kawai ta ji ya bushe da wata iriyar dariya, da sai da ta tsorata ta ɗan ja da baya, saboda yadda sautin" dariyar ya karaɗe ilahirin gurin. "Ya tsagaita da dariyar ya ce ""Kar ki damu, ki kwantar da hankalinki ban ga komai ba, ba abun da na ganu""" ta yi tsuru -tsuru amma ta kasa magana. "Ya ce ""Ki maze fa kamar babu abin da ya faru, babu abin da na gani, ai ku na cikin duhu, kuma duk da" "haka ma, lamari ne mai girman gaske da bai dace na ga ƙwaƙwaf ba. Sai na yi gaba abuna"" ya yi maganar" yana tashi tsaye. "Ya nufi gurin wasu kwalabe, yana duddubawa ""Ki saki ranki fa, sai dai ban sani ba ko kin gano sakamakon" "binciken naki, na mutum ne ko kuma aljani da ki ka iya amincewa wani abu ya faru tsakanin ku. Abin da mamaki yadda jikin ɗan Adam yake iya ɗaukar zafi kamar an saka shi a cikin wuta, kuma bai mutu ba. Kodayake ai haryanzu ban tabattar ba ko wani abun ya faru ba, tun da a cikin duhu ne, amma tsaya a tsakanin ke da shi waye ya kashe muku fitilar ne? Ko ita ta kashe kanta?"" Ya sake bushewa da dariya, ya yi wata irin hajijiya, guguwa ta tashi, ta cikin guguwar muryasa ke tashi ya ce ""Kamar dai yadda na gaya" "miki ne, ban ga komai ba ki daina sinne kai"" guguwar ta yi waje ta daina jin muryarsa." "Ta yi ajiyar zuciya tana tunani, ta din ga jin tamkar wadda ta aikata saɓo." "Ba saɓo ki aikata ba Nana, makomar ki ki ke tunani. Wata zuciyar ta tunatar da ita. Tabbas zancen rashin" "sanin waye shi, yana damun zuciyarta. Amma ita ma mutum ce ba gini ba, ta yaya za ta iya tsallake dabaibayin da ya yi mata a daren." Ayshacool "Idaonta ya sauka a kan tarin litattafan da suke gurin da ya zauna, da hanzari ta tashi ta tafi ta hau caje" litattafan. Bisa tsananin sa'a ta ci karo da littafin da take ta ƙuzun son jin ci gaban sa. "Da hanzari ta buɗe, sai dai tana buɗewa kawai ya kai ta daidai gurin da ta tsaya." Ta nutsu ta ajiyar zuciya ta fara karantawa. "Lanti ta yi alwashin ko tilon 'yar ta, za ta rasu ba za ta taɓa kai wa sarkin aska yarinyarta ba ya bata" "magani. Mijinta ya rarrashe ta a kan ta yi haƙuri, su kai yarinyar ko za a dace da maganin." "Cikin damuwa ta ce ""Duk da yarinyar nan ce kaɗai nake da ita a yanzu, ba kuma ni da tabbacin sake" "samun wani ɗan, amma gara na rasa ta da na je gurin maƙiyina nema mata magani, ni na san abin yi, ka" "bar ni kawai""" "Lanti ta shirya, ta ɗauki yarinyarta, ta tafi garin da aka ɗaukko bokan da ya yi wa sarkin aska girka." "Ko da ta je garin ta iske ya tsufa sosai, ga rashin lafiya yana ta fama da ita." Ta gaya masa abin da yake tafe da ita. "Ta ce ""Ka ga halin da yarinyata take ciki nan, ni kuma ba zan iya kai wa sarkin aska ita ba ya bani magani," "saboda a duniya ba ni da maƙiyin da ya fi shi yanzu a duniya. Kuma ina son na dakatar da zaluncin da yake yi wa mutanen ƙauyenmu, da sunan Aljanu ne suke saka shi""" "Ya yi shiru sannan ya ce ""Ni kaina na yi dana sanin girkar da na yi wa sarkin aska, kafin ke wasu da dama" "sun zo a kan haka, ciki har da mai garin ku, su na neman mafita. Sai dai hatta ni kaina yanzu sarkin aska" "ya fi ƙarfina, da na san haka ne da ban yi masa girkar nan ba""." "Cikin damuwa ta ce ""Yanzu mene ne abin yi?""" "Ya ce ""Babu wani abu da zan iya, sai dai ki koma gurin kakanki, mahaifin sarkin baka, ki ce masa ni na" "turo ki, ni boka Giyaz""" """Kakana kuma? Kakana ne yake da yadda za a yi da Sarkin Aska?""" """Ke dai ki je ki same shi, ki ce masa ni na aiko ki""" "Ta jinjina kai ta ce ""To shikenan"" ya bata magani, bayan kwanaki uku, ta koma garinsu." "Kai tsaye gurin kakanta ta fara zuwa, bayan sun gaisa ya yi mata sannu da zuwa." """An aiko ni gurinka""" "Ya ce ""Tun kafin ki dawo aka aiko mini da 'yan aike, suka sanar da ni zuwan mi""" "Cikin mamaki ta ce ""Su wa kenan?""" "Ya yi murmushi ya ce ""lokacin da aka zo da ni garin nan, ina ɗan ƙarami sosai da sosai na san wasu daga" "cikin gwagwarmaya da dambarwa da aka din ga yi da aljanu kafin mu samu zaman lafiya. Sai dai alƙawarin aljani ba shi da tabbas, duk da yarjejeniyar zaman lafiya da muka yi, sun ƙi yarda mu zauna lafiya, su na kawo mana farmaki, lokaci zuwa lokaci. Yanzu dai ki na da burin kawo ƙarshen sarkin baka," "kuma kina burin ganin 'yar ki ta warke gaba ɗaya, abu ɗaya za ki yi sai dai abin da wahala""" "Cikin zaƙuwa ta ce ""Ka gaya mini, ko mene ne zan yi, muddin burina zai cika""" """Burinki zai cika, amma sai dai ki amince a yi miki girkar aljanu, ya zamana ke ma ki na da aljanun da ki ke" "iya sarrafawa, sannan za ki iya ja da shi, har ma garin nan ya zauna lafiya. Amma sai dai ki samu masu" "ƙarfi da za su iya jayayya da na Sarkin Aska.""" "Ta numfasa ta ce ""Kakana na amince ka yi mini girkar aljanu, dole na kawo ƙarshen sarkin aska a garin" "nan""" """Lanti, ki je ki ya shawara tukuna. Girkar Aljanu ba hukunci ne da zaka yanke kai tsaye ba tare da" "cikakken shiri, da nazari ba""" "Ta tari numfashin sa da cewa ""Ba na buƙatar yin shawara, na gama yanke hukunci na amince a yi mini" "girkar Aljanu""" "Ya jinjina kai ya ce ""To shikenan, babu laifi za ki je sai nan da sati biyu, zan haɗa tsumin da za a yi miki" "amfani da shi, gurin yin aikin zan shafe kwanaki ina aiki a kai, domin yi miki girkar. Sai dai ina son ja bakinki, ki yi shiru har zuwa lokacin da za a yi aikin""" """To kakana, babu wanda zai ji wannan maganar, daga ni sai kai, amma ya aka yi ka iya wannan" "abubuwan haka?""" "Yayi murmushi ya ce ""Kamar yadda na gaya miki, tun ina yaro aka zo da ni garin nan, lokacin ana kan" "ganiyar rashin zaman lafiya da ainihin aljanun da suke zaune a garin nan. Bayan na ɗan tasa na fara yawon farauta, a nan na yi karo da wani matashin saurayin, sa'ana muke shiga tare da shi daji, gurin yin" farauta sai dai ya fi ni rashin ji. Ayshacool "Shi ne ya koya mini farauta, da siddabaru kala-kala da hatsabibanci, ban san gidan su ba, kullum a hanya" "muke haɗuwa mu tafi Daji. Sai daga bisani na fahimci ba mutum ba ne ba. Aljani ne yake shiga jikinsa, muke wannan abotar, shi ne ya koya mini harkokin farauta da magunguna har mahaifinki ya gada. Kuma ba kowa ba ne face wannan bokan da aka kawo shi garin nan ya yi wa sarkin aska girka, wanda ki ka je" "gurinsa yanzu. Jikinsa aljanin yake shiga, kuma shi ya haɗa mu abota da boka Giyaz.""" "Lanti ta jinjina kai cike da mamaki, dan duk labaran da yake ba ta, bai taɓa ba ta wannan labarin ba." "Ta koma gida ta yi shiru da bakinta, ko mijinta ba ta sanarwa ba." "Kakan Lanti ya shirya ya tafi daji, ya shafe makonni biyu, yana tattara saiwowayi, sassaƙe da kuma sassan" jikin dabbobin da yake buƙata gurin yi wa jikarsa Lanti girkar aljanu. """Dattijo ka yi a hankali, za ka yi mini ɓarna fa"" kakan Lanti ya ɗago tare da faɗin muryar wa nake ji haka," "rai kan ga rai Uban duƙusa?""" """Ƙwarai kuwa, na zata ka mutu ai""" "Kakan Lanti ya bushe da dariya ya ce ""Ban mutu ba tukuna, ina nan raye ina ka tafi tsawon wannan" "lokacin haka? Kuma a ina ka samo gangar jikin da ka shiga haka ka zo mini?""" "Kyakyawan farin matashin da yake tsaye a gaban kakan Lanti yayi murmushi ya ce ""Labarin dogo ne, na" "yi balaguro ne zuwa gabashin duniya, na samo labarai daban-daban da zan rubuta""" """Yanzu neman labarin ne, kusan shekaru hamsin babu amonka""" """Shekaru hamsin mu a gurinmu ai babu yawa. Bani labari na ga gari ya zama alƙarya abubuwa sun canza" "sosai da sosai. Saukata kenan da kai na fara karo na ce bari na bayyana na kwashi gaisuwa""" """Tuba nake uban gidana, ai ni yakamata na zo kwasar gaisuwa."" Nan kakan Lanti ya bawa uban duƙusa" labarin abin da ya faru. "Cikin damuwa ya kalli kakan Lanti ya ce ""Yanzu duk da yarjejeniyar zaman lafiya da aka yi, sai da aka saɓa" "ta? Waye ya yi wa sarkin askar girka?""" """Giyaz ne, mutane sai wahala suke yi a garin nan, saboda abin da sarkin aska yake yi. Ya sadaukarwa" "wasu daga ahalinku jini, ya mayar da su baƙaƙen aljanu da sunan zai taimaka musu gurin ɗaukar fansar abin da mutanen garin nan suka yi muku""" "Matashin ya shafi fuskarsa cikin damuwa, ya ce ""Yanzu wa za ka yi wa girkar?""" """Jikata ce, da nake kyautata zaton sarkin aska ne ya kashe babanta, saboda yana bayar da magani""" "Uban duƙusa ya jinjina kai ya ce ""Gaskiya ne, shikenan zan je gida, zan huta kafin ranar da za ka yi mata" "girkar, amma ka tabattar za ta iya ɗauka? Ka san idan aka samu akasi, za ta iya haukacewa fa""" """Za ta iya, tana da juriya, kuma tana fatan ɗaukar fansar abin da aka yi wa mahaifinta""" """To shikenan, zan sake dawowa""" """To shikenan ubangidana, ina godiya da wannan ziyara ta bazata"" suka yi sallama." "Kakan Lanti ya koma gida, ya shiga wani ɗaki a cikin gidansa, ya haƙa rami ya saka wata randa. Ya kawo" "saiwoyin da ya zo da su ya zuba a ciki, ya kawo tarkacen magunguna kala-kala ya zuba a ciki. Ya kawo" "ƙasusuwa da wasu sassa na jikin dabbobin daji, a zuba a ciki. Ya kawo turare ɗan goma, da farin goro duk" "ya zuba a ciki ya rufe randar, sannan ya mayar da ƙasar ya binne." "Sai da aka kwana biyu, daren na uku da zai buɗe randar, wanda saura kwana biyu ya yi wa jikarsa Lanti" "girkar aljanu. Yana cikin bacci, ya ji wata irin ƙara, sanyi yana ratsa shi, ya tashi da nufin neman abin rufa," "amma ya gan shi a tsakiyar daji, gurin da suka haɗu da uban duƙusa." "Cikin mamaki ya ce ""Ubangidana lafiya aka kira ni a wannan daren haka? Idan na yi laifi ne ina neman" "afuwa"" uban duƙusa ya fito daga bayan bishiyoyi ya ƙaraso gaban tsohon nan ya ce ""Ba ka aikata mini wani laifi ba abokina, Ina mai baƙin cikin sanar da kai mutuwar Giyaz""" """Wayyo, Giyaz ya mutu?""" """Ƙwarai Giyaz ya mutu, sannan na yi baƙin cikin abin da na zo na riska, galibin 'yan uwana, sun koma" "baƙaƙen aljanu, kuma sarkin aska yana sarrafa su ta mummunar hanyar da ba ta dace ba. Su na sanya" muku miyagun cututtuka. Tabbas idan ku ka yi sake sai sun shafe tarihin mutanen garin nan. Ban ji daɗin yadda aka saɓa alƙawri da yarjejeniyar mu ba. Ayshacool Kakan Lanti ya ci gaba da shirye-shiryen yi wa jikarsa girka. "Ya samo ƙaramin ƙoƙo, da 'ya'yan wuri, da tsirkiya ya haɗa garaya." "Ya haɗa caki, ta hanyar samun butar duma ya fafe ta, ya zuba busassun 'ya'yan tafasa, da zogale a ciki," ya toshe bakin. "Ya tsayar da ranar yi wa Lanti girkar aljanu, ya sanya ranar Lahadi, a matsayin ranar da za a aiwatar da" "girkar. A sirrance ya aika saƙon gayyata zuwa ga bokayen maƙotan garin, da 'yan bori, a kan su halarci" gurin taron bikin yi wa Lanti girkar Aljanu. "Bayan almuru, yaje ya samu ƙatuwar Bishiyar kukar da ke can wajen garin, ya je ya samu, ya naɗe da" farin yadi. "Ya koma gida, ya tono randar nan, ya ajiye ta a tsakar gida, ta kwana tsumin cikinta ya yi sanyi." "Ya koma ya dafa wani magani, ya zuba a cikin kwatanniya. Mutanen garin kuwa, suka din ga mamaki" "wayewar gari, da suka ga wannan farin yadi a jikin bishiyar kuka, aka din ga surutun mene ne dalilin haka , har labari ya iske mai gari." "Aka yi ta yekuwar wa ya aikata wannan abu, kar a je wata fitinar ce za ta taso." "Kakan Lanti da kansa ya je ya samu Mai gari, bayan sun gaisa ya ce ""Ranka ya daɗe, ni ne na ɗaura" "wannan farin ƙyalle, yau da yamma zan yi wa jikata Lanti, girkar aljanu""" "Mai gari ya waro ido ya ce ""Girkar aljanu kuma? Kar ka janyo mana bala'i bayan wanda muke ciki, kuma" "ya za mu yi idan sarkin aska ya ji, kar aljanu su fushi da mu fa?""" """Babu abun da zai faru sai alkhairi, ba zamu dauwwama Sarkin aska, yana juya mu yadda yake so ba, ina" "son ka yi haƙuri ka bani wannan damar""" "Da ƙyar ya shawo kan mai gari ya amince, aka din ga shela ana gayyatar mutane, gurin yin bikin girka." "Mutane suka din ga al'ajabi, tare da jiran yammacin ranar lahadin, domin ba su taɓa sanin yadda ake" "gudanar da girkar ba. Nana da labari har maƙwabtan garin, aikuwa jama'a suka din ga ɓarkowa cikin garin." "Kakan Lanti tun safiyar ranar, ya sanya ta yi lalle dungulmi, hannu da ƙafa. Ya bata fararen kaya na saƙi," "ta saka ya kawo warki, na fatar kura da aka jeme, aka saka ta a shuni, ta ɗaura a ƙugunta, sannan ya kawo wuri ya bata shi ma ta sanya a ƙugun nata." "Daga bisani ya kawo wasu irin guraye, ta ɗaura a damatsenta." "Ya kawo sandar dargaza ya bata, sanda ce da aka yi da itacen tsamiya, aka naɗe ta da fatocin dabbobi" "daban-daban, suka yi beza a jikinta." "Tun daga gidan kakan Lanti, ta samu rakiyar mutane, ɗuuuu tamkar ƙudaje zuwa filin girka." "Fili ya cika ya tumbatsa, aka shimfiɗa saƙi kala-kala a gurin." "Ya bata wani kwalli ta sanya a gurin, ya ba ta goro da fure, ta saka a bakinta ta tauna, laɓɓanta suka yi" jawur. Idanunta su ka yi rabajau da kwalli. "Tuni makaɗan borin, da kakan ya gayyato daga wasu garuruwan suka jeru, suka fara kaɗa garaya da" goge. "Ya bawa Lanti, wannan tsumin na cikin kwatanniya ta sha, ya saka ta zauna a kan shimfiɗar nan. Ya din" "ga ɗebo ruwan cikin randar nan yana zuba mata, wani irin sanyi ya din ga ratsa ta, har zabura take yi saboda sanyi." "Ya kawo turare ɗan goma ya shashshafa mata, ya kawo wani gwado, ya rufa mata. Sannan aka koma" gefe aka kunna hayaƙi. Ya koma gefe shi ma ya hau kaɗa kacakaurar da ya haɗa. "An ɗauki dogon lokaci a haka, kafin ta fara murƙususu a cikin gwadon da aka rufe ta da shi, tana wani" "irin kakari. Shewa masu kiɗan borin suka hau yi, ana murnar aljanun sun fara hawa kanta, dan haka suka" ƙara ƙaimi gurin ci gaba da kiɗan borin. "A hankali ta tashi tsaye, tana wata irin girgiza, bakinta na fitar da kumfa, ta ɗaga wannan sandar ta" "dargaza, ta fara tangaɗi a gurin." "Mutane suka ɗauki sowa, gwargwadon tashin kiɗan, gwargwadon tangaɗin da take yi, tana girgiza" dogon gashin kanta. "Babu tsammani, gari ya yi duhu, wani irin hadari ya haɗu, sai dai hadarin na guguwa ne. A take jama'ar" "gurin, suka tsatstsaya, su na kallon yadda garin ya canza, su na jiran ganin abun da zai faru." "Tukunyar tsumin da aka zo da ita ta tarwatse, wata irin gigitacciyar guguwa ta turnuƙe gurin, har wani ba" ya iya ganin wani. "Sarkin aska ne ya bayyana tamkar an jefo shi, a hankali kuma ƙurar ta fara lafawa." Ayshacool "Lanti kuwa cak ta tsaya, hannunta riƙe da dargazarta, ta sunkuyar da kanta ƙasa. Sarkin aska ya nufo" "inda Lanti take, cikin azama kakanta ya shiga tsakaninsu, ya tari Sarin Aska, wani irin jifa ya yi da tsohon a gefe. Lanti ta ɗago da kanta, suka yi ido huɗu da Sarkin Aska. Cak ya tsaya yana kallonta cike da" "mamaki ya ce ""Uban duƙusa""" """Ka durƙusa akan gwiyoyinka, ka nemi afuwar uwar gijiyata, kafin raina ya ɓaci"" ta yi maganar cikin wani" irin sautin muryar da ba tata ba. "Sarkin aska ya ce ""Kai yanzu da kai aka yi wa maƙiyanmu girka? Ka manta zaluncin da bil adama suka yi" "mana? Ka manta gargaɗin da kakaninmu suka yi mana a kansu?""." """Ban manta ba, kuma ina bayan gaskiya har abada, ku kuka fara karya yarjejeniyar zaman lafiya da aka yi," "dan haka ba zan bi bayan ɓarna ba, dan haka ka yi abin da na ce""" """Har abada. Har abada ba zamu yi maka biyaya ba, duk da kasancewar ka abu mafi soyuwa a zuriyarmu.""" "Nana ji ta yi an yarfa mata ruwa a fuska, ta buɗe idonta da sauri. Ido huɗu suka yi, ya sakar mata" "tattausan murmushi. Ya ajiye matajin da yake taje kansa da shi ya nufo ta, cikin hanzari ta shige cikin bargo da kanta." "Ya zauna a kusa da ita, ya saka hannu ya janye bargon, ta ƙi buɗe idonta, sai ma miƙa da ta yi, saboda" "duk jikinta ciwo yake yi, kuma sam baccin bai ishe ta ba. Ya zuba mata ido, murmushi ya gaza barin fuskarsa." """Ina kwana"" ya faɗa yana kallon ta. Kasa kallon sa ta yi, ta sunkuyar da kanta tana basarwa." """A tashi a karya"" ya yi maganar murmushi ya kasa barin fuskarsa. Ta ja jikinta ta tashi zaune da ƙyar." """Bari na yi brush"" ta tashi ta nufi toilet." "A banɗaki ta tsaya ta yi shiru tana tunanin littafin da take karantawa na Ƙaisar, ta san yanzu kafin ta sake" samun littafin sai an daɗe. Kenan da gaske dai shi ne uban duƙusa? Ya aka yi sunansa ya canza zuwa Ƙaisar? Ta wanke fuskarta ta yi brush ta fito. Har ya karkaɗe mata shimfiɗa. "Ta zauna, ya ɗaukko kofi da murfi ya miƙo mata. Ta saka hannu ta karɓa, ta buɗe ta ga abu a kofin kamar" "madara, da ɗan wani gari gari a kai." "Ta kalle shi ya ce ""Sha"" ta kai bakinta, ta ji babu ƙarni, ta yi bismillah ta fara sha." "Babu zaƙi, sai dai akwai garɗi da maiƙo a baki, ga ɗumi kuma babu ƙarni mai damu. Sai da ya saka ta" "shanye tas, ta kalle shi ta ce ""Wai mene ne wannan?""" "Ya yi murmushi ya ce ""Nonon raƙumi ne""" """Raƙumi kuma? A ina ka samu Nonon Raƙumi?""" "Ya ce ""Habu na saka ya kawo miki, jikinki zai yi ƙwari, ga abinci ma sun haɗo da shi, na ce ba ki da lafiya""" """Gaya musu ka yi?""" "Ya ce ""Me?""" """Abin da ya faru jiya?""" """A'a ban ce musu, kin kore ni waje ruwa ya jiƙa ni saboda ki na tsoro na ba""" "Ta ce ""Ba wannan ba""" """To me?""" """Ba komai"" tayi maganar cikin basarwa." "Ya yi dariya ya ce ""Ban faɗa ba, daga ni sai ke kawai wannan"" ta yi shiru wata irin kunya tana mamaye ta." "Babu babban abin da yake ƙara sanya Nana farin ciki, sama da samun abinci sau uku a rana da take yi a" "wadace, babu geji kuma babu hantara." "Ƙaton buredi ne lafiyayye, aka soya ƙwai fal, shayin ma shi ya zuba mata. Tana ci yana ƙare mata kallo." """Ka daina kallona, ko na tashi""" """A'a""" "Ta ce ""A'a me?""" """Ba zan daina ba""" "Ta juya gefen sa, yadda sai dai ya kalli side ɗin fuskarta, ta gama ci ta koma gefe." "Shi ya yi mata komai, da ta motsa sai ya ce ta zauna. Sai dai ya lura gaba ɗaya ta zama so silent yau, ba" "karaɗi da surutu. Duk sai ya ji hakan babu daɗi. Ita kuwa ta yi matuƙar mamaki, ganin yau bai fice ya bar" ta ita kaɗai ba. "Ya dawo kusa da ita ya zauna, har gashin sa yana taɓa wuyanta, kasancewar bai tufke shi ba, sakin sa ya" yi. """Me ya faru?"" Yayi maganar yana ɗora hannunsa a nata." "Ta girgiza masa kai, alamar babu komai." """Ko ana fushi ne?"" Ta ɗaga kai alamar eh." """Me yasa?"" Ya tambaye ta, yana shafa jikinta." "A ranta ta ce ""Ikon Allah, ji mutumin nan da samun guri""" """Ba ki ce mini ya jiki ba, kin kore ni ruwa ya jiƙa ni, ba ni da lafiya""" "Nana ta tura baki ta ce ""Ba ga shi ka warke ba, kuma ai ba ina sane bane ba """ Ayshacool "Nana ta haɗiye wani abu mai matuƙar ɗaci, ta ji zafin maganganun da aka gaya wa mijin nata. Duk da ta" "san ya yi laifi amma kalmomin sun yi tsauri. Ta kalli idonsa ta ga ya yi jawur, hannayen sa na rawa, launin fatarsa ya canza zuwa ja." "Ta zauna a kusa da shi a kan bencin, ta ɗora hannunta a bayansa ta ce ""Sayyid. Ka yi haƙuri na fika jin" "zafin abin da ta gaya maka, amma ka yi haƙuri ka ji?"" Kawai ya jinjina mata kai." "Ta sake kallon idanunsa, yadda suke ƙara rinewa zuwa launin ja, hakan ya ƙara bayyanar da matsanancin" ɓacin ran da yake ciki. """Taso mu koma ciki to, tun da ka buɗe mata"" ya girgiza mata kai alamar a'a." "Jiki a sanyaye Nana ta tashi ta ƙyale shi, dan ya fara ba ta tsoro." "Duk da yanayin da take ciki, ta ji daɗin hirar da suka ɗan yi da shi." Ta kama aikace-aikacen ta a cikin ɗakin. * Jamila ce take gaya wa Mama batun unguwar da Hajiya Sa'a ta ce za ta raka ta. "Mama ta ce ""To mene ne a ciki? Ai babu komai yadda take nuna miki ƙauna, ni ko bangon duniya ta ce" "za ku je, ai ba zan hana ba""" """To Mama Baba fa? Ni ba na son masifar nan tasa""" """Dalla rabu da shi, uwar me yake bamu a gidan, Ubangiji Allah ya haɗa ki da iyayen ɗaki masu ƙaunar ki," "mu na samun alkhairi ta hannunsu, za ki din ga kawo zancen sa, ki yi tafiyar ki, ni na san abin da zan gaya masa""" "Jamila ta yi murmushi ta ce ""To shikenan, ni dama ba na jin ki, na san za ki bar ni""" "Can Asibiti kuwa, likitoci sun yi deciding, tiyata za a yi wa Shukura a cire jaririn cikinta, saboda a tseratar" da rayuwarta da ta abin da yake cikinta. "Sai dai da Jininta ya sauka sai ya sake hawa, saboda gaba ɗaya a tsorace take, ta yanke tsammani da" rayuwar duniya ba ki ɗaya. Duk da irin rarrashi da ƙoƙarin kwantar da hankalinkin da ake yi mata. "Bayan Nana ta ɗora girki, ta kira Hajiya Amina su gaisa, a nan take gaya mata halin da ake ciki, cewar su" "na Asibiti an kwantar da Shukura. Hankalin Nana ya tashi sosai da sosai, tana son zuwa duba Baba da Jamila ma, ga kuma wannan maganar ta rashin lafiyar Shukura. Sai dai yadda ransa yake a ɓace ta san ba" ta da damar yi masa magana. "Tun da abin nan ya faru, bai sake shigowa ɗakin ba, ta je ta same shi a kan ta gama girki ya yi mata shiru." 'yar walwalar da ya fara yi ta gushe baki ɗaya. "Gaba ɗaya abin ya dame ta sosai da sosai, ko abincin kirki ta kasa ci." "Sai bayan sallar isha'i ya shigo ɗakin ya nemi guri ya zauna, ba tare da ya furta komai ba." """Sayyid ba ka ci abinci ba fa tun na safe ba ka kuma cin komai ba, dan Allah ka yi haƙuri ka ci abinci""." "Bai ko kalle ta ba, balle ta saka ran zai ci, ƙarshe sai haƙura ta yi ta zura masa ido." "Ta gama shirinta, ta nemi guri ta kwanta, amma yana zaune. Nana ta jinjinawa girman zuciyar sa. Ya jima" a zaune sannan ya tashi ya canza kayan jikinsa. "Bacci har ya fara ɗaukar Nana, ta ji yana shigowa cikin bargonta, gabanta ya faɗi tuna abin da ya faru jiya," "sai dai ba ta motsa ba, sai addu'a da take yi a karkashin zuciyarta." "Ya matsa sosai ya rungume ta, yana yi mata numfashi a wuya." """Idan ina fushi, ki daina kula ni"" ya faɗa kamar mai raɗa." "Ba ta iya tanka masa ba, bai kuma sake ce mata komai ba, sai da ta ga babu alamar zai yi mata wani abu," sannan nannauyan bacci ya ɗauke ta. "Tamkar wani zai ƙwace ta, ya ƙara ƙanƙame ta a jikinsa. Sai ƙamshin turaren sa take yi." "A cikin baccin ta ji muryar Ƙaisar ""Ba kin shige cikin bargo ba, idan ki ka kuma ɗaukar littafin nan ki ka" "karanta, sai na baki mamaki, sai na yi miki abin da ba ki taɓa tsammani ba""" """To ina ruwanka da bargon da na shiga, ya naga kamar ka na kishi da mijin nan nawa ne?""" "Tsaki ya ja ya ce ""Da me zan yi kishin? Haryanzu ba ki san a hatsarin da ki ke ba, wauta da shirme ne" "kawai yake ɗawainiya da ke. Kin ƙi ki buɗe ido ki kalli gaskiya. Gaba ɗaya kin ma manta da batun tantance waye shi, duk da irin abubuwan da ki ke gani da ya saɓa da ɗabi'ar bil adama""" Ayshacool """A'a ba kyau zurfafa bincike, tun da Allah ya sa ina samun shinkafar da zan ci, ba ya saka ni kuka, babu" tashin hankali ai gara na haƙura na lallaɓa haka. Duk wani abu da yake yi da ya saɓawa ɗabi'ar Adam "wannan kuma na san kai ne, kai ka ke ƙulla komai. Na san so ka ke ka kashe mini aure, saboda kai duk" "yadda za ka yi hana ni jin daɗin rayuwata, shi ka ke yi""" "Galala yake bin Nana da kallo baki buɗe cikin mamaki. Ya ce ""Gaskiya ne, idan ya gama baki jin daɗin za" "kuma ki ɗanɗana kuɗar ki, banda ina duba wani abu da da kaina zan bayar da jininki ga matsafan nan ki mutu uban kowa ma ya huta!""" Ayshercool 08081012143 Ayshacool "Nana ta saci kallon ƙaisar, jikinsa har fitar da hayaƙi yake yi saboda fusata." "Ko a jikinta ta ce ""Amm dan Allah ka gaya mini ya aka yi da Lanti a gurin yin girka? Ya aka yi ka hau kanta," "tun da na ga ba da kai a ka fara yi mata girka ba, kuma ya aka yi ka canza sunanka? Ya aka ƙarke da sarkin aska kuma a garin? Ta yaya duk nake da alaƙa da wannan abubuwan?""" "Wani irin takaici ya turnuƙe Ƙaisar, ya tashi a fusace da niyyar ya yi jifa da ita, ko ya samu ya huce, sai" kuma ya fasa kawai ya fice ya bar ta a gurin. "Ta ce ""Wallahi sai na kai ƙarshen littafin nan, ko da kuwa za ka kashe ni ne, sai na ga ƙwal uwar daka, sai" "na karanta har ƙarshe ko me za ka yi sai dai ka yi""" "Sannu a hankali yake shafa fuskarta, yana kallonta, kamar wata jaririya haka ta yi miƙa sannu a hankali," "sai da ta banƙare gaba ɗaya. Ita gaba ɗaya ta manta da shi a kan katifar, a zatonta ita kaɗai ce a kan" "katifar, sai da ta ji ta a jikin mutum. Ta buɗe idonta ta kalle shi. Sai kuma ta ɗan tsorata, ta yinƙura da sauri. Amma ya riƙe ta yana kallon ta." """Amm lokacin salla ya yi ko?"" Ya ɗaga mata kai alamar eh." """To bari na je na yi alwala""" "Ya cika ta tashi, ta je ta yi alwala, sai da ta fito sannan ya ce ""Zan yi wanka""" "Ta ce ""Wanka kuma? Yanzu?""" Ya ɗaga mata gira daga kwance. """Ka yi da safe mana, gari da sanyi yanzu""" "Ya lumshe idanunsa ya buɗe, ya ce ""Tare mu ka kwana a shimfiɗa, kuma ya dai kamata na yi wanka""" "Ba ta ce komai ba, ta yi shiru, Allah ya taimake ta, tana da ruwan zafi a tea flask ta haɗa masa. Ya yi" wanka ya yi alwala ya fita Masallaci. "Nana kuwa bayan ta idar da sallar asuba, ta zauna a inda take ta fara karatun Alqur'ani." "Ya dawo ya tarar da ita, ya tsallake ta, ya nemi guri ya kwanta." "Wajen ƙarfe takwas ya farka, tuni Nana ta gyara ɗakin yana ta ƙamshi, tana zaune a kusa da socket, tana" caji tana danna waya. "Ya ɗora hannunsa a kan cinyarta, ya rufe fuskar wayar, ta waiwayo ta kalle shi ya ce ""Ina kwana?""" "Murguɗa masa baki ta yi ta ture hannunsa. Ya tashi zaune, ya matsa kusa da ita ya ce ""Na yi laifi ne?""" """Ai ka san me ka yi mini""" "Ya ce ""A'a abun tun shekaranjiya ba ya wuce ba?""" """Ni ba wannan ba, jiya na yi ta baka haƙuri amma ka haɗe rai ka ƙi kula ni, ka ƙi cin abinci ma"" ta ƙarasa" maganar tana hararsa "Ya ɗan yi murmushi ya sake matsawa, tamkar zai shige cikinta ya ce ""Na ce idan ina fushi ki daina kula" "ni""" "Ta noƙe kafaɗa ta ce ""Ni ba zan iya ba""" "Murmushin fuskarsa ne ya faɗaɗa cikin matsanancin farin ciki ya kama hannunta ya ce ""Ki yi haƙuri, idan" "raina ya ɓaci, ko bani da lafiya, bana iya magana. Wasu lokutan ina kasa magana haka kawai, amma ya fi idan raina ya ɓaci.""" """To ni da ba ni na yi laifin ba, sai ka daina yi mini magana? Na fi ka jin haushin abin da aka yi maka fa""" """Na sani, ban san ya aka yi nake iya magana sosai ba idan ina tare da ke, ina iya yin sati ban iya yin" "magana ba, kuma ina son na yi amma ba ta fitowa. Amma ke yanzu ina yin magana da ke sosai, ina jin daɗi""" "Nana ta kwashe da dariya ta ce ""Bagware idan ka yi magana dole sai mutum ya gane kai ba bahaushe ba" "ne ba""" "Yayi dariya ya ce ""Na fiki iya Hausa sosai, buzuwata saka kaya muje sayo abun karyawa1""" "Cikin murna Nana ta ce ""Yauwwa, dama ina son na fita na ga waje, tun da aka kawo ni ban taɓa fita ba""." "Dama ta yi wanka, ta saka hijjabi a kan kayanta, shi ma ya saka kaya, suka rufe ɗakin su ka fita." "Sosai unguwar ta yi wa Nana kyau, duk da ruwan da ake yi, babu alama a unguwar saboda akwai" "wadatattun magudanan ruwa, ba kamar unguwarsu ba, da ruwa ɗaya sai unguwar ta shafe kwana uku" maƙil da ruwa da azababben sauro. "Ya saka hannunsa ya riƙo na Nana, ta ɗaga kai ta kalle shi, ya kashe mata ido. Sosai abin ya ƙayatar da ita." """Sayyid""" "Ya kalle ta, yana jiran jin abin da za ta ce." """Dan Allah ina son ka bani dama, na je gida na duba Baba, yana ciwon ƙafa tun bayan biki ƙanwata ma" "da suka zo, ba ta da lafiya. Kuma ka ga a al'adarmu yakamata mu je mu yi wa mutane bangajiya""" """Mene hakan?""" "Ta yi murmushi ta ce ""Mu yi musu sannu, saboda hidimar biki da suka yi, ka ga Shukura ma babu lafiya" "tana asibiti, maman yaron da nake raino""" """Tom""" Ayshacool "Nana ta ce ""To yaushe za mu je?""" """Zan gaya miki""" """To na gode sosai mai rawani""" "Gurin da yake zuwa sayen ƙosai suka je, Nana ta yi mamaki ganin har a manyan motoci ake zuwa gurin" "sayen ƙosai, da kunu gurin matar." Nana ce ta yi wa mai ƙosan magana ta gaishe ta. "Matar ta ce ""Laa kece matarsa ko 'yar uwassa?""" Nana ta yi murmushi ba ta ce komai ba. """Allah sarki, yana zuwa sayen ƙosai ai, na nawa za a baku? Ki ce masa na ce kwana biyu bai zo sayen" "ƙosai ba, ban iya maganar su ba""" "Nana ta ce ""Ai yana jin ki""" "Matar ta ce ""Haba dai? Ba kurma ba ne?""" "Nana ta kwashe da dariya ta ce ""Yana magana""" """To ai kullum ya zo kuɗi yake bayarwa kawai, ko ya rubuta""" "Ya yi mirsisi kamar ba a kan shi ake magana ba, ya ciro kuɗi a aljihunsa ya bawa Nana." "Kamar Nana ta san matar, suka din ga hira, ta sallame su, suka nufi gida." """Sayyid dan Allah ka din ga yi wa mutane magana, ko dan saboda yanayin rayuwa. Ka ga da yawa ana" "ɗauka ko kai kurma ne"" shiru ya yi mata, haryanzu ba ta gama fahimtar sa ba." "Ba ta damu da rashin bata amsar waccan maganar ba ta sake cewa ""Yauwwa, dan Allah akwai gidaje a" "bayan gidan nan ne? Ina son sanin gidan Anty Haula, ina son na kai mata ziyara nima""" """Babu gidaje a baya""" """Amma ta ce mini gidanta a bayan inda muke yake""" "Ya ce ""Mu duba tare"" ya biyo da ita ta bayan layin, wasu irin manyan gidaje ake yi, sai dai duk kangwaye" "ne, babu ma alamar wani gida da yake da mutane a gurin." """Ina ga ban gane kwatancen ba, idan ta sake zuwa na tambaye ta. Amma sai na din ga jin hayaniya a" "bayan ɗakin, kamar akwai mutane a gidan"" kawai ya kalli Nana ba tare da ya ce mata uffan ba." "Ko da suka gama karyawa, roƙonsa ta yi tana son shiga cikin gidan, ta gaida Hajiyar. Ya ce ""A dawo lafiya," "idan kuma da maza ki dawo"" ta jinjina masa kai tana murmushi." "Yau ma a falon saman benen, ta iske Hajiyar gidan, tana waya a matuƙar fusace." """Ni wallahi na gaji, idan ka dawo ka san yadda za ka yi da ita. Ni me ake yi wa Yusra a gidan nan, balle a" "ce depression ya kama ta? Ga anti depressants ɗin nan, mun je mun ga Likita an bata, amma ta ƙi sha. Sai kuka, ba damar na yi mata magana ko nasiha ce sai ta hau kuka ta ƙule ta wuni a ɗaki""" "Nana ba ta iya jin abin da ake faɗa a cikin wayar, ta gama bambaminta, ta kashe wayar." "Nana ta gaisheta ta amsa, ta ɗora da cewa ""Yi haƙuri kin same ni ina waya ne""" "Nana ta ce ""Babu wani abu, bari na gyara falon""" "Matar ta ce ""Yauwwa dan Allah da kitchen ma""" "Nana ta ce ""To"" ta fara gyara ɗakin, tana cikin mopping ta fara jiyo wani sauti, da ta rasa sautin mene ne," kamar ana buga wani abu. Ta basar ta ci gaba da aikinta amma sautin ya ci gaba da fitowa daga wata siriryar hanya. """Ƙaisar"" ta furta a hankali. Kwana biyu hankalinta ya ɗan fara kwanciya, amma ta fuskanci matsalolinta" na ƙoƙarin sake dawowa. "Ta gama mopping ɗin falon, ta tafi kitchen ɗin, nan ma ta fara tattarewa kamar ba kitchen ɗin mata ba." Kaca-kaca ga tarkacen kwanuka wasu abinci duk ya bushe. "Ta haɗa kwanukan a sink, ta fara wankewa." "A hankali ta ji sautin nan ya biyo ta har kitchen ɗin, ya ci gaba da nufo inda take, ba ta waiwaya ba, ta" fara karanto addu'oin da suka sauwwaƙa a bakin ta. "Aka jefo mata kofi a cikin sink ɗin, mai jefowar ta nufi hanyar barin kitchen ɗin. Tamkar an dasa Nana ta" "kasa motsi, sai da ƙyar ta kalli ƙasan rigar matar har ta fice." "A hankali Nana ta fara jin sanyi, gabanta ya fara faɗuwa, hakan ya tabattar mata da akwai matsala." Kawai ta ɗauraye hannunta ta bi bayan matar. "Tamkar ana hankaɗata ta ƙarasa ta buɗe ƙofar ɗakin. Wata farar mace ta gani a ɗakin, a zaune fuskarta" ta yi ja alamar ta yi kuka. Ta zubo wa Nana ido. "Nana ta taka a hankali ta nufi gadon da matar take, ta zauna a kusa da ita." """Sannu""" """Yauwa"" ta amsawa Nana." """Shigowata ta uku kenan, ban taɓa ganin ki ba"" matar ta yi ƙurii da ido tana kallon Nana." "Nana ta miƙa mata hannu, da nufin su gaisa." "Tamkar doluwa, matar ta bawa Nana hannu da nufin su yi musabaha." "Su na gaisawa jikin Nana ya hau rawa, ita kuma launin fatar matar, ya ƙara yin jawur, idanunta ya fara" zubar da hawaye. "Nana ta ce ""Wace ce ke?""" Ayshacool "Bakinta yana rawa ta ce ""Ha...ha..Haulat""" """Me yasa ki ka yi mini ƙarya? Ki ka zo mini a matsayin mutum? Kuma me ki ke yi a jikin bil'adama?""" """Fansa na ɗauka, nan gidan a nan mune rayuwa da 'yan uwana, kawai su ka gina gida, hankalinsu" "kwance su ka yi zaman su, ba su yi tunanin akwai wata halittar a gurin ba. Da sun gabatar da karatun" "Alkur'ani ne ma, da mun haƙura mun tashi, amma kawai suka yi gini suka zauna""" "Nana ta numfasa ta ce ""Kuma sai ki shiga jikin wanda bai ji ba bai gani ba ki zauna? Kun san ba ma ganin" "ku, me yasa za ku din ga zaluntar mu, ba za ku yi mana uzuri ba? Yanzu kin kyauta an ce matar nan ba ta ci ba ta sha, sai kuka kin yi adalci kenan?""" """Nima ba a yi mana adalci ba, ramawa muke yi""" "Buzu yana zaune a kan benci, ya saka hanyar fitowa daga gidan, yana jiran ya ga ta ina Nana za ta fito," dan tana fita ya ji zaman ɗakin ya dame shi. "Kawai ya hango ta, ta fito idanunta a rufe, ta nufo shi. Sai da ta kusa ƙarasowa, sannan ya nufe ta yana" son tambayarta ko lafiya. Kawai ta tafi za ta faɗi ƙasa. Riƙe ta ya yi yana mamakin me ya same ta haka? "Ɗakinsu ya shigar da ita, ya kwantar da ita, yana mamakin yadda jikinta ya yi sanyi ƙalau." "Mamaki ne ya cika Nana bayan da ta ganta a tsakiyar daji, da ita da Haula." """Wace ce ke? Kuma me yasa ki ka yaudare ni ki ka zo mini a matsayin mutum?""" "Haula ta yi dariya ta ce ""Kamar dai yadda na gaya miki, laifi aka yi mini nake ramawa. Kwatsam kuma ke" "ma sai na haɗu da ke. Yanzu a duniya babu abin da nake ƙauna sama da hadimin ki, shi ya sanya ma har na yi yinƙurin taimakon ki, dan na samu shiga a gurin ki""" "Cikin rashin fahimta Nana ta ce ""Waye Hadimin nawa?""" """Ƙaisar, tun da na buɗi ido a duniya ban taɓa ganin kyakyawan matashin Aljani mai kyau da cikar zati" "kamar sa ba""" "Galala Nana ta kalle ta, ta ce ""Ƙaisar ɗin? Wannan zanƙalelen abin?""" """Ƙwarai shi, saboda na burge shi na zo na cinye gubar da aka kawo miki a wainar fulawa, sai dai kash!" "Haƙa ta ba ta cimma ruwa ba. Ina roƙon ki, ki taimaka mini na samu Ƙaisar, ni kuma na yi miki alƙawarin" "barin jikin matar can, da taimaka miki da duk abin da ki ke so""" """Tirrr Allah ya yi mini tsari da sake ja wa kaina wata jarabar, ta hanyar haɗa kaina da ku, shi ma maraba" "nake nema da shi, ido rufe, balle na sake rakito ki, ki je can Allah ya daidaita ku. A'uzu bi kalimattilahi tammat"" Nana ta furta a zahiri tana hamma. Ta tashi zaune ta ga an rurrufe ko ina na ɗakin, an kuna garwashi a ɗan kaskon dafa shayinsa." """Sayyid"" ta kira sunansa da ɗan ƙarfi, amma ta ji shiru." "Ta yi mamakin dalilin da yasa ya rufe ko ina haka. Ta shiga banɗaki ta yi alwala, saboda an idar da sallar" azahar ma. "Da ya shigo ɗakin ya tarar da ita ta idar da salla, bai ce mata komai ba, ta ɗora girki tana yi masa hira," "saboda ba ta iya tuna komai ba. Jin ya yi shiru ba ya tanka mata, ya sanya ta yin shiru." * "Yaya Atine ce ta zo gida duba Baba, ta ga yadda yake tafiya da ƙyar saboda ciwon ƙafa." "Ta jinjina kai ta ce ""Wai Isa wannan ƙafar taka, ka je asibiti kuwa?""" """Atine da wani kuɗin? Kin san auren 'ya na yi kwanan nan ai, mai nasara nake saya da aboniki sai a ji" "garau da nake haɗiya, shi ne nake samun afuwa na yi bacci""" "Ta kwaɓe baki ta ce ""Yanzu kana nufin duk kuɗaɗen da ka samu, da auren Nanan babu wanda za ka je" "Asibiti, ni fa zuwa na yi idan zan samu wani abu ma ka ɗan bani, gidana ko ƙwayar shinkafa babu""" """Haba Yaya Atine, ina su Nazifin da za ki zauna babu abinci?""" """Kai ina Gaddafi, ka ke zaune a haka?""" "Baba ya ce ""Gaddafi tun auren Nana ya tafi Ikko""" """Ka ga kawai ka fito da kuɗi, idan kuma matarka ta saka ka a gaba, ta tatse ka shikenan dama ka saba" "abin kunya""" "Caraf Mama ta ce ""Ina zunubin yake balle romonsa? Ina abin yake ni kar a yi mini sharri, ban ci komai" "ba""" """Idan ma kin cin ai ba za ki ce kin ci ba, ni Wallahi kamata ya yi ka mayar da hankali su ma su Jamila ka" "aurar da su, ko ka samu ka huta. Ni ina suke nema tun da na shigo ban gan su ba""" """Su na nan sun je gidanmu"" Mama ta ba ta amsa tana tsuke fuska, saboda kar ma ta ja zancen." "Ta gama surutanta, ta tashi ta tafi""" Ayshacool **** "Nana kuwa haka su ka ƙarasa wunin su, ba tare da wani yana kula wani ba, ya koma mata buzunsa. Sai" "dai hakan bai damu Nana sosai ba, saboda ya yi mata bayani. Duk da shirun bai yi mata daɗi ba, ɗan kulatan da yake yi, ba ƙaramin daɗi take ji ba." "Sai dai tana zaune, tana addu'ar kwanciya bacci, ya shigo ya gama abin da zai yi ya ɗane kan katifa. Ya" zauna ta ƙarasa addu'a ta shafa shi ma ya shafa. "Yana shirin ya ga ta kwanta, amma ta ƙi kwanciya." "Ya ce ""Mu kwanta""" "Ta murguɗa baki ta ce ""Ni ba bacci zan yi ba""" """To mu zauna""" """Ni kawai sai ka wani din ga yi mini shiru, ni ka daina irin haka ba na so"" Zuciyarsa na azalzalarsa ya" "tambaye ta abin da yake cikin zuciyarta, saboda har wani irin zafi yake ji a ƙirjinsa, amma ya kasa furta" komai. Ya rasa me ma zai yi gaba ɗaya. """Ba zaka kula ni ba ko?""" """Husnahhh"" ya furta a kunenta. Zirrr tsigar jikin Nana ta tashi." """Ki amsa ni""" """Na'am"" ta furta a tsorace. ""Ni mahaukaci ne, nima ba na gane rayuwar da nake yi, rayuwata ta" "banbanta da yadda sauran mutane suke ta su. Ni baƙo ne a duniyar nan taku. Ke kaɗai ce Ahalina, da ke kaɗai nake gane kan wannan rayuwar. Ba zan iya zama yadda ku ke ba gaba ɗaya, duk da ke ma wasu lokutan kin bambanta da rayuwar sauran mutane. Amma ki yi haƙuri da yadda ki ka same ni""" """Sayyid""" "Ya amsa mata da ""Ma vie""" """Dan Allah ka gaya mini gaskiya, zan karɓe ta a duk yadda take, dan Allah kai wane jinsi ne? Ka na tsorata" "ni wasu lokutan""" "Hannunsa bai daina yawo a jikinta ba ya ce ""Na fi yadda ni halitta ne kamar ke, mutum ne ni, amma ban" "san ya ake yi... Sai kuma ya yi shiru, kuma ya hana Nana sake cewa uffan, ta hanyar jan su zuwa duniyar ma'aurata, mai cike da al'amura masu tsayawa a zukata da wahalar mantawa." "Duk da, da faransanci yake gaya mata wasu kalamai, da ba ta san ma'anarsu ba, amma kai tsaye" "maganganun nasa suke shiga zuciyarta, tare da haifar mata da wata irin nutsuwa, duk da wahalar da ya bata." "Ta ƙara narkewa a jikinsa, ga bacci na son ɗaukar ta, amma zuciyarta da ƙwaƙwalwarta, na kan kalaman" "da ko fassarar su ba ta sani ba, sai dai tsananin daɗin da suke yi mata, ya sanya ta ci gaba da sauran su." "Sun shafe lokaci a haka, sannan da ƙyar ta tashi ta fara yin wanka, sannan shi ma ya tashi, sai dai kan ya" dawo tuni bacci ya yi awon gaba da ita. * "Tamkar Nana ta taka rawa yau, saboda murnar za su fita yau, ya ce mata tare za su je dubiyar." """Amma babu matsala ba za su buƙace ka ba mutanen gidan? Kar mu yi laifi""" """Na gaya musu""" "Da wuri ta gama komai, suka shirya suka fita tare." "Ta ɗaukko dubu goma a kuɗin hannunta, ta tsaya ta yi sayayya a hanya, sannan suka tafi." Asibitin da aka kwantar da Shukura suka fara zuwa. "Haidar ne ya fara gano ta, ya zabura daga jikin mahafinsa ya nufo Nana da wani irin gudu, cikin" matsanancin farin ciki. "Caraf Nana ta ɗaga shi, ta rungume tana juyi da shi a gurin. Kawai ya ƙara ƙanƙame ta ya saka kuka." "Ita kanta Nana hawaye ne ya cika mata ido, cikin sanyin murya ta ce ""Is ok sweetheart, ya isa haka"" ta yi" maganar tana shafa kansa cike da ƙaunar sa. "Yanayin kamaninsu da ta gani da Sagir, ya sanya ta gane shi ne mahaifin sa." "Ta ƙarasa suka gaisa, ta ce masa ""Dan Allah a wane ɗakin suke?""" """Su na ciki room 2 VIP, sai dai ba sa bari a shiga""" "Ta ce ""Subhnallah jikin har ya yi tsanani haka, Ubangiji Allah ya ba ta lafiya, Hajiyan na ciki ne?"" A fusace" "Sayyid ya ja hannunta, zuwa cikin asibitin. Sagir ya miƙe da sauri ya bi bayan su, saboda ga Haidar a gurin" "Nana, shi kuma ya ja Nana sun yi ciki ba sallama ba komai." "A ƙofar ɗakin suka tsaya, Sagir ya ƙaraso ya ce ""Bari na yi wa Mummyn magana"" ya shiga cikin ɗakin," "Nana ta dubi Sayyid ta ce ""Daga tsayawa tambaya, sai ka ja hannuna mu tafi ai ba zai ji daɗi ba""" "Wani mugun kallo ya yi mata, da ya tilasta mata yin shiru da bakin ta." "Hajiya Amina ce ta fito fuskarta ɗauke da fara'a tana faɗin ""Ga 'ya ta, ga 'ya ta"" ta rungume Nana. Nana" ta durƙusa har ƙasa tana gaida Hajiya Amina. """Lafiya ƙalau Nana, kin ga yadda ki ka yi kyau tubarkallah? Haidar yau ga Nana""" Ya yi murmushi yana sake riƙe hannun Nana. Ayshacool "Hajiya Amina ta ce ""Allah sarki, tare da mai gidan ku ke ashe, mu na ta ƙin abin nan da ganin an zalunce" "ki, Allah dai ya ƙulla lamarin. Sannu ka ji ya gidan?"" Hannu ya ɗaga wa Hajjya Amina tare da risunar da" "kansa ƙasa cikin girmamawa, ba tare da ya yi magana ba." "Nana za ta yi magana, mijin Shukura ya leƙo ya kalli Nana ya ce ""Ta ce ki shigo"" mamaki ya kama Nana," "amma ta ɓoye hakan. Ya karɓi Haidar saboda kar ta shiga da shi, ya damu Shukura. Nana ta shiga ɗakin da sallama, babu haske sosai a ɗakin, amma ana iya ganin komai da yake ɗakin. Nana ta ƙarasa gaban" gadon da Shukura take. Sai dai ta ɗan tsorata ganin Shukura duk a kumbure. """Sannu Maman Haidar, ya ƙarfin jiki?""" "Ta yinƙura da kyar, Nana ta taimaka mata ta jingina da jikin gadon ta ce ""Jiki da sauƙi Nana, dama za ki" "zo duba ni?""" """Haba Maman Haidar, me zai hana? Ni ban za ci za ki kawo yanzu ba ki haihu ba ma. Sannu"" Ta jinjina kai" "ta dudduba ɗakin ta ga daga ita sai Nana a ɗakin. Ta kama hannun Nana ta ce ""Na san a zamana da ke," "wataƙila na yi miki abubuwa marasa daɗi, duk da ina yaba ɗawainiyar da ki ke yi da Yarona. Sai dai" "kowane mutum akwai irin baiwar da Allah ya yi masa, komai kallon ƙasƙancin da ka ke yi masa." "Wannan maganganun nawa, ba sa rasa nasaba, da yawan miyagun mafarkin da nake yi da ke""" "Gaban Nana ya yi wata irin mummunar faɗuwa, ta kalli Shukura ta ce ""Da ni kuma?""" "Sai kuma Shukura ta rikice, ba ta san ta ina za ta fara yi wa Nana wannan bayanin ba, amma ta dake ta ce" """Mafarkai nake yi marasa daɗi, kuma ina yawan ganinki kin zo za ki taimaka mini. Ni dai kawai ki saka ni a addu'a a tsorace nake, ji nake yi tamkar zan bar duniya, ba zan rayu ba""." """A'a maman Haidar, kamar ba wayayyi ba, mafarki fa ba gaske ba ne ba, duk da wasu lokutan ishara ne," "amma mafarkin annabawa ne yake ɗari bisa ɗari gaskiya. Sai kuma wasu bayin Allah da a kan yi wa ishara a mafarki. Wasu lokutan shaiɗan ne kawai yake wasa da hankulanmu, amma ki kwantar da hankalinki ki saka a ranki babu wani mai yi sai Allah, kuma babu wanda ya isa ya yi miki abin da Allah bai yi miki ba. Sannan in sha Allah zan saka ki a cikin addu'a ba dan ki yarda cewa ganina da ki ke a mafarki a zahiri nice zan taimake ki ba, Ubangiji za mu nufa da buƙatunmu baki ɗaya, shi zai magance koma mene" "ne, ki kwantar da hankalinki dan Allah""" "Shukura ta jinjina kai ta ce ""Haka ne, na gode sosai da sosai Nana, na gode""" """Ba komai Allah ya ƙara afuwa, bari na je, na ji an ce ba a bari a shigo a gan ki""" """To shikenan na gode"" ta ji daɗin kalaman Nana, mussaman da ta yi ta nanata mata, mafarki ba gaskiya" "ba ne, wasu lokutan sharrin shaiɗan ne kawai." "Nana ta fito daga ɗakin, jikinta duk a sanyaye." "Hajiya Amina ta taso tana faɗin ""Nana kin fito?""" """Eh Hajiya, Ubangiji Allah ya bata ingantacciyar lafiya, Ubangiji Allah ya raba ta da cikin nan lafiya""" """Amin ya Allah Nana""" """A'a Hajiya ina Haidar ɗin?""" """Babansa ne ya tafi da shi yanzun nan""" "Jiki a sanyaye Nana ta ce ""Kash, ban gama ganinsa ba Hajiya""" """Ki yi haƙuri, jiransa ake yi, yana tafiya da Haidar ne gurin kakarsa ake kai shi, ni kin ga ga jinya, abin zai" "yi mini yawa ne. Amma in sha Allah zan saka a kawo miki shi har gida.""" """To shikenan, ga wannan a bawa yarona, wannan kuma a saya wa Maman Haidar wani abin, ban san me" "take so ba""" "Hajiya Amina ta ce ""Nana har da ɗawainiya har haka, dan Allah ki bari kar ki takura kan ki, zuwan ma da" "ki ka yi na ji daɗi sosai da sosai """ "Nana ta ce ""A'a Hajiya, idan ba ki karɓa ba ba zan ji daɗi ba, dan Allah ki karɓa""" "Hajiya Amina fuskarta ɗauke da murmushi ta karɓa ta ce ""To Allah ya saka da alkhairi, ki yi wa mijinki" "godiya ma ya ba wa Haidar kuɗi, Allah ya saka da alkhairi. Na ga haryanzu ba ya magana""" "Nana ta ɗan saci kallonsa, ta yi murmushi ta ce ""Ba komai Hajiya""" "Ganin hirar ta ssu ba zata ƙare ba, ya sanya shi yin gaba, Nana na ganin ya yi gaba, ta yi wa Hajiya Amina" "sallama a gurguje, ta nufi hanyar da ya bi." """Shi ne za ka yi gaba ka bar ni?"" Ya waiwayo ya kalle ta ya ci gaba da tafiya." Ayshacool "Ta tsaya tana yi wa Nurses ɗin gurin sallama, ya ja ya tsaya tare da waiwayowa yana hararar Nana. Ta yo" "gaba tana murmushi, tare da mamakin yadda yake so ta ƙarfin tsiya sai ya mayar da ita irin sa, na rashin" kula mutane. "Yana zuwa bakin ƙofar fita, ya ja ya tsaya, Nana ta ƙaraso tana ƙoƙarin duba, abin da ya hana shi fita" "amma ya tare ta, shi bai shiga ba, kuma ba dawo ba. Ta leƙa ta gefensa, ta ga mene ne ya hana shi" "wucewa, kawai ta ga Alhaji Zailani, tare da Doctor Sharif, a take gabanta ya yi wata irin mummunar faɗuwa, ta ja ta tsaya cike da razani da fargaba." Ayshercool 08081012143 Ayshacool "Alhaji Zailani ma gabansa ne ya faɗin, cikin fargaba yake bin ƙwayar idon Buzun da kallo, tare da" mamakin ganinsa a gurin a dai-dai wannan lokacin. "A hankali Sayyid ya ja da baya, taku biyu, ya sanya hannunsa ya riƙo Nana ta bayansa, ya ba su hanya." "Alhaji Zailani ji yayi tamkar an zare masa lakar jikinsa, jikin nasa ya yi wani irin sanyi, wani abu mai kama" "da tsoro ya shige shi. A hankali ya taka ya shigo, yana ƙoƙarin kallon Nana da ke tsaye a bayan Sayyid," "amma Sayyid ɗin ya hana hakan, saboda yadda ya ƙare babbakewa ya kare ta." "Ita kanta Nana ji ta yi yanayin ta na ƙoƙarin canzawa, ta saka hannu ta riƙe na Sayyid, tana addu'a a cikin" zuciyarta. "Wani irin baƙin ciki ya mamaye zuciyar Alhaji Zailani, ganin yanzu wannan Buzun ne mijinta, da ya aure" "ta ya san da yanzu buƙatar sa ta biya, wani abin yake hari ba wannan ba, amma Mahaifinta ya yi masa" sagegeduwa. "Doctor Sharif ya ce ""Alhaji lafiya kuwa?""" """Eh lafiya ƙalau"" Har Alhaji Zailani ya yi gaba, ya tsaya ya sake waiwayowa, amma ya sake ido huɗu da" "Sayyid, ya kange Nana, ya kare ta babu yadda za a yi ya iya hango Nana yadda yakamata. Sai da Sayyid ya tabattar Alhaji Zailani ya bar gurin, sannan ya waiwayo ya kalli Nana, yadda duk jikinta ya yi sanyi, ya kamo hannunta suka fita waje." "Bai dai ce mata komai ba, ta tare musu abin hawa, ta gaya masa inda zai kai su." "Gaba ɗaya Nana ta rasa abin da yake yi mata daɗi, ta rasa dalilin da ya sanya, gaba ɗaya ta rasa abin da" "yake yi mata daɗi. Duk da tana zaton hakan baya rasa nasaba da mugun nufin da Alhaji Zailani ya taɓa nuna mata, amma ta rasa dalilin da ya sanya gaba ɗaya take nema ta rikice, ta fita daga hayyacinta." "A hankali ta kwanta a jikin Sayyid. Cikin damuwa ya dube ta, ya dafa ta ya ce ""Ba lafiya ne?""" "Ta ce ""A'a""" """To Meyafaru?""" """Ba komai"" ta furta a hankali kamar mara lafiya." """Ko mu koma gida ne?"" Ta girgiza masa kai alamar a'a." """Sannu"" ta jinjina masa kai." "Sai da suka je daf da titin unguwar su, sannan ta tashi daga jikinsa, tana kallon titin nasu." "Suka je gurin da za su sauka, ya ciro kuɗi a aljihunsa ya miƙa wa mai Napep ɗin su ka tafi." """Sayyid""" Ya waiwayo ya kalle ta. "Sai kuma ta yi shiru, dan rasa me za ta ce masa ta yi." Tsayawa ya yi yana ƙare wa ƙofar gidan su Nana kallo. Ko ina faci ga uwar kwata a layin. """Bari na shiga na yi musu magana, sai ka shigo""" "Ya jinjina mata kai ya ce ""Zan je masallaci """ "Ta ce ""To shikenan, a yi mini addu'a""" "Ya ɗaga mata hannu, tare da jinjina mata kai, ita kuma ta shiga cikin gidan." "Sallama ta yi, Nasiru yana tsakar gida yana goge takalminsa, yana ganin Nana ya tashi da gudu ya nufe ta." "Nana ta rungume shi tana murmushi, ""Nasiru ya garin?""" """Lafiya ƙalau""" """Ina mutanen gidan ne?""" """Mama ta ɗan fita, Baba kuma ya je masallaci""" "Nana ta ce ""Samo mini tabarma na zauna a nan, ina su Jamila?""" """Jamila daga warkewarta ta tafi yawo, Suwaiba ma ba ta nan""" """Ohh ya jikinta kuwa, mu ka yi waya da Ummi, ta ce mini tun da ku ka dawo ba ta da lafiya """ "Nasiru ya ce ""Eh, amma ta warke, Mama ta ce wai me magani ya ce Aljani suka yi wa laifi. Aka yi sadakar" "ƙosai, aka dafa zakara aka bin..." """Ammm ya jikin Baba kuma"" Nana ta katse maganar Nasiru." """To ga shi nan dai, yanzu zai shigo ai ki gan shi""" "Nana ta ɗaukko wayarta ta ce ""Nasiru ga wayata, ga kuɗi ka yo mini turin fina-finai dan Allah"" ya karɓa" ya miƙe tsaye tare da faɗin an gama yanzu kuwa. "Nana ta tashi ta fara tattare tsakar gidan, saboda yadda aka bar shi kaca-kaca. Ta gama sharewa Baba ya" "yi sallama, ta ɗago ta kalle shi. Da ƙyar yake taka ƙafarsa yana bin bango. Ya tsaya sororo ya ce ""Ke me ki ke yi a gida kuma?"" Duk da Nana ba ta ji dadin tambayar da ya yi ba, saboda ta san yana tunanin ko auren ya samu matsala ne, amma ta yi murmushi ta ce ""Baba duba ku na zo yi"" Ta yi maganar tana gyara" masa tabarma a tsakar gida. "Ya ƙarasa ya zauna da ƙyar, Nana ta koma gefensa ita ma ta zauna ta ce ""Sannu ya jikin naka?""" """Jiki ga shi nan mu na lallaɓawa abu ya ƙi ci, ya ƙi cinyewa""" "Ta kalli ƙafafuwan nasa ta ce ""Wacce ce take ciwon a ciki?""" Ayshacool "Ya ce ""Duka, sai dai wannan ta fi ciwon"" ya yi maganar yana nuna mata ƙafarsa ta hagu." """To Baba ka je Asibiti?""" """Da wane kuɗin zan je Asibitin? Na gargajiya zan koma, ina fatan dai ba wata matsalar ba ce ta dawo da" "ke gidan nan?""" "Nana ta yi murmushi mai ciwo tana buɗe jakarta, ta fito da leda tana faɗin ""Baba idan matsala ta dawo" "da ni, ba zaka karɓe ni ba ko? Ai ka yi mini addu'a ka ce Allah ya bani zaman lafiya, in sha Allah matsala ba za ta kawo ni ba sai alkhairi"" ta yi maganar tana ɓare dafaffen ƙwan da ta fito da shi daga leda." "Ta gama ɓare ƙwan, ta miƙa wa Baba, ya saka hannu ya amshe, yawun bakinsa na tsinkewa." """Baba na san ni mai laifi ce a gurinka, na ɓata maka rai a kan abubuwa da dama, mussaman na bijirewa" "auren waɗanda ka so na aura, amma ina son mu saka a ranmu cewa, dukkanin su Allah bai ƙaddara akwai mijina a cikin su ba. Ni yanzu babban fatana ka daina yi mini kallon mutuniyar banza, na san dole na fuskanci tuhuma na abin da ya kai ni ɗakin su magadi, amma ba abin da ka ke tunani ba ne Baba, da zan lalace da ban kawo wannan lokacin ban lalace tun a baya ba."" Tuni hawaye ya wanke mata fuska, zuciyarta na wani irin tafasa da raɗaɗi. Baba bai ce mata komai ba, sai karɓe ƙwan da yake yi yana" lamushewa. "Ta goge hawayen ta, sai da ta ɓare masa dafaffen ƙwan nan guda biyar, ta ɗebo ruwan randa ta kawo" masa ya karɓa yana sha. "Ta ɗaura alwala ta yi sallar azahar, bayan ta idar, Nasiru ya shigo gidan yana faɗin ""Nana ga wayar ki, an" "ciko miki ita da fina-finai fal""" "Ta yi murmushi ta ce ""Na gode yaron kirki""" "Mama ta yi sallama ita da Suwaiba, sai da suka ɗan yi turus ganin Nana a gidan babu tsammani." """Lafiya dai na ganki a gida? Ba dai auren ne ya samu matsala ba""" "Nana ta waiwaya ta kalle ta, ta yi murmushi ta ce ""A'a ganin ku na zo yi, na gaishe ku, aurena bai samu" "matsala ba"" Mama ta kwaɓe baki tana rataye mayafinta a kan igiya." "Nana har kallon Mama take yi, tana mamakin wai ita ba ta san ƙarara a fili take nuna ƙiyayyar da take yi" mata ba. "Nana ta ce ""Suwaiba ya ku ka zo gida?""" """Lafiya ƙalau wallahi, mu na dawowa Jamila ta kwanta rashin lafiya""" """Haka Ummi take gaya mini, shi yasa yau na yinƙuro na fito. Nasiru duba idan ya idar da salla, ya shigo ya" "duba Baban mu tafi, ban yi girki ba""" Nasiru ya ce to. "Suwaiba ta ce ""Nana wai waye yake ba ku Abinci? Gidan da ku ke aikin ne suke ba ku?""" "Nana ta yi murmushi ta ce ""A'a wanda ya ajiye ni ne yake kawowa, ba kuna nan ya kawo muku fura ba""" "Nasiru ya ce ""Yana waje, na yi masa magana bai kula ni ba""" "Nana ta yinƙura ta ce ""Bari na yi masa magana""" Yana zaune a wani dakali da yake kallon gidan su Nana. Yana ganin ta fito ya miƙe tsaye yana kallon Nana. "Ta ƙarasa ta ce ""Sayyid, zo mu je ku gaisa da Baban""" """Wai in shiga?""" "Ta ce ""Eh, ku gaisa da Babana ka duba shi""" "Nana ta yi gaba ya bi bayanta," "Gaba ɗaya suka zubo masa ido, sai dai kansa a sunkuye, har suka isa gaban Baba." """Sannu"" ya furta a hankali yana tunanin ko haka ya kamata ya ce?" """Yauwwa sannu, ya iyalin?""" "Ya ce ""Alhamdilillah""" "Baba ya ce ""To madalla""" "Nana ta ce ""Sayyid, ga ƙanwata wadda su ka zo ranar, ga mamana, ga kuma Nasiru da suka zo a tare""" "Bai kalli inda Mama take ba, ya ce ""Sannu""" "Yanzun ma kwaɓe baki ta yi ta ce ""Ji wata irin gaisuwa, haka ake gaida sirikai?""" "Nana ta ce ""Ki yi haƙuri, ba hausa sosai ne""" "Buzu dai bai tanka musu ba, ya miƙa hannu ya ɗora a kan ƙafar Baba, ya ce ""Allah ya sauwwaƙe""" """Amin na gode"" ya ɗan jima yana kallon ƙafat, sannan ya ɗauke hannunsa, ya saka a aljihunsa, ya ciro" kuɗi ya ajiye wa Baba a gefen ƙafarsa ya tashi tsaye. "Nana ta bi kuɗin da kallo, ba tare da ta san ko adadin nawa ba ne ba." "Baba ya ce ""Duk wannan haka, to na gode sosai Allah ya yi albarka""" "Nana ta ce ""Baba bari mu tafi gida, Allah ya baka lafiya ya ƙara afuwa, dan Allah a gaida Jamila idan ta" "dawo""" "Sayyid tu ni ya yi waje, domin shiga gidan su Nana ji ya yi tamkar ya yi tsirara, gaba ɗaya idanun" mutanen gidan da bai saba da su ba ya ji ya takura masa. "Suwaiba ta ce ""Ke Nana wai mijin nan naki kamar dodo, baya sauke wannan takunkumin na fuskar shi," "ko ba shi da haƙora ne?""" Ayshacool "Nana ta yi dariya ta ce ""Biyo ni waje na saka ya sauke miki rawanin ki gan shi. Baba Allah ya sauwwaƙe" "idan Jamila ta dawo a yi mata sannu"" Nana ta ja takalmanta ta yi waje." "Tana fita waje, ta yi karo da Gaddafi. Turus Nana ta tsaya cikin tsoro, sai ma ta rasa me za ta ce masa." """Nana me ki ke yi a gida?""" """Zuwa na yi duba Baba, ina wuni?""" """Lafiya ƙalau, ya ki ke ya gidan?""" """Lafiya ƙalau, ashe ka dawo""" """Eh na dawo shekaranjiya"" Nana ta yi tsuru-tsuru, tana hango Sayyid da ya tsaya yana kallon ta, ya tsuke" fuska tamkar ya fashe. """Amm ai tare ma muke da shi"" ta faɗa cikin kame-kame." "Gaddafi ya waiwaya, ya kalli Buzu ya mayar da idonsa kan Nana ya ce ""Amma babu wata matsala dai" "ko?"" Nana ta jinjina masa kai." "Gaddafi ya saka hannu a aljihunsa ya ɗaukko kuɗi ya miƙa mata ya ce ""Ga wannan, kya sai wani abun""" "Ta saka hannu biyu ta karɓa, tana mamakin yadda duk Gaddafi ya canza." """Nana duk yadda za a yi, ki riƙe auren ki, ki ƙaddara wannan shi ne zaɓi mafi alkhairi da Allah ya yi miki," "kin san zaman gidan nan namu ba daɗi ne da shi ba""" "Nana ta jinjina kai ta ce ""Na gode sosai da sosai Yaya""" "Ta nufi inda Sayyid yake, idanunsa kawai suka tabattar mata da a hasale yake." Har suka je gida bai sake tanka ta ba. "Su na zuwa a gurguje Nana ta yi sallar la'asar, ta ɗora girki, dan ba su ci komai ba." "Shi kuwa tuni ya haɗa kayan shayinsa, yana ta tafasawa yana sha." "Ta ɗaga labule ta ce ""Sayyid, na gama girki, ka zo ka ci"" ya ɗago ya kalle ta ya mayar da hankali ya ci gaba" da shan shayinsa. "Sai da ya gama jan ajin, sannan ya shigo ɗakin, ya ɗauki nasa abincin ya fara ci." * "Mutumin yana zaune a kan kujera, a wani katafaren falo, ya ƙare wa Jamila kallo ya ce ""Wannan ce" "yarinyar?""" "Hajiya Sa'a ta ce ""Ita ce ranka ya daɗe""" """Kuma kin tabattar za ta riƙe amana? Ba za ta tona asirin ƙungiya ba?""" """Ƙwarai kuwa, na yi mata duk abin da ya kamata""" "Ya yi dariya ya ce ""Babu laifi, wannan Shekarar da ita za mu yi taronmu na shekara""" "Ita dai Jamila ba ta iya cewa komai ba, sai tsananin mamaki, ganin daular da ba ta taɓa tunanin akwaita" ba. "Bayan Hajiya Sa'a sun gama magana da mutumin, ta ɗauki Jamila su ka fita." """Hajiya yanzu dama haka garin Abuja yake? Lallai na zaune bai ga gari ba, kalli gidaje""" "Hajiya Sa'a ta yi dariya ta ce ""Jamila kenan, a garin nan gidajane sun fi huɗu, akwai arziki Jamila, muddin" "za ki yi biyayya ki riƙe sirri, to za ki samu arzikin da sai ya kankare baƙin talaucin da yake bibiyar zuriyar" "ku. Dan ma mun kasa samun jinin yayar ki ne, da tuni ta fashe mana tana da taurarin arziki amma ba ta san yadda za ta yi amfani da su ba ne ba""" "Cikin shauƙi da zumuɗi Nana ta ce ""Kai in sha Allah, zan riƙe amana da sirri babu wanda zai ji komai""" """Yauwwa yarinyar kirki, wannan yana ɗaya daga cikin shugabannin ƙungiyarmu, tun da ya amince da ke," "tare da ke za mu je taron shekara, ina saka ran a karɓe ki a ƙungiya""" * "Har wajen ƙarfe goma na dare, bai shigo ɗakin ba, Nana ta kashe fitila, ta ɗaga labule, ta hange shi a" "zaune a kan benci yana ta kore sauro, yana shan shayi." "Kawai ta girgiza kai ta nemi guri ta zauna, ta yi addu'oin kwanciya bacci, ta kwanta." "Ta kai a ƙalla mintuna arba'in, tana tunanin yadda rayuwa za ta ci gaba da juyawa a haka. Zama da" mutumin da ba ta san ma waye shi ba. "Tana kallon ƙofa, ta ga ya shigo, ya ajiye kayan shayinsa ya tafi banɗaki. Ya jima a ciki sannan ya fito daga" "ciki, ya rataye kayan da ya cire, ya nufo kan katifar." "A ranta take jinjina ƙarfin hali na maza, da a ƙasa yake zamansa, ko ya kwana a waje a kan benci, amma" yanzu kansa tsaye yake ɗarewa katifa. "Ba ta gama tunanin ba, ta ji shi a jikinta." """Me yasa ki ke kallona?""" """Ya aka yi ka san ina kallon ka a duhu?""" """Na sani, tun da na shigo ki ke kallona""" """Shi ne tun da mu ka dawo, ka ƙi kula ni""" "Ya ɗan yi shiru kamar ba zai yi magana ba sannan ya ce ""Ba na son na ga wani yana yi miki magana," "zuciyata na yi mini ciwo. Ba na son kowa ya kalle ki, ba na son kowa ya ji muryar ki, ba na son wani ya raɓi inda ki ke, sai nikaɗai ban san dalili ba amma ina jin kamar zuciyata za ta tsaya ne, ba na so""" Ayshacool """Amma wanda ka ganmu tare, Yayana ne fa, babanmu ɗaya da shi"" Ya yi shiru bai yi magana ba." "Ita ma ta ɗan yi shiru sannan ta ce ""Sayyid a ina ka samu kuɗi ne? Na ga ka bawa Haidar, ka bawa Baba," "kuma ka na sayo mana abubuwa""" """Allah ne ya bani""" """Eh na sani, amma waye yake baka?""" """Habu"" ya amsa kai tsaye." """Shi ba shi da nasa buƙatun zai din ga kashe mana kuɗi har haka?""" Ya yi shiru bai amsa mata ba. "A hankali Nana ta ce ""Sayyid""" """Husnahh""" """Dan Allah ya ake yi ka ke yin wasu abubuwan, ka san na ce maka, ba ni da cikakkiyar lafiya wasu lokutan" "gaba ɗaya a rikice nake ba na tantance ainihin zahiri da mafarki, amma sai na ga kana abubuwan da mutane normal ba sa iya yi""" """Kamar me?""" "Ta ce ""Ammm ka na shigowa cikin mafarkina""" "Kawai ta ji ya yi dariya ""Dama wani na shiga cikin mafarkin wani ne? Ba mafarkinki nake shiga ba, ruhina" "ne yake rayuwa a cikin naki, kuma naki yake rayuwa a nawa. Na fuskanci hakan a ranar da na fara ganin ki, zuwa ranar da aka ɗaura mana aure""" """Ban gane ba, ka yi mini bayani sosai""" "Ya yi ajiyar zuciya ya ce ""Ƙirjina ya fara nauyi""" """Saboda me?""" Ya yi mata shiru. """Amma Sayyid ""Shhhh zan yi bacci""" "Ta ce ""Tambaya ɗaya zan yi maka dan Allah""" """A'a""" """Allah fa na ce""" """Na ce A'a""" "Ta ɗan ja numfashi ta ce ""To amm... Tsit ta yi dalilin bakinsa da ta ji a nata." Ya riƙe hannunta a nasa yana matsa nata a hankali. """Dan Allah ka bari yau mu samu isasshen bacci, ni dan Allah ka ƙyale ni""" "Ya ce ""Idan ma kin yi baccin, zan biyo ki har cikin baccin naki. Na gaya miki ruhinki a cikin nawa yake" "rayuwa, ko fushi ki ke yi a cikin jikina nake ji""." "Haka ya yi ta tsaro maganganun, da suka ci gaba da dagulawa Nana lissafi, da birkita mata ƙwaƙwalwa," "wanda ba ta gama warwarar su ba, har ya nufi inda yake son zuwa." * "Tun bayar tafiyar Nana, da Shukura ta ga mahaifinta ta ji gabanta ya faɗi, ta kalle shi cike da tsoro da" razani. "Cikin kulawa ya ce ""Sannu Auta, haka ki ka koma? Ya jikin naki?""" "A tsorace ta ce ""Daddy dama yau zaka dawo, Mummy ba ta gaya mini ba""" "Cikin damuwa ya ce ""Ina can hankalina ya ƙi kwanciya, na ce bari na zo na ganki, na kira Sharif ya ce mini" "jikinki da saura, shi yasa na ce gara na zo na gan ki""" "Ta dai yi shiru, gabanta na ci gaba da faɗuwa, ya gama yi mata sannu ya tashi suka fita tare da doctor" Sharif. """Sharif """ """Na'am ranka ya daɗe""" """Muddin yaron nan zai rayu, ka yi duk mai yiwuwa a cire shi kawai, a matsa nake""" """Zan yi iya ƙoƙarina, amma ka san wannan sabga ce mai haɗarin gaske, sai an yi taka tsantsan yadda ba" "za a bar duk wani trace da za a gane wani abu ba, zan yi setting date da komai da yadda abin zai kasance""" """Better"" Alhaji Zailani ya furta yana yin gaba." "Gidansu Nana har ƙarfe goma na dare Jamila ba ta dawo ba, Baba yana tsakar gida yana yi wa Mama" bala'i. """Yanzu Rabi sakarcin naki har ya kai Jamila ta kai bayan goma a waje? Gidan uwar wa ta tafi haka?""" """Wai dan Allah Jamila za ta gudu ne? Na ga dai ba yarinya ce ƙarama ba, na ce maka za ta dawo""" """Za ta dawi gidan uban ta je? Goma na dare ta riga ta wuce, me take yi a waje a wannan lokacin?""" """Dan Allah ni kar ka ɗaga mini hankali, na ga dai yarinyar nan ba sauke hakkin da Allah ya ɗora maka ka" "ke yi ba, abinci ma ba bamu ka ke yi ba, sai ma dai ta samo ka ci""" """Da ba na sana'a sai na zuba ido su lalace? Sana'ar uwar me take fita?""" """Ni fa 'ya ta ba lalacewa ta yi ba, na ga dai nan Nana take nata yawo, ba ka yi magana ba""" """Ai Nana na san me take fita yi, Jamila fa, na san dai tana yawon maƙota, bayan wannan uwar me take" "yi?"" Sosai su ka ci gaba da jayayya tsakanin Mama da Baba, sai sha ɗaya da rabi na dare, sai ga Jamila ta" "yi sallama, hannunta niƙi-niƙi da ledoji." "Duk da ledojin hannunta, sun ɗauki hankalin Baba, amma ya dake ya fara tuhumar ta daga ina take." "Mama ta kankane, ta hana Jamila magana, ta din ga karewa." "Ƙarshe sai haƙura ya yi, ya rabu da su." Ayshacool "Ita kanta Suwaiba jiki a sanyaye take kallon kayan da Jamila ta zo da su, tana fargabar Allah ya sa ba" "kauce hanya 'yar uwarta ta fara yi ba. Sai dai Mama ko a jikinta, musamman da Jamila ta ce mata, Hajiya Sa'a ce ta saya mata, wai gidan 'yar uwatta ta raka ta." "Wajen Sha biyu na dare, Jamila na ta bawa Suwaiba, labarin abin duniyar da ta gani." "Suwaiba ta yi tsuru da ido tana kallon Jamila, daga bisani ta ce ""Ni dai Jamila na fara jin tsoron matar nan," "anya haka kurum take yi miki wannan ɗawainiyar. Jamila kar ki kai kan ki ga halaka, idan rayuwar ki ta lalace ba ki da wata makoma wallahi""" "Jamila ba ta yi magana ba, Gaddafi ya faɗo ɗakin ya kalli Suwaiba ya ce ""Bar ɗakin nan"" Jamila ta miƙe ita" "ma a tsorace tana kallon sa""" """Fita na ce"" ya yi wa Suwaiba tsawa." "Jamila na ƙoƙarin fita, ya danna ƙofar ɗakin ya saka sakata, ya fito da wani irin danƙo na injin markaɗe," "ya kalle ta ya ce ""Gidan uban wa ki ka je, ki kai yanzu ba ki dawo ba?""" "Jamila ta rikice jikinta yana tsuma, amma ta kasa magana." """Ba magana nake yi miki ba?""" """Babu inda na je?""" """Ƙarya ki ke yi, uban waye ya sauke ki a mota?""" """Hajiya Sa'a ce""" """Babar ki ce ita? Meye tsakanin ki da ita?"" Jin ta tsaya inda inda, ya sanya ya fara zuba mata danƙon nan" a jikinta. "Cikin kururuwa Mama take dukan kofar ɗakin, tana neman agajin mutane, kar Gaddafi ya kashe mata 'ya." "Ya zuba wa Jamila danƙon nan, ya fi sau sha biyar, sai da ya zamana daga ita sai underwear." "Sai da aka taru aka yi ta yi masa magiya, sannan ya buɗe ƙofar ɗakin ya yo ball da ita waje." "Mama hankali a tashe ta nufi Jamila tana salati, saboda wahala ko kukan ba ta iya yi, sai wani yawu da" yake fita daga bakinta. "Baba ya ce 'Haba Gaddafi, ba kowane lokaci duka da zuciya yake aiki ba, yanzu idan ka illata ta fa, mace" "ce fa""" "Gaddafi bai saurari Baba ya ce ""Wallahi ta sake sai na karairayata, ba za ta ɓata mana suna a banza ba""" "Cikin ƙaraji Mama ke faɗin ""Wallahi ba zan yarda ba, sai na kai ka gurin hukuma""" "Nasiru da yake gefe ya ce ""Allah sarki, Nana na can, da yanzu an ce ta hana mutane bacci"" babu wanda" "ya saurari abin da Nasiru yake faɗa, suka ci gaba da hayaniyar su." **** "Ko da Nana ta fito daga wanka, yana tsaye a ƙofar banɗaki yana jiran ta, ta murguɗa masa baki, za ta" "wuce ya riƙe ta yana murmushi ya ce ""Meya faru?""" """Ni rabu da ni, ka hana ni bacci, ga jiƙa kai sai na yi ciwon kai""" """Ba dai fi na gashi ki ka yi ba"" ya yi maganar yana taɓa gashin nata." "Nana ta kalle shi ta ce ""To yi mini gori"" bakinta ya sake sumbata yana murmushi." "Ta gyara shimfiɗa ta hau, shi ma ya haye yana buɗe bargo." """Ni gaskiya katifar nan ta yi mana kaɗan""" "Ya ce ""Ya za ayi?""" """Ka saukar mini daga kan katifa, ai na ga ma ba a ɗakin nan ka ke kwana ba""" """Na gama yi miki amfani dole ki kore ni, ba inda zan je"" ya yi maganar yana kwanciya""" "Nana ta ce ""Na shige su, idan muka futa sai ka yi gumm, sai na yi ta yi wa mutane bayanin ka na magana," "ba kurma ba ne ba, amma daga ni sai kai ka yi ta wasu maganganu""" "Tana jin sautin dariyar sa, cikin nutsuwar sa, da ta fi kama da Iyayi ya ce ""Asma'u ke duniyata ce, tun da" "na farka a cikin wannan duniyar, nake jin tamkar nikaɗai ne baƙo, Habu yana iya ƙoƙarin sa a kaina," "amma ba ya wadatar da ni. Fatana da burina na yi na gama mafarkin nan na tashi, na koma ainihin rayuwata." "Ba na jin daɗin komai a wannan rayuwar, sai ranar da na fara ganin ki, tare da yayar ki da suka zo kun je" "gidan mai magani, har ki ka faɗi. Ina ganin ki na ji kamar ina da wata alaƙa mai ƙarfi da ke.""" """Ni ɗin? Yanzu dama kai na gani ranar da muka je?""" """Mun haɗu a gidan sarkin baka ma.""" "A zabure ta ce ""Sayyid ka san sarkin baka?""" "Ya ce ""Na sani, Habu sun kai ni, ko zan iya tuna ni waye. Ban taɓa maganar awanni biyu cikakkiya a rana" "ba, ban taɓa shafe sati guda ina iya magana ba. Duk sai bayan zamanmu a guri guda. Ni na ce Habu ya biya mini sadakin auren ki, tun ranar da na ganki kullum sai na yi mafarki da ke. Shi yasa da mai gidan da muke yi wa gadi ya ce na sake ki, zai biya ni na na ji kamar na kashe shi. Na san ni mahaukaci ne, amma" mahaukaci bai kyautu a kyautata rayuwar sa ba. Ayshacool "Ke Duniyata ce, a tare da ke nake iya doguwar magana, na ci abinci, na daɗe hankalina bai gushe ba. Ba" "na son kowa ya raɓe ki, ko ya kula ki, saboda ina jin tsoron kar na buɗe ido na ga ba kya kusa da ni.""" "Ya kwantar da kansa a ƙirjinta ya ce ""Ke ce Ahalina, kuma Duniyata. Ke Duniyata ce""" "Haka ya din ga maimaitawa har muryarsa ta fara rawa, tamkar zai fashe da kuka." "Nana ta saka hannu ta zagaye bayansa, ta rintse idanunta, sai dai ta kasa magana a dalilin sanyi da ta" fara ji. "Sauti ta fara ji na tasowar guguwa, ta buɗe idonta, ta gansu a cikin sahara tsakiyar dare, sai hasken farin" wata da ya gauraye ko ina. "Tsohon nan ta gani a tsaye a kan su, hannunsa riƙe da sandarsa." Ayshercool 08081012143 Ayshacool """La'ila ha illa anta subhanaka inni kuntu mina zalimin"" Haka Nana ta rintse idanunta tana maimaitawa." "Tana jin yadda yake sauke numfashi a jejjere, yana ƙara ƙanƙame ta." "Ta sake buɗe idanunta a hankali, ta gansu still a cikin saharar nan." "Tamkar wani zai ƙwace shi, haka ita ma ta rirriƙe shi, tana ci gaba da karanto addu'oin da suka sauwwaƙa" "a bakinta. Zuwa jimawa ta daina jin sanyin, ta buɗe idanunta ta gansu a cikin ɗaki, jikinta ya gaji saboda yadda ya sakar mata nauyin shi gaba ɗaya a jikinta." """Sayyid"" ta kira shi a hankali. Amma shiru, sai dai tana jin yadda cikin sa yake ɗagawa yana sauka a" "hankali alamar bacci yake yi. Ta motsa a hankali ta gyara kwanciyarta ta ci gaba da shafa kansa, tana tofa masa addu'a." "Wani irin nishi ta ji ya yi, ya yinƙura a gigice ya tashi zaune cikin ɗaga murya ya ce ""Sultan""" "Cikin azama Nana ta tare shi, duk da ya fi ƙarfinta, ta riƙe shi gam." Haki yake yi tamkar wanda aka biyo ya ƙwace da ƙyar. "Ta yinƙura ta kunna fitilar ɗakin, ta dawo ta zauna a kusa da shi. Cikin sanyin murya ta ce ""Sayyid. Me ya" "faru? Waye Sultan ɗin?""" "Hannunta ya kamo, ya ɗora a saitin zuciyarsa, ya riƙe hannun nata yana sauke numfashi." """Sannu"" ya jinjina kai." "Ya sunkuyar da kansa ya yi shiru, fuskar sa na bayyanar da matsananciyar damuwa da tashin hankali. Ta" "sanya ɗaya hannun nata ta dafa shi ta ce ""Sayyid mene ne?"" Ya ɗago da ƙyar ya kalle ta, ya buɗe baki zai yi magana amma sai ya kasa." "Can tamkar an jefo maganar bakinsa ya ce ""Wani abu ne yake damun zuciyata, ban san mene ne ba," "amma ya yi mini nauyi, kamar zan bar duniya""" "Ta ce ""Ya isa, ya isa haka ka yi shiru, in sha Allah babu wani abu, ka yi haƙuri"" ta yi maganar tana shafa" "gadon bayansa. Ga mamakin ta kawai ta ga hawaye na gangarowa daga idanunsa. Rikicewa ta yi cikin tashin hankali ta ce ""Sayyid mene ne? Meye ya saka ka kuka?""" Ya girgiza mata kai alamar bai sani ba. "Tun yana yi a hankali, kukan nasa ya din ga ƙaruwa, har da jijjiga. Ganin ta rasa abin yi kawai ta fashe da" "kukan ita ma, ta hau taya shi." "Ya janye ta daga jikinsa, ya kwantar da ita a kan pillow, shi ma ya kwanta a gefen ta, yana son ya yi mata" magana amma tilas ya haƙura ya kasa ce mata uffan. * "Hajiya Amina na kwance tana bacci, a kan carfet, a ɗakin da take jinyar Shukura, ita kuma tana kan" "gadon marasa lafiya tana bacci, ta ji an kama hannunta. Ta yinƙura za ta yi magana amma wani irin jiri ya ɗebe ta daga kwancen da take, duk yadda ta so ta yi wani yinƙuri ko ta yi magana, ta kasa sannu a hankali jikinta ya yi sanyi, ya mutu murus, daga nan hankalinta ya gushe baki ɗaya." * "Fuska ɗauke da damuwa, Nana take kallon inda Ƙaisar yake ta haɗe-haɗen maganunansa, ba tare da ya" dubi inda ma Nanan take ba. """Ƙaisar""" """Na'am""" """Karo na farko zan roƙi alfarmarka""" """Ina jin ki"" ya amsa ba tare da ya kalli inda take ba." """Abu na farko ina roƙon ka, dan Allah ka yi haƙuri, ka saki ƙafar mahaifina, abu na biyu dan Allah ka bar" "ni mu zauna lafiya da mijina, ka daina wahalar da mu har haka dan Allah ka yi haƙuri.""" "Ya ajiye abin da yake yi, ya dawo gaban Nana ya zauna, ya kalle ta ya ce ""Na riga na rantse sai na" "hukunta mahaifinki, mijinki ya shiga gona ta, ya kwance ƙullin da na yi wa mahaifinki a ƙafa, zai ɗanɗana kuɗarsa zan nuna masa gaba ma akwai gabanta""" "Cikin rashin fahimta Nana ta ce ""Ta yaya ya kwance ƙullin da yake ƙafar Baba?""" """Oho ya dai kwance, kuma zai ga abin da zan yi a kai, sannan ki daina yi mini magiya a kan abin da yake" "faruwa, wannan wani abu ne da ki ka amince da shi da kan ki, dan haka dole ki jure duk abin da za ki gani." "Sauran tambayoyin da ki ke son yi mini kuma ki adana abin ki, dan amsa miki su, dai-dai yake da amincewa da sharuɗana""" "Cikin kuka Nana ta ce ""Dan Allah Ƙaisar kar ka cutar da shi, shi kansa bai san wasu abubuwan na faruwa" "ba""" "Ƙaisar ya miƙe tare da cewa ""Allah ko?""" """Da gaske, bai san su na faruwa ba, dan Allah ka bar mu, mu ji da ƙalubalen rashin lafiyarsa, da rashin" "sanin waye shi""" "Wata irin guguwa ce, ta gauraye cikin Libraryn, da sauri Ƙaisar ya buɗe rigarsa, ya kare Nana." Ayshacool "Tsohon nan ne ya bayyana a cikin libraryn, ya tsaya yana kallon Nana." "Ƙaisar ya tsaya a gaban Nana ya ce ""Me ya kawo ka inda nake? Da izinin wa ka shigo gurin nan?""" """Ba na buƙatar izini, kafin zuwa inda farauta ta yake""" "Ƙaisar ya ce ""Kar ka ƙetare layin da ka iya kawo, gagarumin tashin hankali da rashin jituwa tsakaninmu""" """Hannun agogo za ka mayar baya, ka gyaro ɓarnar da ka tafka, idan kuwa ba zai gyaru ba, to ba zaka" "hana ni, aikata abin da na yi niyya ba""." """Ka aikata duk abin da ka so, amma ka taɓa uwar gijiyata a wannan karon ƙarshen rayuwarka zan kawo a" "doron Duniya""" "Jin tarin da Nana ta yi ne, ya sanya ta farkawa." "A ƙasa ta hango shi, maimakon kan katifa, yana wannan jijjigar da ya yi." "A rikice ta tashi ta nufe shi, tana ambaton Allah." """Sayyid jikin ne dai?""" "Wayarta ta ɗaukko, ta kunna karatun Alqur'ani, sannan ta ɗakko bargo ta lulluɓe shi da shi, ta zauna ta" "saka shi a gaba, ta zura masa ido cike da damuwa." "Har gefin Asuba, sannan Allah ya sanya ya daina wannan rawar sanyin." * "An kai ruwa rana da Mama sosai da sosai, kafin ta amince ta haƙura, amma da rantsuwa ta yi a kanz sai" "ta kai Gaddafi gurin 'yan sanda. Ana bata haƙuri shi kuma ya ce ""Idan ba ta kai shi gurin 'yan sanda ba, ba" "Hudu mai ice ne ya haife ta ba"" wato mahaifinta." "Duk da Baba yana cikin wannan tashin hankali, amma ya lura da sauƙin da ya samu, game da ciwon da" "ƙafarsa take yi masa tun jiya. Sai dai damuwa da tashin hankali ya sanya, bai mayar da hankali a hakan ba, ya karkata ga son kashe wutar da ta taso a gidansa." **** "Hajiya Amina na tsaye cikin matuƙar damuwa, Doctor Sharif ya ce ""Hajiya ki yi haƙuri, amma a daren nan," "za mu yi mata tiyata domin a ceto ta, da abin da yake cikinta." """Kuma Doctor babu wata matsala, babanta ba ya kusa, haka ma mijinta""" """To Hajiya ai ba zamu bar ta haka a cikin ciwo ba, ki na kallo ba ta hayyacinta dole mu ceto ta da abin da" "za ta haifa""." "Jiki a sanyaye Hajiya Amina ta karɓi consent form, ta saka hannu, tana mamakin yadda suka kwanta" "lafiya ƙalau da Shukura, har likitan da ya ganta da yamma, yana faɗin za a sallame ta washegari, a ce lokaci ɗaya ta rikice, duk da ba a tara sani da Allah, kuma babu kusa babu nesa a gare shi." "Haka tana tsaye aka turo Shukura a kan gado, aka shiga da ita tiyata. Ta koma gefe jikinta a sanyaye tana" "ta adduo'i daban-daban, tana fatan Allah ya sa ba abin da Shukuran take faɗa ne, zai faru ba, da take cewa tana ji a jikinta kamar mutuwa za ta yi, ba za ta rayu ba." "Shukura a hankali ta buɗe idonta, tana kallon likitoci a kanta, ba ta san me suke yi mata ba, ita dai tana" jin ana girgiza ta. "Anesthetic ɗin ya ce ""Kin farka?"" Ta lumshe idanunta ta buɗe alamar eh." """Ɗaga ƙafarki sama mu gani""" """Ba zan iya ba"" ta faɗa a hankali." "Ya ce ""To yauwwa, suma ki ka yi ne, shi yasa saboda kar a rasa ki, a rasa babyn, ake yi miki tiyata ba zai" "yiwu mu ci gaba da barin ki da shi ba, sai mu rasa ku, kuma ba mu sani ba sarkinmu ne na gobe ko" "shugaban ƙasa"" ya yi maganar da sigar wasa." "Ta kasa dauke idanunta daga kan Doctor Sharif, da ya haɗa gumi suke ta ƙoƙarin ciro jaririn." **** "Ƙarfe bakwai da rabi, Nana ta dafa ruwa, ta kai masa banɗaki." "Ta zo kansa ta ce ""Sayyid taso ka watsa ruwa, za ka ji daɗin jikinka sosai da sosai""" "Ya tashi ya zauna, ya ɗan jima a zaune, sannan ya yinƙura, ta bi bayansa ta raka shi ƙofar banɗakin, ta" "miƙa masa zanin hannunta ta ce ""Idan ka gama ka lulluɓa sai ka fito"" bai karɓi zanin ba, ya kalle ta, sannan ya kalli banɗakin." "A take ta gane Abin da yake nufi, amma wani irin nauyin sa take ji, saboda ba su yi sabon da za a ce ta" "sake ta saba da shi haka ba. Amma ganin ya ja ya tsaya, ya ƙi gaba ya ƙi baya, ya sanya ta wuce shi, ta" shiga banɗakin. "Bayan ta ya biyo, yana bin bango, saboda jirin da yake ji, Nana ta din ga sinne kai, tamkar ta gudu saboda" tsananin kunyar da ta lulluɓe ta. Ayshacool "Kafin a gama wankan, ita ma sai da ya jiƙa ta jalaf da ruwan, tamkar ɗan ƙaramin yaron goye. Tana zuba" "masa ruwa a jiki yake zabura, kamar zai shiɗe, sai ya rirriƙe ta. Da dabara a hankali ta ci gaba da zuba" ruwan a jikinsa. Ta gama ta goge masa jikinsa su ka fito. "Da ta kalle shi, sai ta ji zuciyarta ta karaya, amma ta din ga dakewa, tana mazewa." "Ta soya dankalin Hausa da suke da shi, ta dafa shayi, ta zuba masa ta ajiye masa a gabansa." """Ko na baka a baki?"" Ya jinjina mata kai alamar eh." "Ta yi murmushi, ta saka hannu tana ba shi." "Ya ƙura mata ido, ko ƙiftawa ba ya yi, ya ɗage girarsa yana ƙoƙarin buɗe bakinsa, sai dai leɓensa ya din" ga rawa. "Nana ta ce ""Ai na san maganar ta ɗauke, ba sai ka yi mini magana ba, na fahimta"" ya sake kallon ta da" mamaki. "Ta ce ""Ka manta ka ce mini ruhinka yana rayuwa a cikin nawa? Shi yasa nake fuskantar yinƙurinka ko ba" "ka furta ba""" "Murmushi ya yi yana jinjina kai, ya haɗa tafukan hannayensa biyu, ya ɗago su daidai ƙirjinsa, ya" risunar da kansa alamar ya gode sosai. "Nana ta sauke hannun ta ce ""Babu godiya tsakanina da kai, duk da ban san wace irin rayuwa ka baro a" "baya ba, amma kula da kai dolena ne Sayyid""" "Idanunsa suka cika da hawaye, ya kamo hannayenta, ya din ga sumbata, ciki da waje. Tausayinsa ya ƙara" "mamaye ilahirin jikinta, cikin dakiya ita ma ta sumbaci hannunsa, ta ci gaba da bashi abinci. Sai da ya" "ƙoshi, sannan ta saka hau kan katifar ya jingina, ta rife masa ƙafafuwan sa da bargo." "Ta tashi tana gyara ɗakin, horn ɗin mota ta ji, ya ɗago ya kalli Nana. Ta ce ""Ka zauna kar ka tashi"" ta saka" Hijjabinta ta fita waje. "Matashin saurayin nan da take gani a gidan, mai tara samari su na kallon Ball ta gani a cikin mota. Ta" "ƙarasa inda motar take ya sauke gilashin motar ta ce ""Sannu da fitowa""" "Ya ce ""Yauwwa sannu""" """Ka ga ba ya jin daɗi ne, ba shi da lafiya, bari na buɗe maka""" "Ya dubi Nana ya ce ""Subhnallah me ya same shi?""" """Zazzaɓi ne yake damun sa""" """Allah sarki, wataƙila malaria ce, unguwar akwai sauro sosai. Kin ga wani magani da likita ya bani ɗaya na" "sha, na ji daɗin sa sosai da sosai, nake yawo da shi a mota. Ki ba shi ga paracetamol ma, zai ji daɗin sa. Je ki kawai zan buɗe ƙofar Allah ya sauwwaƙe""" "Nana ta saka hannu biyu ta karɓa ta ce ""Na gode sosai da sosai""" """Ahh ba damuwa"" Nana ta ji dadin mutuntawar da ya yi mata, duk da za su yi sa'anni da shi, amma ya yi" "mata karamci saɓanin 'yar uwassa da ta wulaƙanta mata miji""" "Ya sauka ya buɗe gate ɗin ya fita, ya dawo ya rufe." "Nana na shiga ɗakin, ta tarar da shi a tsakiyar ɗakin a tsaye, yana muzurai." """Ya na ganka a tsaye kuma? Ka kwnata ka huta, ga magani ma ya bayar ya ce a baka, sai ka samu ka sha""" "Ya koma kan katifar, ya kwanta, ba tare da ya tanka mata ba." * Shukura ba ta san adadin lokacin da ta shafe ba ta hayyacinta ba. "A hankali ta buɗe idonta, amma sai dai dishi-dishi take gani, tana jin maganganu, amma sama-sama, ba" ta gane me ake cewa. Sai sannu a hankali idanunta suka washe ta gane komai. "Mummy ta taso tana faɗin ""Sannu Shukura ya jikin""" "A wahale ta ce ""Mummy""" """Na'am Shukura""" """Ina abin da na haifa?""" """Ki kwantar da hankalinki, an kai shi nursery ne, an saka shi kwalba""" "Kawai Shukura ta fashe da kuka tana faɗin ""Innalillahi wa innalillahi raji'un, Allah ya sa ba mafarkina ne" "zai tabatta ba, dan Allah Mummy ni a karɓo mini ɗa na, a ciro shi daga kwalbar ba na so a dawo mini da jaririna ba na son wata kwalba""" "Cikin damuwa Mummy ta ce ""Innalillahi wa innalillahi raji'un, Shukura yanka ki aka yi fa, ko awa uku ba a" "yi ba, sai kin yi wa kan ki illa? Mene ne dan an kai shi nursery?""" """Ni dai ba na so, ki ce su dawo mini da ɗa na, wallahi zan tashi na je na karɓo ɗa na, idan ba za ki karɓo" "mini ɗa na ba""" """Shukura ina za ki tashi ki je, jikinki da ciwo meye haka ne?""" "Iya ƙarfinta take ƙoƙarin tashi da gaske, sai ta tashi sai dai ƙafafuwanta suka ƙi motsawa. Hargowar" "Shukura da kukanta, ya janyo hankalin ma'aikatan gurin. Suka haɗu a kanta ana ba ta haƙuri, amma fafur ta ƙi yin shiru. A dole aka yi mata allurai ta koma bacci." "Sosai yake tsala gudu a kan titin, yana fatan ya isa gari ya waye." Ayshacool "Yana yi yana kallon inda ya kwantar da jaririn a gefensa, jikinsa kaca-kaca da ƙazantar haihuwa da sauran" "jini, ga mahaifarsa a gefe ita ma kaca-kaca da jini a jiki." "Yaron baya iya kuka, sai kaɗan-kaɗan, bakinsa sai rawa yake yi, saboda azabar sanyin da yake ji." "Alhaji Zailani yana yi yana kallon yaron, sai dai ƙirjinsa ya yi masa nauyi, ya rasa dalilin hakan. Yana" "matuƙar ƙaunar Shukura, haka kurum ya din ga jin kamar bai kyauta mata ba. Amma da ya tuna girman buƙatar sa, na mamaye duniyar sa da samun duk abin da ya sanya a gaba, sai ya ƙara azama da ƙara gudun giyar motar." "Daji ne sosai da sosai, ya yi parking ya ɗaukko jaririn, ya fita ya nausa cikin duhun duƙununun dajin." "Yana tafe ya hango wuta tana ci, ya ƙarasa gurin da wutar take ci. Malam Gambo ne sanye da jajayen" "kaya, ya nufo shi yana faɗin ""Ka kusa makara fa""" """A yi mini afuwa, amma ina fatan wannan aikin zai zama daidai da sadaukarwata ta shekara""." """Ƙwarai kuwa, ba za a sake neman jini daga gare ka ba a wannan shekarar""" "Ya miƙa wa Malam Gambo jaririn, ya saka hannu ya karɓi yaron, ya ɗaga jaririn kansa a ƙasa," "ƙafafuwansa a sama, ya danna tafin ƙafar jaririn, a take ya tsanyara ihu, ihun jaririn ya cika dajin." "Malam Gambo ya haska fitila, ya ɗaukko wani abu a cikin wata jaka, ya saka shi a wuta, ya yi ja ya juya" "bayan yaron, ya zana wani hatimi a jiki, ya sanya sunan Fatuhu Magaji a cikin hatimin. Yaron ya din ga tsala ihu tamkar ana zare masa rai." "Suka haɗu da shi da Malam Gambo, suka tona rami, suka binne jaririn da ransa." "Duk da ba yau Alhaji Zailani ya saba irin wannan abubuwan ba, amma na wannan karon shi kansa ya" girgiza zuciyarsa. "Malam Gambo ya ɗauki mahaifar, ya ce ""Wannan na 'yan aike ne, su za su cinye ta, kai za ka iya tafiya," "bayan kwana talatin za mu zo a cire ƙwarangwal ɗin, za a yi wani aikin da shi. Ka huta ka yi yadda ka ke so Alhajin Allah, in dai Duniya ce ka same ta yadda ka ke so""." "Suka yi sallama Alhaji Zailani, ya hau motarsa ya nufi gida." "A wani irin mugun razane Nana ta tashi daga nannauyan baccin da take yi, ta tashi zaune. Tsaf abin da ta" gani ya dawo mata kai fes ba ta manta komai ba. """Innalillahi wa innalillahi raji'un, Allah ka duba lamarin nan, Allah ya sa shirmen mafarki ne""" "Tashi ya yi zaune shi ma ya ce ""Me ya faru?""" "Ta yi ƙoƙarin ɓoye damuwarta ta ce ""Babu komai, maganar ta dawo?""" """Eh"" ya faɗa a taƙaice." """Sannu ya jikin?""" """Alhamdilillah""" """Ko na ɗaukko maka maganin da aka bani, ya ce yana da kyau ka jarraba sha""" "Ya ce ""Ba na sha"" ya yi maganar yana kwanciya." "Ta dafa shi ta ce ""Sayyid, duniya ba za ta yiwu mu rayu mu biyu ba kawai, dole wasu lokutan mu na" "buƙatar taimakon mutane, dan mu rayu cikin aminci mu ma. Na san haƙƙoƙinka na aure da suke kai na," dan baka da cikakkiyar lafiya ba ya nufin zan ci amanar auren ka. "Na san ni Ahalinka ce, kuma wani shinge da babu wanda zai ratsa shi."" Ya yi mata shiru." "Ta kwanta a gefensa, tana shafa gashin sa, ta ce ""Sayyid ka yi mini magana mana""" """Ba ki san me nake ji ba ne""" """Na sani mana, ka manta ruhinmu ɗaya ne?"" Ya yi shiru ya lumshe idanunsa yana jin daɗin, yadda take" wasa da gashin sa. """Sayyid""" """Ma vie""" """Dan Allah da gaske Alhaji Zailani ya ce maka ka sake ni?""" "Kamar ba zai yi magana ba ya ce ""Eh, ya ce zai ba ni kuɗi. Zuciyata kamar zan mutu a ranar""" "Ta ce ""Me ka ce masa?""" """Ba zan iya tunawa ba, kawai dai na ji numfashina zai ɗauke ne, na manta meyafaru""" "Ta ɗan yi murmushi ta ce ""Rayuwa kenan, daga ni har kai dai gamu nan kawai, Allah ya shiga" "al'amarinmu. Sayyid ina jin tsoron kar ka tuna waye kai, ni kuma ka manta da ni""" "Ta ji shiru, bai yi magana ba. ""Sayyid "" ta kira sunansa, amma tuni ya yi bacci. Saurin baccinsa har" mamaki yake bata. "Zuciyarta kuma ta ci gaba da hasko mata mummunan mafarkin da ta yi, da Alhaji Zailani, dan haka take" "ta fatan, gari ya waye, ta kira Hajiya Amina ta ji yaya ake ciki." "Sai dai ta kasa komawa bacci, ta din ga tunane-tunane daban-daban a cikin ranta." "Ba ta san adadin lokacin da ta shafe a haka ba, ta ji ya ce ""Ba ki yi bacci ba haryanzu? Mafarki ba gaske" "ba ne ba fa""" Ayshacool "Nana ta ce ""Ba mafarki na yi ba, na kasa baccin ne""" """Ƙarya babu kyau, kin tsorata a mafarki. Kuma kin gaji ma yau sosai, kina ta kula da ni, na gode sosai bari" "na yi miki tausa""" """A'a ci gaba da baccinka, daga tausar nan har a yi asuba ba zan yi bacci ba, bar ni kafin a kira salla na" "rage na yi baccin""" "Dariya ta ji yana yi ya ce ""To a bari sai bayan sallar asuba""" """A'a ba ni da lafiya"" ya ƙara matsawa kusa da ita, ta ji shiru har ya sake komawa bacci." "Ƙaisar ta gani yana ɗaure Sayyid a jikin wata itaciya. A razane ta nufe shi ta ce ""Ƙaisar mene ne haka? Me" "ya yi maka?""" """Kar ki kuskura ki zo gurin nan, ai na gaya miki tun da ya kwance ƙullin nan, sai ya ɗanɗana shi ma""" "Nana ta ce ""Wai tayaya ya kwance ɗaurin da ka yi? Shi da ba aljani ba, kuma bai san abin da yake ɓoye" "ba, ka sauke shi dan Allah""" """Ke ki ke ganin shi mutum kamar kowa, na gaya miki kar ki kuskura ki zo gurin nan, zan yi miki illa""" Ba ta tsaya ba ta ci gaba da tunkarar sa. "Hankaɗe ta ya yi gefe, ya cigaba da ɗaure Sayyid a jikin itacen nan." "Ta yinƙura ta tashi da ƙyar, ta sake nufar sa, sai dai kafin ta ƙarasa, tsohon nan ya bayyana ya make" Ƙaisar gefe. "Da sauri Nana ta ƙarasa, ta hau kwnace Sayyid da yake a galabaice, ya fita daga hayyacinsa. Faɗa ne ya" kaure tsakanin Ƙaisar da tsohon. "Sayyid ya yi shiru, ya zubawa Nana ido, yana jin duk yadda take, furta abin da take gani a cikin" mafarkinta a zahiri. "Ya cigaba da kallon fuskarta, ds yadda gumi ya tsatstsafo mata a goshinta, ta rirriƙe shi gama tana kuka." "Ya saka yatsunsa biyu a ƙyerta ya danna, a take ta yi shiru, jikinta ya saki." "Da Safe yana ta bacci, ta tashi ta yi aikace-aikacen ta." "Bayan tashin sa ya karya, ya yi wanka ya fita waje, sai dai tun da ya tashi bai yi magana ba." "Ta gama aikinta ta fito, ta nufe shi ta zauna a kusa da shi tana yi masa hira, yana jin ta amma ba ya" magana. "Kubra ce ta nufo inda suke zaune, tana tahowa ya sunkuyar da kai." "Nana ta tashi ta ƙarasa inda take, ta ce ""Sannu ina zuwa haka?""" """Fita zan yi""" """Ki je ina?""" """Fita kawai zan yi"" ta bawa Nana amsa." Nana ta miƙa mata hannu da nufin su gaisa. "Ita ma ta miƙa mata suka gaisa, sai dai a wannan karon Nana ba ta ji sanyi ba. Nana ta kalle ta daga sama" "zuwa ƙasa, riga da wando ne na bacci a jikinta, kanta ko ɗan kwali babu." "Nana ta ja ta ɗakinsu, ta shimfiɗa mata sallaya ta ce ""Zauna"" babu musu ta zuna." "Nana ta zuba mata abinci ta ce ""Na ji an ce ba kya cin abinci, bismillah mu ci"" babu musu ta kama cokali" ta na cin abincin. "Cikin tausaywa Nana take kallonta, tana matuƙar jin tausayin mai fama da irin wannan larurar, wanda" "duk ba shi yake ɗauke da larurar ba, ba zai gane wahalarta ba. Mussaman idan na kusa da shi, ba su fahimci kan ciwon ba." "Ta cinye tas, Nana ta ɗauke kwanon ta kalli Nana ta ce ""Na daɗe ban ci Abinci da yawa ba""" "Cikin kulawa Nana ta ce ""Me yasa?""" """Ba na so kwata-kwata. Ba ma na iya bacci.""" """To me ki ke ji a jikin ki?""" "Ta ɗan yi shiru ta ce ""Kawai dai ji nake mutuwa zan yi, sai na yi ta kuka""" "Nana ta tashi ta ɗaukko mata pillow, ta ajiye mata ta ce ""Kwanta da yardar Allah za ki yi bacci"" ta kwanta" "ta yi shiru, Nana ta kunna mata karatun Alkur'ani. Ta nutsu tana saurara, har bacci ya ɗauke ta. Farin ciki ya kama Nana, ganin ta yi bacci. Ta ce ""Ya Allah, kai ka ke jarraba bayinka da larura, wasu ka haska musu" "maganinta, wasu kuma ka ɓoye. Ya majiɓancin lamarinmu, Allah ka yaye mana wannan larurar""." * "Misalin ƙarfe goma da rabi da safe, Baba yana ya bala'in an ba shi koko ɗan kaɗan babu sugar, alhalin an" san ba isar sa zai yi ba. "Mama ta ce ""Da ka samu wannan ɗin ma, Jamila ce ta bayar da kuɗin gasarar, yarinyar da ka ke nufi da" "sharri kai da ɗan ka, sai ka bari idan ka nemo, ka fara kawowa sai ka nuna isa da iko""" "Sallamar da aka yi ya amsa, yana jiran ya ga suwaye, sai dai ya saroro baki buɗe yana kallon masu" sallamar. Su ka shigo niƙi-niƙi da kaya a hannun su. "Mama ta fito daga kitchen, ta ga suwaye, ta ce ""Too ikon Allah, yau kuma da abin da muka tashi kenan?""" """Lafiya yaya aka yi?"" Ya tambaye su kamar ya ga annoba." """Malam Isa ai kwa bamu guri mu tsuguna tukuna""" Ayshacool """Ba wani a baku guri ku tsuguna, ba na son fitina, meya kawo ku?""" "Ɗaya daga cikin su ta ce ""A'a duk ba abin zafi ba ne ba ai, labarin auren Nana mu ka ji, shi ne muka zo mu" "tabattar""" "Baba ya ce ""Eh, haka ne na aurar da Nana, tun da 'yata ce, kuma ina da hurumin aiwatar da hakan""" "Saude ta ce ""Haka ne, amma mahaifiyarta da mu ma, mu na da hakki a kan ta, ai yakamata a sanar da" "mu""" """Ba zan sanar ba, na ce ba zan sanar ba ɗin? Me sanar mukun zai amfanar?""" "Mama ta ce ""Rakiya auren ne fa aka yi shi babu shiri, saboda magana ta nemi ta ɗaukko mana aka yi shi," "ba wani taron kirki aka yi ba""" """Amma duk da haka, ai ya kyautu mu sani""" "Baba ya taso kamar zai dake su ya ce ""Kin ga ku bi hanyar da ku ka shigo mini gida ku fita""." """Dan Allah Malam Isa ka yi haƙuri, abin duk bai kai haka ba, ka bari a kaimu ko gidan nata ne, mu ga" "ɗakinta, mu gaisa da ita, mu ba ta saƙon mahaifiyarta""" """Na yi muku iyaka da 'ya ta, ba zaku taɓa ganinta ba, ba ta buƙatar ku, ku bar mini gida, kafin na yi muku" "ɗibar albarka""" "Ganin babu mutunci a lamarin Malam Isan, ya sanya suka kwashi kayan da suka zo da su, su ka fice." Ayshercool 08081012143 Ayshacool "Hargowa da bala'in da Baba ya yi wa su Adda Rakiya, ya yi masifar ɓata musu rai, a zaton su duk" "abubuwan da suka faru a baya sun riga sun wuce, dan aure ya mutu ba ya nufin a wanzar da gaba a" "tsakanin yara da mahaifiyar su, ko a yanke duk wata da za su yi alaƙa da ita." "Ga gajiyar tafiya da su ka sha a mota, amma Baba ya yi musu wannan mummunar tarbar." "Can gidan su Nana kuwa, ana ta neman Yusra, ba a ganta ba, hankalin Hajiya Halima ya yi mugun tashi," suka fito neman ta harabar gidan tare da Siyama. "Gurin Sayyid su ka nufo, Hajiyar take tambayarsa ""Dan Allah yarinya ba ta zo ka buɗe mata ƙofa ta fita" "ba? Wata 'yar fara haka?"" Ya girgiza mata kai alamar a'a." """Na shiga uku, ni kuwa ina yarinyar nan ta shiga haka? Kirawo mini Nuradeeni a waya, ko sun fita tare?""" "Siyama ta ce ""Su fita tare su je ina, su da ba shiri suke yi ba, ina zai kai ta? Wataƙila tana cikin gidan nan" "wani gurin ta samu ta shige kawai""" """To tana cikin gidan nan, mu ganta mana""" """Ki yi haƙuri mu koma, mu ci gaba da duddubawa""" "Nana kuwa ba ta san me ake yi ba, tana zaune a gefen Yusra, tana bin karatun Alkur'ani da ta kunna a" "wayarta. Ta ji daɗin yadda take raira karatun yau, ba tare da ta ji kanta ya fara ciwo ba, ko ta fara jin sanyi ba. Yusra kuwa baccinta take yi da gaske." "A ƙalla ta kai awanni biyu tana bacci, har Nana ta idar da karatun Alƙur'anin, ta ɗora girki. Ta kammala" "babu jimawa ta farka daga baccin. Nana ta saka ta yi alwala, ta ba ta hijjabi ta yi alwala ta yi salla. Ta sake zuba mata abinci ta ci, sannan ta ce ""Mu je na raka ki cikin gidan, zan zubawa mijina abinci shi ma na ba" "shi""" "Ta kalli Nana ta ce ""Ki na da miji?""" "Nana ta jinjina kai ta ce ""Eh, ina da shi, shi ne a waje yake yi muku gadi""" "Yusra ta ce ""Mhmm ni da na fara rashin lafiya, shekara biyu kenan, mijina ya sake ni, ya ma yi aure ba zai" "zauna da ni ba. Ba wanda ya san me nake ji, amma ke na ga kamar kin san me yake damuna, ke ba za ki" "ce ƙarya nake yi ba. Mami ta ce ""Ina sane na kashe aurena, na ji haushi sosai da sosai""" "Nana ta riƙe hannunta ta ce ""Ki yi haƙuri, na ki ƙalubalen kenan, tabbas na san ciwon nan, na san babu" "daɗi, kuma babbar jarrabawa ce a ce na kusa da mu sun kasa fahimtar mu, su din ga ganin muna sane muke yin abin da muke. Dan haka dolenmu ne, mu dage mu yi ta adduo'i da azkar domin Allah ya bamu" "lafiya""" "Ta jinjinawa Nana kai ta ce ""Na gode sosai da sosai""" "Nana ta tashi suka fito daga ɗakin, dama Sayyid a matse yake ya shiga ɗakin, zaman Yusra a ɗakin ya" hana shi shiga. """Wannan ne mijin naki?""" """Eh shi ne""" "Ta ce ""Sannu dattijo""" "Ya ɗago ya kalle ta, ya ɗaga mata hannu. Ta yi murmushi kawai." "Nana ta ce ""Dattijo kuma?""" """Eh, ke matashi ki ke gani, ni kuma Dattijo nake gani, duk da kema ki na ganin haryanzu dai ki na wasi-" "wasi ne""" "Nana ta ce ""Haula""" "Ta amsa da ""Na'am uwar gijiyar Ƙaisar""" """Amma me yasa za ki yi mini haka? Matar ta farfaɗo ta samu ta ci abinci, ta yi bacci kuma kawai sai ki zo" "za ki sake burkita ta""" "Yusra ta yi murmushi ta ce ""Tuba nake, wallahi ba da wata manufar na zo ba, gaisuwa na zo kwasa kuma" "na yi sai anjima""" "Nana ta ɗan ƙura wa Sayyid ido, amma ya ƙi kallonta, ya tafi ɗakin su. Ta jinjina kai a hankali ta ce ""Biri" "ya yi kama da mutum""" "Har cikin falon Nana, suka shiga tare da Kubra. Hajiya Halima na ganinsu ta miƙe ta ce ""Laa a ina ki ka" "ganta? Tun ɗazu muke bulayin neman ta a cikin gidan nan""" "Nana ta ce ""Subhnallah, wallahi ban sani ba, gani na yi za ta fita na hana ta, mu na tare da ita a ɗakina," "kuma na yi ragon azancin ban zo na sanar miki ba""." """Mami ta bani abinci, kuma na yi bacci ma""" """Ikon Allah, yau kin yi baccin kenan?""" "Yusra ta ce ""Eh, na yi bacci sosai mai daɗi, na ga ma Sagir a baccin""" "A fusace Hajiya Halima ta ce ""Ba za ki daina maganar Sagir ɗin nan ba ko? Mutumin da ya riga ya sake ki," "ba zai zama da ke ba, mene ne na zancen sa """ "Siyama kuwa da ranta ya ɓaci ta ce ""Amma baiwar Allah wannan shiga hakki ne, tun ɗazu mu ke neman" "ta fa, kuma saboda wulaƙanci da rashin mutunci mijinki ya ce bai ganta ba, wannan ai gidadanci ne da" "rashin hankali""" Ayshacool """Laifina ne, ba nasa ba ki daina zaginsa dan Allah, ba na jin daɗin hakan""" "Hajiya Halima ta ce ""Siyama ya isa haka dan Allah, amm Nana sunan ko? Mun gode sosai da sosai""" "Nana ta juya za ta tafi, Yusra ta ce ""Ƙawata sai anjima""" "Nana ta yi mata murmushi ta ce ""Kar ki manta abubuwan da na gaya miki fa""" "Ta amsa mata da ""To""" * "An ɗaga Shukura daga kwanciyar da take yi, an yi mata wanka, aka kawo mata abinci, amma ta ƙi ci, tana" zaune tamkar gawa. """Shukura yanzu haka rayuwa za ta kasance mutum babu tawakalli kenan? Da Allah ya baki lafiyar ba za ki" "gode masa ba kenan?""" """Mummy""" """Naam""" """Kin ga gawar abin da na haifa?""" "Hajiya Amina ta ce ""Eh mana, awansa shida a nursery ya rasu, sai da na gan shi sannan Sagir ya tafi da" "shi ya binne.""" "Hawaye ya gangaro kan kumatunta, ta ce ""Amma me yasa ba a bari na gan shi ba?""" """Shukura ba kya cikin hayyacinki, za a yi ta zama da gawa ne ba a binne ba? Ai ba zai yiwu ba""" "Ta ce ""Haka ne, amma ina baban Haidar ɗin yake?""" """Bai daɗe da tafiya ba ki ka tashi, kuma da na san za ki farka da wuri an jira, kin gan shi. Amma na san ya" "ɗaukar miki shi a hoto ai. Na tura family group ma, amma dai na ƙara gaya musu, ban da zuwa dubiya ba" "kya jin daɗi""" "Ta ce ""To Mummy na gode sosai, tun da dai kin ce mini kin ga gawar babyn shikenan, Allah ya sanya mai" "ceto ne. Ke ma Allah ya baki ladan ɗawainiyar da ki ke ta yi da mu""" "Cikin jin daɗi Hajiya Amina ta ce ""Amin ya Allah, ko ke fa Auta, dan Allah ki ci abincin ko na ji daɗi""" """To Mummy amma saboda ki ji daɗi zan ci kaɗan, ba na son cin komai""" """Ba komai, hakan ma na gode sosai da sosai Autar Mummy""" "Haka Shukra ta din ga yaƙi da zuciyarta, da ƙoƙarin kawar da tunanin mafarkan da take yi." * "Har Gaddafi ya gota matan, da suke zaune a kan barandar ƙarshen layin, sai kuma ya dawo da baya ya ce" """Sannun ku""" "Su ka amsa masa da ""Yauwwa sannu""" "Ya ce ""Kamar 'yan uwan babar su Imrana""" "Adda Rakiya ta ce ""Laa Gaddafi kai ne?""" "Sai ya gyara tsayuwarsa, su ka gaisa. Ya ce ""Ya na gan ku a nan?""" "Adda Rakiya ta so ta kare, amma Fati ta gaya masa abin da ya faru." "Ya girgiza kai ya ce ""Ku yi haƙuri, abu ne da ya faru ya riga ya wuce, amma an ƙi bari ya wuce, ake ta" "nanatawa, bari na nemo muku Nasiru, ya raka ku.""" "Bayan tafiyar sa Rakiya ta ce ""Fati, wannan ba Gaddafi ba ne ba, mai cewa zai daki Mai Jidda, yau shi ne" "da gaishe mu""" "Fati ta ce ""Wallahi nima abin ya bani mamaki sosai da sosai""" "Su na cikin tattaunawa, Gaddafi ya kawo musu ruwan sanyi da lemo, ya nemo Nasiru, ya tarar musu abin" "hawa, ya biya kuɗin suka tafi." * """Sayyid""" Ya ɗaga ido ya kalle ta. "Ta ce ""Ko dattijon ne?""" """Wane dattijon?""" """No ba komai""" """Ki daina kallona, kamar ki na tuhuma ta""" "Ta ce ""Tuhumar ta ka nake yi ai""" "Ya tsaya da cin abincin ya ce ""Da me?""" """Ci abincinka, zan gaya maka""" "Ya ci gaba da ci, ta sake kiran sunansa." Ya ɗago ido ya kalle ta. "Za ta yi magana, su ka ji an buɗe gate ɗin gidan an shigo." """Laa a buɗe ka bar gate ɗin?""" "Ya ce ""Eh na manta ne""" "Sallamar Nasiru ta ji, ta yinƙura ta tashi ta leƙa." "Kasancewar jikinta babu hijjabi, ko ɗan kwali babu a kanta, kafin ya yi magana tuni ta yi wani irin ihu, ta" "yi waje da gudu. Tashi ya yi da sauri, ya bi bayan ta, domin ganin abin da ya sanya ta wannan ihun haka." Gani ya yi ta rungume ɗaya daga cikin matan da suka shigo tare da Nasiru. Ya koma da sauri ya rufe "abincin da yake ci, ya kawar da kwanukan ya koma gefe ya tsaya." "Tare suka shigo da matan, ɗayar na share hawaye ita ma. Su na shigowar ya fice daga ɗakin." Nana ta kasa magana saboda kukan da ya ci ƙarfinta. "Adda Saude ta ce ""Nana kukan ya isa haka""" """Adda ina mamanmu?""" """Yanzu dai ki yi haƙuri, mu gaisa mana Nana""" "Ta basu gurin zama, sai dai ta kasa daina kuka, ta kawo musu ruwan roba, ta koma gefe ta zauna ta" cigaba da kuka. "Anty Fati ta ce ""Haba Nana, ki yi shiru mana""" """Dan Allah ina Maman take? Yanzun ma ba za ta zo ba?""" Ayshacool "Adda Saude ta ce ""Ki yi haƙuri Nana, auren nan na ki ma ba mu sani ba, waiwai mu ka ji, tare za mu taho" "da ita da, amma mijinta ya hana, yanzu haka ma babanki da korar mu ya yi, Gaddafi ne ya haɗo mu da yaro ya rako mu, har ya biya mana kuɗin mota""" "Cikin kuka Nana ta ce ""Na kira ta, Baban su Walida ya ɗauka, bai haɗa ni da ita ba""" """Ki haƙuri Nana, lamarin iyayen naki ne sai haƙuri, ita kanta babu yadda ba ta yi ba ta zo, amma ya hana" "har da barazanar saki. Amma ga kayan aurenki nan da ta bayar a kawo miki, mu ma da abin da Allah ya yassare mana. Yanzu zamu haɗa ki da ita a waya, zan kira Lawan ya kai mata sai ku gaisa""" "Nana ta ci gaba da kuka, tana jin kewar mahaifiyarta, amma gaba ɗaya ba ta da maraba da marainiya." "Anty Fati ta ce ""Nana, mijin naki buzu ne kenan? Ke kuwa yaya aka yi ku ka haɗu har danginsa su ka bari," "ya aure ki, ai ba sa auren bare da wahala. Har gara matan su, idan ka na da kuɗi za su baka, amma mazan dai ba sa auren wasu matan idan ba na su ba""." "Ras gaban Nana ya yi wata irin mummunar faɗuwa, amma ta dake ta ce ""A gidan da yake gadi mu ka" "haɗu""" "Adda Sauda ta miƙo wa Nana waya, Nana ta karɓa jikinta yana rawa." """Salamu Alaikum Nana, ki na ji na?""" """Mama"" ta furta cikin rauni, tana fashewa da wani irin kuka tamkar za ta shiɗe." "Maijidda ma kukan ta saka ta ce ""Nana ki yi haƙuri, na san ni mai laifi ce a gurinku, dan girman Allah ku" "yafe mini an fi ƙarfina ne, na rasa yadda zan yi. Imrana ma ya daina zuwa inda nake""" """Mama dan Allah ki zo, ni ba na son na zo na saka ki a matsala ina son na ganki, dan Allah""" """Nana in sha Allah zan zo Nana, da gaske an yi miki auren ko? Kodayake daga majiya mai ƙarfi na ji," "Babanku bai kyauta mini ba. Ga ɗan abin da na tara miki nan babu yawa, ki yi haƙuri Nana, ki ba wa ɗan uwanki haƙuri dan Allah ku yafe mini. Wallahi ku na raina ban taɓa mantawa da ku ba, babu yadda na iya, mijin da nake aure ba shi da fahimta, kansa kawai ya sani shi ma"" Nana ta kasa magana sai wata irin" sheshsheƙar kuka da take yi. "Ta sake cewa ""Ki na ji na Nana, ki yi haƙuri da rayuwa, jariri ma ana haihuwar sa, mahaifiyarsa ta koma" "ga Allah, kuma ya rayu cikin ikon Allah, ki zama mai juriya, ki yi wa mijinki biyayya. Har yadda aka yi aka" "yi auren ki, an gaya mini, amma ko 'yan uwana ban gaya wa ba, kowace mace ko na ce ko wane dan" "Adam akwai kalar tasa jarrabawar. A raina, ban taɓa jin za ki aikata, wani abu da zai tozarta ki ba. Ki yi" "haƙuri ki rungumi auren ki Nana, shi ne mutuncinki da suturar ki." "Yaya jikin ki kuma?""" """Da sauƙi"" ta faɗa muryarta na fita da ƙyar." """To ki riƙe Addu'a, ki riƙe Allah. Ki riƙe auren ki da kyau, ki yi haƙuri Nana, ki yi haƙuri ku yafe mini. Dan" "Allah kar ki yi fushi da ni, kamar yadda ɗan uwan ki ya yi, wallahi ku na raina.""" """To Mama, na gode sosai, na gode"" suka yi sallama, Adda Saude na ta rarrashinta da ba ta haƙuri." "Gyaran muryarsa ta ji a ƙofar ɗakin, Nana ta tashi da ƙyar ta nufi ƙofar ɗakin." "Zuciyarsa ce ta buga da ƙarfi, a razane ya ajiye ledojin hannunsa ya ce ""Mene ne?""" Nana ta yi shiru tana kallon sa. """Yi magana Husna, mene ne?""" "Nana ta goge hawayenta, ta ce ""Babu komai fa""" """A'a launin idonki ya canza, ba kuka ne kawai ba, akwai matsala ne""" "Nana ta yi ajiyar zuciya ta ce ""Ka kwantar da hankalinka, zan yi maka bayani bari baƙina su tafi""" """Zuciyata babu daɗi, ki daina kuka na roƙe ki""" "Cike da jarumta, ta ƙaƙalo murmushi ta ce ""Na daina"" ya jinjina kai, ya ɗauki ledojin ya ba ta." "Ta koma cikin ɗakin, su ma fruit ne, da fura da Nono ya kawo." "Ta hau fafutukar ɗora musu girki, a hankali ta ɗan ware, su ka yi ta hira, Nana ta ce ""Me yasa ba a zo" "mini da ko Walida ba, rabona da su tun su na yara sosai""" "Anty Fati ta ce ""Wa zai ɗaukko su, ya zo ya yi ta jaraba, mussaman ya san in da aka tafi da su. Ai Maijidda" "ba ta yi dacen mazaje ba, daga Baban naku, har Iliyasun." "Suka yi salla, Nana ta kammala girki, ta ɗebarwa Sayyid nasa, su na ta yi wa Nana hira, sai dai zuciyarta" cike da damuwa. "Nana ta fita ta samu Sayyid, ya miƙe tsaye yana kallon kumburarriyar fuskarta cike da damuwa." Ayshacool """Sayyid ka zo za ku gaisa da 'yan uwan Mamana, su ne suka kawo mana ziyara ka zo mu je ku gaisa." "Amma idan da hali ka yi musu magana dan Allah""" "Ya ce ""To, amma idan ina kallon fuskarki a haka, ba zan iya magana ba""" "Ta yi murmushi ta ce ""Ba na son rigima, mu je to""" """Ina jin kunya, wuce gaba na biyo ki""" "Ta yi murmushi, ta yi gaba ya bi bayan ta." "Ya yi sallama sannan ya shigo, ya tsugunna, ya sauke takunkumin fuskar sa ya ce ""Barkanku da zuwa, ya" "hanya?""" "Jin gaisuwar ta sa suka yi banbarakwai, amma Adda Saude ta ce ""Lafiya ƙalau, mun same ku lafiya? Ya" "iyalin?""" "Ya ce ""Alhamdilillah mun gode Allah""" """To ma sha Allah, Ubangiji Allah ya sanya alkhairi ya baku zaman lafiya, bamu samu mun halarci taron" "biki ba, sai yanzu muka zo. Allah ya baku zaman lafiya. Sannan a yi ta haƙuri, shi aure ɗan haƙuri ne, ba farkon auren ba, sai zama ya yi zama ake gane haƙurin. Ubangiji Allah ya yi muku albarka, dan Allah ka yi haƙuri da ita ka riƙe ta amana""" """In sha Allah""" "Anty Fati ta ce ""To ina fatan dai ba za ka yi mata kishiya ba, tun da ta ciri tuta ka aure ta, tun da dai an ce" "ba kwa auren wanda ba ƙabilar ku ba? Dan ni 'ya ta daidai take da mata huɗu, har da ɗoriya.""" "Miƙewa ya yi yana murmushi, ya nufi hanyar fita. Nana cikin shagwaɓa ta ce ""Sayyid ba fa ka ba da amsa" "ba""" "Yatsansa manuniya ya nuna mata, ya ce ""Ke kaɗai ce Ma vie""" """Anty Fati ki zama shaida""" "Ya fice yana murmushi, Anty Fati ta ce ""Ke babu ruwana, namiji na mata huɗu ne, wasa nake yi kar ki" "saka a hakan a ranki""" "Nana ta basar da maganar, dan wani irin zafi ta ji ya fara taso mata." "Adda Saude ta ce ""Nana an baki 'yan abubuwa kuwa na gyara, ko kuwa haka kawai su ka ninko ki, su ka" "kawo ki?"" Nana ta yi shiru, tare da sunkuyar da kai, wa ya tsaya bin ta kan ba ta wani abu, har gara Ummi ta kawo mata, ranar da su ka zo da su Jamila, ta rubuta mata yadda za ta yi amfani da shi, amma tun da ta jefa ledar a drower, ba ta sake bi ta kan su ba, saboda pressure gabanta ta ishe ta, ba ma ta" taɓa tsammanin wani abu zai shiga tsakaninsu ba. "Anty Fati ta yi wa Nana tambayoyi, a kan matsalar sanyi, Nana ta ce ita ba ta jin komai na alamar sanyi." """To duk da ke kaɗai ce a gurin mijinki, amma kar ki zauna ki miƙe ƙafa Nana, kar ki ga ba shi da ƙarfi, tsaf" "'yan mata za su din ga kawo masa farmaki, ki na ganinsa tubarkallah da shi. Nana ki yi addu'a, ki yi gyara kuma ki yi biyayya, za ki zauna lafiya in sha Allah. Nana ki yi kissa, kar ki zauna haka sai abin da ya zo miki, ki zama mace mai tunani Allah ya baku zaman lafiya""" "Suka yi ta yi mata nasiha, har aka yi sallar la'asar. Su na yin sallar la'asar, su ka ce za su tafi, saboda kar su" yi dare a hanya. "Nana ta ce ""Bari ya dawo daga masallaci, sai na raka ku"" Duk s karɓi lambobin wayar su, su ma suka" karɓi ta ta. "Suka shirya tsaf za su tafi, Nana ta fito ta tarar ya dawo daga masallacin." "Ta ce ""Sayyid, za su tafi zan raka su ko bakin titi ne, su hau adaidaita sahu, su je tasha""." "Ya ce ""Bari mu je tare""" """Idan mutanen gidan su na neman ka fa?""" """Wata ta ƙone a gidan, sun tafi kai ta Asibiti""" "Nana ta waro ido, ta ce ""Wace ta ƙone?""" """Ban sani ba, kawai na buɗe gate sun ce mini za su Asibiti, wata ta ƙone da ruwan zafi""" "Nana ta ce ""Ikon Allah, Allah ya sauwwaƙe.""" "Su Adda Saude, su ka fito, suka tafi raka su tare da Sayyid." "Su na tafe su na ci gaba da yi musu nasiha, a bakin titi, suka tarar musu adaidaita sahu. Nasiru dama tun" "da ya raka su, gida ya koma saboda zai je makarantar Islamiyya." "Nana ta tambayi mai Napep ta ce ""Nawa za ka kai su tasha"" hararta Buzu ya yi, ya saka hannu a aljihunsa" "ya ciro dubu biyu, ya bawa mai adaidaita sahun." "Ya sake ɗaukko baƙar leda, ya ajiye wa Anty Fati a kan cinyar ta, ya ce ""Mun gode sosai""" """A'a ba zamu karɓa ba, ɗawainiyar ta yi yawa""" "Nana ta ce ""A'a Anty Fati, ba zai ji daɗi ba. A ce ina gaida Mama, ina kewar ta sosai da sosai"" ta yi" magana idanunta na cika da hawaye. """A'a Nana, kar fa ki je ki zauna ki yi ta koke-koken nan, idan haka ne, za mu daina zuwa""" "Ta goge hawayen ta ce ""Na daina, ku gaida gida""" "Sai da su ka ja motar su ka tafi, sannan su ka dawo gida." Ayshacool "Nana ta zuba masa Abinci, ya ce ""A'a ba na jin yunwa yanzu""" """Sayyid ina jin daɗin yadda ka ke mutunta 'yan uwana idan sun zo, kuma na ji daɗin yadda yau ka yi" "magana da su, har ka yi raha, har cikin zuciyata na ji daɗi sosai da sosai. Allah ya nuna mini 'yan uwanka haka, zan yi iya yi na, na kyautata musu nima, Allah ya sa su amince su karɓe ni a matsayin ɗaya daga" "cikin ahalainsu""." """Na ji kin ce a gaida Mama, mamanki na nan ta bari, a ka aura miki ni?""" "Ta yi murmushi mai ciwo ta ce ""Ba ga Maman nawa nan ka gani ba, ranar da mu ka je duba Baba?""" """Ba maman ki ba ce, kuma ko mamanki ba ta so na, ba za ta din yi mana irin kallon da waccan matar ta yi" "mana ba. Amma wannan da su ka zo, na ga su na murna sosai da sosai da ganina, har suka yi mana addu'a, duk da ban san me yasa ki ka yi kuka ba da suka zo""" "Nana ta haɗiye abu mai ɗaci da ya tsaye mata a wuyanta, ta san yanzu ba ta da wani mutum mafi" "kusanci da ita, sama da shi, dan haka babu buƙatar ɓoye masa komai, dan haka ta numfasa ta ce ""Tabbas ba Mamana ba ce wadda ka gani a gidanmu. Mamana sun rabu da Baba, tun ban fi shekaru tara ba. Ba komai nake iya tunawa ba, kawai dai na san Mama ba sa jituwa da dangin su Babanmu, su na yawan samun saɓani. Har dai suka rabu. Ta ce Baba ya bata mu, ni da yayana amma ya hana ta. Ba ta daɗe da rabuwa da shi ba, ta yi wani auren. Abin ya ɓata wa Baba rai sosai da sosai, ya ce kamar ta sane ta kashe" "auren dan ta fita ta auri wani, wanda ta aura ɗin kuma an ce ya taɓa son ta, ba ta aure shi ba." "Adda Saude ta zo ta ɗauke ni ta ƙarfin tsiya, ta tafi da ni, amma da ƙyar na kwana a gidan da Mama take," "mijinta ya ce sai an fita da ni. Abin dai duk babu daɗi, aka sake mayar da ni gidan Baba. Na fi shekara bakwai ban ganta ba, ina kewar ta sosai da sosai"" ta yi maganar tana fashewa da kuka." Ya rungume Nana a jikinsa yana shafa bayanta a hankali. """Ki daina kuka, za mu je mu ganta in sha Allah, ke gara ke a kan ni ai. Ban sani ba ma ina da maman ko ba" "ni da ita, ni ke kaɗai na sani""" "Ya jima yana rarrashinta, sannan ta ɗan tsagaita da kukan da take yi. Ta fara buɗe kayan da suka kawo" "mata. Ba masu tsada ba ne ba, amma ta yi ƙoƙari. Bedsheet kawai biyar ne, huɗu na gida, ɗan waje ɗaya. Ga kwanuka har da kayan sakawa." "Sai da ta bari an kira magariba ya fita, sannan ta sake fashewa da kuka, ta yi kuka sosai sai da kanta ya" "fara ciwo, sannan ta haƙura ta yi shiru." * "Jikin Shukura ya yi kyau, ta warware, wannan kumburin duk ta sace, aka rubuta mata sallama." "Doctor Sharif ya sha jinin jikinsa, dan sai da ya tsorata ya fara wasi-wasin ko dai Shukura ta san abin da" "ya aikata mata, saboda yadda ta canza gaba ɗaya. Wasa da dariyar ma da suke yi, gaba ɗaya ta daina, da" "ya shigo sai ta tsuke fuska. Sai dai wani sashi na zuciyarsa ya din ga ba shi, kawai yanayin da take ciki ne, na rasa ɗan ta da ta yi, ya sanya duk ta canza ta daina walwala." "Hajiya Amina ta dube ta, ta ce ""To Shukura yaya? Gidanki zan mayar da ke, ko gida za ki taho?""" """Mummy mu je gida na ɗan huta tukuna""" "Sagir ya harari Shukura ya ce ""Mummy, a dawo da ita kawai, ke ma ki huta da ɗawainiya tun da ta samu" "lafiya""" "Su na cikin mujadalar, Alhaji Zailani ya kira waya, ya ce ""An sallame ku ne ko kuwa? Ya ce mini yau za a" "sallame ku""" """Eh, an sallame mu, ta ce gidan zata taho, mijinta ya ce ta koma gida""" """Saboda me? Ta koma ta yi masa me? A dawo mini da 'ya ta gida ta huta, kafin ta koma, me za ta je ta yi" "masa da yanka a jikinta""." "Hajiya Amina ya ce ""A'a kar a yi haka, mijinta ne fa""" """Ni kuma ubanta ne, ki ce masa na ce a kai mini 'ya ta gida ta huta, idan ba za ki faɗa ba, ni zan kira shi""" "Sagir yana ji yana gani, haka ya haƙura, aka mayar da Shukura gida, maimakon gidansa." **** "Nana ta kira su Adda Saude, suka tabattar mata da sun je Bauchi lafiya, ta yi musu bangajiya." "Yana ta shirin kwanciya, Nana kuma ta ƙura masa ido, zuciyarta ta yi mata nauyi, ba ta jin daɗin komai." "Ya zo kusa da ita, hannunsa riƙe da kofi ya miƙa mata. Ta saka hannu ta karɓa, tana kallon sa." """Na ga ba ki ci abinci ba, madara ce na kuma karɓo miki""" Ayshacool "Ta buɗe kofin, ta kalli madarar, da wani baƙin abu a kai." """Habattussauda ne a ciki, ko na fara sha ne?"" Ya yi magana yana miƙa hannunsa zai karɓi kofin." "Ta kafa kai, ta fara shan madarar, sai da ta shanye ta ajiye kofin." "Ta dube shi ta ce ""Me yasa ka ke bani madarar nan?""" """Na ji wani likita ya faɗa a radiona, yana ƙara wa mata lafiya sosai""" "Ta ɗan yi murmushi, sannan ta numfasa ta ce ""Sayyid, da gaske ƙabilarku, ba sa auren macen da ba ta su" "ba?""" "Ya yi shiru kamar ba zai yi magana ba, sannan ya ce ""Duk abin da zai fito daga bakina a yanzu, ƙarya zan" "yi miki, saboda ba zan iya tuna komai a kan ƙabilar tamu ba""" "Cikin rawar murya ta ce ""To yanzu idan Allah ya sa ka tuna waye kai, da asalin rayuwar ka, ni mece ce" makomata? Za ka karɓe ni a matsayin matarka kuwa?. Idan kuma aka samu akasi ka manta da ni baki "ɗaya fa? Yaya zan yi? Mece ce makomata?""" Ayshercool 08081012143 Ayshacool 41 "Ya yi shiru yana nazarinta, hawaye ya wanke mata fuska, har cikin ranta maganganun da suke fitowa" "daga bakinta. Tabbas! Tambayoyin nata a kan hanya suke, kuma sun cancanci ta samu amsar su, amma ta yaya zai bayar da amsar abin da shi kansa bai sani ba?" "Ya dake ya tattaro nutsuwar sa, ya ɗago fuskarta, su ka haɗa ido." """Ba na so, ganin wannan na ɗaya daga cikin abin da yake tayar mini da hankali, na rasa nutsuwa," "hawayen ki zafi yake haifar mini a zuciyata, kuma yau wuni ki ka yi kuka"" ya yi maganar yana share mata hawayen da yake kan fuskarta." """Sayyid ka bani amsa, zuciyata ta cika da tsoro da fargaba, da kuma wasi-wasi""" "Ya sassauta muryarsa ya ce ""Ma vie. Idan har tunawa da rayuwata da waye ni, zai sanya na manta da ke" "a cikin rayuwata, ina fatan na dauwwama ba tare da na tuna waye ni ba. A jikina ina jin rayuwar da nake yi tare da ke, ita ce rayuwa mafi aminci da kwanciyar hankali. Ba ki yadda ba da na ce miki rayukanmu na cikin na juna ba? Muddin ruhinki na yawo a doron duniya, ba zai taɓa barin ruhina cikin nutsuwa ba," "saboda abokan rayuwa ne""" """Sayyid""" """Duniyata""" "Wani kyakyawan murmushi ne ya suɓucewa Nana, ta ce ""Kalaman ka na ƙara mini ƙwarin gwiwa, har ba" "na son na ji muryar ka ta ɗauke ko sau ɗaya""" """Da gaske?""" "Ta jinjina masa kai alamar eh. Ya sumbaci goshinta yana murmushi, mai ƙayatarwa." "Sai da zuciyarta ta motsa, wani irin shauƙi ya mamaye ta, ji take tamkar ta furta abin da take ji a cikin" "zuciyarta, amma ta danne, sai kallonsa da take yi." "Ya ce ""Faɗi mana, ki furta""" """Me zan furta?""" """Abin da yake zuciyar ki, da ki ke son faɗa"" ta girgiza kai ta ce ""Babu komai""" """A'a, ruhina ne a jikinki fa, ko in gaya miki abin da ki ke son cewa?""" "Ta girgiza kai alamar a'a. Ya saki wani irin murmushi, mai cike da ƙasaita yana kallon fuskarta." "Haka ya sakankance, ya tattara duk hankalinsa da lokacinsa a kan Nana, sai da ya mantar da ita damuwar" "da ta shiga, wani nannauyan bacci, ya sace ta." * "Hajiya Sa'a ce take mita iya yin ta, ""Wallahi Jamila, ban da yayan ki ne ya yi miki wannan dukan, da sai na" "rufe shi, wannan ai take haƙƙin ɗan Adam ne. Tun da kin kai shekaru goma sha takwas, ai kin sa abin da ya dace da rayuwar ki""." """Wallahi haka Mama ma ta faɗa, da police station za a kai shi, Baba ya yi ta bata haƙuri, nima na ce kar a" "kai shi, ta yi haƙuri""" """Saboda me ki ka hana a kai shi, ai gara a kai shi, ya san cewa ke da shi akwai bambanci yanzu""" "Jamila ta ce ""Kaii babban yayanmu ne fa Mummy""" """Shi ɗin fa, shi ba dukan ki ya yi ba?""" """A'a ai bai kamata ba, da kunya abun""" """Ke Jamila, kalle ni da kyau. Irin wannan lamarin, dole ki sakawa kowa tsoron ki idan ki na son ki zauna" "lafiya ki taka duk wanda ki ke so. Ba a tausayi ba kuma a tuna danganta kan ki kawai za ki kalla, ki gina" "rayuwar ki. Babu wani abu da dangantaka ke ƙara wa banda koma baya da hassada da fitintinu""" "Jamila ta jinjina kai ta ce ""Haka ne""" """Dan haka duk wanda ya yi yinƙurin taɓa ki, ki yi maganinsa kawai. Ni zan fita ba daɗewa zan yi ba" "amma""" """To a dawo lafiya"" Jamila ta yi maganar tana kashingiɗa a jikin kujerar 3 seater da ke ɗakin." "Har bacci ya fara ɗaukar ta, ta ji ana sallama, ta buɗe idonta ya ce ""Yi haƙuri na tashe ki, Mummy ta fita" "ne?""" Ta jinjina masa kai tana ƙoƙarin mayar da kai ta kwanta. """Ta daɗe da fita ne?""" """A'a""" "Ya ce ""Ok thanks "" ta mayar da idonta, ta lumshe shi kuma ya ɗan ƙura mata ido, kan ya fice." **** "Alhaji Zailani na zaune, yana jiran ta gama haɗa tea ta ba shi, kiran wayar Hajiya Sa'a ya shigo wayarsa." "Ya ɗaga su ka gaisa. Ta ce ""Zailani, matarka ta fi ƙarfin ta je duba Hanifah a Asibiti, har an sallame su sun" "koma gida""" """Dan Allah ki daina kamabama abu, wane irin fin ƙarfi, ni na je, su Rauda su je, maman su ta je, duk bai" "isa ba? Ba ta da lafiya ne, mu na ta yawon asibiti""" """Ba ta da lafiya me ya same ta?""" "Ya ce ""We are expecting another Muhsin in sha Allah, cikin yana ta ba da matsala ne yana neman ya fita," "so an bata complete bed rest ne, kin ga ba zai yiwu ta din ga yawo ba""" "Hajiya Sa'a ta ɗan yi jimm sanan ta ce ""Yayi Allah ya raba lafiya""" Ayshacool "Uwargidan sa da ke ƙoƙarin haɗa masa tea kuwa, ji ta yi tamkar ta kurma ihu. Da ta ji batun cikin Fadila," kuma wani namijin ne. Ita nata yaran biyar duk mata ne. """Ya dai lafiya kuwa?"" Ya yi maganar yana kallon ta." "Ajiye masa tea ɗin ta yi, ta bar falon saboda takaici, dan kuwa ji ta yi, tamkar ta watsa masa shayin a" kansa. "Ya karya abin sa a nutse, yana yi yana communicating da mutane ta waya." "Tashi ya yi zai je ya duba Fadila, dan ba a gurin ta ya kwana ba, kuma ba ta jin daɗi sosai. Sai dai ya ji" "tamkar an ɗora masa dutse a kansa, kuma an saka igiya an ɗaure shi. Ya yi miƙa ko zai ji dai-dai, amma ya kasa jin ya dawo normal." "Ya lallaɓa ya fita, kansa na sara masa ya nufi sashin ta. Ya yi iya ƙoƙarin sa, bai bari ta fahimci wani abu" "ba, saboda kar ya ƙara mata damuwa, ya zauna har su ka yi hira, sannan ya fita." **** "Ya na zaune yana kallon Nana, ta na ta fafutukar yin breakfast, saboda ƙoƙari meatpie ta tsiri yi da safen." "Ta kammala ta zuba masa nasa, ta haɗa masa tea. Ta zuba masa ido. Ya saka hannu ya ɗauka ya kai" "bakinsa ya ci, ya yi murmushi ya sake kaiwa bakinsa." "Ta ce ""Da daɗi?""" "Ya ɗaga mata babban yatsansa, alamar jinjina." """To ka ce Allah ya yi mini albarka""" "Murmushin sa ya ƙara faɗaɗa ya sumbaci goshinta, sannan ya shafa gashinta ya ce ""Allah ya yi albarka""" """Amin Shugabana"" ta yi maganar tana dariya." """Ga Nonon can a kan mudubi, ki fara sha kan ki karya""" "Ta tsuke fuska ta ce ""Nonon raƙuma dai ba nawa ba"" A tare su ka tuntsure da dariya, har ya kusa" "ƙwarewa, ta ɗaukko ruwa ta ba shi ya sha." "Ta ce ""Ba ruwana, kar ka ƙware ka ce ni ce""" "Duk da ba ta da cikakkiyar masaniyar dalilin ba ta Nonon raƙumin, amma ta fara jin daɗin sa sosai da" sosai a jikinta. """Sayyid, bari na kaiwa ƙawata ko za ta ci""" """Wa?""" """Yusra"" ya jinjina kai. Ta fita ta shiga cikin gidan." "Ko da ta yi sallama, a falo ta tarar da Siyama, hannunta duk ya ƙone, a ɓare mata ƙunar." """Sannu ina kwana?""" "Ta kalli Nana ta amsa ciki-ciki. Ba ta sake bi ta kan Siyama ba, ta haye benen. Ɗakin Yusra ta shiga da" sallama. "Yusra ta ɗago, amma ba ta amsa ba. Ta ganta a zaune a kan gado ta yi tagumi, amma tana ganin Nana ta" saki murmushi. "Nana ma ta yi mata murmushi ta ƙarasa ta zauna a kusa da ita ta ce ""Yayata, kin tashi lafiya?""" "Yusra ta ce ""Lafiya ƙalau""" """Abinci na kawo miki, ko kin karya?"" Ta ce ""A'a""" """To ga wannan"" ta saka hannu biyu ta karɓa ta ce ""Na gode"" Nana ta din ga yi mata hira, har ta cinye" meatpie ɗin. "Ta ɗan numfasa ta ce ""Dan Allah Nana, kema ki na jin kin gaji da duniya, idan ki ka ga wuƙa ki ji kamar ki" "cakawa kanki, ko ki faɗo daga saman bene ki mutu? Irin duniyar babu daɗi ɗin nan?""" "Nana ta jinjina kai ta ce ""Sosai, na taɓa yinƙurin kashe kaina ma, amma addu'a nake yi sosai da sosai. Ina" "roƙon Allah ya kiyaye ni. Kuma nake yin alwala sosai nake zama da ita""" """Kin tabattar idan na yi hakan zai daina ji, idan na yi addu'a Allah ba ya karɓa, salla ma kamar ba daidai" "nake yi ba."" Nana ta rufe mata baki ta ce ""Ki daina faɗar haka, nima da ina wannan tunanin amma na yi ta istigfari. Allah ya na karɓar addu'armu, ba dan haka ba da wataƙila haukacewa zamu yi gaba ɗaya""" "Yusra ta ce ""Haka ne, wallahi na ji daɗin zuwan ki gidan nan, duk kin san me nake ji, kuma kin san" "abubuwan da nake ji ba ƙarya nake yi ba""" """Ai kamar yadda na gaya miki ne, mukaɗai mu ka san abin da muke ji. Ki daina damuwa sai kowa ya san" "halin da ki ke ciki, an fahimce ki an daina cewa ƙarya ki ke yi. Idan an kai ki gurin likita ya baki magani, ki" "din ga sha. A gefe kuma ki din ga addu'a ki na fatan Allah ya yaye miki""" "Ta girgiza kai ta ce ""Ba na son maganin likitan nan, bacci suke saka ni, kuma ba na iya baccin sam, sai dai" "jikina ya mutu, kuma damuwa ta ƙara yi mini yawa"". Nana ta din ga rarrashinta da ba ta haƙuri." "Sun yi hira sosai, sannan ta ce za ta raka Nana bakin ƙofa." "Su na tafe ta ce ""Kin ga Siyama ta ƙone ko? Tana shiga kitchen za ta juye ruwa a flask, na sheƙe mata shi" "a hannunta. Nana ta tsaya cak ta ce ""Saboda me?""" Ayshacool """A'a kar ki yi kuka""" """To ni ka daina yi mini irin haka""" """To na daina"" ya faɗa yana kai hannunsa fuskarta." """Kar ki yi kuka fa"" jin yadda ya shiga damuwa nan da nan, ya sanya ta ci gaba da kunna shi, ta hanyar yin" taɓara iri-iri. "A ranta ta ce ""Ohh, wai yau ni ce ba a son na yi kuka, da uban wa ya damu idan ma rijiya zan cika da" "hawaye?""" "Ta ƙarfin tsiya ta saka ya din ga rarrashinta, da Hausa da French." "Da Asuba kuwa sam bai tashi da alamar ma ya yi fushi ba, saboda kar ta yi kuka." "Bayan ya dawo daga salla, tana kwance a jikinsa ta ce ""Dan Allah Sayyida ka bar ni na je a yi mini kitson" "nan, na je gurin 'yar uwata dan Allah""" """A'a""" """Dan Allah Sayyid.""" """Idan kin tafi wa zai kula da ni?""" "Ta yi murmushi ta ce ""Zan ajiye maka duk abin da ka ke buƙata, dan Allah ka bari na je Please. Ba dan kar" "na zaunar da kai ba, sai mu tafi tare ma, to ka ga bai kamata na bari ka na jira na ba""" """A dawo lafiya"" ta zabura ta ce ""Ka yadda na je?""" "Ya jinjina kai. ""Allah ya saka mini kai a aljanna na gode sosai Shugabana""" "Ya yi murmushi ya ce ""Sayyid yanzu kuma Shugaba""" """To ai duk abu ɗaya ne"" kyakyawar sumbata ya samu a bakinsa, daga matarsa saboda tsananin farin ciki" da ta shiga. "Da safe ta ya ƙoƙarin gama girki da wuri, ta ɗora masa na rana, ta dafa ruwan zafi ta zuba masa a flask da" duk abin da take sanya ran zai nema. "Ta yi wanka ta fara shiri, su ka yi waya da Hajiya Amina, take gaya mata kwana huɗu kenan, an yi wa" "Shukura aiki yaron ya rasu. Nana ta ji ta damu sosai da sosai, ta yi mata jaje ta ce za ta je ta duba ta." "Ko da ta ajiye wayar, ta kalle shi ta ce ""Sayyid, ka ji Shukura ta haihu yaron ya mutu, dan Allah zan biya" "na duba ta, sai na tafi gidan Ummi.""" """A'a""" "Ta marairaice ta ce ""Dan Allah, kar su ga kamar wulaƙanci ne, an gaya mini abu ban je ba""" "Ya kalle ta ransa a haɗe, ya ce ""Kar ki je gidan nan"" ta tsuke bakinta, kar ta je gidan Ummin ma, ya hana" ta zuwa. "Har bakin hanya ya raka ta, sannan ya koma." "Ta yi tunani ta ga yadda ya tsuke fuskar nan, babu lallai ya bari ta je, kuma Hajiya Amina ba ta cancanci" "haka daga gare ta ba. Duk da ba shiri suke yi da Shukura ba a baya, amma tana matuƙar tausayinta." "Kawai ta yanke shawarar ta je a gurguje, ta duba ta ta wuce gidan Ummi." "Habu ne ya buɗe mata gate, yana ganin ta, ya yi murmushi suka gaisa ya ce ""Ina mutumin?""" "Ta ce ""Yana gida, bai san zan zo ba, wata unguwar na tambaye shi, dan Allah kar ka gaya masa na zo""" """A'a kar ki damu, ba zan gaya masa ba, ina fatan duk ku na lafiya?""" "Nana ta ce ""Lafiya ƙalau, ba ka zuwar mana kwana biyu""" """Ai na ga babu wata matsala ne, ku na lafiya shi yasa""" """Ko kuma shi ne ya hana ka zuwa, Sayyid kishinsa ya yi yawa""" "Ya yi murmushi ya ce ""Sayyid kuma?""" "Nana ta jinjina kai ta ce ""To na rasa da sunan da zan kira shi, amma dan Allah da wani sunan aka ɗaura" "mana aure da shi ne?""" """Kamar dai yadda na gaya miki ban san komai a kansa ba, kawai cewa na yi a saka Muhammad, amma" "ban san sunansa ba nima""" "Ta jinjina kai ta ce ""To da gaske kai ne ka ke ba shi kuɗin da yake kashe mana? Na ga kuɗin aikin gadin ba" "wani yawa ne da su ba""" "Ya ɗan yi dariya ya ce ""Ai ainihi ba gadi ne sana'ata ba. Ina safarar dabino ne, da mazarƙwaila da cukui da" "sassan raƙumi, daga Nijar zuwa Nigeria na rarrabawa 'yan kasuwa. A garin haka ma na tsince shi. Na fara" "gadi ne saboda na samu na zauna guri ɗaya, a nema masa magani, amma haryanzu ba a dace ba, masu maganin sai su ce abin ya fi karfinsu""" """Amma Malam Habu, me aka ce muku yana damunsa?"" Horn ɗin mota su ka ji, ya ce ""Bari na buɗe ƙofa""" "Ta ce ""Shikenan, nima bari na hanzarta""" "Ta shiga cikin gidan, Jummai ta din ga murna da ta ga Nana, ta yi mata jagora har ɗakin Hajiya Amina," inda Shukura take jinya. "Sosai Nana ta jajantawa Shukura, tare da ba ta haƙuri, da ƙarfafa mata gwiwa a kan girma da" muhimmancin tawakalli ga Musulmi. "Hajiya Amina har so take Nana ta zo, ko tana cikin damuwa, ire-iren wa'azinta, a kan tawakalli da dogaro" ga Allah na ƙara mata ƙwarin gwiwa. "Nana ta tambayi ina Haidar, aka ce mata yana gidan kakarsa." Ayshacool "Muryar Alhaji Zailani ta ji ya shigo ɗakin, yana kiran sunan Hajiya Amina." "Gabanta ya faɗi, ƙwaƙwalwarta ta shiga fafutukar tuno mata, da abin da ta gani a mafarki amma ta kasa," "duk da zuciyarta na raya mata mummunan abu ne, kuma kamar a zahiri ya faru. Saboda kaucewa zargi, Nana ta yi ta maza ta gaishe shi." "Shi kansa ya yi mamakin ganin Nana, ya daidaita nutsuwar sa, ya amsa mata ya ce ""Ashe amarya ce ya" "mai gidan?""" """Yana nan lafiya ƙalau. Hajiya bari na tafi ina sauri ne, sai na sake dawowa.""" "Cikin sauri ta ɗauki jakarta ta yi waje, Shukura na ta yi mata godiya." "Ba ta tarar da Habu ba, kawai ta buɗe gate ɗin ta fice. Ganin da ta yi wa Alhaji Zailani, ta din ga jin" tamkar ta aikata wani mummunan saɓo ne. "Tana ta sauri, unguwar shiru babu kowa, ta ga an sha gabanta da mota. Ta ja ta tsaya ƙirjinta na dukan" uku-uku. "Duk wannan saurin, na ki tsere mini ne? Idan na so kamo mini ke zan saka a yi, na yi duk abin da nake so," "kuma babu wanda ya isa ya ce dan me, ko ya tuhume ni. Biyo ki na yi na ƙara tabattar miki da ina nan a kan baka ta, wallahi ba zan rabu da ke ba, sai buƙata ta ta biya.""" "Cikin dakiya ta ce ""Allah ko? A baya ban taɓu ba, sai a yanzu ka ke tunanin zan taɓu? To kar ka fasa, ka ci" "gaba da bibiyata da mugun nufinka, kar ka fasa"" ta zagaye motar ƙasan zuciyarta tana tsananta addu'a ta" bar gurin. "Gidan Ummi ta tafi, Ummi ta yi farin cikin ganinta sosai da sosai, su na hira ana gyara Nana. Nana ta bata" wasu daga cikin kayan da su Adda Saude suka kawo mata. "Aka wanke mata kai, aka yarfa mata kitso ƙanana, ta yi mata dilka ta zana mata lalle ja da baki, ta turara" ta da turarukan wuta. "Nana ta ce ""Inyee ko ranar aurena ban samu wannan gatan ba""" """Ai biya za ki yi, ki je gida ki ce ya biya kuɗin gyaran da na yi miki""" """Ba zamu biya ba ɗin"" ta yi maganar tana dariya." "Ummi ta bata labarin yadda Saleh, duk ya shiga damuwa da tashin hankali, saboda auren da ta yi, ya" "tattara ya koma Lagos ma. Daga haka kuma suka koma tattaunawa a kan matsalolin gidan su, yadda Baba ya bar ragamar gida a hannun Mama, gantalin da Jamila take yi, har ta bata labarin dukan da Gaddafi ya yi mata, ga Imarana babu ma wanda yake cigiyarsa. Suka ci gaba da jajanta matsalolin na su, da a yanzu ba su san ma hanyar saita wannan gida na su ba. Gefe ɗan gidan Yaya Atine ya ce yana son" "Suwaiba, Mama ta ce ba za ta bawa Faƙiri 'yar ta ba." "Sun daɗe su na hira, Nana ta bawa Ummi kayanta da take so a ɗiɗɗinka mata." "Ummi ta duddubo mata wasu kayan kwalliya, da sauran 'yan kayan buƙatu ta rako ta titi, ta samu abin" hawa ta tafi gida. "Ana ta kiraye-kirayen sallar magariba Nana ta isa gida, sai dai ba ta tarar da shi ba." "Ta yi salla, kasancewar ta zo da abinci daga gidan Ummi, ya sanya ba ta ɗora girki ba, ta dai kunna gas ta" ɗora masa shayi. "Har aka yi sallar isha'i shiru bai shigo ba, sai kuma abin ya fara damunta. Ga shi shi ba waya ba, wayarta" "ma tana hannunsa, ba waya ta fita." "Tana nan tana kallon hanya, ta ji yana rufe gate. Ajiyar zuciya ta yi, ta jira ya shigo ɗakin." """Sayyid, duk na damu na ji ka shiru, ina ka tafi ne?""" "Ko kallon gurin da take bai yi ba, ya wuce ta ya shiga banɗaki. Sororo ta tsaya tana mamaki." "Ta koma gefe ta jira, ya fito. Ya sake nufar wardrobe. Ta bi bayansa ta na magana. ""Sayyid wai meyafaru" "ne? Ina ta magana ka yi mini shiru""" "Ya duba jallabiyar da zai saka ya kwanta. ""Sayyid ka yi magana mana""" "Ya ajiye jallabiyar, ya kalli Nana a tsanake ya ce ""Me yasa na ce kar ki yi abu ki ka yi?""" "Gabanta ya faɗi, ce rauni ta ce ""Me na yi?""" """Tambayata ki ke yi? Ban ce kar ki je gidan mutumin nan ba? Ban gaya miki ba?"" Ya yi maganar cikin" ɗaga murya. "Cikin sauri ta girgiza kai ta ce ""A'a ban..." """Kar ki yi mini ƙarya kin je, me yasa ki ka je?""" "Ta girgiza kai tana tsuma, saboda yadda ya burkice mata." "Ya Kano hannunta ɗaya ya ɗora a ƙirjinta, ya kama ɗaya ya sanya a ƙirjinsa, ta ji yadda zukatansu ke" bugawa a tare. """Haryanzu ki na tunanin ƙarya nake yi, da nace miki akwai ruhina a jikinki?""" "Ya saki hannayenta, ya kuma tsare ta da ido, ya ce ""Me yasa ki ka je bayan na ce kar ki je?""" Nana ta yi shiru ta ƙi magana. Ayshacool """Magana nake yi miki"" ya ƙara maganar yana ɗaga mata murya." "Ta ɗaga kai ta kalle shi, ta ga gaba ɗaya ya canza, fuskar sa kamar bai taɓa dariya ba, jikinsa yana tsuma." "Tsorata ta yi, ta ƙara ja da baya, kawai ta ji ya riƙe wuyanta." Ayshercool 08081012143 Ayshacool "Idanun Nana suka yo waje, ta ji numfashinta ya yi sama, ta saka hannu ta rirriƙe nasa tana kakari." "Da ƙyar ta kalli fuskarsa, gaba ɗaya ta canza naman fuskarsa sai rawa yake yi. Tsohon nan ta ga ya" "bayyana a gefensa, riƙe da sandarsa yana kallon ta yana dariya." "Jikinta ne ya saki a hankali, ta sauke hannunta. Ya yi jifa da ita kan katifa ya yi baya, yana jin tamkar ana" jan kansa. "Tana durƙushe tana wani irin tari, haɗi da kakari, tana ta yinƙurin amai, amma babu abin da yake fita" "daga bakinta sai wani irin yawu mai yauƙi. Ta ja jikinta da ƙyar ta jingina, ta lumshe idanunta ta buɗe a" hankali. Ta ga Ƙaisar ya zura mata ido. "Ya gyara zamansa ya ce ""Yanzu da ki ka fara ɗanɗana kuɗarki, wataƙila za ki yarda da abin da nake gaya" "miki. Laifi na biyu kenan da ya aikata mini, zan kuma taɓa shi a inda ba ya zato""." "A wahale Nana ta ce ""A'a Ƙaisar, koma dai mene ne, ni ya yi wa dan Allah ka rabu da shi, wannan tsohon" "na gani a tare da shi, kuma idan ka ce za ka yi masa wani abu, kai ma wannan tsohon wahalar da kai yake yi.""" """Ba ke za ki gaya mini abin da zan yi, ki rufe mini baki. Kuma kuskure mafi girma da ki ka aikata, bayan" "ƙin amincewa da buƙata ta, shi ne ɗaukar cikin da ki ka yi, ba zan taɓa lamunta a samu zuriya ta" "tsatsonki ba, na ci gaba da ƙuntata rayuwata ina wahalar banza a kan mutane marasa alaƙawri kamar ku" "ba""" "Nana ta kalli cikinta ta kalle shi ta ce ""Ciki kuma?""" """Ƙwarai, ga ɗan tayi nan a cikin ki, tun a ranar farko da ku ka kasance tare. Kin ɗauki abin da ke kan ki ba" "ki da tabbacin wane jinsi ne""" """Mutum ne, Sayyid bil'adama ne, da aljani ne ba zai iya tarayya da ni a zahiri ba, sai dai a cikin bacci, ko" "ta hanyar amfani da gangar jikin ɗan Adam """ """Ko?""" """Eh"" ta ba shi amsa." """Yaro yaro ne. Kin tabattar bil adama ne, daga ina? Daga wace nahiyar? Wane shiri ki ke da shi, a kan" "sanin waye shi da inda ya fito? Har ki ka sakankance ki ka amince da ɗaukar ciki?""" "Ƙoƙarin juyawa Nana ta yi a kan katifar, amma ta ji jikinta a ɗaɗɗaure kamar an yi mata duka. Ga wani" "irin azabar sanyi da yake ratsata ko ta ina, tamkar an ajiye ta a cikin ƙanƙara. A cikin kunnuwanta kuma" take jin yadda zuciyarta ke bugawa da ƙarfi da kuma sauri. Ga wani irin nauyi da kanta ya yi mata tamkar "an ɗora mata. Ga azababben ciwo da yake yi mata, tamkar zai rabe." "Ta juya da ƙyar tana numfarfashi, tana son lalubar abin da za ta rufa, wani irin huci ne ya daki fatarta, ta" "buɗe idanunta da ƙyar, ta kalli gefenta." "Yana kwance jiginsa na ta jijjiga, yana numfarfashi." "Ta din ga jan jikinta a hankali, ta matsa ta hau kan ƙirjinsa ta kwanta, ba tare da fargabar zai sake" yinƙurin cutar da ita ba. "A hankali ta ji zafin jikinsa, ya fara ratsa ta, ta fara rage jin sanyin da take ji, wani wahalallen baccin ya" sake yin awon gaba da ita. """Asmy"" ta ji ya kira ta da wani sunan kuma. Ta buɗe idonta da ƙyar ta kalle shi." Garau da shi kamar babu abin da ya faru. """Salla"" ya faɗa a taƙaice, jikinsa duk danshin ruwan alwala, ya fice ya tafi masallaci." "Da ƙyar ta tashi, tana daddaga bango, ta shiga ta yi alwala, ta dawo ta yi salla a zaune, ta kwanta." "Ganin ba ta tashi da wuri ba, ya sanya shi fara rage aikace-aikacen ɗakin, amma ya ga babu alamar za ta" "tashi balle ta ɗora girki. Ya matsa kusa da ita ya tashe ta. Ta tashi zaune da ƙyar, kanta kamar ana buga" mata guduma. "Ya ƙura mata ido ya ga duk ta canza, sai dai ta yi masa kyau a ido sosai, ƙanan kitson kanta, sun dace ba" "ƙin gashinta, ga hannunta lalle ja da baƙi ya yi mata kyau sosai da sosai." "Ta saukko daga kan katifar, ta ɗauki wata roba, ta ɗaukko lemon tsami ta yanka, ta fara matsawa a" "bakinta. A hankali tashin zuciyar da take ji, ya fara raguwa. Shi dai ya zuba mata ido." Ta gama ta sake ƙoƙarin kwanciya. """Ki ci abinci, ga ƙosai"" ya yi maganar yana nuna mata ledar da ke kusa da gas." Ta girgiza masa kai ta nemi guri ta kwanta. """Kin yi mini laifi ki na fushi da ni kuma? Na ce kar ki yi abu kin yi, kuma kina fushi?""" Ayshacool "Ta kalle shi idonta fal hawaye ta ce ""Kuma shi ne sai ka shaƙe ni? Har na yi maka laifin da za ka yi" "yinƙurin kashe ni, dama ba so na ka ke yi ba"" A rikice ya zaro ido ya kalle ta ya ce ""Ni? A'a ban shaƙe ki ba. Me yasa zan shaƙe ki kuma? Raina ya ɓaci ne, zuciyata ta kama da wuta, sosai da sosai amma ban shaƙe" "ki ba. Kamar bacci ma na yi daga lokacin""" "Idonta fal hawaye ta ce ""Bayan ga shaidar faratanka a wuyana""" "Kamar ya yi kuka ya ce ""A'a, kin manta kin yanke mini farce, amma ban taɓa ki ba ma, kalli hannuna"" ya" yi maganar yana nuna mata yatsun sa. "Ya miƙa hannunsa wuyanta, dan ya duba shaidar faratan da ta ce, amma ya ji jikinta zafi rauuu." "Sake rikicewa ya yi ya ce ""Ma vie. (Rayuwata) tu as de la fièvre ? (Zazzaɓi ki ke yi?"" Ya yi maganar a rikice." "Ba ta kula shi ba ta kwanta, tana jin yadda jikinta yake ɗaukar zafi, cikin ta yake yamutsawa." "Wayarta ya ɗauka ya danna, ya kara a kunnensa. Da French ya yi magana, ya ajiye wayar a kan mudubi," "ya dawo inda take ya ce ""Tashi ki saka kaya, na kira Habu""" """Sayyid da ba ka kira shi ba, zan warke fa""" """A'a jikin ki ya yi zafi sosai""" "Ya nemi guri ya zauna a musa da ita, yana ci gaba da kallonta cikin damuwa." * "Sannu a hankali yake jujjuya wayar hannunsa, yana sake karanta saƙon da ya shigo wayarsa." "An shirya tsige shi, daga shugabancin 'yan kasuwa, bisa zargin sa da yin sama da faɗi da wasu kuɗaɗe, na" ƙananan 'yan kasuwa. "Tabbas akwai kuɗaɗen wasu a hannunsa, har da wanda kuɗinsu bai kai ba, da zai yi wa ciko ya ba su" "bashin kaya. Kuma ya tattara kuɗin ya yi order kayan, sai dai sun ƙara wata guda a kan lokacin da yakamata su zo, shima yana ta bibiya ne. Amma ya yi wuri a ce an ɗauki wannan matakin, duk da ba yau ya saba yi wa ƙananan 'yan kasuwan irin wannan tallafin ba, har ma da manyan, amma ba a duba hakan" ba. "Fadila ce ta nufo shi, hannuna da ɗan ƙaramin tray, ɗauke da fruit, ta nemi guri ta zauna." "Ta ce ""Daddy, ga fav ɗin ka, banana, ga kuma smoothie na yi maka, na ga kamar a gajiye ka ke""" "Ya yi murmushin yaƙe ya karɓa ya ce ""Na gode sosai da babyna""" "Jiki a sanyaye ta ce ""Daddy"" ya kalle ta ya ce ""Na'am""" """Me yake faruwa ne?""" "Ya ce ""A ina?""" """Damuwa ce a fuskarka, dan Allah gaya mini, meyafaru?""" "Ya yi murmushi ya ce ""Tsabar gajiya ce kawai, kin san yanayin harkokin namu, babu hutu""" "Fadila ta riƙo hannunsa ta ce ""Na san wataƙila har da damuwar kayan nan, da suma suka yi delay, amma" "dan Allah ka yi haƙuri ka daina damuwa, yadda wancan suka kuɓuta, wannan ma da yardar Allah za su tsira. Kar ka damar mini kanka dan Allah""" "Maganganun nata sun ɗan ba shi ƙwarin gwiwa, shi bai damu da batun tsige shi daga shugabancin ba," "shi haƙƙoƙin mutane da suke kansa, su ne suka dame shi. Yana jin daɗin tattauna matsalolin sa da Fadila. Duk da ba ta kai uwargidan sa shekaru ba, amma yau shekara bakwai da auren Fadila, ta tattara duk ta tsane shi, tana ganin ya ci amanarta, sun yi wahala tare ya ƙaro aure. Duk da duk wani abu na jin daɗi na hakkinta yana sauke mata. Ko ya gaya mata damuwarsa, sai dai ta taɓe baki kawai ta ce Allah ya kyauta," ko ma ta ce masa alhakinta ne. "Fadila kuwa ko sun samu saɓani, da ya shiga damuwa, take ruɗewa har sai ya samu mafita, sai dai a" "wannan karon, ba zai iya gaya mata ba, saboda ba cikakkiyar lafiya ce da ita ba ita ma." **** """Husnah"" ta buɗe idonta ta kalle shi, lokacin agogon ɗakin ya nuna ƙarfe sha ɗaya da rabi na safe." """Tashi ki saka kaya, ga Habu can ya zo, za mu je a duba ki""" """Na ce ka daina gaya musu, mu daina saka su ɗawainiya""" """Tashi ki daina yi mini jayayya"" ya yi maganar, yana tsuke fuska." "Ta tashi da ƙyar, ya taimaka mata ta saka kaya, ta saka hijjabi, a harabar gidan suka tarar da Habu. Ya yi" mata sannu suka fice. "Tun da ya kira Habu ya sanar masa, dama da adaidaita sahu ya zo. Wani ƙaramin asibiti suka je. Buzu" "yana tare da Nana, Habu ya yi ta shiga yana fita." "Ya sayo kati aka duba ta, aka ba ta gwaje-gwaje. Sun ɗan jima a gurin ɗaukar jinin, ta gaji da zaman, ta" "zame tana ƙoƙarin kwanciya a gurin, amma ya riƙo ta tsam a jikinsa." Ayshacool "Suka koma gaban likita da sakamakon, ya duba ya kalli Nana ya ce ""Yaushe rabon ki da Al'ada?""" "Tamkar ya sokawa Sayyid mashi, ji ya yi ina ruwansa da zai yi mata wannan tambayar? Amma ya dake" bai yi magana ba. "Nana ta gaya masa, ya ce ""Ok, to akwai ciki ne, sai kuma malaria++ bai kamata a ce, ga juna biyu ba" "kuma ga malaria ki na fama ba. A kula sosai. Zan rubuta ruwa da allurai a saka miki, za ki ɗan ji ƙwarin" "jikin ki in sha Allah""" "Ya yi rubuce-rubuce ya basu, Sayyid ya karɓa suka fito." "Ya miƙa wa Habu katin, aka nuna musu inda za su kai Nana." "Habu ya kalle shi ya yi masa magana da yaren su, ya cewa Habu ""Tsaya"" ya saka hannu a aljihunsa ya" "ɗaukko kuɗi ya ba wa Habu""" "Habu ya kalli kuɗin ya kalle shi, ya ce ""Da can kuɗin yi wa Nana amfani da su." "Wani ma'aikaci ne, ya shigo ward ɗin zai sanyawa Nana cannular. Nana ta miƙa masa hannun, ya kai" hannu zai kama ya saka mata Buzu ya riƙe hannun Nana. "Ma'aikacin ya ce ""Allurai zan yi mata, zan saka mata cannula ne"" ya yi shiru ya ƙi magana. Nana ta kalli" "yadda launin idonsa ya canza. A ranta ta ce ""Allah ya yaye maka wannan azabar kishin Sayyid""" "Habu ya yi gyaran murya, ya ""Ka yi haƙuri, a saka mata, ka ga tana shan wahala sosai." "Ya yi mursisi, ya murtuke fuska, ya riƙe hannunta gam, ya ƙi saki." "Sai da Habu ya zauna ya din ga yi masa bayani da yarensu, cikin tattausar murya. Ƙarshe ma'aikacin gefe" "ya koma, ya zubawa sarautar Allah ido." "Tamkar gunki ya yi gum, ya ƙi motsi kuma ya ƙi magana." """Ni idan ba zai yarda a saka mini ba, dan Allah ku mayar da ni gida, na je na kwanta na gaji"" ta yi" "maganar a raunane, cikin yanayin rashin lafiya." "Da ƙyar ya saki hannun Nana, sai dai ya kawar da kansa gefe, saboda yadda zuciyarsa ke tafasa da ganin" ya kama hannun Nana ya saka mata ruwa. "Har huɗu su na Asibiti, sai dai ta ji dadin jikinta, zazzaɓin ya sauka." "Aka gama saka mata ruwan, sannan suka tafi gida. Ba ya jin nauyi ko kunyar Habu, haka yake rungume" "da Nana yana shafa ta, kamar zai lashe ta ya mayar da ita cikin sa." "Suka koma gida, Nana ta samu ruwa ta yi wanka, ta saka kankanar da ya saya mata a gaba, ta din ga sha," saboda itakaɗai ce ta ji ta yi mata daɗi. "Suna harabar gidan, Habu yana yi masa magana, sai ga babar su Yusra ta ƙaraso." """Kai mai gadi, ina ka tafi baka yi wa kowa bayani ba? Zamu kai Siyama wankin ƙonuwar da ta yi, amma" "ka yi tafiyarka yawon ka?""" "Habu ya ce ""Ki yi haƙuri Hajiya, mai ɗakin nasa ce babu lafiya, ba a nuste yake ba, hankali tashe mu ka" "tafi Asibiti ki yi haƙuri dan Allah""" """Ni ma tawa 'yar babu lafiya ai, ba sai ya yi bayani ba. Tun da idan zai je wani guri yana rubutawa Jamil" "ba, sai Jamil ne ya buɗe mana muka tafi, ƙonuwar na ta jini""" "Habu ya sake cewa ""Ki yi haƙuri dai dan Allah""" "Ko ɗaga kai bai yi ya kalle ta ba, balle ya kula ta, ko ta saka ran zai ba ta haƙuri, ya bar ta ita da Habu." """Sannu""" "Ta jinjina kai ta ce ""Sayyid da ka sani ka ba ta haƙuri, ba na son wannan faɗan da ake yi maka""" """Ya jikin? Kin daina jin zazzaɓin?""" """Amma ka san mun yi laifi, bai kamata mu tafi ba su sani ba""" """Da suka buɗe ƙofar sun mutu ne?""" "Nana ta sauke numfashi ta ce ""Aishikenan, idan ka janyo aka kore mu, ka nemo mana inda za mu zauna" "ai"" ya yi shiru, bai kuma cewa komai ba." "Daga bisani ya ce ""Me za ki ci?""" """Ba komai, ba na son komai, kankanar nan ta ishe ni""." "A hankali ya kai hannunsa, ya shafa gashin ta, ya saki murmushi ya ce ""Kitson nan ya yi kyau sosai, ya" "dawo da hannunsa kan hannunta, ya jujjuya hannun, ya kai bakinsa ya sumbata ya ce ""Kin yi mini kyau""" "Ta kalle shi galala ta ce ""A hakan da na fita hayyacina. Tun jiya na so ka kalla ka yaba ba, ka share ni ka yi" "ta yi mink faɗa""" """Idan na ce kar a yi, to a bari ne kawai, ba na so. Me yasa zan ce kar ki je guri ki je?""" "Jiki a sanyaye ta ce ""Na san na yi laifi, ka yi haƙuri. Za su ga kamar wulaƙanci ne, sun gaya mini abu na" "tashin hankali, amma na kasa yi musu jaje. Sayyid ban ji ka ce komai ba, a kan abin da aka ce""" """Wanne?""" """Da likitan ya ce... Sai kuma ta yi shiru." """Ya ce me?""" """Ina da juna biyu, tsoro nake ji"" ta yi maganar tsoron na bayyana ƙarara a kan fuskarta." """Tsoron me?""" Ayshacool "Abin da ta so furtawa daban, amma ta kauce faɗar hakan, kar ta tayar masa da hankali ta ce ""Ban ga ka" "yi murna da hakan ba""" "Ya gyara zamansa ya dubi Nana a tsanake ya ce ""Wata irin wutar zafin, ganin wani ya taɓa ki ne, take ci" "mini zuciya. Amma wallahi ina cikin murna zamu ƙara yawa, nima Ahalina zai cika, ki haifi namiji mai" "kama da ni. Ko kuma mace mai kama da ke""" "Murmushin dole Nana ta yi, ba dan ya kai zuciyarta ba ta ci gaba da tauna kankanar bakinta a hankali." * "Yanayin yadda aka banko ƙofar gidan, sai da Baba ya tsorata kamar ya zura da gudu. Ya dai tsaya ya ce" """Kai wani mara hankalin ne ya ke yi mana wannan banzan bugun haka?""" "Bai yi magana ba, sai ganinsa Baba ya a tsakiyar gida, tamkar ya faɗo daga sama." """Uban me ya kawo ka gidana?""" """Gidan Ubana ne"" ya faɗa yana ɗan rarraba ido yana kallon gidan." """To uban me ya dawo da kai? Nan ka saka 'yan sanda suka din ga yi mini sintiri a gida, ka kai Gaddafi ƙara," "kuma ka gudu, da yake kai duk inda ka tsuguna babu alkhairi tsiya ce take biyo baya. Ka bar mini gida kafin 'yan sanda su zo neman ka""" """Ni fa ban kashe kowa ba wanda suka yi abin ma an kama su, kawai ka wani din ga kora ta, idan na gama" "abin da nake yi da kaina zan bar maka gidan ai. Ka yi ta wani gidanka kamar wani gidan arziki""" "Baba ya ce ""Tun da ba na arziki ba ne ba, zo ka fice""" "Imarana ya ce ""Wallahi ba zan tafi ba. Ina Nana? Ke Nana""" "Nasiru ne ya yi sallama a gidan, hannunsa riƙe da ledar kayan miya, yana ganin Imarana ya tafi da gudu" ya rungume shi. "Imarana ya ce ""Nasiru, na ga kana nema ka kamo ni a tsawo. Wai ina Nana ne?"" Baba yana ƙiftawa" "Nasiru ido, amma tuni ya kwatsa wa Nasiru bayani." """Ai an yi mata aure""" "Turus Imrana ya yi ya ce ""Kamar yaya? Uban waye ya yi mata auren ban sani ba?""" """Ni ne nan ubanta, idan kuma kai ka haife ta da sai an sanar da kai sai na ji""" """Kut.. aure fa, wa ka aura mata, ina fatan ba wannan ajawon bane Salisu yake ko wa?""" """Ba Saleh ba ne, wani Buzu ne mai gadi"" Nasiru ya sake ba wa Imrana amsa." "Kai tsaye ya ƙundumo ashariya ya ce ""Wane irin Buzu kuma? Kai ina ne gidan da aka kai ta?""" "Baba ya ce ""Wallahi ka taka ka je gidanta ban yafe maka ba. Kar ka kuskura ka je ka yi mata hauka ka" "kashe mata aure""" """Wallahi sai na je, dama kula ka ke da ni, shi ne za ka yi mini Allah ya isa ta kama ni, amma tun da ni nake" "kula da kaina ba za ta kama ni ba. Kai Nasiru wuce mu je ka raka ni""" "Baba ya ce ""Nasiru idan ka raka shi, sai na yi maka dukan tsiya""" """Kai mu je zan baka dubu biyu""" "Nasiru ya waiga yana kallon Baba, ga batun kuɗi ya ji, ya maze ya bi Imarana suka fice, Baba na ƙwala" masa kira amma ya fifita dubu biyu a kan kiran Baba. "Su na tafe a hanya, Nasiru yana ba wa Imarana labarin, abin da ya faru da yadda aka yi auren Nana. Ba" ƙaramin fusata Imarana ya yi ba. "Mussaman da ya gaya masa, gadi Buzu yake yi." """Uban me mai gadin zai tsinana mata, Allah na tuba mu dai ba mu yi dacen uba ba wallahi mu dai kawai" "ya kawo mu Duniya yana neman maraba da mu.""" "Sayyid na zaune yana shan shayi, a harabar gidan ya ji an taɓa gate. Ya rufe fuskar sa da sauri, ya tashi ya" "je ya buɗe, ya tsaya yana kallon Imran, saboda tsananin kamnninsa da Nana." "Babu jiran komai, Imrana ya ƙarasa hankaɗa ƙofar ya shiga, Nasiru ya bi bayansa." "Nasiru ya ce ""Ga mijin Nanan nan"" ya yi maganar yana nu na masa Buzu." "Imran ya ƙare masa kallo, ya ce ""Ikon Allah, kai ka auri Nana? Tana ina?"" Sayyid ya yi shiru yana kallon" Imrana. """Malam magana nake yi, ko kurma ne? Ina take?""" "Nasiru ya ce ""Kamar fa ba ya magana, amma Nanan tana cikin ɗakin nan""" """Dan Allah ji wulaƙanci, ɗakin mai gadi, ba ta samun arzikin a ajiye ta a gida ba ma, sai ɗakin daga shi" "waje, koma mene ne ya zo ya afka mata""" "Nana tun tana banɗaki take jiwo, kamar muryar Imran, amma ta kawar da tunanin, a ganinta mai zai" kawo shi yanzu. "Ta fito daga banɗakin ya shigo, Nana ta zabura ta ce ""Imrana"" sai kuma ta tsaya da tuna halin Buzu a kan" kishin tsiya. Ayshacool """Ke ashe ba ki da hankali? Ki ka zauna aka aura miki mutum kawai ki ka biyo shi yawon gadi? Gidan" "babanki ba mamora gidan miji ma haka? To wallahi sai kin bar gidan nan, sako hijjabinki mu tafi""" """Imarana mu tafi mu je ina?""" """Ko ma ina ne. Amma wallahi ba za ki zauna a gurin nan ba. Haka zamu zauna babu ci gaba?""" """To ka zauna mana, ka sha ruwa ka ci abinci, sai mu yi magana. Mama ma ta yi mini aike su Adda Saude" sun zo... """Dalla rufe mini baki, ina ruwana da wata? Addar wofi da can ba su zo ba sai yanzu. Ki ɗaukko hijjabinki" "mu tafi daga nan har human rights, na san biyayya kawai ki ka yi wa Baba ki ka auri mutumin nan, tun da dama ke ba sanin ciwon kanki ki ka yi ba""" "Nana ta yi shiru, tana kallon in da Sayyid yake tsaye, ya tsare ta da ido. Tsoro take ji kar Sayyid ya yi wani" "abun da zai tunzura Imran, dan ta san ko zai kashe shi ba zai yi shiru ba." """Imran na gode da ziyara, da kuma soyayyar da ka ke nuna mini. Amma ka yi haƙuri ina son aurena""" "Wani irin takaici ya kama Imran ya ce ""Nana me za ki zauna ki yi a shago, ɗakin nan meye marabarsa da" "shago? Na san zaman gidanm ne ba kya so, ba can za ki koma ba. Harkoki sun fara buɗe mini, karatu zan mayar da ke, kyakyawar rayuwa nake so na ga kin yi""" "Ta sake kallon Buzu, da ya zubo mata idanunsa, Imran ya waiwaya ya ga abin da take kallo." Sayyid ya shigo cikin takunsa na kamala da nutsuwa. "Ya sauke takunkumin fuskar sa, ya sakar wa Imrana murmushi, ya ce ""Kun yi kama sosai, da alama ku na" "da alaƙa sosai"" ya yi maganar yana miƙa wa Imran hannu su gaisa." """Ba zan gaisa da kai ba, ƙanwata za ka sakar mini, Nasiru ya gaya mini duk wani abin da ya sani. Ni ban ji" "na gamsu da wannan auren ba ko kaɗan. Ya za a yi sama ta ka a aura miki mutumin da ba ƙabilarmu ba," "babu wani dogon bincike. Ni jikina yana bani wani abu, ni ban yarda da auren nan ba gaskiya.""" """Nima na fuskanci akwai sharuɗɗan da ban cika ba, aka yi wannan auren. Amma ko me za a yi mini, ba" "zan iya rabuwa da ita ba, tana ɗauke da ruhina a jikinta. Idan ka raba ni da ita, ni ya zan yi? Zan kula da" "ita, ka daina raina inda Allah ya ƙaddara zamana da ita, ba ka san gobe ba""" "Imrana ji yake kamar ya mangare Buzun nan ya huta, haka kurum ya ji bai yi masa ba. Kuma ya san" "wannan kyawun ne ya ruɗi Nana, har take cewa ita ba za ta rabu da shi ba." "Ya sake kallon Nana ya ce ""Kin zaɓi zama ko Nana?""" "Idonta fal hawaye ta ce ""Ka yi haƙuri Imran, Allah ne ya haɗa ƙaddarorinmu, ba komai zan iya yi maka" "bayani ba, amma ina son aurena. Sayyid na buƙata ta a rayuwarsa""." "Imran ya haɗiye wata irin ƙwallar takaici. Ya zura hannu a jakarsa, ya ƙirgo kuɗi, ya tako gaban Nana, ya" "kamo hannunta ya saka mata ya ce ""Ga wannan babu yawa, cikin abin da nake tarawa ne, domin na dawo gida na inganta rayuwar ki. Dama Saboda ke na dawo, daga nan ko gida ba zan kma ba, zan tafi inda na fito. Kai kuma tun da ta zaɓi zama da kai, idan ka ci amana na bar ka da mai hudowar rana da" "faɗuwar ta""" "Ras Sayyid ya ji gabansa ya faɗi, ya ji maganar Imran ta yi masa nauyi da yawa." "Ya kalli Nasiru ya ce ""Mu tafi""" "Nana da tuni hawaye ya wanke mata fuska ta ce ""Imrana ba zaɓarsa na yi a kan ka ba...." """Shhh ba sai kin yi mini bayani ba ai, tun da ki na farin ciki da auren ki Alhamdilillah"" ya juya zai fita ta" "sake cewa ""Ka bani lambar wayar ka, da zan din ga kiran ka a waya"" bai waiwayo ba ya girgiza kai, ya ce" """Babu buƙata""" "Daga bayansa, yanayin yadda ya kai hannu fuskarsa, Ya sanya Nana gane Imran kuka yake yi. Sakin kuɗin" hannunta ta yi a ƙasa ta durƙushe a gurin ta fashe da kuka mai tsuma zuciya ita ma. Ayshercool 08081012143 Ayshacool """Jiki Alhamdilillah "" ta yi maganar tana mayar da hankalinta, kan Hajiya Amina." """Mummy, wai dan Allah lokacin da aka yi mini tiyata, da a ka fito da ni, an baki babyn a hannunki kin" "gani""" "Hajiya Amina ta ce ""Sau nawa zan yi miki bayani Shukura, ke kaɗai aka fito da ke, ba a bani jaririn ba." "Doctor Sharif ya ce na ɗan jira, jaririn ne ake fama, ko ba bu wadatacciyar iska ko me, oho maganganun su na likitoci. Na dawo ɗaki gurin ki, ya shigo ya ce mini, an kai babyn Nursery, da safe na je na gan shi""" "Alhaji Zailani ya yi gyaran murya ya ce ""Shukura, duk wani abu da za ki yi, abin da ya faru ya faru, ba za ki" "yi jayayya da ikon Allah ba. Kamata ya yi ki gode wa Allah, da ya baki lafiya. In dai da rai da lafiya, Allah zai baki wani mai amfani. Yanzu lafiyar ki muke buƙata, wannan damuwar ba ta dace da ke ba. Kin rasa babynki, nima ba zan so rasa tawa babyn ba, Please ki yi tawakalli na san kin sha wahala a kan cikin nan," "amma ki yi haƙuri""" "Shiru Shukura ta yi, zuciyar ta fal wasi-wasi. Ta ƙara ƙaimi gurin yaƙar mummunan tunanin da yake ta yi" "mata yawo a zuciya, ta hanyar kawar da batun mafarki da ta san ba gaskiya ba ne ba." "Duk mahaifiyarsu ta rasu, amma ba su tashi da zafin maraici ba, Alhaji Zailani ya yi aiki tuƙuru a kan" "rayuwar su, Hajiya Amina ma kuma ba ta taɓa yi musu mugunta ba, ta riƙe su da gaske tamkar 'ya'yanta. Saboda haka take ganin tamkar zuciyarta ba ta yi mata adalci ba. Amma fafur take jin ƙiyayyar mahaifin nata a cikin zuciyarta, ta kuma kasa yarda da cewa ɗan ta mutuwa ya yi ta haƙiƙa, ba wani abin ne ya" faru ba. **** "Kwana biyu Nana ta samu sauƙin jikinta, jikinta ya ɗan yi ƙwari babu zazzaɓin. Sai dai abinci ne ba ya" ciwuwa ta daɗin rai. "Ta saka Sayyida a gaba, a kan lallai sai ta yi wa gashinsa kitso, ta gaji da ganin kan a haka. Yana kwance a" "kan cinyarta, ta saka kibiya tana tsaga gashin nasa. Ta ce ""Sayyid kishi nake da gashin nan naka, gaskiya aske shi zan yi, ya za ayi ina matarka a ce ka fi ni gashi?""" "Ya yi dariya ya ci gaba da kallon da yake yi da wayarta. Ta yi guda biyu ta ce ""To gyara, a yi na can" "ɓangaren""" "Ya girgiza kai ya ce ""Ki ƙyale ni""" "Ta ce ""A'a sai an ƙarasa""" "Fafur ya ƙi gyarawa, ya ce shi fa kitson da zafi." """Dan Allah ka yi haƙuri mu ƙarasa, haba Shugaba ba ka ga yadda kitson nan ya yi kyau ba. Yauwwa" "nawan"" ya ɗago kansa ya harare ta. Ta sakar masa murmushi tana lumshe masa ido." "Ya gyara kwanciyar, ta ci gaba da kitsa gashin nasa, mai matuƙar santsi da laushi." "Babu tsammanni aka bankaɗo labulen ɗakin, sai da Nana ta razana, a hankali ya ɗaga kai ya kalli ƙofar." "Siyama suka gani a tsaye, Kunya ta kama Nana,yanayin da ta tarar da su. Shi kansa dogon wando kawai a" "jikinsa, ya ɗora kansa a kan cinyar Nana, tana yi masa kitso." """Amm dama Mami ce ta ce na zo na duba, ko Yusra ta zo ba mu ganta ba da ma. Amma shikenan"" Ta" "saki labulen a hankali ta ja da baya, saboda yadda jikinta ya yi sanyi." "Kamar babu abin da ya faru, ya ci gaba da kallon wayarsa." """ Ya jikinki ya yi sanyi? Me ya faru?""" """Ba komai"" ta furta a hankali." "Ya juyo sosai ya kalle ta, sai kuma ya fasa maganar da ya yi niyya, ya sake gyara kwanciyar sa." "Dannewa kawai Nana ta yi, amma sai da ta ji tamkar ta ɗura wa Siyama ashar, saboda kawai su na masu" "gadi, ya ba ta damar ta shigo musu ɗaki, ba bu izini. Danne fushin ta ta yi, saboda kar ta saka shi a damuwa, amma tana ji a ranta wataran sai ta zagi Siyama." "Da yamma, Nana ta yi kwalliya cikin doguwar rigar material mai taushi, da hula. Ta fesa turare sannan ta" "ɗora girkin dare, sannan ta kunna turaren wuta a ɗakin." "Neman guri ya yi ya zauna a ɗakin ya ƙi fita, sai aikin kallonta kawai da yake yi." """Shugaba, ba zaka fita shan shayin ba ne?""" "Ya yi dariya ya ce ""Kin yi kyau sosai da sosai, ba zan fita ba""" "Ta sake cewa ""Ka ga yadda ka yi kyau da kitson nan kuwa? Zo ka ga""" "Ya yinƙura ya taso, ya zo ya tsaya a gaban ta, ta nuna masa mudubi ta ce ""Kalli yadda ka yi kyau fa""" "Ya shafa kansa ya ce ""Na zama kamar mace""" "Ta yi dariya ta ce ""Ka yi mini kyau sosai a haka, dama nikaɗai ya dace na ga ka yi kyau""." Ya sunkuyo ya yi mata kiss a goshinta. Ayshacool "Cikin dariya ta ce ""Ni idan ka na yi mini wannan abun, kunya ka ke bani""" "Ya ce ""Wanne?""" """Ko wanne"" ya ƙara tsare ta da ido, da sai da ya sanya ta sunkuyar da kanta saboda kunya." """To matsa na wuce""" """A'a kirana fa ki ka yi""" Ya yi maganar yana haɗa bakinsa da nata. "Bayan ya cika ta, ta sunkuyar da kanta tana jin kunya. Ji ta yi jikinta ya fara sanyi, ƙirjinta yana bugawa," "ta kalle shi ta ga fara'ar fuskarsa ta kau, ya haɗe rai. A tsorace ta ɗan ja jikinta, tana tunanin me ta yi masa. Tana kallon mudubin ta ga duhu ya gauraye ɗakin sai iya wannan tsohon ta iya gani a cikin" "mudubin a tsaye, sai dai a wannan karon ci yake yi da wuta." "Tattara nutsuwarta ta yi, ta fara Addu'a a cikin zuciyarta, ta waiwayo ta kalle shi." Ta ga fuskar sa ɗauke da murmushi. "Ya miƙo hannunsa zai taɓa ta, ta riƙe hannunsa, ta yi yinƙurin kallon idonsa amma ta kasa, ta ji tamkar" zuciyarta za ta buɗe. """Waye kai?""" "Ya amsa da ""Mijinki mana""" "Ta yi murmushi ta ce ""Ba Sayyid ba ne? Ai na riga na ganka. Me yasa ka zaɓi muzgunawa rayuwata ne?" "Da ina zargin ko Ƙaisar ne, amma na fara fahimtar kai daban shi daban. Mece ce manufarka a kaina? Me ka ke buƙata?""" AYSHERCOOL 08081012143 Ayshacool "Wata irin dariya ya saki, ya ce ""Har kin yi ƙwarin da ki ka daina razana da ganina kenan. Haka nake so" "fansa zan ɗauka, yanzu ne lokacin da ya dace na ɗauki fansata""" """Wani laifi na aikata maka da ka ke iƙrarin ɗaukar fansa a kaina""" "Ba tare da tsammani ba, ya shaƙe ta, ya ɗaga ta ya yi jifa da ita, ta bugu da jikin wardrobe ta faɗi." "Ɗakin ya gauraye da matsanancin duhu, ta riƙe wuyanta tana numfarfashi cikin yanayi mai kama da" ɗimuwa da kuma suma. Ta daɗe a haka kan ta ji kamar daga sama muryar Sayyid. """Rayuwata bacci kuma daf da magariba a ƙasa? Ga abincinki ya fara ƙonewa""" "Nana ta ɗaga kai ta kalle shi suka haɗa ido, amma ba ta ji komai ba. Ta tashi da ƙyar ta ji mararta ta ƙulle," "ga hannunta da ta bugu. Amma ta daure ta kashe gas din, ta shiga yin alwala." "Abubuwa da dama su ka zo zuciyarta, tabbas wannan sabon ƙalubale ne a gare ta. Muddin zai cigaba da" "fita daga hayyacinsa yana yi mata haka, to tana tsoron wataran ya yi mata illa." "Haka kurum yake jin sa cikin farin ciki, sai dai lokaci ɗaya ya lura ita ba ta cikin walwala." "Su na cin abinci, ya ɗan shafa cinyarta. Ta farga ta kalle shi." "Ya ce ""Ba kya cin abinci mene ne?""" "Ta yi murmushi ta ce ""Lafiya ƙalau, Abincin ne ba na so""" "Cikin damuwa ya ce ""Na sayo miki buredi za ki ci? Ko ƙos""" """A'a zan ci wannan ɗin"" da ƙyar ta tilasta kanta, ta ci." "Yanayin yadda yake ta bin ta da ido, ya sanya ta san akwai abin da yake so, sai dai a ɗan tsorace take." Haka ta ci gaba da addu'oi da neman ɗaukin Ubangiji. "Duk da haryanzu tana jin nauyin sa, amma ta shirya cikin kayan baccinta na gwanjo, da Ummi ta ba ta ta" shafa turare. Sai dai zuciyarta gaba ɗaya a tsinke take. "Kwanciyarta babu jimawa, ya zo ya kwanta shi ma." """Rayuwata duk kin rage walwala""" "Ta ɗan ja numfashi ta ce ""'yan kwanakin nan, baki ya buɗe, Ubangiji Allah ya ɗorar da lafiya""" """Amin ma vie. Ina jin daɗin haka sosai""" """Saura kuma, Ubangiji Allah ya sanya ka tuna waye kai. Hankalina zai fi kwanciya""" "Ya ɗan yi shiru ya ce ""Ina wannan ƙoƙarin, ji nake kamar abin ya fi ƙarfina. Amma ko da nan gaba, idan" "ban tuna waye ni ba, ki nuna wa ɗa na su Habu a matsayin dangina, tun da ku kaɗai na sani"" Ya yi maganar muryarsa na rawa." """Shikenan mu bar wannan maganar."" Ya yi shiru bai kuma magana ba." """Sayyid fushi ka yi ne?""" """A'a ban yi fushi ba""" "Ta din ga shafa kansa zuwa bayansa, sai dai daga ƙoƙarin rarrashin sa, ya fara ƙoƙarin zarcewa." "A hankali ta fara jin wannan ƙamshin turaren, yana ratsa kafofin hancinta." """Sayyid ba ka jin wani ƙamshin turare?""" """Ina ji a jikinki""" """A'a ji nake kamar ba a ɗakinmu muke ba""" "Ya yi dariya, ya cika ta ya ce ""Ba sai kin yi mini wayo ba, na ƙyale ki"" Ya ɗan ja jikisa ya koma gefe, yana" "ajiyar zuciya. Ta ɗora hannunta a kan nasa ta ce ""Ba wayo zan yi maka ba, ai ka san ba na gudun ka.""" """Kar ki damu, ki yi bacci"" ya ɗora kanta a ƙirjinsa yana shafa bayanta." * "Shukura ji take yi, tamkar za ta haukace, sai kokawa take da sashe daban-daban na ƙwaƙwalwarta," domin samawa kanta nutsuwa. "Gari ya tsit amma ita sai kaiwa take yi tana komowa a cikin ɗaki, tamkar mai jiran saƙon wani abun." Ta zauna ta haɗa kai da gwiwa ta yi tagumi. "Ta sake tashi tsaye, ta tafi bakin taga ta tsaya tana kallon waje. Ta ƙudurce a ranta, sai ta tuntuɓi doctor" Sharif ta ji mene ne ya kashe mata ɗa? Haryanzu ta kasa samun nutsuwa da kwanciyar hankali. "Alhaji Fatuhu kuwa, ƙarfin hali kawai yake yi, ji yake tamkar an daddane rayuwarsa da jikinaa gaba ɗaya." "Babu abin da yake yi masa daɗi, ya daina jin daɗin komai, tamkar ya fasa ihu ko zai ji sanyi a ransa." "Ƙarfin hali ya yi gurin sanya Fadila farin ciki, har ya samu ta yi bacci, tun da ta yi bacci ya raba ta da" "jikinsa a hankali, ya tashi zaune ya rafka tagumi ya din ga jin tamkar ana buga masa abu mai nauyi a kansa." "Ya shiga banɗaki ya yi wanka, ya yi alwala ya zo ya tayar da salla, amma tunani da wasi-wasi ya mamaye" "shi, ya kasa nutsuwa a cikin salla. Ya din rafkanuwa. Ya din ga sallamewa yana sake tayarwa har ya gaji ya nemi guri ya zauna." Ayshacool "Tunanin yadda kayansa za su iso, a sallami mutane ya ƙara mamaye kansa, ya rasa bakin zaren matsalar" "baki ɗaya, haka ya zauna har aka yi kiran sallar asuba." **** "Tari ne ya sarƙe Nana, ta tashi ta ji kamar wadda ta ƙware tana numfashi sama-sama. Ta shafa ta ji" "Sayyid ba ya gurin, ta ji an kama hannunta an bata kofi, ta karɓa ta shanye ruwan, ta ajiye kofin saboda yadda wani irin nannauyan bacci ya yi awon gaba da ita." "Ƙaisar ta gani a tsaye yana kallonta, jikinsa duk a ƙone, bai yi mata magana ba, ya danƙi wuyanta ya zuba" mata wani abu mai kama da hayaƙi a cikin bakinta. "A take ta ji cikinta ya hautsuna, mararta ta ƙulle, ta kalle shi a razane ta ce ""Ƙaisar me ka yi mini?""." """Cikin jikinki ba shi da amfani, dole ya bar jikin ki""" """Saboda me, ina ruwanka da cikina?""" """Saboda ba zan ƙarar da rayuwata a matsayin bawa ga zuriyar ku ba, ki na wahalar da ni.""" "Kafin ta yi magana, ta ji tamkar ana fizgar naman cikin mararta, ta yinƙura ta tashi a gigice." """Subhnallah, Sayyid, Sayyid"" ta kira sunansa a wahale." "Daga banɗaki ya fito a tsorace, ya nufo ta. Ta miƙa masa hannu, ya riƙe ta." """Kai ni banɗaki"" ta faɗa tana rintse idanunta." "Ya kamata ta miƙe, jini ya fara biyo ƙafafuwanta, ya kai ta banɗaki. Su na shiga ta durƙusa a kan" "gwiwoyinta, ta saka hannu ɗaya ta rirriƙe ƙafarsa tana girgiza kanta cikin matsanancin ciwo. Da ta ja numfashi da ƙarfi, sai ta ji jinin yana zuba da yawa." "Ya rasa yadda zai yi, ga baki ya rufe ya kasa magana." "Can ta yi wani irin nishi, ta ƙara rirriƙe ƙafarsa da ƙarfi, sai ga gudan jini ya faɗo. A hankali ta din ga" "samun releif, ta jinginar da kanta a jikin ƙafarsa ta kasa motsi. Jin yadda ƙarnin jinin ya ishe ta, ya sanya ta motsa a hankali, ta yinƙura ya kama ta, ta tashi tsaye." """Ka canza kaya ka yi sallar, bari na wanke jikina""" "Ya motsa baki, amma magana ta gagara, ya dage yana ƙoƙarin yi, amma gumi ya fara tsatstsafo masa." """Ya lafa mini, ka yi salla kar ka makara, zan wanke jikina"" da ƙyar ya fita, ta rufe banɗakin ta wanke" "jikinta, duk da tana jin sauran ciwon kaɗan kaɗan." "Ta fito yana salla, ta ɗaura zani, kan ya idar ta goge gurin da ta ɓata, ya idar ya ƙaraso gefen katifar da ta" "zauna, idanunta har sun faɗa saboda wahala." "Ya zauna ya saka ta a gaba, ga magana amma abu ya gagara, ta kwanta a kan cinyarta, ga ciwon buguwar" "jiya, ga rashin lafiya da ba ta gama warkewa ba, ga kuma wannan matsalar da ta tashi da ita." "A hankali yake shafa jikinta, yana ɗan matsa mata, ta ji daɗin hakan sosai da sosai." "Wajen ƙarfe bakwai, ta kira Ummi, Ummi ta ɗaga ta ce ""Lafiya, kira da sassafe?""" """Kira ni kuɗina ba su da yawa""" "Ummi ta kira ta, ta ce ""Lafiya na ji muryarki a haka?""" """Ba na jin daɗi ne Ummi, dan Allah tambayar ki zan yi, idan mutum yana da ciki yana period ne?""" """Wane irin period kuma? Dama ciki ne da ke? Haba ni fa in ce ranar da ki ka zo na ga alama wallahi." "Meyafaru?""" """An ce akwai, kuma yau na tashi da ciwon mara ina zubar da jini""" """Kai, subhnallah bari na sallami yara, gani nan zuwa gidan naki""" "Duk da jikinta babu ƙwari, ta tashi ta saka kaya, ta kunna turaren wuta, Saboda a hancinta ba ta daina jin" ƙarnin jinin nan ba. Wajen tara da rabi sai ga Ummi. "Ummi ta gaishe shi, ya ɗaga mata hannu tare risunar da kansa, ranar farko da Ummi ta gan shi babu" "rawani, ya sha kitso a kansa jelar ta sauka a kafaɗarsa." "Ta ƙarasa inda Nana take cikin kulawa ta ce ""Sannu Nana ya jikin?""" """Alhamdilillah""" """Gaskiya ki zo mu je a yi scanic, mu tafi Asibiti""" "Nana ta girgiza kai ta ce 'A'a ba sai mun je ba, ni ba na son mu je, a yi ta huda ni""" """To Nana lafiyarki ba ta fi komai ba, tashi mu je""" "Nana ta kalle shi, yadda ya tsare su da ido, ta ce ""Sayyid za ta raka ni Asibiti, ka zauna kar su zo yau ma a" "neme ka, baka nan ya zama abin magana.""" "Ta kalli fuskarsa ta ce ""Na gane, ba sai ka yi magana ba""" "Ya tashi ya buɗe wardrobe ɗin sa, ya ɗaukko kuɗi, ya miƙa wa Nana." """Ka bari da kuɗi a gurina, wanda Imrana ya bani""" "Tsuke fuska ya yi, dole ta saka hannu ta karɓa, ya ɗauki mayafin yin rawaninsa ya yafa a kansa, ya biyo su" "har bakin gate, yana kallon Nana." Ayshacool "Ta ɗaga masa hannu tare da yin murmushi, shi ma ya ɗaga mata." "Su na fita Ummi ta dasa mita, ta ce ""Jaraba, wannan kallon da yake yi miki, sai da na ji kamar na bar" "masa ke na yi tafiyata, Nana sai ka ce auren Soyayya bawan Allah duk a rikice yake. Kuma dan Allah yana magana, anya na taɓa jin maganarsa kuwa?""" "Nana ta yi murmushi ta ce ""Yana yi mana""" """To ai ban taɓa ji ya yi ba. Kai tubarkallah Nana Allah ya baki kyakyawan miji, sai ki yi ta kaffa-kaffa" "saboda 'yan mata. Kodayake yadda yake yi ɗin nan ma wace za ta ce tana so?.""" Nana ta yi murmushi. "Ummi ta sake cewa ""Na ji daɗin ganin yadda ya nuna damuwarsa a kan ki, Ubangiji Allah ya sanya ya" "ɗore. Nana idan hankalin mace a kwance yake a gidan mijinta, komai mai sauƙi ne""" "Da haka suka ƙarasa Asibiti, su na zuwa aka tura su scanic, da suka yi suka koma, aka tabattar da cikin ya" fita. Aka ba wa Nana magunguna suka dawo gida. "Yana ganin dawowar su, ya tashi. Nana ta yi masa murmushi suka wuce ɗaki." "Nana ta cewa Ummi""Kar ki gaya masa, zan gaya masa da kaina""" "Ummi ta ce ""To shikenan"" ta wanke wa Nana kayan da ta ɓata, ta ƙara gyara mata ɗakin, ta yi mata girki." "Duk yana waje ya kasa shigowa. Sai da Ummi ta gama ta yi wa Nana sallama, ta fito za ta tafi, sannan ya taso." "Da ƙyar ya iya cewa ""Na gode"" shi ma sai da ya ji tamkar numfashinsa zai ɗauke." "Ummi ta ce ""Ba komai Allah ya ƙara lafiya""." "Ya shiga ɗakin da sauri, ya tarar da Nana a zaune a gefen katifa, ya zauna a kusa da ita, ya kamo" "hannunta, tare da tsare ta da ido. Yana jiran ta yi magana." "Ta numfasa ta ce ""Sayyid, ɓari na yi""" Yanayin fuskarsa ya sanya ta fahimci bai gane me take nufi ba. """Cikin babu, ya fita, jinin da na zubar cikin ne ya zube""" "Ji ta yi tamkar hannunsa da ya riƙe ta da shi, ya yi mata shocking, saboda wani irin zirr da ta ji." "A take fuskarsa ta yi jawur, ya ji tafukan hannayensa sun ɗauki zafi, jijiyoyin kansa sun mimmiƙe. Ya ci" "gaba da motsa bakinsa zai yi magana, amma ya kasa." """Sayyid lafiya kuwa? Ko wani laifin na yi maka?""" "Ya din ga murza tafukan hannayenta da ɗan ƙarfi, yana sauke numfashi." """Sayyid mene ne?""" "Bai yi magana ba, jin ya kasa maganar ya sanya, ya saki hannunta, ya nemi guri ya kwanta yana haki" sama-sama. "Abun duk sai ya ɗaure wa Nana kai, to mene ne ma'anar hakan? Me ya sanya shi canzawa haka lokaci" "guda? Ta waiwaya ta kalle shi, ta ga ya lumshe idanunsa. Ta ɗan matsa kusa da shi, ta taɓa jikinsa ya ji ya fara ɗaukar wannan zafin. Kafin ta yi wani yinƙuri tuni ya fara wannan jijjigar, jikinsa yana kakkafewa." "Kawai ta zuba wa sarautar Allah ido, tare da rashin sanin cikakken abin yi." Ayshercool 08081012143 Ayshacool "Ganin abun ba na ƙare ba ne, ya sanya Nana yinƙurawa da ƙyar, jikinta babu ƙwari, ga sanyi tana ji." "Ta ɗauki hularta, ta zubo ruwa a kwano, ta zo ta ajiye a gefensa, ta zauna da niyyar karanta abin da ya" "sauwwaƙa a Alƙur'ani, ta busa a ruwan ta shafa masa. Amma ta ji komai ya ɗauke daga kanta, ta kaɗa ta raya amma ta kasa tuna komai." "Ta janyo wayarta, ta fara laluben folder karatun Alkur'ani, amma wayar ta fara haske tana ɗaukewa" "tamkar ta ci screen, abin fa ba taɓa yi ba sai yau." "Ta ajiye wayar jikinta yana rawa, ta rasa abin yi, ga shi yana kwance sai tsuma yake yi. Tashi ta yi ta nufi" "wardrobe, ta buɗe watso kayanta ƙasa. Jakar gurin sarkin baka, ce ta faɗo daga cikin kayan. Nana ta" "durƙusa ta ɗauka, ta nufi gurin da yake kwance. Ta ɗora masa a ƙirjinsa. Kamar ta ɗora masa wuta, haka ya zabura, ya juya a hankali ya gyara kwanciyar sa, ya daina wannan tsumar ya hau bacci." "Ta saka hannu ta ɗauki jakar, tana ƙare mata kallo. Sam ba ta ga wani abu na musamman a tattare da" "jakar ba. Ta ajiye ta, ta kwanta a gefe tana jin yadda jikinta yake yi mata ciwo." "Bayan wani ɗan lokaci ya yi juyi a hankali, ya kalli agogon ɗakin, ya kalle ta ya yinƙura ya tashi, ya yi" "alawala ya yi sallar la'asar. Ya zauna a kan sallayar ya yi shiru, fuskarsa na bayyanar da damuwa." "Nana ta tashi daga gurin da take. Ta ja ta zauna sosai ta gyara zamanta. Ta ce ""Sayyid na kasa fahimtar" "abin da yake faruwa, ban sani ba ko na yi wani abun da na ɓata maka rai ba.""" "Ya sunkuyar da kai ya yi shiru, na wani ɗan lokaci, ba tare da ta yi tsammani ba ya yi magana." """Duk na yi ƙoƙarin ɓoye matsanancin farin cikin da na shiga, da na ji za ki haihu. Na kasa ɓoye damuwar" "da na shiga, da na ji na rasa abin da yake cikinki" "Ban san dalili ba kawai na ji ina matsanancin son, abin da ban taɓa gani ba, kuma yanzu na rasa shi, ba" "tare da na yi tsammanin hakan ba""." "Jiki a sanyaye Nana ta ce ""Sayyid idan kai ka ce haka, ni na ce me?""" "Ya ɗan girgiza kai ya ce ""Ba za ki gane ba"" ya tashi ya naɗa rawaninsa, ya fice daga ɗakin." "Nana duk ta gaji da kwanciyar, ta yinƙura ta fara mayar da kayan wardrobe ɗin da ta watso." "Ta ɗaga labulen window, dan iska ta ƙara wadatar ɗakin, kawai ta hango Siyama ta fito, sanye da" "doguwar riga da ɗan ƙaramin mayafi, ƙonuwar hannunta, ko gama warkewa ba ta yi ba." Sai dai Nana ta ga Sayyid take tunkara. "Ganin tana tunkaro shi, ya sanya ya sunkuyar da kansa, daga kallon gurin da take tahowa. Sai dai tana" "ƙarasowa inda yake ta tsaya tare da yin murmushi ta ce ""Sannu da ƙoƙari"" ya jinjina mata kai, ba tare da" ya kalli inda take ba. """Amm dan Allah magana nake son mu yi""" Ya ɗaga kai ya kalle ta cikin mamaki. "Ta ɗan sunkuyar da kanta ta yi murmushi, ta ce ""Dan Allah a abubuwan da suka ɗan faru, na rashin" "kyautawa da na yi maka, nake son ka yafe mini na san na yi kuskure, ka yi haƙuri""" "Ya ɗaga idanunsa ya kalle ta, ya mayar da kansa ya sunkuyar." """Ka yi magana mana"" ta yi maganar cikin iyayi." "Jinjina kai ya yi, yana ƙara kawar da kansa gefe." "Ta sake cewa ""To ai ba zan gane ba, idan ka haƙura, ka yi magana""" """Ya wuce""" "Ta saki murmushi ta ce ""Na gode sosai"" ta juya ta koma cikin gida tana murmushi. Tabbas Buzun nan, irin" "mutanen da idan ka ɗora kana relationship da su, za a ga ka haye, ya haɗu ta kowane ɓangare. Ta yi maganar a zuciyarta." "Nana rasa abin yi ta yi gaba ɗaya, ta ji ƙirjinta tamkar ta haɗiyi kibiya, wani abu ya tsaya a tsakanin" maƙogwaronta da ƙirjinta. "Ta zauna ta yi shiru, kawai ta ji sallamar Siyama. Nana ta ɗaga kai ta kalle ta, sai dai ta kasa magana." "Siyama ta zauna a kusa da ita ta ce ""Ƙawata kwana biyu ba ki zo ba""" "Nana ta kalle ta ta ce ""Kina lafiya?""" """Ashe kuma ba ki da lafiya? Ya jikin naki?""" "Nana ta kalli Yusra ta ce ""Ya aka yi ki ka san ba ni da lafiya? Waye ya gaya miki?""" """Sai an gaya mini, ina ganin komai ai. Ko kin manta gidanmu ne nima? Allah ya baku wani.""" "Nana ta ce ""Ina cikin damuwa, dan Allah kar ki dame ni""" "Yusra ta yi murmushi ta ce ""Na sani, amma kin san faɗa ya kaure a tsakanin Ƙaisar da dattijo? Kuma duk" "a kan ki?""" "Nana ta ce ""Waye dattijo?""" Ayshacool """Wanda ya ke kawo muku ziyara, da ke da mijinki, idan ba ki yi wasa ba, abu mara daɗi zai iya faruwa." "Kodayake kar na yi shishshigi, gurin shiga hurumin da ba nawa ba. Amma abubuwa na daf da rikicewa. Me ma ya faru kafin ki yi ɓarin cikin jikinki?""" "Nana ta ɗan yi shiru tana son ta yi tunani, amma ba ta iya tuna komai ba, tana ɗagowa ta nemi Yusra ta" rasa. "Damuwa da rashin sanin abin yi, ga takaicin abin da ta gani ya haɗu ya sanya, ta tashi ta sake watso" kayan wardrobe tana gyarawa. "A cikin kayansa, ta ci karo da wata 'yar ƙaramar jakar fata, mai kama da laya, sai dai ta fi laya girma, da" ya kan saka a wuyansa wasu lokutan. "Ta yi shiru tana kallon jakar, ta yi ƙoƙarin ta ga ta ina za ta buɗe ta, ta ga mene ne a ciki, amma ta kasa." "Ta ajiye ta, ta ci gaba da gyaran kayan, ta sake ɗaga wata riga, sai ga kuɗi turmus a ciki, na Nigeria da na" Nijar. "Har ta kai hannu za ta ɗauka, ta waiwaya ta gan shi a tsaye yana kallonta." Ta kalli kuɗin ta kalle shi. """Wannan kuɗin fa?""" """Nawa ne?""" "Ta kalle shi ta ce ""A ina ka samu?""" "Wani irin kallo ya yi mata, jin tambayar da ta yi masa." """Me ki ka ce?""" "Ba ta ji ko ɗar ba, ta sake maimaitawa." """A ina ka samu?" """A ina ma samu? A gurin Habu. Ai ya gaya miki sana'ar da yake yi ko?""" """Dama shi ya gaya maka, na je gidan kenan?""" "Ya girgiza kai yana mayar da kayansa ya ce ""A'a""" "Da ta tuno yadda ta ga ya kalli Siyama, wani narkakken baƙin ciki yake tokare mata zuciya, kamar ta" kwaɗe shi ko ta samu ta huce. * "Alhaji Zailani ne, tare da Alhaji Fatuhu, zaune a kan fararen kujeru a wata farfajiya." "Fuskar Alhaji Fatuhu, cike da ƙwarin gwiwa yake duban Alhaji Zailani ya ce ""Zailani, babu komai dan Allah" "ka karɓi shugabancin nan, na san za ka iya. Da a bawa wani da ba a san yanayin amanarsa ba, ba gara a baka ba?""" "Fuskarsa ɗauke da damuwa ya ce ""Haba Alhaji Fatuhu, yaya za a yi kana abokina, aminina a yi maka" "wannan cin kashin, kuma ka ce na karbi shugabancin nan na yi yaya da shi?""" """Wallahi za ka iya. Na fi jin tausayin ƙanan 'yan kasuwa, idan aka bawa wanda bai dace ba shugabanci, za" "a karya masu ƙaramin jari""" """Ƙananan 'yan kasuwar, da su suka yi wannan bita da ƙullin, da rubuta takardar lallai a sauke ka daga kan" "shugabancin nan, su ka ke tausayawa?""" "Alhaji Fatuhu ya yi murmushi ya ce ""Nima da ƙaramin ɗan kasuwa ne, kafin Allah ya kai ni matsayin da" "nake a yanzu. Kuma na san ba dukkannin su ne, su ka yi mini haka ba. Ni dai fatana dan Allah ka karɓi" "tayin riƙon ƙwaryar shugabancin nan da aka yi maka"" Alhaji Fatuhu ya ɓata lokaci sosai da sosai, kafin ya shawo kan Alhaji Zailani ya amince zai karɓa." * "Gaddafi tuni ya koma gurin neman khɗinsa, saboda takaicin abubuwan suke faruwa a gidansu, ya fara" damunsa. "Baba ƙiri-ƙiri haka ya zuba ido ya yi shiru, ba ya iya cewa uffan, sai dai ya zuba ido a kan lamarin gidansa." "Sai ma dai idan an dafa a zuba a ba shi ya ci. Sosai al'amuran gidan su Nana, suka fara canzawa kullum sai an ɗora abinci sau uku a rana saboda hidimar da Jamila take yi da su. Ƙarewa ta saka ana ta yi musu" gyare-gyare a cikin gidan. "Babban abin da yake damun Hajiya Sa'a da Jamila, shi ne yadda take ta ƙoƙarin janyo ta, cikin ɗaya" mummunar ɗabi'ar da suke aikatawa ta lesbian. "Sai dai Jamila ta kafe da kai da fata, taƙi amincewa da hakan." "Sai da Hajiya Sa'a ta yi mamaki, saboda a ƙulumboton da ta yi wa Jamila, babu yadda za a yi ta iya" "kaucewa duk wata buƙata da ta zo mata da ita, amma ta kasa galaba a kan Jamila." "Duk wani shashashanci da suke yi tana kallo, amma sam ba ta ji abin ya kama hankalinta ba, balle ta yi" sha'awar aikatawa. "Ta fito harabar gidan tana shirin tafiya, sai ga Mus'ab ɗa ɗaya tilo ga Hajiya Sa'a. Yana ganin Jamila ya" "tsaya. Duk da ba shiga harkarsa take yi ba, amma ta yi ƙoƙarin tare shi daga shiga cikin gidan, ya yi" mummunan gani. """Ina wuni?""" """Lafiya ƙalau Jamila. Ya ki ke?""" """Lafiya ƙalau Alhamdilillah. Amm Yaya Mus'ab ko za ka ajiye ni a hanya ne, ba na jin daɗi""" "Ya yi murmushi ya ce ""Me zai hana? Bari na kai wa Mummy saƙon nan""" "Da sauri ta ce ""A'a ai bacci take yi, ta ce kuma kar a tashe ta""" Ayshacool """Ok to mu je na ajiye ki"" ta yi gaba ya bi ta a baya." * "Nana kuwa ita ma a wannan karon, basar da Sayyid ta yi, ta ƙi kula shi sam. Shi ma ya maze ya share ta." Baccinta ya yi nisa sosai ta ganta a daji ita kaɗai ƙwal. Ta ɗaga kanta ta ga wani ƙaton tsuntsu yana shawagi a saman kanta. "Ba ta tsorata ba, ta ɗan ja numfashi ta ce ""Ƙaisar laifin me na yi maka, ka zaɓi ka hukunta ni ta wannan" "hanyar? Me ya sa za ka zama dalilin zubewar cikina?""" "Tsuntsunan nan saukko ƙasa, ya yi girgiza Ƙaisar ya bayyana. Ya zauna yana fuskantar ta ya ce ""Komai ma" "kin yi mini, babu abin da ba ki yi mini ba, abin da ya dace nake yi""" """Ba ka tsoron Allah Ƙaisar, ba ka tsoron Allah ya kama ka da hakkina, abubuwan da ka ke aikata mini na" cutarwa. "Kai ka yi mini, wannan tsohon ya yi mana, mijin nawa ma na fara daina gane kansa. Ya fara ƙoƙarin cutar" "da ni""" "Ya ɗan kalli saman bishiya sannan ya ce ""Babu abin da ban gaya miki ba ai. Amm kin tuna abin da na" "nuna miki, Alhaji Zailani yana yi wa abokinsa? Da gaske ya faru a zahiri. Kuma tsafi gaskiyar mai shi, domin kuwa al'anura sun fara juya wa Alhaji Zailani baya. Nan zuwa wani ɗan lokaci zai rasa komai nasa." "Lafiyar sa da dukiyarsa.""" "Cikin matsananciyar damuwa Nana ta ce ""Dan Allah idan ka na dama ka yi wani abu a kai mana. Ka tona" "abin da aka yi masan""" "Ya girgiza kai ya ce ""Ba ma shiga abin da babu ruwanmu, ko warware wani abu da aka yi wa wani," "muddin ba yarjejeniya aka yi damu, aka bamu damar yin hakan ba. Zan iya taimakonsa ne kawai bisa amincewar ki, da kuma umarnin ki. Zan gaya miki inda abin yake ya saka a je a tone, ko kuma ki je ki tone. Idan ba haka ba nan da kwanaki uku rak za a tono ƙwarangwal ɗin yaron nan, a kuma yin wani tsafin da" "ita.""" "Har Nana ta motsa baki za ta yi magana, sai kuma ta fasa, dan tana amincewa a taimaki Alhaji Fatuhu ba" "ta san me zai biyo bayan hakan ba, ka iya tabbatar da buƙatar Ƙaisar a kanta." "Kasancewar ba ta salla, ya sanya har gari ya waye tana bacci." "Bayan ta yi wanka ta rasa abin yi, ta ɗebo kayan wankin ta, ta shiga banɗaki ta wanke. Nasa dama Habu" ne yake zuwa ya ɗauka. "Ta gama, ta saka hijjabinta, ta ɗaukko bokitin, ta fito daga ɗakin. Yana kan kujera a daf da gate ɗin, yana" "aikin dafa shayi, gefensa ga radio tana yi." "Ba ta kula shi ba, ta zagaya baya, ta yi shanyar kayan nata. Ta fito ta ja ta yi turus tana kallon ikon Allah." "Siyama ce a tsaye, da ɗan ƙaramin flask a hannunta. Nana ba ta san me take ce masa ba, ta ga ya sauke" "rawanin fuskarsa ya saka hannu ya karɓi flask ɗin, ya yi magana." "Kawai ta shiga ɗaki, a ƙofar banɗakin, ta jefar da bokitin jin wani irin matsanancin ɗaci yana taso mata." "Ta cire hijjabinta kawai ta tsaya ta riƙe ƙugunta, ta tsaya tana jiran ya shigo, amma bai shigo ba," "zuciyarta ta din ga raya mata, yana can su na hira da Siyama." "Kawai ta buɗe ƙofa ta shiga banɗaki, sai dai ta rasa uban abin da ya kai ta banɗakin ma. Ta gama" tsayuwarta ta fito daga banɗakin. "Tana fitowa ta gan shi a tsaye, da flask ɗin a hannunsa, ya nufo ta zai yi magana, ta riga ta ɓarar da flask" ɗin. Farfesun kifi da dankalin ya tarwatse a ƙasa. "Ya kalli gurin ya kalli yadda take huci, zuciya ta yinƙuro shi, sai dai ya ga Ƙaisar a bayan Nana, ya zubo" masa ido. "Ya haɗiye wani abu, mai ɗaci. Ya kalli Nana ya ga yadda idonta ya rufe, ta fara ƙoƙarin wuce shi ta fita. Ya" riƙe ta yana ci gaba da kallon Ƙaisar. "Ya kwantar da Nana a kan katifa, idanunta a rufe sai hawaye da yake fita, ta gefen idonta." Ya durƙusa ya gyara gurin ta ɓarar da abincin. "Ya sake kallon yadda Ƙaisar ya jingina da bango, ya tsaya a kan Nana." """Tun da ka yi abin da ka yi, ya kamata ka bani guri"" Ya yi maganar yana kallon inda Ƙaisar yake." """Gurin ka na zo ne? Idan ba gurin ka na zo ba, sai ka ƙyale ni""" """Ka zubar mini da ciki, kuma saboda rashin kunya, ka zo haɗa fitina a tsakaninmu""" "Ƙaisar ya yi murmushi ya ce ""Ina mamakin yadda Aljani yake shiga al'amuran bil adama har haka. Kai ka" "fara lalata cikin, ni kuma na zubar da shi.""" "Sayyid ya shafi fuskarsa ya ce ""Waye Aljanin a tsakanin ni da kai?""" "Ƙaisar ya ce ""Ba da kai nake ba. Ka san da wanda nake""" Ayshacool "Buzu ya ɗan yi shiru sannan ya ce ""Ka gaya mini, wane ne ni? Daga ina nake? Kuma suwaye iyayena? Me" "ya kawo ni ƙasar nan?""" """Ba ni za ka yi wa wannan tambayar ba, zuwa yanzu na san ka bambance tsakanin ni da shi""" """Haka ne, na banbance, yanzu ka tafi ka bani guri, ka bar ni da matata""" """Ba zan tafi ba""" "Buzu ya durƙusa ya kwance rawanin kansa, ya cire rigar jikinsa, ya ɗago Nana da take cikin yanayin" gushewar hankali. "Ya fara cire kayan jikinta, tamkar an aiko wa Ƙaisar saƙon mutuwa ya murtuke fuska." "Bai tsinke da lamarin ba, sai da Sayyid ya rungume Nana yana sumbatar bakinta." "Jikin Nana ya din ga rawa, tana fatan ta saka baki a maganganun su, amma ta kasa, tana ganin duk abin" "da yake faruwa, amma tamkar an ɗaure ta, ta kasa motsa ko da ƙaramin yatsanta." "Da ƙyar ta fizgo numfashi ta tashi a zabure, ta ce ""Sayyid"" ya taso da sauri daga inda yake zaune ya nufo" ta. "Ya kasa magana, ita ma kuma ta kasa cewa komai, sai rarraba ido da take yi, ta yi zaton mafarki ne," "amma ta ji ɗakin yana ƙarnin kifi, ga kuma flask ɗin da ya shigo da shi." "Da ƙyar ta ce ""Ina wanda ku ke magana da shi?""" "Ya kalli ɗakin ya ce ""A ina?""" "Ta kalli daidai gurin da Ƙaisar ya tsaya, ta ce ""Wanda ya tsaya a nan, wani dogo""" """Ban yi magana da kowa ba"" ya yi maganar yana girgiza mata kai." "Ta yi ajiyar zuciya ta ja ta zauna, tana jin kanta yana ciwo." **** """Suwaiba"" Alhaji Fatuhu ya kira sunanta." "Ta kalle shi ta ce ""Ya dai?""" """Ba na jin daɗin jikina ne, kuma wani abu ne yake damuna""" """Me ke nan?""" """Ƙara ta za a kai kotu""" "Ta waro ido ta ce ""Kotu kuma? Me ka yi?""" """Kayan nan da suka yi ɓatan dabo, ranar Litinin zamu shiga kotu da 'yan kasuwa. Kujerata ma an sauke ni." "Amma bai dame ni ba, kayan mutane nake tunani""" "Ta kwaɓe baki ta kaɗa kai ta ce ""Ai Alhaji Fatuhu duk ɗan da ya hana uwassa bacci, shi ma ba zai yi ba." "Babu irin wahalar da bamu sha tare ba, amma abin Duniya na samuwa, ka auro yarinya ƙarama saboda ka ƙuntata mini, ka ci duniyarka da tsinke. Ai ga shi kai ma Allah ya kama ka"" Ya yi zuru da ido yana" kallonta. Ta gama maganganunta ta bar masa ɗakin. "Tana zuwa bedroom ɗin ta, ta rufe ƙofa, hawayen da ta maƙale ta ba su damar gangarowa." "Ta hau nanata ""Innalillahi wa innalillahi raji'un""" Ta ɗauki wayarta ta kira Yayanta. "Yana ɗagawa ya ji muryarta wani iri, ya ce ""Lafiya kuwa?""" """Yaya Baban su Raudah wai za a kai kotu, 'yan kasuwa su na zargin ya cinye musu kuɗi, dan Allah ka yi" "wani abu a kai dan Allah""" """To ikon Allah, amma ba sai ki bari sai da Safe ba, kya kira ni. Amma ku kuma kin tabattar bai ci kuɗin" "ba?""" "Suwaiba ta ce ""Yaya kai ma ka san shi da gudun Duniya, da abin mutane wallahi zan iya rantsuwa bai ci" "kuɗin kowa ba""" """Ki bari zan kira ki da Safe"" ta ajiye wayar jiki a sanyaye cikin damuwa." "Kasancewar a sashen Fadila yake, ta fahimci damuwa a tattare da shi, sai dai fafur ya ƙi gaya mata, ya" lallaɓa ta ta yi bacci. * "Da daddare Nana ta kasa karanta Alqur'ani, amma wannan karon ta samu ta saka a wayarta, ta daɗe" tana saurara tana jin nutsuwa na ratsa ta. "Kasancewar jini ya ɗauke, ya sanya ta yi sallar Isha'i, ta kwanta karatun Alqur'ani yana tashi ƙasa-ƙasa a" wayarta. "Tana kallon Sayyid, ya shirya ya kwanta a ƙasa, gurin da yake kwanciya da. Gaba ɗaya sai ta ji ta damu." "Ta daɗe idonta biyu, tana jira ta ga ko zai ta so, amma bai tashi daga gurin ba." "Ta tashi a hankali ta nufe shi, har ta ƙarasa kusa da shi, ta kwanta." "Ba ta ce masa uffan ba, ta caza masa hankali har ya biye mata." "Bayan wani ɗan lokaci ya numfasa ya ce ""Kin daina fushin?""" """Ba kai ka saka na yi fushin ba? Amma ka yi haƙuri""" """Me na yi miki?""" """Me yasa za ka yi wannan yarinyar magana, har ta baka abu ka shigo mini da shi ɗaki?""" """Ki na gurin kin san meyafaru?""" "Ta tashi daga jikinsa, ta ce ""Ni ba na son jin meyafaru kawai babu ruwanta da kai, kar ka sake kula ta." "Dan wallahi za ka iya nema ta ka rasa. Idan ka na son ta maye gurbina ba wani abu, ni zan iya tafiya ta na baku guri""." """Ki daina faɗar abin da ba za ki iya aikatawa ba""" """To ka ci gaba, zan baka mamaki kuwa"" ta yi maganar tana tashi zaune, da nufin ta bar masa gurin.""" Ayshacool "Buzu ya ɗan yi shiru sannan ya ce ""Ka gaya mini, wane ne ni? Daga ina nake? Kuma suwaye iyayena? Me" "ya kawo ni ƙasar nan?""" """Ba ni za ka yi wa wannan tambayar ba, zuwa yanzu na san ka bambance tsakanin ni da shi""" """Haka ne, na banbance, yanzu ka tafi ka bani guri, ka bar ni da matata""" """Ba zan tafi ba""" "Buzu ya durƙusa ya kwance rawanin kansa, ya cire rigar jikinsa, ya ɗago Nana da take cikin yanayin" gushewar hankali. "Ya fara cire kayan jikinta, tamkar an aiko wa Ƙaisar saƙon mutuwa ya murtuke fuska." "Bai tsinke da lamarin ba, sai da Sayyid ya rungume Nana yana sumbatar bakinta." "Jikin Nana ya din ga rawa, tana fatan ta saka baki a maganganun su, amma ta kasa, tana ganin duk abin" "da yake faruwa, amma tamkar an ɗaure ta, ta kasa motsa ko da ƙaramin yatsanta." "Da ƙyar ta fizgo numfashi ta tashi a zabure, ta ce ""Sayyid"" ya taso da sauri daga inda yake zaune ya nufo" ta. "Ya kasa magana, ita ma kuma ta kasa cewa komai, sai rarraba ido da take yi, ta yi zaton mafarki ne," "amma ta ji ɗakin yana ƙarnin kifi, ga kuma flask ɗin da ya shigo da shi." "Da ƙyar ta ce ""Ina wanda ku ke magana da shi?""" "Ya kalli ɗakin ya ce ""A ina?""" "Ta kalli daidai gurin da Ƙaisar ya tsaya, ta ce ""Wanda ya tsaya a nan, wani dogo""" """Ban yi magana da kowa ba"" ya yi maganar yana girgiza mata kai." "Ta yi ajiyar zuciya ta ja ta zauna, tana jin kanta yana ciwo." **** """Suwaiba"" Alhaji Fatuhu ya kira sunanta." "Ta kalle shi ta ce ""Ya dai?""" """Ba na jin daɗin jikina ne, kuma wani abu ne yake damuna""" """Me ke nan?""" """Ƙara ta za a kai kotu""" "Ta waro ido ta ce ""Kotu kuma? Me ka yi?""" """Kayan nan da suka yi ɓatan dabo, ranar Litinin zamu shiga kotu da 'yan kasuwa. Kujerata ma an sauke ni." "Amma bai dame ni ba, kayan mutane nake tunani""" "Ta kwaɓe baki ta kaɗa kai ta ce ""Ai Alhaji Fatuhu duk ɗan da ya hana uwassa bacci, shi ma ba zai yi ba." "Babu irin wahalar da bamu sha tare ba, amma abin Duniya na samuwa, ka auro yarinya ƙarama saboda ka ƙuntata mini, ka ci duniyarka da tsinke. Ai ga shi kai ma Allah ya kama ka"" Ya yi zuru da ido yana" kallonta. Ta gama maganganunta ta bar masa ɗakin. "Tana zuwa bedroom ɗin ta, ta rufe ƙofa, hawayen da ta maƙale ta ba su damar gangarowa." "Ta hau nanata ""Innalillahi wa innalillahi raji'un""" Ta ɗauki wayarta ta kira Yayanta. "Yana ɗagawa ya ji muryarta wani iri, ya ce ""Lafiya kuwa?""" """Yaya Baban su Raudah wai za a kai kotu, 'yan kasuwa su na zargin ya cinye musu kuɗi, dan Allah ka yi" "wani abu a kai dan Allah""" """To ikon Allah, amma ba sai ki bari sai da Safe ba, kya kira ni. Amma ku kuma kin tabattar bai ci kuɗin" "ba?""" "Suwaiba ta ce ""Yaya kai ma ka san shi da gudun Duniya, da abin mutane wallahi zan iya rantsuwa bai ci" "kuɗin kowa ba""" """Ki bari zan kira ki da Safe"" ta ajiye wayar jiki a sanyaye cikin damuwa." "Kasancewar a sashen Fadila yake, ta fahimci damuwa a tattare da shi, sai dai fafur ya ƙi gaya mata, ya" lallaɓa ta ta yi bacci. * "Da daddare Nana ta kasa karanta Alqur'ani, amma wannan karon ta samu ta saka a wayarta, ta daɗe" tana saurara tana jin nutsuwa na ratsa ta. "Kasancewar jini ya ɗauke, ya sanya ta yi sallar Isha'i, ta kwanta karatun Alqur'ani yana tashi ƙasa-ƙasa a" wayarta. "Tana kallon Sayyid, ya shirya ya kwanta a ƙasa, gurin da yake kwanciya da. Gaba ɗaya sai ta ji ta damu." "Ta daɗe idonta biyu, tana jira ta ga ko zai ta so, amma bai tashi daga gurin ba." "Ta tashi a hankali ta nufe shi, har ta ƙarasa kusa da shi, ta kwanta." "Ba ta ce masa uffan ba, ta caza masa hankali har ya biye mata." "Bayan wani ɗan lokaci ya numfasa ya ce ""Kin daina fushin?""" """Ba kai ka saka na yi fushin ba? Amma ka yi haƙuri""" """Me na yi miki?""" """Me yasa za ka yi wannan yarinyar magana, har ta baka abu ka shigo mini da shi ɗaki?""" """Ki na gurin kin san meyafaru?""" "Ta tashi daga jikinsa, ta ce ""Ni ba na son jin meyafaru kawai babu ruwanta da kai, kar ka sake kula ta." "Dan wallahi za ka iya nema ta ka rasa. Idan ka na son ta maye gurbina ba wani abu, ni zan iya tafiya ta na baku guri""." """Ki daina faɗar abin da ba za ki iya aikatawa ba""" """To ka ci gaba, zan baka mamaki kuwa"" ta yi maganar tana tashi zaune, da nufin ta bar masa gurin.""" Ayshacool "Amma ya riƙe ta gam, yana yi mata numfashi a wuya. A gurin suka kwana tare. Sai Asuba bayan ta yi" "wanka ta yi salla, ta koma kan katifa." "Tana tsaka da bacci, ta ji yana tattaɓa ta, ta buɗe idonta ta kalle shi tana yanutsa fuska, saboda bacci ne" a kan ta sosai. Wayarta ya ajiye mata a daidai kunnenta. "Waƙar Ali jita ce take tashi, ta Aminiya. Shiru ta yi tana sauraren baitukan tana kallon kyakyawar" fuskarsa da ya tsare ta da manyan idanunsa yana kallonta yana murmushi. "Ita ma murmushin ta sakar masa, ta yinƙura ta tashi zaune, ita sam ba ta san da waƙar ma a wayar ba," "kasancewar ba gwanar jin waƙa ba ce, amma har cikin zuciyarta take jin baitukan, tamkar shi ne yake" rairai mata. "Gaba ɗaya suka manta, da batun saɓanin da ya shiga tsakaninsu." (BAYAN MAKONNI BIYU) "Gaba ɗaya Fadila ta rasa abin da yake yi mata daɗi, hankalinta ya ƙi kwanciya, tun da aka fara zaman" "kotu ta ji halin da ake ciki ta rasa abun da yake yi mata daɗi, yanayin yadda shari'ar ke gudana, za ka san da gayya ake yi, kawai shi ake son ya tozarta." "Dan tashin farko Alƙali cewa ya yi a tsare shi, sai an ajiye wasu miliyoyi da kadarori, za a sake shi." "Wasu tuhume-tuhumen ma, bai san da su ba, sai ranar da aka fara zaman kotun, sannan ya san da su." "Har wasu maƙudan kuɗin, da ake zarginsa da sama da faɗi da su, a lokacin da yake shugabanci." "Haka aka sayar da wasu daga kadarorinsa, aka bayar sannan aka ba da belinsa." Kotu ta yi umarnin a yi gwanjon kadarorinsa a sallami mutane kuɗinsu. * "Alhaji Zailani, tare da Malam Gambo suka koma gurin da suka binne, jaririn nan, su ka tono ƙwarangwal" "ɗin sa, duk ya zagwanye. Suka saka a akwati, suka tafi da shi." "Ɗakin da Malam Gambo yake tsaface-tsafacensa su ka je. Ya ɗaukko ƙwarangwal ɗin jaririn, aka babbaka" "wata irin wuta, aka ɗauki ƙwarangwal ɗin jaririn nan, ya rubuce jikin da sunan Alhaji Fatuhu, ya zana wasu hatimai, ya nannaɗe su a jikin ƙwarangwal ɗin aka saka a cikin wutar nan." "Malam Gambo ya din ga zuba wani magani a cikin wutar, ya kawo wasu irin layoyi da ya zana hatimai" "daban-daban, ya din ga jefawa a cikin wutar. Alhaji Zailani kuma yana kiran sunan Alhaji Fatuhu." "Sai da ƙwarangwal ɗin nan ya yi baƙi ƙirin, zaren da aka naɗe ƙwarangwal ɗin, ya kama jikin sosai. Ya" "kuma naɗe shi da wani zaren, sannan ya naɗe da likkafani, su ka je suka samu wata tsohuwar rijiya, suka jefa a ciki." "Alhaji Zailani ya koma gida, kulle kansa a cikin ɗaki, ya din ga ɓaɓɓaka wata irin mahaukaciyar dariya," tamkar zai haukace. "Ya ce ""Alhaji Fatuhu ka gama yawo, yanzu sai na ga wanda za ka hura wa hanci, wai ka ga mai kuɗi kuma" "mai tsoron Allah, mu zuba mu gani. Wannan burin nawa ya cika, saura kuma waccan yarinyar""" "Alhaji Fatuhu kuwa, sun dawo daga kotu, Yayan Hajiya Suwaiba, lauyan da ya tsaya masa, yana ta yi" masa nasiha a kan ya karɓi ƙaddara. "Alhaji Fatuhu ya ce ""Wallahi Barrister, na karɓi ƙaddarata. Na kuma gode wa Allah. Abu ɗaya nake tunani" "iyalina na saba musu da rayuwar jin daɗi da kwanciyar hankali. Ina jin tausayinsu fiye da abin da ya same ni""" "Cikin tausaywa Barrister ya ce ""Na sani Alhaji, tabbas kai mutum ne mai kyautatawa iyali. To yanzu ne" "ranar da za su nuna maka halacci su ma, a yi haƙuri""" "Alhaji Fatuhu ya ce ""Babu komai, mun gode Allah""" "Ji ya yi tamkar ana ƙoƙarin fizgo ƙwaƙwalwarsa. Ya yi wata irin zabura, ya riƙe kansa gam. Barrister ya ce" """Alhaji lafiya dai?""" "Ya girgiza kai ya ce ""Zafi nake ji"" kafin ya kuma wata maganar, ya yanke jiki ya faɗi a gurin." "Nana tamkar tana kallon talabijin, haka ta ga komai a cikin mudin da Ƙaisar yake nuna mata." "Yana gefe yana rubutunsa, ita kuma ta zuba uban tagumi tana kallon mudubin." """Shigen irin wannan sihirin aka yi wa mijinki, shi ne wannan wutar da yake cewa tana ci a jikinsa. Sai dai" "shi nasa ya sha bamban da wannan ta wasu fannukan""" "Nana ta zabura ta kalle shi ta miƙe tsaye ta ce ""Ƙaisar ka yi mini bayani, waye ya yi masa asirin? Kuma" "daga ina yake? Suwaye iyayensa?""" "Ya ɗago ya kalle ta ya ce ""Kin manta sharaɗin ne?""" "Ta yinƙura za ta yi magana, ta yi ido huɗu da Sayyid, yana kusa da ita, ya zuba mata ido." Ta yi ajiyar zuciya. Ayshacool """Me yasa za ki saka shi buɗe gate, ina tunanin aikinmu da ku ya ƙare, tun da yau za mu bar gidan nan," "kuma ba cikakkiyar lafiya ce da shi ba.""" """Na kasa da ke ne? Tun da ba ku bar gidan ba, dole ya yi aiki, ko da aka ba ki kuɗi kin rage wani abu," "saboda ba ku yi mana aiki ba?""" """Ban rage ba kuma ba zan rage ba. A yau za mu bar gidan nan, idan ki ka ƙetare layi za ki sha mamaki.""" """Me za ki yi?""" "Ya nufo Nana, da jikinta ya fara tsuma ya ce ""Ki yi haƙuri mu rabu lafiya""" """Ka rabu da ni Sayyid"" Murmushi ya yi,ya saka hannu ya riƙe Nana, da ranta gaba ɗaya ya ɓaci, har take" tsuma. Ummi ta fito tana tambayar ko lafiya. "Siyama ta ce ""Ni kuma zan ga ƙaryar hauka da rashin hankali, ku zauna a ƙarƙshinmu, ku ci arzikinmu," "kuma ki tsaya za ki yi mini rashin kunya?""" "Ummi ta ce ""Dan Allah ki yi haƙuri baiwar Allah, kin san zuciya. Ki yi haƙuri dan Allah ba ta kyauta ba""" "Nana tuni ta fita daga hayyacinta a hannun Sayyid, jikinta ya saki idanunta a lumshe sai hawaye da yake fita ta gefen idonta." "Ummi ta tafi lallaɓa Siyama, Sayyid ya kai Nana ɗaki ya kwantar da ita. Jikinta ne ya fara karkarwa" tamkar ana girgizata. "Ummi ta dawo ɗakin, ta ga yadda ya rungume Nana a jikinsa, cikin damuwa take kallon Nana, tana" "mamakin dama haryanzu ba ta daina iskoki ba, ta ga wasu idan an yi musu aure abin yana lafawa, da ta ji Nana shiru bayan auren, ta ɗauka ta daina." "Cikin damuwa ta ce masa ""Dama tana yin haka haryanzu?""" "Ya ce ""Ba kullum ba, sai ta yi fushi""" "Sosai Nana take kuka tana karkarwa dama Ummi matsoraciya ce, ko kafin ta yi aure, idan Nana tana yi" tsoro take ji. "Ya kai bakinsa kunnenta murya ƙasa-ƙasa ya ce ""Ki yi addu'a Husnah, ko ba za ta fito a bakinki ba, ki yi a" "zuciyar ki, ki daina kuka, ki yi haƙuri. Yi addu'a sosai ki daina kuka"" A sama kamar cikin mafarki take jiyo" "muryarsa kawai, amma ba ta ganinsa, sai ita kaɗai a cikin sahara. Ta dage iya ƙarfinta tana Addu'a cikin ɗaga murya, amma a zahiri ba ta iya furtawa a kan harshenta, sai dai a cikin zuciyarta kawai." "Tana zaune a cikin saharar, sai ga Yusra ta nufo ta. Nana ta yi shiru tana kallon ta." """Ƙawata""" "Nana ta ce ""Yusra ko Haula?""" """Haular dai. Ashe tashi za ku yi kuma?""" """Eh, ina Yusra, ina fatan ba kya cutar da ita?""" "Ta yi murmushi ta ce ""Bayan kin gaya mata abubuwan da za ta hana ni sukuni, zama take yi da alwala, ta" "daina tsorata ko na tsorata ta, hankalina ma dai ba a kanta yake ba sosai, ina can fafutukar neman" "soyayyar Ƙaisar""" "Nana ta yi shiru tana mamakin, yaya aka yi ita, ko ta yi alwalar ta yi addu'a, Ƙaisar ba ya fasa cutar da ita." """Da kin sani kin bar ni da matar nan, na ci gaba da wahalar da ita, yadda babarta za ta ƙara ɗanɗanar" "takaici, ba ta da mutunci shi yasa ma aka sakar mata 'yar ta""" "Nana ta ce ""Ai ke ki ka saka a ka sakar mata 'yar, kuma Yusra ba bu wani abu da ta yi miki na laifi. Kuma" "ita kanta Hajiyar, tana da gaskiya mijina ba shi da lafiya ba ta yi ba dai-dai ba""." """Ai shikenan, yanzu haka za ki tafi na daina jin ƙamshin girkinki mai daɗi""" """Haula, dan Allah ko ke kin san waye Sayyid, daga ina kuma yake?""" "Haula ta waro ido ta ce ""Taɓ, so ki ke dattijo ya kashe ni? Ko kuma ya azabtar da rayuwata. Yo bai bar" "ɗansa ba balle ni. Babu ruwana""" "Nana ta marairaice ta ce ""Dan Allah ki gaya mini, babu abin da zai yi miki """ """A'a ba ruwana. Ai Ƙaisar ya gaya miki, shigen Asirin da aka yi wa Alhaji Fatuhu, aka yi wa mijinki, amma" "ke ni babu ruwana a wannan lamarin naku""" "Nana ta ɗan yi shiru sannan ta ce ""Da gaske, abin da Ƙaisar ya nuna mini a mafarki ya faru? Alhaji Zailani" "ya yi wa Alhaji Fatuhu Asiri da ɗan Shukura?""" """Sosai da gaske ne, ba ƙarya ya yi miki ba. Da zai ci gaba da buɗe miki ido, ki cigaba da ganin ɓarnar da" "bil'adama ku ke yi wa junanku, sai kin haukace." "Alhaji Zailani yana gadon Asibitin, da aka ɗauke wa kishiyar Yusra ɗa""" """Wace Yusran?""" """Ƙawar ki mana, ita ce matar Sagir ta farko. Kin ga tafiyata kar na yi laifi, garin ɓare-ɓare na faɗi abin da" "za a hukunta ni"" Nana ta zabura ta damƙi hannun Yusra da sauri, domin sake tambayar ta. Amma ta ji jikinta ya yi sanyi ƙalau, ta buɗe idonta, ta kalli Sayyid, da ta riƙe masa hannu gam." Ayshacool "Ta yinƙura ta tashi zaune, yanayin yadda ta ji jikinta, ta gane abin da ya faru." "Ummi ta ce ""Nana kin tashi? Ki wanke fuskar ki, masu ƙurƙurar sun kusa ƙarasowa.Ta tashi ta wanko" fuskarta. "Tana fitowa kuwa, masu motar suka ƙaraso." "Aka kwashe kayan su Nana tsaf, sosai Nana take jin kewar barin ɗakin nasu. Ummi ta raka ta, suka shiga" "gurin Hajiy Halima, suka yi mata sallama." "Tar Nana take jin hirar da suka yi da Haula a bacci, tana dawo mata kanta, ba tare da ta manta komai" daga hirar ta su ba. "Sai dai ta ƙi yarda zuciyarta ta gazagata komai a cikin maganganun Haula, ta dage wa zuciyarta da cewa" "shirmen mafarki ne, saboda tana yawan tunanin Yusra da take yi." "Duk da tana jin kamar wani abu makamancin haka ya faru, wani abu mai kama da Alhaji Zailani ya yi wa" "Alhaji Fatuhu asiri, da kuma maganar jariri, amma ta kasa tuna komai." "Ummi ta fita waje, domin tabattar da an shirya komai, a kan motar." "Nana ta tarar da Sayyid a cikin ɗakin, yana ƙare wa ɗakin kallo." """Shugabana"" ya waiwayo a hankali yana kallon ta." """An tafi samo abin hawa, za mu tafi, na ga ka zo ka tsaya a nan""" """Nana""" """Na'am Sayyid""" """Ina kewar rayuwar da muka yi a ɗakin nan tare da ni da ke, ban san ya zan misalta miki ba. Ga ki dai a" "tare da ni, amma ina kewar ɗakin sosai. Sai na ji kamar ba zamu sake Rayuwa mai daɗin da muka yi a cikin sa ba""" "Ta girgiza kai ta ce ""In sha Allah, sai mun yi wadda ta fita komai da komai, da yardar Ubangijin talikai." "Taho mu tafi"" Da ƙyar ta riƙo hannunsa, suka fito idanunsa jawur." "A adaidaita sahu suka tafi, da shi da ita da Ummi, sai dai ya ƙura wa gidan ido, tamkar ya ce a tsaya ya" "koma. Nana ta riƙo hannunsa cikin nata ta ce ""Mu kyautatawa Allah zato, ina da yaƙinin rayuwar da" "zamu ci gaba, ta fi wadda ka ke kewa daɗi""" """Ina fatan haka Rayuwata""" "Ummi ji ta yi tamkar ta yi tsuntsuwa, ta fita, ba ta san lokacin da Nana ta fitsare haka ba. Ta yi ta biye" "masa su na abu a gaban mutane, idan shi ba bahaushe ba ne, ai ita bahaushiya ce." "Sun ɗan yi doguwar tafiya, daga Tudun yola, zuwa Kurna." "Babban abin da ya soki zuciyar Sayyid, bai wuce ganin gidan akwai maza ba, duk da masu aure ne, amma" "har cikin zuciyarsa hakan bai yi masa tsari ba. Amma babu yadda ya iya, tun da ba shi da wata mafitar." "Ɗakin nasu bai kai wanda suka baro girma ba. Cif ya ɗauke kayan su, sai dai babu sauran space ɗin kirki a" "ɗakin. Ga zafi saboda wata 'yar ƙaramar taga ce a ɗakin, kamar ɗakin tattabara." "Abin takaicin bai wuce yadda yaran layin suka cika gidan ba, saboda ganin ana sauke kaya ana shiga da" su cikin gidan. "Sai da Ummi ta din ga korar yara, suka saka Sayyid a gaba da kallo, saboda ya yi shigar buzaye da rawani." "Abin takaici har matan layin, wasu suka din ga leƙowa, masu son ganin ƙwal uwar daka kuwa, gidan suka din ga shigowa, da sunan sun zo gurin sauran matan da suke gidan, amma a zahiri, zuwa suka yi su ga suwaye kuma suka tare a gidan." "Ummi tana tare da su Nana, har aka gama shirya ɗakin tsaf, duk da Nana su na da sauran kayan Abinci," "amma ta yi waya aka kawo mata kayan abinci daga gidanta, ta girka wa Nana. Kasancewar Nana ba ita ta dafa ba, sai ta samu ta ci sosai." "Sai da Ummi ta aiko musu da maganin sauro, saboda akwai sauro sosai da sosai a gidan, ga zafi, shi kuma" ga yanayin ciwonsa ba ya son zafi yana buƙatar wadatacciyar iska. Haka Nana ta yi ta aikin fifita. "Da safe Ummi ta sake aiko musu da Abin karyawa. Sai dai daga shi har ita, ba wani ci suka yi ba. Nana ta" "shirya ta ce ""Sayyid, bari na je na yi musu sallama, mu gaisa da mutanen gidan""" """To""" """Yauwwa, kai ma zaka gaisa da mazajen su dan Allah, haka ake yi idan an je gurin, da ba a san mutum" "ba"" kallon ta ya yi, ya maze kamar bai ji me ta ce ba, amma ta san ya ji ta sarai." "Ta fita tsakar gidan, ta yi sa'a matan na tsagar gida, su na aikace-aikace. Nana ta ce ""Sannu ina kwanan" "ku""" Suka amsa mata cikin sakin fuska. "Nana ta ce ""Sunana Nana, ni ce muka tare a wannan ɗakin""" """Allah sarki, sannu, ni sunana Barira, ga kuma Sajida, mai wancan ɗakin""" Ayshacool "Nana ta ce ""Allah sarki, to ma sha Allah, Allah ya iya mana"" sun so jan Nana da hira, amma ta tashi tsam" "ta koma ɗaki, gurin mijinta." **** """Alhajin Allah, aka ce ka tafi umara?""" "Alhaji Zailani ya ce ""Ɗagawa na yi Alhaji Magaji, Madam ta tafi, saboda tafiyar ta yi karo da wani taro da" "za mu yi na shekara, shi yasa na ɗaga. Ashe kai ma na garin Abujan?""" """Wallahi kuwa, na ma kwana biyu, ina neman wata kwangila ne. Ya jikin amininka kuwa, Fatuhu?""" "Alhaji Zailani ya yi wani irin makirin murmushi ya ce ""Yana can ya kwanta dama""" """Subhanallah, rasuwa ya yi?""" """A'a na fa, yana nan a raye, amma rai ne kawai a jikinsa""" """Innalillahi wa Innalillahi raji'un, wallahi na yi mamakin yadda rayuwa ta yi wa mutumin nan tsutsun jaki" "lokaci guda, ga asarar dukiya, komai nasa an ƙwace an biya masa bashi. Kai Allah dai ya kyauta. Da tuni" "yanzu ya ja tawagar tafiyar umarar maulidin nan, da shi da 'yan uwa da abokan arziki""" "Alhaji Zailani ya ce ""Sosai kam, faɗuwar wani ai tashin wani, yanzu waɗanda ya tare wa ƙofar arziki tun" "da ya gusa su ma za su ɗago"" suka tafa su na wata irin ƙyaƙyacewa da dariya." * "Jamila bakinta ya ƙi rufuwa, kasancewar a wannan karon a jirgi za su tafi babban birnin tarayya tare da" Hajiya Sa'a. "Hajiya Sa'a ta ce ""Ai sai ranar da za mu je Dubai, ko Qatar ma, wannan ai ba wani abu bane ba sam. Sai" "kin gaji da hawa jirgi, muddin za ki ci gaba da bayar da haɗin kai""" "Jamila ta ce ""Kai, wa ya ganni a Qatar""" """Amm Jamila ina Nana kuwa?""" """Tana gidanta, kwanaki ma na ji an ce ta yi ɓari""" "Hajiya Sa'a ta jinjina kai kawai. Daga airport aka zo da mota, aka ɗauke su aka tafi da su. Wani irin" "katafaren gida ne, da ko a irin finafinan Hausa da Jamila take gani, ba a taɓa hasko mai girma da kyansa ba." """Hajiya amma nan Hotel ne ko?""" """A'a gida ne, a nan za mu yi taron shekara""" """Ikon Allah, ai ganin gidan na yi ƙato guri-guri. To gidan waye?""" """Gidan wani ne"" Hajiya Sa'a ta bata amsa tana dariyar, ganin yadda gidan ya ƙayatar da Jamila." **** "Kwanakin su Nana uku a gidan da suka koma, amma ita kanta, ba ta jin daɗin zaman gidan, duk da a" "gehtto area ta tashi ita ma, amma zaman gidan nan sam babu daɗi. Inda suka baro, sai ka wuni ba ka ji ƙwaƙwƙwaran sauti ba, sai na giftawar motoci. Amma gidan nan, musamman idan yamma ta yi, mata ne suke cika shi dam. A yi ta hayaniya, ana gulmace-gulmace, ga zantuttukan batsa da suke bajekolinsu a cikin gidan. A kafa dashi, a ci bashi, a yi gulmar wannan a yi ta mijin waccan. Hatta shimfiɗar aurensu ba" "su bar ta ba, bajekolin ta suke yi a wannan gidan." "Yanzu ma yana kwance ya lumshe idanunsa, su na ta hayaniya su na musu, a kan kuɗin cefane." """Shugaba"" ya ɗago idonsa ya kalle ta." """Sannu ya jikin?"" Ya sake lumshe idanunsa ya ce ""Na warke""" "Ta yi murmushi ta ce ""Sayyid, na san ba ka jin daɗin zaman gidan nan, amma ka yi haƙuri in sha Allah," "idan muka samu hali sai mu bar gidan nan""" "Ya girgiza kai ya ce ""Ba na buƙatar sauran jin daɗi, in dai ki na kusa da ni"" ya yi maganar yana shafa" fuskarta. """Sayyid""" """Husnah"" sai kuma ta yi shiru. ""Faɗi mana""" """Ba komai fa""" """Shikenan zan shigo mafarkin ki, na ji""" "Ta ɗan yi dariya ta ce ""Allah ne ya san dalilin da ya sanya ya haɗa mu, gaba ɗaya rayuwarmu wata iri," "daban da ta sauran mutane, mu dai gamu nan""" "Ya yi murmushi ya ce ""Shi yasa ba zan daina yi wa Allah godiya ba, da ya haɗa ni da ke. Rayuwa da ke" "wata afuwa ce a gare ni Rayuwata"" ta ɗora hannunta a kan nasa tana murmushi. A hankali murmushin fuskarsa ya gushe, ya ce ""Ba ni wayar nan, mu sake dubawa, ko wayar Habu za ta shiga""" "Nana ta ɗaukko wayar daga gefen ta, ta miƙa masa, ya karɓa ya danna lambar Habu, amma ta ƙara" "maimaita masa, wayar a kashe take. Ya sauke hannunsa cike da damuwa da fargaba." """Sayyid ka daina damuwa, in sha Allah su na cikin ƙoshin lafiya""" """Asmy, rayuwa ba za ta tafi a haka ba. Akwai ɗawainiya da yawa. Ki yi haƙuri na san juriya da rashin son" "damuwata ya sanya, ki ke danne wa. Da nuna mini ba komai, amma na san ɗawainiyar nan ta yi miki yawa. Wallahi zuciyata na yi mini zafi, idan na ga ki na wahala""" """Ni ba wahala nake yi ba"" ta yi maganar tana tsuke baki." Ayshacool """Shikenan, na daina maganar""" "Jin wayar na vibrating, ya sanya suka kai hankalinsu kan wayar a tare. Amma sunan Adda Saude ne yake" "yawo, a kan screen ɗin wayar." "Nana ta ɗaga tare da yin sallama. Adda Saude ta amsa Nana ta ce ""Adda ina wuni?""" """Lafiya ƙalau Nana, ya ki ke ya mijin naki?""" """Lafiya ƙalau, ina Adda Fati?""" """Tana gidanta, ga Maijidda take son yin magana da ke"" wata irin zabura Nana ta yi cikin murna ta ƙara" nutsuwa. """Assalamu alaikum""" """Mama""" """Na'am Nana ya ki ke?""" """Lafiya ƙalau, ya gida ya su Walida?""" """Su na nan lafiya ƙalau Alhamdillah, ya mai gidan na ki?""" """Lafiya kalau Mama""" "Sayyid ya ƙura wa Nana ido, yana ayyana abin da take ji a zuciyarta. Saboda fara'ar da ta mamaye" fuskarta. """Ki na ji Nana, ina nan ina ƙoƙari, duk yadda zan yi zan zo Kano, na ganku in sha Allah, ki ƙara haƙuri, na" "san kin yi ki ƙara, ina nan tafe in sha Allah""" """Kar ki damu Mama, ni jin muryar nan ta ki ma da na yi, na ji daɗi sosai. Kuma in sha Allah kafin ki zo, za" "mu riga ki zuwa da yardar Allah""" """A'a ni ɗin dai zan zo na gan ku in sha Allah, ina fatan dai babu wata matsala?""" """Babu matsalar komai Mama""" """Yauwwa Nana, zan ci gaba da jaddada miki, ki riƙe Allah ki riƙe addu'a. Ki bi mijinki ku zauna lafiya. Ina" "fatan kin fafa sana'a Nana?""" """A'a Mama, amma zan fara in sha Allah""" """A'a Nana, kullum ki ce mini za ki fara, amma ba ki fara ba. Ina da buhun barkono, zan sayar na turo miki" "kuɗin, ki fara sayar da wani abin. Idan kuma barkonon ki ke so, na aiko miki Nana. Ni dai ban taɓa ganin mijin nan naki ba, amma yadda su Fati suka bani labari, da yadda nake jin muryarki, a duk lokacin da na kira waya, ina samun nutsuwa. Allah ya ƙara muku zaman lafiya. Amma ki yi sana'a, tun da mai ƙaramin ƙarfi ne, ki taimaka masa, kar ki sakar masa nauyi gaba ɗaya""" """To in sha Allah Mama, amma dan Allah ki bar barkonon ki, zan yi sana'ar nan da yardar Allah, na rasa" "abin da zan fara sayarwa ne. Amma zan fara""" """A'a zan sako miki buhu ɗaya a mota, ki gwada, kar ki zauna haka ba kya juya taro da sisi""" """To Mama in sha Allah, na gode sosai da sosai """ """Yauwwa, haryanzu ba ki da lambar Imrana ki turo mini""" "Nana ta ce ""Ba ni da ita Mama""" """To shikenan, ki gaida mijin naki"" suka yi sallama, ta sauke wayar a hankali, ta yi shiru tana zancen zuci." "Ta san da Mamanta su na tare da Baba, da ko ba za ta ɗauke mata ɗawainiyar da take ciki ba, za ta tausaya mata ta taya ta jajanta lamarin. Amma tun da ta je gida ta sanar da Baba halin da take ciki, ko ta waya bai kira ya tambayi ya suka ƙare ba, ya kuma mai jikin ba. Dama Mama ba a magana, mutanen da" "tun da ta yi aure, ba su taɓa taka gidan da take ba, yaushe za ta sanya ran su damu da halin da take ciki." "Tana iya ƙoƙarinta, gurin rintse idanunta, daga aibun iyayenta, saboda kar zuciya ta ɗebe ta, ta afka cikin" "fushin Ubangiji, amma daga yadda Baba ya yi mata gurin aurenta, zuwa yanzu zuciyarta na ƙoƙarin" bijirewa. """Ya ne?"" Ta ji muryarsa. Firgigit, ta kalle shi ta ce ""Babu komai. Mama na gaishe ka""" """Ina amsawa, ina son na yi magan da ita, amma ina tsoron na karɓi wayar, maganar ta ɗauke""" "Nana ta ce ""Haka ne, bari na fita da gas ɗina waje, na dafa mana taliya, ga kayan miya na aika yaran" "Ummi, sun sayo mini, ai za ka ci ko?""" """Ke ma za ki ci ko?""" "Ta yi dariya ta ce ""In sha Allah"" Ta ɗauki kayan girkinta, ta fita kusa da ɗakinta, ta ɗora." "Gaisawa kawai suka yi da matan gidan, ta nutsu a kan aikinta. Tana zaune mata na ta shiga suna fita," "kowacce da abun da yake kawo ta. Da tana da isasshen guri, a ɗakinta, da babu abin da zai fito da ita waje yin girki, balle ta din ga kallon tumasancin da matan suke yi. Har da wadda daga ita sai hijjabi, da zani, babu riga babu brezia. Idan masu gidan suka dawo, haka suke tsallake mata su shiga ɗakunan su." "Tun da Nana ta kammala girki, ta tattara komai nata ta shige ɗaki." "Ta ji daɗin ganin yadda yau yake iya cin abinci, dan haka ita ma ta zage, duk da ba wani daɗi yake yi mata" ba. "Saboda rashin kamun kai na matan layin nan, sukan kai har goma da rabi, su na shiga su na fita a gidan" tamkar bariki. Ayshacool "Nana har ta fara murnar abincin da ta ci ya zauna, lokaci ɗaya ya taso sai da ta amayar da shi baki ɗaya." "Tana fitowa daga banɗakin, ya ƙura mata ido, har ta ƙaraso ta kwanta a jikinsa, tana ɓata fuska." Ya ƙanƙame ta yana faɗin sannu. """ Ɗan ka ya hana ni cin abinci, kuma yunwa nake ji"" ta yi maganar hawaye na cika mata ido." """Yi haƙuri, sannu, to mu je Asibiti""ya yi maganar a jere." """A'a Sayyid, dole mu din ga tattala kuɗi yanzu. Yunwa nake ji sosai"" ta yi maganar cikin shagwaɓa." """Me zan sayo miki?""" """Ba komai"" ji ta yi numfashinsa yana fita da sauri da sauri, a tsorace ta kalle shi ta ce ""Sayyid jikin ne?""" """A'a"" ya furta a hankali." """Dan Allah ka yi haƙuri, da wasa nake yi maka, ai na san mata masu ciki, su na fuskantar irin haka, dan" "Allah ka kwantar da hankalinka. Ba na so mu zauna shiru, shi yasa na tsokane ka""" """Tom"" ya amsa a hankali." "Kasancewar jikinta babu ƙwari, ya sanya ta kwanta da wuri, ganin shi ma ya samu bacci." "A cikin bacci ta din ga jin wani irin rugugi, tamkar na hadari, ga shi ba lokacin damina ba ne. Ta buɗe" "idonta, ta ji wani irin huci, na fitowa daga gurin da yake kwance, ga wani irin nishi da kakari da yake yi, tamkar an yanka rago." Ayshercool 08081012143 Ayshacool "Ta ja ta zauna ta yi shiru, abin duniya ya ishe ta, sai kuma ta koma tunani kamar yanzu ta yi rauni a ibada," "shaiɗan ya yi galaba a kanta, kan cewar idan ta yi addu'a wahala ta fi tsananta a gare ta. Domin hatta" "addu'a kwanciya bacci, ranar da ba ta yi ba, sai ta kwanta ta tashi lafiya ƙalau, ba mafarkai babu ciwon ƙafa ko baya, ko ma jikin baki ɗaya. Azkar ma ba ko yaushe take iya yi safe da yamma ba." "Ta yinƙura ta tashi, ta je ta ɗauro alwala, ta zo ta sake haska shi, ta ga bacci yake yi, ta nemi guri ta" "kwanta, ta ɗora hannunta a goshinsa, tana karanto addu'oin kwanciya bacci." * "Jamila na miƙe a kan katafaren gadon, ga chips a gaban ta, ga kakkauran shayi, hannunta riƙe da" zuƙeƙiyar wayarta. "Abba ne ɗan gidan Hajiya Sa'a, yake yi mata magana ta what's app. ""Ƙanwata, shi ne tun da ku ka sauka," "ba ki neme ni ba ko?""" """Ba haka ba ne, ba ni da data ne""" """Kuma ba ki gaya mini ba, bari na saka miki. Ina Mummy?""" """Ta fita""" """Wai ina ku ka je ne a Abujan?""" "Jamila ta yi masa reply da ""Ban san sunan gurin ba, wani gida ne dai mai kyau sosai""" """Ok, to dan Allah ki kula da kan ki sosai da sosai, Allah ya bayar da nasarar abin da aka je nema, na ji ta" "ce taron kasuwanci ne ko?""" """Wallahi dai ban sani ba tukuna""" """Haka ta ce mini ni, ta tafi da ke ku ka bar ni a gida, ai shikenan"" har za ta rufe data ta ga 10gb na data." "Sai ta washe baki ta ce ""Har 10gb na gode sosai da sosai""" "Abba ya ce ""Babu godiya tsakanin, Yaya da ƙanwarsa, ki kwanta da wuri ki yi bacci. Ki yi addu'a kuma, sai" "da safe""" """To yayana na gode sosai da sosai"" suka yi sallama, ta rufe laste seen ɗin ta da online, ta tafi kallon" videos a tiktok. "Hajiya Amina ce ta shigo ɗakin, ta ce ""Jamila ba ki yi bacci ba?""" """Eh Mummy, kin dawo?""" """Eh zan sake zuwa wani gurin ne, babu lallai na dawo da wuri, za mu yi meeting, ki yi kwanciyar ki""" """To shikenan, sai kin dawo""" """Yauwwa amma ba kya buƙatar wani abu, ko jin yunwa ko?""" "Ta ce ""A'a a ƙoshe nake""" """To sai na dawo"" Hajiya Sa'a ta fice, ta rufe wa Jamila ƙofar." **** "Nasiru tun ranar da ya je gidan Ummi, su Nana suka tashi, ya koma gida ya ba wa Baba labari. Baba ya ce" """To shikenan ma, ta kwana gidan sauƙi, tun da sun samu mafita." "Ni na san babu yadda za'a yi ma a kore su haka kurum, dan mijinta ba shi da lafiya akwai dai abin da suka" aikata. """Dama wasu Buzaye abin yarda ne, kalli kayan da suka kawo mata fa, Allah ka dai ya san mugun abin da" "suke aikatawa, har aka kama su. Kai Nasiru to ya gidan da suka koma yake?"" Cewar Mama cike da son jin" ƙwaƙwaf. "Nasiru na tauna rake ya ce ""Normal dai gida ne, amma da wasu a gidan, wancan gidan da suka baro ya fi." "Ɗakinsu ya fi kyau da girma, banɗakin har da famfo ga wuta, wannan kuwa gaskiya bai yi kyau ba""" "Ta sake cewa ""Kuma da gaske mijin nata ba shi da lafiya?""" "Ya ɗaga kai ya ce ""Kai, sosai yana daurewa ne kawai, idan ya yi magana haki yake yi fa, wannan karon na" "ga ya yi magana sosai. Da an yi abu sai ya ce mata Rayuwata, ki yi a hankali ki zauna ki huta""" "Sai ta sake zabura ta ce ""Au rayuwata yake ce mata""" """Kai Mama dan Allah ki rabu da ni, haba wannan tambayoyin kamar a kabari""" """Kai a gidan uban wa ka san kabarin, sai ka yi saɓo tukuna"" ya yi mata shiru, ya tashi ya ɗauki rakensa da" "yake sayarwa a ƙofar gida, da wuƙa ya fice." * "Tun da garin Allah ya waye, Nana take tashin sa, amma ya ƙi tashi, irin wannan baccin da ta farka ta ga" yana yi dai shi yake yi. "Gaba ɗaya ta tsorata, ga dai numfashi yana yi, idan ta taɓa zuciyarsa tana bugawa da ƙarfi jefi-jefi." "Ta saka shi a gaba, ta ma rasa abin da ya kamata ta yi. Ummi takira ta a waya, ta tambaye ta babu" "matsala babu wani abu da take buƙata, ta ce mata eh." "Har sha biyu na rana Nana ta rasa abin yi, ta kunna karatun Alƙur'ani a wayarta, ta ajiye masa sai dai bai" fi mintuna talatin ba wayar ta ɗauke. Ji ta yi ana bubbuga ƙofar ɗakin nasu. Ta yinƙura ta tashi ta saka "hijjabi, ta je ta buɗe." "Sajida ta gani a tsaye, ta ɗan saki fuskarta su ka gaisa. Sajida ta ce ""Mun ji shiru ne, ko ƙofa ba ku buɗe" "ba, shi ne na ce bari na ƙwanƙwasa ko lafiya?""" Ayshacool "Nana ta ce ""Lafiya ƙalau Alhamdillah, ba ma jin daɗi ne daga ni har shi, shi yasa ba mu fito ba, amma" "lafiya ƙalau muke""" """Ok Allah sarki, ko dai amarya ce ne, haryanzu ba a gama cin amarci ba?"" Ta yi maganar tana kallon" Nana. "Nana kawai ta yi murmushi, ta koma ɗakin, ta buɗe ƙofar ta saki labule. Dama ta gyara komai a ɗakin. Ta" "dafa shayi da habbatussauda, da citt, kanumfari, kimba, na'ana'a kamar yadda yake dafawa, ta zuba a flask ta rasa me za ta dafa, dan ba ta son cin komai." "Tana nan zaune, sai ga 'yar gidan Ummi ta zo, Islam. Ta kawo wa Nana faten doya da wake, ya sha" "alayyahu. Ƙamshin attaruhun da ya daki hancin Nana, sai da ta haɗiye yawu. Ta ba wa yarinyar wayarta," ta miƙa mata caji. "Ta ɗan zuba abincin tana ci, ta zuba masa ido, tana tunanin ko Asibiti za ta nemo mota su tafi, amma" kuma sai ta tuna abin da ya yi jiya ba shi da alaƙa da ciwon Asibiti. "Tana ta tunanin mene ne mafita, kuma ba ta son waɗannan maganannun matan, suk san halin da suke" ciki ita da mijinta. "Tana nan zaune tana bin sa da kallo, ta jiyo hirar Sajida da Barira, da wasu maƙwabta. Barira ta ce ""Sajida," "jiya da daddare, kin ji kamar ana nishi cikin dare?""" "Sajida ta ce ""Wani irin nishi kuma? Ni ban ji ba""" """Wallahi nishi, kamar ana kokowa kamar wani gurnani, ga Amiru ya yi bacci, na din ga jin tsoro na kasa" "bacci, na ce ko gamo na yi da aljanu""" """Ba wasu aljanu, ba wani aljani da yake razana mutum, da wani sauti ko wani abu, duk ƙaryar banza ce""" """Kai ni dai na tsorata, kuma daga nan haka na din ga jiyo sautin, wajen nan"" ta yi maganar tana nuna" ɗakin Nana. "Sajida ta yi magana ƙasa-ƙasa, Nana ba ta ji me su ka ce, sai ji ta yi sun tuntsure da dariya. Ta yi ajiyar" "zuciya, ta fara tunanin ko dai wani gidan za su kama, ta san idan suka ci gaba da zama a gidan nan, asirin su na iya tonuwa, wanda ba za ta so hakan ba." "Babu tsammani ta ga ya tashi zaune, ta tashi da sauri ta nufe shi cikin kulawa ta ce ""Sannu Sayyid, ka" "tashi?"" Shiru ya yi yana bin ta da kallo, tamkar ya ga wata baƙuwar halitta daban." """Sannu ya jikin naka?"" Yanzun ma bai yi magana ba, ya ci gaba da bin ta da ido. Ta yi ta magana ya yi" "shiru, tamkar kurma. Can kuma ya tashi ya shiga banɗaki ya fito ya nemi guri ya zauna." """Sayyid, za ka yi sallolin da ba ka yi ba, Asuba da kuma Azahar, duk ba ka yi ba"" ya yi mata shiru, ya" "kawar da kansa gefe. Ta tsiyayo ruwan shayi a kofi, ta zo gabansa da cokali ta zauna ta ce ""To ɗan sha tea ɗin, sai ka ci abinci ka yi sallar"" ya kawar da kansa ya yi mata shiru. Ta ƙara matsawa kusa da shi, kawai ya hamɓare kofin ruwan zafin ya kware mata, a wuyanta zuwa jikinta. Wata irin zabura ta yi, ta ja da baya tana tsuma, saboda yadda zafin ya ratsa fatarta. Ko kallon inda take bai yi ba, ya ja gefe ya ci" gaba da huci. "Ranta ya yi mummunan ɓaci, amma ta kalli fuskarsa, ta tabattar da yana hayyacinsa, babu yadda za a yi" "ya yi mata haka, dan haka ta yi shiru ba ta ce komai ba, ta tashi ta cire kayan, ta saka wasu." "Haka suka wuni a ɗakin, bai yi salla ba, bai ci abinci ba, kuma bai yi magana ba." "Ana yin sallar magariba, ya haura kan katifa ya kwanta." "A jikin mudubi ta tsaya, tana haska ƙirjinta, yadda inda ruwan zafin ya zuba a ƙirjinta, ya ɗuri ruwa." "Ta hasaka kan katifar, ta ga ya ci gaba da wannan baccin, mai rabin idonsa a buɗe, ta nemi guri a ƙasa" "lungun wardrobe ta kwanta. Sai dai yau ta kwanta cike da fargaba da kuma zullumin abin da zai faru, kar" ta je ya sake shaƙe ta. "Sam ta kasa bacci, da ta fara sai ta razana ta buɗe idonta, dama a kunne ta bar fitila ba ta kashe ta ba." **** "Shukura ce tare da Sagir a zaune a cikin mota, ta zuba wa ƙofar gate ɗin Asibitin ido. Ya ce ""Ya dai? Ki" "shiga ki fito ina nan ina jiran ki""" """Wallahi haka kurum gabana yake faɗuwa, ko hanyar Asibitin nan ba na son na ni an faɗi sunan ta""" """Shukura duk saboda da ɗan ki ya rasu, ban taɓa ganin mutum mara tawakkalli kamar ke ba""" """Ba haka ba ne, wallahi yanzu ma ban da Mummy ta matsa, ba zan zo ba, bari na je na dawo""" "Sagir ya ce ""Tom ki yi masa sannu, ni na zo na duba shi dama"" ta jinjina kai ta fice daga motar." Ayshacool "Tana shiga cikin Asibitin, ta din ga jin kamar a lokacin ne, za a yi mata aiki a cire ɗan cikinta, wata irin" fargaba da yanayi mara daɗi ta din ga ji a jikinta. "Ta ci gaba da jan ƙafafuwanta, jiki babu ƙwari ta nufi ɗakin da Hajiya Amina ta kwatanta mata. Sai da ta" "yi knocking sannan ta tura ƙofar ta shiga. Fadila na zaune a gefen gadon kusa da Alhaji Fatuhu, ga cikinta" "ya yi wani irin girma, tamkar tana yinƙurawa ɗa zai faɗo. Sai dai gaban Shukura ya yi mummunar faɗuwa," "ganin yadda Alhaji Fatuhu ya koma. Dogon mutum mai jiki, mai hasken fata, ya koma baƙi ƙirin ya yi wata irin mahaukaciyar rama, jikinsa tamkar fata kawai aka yafa wa ƙashi. Ta ji kanta ya sara, wani irin abu ya soki zuciyarta. Wani irin wari ɗakin yake yi, tamkar na mushe, ga shi dai babu ƙazanta a jikinsa, ga ɗakin a share a goge yana ƙamshin turaren wuta, amma ita warin mushe ta din ga ji, da ba ta san daga" ina yake fitowa ba "Fadila tana yi mata sannu da zuwa, amma ba ta kula ba, ta ƙarasa kan gadon, ta zaune. Yana daga zaune," "ya kalle ta ya yi murmushi tamkar mai raɗa ya ce ""Shukura""" """Daddy, haka jikinka ya koma?"" Ta yi maganar cikin matsanancin tashin hankali, da tuni hawaye ya" wanke mata fuska. "Ya ce ""Alhamdillah, ai na ji sauƙi ko Maman Muhsin?"" Fadila ta jinjina kai hawaye na zubo wa daga" idonta ita ma. """An ce mini kin haihu ɗan ya rasu, ban zo na duba ki ba, na haɗu da wannan larurar""" "Cikin kuka ta ce ""Dan Allah ka yi haƙuri ban zo na duba ka a kan lokaci ba. Ban zaci abin ya kai har haka" "ba""" "Ya yi murmushi yana jinjina kai, aka turo ƙofar ɗakin,gaba ɗaya suka waiwaya Doctor Sharif ne ya shigo," tare da wata nurse. "Yana ganin Shukura ya yi murmushi ya ce ""Hajjaju kwana da yawa, ni da na yi zaton zuwa yanzu ma, kin" "dawo mana awo? Ya gida ya mai gidan?""" """Lafiya kalau"" daga haka ta ja baki ta tsuke. Sai da ya sha jinin jikinsa, da irin amsawar da ta yi masa." "Ya kalli Fadila ya ce ""Uwar biyu, ya mai jikin?""" "Fadila ta ce ""Alhamdillah mun gode Allah""" """Ma sha Allah. Na ce ki je a duba ki, idan inducing ɗin ki za a yi, idan ma tiyata ya kamata a yi miki to." "Amma kin ƙi""" """Kar ki soma yarda, a kashe miki ɗa, gara ki je wani Asibitin"" tsit suka yi baki ɗaya, suka waiwayo su na" kallon ta. "Jikinsa ne ya yi wani irin sanyi, wani irin tsoro ya ziyarci zuciyarsa. Cikin damuwa ya ce ""A kashe mata ɗa" "kuma Shukura""" """Nawa ba a hannunku ya rasu ba?""" """Kuma ai ba kya ce za a kashe mata ɗa ba, nakin ma, Allah ne ya kawo ajalinsa""" "Shukura ta ce ""Ba zan dai sake zuwa Asibitin nan na haihu ba. Daddy Allah ya ƙara afuwa. Maman" "Muhsin sai anjima Allah ya raba lafiya""" "Fadila ta ce ""Amin, mun gode sosai da sosai Shukura, ki gaida gida. Mummy ma an ce ta tafi Umara ko?""" """Eh wallahi. Allah ya raba lafiya"" har Shukura ta fice, jikin Doctor Sharif tsuma yake yi, amma ya dake" tare da ɓoye hakan. * "Jamila na tsaka da bacci, ta ji ana tashin ta. Ta buɗe idonta ta ga Hajiya Sa'a a tsaye amma fitilar ɗakin a" kashe. """Hajiya lafiya kuwa?""" """Lafiya ƙalau, tashi ki saka wannan rigar mu tafi""" "Cikin mamaki ta ce ""Ina?""" """Ki saka sai mu je ki gani. Ki cire komai na jikinki ki saka ta""" "Bakinta fal tambayoyi, amma babu damar yi. A duhun ta karɓi rigar ta saka, kanta babu ko ɗan kwali," "Hajiya Sa'a ta kama hannunta suka fice. Sun yi doguwar tafiya sosai, su na ratsa guri-guri, sai dai duk a cikin duhu ne. Jamila ba ta san ina suke bi ba, da kuma inda za su je ba." "Aka buɗe musu wata ƙofa suka shiga, ta ja ta tsaya. Yanayin gurin babba ne yana da girma sosai. Sai dai" "da mutane a ciki, galibinsu maza ne. An kunna kyandira a gurin. A haka ta lura kayan jikinsu jajaye ne da" baƙaƙe. "Sun kewaye wata ƙatuwar tukunya a tsakiyar ɗakin, fuskokin su a rurrufe." Hajiya Sa'a ta ja ta suka samu guri suka zauna. "Wani irin gurnani mutanen ɗakin suke yi, su na wasu irin maganganun da ba ta fahimtar abin da suke" "faɗa. Da alama ɗaya daga cikin su ne yake jagorantar abin da suke yi, mai kama da ibadar bautar wani abin." """Mun yi baƙuwa a gurin nan"" cewar mutumin da yake zagaye tukunyar, yana faɗar abin da yake faɗa" suna yi masa amshi. Ayshacool "Hajiya Sa'a ta ce ""Eh, baƙuwar mu ce, da na sanar da zuwan ta wannan bugiren""" """Ita ce aka kasa samo jinin 'yar uwatta, uwar gijiyar uban duƙusa?""" """Eh ita ce""" """Mu na yi mata maraba da zuwa ƙungiya, za ta samu abin da take so. Idan duniya ce kun same ta kun" "gama. Babu wani abu da zai gagare ku. Can kuma wannan matsalar ku ce, ku neme ta ku rasa nan, ko ku nemi nan can kuma sai abin da hali ya yi. Mu na yi wa wanda ba su bayar da sadaukarwar su ta wannan shekarar ba, idan lokaci ya yi za su ga abin da ba su zata ba. Wanda suka riga su ka yi, mu na taya su murna da ƙara tabattar musu sun samu duniya, su taka wanda suka so, babu mai ganin bayansu, masu neman ɗaukaka za su samu, masu neman ilimi za su dace. Masu neman kuɗi sun samu, haka ma masu neman madafun iko. Mu na sake jaddada muku dokokin ƙungiyarmu, babu fita bayan an shiga. Babu tona asirin ƙungiya. Duk wanda ƙungiya ta buƙata za ka bayar, babu jayayya babu musu. Akasin haka" "jininka ya zama mallakin dodon ƙungiya""." """Mun yarda, mun yi mubayi'a, mun bi dodon ƙungiya, mun bi sarkin ƙungiya, ranmu da jukkunanmu" "fansa ne a gare ku, muna son duniya, mu na son tabattuwar duniyarmu"" suka haɗa baki su na maimaitawa. Jamila bin su kawai take yi da kallo, jin abin take yi tamkar a mafarki, kuma kamar wani film. Wani irin sauti mara daɗin ji ya karaɗe ilahirin gurin." "Miƙewa mutanen suka yi, suka risuna tamkar za su yi sujuda. Su na ci gaba da karanto wasu irin" "abubuwa. Wani abu mai kama da guguwa, ya kashe kyanduran gurin. Ƙarar sautin abin, da surutun da suke yi ya karaɗe gurin, baka iya gane komai. Can bayan wani lokaci kuma, sai gurin ya yi tsit hasken kyanduran ya dawo. Suka ɓarke da wata irin shewa. Hasken ya haska gurin sosai da sosai, sai dai ba ta iya gane suwaye a gurin, kuma ta nemi Hajiya Sa'a ta rasa a gurin. Sai daga baya ta fahimci ashe akwai" mata a gurin ba wai maza ne kawai ba. "Aka din ga raba wani abu a cikin kofi, aka zo kanta a ka ba ta, ta karɓa ta sinsuna ta ji wani irin ƙarni" "mara daɗin ji ya daki hancin ta. Ta kawar da kanta yawu na taruwa a cikin bakinta. Ji ta yi an damƙi hannunta, an nufi wata ƙofa da ita. Tana ta ƙoƙarin gane waye, amma abu ya faskara ta kasa gane waye." "Su na shiga ƙofar ta ga duhu ya ƙara gaurayewa, amma ta ji sanyin AC na ratsa ta." "Ta ji an shaƙe mata wuya, an toshe mata hanci, ta fara kiciniyar ƙwacewa amma abu ya gagara, ta buɗe" "bakinta za ta yi numfashi ta ji an zuba mata wani abu, da ya fi ruwa kauri kaɗan, mara ɗanɗano. Tana gama haɗiyewa ta ji wannan ƙarnin ya mamaye mata hancinta da bakinta. Take ta yi yinƙuri ta fara amai," "sai dai ba ta gama aman ba, ta ji jiri ya kwashe ta." **** "Bangaren Nana kuwa, aka shiga kwana biyu, ba tare da ko ruwa Sayyid ya saka a cikin sa ba. Balle Abinci," "ba wanka babu salla balle ya sha magungunan sa na matsalar zuciya. Ga shi kuma bai daina haki ba. Idanunsa sun yi jawur tamkar gauta. Laɓɓansa sun yi wata irin bushewa. Ga gashin nan butsu-butsu a hargitse babu gyara, ya koma mahaukaci sosai da sosai. Ga shi da ta tunkaro inda yake, ko ya hankaɗe ta, ko ya shaƙe ta. Ko kallonsa ta fiye yi, sai ya hau huci yana zabure-zabure tamkar zai kai mata duka. Ta yi" "iya ƙoƙarin ta, babu wanda yake shigar mata ɗaki." "Ga laulayin ciki ya saka ta a gaba, ita kanta lallaɓawa kawai take yi. Ba ta yi da yawa ba a rana ta yi amai" "sau goma, tun cikin dare take farawa. Tun tana sha'awar ta ci wani abu har ta daina. Daga shayi sai ruwa, ko juice ɗin lemon tsami. Idan ta ga jikinta ya bushe ne, sai ta aika a sayo mata ruwan gishiri ta haɗa ta sha. Ga ranar da za su koma follow up, na Asibiti ya yi amma yana cikin wannan yanayin, a dole ta rabu" "da shi, ta ci gaba da addu'a." Sai dai yau gaba ɗaya Jamila ce take ta kaiwa tana komowa a ranta. Sannan ƙasan zuciyarta kuma haka "kurum, take tunanin abin da ya sanya ta daina ganin Ƙaisar kwana biyu." """Allah ya sa dai lafiya"" ta furta a fili, sai kuma ta yi saroro bayan wata zuciyar ta ce ""Ina ruwan ki da lafiya" "ko ma babu, abin da ki ke neman maraba da shi?""" Ayshacool "Sayyid take kallo, zuciyarta na raya mata, ta matsa kusa da shi, ta jarraba yi masa karatu, amma tsoro ya" "kama ta, saboda gudun kar ya cutar da ita, ga ƙaramin ciki a jikinta, da take ta lallaɓawa tana fatan Allah ya bar mata." **** "A hankali Jamila ta buɗe idonta, ta ganta a ɗakin da suka sauka da Hajiya Sa'a. Ta yinƙura za ta yaye" "bargon da take lulluɓe da shi, amma ta ji jikinta na yi mata wani irin ciwo mai tsanani. Ga wani irin raɗaɗi" "da azaba da ta ji a ƙasanta zuwa gurin bayan gidanta, tamkar an sanya abu mai kaifi an haɗe guraren biyu." "Ta yaye bargon ta ganta a tsirara, jikinta duk an yi mata zane da jini, ta ɗaga ƙafarta ɗaya tana ƙoƙarin" "tashi zaune, amma ta ji ba za ta iya ba, saboda azabar raɗaɗi da zafin da take ji." """Wayyo Allah Mama, na shiga uku mene ne ya same ni haka? Nana, Suwaiba dan Allah ku taimake ni na" "shiga uku""" "Hajiya Sa'a ce ta shigo da sauri, tana faɗin ""Daughter kin tashi?""" """Mene ne ya same ni, me ya faru da ni?""" """Yi shiru, ki kwantar da hankalinki, zan yi miki bayani. Amma ki daina wannan kukan." "Taso mu je, ki yi wanka ki gasa jikin ki, ki karya tukuna." "Cikin kuka ta ce ""Ba na so, ki yi mini bayanin mene ne ya same ni? Ina ne nan? Me yasa nake jin wannan" "zafin, kuma me ye wannan rubutun a jikina?""" "Hajiya Sa'a ta ce ""Ke ba na son hauka. A lokacin da Safiyya ta haɗa ni da ke. Nake kashe miki kuɗaɗe a" "banza zan yi miki ne, ba tare da na amfani komai a tattare da ke ba? Kin gaza kawo mini jinin 'yar uwakki," "kin ƙi shiga cikin harkar mata yadda nake so, kuma ga burinki na son abin Duniya, dan haka tallafawa" "burinki kawai na yi cicciɓa ki""" "Hawaye na kwarara daga idonta cikin sanyin murya ta ce ""Yanzu me ya same ni?""" """Taronmu na ƙungiya ki ka zo, kuma na nema miki sassauci ta hanyar ki bayar da budurcinki, ga sarki da" kuma dodon ƙungiya maimakon a ce ki kawo jini tashin farko. "Aljanin da ke da alhakin bamu kuɗaɗe,da jagorantar ƙungiyar, shi ne ya shiga jikin sarkin ƙungiya ya" "kwanta da ke, a matsayin barka da zuwa na ƙungiya kuma da sadaukarwar ki ta shekara!!!" "(Alhamdillah, da haka muka kawo ƙarshen book 1, sai mun haɗe a kashi na biyu)." Ayshercool 08081012143 Ayshacool "Ya gama ci, ta dafa ruwa ta kama hannunsa zuwa banɗaki, tamkar jaririn goye ta yi masa wanka. Shi" "kansa a lokacin ya din ga jin wata lafiyayyiyar iska na shigar sa. Ta saka ya yi alwala, ya fito ya zauna ya fara jero sallolin da ake bin sa." "Ta ce ""Sayyid kar ka ce sai yi a yanzu duka, sallolin da yawa.ka bari ka din ga ramawa a hankali." "Ya jinjina mata kawai kawai, tun yana yi a tsaye ya kasa tsaiwar ya koma yi a zaune. Ta yi shiru tana" "kallonsa, ta wasu guraren suna da kamanceceniyar halayya ita da shi." "Duk yanayin da yake ciki, muddin ba hankalinsa ne ya gushe gaba ɗaya ba, ba ya wasa da salla ko kaɗan." Hakan ya sanya take jin ko a ainihin rayuwarsa haka ya siffantu da kiyaye salla a kan lokaci. "Har ƙarfe uku da rabi, dan kansa ya ce ""Ba zan iya ƙarasawa ba, numfashina""" "Ta ce ""To ko za ka yi a kwance?""" "Ya girgiza kai ya ce ""Na fi so na yi a zaune, ko a tsaye""" "Ta ɗage masa labule, ganin yadda yake ta gumi. Ta shimfiɗa masa sallaya a bakin ƙofa, ta jera masa" "fululluka, ya kwanta.ta zauna a gefen sa tana yi masa fifita. Ta ɗora hannunta a goshinsa tana karanta masa abin da Allah ya sa ta tuna a zuciyarta." "Hannunsa ta ji yana saka wa a rigar ta, duk da idonsa a lumshe yake. Murmushi ta yi ta ci gaba da abin" "da take yi. Jin yana yi mata cakulkuli, ya sanya ta kwanta a jikinsa tana dariya. Shi ma dariyar ya yi. Ya ce ""Ki kwanta a kusa da ni"" ya yi maganar yana nuna mata kusa da shi. Kafin ta yi magana ta ga an dalle su" da fitila. "Cikin hanzari ya juya kansa, ya ɓoye fuskarsa a cinyar Nana, gashin sa ya kwanta a kan filon. Nana ta saka" hannu ta kare fuskarta. "Muryar Barira ta ji ta ce ""Yi haƙuri dan Allah, jin motsi ya yi wa na fara jin tsoro, shi ne na fito na duba, ku" yi haƙuri. "Ta kashe fitilar ta koma ɗaki. ""Sayyid ka yi haƙuri, na san ba ka ji daɗi ba, ka yi haƙuri""" "Ya yi mata shiru, kuma bai ɗago daga kan cinyarta ba. Ta shafa gashin ta ce ""Shugabana, ka yi magana" "mana, ko na ji daɗi, kwana huɗu ka na bacci, ba ka yi mini magana dan Allah kar laifin wani ya shafe ni""" "Sai kuma ya juyo a hankali, ta ce ""Yauwwa Rayuwata""" """Kin daina aman?"" Ta ji ya tambaye ta babu tsammani." """Eh na daina""" """Allah ya sa ki haihu wannan karon """ """Amin, kuma Allah ya baka lafiya na haɗa jariraina biyu, babba da ƙarami""" "Ya yi murmushi ya ce ""In sha Allah, kafin ki haihu, idan na ji sauƙi zan nemi aiki, na kula da ku da kaina""" """To Allah ya amince. Amma Sayyid ina kuɗin nan da na gani rannan, a cikin wardrobe ɗin ka? Da na haɗa" "mana kaya ban gan su ba. Da sai mu ɗauka a yi maka magani, kuma mu canza gida""" """Ai Habu ya karɓa, ranar da ya zo na ƙarshe, ya karɓi kuɗin Nigeria da yawa, ya bar mini wasu, ya ce na" "Nijar ne. Kuma da kin duba kayan nawa sosai, su na ciki""" """A'a ni ba na caje maka kaya, idan Allah ya kaimu gobe, sai a lissafa mu gani idan za su isa.""" "Ya ce ""To. Kwanta ki yi bacci"" ya yi maganar ya ƙara matsa mata. Ta kwanta tana murmushi." """Sayyid, idan har ba a ga su Habu ba, ina ga da ni da kai zamu je Nijar, mu nemi danginka da kanmu""" "Ya yi shiru bai yi magana ba, ta ɗan taɓa shi ta ji har ya yi bacci." * "Jamila a dole ta saki ranta, jikinta ta ɗan samu ƙwari, ya daina yi mata wannan mugun ciwon da yake yi" "mata. Raɗaɗin ma duk babu. Sai dai tana jin ƙasan zuciyarta kamar za ta yi bindiga, saboda damuwa da" "tashin hankali. Sosai abin da ya faru ya tsaye mata, ta shiga banɗaki ta sha kuka. Wai ita Aljani ya kwanta" "da ita, ta gaba da baya aka ci zarafin ta ta wannan mummunar hanyar." "Tana kwance a cikin bargo, Hajiya Sa'a ta fita shashashancinta. Wayarta ta fara ringing. Ta janyo ta ɗaga." "Muryar Abba ta ji ya ce ""Ƙanwata, wunin yau ban jiki ba, lafiya kuwa?"" Wani irin abu mai zafi ya taso" "mata, ya haddasa mata karaya. Muryarta na rawa ta ce ""Yaya Abba ba ni da lafiya""" """Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Me ya same ki?""" "Rasa abin da za ta ce masa ta yi, kawai ta saka kuka. Aikuwa ya rikice ya din ga rarrashin ta." Da ƙyar ya lallaɓa ta ta ce masa cikinta ne yake ciwo. """To ina Mummyn take? Ba ta kai ki Asibiti ba?""" Ayshacool """Ta kai ni, an ba ni magunguna ma, dan Allah kar ka yi mata zancen, ta yi mini iya ƙoƙarin ta,kar ka yi" "mata zancen dan Allah""" """No ai ba zan yi mata ba, ba ta san ma ina da lambar ki, mu na magana ba. Ki kwanta ki samu hutu kin ji" Ƙanwatax """To shikenan na gode sosai"" suka yi sallama ta ajiye wayar, ta kwanta hawaye na ci gaba da bin idanunta." * "Yana zaune a cikin mota, yana ƙoƙarin kunnawa, wayarsa ta fara vibrating. Ya kalli screen ɗin wayar, ya" ga baƙuwar lamba. Ya ɗauki wayar ya ɗaga ya saka a kunnensa. """Hello"" muryarta ta doki dodon kunnensa. Ɗan waro ido ya yi, ya gyara zaman sa ya ce ""Wa ke" "magana?""" "A raunane ta ce ""Beb abin har ya kai ka manta muryata ma? Shikenan na gode"" ta kashe wayar." "Da sauri ya bi kiran wayar, amma ta ƙi shiga, ya yi ya yi, amma ta ƙi shiga, sai haƙura ya yi ya ja motar." "Shukura mamakin abin da ya zaunar da shi a cikin mota take yi, bai tafi ba har yanzu, sai dai tana ɗaga" "labule, ta hango ya ja motar ya tafi." "Video call ɗin Hajiya Amina, Shukura ta gani, ta ɗaga cikin fara'a tana faɗin ""Hajiya Mummy, ya ibada?""" """Ibada Alhamdillah, Shukura dan Allah me yasa ba kya ji ne? Ina zaman zamana, ina ibada kin jawo mini" "ɓacin rai da damuwa""" "Cikin rashin fahimta, ta ce ""Ni ɗin kuma? Me na yi?""" """Baban ki ya kira ni, bai taho ba tukuna yana Abuja. Yana yi mini faɗan wai ke ba ki san ƙaddara ba ne?" "Doctor Sharif ya kira shi cikin damuwa, yana gaya masa a gaban mutane ki na cewa yana kashe mutane, haka ake yi a kan ki a ka fara rasa ɗa? Me yasa ba za ki girma ba ne Shukura""" """Mummy ki na ji na, network ɗin ki mai ƙarfi ne ko?""" "Ta ce ""Eh, ina jin ki, kuma ina kallon ki""" """Ina son idan kin je gaban ka'aba, ki yi mini addu'a, muddin a kan gaskiya ta nake, Ubangiji Allah ya shiga" "lamarina ya ƙarfafa mini gwiwa. Idan kuma ba a kan daidai nake ba, Ubangiji Allah ya kawar da kaina" daga kai. Ya bani juriya da dangana na daina jin abin da nake ji a zuciyata. "Sai dai kin dawo amma akwai matsala ne fa.""" """Shukura matsala wace iri ce, za ta sanya musulmi kasa yin tawakkalli?""" """Ki bari dai ki dawo ɗin""" """To shikenan, amma gaskiya mahaifinki ya yi fushi bai ji daɗin abin da ki ka yi ba sam""" "Shukura ta lallaɓa ta, ta ajiye wayar." * "Nana tana jan ruwa a rijiya, tana zubawa a cikin bokitanta, za ta kai banɗaki." "Barira ta ce ""Nana ki yi haƙuri dan Allah, jiya na haska ku, ba a son raina ba ne, kuskure ne"" Nana ta ce" """Babu komai""" "Sajida ta ce ""Uban me ki ka haska ki ka gani?""" "Barira ta kwashe da dariya ta ce ""Ni babu abin da na gani, duk da bai kyautu ba abin da na gani ɗin." "Amma Nana mijinki balarabe ne ko bature?"" Nana ta ɗaga ta kalle ta." """Tun da ku ka zo dama bamu taɓa ganinsa ba, gashi na gani kamar na mace dogo sosai""" "Nana ta maze ba ta kula ta ba, ta kwashi kayan ruwanta, ta nufi ɗakin su." "Sajida ta tuntsure da dariya ta ce ""Maganinki da shegen shishshigi, ga shi ta gwale ki""" """Shegiya ba, ta fiye jin kan ta,kamar 'yar uban wani, kuma da 'yar uban wanin ce, da ba su kama hayar" "ɗaki ɗaya ba"" Duk abin da suke faɗa a kunnen Nana, amma ta yi kamar ba ta ji ba." "Bayan ta gama wanke banɗaki ta fito, ta zo gabansa ta zauna. Ya ɗaukko sauran kuɗin nan, ya ajiye a" gaban ta. "Ta kalle shi ta ce ""A ina ka ɓoye ne, ban gan su ba?""" "Ya yi murmushi ya ce ""Su na cikin kayana fa, ba ki duba bane ba. A cikin leda suke. Kuma da sun fi haka" "yawa, Habu ne ya karɓa""." "Nana ta duba kuɗin, sai tarin kuɗin nijar, na Nigeria ba su dubu ɗari da goma ba." "Ta ce ""Sayyid, idan ka ɗan ƙara hutawa, ko zuwa gobe in Allah ya kaimu ne, za mu koma Asibiti a sake" "duba ka. Da za su kai da na haɗa da sauran na guri na, a fara yi maka allurar nan ko guda ɗaya ce""" """A'a, kin manta yanzu mu zamu din ga sayen Abinci. Idan su ka ƙare ba mu da hanyar samun kuɗi. Kuma" "da akwai isassun kuɗi, gara mu bar gidan nan, da a yi mini magani""" """Ni kaina Sayyid ba na son gidan nan. Mama za ta aiko mini buhun barkono, idan aka kawo, na ga ana" "ciniki, sai mu ci gaba da sayarwa""." "Ya jinjina kai ya ce ""To, in anjima ki raka ni masallaci"" Ta kalle shi ta ce ""Da gaske masallaci za ka je?""" Ayshacool """Eh, ina son zuwa masallaci. Idan ki ka raka ni, sai ki dawo""" "Ta yi murmushi ta ce ""To shikenan, Alhamdillah sauƙi yana samuwa. In sha Allah zan kai ka. Bari na ajiye" "kuɗin nan, idan na raka ka ma, dan Allah zan je gidan Ummi"" ya jinjina kai. Har za ta tashi ya riƙo ta, ya" cire hijjabin da yake jikinta. "Ƙonuwar da take wuyanta ya gani, ya ƙura wa gurin ido sosai sannna ya ce ""Mene ne wannan?""" "Ta ɗan basar ta ce ""Ba komai fa, ɗan ƙonewa ne kawai na yi""" """Ba ɗa ba ne ba, me ya kai ruwan zafi wuyan ki? Waye ya zuba miki?""" """Ba wanda ya zuba mini, sha nake yi ya zube"" kawai ya rabu da ita, ba dan ya gamsu da amsar da ta ba" shi ba. "Ta tattare kuɗin nan, na Nijar ta zuba su a cikin jakar gidan Sarkin Baka. Na Nigeria kuma ta haɗe su, ta" "saka a cikin kayan ta. Ana kiran salla, ya yi alwala, Nana ta ba shi mayafin rawaninsa, ya yafa a kan sa." "Nana ce ta fito tsakar gida. Barira ta gani, tana girki sanye da wata 'yar riga, milik ce amma ta yi baƙi" "saboda dauɗa, ko brezia babu a jikinta. Ga gashin hammata ya fito zaro-zaro idan ta ɗaga hannunta." "Zanin jikinta ma baƙi ƙirin, tamkar an yi matsar man ƙuli da shi, sai annakiya take yi." "Nana ta ce ""Barira, dan Allah ko za ki gyara, zamu wuce""" "Barira ta ce ""Bismillah ki wuce mana""" """A'a ai ni da mijina ne""" """Ku wuce ba wani abu ai"" Nana ta yi shiru tana jinjina tumasanci da rashin sanin ciwon kai, na mutanen" "gidan. Babu yadda ta iya, haka ta kammo hannun Sayyid, ya fito ta rufe ɗakin. Ya ja mayafin ya rufe fuskarsa da rawanin, saboda yanzu ba ya iya naɗa shi, saboda numfashinsa." "Tun da ya fito Barira take kallon sa, ta na son ganin ainihin fuskarsa, amma ya sunkuyar da kai, kuma ya" rufe fuskar sa suka fice. "Su na tafe Yana hutawa, saboda haki, a hankali har suka isa masallacin. Ta ce ""Za ka jira ni na je gidan" "Ummin na dawo?""" """Zan koma gida da kaina""" """Har ka gane hanya?""" "Ya ce ""Eh ki gaishe ta""" "Nana ta ce ""Ai ba daɗewa zan yi ba ma""" Ya shiga Masallaci Nana kuma ta tafi gidan Ummi. "Su Nana na fita, Barira ta buga banɗakin tsakar gida ta ce ""Ke Sajida kashin danƙo ki ke yi ne? Ki na" "manne a banɗaki yau mijin 'yar rainin hankalin nan dai ya fito. Ashe dole ta ɓoye shi, fari ne tas wannan gashin da na gani, da gaske nasa ne.""" "Sajida ta fito da buta a hannunta ta ce ""Kai haba, ban gama ba ne shi yasa ban fito ba, zogala na ci da ƙuli" "ya ruɗa mini ciki""" """Aikuwa kin rasa, ba ki gan shi ba. Sai na ga kamar mata na rako, da na tuna Gali, ga baƙi ga ƙeya""" "Sajida ta ce ""Ba gara Gali ba da nawa mijin? Ke Gali na da tsawo, ni nawa ga gajarta ga muni""" """Gaskiya Sajida mijinki akwai muni kam, dogon baki kamar dangin burrai""" "Sajida ta tsuke fuska ta ce ""Ba na son iskanci kuma. Gara shi dai a kan Galin, da ki ka ce ba ya iya tsinana" "miki komai a shimfiɗa. Kalarsa kalar... Kafin ta ƙarasa Barira ta ƙunduma mata Ashariya, take faɗa ya" "kaure, suka ci wa junan su mutunci tsaf, suka tona wa kan su Asiri. Suka gaji dan kan su, suka haƙura." **** Nana ta bawa Ummi labarin barkono da za a kawo mata. "Ta ce ""Amma Ummi sai dai a kawo miki nan, can ɗakinmu babu gurin da zan ajiye a can""" """Bakomai a kawo, kuma nan da nan za ki ga an saye shi ba, ai unguwar nan fuskar jama'a ce, idan ka kasa" "kaya za ka samu alkhairi""" "Su na tsaka da hira, babu zato babu tsammani sai ga Saleh ya afko cikin gidan. Wata irin mummunar" "faɗuwar gaba ta ziyarci Nana, bayan da ta gan shi babu tsammani. Duk ya ƙara lalacewa." "Turus ya yi yana kallon Nana, cikin mamaki ya ce ""Nana, dama kina nan?""" """Eh"" ta amsa a taƙaice." """Nana da yanzu nine mijinki, amma ki ka guje ni""" "Ummi ta haɗe rai ta ce ""Saleh Nana fa matar aure ce, dan haka babu ruwan ka da ita dan Allah""" "Saleh ya ce ""Dan matar aure ce, kuma shikenan ba za mu yi zumunci ba? Nana kina lafiya? Na ji an ce" "wani baroroji aka aura miki ko?""" "Nana ta haɗe rai ta tashi ta ce ""Ummi zan tafi, zuba mini Abincin idan kin gama""" "Ummi ta ce ""Bari na wanke babban flask, kuma idan Islam ta zo ki ba ta kwano na, dan ba zan bar miki" "ba""" Ayshacool "Nana ta ce ""Gaskiya sai kin bar mini, ki zo ɗakina, ki ɗauki duk abin da ya yi miki. Kuma a ƙaramin kwano" "za ki zuba mini. Sayyid na yi masa girki, ni zan ci wannan""" "Ummi ta ce ""Hajiya Nana, an sake haɗiyar wake kenan, to Allah ya inganta""" """Dawa na haɗiya ba wake ba""" "Tsulum Saleh ya sake cewa ""A nan unguwar gidanki yake kenan? Na ji Ummi ta ce Islam na zuwa gidan" "naki. Da aka ce mijin naki gadi yake yi""" "A ƙufule Ummi ta ce ""Dan zatin Allah Saleh ka fita, ba da kai muke magana ba, babu ruwan ka da mu." "Wai har ka manta har ubanmu ka saka a rufe saboda kuɗinka, dan rashin kunya kuma, ka zo zaka addabe mu?""" "Sum-sum Saleh ya fice daga gidan. Ummi ta zubawa Nana tuwon shinkafa da miyar yauƙi, har da man" "shanu, Nana sai haɗiye yawu take yi cikin farin ciki, kamar ta durƙusa ta ci a gurin." "Ummi ta shiga ɗaki, ta ɗaukko wa Nana dambun kifi ta ce ""Ungo, jiya na yi shi aka kai mini shago, na" "ɗebar miki""" "Nana ta karɓa tana murmushi ganin sa fal a roba, ta ce ""Allah ya yi miki abin da ki ke yi mini na alkhairi" "na gode sosai"" suka yi sallama Nana ta fita." "Tana cikin bin wani lungu, ta ji Muryar Saleh na kiran ta. Ta ƙara saurin da take yi, amma ya cimma ta." """Nana dan Allah ki saurare ni""." "Rikicewa ta yi, gani take a kowane lokaci za ta iya ganin Sayyid, ba ta san da wani yaren za ta yi masa" bayani ba ya fahimta. """Nana ki tsaya ki ji mana""" """Wallahi zan yi maka ihun kwarto, wace irin jaraba ce wannan ina ruwan ka da ni ne?"" Ganin tana ɗaga" "murya, kuma Akuyarsa ta yi kuka a unguwar, ya sanya sum-sum ya koma da baya." "Tana zumbuɗa sauri, ta je gida, ta san yana can yana jiran ta. Kawai ta ci karo da shi a wani lungu, yana" "zaune a kan wata sokawe, ya jingina da jikin bango, shikaɗai ƙwal a layin. Sai da ta razana, ta waiwaya" "bayan ta, cike da tsoron ko Saleh ya biyo ta." """Sayyid me ka ke yi a nan kuma, ba ka shiga shiga gida ba?""" """Ba zan iya shiga nikaɗai ba"" Ta miƙa masa hannu ta ce ""Taso mu tafi"" ya miƙa mata hannunsa. Sai dai" "tun da ya saka hannunsa a nata, sai da ya kalli fuskar ta." "Da suka je gidan, danƙam da mata, ana ta hayaniya. Ya rufe fuskarsa Nana ta yi sallama. Gaba ɗaya suka" "yi tsit, suka zubo wa su Nana ido, musamman ganin hannunta riƙe da na Sayyid." "Kawai ta ja hannunsa, suka nufi ɗakin su." """Nana kun dawo"" Sajida ta yi maganar, tana kokowa da zaninta tana fitowa daga ɗakinta, saboda kar su" wuce ba ta gan su ba. """Eh sannun ku"" daga haka ya tura ƙofar ya fara shigewa. Suna shiga ɗakin matan suka saka shewa, ɗaya" "ta ce ""In dai Namiji ne, yarinya za ta gama wannan iyayin ne""" "Nana su na shiga ɗaki Sayyid ya tsare ta da ido ya ce ""Nana ba ki da gaskiya""" "Gabanta ya faɗi cikin tsoro ta ce ""Me na yi?""" """Gumi ki ke yi a iya goshin ki, da karan hancin ki. Kuma tafin hannunki ya ya sanyi, zuciyar ki na bugawa" "da ƙarfi kuma da sauri. Kin yi wani abu da ki ke ɓoye mini ko?"" Haɗe rai ta yi ta fara ƙoƙarin ƙwace" hannunta daga nasa. "Sai kuma ya sassauta muryarsa ya ce ""Ki daina fushi, ba zan iya barin, duk wani abu na ƙi ya tunkaro" "rayuwata da ke ba, ki daina fushi""" """To sai ka din ga zargina da rashin gaskiya"" ta faɗa a hasale." "Ya girgiza kai ya ce ""Ba zargin ki nake yi ba. Na tabattar da wani abu ya faru ne, da ba za ki so na sani ba," "idan na sani zamu samu saɓani. Kin manta mu ba kamar sauran mutane ba ne. Kuma ina iya jin abin da yake ranki, kin manta ne?"" Ya yi maganar yana murmushi da shafo fuskarta. Dole ta saki murmushi." "Nana dai ta din ga yi wa Allah godiya, da ba ganta da Saleh ba." "Nana tana yi wa Allah godiya, ganin yadda jikinsa ya yi kyau. Duk da yana haki bai daina ba, amma yanzu" "yana cin abinci. Sayyid na matuƙar son zuwa masallaci salla, amma dole yake haƙura. Saboda da gayya matan gidan suke wata shigar, duk da ba tsayawa kallon su yake yi ba. Ga shi ba ya son kallo, amma yana fitowa sai su yi shiru su zura masa ido." "Ita kanta Nana lamarin gidan ya ishe ta, ba ta ƙaunar zaman gidan nan ko kaɗan." "Maman Nana ta aiko mata da barkonon nan, har da awon kayan Abinci, tamkar ta san a halin da take ciki." "Ummi da kanta, ta je ta ɗauki barkonon, domin kuwa Nana daina zuwa gidan Ummi ta gaba ɗaya saboda" Saleh. Ayshacool "Abu kamar wasa har zuwa wannan lokacin, Sayyid ya kasa gane kansa, abin ya fara damunsa sosai da" "sosai. Ga shi ya kasa cewa Nana komai a kan hakan. Ita ma kuma ba ta ce masa ba, sabgoginta kawai take yi." "Tun Yamma Nana, ke ƙoƙarin shirya duk abin da za su buƙata, saboda washegari za su tafi Asibiti, kuma" "sammako take so su yi, saboda su ga likita da wuri." "Sai dai duk dauriya kawai take yi, wani irin zazzafan zazzaɓi ne a jikinta, ta kasa cin abinci. Babu abin da" "take son ci, sama ds kazar da Habu ya kawo farkon auren su. Ga shi ba ta son yin duk wani abu da zai" "ɗaga wa Sayyid Hankali. Ta fuskanci ko saɓani suka samu, ƙaramar magana sai ta sanya ya fara haki, ya" fara nema ya faɗi. "Tana ƙofar ɗakinta, tana soya miya, su Barira su na hira, tana yi wa wata maƙwabciyar su kitso. Suke" "zancen wata mata a bayan layin, wai sai mijinta ya neme ta ya rasa, sai a yi kwanaki ba a ganta ba, sai bayan wani lokaci a tsinto ta a wani gurin, ko a ganta a ɗaki." "Barira ta kada baki ta ce ""Amma ta mayar da mijin nan tasono, ƙarya take yi gantalinta kawai take tafiya." "Meye matan auren ba sa yi yanzu?""" "Sajida ta ce ""A'a Barira, ki daina cewa ƙarya ne""" """Ke wallahi, ko rantsuwa na yi ba zan yi kaffara ba, a gidan uban wa Aljani zai ɗauke mutum ya kai shi" "wani gurin? Ke ni fa da ake cewa ana ganin aljanu, ko su tsorata mutum ban taɓa yadda ba, iskanci ne" "kawai da ƙaryar banza ce, ba wani aljan duk 'yan iska ne kawai." "Nana ta ji wani abu mai zafi ya soki zuciyarta, duk da ba da ita suke ba, kawai ta ƙura wa Barira ido, ko" ƙiftawa ba ta yi. "Tun Barira ba ta ankara ba, har ta lura, take ta ji tamkar an kwarara mata ruwan sanyi a jikinta, sai kuma" "ta ɗan tsorata ta ce ""Nana lafiya kuwa?""" Ayshercool 08081012143 Ayshacool """Ni fa ba na son kurman baƙi, a masu shigowa ne mayun, ko kuma zaunannun gidan""" """Na ce ki zuba ido ki ga ikon Allah""" "Bai fi mintuna biyar ba, wani irin hayaƙi, mai azabar yaji, ya turnuƙe gidan." "Nana da take lafiya ƙalau ma, ta fara tari." "Shi m tarin yake yi, numfashinsa kamar zai ɗauke, ta ɗaukko mafici ta din ga yi masa fifita. Ta gaji ta tashi," "da nufin ta je ta ga me ake ƙonawa yake wannan uban hayaƙin haka. Amma ya riƙe hannunta ya hana ta. Haka suka wuni a galabaice. Sajida ma sai bala'i take yi, tana cewa Barira za ta kashe ta da hayaƙi." """Wai Sajida ko ke ce mayyar nan ne?""" """Ke kama bakin ki, wallahi ki ka ce mini mayya, sai mun yi shari'a da ke""" "Barira ta ce ""Sai ki saurara mini, tun da dai ba ke ba ce"" Haka suka wuni, Barira tana gana musu azaba," da wannan azababben abin da take zubawa a cikin murhu. "Washegari ma, azabar hayaƙin nan ce ta tashi su Nana, numfashin Sayyid tamkar zai ɗauke saboda azaba." "Nana dai ta ci gaba da daurewa, amma yamma na yi, Barira ta sake cika kurfoti da gawayi, ta tayar da" wuta ta afka hayaƙin nan. "A fusace Nana ta fita, ta tarar da ita tana ta girgiza kurfotin, tana zuba wani abu a ciki." "Nana ta ce ""Barira, dan zatin Allah ki daina zuba wannan abin. Ina da mara lafiya a ɗaki. Yana da" "matsalar numfashi, jiya kwana muka yi babu bacci. Kuma da sassafe kin banka wani, kuma yanzu ma ga shi kina sake kunnawa""" "Ta kalli Nana ta ce ""Ai duk wanda ya hana uwar shi bacci, wallahi shi ma ba zai yi ba""" "Nana ta ce ""Kamar yaya kenan?""" """Kamar yadda ki ka ji""" """Ni dai koma mene ne, ki yi haƙuri idan ba ki yadda ba, zo mu je ɗakin ki ga halin da yake ciki""" """Babu ruwana da halin da yake ciki, kurwata ce ta fi ƙarfin duk wani maye wallahi""" "Nana ta ce ""Barira mu ne mayun da ki ke faɗa dama? To Barira ko za mu ci mutum ma ci taki, jiki duk" "dauɗa?""" """Ko ma duk uban mene ne, tun da aka kama ni aka lasa, an ji zaƙin kurwa ta, wallahi sai mutum ya ci" "ubansa, miyagun banza kawai""" """Mu ne mayun Barira?""" """Eh ku ne, ko na ce ke""" "Nana ta ƙarasa daf da Barira ta damƙi tsintsiyar hannun Barira ta ce ""Ki ka ce ni mayya ce?"" Barira ta" "yinƙura za ta fizge hannunta, ta yi bala'i. Kawai ta ji jikinta ya yi wani irin nauyi, kuma jikin ya yi mata" "wani irin sanyi, ta kasa motsa komai. Kawai ta silale ta faɗi ƙasa." Ayshercool 08081012143 Ayshacool "Tun da Jamila ta koma gida, jikinta a sanyaye yake, gani take yi, duk wanda ya ganta ya san abin da ya" "faru da ita. Mama kuwa baki ya ƙi rufuwa, saboda Jamila ta zo da abin Duniya. Kuma kamar yadda ta" "gaya mata, sarin kaya ta raka Hajiya, babu wani bincike ta yarda da hakan ta amince." "Ta zo ba ta iya bacci sam, da ta kwanta bacc6, sai ta ga tamkar za ta buɗe ido, ta sake ganinta, a wannan" gurin da suka je da Hajiya Sa'a. """Jamila"" Suwaiba ta kira sunanta, ta waiwaya ta kalle ta." """Wai ya na ga ki na abu kamar mara gaskiya ne?""" "Gaban Jamila ya faɗi ta ce ""Me na yi na rashin gaskiyar, me ki ka gani?""" """To ai gani na yi kin kasa sukuni, ki na ta wani mutsu-mutsu gaki nan dai""" """Dan Allah Suwaiba ki ji da abin da yake damun ki, ni babu abin da ya same ni, lafiya ƙalau nake """ "Suwaiba ta ce ""To ai shikenan""" **** "Nana duk sammakon da suka yi, su ne na goma sha ɗaya, a gurin ganin likita." "Wajen sha ɗaya na safe aka zo kan su, Nana suka shiga, sai dai wannan karon wani likitan daban suka" "samu. Suka gaisa Nana ta yi wa likitan bayanin komai. Tare da ba shi takardun gwaje-gwajen da aka yi masa, da kuma katin da aka rubuta masa magunguna." "Ya karɓa ya duba a tsanake, ya duba Bp ɗin Sayyid, ya duba ƙirjinsa da stethoscope." "Nana ta ce ""Doctor yaya jikin nasa? Me ka gani?""" "Bai kalli Nana ba ya ce ""Me yasa ba ku dawo follow up ba""" "Ta ce ""Ai ba a bamu lokacin dawowa ba. Dama ni ce naga yakamata mu dawo ɗin. mu na ta ƙoƙarin" "kuɗin allurar su haɗu ne, ko ba su haɗu ba, zamu yi ƙoƙari ko a anan Asibitin gwamnatin ne, sai mu yi" "booking a fara yi masa""" "Likitan ya ce ""Ki na ji na 'ya ta?""" "Ta ce ""Eh""" """Ai mijinki ne ko?""" "Sayyid ya jinjina kai. ""To a duniya babu wani abu da Allah ba zai iya ba, babu shi. Batun allura ki bar" "wannan a hannun Allah. Kuma dan babu kuɗin allaura ba za a daina ganinsa ba. Zamu ci gaba da gwada shi, mu na ba shi magungunan da suka dace. Idan Allah ya yassare kwa zo a yi daga baya. Kuma jikinsa Alhamdillah da sauƙi sosai da sosai. Jinin dai haryanzu bai sauka yadda ake so ba. Amma zai sauka da yardar Allah. Kawai ki din ga kiyaye damuwarsa da ɓacin ransa. Idan kuma akwai wani abu da yake damunsa, ki zauna da shi ku tattauna ki ga ta ina za ku shawo kan matsalar?. Amma babu wani abu in sha Allah"" Duk da ba lafiya likitan ya ba su ba, amma kalamansa akwai dattaku da ƙwarewa a kan aiki a" cikin sa. Dan haka sosai Nana ta samu relief. "Ya rubuta musu lambarsa ya ce ""Duk lokacin da za ku zo, ku kira ni, na baku ranar da nake aiki, ya zo ya" "din ga ganina."" Nana ta din ga yi masa godiya da addu'a shi da iyayensa." "Sayyid ya ja wata takarda, ya yi rubutu ya miƙa wa likitan. Likitan ya karɓa ya duba. Ya yi murmushi ya ce" """Madam, ashe kema babu lafiya ya ce na duba masa ke""" "Nana ta yi murmushi ta ce ""Rashin lafiyata, ai ba komai ba ce a kan tasa, ni na fi damuwa da shi ɗin dai""" """A'a tun da ya nemi alfarma, ai dole a yi masa""" "Ya duba Nana, ya yi wa Sayyid bayanin laulayi ne kawai yake damunta, ya rubuta mata abin da zai rubuta" "mata na magani. Ya kuma ba ta gwaje-gwaje. Sayyid ya ƙi tafiya, sai da suka yi gwaje-gwajen." "Suka koma, ya tabattar musu da babu wata matsala, satin cikinta uku da kwanaki, ya rubuta mata" magungunan da za ta yi amfani da su. "Suna tafe a adaidaita sahu, Sayyid ya kasa riƙe murmushinsa, ya kai bakin sa kunnen Nana ya ce ""Saura" "kwana nawa ki haihu?""" "Ta kwashe da dariya, ta ce ""Ina na sani, ko cika wata ɗaya bai yi ba ma, mu dai ci gaba da addu'a Allah ya" "bar mana, ya bamu ɗa na gari""" "Ya amsa da ""Amin.""" "A bakin titi, Nana ta yi sayayyar salak, saboda shi take sha'awar ci. Suka shiga layin gidan na su." "Su na zuwa gidan, Nana da sauri ta shiga banɗaki, saboda fitsarin da ya cika mata mara. Sayyid tsayawa" "ya yi, yai shiru yana ƙare wa ɗakin kallo." "Nana ta fito bai ce mata komai ba, ta ɗauki cylinder gas, ta ce ""Sayyid gas ya kusa ƙarewa, idan zaka iya" "fita in anjima sai mu je titi tare mu ɗuro""" "Ya ce ""To""" """Bari na sake ɗumama miyar""" "Ta fito tsakar gidan kenan, Sajida ta ce ""Nana, Allah ya taimake ki, da tuni da ke za a tafi bayar da shaida""" "Cikin rashin fahimta Nana ta ce ""Shaidar me?""" Ayshacool """Jiya hirar da ku ka yi, har ki ke yi wa Barira faɗa, a kan matar nan. Daga jiyan nan zuwa yau magana har" "ta kai kunnen matar. Ta din ga kuka mijin ya ce ba zai yarda ba da 'yan uwanta. Da yyayyenta ne za su zo su zane Barira. Mijin matar ya hana aka kai ta police station. Tun bayan fitar ku tana can, duk sai da" "muka je bayar da shaida. Wataƙila dai kafin magariba a sako ta, ta dawo gida.""" "Nana ta numfasa ta ce ""Gara da Allah ya sa ba na nan, dan babu inda zan je, shi yasa a rayuwa yake da" "muhimmanci mutum ya iya bakinsa. Wannan tara matan da ku ke yi, ku na surutai marasa amfani duk ba hanya ce mai ɓullewa ba""" "Sajida ta ce ""Wallahi haka ne, shi yasa ki ke burge mu ma""" """Allah ya kyauta""" "Har Nana ta yi haɗin salak ɗin ta, ta fara ci, ya lura ba ta fahimci abin da yake faruwa ba, shi ma kuma bai" "gaya mata ba, ya ci abincin. Ta gama ci ta kalle shi ta ce ""Sayyid, ka yi mini addu'a, Allah ya sanya kar na yi aman salad ɗin nan, na rufe sauran anjima zan sake ci""" """Kin cika yaji, sai kin yi ciwon ciki ko?""" "Ta ɗan waro ido ta ce ""Dama ka gani?""" """Eh ina kallon ki""" "Ta ɗan yi murmushi ta ce ""Idan babu yajin, ba zai yi daɗi sosai ba. Amma yanzu ya ka ke ji a jikin ka?""" """Ba sauƙi""" """Subhanallah, ba sauƙi kuma?""" "Ya ce ""Eh, kin je ki na hira da likita a gabana""" """Amma ko ba komai, ya kwantar mini da hankali, bai ce mini zaka mutu ba, kalamansa sun bani ƙwarin" "gwiwar da yakamata na samu"" ta yi maganar ƙwalla na cika mata idanu." "Ya girgiza mata kai ya ce ""Kar ki bari su zubo""." """To ba kai ne ba, komai na yi sai ka ji haushi na?""" "Murmushin sa mai matuƙar ƙayatarwa ya yi, ya ce ""Ba haushinki nake ji ba, tsaro nake ba ki, saboda" "tawa ce nikaɗai. sourire (smile) ki yi murmushi mana"" ta noƙe kafaɗarta tana tura baki,ta juya masa baya." "Ya matsa bayan nata, ya sumbaci saman bayan ta, ya zagayo da hannunsa ta cikinta, ya kwantar da" "kansa a kan kafaɗarta. Gaba ɗaya jikinta ya yi sanyi. Damuwa ce ya ziyarce zuciyarsa, jin yadda Nana ta saki jiki sosai da rungumar da ya yi mata, ko ba a gaya masa ba ya san abin da yake ranta, tuna cewar babu abin da zai iya tsinana mata, ya sanya a hankali ya raba jikinsa da nata, wani irin tausayinta na ratsa" ilahirin jikinsa. "Ta maze cikin yaƙe ta ce ""Sayyid, ya na ji ka yi shiru ne?""" "Ya girgiza kai ya ce ""Babu komai""" """A'a akwai wani abu. Dama likita ya ce mu zauna na tambaye ka, ko akwai wani abu da yake damun ka," "haryanzu fa jininka bai sauka ba Sayyid""" "Ya ɗan sake yin guntun murmushi ya ce ""Damuwa ai akwai ta, ba na son ɗaga miki hankali ne kawai." "Haryanzu ina tunanin inda su Habu suka tafi, suka bar ki da ɗawainiya, Kodayake ko suna nan ma, kula" "da ni ba dolen su ba ne. Sai wahala ki ke sha, wallahi idan ina tuna hakan, sai na ji tamkar numfashina zai" "ɗauke a cikin damuwa nake sosai da sosai. Ba na son saka ki a damuwa ne kawai""." "Nana ta tattara hankalinta ta matsa kusa da shi, ta riƙo hannunsa, ta kalli idanunsa da suka yi jawur." """Idan su Habu ba hakkinsu ba ne kula da ki. Ni yanzu ya zama haƙƙina, na san ba a banza Allah ya haɗa mu ba. Mu ci gaba da addu'a Allah ya kawo mana komai da sauƙi. Amma ina fatan dan Allah ka daina damuwa, idan ciwon nan ya matsanta maka a jikina nake ji, ka daina ba na so"" ta ƙarasa maganar cikin" shagwaɓa. "Kafaɗarta ya ciza cikin wasa, yana rungume ta. Tamkar ba a cikin damuwa suke ba, suka ci gaba da raha," "duk da yadda hayaniyar mata ta cika gidan, tamkar a na taro, saboda dawowar Barira, an cika gidan ana mayar da yadda aka yi." "Ana fara kiran sallar magariba, ta kai masa ruwan ɗumi banɗaki ya yi alwala." """Za ka je masallaci ne?""" """A'a a nan zan yi""" """To yi sallar. Nima sai na yi muje mu ɗuro gas, ko rabi ne sai kuma na sayo gawayi, Ummi ta bani kurfoti," "na din ga haɗawa da shi"" Ya jinjina mata kai ya tayar da salla." "Yana kallon ta ta idar, ta buɗe jakarta ta ɗebo sauran kuɗin da suka dawo da su, ta nufi wardrobe ta" haɗa su da waɗancan kuɗin. Kawai ta ga kayan wardrobe ɗin a hargitse. "Mamaki ya kama ta, ta san Sayyid ba ya taɓa mata wardrobe, kuma ita ba a haka ta bar wardrobe ɗin ba." Ayshacool "Ta janyo jakar gidan Sarkin baka, ta duba ta ga kuɗin nijar a ciki. Ta laluba ta ɗauki ledar, da kuɗin" "Nigeria ke ciki ta rasa. Ta watso kayan wardrobe ɗin gaba ɗaya, tana ƙara haskawa da fitilar wayarta." "Yana tsaye yana kallon ta. Muryarta na rawa ta ce ""Sayyid""" "Ya kalle ta. ""Kuɗinmu, kuɗin da ka bani na saka a cikin wardrobe na...naa..ajiye a nan ban gani ba, ko ka" "ɗauka?""" "Ya yi shiru yana kallon ta, a zuciye ta nufi hanyar fita daga ɗakin, ya riƙe ta. Jikinta yana tsuma take" "ƙoƙarin fizgewa amma ya riƙe ta yana girgiza kai ya ce ""Kar ki yi magana, ki yi shiru ko waye mu bar wa" "Allah. Tun da na shigo, na ga alamar an buɗe ɗakin. Kuma laifinmu ne, da ba mu saka mukulli ba, muka rufe ɗakin kawai.""" """Sayyid ba a yi mana adalci ba. Kuɗin Abincinmu da maganinka, sun kwashe gaba ɗaya wace irin masifa" "ce wannan? Daga wannan sai wannan ya ake so na yi ne?"" Ya riƙe ta gam yana shafa bayan ta, a hankali ya ce ""Ki yi haƙuri, ki daina ɗaga murya, akwai Allah""" "Kuka take yi iya ƙarfinta, tana sheshsheƙa, ya rungume ta gam a jikinsa, shi kansa ya ji zafi da raɗaɗin" "satar da aka yi musu. Ba iya kuɗi ba, har da wasu daga kayan amfaninsu na ɗakin an ɗauka, ya san kuma" "hakan sabon ƙalubale ne, saboda ba su da wata hanyar samun kuɗi a yanzu." "Ji ya yi jikin Nana ya saki, kuma jikin yana ɗaukar sanyi. Karkarwa ta fara yi, tamkar ana jona mata" shocking. "Cikin matsananciyar damuwa, ya zauna da ita a jikinsa, ya ɗauki wayarta da ta saki a gurin, yana haska" "fuskarta. Ya ga hawaye na fita ta gefen idonta. Hannayenta da ƙafafuwanta su na lanƙwashewa, goshinta" kuma yana tsatstsafo da gumi. "Jin ta ta yi, jingine da wani abu da ba ta san ko mene ne ba. Ta shafa abin ta ji ƙurzunu-ƙuruzunu, tamkar" "dutse. Gurin baƙi ƙirin duhu ya gauraye gurin, ko tafin hannunta ba ta iya gani. A hankali haske ya fara" "shigowa gurin, har gurin ya yi haske ba ki ɗaya. Ta ɗaga kanta ta ga ba ta iya gano ƙarshen ɗakin." "Jin tari ta yi a bayan ta, ta waiwaya da sauri, ta ga Ƙaisar a zaune lulluɓe da wani abu mai haske sosai." """Ƙaisar. Ba ka da lafiya?"" Ta yi maganar tana nufar inda yake." "Ya yi shiru bai yi magana ba. Ta sake cewa ""Dama kuma ku na rashin lafiya, kamar ka canza gaba ɗaya""" "ya yi murmushi ya ce ""Mu na rashin lafiya mana, guba na ci"" Ta waro ido ta ce ""Guba kuma? Me yasa?""" """Tsohon nan na jikin mijinki, ya bani.""" """Kuma ka sha? Wai meye alaƙar ka da shi? Kuma dan Allah me yasa yake bibiyar mijina?""" """Ba wannan ba, me yasa ki ka kira ni?"" Cikin mamaki ta kalle shi ta ce ""Kamar yaya? Ni ban kira ka ba ai""" """Fushi da ɓacin rai, duk wanda ki ka yi tamkar kin kira ni ne. Kuma ni yanzu ba ni da wani tasiri sosai," "saboda jinya nake yi. Babu wanda ya san ina nan. Giyaz ya saka ni a gaba, ya mamaye Library ɗi na, yanzu rashin ganina zai sanya ya ci gaba da cutar da ku. Ba zan iya wani abu ba sosai yanzu, sai dai zan" iya tasiri a kan bil'adama. "Duk ba wannan ba, duba can.""" "Ta ɗaga kai ta kalli inda ya nuna mata, Library ɗin Ƙaisar ta gani. Ta ga gangar jikin Sayyid a kwance." "Tsohon nan ya ɗaɗɗaure shi da wata irin igiyar ƙarfe. Ƙasan gadon da yake kai kuma, wata irin wuta ce take ci a ƙasa. Nana ta zabura a rikice, ta ce ""Wannan ai Sayyid ne""" """Ƙwarai shi ne, ba wani ba. Kuma Giyaz shi ya sanya masa matsalar da ku ke ciki na auratayya. Sai dai" "abu ɗaya zan iya gaya miki. Matsalar zuciya da hawan jini da yake fama, wannan ciwo ne yake damun sa. Amma Giyaz na assasa wani abin. Kuma... Amma dai shikenan""" "Nana ta buɗe baki za ta yi magana, ya ce ""Kar ki tambaye ni komai, kin san sharaɗin. Kalli"" ya yi maganar" yana sake nuna mata gurin. "Alhaji Fatuhu ta gani, ta yi ƙuri da ido ta ce ""Kamar na san wannan""" """Ba kama ba ce ba kin san shi, ciwo ne da zafin sihirin da aka yi masa ya mayar da shi haka. Sai kuma" "albishir da nake yi miki, da ƙanwar ki ta zama cikakkiyar 'yar ƙungiyar asiri. Ɗayar kuma wannan bararojin da ta taɓa baki magani, ta aura mata ɗanta, wanda yake baƙin aljani ne. Kuma ta tarkato kan iyalanta duk su na jikinta. Kuma kowanne akwai abin da yake mora a jikinta. Ke in taƙaice miki ma, a" kowane lokaci za ta iya rasa hankalinta ko ma rayuwarta gaba ɗaya. Ayshacool "Shikenan bissalam""" """Ƙaisar"" sai kuma ta yi ido huɗu da Sayyid." """Kin tashi?"" Ta yinƙura ta tashi zaune, tana kallon ɗakin." "Sayyid ya ce ""Ƙaisar ɗin ba shi da lafiya ne?"" Ya yi maganar yana tsare ta ido." """Wane Ƙaisar ɗin?""" """Tambayata ki ke yi?"" Shiru ta yi, ita ba ta iya tuna koma ma a cikin abin da ya faru ba. Idonta ne ya" "sauka a kan kayan da suke gaban wardrobe a ƙasa, sai kuma abin da ya faru ya faɗo mata. Afujajan ta tashi ta sake nufar wardrobe ɗin, tana zazzage kayan tana kuka." """Kuɗin nan fa babu su, an kwashe ki daina wannan dube-duben"" ya zauna ta yi shiru ta sanya kayan a" gaba tana kallo. "Ya yi mata shiru ya ƙi kula ta, ya kwanta a kan katifa, yadda take a hasalen nan, idan ya matsa faɗa za su" yi. Cikin ƙanƙanin lokaci nannauyan bacci ya yi awon gaba da shi. "Barira na kwance a ɗakinta, ta yi ɗaiɗai tana bacci, ta ji kamar ana karta mata farce a ƙafafuwanta. Har" "ta maze ta ci gaba da bacci, amma ta ji an cigaba. A fusace ta ce ""Gali meye haka, za ka din ga karta mini" "faratanka, ina cikin bacci ne?"" Shiru bai amsa ba. Ta laluba ta ji yo ƙeyarsa a can ƙarshen gado, yana" "bacci. Ta koma ta kwanta, amma ta ji an cigaba, ta tashi zaune tana zabga ashariya." "Ta kunna fitila, ta ga babu kowa. Ta yi tsaki ta sauka daga kan gadon, ta fito tsakar gida domin ta yi fitsari." "Bayan ta fito daga banɗakin, kanta ko ɗan kwali babu, kawai ta yi karo da Nana a tsakiyar tsakar gidan tana yi mata wani irin mugun kallo." "Ta haska Nana ta ce ""Nana lafiya kuwa?""" "Sai dai Nana ba ta yi magana ba, ta sake haska ta, za ta yi magana. Ta ga ta rikiɗe ta zama wata irin" "ƙatuwar mage, baƙa ƙirin, girman ta ya yi na tunkiya ƙosashiya da ita, ta yo kanta tana buɗe haƙora." "Da gudu Barira ta shiga ɗakinta, tana ihu tana kiran sunan Gali." """Ke mahaukaciya, mene ne haka za ki din ga ihu kina kiran sunana a tsohon daren nan?""" "Ba ta ce masa uffan ba, ta duƙunƙune, tana mayar da numfashi. Ta tsorata sosai da sosai, da ƙyar ta" "samu ta yi bacci. Sai dai a cikin baccin ma, mafarkin magen nan kawai ta din ga yi tana bin ta, tana karta mata farata tana cizon ta." "Sayyid kuwa yana jiyo kururuwar Barira, hakan bai dame shi ba, sai ganin Nana da ya yi a zaune, ta haɗa" kai da gwiwa. "Ya yinƙura ya tashi zaune, bai ce mata komai ba, ya kwantar da ita a kan katifar, ya rufe su da bargo ya" "rungume ta yana shafa bayanta. Yana jin ta tana kuka, har ta yi ta gaji bacci ya ɗauke ta." "Dauriya kawai yake yi, amma ji yake tamkar ya taya ta kukan." "Washegari, Barira ta tashi da matsanancin zazzaɓi da ciwon kai, ta din ga yi wa mijin kuka, tana cewa ya" "mayar da ita gidansu, mayu sun kama ta a nan gidan, ba za ta yadda a kashe ta a banza ba. Babu yadda ya iya ya tattara ta ya kai ta gidansu." "Kwanki biyu da sace kuɗin nan, Nana ta rasa abin da yake yi mata daɗi. Dubu talatin ce ta ragu a" "hannunta, shi ma cikin irin kuɗin da ta zuba a jakarta ne suka fita da su. Kuɗin Nijar ɗin kuma ba ta san ma ina za ta a canza su ba. Bayan haka tayi tunanin idan Habu ya dawo fa, me za ta ce masa? Ta din ga tunanin yadda za ta yi da dubu talatin ɗin nan, ba tare da ta rushe gaba ɗaya ba. Ga shi magungunan da" "yake sha kawai, na wata ɗaya dubu goma sha biyu take sayen su." "Sai dai kamar yadda yake nanata mata, ta yi haƙuri, ya sanya ta fauwwala wa Allah lamarin." "Kwana biyar da kwashe kuɗin nan, Sayyid ya hana Nana gaya wa kowa. Sai dai cikin dare ba ta iya bacci," "saboda lissafi da tunani. Ta kira Ummi ta tambaye ta batun barkono, ta ce ana ta saya, ta sayar da ya kai rabin buhun. Kayan Abinci da Mama ta haɗo mata da su, take ta cancana musu." "Da daddare ba ta iya bacci, saboda damuwa da tunani, sai dai abin yana damun sa fiye da yadda yake" "damun ta. Su ka wayi gari, ya tashi jikinsa babu daɗi, yana ta numfarfashi." "Abin Duniya ya ƙara damunta, ya kuma ƙi cin komai. Muryar Barira ta jiyo a tsakar gida, da ta dawo, tana" maganganu tana ba wa su Sajida labari. """Mayu sun kama ni a gidan nan, kuma da ƙarfina na dawo, wallahi sai sun ci uban su, kurwata ta fi ƙarfin" "mutum""." "Sajida ta ce ""Ban gane mayu ba, suwaye mayun kuma?""" "Barira ta ce ""Oho, ki zuba ido ki gani, Allah zai tona musu asiri""" Ayshacool "Ya gama ci, ta dafa ruwa ta kama hannunsa zuwa banɗaki, tamkar jaririn goye ta yi masa wanka. Shi" "kansa a lokacin ya din ga jin wata lafiyayyiyar iska na shigar sa. Ta saka ya yi alwala, ya fito ya zauna ya fara jero sallolin da ake bin sa." "Ta ce ""Sayyid kar ka ce sai yi a yanzu duka, sallolin da yawa.ka bari ka din ga ramawa a hankali." "Ya jinjina mata kawai kawai, tun yana yi a tsaye ya kasa tsaiwar ya koma yi a zaune. Ta yi shiru tana" "kallonsa, ta wasu guraren suna da kamanceceniyar halayya ita da shi." "Duk yanayin da yake ciki, muddin ba hankalinsa ne ya gushe gaba ɗaya ba, ba ya wasa da salla ko kaɗan." Hakan ya sanya take jin ko a ainihin rayuwarsa haka ya siffantu da kiyaye salla a kan lokaci. "Har ƙarfe uku da rabi, dan kansa ya ce ""Ba zan iya ƙarasawa ba, numfashina""" "Ta ce ""To ko za ka yi a kwance?""" "Ya girgiza kai ya ce ""Na fi so na yi a zaune, ko a tsaye""" "Ta ɗage masa labule, ganin yadda yake ta gumi. Ta shimfiɗa masa sallaya a bakin ƙofa, ta jera masa" "fululluka, ya kwanta.ta zauna a gefen sa tana yi masa fifita. Ta ɗora hannunta a goshinsa tana karanta masa abin da Allah ya sa ta tuna a zuciyarta." "Hannunsa ta ji yana saka wa a rigar ta, duk da idonsa a lumshe yake. Murmushi ta yi ta ci gaba da abin" "da take yi. Jin yana yi mata cakulkuli, ya sanya ta kwanta a jikinsa tana dariya. Shi ma dariyar ya yi. Ya ce ""Ki kwanta a kusa da ni"" ya yi maganar yana nuna mata kusa da shi. Kafin ta yi magana ta ga an dalle su" da fitila. "Cikin hanzari ya juya kansa, ya ɓoye fuskarsa a cinyar Nana, gashin sa ya kwanta a kan filon. Nana ta saka" hannu ta kare fuskarta. "Muryar Barira ta ji ta ce ""Yi haƙuri dan Allah, jin motsi ya yi wa na fara jin tsoro, shi ne na fito na duba, ku" yi haƙuri. "Ta kashe fitilar ta koma ɗaki. ""Sayyid ka yi haƙuri, na san ba ka ji daɗi ba, ka yi haƙuri""" "Ya yi mata shiru, kuma bai ɗago daga kan cinyarta ba. Ta shafa gashin ta ce ""Shugabana, ka yi magana" "mana, ko na ji daɗi, kwana huɗu ka na bacci, ba ka yi mini magana dan Allah kar laifin wani ya shafe ni""" "Sai kuma ya juyo a hankali, ta ce ""Yauwwa Rayuwata""" """Kin daina aman?"" Ta ji ya tambaye ta babu tsammani." """Eh na daina""" """Allah ya sa ki haihu wannan karon """ """Amin, kuma Allah ya baka lafiya na haɗa jariraina biyu, babba da ƙarami""" "Ya yi murmushi ya ce ""In sha Allah, kafin ki haihu, idan na ji sauƙi zan nemi aiki, na kula da ku da kaina""" """To Allah ya amince. Amma Sayyid ina kuɗin nan da na gani rannan, a cikin wardrobe ɗin ka? Da na haɗa" "mana kaya ban gan su ba. Da sai mu ɗauka a yi maka magani, kuma mu canza gida""" """Ai Habu ya karɓa, ranar da ya zo na ƙarshe, ya karɓi kuɗin Nigeria da yawa, ya bar mini wasu, ya ce na" "Nijar ne. Kuma da kin duba kayan nawa sosai, su na ciki""" """A'a ni ba na caje maka kaya, idan Allah ya kaimu gobe, sai a lissafa mu gani idan za su isa.""" "Ya ce ""To. Kwanta ki yi bacci"" ya yi maganar ya ƙara matsa mata. Ta kwanta tana murmushi." """Sayyid, idan har ba a ga su Habu ba, ina ga da ni da kai zamu je Nijar, mu nemi danginka da kanmu""" "Ya yi shiru bai yi magana ba, ta ɗan taɓa shi ta ji har ya yi bacci." * "Jamila a dole ta saki ranta, jikinta ta ɗan samu ƙwari, ya daina yi mata wannan mugun ciwon da yake yi" "mata. Raɗaɗin ma duk babu. Sai dai tana jin ƙasan zuciyarta kamar za ta yi bindiga, saboda damuwa da" "tashin hankali. Sosai abin da ya faru ya tsaye mata, ta shiga banɗaki ta sha kuka. Wai ita Aljani ya kwanta da ita, ta gaba da baya aka ci zarafin ta ta wannan mummunar hanyar." "Tana kwance a cikin bargo, Hajiya Sa'a ta fita shashashancinta. Wayarta ta fara ringing. Ta janyo ta ɗaga." "Muryar Abba ta ji ya ce ""Ƙanwata, wunin yau ban jiki ba, lafiya kuwa?"" Wani irin abu mai zafi ya taso" "mata, ya haddasa mata karaya. Muryarta na rawa ta ce ""Yaya Abba ba ni da lafiya""" """Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Me ya same ki?""" "Rasa abin da za ta ce masa ta yi, kawai ta saka kuka. Aikuwa ya rikice ya din ga rarrashin ta." Da ƙyar ya lallaɓa ta ta ce masa cikinta ne yake ciwo. """To ina Mummyn take? Ba ta kai ki Asibiti ba?""" Ayshacool """Ta kai ni, an ba ni magunguna ma, dan Allah kar ka yi mata zancen, ta yi mini iya ƙoƙarin ta,kar ka yi" "mata zancen dan Allah""" """No ai ba zan yi mata ba, ba ta san ma ina da lambar ki, mu na magana ba. Ki kwanta ki samu hutu kin ji" Ƙanwatax """To shikenan na gode sosai"" suka yi sallama ta ajiye wayar, ta kwanta hawaye na ci gaba da bin idanunta." * "Yana zaune a cikin mota, yana ƙoƙarin kunnawa, wayarsa ta fara vibrating. Ya kalli screen ɗin wayar, ya" ga baƙuwar lamba. Ya ɗauki wayar ya ɗaga ya saka a kunnensa. """Hello"" muryarta ta doki dodon kunnensa. Ɗan waro ido ya yi, ya gyara zaman sa ya ce ""Wa ke" "magana?""" "A raunane ta ce ""Beb abin har ya kai ka manta muryata ma? Shikenan na gode"" ta kashe wayar." "Da sauri ya bi kiran wayar, amma ta ƙi shiga, ya yi ya yi, amma ta ƙi shiga, sai haƙura ya yi ya ja motar." "Shukura mamakin abin da ya zaunar da shi a cikin mota take yi, bai tafi ba har yanzu, sai dai tana ɗaga" "labule, ta hango ya ja motar ya tafi." "Video call ɗin Hajiya Amina, Shukura ta gani, ta ɗaga cikin fara'a tana faɗin ""Hajiya Mummy, ya ibada?""" """Ibada Alhamdillah, Shukura dan Allah me yasa ba kya ji ne? Ina zaman zamana, ina ibada kin jawo mini" "ɓacin rai da damuwa""" "Cikin rashin fahimta, ta ce ""Ni ɗin kuma? Me na yi?""" """Baban ki ya kira ni, bai taho ba tukuna yana Abuja. Yana yi mini faɗan wai ke ba ki san ƙaddara ba ne?" "Doctor Sharif ya kira shi cikin damuwa, yana gaya masa a gaban mutane ki na cewa yana kashe mutane, haka ake yi a kan ki a ka fara rasa ɗa? Me yasa ba za ki girma ba ne Shukura""" """Mummy ki na ji na, network ɗin ki mai ƙarfi ne ko?""" "Ta ce ""Eh, ina jin ki, kuma ina kallon ki""" """Ina son idan kin je gaban ka'aba, ki yi mini addu'a, muddin a kan gaskiya ta nake, Ubangiji Allah ya shiga" "lamarina ya ƙarfafa mini gwiwa. Idan kuma ba a kan daidai nake ba, Ubangiji Allah ya kawar da kaina" daga kai. Ya bani juriya da dangana na daina jin abin da nake ji a zuciyata. "Sai dai kin dawo amma akwai matsala ne fa.""" """Shukura matsala wace iri ce, za ta sanya musulmi kasa yin tawakkalli?""" """Ki bari dai ki dawo ɗin""" """To shikenan, amma gaskiya mahaifinki ya yi fushi bai ji daɗin abin da ki ka yi ba sam""" "Shukura ta lallaɓa ta, ta ajiye wayar." * "Nana tana jan ruwa a rijiya, tana zubawa a cikin bokitanta, za ta kai banɗaki." "Barira ta ce ""Nana ki yi haƙuri dan Allah, jiya na haska ku, ba a son raina ba ne, kuskure ne"" Nana ta ce" """Babu komai""" "Sajida ta ce ""Uban me ki ka haska ki ka gani?""" "Barira ta kwashe da dariya ta ce ""Ni babu abin da na gani, duk da bai kyautu ba abin da na gani ɗin." "Amma Nana mijinki balarabe ne ko bature?"" Nana ta ɗaga ta kalle ta." """Tun da ku ka zo dama bamu taɓa ganinsa ba, gashi na gani kamar na mace dogo sosai""" "Nana ta maze ba ta kula ta ba, ta kwashi kayan ruwanta, ta nufi ɗakin su." "Sajida ta tuntsure da dariya ta ce ""Maganinki da shegen shishshigi, ga shi ta gwale ki""" """Shegiya ba, ta fiye jin kan ta,kamar 'yar uban wani, kuma da 'yar uban wanin ce, da ba su kama hayar" "ɗaki ɗaya ba"" Duk abin da suke faɗa a kunnen Nana, amma ta yi kamar ba ta ji ba." "Bayan ta gama wanke banɗaki ta fito, ta zo gabansa ta zauna. Ya ɗaukko sauran kuɗin nan, ya ajiye a" gaban ta. "Ta kalle shi ta ce ""A ina ka ɓoye ne, ban gan su ba?""" "Ya yi murmushi ya ce ""Su na cikin kayana fa, ba ki duba bane ba. A cikin leda suke. Kuma da sun fi haka" "yawa, Habu ne ya karɓa""." "Nana ta duba kuɗin, sai tarin kuɗin nijar, na Nigeria ba su dubu ɗari da goma ba." "Ta ce ""Sayyid, idan ka ɗan ƙara hutawa, ko zuwa gobe in Allah ya kaimu ne, za mu koma Asibiti a sake" "duba ka. Da za su kai da na haɗa da sauran na guri na, a fara yi maka allurar nan ko guda ɗaya ce""" """A'a, kin manta yanzu mu zamu din ga sayen Abinci. Idan su ka ƙare ba mu da hanyar samun kuɗi. Kuma" "da akwai isassun kuɗi, gara mu bar gidan nan, da a yi mini magani""" """Ni kaina Sayyid ba na son gidan nan. Mama za ta aiko mini buhun barkono, idan aka kawo, na ga ana" "ciniki, sai mu ci gaba da sayarwa""." "Ya jinjina kai ya ce ""To, in anjima ki raka ni masallaci"" Ta kalle shi ta ce ""Da gaske masallaci za ka je?""" Ayshacool """Eh, ina son zuwa masallaci. Idan ki ka raka ni, sai ki dawo""" "Ta yi murmushi ta ce ""To shikenan, Alhamdillah sauƙi yana samuwa. In sha Allah zan kai ka. Bari na ajiye" "kuɗin nan, idan na raka ka ma, dan Allah zan je gidan Ummi"" ya jinjina kai. Har za ta tashi ya riƙo ta, ya" cire hijjabin da yake jikinta. "Ƙonuwar da take wuyanta ya gani, ya ƙura wa gurin ido sosai sannna ya ce ""Mene ne wannan?""" "Ta ɗan basar ta ce ""Ba komai fa, ɗan ƙonewa ne kawai na yi""" """Ba ɗa ba ne ba, me ya kai ruwan zafi wuyan ki? Waye ya zuba miki?""" """Ba wanda ya zuba mini, sha nake yi ya zube"" kawai ya rabu da ita, ba dan ya gamsu da amsar da ta ba" shi ba. "Ta tattare kuɗin nan, na Nijar ta zuba su a cikin jakar gidan Sarkin Baka. Na Nigeria kuma ta haɗe su, ta" "saka a cikin kayan ta. Ana kiran salla, ya yi alwala, Nana ta ba shi mayafin rawaninsa, ya yafa a kan sa." "Nana ce ta fito tsakar gida. Barira ta gani, tana girki sanye da wata 'yar riga, milik ce amma ta yi baƙi" "saboda dauɗa, ko brezia babu a jikinta. Ga gashin hammata ya fito zaro-zaro idan ta ɗaga hannunta." "Zanin jikinta ma baƙi ƙirin, tamkar an yi matsar man ƙuli da shi, sai annakiya take yi." "Nana ta ce ""Barira, dan Allah ko za ki gyara, zamu wuce""" "Barira ta ce ""Bismillah ki wuce mana""" """A'a ai ni da mijina ne""" """Ku wuce ba wani abu ai"" Nana ta yi shiru tana jinjina tumasanci da rashin sanin ciwon kai, na mutanen" "gidan. Babu yadda ta iya, haka ta kammo hannun Sayyid, ya fito ta rufe ɗakin. Ya ja mayafin ya rufe fuskarsa da rawanin, saboda yanzu ba ya iya naɗa shi, saboda numfashinsa." "Tun da ya fito Barira take kallon sa, ta na son ganin ainihin fuskarsa, amma ya sunkuyar da kai, kuma ya" rufe fuskar sa suka fice. "Su na tafe Yana hutawa, saboda haki, a hankali har suka isa masallacin. Ta ce ""Za ka jira ni na je gidan" "Ummin na dawo?""" """Zan koma gida da kaina""" """Har ka gane hanya?""" "Ya ce ""Eh ki gaishe ta""" "Nana ta ce ""Ai ba daɗewa zan yi ba ma""" Ya shiga Masallaci Nana kuma ta tafi gidan Ummi. "Su Nana na fita, Barira ta buga banɗakin tsakar gida ta ce ""Ke Sajida kashin danƙo ki ke yi ne? Ki na" "manne a banɗaki yau mijin 'yar rainin hankalin nan dai ya fito. Ashe dole ta ɓoye shi, fari ne tas wannan gashin da na gani, da gaske nasa ne.""" "Sajida ta fito da buta a hannunta ta ce ""Kai haba, ban gama ba ne shi yasa ban fito ba, zogala na ci da ƙuli" "ya ruɗa mini ciki""" """Aikuwa kin rasa, ba ki gan shi ba. Sai na ga kamar mata na rako, da na tuna Gali, ga baƙi ga ƙeya""" "Sajida ta ce ""Ba gara Gali ba da nawa mijin? Ke Gali na da tsawo, ni nawa ga gajarta ga muni""" """Gaskiya Sajida mijinki akwai muni kam, dogon baki kamar dangin burrai""" "Sajida ta tsuke fuska ta ce ""Ba na son iskanci kuma. Gara shi dai a kan Galin, da ki ka ce ba ya iya tsinana" "miki komai a shimfiɗa. Kalarsa kalar... Kafin ta ƙarasa Barira ta ƙunduma mata Ashariya, take faɗa ya" "kaure, suka ci wa junan su mutunci tsaf, suka tona wa kan su Asiri. Suka gaji dan kan su, suka haƙura." **** Nana ta bawa Ummi labarin barkono da za a kawo mata. "Ta ce ""Amma Ummi sai dai a kawo miki nan, can ɗakinmu babu gurin da zan ajiye a can""" """Bakomai a kawo, kuma nan da nan za ki ga an saye shi ba, ai unguwar nan fuskar jama'a ce, idan ka kasa" "kaya za ka samu alkhairi""" "Su na tsaka da hira, babu zato babu tsammani sai ga Saleh ya afko cikin gidan. Wata irin mummunar" "faɗuwar gaba ta ziyarci Nana, bayan da ta gan shi babu tsammani. Duk ya ƙara lalacewa." "Turus ya yi yana kallon Nana, cikin mamaki ya ce ""Nana, dama kina nan?""" """Eh"" ta amsa a taƙaice." """Nana da yanzu nine mijinki, amma ki ka guje ni""" "Ummi ta haɗe rai ta ce ""Saleh Nana fa matar aure ce, dan haka babu ruwan ka da ita dan Allah""" "Saleh ya ce ""Dan matar aure ce, kuma shikenan ba za mu yi zumunci ba? Nana kina lafiya? Na ji an ce" "wani baroroji aka aura miki ko?""" "Nana ta haɗe rai ta tashi ta ce ""Ummi zan tafi, zuba mini Abincin idan kin gama""" "Ummi ta ce ""Bari na wanke babban flask, kuma idan Islam ta zo ki ba ta kwano na, dan ba zan bar miki" "ba""" Ayshacool "Nana ta ce ""Gaskiya sai kin bar mini, ki zo ɗakina, ki ɗauki duk abin da ya yi miki. Kuma a ƙaramin kwano" "za ki zuba mini. Sayyid na yi masa girki, ni zan ci wannan""" "Ummi ta ce ""Hajiya Nana, an sake haɗiyar wake kenan, to Allah ya inganta""" """Dawa na haɗiya ba wake ba""" "Tsulum Saleh ya sake cewa ""A nan unguwar gidanki yake kenan? Na ji Ummi ta ce Islam na zuwa gidan" "naki. Da aka ce mijin naki gadi yake yi""" "A ƙufule Ummi ta ce ""Dan zatin Allah Saleh ka fita, ba da kai muke magana ba, babu ruwan ka da mu." "Wai har ka manta har ubanmu ka saka a rufe saboda kuɗinka, dan rashin kunya kuma, ka zo zaka addabe mu?""" "Sum-sum Saleh ya fice daga gidan. Ummi ta zubawa Nana tuwon shinkafa da miyar yauƙi, har da man" "shanu, Nana sai haɗiye yawu take yi cikin farin ciki, kamar ta durƙusa ta ci a gurin." "Ummi ta shiga ɗaki, ta ɗaukko wa Nana dambun kifi ta ce ""Ungo, jiya na yi shi aka kai mini shago, na" "ɗebar miki""" "Nana ta karɓa tana murmushi ganin sa fal a roba, ta ce ""Allah ya yi miki abin da ki ke yi mini na alkhairi" "na gode sosai"" suka yi sallama Nana ta fita." "Tana cikin bin wani lungu, ta ji Muryar Saleh na kiran ta. Ta ƙara saurin da take yi, amma ya cimma ta." """Nana dan Allah ki saurare ni""." "Rikicewa ta yi, gani take a kowane lokaci za ta iya ganin Sayyid, ba ta san da wani yaren za ta yi masa" bayani ba ya fahimta. """Nana ki tsaya ki ji mana""" """Wallahi zan yi maka ihun kwarto, wace irin jaraba ce wannan ina ruwan ka da ni ne?"" Ganin tana ɗaga" "murya, kuma Akuyarsa ta yi kuka a unguwar, ya sanya sum-sum ya koma da baya." "Tana zumbuɗa sauri, ta je gida, ta san yana can yana jiran ta. Kawai ta ci karo da shi a wani lungu, yana" "zaune a kan wata sokawe, ya jingina da jikin bango, shikaɗai ƙwal a layin. Sai da ta razana, ta waiwaya" "bayan ta, cike da tsoron ko Saleh ya biyo ta." """Sayyid me ka ke yi a nan kuma, ba ka shiga shiga gida ba?""" """Ba zan iya shiga nikaɗai ba"" Ta miƙa masa hannu ta ce ""Taso mu tafi"" ya miƙa mata hannunsa. Sai dai" "tun da ya saka hannunsa a nata, sai da ya kalli fuskar ta." "Da suka je gidan, danƙam da mata, ana ta hayaniya. Ya rufe fuskarsa Nana ta yi sallama. Gaba ɗaya suka" "yi tsit, suka zubo wa su Nana ido, musamman ganin hannunta riƙe da na Sayyid." "Kawai ta ja hannunsa, suka nufi ɗakin su." """Nana kun dawo"" Sajida ta yi maganar, tana kokowa da zaninta tana fitowa daga ɗakinta, saboda kar su" wuce ba ta gan su ba. """Eh sannun ku"" daga haka ya tura ƙofar ya fara shigewa. Suna shiga ɗakin matan suka saka shewa, ɗaya" "ta ce ""In dai Namiji ne, yarinya za ta gama wannan iyayin ne""" "Nana su na shiga ɗaki Sayyid ya tsare ta da ido ya ce ""Nana ba ki da gaskiya""" "Gabanta ya faɗi cikin tsoro ta ce ""Me na yi?""" """Gumi ki ke yi a iya goshin ki, da karan hancin ki. Kuma tafin hannunki ya ya sanyi, zuciyar ki na bugawa" "da ƙarfi kuma da sauri. Kin yi wani abu da ki ke ɓoye mini ko?"" Haɗe rai ta yi ta fara ƙoƙarin ƙwace" hannunta daga nasa. "Sai kuma ya sassauta muryarsa ya ce ""Ki daina fushi, ba zan iya barin, duk wani abu na ƙi ya tunkaro" "rayuwata da ke ba, ki daina fushi""" """To sai ka din ga zargina da rashin gaskiya"" ta faɗa a hasale." "Ya girgiza kai ya ce ""Ba zargin ki nake yi ba. Na tabattar da wani abu ya faru ne, da ba za ki so na sani ba," "idan na sani zamu samu saɓani. Kin manta mu ba kamar sauran mutane ba ne. Kuma ina iya jin abin da yake ranki, kin manta ne?"" Ya yi maganar yana murmushi da shafo fuskarta. Dole ta saki murmushi." "Nana dai ta din ga yi wa Allah godiya, da ba ganta da Saleh ba." "Nana tana yi wa Allah godiya, ganin yadda jikinsa ya yi kyau. Duk da yana haki bai daina ba, amma yanzu" "yana cin abinci. Sayyid na matuƙar son zuwa masallaci salla, amma dole yake haƙura. Saboda da gayya" "matan gidan suke wata shigar, duk da ba tsayawa kallon su yake yi ba. Ga shi ba ya son kallo, amma yana" fitowa sai su yi shiru su zura masa ido. "Ita kanta Nana lamarin gidan ya ishe ta, ba ta ƙaunar zaman gidan nan ko kaɗan." "Maman Nana ta aiko mata da barkonon nan, har da awon kayan Abinci, tamkar ta san a halin da take ciki." "Ummi da kanta, ta je ta ɗauki barkonon, domin kuwa Nana daina zuwa gidan Ummi ta gaba ɗaya saboda" Saleh. Ayshacool "Abu kamar wasa har zuwa wannan lokacin, Sayyid ya kasa gane kansa, abin ya fara damunsa sosai da" "sosai. Ga shi ya kasa cewa Nana komai a kan hakan. Ita ma kuma ba ta ce masa ba, sabgoginta kawai take yi." "Tun Yamma Nana, ke ƙoƙarin shirya duk abin da za su buƙata, saboda washegari za su tafi Asibiti, kuma" "sammako take so su yi, saboda su ga likita da wuri." "Sai dai duk dauriya kawai take yi, wani irin zazzafan zazzaɓi ne a jikinta, ta kasa cin abinci. Babu abin da" "take son ci, sama ds kazar da Habu ya kawo farkon auren su. Ga shi ba ta son yin duk wani abu da zai ɗaga wa Sayyid Hankali. Ta fuskanci ko saɓani suka samu, ƙaramar magana sai ta sanya ya fara haki, ya fara nema ya faɗi." "Tana ƙofar ɗakinta, tana soya miya, su Barira su na hira, tana yi wa wata maƙwabciyar su kitso. Suke" "zancen wata mata a bayan layin, wai sai mijinta ya neme ta ya rasa, sai a yi kwanaki ba a ganta ba, sai bayan wani lokaci a tsinto ta a wani gurin, ko a ganta a ɗaki." "Barira ta kada baki ta ce ""Amma ta mayar da mijin nan tasono, ƙarya take yi gantalinta kawai take tafiya." "Meye matan auren ba sa yi yanzu?""" "Sajida ta ce ""A'a Barira, ki daina cewa ƙarya ne""" """Ke wallahi, ko rantsuwa na yi ba zan yi kaffara ba, a gidan uban wa Aljani zai ɗauke mutum ya kai shi" "wani gurin? Ke ni fa da ake cewa ana ganin aljanu, ko su tsorata mutum ban taɓa yadda ba, iskanci ne" "kawai da ƙaryar banza ce, ba wani aljan duk 'yan iska ne kawai." "Nana ta ji wani abu mai zafi ya soki zuciyarta, duk da ba da ita suke ba, kawai ta ƙura wa Barira ido, ko" ƙiftawa ba ta yi. "Tun Barira ba ta ankara ba, har ta lura, take ta ji tamkar an kwarara mata ruwan sanyi a jikinta, sai kuma" "ta ɗan tsorata ta ce ""Nana lafiya kuwa?""" Ayshercool 08081012143 Ayshacool "Tun da Jamila ta koma gida, jikinta a sanyaye yake, gani take yi, duk wanda ya ganta ya san abin da ya" "faru da ita. Mama kuwa baki ya ƙi rufuwa, saboda Jamila ta zo da abin Duniya. Kuma kamar yadda ta" "gaya mata, sarin kaya ta raka Hajiya, babu wani bincike ta yarda da hakan ta amince." "Ta zo ba ta iya bacci sam, da ta kwanta bacc6, sai ta ga tamkar za ta buɗe ido, ta sake ganinta, a wannan" gurin da suka je da Hajiya Sa'a. """Jamila"" Suwaiba ta kira sunanta, ta waiwaya ta kalle ta." """Wai ya na ga ki na abu kamar mara gaskiya ne?""" "Gaban Jamila ya faɗi ta ce ""Me na yi na rashin gaskiyar, me ki ka gani?""" """To ai gani na yi kin kasa sukuni, ki na ta wani mutsu-mutsu gaki nan dai""" """Dan Allah Suwaiba ki ji da abin da yake damun ki, ni babu abin da ya same ni, lafiya ƙalau nake """ "Suwaiba ta ce ""To ai shikenan""" **** "Nana duk sammakon da suka yi, su ne na goma sha ɗaya, a gurin ganin likita." "Wajen sha ɗaya na safe aka zo kan su, Nana suka shiga, sai dai wannan karon wani likitan daban suka" "samu. Suka gaisa Nana ta yi wa likitan bayanin komai. Tare da ba shi takardun gwaje-gwajen da aka yi masa, da kuma katin da aka rubuta masa magunguna." "Ya karɓa ya duba a tsanake, ya duba Bp ɗin Sayyid, ya duba ƙirjinsa da stethoscope." "Nana ta ce ""Doctor yaya jikin nasa? Me ka gani?""" "Bai kalli Nana ba ya ce ""Me yasa ba ku dawo follow up ba""" "Ta ce ""Ai ba a bamu lokacin dawowa ba. Dama ni ce naga yakamata mu dawo ɗin. mu na ta ƙoƙarin" "kuɗin allurar su haɗu ne, ko ba su haɗu ba, zamu yi ƙoƙari ko a anan Asibitin gwamnatin ne, sai mu yi" "booking a fara yi masa""" "Likitan ya ce ""Ki na ji na 'ya ta?""" "Ta ce ""Eh""" """Ai mijinki ne ko?""" "Sayyid ya jinjina kai. ""To a duniya babu wani abu da Allah ba zai iya ba, babu shi. Batun allura ki bar" "wannan a hannun Allah. Kuma dan babu kuɗin allaura ba za a daina ganinsa ba. Zamu ci gaba da gwada shi, mu na ba shi magungunan da suka dace. Idan Allah ya yassare kwa zo a yi daga baya. Kuma jikinsa Alhamdillah da sauƙi sosai da sosai. Jinin dai haryanzu bai sauka yadda ake so ba. Amma zai sauka da yardar Allah. Kawai ki din ga kiyaye damuwarsa da ɓacin ransa. Idan kuma akwai wani abu da yake damunsa, ki zauna da shi ku tattauna ki ga ta ina za ku shawo kan matsalar?. Amma babu wani abu in sha Allah"" Duk da ba lafiya likitan ya ba su ba, amma kalamansa akwai dattaku da ƙwarewa a kan aiki a" cikin sa. Dan haka sosai Nana ta samu relief. "Ya rubuta musu lambarsa ya ce ""Duk lokacin da za ku zo, ku kira ni, na baku ranar da nake aiki, ya zo ya" "din ga ganina."" Nana ta din ga yi masa godiya da addu'a shi da iyayensa." "Sayyid ya ja wata takarda, ya yi rubutu ya miƙa wa likitan. Likitan ya karɓa ya duba. Ya yi murmushi ya ce" """Madam, ashe kema babu lafiya ya ce na duba masa ke""" "Nana ta yi murmushi ta ce ""Rashin lafiyata, ai ba komai ba ce a kan tasa, ni na fi damuwa da shi ɗin dai""" """A'a tun da ya nemi alfarma, ai dole a yi masa""" "Ya duba Nana, ya yi wa Sayyid bayanin laulayi ne kawai yake damunta, ya rubuta mata abin da zai rubuta" "mata na magani. Ya kuma ba ta gwaje-gwaje. Sayyid ya ƙi tafiya, sai da suka yi gwaje-gwajen." "Suka koma, ya tabattar musu da babu wata matsala, satin cikinta uku da kwanaki, ya rubuta mata" magungunan da za ta yi amfani da su. "Suna tafe a adaidaita sahu, Sayyid ya kasa riƙe murmushinsa, ya kai bakin sa kunnen Nana ya ce ""Saura" "kwana nawa ki haihu?""" "Ta kwashe da dariya, ta ce ""Ina na sani, ko cika wata ɗaya bai yi ba ma, mu dai ci gaba da addu'a Allah ya" "bar mana, ya bamu ɗa na gari""" "Ya amsa da ""Amin.""" "A bakin titi, Nana ta yi sayayyar salak, saboda shi take sha'awar ci. Suka shiga layin gidan na su." "Su na zuwa gidan, Nana da sauri ta shiga banɗaki, saboda fitsarin da ya cika mata mara. Sayyid tsayawa" "ya yi, yai shiru yana ƙare wa ɗakin kallo." "Nana ta fito bai ce mata komai ba, ta ɗauki cylinder gas, ta ce ""Sayyid gas ya kusa ƙarewa, idan zaka iya" "fita in anjima sai mu je titi tare mu ɗuro""" "Ya ce ""To""" """Bari na sake ɗumama miyar""" "Ta fito tsakar gidan kenan, Sajida ta ce ""Nana, Allah ya taimake ki, da tuni da ke za a tafi bayar da shaida""" "Cikin rashin fahimta Nana ta ce ""Shaidar me?""" Ayshacool """Jiya hirar da ku ka yi, har ki ke yi wa Barira faɗa, a kan matar nan. Daga jiyan nan zuwa yau magana har" "ta kai kunnen matar. Ta din ga kuka mijin ya ce ba zai yarda ba da 'yan uwanta. Da yyayyenta ne za su zo su zane Barira. Mijin matar ya hana aka kai ta police station. Tun bayan fitar ku tana can, duk sai da" "muka je bayar da shaida. Wataƙila dai kafin magariba a sako ta, ta dawo gida.""" "Nana ta numfasa ta ce ""Gara da Allah ya sa ba na nan, dan babu inda zan je, shi yasa a rayuwa yake da" "muhimmanci mutum ya iya bakinsa. Wannan tara matan da ku ke yi, ku na surutai marasa amfani duk ba hanya ce mai ɓullewa ba""" "Sajida ta ce ""Wallahi haka ne, shi yasa ki ke burge mu ma""" """Allah ya kyauta""" "Har Nana ta yi haɗin salak ɗin ta, ta fara ci, ya lura ba ta fahimci abin da yake faruwa ba, shi ma kuma bai" "gaya mata ba, ya ci abincin. Ta gama ci ta kalle shi ta ce ""Sayyid, ka yi mini addu'a, Allah ya sanya kar na yi aman salad ɗin nan, na rufe sauran anjima zan sake ci""" """Kin cika yaji, sai kin yi ciwon ciki ko?""" "Ta ɗan waro ido ta ce ""Dama ka gani?""" """Eh ina kallon ki""" "Ta ɗan yi murmushi ta ce ""Idan babu yajin, ba zai yi daɗi sosai ba. Amma yanzu ya ka ke ji a jikin ka?""" """Ba sauƙi""" """Subhanallah, ba sauƙi kuma?""" "Ya ce ""Eh, kin je ki na hira da likita a gabana""" """Amma ko ba komai, ya kwantar mini da hankali, bai ce mini zaka mutu ba, kalamansa sun bani ƙwarin" "gwiwar da yakamata na samu"" ta yi maganar ƙwalla na cika mata idanu." "Ya girgiza mata kai ya ce ""Kar ki bari su zubo""." """To ba kai ne ba, komai na yi sai ka ji haushi na?""" "Murmushin sa mai matuƙar ƙayatarwa ya yi, ya ce ""Ba haushinki nake ji ba, tsaro nake ba ki, saboda" "tawa ce nikaɗai. sourire (smile) ki yi murmushi mana"" ta noƙe kafaɗarta tana tura baki,ta juya masa baya." "Ya matsa bayan nata, ya sumbaci saman bayan ta, ya zagayo da hannunsa ta cikinta, ya kwantar da" "kansa a kan kafaɗarta. Gaba ɗaya jikinta ya yi sanyi. Damuwa ce ya ziyarce zuciyarsa, jin yadda Nana ta saki jiki sosai da rungumar da ya yi mata, ko ba a gaya masa ba ya san abin da yake ranta, tuna cewar babu abin da zai iya tsinana mata, ya sanya a hankali ya raba jikinsa da nata, wani irin tausayinta na ratsa" ilahirin jikinsa. "Ta maze cikin yaƙe ta ce ""Sayyid, ya na ji ka yi shiru ne?""" "Ya girgiza kai ya ce ""Babu komai""" """A'a akwai wani abu. Dama likita ya ce mu zauna na tambaye ka, ko akwai wani abu da yake damun ka," "haryanzu fa jininka bai sauka ba Sayyid""" "Ya ɗan sake yin guntun murmushi ya ce ""Damuwa ai akwai ta, ba na son ɗaga miki hankali ne kawai." "Haryanzu ina tunanin inda su Habu suka tafi, suka bar ki da ɗawainiya, Kodayake ko suna nan ma, kula" "da ni ba dolen su ba ne. Sai wahala ki ke sha, wallahi idan ina tuna hakan, sai na ji tamkar numfashina zai" "ɗauke a cikin damuwa nake sosai da sosai. Ba na son saka ki a damuwa ne kawai""." "Nana ta tattara hankalinta ta matsa kusa da shi, ta riƙo hannunsa, ta kalli idanunsa da suka yi jawur." """Idan su Habu ba hakkinsu ba ne kula da ki. Ni yanzu ya zama haƙƙina, na san ba a banza Allah ya haɗa mu ba. Mu ci gaba da addu'a Allah ya kawo mana komai da sauƙi. Amma ina fatan dan Allah ka daina damuwa, idan ciwon nan ya matsanta maka a jikina nake ji, ka daina ba na so"" ta ƙarasa maganar cikin" shagwaɓa. "Kafaɗarta ya ciza cikin wasa, yana rungume ta. Tamkar ba a cikin damuwa suke ba, suka ci gaba da raha," "duk da yadda hayaniyar mata ta cika gidan, tamkar a na taro, saboda dawowar Barira, an cika gidan ana mayar da yadda aka yi." "Ana fara kiran sallar magariba, ta kai masa ruwan ɗumi banɗaki ya yi alwala." """Za ka je masallaci ne?""" """A'a a nan zan yi""" """To yi sallar. Nima sai na yi muje mu ɗuro gas, ko rabi ne sai kuma na sayo gawayi, Ummi ta bani kurfoti," "na din ga haɗawa da shi"" Ya jinjina mata kai ya tayar da salla." "Yana kallon ta ta idar, ta buɗe jakarta ta ɗebo sauran kuɗin da suka dawo da su, ta nufi wardrobe ta" haɗa su da waɗancan kuɗin. Kawai ta ga kayan wardrobe ɗin a hargitse. "Mamaki ya kama ta, ta san Sayyid ba ya taɓa mata wardrobe, kuma ita ba a haka ta bar wardrobe ɗin ba." Ayshacool "Ta janyo jakar gidan Sarkin baka, ta duba ta ga kuɗin nijar a ciki. Ta laluba ta ɗauki ledar, da kuɗin" "Nigeria ke ciki ta rasa. Ta watso kayan wardrobe ɗin gaba ɗaya, tana ƙara haskawa da fitilar wayarta." "Yana tsaye yana kallon ta. Muryarta na rawa ta ce ""Sayyid""" "Ya kalle ta. ""Kuɗinmu, kuɗin da ka bani na saka a cikin wardrobe na...naa..ajiye a nan ban gani ba, ko ka" "ɗauka?""" "Ya yi shiru yana kallon ta, a zuciye ta nufi hanyar fita daga ɗakin, ya riƙe ta. Jikinta yana tsuma take" "ƙoƙarin fizgewa amma ya riƙe ta yana girgiza kai ya ce ""Kar ki yi magana, ki yi shiru ko waye mu bar wa" "Allah. Tun da na shigo, na ga alamar an buɗe ɗakin. Kuma laifinmu ne, da ba mu saka mukulli ba, muka rufe ɗakin kawai.""" """Sayyid ba a yi mana adalci ba. Kuɗin Abincinmu da maganinka, sun kwashe gaba ɗaya wace irin masifa" "ce wannan? Daga wannan sai wannan ya ake so na yi ne?"" Ya riƙe ta gam yana shafa bayan ta, a hankali ya ce ""Ki yi haƙuri, ki daina ɗaga murya, akwai Allah""" "Kuka take yi iya ƙarfinta, tana sheshsheƙa, ya rungume ta gam a jikinsa, shi kansa ya ji zafi da raɗaɗin" "satar da aka yi musu. Ba iya kuɗi ba, har da wasu daga kayan amfaninsu na ɗakin an ɗauka, ya san kuma" "hakan sabon ƙalubale ne, saboda ba su da wata hanyar samun kuɗi a yanzu." "Ji ya yi jikin Nana ya saki, kuma jikin yana ɗaukar sanyi. Karkarwa ta fara yi, tamkar ana jona mata" shocking. "Cikin matsananciyar damuwa, ya zauna da ita a jikinsa, ya ɗauki wayarta da ta saki a gurin, yana haska" "fuskarta. Ya ga hawaye na fita ta gefen idonta. Hannayenta da ƙafafuwanta su na lanƙwashewa, goshinta" kuma yana tsatstsafo da gumi. "Jin ta ta yi, jingine da wani abu da ba ta san ko mene ne ba. Ta shafa abin ta ji ƙurzunu-ƙuruzunu, tamkar" "dutse. Gurin baƙi ƙirin duhu ya gauraye gurin, ko tafin hannunta ba ta iya gani. A hankali haske ya fara" "shigowa gurin, har gurin ya yi haske ba ki ɗaya. Ta ɗaga kanta ta ga ba ta iya gano ƙarshen ɗakin." "Jin tari ta yi a bayan ta, ta waiwaya da sauri, ta ga Ƙaisar a zaune lulluɓe da wani abu mai haske sosai." """Ƙaisar. Ba ka da lafiya?"" Ta yi maganar tana nufar inda yake." "Ya yi shiru bai yi magana ba. Ta sake cewa ""Dama kuma ku na rashin lafiya, kamar ka canza gaba ɗaya""" "ya yi murmushi ya ce ""Mu na rashin lafiya mana, guba na ci"" Ta waro ido ta ce ""Guba kuma? Me yasa?""" """Tsohon nan na jikin mijinki, ya bani.""" """Kuma ka sha? Wai meye alaƙar ka da shi? Kuma dan Allah me yasa yake bibiyar mijina?""" """Ba wannan ba, me yasa ki ka kira ni?"" Cikin mamaki ta kalle shi ta ce ""Kamar yaya? Ni ban kira ka ba ai""" """Fushi da ɓacin rai, duk wanda ki ka yi tamkar kin kira ni ne. Kuma ni yanzu ba ni da wani tasiri sosai," "saboda jinya nake yi. Babu wanda ya san ina nan. Giyaz ya saka ni a gaba, ya mamaye Library ɗi na, yanzu rashin ganina zai sanya ya ci gaba da cutar da ku. Ba zan iya wani abu ba sosai yanzu, sai dai zan iya tasiri a kan bil'adama." "Duk ba wannan ba, duba can.""" "Ta ɗaga kai ta kalli inda ya nuna mata, Library ɗin Ƙaisar ta gani. Ta ga gangar jikin Sayyid a kwance." "Tsohon nan ya ɗaɗɗaure shi da wata irin igiyar ƙarfe. Ƙasan gadon da yake kai kuma, wata irin wuta ce take ci a ƙasa. Nana ta zabura a rikice, ta ce ""Wannan ai Sayyid ne""" """Ƙwarai shi ne, ba wani ba. Kuma Giyaz shi ya sanya masa matsalar da ku ke ciki na auratayya. Sai dai" "abu ɗaya zan iya gaya miki. Matsalar zuciya da hawan jini da yake fama, wannan ciwo ne yake damun sa. Amma Giyaz na assasa wani abin. Kuma... Amma dai shikenan""" "Nana ta buɗe baki za ta yi magana, ya ce ""Kar ki tambaye ni komai, kin san sharaɗin. Kalli"" ya yi maganar" yana sake nuna mata gurin. "Alhaji Fatuhu ta gani, ta yi ƙuri da ido ta ce ""Kamar na san wannan""" """Ba kama ba ce ba kin san shi, ciwo ne da zafin sihirin da aka yi masa ya mayar da shi haka. Sai kuma" "albishir da nake yi miki, da ƙanwar ki ta zama cikakkiyar 'yar ƙungiyar asiri. Ɗayar kuma wannan bararojin da ta taɓa baki magani, ta aura mata ɗanta, wanda yake baƙin aljani ne. Kuma ta tarkato kan iyalanta duk su na jikinta. Kuma kowanne akwai abin da yake mora a jikinta. Ke in taƙaice miki ma, a" kowane lokaci za ta iya rasa hankalinta ko ma rayuwarta gaba ɗaya. Ayshacool "Shikenan bissalam""" """Ƙaisar"" sai kuma ta yi ido huɗu da Sayyid." """Kin tashi?"" Ta yinƙura ta tashi zaune, tana kallon ɗakin." "Sayyid ya ce ""Ƙaisar ɗin ba shi da lafiya ne?"" Ya yi maganar yana tsare ta ido." """Wane Ƙaisar ɗin?""" """Tambayata ki ke yi?"" Shiru ta yi, ita ba ta iya tuna koma ma a cikin abin da ya faru ba. Idonta ne ya" "sauka a kan kayan da suke gaban wardrobe a ƙasa, sai kuma abin da ya faru ya faɗo mata. Afujajan ta tashi ta sake nufar wardrobe ɗin, tana zazzage kayan tana kuka." """Kuɗin nan fa babu su, an kwashe ki daina wannan dube-duben"" ya zauna ta yi shiru ta sanya kayan a" gaba tana kallo. "Ya yi mata shiru ya ƙi kula ta, ya kwanta a kan katifa, yadda take a hasalen nan, idan ya matsa faɗa za su" yi. Cikin ƙanƙanin lokaci nannauyan bacci ya yi awon gaba da shi. "Barira na kwance a ɗakinta, ta yi ɗaiɗai tana bacci, ta ji kamar ana karta mata farce a ƙafafuwanta. Har" "ta maze ta ci gaba da bacci, amma ta ji an cigaba. A fusace ta ce ""Gali meye haka, za ka din ga karta mini" "faratanka, ina cikin bacci ne?"" Shiru bai amsa ba. Ta laluba ta ji yo ƙeyarsa a can ƙarshen gado, yana" "bacci. Ta koma ta kwanta, amma ta ji an cigaba, ta tashi zaune tana zabga ashariya." "Ta kunna fitila, ta ga babu kowa. Ta yi tsaki ta sauka daga kan gadon, ta fito tsakar gida domin ta yi fitsari." "Bayan ta fito daga banɗakin, kanta ko ɗan kwali babu, kawai ta yi karo da Nana a tsakiyar tsakar gidan tana yi mata wani irin mugun kallo." "Ta haska Nana ta ce ""Nana lafiya kuwa?""" "Sai dai Nana ba ta yi magana ba, ta sake haska ta, za ta yi magana. Ta ga ta rikiɗe ta zama wata irin" "ƙatuwar mage, baƙa ƙirin, girman ta ya yi na tunkiya ƙosashiya da ita, ta yo kanta tana buɗe haƙora." "Da gudu Barira ta shiga ɗakinta, tana ihu tana kiran sunan Gali." """Ke mahaukaciya, mene ne haka za ki din ga ihu kina kiran sunana a tsohon daren nan?""" "Ba ta ce masa uffan ba, ta duƙunƙune, tana mayar da numfashi. Ta tsorata sosai da sosai, da ƙyar ta" "samu ta yi bacci. Sai dai a cikin baccin ma, mafarkin magen nan kawai ta din ga yi tana bin ta, tana karta mata farata tana cizon ta." "Sayyid kuwa yana jiyo kururuwar Barira, hakan bai dame shi ba, sai ganin Nana da ya yi a zaune, ta haɗa" kai da gwiwa. "Ya yinƙura ya tashi zaune, bai ce mata komai ba, ya kwantar da ita a kan katifar, ya rufe su da bargo ya" "rungume ta yana shafa bayanta. Yana jin ta tana kuka, har ta yi ta gaji bacci ya ɗauke ta." "Dauriya kawai yake yi, amma ji yake tamkar ya taya ta kukan." "Washegari, Barira ta tashi da matsanancin zazzaɓi da ciwon kai, ta din ga yi wa mijin kuka, tana cewa ya" "mayar da ita gidansu, mayu sun kama ta a nan gidan, ba za ta yadda a kashe ta a banza ba. Babu yadda ya iya ya tattara ta ya kai ta gidansu." "Kwanki biyu da sace kuɗin nan, Nana ta rasa abin da yake yi mata daɗi. Dubu talatin ce ta ragu a" "hannunta, shi ma cikin irin kuɗin da ta zuba a jakarta ne suka fita da su. Kuɗin Nijar ɗin kuma ba ta san ma ina za ta a canza su ba. Bayan haka tayi tunanin idan Habu ya dawo fa, me za ta ce masa? Ta din ga tunanin yadda za ta yi da dubu talatin ɗin nan, ba tare da ta rushe gaba ɗaya ba. Ga shi magungunan da" "yake sha kawai, na wata ɗaya dubu goma sha biyu take sayen su." "Sai dai kamar yadda yake nanata mata, ta yi haƙuri, ya sanya ta fauwwala wa Allah lamarin." "Kwana biyar da kwashe kuɗin nan, Sayyid ya hana Nana gaya wa kowa. Sai dai cikin dare ba ta iya bacci," "saboda lissafi da tunani. Ta kira Ummi ta tambaye ta batun barkono, ta ce ana ta saya, ta sayar da ya kai rabin buhun. Kayan Abinci da Mama ta haɗo mata da su, take ta cancana musu." "Da daddare ba ta iya bacci, saboda damuwa da tunani, sai dai abin yana damun sa fiye da yadda yake" "damun ta. Su ka wayi gari, ya tashi jikinsa babu daɗi, yana ta numfarfashi." "Abin Duniya ya ƙara damunta, ya kuma ƙi cin komai. Muryar Barira ta jiyo a tsakar gida, da ta dawo, tana" maganganu tana ba wa su Sajida labari. """Mayu sun kama ni a gidan nan, kuma da ƙarfina na dawo, wallahi sai sun ci uban su, kurwata ta fi ƙarfin" "mutum""." "Sajida ta ce ""Ban gane mayu ba, suwaye mayun kuma?""" "Barira ta ce ""Oho, ki zuba ido ki gani, Allah zai tona musu asiri""" Ayshacool """Ni fa ba na son kurman baƙi, a masu shigowa ne mayun, ko kuma zaunannun gidan""" """Na ce ki zuba ido ki ga ikon Allah""" "Bai fi mintuna biyar ba, wani irin hayaƙi, mai azabar yaji, ya turnuƙe gidan." "Nana da take lafiya ƙalau ma, ta fara tari." "Shi m tarin yake yi, numfashinsa kamar zai ɗauke, ta ɗaukko mafici ta din ga yi masa fifita. Ta gaji ta tashi," "da nufin ta je ta ga me ake ƙonawa yake wannan uban hayaƙin haka. Amma ya riƙe hannunta ya hana ta. Haka suka wuni a galabaice. Sajida ma sai bala'i take yi, tana cewa Barira za ta kashe ta da hayaƙi." """Wai Sajida ko ke ce mayyar nan ne?""" """Ke kama bakin ki, wallahi ki ka ce mini mayya, sai mun yi shari'a da ke""" "Barira ta ce ""Sai ki saurara mini, tun da dai ba ke ba ce"" Haka suka wuni, Barira tana gana musu azaba," da wannan azababben abin da take zubawa a cikin murhu. "Washegari ma, azabar hayaƙin nan ce ta tashi su Nana, numfashin Sayyid tamkar zai ɗauke saboda azaba." "Nana dai ta ci gaba da daurewa, amma yamma na yi, Barira ta sake cika kurfoti da gawayi, ta tayar da" wuta ta afka hayaƙin nan. "A fusace Nana ta fita, ta tarar da ita tana ta girgiza kurfotin, tana zuba wani abu a ciki." "Nana ta ce ""Barira, dan zatin Allah ki daina zuba wannan abin. Ina da mara lafiya a ɗaki. Yana da" "matsalar numfashi, jiya kwana muka yi babu bacci. Kuma da sassafe kin banka wani, kuma yanzu ma ga shi kina sake kunnawa""" "Ta kalli Nana ta ce ""Ai duk wanda ya hana uwar shi bacci, wallahi shi ma ba zai yi ba""" "Nana ta ce ""Kamar yaya kenan?""" """Kamar yadda ki ka ji""" """Ni dai koma mene ne, ki yi haƙuri idan ba ki yadda ba, zo mu je ɗakin ki ga halin da yake ciki""" """Babu ruwana da halin da yake ciki, kurwata ce ta fi ƙarfin duk wani maye wallahi""" "Nana ta ce ""Barira mu ne mayun da ki ke faɗa dama? To Barira ko za mu ci mutum ma ci taki, jiki duk" "dauɗa?""" """Ko ma duk uban mene ne, tun da aka kama ni aka lasa, an ji zaƙin kurwa ta, wallahi sai mutum ya ci" "ubansa, miyagun banza kawai""" """Mu ne mayun Barira?""" """Eh ku ne, ko na ce ke""" "Nana ta ƙarasa daf da Barira ta damƙi tsintsiyar hannun Barira ta ce ""Ki ka ce ni mayya ce?"" Barira ta" "yinƙura za ta fizge hannunta, ta yi bala'i. Kawai ta ji jikinta ya yi wani irin nauyi, kuma jikin ya yi mata" "wani irin sanyi, ta kasa motsa komai. Kawai ta silale ta faɗi ƙasa." Ayshercool 08081012143 Ayshacool """Gidan Nana kuma? Ina ne gidan Nanan, kuma matsalar mene?""" """Baba mutanen unguwa sun taru, za su dake ta, kar su kashe ta ni ban ya zan yi ba""" "A sukwane Baba ya miƙe ya ce ""Ƙarya ne. Nanan za su kashe mini, ai zan yarda kowa zai iya ɗaukko" "magana a cikin ku, amma ban da Nana. A can gidan gadin nata ne za su dake ta?""" """Baba wane gidan gadi kuma, ai sun bar gidan tana nan kusa da ni, ka manta ne? Ka cewa Nasiru ya rako" "ka ya san gidan""" """Gani nan zuwa"" ya kashe wayar ya yi waje da sauri." "Ummi ta tsaya a bakin ƙofar, tana ta ba su haƙuri. Amma sai nema suke yi su ture ta, su shiga ɗakin." """To ban da wulaƙanci ma, ta shige ɗaki taƙi fitowa, da yake ba ta da gaskiya. Maimakon mijinta ya fito ya" "bayar da haƙuri, shi ma ya yi zamansa saboda rashin tsoron Allah, da rashin gaskiya""" "Ummi ta ce ""Mijinta ba shi da cikakkiyar lafiya, ita ma aljanu sun buge ta, dan Allah ku yi haƙuri"" Sai dai" "abin ya fi ƙarfin Ummi, ƙoƙarin hankaɗe ta kawai suke yi, su cimma Nana." "Ana haka sai ga maƙwabcin su Nana, tare da jami'an tsaro. A dole mutanen suka saurara. 'yan sanda" "suka ce, a tafi da Barira Asibiti, abin da likitoci suka ce, da shi za a yi amfani." "Ana haka Baba ya ƙaraso, cikin tashin hankali." "Ummi na ganin sa ta yi ajiyar zuciya. Ummi ta ce ""Baba ka zo?""" """Eh, ina Nanan take, kuma uban me ta yi za a dake ta da?""" """Ai gama 'yan sanda sun zo, saɓani suka samu da wanda suke zaune gida ɗaya, shi ne suka ce mayya ce""" "Baba ya ce ""Maita kuma? In ji uban wa?""" "Mijin Barira ya ce ""Ga shaida Baba, kalli matata a baje a kwance""" """Kuma sai ka ce 'yata mayya ce? To wallahi ƙarya ne, kaf danginmu babu mayu, ku dai nemo wani abun," "ba maita ba wallahi"" 'Yan sanda suka shiga maganar, aka tafi da Barira Asibiti." "Sai da aka bar 'yan sanda biyu, gudun abin da ka iya faruwa, saboda matan da abun ya faru a gaban su," su na ta ƙara balbalawa wutar fetur. Tare da mayar da abin da aka yi da wanda ma ba a yi ba. Gaba ɗaya zancen ya zagaya unguwa. "Har sha ɗayan dare case bai ƙare ba, Nana ta farfaɗo ta ga Ummi a ɗakin su, ga duhun dare ya fara yi." """Ummi lafiya kuwa?""" """Ina fa lafiya Nana, meya haɗa ki da mutanen gidan nan, ga shi ana cewa ke mayya ce""." """Mayya kuma?""" """Eh mana, yanzu case na hannun 'yan sanda, Baba yana can tare da su, ana jiran likitoci su faɗi" "sakamakon binciken su.""" "Nana ta gaya wa Ummi iya abun da ta iya tunawa. Sai dai ta sha mamaki, ta ji wai Baba ya zo kan" matsalar ta. "Ta kalli Sayyid da yake kwance lamo, abin Duniya duk ya dame shi." "Sajida ta haɗa kayanta, ta gudu ta ce ba za ta iya kwana da Nana a gidan ba." "Sai zuwa da safe, Likitoci suka tabattar da anemic shock ne ta samu, bayan binciken ƙwaƙwaf da suka yi," "suka gano ta yi ɓari sati biyu baya, ta kuma zubar da jini sosai ba ta je Asibiti ba. Ta zo ta yi zazzafan zazzaɓi na typhoid amma suka alaƙanta hakan da mayu, nan ma ba a je Asibiti ba. Hakan ne ya haddasa faɗuwar ta. Bayan fito da sakamakon, mijinta da 'yan uwanta suka ce ba su yarda ba, sakamakon ƙarya" ne kawai aka gaya musu. "Ga Barira ta farfaɗo, tun a cikin daren ma, har ta ci Abinci, amma suka ci gaba da surutu a kan Nana" mayya ce. "Ummi tare da su Nana ta kwana, saboda tsananin tsoro. Dan da gidanta akwai guri can za su tafi ma. Sai" "dai tashin hankalin abin da ya faru, ya sanya jikin Sayyid rikicewa gaba ɗaya, ya zamana kamar ma ba ya gane wanda yake kansa." "Hankalin Nana ya yi mummunan tashi, ga shi babu isasshen kuɗin tafiya Asibiti. Ta kuma san tashin" "hankali, da damuwar abin da ya faru ne, ya sanya jikin nasa ƙara rikicewa." "Nana ta rasa abin da yake yi mata daɗi, ga matan gidan kowacce ta koma gidansu, sun ƙi dawowa gidan" wai tsoro suke ji. "Ummi ce ta yi sallama, Nana ta amsa ta yi mata izini ta shiga ɗakin. Hannunta riƙe kular Abinci. Ta kalli" "inda Sayyid ke bacci a wahale, numfashinsa na fita sama-sama. Cikin damuwa Ummi ta ce ""Yanzu Nana haka jikin nasa ya koma?""" """Wallahi Ummi, gaba ɗaya hankalina a tashe yake""" """Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ana wata ga wata""" "Cikin damuwa da rashin fahimta ta ce ""Me ya faru?""" Ayshacool "Cike da karaya, da matsanancin tausayin ƙanwarta ta ce ""Mai gidan nan ne, ya je ya same ni, ya bani" "dubu goma sha biyu, wai ga sauran kuɗin ku nan, ku tashi. Ba ya son tashin hankali, kuma ga sauran 'yan" "hayar sun ce ko ku tashi, ko ya mayar musu da kuɗinsu su tashi. Nayi-Nayi ya ƙara wani abu, tun da ko wata ba ku yi ba, amma ya ƙi wai wannan ɗin ma da ƙyar ya samo su ya kawo.""" "Nana ta jingina da jikin bango tana maimaita ""Innalillahi wa Innalillahi raji'un""" """Nana mene ne abin yi yanzu?""" "Nana ta girgiza kai, jiki a sanyaye ta ce ""Ban sani ba Ummi""" """To ko wani gidan za a nemo? Sai na koma na neme shi, na roƙi alfarmarsa?""" "Ta girgiza kai ta ce ""A'a Ummi, an riga an yi mini mummunan tambari a unguwar nan, abu ne mai wahala" "ma mu sake samun wani gidan a unguwar nan""" """Bari na kira Baba na ji me zai ce""" "Nana ta ce ""A'a Ummi, kin san halin Baba, kar ranki ya ɓaci""" """To Nana ya zamu yi, dole a kira shi mu ji me zai ce"" Ummi ta kira lambar Baba, yana ɗaga wayar" "muryarsa a sama ya ce ""Ya kuma aka yi, ba an kashe case ɗin a gurin 'yan sanda ba?""" "Ummi sai da ranta ya sosu, amma ta maze ta ce ""Baba ba wannan ba ne. An kori su Nana daga gidan da" "suke ne, mai gidan da suke ya ce sai sun tashi""" """To sai kuma aka yi yaya? Ni zan nemo musu wani gidan? Ko kuma mijinta ne yakamata ya nemo musu" "wani?""" """Baba ka fa zo gidan nan, ka ga halin da mijin nata yake ciki na rashin lafiya, saboda haka aka kore shi" daga gurin aikin gadi. Dan Allah Baba ka yi wani abu a kan yarinyar nan. Nana yarinya ce ƙarama "pressure ta yi mata yawa.""" """To Ummi ya ki ke so na yi? Ni dai nan gidan babu gurin da zan ajiye ta, ita da mijin nata, idan kuma ke ki" "na da guri ki taimaka ki ba su. Idan ba haka ba ta nemo 'yan uwansa su ɗauke shi, su rakata inda danginsa suke. Kin san dai nan gidan idan ta dawo, abin da za ta ci ma aiki ne. Nima yanzu sai abun da aka samo aka bani""" "Hawaye ya cika idon Ummi, cike da takaicin yadda Baba bai fiye damuwa da damuwarsu ba. Ta ce ""Baba" "da ina da inda zan ajiye Nana da mijinta, wallahi ba zan kira ka ba""" "Nana ta ce ""Ummi, dan Allah ki katse kiran nan, nima ba zan koma can gidan ba.""" "Tarin Sayyid ta ji, ta mayar da hankalinta kan sa, ta nufe shi tana faɗin ""Sannu Sayyid""" """Ki ba ni ruwa"" ta amsa da to. Ta ɗaukko ruwan leda, ta buɗe masa ya tashi zaune ta fara bashi." """Sannu Sayyid"" Ummi ta faɗa cikin tausayawa, kallo ɗaya ta yi masa ta gane yana jin jiki. Da da ne, kome" "za a yi,ba zai bar gashin nan a buɗe ba. Amma yanzu ba ta gashin yake yi ba, ga fuskarsa duk ta kumbura. A zuciya irin ta Nana, ta san ko a titi ta tsince shi a wannan yanayin, ba za ta iya tafiya ta rabu da shi ba," balle mijinta. "Ƙarar da wayarta ta yi ne, ya sanya ta dawo hayyacinta. Ta ɗaga wayar tare da yin sallama." """Ke Hansai, ina ta kiran wayar ki, amma ki ka ƙi ɗagawa?""" "Ummi ta ce ""Eyya, ba haka ba ne Uwani,ba na kusa ne, ya gida ya mutanen garin?""" """Lafiya ƙalau, ya na ji muryar ki ƙasa-ƙasa, laulayi ko rashin lafiya""" "Ummi ta yi yaƙe ta ce ""Ba gara a ce laulayi nake ina kwance ba, da abin da yake faruwa""" """Subhanallah, meyafaru?"" Kasancewar Uwani kaka ce a gurin su Nana, ƙanwar kakarsu ce, da kakarsu" "wadda Nana ta ci sunanta da Uwani, uwa ɗaya uba ɗaya suke. Sai dai ita tana can Garko da iyalinta. Ummi ba ta ɓoye mata komai ba, ta gaya mata. Uwani ta rafka salati. Ta ce ""Sai an yi magana ku nuna ku mutanen birni, kun fi mutanen karkara wayewa. Ina wayewar take. Aikuwa sai na kira Isa na ci ubansa mara mutunci. Tuntuni nake ganin take-takensa kamar har da ƙiyayyar uwar su, take shafar su a gurinsa. Ai Imrana yana zuwar mini nan. Ya hana kowa riƙe su kuma shi yana yi musu riƙon sakainar kashi. Yanzu ina duk sauran 'yan uwanki Ummi, ina 'ya'yan Atine, ina su Gaddafi da ba za ku iya taruwa ku rufa wa" "'yar uwakku asiri ba?""" AREWABOOKS """Wallahi Uwani mun yi iya yinmu ne..""" Ayshacool """Rufe mini baki, ina wani iya yinku, kuma duk wanda ya ce mana mayu Allah ya isa bamu yafe ba. Mu" "bamu gaji maita ba, balle a saka yarinya a gaba a tsangwame ta." "Na san babu lallai ta iya zaman ƙauye, amma mu nan akwai ɗakuna, har ma da gida da babu kowa, idan" "za su iya zama ta yi jinyarsa. Babu mai damun ta, kuma babu mai cewa ta tashi." "Amma tabbas kun ji kunya, idan har ku ka bari Asma'u ta wulaƙanta, a ce an rasa inda za ta zauna, ta yi" "jinyar mijinta, yawan ku kun zama taron tsintsiya babu shara."" Ummi ta yi shiru, Uwani akwai kirki da karamci, amma idan ta botsare tana faɗa, to duk gaskiyar ka, sai dai ka yi haƙuri. Ta gama faɗan ta, Ummi ta kashe wayar." "Ta kalli Nana, ta ga yadda ta tattara hankalinta a kan mijinta, tana ba shi Abincin da ta kawo musu, sai" "lallaɓa shi take, da alamu abincin ma ba ya so." """Nana, kin ji abin da Uwani ta ce?""" "Nana ta girgiza kai ta ce ""A'a." """Cewa ta yi idan za ki iya zama, ku tafi can Buda ki kula da shi, akwai inda za ku zauna. Kin ga nan tun" "Baba ya san maganar maitar nan, kamar Mama ta ji ne. Ita kuma kin san gishiri za ta ƙarawa abin ta yi ta" "bayar da labari. Amma ban sani ba ko ki na da wata shawarar?""" """Ummi wace shawara? wanda yake ruwa ko takobi aka miƙa masa, ai karɓa zai yi. Sai dai shi nake" "tausayawa, amma ba ni da wata mafita da ta wuce wannan ɗin. Ni in dai zan samu inda zamu zaune na" "kula da shi, ba komai zan zauna ko a cikin dutse ne ba ƙauye ba""" """Kin tabattar Nana? Da wayonki fa sau ɗaya Baba ya taɓa bari, muka je muka kwana biyu""" "Nana ta ce ""Ba komai, zan zauna""" "Sayyid ya sanya hannunsa biyu, ya damƙe na Nana." "Nana ta kalle shi ta ce ""Sayyid, mene ne?""" "Idanunsa sun kaɗa sun yi jawur, wata jijiya a saman goshinsa ta ɗaga ta kumbura, fuskarsa ta yi jawur." "Laɓɓansa sauka din ga karkarwa yana son ya yi magana, Nana ta girgiza kai ta ce ""Ba sai ka yi magana ba Sayyid. In sha Allah duk rintsi ina tare da kai, har Allah Ubangiji ya baka lafiya"" Ummi ta kasa jurewa ta" fashe da kuka. "Nana ta ce ""Ummi idan ki ka yi kuka,ni ya zan yi? Kun saka ni a tsakiya, nama fi ku juriya, har da kai ma""" "ta yi maganar tana murmushi bayan saka idanunta cikin na Sayyid, duk da idon nata a cike da hawaye." """Ummi ki gaya wa Uwani na amince""" "Ummi ta share hawayenta ta ce ""To shikenan, ya za a yi tafiyar to?""" """Ina ga a sayar da kayan ɗakin nan, katifar ta ishemu, sai a sai ledar ɗaki, sai kayan sawarmu""" """Nana, kina amarya amma a ce ɗakin ki babu kayan ɗaki, haka za ki je ki zauna? Kin san mutanen ƙauye" "ba sa raina abin surutu dai""" """Ummi ai ba ado da kwalliya zan je ba. Kuɗin kayan ma riƙe saboda ɗawainiyar abinci da kuma magani""" "Ummi ta ɗan yi shiru ta ce ""Kuma haka ne, yanzu zuwa gobe in Allah ya kaimu, zan samo dillalai su saya""" "Cikin sauri Nana ta ce ""A'a Ummi, ba na son ci gaba da zama a unguwar nan, ban san me za su yi mana" "ba. Idan da hali a nemo su yau kawai. Su saya gobe in Allah ya kaimu mu tafi""" """To shikenan, bari na fita na gani""" * "Yana zaune a cikin office ɗin sa, ya ɗora ƙafafuwansa a kan tebur, yana juyi, ya din ga kiran lambar cike" "da fatan a ɗauka. Har ya yanke tsammani, kawai ya ji ta ɗauka, sai dai ta yi shiru." "Da sauri ya sauke ƙafafuwansa ya ce ""Hello"" ta yi shiru ba ta amsa ba." """Hello ki na ji na?""" """Eh"" ta amsa a raunane." """To ba za ki yi mini magana ba?""" """Ba cewa ka yi ba ka gane ni ba, ranar da na kira ka?"" Ya ɗan yi guntun murmushi ya ce ""Ki yi haƙuri, sai" "daga baya na ɗauki muryar ne. Ya ki ke ina fatan kina lafiya?""" """Ai baka damu da ina lafiya ba, tun da ka sake ni baka ƙara nema na ba, saboda ka yi aure matarka ta" "haihu, dama ni haushina ka ke ji, ba na haihuwa""" """A'a Yusra, kar mu fara haka da ke. Kin san ko bayan mun rabu, na yi ta neman lambarki, amma ba ta" "shiga har na haƙura. Ya jikin ki?""" """Da sauƙi, amma ni ba mahaukaciya ba ce""" "Sagir ya ce ""Ai dama ban ce ba""" """Lokacin da muna tare ai ka ce"" ya yi murmushi ya ce ""Wannan ba ya wuce ba? Amma Mami ba ta san" "kin kira ni ba ko?""" """Eh, ina gidan Mummy Zahra, da wata na haɗu sunanta Nana, ita ma ta san irin rashin lafiyata. Ita ma" "tana yi""" "Ya ce ""Haba dai?""" Ayshacool """Wallahi. Ita ta din ga ba ni shawara, ita ce ma ta ce na kira ka fa, na ma zata ba zaka ɗauka ba, ka ɗauka" "amma ka nuna ba ka gane ni ba"" dariya ya yi ya sakankance sosai, yana sauraren Yusra. A yanayin surutun da take yi, ya fuskanci jikinta da saura, ba ta warke ba, amma ya tattara hankalinsa yana sauraren ta. Hirar ta din ga tuna masa da yadda suka zuba soyayya a baya kafin aure. Yana kallon kiran" Shukura amma ya ƙi ɗagawa ya ba wa Yusra lokacin sa. """Ki na ji na""" """Eh""" """Yanzu ina gurin aiki, kuma lokacin salla ya yi, zan sake kiran ki, in sha Allah""" """Tom sai anjima""" """To 'yar farata, bye-bye""" "Kamar tana gabansa ta saki murmushi, cike da sanyin jiki, saboda ta yi kewar jin sunan." "Shi ma murmushin ya yi, yana tuna wasu abubuwa da suka wuce." "Ya kira Shukura, sai da ta kusa katsewa sannan ta ɗaga. ""Madam ya aka yi ne?""" """Ina ta kiran ka, kana waya, har da rejecting kirana""" """Sarkin ƙorafi, kin san da wa nake wayar ne?""" """Ai ba sai ka gaya mini ba, na san 'yan matanka ne""" """Ni ba da 'yan mata nake waya ba. Ya aka yi?""" "Shukura ta ce ""Ba komai""" """Madam Shukura, bakomai ɗin ki, na nufin akwai komai. Yanzu dai a yi mini afuwa da ni da 'yan matan" "nawa.""" """Ni shikenan kawai"" ta kashe wayar. Ya girgiza kansa tare da ɗan lumshe idonsa." **** "A ranar dillalai, suka saye wardrobe da mudubin Nana, da sauran kayan da take ganin za su zame musu" shirgi. "Ta tattare musu kayan su cikin bagcco, duk wani kayan amfaninsu ta tattare. Da safe ƙarfe goma, ita da" Ummi suka je suka samo taxi. Har fargaba take yi kar mijin Ummi ya yi ƙorafi a kan yawon da take yi saboda ita. Duk da ba mazauni ba ne. Suka yi cinikin a nawa zai kai su Garko cikin ƙauyen Buda. "Aka ɗaure katifa a saman taxi, aka loda kayan su a ciki." "Ummi ta shiga gaban motar, ita da babbar 'yar ta Islam." "Nana kuma suka shiga bayan motar, tare da Sayyid." "Ya kwanta a jikin Nana ya yi shiru, ita kuma ta riƙe hannunsa tana matsa masa a hankali cike da kulawa." "Awa ɗaya da rabi, suka isa har cikin garin Buda. Sai dai shigar su garin ke da wuya, Nana ta fara jin sanyi" yana ratsa ta. "Addu'a ta din ga yi, a kan Ubangiji Allah ya rufa mata asiri, ya kawo musu ɗauki, ya shiga tsakaninsu da" su Ƙaisar. """Ma vie"" ta ji ya yi magana." """Na'am Sayyid"" Sai kuma ya yi shiru, bai sake cewa komai ba. Yara suka firfito suka tatstsaya bayan ganin" mota ta tsaya a ƙofar gidan Uwani. "Uwani da kanta ta fito tana tafa hannu, tana ""Maraba da mutan birni. Ina yayar tawa take?"" Nana ta" buɗe motar ta fito tana murmushi. "Ummi ta sallami mai motar, Uwani ta ce ""Ina mai gidan?""" "Nana ta buɗe taxi ɗin, ya fito a hankali, kansa rufe da mayafi." "Uwani bakinta fal magana, amma ta haɗiye ta yi musu maraba, zuwa cikin gidan. Babban gida ne mai" "ɗauke da ɓangarori. Ta kai su sashen ta, aka yi shimfiɗa Sayyid ya zauna ya jingina da bango." "Abin da dai ba ya ƙauna, ya sake tararwa a garin, kallo. Ba ya son a zura masa ido, amma ya lura da" yadda ake ta kallon sa. "Uwani ta karrama su da ruwan pure water, da abinci shinkafa da wake." "Ummi ta ce ""Kafin cin abinci, Uwani a ina za su zauna, a gyara musu?""" "Sai da Uwani ta sake yi wa Ummi ta tas, tamkar ita ce Baban, sannan ta kalli Nana ta ce ""Yayata, kin ga" "cikin gidan nan, akwai ɗakuna, idan ma ba zaku zauna a nan ba, nan baya tafiyar babu nisa, akwai gida da ɗakuna biyu da tsakar gida. Babu kowa a gidan idan za ku zauna""." "Nana ta ce ""Gara su zauna a inda babu kowa""" "Ummi ta ce ""Maimakon ku zauna a cikin mutane, yadda ko wani abin ne, a taimaka muku""" "Nana ta ce ""Akwai dalili gara mu zauna inda babu kowan"" Nana kuwa ta yi hakan ne, domin samun rufin" asiri na larurar da suke fama daga ita har Sayyid. Ga uwa uba takura da Sayyid ba ya so. "Uwani ta saka yara, su ka je su ka share gidan tas, aka wanke." "Nana ta ce ""Sayyid, bari mu je da Ummi, a gyara gidan, sai mu zo mu tafi da kai"" Ya saka hannu ya riƙe" "nata, tare da girgiza mata kai alamar a'a." """Mu tafi tare za ka iya tafiya?"" Ya jinjina mata kai alamar eh." """To ta so"" Ya yinƙura a hankali ya tashi tsaye." "Uwani ta ce ""Nana, ku bar shi a nan mana, tun da ba shi da lafiya, ke ku je, ku gyara gidan""" Ayshacool "Nana ta ce ""Ai ba zai zauna ba, ya ce bin mu zai yi""" """Ikon Allah, ni da bita zai-zai, to Allah ya taimaka"" Nana ta yi murmushi kawai, tare da jin nauyin abin da" Sayyid ɗin ya yi. "Sauran yaran gidan Uwani, suka bi su Nana, su taya su shirya kaya. Wanda galibi Nana ba ta ma san su ba," "saboda ba zuwa garin suke yi ba, domin ita rabonta da garin ma, har ta manta." "Gidan ƙasa ne tsura, da zunzurutun turɓaya. Ɗaki ɗaya ne gyararrre, sai aka yi masa siminti, da plasta," "aka shafa farar ƙasa, da ƙofar langa-langa. Sai wani ɗakin kuma, si kuma ko rufi babu, sai banɗaki." "Duk lalacewar gidan su Nana ya fi nan nesa ba kusa ba, Ummi jarumta kawai take yi, zuciyarta a" "cunkushe babu daɗi, biyo bayan tuna cewar a nan Nana za ta rayu. Sai dai ta ga tsantsar tawakkalli a" "fuskar Nana. Su ka gyara ɗakin aka shimfiɗa leda, sai katifar su. Sai kuma tarin kayan su, na girki sai na sakawa a cikin bagco." "Uwani ta aiko musu da Abinci. Da la'asar bayan Ummi ta yi salla, ta ba wa Nana kuɗin barkononta da aka" "sayar, ta yi ta mata nasiha da kwantar mata da hankali, sannan ta yi musu sallama." "Ɗan gidan Uwani ya ɗauke ta a kan babur, ya tafi da ita." "Nana ta ƙarasa gaban Sayyid, da ya zuba mata idanu tamkar bai taɓa ganinta ba." "Ta riƙo hannayen sa ta ce ""Sayyid, duk da ban san wace irin rayuwa ka yi a baya ba. Amma wadda muka" "yi, mun yi ta ƙarƙashin kulawar su Habu, ba mu taɓa neman abu mun rasa ba. Amma Allah shi ne abin godiya. Wannan yanayin da muke ciki, ba zai dauwama ba in sha Allah. Ina fatan Allah ya baka lafiya, ya" "kuma baka haƙuri da juriyar a yanayin da muka tsinci kanmu a ciki""." "Ya sanya tafukan hannayen sa biyu, a fuskarta laɓɓansa na rawa, amma magana ta gagara." "Ta girgiza masa kai tana murmushi, ta ce ""Ruhinka yana cikin jikina, kar ka damu kanka lallai sai ka yi" "magana. A jikina ina jin abin da ka ke son faɗa"" ɗan guntun murmushi ya yi, duk da yadda yake matuƙar" son ya furta wani abu. "Da daddare Uwani ta aiko musu da tuwon dawa, da miyar karkashi, ta sha daddawar kalwa har ɗaurin" yajin daddawa. "Ta san ba lallai ya iya ci ba, ta ba wa yaran da suka kawo kuɗi, ta ce su sayo mata buredi da shayi, na" "gurin masu sayarwa, da kuma maganin sauro, saboda azabar sauron da ke ɗakin." "Sai dai ya ƙi shan shayin, buredi kawai ya ci ya kwanta. Nana jikinta na rawa ta ci tuwon, saboda yadda" "ranta ya biya, amma ƙarshe amai har ta hancinta sai da ta yi shi." "Kan su kwanta, ta kunna maganin sauro, ta gyara masa shimfiɗa ya kwanta. Ita ma ta hau katifar ta tofa" "masa Addu'a, sannan ta kwanta a kusa da shi, tana yi masa fifita." "Ta daɗe idonta biyu, kafin bacci ɓarawo ya sace ta. Sai dai kamar a zahiri, kuma kamar a mafarki ta fara" "jin hayaniya a kanta. Ba ta gama tantance hayaniyar mece ce ba, ta ji wani abu na wucewa ta saman roofin ɗakin. Idan abin ya daki kwanon ɗakin da abin da yake takawa, tamkar kwanon zai buɗe ya faɗo" musu a ka. Ayshercool 08081012143 Ayshacool https://chat.whatsapp.com/KJoPVAmFgseJj2f8Y9wQqg?mode=ac_t Free class Free class Free class "Imagine a ce za,a koyar da ke kayan mata masu kyau da inganci kyauta Sannan kuma ace Zaki samu" horun daga kwarariyar Mai kayan mata nan ta jahar sokoto wato maman Maryam organic aphrodisiac sokoto yar uwata mi kike jira maza kama wurin zamanki kafin ajin ya cika domin samun damar dogaro da Kai ko hutar da kanki wurin sayen kayan mata. "Wata irin yinƙurawa Nana ta yi, cikin azama da tashin hankali ta kifa a kan Sayyid, saboda kar abin da" "yake takun koma mene ne, ya faɗo masa a ka." """Ma vie"" ya furta da ƙyar can ƙasan maƙoshinsa. Ta ɗago ta fara laluben fuskarsa a cikin duhu." """Sayyid, ba ka ji wani abu zai faɗo mana ba?""" """A'a""" "Ta sake cewa maganar ta dawo ""Maganar ta dawo?""" """Eh""" """To sannu"" ta furta a hankali cikin tsoro, ta mayar da kanta kan ƙirjinsa a tsorace. Sai dai kamar dole, ta" "ƙarfin tsiya, wani baccin ya sake awon gaba da ita, tana cijewa da ƙoƙarin hana idonta sake yin bacci," "amma abu ya ci tura, baccin ya kuma awon gaba da ita." "Ganinta ta yi a tsaye a tsakiyar ɗakin, itakaɗai babu Sayyid. Ana ta cigaba da hayaniyar da ba ta gane me" "ake faɗa. Ta din ga waige-waige tana tunanin ina ya shiga haka? Sai dai ba ta gama tunanin ba ta ji muryoyi daban-daban suna faɗin ""Lale da manyan baƙin garin Buda. Barka da zuwa."" Sai kuma ta ji ana" dariya tare da ci gaba da hayaniya. "Idonsa biyu, yana jin yadda ta yi wa hannayensa wata irin muguwar damƙa, ta nutsa faratanta a jikin" "fatarsa, dan tuni ya karaya jini ne yake fita daga fatar tasa. Ta din ga juya kanta a kan ƙirjinsa tana kuka tana faɗin ""A'a, mu ba baƙin ku ba ne ba, ba gurinku muka zo ba, mu ba baƙinku ba ne"" jin ta fara ɗaga murya, ya sanya ya murginata gefensa, ya zame hular kanta yana shafa gashinta a hankali, tare da hura" "mata iskar bakinsa a kunnenta. Daga haka sai ta yi shiru, ta ci gaba da bacci." **** "Barira sai da ta sha jini leda biyu a Asibiti da allurai da magunguna, amma tana komawa gida, abu ya ƙara" "rikicewa. Domin kuwa babu damar ta sanya haƙarƙarinta a ƙasa ta fara bacci, wannan jibgegiyar magen" "za ta bayyana, su hau kokowa da ita. Duk sai magen ta yayyage mata fuska da jikinta. Idan ta tashi sai ta ji jikinta na yi mata wani irin zugi da raɗaɗi." "Ta cewa mijinta ita fa ba za ta koma wannan gidan ba. Ya sanar mata an tashi su Nana, daga su sai su" "Sajida a gidan kamar da, amma ta hau kujerar naƙi ta ce gidan ne ba za ta koma ba. Shi kuma ya ce sai" "dai ta yi ta zama a gidansu, dan ba shi da kuɗin kama wani gurin." "Shukura ce tare da Hajiya Amina, suke hira. Ta je yi mata sannu da zuwa dawowar da ta yi daga umara." Alhaji Zailani ya yi sallama ya shigo falon. """Daddy sannu da zuwa""" "Ya ƙare mata kallo ya ce ""Yauwwa, mara tawakalli da ba ta san ƙaddara ba"" Ta yi shiru tare da sunkuyar" "da kai. Duk irin kashedin da nake yi miki, da rarrashin da na yi miki, ba ki ji ba abin har ya kai ki dizga" "bawan Allah nan, a gaban mutane kina cewa yana kashe mutane, idan ya yi ƙarar ki kina da shaida a kan" "haka?""" "Ta yi shiru ta sunkuyar da kai. ""Tambayarki nake yi"" Ta girgiza kai alamar a'a." """Amma ki ke wannan iƙirarin, maimakon ki mayar da hankali a kan fatan Allah ya raya na gabanki, ya ba" "ki wani. Ba ki kyauta ba"" Hajjya Amina ta yi ta kallon Shukura ko za ta ba shi haƙuri, amma ta yi mursisi." "Ko da ya shiga ɗakinsa, babbar rigarsa ya cire saboda azabar gumin da yake yi. Dan tun da Doctor Sharif" "ya gaya masa ga yadda suka yi da Shukura hankalinsa ya yi mummunan tashi. Ya kuma sake jaddada wa Sharif, muddin wani abu ya fita to babu hannunsa a ciki. Kuma likitan ya yi masa bayanin process ɗin da" "ya bi, abu ne mai wahala a gano. Ya yakice gumi ya nemi guri ya zauna." "Hajiya Amina ta ce ""Me yasa ba ki ba shi haƙuri ba, kina kallon yadda ya yi fushi?""" """Mummy, duk wannan abubuwan kamata ya yi a tsaya a saurare ni, a kuma fahimce ni. Da hankalina fa" ta yaya zan din ga iƙirarin an kashe mini ɗa haka kurum. Ayshacool "Mummy ranar da za a yi mini aiki, kina bacci cikin dare, na kasa bacci saboda damuwar da nake ciki, aka" "buɗe ƙofar ɗakin, aka zo aka kama hannuna aka laluba cannula, aka yi mini wata allura a cikin duhun nan. Tun da aka yi mini allurar nan. Na ji kaina ya fara juyawa, ina neman na fita hayyacina, duk iya ƙoƙarina na kasa, na ji jikina na ƙamewa kamar zan yi jijjiga. Saɓanin da da idan za a yi mini allura cikin dare, za a" "ƙwanƙwasa ɗakin, sai kin tashi kin ce a shigo tukuna, a kunna ftila a yi mini""" "Mummy ta ɗan yi shiru, cike da mamakin me yasa tuntuni ba ta faɗa ba, amma domin kawo ƙarshen" "maganar, sai kawai ta kawo gigin ciwo ne ya sanya ta ga haka a lokacin. Dan haka ta ce ""Duk da haka wannan ma ba hujja ba ce, ke da ki ke fama da ciwo ina za ki tantance wani abu ma. Dan Allah ki bar zancen nan""" "Shukura ta yi murmushi ta ce ""Shikenan, na bar shi""" "Sai kuma ta sake cewa ""Mummy, Nana shiru, ni yakamata ki kwatanta mini gidan da suke na kai mata" "Haidar""" """Gidan Alhaji Garba giwa ne fa, kuma fafur babanku ya hana ni zuwa ban san dalili ba"" Dummm! Ƙirjin" "Shukura ya buga, ta ce ""Saboda ne ya hana ki zuwan?""" """Ban san dalili ba, za ki je ne? Sabon gidansa nan Kano""" "Shukura ta ce ""Wace matar ce a gidan?""" """Halima ce, uwar gidan sa""" "Shukura ta girgiza kai ta ce ""Ba zani ba, gidansu tsohuwar matar Sagir ce""" "Mummy ta waro ido ta ce ""Ke haba? Dama 'yar Halima ce matar Sagir ɗin?""" """Eh mana""" """Ikon Allah, da na ce wa Daddy, ya taimaka musu, a samo wa mijin Nana, gurin da zai yi gadi, su samu su" "zauna, shi ne aka samo gidan""" "Shukura ta ce ""wai canza masu gadi ku ka yi ne?""" """Ina fa, ina nan cikin gida, daga baya ma Yusuf yake gaya mini. Wai zuwa aka yi da motoci da alama daga" "ƙasar su ne ma, motocin duk rubutun fransanci aka kwashe su kaf, kuma babu wanda aka yi wa bayanin me yasa""" """Ikon Allah, kuma ba laifi suka yi ba?""" """To ina zan sani, ina nan cikin gida?"" Suka ci gaba da tattaunawa da jajanta lamarin. Har wayar Nana" "suka jarraba kira, su ji ko ita nata mijin yana nan, ba a kama shi ba amma wayarta ba ta shiga sam." **** "Da safe Nana ta tashi, ta fara alwala sannan ta zuba wa Sayyid ruwan da yara suka ɗebo musu jiya, dan" "gidan babu ruwa. Ya yi alwala a ƙofar ɗakin, sannan suka koma ciki ya yi salla. Sai dai bai ga alamun ta san abin da ta yi cikin daren jiya ba." "Ƙarfe tara da rabi, Uwani ta aiko yara da kunu da 'yar tsala aka kawo wa su Nana." "'yar aiken ta ce ""Uwani ta ce idan kin gama karayawa, wai ki je""" "Nana ta ce ""To, zan zo a ce mata mun gode sosai da sosai, Allah ya biya ta""" "Ta koma ta zauna a gaban Sayyid ta ce ""Sayyid, ka ga kunu ne da 'yar tsala za ka iya ci, ko na nemo maka" "wani abin?"" Ya girgiza kai." """To za ka iya cin wannan ɗin?"" Ya gyaɗa mata kai." "Kunun tsamiya ne, na daka ba niƙa ba, ya sha kayan ƙamshi, sai dai babu suga ko kaɗan a ciki, ga" tsamiyar nan cau har ka. "Ƙuli-ƙulin 'yar tsalan, ya sha barkono, ta zuba masa a kofi ta ba shi. Ya saka hannu ya karɓa." "Tun da ya yi kurɓa ɗaya, ya yi shiru. Nana ta ce ""Za ka iya sha kuwa?"" Ya jinjina kai ya ci gaba da sha," saboda Nana. "Ya haɗa da 'yar tsalan nan, duk da ba son Abincin yake yi ba." """Sayyid, idan ba zaka iya cin Abincin nan ba, ka bari na nemo maka wani""" "Ya ɗaga kai ya kalle ta, sai dai ba baki, dan haka ya harare ta, ya ci gaba da cin abincin." "Ta yi murmushi ta ce ""Ni ka ke harara ko, aishikenan""" "Ya gama karyawa, ta saka ɗankwalinta, ta goge masa bakinsa da hannunsa. Ta ce ""Bari na je kiran da" "Uwani take yi mini, daga nan na saka a raka ni, na ɗan yi mana sayayya, dan na san dole za ta daina bamu Abinci yau da gobe sai Allah""" "Bai ba ta amsa ba, ya jingina da bango, saboda yadda yake jin daɗin hakan, yana lumshe ido." """In je?"" Ya yi mata shiru, kuma yaƙi yi mata wata alamar, da za ta gane ya amince ko a'a." "Cikin shagwaɓa ta ce ""Sayyid"" ya kawar da kansa gefe, ya ƙi buɗe ido." """Duk da maganar nan ɗaukewa take yi, amma dai tun asalinka miskili ne, ina ta magana ka ƙi kula ni, ni" "ce fa rayuwartaka guda ka ke wa haka?""" "Murmushi ya yi, tare da saka hannunsa a cikinta, yana shafawa a hankali." Ayshacool """Wai ba za ka kalle ni ba?"" Ta yi maganar tana juyo da fuskarsa. Ya ƙara rintse idanunsa, wai ba zai kalle" ta ba. Nana ta din ga dariya. "Ya ja jikinsa a hankali, ya kwanta a kan cinyarta, ya zuba wa cikinta ido, tamkar zai gano abin da yake" cikin. """Idan na haihu na ga yadda za a yi, da kai da jaririn wa zai bar wa wani cinyar nan"" Ta yi maganar tana" shafa gashin sa. * "Hajiya Sa'a ce take cin abinci, tana kallon Jamila, da take ta cakala kaɗan-kaɗan." """Jamila ya ne? Ki saki jiki ki ci abinci mana"" Jamila ta jinjina kai ba tare da ta ce komai ba." """Ko dai haryanzu abin da ya faru ɗin ne yake damun ki? Tun wuri ki ajiye wannan abin, ki ci gaba da" "rayuwar ki cikin kwanciyar hankali. Ɗan ƙaramin abu ne fa, ranar da aka ce ki bayar da jini kuma ya zaki yi? Ki na gani Safiyya ta tafi Dubai ma sarin kaya, kuma duk harka ce ta ƙungiya ta ɗaukakata haka. Har gara ke ma da ba ki da aure, Safiyya da aurenta, amma kalli yadda ta kama ƙasa, mijin ma ita yake yi wa" "biyayya, ki saki jikinki dan Allah ki daina wannan damuwar." "Ki ƙarasa cin abincin, Talatu ta gyara gidan, idan an zo ana son kaya, kin san gurin da suke, zan je sake" "duba Fatuhu ne, daga nan na je a gyara mini kaina""" """To Mummy a dawo lafiya""" """Yauwwa Daughter Allah ya sa""" "Ta gama abin da take yi ta fita, bayan fitar ta, Jamila ta tashi ta nufi harabar gidan, tana kallon flowers" "ɗin da aka ƙawata harabar da su. Jibga-jibgan motocin Hajiya Sa'a uku na hawa. Ga na ɗanta Abba biyu. Iya harabar gidan abar burgewa ce, ta yadda duk mai rai zai yi fatan ya samu wannan wadatar. Sai dai kash, hanyar da aka bi gurin tara dukiyar, duk wanda ya ji muddin yana da imani, sai ya gudu da" ƙafafuwansa. "Ji ta yi kamar wani abu yana bin wuyanta, ta juya a hankali ta ga Abba ne a tsaye, yana saka abin fulawa" a wuya. "Ta yi guntun murmushi ta ce ""Yaya Abba""" """Na'am ƙanwar Abba. Ya na ganki nan lafiya dai ko?""" """Lafiya ƙalau, ba ka fita ba?""" """Yau ba zan fita ba, ba na jin daɗi ne gaba ɗaya, dan da zazzaɓi ma na kwana wallahi""" "Cikin tausayawa ta ce ""Kash, sannu Allah ya ba ka lafiya. Ka je Asibiti mana""" "Abba ya ɗan numfasa ya ce ""Na sha magani already, dan haka ba sai na je ba, zo mu je mu zauna ki yi" "mini hira, na san zazzaɓin zai sauka gaba ɗaya"" Dariya ta ɗan yi ta ce ""Ai ni ban iya hira ba""" """Ba wani nan, amma ki na yi da Mummy ai, gaskiya mu je sai kin yi mini"" Tana dariya ya wuce gaba ta bi" bayan sa. Sanyin halin Abba ya fara tasiri a zuciyar Jamila. * "Alhaji Fatuhu na zaune, Hajiya Suwaiba ta gama gyara jikinsa, fuskarsa ɗauke da damuwa, ya kalli uwar" "'ya'yan nasa ya ce ""Haryanzu Fadilan ba ta haihu ba?"" Ta taɓe baki ta ce ""Tana can ba ta haihun ba tukuna.""" """Allah ya sauke ta lafiya"" ta yi shiru ba ta amsa ba." """Yakamata a sallame ni na koma gida haka, na gaji da zaman Asibitin nan gaba ɗaya""" "A hasale ta ce ""To mu koma gida mu yi yaya ne? Nan ɗin ba dai magani ake baka ba ana kula da kai," "komai sai ka nuna kai ba a kyauta maka ba, ba a iya ba haba dan Allah""" "Jiki a sanyaye ya ce ""Yi haƙuri, Allah ya baki haƙuri"" daga haka ya sunkuyar da kansa." "Sai kuma jikinta ya yi sanyi, ta zauna a kusa da shi, tana tunanin ta yi magana. Ta ga yana share hawaye." "Cikin damuwa ta ce ""Alhaji kuka ka ke yi? Dan Allah ka yi haƙuri raina ne a ɓace, amma dan Allah ka yi" "haƙuri""" "Ya yi mata shiru, gaba ɗaya ta rikice ta rasa abin da za ta ce. Raudah ce ta turo ƙofa hannunta da towel" "ta ce ""Daddy guess what?"" Ta miƙa masa narkeken jaririn da Fadila ta haifa." "Hannunsa na karkarwa ya riƙe jaririn ya ce ""Another Muhsin"" ya yi maganar yana murmushi." "Ya din ga yi wa jaririn kiss, yana shafa shi kamar ba a taɓa yi masa haihuwa ba." **** "Fafur Sayyid ya hana Nana zuwa ko nan da can, har aka yi azahar.Uwani ta sake aiko musu da dambu, ta" "ce a cewa Nana ba za ta zo ba, sai ta zo da kanta." "Cikin damuwa ta ce ""Sayyid dan Allah ka bari na je, na ji kiran me take yi mini"" fafur ya sha kunu ya tsuke" fuska. Ayshacool "Babu yadda Nana ta iya, ta zauna ta ƙi fita. Ta zazzage kayansu, tana ƙara gyara musu, ta fito da kayan" "wankin gashinsa, da turarrukansa da duk wata sai su Habu sun sayo sun kawo. Ta ɗaga kai ta ga ita yake kallo, ta ɗan yi murmushi ta haɗe su a guri ɗaya da combs ɗin sa na taje gashi." "Sai yamma bayan sallar la'asar, ta yayyafawa tsakar gidan ruwa, ta share shi." "Ta yi shimfiɗar tabarma a tsakar gidan, ta saka wa Sayyi fululluka ta kamo hannunsa zuwa waje." "Ya zauna, ta ɗaukko mayafin rawaninsa ta yafa masa a kansa." "Babu jimawa sai ga Uwani ta zo, tana faɗin ""Tun da ba za ki zo ba, ni ga ni na zo da kaina""" "Nana ta ce ""Ba ƙin zuwa na yi ba Uwani, yanayin jikinsa ne sai a hankali, shi yasa ban fito ba""" """Koma dai mene ne gani na zo ai"" Ta kalli Sayyid ta ce ""Sannu ko"" ya jinjina mata kawai." """Dama kiran ki nake yi, na ji idan akwai wani abu da ku ke buƙata?""" """Eh, ina son yin sayayya ba mu da fitila sai ta waya, da kuma 'yan kayan buƙatu""" """To da kin sanar, ai da na saka yara sun raka ki, dama zan ce miki kuma idan an kwana biyu, yakamata ki" "zo a ɗan zagaya da ke cikin dangi, su san kina garin nan, tun da dama ba zuwa ku ke yi ba, dui ba sanin ku aka yi ba""" "Nana ta jinjina kai ta ce ""To in sha Allah""" """Wai ni Nana ina Mai jidda kuwa?""" """Tana can Bauchi inda take aure""" "Uwani ta ce ""Kuma tana zuwa?"" Jiki a sanyaye Nana ta girgiza kai." """Ai dama na san babu lallai ta zo, ko dan saboda baƙin halin Isa. Ai ya bamu mamaki. Ita ma tun da suka" "rabu ba ta sake zuwa garin nan ba. Kuma yakamata mu je na zagaya da ke, har inda danginta suke a nan""" "Cikin mamaki ta kalli Uwani ta ce ""Danginta kuma?""" """Ƙwarai da gaske, tushen Maijidda garin Buda ne. Kakanninta 'yan nan garin ne, can wajen unguwar" "Wanzamai, ƙarewa ma a nan garin suka haɗu da babanku. Ai kakarta aka raina a Bauchi, aka haifi babarta da ita a can." "Har an saka mata rana, suka zo garin nan, ke ma Babanki ya zo gida, suka haɗu a dandali. Aka yi ta ɗauki" "ba daɗi suka ƙulla soyayya. Ga shi can garinsu an saka mata rana da wani, ina ga shi ne mijinta na yanzu da take aure. Asali tun kan ta auri babanku da shi aka fara saka mata rana. Kakarta ta ce sai an warware wancan baikon ta auri babanku, ko ba komai sa din ga zuwa gida a kai kai. Haka aka mayarwa da wancan" kuɗinsa ta auri babanku. "Ya Babanku ya so ta sosai da sosai, kuma aka ƙulla auren nasu da tunanin hakan ya ƙara kawo zaman" lafiya a tsakanin zuriyarmu da zuriyar wanzamai kin san a tarihin garin nan ba zaman lafiya ake ba. "Kuma dai cikin ikon Allah sun fara zamansu lafiya gwanin sha'awa, amma Allah ya ƙaddara rabuwar su.""" "Nana ta yi shiru tana tunanin, kamar ta san wani abu mai kama da wannan labarin da Uwani take ba ta," "amma sam ta kasa tunawa. Gaba ɗaya hirar ta Uwani ta gundure ta, saboda ta san shi kansa Sayyid a takure yake, ba ya son mutane ko kaɗan, balle uwa uba dogon surutu. Ita kuwa Uwani tamkar an ƙona ta a ka ko gajiya ba ta yi. Babu wanda ya taɓa ba ta wannan labarin, sai yanzu babu wanda ya taɓa gaya" "mata cewar mahaifiyarsu tushenta a garin Buda yake, sai dai kamar ta san labarin da Uwanin ta bata." """Ga wata 'yar rama na zo muku da ita, sai ku ci kafin Abincin dare ya sauka. Wai shi mijin naki kurma" "ne?""" """A'a ai kin ga ba shi da lafiya ne""" """Eh gaskiya ne, Allah ya ba shi lafiya, amma a ina ki ka samo Buzu haka? Ni wai anya ma labarin da Rabi" "ta din ga bayar wa ranar bikinki nan gaskiya ne? Abin dai da mamaki. Allah ya ba shi lafiya bari na tafi, dan Allah idan ki ka samu lokaci kya zo a je a gaggaisa." """To in sha Allah zan zo""" """Yauwwa, zan din ga turo miki yara, idan da aike kya din ga ba su, duk 'yan uwanki ne, 'ya'yan 'yan uwa" "ne. Kuma ki kwantar da hankalinki duk abin da ku ke buƙata ku sanar mini, da yardar Allah ba zai gagara" "ba""" "Nana ta ce ""In sha Allah, mun gode sosai da sosai""" """Ba komai, ki yi haƙuri ki riƙe mijinki ki kula da shi, sai ki ga kaf ayyukan ki, Allah bai karɓa ba, silar" "wannan jinyar ta sa ki shiga aljanna, a yi ta haƙuri yayata""" "Nana ta tashi ta raka ta, ta ce ""In sha Allah""" Ayshacool "Ta yi ƙasa da murya ta cewa Nana ""Dan ubanki, ki din ga ɓoye mijinki, kar ki bari 'yan mata su din ga" "zuwa su na kallon sa."" Uwani ita iya rage muryarta kenan, amma Sayyid na jin ta. Nana ta ɗaga kai suka yi ido huɗu, ya yi murmushi yana sunkuyar da kai." * "Alhaji Fatuhu, farin cikinsa ya kasa ɓuya, duk da halin rashin lafiya da yake ciki, idan aka zo duba shi, sai" ya yashe haƙoransa da sukaɗai suka rage farare a jikinsa. "Alhaji Zailani ya ƙura wa jaririn ido, ya kalli Alhaji Fatuhu da yake ta yashe baki." "Hajiya Sa'a ta ce ""Kai Fatuhu. Sai ka ce ba a taɓa yi maka haihuwa ba, ji yadda ka ke washe baki, kana" "fama da kan ka""" "Hajiya Suwaiba ta kwaɓe baki ta ce ""Abin da na gani kenan""" "Alhaji Zailani ya ce ""A'a ku bar shi ya yi, ɗan mutum fa, kyauta ce Allah ya ba shi, da duk Duniya babu mai" "ba shi. Ni ba gani ba 'ya'yan duk babu sai biyu ne suka tsaya."" Ya yi maganar yana zuba wa jaririn ido," "yana tuna na Shukura. Tun da yake harkar ƙungiya, bai taɓa bayar da jinin da ya tsaya masa ya kasa" "mantawa ba, sai na Shukura. Mussaman idan yana tuna irin baƙar wahalar da ta sha." "Ya kalli Fadila, da take ɗakin a zaune, ga jego tana yi, amma ta tare a Asibiti da ɗanyen jaririn da ko suna" ba a yi ba. "Ya yi ajiyar zuciya ya ce ""Wane sunan za ka saka masa?""" """Muhsin ɗina zan mayar"" ya yi maganar muryarsa ɗauke da rauni." "Hajiya Sa'a ta ce ""Wai an din ga saka Muhsin ɗin kenan?""" """Sunan mahaifin Fadila ne, shi za a mayar mu ci gaba da kiransa Muhsin, ni na yi mata alƙawari shi yasa." "Na so Muhsin ɗina da ya rasu sosai da sosai. Na ji zafin rashin sa, sai dai ina tausayawa wannan Muhsin ɗin. Ya zo lokacin da mahaifinsa ba shi da komai, ba zan iya ɗaukar nauyinsa na kula da shi ba. Wataƙila ma kafin ya yi wayon sani na na rasu. Ga shi ko hakika ba zan iya yi masa ba"" ya yi maganar hawaye na" zubowa daga idanunsa. """Haba Fatuhu, ya haka? Dan dai Hakikar da za ayi wa jaririn nan, ka san ba za ta gagara ba, amma ya za" "ka zauna kana kuka kamar ƙaramin yaro, a gaban iyalinka da 'yan uwanka hakan bai kyautu ba ai""." "Alhaji Fatuhu ya ɗago idanunsa da suka yi jawur ya ce ""Zailani. Ka san me nake ji kuwa? Gidaje da" "motocin hawa nake da, ina kyautar maƙudan kuɗaɗe ba tare da na ji komai ba, da abu ya dame ni, zan sai ticket na tafi umara. Ina da shaguna dukiya Allah ya yarje mini, bayan gwagwarmaya da na sha ta" "rayuwa. Astagfirillah ba ƙarar Allah nake kawowa ba, ko rashin imani da ƙaddara ba, ina jinjina girman" "lamarin Ubangiji, kuma ina jin babu daɗi ɗa na na cikina, ba zan iya saya masa ko wando ba""" "Fadila ta ce ""Dan Allah Daddy ka yi haƙuri. Mu na murna sauƙi yana samuwa, ga shi ka na ta magana" "sosai da sosai, kukan nan karya mana zuciya yake yi. Kuma da ka yi mana a baya, yanzu kuma da Allah ya" "kawo jarrabawa shikenan sai a yi haƙuri""" "Su na nan zaune, sai ga ƙanin Baban Fadila, ya zo duba Alhaji Fatuhu ya kuma jaririn Fadila, wanda shi ne" waliyyin Fadila. Sai dai shi ma ya tsorata da ganin Alhaji Fatuhu. """Alhaji haka jiki ya zama? Subhanallah Allah ya baka lafiya""" """Amin kawu, amma jiki ya yi kyau Alhamdillah, tun da ina ta magana""" """Haka ne, amma menene takamaiman abin da aka ce ya same ka ne?""" "Fadila ta ce ""Haryanzu ba a gano takamaiman mene ne ba, yau a ce ƙodarsa ta kumbura, gobe a ce ko" "cancer ce, an yi gwaji ba ita ba ce. An yi gwajin zuciya shi ma lafiya ƙalau""" "Cikin damuwa ya ce ""Amma Fatuhu ana haɗa maka da na addini kuwa? Ka san muna da ido ne ba na" "ganin gari ba. Mussaman ku da ku ke shahararrun mutane da Allah ya ba wa wadata. Yakamata a yi na sihiri da shaiɗanu""" "Alhaji Zailani ya ce ""A'a ga likitoci su na kula da shi, ya za a yi a ce kuma a kawo wani abu daban?" "Magungunan gargajiyar nan kashe mutane suke yi ai, tun da ba auna su ake yi ba""." "Alhaji Fatuhu ma ya ce ""A'a ba wannan ba ne, wa ya damu da ni da zai yi mini sihiri. Larura ce kawai" "kuma likitoci na kula da ni""" Ayshacool """Kai, kalle ni da kyau. Duk bokon ka, nima ɗan boko ne, kuma na san ilimin addini, amma sihiri da" "shaiɗanu gaskiya ne. Tun da aka yi Annabi Sallallahu alaihi Wasallam sihiri, duk duniya ban ga wanda ba za a yi wa ba." "Ciwo ya ƙi ci ya ƙi cinye wa ai akwai alamar tambaya, ga lalacewar dukiya lokaci guda. A dai tsananta" "addu'a. Ya gama bambaminsa ya fita. Alhaji Zailani ya din ga ziga Alhaji Fatuhu, tare da kushe magungunan gargajiya. Ba tare da jin nauyin Fadila da take gurin ba." "Ya gama soki burutsunsa, ya tashi ya yi musu sallama, tare da cewa zai aiko da abin hakika." "Har ya kusa ƙarasa wajen motarsa, ya waiwaya ya ga Hajiya Sa'a ta nufo shi, ya tsaya ta ƙarasa." "Ya ce ""Ya dai?"" Ya yi maganar yana kallonta." """Zailani""" """Na'am""" """An sauke ɗan uwana daga shugabancin 'yan kasuwa an ɗora ka, ka saka an dawo da shi Asibitin nan," "ƙarƙashin kulawarka, an ce a yi masa maganin gargajiya ka haƙiƙance kana kushewa." "Kar ka kuskura na tarar da sanya hannunka, a cikin wannan abubuwan da suke faruwa da ɗan uwana""" "Ya gyara tsayuwarsa ya yi murmushi ya ce ""Babu sanya hannuna a ciki. Ina ƙoƙarin zama aboki mai" halacci ne kawai. "Sannan ki daina mazewa kamar ke ɗin mai ƙaunarsa ce, bayan sadaukar da 'ya'yansa maza da ki ke yi""" """Duk da haka, munin abin da na yi bai kai wanda ka ke aikatawa ba, ka fi ni sanin kai da me da me ka" "sadaukar, dan haka ka kiyaye ni"". Ta juya ta koma. Bin bayanta ya yi da kallo, ya ji wani abu ya tsirga masa, tabbas idan Hajiya Sa'a ta ci gaba da wannan gigin, zai ɗauki matakin da ya dace a kanta.""" * "Cikin bacci, take jin hayaniya a bayan ɗakin, tamkar ana cin kasuwa. Ga wata irin sukuwa da take ji a" "roofing ɗakin, tamkar ta dawakai." "Tun da ta farka sai juyi take yi, bacci ya gagari idanunta, ayatul kursiyyu ce ta zo bakinta ta din ga" "maimaitawa, har ta samu nutsuwa daga razanin da take ciki." "Ta ruge idanunta, sai dai a maimakon ta yi bacci, sai wata irin kewar Sayyid take addabar ta. Ta rasa" "dallin da ya sanya, ba ya kula ta yanzu. Duk da ba shi da lafiya tana yi masa wannan uzurin, amma duk da" "haka da ya kan yi attempting sai ya ƙyale ta, yanzu kuma gaba ɗaya ya daina yinƙurin aikata komai ma." "Wanda da idan ya sako ta gaba, har takura take yi." "Ta tashi zaune ta gyara maganin sauro, ta taka a hankali ta ɗaga labulen ɗakin, saboda zafi. Ta dawo ta" "ɗauki fitilar wayarta ta kunna. Ta haska shi ta ga idanunsa a lumshe, yana bacci. Ta zuba masa ido, ta" "fara tunanin ko ita ce mai matsala gaya mata ne bai yi ba, ko ma sharrin Ƙaisar ne?." "Ta yi ajiyar zuciya, ta kashe fitilar, ta kwanta a gefen sa tana wasa da gashin ƙirjinsa. Zuwa na fuskarsa." "Ta sake matsawa a hankali, tana sumbatar leɓansa, tamkar mara gaskiya. Gaba ɗaya a tunaninta bacci" "yake yi, sai da ta ji ya sanya hannayen sa, ya zagaye ta, tare da ba ta damar sumbatar bakin nasa." "Nana za ta iya cewa, tun da Allah ya sa ta buɗi ido a duniya, ba ta taɓa jin kunya irin ta yau ba, cikin sauri" "ta fara ƙoƙarin rabuwa da jikinsa ta matsa, amma ya mirgina ya rungume ta gam a jikinsa yana numfashi" a hankali. Ayshercool 08081012143 Ayshacool https://chat.whatsapp.com/ItWyjFX6W6447Co1XrARAH?mode=ac_t "Yana jin yadda jikinta yake tsuma, tamkar wadda aka kama tana aikata wani abin ashsha! Ko kuma" wadda ake kaɗawa mazari. "Magana yake son yi mata, amma abu ya gagara, duk ƙoƙarin da ya yi amma abu ya ci tura." "Ya ƙara ƙanƙame ta tamkar wani zai ƙwace ta, ya din ga murza hannunta har ta fara jin zafin riƙon da ya" "yi mata. Yanayin ya ƙara ninka mata halin da take ciki, ta rintse idanunta." "A hankali ta ji yana hura mata iska a cikin kunnenta, tamkar yana zuba mata wani sindari, haka ta ji wani" irin nannauyan bacci ya yi awon gaba da ita. "Ƙamshin nan ta ji yana ratsa hancinta, ta buɗe idonta a hankali, kamar yadda ta yi tsammani, a wannan" "ɗakin ta gan su. Ta hau waige-waige. Ta wata ƙofa ta ga ya fito, ƙugunsa ɗaure da wani abu kamar zani, ya zauna a kusa da ita yana kashe mata ido." """Sayyid ka warke?""" """Eh mana""" """Ka daina jin duk abin da ka ke ji?"" Ya jinjina kai yana murmushi. ""To ka yi mini magana mana""" """Ma vieee"" ya faɗa yana ɗan jan maganar yana kwanciya a gefen ta. ""Har na ji daɗi da ka samu lafiya," "Allah ya ɗorar maka da sauƙin nan Sayyid""" """Amin rayuwata, matso ki kwanta mu yi bacci""" "Ta noƙe kafaɗa ta ce ""A'a""ya saki murmushi yana kama hannunta. Duhu ne ya gauraye ɗakin. Dariya ta" fara jin Sayyid ɗin yana yi mata cakulkuli. Ta kasance da shi cikin wani yanayi mai tsayawa a zukata. "Ba ta iya tantance a wani hali take, ta daina ganinta a ɗakin, sai a libraryn Ƙaisar." "Ta tsaya tana kallon gurin, tana tunanin yaushe rabon da ta zo gurin nan." "Ƙaisar ta hanga, a tsaye yana gyara litattafan sa." """Ƙaisar ka warke kenan?""" "Yayi shiru yana goge wani littafi, ya gama ya ajiye littafin sannan ya ce ""Eh, na warke. Waye ya ce ki je" "ƙauyen nan?""" """Ban gane waye ya ce na je ba? Zan kwana a titi ne? Ga mara lafiya ina da shi""" """Gaskiya ne, bai kamata ki kwana a titi ba. Wannan dalilin ya sanya tun a farkon auren nan, na din ga" "haska miki matsalolin da za ki iya fuskanta, amma gani ki ke yi kamar ƙarya nake yi, to yanzu sai ki san yadda za ki yi, ki rayu da ke da wannan lanjararren mijin naki, da duk larurar duniya ta ƙare a kansa""." "A ƙule Nana ta ce ""Larura Allah ne ya ɗora masa, kuma kun taka muhimmiyar rawa a larurarsa. Kuma ka" "daina ganin laifina. Zan tsallake shi ne a wannan yanayin da yake ciki, na bar shi? Mu bil adama mu na da bambanci da ku, mu na da tausayi da kuma nuna kulawa ga waɗanda muke ƙauna""" """A'a kar ki tsallake ki bar shi, amma ki yi ɗamara fiye da ta baya, garin Buda ki ka zo za ki zauna, ban sani" "ba ko kin fahimci abin da nake faɗa ko ba ki fahimta ba. Idan ma ba ki fahimta ba, za ki gane daga baya. Bil adama ku na tausayi da nuna kulawa ga wanda ku ke ƙauna, ku ke iya ɗaukar jinin makusantanku ku bayar, a yi muku tsafi ko? Da kyau matsala kuma ki sani, ba ki ga komai ba"" Daga haka ya ɓace ɓat. Ta" buɗe idonta a hankali. "Tana buɗe idonta, ta ji ana kaɗa kacakaura, da garaya a tsakar gidan su. Ana ta hayaniya tamkar ana cin" kasuwa a tsakar gidan. "Sanyi ta fara ji yana ratsa ta, bugun zuciyarta ya ƙaru, fiye da da, waiwaya ta yi tana son ganin ta inda za" "ta ga Ƙaisar, ko makamancin hakan amma ba ta ga kowa ba." "Wata irin guɗa ta ji an rangaɗa da wata irin murya, mai sauti, sai kuma aka ce ""Yeeee barka da zuwa" "wakilin rafi, ku matsa ku bayar da hanya ga ango mairamu ya iso"" ta ji wata murya na faɗa, ana ci gaba da shewa da kaɗe-kaɗen garaya." """Ku kawo Nono da suga, a kirawo 'yar Mairo ga mijinta ya iso. Ga farin goro ƙwarya dubu biyu ta rafi ta" "ce a bawa mamman wakilin rafi, gaisuwar iyaye"" sai kuma aka saka shewa. Ba yau Nana ta fara ire-iren wannan jiye-jiyen ba, amma ta tsorata da wannan sosai da sosai. Ta rirriƙe Sayyid, ga sanyin da take ji ya" fara damunta. "Cas cas cas, ta fara jin sautin kaɗawar wani abu mai kama da abin ado na mata." "Ta kalli tsakar gidan ta hango wata irin zanƙaleliyar mata, mai tsawon gaske ƙafafuwanta duk sarƙoƙi, ta" "yi shigar Fulani, sai dai ita ma ba a iya ganin sawayenta tamkar a kan iska take tafiya. Ta ɗan ƙara buɗe idonta, ta ga rana ce tarwai a tsakar gidan, ga dandazon mutane ana ta hada-hada." Ayshacool "Sai dai shigar mutanen irin na zamanin da ne can baya sosai, kamar dai taron wani abu ake yi." "Wata mata ta hango sanye da kayan saƙi farare tas, ƙugunta sanye da wuri, kanta babu ɗan kwali duk ta" "yi wa tulin gashinta adon wurin, hannunta riƙe da sandar dargaza, tana kaɗa ta tana juyi." "Wannan bafulatanar ce ta tsaya a bakin ƙofar ɗakin Nana ta ce ""Baƙuwarmu, bikin girka ake yi, ko za ki" "taso ki ga yadda muke gudanar da al'adun bikin girka?"" ta yi maganar tana zuro zanƙalelen hannunta" "cikin ɗakin Nana""." """La'ilahaillalah, Sayyid, Sayyid wayyo Baba"" ta tashi a gigice, rirriƙe ta ya yi, ya janyo wayarta, ya haska ta." "Fuskar sa cike da mamaki yake kallon ta, yanayin fuskarsa ke bayyanar da alamar tambaya." """Sayyid wata mata ce, wata mata ce take ziro hannunta, tsoro nake ji, wasu mutane ne a tsakar gidan" "nan"" ya haska ɗakin ta ga babu komai, haka tsakar gidan ma dare nesai hasken farin wata, babu komai." "Sai a lokacin ta fahimci mafarki take yi. Ya ji jikinta ya yi sanyi ƙalau, amma bai ga Ƙaisar a gurin ba, bai" kuma ga wata alama da take nuna yana gurin ba. "Gaba ɗaya ta nemi ko addu'a ɗaya, ta rasa a cikin kanta. Ta kaɗa ta raya amma babu abin da ya zo da" "kanta. Tana so ta karɓi wayarta ta kunna karatun Alƙur'ani, amma ko ƙwaƙƙwaran motsi ba ta son yi," saboda tsoron da take ji. Da ƙyar wani baccin ya ƙara sace ta. "Babu babban abin da ya ba shi mamaki, irin yadda da safe take komawa normal, babu ma alamar akwai" wani abu da yake ba ta tsoro cikin daren. "Haka ta ci gaba da sabgoginta. Sai dai gaba ɗaya a kunyace take, ko idonsa ba ta iya kallo, saboda abin da" "ta aikata ya kama ta cikin dare. Shi ga tausayin kan su, ga kuma dariya ta ba shi." * "Baba yana zaune yana shan koko da ƙosai a tsakar gida, sai ga kiran wayar Uwani." "Ya kalli wayar tasa ya ce ""Tofa! Wannan jarababbar tsohuwar ko me za ta ce mini, take kira na da safiyar" nan oho. Ya ɗaga kiran ya saka a kunnensa. Sai dai ba ya jin ta sosai saboda rashin network. Ba ta haƙura ba ta din ga kira har sai da ransa ya fara ɓaci. """Uwani ko a haƙura da wayar ne, kin ga babu network ne""" """A'a ina jin ka yanzu. Amm dama kiran ka na yi, na tambaye ka ina Nana kuwa?""" """Nana, tana gidan mijinta""" """Gidan mijinta wanne?""" """Mijinta dai na aure""" "Uwani ta ce ""Eh a ina gidan yake?""" """Amm can wajen gidan Ummi ne""" """Rufe mini baki, mutumin banza da na wofi. Ai kwana uku kenan ina neman layinka, amma bana samu" "saboda garin nan bamu da natiyok ake cewa ko me?""" """Uwani wai me ya faru ne?""" """Ai ba za ka san meyafaru ba, tun da ka bar yarinya tana ragaita ita kaɗai ranta ga miji mai larura,an kore" "su daga gidan haya, ba su san ma inda za su je ba, kana zaune hankalinka kwance. Ai ko 'yar riƙo ce Nana" "ka duba lamarinta""" "Ta inda ta shiga ba ta nan take fita ba, ta wanke shi ta tas, ta ƙare masa zagi da cin mutunci, ta ce kuma" "za ta kira Yaya Atine ma, sai ta ci ubanta." "Ran Baba ya yi mummunan ɓaci, kenan Ummi da Nana haɗa kai suka yi, suka kai ƙararsa gurin Uwani. Ya" "kira Ummi ita ma ya fara sauke mata kwandon tijara. Ranta ya ɓaci ta ce ""Ni fa Baba ban kai ƙarar ka" "gurin kowa ba, Uwani ce ta kira waya, mu na tsaka da alhinin halin da Nana ne ciki, na gaya mata komai, kuma ni na faɗa ba Nana ba. Shi ne ta ce Nana su koma Ƙauye can gurin ta""." "Sai kuma Baba ya yi sak. ""Ƙauye kuma? Ta yi me a ƙauye?""" """To Baba zaman nan ɗin ya ƙi, kai kuma ka ƙi taimakawa, babu yadda muka iya Nana tana Buda""" """Ke Ummi ki na ji na, duk yadda za ki yi, ki nemi kuɗin mota, ki je Buda ki taho mini da 'ya ta. Lallai ya" "sakar mini 'ya ku taho tare, ya je Allah ya ba shi lafiya""" """Baba ya sake ta, 'yan uwansa ma ba a sa inda suke ba, wa za ta bar wa shi a can?"" Yana cikin bambami" kuɗin wayar suka ƙare. "Dama Mama na tsaye tana jiran ya gama wayar, yana gamawa ta dube shi ta ce ""Wato Nana ta kaso" "aurenta ta dawo ko? To wallahi ta dawo gidan nan ba ta da gurin zama, wai har ka manta irin zaman" "azabar da muka yi da yarinyar nan a cikin gidan nan? Babu bacci kullum bala'i da tashin hankalin iskokai," "ba zai yiwu ba wallahi""" Ayshacool "Sai dai kafin Baba ya ba ta amsa, suka ji Suwaiba ta ƙyaƙyace da wata irin dariya mara daɗin ji tana faɗin" """Asma'u a ƙauyen Buda, tushiya masomar dawa, kowa ya bar gida gida ya bar shi"" ta yi maganar tana ci gaba da ƙyaƙyata dariya kamar ba mace ba." """Ke Suwaiba meye haka, wannan wace irin dariya ce? Ban hana ki irin wannan dariyar ba kamar ba mace" "ba?""" "Suwaiba ta ce ""Ina ruwan ki da dariyata""" "Baba kawai ya gyaɗa kai, ya gyara hularsa ya fice ya bar gidan gaba ɗaya." **** "Rashin maganar nan ta Sayyid, ba ƙaramin damun Nana take yi ba, abin ya yi yawa sosai." "A wannan karon ta yi sa'a, ya bar ta ta je gurin Uwani, daga nan kuma ta je ta yo musu sayayya. Ta tafi ta" "bar shi da wayarta, domin ta ɗebe masa kewa." * "Alhaji Zailani ya saka sabon layin da ya sayo a cikin waya, ya kira lambar Nana. Sayyid yana kwance yana" "jin yadda wayar take ta vibrating, amma ya yi banza. Saboda ko ya ɗaga ba iya magana zai yi ba." "Jin mai kiran ba shi da niyyar daina kiran, ya sanya ya ɗauki wayar zai kashe. Sai dai ya fasa kawai ya" ɗaga kiran ya kara a kunnensa. """A tunanki dan kin yi blocking ɗin lambata, zai sanya na kasa cimma burina a kan ki ne? Yanzu hankalina" "ya dawo gare ki, na saka an kori mijinki daga gurin aiki. Kuma zan nemo ki duk inda ki ka shiga sai na cika burika a kanki"" wani irin jiri Sayyid ya ji ya fara ɗibar sa." """Ba za ki yi magana ba?"" Alhaji Zailani ya yi maganar yana kallon wayarsa. Wani irin haske ya ga wayar" "tana yi, tana fafar fafar za ta ɗauke. Mamaki ya kama shi, dan wayar ba ta taɓa yin haka ba. Fitilun ɗakin suka ɗauke, duhu ya gauraye ɗakin nasa. Sai ya rikice ya tashi tsaye yana waige-waige." """Karo na biyu, ka sake shigowa hanyata, duk da gargaɗin da na yi maka, cewar mallakina ce, ina sake yi" "maka gargaɗi, kafin na tona maka asiri."" Alhaji Zailani ya toshe kunnensa, saboda wani irin sauti da yake ji mara daɗi, ga ɗakin yana ta jujjuya masa." "Can ya ji shiru ya daina jin sautin, ya buɗe idanunsa a hankali. Sai dai ya ga Shukura a tsaye a gabansa," "jini yana bin ƙafafuwanta, ga wuƙa a hannunta, tsirara ta." "Ya miƙe cike da razani, ya fara ja da baya." """Daddy ina jaririna? Ka bani jaririna Daddy"" Ya ci gaba da ja da baya. Da gudu ta bi shi, da wuƙar" tsirararta. Ya fita da gudu yana ihu. """Alhaji lafiya kuwa? Anya hawan jinin nan bai fara taɓa maka ƙwaƙwalwa ba, ya ya zaka din ga ihu" "haka?"" Hajiya Amina ta yi maganar cikin mamaki tana kallonsa. Ya kalli gurin ya gan shi a kan gado, a ɗakinsa. Yana son yi wa Hajiya Amina tambayoyi, amma abu ya gagara saboda tsabar razani da tashin hankalin da yake ciki." AREWABOOKS * "Uwani ta din ga yawo da Nana a cikin ƙauyen nan, tana nuna ta a dangi, tana gaya musu 'yar gurin Isa ce." Dan galibi ba su santa ba. "Nana gaba ɗaya hankalinta yana kan Sayyid da ta baro a gida, shikaɗai tana gudun kar ta je yana buƙatar" "wani abin. Ganin gantalin ya yi yawa, ga duk inda suka je sai Uwani ta tsuguna ta surutu kamar babu gobe." "Tun Nana tana jurewa, har ta gaji ta ce ""Uwani, na bar mara lafiya a gida, ko za mu je inda zan yi" "sayayyar, na koma kar na je yana buƙatar wani abin." "Uwani ta ce ""Kuma fa haka ne, to mu je na raka ki. Na so ma sai ranar kasuwa za ki je sayayyar, an fi" "samun rahusa. Ai tun da Allah ya sa ki ka zo garin nan, za ki yi ta ganin 'yan uwa da dangi, za a yi ta zuwa duba mijin naki ma""" "Ita dai Nana ta yi shiru, dan duk surutunta, Uwani sai da ta saka ta gaji, ga azabar tafiyar ƙafa da suka sha." "Ta rakata inda ta yo musu 'yan sayayyar kayan abinci, gaba ɗaya tsoron taɓa kuɗin take yi. Gani take yi" kamar ƙarewa za su yi. "Uwani ta raka ta har gida, sannan ita ma ta zagaya, ta koma nata gidan." "Nana ta shiga ɗakin da Sallama, tana faɗin ""Sayyid, ka ganni sai yanzu ko, ka yi haƙuri Uwani ce ta din ga" "ja na, ƙafafuwana kamar su karye"" Sak dai ta yi shiru ganin wata irin kwanciya da ya yi a kife a kan cikinsa, hannunsa a lanƙwashe, kuma ba kamar mai ruf da ciki ba." "Ga shi a tsakiyar ɗakin, ba inda ta tafi ta bar shi ba." Ayshacool "Ta zube kayan ta nufe shi jikint a sanyaye, gabanta na bugawa saboda fargaba da tsoron ko mutuwa ya" yi. Aikuwa tana juya shi ta ɗan ja da baya a tsorace tana sauke numfashi. "Wayarta ta gani a ƙarƙashin inda ya kifa, idanunsa a kakkafe, babu baƙar ƙwayar idon, sai farar. Ga jikin" zafi rauuu tamkar wuta. "Ajiyar zuciya ta yi cike da damuwa, ta matsa kusa da shi ta yi Bismillah ta fara rage masa kayan jikinsa. Ta" ɗebo ruwa ta din ga shashshafa masa tana sake nanata Bismillah. "Ta je ta rufe ƙofar gidan, ta dawo ta cire rigar jikinta, ta kwanta a jikinsa, tana rintse idanunta saboda" raɗaɗin da take ji a fatarta. "Wani irin nishi yake, tamkar zai yi gurnani, yana miƙa jikinsa yana ƙara sandarewa." "A hankali ta ji tamkar hankalinta yana gushewa, ita ba a farke be, kuma ita ba mai bacci ba. Ta ɗan ɗaga" "idonta, ta ga Ƙaisar tsaye a jikin ƙofar ɗakin yana kallon su. Ta yi shiru ba ta yi motsi ba, kuma ba ta yi magana ba, fatanta Sayyid ya samu sassauci daga azabar raɗaɗin da yake ji." """Ko dai ki bi a hankali, ko wannan ɗan tayin na cikinki ya yo waje saboda zafin jikinsa. Ko kuma Giyaz ya" "yi masa mummunar illa."" Nana ta ɗaga kai ta kalli inda Ƙaisar yake, jikinta ya yi mata wani irin nauyi, ba" ta ko iya motsa ɗan yatsanta. """Babu irin kashedin da ban yi miki ba tun da fari, ki ka yi burus da ni, gani ki ke kawai cutar da ke ne" kaɗai abin da nake yi. "Amma tun da jimirnki taurin kai, wahala sai ranar da Allah ya yanke miki, tukuna ma."" A hankali ta" lumshe idanunta har ta daina jin muryar Ƙaisar. **** "Cikin damuwa Maijidda take kallon Saude ta ce ""Yaya Saude haryanzu lambar Nanan ba ta shiga ko?" "Gaba ɗaya na kasa nutsuwa duk ji nake hankalina a tashe""." "Saude ta ce ""Dan Allah ki daina damun kan ki, in sha Allah tana cikin ƙoshin lafiya, kin san sharrin" "wayoyin nan, da rashin network, amma zan ci gaba da kiran ta, da na same ta zan sanar miki, kuma zan sake zuwa har gida na haɗa ki da ita.""" """To Allah ya sa dai lafiya, kin ga na yi, na yi, na kaɗa na raya, Baban su Walida ya ƙi ba ni wayata, tsawon" "wannan lokaci haka nake zaune babu waya. Kuma duk wasu dabaru da zan yi na samu dama na je Kano na samu na ga yaran nan, abu ya ci tura sai ka ce ba Muslimi ba, ba ya jin magiya ba ya jin rarrashi""." """A'a kul Maijidda, uban 'ya'yan naki ki ke cewa kamar ba musulmi ba, kar ki sake. Ki rabu da shi da" "halinsa. Duk da Nana tana cewa za ta zo ita da mijinta, idan ma ba su zo ba, ni zan sake komawa na gano miki ita in Allah ya yarda. Iliyasu kuma ki rabu da shi ku lallaɓa kar ki fusata shi ya yi wani abin da ba a" "fata""" "Maijidda ta yi ajiyar zuciya, ta jinjina kai kawai, amma gaba ɗaya ba ta cikin nutsuwarta." **** "Abu kamar wasa, aka shafe kwanaki biyar, Sayyid yana cikin wannan yanayin, sai dai Nana ta juya shi, ta" "goge masa jikinsa, ta yi masa ƙanin wanka a ɗaki, ta shafa masa turare ta saka masa kaya." "Ga shi juya shi kawai aiki ne, saboda yadda ya yi mata nauyi, ga jikinta babu ƙwari saboda azabar laulayi." "Juriyarta ce kawai ta sanya ba a gane mawuyacin halin da take ciki, dan ba ta taɓa yarda ta kwanta." "Ga shi jikinsa duk ya kumbura, mussaman ƙafafuwansa." "Tana zaune ta yi shiru tana kallonsa, kawai tamkar an yaye mata wani abu daga kanta, sarkin baka ya" faɗo mata. Sai da ta ɗan zabura ta tafi tunanin ko yana wani hali yanzu?. """Ko dai can zan kai ka Sayyid?"" Ta yi maganar tana kallonsa." """To ni da ban ma san a ina yake ba, ta yaya zan kai ka?""" """Kul mene ne sahihancin magungunan da yake bayarwa? Mene ne halacci ko haramcin abin da yake yi," "da za ki je neman magani gurinsa?"" Wata zuciyar ta gargaɗe ta." "Sai kuma ta yi shiru, tana tuna irin wahalhalun da ta sha, da faɗi tashin gurin masu magani, ita dai tana" "da yaƙinin har gurin bokaye da 'yan tsubbu an kai ta, domin a nema mata magani. Domin wasu ƙarara" "ayyukansu da abubuwan da suke faɗa, ne nuni da kaucewa hanyar gaskiya." Ayshacool """Allah na tuba, Allah ya sanya ba wannan ne dalilan da ya sanya nake ta shan wannan wahalar ba. Allah" "ka yafe mini, ba da son raina aka din ga kai ni wasu guraren ba." "Allah ka bamu lafiya da ni da mijina, Ubangiji Allah ka yaye masa wannan larurar, ka dawo masa da" "tunaninsa. Allah ban yanke tsammanni da daga falalarka da ni'imamominka ba""" "Ta juyo a hankali ta dubi gurin da yake, ta ga idanunsa sun dawo daidai yana kallon ta. A rikice ta ce" """Sayyid""" """Ma vie""" "Cikin tsananin murna ta ce ""Alhamdillah, ka tashi?"" Ya jinjina kai yana lumshe idanunsa da suka yi masa" "nauyi. Ya ja jikinsa ya tashi zaune da kyar. Sai dai jikin nan duk a kumbure,ga kuma haki da ya farfaɗo da shi. Haka yau ma ta taimaka masa ya yi wanka ya ci Abinci ya fara rama sallolinsa a zaune." "Kallonsa take yi cikin damuwa, yakamata a ce sun koma Asibiti. Amma kafin a nemo mota a saka shi, su" "yi sammako su koma Asibiti, aiki ne. Mussaman da babu wadattacen kuɗi a hannun ta." "A take ta tuna da maganin da sarkin baka yake haɗawa masu hawan jini, da wanda ɓarin jikinsu ya" shanye a sakamakon hawan jini da matsalar zuciya. "Ba ta jira ya idar ba, ta zari hijjabi ta yi waje. Ta din ga tuhumar kanta da yadda aka yi tuntuni ba ta tuna" "ba, sai yanzu. Tun da su magunguna ne da yake haɗa s da saiwoyi ba wani surkullen ya yi ba." Ta dawo ta tarar ya dawo bakin ƙofa ya zauna yana kallon hanya. "Tafiya mai nisa ta yi sosai da ta fita, ta samo ɓawon kwakwa da sassaƙen zogale, sai kuma farin zoɓo." "Ta hura wuta ta wanke su, duk ta zuba a tukunya ta zuba ruwa, ta kawo ɗan kanumfari ta zuba a ciki." "Sai da ta kammala sannan ta koma gurinsa, ta ce ""Ka yi haƙuri, magunguna na je samo maka, na fita ka" "na salla""" """To na gode""" """Allah ya baka lafiya shugabana, Allah ya sanya ya wuce kamar ba a yi ba""" """Amin. Ke ma Allah ya baki lada, ya saka mini ke a aljanna. Ya sanya ki maƙwabci Manzon Allah Sallallahu" "alaihi Wasallam a aljanna"" waro ido ta yi ta gigice gaba ɗaya hawaye ya fara zirarowa daga idanunta ta ce ""Sayyid ba ni da aikin da zai kai ni wannan matsayin. Amma ban san matsayinka a gurin Allah ba. Ban sani ba ko Allah ya karɓi addu'ar da ka yi mini. Amma a ce na maƙwabci Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam. Innalillahi wa Innalillahi raji'un Sayyid na rasa me zan ce. Baiwa ce mai tarin zunubai kuma mai tarin rauni. Amma Allah kai mai yawan rahama ne da falala, Allah ka amsa wannan addu'a da ya yi" "mini shi ma ka ba shi abin da ya roƙa mini""" "Ya yi murmushi ya ce ""Amin rayuwata""" """Sayyid, anya an taɓa yi mini addu'a da ta tsuma ni kamar wannan? Subhanallah, subhanallah. Na ji daɗi" "wallahi""" "Shima idanunsa ne ya cika da hawayen, ya ci gaba da bin ta da idanunsa. Kawai sai Nana ta ji ta manta" kaso mafi yawa na damuwarta. Da ta tuna Addu'ar da ya yi mata sai murmushi ya kasa barin fuskarta. "Maganinta ya daɗe yana dahuwa, ta sauke ta mayar da ruwan girki. Ta tsiyaya masa a kofi, ta je ta zauna" a gaban sa. """Sayyid ga magani na dafa maka, mu jarraba, bamu sani ba, ko Allah zai sanya a dace"" ya kalli kofin ya" "kawar da kansa gefe, yana ɓata rai." "Ta marairaice ta ce ""Dan Allah ka sha, babu ɗaci ko bauri fa""" """Ba na son magungunan nan, babu yadda na iya ne nake shan na Asibitin ma, ni wahalar da ni suke yi""" """To ai wannan ba na Asibiti ne ba, dan Allah ka daure ka taimaka, ba dan ni ba""" "Da ƙyar ya yarda ya karɓa, ya ɗanɗana ya ji babu ɗaci, sannan ya ci gaba da sha, sai ma ya ji ɗumin" maganin ya yi masa daɗi. "Bayan ya shanye, ta dafa masa shayi kuma, ya ɗora dan duk wahalar ciwon da yake ciki, ba ya iya haƙura" da shan shayi. "Nana ta dage da bawa Sayyid, wannan ruwan maganin, tana addu'ar Ubangiji Allah ya taimake su, ya" sanya ya karɓe shi. "Cikin ikon Allah, sai kumburin da ya yi, ya fara sacewa a hankali, har yana iya cin Abinci sosai. Nana" kamar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha. "Nana ta din ga murna, ganin ana samun ci gaba a yanayin jikinsa. Har banɗaki yana iya zuwa, ba tare da" "ta kama shi ba, yana tafiya a hankali a hankali da kansa yana iya yi wa kansa Wasu abubuwan." "Yana zaune tsakar gida, yana shan shayi ta ce ""Ashe maganin Sarkin baka yana yi""" Ayshacool "Ya kalle ta, ta ce ""Ka san Sarkin baka?"" Ya ɗan yi shiru yana kallon ta." """Ranar da aka kai ni, kai ma an kai ka, zaku tafi lokacin, ni kuma a lokacin ni kuma a lokacin na ji na fita" "daga hayyacina. Kai mun fa daɗe muna haɗuwa da kai.""" "Ya yi murmushi ya ce ""Ruhina ne ya addabe ki, sai da ki ka nemo ni, ki ka aure ni ki ka nutsu""" "Ta ɓata fuska ta ce ""Ba wani nan, kai ne ka din ga bi na dai, har ka aure ni""." "Ya ɗan sake zuƙa shayin hannunsa ya ce ""A'a. Har gidan da nake ki ka bi ni fa""" """Ni ba bin ka na yi ba, kuma ai kai ka ce a biya maka sadakin aurena""" "Ya maze ya ce ""Ai gani na yi kin liƙe mini, har cikin ɗakinmu na gadi ki ka bi ni, na ce kai yarinyar nan idan" "ban aureta ba, akwai matsala haka za ta yi ta bina saboda ruhinta da yake jikina. Kina ganina kuma ki ka rikice""" """Ni ba ina sane na shiga ɗakinku ba, Jummai ce ta ce na ajiye muku Abinci, kawai na ji ana kirana a cikin" "ɗakin, ban ma na san na shiga ba. Kuma ni da na shiga wannan tsohon na gani. Kuma ai kai ma idan ka ganni kallona ka ke yi""" """A'a faɗi gaskiya dai, ni ki ka leƙo ki gani, ranar ba ki ganni ba, sh... Kawai ya ga tana hawaye. A diririce ya" "ajiye kofin hannunsa ya ce ""Mene ne?"" Ta yi masa shiru." """Laifi na yi miki? Wasa fa nake yi"" ta yi masa shiru, tana matse ƙwalla. Ba wai wasan da yake yi mata ne" "ya sanya ta kuka ba. Tuna yadda aka yi auren abin da Baba ya din ga faɗa da wanda Mama ta din ga yamaɗiɗi da ita, abin ne kawai ya dawo mata." "Ji ta yi yana goge mata hawaye, fuskarsa ɗauke da damuwa, ya ce ""Ba zan sake ba"" Kwaɓe baki ta yi cikin" "shagwaɓa, wasu hawayen na ziraro mata." """Na ce na daina fa, ki bari ƙirjina ya fara nauyi"" da sauri ta saka bayan hannunta, tana goge hawayen" fuskarta. """Yauwwa dama ina so mu yi wata magana, mai muhimmanci da ke""" "Ta tattara hankalinta, gabanta na dukan uku-uku cike da wasi-wasin wace maganar zai yi da ita haka?." Ayshercool 08081012143 Ayshacool "Ya yi mata alama da hannunsa, a kan ta nutsu ta kwantar da hankalinta. Ta jinjina masa kai, duk da" gabanta na ci gaba da faɗuwa. """Amm na san kina haƙuri a kan abubuwan da suke faruwa, duk da kin ce mini ba kya so na din ga irin" "wannan maganganun, amma sun zama dole na yi. Ina ƙara yi miki godiya da nema miki yardar Allah, na" san ba ni da abin da zan biya ki da shi a wannan Duniyar. Ke ce komai nawa da ki ka rage Asmy. Sannan "ɓangaren abin da ya shafi auratayyarmu, shi ma na san..." "Ta katse sh6ta hanyar cewa ""Amm ni dai a bar wannan zancen, bari na je na ɗora wakena""" """A'a ki tsaya mu yi magana""" """A'a ba sai mun yi ba""" """To kar na sake jin kin bi dare ki na taɓa ni"" Kamar ta yi tsuntuwa ta ɓace, saboda azabar kunya, ita a" "zatonta ma ya manta gaba ɗaya. Cikin azama ta miƙe ta ɗauki robar wakenta, ta nufi inda take girki. Tana tashi ya kashingiɗa yana dariya." "Nana tana ta fifita wuta, yana daga zaune yana kallonta. Wani irin abu ne yake yi masa yawo a jikinsa, a" game da ita. "Yana jin zai iya yin komai, dan tabattar da ci gaba da zamanta mallakinsa, shikaɗai." "Juriyarta, sadaukarwa da kuma tsananin tausayinta, ya sanya yake jin ina ma yana da wani abu da zai iya" "kamanta faranta mata rai, kamar yadda take ta wannan ɗawainiyar da shi. Ya san in dai a wannan Duniyar ne ba shi da abin da zai biya ta. Duk da matsananciyar damuwar da ya kan shiga, da jin cewa ya zama silar nakasta rayuwarta, ta zama tana rayuwa ba tare da tunanin wani abu da take so ta cimma ba." Kullum tunaninta a kan sa ne kawai. "Tana ɗagowa suka haɗa ido, ta murguɗa masa baki, ta ci gaba da fifitar wutar gabanta." Ya tako zuwa gaban murhun ya tsuguna. """Dan Allah ka tashi, saboda numfashinka fa""" """Kawo na yanka miki salak ɗin""" """A'a kar ka yanke hannu""" "Ya ce ""Ki kawo zan iya"" Ta tsuke fuska ta kalle shi ta ce ""Saboda sauƙi ya samu, kana iya fitowa da kanka" "yanzu, shi ne za ka din ga damuna ko?""" "Ya yi murmushi, ya zauna a gefe yana kallon ta, da ta ɗaga ido, sai su yi ido huɗu da shi, sai ya yi mata" murmushi. "Su na cikin cin abinci, ya ce ""Ki na kiran Ummi?""" """Ba na samun ta, ita ma ta kira ni wayar ba na ji. Uwani ta ce haka garin nan yake babu network, sai a yi" kira fiye da sau goma ba ka samu mutum ba. """Idan na ƙara jin sauƙi, zamu je mu gaishe ta, mu yi mata godiya""" "Ta ce ""Alhamdillah, lallai sauƙi ya samu.""" "Ya ce ""Eh, ina jin hakan a jikina nima. Mu je waje na ɗan tattaka na ga gari""" "Nana ta faɗaɗa murmushinta ta ce ""Allah abin godiya, wallahi Sayyid da har na fara fitar da rai da kai, na" "karaya sosai wallahi"" Cikin murna ta saka hijjabinta, suka fita. Su na tafe a hankali ta kalle shi ta ce ""Gaskiya na yi mamaki, ashe da gaske magungunan sarkin Baka yana yi""" "Ya tsuke fuska ya ce ""Na gaji da jin zancen Sarkin Bakar nan""" "Nana ma ta yamutsa fuska ta ce ""Sayyid ka yi haƙuri, amma na yi farin cikin yadda maganin da na gani a" "gurinsa ya yi maka aiki. Ina yi masa fatan idan a kan daidai yake, Ubangiji Allah ya ƙarfefe shi ya dafa masa, ko dan saboda yadda yake taimakon mutane. Idan kuma a kan kuskure yake Ubangiji Allah ya ganar da shi, ya ba shi ikon tuba kafin lokaci ya ƙure masa.""" "Sayyid ya yi mata banza, suka ci gaba da takawa a hankali su na zagayawa." "Wani irin sanyi ne ya fara ratsa Nana, ganin Sayyid ya durfafi wata hanya, ta kuma kasa ce masa uffan," "balle ta hana shi. Su na tunkarar gurin, ƙirjinta na bugawa da sauri da sauri." Wata irin narkekiyar bishiyar kuka suka tarar a gurin mai ban tsoro. Yanayin yadda take ɗauke da wasu "irin murɗaɗɗun rassa, da yadda murtuka-murtukan jijiyoyinta suka huda ƙasa suka mamaye gurin. Ga wani irin ƙaton kogo a jikinta, hakan ya nuna daɗewar da bishiyar ta yi da wanzuwa a gurin." """Asma'u"" ya kira sunanta kai tsaye. Ta kalle shi cikin matsanancin mamakin yadda ya kira sunanta na" yanka kai tsaye. """Ji nake yi kamar na san gurin nan""" Ayshacool "Jiki a sanyaye Nana ta ce ""Nima haka, amma ni dai na san ban taɓa zuwa gurin nan ba, amma ina jin" "kamar na san gurin, amma dai... Sai kuma ta yi shiru bayan da gurin ya gauraye da duhu aka yi wata irin walƙiyya, haske ya mamaye gurin. Tsohon nan ta gani a tsaye, riƙe da sandarsa ya zubo wa Nana idanunsa marasa kyan gani. Jikinta ne ya ɗau kyarma, ta ƙara rikicewa bayan ganin a hankali wasu halittu" da take kyautata zaton ire-iren su Ƙaisar ne su na bayyana a bayansa. "Tsohon ya kalle ta, ya buɗe baki ya fara magana. ""Ina sake yi miki barka da zuwa, garin da kakanin" "kakaninki su ka durƙusa suka haifo matsalar da har abada ba za ta daina bibiyar zuriyar su ba. Zan ci gaba da azabtar da rayuwarki, za ki ci gaba da biyan bashin nan, ko bayan ranki, muddin aka ci gaba da samun haihuwar masu irin tauraronki.""" "Yana rufe bakinsa, ɗaya daga cikinsu da Nana take kyautata zaton jininsin mace ce, saboda yanayin wani" irin tsohon mayafi da ta yafa a kanta. Ta tunkaro Nana gadan-gadan. "Tana zuwa matar, ta hankaɗa Nana ƙasa, sauran suka rufu a kan Nana, su na zira hannunsu a mararta, su" na ciro gudan jini. """Ya hayyu ya ƙayyum ya Allah. Allah ka kawo mini ɗauki, Sayyid, Sayyid, Sayyid ka tashi"" Ta yi maganar" tana jijjiga Sayyid da yake kwance a gefen ta yana bacci. "Ya ja jikinsa ya tashi ya ce ""Ma viee lafiya kuwa?""" """Sayyid marata ciwo take yi. Sayyid marata. Sayyid babyna. Ba na son na rasa jaririna a wannan karon," "Dan Allah ka taimake ni""" "Cikin rashin fahimta ya ce ""Meyafaru ne?""" """Marata ce take ciwo, Sayyid ba na son cikina ya zube, ina son jaririna Sayyid ciwo marata take yi sosai""" "Ta yi maganar tana zubar da hawaye. Ya saka hannunsa a mararta, ta saka hannayenta ya dafe hannunsa tamkar hakan ne zai hana cikin zubewa." "Ya ce ""Ki yi Addu'a"" Kawai ta jinjina kai, amma Addu'a kam, ko ɗaya ba ta zo kanta ba, dan ta manta" komai daga cikin kanta. "Cikin rauni Nana ta ce ""Sayyid fitsari nake ji, ya matse ni""" "Ya ce ""To mu je ki yi""" "Ta girgiza kai ta ce ""A'a ba na son na je na ga jini ya zubo, cikin ne zai zube""" "Ya ce ""A'a ba za ki gani ba"" . Ta miƙe ya kama hannunta, ya haska fitila har banɗaki, su na zuwa a tsorace" "ta yi fitsarin, sai dai tana yi sai ga jini. Wani irin kuka ta fashewa da Sayyid. Ta miƙe jikinta yana rawa." "Ya rungume ta ya ce ""Ki yi haƙuri, kin ga dare ne, ki daina kuka. Kuma idan za ki yi ɓari, jinin da ki ke" "zubarwa ya fi wannan kin manta?""" """A'a idan jini ya fara zuba, shikenan ciki zai zube""" "Ya ce ""A'a, ba haka ba ne, ai bai zuba da yawa ba"" Ya lallaɓa ta da ƙyar, ta gyara jikinta, ta ɗauraye jikinta," da banɗakin su ka koma ɗaki. "Karatun Alkur'ani ya kunna a waya, ya ajiye a gefen katifar da suke kai, kamar yadda ya ga tana yi, a duk" lokacin da su ka shiga yanayi na tsoro. "Suka kwanta yana ɗan shafa ta, cikin sigar rarrashi." "A hankali ta ce ""Sayyid""" """Na'am""" """Da gaske mun fita ɗazu ko?""" """Eh mun fita""" """Mun je can bayan gari, har ka ce mini kamar ka san gurin?""" """Eh haka aka yi, mun je""" "Ta sake cewa ""To daga nan meyafaru?""" """Faɗuwa ki ka yi, na riƙe ki muka dawo gida. Tun da muka dawo kuma ki ke bacci""" "Ta yi shiru ba ta sake cewa komai ba, ta ƙara lafewa a jikinsa cikin tsoro. Yau ma kwana suka yi, tana" gane-gane da jin abubuwa daban-daban masu razanarwa. "Wannan bafulatanar matar ce, ta ƙara zuwa ta tsaya a saitin tagat Nana tana kiran ta, a kan lallai sai ta" fito ta ga yadda suke gudanar da bikin girka. Nana ta ƙara rintse idanunta tare da ƙanƙame Sayyid. "Da safe ta tashi da wani irin nauyin jiki, ga sanyi da ta kasa daina ji. Ta duba ta ga ba ta kuma ganin jinin" "nan ba. Ta yi wanka ta rama sallolinta, sai dai Sayyid bai tashi ba. Da ƙyar ta samu ya yi alwala ya yi salla." "Ta gaishe shi, amma bai yi magana ba sai kallonta da yake yi. Hakan ya sanya ta fuskanci maganar ta" ɗauke. "Ta tambaye shi za ta fita, amma bai ko ɗaga kai ya kalle ta ba. Ta saka hijjabi ta fita ta bi 'yan matan" gidan Uwani gona roron gyaɗa a gona. "Allah ya taimake ta, ta samo da yawa ta zo tsakar gida ta baje ta domin ta sha iska." Ayshacool "Ta kai hannu ta janyo hannun nasa, dan ta damƙa masa kofin kunun, amma ta ji hannun a ƙame ƙam. Ta" "sake ƙoƙarin janyowa, amma ta ji tamkar tana jan itace." "Ta kalli hannun sosai, sai ta ga shanyewa ya yi." "Gabanta ya yi wata irin mummunar faɗuwa, ta ce ""Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Sayyid me ya same ka" "haka? Me ya samu hannunka? Ya Allah!"" Ta yi maganar tana kuma ƙoƙarin ganin ta miƙar da hannun nasa, amma hannun yana maƙale, kamar an tsotse shi." "Ya sunkuyar da kai ya yi shiru, fuskarsa ɗauke da damuwa. Ta aro jarumta, ta matsa daf da shi, ta ɗebo" "kunun ta kai bakinsa. Amma ya tsaya yana kallonta, bai buɗe bakinsa ba." """Buɗe baninka na baka"" Ta yi maganar tana ƙoƙarin danne hawayen da ke ƙoƙarin ƙwace mata." "A hankali ya buɗe bakin, sai ta ga shi ma bakin ya karkace, yawu na ƙoƙarin zubowa. Kawai ya rufe bakin" "hawaye ya fara gangarowa daga cikin idanunsa. Ta ajiye kofin kunun ta rasa abin yi. Kawai rungume shi, ta fashe da matsanancin kuka, sai da ta yi iya yin ta." "Sannan ta cika shi, ta share masa hawayensa." "Ta fara ƙoƙarin ba shi kunun, sai dai tana ba shi, ya haɗiye wani kuma ya zubo." "Ta na yi tana goge masa wanda yake zubowa, ta gama ba shi, ta kama hannunsa su ka je waje, ta" taimaka masa ya yi alwala. Ya dawo ya rama sallolin da ta gaya masa ana bin sa. Sai dai ba magana ga "hannu a maƙale, da ta kalle shi sai ta ji hawaye ya cika mata ido." "Ganin yana gyangyaɗi a zaune, ya sanya ta saka masa pillow ya kwanta, ta saka hijjabi ta fita." "Tafiya mai nisa ta yi, ta je ta samu wani chemist, bayan sun gaisa ta ce ""Dan Allah malam, idan babu" "damuwa, Bp nake son mu je ka gwadawa mijina a gida""" "Ya kalle ta ya ce ""A ina ne?""" """Cikin Budu ne, nan unguwar maharba""" """Taɓ gaskiya da nisa gurin nan ba kaɗan ba, ba zan iya zuwa ba sai dai ki je ku zo tare a yi masa""" """Wallahi da zai yiwu, da ba zan zo na roƙe ka ba, yana kwance babu lafiya ka taimaka mini dan Allah""" "Ya ce ""Gaskiya kin san cajin zuwa gida ma ka yi wa mutum abu daban yake, sai dai idan za ki ba ni dubu" "biyu""" "Nana ta ce ""Eh na yarda mu je zan baka in sha Allah"" Ya rufe chemist ɗin ya bi Nana." "Su na zuwa gidan, Nana ta shiga ta tarar da shi a zaune ya tashi, ta ce ""Sayyid kar ka ga na fita ban gaya" "maka ba. Na je na samo wani ma'aikaci ne, ya zo ya duba jininka a gani, idan jinin ne ya hau ya sanya" "hannunka ya shanye, mu tafi Asibiti. Idan kuma ba shi ba ne, sai mu san abin yi."" Bai ce komai ba, ta yi" "wa mai chemist magana, ya shigo ya gwada jininsa." "Ya gwada ya kalli Nana ya ce ""Jininsa bai wani hau sosai ba, 140/90 ne"" Ajiyar zuciya Nana ta yi. Ta ce ""A" ganinka wannan hawan zai iya sanya masa shanyewar hannu?. "Ya girgiza kai ya ce ""Gaskiya ba na tunanin haka, amma ban tabattar ba tun da ni ba likita ba ne ba." "Amma a shekarunaa bana tunanin jinin 140 zai shanye masa wata gaɓa a jikinsa, amma dai ku je Asibiti a" "ƙara bincikawa""" "Nana ta ba shi kuɗin sa, ta yi tai masa godiya. Ta koma ɗaki ta zauna ta yi shiru, tana tunanin ko Uwani" "za ta tambaya, idan akwai wani mai magani, ta raka su, sai dai ta fasa saboda akwai sauran ɓurɓushin jahilci a tattare su, ba ta son surutu kuma tana tsoron a kai su gurin da ba shikenan ba." **** "Alhaji Fatuhu kuwa kamar yadda ya matsa, sai da aka sallame shi ya koma gida. Gidan nasa ma wani" "abokin kasuwancinsa ne ya saya, ya bar shi a ciki ya zauna ya bar masa aro." "Sagir yana kwance a kan gadonsa, yana kaɗa ƙafa ya ƙura wa screen ɗin wayarsa ido. Yusra ce zaune" "sanye da doguwar rigar material, kanta ko ɗan kwali babu, dogon gashin kanta ya sha gyara. Tana ta zuba masa surutu." "Har mamaki yake yi, yadda Yusra ta zama mai ɗan karen surutun tsiya, wanda da ba haka take ba." """Ya ka yi shiru ne?"" Ya wani lumshe ido ya ce ""Ina jin ki ai""." """So talk, ka yi magana mana"" ta yi maganar tana cika bakinta da guggurun hannunta." """Ina ga zan shigo Abuja mu haɗu very soon in sha Allah"" wata irin zabura ta yi ta ce ""Are You serious, dan" "Allah da gaske?""" """Da gaske nake, zan zo na ganki, amma ki na ganin babu matsala a zuwan nawa? Kar a yi miki faɗa fa, ba" "zan ji daɗi hakan ba""" Ayshacool "Yusra ta ce ""Babu wata matsala, ba za a yi mini faɗa ba, ai ba na tare da su Mami, ina gidan Anty" "Sumayya. Dan Allah ka zo""" "Sagir ya yi murmushi ya ce ""Kin yi missing ɗina ne?""" Ta gyaɗa masa kai tana murmushi. """Shikenan, i miss you too, ban taɓa tunanin ma za ki neme ni ba, na za ta ki na jin haushina haryanzu," "amma in sha Allah zan shigo, zan sanar miki lokacin da zan shigo na zo na ganki"" ya yi maganar yana kashe mata ido." "Shukura ce ta turo ƙofar ɗakin ta shigo, a burkice ya kif wayar yana kallon ta. Ƙarara yanayinsa ya nuna" "alamun rashin gaskiya, amma ta share shi, ta haye kan gadon ta ja bargo ta lulluɓe jikinta." "Ya matsa kusa da ita yana ɗan shafa ta ya ce ""Sweetheart, ya na gan ki kamar a fusace ne? Lafiya dai" "ko?""" """Lafiya ƙalau"" ta amsa a taƙaice. Ɗan shiru ya yi yana tunanin ko dai ji wayar da yake yi ne? Amma a" "yadda ya santa da azababben kishi, da zargi da ta ji sai ta yi masa magana. Sai dai ya bar abin a haka bai matsa mata da tambayoyi ba gudun kar su yi faɗa." "Tana ankare da take-taken Sagir, na rashin gaskiya. Sai dai ita yanzu ba wannan ne a gabanta ba, bin" diddigin mutuwar ɗanta take son yi. Dan haryanzu zuciyarta ta kasa amincewa da natural mutuwa ya yi. Domin haryanzu tana mafarke-mafarke marasa daɗi da mahaifinta da kuma Doctor Sharif. **** "Aka shiga sati na biyu, Sayyid yana cikin wannan yanayi na rashin lafiya, kuma hannunsa bai saki ba, yana" nan a maƙale. "Ga hauka da yake yi tuburan wasu lokutan, wasu lokutan idan ya burkice sai ya shaƙe ta, ko ya hankaɗe" "ta ƙasa, sai dai ta yi ƙoƙarin kare cikinta. Ko kuma Ya ya ta watsi da duk abin da ya ci karo da shi, a ɗaki" "ko a tsakar gida. Wasu lokutan ma katangar ɗakin yake duka da kansa. Ya ƙi cin abinci ya ƙi shan magani," "ba salla, komai sai dai ta yi masa cikin rarrashi da ban haƙuri. Tun tana jin tsoron ya yi mata wani abin," "har ta daina ji, ta zuba wa sarautar Allah ido." "Sannu a hankali ta rage yawan amai, sai dai zazzaɓi da rashin son cin abinci da take yi, hakan ya sanya ta" "tabattar da cikin jikinta bai fita ba haryanzu. Sai dai ba ma ta cikin nutsuwar da za ta nemi inda Asibiti yake ta je, ta tabattar da halin da suke ciki ita da jaririn saboda tashin hankalin da take ciki." "Yanayin yadda uwani ta lura kamar Nana na ɓoye wani abu, ya sanya ta daina zuwa gidan,ta rage aika" "yara ma. Sai dai lokaci lokaci, ta kan aika mata da Abinci." "Haka sauran 'yan uwansu na garin ma, su kan aiko mata da sha tara ta arziki saboda su na tausayin Nana," sun san mijinta a kwance yake babu lafiya. "Yawon roro a gona kuwa yanzu Nana ta ƙware, ranar kasuwa ta je ta sayar da abin ta." "Kasancewar ranar Asbar kasuwar garin take ci, sai ta tashi ta yi fanke da sassafe, jikan Uwani Haladu, ya" kai mata kasuwa. Ko ta dafa masa zoɓo ta ƙuƙƙula ya tafi da shi. "Idan ta gama komai kuma, ta bi yara gona roro." "Dare ya tsala, amma Nana tana zaune tunkurkur, wuni Sayyid ya yi yana wani irin nishi, ga wannan" azababben zafin jiki da yake fama da dhi. "Tana zaune tana tunani, tana jin yadda mararta take motsi, cikin jikinta yake motsawa." "Ba ta da sauran wanda za ta kai kukanta bayan Ubangiji. Ta fara tunanin ƙoƙarin tara musu kuɗin mota," "su tafi Nijar, neman danginsa, sai dai idan sun je Nijar ɗin ina za su nufa? Babu tsammani ta ji Sayyid ɗin ya laluba cinyarta, ya kwantar da kansa." "Ta shafa gashinsa ta ce ""Sayyid"" bai amsa ba, sai dai ya riƙe hannunta. Hakan ya tabattar mata da ya" "dawo hayyacinsa ne. Haka ta tashi a cikin daren ta tsiyayo ruwan zafi, ta ba shi shayi ta yi masa wanka suka kwanta, ta lulluɓe su da bargo." "Sheshsheƙar kukansa ta ji, duk da yadda ta san ya daɗe yana dauriya, da son ɓoye gazawarsa, sai dai ta" ga hakan a idanunsa. """Sayyid idan ka na kuka, ni kuma ya zan yi kenan? Dan Allah ka daina"" ta yi maganar muryarta na rawa." "Ta din ga shafa bayansa a hankali, har ya yi shiru, bacci ya ɗauke shi." Ayshacool "Sai dai tun daga wannan, haka aka sake shafe kwanaki biyu, bai sha ko ruwa ba. Dama rashin maganarsa" ya daina damunta. "Ga shi yau abin ya tashi sosai, haukan yake yi da gaske. Ta rufe shi a gidan, ta je ta samo gasara a gidan" "Uwani, ta dawo ta dama masa kunu. Ta nufi ɗakin cike da fargaba tare da fatan ya samu ya sha ko kaɗan ne." Sai dai ta ji wata irin guguwa ta taso mai ƙarfi. "Jin yadda guguwar ta taso da ƙarfinta, take fatali da duk abin da ta ci karo da shi a tsakar gida, ya sanya" "ta tashi da azama, ta fara ƙoƙarin rufe ƙofar katakon da take ɗakin. Sai dai tana danna ƙofar guguwar ma na danno ƙofar." "A take ta fara karanto ""A'uzubillah, Allahumma inni as'aluka khairiha wa a'uzubika min sharriha." "Allahumma inni as'aluka khairiha wa khairi ma fihi, wa khairi ma ursulat bihi, wa a'uzubika min sharriha wa sharri ma fiha, wa sharri ma urisilat biha"" take ta ji nauyin da ƙofar ta yi ya ragu, ta samu ta rufe ta, ta juya da sauri ta nufin gurin da yake." "Da fari yana zaune a guri ɗaya ne, amma yanzu Jifa yake da kayan ɗakin da hannu ɗaya, da sauri ta" "fara bi tana tattarewa, cike da damuwa." "Cikin siriryar muryarta ta ce ""Sayyid za ka ji wa kan ka ciwo, ka saurara ka saurari muryar matarka, ni ce a" "gare ka, ni ce fa, Husnan ka ce fa"" Ta ƙarasa maganar a raunane, duk yadda take ƙoƙarin tare shi ta kasa, domin ta gama firgita da lamarinsa. Tun safe take fama da shi, ya ƙi cin komai, kuma ta kasa sarrafa shi" duk rarrashin da ta yi a banza. "Cikin matsananciyar damuwa, hawaye na bin kuncinta ta ce ""Ubangiji ka dubi mijin Nana, ka cire masa" "zafi da raɗaɗin da yake ji, ka saita masa tunani da ƙwaƙwalwarsa, ya yi rayuwa mai cike da nutsuwa da" "farin ciki irin na sauran mutane"" sai kuma ya tsaya cak, ya juyo yana kallonta." "Ta ƙarasa gurinsa, ba tare da fargaba ba ta riƙo hannunsa cikin nata jikinsa zafi sosai. Ta kalli cikin" "idanunsa sai taga yana birkice mata yana rikiɗewa kamar ba Sayyid ɗin ta ba, idanunsa har wani hayaƙi" "yake fitarwa, gaba ɗaya kaminsa sun sauya." "Ta lallaɓa ta zaunar da shi, Ta yunƙura zata tashi, domin ta ɗaukko kununsa ta sake jarraba ba shi, ta ji ya" "cafko ta yana wani irin sambatu bakinsa na kumfa da dalalar da yawu, da alama magana yake son ya yi" "mata. Rashin ƙarfin jiki ya sanya ta faɗa jikinsa. Ya ƙanƙame ta sosai, saboda zafin da yake ji, ita kuma" "jikinta sanyi ƙalau. Ita ma jikinta ya ɗauki rawa, ta lafe a jikinsa ta kwantar da kanta a ƙirjinsa tsawon" "mintuna, jin ya ɗan nutsu jikinsa ya rage zafin ya sanya ta zare jikinta a hankali." "Ta ɗaukko kofin kunun da cokali, sai wani ɗan ƙaramin tsumma, ta zauna a gabansa ta ɗebo kunun a" "cokali ta kai bakinsa, sai dai ya tsaya yana bin ta da ido, kamar ya ga baƙuwar halitta, ta buɗe nata bakin, ya kalleta shi ma ya buɗe nasa." "Ta fara zuba kunun a bakinta ta haɗiye, sannan ta zuba masa a bakinsa shi ma. Ya haɗiye sai dai wani na" "biyo gefen bakinsa, bai haɗiye duka ba. Tana bashi tana goge masa wanda yake zubowa. Sai da ta" "tabattar ya ƙoshi, sannan ta goge masa bakinsa. Ta ɗauki kofin ta nufi ƙofa ta buɗe a hankali ta ga an daina iskar, ta fita da kofin ta ajiye, ta tattara abin da guguwar ta watsa sannan ta dawo ɗakin." "Jiki a sanyaye, ta zauna a gabansa tana ƙare wa kyakyawar fuskarsa kallo. Da ƙyar yake jan numfashi" "yana saukewa. Ta sanya hannayenta biyu, ta gyara masa gashinsa, da ya rufe masa gefen idonsa, ta saka idonta a cikin nasa, cikin rauni da karaya, idanunta na zubar da hawaye ta motsa bakinta, ta fara magana" """Sayyid, dan Allah ka yi magana ko na ji daɗi, wannan karon ka daɗe ba ka ce mini komai ba. Da na sanya" "ran ka fara samun lafiya, amma kullum lamarin nan gaba yake yi. Ka gaya mini wane ne kai? Daga ina ka ke? Ina zan samu danginka da 'yan uwanka, wataƙila kai naka dangin ba za su guje mu ba, za su karɓe mu, tare da sarƙar da ta haɗa ƙaddarorinmu wuri guda, duk da ban kasance ɗaya daga cikinku ba, ni fatana a nema maka magani ka samu lafiya, ba na son ganin ka cikin wannan mummunan yanayin, idan na ci gaba da ganain ka a haka, zuciyata za ta iya bugawa. Dan Allah ka yi magana"" Ta yi maganar wasu" hawayen na zirarowa daga cikin idanunta. "Ya haɗiye wani irin yawu, da yake yi masa zafi a ƙirjinsa, yayi ƙoƙarin ɗago hannunsa na dama, sai ya" "tuna ya riga ya shanye, ba ya iya komai da shi. Ya buɗe baki da nufin ya kira sunanta, saboda tasiri da kuma ciwon da kukanta yake yi masa a zuciyarsa, amma ya gaza bakin ya karkace yawu ya fara zubowa daga bakin nasa, maimakon kiran sunanta da ya yi yinƙurin yi." "Tana kuka, ta sanya tsumman da tayi amfani da shi wurin ba shi abinci, ta goge masa bakinsa. Ba shi da" "zaɓin da ya wuce, ba wa hawayen da yake maƙale a cikin idanunsa damar zubowa, ko shi ma ya samu" sassauci abin da yake ji. "A hankali ya hura mata iskar bakinsa a fuskarta, a take ta silale ta faɗi a jikinsa." "Ya sanya hannunsa mai lafiya, ya rungume ta, ya ci gaba da kuka. Jikinta gaba ɗaya ya saki." "Ƙaisar ta gani a gurin haɗe-haɗen magungunan sa, yana ta haɗa wani abu a cikin kwalba. Zuciyarta ce" "take ta azalzalarta, da ƙoƙarin ingizata, sai dai ba ta yi magana ba." "Babu tsammanni, ta ji ya fara magana ""Zaɓi ɗaya ya rage miki, a halin yanzu, ko dai ki yadda da abin da" "na zo miki da shi, ki rungumi ƙaddararki, ko ki na kallo Buzun nan zai mutu, domin ba zai taɓa tuna waye shi ba har abada, muddin Giyaz yana tare da shi. Dan ba na tunanin akwai wanda zai iya raba shi da shi. Idan har bai iya tuna waye shi ba, shikenan kin ga ba ki da wata makoma. Abu ɗaya zai sanya a wannan karon na bar miki abin da yake cikinki, duk da ba ni da tabbacin zai zama mai cikakkiyar lafiya ko akasin haka, Giyaz da muƙarrabansa sun riga sun fara taɓa shi a cikin ki. Kin san meyasa ban ƙarasa lalata wannan cikin ba?"" Bai jira ta ba shi amsa ba ya ce ""Saboda zan so na ga yadda za ki yi, a lokacin da ɗan zai amsa sunan shege, kuma ba za ki iya hanawa ba, domin ba ki da hujjar kare kanki. Idan Buzun nan ya rayu bai san waye shi ba, ga kuma nakasa. Idan kuma ya mutu suwaye dangin baban ɗan ki? Daga ina yake? Suwaye ahalinsa? Kin san ku a jinsinku na bil'adam da uba ake ado ba riga ba. Babu wanda zai damu da wacece ta haifi mutum, amma za a damu da waye ubansa meye nasabarsa? Tun da ki ka zo garin nan, zuriyarmu suke alwashin yadda fansar su za ta kasance a kan ki. Kafin zuwa wannan ƙadamin" "babu abin da ban gaya miki ba, na gargaɗi. Dan haka dabara ta rage ga mai shiga rijiya""" "Cikin kuka Nana ta hau girgiza kai ta ce ""Ba zan yi bori ba Ƙaisar, ba zan yi shirka da Allah ba. Babu" "tsanani ko wahalar da za ta sanya na rabu da imanina. Amma na rasa gaba na rasa baya, ba dan ina neman taimakon ka ba, ko ka kawo mini ɗauki ba. Na san Ubangiji Allah shi zai taimake ni." "Amma dan zatin Allah idan ka na da hannu a ciwon Sayyid, ka yi mini rai ka rabu da shi, shi ne kaɗai" "duniyata. Ina matuƙar tausayin sa, ban damu da jinya da nake yi ba, wahalar da yake sha ta isa haka. Idan kuma laifikan zuriyarmu ne suke shafar sa, dan Allah ku yi haƙuri ki ƙyale shi haka""" "Cikin sautin muryarsa mai ban tsoro, da ya kan yi amfani da ita, idan ya so razana ta, ko yi mata magana" "mai muhimmanci ya ce ""Na sha gaya miki na maimaita miki, daga lokacin da ki ka fara bani umarni, kin yadda kin amince da buƙata ta ne. Ba ni da hannu a ciwon mijinki, kuma bai ya cikin zuriyar ku, sai dai ƙaddara mai ƙarfin gaske, ta haɗa ku tarayya guri guda. Amma muddin ki na son ya warke daga wannan" "rashin lafiya, ba ma iya haka ba, ya tuna waye shi, sai kin karɓi ƙaddararki.""." "Nana ta sake marairaicewa ta ce ""Ba zan iya shirka ba, ba zan iya zama 'yar bori ba. Zan jure jarrabawata" "komai zafinta amma ba zan yadda rasa imanina ba""" "Ƙaisar ya ce ""A cikin biyu dole abu ɗaya ya faru, tunda kakaninki su suka ƙyanƙyashi wannan matsalar." "Na yi iya ƙoƙarina gurin dakatar da ita a wancan lokacin, amma ta sake tasowa a wannan karon. Dole a cikinku ɗaya zai warke ya rayu ɗaya ya mutu a haka, dan babu alamar Giyaz zai sassauta wannan mummunan ƙudirin nasa a kan zuriyar ku. Gefe ga aikin da ya karɓa yake yi a akan mijinki, ko dai ki ci gaba da rayuwa da shi, laifukan ku na shafar sa, ko kuma ki yarda ki karɓe ni a matsayin hadiminki ki yi" "abin da nake so, ni kuma na san yadda zan yi da Giyaz, na baki maganin da mijinki zai warke""" """Ta yaya? Me yasa sai ni? Me yasa ni zan biya zunubin da lokacin da aka aikata shi ba na nan, zunubin da" "zamanin da aka aikata shi, ya yi nisa da nawa zamanin? Me ya sa kakannina suka zaɓi zama 'yan bori? Suka gada mini wahala da masifa take ta bibiyar rayuwata. Na zama mujiya a cikin mutane, duk inda na tsuguna sai wata masifa ta afku, da za a jefa mini zargi, kasantuwata ni ba mutum ba ni ba wani jinsi daban ba? Me yasa zan girbe baƙar shukar da ban san a lokacin da aka dasa ta ba? Ina son mijina duk da" "daga ni har shi, ba mu san waye shi ba." "Duk da Nijar ba ɗaki ɗaya bane ba, ba kuma ƙaramar alƙarya ba ce ba, ƙasa guda ce, na gwammace" "zagaye ta neman ahalinsa na damƙa shi a gare su, da na ci gaba da zama da shi, mummunar ƙaddarata tana shafarsa, ko kuma na zama 'yar bori na ci gaba da gadar da wahala da masifa ga zuriyarmu, gara ko ma mene ne ya ƙare a kaina."" Ta ƙarasa maganar cikin ƙaraji, tana kuka mai bayyanar da tsantsar baƙin" cikin da yake binne a cikin zuciyarta. * "A hankali yake driving cikin nutsuwa, yana sauraren Jamila, da ke bin waƙar da ke tashi a cikin motar" "ƙasa-ƙasa, sai kuma ta yi shiru." """Ya ki ka yi shiru kuma?"" Ta ce ""Au wai ka na ji na?""" "Abba ya ce ""Eh mana, har kin fi masu waƙar ma iyawa"" Dariya ta yi ta ce ""Ka ji ziga, muryar ta su da aka" "tace, aka goge tawa kuma a haka, ka ke cewa na fi su iyawa""" """Au ba ki yarda ba? To shikenan ni dai na san kin fi iyawa"" ya yi maganar yana parking ɗin motar a" "harabar gurin shan ice-cream ɗin. Abba bai taɓa soyayya ba, duk wannan abubuwan da yake yi wa Jamila, bai taɓa furta mata cewar yana sonta ba. Sai dai ita sarai ta gane sonta yake yi, so kuma ba na wasa ba. Sai dai tana mamakin yadda duk wannan abin da yake yi mata, ba ya iya nuna wa a gaban" "Hajiya Sa'a, hakan ya sanya ta fara tunanin ko dai yana da wata manufa a kanta ne." "Sai dai ta lura halaye da ɗabi'unsa, sun sha banban da na Hajiya Sa'a, shi Abba akwai tsantseni, da gudun" "saɓa wa Allah. Dan duk da son da yake yi mata, sai da ya yi mata faɗa a kan shigar banza da ta kan yi wasu lokutan." "Ice cream su ka sha, yana ba ta labarin yadda ya yi karatu, da irin ƙalubalen da ya fuskanta na rayuwa. Su" ka gama ya ɗauke ta ya mayar da ita gida. "Bayan ta shiga gida, Mama ta ce ""Yauwwa ke nake jira dama, gas ya ƙare na kira wayar ki kuma ba ki" "ɗaga ba""" """Ina hanya ne, ga ATM ɗina, a bawa Nasiru ya je ya ɗuro. Har za ta shiga ɗaki sai ta fasa ta ce ""Ni kuwa" "jama'a ina Nana ne? Wayarta ba ta shiga, shekaranjiya waccan ma na biya gidan da mijinta yake gadi, na ga kamar babu kowa a gidan""" "Mama ta taɓe baki ta ce ""Au ke ba ki san abin da yake faruwa ba dama?""" "Ta tsaya tana kallon Mama ta ce ""Mene ne yake faruwar?""" """Ai tuni aka kore su daga wannan gida. Ke ba zama ki ke yi ba ne shi yasa, suka koma unguwar su Ummi," "to kin santa duk inda ta zauna bala'i ne yake bibiyar gurin, hatsaniya ta haɗa ta da matan gidan da suke, suka ce mayya ce aka tashe su. Ai nan Babanku ya je aka yi ta fafatawa, da ta kwaso jiki ta taho nan, wai za ta dawo mijinta babu lafiya, na ce bani da gurin jinya a gidan nan. Allah ya raba ni da masifa, ba za ta" "dawo mini ba, to ƙarshe dai wai yanzu tana ƙauye, can gurin Uwani a can take jinyar mijin nata""" "Jamila ta yi sak, ta ce ""Mama Nana tana ƙauye fa ki ka ce?""" """Eh mana, to idan ba ƙauyen ba ina za ta je? Tana can""" """To waye yake ba ta Abinci?""" "Mama ta ce ""Oho ina na sani?""" """Amma ya aka yi tsawon wannan lokacin ban sani ba? Yanzu ba kamar da ba ne, ban ji daɗin abin da ki" "ka yi ba Mama, bai kamata a kore ta ba a ce ta koma ƙauye da zama ba. Da ina nan ko na sani, da na kama musu wani gidan, gaskiya sai ta baro ƙauye""" """To ke ina ruwanki? Mene ne naki a ciki uwar Iya? Kina kallon irin baƙar azabar da na sha, a kan zamana" da ita a gidan nan. Na meye za ki kuma jajubo mana ita. Gara ki bani kuɗin da za ki kama mata hayar na "bawa ɗanLadi, ɗan autanmu ya tafi kasuwa da zaman banzae da yake yi, na yi masa aure tun da Allah ya sanya kuttun arziki ya fashe mana, ba ki kai kuɗi inda babu amfani ba""" "Jamila ta dubi Mama ta ce ""Wannan ɗan uwanki ne, sai ki nemi kuɗinki ki yi masa, nima 'yar uwata nake" "tunani. Haba Mama, ko wani Nana ta kashe miki ƙiyayyar ta isa haka ai. Ai yakamata a tausaya mata, miji babu lafiya ga zaman ƙauye, ita Uwanin za ta ɗauki nauyin Abincinsu ne? Tun da muka tashi a wahala muke a gidan nan, amma ita nata ya fi na kowa ma"" Jamila ta ƙarasa maganar cikin damuwa, ta shige" "ɗaki, ta bar Mama da buɗaɗɗen baki." * "Kallonsa Nana take yi, suna zaune sun yi juguum daga ita har shi. Bayan ta gama yi masa kitson zanen" "hannu guda takwas, ta yanke masa faratansa na hannu da na ƙafa." "Kamar wadda aka mintsina ta tashi tsaye, ta kalle shi ta ce ""Sayyid, bari na je na dawo"" ya bi bayanta da" kallo har ta fice. "Sai dai a ƙalla ta kai awanni biyu kafin ta dawo, ko da ta dawo ta tarar da shi ya haɗe fuska, ta yi shiru ba" "ta kula shi ba, ta koma tsakar gida." "Ta laluba kayanta, ta ɗaukko wata takarda mai ɗauke da ayoyin ruƙiyya da na karya sihiri, sannan ta hura" wuta a cikin murhu. "Ta dawo tsakar gida ta zauna, ta fara da Bismillah da karanta Suratul fatiha, sai Suratul falaƙi da nasi. Ta" "karanta ayoyi biyar ɗin farko na Suratul Baƙara, ta fara karanta Suratul mulk, a hankali sai ta fara gani" "dishi-dishi, ta fara daina ganewa. Ta busa ayoyin a cikin ruwan, Sai ta ajiye takardar. Ta ɗauki wata leda da ta zo da ita, ta fito da man habbatussauda da jan Almiski." "Saboda wauta sai ta buɗe miskin, ta kai hancinta, da sauri ta dungurar da shi a gurin, ta ja da baya, dan" tuni ta ji jikinta ya fara tsuma. "Sai da ta ɗan samu nutsuwa, sannan ta zazzaga tazargaɗe a cikin bokitin, ta kawo ganyen magarya guda" "bakwai, ta saka a leda ta ɗan bubbuga musu muciya, ta haɗa a cikin ruwan. Ta yi shiru tana tunani a ranta ta ce ""Allah ya sa ba mai magani na zama ba, Ƙaisar bai mayar da ni 'yar bori mai bayar da magani ba, larurar Sayyid ta saka na fara koyi da magungunan sarkin baka.""" """Amma ai ayoyin Alkur'ani ki ka karanta, shi ma kuma Sarkin Bakar yana amfani da Alkur'ani"" wata" zuciyar ta tunatar da ita. Haka dai ta ci gaba da wasi-wasi. "Can yamma, bayan ta tabbatar da ganyen magarya da tazargaden sun tsumu, ta ɗumama ruwa ta tsiyayi" "ruwan tofin ta tace ta haɗa da ruwan ɗumin, ta kawo man habbatussauda ta tsiyaya a ciki, ta kawo jan miskin nan da ta saka kwalbar a ruwan ɗumi, ya narke ta tsiyaya a ciki, ta ɗebo garwashi a kasko ta shiga ɗakin. Yana ganin Nana ya tashi zaune yana kallon ta, ya ga ta samu ƙyalle ta ɗaure hancinta da bakinta." "Ta nufo shi ya ga ta hau tuɓe masa kaya, ya din ga bin ta da ido, ta bar shi daga shi sai gajeren wando." "Hannunsa da yake maƙale take kallo cikin damuwa, ta shafa hannun." Sai kuma ta yi Bismillah ta fara shafa masa wannan ruwan. Tun daga cikin kansa. "Girgiza kai ya fara yi, yana ture ta da lafiyayyen hannunsa, yana toshe hancinsa. Ya din ga girgiza kai" "jikinsa yana karkarwa bakinsa yana rawa, ya din ga wani irin gunji yana miƙa. Amma sai da Nana ta jiƙe" shi da ruwan nan tsaf. "Ta kunna kiran salla a wayarta. Ta kawo tazargade, da habbatussauda da ganyen magarya ta zuba su a" "kan garwashin nan, hayaƙin ya turnuƙe ɗakin, ta ajiye shi a nesa da shi kaɗan. Ta fice daga ɗakin ta kulle shi a ciki. Ta tafi ta din ga wanke hannunta. Wani irin jiri ya din ga ɗaukar ta, ga matsanancin ciwon kai, ɓari ɗaya da ya sanya take jin, tamkar kan zai yi bindiga ya rabe." "Ta samu guri ta zauna a tsakar gida, ta dafe saitin zuciyarta da yake ta bugawa da sauri." "Bayan wasu mintuna, ta tashi ta je ta leƙa ta window, ta hango shi a kwance a ƙasa. A tsorace ta buɗe shi," ta nufe shi da sauri tana kiran sunansa. "Gaba ɗaya ƙwayar idonsa baƙar ta ɗauke sai farar, ta durƙusa a kansa kawai ya miƙo hannu zai shaƙe ta," "amma ta riƙe hannunsa. Hannun ya din ga rawa, ya sauke shi a hankali." """Sayyid"" tana ambatar sunansa, ƙwayar idonsa ta dawo ya kalle ta." """Sannu Shugaba"" hararta ya yi ya juya mata baya. Dariya ta fara yi ƙasa-ƙasa." "Ta ce ""Haba Shugaba, ya ka juya mini baya, juyo ka kalle ni"" ya ƙi juyowa. Ta tashi ta buɗe labule saboda" yadda warin ita ma ya fara damunta. "Ta ɗaukko tsumma, ta hau goge masa jikinsa, saboda ya daina warin miskin nan ita ma ba ta so." "Ya tashi zaune, tana goge masa. Ta ce ""Ko a yi wanka?"" Ya ɗaga idonsa yana hararta, jikinsa ya koma" jawur kamar wanda ya ƙone. "Ta din ga ɓoye dariyarta, ta yi masa wanka, ya din ga sinsuna jikinsa yana yamutsa fuska." "Ya shafa fuskarsa ta ce ""Ka yi haƙuri, magani ne, ina son ran Ubangiji Allah ya kawo mana afuwa"" Ya ture" ta daga jikinsa. Amma ta manne masa ta hau cinyarsa ta zauna tana dariya. "Ta juyo da fuskarsa suna kallon juna, ta lumshe ido ta buɗe ta ce ""Sannu shugaba"" Ya jinjina mata kai. ""In" "zubo Abinci ne?"" Ya girgiza kai." """Sai an yi salla?"" Ya gyaɗa mata kai." "Ya yi sallar magariba da isha'i, ta zubo masa Abinci." "Washegari ma da sassafe, ta kuma rutsa shi tana shafa masa ruwan nan. Yau ma ture ta ya din ga yi yana" "girgiza mata kai. Ta kunna masa hayaƙi, ta gudu ta rufe shi a ɗakin. Haka ta sake tarar da shi, ya koma ja ya haɗa uban gumi. Ta yi masa wanka. Ta ba shi Abinci ya karya." "Allah ya dafa wa Nana, ba su taɓa rasa abin da za su ci ba. Kuma haka take ta jujjuya kuɗin." "Sai da ta gama yi masa duk abin da zai buƙata, sannan ta tashi za ta yi wanka, tana tsaye daga ita sai bra" "da zani a ƙugunta, sai cika bakinta take da aya mai gishiri, ga cikinta ya ɗaga sosai." "Ta waiwayo suka haɗa ido. ""Ya ake kallona haka?""" Ya yi mata alama da hannunsa mai lafiya ta zo. "Ta ƙaraso gabansa ta durƙusa ta ce ""Gani"" ya nuna mata cinyarsa." "Ta ce ""Ina da nauyi fa, jiya ma dan na tsokane ka na zauna, ka ga baka da lafiya"" ya saka hannu ya janyo" "ta, ta hau cinyar tasa tana dariya." "Yatsansa ya saka ya ɗan latsa cikinta, ya kalle ta yana murmushi. Ita ma murmushin ta yi ta ce ""Kullum" "sai ya ce ko ta ce tana gaishe ka"" Da hannunsa yake tambayarta yaushe za ta haihu?" """Nima ban sani ba, amma dai bai fi wata huɗu ba, saura wata biyar in Allah ya sa mu na raye. Idan ka" "samu lafiya sosai, za mu je mu ƙara dubawa idan su Habu sun dawo, idan ba su dawo ba sai mu tafi Nijar. Duk da na san da sun dawo zuwa yanzu za su neme mu"" Ya yi shiru yana ci gaba da kallon cikinta, da lokaci lokaci yake dan harbawa." """Zan je na yi wanka""" "Da hannunsa ya yi mata alamar, su je ya yi mata." """Kana fama da kanka za ka yi mini wankan? Wato a ramawa kura aniyarta ko? To na yafe idan Allah ya" "baka lafiya sai ka yi mini Rayuwata"" Cikin murmushi ya sunkuyo da kanta ya sumbaci goshinta ta da laɓɓanta. Hira yake so ya yi da ita, amma ya kasa sai dai ya kalle ta yana murmushi ko kuma ya din ga yi" mata nuni da hannunsa. "Ya ɗauki wayarta, ya kunna waƙar da take yi masa, yana yi mata nuni da ta yi masa. Ta ce ""A'a karatu za" "mu ji ba waƙa ba, a wannan yanayin da muke ciki, ai ba mu ga ta waƙa ba Sayyid"" Ya tsuke fuska yana hararta. Ta ce ""To shikenan, bari a kashe waƙar, sai na raira maka da bakina ko?"" Kawai ya tsare ta da" ido yana wani lumshe ido. "Tana dariya ta ce ""Wai Sayyid ni fa ban gane maka ba kwana biyun nan, rigima ka ke ji, amma" Alhamdillah alamun sauƙi ne da nasara. "Aka shiga kwana na huɗu, tana shafa masa tofi tana kunna masa hayaƙi ta gudu ta bar shi a ɗaki. Yau sai" "dai ta gama shafa masa, za ta gudu ya riƙe ta gam. Duk yadda ta so guduwa ta kasa. Ya kalle ta yana murmushin mugunta. Aikuwa jikinta ya fara tsuma ta saka masa kuka, jin yadda gaba ɗaya duniyar take juya mata, tana shirin fita hayyacinta." "Har dare ya yi suka kwanta, ba ta kula shi ba, dan gaba ɗaya jikinta ya mutu murus, babu abin da yake yi" mata daɗi. "Can cikin bacci ta ji ya yi magana""Ma viee""" """Sayyid""" """Na'am""" """Magana ka yi?""" """Eh, yanzu na ji ta zo""" "Ta tashi zaune cikin murna tana taɓa shi ta ce ""Alhamdillah Sayyid, Allah ya ƙara lafiya""" """Taɓa ni na ji, ko zan ji wani abu""" "Ta ce ""Ga shi ina taɓa ka""" "Ya ce ""Ba wannan ba"" ya yi maganar yana rungumota da duk hannayen sa biyu." """Sayyid hannunka ya warke?"" Ta tambaye shi a kiɗime cikin farin ciki." """Eh"" ya amsa a taƙaice yana ƙoƙarin yin wani abin daban." """Bari na lalubo waya na haska ka na gani""" """Kar ki haska ni""" """Me yasa ganinka fa zan yi, hannun zan gani""" """Kar ki haska ni"" ya sake maimaitawa." "A ɗan tsorace ta ce ""Anya kai ne?"" Ya yi dariya ya ce ""A'a Ƙaisar ne. Idan ma ba ni ba ne, ai kina ganewa""" "Ta yi dariya ta ce ""Wai Sayyid ya haka ne? Ka tsaya mu yi murnar ka samu sauƙi""" "Ruf ya rufe bakin Nana, bayan ya tabattar da lafiyarsa ta dawo. Duk da ya yi farin ciki da miƙewar da" "hannunsa ya yi, wanda farkawa ya yi daga bacci kawai ya ji hannun ya saki, duk da ya yi masa wani iri babu daɗi." "Bayan wani lokaci, ya saka hannunsa ya ɗaukko fitila a gefen Nana, ya kunna ya haske ta. Rufe fuskar ta" "ta yi, ta juya bayan ta da sauri." "Ya kwanta a jikinta yana yi mata raɗa a kunnenta. ""To tashi ki haska ni ki ganni, kin ga hannun"" Nana ta" "ƙare rufe fuskarta a fulo, ta ƙi ɗagowa." """Kin ga"" ya yi maganar yana taɓa ta da hannun. Shi wannan abubuwan da take yi ma, ba ƙaramar dariya" take ba shi ba. "Da ƙyar ta tashi, tana kallon hannun nasa da take ganin, tamkar almara ya miƙe." "Ta ja hannun ta ga ya miƙe, ta ce ""Kuma ba ya ciwo?""" "Ya girgiza kai yana taɓa hannun ya ce ""Ba ya yi""" """Allah ya ƙara maka lafiya mai ɗorewa""" """Amin. Na gode. Na gode"" ta rufe bakinsa ta ce ""Ya isa haka. Allah za mu godewa""" """Alhamdillah. Amma ya zama dole na yi godiya, kuma na jinjina miki, saboda"" bai ƙarasa maganar ba ta" "cije shi a kafaɗarsa, kamar yadda ya kan yi mata, idan yana jin raha." "Kamar ba su ne cikin zullumi da damuwa ba, suka koma shagalinsu. Dare ya tsala amma tamkar rana a" "gare su, ƙarshe ma zaman hira suka zauna. Da anjima sai ta tattaɓa hannun nasa, dan ta tabattar lafiya" kalau yake bai kuma maƙalewa ba. "Haka suka kwana cikin nishaɗi, da kewar juna." "Da safe ta gama abin da take yi, ta shigo da maganin da take shafa masa, ya kalle ta ya ce ""Wallahi ki ka" "zo kaina da wannan abun, sai na yi miki wanka da shi, ke ma na kulle ki a ɗakin, ki ji abin da nake ji"" Ganin yadda ya haɗe rai ya sanya ta rabu da shi." "Wunin yau ma lafiya suka yi shi, babu damuwa, duk da jikinsa babu ƙarfi sosai." Ya ci Abincinsa ya yi sallolinsa babu wata matsala. Sai dai yau ma Nana ba ta samu rintsawa yadda "yakamata ba, sai da ta san ya warke. Wani nannauyan bacci ya yi awon gaba da ita." "Wani mutum ta gani a tsaye a jikin bishiya, ya lulluɓe jikinsa da mayafi. Ta yi tsuru tana son ta ga waye" haka. "Yana ɗaga mayafin ta ga fuskarsa, ta ja da baya, ta tsorata. Tsohon nan ta gani, jikinsa yana ta fitar da" "wani irin baƙin abu, fuskarsa ta yi baƙi ƙirin, ga hayaƙi na fitowa daga cikin bakinsa da hancinsa gaba ɗaya siffarsa ta yi muni babu kyawun gani." "Sai da Nana ta ja da baya, cikin tsoro da razani." """Kin tafka kuskure yarinya, kuma za ki san kin taɓa Giyaz bin Jaddul Jinn. Babu wanda ya taɓa karya" "alkadarina, abu ya yi tasiri sosai haka a jikina. Dan a duk lokacin da aka yi yinƙurin illata ni, barin guri nake yi. Sai dai kash kina ɗauke da abin da aka yi mini tarko da shi a wancan karon."" Ya jefo mata wani littafi jikinta ya ce ""Ga shi nan, littafin da ki ke ta bibiya sai kin ji ƙwaƙwaf, ki ƙarasa karantawa kafin na je na yi jinya na dawo. Amma ki sani dawowata ba za ta haifar miki da ɗa mai ido ba. Domin illar da ki ka yi" "mini sai na ninka wa mijinki, wahalar da ki ka sha ba ki ga komai ba."" Kawai ya ɓacewa ganin Nana." "Nana ta kalli littafin hannunta, na gurin Ƙaisar ne, da take ta bibiyar sai ta karanta hanata." "Da kansa littafin ya buɗe, a daidai shafin da tsaya da karantawa wancan karon." Jiki na tsuma ta ci gaba da karantawa. "Jama'ar da suke gurin girkar, wasu suka watse a dalilin gakin sarkin Aska ya bayyana a gurin, kar ya gansu" "ya hukunta su. Bayan musayar yawu a tsakanin Duna da uban duƙusa, Sarkin Baka ya yi girgiza ya ɓace." "Uban duƙusa ya saka aka ɗauki kakan Lanti, a ka kai shi gida. Ita ma Lantin tana zuwa gida ta faɗi ƙasa." "Ba ta sake farfaɗowa ba sai washegari. Sai dai bayan farfaɗowarta, ta tarar da kakanta cikin mawuyacin" "hali, wanda hakan ba ƙaramin ɗaga mata hankali ya yi ba." "Cikin damuwa mijinta ya ce ""Lanti sai da na gaya miki ina jin tsoron wannan abun, ki ka ce babu komai," "ina tsoron kar rikici ya ɓarke a garin nan""" """Babu rikicin da zai ɓarke, ka kwantar da hankalinka, ni dai kawai fatana na kawo ƙarshen Sarkin Aska.""" "Kakan Lanti da ya yi tari, sai aman jini, dama ga jikin tsufa, ya zamana ko tashi baya iya yi saboda" "buguwar da ya yi. Kwanaki huɗu da faruwar lamarin, Lanti tana yi masa hayaƙi da ganyen ɓaure. Ya riƙo hannunta ya ce ""Ya ke jikata, ki sani na yi miki Girka da babban Aminina, kuma ya ɗaukar mini alƙawarin ba ki duk wata kariya, da zama mai hidima a gare ki, kuma ya yi alƙawarin bawa zuriyarmu kariya daga cutarwar miyagun Aljanun cikin su. Dan haka a duk lokacin da ki ke buƙatar ganawa da shi, ki sanya kayan saƙin ki, ki ɗaura gurunki. Sai dai kar ki kira shi a guri mai ƙazanta, ba ya son zama a guri mai ƙazanta, kuma ba ya zama a guri mai najasa. Sannan 'yar ki Duna ne ya shafe ta, kuma ga wannan abu da ya faru, abu ne mawuyaci ta warke, sai dai idan uban duƙusa ne ya samo mata magani. Ni na san ba zan rayu ba, Duna ya riga ya yi mini illa, dan haka ki kula da mutanen Buda. Yana gama faɗin haka wuyansa ya karye. Lanti ta fashe da kuka, ya buɗe baki yana son ya yi mata magana amma ya kasa, har ya daina" motsi ya mutu. "Nana ta yi kuka ba kaɗan ba, da mutuwar Kakanta." "Ƙaisar ne a tsaye a kan wani dogon tsauni, gabansa kuma Giyaz ne, da yake kamannin da shi sak, tamkar" ya yi kaki ya ajiye. """A kan me za ka je ka aikata wannan shirmen da ka yi? Ko har ka manta da cewar fansarmu za mu ɗauka" "a kan abin da mutanen nan suka yi mana?""" """A'a Giyaz, mutanen nan ba su ne ainihin waɗanda suka fara rigimar nan ba, kuma ɓarnar da aka yi musu" "ta yi yawa. Babu amfani rashin zaman lafiya da tashin hankali. Kuma ka duba irin cutarwar da abokinka Duna ya haɗa kai da sarkin Aska yake yi wa mutanen garin nan. Yakamata a zauna lafiya, haɗa kai da bil'adama ana cutar da jinsinsu ba zai haifar da ɗa mai ido ba.""" """Rufe mini baki Ƙaisar"" Ƙaisar ya kalli mahaifinsa jin ya kira shi da sunansa na yanka, saɓanin sunan da" "yake masa kara da shi, na uban duƙusa wanda da shi ake kiransa saboda kara ga mahaifinsa. Dan duk cikin bataliyar 'ya'yan da ya haifa, ya fi ƙaunar sa. Ya ɗora da cewa ""Kar ka manta abin da suka yi wa" "Mahaifina Jaddul Jinn wanda yake kaka ga duk wani Aljani da yake nahiyar nan, da yadda ake girmama" "shi, sai mene ne dan a azabtar da su. Dan mene zaka hau kan bil'adama a matsayin bawa, duk da" "kasancewar ka ƙasaitaccen matashin aljani da ake ji da shi a jinsinmu"" ya yi maganar cikin ɗaga murya, muryarsa na amsa kuwwa a ilahirin dajin." """Zaman lafiya da kwanciyar hankali, mu rayu mu da su babu cuta babu cutarwa. Lalata musu amfanin" "gona, sanya musu rashin lafiya da makamantansu duk ba zai sanya ku huce ba, tun da waɗanda suka yi laifin na sun mutu basa nan""" """Uban duƙusa yanzu ka fifita bil'adama a kan ni mahaifinka?""" """Ko ɗaya, sai dai ka san muna mutunta yarjejeniya. Mun yi yarjejeniya da abokina, zan ci gaba da bawa" "zuriyarsa kariya, zan kula 'yar sa zan din ga kawo mata magunguna tana bayarwa. Kuma ya yarje mini ci gaba da yi wa zuriyarsa hidima, da bayar da magani ta hanyar waɗanda aka haifa da tauraron 'yar sa Lanti""" """Ƙarya ka ke yi Ƙaisar. Ɗana ba zai zama bawa ga gajiyayyun halittu kamar bil'adama ba, ka sani yadda" "suke yi mana kallon halittu maƙaryata, haka su ma ba su da cika alƙawari. Ka tuna kai makaranci ne, manazarci kuma marubuci. Ka karanta litattafai da ni kaina ban san adadinsu ba. A ɗakin karatun ka akwai litattafan da aka rubuta dubbanin shekaru kafin zuwanka Duniya. Ka yi yawace-yawace a Duniya domin neman abubuwan rubutawa, kuma ina da tabbacin ka karanta tarin kashedin da magabantanmu suka yi mana a kan bil'adama. Dan haka ba zan bari iliminka da soyayyar da nake yi maka, su ƙare a kan yi wa biladama hidima ba, ba ma su su yi maka ba. Sai dai ka zaɓa, zama da mu ko kuma hidima ga" "bil'adama!""" Ayshercool 08081012143 Ayshacool "Sai da ta shekara biyar, tana aikin jakar nan, tare da jiƙata da magunguna daban-daban. Ban da zanen" hatimai kala-kala da yake cikin jakar. "Ta haɗa kai da ɗan uwan Sarkin Aska, baya nan ya je ya ajiye masa jakar a ƙasan abin kwanciyar sa. Kuma" "ƙaisar ya ɓatar da sahun sa, ta yadda babu wanda ya gane a cikin aljanun da suke yi masa hidima. Tun da ya kwana a kan jakar, Aljanun da suke yi masa aiki, suka watse suka bar shi, ya kamu da matsananciyar" "rashin lafiya da sai da ta yi ajalinsa. Yana mutuwa kuma aljanun suka fantsama kan 'ya'yansa da jikokinsa," "sai dai aka rasa wanda zai gaje shi gurin ci gaba da aikin zaluntar al'ummar da yake yi. Sosai mutanen gari suka yi murna da mutuwar sa. Babban ɗan sa da suke bokancin tare ma, cewa ya yi ba zai iya ba." "Ƙin samun wanda zai gaje shi, ya sanya aljanun fara sanya wa iyalansa cututtuka. Wasu kuturta wasu" "suka makance, har da waɗanda suka haukace. Aka din ga ɗauki ba daɗi da Lanti, a kan sai ta warkar da" su. Ƙaisar ya gargaɗe ta a kan babu ruwanta ta rabu da su. "Lanti ta shafe shekaru Ashirin da bakwai, tana aiki tare da Ƙaisar tana harkokinta na bori da bayar da" "magani, haka zalika ita ma ta yi wa mutane da dama girka, masu sha'awar harkar bori. Akwai bikin 'yan bori da ake gudanarwa da nuna bajinta duk shekara, wanda a nan ake yi wa masu so girka, ake bikin bajekolin abubuwan ban mamaki, na gidaje daban-daban." "Maharba su yi na su, wanzamai, 'yan bori da dai sauran su." "Domin bayan mutuwar Sarkin Aska an ɗan samu zaman lafiya, tun da dama shi yake assasa duk wata" "fitina da rashin zaman lafiya. Sai dai aljanu ba su fasa cutar da su da razana su ba, duk da Lanti tana iya kokarinta. Sai dai ita ma bayan wannan shekarun ta koma ga Allah." "Sai dai kan ta mutu, a cikin jikokinta an samu guda ɗaya da take da irin tauraronta." "Dan haka bayan mutuwar Lanti, aka ci gaba da ba ta kashi tsakanin mutanen garin, da Aljanun da sarkin" "Aska ya yi aiki da su, har ma da waɗanda ba 'yan asalin garin ba ne." "Sai dai babu yadda Ƙaisar zai yi, a lokacin jikar Lanti ba ta kai lokacin da za ta iya bayar da magani ba." Kuma har a lokacin ba a fasa yi masa magiyar ya rabu da bil'adama ba. Gaba ɗaya ya nesan ta kansa da Ahalinsu. "Bayan jikar Lanti ta fara tasawa, Ƙaisar ya fara bijiro mata, domin yin gadon kakarta, sai ta kasa ɗauka sai" "ma taɓin hankali da ta samu, duk da ta ɗan taɓa bayar da maganin amma ba sosai ba. A hakan ita ma ta yi aure ta hayayyafa." "A cikin 'ya'yanta aka samu wadda ta gaje ta, duk da ba irin tauraronta ɗaya da Lanti ba. A lokacin" "Musulunci ya shigo cikin mutane, duk da bai yi ƙarfi a garin Buda ba." "Asma'u ta bayar da magani ita ma, ta yi aiki tare da Ƙaisar, sai dai ba ta da ƙarfin zuciya da juriya irin ta" "Lanti. Gaba ɗaya ita ma ba wani daɗin aiki ya ji da ita ba. Ko yaya ya buɗe mata ido ta ga abu, sai ta kwanta ta hau jinya. Daga baya ma ta watsar ta tattara komatsan borin ta ajiya, ta ce ta tuba ta daina." "Ganin ba a samun masu irin tauraron Lanti, ya sanya Ƙaisar fara sarewa, da haƙura da batun bayar da" "magani ta hanyar bil'adama. Sai dai yana iya yin sa gurin bawa zuriyar su Lanti kariya, daga cutarwar zuriyarsu." "Duk abin da yake faruwa, Giyaz yana ankare da Ƙaisar, kuma yana murnar yadda ɗan sa ba zai ci gaba da" zama bawa ga bil'adama ba. "Aka din ga samun ci gaba a garin Buda, wasu suka din ga barin garin su na tafiya fatauci, wasu kuma" "tashin hankalin Aljanun da ya addabi garin ne ya sanya suka bar garin, ciki har da wasu daga cikin zuriyar Lanti." "A can Bauchi aka haifi Maijidda, har ta girma, an saka mata rana saura watanni uku aurenta, su ka zo" "Buda, a nan suka haɗu da Isa, ya ƙallafa rai a kanta." "Yayar kakarta ta ce sai an warware wancan baikon da aka yi da na can garin Bauchi, an yi da Isa, saboda" "ƙara danƙon zumunci, kuma hakan zai sanya su din ga kawo musu ziyara a kai a kai, da ƙara samun" zaman lafiya a tsakanin zuriyar maharba da ta wanzamai. Ayshacool "Aka mayar wa da wancan na Bauchi kuɗinsa, ita kuma ta auri Isa." "Gidansa na Kano, inda yake harkokin kasuwancinsa, nan ya tafi da ita. Ya ajiye ta a gidansa da suke tare" da matarsa babar Gaddafi. "Ya ɗora wa Maijidda son duniya, kamar a kanta ya taɓa aure. Ba uwargidansa ba, hatta 'yan uwansa sai" "da suka fara jin haushin Maijidda saboda ba ya ɓoye son da yake yi mata, ga ta yarinya ƙarama amma su" "na ganin kamar ta mallake shi, dan shekarunta goma sha shida a lokacin." "Kasancewar daga zuriyar Sarkin Aska Maijidda take, ta auri ɗan zuriyar Sarkin Baka, sai Aljanun da suka" "yi wa sarkin Aska hidima, suka shiga cikin lamarin auren, su ka fara haddasa musu matsala. Haka kurum" "sai ta ji ta tsani Isa, ba ta ƙaunar ganinsa ga yawan rashin lafiya. Kishiya da facaloli suka sako ta a gaba," ga jarabar dangin miji. "Ana haka ya samu matsala da uwargidansa, da ta haifa masa Gaddafi da Ummi, ya sake ta. Nan ma aka" ce Maijidda ce sila. "Ya auri Rabi, suka zama ita da Maijidda. Yayarsa Atine ta ƙara haɗe kai da Rabi, su na cizguna mata." "Maijidda ke riƙon su Gaddafi, tana iya kokarinta amma kullum cewa ake yi tana azabtar da su." "Kasancewar Gaddafi ya fi Ummi wayo, ya tsani Maijidda cewa yake saboda ita aka saki babar su, kamar yadda Yaya Atine take faɗa. Ita kuma Ummi tana matuƙar ƙaunar Maijidda." "Nan ma Rabi ta saka Maijidda a gaba, da kishi da ƙage kala-kala." "Bayan haihuwar Imran sai da ya shekara uku da rabi, ta haifi Nana. A lokacin Isa ji yake kamar ba a taɓa" "yi masa haihuwa ba sai a kan Nana. Ya saka mata suna Asma'u, sunan kakarsa da ta riƙe shi take bala'in son sa. Hatta hakika biyu ya yi wa Nana, Ummi ma da ya saka mata sunan mahaifiyarsa bai yi mata abin da yake yi wa Nana ba." "Isa kofur ne na 'yan sanda, abokan aikinsa suka yi masa ƙage, aka kore shi daga aiki har da prison. Ya" "koma harkar fawa, ya fara samun rufin asiri, harka ta buɗe masa yana samun rufin asiri sosai , sai dai kasancewar sa mutum ne da ba shi da sirri, duk samun sa sai ya bayar da labari, abokansa suka jefe shi" "sana'ar ta fita daga ransa ya daina zuwa ko ina, sai zaman gida." "Tun da Allah ya sanya aka haifi Nana Ƙaisar ya ganta ya rikice, tamkar Lanti ta yi kaki ta ajiye saboda" "kamanin su. Ga irin tauraronta ɗaya da Lanti. Gaba ɗaya Ƙaisar ya tattara hankalinsa a kan Nana Asma'u yana ganin, ya samu uwar gijiya a zuriyar Lanti. Giyaz na fuskantar abin da ke shirin faruwa, ya fara ƙoƙarin raba Ƙaisar da Nana. Dan kullum yana tattare da ita. Wasu lokutan ya zungure ta tayi ta kuka." "Manyan bokaye da ƙungiyon Asiri na zawarcin son yin aiki da Ƙaisar, saboda tarin baiwa da kuma ilimi da binciken ƙwaƙwaf da yake yi. Wanda za su aiki da shi ne, ya din ga taimaka musu, su kuma su din ga yi" "masa hidima, amma fafur ya ƙi. Saboda ba ya son duk wata alaƙa da jini." "Ƙaisar ya yi tafiya zuwa wata ƙasa, ganawa da wani tsohon Aljani, a kan wani rubutu da yake yi, ya dawo" "ya tarar an saki Babar Nana, ita kuma Nana ta daina magana, ta daina tafiya ga Baba ya ƙwace ta, ya" hana Maijidda ita. Ya fuskanci aikin mahaifinsa ne Giyaz. Ya je ya same shi yake tambayar sa me yasa ya yi wa Nana haka. "Giyaz ya ce ""Ka sani ba zan taɓa sake yadda, ka zama bawan bil'adama ba, da ka sake zama bawan" "bil'adama gara na kashe ta ko na kashe ka, kowa ma ya huta.""" "Ƙaisar ya san Giyaz ba ya magana biyu, idan ya faɗi magana sai ya aikata." "Dan haka Ƙaisar ya fara ƙoƙarin kare Nana, ya yi amfani da jakar da ya saka Lanti ta haɗa, ta yi amfani da" "ita gurin kashe Sarkin Aska. Ya ƙara yi mata aiki, da saiwoyi da wasu hatimai, ya yi wa Giyaz tarko da ita." "Cikin matsananciyar sa'a, Giyaz ya faɗa tarkon Ƙaisar, saboda ya san muddin ya bar Giyaz, zai iya nakasta" "Nana nakasa ta har abada, ko ma ya kashe ta, kamar yadda ya furta." "Ya ɗauki Giyaz, ya kai shi can nesa ya sadaukarwa wani boka shi, bisa musayar da za su yi, zai ba shi wani" abu mai muhimmanci. Wanda ya yi hakan domin nesan ta shi da Nana da zuriyar Lanti. Ayshacool "Duk da abin da ya yi ya dawo ya dame shi, yana matuƙar ƙaunar mahaifinsa, duk da saɓanin da suka" "samu, amma babu yadda iya, hakan ne kawai zai sanya ya nisanta shi da Nana." "Sauran 'yan uwan Ƙaisar da tuntuni suke jin haushinsa, suka yo caaa a kan Ƙaisar, har suka nemi hallaka" "shi, saboda abin da ya yi wa mahaifinsu, amma sun san ko sun hallaka shi, idan Giyaz ya kuɓuta suma sai ya kashe su." "Ɗan uwan Giyaz Duna, ya yi ta ƙoƙari gurin ganin ya kuɓutar da Giyaz, amma abu ya gagara." "Nan suka din ga kai wa Nana hari, da yinƙurin hallaka ta." "Maijidda kuwa bayan mutuwar aurenta, tana gama idda, Iliyasu tsohon saurayinta ya sake dawowa ya" "aure ta. Ko da Baban Nana ya samu labari, sai ya ce tana sane, ta ƙi zama da shi, saboda ta koma ta auri" "Iliyasu, dama son zama da shi take yi ba." "Nana ta ga garari tun da ƙuruciya, babu cikakkiyar kulawa, kuma tun ba ta fi shekara uku ba take ganin" "Ƙaisar, da ma sauran 'yan uwansa da suke ta kokarin azabtar da ita." "Maijidda ta so karɓar ko Nana ce, saboda rashin cikakkiyar lafiya, amma Isa ya hana fafur, ita ma can" "mijinta ko yaya ta motsa tana son ganin 'ya'yanta, sai ya hau bala'i wai za ta gurin tsohon mijinta." "Tun Nana na ƙarama, take nuna alamun rashin lafiya, amma babu wanda ya kula. Ta kan wuni tana bacci" "tun safe, har dare babu wanda zai damu. Wasu lokutan ta daina magana ma ko tafiya gaba ɗaya. Idan" kuma ta warware ta din ga fitinar da ta fi ƙarfin shekarunta nesa ba kusa ba. "Ta kan ga Ƙaisar a zahiri, ko kuma a cikin bacci. Babu wanda ya damu da ta ci Abinci ko ba ta ci ba," "mussaman da Baba ya daina sana'ar komai, sai dai Imran ya nema ya bata. Idan ta fita Ƙaisar ya kan zo a suffar mutum, ya ba ta abinci. Allah ya sanya masa matsananciyar ƙaunarta. Ya fara bayyana a jikinta ne," "tun wani duka da Mama ta yi mata, bayan faɗa ya haɗa ta da Jamila." "Sai da ta kwana biyu a sanƙame, tun daga nan suka gane halin da take ciki. Da ranta ya ɓaci sai" "hankalinta ya gushe. Ƙaisar ya sha ɗauke Nana, a neme ta a rasa kwana ɗaya ko biyu ya je ya ajiye ta gurin sa." "Baba ya yi ƙoƙarin nema wa Nana magani, amma abu ya gagara. Labari ya iske Maijidda halin da Nana ne" "ciki, bayan da su Adda Saude suka zo ganin su Nana. Rabi ta haɗa tuggu a gurin Baba, ya ce kar su sake zuwar masa gida, kuma ba zai bayar da Nana ba. Wahala ta saka Imrana fara sace-sace saboda su ci Abinci, Rabi ta saka Baba ya kore shi daga gidan. Haka Nana ta tashi a cikin wahala, ga wanda bil'adama" "suke yi mata, ga wadda Ƙaisar yake yi mata da sunan kulawa." "Ji ta yi tamkar an sanya hannu an shaƙe ta, a dole ta saki littafin ta ja da baya tana tari." "Ta ɗaga kai ta kalli Ƙaisar, bai ce mata komai ba, ya ɗauki littafinsa ya juya ya tafi. Yana barin gurin Haula" "ta zagayo ta dafa Nana. Ta ɗaga kai ta kalle ta ta ce ""Ƙawata, kwana biyu. Hadiminki ya ƙi saurarata balle" "na sanya ran zai karɓi buƙata ta, ki yi wani abu a kai dan Allah""" "Nana ta ce ""Haula, gaba ɗaya jinsinku ba abin yadda ba ne, ki rabu da ni da wannan maganar ta ku""" """Shikenan, na rabu da ke, amma kin yi ganganci abin da ki ka yi wa dattijo, Allah kaɗai ya san me zai yi" "miki idan ya gama jinya. Kuma har Ƙaisar ki ka janyowa shi ma ba zai bar shi ba""" """Duk hukuncin da ya yi wa Ƙaisar yayi daidai, ɗa na gari ba zai taɓa yi wa babansa abin da ya yi wa nasa" "mahaifin ba""" "Haula ta ce ""Kash! Nana kar ki zama butulu mana. Sai dai ina fatan kin fuskanci jakar gurin Sarkin baka da" "ya baki, wace jakar ce""" "Nana ba ta ba wa Haula amsa ba, Sayyid ya tashe ta." """Ma vie"" yayi maganar yana matsawa jikinta sosai. Jiki a sanyaye ta amsa masa. Ya ce ""Lafiya dai?""" """Mmm""" """Ko Ƙaisar ɗin ne?""" """A'a""" """To me yasa ki ka tsorata? Mene ne ya baki tsoro?""" """Bakomai""" """es-tu sûr? (Kin tabatta?)""" "Ta ce ""Eh. Haryanzu hannunka lafiya ƙalau ko?""" """Eh, amma akwai abin da ya tsorata ki, gaya mini mene ne?""" "Ji ta yi tamkar ta gaya masa, dan a wannan karon ba ta manta abin da Giyaz ya gaya mata ba, a kan idan" ya warke zai sake waiwayar su. """Ma viee""" """Sayyid"" ta amsa a hankali." "Ya yi maganar yana taɓa wuyanta ""Sanyi ki ke ji Rayuwata""" """Eh, amma ba sosai ba""" Ayshacool """In baki ɗumi ne?"" Yayi maganar muryarsa ƙasa-ƙasa" "Dariya ta yi ta ce ""A'a na yafe, ƙona ni za ka yi""" "Shi ma dariyar ya yi ya ce ""To ni ki bani sanyin ina so"" Ya yi maganar da sigar shawaɓa." """Wai kai ba ka jin bacci ne? Kawai ka farka cikin dare?""" """Soyayya ce ta tashe ni"" Sai da jikin Nana ya ɗan yi sanyi, ta ce ""Soyayya kuma Sayyid?""" """Eh, je t'aime ma femme""" """To ai ban san me ka ce ba""" "Ya yi kissing ɗin goshinta ya ce ""Ina sonki matata"" wani abu ne ya tsirgawa Nana, tun daga tsakiyar kanta," har tafin ƙafarta. "Shafa hannunsa ta yi, kamar mai tantamar abin da ya ce, ta ce ""Sayyid""" """A'a, kar ki yi tantama, ko ki yi kokwanto, shi yasa na baki sunan Rayuwata. Ko a wannan Duniyar, ko ma" "a wace Duniyar, kawai ina son matata, saboda ita ɗin Rayuwata ce. Babu abin da zai canza hakan.""" """Sayyid ina tsoron idan ka tuna waye kai, ka ji ba ka so na, zan cutu da yawa, zamana da kai na shaƙu da" "kai sosai zuciyata ba za ta iya ɗauka ba"" Ta yi maganar cikin rauni da tsoro." "Ya ɗaga kan Nana, ya sanya hannunsa a wuyanta, ta lumshe idanunta hawaye na bin gefen fuskarta." """Ƙa'idar ba za ta canza ba har abada, babu ruhin da zai samu nutsuwa a gangar jikin ɗayanmu muddin ba" "ma tare, ki saka haka a ranki. Sayyid yana son Rayuwarsa. Ko babu raina fatalwata za ta ci gaba da sonki"" Nana ta yi ajiyar zuciya tare da dariya, ta shafa gashin kansa." """Allah ya sa haka. Ina son mijina sosai nima"" murmushi ya yi yana kissing ɗin ta." "Har garin Allah ya waye, maganganun Sayyid ne ke kai komo a cikin ƙwaƙwalwa, zuciya da kuma gangar" "jikin Nana. Wani irin shauƙi da farinciki ne yake kama ta, da tuna kalamansa." """Amarya"" ya yi maganar yana kallon ƙwayar idonta." """Amarya da wannan ɗin?"" Ta yi maganar tana nuna cikinta da ya fito sosai." "Yayi murmushi yana shafa cikin ya ce ""Duk da haka amarya ce ai, ko kin manta?"" Ya yi maganar yana" kashe mata ido. Ta yi murmushi tana ci gaba da ninkin kayan da ta wanke. """Sayyid, bari na je kasuwa na nemo kayan magungunan ka, na dafa maka, ka ci gaba da sha, kuɗin" "hannuna sun ɗan taru, zuwa ranar Monday in Allah ya kaimu, duk yadda za a yi, mu tafi Kano Asibiti. Na" "ji haryanzu zuciyarka ba ta bugawa sosai, na san ƙarfin hali kawai ka ke yi""" """Gaskiya kin fiye saka ido, ya aka yi ki ka gane hakan, mai magani?""" "Ta jinjina kai ta ce ""Au haka ma za ka ce ko? Hmm ai shikenan, za ka ga mai magani, yau sai na wanke ka" "da magani na kulle ka a ɗaki""" """Eh saboda cin zali ba, kuma ke ki gudu, alhalin kamata ya yi ki yi mana tare""" "Ganin yadda yake rungumota ta ce ""Sayyid na gama shiryawa, fita fa zan yi""" "Ya ce ""Na sani""" """Ka sani kuma ka ke son na ɓata lokaci? Dan Allah Sayyid jiya throughout the night mu na tare, yanzu" kuma... """Shhhh... Ba ki ji jikina ya fara zafi ba""" """Wallahi lafiyarka ƙalau, normal babu zafi a jikinka, wai wannan surutun duk daga ina?""" "Haka ya hana Nana fita, har bayan Azahar, kawai ta zuba wa Sarautar Allah ido. Kuma a fuskar sa take" "ganin tsantsar ƙarfin hali, amma ba shi da lafiya." "Sai bayan la'asar ta marairaice ta ce ""Dan Allah ka bar ni na je na haɗo kayan nan Sayyid, ko haryanzu ba" "ka gama jin Sanyin ba?""" "Ya ɗaga mata gira. ""To ga mafici, yi ta fifita, har na dawo"" Dariya ya yi yana ɗan jan hancinsa. Ya kamo" "hannunta ya ɗora a wuyansa ya ce ""Kin ji da zafi ko?""" """Ba wani zafi. Waccan ranar ma wayo ka yi mini, wai na baka sanyin jikina""" "Dariya yake son yi sosai, amma sai ya yi kaɗan ya cije, ya ce ""Ai ni Ƙaisar wasu lokutan taimakona yake" "yi""" "A sanyaye ta ce ""Shi me yasa ba ka kishi da shi?""" """In ji wa? Kawai abu ɗaya ne da babu yadda muka iya. Alaƙarsu ta ɗa da mahaifi tana tasiri a rayuwarmu" "ni da ke""" "Cikin mamaki Nana ta ce ""Ta yaya? Kuma ya aka yi ka san Ƙaisar ɗan Giyaz ne?""" """Yadda ki ke ganin Ƙaisar ku yi magana, haka nake ganin Giyaz, kuma na fuskanci waye shi a tattare da ni." "Yanzu ki je ki dawo""" """Kai amma na yi mamaki fa, kuma ba ka taɓa gaya mini ba. Bari na je na dawo, ina da tarin tambayoyin" "da zan yi maka""" """Tom sai kin dawo""" "Ta saka hijjabinta, har za ta fita ya kirawo ta. Ya ce ""Ba ki yi mini ba""" "Ta yi masa kiss a goshinsa, da bakinsa." Ayshacool """Allah ya yi miki albarka. Ki kula mini da kanki, kar wani ya kula mini ke, ki kular mini da babyna ki tafi a" "hankali ki je ki dawo""" "Ta kalli cikin ta ce ""To Shugaba, in sha Allah""" """To a dawo lafiya, I love you""" "Cikin murmushi ta ce ""Inyee ɗan gayu, ka yi furansanci, ka yi turanci, ka yi hausa ga kuma yarenku. Zan" "koyo yaren da baka iya ba, na din ga tashin kanka da kalaman soyayya""" "Ya ce ""Je ki dawo ki yi mini waƙa""" """Sai dai na je na dawo, na yi maka tsifa, na yi maka sabon kitso"" ya tsuke fuska yana hararata. Ta fita" tana waigensa tana murmushi. "Tana fita ya jingina da jikin bango, yana dafe saitin zuciyarsa, yana haki sama-sama. Ya fito tsakar gida da" "kyar, ya zauna yana sake danne saitin zuciyarsa da yake jin wani irin abu kamar shocking daga zuciyarsa yana zagayawa bayansa har cikin kansa." "Tsayuwar motoci ya ji a waje, sai dai hankalinsa ba ya kan hakan. Ya ji an daki ƙofar gidan da ƙarfi. Ya" ɗaga kai ya ga wasu murɗaɗɗun ƙarti sun shigo cikin baƙaƙen kaya. "Duk da mawuyacin halin da yake ciki, haka ya yinƙura ya tashi da ƙyar, ganin an shigo da Habu hannunsa" da sarƙa. "Ya din ga bin mutanen da kallo, Habu cikin matsananciyar damuwa ya zube a kan gwiwoyinsa ya ce ""Ka" "yi mini Afuwa Imam, ba laifina ba ne ka yi haƙuri, na gaza baka kariyar da ta dace"" Sayyid ya din ga bin sa" "da kallo, da alama ma ba ya gane me Habu yake nufi." "Ƙartin nan biyu daga cikin su, suka yo kansa, suka riƙe shi." "A rikice ya ce ""A'a, ku rabu da ni. Me na yi muku?""" "Ƙoƙari suke su tasa shi su tafi da shi cikin salama, amma ya turje. Suka juya yare zuwa faransanci, su na" "rarrashin sa, ya wuce su tafi." """Ba zan je ko ina ba? Ina zan tafi na bar matata"" Habu ya din ga girgiza masa kai da alamar ya daina faɗar" maganar da yake yi. """Ku rabu da ni, ina zaku kai ni na tafi na bar Nana"" maganar da yake yi cikin ɗaga murya, ga ƙoƙarin" "turjewa da yake yi, ya sanya zuciyarsa yin rauni, ya yi baya zai faɗi. Suka tare shi suka saɓa shi suka yi waje da shi." "Aka saka Habu a cikin wata motar daban, Sayyid kuma aka saka shi a cikin wata baƙar Highlander mai" "tint glass, aka rufe suka tafi da shi." "Nana tana tsaye ta bayar da kuɗi, za a bata kankana, dan daga ita har Sayyid, kawai ta ji gabanta ya yi" "wata irin mummunar faɗuwa. Ta yi shiru, ta jiki gaba ɗaya jikinta ya yi sanyi. Kawai ta juya ta tafi. Mai kayan yana ta yi mata magana, amma ba ta tsaya ba, ta nufi gida har da ɗan gudu saboda azabar sauri." "Tana zuwa ƙofar gidan ta ga ƙofar gidan a ɓalle, da hanzari ta shiga gidan, tana kiran sunan Sayyid." "Amma wayam ba ya nan, ta shiga ɗaki baya nan. Ta duba banɗaki nan ma ba ta gan shi ba." "Ta fita waje da sauri, tana kalle-kalle, ta tafi hanyar inda bishiyar kukar nan take, tana tunanin ko jikinsa" "ne ya motsa, ya tafi can, sai dai can ma baya nan." "Ta sake komawa gidan cikin tashin hankali, da wani yaro da yake zuwar mata aike ta haɗu a ƙofar" "gidanta ta ce ""Ashiru, ko ka ga Sayyid ya fito daga gidan nan? Wannan mutumin na gidana farin nan?""" """Wasu mutane ne suka shiga gidan suka tafi da shi, a mota suka zo""" "Sak Nana ta tsaya, tana ƙure Ashiru da ido, tamkar ma ba ta gane yaren da yaron yake yi." Ayshercool 08081012143 Ayshacool "Cikin rawar murya Nana ta ce ""Wace irin mota kuma Ashiru? Ka tabattar kuma Sayyid ne?""" """Wallahi na tabattar, ina nan ina wasa suka zo, a motoci wannan farin na gidanki suka ɗaukko.""" "Tamkar mahaukaciya ta bi sahun motar, ita ce har titi ko za ta ga motar da Ashiru ya ce, amma babu" wata alama na za ta ga motar da aka daukar mata Sayyid aka saka a ciki. "Gaba ɗaya ta kasa kuka, sai tsuma da jikinta yake yi tamkar mazari. Tuni rana ta faɗi, an fara kiran sallar" "magariba, ba ta san tafiyar da ta yi da nisa ba, sai da ta tashi dawowa." "Gidan Uwani ta nufa, ta tarar da ita ta yi alwala, za ta yi sallar magariba." "Uwani ta ce ""Ke Nana, uban me ya fito da ke da magaribar nan, ga juna biyu kina da shi, duk da na san" "ba ki da ɗan aike amma koma mene ne, ai kya bari a idar da salla ko?"" Nana ba ta yi magana ba, ta nemi" guri ta zauna a ƙasa. """Ke lafiya kuwa?"" Uwani ta yi maganar tana tattara hankalinta a kan Nana. Amma Nana ta kasa magana," "sai murza zoben hannunta da take yi, tana ajiyar zuciya." """Ke ki yi mini magana, kar ki tayar mini da hankali mana""." """Sayyid ne ya ɓata""" """Kamar yaya sai ka ce wani zakara?""" """Da gaske nake""" """To ai ban gane ya ɓatan ba ne? Mutumin da yake jinyar ne ya iya tashi ya fita har ya ɓata?""" """Ai kwana biyu jikin da ɗan sauƙi, dan har ya ce mu zo nu gaishe ki"" Ta yi maganar ba tare da tana iya" tantance me ma take faɗa ba. """A'a Nana, wataƙila dai wani wajen ya je zai dawo. Tashi ki yi sallar magariba, zuwa anjima a raka ki" "gidan ko ya dawo""" "Nana jin Uwani kawai take yi, ta tashi ta yi sallar magariba, aka yi isha'i. Uwani ta saka Nana a gaba zuwa" "gidanta, sai dai kamar yadda Nana ta bar gidan wayam babu Sayyid babu dalilinsa." "Nana dai ba ta gaya wa Uwani abin da Ashiru ya gaya mata ba, na ya ga an zo da mota an tafi da shi ba." "Sai wajen goma na dare, hankalin Uwani ya tashi. Ta sanar da samarin gidan halin da ake ciki. Nan suka" "bazama a cikin Buda yawon neman Sayyid, duk da galibi ma ba su san shi ba, kwatancensa Uwani ta yi musu, suka tafi yawon neman sa, har gurin jami'an tsaro aka kai rahoto." "Sai dai har bayan sha biyun dare, babu wanda ya ji ko ɗuriyarsa." "Uwani ta saka aka rufe gidan, ta ce Nana ta zauna a nan, ko zuwa dare zai dawo." "Nana a ranta ta ce ""Wane dare kuma bayan wannan""" Daren ya zame wa Nana dare mafi tsawo a rayuwarta. Damuwa da tunani ya cika mata zuciya. Ba ta "tunanin Sayyid zai iya tafiya ya bar ta. Idan kuma da gaske zuwa aka yi aka tafi da shi, to suwaye su ka tafi da shi? Ina suka kai shi, me ya yi musu? Ko dai wani laifin suke aikatawa ba ta sani ba? Amma shi da yake kwance babu lafiya, kullum tana tare da shi a gida, yaushe har yake aikata wani rashin gaskiya da" ba ta sani ba. "A haka har aka yi assalatu, a kan kunnenta." **** "Dare malafar rana, kowa ya bika ya shirya maka." "Danƙareriyar mota ce, ƙirar highlander baƙa, take ta kwarara gudu a saman kwalta, tamkar hanyar" domin direban kawai aka yi ta. "Gefe da gefen hanyat baki ɗaya babu komai, banda yashin sahara, sai busassun bishiyu jefi jefi." "Kasancewar dare ne, wata ya kai kwana goma sha huɗu, ya haska ko ina, ga taurari sun yi wa sararin samaniyar ado." "Titin ta tsakiyar sahara ya ratsa, wadda yashin saharar ya bayar da sassanyan yanayi." "Kallon sa ya yi, daga bisani ya ce ""Kilomètre nawa ce ta rage mana ne?""" "Direban ya waiwayo ya kalli mai maganar wandaa fuskarsa a rufe take cikin rawani ya ce ""Bai fi 95" "kilomètre ba""" """Dans quelques minutes ?? (Nan da wani lokaci?)""." """Bai fi awa ɗaya ya rage mana ba""" """Dole fa mu ƙarasa dai-dai lokacin da aka umarce mu, ni ina tsoron ma kar ya farka. Ka ƙara sauri""" "Ya yi maganar yana haska fuskar Sayyid, da yake kwance a jikinsa ya haɗa gumi, cikin wani yanayi kamar" "bacci kamar suma, sai dai yadda yake gumi ya nuna a wahale yake baccin, babu in da yake motsi a" "jikinsa, sai ƙirjinsa da yake ɗagawa yana sauka lokaci zuwa lokaci, numfashinsa yana fita da ƙyar." "Ya kai hannunsa, ya ɗora a kan ƙirjin Sayyid, idan zuciyar sa ta buga sau ɗaya, sai ta jima kafin ta sake" "bugawa. Sai dai duk bugawar da za ta yi, da ƙarfi take bugawa tamkar za ta tsaga ƙirjinsa ta fito dummm!." Ayshacool "Cikin damuwa ya ce ""Lowalli, sai ka ƙara gudu fa, kar ya mace mana, bugun zuciyarsa raguwa fa yake yi." "Kuma ka san idan ya mace mana mun shiga uku mun lalace""" "Lauwalli ya jinjina kai yana ƙara gudun motar. Ya ce ""In sha Allah a raye za mu kai shi, ba za a samu" "matsala ba. Dan dai ka ƙi yarda ne, da na ce mu tsaya a Asibiti""." """Kai dalla ka daina maganar tsayawa a wani Asibitin nan. Ka yi ka hanzarta mu cika umarnin nan," "mukaɗai ake dako""" """To shikenan, mun kusa in sha Allah"" ya yi maganar yana ƙara gudun motar." **** "Antin Yusra ce ta kalle ta, ta ce ""Yusra duk wannan kwalliyar fa? Ta karɓar baƙon ce?""" """Eh mana Mami, yana hanya ma ai"" ta yi maganar tana tafiya ɗakinta, ta fesa turare." "Wayarta ce ta fara ringing, ta ɗaga wayar tana murmushi ya ce ""Gani a layin""" """Duba lambar gidan, za su buɗe maka""" "Ya ce ""Ok""" "Bayan mintuna goma sha biyar, ta fito ta ce ""Mummy na tafi""" """To a gaida baƙon, ya tabattar mana da alkhairi""" "Kawai ta fice tana murmushi. Tana zuwa ta gan shi a tsaye a cikin falon, yana kallon ƙaton frame na" "hoton mai gidan, da yake retired soja." "Ganin abin take tamkar a mafarki, wai Sagir ɗin ta ne a gabanta." Jin ƙamshin turarenta ne ya sanya ya waiwaya. Da gudu ta ƙarasa inda yake ta faɗa jikinsa. "Babu tunanin komai, Sagir ya ƙanƙame ta a jikinsa, bar siririn mayafin da ta yafa a kanta, yana zamewa" "gyararren gashin kanta, da yake ta ƙamshin mayuka ya bayyana." "Ya din ga shafa bayanta yana murmushi, kawai ya ji tana sheshsheƙar kuka. A ɗan rikice ya ce ""Lafiya," "kuka kuma Yusra?""" "Ya zauna tare da ita a jikinsa, ya ce ""Ina ta murna zan zo na gan ki, amma in zo ki din ga kuka, ko ba kya" "son ganina ne?"" Ta girgiza masa kai alamar a'a." """To mene ne""" """Ka daina so na, tun da ka sake ni ba ka ƙara nema na ba"" Ya ɗago fuskarta su na kallon juna yace ""Da na" "daina son ki, ba zan zo nan ba Yusra, kin san yadda rabuwarmu ta kasance, ban daina sonki ba, ban kuma daina tunanin ki ba""" """Almost three years, ba ka sake nema na ba""" "Sagir ya marairaice murya ya ce ""To yanzu ba gani na zo har nan saboda ke ba? Haba wifey"" ta zumɓura" "baki cikin ɗabi'arta ta shagwaɓa. Duk da ya zuciyarsa na tunatar da shi, tare da gargaɗin sa a kan Yusra" "ba muharramarsa ba ce, amma ya kasa yaƙar kansa, ya ƙyale ta a jikinsa yana jin yadda ya yi kewarta." """Talk mana, na zo kuma kin haɗe rai?"" Tashi ta yi daga jikinsa, ta zauna a kusa da shi ta ce ""Ya hanya?""" """Alhamdillah, ki na lafiya ya jikin naki?""" """Da sauƙi""" """Kin warware?""" "Ta girgiza kai ta ce ""Bayan ƙin yadda ku ka yi da gaske ba ni da lafiya. Sai ga shi na haɗu da wata Nana, ita" "ma tana irin ciwon da nake ji, ai ita ta san ba ƙarya nake yi ba.""" "Ya ce ""To yanzu dai duk ba wannan ba, i miss you Yusra, irin sosai da sosai ɗin nan fa""" """Bayan ka yi aurenka, ba wani missing ɗina da ka yi"" ta yi maganar tana tsiyaya masa lemo a cup ta miƙa" masa. "Ya karɓa ya kai bakinsa yana tsare ta da ido. Ta kalli screen ɗin wayarsa da ya kawo haske, hoton Haidar" "ya bayyana a kan screen ɗin. Ta ɗauki wayar tana kallon yaron ta ce ""Waye wannan?""" """Ɗanki ne Haidar, recently ma ta kuma haihuwa ɗan ya rasu"" ta yi masa wani kallo, da bai tantance na" "mene ne ba ta ce ""Da tuni nima wataƙila na haihu""" "Ya yi murmushi ya yi shiru, yana cin abincin da ta zuba masa. Cikin hikima ya karkatar da zancen suka ci" gaba da hira. "Wayarsa ce ta fara ringing, ta ajiye masa ganin hoton heart a kan sunan. Ya ɗaga wayar tare da yin" "sallama ""Hello love""" """Ka sauka lafiya?""" """Alhamdillah am good dear""" "Shukura ta ce ""To sai ka dawo, Allah ya tsare mana kai, take care""" "Ya yi murmushi ya ce ""In sha Allah dear"" wani abu ne ya tokare wa Yusra a ƙirji, ta zuba masa ido." "Ya ajiye wayar, bai kalle ta ba ya ce ""Yusy, kin san na yi missing ɗin girkinki over?""" "Jin ta yi shiru ya sanya ya ɗaga kai ya kalle ta, ya ga tana hararsa. Ya yi murmushi ya ɗebo Abincin ya kai" bakinta. Ta murguɗa masa baki ta tsuke fuska. """Smile, haba sweetheart"" ta buɗe bakin ya saka mata Abincin. Haka ya ribace ta, suka ci gaba da hira." "A nan ya yi sallar la'asar, sannan ta fito raka shi." "A jikin motarsa suka tsaya, tana yi masa wani irin kallo mai ƙayatarwa." Ayshacool """Tom sai yaushe zan dawo?""" """An jima kaɗan""" "Ya yi murmushi ya sake kallon ta ya ce ""Yusra""" "Ta ce ""Na'am""" """Yaushe za ki dawo gidana, ji nake kamar na ɗauke ki, na tafi da ke Kano, ina kewar ki sosai da sosai." "Yaushe za ki dawo gidana?""" "Ta girgiza masa kai ta ce ""Ba zan dawo ba""" "Cikin mamaki ya ce ""Saboda me?""" """Ka auri wata, kuma Hajiyarka ba za ta bari na dawo ba, su Mami ma ba za su bar ni ba, kuma ma" "haryanzu ban gama warkewa ba""" """Haryanzu ki na so na?"" Ta kalle shi ta sunkuyar da kanta ƙasa." """Idan ba kya so na, me yasa ki ka nemi lambata, ki ka kira ni? Kuma har ki ka ba ni dama na zo?"" Ta" sunkuyar da kanta ta ci gaba da murza yatsun hannunta. """Yusra Sagir ɗin ki ne fa, ɗago ido kalle ni"" Kawai ya ga hawaye na bin fuskarta." """Sagir ɗina, da ya rabu da ni, saboda ba ni da lafiya ba"" Ta yi maganar tana sheshsheƙa. Ganin babu" "kowa a gurin da suke, ya sanya ya janyo ta jikinsa, ya ɗago kanta yana kallon idonta ya ce ""Yusra, ki na so na haryanzu?"" Ta yi shiru hawaye na ci gaba da bin idanunta." """Ki na so na har yanzu, shi yasa ki ka neme ni. Dan haka batun ina da aure, Hajiyata ba za ta bari ba, 'yan" "uwana ba sa son ki, haryanzu ba ki da lafiya, duk ba ta taso ba. Za ki dawo gidana a karo na biyu in sha Allah. Haryanzu ina son ki Yusra""" """Amma..." """Babu amma tsakaninmu, believe me zan dawo da ke gidana in sha Allah"" Jikinta ya yi sanyi. Ya cika ta a" "hankali, ya shiga motarsa. Ta tsaya ƙyam tana kallonsa, shi kansa da kyar ya tafi, tamkar ya ɗauki Yusra ya tafi da ita." "Har ya kama hanyar Kano, zuciyarsa cike da tunanin ta ina zai fara. Dan shi har ga Allah yana son matarsa," "ba a son ransa ya rabu da Yusra ba. Yanzu kuma da ya ganta, gaba ɗaya ya ƙara rikicewa ba abin da yake" "sai tuno soyayyar da suka yi, daga saurayi da budurwa zuwa auren su." "Ko da ya je gida, Shukura ta karɓe shi tana yi masa sannu da zuwa." "Amsa mata ya yi yana kallon ta, kafin ya ƙaraso ta kira shi ya fi sau biyu, yana zuwa hatta ruwan da zai yi" wanka ta tanadar masa. "Ya cire kayansa ya shiga wanka, kamar ta san ba zai iya salla ba, sai ya tsarkake jikinsa, saboda rungumar" da ya yi wa Yusra. "Tana cikin tattare kayansa, hancinta ya ji ƙamshin turaren da ba na sa ba a jikin kayansa. Turarensa ɗaya" "ne da ta san shi da shi. Jikinta ne ya yi sanyi, domin ta daɗe da karantar alamomin rashin gaskiya a tattare da shi. Wani abu ne ya soki zuciyarta amma ta yi ta maza ta haɗiye tare da ajiye kayan." **** "Aka shiga kwana na biyar, ba tare da jin ko ɗuriyar Sayyid ba." "Nana duk ta fita hayyacinta, ba ta iya cin abinci, ba ta bacci. Ga Uwani tun tana rarrashinta, ta koma yi" mata faɗa tana ganin ta ƙi tawakalli ta ci gaba da addu'a. "Ga shi ta hana ta komawa gidan nasu, a nan gurinta take zaune tare da ita." "Yanzun ma Uwanin ce ta miƙo mata kofi da fura a ciki ta ce ""Ungo ki samu ki sha furara nan Nana, ko ɗan" "cikinki ya samu wani abu shi ma. Rayuwa ba za ta yiwu a haka ba kina zaune babu Abinci, ga juna biyu ba. Idan wani gurin mutumin nan ya tafi, idan da rabo zai dawo ai""" "Nana ta karɓi kofin, tana ajiyar zuciya. ""Maza ki shanye, kan na fito daga banɗaki"" Nana ta jinjina kai" tana kallon kofin. "Uwani na shiga banɗaki, Nana ta ɗauki mukullin da aka kulle gidansu, ta tafi." Gani take kamar tana shiga za ta tarar da shi a inda ta bar shi. Ƙofar dama a lanjare take aka rufe ta. "Ta shiga ɗakinsu, amma ta tarar wayam babu kowa a ciki." "Ta kalli kan katifar su, ta ga abin hiraminsa na rawani a kai. Ta durƙusa a kan gwiwoyinta, ta damƙi" "hiramin nan, da yake ta ƙamshin turaren sa. Tamkar ta damƙi Sayyid ɗin. Cikin kuka ta ce ""Haba Sayyid, daga cewa na je na dawo, sai ka tafi ka bar ni? Haba Sayyid yau kwananka biyar ba ka tare da ni. Da mutuwa ka yi na san wannan hukuncin Allah ne, dole na tawakalli, amma me yasa zaka tafi ban san halin da ka ke ciki ba. Haba Sayyid Haba Sayyid Nana ce fa"" ta din ga soki burutsu tamkar zararriya. Wani irin" kuka take yi mai haɗe da gunji da ƙunar zuciya. "Ba ta san lokacin da Uwani ta shigo ba, tare da abokiyar zamanta Sabuwa ba, sai ji ta yi ta taɓa ta ta ce" """Nana shi ne sai da ki ka fito ki ka zo ko? Ba na ce kar ki fito ba?""" Ayshacool """Uwani. Sayyid ya tafi ya bar ni, na zata mafarki nake yi, me yasa zai tafi ya bar ni?""" """Ke ki ji mini 'ya da rashin ta ido, yo ina zan san dalilin da ya sanya ya tafin ni? Ke ba za ki iya dakewa ki" "kama kanki ba, idan guduwa ya yi fa?""" "Sabuwa ta ce ""A'a Yaya, su fa yaran birni su na nunawa junansu kulawa, ya za a yi mutum mara lafiya a" "neme shi a rasa, ki ce hankalinta ba zai tashi ba? Kina kallon yadda take tiri-tiri da shi take nula da abin ta" "ke kin san ba ƙaramin so take yi masa ba, ai da tausayi""" "Uwani ta ce ""Kuma haka ne, amma tun da shi ya tafi nima jikata nake yi wa kar wani abu ya same ta, ga" "ciki. Ke Nana kuma ba garinsu ya tafi ba bai gaya miki ba? Ba kin ce ɗan Nijar ba ne?""" """Ba shi da lafiya fa, ba zai iya wannan tafiyar ba""" """A'a kar ki ce haka, idan ki ka bibiya ma, can ɗin ya tafi, amma yanzu ki yi haƙuri ki tashi mu tafi gida""" """Uwani, dan Allah ki yi mini alfarma ki bar ni na kwana a nan""" """To ya za ki kwana a gida ke kaɗai haka ake yi?""" """Ni dai dan Allah ki bar ni a nan, wallahi da safe zan dawo na yi miki alƙawari""" """A'a sai dai na turo yarinya ɗaya ta tayaki kwana"" Nana ta amince da hakan, aka turo mata yarinya." "Tuni yarinyar ta yi bacci, Nana kuma kwana ta yi aikin kuka." "Lokaci Lokaci, sai ta yi tasbihi tare da ajiyar zuciya." Washegari da sassafe Uwani ta zo ta kawo mata abin karyawa. "Yadda idanun Nana suka kumbura, ya sanya ta fahimci Nana ba ta yi bacci ba." """Wai ni Nana, babu wani wanda za ki kira, ki tambaye shi ko yaje? Ko kuma wani guri da za ki je a duba?""" "Jiki a sanyaye Nana ta girgiza mata kai. ""To shikenan sha kunun nan da ƙosai, kar su huce""" "Nana ta karɓi kunun tana kurɓa a hankali, ji take tamkar tana shan magani, saboda wani irin ɗaci da take" "ji kunun yake yi mata a bakinta. Amma saboda ba ta son faɗan Uwani, haka ta din ga shan kunun nan da" ƙyar. "Ta ɗan saci kallon Uwani ta ce ""Uwani, ina ga gobe in Allah ya kaimu zan shirya na koma Kano""" """Gurin wa?"" Uwani ta jefe ta ta tambayar." "Nana ta ɗan yi shiru, Uwani ta ce ""Gurin wannan masoron Ubannaki da bai san ciwon kansa ba balle ya" "san naki? Ya kasa tallafa miki da larura ta samu mijinki, yanzu ne idan kin koma zai tsinana miki wani abu? Ga cikin fari ke ba sanin kan abubuwa ki ka yi ba, ga wannan shu'umar matar tasa, da ƙafa duk dama ba tsayawa za ta yi ta kula da ke ba?. Ban ƙi ba ki kira shi, ki sanar masa abin da yake faruwa a matsayin sa" "na ubanki ba, amma ba dai ki koma wannan gidan ba. Ki yi zaman ki a nan ki haihu, ki yi biƙinki idan mijin" "naki bai dawo ba, a san abin yi""" "Tabbas Uwani tana da gaskiya, idan ta koma gidansu rayuwarta ta sake komawa baya, ta san babu wani" "abin kirki ko kulawa da za ta samu a gidan, wataƙila ma a kore ta. Ummi kuma ta yi mata ɗawainiya da yawa, tana jin nauyin ta sake koma mata da matsala." "Kuma ba ta ji a ranta za ta iya sake ko nufar hanyar gidan Alhaji Zailani ba, saboda yin hakan tamkar cin" "amanar Sayyid ne, kuma ita ba dolensu ba ce, da za ta je ta ɗora musu ɗawaniya. Dan haka Uwani na da gaskiya. Amma zamanta a nan ɗin ma, shi ma dai ɗawainiyar ce." "Ta sake ɗago kai ta ce ""To ina son na je Bauchi gurin Mamana""" """Kai Nana ki na da gardama, gurin nawa ne dai ba za ki zauna ba, kin ƙallafa rai tun da mijinki ya bar" "garin nan kema sai kin bar shi?""" """Ba haka ba ne Uwani, ina da dalili dan Allah ki bani damar hakan""" """Shikenan Nana, ba zan matsa miki ba, Ubangiji Allah ya tabattar da alkhairi, amma ki bari kamar nan da" "sati ɗaya, ki ɗan ƙara samun nutsuwa. Nima na lalubi na mota na baki""" """Ai ina da kuɗin mota""" """Nima na san ki na da kuɗin motar, na ce zan baki ai"" Nana ta ja bakinta ta tsuke." **** "Jamila ta yi shirin fita, tana tsaye tana latsa wayarta ta ce ""Baba har ya fita ne?""" "Mama ta ce ""Tun da uwar kashinsa ta cika ya fita. Da dai bai ci ba da yanzu yana nan yana bin bango" "yana zabga hamma yana faɗa da ƙadangaru da bokitai""" "Jamila ta basar ta ce ""Sonake ya bani cikakken kwatancen Buda, zan saka a kai ni, na je na ga Nana""" """Wai ba za ki bar maganar Nanan na ba ko Jamila?""" """Mama meye laifi idan na je na gan ta ne wai?""" Ayshacool "Nasiru ya ce ""Laaa rannan kuwa wannan ɗan uwan mijin nata, da suka zo a ka kaita gidanta ranar biki," "suka zo shi da wasu mutane, suka ce mini wai yanzu Nana a ina suke. Na dawo daga makarantar allo, na ce musu tana Buda can garin su Baba, shi ne ya ce na gaida Baba""" "Mama ta ce ""Ikon Allah, amma yarinyar nan ta ce 'yan uwansa an neme su an rasa. Kai Nana muguwar" "makira ce ta ƙarshe""" "Jamila ta ce ""Amm na tafi sai na dawo""" """To Allah ya tsare, a gaida Hajiyar""" """ Za ta ji"" ta amsa a taƙaice ta fita." Nana ta zauna ta haɗa kayan da za ta buƙata a cikin jaka guda ɗaya. "Tattara sauran guri ɗaya, ta ɗauki jakar gurin Sarkin Baka, da kuɗin Nijar ɗin da suke ciki. Ta tattara" "sauran kuɗin da suke ɗakinta, tana tunanin ta tafi ko da Uwani ba ta sani ba." "Ta tattara kayan kitchen ɗin ta, ta ce wa Uwani sayarwa za ta yi." """Me yasa za ki sayar da kayan ki Nana?""" """Kawai kuɗin nake buƙata ne""" """Gaskiya ba za ki sayar da kayan nan ba, ki bari ranar kasuwa, zan kai Tinkiyata kasuwa, na baki kuɗin" "amma ba za a sayar da kayan ba"" Gaba ɗaya Nana ta ji ta damu yadda ta ɗorawa Uwani ɗawainiya." """Uwani kar ki sayar da Tinkiyarki dan Allah, gara a sayar... ""Za ki rufe mini wannan dogon bakin naki, ko" "sai na kwaɗe ki? Ke ki ka sani na sayar? Ke dai akwai gardama""" "Babu yadda Nana ta iya, haka ta haƙura sai ranar kasuwa, aka sayar da Tinkiyar. Uwani ta ɗauki dubu" "talatin a kuɗin ta bawa Nana ta ce ""Ban san iya adadin kuɗin da ki ke buƙata ba, amma ga wannan kya jalauta. Dan Allah ki kula da kan ki Nana, duk inda ki ka je idan kin ga akwai matsala, ki dawo mini nan ni zan riƙe ki na kula da ke"" Nana ta din ga juya kuɗin, ta kalli Uwani idonta fal hawaye ta ce ""Na gode sosai" "da sosai, Allah ya saka miki da mafificin Alkhairi na gode""" """Babu komai, Ubangiji Allah ya sauke ki lafiya, ya bayyana mijinki cikin aminci. Nan ma za mu ci gaba da" "jiran jami'an tsaro ko za a samu wani labari daga gurinsu. Allah ya bayyana shi""" "Nana ta amsa da Amin. Jin washegari Nana za ta bar garin, ya sanya 'yan uwa, suka din ga kawo mata" "abin alheri cikin mutunci da karramawa, tare da yi mata fatan alkhairi." "Washegari da sassafe, Nana ta yi sallama da su Uwani, aka ɗauke ta a babur aka kai ta tashar ƙauyen." "Aka kaita Garko, daga nan ta hau motar Kano. A Kano ta hau motar da za ta sada ta da garin Bauchi." "Tsawon awanni huɗu da aka shafe, ana tafiya a motar, babu abin da Nana take yi, banda tunani ta saƙa" "wannan ta kwance wancan. Tunaninta a wani hali yake ciki, ya jikinsa? Su waye suka ɗauke shi? Mene ne makomarta idan bai dawo ba." "Lokaci-lokaci ta kan shiga hijjabinta ta yi kuka, ta share hawayenta." "Da ta sauka a tasha ƙarfe sha biyu na rana, ta samu abin hawa, har sunan unguwar da Mamanta take ta" "sani, sai dai ba ta san takamai ina ne gidan ba. Shi ma daga tashar zuwa garin da maman nata take, sai da aka yi tafiyar awa ɗaya da rabi. Ƙafafun Nana duk sun kumbura, da ƙyar take jan su. Ta ɗaukko wayarta ta kira lambar Anty Fati, ta ji ba ta shiga. Ta kira ta Adda Saude ba ta ɗaga ba. Ta nemi guri ta" "zauna, ta ci gaba da kiran wayar Adda Saude da ita kaɗai take shiga." "Sai dai still ba a ɗaga wayar, ga shi ba ta san daga garin, ina ce unguwar da za ta nufa ba." "Ta samu guri ta yi alwala, ta ciro sallaya a kayanta, ta shimfiɗa ta yi sallar azahar." "Bayan Azahar sosai, Adda Saude ta kira wayar Nana." "Nana ta ɗaga tare da yin sallama. Ta amsa mata ta ce ""Nana yi haƙuri, caji na kai wayar ne aka kunna" "mini, ya ki ke ya gida?""" """Lafiya kalau Adda, kin ganni na zo Bauchi ne na sauka, sai dai ban san sunan unguwar da Mama take" "ba""" """Ke haba dai, da gaske ki na Bauchi Nana?""" """Eh Adda, na sauka ma tun ɗazu""" """Subhanallah, ai ba ki gaya mini za ki zo ba, da tuni an shirya karɓar ki, ban sani ba an bar ki ki na jira," "dan Allah ki yi haƙuri yanzu ki na daidai ina, na zo na tafi da ke?""" "Nana ta ce ""Kar ki wahalar da kan ki dan Allah, ina garin ma, sunan Unguwar za ki gaya mini"" Sai da Adda" "Saude ta ɗan ji dumm, amma ta maze ta cewa Nana ta samu abin hawa, ta haɗa ta da mai abin hawan ta yi mata kwatance." Ayshacool "Nana ta ce ""To"" ta samu abin hawa, ta haɗa su ta kwatanta masa, sannan ta hau." "Nana ba ta isa gidan da Mamanta take ba, sai ana kiraye-kirayen sallar la'asar." "Mama na tsakar gida tana ta fama da yara, kawai ta ji sallamar Nana. Ta ɗago da hanzari, sai dai ta kasa" amsa sallamar ta nufi Nana da sauri suka rungume juna su na kuka. "Ta ɗago Nana ta ce ""Nana ba ki yi fushi da ni ba?""" "Nana ta girgiza kai ta ce ""Ban yi ba""" "Ta ja hannun Nana zuwa ɗaki, ta saka yaran su shigo mata da ƙatuwar jakarta." """Sannu da zuwa, tare ku ke da mai gidan naki ne?"" Nana ta sunkuyar da kai jikinta a sanyaye ta girgiza" kai alamar a'a. """To yana ina shi?"" Nana ta yi shiru." "Cikin tashin hankali Mama ta ce ""Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Nana ba dai auren naki ne ya mutu ba?""" Nan ma ta girgiza kai hawaye na bin fuskarta. """Shikenan, yanzu nutsu. Bari na ɗora miki ruwa ki yi wanka, sai ki yi salla"" Nana tana iya ganin tsantsar" "farinciki a kwance a fuskar mahaifiyarta. Ƙannenta suka kewaye ta, Nana ta din ga kallon su cike da so da ƙauna. Har gara Walida ta ɗan santa sauran kuwa duk ba su san Nana ba." "Ruwa mai ɗumi ta haɗa wa Nana, ta yi wanka, ta yi sallar la'asar." "Ta zubo wa Nana lafiyayyen Abinci, duk da yadda ranta ya biya a kan Abincin, amma ta kasa sakin jiki ta" ci. "Mama ta din ga kaiwa tana komowa, tana ta ɗawainiya da Nana tamkar ta goya ta, sai ta ji ina ma" tuntuni ta samu irin wannan kulawar ta uwa. """Nana ina Imrana kuwa, ya daina zuwa gaba ɗaya""" "Nana ta ce ""Lagos yake tafiya neman kuɗi""" "Ta yi ajiyar zuciya ta ce ""Ai shikenan, ya aka yi ina mijin naki ne? Me ya faru?""" """Nemansa na yi na rasa""" "Cikin rashin fahimta ta ce ""Kamar yaya?""" "Nana tana kuka ta yi mata bayani. Cikin mamaki ta ce ""To ina 'yan uwansa? A ina yake a Nijar ɗin?"" Sai a" "lokacin ta fayyace wa Maman komai, game da auren zuwa ɓatan sa." """Nana, me yasa baki neme ni kin gaya mini ba? Yanzu duk wannan abin yake faruwa amma idan muka yi" "waya sai ki ce mini komai lafiya ƙalau? Ni kaina nan kina raina, ina ta fafutuka na ga yadda zan yi na zo" "na gan ki. Ba ki kyauta ba Nana, komai lalacewata, ni mahaifiyarki ce, yakamata a ce kin sanar da ni." "Yanzu dai ki zauna a nan, mu ga abin da Allah zai yi, kafin ki haihu mu gani ko Allah zai sanya a ga mijin" naki. Amma na yi mamaki matuƙa da mahaifinki ya aura miki wanda bai san usulinsa ba? Yanzu ƙiyayyar da yake yi minin har ta kai haka? "Ko yana jin haushina amma ai ke 'yar sa ce, bai cancanci ya yi miki haka ba, amma babu komai." "Nana abin da nake so da ke, daga yanzu duk abin da ya faru Nana, ko ba zan yi miki komai ba, ki sanar da" "ni, ki bani dama na taka rawa ta ta uwa a rayuwar ki ko yaya ne"" Ta yi maganar tana riƙe hannun Nana." "Sallamarsa ce ta tilastawa Nana haɗiye abin da take shirin furtawa, cike da tsoro." "Ba ita ba hatta Maijidda, sai da zuciyarta ta buga da ƙarfi cike da tsoro." AYSHERCOOL 08081012143 Ayshacool "Nana ta ce ""To"" ta samu abin hawa, ta haɗa su ta kwatanta masa, sannan ta hau." "Nana ba ta isa gidan da Mamanta take ba, sai ana kiraye-kirayen sallar la'asar." "Mama na tsakar gida tana ta fama da yara, kawai ta ji sallamar Nana. Ta ɗago da hanzari, sai dai ta kasa" amsa sallamar ta nufi Nana da sauri suka rungume juna su na kuka. "Ta ɗago Nana ta ce ""Nana ba ki yi fushi da ni ba?""" "Nana ta girgiza kai ta ce ""Ban yi ba""" "Ta ja hannun Nana zuwa ɗaki, ta saka yaran su shigo mata da ƙatuwar jakarta." """Sannu da zuwa, tare ku ke da mai gidan naki ne?"" Nana ta sunkuyar da kai jikinta a sanyaye ta girgiza" kai alamar a'a. """To yana ina shi?"" Nana ta yi shiru." "Cikin tashin hankali Mama ta ce ""Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Nana ba dai auren naki ne ya mutu ba?""" Nan ma ta girgiza kai hawaye na bin fuskarta. """Shikenan, yanzu nutsu. Bari na ɗora miki ruwa ki yi wanka, sai ki yi salla"" Nana tana iya ganin tsantsar" "farinciki a kwance a fuskar mahaifiyarta. Ƙannenta suka kewaye ta, Nana ta din ga kallon su cike da so da ƙauna. Har gara Walida ta ɗan santa sauran kuwa duk ba su san Nana ba." "Ruwa mai ɗumi ta haɗa wa Nana, ta yi wanka, ta yi sallar la'asar." "Ta zubo wa Nana lafiyayyen Abinci, duk da yadda ranta ya biya a kan Abincin, amma ta kasa sakin jiki ta" ci. "Mama ta din ga kaiwa tana komowa, tana ta ɗawainiya da Nana tamkar ta goya ta, sai ta ji ina ma" tuntuni ta samu irin wannan kulawar ta uwa. """Nana ina Imrana kuwa, ya daina zuwa gaba ɗaya""" "Nana ta ce ""Lagos yake tafiya neman kuɗi""" "Ta yi ajiyar zuciya ta ce ""Ai shikenan, ya aka yi ina mijin naki ne? Me ya faru?""" """Nemansa na yi na rasa""" "Cikin rashin fahimta ta ce ""Kamar yaya?""" "Nana tana kuka ta yi mata bayani. Cikin mamaki ta ce ""To ina 'yan uwansa? A ina yake a Nijar ɗin?"" Sai a" "lokacin ta fayyace wa Maman komai, game da auren zuwa ɓatan sa." """Nana, me yasa baki neme ni kin gaya mini ba? Yanzu duk wannan abin yake faruwa amma idan muka yi" "waya sai ki ce mini komai lafiya ƙalau? Ni kaina nan kina raina, ina ta fafutuka na ga yadda zan yi na zo" "na gan ki. Ba ki kyauta ba Nana, komai lalacewata, ni mahaifiyarki ce, yakamata a ce kin sanar da ni." "Yanzu dai ki zauna a nan, mu ga abin da Allah zai yi, kafin ki haihu mu gani ko Allah zai sanya a ga mijin" naki. Amma na yi mamaki matuƙa da mahaifinki ya aura miki wanda bai san usulinsa ba? Yanzu ƙiyayyar da yake yi minin har ta kai haka? "Ko yana jin haushina amma ai ke 'yar sa ce, bai cancanci ya yi miki haka ba, amma babu komai." "Nana abin da nake so da ke, daga yanzu duk abin da ya faru Nana, ko ba zan yi miki komai ba, ki sanar da" "ni, ki bani dama na taka rawa ta ta uwa a rayuwar ki ko yaya ne"" Ta yi maganar tana riƙe hannun Nana." "Sallamarsa ce ta tilastawa Nana haɗiye abin da take shirin furtawa, cike da tsoro." "Ba ita ba hatta Maijidda, sai da zuciyarta ta buga da ƙarfi cike da tsoro." AYSHERCOOL 08081012143 "Har zai gifta, zai shiga ɗaki ya hango Nana, cikin rawar baki, Nana ta gaishe shi, ya amsa mata sama-sama" "ya wuce, dan kallo ɗaya ya yi mata, ya gane ta." "Jiki a sanyaye Maijidda ta tashi ta bi shi ɗaki, tana ɗan sinne kai, tana jiran ta ji me zai ce, amma bai ce" "komai ba. Ta kawo masa Abinci, tana jiran ta ji me zai ce, ga hankalinta a kan Nana, tana so ta je ta yi hira da 'yar ta, su yi hira ta ji ɗuminta, amma ta haƙura." "Nana ma na ta gaban ne yake faɗuwa, tana tsoron abin da zai ce, saboda ba ta manta karan battarsu." Haka dai a ɗarare suke hira da yaran gidan. "Maijidda na ta son yi masa magana, amma ta kasa." "Ya gama cin abincin ya fita, ba tare da ya ce komai ba." "Yana fita ta koma gurin Nana, suka ci gaba da hira, Nana ta kwanta a kan cinyar Mamanta, tana jin wani" irin farinciki yana ratsa ta. """Kin fara zuwa awo ne Nana?""" "Wata irin kunya ta kama Nana, ta ɗan sinne kai ta girgiza mata kai. ""Gaskiya yakamata, wata nawa ne" "cikin? Mu je a yi awo a duba, mu ga abin da zamu fara ajiyewa. Mu jira mu ga ikon Allah, idan an ga mijin naki shikenan, idan ba a gan shi ba kuma, ma san abin yi"" Nana dai ta yi shiru, sai kuma ta ce ""Mama ki yi" "mini addu'a, ki ce Allah ya bayyana shi cikin aminci""" "Mama ta yi dariya, ta ce ""Lallai kam, to shikenan, Ubangiji Allah ya bayyana mini sirikina cikin aminci""" "Nana ta yi murmushi, dan kunya ce ta kama ta daga baya, da tuna katoɓarar da ta yi." "Da daddare Mai Jidda ta yi wa Nana shimfiɗa, ta saka nata net. Sannan ta tafi nata ɗakin gurin mijinta," "har za su kwanta, Mai Jidda ta dubi Iliyasu, jiki a sanyaye cikin ladabi ta ce ""Baban Walida, na ga ka dawo ka ga Nana a gidan nan, ba ka ce komai ba""" "Ya dube ta ya ce ""To me ki ke so na ce?""" """Ahh dama kar ka ce ban gaya maka ba ne, dama ta ɗan zo ta zauna da ni ne, duba da yadda..." """Kin ga dakata, na ɗaga miki ƙafa ne na yi shiru, na ga gudun ruwanki, kar ta wuce mini gobe a gida, ta" "wuce ta koma inda ta fito""" """Dan Allah ka yi haƙuri Baban Walida, Nana ta samu matsala a aurenta ne, dan Allah ka yi haƙuri ba za ta" "daɗe ba, amma dan Allah kar ka ce ta tafi yanzu. Ni ko ruwan gidanka ka ce ba za ta sha ba, na amince dan Allah""" """Ke Maijidda, bari ki ji na gaya miki, wallahi sai yarinyar nan ta bar gidan nan""" "Ya nemi guri ya yi kwanciyar sa, takaici ya ishi Maijidda." "Nana kuwa tana jiyo hayaniyar su sama-sama, abin ya tsaye mata ta kasa bacci sam. Sai juye-juye, ga" mararta ta ƙulle duk jikinta ma ciwo yake yi mata. "Kwance yake a kan gadon Asibiti, jikinsa babu riga, sai dogon wando an rufe iya ƙafafuwansa da koren" yadi. Ƙirjinsa kuma an manna masa abin ECG. Sai gashin sa a rufe da hular Asibiti. Na'urorin gefen gadonsa sai sauti suke fitarwa. "Dattijo ne a tsaye a kansa, dogo fari tas, ya ɗaura hirami a iya kansa, ga gemunsa dogo duk farin gashin" furfura a jiki. "Ya kalli mutumin da yake tsaye ya ce ""médecin (Likita) yanzu mene ne abin yi?""" """Eh, gaskiya za a yi masa wannan allurar ne kamar yadda na yi maka bayani, idan kuma ba haka ba," "gaskiya sai dai a saka masa na'ura a zuciyarsa wadda za ta din ga taimakawa bugun zuciyarsa""" "Na kusa da Dattijon mai sanye da shuɗiyar shadda, da babbar riga, kansa ya yi naɗi da baƙin rawani ya ce" """Ka gani ko Sultan, Allah kaɗai ya san abin da suka yi masa a Nigeria. Dole yaron nan ya ɗanɗana kuɗarsa a ci gaba da tsare shi, har sai ya yi bayanin abin da ya yi masa a Nigeria, da aka neme shi aka rasa tsawon wannan lokacin. Su kan su sauran da aka kama su tare, dole a killace su a guri ɗaya, haryanzu ban bari an" "sake su ba, saboda idan maganar nan ta fasu akwai matsala""" "Sultan ya numfasa cikin damuwa ya ce ""Ni wannan bai dame ni ba, na bar ragamar komai a hannunka, ni" "lafiyar sa ce a gabana yanzu. Likita ku yi duk abin da ya dace kawai. Lafiyarsa ce damuwata a halin yanzu""" "Likitan ya ce ""In sha Allah"" Dattijon ya saka hannunsa a cikin na mara lafiyan,yana kallonsa cikin" "matsananciyar damuwa. Kamar mafarki ya ga yana motsawa a hankali, sai ya ƙara tattara hankalinsa a" kansa yana kiran sunansa. "Wata irin miƙa ya yi, yana ƙoƙarin buɗe idanunsa, amma ya ji tamkar an cika masa idanun nasa da" barkono. """Imam.." "Hannunsa ya ɗora a ka yayi wata irin kururuwa, jin yadda naman jikinsa yake yi masa wata irin azaba," tamkar ana cizgar naman jikin nasa. Ga wani irin zafi da raɗaɗi da yake ji kamar yana cikin wuta. """Zafi! Wayyo wuta Innalillahi wa Innalillahi raji'un, wuta zafi jikina""" "Kansa suka yi gaba ɗaya cikin tashin hankali, su na ƙoƙarin rirriƙe shi, amma ya watsar da su ya diro daga" "kan gadon, yana girgiza kansa da yake yi masa wata irin azaba tamkar zai tarwatse. Tunaninsa ne ya hargitse gaba ɗaya, ƙwaƙwalwarsa na ta kokawar ƙwato wani abu daga cikin memories ɗin sa, amma abu ya kacame, gaba ɗaya tunaninsa ya hargitse, ya kasa tantance komai. Fizge-fizge ya din ga yi yana kururuwa jikinsa na rawa. Dattijon nan cikin jarumta da ƙarfin hali, ya bi shi da sauri ya damƙe shi iya" ƙarfinsa. "Kokawa suka din ga yi, a rikice likita da ɗaya mutumin suka yo kansu, likitan ya haɗa wata allura ya yi" masa. Jikinsa ya saki a hankali bacci ya ɗauke shi. Kan gadon suka mayar da shi suka kwantar. Ɗaya "mutumin ya kalli likitan ya ce ""Ka na ji na?"" Likitan ya jinjina kai cikin nutsuwa." """Ka san dai waye wannan, kuma ka san matsayinsa da girmansa ko?"" Ya yi maganar yana nuna masa" mara lafiyan. "Ya jinjina kai ya ce ""Na sani""" """To muddin mu ka ji maganar abin nan da ya yi, ya fita waje, to ba wani ba ne ba kai ne, dole ka yi shiru" "da bakinka, kare sirrinsa wajibi ne a kan duk wani wanda yake yankin nan, idan kuma aka samu akasi ka furta wani abu, da rayuwarka za ka biya""" "Likitan yana tsuma ya ce ""In sha Allah ba zan faɗa ba""" "Da safe mijin Maijidda ya shura takalmansa ya fice, bayan sun gama jayayya da ita, tana ta roƙonsa tana" yi masa magiya. Gaba ɗaya Nana ta ji dana sanin zuwa Bauchi da ta yi. "Babban abin da ya bata mamaki, ƙatuwar kaza Maman ta saka aka yanka, ta gyare ta tsaf, ta yi wa Nana" "farfesunta, aka sayo mata ƙaton buredi ta haɗa mata shayi." """Mama daga zuwana na ɗora miki ɗawainiya, ba ma na iya cin Abincin ni""" """Ɗawainiyar ƙaniyarki, da can na yi miki ne Nana? Dan Allah ki daure ki mayar da hankali ki ci ki ƙoshi," "idan kuma ki na son cin wani abin, ki gaya mini sai na dafa miki""" """A'a ba na son cin komai, amma ki zo mu ci tare da su Walida""" "Maijidda ta ce ""A'a, babu wanda zai ci, da rana ma ci Abincin tare, wannan dai na ki ne"" Haka ta takura" "Nana, ta karya." "Nana ta fito da nufin, ta kama musu ayyukan gida, amma Mama ta hana, ta dafa mata ruwa ta yi wanka." Ta fito ta tarar Mama tana wanke kayan da ta cire. """Haba Mama dan Allah ki bari na wanke da kaina, ya za ki din ga yi mini wanki?""" """Tafi ɗaki ki je ki zauna ki huta, ga lemon fata can da rake, ki ɗan sha saboda ɗanɗanon bakinki. Akwai" "riɗi ma mai gishiri da mai suga, idan da wanda ki ke so"" kawai Nana ta tsaya tana kallon ta, tana murmushi." "Maijidda ta ce ""Ya dai?""" "Ta girgiza kai ta ce ""Ba komai Mama, na gode sosai""" "Nana ta shirya ta canza kaya, Khadija da take 'yar autar Mama, Nana ta kama ta tana tsefe mata kai. Ta" "ɗauki wayar Nana tana kallon hotuna. Sai ta buɗe wani video da Nana ta yi wa Sayyid, ta yi masa kitso sai hararta yake yi tana cewa ""Ka ga yadda ka yi kyau 'yan matana, yi murmushi mana"" ya ɗago kansa ya hargitse idanunsa. Nana tana dariya. Sai da tsigar jikin Nana ta tashi, gani take kamar ta shiga cikin wayar" ta ga Sayyid ɗin ta. """Anty Waye wannan?""" """Mijina ne"" ta ba ta amsa tana murmushi." """Ya na gan shi da kitso, kuma fari?""" "Nana ta yi dariya ta ce ""Ni kuma baƙa ko?""" """Eh, kuma ba kyau maza su yi kitso fa""" """Wai in ji wa? Ba ki ga gashin nasa ne da yawa ba?""" "Khadijah ta ce ""Eh, to yana ina yanzu?""" """Ya je unguwa, zai dawo ya ɗauke ni mu tafi""" """To ki nuna mini shi idan ya zo"" Nana ta ce ""To in sha Allah""" "Mama ta ce ""Ke Khadijah, tashi ki bar ta ta huta, Nana kwanta ki huta, ki rabu da surutun yarinyar nan""" "Khadijah ta tashi tana zumɓura baki, Nana ta ɗan kashingiɗa kawai wani abu mai kama da bacci ya yi" "awon gaba da ita, kasa tantance ma me take yi ta yi, bacci ne ko kuma ido biyu." """Ma Vie"" ta ji muryarsa a kunnenta. A razane ta waiwaya cikin damuwa. A tsakiyar sahara ta hange shi ta" "ce ""Sayyid""" "Ganinsa ta yi a tsaye a kanta, kayan jikinsa duk a yayyage, ya yi baƙi kamar ya ƙone, gashin kansa a" "hargitse jikinsa sai fitar da hayaƙi yake, ya ce ""Ma Vie sun mayar da ni inda za su kashe ni, dan Allah ki zo" "kar su kashe miki ni."" Yayi maganar yana hawaye." "Ta tashi cikin tashin hankali ta ce ""Suwaye? Kuma a ina suke?""" """Dan Allah ki zo, ni ban san su ba, amma na san mutuwa zan yi, dan Allah Husnah ki zo gurina, za su" "kashe ni. Idan kuma sun kashe ni, ki kular mini da ɗa na""" """Sayyid, dan Allah kar ka tafi ka bar ni, dan Allah Sayyid ka dawo? Ka gaya mini kana ina, sai na zo na" "same ka na tafi da kai""" "Guguwar Sahara ce, ta taso ta turnuƙe gurin." "Nana ta din ga tari, muryar Mama ta ji a kanta tana faɗin ""Tari ki ke haka Nana?""" "Kawai ta ga Nana ta tashi, ta yi waje. Ta riƙe ta ta ce ""Ina za ki ke?""" "Idanunta a rufe, fuskarta a murtuke ta ce ""Ba ki ji Sayyid ne yake kirana ba?""" """Waye hakan?""" """Mijina mana"" ta faɗa a fusace." """A'a babu wanda ya kira ki fa""" "Nana ta fara ƙoƙarin fizge hannunta ta ce ""Yanzun nan fa ya fita daga ɗakin nan""" """Nana babu kowa fa a gurin nan, daga mu sai ke""" """Ni ki cika ni, na ji Muryar mijina gurinsa zan je yana kirana""" "Tsawa ta daka wa Nana ta ce ""Ina magana ki na ɗaga mini murya? Wuce ki zauna babu wani wanda yake" "kiran ki"" Nana ta buɗe idanunta, ta kalli Mamanta, sai dai ba ta yi magana ba, kawai ta ga Nana ta yi baya za ta faɗi. Ta riƙe ta ta kwantar da ita. Jikin Nana ya hau karkarwa, idanunta na fitar da hawaye." "Cikin matsananciyar damuwa take kallon Nana, tana tunanin dama har zuwa yanzu, tana fama da larurar" nan?. "Ta rungume Nana a jikinta, ta kama goshinta, ta fara karanta mata Suratul Jinn, tana tofa mata a" fuskarta. A hankali jikin Nana ya saki ta fara bacci. "Ta yi shiru tana kallon fuskar Nana, tana tuna lokacin da take rungume da ita tana jaririya, cike da so da" "ƙauna. Tare da tuno irin soyayya da rawar ƙafar da Isa ya din ga yi lokacin da aka haifi Nana, ba ta taɓa tunanin zai yi wannan riƙon sakainar kashin da rayuwar Nana ba." "Adda Saude ce ta yi sallama, Mama ta amsa mata." "Ta ɗan yi turus ta ce ""Ya dai Nanan ba ta da lafiya ne, na ganta a kwance a jikinki haka?""" """Wallahi kuwa, shigo daga ciki"" ta zauna ta ajiye kayan da ta zo da su. Ta ce ""Tun jiya na so zuwa, tun da" "muka yi waya da ita da ta ce mini tana garin nan, babansu ne baya nan bai dawo da wuri ba ga yara gidan babu kowa. Ikon Allah ciki ne ma da ita haka?""" """Ga shi nan dai, har ya yi girma ma""" """Ikon Allah, na yi mamaki da na ji zuwa ta yi babu sanarwa, tare da mijin suka zo?""" "Maijidda ta numfasa ta ce ""A'a, matsala ma aka samu, ba a san inda mijin nata yake ba""" """Innalillahi wa Innalillahi raji'un, garin yaya ina ya tafi?""" BK 2 52 Jamila ta fashe da wani irin kuka tana tsuma, ta ce "Na shiga uku, yanzu Aljani ne ya kwanta da ni?" "Eh amma a jikin bil'adama ya shiga, ya yi amfani da ke" ta gaya wa Jamila kai tsaye, ba tare da ta ji nauyin hakan ba. "Na shiga ku, yanzu waye zai aure ni a haka? Ya zan yi. Na lalata rayuwata" Hajiya Sa'a ta riƙo hannun Jamila ta ce "Na sha gaya miki, matsoraci ba ya zama gwani Jamila. Shi fa auren nan ba dole ba ne ba. Idan kina tare da ni duk abin da ki ke so za ki samu a tare da ni. Idan ma auren ki ke so miji sai kin zaɓa, kuma tsaf za a yi miki gyara babu wanda ya isa ya gane an taɓa amfani da ke. Kuma ƙungiya ta bayar da kuɗinki na shekara. Su na gurina zan din ga baki a hankali saboda kar a gane. Ki kwantar da hankalinki, ki ƙwarara jikinki, kar wani abu ya razana ki. Kuɗi kin same su kin gama ki saki jikinki ki mori duniya. Ke ce yarinya mafi ƙanƙanta a cikin ƙungiya. Ni dai ina matuƙar ƙaunar ki ne. 'yar uwakki na so na kawo, amma abu bai yiwu ba, ina tausayawa rayuwar da ku ke yi a gidanku ne. Ki cire duk wata damuwa daga zuciyarku, ki cire tsoro da tausayi baki ɗaya za ki je inda ba ki taɓa zato ba. Jamila ta ɗaga kai ta yi wa Hajiya Sa'a wani irin kallo, da ita kaɗai ta san ma'anarsa. Ta share hawayenta ta ce "To shikenan" Hajiya Sa'a ta yi murmushi ta ce "Yauwwa Daughterna, tashi mu je na gasa ki, ki karya likitan ƙungiya zai shigo ya duba ki" Jamila ta ja jikinta da ƙyar, Hajiya Sa'a ta kama ta suka je banɗaki. **** Yau kwana na huɗu kenan, Sayyid yana cikin wannan yanayin. Babban abin da yake damun Nana rashin cin abinci da kuma salla da ba ya yi, daga bacci sai zaman shiru. Ba ya cewa uffan, sai dai ya yi ta bin ta da kallo. Ta din ga Addu'a Allah ya taimake ta, ko Ummi ba ta zo gurin ta ba, balle ta san halin da suke ciki. Ƙarfe tara na dare ta na zaune a ƙasa inda ta ajiye fulo tana kallonsa a kwance a kan katifar. Ta ɗaga hannayenta kamar za ta yi addu'a, ta karanta suratul mulk, da ayatul kursiyyu, da Suratul falaƙi da Nasi. Ta tofa a hannunta, ta ƙarasa kusa da shi a ɗan tsorace ta shafa masa a fuskar sa. Ta ja da baya tana jira ta ga abin da zai yi, amma ta ga bai yi komai ba. Ta nemi guri ta kwanta tana ta tunani a ranta. A cikin bacci ta ji ana ture ta, ta buɗe ido da sauri, ta ga yana ƙoƙarin kwanciya a gefen ta, duk da yadda gurin ya matse su. "Sayyid" ta kira sunansa. "Na'am" Wata irin ajiyar zuciya ta yi, ta riƙo hannunsa ta ce "Mene ne?" "Na kasa bacci, kin bar ni nikaɗai a kan katifa" Cikin farin ciki da kulawa, ta shafa bayansa ta ce "Gani na yi ka na numfashi da ƙyar, kamar na matse ka shi yasa na saukko nan" "Ma vie" "Na'am Shugabana" "Yunwa nake ji, kamar ban taɓa cin abinci ba" "Bari na yi sauri na dafa maka wani abin, amma zo mu je ka wanke bakin ka, ka ga yanzu tsakiyar dare ne"  Ya yinƙura ya tashi, ta kama shi, yana ta jiri, saboda yunwa ga rashin lafiya, ga kuma mutuwar jiki. Ta kai shi banɗaki, ya wanke bakinsa, ta dawo da shi ya zauna. Ta feraye doya a cikin ɗakin, ta ɗaukko gas ɗin ta, ta ajiye a bakin ƙofa ta ɗora. Ta ɗaukko mafici tana ta yi masa fifita. "Rayuwata" "Sayyid" "Kamar yau ba mu ci abincin safe ba ko?" Nana ta ce "Kwanan ka huɗi fa ka na bacci. Babu abin da zan ce wa Allah sai godiya, da ka farka" ya yi shiru bai kuma cewa komai ba. Ta sauke doyar ta dafa masa shayi, ta ajiye tana jira ya sha iska, ta ba shi da kanta. Amma bai jira ta ba, ya din ga hannu baka hannu ƙwarya. Sai dai hakan ya yi wa Nana daɗi, ganin ya ci Abinci da yawa yau. Ya gama ci, ta dafa ruwa ta kama hannunsa zuwa banɗaki, tamkar jaririn goye ta yi masa wanka. Shi kansa a lokacin ya din ga jin wata lafiyayyiyar iska na shigar sa. Ta saka ya yi alwala, ya fito ya zauna ya fara jero sallolin da ake bin sa. Ta ce "Sayyid kar ka ce sai yi a yanzu duka, sallolin da yawa.ka bari ka din ga ramawa a hankali. Ya jinjina mata kawai kawai, tun yana yi a tsaye ya kasa tsaiwar ya koma yi a zaune. Ta yi shiru tana kallonsa, ta wasu guraren suna da kamanceceniyar halayya ita da shi. Duk yanayin da yake ciki, muddin ba hankalinsa ne ya gushe gaba ɗaya ba, ba ya wasa da salla ko kaɗan. Hakan ya sanya take jin ko a ainihin rayuwarsa haka ya siffantu da kiyaye salla a kan lokaci. Har ƙarfe uku da rabi, dan kansa ya ce "Ba zan iya ƙarasawa ba, numfashina" Ta ce "To ko za ka yi a kwance?" Ya girgiza kai ya ce "Na fi so na yi a zaune, ko a tsaye" Ta ɗage masa labule, ganin yadda yake ta gumi. Ta shimfiɗa masa sallaya a bakin ƙofa, ta jera masa fululluka, ya kwanta.ta zauna a gefen sa tana yi masa fifita. Ta ɗora hannunta a goshinsa tana karanta masa abin da Allah ya sa ta tuna a zuciyarta. Hannunsa ta ji yana saka wa a rigar ta, duk da idonsa a lumshe yake. Murmushi ta yi ta ci gaba da abin da take yi. Jin yana yi mata cakulkuli, ya sanya ta kwanta a jikinsa tana dariya. Shi ma dariyar ya yi. Ya ce "Ki kwanta a kusa da ni" ya yi maganar yana nuna mata kusa da shi. Kafin ta yi magana ta ga an dalle su da fitila. Cikin hanzari ya juya kansa, ya ɓoye fuskarsa a cinyar Nana, gashin sa ya kwanta a kan filon. Nana ta saka hannu ta kare fuskarta. Muryar Barira ta ji ta ce "Yi haƙuri dan Allah, jin motsi ya yi wa na fara jin tsoro, shi ne na fito na duba, ku yi haƙuri. Ta kashe fitilar ta koma ɗaki. "Sayyid ka yi haƙuri, na san ba ka ji daɗi ba, ka yi haƙuri" Ya yi mata shiru, kuma bai ɗago daga kan cinyarta ba. Ta shafa gashin ta ce "Shugabana, ka yi magana mana, ko na ji daɗi, kwana huɗu ka na bacci, ba ka yi mini magana dan Allah kar laifin wani ya shafe ni" Sai kuma ya juyo a hankali, ta ce "Yauwwa Rayuwata" "Kin daina aman?" Ta ji ya tambaye ta babu tsammani. "Eh na daina" "Allah ya sa ki haihu wannan karon " "Amin, kuma Allah ya baka lafiya na haɗa jariraina biyu, babba da ƙarami" Ya yi murmushi ya ce "In sha Allah, kafin ki haihu, idan na ji sauƙi zan nemi aiki, na kula da ku da kaina" "To Allah ya amince. Amma Sayyid ina kuɗin nan da na gani rannan, a cikin wardrobe ɗin ka? Da na haɗa mana kaya ban gan su ba. Da sai mu ɗauka a yi maka magani, kuma mu canza gida" "Ai Habu ya karɓa, ranar da ya zo na ƙarshe, ya karɓi kuɗin Nigeria da yawa, ya bar mini wasu, ya ce na Nijar ne. Kuma da kin duba kayan nawa sosai, su na ciki" "A'a ni ba na caje maka kaya, idan Allah ya kaimu gobe, sai a lissafa mu gani idan za su isa." Ya ce "To. Kwanta ki yi bacci" ya yi maganar ya ƙara matsa mata. Ta kwanta tana murmushi. "Sayyid, idan har ba a ga su Habu ba, ina ga da ni da kai zamu je Nijar, mu nemi danginka da kanmu" Ya yi shiru bai yi magana ba, ta ɗan taɓa shi ta ji har ya yi bacci. ***** Jamila a dole ta saki ranta, jikinta ta ɗan samu ƙwari, ya daina yi mata wannan mugun ciwon da yake yi mata. Raɗaɗin ma duk babu. Sai dai tana jin ƙasan zuciyarta kamar za ta yi bindiga, saboda damuwa da tashin hankali. Sosai abin da ya faru ya tsaye mata, ta shiga banɗaki ta sha kuka. Wai ita Aljani ya kwanta da ita, ta gaba da baya aka ci zarafin ta ta wannan mummunar hanyar. Tana kwance a cikin bargo, Hajiya Sa'a ta fita shashashancinta. Wayarta ta fara ringing. Ta janyo ta ɗaga. Muryar Abba ta ji ya ce "Ƙanwata, wunin yau ban jiki ba, lafiya kuwa?" Wani irin abu mai zafi ya taso mata, ya haddasa mata karaya. Muryarta na rawa ta ce "Yaya Abba ba ni da lafiya" "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Me ya same ki?" Rasa abin da za ta ce masa ta yi, kawai ta saka kuka. Aikuwa ya rikice ya din ga rarrashin ta. Da ƙyar ya lallaɓa ta ta ce masa cikinta ne yake ciwo. "To ina Mummyn take? Ba ta kai ki Asibiti ba?" "Ta kai ni, an ba ni magunguna ma, dan Allah kar ka yi mata zancen, ta yi mini iya ƙoƙarin ta,kar ka yi mata zancen dan Allah" "No ai ba zan yi mata ba, ba ta san ma ina da lambar ki, mu na magana ba. Ki kwanta ki samu hutu kin ji Ƙanwatax "To shikenan na gode sosai" suka yi sallama ta ajiye wayar, ta kwanta hawaye na ci gaba da bin idanunta. ***** Yana zaune a cikin mota, yana ƙoƙarin kunnawa, wayarsa ta fara vibrating. Ya kalli screen ɗin wayar, ya ga baƙuwar lamba. Ya ɗauki wayar ya ɗaga ya saka a kunnensa. "Hello" muryarta ta doki dodon kunnensa. Ɗan waro ido ya yi, ya gyara zaman sa ya ce "Wa ke magana?" A raunane ta ce "Beb abin har ya kai ka manta muryata ma? Shikenan na gode" ta kashe wayar. Da sauri ya bi kiran wayar, amma ta ƙi shiga, ya yi ya yi, amma ta ƙi shiga, sai haƙura ya yi ya ja motar. Shukura mamakin abin da ya zaunar da shi a cikin mota take yi, bai tafi ba har yanzu, sai dai tana ɗaga labule, ta hango ya ja motar ya tafi. Video call ɗin Hajiya Amina, Shukura ta gani, ta ɗaga cikin fara'a tana faɗin "Hajiya Mummy, ya ibada?" "Ibada Alhamdillah, Shukura dan Allah me yasa ba kya ji ne? Ina zaman zamana, ina ibada kin jawo mini ɓacin rai da damuwa" Cikin rashin fahimta, ta ce "Ni ɗin kuma? Me na yi?" "Baban ki ya kira ni, bai taho ba tukuna yana Abuja. Yana yi mini faɗan wai ke ba ki san ƙaddara ba ne? Doctor Sharif ya kira shi cikin damuwa, yana gaya masa a gaban mutane ki na cewa yana kashe mutane, haka ake yi a kan ki a ka fara rasa ɗa? Me yasa ba za ki girma ba ne Shukura" "Mummy ki na ji na, network ɗin ki mai ƙarfi ne ko?" Ta ce "Eh, ina jin ki, kuma ina kallon ki" "Ina son idan kin je gaban ka'aba, ki yi mini addu'a, muddin a kan gaskiya ta nake, Ubangiji Allah ya shiga lamarina ya ƙarfafa mini gwiwa. Idan kuma ba a kan daidai nake ba, Ubangiji Allah ya kawar da kaina daga kai. Ya bani juriya da dangana na daina jin abin da nake ji a zuciyata. Sai dai kin dawo amma akwai matsala ne fa." "Shukura matsala wace iri ce, za ta sanya musulmi kasa yin tawakkalli?" "Ki bari dai ki dawo ɗin" "To shikenan, amma gaskiya mahaifinki ya yi fushi bai ji daɗin abin da ki ka yi ba sam" Shukura ta lallaɓa ta, ta ajiye wayar. ***** Nana tana jan ruwa a rijiya, tana zubawa a cikin bokitanta, za ta kai banɗaki. Barira ta ce "Nana ki yi haƙuri dan Allah, jiya na haska ku, ba a son raina ba ne, kuskure ne" Nana ta ce "Babu komai" Sajida ta ce "Uban me ki ka haska ki ka gani?" Barira ta kwashe da dariya ta ce "Ni babu abin da na gani, duk da bai kyautu ba abin da na gani ɗin. Amma Nana mijinki balarabe ne ko bature?" Nana ta ɗaga ta kalle ta. "Tun da ku ka zo dama bamu taɓa ganinsa ba, gashi na gani kamar na mace dogo sosai" Nana ta maze ba ta kula ta ba, ta kwashi kayan ruwanta, ta nufi ɗakin su. Sajida ta tuntsure da dariya ta ce "Maganinki da shegen shishshigi, ga shi ta gwale ki" "Shegiya ba, ta fiye jin kan ta,kamar 'yar uban wani, kuma da 'yar uban wanin ce, da ba su kama hayar ɗaki ɗaya ba" Duk abin da suke faɗa a kunnen Nana, amma ta yi kamar ba ta ji ba. Bayan ta gama wanke banɗaki ta fito, ta zo gabansa ta zauna. Ya ɗaukko sauran kuɗin nan, ya ajiye a gaban ta. Ta kalle shi ta ce "A ina ka ɓoye ne, ban gan su ba?" Ya yi murmushi ya ce "Su na cikin kayana fa, ba ki duba bane ba. A cikin leda suke. Kuma da sun fi haka yawa, Habu ne ya karɓa". Nana ta duba kuɗin, sai tarin kuɗin nijar, na Nigeria ba su dubu ɗari da goma ba. Ta ce "Sayyid, idan ka ɗan ƙara hutawa, ko zuwa gobe in Allah ya kaimu ne, za mu koma Asibiti a sake duba ka. Da za su kai da na haɗa da sauran na guri na, a fara yi maka allurar nan ko guda ɗaya ce" "A'a, kin manta yanzu mu zamu din ga sayen Abinci. Idan su ka ƙare ba mu da hanyar samun kuɗi. Kuma da akwai isassun kuɗi, gara mu bar gidan nan, da a yi mini magani" "Ni kaina Sayyid ba na son gidan nan. Mama za ta aiko mini buhun barkono, idan aka kawo, na ga ana ciniki, sai mu ci gaba da sayarwa". Ya jinjina kai ya ce "To, in anjima ki raka ni masallaci" Ta kalle shi ta ce "Da gaske masallaci za ka je?" "Eh, ina son zuwa masallaci. Idan ki ka raka ni, sai ki dawo" Ta yi murmushi ta ce "To shikenan, Alhamdillah sauƙi yana samuwa. In sha Allah zan kai ka. Bari na ajiye kuɗin nan, idan na raka ka ma, dan Allah zan je gidan Ummi" ya jinjina kai. Har za ta tashi ya riƙo ta, ya cire hijjabin da yake jikinta. Ƙonuwar da take wuyanta ya gani, ya ƙura wa gurin ido sosai sannna ya ce "Mene ne wannan?" Ta ɗan basar ta ce "Ba komai fa, ɗan ƙonewa ne kawai na yi" "Ba ɗa ba ne ba, me ya kai ruwan zafi wuyan ki? Waye ya zuba miki?" "Ba wanda ya zuba mini, sha nake yi ya zube" kawai ya rabu da ita, ba dan ya gamsu da amsar da ta ba shi ba. Ta tattare kuɗin nan, na Nijar ta zuba su a cikin jakar gidan Sarkin Baka. Na Nigeria kuma ta haɗe su, ta saka a cikin kayan ta. Ana kiran salla, ya yi alwala, Nana ta ba shi mayafin rawaninsa, ya yafa a kan sa. Nana ce ta fito tsakar gida. Barira ta gani, tana girki sanye da wata 'yar riga, milik ce amma ta yi baƙi saboda dauɗa, ko brezia babu a jikinta. Ga gashin hammata ya fito zaro-zaro idan ta ɗaga hannunta. Zanin jikinta ma baƙi ƙirin, tamkar an yi matsar man ƙuli da shi, sai annakiya take yi. Nana ta ce "Barira, dan Allah ko za ki gyara, zamu wuce" Barira ta ce "Bismillah ki wuce mana" "A'a ai ni da mijina ne" "Ku wuce ba wani abu ai" Nana ta yi shiru tana jinjina tumasanci da rashin sanin ciwon kai, na mutanen gidan. Babu yadda ta iya, haka ta kammo hannun Sayyid, ya fito ta rufe ɗakin. Ya ja mayafin ya rufe fuskarsa da rawanin, saboda yanzu ba ya iya naɗa shi, saboda numfashinsa. Tun da ya fito Barira take kallon sa, ta na son ganin ainihin fuskarsa, amma ya sunkuyar da kai, kuma ya rufe fuskar sa suka fice. Su na tafe Yana hutawa, saboda haki, a hankali har suka isa masallacin. Ta ce "Za ka jira ni na je gidan Ummin na dawo?" "Zan koma gida da kaina" "Har ka gane hanya?" Ya ce "Eh ki gaishe ta" Nana ta ce "Ai ba daɗewa zan yi ba ma" Ya shiga Masallaci Nana kuma ta tafi gidan Ummi. Su Nana na fita, Barira ta buga banɗakin tsakar gida ta ce "Ke Sajida kashin danƙo ki ke yi ne? Ki na manne a banɗaki yau mijin 'yar rainin hankalin nan dai ya fito. Ashe dole ta ɓoye shi, fari ne tas wannan gashin da na gani, da gaske nasa ne." Sajida ta fito da buta a hannunta ta ce "Kai haba, ban gama ba ne shi yasa ban fito ba, zogala na ci da ƙuli ya ruɗa mini ciki" "Aikuwa kin rasa, ba ki gan shi ba. Sai na ga kamar mata na rako, da na tuna Gali, ga baƙi ga ƙeya" Sajida ta ce "Ba gara Gali ba da nawa mijin? Ke Gali na da tsawo, ni nawa ga gajarta ga muni" "Gaskiya Sajida mijinki akwai muni kam, dogon baki kamar dangin burrai" Sajida ta tsuke fuska ta ce "Ba na son iskanci kuma. Gara shi dai a kan Galin, da ki ka ce ba ya iya tsinana miki komai a shimfiɗa. Kalarsa kalar... Kafin ta ƙarasa Barira ta ƙunduma mata Ashariya, take faɗa ya kaure, suka ci wa junan su mutunci tsaf, suka tona wa kan su Asiri. Suka gaji dan kan su, suka haƙura. **** Nana ta bawa Ummi labarin barkono da za a kawo mata. Ta ce "Amma Ummi sai dai a kawo miki nan, can ɗakinmu babu gurin da zan ajiye a can" "Bakomai a kawo, kuma nan da nan za ki ga an saye shi ba, ai unguwar nan fuskar jama'a ce, idan ka kasa kaya za ka samu alkhairi" Su na tsaka da hira, babu zato babu tsammani sai ga Saleh ya afko cikin gidan. Wata irin mummunar faɗuwar gaba ta ziyarci Nana, bayan da ta gan shi babu tsammani. Duk ya ƙara lalacewa. Turus ya yi yana kallon Nana, cikin mamaki ya ce "Nana, dama kina nan?" "Eh" ta amsa a taƙaice. "Nana da yanzu nine mijinki, amma ki ka guje ni" Ummi ta haɗe rai ta ce "Saleh Nana fa matar aure ce, dan haka babu ruwan ka da ita dan Allah" Saleh ya ce "Dan matar aure ce, kuma shikenan ba za mu yi zumunci ba? Nana kina lafiya? Na ji an ce wani baroroji aka aura miki ko?" Nana ta haɗe rai ta tashi ta ce "Ummi zan tafi, zuba mini Abincin idan kin gama" Ummi ta ce "Bari na wanke babban flask, kuma idan Islam ta zo ki ba ta kwano na, dan ba zan bar miki ba" Nana ta ce "Gaskiya sai kin bar mini, ki zo ɗakina, ki ɗauki duk abin da ya yi miki. Kuma a ƙaramin kwano za ki zuba mini. Sayyid na yi masa girki, ni zan ci wannan" Ummi ta ce "Hajiya Nana, an sake haɗiyar wake kenan, to Allah ya inganta" "Dawa na haɗiya ba wake ba" Tsulum Saleh ya sake cewa "A nan unguwar gidanki yake kenan? Na ji Ummi ta ce Islam na zuwa gidan naki. Da aka ce mijin naki gadi yake yi" A ƙufule Ummi ta ce "Dan zatin Allah Saleh ka fita, ba da kai muke magana ba, babu ruwan ka da mu. Wai har ka manta har ubanmu ka saka a rufe saboda kuɗinka, dan rashin kunya kuma, ka zo zaka addabe mu?" Sum-sum Saleh ya fice daga gidan. Ummi ta zubawa Nana tuwon shinkafa da miyar yauƙi, har da man shanu, Nana sai haɗiye yawu take yi cikin farin ciki, kamar ta durƙusa ta ci a gurin. Ummi ta shiga ɗaki, ta ɗaukko wa Nana dambun kifi ta ce "Ungo, jiya na yi shi aka kai mini shago, na ɗebar miki" Nana ta karɓa tana murmushi ganin sa fal a roba, ta ce "Allah ya yi miki abin da ki ke yi mini na alkhairi na gode sosai" suka yi sallama Nana ta fita. Tana cikin bin wani lungu, ta ji Muryar Saleh na kiran ta. Ta ƙara saurin da take yi, amma ya cimma ta. "Nana dan Allah ki saurare ni". Rikicewa ta yi, gani take a kowane lokaci za ta iya ganin Sayyid, ba ta san da wani yaren za ta yi masa bayani ba ya fahimta. "Nana ki tsaya ki ji mana" "Wallahi zan yi maka ihun kwarto, wace irin jaraba ce wannan ina ruwan ka da ni ne?" Ganin tana ɗaga murya, kuma Akuyarsa ta yi kuka a unguwar, ya sanya sum-sum ya koma da baya. Tana zumbuɗa sauri, ta je gida, ta san yana can yana jiran ta. Kawai ta ci karo da shi a wani lungu, yana zaune a kan wata sokawe, ya jingina da jikin bango, shikaɗai ƙwal a layin. Sai da ta razana, ta waiwaya bayan ta, cike da tsoron ko Saleh ya biyo ta. "Sayyid me ka ke yi a nan kuma, ba ka shiga shiga gida ba?" "Ba zan iya shiga nikaɗai ba" Ta miƙa masa hannu ta ce "Taso mu tafi" ya miƙa mata hannunsa. Sai dai tun da ya saka hannunsa a nata, sai da ya kalli fuskar ta. Da suka je gidan, danƙam da mata, ana ta hayaniya. Ya rufe fuskarsa Nana ta yi sallama. Gaba ɗaya suka yi tsit, suka zubo wa su Nana ido, musamman ganin hannunta riƙe da na Sayyid. Kawai ta ja hannunsa, suka nufi ɗakin su. "Nana kun dawo" Sajida ta yi maganar, tana kokowa da zaninta tana fitowa daga ɗakinta, saboda kar su wuce ba ta gan su ba. "Eh sannun ku" daga haka ya tura ƙofar ya fara shigewa. Suna shiga ɗakin matan suka saka shewa, ɗaya ta ce "In dai Namiji ne, yarinya za ta gama wannan iyayin ne" Nana su na shiga ɗaki Sayyid ya tsare ta da ido ya ce "Nana ba ki da gaskiya" Gabanta ya faɗi cikin tsoro ta ce "Me na yi?" "Gumi ki ke yi a iya goshin ki, da karan hancin ki. Kuma tafin hannunki ya ya sanyi, zuciyar ki na bugawa da ƙarfi kuma da sauri. Kin yi wani abu da ki ke ɓoye mini ko?" Haɗe rai ta yi ta fara ƙoƙarin ƙwace hannunta daga nasa. Sai kuma ya sassauta muryarsa ya ce "Ki daina fushi, ba zan iya barin, duk wani abu na ƙi ya tunkaro rayuwata da ke ba, ki daina fushi" "To sai ka din ga zargina da rashin gaskiya" ta faɗa a hasale. Ya girgiza kai ya ce "Ba zargin ki nake yi ba. Na tabattar da wani abu ya faru ne, da ba za ki so na sani ba, idan na sani zamu samu saɓani. Kin manta mu ba kamar sauran mutane ba ne. Kuma ina iya jin abin da yake ranki, kin manta ne?" Ya yi maganar yana murmushi da shafo fuskarta. Dole ta saki murmushi. Nana dai ta din ga yi wa Allah godiya, da ba ganta da Saleh ba. Nana tana yi wa Allah godiya, ganin yadda jikinsa ya yi kyau. Duk da yana haki bai daina ba, amma yanzu yana cin abinci. Sayyid na matuƙar son zuwa masallaci salla, amma dole yake haƙura. Saboda da gayya matan gidan suke wata shigar, duk da ba tsayawa kallon su yake yi ba. Ga shi ba ya son kallo, amma yana fitowa sai su yi shiru su zura masa ido. Ita kanta Nana lamarin gidan ya ishe ta, ba ta ƙaunar zaman gidan nan ko kaɗan. Maman Nana ta aiko mata da barkonon nan, har da awon kayan Abinci, tamkar ta san a halin da take ciki. Ummi da kanta, ta je ta ɗauki barkonon, domin kuwa Nana daina zuwa gidan Ummi ta gaba ɗaya saboda Saleh. Abu kamar wasa har zuwa wannan lokacin, Sayyid ya kasa gane kansa, abin ya fara damunsa sosai da sosai. Ga shi ya kasa cewa Nana komai a kan hakan. Ita ma kuma ba ta ce masa ba, sabgoginta kawai take yi. Tun Yamma Nana, ke ƙoƙarin shirya duk abin da za su buƙata, saboda washegari za su tafi Asibiti, kuma sammako take so su yi, saboda su ga likita da wuri. Sai dai duk dauriya kawai take yi, wani irin zazzafan zazzaɓi ne a jikinta, ta kasa cin abinci. Babu abin da take son ci, sama ds kazar da Habu ya kawo farkon auren su. Ga shi ba ta son yin duk wani abu da zai ɗaga wa Sayyid Hankali. Ta fuskanci ko saɓani suka samu, ƙaramar magana sai ta sanya ya fara haki, ya fara nema ya faɗi. Tana ƙofar ɗakinta, tana soya miya, su Barira su na hira, tana yi wa wata maƙwabciyar su kitso. Suke zancen wata mata a bayan layin, wai sai mijinta ya neme ta ya rasa, sai a yi kwanaki ba a ganta ba, sai bayan wani lokaci a tsinto ta a wani gurin, ko a ganta a ɗaki. Barira ta kada baki ta ce "Amma ta mayar da mijin nan tasono, ƙarya take yi gantalinta kawai take tafiya. Meye matan auren ba sa yi yanzu?" Sajida ta ce "A'a Barira, ki daina cewa ƙarya ne" "Ke wallahi, ko rantsuwa na yi ba zan yi kaffara ba, a gidan uban wa Aljani zai ɗauke mutum ya kai shi wani gurin? Ke ni fa da ake cewa ana ganin aljanu, ko su tsorata mutum ban taɓa yadda ba, iskanci ne kawai da ƙaryar banza ce, ba wani aljan duk 'yan iska ne kawai. Nana ta ji wani abu mai zafi ya soki zuciyarta, duk da ba da ita suke ba, kawai ta ƙura wa Barira ido, ko ƙiftawa ba ta yi. Tun Barira ba ta ankara ba, har ta lura, take ta ji tamkar an kwarara mata ruwan sanyi a jikinta, sai kuma ta ɗan tsorata ta ce "Nana lafiya kuwa?" Ayshercool 08081012143 53 "Barira, kin taɓa haihuwa?" Nana ta tambaye ta. "A'a me ki ka gani?" "Amma dai ki na ganin mata su na ɗaukar ciki su haihu. Kuma kin yarda da abin da suke faɗa cewar haihuwa akwai wahala, duk da ba a bakin mutum ɗaya ko biyu ki ka ji ba. Kin yarda wannan ciwon na haihuwa akwai shi, duk da ba ki taɓa yi ba?" Barira ta ce "Eh mana, ai wannan kowa ya san haihuwa akwai wahala" "Kin yadda akwai ciwon haihuwa, amma ba ki yadda akwai na aljanu ba, saboda Allah bai jarabce ki ba, har ki ke ƙarar da cewa matar mutane yawon iskanci take tafiya? Duk wanda zai shaide ta, barin mijinta ne, tun da yake zaune da matarsa a haka, ke mene ne naki da za ki ce mutuniyar banza ce? Idan aka rutsa ki shaidar ina take tafiya iskancin za ki faɗa? Idan aka faɗi abu, ko baki yarda ba gara ki yi shiru ki ce Allah ya kyauta, musamman larura. Idan ba haka ba maganganu irin naki za su iya zama cutarwa a gare su". Jin Nana yau ta saka musu baki a magana ya sanya suka din ga goyon bayan abin da Nana ta faɗa gaskiya ne. Da fari jikin Barira ya yi sanyi, daga baya ganin kowa ya hayayyaƙo mata, ya sanya ta hau bala'i, har abin ya koma faɗa. Ita kuwa Nana tun da ta gama zazzagar abin da yake ranta, ta kammala girkinta, ta kwashe kayanta, ta koma ɗaki ta bar su da mayar da zance. Dama ga zafin laulayi, ga takaicin mutanen da ake tarawa a gidan babu dalili, ga kuma zafin ƙazafin da Barira ta yi wa matar, da ita kanta Nana ba ta sani ba, amma maganar da ta yi ta ji sanyi a ranta. Yana daga kwance a kan katifa ya ce "Rayuwata" Ta ɗaga kai ta kalle shi ya ce "viens(zo) yana yi mata alama da hannunsa. Ta ƙarasa gabansa ta zauna. "Dan Allah ki daina shiga maganar mutanen nan, ki daina kula su. Ni na daɗe ban ji mutanen da ba na ƙauna kamar su ba. Ba na son su zo su yi miki abin da ba zamu ji daɗi ba" Ta jinjina kai ta ce "Haka ne, ka yi haƙuri nima ban so na shiga ba, haka kurum na ji maganar ta su kamar da ni suke yi. Sayyid ni da kai mun san azaba da raɗaɗin larurar nan. Ire-iren waɗannan maganannun da yadda wasu suke ganin kamar ciwon nan ƙarya ne, ya sanya da yawa masu larurar da dama a cikin wata damuwar ciwon ya yi musu illa, tun da ba a yarda da ciwon ba balle a ɗaukar musu mataki." "To ai ba su ce da ke suke ba" Murya a sanyaye ta ce "Sayyid, duk lokacin da aka yi maganar irin wannan larurar, ina jin tamkar da ni ake. Nima wasu lokutan na kan shiga ɗimuwa, na bar gida a gano ni a wani gurin, duk da ni ban taɓa kwanaki ba a ganni ba. Ta kai ta kawo har a zahiri ina ganin abubuwan nan. Sayyid kai ma fa wasu lokutan ina yi a gabanka ka na gani, to yaya za a ce mutum yana sane ya din ga mayar da kansa mahaukaci? Wanda kuwa duk aka samu da yin ƙaryar irin wannan ciwon, yana buƙatar kai shi gurin likitocin ƙwaƙwalwa, Sayyid ciwon nan babu daɗi, akwai wahala" ta yi maganar hawaye na zirarowa daga cikin idanunta. Ya tashi zaune ya kai hannunsa jikinta zai rungumota, zafin zazzaɓin jikinta ya ziyarce shi. Ya kalle ta a tsorace ya ce "Ba ki da lafiya?" Ya furta maganar haɗe da haki, saboda yadda ya ji zafin a bazata. Da sauri ta ɗora hannunta a ƙirjinsa ta ce "Sayyid dan Allah ka din ga ɗaukar al'amurana da sauƙi. Ga shi har girki na yi, ina komai nawa lafiya. Ka san lallaɓawa muke yi, ba ka da cikakkiyar lafiya. Ka daina saurin tsorata ko fusata. Ya saka hannun sa yana ƙara danne hannunta a saitin zuciyarsa. Yana iya ƙoƙarin sa a kan ya din ga saita al'amuransa. Amma ya rasa dalili duk abin da ya shafi Nana, kai tsaye yake jin sa a tsakiyar zuciyarsa. Ba ya iya yi masa shinge ko ya dakatar da shi. Yana so Nana ta haihu da shi, amma wahalar da ya ga tana sha, sai da ya ji dama cikin ya zube ko zata huta. ***** Tun da Jamila ta koma gida, jikinta a sanyaye yake, gani take yi, duk wanda ya ganta ya san abin da ya faru da ita. Mama kuwa baki ya ƙi rufuwa, saboda Jamila ta zo da abin Duniya. Kuma kamar yadda ta gaya mata, sarin kaya ta raka Hajiya, babu wani bincike ta yarda da hakan ta amince. Ta zo ba ta iya bacci sam, da ta kwanta bacc6, sai ta ga tamkar za ta buɗe ido, ta sake ganinta, a wannan gurin da suka je da Hajiya Sa'a. "Jamila" Suwaiba ta kira sunanta, ta waiwaya ta kalle ta. "Wai ya na ga ki na abu kamar mara gaskiya ne?" Gaban Jamila ya faɗi ta ce "Me na yi na rashin gaskiyar, me ki ka gani?" "To ai gani na yi kin kasa sukuni, ki na ta wani mutsu-mutsu gaki nan dai" "Dan Allah Suwaiba ki ji da abin da yake damun ki, ni babu abin da ya same ni, lafiya ƙalau nake " Suwaiba ta ce "To ai shikenan" **** Nana duk sammakon da suka yi, su ne na goma sha ɗaya, a gurin ganin likita. Wajen sha ɗaya na safe aka zo kan su, Nana suka shiga, sai dai wannan karon wani likitan daban suka samu. Suka gaisa Nana ta yi wa likitan bayanin komai. Tare da ba shi takardun gwaje-gwajen da aka yi masa, da kuma katin da aka rubuta masa magunguna. Ya karɓa ya duba a tsanake, ya duba Bp ɗin Sayyid, ya duba ƙirjinsa da stethoscope. Nana ta ce "Doctor yaya jikin nasa? Me ka gani?" Bai kalli Nana ba ya ce "Me yasa ba ku dawo follow up ba" Ta ce "Ai ba a bamu lokacin dawowa ba. Dama ni ce naga yakamata mu dawo ɗin. mu na ta ƙoƙarin kuɗin allurar su haɗu ne, ko ba su haɗu ba, zamu yi ƙoƙari ko a anan Asibitin gwamnatin ne, sai mu yi booking a fara yi masa" Likitan ya ce "Ki na ji na 'ya ta?" Ta ce "Eh" "Ai mijinki ne ko?" Sayyid ya jinjina kai. "To a duniya babu wani abu da Allah ba zai iya ba, babu shi. Batun allura ki bar wannan a hannun Allah. Kuma dan babu kuɗin allaura ba za a daina ganinsa ba. Zamu ci gaba da gwada shi, mu na ba shi magungunan da suka dace. Idan Allah ya yassare kwa zo a yi daga baya. Kuma jikinsa Alhamdillah da sauƙi sosai da sosai. Jinin dai haryanzu bai sauka yadda ake so ba. Amma zai sauka da yardar Allah. Kawai ki din ga kiyaye damuwarsa da ɓacin ransa. Idan kuma akwai wani abu da yake damunsa, ki zauna da shi ku tattauna ki ga ta ina za ku shawo kan matsalar?. Amma babu wani abu in sha Allah" Duk da ba lafiya likitan ya ba su ba, amma kalamansa akwai dattaku da ƙwarewa a kan aiki a cikin sa. Dan haka sosai Nana ta samu relief. Ya rubuta musu lambarsa ya ce "Duk lokacin da za ku zo, ku kira ni, na baku ranar da nake aiki, ya zo ya din ga ganina." Nana ta din ga yi masa godiya da addu'a shi da iyayensa. Sayyid ya ja wata takarda, ya yi rubutu ya miƙa wa likitan. Likitan ya karɓa ya duba. Ya yi murmushi ya ce "Madam, ashe kema babu lafiya ya ce na duba masa ke" Nana ta yi murmushi ta ce "Rashin lafiyata, ai ba komai ba ce a kan tasa, ni na fi damuwa da shi ɗin dai" "A'a tun da ya nemi alfarma, ai dole a yi masa" Ya duba Nana, ya yi wa Sayyid bayanin laulayi ne kawai yake damunta, ya rubuta mata abin da zai rubuta mata na magani. Ya kuma ba ta gwaje-gwaje. Sayyid ya ƙi tafiya, sai da suka yi gwaje-gwajen. Suka koma, ya tabattar musu da babu wata matsala, satin cikinta uku da kwanaki, ya rubuta mata magungunan da za ta yi amfani da su. Suna tafe a adaidaita sahu, Sayyid ya kasa riƙe murmushinsa, ya kai bakin sa kunnen Nana ya ce "Saura kwana nawa ki haihu?" Ta kwashe da dariya, ta ce "Ina na sani, ko cika wata ɗaya bai yi ba ma, mu dai ci gaba da addu'a Allah ya bar mana, ya bamu ɗa na gari" Ya amsa da "Amin." A bakin titi, Nana ta yi sayayyar salak, saboda shi take sha'awar ci. Suka shiga layin gidan na su. Su na zuwa gidan, Nana da sauri ta shiga banɗaki, saboda fitsarin da ya cika mata mara. Sayyid tsayawa ya yi, yai shiru yana ƙare wa ɗakin kallo. Nana ta fito bai ce mata komai ba, ta ɗauki cylinder gas, ta ce "Sayyid gas ya kusa ƙarewa, idan zaka iya fita in anjima sai mu je titi tare mu ɗuro" Ya ce "To" "Bari na sake ɗumama miyar" Ta fito tsakar gidan kenan, Sajida ta ce "Nana, Allah ya taimake ki, da tuni da ke za a tafi bayar da shaida" Cikin rashin fahimta Nana ta ce "Shaidar me?" "Jiya hirar da ku ka yi, har ki ke yi wa Barira faɗa, a kan matar nan. Daga jiyan nan zuwa yau magana har ta kai kunnen matar. Ta din ga kuka mijin ya ce ba zai yarda ba da 'yan uwanta. Da yyayyenta ne za su zo su zane Barira. Mijin matar ya hana aka kai ta police station. Tun bayan fitar ku tana can, duk sai da muka je bayar da shaida. Wataƙila dai kafin magariba a sako ta, ta dawo gida." Nana ta numfasa ta ce "Gara da Allah ya sa ba na nan, dan babu inda zan je, shi yasa a rayuwa yake da muhimmanci mutum ya iya bakinsa. Wannan tara matan da ku ke yi, ku na surutai marasa amfani duk ba hanya ce mai ɓullewa ba" Sajida ta ce "Wallahi haka ne, shi yasa ki ke burge mu ma" "Allah ya kyauta" Har Nana ta yi haɗin salak ɗin ta, ta fara ci, ya lura ba ta fahimci abin da yake faruwa ba, shi ma kuma bai gaya mata ba, ya ci abincin. Ta gama ci ta kalle shi ta ce "Sayyid, ka yi mini addu'a, Allah ya sanya kar na yi aman salad ɗin nan, na rufe sauran anjima zan sake ci" "Kin cika yaji, sai kin yi ciwon ciki ko?" Ta ɗan waro ido ta ce "Dama ka gani?" "Eh ina kallon ki" Ta ɗan yi murmushi ta ce "Idan babu yajin, ba zai yi daɗi sosai ba. Amma yanzu ya ka ke ji a jikin ka?" "Ba sauƙi" "Subhanallah, ba sauƙi kuma?" Ya ce "Eh, kin je ki na hira da likita a gabana" "Amma ko ba komai, ya kwantar mini da hankali, bai ce mini zaka mutu ba, kalamansa sun bani ƙwarin gwiwar da yakamata na samu" ta yi maganar ƙwalla na cika mata idanu. Ya girgiza mata kai ya ce "Kar ki bari su zubo". "To ba kai ne ba, komai na yi sai ka ji haushi na?" Murmushin sa mai matuƙar ƙayatarwa ya yi, ya ce "Ba haushinki nake ji ba, tsaro nake ba ki, saboda tawa ce nikaɗai. sourire (smile) ki yi murmushi mana" ta noƙe kafaɗarta tana tura baki,ta juya masa baya. Ya matsa bayan nata, ya sumbaci saman bayan ta, ya zagayo da hannunsa ta cikinta, ya kwantar da kansa a kan kafaɗarta. Gaba ɗaya jikinta ya yi sanyi. Damuwa ce ya ziyarce zuciyarsa, jin yadda Nana ta saki jiki sosai da rungumar da ya yi mata, ko ba a gaya masa ba ya san abin da yake ranta, tuna cewar babu abin da zai iya tsinana mata, ya sanya a hankali ya raba jikinsa da nata, wani irin tausayinta na ratsa ilahirin jikinsa. Ta maze cikin yaƙe ta ce "Sayyid, ya na ji ka yi shiru ne?" Ya girgiza kai ya ce "Babu komai" "A'a akwai wani abu. Dama likita ya ce mu zauna na tambaye ka, ko akwai wani abu da yake damun ka, haryanzu fa jininka bai sauka ba Sayyid" Ya ɗan sake yin guntun murmushi ya ce "Damuwa ai akwai ta, ba na son ɗaga miki hankali ne kawai. Haryanzu ina tunanin inda su Habu suka tafi, suka bar ki da ɗawainiya, Kodayake ko suna nan ma, kula da ni ba dolen su ba ne. Sai wahala ki ke sha, wallahi idan ina tuna hakan, sai na ji tamkar numfashina zai ɗauke a cikin damuwa nake sosai da sosai. Ba na son saka ki a damuwa ne kawai". Nana ta tattara hankalinta ta matsa kusa da shi, ta riƙo hannunsa, ta kalli idanunsa da suka yi jawur. "Idan su Habu ba hakkinsu ba ne kula da ki. Ni yanzu ya zama haƙƙina, na san ba a banza Allah ya haɗa mu ba. Mu ci gaba da addu'a Allah ya kawo mana komai da sauƙi. Amma ina fatan dan Allah ka daina damuwa, idan ciwon nan ya matsanta maka a jikina nake ji, ka daina ba na so" ta ƙarasa maganar cikin shagwaɓa. Kafaɗarta ya ciza cikin wasa, yana rungume ta. Tamkar ba a cikin damuwa suke ba, suka ci gaba da raha, duk da yadda hayaniyar mata ta cika gidan, tamkar a na taro, saboda dawowar Barira, an cika gidan ana mayar da yadda aka yi. Ana fara kiran sallar magariba, ta kai masa ruwan ɗumi banɗaki ya yi alwala. "Za ka je masallaci ne?" "A'a a nan zan yi" "To yi sallar. Nima sai na yi muje mu ɗuro gas, ko rabi ne sai kuma na sayo gawayi, Ummi ta bani kurfoti, na din ga haɗawa da shi" Ya jinjina mata kai ya tayar da salla. Yana kallon ta ta idar, ta buɗe jakarta ta ɗebo sauran kuɗin da suka dawo da su, ta nufi wardrobe ta haɗa su da waɗancan kuɗin. Kawai ta ga kayan wardrobe ɗin a hargitse. Mamaki ya kama ta, ta san Sayyid ba ya taɓa mata wardrobe, kuma ita ba a haka ta bar wardrobe ɗin ba. Ta janyo jakar gidan Sarkin baka, ta duba ta ga kuɗin nijar a ciki. Ta laluba ta ɗauki ledar, da kuɗin Nigeria ke ciki ta rasa. Ta watso kayan wardrobe ɗin gaba ɗaya, tana ƙara haskawa da fitilar wayarta. Yana tsaye yana kallon ta. Muryarta na rawa ta ce "Sayyid" Ya kalle ta. "Kuɗinmu, kuɗin da ka bani na saka a cikin wardrobe na...naa..ajiye a nan ban gani ba, ko ka ɗauka?" Ya yi shiru yana kallon ta, a zuciye ta nufi hanyar fita daga ɗakin, ya riƙe ta. Jikinta yana tsuma take ƙoƙarin fizgewa amma ya riƙe ta yana girgiza kai ya ce "Kar ki yi magana, ki yi shiru ko waye mu bar wa Allah. Tun da na shigo, na ga alamar an buɗe ɗakin. Kuma laifinmu ne, da ba mu saka mukulli ba, muka rufe ɗakin kawai." "Sayyid ba a yi mana adalci ba. Kuɗin Abincinmu da maganinka, sun kwashe gaba ɗaya wace irin masifa ce wannan? Daga wannan sai wannan ya ake so na yi ne?" Ya riƙe ta gam yana shafa bayan ta, a hankali ya ce "Ki yi haƙuri, ki daina ɗaga murya, akwai Allah" Kuka take yi iya ƙarfinta, tana sheshsheƙa, ya rungume ta gam a jikinsa, shi kansa ya ji zafi da raɗaɗin satar da aka yi musu. Ba iya kuɗi ba, har da wasu daga kayan amfaninsu na ɗakin an ɗauka, ya san kuma hakan sabon ƙalubale ne, saboda ba su da wata hanyar samun kuɗi a yanzu. Ji ya yi jikin Nana ya saki, kuma jikin yana ɗaukar sanyi. Karkarwa ta fara yi, tamkar ana jona mata shocking. Cikin matsananciyar damuwa, ya zauna da ita a jikinsa, ya ɗauki wayarta da ta saki a gurin, yana haska fuskarta. Ya ga hawaye na fita ta gefen idonta. Hannayenta da ƙafafuwanta su na lanƙwashewa, goshinta kuma yana tsatstsafo da gumi. Jin ta ta yi, jingine da wani abu da ba ta san ko mene ne ba. Ta shafa abin ta ji ƙurzunu-ƙuruzunu, tamkar dutse. Gurin baƙi ƙirin duhu ya gauraye gurin, ko tafin hannunta ba ta iya gani. A hankali haske ya fara shigowa gurin, har gurin ya yi haske ba ki ɗaya. Ta ɗaga kanta ta ga ba ta iya gano ƙarshen ɗakin. Jin tari ta yi a bayan ta, ta waiwaya da sauri, ta ga Ƙaisar a zaune lulluɓe da wani abu mai haske sosai. "Ƙaisar. Ba ka da lafiya?" Ta yi maganar tana nufar inda yake. Ya yi shiru bai yi magana ba. Ta sake cewa "Dama kuma ku na rashin lafiya, kamar ka canza gaba ɗaya" ya yi murmushi ya ce "Mu na rashin lafiya mana, guba na ci" Ta waro ido ta ce "Guba kuma? Me yasa?" "Tsohon nan na jikin mijinki, ya bani." "Kuma ka sha? Wai meye alaƙar ka da shi? Kuma dan Allah me yasa yake bibiyar mijina?" "Ba wannan ba, me yasa ki ka kira ni?" Cikin mamaki ta kalle shi ta ce "Kamar yaya? Ni ban kira ka ba ai" "Fushi da ɓacin rai, duk wanda ki ka yi tamkar kin kira ni ne. Kuma ni yanzu ba ni da wani tasiri sosai, saboda jinya nake yi. Babu wanda ya san ina nan. Giyaz ya saka ni a gaba, ya mamaye Library ɗi na, yanzu rashin ganina zai sanya ya ci gaba da cutar da ku. Ba zan iya wani abu ba sosai yanzu, sai dai zan iya tasiri a kan bil'adama. Duk ba wannan ba, duba can." Ta ɗaga kai ta kalli inda ya nuna mata, Library ɗin Ƙaisar ta gani. Ta ga gangar jikin Sayyid a kwance. Tsohon nan ya ɗaɗɗaure shi da wata irin igiyar ƙarfe. Ƙasan gadon da yake kai kuma, wata irin wuta ce take ci a ƙasa. Nana ta zabura a rikice, ta ce "Wannan ai Sayyid ne" "Ƙwarai shi ne, ba wani ba. Kuma Giyaz shi ya sanya masa matsalar da ku ke ciki na auratayya. Sai dai abu ɗaya zan iya gaya miki. Matsalar zuciya da hawan jini da yake fama, wannan ciwo ne yake damun sa. Amma Giyaz na assasa wani abin. Kuma... Amma dai shikenan" Nana ta buɗe baki za ta yi magana, ya ce "Kar ki tambaye ni komai, kin san sharaɗin. Kalli" ya yi maganar yana sake nuna mata gurin. Alhaji Fatuhu ta gani, ta yi ƙuri da ido ta ce "Kamar na san wannan" "Ba kama ba ce ba kin san shi, ciwo ne da zafin sihirin da aka yi masa ya mayar da shi haka. Sai kuma albishir da nake yi miki, da ƙanwar ki ta zama cikakkiyar 'yar ƙungiyar asiri. Ɗayar kuma wannan bararojin da ta taɓa baki magani, ta aura mata ɗanta, wanda yake baƙin aljani ne. Kuma ta tarkato kan iyalanta duk su na jikinta. Kuma kowanne akwai abin da yake mora a jikinta. Ke in taƙaice miki ma, a kowane lokaci za ta iya rasa hankalinta ko ma rayuwarta gaba ɗaya. Shikenan bissalam" "Ƙaisar" sai kuma ta yi ido huɗu da Sayyid. "Kin tashi?" Ta yinƙura ta tashi zaune, tana kallon ɗakin. Sayyid ya ce "Ƙaisar ɗin ba shi da lafiya ne?" Ya yi maganar yana tsare ta ido. "Wane Ƙaisar ɗin?" "Tambayata ki ke yi?" Shiru ta yi, ita ba ta iya tuna koma ma a cikin abin da ya faru ba. Idonta ne ya sauka a kan kayan da suke gaban wardrobe a ƙasa, sai kuma abin da ya faru ya faɗo mata. Afujajan ta tashi ta sake nufar wardrobe ɗin, tana zazzage kayan tana kuka. "Kuɗin nan fa babu su, an kwashe ki daina wannan dube-duben" ya zauna ta yi shiru ta sanya kayan a gaba tana kallo. Ya yi mata shiru ya ƙi kula ta, ya kwanta a kan katifa, yadda take a hasalen nan, idan ya matsa faɗa za su yi. Cikin ƙanƙanin lokaci nannauyan bacci ya yi awon gaba da shi. Barira na kwance a ɗakinta, ta yi ɗaiɗai tana bacci, ta ji kamar ana karta mata farce a ƙafafuwanta. Har ta maze ta ci gaba da bacci, amma ta ji an cigaba. A fusace ta ce "Gali meye haka, za ka din ga karta mini faratanka, ina cikin bacci ne?" Shiru bai amsa ba. Ta laluba ta ji yo ƙeyarsa a can ƙarshen gado, yana bacci. Ta koma ta kwanta, amma ta ji an cigaba, ta tashi zaune tana zabga ashariya. Ta kunna fitila, ta ga babu kowa. Ta yi tsaki ta sauka daga kan gadon, ta fito tsakar gida domin ta yi fitsari. Bayan ta fito daga banɗakin, kanta ko ɗan kwali babu, kawai ta yi karo da Nana a tsakiyar tsakar gidan tana yi mata wani irin mugun kallo. Ta haska Nana ta ce "Nana lafiya kuwa?" Sai dai Nana ba ta yi magana ba, ta sake haska ta, za ta yi magana. Ta ga ta rikiɗe ta zama wata irin ƙatuwar mage, baƙa ƙirin, girman ta ya yi na tunkiya ƙosashiya da ita, ta yo kanta tana buɗe haƙora. Da gudu Barira ta shiga ɗakinta, tana ihu tana kiran sunan Gali. "Ke mahaukaciya, mene ne haka za ki din ga ihu kina kiran sunana a tsohon daren nan?" Ba ta ce masa uffan ba, ta duƙunƙune, tana mayar da numfashi. Ta tsorata sosai da sosai, da ƙyar ta samu ta yi bacci. Sai dai a cikin baccin ma, mafarkin magen nan kawai ta din ga yi tana bin ta, tana karta mata farata tana cizon ta. Sayyid kuwa yana jiyo kururuwar Barira, hakan bai dame shi ba, sai ganin Nana da ya yi a zaune, ta haɗa kai da gwiwa. Ya yinƙura ya tashi zaune, bai ce mata komai ba, ya kwantar da ita a kan katifar, ya rufe su da bargo ya rungume ta yana shafa bayanta. Yana jin ta tana kuka, har ta yi ta gaji bacci ya ɗauke ta. Dauriya kawai yake yi, amma ji yake tamkar ya taya ta kukan. Washegari, Barira ta tashi da matsanancin zazzaɓi da ciwon kai, ta din ga yi wa mijin kuka, tana cewa ya mayar da ita gidansu, mayu sun kama ta a nan gidan, ba za ta yadda a kashe ta a banza ba. Babu yadda ya iya ya tattara ta ya kai ta gidansu. Kwanki biyu da sace kuɗin nan, Nana ta rasa abin da yake yi mata daɗi. Dubu talatin ce ta ragu a hannunta, shi ma cikin irin kuɗin da ta zuba a jakarta ne suka fita da su. Kuɗin Nijar ɗin kuma ba ta san ma ina za ta a canza su ba. Bayan haka tayi tunanin idan Habu ya dawo fa, me za ta ce masa? Ta din ga tunanin yadda za ta yi da dubu talatin ɗin nan, ba tare da ta rushe gaba ɗaya ba. Ga shi magungunan da yake sha kawai, na wata ɗaya dubu goma sha biyu take sayen su. Sai dai kamar yadda yake nanata mata, ta yi haƙuri, ya sanya ta fauwwala wa Allah lamarin. Kwana biyar da kwashe kuɗin nan, Sayyid ya hana Nana gaya wa kowa. Sai dai cikin dare ba ta iya bacci, saboda lissafi da tunani. Ta kira Ummi ta tambaye ta batun barkono, ta ce ana ta saya, ta sayar da ya kai rabin buhun. Kayan Abinci da Mama ta haɗo mata da su, take ta cancana musu. Da daddare ba ta iya bacci, saboda damuwa da tunani, sai dai abin yana damun sa fiye da yadda yake damun ta. Su ka wayi gari, ya tashi jikinsa babu daɗi, yana ta numfarfashi. Abin Duniya ya ƙara damunta, ya kuma ƙi cin komai. Muryar Barira ta jiyo a tsakar gida, da ta dawo, tana maganganu tana ba wa su Sajida labari. "Mayu sun kama ni a gidan nan, kuma da ƙarfina na dawo, wallahi sai sun ci uban su, kurwata ta fi ƙarfin mutum". Sajida ta ce "Ban gane mayu ba, suwaye mayun kuma?" Barira ta ce "Oho, ki zuba ido ki gani, Allah zai tona musu asiri" "Ni fa ba na son kurman baƙi, a masu shigowa ne mayun, ko kuma zaunannun gidan" "Na ce ki zuba ido ki ga ikon Allah" Bai fi mintuna biyar ba, wani irin hayaƙi, mai azabar yaji, ya turnuƙe gidan. Nana da take lafiya ƙalau ma, ta fara tari. Shi m tarin yake yi, numfashinsa kamar zai ɗauke, ta ɗaukko mafici ta din ga yi masa fifita. Ta gaji ta tashi, da nufin ta je ta ga me ake ƙonawa yake wannan uban hayaƙin haka. Amma ya riƙe hannunta ya hana ta. Haka suka wuni a galabaice. Sajida ma sai bala'i take yi, tana cewa Barira za ta kashe ta da hayaƙi. "Wai Sajida ko ke ce mayyar nan ne?" "Ke kama bakin ki, wallahi ki ka ce mini mayya, sai mun yi shari'a da ke" Barira ta ce "Sai ki saurara mini, tun da dai ba ke ba ce" Haka suka wuni, Barira tana gana musu azaba, da wannan azababben abin da take zubawa a cikin murhu. Washegari ma, azabar hayaƙin nan ce ta tashi su Nana, numfashin Sayyid tamkar zai ɗauke saboda azaba. Nana dai ta ci gaba da daurewa, amma yamma na yi, Barira ta sake cika kurfoti da gawayi, ta tayar da wuta ta afka hayaƙin nan. A fusace Nana ta fita, ta tarar da ita tana ta girgiza kurfotin, tana zuba wani abu a ciki. Nana ta ce "Barira, dan zatin Allah ki daina zuba wannan abin. Ina da mara lafiya a ɗaki. Yana da matsalar numfashi, jiya kwana muka yi babu bacci. Kuma da sassafe kin banka wani, kuma yanzu ma ga shi kina sake kunnawa" Ta kalli Nana ta ce "Ai duk wanda ya hana uwar shi bacci, wallahi shi ma ba zai yi ba" Nana ta ce "Kamar yaya kenan?" "Kamar yadda ki ka ji" "Ni dai koma mene ne, ki yi haƙuri idan ba ki yadda ba, zo mu je ɗakin ki ga halin da yake ciki" "Babu ruwana da halin da yake ciki, kurwata ce ta fi ƙarfin duk wani maye wallahi" Nana ta ce "Barira mu ne mayun da ki ke faɗa dama? To Barira ko za mu ci mutum ma ci taki, jiki duk dauɗa?" "Ko ma duk uban mene ne, tun da aka kama ni aka lasa, an ji zaƙin kurwa ta, wallahi sai mutum ya ci ubansa, miyagun banza kawai" "Mu ne mayun Barira?" "Eh ku ne, ko na ce ke" Nana ta ƙarasa daf da Barira ta damƙi tsintsiyar hannun Barira ta ce "Ki ka ce ni mayya ce?" Barira ta yinƙura za ta fizge hannunta, ta yi bala'i. Kawai ta ji jikinta ya yi wani irin nauyi, kuma jikin ya yi mata wani irin sanyi, ta kasa motsa komai. Kawai ta silale ta faɗi ƙasa. Ayshercool 08081012143 54 Ihu Sajida ta saka, tare da sauran matan da suke zaune, tamkar ana bajekolin kasuwar ƙauye, suka dare ganin daga riƙe hannun Barira da Nana ta yi, ta faɗi ƙasa. Faɗuwar da ba su da tabbacin, tana raye ko mutuwa ta yi. Wasu suka yi waje da gudu su na ihu, tamkar garken tumakin da ba su san inda suka dosa ba. Nana kuwa idanunta a rufe, ta nufi ɗakin su tana tangaɗi, Sayyid kuwa da ƙyar ya lallaɓa ya tashi yana ƙoƙarin fitowa, amma mai afkuwa ta riga ta afku. Nana na shiga ɗakin ta faɗa jikinsa, ya taro ta. Gaba ɗaya jikinta ya saki kuma ya yi sanyi ƙalau, shaidar Ƙaisar ya buge ta. Ya ɗauki wayarta, ya tura wa Ummi saƙo. Tuni aka kira mijin Barira, jikinsa na rawa ya shigo gidan, tare da rakiyar wasu mazan. Ya durƙusa a kan Barira ya taɓa ta, ya ɗago ta, sai dai ya ga tana numfashi, sai dai idanunta a kakkafe, ya girgiza ta yana kiran sunanta "Barira. Barira ki buɗe idonki. Ki na ji na?" Barira ba ta motsa ba, kuma ba ta yi magana ba. Sai dai numfashinta yana fita normal. Mijinta ya ce "Dan a samo adaidaita sahu mu tafi Asibiti" Ɗaya daga matan da abin ya faru a gaban su ta ce "Wane Asibiti, ai ko an je Asibiti babu abin da za a gani, Nanan za a janyo daga ɗakin, a yi wa dukan tsiya a sanya ta tsallaka ta, shi ne za ta tashi, kama mata kurwa ta yi" Ɗaya daga mazan ya ce "A'a ba za a dake ta ba, a kai ta dai gurin hukuma, a san abin yi." Mijin Barira ya ce "Wane irin kar a dake ta, kana kallon halin da matata take ciki" Ya miƙe ya nufi ƙofar ɗakin su Nana, cikin ɗaga murya ya ce "Kina ina, ki fito ki tsallake mini mata, ki sakar mata kurwa" Sai dai ya ji shiru, babu wanda ya yi magana. "Ki fito ko na shigo wallahi" Wani ya ce "Kar a yi haka Gali, ka ga matar aure ce, bai kamata a bi abin da mata suka faɗa ba, kamata ya yi a zurfafa bincike tukuna, kar a ɗauki doka a hannu, a zo daga baya a ji kunya" Gali ya ce "Malam ni dai ba zan ji kunya ba da yardar Allah, kalli halin da yarinyar nan fa take ciki. Idan ta mutu fa? Wallahi ba zan yarda ba" A fusace maƙwabcin na su ya ce "To a je Asibiti mana a duba, sai haƙilo ka ke yi, matarka matarka. Kamar ba nan ka ke jibgarta, ake ƙwatar ta da ƙyar ba, sai da aka haɗa ka hukuma ka daina, auren da ko shekara biyu bai yi ba, a lokacin ba ka yi tunanin ta mutun ba sai yanzu?" A fusace Gali ya ce "Kar ka gaya mini maganar banza mana, ina ruwan ka da dukan da nake yi mata, dama munafunci ne ya sanya ku ke yi mana sulhun?" Ummi ce ta yi sallama, Sajida ta yi caraf ta ce "Yauwwa ga yayarta, ita ce dama ta kawo ta gidan nan" Cikin mamaki Ummi ke bin dandazon jama'ar da kallo. Ta ce "Wai lafiya me ya faru?" Mijin Barira ya ce "Mene ma bai faru ba, kin kawo mana mayya ta kama mini kurwar mata. Dan haka sai ki shiga ki fito da ita ta tsallaka ta" Tuni idon Ummi ya cika da hawaye, saboda ba ta ƙaunar tashin hankali ta ce "Wallahi mu ba mayu ba ne ba. Nana ƙanwata ce, akwai dai abin da ya faru amma ba wai Nana ta kama kurwar wani ba" "To ƙarya aka yi mata? Ba ga Bariran can a kwance ba, ta tashi mana". Cikin tashin hankali Ummi ta ce "Wallahi kaf zuriyarmu babu mayu, Nanan ma matsalar mutanen ɓoye ne da ita, amma ba maita ba, bari na duba ta" Ta nufi ɗakin da su Nana suke. Tuni gidan ya sake ɗinkewa da mutane, ya cika fal wasu suna a fito da Nana, a zane ta a saka ta tsallake Barira. A zaune ta tarar da Sayyid, rungume da Nana a jikinsa. Cikin damuwa da tashin Ummi ta ce "Wai me ya faru ne?" Ya yi shiru yana kallon Ummi, sannan ya mayar da idonsa kan Nana. Ta ɗauki wayarta ta kira Baba. Tana jin ya ɗaga ta fashe da kuka. Baba ya ce "Ke meye haka lafiya?" "Baba babu lafiya, dan Allah ka zo gidan Nana, akwai matsala ne" "Gidan Nana kuma? Ina ne gidan Nanan, kuma matsalar mene?" "Baba mutanen unguwa sun taru, za su dake ta, kar su kashe ta ni ban ya zan yi ba" A sukwane Baba ya miƙe ya ce "Ƙarya ne. Nanan za su kashe mini, ai zan yarda kowa zai iya ɗaukko magana a cikin ku, amma ban da Nana. A can gidan gadin nata ne za su dake ta?" "Baba wane gidan gadi kuma, ai sun bar gidan tana nan kusa da ni, ka manta ne? Ka cewa Nasiru ya rako ka ya san gidan" "Gani nan zuwa" ya kashe wayar ya yi waje da sauri. Ummi ta tsaya a bakin ƙofar, tana ta ba su haƙuri. Amma sai nema suke yi su ture ta, su shiga ɗakin. "To ban da wulaƙanci ma, ta shige ɗaki taƙi fitowa, da yake ba ta da gaskiya. Maimakon mijinta ya fito ya bayar da haƙuri, shi ma ya yi zamansa saboda rashin tsoron Allah, da rashin gaskiya" Ummi ta ce "Mijinta ba shi da cikakkiyar lafiya, ita ma aljanu sun buge ta, dan Allah ku yi haƙuri" Sai dai abin ya fi ƙarfin Ummi, ƙoƙarin hankaɗe ta kawai suke yi, su cimma Nana. Ana haka sai ga maƙwabcin su Nana, tare da jami'an tsaro. A dole mutanen suka saurara. 'yan sanda suka ce, a tafi da Barira Asibiti, abin da likitoci suka ce, da shi za a yi amfani. Ana haka Baba ya ƙaraso, cikin tashin hankali. Ummi na ganin sa ta yi ajiyar zuciya. Ummi ta ce "Baba ka zo?" "Eh, ina Nanan take, kuma uban me ta yi za a dake ta da?" "Ai gama 'yan sanda sun zo, saɓani suka samu da wanda suke zaune gida ɗaya, shi ne suka ce mayya ce" Baba ya ce "Maita kuma? In ji uban wa?" Mijin Barira ya ce "Ga shaida Baba, kalli matata a baje a kwance" "Kuma sai ka ce 'yata mayya ce? To wallahi ƙarya ne, kaf danginmu babu mayu, ku dai nemo wani abun, ba maita ba wallahi" 'Yan sanda suka shiga maganar, aka tafi da Barira Asibiti. Sai da aka bar 'yan sanda biyu, gudun abin da ka iya faruwa, saboda matan da abun ya faru a gaban su, su na ta ƙara balbalawa wutar fetur. Tare da mayar da abin da aka yi da wanda ma ba a yi ba. Gaba ɗaya zancen ya zagaya unguwa. Har sha ɗayan dare case bai ƙare ba, Nana ta farfaɗo ta ga Ummi a ɗakin su, ga duhun dare ya fara yi. "Ummi lafiya kuwa?" "Ina fa lafiya Nana, meya haɗa ki da mutanen gidan nan, ga shi ana cewa ke mayya ce". "Mayya kuma?" "Eh mana, yanzu case na hannun 'yan sanda, Baba yana can tare da su, ana jiran likitoci su faɗi sakamakon binciken su." Nana ta gaya wa Ummi iya abun da ta iya tunawa. Sai dai ta sha mamaki, ta ji wai Baba ya zo kan matsalar ta. Ta kalli Sayyid da yake kwance lamo, abin Duniya duk ya dame shi. Sajida ta haɗa kayanta, ta gudu ta ce ba za ta iya kwana da Nana a gidan ba. Sai zuwa da safe, Likitoci suka tabattar da anemic shock ne ta samu, bayan binciken ƙwaƙwaf da suka yi, suka gano ta yi ɓari sati biyu baya, ta kuma zubar da jini sosai ba ta je Asibiti ba. Ta zo ta yi zazzafan zazzaɓi na typhoid amma suka alaƙanta hakan da mayu, nan ma ba a je Asibiti ba. Hakan ne ya haddasa faɗuwar ta. Bayan fito da sakamakon, mijinta da 'yan uwanta suka ce ba su yarda ba, sakamakon ƙarya ne kawai aka gaya musu. Ga Barira ta farfaɗo, tun a cikin daren ma, har ta ci Abinci, amma suka ci gaba da surutu a kan Nana mayya ce. Ummi tare da su Nana ta kwana, saboda tsananin tsoro. Dan da gidanta akwai guri can za su tafi ma. Sai dai tashin hankalin abin da ya faru, ya sanya jikin Sayyid rikicewa gaba ɗaya, ya zamana kamar ma ba ya gane wanda yake kansa. Hankalin Nana ya yi mummunan tashi, ga shi babu isasshen kuɗin tafiya Asibiti. Ta kuma san tashin hankali, da damuwar abin da ya faru ne, ya sanya jikin nasa ƙara rikicewa. Nana ta rasa abin da yake yi mata daɗi, ga matan gidan kowacce ta koma gidansu, sun ƙi dawowa gidan wai tsoro suke ji. Ummi ce ta yi sallama, Nana ta amsa ta yi mata izini ta shiga ɗakin. Hannunta riƙe kular Abinci. Ta kalli inda Sayyid ke bacci a wahale, numfashinsa na fita sama-sama. Cikin damuwa Ummi ta ce "Yanzu Nana haka jikin nasa ya koma?" "Wallahi Ummi, gaba ɗaya hankalina a tashe yake" "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ana wata ga wata" Cikin damuwa da rashin fahimta ta ce "Me ya faru?" Cike da karaya, da matsanancin tausayin ƙanwarta ta ce "Mai gidan nan ne, ya je ya same ni, ya bani dubu goma sha biyu, wai ga sauran kuɗin ku nan, ku tashi. Ba ya son tashin hankali, kuma ga sauran 'yan hayar sun ce ko ku tashi, ko ya mayar musu da kuɗinsu su tashi. Nayi-Nayi ya ƙara wani abu, tun da ko wata ba ku yi ba, amma ya ƙi wai wannan ɗin ma da ƙyar ya samo su ya kawo." Nana ta jingina da jikin bango tana maimaita "Innalillahi wa Innalillahi raji'un" "Nana mene ne abin yi yanzu?" Nana ta girgiza kai, jiki a sanyaye ta ce "Ban sani ba Ummi" "To ko wani gidan za a nemo? Sai na koma na neme shi, na roƙi alfarmarsa?" Ta girgiza kai ta ce "A'a Ummi, an riga an yi mini mummunan tambari a unguwar nan, abu ne mai wahala ma mu sake samun wani gidan a unguwar nan" "Bari na kira Baba na ji me zai ce" Nana ta ce "A'a Ummi, kin san halin Baba, kar ranki ya ɓaci" "To Nana ya zamu yi, dole a kira shi mu ji me zai ce" Ummi ta kira lambar Baba, yana ɗaga wayar muryarsa a sama ya ce "Ya kuma aka yi, ba an kashe case ɗin a gurin 'yan sanda ba?" Ummi sai da ranta ya sosu, amma ta maze ta ce "Baba ba wannan ba ne. An kori su Nana daga gidan da suke ne, mai gidan da suke ya ce sai sun tashi" "To sai kuma aka yi yaya? Ni zan nemo musu wani gidan? Ko kuma mijinta ne yakamata ya nemo musu wani?" "Baba ka fa zo gidan nan, ka ga halin da mijin nata yake ciki na rashin lafiya, saboda haka aka kore shi daga gurin aikin gadi. Dan Allah Baba ka yi wani abu a kan yarinyar nan. Nana yarinya ce ƙarama pressure ta yi mata yawa." "To Ummi ya ki ke so na yi? Ni dai nan gidan babu gurin da zan ajiye ta, ita da mijin nata, idan kuma ke ki na da guri ki taimaka ki ba su. Idan ba haka ba ta nemo 'yan uwansa su ɗauke shi, su rakata inda danginsa suke. Kin san dai nan gidan idan ta dawo, abin da za ta ci ma aiki ne. Nima yanzu sai abun da aka samo aka bani" Hawaye ya cika idon Ummi, cike da takaicin yadda Baba bai fiye damuwa da damuwarsu ba. Ta ce "Baba da ina da inda zan ajiye Nana da mijinta, wallahi ba zan kira ka ba" Nana ta ce "Ummi, dan Allah ki katse kiran nan, nima ba zan koma can gidan ba." Tarin Sayyid ta ji, ta mayar da hankalinta kan sa, ta nufe shi tana faɗin "Sannu Sayyid" "Ki ba ni ruwa" ta amsa da to. Ta ɗaukko ruwan leda, ta buɗe masa ya tashi zaune ta fara bashi. "Sannu Sayyid" Ummi ta faɗa cikin tausayawa, kallo ɗaya ta yi masa ta gane yana jin jiki. Da da ne, kome za a yi,ba zai bar gashin nan a buɗe ba. Amma yanzu ba ta gashin yake yi ba, ga fuskarsa duk ta kumbura. A zuciya irin ta Nana, ta san ko a titi ta tsince shi a wannan yanayin, ba za ta iya tafiya ta rabu da shi ba, balle mijinta. Ƙarar da wayarta ta yi ne, ya sanya ta dawo hayyacinta. Ta ɗaga wayar tare da yin sallama. "Ke Hansai, ina ta kiran wayar ki, amma ki ka ƙi ɗagawa?" Ummi ta ce "Eyya, ba haka ba ne Uwani,ba na kusa ne, ya gida ya mutanen garin?" "Lafiya ƙalau, ya na ji muryar ki ƙasa-ƙasa, laulayi ko rashin lafiya" Ummi ta yi yaƙe ta ce "Ba gara a ce laulayi nake ina kwance ba, da abin da yake faruwa" "Subhanallah, meyafaru?" Kasancewar Uwani kaka ce a gurin su Nana, ƙanwar kakarsu ce, da kakarsu wadda Nana ta ci sunanta da Uwani, uwa ɗaya uba ɗaya suke. Sai dai ita tana can Garko da iyalinta. Ummi ba ta ɓoye mata komai ba, ta gaya mata. Uwani ta rafka salati. Ta ce "Sai an yi magana ku nuna ku mutanen birni, kun fi mutanen karkara wayewa. Ina wayewar take. Aikuwa sai na kira Isa na ci ubansa mara mutunci. Tuntuni nake ganin take-takensa kamar har da ƙiyayyar uwar su, take shafar su a gurinsa. Ai Imrana yana zuwar mini nan. Ya hana kowa riƙe su kuma shi yana yi musu riƙon sakainar kashi. Yanzu ina duk sauran 'yan uwanki Ummi, ina 'ya'yan Atine, ina su Gaddafi da ba za ku iya taruwa ku rufa wa 'yar uwakku asiri ba?" AREWABOOKS "Wallahi Uwani mun yi iya yinmu ne.." "Rufe mini baki, ina wani iya yinku, kuma duk wanda ya ce mana mayu Allah ya isa bamu yafe ba. Mu bamu gaji maita ba, balle a saka yarinya a gaba a tsangwame ta. Na san babu lallai ta iya zaman ƙauye, amma mu nan akwai ɗakuna, har ma da gida da babu kowa, idan za su iya zama ta yi jinyarsa. Babu mai damun ta, kuma babu mai cewa ta tashi. Amma tabbas kun ji kunya, idan har ku ka bari Asma'u ta wulaƙanta, a ce an rasa inda za ta zauna, ta yi jinyar mijinta, yawan ku kun zama taron tsintsiya babu shara." Ummi ta yi shiru, Uwani akwai kirki da karamci, amma idan ta botsare tana faɗa, to duk gaskiyar ka, sai dai ka yi haƙuri. Ta gama faɗan ta, Ummi ta kashe wayar. Ta kalli Nana, ta ga yadda ta tattara hankalinta a kan mijinta, tana ba shi Abincin da ta kawo musu, sai lallaɓa shi take, da alamu abincin ma ba ya so. "Nana, kin ji abin da Uwani ta ce?" Nana ta girgiza kai ta ce "A'a. "Cewa ta yi idan za ki iya zama, ku tafi can Buda ki kula da shi, akwai inda za ku zauna. Kin ga nan tun Baba ya san maganar maitar nan, kamar Mama ta ji ne. Ita kuma kin san gishiri za ta ƙarawa abin ta yi ta bayar da labari. Amma ban sani ba ko ki na da wata shawarar?" "Ummi wace shawara? wanda yake ruwa ko takobi aka miƙa masa, ai karɓa zai yi. Sai dai shi nake tausayawa, amma ba ni da wata mafita da ta wuce wannan ɗin. Ni in dai zan samu inda zamu zaune na kula da shi, ba komai zan zauna ko a cikin dutse ne ba ƙauye ba" "Kin tabattar Nana? Da wayonki fa sau ɗaya Baba ya taɓa bari, muka je muka kwana biyu" Nana ta ce "Ba komai, zan zauna" Sayyid ya sanya hannunsa biyu, ya damƙe na Nana. Nana ta kalle shi ta ce "Sayyid, mene ne?" Idanunsa sun kaɗa sun yi jawur, wata jijiya a saman goshinsa ta ɗaga ta kumbura, fuskarsa ta yi jawur. Laɓɓansa sauka din ga karkarwa yana son ya yi magana, Nana ta girgiza kai ta ce "Ba sai ka yi magana ba Sayyid. In sha Allah duk rintsi ina tare da kai, har Allah Ubangiji ya baka lafiya" Ummi ta kasa jurewa ta fashe da kuka. Nana ta ce "Ummi idan ki ka yi kuka,ni ya zan yi? Kun saka ni a tsakiya, nama fi ku juriya, har da kai ma" ta yi maganar tana murmushi bayan saka idanunta cikin na Sayyid, duk da idon nata a cike da hawaye. "Ummi ki gaya wa Uwani na amince" Ummi ta share hawayenta ta ce "To shikenan, ya za a yi tafiyar to?" "Ina ga a sayar da kayan ɗakin nan, katifar ta ishemu, sai a sai ledar ɗaki, sai kayan sawarmu" "Nana, kina amarya amma a ce ɗakin ki babu kayan ɗaki, haka za ki je ki zauna? Kin san mutanen ƙauye ba sa raina abin surutu dai" "Ummi ai ba ado da kwalliya zan je ba. Kuɗin kayan ma riƙe saboda ɗawainiyar abinci da kuma magani" Ummi ta ɗan yi shiru ta ce "Kuma haka ne, yanzu zuwa gobe in Allah ya kaimu, zan samo dillalai su saya" Cikin sauri Nana ta ce "A'a Ummi, ba na son ci gaba da zama a unguwar nan, ban san me za su yi mana ba. Idan da hali a nemo su yau kawai. Su saya gobe in Allah ya kaimu mu tafi" "To shikenan, bari na fita na gani" ***** Yana zaune a cikin office ɗin sa, ya ɗora ƙafafuwansa a kan tebur, yana juyi, ya din ga kiran lambar cike da fatan a ɗauka. Har ya yanke tsammani, kawai ya ji ta ɗauka, sai dai ta yi shiru. Da sauri ya sauke ƙafafuwansa ya ce "Hello" ta yi shiru ba ta amsa ba. "Hello ki na ji na?" "Eh" ta amsa a raunane. "To ba za ki yi mini magana ba?" "Ba cewa ka yi ba ka gane ni ba, ranar da na kira ka?" Ya ɗan yi guntun murmushi ya ce "Ki yi haƙuri, sai daga baya na ɗauki muryar ne. Ya ki ke ina fatan kina lafiya?" "Ai baka damu da ina lafiya ba, tun da ka sake ni baka ƙara nema na ba, saboda ka yi aure matarka ta haihu, dama ni haushina ka ke ji, ba na haihuwa" "A'a Yusra, kar mu fara haka da ke. Kin san ko bayan mun rabu, na yi ta neman lambarki, amma ba ta shiga har na haƙura. Ya jikin ki?" "Da sauƙi, amma ni ba mahaukaciya ba ce" Sagir ya ce "Ai dama ban ce ba" "Lokacin da muna tare ai ka ce" ya yi murmushi ya ce "Wannan ba ya wuce ba? Amma Mami ba ta san kin kira ni ba ko?" "Eh, ina gidan Mummy Zahra, da wata na haɗu sunanta Nana, ita ma ta san irin rashin lafiyata. Ita ma tana yi" Ya ce "Haba dai?" "Wallahi. Ita ta din ga ba ni shawara, ita ce ma ta ce na kira ka fa, na ma zata ba zaka ɗauka ba, ka ɗauka amma ka nuna ba ka gane ni ba" dariya ya yi ya sakankance sosai, yana sauraren Yusra. A yanayin surutun da take yi, ya fuskanci jikinta da saura, ba ta warke ba, amma ya tattara hankalinsa yana sauraren ta. Hirar ta din ga tuna masa da yadda suka zuba soyayya a baya kafin aure. Yana kallon kiran Shukura amma ya ƙi ɗagawa ya ba wa Yusra lokacin sa. "Ki na ji na" "Eh" "Yanzu ina gurin aiki, kuma lokacin salla ya yi, zan sake kiran ki, in sha Allah" "Tom sai anjima" "To 'yar farata, bye-bye" Kamar tana gabansa ta saki murmushi, cike da sanyin jiki, saboda ta yi kewar jin sunan. Shi ma murmushin ya yi, yana tuna wasu abubuwa da suka wuce. Ya kira Shukura, sai da ta kusa katsewa sannan ta ɗaga. "Madam ya aka yi ne?" "Ina ta kiran ka, kana waya, har da rejecting kirana" "Sarkin ƙorafi, kin san da wa nake wayar ne?" "Ai ba sai ka gaya mini ba, na san 'yan matanka ne" "Ni ba da 'yan mata nake waya ba. Ya aka yi?" Shukura ta ce "Ba komai" "Madam Shukura, bakomai ɗin ki, na nufin akwai komai. Yanzu dai a yi mini afuwa da ni da 'yan matan nawa." "Ni shikenan kawai" ta kashe wayar. Ya girgiza kansa tare da ɗan lumshe idonsa. **** A ranar dillalai, suka saye wardrobe da mudubin Nana, da sauran kayan da take ganin za su zame musu shirgi. Ta tattare musu kayan su cikin bagcco, duk wani kayan amfaninsu ta tattare. Da safe ƙarfe goma, ita da Ummi suka je suka samo taxi. Har fargaba take yi kar mijin Ummi ya yi ƙorafi a kan yawon da take yi saboda ita. Duk da ba mazauni ba ne. Suka yi cinikin a nawa zai kai su Garko cikin ƙauyen Buda. Aka ɗaure katifa a saman taxi, aka loda kayan su a ciki. Ummi ta shiga gaban motar, ita da babbar 'yar ta Islam. Nana kuma suka shiga bayan motar, tare da Sayyid. Ya kwanta a jikin Nana ya yi shiru, ita kuma ta riƙe hannunsa tana matsa masa a hankali cike da kulawa. Awa ɗaya da rabi, suka isa har cikin garin Buda. Sai dai shigar su garin ke da wuya, Nana ta fara jin sanyi yana ratsa ta. Addu'a ta din ga yi, a kan Ubangiji Allah ya rufa mata asiri, ya kawo musu ɗauki, ya shiga tsakaninsu da su Ƙaisar. "Ma vie" ta ji ya yi magana. "Na'am Sayyid" Sai kuma ya yi shiru, bai sake cewa komai ba. Yara suka firfito suka tatstsaya bayan ganin mota ta tsaya a ƙofar gidan Uwani. Uwani da kanta ta fito tana tafa hannu, tana "Maraba da mutan birni. Ina yayar tawa take?" Nana ta buɗe motar ta fito tana murmushi. Ummi ta sallami mai motar, Uwani ta ce "Ina mai gidan?" Nana ta buɗe taxi ɗin, ya fito a hankali, kansa rufe da mayafi. Uwani bakinta fal magana, amma ta haɗiye ta yi musu maraba, zuwa cikin gidan. Babban gida ne mai ɗauke da ɓangarori. Ta kai su sashen ta, aka yi shimfiɗa Sayyid ya zauna ya jingina da bango. Abin da dai ba ya ƙauna, ya sake tararwa a garin, kallo. Ba ya son a zura masa ido, amma ya lura da yadda ake ta kallon sa. Uwani ta karrama su da ruwan pure water, da abinci shinkafa da wake. Ummi ta ce "Kafin cin abinci, Uwani a ina za su zauna, a gyara musu?" Sai da Uwani ta sake yi wa Ummi ta tas, tamkar ita ce Baban, sannan ta kalli Nana ta ce "Yayata, kin ga cikin gidan nan, akwai ɗakuna, idan ma ba zaku zauna a nan ba, nan baya tafiyar babu nisa, akwai gida da ɗakuna biyu da tsakar gida. Babu kowa a gidan idan za ku zauna". Nana ta ce "Gara su zauna a inda babu kowa" Ummi ta ce "Maimakon ku zauna a cikin mutane, yadda ko wani abin ne, a taimaka muku" Nana ta ce "Akwai dalili gara mu zauna inda babu kowan" Nana kuwa ta yi hakan ne, domin samun rufin asiri na larurar da suke fama daga ita har Sayyid. Ga uwa uba takura da Sayyid ba ya so. Uwani ta saka yara, su ka je su ka share gidan tas, aka wanke. Nana ta ce "Sayyid, bari mu je da Ummi, a gyara gidan, sai mu zo mu tafi da kai" Ya saka hannu ya riƙe nata, tare da girgiza mata kai alamar a'a. "Mu tafi tare za ka iya tafiya?" Ya jinjina mata kai alamar eh. "To ta so" Ya yinƙura a hankali ya tashi tsaye. Uwani ta ce "Nana, ku bar shi a nan mana, tun da ba shi da lafiya, ke ku je, ku gyara gidan" Nana ta ce "Ai ba zai zauna ba, ya ce bin mu zai yi" "Ikon Allah, ni da bita zai-zai, to Allah ya taimaka" Nana ta yi murmushi kawai, tare da jin nauyin abin da Sayyid ɗin ya yi. Sauran yaran gidan Uwani, suka bi su Nana, su taya su shirya kaya. Wanda galibi Nana ba ta ma san su ba, saboda ba zuwa garin suke yi ba, domin ita rabonta da garin ma, har ta manta. Gidan ƙasa ne tsura, da zunzurutun turɓaya Ɗaki ɗaya ne gyararrre, sai aka yi masa siminti, da plasta, aka shafa farar ƙasa, da ƙofar langa-langa. Sai wani ɗakin kuma, si kuma ko rufi babu, sai banɗaki. Duk lalacewar gidan su Nana ya fi nan nesa ba kusa ba, Ummi jarumta kawai take yi, zuciyarta a cunkushe babu daɗi, biyo bayan tuna cewar a nan Nana za ta rayu. Sai dai ta ga tsantsar tawakkalli a fuskar Nana. Su ka gyara ɗakin aka shimfiɗa leda, sai katifar su. Sai kuma tarin kayan su, na girki sai na sakawa a cikin bagco. Uwani ta aiko musu da Abinci. Da la'asar bayan Ummi ta yi salla, ta ba wa Nana kuɗin barkononta da aka sayar, ta yi ta mata nasiha da kwantar mata da hankali, sannan ta yi musu sallama. Ɗan gidan Uwani ya ɗauke ta a kan babur, ya tafi da ita. Nana ta ƙarasa gaban Sayyid, da ya zuba mata idanu tamkar bai taɓa ganinta ba. Ta riƙo hannayen sa ta ce "Sayyid, duk da ban san wace irin rayuwa ka yi a baya ba. Amma wadda muka yi, mun yi ta ƙarƙashin kulawar su Habu, ba mu taɓa neman abu mun rasa ba. Amma Allah shi ne abin godiya. Wannan yanayin da muke ciki, ba zai dauwama ba in sha Allah. Ina fatan Allah ya baka lafiya, ya kuma baka haƙuri da juriyar a yanayin da muka tsinci kanmu a ciki". Ya sanya tafukan hannayen sa biyu, a fuskarta laɓɓansa na rawa, amma magana ta gagara. Ta girgiza masa kai tana murmushi, ta ce "Ruhinka yana cikin jikina, kar ka damu kanka lallai sai ka yi magana. A jikina ina jin abin da ka ke son faɗa" ɗan guntun murmushi ya yi, duk da yadda yake matuƙar son ya furta wani abu. Da daddare Uwani ta aiko musu da tuwon dawa, da miyar karkashi, ta sha daddawar kalwa har ɗaurin yajin daddawa. Ta san ba lallai ya iya ci ba, ta ba wa yaran da suka kawo kuɗi, ta ce su sayo mata buredi da shayi, na gurin masu sayarwa, da kuma maganin sauro, saboda azabar sauron da ke ɗakin. Sai dai ya ƙi shan shayin, buredi kawai ya ci ya kwanta. Nana jikinta na rawa ta ci tuwon, saboda yadda ranta ya biya, amma ƙarshe amai har ta hancinta sai da ta yi shi. Kan su kwanta, ta kunna maganin sauro, ta gyara masa shimfiɗa ya kwanta. Ita ma ta hau katifar ta tofa masa Addu'a, sannan ta kwanta a kusa da shi, tana yi masa fifita. Ta daɗe idonta biyu, kafin bacci ɓarawo ya sace ta. Sai dai kamar a zahiri, kuma kamar a mafarki ta fara jin hayaniya a kanta. Ba ta gama tantance hayaniyar mece ce ba, ta ji wani abu na wucewa ta saman roofin ɗakin. Idan abin ya daki kwanon ɗakin da abin da yake takawa, tamkar kwanon zai buɗe ya faɗo musu a ka. Ayshercool 08081012143 55 Wata irin yinƙurawa Nana ta yi, cikin azama da tashin hankali ta kifa a kan Sayyid, saboda kar abin da yake takun koma mene ne, ya faɗo masa a ka. "Ma vie" ya furta da ƙyar can ƙasan maƙoshinsa. Ta ɗago ta fara laluben fuskarsa a cikin duhu. "Sayyid, ba ka ji wani abu zai faɗo mana ba?" "A'a" Ta sake cewa maganar ta dawo "Maganar ta dawo?" "Eh" "To sannu" ta furta a hankali cikin tsoro, ta mayar da kanta kan ƙirjinsa a tsorace. Sai dai kamar dole, ta ƙarfin tsiya, wani baccin ya sake awon gaba da ita, tana cijewa da ƙoƙarin hana idonta sake yin bacci, amma abu ya ci tura, baccin ya kuma awon gaba da ita. Ganinta ta yi a tsaye a tsakiyar ɗakin, itakaɗai babu Sayyid. Ana ta cigaba da hayaniyar da ba ta gane me ake faɗa. Ta din ga waige-waige tana tunanin ina ya shiga haka? Sai dai ba ta gama tunanin ba ta ji muryoyi daban-daban suna faɗin "Lale da manyan baƙin garin Buda. Barka da zuwa." Sai kuma ta ji ana dariya tare da ci gaba da hayaniya. Idonsa biyu, yana jin yadda ta yi wa hannayensa wata irin muguwar damƙa, ta nutsa faratanta a jikin fatarsa, dan tuni ya karaya jini ne yake fita daga fatar tasa. Ta din ga juya kanta a kan ƙirjinsa tana kuka tana faɗin "A'a, mu ba baƙin ku ba ne ba, ba gurinku muka zo ba, mu ba baƙinku ba ne" jin ta fara ɗaga murya, ya sanya ya murginata gefensa, ya zame hular kanta yana shafa gashinta a hankali, tare da hura mata iskar bakinsa a kunnenta. Daga haka sai ta yi shiru, ta ci gaba da bacci. **** Barira sai da ta sha jini leda biyu a Asibiti da allurai da magunguna, amma tana komawa gida, abu ya ƙara rikicewa. Domin kuwa babu damar ta sanya haƙarƙarinta a ƙasa ta fara bacci, wannan jibgegiyar magen za ta bayyana, su hau kokowa da ita. Duk sai magen ta yayyage mata fuska da jikinta. Idan ta tashi sai ta ji jikinta na yi mata wani irin zugi da raɗaɗi. Ta cewa mijinta ita fa ba za ta koma wannan gidan ba. Ya sanar mata an tashi su Nana, daga su sai su Sajida a gidan kamar da, amma ta hau kujerar naƙi ta ce gidan ne ba za ta koma ba. Shi kuma ya ce sai dai ta yi ta zama a gidansu, dan ba shi da kuɗin kama wani gurin. Shukura ce tare da Hajiya Amina, suke hira. Ta je yi mata sannu da zuwa dawowar da ta yi daga umara. Alhaji Zailani ya yi sallama ya shigo falon. "Daddy sannu da zuwa" Ya ƙare mata kallo ya ce "Yauwwa, mara tawakalli da ba ta san ƙaddara ba" Ta yi shiru tare da sunkuyar da kai. Duk irin kashedin da nake yi miki, da rarrashin da na yi miki, ba ki ji ba abin har ya kai ki dizga bawan Allah nan, a gaban mutane kina cewa yana kashe mutane, idan ya yi ƙarar ki kina da shaida a kan haka?" Ta yi shiru ta sunkuyar da kai. "Tambayarki nake yi" Ta girgiza kai alamar a'a. "Amma ki ke wannan iƙirarin, maimakon ki mayar da hankali a kan fatan Allah ya raya na gabanki, ya ba ki wani. Ba ki kyauta ba" Hajjya Amina ta yi ta kallon Shukura ko za ta ba shi haƙuri, amma ta yi mursisi. Ko da ya shiga ɗakinsa, babbar rigarsa ya cire saboda azabar gumin da yake yi. Dan tun da Doctor Sharif ya gaya masa ga yadda suka yi da Shukura hankalinsa ya yi mummunan tashi. Ya kuma sake jaddada wa Sharif, muddin wani abu ya fita to babu hannunsa a ciki. Kuma likitan ya yi masa bayanin process ɗin da ya bi, abu ne mai wahala a gano. Ya yakice gumi ya nemi guri ya zauna. Hajiya Amina ta ce "Me yasa ba ki ba shi haƙuri ba, kina kallon yadda ya yi fushi?" "Mummy, duk wannan abubuwan kamata ya yi a tsaya a saurare ni, a kuma fahimce ni. Da hankalina fa ta yaya zan din ga iƙirarin an kashe mini ɗa haka kurum. Mummy ranar da za a yi mini aiki, kina bacci cikin dare, na kasa bacci saboda damuwar da nake ciki, aka buɗe ƙofar ɗakin, aka zo aka kama hannuna aka laluba cannula, aka yi mini wata allura a cikin duhun nan. Tun da aka yi mini allurar nan. Na ji kaina ya fara juyawa, ina neman na fita hayyacina, duk iya ƙoƙarina na kasa, na ji jikina na ƙamewa kamar zan yi jijjiga. Saɓanin da da idan za a yi mini allura cikin dare, za a ƙwanƙwasa ɗakin, sai kin tashi kin ce a shigo tukuna, a kunna ftila a yi mini" Mummy ta ɗan yi shiru, cike da mamakin me yasa tuntuni ba ta faɗa ba, amma domin kawo ƙarshen maganar, sai kawai ta kawo gigin ciwo ne ya sanya ta ga haka a lokacin. Dan haka ta ce "Duk da haka wannan ma ba hujja ba ce, ke da ki ke fama da ciwo ina za ki tantance wani abu ma. Dan Allah ki bar zancen nan" Shukura ta yi murmushi ta ce "Shikenan, na bar shi" Sai kuma ta sake cewa "Mummy, Nana shiru, ni yakamata ki kwatanta mini gidan da suke na kai mata Haidar" "Gidan Alhaji Garba giwa ne fa, kuma fafur babanku ya hana ni zuwa ban san dalili ba" Dummm! Ƙirjin Shukura ya buga, ta ce "Saboda ne ya hana ki zuwan?" "Ban san dalili ba, za ki je ne? Sabon gidansa nan Kano" Shukura ta ce "Wace matar ce a gidan?" "Halima ce, uwar gidan sa" Shukura ta girgiza kai ta ce "Ba zani ba, gidansu tsohuwar matar Sagir ce" Mummy ta waro ido ta ce "Ke haba? Dama 'yar Halima ce matar Sagir ɗin?" "Eh mana" "Ikon Allah, da na ce wa Daddy, ya taimaka musu, a samo wa mijin Nana, gurin da zai yi gadi, su samu su zauna, shi ne aka samo gidan" Shukura ta ce "wai canza masu gadi ku ka yi ne?" "Ina fa, ina nan cikin gida, daga baya ma Yusuf yake gaya mini. Wai zuwa aka yi da motoci da alama daga ƙasar su ne ma, motocin duk rubutun fransanci aka kwashe su kaf, kuma babu wanda aka yi wa bayanin me yasa" "Ikon Allah, kuma ba laifi suka yi ba?" "To ina zan sani, ina nan cikin gida?" Suka ci gaba da tattaunawa da jajanta lamarin. Har wayar Nana suka jarraba kira, su ji ko ita nata mijin yana nan, ba a kama shi ba amma wayarta ba ta shiga sam. **** Da safe Nana ta tashi, ta fara alwala sannan ta zuba wa Sayyid ruwan da yara suka ɗebo musu jiya, dan gidan babu ruwa. Ya yi alwala a ƙofar ɗakin, sannan suka koma ciki ya yi salla. Sai dai bai ga alamun ta san abin da ta yi cikin daren jiya ba. Ƙarfe tara da rabi, Uwani ta aiko yara da kunu da 'yar tsala aka kawo wa su Nana. 'yar aiken ta ce "Uwani ta ce idan kin gama karayawa, wai ki je" Nana ta ce "To, zan zo a ce mata mun gode sosai da sosai, Allah ya biya ta" Ta koma ta zauna a gaban Sayyid ta ce "Sayyid, ka ga kunu ne da 'yar tsala za ka iya ci, ko na nemo maka wani abin?" Ya girgiza kai. "To za ka iya cin wannan ɗin?" Ya gyaɗa mata kai. Kunun tsamiya ne, na daka ba niƙa ba, ya sha kayan ƙamshi, sai dai babu suga ko kaɗan a ciki, ga tsamiyar nan cau har ka. Ƙuli-ƙulin 'yar tsalan, ya sha barkono, ta zuba masa a kofi ta ba shi. Ya saka hannu ya karɓa. Tun da ya yi kurɓa ɗaya, ya yi shiru. Nana ta ce "Za ka iya sha kuwa?" Ya jinjina kai ya ci gaba da sha, saboda Nana. Ya haɗa da 'yar tsalan nan, duk da ba son Abincin yake yi ba. "Sayyid, idan ba zaka iya cin Abincin nan ba, ka bari na nemo maka wani" Ya ɗaga kai ya kalle ta, sai dai ba baki, dan haka ya harare ta, ya ci gaba da cin abincin. Ta yi murmushi ta ce "Ni ka ke harara ko, aishikenan" Ya gama karyawa, ta saka ɗankwalinta, ta goge masa bakinsa da hannunsa. Ta ce "Bari na je kiran da Uwani take yi mini, daga nan na saka a raka ni, na ɗan yi mana sayayya, dan na san dole za ta daina bamu Abinci yau da gobe sai Allah" Bai ba ta amsa ba, ya jingina da bango, saboda yadda yake jin daɗin hakan, yana lumshe ido. "In je?" Ya yi mata shiru, kuma yaƙi yi mata wata alamar, da za ta gane ya amince ko a'a. Cikin shagwaɓa ta ce "Sayyid" ya kawar da kansa gefe, ya ƙi buɗe ido. "Duk da maganar nan ɗaukewa take yi, amma dai tun asalinka miskili ne, ina ta magana ka ƙi kula ni, ni ce fa rayuwartaka guda ka ke wa haka?" Murmushi ya yi, tare da saka hannunsa a cikinta, yana shafawa a hankali. "Wai ba za ka kalle ni ba?" Ta yi maganar tana juyo da fuskarsa. Ya ƙara rintse idanunsa, wai ba zai kalle ta ba. Nana ta din ga dariya. Ya ja jikinsa a hankali, ya kwanta a kan cinyarta, ya zuba wa cikinta ido, tamkar zai gano abin da yake cikin. "Idan na haihu na ga yadda za a yi, da kai da jaririn wa zai bar wa wani cinyar nan" Ta yi maganar tana shafa gashin sa. ***** Hajiya Sa'a ce take cin abinci, tana kallon Jamila, da take ta cakala kaɗan-kaɗan. "Jamila ya ne? Ki saki jiki ki ci abinci mana" Jamila ta jinjina kai ba tare da ta ce komai ba. "Ko dai haryanzu abin da ya faru ɗin ne yake damun ki? Tun wuri ki ajiye wannan abin, ki ci gaba da rayuwar ki cikin kwanciyar hankali. Ɗan ƙaramin abu ne fa, ranar da aka ce ki bayar da jini kuma ya zaki yi? Ki na gani Safiyya ta tafi Dubai ma sarin kaya, kuma duk harka ce ta ƙungiya ta ɗaukakata haka. Har gara ke ma da ba ki da aure, Safiyya da aurenta, amma kalli yadda ta kama ƙasa, mijin ma ita yake yi wa biyayya, ki saki jikinki dan Allah ki daina wannan damuwar. Ki ƙarasa cin abincin, Talatu ta gyara gidan, idan an zo ana son kaya, kin san gurin da suke, zan je sake duba Fatuhu ne, daga nan na je a gyara mini kaina" "To Mummy a dawo lafiya" "Yauwwa Daughter Allah ya sa" Ta gama abin da take yi ta fita, bayan fitar ta, Jamila ta tashi ta nufi harabar gidan, tana kallon flowers ɗin da aka ƙawata harabar da su. Jibga-jibgan motocin Hajiya Sa'a uku na hawa. Ga na ɗanta Abba biyu. Iya harabar gidan abar burgewa ce, ta yadda duk mai rai zai yi fatan ya samu wannan wadatar. Sai dai kash, hanyar da aka bi gurin tara dukiyar, duk wanda ya ji muddin yana da imani, sai ya gudu da ƙafafuwansa. Ji ta yi kamar wani abu yana bin wuyanta, ta juya a hankali ta ga Abba ne a tsaye, yana saka abin fulawa a wuya. Ta yi guntun murmushi ta ce "Yaya Abba" "Na'am ƙanwar Abba. Ya na ganki nan lafiya dai ko?" "Lafiya ƙalau, ba ka fita ba?" "Yau ba zan fita ba, ba na jin daɗi ne gaba ɗaya, dan da zazzaɓi ma na kwana wallahi" Cikin tausayawa ta ce "Kash, sannu Allah ya ba ka lafiya. Ka je Asibiti mana" Abba ya ɗan numfasa ya ce "Na sha magani already, dan haka ba sai na je ba, zo mu je mu zauna ki yi mini hira, na san zazzaɓin zai sauka gaba ɗaya" Dariya ta ɗan yi ta ce "Ai ni ban iya hira ba" "Ba wani nan, amma ki na yi da Mummy ai, gaskiya mu je sai kin yi mini" Tana dariya ya wuce gaba ta bi bayan sa. Sanyin halin Abba ya fara tasiri a zuciyar Jamila. ***** Alhaji Fatuhu na zaune, Hajiya Suwaiba ta gama gyara jikinsa, fuskarsa ɗauke da damuwa, ya kalli uwar 'ya'yan nasa ya ce "Haryanzu Fadilan ba ta haihu ba?" Ta taɓe baki ta ce "Tana can ba ta haihun ba tukuna." "Allah ya sauke ta lafiya" ta yi shiru ba ta amsa ba. "Yakamata a sallame ni na koma gida haka, na gaji da zaman Asibitin nan gaba ɗaya" A hasale ta ce "To mu koma gida mu yi yaya ne? Nan ɗin ba dai magani ake baka ba ana kula da kai, komai sai ka nuna kai ba a kyauta maka ba, ba a iya ba haba dan Allah" Jiki a sanyaye ya ce "Yi haƙuri, Allah ya baki haƙuri" daga haka ya sunkuyar da kansa. Sai kuma jikinta ya yi sanyi, ta zauna a kusa da shi, tana tunanin ta yi magana. Ta ga yana share hawaye. Cikin damuwa ta ce "Alhaji kuka ka ke yi? Dan Allah ka yi haƙuri raina ne a ɓace, amma dan Allah ka yi haƙuri" Ya yi mata shiru, gaba ɗaya ta rikice ta rasa abin da za ta ce. Raudah ce ta turo ƙofa hannunta da towel ta ce "Daddy guess what?" Ta miƙa masa narkeken jaririn da Fadila ta haifa. Hannunsa na karkarwa ya riƙe jaririn ya ce "Another Muhsin" ya yi maganar yana murmushi. Ya din ga yi wa jaririn kiss, yana shafa shi kamar ba a taɓa yi masa haihuwa ba. **** Fafur Sayyid ya hana Nana zuwa ko nan da can, har aka yi azahar.Uwani ta sake aiko musu da dambu, ta ce a cewa Nana ba za ta zo ba, sai ta zo da kanta. Cikin damuwa ta ce "Sayyid dan Allah ka bari na je, na ji kiran me take yi mini" fafur ya sha kunu ya tsuke fuska. Babu yadda Nana ta iya, ta zauna ta ƙi fita. Ta zazzage kayansu, tana ƙara gyara musu, ta fito da kayan wankin gashinsa, da turarrukansa da duk wata sai su Habu sun sayo sun kawo. Ta ɗaga kai ta ga ita yake kallo, ta ɗan yi murmushi ta haɗe su a guri ɗaya da combs ɗin sa na taje gashi. Sai yamma bayan sallar la'asar, ta yayyafawa tsakar gidan ruwa, ta share shi. Ta yi shimfiɗar tabarma a tsakar gidan, ta saka wa Sayyi fululluka ta kamo hannunsa zuwa waje. Ya zauna, ta ɗaukko mayafin rawaninsa ta yafa masa a kansa. Babu jimawa sai ga Uwani ta zo, tana faɗin "Tun da ba za ki zo ba, ni ga ni na zo da kaina" Nana ta ce "Ba ƙin zuwa na yi ba Uwani, yanayin jikinsa ne sai a hankali, shi yasa ban fito ba" "Koma dai mene ne gani na zo ai" Ta kalli Sayyid ta ce "Sannu ko" ya jinjina mata kawai. "Dama kiran ki nake yi, na ji idan akwai wani abu da ku ke buƙata?" "Eh, ina son yin sayayya ba mu da fitila sai ta waya, da kuma 'yan kayan buƙatu" "To da kin sanar, ai da na saka yara sun raka ki, dama zan ce miki kuma idan an kwana biyu, yakamata ki zo a ɗan zagaya da ke cikin dangi, su san kina garin nan, tun da dama ba zuwa ku ke yi ba, dui ba sanin ku aka yi ba" Nana ta jinjina kai ta ce "To in sha Allah" "Wai ni Nana ina Mai jidda kuwa?" "Tana can Bauchi inda take aure" Uwani ta ce "Kuma tana zuwa?" Jiki a sanyaye Nana ta girgiza kai. "Ai dama na san babu lallai ta zo, ko dan saboda baƙin halin Isa. Ai ya bamu mamaki. Ita ma tun da suka rabu ba ta sake zuwa garin nan ba. Kuma yakamata mu je na zagaya da ke, har inda danginta suke a nan" Cikin mamaki ta kalli Uwani ta ce "Danginta kuma?" "Ƙwarai da gaske, tushen Maijidda garin Buda ne. Kakanninta 'yan nan garin ne, can wajen unguwar Wanzamai, ƙarewa ma a nan garin suka haɗu da babanku. Ai kakarta aka raina a Bauchi, aka haifi babarta da ita a can. Har an saka mata rana, suka zo garin nan, ke ma Babanki ya zo gida, suka haɗu a dandali. Aka yi ta ɗauki ba daɗi suka ƙulla soyayya. Ga shi can garinsu an saka mata rana da wani, ina ga shi ne mijinta na yanzu da take aure. Asali tun kan ta auri babanku da shi aka fara saka mata rana. Kakarta ta ce sai an warware wancan baikon ta auri babanku, ko ba komai sa din ga zuwa gida a kai kai. Haka aka mayarwa da wancan kuɗinsa ta auri babanku. Ya Babanku ya  so ta sosai da sosai, kuma aka ƙulla auren nasu da tunanin hakan ya ƙara kawo zaman lafiya a tsakanin zuriyarmu da zuriyar wanzamai kin san a tarihin garin nan ba zaman lafiya ake ba. Kuma dai cikin ikon Allah sun fara zamansu lafiya gwanin sha'awa, amma Allah ya ƙaddara rabuwar su." Nana ta yi shiru tana tunanin, kamar ta san wani abu mai kama da wannan labarin da Uwani take ba ta, amma sam ta kasa tunawa. Gaba ɗaya hirar ta Uwani ta gundure ta, saboda ta san shi kansa Sayyid a takure yake, ba ya son mutane ko kaɗan, balle uwa uba dogon surutu. Ita kuwa Uwani tamkar an ƙona ta a ka ko gajiya ba ta yi. Babu wanda ya taɓa ba ta wannan labarin, sai yanzu babu wanda ya taɓa gaya mata cewar mahaifiyarsu tushenta a garin Buda yake, sai dai kamar ta san labarin da Uwanin ta bata. "Ga wata 'yar rama na zo muku da ita, sai ku ci kafin Abincin dare ya sauka. Wai shi mijin naki kurma ne?" "A'a ai kin ga ba shi da lafiya ne" "Eh gaskiya ne, Allah ya ba shi lafiya, amma a ina ki ka samo Buzu haka? Ni wai anya ma labarin da Rabi ta din ga bayar wa ranar bikinki nan gaskiya ne? Abin dai da mamaki. Allah ya ba shi lafiya bari na tafi, dan Allah idan ki ka samu lokaci kya zo a je a gaggaisa. "To in sha Allah zan zo" "Yauwwa, zan din ga turo miki yara, idan da aike kya din ga ba su, duk 'yan uwanki ne, 'ya'yan 'yan uwa ne. Kuma ki kwantar da hankalinki duk abin da ku ke buƙata ku sanar mini, da yardar Allah ba zai gagara ba" Nana ta ce "In sha Allah, mun gode sosai da sosai" "Ba komai, ki yi haƙuri ki riƙe mijinki ki kula da shi, sai ki ga kaf ayyukan ki, Allah bai karɓa ba, silar wannan jinyar ta sa ki shiga aljanna, a yi ta haƙuri yayata" Nana ta tashi ta raka ta, ta ce "In sha Allah" Ta yi ƙasa da murya ta cewa Nana "Dan ubanki, ki din ga ɓoye mijinki, kar ki bari 'yan mata su din ga zuwa su na kallon sa." Uwani ita iya rage muryarta kenan, amma Sayyid na jin ta. Nana ta ɗaga kai suka yi ido huɗu, ya yi murmushi yana sunkuyar da kai. ***** Alhaji Fatuhu, farin cikinsa ya kasa ɓuya, duk da halin rashin lafiya da yake ciki, idan aka zo duba shi, sai ya yashe haƙoransa da sukaɗai suka rage farare a jikinsa. Alhaji Zailani ya ƙura wa jaririn ido, ya kalli Alhaji Fatuhu da yake ta yashe baki. Hajiya Sa'a ta ce "Kai Fatuhu. Sai ka ce ba a taɓa yi maka haihuwa ba, ji yadda ka ke washe baki, kana fama da kan ka" Hajiya Suwaiba ta kwaɓe baki ta ce "Abin da na gani kenan" Alhaji Zailani ya ce "A'a ku bar shi ya yi, ɗan mutum fa, kyauta ce Allah ya ba shi, da duk Duniya babu mai ba shi. Ni ba gani ba 'ya'yan duk babu sai biyu ne suka tsaya." Ya yi maganar yana zuba wa jaririn ido, yana tuna na Shukura. Tun da yake harkar ƙungiya, bai taɓa bayar da jinin da ya tsaya masa ya kasa mantawa ba, sai na Shukura. Mussaman idan yana tuna irin baƙar wahalar da ta sha. Ya kalli Fadila, da take ɗakin a zaune, ga jego tana yi, amma ta tare a Asibiti da ɗanyen jaririn da ko suna ba a yi ba. Ya yi ajiyar zuciya ya ce "Wane sunan za ka saka masa?" "Muhsin ɗina zan mayar" ya yi maganar muryarsa ɗauke da rauni. Hajiya Sa'a ta ce "Wai an din ga saka Muhsin ɗin kenan?" "Sunan mahaifin Fadila ne, shi za a mayar mu ci gaba da kiransa Muhsin, ni na yi mata alƙawari shi yasa. Na so Muhsin ɗina da ya rasu sosai da sosai. Na ji zafin rashin sa, sai dai ina tausayawa wannan Muhsin ɗin. Ya zo lokacin da mahaifinsa ba shi da komai, ba zan iya ɗaukar nauyinsa na kula da shi ba. Wataƙila ma kafin ya yi wayon sani na na rasu. Ga shi ko hakika ba zan iya yi masa ba" ya yi maganar hawaye na zubowa daga idanunsa. "Haba Fatuhu, ya haka? Dan dai Hakikar da za ayi wa jaririn nan, ka san ba za ta gagara ba, amma ya za ka zauna kana kuka kamar ƙaramin yaro, a gaban iyalinka da 'yan uwanka hakan bai kyautu ba ai". Alhaji Fatuhu ya ɗago idanunsa da suka yi jawur ya ce "Zailani. Ka san me nake ji kuwa? Gidaje da motocin hawa nake da, ina kyautar maƙudan kuɗaɗe ba tare da na ji komai ba, da abu ya dame ni, zan sai ticket na tafi umara. Ina da shaguna dukiya Allah ya yarje mini, bayan gwagwarmaya da na sha ta rayuwa. Astagfirillah ba ƙarar Allah nake kawowa ba, ko rashin imani da ƙaddara ba, ina jinjina girman lamarin Ubangiji, kuma ina jin babu daɗi ɗa na na cikina, ba zan iya saya masa ko wando ba" Fadila ta ce "Dan Allah Daddy ka yi haƙuri. Mu na murna sauƙi yana samuwa, ga shi ka na ta magana sosai da sosai, kukan nan karya mana zuciya yake yi. Kuma da ka yi mana a baya, yanzu kuma da Allah ya kawo jarrabawa shikenan sai a yi haƙuri" Su na nan zaune, sai ga ƙanin Baban Fadila, ya zo duba Alhaji Fatuhu ya kuma jaririn Fadila, wanda shi ne waliyyin Fadila. Sai dai shi ma ya tsorata da ganin Alhaji Fatuhu. "Alhaji haka jiki ya zama? Subhanallah Allah ya baka lafiya" "Amin kawu, amma jiki ya yi kyau Alhamdillah, tun da ina ta magana" "Haka ne, amma menene takamaiman abin da aka ce ya same ka ne?" Fadila ta ce "Haryanzu ba a gano takamaiman mene ne ba, yau a ce ƙodarsa ta kumbura, gobe a ce ko cancer ce, an yi gwaji ba ita ba ce. An yi gwajin zuciya shi ma lafiya ƙalau" Cikin damuwa ya ce "Amma Fatuhu ana haɗa maka da na addini kuwa? Ka san muna da ido ne ba na ganin gari ba. Mussaman ku da ku ke shahararrun mutane da Allah ya ba wa wadata. Yakamata a yi na sihiri da shaiɗanu" Alhaji Zailani ya ce "A'a ga likitoci su na kula da shi, ya za a yi a ce kuma a kawo wani abu daban? Magungunan gargajiyar nan kashe mutane suke yi ai, tun da ba auna su ake yi ba". Alhaji Fatuhu ma ya ce "A'a ba wannan ba ne, wa ya damu da ni da zai yi mini sihiri. Larura ce kawai kuma likitoci na kula da ni" "Kai, kalle ni da kyau. Duk bokon ka, nima ɗan boko ne, kuma na san ilimin addini, amma sihiri da shaiɗanu gaskiya ne. Tun da aka yi Annabi Sallallahu alaihi Wasallam sihiri, duk duniya ban ga wanda ba za a yi wa ba. Ciwo ya ƙi ci ya ƙi cinye wa ai akwai alamar tambaya, ga lalacewar dukiya lokaci guda. A dai tsananta addu'a. Ya gama bambaminsa ya fita. Alhaji Zailani ya din ga ziga Alhaji Fatuhu, tare da kushe magungunan gargajiya. Ba tare da jin nauyin Fadila da take gurin ba. Ya gama soki burutsunsa, ya tashi ya yi musu sallama, tare da cewa zai aiko da abin hakika. Har ya kusa ƙarasa wajen motarsa, ya waiwaya ya ga Hajiya Sa'a ta nufo shi, ya tsaya ta ƙarasa. Ya ce "Ya dai?" Ya yi maganar yana kallonta. "Zailani" "Na'am "An sauke ɗan uwana daga shugabancin 'yan kasuwa an ɗora ka, ka saka an dawo da shi Asibitin nan, ƙarƙashin kulawarka, an ce a yi masa maganin gargajiya ka haƙiƙance kana kushewa. Kar ka kuskura na tarar da sanya hannunka, a cikin wannan abubuwan da suke faruwa da ɗan uwana" Ya gyara tsayuwarsa ya yi murmushi ya ce "Babu sanya hannuna a ciki. Ina ƙoƙarin zama aboki mai halacci ne kawai. Sannan ki daina mazewa kamar ke ɗin mai ƙaunarsa ce, bayan sadaukar da 'ya'yansa maza da ki ke yi" "Duk da haka, munin abin da na yi bai kai wanda ka ke aikatawa ba, ka fi ni sanin kai da me da me ka sadaukar, dan haka ka kiyaye ni". Ta juya ta koma. Bin bayanta ya yi da kallo, ya ji wani abu ya tsirga masa, tabbas idan Hajiya Sa'a ta ci gaba da wannan gigin, zai ɗauki matakin da ya dace a kanta." ***** Cikin bacci, take jin hayaniya  a bayan ɗakin, tamkar ana cin kasuwa. Ga wata irin sukuwa da take ji a roofing ɗakin, tamkar ta dawakai. Tun da ta farka sai juyi take yi, bacci ya gagari idanunta, ayatul kursiyyu ce ta zo bakinta ta din ga maimaitawa, har ta samu nutsuwa daga razanin da take ciki. Ta ruge idanunta, sai dai a maimakon ta yi bacci, sai wata irin kewar Sayyid take addabar ta. Ta rasa dallin da ya sanya, ba ya kula ta yanzu. Duk da ba shi da lafiya tana yi masa wannan uzurin, amma duk da haka da ya kan yi attempting sai ya ƙyale ta, yanzu kuma gaba ɗaya ya daina yinƙurin aikata komai ma. Wanda da idan ya sako ta gaba, har takura take yi. Ta tashi zaune ta gyara maganin sauro, ta taka a hankali ta ɗaga labulen ɗakin, saboda zafi. Ta dawo ta ɗauki fitilar wayarta ta kunna. Ta haska shi ta ga idanunsa a lumshe, yana bacci. Ta zuba masa ido, ta fara tunanin ko ita ce mai matsala gaya mata ne bai yi ba, ko ma sharrin Ƙaisar ne?. Ta yi ajiyar zuciya, ta kashe fitilar, ta kwanta a gefen sa tana wasa da gashin ƙirjinsa. Zuwa na fuskarsa. Ta sake matsawa a hankali, tana sumbatar leɓansa, tamkar mara gaskiya. Gaba ɗaya a tunaninta bacci yake yi, sai da ta ji ya sanya hannayen sa, ya zagaye ta, tare da ba ta damar sumbatar bakin nasa. Nana za ta iya cewa, tun da Allah ya sa ta buɗi ido a duniya, ba ta taɓa jin kunya irin ta yau ba, cikin sauri ta fara ƙoƙarin rabuwa da jikinsa ta matsa, amma ya mirgina ya rungume ta gam a jikinsa yana numfashi a hankali. Ayshercool 08081012143 56 Yana jin yadda jikinta yake tsuma, tamkar wadda aka kama tana aikata wani abin ashsha! Ko kuma wadda ake kaɗawa mazari. Magana yake son yi mata, amma abu ya gagara, duk ƙoƙarin da ya yi amma abu ya ci tura. Ya ƙara ƙanƙame ta tamkar wani zai ƙwace ta, ya din ga murza hannunta har ta fara jin zafin riƙon da ya yi mata. Yanayin ya ƙara ninka mata halin da take ciki, ta rintse idanunta. A hankali ta ji yana hura mata iska a cikin kunnenta, tamkar yana zuba mata wani sindari, haka ta ji wani irin nannauyan bacci ya yi awon gaba da ita. Ƙamshin nan ta ji yana ratsa hancinta, ta buɗe idonta a hankali, kamar yadda ta yi tsammani, a wannan ɗakin ta gan su. Ta hau waige-waige. Ta wata ƙofa ta ga ya fito, ƙugunsa ɗaure da wani abu kamar zani, ya zauna a kusa da ita yana kashe mata ido. "Sayyid ka warke?" "Eh mana" "Ka daina jin duk abin da ka ke ji?" Ya jinjina kai yana murmushi. "To ka yi mini magana mana" "Ma vieee" ya faɗa yana ɗan jan maganar yana kwanciya a gefen ta. "Har na ji daɗi da ka samu lafiya, Allah ya ɗorar maka da sauƙin nan Sayyid" "Amin rayuwata, matso ki kwanta mu yi bacci" Ta noƙe kafaɗa ta ce "A'a"ya saki murmushi yana kama hannunta. Duhu ne ya gauraye ɗakin. Dariya ta fara jin Sayyid ɗin yana yi mata cakulkuli. Ta kasance da shi cikin wani yanayi mai tsayawa a zukata. Ba ta iya tantance a wani hali take, ta daina ganinta a ɗakin, sai a libraryn Ƙaisar. Ta tsaya tana kallon gurin, tana tunanin yaushe rabon da ta zo gurin nan. Ƙaisar ta hanga, a tsaye yana gyara litattafan sa. "Ƙaisar ka warke kenan?" Yayi shiru yana goge wani littafi, ya gama ya ajiye littafin sannan ya ce "Eh, na warke. Waye ya ce ki je ƙauyen nan?" "Ban gane waye ya ce na je ba? Zan kwana a titi ne? Ga mara lafiya ina da shi" "Gaskiya ne, bai kamata ki kwana a titi ba. Wannan dalilin ya sanya tun a farkon auren nan, na din ga haska miki matsalolin da za ki iya fuskanta, amma gani ki ke yi kamar ƙarya nake yi, to yanzu sai ki san yadda za ki yi, ki rayu da ke da wannan lanjararren mijin naki, da duk larurar duniya ta ƙare a kansa". A ƙule Nana ta ce "Larura Allah ne ya ɗora masa, kuma kun taka muhimmiyar rawa a larurarsa. Kuma ka daina ganin laifina. Zan tsallake shi ne a wannan yanayin da yake ciki, na bar shi? Mu bil adama mu na da bambanci da ku, mu na da tausayi da kuma nuna kulawa ga waɗanda muke ƙauna" "A'a kar ki tsallake ki bar shi, amma ki yi ɗamara fiye da ta baya, garin Buda ki ka zo za ki zauna, ban sani ba ko kin fahimci abin da nake faɗa ko ba ki fahimta ba. Idan ma ba ki fahimta ba, za ki gane daga baya. Bil adama ku na tausayi da nuna kulawa ga wanda ku ke ƙauna, ku ke iya ɗaukar jinin makusantanku ku bayar, a yi muku tsafi ko? Da kyau matsala kuma ki sani, ba ki ga komai ba" Daga haka ya ɓace ɓat. Ta buɗe idonta a hankali. Tana buɗe idonta, ta ji ana kaɗa kacakaura, da garaya a tsakar gidan su. Ana ta hayaniya tamkar ana cin kasuwa a tsakar gidan. Sanyi ta fara ji yana ratsa ta, bugun zuciyarta ya ƙaru, fiye da da, waiwaya ta yi tana son ganin ta inda za ta ga Ƙaisar, ko makamancin hakan amma ba ta ga kowa ba. Wata irin guɗa ta ji an rangaɗa da wata irin murya, mai sauti, sai kuma aka ce "Yeeee barka da zuwa wakilin rafi, ku matsa ku bayar da hanya ga ango mairamu ya iso" ta ji wata murya na faɗa, ana ci gaba da shewa da kaɗe-kaɗen garaya. "Ku kawo Nono da suga, a kirawo 'yar Mairo ga mijinta ya iso. Ga farin goro ƙwarya dubu biyu ta rafi ta ce a bawa mamman wakilin rafi, gaisuwar iyaye" sai kuma aka saka shewa. Ba yau Nana ta fara ire-iren wannan jiye-jiyen ba, amma ta tsorata da wannan sosai da sosai. Ta rirriƙe Sayyid, ga sanyin da take ji ya fara damunta. Cas cas cas, ta fara jin sautin kaɗawar wani abu mai kama da abin ado na mata. Ta kalli tsakar gidan ta hango wata irin zanƙaleliyar mata, mai tsawon gaske ƙafafuwanta duk sarƙoƙi, ta yi shigar Fulani, sai dai ita ma ba a iya ganin sawayenta tamkar a kan iska take tafiya. Ta ɗan ƙara buɗe idonta, ta ga rana ce tarwai a tsakar gidan, ga dandazon mutane ana ta hada-hada. Sai dai shigar mutanen irin na zamanin da ne can baya sosai, kamar dai taron wani abu ake yi. Wata mata ta hango sanye da kayan saƙi farare tas, ƙugunta sanye da wuri, kanta babu ɗan kwali duk ta yi wa tulin gashinta adon wurin, hannunta riƙe da sandar dargaza, tana kaɗa ta tana juyi. Wannan bafulatanar ce ta tsaya a bakin ƙofar ɗakin Nana ta ce "Baƙuwarmu, bikin girka ake yi, ko za ki taso ki ga yadda muke gudanar da al'adun bikin girka?" ta yi maganar tana zuro zanƙalelen hannunta cikin ɗakin Nana". "La'ilahaillalah, Sayyid, Sayyid wayyo Baba" ta tashi a gigice, rirriƙe ta ya yi, ya janyo wayarta, ya haska ta. Fuskar sa cike da mamaki yake kallon ta, yanayin fuskarsa ke bayyanar da alamar tambaya. "Sayyid wata mata ce, wata mata ce take ziro hannunta, tsoro nake ji, wasu mutane ne a tsakar gidan nan" ya haska ɗakin ta ga babu komai, haka tsakar gidan ma dare nesai hasken farin wata, babu komai. Sai a lokacin ta fahimci mafarki take yi. Ya ji jikinta ya yi sanyi ƙalau, amma bai ga Ƙaisar a gurin ba, bai kuma ga wata alama da take nuna yana gurin ba. Gaba ɗaya ta nemi ko addu'a ɗaya, ta rasa a cikin kanta. Ta kaɗa ta raya amma babu abin da ya zo da kanta. Tana so ta karɓi wayarta ta kunna karatun Alƙur'ani, amma ko ƙwaƙƙwaran motsi ba ta son yi, saboda tsoron da take ji. Da ƙyar wani baccin ya ƙara sace ta. Babu babban abin da ya ba shi mamaki, irin yadda da safe take komawa normal, babu ma alamar akwai wani abu da yake ba ta tsoro cikin daren. Haka ta ci gaba da sabgoginta. Sai dai gaba ɗaya a kunyace take, ko idonsa ba ta iya kallo, saboda abin da ta aikata ya kama ta cikin dare. Shi ga tausayin kan su, ga kuma dariya ta ba shi. ***** Baba yana zaune yana shan koko da ƙosai a tsakar gida, sai ga kiran wayar Uwani. Ya kalli wayar tasa ya ce "Tofa! Wannan jarababbar tsohuwar ko me za ta ce mini, take kira na da safiyar nan oho. Ya ɗaga kiran ya saka a kunnensa. Sai dai ba ya jin ta sosai saboda rashin network. Ba ta haƙura ba ta din ga kira har sai da ransa ya fara ɓaci. "Uwani ko a haƙura da wayar ne, kin ga babu network ne" "A'a ina jin ka yanzu. Amm dama kiran ka na yi, na tambaye ka ina Nana kuwa?" "Nana, tana gidan mijinta" "Gidan mijinta wanne?" "Mijinta dai na aure" Uwani ta ce "Eh a ina gidan yake?" "Amm can wajen gidan Ummi ne" "Rufe mini baki, mutumin banza da na wofi. Ai kwana uku kenan ina neman layinka, amma bana samu saboda garin nan bamu da natiyok ake cewa ko me?" "Uwani wai me ya faru ne?" "Ai ba za ka san meyafaru ba, tun da ka bar yarinya tana ragaita ita kaɗai ranta ga miji mai larura,an kore su daga gidan haya, ba su san ma inda za su je ba, kana zaune hankalinka kwance. Ai ko 'yar riƙo ce Nana ka duba lamarinta" Ta inda ta shiga ba ta nan take fita ba, ta wanke shi ta tas, ta ƙare masa zagi da cin mutunci, ta ce kuma za ta kira Yaya Atine ma, sai ta ci ubanta. Ran Baba ya yi mummunan ɓaci, kenan Ummi da Nana haɗa kai suka yi, suka kai ƙararsa gurin Uwani. Ya kira Ummi ita ma ya fara sauke mata kwandon tijara. Ranta ya ɓaci ta ce "Ni fa Baba ban kai ƙarar ka gurin kowa ba, Uwani ce ta kira waya,  mu na tsaka da alhinin halin da Nana ne ciki, na gaya mata komai, kuma ni na faɗa ba Nana ba. Shi ne ta ce Nana su koma Ƙauye can gurin ta". Sai kuma Baba ya yi sak. "Ƙauye kuma? Ta yi me a ƙauye?" "To Baba zaman nan ɗin ya ƙi, kai kuma ka ƙi taimakawa, babu yadda muka iya Nana tana Buda" "Ke Ummi ki na ji na, duk yadda za ki yi, ki nemi kuɗin mota, ki je Buda ki taho mini da 'ya ta. Lallai ya sakar mini 'ya ku taho tare, ya je Allah ya ba shi lafiya" "Baba ya sake ta, 'yan uwansa ma ba a sa inda suke ba, wa za ta bar wa shi a can?" Yana cikin bambami kuɗin wayar suka ƙare. Dama Mama na tsaye tana jiran ya gama wayar, yana gamawa ta dube shi ta ce "Wato Nana ta kaso aurenta ta dawo ko? To wallahi ta dawo gidan nan ba ta da gurin zama, wai har ka manta irin zaman azabar da muka yi da yarinyar nan a cikin gidan nan? Babu bacci kullum bala'i da tashin hankalin iskokai, ba zai yiwu ba wallahi" Sai dai kafin Baba ya ba ta amsa, suka ji Suwaiba ta ƙyaƙyace da wata irin dariya mara daɗin ji tana faɗin "Asma'u a ƙauyen Buda, tushiya masomar dawa, kowa ya bar gida gida ya bar shi" ta yi maganar tana ci gaba da ƙyaƙyata dariya kamar ba mace ba. "Ke Suwaiba meye haka, wannan wace irin dariya ce? Ban hana ki irin wannan dariyar ba kamar ba mace ba?" Suwaiba ta ce "Ina ruwan ki da dariyata" Baba kawai ya gyaɗa kai, ya gyara hularsa ya fice ya bar gidan gaba ɗaya. **** Rashin maganar nan ta Sayyid, ba ƙaramin damun Nana take yi ba, abin ya yi yawa sosai. A wannan karon ta yi sa'a, ya bar ta ta je gurin Uwani, daga nan kuma ta je ta yo musu sayayya. Ta tafi ta bar shi da wayarta, domin ta ɗebe masa kewa. ***** Alhaji Zailani ya saka sabon layin da ya sayo a cikin waya, ya kira lambar Nana. Sayyid yana kwance yana jin yadda wayar take ta vibrating, amma ya yi banza. Saboda ko ya ɗaga ba iya magana zai yi ba. Jin mai kiran ba shi da niyyar daina kiran, ya sanya ya ɗauki wayar zai kashe. Sai dai ya fasa kawai ya ɗaga kiran ya kara a kunnensa. "A tunanki dan kin yi blocking ɗin lambata, zai sanya na kasa cimma burina a kan ki ne? Yanzu hankalina ya dawo gare ki, na saka an kori mijinki daga gurin aiki. Kuma zan nemo ki duk inda ki ka shiga sai na cika burika a kanki" wani irin jiri Sayyid ya ji ya fara ɗibar sa. "Ba za ki yi magana ba?" Alhaji Zailani ya yi maganar yana kallon wayarsa. Wani irin haske ya ga wayar tana yi, tana fafar fafar za ta ɗauke. Mamaki ya kama shi, dan wayar ba ta taɓa yin haka ba. Fitilun ɗakin suka ɗauke, duhu ya gauraye ɗakin nasa. Sai ya rikice ya tashi tsaye yana waige-waige. "Karo na biyu, ka sake shigowa hanyata, duk da gargaɗin da na yi maka, cewar mallakina ce, ina sake yi maka gargaɗi, kafin na tona maka asiri." Alhaji Zailani ya toshe kunnensa, saboda wani irin sauti da yake ji mara daɗi, ga ɗakin yana ta jujjuya masa. Can ya ji shiru ya daina jin sautin, ya buɗe idanunsa a hankali. Sai dai ya ga Shukura a tsaye a gabansa, jini yana bin ƙafafuwanta, ga wuƙa a hannunta, tsirara ta. Ya miƙe cike da razani, ya fara ja da baya. "Daddy ina jaririna? Ka bani jaririna Daddy" Ya ci gaba da ja da baya. Da gudu ta bi shi, da wuƙar tsirararta. Ya fita da gudu yana ihu. "Alhaji lafiya kuwa? Anya hawan jinin nan bai fara taɓa maka ƙwaƙwalwa ba, ya ya zaka din ga ihu haka?" Hajiya Amina ta yi maganar cikin mamaki tana kallonsa. Ya kalli gurin ya gan shi a kan gado, a ɗakinsa. Yana son yi wa Hajiya Amina tambayoyi, amma abu ya gagara saboda tsabar razani da tashin hankalin da yake ciki. AREWABOOKS ***** Uwani ta din ga yawo da Nana a cikin ƙauyen nan, tana nuna ta a dangi, tana gaya musu 'yar gurin Isa ce. Dan galibi ba su santa ba. Nana gaba ɗaya hankalinta yana kan Sayyid da ta baro a gida, shikaɗai tana gudun kar ta je yana buƙatar wani abin. Ganin gantalin ya yi yawa, ga duk inda suka je sai Uwani ta tsuguna ta surutu kamar babu gobe. Tun Nana tana jurewa, har ta gaji ta ce "Uwani, na bar mara lafiya a gida, ko za mu je inda zan yi sayayyar, na koma kar na je yana buƙatar wani abin. Uwani ta ce "Kuma fa haka ne, to mu je na raka ki. Na so ma sai ranar kasuwa za ki je sayayyar, an fi samun rahusa. Ai tun da Allah ya sa ki ka zo garin nan, za ki yi ta ganin 'yan uwa da dangi, za a yi ta zuwa duba mijin naki ma" Ita dai Nana ta yi shiru, dan duk surutunta, Uwani sai da ta saka ta gaji, ga azabar tafiyar ƙafa da suka sha. Ta rakata inda ta yo musu 'yan sayayyar kayan abinci, gaba ɗaya tsoron taɓa kuɗin take yi. Gani take yi kamar ƙarewa za su yi. Uwani ta raka ta har gida, sannan ita ma ta zagaya, ta koma nata gidan. Nana ta shiga ɗakin da Sallama, tana faɗin "Sayyid, ka ganni sai yanzu ko, ka yi haƙuri Uwani ce ta din ga ja na, ƙafafuwana kamar su karye" Sak dai ta yi shiru ganin wata irin kwanciya da ya yi a kife a kan cikinsa, hannunsa a lanƙwashe, kuma ba kamar mai ruf da ciki ba. Ga shi a tsakiyar ɗakin, ba inda ta tafi ta bar shi ba. Ta zube kayan ta nufe shi jikint a sanyaye, gabanta na bugawa saboda fargaba da tsoron ko mutuwa ya yi. Aikuwa tana juya shi ta ɗan ja da baya a tsorace tana sauke numfashi. Wayarta ta gani a ƙarƙashin inda ya kifa, idanunsa a kakkafe, babu baƙar ƙwayar idon, sai farar. Ga jikin zafi rauuu tamkar wuta. Ajiyar zuciya ta yi cike da damuwa, ta matsa kusa da shi ta yi Bismillah ta fara rage masa kayan jikinsa. Ta ɗebo ruwa ta din ga shashshafa masa tana sake nanata Bismillah. Ta je ta rufe ƙofar gidan, ta dawo ta cire rigar jikinta, ta kwanta a jikinsa, tana rintse idanunta saboda raɗaɗin da take ji a fatarta. Wani irin nishi yake, tamkar zai yi gurnani, yana miƙa jikinsa yana ƙara sandarewa. A hankali ta ji tamkar hankalinta yana gushewa, ita ba a farke be, kuma ita ba mai bacci ba. Ta ɗan ɗaga idonta, ta ga Ƙaisar tsaye a jikin ƙofar ɗakin yana kallon su. Ta yi shiru ba ta yi motsi ba, kuma ba ta yi magana ba, fatanta Sayyid ya samu sassauci daga azabar raɗaɗin da yake ji. "Ko dai ki bi a hankali, ko wannan ɗan tayin na cikinki ya yo waje saboda zafin jikinsa. Ko kuma Giyaz ya yi masa mummunar illa." Nana ta ɗaga kai ta kalli inda Ƙaisar yake, jikinta ya yi mata wani irin nauyi, ba ta ko iya motsa ɗan yatsanta. "Babu irin kashedin da ban yi miki ba tun da fari, ki ka yi burus da ni, gani ki ke kawai cutar da ke ne kaɗai abin da nake yi. Amma tun da jimirnki taurin kai, wahala sai ranar da Allah ya yanke miki, tukuna ma." A hankali ta lumshe idanunta har ta daina jin muryar Ƙaisar. **** Cikin damuwa Maijidda take kallon Saude ta ce "Yaya Saude haryanzu lambar Nanan ba ta shiga ko? Gaba ɗaya na kasa nutsuwa duk ji nake hankalina a tashe". Saude ta ce "Dan Allah ki daina damun kan ki, in sha Allah tana cikin ƙoshin lafiya, kin san sharrin wayoyin nan, da rashin network, amma zan ci gaba da kiran ta, da na same ta zan sanar miki, kuma zan sake zuwa har gida na haɗa ki da ita." "To Allah ya sa dai lafiya, kin ga na yi, na yi, na kaɗa na raya, Baban su Walida ya ƙi ba ni wayata, tsawon wannan lokaci haka nake zaune babu waya. Kuma duk wasu dabaru da zan yi na samu dama na je Kano na samu na ga yaran nan, abu ya ci tura sai ka ce ba Muslimi ba, ba ya jin magiya ba ya jin rarrashi". "A'a kul Maijidda, uban 'ya'yan naki ki ke cewa kamar ba musulmi ba, kar ki sake. Ki rabu da shi da halinsa. Duk da Nana tana cewa za ta zo ita da mijinta, idan ma ba su zo ba, ni zan sake komawa na gano miki ita in Allah ya yarda. Iliyasu kuma ki rabu da shi ku lallaɓa kar ki fusata shi ya yi wani abin da ba a fata" Maijidda ta yi ajiyar zuciya, ta jinjina kai kawai, amma gaba ɗaya ba ta cikin nutsuwarta. **** Abu kamar wasa, aka shafe kwanaki biyar, Sayyid yana cikin wannan yanayin, sai dai Nana ta juya shi, ta goge masa jikinsa, ta yi masa ƙanin wanka a ɗaki, ta shafa masa turare ta saka masa kaya. Ga shi juya shi kawai aiki ne, saboda yadda ya yi mata nauyi, ga jikinta babu ƙwari saboda azabar laulayi. Juriyarta ce kawai ta sanya ba a gane mawuyacin halin da take ciki, dan ba ta taɓa yarda ta kwanta. Ga shi jikinsa duk ya kumbura, mussaman ƙafafuwansa. Tana zaune ta yi shiru tana kallonsa, kawai tamkar an yaye mata wani abu daga kanta, sarkin baka ya faɗo mata. Sai da ta ɗan zabura ta tafi tunanin ko yana wani hali yanzu?. "Ko dai can zan kai ka Sayyid?" Ta yi maganar tana kallonsa. "To ni da ban ma san a ina yake ba, ta yaya zan kai ka?" "Kul mene ne sahihancin magungunan da yake bayarwa? Mene ne halacci ko haramcin abin da yake yi, da za ki je neman magani gurinsa?" Wata zuciyar ta gargaɗe ta. Sai kuma ta yi shiru, tana tuna irin wahalhalun da ta sha, da faɗi tashin gurin masu magani, ita dai tana da yaƙinin har gurin bokaye da 'yan tsubbu an kai ta, domin a nema mata magani. Domin wasu ƙarara ayyukansu da abubuwan da suke faɗa, ne nuni da kaucewa hanyar gaskiya. "Allah na tuba, Allah ya sanya ba wannan ne dalilan da ya sanya nake ta shan wannan wahalar ba. Allah ka yafe mini, ba da son raina aka din ga kai ni wasu guraren ba. Allah ka bamu lafiya da ni da mijina, Ubangiji Allah ka yaye masa wannan larurar, ka dawo masa da tunaninsa. Allah ban yanke tsammanni da daga falalarka da ni'imamominka ba" Ta juyo a hankali ta dubi gurin da yake, ta ga idanunsa sun dawo daidai yana kallon ta. A rikice ta ce "Sayyid" "Ma vie" Cikin tsananin murna ta ce "Alhamdillah, ka tashi?" Ya jinjina kai yana lumshe idanunsa da suka yi masa nauyi. Ya ja jikinsa ya tashi zaune da kyar. Sai dai jikin nan duk a kumbure,ga kuma haki da ya farfaɗo da shi. Haka yau ma ta taimaka masa ya yi wanka ya ci Abinci ya fara rama sallolinsa a zaune. Kallonsa take yi cikin damuwa, yakamata a ce sun koma Asibiti. Amma kafin a nemo mota a saka shi, su yi sammako su koma Asibiti, aiki ne. Mussaman da babu wadattacen kuɗi a hannun ta. A take ta tuna da maganin da sarkin baka yake haɗawa masu hawan jini, da wanda ɓarin jikinsu ya shanye a sakamakon hawan jini da matsalar zuciya. Ba ta jira ya idar ba, ta zari hijjabi ta yi waje. Ta din ga tuhumar kanta da yadda aka yi tuntuni ba ta tuna ba, sai yanzu. Tun da su magunguna ne da yake haɗa s da saiwoyi ba wani surkullen ya yi ba. Ta dawo ta tarar ya dawo bakin ƙofa ya zauna yana kallon hanya. Tafiya mai nisa ta yi sosai da ta fita, ta samo ɓawon kwakwa da sassaƙen zogale, sai kuma farin zoɓo. Ta hura wuta ta wanke su, duk ta zuba a tukunya ta zuba ruwa, ta kawo ɗan kanumfari ta zuba a ciki. Sai da ta kammala sannan ta koma gurinsa, ta ce "Ka yi haƙuri, magunguna na je samo maka, na fita ka na salla" "To na gode" "Allah ya baka lafiya shugabana, Allah ya sanya ya wuce kamar ba a yi ba" "Amin. Ke ma Allah ya baki lada, ya saka mini ke a aljanna. Ya sanya ki maƙwabci Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam a aljanna" waro ido ta yi  ta gigice gaba ɗaya hawaye ya fara zirarowa daga idanunta ta ce "Sayyid ba ni da aikin da zai kai ni wannan matsayin. Amma ban san matsayinka a gurin Allah ba. Ban sani ba ko Allah ya karɓi addu'ar da ka yi mini. Amma a ce na maƙwabci Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam. Innalillahi wa Innalillahi raji'un Sayyid na rasa me zan ce. Baiwa ce mai tarin zunubai kuma mai tarin rauni. Amma Allah kai mai yawan rahama ne da falala, Allah ka amsa wannan addu'a da ya yi mini shi ma ka ba shi abin da ya roƙa mini" Ya yi murmushi ya ce "Amin rayuwata" "Sayyid, anya an taɓa yi mini addu'a da ta tsuma ni kamar wannan? Subhanallah, subhanallah. Na ji daɗi wallahi" Shima idanunsa ne ya cika da hawayen, ya ci gaba da bin ta da idanunsa. Kawai sai Nana ta ji ta manta kaso mafi yawa na damuwarta. Da ta tuna Addu'ar da ya yi mata sai murmushi ya kasa barin fuskarta. Maganinta ya daɗe yana dahuwa, ta sauke ta mayar da ruwan girki. Ta tsiyaya masa a kofi, ta je ta zauna a gaban sa. "Sayyid ga magani na dafa maka, mu jarraba, bamu sani ba, ko Allah zai sanya a dace" ya kalli kofin ya kawar da kansa gefe, yana ɓata rai. Ta marairaice ta ce "Dan Allah ka sha, babu ɗaci ko bauri fa" "Ba na son magungunan nan, babu yadda na iya ne nake shan na Asibitin ma, ni wahalar da ni suke yi" "To ai wannan ba na Asibiti ne ba, dan Allah ka daure ka taimaka, ba dan ni ba" Da ƙyar ya yarda ya karɓa, ya ɗanɗana ya ji babu ɗaci, sannan ya ci gaba da sha, sai ma ya ji ɗumin maganin ya yi masa daɗi. Bayan ya shanye, ta dafa masa shayi kuma, ya ɗora dan duk wahalar ciwon da yake ciki, ba ya iya haƙura da shan shayi. Nana ta dage da bawa Sayyid, wannan ruwan maganin, tana addu'ar Ubangiji Allah ya taimake su, ya sanya ya karɓe shi. Cikin ikon Allah, sai kumburin da ya yi, ya fara sacewa a hankali, har yana iya cin Abinci sosai. Nana kamar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha. Nana ta din ga murna, ganin ana samun ci gaba a yanayin jikinsa. Har banɗaki yana iya zuwa, ba tare da ta kama shi ba, yana tafiya a hankali a hankali da kansa yana iya yi wa kansa Wasu abubuwan. Yana zaune tsakar gida, yana shan shayi ta ce "Ashe maganin Sarkin baka yana yi" Ya kalle ta, ta ce "Ka san Sarkin baka?" Ya ɗan yi shiru yana kallon ta. "Ranar da aka kai ni, kai na an kai ka, zaku tafi lokacin, ni kuma a lokacin na ji na fita daga hayyacina. Kai mun fa daɗe muna haɗuwa da kai." Ya yi murmushi ya ce "Ruhina ne ya addabe ki, sai da ki ka nemo ni, ki ka aure ni ki ka nutsu" Ta ɓata fuska ta ce "Ba wani nan, kai ne ka din ga bi na dai, har ka aure ni". Ya ɗan sake zuƙa shayin hannunsa ya ce "A'a. Har gidan da nake ki ka bi ni fa" "Ni ba bin ka na yi ba, kuma ai kai ka ce a biya maka sadakin aurena" Ya maze ya ce "Ai gani na yi kin liƙe mini, har cikin ɗakinmu na gadi ki ka bi ni, na ce kai yarinyar nan idan ban aureta ba, akwai matsala haka za ta yi ta bina saboda ruhinta da yake jikina. Kina ganina kuma ki ka rikice" "Ni ba ina sane na shiga ɗakinku ba, Jummai ce ta ce na ajiye muku Abinci, kawai na ji ana kirana a cikin ɗakin, ban ma na san na shiga ba. Kuma ni da na shiga wannan tsohon na gani. Kuma ai kai ma idan ka ganni kallona ka ke yi" "A'a faɗi gaskiya dai, ni ki ka leƙo ki gani, ranar ba ki ganni ba, sh... Kawai ya ga tana hawaye. A diririce ya ajiye kofin hannunsa ya ce "Mene ne?" Ta yi masa shiru. "Laifi na yi miki? Wasa fa nake yi" ta yi masa shiru, tana matse ƙwalla. Ba wai wasan da yake yi mata ne ya sanya ta kuka ba. Tuna yadda aka yi auren abin da Baba ya din ga faɗa da wanda Mama ta din ga yamaɗiɗi da ita, abin ne kawai ya dawo mata. Ji ta yi yana goge mata hawaye, fuskarsa ɗauke da damuwa, ya ce "Ba zan sake ba" Kwaɓe baki ta yi cikin shagwaɓa, wasu hawayen na ziraro mata. "Na ce na daina fa, ki bari ƙirjina ya fara nauyi" da sauri ta saka bayan hannunta, tana goge hawayen fuskarta. "Yauwwa dama ina so mu yi wata magana, mai muhimmanci da ke" Ta tattara hankalinta, gabanta na dukan uku-uku cike da wasi-wasin wace maganar zai yi da ita haka?. Ayshercool 08081012143 57 Ya yi mata alama da hannunsa, a kan ta nutsu ta kwantar da hankalinta. Ta jinjina masa kai, duk da gabanta na ci gaba da faɗuwa. "Amm na san kina haƙuri a kan abubuwan da suke faruwa, duk da kin ce mini ba kya so na din ga irin wannan maganganun, amma sun zama dole na yi. Ina ƙara yi miki godiya da nema miki yardar Allah, na san ba ni da abin da zan biya ki da shi a wannan Duniyar. Ke ce komai nawa da ki ka rage Asmy. Sannan ɓangaren abin da ya shafi auratayyarmu, shi ma na san... Ta katse sh6ta hanyar cewa "Amm ni dai a bar wannan zancen, bari na je na ɗora wakena" "A'a ki tsaya mu yi magana" "A'a ba sai mun yi ba" "To kar na sake jin kin bi dare ki na taɓa ni" Kamar ta yi tsuntuwa ta ɓace, saboda azabar kunya, ita a zatonta ma ya manta gaba ɗaya. Cikin azama ta miƙe ta ɗauki robar wakenta, ta nufi inda take girki. Tana tashi ya kashingiɗa yana dariya. Nana tana ta fifita wuta, yana daga zaune yana kallonta. Wani irin abu ne yake yi masa yawo a jikinsa, a game da ita. Yana jin zai iya yin komai, dan tabattar da ci gaba da zamanta mallakinsa, shikaɗai. Juriyarta, sadaukarwa da kuma tsananin tausayinta, ya sanya yake jin ina ma yana da wani abu da zai iya kamanta faranta mata rai, kamar yadda take ta wannan ɗawainiyar da shi. Ya san in dai a wannan Duniyar ne ba shi da abin da zai biya ta. Duk da matsananciyar damuwar da ya kan shiga, da jin cewa ya zama silar nakasta rayuwarta, ta zama tana rayuwa ba tare da tunanin wani abu da take so ta cimma ba. Kullum tunaninta a kan sa ne kawai. Tana ɗagowa suka haɗa ido, ta murguɗa masa baki, ta ci gaba da fifitar wutar gabanta. Ya tako zuwa gaban murhun ya tsuguna. "Dan Allah ka tashi, saboda numfashinka fa" "Kawo na yanka miki salak ɗin" "A'a kar ka yanke hannu" Ya ce "Ki kawo zan iya" Ta tsuke fuska ta kalle shi ta ce "Saboda sauƙi ya samu, kana iya fitowa da kanka yanzu, shi ne za ka din ga damuna ko?" Ya yi murmushi, ya zauna a gefe yana kallon ta, da ta ɗaga ido, sai su yi ido huɗu da shi, sai ya yi mata murmushi. Su na cikin cin abinci, ya ce "Ki na kiran Ummi?" "Ba na samun ta, ita ma ta kira ni wayar ba na ji. Uwani ta ce haka garin nan yake babu network, sai a yi kira fiye da sau goma ba ka samu mutum ba. "Idan na ƙara jin sauƙi, zamu je mu gaishe ta, mu yi mata godiya" Ta ce "Alhamdillah, lallai sauƙi ya samu." Ya ce "Eh, ina jin hakan a jikina nima. Mu je waje na ɗan tattaka na ga gari" Nana ta faɗaɗa murmushinta ta ce "Allah abin godiya, wallahi Sayyid da har na fara fitar da rai da kai, na karaya sosai wallahi" Cikin murna ta saka hijjabinta, suka fita. Su na tafe a hankali ta kalle shi ta ce "Gaskiya na yi mamaki, ashe da gaske magungunan sarkin Baka yana yi" Ya tsuke fuska ya ce "Na gaji da jin zancen Sarkin Bakar nan" Nana ma ta yamutsa fuska ta ce "Sayyid ka yi haƙuri, amma na yi farin cikin yadda maganin da na gani a gurinsa ya yi maka aiki. Ina yi masa fatan idan a kan daidai yake, Ubangiji Allah ya ƙarfefe shi ya dafa masa, ko dan saboda yadda yake taimakon mutane. Idan kuma a kan kuskure yake Ubangiji Allah ya ganar da shi, ya ba shi ikon tuba kafin lokaci ya ƙure masa." Sayyid ya yi mata banza, suka ci gaba da takawa a hankali su na zagayawa. Wani irin sanyi ne ya fara ratsa Nana, ganin Sayyid ya durfafi wata hanya, ta kuma kasa ce masa uffan, balle ta hana shi. Su na tunkarar gurin, ƙirjinta na bugawa da sauri da sauri. Wata irin narkekiyar bishiyar kuka suka tarar a gurin mai ban tsoro. Yanayin yadda take ɗauke da wasu irin murɗaɗɗun rassa, da yadda murtuka-murtukan jijiyoyinta suka huda ƙasa suka mamaye gurin. Ga wani irin ƙaton kogo a jikinta, hakan ya nuna daɗewar da bishiyar ta yi da wanzuwa a gurin. "Asma'u" ya kira sunanta kai tsaye. Ta kalle shi cikin matsanancin mamakin yadda ya kira sunanta na yanka kai tsaye. "Ji nake yi kamar na san gurin nan" Jiki a sanyaye Nana ta ce "Nima haka, amma ni dai na san ban taɓa zuwa gurin nan ba, amma ina jin kamar na san gurin, amma dai... Sai kuma ta yi shiru bayan da gurin ya gauraye da duhu aka yi wata irin walƙiyya, haske ya mamaye gurin. Tsohon nan ta gani a tsaye, riƙe da sandarsa ya zubo wa Nana idanunsa marasa kyan gani. Jikinta ne ya ɗau kyarma, ta ƙara rikicewa bayan ganin a hankali wasu halittu da take kyautata zaton ire-iren su Ƙaisar ne su na bayyana a bayansa. Tsohon ya kalle ta, ya buɗe baki ya fara magana. "Ina sake yi miki barka da zuwa, garin da kakanin kakaninki su ka durƙusa suka haifo matsalar da har abada ba za ta daina bibiyar zuriyar su ba. Zan ci gaba da azabtar da rayuwarki, za ki ci gaba da biyan bashin nan, ko bayan ranki, muddin aka ci gaba da samun haihuwar masu irin tauraronki." Yana rufe bakinsa, ɗaya daga cikinsu da Nana take kyautata zaton jininsin mace ce, saboda yanayin wani irin tsohon mayafi da ta yafa a kanta. Ta tunkaro Nana gadan-gadan. Tana zuwa matar, ta hankaɗa Nana ƙasa, sauran suka rufu a kan Nana, su na zira hannunsu a mararta, su na ciro gudan jini. "Ya hayyu ya ƙayyum ya Allah. Allah ka kawo mini ɗauki, Sayyid, Sayyid, Sayyid ka tashi"  Ta yi maganar tana jijjiga Sayyid da yake kwance a gefen ta yana bacci. Ya ja jikinsa ya tashi ya ce "Ma viee lafiya kuwa?" "Sayyid marata ciwo take yi. Sayyid marata. Sayyid babyna. Ba na son na rasa jaririna a wannan karon, Dan Allah ka taimake ni" Cikin rashin fahimta ya ce "Meyafaru ne?" "Marata ce take ciwo, Sayyid ba na son cikina ya zube, ina son jaririna Sayyid ciwo marata take yi sosai" Ta yi maganar tana zubar da hawaye. Ya saka hannunsa a mararta, ta saka hannayenta ya dafe hannunsa tamkar hakan ne zai hana cikin zubewa. Ya ce "Ki yi Addu'a" Kawai ta jinjina kai, amma Addu'a kam, ko ɗaya ba ta zo kanta ba, dan ta manta komai daga cikin kanta. Cikin rauni Nana ta ce "Sayyid fitsari nake ji, ya matse ni" Ya ce "To mu je ki yi" Ta girgiza kai ta ce "A'a ba na son na je na ga jini ya zubo, cikin ne zai zube" Ya ce "A'a ba za ki gani ba" . Ta miƙe ya kama hannunta, ya haska fitila har banɗaki, su na zuwa a tsorace ta yi fitsarin, sai dai tana yi sai ga jini. Wani irin kuka ta fashewa da Sayyid. Ta miƙe jikinta yana rawa. Ya rungume ta ya ce "Ki yi haƙuri, kin ga dare ne, ki daina kuka. Kuma idan za ki yi ɓari, jinin da ki ke zubarwa ya fi wannan kin manta?" "A'a idan jini ya fara zuba, shikenan ciki zai zube" Ya ce "A'a, ba haka ba ne, ai bai zuba da yawa ba" Ya lallaɓa ta da ƙyar, ta gyara jikinta, ta ɗauraye jikinta, da banɗakin su ka koma ɗaki. Karatun Alkur'ani ya kunna a waya, ya ajiye a gefen katifar da suke kai, kamar yadda ya ga tana yi, a duk lokacin da su ka shiga yanayi na tsoro. Suka kwanta yana ɗan shafa ta, cikin sigar rarrashi. A hankali ta ce "Sayyid" "Na'am" "Da gaske mun fita ɗazu ko?" "Eh mun fita" "Mun je can bayan gari, har ka ce mini kamar ka san gurin?" "Eh haka aka yi, mun je" Ta sake cewa "To daga nan meyafaru?" "Faɗuwa ki ka yi, na riƙe ki muka dawo gida. Tun da muka dawo kuma ki ke bacci" Ta yi shiru ba ta sake cewa komai ba, ta ƙara lafewa a jikinsa cikin tsoro. Yau ma kwana suka yi, tana gane-gane da jin abubuwa daban-daban masu razanarwa. Wannan bafulatanar matar ce, ta ƙara zuwa ta tsaya a saitin tagat Nana tana kiran ta, a kan lallai sai ta fito ta ga yadda suke gudanar da bikin girka. Nana ta ƙara rintse idanunta tare da ƙanƙame Sayyid. Da safe ta tashi da wani irin nauyin jiki, ga sanyi da ta kasa daina ji. Ta duba ta ga ba ta kuma ganin jinin nan ba. Ta yi wanka ta rama sallolinta, sai dai Sayyid bai tashi ba. Da ƙyar ta samu ya yi alwala ya yi salla. Ta gaishe shi, amma bai yi magana ba sai kallonta da yake yi. Hakan ya sanya ta fuskanci maganar ta ɗauke. Ta tambaye shi za ta fita, amma bai ko ɗaga kai ya kalle ta ba. Ta saka hijjabi ta fita ta bi 'yan matan gidan Uwani gona roron gyaɗa a gona. Allah ya taimake ta, ta samo da yawa ta zo tsakar gida ta baje ta domin ta sha iska. Ta ɗora musu Abinci, ta kammala ta fara dafa masa maganinsa, kawai ta ga ya fito daga cikin ɗakin. A zaton ta, ko banɗaki zai shiga, ta tashi da nufin kai masa ruwa, kawai ta ga ya nufi fita waje. Da sauri ta bi shi tana faɗin "Sayyid ina za ka je ne haka?" Ya yi mata shiru yana ƙoƙarin buɗe ƙofar. Ta riƙo hannunsa, amma ya waiwayo fuskarsa a ɗaura kamar bai taɓa dariya ba, saka hannu ya hankaɗe ta, ta faɗi a gurin, ya saka kai ya fice daga gidan. Da gudu ta shiga ɗaki, ta ɗaukko hijjabi, ko takalmi ba ta saka ba, ta bi bayan sa. Ga yamma ta yi liƙis, hanya babu kowa, ta ga ya nufi hanyar inda wannan bishiyar ta kuka take. "Sayyid dan Allah, dan Allah kar ka koma gurin nan. Me za ka je ka yi?" Sai dai tamkar ba mara lafiya ba, saboda yadda yake sauri. Sai da ta ɗan haɗa da gudu, Saboda saurin da yake yi, amma ta ji gefen mararta ya ƙulle. Ta daure ta cim masa. Babu tsammani ta furta "Bismillah wa hifzan min kulli shaiɗanin marid." Aya ta bakwai cikin suratul saffat, kamar yadda Malam Auwal ya taɓa cewa ta yawaita nanata ayar. Gaba ɗaya ta shafe a cikin kanta, sai da ta faɗo mata yanzu. Tana karanta ayar, ta riƙe hannunsa ya ja ya tsaya ya yi shiru ya sunkuyar da kai. "Mu koma gida" ta yi maganar tana jan hannunsa, tamkar raƙumi da akala, ya bi ta suka koma gida. Allah ya taimake ta, babu wanda ya gan su har su ka isa gida. Ta rufe ƙofar. Su ka shiga ɗaki, ta kunna fitila ta kalli Sayyid cikin damuwa ta ce "Sayyid me yasa ka fita? Me za ka je ka yi a wajen da?" Ya yi shiru ya sunkuyar da kansa ƙasa fuskarsa babu annuri a ciki. Ba ta sake ce masa komai ba, ta fita banɗaki ta yi alwala, ta dawo ta yi salla, amma ta ga ba shi da niyyar tashi ya yi. "Sayyid, ba ka yi salla ba fa" Nan ma bai kula ta ba, dan haka ba ta sake magana ba, ta zubo masa Abinci ta zo gaban sa ta ajiye. Ta tashi ta ninke hijjabinta, tana waiwayowa, ta ga ya kifar da Abincin ya tarwatse a tsakar ɗakin, yana wani irin huci. "Sayyid wai meye haka ne? Idan ba ka cin abincin sai ka zubar mini a ƙasa?" Sai dai tana rufe baki, ya wulwula kwanon ya yi jifa da shi guri ɗaya. Ya miƙe ya fara fatali da kayan ɗakin. Take Nana ta fuskanci ba lafiya ba. Jiki a sanyaye ta rakuɓe tana kallon sa. Tana tunanin yanzu kuma abin har ya kai ga haka? Ba ta yi yinƙurin hana shi ba, ya yi kaca-kaca da ɗakin, ya fita tsakar gida ya nemi guri ya kwanta a dandaryar ƙasa. Inda ta yi wa Allah godiya ba su da maƙwabta, da kowa sai ya san abin da ya faru. Haka ta durƙusa ta hau aikin gyaran ɗakin, ta kintsa abin da za ta iya kintsawa. Ta dawo tsakar gida inda yake kwance. Ta durƙusa a kan sa, ta dafa shi ta ce "Tashi mu je ka kwanta a ɗaki, nan akwai sauro kuma ƙwari za su cije ka" Da ƙyar ya tashi, suka koma ɗaki, ya nemi guri ya kwanta a ƙasa. Kawai Nana ta zauna ta zura masa ido, cikin matsananciyar damuwa, duba da yadda take maganin ƙaba amma kai na daɗa kumbura. A haka dare ya tsala, ta gaji ta kwanta a gefen sa, zuciyarta fal da damuwa. Bacci na ƙoƙarin ɗaukar ta, ta ji tasowar guguwa ta buɗe idonta, ta gan su kwance a cikin sahara, ga yashin saharar na wani irin hanƙoro iska za ta mamaye su. Ta saka hannu ta rungume shi saboda guguwar saharar. Sautin tsohon nan ta ji yana wata irin dariya. Ji ta yi an hankaɗa ta, sai da ta wuntsula ɗakin gauraye da duhu, amma ta ga alamun Sayyid ne zaune a kan katifa shi ne ya hankaɗa ta. Ya tashi ya koma bakin ƙofa ya yi zamansa. Da kyar ta sake lallaɓa shi, ya koma ya kwanta. Ita ba ta sake komawa bacci ba, ta yi alwala ta zauna tana tasbihi har aka yi sallar asuba. Sai dai fafur ya yi salla ya ƙi yi. Ya nemi guri ya zauna ƙyam yana kallon ta. Ta dama masa kunu, ta soya fanke, ta zo ɗaki ta zauna a gaban sa. Ta ce "Ga kunu ka sha, amma dan Allah kar ka zubar Sayyid ka ji?" Ta yi maganar tana miƙa masa kofin kunun. Sai ya miƙo hannun hagu zai karɓa. Ta janye kofin ta ce "Hannun dama dai, wannan hannun za ka bani" Ta yi maganar tana nuna hannun damansa, amma bai miƙo mata ba, ya zura mata ido. Ta kai hannu ta janyo hannun nasa, dan ta damƙa masa kofin kunun, amma ta ji hannun a ƙame ƙam. Ta sake ƙoƙarin janyowa, amma ta ji tamkar tana jan itace. Ta kalli hannun sosai, sai ta ga shanyewa ya yi. Gabanta ya yi wata irin mummunar faɗuwa, ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Sayyid me ya same ka haka? Me ya samu hannunka? Ya Allah!" Ta yi maganar tana kuma ƙoƙarin ganin ta miƙar da hannun nasa, amma hannun yana maƙale, kamar an tsotse shi. Ya sunkuyar da kai ya yi shiru, fuskarsa ɗauke da damuwa. Ta aro jarumta, ta matsa daf da shi, ta ɗebo kunun ta kai bakinsa. Amma ya tsaya yana kallonta, bai buɗe bakinsa ba. "Buɗe baninka na baka" Ta yi maganar tana ƙoƙarin danne hawayen da ke ƙoƙarin ƙwace mata. A hankali ya buɗe bakin, sai ta ga shi ma bakin ya karkace, yawu na ƙoƙarin zubowa. Kawai ya rufe bakin hawaye ya fara gangarowa daga cikin idanunsa. Ta ajiye kofin kunun ta rasa abin yi. Kawai rungume shi, ta fashe da matsanancin kuka, sai da ta yi iya yin ta. Sannan ta cika shi, ta share masa hawayensa. Ta fara ƙoƙarin ba shi kunun, sai dai tana ba shi, ya haɗiye wani kuma ya zubo. Ta na yi tana goge masa wanda yake zubowa, ta gama ba shi, ta kama hannunsa su ka je waje, ta taimaka masa ya yi alwala. Ya dawo ya rama sallolin da ta gaya masa ana bin sa. Sai dai ba magana ga hannu a maƙale, da ta kalle shi sai ta ji hawaye ya cika mata ido. Ganin yana gyangyaɗi a zaune, ya sanya ta saka masa pillow ya kwanta, ta saka hijjabi ta fita. Tafiya mai nisa ta yi, ta je ta samu wani chemist, bayan sun gaisa ta ce "Dan Allah malam, idan babu damuwa, Bp nake son mu je ka gwadawa mijina a gida" Ya kalle ta ya ce "A ina ne?" "Cikin Budu ne, nan unguwar maharba" "Taɓ gaskiya da nisa gurin nan ba kaɗan ba, ba zan iya zuwa ba sai dai ki je ku zo tare a yi masa" "Wallahi da zai yiwu, da ba zan zo na roƙe ka ba, yana kwance babu lafiya ka taimaka mini dan Allah" Ya ce "Gaskiya kin san cajin zuwa gida ma ka yi wa mutum abu daban yake, sai dai idan za ki ba ni dubu biyu" Nana ta ce "Eh na yarda mu je zan baka in sha Allah" Ya rufe chemist ɗin ya bi Nana. Su na zuwa gidan, Nana ta shiga ta tarar da shi a zaune ya tashi, ta ce "Sayyid kar ka ga na fita ban gaya maka ba. Na je na samo wani ma'aikaci ne, ya zo ya duba jininka a gani, idan jinin ne ya hau ya sanya hannunka ya shanye, mu tafi Asibiti. Idan kuma ba shi ba ne, sai mu san abin yi." Bai ce komai ba, ta yi wa mai chemist magana, ya shigo ya gwada jininsa. Ya gwada ya kalli Nana ya ce "Jininsa bai wani hau sosai ba, 140/90 ne" Ajiyar zuciya Nana ta yi. Ta ce "A ganinka wannan hawan zai iya sanya masa shanyewar hannu?. Ya girgiza kai ya ce "Gaskiya ba na tunanin haka, amma ban tabattar ba tun da ni ba likita ba ne ba. Amma a shekarunaa bana tunanin jinin 140 zai shanye masa wata gaɓa a jikinsa, amma dai ku je Asibiti a ƙara bincikawa" Nana ta ba shi kuɗin sa, ta yi tai masa godiya. Ta koma ɗaki ta zauna ta yi shiru, tana tunanin ko Uwani za ta tambaya, idan akwai wani mai magani, ta raka su, sai dai ta fasa saboda akwai sauran ɓurɓushin jahilci a tattare su, ba ta son surutu kuma tana tsoron a kai su gurin da ba shikenan ba. **** Alhaji Fatuhu kuwa kamar yadda ya matsa, sai da aka sallame shi ya koma gida. Gidan nasa ma wani abokin kasuwancinsa ne ya saya, ya bar shi a ciki ya zauna ya bar masa aro. Sagir yana kwance a kan gadonsa, yana kaɗa ƙafa ya ƙura wa screen ɗin wayarsa ido. Yusra ce zaune sanye da doguwar rigar material, kanta ko ɗan kwali babu, dogon gashin kanta ya sha gyara. Tana ta zuba masa surutu. Har mamaki yake yi, yadda Yusra ta zama mai ɗan karen surutun tsiya, wanda da ba haka take ba. "Ya ka yi shiru ne?" Ya wani lumshe ido ya ce "Ina jin ki ai". "So talk, ka yi magana mana" ta yi maganar tana cika bakinta da guggurun hannunta. "Ina ga zan shigo Abuja mu haɗu very soon in sha Allah" wata irin zabura ta yi ta ce "Are You serious, dan Allah da gaske?" "Da gaske nake, zan zo na ganki, amma ki na ganin babu matsala a zuwan nawa? Kar a yi miki faɗa fa, ba zan ji daɗi hakan ba" Yusra ta ce "Babu wata matsala, ba za a yi mini faɗa ba, ai ba na tare da su Mami, ina gidan Anty Sumayya. Dan Allah ka zo" Sagir ya yi murmushi ya ce "Kin yi missing ɗina ne?" Ta gyaɗa masa kai tana murmushi. "Shikenan, i miss you too, ban taɓa tunanin ma za ki neme ni ba, na za ta ki na jin haushina haryanzu, amma in sha Allah zan shigo, zan sanar miki lokacin da zan shigo na zo na ganki" ya yi maganar yana kashe mata ido. Shukura ce ta turo ƙofar ɗakin ta shigo, a burkice ya kif wayar yana kallon ta. Ƙarara yanayinsa ya nuna alamun rashin gaskiya, amma ta share shi, ta haye kan gadon ta ja bargo ta lulluɓe jikinta. Ya matsa kusa da ita yana ɗan shafa ta ya ce "Sweetheart, ya na gan ki kamar a fusace ne? Lafiya dai ko?" "Lafiya ƙalau" ta amsa a taƙaice. Ɗan shiru ya yi yana tunanin ko dai ji wayar da yake yi ne? Amma a yadda ya santa da azababben kishi, da zargi da ta ji sai ta yi masa magana. Sai dai ya bar abin a haka bai matsa mata da tambayoyi ba gudun kar su yi faɗa. Tana ankare da take-taken Sagir, na rashin gaskiya. Sai dai ita yanzu ba wannan ne a gabanta ba, bin diddigin mutuwar ɗanta take son yi. Dan haryanzu zuciyarta ta kasa amincewa da natural mutuwa ya yi. Domin haryanzu tana mafarke-mafarke marasa  daɗi da mahaifinta da kuma Doctor Sharif. **** Aka shiga sati na biyu, Sayyid yana cikin wannan yanayi na rashin lafiya, kuma hannunsa bai saki ba, yana nan a maƙale. Ga hauka da yake yi tuburan wasu lokutan, wasu lokutan idan ya burkice sai ya shaƙe ta, ko ya hankaɗe ta ƙasa, sai dai ta yi ƙoƙarin kare cikinta. Ko kuma Ya ya ta watsi da duk abin da ya ci karo da shi, a ɗaki ko a tsakar gida. Wasu lokutan ma katangar ɗakin yake duka da kansa. Ya ƙi cin abinci ya ƙi shan magani, ba salla, komai sai dai ta yi masa cikin rarrashi da ban haƙuri. Tun tana jin tsoron ya yi mata wani abin, har ta daina ji, ta zuba wa sarautar Allah ido. Sannu a hankali ta rage yawan amai, sai dai zazzaɓi da rashin son cin abinci da take yi, hakan ya sanya ta tabattar da cikin jikinta bai fita ba haryanzu. Sai dai ba ma ta cikin nutsuwar da za ta nemi inda Asibiti yake ta je, ta tabattar da halin da suke ciki ita da jaririn saboda tashin hankalin da take ciki. Yanayin yadda uwani ta lura kamar Nana na ɓoye wani abu, ya sanya ta daina zuwa gidan,ta rage aika yara ma. Sai dai lokaci lokaci, ta kan aika mata da Abinci. Haka sauran 'yan uwansu na garin ma, su kan aiko mata da sha tara ta arziki saboda su na tausayin Nana, sun san mijinta a kwance yake babu lafiya. Yawon roro a gona kuwa yanzu Nana ta ƙware, ranar kasuwa ta je ta sayar da abin ta. Kasancewar ranar Asbar kasuwar garin take ci, sai ta tashi ta yi fanke da sassafe, jikan Uwani Haladu, ya kai mata kasuwa. Ko ta dafa masa zoɓo ta ƙuƙƙula ya tafi da shi. Idan ta gama komai kuma, ta bi yara gona roro. Dare ya tsala, amma Nana tana zaune tunkurkur, wuni Sayyid ya yi yana wani irin nishi, ga wannan azababben zafin jiki da yake fama da dhi. Tana zaune tana tunani, tana jin yadda mararta take motsi, cikin jikinta yake motsawa. Ba ta da sauran wanda za ta kai kukanta bayan Ubangiji. Ta fara tunanin ƙoƙarin tara musu kuɗin mota, su tafi Nijar, neman danginsa, sai dai idan sun je Nijar ɗin ina za su nufa? Babu tsammani ta ji Sayyid ɗin ya laluba cinyarta, ya kwantar da kansa. Ta shafa gashinsa ta ce "Sayyid" bai amsa ba, sai dai ya riƙe hannunta. Hakan ya tabattar mata da ya dawo hayyacinsa ne. Haka ta tashi a cikin daren ta tsiyayo ruwan zafi, ta ba shi shayi ta yi masa wanka suka kwanta, ta lulluɓe su da bargo. Sheshsheƙar kukansa ta ji, duk da yadda ta san ya daɗe yana dauriya, da son ɓoye gazawarsa, sai dai ta ga hakan a idanunsa. "Sayyid idan ka na kuka, ni kuma ya zan yi kenan? Dan Allah ka daina" ta yi maganar muryarta na rawa. Ta din ga shafa bayansa a hankali, har ya yi shiru, bacci ya ɗauke shi. Sai dai tun daga wannan, haka aka sake shafe kwanaki biyu, bai sha ko ruwa ba. Dama rashin maganarsa ya daina damunta. Ga shi yau abin ya tashi sosai, haukan yake yi da gaske. Ta rufe shi a gidan, ta je ta samo gasara a gidan Uwani, ta dawo ta dama masa kunu. Ta nufi ɗakin cike da fargaba tare da fatan ya samu ya sha ko kaɗan ne. Sai dai ta ji wata irin guguwa ta taso mai ƙarfi. Jin yadda guguwar ta taso da ƙarfinta, take fatali da duk abin da ta ci karo da shi a tsakar gida, ya sanya ta tashi da azama, ta fara ƙoƙarin rufe ƙofar katakon da take ɗakin. Sai dai tana danna ƙofar guguwar ma na danno ƙofar. A take ta fara karanto "A'uzubillah, Allahumma inni as'aluka khairiha wa a'uzubika min sharriha. Allahumma inni as'aluka khairiha wa khairi ma fihi, wa khairi ma ursulat bihi, wa a'uzubika min sharriha wa sharri ma fiha, wa sharri ma urisilat biha" take ta ji nauyin da ƙofar ta yi ya ragu, ta samu ta rufe ta, ta juya da sauri ta nufin gurin da yake. Da fari yana zaune a guri ɗaya ne, amma yanzu Jifa yake da kayan ɗakin da hannu ɗaya, da sauri ta fara  bi tana tattarewa, cike da damuwa. Cikin siriryar muryarta ta ce "Sayyid za ka ji wa kan ka ciwo, ka saurara ka saurari muryar matarka, ni ce a gare ka, ni ce fa, Husnan ka ce fa" Ta ƙarasa maganar a raunane, duk yadda take ƙoƙarin tare shi ta kasa, domin ta gama firgita da lamarinsa. Tun safe take fama da shi, ya ƙi cin komai, kuma ta kasa sarrafa shi duk rarrashin da ta yi a banza. Cikin matsananciyar damuwa, hawaye na bin kuncinta ta ce "Ubangiji ka dubi mijin Nana, ka cire masa zafi da raɗaɗin da yake ji, ka saita masa tunani da ƙwaƙwalwarsa, ya yi rayuwa mai cike da nutsuwa da farin ciki irin na sauran mutane" sai kuma ya tsaya cak, ya juyo yana kallonta. Ta ƙarasa gurinsa, ba tare da fargaba ba ta  riƙo hannunsa cikin nata jikinsa zafi sosai. Ta kalli cikin idanunsa sai taga yana birkice mata yana rikiɗewa kamar ba Sayyid ɗin ta ba, idanunsa har wani hayaƙi yake fitarwa, gaba ɗaya kaminsa sun sauya. Ta lallaɓa ta zaunar da shi, Ta yunƙura zata tashi, domin ta ɗaukko kununsa ta sake jarraba ba shi, ta ji ya cafko ta yana wani irin sambatu bakinsa na kumfa da dalalar da yawu, da alama magana yake son ya yi mata. Rashin ƙarfin jiki ya sanya ta faɗa jikinsa. Ya ƙanƙame ta sosai, saboda zafin da yake ji, ita kuma jikinta sanyi ƙalau. Ita ma jikinta ya ɗauki rawa, ta lafe a jikinsa ta kwantar da kanta a ƙirjinsa tsawon mintuna, jin ya ɗan nutsu jikinsa ya rage zafin ya sanya ta zare jikinta a hankali. Ta ɗaukko kofin kunun da cokali, sai wani ɗan ƙaramin tsumma, ta zauna a gabansa ta ɗebo kunun a cokali ta kai bakinsa, sai dai ya tsaya yana bin ta da ido, kamar ya ga baƙuwar halitta, ta buɗe nata bakin, ya kalleta shi ma ya buɗe nasa. Ta fara zuba kunun a bakinta ta haɗiye, sannan ta zuba masa a bakinsa shi ma. Ya haɗiye sai dai wani na biyo gefen bakinsa, bai haɗiye duka ba. Tana bashi tana goge masa wanda yake  zubowa. Sai da ta tabattar ya ƙoshi, sannan ta goge masa bakinsa. Ta ɗauki kofin ta nufi ƙofa ta buɗe a hankali ta ga an daina iskar, ta fita da kofin ta ajiye, ta tattara abin da guguwar ta watsa sannan ta dawo ɗakin. Jiki a sanyaye, ta zauna a gabansa tana ƙare wa kyakyawar fuskarsa kallo. Da ƙyar yake jan numfashi yana saukewa.  Ta sanya hannayenta biyu, ta gyara masa gashinsa, da ya rufe masa gefen idonsa, ta saka idonta a cikin nasa, cikin rauni da karaya, idanunta na zubar da hawaye ta motsa bakinta, ta fara magana "Sayyid, dan Allah ka yi magana ko na ji daɗi, wannan karon ka daɗe ba ka ce mini komai ba. Da na sanya ran ka fara samun  lafiya, amma kullum lamarin nan gaba yake yi. Ka gaya mini wane ne kai? Daga ina ka ke? Ina zan samu danginka da 'yan uwanka, wataƙila kai naka dangin ba za su guje mu ba, za su karɓe mu, tare da sarƙar da ta haɗa ƙaddarorinmu wuri guda, duk da ban kasance ɗaya daga cikinku ba, ni fatana a nema maka magani ka samu lafiya, ba na son ganin ka cikin wannan mummunan yanayin, idan na ci gaba da ganain ka a haka, zuciyata za ta iya bugawa. Dan Allah ka yi magana" Ta yi maganar wasu hawayen na zirarowa daga cikin idanunta. Ayshercool 08081012143 58 Ya haɗiye wani irin yawu, da yake yi masa zafi a ƙirjinsa, yayi ƙoƙarin ɗago hannunsa na dama, sai ya tuna ya riga ya shanye, ba ya iya komai da shi. Ya buɗe baki da nufin ya kira sunanta, saboda tasiri da kuma ciwon da kukanta yake yi masa a zuciyarsa, amma ya gaza bakin ya karkace yawu ya fara zubowa daga bakin nasa, maimakon kiran sunanta da ya yi yinƙurin yi. Tana kuka, ta sanya tsumman da tayi amfani da shi wurin ba shi abinci, ta goge masa bakinsa. Ba shi da zaɓin da ya wuce, ba wa hawayen da yake maƙale a cikin idanunsa damar zubowa, ko shi ma ya samu sassauci abin da yake ji. A hankali ya hura mata iskar bakinsa a fuskarta, a take ta silale ta faɗi a jikinsa. Ya sanya hannunsa mai lafiya, ya rungume ta, ya ci gaba da kuka. Jikinta gaba ɗaya ya saki. Ƙaisar ta gani a gurin haɗe-haɗen magungunan sa, yana ta haɗa wani abu a cikin kwalba. Zuciyarta ce take ta azalzalarta, da ƙoƙarin ingizata, sai dai ba ta yi magana ba. Babu tsammanni, ta ji ya fara magana "Zaɓi ɗaya ya rage miki, a halin yanzu, ko dai ki yadda da abin da na zo miki da shi, ki rungumi ƙaddararki, ko ki na kallo Buzun nan zai mutu, domin ba zai taɓa tuna waye shi ba har abada, muddin Giyaz yana tare da shi. Dan ba na tunanin akwai wanda zai iya raba shi da shi. Idan har bai iya tuna waye shi ba, shikenan kin ga ba ki da wata makoma. Abu ɗaya zai sanya a wannan karon na bar miki abin da yake cikinki, duk da ba ni da tabbacin zai zama mai cikakkiyar lafiya ko akasin haka, Giyaz da muƙarrabansa sun riga sun fara taɓa shi a cikin ki. Kin san meyasa ban ƙarasa lalata wannan cikin ba?" Bai jira ta ba shi amsa ba ya ce "Saboda zan so na ga yadda za ki yi, a lokacin da ɗan zai amsa sunan shege, kuma ba za ki iya hanawa ba, domin ba ki da hujjar kare kanki. Idan Buzun nan ya rayu bai san waye shi ba, ga kuma nakasa. Idan kuma ya mutu suwaye dangin baban ɗan ki? Daga ina yake? Suwaye ahalinsa? Kin san ku a jinsinku na bil'adam da uba ake ado ba riga ba. Babu wanda zai damu da wacece ta haifi mutum, amma za a damu da waye ubansa meye nasabarsa? Tun da ki ka zo garin nan, zuriyarmu suke alwashin yadda fansar su za ta kasance a kan ki. Kafin zuwa wannan ƙadamin babu abin da ban gaya miki ba, na gargaɗi. Dan haka dabara ta rage ga mai shiga rijiya" Cikin kuka Nana ta hau girgiza kai ta ce "Ba zan yi bori ba Ƙaisar, ba zan yi shirka da Allah ba. Babu tsanani ko wahalar da za ta sanya na rabu da imanina. Amma na rasa gaba na rasa baya, ba dan ina neman taimakon ka ba, ko ka kawo mini ɗauki ba. Na san Ubangiji Allah shi zai taimake ni. Amma dan zatin Allah idan ka na da hannu a ciwon Sayyid, ka yi mini rai ka rabu da shi, shi ne kaɗai duniyata. Ina matuƙar tausayin sa, ban damu da jinya da nake yi ba, wahalar da yake sha ta isa haka. Idan kuma laifikan zuriyarmu ne suke shafar sa, dan Allah ku yi haƙuri ki ƙyale shi haka" Cikin sautin muryarsa mai ban tsoro, da ya kan yi amfani da ita, idan ya so razana ta, ko yi mata magana mai muhimmanci  ya ce "Na sha gaya miki na maimaita miki, daga lokacin da ki ka fara bani umarni, kin yadda kin amince da buƙata ta ne. Ba ni da hannu a ciwon mijinki, kuma bai ya cikin zuriyar ku, sai dai ƙaddara mai ƙarfin gaske, ta haɗa ku tarayya guri guda. Amma muddin ki na son ya warke daga wannan rashin lafiya, ba ma iya haka ba, ya tuna waye shi, sai kin karɓi ƙaddararki.". Nana ta sake marairaicewa ta ce "Ba zan iya shirka ba, ba zan iya zama 'yar bori ba. Zan jure jarrabawata komai zafinta amma ba zan yadda rasa imanina ba" Ƙaisar ya ce "A cikin biyu dole abu ɗaya ya faru, tunda kakaninki su suka ƙyanƙyashi wannan matsalar. Na yi iya ƙoƙarina gurin dakatar da ita a wancan lokacin, amma ta sake tasowa a wannan karon. Dole a cikinku ɗaya zai warke ya rayu ɗaya ya mutu a haka, dan babu alamar Giyaz zai sassauta wannan mummunan ƙudirin nasa a kan zuriyar ku. Gefe ga aikin da ya karɓa yake yi a akan mijinki, ko dai ki ci gaba da rayuwa da shi, laifukan ku na shafar sa, ko kuma ki yarda ki karɓe ni a matsayin hadiminki ki yi abin da nake so, ni kuma na san yadda zan yi da Giyaz, na baki maganin da mijinki zai warke" "Ta yaya? Me yasa sai ni? Me yasa ni zan biya zunubin da lokacin da aka aikata shi ba na nan, zunubin da zamanin da aka aikata shi, ya yi nisa da nawa zamanin? Me ya sa kakannina suka zaɓi zama 'yan bori? Suka gada mini wahala da masifa take ta bibiyar rayuwata. Na zama mujiya a cikin mutane, duk inda na tsuguna sai wata masifa ta afku, da za a jefa mini zargi, kasantuwata ni ba mutum ba ni ba wani jinsi daban ba? Me yasa zan girbe baƙar shukar da ban san a lokacin da aka dasa ta ba? Ina son mijina duk da daga ni har shi, ba mu san waye shi ba. Duk da Nijar ba ɗaki ɗaya bane ba, ba kuma ƙaramar alƙarya ba ce ba, ƙasa guda ce, na gwammace zagaye ta neman ahalinsa na damƙa shi a gare su, da na ci gaba da zama da shi, mummunar ƙaddarata tana shafarsa, ko kuma na zama 'yar bori na ci gaba da gadar da wahala da masifa ga zuriyarmu, gara ko ma mene ne ya ƙare a kaina." Ta ƙarasa maganar cikin ƙaraji, tana kuka mai bayyanar da tsantsar baƙin cikin da yake binne a cikin zuciyarta. ***** A hankali yake driving cikin nutsuwa, yana sauraren Jamila, da ke bin waƙar da ke tashi a cikin motar ƙasa-ƙasa, sai kuma ta yi shiru. "Ya ki ka yi shiru kuma?" Ta ce "Au wai ka na ji na?" Abba ya ce "Eh mana, har kin fi masu waƙar ma iyawa" Dariya ta yi ta ce "Ka ji ziga, muryar ta su da aka tace, aka goge tawa kuma a haka, ka ke cewa na fi su iyawa" "Au ba ki yarda ba? To shikenan ni dai na san kin fi iyawa" ya yi maganar yana parking ɗin motar a harabar gurin shan ice-cream ɗin. Abba bai taɓa soyayya ba, duk wannan abubuwan da yake yi wa Jamila, bai taɓa furta mata cewar yana sonta ba. Sai dai ita sarai ta gane sonta yake yi, so kuma ba na wasa ba. Sai dai tana mamakin yadda duk wannan abin da yake yi mata, ba ya iya nuna wa a gaban Hajiya Sa'a, hakan ya sanya ta fara tunanin ko dai yana da wata manufa a kanta ne. Sai dai ta lura halaye da ɗabi'unsa, sun sha banban da na Hajiya Sa'a, shi Abba akwai tsantseni, da gudun saɓa wa Allah. Dan duk da son da yake yi mata, sai da ya yi mata faɗa a kan shigar banza da ta kan yi wasu lokutan. Ice cream su ka sha, yana ba ta labarin yadda ya yi karatu, da irin ƙalubalen da ya fuskanta na rayuwa. Su ka gama ya ɗauke ta ya mayar da ita gida. Bayan ta shiga gida, Mama ta ce "Yauwwa ke nake jira dama, gas ya ƙare na kira wayar ki kuma ba ki ɗaga ba" "Ina hanya ne, ga ATM ɗina, a bawa Nasiru ya je ya ɗuro. Har za ta shiga ɗaki sai ta fasa ta ce "Ni kuwa jama'a ina Nana ne? Wayarta ba ta shiga, shekaranjiya waccan ma na biya gidan da mijinta yake gadi, na ga kamar babu kowa a gidan" Mama ta taɓe baki ta ce "Au ke ba ki san abin da yake faruwa ba dama?" Ta tsaya tana kallon Mama ta ce "Mene ne yake faruwar?" "Ai tuni aka kore su daga wannan gida. Ke ba zama ki ke yi ba ne shi yasa, suka koma unguwar su Ummi, to kin santa duk inda ta zauna bala'i ne yake bibiyar gurin, hatsaniya ta haɗa ta da matan gidan da suke, suka ce mayya ce aka tashe su. Ai nan Babanku ya je aka yi ta fafatawa, da ta kwaso jiki ta taho nan, wai za ta dawo mijinta babu lafiya, na ce bani da gurin jinya a gidan nan. Allah ya raba ni da masifa, ba za ta dawo mini ba, to ƙarshe dai wai yanzu tana ƙauye, can gurin Uwani a can take jinyar mijin nata" Jamila ta yi sak, ta ce "Mama Nana tana ƙauye fa ki ka ce?" "Eh mana, to idan ba ƙauyen ba ina za ta je? Tana can" "To waye yake ba ta Abinci?" Mama ta ce "Oho ina na sani?" "Amma ya aka yi tsawon wannan lokacin ban sani ba? Yanzu ba kamar da ba ne, ban ji daɗin abin da ki ka yi ba Mama, bai kamata a kore ta ba a ce ta koma ƙauye da zama ba. Da ina nan ko na sani, da na kama musu wani gidan, gaskiya sai ta baro ƙauye" "To ke ina ruwanki? Mene ne naki a ciki uwar Iya? Kina kallon irin baƙar azabar da na sha, a kan zamana da ita a gidan nan. Na meye za ki kuma jajubo mana ita. Gara ki bani kuɗin da za ki kama mata hayar na bawa ɗanLadi, ɗan autanmu ya tafi kasuwa da zaman banzae da yake yi, na yi masa aure tun da Allah ya sanya kuttun arziki ya fashe mana, ba ki kai kuɗi inda babu amfani ba" Jamila ta dubi Mama ta ce "Wannan ɗan uwanki ne, sai ki nemi kuɗinki ki yi masa, nima 'yar uwata nake tunani. Haba Mama, ko wani Nana ta kashe miki ƙiyayyar ta isa haka ai. Ai yakamata a tausaya mata, miji babu lafiya ga zaman ƙauye, ita Uwanin za ta ɗauki nauyin Abincinsu ne? Tun da muka tashi a wahala muke a gidan nan, amma ita nata ya fi na kowa ma" Jamila ta ƙarasa maganar cikin damuwa, ta shige ɗaki, ta bar Mama da buɗaɗɗen baki. ***** Kallonsa Nana take yi, suna zaune sun yi juguum daga ita har shi. Bayan ta gama yi masa kitson zanen hannu guda takwas, ta yanke masa faratansa na hannu da na ƙafa. Kamar wadda aka mintsina ta tashi tsaye, ta kalle shi ta ce "Sayyid, bari na je na dawo" ya bi bayanta da kallo har ta fice. Sai dai a ƙalla ta kai awanni biyu kafin ta dawo, ko da ta dawo ta tarar da shi ya haɗe fuska, ta yi shiru ba ta kula shi ba, ta koma tsakar gida. Ta laluba kayanta, ta ɗaukko wata takarda mai ɗauke da ayoyin ruƙiyya da na karya sihiri, sannan ta hura wuta a cikin murhu. Ta dawo tsakar gida ta zauna, ta fara da Bismillah da karanta Suratul fatiha, sai Suratul falaƙi da nasi. Ta karanta ayoyi biyar ɗin farko na Suratul Baƙara, ta fara karanta Suratul mulk, a hankali sai ta fara gani dishi-dishi, ta fara daina ganewa. Ta busa ayoyin a cikin ruwan, Sai ta ajiye takardar. Ta ɗauki wata leda da ta zo da ita, ta fito da man habbatussauda da jan Almiski. Saboda wauta sai ta buɗe miskin, ta kai hancinta, da sauri ta dungurar da shi a gurin, ta ja da baya, dan tuni ta ji jikinta ya fara tsuma. Sai da ta ɗan samu nutsuwa, sannan ta zazzaga tazargaɗe a cikin bokitin, ta kawo ganyen magarya guda bakwai, ta saka a leda ta ɗan bubbuga musu muciya, ta haɗa a cikin ruwan. Ta yi shiru tana tunani a ranta ta ce "Allah ya sa ba mai magani na zama ba, Ƙaisar bai mayar da ni 'yar bori mai bayar da magani ba, larurar Sayyid ta saka na fara koyi da magungunan sarkin baka." "Amma ai ayoyin Alkur'ani ki ka karanta, shi ma kuma Sarkin Bakar yana amfani da Alkur'ani" wata zuciyar ta tunatar da ita. Haka dai ta ci gaba da wasi-wasi. Can yamma, bayan ta tabbatar da ganyen magarya da tazargaden sun tsumu, ta ɗumama ruwa ta tsiyayi ruwan tofin ta tace ta haɗa da ruwan ɗumin, ta kawo man habbatussauda ta tsiyaya a ciki, ta kawo jan miskin nan da ta saka kwalbar a ruwan ɗumi, ya narke ta tsiyaya a ciki, ta ɗebo garwashi a kasko ta shiga ɗakin. Yana ganin Nana ya tashi zaune yana kallon ta, ya ga ta samu ƙyalle ta ɗaure hancinta da bakinta. Ta nufo shi ya ga ta hau tuɓe masa kaya, ya din ga bin ta da ido, ta bar shi daga shi sai gajeren wando. Hannunsa da yake maƙale take kallo cikin damuwa, ta shafa hannun. Sai kuma ta yi Bismillah ta fara shafa masa wannan ruwan. Tun daga cikin kansa. Girgiza kai ya fara yi, yana ture ta da lafiyayyen hannunsa, yana toshe hancinsa. Ya din ga girgiza kai jikinsa yana karkarwa bakinsa yana rawa, ya din ga wani irin gunji yana miƙa. Amma sai da Nana ta jiƙe shi da ruwan nan tsaf. Ta kunna kiran salla a wayarta. Ta kawo tazargade, da habbatussauda da ganyen magarya ta zuba su a kan garwashin nan, hayaƙin ya turnuƙe ɗakin, ta ajiye shi a nesa da shi kaɗan. Ta fice daga ɗakin ta kulle shi a ciki. Ta tafi ta din ga wanke hannunta. Wani irin jiri ya din ga ɗaukar ta, ga matsanancin ciwon kai, ɓari ɗaya da ya sanya take jin, tamkar kan zai yi bindiga ya rabe. Ta samu guri ta zauna a tsakar gida, ta dafe saitin zuciyarta da yake ta bugawa da sauri. Bayan wasu mintuna, ta tashi ta je ta leƙa ta window, ta hango shi a kwance a ƙasa. A tsorace ta buɗe shi, ta nufe shi da sauri tana kiran sunansa. Gaba ɗaya ƙwayar idonsa baƙar ta ɗauke sai farar, ta durƙusa a kansa kawai ya miƙo hannu zai shaƙe ta, amma ta riƙe hannunsa. Hannun ya din ga rawa, ya sauke shi a hankali. "Sayyid" tana ambatar sunansa, ƙwayar idonsa ta dawo ya kalle ta. "Sannu Shugaba" hararta ya yi ya juya mata baya. Dariya ta fara yi ƙasa-ƙasa. Ta ce "Haba Shugaba, ya ka juya mini baya, juyo ka kalle ni" ya ƙi juyowa. Ta tashi ta buɗe labule saboda yadda warin ita ma ya fara damunta. Ta ɗaukko tsumma, ta hau goge masa jikinsa, saboda ya daina warin miskin nan ita ma ba ta so. Ya tashi zaune, tana goge masa. Ta ce "Ko a yi wanka?" Ya ɗaga idonsa yana hararta, jikinsa ya koma jawur kamar wanda ya ƙone. Ta din ga ɓoye dariyarta, ta yi masa wanka, ya din ga sinsuna jikinsa yana yamutsa fuska. Ya shafa fuskarsa ta ce "Ka yi haƙuri, magani ne, ina son ran Ubangiji Allah ya kawo mana afuwa" Ya ture ta daga jikinsa. Amma ta manne masa ta hau cinyarsa ta zauna tana dariya. Ta juyo da fuskarsa suna kallon juna, ta lumshe ido ta buɗe ta ce "Sannu shugaba" Ya jinjina mata kai. "In zubo Abinci ne?" Ya girgiza kai. "Sai an yi salla?" Ya gyaɗa mata kai. Ya yi sallar magariba da isha'i, ta zubo masa Abinci. Washegari ma da sassafe, ta kuma rutsa shi tana shafa masa ruwan nan. Yau ma ture ta ya din ga yi yana girgiza mata kai. Ta kunna masa hayaƙi, ta gudu ta rufe shi a ɗakin. Haka ta sake tarar da shi, ya koma ja ya haɗa uban gumi. Ta yi masa wanka. Ta ba shi Abinci ya karya. Allah ya dafa wa Nana, ba su taɓa rasa abin da za su ci ba. Kuma haka take ta jujjuya kuɗin. Sai da ta gama yi masa duk abin da zai buƙata, sannan ta tashi za ta yi wanka, tana tsaye daga ita sai bra da zani a ƙugunta, sai cika bakinta take da aya mai gishiri, ga cikinta ya ɗaga sosai. Ta waiwayo suka haɗa ido. "Ya ake kallona haka?" Ya yi mata alama da hannunsa mai lafiya ta zo. Ta ƙaraso gabansa ta durƙusa ta ce "Gani" ya nuna mata cinyarsa. Ta ce "Ina da nauyi fa, jiya ma dan na tsokane ka na zauna, ka ga baka da lafiya" ya saka hannu ya janyo ta, ta hau cinyar tasa tana dariya. Yatsansa ya saka ya ɗan latsa cikinta, ya kalle ta yana murmushi. Ita ma murmushin ta yi ta ce "Kullum sai ya ce ko ta ce tana gaishe ka" Da hannunsa yake tambayarta yaushe za ta haihu? "Nima ban sani ba, amma dai bai fi wata  huɗu ba, saura wata biyar in Allah ya sa mu na raye. Idan ka samu lafiya sosai, za mu je mu ƙara dubawa idan su Habu sun dawo, idan ba su dawo ba sai mu tafi Nijar. Duk da na san da sun dawo zuwa yanzu za su neme mu" Ya yi shiru yana ci gaba da kallon cikinta, da lokaci lokaci yake dan harbawa. "Zan je na yi wanka" Da hannunsa ya yi mata alamar, su je ya yi mata. "Kana fama da kanka za ka yi mini wankan? Wato a ramawa kura aniyarta ko? To na yafe idan Allah ya baka lafiya sai ka yi mini Rayuwata" Cikin murmushi ya sunkuyo da kanta ya sumbaci goshinta ta da laɓɓanta. Hira yake so ya yi da ita, amma ya kasa sai dai ya kalle ta yana murmushi ko kuma ya din ga yi mata nuni da hannunsa. Ya ɗauki wayarta, ya kunna waƙar da take yi masa, yana yi mata nuni da ta yi masa. Ta ce "A'a karatu za mu ji ba waƙa ba, a wannan yanayin da muke ciki, ai ba mu ga ta waƙa ba Sayyid" Ya tsuke fuska yana hararta. Ta ce "To shikenan, bari a kashe waƙar, sai na raira maka da bakina ko?" Kawai ya tsare ta da ido yana wani lumshe ido. Tana dariya ta ce "Wai Sayyid ni fa ban gane maka ba kwana biyun nan, rigima ka ke ji, amma Alhamdillah alamun sauƙi ne da nasara. Aka shiga kwana na huɗu, tana shafa masa tofi tana kunna masa hayaƙi ta gudu ta bar shi a ɗaki. Yau sai dai ta gama shafa masa, za ta gudu ya riƙe ta gam. Duk yadda ta so guduwa ta kasa. Ya kalle ta yana murmushin mugunta. Aikuwa jikinta ya fara tsuma ta saka masa kuka, jin yadda gaba ɗaya duniyar take juya mata, tana shirin fita hayyacinta. Har dare ya yi suka kwanta, ba ta kula shi ba, dan gaba ɗaya jikinta ya mutu murus, babu abin da yake yi mata daɗi. Can cikin bacci ta ji ya yi magana"Ma viee" "Sayyid" "Na'am" "Magana ka yi?" "Eh, yanzu na ji ta zo" Ta tashi zaune cikin murna tana taɓa shi ta ce "Alhamdillah Sayyid, Allah ya ƙara lafiya" "Taɓa ni na ji, ko zan ji wani abu" Ta ce "Ga shi ina taɓa ka" Ya ce "Ba wannan ba" ya yi maganar yana rungumota da duk hannayen sa biyu. "Sayyid hannunka ya warke?" Ta tambaye shi a kiɗime cikin farin ciki. "Eh" ya amsa a taƙaice yana ƙoƙarin yin wani abin daban. "Bari na lalubo waya na haska ka na gani" "Kar ki haska ni" "Me yasa ganinka fa zan yi, hannun zan gani" "Kar ki haska ni" ya sake maimaitawa. A ɗan tsorace ta ce "Anya kai ne?" Ya yi dariya ya ce "A'a Ƙaisar ne. Idan ma ba ni ba ne, ai kina ganewa" Ta yi dariya ta ce "Wai Sayyid ya haka ne? Ka tsaya mu yi murnar ka samu sauƙi" Ruf ya rufe bakin Nana, bayan ya tabattar da lafiyarsa ta dawo. Duk da ya yi farin ciki da miƙewar da hannunsa ya yi, wanda farkawa ya yi daga bacci kawai ya ji hannun ya saki, duk da ya yi masa wani iri babu daɗi. Bayan wani lokaci, ya saka hannunsa ya ɗaukko fitila a gefen Nana, ya kunna ya haske ta. Rufe fuskar ta ta yi, ta juya bayan ta da sauri. Ya kwanta a jikinta yana yi mata raɗa a kunnenta. "To tashi ki haska ni ki ganni, kin ga hannun" Nana ta ƙare rufe fuskarta a fulo, ta ƙi ɗagowa. "Kin ga" ya yi maganar yana taɓa ta da hannun. Shi wannan abubuwan da take yi ma, ba ƙaramar dariya take ba shi ba. Da ƙyar ta tashi, tana kallon hannun nasa da take ganin, tamkar almara ya miƙe. Ta ja hannun ta ga ya miƙe, ta ce "Kuma ba ya ciwo?" Ya girgiza kai yana taɓa hannun ya ce "Ba ya yi" "Allah ya ƙara maka lafiya mai ɗorewa" "Amin. Na gode. Na gode" ta rufe bakinsa ta ce "Ya isa haka. Allah za mu godewa" "Alhamdillah. Amma ya zama dole na yi godiya, kuma na jinjina miki, saboda" bai ƙarasa maganar ba ta cije shi a kafaɗarsa, kamar yadda ya kan yi mata, idan yana jin raha. Kamar ba su ne cikin zullumi da damuwa ba, suka koma shagalinsu. Dare ya tsala amma tamkar rana a gare su, ƙarshe ma zaman hira suka zauna. Da anjima sai ta tattaɓa hannun nasa, dan ta tabattar lafiya kalau yake bai kuma maƙalewa ba. Haka suka kwana cikin nishaɗi, da kewar juna. Da safe ta gama abin da take yi, ta shigo da maganin da take shafa masa, ya kalle ta ya ce "Wallahi ki ka zo kaina da wannan abun, sai na yi miki wanka da shi, ke ma na kulle ki a ɗakin, ki ji abin da nake ji" Ganin yadda ya haɗe rai ya sanya ta rabu da shi. Wunin yau ma lafiya suka yi shi, babu damuwa, duk da jikinsa babu ƙarfi sosai. Ya ci Abincinsa ya yi sallolinsa babu wata matsala. Sai dai yau ma Nana ba ta samu rintsawa yadda yakamata ba, sai da ta san ya warke. Wani nannauyan bacci ya yi awon gaba da ita. Wani mutum ta gani a tsaye a jikin bishiya, ya lulluɓe jikinsa da mayafi. Ta yi tsuru tana son ta ga waye haka. Yana ɗaga mayafin ta ga fuskarsa, ta ja da baya, ta tsorata. Tsohon nan ta gani, jikinsa yana ta fitar da wani irin baƙin abu, fuskarsa ta yi baƙi ƙirin, ga hayaƙi na fitowa daga cikin bakinsa da hancinsa gaba ɗaya siffarsa ta yi muni babu kyawun gani. Sai da Nana ta ja da baya, cikin tsoro da razani. "Kin tafka kuskure yarinya, kuma za ki san kin taɓa Giyaz bin Jaddul Jinn. Babu wanda ya taɓa karya alkadarina, abu ya yi tasiri sosai haka a jikina. Dan a duk lokacin da aka yi yinƙurin illata ni, barin guri nake yi. Sai dai kash kina ɗauke da abin da aka yi mini tarko da shi a wancan karon." Ya jefo mata wani littafi jikinta ya ce "Ga shi nan, littafin da ki ke ta bibiya sai kin ji ƙwaƙwaf, ki ƙarasa karantawa kafin na je na yi jinya na dawo. Amma ki sani dawowata ba za ta haifar miki da ɗa mai ido ba. Domin illar da ki ka yi mini sai na ninka wa mijinki, wahalar da ki ka sha ba ki ga komai ba." Kawai ya ɓacewa ganin Nana. Nana ta kalli littafin hannunta, na gurin Ƙaisar ne, da take ta bibiyar sai ta karanta hanata. Da kansa littafin ya buɗe, a daidai shafin da tsaya da karantawa wancan karon. Jiki na tsuma ta ci gaba da karantawa. Jama'ar da suke gurin girkar, wasu suka watse a dalilin gakin sarkin Aska ya bayyana a gurin, kar ya gansu ya hukunta su. Bayan musayar yawu a tsakanin Duna da uban duƙusa, Sarkin Baka ya yi girgiza ya ɓace. Uban duƙusa ya saka aka ɗauki kakan Lanti, a ka kai shi gida. Ita ma Lantin tana zuwa gida ta faɗi ƙasa. Ba ta sake farfaɗowa ba sai washegari. Sai dai bayan farfaɗowarta, ta tarar da kakanta cikin mawuyacin hali, wanda hakan ba ƙaramin ɗaga mata hankali ya yi ba. Cikin damuwa mijinta ya ce "Lanti sai da na gaya miki ina jin tsoron wannan abun, ki ka ce babu komai, ina tsoron kar rikici ya ɓarke a garin nan" "Babu rikicin da zai ɓarke, ka kwantar da hankalinka, ni dai kawai fatana na kawo ƙarshen Sarkin Aska." Kakan Lanti da ya yi tari, sai aman jini, dama ga jikin tsufa, ya zamana ko tashi baya iya yi saboda buguwar da ya yi. Kwanaki huɗu da faruwar lamarin, Lanti tana yi masa hayaƙi da ganyen ɓaure. Ya riƙo hannunta ya ce "Ya ke jikata, ki sani na yi miki Girka da babban Aminina, kuma ya ɗaukar mini alƙawarin ba ki duk wata kariya, da zama mai hidima a gare ki, kuma ya yi alƙawarin bawa zuriyarmu kariya daga cutarwar miyagun Aljanun cikin su. Dan haka a duk lokacin da ki ke buƙatar ganawa da shi, ki sanya kayan saƙin ki, ki ɗaura gurunki. Sai dai kar ki kira shi a guri mai ƙazanta, ba ya son zama a guri mai ƙazanta, kuma ba ya zama a guri mai najasa. Sannan 'yar ki Duna ne ya shafe ta, kuma ga wannan abu da ya faru, abu ne mawuyaci ta warke, sai dai idan uban duƙusa ne ya samo mata magani. Ni na san ba zan rayu ba, Duna ya riga ya yi mini illa, dan haka ki kula da mutanen Buda. Yana gama faɗin haka wuyansa ya karye. Lanti ta fashe da kuka, ya buɗe baki yana son ya yi mata magana amma ya kasa, har ya daina motsi ya mutu. Nana ta yi kuka ba kaɗan ba, da mutuwar Kakanta. Ƙaisar ne a tsaye a kan wani dogon tsauni, gabansa kuma Giyaz ne, da yake kamannin da shi sak, tamkar ya yi kaki ya ajiye. "A kan me za ka je ka aikata wannan shirmen da ka yi? Ko har ka manta da cewar fansarmu za mu ɗauka a kan abin da mutanen nan suka yi mana?" "A'a Giyaz, mutanen nan ba su ne ainihin waɗanda suka fara rigimar nan ba, kuma ɓarnar da aka yi musu ta yi yawa. Babu amfani rashin zaman lafiya da tashin hankali. Kuma ka duba irin cutarwar da abokinka Duna ya haɗa kai da sarkin Aska yake yi wa mutanen garin nan. Yakamata a zauna lafiya, haɗa kai da bil'adama ana cutar da jinsinsu ba zai haifar da ɗa mai ido ba." "Rufe mini baki Ƙaisar" Ƙaisar ya kalli mahaifinsa jin ya kira shi da sunansa na yanka, saɓanin sunan da yake masa kara da shi, na uban duƙusa wanda da shi ake kiransa saboda kara ga mahaifinsa. Dan duk cikin bataliyar 'ya'yan da ya haifa, ya fi ƙaunar sa. Ya ɗora da cewa "Kar ka manta abin da suka yi wa Mahaifina Jaddul Jinn wanda yake kaka ga duk wani Aljani da yake nahiyar nan, da yadda ake girmama shi, sai mene ne dan a azabtar da su. Dan mene zaka hau kan bil'adama a matsayin bawa, duk da kasancewar ka ƙasaitaccen matashin aljani da ake ji da shi a jinsinmu" ya yi maganar cikin ɗaga murya, muryarsa na amsa kuwwa a ilahirin dajin. "Zaman lafiya da kwanciyar hankali, mu rayu mu da su babu cuta babu cutarwa. Lalata musu amfanin gona, sanya musu rashin lafiya da makamantansu duk ba zai sanya ku huce ba, tun da waɗanda suka yi laifin na sun mutu basa nan" "Uban duƙusa yanzu ka fifita bil'adama a kan ni mahaifinka?" "Ko ɗaya, sai dai ka san muna mutunta yarjejeniya. Mun yi yarjejeniya da abokina, zan ci gaba da bawa zuriyarsa kariya, zan kula 'yar sa zan din ga kawo mata magunguna tana bayarwa. Kuma ya yarje mini ci gaba da yi wa zuriyarsa hidima, da bayar da magani ta hanyar waɗanda aka haifa da tauraron 'yar sa Lanti" "Ƙarya ka ke yi Ƙaisar. Ɗana ba zai zama bawa ga gajiyayyun halittu kamar bil'adama ba, ka sani yadda suke yi mana kallon halittu maƙaryata, haka su ma ba su da cika alƙawari. Ka tuna kai makaranci ne, manazarci kuma marubuci. Ka karanta litattafai da ni kaina ban san adadinsu ba. A ɗakin karatun ka akwai litattafan da aka rubuta dubbanin shekaru kafin zuwanka Duniya. Ka yi yawace-yawace a Duniya domin neman abubuwan rubutawa, kuma ina da tabbacin ka karanta tarin kashedin da magabantanmu suka yi mana a kan bil'adama. Dan haka ba zan bari iliminka da soyayyar da nake yi maka, su ƙare a kan yi wa biladama hidima ba, ba ma su su yi maka ba. Sai dai ka zaɓa, zama da mu ko kuma hidima ga bil'adama!" Ayshercool 08081012143 59 Ƙaisar ya ce "Haƙiƙa kai Babana ne, ka so ni mai sonka ma ya so ni. Kuma na san ni ne ruhi mafi soyuwa a gare ku. Ka tallafawa burikana da bani damarmaki a matsayina na ɗanka. Sai dai ka tuna, na kawo girman da zan iya yankewa rayuwata hukunci. Kamar yadda ka faɗa; na karanta kashedin da aka yi mana a litattafan magabata, na yi yawon neman labarai a duniya, amma babu inda na ga an ci riba da tashin hankali da yaƙar juna. Kuma Aljani bai taɓa nasara a kan bil'adama ba, komai tasirin cutarwar da ya yi masa. Na yi abota da bil'adama, na karanci wasu abubuwa masu muhimmanci dangane da zamantakewar su. Kuma ina son na yi amfani da ilimina na sanin magunguna, na sanar da wasusn su, domin samun waraka daga wasu cututtukan da mu ne muke haddasa musu su. Dan haka ina mai baka haƙuri, na riga na yi alƙawari ba zan iya warwarewa ba. Sannan ba a banza zan yi wa zuriyar sarkin baka wannan aiki ba. Kamar yadda na gaya maka, sun sadaukar mini da duk wani mai irin tauraron Lanti, domin gudanar da burina na son yaɗuwar ilimin bayar da magani" Cike da ƙunar rai Giyaz ya numfasa ya ce "Shikenan, ka yi abin da ka ke so, amma ka je, na sallama ka daga cikin zuriyaramu, kar ka sake danganta kanka da mu" daga haka Giyaz ya ɓace. Lanti ta damu da mutuwar kakanta, sai dai ba a rufa sati ba, 'yar ta ma mai larurar shan Inna ta mutu. Ta shiga tashin hankali sosai da sosai, tamkar za ta zauce. Hankalin Sarkin Aska kuwa ya yi mummunan tashi, bayan da Duna ya sanar da shi cewar, da Uban duƙusa aka yi wa Lanti girka. Kuma cutar da Uban duƙusa ka iya kawo fitina da tashin hankali a tsakanin su kan su Aljanun. Duk da zafin bil'adama da Giyaz yake ji a kan abin da suka yi wa mahaifinsa, amma ba zai lamunci kowane Aljani ya taɓa masa ɗa ba. Sarkin Aska ya ji baƙin ciki ba kaɗan ba,  da abin da Duna ya gaya masa, bayan tabattar da cewa ya samu abokiyar hamayya a garin. Ƙaisar ya fara bawa Lanti magunguna, ta fara aikin bayar da magani a garin. Babu nasiha da rarrashin da ahalin Ƙaisar ba su yi masa ba, a kan ya janye daga harkar taimakon biladama, amma fafur ya ƙi ya ce ba zai daina ba. Akwai kyakykywar fahimta a tsakanin Lanti da kuma Ƙaisar. Lanti ta kuma samun juna biyu, ta haihu sai dai ɗan da ta haifa, ba ta haife shi da irin taurarinta ba. Aka shiga zazzafan takun saƙa, a tsakanin Lanti da Sarkin Aska, dan mutane suna tururuwar karɓar magani a gurinta. Domin ita ba ta tsauwwala wa mutane, kuma ba ta neman su kawo wani abu da ya fi ƙarfinsu. Duk da Giyaz ya sallama Ƙaisar, amma hakan bai bayar da damar, 'yan uwansa su iya cutar da shi ba. A lokacin sai zuriyar Jaddul Jinn wasu suka goyi bayan zaman lafiya, kamar yadda Ƙaisar ya yi, wasu kuma suka zauna a kan bakar su na lallai sai an ci gaba da cutar da bil'adama da duk wanda ya fito daga wannan tushe na Buda. Sarkin Aska ya ci gaba da jan Aljanu, yana sadaukar musu da jini, yana amfani da su ta hanyar tsafi, da kuma alwashin taimaka musu a duk lokacin da suke buƙatar hakan. Cike da baƙin ciki, Giyaz ya zura wa Ƙaisar ido, babu yadda ya iya da shi. Ganin abin da Sarkin Aska yake ci gaba da yi, duk a ƙoƙarin sa na mamaye garin a ci gaba da tsoron sa, ya sanya Lanti ta ƙara zage damtse a kan harkar bayar da magani da laƙantar hanyoyin da za ta kawo ƙarshen Sarkin Aska. A haka ta haifi yara biyar maza, duk babu mai irin tauraronta, gaba ɗaya abin ya damu Ƙaisar, ganin babu wanda zai iya gadar ayyukan Lanti. Sai dai a jininsin mutane ma, 'yan uwan Sarkin Aska ba sa ƙaunar abin da yake aikatawa na zaluntar mutane. Wata jakar fatar damusa, Ƙaisar ya sanya Lanti ta fara haɗawa, wadda da ita take burin kawo ƙarshen Sarkin Aska, saboda babu irin mugun hari da yinƙurin da Sarkin Aska ba ya yi, dan ya kashe ta. Sai da ta shekara biyar, tana aikin jakar nan, tare da jiƙata da magunguna daban-daban. Ban da zanen hatimai kala-kala da yake cikin jakar. Ta haɗa kai da ɗan uwan Sarkin Aska, baya nan ya je ya ajiye masa jakar a ƙasan abin kwanciyar sa. Kuma ƙaisar ya ɓatar da sahun sa, ta yadda babu wanda ya gane a cikin aljanun da suke yi masa hidima. Tun da ya kwana a kan jakar, Aljanun da suke yi masa aiki, suka watse suka bar shi, ya kamu da matsananciyar rashin lafiya da sai da ta yi ajalinsa. Yana mutuwa kuma aljanun suka fantsama kan 'ya'yansa da jikokinsa, sai dai aka rasa wanda zai gaje shi gurin ci gaba da aikin zaluntar al'ummar da yake yi. Sosai mutanen gari suka yi murna da mutuwar sa. Babban ɗan sa da suke bokancin tare ma, cewa ya yi ba zai iya ba. Ƙin samun wanda zai gaje shi, ya sanya aljanun fara sanya wa iyalansa cututtuka. Wasu kuturta wasu suka makance, har da waɗanda suka haukace. Aka din ga ɗauki ba daɗi da Lanti, a kan sai ta warkar da su. Ƙaisar ya gargaɗe ta a kan babu ruwanta ta rabu da su. Lanti ta shafe shekaru Ashirin da bakwai, tana aiki tare da Ƙaisar tana harkokinta na bori da bayar da magani, haka zalika ita ma ta yi wa mutane da dama girka, masu sha'awar harkar bori. Akwai bikin 'yan bori da ake gudanarwa da nuna bajinta duk shekara, wanda a nan ake yi wa masu so girka, ake bikin bajekolin abubuwan ban mamaki, na gidaje daban-daban. Maharba su yi na su, wanzamai, 'yan bori da dai sauran su. Domin bayan mutuwar Sarkin Aska an ɗan samu zaman lafiya, tun da dama shi yake assasa duk wata fitina da rashin zaman lafiya. Sai dai aljanu ba su fasa cutar da su da razana su ba, duk da Lanti tana iya kokarinta. Sai dai ita ma bayan wannan shekarun ta koma ga Allah. Sai dai kan ta mutu, a cikin jikokinta an samu guda ɗaya da take da irin tauraronta. Dan haka bayan mutuwar Lanti, aka ci gaba da ba ta kashi tsakanin mutanen garin, da Aljanun da sarkin Aska ya yi aiki da su, har ma da waɗanda ba 'yan asalin garin ba ne. Sai dai babu yadda Ƙaisar zai yi, a lokacin jikar Lanti ba ta kai lokacin da za ta iya bayar da magani ba. Kuma har a lokacin ba a fasa yi masa magiyar ya rabu da bil'adama ba. Gaba ɗaya ya nesan ta kansa da Ahalinsu. Bayan jikar Lanti ta fara tasawa, Ƙaisar ya fara bijiro mata, domin yin gadon kakarta, sai ta kasa ɗauka sai ma taɓin hankali da ta samu, duk da ta ɗan taɓa bayar da maganin amma ba sosai ba. A hakan ita ma ta yi aure ta hayayyafa. A cikin 'ya'yanta aka samu wadda ta gaje ta, duk da ba irin tauraronta ɗaya da Lanti ba. A lokacin Musulunci ya shigo cikin mutane, duk da bai yi ƙarfi a garin Buda ba. Asma'u ta bayar da magani ita ma, ta yi aiki tare da Ƙaisar, sai dai ba ta da ƙarfin zuciya da juriya irin ta Lanti. Gaba ɗaya ita ma ba wani daɗin aiki ya ji da ita ba. Ko yaya ya buɗe mata ido ta ga abu, sai ta kwanta ta hau jinya. Daga baya ma ta watsar ta tattara komatsan borin ta ajiya, ta ce ta tuba ta daina. Ganin ba a samun masu irin tauraron Lanti, ya sanya Ƙaisar fara sarewa, da haƙura da batun bayar da magani ta hanyar bil'adama. Sai dai yana iya yin sa gurin bawa zuriyar su Lanti kariya, daga cutarwar zuriyarsu. Duk abin da yake faruwa, Giyaz yana ankare da Ƙaisar, kuma yana murnar yadda ɗan sa ba zai ci gaba da zama bawa ga bil'adama ba. Aka din ga samun ci gaba a garin Buda, wasu suka din ga barin garin su na tafiya fatauci, wasu kuma tashin hankalin Aljanun da ya addabi garin ne ya sanya suka bar garin, ciki har da wasu daga cikin zuriyar Lanti. A can Bauchi aka haifi Maijidda, har ta girma, an saka mata rana saura watanni uku aurenta, su ka zo Buda, a nan suka haɗu da Isa, ya ƙallafa rai a kanta. Yayar kakarta ta ce sai an warware wancan baikon da aka yi da na can garin Bauchi, an yi da Isa, saboda ƙara danƙon zumunci, kuma hakan zai sanya su din ga kawo musu ziyara a kai a kai, da ƙara samun zaman lafiya a tsakanin zuriyar maharba da ta wanzamai. Aka mayar wa da wancan na Bauchi kuɗinsa, ita kuma ta auri Isa. Gidansa na Kano, inda yake harkokin kasuwancinsa, nan ya tafi da ita. Ya ajiye ta a gidansa da suke tare da matarsa babar Gaddafi. Ya ɗora wa Maijidda son duniya, kamar a kanta ya taɓa aure. Ba uwargidansa ba, hatta 'yan uwansa sai da suka fara jin haushin Maijidda saboda ba ya ɓoye son da yake yi mata, ga ta yarinya ƙarama amma su na ganin kamar ta mallake shi, dan shekarunta goma sha shida a lokacin. Kasancewar daga zuriyar Sarkin Aska Maijidda take, ta auri ɗan zuriyar Sarkin Baka, sai Aljanun da suka yi wa sarkin Aska hidima, suka shiga cikin lamarin auren, su ka fara haddasa musu matsala. Haka kurum sai ta ji ta tsani Isa, ba ta ƙaunar ganinsa ga yawan rashin lafiya. Kishiya da facaloli suka sako ta a gaba, ga jarabar dangin miji. Ana haka ya samu matsala da uwargidansa, da ta haifa masa Gaddafi da Ummi, ya sake ta. Nan ma aka ce Maijidda ce sila. Ya auri Rabi, suka zama ita da Maijidda. Yayarsa Atine ta ƙara haɗe kai da Rabi, su na cizguna mata. Maijidda ke riƙon su Gaddafi, tana iya kokarinta amma kullum cewa ake yi tana azabtar da su. Kasancewar Gaddafi ya fi Ummi wayo, ya tsani Maijidda cewa yake saboda ita aka saki babar su, kamar yadda Yaya Atine take faɗa. Ita kuma Ummi tana matuƙar ƙaunar Maijidda. Nan ma Rabi ta saka Maijidda a gaba, da kishi da ƙage kala-kala. Bayan haihuwar Imran sai da ya shekara uku da rabi, ta haifi Nana. A lokacin Isa ji yake kamar ba a taɓa yi masa haihuwa ba sai a kan Nana. Ya saka mata suna Asma'u, sunan kakarsa da ta riƙe shi take bala'in son sa. Hatta hakika biyu ya yi wa Nana, Ummi ma da ya saka mata sunan mahaifiyarsa bai yi mata abin da yake yi wa Nana ba. Isa kofur ne na 'yan sanda, abokan aikinsa suka yi masa ƙage, aka kore shi daga aiki har da prison. Ya koma harkar fawa, ya fara samun rufin asiri, harka ta buɗe masa yana samun rufin asiri sosai , sai dai kasancewar sa mutum ne da ba shi da sirri, duk samun sa sai ya bayar da labari, abokansa suka jefe shi sana'ar ta fita daga ransa ya daina zuwa ko ina, sai zaman gida. Tun da Allah ya sanya aka haifi Nana Ƙaisar ya ganta ya rikice, tamkar Lanti ta yi kaki ta ajiye saboda kamanin su. Ga irin tauraronta ɗaya da Lanti. Gaba ɗaya Ƙaisar ya tattara hankalinsa a kan Nana Asma'u yana ganin, ya samu uwar gijiya a zuriyar Lanti. Giyaz na fuskantar abin da ke shirin faruwa, ya fara ƙoƙarin raba Ƙaisar da Nana. Dan kullum yana tattare da ita. Wasu lokutan ya zungure ta tayi ta kuka. Manyan bokaye da ƙungiyon Asiri na zawarcin son yin aiki da Ƙaisar, saboda tarin baiwa da kuma ilimi da binciken ƙwaƙwaf da yake yi. Wanda za su aiki da shi ne, ya din ga taimaka musu, su kuma su din ga yi masa hidima, amma fafur ya ƙi. Saboda ba ya son duk wata alaƙa da jini. Ƙaisar ya yi tafiya zuwa wata ƙasa, ganawa da wani tsohon Aljani, a kan wani rubutu da yake yi, ya dawo ya tarar an saki Babar Nana, ita kuma Nana ta daina magana, ta daina tafiya ga Baba ya ƙwace ta, ya hana Maijidda ita. Ya fuskanci aikin mahaifinsa ne Giyaz. Ya je ya same shi yake tambayar sa me yasa ya yi wa Nana haka. Giyaz ya ce "Ka sani ba zan taɓa sake yadda, ka zama bawan bil'adama ba, da ka sake zama bawan bil'adama gara na kashe ta ko na kashe ka, kowa ma ya huta." Ƙaisar ya san Giyaz ba ya magana biyu, idan ya faɗi magana sai ya aikata. Dan haka Ƙaisar ya fara ƙoƙarin kare Nana, ya yi amfani da jakar da ya saka Lanti ta haɗa, ta yi amfani da ita gurin kashe Sarkin Aska. Ya ƙara yi mata aiki, da saiwoyi da wasu hatimai, ya yi wa Giyaz tarko da ita. Cikin matsananciyar sa'a, Giyaz ya faɗa tarkon Ƙaisar, saboda ya san muddin ya bar Giyaz, zai iya nakasta Nana nakasa ta har abada, ko ma ya kashe ta, kamar yadda ya furta. Ya ɗauki Giyaz, ya kai shi can nesa ya sadaukarwa wani boka shi, bisa musayar da za su yi, zai ba shi wani abu mai muhimmanci. Wanda ya yi hakan domin nesan ta shi da Nana da zuriyar Lanti. Duk da abin da ya yi ya dawo ya dame shi, yana matuƙar ƙaunar mahaifinsa, duk da saɓanin da suka samu, amma babu yadda iya, hakan ne kawai zai sanya ya nisanta shi da Nana. Sauran 'yan uwan Ƙaisar da tuntuni suke jin haushinsa, suka yo caaa a kan Ƙaisar, har suka nemi hallaka shi, saboda abin da ya yi wa mahaifinsu, amma sun san ko sun hallaka shi, idan Giyaz ya kuɓuta suma sai ya kashe su. Ɗan uwan Giyaz Duna, ya yi ta ƙoƙari gurin ganin ya kuɓutar da Giyaz, amma abu ya gagara. Nan suka din ga kai wa Nana hari, da yinƙurin hallaka ta. Maijidda kuwa bayan mutuwar aurenta, tana gama idda, Iliyasu tsohon saurayinta ya sake dawowa ya aure ta. Ko da Baban Nana ya samu labari, sai ya ce tana sane, ta ƙi zama da shi, saboda ta koma ta auri Iliyasu, dama son zama da shi take yi ba. Nana ta ga garari tun da ƙuruciya, babu cikakkiyar kulawa, kuma tun ba ta fi shekara uku ba take ganin Ƙaisar, da ma sauran 'yan uwansa da suke ta kokarin azabtar da ita. Maijidda ta so karɓar ko Nana ce, saboda rashin cikakkiyar lafiya, amma Isa ya hana fafur, ita ma can mijinta ko yaya ta motsa tana son ganin 'ya'yanta, sai ya hau bala'i wai za ta gurin tsohon mijinta. Tun Nana na ƙarama, take nuna alamun rashin lafiya, amma babu wanda ya kula. Ta kan wuni tana bacci tun safe, har dare babu wanda zai damu. Wasu lokutan ta daina magana ma ko tafiya gaba ɗaya. Idan kuma ta warware ta din ga fitinar da ta fi ƙarfin shekarunta nesa ba kusa ba. Ta kan ga Ƙaisar a zahiri, ko kuma a cikin bacci. Babu wanda ya damu da ta ci Abinci ko ba ta ci ba, mussaman da Baba ya daina sana'ar komai, sai dai Imran ya nema ya bata. Idan ta fita Ƙaisar ya kan zo a suffar mutum, ya ba ta abinci. Allah ya sanya masa matsananciyar ƙaunarta. Ya fara bayyana a jikinta ne, tun wani duka da Mama ta yi mata, bayan faɗa ya haɗa ta da Jamila. Sai da ta kwana biyu a sanƙame, tun daga nan suka gane halin da take ciki. Da ranta ya ɓaci sai hankalinta ya gushe. Ƙaisar ya sha ɗauke Nana, a neme ta a rasa kwana ɗaya ko biyu ya je ya ajiye ta gurin sa. Baba ya yi ƙoƙarin nema wa Nana magani, amma abu ya gagara. Labari ya iske Maijidda halin da Nana ne ciki, bayan da su Adda Saude suka zo ganin su Nana. Rabi ta haɗa tuggu a gurin Baba, ya ce kar su sake zuwar masa gida, kuma ba zai bayar da Nana ba. Wahala ta saka Imrana fara sace-sace saboda su ci Abinci, Rabi ta saka Baba ya kore shi daga gidan. Haka Nana ta tashi a cikin wahala, ga wanda bil'adama suke yi mata, ga wadda Ƙaisar yake yi mata da sunan kulawa. Ji ta yi tamkar an sanya hannu an shaƙe ta, a dole ta saki littafin ta ja da baya tana tari. Ta ɗaga kai ta kalli Ƙaisar, bai ce mata komai ba, ya ɗauki littafinsa ya juya ya tafi. Yana barin gurin Haula ta zagayo ta dafa Nana. Ta ɗaga kai ta kalle ta ta ce "Ƙawata, kwana biyu. Hadiminki ya ƙi saurarata balle na sanya ran zai karɓi buƙata ta, ki yi wani abu a kai dan Allah" Nana ta ce "Haula, gaba ɗaya jinsinku ba abin yadda ba ne, ki rabu da ni da wannan maganar ta ku" "Shikenan, na rabu da ke, amma kin yi ganganci abin da ki ka yi wa dattijo, Allah kaɗai ya san me zai yi miki idan ya gama jinya. Kuma har Ƙaisar ki ka janyowa shi ma ba zai bar shi ba" "Duk hukuncin da ya yi wa Ƙaisar yayi daidai, ɗa na gari ba zai taɓa yi wa babansa abin da ya yi wa nasa mahaifin ba" Haula ta ce "Kash! Nana kar ki zama butulu mana. Sai dai ina fatan kin fuskanci jakar gurin Sarkin baka da ya baki, wace jakar ce" Nana ba ta ba wa Haula amsa ba, Sayyid ya tashe ta. "Ma vie" yayi maganar yana matsawa jikinta sosai. Jiki a sanyaye ta amsa masa. Ya ce "Lafiya dai?" "Mmm" "Ko Ƙaisar ɗin ne?" "A'a" "To me yasa ki ka tsorata? Mene ne ya baki tsoro?" "Bakomai" "es-tu sûr? (Kin tabatta?)" Ta ce "Eh. Haryanzu hannunka lafiya ƙalau ko?" "Eh, amma akwai abin da ya tsorata ki, gaya mini mene ne?" Ji ta yi tamkar ta gaya masa, dan a wannan karon ba ta manta abin da Giyaz ya gaya mata ba, a kan idan ya warke zai sake waiwayar su. "Ma viee" "Sayyid" ta amsa a hankali. Ya yi maganar yana taɓa wuyanta "Sanyi ki ke ji Rayuwata" "Eh, amma ba sosai ba" "In baki ɗumi ne?" Yayi maganar muryarsa ƙasa-ƙasa Dariya ta yi ta ce "A'a na yafe, ƙona ni za ka yi" Shi ma dariyar ya yi ya ce "To ni ki bani sanyin ina so" Ya yi maganar da sigar shawaɓa. "Wai kai ba ka jin bacci ne? Kawai ka farka cikin dare?" "Soyayya ce ta tashe ni" Sai da jikin Nana ya ɗan yi sanyi, ta ce "Soyayya kuma Sayyid?" "Eh, je t'aime ma femme" "To ai ban san me ka ce ba" Ya yi kissing ɗin goshinta ya ce "Ina sonki matata" wani abu ne ya tsirgawa Nana, tun daga tsakiyar kanta, har tafin ƙafarta. Shafa hannunsa ta yi, kamar mai tantamar abin da ya ce, ta ce "Sayyid" "A'a, kar ki yi tantama, ko ki yi kokwanto, shi yasa na baki sunan Rayuwata. Ko a wannan Duniyar, ko ma a wace Duniyar, kawai ina son matata, saboda ita ɗin Rayuwata ce. Babu abin da zai canza hakan." "Sayyid ina tsoron idan ka tuna waye kai, ka ji ba ka so na, zan cutu da yawa, zamana da kai na shaƙu da kai sosai zuciyata ba za ta iya ɗauka ba" Ta yi maganar cikin rauni da tsoro. Ya ɗaga kan Nana, ya sanya hannunsa a wuyanta, ta lumshe idanunta hawaye na bin gefen fuskarta. "Ƙa'idar ba za ta canza ba har abada, babu ruhin da zai samu nutsuwa a gangar jikin ɗayanmu muddin ba ma tare, ki saka haka a ranki. Sayyid yana son Rayuwarsa. Ko babu raina fatalwata za ta ci gaba da sonki" Nana ta yi ajiyar zuciya tare da dariya, ta shafa gashin kansa. "Allah ya sa haka. Ina son mijina sosai nima" murmushi ya yi yana kissing ɗin ta. Har garin Allah ya waye, maganganun Sayyid ne ke kai komo a cikin ƙwaƙwalwa, zuciya da kuma gangar jikin Nana. Wani irin shauƙi da farinciki ne yake kama ta, da tuna kalamansa. "Amarya" ya yi maganar yana kallon ƙwayar idonta. "Amarya da wannan ɗin?" Ta yi maganar tana nuna cikinta da ya fito sosai. Yayi murmushi yana shafa cikin ya ce "Duk da haka amarya ce ai, ko kin manta?" Ya yi maganar yana kashe mata ido. Ta yi murmushi tana ci gaba da ninkin kayan da ta wanke. "Sayyid, bari na je kasuwa na nemo kayan magungunan ka, na dafa maka, ka ci gaba da sha, kuɗin hannuna sun ɗan taru, zuwa ranar Monday in Allah ya kaimu, duk yadda za a yi, mu tafi Kano Asibiti. Na ji haryanzu zuciyarka ba ta bugawa sosai, na san ƙarfin hali kawai ka ke yi" "Gaskiya kin fiye saka ido, ya aka yi ki ka gane hakan, mai magani?" Ta jinjina kai ta ce "Au haka ma za ka ce ko? Hmm ai shikenan, za ka ga mai magani, yau sai na wanke ka da magani na kulle ka a ɗaki" "Eh saboda cin zali ba, kuma ke ki gudu, alhalin kamata ya yi ki yi mana tare" Ganin yadda yake rungumota ta ce "Sayyid na gama shiryawa, fita fa zan yi" Ya ce "Na sani" "Ka sani kuma ka ke son na ɓata lokaci? Dan Allah Sayyid jiya throughout the night mu na tare, yanzu kuma... "Shhhh... Ba ki ji jikina ya fara zafi ba" "Wallahi lafiyarka ƙalau, normal babu zafi a jikinka, wai wannan surutun duk daga ina?" Haka ya hana Nana fita, har bayan Azahar, kawai ta zuba wa Sarautar Allah ido. Kuma a fuskar sa take ganin tsantsar ƙarfin hali, amma ba shi da lafiya. Sai bayan la'asar ta marairaice ta ce "Dan Allah ka bar ni na je na haɗo kayan nan Sayyid, ko haryanzu ba ka gama jin Sanyin ba?" Ya ɗaga mata gira. "To ga mafici, yi ta fifita, har na dawo" Dariya ya yi yana ɗan jan hancinsa. Ya kamo hannunta ya ɗora a wuyansa ya ce "Kin ji da zafi ko?" "Ba wani zafi. Waccan ranar ma wayo ka yi mini, wai na baka sanyin jikina" Dariya yake son yi sosai, amma sai ya yi kaɗan ya cije, ya ce "Ai ni Ƙaisar wasu lokutan taimakona yake yi" A sanyaye ta ce "Shi me yasa ba ka kishi da shi?" "In ji wa? Kawai abu ɗaya ne da babu yadda muka iya. Alaƙarsu ta ɗa da mahaifi tana tasiri a rayuwarmu ni da ke" Cikin mamaki Nana ta ce "Ta yaya? Kuma ya aka yi ka san Ƙaisar ɗan Giyaz ne?" "Yadda ki ke ganin Ƙaisar ku yi magana, haka nake ganin Giyaz, kuma na fuskanci waye shi a tattare da ni. Yanzu ki je ki dawo" "Kai amma na yi mamaki fa, kuma ba ka taɓa gaya mini ba. Bari na je na dawo, ina da tarin tambayoyin da zan yi maka" "Tom sai kin dawo" Ta saka hijjabinta, har za ta fita ya kirawo ta. Ya ce "Ba ki yi mini ba" Ta yi masa kiss a goshinsa, da bakinsa. "Allah ya yi miki albarka. Ki kula mini da kanki, kar wani ya kula mini ke, ki kular mini da babyna ki tafi a hankali ki je ki dawo" Ta kalli cikin ta ce "To Shugaba, in sha Allah" "To a dawo lafiya, I love you" Cikin murmushi ta ce "Inyee ɗan gayu, ka yi furansanci, ka yi turanci, ka yi hausa ga kuma yarenku. Zan koyo yaren da baka iya ba, na din ga tashin kanka da kalaman soyayya" Ya ce "Je ki dawo ki yi mini waƙa" "Sai dai na je na yi maka tsifa, na yi maka sabon kitso" ya tsuke fuska yana hararata. Ta fita tana waigensa tana murmushi. Tana fita ya jingina da jikin bango, yana dafe saitin zuciyarsa, yana haki sama-sama. Ya fito tsakar gida da kyar, ya zauna yana sake danne saitin zuciyarsa da yake jin wani irin abu kamar shocking daga zuciyarsa yana zagayawa bayansa har cikin kansa. Tsayuwar motoci ya ji a waje, sai dai hankalinsa ba ya kan hakan. Ya ji an daki ƙofar gidan da ƙarfi. Ya ɗaga kai ya ga wasu murɗaɗɗun ƙarti sun shigo cikin baƙaƙen kaya. Duk da mawuyacin halin da yake ciki, haka ya yinƙura ya tashi da ƙyar, ganin an shigo da Habu hannunsa da sarƙa. Ya din ga bin mutanen da kallo, Habu cikin matsananciyar damuwa ya zube a kan gwiwoyinsa ya ce "Ka yi mini Afuwa Imam, ba laifina ba ne ka yi haƙuri, na gaza baka kariyar da ta dace" Sayyid ya din ga bin sa da kallo, da alama ma ba ya gane me Habu yake nufi. Ƙartin nan biyu daga cikin su, suka yo kansa, suka riƙe shi. A rikice ya ce "A'a, ku rabu da ni. Me na yi muku?" Ƙoƙari suke su tasa shi su tafi da shi cikin salama, amma ya turje. Suka juya yare zuwa faransanci, su na rarrashin sa, ya wuce su tafi. "Ba zan je ko ina ba? Ina zan tafi na bar matata" Habu ya din ga girgiza masa kai da alamar ya daina faɗar maganar da yake yi. "Ku rabu da ni, ina zaku kai ni na tafi na bar Nana" maganar da yake yi cikin ɗaga murya, ga ƙoƙarin turjewa da yake yi, ya sanya zuciyarsa yin rauni, ya yi baya zai faɗi. Suka tare shi suka saɓa shi suka yi waje da shi. Aka saka Habu a cikin wata motar daban, Sayyid kuma aka saka shi a cikin wata baƙar Highlander mai tint glass, aka rufe suka tafi da shi. Nana tana tsaye ta bayar da kuɗi, za a bata kankana, dan daga ita har Sayyid, kawai ta ji gabanta ya yi wata irin mummunar faɗuwa. Ta yi shiru, ta jiki gaba ɗaya jikinta ya yi sanyi. Kawai ta juya ta tafi. Mai kayan yana ta yi mata magana, amma ba ta tsaya ba, ta nufi gida har da ɗan gudu saboda azabar sauri. Tana zuwa ƙofar gidan ta ga ƙofar gidan a ɓalle, da hanzari ta shiga gidan, tana kiran sunan Sayyid. Amma wayam ba ya nan, ta shiga ɗaki baya nan. Ta duba banɗaki nan ma ba ta gan shi ba. Ta fita waje da sauri, tana kalle-kalle, ta tafi hanyar inda bishiyar kukar nan take, tana tunanin ko jikinsa ne ya motsa, ya tafi can, sai dai can ma baya nan. Ta sake komawa gidan cikin tashin hankali, da wani yaro da yake zuwar mata aike ta haɗu a ƙofar gidanta ta ce "Ashiru, ko ka ga Sayyid ya fito daga gidan nan? Wannan mutumin na gidana farin nan?" "Wasu mutane ne suka shiga gidan suka tafi da shi, a mota suka zo" Sak Nana ta tsaya, tana ƙure Ashiru da ido, tamkar ma ba ta gane yaren da yaron yake yi. Ayshercool 08081012143 60 Cikin rawar murya Nana ta ce "Wace irin mota kuma Ashiru? Ka tabattar kuma Sayyid ne?" "Wallahi na tabattar, ina nan ina wasa suka zo, a motoci wannan farin na gidanki suka ɗaukko." Tamkar mahaukaciya ta bi sahun motar, ita ce har titi ko za ta ga motar da Ashiru ya ce, amma babu wata alama na za ta ga motar da aka daukar mata Sayyid aka saka a ciki. Gaba ɗaya ta kasa kuka, sai tsuma da jikinta yake yi tamkar mazari. Tuni rana ta faɗi, an fara kiran sallar magariba, ba ta san tafiyar da ta yi da nisa ba, sai da ta tashi dawowa. Gidan Uwani ta nufa, ta tarar da ita ta yi alwala, za ta yi sallar magariba. Uwani ta ce "Ke Nana, uban me ya fito da ke da magaribar nan, ga juna biyu kina da shi, duk da na san ba ki da ɗan aike amma koma mene ne, ai kya bari a idar da salla ko?" Nana ba ta yi magana ba, ta nemi guri ta zauna a ƙasa. "Ke lafiya kuwa?" Uwani ta yi maganar tana tattara hankalinta a kan Nana. Amma Nana ta kasa magana, sai murza zoben hannunta da take yi, tana ajiyar zuciya. "Ke ki yi mini magana, kar ki tayar mini da hankali mana". "Sayyid ne ya ɓata" "Kamar yaya sai ka ce wani zakara?" "Da gaske nake" "To ai ban gane ya ɓatan ba ne? Mutumin da yake jinyar ne ya iya tashi ya fita har ya ɓata?" "Ai kwana biyu jikin da ɗan sauƙi, dan har ya ce mu zo nu gaishe ki" Ta yi maganar ba tare da tana iya tantance me ma take faɗa ba. "A'a Nana, wataƙila dai wani wajen ya je zai dawo. Tashi ki yi sallar magariba, zuwa anjima a raka ki gidan ko ya dawo" Nana jin Uwani kawai take yi, ta tashi ta yi sallar magariba, aka yi isha'i. Uwani ta saka Nana a gaba zuwa gidanta, sai dai kamar yadda Nana ta bar gidan wayam babu Sayyid babu dalilinsa. Nana dai ba ta gaya wa Uwani abin da Ashiru ya gaya mata ba, na ya ga an zo da mota an tafi da shi ba. Sai wajen goma na dare, hankalin Uwani ya tashi. Ta sanar da samarin gidan halin da ake ciki. Nan suka bazama a cikin Buda yawon neman Sayyid, duk da galibi ma ba su san shi ba, kwatancensa Uwani ta yi musu, suka tafi yawon neman sa, har gurin jami'an tsaro aka kai rahoto. Sai dai har bayan sha biyun dare, babu wanda ya ji ko ɗuriyarsa. Uwani ta saka aka rufe gidan, ta ce Nana ta zauna a nan, ko zuwa dare zai dawo. Nana a ranta ta ce "Wane dare kuma bayan wannan" Daren ya zame wa Nana dare mafi tsawo a rayuwarta. Damuwa da tunani ya cika mata zuciya. Ba ta tunanin Sayyid zai iya tafiya ya bar ta. Idan kuma da gaske zuwa aka yi aka tafi da shi, to suwaye su ka tafi da shi? Ina suka kai shi, me ya yi musu? Ko dai wani laifin suke aikatawa ba ta sani ba? Amma shi da yake kwance babu lafiya, kullum tana tare da shi a gida, yaushe har yake aikata wani rashin gaskiya da ba ta sani ba. A haka har aka yi assalatu, a kan kunnenta. **** Dare malafar rana, kowa ya bika ya shirya maka. Danƙareriyar mota ce, ƙirar highlander baƙa, take ta kwarara gudu a saman kwalta, tamkar hanyar domin direban kawai aka yi ta. Gefe da gefen hanyat baki ɗaya babu komai, banda yashin sahara, sai busassun bishiyu jefi jefi. Kasancewar dare ne, wata ya kai kwana goma sha huɗu, ya haska ko ina, ga taurari sun yi wa sararin samaniyar ado. Titin ta tsakiyar sahara ya ratsa, wadda yashin saharar ya bayar da sassanyan yanayi. Kallon sa ya yi, daga bisani ya ce "Kilomètre nawa ce ta rage mana ne?" Direban ya waiwayo ya kalli mai maganar wandaa fuskarsa a rufe take cikin rawani ya ce "Bai fi 95 kilomètre ba" "Dans  quelques minutes ?? (Nan da wani lokaci?)". "Bai fi awa ɗaya ya rage mana ba" "Dole fa mu ƙarasa dai-dai lokacin da aka umarce mu, ni ina tsoron ma kar ya farka. Ka ƙara sauri" Ya yi maganar yana haska fuskar Sayyid, da yake kwance a jikinsa ya haɗa gumi, cikin wani yanayi kamar bacci kamar suma, sai dai  yadda yake gumi ya nuna a wahale yake baccin, babu in da yake motsi a jikinsa, sai ƙirjinsa da yake ɗagawa yana sauka lokaci zuwa lokaci, numfashinsa yana fita da ƙyar. Ya kai hannunsa, ya ɗora a kan ƙirjin Sayyid, idan zuciyar sa ta buga sau ɗaya, sai ta jima kafin ta sake bugawa. Sai dai duk bugawar da za ta yi, da ƙarfi take bugawa tamkar za ta tsaga ƙirjinsa ta fito dummm!. Cikin damuwa ya ce "Lowalli, sai ka ƙara gudu fa, kar ya mace mana, bugun zuciyarsa raguwa fa yake yi. Kuma ka san idan ya mace mana mun shiga uku mun lalace" Lauwalli ya jinjina kai yana ƙara gudun motar. Ya ce "In sha Allah a raye za mu kai shi, ba za a samu matsala ba. Dan dai ka ƙi yarda ne, da na ce mu tsaya a Asibiti". "Kai dalla ka daina maganar tsayawa a wani Asibitin nan. Ka yi ka hanzarta mu cika umarnin nan, mukaɗai ake dako" "To shikenan, mun kusa in sha Allah" ya yi maganar yana ƙara gudun motar. **** Antin Yusra ce ta kalle ta, ta ce "Yusra duk wannan kwalliyar fa? Ta karɓar baƙon ce?" "Eh mana Mami, yana hanya ma ai" ta yi maganar tana tafiya ɗakinta, ta fesa turare. Wayarta ce ta fara ringing, ta ɗaga wayar tana murmushi ya ce "Gani a layin" "Duba lambar gidan, za su buɗe maka" Ya ce "Ok" Bayan mintuna goma sha biyar, ta fito ta ce "Mummy na tafi" "To a gaida baƙon, ya tabattar mana da alkhairi" Kawai ta fice tana murmushi. Tana zuwa ta gan shi a tsaye a cikin falon, yana kallon ƙaton frame na hoton mai gidan, da yake retired soja. Ganin abin take tamkar a mafarki, wai Sagir ɗin ta ne a gabanta. Jin ƙamshin turarenta ne ya sanya ya waiwaya. Da gudu ta ƙarasa inda yake ta faɗa jikinsa. Babu tunanin komai, Sagir ya ƙanƙame ta a jikinsa, bar siririn mayafin da ta yafa a kanta, yana zamewa gyararren gashin kanta, da yake ta ƙamshin mayuka ya bayyana. Ya din ga shafa bayanta yana murmushi, kawai ya ji tana sheshsheƙar kuka. A ɗan rikice ya ce "Lafiya, kuka kuma Yusra?" Ya zauna tare da ita a jikinsa, ya ce "Ina ta murna zan zo na gan ki, amma in zo ki din ga kuka, ko ba kya son ganina ne?" Ta girgiza masa kai alamar a'a. "To mene ne" "Ka daina so na, tun da ka sake ni ba ka ƙara nema na ba" Ya ɗago fuskarta su na kallon juna yace "Da na daina son ki, ba zan zo nan ba Yusra, kin san yadda rabuwarmu ta kasance, ban daina sonki ba, ban kuma daina tunanin ki ba" "Almost three years, ba ka sake nema na ba" Sagir ya marairaice murya ya ce "To yanzu ba gani na zo har nan saboda ke ba? Haba wifey" ta zumɓura baki cikin ɗabi'arta ta shagwaɓa. Duk da ya zuciyarsa na tunatar da shi, tare da gargaɗin sa a kan Yusra ba muharramarsa ba ce, amma ya kasa yaƙar kansa, ya ƙyale ta a jikinsa yana jin yadda ya yi kewarta. "Talk mana, na zo kuma kin haɗe rai?" Tashi ta yi daga jikinsa, ta zauna a kusa da shi ta ce "Ya hanya?" "Alhamdillah, ki na lafiya ya jikin naki?" "Da sauƙi" "Kin warware?" Ta girgiza kai ta ce "Bayan ƙin yadda ku ka yi da gaske ba ni da lafiya. Sai ga shi na haɗu da wata Nana, ita ma tana irin ciwon da nake ji, ai ita ta san ba ƙarya nake yi ba." Ya ce "To yanzu dai duk ba wannan ba, i miss you Yusra, irin sosai da sosai ɗin nan fa" "Bayan ka yi aurenka, ba wani missing ɗina da ka yi" ta yi maganar tana tsiyaya masa lemo a cup ta miƙa masa. Ya karɓa ya kai bakinsa yana tsare ta da ido. Ta kalli screen ɗin wayarsa da ya kawo haske, hoton Haidar ya bayyana a kan screen ɗin. Ta ɗauki wayar tana kallon yaron ta ce "Waye wannan?" "Ɗanki ne Haidar, recently ma ta kuma haihuwa ɗan ya rasu" ta yi masa wani kallo, da bai tantance na mene ne ba ta ce "Da tuni nima wataƙila na haihu" Ya yi murmushi ya yi shiru, yana cin abincin da ta zuba masa. Cikin hikima ya karkatar da zancen suka ci gaba da hira. Wayarsa ce ta fara ringing, ta ajiye masa ganin hoton heart a kan sunan. Ya ɗaga wayar tare da yin sallama "Hello love" "Ka sauka lafiya?" "Alhamdillah am good dear" Shukura ta ce "To sai ka dawo, Allah ya tsare mana kai, take care" Ya yi murmushi ya ce "In sha Allah dear" wani abu ne ya tokare wa Yusra a ƙirji, ta zuba masa ido. Ya ajiye wayar, bai kalle ta ba ya ce "Yusy, kin san na yi missing ɗin girkinki over?" Jin ta yi shiru ya sanya ya ɗaga kai ya kalle ta, ya ga tana hararsa. Ya yi murmushi ya ɗebo Abincin ya kai bakinta. Ta murguɗa masa baki ta tsuke fuska. "Smile, haba sweetheart" ta buɗe bakin ya saka mata Abincin. Haka ya ribace ta, suka ci gaba da hira. A nan ya yi sallar la'asar, sannan ta fito raka shi. A jikin motarsa suka tsaya, tana yi masa wani irin kallo mai ƙayatarwa. "Tom sai yaushe zan dawo?" "An jima kaɗan" Ya yi murmushi ya sake kallon ta ya ce "Yusra" Ta ce "Na'am" "Yaushe za ki dawo gidana, ji nake kamar na ɗauke ki, na tafi da ke Kano, ina kewar ki sosai da sosai. Yaushe za ki dawo gidana?" Ta girgiza masa kai ta ce "Ba zan dawo ba" Cikin mamaki ya ce "Saboda me?" "Ka auri wata, kuma Hajiyarka ba za ta bari na dawo ba, su Mami ma ba za su bar ni ba, kuma ma haryanzu ban gama warkewa ba" "Haryanzu ki na so na?" Ta kalle shi ta sunkuyar da kanta ƙasa. "Idan ba kya so na, me yasa ki ka nemi lambata, ki ka kira ni? Kuma har ki ka ba ni dama na zo?" Ta sunkuyar da kanta ta ci gaba da murza yatsun hannunta. "Yusra Sagir ɗin ki ne fa, ɗago ido kalle ni" Kawai ya ga hawaye na bin fuskarta. "Sagir ɗina, da ya rabu da ni, saboda ba ni da lafiya ba" Ta yi maganar tana sheshsheƙa. Ganin babu kowa a gurin da suke, ya sanya ya janyo ta jikinsa, ya ɗago kanta yana kallon idonta ya ce "Yusra, ki na so na haryanzu?" Ta yi shiru hawaye na ci gaba da bin idanunta. "Ki na so na har yanzu, shi yasa ki ka neme ni. Dan haka batun ina da aure, Hajiyata ba za ta bari ba, 'yan uwana ba sa son ki, haryanzu ba ki da lafiya, duk ba ta taso ba. Za ki dawo gidana a karo na biyu in sha Allah. Haryanzu ina son ki Yusra" "Amma... "Babu amma tsakaninmu, believe me zan dawo da ke gidana in sha Allah" Jikinta ya yi sanyi. Ya cika ta a hankali, ya shiga motarsa. Ta tsaya ƙyam tana kallonsa, shi kansa da kyar ya tafi, tamkar ya ɗauki Yusra ya tafi da ita. Har ya kama hanyar Kano, zuciyarsa cike da tunanin ta ina zai fara. Dan shi har ga Allah yana son matarsa, ba a son ransa ya rabu da Yusra ba. Yanzu kuma da ya ganta, gaba ɗaya ya ƙara rikicewa ba abin da yake sai tuno soyayyar da suka yi, daga saurayi da budurwa zuwa auren su. Ko da ya je gida, Shukura ta karɓe shi tana yi masa sannu da zuwa. Amsa mata ya yi yana kallon ta, kafin ya ƙaraso ta kira shi ya fi sau biyu, yana zuwa hatta ruwan da zai yi wanka ta tanadar masa. Ya cire kayansa ya shiga wanka, kamar ta san ba zai iya salla ba, sai ya tsarkake jikinsa, saboda rungumar da ya yi wa Yusra. Tana cikin tattare kayansa, hancinta ya ji ƙamshin turaren da ba na sa ba a jikin kayansa. Turarensa ɗaya ne da ta san shi da shi. Jikinta ne ya yi sanyi, domin ta daɗe da karantar alamomin rashin gaskiya a tattare da shi. Wani abu ne ya soki zuciyarta amma ta yi ta maza ta haɗiye tare da ajiye kayan. **** Aka shiga kwana na biyar, ba tare da jin ko ɗuriyar Sayyid ba. Nana duk ta fita hayyacinta, ba ta iya cin abinci, ba ta bacci. Ga Uwani tun tana rarrashinta, ta koma yi mata faɗa tana ganin ta ƙi tawakalli ta ci gaba da addu'a. Ga shi ta hana ta komawa gidan nasu, a nan gurinta take zaune tare da ita. Yanzun ma Uwanin ce ta miƙo mata kofi da fura a ciki ta ce "Ungo ki samu ki sha furara nan Nana, ko ɗan cikinki ya samu wani abu shi ma. Rayuwa ba za ta yiwu a haka ba kina zaune babu Abinci, ga juna biyu ba. Idan wani gurin mutumin nan ya tafi, idan da rabo zai dawo ai" Nana ta karɓi kofin, tana ajiyar zuciya. "Maza ki shanye, kan na fito daga banɗaki" Nana ta jinjina kai tana kallon kofin. Uwani na shiga banɗaki, Nana ta ɗauki mukullin da aka kulle gidansu, ta tafi. Gani take kamar tana shiga za ta tarar da shi a inda ta bar shi. Ƙofar dama a lanjare take aka rufe ta. Ta shiga ɗakinsu, amma ta tarar wayam babu kowa a ciki. Ta kalli kan katifar su, ta ga abin hiraminsa na rawani a kai. Ta durƙusa a kan gwiwoyinta, ta damƙi hiramin nan, da yake ta ƙamshin turaren sa. Tamkar ta damƙi Sayyid ɗin. Cikin kuka ta ce "Haba Sayyid, daga cewa na je na dawo, sai ka tafi ka bar ni? Haba Sayyid yau kwananka biyar ba ka tare da ni. Da mutuwa ka yi na san wannan hukuncin Allah ne, dole na tawakalli, amma me yasa zaka tafi ban san halin da ka ke ciki ba. Haba Sayyid Haba Sayyid Nana ce fa" ta din ga soki burutsu tamkar zararriya. Wani irin kuka take yi mai haɗe da gunji da ƙunar zuciya. Ba ta san lokacin da Uwani ta shigo ba, tare da abokiyar zamanta Sabuwa ba, sai ji ta yi ta taɓa ta ta ce "Nana shi ne sai da ki ka fito ki ka zo ko? Ba na ce kar ki fito ba?" "Uwani. Sayyid ya tafi ya bar ni, na zata mafarki nake yi, me yasa zai tafi ya bar ni?" "Ke ki ji mini 'ya da rashin ta ido, yo ina zan san dalilin da ya sanya ya tafin ni? Ke ba za ki iya dakewa ki kama kanki ba, idan guduwa ya yi fa?" Sabuwa ta ce "A'a Yaya, su fa yaran birni su na nunawa junansu kulawa, ya za a yi mutum mara lafiya a neme shi a rasa, ki ce hankalinta ba zai tashi ba? Kina kallon yadda take tiri-tiri da shi take nula da abin ta ke kin san ba ƙaramin so take yi masa ba, ai da tausayi" Uwani ta ce "Kuma haka ne, amma tun da shi ya tafi nima jikata nake yi wa kar wani abu ya same ta, ga ciki. Ke Nana kuma ba garinsu ya tafi ba bai gaya miki ba? Ba kin ce ɗan Nijar ba ne?" "Ba shi da lafiya fa, ba zai iya wannan tafiyar ba" "A'a kar ki ce haka, idan ki ka bibiya ma, can ɗin ya tafi, amma yanzu ki yi haƙuri ki tashi mu tafi gida" "Uwani, dan Allah ki yi mini alfarma ki bar ni na kwana a nan" "To ya za ki kwana a gida ke kaɗai haka ake yi?" "Ni dai dan Allah ki bar ni a nan, wallahi da safe zan dawo na yi miki alƙawari" "A'a sai dai na turo yarinya ɗaya ta tayaki kwana" Nana ta amince da hakan, aka turo mata yarinya. Tuni yarinyar ta yi bacci, Nana kuma kwana ta yi aikin kuka. Lokaci Lokaci, sai ta yi tasbihi tare da ajiyar zuciya. Washegari da sassafe Uwani ta zo ta kawo mata abin karyawa. Yadda idanun Nana suka kumbura, ya sanya ta fahimci Nana ba ta yi bacci ba. "Wai ni Nana, babu wani wanda za ki kira, ki tambaye shi ko yaje? Ko kuma wani guri da za ki je a duba?" Jiki a sanyaye Nana ta girgiza mata kai. "To shikenan sha kunun nan da ƙosai, kar su huce" Nana ta karɓi kunun tana kurɓa a hankali, ji take tamkar tana shan magani, saboda wani irin ɗaci da take ji kunun yake yi mata a bakinta. Amma saboda ba ta son faɗan Uwani, haka ta din ga shan kunun nan da ƙyar. Ta ɗan saci kallon Uwani ta ce "Uwani, ina ga gobe in Allah ya kaimu zan shirya na koma Kano" "Gurin wa?" Uwani ta jefe ta ta tambayar. Nana ta ɗan yi shiru, Uwani ta ce "Gurin wannan masoron Ubannaki da bai san ciwon kansa ba balle ya san naki? Ya kasa tallafa miki da larura ta samu mijinki, yanzu ne idan kin koma zai tsinana miki wani abu? Ga cikin fari ke ba sanin kan abubuwa ki ka yi ba, ga wannan shu'umar matar tasa, da ƙafa duk dama ba tsayawa za ta yi ta kula da ke ba?. Ban ƙi ba ki kira shi, ki sanar masa abin da yake faruwa a matsayin sa na ubanki ba, amma ba dai ki koma wannan gidan ba. Ki yi zaman ki a nan ki haihu, ki yi biƙinki idan mijin naki bai dawo ba, a san abin yi" Tabbas Uwani tana da gaskiya, idan ta koma gidansu rayuwarta ta sake komawa baya, ta san babu wani abin kirki ko kulawa da za ta samu a gidan, wataƙila ma a kore ta. Ummi kuma ta yi mata ɗawainiya da yawa, tana jin nauyin ta sake koma mata da matsala. Kuma ba ta ji a ranta za ta iya sake ko nufar hanyar gidan Alhaji Zailani ba, saboda yin hakan tamkar cin amanar Sayyid ne, kuma ita ba dolensu ba ce, da za ta je ta ɗora musu ɗawaniya. Dan haka Uwani na da gaskiya. Amma zamanta a nan ɗin ma, shi ma dai ɗawainiyar ce. Ta sake ɗago kai ta ce "To ina son na je Bauchi gurin Mamana" "Kai Nana ki na da gardama, gurin nawa ne dai ba za ki zauna ba, kin ƙallafa rai tun da mijinki ya bar garin nan kema sai kin bar shi?" "Ba haka ba ne Uwani, ina da dalili dan Allah ki bani damar hakan" "Shikenan Nana, ba zan matsa miki ba, Ubangiji Allah ya tabattar da alkhairi, amma ki bari kamar nan da sati ɗaya, ki ɗan ƙara samun nutsuwa. Nima na lalubi na mota na baki" "Ai ina da kuɗin mota" "Nima na san ki na da kuɗin motar, na ce zan baki ai" Nana ta ja bakinta ta tsuke. **** Jamila ta yi shirin fita, tana tsaye tana latsa wayarta ta ce "Baba har ya fita ne?" Mama ta ce "Tun da uwar kashinsa ta cika ya fita. Da dai bai ci ba da yanzu yana nan yana bin bango yana zabga hamma yana faɗa da ƙadangaru da bokitai" Jamila ta basar ta ce "Sonake ya bani cikakken kwatancen Buda, zan saka a kai ni, na je na ga Nana" "Wai ba za ki bar maganar Nanan na ba ko Jamila?" "Mama meye laifi idan na je na gan ta ne wai?" Nasiru ya ce "Laaa rannan kuwa wannan ɗan uwan mijin nata, da suka zo a ka kaita gidanta ranar biki, suka zo shi da wasu mutane, suka ce mini wai yanzu Nana a ina suke. Na dawo daga makarantar allo, na ce musu tana Buda can garin su Baba, shi ne ya ce na gaida Baba" Mama ta ce "Ikon Allah, amma yarinyar nan ta ce 'yan uwansa an neme su an rasa. Kai Nana muguwar makira ce ta ƙarshe" Jamila ta ce "Amm na tafi sai na dawo" "To Allah ya tsare, a gaida Hajiyar" " Za ta ji" ta amsa a taƙaice ta fita. Nana ta zauna ta haɗa kayan da za ta buƙata a cikin jaka guda ɗaya. Tattara sauran guri ɗaya, ta ɗauki jakar gurin Sarkin Baka, da kuɗin Nijar ɗin da suke ciki. Ta tattara sauran kuɗin da suke ɗakinta, tana tunanin ta tafi ko da Uwani ba ta sani ba. Ta tattara kayan kitchen ɗin ta, ta ce wa Uwani sayarwa za ta yi. "Me yasa za ki sayar da kayan ki Nana?" "Kawai kuɗin nake buƙata ne" "Gaskiya ba za ki sayar da kayan nan ba, ki bari ranar kasuwa, zan kai Tinkiyata kasuwa, na baki kuɗin amma ba za a sayar da kayan ba" Gaba ɗaya Nana ta ji ta damu yadda ta ɗorawa Uwani ɗawainiya. "Uwani kar ki sayar da Tinkiyarki dan Allah, gara a sayar... "Za ki rufe mini wannan dogon bakin naki, ko sai na kwaɗe ki? Ke ki ka sani na sayar? Ke dai akwai gardama" Babu yadda Nana ta iya, haka ta haƙura sai ranar kasuwa, aka sayar da Tinkiyar. Uwani ta ɗauki dubu talatin a kuɗin ta bawa Nana ta ce "Ban san iya adadin kuɗin da ki ke buƙata ba, amma ga wannan kya jalauta. Dan Allah ki kula da kan ki Nana, duk inda ki ka je idan kin ga akwai matsala, ki dawo mini nan ni zan riƙe ki na kula da ke" Nana ta din ga juya kuɗin, ta kalli Uwani idonta fal hawaye ta ce "Na gode sosai da sosai, Allah ya saka miki da mafificin Alkhairi na gode" "Babu komai, Ubangiji Allah ya sauke ki lafiya, ya bayyana mijinki cikin aminci. Nan ma za mu ci gaba da jiran jami'an tsaro ko za a samu wani labari daga gurinsu. Allah ya bayyana shi" Nana ta amsa da Amin. Jin washegari Nana za ta bar garin, ya sanya 'yan uwa, suka din ga kawo mata abin alheri cikin mutunci da karramawa, tare da yi mata fatan alkhairi. Washegari da sassafe, Nana ta yi sallama da su Uwani, aka ɗauke ta a babur aka kai ta tashar ƙauyen. Aka kaita Garko, daga nan ta hau motar Kano. A Kano ta hau motar da za ta sada ta da garin Bauchi. Tsawon awanni huɗu da aka shafe, ana tafiya a motar, babu abin da Nana take yi, banda tunani ta saƙa wannan ta kwance wancan. Tunaninta a wani hali yake ciki, ya jikinsa? Su waye suka ɗauke shi? Mene ne makomarta idan bai dawo ba. Lokaci-lokaci ta kan shiga hijjabinta ta yi kuka, ta share hawayenta. Da ta sauka a tasha ƙarfe sha biyu na rana, ta samu abin hawa, har sunan unguwar da Mamanta take ta sani, sai dai ba ta san takamai ina ne gidan ba. Shi ma daga tashar zuwa garin da maman nata take, sai da aka yi tafiyar awa ɗaya da rabi. Ƙafafun Nana duk sun kumbura, da ƙyar take jan su. Ta ɗaukko wayarta ta kira lambar Anty Fati, ta ji ba ta shiga. Ta kira ta Adda Saude ba ta ɗaga ba. Ta nemi guri ta zauna, ta ci gaba da kiran wayar Adda Saude da ita kaɗai take shiga. Sai dai still ba a ɗaga wayar, ga shi ba ta san daga garin, ina ce unguwar da za ta nufa ba. Ta samu guri ta yi alwala, ta ciro sallaya a kayanta, ta shimfiɗa ta yi sallar azahar. Bayan Azahar sosai, Adda Saude ta kira wayar Nana. Nana ta ɗaga tare da yin sallama. Ta amsa mata ta ce "Nana yi haƙuri, caji na kai wayar ne aka kunna mini, ya ki ke ya gida?" "Lafiya kalau Adda, kin ganni na zo Bauchi ne na sauka, sai dai ban san sunan unguwar da Mama take ba" "Ke haba dai, da gaske ki na Bauchi Nana?" "Eh Adda, na sauka ma tun ɗazu" "Subhanallah, ai ba ki gaya mini za ki zo ba, da tuni an shirya karɓar ki, ban sani ba an bar ki ki na jira, dan Allah ki yi haƙuri yanzu ki na daidai ina, na zo na tafi da ke?" Nana ta ce "Kar ki wahalar da kan ki dan Allah, ina garin ma, sunan Unguwar za ki gaya mini" Sai da Adda Saude ta ɗan ji dumm, amma ta maze ta cewa Nana ta samu abin hawa, ta haɗa ta da mai abin hawan ta yi mata kwatance. Nana ta ce "To" ta samu abin hawa, ta haɗa su ta kwatanta masa, sannan ta hau. Nana ba ta isa gidan da Mamanta take ba, sai ana kiraye-kirayen sallar la'asar. Mama na tsakar gida tana ta fama da yara, kawai ta ji sallamar Nana. Ta ɗago da hanzari, sai dai ta kasa amsa sallamar ta nufi Nana da sauri suka rungume juna su na kuka. Ta ɗago Nana ta ce "Nana ba ki yi fushi da ni ba?" Nana ta girgiza kai ta ce "Ban yi ba" Ta ja hannun Nana zuwa ɗaki, ta saka yaran su shigo mata da ƙatuwar jakarta. "Sannu da zuwa, tare ku ke da mai gidan naki ne?" Nana ta sunkuyar da kai jikinta a sanyaye ta girgiza kai alamar a'a. "To yana ina shi?" Nana ta yi shiru. Cikin tashin hankali Mama ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Nana ba dai auren naki ne ya mutu ba?" Nan ma ta girgiza kai hawaye na bin fuskarta. "Shikenan, yanzu nutsu. Bari na ɗora miki ruwa ki yi wanka, sai ki yi salla" Nana tana iya ganin tsantsar farinciki a kwance a fuskar mahaifiyarta. Ƙannenta suka kewaye ta, Nana ta din ga kallon su cike da so da ƙauna. Har gara Walida ta ɗan santa sauran kuwa duk ba su san Nana ba. Ruwa mai ɗumi ta haɗa wa Nana, ta yi wanka, ta yi sallar la'asar. Ta zubo wa Nana lafiyayyen Abinci, duk da yadda ranta ya biya a kan Abincin, amma ta kasa sakin jiki ta ci. Mama ta din ga kaiwa tana komowa, tana ta ɗawainiya da Nana tamkar ta goya ta, sai ta ji ina ma tuntuni ta samu irin wannan kulawar ta uwa. "Nana ina Imrana kuwa, ya daina zuwa gaba ɗaya" Nana ta ce "Lagos yake tafiya neman kuɗi" Ta yi ajiyar zuciya ta ce "Ai shikenan, ya aka yi ina mijin naki ne? Me ya faru?" "Nemansa na yi na rasa" Cikin rashin fahimta ta ce "Kamar yaya?" Nana tana kuka ta yi mata bayani. Cikin mamaki ta ce "To ina 'yan uwansa? A ina yake a Nijar ɗin?" Sai a lokacin ta fayyace wa Maman komai, game da auren zuwa ɓatan sa. "Nana, me yasa baki neme ni kin gaya mini ba? Yanzu duk wannan abin yake faruwa amma idan muka yi waya sai ki ce mini komai lafiya ƙalau? Ni kaina nan kina raina, ina ta fafutuka na ga yadda zan yi na zo na gan ki. Ba ki kyauta ba Nana, komai lalacewata, ni mahaifiyarki ce, yakamata a ce kin sanar da ni. Yanzu dai ki zauna a nan, mu ga abin da Allah zai yi, kafin ki haihu mu gani ko Allah zai sanya a ga mijin naki. Amma na yi mamaki matuƙa da mahaifinki ya aura miki wanda bai san usulinsa ba? Yanzu ƙiyayyar da yake yi minin har ta kai haka? Ko yana jin haushina amma ai ke 'yar sa ce, bai cancanci ya yi miki haka ba, amma babu komai. Nana abin da nake so da ke, daga yanzu duk abin da ya faru Nana, ko ba zan yi miki komai ba, ki sanar da ni, ki bani dama na taka rawa ta ta uwa a rayuwar ki ko yaya ne" Ta yi maganar tana riƙe hannun Nana. Sallamarsa ce ta tilastawa Nana haɗiye abin da take shirin furtawa, cike da tsoro. Ba ita ba hatta Maijidda, sai da zuciyarta ta buga da ƙarfi cike da tsoro. AYSHERCOOL 08081012143 61 Har zai gifta, zai shiga ɗaki ya hango Nana, cikin rawar baki, Nana ta gaishe shi, ya amsa mata sama-sama ya wuce, dan kallo ɗaya ya yi mata, ya gane ta. Jiki a sanyaye Maijidda ta tashi ta bi shi ɗaki, tana ɗan sinne kai, tana jiran ta ji me zai ce, amma bai ce komai ba. Ta kawo masa Abinci, tana jiran ta ji me zai ce, ga hankalinta a kan Nana, tana so ta je ta yi hira da 'yar ta, su yi hira ta ji ɗuminta, amma ta haƙura. Nana ma na ta gaban ne yake faɗuwa, tana tsoron abin da zai ce, saboda ba ta manta karan battarsu. Haka dai a ɗarare suke hira da yaran gidan. Maijidda na ta son yi masa magana, amma ta kasa. Ya gama cin abincin ya fita, ba tare da ya ce komai ba. Yana fita ta koma gurin Nana, suka ci gaba da hira, Nana ta kwanta a kan cinyar Mamanta, tana jin wani irin farinciki yana ratsa ta. "Kin fara zuwa awo ne Nana?" Wata irin kunya ta kama Nana, ta ɗan sinne kai ta girgiza mata kai. "Gaskiya yakamata, wata nawa ne cikin? Mu je a yi awo a duba, mu ga abin da zamu fara ajiyewa. Mu jira mu ga ikon Allah, idan an ga mijin naki shikenan, idan ba a gan shi ba kuma, ma san abin yi" Nana dai ta yi shiru, sai kuma ta ce "Mama ki yi mini addu'a, ki ce Allah ya bayyana shi cikin aminci" Mama ta yi dariya, ta ce "Lallai kam, to shikenan, Ubangiji Allah ya bayyana mini sirikina cikin aminci" Nana ta yi murmushi, dan kunya ce ta kama ta daga baya, da tuna katoɓarar da ta yi. Da daddare Mai Jidda ta yi wa Nana shimfiɗa, ta saka nata net. Sannan ta tafi nata ɗakin gurin mijinta, har za su kwanta, Mai Jidda ta dubi Iliyasu, jiki a sanyaye cikin ladabi ta ce "Baban Walida, na ga ka dawo ka ga Nana a gidan nan, ba ka ce komai ba" Ya dube ta ya ce "To me ki ke so na ce?" "Ahh dama kar ka ce ban gaya maka ba ne, dama ta ɗan zo ta zauna da ni ne, duba da yadda... "Kin ga dakata, na ɗaga miki ƙafa ne na yi shiru, na ga gudun ruwanki, kar ta wuce mini gobe a gida, ta wuce ta koma inda ta fito" "Dan Allah ka yi haƙuri Baban Walida, Nana ta samu matsala a aurenta ne, dan Allah ka yi haƙuri ba za ta daɗe ba, amma dan Allah kar ka ce ta tafi yanzu. Ni ko ruwan gidanka ka ce ba za ta sha ba, na amince dan Allah" "Ke Maijidda, bari ki ji na gaya miki, wallahi sai yarinyar nan ta bar gidan nan" Ya nemi guri ya yi kwanciyar sa, takaici ya ishi Maijidda. Nana kuwa tana jiyo hayaniyar su sama-sama, abin ya tsaye mata ta kasa bacci sam. Sai juye-juye, ga mararta ta ƙulle duk jikinta ma ciwo yake yi mata. **** Kwance yake a kan gadon Asibiti, jikinsa babu riga, sai dogon wando an rufe iya ƙafafuwansa da koren yadi. Ƙirjinsa kuma an manna masa abin ECG. Sai gashin sa a rufe da hular Asibiti. Na'urorin gefen gadonsa sai sauti suke fitarwa. Dattijo ne a tsaye a kansa, dogo fari tas, ya ɗaura hirami a iya kansa, ga gemunsa dogo duk farin gashin furfura a jiki. Ya kalli mutumin da yake tsaye ya ce "médecin (Likita) yanzu mene ne abin yi?" "Eh, gaskiya za a yi masa wannan allurar ne kamar yadda na yi maka bayani, idan kuma ba haka ba, gaskiya sai dai a saka masa na'ura a zuciyarsa wadda za ta din ga taimakawa bugun zuciyarsa" Na kusa da Dattijon mai sanye da shuɗiyar shadda, da babbar riga, kansa ya yi naɗi da baƙin rawani ya ce "Ka gani ko Sultan, Allah kaɗai ya san abin da suka yi masa a Nigeria. Dole yaron nan ya ɗanɗana kuɗarsa a ci gaba da tsare shi, har sai ya yi bayanin abin da ya yi masa a Nigeria, da aka neme shi aka rasa tsawon wannan lokacin. Su kan su sauran da aka kama su tare, dole a killace su a guri ɗaya, haryanzu ban bari an sake su ba, saboda idan maganar nan ta fasu akwai matsala" Sultan ya numfasa cikin damuwa ya ce "Ni wannan bai dame ni ba, na bar ragamar komai a hannunka, ni lafiyar sa ce a gabana yanzu. Likita ku yi duk abin da ya dace kawai. Lafiyarsa ce damuwata a halin yanzu" Likitan ya ce "In sha Allah" Dattijon ya saka hannunsa a cikin na mara lafiyan,yana kallonsa cikin matsananciyar damuwa. Kamar mafarki ya ga yana motsawa a hankali, sai ya ƙara tattara hankalinsa a kansa yana kiran sunansa. Wata irin miƙa ya yi, yana ƙoƙarin buɗe idanunsa, amma ya ji tamkar an cika masa idanun nasa da barkono. "Imam.. Hannunsa ya ɗora a ka yayi wata irin kururuwa, jin yadda naman jikinsa yake yi masa wata irin azaba, tamkar ana cizgar naman jikin nasa. Ga wani irin zafi da raɗaɗi da yake ji kamar yana cikin wuta. "Zafi! Wayyo wuta Innalillahi wa Innalillahi raji'un, wuta zafi jikina" Kansa suka yi gaba ɗaya cikin tashin hankali, su na ƙoƙarin rirriƙe shi, amma ya watsar da su ya diro daga kan gadon, yana girgiza kansa da yake yi masa wata irin azaba tamkar zai tarwatse. Tunaninsa ne ya hargitse gaba ɗaya, ƙwaƙwalwarsa na ta kokawar ƙwato wani abu daga cikin memories ɗin sa, amma abu ya kacame, gaba ɗaya tunaninsa ya hargitse, ya kasa tantance komai. Fizge-fizge ya din ga yi yana kururuwa jikinsa na rawa. Dattijon nan cikin jarumta da ƙarfin hali, ya bi shi da sauri ya damƙe shi iya ƙarfinsa. Kokawa suka din ga yi, a rikice likita da ɗaya mutumin suka yo kansu, likitan ya haɗa wata allura ya yi masa. Jikinsa ya saki a hankali bacci ya ɗauke shi. Kan gadon suka mayar da shi suka kwantar. Ɗaya mutumin ya kalli likitan ya ce "Ka na ji na?" Likitan ya jinjina kai cikin nutsuwa. "Ka san dai waye wannan, kuma ka san matsayinsa da girmansa ko?" Ya yi maganar yana nuna masa mara lafiyan. Ya jinjina kai ya ce "Na sani" "To muddin mu ka ji maganar abin nan da ya yi, ya fita waje, to ba wani ba ne ba kai ne, dole ka yi shiru da bakinka, kare sirrinsa wajibi ne a kan duk wani wanda yake yankin nan, idan kuma aka samu akasi ka furta wani abu, da rayuwarka za ka biya" Likitan yana tsuma ya ce "In sha Allah ba zan faɗa ba" **** Da safe mijin Maijidda ya shura takalmansa ya fice, bayan sun gama jayayya da ita, tana ta roƙonsa tana yi masa magiya. Gaba ɗaya Nana ta ji dana sanin zuwa Bauchi da ta yi. Babban abin da ya bata mamaki, ƙatuwar kaza Maman ta saka aka yanka, ta gyare ta tsaf, ta yi wa Nana farfesunta, aka sayo mata ƙaton buredi ta haɗa mata shayi. "Mama daga zuwana na ɗora miki ɗawainiya, ba ma na iya cin Abincin ni" "Ɗawainiyar ƙaniyarki, da can na yi miki ne Nana? Dan Allah ki daure ki mayar da hankali ki ci ki ƙoshi, idan kuma ki na son cin wani abin, ki gaya mini sai na dafa miki" "A'a ba na son cin komai, amma ki zo mu ci tare da su Walida" Maijidda ta ce "A'a, babu wanda zai ci, da rana ma ci Abincin tare, wannan dai na ki ne" Haka ta takura Nana, ta karya. Nana ta fito da nufin, ta kama musu ayyukan gida, amma Mama ta hana, ta dafa mata ruwa ta yi wanka. Ta fito ta tarar Mama tana wanke kayan da ta cire. "Haba Mama dan Allah ki bari na wanke da kaina, ya za ki din ga yi mini wanki?" "Tafi ɗaki ki je ki zauna ki huta, ga lemon fata can da rake, ki ɗan sha saboda ɗanɗanon bakinki. Akwai riɗi ma mai gishiri da mai suga, idan da wanda ki ke so" kawai Nana ta tsaya tana kallon ta, tana murmushi. Maijidda ta ce "Ya dai?" Ta girgiza kai ta ce "Ba komai Mama, na gode sosai" Nana ta shirya ta canza kaya, Khadija da take 'yar autar Mama, Nana ta kama ta tana tsefe mata kai. Ta ɗauki wayar Nana tana kallon hotuna. Sai ta buɗe wani video da Nana ta yi wa Sayyid,  ta yi masa kitso sai hararta yake yi tana cewa "Ka ga yadda ka yi kyau 'yan matana, yi murmushi mana" ya ɗago kansa ya hargitse idanunsa. Nana tana dariya. Sai da tsigar jikin Nana ta tashi, gani take kamar ta shiga cikin wayar ta ga Sayyid ɗin ta. "Anty Waye wannan?" "Mijina ne" ta ba ta amsa tana murmushi. "Ya na gan shi da kitso, kuma fari?" Nana ta yi dariya ta ce "Ni kuma baƙa ko?" "Eh, kuma ba kyau maza su yi kitso fa" "Wai in ji wa? Ba ki ga gashin nasa ne da yawa ba?" Khadijah ta ce "Eh, to yana ina yanzu?" "Ya je unguwa, zai dawo ya ɗauke ni mu tafi" "To ki nuna mini shi idan ya zo" Nana ta ce "To in sha Allah" Mama ta ce "Ke Khadijah, tashi ki bar ta ta huta, Nana kwanta ki huta, ki rabu da surutun yarinyar nan" Khadijah ta tashi tana zumɓura baki, Nana ta ɗan kashingiɗa kawai wani abu mai kama da bacci ya yi awon gaba da ita, kasa tantance ma me take yi ta yi, bacci ne ko kuma ido biyu. "Ma Vie" ta ji muryarsa a kunnenta. A razane ta waiwaya cikin damuwa. A tsakiyar sahara ta hange shi ta ce "Sayyid" Ganinsa ta yi a tsaye a kanta, kayan jikinsa duk a yayyage, ya yi baƙi kamar ya ƙone, gashin kansa a hargitse jikinsa sai fitar da hayaƙi yake, ya ce "Ma Vie sun mayar da ni inda za su kashe ni, dan Allah ki zo kar su kashe miki ni." Yayi maganar yana hawaye. Ta tashi cikin tashin hankali ta ce "Suwaye? Kuma a ina suke?" "Dan Allah ki zo, ni ban san su ba, amma na san mutuwa zan yi, dan Allah Husnah ki zo gurina, za su kashe ni. Idan kuma sun kashe ni, ki kular mini da ɗa na" "Sayyid, dan Allah kar ka tafi ka bar ni, dan Allah Sayyid ka dawo? Ka gaya mini kana ina, sai na zo na same ka na tafi da kai" Guguwar Sahara ce, ta taso ta turnuƙe gurin. Nana ta din ga tari, muryar Mama ta ji a kanta tana faɗin "Tari ki ke haka Nana?" Kawai ta ga Nana ta tashi, ta yi waje. Ta riƙe ta ta ce "Ina za ki ke?" Idanunta a rufe, fuskarta a murtuke ta ce "Ba ki ji Sayyid ne yake kirana ba?" "Waye hakan?" "Mijina mana" ta faɗa a fusace. "A'a babu wanda ya kira ki fa" Nana ta fara ƙoƙarin fizge hannunta ta ce "Yanzun nan fa ya fita daga ɗakin nan" "Nana babu kowa fa a gurin nan, daga mu sai ke" "Ni ki cika ni, na ji Muryar mijina gurinsa zan je yana kirana" Tsawa ta daka wa Nana ta ce "Ina magana ki na ɗaga mini murya? Wuce ki zauna babu wani wanda yake kiran ki" Nana ta buɗe idanunta, ta kalli Mamanta, sai dai ba ta yi magana ba, kawai ta ga Nana ta yi baya za ta faɗi. Ta riƙe ta ta kwantar da ita. Jikin Nana ya hau karkarwa, idanunta na fitar da hawaye. Cikin matsananciyar damuwa take kallon Nana, tana tunanin dama har zuwa yanzu, tana fama da larurar nan?. Ta rungume Nana a jikinta, ta kama goshinta, ta fara karanta mata Suratul Jinn, tana tofa mata a fuskarta. A hankali jikin Nana ya saki ta fara bacci. Ta yi shiru tana kallon fuskar Nana, tana tuna lokacin da take rungume da ita tana jaririya, cike da so da ƙauna.  Tare da tuno irin soyayya da rawar ƙafar da Isa ya din ga yi lokacin da aka haifi Nana, ba ta taɓa tunanin zai yi wannan riƙon sakainar kashin da rayuwar Nana ba. Adda Saude ce ta yi sallama, Mama ta amsa mata. Ta ɗan yi turus ta ce "Ya dai Nanan ba ta da lafiya ne, na ganta a kwance a jikinki haka?" "Wallahi kuwa, shigo daga ciki" ta zauna ta ajiye kayan da ta zo da su. Ta ce "Tun jiya na so zuwa, tun da muka yi waya da ita da ta ce mini tana garin nan, babansu ne baya nan bai dawo da wuri ba ga yara gidan babu kowa. Ikon Allah ciki ne ma da ita haka?" "Ga shi nan dai, har ya yi girma ma" "Ikon Allah, na yi mamaki da na ji zuwa ta yi babu sanarwa, tare da mijin suka zo?" Maijidda ta numfasa ta ce "A'a, matsala ma aka samu, ba a san inda mijin nata yake ba" "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, garin yaya ina ya tafi?" "Wallahi ban sani ba, na dai ce ta zauna a nan, kafin nu ga abin da Allah zai yi. Ashe rashin lafiya ya sha, yarinyar nan ba ta taɓa gaya mini ba. Ga babanta bai karɓe ta ba, ƙarshe ma sai Buda ta koma ta yi jinyarsa, kuma dai ma ya tafi ba a san inda yake ba" Cikin jimami Saude ta ce "Kai subhanallah, abin nan bai yi daɗi ba, yanzu meya same ta haka?" "Iska ne ya buge ta, na ba ta abinci ta karya, ta fara bacci kawai ta tashi wai mijin ne yake kiranta. Ashe haryanzu tana fama da wannan matsalar. Wallahi Adda na yi dana sanin biye wa Iliyasu na watsar da yaran nan." Ta yi maganar hawaye na cika mata ido. "Ki yi haƙuri, amma yanzu ya ku ka yi da shi?" "Hmm mu na nan muna ta bugawa, wai sai ta bar gidan nan, ni kuma Nana ba za ta bar gidan nan ba, sai dai mu tafi tare" A ɗan tsorace Adda ta ce "A'a Maijidda, idan da matsala, a kaita gidan Fati tun da tana da yalwar guri, ko gurin Yakumbo,kar ku samu matsala" Ta girgiza kai ta ce "Ni na ke son kula da Nana da kaina. A cikin su ban san wanda zai ji ƙan wani ba, dukkaninsu su na buƙatata". Nana ta farka tana ɗan yin miƙa, ta cewa Maijidda fitsari za ta yi, ta raka Nana banɗaki ta je ta yi fitsari, ta saka ta ta yi alwala ta koma ta kwanta. Har zuwa yamma Adda na gidan, sai daf da magariba ta tafi, Nana kuma ta wartsake sai ciwon jiki da mararta da ke ɗan murɗawa. "Nana, ranar Litinin in sha Allah za mu je Asibiti, a fara yi miki awo, kuma zan duba gurin masu magungunan islamic ɗin nan, mu je a duba ki" Nana dai ta yi shiru ba ta ce komai ba. Da sallar Isha'i, Baban su Walida ya dawo, tun da ya hangi Nana a ɗaki, ya turnuƙe fuska ya kalli Mai Jidda ya ce "Me na ce miki a game da yarinyar nan?" "Baban Walida, ba a yi wa ɗa mugunta, dan Allah ka yi haƙuri ka bar Nana a gidan nan, ka ga 'yan uwanta ma duk ba su santa ba, ba su saba ba. Kuma ba a san me gobe za ta haifar ba. Wataƙila ita ce mai tallafar rayuwar ƙannen nata nan gaba." "Ni ba nusari ne kamar ubanta ba, ni zan tallafi rayuwar 'ya'yana. Ba na buƙatar ko sisinta a kan yarana. Ta koma gidan mijinta ko gidan ubanta, idan ba haka ba sai dai ki zaɓa, ko ta bar mini gida, ko kuma auren ki." Kafin ya rufe bakinsa ta tari numfashinsa ta ce "Na zaɓi 'ya ta, zan tafi tare da Nana, ko a daji ne na rayu da ita na kula da ita. Tun da ba dan wahala da bautarka da ta 'ya'yanka kawai Allah ya yi ni ba. Ba ka da kara Iliyasu. Nan har 'ya na riƙe maka na aurar da ita ban yi mata mugunta ba. Har 'ya'yan 'yan uwanka ka kawo mini na riƙe, ban taɓa muzguna musu ba, na riƙe maka, nawa 'ya'yan ne na banza kenan? Ƙiri-ƙiri ɗan da na durƙusa na haifa ya tsane ni, saboda yana ganin na kawo su Duniya amma ban damu da su ba. Su 'ya'yan da na riƙe maka haifar su na yi? Ko kuma dolena ne su, ni 'yar guda ɗaya ka gaza yi mini kara a kanta? To ka sani duka yau duka gobe shi ke sanya baƙin ba'auzine yin tawaye. Zan zube maka yaranka na ɗauki 'ya ta na tafi da ita, na kula da ita. Ka kwaɗa gidan ka cinye da kai da 'ya'yan naka" Cikin matsanancin mamaki ya ce "Maijidda, ni ki ke gaya wa wannan maganganun?" Cikin ƙunar rai ta ce "Na faɗa ɗin, shekara nawa na rayu da baƙin cikin rashin ganin 'ya'yana, kullum na motsa zargina ka ke da tsohon mijina. Ƙaddarar haihuwar yaran nan biyu ta sanya ban aure ka da fari ba na fara auren sa, amma a kan dalilinku marasa tushe balle makama kun azabtar da ni da nesan ta ni da yarana. Wallahi wannan karon na zaɓi 'ya ta" Kamar zubar wuta, haka Nana take jiyo cece kucen su. Dana sanin zuwa gidan ya cika mata zuciya. Tabbas ba za ta so mahaifiyarta ta kashe aurenta, da wannan gayyar 'ya'yan saboda ita kaɗai ba, idan ta bari hakan ya faru ba ta yi musu adalci ba baki ɗaya. Zurfin tunanin da ta tafi, bai bari ta gama jin yadda rigimar ta su ta kaya ba. A cikin daren bayan gari ya yi tsit, ta tashi ta haɗa kan kayanta cif. Ta laluba jakunkunan yaran na makarantar boko, ta samu biro da takarda ta yi rubutu, ta ninke ta ajiye a kan katifar ta. Da Asuba, Mama ta zo ta tashe ta, ta yi alawala ta yi sallar Asuba. Ganin yaran na ɗaya ɗakin su na salla, Mama ma tana bedroom ɗinta, tana salla, ya sanya ta lallaɓa ta ɗauki jakarta ta fice daga gidan. Ta din ga zumbuɗa sauri, tamkar za ta tashi sama, ga faggon kaya. Tafiyar ƙafa ta ci sosai da sosai, har sai da gari ya yi haske, masu abin hawa suka fara fitowa, ta tari wani ta ce ya kai ta tasha. Yana kai ta tasha, ta yi sa'a an yi lodi saura gurin mutum biyu, tare da wata mata suka shiga tasha suka nufi babbar tashar Bauchi. Daga babbar tashar Bauchi, ta hau wata motar, duk da zuciyarta na raya mata kamar matakin da ta ɗauka ya yi tsauri, wata zuciyar kuma na raya mata shi ne mataki mafi cancanta da za ta ɗauka, mussaman idan ta tuna yanayin yadda ta yi mafarkin Sayyid. Wayarta ta ciro, ta shiga lambar Ummi, ta rubuta mata saƙo, sai da ta tabattar ya tafi, sannan ta kashe wayar, ta cire layinta daga cikin wayar. Gari ya ɗan fara haske, Baban su Walida ya fice, a matuƙar zuciye, ya yanke shawarar tafiya ya kai ƙarar ta, tun da dama ya san ya saba samun goyon baya, ba ga taɓa kai ƙararsa ba, amma shi ya kai ta ta, ya fi sau shurin masaƙi. Su Khadija har sun fara ƙiriniya a tsakar gida, a zuciye kasancewar da takaicin ubansu ta kwana ta daka musu tsawa, ta ce su koma ɗaki, kar su tashi Nana. A zaton ta Nana tana cikin ɗaki tana bacci. Jamila ce zaune a gidan Ummi, tana jajanta abubuwan da suka faru da Nana, ba tare da ta san ma hakan ya faru ba. "Wallahi Ummi da an sanar da ni zancen matar nan, da suka ce Nana mayya ce, wallahi da sai na saka an rufe ta, sai na ja shari'a da su har gaban Alƙali, sun san girman sharrin maita kuwa?" "Hmm ke dai a yi sha'ani, ga shi Nana ta bar gidan, amma an ce Haryanzu tana kwance babu lafiya matar, ni na fi tunanin ko Aljanun Nanan ne suka yi mata wani abin, tun da ta ce Nana take gani. Jamila wayar Nana fa ba ta shiga, ni kaina sai na shafe sati biyu ban yi magana da ita ba, saboda garin babu network. Haka nan za mu tafi kawai." Ummi ta shirya, da Jamila Abba ta so ya kai su, sai ta yi wani tunani ta fasa, dan ba ta san a yanayin da za su je su tarar da su Nana ba. Sai dai Ummi ta sha mamaki da suka isa garin, suka tarar da gidan Nana a garƙame. "Ikon Allah, ita kuwa Nana ina tafi haka? Ko sun je Asibiti ne?" Jamila ta ce "Asibiti yau Asabar?" "To maybe emergency suka je, kin san matsalar Zuciya yake fama. Mu ƙarasa gidan Uwani". Suka zagaya gurin Uwani, ta yi murna sosai da sosai da ganinsu, sai dai ta hau Jamila da faɗan ba sa zuwa sai yanzu, da yake Nana ce a garin. Ummi ta yi ta bata haƙuri, ta ce sun zo duba Nana ne, sun tarar da gidan a rufe. "Ohh abin tsiya, ba ma kwa bibiyar halin da take ciki, to Nana tun shekranjiya ta bar Buda, mijinta aka nema aka rasa ko sama ko ƙasa sama da sati biyu, ta ce mini gurin Babarta za ta tafi a Bauchi, babu yadda ban yi da ita mu yi zamanmu da ita a nan, amma fafur ta ce in ƙyale ta, tafiya za ta yi". Jamila ta ce "Danƙari" Ummi kuwa "Innalillahi wa Innalillahi raji'un" kawai take maimaitawa. "Amma me yasa Nana ba ta dawo gida ba, sai ta tafi Bauchi, bayan ta san halin Baba" "Baban wofi, uban me zai tsinana mata, ko ta je gurin nasa" Suka gama jimamin da za su yi, suka tashi suka tafi. Jamila ta ce "Anya Ummi mu gaya wa Baba kuwa?" Ummi ta ce "Tun da shi ya haife mu, ba dole a gaya masa ba. Wallahi duk cikinmu babu wanda ya sha azabar ds Nana take sha a rayuwarta, da kin ga yadda take shan wahala da mutumin nan, sai kin tausaya mata, gaskiya idan guduwa ya yi ya bar ta, bai yi wa kansa adalci ba." Suka ci gaba da jajanta lamarin. Da suka shigo gari, Jamila ta tafi gida, Ummi ma ta tafi nata gidan. Mama na ganin Jamila ta dawo, ta fara yi mata tambayoyi, amma Jamila ta yi burus, ba ta gaya wa Mama komai ba. **** Tare da Kawun Mai jidda Iliyasu ya dawo, yana ta faman bambamin ta lalace, abin da ta ga dama shi take aikatawa. Sai kuma Adda Saude da suka taho tare, dama sai da ta yi tunanin a samu matsala saboda zuwan Nana. Suka tarar da Maijidda idanunta jawur, fuskarta babu annuri. Suka zazzauna a falonta, kawunta ya dube ta ya ce "Mai Jidda ban san ki da rashin ji ba, me yake faruwa ne?" Jiki a sanyaye ta miƙa masa takardar da Nana ta bari a kan shimfiɗarta. "Wannan ɗin na mene ne?" "Ku duba" ta yi maganar hawaye na zubo wa daga idonta. Adda Saude ta karɓa, ta buɗe takardar "Assalamu alaikum, na san lokacin da za ki ga takardata, na riga na yi nisa. Mama ina mai baki haƙuri da matakin da na ɗauka ban sanar da ke ba. Ba zan so a dadlilina nikaɗai ki bar ƙannena ba, dan Allah Mama ki yi haƙuri ki zauna da su. Na tafi neman mijina, a bawa baban su Walida haƙuri, amma kwana biyun nan da muka yi tare, ya fi kowane kwanaki yi mini daɗi a rayuwata na gode sosai Nana Asma'u" Shiru suka yi bayan da Adda Saude ta gama karanta rubutun, sai sautin kukan Maijidda da yake tashi. Cikin kuka ta ce "Shekara nawa ina yi masa kara, na riƙe nasa 'ya'yan? Amma ni sau ɗaya ya gaza yi mini kara, 'ya'yana sun tsane ni, a kan laifin da ba su suka yi ba, bai yadda su zo inda nake ba, nima kuma ba zan je ba. Idan na yi magana a ce na yi haƙuri, yarinyar nan ga tsohon ciki ina za ta tafi? Mijin da ita kanta ba ta san a ina yake ba" ta ƙarasa maganar tana ƙara rushewa da kuka. Kawu cikin sanyin jiki ya ce "To ita Nanan ya aka ta tafi babu sanarwa?" "Tun da ta zo yake masifar sai ta bar gidan nan, babu irin magiyar da ban yi masa ba, amma ya din ga ɗaga murya yana bala'i, gaskiya bayan Nana zan bi, ko zan ganta, ban san ina za ta je ba, da ta fita da tsohon cikin nan" "A'a ba za a yi haka ba, ki yi haƙuri Mai Jidda, rashin kyautawa Iliyasu ba ka kyauta ba, shi ɗa na kowa ne. Kuma tabbas mun daɗe mu na tausar ta, a kan ra'ayinka, ba tare da ba ta damar jin ta bakinta ba. Ka san raɗaɗin da yake cikin raba ɗa da uwa kuwa? Ba ka kyauta ba" Cikin kuka ta ce "Kawu dama ya bani zaɓi, na zaɓi 'ya ta, ya sauwwaƙe mini na fita na nemi yarinyata" Kawu ya ce "A'a ba za a yi haka ba, duk inda Nana take yanzu ta yi nisa, kuma idan aka ƙyale ki, ke kan ki ba ki san ina za ki nufa ki neme ta ba. Amma tun da ba yarinya ce ƙarama ba, na san duk inda take Allah zai kare ta, ki ci gaba da yi mata addu'a. Na san ina sha Allah, babu abin da zai same ta, amma batun ki ce ki kashe aure, ki bi ta ki zauna da ita ba mafita ba ce ba, haƙuri kin saba yin sa, a wannan karon ma shi ɗin dai zan baki, na san duk wanda aka ce wa ya yi haƙuri an zalunce shi ne, amma dai ki yi haƙuri. Kai kuma Iliyasu magana ta domin Allah, ba ka yi kara ba, ba ka kyauta ba ko kaɗan. Yaran nan saboda halinka sun daina zuwa inda take tsawon shekaru, amma daga zuwan yarinyar ka hau bala'i har ta ji, ta yanke wannan hukuncin. Ina kai auren ƙanwarka ne ya mutu, mijinta ya ƙi riƙe 'yar ka karɓo ka kawo mata ta riƙe maka? Har zama fa ta yi da ƙanwarka ta riƙe maka kan ta sake wani auren, amma kai ka kasa yi mata kara, a kan yarinya guda ɗaya tal". Iliyasu ya zata a wannan karon ma, za a goya masa baya, kamar yadda aka saba tsawon shekaru goma sha, sai dai ya ji wannan karon ba a goyi bayansa ba, sai ya yi tsuru-tsuru, dan haƙuri tabbas ya san Mai Jidda na da haƙuri da kawaici. Kawai ya tsani babansu Nana ne, saboda yadda aka fasa aurensa da ita, ta aure shi, shi yasa tsanar ta shafi su Nana. Haka aka din ga ba ta haƙuri, Kawunta ya yi ta rarrashinta. Nana tana zaune a cikin mota, daga jikin taga, tana kallon hanya, yadda ake ta kwarara gudu a motar, tamkar direban zai tashi sama. Gudun da motar take yi, bai dame ta ba, fatanta Allah ya sanya matakin da ta ɗauka, ya zama alkhairi a gare ta. Duk da ta san Nijar ba gida ne ba, ba unguwa ba ba kuma ɗan ƙaramin gari ba, ƙasa ce sukutum, mai ɗauke da garuruwa daban-daban da ƙabilu masu tarin yawa, balle kai tsaye tana zuwa ta doshi inda za ta gan shi. Duk ba abu ne mai sauƙi neman mutumin da ko ainihin sunansa ba ta sani ba a gari kamar wannan, amma tana jin a ranta motsi ya fi laɓewa, kuma rashin jini rashin tsagawa. Wannan shi ne mataki na ƙarshe da za ta iya ɗauka domin nemawa kanta mafita. Ta yarda da cewa Sarƙar, ƙaddara ce ta haɗa ta da Sayyid, ta yi wa rayuwarta dabaibayi, mussaman da ya tafi ya bar ta da ajiyarsa a tare da ita. Sai dai bayan wannan tana cike da zullumin halin da yake ciki, saboda ta san kaso mafi yawa na mafarkin ta ya kan zama gaske, a jikinta take jin duk a inda yake, yana buƙatarta a kusa da shi. Hankalinta ne ya dawo jikinta, bayan da ta ji ana cewa, an tsallaka boda sun shiga ƙasar Nijar!. AYSHERCOOL 08081012143 62 Jamila na ɗaki tana jiyo maganar Baba ya dawo, ba ta fito ba, sai da aka jima sannan ta fito tsakar gida. Ya ce"Jamila kun dawo ashe? Yaya ku ka baro Nanan?" Jamila ta yamutsa fuska ta ce "Bamu tarar da Nana ba, ta bar Buda ta tafi Bauchi gurin mamanta, kamar yadda Uwani ta gaya mana" A fusace ya ce "Bauchi gurin Maijidda? Lallai yarinyar nan ta riƙa ba ta ganin mutuncina, gidan ubanta ne a Bauchin da ta tafi? Uban me za ta yi a can?" Jamila ta ce "A'a Baba, kar ka ga laifinta fa, a lokacin da take buƙatar taimako, ba a duba ta ba. Na san ta bar Buda ne dan kar ta din ga ɗora wa Uwani ɗawainiya" Cikin kumfar baki ya ce "Wallahi ba zai yiwu ba, sai ta baro Bauchin nan, tun da dai ba gidan ubanta ba ne ba, kuma laifin Uwani ne ai da sai ta sako ta a gaba ta dawo da ita nan Kano, dan me za ta tafi wata Bauchi" Ummi ce ta yi sallama, suka amsa su na kallon ta. Jamila ta ce "Ummi ya dai? Ya na gan ki kuma?" "Ke Ummi, ke ce babbar algunguma, na san duk abin da Nana take yi kin sani, tun da da ke take shawara, ke ki ka bata shawarar ta tafi Bauchi ko?" Ummi ta girgiza kai ta ce "A'a, ba ni ba ce ba.  Dan hatta ɓatan mijinta ni ban sani ba, ba ta gaya mini ba sai yau da muka je Buda". Cikin rashin fahimta Baba ya ce "Ɓatan mijinta kamar yaya?" Ummi ta ce "Baba, duk ba wannan ba. Jamila bayan rabuwarmu ina shiga gida, saƙon Nana ya faɗo wayata, hankalina a tashe yake fa" "Ban gane ba, saƙon mene ne, ke Ummi ki yi mini bayani gwari-gwari sai wani kwalo-kwalo ki ke yi mini" "Baba, yau da muka je Buda, Uwani ta sanar mana, mijin Nana an neme shi an rasa kusan sati biyu. Har gurin 'yan sanda suka kai cigiya ba a san inda ya tafi ba. Bayan mun dawo ina shiga gida, saƙon tex message ɗin ta, ya shigo wayata. Ungo ka karanta message ne kusan kashi uku ga shi nan" Ya saka hannu ya karɓa, cike da fargabar abin da zai gani. "Assalamu alaikum, Ummi ya ki ke, ya su Islam. Ki yi haƙuri ban sanar miki ba, ba na son ɗaga miki hankali ne. Sayyid fa ya ɓata, daga na je sayo abu, na dawo na neme shi na rasa, ba na son ci gaba da ɗora miki ɗawainiya, ita ma Uwani yau da gobe sai Allah, ba ƙarfi ne da ita ba. Na je Bauchi Mama ta karɓe ni hannu bibbiyu, amma kamar zuwana zai zame mata matsala a gurin mijinta. Na san ko na koma gida, babu lallai Baba ya karɓe ni, na yanke shawarar na tafi Nijar, ko zan ga Sayyid ko danginsa. Kar ku ɗaga hankali gurin nema na, in sha Allah ba zan aikata abin da zai zame mana abin Allah wadai ba. Yanzu haka ina hanyar Niger, kar ku yi wahalar nema na, in sha Allah zan kasance cikin aminci, ku taya ni da addu'a. Nana Asma'u" A fili Baba ya karanta saƙon. Cikin fusata da tashin hankali ya ce "Wace irin mahaukaciyar yarinya ce Nana? Uban wa ye da ita a Nijar ɗin da ta wanke ƙafa  ta tafi can? Banda tsabar hauka da rashin hankali da wauta, a gidan uban wa za ta sauka? Ba nan ta ce mini ba ta san suwaye danginsa a can ɗin ba, to gidan uban wa ta tafi?" "To Allah dai ya kiyaye ya sa ba ɗaukar magana ta tafi ba" Mama ta yi maganar tana kwaɓe baki, wanda tun da aka fara magana da ba ta saka baki ba. Bai kula ta ba ya ce wa Ummi "Ke kira mini ita dan ubanta ta dawo gida, ko ƙasa nake ci ta zauna mu ci tare" Ummi ta ce "Baba wayarta fa ba ta shiga, tun kafin na zo gidan nan, nake ta gwadawa, amma ba ta shiga." "Ki sake kira ki ji dai" Ummi ta karɓi wayar ta kira Nana, amma aka ce wayar a kashe take. Baba ya dasa faɗa, Ummi a sanyaye ta ce "Dan Allah Baba kar ka yi mata baki, wallahi idan aka nustu Nana ba ta da laifi a cikin lamarin nan. Tin fil azal fa ba bincike aka yi ba, ba a san daga ina mutumin nan yake ba, ka aura mata shi, saboda kawai ka na tunanin su na aikata ɓarna, alhalin babu cikakkiyar hujja da ta nuna hakan. Ba ta bujire maka ba ta yi biyayya, duk dan kar ta dawo gidan nan, kamar yadda ka gindaya mata cewar babu zawarci, ya sanya ta dage kai da fata, ta yi aiki tuƙuru ta jure wahala da ƙalubale take jinyar mutumin nan. Ka san Nana da gudun magana, duk tsoron abin da ka iya biyo baya ya sanya ta yanke wannan hukuncin, ka yi haƙuri a yi mata addu'a kamar yadda ta buƙata " "Amma Ummi, Nana ko yayyanka Naman jikinta zan yi na cinye dan ba'i ba gara ta dawo mini nan ba! Dan me za ta kama hanya ta tafi Nijar? Gurin uban wa za ta je?" Jamila ma ta ce "Tun da dai ta riga ta tafi, dan Allah ka yi haƙuri" Baba ya rasa abin da yake yi masa daɗi, ya shuri takalmansa ya yi waje. ***** Su na tafe a hanya, Nana tana addu'a, tana fatan Ubangiji Allah ya sauƙaƙa mata, ya taƙaita mata wahala. Ya haɗa ta da Sayyid cikin aminci, tare da fatan duk inda Sayyid yake, ya kasance cikin aminci. Ta maimaita Hsbunallahu wa ni'imal wakil, babu adadi, tare da tawasalli da ayoyin Alƙur'ani a kan Allah ya shiga lamarin ta, ya sauƙaƙa mata wahala. Ƙarfe shida saura, Nana suka sauka a  Maraɗi. Tun a Nigeria ta sai 'yan kayan ciye-ciye ta zuba a Jakarta. Ta yi sallar la'asar ƙasaru, sannan ta tsaya tana ƙarewa tashar motar kallo, tana tunanin ma ta ina za ta fara. Ta ji ƙafafuwanta kamar ba a jikinta suke ba, saboda nauyi, sun kumbura sun yi suntum, saboda azabar nauyi da gajiyar tafiya. Ga ɗan cikinta ya yi jingim ko motsi ta ji ya daina yi saboda azabar wahalar tafiya, Bayanta da mararta suka ƙulle mata, saboda azabar wahala. Ga jikinta tamkar an sassara ta, saboda gajiya babu isasshen gurin miƙe ƙafa. Masu babur na ta tambayarta ina za ta je, amma ta yi musu shiru, ta ɗauki bagcon kayanta, ta yi gaba. Tamkar ba ta jin jikinta, haka ta din ga jefa ƙafa tana tafiya. Ta yi nisa sosai da tasha, ta fara hango unguwanni da gidaje. Duhun magariba ya rufa, ta samu wani gida kawai ta shiga. Matar na tsugune tana tuƙa tuwo Nana ta yi sallama. Suka gaisa da Nana, matar ta tsaya tana kallon ta, ta ji abin da ya kawo ta. Nana ta ce "Dan Allah baiwar Allah, ni baƙuwa ce, hanya ce ta biyo da ni, dan Allah salla nake son na yi, idan babu damuwa zan kama ruwa ne na yi alwala". Matashiyar matar ta ce "To ba komai. Ga banɗaki nan da buta a ciki" Nana ta ajiye kayanta, ta shiga banɗakin ta zubar da uban fitsarin da ya cika mata mara dam. Ta yi miƙa saboda gaɓoɓinta da suke yi mata ciwo. Sannan ta yi alwala, bayan ta yi alwalar, ta tsaya ta ɗaga cikinta, tana ɗan tattaɓawa cike da damuwa, jin sa shiru bai dame ta da motsi ba. "Haba yaron kirki, ka motsa mana ko na ji daɗi, haba ɗan Baba. Nana na cikin damuwa dan Allah ka motsa" ta yi maganar a hankali cikin tsoro da damuwa, dan ta ji ana cewa idan ɗa ba ya motsi, to mutuwa ya yi. Har ta fitar da ran ɗan nan zai motsa, ta tsorata idonta ya fara cika da hawaye, kawai ta ji ya motsa a hankali, sai kuma ya ci gaba da motsawa. Wata irin ajiyar zuciya ta yi, ta shafa cikin ta ce "Alhamdillah, Allah ya bayyana mana Sayyid ɗinmu cikin aminci" Gaba ɗaya ta manta a banɗaki take. Ta fito matar ta ba ta dadduma a ɗaki, ta shiga ta tayar da salla. Bayan ta idar da sallar, ta zauna a kan sallaya, ta din ga tasbihi tana gaya wa Allah damuwarta, har aka yi sallar isha'i. Nan ma ta tayar da salla ta yi, tana cikin addu'a matar ta shigo da kwanuka, ta ajiye. Nana ta shafa Addu'ar ta kalli matar ta ce "'yar uwa Na gode sosai da sosai, Allah ya saka miki da mafificin Alkhairi na gode ƙwarai da gaske" "A'a babu komai, musulmi ai ɗan uwan musulmi ne, ki ci abinci kafin ki tafi dan Allah" Nana ta ce "A'a, na ƙoshi Alhamdillah, Allah ya saka da alkhairi, ya biya miki buƙatunki na alkhairi" Matar ta ce "A'a daga gani daga tafiya ki ke, ga juna biyu, ai sai wahala, dan Allah ki ci ko kaɗan ne kafin ki tafi" Nana ta dage matar ma ta dage. Da ƙyar Nana ta amince ta ɗan ci Abincin kaɗan sai dai babu abin da take tunani, sai yadda za ta yi da gurin kwana. Ta rufe sauran Abincin ta ce "Na gode sosai da sosai 'yar uwa, Allah ya saka da alkhairi" Matar ta amsa da "Amin, Allah ya kiyaye hanya" Nana ta amsa da Amin, ta ɗauki jakar kayanta ta yi waje. ***** Babar Nana wuni ta yi sukuku, gaba ɗaya hankalinta a tashe, sai koke-koke take yi. Baban su Walida kuma ya yi burus da ita. Ganin kuka da damuwa ba zai fishshe ta ba, ya sanya ta yi alwala ta hau kan sallaya, ta gabatar da salatul haja, sallar neman biyan buƙata a gurin Allah. Ta ɗaga hannayenta tana kuka, take yi wa Allah kirari da magiya. "Allah kai ne Allah, Allah kai ne ka halicce ni ka kuma halicci Nana, ka rayata ta girma cikin ikonka da kulawarka. Ya rabbil arshil azim duk inda yarinyar nan take, Ubangiji Allah ka kai mata ɗauki, da ita da abin da yake cikinta. Allah ka kare ta daga dukkanin sharrin abin ƙi, Allah ka zama gatanta ka tsare mini ita. Ya hayyu ya ƙayyum domin kyawawan sunayenka maɗaukaka masu girma, Ubangiji Allah ka kai wa Nana ɗauki, ta inda ba ta zata ba" ko abinci ba ta iya ci ranar ba, gaba ɗaya addu'ar wunin ranar, Nana kawai take yi wa. Can gida Baban su Nana ma, an ba shi Abincin dare, amma ya gagara ci sai uban tagumi da ya rafka. Lissafinsa kawai gidan uban wa za ta ga je a Nijar? Hannun wa za ta faɗa kuma a ina za ta kwana? Nasiru kuwa tun da ya samu labari shi ma abin duniya ya dame shi, kuma ya ɗora alhakin hakan a kan mahaifin su. Mama ta ce "Wai baban Jamila ba za ka ci Abincin ba sai ya sandare?" "Wai wane Abinci zan iya ci? Wanan shashashar yarinyar, tana can babu uban da ya san a yaya za ta kwana? Kai Nana muguwar sokuwa ce. Kin ga ɗauke Abincin nan, gurin Malamin Almajiran can zan je na gaya masa, ko kiranye ne a yi mata ta dawo gida dan ubanta". "Kiranye kuma?" "Eh mana, tun da dai shi mijin nata mutumin banza ne, bai san abin da ya dace ba, ya tafi ya bar ta, ai sai ta dawo gida, tun da ba ƙanin ubanta ba ne" Jamila ta ce "Kayya! Ba na tunanin wani kiranye zai yi wa Nana tasiri, ka san tana da haƙuri amma akwai taurin kai" "Aikuwa wannan karon, dole ya kama ta, duk gidan uban da ta tafi, sai ta dawo" ya yi maganar a fusace ya fice fuuuuu. Sagir yana tsaka da bacci, ya buɗe idonsa ya ga Shukura a zaune. "Sweetheart lafiya kuwa? Ya na gan ki a zaune?" Ji ta yi tamkar ta kifa masa mari, amma ta maze ta ce "Ba na jin daɗi ne" Ɗan rikicewa ya yi, ya tashi ya matsa kusa da ita. Da gaske jikinta da zafi. "Ya salam, bari na duba miki pcm" ya tashi ya kunna fitila, ya kawo mata ruwa da magani. A dole ta karɓa ta sha. Ya kashe fitilar ya zauna a kusa da ita, ya riƙe hannunta yana ɗan murzawa a hankali. "Sannu" "Yauwwa" ta amsa a taƙaice. "Beb anya ba wani cikin ba ne?" "Ahha haba dai, ba wani ciki maybe malaria ce" Sagir ya ce "Ban yadda ba, gobe in Allah ya kaimu zan kai ki Asibiti a sake duba mini ke. Ubangiji Allah ya sa cikin ne" shiru ta yi ba ta amsa masa ba, shi kum hakan bai dame shi ba. Duk haushin Sagir da take ji, yana da halayen da duk ƙiyayyarka da shi, muddin za ka yi masa adalci dole ka kira shi mutumin kirki. Yana da matuƙar tausayi, duk faɗan da za su yi, da ya ganta a yanayi na rashin lafiya, zai rikice gaba ɗaya. Haka ya lallaɓa ta ta kwanta, sai dai da ya fara bacci sai ya farka, ya taɓa goshinta da wuyanta. Ita kuma idonta biyu duk abin da yake yi tana jin sa. **** Sai da Nana ta tabattar da sawu ya ɗauke, sannan ta ɗauki jakarta, ta koma gidan da ta shiga ta yi salla. An kulle ƙofar gidan, amma ƙofar rilar gidan a buɗe. Ta shiga rilar, ta ciro daddumarta ta shimfiɗa, ta ɗaukko zani a kayanta ta yi kwanciyar ta. Har a wannan lokacin, da take shirin kwana a waje haka, ba ta ji ta yi nadamar tahowarta Nijar ba. Sai ma ji da take yi ta zo inda babu wanda ya santa, balle a din ga gudunta, a din ga ganin da ta rabu mutum sai wata masifar ta afka masa. Ta saka hannu ta tallafo cikinta, da ita ma take jin nauyinsa, ya wuce adadin watannin da take tunani. Tana jin yadda yake motsi, wanda motsin nasa kaɗai, wani irin farinciki da nishaɗi yake sanya ta. Sai kuma damuwa ta biyo bayan farincikin nata, bayan da ta tuno Sayyid, da kuma rashin sanin halin da yake ciki. Da haka bacci nannauya ya yi awon gaba da ita a gurin. Ko da dare yayi, Maijidda bacci gagarar idanunta ya yi, ta tattara Iliyasu ta watsa a gefe, addu'a kawai take yi Ubangiji Allah ya sanya Nana ta kasance cikin aminci da kwanciyar hankali. Tana zaune a kan gado, ta yi shiru abin duniya ya ishe ta. Ji ta yi yana lalubata, wani irin baƙin ciki ya turnuƙo zuciyarta. Ƙoƙarin janyo ta yake yi, ta buge hannunsa a fusace, saboda ko ƙaunar ganinsa ba ta son yi. Ya ce "Mai Jidda meye haka ne wai?" "Dan Allah ni ka rabu da ni, wallahi ko ƙaunar ganin ka ba na yi. Ni dan zatin Allah ka sake ni, gara na yi zaman 'ya'yana kawai, da na ci gaba da zama da mutumin da ba ya ƙaunata, na yi kuskure tun farko da na biye wa son zuciyarka na banzatar da 'ya'yana" Ta yi maganar tana kuka mai ƙunar zuciya. "Maijidda da ba na sonki, ke kin san ba za ki je ki yi wani auren ki fito na aure ki ba. Ni kishinki nake yi, kuma na gaya miki tsanar da na yi wa mijinki ne ya shafi 'ya'yansa" "Ka na ƙaunata, ina cikin wannan mawuyacin halin, da kai ne sila, za ka zo ka na naniƙata buƙatarka ce kawai a gabanka? Wallahi ba ka ƙauna ta. Kuma haƙurina ya riga ya ƙare, ka sauwwaƙe mini kawai, ni zan tafi neman 'ya ta. Allah kaɗai ya san a yaya za ta kwana a ƙasar da ba ta san kowa ba, ga tsohon ciki" Kasancewar buƙatarsa a gabansa, ya sanya ya kwantar da murya, kamar yadda ya saba ba ya tashi kalailaye ta, da kwantar da murya sai a irin wannan lokacin. "Wataƙila ma fa ba Niger ɗin ta tafi ba, ai ba yarinya ce ƙarama ba, na san gidan babanta ta koma, ki ke ta ɗaga hankalinki" "Da akwai damar zama a gurin Baban nata, ka na ganin za ta zo inda nake ne? Nana ba za ta ajiye mini wannan rubutun ta koma gidan babanta ba, ni ka riga ka cuce ni" Ta yi maganar tana sauka daga kan gadon. Ya bi bayan ta yana lallaɓa ta, amma ta wuce ko saurarasa ba ta yi ba ta bar ɗakin, abin da ba ta taɓa yi masa ba a tsawon zaman su. Baba ma abin Duniya ya dame shi, ya fito ƙofar gida yana takaicin abin da Nana ta yi, sai ga kiran Uwani. Kamar ya share sai kuma ya ɗaga, suka gaisa Uwani ta ce "Isa kiran ka na yi na ja maka kunne, tun jiya da su Ummi suka taho nake son na kira ka na ja maka kunne, kar ka kuskura ka kira yarinyar nan ka ce za yi mata faɗa, ko ka kira uwatta ka yi musu jaraba, saboda Nana ta tafi can, ita ma mafitarta take nema, tuntuni da ka kama 'yar ka ka riƙe, babu yadda za a yi ta tafi Bauchi gurin babarta. Kuma ga halin da take ciki an nemi miji an rasa, ba a san kowa nasa ba, yarinyar nan na cikin wani hali, dan haka kar ka ce za ka yi mata faɗa tun da kai ne ummul aba'isin duk wannan lamarin. Da ka binciki dangin mutumin nan kafin ka aura mata shi, da duk haka ba ta faru ba". "Uwani" "Na'am" "Nana fa ba ta Nigeria ma gaba ɗaya, mijin Babarta ya kore ta, ta rubuta wa Ummi saƙo ta tafi Niger neman mijinta" "Me? Ta tafi Nijar ta san a inda za ta gan shi ne?" "Oho ina san mata ma, na samu wani malami, na ba shi abin sadaka ya yi mata kiranye, gaba ɗaya yarinyar nan ba ta da lissafi" "A'a ai duk kai ka janyo, amma Nana ba ta yi dabara ba, wallahi da na san abin da zai faru kenan, da ban bari ta tafi ba" "Sai anjima bari na koma gurin malamin na gode " ya kashe wayar dan ita kanta Uwanin haushinta yake ji. Yana shirin yin gaba, sai ga wata mota ta tsaya a gaban Baba. Har Baba zai wuce, sai kuma ya tsaya. Wani matashin saurayi ne ya fito Baba ya din ga yi masa kallon sani. Matashin ya ƙaraso su ka gaisa. Matashin ya ce "Baba dama, Mamanmu ce ta aiko ni, can gidan da Nana ta yi aikin rainon yaro. To wai Hajiya ce kwana biyu suna ta kiran wayarta, ba ta shiga sam, kuma an je can gidan da suke gadi, amma ba sa nan, shi ne ta ce na zo gida na tambaya ko lafiya, ko kuma a bani lambarta da take shiga na kai mata" Baba ya kwaɓe fuska ya ce "Kai ne ta auri Buzun yaron nan a gidanku kenan?" "Eh ni ne Baba" "To ai 'yan uwansa ne suka fara guduwa, ya yi ta rashin lafiya, to yanzu dai shi ma ya gudu, ta tafi can Nijar neman sa". Yusuf ya yi sororo cikin rashin fahimta ya ce  "Ya gudu ta tafi nemansa kuma?" "Eh kamar dai yadda ka ji na gaya maka" Ganin kamar Baba a fusace yake, ya sanya Yusuf cewa "To shikenan Baba, Allah ya kyauta, ya bayyana su cikin aminci" Ya koma ya shiga motarsa ya tafi. ***** Sanyin iskar sahara ce ta din ga ratsa Nana, har ta fara karkarwa saboda sanyin. Ta ɗaga kai, ta ga sararin samaniya ta yi tarwai, sai hasken farin wata da ya haska cikin saharar. Wani irin ƙugi ta ji saharar tana yi, da alamun tasowar iska. Ta kalli gabas ta ga iskar sahara daga nesa, tana wani irin hanƙoro da alama iskar tana da ƙarfi. Sauke Numfashin Sayyid ta din ga ji a cikin saharar. Waige-waige ta fara tana neman ina za ta gan shi. "Sayyid, ka na ta ina ban ganka ba" "Ma viee" "Na'am Sayyid, ka na ina ne?" "Za su kashe ni, dan Allah ki zo mu koma gida, na fi son rayuwata da ke, na nufi nutsuwa" Cikin rauni ta ce "Sayyid ba na ganin ka, ka na gurin ina?" "Husna" ta sake jin muryarsa yana ajiyar zuciya. Gadan-gadan Nana ta nufi inda ƙurar Saharar nan take tasowa, saboda daga nan take jin sautin muryarsa. A ɗan razane ta farka, saboda taɓa ƙofar gidan da aka yi. Tana kwance a cikin duhu, ta hangi mai gidan ya fito, da alama masallaci ya tafi. Ta tashi da ƙyar, ta buɗe kayan ta, ta ɗauki ruwa pure water, ta kama ruwa ta yi alwala. Tana jin yadda magidanta suke buɗe gidaje, su na tafiya masallaci. Ita ma ta tayar da salla. Kusan mintuna Arba'in mai gidan ya dawo, sai da ya tsorata kasancewar gari ya fara haske. Ya ga mace tana salla a kan dadduma a cikin rilar gidan. Nana ta ɗaga kai ta kalle shi, ta mayar ta sunkuyar ta ci gaba da tasbihi. Sai dai duk iya ƙoƙarinsa a kan ya yi mata magana, ya kasa kamar an saka masa sakata a bakinsa. Ya lallaɓa ya buɗe ƙofa ya shiga gidansa, ya tarar da matarsa tana bacci, kasancewar Al'ada take yi, ba ta salla. Kamar ya tashe ta ya gaya mata batun matar da ya gani, amma ya kasa, ya haƙura ya ƙyale ta. **** Jamila bata taɓa sanin ta damu da Nana har haka ba, duk da takun saƙa da sukan yi wasu lokutan, saboda ƙuruciya da sakunta, wasu lokutan kuma saboda zigar Mama. Amma ta damu sosai da halin da Nanan ke ciki. Jikinta ya yi sanyi sosai da sosai, da Ummi ta ba ta labarin wahalar da ta yi ta faman yi, ga miji ga laulayin ciki. Yanzu mai ɗungurungun ta tafi inda babu mataimaki sai Allah. "Amm Jamila" "Na'am Mummy" "Kwana biyu na ɗaga miki ƙafa da batun Nana, saboda ki samu ki ƙara sakin jikinki, yanzu dai ki na ganin yadda al'amuran ƙungiya suke wakana, kuma na ga kin saki jikinki yanzu. Dole fa ki yi ƙoƙari a wannan karon, ki samo mana jinin Nana, saboda ba ƙaramin alkhairi ne a tattare da taurarinta ba. Tun da dai kin ga Uba ku ka haɗa kawai da ita." Jamila ta yi murmushi cike da takaici, amma a zahiri ta danne ta ce "To ai Nana mijinta ya ɗauke ta, ya tafi da ita can ƙasar su Nijar a can ma ina ga za ta haihu" "What? Jamila amma ya aka yi ba ki gaya mini ba, bayan kin san ƙudurina a kanta?" Jamila a ranta ta ce "Da yake ki ka halicce ta ba" A zahiri ta ce "To ai ni ban san haryanzu ana buƙatar jininta ba, da na ga ba ki kuma yi mini maganarta ba, na zata shikenan ya wuce" Kamar ta rufe Jamila da duka ta ce "Amma wallahi ba karamar shashasha ba ce, ɗaga miki ƙafa kawai na yi ki ƙara dawowa hayyacinki, aikuwa ko ki nemo Nana a samu jininta, ko kuma ƙungiya ta nemi jinin wani shaƙiƙinki, sai ki zaɓa". Jamila ta waro ido ta ce "Shaƙiƙina kuma Mummy, na shiga uku na lalace" "Ahh to dabara ta rage ga mai shiga rijiya ai, sai ki yi tunani, ni na haura sama zan yi bacci" Gaba ɗaya jikin Jamila ya yi sanyi, ta bi bayan Hajiya Sa'a da wani irin kallo. Har rana ta ɗaga gurin ƙarfe goma, Nana na zaune a rilar gidan nan, sai da rana ta tarar da ita, sannan ta yinƙura, ta ɗauki jakar kayanta, ta koma barandar da ke kallon gidan, ta zauna. Mai gidan da ta kwana ya fito zai tafi kasuwa, kawai ya sake ganin Nana, da hijjabinta da wannan bagcon kayan nata ya gane ta. Ƙarasa fitowa ya yi, da niyyar ya tambayi Nana me take nema ne? Amma su na haɗa ido da Nana ya kawar da kansa cikin sauri, saboda wata irin mummunar faɗuwar gaba da ta ziyarce shi. Sum-sum ya wuce ya tafi, ba tare da ya ce wa Nana komai ba. Rana ta fara zafi, ta sake ɗaukar jakarta ta yi gaba, ta din ga nanata lahaula wa la ƙuwwata illa billah. Hasbunallahu wa ni'imal wakil. ***** Alhaji Zailani yana zaune a falo, tare da Hajiya Amina, Yusuf ya shigo falon. Hajiya Amina ta kalle shi ta ce "Yusufa daga ina?" "Aiken ki na je Mami" Ta ce "Wanne daga ciki?" Ya zauna tare da faɗin "Ba shekaranjiya muka yi zancen Nana da ku ba? Gidansu na je, daga gidan nake na samu babanta a waje, ya gaya mini wai mijinta ne ya ɓata ta bi shi Nijar neman sa" Hajiya Amina ta dafe ƙirji ta ce "Ya ɓata kuma garin yaya? Ko shi ma ɗauke shi aka yi kamar yadda aka tafi da 'yan uwansa? Anya ba wani laifin suke aikatawa ba hakan ta faru? To ta san inda yake a Nijar ɗin ne?" Yusuf ya ce "Wallahi nima ban sani ba, haka dai ya ce mini" Alhaji Zailani da hantar cikinsa ta kaɗa ya ce "Wai maganar wa ku ke yi ne?" Cikin dakiya ta ce "Nana mana, yarinyar nan da ta kula da Haidar, wadda babanta ya aura wa Buzun nan" "To sai aka yi yaya?" Yayi maganar yana tsare ta da ido, yana tunanin ko Hajiya Amina ta ci gaba da bibiyarta, ta gaya mata abin da yake tsakaninsu. "A'a dama Shukura ce ta ce, kwana biyu shiru, kuma ba ta samun ta a waya, nima kuma ba na samun ta, shi ne na ce masa dan Allah idan ya biya ta hanyar gidanta, ya tsaya ya karɓo mini lambarta, to kuma wai sun tashi daga gidan. Shi ne ya je gidansu aka sanar masa da ta bi mijin Nijar" Ya yi wata ɓoyayyiyar ajiyar zuciya ya yi shiru bai kuma cewa komai ba. Hajiya Amina ta yi ta jajanta lamarin, tare da tausayawa Nana. Alhaji Zailani kuwa rikicewa ya yi, cike da kiɗima. Domin yana ta tsara yadda zai samu Nana ko ta halin ƙaƙa domin samun biyan buƙatar sa. Yaronsa da ya bawa ragamar bibiyarta, bai taɓa gaya masa ba, ce masa kawai ya yi ta koma Kurna. Wani irin gumi ya fara keto masa, ta ina za a fara neman ta yanzu har a gano ta, a Nijar. Sai ya ɗora wa kansa alhakin sakacinsa ne, da ya din ga bin al'amuran a sannu, duk da hakan ya faru a dalilin halin da yake shiga, a duk lokacin da ya yi yinƙurin aiwatar da wani abu a kan Nanan. **** Nana kuwa wuni ta yi tana gararanba a titi, daga wannan inuwa ta koma waccan, ga uban kaya ga kuma ciki. Dama Abinci ba damunta ya yi ba. Buredinta da ta yi guzuri ta ci abin ta, ta kora da ruwa. Tana son samun muhalli, tun da akwai kuɗi a hannunta, akwai na Nigeria akwai na Nijar, sai dai amana ta yi ƙaranci, ba ta san wa za ta tunkara ya taimake ta ba, tana tsoron a cutar da ita. Dare ya yi bayan sallar Isha'i, ta sake lallaɓawa ta koma gidan nan ta kwana a rila, da Asuba mijin matar ya sake ganin ta, hakan ya sanya hankalinsa fara tashi, ga shi ya kasa magana kamar wanda aka yi wa asiri. Yau bayan magariba da ya koma gida, sai ya sanya wa rilar sakata, ya kulle ta ciki. Sawu ya ɗauke, Nana ta lallaɓo ta zo ta kwana, kawai ta tarar da rilar a rufe, ta jijjiga ta ji an garƙame ta ciki. Jikinta ya yi sanyi, ga shi duk inda ta tafi ko ta yi niyyar ta yi gaba ta tafi wani gurin, sai hankalinta ya kasa kwanciya sai dai ta koma gidan nan. Ga yau wani irin bacci take ji, kamar ta kifa, ga shi tana son yin wanka, saboda yadda kayan jikinta suke mintsininta, tun da ta zo da su take yawo. Ta samu gefen gidan ta takure, tun tana hamma har bacci sosai ya yi awon gaba da ita. Da Asuba ta ciro jarkar ruwan da ta saka wasu yara suka zuba mata a cikin ƙaramar jarka, ta yi alwala ta yi raka'atanul fajr. Tana kallon mai gidan ya fito ya tafi masallaci yana haske-haske, amma bai gan ta ba, har ya tafi. Ya dawo daga masallaci kansa tsaye zai shiga gida, ya ga Nana a cikin rilar. Wata irin razana ya yi, ya kuma kasa magana sai kallonta da yake yi fuskarsa na bayyanar da tsoro ƙarara. Nana ta ce "Ka kulle rilar gidanka, jiya a waje na kwana, duk da ban ga laifin ka ba, amma da ka tambaye ni, me yasa nake kwana a nan" "Wa..wa.wace ce ke? Me ki ke yi a nan?" Ayshercool 08081012143 63 Nana ta ce "Dan Allah ka kwantar da hankalinka, kar ka tsorata wallahi ni mutum ce, ba abin da na isa na yi maka na cutarwa, ba kuma ni da nufin cutar da ku" "To me ki ke yi mini a gida?" "Wallahi baƙuwa ce ni, ranar da na sauka a garin nan, na shiga gidanka, matarka ta bani gurin salla, har da abinci, dan Allah taimakona za ku yi" Ya ce "Baiwar Allah wallahi mu ma talakawa ne, ba wani taimako da za mu iya yi miki" Ta ce "A'a amma ai ku musulmai ne, gudun zargi dan Allah idan babu damuwa, mu shiga ciki a yi maganar a gaban matarka, ku ji taimakon da nake buƙata idan za ku iya yi mini, idan kuma ba za ku iya yi mini ba, babu komai sai na nema a gaba" Kamar ya ce a'a, amma yanayin Nana sai ta ba shi tausayi, ya bata dama suka shiga gidan, yana gaba tana bin sa a baya. Nana ta tsaya a tsakar gida, ya shiga ya taso matarsa. Ta fito tana mustustuke ido, ya nuna mata Nana ya ce "Kin san wannan?" Ta ɗan yi shiru sannan ta ce "Kamar shekaranjiya ta zo, ta ce mini baƙuwa ce za ta yi salla" Ya ce "Yauwwa, sau uku ina ganinta a rilar gidan nan. Wai a nan take kwana, ta ce mini taimako take nema, amma a zo a gaban ki, sannan ta faɗi me take son mu yi mata". Matar ta kalli Nana,ta ce "Baiwar Allah, wane taimako za mu yi miki?" Nana ta ce "Ni baƙuwa ce daga Nigeria, dan Allah ku taimaka mini da inda zan zauna, ban san kowa a ƙasar nan ba. E" "Gaskiya baiwar Allah, ba bu gurin da za mu iya ajiye ki a gidan nan" matar ta tari numfashin Nana. Nana ta ce "A'a ba a nan za ku ba ni gurin zama ba, da kuɗi a gurina, sai dai ban san kan kuɗinku na ƙasar nan ba, ina da wasu ma na Nigeria, ban san yadda zan canza su ba. Kuma ina tsoron na faɗa hannun da ba na gari ba a cutar da ni. Haka kawai na ji na nutsu da nan tun lokacin da ki ka karrama ni, ko na tafi sai na dawo nan na kwana nake samun nutsuwa. So nake ku taimaka a sama mini gidan haya, ko ɗaki da zan kama dan Allah. Kuma wallahi ni ba macuciya ba ce ba zan cutar da ku ba. Ku yi wa Allah da ma'aiki ku taimaka mini, dan Allah" Ya kalli matar matar ta kalle shi, ta ɗan jinjina masa kai. Ya kalli Nana ya ce "Kin san harkar taimakon ce wuya ne da ita yanzu, sai ka taimaki mutum amma ya sanya ka a masifa. Nana ta ce "In dai kun yi niyyar taimakona, ko macuciya ce ni, Allah ba zai ba ni damar cutar da ku ba. Ku taimaka mini dan Allah, ko iya gidan hayar a sama mini" Ya kalli matarsa ya ce "Hajara, bata guri ta zauna, zuwa gari ya ƙarasa wayewa, sai mu san abin yi, mu duba girman Allah da ta haɗa mu da shi" Hajara ta ce "To shikenan babu damuwa" wata irin ajiyar zuciya Nana ta yi, ta risuna ta ce "Na gode, Ubangiji Allah ya saka muku da mafificin Alkhairi, yadda ku ka taimaka mini Allah ya taimake ku haka" Suka amsa da Amin. Matar ta kai Nana wani ɗaki, ta ɗaukar mata kayanta ta shiga da su. Tana fita daga ɗakin, Nana ta zube ta yi sujjada tana gode wa Ubangiji buwayi gagara misali, ta san wannan ɗaukin kai tsaye daga gare shi ne, amma ba dan haka ba ta san ba ƙaramar wahala za ta sha ba. Sai yanzu da ta nustu, ta din ga jin ta a takure, saboda rashin wanka, ga cizonta da kayan jikinta suke yi. Gari ya yi haske matar ta shigo ta ce wa Nana "Ki na buƙatar wani abu ne?" Nana ta ce "Eh dan Allah zan yi wanka" "To shikenan babu damuwa, da kin sani tun ranar da ki ka zo, ki ka yi mini bayani, ga ki da juna biyu, amma a ce ki na kwana a waje bai dace ba" Nana ta ce "Larura ce, ba yadda zan yi, kuma babu daɗi ka ɗora wa mutane ɗawainiya sama ta ka" Ta ce "Haka ne" ta haɗa wa Nana ruwa, Nana ta duba kayanta ta ɗauki soso da sabulu, da brush. Ba ƙaramin daɗin wankan nan Nana ta ji ba. Ta koma ɗakin da suka sauke ta, ta fito koma ɗakin da aka sauke ta. Ta fito da mai ta shafa, ta saka kaya. Ta ji wata sassanyar iska na ratsa ta. Ta ɗaukko jakar kayan turarrukan Sayyid, da kayan gyaran gashin sa, ta yi zuru da ido, tana kallonsu. "In sha Allah za mu haɗu Sayyid, ina fatan Allah ya ƙaddara haɗuwarmu nan kusa" ta yi maganar a sanyaye. Sallamar Hajara ce ta sanya ta mayar da kayan cikin bagcconta, ta mayar da hankalinta kan ta. "Ko ki na buƙatar wani abun ne?" Nana ta girgiza kai fuskarta ɗauke da murmushi ta ce "A'a ba na buƙatar komai, na gode sosai da sosai" "Ba komai, bari na kusa gama abin karyawa" Cikin murmushi Nana ta ce "Ba raina miki na yi ba, amma ni wannan taimakon da ku ka yi mini ya wadatar, ba sai kun ba ni Abinci ba, na gode sosai da sosai" Hajara ta ce "Haba dai, ya ma za ayi ki na baƙuwarmu a ce ba za mu ba ki Abinci ba, ai ba zai yiwu ba sam" "Ai kar ɗawainiyar ta yi yawa ne, abin da ku ka yi mini ma, na gode Allah ya biya ku" "A'a babu wata ɗawainiya" ta yi maganar tana fita waje. Ta so tambayar Nana me ya kawo ta Nijar, ga tsohon ciki, kuma ta ce ba ta da kowa, amma ta kasa saboda wani irin kwarjini da Nanan ta yi mata. Tun da ta bawa Nana abincin safe, da rana ta bata fura Nana take amai. Har sai da Hajara ta ji babu daɗi, ta yi zaton ko Abincinta ne ya saka Nana amai. A sanyaye ta ce "Ko Abincin nawa ne ya saka ki amai?" Nana ta yi murmushi ta ce "A'a kar ki damu, dama haka nake fama tun farkon cikin, ni na riga na saba ma" "Kayya ai ba a sabo da wahala, kin yi amai ya kusa goma, ko Asibiti zamu je?" "A'a zan daina in sha Allah" Gaba ɗaya Hajara ta damu, ganin yanayin da Nana take ciki. Nana ta ce "Ba ki taɓa haihuwa ba ne? In dai mutum ya haihu ya san irin wannan larurar ta ciki ai" Hajara ta ce "Ina fa? Watanmu takwas da aure, ban haihu ba". Nana ta yi murmushi ta ce "Allah ya kawo mai albarka" "To ai ni duk na tsorata ne, wannan aman ya yi yawa" "Ai ni na riga na saba ma, ba ya damuna yanzu" haka suka ɗan din ga taɓa hira. Mijin Hajara bai dawo ba sai isa'i, Nana na ɗaki tana shafa'i da wuturi. Ya ce wa Hajara "Ina baƙuwarmu?" "Tana nan sai dai ba ta da lafiya" "Me ya same ta?" "Wallahi tun da na ba ta Abinci take amai, haryanzu jikina duk ya yi sanyi" Ya ce "Subhanallah, kuma bai tsaya ba?" "Tana dai ta yi" Nana ta idar ta yi addu'a, sannan ta fito, ta durƙusa ta gaishe shi, ya amsa yana yi mata ya jiki. Ta ce "Jiki Alhamdillah" Ya ce "Baiwar Allah ba a samu gidan haya ba, duk inda na tambaya, sai masu tsada, kuma babu lallai a bayar, mussaman idan aka san ke kaɗai za ki zauna, kuma zaman ki ke kaɗai babu Namiji babu tsaro ko kaɗan. Amma na kuma bayar da cigiya ko za a samu wani, wanda yake da mutane a ciki sai a kama" Nana ta jinjina kai ta ce "Na saku ɗawainiya, Allah ya saka da alkhairi" Ya ce "Ba komai" ya kalli Hajara ya ce "Bari na je na dawo, ko za ku yi hira kar na takura muku" Nana ta ce "A'a ba komai, ka zauna ni sai na koma ɗaki" Ya ce "A'a dama zan fitan" Hajara ta raka shi soro, ta tsaya can su na hira Nana tana jiyo dariyar su. Sayyid ya faɗo mata a rai. Yana daga cikin manyan ni'imomi da nasarorin rayuwa, mutum ya auri wanda yake son sa, ya kuma dace da shi. Ta yi musu addu'a da fatan samun dauwamammen zaman lafiya da kuma zuriya ta gari masu albarka. Hajara ta dawo, ta zauna su ka ci gaba da ɗan taɓa hira da Nana. Ta cewa Nana "Ko sunanki ban sani ba" "Nana Asma'u, amma Nana ake ce mini" Ta ce "Allah sarki, amma ki na da aure ne?" Nana ta yi murmushi, ta ce "Kin yi mamakin yadda na taho inda ban san kowa ba ga tsohon ciki ko? Na san wataƙila, kina tunanin ina na samo ciki ne?" Hajara ta ce "Laaa a'a wallahi" Nana ta ce "Ai babu damuwa idan ma kin yi tunanin haka, ɗabi'ar zuciya ce. Matar aure ce ni, ko a yanzu haka ka ma ina da igiyoyin aure uku a kaina, wani dalili ne ya kawo ni ƙasar nan, kuma in sha Allah da na kammala, zan koma gida" "Allah sarki, Allah ya tabattar da alkhairi, ya sanya a samu abin da aka zo nema" Nana ta amsa da "Amin na gode sosai" ***** Su na zaune sun tattara hankalinsu a kan likitan, cikin matsananciyar girmamawa Likitan ya gaishe su. "Ya ya jikin Imam?" Ya amsa da "Jikinsa Alhamdillah, yana samun sauƙi sosai da sosai" "Ba yana samun sauƙi muke son ji ba, mene ne sakamakon binciken ku da aka gudanar?" Likitan ya ce "Eh sakamakon gwaje-gwaje, ya nuna babu abin da aka yi masa na cutarwa a jikinsa, gaba ɗaya babu wani abu na cutarwa a tare da shi" "Shi kuma matsalar zuciyar fa?" "Wannan yana da nasaba da hawan jini da yake da shi tuntuni, wataƙila ya daɗe ba a kan magani ba. Shi yasa ya shafi zuciyarsa. Sai dai matsala ɗaya" Cikin damuwa dattijon ya ce "Wace matsalar?" "Ƙwaƙwalwarsa, mun kasa gano abin da yake faruwa da ƙwaƙwalwarsa, haryanzu bai samu nutsuwar da zamu tattauna da shi ba, yana buƙatar kulawa ta musamman a bangaren ƙwaƙwalwa" Sultan ya dafe goshinsa, cikin matsananciyar damuwa da tashin hankali, idanunsa suka yi jawur. Ya ɗago ya kalli Likitan ya ce "Ko gida za a mayar da shi, a saka duk abin da ake buƙata na kula da shi a ɗakin, ya zamana yana kusa da ni, hankalina ba ya kwanciya, yana nan ina can" Abduou ya ce "A'a Sultan, idan aka mayar da shi gida, za a iya gane halin da yake ciki, wanda ba ma fatan hakan, dole a ci gaba da toshe duk wata kafa da za a san halin da yake ciki, har zuwa lokacin da zai warware. Kuma za a ci gaba da matsa yaran can, har sai ya yi mana bayanin abin da suka yi masa a Nigeria. Kuma Asibitin nan akwai tsaro babu wanda ya san yana nan. A kula da shi har zuwa lokacin da za a yi tafiyar" Sultan ya yi ajiyar zuciya cike da gamsuwa, ya miƙe tsaye ya ce "Mu je na gan shi" Su ka miƙe gaba ɗaya, Likitan yana gaba su na biye da shi a baya. Cikin sauri suka ƙarasa gaban gadon. Idanunsa a rufe yana bacci. Sultan ya ƙarasa gaban gadon, fuskarsa ɗauke da damuwa. Ya din ga dudduba jikinsa, tamkar yana son gano wani abin. Ya kalli Likitan ya ce "Kun tabattar a jikinsa babu wani abu na illa ko cutarwa a tattare da shi?" "Babu ranka ya daɗe, lafiya kalau yake, ba a yi masa komai ba, sai wannan matsalar ta ƙwaƙwalwarsa. Ba na tunanin an tafi da shi Nigeria ne dan a cutar da shi, akwai dai wani abu... "Ya isa ba kai ke hurumin zartar da wannan hukuncin ba, sai abin da bincike ya tabattar" Babu shiri likitan ya ja bakinsa ya tsuke. Sultan ya ɗago hannun Imam na hagu, ya kalli yatsunsa ya ga yatsunsa biyu sanye da zobuna, ya ɗago hannun damansa, ya ga babu azurfa ɗaya sai ɗaya. Cikin tashin hankali ya ce "Abduou. Babu zoben Imam guda ɗaya" Cikin sauri Abdou ya ce "Wanne daga ciki?" Ya ɗago wa Abdou hannun Imam. A rikice Abduou ya kama hannunsa ya duba, ya kalli Sultan ya ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ka ga abin da nake gaya maka ko? Kai ne ka ke ƙoƙarin kare yaron can, ka ke cewa a bi shi a sannu ba ka tunanin zai iya cutar da shi, to ga shi nan ai ga irinta nan, tabbas ya san inda zoben nan yake, dole a matsa shi a fito da shi. Dalilin da ya sanya su ka sace shi kenan ma, su ka bar ƙasar nan da shi, su ka kai Nigeria. Zoben suke so su sace" Sultan ya dafe kansa, ya rasa abin da yake yi masa daɗi. "Sultan wannan ma wani sabon sirri ne, da yake buƙatar duk tsanani a rufa shi, a ci gaba da addu'a, amma dole a nemo zoben nan, idan ba haka ba zai fita daga sahun Imams" Sultan ya sauke wata irin nannauyar ajiyar zuciya yana kallon yadda yake bacci a kan gadon. **** Sai da Nana ta shafe kwanaki huɗu a gidan Hajara, ba a samu inda za ta zauna ba. Nana ma abin daya dame ta, sai ɗawaniya suke faman yi da ita, ga shi tana tsoron kar su ƙosa da ita, dan babu mai jurewa yau da kullum sai Ubangijin da ya halicci bawa. Ranar kwana na huɗu da yamma mai gidan ya dawo, Hajara ta kira Nana. Bayan sun sake gaisawa ya ce "Malama Nana, wallahi ba a samu gida ba, sai dai ina tafe a hanya wata shawara ta faɗo mini. Akwai wata 'yar uwar Babana a can wata unguwa, itakaɗai take zaune a gidanta, kuma akwai ɗakuna a gida, kuma ba mazauniya ba ce, tana fita sana'iinta. Sai dai fa mace mafaɗaciya, tana da yawan faɗa, ba wuya ta hasala. Ban sani ba ko za ki iya zama da ita?" Cikin farin ciki Nana ta ce "Zan iya zama da ita, in dai ta amince" "A'a dai ki yi tunani, mafaɗaciya ce sosai, idan kin amince zan tafi na je na same ta a daren nan, na yi mata bayani" Nana ta ce "Wallahi kar ka damu, zan iya zama da ita" Ya ce "To Allah ya sa, zan ne yi mata magana, idan ya so ko kuɗin hayar ne ita sai a bata" Nana ta yi ta masa godiya tana murna. Har Nana ta yi bacci bai dawo ba, sai washegari da safe, bayan ta karya,  Hajara ta cewa Nana ta shirya, za su tafi can gidan matar. Nana ta yi wanka ta shirya, suka fita suka hau abin hawa. Hajara ta ce "Nana kamar kar ki tafi, kwana biyun nan har na saba da ke" Nana ta yi murmushi ta ce "Nima haka, sai dai har Abada ba zan taɓa daina yi muku godiya da fatan Alkhairi, ba dan ba ƙaramin jihadi ku ka yi ba, ne ceton rayuwata" "Ba komai, mu ma bamu san ta inda Allah zai taimake mu ba". Sun yi tafiya mai ɗan nisa, kafin su je unguwar da matar take. Mijin Hajara ya sallami mai abin hawan, ya ɗauki kayan Nana su ka shiga layin gidan. A tsakar gida suka tarar da matar, ta cake ɗauri tana ta lissafin kuɗi. Ta amsa musu sallamar tana yi musu maraba. Suka shiga ɗaya daga cikin ɗakunanta. Ta kawo musu ruwa da lemo ta ajiye. Cikin girmamawa Nana ta gaida matar. Ta kalli mijin Hajara ta ce "Wannan ce yarinyar?" Ya ce "Eh Nene" "To a haka dai ta yi zubin nutsuwa, dan dai ka matsa ne, amma ni ba na son yayime-yayime na je na ɗaukko wadda za ta hana ni sukuni, shi yasa duk girman gidan nake zamana nikaɗai abina. Sannan zan fara zama da ita na wata ɗaya, idan ba ta da matsala mu ci gaba da zama, idan akwai matsala na mayar mata da kuɗinta ta tashi ta bani guri. Kuma wallahi dan ma dai kai ne, da ba zan yadda ba". Nana cikin girmamawa ta ce "In sha Allah ba za ki same ni da matsala ba, in Allah ya yarda". Nene ta ce "To Allah ya sa, bari na buɗe ɗaya daga cikin ɗakunan ta zaɓa" Mijin Hajara ya ce "Ɗakunan a rufe, ai na san sun sha ƙura yanzu, ki yi haƙuri tun da akwai gyararru ki kwashe kayanki daga ɗaya ki ba ta. Kin ga ɗakin da ba komai, sai an nemi labule, da sauran abubuwa". Haka ya takure Nene, ta bawa ɗaki ɗaya, mai ɗauke da labulaye da carfet. Nana ta din ga godiya, ta ce  "Saura kuɗin hayar, nawa ne zan biya?" "Ai na biya ta, ba wani abu in sha Allah, ki zauna kawai" Nana ta ce "Ai da kuɗi a gurina" Hajara ta ce "Kar ki damu, ba wani abu ya biya, idan akwai wata matsala ko ba za ki iya zama ba, ki ce Nene ta kira mu a waya, in sha Allah babu wani abu" Nana sai da ta yi hawayen murna, ta raka su har waje sannan ta dawo. Ta tarar da Nene ta fito da wake fal za ta tsince. Nana ta lallaɓa ta zauna a kan tabarmar ta ce "Kawo na tsince miki" Nene ta ce "A'a ke da ki ke baƙuwa, yi zaman ki ki huta, kan Auwwalu ya dawo ya ce ina azabtar da ke, tun da ya ce ni masifaffiya ce". Ita Nana har ta gama zaman gidan ma, ba ta san sunansa ba. Ta yi murmushi ta ce "A'a ba komai, dan Allah ki bani na taya ki, ai na ga waken da yawa, kuma daga zaune zan taya ki" Ta dawo da robar waken tsakiyar su, ta kalli Nana ta ce "Nana ko?" Nana ta jinjina kai ta ce "Eh" "Ciki ne da ke haka ne?" Nana ta sunkuyar da kai tana tsince wake. "Ke kuwa me ya yi miki zafi, ki ka baro ƙasar ku da wannan tsohon ciki ki ka taho inda ba ki da kowa? Amma fa ki yi haƙuri da tambayoyina, kin san yanzu duniya babu gaskiya sosai" Nana ta ce "Haka ne. Mijina ɗan ƙasar nan ne, nice 'yar Nigeria. Na zo neman danginsa ne a nan" "Allah sarki, to a ina dangin nasa suke? Kuma shi yana ina" Nana ba ta son yayata halin da take ciki, ta fi son sai ta nutsu, ta ga kamun ludayin mutanen ƙasar tukuna, kafin ta saki jiki, amma ga Nene ta saka ta a gaba da tambayoyi. Kafin ta ba ta amsa, Allah ya taimake ta, aka kira Nene a waya, hakan ya sanya ba su ci gaba da zancen ba. **** Cikin tsananin tausayawa, yake bin matashin da kallo, saboda yadda duk ya fita daga hayyacinsa. Cikin damuwa ya kira sunansa a hankali ya ce "Mahmudu" ya ɗago idanunsa a galabaice, ya kalli wanda ya kira sunan nasa. "Ka yi musu bayanin duk abin da ya faru, ka faɗa musu iya gaskiyarka, ko Allah ya sanya su rabu da kai, wannan wahalar da ka ke yi ta isa haka?" Murya a cunkushe ya ce "Me zan gaya musu? Me zan ce da ka ke tunanin idan na faɗa za su yarda da ni?" "Iya abin da ka sani ɗin zaka faɗa" "A tunaninka tsawon wannan lokacin, ba iya abin da na sani ɗin ba nake gaya musu? Sai dai akwai abin da ko za a kashe ni, ba zan furta ba" "A'a Mahmudu, idan har za ka ci gaba da shiru da ɓoye wasu abubuwan, ba fa za a ƙyale ka ba, za su ci gaba da azabtar da kai ne kawai a banza. Ni dai zan faɗi abin da na sani" Mahmudu ya ce "Ka kwana da sanin, ka na furta wani abu, to tabbas kai ma za ka tsinci kanka, a halin da nake ciki yanzu. Ka yi shiru mu bar komai a yadda yake. Rufe sirrin Imam wajibi ne, akwai abin da idan na furta, zai iya janyo asarar rayuka ba ɗaya ba ba biyu ba, in dai wahala ce na san ɗayan biyu ne, ko na mutu ko ta wuce. Abu ɗaya nake so da kai, shi ne; dan Allah Ashiru, ka binciko a wani hali yake ciki? Tun da muka baro Nigeria, ba a haɗa mu a mota ɗaya ba ma, ban san ina aka yi da shi ba" Ashiru ya ce "Kai wannan fa babban aiki ne, tun ɓatansa fa, ba a bari labarin ma ya fita ba, balle a sanya ran jin halin da ake ciki yanzu, amma dai zai ɗan ƙyanƙyasa a ɓoye, na ga ko za a samu wani bayani. Sannan ina ƙara neman afuwarka a kan abin da ya faru" "Babu komai kar ka damu, an saki sauran ko? Su Sulei" "Eh an sake su, ai tun da suka fuskanci, ba su ma san a kan me ake binciken ba, an sake su amma fa an killace su" "Shikenan tashi ka je, kar a fahimci wani abu" Haka Ashiru ya tashi ya tafi yana waiwayen sa. ***** Sannu a hankali take tafiya, yana zaune a cikin mota yana hangen ta, ta tsallako titi, ta nufo motarsa tana murmushi. Ta buɗe motar ta shiga ta ce "Yaya Abba me ka ke jira a titin ne haka?" Ya lumshe idanunsa, jin yadda ƙamshin turaren jikinta, ya gauraye motar baki ɗaya. Ya ce "Wa zan jira ban da ƙanwata, kwana biyu ban gan ki ba, da gida zan bi ki ma, to sai na ji tsoron kar na je ko ki na da baƙo, ban sanar da ke zan zo ba. Kawai na tsaya a nan na ce bari na jira fitowar ki" Ta yi murmushi ta ce "Ko akwai baƙo, ba dolena na sallame shi na saurari yayana ba, kuma wani baƙi zan yi da safe haka?. To me ma zan samu ne?" Ta yi maganar tana laluba motar. Ya yi dariya ya ce "Laluba ki ɗauki duk abin da ki ke so" ta yi dariya ta ce "Dan ka san ba ka ajiye komai ba ko? Mu je kar Mummy ta yi ta jira na" Ya ce "Ok" ya fara tuƙa motar a hankali. Yana tuƙi yana satar kallon Jamila, wani irin kyau take ƙarawa a idanunsa kullum. Kullum ƙara shiga ransa take yi, ga shi ya kasa fitowa ya sanar mata da ainihin abin da yake cikin zuciyarsa. Duk wasu alamu da zai nuna mata sonta yake yi, ya yi amma ya kasa gaya mata baki da baki. Su na daf da shiga layin gidan ya tsaya ya ce "Ƙanwata" "Na'am Yaya Abba" "Ina son za mu yi wata magana da ke, amma maybe sai na dawo tukuna" Ta yi murmushi tare da gyara zaman mayafinta, ta ce "To shikenan babu laifi, a dawo lafiya" "Allah ya sa, ki kula mini da kan ki Please, zan kira ki idan na je kasuwa" Ta ce "To, ka sayo mini aya mai sukari a kasuwa" Yayi dariya ya ce "Aya kawai?" "Eh ita kawai" "To an gama ranki ya daɗe" ta fita daga motar tana ɗaga masa hannu" Da ta shiga cikin gida,ba ta tarar da Hajiya Sa'a a falo na, dan haka ta bi ta bedroom. Ta tarar tana wanka, ta nemi guri ta zauna tana danna wayarta. Can Hajiya Sa'a ta fito daga ita sai towel. Jamila ta kalle ta ta kawar da kai. "Jamila har na fitar da ran za ki zo ai" "Ba na jin daɗi ne, shi yasa da kamar ma ba zan zo ba fa" "Eyya sannu, bari na shirya ki raka ni mu je na duba Fatuhu" Jamila ta ce "Tom" Hajiya Sa'a ta zauna a kusa da Jamila, ta ɗan riƙo hannunta ta ce "Daughter wai ke haryanzu ba za ki waye ki faso gari ba? Ina ta saita ki a hanya kin ƙi yarda ki shiga layi" Jamila ta ɗan ɓata fuska tana zame hannunta ta ce "Gaskiya ni Mummy ba na so, ni me zan tsinta a jikin mace 'yar uwata, ni abin ma bai yi mini tsari ba sam wallahi" Ta yi murmushi ta sake matsawa kusa da Jamila ta ce "Ai da gwaji jirgin sama ma ya tashi Jamila, da za ni jarraba da kin gane abin da nake nufi. Shi ne za ki yi babu ruwanki da damuwa da aure, ko tashin hankalin yin planing saboda ɗaukar ciki. Kuma... "Ni dai gaskiya Mummy ba na so, ni me zan tsinta a jikin mace 'yar uwata, ni abin ma bai yi mini tsari ba sam wallahi" Ta yi murmushi ta sake matsawa kusa da Jamila ta ce "Ai da gwaji jirgin sama ma ya tashi Jamila, da za ni jarraba da kin gane abin da nake nufi. Shi ne za ki yi babu ruwanki da damuwa da aure, ko tashin hankalin yin planing saboda ɗaukar ciki. Kuma... "Ni dai gaskiya Mummy ba na so, ni ban ga abin da mace za ta tsinana mini ba, ni bai ma yi mini tsari ba gaba ɗaya gaskiya. Ba gara na bi maza ba" Hajiya Sa'a ta kwashe da dariya, ta ce "Yaro man kaza, ai shikenan Daughter, bari na shirya mu fita". A gaban Jamila ta gama shirinta, ba tare da jin nauyin abin da ta tunkari Jamilan da shi ba, ta gama suka fita. Umman Fadila ce take kallonta a tsanake, bayan ta gama yi mata komai za ta tafi. "Fadila" "Na'am Umma" "Na san yanzu da da ba ɗaya ba ne ba, amma ko yaya ɗan abin da ki ke da shi idan ya samu, ko abinci ko kuɗi, ki din ga bayar da sadaka, da nufin Ubangiji Allah ya kawo muku ɗauki,ya sassauta muku wannan yanayin da ku ka tsinci kan ku a ciki" Fadila ta jinjina kai ta ce "In sha Allah" "Tun kwanank da kawunki, ya zo ya duba mijinki, ya kira ni yake mitar, kun tare ku na maganin Asibiti, kun ƙi mayar da hankali ku yi na gargajiya. Na ce masa mijin naki ne ɗan aƙida, kuma ke na haifa ba shi ba, balle na yi masa dole. Amma nima hankalina ya fara karkata ga a yi na hausan, mijinki mutumin kirki ne, ba zan manta halaccinsa a gare mu ba, dan haka na bayar da kuɗi a yi saukar Alqur'ani, da fatan Ubangiji Allah ya yaye masa koma mene ne, tun da shi Alqur'ani waraka ne. Ki yawaita karanta masa, ko ki kunna ya saurara, ko ki din ga busa wa a abincinsa ko abin shan sa. Ba mu san a inda za a dace ba, wannan abu ya ƙi ci ya ƙi cinyewa, na Asibitin ba wani haske da ake gani, idan hagu ta ƙi ai sai a koma dama ko?" Fadila ta ce "Haka ne Umma, in sha Allah, zan yi duk abin da ki ka ce, kuma addu'a mu na yin ta sosai, ina yi masa. Sai dai kin san lamarin Ubangiji ba a yi masa dole, duk addu'arka sai lokacin yankewar abu ya yi tukuna". Umma ta ce "Haka ne, amma hakan ba ya nufin a sare, a ce an haƙura gaba ɗaya ba za a yi ba" Sosai Fadila take jin daɗin rarrashi da nasihar da Umma take yi mata a duk lokacin da ta zo gidan. Ko da su Hajiya Sa'a suka je gidan Alhaji Fatuhu, Alhaji Zailani yana gidan. Yana sashen Alhaji Fatuhu tare. Alhaji Zailani ya din ga kallon Jamila, yana ganin kamar ya santa, amma ya manta a inda ya san fuskarta. Suka gaisa Hajiya Sa'a ta kalli Fatuhu ta ce "Yaya ya jikin naka?" Ya jinjina kai ya ce "Alhamdillah" "Ka na samun sauƙi, ko dai haryanzu babu afuwa?" Ya yi murmushi ya ce "Da sauƙi" Daga haka suka koma hira da ita da Alhaji Zailani, tamkar ba dubiya su ka zo ba, bar sai da abin ya ba wa Jamila mamaki. Sun jima sannan su ka shiga suka gaisa da matansa suka tafi. Su na tafe a hanya Jamila ta ce "Mummy, mara lafiyar nan shi ne wanda ɗan sa ya mutu kwanaki ko? Yaran da Nana take koyarwa a makaranta" "Eh shi ne" "Allah sarki, to shi wannan Alhaji Zailanin, ko shi ne a can quaters ɗin bayan makarantar nan na ƙofar famfo?" Hajiya Sa'a ta kalle ta ta ce "Ya aka yi ki ka san shi?" "A'a na tambaya ne dai kawai, kenan shi ma Nana ta yi aiki a gidansa, yana da 'ya Shukura ko?" Hajiya Sa'a ta jinjina kai tana kallon Jamila. "To ai da Nanan gidanmu zai aura, ba a yi ba, aka yi aurenta da wannan Buzun, lokaci ɗaya kawai ya fito ya ce wai zai aure ta" Shiru Hajiya Sa'a ta yi tana kallon Jamila, ta san abu ne mawuyaci a ce haka kurum Alhaji Zailani ya ce zai auri yarinyar da ta fito daga gida kamar na su Nana, da ƙyar idan ba ya san sirrin da ke tattare da Nanan ba. A take gabanta ya faɗi, dan kuwa ko me za a yi ba za ta taɓa barin Alhaji Zailani ya riga ta amfani da jinin Nana ba" Jamila ta ce "Mummy ya na ji kin yi shiru ne?" Ta girgiza kai ta ce "Babu komai Jamila, dole mu nemo Nana ne duk inda ta shiga" Jamila ta ce "Saboda me?" "Saboda ƙungiya, za ta iya neman ki kawo jinin mafi kusanci da ke, a kowane lokaci! Ayshercool 08081012143 64 Jamila a ranta ta ce "Ni kuwa zan ga abin da ya ture wa Buzu naɗi, zan ga abin da zai faru idan na bijirewa buƙatar ƙungiyar" Jamila ta numfasa ta ce "Mummy, dan Allah tambayar ki zan yi" "Ina jin ki" "Wai dan Allah, ya aka yi ki ka shiga ƙungiyar nan?" Hajiya Sa'a ta kalli Jamila, sannan ta mayar da hankalinta kan tuƙin da take yi tana murmushi. Ta ce "Dogon labari ne Jamila, amma me yasa ki ka tambaye ni?" "Ina son na ji tarihin gwagwarmayar ki ne, ko nima zan daure na yi koyi da jarumtar ki, haryanzu wasu lokutan zuciyata tana rawa ne a kan lamarin" "Ai na ga alama kam. Jamila na sha gaya miki, muddin ki na son cimma abin da ki ke buri a rayuwa, babu ruwanki da kowa kan ki kawai za ki din ga dubawa. Na tashi a gidanmu bamu da komai, babata da babar Fatuhu, su ne ƙanana a matan gidan, kamar dai yanayin rayuwar gidanku, a haife ka, ba a damu da ɗawainiyarka ba. Manyan yayyenmu babu ruwansu da mu, saboda iyayen su mata sun cusa musu aƙidar ƙin iyayenmu. Babanmu ya mutu shi ma saboda bai bar komai ba, babu wanda ya damu da mu. Yayyenmu iyayensu kadai suke taimako da ƙannen su, mu kuma namu iyayen ke ta fafutuka da wahala. Fatuhu ya yi ta faɗi tashi da rayuwarsa, da ta mahaifiyarsa, sai dai yana tunawa da ni. Zailani tsohon saurayina ne, da rashin abin yi ya hana mu yin aure da shi. Ya shiga makaranta, bisa tallafin karatu, a can ya samo mana wannan ƙungiyar. Shi kuma lokacin Fatuhu ya fara zuwa kasuwa, ni kuma na riga na yi aure. Zailani ya gaza jan Fatuhu ƙungiya, saboda mutum ne mai tsantseni da ra'ayin riƙau. Ni kuma har a lokacin mijin da nake aure, ba shi da komai ba na samun irin rayuwar da nake so. Sannu a hankali na ci gaba da hulɗa da Zailani ya kai ni ƙungiya, ya zamana ba na rasa kuɗin kashewa dai. Fatuhu kuma ya ja Zailani kasuwa, suke kasuwanci tare, sai dai duk da tasirn ƙungiya, Zailani ya kasa tara abin da Fatuhu yake da shi. Kin san waye mutum na farko da na fara bayarwa?" Jamila ta girgiza kai alamar a'a. "Babban yayanmu, da iyayensu su ka mayar da mu saniyar ware a gida" Jamila ta jinjina kai a ɗan tsorace ta ce "Sai kuma ki ka ba da wa?" Hajiya Sa'a ta yi murmushi ta ce "Zan ƙarasa miki nan gaba kaɗan, yanzu bari mu ƙarasa gida, akwai abin da nake son yi" Jamila ta jinjina kai tana satar kallon Hajiya Sa'a. Hajiya Sa'a ta ajiye Jamila, sannan ta ja motar ta tafi. Tana tafe ta kira layin Alhaji Zailani. Sai da ta kusa katsewa, sannan ya ɗaga tare da yin sallama. Ta ce "Ai na zata ba ka ɗaga ba ne" Ya ce "A'a ina tuƙi ne? Lafiya?" "Ƙalau, tambayarka abu zan yi" Ya ce "Ok, ina jin ki" "Ashe kwanaki da aure zaka yi?" Ya ce "Yaushe?" "Kwanakin baya mana, za ka auri wata yarinya Nana" Kamar tana gabansa ya tsuke fuska ya ce "Waye ya gaya miki" "A'a ba sai ka ji wanda ya gaya mini ba, zancen Duniya ba ya ɓuya ai, sai dai ka sani na san da abin da ka ke nema, ni ma shi nake farauta" "Sa'a ban fahimci abin da ki ke nufi ba fa, ki yi mini bayani gwari-gwari " "Za ka fahimta ne, ka je ka nutsu ka yi nazari" ta kashe wayar ta ajiye ta ci gaba da tuƙinta. ***** Yana zaune a takure a gurin, ya yi shiru tamkar mai jiran tsammannin wani abun, aka buɗe ƙofar ɗakin da yake . Wasu tiƙa-tiƙan murɗaɗɗun maza suka shigo. Ba su yi wata-wata ba, suka yi sama da shi, suka fito da shi daga gurin da yake zaune. Wani ɗakin aka sake kai shi, sai dai yana shiga ya yi turus, ganin mutumin da yake zaune a cikin ɗakin. Ƙartin suka juya suka fice, suka bar shi daga shi sai mutum biyu a ɗakin. "Bismillah ka zauna mana" cike da tsoro ya ƙarasa ya zauna yana rarraba ido, ya sunkuyar da kansa. "Mahmudu, ɗagowa za ka yi ka kalle ni ai" Ya ɗaga kai ya saci kallon mutumin, ya mayar da kansa ya sunkuyar. "Na san wannan zaman takurar ya ishe ka zuwa yanzu, kasancewarka mutum da ya saba da 'yanci a baya. Ina son ka buɗe kunne ka saurare ni da kyau, tambayoyi nake son na yi maka, muddin ka gaya mini gaskiya ka bani amsa, zaka iya samun sassauci, ko ma na yi umarnin a sake ka, ka yi tafiyarka gaba ɗaya" Ya jinjina kai ba tare da ya ɗago ba. Mutumin ya sauke rawnain fuskarsa ya ce "Na san an yi maka wannan tambayoyin an kum a baya, yanzu ma zan sake jaddada maka su, me yasa ka sace Imam ka kai shi Nigeria, da ka kai shi kuma me ka yi masa?" Kamar ba zai yi magana ba, sai kuma ya girgiza kai ya ce "Ban sace shi ba, kuma ban yi masa komai na cutarwa a Nigeria ba" "To me yasa ka tafi da shi Nigeria ba ka sanar da kowa ba?" Mahmudu ya ce "Wannan wani sirri ne da ba zan iya tona shi ba, ko da za ku salwantar da rayuwata, wani abu wanda daga ni sai shi Imam" Abduou ya jinjina kai ya ce "Da amincewar sa ku ka tafi Nigeria kenan?" "A'a hasalima bai san komai ba, ba wani da zaɓi ne da ya rage, sai abin da na aikata ɗin" "Mahmudu, na fuskanci zama da maɗaukin kanwa ya sanya maka farin kai. Rayuwa da Imam ya sanya ka koyi baƙin taurin kai irin nasa. Amma ka snai, kama da wane ba ta wane, kuma  ina fatan ka san da tun da aka ɗaukko shi daga Nigeria har yau ba ya hayyacinsa, bai yi magana da kowa ba?" Mahmudu ya girgiza kai ya ce "A'a ranka ya daɗe. Rashin gane kowansa ba shi da nasaba da zuwansa Nigeria" "Saboda me?" "A can ɗin ma ba gane kowan yake yi ba" Abduou ya ɗan yi shiru sannan ya ce "Zoben Azurfarsa fa guda ɗaya da baya hannunsa, ina fatan ka san inda wannan yake?" A zabure Mahmudu ya kalli Abdou matawalle, jin abin da ya faɗa. "Ka daina zaro mini ido, kwanaki biyu kawai ka ke da su, ka faɗi inda zoben yake, ko kuma ka rasa rayuwar ka baki ɗaya, zaɓi ya rage naka" Abdou ya miƙe, ya ja rawaninsa ya rufe fuskarsa ya fice daga ɗakin. Cikin matsanancin tashin hankali, ya bi bayan matawalle da kallo. A Nigeria babu wanda ya san ma'anar zobunan da suke hannun Imam. Kuma ya yi iya ƙoƙarinsa gurin ba shi dukkanin kariya, balle ya ce wani ya san muhimmancin su ne ya karɓa. Matuƙa ya ji yana son ya ga Imam, ya gana da shi, sai dai ya san ko mai zai yi babu mai ba shi wannan damar. Ga shi ya ji Abdou ya ce tun da aka dawo da shi, bai farfaɗo ba balle ya yi magana. Gefe guda kuma yana jin tsoron kar a koma a Nigeria a bibiyi Nana, saboda za ta shiga matsala ba kaɗan ba. Koma a wani hali take ciki yanzu? Ya tambayi kansa yana jin wata irin damuwa ta mamaye zuciyarsa, tare da ɗora wa kansa laifi amincewa da auren Imam da Nana, ya kuma ɓoye mata komai a kan Imam ɗin. Ya dafe kansa da yake jin tamkar zai tarwatse dan damuwa. **** Nana ta nutsu da zaman gidan Nene, duk Nenen akwai faɗa kamar yadda Hajara da mijinta suka din ga faɗa, amma sam hakan bai damu Nana ba, dan ba ta yi mata abin da za ta yi faɗan. Nana ta fuskanci Nene sana'ar Abinci take yi, wasu lokutan tun safe idan ta fita sai daf da magariba take dawowa. Ta kan dawo tar e da yaran da suke yi mata aiki, su fara rage aikin Abincin sayarwar da za a yi washegari. Nana tana jin yadda Nene take yi musu bala'i bisa kuskure kaɗan. Nene ta din ga gwada Nana, da ajiye kuɗi ko ina ta ga dama, ko ma ta fita ta bar ɗakunanta a buɗe, amma ko allura ba ta taɓa rasawa ba. Kullum sai ta ba wa Nana Abinci, na safe kan su fita na sayarwa ta ba ta na rana, idan sun dawo ta ba ta na dare, har da ma tsaraba ta masu ciki. Ma'aikatan Nene sun ɗauka ma, Nana 'yar uwatta ce. Idan sun dawo Nana kan fito ta ce za ta taya su aiki, Nene ta yi ta faɗa ta ce ba za ta yi ba. Sai dai hakan ba ya hana Nana kama musu wasu ayyukan. Nana ta shafe kusan wata guda a gidan Nene, ta ga kullum sai Nene ta ba ta Abincin nan sau uku, ba ta taɓa nuna mata ta gaji da ciyar da ita da take yi ba, wasu lokutan har tambayarta take yi, ko tana son cin wani abin ne daban. Da daddare ta kira Nana, Nana ta fito ta zauna a kusa da ita. Ta buɗe takarda fal kifi ta ce "Nana ga kifi ko za ki iya ci, idan ƙarnin ba zai dame ki ba". Nana ta dube ta ta ce "Nene, dama ina son mu yi magana ne" Nene ta ce "To ina jin ki" "Na ga kullum sai kin bani Abinci sau uku a rana, na ce ko za ki ba ni wani aikin na din ga yi miki, a maimakon Abincin da ki ke ba ni, ko gurin sayar da Abincin sai na din ga bin ki, ko wanke-wanke na din ga yi miki" Ta dubi Nana, sannan ta numfasa ta ce "Ni kuwa duk rashin imanina, da wannan tsohon cikin sai na saka ki aiki, dan dai abin da za ki ci sau uku ba zai gagara ba. Ban san takamaiman abin da ya kawo ki ƙasar nan ba, ban san kuma lokacin komawar ki ba, amma ba na tunanin abin da za mu ci ni da ke zai gagare ni. Ba zan ɓoye miki da fari ban so zamana da ke a gidan nan ba, saboda ba na son matsi da takura ko kaɗan, da su Auwwalu sun matsa ne, dan kora da hali na so yi miki. Amma yanayin ki ya nuna mini ki na ɗauke da damuwa mai nauyi a zuciyarki. Ba ƙaramin dalili ne zai sanya yarinyar mace, mai ƙanan shekaru kamar ki, ta baro gida ta taho uwa Duniya ba ga juna biyu. Kuma ki na yawan zama ki yi shiru, fuskar ki ɗauke da damuwa. Na kuma jarraba ki ta ɓangarori da dama, ban ga alamar rashin nutsuwa a tare da ke ba, shi yasa na ji zan iya zama da ke. Amma Nana tsakaninki da Allah wannan juna biyun na ki, na halal ne? Kuma da sanin iyayenki ki ka taho nan?" Tambayar Nene ta yi wa Nana mugun zafi a ƙirjinta, amma sam ba ta ji haushinta ba, dan kowaye dole ya yi irin wannan tambayar. Sai da ta ji hawaye ya cika mata ido, da tuna ire-iren waɗannan tambayoyin dole ta ci gaba da amsa su, a cikinta da abin da za ta haifa, muddin ba gano inda Sayyid yake ta yi ba. Ta haɗiye wani irin yawu mai zafi ta ce "Nene cikina na halal ne, ni matar aure ce, ban kuma gaya wa iyayena zan taho nan ba, sai da na riga na yo nisa da gida" "To saboda me, kuma ina mijinki?" Kawai Nana ta fashe da kuka, ta ce "Shi na fito nema, mijina da danginsa" Nene ta ce "Shikenan, ya isa haka ki kwantar da hankalinki, mu bar maganar ma yi wani lokacin. Amma sai dai ki yi haƙuri, dan dole sai mun ƙarasa wannan maganar Nana, saboda ni uwa ce, dole na mu'amalance ki na yi miki nuni da abin dai-dai da akasin haka. Ban ga alamar ki na magana da wani a can gida ba, ko ta tarhon hannunki ce ba. Mahaifiyarki tana raye?" Nana ta jinjina kai tana share hawayenta. Nene ta ce "Shikenan, share hawayenki mu ci kifin" Ta girgiza kai ta ce "Ƙarnin hawa kaina yake yi na ƙoshi" daga haka Nana ta tashi, ta koma ɗakinta. Sai dai ta din ga kuka, saboda ita kanta ba ta san ta ina al'amuran za su warware ta cimma abin da ta fito nema ba. Shukura ta rasa gane kanta da kanta, saboda rashin lafiya da take ta fama, ga Sagir ya rage ba ta kulawa, duk da yana ta ɓoye-ɓoye amma tuni ta daɗe da gano shi, sai dai ta maze ita ma ba ta nuna masa ba. Hajiya Amina ce ta je gidan, Shukura ta ji daɗin zuwanta sosai da sosai, a nan Hajiyar take gaya mata batun Nana. Cikin damuwa Shukura ta ce "Wallahi Mami, tun da aka yi auren nan, nake jin tausayinta, gaba ɗaya ban ga riba a abin da babanta ya yi mata ba. Babu bincike babu komai a ce an aura mata mutum, wasu lokutan na kan rasa ina tunanin mutanenmu yake tafiya" "Ke dai a yi sha'ani kawai, amma na jinjina batun ni kaina" "Shikenan an saka rayuwarta a gagari, ga ƙarancin shekaru" suka ci gaba da jajanta lamarin. Hajiya ta fuskanci yanayin Shukura kamar ba ta da cikakkiyar lafiya, ta kira Doctor Sharif ya zo ya duba ta. Shukura ba ta so ba sam, dan ko ƙaunar ganin Sharif ɗin ba ta yi, amma tuna ta yi wa Hajiya Alƙawarin komai ya wuce, ta yi tawakalli ta dangana ya sanya ta haƙura. Ya zo har gida ya yi mata gwaje-gwaje, ya kuma tabattar mata da tana da juna biyu. Hajiya Amina ta din ga murna, a duk lokacin da aka ce ga wata mace da ciki, sai ta yi ta murna, ta ji dama ita ce. Shukura ba ta wani yi murna ba, saboda ita gaba ɗaya haihuwar ma ta fita daga kanta. Da yamma Hajiya Amina ta koma gida, saboda tsabar zumuɗi, tana zuwa ta tarar da Alhaji Zailani a gida, ta hau ba shi labarin Shukura wani cikin ne da ita. Wata irin mummunar faɗuwar gaba ce ta ziyarce shi, yana tsoron a wannan karon ma, kar a nemi ya bayar da wani abu da ya danganci iyalinsa. Hajiya Amina ta din ga jin wani irin bacci, tana idar da sallar isha'i, ta ɓungire a gurin ta hau bacci. Ita da Nana ta gani a falo, a zaune suna hira, kamar yadda suka taɓa yi kwanaki lokacin Nanan, na zuwa gidan rainon Haidar. Ta ce "Hajiya, kin kuwa ci gaba da bibiyar Likitoci a kan matsalar rashin haihuwar ki?" Hajiya Amina ta ce "Nana ai ni na haƙura ma na bar wa Allah, yanzu shekaruna sun wuce na haihuwa" Nana ta ce "A gurinki ba, a gurin Allah yana bayar da falalarsa a inda ya so, da kuma lokacin da ya so ne. Ki daina biye wa wannan mijin naki, ya din ga sarrafa rayuwar ki yadda yake so. Ki nemi mafita a kan matsalolinki. Kuma Shukura ta dage da Addu'a, kar wannan ɗan ma ya sake raba ta da shi" Maganar Alhaji Zailani ce ta tashi Hajiya Amina daga mafarkin da take yi, tana kallonsa kawai ta ji gabanta ya faɗi" "Lafiya ki ke kwance a ƙasa haka ki ke bacci?" Ta ce "Bacci ne ya ɗan ɗauke ni ban sani ba" Ya ce "To ki tashi ki koma gado mana, kar wuyanki ya yi ciwo" Ta yinƙura ta tashi ta canza kaya ta hau gado ta kwanta, sai dai ta din ga jin mafarkin da ta yi da Nana a jikinta, tamkar a zahiri ya faru. Fadila ce zaune a kusa da Alhaji Fatuhu, gefenta kuma jaririnta ya yi wayo, yana ta bacci. Ta miƙa masa lemon da ta haɗa masa a kofi, ta zuba masa ido, yana sha a hankali. A ranta take faɗin "Ubangiji Allah ka bawa wannan bawa naka lafiya, albarkacin ayoyin Alkur'ani' Ta kalle shi tsaf, ya yi rama ta ban mamaki, dan ma yanzu ya ɗan ciko, ba kamar da ba" ya shanye ya miƙa mata kofin, ta karɓa ta ajiye a gefe. Ta matsa kusa da shi tana ɗan ƙara gyara masa filulluka. Ya ce "Na gode sosai, Allah ya yi miki albarka, ya raya miki Muhsin" Ta ce "Amin Daddy" "Da lafiyata ƙalau, da mun yi sauri, nan da wata wata taran, ki kuma haifo mana wani" Murmushi ta yi ta ce "Allah ya baka lafiya ya tashi kafaɗunka" ya amsa da Amin yana riƙe hannunta cikin nasa da ya yamuste kamar na tsoho. Hajiya Suwaiba ta ce ta shigo ɗakin, Fadila ta ɗan zabura ta ja da baya. Hajiyar ta ja tsaki ta ce "A hakan ma da kake wani abin ka ke ƙoƙarin yi, ai sai ku rufe ƙofa kar yara su faɗo, a lalata mini tarbiyyar yara" Fadila ta ce "Haba Hajiya, abu na ba shi ya riƙe hannuna, and laifi ne dan ya riƙe hannuna wani abin ki ka ga na yi?" "Kar ki yi mini rashin kunya dai? Idan ma yin ku ke, ku ƙarata ku da Allah" Ran Fadila ya yi mummunan ɓaci, ta yinƙura da niyyar, ta ɗauki ɗan ta ta bar ɗakin, amma ya riƙe hannunta, ya hana ta tafiya. Hajiya Suwaiba ta gama bala'inta ta tafi ta bar su. Idan ya ce Suwaiba ba ta ƙoƙari a kan rashin lafiyarsa ya yi ƙarya, tana iyakar ƙoƙarinta amma wasu lokutan tana da saurin ƙosawa gashi haryanzu azababben kishi na ɗawainiya da ita. **** Gidan Maijidda kuwa, Iliyasu bai taɓa tsammanin,    Maijidda na da taurin kai haka ba. Gaba ɗaya ta tarkata shi ta yi watsi da shi. Iyakarta da shi, ta girka Abinci ta ba shi, idan buƙatarsa ta tashi, ya yi kiɗansa ya yi rawarsa. Gaba ɗaya ta sanya damuwa a ranta, ta rame sosai da sosai, dan ko Abincin kirki ba ta iya ci, kusan kullum cikin kuka take, ko ta zauna ta yi shiru. Ga shi ya lura 'yan uwanta sun fara gajiya da sinturin kai ƙararta da yake yi, ba yau ba gobe. "Anya ka na ganin haka rayuwar Imam za ta ci gaba, duk lokacin da ya farka sai ihu da fizge-fizge, sai dai a yi ta yi masa allurar da zai yi bacci? Idan aka bar shi a haka rayuwarsa fa ta nakasa kenan har abada" Sultan ya ce "Abdou, ni kaina ala'amarin nan yana damuna, na rasa yadda zan yi. A ɓangaren ƙwaƙwalwar ma, babu wani gamsashshen bayanin abin da ya faru da shi. Ta ɓangarenka ma babu wani nagartaccen bayani daga bakin shi yaron, balle mu ji ko wani abin ɗin aka yi masa". "Sultan, ka ƙi bayar da dama a sanya 'yan doka, su maguza yaron nan, ya faɗi gaskiya ko ya ƙi Allah" Sultan ya girgiza kai ya ce "A'a, duk ranar da Imam ya samu lafiya, muddin ya ji labarin an cuzguna masa, zai yi fushi, kuma zai ji babu daɗi kai ka san irin alaƙar da take a tsakaninsu." "Amma yanzu ai yanzu a kan gaɓar bincike a ke Sultan. Amma tun da haka ka ce Shikenan, za a ci gaba da bin komai sannu a hankali" Sultan ya amsa da "Yauwwa" BAYAN WATA ƊAYA Sabo turken wawa, rashin ganin Ƙaisar da Nana ta daina yi, ya sanya ta din ga tunanin ko wani abin ne ya faru da shi. Sai dai yau kwatsam cikin barcinta, ta ganta a cikin Librarynsa. Sai dai ta gurin ƙwalam babu litatafai babu kayan rubutunsa sai mudubin da yake nuna mata abubuwa a cikinsa. Ta waiwaya ta lelleƙa, amma babu Ƙaisar babu alamunsa. Wani littafi guda ɗaya tal, ta hango a kan teburin rubutun Ƙaisar, ta ƙarasa ta nufi teburin ta ɗauki littafin. Bangon littafin na fatar wata dabba ne. Dan har da gashi-gashi a jiki. Yanayin bangon littafin ya sanya ta yi tunanin, ko mene ne a rubuce a littafin ba yanzu ya faru ba, ya kwana biyu da faruwa. Littafin ba wanda ta karanta tarihin su Lanti ne a ciki ba, wani ne daban. Hoton wata alƙarya ce, da ke tsakanin duwatsu, da aka rarake aka samar da katafariyar daula. Ta buɗe littafin shafin farko, ta fara karantawa. "Tushiya..." Shi ne abin da ke rubuce a shafin farko na littafin. "Ka sani,har abada da ɗan Gari a kan ci gari. Kuma ba a cimma buri da tausayi ko jin ƙai. Wannan mataki na farko kawai ka cimma, na sharar fagen cimma nasararka. Ka na buƙatar sanya wa mutane tsoronka, da shakkarka domin cimma burinka, kuma hakan ba zai taɓa yiwuwa ba sai ka zubar da jini, duk wanda ya biyo ta hanyarka ka datse rayuwarsa, kar ka damu da adadin rayukan da za a rasa, ka zubar da jini ba ƙaƙƙautawa har sai mutane sun fara jin fitsari a duk lokacin da aka ambaci sunanka. Ka kame mutanen gefen alƙaryar nan, ka mayar da su bayi, matansu ka mayar da su naka, mazansu su zama bayinka, ka yi amfani da ƙarfinsu da fikirarsu ka gina alƙaryar da babu wani mahaluki da zai iya ɗaga maka yatsa, kar ka gushe kana aikata hakan, har sai buƙata ta biya. Zaka kasance cikin sanyawar albarkar Aljanu, za su baka dukkanin goyon bayan da ka ke buƙata kar ka saurarwa kowa" Cikin damuwa mutumin ya kalli mai maganar ya ce "Ka sanya ni na kashe mahaifina da hannuna, yanzu ga wani abin ka sake zuwar mini da shi, kar ka manta ina da 'yan uwa maza, ba za su zuba mini ido, duk na yi wannan ba, na ɗauki abin da ba nawa ba, alhalin su na gaba da ni ba" Ji ta yi mudubin gurin yana wata irin ƙara tamkar zai tsage, a take ta ajiye littafin ta nufi mudubin tana kallonsa. Wata irin wuta ta gani tana ci a cikin mudubin. Wutar mai matuƙar ban tsoro saboda yadda take ci. Wani mashi ta gani a soke a jikin wani ƙwarangwal, ɗaya gefen mashin an yi rubutu a jikin wani abu mai kama da takarda. Ta ƙara matsawa domin karanta mene ne a jikin takardar amma ta ga mudubin yana hayaƙi yana baƙi yana washewa. A kusa da wutar ta ga wani abu mai kama da mutum, a lulluɓe da wani mayafi yana zuba wani abu a cikin wutar wanda yake ƙara sanya wutar ƙara balbala. Imam... ta iya gani a rubuce a jikin abin, mai kama da takarda, a gaban Imam ɗin akwai wani sunan, sai dai ba ta iya karanta sunan ba. A jikin wutar ta ga taswirar fuskar Sayyid yana jijjiga jikinsa na ƙonewa yana kururuwa yana kiran sunanta. Wata irin zabura ta yi ta kuma tunkarar mudubin gadan-gadan, mudubin ya yi wata irin tsawa ta ja da baya ta faɗi ƙasa. A gigice Nana ta farka, ta haɗa uban gumi ta yi sharkaf, ga wata irin ƙullewa da cikinta ya yi haɗi da mararta. Ta yinƙura da ƙyar ta tashi ta tafi banɗaki, a zatonta fitsari take ji, ko kuma bayan gida, amma ta ji ba bayan gida take ji ba, ta fitsarin amma still mararta kamar an saka wani abu an ɗaure mata. Ta yi alawala ta koma ɗakinta. A zaune take salla saboda yanayin girma da nauyin da cikin ya yi. Ta kasa tuna abin da ta gani, sai iya wutar nan da wannan tsawar da mudubin ya yi su kawai take iya tunawa. "Allahumma ajirni mina narr" Ta maimaita da tuno yadda ta ga wutar nan. Ta ji sam mafarkin nan bai yi mata daɗi ba, ko mene ne babu Alkhairi a tattare da shi sam. Sai da gari ya waye, sannan ta samu afuwa daga wannan ɗaurewar da mararta ta yi da bayanta. Jikinta babu daɗi, haka nan take lallaɓawa ta daure kar Nene ta fuskanci wani abu. Nana ta dama kunu da kanta, ta tashi tana tafe da kyar, Nene ta ce "Nana wai cikin nan naki wata nawa ne?" Ta ɗan yi shiru ta ce "Ina ga bakwai ne" "Anya kuwa Nana, kalli yadda ya cure guri ɗaya ya yi ƙasa sosai a ce cikin nan na watanni bakwai ne kawai? Amma ban sani ba ko biyu ne. Yakamata ma mu je Asibiti a duba ki, ni wallahi na ma manta shaf ana zuwa awo. Ko danmu lokacinmu ba awon ake yi ba oho" Nana dai ta yi murmushi kawai tana jin yadda ɗan yake ta motsi yana danno ta. Da ba rufe cikakken sati, mijin Hajara bai zo gidan ba, dama yana fargabar kar Nana ta kasa zama da Nene, saboda faɗanta, kuma cikin ikon Allah ya ga lafiya kalau suke zaune. Dan haka ya rage zuwa sosai. Tun da Nana ta je gidan, Neme ba ta barin ta ta fita, saboda ta ce mata tana da aure, kuma tana yawan gaya mata, ba a son mace mai ciki ta din ga yawo jama'a su na kallonta, saboda baki da ido. Ma'aikatan Nene duk sun saba da Nana, duk a tunaninsu 'yar uwatta ce, sai dai sukan tambayi Nana, ya aka yi hausarta ba irin tasu ba. Wasu lokutan sai Nene ta cewa Nana ta zauna a ɗaki kar ta fito, dan haka babu inda Nana ta sani a garin. Nana ta kwana huɗu, tana fama da wannan ciwon a tsaitsaye. Sai dai na yau ya fi na kullum, dan sam ba ta yi bacci ba, kuma ba ta gaya wa Nene ba. Da safe kan Nene ta fito, Nana ta yi shara ta wanke banɗaki, ta ɗora abin karin kumallo. Ta kuwa sha faɗa a gurin Nenen, sai dai ita ko a jikinta. Sun gama karyawa, Nene ta shiga ɗaki, ta ji Nana na kiran sunanta, cikin mawuyacin hali. Nene ta fito da sauri ta ce "Nana lafiya?" "Nene yoyon fitsari nake yi, ba na iya riƙe fitsari" gaban Nene ya faɗi ta ce "Kamar yaya?" "Ji na yi kawai fitsari yana bin ƙafata, kin ga" ta yi maganar tana ɗaga wa Nene doguwar rigarta, ruwa na ta bin ƙafafuwanta". "Nana wannan ai kamar naƙuda ki ke yi, anya ba ruwan mahaufa ba ne?" Duk da ƙoƙarin da ta yi, za ta yi magana, sai ta kasa saboda wani irin gigitaccen ciwo da ta ji. Har Nene ta fita suka samo abin hawa, Nana na cikin halin ciwo, ba ta iya gane komai. Nene ta ɗaukko wa Nana wasu kayan, su ka fita suka tafi Asibiti. A Asibitin ma, da aka tambayi Nana, cewa ta yi cikinta wata bakwai ne, sai dai da aka yi hoton cikin, ya nuna satin cikinta arba'in da biyu. Likitan ya yi mata tambayoyi, yaushe ta yi al'ada na ƙarshe, ta ce ita ba za ta iya ganewa ba, saboda ɓari kawai take yi a jere. Ya tabattar mata a cikin ɓarin da ta din ga yi, tun da ba Asibiti take zuwa a duba ba, akwai wanda bai fita ba ya ci gaba da girma, dan haka naƙuda take yi. Gaba ɗaya Nene ta rikice, kamar 'yar ta ce za ta haihu, sai a lokacin ta fita, ta sayo kayan jariri da ba ta san ma na wani jinsi ba ne, da ɗan abin da za a buƙata. Ma'aikata na tsaye a kan Nana, su na ƙoƙari, duk ta galabaita ma ta kasa nishin can ta ce "Ya hayyu ya ƙayyum" ta yi yinƙuri sai ga kan ɗan ya fito. Ita dai ba ta san yadda aka ƙarasa ba, ta ji kukan jariri ya cika ɗakin. Likita ta ɗago mata jaririn ta ce "Kalli me ki ka haifa?" Nana haushi ya kama ta, ta gama shan wannan uwar wahalar ga ɗan a hannunta, kuma a din ga tambayarta me ta haifa. Ta kalli yaron namiji ne, ta ga wani irin shirgegen ɗa, kamar ɗan wata biyu, sai ta hau mamakin yanzu wannan ɗan duk girmansa a jikinta ya rayu, kuma ta ɗan wannan gurin ya fito? Wata irin zabura ta yi ganin fuskar yaron, ta miƙa hannunta gaba ɗaya tana ƙoƙarin karɓe yaron daga hannun Likitar a kiɗime. Yana kan gadonsa na marasa lafiya a kwance, su ka ga ya yi wata jijjiga sai da gadon ya girgiza kamar an jona masa wani abu, kawai suka ga ya buɗe idonsa. A rikice suka kewaye shi, su na kiran sunansa, sai dai babu wanda ya amsawa sai bin su da yake da ido, kamar ya ga baƙin halittu. Sultan ya riƙo hannunsa ya ce "Imam ka gane mu kuwa?" Ya yi shiru yana bin Sultan da kallo. Abduou ya ce "Ikon Allah, ka ga wannan karon bai tashi da ihun ba, sannu Imam" Kawai ya yi shiru kamar saƙago, sai ƙwayar idonsa da yake juyawa. Ayshercool 08081012143 65 Nana kuwa da sauri wata ma'aikaciya ta mayar da ita ta kwantar, ta ce "Kar ki tashi, ai miƙo miki shi za a yi" Abin da ya razanata kuwa, bai wuce yadda ta ga fuskar Sayyid sak, a jikin ƙaton jaririn nata ba, ga sumar kansa a cike har goshinsa. Ga shi jariri amma hatta girar sa da gashi, haka jikinsa ma akwai gashi sosai. Aka ɗora mata shi a ƙirjinta, ta yi wata nannauyar ajiyar zuciya, tare da furta Alhamdillah. Ta sanya hannayenta, ta zagaye shi, ta ɗora hannunta a kansa ta din ga karanto masa addu'oi. Ta din ga hasko irin murnar da Sayyid zai yi, da ya na nan aka haifi jaririn nan. Hawaye ya din ga gagangarowa ta gefen idonta. Tana jin Likitan tana tsokanarta da har da kukan daɗi, ba za ta bayar da jaririn ba sai an ba ta tukuici mai tsoka. Nana dai ta lumshe idanunta tana murmushi. Aka ɗauke jaririn aka gyara ta, aka yi mata ɗinki, sannan aka kai ta ɗakin hutu. Bakin Nene ya ƙi rufuwa, ta din ga kallon jaririn. Ta kira wayar su Hajara, ta gaya musu baƙuwar su Nana ta haihu. Nana ta din ga kallon Nene, da mamakin yadda take ta murnar haihuwar nan, tamkar ita ta haihu. Sai dai da Nana ta kalli fuskar jaririn sai jikinta ya yi sanyi, ta rasa abin da yake yi mata daɗi, tana tsoron idan ba ta haɗu da Sayyid ko 'yan uwansa ba, yaya za ta yi mene ne makomar yaron kenan? Ga fargaba da tsoron kar su Ƙaisar su yi masa wani abu, kar shi ma ya yi mummunan gado kamar yadda ta yi. Haka dai ta ɗan saki fuska babu yabo ba fallasa. Bayan awanni shida aka sallame ta daga Asibitin suka koma gida. Aka bata magungunan da suka dace ta yi amfani da su, duk Nene ta biya komai. Nene ta shiga hidima da Nana sosai, ruwan wankanta da na jariri. Ga lafiyayyen Abinci, Hajara kanta idan za ta zo, sai ta yi girki. Kowa ya ɗauki jaririn Nana, sai ya burge shi. Ita kanta Nana tasirin Addu'a ne ya sanya Allah ya kawo mata wannan ɗaukin da gaggawa, mutanen da ta haɗu da su suke sonta. Kwana na biyar da haihuwarta, ta ɗebo kuɗi a cikin jakar gurin Sarkin baka, ta samu Nene ta ce "Nene kuɗin nan za su isa a sai wa yaron nan abin yanka?" Nene ta ce "Kar ki damu, mun yi magana da Auwwalu za a samo abin yanka in sha Allah" Nana ta ce "A'a Nene, ko ke ki ka haife ni, wahalar da za ku yi mini kenan, kuɗinki na sana'a ne. Ina son a saya masa kaya, a saya masa abin yanka, ko ba za su isa ba, a karɓa a ƙara irin kuɗin mahaifinsa ne, dan Allah kar ki ce a'a" Da ƙyar Nene ta karɓa. Dan kuɗin da yawa, aka sayo ƙaton rago, Nene har da ɗawainiyar yin girki, ta gayyaci maƙwabtanta suna. Muhammad Muhsin, shi ne sunan da Nana ta sanya wa jaririn, Muhsin saboda sunan ɗan gidan Alhaji Fatuhu da har abada ba za ta manta da mutuwarsa ba. Maƙwabtan Nene da ma'aikatanta sun yi wa Nene kara, sosai suka tara mata abin alheri na kuɗi, da kayan sakawa kasancewar Nene duk masifarta akwai kyauta, shi yasa take shiri da mutane. Da daddare Nene ta yi wa Muhsin wanka, Nana ma ta yi ta ba ta jaririn ta shayar da shi. Ta fita tsakar gida ta ƙarasa aikace-aikacenta. Kukan jaririn ta din ga ji, Nene ta ce "Nana ya ne, ki kula da shi mana" Amma Nana ba ta amsa ba, sai kukan jaririn da ta ci gaba da ji. Ta koma ɗakin ta ɗaga labule, kawai ta tarar da Nana, ta saka jaririn a gaba tana ta uban kuka. Hankali tashe ta shiga ɗakin cikin damuwa ta ce "Ke lafiya, kukan me ki ke yi?" Nana ta kasa magana, ta ci gaba da kuka, ga jaririn a kan cinyarta amma ta kasa riƙe shi. Nene ta ƙarasa ta ɗauke jaririn ta ce "Ba za ki illata ɗan mutane ba, maza yi ta kukan, idan kin gama kya kula da shi" Nene ta goye shi a bayan ta, ta ci gaba da sabgoginta ta ƙyale Nana. Ba ta sake kula Nana ba, sai da ta yi kuka mai isarta ta gaji. Nene ta gyara shimfiɗarta, ta kwantar da Muhsin da ya yi bacci. Ta koma gurin Nana, ta zauna. "Nana" ta kira sunanta. Nana ta ɗaga kai ta kalle ta. "Ki gaya mini tsakaninki da Allah, yaron nan ta hanyar aure ki ka haife shi ko kuwa? Na san tambayar nan tana baƙanta miki rai, amma haƙuri za ki yi da ni" Nana ta share hawayenta ta ce "Nene ni ba ƙarya na yi miki ba, ina da aure wallahi ɗan sunna ne" "To Alhamdillah, dama jira nake Allah ya sauke ki lafiya, idan ta kama da kaina sai na je Nigeria, na mayar da ke gaban iyayenki Nana, wannan zaman naki kina yarinyar mace, ba kamace ki ba" "A'a ba zan koma ba Nene" "To saboda me?" Hawaye na ambaliya a fuskar Nana ta ce "Sai na haɗu da Babansa, ko danginsa. Ai sun san na taho neman sa" Nene ta ce "To a wane garin baban nasa yake?" Ta girgiza kai ta ce "Nima ban sani ba" "Kamar yaya? Meye sunansa da garin da yake ko hotonsa, sai a taya ki cigiyarsa" Nana ta sake girgiza kanta ta ce "Ban sani ba" "Wacce daga cikin tambayar ce ba ki sani ba?" "Nene ban san garin su ba, ban san sunansa ba, kuma ba ni da hotonsa" Nene ta ce "Ke kar ki raina mini wayo mana, na kwaɗe ki, ta yaya za ki auri mutum ba ki san sunansa ba, ba ki san sunan garinsu ba kawai ki ka kamo hanya ki ka taho? Me ki ke ɓoye mini ne?" Nana ta ɗan yi shiru ta numfasa ta ce "Ƙaddara ce ta haɗa ni da shi muka yi aure, ban san sunansa na gaskiya ba, ni ba shi sunan Sayyid. Ba shi da cikakkiyar lafiyar ƙwaƙwalwa kuma." Nan Nana ta warware mata komai da ya danganci aurenta da shi, duk da ba komai ta gaya mata ba. Nene ta yi shiru sannan ta jinjina kai ta ce "Ikon Allah, dama shi ne Sayyid ɗin da ki ke ambata idan kina bacci? Amma Nana iyayenki sun yi ganganci. Ke yanzu ko hotonsa ba ki da shi. Kawai Nana ta ɗaga mata kai alamar eh. "To ai Nana zama guri ɗaya a haka, ba zai sanya a gano shi ba, dole sai an taɓuka wani abin, wane ƙabilar ne ko shi ma ba ki sani ba?" Nana ta yi shiru ta rasa ma me za ta cewa Nene. Nene ta ce "To shikenan, amma ba kya ganin yakamata gidanku su san kin haihu?" "Nene babu buƙata goben jaririn nan nake hange" "Haka ne, to Ubangiji Allah ya kyauta, amma wannan lamarin naki akwai sarƙaƙiya Nana. Amma ba komai Allah ya taƙaita" Nana ta amsa da Amin. **** Baba yana tsakar gida yana shan kunu, sai ga Suwaiba ta fito, gaba ɗaya ta zama wata iri kamar shiri-shiri. Ta kalli Baba ta cake a ƙofar ɗaki ta ce "Nana fa ta haihu" ba shiri ya ajiye ludayin kunun ya kalli Suwaiba ya ce "In ji wa? Waye ya gaya miki?" "Nanan ce ta gaya mini" "Ke a ina ki ka ganta?" "Ina bacci a ɗaki, na ganta da jaririn, ta ce mini haihuwa ta yi" Wani uban tsaki Baba ya ja, saboda jin shiritar da Suwaiban take faɗa. Dan da fari ya zata ma da gaske take yi. Alhaji Zailani ne tare da Malam Gambo, su na zaune fuskarsa ɗauke da damuwa. Malam Gambo ya ce "Wai duk me yasa ka damu ne har haka? Ka na tsoron ƙungiya ta sake cewa ka kawo jininka ne?" Alhaji Zailani ya numfsa ya ce "Abu na farko burukana biyu, ɗaya ya cika na durƙusar da Fatuhu. Amma samun yarinyar nan ya zame mini bala'i, ƙarewa ma da yake azzaluma ce mai baƙin hali, wai ta tafi Nijar. Ban kuma san ta yadda zan yi na same ta ba. Babu yadda ban yi na samu yarinyar nan ba, amma duk lokacin da na yi wani yinƙuri a kanta, sai hankalina ya gushe. Yanzu babban tashin hankalina wannan jarababbiyar Sa'a, ashe ita ma ƙoƙari take yi, ta mallaki jinin yarinyar nan. Ga shi na rasa dalilin da ya sanya Shukura take ta zargin likitan da yake yi mini aiki, da kisan jaririnta." Malam Gambo ya numfasa ya ce "Ka tattara nutsuwarka guri guda, nasara na buƙatar kasada a kowane lokaci. Ita waccan yarinyar ka jingine batunta a yanzu tukuna, tun a wancan lokacin ai na gaya maka tana ɗauke da wani shu'umin aljani ne mai taurin kai a kanta ba zai taɓa barin burinka ya cika ta daɗin rai a kanta ba. Ba kai kaɗai ba koma waye kuwa. Sannan ƙungiya idan ta sake buƙatar jini, sai ka bayar da na ɗaya daga 'ya'yanka ko namijin, ko kuma ita yarinyar taka a bar jaririn nata ba shikenan ba. Kawai ya zuba wa Malam Gambo ido, idanunsa suka yi jawur sai dai bai ce komai ba ya tashi ya fita. **** Ɓangaren Sagir kuwa, sosai yake sintiri tsakanin Kano da Abuja, saboda Yusra, saboda soyayyar da suke yi ma a yanzu, ba su yi ta a lokacin da suke saurayi da budurwa ba. Wata irin muguwar shaƙuwa suka yi, da shaiɗan ke barazanar shiga cikin lamarin nasu, ga shi ya rasa ta inda zai tunkari Hajiyarsa da batun, domin ba son Yusra suke yi ba. Shukura tuni ta daɗe da gano inda ya dosa, amma ta zuba masa ido ta ga ina ne ƙarshen alewar zai kasance. **** Kwanci tashi asarar mai rai, Nana ta yi wata guda da haihuwa, Nene ta tattara ta daina fita gurin sana'arta. Sai aikin kula da Nana, ga shi kullum da sassafe kan ta ci komai, ake kawo nonon raƙumi fresh Nana ta sha, sannan ta ci Abinci. Nana tana kwance tana bacci da azahar, saboda yadda Muhsin ba ya barin su bacci da daddare, saboda ba ya ɗaga wa Nana ƙafa da tsotso, ga kuka sai dai Nene ta taya ta riƙonsa. Yana gabanta yana bacci, ita ma ya ɗauke ta, ta ɗaga kai ta ga ya shigo ta ƙofar ɗakin. Tana kwance ba ta motsa ba ta ga ya ƙaraso ya zuba musu ido, daga ita har Muhsin, ya sanya hannunsa ya shafa gashin jaririn, ya durƙusa ya sumbaci gishin yaron. Sannan ya kalli Nana idanunsa cike da hawaye. "Sayyid, yaushe za ka zo ka ganmu? Mu na buƙatar ka a kusa da mu, dan Allah kar ka tafi ka bar mu" Ya kama hannayenta ya riƙe a cikin nasa, sai dai bai yi magana ba. Sai da aka jima sosai yana murza yatsun ta a hankali sannan ya ce "Ma vie" "Na'am" "Gangar jikina ta kasa samun nutsuwa, rayukanmu su na kewar juna, ki kula mini da rayuwata da ke jikin ki, da jikin ɗa na, ina ƙaunarku Nana" Riƙe Sayyid ta yi, tana kuka tana "Dan Allah Sayyid kar ka tafi ka bar mu, mu na buƙatar ka a rayuwarmu, dan Allah Sayyid, dan Allah" Nene ta yi shiru tana kallon yadda Nana ta riƙe ta tana kuka. Da yake sheshsheƙar Nanan ta jiyo, ta taho ɗakin tana zuwa ta tarar da Nana tana nema ta danne jaririn. Bayan ta ɗauke shi ne, Nana ta riƙe mata riga. Nene ta zuba wa Sarautar Allah ido, Nana ta buɗe idanunta a hankali ta ga yadda ta riƙe Nene gam. A hankali ta cika ta tana sunkuyar da kai. Sai dai ta ɗaga kanta tana kallon ɗakin, tana jin ƙamshin turaren Sayyid a hancinta. Nene ba ta ce mata komai ba, ta goya Muhsin ta fice da shi daga ɗakin. Nana ta lallaɓa, ta tafi gurin da kayanta suke, ta bubbuɗe jakar kayan shafe-shafensa, da take ta adanawa tana kallon su tana jin daɗi. Sai dai a wannan karon hawaye take yi, tare da jin zuciyarta tamkar za ta buga. Ta zazzage kayan ta din ga bin su da kallo, ta ɗago Azurfarsa da ya ba ta, ta ce ya yi mata yawa, ya ce ta ɗaure da zare ta yi sarƙa da shi. A hankali ta furta "Da mutuwa ka yi na san Allah ne ya karɓe ka babu yadda na iya, da aurenmu ne ya ƙare shi ma na san wannan ƙaddara ce, ba a kaina a ka fara ba. Amma ban san a wani hali ma ka ke ba, duk a inda ka ke ina fatan Ubangiji Allah ya sanya ka na cikin aminci da kwanciyar hankali Sayyid. **** Yana zaune a kujerar da ke cikin ɗakin, da abu a cikin kofin yana sha a hankali. Murmushi ya gaza barin fuskar Sultan, ya zauna a kusa da shi yana murmushi ya ce "Alhamdillah, sauƙi yana samuwa Imam, ya jikin naka?" Ya kalli Sultan ya mayar da hankali ya ci gaba da shan shayin da ke cikin kofin hannunsa ba tare da ya furta komai ba. Cikin damuwa Sultan ya ce "Har yanzu ba ka gane ni ba Imam?" Har yanzun dai bai yi magana ba, bai kuma fasa shan shayinsa ba. Sultan ya riƙo hannunsa guda ɗaya cikin nasa, ya ce "Imam ka kalli Abbanka mana, ka yi magana ko hankalina zai kwanta" Ya waiwaya ya kalli dattijon. Cikin murna Sultan ya ce "Ka na jin abin da nake faɗa?" Ya yi shiru yana ci gaba da kallonsa, bai yi magana ba. "Ka yi mini magana ka ce wani abu mana" A hankali ya zame hannunsa daga na dattijon, ya tashi daga kan kujerar ya koma gadonsa na marasa lafiya ya kwanta. Sultan ya yi shiru yana kallonsa, sai dai ya rasa abin da yake yi masa daɗi. Kar a ce ƙwaƙwalwar ɗan sa ta taɓu. A yadda alaƙarsa da ɗan sa take, ba ƙaramin abu ne zai sanya ya yi masa haka ba. Kwanciyarsa ke da wuya, ya fara jijjiga, a rikice Sultan ya nufe shi. Sai dai ya fara kururuwa yana faɗin "Wuta zafi" Matawalle ne ya shigo ɗakin da sauri, suka rufu a kansa, Sultan ya din ga tofa masa Addu'a. Har ya daina jijjigar. Abdou ya kalli Sultan ya ce "Abubuwa fa kamar ƙara rikicewa suke yi, mene ne abin yi yanzu. Ina tsoron a bi diddigi a gano halin da yake ciki fa" "A fita da shi waje kawai, wataƙila a dace a can, ni na kasa gane kan abubuwan da ake yi masa a nan" "A wannan yanayin, da ihun da yake yi" "Abduou" Sultan ya kira sunansa cikin ɗaga murya. Abduou ya risunar da kai ya ce "Za a shirya duk abin da yakamata, za a yi abin da ka ce". Jamila ce take ta juyi a kan katifarta, tana jiran reply ɗin Abba, saboda chatting suke yi. Sai dai shiru bai yi reply ba har ta gaji ta yi bacci. Da safe sai gurin sha ɗaya ta tashi daga bacci, da yake tana fashin salla. Ta duba wayar, ta tarar da tarin messages ɗin sa da kiran waya, ta share ta je ta yi wanka ta shirya. Daga tsakar gida ta ce "Mama ni na wuce" "Ba za ki tsaya ki karya kumallo ba?" "Zan ci a can, sai na dawo" Suwaiba na tsakar gida, tana goge kaushi, ta ce "Jamila" "Yes" Jamila ta amsa. "Nana fa na gaishe ki, ba ki ga jaririnta ba" Jamila ta ce "Ai dama ke da Nanan, kan ku ba ƙalau ba, shi yasa ke kaɗai take kawowa ziyara a mafarki." Sai kuma ta ɗan yi shiru cikin damuwa ta ce "Allah sarki Nana, ko ta na wani halin yanzu oho" ta ɗan ja numfashi ta sauke ta fita, tana ci gaba da tunanin Nana. A falon Hajiya Sa'a ta tarar da Abba yana zaune yana Video game. Tana shigowa ya yi murmushi ya tashi zaune ya ce "Sannu da zuwa" Ta murguɗa masa baki ta nufi bedroom ɗin Hajiya Sa'a. "To ai ba ta nan" ya yi maganar yana miƙewa ya bi bayanta. "Me na yi miki ne ki ke hararata? Na tura miki saƙo duk ba reply" Ta kalle shi ta ce "Ba jiya na yi ta jiranka da daddare ba, ka ƙi kula ni" "Eyya, bacci ne ya kwashe ni, ki yi haƙuri" "Ba wani nan, da budurwarka ka ke chatting ka share ni" Ya waro ido ya ce "Wallahi ba ni da wata budurwa bayan ke, kema kin san ba na iya kula 'yan mata kema da ƙyar ai na gaya miki ina son ki" sai kuma ta tuntsure da dariya ya taya ta shi ma. Za ta yi magana kawai Hajiya Sa'a ta shigo falon, ta gan su a zaune a kan dining suna hira har da dariya, alhalin a gabanta basar da juna suke yi. Ɗan saroro Hajiya Sa'a ta yi tana kallon su, Jamila cike da bariki ta ce "Mummy sannu da zuwa" "Yauwwa" ta amsa a taƙaice. Abba ma kam kasa magana ya yi gaba ɗaya. Ya yi wa Jamila sallama ya fita, sai dai Hajiya Sa'a ta yi kicin-kicin ta ƙi sakar wa Jamila fuska gaba ɗaya. Jamila kuwa ta din ga ƙissimawa a ranta, muddin abin da take zargi ya zama gaskiya game da Hajiya Sa'a za ta ba ta mamaki ba kaɗan ba. ***** Kwanci tashi asarar mai rai, Nana ta kwana arba'in cif da haihuwa. Sai da Nene ta kwana goma sha biyar, ba ta fita gurin sana'arta, saboda jegon Nana sai dai yaranta su je, sai bayan kwana sati biyun sannan ta fara fita, shi ma da wuri take dawowa. Ranar da Nana ta kwana arba'in, ta saka Nana ta shirya suka je gidan su Hajara. Sun yi murna sosai da sosai da ganin Nana, duk da ta rame, amma yanayin ta akwai nutsuwa a tattare da ita. Auwwalu ya ɗauki Muhsin ya ce "Ohh Allah ka bamu mu ma ɗan kyakykywan jariri, ka ga ɗa kamar na larabawa" Hajara ta amsa da "Amin dai" Nene ta ce "Ka ga fitsararru, babu ko kunyar idona?" Auwwalu ya ce "To ai addu'a muka yi. Ban da rashin kara ma, a ƙa'ida fa ɗan nan, sunana na ya kamata a saka masa" Nene ta ce "Saboda kai ɗin waye?" Nana ta yi murmushi ta ce "Yaya Auwwal, ai sunanka ne da shi, laƙanin ne kawai ba ɗaya ba" Ya yi murmushi ya ce "Kuma fa haka ne" sosai suka karrama su Nana. Da suka tashi tafiya ma, sai da suka kuma bawa Jaririn kyautar kuɗi da kaya, a so samu Nana ba ta so suka karɓa ba, amma Nene ta amshe. Da suka dawo kuma ta zagaya da Nana gidajen maƙwabta, suka gaggaisa. Tun da suka doshi wani gida, Nana ta din ga jin gabanta na faɗuwa, kamar ta cewa Nene ba za ta shiga ba, amma ta kasa. Ta din ga addu'a tare da fatan Allah ya rufa mata asiri ya sanya ba wani abin ne zai faru da ita ba, ko Ƙaisar ne zai dawo ya hana ta sukuni a ƙasar da ba ta da kowa ba. Ko da su ka shiga cikin gidan, sai Nana ta fara jin sanyi, yana ratsa ta a hankali. Aka shimfiɗa su tabarma, da ƙyar Nana suka gaisa da mutanen gidan, ta nemi guri ta zauna. Sai ta daina gane abin da Nene suke faɗa ma. Ta din ga jiyo muryar su Nene can nesa da ita, hakan ya tabattar mata da gidan akwai wani abu. Wani irin sauti ta din ga ji, a cikin kunnunwanta, kamar gurnani kamar nishi. Ta daina ganin su Nene gaba ɗaya, sai wata mata da ta fito ta tunkaro ta. Ga matar babba da ita amma jikinta ɗauke da zaren mahaifa daga cibiyarta dogon zaren har kan wani baƙin ƙwarangwal da yake bin ta, hannun ƙwarangwal ɗin kuma mahaifa ce yake lasa da jini da komai a jiki. Jikin Nana ya hau tsuma, ta din ga kallon matar da ƙwarangwal ɗin, tana son yin addu'a ta kasa. "Nana" ta ji muryar Nene ta kira sunanta. Sai ta buɗe ido ta kalli Nene. "Tashi mu tafi yamma ta yi" Nana ba ta motsa ba, ta ga matar da ta gani yanzu tare da ƙwarangwal ta nufo ta. Matar gidan ta ce "Kar ki kuskura ki taɓa ta, yi haƙuri dan Allah ba ta da cikakkiyar lafiya ne" ta yi maganar tana kallon Nana. Sai dai matar ba ta tsaya ba, ta yi kan Nana gadan-gadan. Wani irin azababben ƙarf ya zo wa da Nana, ta ji zuciyarta na tafasa jira take matar kawai ta ƙaraso gare ta, ta illata ta. Amma Nene ta danƙi hannun Nana, ta hana matar ƙarasawa gurin Nana ta ce "Ke Ashura, meye haka ne? Ba ki ga baƙuwa ba ce?" Matar cikin wata irin harɗaɗiyar magana da zubar da yawu ta ce "Magana zan yi mata, ta saka wannan ƙwarangwal ɗin ya daina bina" gaba ɗaya suka kalli Nana. Ɗaya matar ta ce "Wani ƙwarangwal ɗin, rabonta da magana ma fa ta fi sati biyu" Kawai matar ta saka kuka, lallai sai ta je gurin Nana, ta cewa ƙwarangwal ya daina bin ta. Nene ta ja hannun Nana suka yi waje. Sai dai ta ji jikin Nana tamkar gawa saboda sanyin da ya yi. Su na zuwa gidan Nana ta nemi guri ta zauna, ba ta cewa Nene uffan ba. Can bayan magariba, sai ga matar da su ka je gidanta ta zo, Nene ta ce "Gaji lafiya kuwa?" "Dan Allah Nene ki taimaka mini, ko 'yar nan taki za ta zo mu je gurin Ashura, sai ihu take tana burgima tun da ku ka tafi" "Ta zo ta yi mata me?" Gaji ta ce "A'a ban sani ba ko akwai wani taimako... "Taimakon me?" Nene ta katse ta. "Kin san dai Ashura ba hankali ne da ita ba, wataƙila almatsutsan haukanta ne kawai ya tashi take wannan abubuwan, ki tafi babu inda Nana za ta zo" Gaji ta fita jiki a sanyaye, dan idan ta matsa sai Nene ta balbale ta da masifa. Nene ta ajiyewa Nana nonon raƙumi, da abincin dare, amma ta ƙi ci saboda sanyin da take ji. Nana ta haɗa kanta gwiwa, tana jin yadda jikinta yake tsuma ta ce "Sayyid sanyi nake ji" "Ke Nana" Nana ta ɗago ido ta kalli Nene. "Ba za ki ci abincin ba ne?" "Na ƙoshi, amma dan Allah Nene mara lafiyar can ta can gidan, ta faɗi wani abu a kaina ne?" Nene ta ce "Za ki ba ta magani ne?" Sai Nana ta yi turus tana kallon Nene, gabanta yana tsananta faɗuwa. "Ba ta ce komai a kan ki ba, amma idan kin amince za ki yi magana da aljanin nata, ko ki bata magani kamar yadda ake so ki yi, sai mu je" Gaban Nana ya faɗi, ta bi Nene da kallo cike da mamakin, yaya aka yi Nene ta san wannan maganar, alhalin ko da wasa ba ta taɓa gaya mata ba. "Nana mamaki ki ke yi? Ai ba a banza na yarda na karɓe ki muke zaune a cikin gidan nan ba da ni da ke. Tun zuwanku na ga abubuwan da na gani a tattare da ke. Na ga inuwar rauhanin aljani a tattare da ke, kuma da alama ko dai kin gamu da baƙin aljani a hanya, ko kuma kin yi rayuwa da shi, saboda akwai warinsa a tattare da ke, saboda yana ta'amalli da jini, har ma warin nasa yana ƙoƙarin danne, ƙamshin rauhanin da yake tattare da ke. Sannan akwai alamu na alaƙa mai ƙarfi a tsakanin wannan rauhani da Aljanin da yake tattare da ke. Jiri ne ya fara ɗibar Nana, cikin wani yanayi mai kama da fitar hayyaci ta ce "Nene, wace ce ke? Ya aka yi ki ka san abin da ban gaya miki ba? Ki gaya mini ke wace ce?" "Nana, masu iya magana suka ce mugu shi ya san makwantar mugu. Ni na yi harkar bori da bayar da magani, ni baƙin aljani ma na gada daga gurin mahaifina. Ya azabtar da ni ya hana ni aure, na ƙi bayar da magani ya shanye mini ƙafafuwa, na daina al'ada na fara hauka tuburan. Sai da na bayar da magani, bayan wasu shekaru, na daina al'ada na fara hauka tuburan. Sai da na bayar da magani, bayan wasu shekaru, na gaji na ce zan ajiye, saboda kullum cikin larura nake, ga shi ya sanya na saka a yi ta zubar masa da jini. Ya sake burkita ni, ya hana ni aure, na koma ciwon hauka yau na kuturce gobe na daina gani, anjima na kasa tafiya. Ya buɗe mini ido nake ganinsu muraran a siffofi na ban tsoro, nake jin maganganun su a cikin kunnuwana. Ya ɗauke ni ya kai ni can wata uwa duniya ya yasar da ni, na yi ta gararamba sannan ya gaji ya dawo da ni. Ko ya saka na yi ta zubar da jini babu ƙaƙƙautawa. Duk inda muka je neman magani, sai a ce sai dai na haƙura na ci gaba da bayar da magani. Da ƙyar wani mai magani ya raba ni da shi, ta hanyar yin amfani da wani aljanin. Ya kafa sharuɗɗa sai da aka yi masa yanka, da sauran abubuwa dai na sharuɗɗa sannan Allah ya raba ni da shi. Bayan mun rabun ma, da ƙyar na samu na yi aure, shi ma dai kusan kullum cikin rigima da miji, na zo babu haihuwa, sai rigima sai dai ya dage ya ƙi rabuwa da ni. Sai daga baya Allah ya bani haihuwar ɗa namiji, daga nan ban sake haihuwa ba. Yarona yana can ƙasarku Nigeria. Mijina kuma Allah ya yi masa rasuwa, ni kuma na ci gaba da sabgogina ban sake wani auren ba, duk da wasu lokutan haryanzu abubuwan na taɓa ni." Nana tana Libraryn Ƙaisar, daga can nesa take jiyo maganar Nene. Kai tsaye gurin mudubin nan ta nufa, cike da fatan ta sake ganin ko fuskar Sayyid ne, amma ta tarar da mudubin wayam, sai ma baƙi ƙirin da ya yi. Ta daɗe a tsaye ta zura wa mudubin idanun amma babu alamar wani abu zai bayyana a mudubin ta gani. Ta hango littafin da ta fara karantawa a yashe a ƙasa, inda ta yasar da shi, hakan ya tabattar mata da Ƙaisar ba ya cikin ɗakin karatun nasa na wani lokaci. Ta sanya hannu ta ɗauki littafin, ta nutsu ta ci gaba da karantawa. "Idan ka bari tsoro ya ɗarsu a cikin zuciyarka, to tabbas ba za ka iya cimma abin da ka ke hari ba. Tun da kawar da mahaifinka bai yi maka wahala ba, wannan ma ba zai gagare ka ba, ka kashe su ɗaya bayan ɗaya, ka yi mulki cike da izza ka tara sojoji da runduna da za ta razana duniya". Ire-iren waɗannan kalamai na ziga da kambamawa, ya sanya matashin saurayin jin kansa na daɗa kumbura, tare da ji a ransa zai aikata komai domin cimma burinsa. Ana tsaka da jimamin mutuwar shugaba a garin, ya ci gaba da tattara sojojin sa na ƙarƙashin ƙasa, da shirya hanyoyin da zai bi gurin kawar da dukkanin wanda ka iya kawo masa tangarɗa. Ganin babu abin da ake yi a farkon littafin, ban da tsagwaron zalunci, zubar da jini da rashin tausayi ko imani, tsananin ƙiyayya da kisan kai a tsakanin 'yan uwa, duk don kowa yana kwaɗayin ɗarewa gadon mulki. Ga bautarwa ta fitar hankali ga na ƙasa ba tare da afuwa ko sassauci ba, sai Nana ta ji gaba ɗaya littafin ya ishe ta, ba ya yi mata daɗin karantawa, har ma gara na tarihin Buda a kan wannan. A hankali ta buɗe idonta, da ya yi mata nauyi, ta ga gari ya yi haske, ta shafa gefenta ta ji babu Muhsin, kawai ta yi zaton ko Nene ce ta goya shi, dan idan Nene na nan, tsakaninta da Muhsin shayarwa ne kawai, ita take yi masa komai kamar ita ta haife shi. Tana ɗaga kai ta ga wannan mahaukaciyar, riƙe da Muhsin a hannunta, gefenta ga wannan ƙwarangwal ɗin baƙi ƙirin da shi kamar an gasa shi da wuta. Ihu Nana ta saka a cike da matuƙar razana, ba wai dan ta ga ƙwarangwal ɗin ba, sai ganin ɗan ta a hannun mahaukaciya ga aljani a bayanta yana ta lasar jinin jikin mahaifar da ke ɗauke da zaren cibi. Ayshercool 08081012143 66 Nece ce ta fito hankali a tashe, ta shiga ɗakin da Nana take ciki, ta tarar da Ashura a tsaye rungume da jaririn Nana. A matuƙar fusace ta ƙarasa ta karɓe Muhsin, ta ajiye shi a kan katifa, ta ce  "Uban me ya shigo da ke ki ka ɗauke shi?" Cikin tsoro ta girgiza kai ta ce "Babu komai" "Uban me ki ka yi masa?" "Wallahi ban yi masa komai ba" Nene ta shaƙe ta, ta ce "Ki gaya mini me ki ka yi masa?" Cikin kuka ta ce "Wallahi ba abin da na yi masa" "To me yasa ki ka shigo?" "Wallahi son shi kawai nake yi" "Ɗan ki ne da za ki ce son shi ki ke yi, wani abin za ki yi masa kenan" cikin kuka ta ce "A'a Nene" Nene ta ce "Wallahi na sake ganinki a gidan nan, sai na yi miki shegen duka, babu ke babu jaririn nan" Nana ta saka hannu ta ture Nene, ta ce "Dan Allah ki yi haƙuri ki daina dukanta, ai ta ce babu abin da ta yi masa" Nene ta ce "Ba dan kin farka ba fa? idan ta yi masa wani abin, ni ina banɗaki ke ki na bacci fa?" Nana ta ce "In sha Allah babu abin da za ta yi masa. Zo mu je na raka ki gida" Nene ta ce "Nana ki rabu da ita ta tafi gidan" Nana ta ce "Nene zan raka ta, ni duk inda na ga mai irin larurar nan, tausayi yake bani" Nene ta ce "Can ta matse muku ke da ita, ku je can ku ƙarata, ni dai na sake ganinta a gidan nan, ta taɓa yaron nan, sai na yi mata shegen duka da itace" Nana ta kama hannun Ashura da ke ta rarraba ido, suka fita daga gidan. ***** Hajiya Sa'a ta tattara hankalinta a kan Abba da yake zaune a gabanta a bedroom ɗin ta. "Magana nake yi maka, ka ɗago ka kalle ni, mene ne a tsakaninka da yarinyar nan Jamila?" Ya ce "Ba komai" "To ka buɗe kunnenka da kyau ka saurare ni, na sanya katanga a tsakaninka da ita, babu kai babu ita, kar ka kuskura na ji wata magana a tsakaninka da ita, kuma matar aure na samo maka ita, zan baka lambarta ka kira ta ku gaisa. Ka je ku gana, kuma nan kurkusa za a yi komai a gama. Ka fita daga harkar Jamila, ka fita daga harkar ta na gaya maka na kuma nanata maka, idan ba haka ba daga kai har ita ba za ku ji daɗin abin da zai biyo baya" Ya jinjina kai jiki a sanyaye ya ce "To in sha Allah zan kiyaye" "Tashi ka bani guri" ya yinƙura ya tashi jiki a sanyaye, ya fice daga ɗakin,  zuciyarsa na wani irin zafi. Bai taɓa zaton za ta nuna adawarta da maganar haka ba, ganin yadda take da Jamila. Ko da ya tafi ɗakinsa, kiran Jamila ya shigo wayarsa, jiki a sanyaye ya ɗaga wayar ya ce "Hello Jamila" "Jamila kuma, yau ba ƙanwartaka?" "Afuwan a yi mini afuwa" Cikin damuwa Jamila ta ce "Yaya lafiya kuwa?" "Lafiya ƙalau, ina fatan kin je gida lafiya, ba ki bari na dawo na mayar da ke ba" "Ina sauri ne, kuma ba na son wahalar da kai gaba ɗaya. Ko dai Mummy ta yi maka magana a kan ka daina kula ni ne?" Da sauri ya ce "A'a ai kin san ba za ta hana ba ko kaɗan" Jamila ta ce "To shikenan, amma dan Allah in anjima ka zo na ganka" Ya yi murmushi ya ce "Ni ki ke son gani?" "Eh mana, ko na haƙura?" "Ina ni na isa, ina yin sallar isha'i za ki ganni a bar ƙaunar Abba" "To abin ƙaunar ƙanwarsa, sai ka zo" ya sauke wayar yana murmushi, sai dai yana sauke wayar ya ɗan yi shiru cikin damuwa, bayan tuna abin da Mummyn ta gaya masa na kashedi. **** Muhsin ɗin Nana tamkar ana hura shi, saboda girma ya cika ya yi fam. Ga shi fafur Nana ta ƙi bari a yi masa aski, ta cewa Nene babansa ma ba ya aski, dan haka a bar masa sumarsa. Nene ta fara jinginar da shi, a tsakanin fululluka tana koya masa zama. Nene ta ce "Nana bari na hanzarta na fita, ki kula da yaron nan dan Allah, ban da shiririta, ko ki ƙyale shi yana kuka ki yi masa banza" Nana ta ce "To Nene ki goya abinki ki tafi da shi mana, tun da kullum ba na yi muku abin arziki" "Kya dai ji da shi, ni dai na gaya miki, kuma wallahi mahaukaciyar can ta shigo, ki ka ɗauki yaron nan ki ka bata, sai na ɓata muku rai daga ke har ita" Nana ta ce "Ni dai ba wannan ba, Nene so nake na fara bin ki gurin sana'ar nan, zaman gidan nan yana damuna, ba akin fari babu na baƙi" Nene ta ce "Nima na yi wannan tunanin Nana, amma bai kamata a ce kina matar aure mu din ga fita bakin titi babu iznin mijinki ba, kin san halin maza wasu ba kirki ne da su ba, mussaman ke ga ƙuruciya ma. Sam ba mutuncinki ba ne ba, dama jira nake yi Muhsin ya ƙara ƙwari, na nema miki ko gurin ɗinki ne ko makamancin haka, ki din ga zuwa sannan mu ga ta ina za mu fara laluben mijinki, amma tun da Muhsin ya yi ƙwari, mu fara lalubawa zaman haka ba zai yiwu ba, motsi ya fi laɓewa ai" Ta jinjina kai ta ce "To shikenan Nene, duk yadda ki ce Shikenan, na gode sosai da sosai Ubangiji Allah ya saka miki da mafificin alkhairi" Nene ta ce "Amin yarinyar kirki" Fitar Nene babu jimawa sosai, sai ga Ashura ta faɗo gidan. Nana ta ba ta ce mata ta shigo ɗakin, amma ta ƙi. Nana ta tashi ta fita ta shimfiɗa mata tabarma, sannan ta ɗaukko Muhsin, ta zo ta zauna ta ba wa Ashura shi. Ta karɓe shi tana buɗe baki cikin murna, ta kalli Nana ta ce "Ina son yaron nan" Nana ta ce "Da gaske?" Ta jinjina wa Nana kai, ya jima a hannun Ashura, sannan ta ba wa Nana shi, Nana ta mayar da shi ɗaki ta kwantar. Sai dai tana dawowa ta tarar da Ashura a tsaye tana kuka, gefenta ga ƙwarangwal ɗin nan. Nana ta ce "Me ka ke buƙata ne?" "Ki na ganina kenan?" "Eh ina ganin ka, sannan wannan mahaifar da ka ke lasa mene ne ma'anar hakan? Tun da ƙazanta ce" Ya ce "Lokacin da aka haife ta ne, da za su dawo daga Asibiti, aka manta mahaifar, shi kuma mai motar ya yar a bola, ni kuma na tsinta na biyo ta." Cikin damuwa Nana ta ce "Amma baka kyauta ba, tun da babu wanda ya yi maka wani laifi ka ke yi mata abin da ka ke yi mata". Ya ce "Ai mu ba sai an yi mana abu ba, idan mu na son mutum. Kin ga ke ma da ki ke addu'a wasu lokutan, ba dan tasirin Addu'a da ki ke yi, da kuma tsoron uban duƙusa da ake yi ba, da bataliyar da za su shiga jikinki da yawa. Saboda da guda ɗaya ya yi hanya, wasu ma suke samun kafar shiga jikin mutum. Kuma Allah ya taimake ki, Sarkin baka ya rage tasirin uban duƙusa a tare da ke, da duk inda muke sai kin din ga ganinmu, kuma muraran za ki din ga ganin cututtuka da sihiri a zahiri, sai kin kusa haukacewa idan ba ki bayar da magani ba. Kawai dai shi yana lallaɓa ki ne" Nana ta ce "Yaya aka yi ka san Ƙaisar, kuma ka san Sarkin baka?" Ya ce "Jaddul Jinn babu wanda bai san shi a nahiyar nan ba, dan haka sanin jikansa uban duƙusa ba abin mamaki ba ne. Sarkin baka kuma shi ne ya mayar da ni ƙwarangwal, mun taɓa artabu da shi da na shiga jikin sata mesa, ya ƙona ni. Kuma na ga kin haɗa jini da shi, ba yadda na iya da ke ne kawai, da sai na ɗauki fansar abin da aka yi mini a kan ki" Nana ta yi shiru jikinta ya yi sanyi, su na gama maganar Ashura ta juya ta fita ya bi ta a baya. Nana ta din ga jinjina azabar naci da riƙo irin na halittun nan. **** BAYAN WANI LOKACI. Girman ɗan mutum babu wuya, in ji masu iya magana, Muhsin ya cika watanni bakwai, Nana na zaune tare da Nene. Nene ta kai ta gurin koyon girke-girke, yanzu kuma tana zuwa koyon ɗinki. Nana har mamakin yadda Nene take yi mata take. Sai dai ta fara karaya da yanke tsammannin haɗuwa da Sayyid. Nene ce ta shigo gidan, bayanta goye da Muhsin, yana ta mamular cukui. Nene ta sauke shi ta zaunar da shi ta ce "Wannan ɗan naki, idan bai nuna mini halinsa ba, ai ba za a ce ɗan buzaye ne ba, mun taho hanya ya ga raƙuma, wai sai dai mu tsaya ya kalli raƙumi, sai zillo yake a bayana yana ihu, sai da na tsaya na ɓata lokaci yana kallon raƙuma yana miƙa musu hannu. Ya cire hular kansa ya yar, kowa ya ga kansa da wannan kitson sai an tambayi mace ce ko namiji. Ke ma da taurin kan tsiya, kin ƙi bari a yi masa aski, kuma kina yi masa kitso kamar wani mace." Nana ta yi murmushi ta ce "Ni babu ruwana, ba shiga faɗanku zan yi ba, balle na ji kunya ku gwale ni" Shi kuwa cukun hannunsa kawai yake mamulawa a bakinsa, Nene ta juya za ta fita tsakar gida ya rarrafa ya bi ta yana kukan ta ɗauke shi. Nana ta sake yin murmushi ta ce "Na haifa wa Nene ɗa" Tana jiyo rigimarsa da Nene, ya hana ta aiki, idan ta hana shi wannan ya koma wancan. Nana ta din ga dariya daga ɗaki, aka jima kuma Nene ta zuba masa shayi sai kuma ya nutsu, guri ɗaya, yana sha yana wasa da gashinsa. Ashura tana son zuwa gidan Nene gurin Nana, amma tana tsoron Nene, ga Muhsin da ya ganta yake sanya ihu, tsoronta yake ji. Ɓangare guda kuma, zuciyar Nana na saƙa mata ya kamata ta gusa ta bar gidan Nene, saboda ta ja lokaci a gidan. Amma tana tuna tijarar Nene, da rashin sanin ina za ta dosa. Ba ta san wani irin mutum ne Sayyid ba, mutumin da za a yi alfahari da haɗa nasaba da shi ne ko akasin haka, duk da tana kyautata masa zato. Shi yasa take ɓoye wasu abubuwan, dan kare mutuncin sa da rashin sanin a yaya za ta haɗu da shi. Washegari da safe Nana ta tashi, ta jiyo hirar Muhsin a tsakar gida. Ta tashi ta fita kar ya yi wata ɓarnar, sai ta gan shi a lungun kitchen ɗin Nene, ya juyo bayansa, kamar dai wani abun ya samu yana wasa da shi. "Kai babyn Sayyid, me ka yi a gurin nan, taho ka sha" bai waiwayo ba ya ci gaba da abin da yake yi. Nana ta nufe inda yake. Wata irin narkekiyar mesa ta gani a cikin lungun, shi kuma yana ta duƙunƙuna kanta da hannu bibbiyu yana hira. Ji ta yi tamkar an ɗaure ta tamau, ta kasa gaba ta kasa baya, kuma ta kasa magana. Mesar ta miƙe sai ga Ƙaisar ya bayyana a gurin. Muhsin ya ɗaga kai yana dariya yana kallon Ƙaisar. Ƙaisar ya ciro wani abu a kwalba, ya buɗe bakin Muhsin ya zuba masa, Nana ta rikice amma ta kasa motsa kowace gaɓa ta jikinta. Muhsin ya kama rigar Ƙaisar yana wasa da ita, yana yi yana kallon Ƙaisar ɗin. Ƙaisar ya saka hannu ya shafa kitson kan sa, ya miƙe tsaye ya ɓace. Sai da ya ɓace Nana ta iya motsawa, amma duk da haka ta kasa zuwa inda Muhsin yake, sai shi ne ya rarrafo ya nufo inda take. Ta saka hannu da ƙyar tana dudduba jikinsa, ko wani abin ya yi masa amma jikinsa lafiya ƙalau. Ta shiga fargaba da tsoron me ya ba shi ya sha?. Ta ja jikinta ta koma jikin bango, ta fara shayar da shi, tana roƙon Ubangiji Allah ya kare mata yaronta daga sharrin su Ƙaisar da kowane irin nau'i na shaiɗani. Nene na fitowa, ya cika Nana ya tafi gurinta, sai da ya gama wasansa, ya sake komawa gurin Nana. Tana shayar da shi, tana ganin fuskar Sayyid a tattare da shi, dan hatta idan ya ɓata rai, tamkar mahaifinsa. Sai dai tunani da tsoron abin da ka iya samun sa, ya gaza barin zuciyarta, tun daga ganin da ta yi wa Ƙaisar da shi. Ta so gaya wa Nene, amma ta ja bakinta ta yi shiru ba ta gaya mata ba. Sai dai tun gabatowar magariba, take jin sanyi. Ta shige ɗakin ta ƙudundune, ta bar su Nene. Tana tsaye a sahara, sai dai a wannan karon babu ƙurar Saharar, ta hangi Sayyid a zaune yana shan shayi, shikaɗai. Ta taka sannu a hankali ta ƙarasa inda yake, ya ɗago ya kalle ta yana murmushi. Ta zauna a kusa da shi, ta ce "Ka warke ne?" "Da sauƙi, na yi nesa da inda nake jin ciwon, kuma na yi nisa da gurin waɗanda za su kashe ni" Cikin damuwa ta ce "Ni fa?" Ya ajiye kofin hannunsa, ya rungumota jikinsa yana kallon fuskarta, idanunsa cike da hawaye ya ce "Yadda ruhinki da gangar jikinki, suka gaza samun nutsuwa, tun bayan rabuwarmu haka nima nawa suka gaza samun nutsuwa. Ina kewarku gangar jikina ta kasa samun nutsuwa, ina buƙatar ki a kusa da ni" Ita Nana gaza riƙe nata hawayen ta yi, tuni ta ba su dama suke zuba. Ya girgiza mata kai tare da cewa "Kar ki manta, muddin kina raye kuma ina raye a doron duniya, gangar jikinmu ba za ta samu nutsuwa ba, sai mun haɗu. Ina kewar ki ma vie." Ya yi maganar yana ƙanƙame ta a jikinsa. Ta buɗe idonta tana ji yadda hawaye ya jiƙa mata fuska. Ta tashi zaune da ƙyar, ta yi shiru ta tafi tunani. "Nana ba a bori da sanyin jiki, ci gaba da zaman ki a gidan nan, tamkar ki na matsawa dattijuwar nan ne da take ɗawainiya da ke, kuma ba za ki taɓa haɗuwa da Sayyid ki na zaune guri ɗaya ba, yakamata ki motsa". Ta tashi ta yi alwala, ta yi sallar magariba da isha'i, ta idar ta shiga ɗakin Nene ta ɗaukko Muhsin, ta dawo da shi ɗakinta saboda ko zai farka cikin dare. Nana ji ta yi tamkar ta fice daga gidan a cikin daren nan, amma ta kasa saboda ba ta san ina za ta nufa ba, a wannan uban daren. Ta haƙura da niyyar da Asubar fari, ta tashi ta fice, amma bacci mai nauyin gaske ya yi awon gaba da ita, sai da aka kusa idar da salla, Nene ta tashe ta yi sallar Asuba. Tana idar da sallar kuma, Muhsin ya tashi ya saka rigima, Nene ta ɗauke shi suka tafi ɗakinta. Tun da wuri yaran Nene suka zo, suka ɗauki kayan Abinci, amma Nene ta ƙi fita ranar ta wuni a gida, yaranta ne suka je suka sayar da Abincin. Abu kamar wasa a jere kwanaki huɗu Nana tana yinƙurin guduwa, amma Nene ta kasa ta tsare tamkar ta san abin da Nana take shiryawa. ***** Jamila ta nuna wa Hajiya Sa'a tamkar ba ta san ita ta taka wa ɗan ta Abba burki a kanta ba, Hajiya Sa'a sai shirin bikin Abba take yi, yayin da gefe guda kuma Jamila ta yi blocking ɗin sa, ta daina ɗaga wayarsa gaba ɗaya. Dama idan Hajiya Sa'a na nan, ba ya iya yi mata magana, da zarar ta fita kuma sai Jamila ta kulle ƙofar sashen. Ya rasa abin da yake yi masa daɗi, har layi ya canza ya kira Jamila, amma tana ɗagawa ta ji muryarsa ta kashe. Ga shi tun da Hajiya Sa'a ta fuskanci abin da yake tsakanin su, ta daina yawan fita ta bar Jamila a gidan, idan ma fita za ta yi sai dai su fita tare. Sai dai yau Jamila ba ta jin daɗi, dan haka Hajiya Sa'a ta fita ita kaɗai, saboda ta sakankance Abba yana can kasuwa. Awa guda da tafiyarta, Jamila na kan doguwar kujera tana bacci, ta ji tsayuwar mutum a kan ta. Ta buɗe idonta a hankali ta ga Abba a tsugune a gabanta yana kallonta. Tashi ta yi zaune tana tsuke fuska tare da gyara zaman rigarta za ta tashi. Cikin zafin nama da tsoron rashin sabo, ya riƙe hannunta ya ce "Dan Allah Jamila ki tsaya ki saurare ni" ya yi maganar cikin marairaicewa kamar zai yi kuka. "In saurare ka ka ce mini me Yaya Abba? Dan Allah ka rabu da ni." Ta yi maganar itama idanunta fal hawaye, saboda ba ta taɓa sanin ta kamu da matsananciyar soyayyar Abba ba, sai yanzu da Hajiya Sa'a take ƙoƙarin farraƙa su. "Jamila dan Allah ki fahimce ni, kin san a son raina ba zan auri wata ke ga ki na bar ki ba, wallahi Jamila ina son ki, ban taɓa son wata 'ya ba sai ke" Ta kalle shi hawaye na zuba daga idonta ta ce "Ko ma mene ne, ai yanzu aure za ka yi, ka rabu da ni dan Allah" Girgiza kai ya yi cikin matsananciyar damuwa da tashin hankali, ganin yadda take zubar da hawaye, zai yi magana ta fizge hannunta ta shiga ɗaya falon, bai yi ƙasa a gwiwa ba, ya sake bin ta yana ƙoƙarin rarrashinta. Sai dai kash, garin ya rarrashi Jamila, sai shaiɗan ya buga musu ganga su ka taka rawa, duk da Jamila ta fuskanci cin zarafi da keta haddi a ƙungiyarsu ta asiri, a wannan karon ma tsoro da rashin sabo suka yi tasiri a a gare ta, duk da a nasa ɓangaren ma haka ne. Daga shi har ita suka saka kuka mai cike da nadama da dana sanin abin da suka aikata. Maganganun Nana suka din ga dawo mata daki-daki, na nasihar da ta din ga yi mata a baya. Duk da babu wanda ya san halin da Nana ne ciki, a tsawon wannan lokacin kusan shekara guda, amma gara Nana da ita, Ko ba komai Nana aure ta yi, ita kuwa fa da fari bokaye da aljanu sun kwanta da ita, a wannan karon kuma ruɗin soyayya da sharrin shaiɗan. "Jamila, dan Allah ki yi haƙuri, ki kuma rufa mini asiri, ke ma kin sa hakan ba halina ba ne ba, amma duk yadda zan yi, zan aure ki, ni na fara aikata ɓarnar nan, kuma zan gyara ta in sha Allah" Jamila ta kalle shi ta kawar da kai, tana jinjina lallai Abba bai san komai ba, tun da bai iya gane ba budurwa ba ce ba, duk da bayan abin da Hajiya Sa'a ta kai ta aka yi mata, bazama ta yi neman magungunan gyara. Ya lallaɓata ta gyara jikinta, ta nemi guri ta kwanta, ya rasa abin da yake yi masa daɗi. Ya koma part ɗin sa ya rufe ƙofa, kawai ya fashe da kuka. Bai taɓa tunanin aikata zina a rayuwarsa ba, ba ta taɓa burge shi ba, bai kuma taɓa kawo ta a ransa ba. Sai dai yau ya wayi gari da aikata ta dumu-dumu. Sai dai wani abin mamaki duk da abin da ya faru a tsakanin su, bai daina jin matsananciyar ƙaunar Jamila ba. Ya rasa dalilin da ya sanya Mummy ba ta son alaƙar su, duk da irin kusancin da yake tsakaninta da Jamilar. A kwance Hajiya Sa'a ta dawo ta tarar da Jamila. Ta ce "Daughter haryanzu jikin ne? Ko Asibiti za mu je ne?" Ta girgiza kai ta ce "A'a Mummy na sha magani ai" "Yakamata ki warke, mun kusa zuwa taron ƙungiya fa na shekara, lokaci ya kusa" Kawai Jamila ta gyaɗa kai. "Ga shi kuma haryanzu babu wani labari da ki ka samo, a kan 'yar uwakki, dan haka sai ki shirya sadaukar da jini" Jamila dai ta yi shiru, tana jin kamar ta kashe tsinnaniyar matar ta huta. ***** Nana na zaune tana shayar da Muhsin, Nene tana gefe tana lissafa kuɗin da aka kawo mata daga gurin sayar da Abincinta. Nana ta numfasa ta ce "Nene wai me yasa kwana biyu ba kya fita gurin Abinci ne?" Nene ta kalle ta ta ce "Na fita ki samu damar guduwa ko?" Nana ta yi turus tana kallon Nene. Nene ta yi murmushi ta ce "Yarinyar nan ki na wasa da ni, tuni na gane duk wani take-taken ki ai, jira nake yi na ga iya gudun ruwanki. Ke yanzu idan ki ka fita gidan uban wa za ki je? Ki na da tabbacin za ki iya sake haɗuwa da mutanen da za su kula da ke ne? Ko an gaya miki kowa ne zai iya yin taimako? Kin tattara kayanki gaba ɗaya, kina ɗauke ɗanki daga ɗakina, jira ki ke yi ki samu dama ki gudu, to ki tafi duk inda za ki tafi, amma ba za ki tafi da jaririn nan kina gararanba a gari ba, tun da duk ƙoƙarin da nake yi a kan ki ba kya gani. Kina zaune a nan na saka ana ta yi mini cigiyar masu gadi da suke zuwa Nigeria, ko akwai wanda ya san mai suna Habu ko Sayyid ki ka ce sunansa ko wa? Anma ba kya gani, to ki fita ki tafi duk inda ki ka ga dama, tun da ba ki da kan gado, kuma ba ki san darajar igiyoyi ukun da ke kan ki ba" Nana ta sha jinin jikinta, da faɗan da Nene take yi mata. Ta ce "Dan Allah Nene ki yi haƙuri, na ga na ɗora miki ɗawainiya ne ga shi haryanzu ina zaune babu wani labari a kan sa". "Ni na ce kin ɗaura mini ɗawainiya ne uwar iya? Ki yi duk abin da ki ka ga dama" Nana ta ce "Dan Allah ki yi haƙuri ba zan sake ba" Nene ta yi mata shiru, daidai lokacin kuma Muhsin ya gantsarawa Nana cizo, da 'yan haƙoran da suka fara leƙowa. A fusace ta dake shi a kan pampers ɗin jikinsa, ta cire shi daga jikin Nonon, ta zaunar da shi tana ƙara tsuke fuska tare da hararsa. Sexy eyes ɗin sa irin na mahaifinsa ya zuba mata, yana kallonta ko ƙiftawa ba ya yi, gaba ɗaya ya rikiɗe fuskarsa ta koma ta Sayyid sak, farar fatarsa ta yi jawur. Nene ta ce "Yaka yaron kirki, ka ƙyale ta da halin ta, shi ne za ki huce a kansa, ai ni na yi miki ba shi ba" Ya rarrafa ya koma jikin Nene ya kwanta yana ci gaba da kallon Nana. Sai kuma jikinta ya yi sanyi ta ji zuciyarta ta yi mata nauyi da abin da ta aikata, ba tare da duba ƙanƙantar ɗan yaron nata ba. Ta shige ɗakinta ta mayar da kayanta da ta haɗe guri ɗaya inda suke. Wayarta ta ɗaukko da babu layi a cikinta, ta duba jakarta ta ɗaukko memorynta ta mayar kan wayar, ta fara duba hotunan Sayyid da ke ciki. Har da hotunan  Haidar ɗan gurin Shukura a cikin wayar, da hotunanta na aure da aka yi mata da wayar. Gaba ɗaya ta ji tana kewar ƙasa Nigeria, amma hakan bai sanya ta ji za ta iya komawa a yanzu ba. Tunaninta ya katse bayan da ta ji muryar wata ƙawar Nene a tsakar gida, wadda ita ta yi hanyar kai Nana gurin koyon girke-girke. Amma Nana ta ƙi fitowa. Hira suke yi da Nene, take ba ta labarin ma'aikata ake nema, wanda suka iya girki sosai a wani restaurant, na wata Hajiya a can cikin birnin Maraɗi. Nene ta ce "Ba na yi wa Nana irin wannan harkar ne, saboda mutanen banza, ba dan haka ba ai da na ce ta je, tun da ta iya girki sosai" Matar ta ce "To ai a ɓangaren girki kawai za ta zauna, su na buƙatar kuku amma mai tsafta wadda ta iya girki, kuma tana biya sosai kin san buzayen nan kamar ba su san ciwon kuɗi ba, buzuwa ce mai gurin" Nene ta ce "Ai kin ga tana da yaro, shayarwa take yi, ai da na ce a kaita, amma idan za su ɗauke ta da yaron shikenan". "Anya kuwa, gaskiya ba na tunanin haka, ba ma za su yadda ba. Idan ta tafi a ƙalla za ta iya yin wata, ba ta zo gida ba, za a ba ta komai a can. bari na tashi na tafi dama tsayawa na yi mu gaisa sai anjima" Suka yi sallama matar ta tafi. Nana ta fito da sauri ta ce "Nene, ina son zuwa gurin abincin buzayen nan" Nene ta ce "Kin yarda mijin naki buzu ne kenan? Daga an ce gurin buzuwa kin rikice za ki je, bayan da kin ce mini ba ki san ƙabilarsa ba, Allah dai ya shirye ki." Nana ta yi shiru, tana mamakin yadda aka yi Nene take iya gano ta idan ta yi mata ƙarya. Nana tun dukan da ta yi wa Muhsin, juyin duniya har la'asar bai ƙara waiwayarta da sunan ta shayar da shi ba. Sai da ta ji sun cika, sun fara damunta, sannan ta ɗauke shi ta ba shi, amma fafur ya ƙi karɓa, ta kaɗa ta raya ya ƙi sha. Nene tana kallon su, ta ƙi magana, ta dama masa kunu ta haɗa da nono ta zaunar da shi ta ba shi ya sha, ya ci gaba da wasan sa. Nana ta ga sun mayar da ita saniyar ware ma. Har garin Allah ya waye, bai saurari Nana ba. Ta sake ɗaukarsa, saboda yadda nonon ya cika, yake yi mata ciwo, amma fafur yaron nan ya ƙi sha. "Dan Allah yaron kirki ka yi haƙuri ka sha, ba zan sake dukan ka ba, dan Allah ka sha ba ka isa yaye ba" Nana ta yi maganar cikin damuwa. Nene ta kwashe da dariya, ta ce "Kin ga ki ƙyale yaron nan, ina ga fa ya yi zuciya ya yaye kansa, sai dai yi haƙuri" Kamar Nana za ta yi kuka ta ce "Nene wata takwas sai ya yaye kansa? Ya yi wuri ai" "To ba ke ki ka janyo koma mene ne ba?, tun da kin ce da babansa yake kama komai da komai, wataƙila har halayensa ya ɗaukko, kuma wataƙila wannan abin da ya yi akwai abin da yake nunawa bamu gane ba. Tun da yana shan kununsa, yana rarrafensa, ki rabu da shi kawai. A haɗa sabaya da sauran saiwoyi, ki yi ta sha saboda kar su lalace". Kamar Nana za ta yi kuka ta ce "Nene wata takwas fa" "To ai ga ki nan ga shi. Sai ki ba shi ya sha ai" Da Nana ta ɗauke shi da nufin, ta shayar da shi, sai ya hau zunduma ihu,yana turjewa sai dai ta ƙyale shi. Nana ta din ga jinjina yadda aka yi, ɗan wata takwas ya san ya yi zuciya da abu. Sai da aka kwana huɗu, Nana ta ga da gaske ya yaye kansa, iyaka ya zo jikinta ya yi wasan sa ya tafi. Nene ta ce "Nana ki daina damuwa fa, girmansa tubarkallah da ƙiriniyarsa kamar ta ɗan shekara guda ce, ki rabu da shi kawai, daga yanzu idan za ki yi magana ki din ga yi masa da girmamawa, ki daina yi masa tsawa, manya ba sa son wargi. Kuma ki din ga duba darajar sunan da ki ka sanya masa" ta yi maganar tana yi wa Muhsin rawa. "To Nene sai na bari ya lalace ba zan ce masa bari ba?" "A'a ban ce kar ki ce masa bari ba, amma a wannan yanayin shi sarki ne, abin da yake so haka za ki yi haƙuri ki yi masa. Da kin tsaya a zare masa ido kawai da haɗe rai, amma saboda na yi miki faɗa, ki ka haɗa masa da duka, kuma ki ka ƙwace ki ka dungurar da shi, dole ya bar miki abin ki ai". Nana kalle shi yana ta wasa da kofi, yana bugawa a ƙasa, shi ma ya ɗago ya kalle ta. Sayyid ta tuna lokacin da ya ritsa ta yana yi mata kashedin a kan daina yi masa tsawa ko ɗaga masa murya. Wani guntun murmushi ya suɓuce mata. Nene ta ce "Ni kuwa Nana ga shawara" Ta ce "To Nene" "Kamar yadda ki ke faɗa motsi ya fi laɓewa, na ce ko dai za a jarraba ki je gurin aikin nan, na harkar dafe-dafen ko Allah zai sanya a dace. Duk da ba na jin a jikina, masu kuɗi a cikin buzaye masu katafaren gurin abinci, za su iya tafiya aikin gadi, amma bamu san ina rana za ta faɗi ba" Nana ta ɗan yi jimm sannan ta ce "Ban san ya zan yi ba ne, tun da kin ga ga Muhsin. Ko za su din ga bari na je na dawo kullum?". Nene ta ce "Ki na ji fa ta ce sai ki yi wata ba ki zo gida ba, kuma akwai tazara a tsakaninmu sosai, kuma ba zai yiwu ki tafi da Muhsin ba, ba za su yarda ba. Amma ga shawara idan kin ga kin yarda da ni, ki bar mini Muhsin a nan, ki je ko ai kin na wata uku ki yi, ko Allah zai sanya a dace, sai ki ci gaba da cigiyarsa a gurin." Ayshercool 08081012143 67 Nana ta yi turus, tana kallon Nene. Nene ta ce "Ba zan yi miki dole ba, dan kuwa wannan magana ce da kowacce uwa sai ta jinjina girmanta da nauyinta. Sai dai ni ba zan takura miki ba kuma ban ce sai kin yadda da ni ba, ko mene ne za mu yi shi ne a gaban hukuma, mu je mu yi yarjejeniya mu saka hannu sannan ki tafi. Ban san dalilin da Allah ya sanya ya haɗa ni da ke ba, duk rashin son mutane na, ki ka shiga raina ba nake tausayinki ke da yaronki. Har ga Allah ina fatan ki haɗu da mijinki ko danginsa, ki samu ki koma gida ki nutsu ki kula da yaronki. Kamar yadda na gaya miki ne, ba zan yi miki dole ba, ki je ki yi shawara idan kin amince shikenan, idan ba ki amince ba babu wani abu, ni dai fatana Ubangiji Allah ya bayyana abin da ki ka fito nema". Nana ta yi shiru, ƙwaƙwalwarta gaba ɗaya ta ɗauki caji da tunani daban-daban. **** Jamila kuwa tun da ta je gida, Mama take tambayarta ko lafiya ta ganta wani iri, amma ta ce mata babu komai. Ta shiga ɗaki ta nemi guri ta kwanta, sallolinta kawai ta yi na magariba da isha'i ta sake kwanciya. Gaba ɗaya abin Duniya ya gama damunta, dana sani da takaici duk ya cunkushe mata zuciya. Wayarta ce ta fara ringing, ta duba ta ga baƙuwar lamba ce, jikinta ya ba ta Abba ne, ta ɗaga kiran ta saka a kunnenta. Muryarsa ƙasa-ƙasa ya kira sunanta ya ce "Ya jikin naki?" "Da sauƙi" ta amsa a hankali hawaye na ci gaba da gangarowa kan kumatunta. "Dan Allah Jamila ina ƙara ba ki haƙuri, kuma ki dubi girman Allah ki rufa mini Asiri, ke ma kin san hakan ba halina ba ne ba. Wallahi na rasa inda zan sanya zuciyata na rasa abin da yake yi mini daɗi. Yanzu haka zazzaɓi ne a jikina. Dan Allah ki yafe mini Jamila, na san koma mene ne duk laifina ne. Amma in sha Allah kamar yadda na yi miki alƙawari zan aure ki Jamila, wallahi ina son ki, duk abin nan laifin Mummy ne amma ki yi haƙuri ki yafe mini" Jamila ta ci gaba da kuka, ta kasa ce masa komai, ya ƙara ruɗewa ya ce "Dan Allah ki yi mini magana, dan Allah ki yafe mini idan ba ki yafe mini ba na san har na koma ga Allah, ba zan samu nutsuwa ba" Ya yi maganar yana kuka mai cike da nadama tamkar ƙaramin yaro. Duk yadda Jamila ta so jin haushinsa sai ta kasa, tabbas ita shaida ce wannan ba halin Abba ba ne, dan da halinsa ne da ba zai din ga wannan kukan ba, zai ga ya ci bulus ne kawai. "Yaya Abba na yafe maka, mu haɗu mu nemi yafiyar Allah, sannan ka daina kukan nan dan Allah, ka sha magani ka kwanta. Kuma Asiri idan na tona kaina na tonawa ba kai ba, Ubangiji Allah ya yafe mana" Ya tashi zaune a kan gadonsa, cikin damuwa ya ce "Da gaske kin yafe mini Jamila?" "Eh Yaya Abba, sai da safe, kaina yana ciwo sosai" "To na zo na kai ki Asibiti ne?" Jamila ta ce "A'a, na sha magani ina jin bacci ma, sai da safe" ta katse kiran tana ƙara duƙunƙunewa a cikin bargo. Wata irin ajiyar zuciya ya din ga yi, ya nemi guri shi ma ya kwanta, zuciyarsa fal tunani daban-daban. ***** Nana hankalinta ya rabu kashi-kashi, a jikinta ba ta jin Nene za ta cutar da ita, duba da yadda take ɗawainiya da ita da ɗanta, tamkar ita ta haife ta. Sai dai ta yaya za ta iya ta tafi ta bar ɗan ta, da matar da babu dangin iya babu na Baba a tsakanin su. Sai dai tabbas akwai buƙatar ta gusa, ta yi wani yinƙuri, domin ci gaba da ƙoƙarin haɗuwa da mijin nata, amma ba ta ji ta gamsu da wannan shawarar ba. Sai dai tun da suka yi maganar nan, da ta kwanta take mafarki ga ta a gurin girke-girken, tana cikin gurin girkin, ta waje sai ga din ga jiyo muryar Sayyid yana magana. Idan ta fita sai ta neme shi ta rasa, sai dai ta ci gaba da jin muryar ta sa, nesa da ita kaɗan, sai dai ba ta san daga wane ɓangaren muryar tasa take ba. Sai ta yi irin wannan mafarkin sai ta farka. Ta rasa abin da yake yi mata daɗi, kawai sai ta ci gaba da addu'a a kan lamarin, ta juya ta ci gaba da bacci, sai dai babu tsammani sai ga ta a ɗakin karatun Ƙaisar, an yi mata gyara sosai, an ƙara yawan litattafan da suke ciki. Ya saka mudubinsa a gaba, yana ta zuba masa wani ruwa yana wanke shi. Bai ce wa Nana komai ba, har ta gaji da tsayuwa, ta ɗan yi gyaran murya. Ya ɗaga kai ya kalle ta. Ta ce "Sannu da aiki" "Yauwwa" ya amsa yana tashi tsaye. Ta ce "Kwana biyu ina ka shiga ne?" Ya ɗaga kai ya kalle ta ya mayar ya sunkuyar yana ɗaukar wani littafi. "Amm dama ina ta son na ganka, na tambaye ka, sannan na roƙe ka alfarma. Dan da kai da Giyaz da duk wani mai son ɗaukar fansa a kan zuriyarmu, ya ɗauka a kaina, dan Allah ku ƙyale mini yarona. Na ga rannan ka ba shi wani abu da ban san ko mene ne ba, dan Allah kar ku yi masa komai" Bai ko motsa ba, balle ta sanya ran zai yi mata magana. "Ƙaisar ka yi magana ma dan Allah" "Na ce miki ne? Ko har kin manta abin da ki ka faɗa a kaina, saboda abin da na yi wa mahaifina a kan na kare ki?" Sai kuma Nana ta yi shiru, ta sha jinin jikinta. Ya wurgo mata littafin nan da ta fara karantawa, ya ce "Ga wannan ki ci gaba da karantawa, wataƙila zai yi miki amfani a gaba" Ta kalli littafin ta kalle shi, ta ce "Me yasa ka amince na karanta wannan littafin, wancan kuma ka hana ni karantawa? Ni ba zan iya ci gaba da karantawa ba, babu komai a ciki sai tashin hankali da zubar da jini na tsagwaron rashin tausayi da adalci, ni bai burge ni ba, ba zan karanta ba" "Ko? Amma idan an yi magana sai ki nuna kamar babu wata halitta da ta kai ɗan Adam tsarki da tsoron Allah. Allah ya karrama ɗan Adam a kan dukkanin halittunsa. Amma ba duk ɗan Adam ne mai tsarkin zuciya ba. Wannan zubar da jinin da kashe-kashen da yake rubuce a cikin littafin nan, da gaske an yi su, domin cimma buƙatar Duniya, kuma haryanzu ana kan yi ma. Abu ne da ya faru wani ƙarni a baya, kuma abin yake ta bibiyar zuriyar har wannan zamanin. Na ce ki karanta kin ƙi, kin ce ba kya so shikenan ba zan yi miki dole ba, amma bari ki ga wani abu. Ya ɗauki littafin ya buɗe cikin wani feji, ɓangare ɗaya na bangon littafin zane ne, ɓangare ɗaya kuma bayanin yadda taswirar zanen take ne. Ya haska littafin a jikin mudubin. A nan take hoton ya bayyana a jikin mudubin, wannan ɗakin da take ganinta a ciki ita da Sayyid shi ne ya bayyana a jikin mudubin, ba iya haka ba har ƙamshin da gurin yake yi ta fara ji a hancinta. A rikice ta ce "Nan gurin? Dama ina son sanin ina ne, yaya aka yi muke zuwa gurin nan ni da Sayyid, kuma idan abu ya faru a gurin kamar gaske." Ƙaisar ya rufe littafin ya ce "Ai kuma kin yi wa kan ki, ba zan bayar ba. Ya jefa littafin sama ya ɓace ɓat ita kuma ta tashi daga baccin. **** Kwana biyu Jamila ba ta je gidan Hajiya Sa'a ba, saboda jikinta da ya matsa, idan Abba ya kira wayarta a kashe, ga shi ba ta zuwa gidansu, shi ba abin ya tambayi Mummy ba. Yana kwance a ɗakinsa, ya tura mata saƙo. "Hankalina a tashe yake ƙanwata, dan Allah ki yi mini ko flashing ne, hankalina na matuƙar tashe dan Allah ki ɗaga wayata" Ya tura mata saƙon, tare da ajiye wayar. Hajjya Sa'a ce ta shiga ɗakin nasa, ta iske shi a kan kujera. Yana ganinta ya tashi zaune. Daga tsaye ta ce "Abba ba zaka fita bane? Baka fito ka karya ba, kuma baka fita kasuwa ba meyafaru ne?" Ya girgiza mata kai ya ce "Babu komai fa" "A'a akwai wani abu, na kasa gane kan ka 'yan kwanakin nan, hatta shirin bikinka nikaɗai nake abina, me yake damunka? Duk saboda Jamila ne?" Ya girgiza kai ya ce "Ba kin ce ba kya son alaƙarmu ba, ni kawai ba ni da lafiya ne" ta yi shiru tana nazartarsa, kawai ta yi ƙwafa ta fice daga ɗakin. Ya koma ya jingina, ya lumshe idanunsa, sai kiran Jamila. Ya ɗauka ya katse kiran ya kira ta cikin azarɓaɓi ya ce "Ƙanwata lafiya kuwa? Ba kya ɗaga wayata ko haryanzu kina fushin ne?" Cikin numfarfashi ta ce "A'a Yaya Abba, ba ni da lafiya ne haryanzu" "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ya aka yi ba ki gaya mini ba? Kina gida ne?" "Eh" ta amsa muryarta ƙasa-ƙasa. "To shirya gani nan, bari na zo mu je Asibiti" "To Yaya Abba, na gode" ta ajiye wayar da ƙyar. Hankalinsa ya yi mummunan tashi, a zatonsa aika-aikar da ya yi ce, ta sanya mata rashin lafiya har haka. Da sauri ya zura kaya, ya ɗauki mukullin motarsa ya yi waje ya tafi gidansu Jamila. Yanayin yadda Jamila ta fito, tamkar ya je ya ɗaukko ta, fuskarta duk ta kumbura, da alama tana jin jiki sosai da sosai. Ya buɗe mata gaban motar ta shiga. Cikin tausayawa ya ce "Sannu ƙanwata, haka jikin naki ya yi ba ki gaya mini ba?" "Ba na son tayar maka da hankali ne, kai ma ba ka da lafiya, amma Mama fa ta kai ni Asibiti" Gabansa ya faɗi ya ce "Allah ya sa ba ta gane komai ba" Ta girgiza kai ta ce "Babu abin da ta gane, zazzaɓi ne fa kawai" A tsorace ya ce "Jamila ko ciki ne?" Ta kalle shi, sai da ta ji kamar ta yi dariya, duk da halin da take ciki. "Tun kan hakan ta faru ai nake rashin lafiya, ba wannan ba ne ba, ba wani ciki". Ya sake cewa "Amma duk da haka kamar ya assasa miki ciwon, amma bari mu je Asibitin" haka ya ja motarsa su ka bar layin. Safiyya ce ta tarar da Hajiya Sa'a ta cika ta yi fam, tana zaune a falonta. Da kyar Hajiya Sa'a ta iya amsa mata sallamarta. Ta zauna a kusa da Hajiya Sa'a ta ce "Mummynmu maganin kukanmu, lafiya kuwa na ga ranki a ɓace?" "Ba dole ki ganni a haka ba? Da gaske fa Abba son Jamila yake yi, nema yake ya bujire mini, kin ga yadda duk ya damu saboda na raba su. Ga bikinsa na ƙaratowa da Yasmin. Maman Khairat ta tuntsure da dariya ta ce "To meye a ciki, idan tana son sa ki bar su mana" Hajiya Sa'a ta kalle ta ta ce "Amma ba ki da hankali, yarinyar da shugaban ƙungiya suka kwanta da ita, sai Abba ya auri ragowa? Ba ma wannan ba, kar ki manta idan ƙungiya ta buƙaci ta bayar da jininsa fa, shikenan ta bayar da jinin tilon ɗan nawa?" Maman Khairat ta ce "Na fahimce ki Mummy, da wasa nake yi miki, amma maganar gaskiya yanzu haka kan na taho ma, na ga motar Abba a unguwarmu, kuma na san ba ku da kowa a unguwar, dan haka gurin Jamila ya je" Cikin matsanancin ɓacin rai ta ce "Gurin Jamila kuma? Yarinyar nan ta zame mini masifa da bala'i ko? Maganinta zan yi, wallahi sai ta rabu da Abba, ko ita ta haifar mini shi" Maman Khairat ta ce "Ki yi dai a hankali, kin san halin yaran zamanin nan" Hajiya Sa'a ta ci gaba da huci, tamkar macijiya saboda takaici. Maman Khairat ta ce "Ina dai ƙara gaya miki, ki bi komai a sannu, kin san halin yaran zamanin nan, sai su baki mamaki. Shi kansa Abban duk yadda yake yi miki biyayya, idan ba ki yi wasa ba, a wannan karon tsaf zai bujire miki". "Ai ga alamu nan ina gani, amma ni zan sanya wa Abba doka, na hana shi abu, amma ya zagaye ya je ya aikata? Shikenan, na san matakin da zan ɗauka. Da ni suke zancen. Alhaji Fatuhu ne zaune a harabar gidan sa, a kan kujera, ya kan ɗan iya dogara sanda ya tashi tsaye yanzu. Idan aka taimaka masa har harabar gidan yake iya fitowa, duk da idan jikin ya tashi kuma, sai ba ya iya hakan ko kaɗan. Yana zaune a harabar gidan, yana kallon ƙaramin ɗan sa na gurin Fadila, yana ta wasa da Ball, yana jin yadda ƙaunar ɗan ke ratsa masa zuciya. Gefe guda yana tausayin yaron nasa, dan bai taɓa iya saya masa abin naira biyar ba da kuɗinsa. Hatta abincin da suke ci, 'yan uwa da abokan arziki ne suke kawo musu, ga shi wanda ya sai gidansa ya ba du aronsa suke zaune a ciki, ya fara ƙishin-ƙishin ɗin yana buƙatar gidan. Fadila ce ta ƙaraso tana murmushi ta ce "Daddy kallon Ball ka ke yi?" Ya yi murmushi ya ce "Eh mana, yana ta in tashi mu yi tare, ina ma zan iya da ko sau ɗaya mun yi tare, no na saka shi farinciki" Ta zauna a ɗaya daga cikin fararen kujerun, ta ce "A hakan ma, ka na sanya shi farin ciki ai" "Fadila" Ta tattara masa nutsuwarta ta ce "Na'am Daddy" "Kin san wani abu?" Ta ce "A'a sai ka faɗa" "Ina yarinyar nan Nana?" "Wace Nanan?" Ya ɗan yi shiru sannan ya ce "Malamar Muhsin, da yake faɗa" Ta ce "Ohh Allah sarki, na tuna ta" "Mafarkinta nake yi" Ta ɗan yi saroro ta ce "Mafarki kuma?" "Eh Fadila, har aikawa na yi gidansu, a yi mini alfarmar a faɗa mini inda gidanta yake, wani abu nake gani da ya fara damuna" Ta danne kishinta ta ce "To ka yi mini bayani mana" "Kin dai san ni ba ma'abocin, biye-biye ba ne ba, da yarda da harkokin shirme da zai sanya na ji wani zai iya cutar da ni ba, amma a jere sau kusan biyar ina mafarki da ita". Cikin ƙosawa ta ce "Daddy ka yi mini bayani, ka na ta kwana-kwana da ni" "Ganinta nake yi a mafarki, tana ce mini an yi mini sihiri, karo kusan biyar fa" Fadila ta yi ajiyar zuciya ta ce "Kuma ka yarda?" "Ba ma son na yarda na gazgata hakan, amma na ji kamar na fara amincewa, saboda yadda nake ganinta abin ya yi yawa, ya wuce a ce shirmen mafarki ne kawai." Fadila ta numfasa ta ce "Ai ni tuntuni na zargi hakan, amma sanin halinka na rashin son irin wannan abubuwan, ya sanya ba na yi maka maganar. Ko wannan sauƙin da ka ke samu, na san tasirin addu'a ne. Dan kuwa Umma kuɗi take bayarwa ana sauke karatun Alqur'ani." Cikin mamaki ya ce "Amma ke kina ganin, akwai wanda zai damu da ni, har ya iya yi mini sihiri? Ina azkar ɗina da addu'oina, gani nake sun wadace ni, babu wanda zai damu da ni ya yi mini wani sihiri." Ta gyara zamanta sosai ta ce "A duk Duniya waye ya koyar da mu azkar ɗin? Na san za ka ce manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam, amma an yi wa fiyayyen halitta sihiri, kuma ya kama shi. Daddy ka yi haƙuri da abin da zan faɗa maka. Kana ibadarka ta farilla daidai gwargwado, amma ba ka damu da nafilfili ba, da tsananta addu'a. Kana ganin Allah ya baka duk abin da ka ke buƙata, ba ka fiye tsananta addu'a da neman kariyar Allah ba. Sannan azkar da ka ke yi, kuma a yi shiri ya kama ka, ba ya nufin Allah baya kare ka, amma wataƙila jarrabawa ce daga gare shi, kamar yadda ya ce zai jarrabe mu, ba a fasa jarraba mai imani, kuma jarrabawa alama ce ta soyayyar Ubangiji. Allah ya jarrabe ka da cuta, ka nemi magani shi ma a cikin jarrabawa ne, amma Daddy ka naɗe ka dage, kai sai na Asibiti kawai, bayan akwai magungunan musulunci da suke na halal babu kauce hanya, idan an jarraba ba a san inda za a dace ba, amma ka ƙi ka ce kai sai na bature, na baturen kuma ba a gano komai ba, kame-kame kawai ake yi." Ya yi shiru yana nazarin kalaman Fadila, ya numfasa ya ce "To yanzu mene ne abin yi? Kin ga yanzu bani da kuɗi, kuma irin wannan abubuwan sai da kuɗi". "Kar ka damu, zan yi wa Kawu magana, shi ma ranar da ya zo duba ka, ai ya ce a yi na islamic, Alhaji Zailani ya ce ba za a yi ba. Da haka za tuntuɓe shi, in sha Allah ba zai gagara ba" Alhaji Fatuhu ya ce "Allah ya sa, dama duk ina tsoron, kar a aikata abin da zai kauce wa hanya ne, amma na amince yanzu a yi ɗin" Ta yi murmushi ta ce "To shikenan, yaya ita yarinyar an gano ta ɗin?" Ya girgiza kai ya ce "Ina fa, an ce wai ba ma ta ƙasar nan, amma ina ta mamakin dalilin da ya sanya nake mafarinta, kuma idan na farka sai na ji kamar a zahiri, shi ya sanya ma na fara yarda" Fadila ta ce "To Allah ya sanya a dace" ya amsa da "Amin" ***** Ɓangaren Nana kuwa, gaba ɗaya kanta ya kulle a kan lamarin nan, kawai sai ta dasa addu'a, a kan idan da alkhairi a tafiyarta, Ubangiji Allah ya sanya mata son tafiyar, ya tsare mata Muhsin, idan kuma babu, Allah ya cire mata abin daga zuciyarta. Kamar yadda ta saba ji haka ma wannan karon, ta ji muryarsa, da gudu ta ajiye abin da take yi, ta nufi taga ta leƙa sai ta hango giftwarsa da doguwar riga baƙa a jikinsa. Da gudu ta fita daga gurin, ta nufe shi tana ƙwala masa kira, amma ya ɓace mata. Cike da takaici ta yi juyi, tare da jan guntun tsaki, kawai ta ji hancinta ya fara shinshino mata, ƙamshin wannan ɗakin na cikin dutse, da take ganinsi tare da Sayyid. Ta buɗe idonta a hankali, ta ji ana shafar cikinta a hankali, tare da yi mata numfashi a wuyanta. "Sayyid" ta furta a ɗan tsorace. "Asmyna, ina kewarki da yawa, gangar jikina na ta kewarki. Idan ina jin zafi babu mai bani sanyin da ki ke bani, babu wanda yake iya fahimtar kurman baƙin rayuwata, ki ƙaraso gare ni Please" ya yi maganar yana shafa wuyanta, tare da yin maganar ƙasa-ƙasa. Ta saka hannu ta shafa gashinsa ta ce "Ina ta gaya wa Allah Sayyid, ya san lokacin da ya dace ya haɗa mu, amma jikina yana ba ni, ina daf da kai in sha Allah" "Ki ƙaraso da wuri Asmyna, ina cikin matsananciyar buƙatarki" "Ina ta ƙoƙari Sayyid, kuma ina gaya wa Allah, na san zai haɗa mu a nan kusa, kuma ina roƙonsa ya kare mini kai a duk inda ka ke, na san kuma yana ji ya kuma amsa in sha Allah" "Nana, wai ba kya salla ne, gari ya fara haske fa" ta ji muryar Nene. Ta tashi tana mustustuke idonta, hancinta na ci gaba da jiyo mata sauran ƙamshin turaren nan. Da ta yi salla ta idar, ta je ta samu Nene a ɗakinta, suka gaisa. Ta ce "Nene na amince" "Da me?" "Zan tafi gurin yin girkin nan" Nene ta ce "Ina fatan ba wani ne ya matsa miki ba? Ko kuma kunyata ki ka ji ba ki ka ce za ki je?" Nana ta girgiza kai ta ce "A'a, wa ma na sani na saba da shi, da zai ziga ni na ɗauka? Babu wanda ya ziga ni" Nene ta ce "To shikenan, zan kira ta a waya na ji, idan ba a samu wata ba, sai ki je. Sai mu je gurin jami'an tsaro mu yi yarjejeniya mu yi rubutu, mu je a yi a gaban su Auwwalu ma da Hajara" Nana ta girgiza kai ta ce "A'a Nene, na yarda da ke, abin duk bai kai haka ba ai" Nene ta ce "A'a, haka kurum wani irin ki ka yarda da ni, ɗan mutum fa zan riƙe miki, a'a, mu je mu yi a rubuce, yadda jami'an tsaro ma za su din ga sanya ido, kar wani abu ya faru ma. Sai dai abin da Allah ya aiko na ƙaddara wannan ba yadda muka iya, kuma na san za ki yi mini uzuri a wannan. Amma idan aka yi haka kema sai kin fi sakewa, hankalinki ya kwanta. Nana ta jinjina kai ta ce "Ni dai, bakin da zan yi miki godiya ba ni da shi, amma ina fatan Allah ya yi miki tukuici da abu mafi dacewa da abin da ki ka yi mini na alkhairi, a duniya da kuma Lahira" "Amin Nana, ai ɗa na kowa ne, Allah ya tabattar mana da alkhairinsa, ya kuma bayyana miki mijinki da ahalinsa cikin aminci". "Amin uwata ta kaina" ta yi maganar tana murmushi. Sai dai tun da Nana ta amince za ta bar wa Nene Muhsin, ta fara jin kewar ɗan nata, ta din ga jin kamar ta ce ta fasa. Saboda kallonsa kawai na sanya mata matsanancin farinciki da nishaɗi, idan ta tuna mallakinta ne shi ɗin. Tana jin ko ba ta ga Sayyid ba tana da ƙaramin Sayyid, duk da tana fatan ta gan shi ɗin, ko ba komai al'umma sa kalli ɗan nata da kima da daraja. Ko da Nene ta kira matar, Matar ta tabbatar wa Nene, akwai sauran space ɗin da Nana, za ta yi musu aiki, sai dai a saka ranar da za su tafi ta kai ta. Haka nan fargabar Nana ta ƙaru, ta rasa murna take ko tsoro, duk da abu mafi rinjaye kewar ɗan jaririn ɗanta ne, da yanzu take ƙara shaƙuwa da shi,ƙaunarsa take ƙara shiga ranta. Tana jin tamkar ta fasa tafiyar nan, amma ƙasan zuciyarta tana jin tafiyar ta ta alkhairi ne. ***** Ɓangaren Abba kuwa, sai da aka yi wa Jamila ƙarin ruwa, typhoid ne ya yi mata mummunan kamu. Sai kuma damuwa da take ciki, jininta ya ɗan hau. Abba ya biya duk bills ɗin, ya janyo kujerar ɗakin, ya zauna a gaban gadonta, ruwan da aka saka yana shiga jikinta. "Ko a kira Mama a waya a sanar mata ne?" Ya yi maganar cikin kulawa. Ta ce "A'a, na gaya mata Asibiti zan je, ana gamawa sai ka mayar da ni gida" Ya ce "To shikenan, mai zan sayo miki ki samu ki ci?" "Ba na son cin komai, kawai kar ka matsa daga kusa da ni, ka zauna a nan" ta yi maganar tana riƙe hannunsa a cikin nata. Ji ya yi zuciyarsa ta narke, da matsanancin tausayin kan su, ya ce "Ina tare da ke matata, har abada in sha Allah" ta yi murmushi tana ƙara riƙe hannunsa. A hankali kuma ta saki hannun nasa, da tuna rashin dacewar hakan, sai dai wani irin abu mai wuyar fassara take ji, game da Abban. Yana kallon kiran Hajiya Sa'a, amma ya ƙi ɗagawa, kawai ya din ga jin zafinta. Har azahar sannan ruwan da ake saka mata ya ƙare, ya ɗauke ta a motarsa, ya yi mata sayayya sannan ya mayar da ita gida. Sai da ya tabattar ta shiga gida, sannan ya kira Mummy. "Sai yanzu ka ga damar ɗaga wayar tawa?" "A'a caji take yi ne, ki yi haƙuri?" "Kana ina ne?" Ya ce "Na ɗan je wani uzuri ne, na zo ne?" "A'a shikenan" ta ƙyale shi, bayan tuna shawarar da Safiyya ta bata, wato maman Khairat. ***** Kamar yadda Nene ta buƙata, sai da suka je gurin jami'an tsaro, suka yi yarjejeniya, aka rubuta da yaren hausa, French da kuma turanci, duk suka sanya hannu, a gaban su Auwwalu da jami'an tsaro. Daga nan suka dawo gida Nene ta ba wa Nana wata 'yar madaidaiciyar Jaka, da za ta haɗa kayanta da za ta buƙata a ciki. Ta kalli Nana ta ce "Nana dan Allah ki kula da kan ki, duk da na san ke kamammiyar yarinya ce, ba mutuniyar banza ba, amma tunatar da mumini abu ne mai kyau, ki riƙe mutuncinki, ki kiyaye hakkin aurenki. Idan ki ka ga wani abu na ba dai-dai ba, ko wanda ya saɓawa addininki, a haƙura da sabgar nan. Kuma cikin hikima za ki din ga bincikawar,ba sai kowa ya fuskanci ainihin abin da ya nai ki gurin bax Nana ta jinjina kai ta ce "In sha Allah Nene zan kula da kaina, ba zan ba ki kunya ba, ki taya ni da addu'a, Ubangiji Allah ya sanya zuwana ya zame mana alkhairi baki ɗaya" "In sha Allah, addu'a ina nan zan ci gaba da yi miki ita da yardar Allah." Nana ta haɗa kayanta, amma ji take kamar ta fasa tafiyar, amma ta ƙarfafi zuciyarta, ta hana hakan yin tasiri a ranta. Ranar Asabar, da safe matar ta zo domin tafiya tare da Nana. Nene ta ce mata "Dan Allah gata nan amana, Hansatu, kar ki kai ta idan za a cutar da ita, kin ga yaro ne da ita ƙarami, dan Allah idan akwai matsala a gurin nan, gara ki saka a sallamo ta ta dawo gida." Hansatu ta ce "Haba Nene, ya ki ke haka kamar ba ki yarda da ni ba ne?" "A'a ba rashin yarda ba ne ba, 'yar amana ce shi yasa nake jadda da miki, ga kuma ƙaramin yaro da take da shi" "Ba ki da matsala fa, ki kwantar da hankalinki" Nana ta kalli Muhsin, da yake jikin Nene, yana wasansa, idanun Nana fal hawaye ta ce "My little Sayyid, zo ka yi sallama da Umminka" ya taso daga jikin Nene ya nufo Nana. Hatta dogayen gaɓoɓin jikinsa, irin na Sayyid ne sak. Ta rungume shi a jikinta, hawaye na zuba daga idanunta "Allah ka kula mini da ɗa na, Allah kar ka saka wani abin cutarwa ya same shi, Ubangiji Allah ka sanya na je na dawo na tarar da shi lafiya" ta furta a hankali ƙasa-ƙasa. Ta ɗago ta kalle shi ta ga yana yi mata murmushi, ta sumbaci goshinsa, ta miƙe ta ɗauki jakar kayan nata, Nene ta rako su har bakin ƙofa, suka hau abin hawan da Hansatu ta zo da shi, suka tafi. 08081012143 68 Nana ta din ga waige, tana hango su Nene tare da Muhsin, har suka ɓacewa ganinta gaba ɗaya. Hansatu su na tafe su na ta  hira da direban motar, aka biya gidanta, aka ɗauki wasu matasan matan sannan suka ɗauki hanyar tafiya. Tana jin yadda suke ta hirarrakinsu a cikin motar, amma ta kasa tofa komai, da ta rufe ido, ɗan jaririnta take hangowa, gefe guda kuma zuciyarta cike da fatan Allah ya sa tafiyar nan, ta yi mata rana. A ƙalla sun yi tafiyar awanni biyu da rabi a mota, sannan suka isa wani gida. Hansatu ta yi musu bayanin, a nan za su sauka su huta, washegari ta kai kowacce inda ta ɗaukko ta za ta kai ta. Nana ta din ga addu'a da fatan Allah ya sanya ba mugun hannu ta faɗo ba, duk da kafin ta taho Nene ta bata layi ta saka a wayarta, ta ce mata duk abin da ta ga ba ta yarda da shi ba, ta kira ta ta sanar mata. A duk lokacin da Nana ta ɗaga wayar ta kalla, sai ta tuna Hajiya Amina, Haidar da kuma sauran jama'arta na Nigeria. A gidan nan suka yi salla, aka ba su abinci suka ci, sai dai Nana ta yi mamaki ganin mata da yawa a gidan. Duk da ƙabilu ne daban-daban matan, akwai Zabarmawa, akwai Bugaje, da hausawa da sauran ƙabilun ma da ba ta sani ba a Nijar. Wai gidan kamar kamfani ne, wannan matan aiki ake nema musu, duk ciki Nana ce kawai 'Nigeria a cikinsu. Gaba ɗaya ta takure kanta ta kasa jikinta da su. Gaba ɗaya daren ranar, Nana ta kasa bacci, ta din ga tunanin Muhsin, da tunanin ko zai yi kukan rashin ganinta. Washegari Hansatu ta ce wa Nana ta shirya, ta ɗauki kayanta su tafi. Haka kuwa aka yi ta sake ɗaukarta su ka fita. Nana ta sha mamaki, ganin haɗuwar da gurin cin abincin ya yi, kuma babban abin da ya ƙara bata mamaki, gurin cin abincin tamkar hotel. Suka shiga cikin gurin, Hansatu ta kai Nana wani katafaren ofishi, da yak3 gurin mai kula da ɗaukar ma'aikatan, da yake namiji ne. Rawaninsa ne ya tabattar mata da buzu ne, ganinsa kawai sai Nana ta ji wani irin sanyi, tamkar ta ga Sayyid. Nana ta gaishe shi, ya amsa sama-sama yana ɗan basarwa. Hansatu ta ce masa "Wannan ita ce ma'aikaciyar, na kawo ta a yi mata gwajin, a gani idan za ku ɗauke ta" Ya ɗaga kai ya  sake kallon Nana ya ce "Sannu ko" Nana cikin girmamawa ta ce "Yauwwa sannu da aiki" Ya miƙo mata ƙunshin wasu takardu ya ce "Ga wannan duba, ki ga yadda tsarin aikin namu yake, ki gani idan sun yi miki, kafin mu je inda za a yi miki gwajin, idan kin ci sai ki sanya hannu a takardun, ki fara aiki da mu" Nana ta saka hannu ta karɓi takardun, amma ta ga rubutun French, ta kalli Hansatu, ta kalle shi ta ce "Ai ban iya fransanci ba" Ya kalli Nana ya ce "Ba ki yi makaranta ba?" Ta ce "Na yi, amma ni ban iya French ba, turanci na iya sai Hausa" Hansatu ta ce "A yi haƙuri Yallaɓai, 'yar Nigeria ce, daga Nigeria take" Sai kuma ya kalli Nana ya faɗaɗa murmushinsa ya ce "Daga Nigeria ki ke? Ki ka baro babbar ƙasa kamar Nigeria ki ka zo jamhuriyar Nijar ki yi aiki da mu?" Nana ta ɗan risunar da kai tana murmushin dole, ganin yana murmushi shi ma. Ya ce "Ahh to ai 'yan Nigeria ƙawayenmu ne, ba ma ƙawaye ba 'yan uwanmu ne. Dan haka zan ba ki aiki amma da sharaɗin za ki koya mini turanci, idan kin yarda na baki aiki" Nana ta yi murmushi, saboda yanayin yadda ya yi maganar cikin zolaya. Ya yi 'yar dariya ya ce "Ai duk wanda ya zo Nijar, mussaman daga Nigeria baƙonmu ne, akwai buƙatar mu karrama shi sosai da sosai, ko dan ƙara zumuncinmu da mutanen Nigeria. Dan haka babu wani abu, wannan wani ci gaba ne ma zan iya cewa gurin Abincinmu ya samu, kin ga girke-girken da ba a yi a nan, na can ƙasar kya din ga yi mana. Mu na da gurin kwana na ma'aikatanmu, awa ashirin da huɗu muke yi mu na aiki. Kamar yadda ki ka gani babban gurin cin abinci ne da manyan mutane ke zuwa cin abinci. Masu sayar da abinci daban, masu girki daban, ke za ki kasance a ɓangaren masu girki ne. Mu je mu zagaya ku ga gurin sosai da sosai. Ya jagoranci su Nana, ya nuna musu gurin, tsarin ya yi wa Nana sosai, duk da abin da ba ta ji daɗi ba, maganar zuwa hutun sati ɗaya ne kacal, duk ƙarshen wata. Su Hansatu za a din ga tura wa albashinta, su cire nasu kason su bawa Nana sauran. Ita Nana duk hakan bai dame ta ba, babban fatanta buƙatarta ta biya kawai. Suka kammala duk cike-ciken da za su yi, aka sallami Hansatu, Nana kuma aka kaita gurin kwanan ma'aikata. Ɗakin da aka kai Nana, su uku ne a ciki, da banɗaki a ciki. Ta ajiye jakar kayanta, Hansatu ta kalle ta ta ce "To Nana, kamar dai yadda ya gaya miki, mu kamfani ne, kuma a ƙarƙashinmu ki ka zo nan, dan haka gurinmu albashinki zai din ga tafiya, mu zamu din ga sallamar ki" Nana hakan ko a jikinta, dan ita ko ba za su ba ta komai ba, indai akwai gurin kwana da abinci, kuma kwalliya za ta biya kuɗin sabulu, hakan ba damuwarta ba ne ba. A fili ta ce "Babu damuwa, hakan ma na gode sosai da sosai, Allah ya saka da mafificin Alkhairi". "Amin, a hakan ma gaskiya kina da sa'a sosai da sosai, sai da muka kawo musu mata uku, da ƙyar suka ɗauki ɗaya, wai duk ba su yi musu ba, wasu kuma sai an zo yi musu gwaji sai su faɗi. Amma ke ya ce ba zai yi miki ma gwaji ba, kawai an ɗauke ki aikin. Abin da zan gaya miki kawai shi ne ki kula, ki kula da kanki sosai da sosai, banda ƙazanta banda son jiki. Sannan kar ki ga kin tsallake wannan matakin, ya ɗauke ki aiki a haka cikin sauƙi, ki zata miƙe ƙafa za ki yi, mace ce mai gurin nan, kuskure kaɗan za ki ta ci mutuncinki ta kore ki. Su kan su ma'aikatan kwantar da kai suke yi, su na yi mata biyayya, duk wata tijara da bala'inta kawai ki toshe kunnenki ki yi haƙuri." Nana ta yi shiru, sai da Hansatu ta gama gaba ɗaya sannan ta numfasa ta ce "To Ubangiji Allah ya iya mana" Hansatu ta amsa da "Yauwwa Amin" Hakanan Nana ta ji a jikinta, ba za ta ɗauki wulaƙanci da cin zarafi ba, duk da kuwa abin da take son cimma. Ko Nene da ake kambama faɗanta da masifarta, ba ta cin mutunci, kuma duk abin da za ta yi faɗa a kai, to a kan gaskiya ne. Amm yanayin yadda Hansatu take yi mata bayanin mai gurin nan, a kaikaice dai ba ta san darajar mutane ba. Ɗakin da Nana take, ita da wasu Zabarmawa ne guda biyu. Ta yi alwala ta yi sallar Azahar. Ta daɗe a kan abin salla, tana gaya wa Allah, cikin magiya a kan ya sanya ta samu abin da ta fito nema, ya kuma raba ta da duk wani sharri da abin ƙi. Bayan ta idar, ɗaya daga cikin 'yan ɗakin, ta ce mata ta zo su je ta zagaya da ita. Can ɓangaren da ake girke-girken ta kai Nana, suka zagaya daga nan ta kaita cikin gurin da ake sayar da abincin. Nana ta yi mamakin girman gurin, da yadda gurin Abincin yake da tarin kwastomomi. Sai dai da gani ka san na manya ne, dan duk waɗanda suke zuwa gurin cin abinci akwai alamun abin hannu a tattare da su. ***** Ɓangaren su  Shukura cikin jikinta ya tsufa sosai, sai dai a wannan karon ta dage fafur ta ƙi yin awo a Asibitin su Doctor Sharif. Gefe Sagir ya jewa mahaifiyarsa, da maganar son dawo da Yusra, amma ta ce ba ta lamunta ba, ba ta buƙatar ya sake rayuwa da Yusra, gara yaje ya auro wata can daban, amma ba Yusra ba. Gaba ɗaya ya shiga damuwa, saboda mugun sabo da shaƙuwar da ya kuma yi da Yusra. Ita ma Hajiya Halima tun da ta samu labarin, Sagir ne tsohon mijin Yusra yake zuwa gurinta, ta din ga bala'i ta ce ko shi ne autan maza, Yusra ba za ta koma hannunsa ba, balle a sake ci mata mutunci a sako ta. Ga shi daga shi har ita su na son junansu. Dan haka ya yanke shawarar tafiya gurin ƙanin mahaifinsa ya yi masa magana. Shi kuma ya kira Hajiya Halima ya din ga yi mata faɗan dan me za ta hana shi mayar da matarsa alhalin sulhu alkhairi ne, wancan karon da auren ya mutu ma, gutsuri tsomarsu ce ta kashe Auren. Mussaman ta kira Sagir gida, ds ya je ya same ta, ta dirarar masa da bala'i. "Wato ƙarata ka je ka kai wa ƙanin ubanka saboda mace ko Sagir?" Ya girgiza kai ya ce "A'a Hajiya ba ƙararki na kai ba" "Rufen baki ko na make ka, ba ƙarata ka kai ba ya kira ni yana faɗa? Tun da abin da ka zaɓa kenan, ka je ka yi duk abin da ka ga dama" Kalaman na Hajiya, tamkar ɗsure shi ne da jijiyoyin jikinsa, gaba ɗaya ya rasa abin da yake yi masa daɗi ba ya son ya yi abin da daga baya zai zo yana dana sani, saboda rashin amincewar Hajiyarsa. **** Daren yau sam Nana ba ta samu isasshen bacci ba, da yake sai washegari aka ce za ta fara aikin, ba ta yi aikin komai ba ranar. Raba dare ta yi tana nafilfili addu'oi, saboda a jikinta tana jin wani abu game da gurin, wanda ta kasa tantance ko mene ne. Washegari da safe, suka shirya ita da 'yan ɗakinsu, suka tafi gurin aikin Abincin. Kayan girki ne ga su nan a zube, kamar abin banza, yanayin yadda aka jibge kayan a gurin, Nana ta sha jinin jikinta, ta san aiki ne tuƙuru za a yi shi gurin. Aka ba su jadawalin abinccicikan da za a girka a ranar, Nana ta san wasu, wasu kuma ba ta san su ba. Su na nan tsaye shugabar ɓangaren na ƙara yi wa Nana bayani, da gurɓatacciyar hausarta, sai ga mutumin jiya shigo. Gaba ɗaya suka wani ruɗe, masu gyara tsayuwa na yi, masu kama aiki suna yi, Nana dai ta ƙame a gurin da take. Ba yabo ba fallasa ya din ga amsa gaisuwar da ake yi masa, sai da ya zo kan Nana ya saki murmushi ya ce "Baƙuwarmu, ya ki ka ga gurin namu, ba dai wata matsala ko?" Nana ta girgiza kai ta ce "Babu matsala" Ya ce "Yauwwa, ki saki jiki ki yi aikinki da mu, kamar kina Nigeria, duk abin da ba ki gane ba, ga shugabar sashin nan, idan kuma ba haka ba ni ki zo ki same ni ki yi mini magana" Ta jinjina kai ta ce "To in sha Allah, na gode sosai da sosai" Ya kalli matar ya ce "Dan Allah kar a ce za a sakar mata aiki lokaci ɗaya, a koya mata abin da ta sani ba a hankali, kafin a sakar mata aiki" Matar ta risuna ta ce "In sha Allah, amma za a yi mata gwajin ne ita ma?" "Kin ji na ambaci hakan ne, a maganata?" Ta girgiza kai ta ce "Tuba nake" Ya ce "'Yar Nigeria, a yi aiki lafiya" "Na gode sosai" Nana ta yi maganar cikin girmamawa. Ya wuce ya fita. Bayan ya fita suka juya yare, suka ɗan yi maganganu, sai dai duk da Nana ba ta jin yaren nasu, ta san gulmarta suke yi. Suna aiki amma gaba ɗaya hankalin Nana ba a kan aikin yake ba, yana kan halin da Sabir yake ciki. Tana ta tunani yaya yake? Yana rigima ko kuwa bai damu ba ya kwantar hankalinsa, haka ta yi ta wasi-wasi a zuciyarta. ***** Hajiya Amina ce ta yi shirin tafiya Umara, ta tsaya a Egypt za ta kwana biyu, ta tsaya a ɗan binciki lafiyarta. Sai dai ta din ga ji a ranta, yakamata a ƙara bincika mata matsalarta ta rashin haihuwa, mussaman da take tuna maganganun Nana. Sai dai gefe guda tana tuna yadda Alhaji Zailani yake gargaɗinta a kan shi ya fauwwala wa Allah, bai damu lallai sai ta haihu ba, tun da an nemi magani ba a dace ba. Sai dai a wannan karon, ta sake jin tana son jarraba da bibiyar lafiyarta, da ganin likita, ko za a dace, tun da ba ta daina al'ada ba ma. Da harshen turanci suka tattauna da Likitan, ta yi masa bayani, ya rubuta mata gwaje-gwaje ya ce ta je ta yi, ciki har da hoto. Kasancewar komai na su ba kamar na ƙasarmu ba, cikin ƙanƙanin lokaci aka yi duk gwaje-gwajen, aka tura wa Likitan sakamakon. Bayan ta koma gurin Likitan ya duba na'ura mai ƙwaƙwalwarsa, ya kalli Hajiya Halima ya ce mata "Sakamakon hoton da aka yi mata, ya nuna babu mahaifa a jikinta gaba ɗaya" wata irin ƙara cikinta yayi, zuciyarta ta buga a jejjere da ƙarfin gaske, sai ta hau kame-kame tana tunanin, ko kunnuwanta ba su ji daidai ba? Ko kuma turancin nata ne ya ƙwace. Cikin rawar murya ta ce "Ka tabattar da abin da ka gaya mini, ko kuma nice ban fahimta ba?" Ya ce "Na tabattar, shi ne sakamakon gwajin da aka turo mini, amma idan ba ki yadda da sakamakon ba, kina iya zuwa wani Asibitin a sake duba ki!. Yammm ta ji kanta yana yi, ta daina gane komai, hankalinta ya rarrabu kashi-kashi, tana son yi wa likitan tarin tambayoyi amma kanta ya kulle. Shin da gaske ana iya samun mace babu mahaifa, ko kuma wani abin ne daban? Ya aka yi duk tsawon lokacin da ta ɗauka tana bulayin neman haihuwa ba a taɓa gaya mata ba ta da mahaifa ba sai yanzu?. Gaba ɗaya Hajiya Amina, ta rasa kalmomin da za ta tattaro ta sake furta wani abu. Jikinta rawa kawai yake yi, wani irin gumi yana tsatstsafowa ta kowace kafa ta gashin jikinta. Likitan ya ci gaba da yi mata bayani, amma ta kasa fahimta. Ba ta san ma da ya aka yi ta bar Asibitin ba, ta koma masaukinta saboda tsabar ɗimuwa. Ta kuma rasa wa za ta kira ta sanarwa wannan maganar. Gaba ɗaya kanta ya juye, dan ba ta ma iya tuna yadda su ka ƙarƙare da Likitan ba. Tana so ta zubar da hawaye, ta ji sanyi a ranta, amma abu ya gagara idanunta suka bushe zuciyarta ta yi nauyi. Babbar tambayarta ita ce, dama ana iya samun macen da ba ta da mahaifa? Ko kuwa ta ta ce ta yi ɓatan dabo?. Tambayar da ta rasa wa za ta yi wa, balle a ba ta amsa. ***** Nana kuwa gurin nan aiki ake yi tamkar babu gobe, duk da ba ta da son jiki, amma aikin yana da yawa ga babu isasshen hutu, sai aikin ɗorawa da saukewa. Ga shi ta kasa sakin jiki da ma'aikatan gurin, saboda yadda suke tsangwamarta, da nuna mata ƙabilanci, saboda ita ba 'yar ƙasar su ba ce ba. Sam ba sa gaban Nana, duk da tana ɗan saka ido ta ga, ko akwai wata mai hankali da za ta ji ta yarda da ita, a kaikaice ta ɗan fara ƙwanƙwasa cigiyar Sayyid. Sai dai gaba ɗaya ba su yi mata ba ma'aikatan gurin, gaba ɗaya ba ta ji ta aminta da ko mutum ɗaya daga cikin su ba. Kullum da safe Al hussain, mutumin da ya ɗauke ta aiki, sai ya zagaya su ya ga yadda suke gudanar da aikin safe da yamma. Da ya zo ma'aikatan suke nutsuwa, kowa ce ta kame kanta, marasa kamun kai kuma su fara ɗan karairaya. Shi kuma ya tsuke fuska yana basarwa. Sai dai da ya ga Nana sai ya saki fuska, ko ba ta kula shi ba, shi sai ya yi mata magana. "'yar Nigeria ya alƙawarinmu ne?" Nana ta ɗan saki fuska ta ce "Wanne?" "Au har kin manta?" Ta yi murmushi ta ce "Duk lokacin da ka shirya, sai mu fara" Ya ce "Kin san akwai wani abokina, sonake kafin na haɗu da shi, ko gaisuwa na iya da turanci, saboda ya iya turanci ni ban iya ba, ya juya yare ya yi ta magana ba na gane me yake cewa, to kin ga yakamata na ba shi mamaki nima" Nana ta ce "Gaskiya ne, shi ma Buzu ne kamar ka?" Al Hussain ya ce "Ya aka yi ki ka san ni Buzu ne?" "Ga rawani nan ka na yi" ya yi dariya ya ce "Kash, to shikenan tun da kin gane, shi ma buzu ne, mun kwana biyu ma bamu haɗu ba, ban je Agadez ba" "Duk Buzaye a Agadez ku ke?" Ya girgiza kai ya ce "A'a, sai dai mun fi yawa a can, ko kina son zuwa ne? Mu na da wani gurin Abincin ma a can, babban wannan sai a mayar da ke can" Nana ta girgiza kai ta ce "A'a tamabaya dai kawai na yi" Ya jinjina kan ya ce "To yaya aikin?" "Alhamdillah" "To ma sha Allah, Allah ya taimaka" Tun da suka fara hirar nan, Nana ta lura da irin kallon da ake yi mata, saboda ya tsaya sun yi hira. Sai dai ita ba kallon ne ya dame ta ba, a jikinta take jin sam ba ta kyauta ba, tsayawa da ta yi tana magana da Al Hussain har take yi masa murmushi ba, saboda ta san da Sayyid yana gurin, ko da makamancin wasa ba za ta taɓa aikata hakan ba, saboda yadda yake tsananin kishinta. A hankali ta ce "Ka yi haƙuri Sayyid, babu yadda na iya ne, duk a ƙoƙarina na son zuwa gare ka ne, ka yi mini afuwa" ta furta a hankali kamar mai raɗa. "Nana wai a ina ki ka san Al Hussain ne?" Nana ta ɗaga kai ta kalli Shugabar gurin nasu, da take yi mata tamabaya cike da tuhuma. Kamar Nana ba za ta yi magana ba, sai kuma ta ce "Waye hakan?" Matar ta ce "Kamar yaya?" Nana ta ce "Wanda ki ke tambayata" Gaba ɗaya suka kalli Nana, jin yadda take bawa Adama, shugabar ɗakin girki. Ita kuwa Nana ko a jikinta da irin amsar da ta bawa Adaman. Cike da takaici Adama ta ce"Mutumin da ya fita yanzu" Nana ta ce "Au sunansa kenan dama? A nan Nijar na san shi, meyafaru?" Ta yi maganar tana tsare Adama da ido, tana jiran abin da za ta sake cewa. Sai dai ta yi shiru ba ta kuma magana ba, su kuma suka hau mamakin irin amsar da Nana ta bata, kuma ba ta iya ce mata komai ba. Gaba ɗaya Nana hankalinta ya koma kan sauran kwanaki nawa ta koma gida, duk da kullum sai ta yi waya da Nene. Amma ta ga kamar kwanakin ba sa matsawa sam. **** Hajiya Amina revers ta yi, ta dawo gida Nigeria, saboda kiɗima da tashin hankali da take ciki, ta rasa wanda za ta fara tunkara da maganar. Ta so samun mijin Alhaji Zailani a waya, ta fara yi masa bayani, amma ba ta same shi a waya ba. Ta koma gida a kiɗime, amma ta tarar da saƙon ya yi balaguro zuwa Abuja. Jikinta na rawa ta kira Doctor Sharif, ya ɗaga yana faɗin "Hajjaju barka da yamma" "Sharif abu zan tambaye ka dan Allah" Gabansa ya faɗi, saboda yadda ya ji muryarta cike da tsoro da kuma damuwa. "Hajiya lafiya dai?" "Lafiya ƙalau, tambaya zan yi maka dan Allah" "To Allah ya sa na sani" "Dan Allah Sharif ana iya samun matar da ba ta da mahaifa dama?" Ya yi shiru sanann ya ce "Me yasa ki ka tamabaya?" "Ka bani amsa kawai" Nutsuwa ya yi ya tattara hankalinsa, kar ya ba ta amsar da zai fallasa wani ɓoyayyen abin da bai kamata ba. Duk da bai san dalilin da ya sanya ta yi tambayar ba. "Eh ana samu Hajiya, sosai ana samu wani abu ne ya faru?" "A'a shikenan na gode sosai" ta kashe wayar, sai a lokacin hawaye ya fara gangaro mata, da ta ƙara tabattar da har abada ba za ta samu haihuwa ba. "Amina butulci za ki yi wa Ubangiji? Sauran ni'imomin da ya yi miki fa?" Wata zuciyar ta tunatar da ita. Sai dai kasancewarta biladama mai ɗauke da zuciya irin ta ɗan adam, sai ta kasa jurewa ta bi nasihar da zuciyarta take yi mata, ta fashe da matsanancin kuka mai taɓa zuciya. Duk da ta daɗe tana yin sa a ɓoye, amma ba ta yanke tsammani ba ta ci gaba da addu'a, amma a wannan karon da ta san ba ta da rabo baki ɗaya, sai ta sare. ***** Shirye-shiryen bikin Abba yayi nisa, dan bai fi saura sati biyu bikin ba, ta ƙara saka masa ido da shi da Jamila. Jamila sam ba ta nuna mata cewar ta san abin da take yi ba, ta rabu da ita. Ya kasance taronsu na ƙungiya lokaci yayi, dan haka suka shirya tafiya a wannan karon har da maman Khairat. Da suka je masaukinsu ma a garin Abuja, Jamila ba ta shiga sabgarsu ba, harkokinta kawai take yi. Maman Khairat ta ce "Wai Jamsy ya ne? Duk kin zama so silenta, babu wannan rawar kan" Jamila ta ɗan taɓe baki kawai. Hajiya Sa'a ta ce "Jamila haushina take ji, ban san me na yi mata ba" Jamila ta ce "Mummy kenan" "A'a ba wani Mummy kenan, magana za ki yi" "To Mummy, ki na ta daughter daughter, amma ƙarara ki ka nuna ba kya ƙaunata, daga ganina tare da Abba, ki ka haɗe rai ki ka yi kicin-kicin, ki ka tashi nema masa aure. Abin ya bani mamaki" Hajiya Sa'a suka haɗa idi da maman Khairat, ta ce "Haba daughter, ya za a yi na ƙi ki da Abba, ke me ma za ki yi da aure? Na daɗe ina gaya miki za ki iya rayuwa ki da kuɗinki, ba tare da kin yi aure ba. Za ki huta ki yi duk abin da ki ke so." "Amma Abba ma ai yana da kuɗi, shi me yasa ba ki ce ya yi rayuwa da kuɗi kawai ba, ki ke shirin yi masa aure? Duk wata ƙasaita, kuɗi da wadatar mace, inuwar aure ginshiƙi ce kuma sutura ce ga 'ya mace. Amma na san saboda ni rayuwata ta gama lalacewa, ke kuma kina son ɗan ki ya yi kyakykywar rayuwa, ki ka yi ƙoƙarin raba ni da shi. Sai dai tun ran gini tun ran zane. Ban ji haushinki ba ko kaɗan Mummy, abin da ki ka yi shi kowacce uwa za ta yi. Ina yi mana fatan dacewa da ƙarshe mai kyau" Tana gama maganar ta yinƙura ta tashi, ta bar ɗakin. Safiyya ta ce "Kin ga Hajiya, ki bi yarinyar nan a hankali, alamu sun nuna hankali ya fara shigarta, ta san ciwon kanta, kuma abin da aka yi mata duk da ta samu kuɗi ya yi mata ciwo. Kar ki bi ta da ƙarfin tsiya ta yi tawaye" Hajiya Sa'a ta numfasa ta ce "Na ga alama, amma ba zan taɓa rainon ɗan kwiykwiyo, ya girma ya fara yi mini haushi ba. Ina son samun jinin 'yar uwatta na riga Zailani samu ko ta halin ƙaƙa, daga nan zan yi maganinta" Safiyya ta jinjina kai. Doctor Sharif ya din ga kiran Alhaji Zailani, ya sanar da shi kiran da Hajiya Amina ta yi masa, amma ya kasa samunsa a waya, saboda su shinga taron manyan ƙungiya da suke yi, wanda sai sun kwana uku suke fitowa, sannan ayi babban taro na kowa da kowa da ke cikin ƙungiya. Ganin kiran Hajiya Amina ya bawa Shukura mamaki, dan idan tana Saudiyya sai dai su yi video call. Ta ɗaga ta ce "Mami, yaya ba ki samu tafiyar ba ne?" "Shukura za ki iya zuwa gida, ban takura miki ba" Cikin tashin hankali Shukura ta ce "Lafiya kuwa, ya na ji muryarki a haka?" "Dan Allah idan da hali ki zo gida" "Shikenan, gani nan zan kira baban Haidar na gaya masa, gani nan Allah ya sa lafiya" Hankali a tashe, ga tsohon ciki haka ta ɗauki mota ta tafi gida. Tana matuƙar jin Hajiya Amina a zuciyarta, saboda bayan rasuwar mahaifiyarsu, tun su na ƙanana babu yadda ba ta so cuzguna mata ba, amma Hajiya Amina babu ruwanta. Ba ta damu da abin da mutane za su ce ba, ta riƙe ta da halin ta, sai da ta ƙara wayo sannan ta gane ba ta da wata uwa da ta wuce ta. Shi yasa take matuƙar jin damuwarta a ranta tamkar uwar da ta haife ta. A bedroom ta tarar da ita, idanunta jawur sun kumbura. Cikin tashin hankali ta ƙarasa ta zauna ta ce "Lafiya kuwa? Ko ba ki da lafiya ne?" Ta girgiza kai ta ce "Yi haƙuri Shukura, na taso ki ga tsohon ciki, na rasa da wanda zan yi zancen nan na ji daɗi a raina." Cikin damuwa ta ce "To meyafaru?" "Shukura wai ba ni da mahaifa" Shukura ta yi saroro, ta ce "Kamar yaya?" Ta share hawayenta ta gaya mata duk abin da ya faru. A ƙarshe ta ce "Na kira Doctor Sharif ya ce mini eh ana iya samun mata da basu da mahaifa, amma na yi mamakin yadda duk yawon Asibiti da na yi a nan, ba a taɓa gaya mini ba" Shukura ta ɗan yi shiru sannan ta ce "Anya kuwa? Kin san fa kin daɗe da daina zuwa Asibiti a kan matsalar nan, Daddy ba ya so. Sannan ku ne ku ke yarda da maganar Sharif ɗin nan, ki rabu da shi mu je wani Asibitin daban, a sake duba ki a tabattar da abin da yake faruwa. Duk da ba na tunanin za a samu matsala a abin da can Egypt ɗin suka gaya miki." Ta girgiza kai ta ce "A'a Shukura, babu inda zan sake zuwa, na yi maganar ne da ke dama na samu sanyi a raina, na kira babanki ba ta shiga" Shukura ta yi shiru, kawai dai ta ji ita abin kamar akwai lauje cikin naɗi. ***** Nana ta shafe sati na biyu, tana aiki a wannan gidan Abinci. Sai dai ita kanta tana mamakin irin yadda Al Hussain yake kyautata mata. Hakan ya sanya gaba ɗaya suka ƙara saka mata ido suka tsangwame ta, mussaman Adama da 'yar ta Raliya, da alamu suka nuna Al Hussain take so. Idan aiki ya ɗan yi sauƙi, Nana kan fita ta shiga cikin gurin cin abincin, ta zagaya ko za ta ga ko mai da Sayyid ne, amma ba ta ga kowa ba. Sai dai gabanta ya kan faɗi a duk lokacin da ta ga masu rawani sun zo gurin cin abinci, sai ta ga kamar za ta gan shi a cikin su. Ta gama zagayenta, ta koma cikin gurin girkin, Adama ta kalle ta ta tsuke fuska ta ce "Daga ina ki ke, ana tsaka da aiki?" "Na ɗan je wani uzuri ne" "Na me, kuma a ina?" Nana ta ce "Uzuri dai na ɗan Adam, na yau da gobe, ai rayuwa na buƙatar sirri ko?" "Ni fa na fuskanci take-takenki na rashin kunya baki da kunya ko kaɗan, saboda kin ga Al Hussain yana tsaya miki, wallahi idan ba ki yi wasa ba sai na kawo ƙarshen aikinki a nan, sai na saka an kore ki daga gurin nan" Kallonta kawai Nana ta yi ta kawar da kai, ta ci gaba da abin da take yi. Har ta gama bala'inta, 'yan korenta suka taya ta, Nana ba ta tanka mata ba. Washegari da sassafe, Nana ta baro ɗakinsu, ta tafi kitchen ta fara aikinta, duk da wasu lokutan suna yi mata mugunta, su din ga sakar mata aiki. "Ina sauran ma'aikatan gurin nan?" Ta ji wata murya ta daki kunnenta, da ba ta san mai ita ba. Ta ɗaga kai ta kalli matashiyar matar, doguwa fara jawur, mai kama da Al Hussain. Kawai ta mayar da kanta ta ci gaba da aikin gabanta. "Ke ba kya ji ina magana ne?" Nana ta ɗago kai ta ce "Su na zuwa" Nana na rufe bakinta, sai ga Adama ta shigo, ita da sauran ma'aikatan. Wata irin rikicewa suka yi, suka hau tsuma su na gaida matar. "Wace ce wannan? Da ba ta da mutunci ba ta da ɗa'a, nake magana tana bani amsa a wulaƙance" ta yi maganar tana nuna Nana. Nana a ranta ta hau mamakin wane wulaƙancin ta yi mata, ita da ta zo guri babu sallama babu gabatar da kai, koma wace ce ba zai wuce ita ce mai gurin da ake faɗa ba. Nana a ranta ta ce "Koma wace ce ke, Allah ya fi ki" sai dai ba ta sake ɗaga kai ta kalle su ba, ta ci gaba da yankan kabejin hannunta. Ayshercool 08081012143. 69 Adama ta risunar da kai ta ce  "Ki yi haƙuri ranki ya daɗe, mu ma haka muke ta fama da ita mu ma, amma ki yi haƙuri baƙuwa ce" "Baƙuwa kuma ba ta iya magana ba, baƙuwa daga ina?" Raliya ta ce "'yar Nigeria ce" " 'yar Nigeria, waye ya saka Al-Husssain ɗaukar wata 'yar Nigeria, dama haka 'yan Nigerian ku ke, ba ku da mutunci ba ku san me ku ke yi ba?" Maganganun matar sun soki zuciyar Nana, tamkar ta mayar mata da martani ta ce "Ku a Nijar ba ku san muhimmancin sallama, da girmama na ƙasa da kai ba" Sai dai ta yi shiru ta ci gaba da aikin gabanta. Haka ya ƙara tunzura matar ta fita fuuuu tana bala'i tana sai Nana ta bar aiki a gurin. Matar na barin gurin Raliya ta kalli Nana ta ce "Allah ya ƙara, idan kina cin ƙasa ai ki kiyayi ta shuri, yau kin taɓo abin da ya fi ƙarfinki, kin yi a bakin aikinki" Babban abin da ya ɗaure musu kai, bai wuce yadda Nana ta ƙara yin burus, ta ci gaba da aikin gabanta. Adama ta ce "Anya yarinyar nan ba mahaukaciya ba ce kuwa?" Ɗayar ta ce "Ko ta mayar da mu mahaukata ba. Amma idan haukan take ji, ai Hasna babarta ce" Wata matashiyar mata ce ta shigo, sanye da uniform a jikinta. Ta yi sallama suka amsa. Ta ce "Ina Nana?" Nana ta ce "Ga ni" "Ki zo ana neman ki a ofishin Al Hussain" Ta ce "To gani nan" ta yi maganar tana ajiye wuƙar hannunta, ta wanke hannunta ta bi bayan matar. Sai dai har matar ta yi gaba ta bar Nana, da ƙyar Nana take iya ɗaga ƙafafuwanta, saboda matsanancin nauyin da ta ji sun yi mata, ga sanyi da ya fara ratsa ta ta ko ina. "Ya hayyu ya ƙayyum. Allah ka taimake ni, Ƙaisar kar ka yi mini haka mana"  Ta furta a hankali zuciyarta na bugawa. Ta saka hannu ta tura ƙofar ofishin. A tsaye ta tarar da matar ɗazu, tana zazzaga masifa, Al Hussain yana zaune yana kallon ta. Sai dai Nana ta yi turus, ganin Ƙaisar a zaune a jikin na'urar sanyaya guri, da ke cikin ɗakin. "Nana ƙaraso mana" muryarsa ta dawo da Nana hayyacinta. A hankali ta ƙarasa ya ce ta zauna a kan kujera. "Al Hussain ka na da lafiya kuwa? Yarinyar ta yi mini rashin mutunci, ka ce ta zauna a kan kujera?" Ya ce "A'a Hasna, na fa san halinki, kuma a aikin da Nana ta yi da mu na ɗan lokaci, ba ta da matsala sam. Nana meyafaru ne?" Nana ta buɗe baki za ta yi magana, Hasna ta tari numfashinta ta ci gaba da masifa. Al-Husssain ya daki tebur ya kalli Hasna, hakan ya sanya ta yin shiru tana harar Nana. Nana ta ce "Ban san wace ce ba ne, ta yi haƙuri" Hasna ta daki tebur ta ce "Ka gani ko, garin kwashe-kwashe ka kwaso mara mutunci, to wallahi sai ta bar gurin nan, tun da ba na ubanta ba ne" Al-Husssain ya ce "Tsakani da Allah, Nana mutuniyar kirki ce mai girmama mutane, ba na tunanin za ta yi miki wani abu na rashin mutunci. Nana ki je ki ci gaba da aikinki" Ta jinjina masa ta kalli Hasna ta ce "Ki yi haƙuri, ban san wace ce ke ba, ba ki gaya mini ba, na zata a cikin abokan aikina ne kaw... "Ke, na yi miki kama da wadda za ta zama abokiyar aikinki?. Za ta ci gaba da magana Nana ta tsare ta da ido, sai ta rikice gaba ɗaya ta rasa abin da za ta ce. Al-Husssain ya ce "Maza jeki ki ci gaba da aikinki" Nana ta miƙe tsaye, kawai ta ji jiri ya ɗebe ta, ta yi saurin riƙe kujerar. Al Hussain ya miƙe da sauri ya ce "Ba ki da lafiya ne?" A sanyaye ta ce "A'a jiri nake ji ne" "Idan ba za ki iya aikin ba, ki je ki kwanta ki samu hutu" Nana ta ce "A'a zan iya ma, in sha Allah" Ta lallaɓa ta fita daga ofishin, sai dai tana jiyo Al Hussain yana ce mata, ki yi a hankali kin san mu na da baƙi, idan kuma ki ka ci gaba da hayayaga mutuncinki ne zai zube, wannan halin naki babu abin da zai janyo miki sai raini. Gaba Nana ta yi, tana bin bango, sai dai sosai ta ji Duniyar na juya mata. Ta lallaɓa ta koma ɗakinsu da ƙyar, sai dai a ɗakin ta din ga jin wani irin sauti mara daɗi, ga sanyi tana ji amma numfashinta tamkar zai ɗauke. Ta buɗe tagogin ɗakin, kasancewar saman bene ne, ta hango wasu irin manyan motoci a harabar gurin. Naɗin kan mutanen ya sanya ta tabattar da Buzaye ne, sai dai suna sanye cikin kaya na alfarma. Nana ta zuba musu ido, tana son ganin fuskar ɗaya daga cikin mutanen da aka buɗewa wata danƙareriyar mota. Wanda haka kurum ta din ga jin kamar akwai wani abu mai matuƙar muhimmanci da yakamata ta sani game da mutumin, da ba ta san ko wane ne ba, duk da yanayin ƙirar jikinsa ba irin na Sayyid ba ne. Wata irin ƙara ta din ga ji cika mata kunne. Ta dafe kunnenta, ta durƙusa hawaye na bin fuskarta. Yanayin gaba ɗaya mara daɗi ne, rashin daɗin da ba za ta iya misaltawa ba sam. Dariyar Giyaz ta din ga ji sama-sama, a hankali dariyar ta cika ilahirin ɗakin. "Hasbunallahu wa ni'imal wakil, wa hifzan min kulli shaiɗanin marid" shi ne abin da ta furta a hankali. "Asmy" ta ji muryarsa cikin karkarwa, yayin da ƙarar iskar sahara take kaɗawa. A galabaice ta ce "Sayyid" "Ma vie" Ta sake cewa "Na'am Sayyid, na fara sarewa, ina jin kamar ba zan yi nasara ba, ba zan ganka ba, na fara karaya." Ta yi maganar tana kuka. "A'a kar ki karaya, kar ki yi mini haka, ina buƙatar ki dan Allah" A hankali take sauke numfashi, idanunta a lumshe ƙirjinta ya yi nauyi kamar numfasihinta zai ɗauke. ***** Daren da Jamila ba za ta taɓa mantawa da shi ba, ya sake maimaita kansa. Daren da ta zama ɗaya daga cikin mambobin ƙungiyar asiri, daren da aka lalata rayuwarta a matsayin maraba da shiga ƙungiyar. Kamar yadda yake ɗabi'ar ƙungiyar, suna sanye da jajayen kaya. Sai dai a wannan karon Jamila ta gusa daga matakin farko na shiga ƙungiyar. Babban abin da ya bawa Jamila mamaki, bai wuce yadda aka fesa wani abu a gurin, sai ganinsu ta yi a dokar daji ba. Wani irin daji mai ban tsoro, mai ɗauke da manyan dogwayen bishiyu, ga shi baƙiƙirin ɗauke da duhu. A wani fili suke a gaban wani dutse, babu tsammanni ta ga wuta takama a tsakiya tana ci bal-bal. Daga bisani dajin ya din ga amsa kuwwa da wata irin ƙara mara daɗin ji. Aka din ga karanto abubuwan da Jamila ba ta iya fahimta. Aka jefowa kowa ƙyalle da abin da zai sadaukar na shekara, kafin zagayowar wani taron. Jamila ta kalli ƙyallen da yake gabanta, jawur da shi. Hannunta na rawa ta ɗauka ta fara ƙoƙarin warwarewa. Da hasken da wutar ta bayar Jamila ta karanta abin da yake rubuce a jiki, da aka rubuta da jini. Ta din ga kallon ƙyallen tare da rubutun. Ta duƙunƙune ƙyallen ta jefa a wuta, kamar yadda kowa ya yi. Sai dai jikinta a sanyaye, gabanta kuma ya tsananta faɗuwa. A wannan karon har da wasu irin dogayen mutane, da ta kasa gane mutanen ne ko kuwa wani jinsin ne, saboda yadda suka shallake kowa tsawo a gurin kuma suna sanye da baƙaƙen kaya har kansu a rufe yake. A wannan karon abubuwan da Jamila ta gani sai da ta tsorata, ashe wancan karon babu abin da ta gani. Ƙungiyar mataki-mataki ce. Su matakin su Alhaji Zailani ma, kowannensu yana da aljanin da kusan bauta masa yake yi. Sun ba wa aljanun jini babu adadi, na makusantansu, da wanda ma ba makusnatansu ba. Aljanun na iya shiga kowane irin hatsari, dan ganin buƙatar irin su ta biya komai wahalarta. Haka suma su Alhaji Zailani, duk abin da Aljanun suka buƙata suna yi musu, domin ɗorewar biyan buƙatunsu. Alhaji Zailani ya kan karɓi saƙonnin nasa Aljanin ta hannun Malam Gambo, wanda su ne manyan malaman da suke gudanar da sihiri a cikin ƙungiyar bayan ɓangaren neman Duniya da samun kuɗi da suke yi. Su kan kira aljanu daban-daban da sanya su aikace-aikace na sihiri. Aljanin Alhaji Zailani ya buƙaci aiki da jinin Nana, da kuma mu'amala da mai irin tauraronta dan biyan buƙatun Alhaji Zailani, sai dai abu ya gagara kamar yadda dariya ta gagari kare. Hakan ya sanya a wannan karon ma ya sake buƙatar jinin Alhaji Zailani, wanda idan ba Shukura ko Yusuf ba, sai dai abin da Shukura za ta haifa. Ɓangaren Hajiya Sa'a ma hakan ne, bayan sanin fa'idar jinin irin na masu tauraron Nana, da yadda bayan haɗuwarta da Nana karon farko, Aljanin ya yi mata bayanin irin tagomashin da za ta samu, idan ya sha jinin Nana, da kuma bautar da zai yi mata idan ya sha jinin ko kuma ta kawo Nana ƙungiya, ta hanyar na ta bokan na cikin ƙungiyar, kuma bokan ya kwaɗai mata damarmakin da za ta iya samu idan ta mallaki Aljanin kan Nana kamar yadda aka gaya wa Alhaji Zailani ma. Ita ma a wannan karon, an sake buƙatar jinin makusancinta, wanda ko dai Abba, ko Alhaji Fatuhu ko kuma dai ɗansa Muhsin, su ne shaƙiƙanta. Jamila a firgice ta farka, a tunaninta ko duk mafarki ne, ta farka da wani irin matsanancin zazzaɓi da ciwon kai, ƙoƙon kanta tamkar zai tarwatse saboda azabar ciwo. Maman Khairat ta taso tana yi mata sannu. Ta ce "Wai ke Jamila wace irin raguwa ce ne haka? Ai yakamata a ce zuwa yanzu kin riga kin saba fa" Hajiya Sa'a ta ce "Dole za ta razana dama, yanzu ta shiga mataki na biyu sai a hankali" Jamila ta ɗan yi shiru tana so ta fuskanci ko a wannan karon ma an yi lalata da ita, amma ba ta ji hakan ba. Sai kanta da yake ta wata irin azaba, ga jikinta tamkar ana ƙona ta saboda zafin zazzaɓi. ***** Shukura ta je awo, likitan da yake duba ta doctor Sabo, ya na ta ƙara kwantar mata da hankali, saboda a wannan karon ma akwai hawan jini a tattare da ita. Har za ta tashi ta tafi ta ce "Doctor dan Allah wata tambaya ce da ni" Ya ce "To Allah ya sanya na sani" "Wai dan Allah ana iya samun mace wadda ba ta da mahaifa?" Ya ɗan yi shiru sannan ya ce "Eh ana samu, amma a mafi ƙanƙantar lokuta sosai, saboda a cikin mata dubu biyar da ƙyar ake samun mace guda ɗaya da irin wannan case ɗin" Ta jinjina kai cike da gamsuwa ta ce "To Doctor kai ka taɓa haɗuwa da irin waɗanda ba su da mahaifar?" Ya girgiza kai ya ce "A'a. Amma me yasa ki ke tambaya?" "Mamana ce ba ta taɓa haihuwa ba, da tana zuwa ganin Likita amma ta daina, sai last week ta je Egypt, aka duba ta ska ce ba ta da mahaifa" Ya waro ido ya ce "Ba ta da mahaifa, kuma ta taɓa haihuwa?" "A'a ba ta taɓa haihuwa ba, step mum ɗina ce" Ya ce "Ikon Allah, kuma ba a taɓa yi mata aiki ba ko makamancin haka?" Ta yi shiru ta girgiza kai ta ce "Bana tunanin haka, amma bari na kira maka ita" Shukura ta kira lambar Hajiya Amina ta ɗaga. Suka gaisa ta ce "Mami, ina Asibiti ne na yi wa likitan da nake awo a hannunsa magana, ya ce na haɗa ku" "Shukura, ba na ce a bar maganar nan ba kawai?" "A'a ki yi haƙuri, na riga na yi magana da shi ai" ta ba wa Doctor Sabo waya. Suka gaisa ya ce "Hajiya garin yaya aka ce ba ki da mahaifa ne?" "Wallahi nima ban sani ba, abin da dai suka ce mini kenan" "A Nigeria an taɓa duba ki a baya an gaya miki hakan?" Ta ce "A'a" "An taɓa yi miki tiyata?" "A'a Likita ba a taɓa yi mini ba" Doctor Sabo ya ce "Ikon Allah, kuma yaushe rabon ki da Al'ada?" Ta ce "Ai dama ba regular nake yi ba, wasu lokutan sai na yi wata shida ma ban yi ba, idan ya zo kuma ba ya fin kwana biyu wataran ma wuni ɗaya ne shikenan" "To dama tun kina budurwa haka ki ke yi?" "A'a gaskiya, da lafiya ƙalau nake al'ada daga baya ne ya koma haka". "Bayan ya koma hakan kin taɓa zuwa an ƙara bincikawa, kuma a baya ba a taɓa gaya miki mene ne ya hana ki haihuwa ba?" Ta girgiza kai kamar yana ganinta ta ce "Ko a baya komai lafiya ƙalau ake ce mini, daga baya kuma da ya koma haka, mijina ya ce na haƙura da yawon Asibitin nan, dan haka ban sake zuwa a kan issue ɗin haihuwa ba. Amma ina fuskantar matsalolin gynea sai dai akwai likita da nake gaya wa ya rubuta mini magani kawai". Doctor Sabo ya ce "Idan babu damuwa, akwai buƙatar ki zo Asibiti mu ƙara bincikawa sosai da sosai, wannan serious issue ne" "Doctor na gode sosai da sosai, amma ba na tunanin zan iya zuwa, na haƙura dama buri ne irin na ɗan Adam amma shekaruna sun ja, na bar wa Allah ikonsa." "A'a kar ki ce haka baiwar Allah, akwai Abubuwan da farwuarsu daga Allah ne mun sani, wasu kuma akwai sababi. Wataƙila akwai wani abu na musamman a tattare da ke da ya dace a bankaɗo. Ina doubting a ce Egypt su bayar da result ɗin da ba shi ba ne ba. Amma dai za mu ƙara bincikawa." Hajiya Amina ta amsa masa da to, ta yi masa godiya amma sam ba ta ji za ta iya zuwa a wani bibiya ba, kamar tana tsoron wani abu. Doctor Sabo ya ce lallai Shukura ta lallaɓo ta, su zo Asibiti yakamata a yi ƙwƙƙwaran bincike a kan lamarin. Alhaji Zailani yana kashingiɗe ya kira Doctor Sharif. Bayan sun gaisa ya ce "Ina cikin uzuri ne kwana biyun nan, shi yasa ban ɗaga wayarka ba, ya ake ciki?" "Dama zan gaya maka ne, Hajiya ce ta kira ni tana tambayata wai ko ana iya samun mace wadda ba ta da mahaifa, to ban san dai mene ne ba, amma na ce maya eh." Wata irin zabura Alhaji Zailani ya yi ya ce "Daga nan me ta ce maka?" "Ba ta ce mini komai ba ta kashe wayar" "Shikenan na gode" ya kashe wayar ya dafe goshinsa, "Amina kin fiye taurin kai, dama kaza garin tone-tonenta take tono wuƙar yanka kanta!" Sannu a hankali Nana take bin doguwar barandar, tana hangen masu shigowa da masu fita daga cikin gurin cin abincin. Tun safe motoci suke shiga su na fita. Sai dai ta jima a tsaye a gurin, ba ta ga wani abu da za ta iya riƙa, ko wani wanda za ta tunkara ta yi wa magana ba. Duk manyan mutane ne na alfarma ba ta tunanin akwai wanda ma zai tsaya saurarta, su kuma ma'aikatan gurin da take sanya ran za ta iya tambaya wani abu, ba zaman lafiya suke yi ba. Jiki a sanyaye ta juya, ta kama hanyar komawa gurin girke-girken, Al Hassan yana hango ta, ta ofishin sa. A kan hanyarta ta komawa, suka yi kiciɓis da Hasna. Nana ta ɗan raɓe gefe ta ce mata "Ina kwana" "Lafiya" ta amsa har za ta wuce Nana, sai ta dawo da baya ta ƙara kallon ta ta ce "Au ashe ke ce fitsararriyar nan ko?" Nana ta girgiza kai ta ce "A'a rashin fahimta ne, yanzu da na san wacece ce ke ai ga shi na gaishe ki" Ta so ta yi wani abu da za ta yarfa Nana da za ta saka ta ji zafi a ranta, amma sai ta kasa. Gaba ɗaya ma sai ta ga Nanan kalar abin tausayi a yau, kamar ba ta da kuzari ko kaɗan fuskarta ɗauke da damuwa. "Amm ki kawo mini shayi ofishina, shayin girfa, kar kuma a cika sugar ba na son sugar da yawa" "To ina ne ofishin" "Ki tambaya" ta amsawa Nana tana yin gaba abin ta. Nana ta koma gurin girkin, ta fara ƙoƙarin dafa shayin girfa, saboda babu shi, Adama ta saka ta wani aikin. Wasu lokutan har rasa yadda za ta yi take yi, sai dai ta kan jure dan kar ta gaza ta sare, dan jikinta yana bata zamanta a gurin nan ka iya sanyawa ta yi nasara. Sai dai abinka da ɗan Adam, wasu lokutan ta kan bujire. Ta kammala ta tambayi ofishin Hasna, aka nuna mata ta kai mata shayin har can. Tana tare da Al Hussain  ta tarar da ita, da wasu manyan mutane guda uku a office ɗin. Cikin girmamawa Nana ta gaishe su, cikin gurɓatacciyar hausa suka amsawa Nana. Hasna ta sake mayar da Nana, wai ta kawowa baƙinsu shayi. Haka Nana ta koma, ta sake kai musu wani shayin, duk da hakan ba aikinta ba ne ba. Ta fito daga ofishin, Al Hussain ya biyo ta yana kiran sunanta. Ta tsaya ta waiwayo ta jira ya ƙaraso. "Nana ko haryanzu jikin ne ba ki warke ba?" Cikin ƙarfin hali ta girgiza kai ta ce "A'a jiki na warke" "A'a idan ba ki warke ba, na saka a kai ki Asibiti, sai a baki hutu" Ta girgiza kai cike da ƙwarin gwiwa ta ce "A'a na ji sauƙi fa, zan ci gaba da aiki in sha Allah, na gode sosai da sosai" Ta juya ta ci gaba da tafiya. Shi dai haka kurum Nana tana ba shi tausayi, sai dai babu wata dama da ta bari, da za a iya zama da ita a ji matsalar ta, ko za a iya taimaka mata. Ya lura ko a cikin ma'aikatan ba ta da sukuni, ba ta sakin jiki da su. Kuma yanayin ta ƙarara yake bayyanar da damuwa duk da tana da ƙoƙarin dakiya. ***** Alhaji Zailani ya din ga kiran lambar Hajiya Amina. Gaba ɗaya ya rikice hankalinsa ya yi mummunan tashi, ya rasa abin da yake yi masa daɗi, yana tsoron kar ta aikata wani abin da zai kawo matsala. Ga jirginsa sai washegari zai koma Kano, ga shi yana da manyan uzururrukan da yake son yi a Abuja, da ba zai iya tsallakewa ya bar su ba. Shukura ta je har gida, ta sake samun Hajiya Amina ta lallaɓa ta a kan ta amince su je gurin Doctor Sabo, amma ta ce babu inda za ta je. Da ƙyar ta amince ta ce ba za ta je a ranar ba sai washegari. Shukura ta ɗan numfasa ta ce "Mami ba na son yi miki maganar nan ki na cikin damuwa, sai dai nima ba a son raina ba, na rasa abin da yake yi mini daɗi" Cikin damuwa Hajiya Amina ta ce "Dan Allah ki kwantar da hankalinki, kar wannan cikin ma ya sake samun matsala mene ne?" Ta numfasa ta ce "Sagir ne fa yake ta ƙoƙarin dawo da tsohuwar matarsa" Hajiya Amina ta ce "To shi ne ki ka damu haka? Dan Allah ki rabu da shi ya ƙarata, ki lallaɓa ki haihu lafiya kalau, kin ga ga hawan jini ki na fama fa" "Wallahi Mami zuba masa idon na yi, takaicina bai gaya mini ba, su na ta ƙwarbai da Hajiya, ta ce ba zai dawo da ita, a bakin ƙannensa nake ji". "To babu ruwanki, su sha'anin dangin mijin nan ba a zaƙalƙale musu, idan ta dawo ɗin ma wataƙila su tattara su haɗe kai, babu ruwan ki ki kula da kan ki, ki sauka lafiya" Shukura ta jinjina kai ta ce "In sha Allah, sannan dan Allah Mami ke ma ki kwantar da hankalinki, nutsuwarki ita ce ta wa, dan Allah Mami ki kwantar da hankalinki kema" "Wallahi Shukura ƙarfin addu'a ya sanya mini nutsuwa da tawakalli, yadda ku ke yi mini biyayya da ke da Yusuf ko ni na haife ku, Alhamdillah na san iya abin da za ku yi mini kenan. Kuma na san ko yau na bar Duniya za ku tuna da ni ku yi mini addu'a" Idon Shukura fal hawaye ta ce "Mami ke uwa ce abar alfahari, har Duniya ta naɗe ke uwa ce a gare mu, kuma muna alfahari da samun ki" Suka rungume juna da ita da Shukura, Hajiya Amina ta ci gaba da gode wa Allah, tana jin da natan ta haifa wataƙila ma ba lallai su yi mata biyayya haka ba. Sai bayan tafiyar Shukura, sannan ta shiga ɗaki, ta tarar da kiran wayar Alhaji Zailani rututu. Yana ganin kiranta ya ɗaga, bai tsaya amsa gaisuwar ta ba, ya hau tambayarta abin da ya hana ta tafiya. Ta ce "Matsala aka samu, kuma na yi ta kiran ka a waya, ba ka ɗaga wa" "Matsalar me?" "Ba komai, idan ka dawo ma yi magana" Ya ce "Yanzu nake son ki gaya mini koma mene ne, meye dalilinki na kiran Sharif kina tambayarsa ana haifar mace babu mahaifa?" Ta ce "Amma laifin me na yi haka? Na tsaya a Egypt su duba lafiyata ne, tun ina can nake neman ka, ban same ka ba, sakamakon gwajinsu ne ya tabattar da ba na ɗauke da mahaifa" "To uban waye ya ce ki je? Ba sai da na ce miki ki bar batun yawon neman haihuwar nan ba, da yake ban isa na saka miki doka ki bi ba, kin raina ni bani da mutunci a idonki?" Duk bayanin da ta so ta yi masa, yaƙi saurararta, ya din ga zazzaga mata bala'i. Ranta ya ɓaci, ta ga Sharif bai kyauta mata ba, ya za a yi daga tambayarsa abu ya ɗau waya ya kira shi ya gaya masa, ai gara ta gaya masa da kanta, duk da ba wani abin ta ce masa ba, tambaya ce kawai ta yi masa. ***** Ɓamgaren Alhaji Fatuhu, Hajiya Suwaiba kamar ta yi bindiga, ganin ya amince ana yi masa maganin gargajiya, a ganinta dan Fadila ta saka baki ne, ta lallaɓa shi yake yi. Yanzun ma Fadila tana ta ƙoƙarin kunna garwashin da za ta yi masa turare, gefe ta kunna mp sautin ayoyin ruƙiyya su na tashi a hankali. Ya kalli Fadila ya ce "Baby, ina fatan dai magungunan nan, babu wani abu na kauce hanya a cikin su?" Ta girgiza kai ta ce "Haba Daddy, kai ma ka san ba zan yi duk wani abu da zai taɓa imaninmu ba in sha Allah, Kawu ne duk ya bayar da su, kuma ka san shi ma masanin Addini ne sosai. Babu wani na shirka a ciki." Ya ce "To ki yi haƙuri, kawai da na tambaya ne, kin san yanayin abin, kar garin magani mu kauce hanya na je na mutu a mummunan tafarki, ya zamana na kasa jure ƙaddarata na kauce hanya" Fadila ta ce "In sha Allah ba zaka mutu yanzu ba, za ka samu lafiya" "To ki yi haƙuri, na ga kin ji haushix Ta girgiza kai ta na ɗan murmushi ta ce "A'a ban ji ba" "Kin ji mana, kin tura baki gaban ne ba ki ji haushi ba?" Sai kuma suka yi dariya a tare. Ya ce "Ki yi haƙuri, in sha Allah ba zan sake magana ba, na yarda da ke, ba zaki cutar da mu ba" Hajiya Suwaiba ta shigo ɗakin, tana basarwa jin yadda ɗakin ya ɗume da ƙamshin jan almiski, da ƙaurin hayaƙi. Ta ɗan taɓa baki a ranta ta ce watakila ma a cikin wannan tsiyatakun take mallake ka. Ta ajiye masa kwanukan Abinci, ta juya za ta fice. Ya ce "Ba magana ne?" "Sannu ya jiki?" Ta faɗa a daƙile. "Jiki Alhamdillah, a hankali ji nake jikina ya yi daɗi, na ɗan samu sassauci daga abin da nake ji kamar an ɗaure ni, ba na iya motsi sai da ƙyar da dabara, da ƙirjina da yake yi mini nauyi nake jin kamar an toshe mini baki da hanci da kokowa nake numfashi" Duk da tana jin haushinsa sai kuma ta saki fuska ta ce "Alhamdillah, sauƙi yana samuwa kenan? Ubangiji Allah ya ɗorar da sauƙi, dama komai nufi ne na Allah" Ta kalli Muhsin da yake ta tattaɓa kwanon abincin da ta kawo. Ta ce "Kai ɗan lukuti acici, ka zubar mini da Abinci sai ka biya ni. Ki zuba masa abincin ko ci zai yi" Ta yi maganar sama-sama tana ɗan kallon Fadila. Duk da matsanancin kishin da Hajiya Suwaiba take yi da ita, yanayin yadda take yi wa Muhsin wasu lokutan ya sanya Fadila ba ta fiye jin haushinta ba. ***** Hasna kuwa ta sako Nana a gaba, bayan aikin da take yi, ta din ga sanya ta wasu ayyukan daban da ba sa cikin jadawalin wanda aka ɗauke ta yi. Wasu lokutan sai ta gama aiki, ta koma ɗakinsu, sai ta saka a taso ta, ta saka ta aiki. Abin ya ishi Nana amma ta danne. A wannan karon ma, har ta yi shirin kwanciyar, aka zo aka kira ta. Kawai ta ji a ranta, ko Hasna za ta kashe ta yau, sai dai ta kashe ta, dan ba za ta yi mata kowane aiki ba, sai dai ta kore ta. Ƙarafe goma sha ɗaya na dare, amma tana ofishinta ba ta tashi ba. Ko da Nana ta je, tsayawa ta yi ƙyam tana jiran ta ji me Hasnan za ta ce. Sai dai ta ci gaba da aikin gabanta, sai da Nana ta fara ƙosawa, sannan ta kalle ta ta ce "Amma an ce 'yar Nigeria ce ke ko?" "Eh" Nana ta amsa a ƙufule. Ta ɗan ƙura wa Nana ido sannan ta ce "Ina da wasu baƙi ne gobe in Allah ya kaimu " Nana ta ɗago tana kallonta, ta ji ina ne ƙarshen zancen, dan kullum cikin baƙi suke kamar gurin boka. "Dan haka ba aikin gurin cin abincin nan za ki yi ba gobe in Allah ya kaimu, aikina za ki yi. Zan saka a sanar musu ma. Ina son ki yi Abinci mai kyau da daɗi na Nigeria. Ina son na sauke su da shi. Wajen la'asar za su zo, dan haka za ki dafa abin karayawa, da abincin rana da na dare, za a zo a ɗauka" Nana ta yi ajiyar zuciya jin ba wani aikin rainin hankalin Hasna ta saka ta ba. "Allah ya kaimu, zan iya tafiya?" Hasna ta ce "Saurin me ki ke yi ne?" "Na gaji ne sosai, bacci nake ji ina son na samu na tashi da wuri" Ta jinjina kai ta ce "Ya yi je ki" Nana ta fice ta tafi ɗakinsu. Sai dai duk gajiyar da ta yi, bacci ya gagari idanunta. Tun bayan sallar Asuba, ta tafi kitchen ɗin ta fara aikin da Hasna ta saka ta. Sai bayan Azahar ta kammala komai, Hasna ta aiko aka ta ɗauki Abincin. Nana ta fara shirin tafiya ta je ta yi wanka ta huta. Adama ta ce "Ina za ki je kuma ga ayyukan kitchen fal?" Nana ta numfasa ta ce "Ki yi haƙuri, Hasna ce ta saka ni aiki, ta ce idan na gama, na je na huta" "A'a ba zai yiwu ba, ni ce mini a aka yi kawai za ki yi mata aiki, dan hakan idan kin gama ki saka hannu ku ci gaba da aikinmu, wa za ki bar wa wannan aikin?" "To ki yi haƙuri, na gaji gaskiya ba na jin daɗi" kawai ta fice, tattaunawa suka shiga yi a tsakanin su, yadda za su kawo ƙarshen Nana a gurin baki ɗaya. A ƙarshe suka yanke shawarar, su ƙara ƙaimi su ɓata ta a gurin Hasna, ganin yadda ita ma ta sako Nana a gaba da tsangwama. Bayan sallar isha'i, Nana ta daɗe a zaune tana tasbihi, tunanin gidansu da 'yan uwanta ya addabi zuciyarta, ga shi abin da ta fito neman har yau babu labari. Ta daɗe tana addu'a kafin ta nemi guri ta kwanta. Washegari ma su na ta aiki tun safe har Yamma, sai ga Hasna ta shigo. Duk yadda Hasna take da kyau, ita da Al Hussain, wannan da suka shigo ta fita kyau, tamkar balarabiya, jawur da doguwa sai dai siririya ce sosai. Fuskarta ta sha make up, sai zuba ƙamshi take yi. Ta yafa ɗan siririn mayafin abayarta a kanta. Sai kallonsu take ɗaya bayan ɗaya tana yatsuna fuska su na yare ita da Hasna. Duk suka gaishe su, Nana kuma ta yi burus. Hasna ta nuna mata Nana ta ce "Kin ganta nan" Asal ta yamutsa fuska ta ce "Ya na ganta baƙa ƙirin haka, ina fatan ba na ƙazanta ba ne?" Nana ta yi mamakin jin Hausa raɗau a bakinta. "Ke ina ruwanki da baƙinta, ba dai Abinci ya yi ba?" "Eh kin san ba na son ƙazanta ne" Hasna ta ce "Sauran ma'aikatan namu ma ai akwai baƙaƙe, kuma kema kin san da ba ta da tsafta, ba zan saka ta yi miki girki ba.Ke Nana ba ki ganni da baƙuwa ba ne?" Nana ta ɗaga kai ta kalle su, ta yi shiru tana wasa da wuƙar hannunta, saboda ciwon da maganganun da suke yi ya yi mata, na cin zarafin baƙar fatarta da danganta ta da ƙazanta, duk ba wai duhu ne da ita sosai ba. Shiru Hasna ta yi ta kamo wata hirar, ganin alamun idan ta matsa Nana za ta yarfa ta ne a gaban baƙuwarta. Ba a taɓa ma'aikacin da ba ya shakkar ta ba sai Nana. Duk abin da ta saka ta na aiki za ta yi, amma ba ta son rainin hankali. Bayan sun fito Asal ta tsaya ta kalli Hasna ta ce "Hasna" "Na'am" "Ina ga yarinyar nan ta yi dai-dai da abin da nake nema" "Wace yarinyar?" Asal ta ce "Wannan 'yar Nigeriar, ina buƙatar za ki ba ni ita" Ayshercool 08081012143 70 Sai da Nene ta tabattar Nana ta ɗan nutsu, sannan suka kwanta. Washegari Nene ta fita, ta bar Nana a gidan tare da Muhsin. Bayan ta dawo daga gurin sama'arta ta cewa Nana, yakamata ta je ta ɗan sai abubuwan da za ta buƙata saboda tafiyar da za ta yi da nisa, kuma ba su san yaya tsarin aikin can ɗin yake ba. Nana ta ce "Ni babu abin da nake buƙata, ki bani wani abin na riƙe a hannuna, sauran kuɗin kuma ki riƙe saboda kula da Muhsin na s... "Biyana za ki yi kenan dan na riƙe miki Muhsin?" Nene ta katse ta. "Allah ya baki haƙuri, ba haka nake nufi na, na ga dole ɗan abubuwan buƙatunsa duk ke ki ke yi masa Nene, tun da ga kuɗi sun" "Kuɗinki ba su isa su saka na riƙe miki ɗa ba ko?" Nana ta ce "Na sani, ai shi ya sanya na ce ki yi haƙuri. Nene ta ce "Ba zan yi haƙurin ba sai na gama, kin iya kunna ni da na fara faɗa ki hau bani haƙuri, wato in ci kaina to sai na idar" Nana ta yi mata shiru ta yi faɗanta ta gama. Washegari Nene ta saka Nana a gaba suka je kasuwa, ta sata ta yi sayayyar kayan sakawa da na ɗan shafe-shafe, ta yi wa Muhsin sayayyar kayan sakawa da pampers. Babu yadda ba ta yi da Nene ba ta ɗauki wani abin ta ce ba za ta ɗauka na. Nana ta haɗe rai ta ce "Eh dama ba ki ɗauke ni 'yarki ba, shi ya sanya duk abin da zan yi miki ba kya karɓa" "Ni za ki yi wa wayo, na ji ban ɗauke ki 'yar ba, ni ga ɗana nan" tayi maganar tana shafo Muhsin da ke bayanta. Da ƙyar sai da suka kai ruwan rana Sannan Nene ta karɓi abin da Nana ta saya mata. Sai dai kan su bar kasuwar har sun shirya. Nana ta ce "Nene kin ce mini ki na da ɗa, amma ban taɓa ganinsa ya zo ba, ba ya zuwa ya gan ki ne?" Nene ta ce "Kamar ban damu da shi ba ko?" "A'a kawai dai tambaya na yi " "Yana can Nigeria" "To me yake yi a Nigeria ba ya zuwa inda ki ke?" "Sana'a yake yi, ai ya zo ki na can gurin aiki" Duk da Nana ba ta gamsu da amsoshin da Nene ta ba ta ba, amma ta basar ta ce "Allah sarki, Allah bai yi zamu haɗu ba". Haka suka ci gaba da hira suka koma gida, Nana ji take yi tamkar ta ɗauke ɗanta ta tafi da shi. Gidansu Ashura Nana ta je, ta samu keke ta ɗiɗɗinka kayan da ta sayo, ta sake haɗa jakarta ta ɗauki muhimman abubuwa a kayanta. Duk da a ɗaki Nene take rufe mata su, ba ta taɓa ganin alamar Nenen tana yi  bincike a cikin kayan ba. ***** Ko da Jamila suka dawo Kano, fakar ido ta yi ta jefar da wannan tarkacen da aka ba ta aka ce da su za ta kai jini. Gaba ɗaya da ta tuna abin tsigar jikinta take tashi, ta ji ciwon kanta da zazzaɓi ya ƙaru. Gefe guda kuma hankalinta yana kan yadda ta ji Hajiya Sa'a tana faɗin za ta sake bayar da ɗan Alhaji Fatuhu. Ta jinjina rashin imaninta mutumin da yake fama da karayar arziki ga ciwo, ya rasa wancan ɗan kuma a sake bayar da wannan kamar ba a yi masa adalci ba. Sai dai gaba ɗaya ba ta san ta ina za ta fara ba, tana jin a ranta kamar yakamata ta tseratar da yaron. A gida ta tarar da Gaddafi, ta sha jinin jikinta da irin mugun kallon da ya yi mata, amma bai ce mata uffan ba. Suwaiba ma ƙura mata ido ta yi tana bin ta da kallo. Ta tsuke fuska ta harsri Suwaiba, sai dai Suwaiba ta tuntsure da dariya, kamar za ta shiɗe. Jamila ta yi tsaki ta shige ɗakinsu. Ba ta tarar da Mama a gida ba, haka ma Baba. ***** Shiru Alhaji Zailani ya yi yana kallon Doctor Sharif yana sauraren shi, har ya gama karanta masa abin da Shukura ta je ta same shi ta yi masa. Ya ja numfashi ya ce "Shikenan, aikinka ya yi kyau Sharif, na kuma gode sosai da sosai da ka ke sanar da ni wannan abubuwan, Allah ya saka maka da mafificin alkhairi. Ka je za ka ga saƙo" Sharif ya yinƙura ya tashi ya tafi. Alhaji Zailani ya numfasa a fili ya ce "Duk da kasancewar ki 'ya mafi soyuwa a cikin zuciyata, an zo gaɓar da ki ka ƙetare layin da bai kamata ki ƙetare ba, kina ƙoƙarin tono abin da zai wargaza zaman lafiya da kwanciyar hankali, dan haka ki yi haƙuri da duk matakin da zan ɗauka a kan ki. ***** Nana ta jingina da jikin gilashin motar, tana kallon tulin yashin saharar da ya mamaye gurin. Fili fetal hagu da dama duk yashi ne. Cikin yanayi mai kama da bacci take ganin abubuwan da ta din ga gani a bacci cikin saharar. Ko a yanzun ma su na tafe Sayyid kawai take gani a kan raƙumi yana biye da su a cikin saharar. Kamar an taɓa ta ta ɗan yi firgigit ta kalli gurin, haryanzu a titin da ya ratsa saharar suke tafiya, zuciyarta ta yi wani irin bugu da sai da ta dafe ƙirjinta. Sanyi ta fara yana ratsa ta har cikin ƙashinta, ta ɗaga ido tana ɗan waige-waige ta ga ta ina za ta gano Ƙaisar ko wata baƙuwar halittar da ba jinsin mutane ba, sai dai ba ta ga komai ba. Ta sake jingina da jikin motar tana ta karanto duk addu'ar da ta zo bakinta. A haka har suka shigo cikin gari sosai da sosai. Nana na son karanta Symbols ɗin da take gani, amma ba komai take iya fahimta ba saboda rubutun French. Babbar hanya mai ɗauke da ƙaton gate ta ciki suka wuce. Ba ƙaramar gajiya Nana ta yi ba, saboda azabar nisan tafiyar da suka shawo ba, ba su ƙarasa ba sai bayan magariba. Kewar ɗan ta ta addabi zuciyarta, tunaninta yadda za ta din ga sintirin tsakanin Agadez da Maraɗi a wannan uwar tafiyar kamar ta ya da shege. Wasu irin gidaje ne manya-manya na alfarma da ƙasaita a cikin gurin. A ƙofar wani gida direban ya tsaya, ya cewa Nana ta fito sun zo. Haka ta saukko ƙafafuwanta duk sun yi tsami saboda azabar gajiya. Ya buɗe bayan motar ya ɗaukko ƙatuwar jakar Nana, ya rufe motar, ya yi gaba Nana ta bi shi a baya tana karanto addu'oin da suka sauwwaƙa. Cikin wani matsakaicin gida suka shiga, gidan ya ƙawatu ya yi kyau sosai da sosai. A falon gidan ya ajiye wa Nana kayanta ya ce "Ki zauna ki jira a nan" Nana ta ce "Amma wa zan jira a nan ɗin, ban ga alamar akwai mutane a gidan nan ba" "Za ki gan su, ni a nan aka yi mini umarnin na kawo ki kawai" Nana ta yi shiru tana nazari, shi kuma ya juya ya fice. Nana ta din ga rarraba ido, tana son ta yi salla amma babu wanda za ta tambaya. Harabar gidan ta fita saboda ta ga famfo ta yi alwala, ta dawo falon ta yi salla. Gajiya ta yi ta koma harabar gidan da kayanta, ta zauna tana rarraba ido. Can ta ji ƙarar mota, aka buɗe ƙofar wani jami'in tsaro ya shigo ya buɗe gate ɗin, aka shigo da wata haɗaɗɗiyar mota aka yi parking ɗin ta. Aka buɗe ƙofar motar, sai ga Asal ta fito sanye cikin doguwar riga, ta ɗaura mayafin a wuyanta, kanta babu ɗankwali. Har bakin ƙofar shiga suka rakata, ta wuce Nana ta shige ciki kamar ba ta gan ta ba. Nanan ma ta yi zamanta ba ta shiga ba, ta jingina da jikin kayanta taka addu'a saboda a gajiye take matuƙa, ga uwar yunwa tana ji ga tulin damuwa. Sannu a hankali take tuna yadda ta shigo ƙasar Nijar ba ta san kowa ba, da yadda ta din ga raragefe har zuwa kan zamanta da Nene. Sai ta tsinci kanta da tattara su baki ɗaya tana yi musu addu'a, da fatan dacewa a Duniya da lahira. Ba ta san iya adadin lokacin da ta ɗauka a gurin ba, ta ji muryar Asal a kanta. "Wai ke wace irin bagidajiya ce, a Nigeria daga wani ƙauyen ki ke ne?" Nana ta ɗaga kai ta kalle ta. "Na saka an kawo ki guri, ki shiga ki jira ni kin zauna a waje, na dawo ma kin nemi guri kin zauna ba za ki shigo ba?" "Ta yaya zan shiga gurin da babu kowa na zauna, ni da ban san ma aikin da ki ka kawo ni na yi miki ba?" Haushi ya kama Asal, ta ce "To idan kin ga dama ki shigo, idan kuma ba ki ga dama ba, ki yi ta zama a gurin" Ta shige ciki Nana ta bi ta da harara, kamar ba za ta tashi ba, sai kuma ta tashi ta ja kayanta, ta shiga falon ta nemi guri ta zauna a kan kujera. Asal ta saci kallon Nana, da yadda take gudanar da lamarinta cike da ƙarfin hali. Nana ba ta kula ta ba, ita ma ba ta kula ta ba, Nana ta gaji da zama, ta saukko ƙasa ta miƙe ta kwanta. Can Asal ta ce mata "Ga kitchen can, akwai abinci" Daga haka ta tashi ta bar falon. Nana ta tashi ta shiga kitchen ɗin, ta tarar da Abinci, ta ɗauka ta ci sannan ta ɗan dawo hayyacinta. A nan falon Nana ta kwana, da Asuba ta yi alwala a harabar gidan, ta koma falon ta yi salla. Duk wannan abin zuciyarta a cike da zullumin aikin da za ta yi wa Asal. Da gari ya yi haske, Asal ta fito Nana ta gaishe ta, amma ta yi kamar ba ta ji ba, ta fice ta bar gidan ta bar Nana. Nana tana nan zaune, aka zo aka ƙwanƙwasa ƙofar falon, ta tashi a ɗan tsorace ta buɗe, wani mutum ya miƙo mata takeaway ya ce "Ga shi nan, aka ce a kawo miki" daga haka ya juya ya tafi. Nana ba ta sake ganin Asal ba sai dare, ba ta saurari Nana ba still. Ta cika gidan ita da ƙawayenta, suka hau saman bene, suka kunna kaɗe-kaɗe har kusan ɗaya na dare su na abu ɗaya, suka hana Nana bacci. Sai gefin Asuba suka daina wannan shirirtar, Nana ta din ga mamakin ita Asal zaman kanta take yi ne, ba ta da magabata ko kuwa? Sai washegari sannan ta saukko ƙasa, a lokacin ƙawayen nata duk sun tafi. Ta kalli Nana ta ce "Daga yau kar ki ƙara kwanar mini a falo, ga ɗaki can kusa da kitchen, a nan za ki din ga kwana. Na kawo ki ne duk da ba yanzu ne za ki yi aikin naki gaba ɗaya ba, amma za ki din ga yi mini girkin Abinci da ni da ƙawayena, da sauran aikace-aikacen gida. Abu na farko dalilin da ya sanya na ɗaukko ki, ke ba ƙabilarmu ba ce ba, ba na son saka ido, ba na son surutu Duk wani abu da za ki ga na yi, ko ina yi babu ruwanki, aikin duk da na saka ki shikaɗai za ki yi mini" Nana ta yi shiru tana tunani, dama duk wannan abin ba wani branch ɗin za a kai ta aiki ba, wannan zuƙaƙƙiyar za ta yi wa bauta, shi ne har da ci mata mutuncin cewa an yi amfani da kuɗi sai ta yi abin da ake so. Kuma me yasa ba ta zaɓi kowa ba sai ita?. "Ba kya ji na ne?" "Na ji" "Ban gane kin ji ba? Haka zan din ga yi miki magana ki na amsa mini, ke ni fa ba Hasna ba ce ba, dole ki yi mini biyayya ki yi duk abin da nake so". Nana ji ta yi tamkar ta yi tsaki, ta ce "Amma yanzu fisabilillahi duk faɗin ƙasar nan ki rasa wanda za ki ɗaukko ya yi miki aikatau sai ni. Ni harkar dafa abinci nake yi, amma kin kawo ni nan in din ga yi miki girki da boyi-boyi ba tare da an yi mini bayanin haka ba, ni gaskiya ba a kyauta mini ba" "Da hakan ki ka dace ai, ko kina ganin kin cancanci wani abin bayan bauta? Idan ba za ki zauna ba ga hanya nan za ki iya tafiya" Ta yi maganar tana miƙewa tsaye. Har ta yi gaba sai kuma ta tsaya ta ce "Duk wani abu da za ki buƙata akwai shi a kitchen, kina iya dubawa, wanda babu kuma ki sanar mini, shi ma idan ba ki ga dama ba kar ki yi aikin" ta yi gaba ta bar Nana da ta gama ƙulewa. ***** Gaba ɗaya Shukura ta burkicewa Sagir, ba ɗaga masa hankali ta yi da rigima ba, tattara shi ta yi ta watsar gaja ɗaya take harkokinta, da gaske take ƙoƙarin gano abin da mahaifinta yake ɓoyewa tsawon wannan lokacin da har ya hana Hajiya Amina bincike a kan lafiyarta. Ga shirin tariyar Yusra Sagir na yi, ga damuwar rashin sakin jiki da shi da Shukura ta yi, ta tattara shi ta watsar. Ɓangarensa ya saka aka gyarawa Yusra, dama ba amfani yake yi da shi ba, aka ƙara gyara shi, aka haɗa gidan gaba ɗaya aka sake yi masa fenti. Daga gaya mata batun dawo da Yusra zuwa gyaran gidan da kawo kayanta, ba a yi sati guda ba, gida ya ɗau harama. Duk yadda ya so ya lallaɓa Shukura, ta saukko ta din ga saurararsa ta yi burus da shi. Nana ta shafe sati guda tana gidan Asal, tana yi mata hidima, ta hantare ta ta kyare ta, dandazon ƙawayen da take tarawa ma, su hana ta sukuni da aiki. Nana ta din ga iya ƙoƙarinta, gurin kai zuciyarta nesa, amma abin ya fara isarta. Tana tsaka da nazarin yadda za ta ɓullowa lamarin, da safe Asal za ta fita ta kalli Nana ta ce "Ki shirya nan da sati ɗaya zamu bar nan, zamu je asalin inda na ɗauke ki ki yi mini aiki a gurin" Nana ta ce "Ina kenan? Kuma aikin me? "Idan mun je za ki gani" Ta ba wa Nana amsar a taƙaice. ***** Jamila tana kwance tana chatting da Abba, bikinsa saura sati biyu. Hajiya Sa'a tana ta zaginsa da yi masa bala'i, a kan yadda yarinyar take ta ƙorafin ba ya kula ta, waya ma sai dai ita ta kira shi, babu abin da ya yi masa zafi da ita. Yanzun ma kamar ya yi wa Jamila kuka. Ita take ta rarrashinsa tana nuna masa babu komai ya yi aurensa kawai. "Ƙanwata ko na yi aure hankalina ba zai kwanta ba, kar ki manta da ɓarnar da ta faru tsakanina da ke, ya zan yi da shi" Ta ce "Na san kai mutumin kirki ne yayana, hakan ne ya sanya ka ke jin damuwa a kan abin da ya faru, amma ka yi haƙuri ka yi aurenka kawai, ina roƙon Ubangiji Allah ya kawo mini wani mijin" "A'a ki daina faɗa mini haka, zuciyata tana sosuwa, baki da wani miji sai ni in sha Allah" haka suka kasance tana ƙarfafa masa gwiwa, shi kuma yana rarrashinta. Ta gama wayar ta ajiye, ta ga Suwaiba ta ƙuro mata ido tamkar ba ta taɓa ganinta ba. "Meye ki ke kallona, lafiya?" Suwaiba ta yi shiru ba ta bata amsa ba, kuma ba ta yi magana ba. Jamila ta ja tsaki, tana ƙoƙarin kwanciya, Suwaiba ta ce "Jamila" "Na'am mene ne?" "Ki ɗauki saƙonki mana" Cikin rashin fahimta ta ce "Wane saƙon?" "Na cikin jakarki" "Cikin jakata kuma? Mene ne a jakar tawa? Wato bincike ki ke yi mini a jakar ko?" "A'a ni tuni kawai nake yi miki da saƙonki na cikin jakar" Jamila ta tashi zaune ta ce "Wai wani saƙon? Miƙo mini jakar dai na gani" Suwaiba ta ce "A'a ba zan taɓa miki jaka ba" Jamila ta janyo jakar ta fara buɗewa ta ga abin da Suwaibabta dame ta a kai. Cin karo ta yi da wannan 'yar tsanar da ta riga ta jefar. Saura ƙiris ta kurma ihu, ta rikice gaba ɗaya jikinta ya hau rawa, a tunaninta tun da ta yar shikenan ta rabu da ita. Suwaiba kuwa ta tuntsure da wata irin mahaukaciyar dariya, ta din ga yi tana ƙyaƙyatawa tana kallon Jamila. Gaba ɗaya Jamila ta kiɗime ta rasa abin da yake yi mata daɗi, gaba ɗaya jikinta ya hau rawa tamkar ta kurma ihu, sannu a hankali kanta ya fara juyawa ta fara gani dishi-dishi, dole ta rufe jakar ta nemi guri ta kwanta. ***** Alhaji Zailani ya kwana biyu bai je gidan Alhaji Fatuhu ba sai yau. Sai dai ya sha mamakin ganinsa a harabar gidan da sanda yana dogarawa yana tattakawa a hankali, yana tsaye a kan ƙafafuwansa yana kallon yadda Muhsin yake ta gudu a harabar gidan. Sai da ya aro jarumta sannan ya iya danne abin da ya ji ya taso masa na tashin hankali da mummunan baƙin ciki. Da ƙyar ya iya washe baki ya ce "Ikon Allah, Abokina kai ne haka nake gani?" Alhaji Fatuhu ya yi murmushi ya ce "Ka ga ikon Allah ko? Sannu da zuwa Bismillah" ya yi maganar yana nuna masa ɗaya daga kujerun da ke ajiye a gurin. Alhaji Zailani ya zauna suka ƙara gaisawa "Bani labari, ya aka yi sauƙi ya samu haka, wani Asibitin ka je ne?" Alhaji Fatuhu ya ce "A'a na ga an yi na Asibitin ne babu wani ci gaba, Fadila ta zauna ta din ga yi mini bayani, na amince muka fara gwada na islamic, cikin ikon Allah sannu a hankali wannan ɗaurewa da nake ji a jikina ya yi mini sauƙi, wannan gigicewar da nake na ji kamar zan yi hauka shi ma Alhamdillah ina daɗewa ban ji ba, wannan warin ma da nake ji ya ragux "Amma Fatuhu ya za a yi ka biye wa mace da shirmen ta, ga na Asibiti ana yi kawai ta saka ka fara wani na shirme, sai ka je ka yi abin da za ka kauce wa hanya tukuna?" "A'a nima na jaddada mata, ta kuma tabattar mini da babu kauce hanya a ciki, kuma nima shaida ne, shi ya sanya ma nake amfani da magungunan kuma ana samun ci gaba" Alhaji Zailani ya miƙe ya ce "Haka ne, to bari na je dama ina da gurin da zan je na biyo, sauri nake yi" "Ba zaka tsaya ku gaisa da mutanen gidan ba?" "Sauri nake yi zan sake dawowa"ya yi maganar yana yin gaba cikin ƙunar rai, ji yake yi tamkar ya kashe Alhaji Fatuhu ya huta, dan shi bai taɓa zaton zai kawo yanzu bai mutu ba. ***** Al Hussain ne a tsaye ya tsare Hasna da ido, yana yi mata faɗa cikin matsanancin ɓacin rai. "A kan me za ki yi haka? Dan me za ku yi mata dole, ai ba ɗaukar ta aiki muka yi saboda buƙatar mutum guda ba. Abin da yake cikin yarjejeniya shi ne ta yi wa gidan Abincinmu aiki, idan ma canza gurin aikin ne, wani reshen zamu mayar da ita, amma dan me za ku haɗa kai ku yi mata haka wannan wulaƙanci ne da cin zarafi, kuma ga shi bama 'yar ƙasarmu ba" "Ni fa Al Hussain na kasa gane maka, ko son yarinyar nan ka ke yi ne? To bari na tuna maka kai Buzu ne, buzun ma farin buzu ka san abin da nake nufi ai, kuma matar aure ce ko bazawara dan ta ce mana tana da ɗa ma" "Ni ba wannan na tambaye ki ba, dan me Asal za ta yi amfani da ƙarfi da kuɗi ta tursasa mata yin abin da ba ta so, ai ba haka ake rayuwa ba" "Ai na san za a yi haka, babu bayanin da ban yi mata ba taƙi yadda, ga shi ni yanzu ka zo ka saka ni a gaba da jaraba, sai ka je ka dawo da ita ni ba zan iya ba" "Ke dai da ki ka yi hakan ki je ki dawo da ita, idan ba haka ba daga ke har ita na rubuta masa abin da ku ka aikata, daida yake da ku" Ta kwaɓe baki ta ce "Wa ya san ma inda yake, mutumin da ake tunanin ya ɓata babu wanda ya san ma yana raye ko yana mace?" "Hakan ya baku damar cin karenku babu babbaka daga ke har Asal ko? Yayi muku kyau" Hasna ta fice tana jin haushin masifar da Al Hussain yake ta yi mata, duk yadda ta yi ƙoƙarin hana Asal ɗaukar Nana. ***** Ana gobe su Nana za su bar wannan gidan, Asal ta sanar da Nana ta shirya washegari za su bar nan. Ita dai Nana ta sanya wa sarautar Allah ido, rayuwarta ta zama tamkar tamaula daga nan zuwa can, ba ma ta da 'yancin tambayar ko sanin inda za a kaita sai dai inda ta tsinci kanta kawai. Ta sha aiki ta gama, ta ɗan zauna a falo tana hutawa, sai ga ɗaya daga gayyar ƙawayen Asal ta saukko ta kalli Nana ta ce "Dan Allah ina son shayi" Nana ta ce "Akwai a kayan Abincin da na girka" "Shayin kanumfari kawai nake so bana son Shan na girfa" "Ga gurin dafawar can, idan ki ka je akwai komai, ki dafa ki sha idan kin matsu" "Ke, kin san wace ce ni ki ke gaya mini haka?" "Ban san wace ce ke ba, kuma ba na buƙatar sani" Asal ta saukko tana tambayar lafiya. Ta gaya mata abin da ya faru, ta kalli Nana ta ce "Wai ke me yasa ba ki da mutunci, ban gaya miki dole ki girmama baƙina ba, mene ne a cikin dafa shayi mintinan nawa ne kin yi kin gama?" Ta kalli Asal ta ce "Ki yi haƙuri, wallahi ko cokali ba zan iya sake ɗauka ba, yau na bautu a gidan nan ke kin sani, kuma ban taɓa yi miki ƙorafi ba, amma yanzu dai na gaji gaskiya" Suka juya yare suka yi magana, ba ta san me suka ce ba, ta ga sun koma kan bene. Washegari da wuri suka ɗau hanya, sai dai ga mammakin Nana, har da rakiyar jami'an tsaro, kuma a wannan karon shigar Shadda Asal ta yi, an yi wa shaddar aiki tun daga sama har ƙasa. Mota ɗaya suka hau, ta ce Nana ta hau gaba, ita kuma ta hau baya. Sai da aka kuma wata tafiyar mai nisa, sannan ta ga sun tunkari wani  irin ginin ƙasa tamkar ginin ganuwar Kano. Ginin ya ƙayatar da Nana sosai da sosai. Jami'an tsaro ne suke gadin ƙatuwar ƙofar gurin, da wasu Buzaye farare tas sanye da rawani. Nana kamar ta ce a tsaya, ta duba buzayen nan ɗaya bayan ɗaya ko za ta ga Sayyid ɗin ta cikinsu. Sai da motar su ta tsaya, suka sauke glass ɗin motar. Da Hausa suka gaisa, suka yi mata sannu da zuwa, ɗaya daga cikin su ya kalli Nana ya ce "Wannan fa?" "Baƙuwata ce" ta ba shi amsa, ya jinjina kai motar ta shige. Su na shiga Nana ta ga ai gari ne guda a cikin ganuwar nan. Sun ɗan yi tafiya kafin su shiga wani ƙaton gida. Nana ta tsaya tana ganin yadda aka yi wa ginin ƙasa wani irin ado mai ƙayatarwa. Tun da suka doshi shiga gidan, ake gaida Asal cikin girmamawa, ita kuma ta yi fuska sai taku take cike da ƙasaita, kamar ba ita ce suke rashin hankali da ƙawayenta a wancan gidan ba. Wannan gidan saɓanin wancan da mutane a ciki, kuma da alama duk a ƙarƙashin Asal suke. "Wace ce ita?" Nana ta tambayi kanta. Sai da suka ƙarasa wani falo, sannan ta yi wa wata dattijuwar magana da yaren su. Matar ta kalli Nana ta ce "Bahaushiya ce ke ko? Zo mu je na kai ki masauki" Babu musu Nana ta bi ta, matar ta kai ta wani daki ta ce nan ne ɗakinta. Sai da Nana ta kwana biyu a gidan, ba ta sake ganin Asal ba, ba kuma ta aikin fari ba ta na baƙi kawai tana zaune, sai dai za a kawo mata Abincin safe, rana da dare sau uku a rana. Sai dai babban abin da ya dame ta, tun da ta shigo gidan, network ɗin wayar ya sauka gaba daya, ko ta kira Nene ba ta shiga sam. A kwana na huɗu, da daddare dattijuwar matar nan ta zo ta kira Nana. Babu musu Nana ta tashi ta bi bayanta. Sun yi 'yar tafiya su na ratsa faluka masu kyau da ado, sannan suka bi wata ƙofa. Sanyin A.C ya daki Nana, ga wani irin haɗaɗɗan ƙamshi. Asal ta hahakimce a kan kujera kaɗa ƙafa. Ta kalli dattijuwar ta ce ta jira a waje. Daga ƙasa wata matar ce a zauna a kan carfet, ta gurfana kamar tana jiran Asal ɗin ta gafarta mata. Nana ta yi turus tana tunanin a ina za ta zauna, sama ko ƙasa. Matar ta kalli Nana cikin zare ido ta ce "Ke ki rage tsawon ki, kin tsaya mata a ka" Nana ta ja guri ta zauna a kan carfet ɗin ita ma. Asal kamar ba za ta yi magana ba, sai da ta gama iyayinta ta sauke ƙafarta ƙasa ta dubi Nana ta ce "Amm na saka an kirawo mini ke, saboda ki san abin da na kawo ki gidan nan ki yi. Ke dai da ganin gidan nan kin san ba gurin da za a yi wasa ne ko shirirta ba, babban gida ne na mulki. Saboda dalilin girki da kuma wani dalili na ƙashin kaina, ya sanya na kawo ki gidan nan. Ba a ɗaukko bare wanda yake ba jinin gidan nan ba, ko ƙabilarmu ba ya yi mana aiki, amma na ga wasu abubuwa a tattare da ke da ya sanya na kawo ki cikin gidan nan. Kamar yadda na gaya miki, ina ƙara jaddada miki, zaman ki a gidan nan dole ki yi taka tsantsan, babu ruwanki da shishshigi, saka ido, gulma ko kuma shiga abin da babu ruwanki. Sannan kar ki kuskura wani ya ce zai haɗa kai da ke a yi wani abu, rayuwarki za ta iya salwanta ba tare da kowa ma ya sani ba, dan haka sai ki san irin zaman da za ki yi." Nana ta yi shiru ta gama sauraren ta, sai dai har a lokacin ba ta ji dalilin da ya sanya Asal kawo ta gidan ba, dafa abinci kowa ma zai iya mai yasa sai ita. Wannan matar da ta tarar a zaune, ta tafi da ita, ta kai ta gurin da ake girke-girken abinci, da gaya mata yadda jadawalin girke-girken gidan yake. Ta ɗaukko kayan ds Asal ta bayar a ba ta, na kayan shafe-shafe da mayukan wanka zuwa kayan sakawa. Da Nana ta koma ɗakinta, ta kalli kayan ta fara tunanin Allah ya sa ba kwance Asal ba ne, dan gara ta saka kwancen Ashura da ta saka na Asal, da ba ta da mutunci. A washegari Nana ta fara aiki a wannan madafa, sai dai madafar daban-daban ce. Akwai wadda ake girkin da ma'aikatan gidan ne suke ci, akwai wadda na baƙin da suke zuwa ne, sai kuma masu girka wa Asal abinci daban, dan haka Nana na cikin masu yi wa Asal girki. Sosai matar nan ta ƙara jan kunnen Nana, a kan ta kula da kanta, dan muddin aka samu matsala ba za ta sha ba. Nana a ranta ta ce "Ji wata jaraba, da wannan wahalar mutum ya girka abin da zai ci mana da kansa." Kwana huɗu da fara aikinta, ranar Alhamis da daddare, tana shirin kwanciya, aka ƙwanƙwasa ƙofar ɗakinta. Ta tashi ta buɗe, ta ga shugabar girke-girke ta gidan, kamar yadda aka gabatar mata da ita a baya. "Ki sako hijjabinki, ki biyo ni" Nana ta saka hijjabinta ta fito tana tunanin ko lafiya. Harabar gidan matar ta yi, Nana ta bi bayanta, ta nuna mata mota. Nana ta kalli dare ya yi kuma an zo da mota an ce a tafi da ita. Cike da mamaki Nana ta shiga motar, sai ta ga mutum uku, da su ma duk tare suke aikin girkin a gidan a cikin motar. Ta shiga ta zauna, ita ma shugabar ta su ta shiga. Nana ta gaza haƙuri ta ce "Dan Allah ina za mu je ne?" "Za ki gani" "Eh amma na ga dare ne fa" "Idan mun je za ki ji dalilin fitar" Nana ta yi shiru tana tunani, ita ba ma wannan ba, hankalinta ya koma kan rashin samun damar kiran waya da ba ta iya yi, kuma ba a kiranta ya shigo. Dan sai da ta tambayi ɗaya daga cikin masu aikin, ko matsalar daga wayarta ne, ta ce mata kar ta kuskura ta bari ma a san tana da waya, dan sai an ƙwace ta. Tana ta zancen zuci, har suka isa inda aka tsaya suka sauka, aka shiga da su. Asal ce a tsaye, tare da dattijuwar matar da ta saka ta raka Nana masauki. Suna tsaye a cikin ɗakin Nanan. Asal ta ce "Zazzage mini kayanta, ki ɗaga mini komai ɗaya bayan ɗaya" Ayshercool 71 Ɗaya bayan ɗaya, aka din ga zazzage kayan Nana. Aka zazzage su tsaf aka Azzage jakar da ta zuba kayan turarukanta da mayukan shafawa, duk ba ta ga wani abu ba, sai jakar gurin sarkin baka. Ta nuna jakar ta ce "Mene wannan?" Ta ɗago jakar ta ce "Jaka ce" "Buɗe ta ki zazzage na gani" Ta fara kokowar buɗe jaka, amma babu gurin da zata buɗe ta. Kawai ta ce "Shikenan" ta fice ta bar ɗakin. Can gurin kuma Nana tara su aka yi, su shida. "Na san za ku yi mamakin dalilin da ya sanya aka kawo ku nan, to zaɓo ku aka yi saboda an yarda da amanarku, ana daf da yin taro da Sultan da kuma dukkanin Imams na gidan nan. Dan haka ku aka zaɓo za ku yi girki na musamman. Amma ku sani kamar yadda wasu sani wasu ba su sani ba, muddin aka samu wata matsala ko ƙware wani ya yi, a sanadin abincin da ku ka dafa, to ku tabattar da rayuwarku za ku biya. Dole ku yi taka tsantsan ku kula." Matar ta yi maganar daki-daki. "In sha Allah" suka amsa mata. Ta ce su bi bayanta, suka je wani ƙaton guri, ɗauke da nau'oin kayan masarufi kala-kala. Ta yi musu bayanin da su ne za su yi amfani su yi girkin, sannan ya zama dole su sanya wa bakinsu sakata su yi aiki cikin amana, kuma kada wanda ya san su aka zaɓa da za su yi wannan girki. Nan ma suka amsa, ita dai Nana sai kallo da ido, dan abubuwan sun daina ba ta mamaki, wannan maganar ce ta sanya aka taso ta a daren nan, sai ka ce wanda za su girkawa wasu waliyyai abinci. Ko da aka mayar da su Nana gida, ta sha mamakin ganin kayanta a hargitse a cikin ɗaki. Da mamaki ta ƙarasa kan kayan nata, ta ɗaɗɗaga. Cikin takaici Nana ta tashi ta fita, sai dai kowa ya tafi makwancinsa ya kwanta. Kawai ta ji taku a bayanta. Ta waiwaya ta ga Asal na fitowa. "Har kun dawo kenan?" "Eh, sai dai na shiga ɗakina na tarar da an caje mini kayana an zubar da su a ƙasa, ban sani ba ko kina da masaniya a kan haka?" Asal ta ce "Me yasa ki ka zarge ni?" "Saboda na ga ba a gudanar da komai a gidan nan sai da izninki" Asal ta yi murmushi ta ce "Haka ne, kina da kaifin ƙwaƙwalwa kamar yadda na yi tsammani, ni na saka aka caje kayanki saboda na san da wa nake zaune" "Me yasa ba ki tambaye ni abin da ki ke buƙatar sani ba, za a caje mini kaya" "Saboda a ƙarƙashina ki ke, a gidana ki ke zaune dole na sani idan da wani abu da ki ke tattare da shi na cutarwa" Nana ta ce "Kin yi kuskure, dan ina zaune a ƙarƙshinki, ina da personal life ɗina, da 'yancin adana abin da yake sirrina, bai halatta ki bincikar mini kaya a bayan idona ba. Yaushe na san ki, da zan ƙulla wani abu da zan cutar da ke? Kina gudun hakan ki jawo ni ki ka kawo ni?" "Yi ƙasa da muryarki, kar ki kuskura ki ɗaga mini murya, kin san matsayina? Za ki iya janyo wa kan ki gagarumar matsala muddin ki ka ci gaba da yi mini magana ba ladabi" "Babu ruwana da matsayinki, da koma me za ki yi mini, kar ki sake shigar mini ɗaki ki taɓa mini kaya, idan kuma ki ka ci gaba za ki iya binciko abin da zai hana ki sukuni, idan kin ji ba ki yarda da ni ba, ki sallame ni na koma inda na fito, ba zai yiwu na zauna da ke kina zargina kuma kina cin dunduniyata ba." Asal ta bi Nana da kallon mamaki, amma ta danne mamakinta ta haɗiye fushinta, ta ce "Gaskiya ne, kin yarda da kan ki har haka kenan? Shikenan amma idan na ga akasin abin da ya fito daga bakinki, za ki sha mamakin abin da zai faru" Nana ta yi mata banza, ta koma ɗakin nata, ta gyara kayanta tsaf. Ta kulle ɗakin ta koma ta ɗaga katifar ɗakin, ta ɗaukko wata jaka, a cikin jakar ta zuba duk tarkacen kayan Sayyid. Ajiyar zuciya ta ts yi, da tayi wannan dabarar ta ɓoye su. Haka kurum take jin kayan na buƙatar sirri. Ta nemi guri ta kwanta tana sauke numfashi a hankali, tana tunanin yadda rayuwa ke ta jujjuyata. ***** Shukura na zaune a ɗakinta tamkar zuciyarta za ta yi bindiga ta fito, Sagir ya buɗe ƙofa ya shigo ɗakin. Kallo ɗaya ta yi masa ta sunkuyar da kai. Tuni t yi shirin kwanciya baccinta, sai ƙamshin turare take zubawa. Ya sha manyan kayansa, hannunsa riƙe da baƙaƙen ledoji. Ya zo ya zauna a kusa da ita, tamkar ta kifa masa mari haka take ji. "Wai har kin yi shirin kwanciya? Na zata zaku gaisa tukuna sai ki kwanta" Mugun kallon da ta yi masa ya sanya shi haɗiye maganar da ya yi niyyar yi. "Ga wannan naki ne" Ya yi maganar yana ajiye mata ledojin hannunsa. Ba ta kalli kayan ba, kuma ba ta motsa ba. Ya matsa kusa da ita, ya riƙo hannunta, ta fizge hannunta ta haye kan gadon ta kwanta. Bai ji haushin abin da ta yi masa ba ko kaɗan, ya san idan ba ta son sa ba za ta yi kishinsa ba, sai dai ita ma Yusra tana buƙatarsa tun da tun farko bai kamata ya sake ta saboda larurarta ba. Ya tashi ya kashe mata fitila, har zai fita ya koma gaban gadon, ya durƙusa daidai fuskarta ya ce "Ki yi mini afuwa Shukura, ban yi haka domin na cutar da ke ba, ko na muzguna miki, dan Allah ki kwantar da hankalinki saboda lafiyarki da abin da yake cikinki" Daga haka ya tashi ya fice. Sai da ya fita sannan ta ba wa hawayen da suka maƙale a ƙirjinta damar zirarowa, zuciyarta ta din ga yi mata ƙuna, tamkar ta tashi ta bar gidan. Duk da ya fita da damuwar halin da Shukura take ciki, amma bayan wani ɗan lokaci tuni ya manta, suka ci suka ƙoshi da shi da Yusra. Bayan sun gabatar da salla, sun yi addu'oi, suka yi zamansu kawai su na hira. Sai gurin ɗaya saura sannan suka tashi suka kwanta. Yadda Sagir yake murna da kasancewa da Yusra, ko aurensu na fari bai yi haka ba, tuni wani nannauyan bacci ya yi awon gaba da su, daga shi har ita. Shukura kuwa yadda ta ga rana haka ta ga dare, ga wani irin zafi da ya addabe ta duk da na'urar sanyaya ɗaki da ke cikin ɗakin. Washegari sai ƙarfe sha ɗaya na safe ya shiga ɗakin Shukura. Idonta kawai ya kalla ya ga alamun rashin bacci a tattare da idanunta, sun yi jawur sun kumbura. "Oum Haidar" ya kira sunanta, yana zama a kan gadon, tana shan tea. "Ina kwana" ta faɗa a taƙaice. Idanunsa ya sauka a kan ledar da ya kawo mata, babu alamar ko taɓa ledar ta yi. "Shukura me yake damunki ne haka? Na kawo abu ko taɓawa ba ki yi ba, kin yi bacci makuwa" "Sagir, dan Allah ka tashi ka bani guri, ni bana buƙatarka a kusa da ni, kaɗaici nake so" "Ni ki ke cewa na fita na baki guri?" Ya yi maganar yana nuna kansa. Ƙoƙarin mayar da hawayen da ke shirin zubo mata take yi, amma abu ya gagara kawai ya fara zubowa ba tare da ta shirya hakan ba. Jikinsa ya yi sanyi, ganin yadda take kuka sosai da sosai. Cikin kwantar da murya, yake ƙoƙarin rarrashinta, amma ta tashi ta shige banɗaki ta bar shi a gurin. Ya yi shiru ya rasa abin da yake yi masa daɗi, shi babbar damuwarsa ma cikin da take ɗauke da shi, ga matsalarta ta hawan jini. ***** Tamkar bayi haka su Nana suke aiki, kullum za a ɗaukkosu daga wancan gidan da Asal take, a kawo su nan su wuni su na aiki. Har mamaki take yi wannan mutanen su kuwa har su nawa ne, dan kamar har da almubazzaranci a cikin lamarin. Sai dai kowa cikin kaffa-kaffa yake aikin tare da fatan kar wani abu ya biyo baya da za a kama su da laifi. Kwana na uku, wanda ranar suka dafa normal Abinci, sauran kwanakin kayan snacks ne suka din ga yi. Duk cikin su Nana ce 'yar Nigeria, sauran duk 'yan Nijar ne, sai dai galibinsu baƙaƙen buzaye ne. Sai da suka kammala aikin, aka ba su wasu kaya fararen dogwayen riguna, da rigar girki, aka saka su kai Abincin wani ɗaki. Katafaren ɗakina da dogon tebur, an gyara shi sai tashin ƙamshi yake yi. Sai dai gabanta ya yi mummunan faɗuwa da jin irin ƙamshin da yake tashi a ɗakin. Take jikinta ya hau rawa, har ta nemi ta kifar da abin da ta ɗaukko. Ta ɗaga kanta a hankali ta kalli jerin manyan frames ɗin da ke ɗakin, sai dai mutanen jikin hotunan, dukkaninsu fuskokinsu a rufe yake, ba ta iya gane kowa daga cikin su ba. "Ke Nana ki kai mana kin ja kin tsaya" Nana ta jinjina kai jiki a sanyaye ta ƙarasa gaban teburin. Ta ajiye kayan, ta ɗaga kai ta kalli yadda ginin ɗakin yake da matuƙar tsayi. Jiki a sanyaye ta ci gaba da kai komo, su na shirya abincin. Bayan sun shaƙe teburin da uban kayan Abinci, aka ba su umarnin su tsaya kar wanda ya fita. Su na tsaye Nana ta kalli agogon ɗakin, ƙarfe goma na dare. Wani ƙaton mutum ya shigo, ya kalli gurin da yadda aka shirya teburin, ya kalli su Nana ya ce "Waɗanan ne suka yi girkin?" Balaraba wadda ita ce ta jagoranci su Nana gurin girke-girken ta risuna ta ce "Eh su ne ranka ya daɗe" "Wace ce wannan? Na ga kamar ba tamu ba ce" Ya yi maganar yana nuna Nana, da gaba ɗaya rabin hankalinta ba ya jikinta. Balaraba ta ce "Gimbiya Asal ce ta zaɓo ta, ta saka ta a cikin masu girkin" Ya yi shiru yana kallon Nana, daga bisani ya jinjina kai ya kalli Balaraba ya ce "Ki je, su su tsaya" Ta jinjina kai ta fice. Wata ƙofa aka buɗe, wani matashi ya shigo fuskarsa ɗauke da murmushi, gaban Nana ya yi mummunar faɗuwa, dogo ne sanye da farar jallabiya ya ɗaura hirami a kansa, ba dan ta yi wa Sayyid kyakykywan sani ba, za ta iya cewa shi ne. Ƙirjinta ya tsananta bugawa, sai dai kafin ta daidaita nutsuwarta, wani ma ya biyo bayansa, shi ma dai kamarsa ɗaya da Sayyid ɗin. Tunani ta fara yi ko Giyaz da Ƙaisar ne suka fara yi mata gizo suke yi mata wasa da tunani. Ɗaya bayan ɗaya suka din ga shigowa, sai da ta ƙirga mutum biyar cif, biyu kamar su ɗaya sak, sauran ukun kuma su na kama amma ba sak da Sayyid ba. Duk suka jeru a kan kujerun teburin nan. Sai dai babbar kujera babu kowa a kai, kujerun gefe da gefen kujerar ma babu kowa a kai. Ɗaya daga cikin su ya ce "Ko waye zai hau wannan kujerar?" Ya yi maganar yana nuna ɗaya daga kujerun da babu kowa a kai. "Wannan karon dai za mu ji me Sultan zai ce mana a kan maganar" "Nima dai abin da nake son ji kenan, magana ta gama cika gari ba a san inda yake ba, ana ma tunanin ko ya mutu suke ɓoyewa" Nana ji ta yi ana busar sarewa a ƙofar bayan su, gaba ɗaya suka ja gefe domin bayar da hanya. Wani dattijo ne fari sol, mai dogon gemu ya shigo jallabiyarsa baƙa, ya lulluɓe kansa da hiraminsa. Gaba ɗaya ta ga abokan aikinta sun rikice, duk sun sunkuyar da kansu ƙasa, Nana kuma ta yi masa ƙuri da ido. Sai dai ba shi take kallo ba, ji take tamkar numfashinta ya ɗauke, kamar ba a cikin duniya take ba, duniyoyin da Ƙaisar ya saba kaita ne ya caza mata kai, banda haka wani irin mummunan gizo ne wannan?. Gaba ɗaya matasan suka miƙe tsaye, cikin matsanancin mamaki suna kallon na bayan dattijon. Tamkar yana tausayin ƙasar haka yake taka ta, yana ɗan yin rangaji kaɗan, sassanyan ƙamshin turaren sa da ko a mafarki ta ji shi tana tantancewa ya karaɗe ilahirin gurin, fiye da ƙamshin turarukan da ke tashi a gurin. Ta kusa da ita ce ta ja hannunta da ƙarfi, saboda yadda ta tsare shi da idanunta ko ƙiftawa ba ta yi. Ya zo zai gifta ta, amma ko gurin da suke bai kalla ba, ɗaya bayan ɗaya suka din ga rungume shi, cike da murnar da wasu har zuci, wasu kuma iya ta fuska ce. Ta ga ya zauna a kan kujerar da ake tababar wa zai zauna a kai kafin ya shigo. Abdou ya ce "Kun yi mamaki ko? Ba ku yi zaton ganinsa ba?" Ɗaya daga cikin su ya ce "Gaskiya ne" Sultan ya yi murmushi ya ce "Kamar dai yadda na gaya muku a baya, Imam Hammad yana Faransa neman lafiya, bayan tsawon wannan lokacin, yau ya kasance tare da mu a liyafarmu ta ƙarshen shekara, dama wannan ne bazatar da na ce zan yi muku" Nana ta kalli hotunan nan, sai ta yanzu hotunan babu rawani, kowa hoton fuskarsa ce. Ta tsayar da idonta a kan hotonsa da aka rubuta Imam Hammad Jalal Agadez. A take ta tuna da sunan gidan cin abinci da ta yi wa su Al Hussain aiki. H.J Agadez. Sunan rukunin gidajen da ta fara zama da Asal shi ma sunan da ke jikin symbol ɗin unguwar kenan. H.J Agadez. Duk surutun da ake yi, da murnar ya dawo, yana ƙame a kan kujera, fuskarsa babu yabo babu fallasa. Sai daga bisani ya saka hannunsa ɗaya a kan ƙirjinsa ya risunar da kansa ya ce musu "Merci(Na gode) Duk da a hankali ya furta, amma ko cikin murya dubu Nana ba za ta gaza tantance ta Sayyid ba. Abduou ya kalli su Nana, ya kalli mutumin ɗazu da yake tambayar wace ce "Guda biyu daga cikin su ta zo ta ɗanɗana Abincin nan" Mutumin ya ƙare musu kallo, ya nuna Nana ya nuna wata ya ce su je su ci kafin a ci. Nana ba ta san a yadda take iya ɗaga ƙafafuwanta ba, saboda ba ta jin su a jikinta, zuciyarta kuwa kamar za ta tarwatse saboda bugun da take yi fiye kima. A hankali ta ƙarasa gaban teburin. Ɗayar ta din ga bubbuɗe Abincin, ta fara ɗanɗanawa. "Ke kina da gaskiya kuwa? Ki ɗanɗana aka ce?" Abduou ya yi mata maganar cikin tsawa. Rikicewa ta yi gaba ɗaya, ya ɗaga idonsa ya kalli inda jikinta yake rawa, suka yi ido huɗu, ya kawar da kansa yana mamakin yadda take a ruɗe. Ta ɗebo shinkafa a cokali, amma hannunta karkarwa kawai yake yi. Sultan ya ce mata "Kina lafiya kuwa?" Ta jinjina masa kai alamar eh. Sultan ya ce "Na fuskanci a tsorace take ne kawai, a kaita ta je ta huta, wataƙila mun yi mata kwarjini ne" Aka saka Nana a gaba aka fitar da ita daga gurin. Fitarsu ke da wuya, jikin Nana ya din ga wata irin kyarma, haƙoranta na haɗuwa da juna, wani irin jiri ya din ga kwasarta. Balaraba ta nufo su da sauri, ganin Nana na dafa bango. Ya kalli Balaraba ya ce "Maza ki kaita ta huta, wataƙila ta yi aiki da yawa ne ta gaji, gaba ɗaya ta rikice, a kirawo likita kuma ya duba ta. ***** A hankali Nana ta yi juyi, ta buɗe idonta ta ganta a ɗakin da take kwana. Wata irin ajiyar zuciya ta yi, da ta tabbatar da mafarki ta yi ba gaskiya ba ne abin da ya faru. Hamdala ta yi ta ce "Ni dai na san mafarki ne da ma, dan babu yadda za ayi Sayyid ya ganni ya kasa kula ni, ya nuna kamar bai sanni ba. To wannan idan gaskiya ne ma, ta ina zan fara bayanin ni matarsa ce a yarda da ni? Mutumin da na ji ana batun ya daɗe a faransa yana jinya, anya ma Sayyid ɗina ne? Tun da dai mafarki ne duk da sauƙi. Sallama aka yi a ɗakin, ta ga Balaraba ta shigo ɗakin. Ta ce "Kin tashi?" Nana ta yi shiru tana kallonta. "Ina ga aiki da ki ka sha a kwanakin nan ne, ya sanya ki ka gaji zazzaɓi ya kama ki, Likita ya ce a bari ki huta sosai da sosai. Gimbiya Asal ta ce a baki hutu na kwana uku ki warware kan ki koma bakin aiki." Nana ta jinjina kai kawai, tana kokawa da ƙwaƙwalwarta, domin ta tabattar gaske ne, ko kuwa dai mafarkin ne? Ta tashi ta yi alwala ta yi salla, sai dai gaba ɗaya jikinta ciwo yake yi mata, ga matsanancin ciwon kai da jiri da take ji, dan haka ta nemi guri ta sake kwanciya. ***** Jamila ta ɗauki jakarta ɗauke da wannan tarkacen da take kira da tarkacen jaraba, ta fita waje, ta samu ta sayo fetur a 'yar jarka, ta samu guri ta zuba musu fetur ɗin ta kunna musu ashana ta ƙone su. Ta tashi tana kallon yadda suka din ga ci da wuta, ta bar gurin. Kai tsaye ta tari abin hawa ta tafi gidan Hajiya Sa'a. Hajiyar ta yi iya ƙoƙarinta gurin ɓoye jin haushin Jamila da take yi, ta karɓe ta hannu bibbiyu har ta taya ta lissafin kuɗin kasuwancinta da kuma kayan da take da su a ƙasa. Bayan sun kammala ta ce "Ni kuwa Jamila, yaya batun ƙungiya wa za ki bayar ne?" Jiki a sanyaye ta ce "Haryanzu ban gama tunani ba ne ba" "Tsoron dai ki ke ji haryanzun ko?" "A'a na rage ji" "To ki yi ki hanzarta ki yi abin da yakamata amma kin tsaya. Ni kalli nawa nan na shirya komai aiwatar wa kawai ya rage mini, sai na je gidan zan yi, na sake bayar da ɗan Fatuhu" Jamila ta kalli drower da Hajjya Sa'a ta janyo, tana nuna mata 'yar tsanar nan. Jamila ta ce "To idan ban kai kowa ba, akwai wani abu da zai faru ne?" Ta ce "Au da kara zube za ki zauna ki ƙi bin umarnin ƙungiya? To idan ba ki kai kowa ba, jininki aljanin zan shanye ki mutu" Cikin Jamila ya yi wata irin ƙara bayan tuna ta ƙona kayan. A tunaninta shikenan ta huta sun rabu. A ranta ta ce "Wannan wane irin bala'i ne na jefa kaina a ciki, Ubangiji Allah ka kawo mini agaji na rabu da wannan masifar. ***** Fafur Nana ta ƙi yadda zuciyarta ta amince abin da ya faru gaskiya ne ba mafarki ba, saboda ta riga ta saba da irin wannan cazan kan da Ƙaisar ya kan yi mata wasu lokutan, har ta gaza banbance abin da yake zahiri da kuma mafarki. Su na ɗakin girki su na ta ɗorawa da saukewa, ta kalli shugabar su ta ce "Dan Allah a gidan nan, babu yadda zan yi na samu waya, ina son na kira gida ne, na ji halin da yarona yake ciki" Balaraba ba ta bata amsa ba, ta ji Muryar Asal ta ce "Babu wannan damar, sai dai idan kina buƙata ki zo gurina ki karɓi wayar ki kira" Nana ta ɗan yi shiru sai kuma ta girgiza kai ta ce "A'a ki bar shi na gode" "Me yasa ki ka ce haka? Kina tunanin wani abu a ranki ne?" "Bana tunanin komai, kawai dai na fasa ne" Ta yi murmushi ta ce "Shikenan, ga saƙo can daga gidan Sultan, tukuicin aikin da ku ka yi na girki" Balaraba ta risuna tana yi wa Asal magana da yarensu, Nana kuma ta cigaba da aikinta, tana sane ta cewa Asal ba ta so, dan ba ta gama gane ina Asal ɗin ta saka gaba ba, da kuma cikakkiyar manufarta a kanta ba. Tana tsoron ta yi amfani da wata dama da za ta samu ta cutar da ita. Dogwayen riguna na alfarma Nana ta samu, guda uku da kuɗi. Ta yi murna sosai da kayan, saboda rigunan na alfarma ne. Katafaren ɗakin bacci ne, mai ɗauke da kayan alatun more rayuwa irin na masu mulki. Duhun dare ne, sai dai hasken fitilun ɗakin ya gauraye ko ina, kai ba ka ce dare ne ba. Yana zaune a gefen gadon, tare da dattijon. Cikin kamala dattijon ya ce "Imam, ina ƙara yi maka gargaɗi da jan kunne a kan ka ƙara kula da kan ka. Kar ka ɗauka kowane murmushi ne na soyayya, wani murmushin na babu yadda aka iya da kai ne. Kar ka kuskura ka faɗi wani abu da zai rusa shirinmu, mun ɓoye abubuwa da dama a game da kai, duk abin da baka fahimta ba, ka tambaye ni, kar ka wani ya buƙaci sanin wani abu daga gare ka, ka sanar masa kawai jinya ka yi tsawon wannan lokacin. "Abii" "Na'am abin ƙaunata" Imam Hammad ya yi murmushi ya ce "Me ka ke ɓoye mini ne, akwai abubuwan da suka hargitse a rayuwata, tsawon wani lokaci na ɗauka ina jinya ba a hayyacina ba?" "Ka na ji na? Haryanzu ba ka warke ba, ka na buƙatar hutu mussaman a ƙwaƙwalwarka, kar ka takurawa kanka da tunanin abubuwan da suka faru. Jita-jitar da ake yaɗawa a kan ka, da surutai daban-daban shi ne dalilin da ya sanya muka dawo da kai ƙasar nan, a shaida dai kana raye, cikin ƙoshin lafiya" "Mahaukaci ne ni kenan? Tun da ina iya tuna yadda ciwon nawa ya fara, amma ban san yaya ya ƙare ba" Sultan ya tsuke fuska ya ce "Ya ishe ka haka. Kar ka kuskura na ji labarin nan ya fita, waye ya ce kai mahaukaci ne? Larurar zuciya ce take damun ka, babu daɗi babu ƙari daga haka. Babu wata larurar hauka a tattare da kai". "Amma Sultan ko zaka saka na ɓoye wa duniya, yakamata na san matsayin lafiyata... "Hammad!" Tilas ya ja bakinsa ya yi shiru, ganin yadda ya fusata Sultan ɗin. ***** Tun da garin Allah ya waye, Nana take jin faɗuwar gaba da matsananciyar fargaba, ga sanyin da take jin yana ratasa ta, ta san ba na lafiya ne kawai ba. Dan haka ta ɗaura alwala take ta addu'a. Bayan fitowarta ta cika da mamakin ganin yadda ma'aikatan gidan, suke ta aiki tuƙuru suke gyara gidan duk da ko ina a gyare yake. Ko ta ina ƙamshin turaruka ne ke tashi daban-daban. Har sun so su yi yawa ma. Ɓangaren da take aiki, sai azalzalarsu ake yi, ta fahimci dai wani baƙo ne mai muhimmanci zai sauka a gidan. Har mamaki take yi yadda suke ba wa abinci muhimmanci, baƙo ɗaya sai a saka a yi masa abinci biyar, kuma duk da an san ba iya cinyewa zai yi ba. Ta fito kenan ta ci karo da Asal, ta sanya zani da doguwar riga na shadda baƙar shadda, kanta babu ɗan kwali, hannayenta da yatsunta duk zobunan gwal ne, uwa uba wata irin sarƙa da ta saka ta zinari tun daga wuyanta har cikinta. Gashinta ya sha ado, ta sake shi har kafaɗarta, shi ma ta sanya masa wata siririyar sarƙa da ta kwanto har goshinta. Duk hassadar mai hassada babu yadda za a yi ka kalle ta ka kushe ta, jawur da ita a cikin baƙar shaddar sai ta haska shaddar. Ita dai Nana tun da ta zo gidan, ba ta taɓa ganin Asal da miji ko 'yan uwa ba, sai tarkacen ƙawayenta, su ma a wancan gidan ne, wannan gidan ba sa biyo ta su zo. Kuma duk abin nan Nana ba ta taɓa bin diddigi ta ji wace ce Asal ba, me yasa kuma take rayuwa a gidan daga ita sai masu yi mata hidima ba. Da daddare Nana ta ji su Balaraba su na yare, su na faɗin sunan Imam, lokaci lokaci su na haɗa wa da Hausa, sai dai ta manta a inda ta taɓa jin Imam ɗin. Babban abin da ya ɗaurewa Imam kai, bai wuce yadda a faransa yake jin sa garau, ba shi da wata damuwa ko wani ciwo da yake ji ba. Amma tun da ya sanya ƙafarsa a Agadez tsawon kwanaki huɗu, ko sau ɗaya zuciyarsa ba ta saurara da bugun da take yi cikin sauri babu ƙaƙƙautawa ba. Nana na ta kai komo a kitchen, ta kammala duk wani aiki da ya shafe ta, tana shirin tafiya ta je ta kwanta. Balaraba ta ce "Saurin me ki ke yi ne Nana?" "Ina son na je na yi wanka na kwanta ne" "Ki je ki yi wankan, nan da mintuna talatin za ki kai wa Gimbiya Asal bunu da madara sashinta" Har Nana za ta yi magana, dan ba ta shiga sashin Asal sai sau ɗaya, ta taɓa zuwa idan sun yi girki akwai waɗanda suke kaɗai suke iya zuwa sashen su kai. Ta fasa maganar ta ce "To" A gurguje Nana ta kintsa, ta koma ta ɗauki kayan za ta yi gaba, Balaraba ta ce "Ai ba sashinta za a kai ba, Ramata raka ta" Ramata ta kalli Nana ta yi mata kallon banza, ta ɗan kwaɓe baki sannan ta yi gaba Nana ta bi bayanta. Duk yadda Nana ta so sarrafa kanta ta kasa, ta ɗaga kai ta din ga kallon ƙawataccen gurin tare da jinjina yadda masu gidan suka ƙware a iya almubazzaranci. Dan ba za ta kira shi ado ba kawai sai dai almubazzaranci. Tana saka ƙafarta a cikin falon, ta ji tamkar an jona mata shocking, saboda rawar da jikinta ya yi, sai da farantin hannunta ma ya girgiza tamkar zai ɓare. Ramata ta kalle ta, ta yi tsaki kawai. Nana ta ajiye kayan a hankali a kan carfet ɗin ɗakin. Bayan ta ajiye ta yi taku huɗu zuwa biyar, ta ji yadda adadin sanyin da take ji yana ƙara yawa. Ta sauke idanunta a kan ƙaton frame da hotonsa a jiki. Danƙarewa ta yi a guri ɗaya, ta kasa motsa ko da ƙafarta. Taku ta fara ji a bayanta, ana tahowa, muryar Asal ta ji tana magana da faransanci cikin shagwaɓa. Ɗan ja ya yi ya tsaya, jin yadda jikinsa ya yi wata girgiza. "Lafiya dai ko?" Ya jinjina mata kai alamar eh. "Amm me ku ke yi a tsaye a gurin nan ne?" Ramata ta ce "Abinci muka kawo" "Waye ya yi?" Ta nuna Nana da ba ta juyo ba. "Zo" ta kira Nana sai dai Nanan ta ƙame ba ta juyo ba. A wulaƙance Ramata ta taɓa ta ta ce "Ana yi miki magana" "Tana ji na rainin hankalin za ta yi mini" Sannu a hankali Nana ta juyo, idonsa na kan wayar hannunsa. Yanzu ta tabattar da mafarki ta yi ba, Sayyid ta gani, sai dai ganinsa bai razana ta ya kiɗimata ba, kamar yadda alamu suka nuna Asal matarsa ce ba. Ta sunkuyar da kanta ƙasa, tana jan ƙafafuwanta a hankali. "Me ya same ki ne?" Ta girgiza kai alamar ba komai. "Ki yi mini magana kina girgiza kai kawai" "Ba ni da lafiya" Asal ta ja tsaki ta ce "Je ki kar ki ɓata mini rai" Ta zuba masa shayin a kofi, ta zuba masa madara, ya ɗauka a hankali ya kai bakinsa yana sha. Nana kuwa a ɗakinta, gaba ɗaya ta burkice, tamkar za ta yi hauka ta ce "Dama abin da ka ke gargaɗina a kai kenan Ƙaisar? Sayyid me yasa za ka yi mini haka, dama ka na da wata matar ka aure ni? Yanzu ka na nufin ka manta ni, Sayyid anya alƙawari ya ce haka? Na haƙura zan ɗauki ɗa na na koma gida, ganinka da wata kawai ya isa ya yi ajalina. Wataƙila alhakin iyayena ne ma da na taho ba da izininsu ba. Yadda ka ke a cikin daular nan, yaya za a yi na ce ina da alaƙa da kai ma a yarda da ni?" Ka ce Ruhina da naka su na rayuwa a tare, kowannenmu yana ɗauke da ruhin ɗan uwansa, ni na yi dakon soyayyarka ashe ka na da matar da ta fi ni komai" Ta yi maganar cikin matsanancin kuka tamkar za ta fita daga hayyacinta. Yana tsaye yana jin yadda ruwan yake ratsa shi daga cikin gashin kansa zuwa jikinsa. Wani irin zafi yake ji a cikin ƙwaƙwalwarsa, tamkar kansa zai tarwatse. Karo biyu yana jin jikinsa ya yi girgiza. Ya yi wankan ya lulluɓo jikinsa da towel. Asal ta sha kwalliya cikin baƙaƙen kaya na bacci. Ta nufo shi tana rangwaɗa, ta cire towel ɗin da ya lulluɓa da shi. Ya ɗan lumshe idanunsa saboda ƙamshin turaren da Asal take yi mai jan hankali. Ta shige jikinsa ta rungume shi, ta ce "Na yi kewarka sosai Imam" "Nima ina jin kewar abin da ban san mene ba, bayan kewarki da na yi" "Akwai abin da ya fi ni muhimmanci dama, da har ka ke kewarsa fiye da ni?" "A'a ban ma san mene ba, kawai dai ina jin akwai wani abu da ba daidai ba" Ya yi maganar yana shafa gefen wuyanta, yana son tambayarta wace ce yarinyar nan, amma ya haɗiye ya fasa. Ya fara ƙoƙarin sumbatar ta, sai dai ya ja da baya da sauri yana dafe kansa, da yake jin wani sauti mara daɗin ji a cikin sa. "Imam jikin ne dai?" Bai yi magana ba, ya hau kan gadon ya kwanta ya lumshe idanunsa. Washegari da safe, idanun Nana sun kumbura suntum, saboda ba ta rintsa ba ko kaɗan. Ta saba da wuri take tashi, ta fara gudanar da aikinta, amma sai da aka zo aka kira ta, ta ce ba za ta yi aikin ba. Bayan mintuna talatin sai ga Asal a ɗakin, ta kalli Nana a wulaƙance cikin isa da gadara ta ce "Ki ka ce ba za ki yi aiki ba yau? Saboda gidanki ne ko zaman kan ki ki ke yi a gidan? An kai wa Imam shayi ya ƙi sha ya ce ba irin na jiya ba ne" "Eh ba zan yi girki ba, kuma barin gidan nan zan yi, na gaji da wannan aikin, zan je na ga yarona" Asal ta yi dariya ta ce "Ai kuma ƙarya ki ke yi. Na ɗaukko ki gidan nan saboda nesanta mijin da waɗanann munafukan hadiman, na kawo bare da baki san komai a kan harkar gidan mulki ba. Kuma ba kya cikin kalar matan da za su iya ɗaukar hankalinsa. Dan haka na kawo ki ne dan ki din ga kula da abin da Imam zai ci aikin da ki ka zo yi gidan nan kenan. Nana ta yi wa Asal wani irin kallo mai cike da tsana, ji take tamkar ta kama Asal ta yi ta jibgarta har sai ta ji ta huce. "Gimbiya Asal, ai an bar kari tun ran tubani. Ba zan yi girki ba sai dai yunwa ta kashe Imam ɗin, ke da yake aure idan ba za ki girka masa ba, to kar Allah ya sa ci, sai na bar gidan nan ba zan zauna ba" Ta yi maganar cikin ɗaga murya da zazzaro ido. Asal ta yi taku biyu, ta hankaɗa Nana baya ta ce "Ki kiyaye harshenki a kan abin da zai din ga fitowa daga bakinki, a kan mijina. Biyan buƙatata ce kawai ta sanya nake ƙyale ki, ki daina ƙoƙarin ƙetare iyaka. Tafiya kuma ga hanya nan maza ki tafi mu gani, idan kina tunanin da ka na kawo ki gidan nan na ajiye" Ayshercool 08081012143 Littafin kuɗi ne, 1k ne via 0069685771 Aisha Adam stanbic bank ku tura mini hakkina kan ku karanta. 72 Sai da Nene ta tabattar Nana ta ɗan nutsu, sannan suka kwanta. Washegari Nene ta fita, ta bar Nana a gidan tare da Muhsin. Bayan ta dawo daga gurin sama'arta ta cewa Nana, yakamata ta je ta ɗan sai abubuwan da za ta buƙata saboda tafiyar da za ta yi da nisa, kuma ba su san yaya tsarin aikin can ɗin yake ba. Nana ta ce "Ni babu abin da nake buƙata, ki bani wani abin na riƙe a hannuna, sauran kuɗin kuma ki riƙe saboda kula da Muhsin na s... "Biyana za ki yi kenan dan na riƙe miki Muhsin?" Nene ta katse ta. "Allah ya baki haƙuri, ba haka nake nufi na, na ga dole ɗan abubuwan buƙatunsa duk ke ki ke yi masa Nene, tun da ga kuɗi sun" "Kuɗinki ba su isa su saka na riƙe miki ɗa ba ko?" Nana ta ce "Na sani, ai shi ya sanya na ce ki yi haƙuri. Nene ta ce "Ba zan yi haƙurin ba sai na gama, kin iya kunna ni da na fara faɗa ki hau bani haƙuri, wato in ci kaina to sai na idar" Nana ta yi mata shiru ta yi faɗanta ta gama. Washegari Nene ta saka Nana a gaba suka je kasuwa, ta sata ta yi sayayyar kayan sakawa da na ɗan shafe-shafe, ta yi wa Muhsin sayayyar kayan sakawa da pampers. Babu yadda ba ta yi da Nene ba ta ɗauki wani abin ta ce ba za ta ɗauka na. Nana ta haɗe rai ta ce "Eh dama ba ki ɗauke ni 'yarki ba, shi ya sanya duk abin da zan yi miki ba kya karɓa" "Ni za ki yi wa wayo, na ji ban ɗauke ki 'yar ba, ni ga ɗana nan" tayi maganar tana shafo Muhsin da ke bayanta. Da ƙyar sai da suka kai ruwan rana Sannan Nene ta karɓi abin da Nana ta saya mata. Sai dai kan su bar kasuwar har sun shirya. Nana ta ce "Nene kin ce mini ki na da ɗa, amma ban taɓa ganinsa ya zo ba, ba ya zuwa ya gan ki ne?" Nene ta ce "Kamar ban damu da shi ba ko?" "A'a kawai dai tambaya na yi " "Yana can Nigeria" "To me yake yi a Nigeria ba ya zuwa inda ki ke?" "Sana'a yake yi, ai ya zo ki na can gurin aiki" Duk da Nana ba ta gamsu da amsoshin da Nene ta ba ta ba, amma ta basar ta ce "Allah sarki, Allah bai yi zamu haɗu ba". Haka suka ci gaba da hira suka koma gida, Nana ji take yi tamkar ta ɗauke ɗanta ta tafi da shi. Gidansu Ashura Nana ta je, ta samu keke ta ɗiɗɗinka kayan da ta sayo, ta sake haɗa jakarta ta ɗauki muhimman abubuwa a kayanta. Duk da a ɗaki Nene take rufe mata su, ba ta taɓa ganin alamar Nenen tana yi  bincike a cikin kayan ba. ***** Ko da Jamila suka dawo Kano, fakar ido ta yi ta jefar da wannan tarkacen da aka ba ta aka ce da su za ta kai jini. Gaba ɗaya da ta tuna abin tsigar jikinta take tashi, ta ji ciwon kanta da zazzaɓi ya ƙaru. Gefe guda kuma hankalinta yana kan yadda ta ji Hajiya Sa'a tana faɗin za ta sake bayar da ɗan Alhaji Fatuhu. Ta jinjina rashin imaninta mutumin da yake fama da karayar arziki ga ciwo, ya rasa wancan ɗan kuma a sake bayar da wannan kamar ba a yi masa adalci ba. Sai dai gaba ɗaya ba ta san ta ina za ta fara ba, tana jin a ranta kamar yakamata ta tseratar da yaron. A gida ta tarar da Gaddafi, ta sha jinin jikinta da irin mugun kallon da ya yi mata, amma bai ce mata uffan ba. Suwaiba ma ƙura mata ido ta yi tana bin ta da kallo. Ta tsuke fuska ta harsri Suwaiba, sai dai Suwaiba ta tuntsure da dariya, kamar za ta shiɗe. Jamila ta yi tsaki ta shige ɗakinsu. Ba ta tarar da Mama a gida ba, haka ma Baba. ***** Shiru Alhaji Zailani ya yi yana kallon Doctor Sharif yana sauraren shi, har ya gama karanta masa abin da Shukura ta je ta same shi ta yi masa. Ya ja numfashi ya ce "Shikenan, aikinka ya yi kyau Sharif, na kuma gode sosai da sosai da ka ke sanar da ni wannan abubuwan, Allah ya saka maka da mafificin alkhairi. Ka je za ka ga saƙo" Sharif ya yinƙura ya tashi ya tafi. Alhaji Zailani ya numfasa a fili ya ce "Duk da kasancewar ki 'ya mafi soyuwa a cikin zuciyata, an zo gaɓar da ki ka ƙetare layin da bai kamata ki ƙetare ba, kina ƙoƙarin tono abin da zai wargaza zaman lafiya da kwanciyar hankali, dan haka ki yi haƙuri da duk matakin da zan ɗauka a kan ki. ***** Nana ta jingina da jikin gilashin motar, tana kallon tulin yashin saharar da ya mamaye gurin. Fili fetal hagu da dama duk yashi ne. Cikin yanayi mai kama da bacci take ganin abubuwan da ta din ga gani a bacci cikin saharar. Ko a yanzun ma su na tafe Sayyid kawai take gani a kan raƙumi yana biye da su a cikin saharar. Kamar an taɓa ta ta ɗan yi firgigit ta kalli gurin, haryanzu a titin da ya ratsa saharar suke tafiya, zuciyarta ta yi wani irin bugu da sai da ta dafe ƙirjinta. Sanyi ta fara yana ratsa ta har cikin ƙashinta, ta ɗaga ido tana ɗan waige-waige ta ga ta ina za ta gano Ƙaisar ko wata baƙuwar halittar da ba jinsin mutane ba, sai dai ba ta ga komai ba. Ta sake jingina da jikin motar tana ta karanto duk addu'ar da ta zo bakinta. A haka har suka shigo cikin gari sosai da sosai. Nana na son karanta Symbols ɗin da take gani, amma ba komai take iya fahimta ba saboda rubutun French. Babbar hanya mai ɗauke da ƙaton gate ta ciki suka wuce. Ba ƙaramar gajiya Nana ta yi ba, saboda azabar nisan tafiyar da suka shawo ba, ba su ƙarasa ba sai bayan magariba. Kewar ɗan ta ta addabi zuciyarta, tunaninta yadda za ta din ga sintirin tsakanin Agadez da Maraɗi a wannan uwar tafiyar kamar ta ya da shege. Wasu irin gidaje ne manya-manya na alfarma da ƙasaita a cikin gurin. A ƙofar wani gida direban ya tsaya, ya cewa Nana ta fito sun zo. Haka ta saukko ƙafafuwanta duk sun yi tsami saboda azabar gajiya. Ya buɗe bayan motar ya ɗaukko ƙatuwar jakar Nana, ya rufe motar, ya yi gaba Nana ta bi shi a baya tana karanto addu'oin da suka sauwwaƙa. Cikin wani matsakaicin gida suka shiga, gidan ya ƙawatu ya yi kyau sosai da sosai. A falon gidan ya ajiye wa Nana kayanta ya ce "Ki zauna ki jira a nan" Nana ta ce "Amma wa zan jira a nan ɗin, ban ga alamar akwai mutane a gidan nan ba" "Za ki gan su, ni a nan aka yi mini umarnin na kawo ki kawai" Nana ta yi shiru tana nazari, shi kuma ya juya ya fice. Nana ta din ga rarraba ido, tana son ta yi salla amma babu wanda za ta tambaya. Harabar gidan ta fita saboda ta ga famfo ta yi alwala, ta dawo falon ta yi salla. Gajiya ta yi ta koma harabar gidan da kayanta, ta zauna tana rarraba ido. Can ta ji ƙarar mota, aka buɗe ƙofar wani jami'in tsaro ya shigo ya buɗe gate ɗin, aka shigo da wata haɗaɗɗiyar mota aka yi parking ɗin ta. Aka buɗe ƙofar motar, sai ga Asal ta fito sanye cikin doguwar riga, ta ɗaura mayafin a wuyanta, kanta babu ɗankwali. Har bakin ƙofar shiga suka rakata, ta wuce Nana ta shige ciki kamar ba ta gan ta ba. Nanan ma ta yi zamanta ba ta shiga ba, ta jingina da jikin kayanta taka addu'a saboda a gajiye take matuƙa, ga uwar yunwa tana ji ga tulin damuwa. Sannu a hankali take tuna yadda ta shigo ƙasar Nijar ba ta san kowa ba, da yadda ta din ga raragefe har zuwa kan zamanta da Nene. Sai ta tsinci kanta da tattara su baki ɗaya tana yi musu addu'a, da fatan dacewa a Duniya da lahira. Ba ta san iya adadin lokacin da ta ɗauka a gurin ba, ta ji muryar Asal a kanta. "Wai ke wace irin bagidajiya ce, a Nigeria daga wani ƙauyen ki ke ne?" Nana ta ɗaga kai ta kalle ta. "Na saka an kawo ki guri, ki shiga ki jira ni kin zauna a waje, na dawo ma kin nemi guri kin zauna ba za ki shigo ba?" "Ta yaya zan shiga gurin da babu kowa na zauna, ni da ban san ma aikin da ki ka kawo ni na yi miki ba?" Haushi ya kama Asal, ta ce "To idan kin ga dama ki shigo, idan kuma ba ki ga dama ba, ki yi ta zama a gurin" Ta shige ciki Nana ta bi ta da harara, kamar ba za ta tashi ba, sai kuma ta tashi ta ja kayanta, ta shiga falon ta nemi guri ta zauna a kan kujera. Asal ta saci kallon Nana, da yadda take gudanar da lamarinta cike da ƙarfin hali. Nana ba ta kula ta ba, ita ma ba ta kula ta ba, Nana ta gaji da zama, ta saukko ƙasa ta miƙe ta kwanta. Can Asal ta ce mata "Ga kitchen can, akwai abinci" Daga haka ta tashi ta bar falon. Nana ta tashi ta shiga kitchen ɗin, ta tarar da Abinci, ta ɗauka ta ci sannan ta ɗan dawo hayyacinta. A nan falon Nana ta kwana, da Asuba ta yi alwala a harabar gidan, ta koma falon ta yi salla. Duk wannan abin zuciyarta a cike da zullumin aikin da za ta yi wa Asal. Da gari ya yi haske, Asal ta fito Nana ta gaishe ta, amma ta yi kamar ba ta ji ba, ta fice ta bar gidan ta bar Nana. Nana tana nan zaune, aka zo aka ƙwanƙwasa ƙofar falon, ta tashi a ɗan tsorace ta buɗe, wani mutum ya miƙo mata takeaway ya ce "Ga shi nan, aka ce a kawo miki" daga haka ya juya ya tafi. Nana ba ta sake ganin Asal ba sai dare, ba ta saurari Nana ba still. Ta cika gidan ita da ƙawayenta, suka hau saman bene, suka kunna kaɗe-kaɗe har kusan ɗaya na dare su na abu ɗaya, suka hana Nana bacci. Sai gefin Asuba suka daina wannan shirirtar, Nana ta din ga mamakin ita Asal zaman kanta take yi ne, ba ta da magabata ko kuwa? Sai washegari sannan ta saukko ƙasa, a lokacin ƙawayen nata duk sun tafi. Ta kalli Nana ta ce "Daga yau kar ki ƙara kwanar mini a falo, ga ɗaki can kusa da kitchen, a nan za ki din ga kwana. Na kawo ki ne duk da ba yanzu ne za ki yi aikin naki gaba ɗaya ba, amma za ki din ga yi mini girkin Abinci da ni da ƙawayena, da sauran aikace-aikacen gida. Abu na farko dalilin da ya sanya na ɗaukko ki, ke ba ƙabilarmu ba ce ba, ba na son saka ido, ba na son surutu Duk wani abu da za ki ga na yi, ko ina yi babu ruwanki, aikin duk da na saka ki shikaɗai za ki yi mini" Nana ta yi shiru tana tunani, dama duk wannan abin ba wani branch ɗin za a kai ta aiki ba, wannan zuƙaƙƙiyar za ta yi wa bauta, shi ne har da ci mata mutuncin cewa an yi amfani da kuɗi sai ta yi abin da ake so. Kuma me yasa ba ta zaɓi kowa ba sai ita?. "Ba kya ji na ne?" "Na ji" "Ban gane kin ji ba? Haka zan din ga yi miki magana ki na amsa mini, ke ni fa ba Hasna ba ce ba, dole ki yi mini biyayya ki yi duk abin da nake so". Nana ji ta yi tamkar ta yi tsaki, ta ce "Amma yanzu fisabilillahi duk faɗin ƙasar nan ki rasa wanda za ki ɗaukko ya yi miki aikatau sai ni. Ni harkar dafa abinci nake yi, amma kin kawo ni nan in din ga yi miki girki da boyi-boyi ba tare da an yi mini bayanin haka ba, ni gaskiya ba a kyauta mini ba" "Da hakan ki ka dace ai, ko kina ganin kin cancanci wani abin bayan bauta? Idan ba za ki zauna ba ga hanya nan za ki iya tafiya" Ta yi maganar tana miƙewa tsaye. Har ta yi gaba sai kuma ta tsaya ta ce "Duk wani abu da za ki buƙata akwai shi a kitchen, kina iya dubawa, wanda babu kuma ki sanar mini, shi ma idan ba ki ga dama ba kar ki yi aikin" ta yi gaba ta bar Nana da ta gama ƙulewa. ***** Gaba ɗaya Shukura ta burkicewa Sagir, ba ɗaga masa hankali ta yi da rigima ba, tattara shi ta yi ta watsar gaja ɗaya take harkokinta, da gaske take ƙoƙarin gano abin da mahaifinta yake ɓoyewa tsawon wannan lokacin da har ya hana Hajiya Amina bincike a kan lafiyarta. Ga shirin tariyar Yusra Sagir na yi, ga damuwar rashin sakin jiki da shi da Shukura ta yi, ta tattara shi ta watsar. Ɓangarensa ya saka aka gyarawa Yusra, dama ba amfani yake yi da shi ba, aka ƙara gyara shi, aka haɗa gidan gaba ɗaya aka sake yi masa fenti. Daga gaya mata batun dawo da Yusra zuwa gyaran gidan da kawo kayanta, ba a yi sati guda ba, gida ya ɗau harama. Duk yadda ya so ya lallaɓa Shukura, ta saukko ta din ga saurararsa ta yi burus da shi. Nana ta shafe sati guda tana gidan Asal, tana yi mata hidima, ta hantare ta ta kyare ta, dandazon ƙawayen da take tarawa ma, su hana ta sukuni da aiki. Nana ta din ga iya ƙoƙarinta, gurin kai zuciyarta nesa, amma abin ya fara isarta. Tana tsaka da nazarin yadda za ta ɓullowa lamarin, da safe Asal za ta fita ta kalli Nana ta ce "Ki shirya nan da sati ɗaya zamu bar nan, zamu je asalin inda na ɗauke ki ki yi mini aiki a gurin" Nana ta ce "Ina kenan? Kuma aikin me? "Idan mun je za ki gani" Ta ba wa Nana amsar a taƙaice. ***** Jamila tana kwance tana chatting da Abba, bikinsa saura sati biyu. Hajiya Sa'a tana ta zaginsa da yi masa bala'i, a kan yadda yarinyar take ta ƙorafin ba ya kula ta, waya ma sai dai ita ta kira shi, babu abin da ya yi masa zafi da ita. Yanzun ma kamar ya yi wa Jamila kuka. Ita take ta rarrashinsa tana nuna masa babu komai ya yi aurensa kawai. "Ƙanwata ko na yi aure hankalina ba zai kwanta ba, kar ki manta da ɓarnar da ta faru tsakanina da ke, ya zan yi da shi" Ta ce "Na san kai mutumin kirki ne yayana, hakan ne ya sanya ka ke jin damuwa a kan abin da ya faru, amma ka yi haƙuri ka yi aurenka kawai, ina roƙon Ubangiji Allah ya kawo mini wani mijin" "A'a ki daina faɗa mini haka, zuciyata tana sosuwa, baki da wani miji sai ni in sha Allah" haka suka kasance tana ƙarfafa masa gwiwa, shi kuma yana rarrashinta. Ta gama wayar ta ajiye, ta ga Suwaiba ta ƙuro mata ido tamkar ba ta taɓa ganinta ba. "Meye ki ke kallona, lafiya?" Suwaiba ta yi shiru ba ta bata amsa ba, kuma ba ta yi magana ba. Jamila ta ja tsaki, tana ƙoƙarin kwanciya, Suwaiba ta ce "Jamila" "Na'am mene ne?" "Ki ɗauki saƙonki mana" Cikin rashin fahimta ta ce "Wane saƙon?" "Na cikin jakarki" "Cikin jakata kuma? Mene ne a jakar tawa? Wato bincike ki ke yi mini a jakar ko?" "A'a ni tuni kawai nake yi miki da saƙonki na cikin jakar" Jamila ta tashi zaune ta ce "Wai wani saƙon? Miƙo mini jakar dai na gani" Suwaiba ta ce "A'a ba zan taɓa miki jaka ba" Jamila ta janyo jakar ta fara buɗewa ta ga abin da Suwaibabta dame ta a kai. Cin karo ta yi da wannan 'yar tsanar da ta riga ta jefar. Saura ƙiris ta kurma ihu, ta rikice gaba ɗaya jikinta ya hau rawa, a tunaninta tun da ta yar shikenan ta rabu da ita. Suwaiba kuwa ta tuntsure da wata irin mahaukaciyar dariya, ta din ga yi tana ƙyaƙyatawa tana kallon Jamila. Gaba ɗaya Jamila ta kiɗime ta rasa abin da yake yi mata daɗi, gaba ɗaya jikinta ya hau rawa tamkar ta kurma ihu, sannu a hankali kanta ya fara juyawa ta fara gani dishi-dishi, dole ta rufe jakar ta nemi guri ta kwanta. ***** Alhaji Zailani ya kwana biyu bai je gidan Alhaji Fatuhu ba sai yau. Sai dai ya sha mamakin ganinsa a harabar gidan da sanda yana dogarawa yana tattakawa a hankali, yana tsaye a kan ƙafafuwansa yana kallon yadda Muhsin yake ta gudu a harabar gidan. Sai da ya aro jarumta sannan ya iya danne abin da ya ji ya taso masa na tashin hankali da mummunan baƙin ciki. Da ƙyar ya iya washe baki ya ce "Ikon Allah, Abokina kai ne haka nake gani?" Alhaji Fatuhu ya yi murmushi ya ce "Ka ga ikon Allah ko? Sannu da zuwa Bismillah" ya yi maganar yana nuna masa ɗaya daga kujerun da ke ajiye a gurin. Alhaji Zailani ya zauna suka ƙara gaisawa "Bani labari, ya aka yi sauƙi ya samu haka, wani Asibitin ka je ne?" Alhaji Fatuhu ya ce "A'a na ga an yi na Asibitin ne babu wani ci gaba, Fadila ta zauna ta din ga yi mini bayani, na amince muka fara gwada na islamic, cikin ikon Allah sannu a hankali wannan ɗaurewa da nake ji a jikina ya yi mini sauƙi, wannan gigicewar da nake na ji kamar zan yi hauka shi ma Alhamdillah ina daɗewa ban ji ba, wannan warin ma da nake ji ya ragux "Amma Fatuhu ya za a yi ka biye wa mace da shirmen ta, ga na Asibiti ana yi kawai ta saka ka fara wani na shirme, sai ka je ka yi abin da za ka kauce wa hanya tukuna?" "A'a nima na jaddada mata, ta kuma tabattar mini da babu kauce hanya a ciki, kuma nima shaida ne, shi ya sanya ma nake amfani da magungunan kuma ana samun ci gaba" Alhaji Zailani ya miƙe ya ce "Haka ne, to bari na je dama ina da gurin da zan je na biyo, sauri nake yi" "Ba zaka tsaya ku gaisa da mutanen gidan ba?" "Sauri nake yi zan sake dawowa"ya yi maganar yana yin gaba cikin ƙunar rai, ji yake yi tamkar ya kashe Alhaji Fatuhu ya huta, dan shi bai taɓa zaton zai kawo yanzu bai mutu ba. ***** Al Hussain ne a tsaye ya tsare Hasna da ido, yana yi mata faɗa cikin matsanancin ɓacin rai. "A kan me za ki yi haka? Dan me za ku yi mata dole, ai ba ɗaukar ta aiki muka yi saboda buƙatar mutum guda ba. Abin da yake cikin yarjejeniya shi ne ta yi wa gidan Abincinmu aiki, idan ma canza gurin aikin ne, wani reshen zamu mayar da ita, amma dan me za ku haɗa kai ku yi mata haka wannan wulaƙanci ne da cin zarafi, kuma ga shi bama 'yar ƙasarmu ba" "Ni fa Al Hussain na kasa gane maka, ko son yarinyar nan ka ke yi ne? To bari na tuna maka kai Buzu ne, buzun ma farin buzu ka san abin da nake nufi ai, kuma matar aure ce ko bazawara dan ta ce mana tana da ɗa ma" "Ni ba wannan na tambaye ki ba, dan me Asal za ta yi amfani da ƙarfi da kuɗi ta tursasa mata yin abin da ba ta so, ai ba haka ake rayuwa ba" "Ai na san za a yi haka, babu bayanin da ban yi mata ba taƙi yadda, ga shi ni yanzu ka zo ka saka ni a gaba da jaraba, sai ka je ka dawo da ita ni ba zan iya ba" "Ke dai da ki ka yi hakan ki je ki dawo da ita, idan ba haka ba daga ke har ita na rubuta masa abin da ku ka aikata, daida yake da ku" Ta kwaɓe baki ta ce "Wa ya san ma inda yake, mutumin da ake tunanin ya ɓata babu wanda ya san ma yana raye ko yana mace?" "Hakan ya baku damar cin karenku babu babbaka daga ke har Asal ko? Yayi muku kyau" Hasna ta fice tana jin haushin masifar da Al Hussain yake ta yi mata, duk yadda ta yi ƙoƙarin hana Asal ɗaukar Nana. ***** Ana gobe su Nana za su bar wannan gidan, Asal ta sanar da Nana ta shirya washegari za su bar nan. Ita dai Nana ta sanya wa sarautar Allah ido, rayuwarta ta zama tamkar tamaula daga nan zuwa can, ba ma ta da 'yancin tambayar ko sanin inda za a kaita sai dai inda ta tsinci kanta kawai. Ta sha aiki ta gama, ta ɗan zauna a falo tana hutawa, sai ga ɗaya daga gayyar ƙawayen Asal ta saukko ta kalli Nana ta ce "Dan Allah ina son shayi" Nana ta ce "Akwai a kayan Abincin da na girka" "Shayin kanumfari kawai nake so bana son Shan na girfa" "Ga gurin dafawar can, idan ki ka je akwai komai, ki dafa ki sha idan kin matsu" "Ke, kin san wace ce ni ki ke gaya mini haka?" "Ban san wace ce ke ba, kuma ba na buƙatar sani" Asal ta saukko tana tambayar lafiya. Ta gaya mata abin da ya faru, ta kalli Nana ta ce "Wai ke me yasa ba ki da mutunci, ban gaya miki dole ki girmama baƙina ba, mene ne a cikin dafa shayi mintinan nawa ne kin yi kin gama?" Ta kalli Asal ta ce "Ki yi haƙuri, wallahi ko cokali ba zan iya sake ɗauka ba, yau na bautu a gidan nan ke kin sani, kuma ban taɓa yi miki ƙorafi ba, amma yanzu dai na gaji gaskiya" Suka juya yare suka yi magana, ba ta san me suka ce ba, ta ga sun koma kan bene. Washegari da wuri suka ɗau hanya, sai dai ga mammakin Nana, har da rakiyar jami'an tsaro, kuma a wannan karon shigar Shadda Asal ta yi, an yi wa shaddar aiki tun daga sama har ƙasa. Mota ɗaya suka hau, ta ce Nana ta hau gaba, ita kuma ta hau baya. Sai da aka kuma wata tafiyar mai nisa, sannan ta ga sun tunkari wani  irin ginin ƙasa tamkar ginin ganuwar Kano. Ginin ya ƙayatar da Nana sosai da sosai. Jami'an tsaro ne suke gadin ƙatuwar ƙofar gurin, da wasu Buzaye farare tas sanye da rawani. Nana kamar ta ce a tsaya, ta duba buzayen nan ɗaya bayan ɗaya ko za ta ga Sayyid ɗin ta cikinsu. Sai da motar su ta tsaya, suka sauke glass ɗin motar. Da Hausa suka gaisa, suka yi mata sannu da zuwa, ɗaya daga cikin su ya kalli Nana ya ce "Wannan fa?" "Baƙuwata ce" ta ba shi amsa, ya jinjina kai motar ta shige. Su na shiga Nana ta ga ai gari ne guda a cikin ganuwar nan. Sun ɗan yi tafiya kafin su shiga wani ƙaton gida. Nana ta tsaya tana ganin yadda aka yi wa ginin ƙasa wani irin ado mai ƙayatarwa. Tun da suka doshi shiga gidan, ake gaida Asal cikin girmamawa, ita kuma ta yi fuska sai taku take cike da ƙasaita, kamar ba ita ce suke rashin hankali da ƙawayenta a wancan gidan ba. Wannan gidan saɓanin wancan da mutane a ciki, kuma da alama duk a ƙarƙashin Asal suke. "Wace ce ita?" Nana ta tambayi kanta. Sai da suka ƙarasa wani falo, sannan ta yi wa wata dattijuwar magana da yaren su. Matar ta kalli Nana ta ce "Bahaushiya ce ke ko? Zo mu je na kai ki masauki" Babu musu Nana ta bi ta, matar ta kai ta wani daki ta ce nan ne ɗakinta. Sai da Nana ta kwana biyu a gidan, ba ta sake ganin Asal ba, ba kuma ta aikin fari ba ta na baƙi kawai tana zaune, sai dai za a kawo mata Abincin safe, rana da dare sau uku a rana. Sai dai babban abin da ya dame ta, tun da ta shigo gidan, network ɗin wayar ya sauka gaba daya, ko ta kira Nene ba ta shiga sam. A kwana na huɗu, da daddare dattijuwar matar nan ta zo ta kira Nana. Babu musu Nana ta tashi ta bi bayanta. Sun yi 'yar tafiya su na ratsa faluka masu kyau da ado, sannan suka bi wata ƙofa. Sanyin A.C ya daki Nana, ga wani irin haɗaɗɗan ƙamshi. Asal ta hahakimce a kan kujera kaɗa ƙafa. Ta kalli dattijuwar ta ce ta jira a waje. Daga ƙasa wata matar ce a zauna a kan carfet, ta gurfana kamar tana jiran Asal ɗin ta gafarta mata. Nana ta yi turus tana tunanin a ina za ta zauna, sama ko ƙasa. Matar ta kalli Nana cikin zare ido ta ce "Ke ki rage tsawon ki, kin tsaya mata a ka" Nana ta ja guri ta zauna a kan carfet ɗin ita ma. Asal kamar ba za ta yi magana ba, sai da ta gama iyayinta ta sauke ƙafarta ƙasa ta dubi Nana ta ce "Amm na saka an kirawo mini ke, saboda ki san abin da na kawo ki gidan nan ki yi. Ke dai da ganin gidan nan kin san ba gurin da za a yi wasa ne ko shirirta ba, babban gida ne na mulki. Saboda dalilin girki da kuma wani dalili na ƙashin kaina, ya sanya na kawo ki gidan nan. Ba a ɗaukko bare wanda yake ba jinin gidan nan ba, ko ƙabilarmu ba ya yi mana aiki, amma na ga wasu abubuwa a tattare da ke da ya sanya na kawo ki cikin gidan nan. Kamar yadda na gaya miki, ina ƙara jaddada miki, zaman ki a gidan nan dole ki yi taka tsantsan, babu ruwanki da shishshigi, saka ido, gulma ko kuma shiga abin da babu ruwanki. Sannan kar ki kuskura wani ya ce zai haɗa kai da ke a yi wani abu, rayuwarki za ta iya salwanta ba tare da kowa ma ya sani ba, dan haka sai ki san irin zaman da za ki yi." Nana ta yi shiru ta gama sauraren ta, sai dai har a lokacin ba ta ji dalilin da ya sanya Asal kawo ta gidan ba, dafa abinci kowa ma zai iya mai yasa sai ita. Wannan matar da ta tarar a zaune, ta tafi da ita, ta kai ta gurin da ake girke-girken abinci, da gaya mata yadda jadawalin girke-girken gidan yake. Ta ɗaukko kayan ds Asal ta bayar a ba ta, na kayan shafe-shafe da mayukan wanka zuwa kayan sakawa. Da Nana ta koma ɗakinta, ta kalli kayan ta fara tunanin Allah ya sa ba kwance Asal ba ne, dan gara ta saka kwancen Ashura da ta saka na Asal, da ba ta da mutunci. A washegari Nana ta fara aiki a wannan madafa, sai dai madafar daban-daban ce. Akwai wadda ake girkin da ma'aikatan gidan ne suke ci, akwai wadda na baƙin da suke zuwa ne, sai kuma masu girka wa Asal abinci daban, dan haka Nana na cikin masu yi wa Asal girki. Sosai matar nan ta ƙara jan kunnen Nana, a kan ta kula da kanta, dan muddin aka samu matsala ba za ta sha ba. Nana a ranta ta ce "Ji wata jaraba, da wannan wahalar mutum ya girka abin da zai ci mana da kansa." Kwana huɗu da fara aikinta, ranar Alhamis da daddare, tana shirin kwanciya, aka ƙwanƙwasa ƙofar ɗakinta. Ta tashi ta buɗe, ta ga shugabar girke-girke ta gidan, kamar yadda aka gabatar mata da ita a baya. "Ki sako hijjabinki, ki biyo ni" Nana ta saka hijjabinta ta fito tana tunanin ko lafiya. Harabar gidan matar ta yi, Nana ta bi bayanta, ta nuna mata mota. Nana ta kalli dare ya yi kuma an zo da mota an ce a tafi da ita. Cike da mamaki Nana ta shiga motar, sai ta ga mutum uku, da su ma duk tare suke aikin girkin a gidan a cikin motar. Ta shiga ta zauna, ita ma shugabar ta su ta shiga. Nana ta gaza haƙuri ta ce "Dan Allah ina za mu je ne?" "Za ki gani" "Eh amma na ga dare ne fa" "Idan mun je za ki ji dalilin fitar" Nana ta yi shiru tana tunani, ita ba ma wannan ba, hankalinta ya koma kan rashin samun damar kiran waya da ba ta iya yi, kuma ba a kiranta ya shigo. Dan sai da ta tambayi ɗaya daga cikin masu aikin, ko matsalar daga wayarta ne, ta ce mata kar ta kuskura ta bari ma a san tana da waya, dan sai an ƙwace ta. Tana ta zancen zuci, har suka isa inda aka tsaya suka sauka, aka shiga da su. Asal ce a tsaye, tare da dattijuwar matar da ta saka ta raka Nana masauki. Suna tsaye a cikin ɗakin Nanan. Asal ta ce "Zazzage mini kayanta, ki ɗaga mini komai ɗaya bayan ɗaya" Ayshercool Ku tura mini hakkina kan ku karanta 0069685771 Aisha Adam stanbic. 73 Ɗaya bayan ɗaya, aka din ga zazzage kayan Nana. Aka zazzage su tsaf aka Azzage jakar da ta zuba kayan turarukanta da mayukan shafawa, duk ba ta ga wani abu ba, sai jakar gurin sarkin baka. Ta nuna jakar ta ce "Mene wannan?" Ta ɗago jakar ta ce "Jaka ce" "Buɗe ta ki zazzage na gani" Ta fara kokowar buɗe jaka, amma babu gurin da zata buɗe ta. Kawai ta ce "Shikenan" ta fice ta bar ɗakin. Can gurin kuma Nana tara su aka yi, su shida. "Na san za ku yi mamakin dalilin da ya sanya aka kawo ku nan, to zaɓo ku aka yi saboda an yarda da amanarku, ana daf da yin taro da Sultan da kuma dukkanin Imams na gidan nan. Dan haka ku aka zaɓo za ku yi girki na musamman. Amma ku sani kamar yadda wasu sani wasu ba su sani ba, muddin aka samu wata matsala ko ƙware wani ya yi, a sanadin abincin da ku ka dafa, to ku tabattar da rayuwarku za ku biya. Dole ku yi taka tsantsan ku kula." Matar ta yi maganar daki-daki. "In sha Allah" suka amsa mata. Ta ce su bi bayanta, suka je wani ƙaton guri, ɗauke da nau'oin kayan masarufi kala-kala. Ta yi musu bayanin da su ne za su yi amfani su yi girkin, sannan ya zama dole su sanya wa bakinsu sakata su yi aiki cikin amana, kuma kada wanda ya san su aka zaɓa da za su yi wannan girki. Nan ma suka amsa, ita dai Nana sai kallo da ido, dan abubuwan sun daina ba ta mamaki, wannan maganar ce ta sanya aka taso ta a daren nan, sai ka ce wanda za su girkawa wasu waliyyai abinci. Ko da aka mayar da su Nana gida, ta sha mamakin ganin kayanta a hargitse a cikin ɗaki. Da mamaki ta ƙarasa kan kayan nata, ta ɗaɗɗaga. Cikin takaici Nana ta tashi ta fita, sai dai kowa ya tafi makwancinsa ya kwanta. Kawai ta ji taku a bayanta. Ta waiwaya ta ga Asal na fitowa. "Har kun dawo kenan?" "Eh, sai dai na shiga ɗakina na tarar da an caje mini kayana an zubar da su a ƙasa, ban sani ba ko kina da masaniya a kan haka?" Asal ta ce "Me yasa ki ka zarge ni?" "Saboda na ga ba a gudanar da komai a gidan nan sai da izninki" Asal ta yi murmushi ta ce "Haka ne, kina da kaifin ƙwaƙwalwa kamar yadda na yi tsammani, ni na saka aka caje kayanki saboda na san da wa nake zaune" "Me yasa ba ki tambaye ni abin da ki ke buƙatar sani ba, za a caje mini kaya" "Saboda a ƙarƙashina ki ke, a gidana ki ke zaune dole na sani idan da wani abu da ki ke tattare da shi na cutarwa" Nana ta ce "Kin yi kuskure, dan ina zaune a ƙarƙshinki, ina da personal life ɗina, da 'yancin adana abin da yake sirrina, bai halatta ki bincikar mini kaya a bayan idona ba. Yaushe na san ki, da zan ƙulla wani abu da zan cutar da ke? Kina gudun hakan ki jawo ni ki ka kawo ni?" "Yi ƙasa da muryarki, kar ki kuskura ki ɗaga mini murya, kin san matsayina? Za ki iya janyo wa kan ki gagarumar matsala muddin ki ka ci gaba da yi mini magana ba ladabi" "Babu ruwana da matsayinki, da koma me za ki yi mini, kar ki sake shigar mini ɗaki ki taɓa mini kaya, idan kuma ki ka ci gaba za ki iya binciko abin da zai hana ki sukuni, idan kin ji ba ki yarda da ni ba, ki sallame ni na koma inda na fito, ba zai yiwu na zauna da ke kina zargina kuma kina cin dunduniyata ba." Asal ta bi Nana da kallon mamaki, amma ta danne mamakinta ta haɗiye fushinta, ta ce "Gaskiya ne, kin yarda da kan ki har haka kenan? Shikenan amma idan na ga akasin abin da ya fito daga bakinki, za ki sha mamakin abin da zai faru" Nana ta yi mata banza, ta koma ɗakin nata, ta gyara kayanta tsaf. Ta kulle ɗakin ta koma ta ɗaga katifar ɗakin, ta ɗaukko wata jaka, a cikin jakar ta zuba duk tarkacen kayan Sayyid. Ajiyar zuciya ta ts yi, da tayi wannan dabarar ta ɓoye su. Haka kurum take jin kayan na buƙatar sirri. Ta nemi guri ta kwanta tana sauke numfashi a hankali, tana tunanin yadda rayuwa ke ta jujjuyata. ***** Shukura na zaune a ɗakinta tamkar zuciyarta za ta yi bindiga ta fito, Sagir ya buɗe ƙofa ya shigo ɗakin. Kallo ɗaya ta yi masa ta sunkuyar da kai. Tuni t yi shirin kwanciya baccinta, sai ƙamshin turare take zubawa. Ya sha manyan kayansa, hannunsa riƙe da baƙaƙen ledoji. Ya zo ya zauna a kusa da ita, tamkar ta kifa masa mari haka take ji. "Wai har kin yi shirin kwanciya? Na zata zaku gaisa tukuna sai ki kwanta" Mugun kallon da ta yi masa ya sanya shi haɗiye maganar da ya yi niyyar yi. "Ga wannan naki ne" Ya yi maganar yana ajiye mata ledojin hannunsa. Ba ta kalli kayan ba, kuma ba ta motsa ba. Ya matsa kusa da ita, ya riƙo hannunta, ta fizge hannunta ta haye kan gadon ta kwanta. Bai ji haushin abin da ta yi masa ba ko kaɗan, ya san idan ba ta son sa ba za ta yi kishinsa ba, sai dai ita ma Yusra tana buƙatarsa tun da tun farko bai kamata ya sake ta saboda larurarta ba. Ya tashi ya kashe mata fitila, har zai fita ya koma gaban gadon, ya durƙusa daidai fuskarta ya ce "Ki yi mini afuwa Shukura, ban yi haka domin na cutar da ke ba, ko na muzguna miki, dan Allah ki kwantar da hankalinki saboda lafiyarki da abin da yake cikinki" Daga haka ya tashi ya fice. Sai da ya fita sannan ta ba wa hawayen da suka maƙale a ƙirjinta damar zirarowa, zuciyarta ta din ga yi mata ƙuna, tamkar ta tashi ta bar gidan. Duk da ya fita da damuwar halin da Shukura take ciki, amma bayan wani ɗan lokaci tuni ya manta, suka ci suka ƙoshi da shi da Yusra. Bayan sun gabatar da salla, sun yi addu'oi, suka yi zamansu kawai su na hira. Sai gurin ɗaya saura sannan suka tashi suka kwanta. Yadda Sagir yake murna da kasancewa da Yusra, ko aurensu na fari bai yi haka ba, tuni wani nannauyan bacci ya yi awon gaba da su, daga shi har ita. Shukura kuwa yadda ta ga rana haka ta ga dare, ga wani irin zafi da ya addabe ta duk da na'urar sanyaya ɗaki da ke cikin ɗakin. Washegari sai ƙarfe sha ɗaya na safe ya shiga ɗakin Shukura. Idonta kawai ya kalla ya ga alamun rashin bacci a tattare da idanunta, sun yi jawur sun kumbura. "Oum Haidar" ya kira sunanta, yana zama a kan gadon, tana shan tea. "Ina kwana" ta faɗa a taƙaice. Idanunsa ya sauka a kan ledar da ya kawo mata, babu alamar ko taɓa ledar ta yi. "Shukura me yake damunki ne haka? Na kawo abu ko taɓawa ba ki yi ba, kin yi bacci makuwa" "Sagir, dan Allah ka tashi ka bani guri, ni bana buƙatarka a kusa da ni, kaɗaici nake so" "Ni ki ke cewa na fita na baki guri?" Ya yi maganar yana nuna kansa. Ƙoƙarin mayar da hawayen da ke shirin zubo mata take yi, amma abu ya gagara kawai ya fara zubowa ba tare da ta shirya hakan ba. Jikinsa ya yi sanyi, ganin yadda take kuka sosai da sosai. Cikin kwantar da murya, yake ƙoƙarin rarrashinta, amma ta tashi ta shige banɗaki ta bar shi a gurin. Ya yi shiru ya rasa abin da yake yi masa daɗi, shi babbar damuwarsa ma cikin da take ɗauke da shi, ga matsalarta ta hawan jini. ***** Tamkar bayi haka su Nana suke aiki, kullum za a ɗaukkosu daga wancan gidan da Asal take, a kawo su nan su wuni su na aiki. Har mamaki take yi wannan mutanen su kuwa har su nawa ne, dan kamar har da almubazzaranci a cikin lamarin. Sai dai kowa cikin kaffa-kaffa yake aikin tare da fatan kar wani abu ya biyo baya da za a kama su da laifi. Kwana na uku, wanda ranar suka dafa normal Abinci, sauran kwanakin kayan snacks ne suka din ga yi. Duk cikin su Nana ce 'yar Nigeria, sauran duk 'yan Nijar ne, sai dai galibinsu baƙaƙen buzaye ne. Sai da suka kammala aikin, aka ba su wasu kaya fararen dogwayen riguna, da rigar girki, aka saka su kai Abincin wani ɗaki. Katafaren ɗakina da dogon tebur, an gyara shi sai tashin ƙamshi yake yi. Sai dai gabanta ya yi mummunan faɗuwa da jin irin ƙamshin da yake tashi a ɗakin. Take jikinta ya hau rawa, har ta nemi ta kifar da abin da ta ɗaukko. Ta ɗaga kanta a hankali ta kalli jerin manyan frames ɗin da ke ɗakin, sai dai mutanen jikin hotunan, dukkaninsu fuskokinsu a rufe yake, ba ta iya gane kowa daga cikin su ba. "Ke Nana ki kai mana kin ja kin tsaya" Nana ta jinjina kai jiki a sanyaye ta ƙarasa gaban teburin. Ta ajiye kayan, ta ɗaga kai ta kalli yadda ginin ɗakin yake da matuƙar tsayi. Jiki a sanyaye ta ci gaba da kai komo, su na shirya abincin. Bayan sun shaƙe teburin da uban kayan Abinci, aka ba su umarnin su tsaya kar wanda ya fita. Su na tsaye Nana ta kalli agogon ɗakin, ƙarfe goma na dare. Wani ƙaton mutum ya shigo, ya kalli gurin da yadda aka shirya teburin, ya kalli su Nana ya ce "Waɗanan ne suka yi girkin?" Balaraba wadda ita ce ta jagoranci su Nana gurin girke-girken ta risuna ta ce "Eh su ne ranka ya daɗe" "Wace ce wannan? Na ga kamar ba tamu ba ce" Ya yi maganar yana nuna Nana, da gaba ɗaya rabin hankalinta ba ya jikinta. Balaraba ta ce "Gimbiya Asal ce ta zaɓo ta, ta saka ta a cikin masu girkin" Ya yi shiru yana kallon Nana, daga bisani ya jinjina kai ya kalli Balaraba ya ce "Ki je, su su tsaya" Ta jinjina kai ta fice. Wata ƙofa aka buɗe, wani matashi ya shigo fuskarsa ɗauke da murmushi, gaban Nana ya yi mummunar faɗuwa, dogo ne sanye da farar jallabiya ya ɗaura hirami a kansa, ba dan ta yi wa Sayyid kyakykywan sani ba, za ta iya cewa shi ne. Ƙirjinta ya tsananta bugawa, sai dai kafin ta daidaita nutsuwarta, wani ma ya biyo bayansa, shi ma dai kamarsa ɗaya da Sayyid ɗin. Tunani ta fara yi ko Giyaz da Ƙaisar ne suka fara yi mata gizo suke yi mata wasa da tunani. Ɗaya bayan ɗaya suka din ga shigowa, sai da ta ƙirga mutum biyar cif, biyu kamar su ɗaya sak, sauran ukun kuma su na kama amma ba sak da Sayyid ba. Duk suka jeru a kan kujerun teburin nan. Sai dai babbar kujera babu kowa a kai, kujerun gefe da gefen kujerar ma babu kowa a kai. Ɗaya daga cikin su ya ce "Ko waye zai hau wannan kujerar?" Ya yi maganar yana nuna ɗaya daga kujerun da babu kowa a kai. "Wannan karon dai za mu ji me Sultan zai ce mana a kan maganar" "Nima dai abin da nake son ji kenan, magana ta gama cika gari ba a san inda yake ba, ana ma tunanin ko ya mutu suke ɓoyewa" Nana ji ta yi ana busar sarewa a ƙofar bayan su, gaba ɗaya suka ja gefe domin bayar da hanya. Wani dattijo ne fari sol, mai dogon gemu ya shigo jallabiyarsa baƙa, ya lulluɓe kansa da hiraminsa. Gaba ɗaya ta ga abokan aikinta sun rikice, duk sun sunkuyar da kansu ƙasa, Nana kuma ta yi masa ƙuri da ido. Sai dai ba shi take kallo ba, ji take tamkar numfashinta ya ɗauke, kamar ba a cikin duniya take ba, duniyoyin da Ƙaisar ya saba kaita ne ya caza mata kai, banda haka wani irin mummunan gizo ne wannan?. Gaba ɗaya matasan suka miƙe tsaye, cikin matsanancin mamaki suna kallon na bayan dattijon. Tamkar yana tausayin ƙasar haka yake taka ta, yana ɗan yin rangaji kaɗan, sassanyan ƙamshin turaren sa da ko a mafarki ta ji shi tana tantancewa ya karaɗe ilahirin gurin, fiye da ƙamshin turarukan da ke tashi a gurin. Ta kusa da ita ce ta ja hannunta da ƙarfi, saboda yadda ta tsare shi da idanunta ko ƙiftawa ba ta yi. Ya zo zai gifta ta, amma ko gurin da suke bai kalla ba, ɗaya bayan ɗaya suka din ga rungume shi, cike da murnar da wasu har zuci, wasu kuma iya ta fuska ce. Ta ga ya zauna a kan kujerar da ake tababar wa zai zauna a kai kafin ya shigo. Abdou ya ce "Kun yi mamaki ko? Ba ku yi zaton ganinsa ba?" Ɗaya daga cikin su ya ce "Gaskiya ne" Sultan ya yi murmushi ya ce "Kamar dai yadda na gaya muku a baya, Imam Hammad yana Faransa neman lafiya, bayan tsawon wannan lokacin, yau ya kasance tare da mu a liyafarmu ta ƙarshen shekara, dama wannan ne bazatar da na ce zan yi muku" Nana ta kalli hotunan nan, sai ta yanzu hotunan babu rawani, kowa hoton fuskarsa ce. Ta tsayar da idonta a kan hotonsa da aka rubuta Imam Hammad Jalal Agadez. A take ta tuna da sunan gidan cin abinci da ta yi wa su Al Hussain aiki. H.J Agadez. Sunan rukunin gidajen da ta fara zama da Asal shi ma sunan da ke jikin symbol ɗin unguwar kenan. H.J Agadez. Duk surutun da ake yi, da murnar ya dawo, yana ƙame a kan kujera, fuskarsa babu yabo babu fallasa. Sai daga bisani ya saka hannunsa ɗaya a kan ƙirjinsa ya risunar da kansa ya ce musu "Merci(Na gode) Duk da a hankali ya furta, amma ko cikin murya dubu Nana ba za ta gaza tantance ta Sayyid ba. Abduou ya kalli su Nana, ya kalli mutumin ɗazu da yake tambayar wace ce "Guda biyu daga cikin su ta zo ta ɗanɗana Abincin nan" Mutumin ya ƙare musu kallo, ya nuna Nana ya nuna wata ya ce su je su ci kafin a ci. Nana ba ta san a yadda take iya ɗaga ƙafafuwanta ba, saboda ba ta jin su a jikinta, zuciyarta kuwa kamar za ta tarwatse saboda bugun da take yi fiye kima. A hankali ta ƙarasa gaban teburin. Ɗayar ta din ga bubbuɗe Abincin, ta fara ɗanɗanawa. "Ke kina da gaskiya kuwa? Ki ɗanɗana aka ce?" Abduou ya yi mata maganar cikin tsawa. Rikicewa ta yi gaba ɗaya, ya ɗaga idonsa ya kalli inda jikinta yake rawa, suka yi ido huɗu, ya kawar da kansa yana mamakin yadda take a ruɗe. Ta ɗebo shinkafa a cokali, amma hannunta karkarwa kawai yake yi. Sultan ya ce mata "Kina lafiya kuwa?" Ta jinjina masa kai alamar eh. Sultan ya ce "Na fuskanci a tsorace take ne kawai, a kaita ta je ta huta, wataƙila mun yi mata kwarjini ne" Aka saka Nana a gaba aka fitar da ita daga gurin. Fitarsu ke da wuya, jikin Nana ya din ga wata irin kyarma, haƙoranta na haɗuwa da juna, wani irin jiri ya din ga kwasarta. Balaraba ta nufo su da sauri, ganin Nana na dafa bango. Ya kalli Balaraba ya ce "Maza ki kaita ta huta, wataƙila ta yi aiki da yawa ne ta gaji, gaba ɗaya ta rikice, a kirawo likita kuma ya duba ta. ***** A hankali Nana ta yi juyi, ta buɗe idonta ta ganta a ɗakin da take kwana. Wata irin ajiyar zuciya ta yi, da ta tabbatar da mafarki ta yi ba gaskiya ba ne abin da ya faru. Hamdala ta yi ta ce "Ni dai na san mafarki ne da ma, dan babu yadda za ayi Sayyid ya ganni ya kasa kula ni, ya nuna kamar bai sanni ba. To wannan idan gaskiya ne ma, ta ina zan fara bayanin ni matarsa ce a yarda da ni? Mutumin da na ji ana batun ya daɗe a faransa yana jinya, anya ma Sayyid ɗina ne? Tun da dai mafarki ne duk da sauƙi. Sallama aka yi a ɗakin, ta ga Balaraba ta shigo ɗakin. Ta ce "Kin tashi?" Nana ta yi shiru tana kallonta. "Ina ga aiki da ki ka sha a kwanakin nan ne, ya sanya ki ka gaji zazzaɓi ya kama ki, Likita ya ce a bari ki huta sosai da sosai. Gimbiya Asal ta ce a baki hutu na kwana uku ki warware kan ki koma bakin aiki." Nana ta jinjina kai kawai, tana kokawa da ƙwaƙwalwarta, domin ta tabattar gaske ne, ko kuwa dai mafarkin ne? Ta tashi ta yi alwala ta yi salla, sai dai gaba ɗaya jikinta ciwo yake yi mata, ga matsanancin ciwon kai da jiri da take ji, dan haka ta nemi guri ta sake kwanciya. ***** Jamila ta ɗauki jakarta ɗauke da wannan tarkacen da take kira da tarkacen jaraba, ta fita waje, ta samu ta sayo fetur a 'yar jarka, ta samu guri ta zuba musu fetur ɗin ta kunna musu ashana ta ƙone su. Ta tashi tana kallon yadda suka din ga ci da wuta, ta bar gurin. Kai tsaye ta tari abin hawa ta tafi gidan Hajiya Sa'a. Hajiyar ta yi iya ƙoƙarinta gurin ɓoye jin haushin Jamila da take yi, ta karɓe ta hannu bibbiyu har ta taya ta lissafin kuɗin kasuwancinta da kuma kayan da take da su a ƙasa. Bayan sun kammala ta ce "Ni kuwa Jamila, yaya batun ƙungiya wa za ki bayar ne?" Jiki a sanyaye ta ce "Haryanzu ban gama tunani ba ne ba" "Tsoron dai ki ke ji haryanzun ko?" "A'a na rage ji" "To ki yi ki hanzarta ki yi abin da yakamata amma kin tsaya. Ni kalli nawa nan na shirya komai aiwatar wa kawai ya rage mini, sai na je gidan zan yi, na sake bayar da ɗan Fatuhu" Jamila ta kalli drower da Hajjya Sa'a ta janyo, tana nuna mata 'yar tsanar nan. Jamila ta ce "To idan ban kai kowa ba, akwai wani abu da zai faru ne?" Ta ce "Au da kara zube za ki zauna ki ƙi bin umarnin ƙungiya? To idan ba ki kai kowa ba, jininki aljanin zan shanye ki mutu" Cikin Jamila ya yi wata irin ƙara bayan tuna ta ƙona kayan. A tunaninta shikenan ta huta sun rabu. A ranta ta ce "Wannan wane irin bala'i ne na jefa kaina a ciki, Ubangiji Allah ka kawo mini agaji na rabu da wannan masifar. ***** Fafur Nana ta ƙi yadda zuciyarta ta amince abin da ya faru gaskiya ne ba mafarki ba, saboda ta riga ta saba da irin wannan cazan kan da Ƙaisar ya kan yi mata wasu lokutan, har ta gaza banbance abin da yake zahiri da kuma mafarki. Nana suna ɗakin girki su na ta ɗorawa da saukewa, ta kalli shugabar su ta ce "Dan Allah a gidan nan, babu yadda zan yi na samu waya, ina son na kira gida ne, na ji halin da yarona yake ciki" Balaraba ba ta bata amsa ba, ta ji Muryar Asal ta ce "Babu wannan damar, sai dai idan kina buƙata ki zo gurina ki karɓi wayar ki kira" Nana ta ɗan yi shiru sai kuma ta girgiza kai ta ce "A'a ki bar shi na gode" "Me yasa ki ka ce haka? Kina tunanin wani abu a ranki ne?" "Bana tunanin komai, kawai dai na fasa ne" Ta yi murmushi ta ce "Shikenan, ga saƙo can daga gidan Sultan, tukuicin aikin da ku ka yi na girki" Balaraba ta risuna tana yi wa Asal magana da yarensu, Nana kuma ta cigaba da aikinta, tana sane ta cewa Asal ba ta so, dan ba ta gama gane ina Asal ɗin ta saka gaba ba, da kuma cikakkiyar manufarta a kanta ba. Tana tsoron ta yi amfani da wata dama da za ta samu ta cutar da ita. Katafaren ɗakin bacci ne, mai ɗauke da kayan alatun more rayuwa irin na masu mulki. Duhun dare ne, sai dai hasken fitilun ɗakin ya gauraye ko ina, kai ba ka ce dare ne ba. Yana zaune a gefen gadon, tare da dattijon. Cikin kamala dattijon ya ce "Imam, ina ƙara yi maka gargaɗi da jan kunne a kan ka ƙara kula da kan ka. Kar ka ɗauka kowane murmushi ne na soyayya, wani murmushin na babu yadda aka iya da kai ne. Kar ka kuskura ka faɗi wani abu da zai rusa shirinmu, mun ɓoye abubuwa da dama a game da kai, duk abin da baka fahimta ba, ka tambaye ni, kar ka wani ya buƙaci sanin wani abu daga gare ka, ka sanar masa kawai jinya ka yi tsawon wannan lokacin. "Abii" "Na'am abin ƙaunata" Imam Hammad ya yi murmushi ya ce "Me ka ke ɓoye mini ne, akwai abubuwan da suka hargitse a rayuwata, tsawon wani lokaci na ɗauka ina jinya ba a hayyacina ba?" "Ka na ji na? Haryanzu ba ka warke ba, ka na buƙatar hutu mussaman a ƙwaƙwalwarka, kar ka takurawa kanka da tunanin abubuwan da suka faru. Jita-jitar da ake yaɗawa a kan ka, da surutai daban-daban shi ne dalilin da ya sanya muka dawo da kai ƙasar nan, a shaida dai kana raye, cikin ƙoshin lafiya" "Mahaukaci ne ni kenan? Tun da ina iya tuna yadda ciwon nawa ya fara, amma ban san yaya ya ƙare ba" Sultan ya tsuke fuska ya ce "Ya ishe ka haka. Kar ka kuskura na ji labarin nan ya fita, waye ya ce kai mahaukaci ne? Larurar zuciya ce take damun ka, babu daɗi babu ƙari daga haka. Babu wata larurar hauka a tattare da kai". "Amma Sultan ko zaka saka na ɓoye wa duniya, yakamata na san matsayin lafiyata... "Hammad!" Tilas ya ja bakinsa ya yi shiru, ganin yadda ya fusata Sultan ɗin. ***** Tun da garin Allah ya waye, Nana take jin faɗuwar gaba da matsananciyar fargaba, ga sanyin da take jin yana ratasa ta, ta san ba na lafiya ne kawai ba. Dan haka ta ɗaura alwala take ta addu'a. Bayan fitowarta ta cika da mamakin ganin yadda ma'aikatan gidan, suke ta aiki tuƙuru suke gyara gidan duk da ko ina a gyare yake. Ko ta ina ƙamshin turaruka ne ke tashi daban-daban. Har sun so su yi yawa ma. Ɓangaren da take aiki, sai azalzalarsu ake yi, ta fahimci dai wani baƙo ne mai muhimmanci zai sauka a gidan. Har mamaki take yi yadda suke ba wa abinci muhimmanci, baƙo ɗaya sai a saka a yi masa abinci biyar, kuma duk da an san ba iya cinyewa zai yi ba. Ta fito kenan ta ci karo da Asal, ta sanya zani da doguwar riga na shadda baƙar shadda, kanta babu ɗan kwali, hannayenta da yatsunta duk zobunan gwal ne, uwa uba wata irin sarƙa da ta saka ta zinari tun daga wuyanta har cikinta. Gashinta ya sha ado, ta sake shi har kafaɗarta, shi ma ta sanya masa wata siririyar sarƙa da ta kwanto har goshinta. Duk hassadar mai hassada babu yadda za a yi ka kalle ta ka kushe ta, jawur da ita a cikin baƙar shaddar sai ta haska shaddar. Ita dai Nana tun da ta zo gidan, ba ta taɓa ganin Asal da miji ko 'yan uwa ba, sai tarkacen ƙawayenta, su ma a wancan gidan ne, wannan gidan ba sa biyo ta su zo. Kuma duk abin nan Nana ba ta taɓa bin diddigi ta ji wace ce Asal ba, me yasa kuma take rayuwa a gidan daga ita sai masu yi mata hidima ba. Da daddare Nana ta ji su Balaraba su na yare, su na faɗin sunan Imam, lokaci lokaci su na haɗa wa da Hausa, sai dai ta manta a inda ta taɓa jin Imam ɗin. Babban abin da ya ɗaurewa Imam kai, bai wuce yadda a faransa yake jin sa garau, ba shi da wata damuwa ko wani ciwo da yake ji ba. Amma tun da ya sanya ƙafarsa a Agadez tsawon kwanaki huɗu, ko sau ɗaya zuciyarsa ba ta saurara da bugun da take yi cikin sauri babu ƙaƙƙautawa ba. Nana na ta kai komo a kitchen, ta kammala duk wani aiki da ya shafe ta, tana shirin tafiya ta je ta kwanta. Balaraba ta ce "Saurin me ki ke yi ne Nana?" "Ina son na je na yi wanka na kwanta ne" "Ki je ki yi wankan, nan da mintuna talatin za ki kai wa Gimbiya Asal bunu da madara sashinta" Har Nana za ta yi magana, dan ba ta shiga sashin Asal sai sau ɗaya, ta taɓa zuwa idan sun yi girki akwai waɗanda suke kaɗai suke iya zuwa sashen su kai. Ta fasa maganar ta ce "To" A gurguje Nana ta kintsa, ta koma ta ɗauki kayan za ta yi gaba, Balaraba ta ce "Ai ba sashinta za a kai ba, Ramata raka ta" Ramata ta kalli Nana ta yi mata kallon banza, ta ɗan kwaɓe baki sannan ta yi gaba Nana ta bi bayanta. Duk yadda Nana ta so sarrafa kanta ta kasa, ta ɗaga kai ta din ga kallon ƙawataccen gurin tare da jinjina yadda masu gidan suka ƙware a iya almubazzaranci. Dan ba za ta kira shi ado ba kawai sai dai almubazzaranci. Tana saka ƙafarta a cikin falon, ta ji tamkar an jona mata shocking, saboda rawar da jikinta ya yi, sai da farantin hannunta ma ya girgiza tamkar zai ɓare. Ramata ta kalle ta, ta yi tsaki kawai. Nana ta ajiye kayan a hankali a kan carfet ɗin ɗakin. Bayan ta ajiye ta yi taku huɗu zuwa biyar, ta ji yadda adadin sanyin da take ji yana ƙara yawa. Ta sauke idanunta a kan ƙaton frame da hotonsa a jiki. Danƙarewa ta yi a guri ɗaya, ta kasa motsa ko da ƙafarta. Taku ta fara ji a bayanta, ana tahowa, muryar Asal ta ji tana magana da faransanci cikin shagwaɓa. Ɗan ja ya yi ya tsaya, jin yadda jikinsa ya yi wata girgiza. "Lafiya dai ko?" Ya jinjina mata kai alamar eh. "Amm me ku ke yi a tsaye a gurin nan ne?" Ramata ta ce "Abinci muka kawo" "Waye ya yi?" Ta nuna Nana da ba ta juyo ba. "Zo" ta kira Nana sai dai Nanan ta ƙame ba ta juyo ba. A wulaƙance Ramata ta taɓa ta ta ce "Ana yi miki magana" "Tana ji na rainin hankalin za ta yi mini" Sannu a hankali Nana ta juyo, idonsa na kan wayar hannunsa. Yanzu ta tabattar da mafarki ta yi ba, Sayyid ta gani, sai dai ganinsa bai razana ta ya kiɗimata ba, kamar yadda alamu suka nuna Asal matarsa ce ba. Ta sunkuyar da kanta ƙasa, tana jan ƙafafuwanta a hankali. "Me ya same ki ne?" Ta girgiza kai alamar ba komai. "Ki yi mini magana kina girgiza kai kawai" "Ba ni da lafiya" Asal ta ja tsaki ta ce "Je ki kar ki ɓata mini rai" Ta zuba masa shayin a kofi, ta zuba masa madara, ya ɗauka a hankali ya kai bakinsa yana sha. Nana kuwa a ɗakinta, gaba ɗaya ta burkice, tamkar za ta yi hauka ta ce "Dama abin da ka ke gargaɗina a kai kenan Ƙaisar? Sayyid me yasa za ka yi mini haka, dama ka na da wata matar ka aure ni? Yanzu ka na nufin ka manta ni, Sayyid anya alƙawari ya ce haka? Na haƙura zan ɗauki ɗa na na koma gida, ganinka da wata kawai ya isa ya yi ajalina. Wataƙila alhakin iyayena ne ma da na taho ba da izininsu ba. Yadda ka ke a cikin daular nan, yaya za a yi na ce ina da alaƙa da kai ma a yarda da ni?" Ka ce Ruhina da naka su na rayuwa a tare, kowannenmu yana ɗauke da ruhin ɗan uwansa, ni na yi dakon soyayyarka ashe ka na da matar da ta fi ni komai" Ta yi maganar cikin matsanancin kuka tamkar za ta fita daga hayyacinta. Yana tsaye yana jin yadda ruwan yake ratsa shi daga cikin gashin kansa zuwa jikinsa. Wani irin zafi yake ji a cikin ƙwaƙwalwarsa, tamkar kansa zai tarwatse. Karo biyu yana jin jikinsa ya yi girgiza. Ya yi wankan ya lulluɓo jikinsa da towel. Asal ta sha kwalliya cikin baƙaƙen kaya na bacci. Ta nufo shi tana rangwaɗa, ta cire towel ɗin da ya lulluɓa da shi. Ya ɗan lumshe idanunsa saboda ƙamshin turaren da Asal take yi mai jan hankali. Ta shige jikinsa ta rungume shi, ta ce "Na yi kewarka sosai Imam" "Nima ina jin kewar abin da ban san mene ba, bayan kewarki da na yi" "Akwai abin da ya fi ni muhimmanci dama, da har ka ke kewarsa fiye da ni?" "A'a ban ma san mene ba, kawai dai ina jin akwai wani abu da ba daidai ba" Ya yi maganar yana shafa gefen wuyanta, yana son tambayarta wace ce yarinyar nan, amma ya haɗiye ya fasa. Ya fara ƙoƙarin sumbatar ta, sai dai ya ja da baya da sauri yana dafe kansa, da yake jin wani sauti mara daɗin ji a cikin sa. "Imam jikin ne dai?" Bai yi magana ba, ya hau kan gadon ya kwanta ya lumshe idanunsa. Washegari da safe, idanun Nana sun kumbura suntum, saboda ba ta rintsa ba ko kaɗan. Ta saba da wuri take tashi, ta fara gudanar da aikinta, amma sai da aka zo aka kira ta, ta ce ba za ta yi aikin ba. Bayan mintuna talatin sai ga Asal a ɗakin, ta kalli Nana a wulaƙance cikin isa da gadara ta ce "Ki ka ce ba za ki yi aiki ba yau? Saboda gidanki ne ko zaman kan ki ki ke yi a gidan? An kai wa Imam shayi ya ƙi sha ya ce ba irin na jiya ba ne" "Eh ba zan yi girki ba, kuma barin gidan nan zan yi, na gaji da wannan aikin, zan je na ga yarona" Asal ta yi dariya ta ce "Ai kuma ƙarya ki ke yi. Na ɗaukko ki gidan nan saboda nesanta mijin da waɗanann munafukan hadiman, na kawo bare da baki san komai a kan harkar gidan mulki ba. Kuma ba kya cikin kalar matan da za su iya ɗaukar hankalinsa. Dan haka na kawo ki ne dan ki din ga kula da abin da Imam zai ci aikin da ki ka zo yi gidan nan kenan. Nana ta yi wa Asal wani irin kallo mai cike da tsana, ji take tamkar ta kama Asal ta yi ta jibgarta har sai ta ji ta huce. "Gimbiya Asal, ai an bar kari tun ran tubani. Ba zan yi girki ba sai dai yunwa ta kashe Imam ɗin, ke da yake aure idan ba za ki girka masa ba, to kar Allah ya sa ci, sai na bar gidan nan ba zan zauna ba" Ta yi maganar cikin ɗaga murya da zazzaro ido. Asal ta yi taku biyu, ta hankaɗa Nana baya ta ce "Ki kiyaye harshenki a kan abin da zai din ga fitowa daga bakinki, a kan mijina. Biyan buƙatata ce kawai ta sanya nake ƙyale ki, ki daina ƙoƙarin ƙetare iyaka. Tafiya kuma ga hanya nan maza ki tafi mu gani, idan kina tunanin da ka na kawo ki gidan nan na ajiye" Ayshercool 08081012143 74 Wata irin tafasa zuciyar Nana ta din ga yi, ta din ga jin tamkar za ta tsaga ƙirjinta ta fito. Asal ta yi wani shu'umin murmushi ta ce "Ko za ki dake ni ne? Na ga kina ta huci tamkar macijiya. Sannan ina mai ƙara jaddada miki, muddin mijina ya ci wani abu da ya samar masa da matsala a dalilin abincinki da rayuwarki za ki biya. Babu tsautsayi babu ƙaddara a gidan nan. Dan haka sai ki tattara dukkanin nutsuwarki ki san abin da ya kamace ki. Sannan babu ruwanki da yi masa magana, ko yi masa shishshigi, ki dafa abinci ki kai sashensa kawai, babu wanda yake da damar zuwa sashen kai tsaye, ke kawai ki ke da wannan damar a cikin bayin gidan nan, dan haka ina ƙara gargaɗinki a kan ki iya kan ki a zaman gidan nan" Kalmar Bayin da Asal ta faɗa, sai da Nana ta ji kamar ta fashe. A gidan uban wa ta zama baiwarta. Za ta yi magana ta ji tamkar an saka abu a danne mata maƙogwaronta, ta kasa magana. Tana ji tana gani Asal ta gama caɓa mata baƙaƙen maganganu, ta fice. Nana ta fashe da wani irin matsanancin kuka, ta rasa wani tunani ma za ta yi, kanta ya kulle ta zauna tana ci gaba da kuka mai sauti da ratsa zuciya. Ta kasa samun sukunin da za ta yi tunanin mafita ma. Asal na komawa sashen Imam, ta tarar da shi ya shirya tsaf da alamar fita zai yi. "Imam, fita kuma zaka yi?" Ya jinjina mata kai. "To ai ba ka karya ba, kuma mu ɗauki tsawon wannan lokacin ba ma tare baka nan, kuma yanzu ka ce fita za ka yi?" Ya ci gaba da ƙoƙarin fita, amma ta tare shi. "Haba Imam, ko kewata ba ka yi ba? Ba ka yi farin ciki da ganina ba ne? ka ke shirin ficewa ka bar ni?" Ya tsaya yana ƙarewa fuskarta kallo ya yi murmushin gefen baki ya ce "Abincin ne ban ji daɗin sa kamar na jiya ba. Sannan Gimbiya Bilkisu zan je na gaisar". Noƙe masa kafa ta yi tana riƙe rigarsa. Ya ajiye agogonsa ya nemi guri ya zauna, hakan ya sanya ita ma ta zauna tana murmushi. Nana kuwa tana tsaka da kuka ta ji an dafa ta, ta ɗaga kanta a hankali ta ganta a ɗakin karatun Ƙaisar. Sai dai wannan karon tsawonsa daidai da ita, ya zauna sosai ya fuskance ta. Ta sunkuyar da kanta hawaye na ci gaba da kwararowa daga cikin idanunta. "Uwar gijiyata" Nana ta ɗaga idanunta a hankali ta dube shi, ta mayar da kanta ta sunkuyar. "Bai kamata ki nuna karaya a wannan gaɓar ba, duk da ina jin zafin yadda ki ka yi burus da ni, da buƙatata da gargaɗin da na din ga yi miki a baya, amma wannan kamar ita ce gaɓa ta ƙarshe mai kuma matuƙar wahala, idan ki ka sare a yanzu wahalar da ki ka yi tuƙuru a baya za ta tashi a banza kenan. Ba ki da tabbacin ya gane ki? Ko kuma bai gane ki ba, sai dai komai ya zo da sauƙi. Ita wannan matar sauƙaƙa miki aiki ta yi, tun da ta kawo ki kusa da shi, ta kawo ki har inda yake, godiya ma yakamata ki yi mata. Ki kawar da kai daga kan duk wani abu na wulaƙanci da za ta yi miki a yanzu, a ƙarshe ke ce da riba, ki fara tantance halin da yake ciki, kafin ki ɗauki mataki na ƙarshe" Cikin kuka Nana ta ce "Ƙaisar na karaya, na sare ba zan iya ba, wa zai yarda da ni matarsa ce, banbancim da ke tsakanina da shi tazara ce mai nisan gaske. Ba na buƙatar ya gane ni, gida zan koma na nemi gafarar iyayena na kula da yarona" "Ba za ki koma gida yanzu ba, yaronki yana hannu na gari a yanzu duk ban san gaba ba. Na daɗe ban ga bil'adama mai juriya sadaukarwa da tsantsar juriya kamar ki ba. Imaninki da Allah ina da tabbacin ba zaki wulaƙanta ba kamar yadda ki ke yawan faɗa mini. Kar ki karaya ki tsaya ki karɓi abin da yake naki ne, idan ki ka karaya ki ka tafi kin yi biyu babu, wahalarki kuma ta tashi a banza" Da wannan maganganun ta buɗe idonta, tana sauke numfashi a hankali. Daki-daki ta din ga jin maganganun Ƙaisar na dawo mata. Ta yi shiru tana nazari, ta tashi zaune a hankali. "Abin da yake nawa? Eh Ƙaisar, Sayyid nawa ne, bai kamata na karaya a wannan gaɓar ba" ta furta idanunta na sake cika da hawaye bayan tuna Asal matarsa ce. Ta din ga tunanin suwaye suka tafi da shi lokacin suna Buda? Ko dai da kansa ya gudu ya bar ta? Ina su Habu, ta gan shi shikaɗai? Da gaske taɓin hankali ya yi a baya ya manta wace ce ita, ko kuwa dai raina mata hankali ya yi, ko kuwa dai duk wannan abin ba Sayyid ɗin ta ba ne?" Wata zuciyar ta ce "Haba dai, ko na makance na shafa na san Sayyid, ko za a ajiye irin sa dubu zan fitar da Sayyid a cikin su. Ina zan samu amsoshin tambayoyina ne?" Ta yi maganar tana dafe kanta da yake yi mata wani irin ciwo. Ƙaisar kuwa yana sakin Nana, ɗakin karatunsa ya gauraye da sautin dariyar Giyaz, dariya ta rashin imani mara daɗin ji. Ƙaisar ya waiwaya, yana kallon inda Giyaz yake shawagi a sama yana ƙyaƙyata dariyar, hakan ya tabattar masa da Giyaz ya gama jinyar abin da Nana ta yi masa. Ya yi wata irin girgiza ya bayyana a gaban Ƙaisar, ya din ga zagaye Ƙaisar yana ci gaba da dariyar cike da mugunta, daga bisani ya tsahirta da dariyar ya ce "'yan samari, yaushe imaninka ya ƙaru haka, har ka ke yi wa uwar gijiyar da ba ta ɗauke a bakin komai ba, nasiha da ba ta shawara?" Ƙaisar ya tsuke fuska ya ce "Ban yi maka iyaka da zuwa inda nake ba?" Giyaz ya ce "Daɗin abin har gori ta yi maka a kan butulcin ka yi mini, amma da yake ba zuciya ce da kai ba, ka na liƙe da ita. To bari na gaya maka abin da ba ka sani ba, ni ne na sake juye tunaninsa na shafe masa wancan tunanin, yadda abin zai yi mata ciwo, dama na gaya mata dawowata ba za ta yi mata daɗi ba, tun da na tashi daga jinya nake tunanin yadda zan ƙuntata mata na ƙuntata maka. Ya ɗagowa Ƙaisar wata kwalba, da wani farin haske yana yawo a cikin ruwan da ke cikin kwalbar. "Ka ga wannan, tunaninsa ne a ciki na duk wani abu da ya shafe ta na rufe shi ba zai taɓa tuna ta ba har abada. Sai dai ta dauwwama gararamba babu makoma. Na ga ka yi wa ɗanta riga-kafi, dan ka hana ni cutar da shi, sai dai ka riga ka makar... Ƙaisar ya ce "Kai ne ka makara, dan cutarwar da ka yi masa a ciki ma bai yi tasiri ba. Kar ka manta Bil'adama ce. Kar ka manta aiki aka baka ka shafe wancan tunanin nasa, ba ka taɓa tunanin zai tuna waye shi ba, sai ga shi yanzu ya tuna waye shi, dan haka wannan ma baka da tabbacin zai manta rayuwarsu har abada" Giyaz ya ce "Za ka gani, ka zuba ido zaka ce na gaya maka, duk wata hanya da zan bi na tsohe farincikin yarinyar nan na ƙuntata mata sai na yi" "Kana tunanin akwai sauran wahalar da ta rage wadda ba ta sha ba a baya? Haryanzu ba ka san suwaye biladama ba, waɗanda ka ke ta'amalli da su miyagun cikinsu ne, hatsabibancinsu kawai ka ke gani. Amma wannan karon ne za mu yi fito na fito na gasken gaske tsakanin ni da kai a kan yarinyar nan. Kar ka manta ka fi ni shekaru da daɗewa a duniya, hasali ma kai ka haife ni, amma ni marubuci ne, kuma manazarci sannan masanin magunguna kar ka ƙetare iyaka, zan iya baka mamaki." Giyaz ya sake kecewa da dariya ya ce "Gaskiya ne marubuci, kuma masanin magani, ka buɗe wannan kwalbar idan ka isa ya tuna waye shi saboda ka taimaki uwar gijiyar ka, ka faranta mata. Ƙaisar ya ce "Kai ka yi imani da cewa ka rufe tunaninsa a kwalba, amma kai zan cewa ka zuba ido ka ga ikon Allah" Giyaz ya ce "Shikenan ina zuba ido" daga haka ya ɓace ɓat daga libraryn. Har bayan azahar Imam yana tare da Asal, sai dai da aka kawo abincin rana, ba Nana ce ta kawo ba, Asal ta yi ta bala'i a kan kar wanda ta sake gani a sashen, idan ba a nemi izini ba ko kuma idan Nana ce ta kawo ba. Ta kira Imam da nufin ya ci abincin rana, sai dai ya yi loma biyu ya  kalli Asal ya yi shiru, ya tsiyayo shayi daga cikin haɗaɗiyar butar shayin, ya kai bakinsa, ya ɗan sha kaɗan ya ajiye, ya ɗauki robar madara ya buɗe yana sha. "Amour" ta furta a shagwaɓe ya ɗaga idanunsa ya kalle ta. "Ba ka ci abincin ba fa" Ya girgiza kai ya ce "Ba irin na jiya ba ne" "To wai meye a cikin na jiyan ne da ya sanya shi daban?" Ya girgiza kai ya ce "Nima ban sani ba, kawai dai wannan ɗin ban ji ɗanɗanonsa ba, kin san haryanzu jikin nawa sai a hankali, ba na cin abinci sai da na dawo ɗin nan" "Kuku fa na samo maka mussaman daga Nigeria, ta iya girki ita ta yi maka na jiyan ma, sai dai muguwar kidahuma ce, kuma ba ta da kirki amma ina da tabbacin ba za ta cutar da mu ba, a can gidan cin abinci na Maraɗi na ɗaukko ta mussaman saboda kai" Ya jinjina mata kai tare da yi mata alamar jinjina. Sai dai a baɗini cikin ƙwaƙwalwarsa, Nigeria da ta ambata sai da tsigar jikinsa ta tashi, gabansa kuma ya faɗi. Duk dabarun da Asal yakamata ta yi ta saka ya ci abincin nan ya ƙo ci, ya sha madarar raƙumi ya ce ta ishe shi ba sai ya ci abincin ba. Asal ta ɗanɗana Abincin, sai dai ba ta ji wani rashin ɗanɗano ba, abincin ya yi daɗi amma shi ya ce babu ɗanɗano. Da daddare Asal ta tafi ta yi wanka, ta je ta samu Nana, idan ba ta yi girkin daren ba, za ta gwada mata mene ne matsayinta a gidan. Sai dai ɓangaren Nana, tun da ta ji su Ramata duk sun ruɗe, wai an yi girki Imam ya ƙi ci, Asal sai bala'i take yi, kuma ta ce kar su sake dafa wani abu a kai masa muddin ba Nana ba ce ba. Yana zaune yana kallon labarai, shikaɗai a falon ya ji yanayinsa ya fara canzawa. Ya yi shiru yana tunanin me yake shirin faruwa da shi ne haka. Ta turo ƙofar ɗakin ta shigo da sallama, tana shigowa idanunsa suka haɗe lokaci guda. A zahiri ya ga shocking ɗin da jikin Nana ya yi, dan sai da farantin hannunta ya yi rawa. Sai dai shi ma na sa jikin ya yi, amma da sauri ta sunkuyar da kanta. Gabanta ya yi mummunan faɗuwa bayan ganin Giyaz da ta yi a tsaye a gefen Sayyid yana kallon ta yana dariya. Ya ƙura mata ido yana son gane wani abu da shi kansa bai san mene ne ba. "Ita ce 'yar Nigeria da Asal ta samo?" Ya tambayi kansa a zuciyarsa. Zaucewa ya kusa yi, bayan da Nana ta ƙaraso daf da shi ta ajiye farantin, ya ji ƙamshin turaren sa na tashi a jikinta. Ko da Nana ta ɗago ta saci kallonsa, ta gan shi a nutse yana kallon talabijin ɗin sa yana kaɗa ƙafafuwansa, kamar ma bai san ɗan Adam ya wanzu a gurin ba. Tuni hawaye ya cika mata ido, ganin mutumin da ta yi rayuwa mai cike da so da ƙauna tare da shi, abokin wasanta abokin hirarta, ya zame mata wani na daban a yanzu. Ba ta kai ƙofa ba Asal ta ƙwala mata kira. Ta yi maza ta goge hawayenta ta juyo. Wani abu ya caki zuciyar Nana, ganin Asal da wata 'yar riga a da guntun wando, babu kunya ko makamancin ganin idon Nana ta ce "Zo zan gabatar wa da amour ke" Ta zauna a kusa da shi tamkar za ta shige cikinsa,  ta ce "Imam, ga wadda nake gaya maka, kukun da na samo maka 'yar Nigeria" Sayyid ya yi wa Asal wani kallo yana ɗan lumshe ido, Nana tamkar ta zunduma ihu, sassaucin da ta samu ɗaya shi ne ganin ƙirjin Asal  babu wani abin kirki na jan hankali, duk da yadda ta taƙarƙare tana banƙarewa. Guntun tsaki ya kusa ƙwacewa Nana. A hankali cikin magana daki-daki ya ce "Babu masu girki a Niger, har sai an tsallaka Nigeria?" "Eh mana, duk dan saboda na burgeka ne" ta yi maganar cikin shagwaɓa tana shafa sajensa. "Idan ba ki burgenin ba fa?" "Haba Imam, me yasa haka dan Allah?" "Na ji, amma idan ta girka a samu mai kawowa ba na son ta din ga shigo mini nan" Nana ta kalle shi, zuciyarta ta tsananta bugawa. "Gaskiya Imam ba na son barorin nan su din ga shigowa sashenka, mugwayen munafukai ne duk nan yadda da su ba,  ba kuma zai yiwu maza su din ga shigo mini" Ya buɗe baki zai yi magana, Nana ta tsare shi da ido. Asal ta kalle ta ta ce "Je ki kawai sai da safe, rigima yake ji" Nana gani take kamar da gayya Asal take wannan abubuwan. Ba ta san lokacin da ta furta "Shegiya" ba a hankali. Bayan fitar ta, Asal ta ce "Imam me yasa baka son ta din ga shigowa ne?" Ya lumshe idanunsa ya buɗe ya ce "Tsoro take bani, idan na ganta gabana faɗuwa yake yi." A zaton Asal, Nanan muni ta yi masa, shi yasa baya ƙaunar ganinta, dan haka wani irin farinciki ya kama ta, ta ci gaba da lallaɓa shi a kan ya yi haƙuri Nana ta din ga shigowa sashen tana kawo masa abincin. Shiru ya yi mata ganin ba ta fahimci mai yake nufi ba, dan da suka yi ido huɗu da Nanan gani ya yi tamkar ta na yi masa kallon tuhuma, shi da bai taɓa ganinta ba, da zai iya zai so ya samu dama ya tambaye ta, ya ji ko laifi ya yi mata. Ko kuma ma ba mutum ba ce ba, da yake jin jikinsa ya canza a duk lokacin da ya ganta. Sai dai ya ci Abincin da ta kawo, da daddaren. Nana kuwa rabi da kwata kwanan tsaye ta yi, tayi kukan har ta gaji. Ita yanzu kawai ta zuba wa sarautar Allah ido. Furucin Sayyid ya rusa duk wani ƙwarin gwiwa da take da shi. Da safe kuwa da ta yi girkin,  da wuri ta kai cikin ikon Allah, ba kowa a falon. Kusan awa ɗaya da rabi da kai Abincin aka aiko kiran Nana, ta san za a rina, saboda abin da ta aikata, ta san dole a neme ta. Kanta tsaye ta shiga falon Imam, ta tarar da fuskarsa jawur hatta idonsa ma ya yi ja. Asal cikin bala'i ta hau Nana da faɗa. "Kashe mini miji za ki yi? Na ɗaukko ki ina tunanin za ki yi abin arziki, amma ki yi yinƙurin kashe shi, ban gaya miki sharaɗin wani abu ya samu mijina a dalilin abincinki ba?" AREWABOOKS Nana ta zuba wa Asal ido, sannan ta kalle shi ta mayar da idonta ga Asal ta ce "To ai ni ba ki gaya mini me na yi ba" "A kan me za ki cika yaji a cikin abinci ki cika tafarnuwa? Bayan ba ya son abinci mai yaji da yawa" "Ki daina yi mini faɗa, tun da ba ki gaya mini baya cin abinci mai yaji ba, kuskure ne bai kamata ki yi mini faɗa ba dan yau ɗaya na yi kuskure ba, amma bari na ɗanɗana Abincin na ji, sai na ga me zan gyara a gaba" Ta nufe shi gadan-gadan ta kalli fuskarsa, yadda ta koma sak lokacin suna tare, tana ba shi abinci mai yaji, ba zai yi magana ba sai dai ta gani a fuskarsa. Ta durƙusa ta ɗauki cokalin da ya ci abinci da shi, ta ɗiba ta kai bakinta, ta ɗago suka yi ido huɗu da shi, ya sunkuyar da kansa da sauri. Ta risunar da kai ta ce "Tuba nake Shugaba, na yi kuskure in sha Allah zan kiyaye hakan ba zan sake ba. Ba a gaya mini ba ka cin yaji da yawa ba ne, amma zan kiyaye" Ya sake ɗaga ido suka yi ido huɗu. Ya rintse idanunsa yana tunanin wace ce wannan? Meye haɗinsa da ita jikinsa yake rikicewa a duk lokacin da ya ganta? Sai dai duk da wannan tambayoyin da yake da su, kalmar shugaba da ta kira shi da ita, ta din ga yawo a cikin kansa. Nana ta miƙe tsaye ta kalli Asal da tsaya tamkar ta fashe, ta ce "Dan Allah ku yi haƙuri zan sake kiyayewa, ba zan sake maimaita kuskuren da na yi ba". Kawai Asal ta janyo Nana, cikin mamaki take kallon Asal. "Nana ina ki ka samu wannan turaren?" Cikin rashin fahimta Nana ta ce "Wane turaren?" "Wanda yake tashi a jikinki, Imam ba ka ji ba?" Shi dai ya yi shiru bai ce komai ba. Nana ta ɗage hijjabin jikinta, doguwar rigar da aka ba ta ta bayyana a jikinta da tamkar sai da aka aunata aka ba ta ta ce "Rigar da aka ba ni ce take ƙamshin, nima a haka aka bani ita" Ta tsaya tana yi wa Nana kallon tuhuma da rashin gamsuwa da abin da ta faɗa, sannan babban abin da ya ƙara ɗaure mata kai, yadda Nanan yau take ɗauke da ƙwarin gwiwa yau. "Cherie, ki sallame ta kawai ya wuce" Asal ta saki Nana tana bin ta da kallo. Ta ce "Na tafi da Abincin na dafo wani ne?" Asal za ta yi magana ya ce "A'a" Nana ta ɗauki farantin Abincin nata ta yi waje tana murmushin nasara, dan ta fuskanci ta fara dagula wa Asal lissafi. ***** "Ba wai-wai nake ki ji ba, gaskiya ne Hammad ya dawo Agadez kuma cikin hayyacinsa ba hauka ba, ya aka yi haka ta faru, kuma har Sultan yana iƙirarin ya yi jinya ne a faransa, yanzu ya warke zai ci gaba da gudanar da ayyukan sa, yaya aka yi aka haihu a ragaya?" "Waye ya ce ya warke ɗin ne? Babu waraka a tattare da Imam Hammad" "Amma kai ka ce zai haukace ya bar ƙasar nan baki ɗaya, amma ya dawo cikin ƙoshin lafiya, an ce ma wai jinya ya yi a faransa" "Imam Hammad bai warke ba, kuma ba jinya ya yi a faransa ba, ya bar ƙasar nan ya yi nisa ya je ya yi rayuwar ƙasƙanci ba tare da tuna waye shi ba ma. Sai dai an samu mushkila inda ya tafi ɗin, wanda a can nake tunanin an ɓata mana fiye da rabin aikin ma, akwai dai yadda aka yi aka gano inda yake, amma tabbas ya yi nisa da gida ba tare da sanin waye shi ba. Amma warkewa kam bai warke ba, an samu matsala ne wani ya shiga cikin aikin ya ɓata wani abu , amma wannan ce gaɓar da ta fi cancanta mu sake hargitsa shi, za a ƙara ƙaimi a kan aikin, komai zai tafi yadda yakamata, a ƙaryata Sultan ya kunyata a idon duniya, a lokacin da ɗan nasa abin ƙaunarsa zai yi hauka tuburan duniya ta sani" "To shikenan, ina nan ina zuba ido, ina kuma jiran ji daga gare ka, da kuma abin da zai faru." ***** Nana ta girka Abincin rana, ta shirya shi a kan tray, ta je ta ajiye a falon Imam. Ta ja ta tsaya ta ƙi tafiya. Ta daɗe a tsaye, kafin su fito tare da Asal. Ganinsu taren ba ƙaramin dukan Nana ya yi ba, amma ta danne ta koma gefe ta sunkuyar da kai. Ja ya yi ya tsaya, saboda yana kusanto Nana, yana jin tamkar zuciyarsa za ta tsaga ƙirjinsa ta fito, ya din ga jin tamkar zai fita hayyacinsa. Asal ta kalle shi ta ce "Yaya dai?" Ya ɗaga kai ya kalli inda Nana take, kawai ya juya ya koma ɗaki. Ta ƙaraso gaban Nana ta ce "Ke ya aka yi ne? Ba cewa na yi miki, ki din ga ajiye abincin ki tafi ba?" Nana ta haɗiye wani abu mai ɗaci ta ce "Ki yi haƙuri, dama wata alfarma zan nema na a gurinki" "Ta me?" "Kin ce dole na kula da abin da mijinki zai din ga ci na yi taka tsantsan, to kuma gurin girkin yana can waje, duk da idan ina girki tsayawa nake yi a gurin girkin, amma ina jin tsoron kar wani ya shiga ya yi wani abu na ba dai-dai ba a yi zaton ko nice, shi ne na ce ko za a yi wa ɗakin girki mukulli a bani?" Asal ta ɗan yi shiru, sannan ta ce "Kuma kin yi magana mai kyau, zan san abin yi in sha Allah, za ki iya tafiya" Bayan Nana ta fita, ta koma da bayata shiga ɗakin, ta tarar da shi a kan gado ya takure jikinsa ya yi shiru, jin motsinta ya sanya ya waiwayo. "Imam, meyafaru ne wai?" "Na ce miki yarinyar nan ta daina shigowa, bana jin daɗin jikina idan na ganta, ina kyautata zaton ma ba mutum ba ce ba" Asal ta tuntsure da dariya ta ce "Mutum ce fa, dan dai kawai ba ka son hayaniya ne, kuma ba hankali ta cika ba. Amma ai Abincinta yana yi maka daɗi, shi ka ke ci fa, kuma idan ba ita ta yi ba baka ci" Ya numfasa ya ce "Ni dai kar ki ɗaukko abin da zai zame mana matsala" Ta karairaye murya ta ce "Imam ba zan taɓa kawo abin da zai cutar da mu ba, ka kwantar da hankalinka za ka daina ji, ka san ita ba ƙabilarmu ba ce, ba kuma 'yar ƙasarmu ba ce ba, shi yasa ka ke jin haka, amma ka kwantar da hankalinka" Ya jinjina mata kai kawai bai ce komai ba, ya san ba za ta taɓa fuskantar halin da yake shiga ba. ***** Yusra da Sagir su na zaune a falonsa, yana ta kallon agogon hannunsa, Shukura yake ta jira ta fito yana so ya haɗa su, ya yi musu nasiha, amma kusan awa guda da yi mata magana, amma shiru ba ta fito ba. Ransa ya ɓaci da irin wannan wulaƙanci da take ta yi, ya rarrashe ta, ya ba ta haƙuri amma ta ƙi sauraren sa, sai wulaƙanci take yi masa yadda ranta ya ga dama. Ga shi yana tausayinta saboda tsohon ciki da yake jikinta, ga hawan jini, amma ko a jikinta tsakaninta da shi gaisuwa ce kawai, bayan wannan idan zai shekara yana magana, ba za ta kula shi ba, sai dai ya gaji ya tashi. Yanzun ma har ya fusata zai je ya same ta, sai ga shi ta fito, fuskar nan babu annuri da alama ma fita za ta yi. Ta zo ta nemi guri ta zauna, ta yi shiru ba ta ce komai ba. Yusra ma ta kalle ta ta basar, ba ta kula ta ba. "Mu na nan mu na ta jiran ki tun ɗazu, amma baki fito ba" Fuska a ɗan tsuke ta ce "Shiryawa na tsaya yi ne" "Ina za ki je ne?" Ta kwaɓe fuska ta ce "Awo" Ta ba shi amsa a taƙaice. Ya numfasa dan ba ya son biye mata, dan ya ga a kusa take, ko alamar ganin Yusra ba ta yi ba. "Amm dama ba wani dalili ya sanya na tara ku a nan gaba ɗaya ba, ina son in gabatar muku da juna, sannan kuma na yi muku nasiha a kan haɗin kai da zaman lafiya. Shukura kamar yadda ki ka sani tun da farko, kafin na aure ki, na auri Yusra sai dai ƙaddara ta gifta mun rabu. Ke ma kuma Yusra na sanar da ke bayan rabuwarmu na auri Shukura. Dan haka ina mai roƙonku a kan zaman lafiya da haƙuri da juna, domin na samu nutsuwa na yi muku adalci. Yusra ga Shukura, Shukura ga 'yar uwakki Yusra" Da ƙyar Yusra ta ce "Sannu" Haushi ya kama Shukura, wai sanni sai ka ce wadda take ciwo, da ya san zai dawo da Yusra dan me zai sake ta ya aure ta. Sagir ya ce "Shukura tana yi miki magana fa" Shukura ta ce "Hankalina na yana kan tafiyata Asibiti ne, ba na jin daɗin jikina. Amarya ina yi miki barka da zuwa, Allah ya sanya alkhairi ya baku zaman lafiya" Ta ƙarasa maganar tare da miƙewa da ƙyar. "Shukura ki tsaya mana mu gama sai ki tafi" Cikin fushi ta ce "Na ce maka fa bani da lafiya, kwana na yi ba na jin daɗin jikina" Sai kuma ya tuna takaicin abin da take yi masa ya sanya bai je ya ganta da daddare ba, ya wuce gurin Yusra. Shukura kuwa tuni ta nufi ƙofa, ya bi bayanta yana "Ki tsaya na sauke ki a Asibitin" Ta girgiza kai ta ce "A'a ka koma gurin amaryarka, kar ka bar ta itakaɗai" Jiki a sanyaye ya kira sunanta, ta ɗaga ido ta kalle shi. Idanunta sun yi jawur sun cika da hawaye. Hannu ya sanya yana share mata hawayen da ya fara gangarowa kan kuncinta, ya ce "Dan Allah Shukura ki daina, ban dawo da Yusra dan na ɓata miki rai, ko na cutar da ke ba, wallahi kukan nan da ki ke yi da rashin walwalar ki yana damuna ba kaɗan ba, dan Allah ki daina" Ta ce "Tom, bari na tafi kar na makara" Ya ce "Bari na canzo kaya na zo na kai ki" Ta ce "Kar ka damu, zan iya driving ai, yanzu zan dawo in sha Allah" "To me za ki sayo mini idan kin tashi dawowa?" Murmushin yaƙe ta yi ta ce "Me ka ke so?" "Abin daɗi, sai kuma uwa uba ki ƙara yi mini murmushin nan dan Allah" Murmushin ta sake yi tana taɓa jakarta. Ya dafa cikinta ya ce "A dawo lafiya Allah ya tsare, ki kular mini da kan ku sosai. Dan Allah ki daina fushin nan da ni Shukura, kin ga yau zan dawo gurinki, kuma ina son zuwa inda ki ke amma yadda ki ke yi mini ne ba na jin daɗi, har fargabar zuwa inda ki ke nake yi. Dan Allah idan na zo kar ki haɗe mini rai dan Allah sweetheart" "Tom" "Tom ɗin nan kuwa ta kai zuci?" Shukura ta ce "Ta kai mana" "Yauwwa babyna, ina jiranki, ki dawo da wuri dan Allah" "To in sha Allah" Ya buɗe mata motar, yana jin daɗin yadda ta sakar masa fuska, tsayawa ya yi janta da hira, yana tsaye a bakin ƙofar motar, ita kuma tana ciki a zaune. Abin mata da miji sai ga Shukura tana dariya, da haka suka yi sallama ta fita. Yusra kuwa sai da haushi ya kama ta, yadda ya yi ficewarsa ya je ya shantake a gurin Shukura, kamar ma ya manta da wanzuwarta a gurin. ***** Duk yadda Asal take ɗokin Imam, gaba ɗaya gani take kamar ba a cikin nutsuwarsa yake ba, kamar wani abu yana damunsa, babu yadda ba ta yi ba a kan ya gaya mata mene ne yake damunsa ba, amma ya ce mata shi babu abin da yake damunsa. A hankali ta yi juyi a kan gadon, ta zuba masa ido yadda yake ta uban gumi, tare da yin haki, har sai da ta ɗan tsorata. Sai dai ta ga ya yi juyi ya ci gaba da baccinsa. Kwana biyu Nana ta daina yadda su haɗu, kamar yadda ya buƙata, sai dai yau da ta shiga ta tarar yana nan. Babu tsammani ya ga Nana, hakan ya sanya ya ɗan zabura, har sai da ta gani. "Sayyid ina kwana" Shiru ya yi yana tunani, sai kuma ya maze bai motsa ba. "Ban san laifin da na yi da ya sanya, ka nemi na daina zuwa inda ka ke ba, amma idan laifi na yi maka, ina neman afuwarka Sayyid" Sannu a hankali kalmomin da ta yi amfani da su, suka din ga shigarsa ɗaya bayan ɗaya, yana jin kalaman na da wata fassara da yakamata ya sani, amma ya kasa gano fassarar, duk da yana jin yaren na hausa, kuma da shi ta yi maganar. Ƙamshin turaren sa da Asal take faɗa, yanzu ma shi yake ji yana tashi a jikinta. Ta miƙe ta yi waje cikin sanyin jiki, kawai ya tashi ya yinƙura, ya bi bayanta. Sai dai ya tsaya a bakin ƙofa yana tunanin to idan ya bi bayanta ina zai je, ko kuma me zai ce mata?. Kawai ya koma da baya ya nemi guri ya zauna. ***** Satin bikin Abba ya kama, Hajiya Sa'a duk ta yi busy, Jamila kuma ta rage zuwa gidan gaba ɗaya. Hajiya Sa'a tana ta jiran Abba za ta aike shi, amma shiru har sha ɗaya na safe bai fito ba, haushi ya kama ta dan muraran yake adawa da auren nan da zai yi. Bala'i take ta yi, tare da alwashin ɗaukar mummunan mataki a kan Jamila. Dan a cewarta ita take ziga shi. Ta shiga ɗakinsa tana bala'i, kawai ta gan shi a kwance yana bacci. "Abba wannan wane irin bacci ne har haka? Kai da muke da hidima a gaba, dan ka nuna mini ban isa ba, shi ne za ka nemi guri ka yi ta baccin asara" Sai dai ya yi shiru bai tashi ba. Ta ƙarasa ta ɗala masa duka a ƙafafuwansa, amma shiru bai tashi ba. A iya saninta, Abba ba shi da nauyin bacci, amma yau dai abin ya yi yawa. Ta jirkita shi, ga mamakinta kawai ta gan jini a hancinsa, da bakinsa ga fatarsa ta yamutse jikinsa ya yi fari ƙwal. Sai dai yanayin jikin nasa ya nuna akwai nutsuwa a tattare da shi. Wani irin magigicin ihu Hajiya Sa'a ta yi, ta hau kururuwa tana jijjiga gawar Abba, tana kiran sunansa da wata irin murya ta tashin hankali, girgiza shi take yi tana ihu da kururuwa a kan gawar, amma Abba rai ya riga ya yi halinsa. Hajiya Sa'a ta tashi da gudu ta nufi cikin gidan, tana ihu tana kururuwa tana "Wayyo Allah na shiga uku, dan Allah ku zo ku taya ni duba ɗana me ya samu Abba, dan Allah ku taimake ni kar Abba ya mutu ya bar ni na shiga uku na lalace" Tuni mutanen da ke gidan, suka fito aka je aka dudduba aka tabattar da mutuwar Abba. Ɗaya daga cikin ƙawayenta ta ce "Kuma ba guba ya sha ba, ko wani abu ko ba shi da lafiya?" Hajiya Sa'a babu baki sai kuka kawai da take yi. Safiyya ta ja ta tayi waje da ita, ba su tsaya a ko ina ba sai bedroom ɗin ta. "Hajiya me ki ka fahimta game da gawar Abba?" Cikin kuka da tashin hankali ta ce "Ni ban fahimci komai ba" "Duk wanda muka bayar a ƙungiya, yana zubar da jini ne ta hancinsa da bakinsa, kuma fatarsu haka take komawa, wani ya bayar da Abba a ƙungiyar Asiri, ko tamu ko wata ƙungiyar". Wani irin ihu Hajiya Sa'a ta zunduma, Safiyya ta toshe mata baki tana faɗin "Hajiya ki rufa mana asiri kar ki tona mana asiri a gano mu" Wayar Safiyya da ke aljihunta ce ta fara ringing, ta ciro ta sai ta ga Jamila ce take kiran wayar. Ta kalli Hajiya Sa'a da ke zunduma ihu sannan ta ɗaga. "Na san zuwa yanzu Hajiya tana cikin mawuyacin hali. Ba za ta iya ɗaga waya ba, amma ina taya mu jaje da ni da ita, Abba ya zama sadaukarwarmu na shekara da ni da ita. Ina fatan zuwa yanzu ta ji abin da ake ji, a duk lokacin da ta bayar da jinin wani ga ƙungiya, ina fatan Allah ya gafarta wa Abba sadaukarwar da ya yi, ya ceci masoyiyyarsa da kuma tseratar da ɗan ƙanin mahaifiyarsa, kuma Abba bai mutu ba, sai da ya san abin da muke aikatawa. Sannan ina taya mu murna, ina ɗauke da cikin Abba a jikina. Ba zan gushe ba ina yi wa Abba a addu'a, da yi masa fatan rahama. Abba mutumin kirki ne, kuma rayayye da ya fita daga cikin matacciya Allah ya sa ya huta" 75 Jamila ta katse wayarta, wani irin kuka ya ƙwace mata, ta din ga wani irin kuka mai gunji. Mama ce ta faɗo ɗakin cikin damuwa ta kalli Jamila, ta ce "Jamila lafiya kuwa, nake jin kukanki tun daga tsakar gida?" Jamila ta yi shiru tana ci gaba da gunjin kuka. Cikin damuwa Mama ta ce "Jamila, ni fa na kasa gane miki a 'yan kwanakin nan, wai mene ne yake damunki ne? Gaba ɗaya ba ki da sukuni, ga koke-koke ko Hajiyar ce ta kore ki ne?" Ta girgiza mata kai alamar a'a. "To mene ne?" "Dan Allah ki ƙyale ni na ji da abin da ya dame ni, Wayyo Allahna" Duk yadda Mama ta kaɗa ta raya, ta yi rarrashin amma fafur Jamila ta ƙi magana, taƙi gaya mata halin da take ciki, haka ta gaji ta bar ta a ɗakin. Tana fita Jamila ta ƙara rushewa da kuka, wani irin zafi take ji a ƙirjinta, soyayyar Abba ta din ga ji sabuwa fil a cikin ranta, ba ta taɓa tunanin al'amura za su kasance kamar yadda suka kasance a yanzu ba. Ji take tamkar ta kashe kanta ta huta, ko ita ma tattara ta shiga uwa duniya kamar yadda yayarta Nana ta yi. ***** "Imam Asad, haba ba kar manta sunan naka, kai jarumi ne, ina mai tabbatar maka da cewa Hammad ba zai zama Sultan a Agadez ba, duk wannan abubuwan da Sultan yake yi da rawar ƙafar da yake yi, mun san abin da yake nufi, dan mun san inda baki ya karkata ta nan yawu yake zuba. Amma Hammad akwai abubuwan da ya rasa, da ƙa'idojin da bai cika ba, dan haka burin Sultan na Hammad ya maye gurbinsa ba zai taɓa yiwuwa ba har abada" Imam Asad ya gyara zamansa, fuskarsa ɗauke da damuwa ya ce "Anya kuwa? Duk abin da Sultan yake so, dole shi muƙarrabansa za su yi su mara masa baya, ina jin tsoron ya furta Hammad ya maye gurbinsa, muddin ya furta ko yana raye ko ba ya raye, sai an zartar da shi, sai dai idan Hammad ne ya bar Duniya" Mutumin ya ce "Kar ka yi la'akari da haka, ko me zai ɗauke mu zamu aikata, ko mene ne, babu wanda zai gaji Sultan sai Imam Asadullahi Jalal, dan haka ka ci gaba da ƙoƙari, burinmu dole ne ya cika" Imam Asad ya jinjina kai cike da gamsuwa. ***** Cikin damuwa Sagir yake kallon agogon hannunsa, yana sake kiran lambar Shukura, ƙarfe biyar da rabi na yamma amma shiru ba ta dawo ba. Duk da Yusra sai da suka yi rigima da shi, a kan yadda ya tafi ya bar ta ɗazu, sai dai ta damu ganin fuskarsa babu walwala yana ta kallon waya. "Baby wai wa ka ke ta kira haka ne?" "Shukura nake kira, ta ce mini 9zata daɗe ba, tun safe da ta fita haryanzu ba ta dawo ba" Yusra ta basar ba ta kuma cewa komai ba, sai dai abin ita ma sai ta ji hankalinta ya tashi, ganin har ya fita masallaci sallar magariba Shukura ba ta dawo ba. Yana dawowa ya dubi Yusar ya ce "Ba ta dawo ba ko?" "Eh ba ta dawo ba, ko ta biya wani gurin ne?" Jiki a sanyaye ya ce "Ba na tunanin hakan, ko za ta biya wani gurin, duk faɗan da muka yi tana gaya mini, ba ma ta da yawan yawo, ba ta fiye son fita ba, idan ba gidansu za ta je ba. Bari na je gidansu, na kuma je Asibitin na ji" "To Allah ya sa tana lafiya, to ko haihuwa ta yi a Asibitin suka riƙe ta, na ga cikin nata ma sha Allah ya tsufa sosai" Ya girgiza kai ya ce "Da haihuwa za ta yi, da tuni an kira ni an sanar mini, bari na je na gani" Yusra ta ce "To Allah ya sa tana nan lafiya dai" Ya amsa da Amin, ya fita. Gaba ɗaya sai Yusra ta ji hankalinta ya tashi. Gidansu ya fara zuwa, ya shiga suka gaisa da Hajiya Amina, sai dai bai ga alamar Shukura ta je gidan ba, ya wayance da nufin zai tafi da Haidar, amma Haidar ɗin ya ƙi bin sa. Hankali a tashe ya tafi Asibitin doctor Sabo, aka ce masa tun safe ta je awo, sha ɗaya da rabi kuma ta bar Asibitin, kamar yadda har a cc camera ya nuna. Nan hankalin Sagir ya dunguzuma, ya ƙara ruɗewa ya burkice, duk inda yake tunanin Shukura za ta je, ya je bai same ta ba. Wayoyinta da su na shiga, amma suka daina. Ya tafi gurin 'yan sanda ya kai report ɗin ɓatan Shukura, bai koma gida ba sai sha biyun dare. Yusra na ganinsa ta tashi tana tambayarsa "Yaya an ganta?" Jiki a sanyaye ya girgiza mata, take gabanta ya faɗi ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Allah ya sa ba saboda ka dawo da ni ne ta tafi ba, Ubangiji Allah ya sa ta dawo, ni zan iya tafiya ma na bar muku gidan, idan zamana ne ba ta so ta bar gidan" "Shukura ba za ta bar gidan nan saboda na dawo da ke ba. Dan kan ta fita mun yi magana ta fahimta da ita, mun daɗe mu na magana, ba saboda ke ne ta bar gidan nan ba" Gaba ɗaya Sagir ya kasa rintsawa, sai damuwa da tashin hankali, haka ita ma Yusra, ƙarshe ma kuka ta saka tana cewa saboda ita ne Shukura ta fita ba ta dawo ba. ***** Yau da Nana ta bushi iska, harabar gidan ta fita tana zagayawa, sai dai zuciyarta a cunkushe take, gaba ɗaya tunaninta yana kan Muhsin, kewar ɗanta take yi sosai da sosai, ga wannan azzalumar matar ta hana ta tafiya, sai dai ita kanta hankalinta ya rabu kashi-kashi ne, ga tunanin Muhsin ga kuma Sayyid da take ganin samu a lokaci guda take ganin rashi. Sai a yau ta ƙara tabattar da girma da ƙasaitar gidan, ba ta taɓa ganin raƙumi da ake faɗa ba, sai yau a cikin gidan. Ban da dawakai, da wasu dabbobin ma da ba ta san sunansu ba, ba kuma ta taɓa ganinsu ba. Asal ta hango hannunta a cikin na Sayyid, an fito da wata danƙareriyar mota, sun shiga an ja sun fice. Nana ta tsaya ta yi shiru cikin damuwa. Cikin matuƙar farin ciki dattijuwar matar fara ƙal, ta miƙe ta rungume Imam Hammad. Cikin girmamawa ya durƙusa zai gaishe ta, amma ta hana shi ta ce "Ai ni yakamata na kwashi gaisuwa shugabana. Ina ta yi wa Sultan ciwon bakin ban gan ka ba, ya ce a bari ka huta kar wanda ya je gida aka dame ka, har sai ka fito dan kan ka" Ya yi murmushi ya ce "Na same ku lafiya?" Ta ce "Alhamdillah, sannu Imam Hammad, an sha jinya Ubangiji Allah ya sanya kaffara" Asal ta ce "Wai ni ba za ki yi mini sanun ba, kin maze kamar ba ki ganni ba" Matar ta ce "Wa yake ta taki, ga mara lafiya" Gimbiya Bilkisu ta yi musu kyakykywar tarba, aka karrama su da Abinci kala-kala, amma ya ƙi ci. Hirar ma idan ta yi sai dai ya yi murmushi kawai, bai fiye tofawa ba. Bayan sun gama da sashen Gimbiya, suka nufi sashen Sultan. Imam Hammad na shiga falon Sultan, Sultan ya miƙe cikin farin ciki fuskarsa ɗauke da murmushi. Abdou ma murmushin ya saki, cikin girmamawa suka gaisa. Imam Nuradden, da Imam Asad duk su na tare da Sultan. Cikin girmamawa suka gaida Hammad, fuskarsa ɗauke da murmushi ya amsa musu. Sun taɓa hira kafin Sultan ya ce "Imam Hammad, zo muje ka raka ni tattaki mana, na miƙe ƙafafuwana" Imam Asad ya ce "Sultan, mu ma mu yi maka rakiyar ne?" "A'a ku da kullum muna tare ga baƙona da muka yi shekaru ba ma tare" Yayi maganar yana riƙe hannun Hammad, suka fita ta wata ƙofa. Imam ya din ga kallon gidan tamkar baƙonsa, kamar ba a ciki yake rayuwa ba a baya. "Hammad" "Na'am Abi" "Kamar wani abu yana damunka, ka gaya mini mene ne" Imam ya yi murmushi ya ce "Babu abin da yake damuna, idan ma akwai ban san mene ne ba" Sultan ya ƙara tattara hankalinsa a kan Hammad ya ce "Ka tabattar? ba ka fa da wanda zaka gaya wa dauwarka idan ba ni ba, ka daina wannan zurfin cikin Imam ba na so ka gaya mini" "Babu abin da yake damun Hammad ɗinka fa" Sultan ya yi murmushi yana dafa kafaɗar Hammad. "Ka san haryanzu miskilin ɗan yaron nan, mai guje-guje a harabar nan nake gani, ya yi guje-gujensa ya faɗi ya ji ciwo, ya zo ya yi ta yi wa Abinsa kuka, ya ce sai na ce ciwon ya daina yi masa zafi, kuma na daki rama masa na daki ƙasar na rama masa" Hammad ya yi dariya sai da haƙoransa suka bayyana ya ce "Duk da wannan gemun na fuskata haryanzu wannan ɗan yaron naka ka ke gani?" "Eh mana, gani nake kamar jiya Sarah ta haifa mini kai. Allah ya jaddada rahama ga Umminka" Ya amsa da Amin cikin sanyin jiki. Sultan ya sake numfasawa ya ce "Hammad, haryanzu babu wani abu da ka iya tunawa bayan fara rashin lafiyarka?" "Ban tuna komai ba" Ya ɗago hannun Hammad ya ce "Bamu san fa inda zobenka yake ba haryanzu, abin ya dame ni, ina tsoron a farga da babu zoben nan, ina tsoron abin da ka iya biyo baya, idan aka gano babu zoben nan" Ya kalli yatsun nasa ya ce "Abiena, duk abin da Allah ya ƙaddara zai faru dole zai faru ka daina damuwa. Ni yanzu ina mamakin Mamudu bai san ina Agadez ba ne?" Sultan ya ɗan ji dumm, sai kuma ya ce "Ni na hana a sanar da dawowarka, sonake ka samu lafiya sosai, amma dole za a sanar masa da dawowarka" Imam ya ce "Ni zan je na same shi, ya ganni a bazata" Sultan ya ce "A'a zan saka a sanar masa, zai zo har gida ya same ka" Ya ji daɗin kasancewa da mahaifinsa, sai dare sannan suka tafi gida tare da Asal. Duk wunin da suka yi bai ci komai ba, har suka koma gida. Nana ta kammala aikinta na yau, ta yi wanka tana zaune a ɗakinta, tana karatun Alkur'ani. Kawai ta din ga jin kamar akwai wani abu da ba daidai ba. Ta ajiye Alqur'anin ta tashi ta tafi ɗakin girkin Abincin Imam. Wata mata ta gani ta kawo kai za ta fita daga kitchen ɗin, alahalin babu wanda yake shiga sai ita sai Balaraba ko Asal. Nana ta ce "Baiwar Allah lafiya kuwa?" "Saƙo ne aka bayar, ke ce mai girkin Imam, dan haka ke za ki kai masa" Cikin rashin fahimta Nana ta ce "Wace ce ke? Kuma waye waye ya bayar da saƙon, kuma saƙon mene ne?" "Ba ni da lokacin amsa tambayoyinki, babu ruwanki da kuma saƙon na mene ne, ga shi can na ajiye miki a cikin kitchen ɗin, kaiwa ne kawai naki" Nana da mamaki ta bi matar ta kallo dan ba ta taɓa ganinta a gidan ba. Ta shiga kitchen ɗin da sauri, ta fara kalle-kalle tana tsoron kar ta je wani abin cutarwa ne. Wani ɗan kwando ta gani ƙarami, an nannaɗe shi ba za ta iya ganin mene ne a ciki ba. Wata zuciyar ta raya mata, ta kwance ta ga mene ne a ciki, wata kuma ta hana ta,sai dai har ta gama grkin dare tana kallon kwandon tana tunanin mene ne a ciki? Waye zai bayar da saƙo babu suna, kuma me yasa sai ita za ta kai? yanayin saƙon dai kamar babu gaskiya a lamarin. Da fargaba ta haɗa da ɗan kwandon ta nufi sashinsa gabanta yana faɗuwa. Yau shikaɗai ne a zaune, babu Asal. Duk da ruɗewar da yake yi idan ya ganta, amma ya ji daɗin ganin ta kawo masa Abinci, dan tun safe bai sake cin komai ba. Sai dai yau ba iya faɗuwar gaban yake ji ba, har da wata ƙara, mara daɗin ji makamanciyar wadda ya din ga ji daren da zai fara ciwo. Ta ajiye kwanukan ta ce "Barka da yammaci Sayyid, fatan ka na lafiya." "Alhamdillah" ya furta ba tare da ya shirya hakan ba, yana mamakin daga ina wannan sautin yake. Ita kanta Nana ba ta zata zai amsa mata gaisuwar da ta yi masa ba. Ganin babu Asal a gurin, ya sanya Nana zuba masa Abinci da shayi. Ta kalle shi duk da yadda yake yi mata wani irin kwarjini da a baya bata taɓa zaton yana da shi ba ta ce "Ko yanzu ma sai na ɗanɗana?" Ya girgiza kai alamar a'a. Ya sauka daga kan kujerar, yana jin ƙarar nan na ci gaba da addabar kunnuwansa. Cike da son basar da abin da yake ji, dan gujewaa sake faruwar abin da ya faru a wancan karon, ya yi Bismillah ya fara cin abincin. Duk da a takure yake da yadda take kallonsa, kuma ba zai taɓa iya cin abinci a gaban wanda bai kamata ya ci ba, amma ya kasa yi mata magana, kuma bai ji hakan da ya yi a matsayin wani laifi ba a matsayin sa na ɗan gidan mulki ba, wanda hakan yana cikin kamewa da suke da ita, musamman ma shi da hakan ya haɗu da ɗabi'unsa. "Sayyid, ina jin yadda mutanen gidan nan suke yabon ka, sosai da sosai da yabon karamcinka. Duk da a baya ban so zuwa gidan nan aiki ba, amma sai dai na ji babu daɗi da yadda ni ban samu wannan karamcin daga gare ka ba, sai ma ƙyama da ka ke nuna mini, da ƙabilanci ban sani ba ko dan ni ba ƙabilarku ba ce, kuma ba 'yar ƙasarku ba ce ba, shi ya sanya ka ke yi mini haka. Amma ina neman afuwa idan na faɗi wani abu ba daidai ba ko ya ɓata maka rai, bana nufin hakan shugabana" Gaba ɗaya babu tsoro ko fargabar Asal ta fito ta tarar da ita a ranta, daɗi ma ta ji na ko ba komai yau ta keɓe tare da shi. A wannan karon ma, jin maganganun nata ya din ga yi da matuƙar muhimmanci. Yaya zai yi mata bayanin ba tsanarta ya yi ba, baya iya tantance abin da ruhinsa da gangar jikinsa ke nufi a kanta ne. Shirun da ta ga ya yi, da yadda yake jujjuya cokalin ya sanya ta yin ajiyar zuciya, ganin alamun saƙonninta na isa kai tsaye inda take so. Ta nuna masa kwandon da aka bayar aka ce a ba shi, ta tashi ta fita. Kitchen ta koma tana ƙarasa goge-goge, kawai. Sai dai ta ji alamun mutum a bayanta. Ta waiwaya ta gan shi a tsaye a ƙofar kitchen ɗin, idanunsa jawur, ga Giyaz a gefensa, cikin suffarsa ta tsohon nan mara kyan gani. Ya fara takowa cikin kitchen ɗin, yana kusanto ta, gabanta yana faɗuwa ta zuba masa ido. Ya ɗago mata wata takarda ɗauke da hoton ƙwarangwal yana ci da wuta, an rubuta Imam Hammad Jalaludeen a jiki. "Waye ya bayar da wannan saƙon?" Kan Nana ya sara mafarkin da ta taɓa yi, ya fara ƙoƙarin zuwar mata kanta. "Waye na ce waye ya bayar da wannan saƙon?" Ya yi maganar cikin wata irin murya da ba ta taɓa jin sa da ita ba a rayuwar da suka yi!!! Cikin rawar murya ta ce "Nima ban sani ba, saƙo ne kawai aka ba ni aka ce na baka" "Waye? Waye ya bayar da saƙon? Ki gaya mini?" Ta kame jikinta cikin tsoro ta ce "Ban santa ba wata ce?" Launin idonsa ne ya fara canzawa, baƙar ƙwayar idon ta ɗauke, sai farin kawai. "Giyaz" Nana ta furta a hankali. AREWABOOKS. Jikinsa ne ya fara ƙamewa, fitilun kitchen ɗin suka ɗauke gaba ɗaya, ta ce "A wannan karon me ka ke buƙata kuma?" Muryar Giyaz ta din ga ji, yana wata irin dariya. "Ai dama na gaya miki, ki jira dawowata". "Na fi ƙarfinka, a waccan rayuwar da ya yi, da wannan ɗin ma, na fi ƙarfinka har abada". "Kar 'yar ƙaramar ƙwarin gwiwar da wancan yaron ya baki, ya sanya ki yi tunanin za ki iya yi mini wani abu, mu zuba mu gani". Nana ji ta yi abu ya faɗo jikinta mai nauyi, suka faɗi ƙasa tare. Wal hasken fitilar kitchen ɗin ya dawo. Imam ta gani a kwance a gefenta. Da sauri Nana ta nufe shi, jikinta na rawa za ta taɓa shi. Amma ta ganta itakaɗai a ɗakin karatun Ƙaisar, cikin azama ta tashi tana waige-waige, ta ga Ƙaisar a tsaya a bayanta. "Yana ina?" Ta faɗa a sanyaye. "Na san abin da ki ke ji, amma ya yi wuri, kuskure kaɗan za ki aikata ki lalata komai. Kar ki yi mamakin a din ga bibiyarki, saboda zaɓar ki da matar nan ta yi a matsayin mai dafa abincinsa, kuskure kaɗan ki na iya kwana a ciki ki shiga matsala. Kuma Giyaz zai yi ta tunzura ki, har ki yi wani abin da za ki saka kan ki a zargi. Ki din ga bin komai a hankali" Nana ta yi ajiyar zuciya, itakaɗai ta san abin da take ji, a kan Sayyid. Dan a gare ta gara lokacin da ya ɓata ba ganinsa take yi ba, amma yanzu ga ta ga shi, amma ya yi mata nisa. ***** Sagir kuwa ya zama tamkar zararre, aka kwana uku babu Shukura babu labarinta, sai a kwana na uku ya sanar da gidansu Shukura halin da ake ciki. Hajiya Amina ta gigice ta rasa inda za ta tsoma ranta. Hankalinta ya yi mummunan tashi. Alhaji Zailani ya din ga yi wa Sagir bala'i, a kan me tun ɓatan Shukura bai gaya musu ba sai yanzu. Aka ƙara sanar da jami'an tsaro, aka kuma baza komar neman Shukura. **** Ummi ce ta kawowa Baba ziyara, sai dai yanzu Baba duk ya zama abin tausayi, duk inda ya zauna sai da ya ja uban tagumi ya yi shiru, da ya samu dama kuma sai ya hau zancen Nana. Yanzun ma hirar da yake ta yi wa Ummi kenan. "Ummi kin ga Nana haryanzu shiru ko? Babu ita babu ɗan uwanta, shi ma tun wannan zuwan da ya yi bai sake zuwa gidan nan ba. Gara shi namiji ne ita kuwa ban san halin da take ciki ba. Nan gida kuma ita Suwaiba yanzu ba ta da maraba da mahaukaciya, na ce a kaita Asibiti babarta ta ƙi yarda. Ita ma Jamila 'yan kwanakin nan, gaba ɗaya ba na gane kanta, dama kuma babarta ta nuna mini in daina shiga sabgarsu 'yarta ce, saboda abin Duniya" Ummi ta ce "Gaskiya ne Baba, abin duk babu daɗi kam, amma Baba wani abun an bar gini tun ran zane ne, wannan abubuwan tun daga tushe yakamata a ce an yi wani abu na kaucewa farwuarsu, yanzu sai dai a yi ta haƙuri ana gaya wa Allah. Ta dai ɗan ba shi baki sannan ta tashi ta shiga cikin gidan. Suka gaisa da Mama a tsakar gida, suka hau hira. "Wai ina Jamila ne?" Mama ta ce "Tana ɗaki" "Amma tana ji na zo, ta yi burus?" Ta yi maganar tana leƙa ɗakin. Ta tarar da Jamila a kwance ta yi rigingine. "Jamila yau 'yar shariya ce babu magana ma?" Jamila ta yinƙura ta tashi zaune, suka gaisa sama-sama. "Wai ba ki da lafiya ne?" Ta jinjina kai alamar eh. "Jamila kin fiye yawan rashin lafiya, Allah ya kawo mana siriki mu sha biki. Ta ga dai mutanen gidan nasu duk sai a hankali, ta yi musu sallama ta tafi. Hajiya Sa'a tamkar za ta haukace, kwana uku amma sai an yi da gaske take cin abinci kaɗan. Ta rame ta zabge kamar ta shekara tana larura. Ko gaisuwar aka yi mata ba ta iya amsawa, idanunta suka koɗe suka yi jawur. Mutane da dama sun ji mutuwar Abba, saboda mutuwar fuju'a ga matashi, tana taɓa zukata, mussaman Abban da yake mutumin kirki ne, ga girmama mutane. Ranar da Abba ya kwana uku da rasuwa, Safiyya ta samu Hajiya Sa'a a ɗaki, ta ce "Hajiya yanzu mene ne abin yi, wani matakin ki ke ganin za ki ɗauka a kan wannan lamarin?" Hajiya Sa'a ta sunkuyar da kai hawaye na zuba daga idanunta ta ce "Duk matakin da zan ɗauka, kafin mutuwarsa yakamata na ɗauke shi, dana sani nake mara amfani na janyo yarinyar nan jikina, sannan idan na matsa, tsaf za ta tona mana asiri, dan haka ba zan saurare ta a yanzu ba, ina cikin matsanancin kewa da alhinin rashin tilon ɗana. Sai dai wallahi sai ta tafi inda Abba ya tafi, ko da kuwa nima zan rasa raina na" Jiki a sanyaye ta ce "Hajiya ki bi a hankali, kar garin neman gira a rasa idanu" "Ki zuba ido kawai" ta faɗa a taƙaice tana share hawaye. Kiraye-kirayen sallar asuba ne ya sanya Nana farkawa, ta ganta a ɗakinta a kwance, ba ta iya tuna abun da ya faru ba tun daga biyo ta da Sayyid ya yi. Ta kalli ƙwan fitilar ɗakin a kunne, ta yinƙura za ta tashi, kawai ta takardar nan, da ya nuna mata yake tambayarta waye ya aiko da ita. A tsorace ta ja gefe, tana kallon takardar. Jikinta na rawa bakinta ɗauke da addu'a, ta ɗauki takardar ta sake ƙare mata kallo. Ta ninke ta ta saka a cikin kayanta, ta shiga banɗaki. ***** Nana na tsaka da aiki a kitchen, ta ji motsi a kitchen ɗin. Ta waiwaya ta kalli inda take jin motsin, ta ga Asal. Cike da takaicin babu yadda ta iya, ta ce mata "Barka da safiya" "Barka, amm na ce akwai abin da ya faru ne? Imam ya ce lallai a tsananta tsaro a gurin girkin nan, ki gaya mini idan da wani abu da ya faru?" Nana ta girgiza kai ta ce "A'a babu wani abu da ya faru fa" Asal ta ce "Kar na kama ki da aikata rashin gaskiya, hukuncin da zan yi miki sai kin gwammace kiɗa da karatu" Nana ta yi mata shiru, a ranta ta ce "Kya ji da shi" Asal ta juya ta fita, Nana ta raka ta da harara. Mahmudu ne durƙushe a kan gwiwoyinsa, a gaban Abdou matawalle. Ya numfasa ya dube shi ya ce "Imam Hammad ya samu lafiya, ya dawo Nijar" Mahmudu ya ɗago kai a zabure, yana kallon Matawalle. "Ka sani, koma me ka ke yi masa da ka ke mallake shi, mu na sane mun zaba maka ido,mun yi maka talala ne mu ga gudun ruwanka. Tun da ya sako ƙafarsa a ƙasar nan, tun ma yana can, yake zancenka yana cewa kana ina?. To ka tsaya da kyau ka saurare ni, zamu sake ka amma hakan ba ya nufin ka yi 'yanci ne, ko kuma mun daina zarginka, mu na nan mu na saka maka ido a ƙarƙashin takunkumi za mu sake ka. Sannan kar ka kuskura ka gaya wa Imam batun sace shi da ka yi da rayuwar da ya yi a Nigeria. Dan babu yadda ba a yi ya tuna wani abu ba, amma abu ya gagara. Dan haka ba a buƙatar ya san ya yi wata rayuwa a Nigeria, balle maganar nan ta fita, idan kuwa ka bari a ka ji maganar nan a waje, hukuncin da zai biyo baya ba zai yi maka daɗi ba. Wannan saƙo ne daga Sultan, ba a buƙatar ya san ya yi wata rayuwar daban, dole ka ja bakinka ka tsuke. Dan ka san hukuncin kisa shi ya dace da kai, an ɗaga maka ƙafa ne, saboda son da Imam yake yi maka, ba a buƙatar abin da zai taɓa masa zuciya" Mahmudu ya saci kallon Matawalle, yana jin zafin yadda mutumin nan yake ɗora masa sace Imam. Haka nan ya risuna ya yi wa Matwalle godiya. ***** Asal ce zaune a gaban Sultan, yake yi mata magana cikin nutsuwa da dattaku. "Yarinyar kirki, na san za ki yi mamakin sake kiran ki da na yi, duk da jiya kun zo gidan nan, to ina da baƙi ne ban samu mun yi magana ba a jiya, shi ya sanya na ce ki zo yau ina son ganinki" Asal ta jinjina kai, tana saurarensa cikin nutsuwa. "Na san kin ɗauki dogon lokaci mijinki baya kusa da ke, wasu faɗi tashin duk da ke aka yi kin san komai. To ga shi Ubangiji Allah ya yi masa dawowa cikin aminci. Sai dai duk da haka haryanzu bai gama samun lafiya ba. Dan Allah dan Annabi ina roƙon ki, ki zama mai haƙuri da juriya da kuma rufa masa asiri. Kin san yadda yake da magauta ta kowacce kusurwa, dan Allah ina sake roƙon ki, ki zama rufin asiri ga Imam, duk abin da ki ka gani wanda ba ki yadda da shi ba, ki zo ki sanar mini ban yarda ki gaya wa kowa ba. Dan Allah ki yi haƙuri da shi ya samu nutsuwa da kwanciyar hankali daga gare ki" Ta jinjina kai ta ce "In sha Allah Abie, ba zaka same ni da wata matsala ba, zan zama mai rufa wa mijina asiri" "Na gode sosai da sosai, Ubangiji Allah ya yi muku albarka, ya baku zuriya ta gari masu jin ƙai" "Amin Abbie, muna godiya sosai da sosai" Sosai Imam Hammad yake son ya ci gaba da gudanar da al'amuransa da ayyukansa da yake yi, kamar a baya, amma abu ya gagara gaba ɗaya ji yake komai ya fita daga ransa. Jin jikinsa yake yi kamar a ɗaɗɗaure duniyar sam ba ta yi masa daɗi, ga shi takamaima bai san abin da yake damunsa ba. Sultan ne ya aika da mota aka ɗauke shi, bai san ina za a kai shi ba, bai kuma tambaya ba. Gidan da ake sauke baƙin Sultan nan aka kai shi. Sai ya fara mamakin ko wata ganawar zai yi da baƙin, amma Sultan bai gaya masa ba?. Sai dai babu zato babu tsammani ya ga Mahmudu. Cikin matsanancin farin ciki suka nufi juna, Imam ya ce "Mahmudu" Ya rungume shi cikin farin ciki. Sai dai wata irin karaya ta shiga zuciyar Mahmoud. Imam ya ce "Tun da na dawo nake cigiyarka, na ce ko ba ka san na dawo ba, a Faransa ma sai da na roƙi a kawo mini kai, mu zauna tare na yi jinyar, amma ba a bani dama ba" sai dai jin sheshsheƙar kukan Mahmoud ya ɗaga masa hankali, ya ɗago shi cikin damuwa ya ce "Mahmoud, ko na yi maka wani abu ne?" Ya girgiza kai yana share hawayensa ya ce "Ai ba ka yi mini laifi, ko me za ka yi mini a duniya kuwa. Murna ce da kewa ta sanya ni kuka" Jiki a sanyaye ya ce "Dan Allah ka bari, zuciyata ta karaya nima" Sai dai maimakon ya yi shirun, tamkar tunzura shi ya yi, ya sake fashewa da kuka. Hawaye ne ya cika idanun Imam, ya ce "Dan Allah ka gaya mini idan wani abin ne ya faru, duk ka sanya jikina ya yi sanyi, kamar ban taɓa ganin kana kuka ba" Ya share hawayensa ya yi ajiyar zuciya ya ce "Na ce maka murna ce kawai nake da ganinka ya shugabana, ina fatan ka dawo cikin ƙoshin lafiya" Ya yi tsaki ya ce "Za ka fara ko? Waye shugaban naka?" "Kai mana Allah ya baka nasara" Kawai ya yi wata dariya ya ce '"Ka ci gaba, zan rama ne" Mahmudu ya yi dariyar shi ma ya ce "Ba zan iya fasalta adadin yadda na yi kewar ka ba, da farincikin da nake ciki, a sanadin dawowarka ba" Imam ya ce "Na fika murna da ganinka" Duk da yau suka haɗu tun dawowarsa, amma ji yake kamar ya gaya wa Mahmudu abubuwan da yake ji, amma sai ya fasa ya ga kamar ya yi wuri. Shi kuma Mahmudu zuciyarsa cike take da karaya, da kuma tunanin tayaya zai gaya wa Imam Hammad cewa ya yi aure a Nigeria, alhalin ga kashedin da aka yi masa. Ita Nana da suka baro a Nigeria mene ne matsayinta. Ya tuna irin ɗawainiyar da ta din ga yi da shi, da rayuwar da suka yi, amma alamu ya nuna sam Hammad bai san an yi hakan na, dan da ya tuna zai yi masa maganar. A ransa ya yanke dole ya shirya da kansa ya tafi Nigeria neman Nana, kuma ko me za a yi masa idan ya gano ta, dole ya kawo ta ya gabatar da abin da ya faru, ko da hakan yana nufin a yanke masa hukuncin kisa ne, gara ya yi da ya mutu da hakkin Nana a kansa. Ya din ga mamaki da tambayar kansa, yaya aka yi a wannan karon, Imam ya dawo hayyacinsa ya sake mantawa da rayuwarsa da Nana, bakinsa fal tambayoyi amma babu halin furta su, saboda kashedin da aka riga aka yi masa. Tare da Mahmoud suka zauna suka sha hira sai dai abincin da aka shirya musu, Imam ya ƙi ci. "Imam, wai ya na ga ba ka cin abincin ne?" "Abincin da ya fito daga hannu ɗaya ne tal yake yi mini ɗanɗano a bakina yanzu, idan ba shi ba duk wanda na ci salam nake ji" Cikin mamaki ya ce "Abincin wani hannu kenan?" Ya ɗan yi shiru ya ce "Asal ce ta kawo wata mai yin girki daga Nigeria, idan ba ita ta dafa ba, ba na gane kan Abincin" Ƙwarewa Mahmud ya yi, Hammad ya miƙa masa ruwa yana yi masa sannu, ya yi shiru ya ce "Daga Nigeria kuma?" "Eh" "Lallai Imam ka na da rigima, amma duk Nijar sai da aka tsallaka Nigeria aka samo ta?" Ya ɗan ɗage kafaɗa ya ce "Ka san rigimar Asal, wai a gurin cin abincin Maraɗi ta gano ta, ta kawo ta nan. Zan saka ta yi girki ka zo ka ci" Mahmoud ya jinjina kai, daga bisani ya kawar da zancen, yana ci gaba da lissafa yadda za je Nigeria ya taho da Nana, dan ya san tun da Hammad ya dawo, yanzu duk inda za shi su na tare. Da ƙwarin gwiwa yanzu Nana take girki, kasancewar ta sa wanda take yi wa girkin. Bayan da Nana ta kammala girkin rana tana shirin, kai wa sashen Imam, Asal ta same ta ta ce "Ba sai kin kai wa Imam Abinci ba, baya nan sai dare zai dawo, ki shirya masa abincin dare kawai" Nana ta amsa mata da to. Tun da Imam ya dawo, yake kaiwa yana komowa yana jiran ya ga ta ina za a kawo Abinci, saboda yunwar da yake ji. Ga shi dududu ƙarfe goma ya dawo, amma Asal har ta kwanta bacci. Ya yi hamma bai san adadinta ba, saboda yunwar da yake ji. Sallamar Nana ta saka ya kalli hanyar shigowa, wannan karon a kwando ta zubo kayan Abincin. Sai dai yau saɓanin hijjabi, doguwar riga ce a jikinta milk, da mayafin rigar. Tun da ta yi sallama ya amsa a ƙasan maƙoshinsa ya sunkuyar da kansa ƙasa bai kuma magana ba. Ta ƙarasa ta ajiye kwamdon, ta sauke kwanukan, har za ta yi masa zancen saƙon nan da aka bayar, sai ta fasa dan kar ta wargaza shirinta. Da wani na iya ganin halin da zuciyar wani ke ciki, da Imam ya daɗe da jin kunya, saboda bugun zuciyarsa, ga wani irin azalzalarsa da take yi, ya sake kallon Nana, dan ba ya tunanin ya taɓa ganin wanda doguwar riga ta yi kyau kamar baƙar kukunsa 'yar Nigeria. Ta zuzzuba masa abincin, ga kayan marmari ga kuma shayi na musamman. Da ta zuzzuba masa. Ta numfasa ta ce "Ɗazu na yi girkin rana, aka sanar mini da baka nan, na ce duk lokacin da ba zaka kasance a gida ba, ina son a yi mini izini na dafa maka ka fita da shi, ba zan so shugabana ya kasance da yunwa ba, tun da alhakina ne girka maka Abinci" Ta yi maganar cikin girmamawa tana sunkuyar da kai. Jin ya yi shiru ya sanya ta ɗaga kanta, ta ga tuni ya ɗauki shayi ya kai bakinsa yana sha. Kawai ta ɗan juya ƙwayar idonta, tare da yin murmushi. Sai da ya kusa ƙwarewa, saboda tabbas ya san irin wannan kallon, amma a ina? Yana matuƙar son ya yi mata magana, amma ba ya iya wa. Nana ba ta ba shi damar ɗaukar wani mataki ba, ta tashi ta nufi hanyar fita. Tun da ta tashi ya bi ta da ido har ta fice. Abin duniya duk ya dame shi, Nana kuwa ta cika da murna, ganin saƙonninta na isa yadda take so, sai dai tana buƙatar ƙara samun kusanci da shi. Cikin marairaicewa yake kallonta, fuskarsa ɗauke da damuwa ganin yadda take kuka tamkar ranta zai fita, ga shi ta yi duhu ta rame, ba kamar yadda ya santa ba a baya. "Ma vie, ki yi mini afuwa, ba laifina ba ne, ina jin yadda ruhinki yake motsi a cikin jikina, dan Allah kar ki yi fushi da ni ki yi mini uzuri " Ya yi maganar yana ƙoƙarin rungume ta ya rarrashe ta. Ja da baya ta yi tana girgiza masa kai tana kuka ta ce "Ba ka so na Sayyid, ka yada alƙawari ka tafi ka bar ni, ka manta da ni, ka bar ni da dakon ruhinka, da ya hanani sukuni sai da na fito nemanka, ba ka yi mini adalci ba Sayyid" "Ma vie, ban ya da alƙawari ba, gangar jikina ce a Nijar, amma ruhina yana Nigeria dan Allah ma vie" Asal ta yi ƙuri da ido tana kallon yadda ya haɗa gumi a cikin bacci, sai numfarfashi yake yi da kyar yana faɗin "Ma vie, ke rayuwata ce, ban yi miki butulci ba" AYSHERCOOL 1K NE VIA 0069685771 Aisha Adam stanbic bank 08081012143 76 Asal ta zuba masa ido tana kallon ikon Allah. Shiru ta yi jikinta ya yi sanyi tana kallonsa, sai dai ta yi shiru ta ci gaba da kallonsa. A razane ya farka, sai dai ya juya ya ci gaba da  baccinsa. Da safe ya lura da Asal ba ta walwala, ta ƙi sakin jiki da shi ma gaba ɗaya. Har ya share ta sai kuma ya tambaye ta ko lafiya? "Lafiya kalau" ta amsa masa a taƙaice. Ya fita ɗan tattaki, yana jin mafarkin da ya yi a jikinsa, amma ya kasa tuna mafarkin abin da ya yi. Cikin girmamawa ma'aikatan ke ta risunawa su na gaishe shi. Babu yabo babu fallasa ya din ga amsa musu. Zuwa ƙarfe goma Nana ta kammala girki. Sai dai yau ba su haɗu ba kwata-kwata. Har lumshe idanunsa yake yi bayan da ya sha kunun gyaɗar da ta yi, ga lafiyayyen ƙosai mai zafi. Ya karya tsaf ya gama, Asal ta fito daga ɗaki ta cika ta batse. Kallo ɗaya ya yi mata ya maze, ganin ya basar da ita ya sanya ta ƙura masa ido ya kalle ta, yana mamakin dalilin da ya sanya ta ke yi masa wannan kallon. "Imam ina fatan inda ka tafi, ba cin amanata ka yi ba" Kallon rashin fahimta ya yi mata ya ce "Me ki ke nufi?" "Ni kaina ban kai ga tantance abin da nake nufi ba, amma na fara ganin wasu abubuwa me da ban gane musu ba, abin ya tsaro ta ni ne" Ya ce "Yi mini bayani" "Ka na kiran wata da rayuwarka a cikin baccinka" Ya yi mata ƙuri da ido, sannan ya ce "Kin tabattaa?" "Ba ka yarda ba ƙarya nake yi maka kenan?" "A'a ban ce haka ba, amma kin ce bacci nake yi, kin ga mai bacci kuma bai san abin da yake aikatawa ba. Wataƙila shirmen mafarki ne kawai, wataƙila ma ke na gani a cikin baccin nake kira da rayuwata" Sai kuma ta yi murmushi ta ce "Kuma haka ne, wallahi har na ji zuciyata ta yi sanyi, ka yi haƙuri da abin da na yi " Ya yi murmushi yana kashingiɗa ya ce "Ban haƙura ba tukuna" Ta ce "Ai ba zan sake ba, ina kishinka ne sosai. Da ina da hali ko fita sai ka daina yi. Ina sane da duk masu ƙoƙarin yi maka kyautar 'ya'aynsu su na so ka aura. Imam kai nawa ne nikaɗai Imam Hammad, babu wata mace da za ta iya samun kafar da za ta shiga zuciyarka. Inda na gode wa Allah, ka yi daban Imam, ba ka da rawar kai, da kule-kulen nan, da ko a cikin barorin nan, da suke rawar ƙafa ka yi saɗaka da su, sai ka saurare su. Shi yasa nake ƙara ƙoƙarin na kare gidana ina fatan ba ka ga laifina ba" Ya sanya hannunsa yana shafa gashin kanta, ya ƙanƙance idanunsa yana kallonta, daga bisani ya saki murmushi ya ce "Gimbiya Asal, sarauniyar mata masu kishi ta duk faɗin Agadez" Ta zumɓura baki ta ce "Ta duk Duniya dai, ni in dai a kan ka ne. Da ina da yadda zan yi ma sai ka daina kallon kowace mace, sai maza kawai" Ta yi maganar har cikin zuciyarta. Kawai ya kama dariya, dan shi gaba ɗaya dariya ma ta ba shi. "Ya ka ke dariya kuma?" Hammad ya ce "To ya ba zan yi dariya ba, ina ji ina gani an bani kyautar mata na mayar da hannun kyauta" Fuskarta ɗauke da damuwa ta ce "Dama ka na so kenan?" "To waye ba ya son mace? Ina so mana. Amma tawa kawai" "So ka ke sai ka saka ni kuka" Ta yi maganar idanunta na cika da hawaye. Lumshe idanunsa ya yi yana buɗewa, yana kallonta. "Ga abinci ki karya" Ta noƙe kafaɗa. Nana ce ta yi sallama, Asal ta kalli inda ta shigo, ta tsuke fuska haka kurum yau ta ji haushin Nana ya ninku a zuciyarta. Nana ta yi saurin sunkuyar da kanta, dan Asal a zaune take a kan cinyar Sayyid. "Zan kwashe kwanuka" ta yi maganar muryarta har harɗewa take yi, saboda abin da ya taso mata. "To ni dai yanzu ka kira ni da rayuwarka a zahiri, tun da ka ce ni ka ke kira a mafarki" Ta yi maganar kamar ba ta san Nana ta shigo ba. Ras gaban Nana ya faɗi, ya lumshe idanunsa yana murmushi ya ƙi magana. Kawai Nana ta fusata ta tattare kwanukan za ta yi waje. "Malama ki ajiye ban karya ba, ki fita kya dawo ki kwashe" Ko waiwayowa Nana ba ta yi ba, wata irin zabura ta yi cikin matsanancin fushi, amma ya riƙe ta ya ce "Cherie na sha gaya miki, irin wannan halayen naki ga na ƙasa da ke, babu abin da za su janyo miki sai tsana da raini. Ita kuma rayuwa a na son ko kana guzurin maƙiyi ka yi na masoyi" "Amma Amour kana kallon abin da ta yi mini, ko sau ɗaya sai na sanya a ladabtar da yarinyar nan ta san matsayina a gidan nan" Ya ce "A'a, ke ce baki kyauta ba abin da ki ka yi. Ita ba ta tashi cikin jerin hadimanki ba, kawai dai kin ɗaukko ta ta yi miki aiki ne, dan haka sai kin din ga yi mata uzuri" "Wane uzuri ne ba na yi mata, abin da ta yi mini wulaƙanci ne tana sane, ban da yadda take kula da abincinka na aminta da ita a kan hakan, da sai na hora ta sannan na kore ta ta bar gidan nan" "Shikenan ki yi yadda ki ke so, tun da ba zan faɗa ki ji ba" Ya yi maganar yana ture ta daga jikinsa. "Imam fushi ka yi da ni a kan wannan mummunar yarinyar?" "Ba a kanta na yi fushi ba, yadda ba kya jin magana ne ya ɓata mini rai, idan ki ka ci gaba da sanya wa ma'aikatanki ƙiyayyarki, babu abin da ba za a iya haɗa kai da su a yi miki ba. Idan na isa a bar maganar nan. Ba na son yadda ki ke tafiyar da ma'aikatanki wasu lokutan, ba na son yawan shiga maganar ne, amma raina ki za su yi" Asal ta yi shiru ta tsuke fuska, ta sauka daga kan cinyarsa baki ɗaya. **** Alhaji Fatuhu ma duk da yadda yake fama da kansa, sai da ya je gurin jana'izar Abba, kuma da shi aka yi zaman makoki. Ya ji mutuwar nan sosai da sosai, saboda Abba mutuminsa ne. Ko da yake jinya a sati ya kan je sau biyu ko uku duba shi. Ya kan zauna su yi hira sosai mussaman idan ya tarar jikin nasa da sauƙi. Kusan kullum Hajiya Sa'a gani take mafarki take yi, idan aka wayi gari za ta ga Abba bai mutu ba, amma ta ga babu alamun hakan. Ba ta ƙara kiɗimewa ba sai ma da aka yi kwana bakwai da mutuwar, kowa ya watse ya bar gidan. Ɗakin Abba ta tafi da daddare, ta buɗe ɗakin tana rintse idanunta tana jin tamkar za ta gan shi ya ɗago, da wannan murmushin nasa irin na fuskar mahifinsa. Amma ta ga ɗakin nasa wayam, babu komai. Wasu irin zafafan hawaye suka shiga sintiri a kan kumatunta, ba ta taɓa dana sanin shiga ƙungiyar asiri da duk wasu miyagun laifuka da take aikatawa ba, sai da ta rasa tilon ɗan da Allah ya ba ta a rayuwa. Wanda babu irin ƙoƙarin da ba ta yi, domin ganin ta kare shi da sadaukarwar ƙungiya. Ashe bonono ta yi rufe da ɓarawo bayan janyo Jamila cikin harkar ƙungiya, wanda ta yi hakan ne, domin janyo Jamila kusa da ita yadda za ta samu mallakar jinin Nana. Ta zauna a gaban ƙatuwar katifarsa, ta din ga wani irin kuka mai sauti, da sai da ƙirjinta ya fara yi mata zafi. ***** Asal ce zaune a kan carfet, saman kujerar da take kai kuma wani babban mutum ne, cikin shigar buzaye, kansa ɗauke da rawani. "Ki na ji na da kyau ko?" Ta jinjina kai cikin nutsuwa, ko ƙwaƙƙwaran motsi ba ta yi. "Ina fatan haryanzu ba ki manta dalilin da ya sanya ki ka auri Hammad ba" Ta amsa da "Eh ban manta ba" "To barka, yanzu ya dawo, kuma babu abin da zai canza, za ki ci gaba da gudanar da aiki, kamar yadda yake a baya. Ba na buƙatar kuskure ko kuma wani uzuri. Duk wani motsinsa da duk abin da yakamata mu sani mai muhimmanci ki sanar da ni, idan kuma ki ka bari ni na gano ba ki sanar da ni ba, ranki zai yi mummunan ɓaci" Jiki a sanyaye ta jinjina kai. "Dole a ci gaba da aiki tuƙuru, domin nesanta shi da kujerar Sultan, da mahaifinsa ke ta ƙoƙarin kusantar da shi da ita, mu na buƙatar kujerar nan ko ta halin ƙaƙa, dan haka ina nan ina saka miki ido da kuma sauraren ki" Asal ta sake jinjina kai, jikinta babu ƙwari ta tashi ta fice. Da ƙyar take ɗaga ƙafafuwanta, damuwa duk ta cika mata kai, ta ma rasa wane tunanin yakamata ta yi. Da ta koma gida, ta tarar da hadimai na gyara ɓangaren Imam, ga ƙamshin turaren sa, da alama bai daɗe da fita ba. Cikin tsawa ta kore su gaba ɗaya, ta ce su ajiye aikin su fita daga sashen, sannan su kira mata Nana. Jiki na rawa suka ajiye suka fita. Nana tana tsaka da karatun Alkur'ani saƙon Asal ya iske ta, sai ta hau tunanin kiran me take yi mata. Duk da ta san abin da ta yi mata da safe. Nana ta tashi cike da ƙwarin gwiwa, dan ji take yi daidai take da Asal, tun da duk abu dai ba za ta raba ta da ranta ba. Nana ta shiga fuskarta a haɗe ita ma, ta shiga ɗakin ta tsaya, tana ta huci tana son ta balbale Nana da faɗa, sai kuma ta kasa ganin yadda Nanan ta tsuke fuska ita ma, ta yi mata wani irin kwarjini. Amma duk da haka ta maze cikin dakiya da ƙarfin hali ta ce "Amm tambaya nake son yi miki, ban sani ba ko nice a ƙarƙashinki, da zan din ga yi miki magana kina ji na ki yi mini banza" Nana ta ɗaga kai tana kallonta. "Ko ba ki gane me nake nufi ba ne? Abin da ki ka aikata da safe" Nana ta ce "Na gane, gani na yi bai kamata na tsaya ina kallon ku a yanayin da ku ke ba, ko na din ga sauraren maganganunku ba. Hakan zai zama kamar munafunci ne, shi ya sanya na tafi, amma ki yi haƙuri" Asal ta watsa mata wani banzan kallo cike da tsana ta yi ƙwafa sannan ta ce "Daga yanzu aikinki ba iya girkin Imam ba ne ba, har da gyaran sashen sa, ba na buƙatar kowa ya din ga raɓar inda yake." "Amma ɗaukko ni ki ka yi na din ga girki kawai, ya za ki haɗa mini da aikin shara da goge-goge. Kuma masu yin aikin su uku ne, ni kuma nikaɗai ce, aikin bai yi mini yawa ba kuwa?" "Kin san a kan kuɗi nawa na biya na ɗaukko ki? Ko a Nigeria ba na tunanin ko za a sayar da kaf danginku, za ku iya biyan kuɗin da na biya na karɓo ki ba. Dan haka ina da hurumin sanya ki duk abin da na ga dama" "To Gimbiya Asal, babu damuwa zan yi abin da ki ke so. Duk da dangina ba za su iya biyan kuɗin da ki ka biya ba. Amma na san wataƙila mijina zai iya biya ya fanshe ni" Nana ta yi maganar tana murmushin da Asal ba ta gama gane kansa ba. Nana ce ta ƙarasa aikin gyaran falon nan, ta yi goge-goge. Haƙurƙurtar da kanta ta din ga yi, da ta tuna mijinta take yi wa wannan aikin. Duk da ayyukan sun yi mata yawa. Ita dai fatanta Ubangiji Allah ya sanya Sayyid ya tuna ta domin ta san matsayinta. Tana kammalawa ta koma kitchen, ta ɗora girkin rana. Ta kammala ta kai ajiye. Ta ƙara goge ɗakin saboda ta san halin Asal sai ta tafi za ta huta, za ta sanya a kirawo ta, ta hau yi mata kinibibi da sanabe kala-kala. Ta gama aikin goge-gogen kenan, ta gano wani photo album. Ta ɗauka ta nutsu tana dubawa, duk rubutun French ne a jiki. Shafin Farko hoton Sultan ne, wanda ba dan yanayin shekaru da fuskarsa ta nuna ba, sai ka ce Imam Hammad ne, wanda tsananin kamannin har Muhsin da ta baro a gurin Nene. Ta buɗe ɗaya shafin ta ga hoton wani, shi ma fari tas mai kama da su Sayyid sai dai shi ma babba ne. Kowanne a ƙasa da sunan sarautarsa. Sai kuma ta shiga wani shafi mai ɗauke da hoton Sayyid a ƙasa an rubuta Imam Hammad Jalal Agadez. Wani murmushi ya suɓuce mata ta ce "Ka fi kowa kyau a cikin album ɗin nan Shugabana." Ta furta cikin murmushi. Hotunan wannan matasan da suka yi wa girki a gidan Sultan su ma kowanne da sunansa a ƙasa. Amma a farkon sunan kowanne da Imam. Nana ta din ga mamakin to kowa ma Imam ne kenan?. Muryar Asal ta jiyo sun nufo cikin falon, ta hanyar da take kyautata zaton a nan turakar Imam take, kuma tana tunanin ɗaya hanyar sashen Asal za ta mayar da kai, kai tsaye. "Imam, wai ina zobenka ne?" Ta yi maganar tana ɗago hannunsa, Nana kuma tana hango su daga inda take zaune. "Ya karye yana gurin gyara" "Gurin gyara kuma Imam? Ya za a yi dakakkiyar azurfa kamar wannan a ce ta karye? Ka san fa muhimmancin da zoben nan yake da shi a gurinka, ya za a yi ya karye?" Daidai lokacin suka ƙaraso tsakiyar falon, ya ce "Zobe ya ɓata ban san inda yake ba, ina fatan kin gamsu yanzu. Kar ki sake yi mini maganarsa. Yanzu zan fita, kar ki manta da saƙona" Sai a lokacin suka ga Nana da ke zaune a cikin falon. "Me ki ke yi a nan?" Asal ta tambaye ta. "Babu komai, gyra ɗakin na yi" "Kuma sai ki nemi guri ki zauna sai ka ce ɗakinki? Imam yana da baƙi anjima, za ki sake dafa wani abin, kuma za su sha shayi, ba na son wauta ko makamancin haka" Nana ta jinjina kai ta kalle shi ta ce "Barka da yammaci Sayyid, in sha Allah zan yi" Asal ta ɗan yi shiru tana nazari jin ta kira shi Sayyid ba Imam ba. A ɗan corridor ɗin ta tsaya tana zancen zuci, jin ana maganar zobe. Wane zoben kenan? Ko dai zoben da ya ɗauka ya ba ta ne? A'a ba ta tunanin haka wataƙila dai wani abin ne daban. Gyaran murya da ya yi da ƙamshin turaren da ya cika gurin ne ya sanya ta farga ta waiwaya, sai ta ga a kan hanya ta tsaya. Ta yi taku biyu ta ba shi guri, ya saci kallonta, zuciyarsa ta din ga raya masa son sanin wace ce ita, sanin na sosai ya yi mata tambayoyi game da wasu abubuwa. Ya haɗiye yawu ya zo zai gifta ta, wani irin daddaɗan sanyi ya ratsa shi, sanyin da zai yi fatan dauwwama a cikin sa, saboda yadda ya saba da zafin jikinsa, wanda duk sanyin da yake guri, a cikin jikinsa yake jin wannan zafin. Sai dai wannan sanyin da ya ratsa shi, har cikin ƙashinsa ya ji sanyin. Ya sake waiwayawa ya kalli Nana, amma ya ga shi take kallo. Ji yake tamkar ya koma da baya ya ƙara samun kusanci da ita, sai ya fi jin sanyin sosai da sosai. Tun da Allah ya jarrabe shi da ciwon nan, bai taɓa jin sanyi mai daɗin wannan ya ratsa shi ba, kuma ya yi imani da Allah daga jikinta wannan sanyin yake, saboda sun samu kusanci sosai da sosai da zai gifta ta. "Allah ya sa ba wani abin ake kuma shirya mini ko wani tarkon ake shirin yi mini da ke ba" Ya yi maganar a zuciyarsa. Nana ta yi mamakin dalilin da ya sanya shi tsayawa haka. Zuciyarsa ta din ga raya masa ya koma da baya, daf da Nana, ko zai fi kin sanyin yadda yake so. AREWABOOKS Nana ta ce "Sayyid ko wani abu ka ke buƙata ne?" Sai da ta yi maganar sannan ya farga, bai ce mata komai ba kawai ya fice ya bar gurin. **** Shukura ce a zaune ta takure jikinta, tana kallon kwanon abincin da aka kawo mata, Abinci mai rai da lafiya sai dai ko sha'awar kai wa bakinta ba ta yi ba, duk da uwar yunwar da take ji, tamkar ta ci babu. Shiru ta yi tana tuna yadda bayan fitowarta daga Asibiti suka yi karo da wani mai adaidaita sahu. Ya fito yana jarabar sai ta biya shi, duk da shi ne da laifi, amma ta kasa fitowa daga motar, ta sauke gilas ta ce ya gaya mata dammage ɗin nawa ta yi masa ta biya shi. Daga sauke glass ɗin nan ba ta sake sanin inda kanta yake ba, sai farkawa da ta yi ta ganta a wannan ɗakin, da sai dai a zuro mata abinci kawai. Ba ta iya banbance adadin lokacin da ta kwashe a gurin ba, sai dai ta kintaci lokacin salla ta yi. Babu tsammani ta ji an buɗe ƙofar ɗakin, hakan ya sanya ta kalli ƙofar da sauri. Sai dai hasken fitilar mai wayarya haske mata ido, ba ta iya gane waye ba. Sannu a hankali ya jingine wayar hannunsa ya zura mata ido. Duk da ta ɗan razana amma abin bai wani ba ta mamaki sosai ba. Ya zuba mata ido sannan ya ce "Kin yi mamaki ko?" Ta girgiza kai ta ce "Ba sosai ba" "Ko me yasa?" "Saboda jikina ya daɗe da bani hakan" "Ta yaya kenan?" "Na daɗe ina zarginka ne, sai dai ana ta dankwafe ni, an hanani" "Gaskiya ne, ban so ki zurfafa ki takura da son sanin abin da bai kamata ki yi ta bibiya sai kin gano ba, amma ban san me ki ka gani ki ka dage kina bin diddigina ba" "Zarginka nake yi da kai da doctor Sharif na kasa yadda ɗa na mutuwa ya yi, saboda har yau ina ji a jikina, mafarkin da na yi gaskiya ne" Alhaji Zailani ya ce "Haka ne, lokuta da dama mafarki ishara ne, duk da ban san abin da ki ka gani ba, amma zarginki gaskiya ne duk da na yi iya yi na a kan na ɓoye komai, sai dai kashi kin zaƙe Shukura, soyayyar da nake yi miki ba za ta hana ni ɗaukar matakin da ya dace a kan ki ba" Shukura ta yi ajiyar zuciya ta ce "Da gaske ka na da masaniya a kan batun mahaifar Mami?" "Ina da ita, haka zalika ina da masaniya a kan jaririnki ma da ki ke ta zargina da Sharif a kai, duk da ban san me ki ka gani a mafarkin ba" Shukura ta yi masa wani irin kallo, zuciyarta na bugawa da sauri da sauri. "Tabbas mafarkinki ishara ne. Amma kafin na yi miki wannan bayanin ina son ki sani, talauci bala'i ne Shukura, babu yadda ban yi a kan na yi yaƙi da shi ba, amma abu ya gagara. Na faɗi na tashi na yi iya yi na amma na kasa nasara a rayuwata. Burina ya gaza cika na mallakar manyan motoci da gidaje da tara manyan kuɗaɗe yadda zan yi nesa da talauci. 'yar makarantar da nake taƙama da ita, abubuwa suka nemi ƙwace mini, bayan faɗuwa a jarrabbawa. A taƙaice dai a makaranta na samu ƙungiyar asiri na shiga, cike da burin na gama makaranta cikin sa'a da fatan cikar burikana na yin arziki mai yawan gaske ta hanya mai matuƙar sauƙi. Bayan na auri mahaifiyarku, ta haifi Sadik, ƙungiya ta fara neman jini a gurina. Na bayar da babban ɗa na Sadik, na kaɗu na shiga tashin hankali, sai dai hakan ne zai ba ni damar taka babban matsayi a ƙungiyar, duk da na bayar da waɗanda ba jinina ba a ƙungiyar amma na ji zafin bayar da Sadik. Aka haifi Yusuf, aka haife ki, ba a sake neman kowa ba, sai da wata buƙata ta sake taso mini, wadda biyan buƙatar na buƙatar na ƙara taka wani matsayi a ƙungiyar. Haka na bayar da matata ta fari, Hafsat da tsohon ciki, na saka mata ƙyallen jini a ƙasan shimfiɗarta ta tashi da ciwon naƙuda ta mutu a gurin haihuwa. Hakan ya sanya dukiyata ƙara haɓaka, na yi kuɗi na yi suna. Duk fafutukar kasuwanci da muke yi tare da Fatuhu, shikaɗai yake abin sa, ni fakewa kawai nake yi da kasuwanci amma ta ƙungiyar asiri nake samun kuɗina. Duk da ina samu ta kasuwancin ma, amma ga mamakina Fatuhu da baya ƙungiyar asiri, ya fi ni samun kuɗi, kuma duk inda muka je an fi son sa. Bayan na auri Amina, aka buƙaci duk wani ɗa da za ta haifa, zan din ga ba wa dodon ƙungiya. Lamarin ya yi mini nauyi, saboda ina jin ɗacin rabuwa da iyalina. Na nemi sassauci, sai aka dasa wa Amina wani jaririn aljani a cikin mahaifarta, duk cikin da ta samu ba ma ta sani yake cinyewa. Sai dai kawai ta wayi gari tana zubar da jini, babu ƙaƙƙautawa. Karo shida na shidan saura ƙiris ta rasa ranta, saboda jini take zubarwa ba kaɗan ba, sai dai a yi ta saka mata jini. Ba a taɓa gane ɓari take yi ba, an zata larura ce kawai,  Asibiti aka kasa gane abin da yake damunta, na kuma hana a yi mata na hausa, tana zaune lafiya kawai sai ta hau zubar da jini babu ƙaƙƙautawa. Ta damu ta damu da matsalar rashin haihuwa, amma na hana ta zuwa Asibiti ta ci gaba da bibiyar lafiyarta. Ni kaina na damu da wahalar da take sha, sai aka nemi na sadaukar da mahaifarta gaba ɗaya ga wannan jaririn aljani, yadda ba sai ta ci gaba da samun ciki ba, cinyewar da yake tana azabtar da ita ba. Haka na amince, cikin dare ta farka tana ihu da buge-bige, ina kunna fitila na haska, na ganmu a cikin jini male-male. Na rirriƙe ta, amma ta fita daga hayyacinta, ihu kawai take tana riƙe mararta, a dole  na ɗauke ta muka yi Asibiti, ganin za ta rasa ranta saboda zubar jinin nan. Ta fi kwana uku ba ta hayyacinta, jini kawai ake saka mata. Aka tura mu scanic, domin a gano musababbin zubar jinin. Na takurawa mai scanic ɗin ya gaya mini me ya gani. Ya sanar da ni babu mahaifa ma a jikinta gaba ɗaya, dan haka bai ma gano daga inda bleeding ɗin yake ba a scanic ɗin, sai dai a ci gaba da bincike. Abin ya bani mamaki, duk da a cikin ƙungiyar asiri nake, ban taɓa tunanin za a ga abin a zahiri a yi scan a ga babu mahaifa ba. Na biya mai scannnic kuɗi, ya rubuta sakamakon da ba daidai ba. Muka koma gurin likita, aka din ga bincike ba a gane komai ba. Ita kuwa sai da ta shafe kwana goma ba ta tantance wanda yake kanta, har an fitar da rai da ita sai kuma ta warke. Na daɗe ina tunanin abin da na yi mata saboda son da nake yi mata. Muka tattauna da malamina, da mamakin yadda a scanic ɗin aka gane bata da mahaifa ma zata a zahiri bs a za a gane ba. Sai ya ce mini idan na ce haka na ƙaryata kungiyar asiri gaskiya ce kenan, amma ya aka yi na yadda da kuɗin da nake samu a cikinta, har nake kashe su a zahiri? Ya ce mini dole na san duk yadda zan yi na ci gaba da rufe mata ba ta da mahaifa, dan kar ta ce za ta bi diddigi duk da ko ta bi diddigin babu abin da za ta iya ganowa. Wannan aljani haryanzu yana rayuwa a cikin Amina, gurbin da mahaifarta take, kan addabe ta da ciwo wasu lokutan, sannan wannan aljani shi ne yake saka ta zubar da jini lokaci zuwa lokaci da take tunanin Al'ada take yi. Wasu lokutan ta zubar da jini fiye da kima wanda take tunanin duk su ne dalilin rashin haihuwarta." Cikin matuƙar tsoro da matsanancin mamakin yadda ya zauna ya wassafa mata wannan mummunan labarin da tun da ta buɗe ido a duniya ba ta taɓa jin labari mai razanarwa da tashin hankali ba. Cikin matuƙar tsoro da matsanancin mamakin yadda ya zauna ya wassafa mata wannan mummunan labarin da tun da ta buɗe ido a duniya ba ta taɓa jin labari mai razanarwa da tashin hankali ba. Da ƙyar ta harhaɗo kalmomin da ta ce "Kai ka kashe Mummy, kuma ka bayar da mahaifar Mami? Da..da.dama aljani duk zai iya yin irin wannan abin?" Yayi dariya ya ce "Ki na mamaki ne? Kodayake mutane duk abin da ba a kanmu ya faru ba, bamu fiye yarda ba, nima da fari kasa yarda na yi, abin ya ɗaure mini kai. Sai dai idan ki ka duba, ba a taɓa yi wa Amina aiki ba, kuma babu alamar tabo na tiyata a jikinta, dan haka ta yaya za ta rasa mahaifarta? Aljani muddin za ka yi masa biyayya, ka yi abin da yake so, to zai zama mai biya maka dukkanin buƙatunka. Da su ake sihiri, da su ake jifa, neman shugabanci, ɗaukaka kungiyoyin asiri da makamantansu. Duk wani siddabaru da za a ce miki sun yi ba abin mamaki ba ne ba" Ya yi maganar yana wata 'yar guntuwar dariya. Shukura ta ƙara rikicewa ta kiɗime. Ta ce "Yanzu Daddy, duk son da mahaifiyarmu ta yi maka kai ka kashe ta? Ga amanarmu da Mami ta riƙe ta kula da mu, ashe dama rashin haihuwarta da ciwon nan na zubar da jini da take yi babu gaira babu dalili, kai ne sila? Kai ka haddassa mata? Yanzu tayaya zaka nemi yafiyar su? Ka rasa imaninka saboda abin Duniya? Kai fa ka kashe su" Ya ce "No in ji wa? Ai ban rasa imanina ba, ai annabi ya ce duk wanda ya ce La'ila ha illalahu zai shiga aljanna" Cikin kuka ta ce "La'ila ha illalahu ba ta fatar baki ba Daddy, tayaya za ka shiga aljanna bayan ka kai buƙatarka gurin wanin Allah da ya buƙaci ka saɓa wa mahaliccinka dan ya biya maka buƙata. Me yasa ka ga buƙatar ka ta yi girman da ta gagari Ubangijinka ka dangana ga waninsa" "Wannan wa'azin naki kin riga kin makara Shukura. Ina da yaƙinin zan tuba kan na mutu, kuma Allah zai yafe mini" "Wa ya baka garantin ganin nan da awa ɗaya ma?" Ta yi maganar tana kuka mai tsuma zuciya. "Ina da shi, dan ko ciwon kai sai na shekara ban yi ba" Ya miƙe tsaye yana faɗin "Ki mayar da hankali ki din ga cin abinci, saboda ke da abin cikinki nake sanya ran ku zama sadsukarwar ƙarshe da zan yi a ƙungiya. Sai dai kafin nan, ina roƙon afuwarki ko ba komai ke ma kin ci albarkacin dukiyata. Ɗanki da ki ka rasa ni na yi amfani da shi" Daga nan ya ɗauki wayarsa ya yi gaba abin sa hankalinsa a kwance, kamar bai aikata komai ba. Wani irin gunji Shukura ta din ga yi tana kuka mai tsuma zuciya, ta din ga fatan ina ma mafarki ne ba gaske ba. Tabbas wannan babbar jarrabawa ce, a ce mutum irin mahaifinta shi ne mahaifinka, gara a ce an haife ka ba ta hanyar aure ba, ko makamancin haka. Amma uba irin Alhaji Zailani ba shi da wani amfani. Duk wata gwagwarmayar sa da faɗi tashinsa a kan iyalinsa ya zama na banza, a dalilin wannan mummunar hanyar mara ɓullewa. Abubuwan da ya gaya mata sun shallake tunaninta, yanzu yadda ya tafi haka zai je ya ci gaba da rayuwa da Hajiya Amina duk da zaluncin da ya yi mata. Ta ji dama ta ba wa Sagir damar kai ta Asibiti wataƙila da ba a samu damar sace ta ba. Cikin kuka take roƙon Ubangiji Allah ya tona wa mahaifinta asiri, saboda a yadda zuciyarsa ta ƙeƙashe ɗin nan, babu wani abu na rashin imani da zalunci da ba zai iya aikatawa ba. Can gida Sagir ko abinci ba ya iya ci. Yusra kuwa abin ka da ba cikakkiyar lafiya ce da ita ba, sai ta kwanta rashin lafiya, saboda yadda ta addabi kanta da ɗorawa kanta alhakin ɓatan Shukura, dan cewa take saboda ta dawo gidan Sagir Shukura ta tafi. Haka Hajiya Amina ma, Addu'a kawai take yi a kan Ubangiji Allah ya bayyana Shukura a duk inda take. Sosai take jin tamkar 'yar cikinta ce ta ɓata, tun tana daurewa har ta kasa ta fara zubar da hawaye, kasancewar babu wani labari mai daɗin ji da zai nuna an kusa gano inda Shukura take. **** Asal ta na tsaye a banɗakin cikin ɗakinta, bayan tabattar da Imam baya ɗakin, ta danna wata lamba ta kira. Can aka ɗauka mutumin ya ce "Na'am ina jin ki" "Ina da labari ne" "Ina sauraren ki" Ta numfasa ta ce "Hannun Imam babu zobensa na tambari, na tambaye shi ya ce mini karyewa ya yi ya kai gyara, daga bisani kuma ya ce mini bai san inda yake ba" "Kin tabattar da hakan, ba kuma ɓoye shi ya yi a wani gurin ba?" Asal ta ce "Eh na tabattar ai zobe ne da ba ya cire shi, tun da ya dawo babu zoben a tare da shi" Mutumin ya numfasa ya ce "Madalla, ki ci gaba da sanya ido da sanar da ni duk wani abu da yakamata na sani" Ta jinjina kai tamkar yana ganinta ta kashe wayar ta fita. Jikin Nana tamkar an yi mata duka, saboda azabar gajiya da ta yi. Ta kammala aikinta tana ta gyaran kitchen, sai ga Balaraba ta shigo da ƙatuwar jarka. Ta ajiye ta ta ce "Gashi nan madarar raƙumi ce da Imam yake sha" "To sannu da ƙoƙari Mama Balaraba" Ta ce "Yauwwa kukun Imam, Allah ya taimake ki" Nana ta yi murmushi ta ce "Kar ki ba ni kunya mana" "Ba kunya zan ba ki ba, ai ke yanzu duk wata kuku a gidan nan a ƙarƙashinki take, ke kaɗai ki ke dafa abincin da zai ci, dole mu girmama ki saboda kema shugabarmu ce" "A'a ni ba shugabarku ba ce ba, ni da nake bare ma a cikinku. Amma dan Allah Mama Balaraba wai su wa ake cewa Imam ɗin nan ne? Dan na ga wanda ake kira da hakan da yawa" "Eh su Biyar ne, galibinsu jikoki ne na gidan sarauta, su na cikin jerin waɗanda za su iya gadon kujerar Sultan. Shi Imam Hammad a gidansu su biyu ne  da shi da Imam Abdallah, sai Imam Zahradeen shi ma jikan marigayi Sultan ne, akwai Imam Asadullah yayan Asal, sai Imam Omar, waɗannan su ne jerin waɗanda ake sanya ran za su gaji kujerar Sultan. Duk da su na ganin cewa Sultan na yanzu nuna son kai ƙarara na son Imam Hammad ya gaje shi a cikin yaransa. Imam Hammad yana da 'yan uwa da suke uba ɗaya amma su biyu ne suka cika ƙa'idojin zama Imam. A ƙasar nan ana girmama duk wani Imam fiye da zatonki, mu na ƙasa mu na son Imam Hammad sosai mussaman baƙaƙen buzaye da fararen ke  yi mana kallon kamar ba 'yan uwansu ne mu ba, bayinsu ne kawai. Idan kin lura galibi hadiman gidan nan baƙaƙen buzaye ne, fararen kaɗan ne ƙarara yake ƙoƙarin yaƙi da kyamar da fararen buzaye suke yi mana, yana ta fafutukar nema mana 'yanci, da ƙoƙarin mu ma a din ga bamu dama a cikin shugabanci, bai kamata iyayenmu sun ƙare a bauta mu ma mu ƙare a haka ba. Amma manyan nan ba sa son shi sam, gani suke yana ƙoƙarin hana su rawar gaban hantsi. Ni tun da ya dawo ma duk ya canza mutum ne mai sanyin hali, amma kaifi ɗaya ne, ba sani babu sabo. Shi ne shugaban majalisar duk Imam ɗin ƙasar nan. Duk da a cikin su akwai wanda suka girme masa, amma a haka dole su girmama shi kamar yadda yake a dokar ƙasar nan. Tarihin masarautar Agadez yana da yawa da kuma faɗi Nana, bari na tafi na je na ci gaba da aikina. Nana ta jinjina kai ta ce "To shikenan na gode sosai da sosai" Bayan fitar Balaraba Nana ta naɗe hannunta a ƙirjinta, tana nazari da tunani. Jiki a sanyaye ta koma ɗakinta, ta duba kayanta ta lalubo takardar nan da aka kawo saƙon aka ce a ba wa Sayyid. Ta ƙare wa takardar kallo. "Ko a cikin Imams ɗin nan ne wani ya aiko da wannan takardar?" Ta yi maganar tana tuna maganganun da ta ji suna yi ranar da aka kai su yin girki a gidan Sultan. Ta koma ta lalubo zoben gurin Sayyid ta din ga jujjuya zoben ta ce "Ko kai a ke nema ne? Idan kai ne ta yaya zan ba shi abin sa, tun da ban san iya adadin muhimmancin sa a gare ka ba, idan na baka ka manta ni ta yaya zan yi bayani a yarda da ni?" Ta din ga surutai ita kaɗai ta gaji ta nannaɗe kayan ta buɗe jakar sarkin baka ta watsa takardar da zoben ta rufe ta ajiye a cikin kayanta. Bayan sallar magariba aka sanar mata baƙin Imam sun iso, su na can sashin karɓar baƙin sa wanda ɗaki ne a can wajen lambun gidan. A kwanduna ta shirya kulolin Abincin, ɗaya daga ma'aikatan gidan, ta taya ta kai wa. Su na zazzaune a ɗakin, gaban su shaƙe da kayan marmari da uban soyayyen nama. Duk wannan Imam Imam ɗin ne, gaba ɗaya zaune a gurin. Ayabar hannun Sayyid ta kalla, da ya kai bakinsa ya gutsura fuskarsa ɗauke da murmushi. A take ta ga jini yana bin bakinsa, ayabar ta koma baƙa ƙirin, wasu abubuwa masu tsini tamkar ƙayoyi suka tsiro a jikinta. Ayshercool 08081012143 77 Rikicewa ta yi, amma ta fara ƙoƙarin daidaita nutsuwarta dan ta san idan ta yi wani gangancin a gurin, babu lallai ta sha ta daɗin rai duba da girman mutanen da suke gurin a zaune. Ganin ta tsaya ta zuba masa ido, ya sanya ya sauke hannunsa a hankali yana kallon ta shi ma. Ta ƙarasa shigowa a hankali ta ajiye musu kwanukan abincin. Zuba mata ido suka yi, gaba ɗaya suka yi shiru daga hirar da suke yi. Ta ce "Shugabana, ga abincin ko zan jira ku duba idan da abin da bai yi ba?" Ya girgiza kai ya ce "Za ki iya tafiya" Sai dai ta kasa tashi, ta ci gaba da rarraba ido. Ya sake cewa "Za ki iya tafiya" "Dan Allah ka taimaka mini da ayabar hannunka, yunwa nake ji" Imam Omar ya ce "Imam Hammad, wai wace ce wannan ɗin? Ta san waye kai kuwa abin hannunka za ka ba ta?" Ya kalli ayabar ya kalle ta, bai kai ga yin magana ba, ta saka hannayenta biyu ta miƙa masa. Tamkar soko haka ya miƙa mata ayabar, ba tare da musun komai ba. Ya ce "Ga wata nan ki ɗauki yadda za ta ishe ki" Ta girgiza kai ta ce "Wannan kawai ta ishe ni, na gode sosai da sosai" Duk su ka bi Nana da ido, wasu cike da takaici, wasu kuma mamakin tsaurin idonta, duk da ba abin mamaki ba ne sosai, tun da ba ta san irin girmansu da matsayinsu ba, kasancewarta bare ba ƙabilarsu ba, kuma ba 'yar ƙasarsu ba. A hankali ta saci kallon hannayensu, sai ta gan su sanye da zobunan nan irin na hannun Sayyid da ya ɗauka ya bata. A take ta koma gefe ta cinye ayabar, sannan ta yinƙura ta tashi. Imam Asad ya fara masifar wace mahaukaciyar haka, da za ta zo ta yi musu wannan rashin hankalin, su zuba ido su na kallonta. Hammad ya ce "Ina mai baku haƙuri, baƙuwa ce a cikin lamarin gidan mulki, ku yi mata afuwa" Nana tuni ta fice daga ɗakin, aikuwa fitarta ke da wuya, jiri ya fara ɗibanta, bango ta dafa tana bi a hankali, sai dai kan ta kai inda take so ta yanke jiki ta faɗi. Faɗan Ƙaisar ne ya sanya ta buɗe ido, a matuƙar galabaice. "Waye ya ce da ki ka karɓa ki ci? Kin san abin da aka yi a jikin ayabar? Ban da na riga na buɗe miki ido ki na ganin abubuwa, da ba zan sake bari ki ga komai a kansa. Sai kin kashe kan ki a banza a kan mutumin nan, gaba ɗaya kin ƙarar da ƙarfinsa a kan ki, wanda ko tabbacin idan ya tuna ki zai miki irin wannan son ba ki da shi" Nana dai kasa magana ta yi, saboda yadda jikinta yake a mace, duniyar take juya mata. Ɗaga bakinta ya yi ya zuba mata wani abu mai kama da turiri, ta yi wani yinƙuri ta hau amai ta hanci da bakinta. Ba ƙaramin galabaita ta yi ba, jin yadda ƙayoyin da suka tsiro a jikin ayabar su na sukar ƙirjinta gurin yinƙurin aman da ta yi. Cikin fusata mutumin yake magana, "Wane irin wawanci ne haka da shirme da rashin hankali, ta yaya zamu shirya abu ka je ka bari ya ɓaci?" Cikin damuwa matashin ya ce "Wallahi Tafawa ba laifina ba ne ba, dan har ya fara ci wata yarinya ce ta hana shi ci, wai ya ba ta yunwa take ji" "Wace yarinyar ce a kaf faɗin Agadez za ta je tsakiyar ku, har Imam zai ci abu ta ce ya bata? Ɗaya daga cikin mugwayen ɗabi'unsa kenan da ya sanya yake zubar da kimar ku a idon mutane maƙasƙanta, har su samu zarafin raina ku. Ban da raini da wulaƙanci har baiwa ta ga abu a hannun Imam na ƙasar Agadez ta ce za ta ci." Ya buɗe baki zai yi magana ya ce "Ka ga tashi ka bani guri ni kafin na mangare ka" Haka ya ja bakinsa ya tashi ya fice jikinsa a sanyaye. ***** Alhaji Zailani ne a zaune a falon Hajiya Sa'a, ya je yi mata ta'aziyyar mutuwar Abba. Ya numfasa ya ce "Wai dama Abban ba shi da lafiya ne?" Ta girgiza kai ta wassafa masa dukkanin abin da ya faru. Cikin kaɗuwa yake jin bayanin nata. Ya ce "Ban da ke Hajiya Sa'a, ina ke ina gayyato yarinya da rana tsaka ki janyo ta jikinki, ga shi ta zame miki masifa, haba Sa'a. Ke kin san ba kowa a ke fallasawa sirrin ƙungiya ba, Allah ya kyauta, ya yi mata gaisuwa ya tafi. ***** Hammad tun bayan tafiyar sauran 'yan uwansa yake tunani daban-daban a ransa. Tuni aka saita masa wayarsa, ya ci gaba da amfaninsa da ita. Wayewar gari yana ta jiran Abinci amma shiru, ya gaji da jira saboda yana jin yunwa, ya tafi ya tashi Asal da take ta bacci. "Imam lafiya kuwa?" "Ba a kawo mini Abinci ba, ina jin yunwa zan fita" Kamar ta yi tsaki, saboda ta ji daɗin baccin, haushi ya kama ta, tare da tunanin uban abin da ya hana Nana tashi ta yi masa girki ko ta makara haka. Ga shi duk hadiman sashen ta kore su, dan haka ta tashi da kanta, ta fita. A zaune ta tarar da Nana ta jingina da bango, idanunta duk sun faɗa kamar ta kwana tana amai da gudawa. "Wani wulaƙancin ne ya sanya ba ki tashi kin yi wa Imam girki ba, har ki ka saka na biyo ki nan?" Nana ta numfasa ta ce "Ba ni da lafiya ne" "Ba ki da lafiya kuma Imam ba zai ci abinci ba? Kin san ba kowane Abinci yake ci ba" Wani malulun takaici ya ƙule Nana, wato lafiyarta ba abin da yake gabanta ba ne, kawai fatanta ta yi wa mijinta girki tun da ga baiwa. "Magana nake yi miki kin yi mini shiru" "To me zan ce miki, ba ni da lafiya, ai ban taɓa ƙin yin girki ba. Ko wani abu da ki ka saka ni ba, amma yau ba ni da lafiya babu abin da zan iya yi. Idan ke ba za ki yi mini uzuri ba, ki gaya masa kukunsa babu lafiya na san, shi zai iya yi mini uzuri" A hasale Asal ta buɗe baki za ta yi magana, Nana ta yi mata wani irin kallo, da a dole ta haɗiye maganganun da ta yi niyyar caɓa wa Nana. Ta haƙura ta juya ta fita, tana tunanin me ta ji ne ko ta gani, ta kasa yi wa Nana rashin mutunci. Tana komawa ya kalle ta ya ce "Ina Abincin?" "Wai ba ta da lafiya" "Me ya same ta?" Ta girgiza kai jiki a mace ta ce "Nima ban sani ba" Ya so sake wata tambayar, amma sanin halin Asal ya sanya shi ta shi, zai fita. Ta ce "To ina za ka je ba ka karya ba?" "Zan samu abin da zan ci, zan je na ga Mahmoud ne" Daga haka bai kuma cewa komai ba ya fita. Bakin Imam Hammad fal maganganu kamar yadda bakin Mahmudu yake fal maganganu, amma kowanne ya kasa furta wa kowa. Hammad ne ya numfasa ya ce "Mahmud ina son na koma kan ayyukana, amma Sultan ya ce mini na dakata, akwai abubuwan da nake son yi da yawa." Mahmoudu ya ce "To ka yi haƙuri, wataƙila akwai dalilin da ya sanya ya ce ka dakata tukuna" Ya numfasa ya ce "Haka ne, wai yaushe za ka shigo gida ne?" Ya girgiza kai ya ce "Ba na son shiga gidan nan naku" "Saboda me?" "Kai ma ka sani ai" Imam ya ce "Ban san komai ba. Jiya Imams sun kawo mini ziyara. Ranar Lahadi za mu yi zagayen raƙuma da shan shayi, ka zo mu je tare" "Imam, ka na manta waye ni, da ƙoƙarin kai ni matsayin da Allah bai kai ni ba, ni dai dan Allah ka yi haƙuri" "Mahmoudu, idan ba kai ba wa ka ke so na janyo jikina? Ka san komai fa? Shikenan haka ni zan zauna?" Yayi maganar muryarsa ɗauke da rauni. "Haba jarumin shugabana, ka na fa da wanda ku ka shaƙu, ku ke da kusanci tsakaninku sosai da sosai" "Waye?" Ya yi maganar yana kallonsa. "Zan haɗa ku kwanan nan, aure zan ƙara yi maka kwanan nan, ka na son 'yar Nigeria?" Ƙanƙance idanunsa ya yi yana kallon Mahmoudu. Ya ce "Ga ka nan ga Asal ai" "Ahh yi haƙuri, kar ka gaya mata sai ta saka a fille mini kai" Hammad ya yi murmushi yana gyara zamansa. Sai da Nana ta shafe kwana uku ba ta aikin komai, haka kurum Imam ya ji abin ya tsaye masa ya dame shi, ko ya yi ƙoƙarin mantawa sai ya kasa. Kwanakin nan uku kame-kame kawai yake yi gurin cin abinci, duk abin da zai ci sai ya ga kamar abin zai cutar da shi. Ga uwa uba rashin ɗanɗanon abinci da ba ya ji gaba ɗaya. Yau da Nana ta lallaɓa ta fito, ta ji ana ta zancen hawan zagayen da za a yi a kan raƙuma. Har ya yi shirinsa zai fita, ya tarar da Abinci a falo. Cikin zaƙuwa ya ƙarasa ya buɗe, tabbas ƙamshin girkinta ne. Wani murmushi ya suɓuce masa cike da farin ciki. Sai dai sam ba su haɗu ba. Har yau jikinta babu ƙwari sosai, bayan fitarsa ta shiga ta gyara abin da za ta gyara, kawai ta nemi guri ta zauna, tana hutawa wani irin bacci ne ya ɗauke ta a gurin. Ba ta jima da fara baccin ba, sai ga ta a Libraryn Ƙaisar. Waiwaye ta fara yi taga ta ina za ta gan shi, sai dai ba ta gan shin ba, sai wata guguwa da ta taso, ta watso mata littafin nan da ta ce ba za ta karanta ba. Ta kalli littafin a gabanta amma ba ta motsa ba, ba kuma ta ɗauka ba. Kawai littafin ya buɗe kansa da kansa, sai mudubin nan ya haska inda ya buɗe ɗin. Sayyid ta gani a tsaye a cikin sahara ana ta harbo masa kibiya ta ko ina, Sultan ta ta gani yana ƙoƙarin tare masa, shi ana samun sa da kibiyar. Har ya fara gazawa aka fara samun Sayyid. Ya na tsaka da tarewar aka janyo shi aka nufi wata wuta da shi, da cin ta yake gwanin ban tsoro. Ba ta iya ganin fuskar wanda yake jan na shi, saboda ya rufe fuskarsa da rawani. Gaba ɗaya Nana ta gigice ta rintse idanunta tana addu'a kar Allah ya ba wa mutumin nasara, can jin shiru sai ta buɗe idonta a hankali. Sai ta daina ganin wancan lamarin, sai wata taguwa da ake ta ɗurawa wasu abubuwa. Sayyid na zuwa ya kama taguwar ya hau, yana hawa ta din ga walagigi da shi, ta nufi kan wani rami da shi. Zumbur Nana ta tashi, tare da miƙewa tsaye a falon. Zuciyarta sai bugawa take yi da sauri. Waje ta yi da wani irin hanzari, ta nufi inda ake shirya raƙuman da za a yi hawan da su. Raƙuman duk jajaye ne, an yi musu wani irin ado, ga su ƙosassu. Gaba ɗaya ta ji ba ta yarda da lamarin ba, ta juya ta sake kwasar hanya ta koma sashen su. Tana zuwa ta ci karo da shi ya fito, sanye da makamanciyar shigar da ya shigo ɗakinta bayan auren su. Takobinsa na soke a gefen ƙugunsa, babbar rigar jikinsa ta sha aiki. Kallon Nana ya yi, fuskarta ta nuna rama sosai da sosai. Nana so take ta yi masa magana amma yana tare da Asal da ta sha kwalliya ita ma, sai hura hanci take yi. Gaba ɗaya yanayinta ya nuna masa a rikice take, kuma magana ce a bakinta. Har za su gifta inda Nana take ya ce "Sayyid excuse me" Asal ta waiwayo ta kalli Nana jin ta ce masa Sayyid maimakon Imam. Ya kalli Asal ya kalli Nana, sai kuma ya yi taku biyu ya matsa daf da Nana, ya sunkuyo daidai tsawonta. Gaba ɗaya sauran barorin da suke gurin ma zubo musu ido suka yi. "Dan Allah kar ka hau Taguwar nan" Ta yi maganar cikin tsoro muryarta har tana rawa. Ya ɗaga idonsa ya saka a nata, wanda hakan ya rikita ta, tamkar ba ta taɓa saninsa ba. Bai ce mata komai ba, ya miƙe ya yi gaba. Asal ta bi shi cikin fushi tana tambayarsa "Wai me ta ce maka?" Ya numfasa ya ce "Da tana son ki ji, ba za ta zaɓi ta gaya mini ba". "Imam ban gane ba, mene ne abin da ba za ta faɗa kowa ya ji ba?" "Ai kin san duk wanda yake ƙarƙashina, ina ba shi lokacina na saurare shi. Kar ki manta mutumin da yake da Asal doka ba ta ba shi dama a kan wata wadda ba ƙabilarsa ba, mussaman baƙar fata, kin fi kowa sani na, ki daina saka wani abu a ranki dan Allah" Ya yi maganar daidai lokacin da suka ƙarasa gurin. Daga nesa Nana take hango an ba shi shayi a kofi, ya karɓa ya shanye, an sake zuba masa ya karɓa ya sha. Aka cika gurin da kaɗe-kaɗe, juyi suka din ga yi tare da sauran 'yan uwansa Imam, su na wasa da takubbansu, gwanin burgewa. Duk da tashin hankalin da Nana take ciki, sai da abin ya ƙayatar da ita. Aka jero raƙuman nan, suka din ga kama su su na hawa. Nana gabanta ya tsananta faɗuwa, cike da ƙwarewa ya kama raƙumin nan ya haye. Idonsa suka sauka a cikin na Nana, fuskarta ɗauke da damuwa, ya lumshe idanunsa ya saita akalar raƙumin nasa, ya wuce gaba sauran suka bi bayansa. Mutane suka rufa musu baya, suka kama hanyar barin gidan. Jiki a sanyaye Nana ta koma. A tsaye ta jingina a gurin girki, tana tunanin abin da ka iya biyo bayan hawan Raƙumar nan da ya yi. But Asal ta faɗo cikin huci, Nana ko motsawa ba ta yi ba sai bin ta da kallo kawai da ta yi. Har gabanta Asal ta zo tana huci "Uban me ki ka gaya wa Imam, kuma saboda me za ki din ga kiransa da Sayyid? Ban yi miki gargaɗi a kan sa ba?" Nana ta kalle ta, ta ga kar ta yi wani abun da zai sanya ta kore ta a yanzu, dan haka ta sassauta murya ta ce "Haba ya shugabata, Sayyid da Imam duk abu ɗaya ne ai, yana nufin shugaba, mu a Nigeria Sayyid muke cewa, kema idan ki na so sai na kira ki Sayyada. Kuma me Sayyid zai yi da baƙar mace 'yar Nigeria, ai ramin kura sai 'ya'yanta. Kawai ne nemi afuwarsa ne a kan rashin samun gudanar da aikina da na yi, a kwanaki da suka gabata, saboda shi ne ƙa'idar gidan sarauta. Ki yi haƙuri iya matsayina da aikina nake tsayawa." Asal ta numfasa tana huci, duk da hankalinta ya ɗan kwanta. "Shikenan na ji, daga yanzu za ki bar ɗakin da ki ke, za ki koma ɗakin hadimai da ke tsakanin sashen Imam da nawa. Sannan akwai gurin girki a gurin girki a gurin, yadda za a din ga sauƙaƙa miki, sai dai babu ke babu fitowa a duk lokacin da yake nan, muddin ba abinci ki ka kawo masa ba, kuma ba gyaran sashen za ki yi ba. An dawo da ke sashen nan ne, domin ƙara tabattar da tsaron abincin da Imam zai ci" Nana ta jinjina kai ta ce "In sha Allah, na gode sosai da sosai" "Ki hanzarta, ki kwaso kayanki ki mayar can, a yau ba sai gobe ba, ku yi magana da Balaraba ta kai ki" Nana ta risuna ta yi wa Asal godiya, haka aka yi, a ranar ta kwashe kayanta ta mayar can ɓangaren, barorin gidan na ta ƙara mamakin, yadda a ke ɗaga likkafar Nana baƙuwar haure sama da su. Nana kuwa murna ta din ga yi, ganin tana ƙara samun kusanci da Imam, ta san addu'a da take yi ce Allah yake taimakonta, kuma tana fatan Allah zai yanke mata wannan wahalar nan kusa. Fita ta yi da nufin ta kwaso kayan wancan ɗakin girkin ta dawo da su nan, ta ga mutane na kaiwa da komowa a sashen. Wani ta gani a cikin mutanen fuskarsa rufe da rawani, amma ta ga kamar ta san shi ta taɓa ganinsa, kamar ta bi bayan mutumin, sai ta ji ana faɗin Imam ne ya faɗo daga kan Taguwarsa.! AREWABOOKS Nana ta rasa wa za ta nufa ta samu cikakken bayanin abin da ya faru. Ta san za a rina, tun da ta ga abin nan kuma ta din ga ji a jikinta, ta san wani abun sai ya faru. A can ɗaki kuma, sannu Asal ta din ga jera masa, ya jinjina mata kai kawai. Ya lumshe idanunsa yana tuna yadda Nana ta roƙe shi kar ya hau Taguwar. "Wace ce ke?" Ya furta a hankali. Asal ta ce "Magana ka ke yi ne?" Ya girgiza mata kai alamar a'a. Tun da ya hau kan Taguwar nan yake jiri, duk yadda ya ƙwarara jikinsa, da ƙoƙarin sarrafata ya kasa, dan daina gani ya yi gaba ɗaya sai jin sa ya yi ya zamo ƙasa. Ya yi ajiyar zuciya yana sauke numfashi. "Imam na saka ta dawo ɗakin Hadaimai kamar yadda ka buƙata, ko za ka ci wani abun a kawo maka?" Ya girgiza mata kai alamar a'a. "Ina ne yake yi maka ciwo to?" Ya yinƙura ya tashi ya ce "Babu ko ina salla zan yi" Yana tangaɗi haka ya shiga ya yi salla, ya sake kwanciya. Nana na ta kai komo falon babu kowa, tana son ta san halin da yake ciki amma babu wanda za ta tambaya. Wata tawaga ta ga sun shigo sashen, kallo ɗaya ta yi masa ta gane Sultan, tana son fita tana jin tsoron kar ta yi laifi, haka ta tsaya tana hangen abin da yake faruwa. Asal ta fito cikin hijjabi suka gaisa, ta yi wa Sultan jagora zuwa cikin ɗakin. Da hanzari ya nufe shi yana faɗin "Hammad, tashi maza a tafi Asibiti" Ya buɗe idonsa ya kalle shi ya ce "Babu abin da yake damuna Sultan, ba sai na je Asibiti ba" Cikin damuwa ya ce "Me yasa ka yi hawan bayan ka san ba cikakkiyar Lafiya ce da kai ba? Kuma da ka ji ba za ka iya ba ai sai ka haƙura" "Lokacin da na yi ba na jin komai a jikina, amma tuba nake ba zan sake ba" Sultan ya ce "Ka tabattar ba ka jin komai a jikinka ba sai mun je Asibiti ba?" "Ba na jin komai Abie, ka kwantar da hankalinka" Ya jinjina kai ya ce "To shikenan, Allah ya tsare gaba ka kwanta ka huta sosai" Ya jinjina masa kai, suka yi sallama ya tafi. Duk yadda Nana ta so sanin halin da yake ciki, haka ta haƙura, sai dai bacci mai daɗi ya gagara ɗaukan ta. Da sassafe ta fita ta hau gyaran sashen, tana jira ko za ta ji motsin Asal, duk yadda za a yi ta tambaye ta, ya jikinsa sai dai ta ji shiru, haka ta ajiye Abincin kari ta koma ɗakin da aka ba ta. Sai wajen sha daya da rabi, ta ji motsi a falon, ta fito ta leƙa. Shiru ta yi tana kallon mutumin da ya zo, kamar shi ta taɓa gani a gidan cin abincin su Al Hussain. Yana tare da Imam Asad. Sayyid yana zaune a ƙasan Carfet, shi kuma yana saman kujera. Allah ya taimaki Nana da Hausa suke magana, ba yarensu ba. "Kai ya aka yi ka faɗo daga kan taguwa, ko ka fara shan wani abu ne ba mu sani ba?" Asal ta ce "A'a Imam ba ya shan komai, dama ba shi da cikakkiyar lafiya ai" "Ina magana kina sanya baki?" Asal ta ja bakinta ta tsuke. Ya mayar da idanunsa kan Hammad ya ci gaba da cewa "Allah ya sauwwaƙe ya kuma kiyaye gaba. Amma ka din ga kulawa dai" Bai ko ɗaga kansa ba, balle ya tanka masa, sai dai jikin Asal ya yi sanyi. Ba ta ji daɗin yadda Tafawa ya zarge shi da shaye-shaye ba. Wuni aka yi zuwa duba Imam Hammad, sai dai ds Yamma Nana na tsaka da gyaran falon ta ga wannan takardar, mai ƙwarangwal ɗin nan yana ci da wuta. Gaban Nana ya faɗi, ta yi shiru tana kallon takardar. Jikinta ya ba ta kowaye yake yi masa wannan aika-aika yana cikin waɗanda suka zo dubiya yau. Nana tana aiki a kitchen, Asal ta same ta, ta miƙa mata wani ƙulli ta ce "Ga shi nan, ki dafa wa Imam a shayi, maganinsa ne" Nana ta karɓa ta amsa da to. Ba ta yi tunanin komai ba, ta dafa shayin ta je ta ajiye a falo. Asal tana zaune tana jiranta a falo. Ta tashi ta karɓa, Nana ta ce "A yi wa shugaba sannu, ina fatan Allah ya ba shi lafiya ya kiyaye gaba" Asal ta amsa da Amin a ciki, ta nufi ɗakin baccinsu. Yau Nana kamar ta fasa ihu, ta cika wata guda a gidan Asal, yau gaba ɗaya hankalinta yana kan ɗan jaririnta. Ga shi tun da ta zo ba su yi waya ba ko sau ɗaya ba. Haka kwanaki suka ci gaba da shuɗewa, kwana uku Asal na ba wa Nana maganin Sayyid tana dafa masa. Sai a na ukun yake fitowa ya zauna a falon, amma ba ya fita. A kai Abincin safiyar kwana na uku, Nana ta haɗu da shi. Cikin girmamawa ta ce "Barka da safiya Sayyid, ashe tsautsayin da ya faru kenan, Ubangiji Allah ya kiyaye gaba." "Ba ki yi mini sannu ba sai yanzu?" Ta ɗaga kai ta kalle shi, duk ta ji abin wani banbarakwai, amma har cikin ranta ta ji dadin maganar da ya yi mata. Ta ɗan juya idanunta ta risunar da kanta ta ce "Tuba nake Shugabana, ban samu damar ganinka ba ne, duk da na yi ƙoƙarin hakan, ba na son uwar gijiyata ta ce na zaƙe ne, amma tuba nake Ubangiji Allah ya ƙara lafiya da nisan kwana mai amfani " "Amin na gode sosai. Ina ganin ƙoƙarin da ki ke ta yi, ina yabawa, ki yi haƙuri da Asal kar ki tsane ta, duk da na san tana takura miki wasu lokutan" "Babu takura a ciki, matuƙar hidima taka ce shugabana" Ya ce "Madalla na gode sosai" Ta tashi ta bar falon, a ranta tana cewa ina Asal ta ga kirki, shi da yake hangenta daga nesa ma, ya san tana ƙoƙari, ita kuwa ban da jaraba da uwar hantara da nuna mata ƙyama babu abin da take yi. Asal ta shirya ta fita tun safe, dan haka Imam ne kawai a sashen. Da Nana ta tashi kai masa abincin rana, ta sha kwalliya cikin doguwar rigar Atamfa. Duk yadda yake jin jikinsa babu daɗi, yana motsa shi da kyar, amma bai hana shi satar kallon Nana ba. Ba ƙaramin kyau ta yi ba, ga ƙamshin turaren sa da yake tashi a jikinta. Ta kalli idanunsa da suka yi jawur, tamkar jini zai zubo daga cikin su. "Sayyid lafiya kuwa?" Kai kawai ya jinjina ya mayar da idonsa ya lumshe, yana jin wannan ƙarar mara daɗin ji a kunnensa. Haka Nana ta tashi ta bar shi a gurin, saboda tsoron abin da ka iya biyo baya. Sai dare Asal ta dawo, kuma itakaɗai Nana ta ga ta ci Abincin dare. Misalin ƙarfe ɗaya da rabi na dare, Nana ta gabatar da sallolinta na dare. Ta zauna tana karanta Alqur'ani, a hankali sai ta daina ganewa. Ziiiiiiiiii ta fara jin ƙarar guguwar iskar sahara tana tasowa. Ta rufe Alqur'anin a hankali ta ajiye, sannu a hankali sanyi ya fara ratsa ta. Ji ta yi tamkar an buga wani abu da ƙarfi, ta zabura ta miƙe tsaye. Cikin hanzari ta buɗe ƙofar ɗakin da take ciki ta fito corridor da ɗakinta yake ta tsaya. "Imam mene ne haka? Meye haka ka ke yi wai?" Sautin kakarinsa ya daki kunnuwan Nana. Gaba ɗaya ta kasa zaune ta kasa tsaye. Asal ta gani ta fito da gudu daga ɗakin, ta yi waje ta fice daga falon, ta ja ƙofar falon da karfi ta rufe. Gaba ɗaya sai kan Nana ya kulle ta rasa abin yi, ta bi bayan Asal, amma ta ji ƙofar a rufe gam. Ta juya a hankali ta kalli hanyar bedroom ɗin da sautin kakarinsa yake ta fitowa. A hankali ta fara takawa tana tunkarar hanyar ɗakin, duk da ba ta taɓa zuwa ko daf da gurin ba. Zuciyarta na bugawa cike da tsoro ta buɗe ƙofar ɗakin. Wani irin sanyin na'urar sanyaya ɗaki ta dake ta, hakan ya ƙara ninka sanyin da take ji. Wani ni'imtaccen ƙamshi ya ziyarci hancinta. Girman ɗakin baccin har tsoro ya ba wa Nana, ita dai tana mamakin yadda suke abubuwan su kamar babu lissafi, ɗakin kwana kawai an yi shi gari guda. Idanunta ya sauka a kan Sayyid da yake shirin faɗowa daga kan gadon yana jijjiga. Ta ƙarasa da sauri daidai lokacin ya faɗo ƙasa. Ta ɗaukko pillow za ta saka masa, kawai ta ga wannan hoton a ƙasan fulonsa. Cikin mamaki take kallon hoton, tare da mamakin yaya aka yi ya zo kan shimfiɗarsa. Ta durƙusa a kansa, ta kalli jikinsa duk wata jijiya da take jikinsa ta miƙe ta kumbura. Ƙwayar idonsa ta koma fara ƙal, gashin kansa ya hargitse, gaba ɗaya ya koma abin tsoro tamkar wani dodo. Ta yi Bismillah ta zauna, tare da jin sai dai komai zai faru ya faru, ko a mutu ko a yi rai, ko da za a zo a kama ta gara balli ya tashi ko za su ƙaryatata gara duk abin da zai faru ya faru, da bar shi a wannan yanayin da bayan shi kansa babu wanda ya kai ta sanin mawuyacin halin da yake shiga. Tamkar mayen ƙarfe haka ya riƙe ta gam, bakinsa yana karkarwa yana furta "Wuta! Zafi!" Ya danneta a ƙasa ya ƙanƙameta, bakinsa na fitar za kumfa. A hankali ta fara karanto suratul Saffat, ta sanya hannunta a cikin gashin kansa tana shafawa a hankali. Sannu a hankali ya daina wannan gurnanin da yake yi ya yi shiru, sanyin jikinta ya fara ɗibarsa. Ya yin da ita kuma take jin tamkar ana gasa ta a tukuba saboda zafin Jikinsa. Sosai Nana ta ƙanƙame shi ita ma, cike da matsananciyar kewarsa, wasu hawaye da ita kanta ba ta san na mene ne ba, suka din ga sintiri a kan fuskarta. "Sai ki tashi ki tafi tun da ya samu bacci, tun da ke dai a rayuwarki ba kya tsoron matsala, tarar aradu kawai ki ke yi da ka. Maimakon ki bari mutumin nan ya gane ki, a yi duk wadda za a yi, amma sai ƙoƙarin kunno wa kan ki matsala ki ke yi" Ƙaisar ya yi maganar cike da takaici yana harar ta. Nana ta ce "Wasu lokutan nasara ns buƙatar sadsukarwa, da kuma tarar aradu da ka. Mu da ku ba irin zubin halittarmu ɗaya ba, ba zan iya jure ganinsa a wannan mawuyacin halin ba. Ina tausaya masa a yanzu fiye da a lokacin da na san shi bai kan sa ba, yake ce mini yana ji a jikinsa rayuwar da yake da ni ya fi wadda ya manta aminci da kwanciyar hankali, ga shi kuma yanzu ina gani. Sai na ƙyale shi a haka?" Ƙaisar ya yi tsaki ya ce "Allah ya sa shi zai iya yin abin da ki ke yi a kan sa" Nana ta numfasa ta ce "Dama ba dan ya rama mini nake yi ba" Sai gefen asuba jikinsa ya saki, ya ci gaba da nannauyan bacci. Ta saka masa filo ta tashi, sai dai jikinta tamkar ana karyata haka take ji, saboda azabar riƙon da ya yi mata. Bayan ta idar da sallar asuba, ta yi adduo'inta ta shiga kitchen. Kafin ƙarfe tara har ta kammala komai, ciki har da gyaran katafaren falon Imam Hammad. Tana son sanin halin da yake ciki, ya farfaɗo ko kuwa bai farfaɗo ba. Tana can tana tunani, shi kuwa tuni ya fito ras da shi, ya hau buɗe-buɗen kwanuka. Har wani murmushi ya yi ganin ƙosai a cikin kayan karyawarsa. Shiru ya yi yana kallon kofin madarar raƙumin da ke gabansa, bayan da ya buɗe ya ga 'ya'yan habbatussauda a kan madarar. Ya ciro wayarsa ya daddana, ya kara a kunnensa. "Al Hussain" "Allah ya taimaki Imam Hammad adalin shugaba abin koyi" "Barka da wannan lokaci ya aiki?" "Alhamdillah, ina nan tafe cikin Agadez a wannan satin, tun da an ce mini yanzu ana ganin ka" Imam ya ce "Eh, ammm tambayarka nake son yi" "Ok Imam, Allah ya sanya ba wani abun aka ce na yi ba" "Akwai yarinya da Asal ta zo da ita, ta ce a nan gurin cin abinci na Maraɗi ta ɗaukko ta, wata 'yar Nigeria" Al Hussain ya ce "Haka ne, sai dai ba na nan suka tursasata Gimbiya Asal ta tafi da ita, na ɗauka ma nan  gidan cin abinci na Agadez za ta dawo da ita" "A ina ku ka samo ta?" Al Hussain ya ji gabansa ya faɗi cike da tsoron, ko wani abin ne ya faru. "Wani kamfani ne suka kawo ta, da muke neman ma'aikata masu ƙwarewa a fannin girki" "A nemo kamfanin, da shugaban kamfanin" "To in sha Allah, amma ina fatan ba wani abin ne ya faru ba?" Imam ya ce "Sarkin ruɗewa, babu abin da ya faru, ina sauraren ka" Daga haka ya ajiye wayar daidai lokacin da Asal ta shigo. Ya ɗaga kai ya kalle ta ya ce "Ke ina ki ka tafi ne? Na yi zaton ma ko ki na sashenki ne?" Ba ta ba shi amsa ba, Sultan ya shigo a rikice. Da mamaki yake kallon su. Sultan ya ƙaraso cikin hanzari ya ce "Hammad ka na lafiya ya jikin naka?" Imam ya ce "Ai ni lafiyata ƙalau, tun ranar da na faɗo fa babu abin da ya same ni" Sultan ya kalli Asal, a rikice ta ce "Wallahi Sultan ba shi da lafiya, ba ka ga riƙon da ya yi mini jiya ba, wasu abubuwa ya din ga yi masu ban tsoro". Imam ya ɗaga kai ya yi mata wani irin kallo, da sai da hantar cikinta ta kaɗa. Ya gyaɗa kai ya ce "Ni ban san me take magana a kai ba, lafiya ƙalau na kwanta kawai dai ba na jin daɗi kaina yana yi mini ciwo, ban sani ba ko ciwon haukan ne ya motsa mini ba" Sultan ya ce "A'a ba ka da wani ciwon hauka, kawai dai rashin fahimta ne, ka san ba ka da cikakkiyar lafiya" Hammad ya miƙe riƙe da kofin madararsa, yana sha a hankali ya ce "Abie zan je na shirya, zan ɗan fita ne" Ya nufi ɗakin sa. Asal ta kalli Sultan ta ce "Wallahi Sultan ba ƙarya nake yi ba" "Na sani, na san ba ƙarya ki ke yi ba, ki yi haƙuri. Dan Allah ki yi shiru da bakinki kar ki gaya wa kowa. Zan san abin da zan yi a kai" Nana kuwa burgima ta din ga yi a ɗaki, saboda azabar ciwon da jikinta yake yi mata, kamar ta saka ihu haka take ji. Tun da ta jiyo muryar sa sama-sama a falo, hankalinta ya kwanta ta san jikinsa da sauƙi. Sai dai wunin yau ma ba su haɗu ba, Asal ta ce mata ta ajiye masa Abincin, za a ɗauka a kai masa inda yake. Ruwan zafi Nana ta dafa, ta shiga ta ya wanka da shi, ko za ta samu afuwa, ta gyara jikinta ta fita. Gidan ya yi shiru saboda dare ne, kowa ya kwanta. Ta shiga kitchen ɗin ta tabbatar komai lafiya ƙalau, sannan ta koma ɗakinta. Tana shiga ɗakin ta ga duhu an kashe fitila, ta nufi gurin kunna fitilar ta ji an mayar da ƙofar ɗakin an rufe. Ayshercool 08081012143 1K NE VIA 0069685771 Aisha Adam stanbic bank 💃💃💃 78 78 Gaban Nana ya faɗi, cikin tsoro da razani ta ce "Waye? Waye a nan?" Sai dai shiru ba a yi mata magana ba. Ta kunna fitilar kawai ta ga Imam Hammad a tsaye a cikin ɗakin. Ja da baya ta yi a razane tana toshe bakinta saboda ihun da take shirin kurmawa saboda razani da tsoro. "Idan ki ka yi ihun da Asal ta ji ki, za ki yi mata bayanin abin da ya kawo ni ɗakin nan, kuma duk hukuncin da ta zartar a kan ki sai an yi miki shi, komai tsaurin sa." Ta marairaice ido tana kallon sa cike da tsoro. Ya tako a hankali ya ƙaraso gabanta, ya zuba mata idanunsa da suka ƙara rikita ta, jikinta har tsuma yake yi. "Wace ce ke?" Ya yi maganar yana kafe ta da idanunsa. "Ni ba kowa ba ce" Ta furta jikinta na tsuma cike da tsoron ko yana hayyacinsa jiya da ta je turakarsa. "Ki gaya mini wace ce ke? Kuma da wace manufar ki ka zo gidan nan?" Ta rintse idanunta tana girgiza masa kai ta ce "Wallahi ni ba kowa ba ce ba, Matarka ce ma ta kawo ni nan" "Kin sanni a wani gurin kafin nan?" Ta ɗago kai ta kalle shi, ta girgiza masa kai a hankali, idanunta na cika da hawaye. "Kin hana ni cin ayaba, kin ci kin yi rashin lafiya, kin hana ni hawa kan taguwa, na hau na faɗo. Idan na ganki ina jin wasu abubuwa da ba na ganewa a jikina, tamkar ke ba ɗan Adam ba ce. Ɗanɗanon Abincinki na yi mini kama da wani Abinci da nake ci a wani guri da ba zan iya tunawa ba, idan ba Abincin da ki ka dafa ba, ba ya yi mini ɗanɗano a bakina. Ki na shafa irin turarena kin ba ni madara da habbatussauda, wani abu da ba kowa ya san ina sha ba. Ki gaya mini wace ce ke, kuma a ina ki ka sanni?" Ya yi maganar yana ƙara matsawa daf da ita yana ƙara ɗaga mata murya. "Ni ban sanka ba, ban taɓa zuwa Agadez ba sai a wannan karon, ni babu abin da na sani game da kai" Ta yi maganar hawaye na ta sintiri a kan fuskarta. Ya numfasa ya ce "Idan wani ne ma ya turo ki, ki ke yi mini wasa da hankali, ki ji tsoron Allah, jarrabawoyin da suka yi wa rayuwata ma ƙawaanya sun ishe ni. Kar ki bari na kama ki da kowane irin nau'i na rashin gaskiya" Ta yi shiru tana sunkuyar da kanta ƙasa. "Nana ko?" Ta jinjina masa kai cikin tsoro. "Ki yi haƙuri na tsorata ki, ba na son Asal ta gane wani abu, za ta ƙara tsanar ki ne." Daga haka ya juya ya bar ɗakin nata. Neman guri ta yi ta zauna tana mayar da numfashi, saboda yadda ta tsorata. ***** Sagir ne ya ɗauki Yusra suka tafi gidan su Shukura, domin ƙara jajantawa juna tare da su Hajiya Amina, ta kuma tabattar da iyayen Shukura ba sa zarginta da ɓatan Yusra kamar yadda take faɗa. A babban falon gidan suka zauna, Hajiya Amina duk ta rame saboda tashin hankali da kuma damuwa. Gefe ga Yusuf yayan Shukura, da shi ma fuskarsa take ɗauke da damuwa. Bayan sun gaisa Hajiya Amina ta ce "Sagir har yanzu babu wani labari game da ɓatan Shukura ko?" "Wallahi Mami babu, na yi sintirin gurin jami'an tsaro amma babu wani labari, kullum sai dai su ce mini a kan bincike. An kasa tracking ɗin in da wayarta take, abin dai sha'anin binciken na rasa gane wane iri ake yi" Hajiya Amina ta ce "Babu komai, akwai Allah mu ci gaba da gaya masa, in sha Allah za ta kuɓuta" Alhaji Zailani ne ya fito da shirin fita, Cikin girmamawa. Bai amsa ba ya ce "Yaya ake ciki da batun Shukura haryanzu babu wani labari?" "Eh Daddy, amma mu na ta addu'a in sha Allah za a gan ta" "Ka ga ni fa na gaji da wannan kwana-kwanar, ta ɓangarena zan ƙara saka wa a tsananta bincike, dan kai kan ka ban yarda da kai ba. Ta yaya za a ce rana tsaka a nemi yarinya a rasa ga tsohon ciki, kai me yasa ba a neme ka an rasa ba ko matarka sai ita?" Hajiya Amina ta ce "Haba Alhaji, ya za a yi Sagir ya sanya a sace Shukura a sace ya kai ta ina?" "Ni ki yi mini shiru, babu abin da ba zai iya faruwa ba" ya gama bambaminsa ya fita. Hajiya Amina ta ce "Ka yi haƙuri Sagir, kawai yana cikin tashin hankali da damuwar ɓatan Shukura ne. Dan Allah kar ka damu za a gan ta da yardar Allah" Yusra ta ce "Da ƙawata tana nan wataƙila da tuni ta gaya muku inda Shukura take". Gaba ɗaya suka kalli Yusra, ta ce "Eh Nana mana, ai kin tuna ta ko?" Ta yi maganar tana kallon Hajiya Amina. Ta jinjina kai. Amma Sagir ya ce "Mami bari mu tafi, kin san ba ta da cikakkiyar lafiya ne" Mami ta ce "Allah sarki, amma ta yi gaskiya na san Nana, a ina ki ka santa?" Yusra sai ta yi shiru, saboda ba ta son ta ji an ce ba ta da cikakkiyar lafiya, amma tun da suka shigo gidan, ta ji ƙamshin Nana. ***** Nana kuwa bayan sallar asuba, ta kashingiɗa tana ta zancen zuci, tana tunanin mece ce mafitarta ta ƙarshe, ta fuskanci kullum al'amuran cikin ƙara rikice mata suke. Wayarta ta ɗaukko tana kallon hotunan Muhsin, kewarsa take yi sosai da sosai, har sai da hawaye ya cika mata ido. Sai ta yanke shawarar neman izini daga gurin Imam, ta je gida, dan ta ga ya fi Asal kan gado. Sai dai wani abu mai kama da bacci ya ɗauke ta, sai dai ta iya kiran shi da dannau, wato sleep paralysis, da wasu kan ce aljani ne yake danne mutum, ya yi iya ƙoƙarinsa gurin tashi amma ya kasa. Iya ƙoƙarinta take son ta yi addu'a, amma ta kasa. Inuwar mutum ta gani ya shigo ɗakin, amma ba ta iya tantance wane jinsin ba ne ba, mace ko namiji. Inuwar na zuwa aka zare wayar da ke hannunta, aka fice. Cikin razani da tsoro ta farka a galabaice tana ta haki tana rarraba ido, amma ba ta ga kowa a ɗakin ba, ta laluba ta nemi wayarya ta rasa. Hankalinta ya yi mummunan tashi, ta ɗaga fulon, ta zazzage inda take zaune, amma babu waya babu dalilinta. Ta tashi cikin azama ta hau buɗe kayanta, ko wayar tana ciki, amma wayam babu waya babu dalilinta. Ta fita da sauri ko za ta ga alamar wanda ya shigo sashen amma ba ta ga kowa ba. Hankalinta ya yi mummunan tashi, saboda rashin sanin wanda ya shigo ya ɗauke mata waya. Gudun masifar Asal idan ta makara gurin hattama abinci ya sanya ta shiga ɗakin girki. Ta fito jiki a sanyaye tana gyaran falon Asal ta fito, kamar Nana ta share ta sai kuma ta ce mata "Barka da wannan lokaci" "Yauwwa. Amm kar ki damu da ajiyewa Imam abinci, tun asuba baya nan, za su yi zaman majalisar Sultan." Nana ta jinjina kai. Idan haka ne ba shi ne ya sake shigar mata ɗaki ba kenan, to ko Asal ce? Da sauri ta ce "Amm ranki ya daɗe, na ce dan Allah.. sai kuma ta yi shiru kar ta tambaye ta, ta canza mata fassara. Asal ta ce "Ina sauraren ki" "Amm shikenan ba komai" Asal ta yi gaba ta yi waje abin ta. Gaba ɗaya hankalin Nana ya ƙi kwanciya, ba ta san a hannun wa wayar take ba, ba ta san ta ina balli zai tashi ba, tun da wayar babu security a kai. Ba kuma ta tunanin ma'aikatan gidan, saboda ba su da ikon shiga wannan sashen. ***** Gaba ɗaya su ke zaune cikin shiga ta alfarma ana tattaunawa, Sultan ya ce "Ina mai farincikin sanar da ku cewa kamfanin masarauta na zinari, zai shiga wata yarjejeniya da ƙasar faransa a kan zinari da kuma sindarin uranium da muke haƙowa. Dan haka ina ganin sai mu tura Imam Hammad da Omar, su je su karanta tsarin yarjejeniyar. Sai kuma a nan gida mu na da taro shi ma, a kan yadda zamu bunƙasa harkar safarar raƙuma da muke yi zuwa ƙasashen ƙetare. Akwai buƙatar fito da sabbin hanyoyi na ƙara faɗaɗa kiwon su da kuma shige da ficen su. Ina ga wannan da kaina zan je taron tare Imam Asad, Zahradeen" Tafawa Maleek ya ce "Wai dan Allah Jalaludeen ba ka jin nauyinmu da ka ke fito da son zuciyarka da son kan ka ƙarara a gaban jama'a?" Gaba ɗaya suka ɗaga kai su na kallon Tafawa. "Za ka tura ɗanka yarjejeniyar Zinari da sinadarin uranium, mu kuma ka haɗa ka 'ya'yanmu da harkar raƙuma" Abduou matawalle ya ce "Tafawa, yakamata ka san abin da ka ke faɗa fa, Sultan ka ke yi wa magana" "Ban saka da kai ba, da ɗan uwana nake magana" Tafawa ya yi maganar yana dakatar da Matawalle. Sultan ya yi murmushi ya ce "Ba abin da ka ke zargi ba ne Tafawa. Hammad ai ɗanka ne, kuma ni duk matsayinsu ɗaya a gurina." "Ba matsayinsu ɗaya ba, me yasa ba ka tura Zahradeen ba sai shi, mutumin da ko cikakkiyar lafiya ba shi da ita?" Imam Zahradeen ya ce "Mai girma Tafawa, da ni da Imam Hammad ai duk ɗaya ne, ni dan ya je masarautar Agadez ya wakilta babu wani abu a ciki" "Yi mini shiru, kai har ka na da zarafin da ina magana da babanka ka din ga sanya baki? Ni na gaji da wannan bambanci da ka ke nunawa, sai ƙoƙari ka ke lallai sai ka tura ɗanka kan kujerar Sultan ta ƙarfin tsiya, bayan bai cancanta ba. Shi ba cikakkiyar lafiyar zuciya ba, ga rashin lafiyar ƙwaƙwalwa, kalli yatsunsa babu zobensa na tambari, ga shi tsawon shekaru da aure ba shi da magaji, ta yaya ka ke tunanin makaho ya jagoranci mai idanu? Ta yaya mutumi  da shi kansa ba zai iya tsayuwa da ƙafarsa ya yi rayuwa ba za a ce ya wakilci masarauta kamar Agadez a harkar kasuwanci" Cikin tsawa Sardaunan Agadez ya ce "Wane irin lafazi ne wannan ka ke yi Tafawa? Kar ka manta da wanda ka ke magana, babu ruwan masarauta da gaba ka ke da Sultan, zamu iya sanyawa a warware rawaninka a hukunta ka. Hammad ba ɗanka ba ne kai ma? 'yar ka fa yake aure, kuma ɗan ɗan uwanka ne, kai ba mai rufa masa asiri ba ne idan ma hakan ne? Batun zoben sa zamu yi bincike a kai, haihuwa kuma Allah ne yake bayar da ita, bai zama hujjar da za a ce an hana shi wata dama ba. Ko yana da ɗa ko babu idan Allah ya nufi ya yi mulkin Agadez wallahi sai ya yi" Gaba ɗaya gurin suka yi tsit. Ya mayar da idonsa ga Sultan cikin girmamawa ya ce "Ina neman afuwa ya shugabana bisa ɗaga murya da na yi a gaban sarki" Hammad ya dubi Sultan a tsanake ya ce "Ina neman a yi mini izini, zan ɗan fita" Da ka Sultan ya yi masa alama, ya yinƙura ya tashi ya fita. Zuciyar Sultan tamkar ta kama da wuta saboda damuwa da jin zafin kalaman ɗan uwansa ga ɗan nasa. Kai tsaye Imam Hammad ya koma gida, zuciyarsa na yi masa wani irin zafi na maganganun da Tafawa ya faɗa a kansa. Ɗakin saukar baƙinsa ya wuce, da nufin ya zauna ya kaɗaice a ciki. Kawai ya tarar da Mahmoudu a ɗakin. Bai kula shi ba kawai ya nemi guri ya zauna idanun nan jawur. Mahmoudu ya tashi ya koma kusa da shi, ya kalli yadda idanunsa suka yi jawur ya ce "Imam, lafiya kuwa?" Yayi shiru kamar ba zai yi magana ba, sai kuma ya ce "Mahmoudu, ina son na roƙi Sultan ya cire ni daga duk wani abu da ya shafi harkar mulkin nan ba na so" Mahmoudu ya waro ido ya ce "Saboda me? Kai ma ka san abin da ba zai yiwu ba ne ai. Ka riga ka kai matsayin Imam kuma ka san me hakan yake nufi" "A cire ni a maye gurbina da wani, tun da akwa masu so. So nake na yi nesa da gidan nan, na samu nutsuwa na yi rayuwata cike da 'yanci yadda babu wanda zai dame ni ya takura mini. Gidan nan ji nake yi tamkar a kan wuta nake. A kan abin da bai taka kara ya karya ba an ci mini mutunci ana ce mini juya. Ni Tafawa yake ci wa mutunci saboda kawai Sultan ya ce na je faransa na wakilci masarauta? Wallahi wataran za su neme ni su rasa" "Mahmoudu a ransa ya ce wancan karon ma da ka gudu ni ka saka a bala'i' A zahiri ya ce "Dan Allah ka yi haƙuri, duk inda ka je ma ba zaka iya zama ba sai ka dawo, dan Allah ka yi haƙuri" Ya yi wa Mahmoudu shiru, ya lumshe idanunsa. Yana kwance a kan cinyarta, ya zuba mata idanu yana kallonta. Sai shafa gashin kansa take yi tana yi masa murmushi mai ƙayatarwa. Bai yi mata magana ba, ita ma ba ta yi masa ba, amma yanayin ya yi masa daɗi sosai da sosai. Wata babbar mace ce a zaune, tana ta huci tamkar za ta fashe, cikin takaici da ƙunar rai take kallon matashin saurayin da yake gabanta. "Zahradeen wai kai wane irin mutum ne mara kishin zuci da bai san ciwon kansa ba? Ina nan na samu labarin ka na cewa Sultan wai a tura Hammad wakilci kai da shi duk abu ɗaya ne, a gidan uban wa ku ke abu ɗaya, ana ƙoƙarin nemo muku 'yanci, amma kai kana shirme da shiririta?. Ƙarara Sultan yake nuna bambanci a tsakaninku ammma kamar ya yi maka asiri ka zama nusari. To wallahi ni ba nusara ba ce, ban tsaya tsayin daka ka zama Imam ba, sai dan ka zama Sultan ɗin Agadez. Dan haka ba zan zuba ido shashancinka ya ɓata mini wahalata ba na gaya maka". Zahradeen ya yi shiru bai ce komai ba, shi sam bai ga wani abu da Sultan yake yi na nuna fifiko a kan Hammad ba, kawai yana ba shi kulawa ta musamman ne, saboda yanayin matsalar hawan jini da yake da ita, da kuma rashin mahaifiya. Aka ci gaba da dambarwa, a kan tafiyar sa Faransa. Ko da aka koma zaman tattaunawa, Mayan 'yan majalisar Sultan ra'ayinsu ya kasu biyu, wasu su na goyon bayan a tura Hammad, saboda nagartarsa da jajircewa ya cancanta mussaman da duk ya fi sauran Imam Imam ɗin ilmi da mu'amala, ga yarurruka da yake ji. Ya yinda wasu suka goyi bayan Tafawa a kan Hammad ba zai ce wakilci Agadez ba, sai sun ji ba'asin zobensa, sai kuma sun ji matakin lafiyar ƙwaƙwalwarsa. Da rahoton lafiyarsa na tsawon shekarun da ya yi a faransa. Wannan ƙa'idoji da suka shimfiɗa ƙa'idoji ne da sai an kwashe lokaci kafin cika su, wanda har lokacin taron ya zo ya wuce, ba a kammala cika su ba. Ganin gurin zai sake yamutsewa, ya sanya Imam Hammad yin gyaran murya. Cikin girmamawa ya ce "Ina godiya matuƙa da wannan dama da aka so ba ni, amma zaman lafiya da kwanciyar hankalin Agadez shi ne a gaba da komai. Ina roƙon a yi mini alfarmar yi mini afuwa, ba zan samu damar yin tafiya wakilcin nan ba, sakamakon hali na rashin lafiya da nake fama, ciwo zai iya kama ni a ko ina, dan haka Tafawa ya yi gaskiya, ina buƙatar hutu" Cikin tsawa Sardauna ya ce "Ba kai ka ke da wannan hurumin ba." "Mai girma Sardauna, gaskiya Tafawa ya faɗa, ban cancanci duk wannan abubuwan ba, shugabancin Imam ma zan sauka na nemi lafiyata" "Mun san ba ka da lafiya, amma ka ka na kan magani, dan haka larura ba za ta hana ka aiki ba" "Larurar ƙwaƙwalwa, mahaukaci ba zai wakilci masu hankali ba, ina neman afuwarku" Daga wannan maganar ya yi waje, saboda yadda idanunsa suka yi jawur, jikinsa ya fara tsuma. Tsit gurin ya yi aka hau kallon-kallo. Sardauna ya ce "Ka ga abin da ka janyo ko?" "Ai ba ƙarya na yi ba, shi ya faɗi cewa ƙarya nake yi ɗan sa ba mahaukaci ba ne?" Ya yi maganar yana kallon Sultan. AREWABOOKS Har wani duhu yake gani a idanunsa, saboda matsanancin ɓacin rai da tashin hankali. Mutumin da yake uba a gare shi, shi ne ya yi masa wannan kausasan laffuzan a gaban jama'a. Ya daɗe yana nuna masa ƙiyayya, amma lamarin bai fito ƙarara ba sai bayan da ya zama Imam.  Mussaman wannan dswowar da ya yi, dan ya matsa a kan lallai sai ya ji wani ciwon ne ya zaunar da shi a ƙasar waje har shekara biyu, kuma aka hana kowa zuwa duba shi? Ya kawo kai cikin falo, Nana tana ta aikace-aikacenta. Ɗan turus ta yi bayan da ta tuna Asal ta ce mata ba yanzu zai dawo ba. Fuuu ta ga ya nufi uwar ɗakinsa. Ta ɗan taɓe baki ta ci gaba da aikin gabanta. Sai dai zuciyarta na kan abin da ya sanya shi cikin fushi da tashin hankali haka. Duk da ba ta da wani kusanci da shi a wannan Duniyar tasa, amma mutum ne mara magana, amma yana da yawan fara'a. Asal ta fito daga wanka ta gan shi kwance a kan gado. Ta kalle shi ta ce "Amour ya na ga ka dawo kuma? Lafiya kuwa?" Muryar Asal kawai ta fusata shi, saboda abin da mahaifinta ya yi masa a fitarsa. Dan haka ya yi mata banza. Ta nufi gaban mudubi ta amsa wayar da take ta ringing, ta ajiye ta dawo ta dube shi ta ce "Sultan yana neman ka a sashen sa yanzun nan" Ya yi mata shiru, bai yi magana ba, ta nufe shi ta zauna a kusa da shi, ta ɗora hannunta a kan kafaɗarsa. Ya tashi zaune a fusace ya ture hannun Asal, ya tashi ya fita. Sororo ta tsaya tana mamakin me yake damunsa haka? Gaba ɗaya ya fita ya bar sashen. **** Cikin matsananciyar damuwa Mama take kallon Jamila da ta yi wata irin rama mara fasali, duk ta bushe ta yi haske sai uban kai ɗauke da gashi. "Jamila ni fa na rasa gane kan ki gaba ɗaya, kalli yadda ki ka koma, dole ki shirya mu je gurin masu magani ko mayu ne suka kama ki, ki ke ta wannan wahalar duk kin ƙi lafiya" "Ni babu wasu mayu da suka kama ni" "To idan ba mayu ba wannan ciwon na mene ne haka? Fitar nan ma da ki ke yi gurin kasuwancin naku kin daina gaba ɗaya" "Ki ƙyale ni zan warke ne" Ta yi maganar cikin ƙosawa da maganganun Mama. Su na haka Yaya Atine ta yi sallama, Mama ta amsa tana yi mata maraba. Mama ta ce "Ke ki ke tafe a yammacin nan?" Ta ce "Wallahi kuwa, na ga kwana biyu ban leƙo ba, na ce bari na shigo, Isan ba ya nan ne?" "Eh ya fita baya nan" "Ita kuma wannan fa?" Cikin damuwa Mama ta ce "Ba ta da lafiya ne, nayi-nayi da ita, mu je gurin mai magani ta ƙi yarda, ga na Asibitin an yi ya ƙi jiki kullum ƙara rikicewa yake yi" "To me yake damunta ne har haka?" Mama ta ce "To gata nan dai, kullum zazzaɓi ba ta kuma son cin abinci ko fita ba ta yi, na Asibitin ya ƙi yi mata, mu koma na gargajiya ta ƙi" Yaya Atine ta ɗan zura wa Jamila ido, har sai da haushi ya kama Jamila, ta tashi ta bar gurin. Yaya Atine ta ce "Mhmm" Ta ɗaukko wata hirar daban. Ba ta wani jima ba ta yi wa Mama sallama ta tafi, sai dai cikin sa'a ta haɗu da Baba a ƙarshen layin, dan haka ta zauna suka dasa hira a hanya. Ta ce "Ashe Jamila babu lafiya?" "Eh wallahi ana ta fama, an kasa gane abin da yake damun ta" "Lallai, to gaskiya yakamata ku zurfafa bincike dan kuwa ɗan yau ka haife shi ne, amma ba ka haifi halinsa ba" Cikin rashin fahimta ya ce "Me ki ke nufi?" "Ni babu abin da nake nufi, balle a ce na ce, ni dai kawai na ce a zurfafa bincike ka ga tafiyata" Ya yi shiru yana nazarin maganganun 'yar uwattasa. **** Cikin fushi Sultan yake kallon Imam Hammad, ji yake yi tamkar ya kwaɗa masa mari ko ya huce. "Sai yanzu ka ga damar amsa kiran nawa?" Ya girgiza kai ya ce "A yi mini afuwa, jikina ne ya so motsa mini shi ya sanya ban samu fitowa ba" Sai kuma ya sassauta murya ya ce "Wani abin ne ya faru da kai bayan tafiyar taka?" Ya girgiza wa Sultan kai. Cikin rarrashi ya ce "Hammad, ba a cin nasara da karaya da kuma miƙa wuya farat ɗaya. Kuma Tafawa Maleeka bai yi ƙarya ba, ina son ka gaje kujerar Sultan ba dan komai ba sai domin ina buri da fatan ka gyara kura-kuran da na aikata a baya. Ni ba ina burin ka zama Sultan domin son zuciya ko wani abu ba, ko iya haka Allah ya yi maka mai kyau a duniya, ina yi maka fatan mai kyau a Lahira. Ka ma da ilimi, ka na da dukiya, ka na da mulki iko ka ke buƙata gurin aiwatar da wasu abubuwan. Kai kaɗai ne kujerata ba ta gabanka, kuma ka fi ni jajircewa da tsayawa a kan ra'ayinka da aƙidarka, burikanka a kan Agadez da ƙudure-ƙudirenka abubuwa ne da za su sauya rayuwar mutane da dama, saɓanin sauran da hawan kujerar ne kawai a gaban su, ba ƙalubale da abubuwan da suka kamata ba. Dan Allah ka yi haƙuri ka jure kar ka watsa mini ƙasa a ido. Wannan nagartar taka ya sanya manyan nan na majalissata suka ƙara tsanarka ba wani abu ba" Imam Hammad ya numfasa ya ce "Abie na ji duk bayananka. Amma ka yi haƙuri na riga na karaya, kalaman da ake jifa na da su sun yi tsauri da muni, su na taɓa zuciyata da yawa" "Na sani, ba na buƙatar ka musanta abin da na zo da shi, ka yi mini biyayya kawai. Kuma majalisa sun zartar da hukunci a kan Tafawa bisa abin da ya aikata" Hammad ya kalli Sultan ya ce "Ina fatan ba wani abin mai tsauri suka yanke a kansa ba, kar alaƙa tsakanina da shi ta ƙara yin tsami, ga 'yar sa ina aure. Ko ba komai uba ne a gare ni, kuma Asal ƙanwata ce kuma matata" Sultan ya girgiza kai ya ce "Kar ka damu, hukuncin ba zai shafi nasaba da dangantaka ba, ka je ka samu ka huta" Ya risuna cikin girmamawa ya yi godiya ya fita. Bayan fitarsa Sultan ya zauna, zuciyarsa cunkushe da damuwa, tunani yake yi yaya aka yi Tafawa ya san batun larurar Hammad. Ya yi tunanin ko Asal ce ta gaya masa, amma ko Asal ba ta san taɓin hankali Hammad ya yi ba, kawai dai ciwo ne yake kama shi, gangar jikinsa ta sauya, ya din ga wannan jijjigar da kakarin. ***** Kaiwa da komowa Tafawa yake yi a cikin falonsa, zuciyarsa a cunkushe da baƙin ciki, bayan tuna yadda wasu daga cikin majalisar Sultan suka ƙaryata shi, bayan da ya faɗi cewa Hammad yana da taɓin hankali. Ya yi ƙwafa ya ce "Da ni ku ke zancen, sai na tabattar wa da Duniya ɗan ka mahaukaci ne, sai ya yi hauka tuburan Duniya ta gani ta shaida, kujerar da ka ke ƙoƙarin cusa shi ya hau, sai ta zama haramiyarsa ta har gaban Abada. Mulkin ai ba da shi aka haifoka ba, da za ka ce lallai ka yi shi ma sai ya yi ba. A wancan karon mu na ji mu na gani, aka ɗora ka aka ce bamu cancanta ba, a wannan karon dole sarauta ta bar gidanka ta dawo gidana, Asadullah sai ya hau kujerar Sultan, ko ka na raye ko ka mutu". ***** Tun da ya koma gida Asal ta share shi, shi ya manta ma abin da ya yi mata, ya ga tana basar da shi ga damuwa da yake ciki. "C'heri'" Ta ɗago ta kalle shi. "Me yake faruwa ne?" Ta girgiza masa kai alamar babu komai. "Idan na yi miki laifi ne, ki yi haƙuri, ina cikin damuwa ne kwanakin nan, ki din ga yi mini addu'a" Ya yi maganar yana hargitsa gashin kanta da ta gyara. Ya nemi guri ya kwanta ya lumshe idanunsa, yana fatan bacci ya ɗauke shi, ko ya samu sauƙin wannan damuwoyin. Yana jin ta ta kashe fitilar ɗakin, sai hasken fitila na gefen gado wanda ba mai takura ba ne. Ta hau kan gadon ta kwanta a bayansa, ta zura hannunta ƙirjinsa. A hankali ya juyo, ya rungumeta sosai a jikinsa yana shafa bayanta, duk da ta ji haushin abun da ya yi mata ɗazu, amma da yake ya ƙware a iya mantar da mutum laifin da ya aikata masa, dole ta ba da kai bori ya hau. A hankali ya ji jikinsa ya fara ɗaukar zafi. Ya raba Asal da jikinsa saboda yadda yake jin san tamkar an saka masa fetur an kunna wuta a jikinsa. Ya miƙe ya din ga kaiwa yana komawa a ɗakin, yana maimaita ya hayyu ya ƙayyum. Ya shiga banɗaki ya haɗa ruwan ɗumi ya yi wanka ya fito. Kasa jurewa ya yi jin yana neman ya fita daga hayyacinsa, ya fita falo. Yana fita ya ji wannan dadaɗan sanyin ya ratsa shi. Kan sa tsaye ya nufi inda yake jin sanyin na fitowa wanda hanyar ɗakin Nana ne. A corridor din gurin ya yada zango, ya samu guri ya zauna, ya jingina da jikin bango yana numfarfashi. ***** Kwanaki biyu a tsakani, aka kuma zama, sai dai a wannan karon ba da duka Imam ɗin aka zauna ba, Hammad ne kawai, sai manyan masu faɗa a ji na kusa da Sultan, wanda an yi zaman ne saboda abin ya shafi Hammad ɗin. Sardauna ya yi gyaran murya ya ce "Imam Hammad, kamar yadda Tafawa ya buƙata da shi da wasu daga cikin 'yan majalissar Sultan. Lallai mu na buƙatar jin gamsashshiyar amsar ina zobenka na tambarin Imam yake? Gamsashshiyar amsa mai cike da hujja muke so, na wai-wai ko kame-kame ba, dan ka san muhimmancin zoben idan babu shi dole za ka sauka daga kan muƙamin da ka ke kai. Abu na gaba, mu na buƙatar sakamakon rahoton lafiyarka, na tsawon lokacin da a ka ce ka shafe a faransa kana jinya. Kuma hakan baya nufin za a canza umarnin da Sultan ya yi? Zuwanka faransa wakiltar Agadez wajibi ne bisa ga sahalewar Sultan. Kai kuma Tafawa, duk da uba ne kai ga Imam Hammad, kuma uba a Agadez za a hukuntaka bisa ɗaga murya da yin jayayya da hukuncin da Sultan ya aiwatar, kamar yadda kwamitin ladabtarwa da sulhu ya yanke. Zaka kawo mana cikakkiyar shaida da hujja, ba wai-wai ko kame-kame ba, a kan Imam Hammad yana ɗauke da larurar ƙwaƙwalwa, akasin haka za'a yanka maka tara mai yawan gaske ka biya shi. Haka zalika an hukuntaka bisa amfani da kausasan laffuza a kan Imam Hammad, wanda yake shugaba ne da yake jagorantar Imam, da ake sanya ran zaman su sarakan gobe. Dan haka an dakatar da kai tsawon watanni shida, har sai ka gabatar da abin da aka nema daga gare ka" Cikin fusata ya miƙe ya ce "Ai dama na sani, wata maƙarƙashiyar da manaƙisar ake ƙulla mini, saboda ba a ƙaunata. Amma shi Jalaludeen ya musa cewar ɗansa mahaukaci ne mana. Ciwon hauka ya yi suka kai shi suka ɓoye amma aka ce jinya ya yi a ƙasar waje. Ba ku burge ni ba da ba sauke ni kuka yi daga muƙamina ba har abada ai. Kuma na faɗa na maimaita, Hammad ba zai taɓa zama Sultan a Agadez ba, ba shi da lafiyar zuciya, ba shi da ta ƙwaƙwalwa kuma ba shi da magaji juya ne, dan haka mai baƙin baya ba zai yi mulki a Agadez ba" Wani irin duka Hammad ya yi wa teburin gabansa da ya bayar da wani irin sauti. Ya kalli Tafawa ya ce "'yar ka zaka tuhuma ya aka yi ba ta haihuwa? Ni mahaukaci ne ka zagaye Agadez kana maimaita hakan, kuma ba ni da lafiyar zuciya shi ma ban damu ba, na yi sarauta ko kar na yi bai dame ni ba, duk abu dai ka san kujerar Sultan ta fi ƙarfinka. Duk abin da za ka faɗa a kaina ka faɗa amma kar ka sake kira na da Juya mai baƙin baya, Asal ita ce juya ita zaka bincika dan ni ina da ɗa, na haihu ba baƙin baya ne da ni ba! Zobe kuma ya ɓata ban san inda yake ba" Ɗif gurin ya yi, tamkar an yi ruwa an shanye, ko kuma babu mai sauran numfashi a gurin, saboda yadda maganganun nasa suke buƙatar fashin baƙi gwari-gwari. ***** Hajiya Amina cikin damuwa da nuna rashin jin daɗinta take duban Alhaji Zailani ta ce "Alhaji ban ji daɗin yadda ka yi wa yaron nan mijin Shukura ba. Tare da mu da shi ake ta faɗi tashin neman Shukura, bai kamata a ce gaya masa maganganun da suke nuni da cewar wai zarginsa ka ke yi da sace Shukura ba" Ya dube ta ya ce "To dan yana mijinta kar na zarge shi? Duniyar nan fa babu abin da ba zai iya faruwa ba, ni bincikena ba zai bar kowa ba, ya zama dole a binciki kowa, kuma ki rabu da ni da abin da yake damuna, ki ƙyale ni da maganar sani mijin Shukura" Ta ce "Shikenan, ni ina gudun kar daga baya a zo a ji kunya ne" Ya ɗan ɗago da sauri ya ce "Me ki ke nufi?" "Ahh a zo a ganta a gano ba shi da hannu a ciki, su ci gaba da zama da matarsa kai ka zo ka na jin kunya" Ya yi guntun tsaki, yana sake miƙe ƙafafuwansa a kan gadon. ***** Jamila ce a kwance dare ya tsala, amma ta yi ƙurii tana kallon roofing ɗakin. Tun da Abba ya koma ga Allah, bacci ya ƙaurace wa idanunta. Idan kuwa bacci ɓarawo ya yi awon gaba da ita, to tabbas mafarkin Abba za ta yi ta yi, tana ganin sun yi aure ga yara ta haifa masa. Sannu a hankali ta tafi tunanin abin da ya faru. Bayan da Hajiya Sa'a ta yi mata bayanin yadda za ta sadaukar da ɗan gidan Alhaji Fatuhu ƙaninta. Abin ya dame ta, ga shi ta san idan ta je ta sanar wa su Alhaji Fatuhu, asiri ne zai tonu har ita, kuma ma mene ne shaidarta, dan ta san tsaf Hajiya Sa'a za ta zame ta bar ta a ciki. Ta yi tunanin ko ta sace 'yar tsanar, amma ta fasa, saboda yadda ta rabu da ta ta da ƙyar. Bayan fitar Hajiya Sa'a, Jamila na kwance a falo bacci ya ɗauke ta, ta yi mafarkin 'yar tsanar nan a ƙone ta yi baƙi ta biyo ta tana ƙoƙari shige mata cikin riga tana wani irin kuka tsiii-tsiii. Cikin ihu ta tashi a razane. Lokacin Abba ya shigo ɗakin, kawai ta cakume shi tana ihu. "Ƙanwata lafiya kuwa?" Ya yi maganar yana kallonta, a hankali ta cika shi, ta nemi guri ta zauna ta ce masa tsorata ta yi a bacci. Ya zauna yana yi mata nasihar mafarki ba gaskiya ba ne, kuma ta din ga addu'a, idan ba haka shaiɗanu za su iya shiga jikinta saboda wannan tsoron da take ji. Sai dai har ta tafi gida, a tsorace take kuma tunani take yi, yaya za ta yi ta tseratar da ɗan Alhaji Fatuhu. Ta rasa abin da yake yi mata daɗi, ga 'yar tsana ta sako ta a gaba a mafarki, yanzu bin ta take yi da sata sharɓeɓiyar wuƙa a mafarkin za ta kashe ta. Kawai ta yanke wata shawara a ranta, wajen ƙarfe sha ɗaya ta je gidan Hajiya Sa'a, lokacin bata nan ta fita gantalinta, cikin sa'a ta duba inda ta ajiye 'yar tsanar da tarkacen kayan tsafin ta ga su na nan. Ta kira Abba a waya, bayan sun gaisa ta tambaye shi yana ina, ya ce mata ya tafi kasuwa ta ce masa ya zo tana gidansu tana son ganinsa. Ba a yi awa ɗaya ba sai ga shi ya dawo, har da tsaraba ya sayo mata, cike da murnar ganinta, dan kwana biyu ta ɗauke ƙafa da zuwa gidan. Yanayin walwalar da ta gani a fuskarsa sai ta ji dana sanin kiransa da ta yi. Sai dai ya takura mata a kan lallai sai ta gaya masa abin da ya sanya ta kirawo shi. Ta ɗebo tarkacen nan na kayan tsafin Hajiya Sa'a, ta Zazzage masa a gabansa. Cikin mamaki ya dube ta ya ce "Mene ne wannan haka?" Ayshercool 08081012143 79 Tabbas ba ka san ko mene ne ba, kuma na san za ka yi mamakin mene ne wannan ɗin, amma ina mai baka haƙurin abin da zai fito daga bakina, ba ni da wani zaɓi ne nima, ina son yin ceton rai, na rasa wanda zan gayawa ya fahimce ni ya sama mini mafita ya rufa mini Asiri sai kai" Ta yi maganar cikin kuka. Cikin damuwa da ƙaguwa ya ce "Babu komai, ko mene ne gaya mini. Wallahi Jamila ina jin ki a raina fiye da yadda ki ke zato, ki gaya mini dan Allah" Ba ta tsallake masa komai ba, tun daga tariyar Maman Khairat a unguwar su, da fara zuwa gidanta zuwa haɗuwa da Hajiya Sa'a, ta gangaro har kan neman jinin Nana yadda suka saka ta a ƙungiyar asiri abin da aka yi mata, hatta labaran da Hajiya Sa'a ta ba ta na yadda ta shiga ƙungiyar sai da ta gaya masa. Jamila za ta iya cewa tun da take, ba ta taɓa ganin idanun ɗan Adam sun yi jan da na Abba suka yi ba. Ya ƙame a guri ɗaya tamkar babu rai a jikinsa. Cikin rikicewa ta ce "Dan Allah Yaya Abba ka yi haƙuri ka yafe mini, ban gaya maka dan na haɗa ka da mahaifiyarka ba ko makamancin haka, ceton rai nake fatan mu yi, bawan Allah nan da yake rashin lafiya kar ya kuma rasa ɗan sa. Kuma dama ni na san mutuwa zan yi, dan ba zan iya bayar da kowa ba ga barazana kuma da ake ta yi mini a mafarki. Dan Allah ka yafe mini ban faɗa dan na haɗa ka da mahaifiyarka ba. Idanunsa suka fara tsiyayar da hawaye, yayi kuka, ya yi kuka, Jamila kuma ta kasa rarrashinsa, can ya ce "Tabbas! Biri ya yi kama da mutum, yanayin facakar da Mummy take yi da kuɗi tamkar ba ta san zafin neman su ba abin yana ɗaure mini kai. Ina kula da harkokin kasuwancinta, amma na san abin da take kashewa ya ninka abin da muke samu. Kuma duk yadda zan bi na gano wani abu sai ta toshe. Jamila na ji daɗi sosai da sosai, da ba ki gaya wa wani abin da take aikatawa ba, kuma na ji daɗin ƙoƙarin kare kisan ɗan ɗan uwanta. Amma na yi mamakin yadda ta iya bayar da mahaifinmu saboda abin Duniya. Ita ma idan ba ta sadaukar da kowa ba mutuwa za ta yi ko?" Jamila ta jinjina masa kai tana kuka. Ya ce "Shikenan, babu komai, ki daina kuka, daga ke har ita ba zaku mutu ba, zan zama abin sadaukarwar ku, sai dai daga ni ina fatan duk yadda za ki yi ki fita daga cikin kungiyar nan. A razane Jamila ta ce "A'a ba zai yiwu ba, ban gaya maka dan ka ɗau wannan ɗanyen hukuncin ba, mafita zaka nemo" Abba ya ce "Wace mafitar Jamila? Na nuna wa Mummy na san abin da take yi? Ko na bari ke ko ita wani ya rasa ransa? Ko kuma ɗan Kawu Fatuhu da bai ji ba bai gani ba? Dan Allah Jamila duk yadda za ki yi kar ki yadda ki bayar da jinin wani, ki kuma bar kungiyar nan. Wallahi Jamila kuɗi ba su ne kwanciyar hankali da nutsuwar ɗan Adam ba." "Yaya Abba to me zaka yi?" "Ni zan zama abin sadaukarwar taku?" Ta girgiza kai ta ce "Ba zai yiwu ba gaskiya, na bayar da jininka kenan, ai gara ni na bayar da jinina ba zai yiwu ba" Ya ce "Ba ke za ki bayar ba, ni zan bayar da kaina, ina fatan hakan ya zame wa Mummy darasi, ya kuma yi silar fitarta daga abin da take aikatawa" Cikin kuka Jamila ta riƙe hannunsa ta ce "Idan ka yi haka ka kashe kanka fa kenan?" "Jamila wa zan tunkara ya lalata Wannan abun asirin Mahaifiyata ya tonu tana Kungiyar asiri? Wane kallo ɗan uwanta zai yi mata? Ke idan aka ce ki na kungiyar asiri wane kallo al'umma za su yi miki ko bayan kin tuba? Ina roƙonki dan Allah ki rufa mata asiri kar ki gaya wa kowa wannan maganar" Ya ƙarasa maganar yana tashi tsaye, ya hau tattare kayan. Rikicewa ta yi tana ƙoƙarin hana shi, amma ya ture ta ya ɗebe, ta riga ta yi masa bayanin duka yadda ake amfani da kayan. Dan haka ya buɗe alawoyin da ta yi niyyar zuwa ta ba wa Muhsin, ya saka a bakinsa. Ya nufi hanyar fita ya dakata ya ce "Idan na rayu shikenan, idan kuma an yi amfani da jinin nawa, ki tabattar wa Mummy ni ne sadaukarwata na shekara, kuma ki roƙa mini ita gafara, da kuma na zama ni ne mutum na ƙarshe da zai rasa ransa a dalilin nan duniyarta, ta tuna inda na tafi ita ma za ta tafi" Jamila ta yi kuka da dana sanin gaya wa Abba maganar nan. Yana zuwa ɗakinsa ya ɗau biro da takarda ya yi rubutu, ya caka alluran nan a jikin 'yar tsanar, kawai ya ga ta ɓace daga hannunsa. Bai razana ba, ya saka hankicin a ƙasan fulonsa. Bai yadda ya haɗu da Hajiya Sa'a ba, har dare ya yi yana ƙule a ɗaki, ya kwana a kan fulon da jan ƙyallen, wanda shi ma ya ɓace daga baya. Jamila ta yi kuka tamkar ranta zai fita, dan faɗiwar gaban da ta ji ce ta tabbatar mata da cewa Abba ya aikata abin da ya ce, kuma ƙungiya sun shanye masa jini. ***** Da ƙyar Abduou matawalle ya yi gyaran murya ya dubi Hammad ya ce "Yanzu Hammad har wuyanka ya yi kaurin da zaka din ga sa in sa da mu? Bamu san ka da haka ba, wannan ba halinka ba ne ba. Kuma ya zama dole a ladabtar da kai bisa nuna rashin ɗa'ar da ka nuna." "Da na ce mahaukaci ne ai ba a yarda ba, yanzu ga haukan nan yana yi " Tafawa ya yi maganar a harzuƙe. Cikin nutsuwa Imam ya ce "A cikin hayyacina nake, ina da ɗa, ka gaya wa ko a ciki da wajen Agadez " Sardauna ya dakatar da taron ya sallami kowa banda Imam Hammad, da Abdou matawalle sai kuma Sultan. Sardauna ya ce "Na san maganganun Tafawa ne suka yi maka zafi ka ke wannan iƙirarin, amma wannan soki burutsun naka, babu abin da zai haifar sai ƙarawa wuta fetur. Kaf faɗin Agadez Asal ce matarka, kuma tun da ku ka yi aure ba ku haihu ba, ko ka na da saɗaka ne bamu sani ba". "Allah ya taimaki Sardaunan Agadez, ni fa ba ƙarya nake yi ba, kuma ba soki burutsu nake yi ba. Ina da ɗa" Matawalle ya ce "Wai wani irin ɗa a na zaune ƙalau? Yaushe Asal ɗin ta haihu ba mu sani ba?" Ya girgiza kai ya ce "Asal ba ta haihu ba, ɗa na kuma ba shi da alaƙa da kowace mace a Agadez a ma Nijar gaba ɗaya" Sultan da ya fara harzuƙa ya ce "Kai ba na son shashanci fa, zan ci maka mutunci yanzun nan, wane irin shirme ne haka? Ko sai ka gazgata maganar Tafawa cewa baka da hankali" Cikin girmamawa ya ce "Tuba nake ranka ya daɗe, amma idan an bani dama zan yi bayanin komai". Abduou matawalle ya ce "Mu na sauraren ka". Ya ciro wayarsa a aljihunsa, ya daddana. "Ga Balaraba can tana jiran ki, ana neman ki a gidan Sultan" Nana ta ajiye tukunyar da take wankewa, ta kalli Asal ta ce ana nema na kuma a gidan Sultan? Laifi na yi?" "Idan kin je kya ji. Nima ban san me ki ka yi ba, Imam ne ya ce a kai ki" Gaba ɗaya sai jikin Nana ya yi sanyi, ta kammala abin da take yi a gurguje, ta shirya ta bi Balaraba. Su na tafe ta ce "Mama Balaraba, ko kin san abin da na yi ake nema na?" "A'a nifa Gimbiya ce kawai ta ce na raka ki? Amma idan kin san babu abin da ki ka yi, bai kamata ki ɗaga hankalinki ba, wataƙila Imam Hammad ne kawai yake neman ki" Cikin sanyin jiki Nana ta ce "Kuma a gidan Sultan?" "Eh wataƙila alkhairi ne, ko kuma girkin za ki yi" Duk da wannan kalaman na ƙwarin gwiwa, da Balaraba ta faɗa wa Nana, ita dai Nana ta ji ba ta gamsu da kiran ba. Tun daga nesa aka dakatar da Balaraba, aka turo wani ya shiga da Nana. Nana ta yi turus, bayan ganin manyan mutane har da Sultan a wajen, gabanta ya yi wata mummunar faɗuwa, suka yi mata wani irin kwarjini ta ja ta tsaya a bakin ƙofar tana rarraba idanu. Su ma duk suka zura mata idanu, su na mamakin ita wannan da aka kirawo, me ya kawo ta nan. "Ƙaraso mana" Sayyid ya yi maganar yana kallonta. Sai ta diririce ta kasa gaba ta kasa baya. Da kansa ya fara takawa, yana tunkarar inda take, yana zuwa ya kamo hannunta, yana tafe tana bin sa a baya har zuwa tsakiyar gurin. Bai saki hannunta ba ya kalli idanunta ya ce "Ma Vie" Gabanta ne ya yi wata irin mummunar faɗuwa, tsigar jikinta ta tashi, numfashinta ya fara fita sama-sama, jin abin da ya fito daga bakinsa tamkar almara. "Ki shaida musu ni ba juya ba ne, ina da yaro" Ƙoƙarin ja da baya ta fara yi, tare da son fizge hannunta tana girgiza masa kai. Sardauna ya ce "Imam, wace ce wannan ɗin? Me ka ke ƙoƙarin yi ne haka?" "Matata ce, ita ta haifa mini yaro" Ya ba shi amsar yana kallon Nana da idonta ya yi ja, ya cika da hawaye. Cikin rashin fahimta Matawalle ya ce "Ta yaya, wace ce wannan ɗin daga ina take?" Hammad ya yi shiru bai ce komai ba, shi kuwa Sultan tuni ya karaya, bayan ganin asirin Hammad ya tonu na taɓin hankali sa saboda soki burutsun da yake yi. Sardauna ya ce "Wai Imam kan ka ɗaya kuwa? Ita wannan ɗin daga ina ka samo ta, ta ina ta zama matarka?" Matawalle ya dubi Nana ya ce "Ke Baiwar Allah, daga ina? Kuma mene ne alaƙarki da shi?" Cikin ruɗewa da hawaye Nana ta ce "Ni babu wata alaƙa tsakanina da shi, aiki kawai Gimbiya Asal ta ɗaukko ni na yi mata, ni ban san shi ba" Hammad ya girgiza kai ya ce "A'a Husnah, kar ki ji tsoro, ina tare da ke. Kar ki yi mini haka dan Allah" "Dan Allah ka yi haƙuri ni ban san ka ba" Ta yi maganar kuka mai ƙarfi na ƙwace mata. "Cika ta tafi" Sardauna ya yi maganar cikin bayar da umarni. A hankali ya saki hannunta, ta juya da sauri ta fice. "Hammad, anya maganar Tafawa babu ƙamshin gaskiya a cikin ta, na ga baƙa ce kamar ma ba 'yar ƙasar nan ba ce? Meye haɗin ka da ita?" Ya yi shiru ya sunkuyar da kai ya ƙi magana. Sultan ya yi gyaran murya ya ce "Ina ga a bari zan yi magana da shi" Nana kuwa tun da ta fita take kuka, tana zuwa babu kowa a falon, ta wuce ɗakinta ta tattare kayanta cif ta yi waje. Sauri take zumbuɗawa tamkar za ta tashi sama, tana tafe tana fatan Allah ya bata nasarar ficewa daga gidan, ba tare da dakarun Asal sun ganta ba su hana ta fita, kamar yadda suka taɓa yi mata aka hana ta fita daga gidan. Sai dai ba ƙaramar tafiya ba ce ba, daga sashen da gidan Imam Hammad yake a cikin gidan zuwa shi kansa gidan. Ta sha doguwar tafiya kafin fita babban gate. Masu gadin ƙofar suka ƙare mata kallo ɗayan ya ce "Maraɗi za ki tafi ko? Ga mota can Imam ya ce a kai ki" Ta girgiza cikin mamaki ta ce "Ba zan hau ba, ni ba can zan je ba" "Idan ba za ki hau ba, ga wannan ya ce a baki" Aka miƙa mata envelope. Ba ta duba meye a ciki ba, ta karɓa suka buɗe mata ƙofa ta fice. Tana tafe tana waiwaye tana fatan kar a biyo ta a mayar da ita gidan nan. Ta ƙudurce a ranta, tana zuwa gidan Nene za ta ɗauke Muhsin ta yi Nigeria. Sai dai tana tafe tana kuka zuciyarta cike da takaici, yanzu dama duk tsawon wannan lokacin Sayyid ya gane ta. Amma ya bari take ta wahala saboda shi, ya ci amanarta bai yi mata adalci ba. Ba ƙaramin gudu motar da ta hau take yi ba, amma gani take kamar ba a sauri. Ta buɗe envelope ɗin da aka ba ta kuɗi sabbi kar a ciki. Sai wata takarda. "Dan Allah ki samu nutsuwa, za mu yi magana Asmy, kar ki yanke mini hukunci a yanayin da ki ke" Wani uban tsaki ta ja a fili. Tana furta "Ba ka yi mini adalci ba, ka cutar da ni" Ta yi maganar kaɗan-kaɗan. Sun sha tafiya ba kaɗan ba a hanya, kafin su isa Maraɗi. Daga nan Nana ta nemi abin hawa zuwa garin da suke da Nene. Sai dai tana zuwa ta tarar da gidan a rufe, ga babu waya a hannunta. Cikin matsananciyar damuwa ta shiga gidan su Ashura. Ashura na ganinta ta hau tsalle ta rungume ta, Nana ta maze suka gaisa cikin yaƙe. Suka din ga yi wa Nana maraba da zuwa, mutan gidan su na ta yaba yadda Nanan ta yi haske ta ƙara ƙiba. Nana da gabanta ke tsananta faɗuwa ta ce "Nene fa, ko ta tafi gurin sayar da Abinci?" "A'a Nene kusan kwana huɗu ba ta nan" Gaban Nana ya faɗi, ta ce "Ba ta nan ina ta tafi?" "Gaskiya ba na tunanin akwai wanda ta yi wa sallama, kawai dai gani muka yi ba ta nan" "Babar Ashura, dan Allah ku bani aron waya na kira ta" Ta yi maganar cikin tashin hankali, muryarta na rawa. Aka ba wa Nana waya, ta saka lambar Nene, wayar ta shiga, amma ba ta ɗauka ba. Nana ta kasa zaune ta kasa tsaye, ji take yi tamkar ta kurma ihu, gaba ɗaya ta rikice, ta ji numfashinta yana fita sama-sama. Da kyar ta iya daidaita nutsuwarta ta gabatar da sallolin da suke kanta. Su ka kawo mata abinci, amma ta ƙi ci, ta yi musu sallama ta ɗauki kayanta ta fice. Gidan Hajara ta nufa, inda suka kawo ta gidan Nene. Hajara ta din ga murna ganin Nana, suka rungume juna cikin farin ciki, duk da Nana cikin tashin hankali take. Hajara ta kawo mata Abinci, ta din ga jan ta da hira. Nana ta numfasa ta ce "Na je gida gurin Nene, na tarar ba ta nan, ga babu waya a hannuna, ko za ki kira mini ita a wayarki?" Hajara ta ce "Bari na kira ta" Sai da aka kira sau biyu, sannan Nene ta ɗaga. Cike da rawar jiki Nana ta ce "Nene" "Na'am Nana, ki na lafiya?" Nana ba ta amsa ba ta ce "Nene na zo ba kya nan, na kira wayarki ba kya ɗagawa ina ku ka tafi?" Nene ta numfasa ta ce "Nana ina mai baki haƙuri, baban ɗan ya zo ya karɓi ɗan sa" Cikin matsanancin tashin hankali Nana ta tashi tsaye ta ce "Nene waye baban ɗan? Nene wa ki ka ba wa ɗa na? Haka muka yi da ke Nene?" "Dan Allah Nana ki yi haƙuri, nima fin ƙarfina aka yi, babu yadda na iya, masu garin ne" "Nene ba ki kyauta mini ba, bamu yi haka da ke ba, dan zatin Allah Nene ki gaya mini inda ɗa na yake, dan Allah Nene, ki yi mini rai ki bani ɗa na" Nene ta ce "Nana da zan cutar da ke, da ban zauna da ke tsawon wannan lokacin ba, yadda muka yi a rubuce, haka ya karɓi ɗan sa a rubuce da hukuma, idan na hana su matsala zan shiga" Cikin rauni da hawaye Nana ta ce "Nene waye ya karɓe shi?" "Imam Hammad Jalaludeen Agadez " "Na shiga uku" Nana ta furta cikin matsanancin kuka da tashin hankali. AREWABOOKS Cikin tausayawa Hajara ta ce "Dan Allah Nana ki yi haƙuri ki daina kukan nan haka? Kuma wai me yake faruwa ne?" Nana ba ta saurari Hajara ba, ta ci gaba da kuka, tare da lissafa yadda za ta ninka ta koma Agadez, ta ƙudurce a ranta gara ajalinta ya riske ta, a yi duk wadda za a yi ta karɓi ɗan ta, ko hakan zai yi silar tarwatsewar Agadez gaba ɗaya.', a kan ta tafi ta bar ɗan ta, a wannan gidan. Bugun ƙofar gidan aka din ga yi da ƙarfi ana sallama. Hajara ta tashi ta fita, ba a jima ba ta dawo, ta dubi Nana ta ce "Ki na da baƙi a waje" Nana ta ɗago jajayen idanunta da suka kumbura saboda kuka ta ce "Suwaye?" "Ki je ki gani, baƙinki ne dai" Nana ta yinƙura ta tashi ta fita, tana jan ƙafafuwanta, mutum biyu ta gani cikin kaaki, sai ɗaya da rawani, ya rufe fuskarsa sinkif, ba ta ganin komai sai idanunsa, duk da hakan bai hana ta yi masa kallon sani ba. Ba ta tsaya takura wa kanta ina ta san shi ba, saboda matsananciyar damuwa da tashin hankalin da take ciki. Cikin girmamawa ya ce mata "Barka da wannan lokaci" "Yauwwa sannu" Ta furta da dasashshiyar muryarta. "Imam Hammad ne ya aiko mu, ya ce mu tafi da ke" Ta yi wa mai maganar wani irin mugun kallo ta ce "Ya aiko ku ku tafi da ni ku kai ni ina? Ba zan bi ku ba, babu in da zan je" "Gurin yaronki za a kai ki" Sai kuma ta yi turus tana kallon su. "Tafiyar da ɗan nisa, ki ɗaukko kayanki, inda yaronki yake ya ce mu kai ki" Ba ta tsaya ta zurfafa tunani ba, ta shiga cikin gidan. Hajara ta ce "Nana yaya?" "Tafiya zan yi" "Ki je ina? Wai ni, me ya haɗa ki da Buzayen nan ma? An ce mini daga gidan Sultan ɗin Agadez aka zo gurinki, me yake faruwa ne?" "Zan yi miki bayani daga baya, bari na je tukuna" Ta ja jakarta, ta yi waje. Wata irin haɗaɗɗiyar mota ce, ta haɗu ga kyau ga wani daddaɗan sanyi da take fitarwa. Sai dai Nana ba ta tsaya tantance kyan motar ba, lissafinta kawai Muhsin ya zo hannunta, ta gudu. Dan ko me za a yi ba za ta bayar da ɗan ta ba, kuma ba za ta bar Nijar ba sai Sayyid ya sake ta. Sun sha tafiya, kafin su isa wani irin ƙaton gida, sai da ta ga an shiga gidan, ta waiwaya ta ga an rufe jibgegen gate ɗin gidan, sai kuma tsoro ya fara kama ta, dan ta san barin wannan gidan ba abu ne da zai yi sauƙi ba. Sai dai hanakalinta baki ɗaya ya fi karkata, ga ta yi tozali da ɗanta, ta san a halin da yake ciki. Ta sauka daga motar ta tsaya tana rarraba ido, mai rawanin ya yi mata jagora zuwa katafaren falon gidan. Ya sauke rawanin fuskarsa ya ce "Akwai banɗaki, da abinci, ki yi salla ki ci abinci kafin Imam ya zo" Wata irin muguwar razana Nana ta yi, ta ce "Sule? Kai ne dama? Me yasa..? Ta rasa wace tambayar ma yakamata ta ƙarasa. "Ki yi haƙuri, ba ni da damar ce miki komai, ki yi salla tukuna" Nana ta ƙara rikicewa kanta ya kulle. Da kyar ta samu ta yi sallolin. Jikinta sai ciwo yake yi saboda azabar zirga-zirgar tafiya ga cikinta babu komai. Gaba ɗaya rarraba ido kawai take yi, tana tunanin ta ina za ta ga Muhsin, ga fafur Sule ya ƙi tsayawa ya yi tafiyarsa ya bar ta sai itakaɗai, balle ya yi mata wani gamsashshen bayani. Jin ana turo ƙofar falon, ya sanya ta miƙe tana ƙara leƙawa ko za  ta ga Muhsin. Sai dai ba ta ga Muhsin ba sai baban Muhsin, yana sanye cikin baƙar jallabiya, ya yafa hirami a kansa, bayansa kuma Mahmoudu ne, wanda ta fi sani da Habu. Razana ta yi, ta tsaya ƙyam tamkar an dasa ta, ta haɗiye wani abu mai masaifar zafi tamkar wuta a maƙogwaronta zuwa ƙirjinta. Ya kalli idonta, yana ƙoƙarin tantance wane irin kallo take yi masa, ya rasa ta ina ma zai fara. "Ina ɗa na?" Ta jefa masa maganar a zafafe tana huci. Habu ya matso gaba ya ce "Nana, ki yi haƙuri ki ci abinci ki huta, ki samu nutsuwa, sai mu yi miki bayani" "Bayani? Wane bayanin nake buƙata bayan wanda na gani? Kun cuce ni, na ƙarar da lokacina ban tsinana wa rayuwata komai ba, na tsaya na yi biyayyar aure na rabauta, ashe mutumin da nake tausayawa azzalumi ne, kuma mugu ne. Kun zalunce ni kun yaudare ni, kun ɓoye mini abubuwa da dama, ba dan ba ni hakkinku ba Allah ya saka muka haɗu ba, da shikenan haia zan ci gaba da gararamba, ba ni da makoma. Ba zan yafe muku ba. Allah ba zai bar zaluncin da ku ka yi mini ba. Ka bani ɗa na dan ba ɗanka ba ne, baka da hurumi da shi Muhsin ba shi da uba na zaɓi ya tashi da wannan tambarin da ya san ubansa azzalumi ne da ya wofantar da rayuwar mahaifiyarsa". Wata irin suka maganganun Nana suke yi wa zuciyarsa, amma ya san koma Nanan ta faɗa a kansa, ba ta yi laifi ba, ya kuma cancanci hakan daga gare ta. Mahmoudu ya ce "Nana, kin san wa ki ke gaya wa haka? Mijinki ne fa?" Cikin kuka ta girgiza kai ta ce "Wannan ba mijina ba ne, mijina Buzu ne da bai san waye shi ba, babu kowa a duniyarsa sai matarsa da ta nuna masa ƙauna saboda Allah. Ba wannan mayaudarin da ya yaudare ni da cewa ni rayuwarsa ce ba, na yi asarar lokacina a kan nemansa ba. Ka bani ɗa na ka haɗa mini da takardar sakina na koma ƙasata na sama wa rayuwata mafita" Ta yi maganar tana riƙe rigarsa tana kuka mai fallasar da dubban damuwoyin da suke binne a ƙarƙashin zuciyarta tsawon lokaci. "Ma vie" ya furta a kasanlance idanunsa fal hawaye, yana kallon ƙwayar idonta. "Kar ka sake kira na da wannan sunan da na fi tsanar ji a rayuwata, Ni da nake mummuna, baƙa 'yar Nigeria da ba kowa ba hadima kuma baiwar da ake ci wa mutunci a gaban wanda yake yi mini iƙirarin ni rayuwarsa ce yana ji kuma yana gani. Wataƙila ma alhakin iyayena ne ya kama ni, da na baro su saboda wauta irin ta soyayya da ƙoƙarin sama wa ɗa na mafitar rayuwa. Ka bani ɗa na ka sake ni na koma inda na fito" Ta yi maganar tana zare masa ido tamkar numfashinta zai ɗauke. Ya saka hannunsa yana ƙoƙarin kamo ta jikinsa, amma ta yi baya tana kai masa duka ta ko ina, cikin kuka tana faɗin "Na tsane ka, na yi nadamar saninka, rayuwata da kai bai amfana mini komai ba, ban taɓa zaton za ku iya haɗa kai ku cutar da ni haka ba, ka bani ɗa na na gaya maka" Mahmoudu sai da ya tsure, ganin yadda kamaninta har canzawa suka yi saboda faɗa, idanunta tamkar ta tauna barkono saboda ja, ga ambaliyar da hawaye suke yi a fuskarta. A ɗan iya sanin da ya yi mata, tana da sanyin hali, banda tsiwa da ta kan yi wasu lokutan, bai taɓa tunanin za ta iya burkicewa haka ba. Shi kansa Imam Hammad sai da ya tsorata, yanayin da take ciki ya tabattar masa, sai ya yi aiki tuƙuru kan ma ya samu ta saurare shi. Ya shammace ta ya damƙe ta, ya nufi wata hanya da ita, ta din ga fizge-fizge, tana ci gaba da kuka da turjewa. "Ki nutsu, kar ki yi mini asarar cikin da yake jikinki" Wani irin burki ta ci, cike da rikicewa jikinta na tsuma, ji take tamkar ba ta ji daidai ba, sai dai kafin ta tantance, jikinta ya saki ta yi baya za ta faɗi ya riƙe ta. Jikinta ya yi sanyi ƙalau, sai hawaye da yake fita daga gefen idonta. Da haka ya yi nasarar shiga da ita ɗakin, ya kwantar da ita a kan gadon. Ya zare mata hijjabin jikinta. Ya zura mata idanunsa, a hankali yake lumshe su yana buɗewa a kan ta. Ya kamo hannayenta a cikin nasa, ya sumbaci hannayen, sannan ya ce "Duk abin da ki ka yi mini, kuma duk abin da ki ka kira ni da shi, na cancanta, ban kyauta miki ba, na sani ban kyauta ba, amma ki bani dama ko sau ɗaya ne ma viee, sau ɗaya tak, ki bani dama na ce wani abu. Na san ba halinki ba ne, wannan ba halin Husna ta ba ce, amma na karɓi laifina ki yi mini afuwa. Ban yi abin da na yi domin na zalunce ki ba" Ya yi maganar yana kwantar da kansa a ƙirjinta yana sauraren yadda zuciyarta ke bugawa da wani irin matsanancin sauri. ***** Asal ce take ta shiga tana fita cikin takaici, bayan jin Nana shiru ba ta kawo Abincin safe ba, ga babu alamar na rana, kuma ba  ta gyara sashen ba. Ita a tunaninta tuni ta dawo daga kiran da aka yi mata a can gidan Sultan. Takaici ya ishe ta, dan ta tsani zuwa ɗakin da Nana take a ganinta ƙasƙanci ne, amma jin shirun ya yi yawa, ta fara duba kitchen ba ta nan, ta wuce ɗakin Nana, saboda ya ci a ce ta dawo, duk da ba ta san kiran me Imam ya yi wa Nana ba. Sai dai tana zuwa ta ga wayam, hatta kayan Nana babu sai katifarta. Cikin tashin hankali ta fito ta tara su Balaraba da sauran ma'aikatan cikin gidan. Duk su ka taru "Wai gidan uban wa yarinyar nan, mai yi wa Imam girki ta tafi? Tun jiya ba ta gidan nan, hatta kayanta ta tattara ta tafi ta bar gidan nan." Cikin girmamawa Balaraba ta ce "Wallahi ranki ya daɗe, bamu ganta ba, kin san ta koma cikin sashenku, ba ganinta ma muke yi ba" "A ce kaf cikinku babu wanda ya ga fitarta?" Suka yi shiru, su na sauraren jarabar Asal. Ta ƙare musu rashin mutunci, ta sallame su. Kai komo ta din ga yi tana tunanin ina Nana ta tattara kayanta ta gudu? Haka kurum ta din ga jin kamar akwai abin da Nana take ƙullawa ta bar gidan. Tana komawa sashenta, ta tarar da tarin missed calls ɗin Tafawa. Cikin rawar jiki ta bi kiran wayar, aikuwa ya ɗaga hasale. "Wace irin wawuya ce ke, ina ta kiran wayarki amma kina can kina shashashanci ba ki ɗaga ba?" "Dan Allah ka yi haƙuri, ina can wani uzuri ne" "Uzurin banza uzurin wofi? Asal kin san me yake faruwa? Yau ni mijinki ya kalla ya ce mini na bincike ki, ke ce juya shi ba juya ba ne ya na da ɗa" Wani irin dumm maganar baban nata ta daki zuciyarta, ta ji wani banbarakwai, banda ba abokin wasanta ba ne, da ta ce ƙarya ya sharara mata, kuma da sai ta hukunta shi a kan hakan" "Na ji kin yi shiru?" "To ai na kasa ganewa ne, wai wane Imam ɗin ne yake da ɗan?" "Wanne ki ke aure? Kuma kaf cikinsu waye ba shi da ɗa ban da mijinki?" Cikin kuka ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, na shiga uku na lalace. Abba ya zan yi, ni Hammad zai yi wa haka? A ina yake da ɗan?" "Ki nutsu ki kwantar da hankalinki, haryanzu ban tabattar ba tukuna, ina ga faɗa kawai ya yi dan ya huce takaicinsa, kuma saboda tsagwaron munafunci aka sallami kowa daga zaman, ba a bari na ji ƙarshen zancen ba, amma zan bincika na tabattar da gaskiyar maganar?" Ba ta iya tantance sauran abin da yake faɗa ba, ta kashe wayar jikinta yana rawa, ta hau kiran lambar Hammad, sai dai shiru wayarsa ba ta shiga, ta kira ya kusa sau hamsin, amma shiru ba ta shiga. Ta yi jifa da wayar tana huci. "Wallahi Hammad, zancen nan ko ba gaskiya ba ne ba, sai ka fuskanci mummunan tashin hankali da abin da ba ka taɓa zato ba. Wallahi ta tabatta ka haihu da wata mace, sai an mutu har Liman." Ta zauna Jikinta yana wata irin tsuma ta tashin hankali. Sultan kansa ya kasa zaune ya kasa tsaye, dan babu yadda ba su yi da shi ya yi magana ba, bayan tafiyar Nana ba amma ya ƙi. Hankalin Sultan ya yi mummunan tashi, Abduou matawalle ne ya din ga rarrashin sa yana kwantar masa da hankalin a kan su bi komai a hankali, har su samu Hammad ya yi musu bayani dalla-dalla. Sultan ya ce "Matawalle, a tsorace nake, Tafawa ya yi nasara, ya yi nasarar tabattar wa da Duniya cewar Hammad mahaukaci ne, idan ba haka ba ta yaya zai zo ya ce yana da ɗa, ɗan ma ba da buzuwa ba, 'yar wata ƙasar bayan ya san me hakan yake nufi. Tafawa ya ce "Kar ka yi mamaki, yanzu dole mu jira ya yi magana, mu ɗan ba shi lokaci ya nutsu, dan mu tabattar jikin ne, ko kuma da gaske yake. Kar ka manta tsawon lokacin da ya shafe ba tare da mu ba, bamu san me da me ya faru ba, kuma kar ka manta a Nigeria a ka gano mana shi" Sultan ya goge gumin da yake tsatstsafo masa ya ce "Matawalle, akwai gagarumar matsala, babu buƙatar mu ba shi wani lokaci na daban, dole ya warware mana zare da abawa mu ji yadda aka haihu a ragaya. Kira mini wayarsa, duk inda yake a nemo shi, kuma a kira mini yarinyar ma" Matawalle ya ce "Haka ne, kuma a nemo  wannan munufukin yaron Mahmoudu, domin tabbas ya san komai, ya san duk abin da ya faru" "Wai ni ita yarinyar ma, ni kamar na taɓa ganinta, a ina aka samo ta ne?" Matawalle ya ce "Eh, lokacin da Hammad ya dawo, tana cikin waɗanda suka yi girki, wai Gimbiya Asal ce ta kawo ta" "Asal kuma?" Sultan ya yi maganar yana nazari. Sai dai duk tarin kiran wayar da aka yi wa Imam Hammad, ko sau ɗaya wayar ba ta shiga ba. Hakan ya ƙara jefa su a tashin hankali. A hankali Nana ta yi miƙa, dan tamkar ta ci wani abu, haka ta yi wani irin nannauyan bacci. Cikinta ne yake wata irin ƙara, saboda azabar yunwar da take ji. Ta yinƙura da ƙyar, za ta tashi zaune, ta yi tozali da kyakykywar fuskarsa, yana kallonta. Ja da baya ta yi tamkar ta yi tozali da wanda ba muharraminta ba. Ta kalli jikinta babu hijjabi, rigar jikinta ma an canza mata wata. "Kin tashi?" "Ina ɗa na yake? Kuma waye ya ce ka taɓa ni ka canza mini riga, waye ya baka wannan damar?" "Sadakina" ya ba ta amsa kai tsaye. Ita tsantsar mamakin halayyarsa take yi ma a yanzu, gaba ɗaya ya canza mata. "Na haɗa ka da girman Allah, ka bani ɗa na, ka bani ɗa na, ni ban sanka ba, ɗana kuma ba ɗan ka ba ne, dan Allah ka bani yarona na tafi, dan Allah ka taimaka mini, na karɓi yarona na koma ƙasata" Ta yi maganar hawaye na bin fuskarta. Ya wani lumshe ido yana murmushi ya ce "To ni kuma ina za ki kai ni idan ki ka tafi?" "Ni ban sanka ba" "Haba?" Yayi maganar yana ƙanƙance idanunsa. Wani marurun takaici ne ya ƙule Nana. "Ki tsaya ki saurare ni, na yi miki bayani" "Ni ba zan ji wani bayaninka ba, duk abin da zai fito daga bakinka, ba zan taɓa yarda da shi ba. Ka bani ɗa na na tafi" Sayyid ya yi ajiyar zuciya ya ce "To ki bari ki haifa mini abin da yake cikinki, ki bani abina, sai mu san abin yi" Daina ganewa Nana ta yi na wani ɗan lokaci, ta yi shiru ta tuna ya ce mata tana ɗauke da juna biyu ma ɗazu. Ta kalli cikinta, ta ɗago ta kalle shi, ya ɗage mata girarsa ɗaya. Ayshercool 08081012143 80 Gaba ɗaya kanta ya kulle, ta zuba masa idanunta da suka yi jawur. A mugun kasanlance ta ce "Ciki kuma?" Ya jinjina mata kai, ta rasa abin da za ta yi gaba ɗaya. Ciki yaushe? Yaushe wani abu ya shiga tsakaninsu da har za ta ɗauki ciki? Ta tambayi kanta, sai dai ta kasa tambayarsa. Sai tsare shi da ta yi da idanunta. Ya gyara zamansa sosai ya ce "Kina ji na?" "Babu abin da zan ji? Kar ka gaya mini komai, ba zan ji ba kuma ba na fatan ji. Abin da ka yi mini haka ma ya isa, ka bar ni na ji da kaina". Ta yi maganar a matuƙar zafafe. Ya ce "Shikenan na ji. Na rabu da ke. Amma ina so ki sani, muddin ba ki saki jikinki ba, ki din ga cin abinci ki rage wa kanki wannan damuwar ba, to fa ba zan ba ki Muhsin ba. Gwargwadon sakin jikinki, da cin abinci da zaki yi, shi zai sanya ki gan shi. Akasin haka kuma zan ci gaba da tsare ki a nan, na kai wa Asal shi ta riƙe shi, tun da dama ita Allah bai ba ta haihuwa ba. Wannan ma idan ki ka haifa ki bani abina tun da ba za ki saurare ni ba" Kallon ba ka da hankali ta yi masa. Ya yinƙura da kyar, jikinsa babu ƙwari, ya ɗauki hiraminsa ya rufe kansa ya fice ya bar ɗakin. A ɗaya falon ya tarar da Mahmoudu, cikin zaƙuwa ya ce masa "Yaya ta saurare ka kuwa?" Jiki a sanyaye ya girgiza kai tare da zama ya ce "Fafur ta ƙi saurar ta, duk wani rarrashi da ban baki da zan yi, taƙi saurarta kawai na ba ta ɗan ta na sake ta ta nanata mini, na rasa yadda zan yi ko na minti ɗaya ta saurare ni. Babban abin da yake ɗaga mini hankali gani nake kamar da gaske Husna ta daina so na" Mahmoudu ya girgiza kai ya ce "Ka yi haƙuri, ɓacin rai ne kawai ya sanya ta faɗar haka, amma a irin so da sadaukarwar da ta yi maka ba zai yiwu a ce ta daina sonka ba" Ya tashi zaune sosai yana kallon Mahmoudu ya ce "Kana ganin idan ta huce, za ta ci gaba da so na kuwa?" "Sosai ma, yanzun ma ɓacin rai ne kawai. Amma za ta ci gaba da sonka da zarar ta huce" Ya koma ya kashingiɗa yana kaɗa ƙafafuwansa. Mahmoudu ya numfasa ya ce "Yanzu Imam mene ne abin yi, na san fa yanzu ana can ana nemanmu, ta ina zaka fara Fuskantar wannan balahirar? Ta ina za a fahimce mu, akwai gagarumar matsala fa" Ya ɗan kwaɓe baki ya ce "Wannan balahairar ba ta kai fushin da Asmy take yi da ni ba. Ni duk yadda za su yi da ni sai dai su yi. Ko su bar ni a raye ko ma su yanka ni, burina da fatana na ga ta haƙura ta yafe mini ta saurare ni." "Yanzu soyayyarka gaba take da gagarumin tashin hankalin da yake gabanmu?" "Nesa ba kusa ba kuwa, idan aka kamanata shi da zunzurutun soyayya mara algus ɗin da na samu. Ko ka manta abu ne da nake nema ido rufe" Mahmoudu ya ce "Turƙashi, to yaya za ka yi da Gimbiya Asal?" Kawai ya saki murmushi, ya shafa sajensa. "Au dariya ma na baka?" "Eh mana, ni fa duk wannan masu sauƙi ne, ban ɗauke su matsaloli ba, zan gaya wa kowa gaskiya ko me za a yi mini sai dai a yi mini, ni fatana Asma'u ta yafe mini" Ya ƙarasa maganar cikin damuwa. "Ka kwantar da hankalinka, in sha Allah za ta saurare ka, ta ɗauki zafi ne, amma tana hucewa za ta saurare ka" ***** Doctor Sharif ne yake kallon matarsa cikin tausayawa, cikinta ya tsufa, amma sai fama take da rashin lafiya, duk da haihuwa ta biyar za ta yi. A dole ya ba ta gado a Asibitin, cikin wata bakwai da sati ɗaya, amma tana ta zubar da ruwa, ga matsalar numfashi da suga da yake hawa yana sauka. Ta kalle shi cikin damuwa ta ce "Gida zaka tafi ka bar ni?" Ya ce "Eh mana, ba ga Yaya za ta kwana tare da ke ba? Kin ga yara su na gida, ga shi gobe in Allah ya kaimu akwai makaranta, dole na koma gida. Da na kai su school zan taho nan, duk wani abu da za a yi miki, na yi shi a rubuce duk za a yi miki" Ta numfasa ta jinjina kai ta ce "To shikenan, sai da safe" "Yauwwa Madam, ki samu isasshen bacci dan Allah" "Idan na kwanta ne, baccin ko na fara sai na ji numfashina yana yi mini sama, kwanciyar babu daɗi sam" "Na sani, ki yi haƙuri sai ki kwanta a side ɗin hannunki na hagu ko na dama" Ta ce "To, sai da safe" Suka yi sallama ya tafi cike da tausayinta, wannan cikin tun yana ƙarami ya zo da tangarɗa yake wahalar da ita, ga shi ya tsufa ma amma ba ta daina wahala ba. Hankalin Alhaji Zailani ya yi mummunan tashi, ganin sauƙi sosai da sosai a tattare da Alhaji Fatuhu. Ga 'yan kasuwa sun yi masa caaa a ka, a kan lallai ba sa son shugabancinsa, sai dai ya sauka a canza wani. Ya tattara nutsuwarsa ya yi burusu da su, domin ba ya son ya rarraba hankalinsa, wani abin ya ƙwace masa. **** Nana kuwa ji ta yi da gaske yunwa na ƙoƙarin hana ta sukuni. Tashi ta yi ta fito, ta fara dube-dube. Yana daga inda yake tsaye yana kallon ta. "Me ki ke nema ne?" Firgita ta yi ta juyo tana kallon inda yake, ganin yadda yake ƙare mata kallo ne, ya sanya ta haɗe rai. "Ina fatan ba wani gurin ki ke shirin tafiya ba, babu hanyar da za ki bi ki je ko ina" "Ni ba guduwa zan yi ba, idan na ci Abincin yau za ka bari na gan shi?" Ya yi murmushi ya ce "Ki ci ɗin tukuna, Bismillah biyo ni" Jiki a sanyaye ta bi bayansa, cikin matsanancin tsoro, dan ganin shi take yi kamar wani mutum na daban. Haɗaɗen bedroom ya kai ta, ta tsaya saroro tana kallon ɗakin, ta ɗaga kai ta kalli agogon ɗakin, ƙarfe ɗaya da rabi na dare. "Zauna ki jira ni a nan" Ta tsaya tana kallon sa. "Ki zauna mana" Ya yi maganar yana nuna mata bakin gado. Ta yi ƙyam tana kallonsa. Bai sake ce mata komai ba, ya fita ta tsaya tana zazzare ido, tana ƙara ƙarewa ɗakin kallo. Ta gaji da tsayuwa, ta samu guri ta jingina da jikin bango, sanyin AC da yake ɗakin ya fara damunta. Falon ta koma, tana nan zaune sai ga shi ya shigo da leda a hannunsa. "Me yasa ki ka fito?" "Sanyi nake ji" Ta ba shi amsa a taƙaice. "Ohh yi haƙuri, mu je sai na kashe miki A.C" Ta girgiza masa kai tana sake haɗe rai. "Shikenan, zauna ga abincin na samo" Ya yi maganar yana riga ta zaman. Ta zuba wa ledar ido, bayan da ya fito da gasassun zabi guda biyu, babu abin da ya faɗo ranta, sai zaman su a gidan Hajiya Halima, lokacin da ya saka Habu ya kawo mata zabbi gasassu. Ya kalle ta ya ce "Ko na dafo miki shayi?" Ta girgiza kai ta tashi tsaye. "ina za ki je?" "Ɗakin da nake zan koma,a can zan ci" Ta ba shi amsa ciki-ciki. "To mu je can ɗin, nima ban ci komai ba, wataƙila idan muka ci tare, zan iya sakin jiki na ci Abincin" Nana ta ƙara haɗe rai ta ce "Ni fa ba zan ci wani abinci tare da kai ba, bana buƙatar duk wani abu da zai ƙara kusanta ni da kai. Ni a yanzu neman maraba nake yi da kai". "Neman maraba ki ke yi da ni?" Ya yi maganar yana murmushi mai ciwo, daga bisani ya ce "Shikenan, ɗauki abincin ki je ki ci, sai ki kwanta ki huta" Ya tashi ya bar mata falon. Ta tattare kan kayan abincin, ta tafi ɗakin da aka ajiye ta. Sosai ta fara ƙoƙarin cin abincin, saboda azabar yunwar da take ji, sai kuma ta tuna da gaske idan ba ta yi girki ba, ba ya cin abincin. Kenan tun da ta tafi bai ci cikakken abinci ba kenan ko yaya? Wata zuciyar ta tambaye ta. Har za ta yinƙura ta tashi, sai ta tuno batun cikin da ya ce tana da shi. A take wani malolon takaici ya ƙule ta, ta ƙuduri aniyar sai ta yi dalilin zubewar cikin nan. To tayaya ma za a yi a ce ina da ciki? Yaushe kuma ta yaya?" Ta tambayi kanta. Gaba ɗaya ta ji kanta yana juya mata, dan haka ta haƙura da tunanin, ta je ta wanke hannunta ta ta rufe abin da ta rage ta kwanta. Sai dai ta ƙi yadda ta yi bacci, saboda gudun kar ya biyo dare ya zo ya yi yinƙurin yi mata wani abin. Sai dai ko mintuna goma ba a yi ba, ta tsinci kanta a cikin Libraryn Ƙaisar. Ta gan shi a kwance a kan wani gado, ya lulluɓa da wani baƙin mayafi. Ya kalli fuskarta da ke ɗauke da damuwa ya ce "Ya dai?" Ta Numfasa ta ce "Ya na gan ka a kwance a nan?" "Eh to zan yi ta zama ba zan kwanta ba ne?" Ta ce "A'a, amma galibi sai ba ka da lafiya ka ke kwanciya a nan gurin" "Lafiyata ƙalau. Na ɗauka zan gan ki cikin murna da farin ciki, tun da mijinki ya dawo hayyacinsa ya gane ki, sai kuma na gan ki cikin damuwa?" Ta nemi guri ta zaune a gefen Ƙaisar ta ce "Ni fa ba na ƙaunar mutumin nan, fatana kawai ya bani ɗa na, na koma Nigeria Ubangiji Allah ya sanya su Baba su yafe mini, ina kyautata zaton alhakinsu ne ya kama ni" Ƙaisar ya ce "Waye ba kya ƙaunar yanzu?" "Sayyid" "Ƙarya ki ke yi" ta ce "Ƙarya kuma?" "Da dai ban san halinki ba ne" Cikin sanyin jiki ta ce "Da gaske nake, ba wasa nake yi maka ba. Ba na ko ƙaunar jin sunansa, ya yaudare ni, sun cutar da ni. Gaba ɗaya kimarsa da son da nake yi masa sun zube a idanuna" Ƙaisar ya yinƙura ya tashi zaune, yana ƙara rufe jikinsa ya ce "Tun da ya ce ki saurare shi, ki tsaya ki ji mai zai ce miki mana. Kar zuciyar da ki ka yi ta sanya ki yanke hukuncin da ba zai ɓulle muku ba" "Ni fa babu abin da zan ji daga bakinsa, ba na buƙatar sa a rayuwata gaba ɗaya" Ƙaisar ya yi murmushi yana gyara zamansa a hankali. Idon Nana ya sauka a kan Jakar Sarkin baka da ke gefen gadon da yake. "Ƙaisar, me ka ke yi da jakar Sarkin baka?" Ya yi mata shiru kamar bai ji ta ba. Miƙewa ta yi da sauri ta ce "Wani abu ya faru tsakaninka da Giyaz ko?" "A'a aron jakar na yi, wani aiki na yi da ita". Nana ta saka hannu ta ɗan ja mayafin da ya rufe jikinsa da shi, wani irin haske ne ya haske mata ido, daga bisani hasken ya ragu a hankali. Jikinsa ya yi wani irin kore-kore, wani gurin kuma ya yi baƙi ƙirin tamkar an ƙona shi. Nana ta ce "Meyafaru? Me ya same ka haka? Giyaz ya yi maka wani abu ne?" "Babu abin da ya faru, zan dawo miki da jakar ki kuma, ki je sai na sake neman ki" Nana ta farka daga baccin da take yi, fuskarta duk hawaye. Gaba ɗaya jikinta a sanyaye ta tashi ta yi alwala, ta yi nafilfili, sannan ta gabatar da sallar asuba. Har gari ya yi haske, tana zaune a ƙasa. Shiru ta yi tana tuna yadda ta ga jikin Ƙaisar, sai ta ji abin ya dame ta sosai da sosai. "Mene ne makomar wannan sakankancewar da nake yi da Ƙaisar yanzu? Me yasa kuma yake taimakona a wasu guraren? Anya ba wani tarkon na yaudara ya yi mini ba, yake son na afka ya yi amfani da damar ba? Ko ma dai yaya ne, Ubangiji Allah ka tsare ni daga sharrin duk wani abin ƙi." Sosai take son mantawa da tunanin Ƙaisar, ta koma tunanin Muhsin, da wannan balahirar ta gabanta, amma abu ya ci tura, a jikinta take jin Ƙaisar, take jin ta damu da halin da ta gan shi a ciki. Sallamarsa ce ta katse mata tunani, ta amsa masa ciki-ciki. Ya je gabanta ya ajiye tray. Ya ɗan tsura mata ido ya ce "Barka da safiya Rayuwata" Wani mugun kallo ta yi masa, haɗi da uwar harara. Ya yi murmushi ya ce "Ga abin karyawa nan, kar ki manta sakin jikinki, da cin abincinki ne zai sanya ki ga ɗana" "Ka daina danganta mini ɗana da kanka, ba shi wata alaƙa da kai" Ta yi maganar cikin tsiwa. "Ba shi da alaƙa da ni, sai da Ƙaisar?" Ya yi maganar ya kallonta yana murmushi. Bai ba ta damar ba shi amsa ba ya ce "Yau zan koma gida, zan je na ji yadda za mu yi da su Sultan, amma ki nutsu ki kwantar da hankalinki dan Allah" "Ba ni da wata nutsuwa ko kwanciyar hankali, idan ba ɗa na na gani ya zo hannuna ba". Ya yi shiru yana tsare ta da idanunsa. Ta ɗaga kai ta kalle shi, ta ji gabanta ya faɗi, ta rasa gane wane irin kallo ne yake yi mata haka. Ta sunkuyar da kanta tana haɗe rai. Ta sake ɗaga ido ta suka haɗa ido, ya yi mata murmushi, ya ce "Ma vie, ban san daga ina nake jin ƙaunarki ba a rayuwata, kar ki hukunta ni da abin da ki ka gani kawai a zahiri. Ina sake roƙonki, ki bani dama ki ji ta bakina" "Ni babu abin da zan ji, na ce maka ɗana kawai nake buƙata" Ya shafi sajensa ya ce "Muhsin ai nawa ne ni da Asal. Idan ki ka haihu kuma nawa ni da ke, shi ma idan ba kya so sai ki bani abina" Wata irin ɗagowa ta yi, cike da takaici, ya shammace ta ya rungume ta ya haɗe bakinsu. Nana ta tattara nutsuwarta, da duk wata jarumta dan ganin ba ta biye wa Sayyid. Ta din ga ture shi iya ƙarfinta tana kai masa duka, amma tamkar dutse ba jikin ɗan Adam take duka ba. Sai da ta gaji ta ƙyale shi. A hankali ya zare bakinsa daga nata ya ɗago fuskarta yana kallonta. Hawaye sharkaf a kan fuskarta, ya ce "Kar ki wahal da rayukanmu, ni da ke abu guda ne Asmy, ko kin tafi kin bar ni, ba za ki taɓa samun nutuswa da kwanciyar hankali ba. Kamar yadda tun da muka rabu nawa ruhin ma bai samu nutsuwa ba. Ina ƙaunarki rayuwata" Duk yadda Nana ta so yi masa rashin kunya, ta gaggaya masa maganganu masu zafin gaske, amma ta kasa tamkar ya saka wani abu a cikin idanunsa da ya yi tasirin da ya hana ta maganar. "Ki yi mana addu'a rayuwata, akwai kaya a ɗakin da muka je jiya, idan kin yi wanka akwai kayan sakawa. Sai akwai kitchen shi ma, duk za ki iya shiga ki dafa mana duk abin da ki ke so. Sai na dawo" Ko tari Nana ba ta kuma yi ba, har ya tashi ya bar ɗakin, ta bi bayansa da harara. Nene ce rungume da Muhsin, ya sha ado cikin kayan buzaye, kayansa iri ɗaya da na jikin babansa, sai ƙoƙarin cire mayafin da aka rufe masa gashinsa da shi yake yi, sai ƙamshin turare yake yi. Hammad ya saka hannu ya karɓe shi fuskarsa ɗauke da murmushi har da wata irin ɓoyayyiyar ajiyar zuciya. Hammad ya ce "Mu je ko?" Nene jiki a sanyaye ta ce "Ina mai neman afuwarka, ni tsoron zuwa gidan nan nake yi. Kuma a wane hali Nana take ciki yanzu, na kasa nutsuwa gaba ɗaya, ina jin ban kyauta ba gaba ɗaya" "Ki kwantar da hankalinki, Nana tana tare da ni, kuma babu wanda zai yi miki komai a cikin gidan, ki taimaka mini dan Allah" AREWABOOKS Nene ta numfasa ta ce "Alfamarka ce kawai za ta sanya na yi maka abin da ka nema, dan na yi alƙawarin babu abin da zai sake haɗa ni da wannan gidan naku, saboda mummunan tabon da yake binne a zuciyata. Kuma da ko me za ka yi mini ba zan ba da ɗan nan ba, saboda ya saɓa alƙawarin da muka yi da Nana, ban kyauta mata ba za ta yi mini kallon mutuniyar banza mara alƙawari. Amma kai ma ɗa ne a gurina, ban da dalilin haka gaskiya ba zan iya ba" "Na sani, kuma na gode sosai da sosai, da wannan alfarma da ki ka yi mini" Ta risunar da kanta cikin girmamawa. Ya miƙa mata Muhsin ta karɓe shi, suka shiga mota. ***** A tsanake Tafawa ya kalli Asad ya ce "Asad, wai waye ka ce ya karɓi ayabar nan ya ci?" "Wata yarinya ce, ni ban santa ma a gidan nan ba gaba ɗaya" "Dole a nemo ko wacece, saboda an tabattar mini, da cin ayabar da ta yi, da gayya ta karɓa ta ci, dan aikin da aka yi ya ɓaci ya lalace." Asad ya yi shiru, ya ce "Gaskiya ban san ko wace ce ba, sai dai ko a tambayi Asal, ko ta santa abinci dai ya kawo mana. Ina kyautata zaton ko kuku ce ko dai makamancin hakan. Ban ma san yadda aka yi ta zo inda muke ba, dan kamar ba buzuwa ba ce gaskiya" Tafawa ya yi shiru yana nazari, ya ce "Babu yadda za a yi wadda ba buzuwa ba, ta tsallako ta shigo gidan sarautar Agadez, ta yi wannan abin, lallai zuwanta na manufa ne, dole a binciko wace ce." Asad ya jinjina kai cike da gamsuwa. Asal duk ta rasa nutsuwarta da kwanciyar hankali, mussaman da Imam ya kwana uku ba ta san inda ya shiga ba, hakan ya sanya ta fara jin kamar akwai ƙamshin gaskiya a maganar da Tafawa ya gaya mata. Ta kasa jurewa ta je ta samu Sultan, tana yi masa kuka. Cikin damuwa ya ce "Yarinyar kirki lafiya kuwa?" "Sultan ji na yi an ce wai Imam yana da ɗa, dama aure ya yi ban sani ba? Kuma tun shekaranjiya ban sake ganinsa ba, kuma ba na samun sa a waya" Sultan ya ce "Waye ya gaya miki?" Ta yi shiru ta sunkuyar da kai. Ya numfasa ya ce "Shikenan na fahimta, amma ki kwantar da hankalinki, na tabattar da Hammad ba zai aikata abin da zai zubar da kima da mutuncin gidan nan ba, dan haka ki yi haƙuri ki bani lokaci, ina kan bincike ne" "Amma Abie, to ina ya tafi, haryanzu ban san inda yake ba, kuma wayarsa ba ta shiga" Sultan ya ce "Na sani, ki yi haƙuri ki kwantar da hankalinki. Zai dawo in sha Allah" Asal ta jinjina kai, ta tashi ta tafi, sai dai zuciyarta ta gaza haƙuri da samun nutsuwa. Washegari, Sultan na tare da Sardauna da kuma Matawalle su na tattaunawa, aka zo neman iso cewar Imam Hammad yana neman izinin shigowa. Cikin takunsa mai burgewa, ya shiga. Gaba ɗaya suka zuba masa ido suna kallonsa. Hammad ya nemi guri ya zauna a ƙasa tare da gaishe su. Matawalle ya amasa masa. Sultan kuwa rasa abin cewa ma ya yi sai daga bisani ya numfasa ya ce "Ina ka tafi tsawon kwanaki uku haka, ka kashe wayoyinka ka tayar mana da hankali?" Hammad ya numfasa ya ce "Ina mai bayar da haƙuri, na laifin da na aikata, na yi hakan ne, domin tabattar muku da abin da na faɗa. Ina cikin hayyacina na faɗi abin da na faɗa, kuma da shaida a kan abin da na faɗa". Sardauna ya ce "Ka na da hankali kuwa? Ka na nufin da gaske ka haihu da matar da ba mu sani ba?" Ya jinjina kai daidai lokacin da Mahmoudu ya shigo ɗakin shima." Matawalle ya ce "Ga munafukin nan, ya san komai" Sardauna ya ce "Ni kun sani a duhu, shi kuma wannan waye ya kawo shi cikin wannan mas'alar?" Sultan ya ce "Bari mu ji ta bakinsa" Mahmoudu ya zauna ya gaishe su. Sannan ya numfasa ya ce "Da fari ina neman afuwar mai girma Sultan, da ahalinsa da 'yan majalissar sa, da ma duk wani wanda abin ya shafa. Na san na aikata laifin da na cancanci hukunci, kuma a shirye nake na karɓi hukuncin laifina, na aikata abin da ya saɓa wa dokar masarauta duk da girman matsayin Imam Hammad a ƙasar nan" Sardauna ya ce "Mu na jin ka, ka yi mana bayani, me ka aikata, kuma me a sani a kan lamarin?" Sultan ya numfasa ya ce "Wato Sardauna mun ɓoye wa mutane abubuwa da dama da suka faru. Magana ta gaskiya Imam Hammad ya samu matsala ya bar ƙasar nan bamu sani ba. Mun yi ta bibiyar inda zamu samo shi. Muka rufe muka ce yana faransa babu lafiya. Da muka rasa shi, aka rasa hadiminsa Mahmoudu, shi ne muka koma binciken Mahmoudu ta ƙarƙashin ƙasa, aka yi nasarar gano su a Nigeria. Sai dai da aka dawo da shi Agadez tamkar ya manta da mu baki ɗaya, baya cikin hayyacinsa. Bamu san haƙiƙanin abin da ya faru a Nigeria ba, sai dai idan sun yi mana bayani yanzu. Abin ya ɗaurewa Sardauna kai, gaba ɗaya bai san lamarin nan ba sai a yanzu, jin abin yake tamkar almara. Mahmoudu ya ce "Bayan na tafi da Shugabana Imam Hammad Nigeria, nema masa magani, bayan da na fuskanci ya manta duk wani abu da ya shafe shi. A can muka haɗu da yarinyar a gidan da muka zauna, mahaifinta ya ba shi aurenta. Shi da kansa ya ce a biya sadakin aurensa da ita. Tun da shugabana ne ba ni da 'yancin yi masa musu. Na yi ƙoƙarin tunatar da shi, amma ko na tuna masa, ba zai iya tuna komai da ya shafe shi ba" Matawalle ya ce "Wai wannan wace irin shiririta ce ku ke karanta mana? Wane irin abu ne haka? Ta yaya mutumin da ya manta komai ya san ya ce a biya masa sadaki ya yi aure?" Mahmoudu ya ce "Imam waye shi, da duk abin da ya shafi Agadez ya manta, amma duk wani abu na rayuwa na yau da kullum ya sani. Kuma ga shi a tambaye shi, tun da yanzu yana iya tuna abubuwan da suka faru a Nigeria" Sardauna ya ce "Shi tunanin nasa network ne kenan, ko zamani da idan wannan ya zo wannan zai wuce?" Kafin Mahmoudu ya bayar da amsa, Matawalle ya ce "Wato Mahmoudu ba ka ji kashedin da na yi maka ba a kan sanar da shi wani abu ba" Mahmoudu ya ce "Ba laifina ba ne ranka ya daɗe, shugabana ne duk abin da ya umarce ni, dole na yi ba ni da zaɓi" Hammad ya miƙe ya ce "Ina zuwa" Ko da Hammad ya fita, Mahmoudu suka ci gaba da yi wa tambayoyi, yana ta ƙoƙarin basu amsa da rufa wasu abubuwan. Tsit suka yi da suka ga Hammad ya dawo, Nene na bin sa a baya da ɗa a hannunta. Matawalle ya ce "Imam me ya kawo wannan matar gidan nan kuma?" Nene ta yi turus tana haɗe rai ta sunkuyar da kai. Kafin su ƙara magana, Muhsin ya jefo mayafin kansa ƙasa, tare da waiwayowa yana kallon mutanen gurin. A sukwane Sultan ya miƙe tsaye. Imam Hammad ya karɓi Muhsin daga hannun Nene, ya nufo Sultan da shi. Jikin Sultan ya hau tsuma, yana kallon yaron da ya jiye tamkar Hammad ɗin sa yana ƙarami. Shi kuwa Muhsin kallon babansa ya din ga yi yana kallon Sultan, ganinsu iri ɗaya. Ya miƙa hannu ya ɗauki Muhsin yana faɗin "La haula wala ƙuwwata illa billah" Su kan su Sardauna da Matawalle, ƙura wa yaron ido suka yi, duk sharrin mai sharri ƙarya ne ya ce wannan ɗan ba na Hammad ba ne ba. Matawalle ya ce "Ikon Allah, da gaske dai Hammad yana da ɗa" Sultan ji yake yi tamkar ya haɗiye Muhsin, da a yake son ya sauke shi ya koma gurin Nene. Ya juya yana miƙawa Hammad hannu ya ɗauke shi. Sardauna ya miƙe ya ce "Yanzu ina uwar yaron take" "Tana nan" Imam ya faɗa yana sunkuyar da kansa ƙasa. Sardauna ya ce "Akwai rikita-rikita a lamarin nan. Dole a san yadda za a yi. Mu na buƙatar ka zo mana da uwar yaron nan, gobe in Allah ya kaimu. Ku kuma zamu tsare ku har sai komai ya daidaita mun gano komai." Nene ta ce "Ranka ya daɗe me zai sanya a tsare ni? Mahmoudu ne naku dama, ku ci gaba da tsare shi da duk abin da za ku yi masa, amma ni ina roƙon alfarma a ƙyale ni na tafi" Matawalle ya ce "Jayayya za ki yi da abin da muka ce kenan?" Nene ta sunkuyar da kai ta yi shiru. Hammad ya ce "Zan cika miki alƙawarin da na ɗauka, babu abin da zai faru in sha Allah, ki yi haƙuri gobe in Allah ya kaimu zan zo da ita" Nene ta yi shiru cikin sanyin jiki. Duk yadda Sultan ya so ƙanƙame Muhsin ya ƙi yadda, ya zamo ya sauka daga jikinsa, ya koma jikin Nene ya kwanta, ya saka hannunsa a baki. Gaba ɗaya Sultan ya kasa zaune ya kasa tsaye, saboda ganin Muhsin, bayan shafe lokaci yana fatan ɗan nasa ya samu haihuwa. Sardauna ya ce "To ita matar Mamman me ya kawo ta cikin wannan lamarin ne? Na ga kamar yaron ma ya santa?x Hammad ya ce "Eh, a gurinta yake ne" Haka aka killace Nene da Mahmoudu, aka hana su zuwa ko ina. ***** Ko da ya shiga sashensa babu kowa, Asal ba ta nan, ya yi mamakin inda ta tafi. Ya tafi kitchen ɗin da Nana take girki, ya shiga ya buɗe fridge ya samu sassanyar madarar raƙuma, ya tsiyaya ya fita. A ƙalla ya kai awanni biyu a zaune, sai ga Asal ta dawo, babu tsammani ta gan shi a falo a zaune. Ɗan turus ta yi tana kallon sa. Ya ce "Ƙaraso mana" Jiki a sanyaye ta ƙarasa ta zauna a kusa da shi. "Ina ki ka je haka?" "Nemanka na je yi" ta furta jiki babu ƙwari. "To zan gudu ne? Ai gani na dawo" "Wancan karon ma ai ka tafi ka bar ni" Ya yi murmushi ya ce "Wannan na larura ne ai Cherié" Ya yi maganar yana miƙewa, har ya nufi bedroom ta ce "Hammad" tsayawa ya yi cak, jin ta kira shi da gundarin sunansa na yanka. "Da gaske ka haihu da wata a waje ban sani ba?" "Waye ya gaya miki?" Asal ta kalle shi ta ce "Kar ka amsa tambayata da tambaya, ka bani amsa ko na samu nutsuwar zuciya, babu abin da yake yi mini daɗi. An ce ka kira ni da juya, kuma ka ce ka na da ɗa, da gaske haka ne?" Ta yi maganar hawaye na cika mata ido. Sai ya fasa shiga ɗakin, ya nufi inda take zaune, ya tsura mata ido sannan ya ce "Ni da ke na taɓa gaya miki haka? Ta girgiza kai jiki a sanyaye. "Wanda ya gaya miki ya so cin mutuncinki ne, amma da bakina na taɓa faɗa?" Ta girgiza kai jikinta a sanyaye. "To ki toshe kunneki daga jin abin da za a zo a gaya miki wai wai, ki jira abin da zai fito daga bakina zuwa kunnuwanki" Ta yi ajiyar zuciya ta ce "To, amma ba ka gaya mini inda ka je ba" "Wani aiki nake yi wa Sultan, ki kwantar da hankalinki" Ya miƙe ya tafi ya bar ta a gurin. Da magariba ta ga yana ta shiri, ta ce "Amour ina zaka je ne?" Ya ce "Eh yanzu zan yi miki bayani, zan je wani aiki da Sultan da ya saka ni ne, sai gobe in Allah ya kaimu zan dawo" "Aiki kuma sai da daddare?" Ya kalle ta ya ce "Asal, wai ki na zargina ne, yau na fara fita yin aiki da daddare, me yasa za ki tsare ni da tambayoyi kamar ba ki yarda da ni ba, shirya mu tafi tare" Yayi maganar yana haɗe rai. Ta risunar da kai cikin girmamawa ta ce "Tuba nake yi, zuciyata ce ta cika fargaba, amma ka yi haƙuri" Ya miƙe ya nufi hanyar fita, haka nan zuciyarta ta tsananta bugawa. Bayan fitarsa ya tsaya a harabar gidan, ya ɗauki wayarsa ya kira Tafawa. Tafawa ya ɗaga tare da yin sallama. Hammad ya amsa tare da cewa "Barka da dare ranka ya daɗe" "Barka dai" Ya amsa a taƙaice. "Yauwwa, dama na kira ka ne na sanar da kai, ka san abin da za ka din ga sanar da Asal, ka daina shiga cikin batun iyalina, idan ba haka ba za ka iya saka wa ta rasa ranta ko lafiyarta" "Hammad, ni ka ke gaya wa haka?" "Kai ka bani damar na gaya maka hakan ai. Abin da ba ka sani ba shi ne, Asal ta riga ta fara so na, tsawon lokacin da ya gabata, ci gaba da gaya mata magana kowace iri a kaina, ka iya haifar mata da matsala. Amma 'yarka ce duk abin da ka ke ganin shi ne daidai ka yi ba wani abu" Ya kashe wayarsa gaba ɗaya, ya shiga mota da kansa ya ja motar ya bar gidan. A zaune ya tarar da Nana a ɗakin da kayanta suke, ta sanya atamfa riga da skirt, kanta babu ɗan kwali. Ta yi parking ɗin black natural hair ɗin ta, da siririn band na yi wa yara kitso. Dan zabura ta yi, da ta ji motsinsa. Hannunsa riƙe da ledoji, ya ƙarasa ya zauna ya ajiye ledojin ya ce "Sannu da gida, na bar ki ke kaɗai ko?" "Dama can ai nikaɗai ɗin nake rayuwata" Ya yi murmushi ya ce "Haka ne, amma dai kin rayu da ni ɗin ko?" Ta yi masa shiru tana kai hannunta ta ɗauki ɗan kwalin kayan, za ga ɗaure kanta. Ya janye ɗan kwalin ya ce "A haka nake son ganinki, kin yi mini kyau sosai da sosai" "Sayyid, duk wannan abubuwan da ka ke yi, ba za su taɓa tasiri a kaina ba, ka bani ɗana kawai na kama gabana" "Gaskiya ne maganganuna ba za su yi tasiri a kan ki ba, ciki har da kirana da Sayyid. Ga abinci na kawo miki, ki ci" Ta kalle shi cikin damuwa ta ce "Ai na ci Abincin kamar yadda ka ce, yaushe za ka ba ni ɗa na?" "Kin ci, amma ba kamar yadda nake buƙata ba, sonake ki ƙara ƙiba, alamu sun nuna ba kya nutsuwa ki ci abinci ki ƙoshi" Ta kawar da kanta gefe, dan kar ma ya ci gaba da jan hirar. Dan ba ta son duk wani abu da zai sanya a ranta ta ji za ta iya ci gaba da rayuwa da shi." Ya kwance rawaninsa, ya rage kayan jikinsa, ta kawar da kanta gefe, ƙirjinta na bugawa da sauri da sauri. Ya zauna a kusa da ita ta ɗago ta kalle shi, gashin nan a kwance ya sha gyara. Ya ɗago mata yatsunsa ya ce "Ina zobena ne? Kin saka an addabe ni a kan zoben nan da yawa" Yana nuna mata yatsunsa. Ta yamutsa fuska ta ce "Na yar da shi" "Kin yar da zobena, kin ajiye turarrukana da mayukan gashina, ki na kallo ki na jin daɗi. Soyayyar gaskiya mara algus. Gobe in Allah ya kaimu za mu je gaban Sultan, mu ji hukuncin da za a yanke mana. Saboda na aikata laifi mai girman da babu wanda ya taɓa aikata shi sai ni." Ayshercool. 08081012143 81 Nana ta taɓe baki ta ce "Wanda za a yanke maka dai, ni babu abin da ya haɗa ni da masarautarku, kawai a bani ɗa na na tafi" Ya zura mata ido, ya jinjina kai ya ce "Kin daina so na dai kenan ko?" "Eh" ta faɗa tana kawar da kanta gefe. "Shikenan, zan ƙara miki lokaci, zuwa lokacin da ki ka ga ya dace ki saurare ni, amma ki sani, ni shugaba ne, kuma wasu lokutan idan aka tashi kawo gyara, toshe kunne muke yi, mu farantawa wani mu ɓatawa wani, domin samar da gayar. Dan haka duk abin da ya kama zan banƙara na aikata, domin ganin ba ki suɓuce mini ba, ko da kuwa abin da zan aikata ɗin na nufin ƙara miki ƙiyayyata. Yanzu dai ga abinci ki samu ki ci, sai ki kwanta ki huta da wuri zamu tafi" Ta murguɗa baki ta sake kawar da kanta gefe. Duk wannan abubuwan da take yi masa, ko sau ɗaya bai ji haushinta ba, shi dai fatansa da roƙonsa ta saurare shi cikin nutsuwa, ya warware mata zare da abawa, saboda ya san ko shi ne haka ta faru a kansa, zai ce wulaƙanci ne aka yi masa. Ganin ya ƙi tashi ya bata guri, ya sanya ta ɗago ta kalle shi, ta ga ya zuba mata ido, kamar zai lashe ta. Ta sake kai hannu ta ɗauki ɗankwalinta, amma ya jefa shi bayansa. Wannan kallon da yake ƙanƙance ido ya fara yi mata, ta ƙara tsuke fuska tana tattara nutsuwarta, amma ya kai hannunsa kan gashinta, ya fara shafawa a hankali. Bai sani ba ko dan ya saba ganin irin gashinsu Asal na buzaye nai laushi da santsi ya sanya na Nana yake burge shi. Baƙi ƙirin da shi natural, mai cika sosai da sosai. Ta hau ture hannunsa, amma yaƙi barin abin da yake yi, sai ma lumshe mata ido da ya hau yi. Duk wani abu da Nana za ta yi ta baƙanta masa rai, tana aikatawa domin gujewa barin nusarar zuciyarta ta sake yarda da shi, ta ba shi wata damar ya cutar da ita. Sai da ya bar ɗakin ta samu ta ci abinci, ta tura ƙofar ɗakin, sai dai babu mukulli yadda za ta datse ƙofar dan kar ya shigo mata. Tana kwanciya bacci, nannauyan bacci ya sake yin awon gaba da ita. ***** Doctor Sharif ne ya tashi a razane, bayan mummunan mafarkin da ya yi da Shukura, ta biyo shi tana kuka jikinta duk jinin haihuwa, da wata sharɓeɓiyar wuƙa tana, ya ba ta jaririnta. Ya din ga gudu yana ihu, ya ɗan tsaya ya waiwaya kawai ya ganta a tsaye a kan matarsa, da wannan wuƙar a hannunta, tana kallon cikin tana kallonsa tana faɗin "Ka zo ka bani jaririna, ko na farka cikin matarka na ɗauke nata, ka ji abin da na ji" A daidai nan ya tashi cikin razani, ya haɗa uban gumi. Ya kalli agogon ɗakinsa ya ga ƙarfe biyu da kwata na dare, kawai ya ji zuciyarsa ta kasa nutsuwa, so yake ya je ya ga halin da matarsa take ciki, amma ya tuna wa zai fita ya bar wa yaransa mata su biyu da suke bacci. Doctor Sharif bai samu haihuwa da wuri ba bayan ya yi aure, sai da suka shekara goma sannan ta haifi yara mata biyu, yanzu za ta yi na uku ciki yana ta wahalar da ita. Tun da ya haɗa kai da Alhaji Zailani ya ba shi jaririn Shukura abin yake damunsa, amma tun da Alhaji Zailani ya shaƙa masa kuɗi, sai ya manta sai kuma yau da ya yi wannan mummunan mafarkin. **** Yau ma Nana a kan gadon rannan ta hango Ƙaisar, lulluɓe da mayafi, hannunsa kawai ya ziro ta ƙasan mayafin yana rubutu a kan wani littafi. Ya ɗago kai ya kalle ta, ya ci gaba da rubutunsa. "Ƙaisar" "Na'am" ya amsa ba tare da ya kalle ta ba. "Wai dan Allah me ya same ka?" "A ina?" "Na ga yanzu kullum ka na kan gadon nan, kuma a lulluɓe. Giyaz ne ya yi maka wani abin ne?" Ya girgiza kai ya ce "A'a me ki ka gani?" "Na san shikaɗai ne yake iya cutar da kai" Ta yi maganar a sanyaye. "In ji wa? Akwai Aljanu masu ƙarfi da suka fi ni ƙarfi da za su iya cutar da ni. Kawai ni ba na shiga harkar kowa ne, ina gefe ina jin daɗin rayuwar kaɗaicina da litattafaina da haɗa magunguna na" Nana ta yi murmushi ta ce "Yaushe za ka yi aure ne kai?" "Sai na girma" "Au yanzu baka girma ba? Ina Haula ne?" Tsuke fuska ya yi ya ce "Je ki ɗakin magungunana, akwai wata kwalba taswirarta kamar zanen Duniya, ki ɗaukko ki kawo mini" Nana ta ce "To" Ta nufi ɗakin da yake ajiye-ajiyen kayan maganinsa. Ta tsaya tana ta kallon kwalaben, da yadda wasu magungunan suke yawo a cikin kwalaben, tamkar abubuwa masu rai. Ta ga wanda ya ce ta ɗaukko ta waiwayo kawai ta ga Giyaz a tsaye a bayanta. "A'uzubikalimatillahi tammat" Ta furta cike da tsoro, a suffarsa ta tsoho tukuf ya bayyana a gabanta. Ya buɗe baki ya ce "Ban taɓa ganin halittar da na tsana a doron ƙasa ba sama da ke, sai na sabauta rayuwarki, sai na kashe ki na ƙarar da zuriyarku na huta da wannan bala'in. Ya ja da baya ya nuna ta da sandarsa, da take ci da wata irin wuta mai tartsatsi. Nana ta ja da baya, ta saka hannayenta ta rufe fuskarta, tana jiran jin wutar ta fara ƙona ta, amma ta ji shiru. Ta buɗe idanunta a hankali ta ga Ƙaisar ya shiga tsakiyarsu, tartsatsin wutar ya ƙona shi, ya faɗi a gefe jikinsa yana hayaƙi. Nana ta saki kwalbar ta nufe shi da gudu. Cikin tashin hankali da tsoro ta ce "Ƙaisar, me ya same ka?" Sai a lokacin ta ga tarin raunukan da suke jikinsa, ga ƙonewar da ya yi yanzu. Giyaz ya ƙaraso kan Ƙaisar da sauri, ya saka hannunsa ya ɗago shi, amma ya ga jikinsa ya saki. "Wallahi muddin ɗa na ya mutu sai na kashe ki har lahira" Cikin dakiya da kawar da tsoro ta ce "Me ka yi masa? Kai wane irin azzalumar halitta ne wai, kowane abu yana alfahari da ɗansa da ƙoƙarin ba shi kariya, amma kai kullum cikin ƙoƙarin cutar da shi ka ke. Ƙaisar ka tashi dan Allah. Ta yi maganar cikin kuka tana ƙoƙarin taɓa shi, amma wani irin matsanancin sanyi ya ratsa ta. Ta buɗe idanunta a hankali cikin sheshsheƙar kuka, har da majina kawai ta ganta a jikin Sayyid ya riƙe ta gam yana kallonta cikin tausayawa. Ta yinƙura za ta tashi amma ya hana ta, ya ce "Ki bari ki ɗan nutsu. Me ya same shi ki ke wannan uban kukan haka? Idan komai ya lafa mini, dole na ɗauki mataki a kansa, dan ba zai yiwu ya din ga bibiyar matata ba, ina baƙin ciki da hakan" "Ba za ka yi masa komai ba, babu ruwanka da shi, tun da dai duk da tsana da abubuwan da nake yi masa, shi bai gudu ya bar ni ba, kamar yadda ka yi mini ba" Ya ɗan zura mata ido har zai yi magana sai kuma ya fasa. Ta zame daga jikinsa ta kwanta, zuciyarta cike da damuwa da tashin hankali, tare da fatan Allah ya sanya ba wata mummunar illar Giyaz ya yi masa ba. Ya tashi ya bar mata ɗakin, dama kukanta da sheshsheƙarta ya jiyo, shi yasa ya fito ya je ɗakin nata. Washegari da safe, ya kawo mata kayan da za ta saka su tafi. Ya kalle ta cikin magiya ya ce "Ma vie, na san ni mai laifi ne a gurinki, amma dan Allah ki tattara nutsuwarki guri guda, domin mu samu mafita. Duk abin da za su tambaye ki, ki sanar musu da komai, kar ki ɓoye musu komai saboda makomarmu" "Ni ba wata makomarmu, kawai ɗa na za a bani na tafi" Ya ce "To na ji, ga riga da za ki saka, ki je ki yi wanka ki shirya, ina jiran ki" Ta kalli rigar kamar ba zata karɓa ba, sai kuma ta karɓa ta ce "Na gode" Ya yi murmushi ya ce "Ko mu je ki yi wankan a ɗakina, akwai mayukan shafawa" "A'a ina da man da zan shafa" "To su ma nawan ne dai ki ke shafawa, saboda tsabar ƙauna" Ta murguɗa baki ta juya ta ajiye kayan, murmushi ya gaza barin fuskar sa. Ya ce "Kin san me na tuna? Lokacin da ki ke yi mini wanka mu na Nigeria, sauran ki yi mini wanka a Agadez". "Sai ka je gurin Gimbiya hamshaƙiya, farar fata da take biladama ta yi maka" Ta yi maganar ba tare da ta juyo ba. Ko da ta yi yinƙurin juyowa, sai jikinsu ya haɗu, sam ba ta san ya ƙaraso bayanta ba, saboda cikin takunsa mai kama da hawainiya ya ƙaraso. Dan sam ba shi da hayaniya ko karakaina. Ya saka hannunsa ya zagaye ƙugunta, ƙirjinta ya tsananta bugawa tsoro ya bayyana ƙarara a fuskarta. "Ma viee banda dalilin soyayyarki, ta sarƙe ni ta ko ina ta hana ni motsi, da sai na saka an sa bulala an zane mini ke. Imam Hammad ki ke yi wa magana a haka? Ki yi mini magana cikin girmamawa, ki daina ɗaga mini murya" Ya yi maganar yana sunkuyo da fuskarsa daidai ta ta har su na jin numfashin juna. Yana murmushi ya ce "Na taɓa yi miki wannan kashedin, kin tuna?" Ya yi maganar yana kashe mata ido. "Dan haka ke za ki yi mini wanka a Agadez da ma" "Ni ka cika ni ba na son irin wannan abin" Ta yi maganar kamar numfashinta zai ɗauke. Ya cika ta ya bar ɗakin, ta zauna tana sauke numfashi. ***** "Jamila ki yi bayani, na kasa gane kan wannan ciwon naki, na fara jin tsoro ki gaya mini me yake faruwa?" Ta girgiza kai ta ce "Babu komai" "Wallahi sai kin gaya mini, damuwarki ta yi yawa, ciwo ya ƙi ci ya ƙi cinyewa mene ne yake faruwa ki ke ɓoye mini" Mama ta yi maganar cikin tashin hankali tana zazzaro ido cikin fargabar abin da Jamilan za ta sanar da ita. Ta girgiza kai hawaye na bin fuskarta ta ce "Dan Allah Mama ki yi haƙuri ki ƙyale ni, ni babu abin da yake damuna" "Wallahi Jamila sai kin gaya mini uban abin da yake damunki, mene ne yake damunki?" "Ni ma ban sani ba" Ta yi maganar tana kuka mai ƙona zuciya. "Wallahi kin sani sai kin gaya mini" Ta yi maganar tana ƙara zazzare wa Jamila ido. Kawai Jamila ta yi mata shiru, ta ci gaba da sheshsheƙar kuka. "Za ki gaya mini ko sai na shaƙe ki?" Jamila ta girgiza kai ta ce "Ciki ne da ni" Wata irin mummunar faɗuwar gaba ta ziyarci Mama, ta ja da baya ta dafe ƙirjinta, tana wani irin haki, tare da kallon Jamila cike da tsoro. "Jaa..jam..jamilahh me ki ka ce? Ciki fa a ina? Kuma garin yaya?" Jamila ta ci gaba da sheshsheƙar kuka ba ta yi magana ba. Mama ta shaƙe Jamila ta ce "Ki gaya mini uban waye ya yi miki ciki kafin na take ki na kashe, da ki janyo mini abin kunya" "Ke Rabi, kina ina ne? Waye yake yi mini kuka, kuma maganar me na ji ana yi?" Muryar Baba ta katse ta. Da hanzari ta saki wuyan Jamila, ta ja da baya tana hararta cikin ƙunar rai. Ta yi ƙwafa ta fito daga ɗakin su Jamila. "Me yake faruwa ne?" "Babu komai, jikinta na shiga na duba" Baba ya ce "Kuma shi ne take ta kuka haka? Ni na gaji da larurar nan ta Jamila, wannan banke-banken hayaƙin da ki ke yi mata duk ba ne ba" Ta ce "To in sha Allah za mu je. Ka san mun je, mun kuma zuwa amma abu ya ƙi ci ya ƙi cinyewa, amma za mu koma" ***** Nana ta tsaya tsuru da rigar nan a jikinta, ita kanta ta san ba dan albarkacin kaza ƙandagare kan sha ruwan kasko ba, ta san ba ta kai ta saka wannan rigar ba. Ta jikin mudubi ta hango shigowarsa, kayansa royal blue, kalar rigar jikinta. Ya ƙaraso gabanta, ya fesa mata turare, ya zura hannu a aljihunsa, ya ciro zobuna da abin hannu ya saka mata. Ta yi ƙuri da ido tana kallon hannun nata, rabon da ta sanya wani abu na ado, har ta manta. A tsorace ta ce "Ni dai zan cire wannan abin tsoro nake ji" Banza ya yi mata ya gyara zaman mayafin rigar a kanta. Ya din ga ƙare mata kallo yana mamakin yadda Asal take aibata Nana da muni, dan kawai baƙar fata ce. Idanunta manya sexy eyes, farare ƙal da su, gwanin ban sha'awa, ga shi rigar tamkar dan jikinta aka yi ta. Ya numfasa ya ce "Ina ƙara tuna miki, duk wani abu da za a tambaye ki, kar wanda ya baki tsoro, kar kuma ki rufa komai, muddin ki na son Muhsin ya dawo hannunki" "Meyasa kai ba za ka yi musu bayani ba kawai?" "Da bayanina ya wadatar, ba zan bari a zo wannan gaɓar ba". Ya ciro niƙab ya saka mata. Sannan ya saka hannunsa ya ciro wayarta daga aljihun rigarsa. Nana ta waro ido ta ce "Wayata, ya aka yi ta zo hannunka? Dama kai ka ɗauka?" "Eh ni na ɗauka, kin ƙi saurarata, balle na yi miki bayanin komai, mu je" Ya yi maganar yana nuna mata hanya. Bakinta fal magana, amma ya yi mursisi, ya yi mata shiru. Ta tarar da takalma a falon gidan. Nana ta din ga ganin abin tamkar a mafarki. Su na zaune a baya ita da shi, ana jan su a motar. Ta yi shiru tana zabga addu'a Ubangiji Allah ya bata nasarar karɓar ɗanta, dan ko kaɗan ba ta sha'awar gidan nan, ɗan zamanta a gidan kawai ta fuskanci akwai kitimurmura a gidan. Tun da aka doshi gidan gaban Nana yake tsananta faɗuwa, haka kurum take jin ba ta ƙaunar gidan. Gefe guda kuma Nana tana ta tunanin halin da Ƙaisar yake ciki. Tun da aka yi parking suka fito, hadimai suke gaida Imam Hammad yana ɗaga musu hannu. Ya riƙe hannun Nana yana ratsa cikin gidan da ita. Gaba ɗaya aka zubo musu ido, ana son sanin wacece wannan ya riƙo hannunta, saboda kowa ya san ba Asal ba ce, saboda ba ta kai Asal tsawo ba, kuma Asal ba ma'abociyar niƙab ba ce, ko kanta ma ba ta damu da rufewa ba. Jikin Nana ya hau rawa, bayan da suka shiga ɗakin zama na musamman na cikin fadar Sultan. A can suka tarar da Sultan ɗin, ga Matawalle ga Sardauna, su na jiran isowarsu. Nana ta ja ta tsaya jikinta yana wata irin rawa, har ƙafafuwanta, gabanta ya din ga faɗuwa. Duk ta kowacwa kusurwar ɗakin, akaai na'urar sanyaya ɗaki, amma Nana ta kasa gane wane irin yanayi ma take ji. Ya kalli Nana ya ce "Ki nutsu mana, kar ki ji tsoro, dan Allah kar ki yi wani abu da zai rusa mana rayuwa, kar haushina da ki ke ji, ya sanya ki makance, ki yanke mana hukuncin da zai cutar da rayuwarmu" Nana dai ta gaza ko ƙwaƙƙwaran motsi. Ya ja hannun Nana, suka ƙarasa tsakiyar ɗakin suka zauna. Duk suka zubo musu ido. Sardauna ya yi wa Nana alama da ta cire niƙabinta. Ta saka hannu ta cire tana sunkuyar da kai. Abdou matawalle ya ce "Wannan kamar na taɓa ganinki ko?" Nana ta sunkuyar da kai. Sardauna ya dube ta ya ce "Ya sunanki?" "Nana Asma'u" Ta yi maganar kanta a sunkuye. "Daga ina ki ke?" Ta ce "Nigeria" "Kin san wannan?" Ya yi maganar yana nuna mata Imam,Nana ta ɗaga kai ta kalli Imam, ta kalli Sardauna, ta sunkuyar da kai. Matawalle ya ce "Ki yi magana mana, kin san shi?" AREWABOOKS Nana ta kalle shi, ya kalle ta, ya tsare ta da idanunsa, yana jiran ya ji me za ta ce. Abdou matawalle ya ce "Mu za ki kalla ki yi wa bayani. Ke ba ke muka gani cikin waɗanda suka kawo abinci ranar da aka yi taro ba?" Ta jinjina kai alamar eh. "To kin san shi ne dama?" Ya sake jefo mata tambayar. Ta jinjina kai. Sardauna ya ce "Ki buɗe baki ki yi magana mana, ki daina amsa mana da kai". "Eh na san shi" "Waye shi a gurinki?" Ta yi shiru tana nazarin amsar da za ta bayar, kar ta zama ta kwafsa su hana ta ɗan ta. Cike da karaya ya sake kallon Nana ya ce "Ma viee, talk ki yi magana mana" "Ni sai na ga Muhsin zan yi magana, dan Allah ka fara nuna mini ɗa na" Ya ce "To shikenan" Ya ce "Ina neman alfarma, zan saka a kawo mata Muhsin, za ta yi magana" Matawalle ya ce "Wane irin abu ne wannan? Ta san a gaban su wa take kuwa?" Sardaunan Agadez ya ce "Bari Matawalle, a saka a kawo shi, mu ji me za ta ce" Sardauna ya ciro wayarsa yana ɗan taɓawa, yana satar kallon Nana. Sultan kuwa rasa abin yi ya yi, ya tuna fuskarta a gurin taron cin abinci da aka yi, ya so ya bibiyi me ya kawo baƙuwa wannan gurin, amma abubuwa suka sha kansa. Wani irin gumi ne yake tsatstsafo masa bayan tuna irin taɓargazar da Hammad ya aikata, ka iya janyowa. Babban abin da ya ƙara sanya masa fargaba, shi ne abin da yake iya gani daga idanun Hammad a kan yarinyar. Ko a yanzu ya tattara hankalinsa a kanta, ta sunkuyar da kai sai zubar da hawaye take, da alama ma tamkar ya manta da zamansu a gurin. Wata hadima ce ta shigo, hannunta ɗauke da Muhsin. Yana ganin Nana, ya yi wani irin zillo daga jikin hadimar, yana wata irin ƙara yana cewa "Naaa" kamar yadda yake kiranta, Nene  kuma ya ce mata umma" Nana ta yi wata irin zabura ta nufe shi da gudu ta ɗauke shi, ta ƙanƙame shi a jikinta, tana zubar da hawaye cikin damuwa da kewar tilon ɗan nata. Shi na Muhsin ɗin, ƙanƙameta ya yi ya fashe da kuka. Jikin Sayyid ya yi sanyi sosai, ya din ga jin abin da ya aikata bai kyauta ba, kamar ya shiga hakkinsu da yawa, amma babu yadda ya iya ne, hakan ne kawai masalaha a garesu baki ɗaya. Sultan ya kalli Abdou matawalle suka haɗa ido, suka mayar kan Nana da ta durƙushe a gurin tana ta uban kuka. Matawalle ya yi gyaran murya ya ce "Wannan yaron wane ne shi a gurinki?" "Ɗa na ne" Ta faɗa cikin kuka. "Shi kuma wannan fa?" Ya nuna mata Hammad. "Mijina ne" Ta furta cikin sanyin jiki. "Waye baban yaron naki?" Ya sake tambayarta. Ta kalli Hammad ta ce "Shine" "Kin tabattar shi ne mahaifin yaron nan, kuma ke ki ka haifi yaron?" Ta jinjina kai ta ce "Na tabattar" "Ya aka yi ku ka haɗu ku ka yi aure?" Ta numfasa ta ce "A Nigeria muka haɗu, a can muka yi aure" "Waye shaidarki cewa mijinki ne shi?" Takaici ya fara kama Nana, wace shaida kuma bayan wannan ɗan wata shaida suke nema?. "Ni ba ni da wata shaida, Allah ne shaidata sai babana da ya ɗaura mana aure." Sardauna ya ce "Yaya aka yi mahaifin naki ya aura miki wanda bai san daga inda yake ba, ko ku ƙasarku ba ka bincike ku ke aure?" Jiki a sanyaye Nana ta ce "Ana yi, akwai 'yan uwansa da suke gadi tare, sun san aure muka yi, su Habu" Matawalle ya ce "Ban gane gadi ba, gadi kamar yaya?" Hammad ya ce "Ina neman alfarma dan Allah a tsagaita yi mata tambayoyin nan haka, duk a rikice take. Ga wannan wayar akwai video da hotuna a ciki, lokacin da muna rayuwa ne da ni da ita a Nigeria" Sulta ya ce "Hammad, ya zama dole ka yi mana shiru, a kammala binciken da yakamata, domin tabattar da gaskiyar lamarin nan" Sardauna ya sake kallon Nana ya ce "Ya aka yi ki ka zo gidan nan yin aiki?" Ta haɗiye yawu ta ce "Mu na Nigeria lokaci ɗaya na nemi 'yan uwansa na rasa, ya haɗu da larurar zuciya, ina tsaka da jinyarsa na neme shi na rasa. Kawai na yanke shawarar na zo Nijar ko zan haɗu da shi" Mamaki ya kama Hammad, yadda kai da fata taƙi bayanin ainihin ciwon da ya din ga yi bayan hawan jini. Matawalle ya ce "Ya aka yi da ku ka haɗu ba ki sanar da kowa mijinki ne ba? Kuma me yasa wacan karon da ya kira ki a nan, ki ka ce ba ki san shi ba? Anya akwai ƙamshin gaskiya a maganar nan?" Imam ya ce "Wancan karon laifina ne, kuma gaba ɗaya a ruɗe take" "Ba kai ake tambaya ba, ita muke tambaya" Matawalle ya katse Sayyid. Cikin kuka Nana ta ce "Dan Allah ku yi haƙuri, ni ba na buƙatar na ci gaba da zama da shi, ku bani ɗa na kawai zan tafi na yi muku alƙawarin ba za ku sake ganina a inda yake ba" Suka yi tsit suna kallon Nana, daga bisani Sardauna ya ce "Haƙiƙa idan ta tabatta kin auri Imam Hammad, to kun tafka babban kuskure mussaman shi da ya san ƙa'ida da dokar masarauta. Sai dai uzuri ɗaya za a yi muku, shi ne shi ya haɗu da larura, ke kuma ba ki san wannan ƙa'idar ba. Babban mai laifi shi ne Mahmoudu kuma sai ya haɗu da tsatsauran hukunci. Babu buƙatar mu ci gaba da bincike da wani bin diddigi. Daga nan za a ɗauke ki a kai ki gidan baƙi na musamman, ki huta kwana biyu zamu haɗa miki sha tara ta arziki, za kuma mu sanya a mayar da ke har ƙasarku. Imam Hammad dole zamu san yadda zamu juya wannan lamarin, mu ɓoye gaskiyarsa, idan haryanzu da aurenka a kanta, zaka sauwwaƙe mata zamu karɓi ɗanmu a mayar da ita Nigeria" Wani irin mugun kallo Hammad ya yi wa Sardauna. Nana kuwa zabura ta yi tana ƙanƙame Muhsin ta ce "A'a Sayyid ne ɗanku, Muhsin kuma ɗa na ne, ba zan baku ɗa na ba, da shi zan tafi Nigeria" Matawalle ya ce "Ba zai yiwu ba, mu zamu karɓi Muhsin ki yi haƙuri. Abu ne da muka daɗe mu na nema daga Hammad. Ki yi haƙuri dole mu kare kimarsa da mutuncinsa a Agadez" Hammad ya miƙe a rikice, jin matakin da za a ɗauka, amma Sultan ya kira sunansa cikin ɗaga murya. Da ido aka yi wa hadimar nan magana, ta nufi Nana gadan-gadan za ta ƙwace Muhsin. Nana ta ƙara ƙanƙame shi tana kuka cikin ɗaga murya ta ce "Ba zan baku ɗa na ba, ku ƙyale mini ɗa na, baku san baƙar azabar da na sha kan na haife shi ba. Zan bar muku naku ɗan har abada nima ku bar mini nawa" Matar ta fi ƙarfin Nana, Muhsin na zunduma ihu, Nana na kuka ta fizge shi. Nana ta bita da gudu tana janta "Ki bani ɗa na, wallahi ba zan bar muku shi ba. Ba za a kassara rayuwarsa kamar yadda aka kassara ta Sayyid ba". Wasu hadiman ne maza suka shigo, za su tasa Nana a gaba su fita da ita. Amma mugun kallon da Imam ya yi musu ya sanya suka tsaya. Ya ƙarasa inda Nana ta riƙe hadimar, ya saka hannu ya cire hannun Nana daga jikin hadimar da ta riƙe gam. "Ka ce su bani ɗa na, kuna ina lokacin da nake gantalin nemanka ba ni da ko muhallin zama da tsohon cikinsa? Ka damu da ɗan naka, ka tafi baka sake waiwayata ba? Ka bani ɗa na na tafi na barku" Idanunsa fal hawaye ya ce "Na sani, ki yi haƙuri Ma viee, ba a son raina ba komai ya faru ki yi haƙuri ki saurare ni" Sai dai tamkar yana ƙara ziga ta, ta ci gaba da cewa "Na yi dana sanin saninka a rayuwata, soyayya da tausayi ba su amfana wa rayuwata komai ba. Da na san abin da zan tarar kenan da na zauna inda Allah ya ajiye ni ban fito neman ka ba. A kan Muhsin zan iya karɓar Ƙaisar da abin da yake so na aikata sai dai masarautar taku ta tarwatse" muryarta tuni ta fara dashewa, saboda ɗaga murya da kukan da take yi mai tsuma zuciya. Matawalle ya ce "Imam wannan wace irin yarinya ce, mara ɗa'a da rashin tarbiyya? Kai ku fita da ita" "Kar wanda ya taɓa mini mata, zan fita da ita da kaina" Ya yi maganar yana ɗaga musu hannu alamar dakatarwa. Nana kuwa tuni ta silale jikinta ya saki, ya riƙe ta a jikinsa ba ta iya cewa uffan sai sauke numfashi da take yi kawai. Sultan ya yi shiru, yana ƙara jujjuya lamarin a cikin zuciyarsa. Imam da kansa ya saka Nana a cikin mota, ya babbake ya hana kowa ya taɓa ta. Ya rufe motar ya zagaya zai buɗe ɗaya ɓangaren ya shiga, amma wasu manyan hadimai suka tsare ƙofar. Ya kalle su ba tare da ya yi magana ba. Ɗayan ya ce "Tuba muke yi, umarni ne daga sama, cewar kar a kuskura a bari ka bar gidan nan" Cikin mamaki ya ce "Daga sama gurin wa?" "Daga sama gurina, kar wanda ya bar shi ya fita ko ina daga gidan nan, har sai mun bayar da umarnin hakan, ku kaita inda muka yi umarni, za mu sanya a mayar da ita Nigeria. Ina sake jaddada muku, kar wanda ya kuskura ya bar Imam Hammad ya fita daga gidan nan sai mun ba da damar hakan" Sardauna ya yi maganar cikin bayar da umarni, aka ji motar da Nana take ciki aka fita da ita daga gidan. Da ya san haka abubuwan nan za su kasance, da babu abin da zai hana ya ɗauki Nana da ɗansa ya bar musu ƙasar gaba ɗaya. Sai dai halin da Sultan zai shiga kawai yake tunani. Cike da baƙin ciki da takaici, ya koma ya iske Sultan, gabansa ya je ya tsaya cikin tashin hankali ya ce "Me yasa za ka yi haka? Idan ni ne a matsayin da take za ka so a yi mini haka? Ka kalli lamarin nan a matsayinka na uba, ba Sultan ba. Dokar masarauta  ba dokar addini ba ce ba. Me yasa 'yan majalissarka za su ziga ka ka yi haka? Babu wata hujja da ake buƙata domin tabattar da Asma'u matata ce, Mahmoudu su suka ɗaura mini aure. Shi ma kun ce a kulle shi ya yi laifi. Aure muka yi da Nana ga yarona ku na gani me yasa za a raba ta da ɗanta kuma a mayar da ita Nigeria haba Abie" "Hammad, ni ka zo gabana ka tsaya ka na gaya mini magana a haka saboda mace? Dole ne mu girmama tare da martaba al'adun masarautar nan, mu samu mu binne babban kuskuren da ku ka aikata ko dan tsira da mutuncinka. Hammad ya girgiza kai ya ce "Sultan, Asma'u ba mace ba ce kawai, ba zan binne laifukana saboda al'ada na je lahira ba ni da abin da zan gaya wa Allah ba. Zan ɗauki matata na bar ƙasar nan gaba ɗaya. Na bar muku sarautar da al'adar. Da na rayu babu su ma babu abin da ya same ni, ka gafarce ni" Mari Sultan ya kifa masa, ya janyo rigarsa yana kallon sa ya ce "Ko ka fara shan wani abu ne Hammad? Ni ka ke gaya wa ka bar mana sarautar za ka ɗauki wata bare ka bar ƙasar nan?" Jiki a sanyaye ya ce "Ba bare ba ce ba, matata ce kuma akwai ɗa a tsakaninmu. A halin yanzu a Duniya bayan kai ba na tunanin akwai wani wanda zai iya yi mini abun da ta yi mini. Gaskiyar da ba ka sona faɗa Abie ina tare da baƙin aljani, da yake burkita ni. Nana na iya ganinsa kuma itakaɗai take iya fahimtar halin da nake ci. Abie Nana ba mace ba ce kawai, waliyya ce a cikin mata, har shanyewar ɓarin jiki na yi, lokacin da ku ka gano su Mahmoudu aka ɗauke su, ba ta da wani mataimaki sai Allah kuma ba ta taɓa gajiya da ni ba. Asma'u har najasata ta wanke da hannunta. Da jikinta da lafiyarta da lokacikta da zuciyarta ta rayu da ni cikin kulawa da tausayawa. Idan na bari aka yi amfani da rashin gatanta saboda ni shafaffe da mai ne aka cutar da ita ban yi wa kaina adalci ba. Tsakanina da ita ba alaƙa ce gangar jiki ba kawai, akwai tasirin ruhika, da kuma tasirin alaƙar uba da ɗa. Wannan wani abu ne da ni da ita ne kawai muka sani. Abie ba za ku iya raba ni da Asma'u ba, idan ma ku ka raba mu, sai kun nemo ta da kanku" Ya ƙarasa maganar yana ja da baya ya fice ya bar ɗakin. Sultan ya dafe gaban goshinsa da yake yi masa wani irin raɗaɗi, ya nemi guri ya zauna. Duk yana jin maganganun Hammad a matsayin soki burutsun neman mafitar yadda zai samu ya zauna da Nana. Shi ma yana ganin ba a kyauta ba, a ƙwace mata yaro kuma a kore ta. Asal kuwa tana can ta gigice, bayan da ta samu labari cewar, an ga Hammad da wata mata ya riƙe hannunta sun shiga sashen Sultan. Ta rasa wa zata dosa domin ta ji gaskiyar lamarin. Tana cikin wannan gigitar, Tafawa ya kira ta, ta ɗaga jikinta yana ta tsuma. Ya ce "Asal, wace hadima ce a gidanki, ta kai abinci lokacin da su Asad suka zo?" Sai ta manta me ma ake nufi da hadima, sai da ya yi mata tsawa sannan ta farga ta ce "Wata hadima ce a gidan nan. Ce mini a ka yi an ga Imam Hammad da wata ya riƙo hannunta sun shiga sashen Sultan, ko ka na da labarin wace ce?" Ya ja tsaki ya ce "Sai me kuma? Ina tambayarki ki na tambayata wani abu daban." "Abbu dan Allah ka gaya mini idan ka san wani abu, ka ga ka ce mini ya ce yana da ɗa, a tsorace nake" Tafawa ya ce "Asal, kina nufin kina son Hammad ne?" Cikin kuka ta ce "Abbu mijina ne fa, ko ba na son sa ina duba makomata nima" Sai dai tana rufe bakinta, Hammad ya banko ƙofar ɗakin da ƙarfin gaske. A razane ta saki wayar hannunta, ta waiwaya tana kallon sa. Da sauri ta tunkare shi tana faɗin "Hammad wace mata a ce an ganku kun shigo tare yau, har kana riƙe da hannunta kun shiga sashen Sultan? Kar dai maganar da aka gaya mini gaskiya ce?" Ko kallon inda take bai yi ba ya nufi kan gadonsa ya faɗa kai. Ta nufe shi a hasale ta ce "Ka tashi ka yi mini bayani, wace matar a ganku tare? Kuma da gaske ka na da ɗa ko ba ka da shi? Yanzu da mutuncinka da kimarka ka zaɓi ka tozarta kanka ka kwanta da wata mace a waje dan ta haifa maka ɗa. Wallahi Hammad baka isa ba, ina yi maka rantsuwa da zatin Allah kowace matar ce sai na sanya an kashe ta, kuma an kashe mini banza dan duk cikin Agadez da kewayenta na san duk wata 'yar gata a bayana take. Ka tashi ka yi mini bayani" Wuyanta ya damƙa, jikinsa na wata irin tsuma, gani ta yi gaba ɗaya ya canza ya koma kamar wani horo, jikinsa ya koma jajawurr tamkar tumatir. Babu baƙar ƙwayar idanunsa sai farar nan tas, duk wata jijiya da taje jikinsa duk sun kumbura. ya faɗo daga kan gadon yana burgima, saboda yadda yake jin tamkar wuta na ci a ƙasan fatarsa. Tofa! Ayshercool 08081012143. Kar dai ku gaji da ni, ina yi muku tuni da cewar labarin Buzu ya shiga gasa a YouTube channel ɗin limamin tsakar gida, wanda da yawan likes na kashi goman farko za a yi amfani gurin alƙalanci. Ku taimaka ku je ku danna like a kashi goman farko na labarin BUZU na gode. 82 LITTAFIN KUƊI NE, KARKI RAINA GIRMAN HAKKI, 1K NE VIA 0069685771 Aisha Adam stanbic 08081012143 Hankalin Sultan da muƙarrabansa ya dunguzuma nesa ba kusa ba. Suka gaza gane kan Imam Hammad ta ko ina. Ga Muhsin shi ma yana ta rikici, ba ya cin abinci sam, sai koke-koke ya ƙi saurar kowa saboda rashin sabo. Cikin tashin hankali Sultan yake kallon Hammad da yake wance kamar itace, ya dubi Matawalle ya ce "Anya Matawalle ba Asibiti zamu kai shi ba. Ina ga wannan ɓoye-ɓoyen da muke yi, lokaci ne ya yi da asirinmu zai tonu. Sai dai ina jin tsoron a san halin da muke ciki". Matawalle ya ce "Wannan ba abin da ya shafi Asibiti ba ne, ko ka manta haka ya yi ta yi a lokacin da aka dawo da shi daga Nigeria? Sai da muka fita faransa sannan ya daina wannan abin,har tunaninsa ya dawo?" Sultan ya ce "Haka ne, amma kamar wannan karon, abin ya ninka wancan da ya yi. Ba ya ci ba ya sha fa" Ya yi maganar cikin damuwa. Matawalle ya ce "Nima abin da ya tsorata ni gaskiya, amma dole mu nemo masu magani da za su duba shi. Amma ya zama dole mu samo waɗanda ba za su furta komai ba, idan ba haka ba nan ma akwai matsala" Sultan ya dafe kansa yana kallon Hammad, tamkar ya fashe da kuka. Asal ta shigo ɗakin da sallama, ta kalle su ta gaishe su cikin girmamawa suka amsa mata baki ɗaya. Cikin damuwa ta ce "Abie yau ma bai farka ba ko?" Sultan ya jinjina kai ya ce "Bai farka ba Asal" Daga nesa inda take tsaya take ɗan leƙa shi ta ce "Baccin dai yake yi?" Matawalle ya ce "Ƙaraso ki gan shi mana" Ta girgiza kai ta ce "A'a shaƙe ni yake yi ya kusa kashe ni, daga nan ma ina hango shi" Babu babban abin da yake sake ɗaga wa Sultan hankali, sama da wannan azababben zafin da jikinsa yake yi mai ban tsoro, kamar ba jikin ɗan Adam ba. Da yamma Sultan na cikin ɗakinsa, yana ta kai komo, ya rasa mene ne mafita, ya san muddin batun ciwon nan na Hammad ya fita, ba su da wata mafita. Aka sanar masa da isowar Imam Zahradeen. Ya bayar da iznin ya shiga. Bayan shigarsa suka gaisa. Ya dubi Sultan ya ce "Abie, wai ko ka aiki Imam Hammad wani gurin ne? Ya saka ni wani aiki, na je gidansa Gimbiya Asal ta ce "Baya nan, kuma a iya sanina ban san ya yi wata tafiya ba" Sultan ya ce "Haka ne, yana ƙarƙashin takunkumi na hana shi zuwa ko ina ne". Ya ce "Na sani, ina son ganinsa ne, a yi mini alfarmar nan, wani saƙo zan isar masa na aikin da ya sanya ni" Sultan ya dubi Zahradeen ya ce "Aikin me kenan?" Zahradeen ya sunkuyar da kai ya yi shiru. Sultan ya ce "Shikenan na fahimta, amma a yanzu dai ka yi haƙuri ba zaka samu ganinsa ba, yana ƙarƙashin takunkumi " Imam Zahradeen ya ɗan yi jimm sannan ya ce "Shikenan, godiya nake ranka ya daɗe" Daga haka ya tashi ya bar sashen. Ya san iya takunkumin hana fita aka ƙaƙaba masa, banda na killace shi a hana ganinsa gaba ɗaya, amma lokaci ɗaya an ce har ganinsa ma ba zai yiwu ba. ***** Nana ce zaune ta saka kwanon abinci a gaba ta yi shiru, Nene ta taɓa ta ta ce "Ki ci Abincin mana, kin bari yana ta shan iska" Nana ta numfasa ta ce "Nene wai zuwa yaushe zan je na karɓo ɗa na ne, ci gaba da zama fa bai kamace ni a garin nan ba, ni duk hankalina ya yi gida wallahi" "Nana na san duk abin da nake yi, ba na son ki faɗa komar mutanen nan, su ci moriyar ganga su yada kwaronta. Mutane ne masu bala'in son kansu fiye da yadda ki ke tunani, dan haka ki ɗan yi haƙuri. Sai dai Nene na rufe baki, wayarta ta fara ringing. Nene ta ɗauki wayar ta saka a kunnenta tare da yin sallama. "Barka da wannan lokaci Ummana" Ta amsa da "Barkanmu dai" "Umma dan Allah Nana tana tare da ke ne? Idan ke ki ka ɗauke ta ki taimaka ki sanar mini inda ki ka kaita, kan Imam Hammad ya farga ba ta nan, wallahi ban san me zan ce masa ba" Nene ta ce "Idan ya fargan me ya yi saura a tsakaninsu? Ba dai ɗanku ba ne kun ƙwace? Takardar sakinta kawai muke jira, zan mayar da ita Nigeria har gidansu" Mahmoudu ya ce "Ummana, wannan wani abu ne da ya shafi Nana da Imam da iyalinshi. Ni fa kamar ya san za a yi haka ya haɗa ni da Imam Zahradeen ya sanya aka killace ku a wannan gidan, kuma lokaci guda sai ki ɗauke ta ki tafi na neme ki na rasa. Dan girman Allah da buwayarsa ki taimaka ki gaya mini inda ku ke" "Kai ka kiyaye ni, ba zan faɗa ba ɗin, ba ku da wani haɗi da Nana, ka gaya wa ubangidanka ya aiko mini da takardar yarinyata, zan mayar da ita gaban iyayenta ta nemi gafararsu" Ta katse wayar. Nana ta ce "Nene to idan ya sake ni ba su bani Muhsin ɗin ba fa?" "Shi Muhsin ɗin da shi aka haife ki ne?" Idon Nana fal hawaye ta ce "Ni dai a bani ɗa na kan ya sake ni" Nene ta girgiza kai ta ce "Nana kina cikin jarrabawa, wannan ɗan shi zai sanya ki lalata komai ki kasa ƙwatarwa kanki 'yanci, ai sai ki yi" Nana ta ɗan ɓata fuska ta ce "Amma Nene, ya aka yi aka saki Mahmoudu na ji sun ce wai sai sun hukunta shi, sun ɗora masa laifin aurenmu, sun sake shi kenan sun fasa hukunta shi?" Nene ta ce "Oho musu, su kashe shi ma kar su bar shi da rai." Nana ta waro ido ta ce "Nene wai ke ba kya son ɗan nan naki ne?" "To Nana idan ma ina son nasa, zan goya shi ne?" "To Nene dama mutum yana daina son ɗansa ne?" Nene kawai ta yi murmushi, ta tashi ta bar Nana da wasi-wasi. ***** Wasa-wasa aka shafe kwana uku curr ba a ga 'yar gidan Doctor Sharif ba, ga matarsa a Asibiti, hankalinsa ya tashi kamar zai haukace. Ga jikin matarsa kullum babu afuwa ga shi ta fara damuwa da ina Hafsa take. Sai dai ya ce mata tana gida ba ta da lafiya. Ya din ga yawo gurin 'yan sanda da gidajen radio, yana bayar da cigiya ko za a ganta. Ya din ga jin tamkar ya ɗora hannu a ka ya zunduma ihu. Gefe guda ga mummunan mafarkin da yake yi da Shukura babu ƙaƙƙautawa har fargabar kwanciya bacci yake yi. Saboda munanan mafarkai ne marasa daɗi. Ya shiga Asibiti ya tarar da wata katoɓara, an yi wa matarsa insulin allurar sauke sugar, fiye da kima suganta ya yi mummunan sauka, har ta shiga shock. Tare da sauran abokan aikinsa likitoci, suka yi ta fafutuka ƙoƙarin ganin sun ceto ranta. Yana tsaka da wannan tashin hankalin 'yan sanda suka kira shi, ya tafi cike da fatan 'yarsa Hafsa aka gani. Sai dai 'yan sanda suka ce masa Asibiti za su je ya ga wata yarinya da aka tsinta aka kaita domin a duba lafiyarta. Suka ɗauke shi a mota suka tafi. Sai dai suna zuwa aka tafi da shi ɗakin adana gawarwaki. Sam bai kawo komai a ransa ba, idonsa ya rufe kawai Hafsansa za a nuna masa. Sai dai aka fito da gawarwaki biyu. Ɗaya a kango a ka tsince ta, an fafe cikinta an kwashe wasu sassa na jikinta a can wata unguwa. Yarinyar sanye da Uniform ɗin makarantar da ya fasaltawa 'yan sanda. Tamkar ba Namiji ba, haka ya kurma uban ihu ya faɗi ƙasa sumamme, bayan ganin 'yarsa Hafsa a wannan mumman yanayi. Bangaren Sagir ma bai fitar da rai ba, yana ta addu'a, da ji a jikinsa Yusransa za ta dawo. Ga shi satin haihuwarta ya kama. Ya daure ya lallaɓa ya je duba Yusra. Wadda ita ma jiki yake a rikice. Sai dai da yaje ya tarar da jikinta da ɗan sauƙi, dan har suka ɗan fara hirar hankali. Ta ce "Haryanzu ba a ga matarka ba ko?" "Haryanzu Yusra, amma kina yi mata addu'a Allah ya bayyanata?" Ta ce "Ina yi mana, ina so Allah ya sanya a ganta, kuma fa a satin nan za ta haihu, dan ta ma fara naƙuda kaɗan-kaɗan" Ya ce "Yaya aka yi ki ka sani?" Ta ce "Mafarkinta na yi mana, tana kulle a wani ɗaki mai duhu, ta ce mini ba ta jin daɗin  zaman gurin, baka gani ba abin tausayi" Idonsa fal ƙwalla ya ce "Duk a mafarkin ki ka ga haka?" "Eh mana, tana ta kuka ma" Ya ce "Shikenan, ya isa haka. Ki ci gaba da yi mata addu'a bari na je gida. Amma yaushe za ki zo mu koma gida, ina fama da kaɗaici" Ta ce "Ko yau ka yi wa Anty magana sai na bika mu tafi" Ya jinjina kai ya ce "To shikenan, babu laifi" Shukura kuwa tana kwance a ƙasa, zama babu daɗi, kwanciya babu daɗi duk inda ta motsa cikin nan sai ya tokare ta. Ga ciwon baya da na ƙafafuwa da take yi da take kyautata zaton naƙuda ta fara a tsaitsaye. Sai dai tana yawan ganin Nana cikin mafarki, tana nanata mata ta yawaita addua babu ƙaƙƙautawa babu ji babu gani. Duk da tana yi ɗin amma ta ƙara ƙaimi gurin yi. ***** Ko da aka shiga kwana na biyar da shigar Hammad halin da yake ciki, Sultan ya gama tsurewa babban tashin hankalinsa rashin cin komai da ba ya yi ga abin kullum gaba yake yi. Tafawa ya samu Sultan a kan lallai a sake zaman majalissa, a ji bayanin Hammad a gaban kowa da kowa a kan yadda aka yi yake da ɗa kamar yadda ya faɗa." Matawalle ne ya amsa masa da cewar "A tunanina wannan maganar ai ta wuce ko?" "Ta wuce ta je ina? Kun san zata wuce ku ka dakatar da ni daga majalissa. Ya faɗi abin da dole sai ya fito ya kare maganar da ya yi. Ya ce yana da ɗa, ina ɗan yake? Kuma wacece uwar yaron? Idan kuma shaci faɗi ne to ta tabatta ba shi da lafiyar ƙwaƙwalwa da na faɗa ku ke ɓoyewa" Matawalle ya ce "Imam Hammad ba mahaukaci ba ne ba, ka san abin da zaka din ga furtawa a kansa, ko babu alaƙar jini a tsakaninku shi shugaba ne." "Eh Hammad ɗa na ne, kuma shugaba ne, amma ba zai yiwu na zuba ido ina ganin ba daidai ba, a ce yana shugaba babu cikakkiyar lafiya ba kuma ku na dannewa ku ɓoyewa ba. Ita larura ai ba abin kunya ba ce, kuma abu ne da yakamata a sani domin a nemi lafiya" Cikin nutsuwa Sultan ya ce "Imam Hammad ba mahaukaci ba ne ba, ban sna meyasa ka ke aibata shi da da wannan larurar ba" "Allah ya taimake ka, idan ba haka ba ne, mene ne gaskiyar batun ɗan da ya ce yana da shi?" Tafawa ya yi maganar yana tsare Sultan da ido. "Abu ne da muke kan bincike a kai, koma mene ne zaka ji daga baya" Ya ce "Shikenan na ji wannan, ina son zan yi magana da shi, magana ce a kan ɗiyata Asal" Sultan ya kalli Tafawa cike da takaici, ya san yana sane yake wannan bin ƙwaƙƙwafin da bin diddigin a kan lallai sai ya ga Hammad." Sultan ya ce "Za ka gan shi, amma nan da wani ɗan lokaci" Hakan ya sanya Tafawa sake tabattar da maganganun Asal. A ransa ya ce "Idan ka san wata baka san wata ba Jalaludeen" ***** Tun washegarin dawowar Nana daga gidan su Hammad, yanayin jikinta take jin babu daɗi, kamar akwai wani abu mara daɗi da yake faruwa. Sai dai ta danganta hakan da kewa da kuma tashin hankali da take ciki a kan Muhsin. Amma idan ta nutsu sai ta ji wannan damuwar daban ce, wannan a cikin jikinta da ruhinta take jin damuwar, sai dai ta yi iya ƙoƙarinta gurin danne damuwar, da duƙufa da addu'a Allah ya dawo mata da ɗanta. Yau da safe Nana ta fito ta tarar da Nana, ta ɗora tukkwane daban-daban har uku a kan murhu, tana ta harhaɗa wasu irin saiwoyi da sassaƙe-sassaƙe tana ta zubawa tana dafawa. Nana ta ce "Umman Muhsin, yau kuma baya aka tuna wa ake dafa wa magani" Nene ta yi murmushi ta ce "Ba kula ki zan yi ba ai ki ƙarata, daɗin abin ƙwaryar sama ce ke dukan ta ƙasa daga ni har ke" Nana ta yi dariya ta ce "Yasin ni ban bayar da magani ba" "A'a tuna dai, tuna dai yarinya" "To ai Sayyid kawai na yi wa" Nene ta ce "Kash, an zo gurin dan haka ki yi mini shiru" Ta ƙarasa maganar tana janyo wayarta da ta yi ƙarar shigowar saƙo. Ta tsuke fuska ta kira Mahmoudu a waya. Ya amsa tare da gaishe ta. Bayan ta amsa ta ce "Wannan uban kuɗin fa da ka sako mini?" "A'a ki yi haƙuri ai ba naki ba ne, na kula da Gimbiyar Imam ne" "Da can ku kuke bani abin kula da ita? Lokacin da take gararambar neman taimakon ba ku neme ta ba ba barin ta ku ka yi tana gantali a titi ba?" Ya ce "Dan Allah ki yi haƙuri, ba zan iya gaya masa haka ba. Haryanzu fa ma ni ban sake ganinsa ba tun ranar da ya je tare da ita. Ba ya gidansa baya fitowa zaman majillisa, ko hawa ba ya fitowa. Duk da na san an saka masa takunkumi shige da fice amma an tsaurara masa sosai. Ki yi haƙuri har gida za mu zo ban haƙuri. Dan Allah ki taya mu rarrashinta dan ta ƙi saurararsa gaba ɗaya, kuma wallahi hankalinsa a tashe yake nesa ba kusa ba. Ga tarin magauta da yake da su a cikin gidan su ma da ba barinsa suka yi ba. Dan Allah ku yi haƙuri Umma ke kin san sha'anin gidan sarauta kin san komai" "Ni rabu da ni sai daɗin bakin tsiya, ai ko mutum zai danne ya yanka sai ka kare shi" Yayi dariya ya ce "Ai ɗanki ne, kin san ba zai aikata haka ba, tuba muke ranki ya daɗe. Wallahi ina ta faɗi tashin na gan shi ne ma, na san halin da yake ciki. Amma a ƙara ba wa Gimbiyar Imam haƙuri" "A'a babu ruwana, idan ku ka zo kwa bata da kanku" Suka yi sallama ta kashe wayar. Ta kalli Nana ta ce "Kafin ki yi wanka, fara ɗibar ruwan maganin nan, ki je ki yi wanka ki gama, sai ki yi wanka da shi. Ki fito ki sha wannan maganin sai ki karya. Nana ta ce "Shi kuma Nene na mene ne?" "Na tsarin jiki da kariya ne, saboda kariya ne" Ta yi maganar tana basarwa, tare da tsuke fuska dan kar Nana ta addabe ta da tambayoyi. Ganin hakan ya sanya Nana amsawa Nene, ba dan tana so ba. ***** Mahmoudu ne ya iske Sultan a gurin shan iskarsa da yamma. Kasancewar shi ma ba shi da iyaka a shiga da fita a gidan Sultan, saboda Hammad, dan haka ganinsa ba wahala yake yi masa ba. Sai dai yau kasancewar Sultan shikaɗai ne, ya fi sakin jiki da shi. "Barka da wannan yammaci Sultan" "Barkanmu dai Mahmoudu, kuna lafiya?" Ya amsa da "Alhamdillah. Alfarma nake nema daga gare ka Sultan" "Ina sauraren ka" "Dan Allah a yi mini izini na ga Imam Hammad ne. Sultan ya numfasa ya ce "Hammad babu lafiya. Ta so muje ka gani" Ya tashi cikin ladabi, ya bi bayan Sultan. Suka yi tafiya mai nisa a sashinsa, can cikin wani ɗaki suka je ya buɗe masa ɗakin. Cikin damuwa ya ce "Mahmoudu ya tabatta Hammad hauka yake yi, haukan ma irin wanda ban taɓa ganin kalarsa ba. Na ce ko a Nigeria da ku ka zauna ya yi irin wannan? Yanzu idan ka je kusa da shi zai iya shaƙe ka, tsawon wannan lokacin bai ci abinci ba, a haka kawai yake" Cikin tashin hankali ya ce "Yayi ciwo daban-daban, amma ban ga ya yi irin wannan ba, ina kyautata zaton mutum ɗaya ne ya san matsalolinsa ciki da waje, ya san bakin zaren wannan ciwon nasa" "Wane ne? Mahmoudu ba ma son asirinmu ya tonu fa" "Da asirinmu zai tonu da tuni ta tona, sai dai a zo da Mahaifiyar Muhsin" AREWABOOKS Cikin rashin fahimta Sultan ya ce "Ban gane me ka ke nufi ba?" Cikin girmamawa ya ce "Matarsa da ya zauna da ita a Nigeria, saboda ni kaina na fuskanci wasu abubuwa masu ban mamaki a tsakanin su, bayan sun yi aure." Ya yi maganar yana kallon inda Imam Hammad yake ta mimmiƙewa yana kakari, kamar ana yanka rago. Cikin damuwa ya ce "Yanzu tun wancan lokacin a haka yake?" Sultan ya jinjina masa kai ya ce "Ko ruwa bai sake sha ba, hankalina a tashe yake. Ga Tafawa ya sako ni gaba a kan Imam Hammad sosai da sosai; Yanzu dai mu je ka yi mini bayani gwari-gwari na fahimta" Bayan sun fito, suka zauna tare da Mahmoudu. Mahmoudu ya numfasa ya ce "Idan ban manta ba, bayan mun dawo daga bikin buɗe gidan cin abincin Imam na Maraɗi, mun dawo ka sanar masa da batun tafiya Damagaran ya wakilceka a taron sarakuna da za a yi a Zinder. Ba zan manta ba an kai ruwa rana sosai a kan tafiyar. A tsukin lokacin ya kan gaya mini cewa, shi gaba ɗaya ji yake yi baya ƙaunar zaman ƙasar nan, yana jin kamar a cikin wani bala'i da masifa yake. Da fari na zata da wasa yake yi, amma sai na fuskanci da gaske yake a lokacin. Na ce masa mu sanar maka ko ɗaga tafiyar za a yi, amma ya ce mini a'a kar na gaya wa kowa, baya son ya ɗaga wa kowa hankali. Tare muke kwana da shi a cikin gidan nan, muna shirin tafiya , kawai ya ce mini na same shi a ɗaya gidan nasa na kusa da gidan tarihi da yamma, mu yi tafiyar. Na ce masa mu tafi tare amma ya ce mini a'a. Haka kurum bayan tafiyarsa hankalina ya ƙi kwanciya. Kawai na kira shi na ce masa yana ina? Ya ce mini ya tafi zagaye can wajen gidan adana kayan tarihi na Agadez. Kawai na hau raƙumi na bi shi. Sai dai na je gidan adana kayan tarihi na tarar bayanan, aka kira ni da ɓoyayyiyar lamba, aka ce mini an san Imam Hammad nake nema, ya bi cikin sahara. Ba tunanin komai na kewaya bayan gidan inda Sahrar nan take. Na yi tafiya ta kai ta awa huɗu, saboda ina ganin sahun raƙumi a gurin. A tsakiyar sahara na ci karo da Imam Hammad cikin fita hayyaci a sume. Abin ya bani mamaki, na ciro shimfiɗa a jikin raƙumina, na yi na kwantar da shi na dudduba jikinsa na ga babu wata alama ta ciwo. Na jira ya farfaɗo ko na ɗauke shi mu koma gida. Cikin ikon Allah ya farfaɗo, na ce masa meyasa ya taho cikin sahara haka? Ko ba shi da lafiya ne?" Ya yi mini shiru. Na ba shi ruwa ya karɓa ya sha. Na ɗora shi a raƙumina ina mamakin yadda yanayinsa ya canza. Muka doshi dawowa, sai dai muna nufo Agadez ya din ga wani irin ihu, ya faɗi a cikin sahara daga kan raƙumin ya din ga burgima yana kururuwa. Na sauka na riƙe shi ina tambayar ko lafiya? Amma ba ya iya magana sai ihu kawai. Hankalina ya tashi na rasa yadda zan yi da shi. Da mun nausa cikin sahara sosai sai ya yi shiru da mun nufo gida, sai ya rikice. Na rasa yadda zan yi ga yamma tana yi. Ba zai yiwu na ɗaukko shi na taho da shi yana wannan kururwar ba kowa yana ganinsa. Kawai aka kira ni da ɓoyayyiyar lambar nan aka ce, kar na dawo Niger da Imam, idan ba haka ba zai yi hauka tuburan ƙarshe ya rasa ransa gaba ɗaya. Na tambayi waye amma ba a bani amsa ba a ka kashe wayar. Na din ga mamakin waye wannan ya kira ni haka? Kasancewar na ga alamun gaskiya a abin da aka faɗa, da na juya da shi yake rikicewa, kawai sai na nufi Nigeria da shi cike da fargaba da zullumi. Akwai abokan hulaɗarmu na Nigeria, da muke kasuwancin asuwaki da dabino wanda da yawa ba su san waye ni ba, kuma ba su san Imam ba, kawai sai na neme su a waya. Aka ci gaba da kirana da wannan lambar ana gargaɗina kar na saka a masarauta a san da abin da ya samu Imam Hammad, saboda za a ce dole sai an dawo da shi, idan aka dawo da shi kuma zai rasa hankalinsa da rayuwar sa. Haka na ɓad da kamanni da ɓoye waye Imam, na shiga da shi Nigeria muka fara neman magani. Sai ya shafe sati bai yi magana ba, ya manta waye shi gaba ɗaya. Sai dai aka ɓoye lambar asusu, aka din ga turo mini kuɗi cikin asusuna, na ci gaba da harkar safarar dabino zuma da asuwaki tsakanin Nijar da Nigeria, ina tsoron taɓa kuɗin da ake turo mini saboda ban san na waye ba. Sai dai duk gurin masu magungunan da muka je, sai su ce mu yi haƙuri ba za su iya ba shi magani ba. Mun je gurin masu magunguna daban-daban amma bamu samu magani ba. Ya manta komai nasa da ya shafi Agadez. Na samu wani gida da abokan hulɗata suke gadi, muka shiga cikinsu. Zai yi wanka zai ci abinci zai yi salla, amma ba zai yi magana ba sai jefi-jefi. Idan kuma abin ya juyo ba ya ko cin abinci ba ya magana. Sai dai gaba ɗaya al'amuransa sun ƙara rikicewa, ya din ga abu kamar yana gane-gane. Kwatsam aka kawo mahaifiyar Muhsin, ita kuma za ta din ga aikin rainon yaro. Duk lokacin da ya ganta ya kan ƙure ta da idanunsa kamar yana ganin wani abu a tare da ita. Sai da na taɓa tambayarsa ko ya santa ya ce mini a'a amma tana da wani abu da yake nema domin ya tuna waye shi. Tsawon wannan lokacin ban taɓa gaya masa waye shi ba, saboda fatana ya tuna da kansa kuma kar na yi wani abu, da asirinmu zai tonu ko a cutar da shi. Kwatsam! Ban san abin da ya faru ba, muka tarar da ita a sume a cikin ɗakinmu, daga ita sai shi. Babu alamun ya yi mata wani abu na cutarwa, sai dai an ce abinci aka bata ta kawo mana ta suma a ɗakin. Mahafinta ya ce ba zai yadda ba ya ce sai ya aure ta. Ba zan ɓoye maka ba Sultan mahaifiyar Muhsin yar masu ƙaramin ƙarfi ce. Aka din ga dambarwa babanta ya ce sai dai Imama ya aure ta. Ina ta lallaɓawa ina bayar da haƙuri, amma ya ce na biya masa sadakin. Ba ni da ikon yin jayayya da shi, dole aka ɗaura musu auren. Sai dai mai kirna a wayar nan ya kira ni, ya sanar mini da ya san batun auren da aka yi wa Imam Hammad. Tun bayan aurensa da ita, ya fara samun sassauci, ya dawo yana magana, wasu daga halayensa suka canza. Yana kishinta fiye da kima, yana sakin jiki da ita ya yi hira da ita, ya yi wasa da ita abin da ba ya yi ma a rayuwarsa ta nan. Na sani akwai abin da ta din ga ɓoye mini game da zaman da take yi da shi, duk da nima ban bayyana mata waye shi ba. Amma na san ciwon nan yana motsa masa, duk da na yi mata bayanin ciwon nasa amma iya abin da na sani. Sai dai har aka je aka ɗauke mu daga Nigeria bata taɓa nuna mini yana yin wani abu na irin wannan rashin lafiyar ba. Dan haka ko dai tana da maganin ciwon sa, ko kuma rufa masa asiri ta yi." Sultan ya sauke wani irin nannauyan numfashi ya ce "Gaskiya na ji daɗi sosai da yadda ka rufa wasu abubuwan a gaban su Matawalle duk kusancina da su, akwai abin da ba zan so su sani ba. Amma ya aka yi ta san yana Agadez ta zo, nifa ina jin tsoron raɓa ɗa na da wanda zai cutar da shi" "Allah ya taimake ka, neman Imam ne ya sanya ta baro Nigeria babu wanda ya sani ta taho da tsohon ciki Nijar. A hannun mahaifiyata ta zauna. Duk da ba komai na sani ba, bayan na baro Nigeria, a bakinta za a ji komai. Amma Umma ta ce mini, ta gaya mata rashin lafiya ya yi sosai bayan an ɗauke mu daga Nigeria" Sultan ya jinjina kai ya ce "Kuma haryanzu baka san waye ya ɓoye lambar yake kiranka ba?" Ya girgiza kai ya ce "Ban sani waye ba, lokacin da aka rufe ni an karɓi wayata, da aka dawo mini da ita ma, ba a sake kirana ba" Sultan ya ɗan yi shiru sannan ya ce "Shikenan, amm zan yi magana da Matawalle, a je a taho da ita, idan ma an mayar da ita Nigeria ne, duk inda take a Nigeria a nemo ta. Amma ko waye yake kiran nan naka, yana da masaniya a kan abin da ya same shi. Amma shikenan" Mahmoudu ya ɗan yi Jimm, yana tsoron a gano Nene ta ɗauke ta, dan kuwa ba ya tunanin an sake waiwayar Nana tun da aka ce a je a killace ta, dan da tuni sun farga an baza nemanta, ko dan kar ta je ta faɗi cewa ita matar Hammad ce. Sultan ya sallame shi ya tashi ya tafi. Sultan ya dafe kansa ya yi shiru, saboda yadda al'amura suke ƙara rincaɓewa. Duk tarin yaransa babu wanda yake tausayi kamar Hammad. Kuma yana burin Hammad ɗin ya gaje shi, amma shi ne wanda jarrabawa kala-kala take bibiya. ***** "Nene, wai wannan naman da nake ta ci kashi-kashi na mene ne, ni gara ki bani hatsi kawai" Nene ta ce "To mijinki ne ya turo kuɗin ciyar da ke, kin ga kuwa dole na baki ingantaccen abinci." "Ni k ƙyale masa kuɗinsa, kawai lokaci nake jira idan ba ki yi wani abu ba, na je duk bala'in da za a yi, a yi a bani ɗa na, kan na basu mamaki wallahi. Dan ko zan mutu sai na raba su da shi" Nene ta ce "Ba ma za ki mutu ba. Za ki karɓi Muhsin, ki koma ɗakin mijinki Gimbiya, ina jinjina lamarin Ubangiji Nana, ashe duk wahalar da ki ka sha, duk zaman da muka yi Gimbiya ce ke Nana" Nana ta ɓata fuska ta ce "Dan Allah Nene ki daina, sai na ji wani banbarakwai, ni Sayyid nake so, ba Imam Hammad ba, ko kaɗan ba na sha'awar wannan gidan. Azabar tension ɗin da na sha a baya ma ta ishe ni, yanzu hutu nake buƙata" Nene kawai dariya tana girgiza kai, ta ce "Yaro man kaza, Nana na taɓa soyayyar nan fa nima, ba za ki yi mini wani alaye ba. Amma ni da ke mun sha banban. Allah ya zaɓa abin da ya fi alkhairi ". Nana ta yi shiru, gaba ɗaya magungunan da Nene take bata, bata taɓa kawo na mene ne ba. Gaba ɗaya tana kwance ta kasa bacci, sai juye-juye take yi, a jikinta take jin yanayinta ya ƙara canzawa fiye da yadda take a baya. Dama lallaɓa rayuwarta take yi a hankali. Shiru ta yi tana tunanin ko wani hali Muhsin yake ciki?. Sai kuma ta tuna ta ji wayar da Nene ta yi da Mahmoudu a kan cewa, an sanya wa Hammad takunkumin fita. Ta tafi tunanin tun daga wane lokaci ya gane ta, amma ya share ya nuna kamar bai santa ba. Guntun tsaki ta ja, ta juya zata gyara kwanciyarta. Ta fara jin wannan ƙamshin na ɗakin nan da take ganinta tare da Sayyid yana ratsa hancinta. "Ina fatan ba da ni ake wannan tsakin ba?" Ba shiri ta buɗe idonta, kamar yadda ta yi tsammani a ɗakin ta gan su sai dai ya rame sosai da sosai. Tsiwa ta so yi masa, sai kuma jikinta ya yi sanyi ta ce "Ba ka da lafiya ne?" "Lafiyata ƙalau, kewarki kawai nake yi, shi ya sanya rame" Ya tashi zaune ya matsa kusa da kta da ita ya rungumota jikinsa ya ce "Ma vie komai zai wuce in sha Allah, amma kar ki yanke hukuncin haƙura da ni, ba zan iya jurewa ba, ruhina da gangar jikina sun yi mugun sabo da ke, sabon da ba zan iya misalta miki ba" Ya yi maganar yana kwantar da kansa a kafaɗarta. Duk da wata zuciyar na azalzalarta da ta ture kan sa daga jikinta. Amma ya sake riƙo hannunta cikin sanyin jiki ya ce "Ki yi magana ko na ji daɗi mana" "Sayyid, ci gaba da rayuwa da kai ba zai haifar wa tawa rayuwar ɗa mai ido ba, zaren ba kalar yadin ba ne, kuma sama ta yi wa yaro nisa" "Ban ma gane me ki ke nufi ba, ni duk wata rayuwa da zan yi. Nutsuwata da kwanciyar hankalina na tattare da ke Ma vie" Ta yi masa shiru daga bisani ta ce "Ni fa gaskiya ka yi mini nauyi, ka ɗaga ni" Ya yi murmushi ya ce "Lokacin da ki ke so na, ba kya jin na yi miki nauyin, lallaɓa ni ki ke yi. Asmy" "Na'am" "Yanayin akwai zafi sosai, ina buƙatar sanyi" "Ko fifita ba zaka samu ba, balle wani sanyi" Sai dai tamkar a zahiri, haka ya ci gaba da lallaɓa Nana, da daɗaɗan kalaman da sai da ta manta da fushin da take yi, ta saki jikinta da shi. Babu tsammani Nana ta farka tana ta ajiyar zuciya. Ta tashi ta zauna ta jingina da bango. Jin yanayinta abin da ya faru ta yi tamkar a zahiri ba mafarki ba. Ta daɗe ba ta yi mafarki makamancin wannan ba. Tana son sanin ainihin abin da yake faruwa take ganinsu a wannan ɗakin. Mararta ta ƙulle ta kifa kanta a kan gwiwoyinta, ta tsorata da ramar da ta ga ya yi, jikinta ya ci gaba da bata yana cikin damuwa. Ga abubuwan da ta gani a cikin gidan game da shi. Ƙarshe dai kasa komawa bacci ta yi, ga tunanin Ƙaisar da shi ma ba ta san halin da yake ciki ba. Wayewar garin Allah, haka Nene ta sake zubowa Nana kajin nan da ɗuminsu sai ƙamshi suke yi. Nana tana ta lissafi da son yin gwajin ciki, domin tabattar da maganar Sayyid, dan sai da ta yi mafarkinsa jiya sannan ma ta tuna. Sai dai tana jin tsoro, ga shi tana jin Kunyar Nene balle ta gaya mata. Yaushe ma za ta fara bayanin ta na da ciki, cikin da ba ta san ya aka yi ya faru ba?. Tana cikin ɗaki tana cin naman nan, ta jiyo muryar Nene na waya. Mahmoudu ka kiyaye ni da batun Nanan nan fa" "Dan Allah Umma ki yi haƙuri, zamu shiga matsala sun farga Nana ba ta nan, yanzu haka nemanta ake yi" "Su neme ta, me ta yi musu?" "Babu abin da ta yi, Sultan ne yake son ganinta" "Sultan, ita ma za a yi mata abin da aka yi mini ɗin ne?" "A'a Umma dan Allah ki yi haƙuri dai, babu wanda ya san inda take. Ni na ce musu na san inda take, yanzu masalaha suke nema. Wallahi an kasa gane kansa gaba ɗaya. Yau kwana na tara kenan yana sume ko ruwa bai shiga cikinsa ba. Dan Allah ki gaya mini kuna ina?" Gaban Nana ya yi wata irin faɗuwa, ta miƙe tsaye tana sauraren me Nene za ta ce. "Zan neme ka zuwa anjima, sai na yi magana da ita, idan ta kama sai dai ku bi ta can Nigeria gurin iyayenta, ku roƙo alfarmarsu, ku ɗaukko ta" "Umma, Nigeria kuma ta koma? Shikenan mun kaɗe." Ta ce "Ka dai saurare ni na ce" Ta kashe wayar. Tana shiga ɗakin ta ga Nana a tsaye. Nene ta ce "Za ki je kenan?" Nana ta yi shiru tana kallon idon Nene. Nene ta yi murmushi ta ce "Ai ba zan hana ki ba. Ban sani ba ko daga nan ki karɓo takardar sakin naki. Ki haɗa abin da ki ke buƙata, zan kira shi na gaya masa su zo su ɗauke ki" Jiki a sanyaye Nana ta ce "Kina ganin idan na je, ban yi wauta ba ko kuma tarko suka yi mini ba?" Nene ta ce "Sam, ba na tunanin hakan, ba za a haɗa kai da Mahmoudu a yi miki haka ba. Ina yi miki fatan nasara." Nana ta ce "Nene mu tafi tare mana" Nene ta girgiza kai ta ce "A'a wace ni, ni da mijina bawa ne, ba sa ƙaunata ba sa son ganina. Ai ke ciwon ido ce, babu yadda suka iya da ke. Mussaman da yake Muhsin a tsakanin ku." Nene ta yi ba ta ƙwarin gwiwa, Nana kuwa addu'a take yi, da fatan Allah ya sanya ba Giyaz ne ya ci gaba da azabtar da shi ba. Bayan la'asar sai ga Mahmoudu a wata hamshaƙiyar mota zai ɗauki Nana. Nene ta yi masa kashedi sosai da sosai a kan ya ji tsoron Allah, kar a haɗa kai da shi, a cutar da Nana. Ya yi wa Nene alƙawarin hakan. Nana ta ɗauki kayanta Nene ta raka su har bakin ƙofa, tare da yi wa Nana fatan alkhairi. A motar Mahmoudu ya ci gaba da ba wa Nana haƙuri ya ce "Idan mun je, kar ki nuna musu fusata ko jin haushin sun ƙwace miki ɗa sun kore ki, bamu san abin da Allah zai yi ba idan mun je tare da ke. Wataƙila rashinki ne a kusa da shi da abin da aka yi miki ya sanya shi a wannan halin. Nana kwanan Hammad takwas ko ruwa bai shiga bakinsa ba, yana sume kawai. Ki yi haƙuri da abubuwan da suke faruwa mu je mu gani ko Allah zai sanya a dace." Nana ta jinjina masa kai, ƙasan zuciyarta tana addu'a. Ta wata hanya da bata taɓa sanin da ita ba, duk da gidan ba ƙaramin gida ba ne, suka bi. Ya yi parking gurin babu kowa an ƙawata shi da wasu irin dakakkun kujeru na gini da fulawoyi. Su na bin wata ƙofa suka shiga, sai ga su a sashen Sultan. Nana ta yi shiru ta ga yadda aka yi wa ƙasa ado da dukiya, kamar ba za a mutu a bar ta ba. Tsahirtawa ta yi da tunanin nata, bayan ganin mutanen da a yanzu ta tsani ganinsu, tun bayan yin ƙarfa-ƙarfar rabata da ɗanta. Sun kame a kan kujeru cikin manyan kayansu da rawani, sai dai sun sauke rawanin fuskarsu tana iya gane kowanne a cikin su. Tuna abin da Mahmoudu ya gaya mata, ya sanya ta daidaita nutsuwarta, ta tsuguna a gabansu ta ce "Ina wuninku" Suka yi shiru ba su amsa mata ba. Mahmoudu ya ce "Barka da yammaci za ki ce musu" Ta ce "Barkanku da yammaci, na same ku lafiya?" Matawalle ya ce "Alhamdillah, sai ki ka ji mun sake neman ki ko?" Ta ce "Eh, ina fatan ba wani laifin na sake yi ba?" Ya girgiza kai ya ce "Ba ki yi laifi ba. Alfarma ma muke nema a gurinki" Ta risuna ta ce "To, Allah ya bani ikon yi" Ya ce "Kafin nan zan tambaye ki. Ke ce ki ka rayu da shi a Nigeria a matsayin matarsa bayan barinsa Agadez. Shin ko yana yin rashin lafiya mai kama da taɓin hankali, bayan larurar da ya yi na manta ko shi waye?" Nana ta ɗan ɗaga kai sannan ta mayar ta sunkuyar. Ta girgiza ta ce "A'a bai taɓa yi ba" Gaba ɗaya sai suka yi shiru su na kallon ta. Sardauna ya ce "Ki na nufin bai taɓa wani na larurar rashin lafiyar ƙwaƙwalwa ba?" Nana ta ce "Eh sai matsalar zuciya da ya yi fama da ita" Sardauna ya ce "To idan haka ne, babu amfani kawo ta kenan, tun da babu wani haske da za ta iya bamu, ko wani abu da za ta iya yi" Nana ta risuna ta ce "Dan Allah ina son a bani dama, ko sau ɗaya na gan shi, dan Allah" Sardauna ya ce "A'a, babu buƙatar hakan" Sultan ya yi shiru yana nazarin fuskar Nana, daga bisani ya ce "Duk da haka, mu je ta gan shi, ko da wani abu da za ta iya yi a kai, ko abinci a samu ya ci" Matawalle ya ce "Gimbiya Asal ma ta gaza yin wani abu, balle ita?" Sultan ya miƙe sannan suka tashi. Su na gaba Nana da Mahmoudu su na baya. Ɗakin kansa an rage hasken fitilun cikinsa, hanyar da suka bi zuwa ɗakin ba zaka taɓa cewa akwai wani ɗaki a gurin ba. Daga nesa Nana ta hango shi, yana kwance a dunƙule guri ɗaya. Gashin kansa ya baje a ƙasa. Sardauna ya kunna fitilun ɗakin haske ya gauraye ɗakin. Ziiiiiiiiii ta fara jin wannan sautun, na turnuƙewar ƙurar sahara. Ta tattare nutsuwarta guri guda, ta din ga ambaton Allah. Kawai ta nufe shi. Sardauna zai yi magana Sultan ya hana shi, dan ba a yi wa Nana iznin zuwa inda yake ba. Ta durƙusa a kansa, ta ga an ɗaure masa hannayensa, jikinsa ya yi jawurr ga wannan hucin zafin da take iya ji, fiye da yadda sauran mutane idan sun raɓe shi suke ji. Ta hau kiciniyar kwance masa hannunsa. Wata irin miƙa ya yi tana gama kwance masa hannun. Ya miƙa hannunsa wuyanta, da wannan kalar idanun nasa mai ban tsoro. Cikin jarumta da dakiya, ta riƙe hannun nasa ta ce "Sayyid, nice. Ka saurari sautin muryar. Asmy ce ka ayyana addu'a a cikin ranka ko ba zaka iya furtawa ba." Bakinsa ne yake karkarwa yana son ya yi magana. Ta ce "Ka yi shiru, kar ka yi magana" Ya yi wani yinƙuri ya fizgota jikinsa da ƙarfi. Ayshercool 08081012143 84 LITTAFIN KUƊI NE, KI BIYA KUƊIN KARATU KAN KI KARANTA. VIA 0069685771.AISHA ADAM STANBIC 08081012143 Gaba ɗaya suka yi cirko-cirko suna kallon ikon Allah. Tamkar matafiyin da ya shafe tsawon lokaci yana tafiya a sahara ba tare da ci ko sha ba, haka cacumar Nana da wani irin gigitaccen ƙarfi. Haka nan Nana ta ji jikinta babu ƙwari sosai. "Habu ku bamu guri" Nana ta furta cikin ƙarfin hali tana ƙoƙarin riƙe hannunsa. Mahmoudu ya ce "Amma kar ya shaƙe ki fa, ko ya yi miki illa" Ta ce "Ba zai yi mini ba, zai dawo daidai in sha Allah, idan ma ya shaƙenin zai dawo daidai in sha Allah, amma ku bani guri" Tamkar zai shige cikinta haka yake ƙoƙarin rungume ta. Gaba ɗaya Sultan ya ruɗe, Mahmoudu ya ce "Ranka ya daɗe, ta ce mu basu guri" Sardauna ya ce "Tayaya za mu tafi mu bar su, idan ta cutar da shi fa?" Mahmoudu ya ce "Ba za ta iya cutar da shi ba. Abin tsoron ma kar ya cutar da ita shi" Haka suka fita suka bar shi da Nana. Su na fita Nana ta sassauta murya ta ce "Sayyid, ka nutsu ka yi addu'a, kar ka yi ihu, ka yi addu'a ka ji" Sai dai sam yanayinsa bai nuna yana cikin hayyacinsa ba. Ta saka hannunta ta zuge rigarta ta cikin hijjabinta. Sai dai tana yi tana kokawa da shi. A hankali ta ba shi damar ƙanƙame ta kamar yadda yake ƙoƙarin yi. Wani irin nishi ya din ga saukewa mai sauti, jin sanyin jikin Nana. Sai dai sanyin bai kai wanda ya saba ji a jikinta ba. A hankali ya yi lamo a jikinta, da fari Nana ta fara ƙoƙarin karanta masa Alqur'ani, sai dai ta kasa jurewa ta fashe da kuka. Saboda wani irin gigitaccen zafi ne yake ratsa ta daga jikinsa kamar an kunna musu wuta. Ga shi yadda ya danne ta ba za ta iya matsawa ba, balle ta samu afuwa. "Ya hayyu ya ƙayyum Allah ka kawo mana ɗauki" Ta furta a lokacin da take jin yana ƙara matseta tamkar zai karya ƙasusuwanta. Sun ɗauki lokaci a haka, kafin ta ji jikinsa ya saki, ya sassauta riƙon da ya yi mata. Ta ture shi da kyar ta ɗaukko pillow ta tayar masa da kansa da shi. Sai dai idanunsa a lumshe kamar mai bacci, saɓanin da da idanun a buɗe tar sai dai babu ƙwayar idon sai farar. Ta koma gefe ta jingina da gadon da yake ɗakin, ko rigarta ba ta iya gyarawa ba, ta gyara hijjabinta ta jingina ta lumshe idanunta. Hawaye ne suka fara bin gefen idonta, wani irin azababben ciwo jikinta yake yi mata, kamar an yi mata dukan tsiya da kulki. Ga raɗaɗin da take ji a kan fatarta. A tsorace take waige-waige, ganin bugiren da Ƙaisar yake kwnaciya babu kowa. Ta duba gurin zamansa nan ma baya nan. Ta fita da sauri zuwa ɗakin magungunansa, nan ma baya nan ga inda Giyaz ya yi ɓarna ba a gyara ba, tabbacin bai da lafiya bai gyara ba. Ta din ga shiga tana fita a cikin Libraryn tana kiran sunansa amma ta ji shiru. Wata siririyar hanya ta bi, da haske ya ratso gurin. Ta bi hanyar sannu a hankali tana addu'a a cikin zuciyarta, da fatan Allah ya sanya ba wani abin ne ya samu Ƙaisar ɗin ba. Bayan Library ɗin ta ɓulla, ta hango shi a cikin tafkin da yake gurin a kwance, ya lumshe idonsa. Da sauri Nana ta ƙarasa tana faɗin "Ƙaisar, wannan ai sai ka tsorata ni, meyasa ka dawo nan ka kwanta, jikin ne dai?" Ya buɗe idanunsa ya kalle ta ya ce "A'a hutawa kawai nake yi" Nana ta samu guri ta zauna a gefe ta ce "A'a ai na san jikin ne, ba zaka faɗa mini ba ne" Ya ce "Ya jikin mijinki?" Ta ɗan yi shiru ta ce "Yana can Giyaz na ci gaba da azabtar da shi. Na rasa me ma zan yi gaba ɗaya, ni kaina a jikina nake jin na ƙone" Ƙaisar ya tashi zaune sosai a cikin ruwan ya ce "Ba Giyaz ba ne kawai, akwai tasirin asirin nan da ake yi masa da wuta. Sannan kuma ga Giyaz, shi Giyaz yana wasa da ƙwaƙwalwarsa ne, ya sanya ya tuna wannan ya manta wancan. Sai kuma ya kan shafe shi sai ya yi wannan suman. Amma wannan ƙonewar yana da alaƙa da wutar da ake hurawa wadda aka yi masa asirin da ita" Cikin damuwa Nana ta ce "To dan Allah waye ya yi masa asirin, kuma a ina aka yi masa?" Ya girgiza kai ya ce "Ki yi haƙuri, ba na shiga duk abin da bai shafe ni ba, saboda ni har kullum zaman lafiya nake fata. Sai dai na ga uwargijiyarki a dalilinki ta tuna gadon nasu gidan, da ke ki ka guji naki. Babu lallai sihiri ya yi tasiri mai ƙarfi a jikinki. Zai iya yiwuwa kina daf da inda aka yi masa sihirin. A wannan karon ne za ki yi faɗan ƙarshe, kar ki yi da wasa ki yi da gasken gaske. Ki buɗe idanunki, kibiyoyin da ki ka gani ana harbinsa da su mahaifinsa na karewa, yanzu ke za ki tare su. Ya fito daga cikin ruwan jikinsa yana ɗigar da ruwa, yana takawa da kyar, jikinsa duk wasu irin ramuka duk ya yi baƙi. Ya gyara zaman rigarsa ya rufe jikinsa sosai. Ya sake duban Nana ya ce "Kar ki yadda ki komawa iyayenki gida, babu wani kyakykywan sakamako. Za ki sake komawa farko dan sunanki zai ɓaci. Kar kuma ki yarda a raba ki da ɗanki, kar ki aminta da duk wani murmushi da za ki gani a fuskokin mutane, kuma kar ki sakankance da ƙiyayyar da za ki gani. Kowanne na iya taimaka miki ki samu haske. Kai da fata ki dage, duk rintsi kar ki kuskura a ci moriyar ganga a yada ke a gefe, saboda kin gama yi musu amfani. Ki kula sosai da sosai. Allah ya ba da sa'a" Cikin damuwa Matawalle ya ce "Shirun nan fa ya yi yawa. Anya ba za mu je mu sake dubawa ba" Sardauna ya ce "Abin da nake tunani kenan, kar abin da ba a so ya faru. Kai Mahmoudu tashi ka wuce gaba ka duba, idan lafiya mu shigo. Ni na kasa samun nutsuwa tun da na ji tana wai mu bata guri." Mahmoudu ne ya fara yin gaba, ya tura ƙofar ɗakin a hankali ya hango Nana a jingine shi kuma yana kwance a kusa da ita a kan fulo. Ya ƙarasa da sauri yana kiran sunan Nana, amma ba ta motsa ba, sai hawaye da yake ta fita daga idanunta da ta lumshe. Ƙarasowa suka yi su ma, suka rufu a kan Hammad. Sai suka ga jikinsa ya saki, idanunsa a rufe wannan jijiyoyin duk sun koma yadda suke. Sardauna ya ce "Ya aka yi ya koma daidai? Me ta yi masa?" Mahmoudu ya ce "Ban san me ta yi masa ba, Nana" Ya yi maganar yana kallonta. Sai dai shiru ba ta amsa ba. Sultan ya taɓa Hammd yana kiran sunansa, amma shi ma bai motsa ba. Kawai su ka ga Nana ta fara jijjiga, duk su ka ɗan ja da baya a tsorace su na kallonta. Mahmoudu ya rasa me zai yi. Sai bin su da kallo. A hankali kuma ta daina ta nemi guri ta kwanta a ƙasa. Matawalle ya ce "Wai ni na kasa fahimtar wannan abin, me ya same su haka?" Mahmoudu ya ce "Kamar akwai wani abu da bamu sani ba, ko za mu ɗan ƙara ba su lokaci?" Matawalle ya ce "Ni kaina duk ya kulle, ban taɓa ganin abu irin haka ba ai" Ƙarshe sai sake fita suka yi, suka bar Nana da Imam Hammad. Can jimawa Nana ta farka, ta yi miƙa tana salati, ta kalli agogon bangon dakin ta ga lokacin sallar magariba ya yi. Ɗakin ba kowa daga ita sai Sayyid da yake bacci. Ta yinƙura da kyar ta tashi tsaye, ta fara dudduba ɗakin, ta samo banɗak a cikin sa. Ta yo alwala ta ɗebo ruwan a wata container ta zo ta ajiye ta tayar da salla. Tana idarwa ta koma kansa, ta ɗauki ruwan da ta ɗebo a container ta yi shiru tana kallon ruwan, a hankali suratul Mulk ta zo kanta. Ta karanta Bismillah ta tofa, ta karanta suratul Mulk har ƙarshe. Wata addu'a ce da Malam Auwwal ya kan yi mata, musamman idan ba ta da lafiya ta faɗo mata, wanda tun da take bata taɓa kwatanta karanta ta ba, ba ma ta taɓa sanin ta iya ba sai yanzu da ta faɗo mata a ka. Da sauri ta yi Bismillah shashshafa masa ruwan da ta yi tofin. Ta dafa kansa ta fara karanto addu'ar "Bismillahi arƙik, min kulli shai'in yu'dika, wa min sharri kulli nafsin, au ainun hasid, Allahu yashfika, Bismillahi arƙik." Ta ɗan koma gefe ta yi shiru tana kallonsa, tana fatan Ubangiji Allah ya ba shi lafiya. Ta tattaɓa shi tana kiran sunansa a hankali "Sayyid ka na ji na?" A hankali ya motsa ya buɗe idanunsa da suka yi jaa ya kalle ta. Ƙara ware idon ya yi sosai domin ya tabattar ita ce ko kuma dai mafarki yake yi. Ya yinƙura gaba ɗaya zai tashi, ya ji wani irin jiri ya kama shi, ga cikinsa a ƙulle. "Alhamdillah" Ta furta tare da faɗin "Sannu yi a hankali" Ta sassauƙe fululluka, ta jingina su a jikin gadon, sannan ta ɗago shi da kyar, ya yinƙura ya zauna sosai ya jingina. Sai dai tamkar zai cinye ta, haka yake bin ta da kallo. Ya motsa baki yana son ya yi magana amma bakin ya din ga rawa. Ta girgiza masa kai ta ce "Kar ka yi magana". Ya yi shiru yana ci gaba da kallonta. Ta ce "Ka sanni ne?" Ya lumshe idanunsa ya buɗe. Ta yinƙura ta nufi wani jibgegen fridge da yake ɗakin, ta je ta buɗe. Ta ɗaukko ruwan roba ta zo ta zauna a kusa da shi. Ta cire masa rigarsa jikinsa. Ta ƙara shashasha masa ruwan nan. Ta lura da yadda jikinsa yake rawa, yake kallon ruwan hannunta da har raɓa yayi saboda sanyi. Ta kalli ruwan hannun nata ta kalle shi, kamar yadda ta gan shi a bacci, ya rame sosai fatarsa duk ta bushe saboda rashin ruwa. Leɓensa har tsagewa yayi. Ikon Allah ne kawai ya raya shi zuwa wannan lokaci ba ci ba sha. Ta ce "Buɗe bakinka" bakin yana rawa ya buɗe. Ta ɗaga jarkar za ta zuba masa ruwan su Matawalle suka sake shigowa. Sardauna ya ce "Ke, mene ne wannan za ki ba shi?" Nana ta ce "Ruwa ne, a fridge ɗin can na ɗaukko" Sultan kuwa sai da ya ɗan rikice ya ce "Matawalle ya tashi" Nana ta fara zuba masa ruwan a bakinsa, ya kai hannunsa biyu ya danƙe jarkar yana ɗaɗɗakar ruwan. Ƙoƙarin ƙwace ruwan Nana take yi, amma ya shanye. Yana shanyewa kuwa ya yi mata amai a jikinta har ta hancinsa haka ya din ga fitowa. Matawalle ya ce "To ko Asibiti za a tafi a kai shi?" Sultan ya ce "Ɗan jira mu gani" Yana gama aman ya kifa a kafaɗar Nana. A hankali ta ce "Ka gani, saboda kar ka yi amai ya sanya na so na baka a hankali. Sannu" Ya yi shiru yana ajiyar zuciya. Ta kalli Mahmoudu ta ce "Taimaka ka kuma ba ni wani ruwan" Da sauri Mahmoudu ya sake ɗaukko ruwa ya kawo mata. Ta ɗago shi ta ce "Yanzu a hankali za ka sha, kar ka kuma yin aman, za din ga zuba maka kana haɗiya" Haka aka yi, ta din ga zuba masa a hankali yana sha, yana yi yana ƙoƙarin kai hannu ya riƙe robar, tana riƙe hannunsa tamkar ƙaramin yaro. Nana tana son ta sake da shi, amma idonsu Sultan, ya sanya ta din ga komai a ɗarare gudun kar ta yi wani abu su yi mata wata fassarar ko sharrin. Ya jingina yana ta haki saboda duk ya galabaita. Mahmoudu ya ce "Kuma ke bai shaƙe kin ba da muka fita?" Nana ta yi murmushi ta ce "Ramin kura ai sai 'ya'yanta Habu. Ka samo mana ko kayan marmari ne da shayin Buzaye ya sha. Ai za ka sha ko?" Ta yi maganar tana kallonsa. Ya ci gaba da kallon ƙwayar idon Nana, maganganu ne fal a cikinsa, amma babu halin furta su" Su na ta jera masa sannu, amma babu wadda ya amsa a ciki. Matawalle ya ce "Bari na yi magana, a sanya hadimai su kawo kayan marmarin ya ci" Nana ta ce "A'a ranka ya daɗe, a saka Mahmoudu ya kawo" Duk suka tsaya suna kallon Nana, amma aka rasa mai magana. Nana ta nuna masa Sultan ta ce "Ka san wannan?" Ya jinjina mata kai alamar eh. Wannan fa? Ta nuna Mahmoudu nan ma ya jinjina kai. Ta ce "Ni fa?" Sai ya yi shiru, har ta fara karaya, da tunanin ko memory ɗin nasa ya sake ƙwacewa ya manta da ita. Kawai hawaye ya fara zirarowa daga idanunsa. AREWABOOKS Cikin damuwa Nana ta yi masa murmushi ta girgiza masa kai. Sultan ya ce "Hammad, me yake damun ka ne? Akwai wata matsala ne?" Ya yi shiru bai kula Sultan ba, Nana ta yinƙura ta ce "Bari na je na wanke aman da ya yi" Sardauna ya ce "Kar ki damu, za a kai ki inda za ki kwana, ba ma son kowa ya san kina nan. Za a baki wasu kayan ma sannan za a zo a gyara gurin. Kai kuma idan ka kawo Abincin sai a ba shi" Nana ta jinjina kai, ta yinƙura da niyyar ta tashi, amma ya damƙe hannunta cikin nasa gam. Ta dube shi ta ce "Mene ne?" Ya tsare ta da idanu. Ta ce "Kar ka damu, ba nisa zan yi ba, zan dawo in sha Allah" Ya damƙe hannunta ya ƙi saki, yana murzawa a hankali. Matawalle ya ce "Ka na ji Imam, zamu je a kai ta masauki ne, inda za ta zauna ta huta, kaima ka ci abinci kafin a san abin yi, an tafi samo mai magani da zai duba ka." Kamar sassaƙe, haka ya yi shiru ya riƙe hannun Nana. Sardauna ya ce "Ina ga mu bar ta tare da shi kawai, zuwa da safe sai mu san abin yi" Haka suka mimmiƙe, ƙiri-ƙiri suna ji suna gani, suka kama hanyar fita, su bar shi da Nana. Nana ta ce "Habu, dan Allah ɗan tsaya ka taimaka mini" Ya ce "To" Bayan fitar su Nana ta ce "Dan Allah ka kawo mini kayana, sannan ka kawo mini kayansa guda biyu. Ka kawo mini Alkur'ani. Sai kuma Abincin nan dan Allah duk yadda za a yi kai tsaye daga hannunka zai zo, kar ya biyo ta hannun kowa. Sai kuma ina son ka kawo mini habbatussauda da tazargade, da ganyen magarya sai almiski ja" Ya ce "In sha Allah ranki ya daɗe, yanzu kuwa. Sai dai su abin da ki ka lissafa ɗin nan, sai dai na shigo da su a ɓoye kar su ce wani abin za a yi masa" Nana ta ce "Idan da matsala ba sai ka kawo su ba, kawo mini Abincin da kayan kawai, kar na saka ka a cikin matsala. Amma lokacin da hakan tana faruwa da shi da muna Nigeria, idan na yi masa amfani da su yana samun sauƙi sosai" Mahmoudu ya ce "Kina nufin a Nigeria, yana irin haka?" Nana ta jinjina kai ta ce "Har ɓarin jikinsa sai da ya shanye, ka kawo mini Abincin da sauri na ba shi" Ya ce "To" Ya kalli Hammad ya ce "Sannu Imam, Ubangiji Allah ya sanya kaffara" Sai da Mahmoudu ya fita sannan ta kalle shi ta ce "Cika ni na je na wanke jikina, ka ga ka yi mini amai a jiki" A hankali ya saki hannunta, amma har ta shiga banɗakin nan kallonta yake yi. Ta wawwanke jikinta ta fito ta ƙara goge gurin da ya ɓata da aman. Matawalle ya ce "Anya abin nan ba shiri ne yaran nan suka yi ba, saboda ya ci gaba da zama da yarinyar nan ba?" Sardauna ya ce "Nima sai da na yi wannan tunanin" Sultan ya ce "Bana tunanin shiri ne, babu yadda za a yi ya kwana takwas babu ci babu sha, a kwance a guri ɗaya a ce shiri ne. Kai Matwalle ka manta abin da ya din ga yi, lokacin da aka gano shi a Nigeria aka dawo da shi. Ba magana ba cin abinci a sume kawai kuma aka rasa abin da yake damunsa sai da muka je faransa sannan ya dawo hayyacinsa?" Ya yi maganar yana ƙoƙarin hana kansa, yi musu cikakken bayanin labarin da Mahmoudu ya ba shi, mussaman cewa da aka yi idan aka dawo da shi Nijar, zai iya haukacewa ko ma ya rasa ransa gaba ɗaya". Sardauna ya jinjina kai ya ce "To ai ita kanta yarinyar abar tsoro ce, ba ku ga abin da take yi ba? Ni abubuwan sun ɗaure mini kai sosai da sosai fa" Sultan ya ce "Tabbas lamarin akwai ɗaure kai, da ayar tambaya, dama Hammad ya gaya mini wani abu, amma dai bari mu ga abin da Allah zai yi, sannan mu jira zuwan mai maganin da aka tafi nema" ***** Mama ce take kallon Jamila cike da baƙin ciki da takaici. Kamar ta danne ta ta yanka ta ce "Jamila, so ki ke sai duniya ta san halin da muke ciki? Kin zaɓi mutuncinmu ya zube a rasa wanda zai aure ki saboda wannan abin kunyar. Tun kafin ya riƙa mu je a cire shi kin ƙi, Jamila kin fi son asirinmu ya tonu ko?" Ta yi maganar muryarta na rawa. Jamila ta girgiza kai hawaye na zuba daga idanunta ta ce "Mama ba zan iya zubar da cikin nan ba wallahi, ni tsoro nake ji, kuma kar zunubin ya yi mini yawa ba ki san adadin tarin zunuban da suke kaina ba. Ki bari na ji da wasu dan Allah, ki ƙyale ni kawai" "Jamila ni ki ke cewa na ƙyale ki? Kin gwammaci ki durƙusa ki haife mana shege a gida, Duniya ta gani a shaida?" Mama "Na duniya daga baya ne, Allah ya riga ya shaida ya ga komai, ni yanzu addu'ata Ubangiji Allah ya yafe mini. Wataƙila haifar ɗan nan ne zai sanya na samu nutsuwa ni dai dan Allah ki ƙyale ni" Cikin takaici ta ce "Jamila kin san haihuwa kuwa? Kin san azabar haihuwar ɗan sunna balle shege, tsaf za ki mutuwa fa" Jamila ta goge hawayenta ta ce "Idan na mutu gurin haihuwa na yi shahada, wataƙila Allah ya yafe mini tarin kura-kuren da na aikata" Cikin tsawa ta ce "Uban waye ya ce miki mai cikin shege za ta yi shahada" Jamila ta ce "Mama ba ki san tarin zunuban da suke kaina ba, tuban da na yi sai Allah ya karɓi shahadata." Takaici ya sanya Mama fara rafka wa Jamila maficin hannunta ta ko ina. Jamila ta tashi da sauri, amma ta bi bayanta tana ci gaba da raɗa mata. Baba ya kawo kai cikin ɗaga murya ya ce "Rabi, wannan wane irin rashin imani ne haka? Yaya yarinya ba ta da cikakkiyar lafiya za ki biyo ta kina duka, me ta yi miki?" Mama ta tsaya tana mayar da numfashi cike da baƙin ciki da takaici. Suwaiba kuwa da take gefe, ta din ga tuntsura wata irin dariya mara daɗin ji, wadda ke bayyanar da rashin cikakken hankali ga mai yin ta. Mama ta rasa ihu za ta zunduma ta ji daɗi, ko kuma me yakamata yi ta ji sanyi. Hutu da fatan arzikin da take da shi a kan 'ya'yanta duk ba ta samu ba, ga mahaukaciya ga karuwa Nasiru shi ma ya fara 'yan ɗauke-ɗauke, dan sau biyu 'yan vigilant na kama shi, da laifin satar tukwanen mutane da kayan ƙarafa ya sayar da sunan gwangwan. Dan tun da Jamila ta cire tallafin da take ba su, ta daina zuwa gurin Hajiya Sa'a, suka koma ruwa. Baba ya ci gaba da yi mata faɗa a kan dukan da ta yi wa Jamila, ba tare da ya tsaya ya ji cikakken abin da Jamilar ta yi ba. Ji ta yi tamkar ta kama shi shima ta jibge shi, ko ta huce. Dan duk wannan masifar shi ne sila da ya tsaya ya sauke nauyin da ya rataya a wuyansa da wataƙila ba su shiga wannan halin ba. Babban abin da ya ƙara ɓata mata rai, shi ne rashin zuwan Hajiya Sa'a ta duba Jamila, duk da taga kwana biyu ba ta zuwa maimakon ta neme su ta ji ko lafiya amma ba ta yi hakan ba. Ga Maman Khairat ta tashi daga unguwar da ta so zuwa a rakata gidan Hajiya Sa'a ta ji ko wani laifin Jamila ta yi wa Hajiya Sa'a haka?. Hajiya Sa'a kuwa tana can tana fama da kanta, dan tun mutuwar Abba ta shiga wani mawuyacin hali, duk lokacin da ta zauna babu abin da take yi sai tunanin ko yaya Abba ya ji da dodon ƙungiya ya zuƙi jininsa har ya mutu? Ta daina bibiyar duk wani abu da ya shafi kungiyar. Kasuwancin ma ta tattara ta ajiye a gefe ta koma guri ɗaya kawai. Daga kuka sai kwanciya da dana sani. Ga shi da ta fara tunanin wani irin mummunan ciwon kai yake yi mata dirar mikiya, har sai ta daina gani sosai. Wasu lokutan haka zata kulle kanta a ɗaki ta wuni, sai dai mai aikinta ta yi ta sabgoginta itakaɗai. Ta ce ko mutanenta sun zo, kar a bar kowa ya shiga inda take, kaɗaici kawai take so. **** Mahmoudu ya dawo, ya kai wa Nana shayi da kayan marmarin da ta ce . Sai kuma kayansu da Alƙur'ani. Ya haɗu da Sultan a hanyar da suke bi su shiga gurin. Domin wani sashi ne a can cikin sashensa da ba kowa ma ya san da shi ba. Hatta iyalansa sai da izninsa suke zuwa gurin. Wasu lokutan ya kan sanar da ya yi tafiya, ya tafi cikin gurin ya kulle kansa ya samu hutu da nutsuwa. Mahmoudu ya ƙarasa gabansa cikin girmamawa. Ya ce "Abincin ka kawo musu?" "Eh ranka ya daɗe" Sultan ya numfasa ya ce "Shikenan, amma ina fatan babu wata matsala barinsa tare da yarinyar nan, duk da na fuskanci tana da hankali akwai abubuwan da take ɓoyewa. Ni kaina ba komai nake son kowa ya sani ba" "In sha Allah Sultan, kare martaba, mutunci da kuma sirrikan Imam Hammad abu ne da ya zama wajibi a gare mu. Kuma tabbaci nake da shi ba yaƙini nake da shi, ba za ta taɓa aikata wani abu da zai cutar da shi ba" Ya jinjina kai ya ce "Na ga alamun haka, duk da na ga wasu abubuwa na ban mamaki a tattare da ita. Dama Hammad ya gaya mini sai mun neme ta, amma ban ɗauki zancen nasa da wani muhimmanci ba. Akwai wasu abubuwa da ya gaya mini da ban gama gane ma'anarsu ba, amma bari mu jira mu gani ya samu sauƙi" Mahmoudu ya risuna ya ce "Godiya muke ranka ya daɗe, Allah ya ƙara maka lafiya da tsawon kwana" Ya ɗaga wa Mahmoudu hannu. Nana na ganin Mahmoudu ta yi ajiyar zuciya, domin shi take ta jira ya kawo abin da za ta ba wa Hammad ya saka a cikinsa. Yana kwance a kan cinyarta tana shafa gashin kansa. Ya ajijiye mata kayan, Nana ta ce "Sannu da ƙoƙari, Ubangiji Allah ya biya ku da kai da mahaifiyarka, na fuskanci kirki da karamci a jininku yake, gado ka yi Nene akwai kirki" Ya ce "Allah ya taimake ki, ai kin ƙwace mini ita" Nana ita abin dariya yake bata, idan ta ji su na girmamata. Ta ce "Sayyid, ga abinci an kawo tashi ka ci" Mahmoudu ya taimaka mata, ta zaunar da shi. Ta zuba shayin a kofi, ta fara ba shi a hankali da cokali. Duk da wata irin yunwa da yake ji, tamkar ya haɗa da Nanan ya cinye, amma haka ya daure ya din ga karɓa a hankali. Ta ce wa Mahmoudu "Ka je ka samu ka huta, amma dan Allah ka zo da wuri, ka san ni da kai na saba, kuma kai kaɗai nake jin zan iya sakin jiki da kai. Sannan dan Allah abincinsa kar a bari ya biyo ta hannun kowa, ta gurinka kawai" Ya ce "In sha Allah, zan yi yadda ki ka ce, sai da safe" Sosai ya din ga cin kayan marmarin nan, yana sake shan shayin girfae da Habu ya kawo. Sai da Nana ta lura jikinsa ya daina rawa. Ya ɗan huta sannan ta tashi tsaye ta ce masa "Sayyid yinƙura a hankali ka tashi mu gani" Ya dafa gadon, ya tashi a hankali amma ya ji kamar kayan cikinsa zai zubo. Ta riƙe hannunsa yana durƙushe yana tafiya a hankali. Ƙofar banɗakin suka je, ta tsaya ta kalle shi ta ce "Mun yi wanka a Nigeria, yau za mu yi a Agadez ko?" Murmushi ya yi mata sai da haƙoransa suka bayyana. Suka shiga banɗakin. Sai dai wata irin kunyarsa da ba ta san daga ina ba, ta bujiro mata. Za ta iya cewa yau jiƙa-jiƙa kawai ta yi masa, saboda yadda ya ƙara yi mata kwarjini take ganin kamar wani aka canza mata. Babban abin da ya ƙara takura ta, shi ne kallon da yake ta bin ta da shi, kamar zai lashe ta. Da kanta ta yi masa brush, hakan ya din ga tuna mata da rayuwarsu ta Nigeria. Ta saka ya yi alwala, suka dawo ɗakin ta saka masa doguwar rigar jallabiya. Ta ce "To an ce kwananka takwas baka hayyacinka, yanzu zaka lissafa sallolin da suke kanka. Ka yi wanda zaka iya yanzu sauran sai ka ci gaba ko gobe in Allah ya kaimu ne" Ya jinjina kai, ya kalli gabas daga zauna ya tayar da salla, saboda ba zai iya tsayuwa ba. Nana ta din ga tunani ko ta roƙi alfarmar su nuna mata ɗanta ta gan shi, tun da nasu ɗan ya farfaɗo, amma wata zuciyar ta hana ta hakan, duk da tarin kewar Muhsin da take yi. Ta shiga banɗakin ita ma, ta yi wanka ta gama ta sako hijjabinta ta fito. Jakar kayanta ta buɗe, tana duddubawa, ta ga magungunan da Nene take bata na sha da wanka a ciki. Kawai ta yi murmushi ta shafa mayukanta, ta duba kaya masu sauƙin nauyi dan ta saka, dan duk da ba shi da lafiya ba za ta kwana shimfiɗa ɗaya da shi ba, da haryanzu ba ta san matsayinta ba, da matsayin kawo ta gurinsa ba, duk da da aka zo ita ta nema. Ga uwa uba rashin tabbacin da gaske tana da juna biyu ko kuwa?. Ta sakankance da salla yake yi, saboda a bayansa take zaune tana ƙoƙarin canza kaya. Kawai ta ji ya faɗo jikinta, suka faɗi ƙasa a gurin, hasken wutar ɗakin ya ɗauke baki ɗaya duhu ya mamaye ɗakin. Ayshercool 85 LITTAFIN KUƊI NE, KI BIYA KUƊIN KARATU KAFIN KI KARANTA. VIA 0069685771 AISHA ADAM STANBIC BANK 08081012143 Nana ta razana ta ce "Sayyid lafiya kuwa?" Ya rirriƙeta jikinsa na rawa. Nana ta yi shiru cike da damuwa, ga shi yanzu ta fara wahala da riƙon da yake yi mata, dan ya ninka wanda yake yi mata su na Nigeria. Haka ta haƙura ƙyale shi. Can bayan wani lokaci, hasken ɗakin ya dawo, a lokacin ya samu bacci, Nana ta yi shiru tana tunani daban-daban a kansa. Tabba! Tana da tarin tambayoyi da take buƙatar samun amsarsu, daga gare shi, dan akwai tarin abubuwan da suke faruwa, da suke ɗaure mata kai. Ta ture shi da kyar, ta tashi ta saka kayanta, ta kwanta a bayansa, tana jin yadda jikinta ya ƙara tsami da ciwo. Sai dai bayan bacci ya ɗauke ta, ta din ga munanan mafarkai marasa kyau da ban tsoro a cikin baccin. Abubuwan da ta din ga gani a gidan, sun tsorata ta. Har da yaƙe-yaƙen da aka din ga yi, kafin kafuwar masarautar, da irin azabar da bayi suka sha haka ta din ga gani. Ban da miyagun Aljanu masu ɗauke da siffofi daban-daban na ban tsoro a cikin baccin. Juyi ta din ga yi tana haɗa wani irin gumi, tana sauke numfashi saboda tsoro. Ga shi a baccin da fari a gefe take tana kallon abin da yake faruwa, kafin daga bisani ta ganta tsamo-tsamo a cikin rikicin da ake yi, daga bisani ma miyagun abubuwan suka din ga nufo ta. Cike da tashin hankali ta farka tana waige-waige. Amma ta yi ido huɗu da Hammad a zaune yana kallon ta, da alama ma sallolinsa ya yi. Mamaki ya kama ta, yaushe ya tashi har ya yi alawala ya zo yana rama sallolin. "Sannu ya jikin naka?" Ya jinjina kai yana kallonta. Ta sake cewa "Ka gama rama sallolin ne?" Ya girgiza mata kai, ta ce "To shikenan, bari na ƙara maka kayan marmarin, zuwa da safe sai ka fara gwada cin abinci" ya jinjina kai ta din ga ɓare masa ayaba yana ci, tana ba shi ruwa yana sha. Sai da ya yi mata nuni da ya ƙoshi. Ta tashi ta tafi banɗaki domin ta yi alwala ta ji mararta ta ƙulle. Ta tsuguna ta yi fitsari kawai ta ga fitsarin haɗe da jini. Ta shi ta yi cikin tsoro, ta gyara jikinta sai dai ta kasa gane jinin Al'ada ne, ko kuma na ɓari? Tun da dai ya ce mata tana da ciki. Ta kintsa jikinta ta fito, tun da ta fito idonsa a kanta, ta ƙaraso tana cewa "Sayyid, ka ce ina da ciki, yanzu kuma na ga jini ya zo mini, period ne ko ɓari?" Ta yi maganar tana tsare shi da ido, cike da son tabbatar da abin da take zargi. Kawai ta ga yana murmushi. Cikin rashin fahimta ta ce "To ka yi mini bayani ko da hannu ne, zan gane. Dan Allah cikin ne da ni da gaske ɓari na yi? Ko kuma ba ni da komai dama?" Ya ci gaba da murmushi yana ƙanƙance idanunsa yana kallonta, kamar ba mara lafiya ba. Ji suka yi ana bubbuga ƙofa, ya tsuke fuska kamar ba shi ne yake murmushi ba. Mahmoudu ya shigo da kwanukan Abinci. Mamaki ya kama Nana yadda ya iya zuwa da duku-dukun nan. Ya ƙaraso suka gaisa da Nana, ya kalli Hammad ya ce "Wai ya na ga daga jiya zuwa yau kamar ba kai ba. Ko dama rashin lafiyar ta ta ce?" Hammad ya ɗauki fulon hannunsa zai kai masa duka, amma ya kauce yana dariya. Sai mamaki ya kama Nana, dama yana wasa da Mahmoudu haka? Kodayake ko da suna Nigeria, su na hira amma ba sosai ba, a nan ma tun da ta fara ganinsu tare, duk maganar da zai yi masa cikin girmamawa yake yi masa. Amma kuma yanzu ta ga yana zolayarsa. Mahmoudu ya ce "Gimbiya ya jikin nasa, duk da daga haka ma Alhamdillah na ga alamun sauƙi a tattare da shi" Nana ta ɗan ɓata fuska ta ce "Dan Allah ka daina ce mini gimbiyar nan." "Wallahi dole a ce da mijin Iya Baba Nana, babu wadda ta dace da wannan sunan a kaf Agadez idan ba ke ba. Ya jikin naka?" Ya ƙarasa maganar yana kallon Imam Hammad. A sanyaye Nana ta ce "Ai maganar ba ta dawo ba tukuna sai a hankali" "Ikon Allah, kenan dai da gaske bayan tafiyata ya ci gaba da irin wannan ciwon, ni fa na zata tun da muka tafi bai sake yi ba. Amma Nana yaya abubuwa suka kasance ne bayan tafiyata, na san akwai tarin abubuwa marasa daɗi. Na san zuciyar musulunci ce ta sanya ki ke saurarenmu a yanzu ma, amma ki yi haƙuri. Har Nigeria aka je aka kama mu tare da su Sule. Sannan aka zo aka matsa ni da azabtarwa sai da na faɗi inda yake. Aka je gidan da ku ke gadi, ba kwa nan. Na raka su gidanku ina tsoron ya san yana da mata saboda gudun kar a cutar da ke. Ƙaninki ne ya gaya mini inda ku ke. Lokacin da aka je da ni shikaɗai muka tarar a gidan ba kya nan. Wallahi har aka ɗaukko shi sunanki kawai yake kira, yana ba zai tafi ya bar ki ba. Babu halin na faɗi cewa ya yi aure saboda na san hukuncin hakan a masarautar nan. Ga shi aka rufe ni a kurkuku da zargin ni ne na sace shi na kai shi Nigeria saboda ra'ayin kaina. Amma duk abubuwan da suka faru Nana ba su faru dan ni da Imam mu zalunce ki ba, dan Allah ki yi haƙuri" Tamkar ya sosowa Nana abin da yake yi mata ƙaiƙayi, da dannewa kawai take yi, ta fara hawaye. Ba Mahmoudu da ya ɗaukko maganar ba, shi kansa Imam Hammad sai ya rikice gaba ɗaya. Mahmoudu ya ce "Dan girman Allah ki yi haƙuri, da na san maganar nan, za ta ɓata miki rai da ban ɗaukko ta ba, ki yi haƙuri" Ta jinjina kai kawai, dan ita kanta ba ta san cikakken dalilin kukan ba, ta san dai tana buƙatar yin kukan ne ta samu afuwa a zuciyarta. Yau Sultan ne kaɗai ya zo duba Imam, sai dai ya ji daɗin yadda ya gan shi. Ya tarar har ya ci abinci ya yi wanka ya canza kaya, sai dai ba magana. Ya kalli Nana, ƙasan zuciyarsa yana yaba wa ƙoƙarinta da ƙarfin halinta. Ya ce "Kuma zai yi magana, na ga haryanzu bai ce komai ba" Nana ta sunkuyar da kai ta ce "Zai yi in sha Allah, sai dai wasu lokutan ya kan jima bai ce komai ba, kafin maganar ta dawo" Sultan ya jinjina kai cike da gamsuwa, ya ce "Muna godiya sosai da sosai. Ko akwai wani abu da ku ke buƙata?" Nana ta girgiza kai alamar a'a. "To shikenan, idan akwai wani abu, ki sanar da Mahmoudu ya gaya mini. An je za a taho da mai magani ya zo ya duba shi, idan kuma abin ba zai yiwu ba zamu kai shi Asibiti" Nana ta jinjina masa kai kawai. Inda Allah ya taimaki Nana, akwai pad a cikin kayanta, sai dai yanayin gurin babu gurin discarding pad ɗin. Cikin ikon Allah kuma ba ta zubar da jinin sosai. **** Sultan na zaune a sashensa, ya gama ganin wasu baƙinsa, aka yi wa Asal iso, ta shiga gurinsa. Bayan sun gaisa ta ce "Abie dama na zo ne ina son duba jikin Imam" Sultan ya gyara zamansa ya ce "Yarinyar kirki, Imam Hammad yana cikin yanayin da ba zai so a cika kawo masa ziyara ba. Dan haka mu na son ya samu hutu ne, kafin lokacin da za a samo mai maganin da zai duba shi" Cikin damuwa Asal ta ce "Ko sau ɗaya ne Sultan, jiya kwana na yi ina mafarkinsa, ina cikin damuwa ne" Ya ce "Na ga alamun hakan a tattare da ke, amma ki yi haƙuri ba za ki samu ganinsa ba, zuwa lokacin da zai samu afuwa sai ki gan shi har ma ku koma gida ma" Ba dan Asal ta so ba, haka ta haƙura ta tashi ta tafi. Tana kan hanya kiran Tafawa ya shigo wayarta. "Yaya ake ciki?" Ya tambayeta ba tare da amsa gaisuwar da ta yi masa ba. Ta ce "Yau ba a bani damar ganinsa ba, Sultan ya ce mini jikinsa ya yi zafi, dan haka ba zan samu ganinsa ba. Dole na jira zuwa lokacin da za a samo mai magani ya duba shi" "Ya dai tabatta haukan yake yi ko? Lokaci ya yi da zan bankaɗa abin nan, yadda Sultan zai kunyata daga shi har ɗan nasa" Asal ta ce "Dan Allah ka yi haƙuri, ba hauka yake yi ba, rashin lafiya... "Ke yi mini shiru, abin da na yanke dole haka za a yi, kar ki sake ki sake yi mini musu" Ya katse ta yana yi mata tsawa da dole ta sanya ta yin shiru. ***** Alhaji Fatuhu ne ya kira wani abokinsa, ya ce ya zo ya kai shi gidan Yayarsa Hajiya Sa'a a motarsa, saboda yadda baya samun ta kwana biyu a waya. Ko da yaje gidan, mai aikinta ta sanar da shi cewa ta ce ko waye ya zo, kar a sake a dame ta. Ya kalli mai aikin ya ce "Ko wannan dokar za ta yi aiki a kan kowa, ba za ta yi a kaina ba, dan haka yi mini magana da ita" Mai aikin ta shiga ta fito, ta ce "Na yi mata magana ba ta kula ni ba" Ba shi da zaɓin da ya wuce ya shiga ɗakin nata da kansa. Ya tarar da ita a zaune, daga mutuwar Abba zuwa yanzu ta yi wani irin tsufa, jikinta duk ya saki. Fuskarta duk ta yi wani iri kamar ba ita ba. A hankali ya taka da sandarsa, sai ta ƙura masa ido tama fara tunanin a ina ma ta san shi? Gaba ɗaya sai kanta ya toshe ta kasa tuna waye shi. Sai da ya ce "Yaya Sa'a, lafiya kuwa?" Yana yin maganar, sai kuma ta tuna shi. Ta yi zuru tana tunanin ya aka yi ya samu lafiya haka har yake iya takawa? "Yaya Sa'a me yake damunki?" Ya yi maganar cikin damuwar halin da ya tarar da ita. Kawai ta fashe da kuka. Cikin damuwa ya ce "Haba ke kuwa, kamar ba musulma ba, yanzu da ke Allah ya jarabta da halin da nake ciki yaya za ki yi? Dan Allah ki yi haƙuri mu ci gaba da yi wa Abba addu'a, amma wannan hanyar da ki ka ɗaukko, ba mai ɓullewa ba ce ba" Ya yi ta rarrashinta da lafuzzan ƙwarin gwiwa. Ya sanya mai aikinta ta kawo Abinci, ya tabbatar ta ci sannan ya yi mata sallama ya tafi. Sai dai bayan tafiyarsa sai ta hau tunanin abin da ya faru gaske ne ya faru, ko kuwa dai mafarki ne. Gaba ɗaya. Haka ta zauna tana ta lissafin yanayin. ***** Bayan majalisar Sultan ta cika, domin ci gaba da gudanar da sha'anin mulki na Agadez. Akwai takardu da a kan turo domin gabatar da su a tattauna. Mai karanto takardun ya warwareta, ya zuba wa takardar ido sannan ya numfasa ya ce "Zuwa ga Sultan da 'yan Majalisar sa baki ɗaya. Sanin duk wanda ya kwana ya tashi a Agadez ne, babu wani abu da muke martabawa, bayan addininmu kamar al'adarmu. Mu na kira ga Sultan da 'yan majalissar sa, su gaggauta duba ga al'amarin Imam Hammad. Babu yadda za a yi ya ci gaba da jagorantar majalissar Imam, ba tare da zoben tambari ba, wanda kawo yanzu babu wani cikakken bayani a kan inda zoben nasa yake. Sannan ya yi iƙirarin yana da ɗa, wanda haryanzu ba mu ji matsayar binciken da aka ce za a gudanar ba. A dan haka muke kira ga sauran 'yan uwanmu na majalissar Sultan, a gaggauta sanar da mutane sakamakon binciken da aka gudanar, sannan Imam Hammad ya fito gaban majalisar sarki, ya kare kansa, ko kuma ya sauka daga kan muƙaminsa na shugaban majalisar Imam, har zuwa lokacin da sakamakon binciken iƙirarin da ya yi na yana da ɗa zai fito. Idan kuma shaci faɗi ne abin da ya faɗa ta tabatta yana da matsalar ƙwaƙwalwa, kamar yadda jita-jita ta yi yawa. 86 A SAUKE HAKKI, A BIYA KUƊIN KARATU 0069685771 AISHA ADAM STANBIC 08081012143 Gaba ɗaya tsit majalissar ta yi, aka rasa wanda zai sake cewa wani abu. Wani abu mai ɗaci ya tsirga wa Sultan a zuciyarsa, yana takaicin kasancewar Tafawa ɗan uwansa, yadda yake nuna son ganin bayan jininsa wato Hammad duk saboda mulki. Ya san ko ba a gaya masa ba, da saninsa aka rubuta wannan takardar aka kawo. Surutu 'yan majalissar suka fara yi ƙasa-ƙasa. Sardauna ya numfasa ya yi gyaran murya, duk aka yi shiru Sannan ya ce "Ina ga wannan maganar mun riga mun yi ta a baya. Ban ga amfanin sake dawo da ita ba, mu na nan ana kan bincike a kan al'amuran kuma za a zo da sakamakon binciken, sake dawo da maganar ba abu ne da zai taimake mu ba, duba da yadda muke da tarin abubu a gabamu, da yakamata a ce an mayar da hankali a kai" Ɗaya daga cikin mutanen majalisar ya ce "A'a Sardauna, ba na tunanin wannan ba maganar da za a tattauna ba ce ba. Kar ka manta goben Agadez ta ta'alaƙƙa da waɗannan Imam da aka naɗa, su ma suke jagorantar wasu al'amuran na sha'anin sarauta, muddin aka ce da tangarɗa kuma ba a ɗauki wani mataki ba, to yana nufin goben ƙasar nan yana cikin hakin da ba a sani ba" Matawalle ya ce "Turaki ai dama sanin gobe sai Allah. Mu muna bulayinmu ne kawai. Amma kamar yadda mai girma Sardauna ya ce, a jira sakamakon binciken ya fito tukuna. Sannan wani batun taɓin hankali da ake danganta Imam Hammad da shi, batu ne mara tushe balle makama, sannan duk wanda muka samu da yaɗa wannan zancen, za a ɗauki ƙwaƙƙwaran mataki a kansa." Haka aka so tayar da hatsaniya, sai da Sultan ya tsawatar, haka aka watse daga zaman babu wata ƙwaƙwƙwarar magana. Sultan ya san tabbas tun da  Tafawa ya samu magoya baya a Majalisa, al'amura za su sake dagulewa ne, kuma za su ci gaba da bibiya su ji ƙwal uwar daka. ***** Shukura ce a kwance a ƙasa, sai burgima take yi, wani irin matsanancin ciwo yana ratsa ta. Sai jujjuya kanta take yi a galabaice. Kamar kullum mai ba ta abinci ya buɗe ƙofar ya ziro abincin ya ajiye mata ya tafi. Sai dai a duk lokacin da aka kawo mata abincin, idan aka rufe ɗakin duhu ne yake gauraye ko ina, amma sai ga yau da sauran haske. Ta ɗaga kanta a mugun galabaice ta kalli ƙofar ta ga kamar ƙofar ce ba ta rufu ba. Ta lumshe idanunta cike da azabar ciwo, wata zuciyar na azalzalarta ta je ta buɗe ƙofar ko a buɗe take, wata zuciyar kuma ta ce mata wahalar ciwo ne kawai amma ƙofar a rufe take. Ta ji ciwon na ƙara tsananta, yayin da wani abu mai ɗumi da ba za ta iya tantance ko na mene ne ba, yake bin ƙafarta. Ta din ga jan jikinta a hankali, ta lalubi bango ta dafa, a durƙushe ta ƙarasa gaban ƙofar ta saka hannu ta ja, kawai ta ga ƙofar ta buɗe. Ta zura kanta ta lelleƙa ta ga babu kowa a harabar gurin, daji ne sosai aka yi ɗakin a cikinsa. Tana faɗin "La'ila ha illa Anta Subhanaka Inni Kuntu mina Zalumin" Ta ci gaba da jan ƙafafuwanta tana takawa a hankali. Ko da ta duba jikinta sai ta ga alamun faya ce ta fashe, ga ruwanan mai haɗe da jini a jikin ƙafafuwanta da rigarta. Ba ta damu da yadda take gani dishi-dishi ba, saboda azabar galabaitar da ta yi, da kuma haske da ya cika mata ido, kawai ta saɓi hanyar da ba ta san ina ne ba, ta hau tafiya. Duk da duk taku ji take yi tamkar ɗan cikinta zai faɗo saboda nauyin cikin da azabar ciwo. Tafe take tana addu'a Allah ya kuɓutar da ita. Alhaji Fatuhu kuwa bayan komawarsa gida su na hira da Fadila ya ce "Fadila yakamata ku je ku duba Yaya Sa'a, saboda tana jin jiki nesa ba kusa ba, duk ta rame ta fita daga hayyacinta. Ta bani tausayi sosai da sosai haryanzu tana jin raɗaɗin mutuwar nan" Fadila ta ce "Allah sarki, har na tuna lokacin da na rasa Muhsin ɗina, da ta ce ba ni da tawakalli kamar a kaina a ka fara haihuwa, Allah sarki yanzu ta ji abin da na ji" Ya tsuke fuska ya ce "A taƙaice dai, gaya mini magana ki ke yi" Ta girgiza kai ta ce "Wace ni? Ai ban isa ba, kawai dai na tuna abin ne, kuma ya daɗe yana yi mini zafi" "To koma dai mene ne yanzu ya wuce, zan gaya wa Suwaiba, yakamata ku shirya ku je ku duba ta, a yi mata sannu, idan babu hali ma ina ga gara ta dawo gidan nan da zama, wataƙila kai komonmu zai rage mata damuwa da kaɗaici" Cikin sanyin ta ce "Ka manta ne? Ka manta mu ma a under notice muke, daga yanzu ko wani lokaci an ce mu fita mu bar gidan nan?" Ya yi shiru ya tafi zancen zuci. Ta ce "Dan Allah kar ka ɗaga hankalinka, mun samu Allah ya sanya ka farfaɗo da kyar. Ni da Maman su Janna za ta yarda da ɗan abin hannuna da nata, mu samu ko karamin gida ne a saya, ni ba na son hayar nan ko ɗaki uku ne mu koma" Ya waro ido ya ce "Ɗaki kuma? Ina ɗaki uku zai ishe mu rayuwa? Ko sashenki ɗakuna huɗu ne da falo biyu, ya yi mana kaɗan" Fadila ta ce "Daddy ka manta wacece Fadilan taka ne? Sai dai ku ya yi muku wahalar rayuwa ai ni na riga na saba, gidanmu ma na da daka auro ni ai ɗaki biyu ne ni da Umma" Ya ce "Ki daina tuna abin da ya wuce mana, ni ba ga shi kin zamo mana alkhairi ba. Da na tsaya duba wani shrime da ƙyale-ƙyale da daga ke har Suwaiba ba na tunanin za ku kasance da ni, duk da halin da muka tsinci kanmu. Ina ƙara yi muku godiya sosai da sosai" Fadila ta ce "Haba Daddy, ka cancanci fiye da haka daga gare mu, lokacin da ka ke da wadata ba mu ba, na kusa da mu ma ka yi musu, ka gatantamu ka kula da mu, sai Allah ya kawo mana jarrabawa kuma mu juya maka baya, da Allah bai barmu ba kuwa" Ya ce "Ke dai a yi sha'ani masoyiyya, idan Allah yana ƙaunar bawa, idan ya jarrabe shi ta nan, sai ya sassauta masa ta can, da yawa idan larura ta same su, iyalan nasu barin su suke yi. Kin san wani abu kuwa?" Ta ce "A'a sai ka faɗa Angona" Ya tuntsure da dariya ya ce "Ango ko?" Ta ɗaga masa gira tana murmushi. Ya ɗan ja kumatunta yana murmushi. Ya ce "Wannan rahar ma da nake yi da ke, ba tare da kin sauya mini ba saboda ba ni da lafiya, kuma ba ni da abin hannun yanzu ba, wallahi ba ƙaramin daɗi nake ji ba. Haƙiƙa larurar nan ta ƙara mini tsoron Allah da imani, ya ƙara kusantar da ni da Ubangijina, a duk lokacin da na motsa ambaton Allah kawai nake yi, gani nake rayuwata ce ta zo ƙarshe. Saɓanin lokacin da nake da dukiya da lafiya, ina ambaton Allah amma ba can sosai ba, ba kamar yadda na ƙara samun kusanci da Ubangiji ba lokacin da na rasa komai. Kuma a jikina nake jin wani tagomashin alkhairi yana kusanto mu in sha Allah" Ta ce "Haka ake so Daddy, ina fatan kuma ka canza tunaninka a kan magungunan gargajiya da na addini yanzu" Ya yi dariya ya ce "Na canza tuni, ke dai madalla da ke matar aljanna" Suka ci gaba da hira cike da nishaɗi. ***** Kwanakin Nana uku tare da Hammad, jikinsa ya yi ƙalau abin sa, sai dai magana ce babu. Nana ta yi iya ƙoƙarinta gurin tana kauce wa duk wani abu da zai sanya faruwar wata mu'amala tsakaninsu. A ƙasa suke kwana, ba ta taɓa kwanciya sai ya yi bacci, sai dai wasu lokutan ta ji ya ƙanƙameta idan ciwon ya motsa Sai dai tun da ya warware sosai, take ganin kamar ya canza mata, wani irin kwarjini yake yi mata yanzu, mussaman idan ya saka ta a gaba da kallo duk sai ta rikice. Ta kasa gane take-taken sa. Sai dai ta riƙi karatun Alkur'ani sosai da sosai. Sai dai tun wannan ganin na ƙarshe da ta yi wa Ƙaisar, ba ta sake ganinsa ba, ko a farke ko a cikin bacci ba. Duk ta damu shi ma ta na son sanin halin da yake ciki. Ga shi gaba ɗaya ta rikice, a kwana ɗayan da ta ga jinin nan, ba ta iya tantance wane jinin ta yi ba. Ɓari ko na haila. Tuni aka ƙara ƙawata ɗakin da kayan alatu, da kayan wanka da shafe-shafe na Imam Hammad, da duk wani abu da za su buƙata. Yana banɗaki yana wanka, ta gama cika cikinta da kayan marmari, dan ba ta fiye cin abincin da Mahmoudu yake kawowa ba, fruit take samu ta ci ta ƙoshi ta ci nama. Sai da ta fara tsorata kanta da tunanin anya ba cikin ne da gaske ba. Ta yi zurfi sosai da sosai a cikin tunani. Razana ta yi jin yadda ba ta ji alamun fitowarsa daga banɗakin ba, sai ji ta yi ya zagaya hannayensa a cikinta. Duk da ɗakin ƙato ne sosai da sosai amma duk ƙanƙantar motsi tana iya jinsa, amma sam ba ta ji motsinsa ba. Tsigar jikinta ta hau tashi, ta ji jikinta ya fara tsuma, tana neman ta rasa nutsuwarta. Ya ɗan yi murmushi ya cika ta, ya nuna mata gadon da yake ɗakin, alamar ta hau ta kwanta. Amma ta yi mursisi ta ƙame a gurin. Ya kama hannunta zai ja ta, amma ta ƙwace hannunta ta ja ta tsaya. Sai ya rabu da ita, yaje ya haye gadon ya kwanta. Ta tsaya a gurin tana rarraba ido, sai da ta ga ya jima da hawa gadon, ta lallaɓa ta ɗauki fulo ta ajiye a ƙasa ta kwanta. Kwanciyarta ke da wuya, ta fara jin sukuwar wasu halittu da ba ta san ko na mene ne ba, a cikin ɗakin. Hayaniyar  halittum ya ci gaba da yin amsa kuwwa a cikin kunnuwanta tamkar a filin yaƙi. Wani mutum ta gani ya shigo ta wata ƙofa, ba a iya tantance jinsinsa, ya rufe ko ina na jikinsa, yana shigowa ya nufi gadon da Sayyid yake kwance, ya ajiye wannan takardar, ya nufi wata ƙofa. Da azama Nana ta bi bayansa duk da yadda yake wani irin gudu kamar iska na kaɗa shi. Sai dai wannan sautin ƙarar ya hana ta ci gaba da bin sa. Rungume ta ya yi a jikinsa, jikinta na ta rawa, duk ta toshe kunnenta da hannayenta biyu. Saboda yadda take jin hayaniyar kamar zata tarwatsa mata kai. Ta ɗaga kai ta kalli Sayyid, ta kalli ƙofar ta ce "Akwai wani abu a nan?" Ya ɗan yi shiru, sai kuma ya yi gaba, ya buɗe ƙofar. Ya riƙo hannunta suka ratsa hanyar da take baƙiƙirin mai ɗauke da duhu, kai ba ka ce a cikin wannan katafaren ɗakin mai ɗauke da hasken fitilu hanyar take ba. Babu tsammanni ta ga sun ɓullo wani guri kamar corridor. Shimfaɗaɗɗen yashin sahara ne a gurin, gurin ya bayar da wani ni'imtaccen sanyi, ga tsilla-tsillar bishiyu da suke a bushe a gurin hasken farin wata ya haske saharar. Ta waiwaya ɗaya gefen, ta hango wani irin gini, mai kama da tsaunin dutse, hasken wuta na ci na tashi ta wata kafa mai kama da taga a jikin ginin Dutsen. Bakinta na rawa ta kalle shi ta ce "Sayyid na san gurin nan, tun kafin na sanka nake mafarkin saharar nan, har na zo na sanka, ina mafarkinka a cikin saharar nan. Kuma a nan nake yawan ganin ka tare da Giyaz. A waccan bishiyar ku ke zama da su Habu ku sha shayi da wasu mutane ma da ban san su ba. Ina ne nan, kuma meyasa abubuwan da nake gani a bacci suke dawo mini a zahiri, haryanzu ina da ayoyin tambaya da dama a kanka" "Yanzu kin yarda da nake gaya miki ruhinmu a haɗe yake? Ɗaya ba zai iya rayuwa babu ɗaya ba" "Ba wannan nake son ji ba, haryanzu akwai wasu abubuwa ɓoyayyu da ban gama fahimta game da kai ba" "Komai zai warware a hankali, za ki fuskanci komai rayuwata, amma ba na nufin cutar da ke ta kowace fuska, amma sannu a hankali za ki fahimci abin da ki ke kokwanto a kai." Ta buɗe idanunta tana ƙarasa jin sautin muryarsa a cikin kunnuwanta. A kan gadon ta gansu tare, fuskarsa na kallon ta ta, yana ta yi mata numfashi a fuska a hankali, wanda hakan ya ƙara dagula mata lissafi dan kuwa ita ta san a zahiri abin ya faru, amma ya rikiɗe ya juye ya koma kamar mafarki. Ga shi yanzu Ƙaisar ba cikakkiyar lafiya ce da shi ba, balle ta ce ko shi ne yake wujijjigata, hakan ya ƙara hargitsa mata tunaninta. Ta  tsura masa ido, kamar a fuskarsa za ta gano gaskiyar abin da take fata. "Meyafaru?" Sautin muryarsa ya doki dodon kunnuwanta. Ba ta ce masa komai ba, ta zame jikinta ta juya masa baya, tana ta tufka da warwara a zuciyarta. Sake matsawa ya yi kusa da ita, sai dai wannan karon bai yi magana ba, sai dai jin manufarsa, ya sanya ta zabura da sauri tana ƙanƙame jikinta. AREWABOOKS Ƙanƙance idanun ya yi, kasancewar fitilar ɗakin a kunne take, ya din ga bin Nana da kallo, yadda ta tsuke fuska ta sanya hannayenta tana kare jikinta. "Nana" Ya kira sunanta kamar yadda ake kiranta. Sai ta ji wani iri gaba ɗaya babu daɗi, ta kalle shi a tsorace. "Me yasa?" Ya furta a hankali. Ba ta ce komai ba ta sunkuyar da kanta, tana ƙoƙarin matsawa kaɗan. "Matata ce fa ke? Da gaske kin daina so na ko?" Ta ce "Ko ina sonka, ba zai yi mini wani amfani ba. Kuma a da ne nake da cikakken 'yanci a matsayin matarka, a Duniyar da nikaɗai ka ke kallo. Wannan duniyar kuma ka yi mini nisa, a yanzu ma na san da na gama amfani za a sallame ni, sake yadda da kai shi ne ganganci mafi muni da zan sake aikatawa" Ya ɗan fesar da wata iska daga bakinsa ya ce "Ki yi mini alfarma ki bani dama, na san tun da ki ka yadda ki ka sake dawowa kina so na, idan ba kya so na ba za ki yarda ki sake zuwa inda nake ba." Ya riƙo hannunta yana murzawa a hankali ya ce "Ba kya yi mini kwatankwacin son da nake yi miki. Kar ki hukunata ni da abubuwan da ki ke gani a zahiri kawai" A ɗan ƙufule ta ce "Ka ke son dai wadda ka ke so, ga matar so can kana da ita, wadda al'adarku ta amince ka so ka zauna da ita. Ai ni ina ga sai dai a saka ni a cikin bayi saboda baƙi da muni" Ta ƙarasa maganar tana tashi zaune. Shi ma tashi zaunen ya yi ya ce "A'a ai ni ban faɗi haka ba, ina da farar amma, nake ta bin ki ina lallaɓa ki. Dan Allah ni dai ki yi haƙuri, daga ni har ke mun yi kawar juna, wallahi ba ƙaramin kawaici nake yi ba kasancewata da ke a guri ɗaya" Baki buɗe take bin sa da kallon mamaki da rashin sanin abin yi. Cike da son tura masa takaici ta ce "Idan ba ka ce ba, amma ai a gabanka ta bautar da ni, ta wulaƙanta ni. Ba ƙaramin tozarta na yi ba da abubuwan da matarka ta yi mini ba. Ka je gurin halattacciyar matarka, da ahalinka suka san da zamanta, ba ni matar ɓoye ba" Ya ce "Haka ki ka ce?" "Eh" ta furta cikin tsiwa. Ya zuba mata ido yana kallonta, shi wani irin kyau mata ƙara masa, zuciyarsa har wani harbawa take yi da sauri kasancewarta a kusa da shi. Shi kansa ba zai iya cewa ga adadin abin da yake ji a kanta ba. A ransa ya ce "Ba komai ki yi yadda ki ke so, kin cancanta" A zahiri kuma sai ya sauka daga kan gadon, ya nufi hanyar fita. A ɗan ruɗe ta sauka daga kan gadon ita ma tana faɗin "Ina zaka je?" Bai yi magana ba ya ci gaba da tafiya, bayansa ta biyo da sauri tana faɗin "Sayyid ba ka da cikakkiyar lafiya fa, ina za ka je?" Ya rufa ta a cikin ɗakin, ya tafi. Ta jijjiga ƙofar amma ta ji ƙofar a rufe. Ta koma ta nemi guri ta zauna jikinta a sanyaye tana tunanin, kar wani abin ya same shi. ***** Tun da ɗan da ke cikin Shukura ya faɗo Duniya, ta fara ganin duhu, saboda wani irin bleeding da ta din ga yi. Matar da ta kawo ta Asibiti, gaba ɗaya a ruɗe take, saboda tun da ta haɗu da ita ba ta yi magana ba. Ga shi ta kawo ta Asibiti har ta haihu ba ta yi magana ba. Likitan ya ba ta shawarar ta kira jami'an tsaro ta sanar musu, saboda kar a je wani abu ya faru da ita. ***** Doctor Sharif kuwa tun da ya farfaɗo ya tashi da shanyewar ɓarin jiki, saboda tashin hankalin yadda ya ci karo da gawar 'yarsa cike da tozarci. Duk da maganarsa ba ta fita sosai, amma ƙoƙari yake yi ya tambayi ina matarsa, ya jikinta. Amma aka ce masa tana samun sauƙi, sai dai abin da bai sani ba shi ne, bayan tafiyarsa gurin 'yan sanda Allah ya yi mata cikawa. ***** Matawalle ne tare da Sultan suke tattaunawa, fuskar Sultan fal damuwa yake faɗin "Na rasa abin da na yi wa Tafawa a rayuwa, da yake nuna wa jinina wannan ƙiyayyar haka, abin da ba zan taɓa yi masa ba" Matawalle ya ce "Ai dama ba halinku ɗaya ba sam, ka kwantar da hankalinka mu bi a sannu, in sha Allah zamu samo mafita. Amma kwana biyu yaya ka ke ganin jikin Imam ɗin?" Ya ce "Jikinsa da sauƙi, ana samun ci gaba, sai dai ba ya magana sam. Jiya da yau nima ban shiga ba, ba na son yawan zarya da nake yi musu, kamar yarinyar a tsorace take da mu. Amma na yi mamakin yadda ta iya sarrafa shi ya dawo hayyacinsa." Matawalle ya ce "Allah ya baka nasara, ni fa ina jin tsoron a sake samun matsala" Sultan ya ce "Matsalar me fa?" "Kar a je wani abu ya faru, kana ganin yadda muke fama, ake tunanin yadda za mu ɓullo da lamarin bayyanawa Duniya ɗan gurin Imam Hammad da bayanin da za mu yi a gamsu. Yanzu kuma mun bar shi ya keɓe da ita idan aka kuma samun matsala fa?" Sultan ya ɗan yi murmushi ya ce "Sai mu karɓi ƙaddara, mu jira ta sake haihuwa. Amma ba na tunanin wani abu ma zai iya faruwa, tun da ba cikakkiyar lafiya ce da shi ba. Kuma mai maganin da aka je ɗaukkowa ne ya ɗan yi balaguro, yana ƙarasa warwarewa za a raba su daga ɗakin, mu ga me ya kamata a yi mata" Matawalle ya ce "Haka ne, Ubangiji Allah ya ba shi ingantacciyar lafiya. Sultan ya amsa da "Amin" Hammad bai sake dawowa ba sai bayan sallar asuba. Da ya shigo ma bai kai ko kalli inda Nana take ba. "Ina kwana" Nana ta gaishe shi tana satar kallon sa, amma ya yi mata shiru bai amsa ba. Gaba ɗaya sai ta ji babu daɗi shirun da ya yi mata. Ya je gaban mudubi yana gyara gashinsa, ta ƙarasa gaban mudubin ta ce "Kawo na gyara maka?" Ya harare ta, ya share ta ya ci gaba da taje gashinsa. Ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin aka yi, ya ajiye comb ɗin, ya kalli Nana ta je ta ɗaukki hijjabinta ta saka. Ya ƙarasa ya buɗe ƙofar. Mahmoudu ya shigo da kwanukan Abinci. Ya gaida Hammad, ya ɗaga masa hannu. Nana ta gaishe shi ya ce "Ni yakamata na din ga gaishe ki, uwar gijiyarmu. Ya mai jiki?" Nana ta ce "Asma'un dai. Mai jiki da sauƙi Alhamdillah ina Nene?" "Tana nan ƙalau, ga saƙon ki nan in ji ta, ina ta lallaɓata ta dawo Agadez, na ajiye ta a gidana amma ta ƙi" Ya yi maganar yana nuna wa Nana flask. Nana ta ce "Dan Allah idan ka koma idan za a bari na ganta, ka ce dan Allah ta taimaka ta zo na ganta, Kodayake da an sallame ni daga nan, gurinta zan je ta ce za ta raka ni gid.. sai dai sauran maganar ba ta fito ba saboda harar da Sayyid ya yi mata. Mahmoudu ma ya kawar da maganar, ya koma yi wa Hammad magana da yarensu. Hammad ya yi shiru yana saurarensa. Ba ta san me suke tattaunawa ba, amma da alama abin da suke tattaunawar ya ɓata masa rai. Ya tashi ya ɗaukko biro da takarda ya fara rubutu. Sai gaban Nana ya faɗi, zuciyarta ta fara raya mata ko takardar saki yake rubuta mata. Ya gama rubutunsa ya miƙa wa Mahmoudu, suka fita tare. Ta yi ajiyar zuciya ta buɗe flask ɗin da Nene ta bayar a kawo mata. Nana ta yi murmushi ganin naman kaza cikin flask ɗin, ta ce "Nene so take sai na fashe saboda girma" Ba ta sake ganin Hammad ba, sai da daddare, da yaje ya yi wanka, ya canza kaya ya nufi hanyar fita. Nana ta ce "Sayyid wai yau ma nikaɗai zan kwana a ɗakin nan? Amma ka san ɗakin nan tsorata ni ake yi" Ya ce "Me zan zauna na yi miki, zan iya ɓata miki rai idan na ci gaba da zama a ɗakin nan, gurin matata zan tafi" Ya yi mata maganar a gadarance. Ƙifta ido kawai ta yi idanunta suka yi jawur. Sai a lokacin ya yi dana sanin abin da ya gaya mata, biyo bayan tuna matsanancin kishi da take da shi. Ji yayi kamar ya bata haƙuri, ya koma ya zauna, amma ya yi jarumta ya fice. Sai dai tun da ya fita abin duniya ya dame shi. Tausayin Nana ya mamaye shi, ya sa dole ta yi kishinda Asal kuma ta ji haushin sa, mussaman yadda Asal ɗin ta din ga yi mata isa da iko, da nuna mata ita ba komai ba ce ba. Tun da ya fita Nana ta kasa zaune ta kasa tsaye, wani abu mai raɗaɗin gaske, ya soke mata a ƙirjinta zuwa wuyanta. Duk da ta saba ganinsu guri ɗaya, tana kishin hakan amma na yau ya yi mata ciwo nesa ba kusa ba. Bacci ɓarawo ne ya ɗauke ta, sai dai wannan mummunan mafarkin, na halittun nan, suka din ga bin ta, gaba ɗaya baccin ya gaza yi mata daɗi. Kafin Asuba ta farka da wani irin zazzafan zazzaɓi da ciwon da kai. A inda ta yi salla ta kifa kanta ta kwanta, zuciyarta cike da damuwa, ga jikinta babu daɗi. Ji ta yi an danne ta, ta buɗe idonta ta ga Muhsin ya ƙanƙame ta. Tashi ta yi zaune a rikice tana faɗin "Muhsin ɗina" Ya ƙanƙameta, ita ma ta rungume shi tana wani irin murmushi tamkar ta mayar da shi cikinta. Ta ɗaga kai ta ga Hammad a gefe, yana karyawa. Muhsin ya tashi daga jikinta, ya je gaban Imam ya ɗaukko dabino, ya dawo ya saka mata a baki, ya sake komawa ya ɗaukko ya kawo mata. Ta saka hannu ta karɓa tana jin wani irin tasirin alaƙa ta tsakanin uwa da ɗa. Sayyid ya ɗauki Muhsin, ya ajiye shi a kusa da shi, yana ba shi Abincin. Ya waiwaya ya kalli Nana ya ce "Naaa" ya din ga nuna mata kusa da shi, wai ta zo ta zauna ta ci. Sam Hammad bai nuna ya san tana gurin ba. Amma duk da haka yanayin ya yi mata daɗi mara misatuwa, yau ga mijinta ga ɗanta a guri ɗaya. Kuma alamu suka nuna mata, a zaman da Muhsin ya yi da su, akwai alaƙa mai ƙarfi a tsakaninsu. Dan duk ƙyuyar Muhsin ba ta ga alamar yana yi masa ba. Ƙarshe ta yi shiru tana kallonsu, ya shirya cikin jallabiya fara ƙal, ya shirya Muhsin da kansa, sai dai ga mamakinta ba ta ga ya naɗa rawani ba, ya saɓa ɗansa a kafaɗarsa ya yi waje. Ƙasan zuciyarsa kuwa raya masa ya din ga yi ya rungume ta, ya ji damuwarta, yana da abubuwan gaya mata da yawa, amma ya daure ya share ta. Sultan yana zaune, yana saka hannu a wasu takardu, tare da Tafawa da Sardauna. Aka shigo aka nema wa Tafawa iso. Gaba ɗaya suka shiga mamakin me ya kawo shi a daidai wannan lokacin. Bayan sun gaisa ya ce "Na samu takardar kiran da ka yi mini ne, shi ne na amsa kiran. Cikin mamaki Sultan ɗin ya ce "Ni ɗin kuma?" Tafawa ya ce "Amma saƙonna samu har gida aka kai mini takarda" Sultan ya ce "Ai ni ba zan aika maka da takarda dan ina neman ka ba, amma da mamaki" Tafawa ya ce "Ikon Allah, to waye ya aikata hakan?" "Ni ne" Imam Hammad ya amsa ya na ƙarasa shigowa gurin. Ayshercool 87 LITTAFIN KUƊI NE, KI BIYA KAN KI KARANTA 08081012143 Ƙwalalo manyan idanunsa Tafawa ya yi, ganin Imam Hammad ya fito gashinsa a buɗe, saboda hakan abu ne mai girman gaske, mussaman ga shugaba kamarsa,hakan kuskure ne. Ba wannan ya fi kaɗa shi ba ma ɗan ƙaramin yaron da yake hannunsa ne ya fi tafiya da tunaninsa. Ya girgiza matuƙa gaya da ganin yaron. Su Sultan ma sak suka yi, su na mamakin yaushe ya Hammad ya samu sauƙi har haka, har bakinsa ya yi wannan buɗewar? Ga uwa uba wautar da ya yi na zuwa da Muhsin ba tare da an gama shirya yadda za a kare hakan ba. Imam Hammad ya nemi guri ya zauna, cikin girmamawa ya gaishe su, bai damu da jiran su amsa ba. Ya dubi Tafawa ya ce "Mai girma Tafawa, ina fatan ban yi laifi ba, kasancewar a ƙarshen wasiƙata, ban sanar da cewa ni nake nemanka ba, ba Sultan ba. Na zaɓi saka gurin haɗuwar ya zama nan ne, saboda sai ya fi dacewa da abubuwan da suke bakina. Kun aika da takarda Majalisar Sultan, sannan an aika da wata majalissar Imams. Duk da kwana biyu ba na samun sukunin zaman majalisar. Na gayyace ka nan ne domin warware maka duk wani abu da ka ke son sani, ba kai ba duk sauran wanda suke son sani ma. Ba sai mun ci gaba da wahalar da shari'a ba. Kamar yadda na gaya maka wannan shi ne ɗa na Muhsin, ina da ɗa, kamar yadda na din ga jaddada maka, ka din ga ganin kamar shaci faɗi ne, wanda nan gaba kaɗan zan bayyana wacece mahaifiyarsa ba na son mu zurfafa a kan wannan bangaren dan abu ne da ya shafe ni. Abu na gaba kuma ana cewa ba ni da cikakkiyar lafiya ba zan ci gaba da gudanar da shugabanci ba. Haka ne, yakamata na matsa gefe na samu cikakken hutu da nutsuwa kamar yadda ku ka buƙata. Sannan kuma babu zobena na tambari a hannuna. Ina mai farincikin sanar da kai cewa daga yau, na sauka daga kan muƙamina na shugabancin majalisar Imam. Ba iya wannan ba ina san a cire ni daga cikin Imam da ake sanya ran a cikinmu ne za mu gaji sarautar Sultan shi ya sanya na fito maka haka babu rawani. Ka na damar maye gurbina na Imam ko ma shugabancin majalisar Imam ɗin baki ɗaya, ko kuma ka ɗora Imam Asadullah na muddin hakan zai sama maka farinciki da kwanciyar hankali. Ka bar mu mu huta da ni da mahaifina. A ƙarshe ina ƙara gabatar maka da ma petit Hammad wato Imam Muhammad H.J Agadez wato Muhsin" Ya yi maganar yana murmushi tare da shafa kan Muhsin. Ya sake kallonsa ya ce "Idan babu sauran magana, za ka iya tafiya, ina muma fatan ka fahimci abubuwan da suka shige maka duhu game da ni" Tafawa mutuwar zaune ya yi, tare da bin Hammad da ido, jin sun Sardauna yi shiru kuma babu wanda ya musa, ko ƙaryata abin da Hammad ya faɗa  ya sanya shi tabattar da abubuwan da Hammad ya faɗa gaskiya ne. Sultan da tuni gumi ya jiƙe shi ya ce "Ina  fatan ka ji daɗi, da ka kai shi bangon da ka sanya ya fito ya tabattar maka da abin da ka ke son tabattarwa? Ina ga shikenan za ka iya tafiya." Tafawa bai iya furta uffan ba, jikinsa a matuƙar sanyaye, ya tashi yana jan ƙafarsa, da yake jin kamar ba a jikinsa take ba, da kyar ya fice. Gaba ɗaya suka yo kan Imam Hammad da faɗa kamar za su dake shi. Hammad ya ce "Ina neman afuwarku, a kan abin da na aikata ba tare da izninku ba. Amma har abada ƙarya fure take yi, ba ta 'ya'ya, ba zamu dauwwama ɓoye wa duniya abin da komai daren daɗewa sai ya bayyana ba. Ba zan iya ci gaba da jure kullum lokacinku ya tafi a kan bani kariya ba, duk na san na aikata laifi, zan tsaya a kan laifina na karɓi duk hukuncin da ya dace". Sardauna ya ce "Kuma saboda shirme sai ka ce ka sauka daga kan kujerar Imam? Dama kai ka ɗora kanka?" Suka din ga yi masa faɗa, shi kuwa ko a jikinsa, dan gara ya ɓallo duk abin da zai ɓallo a san abin yi, duk abin da za a yi masa a yi masa, ya san yadda zai da matarsa da ɗansa. ***** Kamar yadda Alhaji Fatuhu ya umarci Fadila,ta shirya tare da babbar 'yarsaJannat, suka tafi duba Hajiya Sa'a. Sai dai Hajiya Suwaiba ba ta je ba, saboda ba ta jin daɗi. Ko da suka je, ƙin fitowa falo ta yi, sai su ne suka shiga cikin bedroom ɗin ta, suka same ta. Sai dai kamar yadda Alhaji Fatuhu ya ba ta labari, haka ta ga tsufan Hajiya Sa'a ya fito. Kamar ba ita ce 'yar ƙwalisar nan mai ado da kwalliya ba. Suka gaishe ta, amma sai dai ta sake shiga halin ɗimuwa ta kasa gane su, kawai dai ta amsa musu. Fadila ta sauke Muhsin da yake bayanta, tana ba shi ruwa saboda daga bacci ya tashi. Hajiya Sa'a ta ƙura masa ido, har sai da ya lafe a jikin mahaifiyarsa yana kawar da kansa daga kallon Hajiya Sa'a. Hajiya Sa'a ta ce "Da tuni wannan tsinannen ɗan ne zai mutu, amma nawa ɗan ya mutu, Allah ya isa ban yafe ba, kuma shi ma in Allah ya yarda sai ya mutu" Cikin mamaki da rashin fahimta Fadila da Jannat suke kallonta. Fadila ta ce "Tsinanne kuma Yaya Sa'a, me ya yi miki? Ba ki gane shi ba ne? Muhsin ne ɗan gurin ƙaninki Alhaji Fatuhu" A fusace ta ce "Shi ɗin fa, Allah ya tsine masa Albarka, shi ma Fatuhun Allah ya tsine masa Allah ya sa ya mutu. Da tuni Abba yana raye, amma bai sha alawar ba sai Abba ya sha ya mutu. Ke ma Allah ya tsine miki shashasha" Waro ido suka yi gaba ɗaya, cike da tsoro. Jannah ta ce "Kin ga Anty, tashi mu tafi na fara jin tsoro, kar ta fara kai mana duka" Babu shiri suka miƙe, Fadila ta goya ɗanta suka bar gidan, sai tsine musu take yi, tana faɗar wasu abubuwa da ba su gane kan abin da take nufi ba. ***** Asal ta sha mamaki, ganin mahaifinta a gidanta wanda idan ba da wani dalili ba baya zuwa, sai dai yanayin fuskarsa ya sanya gabanta faɗuwa. Kan ta yi magana ya ce "Hammad da gaske yake yana da ɗa, domin na ga ɗan nasa yau ido da ido, aurenki da shi bai amfana mini komai ba gurin cikar muradina ba, kaiconki da gaza cika wa mahaifinki burinsa" A burkice ta ce "Wane Hammad ɗin, yana tsare babu lafiya bai san waye a kansa ba ma?" Cikin tsawa ya ce "Zan yi miki ƙarya ne? Daga cikin gidan Sultan nake, lafiyarsa ƙalau sai dai idan raina miki hankali suke yi, na yi magana da shi, kuma har ɗan nasa na gani da idanuna" Hannu Asal ta ɗora a ka, tana lissafa maganganun da mahaifinta yake gaya mata. Da ta rasa mene ne gaskiyarsu. Imam Hammad kuwa, tun da ya shiga ɗakin, ya hango Nana ta yi ruf da ciki a kan gadon, ga sautin sheshsheƙar kukanta na tashi. Ya rufe ƙofar ya ƙarasa gaban gadon da hanzari. Ya ɗora hannunsa a bayanta ya ce "Ma vie" Tashi ta yi zaune idanunta jawur, ta ce "Ina Muhsin ɗin?" "Na mayar da shi inda yake. Ya na ji kamar jikinki da zafi ne? Meyafaru ma ki ke kuka? Wani ya shigo ne, ko an yi miki wani abu ban sani ba?" "Ni ka mayar da ni gurin Nene, tun da ka samu lafiya" "Yaushe na samu lafiyar? Ni ban samu lafiya ba tukuna, ba ki san me nake ji a jikin nan nawa ba" Yayi maganar yana ci gaba da shafa ta a hankali. Cikin kulawa ya ce "Ba ki da lafiya rayuwata, jikinki da zafi. Ga shi haushina ki ke ji kin ƙi yadda da ni, balle na ce ko Muhsin ne zai samu ƙani" Nana ta ci gaba da kuka, da ita kanta ta kasa tantance kukan me take yi. Ya yi murmushi ya ce "Yanzu kishin ne ya saka miki zazzaɓi ma viee?" Ture hannunsa ta yi tana kuka. Ya rungume ta a jikinsa ya ce "Da wasa nake miki, ban je ko ina ba fa da na bar ɗakin nan, a ƙofar ɗakin nan nake kwana, saboda idan mu na tare guri ɗaya akwai matsala ne. Ba kuma na son ɓata miki rai" Kwanciya ta yi sosai a jikinsa, ta saka hannu ta zagaye bayansa ita ma, ta yi shiru tana mayar da numfashi. Ya din ga murmushi yana shafa bayanta ya ce "Ki yi haƙuri, ba na ƙaunar na din ga aikata duk wani abu da zai sanya mini ke fushi da damuwa. Je vous aime ina son ki rayuwata". Nana ta ɗago tana kallon ƙwayar idonsa, idanunta fal hawaye. Ya jinjina kai ya ce "Da gaske nake Asmy, ina yi miki so mai tsananin gaske. A jinina nake jinki ba iya zuciyata ba" "Sayyid" "Na'am rayuwata" "Kar na sakankance da kai, 'yan uwanka su ce ba zaka zauna da ni ba, ban san ya zan yi ba Sayyid. Ba gudunka nake dan na daina sonka ba, tsoro nake ji. Na azabtu ko a iya haka a tsaya, ina son na samu nutsuwar ƙwaƙwawa da zuciya. Na kasance da abubuwan da za su sanya ni farinciki" Ta yi maganar a raunane. "Ke jaruma ce Asmy, kar wani abu ya baki tsoro, kai da fata komai zai faru ina tare da ke, zan zaɓe ki da ɗana a kan komai, babu butulci tsakanina da ke, ai na san babu wani abu da zan yi miki da zai sanya na biya ki ko na kamanta abin da ki ka yi wa rayuwata ba. Kuma ina fatan a wannan karon za ki ba ni dama ki saurari uzurina, inda na yi miki kuskure kuma ki yafe mini. Ki bani dama mu ɗora ginin rayuwarmu rayuwa mai kyau da aminci" "Ni ba biyana za ka yi ba, ban yi dan ka biya ni ba, ni kawai su bar mini kai, kuma su dawo mini da Muhsin mu rayu tare" Ta yi maganar tana kuka. Ya yi murmushi idanunsa na cika da hawaye, ya ce "An bar miki ni, halak malak. Hammad naki ne rayuwata" Ya yi maganar yana haɗe bakinsa da Nana. Babu tsammani aka banko ƙofar ɗakin, Nana ta yi wata irin zabura, shi kuwa cikin nutsuwa ya waiwaya ya ga waye wannan ya shigo musu babu neman izni. Da Asal ya yi tozali, jikinta na wata irin tsuma take bin su da kallo. Ta nuna Nana da yatsanta bakinta yana wata irin rawa, jikinta ma karkarwa kawai yake yi, tamkar ana kaɗa mata gangi. Ba ta taɓa tsammanin abin da za ta gani ba kenan, ko a hasashe da tsammani ba ta taɓa hasko ganin Nana tare da mijinta ba. Kasamcewarta baƙar fata da ba ƙabilarsu ba. "Ham..Ha.ha...Hammad!" Ta faɗa cikin wani irin ƙaraji mai razanarwa. Bakin Asal ne ya ci gaba da rawa, dan da fari ma kanta gaba ɗaya kullewa ya yi, ta manta wace ce ma Nana. Ita da ta zo tambayarsa ba'asin ina ya samu ɗa, sai ta riski abin da ya fi maganar da ta zo da ita tashin hankali. Hankali kwance Nana ta gyara rigarta, ba tare da abin da ya faru ya ɗaga mata hankali ba. Ja da baya Asal ta fara yi, numfashinta na fita da kyar, jikinta na wata irin kyarma. A sukwane Imam Hammad ya diro daga kan gadon ya nufe ta, cikin tashin hankali bai so Asal ta san alaƙarsa da Nana ta wannan sigar ba. Amma ya san babanta shi ne ya lalata komai. "Kar ka taɓa ni, kar ka ƙaraso inda nake Hammad. Ka yaudare ni ka zalunce ni, dama rashin lafiyar da ka ke yi ƙarya ka ke yi? Ka haɗa kai da mahaifinka ne dan ku yaudare ni ku cutar da ni? Lalata da wannan ƙasƙantacciyar ƙazamar matar? Na zaɓo ta a matsayin kukunka dan kawar da kanka daga kalle-kallen wasu matan, ashe yaudarata ka ke yi? Tun tsawon lokacin da ta gudu na neme ta na rasa, a she a nan ka ɓoye ta ku ke lalata." Cikin azama Hammad, ya danƙo hannun Asal, da take ta fizge-fizge ya danna ƙofar ya datse ta. Ya kalli Asal ya ce "Ki nutsu cherié zan yi miki bayani, ni ba lalata nake yi da Asmy ba" Cike da baƙin ciki take kokowar fizgewa cikin ƙaraji ta ce "Idan ba lalata ku ke yi ba, me ku ke yi? Tsawon wannan lokacin da ba ta nan, ashe ku na tare ka ji kunya ba ka ji daɗin halinka ba. Ke kuma 'yar iska mazinaciya wallahi sai na ƙasaƙantar da ke, sai na saka an kashe mini ke a kashe banza" Nana ta ce "Point of correction my dear, ba da kukun mijinki ki ke magana ba a yanzu,  kuma ni ba mazinaciya ba ce ba. Ki dai nemi wani sunan ki kira ni da shi" Ya kalli Nana da ta tsuke fuska ya ce "Ma vie dan Allah ki yi shiru, mu warware matsalar nan a hankali" AREWABOOKS Daskarewa Asal ta yi jin sunan da ya kira Nana da shi, wanda shi gaba ɗaya ya manta, saboda yadda sunan ya shiga bakinsa ya zauna. "Hammad gaskiya ne abin kunnuwana suke jiye mini? A gabana? Hammad" Ta furta tana ajiyar zuciya mai ɗauke da nannauyan baƙin ciki da tashin hankali. Damƙar hannun Asal ya yi, ya buɗe ƙofar suka fita tare. Kokowa ya shiga yi da Asal, yadda take kai masa duka, tana fizge-fizge. "Asal, ki tsaya ki saurare ni, kar ki ji wa kan ki ciwo mana" "Ba zan saurare ka ba, ba na buƙatar duk wasu kalaman yaudara da ƙarya da za su fito daga bakinka. Me ya rage bayan abin da na gani? Da girmanka da mutuncinka ka ɓoye kukunka a sashen mahaifinka kana zina da ita, ba ka ji daɗin halinka ba" Kalaman Asal sun yi wa Hammad zafi nesa ba kusa ba, da kyar ya haɗiye wani yawu mai zafi ya ce "Ni ba zina nake yi ba, idan ba ki tsaya kin saurare ni ba, ki ka fita ki ka yayata abin da ba shikenan ba za ki cutar da ni dan kin yi mini ƙazafi" Kallonsa take yi, tana jinjina girman yadda ya ƙware a iya wasa da hankali, ta ci gaba da ƙoƙarin fizgewa, amma ya riƙe ta gam. "Hammad ka gama raina mini hankali, dama ga batun ɗa ana yi, an ce ka na da ɗa da a ƙalla ya shekara biyu, yanzu kuma na kama ka da wata, amma kana iƙrarin zan cutar da kai? Da ni da kai waye ya cutar da wani? Wadda ka yi wa ciki ba ta ishe ka ba, ka ɗauki kukunka ka sanya a sashen Sultan ka ke lalata da ita" "Ban taɓa cutar da ke ba Asal, a shekara goma sha biyu da muka yi da ke, idan zan iya aikata abin da ki ka faɗa kin sani, idan akasin hakan ne ma kin sani. Amma mu je gurin Sultan ɗin ki ji komai daga bakinsa. Nana kuwa guntun tsaki ta yi bayan fitarsu, ta tashi ta shiga banɗakin ta yi wanka, ta yi alwala. Ta ƙura wa kanta ido a mudubin banɗakin, tana tunanin yadda Asal ta din ga yi mata kallon ƙasƙanci, da bautar da ita ta ƙarfi da yaji, saboda tana da kuɗi da mulki, a matsayinta na kishiyarta, kuma ta daure ta haɗiye. Ta ci gaba da tunanin daga bisani ta fito da niyyar ta canza kaya, amma ta kasa, ta nemi guri ta zauna ta yi shiru. A zuciyarta take addu'a ta ce "Allah ga Nana, bakwarka ce ni mai raunin gaske, ga ɗan jaririn ɗa na da nake fatan ya samu kyakykywar rayuwa ya tashi a tsakanin uwa da uba. Ubangiji Allah ka na ji ka na gani, ka ga wahalar da na sha a baya, ga shi na zo wani bugire da nake sanya ran samun afuwa, sai dai alamu sun nuna an fi ƙarfina. Allah idan sun fi ƙarfina ba su fi ƙarfinka ba, da ni da su duk bayinka ne. Ubangiji Allah ka sassauta mini ka kawo mini ɗauki. Ubangiji Allah ka yaye mini wannan kishin da nake ji, ka sanya su bar ni na rayu da mijina da ɗa na. Ubangiji Allah ka ba wa mijina ingantacciyar lafiya ka yaye masa abin da yake damunsa, Allah ka ba kare mini ɗana daga dukkanin sharrin da ido ka iya gani, da wanda ma baya gani. Ƙaisar ma bawanka ne, Allah ka ba shi lafiya. Allah ka ga wahalar da na sha a baya, yanzu idan na koma suka raba ni da ɗa na, wata wahalar zan shiga, Allah ka kawo mini agaji" Sai kuma ta yi shiru tana nazari, duk abin da take faɗa ai Allahan yana ji yana gani. 'Idan ba ubangijina ba, wa nake da shi da zan kaiwa kukana kai tsaye ya share mini. Na san ya sani amma ƙara gaya masan, yana sama mini nutsuwa da kwanciyar hankali, ko da ina cikin damuwa. Ta ba wa kanta amsa. Asal ce a gaban Sultan, tana ta uban kuka, fuskar nan ta yi jawurr, idanunta sun kumbura sosai da sosai. Sultan ya yi shiru, saboda yadda abubuwan shi kansa suka kulle masa kai. Gaba ɗaya bai yi tunanin abubuwan za su damalmale har haka ba, ya ma rasa ta ina zai fara. Ya ce "Ki na ji na Asal. Wannan maganar abu ne mai faɗin gaske, da ko ba ki gano ba, dole za a yi miki bayani. Amma wannan bayanin ba ke kaɗai yakamata mu yi wa ba, a gaban mahafinki yakamata mu yi shi. Tabbas da gaske Imam Hammad ba shi da lafiya, kuma ke ma shaida ce, saboda kin zo kin gan shi a halin da yake ciki. Sai dai ita wannan yarinyar tana da alaƙa da samun sauƙinsa. Yanzu bayanin da zan yi miki ba za ki gane ba, ina son sai mun zauna gaba ɗaya za mu yi miki bayani. Amma ki samu nutsuwa ki kwantar da hankalinki. Gaba ɗaya Asal ba ta fahimci abin da Sultan yake gaya mata ba, gani take kawai yana ƙoƙarin goyon bayan ɗansa ne. Muryarsa ta sake tsinkayowa yana faɗin "Kar ki bari kowa ya ji maganar nan, sai mun zauna an yi miki bayani tukuna dan Allah." Ya dubi Imam Hammad ya ce masa ya kai Asal gida, ya rarrashe ta, ta samu nutsuwa kafin a yi mata bayanin komai. Nana kuwa kajin gurin Nene ta samu ta ci, saboda taga alamun idan ta biye ta kishin nan, yunwa ce za ta kar ta a banza, duk da yanzu naman duk ya ishe ta, abinci take so ta ci sosai. Ga shi ta yi zaton ko zai dawo mata da Muhsin, amma bai dawo mata da shi ba. Ba ta sake ganin Hammad ba, sai bayan sha ɗaya na dare. Idanunsa jawur da alama yana cikin damuwa kuma ko abinci ba ta tunanin ya ci. Sau ɗaya ta kalle shi ta basar, ba ta ko kula shi ba. Gani ta yi ya cire rigar jiknsa ya yar a ƙasa, ya hau kan gadon ya kwanta, ba ta motsa ba ta ci gaba da zamanta, dan haushinsa ne ma ya kama ta. Jin ya fara numfarfashi ya sanya ta tashi tsaye. Ta kalle shi ta ga ya fara komawa ja. Sai kuma jikinta ya yi sanyi, abin da ta lura da shi kamar ciwon ya fi tsananta masa a Niger. Ta fara ƙoƙarin ninke masa rigar, kawai wannan takardar ta faɗo daga aljihun rigar. Ta ɗauki takardar ta yi shiru tana kallon takardar. Ta hau kan gadon ta juya shi da kyar, taga yana ta taune leɓensa yana jujjuya kansa. "Ki yi mini addu'a, zan mutu" ya furta da kyar kamar numfasihinsa zai ɗauke. Suratul Fatiha ta din ga karantawa da Bismillah tana tofa masa. Fizge-fizge ya fara yana girgiza kai ya ce "Tashi mu tafi" Cikin rashin fahimta ta ce "mu je Ina?" "Ki tashi nu tafi, kafin na rasa raina" Ya ƙarasa maganar yana dafe kansa da yake jin kamar zai yi bindiga. Ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin aka yi. Amma ba damar Nana ta tashi, saboda yadda ya rirriƙeta. Ga shi ta san ko ta ce a shigo babu lallai a jiyota daga waje. Mai bugun ne ya gaji da bugawa, ya turo ƙofar, Sultan ne tare da wata babbar mace fara solnda ita. Sai kuma Mahmoudu. A rikice suka ƙarasa gaban gadon, cikin tashin hankali Sultan ya ce "Jikin ne?" "Ki tashi mu tafi, zan rasa raina, ƙwaƙwalwata za ta tarwatse. Ki yi mini addu'a" Tuni Nana ta fara kuka, ta ce "Ina yi maka, kai ma ka din ga yi ko a zuciyarka ne. In sha Allah babu abin da zai same ka" Matar ta ce "Wannan ce matar tasa?" Sultan ya jinjina kai ya ce "Ita ce" Ta ce "Ikon Allah, lallai Allah gwani ne" Mahmoud kuwa jiki a sanyaye ya ce "Sannu Imam" "Hamud, dan Allah ka ɗauke ni ka sake tafiya da ni, ba na son zaman garin nan, ba ku san me nake ji ba." Mahmoudu ya kalli Sultan ya ce "Ranka ya daɗe, a irin wannan yanayin fiye ma da wannan, na bar Niger da shi a wancan lokacin. To kuma na ga alamar jikin na neman sake dawowa. A hankali ya fara fita hayyacinsa, ya fara lanƙwasa Nana, ta rintse idanunta Sultan ya ƙarasa da sauri yana faɗin "Kai kar ka yi wa 'yar mutane illa, Hammad" Mahmoudu rasa abin yi ya yi, dan ya san ganganci mafi girma da zai aikata shi ne ya taɓa jikin Nana garin ƙoƙarin ɓanɓare shi daga jikinta. Sai kuma Sultan ya ja ya tsaya shi ma ya rasa abin yi. "Ke kin san me nake ji ai" ya sake futawa cikin ƙarfin hali. "Na sani, shi ya sanya nake yi maka addu'a" Sultan ya ce "Hammad, kar ka ji mata ciwo fa" A hankali Nana ta ce "Ba zai ji mini ba in sha Allah" Addu'a ta ci gaba da yi masa, tana tofa masa. Sultan kam kasa jurewa ya yi, saboda ba ƙaramin tashin hankali yake shiga ba, idan ya ga ɗan nasa a cikin wannan yanayin. Sai kusan ƙarfe biyu na dare sannan ya dawo hayyacinsa gaba ɗaya. Ya yinƙura ya tashi zaune yana kallon Nana. Ta ce "Sannu. Ka daina jin abin da ka ke ji ɗin?" Ba ta yi zaton zai iya magana ba ta ji ya yi, ya ce "Ina ji amma ya lafa mini" Ta ce "To Allah ya baka lafiya ingantacciya. Amm ka yi haƙuri kana cikin yanayin larura zan tambaye ka abu" ya yi shiru yana kallon ta. Ta ɗago masa wannan takardar ta ce "A cikin rigarka na ganta, waye ya saka maka ita?" Ya girgiza kai ya ce "Nima ban sani ba" Ta sake cewa "Shekaranjiya wani abu mai kama da mafarki ya faru, har muka fita ta wata ƙofa, gaske ne ko kuma mafarki nake yi?" "Gaske ne" Ya bata amsa kai tsaye. "Ina buƙatar fahimtar wasu abubuwan, dan ka na yin abubuwan da ba kowane ɗan Adam ne zai iya ba. Tun mu na Nigeria ka ke yin wasu abubuwan. Kuma ina buƙatar na ji abubuwan da suka faru wanda ban sani ba" Ya numfasa ya ce "Zo ki raka ni shan iska tukuna" Suka sauka daga kan gadon. Ya zira rigarsa ya buɗe ƙofar nan, suka ƙara ratsa duhu suka fita wannan corridor. Yau ma saharar ta gani, gurin ya ɗauki sanyi sosai da sosai. Ta kalli Wannan tsaunin dake gefen saharar ta ce. "Wai mene ne a cikin dutsen can, shi nake son sani" Ya kalli gurin ya ce "Nan ne ainihin inda kakanninmu suka fara mulki, dan haka duk wani kayan tarihi, a ciki a ke adana su" Nana ta ce "To ka gaya mini abin da na tambaye ka, kuma ina son ka kai ni na ga abubuwan tarihin garin naku" "Zan kai ki, kuma zan yi miki bayanin amma yanzu ba na jin daɗi" Ta ɗan shafa bayansa ta ce "Sannu" ya jinjina mata kai. Ya matsa kusa da ita, ya rungume ta, sanyin gurin ya din ga ratsa su a tare. Ta ɗaga kai tana kallon wannan tsaunin, da ya ce mata gidan tarihi ne, tana jin kwaɗaituwa da son sanin abin da gidan ƙunsa. Tana jin kewar Ƙaisar, ta damu sosai ta san ya jikinsa, amma ko sama ko ƙasa ta daina ganinsa. Ta lumshe idanunta ta buɗe, kewar gida kuma na sake bijiro mata, tana cikin matuƙar fargaba a kan irin karɓar da za a yi mata idan ta koma. "Ma viee" "Na'am Shugabana" "Ina da wani kyakykywan albishir da zan baki, amma ba yanzu ba" Ta yi murmushi ta ce "Sai yaushe?" "Sai an wa Muhsin ƙani" Ta ce "Babu rana kenan" "Akwai mana nan kusa" yayi maganar yana ƙara ƙanƙameta. Asal kuwa yadda ta ga rana haka ta ga dare, dan faɗa suka yi kaca-kaca da Hammad, duk da rarrashin da Sultan ya yi mata. Ta kira Hasna a waya, Hasna ta ɗaga tana "Faɗin Gimbiya Asal, kwana biyu" Cikin kuka ta ce "Hasna, kin san abin da Hammad ya yi mini kuwa?" Gaban Asal ya faɗi ta ce "Meyafaru?" "Hasna wai Hammad yana da ɗa" "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ɗa kuma kamar yaya?" Cikin kuka ta ce"Ɗa dai ya haihu da wata, Tafawa kuma ya tabattar mini da hakan, kin san ba zai yi mini ƙarya ba. Kuma ba na ce miki yarinyar nan ta gudu ba, mai yi masa girki ba, har nake ce miki duk inda ta gudu zan saka a nemo ta" Hasna ta ce "Eh haka ne" "Na je na kama shi da ita, a can cikin sashen Sultan, duk tsawon lokacin da aka shafe ba ta nan, suna tare su na lalacewa, na shiga uku Hasna, ji nake kamar na kashe kaina na huta. Na tsani Hammad na tsane shi, ban taɓa cin karo da abin da ya gigita ni ba, kamar abin da na gani yau ba. Kuma Sultan goyon bayansa yake yi, wai in bari za a yi mini bayani, bayanin me za a yi mini an cuce ni Hasna" Ta yi maganar tana ƙara rushewa da kuka, kamar wadda aka nuna wa ranar mutuwarta. Hasna ta ɗan yi shiru sannan ta ce "Asal, ki yi haƙuri ki nutsu, ki tattara hankalinki guri ɗaya kar ki yi ganganci da rayuwarki. Amma ni kwanaki na ji Al Hussain yana cewa ya kira shi ya ce ya yi masa bincike a kanta, a nemo kamfanin da suka kawo ta. To ni ban kawo komai a raina ba, na ɗauka da saninki, amma zan tambaye shi ko ya san wani abu. Amma dan Allah ki yi haƙuri ki kwantar da hankalinki" "Ba ki san me nake ji ba, hankalina ba zai taɓa kwnaciya ba" Haka Asal ta kwana ido biyu, babu abin da take hangowa sai abin da idanunta suka gane mata a tsakanin mijinta da wannan baƙar yarinyar. Bangaren su Nana da safe, da Mahmoudu ya kai musu abinci, ya sanar musu da cewa Sultan ya ce su zo gaba ɗayansu, mai maganin ya ƙaraso. Hammad ya ce "Waye mai maganin?" Ya ce "Ban san waye ba, kawai dai saƙon da ya bani kenan" "Ni fa ba na buƙatar wani mai magani, ga maganina nan a gefe na" Ya yi maganar yana kashewa Nana ido. Ta basar da shi, ta ɗan yi murmushi. Ya karya sannan suka rankaya suka fita tare. Tun da aka kawo Nana, sai a lokacin ta samu damar sake fitowa daga ɗakin da suke. Sai dai wani surƙuƙin ɗakin suka shiga. Abin har mamaki yake ba wa Nana, yadda ake ɗakuna a lunguna da saƙo na gidan, kamar marasa gaskiya, inda ba ka yi zato ba ma, sai ka ga ɗaki ne. Da Asal ta yi tozali a ɗakin, idanunta jawur, tana ganin Nana ta sake tsuke fuska, kamar ta tashi ta kashe ta ta huta. Suka je gaban Sultan suka gaishe shi, Nana ta basar ko kallon inda Asal take ba ta yi ba. Sultan ya ce "Asal, na saka an kira ki ne, saboda a yi komai a gaban idonki, a ji me mai maganin zai ce, saboda kina da hakki ki sani kar ki ga ana ci gaba da rufe ki a kan abubuwa, tun da mijinki ne" Ta yi shiru, saboda shi kansa Sultan ɗin haushin sa take ji. Sallamar da aka yi ne ya sanya Sultan yin shiru, Nana kuma ta miƙe tana faɗin "Kaii Sarki, dama ka na nan?" Ya yi dariya ya ce "Tuba nake uwar gijiyata, tuba nake uwar ɗakina" Bakin Nana ya ƙi rufuwa, tamkar ta ga wani ɗan uwanta na jini. Cikin murmushi ta sake cewa "Sarki mai baka mai aska, kai ne mai maganin da zaka duba Sayyid?" Ya ce "Ni ne uwar gijiyata, an yi mini lamuni, ko kuwa na koma ba a bani dama ba?. Ayshercool 08081012143 88 1K NE VIA 0069685771 AISHA ADAM STANBIC IBTC BANK 08081012143 Nana ta kalli Sarkin baka ta yi murmushi ta ce "Wane mutum! Dama zan sake ganinka?" Ya yi murmushi, hadimin da ya rako Sarkin baka, ya ankarar da shi Sultan. Cikin girmamawa Sarkin baka ya risuna ya kwashi gaisuwa a gaban Sultan. Sultan ya ce "Na ga kamar ka santa ko?" Ya jinjina kai ya ce "Ƙwarai uwar gijiyata ce" Sai kuma ya sauke idanunsa a kan Sayyid, ya yi murmushi ya kalli Mahmoudu ya ce "Kamar ba ka gane ni ba ko?" Mahmoudu ya ce "Ina dai yi maka kallon sani" Ya matsa gaban Hammad, ya zuba masa ido ya ce "Ka tuna ni?" Hammad ya yi shiru sannan daga bisani ya ce "Na tuna ka" "Waye ni?" "Ba zan iya cewa ga waye kai ba, amma mun je gurinka a Nigeria" Sarkin baka ya yi murmushi ya ce "Yanzu tunaninka kaf na zamanka a Nigeria ya dawo kana tuna komai?" Ya jinjina masa kai alamar eh. Ya dubi Nana ya ce "Kin ga batutuwan duk da na gaya miki sun dawo ko? Kin yarda ko haryanzu kina da ja?" Nana ta girgiza kai ta ce "Ba ta sauya zani ba, ina nan a kan bakana" Ya ce "Babu laifi, amma an bani dama ko kuma na bar lamarin tun da na manya ne?" Matawalle ya ce "Bawan Allah, ina ganin ka yi abin da aka kawo ka ka yi mana. Idan ma wani abu ne a tsakaninku, kwa tattauna daga baya. Nan ba gurin wasa ba ne" Sarkin Baka ya tsuke fuska ya kalli Matawalle ya ce "Duk cikin aikina ne, kai ka san wacece wannan kuwa? Ku na da maganin matsalarku a tare da ku, amma ba ku sani ba" Gaba ɗaya suka kalli Nana, ita ma ta yi sororo cikin mamaki. Sarkin baka ya ce "Allah ne ya taƙaita masa, ba domin tana tare da shi ba, da sai ya zare ko ya mutu" Sultan da Mahmoudu suka haɗa ido. Sarkin Baka ya ce "Ni yanzu  abu ɗaya zuwa biyu zan ce, sauran magana ce tsakanina da ni da shi da Nana Asma'u Uwar ɗakina ba Allah ya taya miki" Ya yi maganar cikin girmamawa da jinjina wa Nana. Nana ta sunkuyar da kai tana murmushi. Mahmoudu ya ce "Bawan Allah, nan fa a gaban Sarki ka ke, in yi maka da yaren da zaka fi ganewa" Sarkin Baka ya ce "Nima Sarki ne, dan haka a bari ni na gudanar da aikina. Kai ka manta Garba ga Baka ga Aska da ku ka kai mini wannan ɗan uwan naku can Nigeria" Mahmoudu ya yi sak ya ce "To ai na ga kamaninka sun canza?" "Eh, ba kamannina ne suka canza ba, dan baka ganni cikin kayan aikina ba ne ba." Sultan ya ce "Asal tashi ki je, duk abin da  aka tattauna za a gaya miki" Asal ta ce "Allah ya baka nasara, dan Allah ina roƙon alfarma, a yi komai a gabana, ina son sanin halin da yake ciki nima". Sardauna ya ce "Ke Asal! Ki nutsu ki saurara tukuna, ki tsaya mu ji kan rashin lafiyar tasa, sannan a yi miki bayani daga baya" Asal ta tashi jiki a sanyaye, tana kallon inda Nana take da kuma Hammad ta fice. Sarkin baka ya kalli Nana ya ce "Nana Asma'u, mene ne labari? Meyafaru bayan tafiyarki ne? Kuma yaya aka yi na ganki a birnin Agadez?" Nana ta yi murmushi ta ce "Komai ma ya faru Sarki, amma dogon labari ne, mai tsayin gaske" Ya murmusa, ya ƙare wa mutanen gurin kallo, sannan ya sake kallon Nana ya ce "Uwar ɗakina, me ya kawo ki Agadez ne?" Nana ta nuna masa Sayyid. Mahmoudu ya yi murmushi ganin abin da Nana ta yi. Ya ce "Uwar gijiyata, kina nan me yasa aka neme ni, kin karɓi aikin gurin uban duƙusa ne?". Nana ta girgiza kai. Ya ce "To bani labari meyafaru?" Sultan ya ce "Bawan Allah, ban fahimta ba me yake faruwa ne?" "Allah ya baka yawan rai, duk cikin aikina ne. Idan babu damuwa ina son na san matsayin kowa a nan" Mahmoudu ya ce "Ga Sultan kana gabansa, shi ne mahaifin Imam Hammad, sarkin Agadez, ga Matawalle da Sardauna, su ma iyaye ne a gare shi, kuma manya ne a Agadez. Sai Gimbiya Asal matarsa da ta fita. Sai kuma" Sai ya yi shiru yana bin su da kallo yana tsoron ya faɗi matsayin Nana ya yi laifi. Sarkin baka ya ce "Ba ka gaya mini matsayin uwar gijiyata ba" Sayyid ya ce "Matata ce" Sarkin baka ya sake yin murmushi ya ce "Na san a rina, an saci zanin mahaukaciya jikina ya bani tun a lokacin da na ganku. Allah ya baka yawan rai, in dai yana tare da Nana Asma'u zai samu sassaucin matsalarsa. Tana ɗaya daga cikin dalilan da ya sanya yake zaune lafiya a Agadez, bai sake ɓallewa ya bar ƙasar nan ba" Sarkin baka ya sake maimaita musu, Nana tana da alaƙa da maganin Hammad. Matawalle ya ce "Me ka ke nufi? Ko dai wani haɗin bakin ne, ku ke son ku yi mana" Sardauna ya yi maganar yana kallon Sarkin baka. Sarkin baka ya ce "Ɗan tsahirta mini tukuna, a kan aikina nake" Ya sake kallon Mahmoudu, ya ce "Ɗan uwana ko za ka iya tuna abin da na gaya muku, lokacin da ku ka je gurina?" Mahmoudu ya jinjina kai ya ce "Ka ce mana asiri aka yi masa, da baƙin aljani, ya manta duk abin da ya shafe shi, ya bar garinsu ba zai iya zama a garinsu ba. Kai kuma ba zaka iya ba shi magani ba, saboda ba aljani ne da za a iya sasantawa da shi ba, sai dai a je a karya asirin da aka yi masa. Na tambaye ka ko zaka iya karya asirin? Ka ce a'a shiga al'amuran aljanin nan akwai matsala, mu koma ƙasarmu a bincika inda aka yi masa sihiri a warware shi a can" Ya ce "Madalla" "Uwar gijiyata, ranar da aka kawo ki gidana neman magani, Meyafaru?" Nana ta ɗan yi shiru sannan ta ce "Ka ce a je a kira buzayen da suka tafi. Aka ce maka sun tafi. Ka ce da an same su, wataƙila ga maganin nasa ciwon ko nawa" Sarkin baka ya ce "To Alhamdillah, an zo gaɓar da nake so a zo" "Allah ya baka nasara. Wannan ita ce rabin maganin abin da yake damunsa" Matawalle ya ce "Kai kalle mu da kyau, kar ka kuskura ka zo nan ku na gaya mana maganar banza. Idan ma haɗa kai ku ka yi, ku ka haɗa baki domin ku raina mana hankali, wallahi muka kama ka da rashin gaskiya, sai mun yi maka mummunan hukunci" Sarkin baka ya ce "Na san dai duk azabar da zaka yi mini ba zaka saka ni a jahannama ba ko? To bayan wuta da Ubangiji zai saka ni a ciki, azaba in dai ta Duniya ce babu wadda ban sha ba, duk wadda za ta biyo baya ɗazu ce. Ban sanku ba ban taɓa ganinku ba, dan me zan yi muku ƙarya? Wani abu ne ya faru da tun a baya, na yi hasashen faruwarsa. Zan yi wani bayani amma a gaban mara lafiya da shaƙiƙansa da ya yarda da su. Idan na faɗa ban ce lallai sai kun yadda ba, amma iya gaskiyata zan gaya muku. Wannan baiwar Allah da na nuna na santa, tabbas na santa amma ni babu wanda na haɗa kai da shi domin na zo nan gurin na yi cuta ba. Saboda duk wani abun duniya da nake fatan samu, Allah ya riga ya bani shi. Ranka ya daɗe zaɓi mutum biyu zamu yi magana. Duk suka yi zuru da ido, suna kallon Imam Hammad. Hammad ya kalli Sultan, Sarkin baka ya yi caraf ya ce "Ɗayar, na zaɓi uwar gijiyata mutum biyu kenan. Allah ya baka yawan rai, idan babu damuwa ina so mu keɓe tare da ku" Sultan ya ce "Babu laifi, Matawalle ko za ku bamu guri?" Sardauna ya ce "Mai girma Sultan, ka yi a hankali kar ka bari su yi maka wasa da hankali, su faɗa maka abin da ba shikenan ba" Sultan ya ce "Babu wani abu in sha Allah" Bayan fitarsu gaba ɗaya, Sarkin baka ya ce "Allah ya baka yawan rai, ba dan ina tsoron hadisin da Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam ya ce Allah yana fushi da ɗan kasuwa mai rantsuwa a kan kasuwancinsa ba, da na yi maka rantsuwa domin nima bayar da magani kasuwancina ne, amma ina baka tabbacin duk abin da zai fito daga bakina gaskiya zan gaya maka. Na san duk alkhairin da zaka yi mini ba zaka yanke mini talauci ba, sai Allah ya yanke mini. Kuma ba zaka talauta ni ba sai Allah ya talauta ni. Babu ƙarya ko haɗin baki ko yaudara a cikin abubuwan da zan yi maka. Wannan bayin Allah biyu babu wanda ba a kawo mini shi gurina neman magani ba. Asma'u ko ba ta bayar da magani ba, tsantsar tauhidinta da yarda da Allah da ta yi, zai iya sanyawa yadda yake tare da ita ya samu lafiya ko dan albarkacin addu'a. Ai Allah shi ya ce a roƙe shi zai amsa. Kafin na ce maka komai, bari na yi maka wasu tambayi m ya ka ji lokacin da ka neme shi ka rasa a ƙasar nan?" Sultan ya ce "Na shiga tashin hankali, ba na iya cin abinci da cikakken bacci saboda rashin sanin inda yake." "Alhamdillah, yanzu da ya dawo ya ka ke ji?" "Murna nake yi mara misaltuwa, da jin cewa zan iya yin komai, dan na ga bai sake yin nesa da ni bax Sarkin baka ya ce "Alhamdillah, ka yi bayani dai-dai da abin da nake son ka faɗa. Wannan yarinyar da ɗanka ba za su rayu guri daban-daban ba. Idan haka ta kasance kuma ɗaya zai rayu cikin wahala. Saboda alaƙarsu akwai tasirin soyayyar uba da ɗa a tsakaninsu" Cikin rashin fahimta Sultan ya kalli Sarkin baka ya ce "Me ka ke nufi?" "Aljanin da aka yi wa ɗanka asiri da shi, ɗansa ne a kanta yake ta ɗawainiya da ita saboda ta yarda ta yi masa wani aiki. Ya ɗauki tsawon shekaru ba sa tare, kwatsam da aka ba shi aiki a kan ɗanka, ya yo Nigeria da shi, suka haɗu da ita. Dan haka duk abin da zai faru, duk rashin jituwar da ke tsakaninsu, uban ba zai bari ɗansa ya ƙara nesa da shi ba. Saboda shi ne ɗa mafi soyuwa a gare shi" Sultan ya yi shiru cike da mamaki, yana bin Nana da Hammad da kallo. Ya ce "To yanzu babu yadda za ayi, a karya sihirin?" "Ni ba na ƙarya dan a so ni, ban san waye ya yi masa asiri ba, ban kuma san a daidai ina aka yi ba, balle na ce kai tsaye ga gurin a je a tona ba. Kuma ba zan yi karambani ba saboda aljanin shu'umi ne zai iya halaka ni. Amma ita tun da ɗansa yana tare da ita, ban sani ba ko ya samu sassauci ko makarin abin a dalilnta ba" Sultan ya yi shiru yana kallon su, lallai biri ya yi kama da mutum, duba da yadda lokaci guda take iya sarrafa shi, idan ciwon nan ya tashi. Sultan ya ce "Yanzu mene ne abin yi?" "Abin yi ɗaya, a ci gaba da addu'a, kuma ku ƙara taka tsantsan, sannan ban sani ba ko uwar gijiyata za ta nema mana alfarmar shugaba, ko akwai abin da zai iya yi a kan lamarin" Nana ta ɗan tsuke fuska tana mazewa. "Wa za ta roƙa mana " Sultan ya yi maganar cikin damuwa. "Ɗan nasa mana, ai hadiminta ne, kuma babu abin da za ta saka shi, ya kasa yi mata" Sultan ya kalli Nana ya ce "To ko za ki roƙa mana ɗin, duba da mawuyacin halin da yake shiga idan ciwon ya tashi" Nana ta yi shiru ta sunkuyar da kanta. Sarkin baka ya ce "Kar a yi gaggwa, a bi ta a sannu tukuna, ta yanke hukunci da kanta" Sultan ya ce "Shikenan, a mayar da kai masauki, kafin na kuma nemanka" Nana ta ce "Allah ya baka nasara, dan Allah zan yi magana da shi, idan babu matsala a hakan" Sultan ya ce "Babu damuwa" Hammad ya haɗe rai, amma Nana ta tashi ta bi shi waje. Ta ce "Sarkin baka, dama kana raye? Ƙaisar ya ce mini kashe ka zai yi" "Nana Asma'u, uban duƙusa bai kashe ni ba, sai dai na ji jiki kamar ba zan rayu ba. Shi ya kawo mini magani ma, sannan ya ƙara yi mini kashedi sosai a kanki. Daga nan ma har wasu magungunan ya sanar da ni" Ta ce "Ikon Allah, sarki ya magunguna ya marasa lafiya? Ina Salamatu da wannan aljanar taka" Ya yi dariya ya ce "Duk su na nan ƙalau" "To ya aka yi ka san cewa asiri aka yi wa Sayyid?" Ya harare ta ya ce "Halinki dai yana nan uwar ɗakina. Mutum mai hankali zai yi abin da mijinki yake yi ne? Abin da nake so da ke, ki ƙara addu'a kar ki yarda da kowa, kunnuwanki da idanunki su zama a buɗe komai na iya faruwa idan Allah ya taimake ki wataƙila ya samu lafiya ta hannunki" Ta ɗan yi shiru sannan ta ce "Ƙaisar ya nuna mini abubuwa da dama, sai dai ba na son gazgatawa ne, na shiga ruɗani, amma har yadda asirin yake na gani, to amma idan ya rabu da Giyaz iya samun lafiya duka?" "Ba na ce ba, tun da ban san a kan me da me aka ba shi aikin ba. Kuma ba shi da fuskar da zan tambaye shi. Amma ina jakar da na baki?" Kafin ta amsa, Sayyid ya fizgi hannunta da ƙarfi ya yi gaba da ita. Bai tsaya da ita ko ina ba, sai da suka je ɗakin da yake jinya. Idanunsa jawur ya ce "Dan wulaƙanci kawai ki je ki tsaya ki na surutun banza da mutumin da ba muharraminki ba" Ta marairaice ta ce "Haba Shugaba, wa nake da shi a nan daga ƙasarmu, yaushe rabon da na ga wani wanda na sani? Kuma Sarkin baka duk da yana wasu abubuwan da nake tantama a kansu, mutum ne da ba zan taɓa mantawa da shi ba. Bayan tafiyarka daga gidansa, abubuwa da yawa sun faru, ni a gidan nasa a ka bar ni" "Ba na son jin koma mene ne ya faru" ya yi maganar yana tsuke fuska. Ta ce "Haba Shugaba, kar ka manta, maganinsa ya taka muhimmiyar rawa lokacin da ka yi rashin lafiya" Yayi mata shiru yana huci, tabbas a rayuwarsu da shi a Nigeria ta san shi da azabar kishi. Ta kwantar da murya, tana shafa bayansa ta ce "Haba Shugaba, dama mutum zai iya fushi da rayuwarsa, tuba nake ɗan manyan mutane, kuma babban mutum" Ɗan guntun murmushi ya saki, ita ma ta yi masa murmushin. Ya ce "Yauwwa, ki yi mini addu'a, in ajima za a sanar da Asal da iyayenta, matsayinki a gurina. Nana ta kwaɓe baki ta ce "Na yi maka addu'a, ta mutu mana, nima ban mutu ba da kishiyata ta mayar da ni baiwa saboda tana da kuɗi, ga kuma mijina ina kallonsu tare, amma ban isa na ce komai ba". Tsam ya miƙe, saboda ya san idan aka ci gaba da jan maganar faɗa za su yi. Ya ce "Ki shirya, idan na dawo yau komai dare, za mu je gurin kayan tarihi na Agadez, kuma zan baki labarin duk abubuwan da suka faru" Ta yi masa shiru ta cika ta yi fam, kamar za ta fashe. Ya tausasa murya ya ce "Na san kin yi haƙuri, amma ina sake baki haƙuri, dan Allah ki saki fuskarki" "Ni ka rabu da ni, ka je ku lallaɓa matar so, da al'adarku ta yarda da ita, ni kuma ka sake ni ku kora ni ƙasarmu" Ta yi maganar har da ƙwallar baƙin ciki. Ya yi murmushi ya ce "Duk wata matar so a bayanki take Gimbiya Ma vie. Kin ci Agadez kin ci Nigeria" ta murguɗa masa baki, ya shammace ta ya yi kissing ɗin bakinta. **** Asal ce a gaban Sultan, da Matawalle da Sardauna, ga kuma Tafawa sai Imam Asadullahi, da Imam Hammad sai Mahmoudu. Matawalle ya ce "Na san za ku yi mamakin dalilin da ya sanya, muka neme ku a yammacin nan, bayan sallar magariba haka. Mun san za ku ji abin wani banbarakwai, amma mu ma haka nan ya zo mana. Duk ana kan dambarwar ɗa da Imam Hammad yake da shi, wani abu ya sake faruwa da dole mu yi muku bayani, domin babu yadda muka iya mu ma, sai dai mu na kan tunanin matakin da za mu ɗauka." Tafawa ya ce "Mai girma Matwalle, wannan kwana-kwanar ta yi yawa, ka yi mana bayani kai tsaye." "Kamar yadda ka yi ta bin diddigi a baya, tabbas Hammad ya yi rashin lafiya, ya kuma je Nigeria jinya. Asal na san abin da ki ka gani ya ɗaga miki hankali kina ta wasi-wasi. Ɗan da Hammad yake da shi, ba ɗan kowa ba ne face ɗan matar da ki ka kawo a matsayin kukunsa. Wannan kukun tasa matarsa ce" AREWABOOKS Wani irin nannauyan numfashi Asal ta ja, tana jin kamar daga shi ba zata sake jan wani numfashin ba. Gaba ɗaya sai ta kasa gane me ma ake son a yi mata bayani. Wace ce ma kukun? Take tambayar kanta. Tafawa ma sak ya yi, yana murza yatsun hannunsa, ya tsare su da idanu ɗaya bayan ɗaya, sannan ya numfasa ya ce "Ku na nufin Imam Hammad ya auri wata wadda ba ƙabilarmu ba, daga Nigeria har ta haifa masa wannan yaron da na gani?" Sardauna ya ce "Haka ne" Ya sake rausayar da kai ya ce "To ina fatan a wannan karon, za ku yi adalci dokar masarauta ta yi aiki a kansa, a yi masa hukunci daidai da abin da ya aikata." Sardauna ya ce "Tukuna dai, sai mun ga abin da hali ya yi, saboda yanzu hankalinmu na kan samun lafiyarsa" "Lafiya, wace irin rashin lafiya kenan yake fama da ita? Kuma me ya kai shi Nigeria? Kuma a kan me ya karya dokar masarauta?" Matawalle ya ce "Wannan duk abu ne da za ka ji daga baya, amma yanzu a kan wannan gaɓar muke, zuwa gaba kaɗan za mu duba abin da ya dace a yi" Wani irin kuka Asal ta fashe da shi ta ce "Hammad, abin da za ka yi mini kenan, ka munafunce ni? Ka cutar da ni, ka ajiye ni hoto ban haihu ba ka je ka haihu da wata. Saboda ka tozarta ni ba ma ka auri Buzuwa daidai ni ba sai wannan ƙazama mummunar yarinyar?" Tafawa ya ce "Rufe mini baki, mutuniyar banza uban waye ya ce ki je ki kawo ta gidan sarauta, a matsayin kukun mijinki, alhalin kin san ba haka dokar masarauta take ba?" Hammad ya kalli Asal ya ce "Ki yi haƙuri, na san na yi miki laifi mai girman gaske, amma ina mai baki haƙuri yadda al'amuran suka kasance ba wai da gangan na yi ba. Kin san babu yadda za a yi ina zaune haka kurum na ɗau jiki na tafi Nigeria na... "Ka yi mini shiru, babu wata magana da zaka faɗa na yarda da kai, maƙaryaci... "Hattara!" Matawalle ya yi mata tsawa. "Ko me ya yi miki, dole ki ambace shi da girmamawa kar ki kuskura ki faɗi wani abu mummuna a kansa, ko me ya yi kuwa. Dan haka ki kiyaye harshenki" Cikin kuka take cewa "Wallahi sai ka sake ni, ba zan zauna da kai ba, kuma na bar ka da Allah sai ka sake ni" Sultan ya yi gyaran murya ya ce "Yarinyar kirki, na san za ki ji abin wani iri, amma babu abin da zai raba aurenki da Imam. Haryanzu mu na kan tattauna matakin da za mu ɗauka amma sai kin bamu cikakken haɗin kai kin nutsu. Haryanzu ke ce halattacciyar matar Imam da kowa ya san da zamanta." A fusace Tafawa ya tashi ya kalli Asal, da gaba ɗaya ta rikice take kuka ya ce "Ke tashi mu tafi" Ta yinƙura ta tashi ta yanke jiki ta faɗi. Hammad ya taso da sauri ya nufo ta, amma Tafawa ya ce "Kar ka kuskura ka taɓa mini 'ya" Ya kalli Asadullah ya ce "Zo ka ɗauke ta mu tafi" Hammad ya ce "Ba zai yiwu ba, ba zai ɗauke ta ba. Kar ya fara taɓa mini mata" "Ni ka ke gayawa kar ya fara taɓa maka mata?" "Ni nake da hurumin ɗaukarta, ko na taɓa ta ban yarda ya taɓa mini mata ba" Ya yi maganar yana tsare Tafawa da ido. Sardauna ya ce "Tafawa ko da an samu rashin fahimta, bai kamata a ce ka hana shi taɓa matarsa ba, sai ka gama wannan ɓaɓatun ita kuma ta baka kunya, ai ba a shiga tsakanin mata da miji. Bari a kira barori mata su zo su ɗauke ta, a kai ta ɓangaren Gimbiya Bilkisu" Ya ce "Babu wanda ya isa, ba wanda zai taɓa mini 'ya" Sultan ya ce "Umarni ne, a kaita sashen Gimbiya Bilkisu, idan ta farfaɗo ta ɗan nutsu sai a kai ta gida" Tafawa ya tsaya cak yana kallon Sultan cikin ƙunar rai. Ƙaninsa yana ba shi umarni kuma dole ya bi. ***** Wata kyakykywar matashiya ce ta shigo ɗakin, ta tarar da ita a zaune tana bawa jaririn Nono. A rikice ta ƙarasa da sauri tana faɗin "Sister kin farfaɗo Alhamdillah, Alhamdillah, Alhamdillah ala kulli halin. Barka da arziki sannu" Ta ƙarasa gaban gadon tana rungume Shukura. Shukura ma ta rungume ta, tana faɗin "Na gode sosai, Allah ya saka da alkhairi" Ta kalli Shukura ta ce "Babu komai, ni dai na gode wa Allah da ya sanya ki ka farfaɗo ki ka tashi. Sannu 'yar uwa" Ta sake maganar cikin iyayi da kulawa. Ta kalli likktar da ta take ta ɗawainiya da Shukura, ta ce "Sannu da ƙoƙari doctor, Allah ya biya ki kema" Doctor ta ce "Ba komai, yi wa kai ne." "Yanzu kawo lambar wani a kira miki" Shukura ta ɗan yi shiru sannan ta ce "To" Ta bayar da lambar Sagir, aka saka a wayar aka danna kiran wayar" Shukura ta miƙa hannu, ta karɓi wayar. Muryar Yusra ce ta yi mata sallama, ta tsuke fuska ta ce "Ina Baban Haidar" Wata irin rikicewa Yusra ta yi, ta ce "Shukura ke ce? Ina ki ka tafi muke ta neman bamu ganki ba? Kina ina?" Sai Shukura ta ɗan yi saroro, jin yadda Yusra ta rikice da murna. "Ina nan, idan yana kusa ba shi wayar" A rikice Yusra ta sake cewa "Baya nan, ki gaya mini kina ina na zo na ɗaukko ki?" "A'a ina nan lafiya kalau, idan ya dawo ki haɗa ni da shi" Yusra ta ce "Baya nan, layinsa ya saka a wayata, ni ban san lokacin da zai dawo ba, ki gaya mini kina ina?" Kamar Shukura ta share ta katse wayar, sai kuma ta gaya mata. Tana can wani Asibitin kuɗi, a can wata local government a wajen Kano. Sannan ta ɗora da cewa "Amma kar ki gaya wa kowa mun yi waya da ke" Yusra ta ce "Har mamanki? Tana can hankalinta a tashe fa ita ma" "Eh har ita, kar ki gaya wa kowa, idan ya dawo ki haɗa ni da shi, ina Haidar? Yana lafiya?" Ta yi maganar hawaye na cika mata ido, cike da fargabar ko shi ma ya salwanta. "Yana makaranta, to kina lafiya cikinki ma yana nan lafiya?" Shukura ta ce "Eh, lafiya kalau" "To dan Allah kar ki je ko ina daga nan gurin" "Tom" Ta faɗa a taƙaice. Matar ta kalli Shukura ta ce " 'Yar uwakki ce?" Ta girgiza kai ta ce "Abokiyar zamana ce" "Allah sarki, gaskiya daga ji tana sonki sosai ji yadda ta rikice" Shukura ta yi murmushi kawai. Sai dai ta tafi tunanin ta yadda za ta fuskanci Duniya ta sanar da cewa mahaifinta shi ke da alhakin sace ta, da salwantar mata da ɗa, da kuma mummunan zaluncin da ya yi wa mahaifiyarta da wadda yake tare da ita yanzu. Ita gaba ɗaya ma ba ta san ta ina zata fara bayanin miyagun ayyukansa a idon duniya ba a matsayinsa na mahaifinta. **** Nana tana son ta ga Sarkin Baka, akwai maganganu da dama a bakinta, amma ƙiri-ƙiri Sayyid ya hana. Ga shi ba ta da damar fita idan ba umarnin hakan a ka ba ta ba, tana son sake ganin Nene ma amma babu halin fita. Zaman Nana a guri ɗaya, ba fita daga ci sai sha da kwanciya, ya sanya ta ƙara yin kyau, ga lafiyayyen Abinci. Sai dai haryanzu kwanciyar hankali da nutsuwar zuciya ne ba ta da shi. Tana zaune tana zancen zuci, har bacci ya fara sace ta, ta ji an taɓa ta. Ta tashi da sauri tana kallonsa. "Har kin fara bacci ba ki jira ni ba?" "Eh, na zata a gurinta zaka kwana ai" "Idan ma na kwana a can ɗin, ai ke ki ka ja, kin daina damuwa da ni, ko tausayina ba kya ji" Ta kwaɓe baki ta ce "Garin tausayinka, na kwashi wani cikin na haihu ku kaɗa ni Nigeria" Ya ɗan marairaice murya ya ce "Haba Ma vie, Sayyid ɗinki ne fa, ke ba kya kewar ɗumin jikina ne" Nana ta kalle shi ta ce "Wane ɗumin, ai yanzu jikinka ba wani ɗumi idan ba azaba ba" Ya rausayar da kai ya ce "Da ɗin ma akwai, kuma kina jurewa" Ta girgiza kai ta ce "Amma bai kai na nan ba" "To ni ki bani Sanyin dan Allah" Ta tsuke fuska ta ce "Sayyid ka daina taɓa ni dan Allah, ni ba ƙin ka nake yi ba, amma ka tausaya mini inga yadda al'amuran za su kaya tukuna, ka san dambarwar da ake ta yi haryanzu ni tsoro nake ji kar a yi mini yadda aka yi wa Nene" Ya kwanta a gefenta ya numfasa ya ce "Ta baki labari kenan?" Ta jinjina masa kai alamar eh. "In sha Allah a kanmu wannan muguwar al'adar za ta zama tarihi, dan ba zan yarda na rabu da rayuwata ba" Nana ta zumɓura baki tana kallonsa, ya ce "Da gaske nake Ma vie" Ya yi maganar sumbatar hannunta. Ta ɗan lumshe ido tana kallonsa. Ya ce "Tashi mu je" "Ina?" "Zo mu je ki gani mana, ko zan cinye ki ne" Ya yi maganar daga kwnace yana ci gaba da kallonta. Ta tashi zaune tana faɗin "Na sani, ko cinye nin zaka yi. To ka tashi mana kuma ka kwanta" Ya yi shiru bai ce mata komai ba. Ta waiwaya ta kalle shi, ta ga yana yi mata wannan kallon yana shafa bayanta. Ta ce "Yane? Ko in kwanciyata ne?" Ya ce "Allah sarki Hammad bawan Allah, kowa baya so na" Ya yi maganar yana tashi zaune. Nana ta yi murmushi ta kai hannu ta shafa gashinsa ta ce "To dama wa zai so rigimamme" "Allah sarki, Ina kewar Ma vie ɗina ta da, mai so na da tausayina, ko motsi na yi hankalinta yana kai na, Allah sarki Asmyna ta Nigeria, soyayyarta ta daban ce a cikin zuciyata" Nana ta ce "Allah sarki Sayyid ɗina na Nigeria, da baya ganin kowa a duniyarsa sai Asmynsa kaɗai. Mai kallona da idon tausayi, wanda nake iya gano ƙaunata da tausayina a idanunsa, mai yaba duk wani motsina da ƙoƙarina. Ina kewar Sayyid ɗina na Nigeria" Ya lumshe idanunsa ya buɗe ya ce "Wannan Imam ɗin na Agadez fa?" Ta kalle shi ta ce "To ga shi nan dai, ban ma san inda ya dosa ba" Ta ƙarasa maganar tana murguɗa baki. Ya yi dariya ya ce "Haka za ki ce ko? Ni ɗin ko? Sayyid ɗinki ne fa" "Sayyid nawa, Hammad na Asal" Ya ce "Wow, sake faɗar sunan na ji?" Ta noƙe masa kafaɗa. Ya ce "Shikenan ma, dama Asal ta fiki iya faɗar sunan" Ta harare shi, tare da sauka daga kan gadon. Shi ma saukkowar ya yi, ya wuce gaba ta bi shi a baya. Daga bisani ya jira ta, suka tafi tare. Ƙofar nan da suke bi su fita hanyar saharar nan, suka shiga, sai dai wannan karon canza akalar hanya, zuwa wata matattakala. Tsoro ya fara kama Nana, amma ta kasa magana, sai rarraba ido kawai da take yi. Wata ƙofa suka iso, ya ce "Kin san ina ne nan muka ɓullo?" Ta ce "A'a" "Gidan tarihi ne na masarautar Agadez" Nana ta ce"Wannan dutsen da nake hangowa?" Ya jinjina kai ya ce "Eh nan ne" Wani takurarren tsoho suka tarar a bakin ƙofar shiga gurin, yanayin ƙofar ya bayyanar da tsufan da ta yi a Duniya. Tsohon ya miƙe jikinsa na rawa, ya risuna yana gaida Imam Hammad. Hammad ya amsa cikin girmamawa. Nana ta ɗan tsaya ta yi shiru, tana nazarin ƙamshin turaren da ta ji a gurin, kamar ta taɓa jin sa a jikin wani, sai dai ba ta ga alamun a jikin wannan tsohon wannan ƙamshin yake tashi ba. Ya buɗe musu ƙofar, suka shiga. Ya kunna makunni, sai ga hasken fitilun ya haske gurin. Ya ci sunansa gidan tarihi, Nana ta faɗa a zuciyarta. Wani irin ƙaton guri ne mai kama da falo, da ƙofofi kashi-kashi a gurin. "Wannan gurin kamar Libraryn Ƙaisar saboda tsufa" Ta ɗaga kai tana kallon tsawon gurin, jikin dutse ne aka rarake aka yi wannan ginin da ƙofofi. Kanta ne ya sara ta yi shiru tana tunanin kamar ta san gurin nan, ta taɓa ganin gurin. A take ta fara jiyo wannan ƙamshin da take ji idan ta gan su a wannan ɗakin tare da Sayyid. Hammad ya kama hannunta ɗaya, ya buɗe ƙofa suka shiga, a take ta sske rikicewa, jikinta ya hau rawa ta kalle shi ta kalli ɗakin, ta sake kallonsa ta kalli ɗakin. "Sayyid wannan ɗakin" "Ɗakin da muke zuwa ko?" Ya yi maganar yana yi mata murmushi. Ta kalli gadon, da mudubin ɗakin, komai irin na da sosai da sosai, sai dai yanayin kayan ya nuna, wanda suka yi amfani da ɗakin masu faɗa a ji ne. Ta dafe kanta da take jin wata irin ƙara a ciki, ga ƙamshin turaren nan ya cika ilahirin gurin. "Sayyid wai ya aka yi haka ta faru a zahiri? Kar daga baya ka ce mini mafarki ne, ka fita da ni daga gurin nan kar na haukace Sayyid" "Ba za ki haukace ba, ki tsaya na yi miki bayani" Wani irin jiri ne ya din ga ɗibarta, ta din ga ganin wasu irin halittu na shawagi a ɗakin, ga hayaniya da suke yi cikin sauti mara daɗin ji. Jikin Nana na tsuma ta ce "Ka fita da ni daga gurin nan, wasu abubuwa nake gani ka fita da ni" "Babu wani abun tsoro fa a gurin nan, ki nutsu zan gaya miki komai daki-daki ciki har da abubuwan da suke shige miki duhu a kaina" Ayshercool 08081012143 89 LITTAFIN KUƊI NE 1K 0069685771 Aisha Adam stanbic 08081012143 A hankali Nana take ƙoƙarin buɗe idanunta, zuciyarta cike da matsanancin tsoron, da rabon da ta ji makamancinsa har ta manta, tare da fatan Allah ya sanya ta farka daga wannan mafarkin mara kan gado. A hankali take jin numfashin sa na sauke a fuskarta. Ta buɗe idonta sosai ta sauke a kan fuskarsa da ya tsare ta da idanunsa, sai dai kan ta yi wani yinƙuri, ƙamshin ɗakin ya mamaye mata hanci, hakan ya sake tabattar mata da ba mafarki ba ne ba zahiri ne. Ta zabura da sauri ta gansu a kan gadon tare ita da shi a cikin ɗakin dai. A gigice ta fara ƙoƙarin sauka daga kan gadon cikin matsanancin tsoro, tana zazzaro masa ido. Sayyid ya riƙe ta ya ce "Dan Allah ki daina tsorata kanki, ki nutsu mana. Babu wani abin tsoro a gurin nan" "Ta yaya zan nutsu, kana caza mini ƙwaƙwalwa, na ma rasa me yake faruwa, kuma sannan ka ce babu abin tsoro a gurin" Ya ce "Zaki fahimci abin da yake faruwar, amma dole ki nutsu, kuma ki saurare ni"  Ya ɗago yatsunsa ya kalli zobunan hannunsa, da space ɗin guda ɗayan sannan ya dubi Nana ya ce "Abubuwan da ki ke gani a tare da ni, su na da alaƙa da wannan zobunan na hannuna. Nana ta kalle shi ta kalli zobunan cikin rashin fahimta. "Ina Zoben da na baki, mu na Nigeria?" Ba ta ba shi amsa ba, kawai ta hau ƙoƙarin tashi ta bar gurin. Ya din ga kokowa da Nana, amma idonta ya rufe, hanya kawai take nema ta gudu ta bar gurin. Dan gani take idan ta ci gaba da zama zaucewa za ta yi. Sai da ƙyar ya  lallaɓa ta ya ce "To shikenan, mu je na mayar da ke mu tafi, tun da ba za ki nutsu ba" Ya riƙo hannunta, sai dai duk a tsorace take, su na fita daga wannan ɗakin ya shiga da ita wani ɗakin. Gurin duk an yi wearing ɗin fitilu, sai dai da ya kunna fitilun gurin ya yi haske. Ta ƙara razana da ganin gurin. Komai na zamanin da ne sosai da sosai. Wasu zane-zanen mutane ne a manyan frames a kafe, har zuwa kan wasu hotunan da suke dishi-dishi na Black and white na da, zuwa kan hotunan da ake iya gane mutanen jiki sosai wanda ya nuna na baya-baya ne hotunan sai hoton Sultan da ya fita fes. Ɗaya bangon Hoton Sultan ne shi ma, da hotunan Imam Imam na Agadez a jere. Sai dai mutanen na jikin zanen da na hiton duk masu kyau ne, kuma yanayinsu ya nuna daga zuriya ɗaya suke. Sai kuma gefe  wasu ƙananan hotunan a wani ɓangare na ɗakin, da suke nuna yaƙe-yaƙe, da yanayi na zamanin bayi. Hammad ya ce "Wannan hotunan da ki ke gani, tun daga kan na zanen nan, hotunan wasu daga cikin sarakunan da suka yi gwagwarmaya gurin kafa masarautar Agadez ne. Waɗannan kuma, wasu daga cikin bayi ne, da suka yi wasu laifuka na rashin kyautawa, wanda tun daga zamanin har kawo yanzu, duk wanda aka haifa a zuriyarsu bawa ne, ciki har da wannan dattijon da yake gadin ƙofar gidan tarihi na Agadez. Idan ya mutu dole zuriyarsu za su bayar da wani wanda zai ci gaba da wannan aikin. SHEKARUN DA SUKA GABATA. Kamar yadda Nana ta fara karantawa, a cikin littafin Ƙaisar. An sha gwagwarmaya da yaƙe-yaƙe tsakanin 'yan uwa da suke ciki ɗaya domin samun damar ɗarewa karagar mulki. Kowane Sultan da ya zo karaga, akwai kalar mulkin da yake shimfiɗawa, wani al'ummarsa su samu sassauci, wasu kuma su shiga halin matsi. Sai dai hawa kan karagar ba shi ne aiki ba, ci gaba da ɗorewar mulkin, saboda a kowane lokaci ana iya samun masu kawo maka farmaki, a haɗa kai da na kusa da kai, a yi maka juyin mulki. Sannan tsugunno ba ta ƙarewa duk wanda ya zama Sultan ba, domin bayan kare kansa dole ya kare iyalinsa, idan ba haka ba 'ya'yansa tun da  ƙuruciya za a yi ta kashe su, ana gwara kansu da kwaɗaita musu kwaɗayin mulki, ta yadda idan ba su kashe junansu ba, za su iya kawar da uban dan su hau karagar mulkin. Ƙasar Agadez Allah ya albarkace ta zinari, wanda tun a wancan lokacin, shi ne babban dalilin da ya sanya kowa ke kwaɗayin ya hau mulki, aka yi ta yaƙe-yaƙe ana zubar da jini, tun da aka fuskanci zinaren abu ne mai matuƙar daraja a lokacin. Suka ci gaba da gudanar da yaƙe-yaƙe su na mamayar mutane su kafa Daular su. Ana tafe da wannan mulki, wanda mai ƙarfi ya kan kifar da na kan mulkin ya ƙwata, ya kashe na kan karagar, har aka zo kan mulkin Sultan Azhar. Zuwan Sulta Azhar ya sauya da yawa daga tarihin Agadez, kowane Sultan yana amfani da wani amintaccen boka, da yake yi masa ta'amalli da Aljanu, domin sanin abin da zai faru da ba shi wata kariya ta mussaman. Sarki Azhar ya gagari duk magautansa, yana da tarin mabiya. Azhar yana cikin manyan kwamandojin yaƙin sarkin wancan lokacin. Kakansa ya taɓa zama Sultan, aka yi masa juyin mulki aka rufe shi a kurkuku. Aka kame 'ya'yansa aka mayar da su fursinoni ciki har da mahaifinsa lokacin shi Azhar yana ƙarami Nono yake sha. Bayan da ya tasa bai fi shekara sha biyu ba, aka kame shi, aka sanya shi cikin sojojin yaƙi. Duk zuriyarsu aka mayar da su bayi, ya tashi da wannan ciwon a ransa, ya zama gawurtaccen Sadauki da ake ji da shi, saboda ƙarfinsa. Ashe yaƙin sunƙuru yake shiryawa Sultan ɗin lokacin ya shammace shi ya kifar da shi, ya ɗare karagar mulkin. Ya kame 'ya'yansa ya kashe su, ya kashe matan Sarkin, har ma da sauran 'yan uwansa da yake tunanin za su iya tasowa su nemi su karɓi sarauta. Ya din ga yaƙar sauran ƙasashen da ke kusa da Agadez, yana mayar da su ƙarƙashin ikonsa, ya kame baƙaƙen buzaye ya mayar da su bayi. waɗanda suka rage a 'yan uwansa wanda su ma sun tasa, yake ganin za su iya kawo masa tarnaƙi ya sanya aka gina wata irin kurku a ƙarƙashin ƙasa, duk aka zuba su a ciki. Wannan cikin dutsen da suke ciki, Bayin zamanin Sarki Azhar ne suka rarake shi, suka gina katafariyar fadarsa, kuma a cikinta aka gina kurkun da ya zuba 'yan uwansa. A cikin kurkukun nan, idan ka mutu a ciki zaka ruɓe ka lalace, a cikin rayayyu za ka gama ruɓewa babu mai fita da gawarka. Babu kalar azabar da ba a ganawa fursinoni a wannan kurkuku. Bayi kuma su na aikin ƙarfi gurin haƙo zinare, da aikinsa a kai wa Sarki Azhar a sarrafa a yi kayan more rayuwa ko a sayar ga maƙwabtan ƙasashen, ko kuma a yi musayarsu da wani abu mai muhimmanci. Ya kame bokayen ƙasar gaba ɗaya, aka haƙa rami aka cinna musu wuta, a cikin wannan fadar tasa. Boka ɗaya ya bari, wanda shi ne ya tallafa masa ya zama Sultan, wanda shi ma iyayensa na cikin amintattun kakan Azhar da ya yi sarauta, kan a yi juyin mulki a kashe su. Bokan nan ya mallaka wa Azhar gangan manyan Aljanu da suke taimaka masa gurin tafiyar da mulkinsa. Duk wata kafa da zai iya bari da za a iya amfani da ita gurin kawo ƙarshen mulkinsa ya toshe ta. Sai da ya fara manyanta, sannan ya auri wata kyakykywar matashiyar budurwa. Ta fara haifa masa 'ya'ya maza. Allah ya ɗora masa tsananin ƙaunar yaran nan kamar ransa. Sanin a kowani lokaci, ana iya amfani da wata dama a cutar da su, ya sanya ya killace su. Ya sanya bokansa sadaukar musu da wasu Aljanu da za su din ga yi musu hidima. Ya sanya doka a kan ko bayan ransa, babu wani wanda zai yi sarauta idan ba a cikin yaran nan ba. Duk dokar da ya kafa, babu mai iya yi masa musu. Babban abin da yake bawa al'ummarsa mamaki bai wuce yadda duk wanda ya fara ƙoƙarin ƙulla wani abu a kan ya kawar da sarkin nan ba, sai dai a wayi gari ya zama gawa. Sultan Azhar ya shimfiɗa mulki da dokoki yadda yake so, ya tara dukiya da haraji, da kuma arzikin zinarin da Agadez take da shi. Duk da haka ya kamanta kawo ci gaba a lokacin, a wani abin talakawa sun samu sassauci, an samu ci gaba a fannin cinikayya a lokacin, sai dai laifi ƙalilan sai a kai ka kurkukun Sultan Azhar wanda har abada babu wanda zai sake ganinka, idan kuma ya so sai a gadar wa zuriyarku da wata hidima ga fada da kai da iyalinka har abada. Sultan Azhar bai bar mulki ya mutu ba, sai da ya tsufa sosai da sosai, yaransa sun tasa sun zama matasa. Bayan ya mutu aka naɗa babban ɗansa a kan karagar mulki. Shi ma ya ɗora daga inda mahaifinsa ya tsaya, kuma shi bai samu tangarɗa da 'yan uwansa ba, saboda ya janyo su cikin harkar mulki. Sai dai mahaifiyarsu ce ta je ta samu bokan mijinta, ta gaya masa kokenta a kan ba ta son kan yaranta ya rarrabu, a kan mulki, ko wani ya kashe wani. Ya ba ta tabbacin hakan, ta hanyar yi mata surkulle daban-daban a kan yaran nata. Kasancewar komai nufin Allah ne, da wanda ya yi addu'a, da wanda ya bi hanyar da ba daidai ba ma, yana iya amsa wa kowa idan ya so, Allah ya taimake ta ba su kashe junansu a kan Mulki ba. Shi ma ya yi tsawon rai a kan karagar mulki, sai dai Aljanun nan sun ci gaba  da bibiyar zuriyar 'ya'yan sarakunan, su na ba su kariya. Bayan mutuwar wannan Sarkin da aka zo naɗa sabon Sarki, a nan aka samu dambarwa, sai da aka yi hatsaniya aka so yin ƙaramin yaƙi daga bisani aka ɗora ɗaya daga jikokin Azhar a kan Mulki wato Sultan Sadam. Har a lokacin matar Azhar tana raye haka Bokansa. Ba ta da wani abokin shawara da ya wuce wannan boka. Ta fuskanci kalubale sosai da sosai, saboda yadda magauta suka sako ta da 'ya'yanta gaba da son tarwatsa mata iyali, dan a banƙara Sarautar ta bar gidansu. Bayan hawan jikanta karagar mulki, a lokacin Bokan nan ya mutu, ɗansa ya gaje shi. Shi ma ya samu kyakykywan kusanci da Sultan Sadam a lokacin. Bokan ya ba shi shawarar mallakawa 'yan'yansa Aljanu, domin su ƙara samun tsaro daga duk wani farmaki. Sarki ya yi shawara da bokan, a kan yana son duk yadda za a yi, ya zamana kar sarauta ta bar gidansu, kar wani daga cikin 'yan'yan 'yan uwansa ko 'yan uwansa su yi sarauta. Sai ya fara da kafa dokar, duk wanda ya haura shekara talatin da biyar, babu shi babu sarauta a Agadez, sai dai ka na kan mulki ka kai wannan shekarun. Kamar yadda ya zo a tarihi da kakansa, da Sultan ɗin da ya gabace shi, duk ba su kai shekaru talatin da biyar ba suka hau kan karagar mulki. Bokan nan ya ƙera masa zobuna da azurfa kowanne yana da mallakin Aljani a jikinsa, da wannan zoben za su iya sarrafa aljanun nan yadda suke so. Tafi a hankali bayan shuɗewar zamaninsa, abubuwa suka ci gaba da juyawa, kowane Sarkin da zamaninsa da kuma yadda yake nasa mulkin. Sai dai Mallakar zoben nan ya zama sabon tashin hankali, dan daga bisani sai ya zamana wanda yake da zoben nan, shi ne kaɗai zai iya zama Sarki. Sai faɗa ya koma kan kowa na son ya mallaki zobe cikin 'ya'yan Sarakuna. Dan sai Zobunan suka zama gado na kowane gida, daga cikin 'ya'yan Sultan ɗin da ya sanya aka ba shi zobe. A hankali ya zama doka, duk wanda zai zama Sultan, sai ya zamana bai kai shekaru talatin da biyar ba, kuma sai ya zamana ya mallaki wannan zoben. Duk wanda ya mallaki zoben, yana da damar sarrafa aljanin da aka ɗora wa alhakin ɗawainiya da mamallakin wannan zobe, da dole sai ya zamana jinin zuriyar Sultan Azhar sannan zai yi masa hidima." Hammad ya numfasa ya fara nuna mata hotunan nan da bayaninsu ya ce "Kamar yadda yake a babban kundin adana tarihin masarautar Agadez, wannan shi ne Kakan Sarki Azhar, ga mahaifinsa, shi ma ga hotonsa, ga 'ya'yansa ga waɗanda suka yi sarauta a cikin 'ya'yansa. Wannan ita ce Gimbiya Saira, ita ce matar Sultan Azhar, da tun da ya mutu zuriyarsa ce kawai suke Mulkin Agadez ba a sake samun wanda ya ƙwaci mulki daga hannun zuriyarsa ba. Nana ta tsare shi da ido, har sai da ya tsargu ya ce "Lafiya kuwa?" "Sayyid, kana nufin ka na ta'amalli da Aljanu kenan, ta hanyar yin amfani da wannan zoben?" "Meyasa za ki yi tsalle ki tafi ƙarshen labarin? Ki jira na kai da kaina mana" AREWABOOKS Ta ɗan nutsu tana sunkuyar da kai. Sai dai ya yi shiru bai ci gaba ba. "Yaya ka yi shiru kuma?" "Ba na son na ci gaba ki yanke mini hukunci ne haka sama ta ka" "Ka yi haƙuri ba zan yi haka ba, in sha Allah na yi shiru har ka kammala" Ya kamo hannunta, suka fito daga cikin wannan ɗakin, ya nuna mata wani ɗakin ya ce "Wannan ɗakin, shi ne inda gawarwakin galibin tsofaffin sarakunan Agadez suke, na kusa da shi kuma ɗakin da a kan binne manyan masu faɗa a ji. Ba zan buɗe miki ba dan za ki iya tsorata. Ya buɗe wani ɗakin ya ce "Nan ɗakin kuma, shi ne ɗakin da ake sarrafa zinari, a cikin fadar Sultan yake. Duk nacin mutum bai isa ya saci zinare ya fita da shi ba, idan kuwa aka kama mutum a kurkukun nan zai mutu. Wannan ɗakin kuma, a ciki duk wani tarihin yaƙe-yaƙen da Agadez ta yi yake. A nan ake adana duk wani kayan Sultan muhimmai, irin su takalmi, kayan yaƙi takobi da sauransu. Shi kuma wancan ɗakin, wasu daga cikin sassan ƙashi. jikin manyan masu laifukan da aka kashe ne, da Sarakunan da aka yi wa juyin mulki aka kashe su. Zamani ya ci gaba da jujjuya, hasken addinin Musulunci ya fara bayyana, duk da nisan da Sarakunan ƙasar suka yi ba sa jin kira, dan hatta turawan mulkin mallaka ba su yadda sun kassara musu sarauta da tattalin arziki ba. Tasirin addinin musulunci ya sanya aka fara rage aikata wasu abubuwan, amma ba a daina wasu ba. Tsaface-tsaface da ta'amalli da Aljanu ba a daina su ba, ga su mutane masu tsatstsauran ra'ayi a kan al'adunsu, da tsafi. Domin ma'abota sarauta sun yarda da cewa, duk wanda ya zauna zai ga zama, mussaman yadda zuriya daban-daban suke farautar kujerar ko ta halin ƙaƙa duk da tushen ɗaya ne, amma kowa burinsa ya zamana Mulkin a gidansu yake. Sai dai dokar Sultan Sadam tana nan, ta sai wanda bai kai shekaru talatin da biyar ba ne zai yi mulki, sannan sai wanda yake da zoben nan shi ne zai yi mulki. Sai dai a baya-baya, aka samu ɓarkewar faɗa a tsakanin zuriyar Azhar, har aka yi ƙaramin yaƙi, suka zubar wa da juna jini, abin da ba a taɓa yi ba a tarihin masarautar. Abin a ya girgiza al'ummar ƙasar mussaman ma'abota sarauta, har suka fara tsoron ko ƙarshen masarautar ne ya zo, aka samu rikicin da ta kai ga 'yan uwan junan da tun zamanin iyaye da kakanni ba su taɓa samun rabuwar kai da ta kai ga amfani da makami ba sai a wannan karon. A lokacin zuwan ilimin addini da na zamani, da kuma wannan hatsaniya da ta faru, sai aka yi wa dokokin masarautar Agadez kwaskwarima. Domin samar da zaman lafiya da ƙara ƙarfafa masarautar sai aka ce sai wanda yake da wasu nagarta da wasu abubuwa masu muhimmanci shi ne zai zamana yana riƙe da zoben a kowanne gida da suka gaji zobunan. Sannan aka ƙara yawan zobunan suka zama uku, kowane gida su na da anihin zoben tambari wanda shi ne mai ɗauke da sihiri da aljanu sai kuma sauran biyu, sannan da abin hannun na tagulla. A zamanin Sultan Ansar, aka yi duk wannan sauye-sauyen, ya ƙirƙiro ƙaramar majalisar masu ɗauke da wannan zobunan, yadda za a din ga shigar da su cikin sha'anin mulki, da koya musu yadda mulki yake. Aka yi yarjejeniya a kan iya wannan masu zoben ne za su iya zama Sultan, sannan a cikin su duk wanda ya haura shekara talatin da biyar za a karɓi zoben daga hannunsa a nemi wanda ya cancanta a ba shi. A lokacin aka ce duk wanda zai mallaki zoben, domin zama ɗaya daga Imam, kamar yadda Sultan Ansar ya yi musu laƙabi da shi, dole ya zamana yana da ilimin addini, ya haddace kaso saba'in na tarihin Agadez, yana jin wasu yarurrukan bayan yaren su na uwa, da kuma hausa. Domin ya zamana mutanen Agadez su na jin Hausa sosai, saboda yanayin cinikayya da ke tsakaninsu. Sai dai har a lokacin akwai baƙaƙen al'adunsu da ba su canza ba, kuma ba a yi wa kwaskwarima ba, ba a daina azabtar da mutane a kurkukun nan ba. Sannan su na ƙyamar ɓakar fata, ta kowace fuska sun daƙile baƙaƙen buzaye, sun bautar da su, sun hana su motsi, dan kar su yi wani yinƙuri su yi musu juyin mulki. Ko a cikin kuyangi, ba a yarda basarake ya yi amfani da baƙar buzuwa ba, saboda kar su haɗa zuriya da su, su sanya ran za su samu 'yanci wataran. Kuma baƙaƙen bayi sun taka muhimmiyar rawa gurin gina daular Agadez, da haɓaka tattalin arzikinta, saboda juriyarsu da aiki tuƙuru. Sun daga lokacin da suka yi 'yanci, za su iya ajiue aikace-aikacen, kuma su na tsoron su ce za su rama bautar da su da aka yi tun zamanin iyaye da kakanni alhalin kakannin kakanninsu, da su aka kafa Daular kuma sun taɓa mulki. Hukunci na iya zama na kora, zaman kurkuku koma kisa, ga duk basaraken da aka kama, da aure ko mu'amala da baƙar buzuwa. Haka duk cinikayyar da suke yi da sauran ƙabilu, ba su yadda auratayya ta haɗa su mussaman da baƙar fata, nasu ma ba su aura ba balle na waje. Sannan yana daga sharuɗɗan da bokaye suka kafa musu, muddin suka yi auratayya da baƙaƙe, ana iya kawo ƙarshen mulkinsu, kuma baƙaƙe ka iya yin galaba a kansu, su ƙwace sarautar baki ɗaya. Zamanin Sultan Ansar bayan tabattar da waɗanann dokoki, shi ma yana da zobuna da abin hannun tagulla na waɗanda za su zama Imam. Lokacin da aka tabbatar da waɗannan dokokin, aka yi musu kwaskwarima, Sultan Ansar yana da tarin 'ya'ya, yana daga cikin dalilan da ya sanya shi ƙara inganta tare da gyara wasu dokokin saboda yana kwaɗayin ɗansa Jalaludeen ya zama Sultan a bayansa, saboda kusan duk abin da aka lissafo yana da su. Kuma ya lura akwai zalamar son Mulkin sosai a wasu daga cikin 'ya'yansa, mussaman babban ɗansa Saifuddeen. 'Ya'yan suka yi ta zuba ido, domin su ga wa zai ba wa zobunan nan, amma ya ƙi bawa kowa, sai daga bisani ya damƙa wa Jalaludeen, ya nemi sauran gidajen da suke da zobunan, su ba wa waɗanda suka zaɓa, a kafa majalisar Imam. Hankalin Saifuddeen da mahaifiyarsa da sauran 'yan uwansa ya yi mummunan tashi, ganin ya ɗauki zobunan tambari ya ba wa Jalaludeen, duk da ga yayyensa. Sai dai maimakon a samu Imam shida, sai aka samu biyar aka rasa inda sauran zobunan suke. Hankalin Saifudeen ya ƙi kwanciya, ya tashi hankalinsa da shi da mahaifiyarsa da wanda suke ɗaki ɗaya, a kan lallai su san yadda za su yi, ko dai a karɓe zoben nan daga hannun Jalaludeen, ko kuma a kashe shi. Sai dai suka fahimci karɓe zoben nan, ba abu ne da zai yiwu ba, saboda ya riga ya mallaki Aljanun da aka wakilta tasrifi da zoben. Duk wani Imam da yake Agadez, askin gashin kai ya haramta a gare shi, haka zalika barin gashin kansa ya haramta. Sannan babu su babu baƙaƙen bayi, a matsayin kuyangi. Sannan akwai nau'in abincin da ba za su ci ba. Bayan majalisar Imam ta kafu, da yawa sauran zuriyar, sun shiga taradaddin ina ɗaya zoben ya shiga?. A dole Saifudeen ya ɓoye hassadar da yake yi wa ɗan uwan nasa, ya ci gaba da ƙoƙarin ganin bayansa ta ƙarƙashin ƙasa. Ya din ga bin bokaye, har da na wata ƙasar a kan a haukata ɗan uwan nasa, ko ma a kashe shi, saboda shi ne ya fi dacewa da matsayin da yake kai, amma abu ya ci tura. Wataran Sultan Ansar ya kira Imam Jalaludeen ya ce masa "Ka Imam Jalaludeen, kana daga cikin manyan dilalan da ya sanya, na dage a kan canza wasu daga cikin dokokin Agadez, wanda za su iya taɓuwa. Iyaye da kakanninmu sun tafka kura-kurai, kura-kuran da yakamata a ce mun yi wasu sauye-sauyen da yakamata al'umma su samu sassauci. Sai dai kai nake ganin zaka iya kamantawa wataƙila ko bayan raina. Ragowar zoben da ake nema, yana gurina, idan Allah ya yi ka zama Sultan a Agadez kar ka  danƙa shi ga kowa, sai mafi cancanta. Na san da duk farmakin da ake kawo maka saboda damar da ka samu, amma ka yi haƙuri ka daure. Sannan zan ci gaba da sanya wa a yi maka duk wani abu na kariya da yakamata. Zan sanya a ƙara sadaukar maka da wasu daga cikin manyan hadiman aljanuna, domin ka samu cikakkiyar kariya. A lokacin an yi ginin zamani, na gidan Sultan, an baro tsohuwar fada ta cikin dutse da ake gudanar da mulki a cikinta. A zamanin Sultan Ansar, ya samu zaɓaɓɓu, aka gina ɗakuna-ɗakuna, a cikin sabuwar masarautar, da hanyoyin tserewa daga cikin gidan, idan an samu farmaki. Saifuddeen dai bai haƙura ba, ya haɗa kai da matarsa, ya aura wa ƙanin nasa ɗaya daga cikin ƙannen matarsa Gimbiya Bilkisu.  Saifuddeen ya din ga shiga yana fita, dan kar Jalaludeen ya zama Sultan, ya haɗa kai da wasu daga cikin Imam na majalisar lokacin, da ziga su kan cewar lallai su dage, su yi ƙoƙari su karɓi sauratarsu, mulki ya dawo hannunsu. Masu kwaɗayin mulki suka din ga yadda da zigarsa, wasu kuma suka din ga yi masa kallon ya za a yi ya nemi sarauta ta bar gidansu. Ya din ga ziga su ɗaya bayan ɗaya, ba tare da wani ya san yana ziga wani ba. Sannan ya koma ya din ga ziga sauran 'yan uwansa, a kan kar su kuskura su yarda su bari, Jalaludeen ya zama Sultan, alhalin duk ga su suna gaba da shi. A kwana a tashi, Sultan Ansar ya koma ga mahaliccinsa, babu ciwo ba komai, ya yi sallar magariba, ya yanke jiki ya faɗi sai gawa. An shiga cikin matsanancin damuwa da tashin hankali, aka yi masa sutura, sai dai manyan 'yan majalisar Sultan na lokacin, ba su bari an wayi gari ba, suka damƙawa Imam Jalaludeen tagullar da kambun Sarautar Agadez, kamar yadda ya bar wasiyya. Sai dai a tsakaninsu ma 'yan majalissar sai da aka so a samu rarrabuwar kai, aka nemi a yi ƙaramin yaƙi a cikin daren. Babban na kusa da Sultan, ya sanya aka je aka ɗaukko masa Imam Jalaludeen, wanda ya san tun da Sultan ya mutu a kowane lokaci za a iya kashe shi. Abin da ba su sani ba shi ne, tun Sultan Ansar yana kan karagar mulki, suke tsara komai da shi da babban amininsa Matawallen Agadez, wanda shi ma duk zuriyar Azhar ne, sun haɗa kakanni. Aka yi ginin ta ƙarƙashin ƙasa, daga sabon gidan Saruta, zuwa tsohon gidan Sarauta, da aka mayar da shi gurin adana kayan tarihi na Agadez. An narka dukiya mai yawan gaske, gurin gina sabon gidan nan, saboda yanayin ƙasar sahara. Da haka ya saka aka ɗaukko masa Imam Jalaludeen, aka biyo da shi ta ƙarƙashin ƙasa, zuwa gidan tarihi, a gidan tarihin ma, cikin kurkukun ƙarƙashin ƙasa, a nan aka ba shi wannan kambun. Cikin kuka Sultan Jalaludeen ya ce "Yaya za a yi ina cikin jimami da alhinin rashin mahaifina, amma ku ta naɗin sarauta ku ke yi, ni ba zan iya karɓar wannan kayan ba" "Dole ka karɓa, ya kai Sultan Jalaludeen Ansar, wannan wasiyyar mahaifinka ce, da ya nemi muddin mu na numfashi a cika masa ita, tun kan a binne shi ya nemi a naɗa ka Sultan a Agadez. Ka zuba ido wayewar gari da an binne mahafinka, yaƙi zai nemi ya ɓarke a Agadez, abin da ba a son faruwarsa a zuriyarku. Dan haka muddin ka na son masaruta ta ci gaba da tsayawa da ƙafafuwanta dole ne ka yi haƙuri, sai dai a wayi gari da sabon Sultan." Haka su ka din ga tausar sa, da ba shi baki har ya yi haƙuri. Sannan suka ba shi wata ƙaramar jakar fata, wadda ta ɗara laya girma, amma ba ta kai girman a kirata jaka ba. Suka sanar masa tun Sultan yana raye, ya sanya bokansa ya yi masa ita, domin tsari da kariya daga miyagu. Kuma a matsayinsa na Sultan, zai iya amfani da ita, gurin sarrafa aljanun gidan Sarauta. Can gidansa kuwa tuni har an kame wasu daga cikin 'ya'yansa, ana ta nemansa ruwa a jallo, an tattare matansa an kame. Sai dai ko sama ko ƙasa aka neme shi a ka rasa. Washegari da sassafe tun kan a binne mahaifinsa aka wayi gari a kan ganshi an kan karagar Mulkin Agadez da duk wani abu da yake nuna shaidar shi ne Sultan a Agadez. Ayshercool 08081012143 90 1K NE A BIYA KUƊIN KARATU KAFIN A KARANTA. 0069685771 Aisha Adam stanbic bank 08081012143 Mutane sun sha mamakin abin da ya faru. Babu wanda ya isa ya ce dan me? Aka kame waɗanda suka yi yinƙurin nemansa su kashe shi. A ka yi jana'izar Sultan Ansar. Gaba ɗaya Jalaludeen baya murna, saboda raɗaɗin mutuwar mahaifinsu, ga kuma wannan nauyi da ya hau kansa da ƙanan shekaru da ba su wuce Ashirin da takwas ba. Sai dai duk zigar da Saifudden ya din ga yi wa Imam da 'yan uwansa, zamewa ya yi ya bar su, aka kama su sukaɗai. Mahaifiyar Jalaludeen ta yi masa nasiha sosai da sosai, a kan gudanar da sha'anin mulki. Duk da ya san tarin ƙiyayyar da Saifudden yake yi masa, da wasu daga cikin 'yan uwansa, amma haka ya janyo su a jikinsa, ya basu sarautu domin ya rage musu raɗaɗin abin da suke ji, kuma ya ƙara musu zaman lafiya da fahimtar juna. Ya yi wa Saifudeen Tafawan Agadez, wanda yana cikin manyan 'yan majalisar Sultan, da suke faɗa a ji. Ya yi wa ɗan uwansa Turakin Agadez, ɗan wan babansa ya yi masa Sardaunan Agadez. Bayan mutuwar Matawallen Agadez ya naɗa ɗansa Matawallen Agadez. Ya saka aka saki Imam Imam ɗin da suka yi zamani tare da su, suka yi yinƙurin halaka shi, sai dai gaba ɗaya ya sauke su daga kan muƙamin ya kuma yi amfani da ƙarfin mulki gurin ƙwace duk zobunansu, ya ce daga lokacin duk wanda zai zama Imam sai ya tantance shi, kuma sai da sahalewar sa. Aka yo caaa a kansa kamar za a cinye shi, su na ganin zai canza musu tsarin Al'ada. Duk gidajen da suke da gadon, suka bayar da wanda suka zaɓo. Hankalin Tafawa ya ƙara dugunzuma bayan da ya san cewa ba shi da makoma, ya san ba zai taɓa mulki a Agadez ba, haka 'ya'yansa, saboda rashin zoben, dan ya san Jalaludeen 'ya'yansa zai bawa. Wata rana Sultan Jalaludeen ya aika aka kira masa ɗan uwansa, ya zo ya same shi ya dube shi ya ce "Ya kai ɗan uwana, na san kai ne gaba da ni,  kuma ka so ka yi mulkin Agadez sosai da sosai, amma Allah bai nufa ba, ina mai sanar da kai cewa zobe ɗaya da aka neme shi aka rasa ya ɓace a tsakanin zuriyarmu, yana nan bai ɓata ba. Dan haka zan damƙa shi a gare ka, ka duba wanda ya dace a cikin 'ya'yanka ka bawa. Wataƙila a bayana a iya samun wani ya yi mulki daga gidanka" Cikin mamaki ya kalle shi ya ce "Amma yaya aka yi ka mallaki zoben da ake tunanin ya ɓace?" "Mahaifinmu ne ya bani shi, bayan nawa da yake hannuna, ya ce bayan ransa na damƙawa wanda ya cancanta" A take Saifudeen ya ji ya ƙara tsanar mahaifinsu, saboda irin wariyar launin fata da aka nuna musu, ya fifita ɗa ɗaya a kan su da ya haifa. Wannan abin da Jalaludeen ya yi bai sanya ya rage ƙiyayya da jin haushinsa da yake yi ba. Sai dai duk da haka majalisar Imam ba ta cika ba, ana ta zuba ido a ga wa Sultan zai bawa sauran zobuna biyun. A lokacin ya auri mahaifiyar Hammad, buzuwar ƙasar Algeriya da mahaifinta ya ba shi ita, bayan da yaje taron tattaunawa na bunƙasa tattalin arziki. Sai dai cikin ikon Allah, jininsu ya haɗu sosai da sosai ta shiga ransa. Imam Jalaludeen yana da kuyangi, da haihu da su, sai dai Gimbiya Bilkisu ta tsani Gimbiya 'yar Algeria Gimbiya Aafaf. Aurota babu daɗewa, ta haifi Hammad, dan watanninta tara cif ta haifo shi. Gimbiya Bilkisu tana da yara huɗu, uku mata sai guda ɗaya namiji Zahradeen, sai kuma 'ya'yan kuyanginsa mata guda biyu. Ba ta taɓa farga Gimbiya Aaafaf tana da juna biyu ba, saboda doguwar mace ce sosai, kuma su kan kwana biyu ba su haɗu ba, babu wanda yake shiga harkar wani. Haihuwar Hammad gaba ɗaya ya gigita Gimbiya Bilkisu, domin ta gama sakankankancewa ɗanta zai iya zama Sultan wataran kasancewar shikaɗai ne namiji. Sai dai ta shiga ɗar-ɗar da tunanin abin da ka iya zuwa ya dawo. Sultan Jalaludeen Amira yake kiran Aafaf da shi saboda ƙauna, ga wani irin so da yake yi Hammad, tamkar shikaɗai ne ɗansa. Sai dai ba Bilkisu ce kawai ta shiga ɗar-ɗar ba, har da sauran waɗanda suke sanya ran 'ya'yansu su zama sarakuna wataran. Bayan haihuwar Hammad, aka ci gaba da zuba ido a ga, ta ina sauran zobunan nan biyu za su ɓullo. Bilkisu a tsaye take sosai da sosai, gurin nema wa 'ya'yanta kariya mussaman Zahradeen, ba ta da yadda ko kaɗan a kansa abinci ma sai wanda ta tantance ta yarda da shi, sannan zai ci. Ba a daina ta'amalli da bokaye ba har a wannan lokacin. Hammad kuwa sai dai Sultan ya sanya a yi masa, dan sam Umminsa ba ta iya irin wannan abubuwan ba. Hammad ya tashi da hazaƙa da karsashi, sai dai ba ya son mutane. Kwatsam yana da shekaru shida, ya yi wata irin rashin lafiya da sai da aka fitar da rai da shi, da kyar da siɗin goshi sannan ya warke. Daga lokacin Sultan ya ƙara tsananta kulawarsa a kan Hammad. Sai dai a lokacin Mamman, mijin Nene, ya san wanda suka ba wa Hammad guba, kasancewar yana cikin manyan hadiman da yake shiri da Gimbiya Bilkisu. Shi yasa da ya aikata wannan laifin, manyan da suke majalisar kusa da Sultan, suka ƙara kambama abin aka yanke masa wannan hukuncin da babu sassauci a cikin sa. Shekarun Hammad bakwai a Duniya, ya haɗu da Mahmoudu, saboda yawan zuwa da Nene take yi da shi, ganin mahaifinsa a kurku, kuma ta kan je gaida Gimbiya Bilkisu. Sai dai sun ƙara shaƙuwa ne lokacin da Raƙuminsa ya taka Mahmoudu. Gimbiya Bilkisu ta so shiga lamarin Maganar mijin Nene, wato Mamman amma Sultan ya ce "Amira, kin ga ke baƙuwa ce a Agadez, kuma ni kaina na taka dokar ƙasar nan aurenki da na yi, dan dai babu yadda za a yi a hukunta ni ne. Idan na matsa aka saki Mamman matsala na iya faruwa. Dan wasu lokutan a kan al'adu babu abin da ba zai iya faruwa ba. Ina matuƙar gudun abin da ka iya biyo bayan sakin Mamman, duk da na san da girman dokar da na karya. Har ta rasu, ba ta daina yi masa magiya ba, da roƙonsa. Sai dai rayuwa ta yi wa Hammad tsanani, bayan rasuwar Umminsa. Al'amuran mulki sun yi wa mahaifinsa yawa, bai fiye samun cikakken lokacin saurarar Hammad ba. Ya ɗauke shi ya ba wa Gimbiya Bilkisu, duk da ya san ba shiri take yi da mahaifiyarsa ba, amma a zatonsa abin ba zai shafi Hammad ba. Mussaman da yake son a ƙara samun haɗin kai a tsakanin iyalinsa, baya son kwaɗayin mulki ya yi silar tarwatsewar kawunansu. Sai dai Gimbiya Bilkisu ta din ga samun shawarari daban-daban a kan Hammad. Ciki har da ta kawar da shi ta huta. Dangin Umminsa sun so a ba su shi, amma Sultan ya ce ko da wasa, kar su ƙara yi masa irin wannan zancen. Gimbiya Bilkisu kan kori Mahmoudu, ta rufe Hammad a ɗaki, tsawon kwanki a cikin sashinta, idan Sultan baya nan, ta hana shi Abinci ba tare da kowa ya sani ba. Ta san idan namansa za ta din ga sara tana zubarwa, ba zai faɗa ba. Sai ta ji Sultan zai dawo zata sake shi. Sai dai su haɗu su yi ta kuka da shi da Mahmoudu, wasu lokutan ma Mahmoudun ne yake kuka ban da shi. Wataran aka kira Mahmoudu, aka ba shi wani lemo ƙato jawur wanda ya ba shi ya ce  "Ka ga wannan lemon, ka je ka ba wa Hammad ya sha, idan ya sha, zan saka a saki babanka, ku tafi gida tare. Amma kar ka gaya wa kowa, kuma kar ka ce ni na baka" Mahmoudu ya karɓa, ya  tafi da murnarsa, ya kai wa Hammad lemon nan. Hammad ba ya tunanin komai idan Mahmoudu ya ba shi abu, ya karɓa ya ɓare har zai kai bakinsa, Mahmoudu ya ƙwace, ya gaya masa abin da ya faru. Hammad ya ce "In dai za a rabu da Abbanka, ka bani zan sha, amma Mahmoudu ya hana shi, cike da ƙuruciya Mahmoudu ya karɓi lemon ya shanye. Haka ya din ga zubar da jini ta hanci ta baki, har da kafofin jikinsa. Hankalin Sultan ya tashi, saboda ya san kusancin da ke tsakaninsa da ɗansa. Ya ɗauki nauyin maganinsa da ƙoƙarin zurfafa bincike a kan abin da ya faru amma ba a gano komai ba. Hammad ya tsallake abubuwa daban-daban na haɗari, na cutarwa a rayuwarsa, wani ya tsallake wani kuma ya rufta ya sha baƙar wahala ya warke. Mahmoudu kuma da yake tare da shi, kullum shi ma cikin farmaki yake da ƙoƙarin son a yi amfani da shi a cutar da Hammad. Duk wata makaranta da Hammad yake yi, tare suke yin ta da Mahmoudu. Saboda Sultan yana jin zafin abin da ya faru da mahaifinsa, ya san har abada Mahmoudu ba zai daina ganin baƙinsa ba. Ga gudunmuwar da kakansa, wato Baban Nene ya ba wa masarautar ta ɓangaren magunan da tsaface-tsaface. Shekarun Hammad sha takwas a duniya, Imam Sultan ya damƙa masa zoben tambari, sai dai ba a son ransa ba, ya kuma damƙawa Zahradeen ɗayan. Sannan ya shugabantar da Imam Hammad a Majalisar, duk da shi ne ƙarami a cikinsu, saboda ko a lokacin ya fisu ilimi sosai da sosai. Nan aka ɗauki surutun ya yi amfani da ƙarfin mulki gurin gwada mugunta, ta hanyar raba wasu gidajen da zobunan tambari, ya ba wa 'ya'yansa da ɗan ɗan uwansa. Sai dai hakan bai ishi Tafawa ba, musamman da ya ga an naɗa Hammad shugaban majalisar, ya ƙuduri aniyar duk yadda zai yi, ko hakan zai janyo yaƙi a Agadez masarautar ta rushe, sai ya yi duk yadda zai yi Asad ya hau karaga, ba zai bari abin da ya faru da su ya faru a kan 'ya'yansa ba, ya zuba ido Jalaludeen ya ɗora ɗansa a kan karaga ba. Tafawa ya je ya samu Sultan Jalaludeen, ya ce masa yadda nauyi ya hau kansa kamar haka, bai kamata a ce ba shi da aure ba, dan haka idan ba damuwa ga ƙanwarsa nan Asal ya ba shi ya aura. Sultan ya ce "Tafawa ai Hammad da Asal duk abu ɗaya ne, kuna duk hukuncin da ka yanke daidai ne. Zan sanar masa, sai dai ina so a bari ya ƙarasa karatunsa" Tafawa ya ce "A'a jinkirin ka iya kawo wani abu daban, a yi auren daga bisani sai ta tare idan ya kammala karatun" Bayan kwana biyu, Sultan ya kira Hammad, su na zaune su na shan shayi, Sultan ya sanar masa da abin da Tafawa ya zo da shi. A take annurin fuskar Hammad ya ɗauke, amma bai yi magana ba. "Na san wataƙila zaɓin bai yi maka ba, amma ka san yadda ake ta sururu a kan abubuwan da na aikata. Ka yi haƙuri ka karɓi auren nan. Hakan shi ne cikar kamala, kuma ka ga 'yar uwakka ce. Sannan na gaya maka, babban burina da fatana, bai wuce ka gaji karagata ba, ina fatan a samu canjin wasu miyagun al'adun a dalilinka" Hammad ya yi shiru, tun da ya zama Imam, ake ba shi kyautar mata duk da ƙarancin shekarunsa, amma Tafawa ya babbake ya hana, yanzu kuma ya zo da wannan maganar. Ya jinjina wa Sultan kai kawai bai ce komai ba. Sai dai da ya je sashensa, kamar ya yi wa Mahmoudu kuka, dan dama shikaɗai ne wanda yake sakin jiki da shi, ya gaya masa duka wata damuwarsa. Mahmoudu ya ce "To mene ne a ciki? Allah ya sanya albarka ya baku zaman lafiya, ai aure abin so ne" "Ba na son Asal Mahmoudu" Mahmoudu ya zaro ido ya ce "Ba ka sonta, 'yar uwakka ce fa" "Ba na sonta kwata-kwata, mahaifinta ba ya ƙaunata, muraran yake nuna mini, duk da yana ɓoye hakan a gaban Abie". "To ai ba ita ce take yi maka ba, bai kamata laifin mahaifinta ya shafe ta ba" Hammad ya ce "Amma ka san ba zai ɗauki 'yarsa ya aura mini haka kurum ba ko? Kamar yadda ya aura wa Abie Gimbiya Bilkisu na sha wahala a hannunta, haka zai aura mini Asal, su ci gaba da azabtar da ni, za kuma ka ce na gaya maka" "A'a kar ka yi wa auren baki mana tun kafin a yi, in sha Allah babu abin da zai faru sai alkhairi" Fuskar nan babu annuri ya kwanta, dan gani yake wannan auren kawai takura wa rayuwarsa za a yi, sai kuma ya numfasa ya kalli Mahmoudu ya ce "Ka san wani abu?" "A'a sai ka faɗa" "Ni wallahi baƙar mace ce take burge ni" AREWABOOKS Mahmoudu ya waro ido ya ce "Dan zatin Allah daga nan, kar ka kuma ɗaga maganar nan, ka san dai illar hakan, da abin da zai haifar" Ya gyaɗa kai ya ce "Ba ina nufin zan auri baƙar ba, amma ni dai su na yi mini kyau sosai da sosai. Da Umma ta yi maka ƙanwa sai na aura" "Dan Allah ka daina wannan maganar, in dai a Agadez ne, mu ba komai ba ne face masu yi muku hidima" Hammad ya ce "Babu aya babu hadisi a kan hakan, ina fatan wataran wannan dokar za ta kau, kowa ya auri wanda yake so, kowane kalar fata ya rayu cikin 'yanci ba tare da bauta ba. Har na koma ga Allah ina jin zafin abin da aka yi muku Mahmoudu. Kuma abin da ya faru da ku, yana daga dalilan da ya sanya nake matuƙar son baƙaƙen buzaye, da ma sauran baƙaƙen fata, duk farin nan namu fa, duk sunanmu 'yan Afrika kuma baƙaƙe to mene ne na ƙymar junan" Mahmoudu ya ce "Ai komai ya wuce ma, dan Allah ka daina wannan maganar kar ma ka sake ɗaga ta dan Allah" Ya ɗan yi shiru sannan ya ce "Na so a ce zan iya ce wa Abie ba zan auri yarinyar nan ba, amma ba zan iya ba" "Dan Allah ko da wasa, kar ka gaya masa haka, ka yi haƙuri dan Allah. Kuma ni gara ka ce ba ka son ta, da dai ka yi waccan kataɓorar da ka faɗa da farko" Hamamd ya gyara kwanciyarsa, ya ce "Da wasa nake yi maka, kawai dai na gaya maka abin da yake raina ne. Fararen matan duk ba ga su nan ba, duk inda na kalla su ne ba. Amma ina son baƙa a ce matata ce, baƙa me kyau tubarkallah ka ga da ka na da ƙanwa, mai kama da Umma, na aure ta baƙaƙen mata su na yi mini kyau ma sha Allah" "Dan zatin Allah ka daina zancen baƙar nan" Yayi murmushi ganin yadda Mahmoudu da gaske baya son zancen, ya juya masa baya yana murmushi. Asal ce zaune a gaban Tafawa, yana zaune daga kan kujera. Ya ce "Ki na ji na ko? Na ba wa ɗan uwanki ke a matsayin matar da zai aura, Imam Hammad dan haka ki shirya a kowane lokaci za a iya ɗaura muku aure". Zabura Asal ta yi ta ce "Aure, kuma da Hammad?" "Eh da shi, mene ne?" Ta sunkuyar da kai tana girgizawa cikin matsananciyar damuwa. "Dan haka ki je zan sanar da mahaifiyarki a yi shiri" Tana barin turakarsa ta saka kuka, ta shiga sashen mahaifiyarta. Cikin damuwa ta ce "Kyakykywata Lafiya kuwa?" "Ammi, Abbu ne ya ce wai aure zai yi mini, dan Allah ban yi ƙarama da aure ba? Kuma wai Imam Hammad zai aura mini" Ta tsuke fuska ta ce "Ban gane ba saboda me? Dama haka ake yi" Asal ta ce "Dan Allah ni ki roƙe shi ya ƙyale ni, kar ya aura mini shi ba na son shi" "Ki kwantar da hankalinki, babu wanda zai yi miki auren dole ina raye". Mahaifiyar Asal ta tashi ta tafi turakar Tafawa, cikin takaici ta ce "Amma meyasa za ka yanke wannan hukuncin ba tare da amincewar yarinyar nan ba, ba ta ƙaunar auren nan fa" "Saboda 'ya ta ce na isa da ita" "Amma rayuwarta fa? Ta yaya za ta zauna da mutumin da ba ta so?" "Ta zauna da shi koma ta yaya ne" Asal ta din ga bori a kan ba ta son Hammad, ba za ta aure shi ba, dan sam ba ta shiryawa aure a lokacin ba, duk da tana da ƙarancin shekaru amma yadda take tsara wa kanta rayuwa sai ta ci Duniyarta da tsinke sannan za ta yi aure. Can kuma Sultan ya saka Hammad a gaba a kan lalai ya je su gaisa da Asal, duk da sun san juna akwai buƙatar su ƙara samun shaƙuwa a kuma tsara yadda biki zai gudana. Da to kawai Hammad yake amsa wa Sultan. Tare da Mahmoudu suka je gurin Asal, sai dai a ƙalla sun shafe awa ɗaya da rabi, Asal ba ta fito ba. Idan ya yi niyyar tafiya, sai Mahmoudu ya hana shi. Daga ƙarshe shi kansa Mahmoudu gajiya ya yi, suka tafi gaba ɗaya. Sai dai washegari, Sultan ya kira Hammad, ya ci masa mutunci abin da bai taɓa yi ba, wai girman kansa zai sanya ya lalata musu zumunci da ɗan uwansa. Yarinya ta gama shiri tana jiransa yana zuwa ya yi tafiyarsa. Abin ya yi wa Hammad ciwo, amma ya daure ya bawa Sultan haƙuri, ya tashi ya tafi. Sai da ya yi zuwa uku, sannan Asal ta zo. Kallo ɗaya ya yi mata ya tuna abin da Sultan ya yi masa saboda ita, ransa ya ƙara ɓaci ya ji wata irin tsanarta ta mamaye shi. Sam Asal ba ta da ɗa'a. Duk da kasancewarsa yaro ƙarami girman sarautarsa ya sanya yana da kamewa da son girma. Amma bai ga hakan a tattare da Asal ba, sai harare-harare da take yi. Ga shi a lokacin shi har cikin zuciyarsa yana son mace mai mamora, Asal kuwa ga yarinta ga babu alamar wani abin kirki a tattare da ita. Haka Tafawa ya din ga haɗa shi da Sultan a kan Asal. Tafawa ya lura idan bai yi a hankali ba, Asal za ta jiƙa masa aiki, ga mahaifiyarta sai bala'i take yi ba za a yi wa 'yarta auren dole ba. Ya same ta da daddare a ɗakinta, ya kifa mata wani uban mari, da sai da ta ga taurari ya ce "Ke kalle ni da kyau, idan ma babarki ce take ziga ki, to ki shiga hankalinki tun da wuri. Ban haɗa auren nan dan ki so ko kar ki so ba. Na haɗa auren nan ne domin cikar muradina. Za ki taimaka mini ne, ina son ɗan uwanki ya gaji karagar mulkin Sultan, dan ba zan bari sarauta ta dauwwama a gidansu ba. Dan haka dole ki haƙura da duk wani abu da ki ke so, domin cikar nawa muradin. Zan aura miki Hammad ne, na wani ɗan lokaci na samu cikar burina, daga nan ki yi duk abin da ki ka ga dama." Asal ta sha kuka sosai da sosai. Ita ta san Hammad ba shi da wata makusa ko kaɗan da za ta nuna a matsayin aibun da za ta ce ba ta son shi, kawai gani take auren kashe mata rayuwa ne. Mussaman yadda Allah ya yi mata kyakykywar halitta. Ko da ta gaya wa mahaifiyarta abin da Tafawa ya ce, zuwa ta yi ta same shi, tana faɗan ya za a yi ita ba da haifar ɗa ba, a tursasa wa 'yarta saboda cikar muradin wani, tun da yana da ƙanne mata a aura wa Hammad ɗin ƙannen Asadullah. Gudun kar ta ɓata masa aiki, ya sanya ya yi mata bayanin ai idan ya aura masa a ƙannen Asad, nan da nan za a gano shi, amma wanda suke ba ciki ɗaya ba, babu wanda zai kawo wani abu. Ya din ga kwaɗai mata abubuwan da za su samu idan Asad ya zama Sultan. Gimbiya Bilkisu ma har gida ta zo ta samu Tafawa, ta ce "Na ji labarin za ka aura wa Hammad ɗanka, duk da na san inda ka dosa, na san dalilinka na yin haka, amma kar ka manta da sauran rina a kaba, tun da Zahradeen ma Imam ne, kuma ɗan Sultan" Tafawa ya ce "Haba Gimbiya Bilkisu, ai ke 'yar uwata ce, ki zo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe mu yi nasarar ganin Hammad bai mulki Agadez ba. Kuma kema kanki kin san alamu sun nuna Hammad yake son ya damƙawa mulkin" Ta ce "Mu haɗa hannu, ka yi mini irin yadda ka yi wa wadancan mutanen da suka haɗa kai da kai. Kuma idan na haɗa kai da kai, waye zai haƙura ya bar wa wani tsakanin Asadullah da Zahradeen iya ruwa fid da kai kawai" Ta ƙarasa maganar tana dariya. Ta shiga gurin mahaifiyar Asal da niyyar su gaisa, amma ta ce mata "Ina fatan idanunki a buɗe suke,a kan auren nan da z a a yi wa 'yarki? Idan burinsa ya cika Asadullah ya zama Sultan Asal ba ta da wata makoma. Ita dai mace ce ba sarauta za ta yi ba. Ki bar ganin shi ya haife ta, buƙatarsa na biya zai ajiye ku gefe" Haka aka din ga ɗauki ba daɗi a kan auren nan, Hammad ya din ga fuskantar kalubale daga Sultan saboda yadda Tafawa yake haɗa su, har sai da Matawallen Agadez mahafin su Hasna da Al-Husssain ya ankarar da shi, Tafawa haɗa shi kawai yake yi da Hammad. Haka Sultan ya saka Hammad haɗawa Asal lefe, na ban mamaki, lefe na 'yar gata. Aka yi gagarumin biki da ya tara manyan mutane, ana ta jinjina yarintar amarya da ango, dan ma dai Hammad a nutse yake sosai. Bayan an yi aure, Hammad ya tsallaka ya tafi karatu tare da Mahmoudu, ba tare da ya sake bi ta kan Asal ba. Bayan ya zo hutu, Tafawa ya dage sai ta tare. Haka aka ginawa Hammad danƙareren gida a cikin gidan sarautar aka saka Asal a ciki. Tun da Asal ta tare, bai taɓa gigin zuwa inda take ba, ta din ga yi masa alwashin tun da ya aure ta, sai ya ga tashin hankali da bala'i. Ta din ga surfa masa rashin mutunci da tijara iri-iri, tun yana jurewa har ya fara gaya wa Mahmoudu zai ɗauki mataki, amma ya din ga rarrashin sa yana ba shi haƙuri. Bayan sun koma makaranta, ita ma Asal aka mayar da ita makaranta, sai dai aka kama mata gida, saboda makarantar nesa ce da Agadez. Idan ya tafi ko son tuna Asal baya yi. Saboda tashin hankali da rashin biyayya, ango na ƙiba shi kuwa ya yi uwar rama. Tafawa kuma ya din ga nanata mata, duk wani motsi na Hammad, ta din ga sanar da shi. A haka aka shafe shekaru uku da aure, ya mayar da hankali a kan karatunsa, da ginin katafaren gurin cin abincinsa a Agadez. Ita kuma mahaifiyar Asal ta fara saduda, tare da kwaɗaitawa Asal ta kwantar da hankalinta, idan Allah ya sanya ta haifi namiji, babu lallai Asadullah ya yi mulki. Ko da suka kammala degree na farko, suka dawo Niger, Asal babu abin da ya yi mata zafi da shi, shi ma bu kula ta yake yi ba, duk inda za ta fita yawonta babu ruwanta da neman izininsa. Wataran da daddare yana zaune a turakarsa, yana duba wasu litattafai ta yi sallama hannunta da tray. Ya amsa mata ta shiga ta ajiye masa ta ce "Ga shayi na dafa maka" Cikin mamaki ya din ga bin ta da kallo. Ya gyaɗa kai ya ce "To na gode" Ta na ɗan murmushi ta tashi ta fita. Bayan fitarta ya din ga kallon flask ɗin shayin, ya murza zoben hannunsa, sannan ya kalli kofin a take sai ga wani irin baƙin hayaƙi yana fitowa daga cikin kofin, shayin ya koma baƙi ƙirin mai kauri. Ya yi shiru yana mamakin yadda ƙiyayyar da take yi masa za ta sanya ta iya cutar da shi, dan tun da ya ga hakan ya san akwai wani abu a cikin shayin. Har ta fara shirin kwanciya, ya shiga ɗakin hannunsa riƙe da kofin. Bai ce mata komai ba ya zauna a kusa da ita ya miƙa mata kofin ya ce "Sha" ta dube shi ta ce "Ai na sha" "So nake ki sake sha ai". Ta girgiza masa kai tana kallon sa. Ya murza zoben hannunsa ya shafi saman kofin da yatsunsa, sai ga Asal ta ga abin da ya gani a cikin kofin. Ya sake kallon ta ya ce "Ki sha, ba za ki kashe ni nikaɗai ba" Ya yi maganar cikin tsawa. Ba ta taɓa tunanin zai yi mata kwarjini haka ba, gaba ɗaya ta rikice ta hau kuka. "Gaya mini wane ne? Waye ya baki wannan abin ki bani, kuma na mene ne?" Ta hau girgiza kai tana kuka. "Ki gaya mini kafin na ɗauki matakin da ya dace" Ta kasa magana ta ci gaba da girgiza kai. "Shikenan, tun da ba za ki faɗa ba, idan na kai ki gaban Sultan kya gaya masa meyasa ki ka yi yinƙurin cutar da ni" Ya fice ya bar ta a ɗakin, hankalinta ya yi mummunan tashi, ta kira lambar Abbanta amma ta ƙi shiga, ta karaya ajalinta ya zo a Agadez. Amma kwana uku shiru babu wanda ya kira ta, kuma ba ta sake ganinsa ba. Kwana na huɗu har ta kwanta, ta tashi ta shiga sashensa, ta gan shi a zaune yana cin dabino yana kallon labarai. Yana ganinta ya tsuke fuska ya tashi ya bar mata falon. Ta tsaya a falon tana wasi-wasi, sai dai ta shiga lissafin halin za za ga shiga idan ya tona mata asiri, ta san duk abin da za a yi mata ba za ta iya tona wa mahaifinta asiri ba. Ta daɗe tana tufka da warwara ta ga dai ba ta da sauran mafita. Dan haka kawai ta bi bayansa, gara duk wadda za a yi, a yi. Sai dai da ta shiga kawai ta tarar yana Video call da wata baturiya. Wani abu mai ɗaci ya tsirga mata ta tsaya tana kallon kyakykywar fuskarsa mai cike da ƙuruciya yana murmushi. Ayshercool 91 Bai daina wayar ba, kasancewar malamarsa ce a faransa. Sai dai bai bari ta fuskanci hakan ba. Ta ƙarasa gabansa cikin ƙunar rai da wani abu da ta kasan gano ma mene ne a ranta. Ta je ta tsaya masa a ka. Bai kula ta ba, ya ajiye system ɗin, ya fara ƙoƙarin kwanciya. Ta zauna a gefen gadon ya ce "Imam gurinka na zo" "An sake aiko kin ne?" Ta girgiza kai cikin sanyin jiki. "Faɗi abin da ya kawo ki zan kwanta" "Dan Allah ka yi haƙuri" shiakɗai ne abin da ta iya furtawa, ta fashe da kuka. "Na yi haƙuri da aka yi me?" "Abin da na yi maka, wallahi ba dan san raina ne ba" Hammad ya ce "Ba da son ranki ba? Bayan kin gaya mini ba kya so na, ba kya ƙaunar zama da ni, sai na yi dana sanin aurenki, ai ba abin mamaki ba ne ba dan an haɗa kai da ke an cutar da ni. Amma ko ba ki kalle ni a matsayin miji ba, yakamata ki kalle ni a ɗan uwanki ki yi haƙuri mu zauna lafiya. Koma waye ya saka ki, ku sani ba zan mutu ba sai wa'adin da Allah ya ɗibar mini ya yi " Asal ta din ga kuka tana ba shi haƙuri, dan ba ta yi zaton zai ma rufa mata asiri na kwanakin da ya yi ba. Daga ƙarshe ya ce "Tashi ki je babu wanda zan gayawa" "Dan Allah da gaske?" Ya tsare ta da ido, sai kuma ta nutsu ta ce "Na gode sosai da sosai, ba zan sake ba in sha Allah" "To ban guri zan kwanta" Ta ce "Dan Allah" sai kuma ta yi shiru. "Mene ne kuma?" "Dan Allah wace ce wadda ku ke waya da na shigo?" Kawai ya kwanta ya share ta. Yana jin yadda take kuka, ya hau baccinsa, saboda haryanzu yana jin ɗacinta, a kan yadda ya iya danne abin da yake ransa ya yi wa iyayensu biyayya, amma ita fuskarta a tasa ta gaya masa, ba ta son sa ba ta ƙaunarsa. Kasancewar ya saba baccinsa shikaɗai a ƙaton gadonsa, ya sanya shi ƙoƙarin yin juyi, amma ya ji kamar an yi masa dabaibayi. Asal ce a jikinsa tana ta bacci. Ya yinƙura zai ture ta saboda yadda ya ji shi wani iri saboda rashin sabo. Amma ta hana shi hakan."Ke ni fa kin matse ni, ki koma ɗakinki mana" Ta yi masa shiru duk da tana jin sa. Ƙarshe dai asancewar su 'yan Adam lafiyayyu, ba su bujirewa abin da gangar jikinsu ta buƙata ba. Tun daga lokacin Asal ta ɗan nutsu, musamman da take tsoron, kar wataran ya faɗi abin da ta yi masa. Duk da ba daina tsiyatakunta ta yi ba, idan ta bushi iska tana yi. Shi kuma baya son duk wani dalili da zai sanya a ga gazawarsa ko ya yi ƙorafi a kanta. Hankalin mahaifiyarta ya koma kan ganin Asal ta samu juna biyu, saboda zigar da Gimbiya Bilkisu take yi mata, a kan lallai ita ma ta yi ƙoƙarin ganin, 'yar ta ba ta zama abar morar Tafawa da ɗansa ba kawai. Dan ta san dole idan Asal ta haihu ta jiƙa musu aiki. Shi ma ɓangaren Hammad, sai Allah ya jarrabe shi da matsanancin son 'ya'ya. Gefe guda Tafawa bai fasa sanya Asal, yi wa Hammad binne-binne ba. Sai dai babban abin da yake ba shi mamaki shi ne yadda abubuwan ba su fiye tasiri a  kansa ba, har kiran Asal yake ya ƙare mata zagi, ya yi zaton ko ita ce ba ta yin aikin dai-dai, duk da wasu lokutan tana tsoron asirinta ya ƙara tonuwa. Aka tafi shekara ta shida da aure, a lokacin ne Hammad haƙurinsa ya fara ƙarewa, saboda haihuwa yake so, kuma ba dan komai ba shi kawai yaran yake so. Duk Imam ɗin ƙasar su na da aure da 'ya'ya amma shi shiru. Ya ce wa Asal su je Asibiti a duba ko lafiya, amma ta ce ba za ta je ba, ya kaɗa ya raya ta ce ba zata ba. Ya ce mata tun da haka ne, shi aure zai yi, ko ya mallaki kuyanga, dan saboda azabar kishinta ya sanya babu ruwansa da barorinsa. Tun da ya faɗi haka ta hau rashin lafiya, Sultan ya je duba ta, ta din ga yi masa kuka a kan ya roƙi Hammad kar ya yi aure, yayi haƙuri tana addu'a ta san za ta haihu wataran. Bata taɓa tunanin ta fara son Hammad har haka ba, sai da ya yi zancen aure, dan har iƙirarin kashe kanta ta yi. Tafawa ya samu Sultan har da kukan munafunci a kan ya saka baki, kar ya rasa Asal, ya rarrashi Hammad. Ganin yadda Asal ta gigice, ya sanya Sultan ya din ga rarrashinta, ya samu Hammad ya ce "Hammad, na san kana yi mini biyayya, kuma kai mutum ne mai haƙur da juriya, dan Allah ina son ka sanya a ranka, rashin haihuwa jarrabawarku ce. Kuma ba a san me Allah zai yi nan gaba ba, dan Allah ka yi haƙuri da batun auren nan, kuma ka daina yi mata zancen haihuwar nan, saboda a samu hankalinta ya kwanta." Karo na farko Hammad ya buɗe baki zai yi magana, amma Sultan ya dakatar da shi ya ce "Baka saba haka ba, kar ka fara a wannan karon, kai mai haƙuri ne, a wannan karon ma ina son ganin tasirin hakan a gare ka" Ya haɗiye yawu mai zafi, idanunsa suka yi jawur. Ya din ga zuwa Asibiti shikaɗai aka duba shi aka ce masa lafiyarsa ƙalau. Asal kuma ta ci gaba da yi masa kuka da magiya a kan ya yi haƙuri su ci gaba da addu'a, ta san wataran za ta haihu, amma ya bar maganar ƙara aure, dan da gaske idan ya yi aure sai ta kashe kanta. Ya so ya yi mata magana a kan to ta bari su je Asibiti, amma ya tuna abin da Sultan ya ce masa, dan haka a dole ya ja bakinsa ya yi shiru ya ci gaba da addu'a. Duk wanda ya yi alkhairi fatansa ya yi masa addu'a Allah ya ba shi haihuwa mai albarka, duk inda ya ji maganin haihuwa, da ya yadda da ingancinsa, sai ya karɓo ya kawowa Asal. Shi kansa Sultan abin ya dame shi, ba yau ba gobe cikin yi wa Hammad addu'a yake, ganin yadda yake ruɗewa idan ya ga 'ya'ya, duk wanda ya haihu a masarauta muddin ya ji labari, sai ya yi masa kyauta mai tsoka ya ce shi ma a yi masa addu'a. Matawalle ya samu Sultan ya ce "Anya ba ka ganin kamar an cutar da Imam Hammad da yawa, da an bari ya jarraba auren wata matar mu gani ko Allah zai sanya a dace" Sultan ya girgiza kai ya ce "In sha Allah zai ga daidai a rayuwarsa. Ina jin tausayin Asal ne, gaba ɗaya hankalinta a tashe yake, amma a ɗan ƙara haƙuri a ci gaba da addu'a. Kuma ka san mahaifinta ba ya raina abin magana, yanzu sai abin ya zama na surutu. Ita kanta Asal abin ya dame ta, mussaman ganin yadda Hammad ɗin yake damuwa da lamarin 'ya'ya, sai dai baya yi mata maganar. Tun da ƙananan shekaru, Hammad ya haɗu da larurar hawan jini ake ta fama. Asal ta ƙara shiga tashin hankali, ganin yadda ake ƙara yi wa Hammad tayin matan aure, ga shi matan ma farmaki suke kawo masa, saboda yadda siffofin kamala da cikar zati ke bayyana a tattare da shi. Su kansu kuyangin gidan su na neman su zama mallakinsa. Sai dai a ransa ko zai yi kuyanga, baƙaƙen nan yake so ba farare ba. Duk ya kawar da kansa saboda Asal. Wataran ya fito zai fita, wata hadima ta risuna cikin girmamawa tana gaishe shi ya ce "Sa'ada na daina ganinki kwana biyu" "Allah ya taimake ka, na yi rashin lafiya ne" "Subhanallah, ai ban sani ba, kin rame sosai da sosai. Maza ki je a duba ki, kuma ki ci abinci sosai, kin fi kyau lokacin da ki ke da ƙiba, Allah ya sauwwaƙe" wasu lokutan Hammad akwai raha, saboda a cewarsa hakan zai ƙara masa kusanci da hadimansa, shi ba ya son wannan tsoron nasa da suke yi. Ta risuna cikin girmamawa tana murmushi ta yi masa godiya. Aikuwa ta sha bala'i a gurin Asal, ƙarshe ta kore ta daga sashen girke-girken gidan, zuwa wani abin daban. Asal ta saka masa kukan, dan me zai kula wannan hadimar, sannan ya yabi jikinta. Ya din ga rarrashinta ya ce shi ba da wani abu ya yi ba. Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya, ana tursasa Hammad jure abubuwa da dama Saboda Asal. Kwatsam Tafawa ya kira Asal, ya ce ta je ta same shi, sai da gabanta ya faɗi tana zaton ko wani laifin ta yi. Ya kira ta cikin turakarsa. Ya ɗaukko mata wata 'yar ƙaramar laya, ya ba ta ya ce ta je ta samu wani guri da ido ba zai kai kanta ba, inda Hammad yake zama ta saƙale ta. Ta yi shiru tana kallon layar, amma babu yadda ta iya haka ta karɓa ta tafi da ita. Ta din ga tunani ta saka ko kar ta saka. Saboda ba ta san ta mece ce ba. A iya zaman da suka yi tsawon shekaru tare, ba za ta iya cewa ga wani abu na cutarwa da Hammad ya yi mata ba, sai ma shi da yake shanye abubuwa da dama take yi masa, komai cutarwar hakan a gare shi. Cikin dare yana tsaka da barci, ya ji tamkar ana girgiza gadon da yake kai, ya din ga ganin wasu irin halittu marasa kyan gani da tsoratarwa. A haka ya wayi gari kansa na neman juyewa, tun gari ya waye ya daina magana. Asal kanta sai da ta tsorata. Sai da suka kwana biyu da kyar yake iya cin abinci, sai ya din ga abu kamar baya cikin hayyacinsa. Tafawa kuma ya din ga kiranta yana tambayarta duk halin da ake ciki. Sai da ta ga da gaske baya magana, ko majalisa baya fita, ta tsorata ta sanar da Sultan halin da ake ciki. Aka kai shi Asibiti amma aka kasa gane abin da yake damunsa. Sai dai jininsa da yake hawa fiye da kima. Ya yi jinya sosai da sosai. Da kyar ya warke, sai dai Tafawa bai haƙura ba, gefe babar Asal ta bazama neman maganin haihuwa tana ba wa Asal. Sai dai kwatsam! Ita ma ta haɗu da jinya, ciwon suga ba ta san tana da shi ba ya yi ajalinta. Asal ba ƙaramin kaɗuwa ta yi ba, da rasuwar mahaifiyarta tamkar za ta zare. Hammad ya yi ta rarrashinta yana ba ta baki. Tafawa bai samu zama ba, ya tashi nan ya faɗi can, duk domin ganin burinsa ya cika, gaba ɗaya rayuwarsa ba shi da cikakken sukuni, haka nan ya hana Asal ta zauna lafiya tare da mijinta. Ya zamana ku san kullum ba shi da cikakkiyar lafiya, yau da lafiya gobe babu. Tafawa ya fara magantuwa a kan yawan rashin lafiya da Hammad yake yi, yakamata ya sauka daga kan shugabancin Majilisar Imam, a bawa wani. A majalisar Sultan aka soke maganar da ya kawo. Hammad kawai yana tafiya ana ganinsa, amma a cikin jikinsa shikaɗai ya san abin yake ji. Ko Asal bai fiye sakin jiki da ita ya gaya mata damuwarsa ba, saboda sam ba ta da alƙibla, kuma tsawon shekaru da suka shafe tare, ba ta iya fahimtar damuwarsa rashin lafiya kai tsaye, sai idan tana da buƙatar wani abu a gurinsa. A haka ta sake neman komawa karatu, lokacin Hammad ya karaya da neman haihuwa. Idan yana salla har kuka yake yi, abin yana burge shi ya ga mutum da ɗan uwansa sun haɗa kai, shi kuma ba shi da wanda suke ciki ɗaya. Mahaifinsa kuma ayyuka sun yi masa yawa, matarsa kuma bai gama gane kanta ba. Dan haka duk wani rikicinsa, shi kuma ba ya gajiya. Wasu lokutan ya na jin daɗin ya bi Mahmoudu gurin Ummansa, su je su wuni, su ci abinci tare. Duk da yana matuƙar jin nauyinta, na abin da aka yi mata a masarautarsu, sai dai bai taɓa ganin hakan a fuskarta ba. Ya yi shiru yana kallon Nana, da ta yi shiru tana saurarensa. "Ya ka yi shiru kuma?" "Na gaji, kuma bacci nake ji" Ta ce "A'a wannan wayo ne na kar ka ƙarasa mini, dama ni ƙarsheƙarshen nan, ba jin daɗinsa na yi ba, gara ma farkon labarin tun da tarihi ne." "Saboda zancen Asal ne?" "Zan iya cewa eh ɗin ma, saboda mutane kaɗan na tsana a Duniya, kuma ta shiga cikinsu" Ta yi maganar tana tsuke fuska. "Amma meyasa?" Nana ta ce "Kawai ba ta yi mini ba" Hammad ya yi shiru ya ce "Ba na tunanin kishi ne kawai ya sanya ki ka faɗi haka, akwai wani dalili, ba kya faɗar magana haka kurum mara ma'ana" Ta ɗan gyaɗa kai ta ce "Ba mai ma'anar ba ce gaskiya, mu je a haka kawai, kishi ne ya sanya na faɗi haka. Yanzu dai ni ka tsallake nan, ka gaya mini yadda aka yi ka din ga wasa da hankalina, da yadda ka gane ni amma ka share ni, nake yi wa matarka aiki cikin ƙasƙanci da wulaƙanci. Kuma alhalin ka na iƙirarin ka na so na. Har kuka na yi mata, da ta ce za ta kawo ni Agadez na ce mata ina da jariri, amma buɗar bakin matar nan ta ce ni ta shafa, tun da talaka ce ni dole na yi abin da take so. Ba zan manta wasu abubuwan da ta yi mini ba na cin mutunci har abada" Ya ɗago da fuskar Nana tana kallonsa ya ce "Ba wannan ne dalilin da ya sanya ki ka ce ba kya sonta ba, akwai dalili. Wannan ba halinki ba ne, idan wannan dalili ne da abin da na yi miki ba za ki sake zuwa inda nake ba" AREWABOOKS Ta kawar da kanta gefe ta ce "Ka ƙarasa mini kawai, mu bar wannan maganar" "Asmy, Asal ko ba aure tsakanina da ita matata ce, ban kuma gaya miki halin da muke ciki, domin na tozartata ba, iya abin da na sani na sanar da ke game da zamantakewar mu, saboda shi ne mahaɗin labarin rayuwata da ke" "Ai dama ban ce kar ka so ta ba, ka je ka yi ta son nata" Ya ce "Ai ba zancen so muka yi da ke ba, ki yi shiru mu ƙarasa an kusa fara kiran Asuba" "Ba na son ji" Ta yi maganar tana kifa kanta tare da tsuke fuska. "Merci ma viee, ba na son ki din ga ɓata ranki, mun bar wannan maganar tun da ba kya so, yadda ba na son kowa ya raɓe ki, ke ma haka ne na sani, kuma na san kin yi ƙoƙari kin yi haƙuri sosai da sosai da juriyar da ki ka cancanci a sara miki, amma ki yi haƙuri mu ƙarasa maganar, daga ƙarshe duk hukuncin da ki ka yanke mini, zan karɓa" Ta ɗago kanta, zuciyarta na yi mata wani irin zafi, azababben kishin Asal yana taso mata, babu abin da yake ƙara ɓata rai irin cin mutuncin da Asal ta din ga yi mata a matsayin kishiyarta. "Kin huce mu ci gaba?" Ta yi masa shiru. Ya ce "Matso na rungume ki, ki nutsu sai mu ci gaba" Ya ƙara matsawa kusa da ita, ya rungumota jikinsa, yana murmushi. Ta kwanta lamo a jikinsa yana shafa bayanta a hankali. A ransa ya ce "Asmy, ba za ki taɓa jin rabi a kwatankwacin abin da nake ji a kan ki ba, ina ƙaunarki ina kishinki, Allah ya bamu haƙurin zama da juna" Asal kuwa na can a tsaye, tamkar ta haɗiyi taɓarya, idanunta suka sauka a kan agogon bangon ɗakin. Idanunta sun bushe, zuciyarta ta ƙeƙashe sai raɗaɗi da idanun kawai suke yi mata. Haryanzu ta kasa yadda Hammad ne yake da wata matar, matar ma baƙar fata da a kyau ba ta kai ta komai ba. Babban abin da ya ƙara rikita ta bai wuce batun ɗa da Tafawa ya tabattar mata da Hammad yana da shi ba, har ɗan shekaru biyu ba. Zuciyarta ta din ga bugawa da sauri da sauri, tsawon lokacin nan ba ta taɓa tunanin son da take yi wa Hammad ya kai haka ba, ashe duk abin da take yi bonono take rufe ƙofa da ɓarawo. Tana zaman zamanta ta janyo masifa da kanta jikinta. Ta din ga tunanin ko dai wata ƙulla-ƙullar ce ta daban aka yi. Sai kuma ta tuna babu yadda za a yi Nana ta samu zarafin shiga har sashen Sultan, su keɓe da Hammad idan ba matarsa ba ce ba. Kenan Sultan ya goyi bayan abin da Hammad ya yi na auren baƙar fata da ba ƙabilarsu ba?. Kawai ta ɗora hannu a ka ta rushe da kuka, hawaye ya ƙi zubo mata sai azabar zafi da zuciyarta take yi. Gimbiya Bilkisu ce ta shigo ɗakin tana faɗin "Asal lafiya kuwa?" "Na shiga uku na lalace Gimbiya, wallahi Hammad ya cuce ni ba zan yafe masa ba. Kuma wallahi sai ya rabu da ita, an cuce ni an cuci rayuwata" Ta rungume Asal tana rarrashinta, ta ce "Ki yi haƙuri, ki daina wannan kukan kar ki samu matsala, ki kwantar da hankalinki na san Sultan ba zai ƙyale shi ba, zai ɗauki mataki" Asal ta ci gaba da kuka da babu abin da yake ƙara mata sai nauyin zuciya. ***** Imam Hammad kuwa a hankali ya ɗan ɗago fuskar Nana ya ce "Bacci ki ke yi ne?" Ta girgiza kai alamar a'a. "To tashi mu ci gaba" Ta noƙe kafaɗa tana ƙara rungume shi. Ta ce "Imam ka ci gaba mu yi mu bar gurin nan, Aljanun gurin nan sun fara tsorata ni, kar a samu matsala" "Kina ganinsu ne?" "Su na bayyana a siffofi daban-daban, tsofaffi tukuf da matasa da wasu halittun daban, duk ina ganinsu addu'a kawai nake yi tun ɗazu" "Ni da ke duniyarm daban take, ƙalubale iri ɗaya, Ubangiji Allah ya bamu lafiya rayuwar Hammad". Ta sake lafewa a jikinsa ta ce "Ka ci gaba to" Ya numfasa. Rayuwa ta ci gaba da tafiya, Hammad na fuskantar suka da ƙalubale kala-kala. A kwana a tashi ya haɗu da larurar zafin jiki, idan jikinsa ya ɗauki zafi tamkar an hura wuta. Babu wanda ya sani sai Asal, dan ya fi kama shi cikin dare, ita ta ɗauka kawai normal zazzaɓi yake yi sai ta yi masa sannu kawai ta ci gaba da sabgoginta. Sultan ya mallaka masa wannan jakar fatar mai kama da laya, wadda ita ma a cewarsa ta tsari ce, kuma tana ɗauke da aljanun da suke yi wa mamallakanta hidima. Duk lokacin da ya murza zobensa, ya kan gansu a suffar tsuntsaye, irin wanda bai taɓa gani ba a duniya, ko suffar wani abun daban. Wasu lokutan ko be murza zoben ba, ya kan gansu, ko ya din ga ganinsu a barci. Duk da ba shiri suke yi da Yayansa Zahradeen ba, saboda Gimbiya Bilkisu ta shiga tsakaninsu, amma ya taɓa tambayarsa, ko yana ganin wannan tsuntsayen shi ma idan ya murza zobunansa. Zahradeen ya ce masa baya ganin komai, an ce duk mai zoben yana iya ta'amalli da aljanun jikin zoben, amma shi baya ganin komai. Ya tambayi Hammad ko yana gani shi. Ya ce masa aa saboda ya karanta tarihin zobunan a littafin Kundin Agadez ne ya sanya ya tambaye shi. Haka ya tambayi sauran Imam ɗin, su ma dai bai ji alamun akwai wanda yake ganin wani abu ba. Abin da bai sani ba, tun zamanin kakansa, aka canza zobunan, na hannunsa ne kawai na ƙwaran da babu wanda ya sani, sai mahaifinsa da kakansa, sai kuma marigayi Matawalle. Kwatsam tafiya ta kama Sultan, ga taron sarakuna da za a yi. Sai ya wakilta Hammad ya ce yaje ya wakilce shi. Nan da nan aka hau surutun da me bai wakilta kowa a majalisar sa ba, zai wakilta yaro ƙarami, maimakon ma a ce a cikin Imam ɗin a zaɓi wanda suka fi shi shekaru. A lokacin Hammad bai daɗe da buɗe sabon branch ɗin gidan abincinsa a Maraɗi ba, ya wakilta cousins ɗin sa Hasna da Al Hussain a matsayin masu kula da gidan cin abincin. Babban abin da yake ƙara ɗaga wa masu son ganin bayansa hankali, bai wuce yadda mutane suke son sa ba. Saboda ya iya shugabanci, shi wannan ƙyamar ma da ake nuna wa baƙaƙen buzaye ba ya yi. Yana damuwa da lamuran na ƙarƙashinsa sosai da sosai, wasu lokutan ma kamar ba basarake ba, saboda yadda yake alaƙa da su. Ga kuma girmama shi da suke yi tamkar Sarki. Hasali ya fi nuna saurata da izzarsa a lokacin da yake cikin 'yan uwansa masu Sarauta. Ga shi manyan mutane na son sa, su na son mu'amala da shi, saboda ladabinsa, da iya magana, fiye da sauran Imam, har ma da 'yan majalisar Sultan ɗin, mussaman da duk wanda ya ga Sultan ya ga Hammad, ya san jininsa ne. Yana ta shirye-shiryen tafiyar taron nan Niemey, a lokacin ga shi nan ne kawai, kansa kamar zai ɓare saboda ciwo. Yana kwance cikin dare tare da Asal su na bacci, ya yi mafarkin wani sanye da baƙaƙen kaya, yana soka masa allura a ka. Ya farka a razane, sai dai ya din ga jin raɗaɗin allurar nan a zahiri. Ya sanya hannayensa biyu ya dafe kansa, yana rintse idanunsa yana ambaton Allah, amma kan tamkar zai yi bindiga. Ya tashi zaune da kyar ya yaye bargon da ya rufe jikinsa kawai ya ga wata takarda. Ya ɗauki takardar ya duba sai ya ga hoton ƙwarangwal na ci da wuta, ga sunansa a jiki. Hakan ya yi daidai da sake jin kamar kwanyarsa za ta zazzago. Ya kifo daga kan gadon ya a rirriƙe kansa, ga jikinsa ya fara wannan zafin. Kawai ya din ga jin idan bai bar garin nan ba, mutuwa zai yi saboda wata irin azaba da yake ji mara misaltuwa. Ya yinƙura ya tashi da kyar, ya ga Asal a zaune a kan gadon tana kallonsa, ya nufi hanyar fita jikinsa na tsuma, amma kasancewar dishi-dishi yake gani, ya faɗi a gurin. Washegari ya tashi normal, sai dai jin da yake yi idan bai bar inda yake ba, kamar zai zauce. Ya yi tafiyarsa ɗaya gidan nasa, ko zai daina jin abin da yake ji, amma abu ya din ga jin cigaba, ya din ga jin kamar a cikin wata masifa yake. Ya yi waya da Mahmoudu a kan tafiyar su, ya ce masa su haɗu a ɗaya gidan nasa. Gaba ɗaya ya ji tashin hankalin na ƙara ƙaruwa, ga wata kururuwa da yake ji a cikin kunnuwansa, ganin wasu irin halittu su na yi masa shawagi a kansa. Su na ta watso masa takardun nan na zanen ƙwarangwal. Yana daga kwance ya din ga jin ana kiransa, ana ya tashi ya je gidan ajiye kayan tarihi ana nemansa. Ya toshe kunnunwansa, amma ya gaza daina jin hayaniyar. Jin da yayi yana neman ya haukace, kawai ya tashi ya fita ya hau tafiya. Duk da da ɗa  nisa daga gidansa na wajen masaruta, haka ya din ga tafiya har ya je gidan tarihin. Yana zuwa mai tsaron ƙofar ya buɗe masa. Da takardar nan mai hoton ƙwarangwal ya sake cin karo,  muraran a zahiri ya din ga ganin aljanun da ke cikin gidan tarihin nan, muraran a siffofi daban-daban. Su na ta fitowa daga cikin ɗakunan nan, wasu su na ratso bango su na fitowa, suka nufo shi su na yi masa wani irin ihu. Ya toshe kunnunwansa, sai ga waɗanda yake gani a suffar tsuntsaye, sun bayyana su na make masu nufo shin. Wata irin guguwa ta tashi a tsakiyar gurin, aka yi wata irin walƙiya mai ban tsoro sai ga Giyaz ya keto ta tsakiyar gidan tarihin ya bayyana a gabansa. Giyaz ya nufo shi, wannan tsuntsayen suka yi kansa, shi kuma Hammad ya tashi ya fice daga gurin, jiri yana ɗibarsa, ya san ya fito daga gidan tarihin sai dai bai san ina ya nufa ba, kawai ya buɗe ido ya gan shi a sahara tare da Mahmoudu. Ya yi shiru yana kallonsa, sai ga Giyaz ya kuma bayyana a cikin saharar, cikin tsofaffin kayan nan tamkar auduga saboda tsufa. Ga wani irin sauti da saharar take yi, tamkar iskar za ta taso. Wata irin dariya Giyaz yake yi mai ban tsoro. Ya ce "Ban sani ba, ko haɗuwa da kai ya sanya na ce na fi kowa sa'a a cikin sararin Duniyar nan, saboda aikin da aka bani a kanka, ya sanya na samu 'yanci. Ni ne Giyaz ibn Jaddul Jinn, ɗaya daga cikin aljanun da suka yi wa kakanninka hidima, daga ƙarshe aka kore shi daga fadar, saboda wani laifi da ya aikata da bai taka kara ya karya ba. Ya tattara iyalansa ya koma Nigeria da zama, ya cigaba da hayyayafa, can ma aka samu waɗanda suka ƙara cutar da shi. Duk da na shafe tsawon shekaru ashirin a tsare, yau wani boka ya bani 'yanci, sannan ya damƙa mini aiki a kanka. Dan haka ko zamu mutu tare sai na cika aikin nan da na karɓa a kan ka" Hammad bai gama gane me Giyaz yake faɗa ba, hankalinsa ya gushe. Bayan ya sake farfaɗowa, ya sake tozali da Habu, sai dai ya manta a inda ya san shi, ko ya taɓa ganinsa. Duk iya ƙoƙarinsa ya kasa tuna komai game da kansa. Shi dai ya san shi mutum ne, duk wani abu da ya shafi rayuwa yana iya tuna shi, amma duk wani abu da ya shafe shi, ya manta. Ko da Habu ya yi yinƙurin mayar da shi Agadez, bin sa kawai yake yi, amma bai san waye shi ba, sai dai su na dosar Agadez Giyaz yake bayyana, yana feso mu wata irin wuta mai ban tsoro, a take sai jikinsa ya ƙara rikicewa ya ji tamkar zai zauce kansa yana wani irin gigitaccen ciwo, bugun zuciyarsa ya ƙaru, ya din ga jin zafin wutar da Giyaz yake feso masa a jikinsa ta na ƙona shi. Gaba ɗaya ya rikicewa Habu. A dole suka bar Agadez suka nufi Nigeria. Su na tafe Hammad yana ganin abubuwan da ya lura abokin tafiyarsa wato Mahmoudu ba ya gani. Duk tambayar da ya yi masa a kan waye shi, ya sunansa ya tuna wani abu game da rayuwarsa amma ya kasa. Da suka shigo Nigeria, suka samu masauki, bai sake ganin Giyaz ba, sai dai lokaci zuwa lokaci wannan zafin jikin yana tayar masa. Tun da suka shigo Nigeria, yake mafarkin wata matashiyar budurwa, tare a cikin sahara. Sai ya kwaɗaitu da son saninta a zahiri. Idan ya kwanta bacci, ba abin da yake mafarki sai wannan yarinyar. A duk lokacin da ya farka, sai ya din ga jin akwai wani abu mai muhimmanci da yake son haɗuwa da shi, duk a duniyar da ya farka, babu wanda ya sani, banda iya mutanen da yake iya gani. Gurin mai magani na farko da suka fara zuwa da su Habu, wata yarinya ta gifta shi, ya ji wani irin daddaɗan sanyi ya ratsa shi, ya din ga jin tamkar ya koma ya bi inda ya ji sanyin nan. Haka da suka sake haɗuwa a gidan Sarkin baka, bai ga fuskarta ba, amma sanyin nan ya ƙara neman ya zauta shi. Sai dai ya sha mamaki, da ganin wani zanƙalelen mutum yana bin ta a baya, sai dai baya iya ganin iyakar tsawon mutumin. Gaba ɗaya ya lura, gane-gane da yake yi,  shikaɗai yake ganin abun sa. Lokaci lokaci ya kan yi mafarki da gidan tarihi, sai dai ya kasa tuna ina ne gurin. Duk lokacin da ya yi mafarkin yarinyar nan, ya kan tashi da matsanancin farin ciki mara misaltuwa, ya kan ji dama su dauwwama a cikin baccin nasa ba sai ya farka ba. Tun da suka fara aiki a gidan Alhaji Zailani, duk lokacin da zai gan shi, yana ganin jini yana bin sa, da wasu ƙanan yara, da wasu mutane su na kuka, amma Alhaji Zailani ba ya ganinsu, sauran mutane ma ba sa ganinsu, sai shikaɗai. Hakan ya jefa shi a cikin damuwa, da jin cewa shi wata halittar ne daban, da sauran mutane. Sai dai babu zato babu tsammani, ya yi ido huɗu da ita, da wani yammaci ta fito daga cikin gidan, wannan dogon mutumin yana biye da ita, sai dai ya ga wannan tsohon ne ya dawo matashi, bai bayyana a suffarsa ta tsohon da ya saba fitowa ba. Sanyin da ya ji ya ratsa shi ya sanya ya rikice, ya ƙudurce a ransa akwai wani abu da bai sani ba, ko yakamata ya sani, kuma wataƙila wannan da suke tare zai iya gaya masa waye shi, kuma daga ina yake!. Ayshercool. 08081012143 LITTAFIN KUƊI NE, VIA 0069685771 AISHA ADAM STANBIC 92 Kafin ya yinƙura ya fito daga ɗakin nasu, wanda yake gani ɗin ya ziro sanda ya hankaɗa shi ya faɗi sumamme. Ya fuskanci mutane kowa yana da ahali, uwa, uba, ɗan uwa, mata 'ya'ya ya san duk abu ne mai muhimmanci game da rayuwar mutum, amma shi ya kasa tuna komai a kan rayuwarsa. Su Habu da yake gani a tare da shi, ya san su na yi masa ƙoƙari amma ba ya jin su sosai da sosai a ransa, yadda za su iya zama wani ɓangare na rayuwarsa. Wasu lokutan idan maganar ba ta ɗauke ba, ya kan yi musu magana cikin iko da isa, ba tare da jin nauyin hakan ba, shi Mahmoudu sam baya damuwa da hakan, amma su Sule wasu lokutan abin yana sosa musu rai. Aka ci gaba da tura wa Habu kuɗaɗe cikin asusunsa. Yana ta tunanin yadda zai sanar da can gida Agadez cewa, ga fa halin da ake ciki, amma aka din ga tura masa saƙonni a kan muddin ya kuskura suka koma Agadez, Hammad zai iya rasa rayuwarsa. Ya tura wa Nene saƙon halin da ake ciki. Ya sanar mata ko an zo an tambayi yana ina ta ce ba ta sani ba kawai. Ya kashe wayarsa ya cire layin ya ajiye, ya samu na Nigeria ya saya ya saka. Sai bayan kwanaki biyu, aka farga ba a samun lambar Hammad, wayarsa na ajiye a ɗakinsa. Sultan ya ce wa Asal, kar ta kuskura ta gaya wa wani cewar Hammad ya ɓace ba a san inda yake ba, ana nan ana bincike a kan nemansa. Hammad kuwa sai ya kintaci lokacin da Nana za ta zo gidan Alhaji Zailani ko kuma ta tafi, sai ya fito harabar gidan ya zauna, ko kuma ya buɗe taga, ya san dole zai ji wannan sanyin. Sai dai duk lokacin da zai ganta, tare da wannan dogon mutumin ne da babu wanda yake ganinsa, sai dai ya fuskanci duk lokacin zai gan shi tare da Nana, ba ya cutar da shi, ko ya yi masa feshin wuta, amma duk lokacin da ya bayyanar masa a suffar tsoho sai ya cutar da shi. Duk lokacin da zai ga Nana yanayin fuskarta na nuna damuwa, dan haka sai ya din ga jin kamar ya je ya tambaye ta mene ne yake damunta fuskarta babu walwala. Wasu lokutan kuma Ƙaisar yake kallo, ita kuma sai ta din ga ganin tamkar yana addabarta da kallo. Ranar da Alhaji Zailani kuwa ya biyo ta, haka kurum ya din ga jin jikinsa babu daɗi, tamkar ya bita cikin gidan. Ko da ya ga Nana ta fito a sukwane kuwa, ya san akwai matsala, sai dai Giyaz ya bayyana a lokacin ya shaƙe Alhaji Zailani. A hankali ya fara lura da tsuntsayen da suke bayyana idan ya murza zoben hannunsa, ko kuma ya matsa jakar fatar da yake ratayawa a wuyansa. Ya kan tambayi tsuntsayen, ko sun san waye shi? Suwaye iyayensa? Da kuma 'yan uwansa? Tun da su na magana wasu lokutan. Ba sa ce masa komai sai dai su zana masa taswirar gidan tarihin Agadez a ƙasa. Idan ya kalla ya san gurin amma ya manta a ina ne. Sannu a hankali ya gane, akwai bambanci a tsakanin Giyaz da Ƙaisar ranar da faɗa ya haɗa su, Giyaz ya yi jifa da Ƙaisar sai da ya sha mamaki, ganin tsananin kammanin da ke tsakanin Giyaz da Ƙaisar. A ranar kuma ya fuskanci Nana ma tana gane-ganen abubuwan da ba kowa ne yake gani ba, hakan ya sanya ya ji a jikinsa ita daidai take da rayuwarsa, ita ce suke iri ɗaya. Amma ta yaya? Tun da yana jin Habu da Sule su na zancen Nigeria da Niger, shi da su irin su ɗaya, ga yarukan da yake iya yi, wanda alamu suka nuna inda suke ba duka yaren da suke yi mutanen gurin suke ji ba. Ɓangaren Ƙaisar ma, tun da ya ga Giyaz a tare da Sayyid ya rikice, domin bai taɓa tsammanin Giyaz zai dawo ba. Wataran bayan shafe kwanki biyar Sayyid yana fama da wannan zafin jikin da yake rikita shi. Ga babu magana abinci ma baya iya ci. Ya wayi gari ya ɗan samu sauƙi. Har ya ci abinci ya shiga ya yi wanka da la'asar. Kawai ya ji wannan sanyin yana kusanto shi. Babu tsammani ya ji muryarta, ta yi sallama sai dai ya yi shiru yana tunanin ko tsabar saka ta a ransa ne ya sanya ya ji muryarta. Yana tsaye cak da matajin hannunsa, ya ji muryar yaro a ɗakin bai ga yaro a ɗakin ba, kawai ya ga ta faɗo ɗakin. Su na haɗa ido ya ga ta yanke jiki ta faɗi. Ya ga Ƙaisar ya bayyana ya tsaya a kanta yana huci, shi dai ya tsaya yana kallonsa dan bai san abin da ya yi mata ba. Ya gama ya sanya kayansa Nana ta kwance, amma sanyin da yake tattare da ita na saukar masa da wata irin nutsuwa da daidaita zafin jikinsa. Tun daga lokacin aka fara dambarwar nan, har ta kai ga ɗaura masa aure da Nana, ya din ga jin amincewa da auren, shi ne hukunci mafi daɗi da zai yankewa wannan rayuwar tasa da yake yi mara kan gado. Ba ya jin ko ɗar sanya Habu ya yi masa duk wani abu da yake buƙata. Bayan aurensa da Nana a  jikinsa yake jin, samun nutsuwa a tattare da wannan duniyar da kuma kwanciyar hankali, idan ya matsa ya tuna wani abu da ya shafe shi game da ainihin waye shi, sai ya ji damuwa da baƙin ciki ya mamaye shi. Habu kuma bai taɓa gangancin gaya masa waye shi ba, kawai ya ƙyale shi a kan duk lokacin da ya tuna wani abin ya sanar da shi. Idan ya kwanta bacci baya mafarkin kowa, sai wannan dai gidan tarihin da yake gani, sai kuma ya din ga ganin wasu abubuwan da suka faru a ƙarnukan baya a wannan gidan sarautar, har ma da mutanen da suka yi rayuwa a gidan. Wasu lokutan har a zahiri yana ganinsa a gidan tarihin amma bai taɓa tuna a ina ya san gidan ba, sai dai bai manta abin da ya faru na ƙarshe a gidan ba, na firfitowar wannan halittun daga ɗakunan tarihin. Sai dai yana yawan ganin gidan, sakamakon aljanun da suke tattare da zobensa da kuma jakar fatarsa, ainihinsu mazauna gidan ne, kuma su ma su kan yi kewar gidan, tun da duk inda yake ya murza zoben sai sun zo. Lokacin da aka yi aurensu, aka kai Nana wannan aljanun na zobensa ne suka din ga rangaɗa guɗa. A duk lokacin da yake son ya yi wasa da hankalin Nana, sai ya murza zoben hannunsa, idan ya danne jijiyar da ke wajen ƙeyarta, sai ta yi bacci. Haka zalika yadda yake ganin gidan tarihin nan, haka ita ma take ganinsa. Da wannan aljanun yake amfani ya burkita mata lissafi, ya yi abu da ita a zahiri amma ta din ga ganin kamar a mafarki ne. Haka zalika Giyaz da yake taka rawa gurin addaba musu, tare da cutar da su, da abubuwa na ban tsoro. Ƙarfin ibadar Nana ne ya sanya suke samun sassauci a wasu abubuwan. Nana ba ta taɓa sanin amfanin zoben nan na hannunsa ba. Ya ɗauki zoben ya ba wa Nana kyautarsa, saboda abin da yake ji a zuciyarsa game da ita. Saboda a jikinsa yake jin zoben na da muhimmancin gaske, dan haka ya ɗauka ya bata. Ƙaisar ya yi ta gargaɗin Nana a kan Sayyid, saboda yana jiye mata tsoron Giyaz, da kuma kar Aljanun da yake ta'amalli da su, su cutar da ita. Duk da yadda Ƙaisar yake jin haushin Sayyid, da yadda Nana ta saki jiki da shi suke rayuwa, amma ya taka muhimmiyar rawa gurin ƙara jirkita hankalin Nana, da sauƙaƙawa Sayyid ɗin wasu abubuwan. A sakamakon yarjejeniya da suka yi da hadiman jikin zoben Sayyid, a kan za su ba shi wasu labarurruka da suka faru a wasu zamani da suka shuɗe, tun kafin a haife shi a cikin Duniya, bisa yarjejeniyar idan suka cutar da Nana ba za su taɓa zama lafiya ba. Duk da tsamin alaƙar da ke tsakanin Giyaz da Ƙaisar, amma yana jin daɗin ganin ɗan nasa, bayan shafe shekaru masu yawa bai gan shi ba. Ya na tsananta cutar da Nana da Sayyid, saboda ya muzgunawa Ƙaisar. Ko lokacin da ya bi Nana, har ya duba Baba, a zahiri ya ga ƙullin da Ƙaisar ya yi a ƙafar Baban, kuma da aljanun jikin zobensa, ya warware ƙullin. Rayuwarsa da Nana yana saka shi jin wata nutsuwa a tattare da shi, ga alaƙar Giyaz da ta Ƙaisar da ta shafi rayuwarsa da Nana. Sau ɗaya ya yi mafarkin Sultan, ya gan shi cikin damuwa da tashin hankali, ya farka a rikice da sunansa a bakinsa amma bai iya tuna ko waye shi ba. Can Agadez kuwa, bayan ɓatan Hammad, aka ankara da ɓacewar Mahmoudu, hakan ya sanya Sultan cewa duk inda Hammad yake yana tare da Mahmoudu. Sultan ba ya iya cin abinci, ba ya isasshen bacci saboda tashin hankalin rashin sanin inda Hammad yake. Ga shi ɓoyewa suke ta yi, duk da yadda Tafawa da muƙarrabansa ke ta ƙoƙarin bin diddigin gano abin da Sultan yake ɓoyewa. Lambar Mahmoudu da ta ƙi shiga, sai aka yi ta tracking lambar Mahmoudu, aka gano last inda ya yi amfani da ita a Nigeria ne. Aka din ga bin diddigi har gidan Alhaji Zailani, aka tafi da motoci gaba ɗaya aka kwaso Buzayen layin kaf. Sai da aka zo Agadez, sannan aka tantance su bayan da aka fahimci su ba su san komai ba, hasali ma wanda ake maganar a kansa ba su san waye shi ba. Aka ɗauke Mahmoudu daga cikinsu, aka din ga tuhumar sa, ina Hammad yake, amma ya ƙi magana saboda yana jin tsoron gargaɗin da aka din ga yi masa, a kan muddin Hammad ya dawo Agadez mutuwa zai yi. Mahmoudu ya sha azaba kala-kala, tamkar ba zai yi rai ba, sai da ya ji azaba sannan ya gaya musu cewar Hammad yana Nigeria. Aka saka shi a gaba zuwa Nigeria, aka taho da Hammad. Sai dai tunda aka taho da shi, sai ƙwaƙwalwar ta sak burkicewa, tunaninsa ya rikice. Bai gama tantance waye shi ba, hankalinsa ya dawo ba, sai da aka fitar da shi Faransa. Dama ƙwaƙwalwar a hargitse take, baya tantance komai, sai dai sannu a hankali tunaninsa na rayuwar da ya yi a Nigeria, ya shafe gaba ɗaya. Sai ainihin tunaninsa na waye shi ya dawo masa. Ganin ya dawo hayyacinsa ya daina iface-ifacen da yake yi, ya nuna ya gane Sultan da Matawalle, suka yi farin ciki sosai, suka tambaye shi ko ya tuna abin da ya faru da yaje Nigeria, sai ya rikice yake tambayar me ya kai shi Nigeria. Daga nan kawai sai suka ɓoye masa, suka ce jinya kawai ya yi mai tsawo a faransa. Likitoci suka din ga ba shi kulawa a kan matsalar zuciya da yake fama. Can a Agadez kuma, aka ci gaba da azabtar da Mahmoud a kan lallai sai ya faɗi dalilin da ya sanya, ya sace Hammad ya tafi da shi Nigeria. Ga Tafawa ya matsa a kan lallai sai an faɗi inda Hammad yake, tun da an doshi shekara biyu, babu wanda ya gan shi, ko kuma a ba su dama su je su duba shi, su gan shi ido da ido su tabattar yana raye babu wani abu da ya same shi. Sai dai Hammad ya kasa yarda da cewa, tsawon wannan lokacin, jinya yake yi. Tiryan-tiryan abin da ya faru na ƙarshe daga gidansa, zuwa gidan tarihi daga nan kuma sai ya rikice ya kasa tuna komai. Ya ce wa Sultan lallai a kawo masa Mahmoudu, Matawalle ya ce "Ko ka tuna wani abu ne? Me Mahmoudun zai yi maka?" Hammad ya ce "Babu komai, ni ba na jin daɗin zama nikaɗai ne, na saba duk inda nake mu na tare, ni dai a kawo mini shi" Matawalle ya ce "Ka yi haƙuri, Likitoci sun ce ba a buƙatar kowa ya zo inda ka ke ne" Ya yi shiru yana tunanin, ina Asal da ko sau ɗaya ba ta zo ba ita ma. Sai dai a jikinsa ya din ga jin kewar wani abu mai muhimmanci a tare da shi, kamar yana jin matsananciyar ƙishirwa. Sultan kuwa ya sanar da Asal batun ganin Hammad, amma ya ce mata rashin lafiya ce ta kama shi a Niemey, aka kai shi wani Asibiti a can, daga baya a ka kai shi faransa. Duk da ta yi mamakin yadda za a ce rashin lafiya ta kama mutum, a kai shi Asibiti amma ba a nemi ahalinsa an sanar da su ba tsawon shekaru. Sai dai hakan ma sai da ta gaya wa Tafawa. Ya ruɗe ya rikice dan ya so a ce wani mummunan abin ne ya samu Hammad. Tun da Asal ta ji labarin Hammad zai iya dawowa a kowane lokaci, take shirin karɓar sa, dan ba ƙaramin kewarsa ta yi ba. Dan ta shiga damuwa da tashin hankalin da sai da suka samun matsala da Tafawa bayan ɓacewar Hammad. Tun da Sultan ya ce a kowane lokaci zai iya dawowa, ta sanya aka yi gyaran gidan sosai. Sannan ta fara lissafin canza kuyangin da za su din ga yi masa hidima. Ga Tafawa ya yi mata alwashin idan ba za ta ci gaba da ba shi haɗin kai ba, zai nemi wani ya yi masa, ko da kuwa ta kama a salwantar da ran Hammad ɗin ne baki ɗaya. Sai dai duk da tunaninsa na Agadez ya dawo, bai fasa fama da wannan matsanancin zafin jikin ba, da yake jin tamkar ana ƙona shi ba. Sai dai ya rage tashi a kai a kai. Haɗuwar Asal da Nana, ya zame wa Asal tamkar tsintar dami a kala, ta ga idan ta kawo Nana gidan sauratar Agdez, kanta a tukunya yake game da sha'anin sarauta, ga girki ta iya, saboda Hammad na son daddaɗan Abinci, ga kuma Nana baƙa ce 'yar Nigeria, babu yadda za a yi ta ɗauki hankalin Hammad, saboda baƙar mace ta haramta a gare su, bisa ga Al'adar Agadez. Sai dai abin da Asal ba ta sani ba shi ne; a rashin sani kaza ta kwana a kan dami. AREWABOOKS Tun da Hammad ya sauka a filin tashi da sauukar jirage, gabansaa yake faɗuwa, ya kuma rasa dalilin hakan. Jin sa yake yi tamkar yana daf da maganin ƙishirwar da ta addabe shi. Bayan Nana ta yi amfani da ƙarfi, gurin tursasa wa Nana zuwa Agadez, ta sanya Nana cikin jerin waɗanda za su yi girkin karɓar Imam Hammad. Gabba ɗaya gida ya ɗauka Hammad zai dawo, bayan shafe dogon lokaci yana jinya. Su kansu wasu daga cikin Imam Imam ɗin, ba haka su ka so ba duk da abin jita-jita ake ta yi, Sultan bai tabattar da hakan ba, kuma a daren za a yi babban taro tare da 'yan majalisar Sarki, da kuma su Imam na shekara da ake gabatarwa. Sai dai babu tsammani, su ka ga Hammad ya bayyana a gurin. Tun da ya shiga gurin, ya ji wani irin daddaɗan sanyi ya ratsa shi, da kowace irin AC aka kunna, sanyin baya wadatar da shi har cikin ƙashinsa ya ji ya gamsar da shi. Ya ji wani irin jiri na neman ya ɗebe shi, amm ya daidaita nutsuwarsa, ya sunkuyar da kansa ƙasa ya rabe ya je ya zauna. Bai ɗago kansa ba, ya ji Matawalle na tambayar me ya kawo wannan nan gurin. Aka sanar masa tana cikin masu girki ne. Bai dai ɗago ba sai murmushi da yake yi, saboda barka da zuwa da ake ta yi masa. Sai dai ƙirjinsa ya tsananta bugawa, da aka ce ta zo ta ɗanɗana Abincin, ta nufo inda suke. Ya kasa jurewa ya ɗaga kansa, sai ya ji kamar sanyin da yake ji yana ƙaruwa. Wani abu ya ji mara daɗi a ƙirjinsa ganin yadda ta ɗaura rigar girki a kan kayanta, ana ganin shape ɗin kyakykyawar surar da Allah ya yi mata ta bayyana. Kalar fatarta ya ɗauki hanklinsa, tsohon muradinsa na son baƙar mace ya motsa a zuciyarsa. A kallo ɗayan da ya yi mata duk ya nazarci wannan abubuwan ya sunkuyar da kansa. Amma ya nemi ya kasa jure bugun da zuciyarsa take yi babu ƙaƙƙautawa. Bai ji daɗin yadda Matawalle ya saka a ka fita da Nana ba, saboda yadda duk ta rikice a gurin. Sai dai ya yi ta mamakin yadda aka ta shiga cikin masu girki, alhalin tana baƙar fata 'yar Nigeria. Da suka tashi daga taron nan kuwa, da Asal ta gan shi, wani irin tsalle ta yi ta maƙalƙale shi, tana murna cikin matsanancin farin ciki har da hawayenta. Ya ɗago ta daga jikinsa yana murmushi yana kallon idanunta, da son gano ainihin abin da yake gani a idanun nata, dan abin da ya faru daren da ya bar Agadez fes yake dawo masa. Ya tsura wa idanun Asal ido, ya ce "Kin yi kewata har haka?" "Imam, kusan shekara biyu ba ma tare ka ce ko na yi kewar ka? tu me manques(Na yi kewar ka sosai) Ta yi maganar idanunta ɗauke da hawaye. Bai bari zuciyarsa ta ci gaba da raya masa abin da take raya masa ba. Ya rungume ta a jikinsa ya ce "tu me manques. Na yi kewar ki sosai cherié. Ina fatan kina lafiya babu abin da ya same ki?" "Ba abin da ya same ni, sai damuwar rashin sanin inda ka ke, ina ka tafi aka neme ka aka rasa haka, ka tayar mini da hankali na shiga damuwa sosai" Ya yi shiru yana mamaki, Sultan ya ce masa faɗuwa ya yi, ya shiga coma na tsawon lokaci, yanzu kuma tana faɗin ya tafi ba a san inda yake ba, ga abin da ya faru na ƙarshe kan barinsa Agadez yana dawo masa. Sai ya kawar da tunanin komai daga cikin zuciyarsa. Duk rawar kan da Asal take yi, da murnar dawowarsa gaba ɗaya hankalinsa ba a kan hakan yake ba. Jin sa yake yi ba daidai ba. Ya yi iya ƙoƙarinsa ya sarrafa tunaninsa da nutsuwarsa gurin ba ta dukkanin kulawa da kuma lokacinsa, amma hankalinsa na kan abin da shi kansa bai san mene ne ba. Da dare ya yi kuwa, ya riga Asal kwanciya dan kar ma ta nemi wani abu a tare da shi, saboda fatansa ya gano takamaiman mene ne yake damunsa. Sannan ya yi mamaki rashin ganin Mahmoudu da bai yi ba. Yana kwanciya bacci surar Nana ta bijiro masa, a ƙasan zuciyarsa ya ji bai ji daɗin fitowarta a haka ba. Da sauri ya yi istigfari dan gudun kar shaiɗan ne yake ƙara ƙawata masa ita. Amma duk da haka bai daina ganin ta a idonsa ba, ds yadda ta zuba masa ido duk ta rikice ba. Ya yinƙura ya tashi zaune, ya ga Asal ta yi bacci, ya yi shiru yana tunanin wa zai tambaya wace ce ita. Ya gaji da zancen zucin ya matsa kusa da Asal ya kwanta tare da rungume ta a jikinsa. Sai ƙamshin turare take yi da alama ta shiryawa dawowarsa sosai. Ya shafa gashin kanta, tare da fatan Allah ya sanya Asal ɗin ta canza gaba ɗaya, tare da yi musu addu'ar samun rabo na alkhairi. Kamar ya tashe ta, sai kuma ya ƙyale ta kawai ya lumshe idanunsa yana addu'a a ƙasan zuciyarsa yana jiran bacci ya ɗauke shi. Yana tsaye a cikin sahara, ya riƙe akalar raƙuminsa, iskar sahara sai kaɗawa take yi, babbar rigar jikinsa na ɗagawa, ta cikin iskar yake jiyo sheshsheƙar kukan mace tana faɗin "Sayyid" ya waiwaya bai ga kowa ba. Shikaɗai ne a cikin saharar, sai dai bai daina jin sheshsheƙar kukan ba. A hankali ya buɗe idanunsa, wannan shi ne karo na bai san adadi ba, yana wannan mafarkin tun da ya buɗe ido a faransa. Jin kiran sallar Asuba ya sanya ya tashi ya tafi salla. Ranar farko da ya sake cin abinci bayan wanda ya ci da ya dawo, sai ya ji kamar ya san ɗanɗanon abincin, amma ya manta a ina ya san shi. Ranar da ya sake ganin Nana, Asal ta kira ta a kan ta zabga yaji a abinci ya kasa ci, sai da zuciyarsa ta kusa tsayawa, ya din ga jin kamar abu malaman haka ya taɓa faruwa, amma bai san a ina ba. Jikinsa ya din ga tsuma sakamakon jin sanyin da ya fara yi, ga kallon da take yi masa da ya sake burkita shi. Ya din ga matsa ƙwaƙwalwarsa, ko za ta ba shi wani abu, amma ya ji ya fara jin jiri. Bai tsaya kammala karin kumallon ba, ya tashi ya fita ya je ya samu Sultan, baya ya kammala zaman Majalissa, yake ce masa shi fa haryanzu bai ga Mahmoudu ba. Sultan ya ce masa ya yi tafiya ne, amma zai dawo. Haka kurum ya ji bai yadda da hakan ba, amma bai kuma cewa komai ba. Cikin hikima ya tambayi Asal inda ta samo Nana, ta sanar masa da a gidan Abincinsa na Maraɗi take aiki, ganin ta iya girki ya sanya ta kawo ta gidan, domin ta din ga dafa masa abinci. Sai dai a kullum abubuwan da Nana take yi, su na ƙara dagula masa lissafi nesa ba kusa ba. Matsin lamba da Hammad ya yi ya sanya aka sako Mahmoudu, kuma Matawalle ya jaddada masa lallai kar ya kuskura ya gaya wa Hammad komai a kan zuwan da suka yi Nigeria, kuma kar ya gaya masa ɗaure shi suka yi. Hammad bakinsa ya ƙi rufuwa, bayan ganin Mahmoudu da ya yi, saboda yadda yake jin Mahmoud a rayuwarsa ba ya jin Zahradeen yayansa da suke uba ɗaya haka. Sai ya yi ta yinƙurin ya yi wa Mahmoudu bayanin abubuwan ban mamakin da yake gani game da Nana, amma sai ya kasa. Babbn abin da ya sake ɗaure masa kai da ita, shi ne lokacin da ya hana ta cin ayaba. Ta karɓa ta ci, a lokacin ya ga Ƙisar a tare da ita. Ganin Ƙaisar ya ƙara hargitsa masa lissafi, saboda yana ganinsa hoton suffar Giyaz ya faɗo masa, amma ya manta a ina ma ya san fuskokin. Sai daga baya sannu a hankali ya tuna yadda Giyaz y fito masa a gidan tarihi, amma wanda ya gani tare da Nana bai kai wancan tsufa ba. Gefe guda kuma Ƙaisar da Giyaz su na ta dambarwa, Giyaz ya ce ba zai taɓa rabuwa da Nana ba, ya mantar da Hammad wace ce Nana da duk wata rayuwa da suka yi a Nigeria saboda ta ci gaba da shan wahala. Bokan da ya sanya Giyaz aikin ɓatar da Hammad kuwa, hankalinsa ya dugunzuma bayan da shi ma wands ya ba shi aikin, ya matsa masa lamba da masifar ya aka yi Hammad ya dawo Agadez bayan an ce har abada shi da Agadez. "Ya kai Giyaz, ina alƙawarin da muka yi da kai? Na baka 'yanci bisa sharaɗin za ka yi mini aiki, amma kwatsam sai na ga wanda na baka aikin a kansa ya dawo Agadez" Giyaz ya ce "A cikin aikin naka wanne ne ban yi ba? Na mantar da shi waye shi, na mantar da shi, ya bar Agadez ya yi nesa da ita, kuma ya yi. Ni da kai ba na tunanin akwai wanda yake bin wani bashi, na cika sharuɗɗanka kaf da muka yi yarjejeniya a kai" Bokan ya ce "Amma ai ga shi ya dawo Agadez cikin ƙoshin lafiya a hayyacinsa" "Eh, ai ba mu yi da kai zai bar Agadez har abada ba, na kuma yi iya abin da muka yi sharaɗi a kai" "Kar ka fusata ni, ka sanya na sake kama ka na rufe ka, ni bami yi haka da kai ba" Giyaz ya ce "Ƙarya ne, ni dai ka kama ni ka sake kulle ni, ba za ka iya wannan ba. Kuma duk abu dole na zauna inda zan iya ganin ɗa na. Kuma ina nan ina ci gaba da gudanar da aikin da ka bani bisa yarjejeniya, tun da haryanzu ina nan tare da shi ban bar shi ba" Bokan ya ce "Waye ɗan naka, kuma a ina yake?" "Babu wannan a cikin yarjejeniyar aikina da kai, ka bar zancen a yadda na bar shi kawai" Bokan nan ya san faɗa da Giyaz ba abu ne da zai haifar musu da ɗa mai ido ba, sai dai dawowar Hammad mayar musu da aiki baya ne. Mahmoudu tunanin Nana ya addabe shi, tare da ganin rashin dacewar abin da ya faru. Ga shi alamu sun nuna ƙiri-ƙiri Hammad bai san ya je ya yi wata rayuwa a Nigeria ba. Ya kuma san muddin ya ce zai je Nigeria sai Hammad ya bi ba'asi, kuma kwana ɗaya ko biyu ya yi kaɗan ya je ya nemi Nana, balle ya yi masa ƙaryar kasuwanci zai je. Ya sha tambayar Mahmoudu a kan ko akwai wani abu dayake damunsa, saboda yanayinsa ya nuna akwai damuwa. Amma ya kan ce masa babu komai. Hammad ya ce wa Asal baya buƙatar sake ganin Nana. Sai murna take saboda ta zata munin Nana yake gani, shi kuwa mafita yake nema, daga burkicewar da yake yi a duk lokacin da ya ganta. Sai dai kuma kwana biyu da ya daina ganinta sai ya shiga damuwa, ya zamana duk ranar da bai ganta ba, sai ya ji shi tamkar a kurku, wunin ranar bai yi masa daɗi ba sam. Yana zaune a ɗakinsa, yake kallon yatsunsa babu zobe guda ɗaya, wanda shi ya fi kowanne muhimmanci. Shi dai Matawalle ya ce masa duk wanda ya tambayi zoben ya ce an kai zoben gyara ya samu matsala. Ya kalli tagullar hannunsa, ya din ga murza ta a hankali yana zancen zuci. Saboda gaba ɗaya a rikice yake, kasancewar Nana ta kai masa abinci tana ƙamshin turarensa da yake amfani da shi. Shi dai ya san babu wanda ya bawa turaren, kuma mai aiki kamar Nana ba za ta iya sayen turaren ba, kuma babu yadda za a yi a ce satar turaren ta yi har ta samu ƙwarin gwiwar shafawa. Yadda take yi masa wasu abubuwan kai tsaye wasu lokutan abin yana ba shi mamaki sosai da sosai. Ganin ya yi hasken wutar ɗakin tana ɗaukewa tana kawowa, daga baya ta tsaya, sai ga wani ɗan gajeren abu a ya bayyana da tsawonsa bai fi 'yar tsana ba, kansa duk wasu ƙayoyi. Hammad ya zuba wa abin ido, ganin yana motsi. "Tuba nake shugabana na tsorata ka, ni ne aljanin da aka wakilta hidima ga duk wanda ya ɗauke da wannan tagullar, tun da ka ke ba ka taɓa nema na ba sai yanzu, me ka ke buƙata?" Hammad ya ce "Waye kai?" "Arun, bawan aljani ga Sultan Azhar, wannan tagullar mallakinsa ce, kuma ni mai hidima ne ga ma mallakin tagullar" Hammad ya zuba ido sosai, ya ga ɗan abin tsoho ne tukuf sosai da sosai. Domin kuwa gemunsa ƙasa yake ja. Ya ce "Amma da idan na murza zoben ba kai nake gani ba" Arun ya ce "Ai ba ni ka ke kira, hadiman wancan zoben daban, nima kuma daban" "To ina zoben nawa yake?" "Ka yi kyautarsa ga wanda ka ke matuƙar ƙauna a matsayin tukuicin soyayya" Hammad ya ce "Soyayya kuma? Ni ɗin? "Ƙwarai ya shugabana" "To wa na bawa, kuma yaushe na yi soyayyar, kuma mace ce ko namiji?" Arun ya sake cewa "Ba na son shiga hurumin da ba nawa ba, ina gudun sake rura wutar fitinar da ke tsakanin gangar jiki buyi, ruhika huɗu, alaƙa huɗu. Gangar jiki ta mutum biyu, ruhi huɗu, na mutum biyu da na aljan biyu, sai kuma alaƙar mata da miji da kuma uba da ɗa, sannu a hankali duk za ka fahimci abubuwan da nake nufi" Daga nan ya ɓace Hammad ya yi shiru yana juya maganganun da suka fi yi masa kama da shirme. Ya tashi ya fita falo, ya san lokacin kawo masa shayin dare ya yi, sai dai tun kafin ya ƙaraso cikin falon yake jiyo sautin muryarta tana waƙa. Daga nesa kaɗan ya tsaya yana kallonta, yana jin yadda zuciyarsa take bugawa da sauri. *_ina zana ganka_* *_saƙo zana baka*_ *Hotona da naka*_ *_Ko ina zana bika*_ *_Kowa tsane ka, ni na tsane shi sanya a ranka*_ *_Zuciyata na baka duk masu ƙin ka su daina shakka*_ *_Rayuwata na baka_* *_Ni ta ya zan guje ka*_ *_Ka dawo gare ni dan zuciya ta bar kewa*_ Gaba ɗaya sai ya daskare a gurin, gumi ya din ga tsatstsafo masa, ƙwaƙwalwarsa ta shiga Kai komo, kansa kamar zai yi tsawa ya fashe. "Tabbas akwai wani abu, ya san wani abu mai kama da haka, amma yaushe? Kuma a ina?" Ya daɗe a tsaye a gurin, kafin ya saita nutsuwarsa ya shiga falon. Murmushi ta yi ta daina waƙar da ta ga ya fito ta risuna ta ce "Barka da dare" Ya jinjina mata kai. "Sayyid ga shayinka nan, ina fatan na kammala komai, zan iya tafiya?" Ya yi shiru yana jujjuya Sayyid da take kiransa da shi. Washegari da sassafe ya kira Mahmoudu a waya, ya sanar masa da yana son ganinsa za su yi magana. Amma Mahmoudu ya ce masa yana hanyar Maraɗi, zai kai wa Nene ziyara ne. Hammad ya yi ta mitar me yasa bai gaya masa su tafi tare, su je su gaishe ta, ya ba shi haƙuri. Sai dai tun da Mahmoudu ya je ya ga Muhsin ya rikice, ya din ga yi wa Nene tambayoyi a kan Muhsin, amma ta ƙi gaya masa haƙiƙanin gaskiyar waye Muhsin. Sai dai yanayin yadda ta ga Mahmoud ya rikice, ya sanya ta tabattar da ya ga abinda take tunani ita ma. Kwanansa ɗaya ya shirya ya nufo Agdez bayan ya faki idon Nene ya ɗauki hotunan Muhsin. Ya nufi Agadez da nufin komai zai faru sai dai ya faru. Hammad kuwa ya lallaɓa Asal ya yi mata wayo ya sanya ta dawo da Nana sashen su, ba tare da ta kawo komai a ranta ba. Amma shi a jikinsa yana jin baƙin abubuwa game da 'yar Nigeria da jikinsa bai ba shi cutar da shi za ta yi ba, amma kasancewarta daf da inda yake yana samun nutsuwa da nishaɗin kallonta. Tun da Mahmoudu ya dawo, Hammad ya lura bakinsa akwai magana, amma ya ƙi ce masa komai. "Mahmoudu na lura bakinka akwai magana, amma ka ƙi gaya mini, duk da ba ma 'yar haka da ni da kai, amma bari ni na gaya maka tawa damuwar". Mahmoud ya ce "Ni babu wani abu da zan gaya maka, amma gaya mini mene ne yake damunka?" "Ina kukun da nake gaya maka Asal ta samo 'yar Nigeria?" Gaban Mahmoud ya faɗi amma ya dake ya ce "Eh meyafaru?" "Wasu abubuwa nake ji game da ita, da tun da nake ban taɓa ji game da wani mutum ba" Mahmoudu ya yi murmushi ya ce "Ko santa ka ke yi ne?" "Anya kuwa, ban dai sani ba, amma ba normal mutum ba ce" "Ka na da mata fa a Nigeriar nan" Hammad ya kalle shi yana jiran ƙarin bayani. Mahmoudu ya ce "Da wasa nake yi, na dai ce zan aura maka 'yar maka 'yar Nigeria idan ka na so. Amma ina da wani abin al'ajabi da nake son nuna maka, amma tashi mu je ka shirya, ka ce mini za ku yi hawan raƙuma kar a yi ta jiran ka" Babu musu ya tashi suka fita. Kowanne a cikin su yana ta saƙe-saƙe a cikin zuciyarsa. Sai dai bayan an yi hawan raƙuman, da Hammad ya faɗo tare da Mahmoudu aka dawo da Hammad gida. Sai dai ya yi mutuwar tsaye, da hango ta tana leƙen mutanen da suke kaiwa da komowa a falon fuskarta ɗauke da damuwa. A jere zuciyar Mahmoudu ta buga, addu'a ya fara yi, a kan Allah ya sanya ba mafarki yake yi ba, ko kuma tsabar saka abin a ransa ne ya sanya ta fara yi masa gizo ba. Ayshercool 08081012143 93 93 LITTAFIN KUƊI NE, KI BIYA KUƊIN KARATU KAFIN KI KARANTA. 08081012143 Cikin hanzari Habu ya ja rawaninsa ya nufi barin falon, yana daf da fita Nana ta waiwaya ta ga wucewarsa, sosai ta tsaya tana kallon bayansa har ya fice tana yi masa kallon sani. Washegari da safe Bayan Tafawa ya zo duba shi, ya tafi zuciyarsa a cunkushe babu daɗi, saboda kausasan kalaman da Tafawa ya yi amfani da su, har da ce masa ko shaye-shaye yake yi, shi ya sanya ya faɗo daga kan Taguwa. Wajen ƙarfe sha ɗaya, da ya ji sauƙi, ya lallaɓa ya fito, yana mamakin dalilin da ya sanya Nana hana shi hawa kan Taguwa, da ya hau kuma ya faɗo. Yana fitowa ya tarar da ita da Asal su na mujadala. Sai dai hangota kawai da ya yi, sai ya ji wani sanyi a ransa. Nana ce take kallon Asal cikin takaici, bayan da Asal ta ce mata ta din ga sanya da hadiman gidan suke sakawa. Nana ta rasa dalilin da ya sanya Asal ke son ƙasƙantar da ita ko ta halin ƙaƙa. Nana ta dube ta ta ce "A gaskiya ba zan iya sanya kayan da hadimai suke sanyawa ba, ko ki haƙura ki kalle ni da kayan jikina, ko kuma ki sallame ni. Tun da ni ba baiwarki ba ce ba, aiki kawai ki ka ɗaukko ni na yi miki" "Idan na so mayar da ke baiwar tawa ina da halin yin hakan, ke kin san ina da abin da ko nawa za a yi miki kuɗi zan iya bayarwa na saye ki" "Ko da Goma ta lalace a gaban biyar take har gaban Abada Gimbiya Asal. Kuma wani garin ya fi gaban kunu.  Ba ki da arzikin da za ki Asma'u a matsayin baiwarki" Nana ta ƙarasa maganar a zafafe. Hammad ya yi gyaran murya, suka tsaya Asal ta haɗiye maganganun da ta yi niyyar caɓawa Nana. "Cherié, ba zai yiwu ki ɗaukko wadda ba hadima ba a cikin gidan nan, alhalin kin san kin taka dokar gidan mulki ba, sannan ki ce ta din ga saka kayan hadimai a nan ta fiki gaskiya." Cikin mamaki Asal ta kalle shi za ta yi magana, amma ya ɗora yatsansa a kan laɓɓansa a dole ta yi shiru. Nana kuwa haɗa su ta yi, tai musu kallon banza ta wuce ta bar su a gurin. Sai dai kallon da ta yi musun, sai da ya kusa ɗimaucewa, ji ya yi tamkar ya bi bayanta. Wani murmushi ya saki ya nufi Asal yana lumshe ido ya ce "Ba girmanki ba ne, ki din ga sa'in sa da ma'aikatanki ai kin wuce nan". "Amma ka na kallo a yadda take yi mini magana, kuma ka hana ni magana?" Ta yi maganar kamar za ta yi kuka. Ya kamo hannunta ya ce "Yawan musayar yawu da na ƙasa da kai, raini yake janyowa, kuma kar ki yadda ki yi fin ƙarfi a abin da ba ki da gaskiya, nan ma raini zai din ga janyo miki" Ya ƙarasa maganar yana rungume Asal, amma a zahiri hanyar da Nana ta bi, ya bi da kallo ƙamshin turarensa da ta shafa ya ci gaba da karaɗa hancinsa. Mahmoudu kuwa bai yi bacci ba, so yake ya tabattar da abin da idanunsa suka gane masa, gaskiya ne ba gizo ba. Ya kira wayar Hammad, amma bai ɗauka ba, ga shi tsoron zuwa gidan yake domin kar su haɗu da Nana, ya san komai zai rikice ne. Ga yaron da ya gani a gurin Ummansa, ga kashedin su Matawalle, ga kuma wannan abu da ya tarar. "Anya yaron na ba ɗan Hammad ba ne?" Ya tambayi kansa. Wayewar garin Allah ya din ga kiran Hammad a waya amma bai ɗaga ba. Takaici ya ishe shi, sai can wajen Azahar sannan ya kira Mahmoudu. "Tun jiya nake kiran ka ka ƙi ɗaga wayata" Hammad ya ce "Ban jin daɗi ne, sai yanzu na duba wayar, ya ake ciki ne?" Mahmoudu ya ce "A ina zamu haɗu, ina da magana da kai" Hammad ya ce "Ina gurin Sultan, haryanzu bai sallame ni ba" "Idan ya sallame ka, mu haɗu a saharar gidan tarihi mu sha shayi, zan nuna maka wani abu" Hammad ya ce "To, saura na ga ba wani abin kirki ba ne, ba za ka yi mini ya jiki ba?" Mahmoudu ya ce "To ya jiki Allah ya kiyaye gaba sai mun haɗu" Hammad ya yi murmushi ya ajiye wayar. Da yamma suka haɗu a sahara, lokacin rana ta yi sanyi. Hammad ya ce "Sai wani nema na ka ke yi, me za ka bani?" Mahmoudu ya ce "Babu komai shayi kawai nake son mu sha tare." Hammad ya yi shiru yana kallon saharar, daga inda suke su na hango gidan tarihi, kuma suna hango wani sashe na gidan sarauta. Ya na shan shayin a hankali yana son ya tuna wani abu, amma ya kasa. Mahmoudu ya ce "Ya na ji ka yi shiru?" "Ina tunanin yarinyar nan ne" "Wacce?" "Wadda Asal ta kawo, a matsayin mai yi mini girki, abubu da dama su na faruwa da na kasa gane kansu" Nan ya sake gaya wa Mahmoudu yadda ta hana shi hawan taguwa, da abubuwan da yake ji game da ita" Mahmoudu ya ce "Kuma kai ba ka santa ba, baka taɓa ganinta ba ko a wani guri?" Ya ɗan yi shiru Sannan ya girgiza kai ya ce "A nan kawai na taɓa ganinta" "Baka tuna komai ba, da muka zo gurin nan?" Nan ma ya girgiza kai duk da yadda ya ji kansa ya fara ciwo. Mahmoudu ya ce "Gaskiya yakamata a ce duk yadda za mu yi, muyi bincike a kanta, mu san daga ina take, kar mu sakankance wani abin ya faru. Ka san ita kanta Gimbiya Asal ba ta yin abu babu dalili, kar mu je shirin Tafawa ne" Hammad ya ce "Gaskiya ne, amma ta ce mini daga gidan cin abinci na Maraɗi ta ɗaukko ta a gurin su Al-Husssain" Mahmoudu ya ciro wayarsa ya daddana, ya miƙa masa ya ce "Ka ga wani ikon Allah" Hammd ya sanya hannu ya karɓa, ya yi shiru ya zuba wa wayar ido. Jiki a sanyaye ya ɗago ya kalli Mahmoudu ya ce "Ina ka samo wannan hoton?" "Samo shi na yi kawai na nuna maka" Ya damƙe wayar da ƙarfi, ƙirjinsa ya yi masa nauyi ya ce "Mahmoudu kuma ka tabatta wannan ba ɗana ba ne ba? Duk wanda ya kalli wannan hoton zai yi zaton ma nine" "Ka na da wata matar ne da zata haifa maka ɗa? Ko kuma Asal ta haihu ne bamu sani ba?" Ya girgiza kai ya ce "Ko ɗaya, amma wannan yaron buzu ne, duk inda iyayensa suke ka nemo mini su a faɗin ƙasar nan" "Me za ka yi musu?" "Zan yi musu alkhairi ne kawai. Amma Mahmoudu kawai ji nake kamar ina da alaƙa da shi, dan Allah ka tura mini hoton nan" Mahmoudu ya karɓi wayar ya ce "Zan tura maka" Gaba ɗaya jikinsa ya yi sanyi, ya kuma kasa shan shayin. Sule ne ya zo gurin a kan babur, ya kafe baburin, ya sauka ya gaida Hammad cikin girmamawa. Hammad dai ya amsa yana bin sa da kallo. Suka gaisa da Mahmoudu ma, ya ga sun sake sun fara hira. Mahmoudu yana ta satar kallon Hammad, ko zai ɗago ya tuna wani abin, amma ya ga babu alamar hakan. Bayan tafiyar Sule, yake gaya masa ai abokin kasuwancinsa ne na Nigeria. Kawai ya jinjina kai. Ƙaisar ne ya bayyana a gaban Giyaz, fuskarsa babu annuri ko kaɗan. Giyaz ya ɗaga kai ya kalle shi, ya ce "Ɗan samari ya dai?" "Zuwa yaushe zaka ci gaba da wannan mugun wasan da ka ke yi?" Giyaz ya ce "Wanne daga ciki?" "Kowanne ma? Ka dawowa da mutumin nan tunaninsa ya tuna da yarinyar nan, ga ɗa a tsakaninsu ko iya yanzu ka ɗauki fansar ai, ka ƙyale ta ta huta haka?" "Yaro yaro ne. Yarinyar da kakaninta suka cutar da mu, ta zo ta ƙona ni ta sanya ni jinya, ita ka ke tunanin na ɗagawa ƙafa ma sassauta mata?" "Ba na son alaƙata da kai ta ƙara tsami, amma zan yi abin da ba ka zato, ba zan zuba ido ka ci gaba da cutar da ita har haka ba" Ƙaisar ya yi maganar cikin ƙunar rai. Giyaz ya ce "To babu laifi, ka yi abin da duk za ka yi" Hammad kuwa da ya koma gida, ya kasa zaune ya kasa tsaye, hoton yaron nan ya din ga kaiwa da komowa a cikin kwanyarsa. Yaya za a yi a ce a samu yaro yana irin wannan kamanin da shi, ba kamanni sama-sama ba, kamanni na zahiri nesa ba kusa ba. Bayan haka yaron ya yi masa kama da wani wanda ya sani ko ya taɓa gani, amma ya manta waye, ya din ga duba wayarsa ko Mahmoudu ya turo masa hoton yaron, amma wayam bai tuta masa ba. Gefe guda ya so haɗuwa da Nana, amma bai ganta ba. Sai washegari da ta kawo masa Abincin safe ta yi masa ya jiki. Ya ce "Sai yanzu za ki yi mini ya jikin?" Ya yi maganar yana tsare ta da manyan idanunsa, saboda wani irin kyau da ta yi masa. Ga ƙamshin da take yi, har wani ƙara nutsuwa ya yi yana kallonta. "Tuba nake ranka ya daɗe" Sayyid ɗin da take kiransa da shi, ya din ga kaiwa yana komowa a cikin kwanyarsa. Haka da rana da ta yi shigar Atamfa, kamar ya sace ta ya gudu. Ta karya ɗaurin ɗan kwali, ta yi kyau. Ya ce "Amm Asma'u ko?" Ta jinjina masa kai duk da yadda ta ji Asma'un banbarakwai a bakinsa. "Cherié ta ce mini a gidan cin abinci na Maraɗi ta ɗaukko ki ko?" "Eh Sayyid" "Me ya kawo ki Niger ne? Ko takanas ki ka nemi aiki da mu, tun daga Nigeria?" Nana ta girgiza kai ta kalle shi ta ce "Abuna ne ya ɓata na zo Niger neman sa, ina son a yi mini izini, nan kusa na koma Nigeria" Ya jinjina kai kawai ba tare da ya gama fahimtar abin da take nufi ba. A daren ne kuma Nana ta jiyo kakarinsa, Asal ta fice ita kuma ta shiga ɗakin. Ƙara lafewa ya yi tamkar ya shige cikin ta, saboda daddaɗan sanyin da ya mamaye jikinsa. A hankali ya buɗe idanunsa, ya ji yadda ta ƙanƙame shi tana kuka. Ya saurara ya yi shiru ya ji ba muryar Asal ba ce. "Allah ka duba mu, ka yaye masa wannan ciwo, Allah ka yi masa maganin abin da yake damunsa. Yana jin yadda take shafa gashinsa tana ci gaba da kuka tana faɗin "Da gaske ba ka gane ni ba Sayyid, ko kuma wasa ka ke yi mini da hankali kawai. Na fara sarewa Sayyid, idan wasa ne ka tausaya mini haka, wahalar da na sha ta isa, ka duba ni ka duba makomar abin da na haifa maka dan Allah" Ta yi maganar tana ƙanƙame shi tana ci gaba da kuka. Gaba ɗaya sai ya rikice, bayan kukanta da maganganun da take yi da suka rikita masa lissafi, gangar jikinsa kuma wani saƙon take aika masa na daban, har wata tsuma ya fara yi. Sai dai Allah ya taimake shi, bai yi wani yinƙuri ba, ya ji tana magana da Ƙaisar, ta kwantar da shi a kan pillow ta koma gefe. Tunani ya din ga yi ina Asal ta tafi? Ya aka yi Nana ta shigo har turakarsa kai tsaye haka, kuma wasu irin maganganu take yi haka? Ya yi lamo kamar bacci yake yi, amma idonsa biyu. Sai gefin Asuba da ta bar ɗakin, ya tashi ya zauna, yana jin wani irin raɗaɗi a tsakiyar kansa, zuwa ƙirjinsa gaba ɗaya ji yake kamar zai fita hayyacinsa ƙwaƙwalwarsa na nema ta hargitse. Garau ya miƙe bayan sallar asuba, ya sake tuna yaron da Mahmoudu ya nuna masa, da maganganun da ya ji Nana tana yi. Ya kira Al Hussain a waya, ya ce masa lallai yana son cikakken bincike a kan Nana. Ga Sultan ya tura shi wakilicin wani ɗaurin aure, amma kusan baya cikin cikakken hayyacinsa, kansa cunkushe da lissafi kala-kala. Maganganun Nana suka din ga karafkiya a cikin kwanyarsa, da rungumar da ta yi masa ba tare da tsoron komai ba. Ko da ya dawo, har ya wuce ɗakinsa, amma kansa ya din ga wani irin ciwo, kawai ya yanke shawarar zuwa ya turke Nana, ta yi masa bayani dalla-dalla. Sai da ya bari Asal ta yi bacci, sannan ya tashi ya tafi ɗakin Nana. Sai dai da ya je ɗakin ya tarar ba ta ciki, sai wayarta da take kan katifarta a ajiye. Har zai juya ya fita, kawai ya nufi kan katifar ya sanya hannu ya ɗauki wayar. Ya jujjuya wayar, yanayin yadda screen ɗin wayar ya dusashe ya sanya ya gane wayar ta kwana biyu. Kawai ya danna madannin gefe a take hoton fuskar Nana da Muhsin ya bayyana a kan screen ɗin wayar. Mutuwar tsaye ya yi zuciyarsa ta yi wani irin mummunan bugawa da ƙarfin gaske. Alamun tahowar Nana ya ji, babu shiri ya jefa wayar kan katifar ya yi sauri ya kashe fitilar ɗakin. AREWABOOKS Ko da Nana ta shigo ɗakin, jikinta ya bata akwai mutum a ciki. Da ta kunna fitilar ta yi arba da shi, ta rikice ta kusa kurma ihu, sai dai duk da a tsorace yake shi ma, amma  kasancewar sa Namiji ɗan gwagwarmaya ya sanya ya danne tsoronsa da tashin hankalin da yake ciki, ya yi mata duk tambayoyin da ya yi mata, sai dai bai tambaye ta haƙiƙanin abubuwan da yake son tambayarta ba. Duk amsoshin da ta ba shi, ba su gamshe shi ba, haka ya fice ya bar ta. Tun da ya bar ɗakin kusan kwanan tsaye ya yi, ya din ga kaiwa yana komowa a ɗakinsa ya dafe kansa, ya zauna ya tashi. Duk wani lissafi da ya yi sai ya ji babu mafita. Shi dai bai taɓa ganin Nana ba, amma meye haɗinta da yaron da Mahmoudu ya nuna masa? Sannan mene ne alaƙarta da shi da ta iya shiga turakarsa ta rungume shi take faɗar wannan maganganun da suke nuna da alaƙa a tsakaninsu. Har aka yi kiran sallar Asuba ko gyangyaɗi bai yi ba. Da Asuba da ya dawo daga masallaci, har zai wuce hanyar ɗakinta, ya koma ya nufi ɗakin nata. Ya jima a gurin yana kallon ƙofar. Ya buɗe ƙofar ɗakin a hankali. Ya tarar da ita tana bacci. Sai dai abin da bai sani ba, Ƙaisar ne ya ƙara wa Nana nauyin bacci, amma duk abin da yake faruwa tana gani, sai dai ba za ta iya motsi ba. Cikin sanɗa Hammad ya ɗauki wayar ya yi waje. Bai ko sake nufar ɗakinsa ba, ya fice. Gidan Mahmoudu ya tafi, ya je ya tarar da shi a zaune yana lazumi. Sai da Mahmoud ya tsorata ya ce "Lafiya na ganka da duku-dukun nan?" "Mahmoudu wane ne yaron nan da ka nuna mini? Kuma wace ce yarinyar da Asal ta kawo a matsayin mai yi mini girki?" Mahmoudu ya kalle shi ya kalli screen ɗin da yake nuna masa, tabbas Nana ce ba wata ba, amma zai so ya yi magana da Nana kafin gaya wa Hammad wani abu. "Ka yi magana ka tsaya ka na kallo na" Ya yi maganar cikin hasala. Mahmoudu ya ce "To ai Asal yakamata ka tambaya ba ni ba, ni fa cin karo kawai na yi da hoton na nuna maka" Zai yi magana kansa ya sara, ya saki wayar ya fara ja da baya yana dafe kansa, ya tafi zai faɗi Mahmoudu ya yi saurin tare shi, ya kwantar da shi a hankali. Ya ɗauki wayarsa ya kira Al-Husssain. Bayan sun gaisa Mahmoudu ya ce "Imam Hammad ya yi maka magana a kan yi masa bincike a kan yarinyar da Asal ta kawo Agadez ta din ga yi masa girki ko?" "Eh ya kira ni, ya yi mini maganar" "To yaya ake ciki, me aka gano a kanta?" Al Hussain ya ce "Eh ina kan yin binciken ne, amma dai wani kamfani ne, da suke samar wa mata, guraren aiki suka kawo ta. To na saka Hasna ta tuntuɓe su, dan ni gaskiya ban wani tantance ta ba, na ɗauke ta aiki, saboda ta ce daga Nigeria take. To gidan aikin sun ce, su ma wata mata ce jami'arsu ta kawo musu ita. Amma za a nemo matar yanzu haka su muke saurare" Mahmoudu ya ce "To shikenan, amma duk abin da aka ƙarasa bincikowa, ni zaka sanar, ka gaya masa tukuna" Sanin alaƙar da take tsakanin Hammad da Mahmoudu ya sanya kai tsaye ya ce masa to. Hammad kuwa yana kwnace, sai jujjuya kansa yake yi yana wani irin gumi. Giyaz yake gani yana yi masa wata irin dariya, da ƙara wadda ta cika masa kunne. Ya lallaɓa ya tashi zaune ya toshe kunnunwansa yana faɗin "Hasbunallahu wa ni'imal wakil" Mahmoudu ya durƙusa a gabansa yana kiran sunansa, amma bai amsa ba ya rintse idanunsa. "Sayyid, Sayyid dan Allah da gaske ba ka tuna ni ba?" Maganganun da Nana ta din ga yi masa ya din ga ji a cikin kunnensa. "Mahmoudu" ya kira sunansa a hankali. "Na'am Imam" "Mene ne alaƙata da yarinyar nan?" "Amm ban sani ba tukuna, ina jiran abin da Al Hussain zai ce ne tukuna" "Ka kirawo ta ka tambaye ta, wane ne yaron nan? Me yasa kuma yake kama da ni?" "Za a yi, amma ka yi shiru da bakin ka mu gano komai tukuna" Sai zuwa yamma Hammad ya ɗan samu nutsuwa, sai dai bai sake ganin Nana ba, abincinsa ma ajiye masa ta yi. Da daddare Asal ta ɗauki hankalinsa sosai, saboda yadda ta sha kwalliya cikin jajayen kayan bacci sai ɗaukar ido take yi. Yana ta ƙoƙarin kar ya shiga hakkinta, saboda damuwoyin da suka yi masa yawa. Sai dai bai iya taɓuka komai ba, hankalinsa ya fara gushewa. Wani irin haske ya din ga gani a cikin baccin nasa yana ɓullowa ta cikin wani mudubi, sama-sama ya din ga hango shi tare da Nana a ciki, cikin yanayin wata rayuwa da take nuna tsananin kusanci da kyakykywar alaƙa a tsakaninsu. Sai dai bai gama fahimtar abin cikin mudubin ba, Giyaz ya bayyana ya huro wata irin wuta a take mudubin ya tarwatse, ya ja da baya yana kare kansa. Giyaz ya gani tare da Ƙaisar, tsananin kamaninsu tsufan Giyaz ne kawai ya sanya shi ya banbance su. Farkawa ya yi jikinsa ya ɗauki wani irin zafi. Tashi ya yi yana zagaye ɗakin, amma ya ci gaba da jin zafin ya tsananta kawai ya fita ya je hanyar ɗakin Nana ya zauna. Zuciyarsa kuma sai azalzalarsa take yi a kan ya je ya samu Nana ya yi magana da ita, amma wata zuciyar ta hana shi hakan. Giyaz kuwa faɗa ne ya kacame tsakaninsa da Ƙaisar. "Ƙaisar muddin ka yi ƙoƙarin saka mutumin nan ya tuna yarinyar nan, zan iya hallakaka, ko kuma na saka shi ya haukace gaba ɗaya" Ƙaisar ya ce "Kafin ka halaka ni, ni zan halakka ka muddin za ka ci gaba da shiga abin da bai shafe ka ba" "Ni zaka hallaka, Giyaz bin Jaddul Jinn?" Ƙaisar ya ce "Ƙwarai kuwa, a kowane lokaci zan iya baka mamaki" Hammad kuwa da duku-duku ya sake tafiya gurin Mahmoudu. Yana ganinsa gabansa ya faɗi. Ya ce "Mahmoudu ka zauna mu yi magana" Mahmoudu ya zauna yana rarraba ido" "Ko dai ka gaya mini abin da ka ke ɓoye mini, ko kuma zan tari duk wanda nake ganin zan samu abin da nake nema, komai zai faru sai dai ya faru. Ka yi mini bayanin waye yaron nan, kuma wacece yarinyar nan" "Matarka ce" Ya ba shi amsa kai tsaye. Zabura ya yi ya ja da baya yana kallon Mahmoudu "Yaushe kuma ta yaya?" "An yi mini gargaɗi sosai da sosai, a kan kar na kuskura na gaya maka, duk da babu wanda ya san da wannan zancen ma. Amma ko zan rasa rayuwata na yi alƙawarin zan gaya maka iya gaskiyata. Nana matarka ce da ka aura a Nigeria. Bisa ga binciken da nake yi ta ƙarƙashin ƙasa kuma, kai ta fito nema ta zo Agadez" Jiki a sanyaye Ya ce " Mahmoudu ban fa gane me ka ke nufi ba, yaushe na je Nigeriar har na aure ta?" "Bayanan da Matawalle ya yi maka ba haka yake ba, ka manta da komai naka, na tafi da kai Nigeria. Yanzu duk bayanin da zan yi maka ba komai zaka fahimta ba, amma Nana Asma'u matarka ce" Hammad ya ce "Mahmoudu, anya ba haukacewa na yi ba kuwa? Ji nake yi kamar ba mutum ne ni ba. Gaskiya" Ya dafa kafaɗar Hammad ya ce "Mutum ne kai, wasu abubuwa ne dai kawai suke faruwa amma ka nutsu, ka yi addu'a. Dan muddin ba ka tuna komai ba, ba zamu iya tunkarar kowa da maganar nan ba. Mutumin da ya zo muna tare a sahara, tare aka kamo ni da su, tare muka yi aikin gadi da su a Nigeria. Hammad ban san yaya zan yi maka bayanin jajircewa da sadaukarwar da yarinyar nan ta yi saboda kai ba." Nan Mahmoudu ya din ga yi masa bayanin wasu abubuwan da ya sani. Ya yi shiru ya rasa gazgatawa zai yi ko ƙaryatawa, idan ya yi duba da wasu abubuwan sai ya ga yakamata ya gazgata batun, dan Mahmoudu ba zai masa ƙarya ba. Amma ya din ga jin sa kamar ba mutum ba, ko kuma a wata Duniyar yake ta daban. Da daddare yana tare da Asal, tana danna waya, Nana ta kawo Abincin dare. Kamar ya yi mata magana ya fasa, sai dai ƙasan zuciyarsa ya din ga fatan Allah ya sanya gaske ne, Nana matarsa ce, ta kowacce fuska ta yi masa. Tun kan ya ji kan wannan burkitaccen labarin yake jin wani abu na sukan zuciyarsa a game da ita. Babban abin da yake ƙara burge shi da ita, sanin mutuncin kanta da ba ta yadda Asal ta taka ta ba. Saɓanin waɗanda suke kwantar da kai Asal ɗin ta taka su saboda abin Duniya. Ya gaza manta rungumar da ta yi masa a turakarsa. Ta ɗago kai suka yi ido huɗu da shi, amma bai sauke idanunsa ba ya ci gaba da kallon ta. A ɗan diririce ta ce "Na gama zan iya tafiya. Bai amsa mata ba ya tuna yadda take ba shi Nonon raƙumi da habbatussauda, ga abinciccikan da yake matuƙar da take gwangwaje shi da su. Asal ta ce "Za ki iya tafiya" Sai da Nana ta je tsakiyar falon sanan ya ce yana buƙatar lemon kankana da shayin citta da kanumfari kawai, ba zai sha na kimba ba. Nana ta yi shiru ta ci gaba da tafiya, Asal ta ce "Kin ji ai" A hankali Nana ta ce "Na ce miki ba ni da kunne ne, da ba zaki iya tsinana wa mijinki uban komai ba" "Ke ba magana nake yi miki ba" Nana ta waiwaya ta ce "Ai na amsa na ce to" Shi kuwa ya yi haka ne, dan ta sake dawowa ya ci gaba da kallon ta ko Allah zai sanya ya iya tuna wani abin. Amma har ta kawo masa shayin tayi tafiyarta bai tuna komai ba. Sosai faɗa ya ɓarke a tsakanin Giyaz da Ƙaisar a kan Nana, Giyaz ya din ga ɗaga Ƙaisar yana bu ga shi da ƙasa. Karfin Ƙaisar da na Giyaz ba ɗaya ba ne ba, duk da Giyaz ya kwana biyu a duniya amma yana da matuƙar ƙarfi. Ƙaisar ya baje a gurin, bayan buga shi da jikin dutsen gidan tarihin Agadez,da Giyaz ya yi, ga ƙona shi da ya din ga yi da wuta. Sai dai ganin Ƙaisar ya baje ko motsi ba ya yi, ya sanya ya nufe shi da sauri yana kiran sunansa, ya ɗago Ƙaisar, amma ya shammaci Giyaz, ya fito da jakar gurin Sarkin Baka daga cikin rigarsa, ya naɗe masa wuya da hannun jakar. Wata irin kururuwa Giyaz ya din ga yi, yana tumami a gurin yana burgima. Ihun nasa sai da ya razana da yawa daga cikin halittun da suke cikin gidan tarihin. Ƙaisar ya miƙe da kyar ya tunkari wani ɗaki, aljanun da suke ƙofar ɗakin su ka dare suka ba shi guri. Ya zura hannunsa a ya ɗaukko kwalbar da Giyaz ya ce tunanin Imam Hammad ne a cikinta. Ya ajiye ta a nesa kaɗan ya ja da baya ya din ga hura iskar bakinsa a jikin kwalbar. A take kwalbar ta yi wata irin ƙara ta tarwatse, a take ɗan hayaƙin da yake cikin kwalbar yana zagayawa a cikin wani ruwa ya bar cikin ta. Ƙaisar ya koma kan Giyaz da ya suma a gurin, ya ɗauke jakar da ya shaƙe shi da hannunta, ya ɓace daga gurin. A hankali yake juyi, ya buɗe bakinsa domin ya jarraba yin magana, ya ji ko maganar ta dawo ya ce "Ma vie" sai dai ya ji shiru. Shi ma shirun ya yi yana ji wani raɗaɗi tun daga cikin kansa har idanunsa. Ya yi juyi ya ji taushin abin da yake kai ya banbanta da nasu. Ya buɗe idanun da suke yi masa raɗaɗi da kyar yana kallon ɗakin. Asal ce ta shigo ya kalle ta, ta ce "Amour ta gama abinci, ka taso ka karya" Ya jinjina mata kansa da ya yi masa wani irin nauyi mara misaltuwa. Tabbas ya san Asal matarsa ce, amma ina Nana. Sai ya yi shiru sannu a hankali ƙwaƙwalwarsa ta tariyo masa yadda aka fita da shi daga gidansu na Buda yana fizge-fizge yana kiran matarsa Nana. Ya rintse idanunsa tare da damƙar gashin kansa yana girgiza kan, saboda yadda ƙwaƙwalwar tasa ta hargiste, tunanin ma ya rasa wanne zai yi. "Hasbunallahu wa ni'imal wakil" ya din ga maimaitawa babu ƙaƙƙautawa. Asal ta sake shigowa ta ce "Amour wai yane? Baccin ne bai ishe ka ba? Sha biyu saura fa na rana, ba ka ko karya ba" Ya yi mata nuni da hannunsa alamun yana zuwa. "Ok, ni zan je gida, Abbu yana jira na" Ya jinjina mata kai" Sannu a hankali ya fara samun nutsuwa, ya miƙe tsaye a hankali, ya shiga banɗaki ya watsa ruwa, sai dai jiri ya din ga ɗibarsa. Ya fito ya zura rigarsa ya fita, ya hau kan doguwar kujera ya kwanta. Ya lumshe idanunsa, abubuwan da suka faru a Nigeria suka din ga dawo masa saɗara-saɗara, zuwa dawo da shi Niger da aka yi. To ya ya aka yi ya manta da ita komai nasa ya shafe da ya baro Nigeria, kuma yaya aka yi ya manta da komai nasa da yaje Nigeria. "Anya babu wata maƙarƙashiya ko wani abu da ban sani ba, game da rayuwata ba?" Bakinta ɗauke da sallama ta shigo ɗakin, hannunta riƙe da kwandon kwanukan Abinci. Wata irin karaya ta ziyarce shi, zuciyarsa ta din ga azalzalarsa ya tashi ya rungume ta, Asmynsa ce, amma zuciyarsa ta din ga gargaɗinsa kar a samu matsala, dan ya san dokar Agadez. "Barka da wannan lokaci Sayyid, ga abincinka, na ga na safe ma baka ci ba, ko ba shi ka ke so ba ne?" Hannu kawai ya ɗaga mata, ya lumshe idanunsa, mamaki ya cika ta, ganin ba shi da niyyar magana, ya sanya ta tashi ta fita cike da damuwa. Tana fita ya haɗe tafukan hannayensa, ya dafe fuskarsa ya fashe da kuka, da wace fuskar zai kalle ta? Me zai ce mata? Ta ina za ta yarda da shi cewar ba yana sane ya ƙi kula ta ba. A hankali ya ci gaba da tuna tsantsar juriya da sadaukarwar da ta yi saboda shi. Ba ta haƙura ba ta taho nemansa, sun haɗu kuma bai gane ta ba. Ya so fita ya je ya samu Habu, amma ba zai iya ba, saboda ji yake yi tamkar an sauya masa gangar jikinsa. Wayarsa da ya bari tun daren jiya a falon tana caji, ya ɗauka ya duba ya ga Mahmudu ne yake kiransa. Ya ɗaga wayar bai yi magana ba, Mahmoudu ya ce "Hammad ina tunanin yaron nan fa ɗan gurin Nana ne, kuma.. "Nana matata ce, ina iya tuna komai yanzu" Mahmoudu a rikice ya ce "Ina fatan ba ka gaya mata ba?" "Babu wanda na gayawa" "Alhamdillah, kar ka ce mata komai, sai mun tabattar da abin da muke bincike, ka zo mu je Maraɗin gurin Umma, na san za ta saurareks fiye da ni. Amma ya aka yi ka tuna komai?" "Maganar ma da kyar nake yi Mahmoudu, ba zan iya fitowa ba. Mu yi magana anjima" Ya ajiye wayar hawaye na ci gaba da zuba daga idanunsa. Haka ya wuni ba tare da ya ci komai ba, jikinsa kuma gaba ɗaya babu ƙwari, kamar wanda aka zarewa laka. Babu abin da yake yi banda tuna rayuwar da suka yi da Nana, da girmama yadda aka yi ya manta da ita, ya kasa tuna ta. Sai dare sannan ya iya samu ya sha shayi kawai. Sai dai zuciyarsa babu daɗi a cunkushe. Ya lallaɓa jikinsa da yake a mace, ya nufi hanyar ɗakin Nana, sai dai ya tsaya a bakin ƙofa yana lissafin me zai ce mata? A hankali ya ɗago hannayensa, ya kalli yatsunsa, ya tuna yadda ya yi mata kyautar zoben, a lokacin da yake tsakiyar jin shauƙin ƙaunarta. A hankali ya murza tagullar hannunsa, sai ga Arun ya bayyana. Ya ce "Na amsa kira ya shugabana" "Ka duba mini; me yarinyar cikin ɗakin nan take yi?" Arun ya risuna ya ce "Tana ninkin kaya ne ya shugabana, amma alamu sun nuna a gajiye take sosai da sosai, kuma akwai damuwa a tare da ita, sai kuma bacci da take ji. Gajiyar da ta yi da damuwar da take ciki ya haifar mata da kasala sosai. Kuma ta yi kuka mai yawa awanni kaɗan da suka gabata". "Ya isa haka, ina son ta yi bacci yanzun nan" Arun ya ce "Shiga kanka tsaye mai gidana, an riga an gama." Hammad ya numfasa ya buɗe ƙofar ɗakin ya shiga, ya mayar da ƙofar ya rufe. Ɗakin sai ƙamshin turaren wuta yake yi. Tana kwance a ƙasa ga kayan ninkin nata a gefe. Daga ita sai zani da ta ɗaura a ƙirjinta, saboda daga wanka ta fito ta zazzage kayan ta hau ninkewa ko za ta ga wayarta da ta nema ta rasa. Jikinsa har rawa yake yi, ya ƙarasa gabanta, bai yi wata-wata ba ya ɗago ta yana kallon kyakykyawar fuskarta. Wata irin karaya da matsanancin tausayinta ya ratsa zuciyarsa. Ya ƙanƙameta a jikinsa yana wani irin kuka zuciyarsa na yi masa zafi da ƙuna. "Ki yi haƙuri Asmyna, ki yi haƙuri ki yafe mini, ni kaina ban san abin da ya same ni ba, ban san yaya aka yi na gaza tunawa da ke ba. Ban yi miki adalci ba amma kk yi haƙuri rayuwata" Ya din ga yi mata surutai ba tare da ta san yana yi ba, saboda wani irin nannauyan bacci da take yi. Duk da yadda burki ya so ƙwace masa, kasancewarsa da Nana a wannan yanayi, da ya din ga tariyo masa irin rayuwar da suka yi ta tsantsar soyayya da ƙauna. Ya yi iya ƙoƙarinsa gurin sarrafa kansa da kyar gurin ganin bai aiwatar da wani abu ba. A ganinsa yin hakan tamkar rashin adalci ne kai tsaye a gare ta. Kamar wani zai ƙwace ta, haka ya matse ta a jikinsa, yana zubar da hawaye, yana sake jin wani abu na ratsa lungu da saƙo na gangar jiki da kuma ruhinsa a game da ita. A duniya ba ya jin yana da wani abu da zai iya aikata wa Nana ya yi ko kwatankwacin saka mata a kan abin da ta yi masa. Har gefin Asuba yana rungume da ita, hawaye kuma bai bar kwarara daga idanunsa ba, lissafi yake yi ko za ta yarda da shi, ta sake ba shi dama ta biyu. Ko kaɗan, tunaninsa da hankalinsa ba sa lissafa masa kalubalen da yake gabansa, na auren wata ƙabila baƙar fata da buzuwa ba. Da kyar ya iya raba jikinsa da ita, ya ɗan yafa mata zaninta, ya gyara mata kwanciyarta, ya durƙusa ya sumbace ta, ya ci gaba da kallonta, daga bisani ya tashi da kyar ya fice ya bar ɗakin. Ko da Nana ta farka ta sha mamakin yadda ta ga jikinta, ita dai ta san ta yi mafarkin tana tare da Sayyid, amma da ta farka ta ga alamun kamar an taɓa ta. Ga shi a iya saninta ninkin kaya take yi, amma ta farka ta ganta rabin tsirara, ta yi tunanin ko Ƙaisar ne, amma cikin hanzari ta kawar da wannan tunanin daga ranta da take jin tamkar saɓo ta aikata, dan ta san Ƙaisar bai taɓa yi mata yawo da hankali a abu makamancin wannan ba. Ta yi iya ƙoƙarinta ta kawar da tunanin komai daga ranta, ta shiga banɗaki ta yi wanka, ta yi alwala ta dawo ta yi sallar asuba tana ta istigfari saboda yadda ta makara. Gari yana yin haske, ya shirya ya tafi gidan Mahmoudu, duk da yadda jikinsa yake a mace. Kallo ɗaya Mahmoudu ya yi masa, ya gane a rikice uban gidan nasa yake. "Mahmoudu, wallahi na gane ta, na tuna ta Nana ce matata ce, to amma yaya aka yi komai ya shafe a cikin kaina na manta da ita?" Mahmoudu ya ce "Ka nutsu ka kwantar da hankalinka, yanzu aiki ne ya ganmu jawur, sai dai ba wannan ba dole mu tsananta bincike a kan abubuwan da suke faruwa da kai." "Ni kaina abubuwan sun ɗaure mini kai Mahmoudu, ji na nake yi wani iri, kamar an ƙwance wani nannauyan dutse daga kaina. Yanzu ta ina zamu fara, ni fa duk abin da za a yi ko Agadez za ta tashi, ba zan rabu da matata ba" Mahmoudu ya ce "Ban gane Agdez ta tashi ba, a'a gaskiya sai dai ku ku tashi kai da ita" Hammad ya ce "Mahmoudu ka daina wasa mana" "Na daina wasa shugabana, amma yanzu ka tuna su Sule?" "Na tuna shi, yanzu ina iya tuna komai fa a cikin ƙwaƙwalwata." "To ma sha Allah, albishirinka" "Mene ne?" "Wallahi sai ka saya, ba zan faɗa a sadaka ba" "Faɗi ko me ka ke so, wallahi zan baka" Mahmoudu ya yi murmushi ya ce "Zan yi tunanin me nake so, amm yanzu yi sujudar godiya ga Allah tukuna" "Zan yi amma fara gaya mini" "Ta tabatta yaron nan, ɗan Nana ne, kuma a bincikena, da Gimbiya ta zo Niger, a hannun Ummana ta sauka. Al-Husssain ya turo mini komai nata, kamar yadda ka sanya shi bincike. A zahirin gaskiya da naje Maraɗi na gano yaron nan a gurin Ummana, shiyasa na damu da matsa bincike. Na kira Umma mun yi magana ta tabattar mini da ɗan Nana ne, kuma ɗanka ne yana daga dalilin da ya sanya ta turo ta Maraɗi aiki gidan cin abincinku, kuma ta ƙarfafeta ta taho Agadez ɗin" A rikice ya damƙi hannayen Mahmoudu a gigice ya ce "Dan Allah da gaske ɗana ne? Ina da ɗa? Mahmoudu? Mahmoudu dama zan haihu zan ga ɗana a Duniya. Subhanallahi wa bi hamdihi subhanallahil Azim. Allahumma lakal hamdu wa laka shukur. Mahmoudu dan Allah da gaske ka ke?" Cikin tausayawa Hammad, mussaman sanin irin ƙalubalen da ya fuskanta na rashin haihuwa da jarabtar da Allah ya yi masa na son 'ya'ya, aka hana shi ƙara aure, kuma Tafawa ya din ga ƙalubalantarsa da hakan yana nemana a sauke shi. Mahmoudu ya dube shi ya ce "Nutsu ka kwantar da hankalinka, ka san ka na da matsalar zuciya kar ciwonka ya tashi, amma ka san ba zan yi maka ƙarya da abin da ka daɗe kana nema ba. Ina da tabbaci a kan abin da na gaya maka, dan sai da na gama bincike na tabattar sannan na gaya maka. Hammad ya saki Mahmoudu, ya yi sujuda yana yi wa Allah godiya, sannan ya tashi fuskarsa sharkaf da hawaye ya ce "Yanzu mene ne abin yi? Ko ka zo mu je ka yi mata bayani, ban yi burus da ita ina sane ba" "A'a kar mu kuskura mu sanar mata komai yanzu, sai mun gama daidaita komai da shirya yadda zamu tunkari jama'ar Agadez da wannan babban al'amari" Ya share hawayensa ya ce "To tashi mu je Maraɗi na ga yarona" "Mu bari sai gobe in Allah ya kaimu" Hammad ya ce "Ba zan iya jira ba, kuma kar wani abu ya same shi, dole na dawo da shi kusa da ni, ko na ajiye su a wani guri keɓantacce, idan yana hannuna sai ta fi tsayawa ta saurare ni. Na san halinta akwai sauƙin kai amma akwai kafiya ba za ta saurare ni ta daɗin rai ba" Mahmoudu ya yi murmushi ya ce "To shikenan, amma ka jira kaɗan Sule ya zo, ku gaisa sai mu je Maraɗin tare da shi" Haka kuwa aka yi, ba a jima ba Sule ya shigo, ya risuna yana kwasar gaisuwa gurin Hammad. Ya rungume Sule tare da yi masa godiya, a kan ɗawainiya da kuma gudunmuwar da suka ba shi a lokacin yana Nigeria. Suka shirya suka tafi Maraɗi gidan Nene, ko da Hammad ya ga Muhsin, ya kasa zaune ya kasa tsaye, ya rungume shi yana kuka, da gode wa Allah da ya sanya yana da rabon haihuwa a Duniya. Duk da sun kai ruwa rana da Nene, ta ce ba zata ba su Muhsin ba, dan ba su yi haka da Nana ba. Hammad ya ce ba ɗaukar Muhsin zai yi ba yana son ya nesanta su da gurin da suke na ɗan wani lokaci, kamar yadda Hammad ma ya yi tunani haka ita ma Nene ta tabattar masa da muddin ya jewa Nana kai tsaye babu abin da zai hana Nana zuwa ta ɗauki Muhsin ta gudu, dan ta san halinta dole ya bi komai a hankali. A hankali Hammad ya ɗago Nana daga jikinsa ya ce "Asmy bacci ki ka yi?". "Idona biyu" Ta ba shi amsa. "Kin yi shiru, Asmy ba da gangan na ganki na ƙi kula ki ba, kin san muddin ina cikin hayyacina babu yadda za a yi na share ki. A lokacin ina ta shirye-shiryen yadda zamu ɓullowa lamarin, Tafawa kuma ya sanya ni a gaba da da haƙilon ba zan yi mulki ba, ni juya ne, ga rashin lafiya ga hauka ga babu zobe. Ya daɗe yana jifana da kalmar juya, abin yana yi mini zafi da ciwo shiyasa na fallasa komai a lokacin da shirin duk abin da zai faru ya faru." Nana ta yi ajiyar zuciya ta ce "Yakamata mu tashi, an kira sallar Asuba". Hammad ya ce "Haka ne, amma ba ki ce komai ba" Ta ce "Zan ce ne, ina jin bacci ne sosai ka ga kwana muka yi ba mu yi bacci ba" Ya ce haka ne. Suka tashi suka koma ɗakin nan zai rufe amma ya tsaya ganin Nana na ƙara kallon ɗakin. Ya ce "Wannan ɗakin tun zamanin Sultan Azhar yake, duk Sultan ɗin da ya zo a nan ɗakin ne turakarsa. Kowane zamani akwai canji da kuma yadda ake ƙawata ɗakin. Kafin daga bisani a daina amfani da gidan gaba ɗaya." Nana ta jinjina kai ta ce "Ni yanzu abu ɗaya nake son ka gaya mini, ina da ciki ko ba ni da shi?" Ta yi maganar a ɗan shagwaɓa tana marairaice fuska. Ya yi murmushi ya ce "A cikin labarin kin ji inda wani abu ya faru ne?" "Eh mana, tun da kana zuwar mini ɗaki ba tare da sanina ba" Ya jinjina kai ya ce "Sosai kuwa, dan tun da na gano ke matata ce, kusan kullum tare muke kwana, ya yi maganar yana rufe ɗakin. Ya damƙi hannunta suka yi gaba, ja ta yi ta tsaya tayi shiru sannan ta ce "Sayyid ba ka nuna mini mene ne a cikin ɗakin can ba" Ya kalli ɗakin ya ce "Hanyar tsohuwar prison ce, inda daga baya ake aikin sarrafa gold a ciki, amma yanzu babu abin da ake yi da gurin" "Ina son ganin mene ne a ciki" Ya ce "To shikenan" Ya ja hannunta zuwa ƙofar gurin, amma suka tarar da ƙaton kwaɗo a jikin ƙofar. Ya ce "To ai gurin a rufe yake ma" "Ya aka yi sauran ƙofofin ba a saka mukulli ba sai wannan? A tambayi mai tsaron gidan ya buɗe mini zan gani" Hammad ya ce "To ai lokacin salla ya yi" Ta ce "Na sani gani kawai zan yi mu tafi" Ya tsaya yana kallon Nana da rikicin tsiya, ya ce "Zo mu je sai mu yi wa mai gadin magana, ya zo ya buɗe mana" ta bi shi a hankali jikinta cike da kasala ga kuma bacci da take ji. Ko da Hammad ya tambayi tsohon nan mai tsaron ƙofar, sai cewa ya yi "Allah ya taimake ka, ban san wanda ya rufe ɗakin nan ba, ya kwana biyu a rufe" Hammad ya ce "Wataƙila ko masu yawon buɗe ido su na ɓarna a gurin, shiyasa aka rufe" Nana ta ce "Waye yake da alhakin rufewar?". "Ma vie, wai lafiya kuwa?" "Hammd sai an buɗe gurin nan kafin na bar Agadez" "Shikenan na ji, za a buɗe amma muje mu yi salla tukuna" Da kyar ya lallaɓa ta suka bar gurin, saboda yadda take nema ta burkice masa gaba ɗaya. ***** Shukura na zaune a kan gadon Asibiti,  ta zuba ido tana kallon ɗan jaririnta, ƙato da shi mai matuƙar kama da Sagir, ta din ga tuno da jaririnta da aka ce ya mutu da haryanzu zuciyarta ta kasa amincewa da hakan. Ji ta yi an turo ƙofar ɗakin ta ɗago da sauri, gabanta ne ya faɗi ta yi turus tana kallon mai shigowar. Ayshercool 08081012143 94 LITTAFIN KUƊI NE, KI BIYA KAFIN KI KARANTA. 0069685771 AISHA ADAM STANBIC Yusra ce ta shigo ɗakin, Shukura ta yi tsuru da ido tana kallonta. Yusra ta ƙarasa gaban gadon Shukura cikin damuwa ta ce "Meyasa ki ka taho nan, ki ka saka ake ta neman ki, duk hankalin mutane ya tashi?" Maimakon Shukura ta bata amsa sai cewa ta yi "Ke kaɗai, ki ka yi driving ki ka zo nan? Ina Baban Haidar ɗin?" "Wayarsa ce lalace, ya saka layin a wayata, yana can gurin meeting, kafin ya dawo kawai na ce bari na zo na ɗauke ki. Wannan ɗan da ki ka haifa ne?" Ta yi maganar tana karɓar jaririn hannun Shukura. Shukura ta jinjina kai jiki a sanyaye. Yausra ta ƙura wa jaririn ido tana kallonsa, tana ɗan murmushi ta mayar da hankali kan Shukura ta ce "Wai meyasa ki ka zo nan gurin ki ka zauna?" "Ba komai" "A'a da komai, kowa kin saka hankalinsa ya tashi sosai, ga ki da tsohon ciki, ki tashi mu tafi gida idan ya dawo kawai sai dai ya ganki. Abbanki har yana cewa zai ɗaure shi, shi ne ya saka ki ka ɓata, ai ba dan ya dawo da ni ki ka tafi ba ko?" Ta yi maganar jikinta a sanyaye tana kallon Shukura. Da mamaki Shukura ta ce "Daddyn ne ya ce zai ɗaure Sagir saboda ɓata na?" Yusra ta jinjina kai ta ce "Wallahi haka ya ce" Ta yi shiru tana zunzurutun ɓarna da zaluncin da ya gaya mata ya aikata. Ta numfasa ta ce "Amma ina fatan ba ki gaya wa kowa ina nan ba?" "Babu wanda na gayawa, ai kin ce kar na faɗa, ga abinci can ma na ɗaukko a mota, da 'yansanda zan gayawa amma na fasa" Shukura ta yi ajiyar zuciya ta ce "Yauwwa gara da ba ki faɗa ba" Yusra ta ce "To ki taso mu tafi" "A'a ai sai an sallame ni tukuna, kuma yakamata ki koma gida saboda ki sanar masa inda nake" "Babu inda zan koma, salon in tafi ki sake guduwa" Ta yi maganar tana ƙara lulluɓe jaririn Shukura da yake hannunta. ***** Cikin damuwa Alhaji Fatuhu yake kallon Hajiya Sa'a, yadda take zubar da yawu tana wani irin ihu, da gurnani duk ta yi najasa a jikinta. Ga ƙafafuwanta sun shanye, ba ta gane kowa sai wannan gurnanin da take yi. Likitoci sai dai su ta mata allurar bacci. Ranar da Fadila ta je duba ta, duk da ba ta magana amma tana ganinta tare da Muhsin ta din ga ihu tana tsine masa tana faɗin "Da tuni wannan shegen ɗan ne zai mutu ba Abbana ba, Allah ya isa ba zan yafe ba" Alhaji Fatuhu yana gurin, ya yi mamakin jin irin wannan maganganun da take yi, amma sai ya bar hakan a sakamakon taɓuwa da aka ce ƙwaƙwalwarta ta yi. Likitan da ya kammala rubutu a kan takarda, ya miƙa wa Alhaji Fatuhu. Alhaji Fatuhu ya karɓa tare da kallon Likitan ya ce "Doctor haryanzu ba a gano takamaiman abin da yake damunta ba?" "To, duk wani abu da yakamata mu duba mun duba, jininta lafiya kalau ba ta da hawan jini. Babu alamar strock a tare da ita. Sai dai idan sakamakon gwaje-gwajenta ya kammala bamu ga komai ba, zamu tura ku ɓangaren ƙwaƙwalwa dama mu nan mun riƙe ta ne domin mu gano maƙasudin shanyewar limbs ɗinta, to haryanzu ba a gano komai ba, zuwa ranar Litinin zamu fara tura ku physiotherapy ko Allah zai sanya a dace" Alhaji Fatuhu ya jinjina kai cike da karaya, tabbas da lokacin da yake da kuɗinsa ne, da kansa zai fitar da ita waje a duba ta. Ko a yanzu ba ya jin daɗin yadda da kuɗinta ake nema mata magani. Haka ya tafi gida jikina a sanyaye. Alhamdillah jikinsa ya yi kyau sosai, duk da haryanzu da sanda yake yawo bai gama warewa ba, amma yana iya fita shikaɗai. 'yarsa Rauda ya samu a gida yake ta yi wa faɗan rashin zuwa duba Hajiya Sa'a da ba son yi. "A ƙa'ida kamata ya yi a ce ke ce a gurinta Raudah, kina kallo lokacin da nake kwance kullum tana tafe" Rauda ta ce "Daddy ni wallahi tsoron ganinta nake yi, kuma duk lokacin da muka je da Maman Muhsin, sai ta yi ta ihu tana tsine masa tana da tuni shi ya mutu ba ɗanta ba, ta yi ta ihu tsoro take bani" "To Raudah ai larura ce, ni da Allah ya jarabbe ni, ba har wari na din ga yi lokacin da nake kan fama da larura ba. Jarrabwa ce Allah ya jarabce mu, kuma ku da ku ke kusa da mu, ku ne zaku ƙarfafa mana gwiwa. Ku din ga haƙuri". Ta jinjina masa kai kawai ta ce "To" **** Nana bayan sun idar da sallar asuba, ta ɓungire ta hau bacci, saboda yadda suka kwana jiya babu bacci. Ya zauna a gabanta ya zuba mata idanunsa, yana jin tamkar ya haɗiyeta ya din ga jinta a cikin jikinsa. Me zai yi wa wannan halitta domin nuna mata ɗumbin godiyarsa da farincikin kasancewa da ita. Ƙarshe ya ɓuge da sumbatarta yana shafa fuskarta, daga bisani ya tashi ya fita. Sashen Gimbiya Bilkisu ya wuce, ya tarar ba ta fito ba, ya wuce ɗakin da yake kyautata zaton Asal tana ciki. Aikuwa tana ciki ɗin fuskarta ta kumbura suntum ta yi jawur, idanunta sun yi wani irin kumburi mai ban tsoro. Jikinsa a sanyaye ya ƙarasa gabanta ya zauna ya zuba mata ido, ta kawar da kanta gefe ta yi shiru, ji take kamar ta shaƙe shi ya mutu ta huta. "Asal" Ya kira sunanta. Ta ɗago ta kalle shi a ƙule. "Ina roƙon ki da kar ki ɗauki damuwa da tashin hankalin lamarin nan ki saka a cikin ranki. Duk abin da ya faru a cikin rayuwarmu abu ne da Allah ya riga ya ƙaddara" "Hammad ba na son jin komai daga gare ka, ka tashi ka tafi ka bani guri. Macuci ma ci amana, ba ka ji daɗin halinka ba" Ya ce "Na ji na kuma yadda, duk abin da za ki kira ni da shi na karɓa, na san kina cikin fushi ne, amma ina mai roƙonki kar wani ya ziga ki ko ya tayar miki da hankali aurenmu ya samu matsala" "Ka riga ka haifar da matsala a cikin aurenmu da kanka, matsalar da ba ta da magani. Har ka yi aure ka haihu ko Hammad, ba ruwanka da matsala ta kanka kawai ka sani. Ka tashi ta fita ka bani guri. Kuma wallahi ina mai yi mka rantsuwa da Allah, sai na yi mata mummunar illar da ba zata moru ba, sannan in saka a hallakata sai ta san ta jangwalo rigima mafi girman da ba zata iya tare ta ba a rayuwarta. Wallahi Hammad kai nawa ne nikaɗai ni Asal ba zan yi tarayya da ƙasƙantaciyar mace a koma mene ne ba" Ya yi murmushi ya ce "Ni dai ina roƙonki ki kwantar da hankalinki, kar ki biye wa zuciyarki dan kaf cika da batsewar Agadez ke Niger gaba ɗaya babu mahalukin da zai raba ni da matata da ɗana. Dan gara na bar muku Agadez ɗin da mulkinku na bi farin ciki da kwanciyar hankalina. Ba zan taɓa wulaƙantaki ko na yarda a wulaƙantaki ba, saboda matata ce ke kuma 'yar uwata. Amma wallahil azim duk abin da ya samu Asma'u ba zan ɗaga wa kowane mahaluki ƙafa ba, a kanta komai kusancina da shi kuwa, dan Asma'u rayuwata ce, dole kuwa na bawa rayuwata dukkan wata kariya dan babu gangar jikin da take fatan rabuwa da ruhi" Wani irin kukan kura ta yi, ta din ga kai masa duka ko ta ina, tana gaya masa maganganu masu zafi, amma ko gezau kawai ya tsaya yana kallonta. Gimbiya Bilkisu ce ta shigo da gudu tana tambayar ko lafiya saboda jin ihun Asal da ta yi. Ta ƙaraso ta rirriƙe Asal ta ce "Imam me ka yi mata?" Ya ce "Babu abin da na yi mata" Asal cikin gunjin kuka ta ce "Ammi ya cuce ni, ya bar gida tsawon lokaci ya je ya yi aurensa a ɓoye ya haihu ban sani ba, sai dai na ji zance sama taka, kuma yarinyar da na kawo a matsayin kukunsa. Wataƙila ma shirya komai suka yi, an cuce ni am zalunce ni, wallahi Ammi ba zan zauna da wata ba. Ya aka yi na fara son shi na bari son Hammad ya yi mini illa. Ni yake gaya wa kaf Agadez babu mai raba shi da waccan ƙasƙantaciyar halittar wallahi sai na kashe ta" Gimbiya Bilkisu ta rungume Asal ta ce "Yi shiru ki daina magana, ki daina faɗar wannan maganar. Ki kwantar da hankalinki" "Ammi zuciyata ciwo take yi mini, ko ganinsa ba na son yi, ya tashi ya tafi ya bani guri" Gimbiya Bilkisu ta numfasa ta ce "Imam, ina ga kamar yadda ta buƙata ka tashi ka tafi kawai, ka bata lokaci ta samu nutsuwa. Domin magna ta domin Allah ba ka kyautawa Asal ba, dole ta shiga damuwa da tashin hankali" Hammad ya ce "Allah ya taimake ki, kar ki zaɓi Asal saboda 'ya take a gurinki, a zamana da ita har zuwa abin da ya faru ban zalunce ta ba. Cikin ƙaraji Asal ta ce "Ammi kin ji ko? Kina jin abin da yake faɗa" "Imam ka tashi ka je kawai" Ya miƙe tsam ya fice daga ɗakin, Asal kuma ta ci gaba da kuka. Fita ya yi, ya nufi wani sashi na gidan, ya yi umarnin a je a zo masa da Sarkin baka. Yana nan zaune hadimai biyu suka shigo, tare da Sarkin baka, ya tarar da Hammad fuskar nan a ɗaure tamau babu annuri. Sarki ya ce "Barka da wannan lokaci" Hammad ya amsa da yauwwa barka. Ya ɗora da cewa "Ammm duk da zan iya cewa baƙon Sultan ne kai, amma saboda ni aka kawo ka gurin nan, kuma ina tunanin ina da damar yin magana da yanke wa kaina hukunci" Sarkin baka ya ce "Wannan gaskiya ne" "Ina ganin tun da babu wani abu da ya yi saura, ka ce ba zaka iya yi mini magani ba, yakamata ka yi magana da Sultan a sallame ka ka tafi" "Saboda ba ka son na kula matarka ko?" Hammad ya yi shiru yana kallon Sarkin baka. Sarki ya yi murmushi ya ce "Ai duk taka tsantsan ɗinka ina da yaƙinin Nana ta fika, kuma ko da take yi mini kallon ba a kan daidai nake ba, ta san ni ba mutumin banza ba ne. Wannan gidan naku ba zan taɓa tafiya na bar Nana a cikinsa ba saboda balahirar da na gani a gidan" Ya kalli Sarkin baka ya ce "A matsayinka na wa?" "A matsayina na ɗan uwanta, ba ka san ina da alaƙa da ita ba? Duk da na san zaka kalli alaƙar ba wata ta kusa ba, amma a yadda ba ta da kowa a cikinku daga ahalinta ina ga zan wakilci ahalinta a nan. Ina da dangantaka ta kakannin kakannin da ita. Ka kwantar da hankalinka ni ba zan cutar da kowa ba, ko na shiga tsakaninku ba amma dole zata buƙace ni, idan kuma ka bari na tafi wallahi ba zan dawo ba bar abada kuma hakan ka iya zame muku matsala. Kuma ya zama dole ka bata duk wata dama ta ganawa da ni a duk lokacin da ta buƙaci hakan, ta nan ne za a iya samun warwarar abubuwan da suka baibaye ka. Ba na son a ji daga bakina ne, kuma ina son ta fahimci akwai abin da idan yana cikin ƙaddararka ba ya nufin ka saɓa wa Allah, amma Allah na iya amfani da kai ya kawo wa wani bawan nasa mafita" Hammad ya yi shiru yana jujjuya maganganun Sarkin baka, duk da ba komai ya gane ba. Amma ya numfasa ya ce a mayar da Sarkin baka masaukinsa. Ya tashi ya fita, ya ɗauki mota ya bar gidan. Ya yi tafiya mai nisa aƙalla ta awa guda sannan ya iso wani makeken katafaren gida. Bayan ya shiga da motar ya ajiye, sai gaishe shi hadiman suke yi yana amsa musu cikin girmamawa. Ya shiga cikin gidan ya bi wata hanya ya hau kan bene. Ya ƙwanƙwasa wata ƙofa, sannan ya saka kansa ya shiga da sallama. Yana zaune ya harɗe ƙafa ɗaya kan ɗaya, yana cin inibi tare da wasu ƙanan yara su uku, jikin bangon ɗakin kuma ƙatuwar TV ce take yi, ana shirin cartoon. Cikin nishaɗi yaran ke ta cin inibin su na zubarwa, ɗaya daga cikinsu kuma yana jikin mutumin yana tana jagwalgwala nasa inibin cikin nutsuwa. Sallamar da ya yi ne ya sanya su waiwayawa, Muhsin ya jefar da inibin hannunsa, ya nufi Mahafinsa da gudu. Hammad ya ɗaga shi yana murmushi ya ƙarasa shiga cikin falon sauran yaran maza su ma suka nufi Hammad. Ya rungume su yana murmushi ya kalli Imam Zahradeen ya ce "Kai ne ka ke wasan da su da sassafen nan?" Zahradeen ya yi murmushi ya ce "To ya na iya, su wannan biyun sun hana mamansu sakat da rigima, shi ma Muhsin sai kuka yake yi yau, yana kiran Umma, duk sun rikitata, shiyasa na kwaso su muka dawo nan" Hammad ya yi murmushi ya ce "Ina godiya sosai da sosai" Zahradeen ya tsuke fuska ya ce "Da aka yi me?" Hammad ya sake yin murmushi ya ce "Tuba nake baban Muhsin" Imam Zahradeen ya zauna sosai ya ce "Yaya ake ciki ne? Sultan bai kuma ce maka komai ba haryanzu?" Hammad ya girgiza kai ya ce "Ina dai jiran abin da zai ce, kawai dai yana yawan ce mini, sai abin da aka yanke na shawara" "Ka ga Imam, ka tsaya ka nutsu da kyau ka duba makomarka da makomar wannan jaririn yaron naka. Yaron nan na buƙatar mahaifiyarsa, kuma ina ganin ka dawo da mahaifiyar Mahmoudu gidan nan, su zauna kafin komai ya daidaita, na ga ya saba da ita sosai. Ka san ba abu ne mai sauƙi su bari ka fito da ita daga gidan nan ba. Saboda ina tsoron shawarwarin da Matawalle da kum Sardauna za su yanke a kan matsalar nan. Ba dan kar na yi musu ƙazafi ba, da na ce sun fi mutunta Al'adar Agadez sama da addininsu." Hammad ya ce "To ina nan dai ina sauraren su, na ji hukuncin da za su yanke ɗin" Imam Zahradeen ya ce "To, Allah ya sanya mu ji alkhairi" Imam ya amsa da Amin. **** Jikin Shukura ne yake tsuma, tana kallon Yusra a inda suke ɓoye, ga ta rungume da jariri da yake ta ƙoƙarin farkawa ya tsala ihu. Yusra na riƙe da jaririn tana yi wa Shukura alama da ta kwantar da hankalinta. Ɗaya bayan ɗaya mutanen suka fita daga cikin ɗakin, ɗayan ya kira wayar Alhaji Zailani. Yana ɗagawa ya ce "Yaya kun same ta?" "Alhaji mun caje Asibitin nan kaf bamu ganta ba, ga shi sun yi mana barazanar kira mana jami'an tsaro kar su kama mu" "An bani tabbacin ta na cikin Asibitin nan, a yadda binciken nan ya nuna, dole ku nemo ta ba sai na ganta ba ku kashe ta kawai, dan ba za ta tona mini Asiri ba" Jaririn hannun Yusra ne ya tsala uban ihu, hankalin mutanen ya dawo kan ɗakin, ɗaya daga cikin su ya juya da sauri ya nufi ɗakin. ***** Nana tana tsaye a gaban mudubi, ta saka riga ta alfarma, gaba ɗaya jin ta take kamar a cikin tarko, ta gaji da zaman guri ɗayan nan, hankalinta na kan a ƙarƙare abin da za a yi, a bata ɗanta ta koma Nigeria. Gefe guda kuma zuciyarta na ci gaba da wasi-wasi da son lallai sai ta ga mene ne a rufe a wannan ɗakin na gidan tarihin Agadez. Asal ce ta bankaɗo ƙofar ɗakin da ƙarfin gaske sai da Nana ta tsorata. Ta kalli Nana cikin doguwar riga mai maɗauri, ko 'yar uwatta mace zata sarawa kyawun dirin da Allah ya bata, balle ɗa namiji. Wani abu ɗacin gaske ya taso wa Asal, Gimbiya Bilkisu ce ta biyo bayan Asal. Nana dai ta tsaya ƙyam tana kallon su. AREWABOOKS Da sauri ya dawo, ya buɗe ɗakin jin kukan jariri, kawai ya tarar da Yusra a zaune a kan gado, tana jijjiga jariri. Cikin tsawa ya ce "Ke, me ki ke yi a nan wace ce ke?" Yusra ta ce "Kamar yaya? Nice a ɗakin nan, lafiya suwaye ku?" "Ya aka yi da muka shigo ɗakin nan bamu ganki ba?" Yusra ta ce "Ku na tsaye a bakin ƙofa na zo na wuce ku, na je na karɓo jaririna daga ɗakin jarirai ne, an sallamo shi daga can" Ɗayan ya ce "Ke ƙarya ki ke yi, mene ne sunanki?" Yusra ta ce "Ban gane mene ne sunana ba, suwaye ku tukuna me kuma ku ke nema a gurina ni ban sanku ba" Ɗayan ya dubi hoton cikin wayarsa, ya kalli Yusra ya ga sam babu haɗi. Ya tunkaro Yusra ya ce "Ki gaya mana mene ne sunanki?" "Yusra, sai kuma me?" "Na ke ce wata mata ta tsinto, ta kawo Asibitin nan ba?" "A ka tsinto kuma kamar wata kuɗi? Ni ban san zancen ba, mijina tare muka je na ɗaukko jaririna. Yanzun nan yayata kuma za ta dawo da take zaune tare da ni. Amma mene ne dalilinku na zuwa ku ritsa ni kuna tuhuma ta." Ta yi maganar cikin dakiya tana tsare mutumin da ido. Ƙasam zuciyarta fata take yi, Ubangiji Allah ya sa kar Shukura ta ce za ta fito ta tona musu asiri. Ɗayan ya ce "Ba fa ita ba ce ba, mu koma mu gaya masa ba ta Asibitin nan, ba a ba shi bayanin daidai ba" Suka ƙara ƙare wa Yusra kallo sannan suka fice. Abin da ya faru kuwa, Shukura babu yadda ba ta yi da Yusra ta tafi ba, amma ta ce babu inda za ta je ƙafarta ƙafarta, ba za ta tafi ta bar ta ba. Ga shi ta uzzura mata da tambayoyin yaya aka yi ta ɓata aka neme ta aka rasa. Alamu ya nuna mata haryanzu Yusra da saura kan babu daɗi dan haka ta ce mata sace ta aka yi, ta kuɓuta da ƙyar shi ne wata mata ta tsinto ta ta kawo ta Asibiti. Yusra ta ce "Lallai kin auna arziki tashi mu tafi to" Shukura ta ce "Ai ba a sallame ni ba, ba zai yiwu mu tafi ba, ba ni da cikakkiyar lafiya fa" "To ba sai mu koma Asibiti a can cikin gari ba, kin ga yadda mamanki ma hankalinta yake a tashe, idan muka je da Baban Haidar ta yi ta kuka" Wata Nurse ce ta yi sallama, suka gaisa da su Shukura, ta yi wa Shukura allurai. Wata ce ta sake shigowa da sauri, ta kalli Shukura ta ce "Ke ce Shukura ko?" Ta jinjina kai. "Wasu mutane ne suka zo, wai 'yar uwassu ce ke dubiya suka zo, amma yanayinsu kamar marasa gaskiya, mun ce babu mai wannan sunan, saboda mun san case ɗinki, amma ga shi can ana ta faɗa da su sun ce sai sun caje Asibitin nan, 'yar uwassu ce ke dole su ganki" Tsoro ne ya bayyana ƙarara a fuskar Shukura. Nurse ɗin ta ce "Ki kwantar da hankalinki, ai an kore su ma, kar ki damu" Bayan sun fita a rikice ta kalli Yusra ta ce "Ina ga wanda suka sace ni ne suka biyo ni nan, dan Allah ki tashi mu tafi " Yusra ta ce "Ai da tuni mun tafi ki ka dage, yanzu bamu san suwaye ba, idan muka fita ai sai a samu matsala. Dole mu jira zuwa anjima sannan mu saci jiki mu gudu." Da ƙyar Shukura ta amince sai dai da aka jima suna tsaka da shirin guduwa, suka ji muryar mutanen a waje, Shukura ta rikice, Yusra ta yi dabarar janta su ɓuya. ***** Bin su da kallo Nana take yi , Asal ta ƙaraso gaban Nana cikin huci da zafin rai, tana kallonta kamar ta kai mata duka. "Munafuka, muguwa, na jawo ki jikina ashe haɗa baki aka yi da ke a cuce ni? Kin auri mijina kin haihu da shi ban sani ba, kuma da yake ke munafuka ce, ba ki taɓa gaya mini saboda ba kya tsoron Allah. Wallahi idan ba ki rabu da shi ba, sai na kashe ki, na kashe ɗan naki dole ki koma inda ki ka fito a yau ba sai gobe ba, 'yar matsaiyata ƙasƙantacciyar halitta" Nana ta dubi Asal ta ce "Subhanallah, ai Allah kaɗai ya san ƙasƙantaciyar halitta ba ke abar halitta ba. Kuma ɗan ja da baya, numfashinki yana takura mini a fuskata, sai na baki amsar maganganun" Asal ta rikice ta kalli Gimbiya Bilkisu ta kalli Nana, ita kanta Gimbiya ganin Nana da ta yi ta ɗauka sokuwa ce ba ta magana. Nana ba ta jira me za su yanke ba ta matsa daga gaban Asal ta ce "Wannan abubuwan da ki ke faɗa, duk ba ni za ki gaya wa ba, Sayyid za ki gaya wa domin igiyar aurena a hannunsa take. Sai ki ji amsar da zai baki. Kuma ni Allah ya bani haƙuri da na zauna ina kallonki da mijina ban nuna miki komai ba, na biki a yadda ki ke so zuwa lokacin da ya dawo hayyacinsa ya gane ni. Dan haka yanzu da ki ka san komai, ni ba baiwarki ba ce, kuma ba kukun mijinki ba ce, matarsa ce wato kishiyarki" Asal cikin ƙaraji ta hankaɗa Nana ta ce "Wallahi na fi ƙarfin na yi kishi da ke 'yar matsiyata ƙazama, baƙa mummuna. Wallahi sai na kashe ki na kashe abin da ki ka haifa." Gimbiya Bilkisu na ƙoƙarin riƙe ta, amma sai fizge-fizge take yi tana ihu. "To Bismillah Asal, ki kashe ni idan har hakan zai sanya ki huce. Ba za ki taɓa canzawa tuwo suna ba, Hammad mijina ne, wanda na fiki ƙaunarsa" "Ke ya ishe ki malama, dan kin ga na yi shiru saboda ba ki da kunya da mutunci sai ki tsaya kina gaya mata maganganun banza? To bari ki ji na gaya miki, sai kin bar gidan nan a yau ba sai gobe ba. Sai kin bar gidan nan buzayen jinin sarauta ba sa raɓar talaka, balle su aure su su rayu da su. Sai kin bar gidan a wulaƙance cikin ƙasƙanci kuma sai an hukunta Hammad kan laifn da ya aikata" Nana ta ƙare wa Gimbiya Bilkisu kallo ta ce "Haba Mama, ke da ba da ke nake kishin ba? Nifa kamata ya yi a sara mini akan haƙurin da na yi. Kuma ko ba komai, dole sunan 'yar matsiyata ya shiga kundin tarihin Agadez, mace ta farko da ta karya tarihi bayan ɗaruruwan shekaru. Ku daina zagina dan ban yi muku komai ba, abin da na sani kawai na fi Asal son Hammad har Duniya ta naɗe, haka zalika ba ni da tsara a zuciyarsa ki yi haƙuri" "Ƙarya ki ke yi, yadda na yi amfani da kuɗi na mallake ki ta ƙarfin tsiya, haka zan yi amfani da su na yi maganinki mummunan a bar ƙyanƙyami" Nana ta ji zafin maganganun Asal, amma ta yi murmushi ta ce "Ke kin ga alamar muni a tare da ni, kalli da kyau Gimbiya Asal. Kodayake ba wannan ba ma; kar ki manta kina magana da matar da ki kai gidan da ki ke kwana kina shaye-shaye da kaɗe-kaɗe da ƙawaye a lokacin da ba ta san halin da mijinta yake ciki ba, kar kuma ki manta matar da ki ke bawa magani ta zuba a shayin Imam Hammad, haka zalika matar da ta san kina ajiye masa takarda mai hoton ƙwarangwal da yake ci da wuta, wanda shi ne yake burkita masa hankali da lafiyar jiki; wannan matar ita ce matar mijinki kuma baƙa mummunar da ki ke ta kushewa ki ke iƙirarin kashewa" Dummm ƙirjin Asal ya buga da ƙarfi, ta ƙwalalo ido tana kallon Nana. Nana ta ci gaba da cewa "Ni ba karabutin mutanen da ki ka saba wulaƙanwatawa ba ne, kasancewar Hammad mijina ya sanya na bar idanuna a buɗe ta kowace kusurwa a kansa, tunda na haihu da shi, har abada ba zan bari wani abu mummuna ya same shi ba" Asal ta tattaro jarumta ta yi murmushin ƙarfin hali, bayan da mararata ta cika taf da uban fitsarin tsoro. "Ƙarya ki ke yi, ba ki da abin da za ki kawo ƙarshena a masarautar Agadez, saboda ba ki za hujja a kan wannan soki burutsun da ki ke yi" Ta yi maganar tana tsare Nana da ido. Nana ta ce "Kwantar da hankalinki, ba na buƙatar wata hujja ko wani abu, dan har gaban Abada ba zan taɓa tona miki asiri ba. Ai Hammad yana sonki kuma ko ba komai 'yar uwassa ce ke, dan haka ki kwantar da hankalinki, amma daga yau da rana mai kamar irin ta yau, muddin ina tare da Hammad da ke da duk wani abu da yake kawowa rayuwarsa wani tarnaƙi" Gimbiya Bilkisu ba ta bari Asal ta sake magana ba, ta kama hannunta suka yi waje. Nana ta ja numfashi tana bin bayansu da kallo, kafin tsunduma tunani. Gimbiya Bilkisu ta kalli Asal ta ce "Ke, kina wani wawanci har ki ka bari ta san kina wannan abubuwan? Asal kina da hankali kuwa?" Cikin kuka ta ce "Ammi yaya zan yi, wallahi ban san da wata alaƙa a tsakaninsu ba, ban sani ba. Kuma ban san za ta kawo wani abu ba. Na shiga uku ba zan iya rayuwa babu Hammad ba wallahi Ammi ina son mijina, kuma ba zan iya buɗe ido na gan shi da wata ba ki taimake ni" "Nutsu ki kwantar da hankalinki, bari na yi wa babanki magana a san abin yi a yau ba sai gobe ba, dole a san yadda za a yi da yarinyar nan ki daina kuka" Da kyar ta din ga rarrashin Asal. Nana na zaune na zaman jiran dawowar Hammad,furucin Asal ya tsorata ta, ta fuskanci da gaske kowa na iya aikata duk abin da yake so, a wannan gidan domin cimma burinsa. Ita ba ta kanta take yi ba, ta ɗan jaririn ɗanta da ba ta san inda yake ba ta shi take yi. Ta ƙudurce a ranta, idan Hammad ya dawo, bori za ta yi masa sai ya fitar da ita daga gidansa komai zai faru, amma ƙasan zuciyarta yana ta azalzalarta a kan son a buɗe wannan dakin na gidan tarihin. Bayan azahar ya shigo, sai dai yanayinsa ya nuna mata a cikin damuwa yake. Ya nemi guri ya kwantar da kansa a kan cinyarta. Nana ta shafa kan a hankali ta ce "Lafiya kuwa?" Ya jinjina mata kai kawai. "Ka ci abinci ne?" "Na ci" ya amsa a hankali. "To meyafaru?" Ya ce "Babu komai" Nana ta numfasa ta ce "To dan Allah ina son ka dawo mini da Muhsin, kuma nifa na damu na koma gida, Sayyid hankalina a tashe yake wallahi, na san iyayena sun gaji da nema na" "Asmy kar ki ƙara mini damuwa dan Allah, ina sane da komai, a tsare nake yin komai in sha Allah zai wuce" Cikin damuwa ta ce "Zai wuce yaushe? Shekera ta uku nake shirin yi a ƙasar nan, nima ina da ahali bai kamata na tare a nan ba" Ya tashi zaune cikin damuwa, ya kalle ta zai yi magana, amma bai yi ba ya ciro wayarsa da take vibrating" Da to kawai ya amsa ya tashi ya fita. Nana ta koma ta nemi guri ta zauna cikin damuwa. Da sallama ya shiga ɗakin, ya tarar da Asal ga Sultan, ga Matawalle ga Tafawa da Sardauna sai Gimbiya Bilkisu da take ta ƙoƙarin rarrashin Asal. Gefe ga Imam Asadullahi ga kuma Imam Zahradeen rungume da Muhsin. Asal ji take kamar ta haɗiyi zuciya ta mutu ganin Muhsin, dan babu abin da ya banbanta shi da Hammad. Yayi mamakin yaushe aka yi masa wannan gangamin har haka? Bayan bai jima da barin gidan Imam Zahradeen ba ya tsaya a gurin Mahmoudu. Sardauna ya ce "Ka je ka zo da babar yaron nan" Babu kara ya karɓi ɗansa a hannun Yayansa Imam Zahradeen, ya tafi inda Nana take. Ya kai mintuna sha biyar, sannan suka dawo tare. Nana suka yi ido huɗu da Asal da idonta ya kumbura, Nana ta sakar mata murmushi ta kawar da kanta gefe. Guri ya tsit sai Muhsin da yake ta hawa jikin Nana yana yi mata surutunsa na yara. Zahradeen ya ce "Imam Muhsin, ka yi shiru" Sardauna ya yi murmushi ya ce "Har ya zama Imam shi ma?" Zahradeen ya ce "Eh mana Allah ya taimake ka. Ɗan Imam ai Imam ne" Suka yi murmushi. Tafawa ya ce "Yakamata mu yi abin da ya tara mu, ba tare da ɓata lokaci ba." Sardauna ya ce "Haka ne kam, Imam Hammad" Hammad ya ɗaga kai ya kalli Sardauna. "Duk da mun san aurenka da ita wannan 'yar Nigeria, ƙaddara ne daga Allah, Amma ina fatan ka sanar da ita matar taka, sharaɗin ƙasar Agadez na rashin auren bare?". Gaban Hammad ya faɗi, Nana kuma ta kalle shi suka yi ido huɗu. Sardauna ya dubi Nana ya ce "Ina fatan ya yi miki bayani?" Nana cikin girmamawa ta ce "Eh ranka ya daɗe. Ya yi mini na sani" Sororo ya bi Nana da kallo. Tafawa ya yi caraf da zancen, ganin ana neman a ɓata masa lokaci. "Amm dama na nemi a yi wannan zaman ne, domin na san mene ne makomar 'yata, sannan wane hukunci za a ɗauka a kan Hammad, bisa karya dokar Agadez" Hammad ya numfasa ya ce "Ai ni ba ni da wata matsala da Asal, ban sake ta ban kuma yi wani abu da... "Kai dalla rufe wa mutane baki, ai na san baka saketan ba, amma mene ne matsayinta? Zaka zauna da ita ne? Ka saki waccan yarinyar ko kuma mene ne?" Hammad ya tsuke fuska ya yi shiru. Matawalle ya ce "Amma mai girma Tafawa, bai kamata a je ga wannan maganar ba. Kana neman sanin matsayar Asal ne?" Tafawa ya ce "Ka bari mu yi magana da shi ka daina saka mini baki" Hammad ya ce "Makomar aurena da Asal, yana daga gare ta, idan tana son zama da ni, ba wani abu dama ni ban ce ba zan rayu da ita ba. Amma ina mai neman afuwarku ina shirye na ɗauki duk wani hukunci da za ku yi mini, amma sau ɗaya a rayuwata, nima ina neman ku yi mini alfarmar nan, ba zan iya sakin Nana ba, mussaman da rabo ya shiga tsakanina da ita. Ba zan iya sakinta ba". Sak suka yi su na bin Hammad da kallo. Sultan ya numfasa ya ce "Hammad, ba kai ka ke da ikon yanke wannan hukuncin ba, sai abin da muka yanke maka. Mai girma Tafawa muna mai baka haƙuri, Hammad ya tabattar da cewa aurensu yana nan daram, dan haka yakamata ta kwantar da hankalinta." "Babu batun kwanciyar hankali a nan, sai zuwa yaushe zamu san matsayarta, yarinyata tana wuni ta kwana babu bacci. Kuma da haka ku ke shashantar da duk wani laifi da zai aikata ba tare da an hukunta shi ba. A wannan karon dole a bar doka ta yi aiki a kansa, kuma a zartar da duk wani hukunci da yakamata a kansa. Ya saki matar nan a yanzu ya bata ɗanta ta tafi inda ta fito shi kuma a hukunta shi" Hammad ya girgiza kai ya ce "Zan karɓi kowane irin hukunci, amma ba zan rama sharri da alkhairi ba" Asal ta rushe da kuka tana rirriƙe Gimbiya Bilkisu. 95 1k ne via 0069685771 Aisha Adam stanbic 08081012143 Tafawa a fusace ya ce "Kun gani ko? Abin har ya kai raini ya shiga tsakaninmu ya faɗi duk abin da ya ga dama. Kamar yaya ba za ka rama sharri da alkhairi ba, waye ya yi maka sharrin waye ya yi maka alkhairin?. Ya yi wa dokokinmu karan tsaye. Kuma dolensa ya yi murabus a gaban majalissa, a ba wa wani tun da ga taka mana doka, ga kuma rashin zobensa sannan wannan ɗan da yake tutiya da shi, babu wanda yake da yaƙinin na halal ne tun da babu waliyyinsa ko ɗaya a lokacin da aka ɗaura auren." "Zan jura komai amma ni ba mutumin banza ba ne ba, kuma kar ka sheganta mini ɗa, ban san da wace kalmar za a yi mana bayanin halin da na shiga har na auri Nana ka yarda ba. Tsawon shekaru ina yi muku biyayya, ko ina so ko ba na so, dokar Agadez ba dokar Allah ba ce ku bari na samu nutsuwar zuciya mana, idan ba so ku ke ku wayi gari ku ga na bar muku duniyar ba. Ta yaya zan yi wa Allah butulci akan abin da nake nema? Yarinyar da ta rayu da ni a lokaci mafi tsananin da babu wanda zai iya zama da ni ina hauka, na haɗu da larurar da hatta najasata ita take gyara mini da hannunta ba tare da ƙyama ta ba. Babu biyayya ga abokin halitta gurin saɓawa mahalicci, Asal na da zaɓin zama da ni ko ta ƙi na bata wannan damar, amma ba zan saki Nana ba ko zaku rataye ni" Sultan ya miƙe tsaye a fusace ya ce "Hammad!" Imam Zahradeen ya miƙe tsaye shi ma, ya dubi Sultan ya ce "Ya kai Abbanmu abin alfaharinmu, a duniya ba na tunanin ka taɓa son wani abu kamar yadda ka ke son Imam Hammad, kuma bana tunanin akwai wani wanda yake yi maka biyayyar da yake yi maka. Tun da ta kai shi ga yin sa in sa da ku, to tabbas ya kai bango. Amma ko sau ɗaya yakamata a ce mai girma Tafawa ya yi maka kara a kan Imam Hammad, amma duk lokacin da wani abu ya faru tsakaninsa da Asal,  ƙarara yake goyon bayanta a turasasawa Hammad yin abu dan faranta mata, sau ɗaya ko dan saboda shi yakamata a yi wa dokar Agadez kwaskwarima. Gimbiya Bilkisu ta ce "Zahradeen kana da hankali kuwa? Waye ya sanya da kai?" "Ummi ki yi haƙuri, kina duba mafitar ɗan uwanki da 'yarsa, nima ta nawa ɗan uwan nake dubawa." "Ni ka ke gaya wa haka Zahradeen?" "Ina neman afuwarki, amma dan Allah kar ki yi mini mummunar fahimta Ummi." A fusace Sardauna ya ce "Ya isa haka, ya isa, kun manta a gaban wa ku ke ne? Ya za a yi kowa ya din ga magana yadda ya ga dama, babu ɗaa da girmamawa?" Kowa ya yi shiru. Nana cikin ladabi ta ce "Ina mai neman afuwarku, na san wannan hatsaniyar ta faru ne duk a dalilina. Amma da na san wannan al'amari zai faru, ko haka dokar ƙasar nan take, ba zan yi gangancin auren Sayyid ba. 'yan uwansa ba su yi mini wannan bayanin ba. Haka zalika ban faɗi haka dan a ga laifinsu ba, kamar yadda suka gaya mini shi ya nemi a biya sadakina ya aure ni. Amma kamar yadda wannan shugaban ya faɗa" Ta yi maganar tana kallon Tafawa. "Na amince zan ɗauki ɗana na koma Nigeria, idan ma kun ce ba ku da alaƙa da shi, na yarda zan zame masa uwa na zame masa uba.." "Babu inda za ki je mini da ɗa, kuma kema babu inda za ki je" Ya katse Nana yana maganar cikin ɗaga murya. Cikin kuka Nana ta ce "Sayyid babu abin da ya fi ahali daɗi da muhimmanci, sai da na baro nawa na fito nemanka na gane hakan, ni na baro nawa ahalin kai ga ka cikin gata, sun baibaye ka da soyayya da ƙauna. Dama gudun rasa ahalin ga Muhsin ne ya sanya na fito nemanka da tsohon cikinsa." Ta saka hannu a hijjabinta ta ciro zoben da ya bata ta ce "Wannan zoben ina kyautata zaton shi ne zoben da ake ta magana a kansa, tun mu na Nigeria Sayyid ya bani shi kyauta, domin jaddada soyayyarsa a gare ni. Muhsin kai wa Abbanka zobensa, kuma ina fatan ba za a ƙwace kujerarsa ta shugabanci ba, sanyin halinsa zai zamo ƙwarin gwiwa ga talakawan da ba su da ƙarfi. Na gode matuƙa da kulawa amma kar ku raba ni da ɗana dan Allah" Kuka Nana take yi sosai da sosai. Imam Zahradeen ya dubi Nana ya ce "Ɗauki yaronki ki koma, za a neme ki" Nana ta durƙusa ta ɗauki Hammad da ya riƙe zoben da Nana ta ba shi yana zura wa a baki. Ta karɓi zoben za ta ajiyewa Hammad shi, amma ya haɗa ya karɓe Muhsin. Asal kamar ta haɗiyi zuciya ta mutu haka take jin yadda a gaban mutane ya nuna wa duniya ita zai iya rabuwa da ita, Nana ce ba zai rabu da ita ba. Tafawa bai yi shiru ba ya ci gaba da zazzaga bala'i kamar zai ari baki. Har sai da ran Sultan ya ɓaci. Ya yi wa Hammad umarnin ya tashi ya tafi kawai. Yana rumgume da Hammad ya ji muryar Asal a bayansa. Ya tsaya ya waiwaya yana kallonta, tamkar mahaukaciya sabon kamu ta ce "Hammad yau nika tozarta a gaban jama'a ka zaɓi bare baƙuwar haure a kaina, ka ƙasƙanta ni a gaban mutane, Hammad ni?" Ya girgiza kai ya ce "Asal ban ƙasƙanta ki ba, kuma har abada ba zan yi ba. Kamar yadda Nana ta faɗa daga ni har ke mu na cikin ahalinmu, muna da cikakkiyar ahali ita kuma fa? Sannan kuma harshenka alƙalinka Asal. Da raina da lafiyata da ƙuruciyata ki ka kalli tsabar idona ki ka din ga jifa na da kalaman ba kya sona ba kya ƙaunata. Duk da na yi miki uzurin ƙuruciya da yarinta a wancan lokacin, amma haryanzu ina ganin wani abu a cikin idaunki da ban tantance so ne ko ƙiyayya ba. Nana ta so ni a bata san waye ni ba, ta so ni a mutum mara asali da makoma auren shahada da kasada, ta rayu da ni da na ɓacewa duniyarta ta ci gaba da bulayin nema na, ba dan tana sanya ran na saka mata ba. Ki duba ratar za ke tsakanin misalan da na baki" Ya wuce rungume da yaronsa ya tafi. A ƙarshe dai Imam Zahradeen ne ya mayar da Sultan turakarsa sai jiri yake yi saboda ɓacin rai. Ya ɗebo ruwa ya ba shi ya karɓa ya sha yana mayar da numfashi. Sultan ya ce "Zahradeen" Ya amsa da "Na'am Abbie". "Na rasa ta ina zan ɓullowa lamarin nan gaba ɗaya" Zahradeen ya numfasa ya ce "Allah ya taimake ka, da Tafawa ne a matsayin da ka ke, komai za a yi ba zai taɓa ƙin goya wa ɗansa baya ba, dan ya faranta muku ba. Ka rintse idanunka ko toshe kunnenka. Ka kamanta yarinyar nan a matsayin 'yar cikin ka. Ana maganar shekara biyu zuwa ta uku rabonta da gidansu. Ka ga dai yadda yake zare idon nan, bai ƙi ya aikata duk wani abin kunya da zai zubar da mutuncin Agadez ba. Abie shin ba ka tunanin wata aya ce Ubangiji Allah ya saukar mana, domin ya nuna mana fari da baƙi halittarsa ce kuma duk yana kishi da son abin sa? Ka lissafa Allah ya hana shi haihuwa duk da ya yi aure da ƙanan shekaru, aka hana shi ƙara aure. Lokaci ɗaya Allah ya jarabce shi da ciwon da sai da ya keta ya bar Niger ya tafi Nigeria rabon wannan ɗan ya kai shi har can. Kuma duk da haka Allah ya jarabce shi da ciwon da sai tana kusa da shi yake samun afuwa. Yanzu idan muka rintse idanu daga hukuncin da Allah ya zartar dan mutunta al'ada muka tozarta baiwarsa kana tunanin Allah zai barmu? Ka duba ɗan jaririn yaron nan da yake kai komo a tsakanin su cikin farin ciki idan aka raba su, duk gatan da za a nuna masa bai kai ya tashi a tsakanin iyayensa ba. Abie Mai girma Tafawa ɗan uwanka ne, kuma ɗan uwan mahaifiyata ne, amma ina mai tabbatar maka ba zai taɓa ƙaunarka ba, har gara ni yana yi mini kara saboda ɗan 'yar uwassa ne, amma ba zai taɓa son Hammad ba. Kai kuma Hammad ɗanka ne komai za a yi ka banƙara shi ma ya samu abin da yake so" Sultan ya yi shiru cikin nazari, ya numfasa ya kalli Imam Zahradeen ya ce "To yanzu kai me ka ke tunani, kuma meyasa ba ka yi mini duk wannan bayanin tuntuni ba?" Zahradeen ya ƙara nutsuwa ya ce "Ina tsoron shiga lamarin ne a baya, amma Hammad da kansa ya same ni da maganar, kuma ya nuna mini yarda ta hanyar ajiye ɗansa a gidana. Yanzu ka bar wani batun Tafawa da wata majalissa kai ne Sultan, idan ka yi doka dole a bi ta. Ka bar Imam Hammad da matarsa, kuma ka soke wannan al'adar da aka ba wa wannan ƙarfin, ka yi musu fatan alkhairi" Sultan ya girgiza kai cikin jimami ya ce "Ba abu ne da zai yiwu cikin sauƙi ba" "Ka duba dai Abie, ka duba makomarsu baki ɗaya" "Shikenan, ka je zan yi tunanin abin yi" Imam Zahradeen ya ce "To shikenan Abie, amma dan Allah kar ka jira sai ka yi shawara da wani a cikin 'yan majalisarka" Sultan ya ce "To shikenan" Imam Zahradeen ya miƙe tsaye, ya ce "Bari na ƙarasa gurinsu, zan karɓi Muhsin na tafi da shi" Sultan ya jinjina kai kawai. Hammad ya shiga ɗakin da Nana take, cike da takaicin yadda ta ce, ita ta haƙura da shi, a bata ɗanta ta koma Nigeria, sai dai ya tarar da ita tana kuka. Ya kwantar da Muhsin da ya yi bacci, ya ƙarasa gabanta ya ce "Meyafaru kuma ki ke kuka?" Ta yi shiru ta ci gaba da kukan. "Mene ne?" Ya sake tambayarta. "Sayyid" Ta kira sunan shi a raunane. Ya zauna a kusa da ita ya ce "Mene ne?" Ya yi maganar yana ɗago ta cikin damuwa. Ta ƙanƙame shi tana kuka ta ce "Sayyid na faɗi haka ne dan su daina yi maka faɗa, amma ina sonka wallahi Sayyid, dan Allah kar su raba ni da kai" Ta yi maganar tana sheshsheƙar kuka. Shi ma rungumota ya yi sosai da sosai a jikinsa, yana wata irin ajiyar zuciya. Da kyar ya tattara nutsuwarsa, ya ce "Ki yi haƙuri Ma vie, Ubangijin da ya haɗa mu ne kaɗai zai raba mu. Ni da ke mutu ka raba in sha Allah" Zata yi magana suka ji ana bubbuga ƙofar ɗakin, Nana ta motsa za ta tashi, amma ya riƙe ta kuma ya yi umarnin a shigo. Imam Zahradeen ne ya buɗe ƙofar ɗakin ya shigo, kunya duk ta kama Nana. Ya ɗan tsaya yana kallonsu ya ce "Kuka ku ke ne?" Nana ta yi saurin tashi tana share hawayenta ta ce "A'a". Imam Zahradeen ya ce "Ga idonki nan duk hawaye. Wai  me ki ke gaya masa ne, ya sanya duk ya rikice haka a kanki" Nana ta sunkuyar da kai tana murmushi. Imam Hammad ya ce "Komai ma gaya mini take yi, shiyasa nake jin tamkar raba ni da ita, raba ni da rayuwata ne" Zahradeen ya jinjina kai ya ce "Na ga alama ai. Amma dan Allah ku kwantar da hankalinku, ku ci gaba da addu'a, in Allah ya yarda a dalilinki za a sauya tsarin wasu dokokin na Agadez. Yanzu dai Muhsin zan ɗauka zamu tafi" Cikin marairaicewa Nana ta ce "Dan Allah ka bar mini shi a nan" Ta yi maganar tana kallon Imam Zahradeen. Ya girgiza kai ya ce "A'a barinsa a nan babu tsaro, tsawon lokacin nan yana tare da ni a can gidana, gobe in Allah ya kaimu za a kawo masa maman Mahmoudu. Idan kuma ba a yarda da ni ba, na bar ku abinku" Nana ta ce "A'a amma dan Allah ka tafi da ni, ina son na zauna tare da shi, kuma na ga Nene." "Wani irin mugun kallo Hammad ya yi mata" Zahradeen ya ce "Ai ko ba ki ce komai ba, dole za ki bar gidan nan, taso mu tafi" Hammad ya ce "Ya haka? Ku tafi ku je ina? Kuma yaya zaka tafi da ita Sultan bai sani ba?" Imam Zahradeen ya ce "Idan zaka biyo mu ne taso" Nana kuwa ta yinƙura ta tashi ta ɗauki jakar kayanta dama da hijjabi a jikinta. Hammad ya miƙe ya ce "Wai bin nasa za ki yi?" "Ni ba na son zama a nan, na gaji" Nana ta furta tana tura baki. Imam Zahradeen ya ɗauki Muhsin, ya kalli Imam Hammad ya ce "Ɗaukko mata jakarta" Zahradeen yana fita, Hammad ya riƙe ta ya ce "Dan me zaki ce za ki bi shi? Meye haka ki ke yi ne?" "Amma Sayyid na ga yayanka ne fa" "Ko ma wane ne, dan me za ki bi shi?" Ta girgiza kai idanunta na cika da hawaye "Ni na gaji da zaman gurin nan? Ni gaba ɗaya ma tsoro nake ji" Sayyid ya ce "Muje kar ki yi mini kuka" Ya saka Nana a gaba, suka bi ta baya, sai ga su a harabar gidan. Zahradeen har ya kwantar da Muhsin a cikin motar. Hammad ya buɗe wa Nana bayan motar, sai hararta yake yi, amma ta basar ta shige cikin motar ta kawar da kai. Haka nan take jin kamar ta fito daga kurku sai wani irin farinciki take ji da nishaɗi, a haka ya bar gidan da Nana a cikin motar. Tafawa kuwa ya ɗauki zafi, ya ci gaba da ziga 'yan majalisar Sultan a kan lallai su sanya ido a hukunta Hamma, sannan ya yi baƙin cikin fito da zoben nan da aka yi. Matar Imam Zahradeen ita ma haka take kyakykyawar gaske, fara sol da ita, yaransu huɗu, kyawawa su ma. Sai dai Nana ta ga matar ba ta ƙyamace ta ba, ta rungume Nana tana faɗin yau ga Umman Muhsin, baƙar Gimbiya ta farko a kaf faɗin Agadez. Nana dai ta kasa sakin jiki da matar, dan duk mutanen Agadez ɗin tsoro suke bata, kusan kowa ba abin yarda ba ne. Ganin Nana ba ta sake da ita ba, ya sanya ta bar ta a ɗakin da aka sauke ta. Washegari da sassafe Hammad ya tafi gidan Imam Zahradeen. Zahradeen ya ce ba zai gansu ba sai bayan Azahar, tun da shi ba shi da kara. Nana tare da Muhsin suka kwana, kasa baccin kirki ta yi ta rungume shi, cikin farin ciki tana shafa shi. Aka kawo mata lafiyayyen Abinci, matar Imam Zahradeen ta kawo mata kaya masu kyau, ta ce ta saka. Hammad ya din ga yi wa Imam Zahradeen magiya. Zahradeen ya ce "Ka ga ba fa magana ake ta kai shugabana ne ba, yanzu muna magana ne a matsayin ya da ƙani, dan haka dole ka jira. Sai da aka yi azahar ɗin, suka yi salla, sai ga Mahmoudu tare da Nene. Hammad suka gaisa da Nene cikin girmamawa. Sai dai shigowar su Nene babu daɗewa, sai ga Sule shi ma ya zo, tare da wani matashin saurayi. Mamaki ya kama Mahmoudu, ganin Sule ya zo gidan, sai dai ya yi ta yi wa matashin kallon sani. Imam Zahradeen ya kalli Hammad ya ce "Ka san wannan?" Ya yi maganar yana nuna masa matashin. Ya yi shiru yana tsare shi da ido, ya ce "Na san shi, amma na manta a ina, na san dai na taɓa ganinsa" Imam Zahradeen ya kira wayar matarsa, ya ce ta zo da Nana. Wani irin kyau Nana ta yi, ɗinki ne na buzaye a jikinta, sai ƙamshin turare take yi ta shigo da sallama. Kasa riƙe farincikinta ta yi, ta nufi Nene da sauri. Sai dai ta yi wani irin wawan burki, bayan yin ido huɗu da matashin saurayin, da girma da kamala suka bayyana a tattare da shi bakinta na rawa ta ce "Imrana!!!" Wata irin sufa Nana ta yi, ta nufi Imrana a gigice, ta rirriƙe rigarsa tana zaro ido, tana son tabattarwa da gaske shi take gani, ko kuma gizo yake yi mata. Cikin rikicewa ta ce "Imrana, Imrana kai ne? Imrana dan Allah mafarki nake yi ko kuma kai ne?" Ya yi murmushi ya rungume ta idanunsa na cika da hawaye ya ce "Ni ne Nana, Imrananki ne" "Imrana ka tafi ba ka sake nema na ba, ka tafi ka bar ni nikaɗai, Imrana" Toshe mata baki ya yi, a hankali jikinta ya saki ya kuma yi sanyi ƙalau. Ƙaisar ta hango a bakin teku, yana kallon ruwan, ta ƙarasa inda yake da sauri, ta ce "Ƙaisar kai ne? Ya jikin naka? Ka warke?" Ta yi maganar tana riƙo hannunsa, sai dai maimakon ta ji ta kama tsoka sai ta ji tamkar ta taɓa ƙanƙara wani irin sanyi ƙalau. Ya dube ta ya ce "Ina taya ki murna" Ta ce "Murnar me?" Ya miƙe tsaye ya ce "Murnar komai ma, alamu sun nuna Ubangiji yana sonki, tsananin da ki ka din ga shiga, ya zame wa wasu silar alkhairi, kuma sannu a hankali Allah yana warware miki komai" Ta ɗan yi shiru ta ce "Ban fahimci me ka ke nufi ba" Ƙaisar ya ce "Ba sai kin fahimta ba. Ina taya ki murnar ganin ɗan uwanki, sai dai haryanzu da ɗan sauran rina a kaba. Shi wannan mijin naki, zuciyarsa da karsashinsa a kanki kawai yake. Amma bai damu da tsayuwa tsayin daka a kan abubuwa ba, ya kan karɓi abu duk yadda ya zo masa, ya tafi a haka komai zafi da raɗaɗin cutarwar da abin yake yi masa. Kar ki kuskura Sarkin baka ya tafi, baku bankaɗo abin da yake faruwa da shi ba, sannan Giyaz haryanzu yana tare da shi, sai dai a galabaice yake yana jinya. Kin san bamu fiye saɓa alƙawari ba, dan haka abu ne mawuyaci ya rabu da mijinki ta daɗin rai, saboda yarjejeniyar da suka yi da bokan nan. Kamar yadda na sanki, ki ci gaba da addu'a, zan iya cewa kusan komai ya zo ƙarshe, sai dai ban san abin da ka iya faruwa a gaba ba." "Ma vie" Ya yi maganar yana shafa fuskarta, a hankali ta buɗe ido ta kalli Sayyid, ta sake ɗaga kanta, ta ganta a jikin Imran. Kuka take sosai da sosai, da ita kanta ta kasa tantance ko na mene ne. Imrana da yake share hawayen ya ce "Ki yi haƙuri ki daina kukan nan haka" "Kukan ne yake zuwa" Ta yi maganar wasu hawayen na ci gaba da zubowa. Ya kalli Muhsin da yake ta guje-guje a ɗakin, ya kalli Imam Zahradeen ya ce "Wannan ne ɗan nata?" Ya yi murmushi ya jinjina masa kai. Nana ta sake cewa "Imrana ya aka yi ka san ina nan?" Ya yi murmushi ya ce "Bacci na kwanta, kawai na farka na ganni a nan" Kukan da take yi bai hana ta yin murmushi ba. Ta ce "Nene kin ga yayana, duk duniya shi ne kaɗai wanda muke ciki ɗaya da shi" Nene ta ce "Allah sarki, ga kammanni nan ku na yi da shi" Imam Zahradeen ya ce "Yakamata a fara ba wa baƙi" Nana ta ja jikinta ta zauna, ta ƙure Imrana da ido, gaba ɗaya ya nutsu, babu wannan hauma-haumar tasa. Shi kansa Imam Hammad kallon Imam Zahradeen yake cike da mamaki yana jiran jin bayani daga bakinsa. ***** Jamila ce a durƙushe tana wani irin kakari, ji take yi tamkar barin duniyar za ta yi saboda matsananciyar azabar da take ji. Ta ɗaga kai da kyar ta kalli Mama, a galabaice ta ce "Mama, me ki ka bani a cikin kukun nan na sha, Mama zan mutu zan rasa raina" Mama ya ce "Ai gara ki mutun na huta Jamila, gara ki tafi asirina ya rufu da wannan masifar da ki ka ɗaukko mini. Ba dai ke taurin kan tsiya ba, ai na san yadda zan yi da ke nima. Ƙwayar zubar da ciki na je na sayo a gurin Mariya Likita na zuba miki, dan ba za ki haife mini shege a gida ba". Jamila ta girgiza kai cikin matsananciyar azaba ta ce "Mama ba ki kyauta mini ba, zan iya rasa rayuwata Mama, kin san azabar da nake ji kuwa?" "Tun da ki ka iya jure miƙawa maza jikinki, dole ki jure azabar fitar cikin" "Wayyo Allahna" Ta faɗa a marairaice tana sake durƙushewa cikin azababben ciwo. ***** Fadila ce ta fito daga banɗain da ta shafe a ƙalla awa ɗaya da rabi a ciki, tana tufaka da warwara, sosai an matsa musu a kan su tashi su bar gidan. Har ta gaji da zuwan da wanda ya sai gidan yake yi yana ɗaga musu hankali kamar ba abokinsa ne ba. Ga shi haryanzu bai gama samun cikakkiyar lafiya ba, lallaɓawa kawai yake yi, shi kansa ya rasa inda zai sanya kansa saboda damuwa, ƙarfin hali kawai yake yi. Tana fitowa ta tarar da shi a tsaye da waya a hannunsa. Cikin damuwa ta ce "Lafiya kuwa?" A sanyaye ya ce "Coustom ne suke nema na a Lagos" Ta ɗan yi saroro ta ce "Suke neman ka kuma, lafiya dai?" Alhaji Fatuhu ya ce "Wallahi ban san mene ne ba, ga shi ko kuɗin motar tafiya ba ni da su. Allah ya sa ba wani abin ne mara daɗi ya sake tasowa ba" Fadila ta ce "Jikina ba ya bani wani mugun abin ne, Ubangiji Allah ya sanya alkhairi ne ya sanya suke neman ka. Bari na kira Umma idan da kuɗi a hannunta ta ara mini" Ya ce "A'a, kin san ba shi ne da ita ba, ba dan halin da Alhaji Zailani yake ciki na ɓatan 'yarsa ba, ai da shi zan cewa ya biya mana, ya raka ni muje mu ji ko mene ne" Ta ɗan tsuke fuska ta ce "Dan Allah Daddy ka daina gayyato mutanen nan haka, mu din ga shiru tukuna idan alkhairi ne idan Allah ya tabattar sai kowa ma ya ji. Da za a samu kuɗin sai Umman su Raudha ta raka ka. Amma hakan nan za ka yi haƙuri mu nemo kuɗi ko ta mota ne ku tafi tare. Ya hayyu ya ƙayyum Ubangiji Allah ka sanya alkhairi ne. Ya amsa da "Amin." **** Gaba ɗaya Shukura ta yi saranda da da ba zata tsira ba, daga ita har jaririnta, Yusra ta ce mata duk za ta yi ta nemi guri ta ɓuya, ba za ta iya fitar da ita da jaririn lokaci ɗaya ba, ta fuskanci mutanen nan, su na harabar inda Asibitin yake. Shukura na kuka ta ce "Yanzu tafiya za ki yi ki bar ni?" Yusra ta ce "To yaya za mu yi, idan ba haka ba daga ke har jaririn za ku iya rasa ranku, ki bari na fita da jaririn, ki san duk yadda za ki yi ki ɓuya ko ki gudu. Amma Shukura suwaye wannan suke binki haka? Kuma me ki ka yi musu?" Shukura na kuka ta ce "Dogon zance ne, ke dai tafi da shi, idan ban rayu ba ma dan Allah ki kula mini da shi" Yausra ta bata mukullin motar da ta zo da ita ta ce "Idan kin samu dama, ki gudu ni zan san yadda zan yi" ta goya jaririn Shukura na kuka, Yusra ta fice daga ɗakin. **** Imran ya ci gaba da kallon Nana cikin zallar farin ciki da shauƙi, tare da kallon Muhsin dukkaninsu cikin shiga ta alfarma da kamala. Ya ce "Nana, ashe zan gan ki cikin farin ciki da kwanciyar hankali haka a rayuwata? Allah na gode maka da ban tursasa ki na kashe miki aure ba, ashe alkhairinki yana tattare da auren. Kasancewar daga Nana sai shi a ɗakin, ta ɗan jinjina kai ta ce "Amma an sha gwagwarmaya Imrana, duk da na gode wa Allah da ka bayyana yanzu, ka zo a gaɓar da na fi tsananin buƙatar ka, amma meyasa ka yi fushi da ni baka sake dawowa ba, dama akwai abin da zan yi maka ka yi irin wannan fushin da ni?" Ya girgiza kai ya ce "Babu shi, abin da za ki yi mini da zai sanya na guje ki. Amma ki yi haƙuri kaɗan za ki ji abin da ya faru. Na yi burin na samu wadata ki huta na gatanta ki Nana, amma Allah ya ƙaddara ke ce zan huta a dalilinki." "Ban gane ba, me ka ke nufi?" Imrana ya ce "Za ki gane ne" "Imrana ina Baba da su Jamila, na san ba zuwa gurin su Mama ka ke yi ba, da gurin su Ummi, ban san da wani idon zan tunkari gida ba, na tafka babban kuskure da bana tunanin za su iya yafe mini" "To kar Allah ya sa su yafe ɗin mana, ke dai ba kin riga kin yi gaba ba, su zauna da rashin yafiyar" Nana ta buɗe baki ta ce "Lallai hali zanen dutse, Imrana kar Allah ya sa su yafe, su Baban?" "Eh ɗin, ai ke yakamata a ce ma sun nemi yafiyarki, idan sun yafe shikenan, idan ma ba su yafe ba za ki ci gaba da rayuwa wataƙila ma babu wanda ya neme ki a cikin su" Hammad ya dubi Imam Zahradeen bakinsa fal tarin tambayoyi, amma yanayin fuskar Zahradeen ɗin babu alamar zai amsa masa tambayoyin nasa" Imam Zahradeen ya ce "Ya na ga ka ƙure ni da ido ne?" Hammad ya ce "Abubuwan da na gani suka ɗaure mini kai nake son ka yi mini bayani" Ya numfasa ya ce "Bayani ya zama dole Hammad, amma ina fatan zaka yi mini afuwa da duk abin da za ka ji a bayanin nawa" Imam Hammad ya ce "In sha Allah" Kamar yadda suka taru a falo ɗazu, haka suka sake taruwa bayan sallar la'asar. Imam Zahradeen ya ce "Ina yi wa kowa barka da zuwa wannan gida nawa. Wasu sun san da zuwan wasu, wasu ba su zan da zuwan wasu ba. Cikinmu akwai yan gidanmu na sarauta, akwai wanda ba su da alaƙa da gidan namu, amma a yanzu tilas mun zama abu guda, kuma zan warware wani abu da na san wasu za su gan shi wani iri, amma yi haƙuri da yadda komai zai zo, duk wanda yake gurin nan abin ya shafe shi ne. Imam Hammad, wannan bawan Allah da ku ke gani Sulei yarona ne, zamanku a tare da shi, da duk wani abu da ku ke ciki, wani abu ne na shiri da na yi shi" Gaba ɗaya suka ɗaga kai suna kallon Sule tare da Imam Zahradeen. Bai damu da kallon da suke yi masa ba, ya ci gaba da cewa; wannan matashin saurayin da yake ɗan uwa ga matarka Hammad wato Imran, bayan da ya je ya same ku, ya yi yinƙurin tafiya da ƙanwarsa, hankalinka ya tashi sosai, ka kira Mahmoudu ka gaya masa, shi kuma sun yi maganar da Sulei, shi kuma Sulei ya gaya mini. Gudun kar ya kawo tangarɗa a rayuwar aurenku, ya sanya na saka aka bi diddigi aka nemo shi. Aka kawo mini shi har Agadez, na yi masa bayanin komai, da ko kai waye, da alfarmar da nake nema ya yi mini na yin shiru da bakinsa ya yi haƙuri ya bari ku rayu da ƙanwarsa, kai mutum ne mai asali da daraja, ƙaddara ce ta faɗa maka. Sai dai ya fututtuke yana ganin kamar rainin hankali ne kawai, idan kana da asali da daraja dan me zan barka a wulaƙance kana gadi. Da kyar ya fahimci abin da nake son ya fahimta, sai dai duk da haka gudun ya ƙara burkicewa saboda na ga rigimamme ne, na aika shi waje karatu. Sunansa yana cikin jerin waɗanda ka ke bawa tallafin karatu a Agadez, a cikinsu na saka shi aka kuma fitar da kuɗin dan kai ka biya masa ba ni ba. Fuskar Hammad ta yi wani irin ja, cikin kakkausar murya ya ce "Zahradeen" "Hammad" Ya miƙe tsaye ya ce "Labarin nan bai cika ba me ka ke ɓoyewa?" Imam Zahradeen ya yi murmushi ya ce "Wannan rigimar cikin gida ce, ka bar maganar a haka" "Ba zan bari ba, sai ka yi mini cikakken bayani" Mahmoudu shi kansa ɗaurewa ya yi, kenan duk wannan abin Sulei, kallon biri yake yi masa yake yi musu na ayaba, ya san komai, ya san waye Imam Hammad, amma ya zauna da su har da yi masa masifar kullum yana ɗawainiya da mutumin da bai san asalinsa ba?" Gaba ɗaya jikin Hammad ya hau tsuma, yana neman ya fita hayyacinsa. Hammad ya riƙe rigar Imam Zahradeen yana tsare shi da idanu cikin tuhuma. Zahradeen ya yi murmushi ya kalli Mahmoudu ya ce "Ni ne nake tura maka saƙon cewar kar ka dawo da Hammad Agadez, lallai ka tafi Nigeria. Kuma ni na shirya yadda aka haɗa ku da Sule har ku ka yi aikin gadi tare. Sule ni yake yi wa aiki, duk wani abu da yake faruwa, da motsinku Sule yana sanar da ni. Kuma nine nake tura maka kuɗaɗe domin kula da Hammad da iyalin da ya aura, kuma aka sanar da ni kwanciyar hankalin da yake ciki. Sai dai bayan kame ku gaba ɗaya na kasa sanin halin da yake ciki, na tura Nigeria a bincika mini, aka tabattar mini da kama ku. Na ci gaba da bibiyar inda Nana take, amma binciken nawa bai cim mata ba, tayi ɓatan dabo, ga kuma alƙawarin da na yi wa ɗan uwanta, na zan tabattar da tana cikin ƙoshin lafiya. Sai dai da Allah ya dubi zuciyata sannu a hankali, komai ya din ga warwarewa, tun kafin ka gane ta, ni na gane ta saboda har hotonta ina da shi. Kuma aka yi sara a kan gaɓa ka zo ka same ni, da maganar cewa ka yi aure a Nigeria. Sai na bika muka tafi a haka, ban nuna maka komai ba, zuwa lokacin da nake ganin ya dace ka san komai!. 96 1k ne via 0069685771 Aisha Adam stanbic 08081012143 Hammad bai iya cewa uffan ba, kawai ya tashi ya nufi hanyar fita. Imam Zahradeen kuma bai motsa daga inda yake ba, ya zuba masa ido. Nana ta tashi a rikice ta ce "Sayyid ina zaka je ne? Kar ka yi fushi, ka tsaya ka saurare shi, kar ka yi wa al'amarin wata mummunar fassara. Bai tsaya ba kawai ya yi gaba, Mahmoudu ma tashi ya yi ya bi bayansa da sauri. Wannan shi ake kira da ga ƙoshi ga kuma kwanan yunwa. Ga farincikin ganin Imrana, amma alamu sun nuna Hammad ya ɗauki zafi da abin da Yayansa ya aikata, duk da ta wani fannin taimakonsa ya yi, amma ta wani fannin abin a saka masa ayar tambaya ne. ***** Sagir kuwa kamar zai haukace, saboda tashin hankali bai fita daga tashin hankalin ɓatan Shukura ba, ga Yusra ma ya neme ta ya rasa, tun safe ana maganar sha biyu saura na dare. Ga shi layin wayarsa yana cikin wayar Yusra, haka a dole yaje police station ya kai rahoton ɓacewar Yusra. Ya fara tunanin kar a fara zarginsa da ko shi ne yake aikata wani abu, matan nasa suke ɓacewa. Ƙarfe shida na safiya, suka ji ana bugun gate, bugu na tashin hankali kamar za a ɓall gate ɗin. Afujajan mai gadi ya buɗe gate ɗin, babu tsammani yaga Yusra a tsaye kamar korarriya. Ya zaro ido yana kallon ta cikin matsanancin mamaki. Gaba ɗaya gari ma bai gama waye ba, ya kalli hannunta ya ga jariri, bai yi magana ba ta banke shi ta wuce cikin gidan. A falo ta tarar da Antynta tare da mai gidanta, saboda bugun ƙofar da suka ji ana yi. Cikin mamaki Antyn ta ce "Yusra lafiya ki ka zo gidan nan da sassafen nan haka? Daga Kanon ki ka taho Abuja" Yusra ta yi shiru ba ta yi magana ba, kallon falon Yusra ta hau yi, tana tunanin yaya aka yi ma ta zo nan. Ita dai ta san ta ɗaukko jaririn ta fito titi, tama tafiya a hankali tana waige-waige, daga nan bata sake sanin abin da ya faru ba, ta ganta a ƙofar gidan Antynta da ta koma hannunta a Abuja. Mai gidan ya ƙarasa gaban Yusra, ya karɓi jaririn da ya fara kuka a hannunta. Yusra ta nemi guri ta zauna tana mayar da numfashi. "Yusra dan waye wannan, a ina ki ka samo shi?" Mai gidanta ya ce "Rabu da ita ta huta, wannan yaron a samo madara a bashi, sannan a kira mijinta mu ji ko da saninsa ta taho, kuma me yake faruwa" Antyn ta jinjina kai cikin damuwa, da fargabar a ina Yusra ta samo ɗa. ***** Jamila kuwa ta din ga zubar da jini babu ƙaƙƙautawa, ga azababben ciwon mara da ta din ga yi. Ta kwana ta wuni tana wata irin burgima da kuka mai ban tausayi. Baba ne ya dawo ya tarar da Jamila a cikin wannan yanayin. Baba ya ce "Rabi wai me yake damun Jamila haka ne, wannan wane irin ciwo ne tun jiya?" Mama ta ce "Ba fa wani abin ba ne ba, al'ada ce ta zo mata take shan wahala." "Haba, wahalar ta isa haka, wane irin ciwo ne haka, anya ba za a kaita Asibiti ba" Mama ta ce "Ba sai an kai ta ba, na bata magani za ta warke" Baba dai bai ji ya gamsu ba, amma ya ƙyale su kafin ta hayayyaƙo masa da masifa. ***** Asal duk ta fita hayyacinta, kullum cikin kuka, ta yi wata irin muguwar rama. Tana zaune a ɗakinta, Tafawa ya shigo ɗakin, ta ɗaga kai ta kalle shi. Ya ce "Dalilin me ne ne ya sanya ba kya cin abinci?" Ta yi shiru ba ta ce masa komai ba. "Kar ki saka damuwar abin da yake faruwar nan a cikin zuciyarki, duk yadda zan yi dole sai na tabattar da an hukunta Hammad, ba zai ci bulus ba abin da ya aikata." Asal ta yi shiru, wani irin baƙin ciki na taso mata a zuciyarta, ta din ga tuna yadda mahaifin nata ya din ga ingizata da tursasa ta aikata Wasu abubuwan. Ya yi wa rayuwarta illa duk a ƙoƙarin sa na ganin ya cimma wani burinsa da abu ne mai wahala ya samu cikarsa. Yana magana amma ta lula Duniyar tunani, ta tuna lokacin da aka kusa auren, ya kawo mata wani abu a ƙoƙo ya ce ta sha, sai bayan da ta sha sannan ya ce bai aura mata Hammad dan taje ta haihu da shi ba, domin har abada baya fatan ya haihu balle ya sanya ran samun magaji ya ƙara dagula masa lissafi gurin cim ma burinsa. Wasu irin zafafan hawaye suka zubo wa Asal, ta daɗe da gane rashin haihuwarta na da nasaba da wannan magani da mahaifinta ya bata, duk da a ɓoye ta je ganin likita a kan matsalar rashin haihuwar, aka ce mata hakan yana da alaƙa da ta'amalli da chemicals masu ƙarfi da ta yi. Da fari ta yi tunanin shaye-shaye da take yi, sai dai ko da shaye-shaye ta fi kyautata zaton maganin da Tafawa ya bata ne sila. Nana ta samu ta sake sosai da sosai da Imran ta din ga bashi labarin abubuwan da suka faru bayan tafiyarsa, wasu guraren sai da ya yi hawaye. Haka kuma ya din ga yi wa Nene addu'a, a kan abin da ta yi wa Nana na taimako. Nene ta ce "Babu komai, ɗa na kowa ne. Kuma in sha Allah Nana daram zata zauna a ɗakin mijinta" Nana ta kalli Imrana ta ce "Imrana tsoro nake ji, ban san yaya su Baba za su kalle ni ba, ban san me zan ce musu ba, ga shu kai ma tun da ka tafi ba ka je gidan ba?" Imrana ya ce "Ba za ki daina wannan zancen ba, ba abin da za su yi miki. Nima ban je ɗin ba" Nene ta ce "Ai dole mu kafa mu tsare, daga nan Agadez a tashi tawaga, su je har gida a bawa iyayenku haƙuri, kaga yanzu kai ne waliyyinta, a tashi manya daga Agadez su je har Nigeria su ba wa iyayenku haƙuri a kan abin da ya faru, sannan kuma a yi. Sannan ya zama dole a yi wa Nana duk wani abu na dukiyar aure, a yi cikakken biki na 'yar gata duniya ta shaida auren yadda yakamata, dan gudun kar ma a zo a samu wata matsala a nan gaba." Imarana ya ce "Wannan gaskiya ne, amma kina ganin za su amince da hakan?" Nene ta ce "Dole za su amince, ko dan son da suke yi wa ɗan su. Tun da ɗansu yana son iyalinsa." Hammad kuwa gidansa ya koma, sai dai ya rasa abin da yake yi masa daɗi, ya din ga juyi yana tunani, tare da tambayar kansa, kenan duk abin da yake faruwa da sanin Zahradeen. Kasa jurewa ya yi ya tashi ya tafi gurin Sultan. Yana zaune Gimbiya Bilkisu ta sanya shi a gaba, tana ta maganganu a kan kar ya nuna son kai akan hukuncin da zai yanke, kuma ya duba Asal ita ma a yi mata adalci. Babu tsammani sai ga Hammad ya shigo, yanayin yadda fuskarsa ta yi jawur, ya sanya Sultan miƙewa yana tambayarsa ko lafiya? Amma Hammad ya yi shiru bai ce komai ba. Sultan ya kama hannunsa ya shiga da shi cikin ɗakinsa, ya zaunar da shi ya ce "Ka gaya mini mene ne?" Sai gumi da yake ta tsatstsafo masa amma bai yi magana ba. Mahmoudu kuwa daga fitowar Hammad ya biyo bayansa, ya neme shi ya rasa, yana son su yi magana, ya lallaɓa shi su bi abin a sannu su fahimci Zahradeen, dan ya ga alamar ya ɗau zafi lamarin ya ɗaure masa kai. Matar Imam Zahradeen ta yi sallama, suka amsa. Ta kalli Nana cikin sakin fuska ta ce "Gimbiyar Imam Hammad, Imam Zahradeen yana kira" Nana ta yi murmushi ta ce "Nana dai za ki ce" "Ina, wa ya isa faɗar sunan Gimbiya" Nana ta yinƙura ta tashi ta bi bayanta. Bayan sun shiga, matar Zahradeen ta koma, Nana ta zauna a ƙasan Carfet. Ya ce "Kin ga mijinki ya ɗauki zafi, yaƙi tsayawa ya saurare ni, balle ya fahimce ni, amma na ga ke kina cikin nutsuwarki, za ki fi fahimtata. Amma kafin nan kin ga ke ki ka zauna da shi, ko za ki iya gaya mini abin da ki ka sani, bayan haɗuwarku lokacin yana cikin rashin lafiya?" Ta jinjina masa kai, sannan ta yi masa bayanin, abin da take ganin ya dace ta gaya masa. Ya ce "Shikenan, Sultan ya kira ni a waya, ya ce yana nema na, na san wataƙila ya gaya masa ne, tare da ke za mu je gobe in Allah ya kaimu da safe" Nana ta amsa masa da "To" ***** Hajiya Halima ta kiɗime, tun bayan da Sagir ya kira wayarta yake tambayarta, ko Yusra ta je gidan. Har ta fara shirin tafiya Kano, Yayar Baban Yusra ta kira ta a waya, ta sanar mata ga Yusra ta zo tun ƙarfe shida na safiya tare da wani jariri da ba su san a ina ta samo shi ba. A kiɗime Hajiya Halima suka shirya, suka tafi gidan Antyn, su na zuwa suka tarar da ita cikin yanayin ɗimuwa, ba ta magana ga kuma wani ƙosashshen jariri da ba a san inda ta samo shi ba. Hajiya Halima ta ce "Ai ni mijinta ya kira ni cikin tashin hankali, yake tambayata wai ko Yusra ta zo, ya neme ta ya rasa. Hankalina a tashe na fara shirin tafiya Kano, kin san uwargidanta fa ita ma an neme ta an rasa. "Mami" Yausra ta faɗa da ƙarfi. "Na'am Yusra, sannu" "Ku gaya wa Daddyn Haidar yaje ya ɗaukko Shukura, za su kuma sace ta" Cikin rashin fahimta ta ce "Suwaye?" "Nima ban san su ba, amma sace ta za su yi, na baro ta a can" Duk yadda suka yi da Yusra ta yi musu bayanin yadda za su gane, ta kasa sai kukan aje a ɗaukko Shukura kar a kuma sace ta. Hajiya Halima ta kira Sagir da lambar da ya kira ta, ta sanar masa ga Yusra a Abuja tare da wani jariri da ba su san a inda a ta samo shi ba. Cikin kiɗima da tashin hankali, ya ɗauki mota ba tare da ya gaya wa kowa ba, ya kama hanyar Abuja. ***** Bayan su Nana sun hallara a gaban Sultan, ta yi tozali da Giyaz a tsaye da sandarsa a bayan Hammad, sai da jikinsa duk rauni ya ƙara tsufa ya yi wani iri. Jikinsa sai hayaƙi yake yi ya zubo mata ido. Sultan ya dubi Imam Zahradeen ya ce "Zahradeen me ka yi wa ɗan uwanka ne, ya ƙi magana, sunanka kawai ya furta ya yi shiru, a nan muka kwana tare da shi, ko sau ɗaya bai yi magana ba. Imam Zahradeen ya haɗiye wani abu mai ɗaci a wuyansa, yana tunanin ta ina zai fara bayani. Nana ta ce "A je a zo da Sarkin baka gurin nan, idan ba haka ba Giyaz zai iya haddasa matsala" Duk suka kalli Nana Imam Zahradeen ya ce "Waye hakan?" "Ku zo da shi dan Allah, kar a samu matsala wani abin yake son aikatawa" Ganin Nana na neman burkicewa, ya sanya Sultan ɗaukko wayarsa ya ɗan daddana, Hammad dai bai ce komai ba. Imam Zahradeen ya ce "Kafin na ce komai, ina mai neman afuwarku a kan abin da zan faɗa, kuma ina neman afuwa da ni da waɗanda zan faɗa a cikin maganata. Na ji daɗi sosai da sosai da ka neme mu a keɓantaccen guri kamar haka, ina roƙon ku rufa mana wannan asirin dan Allah" Sultan ya ce "Zahradeen, ka tafi kai tsaye ka yi mini bayani, kana ta zagaye-zagaye daga mu sai mu a gurin nan" Ya ƙarasa maganar yana kallon wayarsa, ya danna ya ce "Ku ba shi dama, shikaɗai ya shigo" Sarkin baka ya shigo da sallama, ya risuna a gaban Sultan ya kwashi gaisuwa, ya juya ya gaida Imam Zahradeen, amma ya yi shiru yana kallon Imam Hammad da kuma Nana. Sultan ya ce "Ga mai maganin an kira shi, ya aka yi?" Sarkin baka ya ce "Uwar gijiyata, meyafaru da Giyaz ne?" "Ƙaisar ya ce mini faɗa suka yi." Ta mayar da idonta kan Sultan ta ce "Allah ya baka nasara, ya ci gaba da maganar a gaban Sarkin baka, shi ma amintacce ne, idan ya fita Giyaz zai iya aikata masa wani abin" Sultan ya ce "Waye Giyaz ɗin ne?" Sarkin baka ya ce "Aljanin da aka yi masa asiri da shi ne ranka ya daɗe" Imam Zahradeen ya fara magana ya ce "Tabbas na san ni mai laifi ne, kuma duk hukuncin da za a yanke mini zan karɓa" Ya ɗan yi shiru sannan ya ce "Mahaifiyata, Gimbiya Bilkisu, sun haɗa baki da ɗan uwanta, mai girma Tafawa, suka yi masa sihiri, aka haɗa shi da aljanin da zai bar garin da shi gaba ɗaya. Wallahi ban san sun yi ba, sai daga baya take gaya mini, saboda su na son ko ni ko Asadullah wani ya gaji kujerar Hammad. Na nuna mata rashin jin daɗina, ta ce mini aikin gama ya riga ya gama, muddin Hammad ya dawo Agadez sai ya haukace, ko ma ya rasa rayuwarsa. Shi ne na ɓoye lamba, na nemi Mahmoudu, a lokacin bai riga ya bar ƙasar ba, abin dai ya fara taɓa shi ne. Yanzun ma ba ni da yadda zan yi ne, amma ban so na tona wa mahaifiyata asiri ba" Hammad ya sunkuyar da kai hawaye na zuba daga idanunsa, Sultan ya rikice cikin tashin hankali da damuwa ya ce "Yanzu Zahradeen amma ka ɓoye mini wannan abin baka gaya mini ba? Yanzu ƙiyayyar da mahaifiyarka take yi wa Hammad har ya kai ga ta nemi ta zauta mini ɗa ya bar gida?" Zahradeen yana kuka ya ce "Dan Allah ka yi haƙuri Abie, ban san komai a kai ba, sai daga baya. Kuma gudun kar idan ya dawo ya samu matsala, shiyasa na ce kar ya dawo Niger" Nana ta ce "Gidan tarihi, a gidan tarihin Agadez aka yi masa sihirin, kuma ba sihiri ɗaya ba ne, mutane daban-daban sun yi masa. Ranar da muka je cikin gidan tarihin tare da shi, na ji ƙamshin turaren Gimbiya Bilkisu a gurin. Sannan bayan ƙamshin turaren ta, na ji ƙamshin turaren wani ma. Gaba ɗaya suka ɗaga kai, su na kallon Nana. "Duk wanda yake ƙamshin nan, da alama yana ziyartar gurin, kuma wanda yake yi musu aikin sihirin a cikin gidan tarihin yake. Idan gidan tarihin nan babu kowa a cikin sa, to wannan mai gadin ne bokan da yake aikin, ko kuma ya san bokan da yake yi. A rikice Sultan ya ce "Wane gidan tarihin wai, waye mai gadin?" Sai kuma ya rufe bakinsa, suka dubi Hammad a rikice, yadda ya runtse idanunsa yana zubar da hawaye. Nana ta rikice ta tashi ta nufe shi, Sarkin baka ya ce "Kar ki taɓa shi, Giyaz ne yake zungurarsa, zai iya yi miki wani abin ya cutar da ke" Ya tafi gaban Hammad, ya kama goshinsa ya din ga karanta Bismillah da suratul Fatiha, yana tofa masa a tsakiyar kansa. Daga bisani ya ɗaga rigarsa ya ciro jakar nan da ya bawa Nana, ya ce "Idan baka tafi ka ƙyale shi ba, zan illataka da jakar nan kamar yadda Ƙaisar ya yi maka" Nana rikicewa ta yi, duk da ba yau ta saba ganin abin mamaki ba, jakar da take hannunta, ta neme ta ta rasa, ta ganta a gurin Ƙaisar, yanzu kuma ta koma hannun mai ita Sarkin baka. Ya kalli Nana ya ce "A gurin ƙamshin turaren wa ki ke ji?" Nana ta yi shiru tana satar kallon Sultan, tana kuma kallon Zahradeen. "Kar ki ji tsoron kowa, gaya mini" Ta ƙi magana tana jinjina yadda za su ɗauki abin. Ya ce "Muje ki nuna mini gurin, ai babu abin da zai gagara da ƙarfin ikon Allah" Sultan ya tashi a rikice jikinsa yana tsuma, idanunsa sun yi jawur saboda ya kaɗu da abubuwan da suka fito daga bakin Imam Zahradeen. Wani irin mugun tausayin Hammad ya mamaye masa zuciya. Ya kalli su Nana ya ce "Yanzu can gidan tarihin za mu je kenan?" N Sarkin baka ya ce "Eh Allah ya baka yawan rai" Imam Zahradeen ya ce "Ko a yi wa su Matawalle magana, a tafi da wani daga cikin su, ko hadimai" "Bana buƙata" Sultan ya faɗa fuskarsa babu annuri, ba tare da ya kalli inda Imam Zahradeen yake ba. Ya dubi Hammad da ya buɗe idanunsa, sai dai baya magana, dan tun da ya zo wa Sultan ya ce masa Zahradeen ne, bai sake yin magana ba. Ya shafa kansa ya ce "Hammad, ka na ji na?" Ya jinjina kai. "Ko zaka bi mu ne?" Ya girgiza kai. "Ka na nan mu je mu dawo?" Ya ɗaga masa kai alamar eh. Ya girgiza kai ya ce "Ina Mahmoudu ne, ban ganku tare da shi ba, a nemo shi ya zo ya zauna da shi tukuna sai mu tafi" Imam Zahradeen ya tafi ciro wayarsa, ya hau laluben lambar Mahmoudu. Sultan da ya kalli Imam Zahradeen sai ya ji ransa ya ɓaci, ya yi mamaki ya kaɗu matuƙa da jin abin da Gimbiya Bilkisu ta yi wa Hammad. Ga abubuwan da Tafawa ya din ga yi masa, da tursasa shi a kan yi masa abubuwan da yake so, da shi da 'yarsa amma hakan bai ishe su ba, suka nemi a ɓatar masa da ɗansa. Sai da Mahmoudu ya zo, Imam Zahradeen ya ce "Imam Hammad ba ya jin daɗi ne, ka zauna tare da shi, zamu je mu dawo" Tiryan-tiryan suka bi ta ɗakin da su Nana suke zaune, suka buɗe wannan ƙofar kamar yadda Nana ta yi musu bayanin ta nan suka bi, suka gangara har gidan tarihin. Mai gadin na ganin Sultan, jikinsa ya hau tsuma ya zube a ƙasa tamkar zai yi masa sujuda yana kwasar gaisuwa. Sai dai gaba ɗaya ya rikice da ganin Sarkin baka. Ko da suka shiga cikin gurin, kawai Sarkin baka ya bushe da dariya, duk suka tsaya suna kallonsa. Ya tsaya yana ƙare wa gurin kallo, yadda aka rarake dutse aka gina wannan gurin, mutanen zamanin da suka yi wannan aikin sun cancanci yabo. Sarkin baka ya sake bushewa da dariya ya ce "Sarki a dawa Sarki a gida, Ni mai Duna ni mai Salamatu, ni mai Mairo 'yar Fulani. Ni ake yi wa inkiya biyu, Garba ga Baka ga Aska, na yi gadon gidanmu, na ƙwaci wanda ban gada ba, na fi 'yan na gada iyawa. Ni Abubakar Garba mai taƙama da ikon Allah. Na ga mutum na ga Aljan, na ga cuta na bada maganinta, idan babu na ce ba ruwan Garba. Ya buga ƙafarsa ɗaya ya ce "Uwar gijiyata, ƙamshin turaren wa ki ka ce kina ji?" Nana ta sake kallon su Sultan, Sarkin Baka ya ce "Faɗi kanki tsaye, ba wanda zai yi miki abin da Allah bai yi miki ba" Ta ɗan sunkuyar da kai ta ce "Akwai wani Imam Omar, wanda ya kawo wa Imam Hammad ayaba tare da Yayan Asal" "Ƙamshin turarensa ne?" Imam Zahradeen ya tambaye ta cikin zaƙuwa. Ta ce "Ni tsoron faɗa nake, ba na son haɗa husuma ne" Sultan ya sassauta murya ya ce "Ki na ji na? Ba haɗa husuma ba ne ba, mijinki za ki taimaka tun da ke Allah ya yarje miki gano wasu abubuwan da mu ba mu gano ba" Bakinta na rawa ta ce "Wannan mai kama shi ɗin, da ku ke yawan zama ku uku, mai saka shuɗin rawani, bayan ƙamshin turaren Gimbiya Bilkisu, ranar da muka zo nan, ƙamshin turarensa ne yake tashi, alamar bai daɗe da tafiya ba" A rikice Imam Zahradeen ya ce "Sardaunan Agadez, ƙamshin turarensa ne" Buɗe baki Sultan ya yi, ya fara numfarfashi yana kallon Nana, ya ce "Me hakan yake nufi? Ina fatan ba dai wani abin ya yi ba?" Nana ta girgiza kai cikin tsoro ta ce "Ba ni da tabbas, tun da kowa yana da damae zuwa gurin nan, mussaman a cikin manyan Agadez kamar yadda Imam Hammad ya gaya mini. Amma me zai kawo shi nan cikin dare wajen ƙarfe sha biyu na dare. Kuma a mudubin Ƙaisar na ga wani abu da ya sanya ban ji na yarda da ɗakin can ba, amma ba ni da tabbas tun da maganar aljani ba abar yadda ba ce ba wasu lokutan" Sarkin baka kawai ya nufi ƙofar ɗakin, da Nana ta yi ta nacin a buɗe ta, yana zuwa ya jijjiga ƙofar, amma ya ga ƙaton mukulli a jiki. A nutse ya ƙare wa sauran ƙofofin kallo, ya saki mukullin ya nufi hanyar fita, yana zuwa ya janyo mai gadin nan har zuwa inda su Sultan suke. Ya kalle shi ido cikin ido Sarkin baka ya ce "Waye kai?" "Mai gadin gidan tarihin Agadez" Ya ba shi amsa. Sarkin baka ya ce "Kai, mugu shi ya san makwantar mugu. Kai da gani idanun nan nawa ka san babu abin da ban gani ba. Waye da waye suke zuwa gurin nan?" Mai gadin ya yi wa Sarkin baka wani irin kallo, ya ce "Kowa ma yana iya zuwa" "Ba kowan ba, muhimman mutanen da ka ke yi wa aiki" "Ni ba ni da wani aiki bayan buɗewa da rufewa, da kula da ababen tarihi" "Ka tabattar?" Ya ce "Eh" Sarkin baka ya numfasa ya fito da jakar nan tasa, ya nuna wa mai gadin nan,ya ce "Idan hatsabibancinka ya kai ya kawo, na san ka san wannan jakar, ko kuma ka ji labarinta, mussaman da Jaddul Jinn ya yi rayuwa a cikin Masarautar nan. Wannan jaka ce da uwar gijiyar Ƙaisar ta farko, Lanti ta haɗa, da gudunmawar uban duƙusa, ta hanyar yin amfani da wani sashi na gashin Jaddul Jinn. Da abubuwa daban-daban da baƙaƙen aljanu ba sa so. Ana iya yi wa aljani tarko da ita, ko ma halaka su baki ɗaya. Yanzu za ka yi mana bayani ne, ko kuma na gwada maka aikin jakar nan, na hallaka baƙin aljanin kanka, na haɗa ka faɗa da Giyaz, sannan na kashe ka?" Ya din ga kallon Sarkin baka, yaƙi magana. Nana ta ji sanyi ya fara ratsata. Mai gadin ya ɗan ja da baya yana kallonta. Ta waiwaya ta ga me yake kallo, kawai ta ga Ƙaisar a gurin. Jikinsa na rawa ya nufi ƙofar ɗakin, ya ciro wani mukulli ya buɗe, yana buɗewa wani irin wari ya daki hancinsu suka ja da baya. Jikin Nana ya hau tsuma, Shi kansa Sultan ja ya yi da baya cikin tsoro, yana kallon gurin. Sarkin baka ya tankaɗa ƙeyar mai gadin nan, suka shiga ɗakin. Ɗakin duhu kafin daga bisani kawai su ga haske ya gauraye ɗakin. Sarkin baka ya waiwaya ya cewa su Imam Zahradeen su shiga. Suka bi wata doguwar hanya, su na shiga suka wari yana ƙara cika musu hanci. Ɗakin tsohuwar kurkuku ce, da daga baya a ka mayar da ita gurin aikin zinaren da ake haƙowa. Wannan kurkukun da aka din ga azabtar da mutane a zamanin sarakunan baya. Gurin gwanin ban tsoro babu kyawun gani ko kaɗan. Nana ta kurma ihu ta ja ta tsaya jikinta yana tsuma, saboda razana da kuma firgicin abin da ta gani. Ƙwarangwal ne na cikakken mutum, an soke shi a jikin mashi, an kuma soke wani abu mai kama da takarda a jikin ƙwarangwal ɗin, da hotonsa a jiki yana ci da wuta, sai kuma sunan Imam Hammad Jalaludeen, a jikin abin mai kama da takarda an soke allurai a jiki. Sak abin da ta gani a cikin mudubin Ƙaisar. Jikinta ya din ga wata irin karkarwa, saboda razani da tsoro. Shi kansa Sultan daskarewa ya yi yana rarraba ido, saboda razani da tsoro. Sarkin baka ya ƙarasa gaban ramin, ramin ba mai zurfi ba ne ba, sai dai wasu irin manya-manyan itace ne a cikin ramin nan. Ya kalli jikin ƙwarangwal ɗin nan, ya yi baƙiƙirin saboda azabar wuta. "Ya ka yi wannan sihirin?" Sarkin baka ya yi maganar yana tsare shi da ido. Ya yi shiru. "Wallahi idan baka faɗa ba, sai na jefa ka a ramin nan na kunna wutar" Ya tsaya ya kalli ramin, ya rufe idanunsa ya faɗi wasu abubuwa, ya kalli ramin a take wata irin wuta ta tashi a cikin ramin. Wata irin ƙara ta din ga tashi a cikin ɗakin. Nana ta toshe kunnenta, ta durƙushe a kan gwiwoyinta, ta toshe kunnenta, ta fashe da wani irin kuka na tashin hankali da gigicewa. Sarkin baka ya ce "waye ya saka ka wannan aikin, kuma yaya aka yi kana mai gadi ka ke bokanci?" Ya numfasa ya ce "Na koyi bokanci ne, domin na rama abubuwan da aka yi wa zuriyarmu. Na bautar da mu tun zamanin kakanni. Nana ta fara neman ta burkice musu gaba ɗaya, saboda sama-sama da numfashinta ya din ga yi. A rikice Sultan, ya ce Zahradeen ya fitar da Nana, kar wani abin ya same ta. Su na fita ta nemi guri ta zauna ta sauke numfashi cikin matsanancin tsoro da razani. ***** Mama ce a gaban Likita kamar ta yi kuka, ta yi ƙasa da murya sai magiya take yi masa. Ya kalle ta ya ce "Hajiya muddin ba ki gaya mini gaskiyar abin da ya faru ba, babu wani abu da zan iya yi a kan 'yarki" Cikin damuwa ta ce "Likita ka san ɗan yau ne, ka haife shi amma ba ka haifi halinsa ba, abin kunya ta kwaso mini, na yi na yi da ita a zubar ta ƙi, shi ne aka gaya mini wata ƙwaya na je na karɓo aka ce na saka mata guda goma a cikin kunu zai fita." Ya yi zuru da ido yana kallonta, ya ce "Amma baiwar Allah ba ki da imani, kin san abin da ki ka aikata kuwa?" "Dan Allah likita ka yi haƙuri,  ka taimake ni kamar yadda Allah ya taimake ka" Sai da ya yi mata faɗa kamar zai yi mata duka, sannan ya rubuta abin da za a yi wa Jamila. Hajiya Sa'a kuwa, ta daina magana gaba ɗaya, komai sai an yi mata. Ƙarshe Asibiti aka sallame ta, ta koma gida, gidan kuma babu mai jinyarta, abin duk ya damu Alhaji Fatuhu amma babu yadda ya iya. ***** Nana har wani irin jiri take yi, jikinta yana tsuma saboda tsoro da razanin da ta shiga. Sultan ya ƙi kallon inda Zahradeen yake, zai ɗauki Muhsin ya tafi da shi, amma ya yi masa tsawa ya ce kar ya taɓa shi. Gimbiya Bilkisu sam ba ta san me yake faruwa ba, da daddare ta shiryo ta zo sashen Sultan. Yana zaune a gefen gado ya yi shiru, ji yake yi tamkar kansa zai tarwatse. Muhsin yana kan makeken gadon Sultan yana bacci, gani yake yi idan ya kawar da ido daga kan yaron, shi ma cutar da shi za a yi, wani irin matsanancin tausayin Hammd ya hana shi sukuni. Da ya rufe idanunsa ya tuna abin da ya gani, sai tsigar jikinsa ta tashi. "Ranka ya daɗe, ko nan zan kawo maka abincin daren naka ne, barori sun shirya maka abinci tun ɗazu fa" Bai yi magana ba, ta mayar da idonta kan Muhsin ta ce "Wannan kuma a ina ka samo shi?" Ta yi maganar tana nufar gadon. Cikin tsawa ya ce "Kar ki kuskura ki taɓa shi" Ta razana ta ce "Sultan lafiya?" "Fita ki bani guri" Cikin rashin fahimta ta ce "Me yake faruwa ne?" "Na ce ki fita ki bani guri, ba na ko ƙaunar ganinki, ki fita kafin na ɗauki mummunan mataki a kanki" Babu shiri ta juya ta fice, ganin yadda jikinsa har rawa yake yi, saboda tsananin ɓacin rai. Ta din ga mamakin mene ne ya tayar masa da hankali ne har haka, yake wannan fushin?. ***** Nana kuwa tun da suka baro gidan tarihin, Sultan ya ce ta zauna a ɗakin nan da suke, ta samu nutsuwa. Da kyar ta samu ta iya yin salla. Tana zaune ta yi shiru, ta ga an buɗe ƙofar ɗakin, Hammad ta gani ya shigo, ba ta yi zaton ganinsa ba ko kaɗan. Ta miƙe tsaye ya ƙaraso fuskarsa ya zauna a kusa da ita, ya jingina da jikin gado. Sai kuma ya ɗago ya kwantar da kansa a jikinta. Nana ta ƙara janyo shi jikinta, ta ƙanƙame shi tana fashewa da kuka, wani irin tausayinsa ya mamaye zuciyarta. "Ya aka yi ne rayuwata, kukan me ki ke yi" Ya furta a hankali yana ƙara shigewa jikinta. "Sonka kawai nake yi" Ta yi maganar tana kuma ƙanƙame shi. "Wannan kukan, ya fi kama da na wanda ake tausayawa, meyafaru ki gaya mini" "Ba komai Sayyid" "To idan dai kina so na sosai, ɗan bani sanyin mana" Yayi maganar yana ɗan shafa jikinta yana murmushi. Jin da gaske kukan take yi, ya sanya ya ɗago, shi ma idanunsa jawur, jikinsa babu ƙwari ya ce "Ki gaya mini, ko wani abin su Sultan suka ce miki?" "A'a" "Mene ne?" "Dan Allah Sayyid duk abin da za a ce maka Asal ta yi, ka yi haƙuri ka yafe mata" Ya yi murmushi mai ciwo, ya ce "Me Asal ɗin ta yi?" "Na san sai Sultan ya gaya maka, amma dan Allah ka yafe mata" Hammad ya ce "Ki na tunanin ban san komai ba ne? Lokaci ya yi da yakamata na huta" Nana ta ce "Wataƙila akwai abin da baka sani ba, dan Allah ko ka sani ka yi haƙuri ka yafe mata" Ya yi shiru ya sake kwanciya a jikin Nana, ta ƙara ƙanƙame shi, cikin matsanancin tausayawa. ***** Sultan na kashingiɗe, yana sauraren Tafawa, da sauran 'yan majalissa, sun kafe kai da fata a kan lallai a san matakin da za a ɗauka a kan Hammad, saboda yadda ya karya musu Al'adar masarauta. Sultan ya ɗago ya numfasa cikin ƙasaita, kamar ba zai yi magana ba, sai kuma ya ce "Amm kamar yadda kowa ya sani, Agadez ta gaji Al'adu da ƙa'idoji daban-daban, wanda wasu an samar da su ne, tun zamanin jahiliyyah kafin zuwan addinin musulunci, ina ga lokaci ya yi da yakamata mu kama addininmu, mu yi watsi da duk al'adun da muke ganin su na kawo mana koma baya. Saboda haka a matsayina na Sultan mai ci na wannan lokaci, na soke wannan Al'ada a ƙasar Agadez. Baƙaƙen buzaye za su samu 'yanci, farin buzu ko buzuwa na da cikakken 'yancin auren duk wata ƙabila ko kalar fatar da yake son aure. Matar da Imam Hammad ya aura, bincikenmu ya tabattar da halattaccen aure suka yi, kuma mun karɓe ta. Hakazalika za mu bayyanawa duniya ɗan da ya haifa tare da matarsa ta Nigeria. 97 1k ne via 0069685771 Aisha Adam stanbic 08081012143 Gaba ɗaya 'yan majalisar suka waiwayo suna kallon Sultan. Tafawa ya ce "Jalaludeen wannan wace irin maganar banza ce, dan me zamu bar gadon al'adun da muka gada daga iyaye da kakanninmu saboda son zuciyarka da ƙoƙarin bawa ɗanka kariya? Babu wanda zai lalata mana dokokinmu da al'adunmu. Dole a hukunta Hammad dai-dai da abin da ya aikata" "Mutanen farko ma, gadon iyaye da kakanni ne ya halakar da su. Daga lokacin da muka gaji al'adun, zuwa yanzu me al'adar ta haifar mana bayan tarin ɓarna kashi-kashi? Kuma ina bayar da wannan umarni ne a matsayina na Sultan, shugaba a Agadez ba magana nake yi ba a matsayin ɗan uwanku ko abokinku ba, duk wanda ya ɗaga murya ko kawo abin da ba shikenan ba, zan hukunta shi dai-dai da abin da ya aikata" Matawalle ya ce "Amma Allah ya baka yawan rai, yanke wannan hukuncin haka kai tsaye, baka tunanin zai sanya wa talakawanka wasi-wasi da kawo tashin tashina a tsakanin masarauta da kuma jama'ar gari" Sultan ya numfasa ya ce "Lokuta da dama, gyara baya buƙatar lallai sai ka yi wa wani daidai, ko kuma sai kowa ya soka, ya yarda da kai mai gaskiya ne ko me kirki ne. Haka zalika zan sauke wasu daga cikin Imam Imam na ƙasar nan, zan yi wa dokokin Agadez garambawul da gudunmuwar dokokin ƙasar Niger, domin kowane ɗan Agadez ya samu cikakken 'yanci kamar sauran ɗan ƙasa ba tare da al'ada ta tauye wasu daga cikin 'yancin da suke da shi ba a ƙasar nan. Sai dai na san da yawa ba zai yi muku daɗi ba, za a ga kamar na yi rashin adalci saboda Hammad ɗana ne, amma kafin ku ce haka, bari mu yi komai a buɗe tare da ku". Ya kalli wani dogarinsa, ya ce "Ina da baƙo a mararrabar fada da hanyar cikin gida, ka ce ya iso" Duk suka yi tsuru-tsuru su na jira. Ba a jima ba, dogarin ya dawo tare da Sarkin baka sai kuma wannan mai gadi a ɗaɗɗaure da igiya tamau kamar ɓarawo. Wanda ba su san me ake ciki ba, suka yi ƙuri su na jiran jin ba'asi, wanda abin ya shafa kuma cikinsu ya ɗuri ruwa. Sarkin baka ya risuna ya yi gaisuwa a fada, cikin shigarsa ta hargi ya shigo hakan ya ƙara sanyawa duk aka zuba masa ido. Sultan ya kalli Sarkin baka ya ce "Yi musu bayani" Sarkin baka ya kalle shi ya ce "Duk da na san, sun sanka amma ka yi musu bayanin waye kai" Ya sunkuyar da kai ya ce "Mai gadin gidan tarihin Agadez" Sarkin baka ya ce "Kuma me?" "Boka da nake yi wa wasu daga cikin manyan Agadez aiki" "Mene ne dalilinka na yin hakan?" Ya numfasa ya saci kallon Sultan ya ce "Na haka ne, saboda huce takaicin yadda ake bautar da mu tun daga kan kakana, wannan dalilin ya sanya lokacin boka Riyan, na koyi harkar bokanci a gurinsa" Sultan ya ce "Ina fatan kun ga ɗaya daga cikin illolin wannan al'adun da muke yi, marasa tsuhe balle makama? Mu na jinka ci gaba" Sarkin baka ya ce "Ba ka ji ka ci gaba mana" "An bani wasu ayyuka, duk da ba kowa ya san ina bokanci ba, sai dai akwai wani babba a masarautar nan da shi ya ƙarfafe ni na koyi harkar bokanci. Ni aka saka na yi wa Imam Hammad Asiri, da aljanin da ya sanya ya bar ƙasar nan, ya manta komai da ya shafe shi, ciki hadda tuna waye shi. Sannan aka bani aikin yi masa asiri da wani tsohon aljani a cikin gidan tarihin, da yake sanya masa wannan zafin jikin da yake gigita shi". Sarkin baka ya sake cewa "Yaya ka ke yi?" "Da fari na haƙa rami a cikin tsohuwar kurkuku, ana kawo mini itace cikin dare, ina tona tsofaffin kabarurruka na cikin gidan, na ɗauki ƙwarangwal ɗin, na saka shi a cikin wuta, da hatimai daban-daban da sunan Imam Hammad, duk lokacin da na babbaka wannan wutar yadda ƙwarangwal ɗin nan yake ƙonewa haka yake jin zafin a jikinsa. Idan ƙwarangwal ɗin ya murmushe saboda zafin wuta, sai na kuma tono wani. Daga baya kuma aka koma kawo mini sababbin gawarwaki na koma yin aikin da su, idan na saka musu wutar nan, haka yake jin wannan zafin a jikinsa" Gurin ya yi tsit, aka rasa wanda zai yi magana. Jikin Matawalle yana rawa ya ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, amma suwaye haka?" Sultan ya ce "Ba sai an faɗe su ba, amma sun san kansu, kuma duk wanda yake da ja a kan maganar, yana iya zuwa gidan tarihin da kansa ya tabattar. Dan haka a yau na kawo ƙarshen zaman yau, dan haka zan zo da sauran bayani da abubuwan da zamu caccanza". Nan aka ci gaba da salallami, aka rasa mai sake cewa komai. Nana tana kwance tare da Hammad, kamar zai shige cikinta, sai shafa gashin sa take yi sannu a hankali. Ta yi shiru tana tunanin abin da ya faru. Yadda bokan nan ya din ga yi musu bayanin, Imam Omar da mahaifinsa Sardauna, suke zuwa da yadda suka yi masa asirin nan na zafin jiki. Kuma da sanin Tafawa, kowa fafutukarsa ɗansa ya samu mulki. Haka zalika Asal ta yi soyayya da Omar, ita take ajiye wa Hammad takardun nan. Ko da auren Hammad sun yi soyayya tare, kafin daga bisani da ta ga babu amfani soyayyar tasu, ta fara son Hammad ta daina biye masa. Sai dai ya ci gaba da yi mata barazanar sai ya tona mata asiri, irin hirarrakin da suke yi. Sai dai babu wani abu na saɓon Allah da ya taɓa shiga tsakaninsu, sai dai duk wasu zantuttuka na banza har da wanda bai kamata ba, suna yi. Babu abin da bai sani ba a game da aurenta, da abubuwan da yake faruwa tsakaninta da Hammad ba. Hatta sirrin shimfiɗar aurensu, babu abin da Omar bai sani ba. Shi ya din ga ziga ta, tun daga lokacin da aka ce za a yi aurenta da Hammad, shi ya din ga ziga ta har bayan auren. Ya ci gaba da zuwa gurin bokan nan, yana karɓar wannan takardar, yana bawa Asal, wanda da ya yi tozali da takardar yake sake ruɗewa, jikinsa ya rikice ya yi ta jin ihun da alajanin nan yake yi a jikin ƙwarangwal ɗin nan, duk ya fita hayyacinsa. Babu yadda Omar bai yi da Bokan nan, ya yi masa abin da Asal za ta yarda shi, amma ya ce ba zai yi wannan cin amanar ba saboda Hammad yana yi masa alheri ta wasu ɓangarorin. Gaba ɗaya bokan ya gaya musu labarin, da abin da yake tsakanin Omar da Asal a baya. Babban abin da ya ɗaga wa Nana hankali, bai wuce yadda bokan ya ce, ko za su kashe shi, zai iya lalata sihirin da ya yi da aljanin jikin ƙwarangwal ɗin da yake amfani da shi, amma ba zai iya raba Hammad da Giyaz ba, saboda Giyaz baya saɓa alƙawari, kuma ga Nana tana tare da Hammad, yana ganin ɗansa a jikinta, idan ba kashe Giyaz za a yi har lahira ba, ba zai rabu da shi ba. Da ta zo nan a tunaninta, ta lumshe idanunta hawaye na zirarowa a hankali. Hammad ya yinƙura ya tashi zaune, ta maze ta goge hawayenta. Ya ƙare mata kallo ya yi wani irin tattausan murmushi, ya shafa gashin kansa ya ce "Ba ƙaramin kyau ki ka yi mini ba ma vie, ina kewa, ɗan yi mini waƙar mana abar ƙauna" Yayi maganar yana sumbatar hannunta, tare da matsawa kusa da ita. Ta ɗan matsa kaɗan ta ce "Ana ta kai ka na ta kaya" "To ni kayan ne suka fi damuna, fiye da kayan ai. Ki kwantar da hankalinki babu abin da zan yi miki, kuma ina roƙon Allah kar ya kama ki da laifin guduna da ki ke yi, saboda kin fi ni gaskiya ta kowace fuska. Amma har abada ni mai ƙaunar ki ne, kuma ba zan taɓa yarda a raba ni da rayuwata ba in sha Allah" Ya yi maganar yana sake rungume ta, wani abu mai sanya nutsuwa na fizagarsa game da ita. "Ka daina yi mini wannan kallon mana" Ta yi maganar tana hararasa cikin wasa. "Idan ban kalle ki ba wa zam kalla, kina nan a yadda ki ke ma vie, kamar baki haifi Muhsin ba" Ta ɗan ɓata fuska ta ce "Da na canza daina sona za ka yi kenan?" Yayi murmushi ya ce "Haryanzu ba ki san waye Hammad ba, ke ɗin nake so ne Asmy, babu abin da zai canza a tattare da ke, na ji na daina sonki ko kaɗan. Ina son Husna" "Sake faɗa" Ta yi maganar tana tsare shi da ido. "Sai kin yi mini waƙa tukuna" Ta yi dariya tana jan hancinsa ta ce "Sai ka biya ni tukuna." Ya ɗan yi shiru ya ce "Ina tuna mutane daban-daban da muka rayu da su a Nigeria, ko ina yayarki ɗin nan, da ta yi ta ɗawainiya da mu? Da 'yan gidanku, da mutumin nan da na tsana, wanda na yi wa gadi da farko. Sai kuma mutanen gidan da muka zauna, da muka yi aure" Nana ta ce "Gidansu budurwarka ko?" Ya ce "Eh nan" "To tashi daga jikina" Hammad ya ce "Ba zan tashi ba, ai ni ban ce budurwata ba, ke ki ka fara." Ta yi murmushi ta ce "Babu abin da ba zai wuce ba sai ikon Allah, ni dai ina ta zaman jiran tsammanin abin da za a yanke a kanmu" Ya ce "Alkhairi in sha Allah, ni nama manta, yana nemanmu anjima, ban san me zai ce mana ba. Amma ina tsammanin alkhairi daga bakinsa" "Allah yasa ina fatan hakan nima, amma dan Allah ka sanya baki, na ga ya yi fushi sosai da sosai da ɗan uwanka, ko zaka saka baki?" "Ba ruwana" Ya bata amsa kai tsaye. Nana ta ce "Kar ka ce haka" Ya miƙe tsaye gaba ɗaya, sannan ya ce mata "Zan je na dawo, ki yi mana addu'a Allah ya sanya hukuncin da Sultan zai yanke, ya yi mana daɗi" Ya ƙarasa maganar yana sumbatar goshinta. Kamar zata tashi sama, haka Gimbiya Bilkisu ta faɗo turakar Sultan hankalinta a tashe, ko haɗiyar yawu ta kasa, saboda bushewar da bakinta yayi. A nutse ya juyo ya kalle ta, bayan ya gama warware rawanin kansa. Sai kuma ta tsaya ta kasa magana. Can kuma ta ce "Sultan, wai da gaske zaka sauke wasu daga cikin Imam? Meyasa? Kuma ina fatan babu Zahradeen a ciki?" "Idan da shi me za ki yi?" "Amma dai ka san bai kamata abin da ka yi, kuma a kan me zaka sauke Zahradeen yana ɗan cikinka? A wancan karon ka naɗa ƙaninsa a matsayin shugabansa, sannan ka zo ka sauke shi ai muzantawar tayi yawa. Zai ma zama abin surutu a Agadez" Cikin nutsuwarsa ya kalle ta ya ce "To shi ne me? Ai gara abin kunyar sauke shi daga Sultan, a kan tona muku asiri da ke da shi da ɗan uwanki Tafawa" Ya ƙarasa maganar cikin hasala. Sak ta yi tana ƙwalalo ido waje tana kallonsa. "Kar ki kalle ni kamar ba ki san abin da ki ka aikata ba, Bilkisu kin cutar da ni, kuma kin cutar da kanki. Kin yi yinƙurin kashe mini mata sau biyu, saboda gudun tonuwar asirinku, yayanki ya yi uwa ya yi makarɓiya ya sanya muka rufe Mamman, waya sani ko a ƙarshe ma ke dai ki ka yi sanadin rayuwar tata? Sannan tilon ɗan da ta bari a duniya ki ka sako a gaba da jaraba, ke kina yi yayanki yana yi, gaba ɗaya Hammad bai ji daɗin rayuwarsa ba, saboda azaba da masifar sihiri da makircinki. Kuma idan ki ka kuskura ki ka buɗe baki ki ka musa mini, sai na tona miki asiri sannan ki bar mini gida. Allah ne ya tona muku asiri a silar matarsa ta Nigeria da ya aura, kuma bokan naku yana hannunmu, ya tabattar da abin da ya aikata. Abu ɗaya zan duba na rabu da ke, 'ya'yan da na haifa tare da ke. Amma daga yau na haramtawa kaina ke har abada a matsayin matata, za ki yi zaman 'ya'yanki ne kawai. Kuma kar Zahradeen ya ƙara ayyana ni a matsayin mahaifinsa, kuma kar ya sake zuwa inda nake. Da ke da duk wanda ku ka aikata hakan, na bar ku da Allah. Faɗar abin da ku ka aikata tamkar tona wa zuriyarmu asiri ne" A rikice ta ce "Dan Allah Jalaludeen ka tsaya ka ji... "Ba zan ji komai ba, fice ki bani guri kafin na canza shawara" Yayi maganar yana yi mata wata irin gigitacciyar tsawa, babu shiri ta fice tana haɗa hanya. Tafawa ne ya shigo falon hankali a tashe, ya tarar da Asal tare da Asadullah. A fusace ya ce "Gidan uban wa ku ka tafi tun safe?" Da mamaki Asad ya ce "Kai ka kira ni a waya ai, ka ce na zo na kai Asal Asibiti, tun lokacin muna Asibiti, ba ta da lafiya sosai. Ya sharce gumin goshinsa ya ce "To, dara ta ci gida yau, Asirinmu ya tonu a fada" Gaba ɗaya suka ɗaga kai suka kalle shi. "Eh, yau da bokan da yake yi mana aiki, na gidan tarihi aka zo fada, ya tona komai sunayenmu ne kawai bai kama ba. Kuma na san ya gaya wa Sultan komai, kuma duk a dalilin haukanki da dabbancinki Asal, haka kurum ki ka je ki ka jajubo masifa ki ka kawo ta har cikin gidan sarauta. Binciken da na yi, wannan yarinyar da ki ka kawo a matsayin kuku, ita ce ɗin dai ta yi sanadin tona asirinmu. Dan haka sai ku shirya baki ɗayanku, dan ban san wane irin hukunci za a ɗauka a kanmu ba. Asal ta ɗora hannu a ka ta ce "Wayyo Allah na shiga uku, Abbu sai da na ce muku mu daina wannan abin, amma kai ka saka ni, Imam Asad ya saka ni, Imam Omar ma ya saka ni da Sardauna, ku ka saka ni a tsakiya wallahi ina son Hammad, idan na rabu da shi ba zan taɓa samun miji kamarsa ba, wallahi ina sonsa" A fusace Asadullah ya ce "Ke rufe wa mutane baki, ke ta wani shashasha ma ki ke yi?" "Kai ne shashasha, dan duk saboda gobenka aka lalata tawa, an cuce ni, komai zan yi yanzu Hammad ba zai taɓa yafe mini ba, balle ya saurare ni" Tafawa ya dubi Asal ya ce "Asal kina da hankali kuwa? Kin san abin da ki ke faɗa kuwa?" "Abbu na san abin da nake faɗa, shikenan bani da makoma, matarsa ta shiga kundin tarihin baƙar mace ta farko da ta auri Imam a Agadez, ni kuma zan shiga kundin tarihin matar da ta sanya hannun gurin tarwatsa rayuwar mijinta"  Miƙewa tayi Tafawa yana kiranta, amma ko waiwayowa ba ta yi ba, ta fice daga ɗakin. **** Alhaji Fatuhu ne ya yi sallama a falonsa, ga mamaki ya ga Fadila tare da uwargidansa Hajiya Suwaiba, suna zaune abin da bai taɓa gani ba. Suna ganin shi suka zuba masa ido, Hajiya Suwaiba ta ce "Ka ce sai gobe in Allah ya kaimi zaka dawo?" Ya ce "Eh, fasawa na yi na taho yau" Fadila ta ce "Amma Daddy lafiya dai ko, Rauda kawo masa ruwan sanyi" Suwaiba ta ce "Wai dan Allah Baban Rauda Meyafaru a Lagos ɗin ne?" Ya ce "Sai kun gaya mini, me ku ke tattaunawa ne, ganinku tare ya sanya ni farinciki" Hajiya Suwaiba ta ce "Abokin nan naka ne ya zo gidan nan, wanda ya sai gidan nan, shi ne muke tattaunawa mu tattara ɗan abin da ya yi saura, a nemo gida mu tashi, tun da mun ga alamar mutumin nan zai iya ci mana mutunci daga mu har kai." Ya yi murmushi tare da jinjina kai. Cikin damuwa Fadila ta ce "Dan Allah Daddy ka gaya mana, meyafaru muna fatan dai ba wani abin ne ya kuma kunno kai ba" Ya saki murmushi ya ce "Da baku ganni a haka ba, Alhamdillah an canza sabon controller na hukumar Coustom na ƙasa. An sakar mini kwantena Arba'i  da bakwai a cikin kwantenonina, da na mutane da na haɗa na yo order kaya" A rikice suka buɗe ido, suna jin abin kamar a mafarki. Hajiya Suwaiba baki na rawa ta ce "Daddy, kenan suna sane suka kama ka kayan naka, ba wani laifin ka yi ba, yanzu kana nufin an saki kayan?" Ya jinjina kai ya ce "An saki wasu daga cikin kayan, Allah ya karɓi addu'a" Gaba ɗaya suka rungume shi tare da yaransa, yana kuka su na kuka, babu abin da bakunansu ke furtawa sai tsantsar yabo da godiya ga Ubangiji Subhanahu wata'ala mai zaɓar wa kowane bawa abin da ya dace da rayuwarsa. Baban su Nana ji yayi tamkar ya ɗora hannu a ka ya zunduma ihu, bayan da likita ya sanar masa abin da yake damun Jamila. Duk da Mama ta roƙe si a kan su rufa musu asiri, amma ganin yadda Baban yake ta sintiri hankalinsa a tashe, an rasa takamaiman dalilin da ya sanya ake ta ƙara wa Jamila jini. Ya sanya ya yi wa Baba bayanin, cikin jikinta da ya zube ne, bai fita gaba ɗaya ba, ga jini ta zubar mai yawan gaske. A tsorace Baba ya kalli Mama ya ce "Rabi, wane cikin? A ina Jamila ta samu ciki?" Ta tsuru-tsuru tana jin kamar ta kama Likitan ta yi ta gwara kansa a gurin. "Rabi, dama abin da yake faruwa kenan ki ka ɓoye mini? Jamila da ciki? Kin cuce ni ba ki yi mini adalci ba, kuma ki ka ɓoye mini baki gaya mini ba ki ka nemi kashe ta da ƙwayoyi. Shikenan kanki ki ka yi wa, na fara zargin alhakin Nana ne duk yake bibiyarmu. Nana duk matsi da wahalar da ta sha a rayuwarta bata ɗaukko mini magana ba, ki ka yi mata sharri ki ka saka na amince na aura mata mutumin da ban san waye shi ba, an wayi gari shekara uku, babu ita babu ɗan uwanta, ke kuma naki 'ya'yan babu na mora daga mahaukaciya mai fama da aljanu sai lalattaciya. Abubuwan da ki ke yi wa Nana sharri da kuma yi mata gori a kai, duk sun kama ki a kan yarnki. Amma kanki ki ka yi wa Allah ya yi muku magani" Har ya gama maganar ya fita, ba ta sake iya cewa Uffan ba sai gursheƙen kuka da take yi. Jamila ma da ke kwance sai kukan da take faman yi. ***** Kasancewar Alhaji Fatuhu yana ɗakin Fadila ne, ta din ga gargaɗinsa a kan ya ja bakinsa ya yi shiru, kar yayi saurin gaya wa jama'a cewar an sakar masa kayansa. Ya ce "Haba masoyiyya, duk yawan jama'ar da suka taru suka jajanta mana, tsawon wannan lokacin, kusan shekara huɗu, kuma sai waraka ta zo mu yi shiru?" Fadila ta ce "Sa gani a hankali, baki yana yi wa abu illa, ka san waɗanda zaka janyo jikinka tukuna, ka lallaɓa ka ga abin da Allah zai yi sannu a hankali ka fara settling komai, amma dan Allah kar ka yi saurin gaya wa jama'a" Ya ce "To shikenan na ji, zan ɗan fita yanzu amma, sannan goben in Allah ya kaimu, gaskiya ki shirya mu je, zamu duba Yaya Sa'a, zan kuma mayar da ita Asibiti in sha Allah" Ta so musa masa zuwan, amma ta ga bai kamata ba, kawai ta haƙura ta shanyeta amsa masa da to. A gida Alhaji Fatuhu ya tarar da Alhaji Zailani, ya tarar da shi ya yi wata irin muguwar rama, bai matuƙar ban tsoro. Ya ce "Alhaji Zailani, lafiya kuwa me yake damunka haka? Ko duk tashin hankalin ɓatan Shukura ne?" Alhaji Zailani ya yi murmushi ya ce "Ba dole hankalina ya tashi ba, 'ya ta ɓace babu ita babu labarinta ba, gefe guda ga ciwon suga ya sako ni a gaba, yanzu an hana ni cin komai sai ganye, kusan ko ruwa na sha sai ya yi sama. Na rasa ma abin da yake yi mini daɗi" Cikin damuwa Alhaji Fatuhu ya ce "Haba kai kuwa, duk lokacin da muka yi waya ce mini ka ke yi kana nan lafiya, ayyuka sun yi maka yawa shiyasa na ce ni bari na zo da kaina, ko zan samu kana gida. Ni nawa jikin Alhamdillah ya yi kyau kai kuma babu lafiya haka. Ka kwantar da hankalinka in sha Allah zaka samu lafiya. Kuma za a ga Shukura da yardar Allah. Amma kai ma ka jarraba na gargajiya ko za a dace, ni na ga alfanun ire-iren magungunan nan wallahi" Alhaji Zailani ya ce "To shikenan, zan gwada da yardar Allah" A baɗini kuwa, Aljanin da yake bawa jini ne, ya fara burkita shi yake shan nasa jinin, saboda rashin bashi abin da ya nema a wannan shekarar. Ga shi ya yi ta mummunan mafarki da Shukura tana caka masa wuƙa tana kuka. Ga shi ya yi ta mafarkin ƙwarangwal ɗin jariri yana sha masa jini, ko yana fizgo kayan cikinsa yana ci. Idan ya tashi sai ya ji jikinsa kamar babu laka, ko hannunsa da kyar yake iya ɗagawa. Da yaje Asibiti aka ce ciwon sugar ne, yanzu ya hau in anjima ya yi ƙasa ko a ganshi normal. Ga shi ya fara surutai idan yana baccinn har Hajiya Amina ta fara tuhumar sa, da yi masa tambayoyi. **** Hammad na gaba, Nana na biye da shi, suka shiga turakar Sultan, karon farko Nana ta gan shi cikin riga da wando na shadda, babu rawani babu takunkumin yana shan shayi, Muhsin na kusa da shi, ya ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya da nasa kofin shi ma yana sha. Ba zaka taɓa cewa Sultan ya haifi su Hammad ba, kamar yayansu ba mahaifinsu ba. Muhsin yana kallon su Nana ya hau murmushi, amma bai tashi daga kusa da Sultan ba. Sultan ya kalli Muhsin ya ce "Suwaye waɗancan? Ka san su?" Kawai ya ci gaba da murmushi yana shan shayinsa. Ita Nana a zatonta, Imam Zahradeen ne ya kuma tafiya da shi gidansa. Ta duƙa ta gaida Sultan, ya saki jiki sosai ya amsa mata, Hammad ma ya gaishe shi, shi ma ya amsa masa yana bin su da kallo, wata nustuwa da farin ciki na ratsa shi. Ya din da gode wa Allah, da bak biye wa su Sardauna ya kori Nana ba. "Ina fatan duk kuna cikin ƙoshin lafiya?" Hammad ya ce "Alhamdillah" "Ma sha Allah, Nana Asma'u" Nana ta ɗago da mamaki jin ya kira sunanta cikke. Ta ce "Na'am Abie" "Da farko ina mai baki haƙuri bisa ga abubuwa da suka faru, kar ki yi zaton ko dan muna sanya ran Hammd ya samu lafiya saboda ke ne, ya sanya na saukko. Ko kaɗan dama mun yi magana sosai da sosai da Mahmoudu ina ta tunanin yadda zan ɓullowa lamarin, ba tare da 'yan majalissata sun ga na nuna son kai ba, sai dai cikin ikon Allah a dalilinki, na fuskanci ingiza mai kantu ruwa suke yi mini. Kuma na koyo darussa daban-daban a dalilin faruwar wannan al'amura tabbas; idan bamu karɓi abin da ya faru a matsayin aya ba, to gaba Allah na iya jarabtarmu ta wani abin da ba zamu iya sa shi ba, a kan muguwar Al'adar da babu abin da ta haifar sai kawo mana koma baya. Yanzu dai ina baki haƙuri da abin da ya faru, wanda aka yi miki da gayya da wanda muka yi miki cikin kuskure. A duniya ko a gurina da na haifi Hammad bai samu nutsuwa da kwanciyar hankalin da ya samu a gurinki ba. Ga mu da kuɗi da wadata, amma Hammad bai tashi cikin kwanciyar hankali ba. Ko dan albarkacin wannan abokin nawa, dole na tabattar da kun ci gaba da rayuwa tare" Ya yi maganar yana shafa gashin Muhsin. Ya ce "Dan haka in sha Allah, muddin ina raye, babu wani abu da zai kawo muku cikas a rayuwar aurenku, Ubangiji Allah ya sanya muku albarka. Na ji duk tarihinki, har Nigeria na aika duk an yi mini binciken da yakamata, kuma na gamsu da abubuwan da na ji game da ke, da kuma rayuwar da ki ka yi da Hammad. Ina goyon bayan ku rayu tare, Hammad ba zai taɓa samun mace kamar ki ba Asma'u" Kawai Nana ta fara zirarar da hawayan farinciki. Hammad ya rikice gaba ɗaya ya ce "Abie, yanzu ka yarda na ci gaba da rayuwa da Nana? A matsayin matata duk da yadda al'adarmu ta hana?" Sultan ya yi murmushi ya ce "Na ma soke wannan dokar, daga yau babu ita a Agadez" Hammad ya tashi ya tafi gaban Sultan ya risuna, amma ya rasa abin da zai ce masa. Sultan ya rungume shi yana murmushi. Ya numfasa ya ce "Hammad, ban san iya adadin abin da ya rage maka na rayuwa ba, amma na baka damar ka yi duk abin da ka ke so wanda bai saɓa wa mahaliccinka ba, da zai sanya ka farinciki. Sannan ka sakar wa Tafawa 'yarsa, dan babu amfani ci gaba da zama da mutumin da yake ƙoƙarin ganin bayanka, yake cutar da kai tsawon lokaci. Ka yi haƙuri kuma ka yi biyayya, Ubangiji Allah ya baka ladan haƙuri da kuma biyayyar da ka yi. Sannan ina roƙon Allah ya baka lafiya ya kuma warware miyagun abubuwan da suka aikata maka."Ɗan uwanka kuma wannan ganin damarka ce ka ci gaba da mu'amala da shi, amma ni na yafe shi a matsayin ɗa na, na girgiza matuƙa da jin abin da suka aikata" Nana zata yi magana Hammad ya girgiza mata kai alamar ta yi shiru. "Ke ma in sha Allah, zamu tura wakilai, zamu je mu ba wa iyayenki haƙuri, kuma kamar yadda mahaifiyar Mahmoudu ta nema, kuma mun amince za mu yi hakan. Duk wata ɗawainiyar aure da ake yi wa mace, da za a aura a Agadez za mu yi miki ita, kuma zamu biki sosai kowa ya san da zamanki" Nana ta risuna ta ce "Na gode sosai da sosai Abie, Ubangiji Allah ya ƙara girma da sutura, ya kare ku daga dukkanin abin ƙi. Amma ni hukuncin da ka yanke mini bisa adalci da tausayi, da bani damar na rayu da Muhsin da mahaifinsa ya fi komai yi mini daɗi, ina ga ba sai an yi bikin nan ba, har dukiyar auren ma na yafe" Sultan ya yi murmushi ya ce "Ba biyanki abin da ki ka yi mana zamu yi ba, kyautatawa ce daga gare mu, dan ƙara nuna martaba da daraja da duk wani ɗan Adam yake da shi, fari ko baƙi koma wani kalar launin fata ne. Ina ƙara amfani da wannan damar, gurin ƙara nuna ɗimbin godiyata a gare ki. Kin sadaukar kin jajirce, mun san bamu da abin biyan ki, amma ina kyautata miki zato da yi miki fatan alkhairi" Nana ta sunkuyar tana murmushi ta kasa magana ma. "Na ɗauki darussa daban-daban, a kan abubuwan da suka faru, komai sila ne, kuma wasu lokutan bawa baya samun ɗaukaka ko cimma nasara, sai an jarraba shi, wasu lokutan mai sauƙi, wasu lokutan kuma mai tsanani. Allah dai ya baku zaman lafiya na har abada. Shi kuma mai magani Sarkin baka ko? Ya ce yana nan tare da shi za a je Nigeria. Ɗan uwanki ma an ce mini yana Agadez yanzu haka, da Zahradeen ya kai shi karatu, zan saka a kawo mini shi nan, shi ma na yi masa godiya na ba shi haƙuri shi ma" Nana ta ce "Dan Allah Abie, ka duba girman abin da Imam Zahradeen ya yi, fiye da laifinsa ka yafe masa. " Yayi murmushi kawai ya ce "Za a duba" Hammad ma ya ci gaba da yi wa Sultan godiya, dan bai taɓa tsammanin zai yanke wannan hukuncin ba. Sultan ya ce Nana zata iya tafiya, bayan tafiyarta Hammad ya sake yi wa Sultan godiya sannan ya ce "Amma Abie hukuncin nan da ka yanke, ba zai janyo surutu da 'yan majalisar ka ba?" Sultan ya ce "Hammad, zan yi duk abin da nake ganin shi ne dai-dai, har abada na daina jiran wani ya sarrafa ni, duk abin da nake ganin shi ne daidai zan zartar da shi." Hammad ya jinjina kai yana sake gode wa Allah. Ya sake cewa "Amma Sultan meyasa ka ce na saki Asal?" "Me za ka yi da ita? Ko ba ka ji abin da ɗan uwanka ya faɗa sun haɗa kai da ubanta da Bilki suna neman ganin bayanka ba?" Hammad ya jinjina kai ya ce "Haka ne" "Amma idan kana son matarka, shikenan ba zan yi maka dole ba" Hammad ya ce "Ba na son aikata abin da za kalle ni a matsayin mara adalci, amma kamar ku ne ɓoye mini wani abu da kai da Maman Muhsin" Sultan ya sake yin murmushi ya ce "To idan ma mun ɓoye maka ai ba laifi muka yi ba, tashi ka yi tafiyarka" ***** Alhaji Fatuhu yaje dubiyar Doctor Sharif tare da Fadila da Suwaiba, sai dai ya tsorata da yanayin da ya gan shi a ciki, tun da ya ga Alhaji Fatuhu yake kuka, amma ya kasa magana, sai da kyar kamar an fizgo maganar ya ce "Ka yi hankali da Alhaji Zailani, kuma ka yafe mini dan Allah" Hakan ma ba komai ake ganewa ba, sai dai maganar ma bata fita da kyau, da kyar suka gane me yake cewa. Daga bisani suka tafi gidan Hajiya Sa'a, tana kwace a cikin najasa, Alhaji Fatuhu ya din ga yi wa masu aikinta faɗa, yana iƙirarin tun da komai ya fara daidaita, gidansa zai mayar da ita. Sai dai haka kurum ƙasan zuciyarsa ya din ga mamakin wani irin nau'in ciwo ne ake ta fama da shi haka. Maganar da Muhsin ya yi, yana ƙoƙarin karɓar wayar mamansa, ya sanya Hajiya Sa'a waiwayo wa da sauri ta kalli yaron. Ayshercool 08081012143 98 1K NE VIA 0069685771 AISHA ADAM STANBIC BANK 08081012143 Cikin mamaki Alhaji Fatuhu yake kallon Hajiya Sa'a, saboda yadda ta ƙure Muhsin da ido. Ya ce "Yaya Sa'a, kin gane ni? Ko Muhsin ki ka gane?" "Ba dole na gane wannan tsinannen yaron da Allah ya tsine wa albarka ba? In sha Allah sai ya mutu kuma kun rasa. Da shi ne ya mutu da Abbana bai mutu ba, ɗan nawa guda ɗaya na rasa shi, ku ga naku nan yana rayuwa " Cikin rashin fahimta Alhaji Fatuhu ya ce "Yaya Sa'a kin san kuwa me ki ke cewa?" Cikin tsawa ta ce "Na sani mana, na sani, ina sane. Yanzu ga Abba ya mutu a banza, ni kuma dodon ƙungiya ya shanye mini wasu sassan jikina." Gaba ɗaya ya yi iya ƙoƙarinsa gurin ganin maganganun da take yi, ba su yi tasiri a zuciyarsa ba. Ya dubi Fadila da ta takure a gefe, tana zare ido ya ce "Fadila, kar fa ku damu ko ku ɗaga hankalinku, kun san ba a hayyacinta take ba, tana fama da matsalar taɓin hankali." Hajiya Suwaiba ta ce "Duk da haka amma mutum ko ba shi da hankali, yana faɗar abin da yake aikatawa ne, amma babu rami mai ya kawo rami?" "Ƙaryata ni za ki yi kenan Suwaiba? Meye haɗin Yaya Sa'a da wani shan jini, kawai raɗaɗin mutuwar ɗanta ne yake damunta" Fafur ya hana su magana, tare da kare Sa'a, duk da ƙasan zuciyarsa maganar Hajiya Suwaiba ta kama zuciyarsa, da ta ce babu yadda za a yi Hajiya Sa'a ta yi wannan maganganu idan bata da alaƙa da su. ***** Imam Zahradeen ne zaune a gaban mahaifiyarsa Hajiya Bilkisu, cikin kuka take yi masa bala'i "Yanzu Zahradeen har zaka iya fifita bare a kaina mahaifiyarka, ka zaɓi ka tona mini asiri? Yanzu amfanin me hakan ya yi maka daga kai har ni. Duk fafutukar da na yi domin ka ne, amma a ƙarshe ka watsa mini ƙasa a idona. Ka lalata komai abin da nake harin ba zaka samu ba, saboda kai ne gwanin na iya da son burgewa, ka tona mana asiri ga shi kaima baka tsira ba" "Ban yi duk abin da na yi, domin tozarta ki ba Ammi, duk abin da na yi, na aikata ne domin kaucewa faɗa wa fushin Ubangiji. Bawa bai taɓa isa ya yi wa bawa abin da Allah bai yi masa ba. Duk ƙoƙarin ku Ammi idan Allah bai ƙaddara mu hau karagar nan ba ba zamu hau ba. A yanzu hakan ku nawa ne ku ke fafutuka, ko da an kawar da Hammad, kuma ba zaku samu zaman lafiya da fahimtar juna ba, kowa na sa yake son ya hau. Ammi Hammad fa shikaɗai ne ɗan uwana namiji... "Tashi ka bani guri, kafin baƙin ciki ya sanya na tsine maka, ka fita ka bani guri" Zuciyarsa cike da ƙuna ya tashi ya bar sashen ta. Murmushin fuskar Nana ya kasa ɓoyuwa, Ƙaisar shi ma murmushin ya yi, kamar koyaushe gyaran litattafansa yake yi. Ya ce "A karo na babu adadi, ina sake taya ki murna ma a wannan karon, tabbas ko a iya haka kin yi nasara. Kuma aya ce ke mai zaman kanta ga mutanen Agadez ba Agadez ba kawai ga duk wani mai hankali ma. Jaruma ce ke ta gaske uwar gijiyata" "Ƙaisar" "Na'am" "Ina yi maka kyakykywan fatan alkhairi na har abada " Ya ajiye littafin hannunsa ya ce "Har kin mantan Allah ya isan da ki ka yi mini a baya" Ta katse shi ta hanyar cewa "Duk wanda yake rinjayar da laifukan mutane, sama da alkhairinsu, to zai zama mara adalci" Ya ce "To ai ni ba mutum bane" Ta yi dariya ta ce "Ni a gurina kai mutum ne. Alkhairinka ya shafe laifukan ka Ƙaisar. Gaba ɗaya ji nake yi kamar ba ni ba, zan rayu da Hammad ɗina, da kuma Muhsin Allah abin godiya kamar komai ba zai wuce ba" Ya zauna yana faɗin "Babu abin da ba ya wucewa sai ikon Allah" Za ta yi magana ta farka daga baccin da ya ɗan ɗauke ta. Da Sayyid ta fara tozali ya ce "Amarya" "Ango" Ta amasa masa tana murmushi. "Nene ta ce sai na mayar mata da ke, wai shirya ki za a yi, ba dai yadda zan yi ne, na fi son ta bar mini ke in din ga jin ɗuminki. Ke ba kya buƙatar duk wani gyara, a gyarenki Allah ya yi ki" Nana ta tashi zaune ta ce "Allah ya shirya mini kai, Nenen zaka gaya wa haka ko? Ni sonake ma na gana da ɗan uwana na yi kewarsa" Hammad ya numfasa ya ce "Kin san Sultan sun samu matsala da Imam Zahradeen, ina ta girgiza miki kai ɗazu, ki bari sannu a hankali zai saukko zan san yadda zan yi na shirya su. Amma da farko ji na yi kamar ba zan yafe masa ba. Amma na duba girman abubuwan da ya yi na alkhairi a gare ni. Kuma ni duk mutumin da zai yi abin da zai kyautata miki to ni ya yi wa, dan haka na ji zan mayar da komai ba komai ba. Kin san wani abu ma vie" Ta girgiza masa kai alamar a'a. "Wallahi idan na kalle ki, na kalli Muhsin, sai in ji zan iya yafe wa kowa ma, Duniyar guda nawa take? Allah ya yi mini tagomashi da abin da na san ba dabara ta ba ce ba. Ba zan fasa gode wa Allah ba" Nana ta ce "Tabbas Allah abin godiya Sayyid. Amma ina da wani roƙo a gare ka; kamar yadda ku ka soke al'adar haramta auratayya tsakaninku da baƙaƙen fata, ina roƙon ku haramta duk wani nau'i na ta'amalli da Aljanu da shaiɗanu" Ta ɗan yi shiru tana satar kallonsa. Ya ce "Ina jinki" Ta ci gaba da faɗin "Ta'amalli da aljanu, da hana iliminku na addini tasiri a cikin rayuwarku, haɗi da riƙo da munanan al'adu su suka ƙara ta'azzara wasu abubuwan. Ga dai zobunanka masu ɗauke da hadiman aljanu, amma hakan bai hana a cutar da kai ba, cuta mai munin gaske. Su ba su baka kariya ba, su ba su hana a cutar da kai ba. Babu wata halitta da zata baka kariya ko ta hana faruwar wasu abubuwan a rayuwarka. Sai dai duk da wannan abin, ina girmama riƙo da ibadarka mussaman salla. Kai ma'abocin salla ne. Dan Allah Imam ka ƙara ƙoƙari gurin ganin an kakkaɓe al'adar amfani da aljanu a cikin harkar mulki. Ga saɓon Allah, ga gadar wa zuriya masifa da tashin hankali. Ni da kai ɗin nan mislai ne akan kanmu, ba zamu yi fatan ire-iren zuriyarmu su gaji wannan bala'in da muka shiga ba. Dan Allah Hammad ka yi ƙoƙari a yi yaƙi da ta'amalli da su, da kuma duk wani abu da ya shafe su. A ɗayanta Allah, a dogara da shi duk ba kwa buƙatar wannan abubuwan muddin kun riƙe Allah ". Ya numfasa ya ce "Maganganunki duk gaskiya ne Ma vie, kuma tuntuni na fara ƙoƙarin neman maraba da su, ni kaina na daɗe ba na son harkar da muke yi da su, amma in sha Allah zan ƙara ƙarfafa hakan, har abada za a daina amfani da duk wani nau'i na gurɓatacciyar al'ada a Agadez" Nana ta rungumo shi ta ce "Yauwwa farincikina, Ubangiji Allah ya saka maka da alkhairi, ya ƙara kare mini kai daga dukkanin wani sharrin. Allah ya ƙara ɗaukaka mini darajarka zuwa inda zato bai taɓa zato ba. Allah ya yi maka kyakykywan tsari daga sharrin duk wani abin ƙi komai ƙanƙantarsa." Ya tsurawa Nana ido, sannan ya ce "Ta yaya ake so na iya rayuwa babu wannan halittar? Halittar da harshenta kullum cikin yi mini addu'a da fatan Alkhairi take. Mai ɗauke da zuciyar da kullum take ƙoƙarin kusantar da ni ga Allah, baiwar Allah da kullum burinta ta sadaukar Saboda da komai saboda ni. In sha Allah mutuwa ce zata raba ni da ke rayuwata. Allah ya yi miki tukuci da gidan aljanna. Ina ƙaunrki Asma'u." Ya yi maganar yana tsare ta da manyan idanunsa, da ba ta san dalilin canzawarsu zuwa ja ba. "Nima ina ƙaunarka mijina, irin sosai da sosai, ban san ya zan misalta maka ba" "Ba sai kin misalita mini ba, na gani a zahiri" Ta sunkuyar da kanta tana ɗan murmushi. Ya ce "Yanzu me za ki shirya mana, na shirin bikin? Sultan ya ce sai an yi biki sosai a Agadez, me za ki shirya mana? Me da me ki ke so?" Ta girgiza kai ta ce "Kai kaɗai kawai nake so, kai kaɗai ka ishi Nana komai" Ya yi dariya ya ce "Zan kawo miki Imrana da Muhsin, har ma da Nene anjima su ɗebe miki kewa" Nana ta ce "Amma kuwa da ka kyauta, na gode sosai da sosai" Ya dungure mata kai yana murmushi. ***** Alhaji Fatuhu kuwa bacci ne ya gagare shi, kamar yadda dariya ta gagari kare, ya gagara yin bacci. Idan ya samu baccin ya fara ɗaukarsa, kawai sai ya ga Hajiya Sa'a, tana kuka tana sake maimaita abin da ta faɗa da suka je. Duk yadda ya din ga addu'a, da ƙoƙarin kawar da tunanin daga zuciyarsa, amma abu ya faskara. Sai dai ya danne ya ci gaba da addu'a. Sai kuma doctor Sharif ya faɗo masa, da shi ma yake cewa ya yafe masa, to ya yafe masa da ya yi masa me? Gaba ɗaya sai al'ajabi, ya hana shi yin farincikin dawowar kayansa. Ga shi ya zo gaya wa Alhaji Zailani,  tun da dama shi ne abokin kasuwancinsa, amma ya tuna yadda Fadila ta gargaɗe shi a kan haka. ***** Sagir kuwa tun da yaje Abuja gidansu Yusra, hankalinsa ya ƙara tashi. Jaririn da ya gani da shi yake kamanni, ya yarda jaririn nan ɗansa ne, amma babu yadda ba a yi da Yusra ta yi magana ba, ta faɗi a ina ta haɗu da Shukura ba. Sai dai ana ta ba wa jaririn madara. Sagir ya ce wa mamanta "Ina ga, zan koma Kano na samu iyayen Shukura na sanar da su cewar, an ga jaririn Shukura" Maman ta ce "A'a kar ka faɗa tukuna, kar a zargi Yusra da wani abu, a ci gaba da addu'a dai da bincike, haryanzu Yusra bata cikin nutsuwarta. Haka ya din ga sintiri tsakanin Abuja da Kano, ga shi ya kasa gaya wa kowa, saboda shi kansa ya san ayar tambaya za a saka wa Yusra. Sai dai al'amuran Yusran su na ba shi tsoro shi kansa, banda yana sonta kuma ya san halin da ta shiga, lokacin da Shukura ta ɓata, da babu abin da zai hana ya ce da sanya hannun Yusra a lamarin ɓatan Shukura, idan ba haka ba a ina ta samu jaririnta? **** Labari ya cika ciki da wajen Agadez, kan cewar Hammad yana da ɗa, ya auri 'yar Nigeria, haka zalika an soke Al'adar hana auren baƙar fata. Wasu daga cikin al'ummar garin hakan yayi musu daɗi, mussaman baƙaƙe, da suka din ga jin tamkar su zuba ruwa a ƙasa su sha. Ɓangaren fararen buzayen kuwa, gani suke yi tamkar rage musu kima ne, da kuma rage karsashin Masarautar. Cikin marasa gaskiya a fadar Sultan kuwa, cikinsu ya ɗuri ruwa cike da tashin hankali, saboda tsoron hukuncin da ka iya biyo bayan tonuwar asirinsu. Ga shi Sultan ya ƙi nuna musu ya san su ne, kuma tun daga ranar da aka kawo bokan nan fadar Sultan, ba a sake zaman majalissar ba. Waɗanda ba su san Nana ba, suka din ga sintirin gidan Sultan, su na son ga Nana, amma Nana na kauwwame a sashin Sultan. Tuni labari ya ishe Asal, wanda hakan ya sake gigitata,  tamkar za ta yi hauka. Wani irin so da matsanancin kishin Hammad ya din ga taso mata, ji take yi tamkar za ta yi hauka. Gani take yi ta ƙasaƙanta ta tozarta, a ce Nana ce kishiyarta, matar da ta ɗauka tamkar baiwar da ta saka kuɗi ta saya, amma yanzu ita ke da komai, ita kuma tana gefe ta zama 'yar kallo. Wasa-wasa Asal ta daina cin abinci sai kuka, ga Tafawa ba ta ita yake yi ba, ta zaman jiran tsammanin abin da za a yanke musu kawai yake yi. Duk matsanancin kishin Hammad, haka ya ƙyale Nana da Imarana, suka kasance tare suna ta hira irin ta 'yan uwantaka, tare bawa junansu labarin gwagwarmayar da suka yi ta rayuwa. Ya ce "Bari na nuna miki wani abu" Imarana ya ɗan tashi ya fita, sannan ya dawo, ko da ya dawo ya miƙa wa Nana waya. Nana ta karɓi wayar tana kallonsa, ya yi mata alama da ta saka a kunnenta. Nana ta saka wayar a kunnenta, zuciyarta na ɗan bugawa da sauri. "Assalamu alaikum, Nana" Muryar Ummansu ce ta doki dodon kunnuwanta, a wani irin rikice Nana ta tashi tsaye, ta rasa ina zata dosa ta ce "Um..umma, muryarki ce ke ce?" "Nice Nana, kina nan lafiya?" Nana ta durƙushe a kan gwiwoyinta, ta ce "Umma, bani da bakin da zan yi miki magana, bani da idon da zan iya kallonki, ni mai tarin laifi ce" "Shhh, Babu abin da ki ka yi mini na ba dai-dai ba Nana. Sai dai tashin hankali da fargaba na shige shi, na rashin sanin inda ki ke, da kuma wani hali ki ke ciki, ga tsohon ciki kin tafi kin bar gida. Amma Imrana ya zo inda nake, tare da Yayan mijinki, sun yi mini bayanin komai. Nana na yi sujuda na gode wa Allah, ba wai domin daular da ki ke ciki ba, ko kina auren wani ba, sai domin murnar kina cikin ƙoshin lafiya tare da ke da yaronki. Sun ce kar na gaya wa kowa, babu wanda ya sani, amma sun zo sun yi mini alkhairi Imrana ya zama babban mutum ya nutsu, kema hankalinki yana kwance. Ni dai fatana su yi su kawo mini ke, ko na wanko ƙafata na taho,amma sun ce na yi haƙuri kaɗan" Cikin kuka Nana ta ce "Ni dai ki yafe mini dan Allah, tashin hankalin da na sanya ku a ciki, dan Allah ku yi haƙuri Umma" Imrana ya karɓe wayar ya ce "Umma sai anjima, da na sani ban haɗa ku ba, nema take ta rikice" **** Hajiya Amina tana zaune tare da Alhaji Zailani, tana ta lallaɓa shi a kan ya ci abinci, amma ya ƙi ci, saboda shikaɗai ya san bala'in da yake ciki. Tun da ya yi mafarkin an huda saitin zuciyarsa, dodon ƙungiya yana sha masa jini, ya farka ya ji saitin zuciyarsa ya yi masa wani irin nauyi. Ga jikinsa sai yi masa wani irin raɗaɗi yake yi, kamar ya yi wanka da yaji. Yana jin yadda wayarsa take ta ringing amma ya ƙi ɗagawa. Daga ƙarshe, Hajiya Amina ta saka hannu ta ɗauki wayar, ta saka a kunnenta tana sallama. Jin ta yi shiru ya sanya Alhaji Zailani ɗagowa ya kalle ta, sai dai ta tsare shi da idanunta ba ta ce masa uffan ba. Jiran Hajiya Amina yake yi ta yi magana, amma ta yi shiru ba ta yi magana ba. Jiki babu ƙwari ya ce "Ya dai? Meyafaru?" Jiki a sanyaye ta ce "Daga makarantar su Yusuf ne, wai yana kwance a Asibiti babu lafiya, yau kwana uku kenan" Ya waro ido ya ce "Yusuf ɗin?" Ta jinjina masa kai. "Ki kira su ki gaya musu, ni ba ni da lafiya, babu lallai na iya driving su dawo mini da ɗana gida" Hajiya Amin ta jinjina kai tare da mayar da hankalinta  kan wayar. ***** Gidan Baba ya zama tamkar maƙabarta, babu walwala ko kaɗan, ko ƙaunar tunkarar gidan baya son ya yi. Saboda matsananciyar damuwa, da takaicin abubuwan da suke faruwa a gidan. Jamila kuwa kullum tana ɗaki, dan ta sha baƙar azaba, sai da ta kwana tara a Asibiti, da kyar aka samo kanta kamar ba zata rayu ba. Ya daina shiga harkar Mama da yaranta gaba ɗaya, ko abincin gidan ya daina ci. Ga damuwa da kewar yaransa Nana da Imrana da suka addabi zuciyarsa. Ya fito daga cikin gida da buta a hannunsa, ya yi alwalar sallar Azahar sai ga wata danƙareriyar mota irin ta matafiya, sabuwa gal sai ƙyalli take yi ta shigo layin. Bai damu ba, ya idar da alwalarsa ya ɗaukko wayarsa, yana son kiran can Buda, saboda yaga kiran wayarsu, bai samu ya ɗaga ba. Sai ya ga motar nan an tsaya da ita a ƙofar gidan. Sai ya yi tsuru yana kallon motar. Sulei ne tare da Mahmoudu suka fito, suka nufo Baba. Ya tsaya saroro har suka ƙaraso inda yake. Suka durƙusa har ƙasa suka gaishe shi, ya amsa musu yana bin su da kallo, kasancewar sun rufe fuskokinsu da takunkumi. Bayan sun gaisa, Mahmoudu ya ce "Baba mu na tare da baƙi ne daga Agadez" Baba ya ɗan yi shiru, shi dai ya san babu wanda ya sani a Agadez, amma ya miƙe ya ce "To bari na kawo muku abin zama" Ya tashi ya shiga cikin gidan, ya ɗaukko tabarma ya shimfiɗa musu, ya koma ya aiki Nasiru ya sayo ruwa. Ya zata iya su Mahmoudu ne baƙin, kawai ya ga Sulei ya je ya buɗe motar, wani dogon mutum mai jiki ya fito da wani matashi, shi ma sanye da rawani suka fito, suka nufo shimfiɗar. Shi dai Baba duk abin ya ɗaure masa kai, tsoro ya shige shi. Ya yi musu barka da zuwa, suka zazzauna, Mahmoudu ya sauke rawanin fuskarsa ya ce "Baba baka gane ni ba?" Baba ya yi shiru ya ce "Kamar dai na sanka, amma ban gane ka ba" Imam Zahradeen ya sauke rawaninsa shi ma, shi ma dai Baban ya yi masa kallon sani. Mahmoudu ya ce "Baba kamar baka gane mu ba ko?" Baba ya ce "Gaskiya dai" "Baƙi ka yi daga Agadez" "To bawan Allah, ni wa nake da shi Agadez, kuma ba ɓatan kai ku ka yi ba?" Mahmoudu ya ce "Ba mu yi ɓatan kai ba, na yi mamaki da ka ce ba ka gane ni ba, amma ai ka tuna buzun da ka aura wa 'yarka shekarun da suka gabata" A razane Baba ya ɗago ya kalli Mahmoudu, sai kuma ya riƙe rigarsa, ya ce "Dama ku ne? Ba ku yi mini adalci ba, ku ka tattara ku ka gudu, ku ka bar mini 'ya da jinyar ɗan uwanku, shi ma daga ƙarshe ya gudu ya bar ta, saboda wauta da rashin hankali wai ta tafi Niger neman shi, haryanzu shekara ta uku kenan, babu wanda ya san inda take, baku kyauta mini ba" Baba yayi maganar yana kuka kamar ƙaramin yaro. Imam Zahradeen ya ce "Baba, ka yi haƙuri abubuwan da suka faru ba a kyauta maka ba. Amma mu na da kyakyawan albishir ne" Baba ya ce "Kai ba kai ne mijin nata ba?" Yayi maganar yana nuna Imam Zahradeen. Zahradeen ya ce "Baba ai na fi wancan tsufa, shi ya fi ni ƙuruciya, ya kuma fi ni kyau, ni yayansa ne. Zancen da nake yi maka, a kowane lokaci mahaifinmu zai iya aiko da mutanensa daga Agadez da kayan auren Nana za a sake gagarumin bikin aurensu" Baba ya ce "Ashsha! Yarinyar da nake gaya muku shekara uku babu wanda ya san inda take, kuma babu wanda ya waiwaye ta tunda ku ka gudu kuka bar ta. Kuma ni mene ne haɗina da Sarkin Agadez da zai kawo kayan aure? Ni dai na yi nadamar abin da na aikata na aurar da 'yata ga mutumin da ban san daga inda yake ba" Imam Zahradeen ya lura ran Baba a ɓace yake. Ya sassauta murya ya ce "Baba sunana Imam Zahradeen Jalaludeen Agadez, ni Yaya ne ga Imam Hammad Jalaludeen Agadez. Kuma 'ya'ya ga Sultan Jalaludeen Agadez, wato Sarkin Agadez na yanzu. Buzun da ka aura wa 'yarka, ɗan uwana ne, kuma  ɗa ne ga Sultan na Agadez." Baba ya kalli Imam Zahradeen kamar yana raina masa hankali. Ya ce "Ɗan sarki ne zai zo baro ƙasarsa ya zo Nigeria yana aikin gadi?" Mahmoudu ya ce "Baba, idan baka manta ba, ko lokacin da aka yi aurensu, a yanayi na rashin lafiya yake,  rashin lafiya ce ta kama shi" "To yaya za a yi a ce ɗan sarki ya zo Nigeria gadi, ni abin ya bani mamaki ne. Kuma na kasa yarda, ni kar ku sake dugunzuma mini hankali bayan halin da nake cikix Zahradeen ya ce "Baba ba dunguzuma maka hankali za mu yi ba. Mun zo mu sanar da kai batun zuwan baƙinka ne daga Agadez, kafin su zo ɗin." "To wai su zo, su yi mini me?" " 'yarka Nana, tana gurinmu tare da ɗanta Muhsin" Baba bai san ya aka yi ya tashi tsaye ba, yana zazzaro ido ya ce "Nana Asma'u dai 'ya ta? Yaya aka yi ku ka same ta? Tana ina? Kun taho mini da ita?" Mahmoudu ya miƙe tsaye ya ce "Baba shi ne bayanin da muke yi maka, Nana tana tare da mu, za a kawo dukiyar aurenta Nigeria za kuma a yi bikin aurensu sosai da sosai. Duk abin da za mu gaya maka yanzu ba za ka fahimce mu ba, saboda a cikin damuwa ka ke, kuma abubuwan da suka faru su na da tsawo da sarƙaƙiya akwai buƙatar a yi maka bayani daki-daki. Ba Nana ba hatta Imrana yana tare da mu a Agadez, akwai tarin bayanai da sai ka nutsu, an yi maka bayani zaka fahimce su" "Amm bawan Allah, ni ko yanzu a shirye nake, mu tafi Agadez ɗin na karɓi 'ya'yana. Bayan Nana kuma me ya haɗa ku da Imrana" Imam Zahradeen ya ce "Alkhairi ne, a cikin satin nan, zuwa mai kamawa in sha Allah; za a sake turo maka baƙi daga can. Kuma za a yi bikin su al'ada saɓanin yadda ya gudana, kuma za a yi maka bayani kamar yadda nake nanata maka. Amma kafin nan mu na son za a gyara maka gidan nan, ko kuma a canza maka wani" Baba ya girgiza kai ya ce "Ba na buƙatar haka, muddin Nana yake so, babu amfani a raina inda ta fito, ni dai fatana na gansu cikin ƙoshin lafiya" Zahradeen ya ce "Ba raina maka aka yi ba, matsayinka da girmanka ne ya sanya za a yi maka." Fafur Baba ya ƙi yarda da hakan, da kyar suka rarrashe shi suka tafi, dan cewa ya yi ba za su bar ƙofar gidansa ba, ba tare da ya ga yaransa ba. Kasancewar duniya makarantar da ko babu malami, ta biya maka darasi dole ka ɗauka ce, ta karanta wa Baba darasin da duk son abin Duniyarsa, yanzu tsoro yake ji. Zuwansu Imam Zahradeen babu wanda ya sanarwa, saboda gani yake yi tamkar ƙarya Buzayen nan suka zo suka sharara masa. Ya kasa gaya wa kowa, sai Uwani ya kira ya sanar mata. Sai dai a ƙarshen maganar Baba ya ce "Amma Uwani ni ban ji na yarda ba, ji nake kamar ƙarya kawai suke yi ban ji na yarda ba" Uwani ta ce "Alhamdillah, ni dai na ji na yarda har cikin zuciyata. Ko ba hakan ba ne, ina fatan Allah ya tabattar da shi ya zama gaske. Wallahi zuciyata ta daɗe tana bani, mijin Nana ba ƙaramin mutum ba ne, to ita Nanan da gaske tana gurinsu, kuma har da Imrana sun haɗa ku ko a waya ne?" Ya ce "A'a, shiyasa na kasa yarda ma gaba ɗaya" "Isa, yarda ni dai na gama ta, zamu duƙufa mu ci gaba da addu'a in sha Allah Nana suna cikin kwanciyar hankali tare da ɗan uwanta" Kalaman Uwani suka ɗan ƙwarara wa Baba gwiwa. Bayan sallar isha'i ya shiga gida, yana zaune yana jin radio, Mama tana cikin ɗaki tare da Jamila da ta koma so silent, ko magana ba ta iya yi. Ihun da Jamila ta yi ne, ya sany Baba jifa da radio ya tashi tsaye yana rarraba ido. "Mama! Mama!! Dan Allah ki taimake ni, dodon ƙungiya zai shanye mini jini. Hajiya Sa'a kin cuce ni, kin cuci rayuwata, na kasa samun aminci da salama. Na baku Abba me kuma ku ke nama a gurina?" Cikin rashin fahimta duk suke kallon Jamila, Baba ya ce "Me yarinyar nan take faɗa ne haka?" Mama ta ce "Nima ban sani ba wallahi, ina ga jikin ne ya motsa." Baba ya ce "Jikinta ya motsa kuma take irin wannan maganganun?" Ba ta ko saurare su ba, ta ci gaba da surutanta. "Ni ban so shiga kungiyar nan ba, dole ki ka yi mini, ga shi kin sanya ni a bala'i, na rasa mutuncina, kin saka nayi kisan kai, yanzu kuma na kasa samun kwanciyar hankali, sai tsorata ni ake yi, nima ana nema na a kashe ni, kin cuce ni" Baba ya ce "Jamila, meyafaru ne? Me ki ke faɗa wai?" "Baba riƙe hannuna, Baba ku taimake ni" Ya ƙarasa ya riƙe hannun Jamila, cikin kuka ta ce "Baba na shiga uku, na aikata mummunar ɓarna, Baba hakki ne zai yi ajalina" Baba ya ce "Jamila, ki gaya mini, me ki ka aikata?" "Ƙungiyar asiri, Baba ƙungiyar asiri aka shigar da ni, saboda na kai jinin Nana" Kamar ta watsa wa Baba wuta, haka ya fizge hannunsa ya ja da baya, yana kallon Jamila da take ta uban kuka. Mama ta ce "A'a baban su Jamila, dan Allah kar ka yarda da abin da ta faɗa, ka san ba ta da cikakkiyar lafiya, wataƙila zafin ciwo ne, amma wace irin magana ce wannan, a ina Jamila za ta ga wata kungiyar asiri ta shiga" Alhaji Zailani ne a durƙushe a gaban gawar ɗansa Yusuf, bayan an dawo da shi daga makaranta, dama babu rai aka dawo da shi. Ba shi ne abin da ya ɗaga masa hankali ba, sama da ganin busashshen jini a baki da kuma hancin Yusuf. Ba dan ya yi iya ƙoƙarinsa ba, da tuni ya aikata abin da zai fallasa kansa. Wani irin raɗaɗi da zafi ya din ga ji a zuciyarsa ya kasa magana, ya kasa ko ƙwaƙwƙwaran motsi. Ba a jima ba, gidansa ya cika da jama'a, Hajiya Amina sai kuka take, ga Shukura ta ɓata, ga kuma mutuwar Yusuf. Ya hau neman lambobin yaransa, da ya sanya su kashe Shukura, a kan kar su kuskura su kashe ta, amma ya kasa samun su. Duk da daɗewar da yayi yana aikata zalunci kala-kala, mutuwar Yusuf ta dake shi, ta tsaya masa. Ya din ga jin tamkar ya yi ta kururuwa yana burgima, ko zai ji daɗi. Ko da aka yi jana'izar Yusuf, Alhaji Zailani tafiya ya yi ya kulle kansa a ɗaki. Kaf yaransa babu kowa sai Shukura yanzu, Shukuran ma ba a san inda take ba. Kuma ita ma baya tsammanin za ga tsallake sharrin dodon ƙungiya, tun da ya gaza bashi jinin shekara. Sosai ake ta shirye-shiryen gudanar da bikin auren Imam Hammad, da matarsa 'yar Nigeria. Ita Nana abin har mamaki yake bata. Tun da Sultan ya amince da auren Nana da Sultan, Nene take sintiri kawo wa Nana kayan gyaran jiki. Ban da matar da ake ware mussaman Nene take zuwa da ita, take yi wa Nana wani irin gyaran jiki na mussaman. Nana ta ce "Nene duk wannan abin fa ihu ne bayan hari" Nene ta ce "Ke, gyaran ne ba kya so?" "To Nene ya riga ya sanni a yadda nake, me kuma zan gyara?" Nene ta ce "To kar ki gyara, komai yana buƙatar gyara ai" Aka ajiye wa Nana kayan sakawa, da na ado irin na Buzaye. Nana ta ƙudurce a ranta, bayan ta tare, kayanta na 'yan Nigeria za ta saka Hammad ya ajiye mata, saboda ita ma tana son tata al'adar. Shi kansa Hammad ya so a ƙyale masa ita a haka, dan shi komai nata ya yi masa. Sai dai gyaran jikin da ake yi matan ba ƙaramin kyau take yi ba. Ga shi tare da Muhsin suke kwana da Nene, hakan ya ƙara sanya ta farin ciki. Hammad ya ce ta fita ta ɗan zagaya, amma ta sanya takunkumi ta rufe fuskarta. Har mamaki Nana take yi, yadda idan Muhsin ya ga raƙuma ko shayi, kamar zai tashi sama saboda murna. Sarkin baka ta hango, suka nufe inda yake. Cikin jinjina ya ce "Barka da tattaki uwar gijiyata" Nana ta yi dariya ta ce "Dan Allah ka daina kunya ka ke bani" Shi ma yana murmushin ya ɗago ya kalli Nene, ya ce "Ni kuwa dama ina ta son na yi miki magana, Allah bai yi ba" Nene ta ce "Ni ɗin ko? Ka sanni ne?" Ya ce "Eh, ai duk inda muka ga juna, muna gane kanmu" Ta yi dariya ta ce "Na ji, ai ban yi zaton haryanzu akawai abin da tattare da ni ba" Sarkin baka ya ce "Ni na ji na gane ai. Kuma ni ɗalibin marigayi Sa'adu Aska ne" Nene ta waro ido ta ce "Kana nufin Babana?" Sarkin baka ya ce "Ƙwarai da gaske, ya sanar da ni magunguna, sai muka kwana casa'in tare da shi, a mabanbantan dazuzzuka, daga bisani muka rabu, ban sake ganinsa ba. Mahaifinki mutumin kirki ne, ba zan manta da shi ba har abada" Nene ta ce "Ikon Allah" Nana ta ce "Sarki kai komai ma ka sani ne? Kuma kowa ya sa ka" Yayi murmushi ya ce "Na san dai abin da Allah ya sanar da ni, kowa ya sanni kuma na sha yawon duniya ne" Yayi maganar yana ɗaukar Muhsin. Nana ta ce "Sarki ka ga Nene ta daina harkar bayar da magani, kaima ina fatan zaka daina?" Ya ce "Meyasa zan daina? Ba a daɗe ba ni ba, ke kanki ki ka bayar da magani zan ce, ko ba ke ki ka tono inda aka yi wa mijinki asiri, meyasa Allah ya zaɓe ki ya nuna miki, duk yawan jama'ar da ke ƙasar nan. Abin da ki ke ta gudun sai da ya faru" Jiki a sanyaye Nana ta ce "Ba ina nufin ka daina bayar da magani ba, ka daina aiki da aljanu, shi ne ɓarnar. Sannan ka yi ilimi na zamani, cikakke domin ka inganta harkar maganin naka. Ya zamana maganunnanka da awo kar ka bayar da abin da zai cutar maimakon a samu lafiya" Yayi dariya, Nene ma ta yi, Ya ce "Yaro yaro ne. Nana a dalilinki wallahi na daina surkullen haɗa ayoyin Alkur'ani da wasu abubuwan na yi sihiri. Saboda uban gidana ma, Allah ya ja zamaninsa uban duƙusa ko in ce Ƙaisar, shi ma ya ce na daina wannan, na kuma daina. Na daina surkulle da sihiri na tuba, amma ba zan iya daina aiki da aljanu ba" Nana ta ce "Amma saboda me?" "Saboda ɗebo mini magani, wasu ayyukan kuma dole su ne nake aikawa su yi wani aikin." "Sarki, ta'amalli da aljanu da ka ke yi ba shi da wani alkhairi shirka ne, dan Allah ka daina. Kana cikin mutanen da nake son mu tsira Duniya da lahira." "Ni ba ni na nemi aljanu na fara aiki da su ba, aljanu su suka takura ni, kamar dai ke da kuma wannan baiwar Allah. Bana ta'amalli da aljanu, na bayar da kuɗi, ko na yi wa wasu sihiri, ko wani abu makamancin haka, ai kin je gurin maganin nawa kin gani" Nana ta ce "Sarki, kar mu shiga wani bugire da bai kamata mu shiga ba, mu kalli gaskiya kai tsaye kar mu yi mata wata kwaskwarima saboda son zuciyarmu" "Asma'u babu kwaskwarima domin ba wa ƙarya kariya a maganganuna. Su turawan da ku ke taƙama da su, su na amfani da ku, da daƙile magungunnku ne, saboda gina nasu kasuwancin. Kuma Nana magunguna na da awo nake bahar da su. Ban ƙi ba akwai masu bayar da magani, saboda neman abinci. Amma wanda ya sani ya sani, wanda bai sani ba, bai sani ba kawai. Kuma banda abin ki tun a zamanin baya magungunan 8su na da awo, wani a ce ka auna da ɓawon gyaɗa,ko farce, wani a ce ka sha safe da yamma, duk sharri ne wasu abubuwan da ake faɗa, da ƙoƙarin kashe mana magungunanmu. Sai a  ce ku daina shan magungunan gargajiya saboda ɗaci, hanta ba ta son ɗaci, amma Allah ya halicci maɗaciya a tsakiyar hanta. Idan hanta ba ta son ɗaci, Allah ba zai sanya matsarmama a cikin hanta ba. Kuma su magungunan baturen, ba ɗaci ne a cikin su ba. Ba zan kushe wa kowa ba, amma kar a kuskura a kushe mini nawa. Yakamata mu daina wannan musun haka,kowa ya riƙe abin da yake ganin shi ne dai-dai " Nana ta ɗan yi jimm tana tunani, daga bisani ta ce "Wasu maganganun naka na kan dai-dai, amma kowa ya riƙe abin da yake ganin shi ne dai-dai!" "To ki daina takura mini a kan lallai sai na yarda da abin da ki ke kai" 99 1k ne via 0069685771 Aisha Adam stanbic 08081012143 Har Nana za ta sake magana, Nene ta riƙo hannunta, ta ce "Nana mu koma ciki, ai kin ɗan tattaka, kin san baya son a ganki, ko a gane ki a yanzu. Ɗan uwa idan muka kuma haɗuwa zamu tattauna sosai mu gaisa. Sosai shirye-shirye suka yi nisa, hankalin Sultan gaba ɗaya ya koma kan shirin zuwa Nigeria da bikin da za a gudanar. Sai dai yana ta fuskantar ƙalubalanta a kan hukuncin da ya zartar. Gimbiya Bilkisu ta rasa inda zata sanya kanta, ta tuntuɓi Tafawa ta sanar masa da matakin da Sultan ya ɗauka a kanta, amma ya ce mata shi ma ta kansa yake yi, hankalinsa a tashe yake. Duk yadda ta kai ga ƙoƙarin yin dabarun da Sultan zai saurare ta, fafur ya ƙi ko kallo ba ta ishe shi ba. Ranar ƙarshe ma da ta je ɗakinsa kamar zai dake ta ya ce "Bilkisu bana ƙaunarki bana ƙaunar ganinki, tun da har za ki yinƙurin sabauta mini rayuwar ɗa, idan ki ka sake zuwa inda nake, sai na yi miki abin da baki taɓa tsammani ba, fice ki bar mini ɗaki kafin na yi miki illa" Abin ya ɗaure mata kai, bata taɓa tunanin zai yi irin wannan fushin har haka ba. Jamila ta koma gata nan gata nan, ita ba mahaukaciya ba, ita ba mai hankali ba, kuma ita ba mara lafiya ba. Shi Baba gaba ɗaya ma yanzu tsoro suke ba shi. Ya riƙe istigfari ba dare babu rana, gaba ɗaya yaransa sun watse babu wani na kamawa. Gaddafi ya zo gida, ya tarar da gidan nasu duk wani iri. Yayi mamakin ganin yadda Jamila ta wani rakwakwkwaɓe, jiki babu ƙwari, ta yi wata irin muguwar rama ta fita daga hayyacinta kamar ba ita ba. Sun dawo daga sallar Asuba, tare da Baba, Baba ya numfasa ya ce "Gaddafi ka ga yadda Allah ya yi da gidanmu ko? Gaba ɗaya babu wani mai ɗan dama-dama" Gaddafi ya ce "Na gani Baba, ina son na yi magana dai na fasa, na ga Suwaiba ta daina magana gaba ɗaya, har da dalalen yawu take yi. Jamila kuma na kasa gane abin da yake damunta" Baba bai ɓoye masa komai ba, jikin Gaddafi ya din ga tsuma, ya dubi Baba ya ce "Baba, Jamila ta yi ciki, kuma tana maganar ƙungiyar asiri? Innalillahi wa Innalillahi raji'un" Cikin matsananciyar damuwa Bab ya ce "Babarta ta ce zafin ciwo ne, amma na kasa yarda nima" Ya yi maganar yana zubar da hawaye. Gaddafi ya ce "Shiyasa Baba na din ga maganar kuɗin da ta din ga ta'amalli da su, amma mahaifiyarta ta nuna ba ta so, ta nuna baƙin ciki nake yi, da ci gaban Jamila ka ga irin abin ko? Shikenan sun lalata mana gida" Baba ya yi kuka ya ce "Ina kyautata zaton hakkin yaran nan ne, su Nana, dan sai daga bayan nan, nake duba wasu abubuwan da na aikata musu na ga sam babu adalci a cikinsa. Amma wasu mutane sun zo wai daga Agadez sun ce mini tana gurinsu" Nana Baba ya gaya wa Gaddafi abin da su Mahmoudu suka zo masa da shi. Gaddafi ya rikice ya ce "Baba kuma baka karɓi lambar wayarsu ba ko ka bi su ba?" Baba ya girgiza kai ya ce  "Ban karɓa ba, ni tsoro ma na ji, ji nake kamar ƙarya suke yi. Na bar wa Allah ikonsa" "Amma Baba akwai mamaki a cikin abubuwan da suka faɗa, masu sarƙaƙiyar gaske" Baba ya ce "To ai shiyasa ban ma gazgata ba, sai abin da hali yayi" Gaddafi ya ce "Ba wani abu, in sha Allah mu tsammaci alkhairi" Baba ya jinjina kai cike da gamsuwa. **** Nana ce a tsaye, tana kallon Ƙaisar, yana zuba wa wata tsuntsuwa abinci a cikin keji. Nana ta kalli tsuntuwar ta ce "Ƙaisar ita kuma wannan fa, a ina ka samo ta?" Ba tare da ya kalli Nana ba ya ce tsinto ta na yi a daji, za ta mutu, ban zaci ma zata rayu ba, sai kuma na ga ta farfaɗo yanzu ta ware ma" Nana ta ƙarasa gaban kejin ta zauna, sannan ta ce "To kuma tsuntsuwa ce ita, ko kuma aljana ce?" Ya kalli Nana ya ce "Dama akwai tsuntsu mutum da aljan ne?" Nana ta ɗan yi shiru tana kallon tsuntsuwar. Ya ce "Mutum jinsinsa daban, aljani daban, haka ma tsuntsu daban. Babu Aljani tsuntsu sai dai Aljani ya shiga jikin tsuntsun, ina fatan kin gane?" Ta gyaɗa kai, ta ce "Haka ne, wai ni kuwa Ƙaisar ina Haulat? Ka fara son nata?" "Ban sani ba" Ya yi maganar yana hararta. Nana ta yi murmushi ta ce "To shikenan kai ba zaka yi aure ba kenan? To sonta ne baka yi ko kuma me ta yi maka?" Yayi mata shiru, yana rufe kejin tsuntsuwar nan. Nana ta numfasa ta ce "Ƙaisar ina kewar gida fiye da tunani, zuciyata kuma ta cika da fargabar rashin sanin abin da zan je na tarar. Ina jin kunyarsu ban san da wani idon zan kalle su ba. Duk da Imrana ya haɗa ni da Mama, ta yi mini Addu'a ta ce na kwantar da hankalina, amma kunyarsu nake ji ban kyauta ba abubuwan da na yi" Ya ce "Za ki tarar da alkhari in sha Allah, da abun da zai yi miki daɗi da wanda ba zai yi miki ba. Ni na din ga shagaltar da ke daga tunaninsu, da tunaninsu ya yi tasiri a zuciyarki, da ba ki cimma wannan nasarar ba, da kin rushe komai, dan idan ki ka koma gidan babu abin da zai canza" Cikin mamaki Nana ta kalle shi ta ce "Ban gane ba, kai ne ka sanya na daina jin damuwar da na din ga ji a baya, da son komawa gida?" "Sosai, saboda ruhi ne mu, mu na iya shiga ko ina a jikin ku, kuma muna iya hargitsa tunani da sanya muku rashin nutsuwa" Ta yi shiru tana nazari, ta sake cewa "Ƙaisar ka sanya ni a fargaba, abin da zan tarar a gida da gaske mara daɗi ne? Kodayake ko ka gaya mini ma idan na tashi na san mantawa zan yi sai abin da na je na tarar kawai" "Kin yi zaton da mugunta kawai nake nuna miki abu na mantar da ke ko?" Nana ta jinjina kai. "Ba haka ba ne, duk da ta wani fannin haka ɗin ne, muguntar ce da takaicin ƙin yarda da abin da na zo miki da su. Mafarki ya kasu kashi-kashi, duk da shi ma ina kan bincike a kansa. Akwai mafarkin da yake daga Allah ne, akwai mutanen da akan yi wa ishara a cikin bacci, na kusantowa ko kuma faruwar wani al'amari da bai faru ba kwata-kwata. Wasu kuma a nuna musu makamancin abin, wasu kuma su ga abu a duƙunƙune sai an fassara musu. Galibi waɗanda aljanu ke nuna wa mutum a mafarki, na haɗin faɗa ne. Abu ne da aka yi shi a bayan idon mutum bai san an yi ba, sai su nuna masa. Kuma ba su fiye nuna abin alkhairi ba sai akasin haka. Wasu idan sun gani su na iya shiru da bakinsu, wasu kuma basa iyawa sai sun faɗa. Sai su sanya a din ga yi wa mutanen wani kallo na daban, wasu a dole dalilin hakan kan sanya su fara bayar da magani. Ke na biyo miki ne ta hanya mai sauƙi, saboda bana son tilasta miki, na fi son ki amince da kanki. Sai na nuna miki abin da ya faru da baki sani ba, ko kuma wanda yake shirin faruwa, ko wanda nake hasashen abu ne mawuyaci bai faru ba. Akwai abin da idan na ƙyale ki, ki ka tashi da shi a ƙwaƙwalwarki, ba za ki iya yin shiru ba, za ki yi yinƙurin ɗaukar mataki, wanda hakan ka iya haifar da fitina, saboda idan ki ka haifar da matsalar ba ki da maganinta, tun da ba ki amince da bayar da magani ba. Ɗan Adam kuna da nau'in ciwo na gangar jiki, da kuma na ruhi, amma ba kwa damuwa da ciwon da yake damun ruhinku, kun fi damuwa da na gangar jiki. Mutum zai iya kashe maƙudan kuɗaɗe, a kan lafiyar gangar jikinsa, amma sam wani baya yadda ma ruhinsa yana rashin lafiya." Nana ta ce "Nima ban gane ba" Yayi murmushi ya gyara zamansa ya ce "Ruhi shi ne asalin rayuwa, da gangar jiki ta dogara a kai, wanda ba a iya ganinsa, ko taɓa shi, amma wanzuwarsa ce take sanya gangar jiki motsawa. Ruhi yana da alaƙa da hankali domin shi ne, ku 'yan Adam ku ke amfani da shi, gurin sarrafa duniyarku da gangar jiki. Lafiyayyen ruhi da tunani suke samar da nutsatsiyar gangar jiki mai cike da karsashi. Rashin lafiyar ruhi, ta fi ta gangar jiki hatsari. Idan ruhi yana rashin lafiya, yana kashe gangar jiki baki ɗaya. Sannan warkar da gangar jiki ya fi sauƙi a kan warkewar ruhi. Na san bayan nan nawa sun ɗan yi miki tsauri, amma bari na ɗan sauƙaƙa miki bayanan. Kamar yadda na ce miki ruhinku yana rashin lafiya, tabbas yana yi ciwukan da ido baya iya gani, sai dai ciwon na sanya hankalinku ya ƙwace, ku aikata abin da ba shi kenan ba. Misali Alhaji Zailani ruhinsa na fama da ciwon Hassada, amma bai taɓa tsayawa ya fahimta ba, saboda hankalinsa ya ƙwace har ya din ga aikata miyagun ayyuka. Wasu lokutan ku kan ji duniya ta yi muku zafi, kun tsani komai babu laifin tsaye babu na zaune, yana daga cikin alamomi na ruhinku na buƙatar kulawa ba shi da lafiya. Dan wasu lokutan shi ne yake taɓuwa sai hankali ya taɓu, nan da nan sai a ce ƙwaƙwalwa babu lafiya, idan ciwon ba shi da alaƙa da irin matsalolin da muke haddasa muku a ruhi. Hassada, ƙyashi, yawan ƙarya baƙin ciki babu dalili, burin gushewar ni'ima ga wani, yawan raya faruwar munan abubuwa. Yanke tsammani daga samun rahama, ko wani abu na alkhairi a rayuwa. da wasu cututtukan ma da ku kan danganta su damu, alamomi ne na rashin lafiyar ruhi, duk da mafi yawa wasu lokutan mu ne muke haddasa rashin lafiya a ruhinku. Idan ku ka ji alamu na ƙyashi ko hassada, ba ku fiye sakankankancewa ku roƙi Allah ya yaye muku ba, ko ku miƙe ku nemi maraba da hakan ba, ba ku fiye ɗaukarsa komai ba. Sai dai a hankali idan ya tsananta sai hankalinku ya gushe gangar jikinku ta aikata ɓarna. Kamar dai abubuwan da suka faru a masarautar su mijinki. Da abubuwan da aka yi masa. Ƙyashi, baƙin ciki hassada, son kai, da makamantansu duk larurar ruhi ce da ke kashe gangar jiki. Sai dai a zamana da ke na ƙara fahimtar wani abu, babu abin da ya kai addu'a kusanta mutum da Ubangiji, kuma duk ruhin da yake da kusanci da Allah zaka same shi cikin nutsuwa. Babu wanda ya san inda ruhin ɗan Adam yake sai Allah, amma galibi cututtukan da suke alaƙa da ƙwaƙwalwa da abubuwan da zuciya ka iya rayawa su na da alaƙa da ruhi. Lokuta da dama sai bawa ya yi ta addu'a, ya ga kamar bata karɓuwa, amma tasirin Addu'a da kusanci da Allah na sanya mutum a cikin nutsuwa, ta yadda zai ga wani da irin kaddararaa koma wadda ba ta kai tasa ba, amma ba shi da nutsuwa da kwanciyar hankali. Yanzu mu tsaya a nan, ma ci gaba wani lokacin, zan je ɗebo wani magani ne" Nana ba ta yi magana ba ta ji Muhsin yana kiran sunanta, yana kiran ruwa. Ba ta motsa ba, ta ji Nene ta tashi ta nemo ruwan ta ba shi. Abubuwan da suka tattauna da Ƙaisar kaf suka dawo kanta. Ya gaya mata wasu abubuwa da hannalinta bai taɓa kai wa kai ba. Tabbas ɗabi'ar zuciya ce jin ƙyashi ko hassada ko son kai wasu lokutan, hakan na nufin ruhin mutum babu lafiya kenan yana buƙatar attention?. ***** Babu kowa a gidan, Mama ta ritsa Jamila, cikin matsananciyar damuwa da tashin hankali take tambayarta "Jamila ki gaya mini gaskiya, da gaske ne abubuwan da ki ke faɗa cewar kin shiga ƙungiyar asiri, ko kema aljanun ne suka taɓa ki ki ke wannan soki burutsun?" Jamila ta sunkuyar da kai. Ta taƙarƙare ta dunƙule hannu ta ɗirka wa Jamila dundu ta ce "Za ki gaya mini ko sai na danne ki da fulo na kashe ki?" "Ki daina duka na, ba soki burutsu nake yi ba, da gaske nake Hajiya Sa'a ta saka ni a ƙungiyar asiri ba tare da sanina ba. Ta ƙulla alaƙa da ni ne, saboda na kawo mata jinin Nana ta ba wa ƙungiyarsu ta yi arziki, da ban kawo jinin Nana ba ta saka ni a ƙungiya. A can aka fara lalata mini rayuwa, sannan tsautsayi ya sake shiga tsakanina da ɗanta Abba, cikin jikina da ya fita nasa ne. Shi ya sadaukar da kansa saboda kar da na bayar da kowa a ƙungiya, amma haryanzu aljanun ƙungiyar bibiyata suke yi, suna nema su kashe ni nima, wannan ce gaskiyar da ki ke son ji Mama, wannan ce bayan ita babu wata kuma" Kafin Mama ta yi magana suka ji muryar Baba yana kuka ya ce "Jamila kin cuci kanki, ba ki kyautawa kanki ba, Jamila ƙungiyar asiri, kuma aka nemi jinin Nana" "Wallahi Baba ban bayar da jinin kowa ba, ba dan son raina na shiga ba, ban san ya aka yi na shiga ba." "Rufe mini baki, ni ta wani fannin na gode Allah da na yi wa Nanan aure ma, ta bar muku gidan. Kuma ki tattara yaranki ku bar mini gida Rabi, ko ƙaunar ganinki bana son yi. Ku je ku da Allah" Yayi maganar yana kuka. Mama ta rasa bakin magana, tabbas ita da din ga ƙara tunkuɗa Jamila jikin Hajiya Sa'a, ba tare da tunanin abin da ka iya faruwa ba. Daga cikin ɗaki Jamila na kuka take faɗin "Dan Allah Baba kar ka yi mini baki, ka yi haƙuri ka yafe mini dan Allah, ko iya haka na sha wahala, ina kan sha ma na san ba tsawon rai zan yi ba, ba za su bar ni haka ba nima kashe ni za su yi" "Gara su kashe ki, sai ya fi mini kwanciyar hankali" Ya goge hawayensa ya fice. Yana fita ya ci karo da Ummi, ta kalle shi ta ce "Baba fita zaka yi, ina ta sauri saboda na cim maka, ina ta kiran wayarka amma ba ta shiga" Ya ce "Eh, fita zan yi Allah ya sa dai lafiya?" "Lafiya ƙalau, mu shiga daga ciki" Ya girgiza kai ya ce "Ba na son sake shiga cikin gidan nan" Ummi ta ce "Amma Baba meyasa, magana ce mai muhimmanci" Ya ce "Ki yi ta a nan kawai" Jiki a sanyaye ta ce "Ranar da 'yan uwan mijin Nana suka zo gurinka sun je gidana" Sai Baba ya gyara tsayuwarsa, ya ce "Yaya aka yi suka san gidanki?" Ta ce "Nima ban sani ba, amma har magana na yi da mijin Nana, ka san lokacin da suka samu matsalar nan, da ba shi da lafiya sun zauna a unguwarmu" "Haka ne, amma nifa ban yarda da abin da suka gaya mini ba" Baba ya nuna wa Ummi guri suka zauna, ya ce "Ummi da gaske ke kin yadda?" Ummi ta ce "Baba ga zahiri nan kana gani, tun daga Nijar suka taho fa. Sun gaya mini ma an so gyara maka gidan nan ka ce ba ka so" Ya ce "Bar ni Ummi, ni yanzu na shiga hankalina da al'amuran rayuwa, babu abin da ya kai kwanciyar hankali da nutsuwa daɗi" Nan ya bata labarin halin da suke ciki da Jamila. Jikin Ummi ya yi sanyi sosai da sosai, ta ce "Baba idan ka kori Jamila ina za ta je yanzu? Ƙaddara ce Allah ya aiko dole a yi haƙuri da ita. Yanzu dai sirukanka za su ranar Lahadi idan Allah ya kaimu, sun kira ni a waya, an ce ba a samun lambarka. Mijin Nana ya sai duk wani abu da za a tarbi 'yan uwansa da za su zo. Kawowa kawai za a yi kafin su iso. Dan Allah ka kwantar da hankalinka ka bar batun Jamila mutanen nan su zo lafiya su tafi lafiya. ***** Asal na kwance a gadon Asibiti, Hasna na gefenta ta riƙe hannunta, sai uban kuka take yi. "Hasna wallahi ina son Hammad, ji nake mutuwa zan yi idan ya sake ni, ga shi haryanzu ban san a wani bugiren ya ajiye ni ba, bai sake ni ba, bai ce mini komai ba. Babanmu ne duk ya janyo mini da zigar Imam Omar." "Asal ki yi haƙuri mana, kar ki illata kanki a kan sa, shi fa yanzu ya samu wata ne da yake rawar ƙafa a kanta, ke sai ki kashe kanki fisabilillahi" "Hasna ba ki san me nake ji ba, wai ni ce nake da kishiya, wadda na ɗauka ƙasƙantacciya mara galihu na shiga uku" Hasna ta rungume ta, ta din ga rarrashinta tana yi mata nasiha. Kwanan Yusuf huɗu da mutuwa, tsufan Alhaji Zailani ya sake fitowa, duk ya fita hayyacinsa ya yi wani iri. Alhaji Zailani ya zo duba shi, yana ta rarrashinsa yana ba shi haƙuri. Mutane jefi-jefi na shigowa su na yin gaisuwa. Wani mutum ne ya yi sallama, suka amsa masa ya shiga, duk suka bi shi da kallo, dan babu wanda ya san shi a cikinsu. AREWABOOKS Sai da suka Shukura ta biyo bayan mutumin, sannan suka rikice gaba ɗaya suka miƙe, banda Alhaji Zailani. Hajiya Amina ta nufi Shukura da gudu har tana neman faɗuwa, ta rungume ta cikin tsananin tashin hankali da manakin ganinta ta ce "Shukura, ke ce? Ina ki ka shiga aka din ga neman ki, ina cikin jikin naki?" Wani irin tausayin Hajiya Amina ya shiga ran Shukura, ta rungume Hajiya Amina tana kuka. Alhaji Fatuhu ma cikin matsanancin mamaki yake faɗin "Ikon Allah, Allah da girma da iko yake. Sannu Shukura" Alhaji Zailani dai yana zaune yana kallon su, bai ko motsa ba. Idanun Shukura suka sauka a cikin nasa, ta ji tamkar ta yi tsalle ta shaƙe shi, saboda wani abu mai ɗaci da ya tsirga mata. Mutanen da ya sabauta rayuwarsu, duk ga su a tare da shi a zaune. Ta ce "Mummy wai na ga rumfa a harabar gidan nan, me yake faruwa ne?" Hajiya Amina ta ce "Ba wani abu bane ba, Shukura ina ki ka tafi?" Kan ta ba wa Hajiya Amina amsa ta durƙusa ta gaida Alhaji Zailani ya amsa mata cikin damuwa ya ce "Shukura kin sanya mu a tashin hankali, meyafaru wannan bawan Allah kuma waye?" Shukura ta numfasa ta ce "Garkuwa aka yi da ni, wannan mutumin Likita ne, shi ne wanda ya taimake ni, a gidansa na ƙarasa jinya" Suka gaisa da mutumin, Alhaji Fatuhu ya din ga yi masa godiya. Hajiya Amina ta ce "Daddy, ba ka ga Shukura ba, Shukura ce fa ta dawo" Ya sauke numfashi ya ce "Na ganta" Alhaji Fatuhu ya ce "Haba Zailani, amma atleast yakamata ka yi farincikin dawowarta ko, yarinyar da ake ta nema ba a gani ba, ta dawo kuma ka yi fuska" Alhaji Zailani ya ce "Ni yanzu ta mutuwar ɗana nake yi, dan Allah ku ƙyale ni" A burkice Shukura ta ce "Wane ɗan nasa?" Tsit suka yi aka rasa mai yi mata bayani, Alhaji Zailani da kansa ya gaya mata Yusuf ne ya mutu. Shukura ta gigice cikin matsanancin tashin hankali ta hau kuka, tana faɗin "Shi ma ka kashe shi ko? Da ni ba a kashe ni ba sai ka kashe mini ɗan uwa, wallahi ba zan yadda ba sai na tona maka asiri Duniya kowa ya san abin da ka ke yi" Likitan da ya rako ta, ya tashi tsam ya yi musu sallama, ya ce zai dawo. Duk yadda suka so Shukura ta nutsu amma ta ƙi, ta din ga surutan da ba su gane kansu ba, kuma Alhaji Zailani ya yi mursisi ya yi shiru. ***** Nana jikinta har wani sheƙi yake yi, ta yi kyau sosai da sosai, sai dai ganin Hammad ya yi mata wahala, saboda yana ta kai kawon shirin bikinsu. Yadda ta lura lamarin ba da wasa suka ɗauke shi ba, sai gayyatar mutane suke yi. Bangaren Sultan yana ta shan suka, da ƙorafe-ƙorafe, a kan ya ci mutuncin Al'adar da aka gada daga iyaye da kakanni. Bai tsaya a iya nan ba, ya ayyana rushe majalisar Imam da ake da ita. Ya sauke Tafawa, ya sauke Sardaunanda wasu daga cikin muƙarrabansa, tare da cewar za a ayyana waɗanda za su maye guraben su, a lokacin shagalin bikin Hammad da matarsa ta ɓoye da zai bayyana wa Duniya yanzu. Nana a ranta take ƙara jinjina ikon Allah, sai dai tana ganin lamarin bikin nasu, kamar a ƙasar turawa, sun yi aure sun haihu har da ɗa, sannan za a yi shagalin bikinsu. Gefe guda sannu a hankali take ƙara yi wa kanta fashin baƙin, bayanan da Ƙaisar ya yi mata a game da rashin lafiya da ya ce ruhin ɗan Adam yana yi. Kuma ga yadda ta fuskanta, babu wani magani tattare da hakan face ka yadda kana da ciwon, sannan ka tsananta addu'a Allah ya raba ka da shi. Tabbas ko a kankin kanta ta ga misali, ta ƙara samun nutsuwa da yarda da komai lokaci ne, lokacin da take addu'a Allah ya kawo mata ɗauki a kan matsalolinta, gani take kamar ba za su wuce ba, kamar waraka ba za ta zo ba. Ashe wannan addu'a da take yi, ke ƙara samar mata da nutsuwa da kwanciyar hankali, tabbas banda haka, da irin azabar da ta ci da tuni ta amince da al'amarin bori, ko ma haukace saboda wahala da yadda ratuwarta ke tafiya kamar ba ta mutane ba. Ta kalli yadda a yanzu ba ta aikin fari bata na baƙi, sai dai kawai a kawo mata ta ci, ta yi ibada ta kwanta. Sai dai ta dage da roƙon Allah, kar Ni'ima ta sanya ta shagala da neman kusancinta da shi. **** Gidansu Nana, Mama ta yi mamaki, ganin Uwani ta zo ranar Asabar, wai zata kwana, da azahar ma sai ga Ummi da uban kayan cefane, har ma da Yaya Atine. Mama ta ce "Wai lafiya duk na ganku, meke faruwa ne?" Uwani ta ce "Kamar yaya meke faruwa? Karɓar kayan auren Nana muka zo ayi da mu mana" Ta yi saroro ta ce "Nana kuma, wace Nanan?" "Nana wacce da wacce ku ke da ita a gidan nan? Ba dangin mijinta ne za su zo daga Agadez ba?" Mama ta ce "Ban fa gane ba, yaushe aka ganta" Uwani ta ce "Ke Ummi, ba ku gaya mata ba ne?" Ummi ta ce "Ina ga Baba bai gaya mata ba, Nana tana Agadez can hannun dangin mijinta, gobe in Allah ya kaimu za su zo kawo kayan aurenta" "Shi ne kuma dan munafunci ba a gaya mini ba? Kuma wane irin kayan aure kuma bayan wanda aka yi" Ummi ta ce "Wallahi nima ban sani ba, sai dai sun zo za mu ji" Mamaki ya cika Mama, domin babu wanda ya tsaya ya yi mata cikakken bayani, kamar ma ba a son ta ji abin da yake faruwa. Washegari tun ƙarfe sha ɗaya na safe, gidan abincin da aka sai Abinci a hannunsu, suka kawo abinci mai rai da lafiya cikin kuloli na alfarma. Baba ya din ga shiga yana fita, shi fatansa kawai ya ga Nana ba wai abin da za a kawo na auren ba. Da azahar motoci biyu suka iso, ɗaya guda ɗaya ta alfarma ɗaya kuma ta matafiya. Ƙaton carfet dama aka shimfiɗa a tsakar gidan, aka shirya wannan uban kayan Abincin. Manyan mutane ne, farare sol Turaki da Matawallen Agadez, sai kum Tafida, sai kuma Imam Zahradeen, Mahmoudu Sulei, sai kuma Imrana. Kai tsaye Imarana ya nufi Baba, aikuwa Baban ya rungume shi yana fashewa da kuka. Yadda ya ga Imarana a nutse cikin kamala kawai ya sanya shi mantawa da tarin baƙin cikin da yake ciki, kuma sai a lokacin ya gazgata mutanen nan da gaske suke. Imrana ya ce "Baba kar ka yi magana, ka ga mu na tare da baƙi" Baba dai kai kawai ya iya jinjinawa yana sake riƙe shi, kamar zai sake guduwa. Ta taga Mama take ɗan leƙowa, ta saki baki tana kallon ikon Allah, suturar jikin buzayen kawai ya fallasa cewar a cikin rufin asiri suke, ba ƙananan mutane ba ne. Bayan Baba ya ɗan nutsu, duk sun nemi guri sun zauna, suka gaggaisa. Imam Zahradeen ya ce "To Baba mun sake dawowa, mun zo mu cika alƙawari da muka ɗauka, waɗanan 'yan uwan mahaifinmu ne, ga shi muka zo tare da su" Suka sake gaisawa Matawalle ya ce "Ɗan uwa, Sultan ne ya aiko mu wakilci mussaman, mu zo mu yi godiya, mu jinjina wa namijin ƙoƙarin da ka yi, na aura wa ɗanmu 'yarka ba tare da sanin waye shi ba. Haƙiƙa mu yarinyarka alkhairi ga ahalinmu da ƙasar Agadez baki ɗaya ma. A madadin Sultan Jalaludeen ya ce "Mu ce maka mun gode, mun sake gode wa. Mu na tafe da dukiyar aurenta, kamar yadda ake yi wa kowace 'ya da ake yi wa kabilar buzaye. Sannan ya ce ita wannan 'ya yanzu ta zama tasa, yana kuma gayyatarka da duk wani wanda yake sha'awar zuwa, gagarumin shagalin bikin yaran nasa. Hammad da kuma Gimbiya Asma'u." Baba ya numfasa yana ganin abin kamar a mafarki, ya ce "To ai tun da dai da aure a tsakaninsu, a ganina da an haƙura da bikin shagalin nan" Turaki ya ce "To ai ɗan gidan mulki ne, abu ne aka yi shi da babu wanda ya sani, kuma ya saɓa wa al'adarmu, wands a dalilinta an soke al'adar ma gaba ɗaya, dan haka dole a yi shagalin bikin domin nuna wa Duniya ita. Saboda gudun abin da ka iya biyo baya, saboda mutum ne mai mulki mai faɗa a ji a garin Agadez. Dan haka nan da mako guda za a yi bikin, duk adadin waɗanda za su je, za a ɗauki nauyinsu tun daga ƙasa Nigeria har can, domin yin wannan shagali" Daga cikin ɗakin Uwani ta rafsa wata irin guɗa mai ɗan karen sauti tana faɗin "Alhamdillah" har sai da hankalinsu ya koma kan inda sautin guɗar ya fito. Gaddafi dai daga baya ya shigo, suka yi ido huɗu da Imrana. Imarana ya tashi ya nufe shi, rungume juna suka yi. Gaddafi ya ce "Imrana, wannan karon nisan kiwon naka har ya kai tsawon wannan lokacin?" Imrana ya ce "Wani nisan kiwo, kame ni a kayi, a ka kai ni makarantar dole, abubuwa ne da yawa suka faru" Ai tuni suka manta da wani batun ba sa jituwa, saboda girman alaƙar jini, suka din ga murnar ganin junansu. Daga nan aka shiga shigo da kayan auren Nana, sai da Baba ya saki baki, a ransa ya fara tunanin anya mutanen nan su na da hankali kuwa. Saboda shi yanzu al'amuran abin duniya tsoro suke ba shi. Domin karrama abin da su Baba suke da shi, su Turaki suka ci abincin da aka kawo musu. Aka gabatar musu da 'yan uwan Nana, Yaya Atine sai rawar kai take, tana nanata musu ita yayar Baban Nana ce uwa ɗaya uba ɗaya, ita ta saki Nono ya kama. Haushi sai da ya kama Imran, Gaddafi ma ya tsuke fuska ya ce "Matar nan duk abin da aka haɗa da ita sai ta yi hauka" Imrana ya ce "Har da wani ita ta saki nono ya kama, kamar nonon akuya, ko kunya ba ta ji ba, kamar ba da ita aka dinga muzguna wa Nana ba" Ta din ga rawar ƙafa tana jan su da hira, sai da ta ba wa kowa haushi. Da suka tashi tafiya kuwa, Haka Ummi ta shiga maƙwabta ta karɓo kayan da aka shirya, na tukuci da za su tafi da shi, dan kar ma wani ya sanya zalama. Kaji, da kayan snacks masu yawan gaske, da dabino kusan kwano biyar da tasoshin turare. Turaki ya ce karramawar da aka yi musu ta isa, ba za su karɓi komai ba, ai Nana 'yar Sultan ce. Gaddafi ya ce idan ba su karɓa ba, ba za su ji daɗi ba. Baba ya ga za su tafi ya yi musu godiya sannan ya ce "To ba za a kawo mini Nanan ba, ita yaushe zan ganta?" Imam Zahradeen ya ce "Zaka ganta Baba, sai kun zo Agadez biki, za ku ganta in sha Allah, ga Imrana mun kawo maka har gida ai" Jiki a sanyaye ya ce "Nanan dai nake son gani, amma shikenan mun gode sosai da sosai" Imrana ya ce "Tun da ni baya son ganina, bari na biku mu koma" Cikin sauri Baba ya ce "A'a Imrana, kai ma na yi murna da ganinka" Suka yi murmushi baki ɗaya, su Mahmoudu ya ce "Duk wanda za su je, a kira a gaya mana adadin mutane, za a ɗauki nauyin zuwansu da dawowar su, sannan kuma idan an gama ganin kayan da su za a tafi. Daga nan suka hau mota suka tafi. Da suka koma gida, aka fara sauke kaya ana bubbuɗewa, Baba komawa ya yi gefe ya fashe da kuka, domin hatta shi akwati guda aka yi masa. Uwani ta ce "Isa meye haka kuma, ai abin farinciki ne, ka daina kukan nan dan Allah" Maƙwabta ma ba a bar su a baya ba, suka din ga shigowa, sun ɗauka ko kayan auren Jamila aka kawo ko na Suwaiba. Mama baƙin ciki ya cika mata ciki, ganin yadda nata 'ya'yan duk suka zama abin da suka zama, babu wani na kirki, ta din ga cizon yatsan ina ma nata 'ya'yan ta saka aka aura wa buzun ba Nana ba. Uwani ta ce "Allah ba azzalumin sarki ba ne, Nana ta sha wahala a rayuwa, ta yi ɗawainiya da yaron nan, da jikinta da ƙarfinta. Allah ya yi tana da rabon jin daɗi tun a Duniya" Ummi ta ce "Wallahi Uwani, Nana ta sha wahala, da shi sosai da sosai, Allah ya nuna ikonsa. Kuma shi ma ya yi halacci" Uwani ta ce "Ba kaɗan ba, Allah dai ya ba su zaman lafiya" Imran ya ce "Dan ma ba ku ji wahalar da ta sha a Niger ɗin nan ba, da yawon nemansa" Nan Imrana ya gaya musu abin da ya sani. Yaya Atine ta ja baki ta yi shiru. Uwani ta ce "To Isa, ina fatan ya zame maka izina, akan abubuwan da ka aikata wa yarinyar nan. Kuma ya zama dole a kira mahaifiyarta a sanar da ita komai, kuma a yi shirin tafiya da ita gurin bikin nan, dan ba za ka ci gaba da wannan jahilcin ba" Imrana ya ce "To ai a Bauchi muka kwana, an je har gida an kai wa Umma lefen ta gani, an yi mata godiya sannan muka taho nan yau" Uwani ta ce "Ikon Allah, haihuwa mai rana" Duk yadda Mama ta so ɓoye ɓakin cikinta abu ya ci tura. Can gidan Umman su Nana, ta yi sujuda babu adadi na tsantsar murna da farinciki. Iliyasu kansa bakinsa ya ƙi rufuwa, amma ko kallo bai ishe ta ba. Dan ta wani fannin guduwar Nana, sauƙi ya sama mata, dan tun da ya san ya yi sanadin ɓatan Nana, duk abin da take yi masa baya cewa uffan. "Mai Jidda kin ga ikon Allah ko? Ashe ta wani fannin gara da Nana ta je neman mijin nata, da tana zaune a nan babu lallai su haɗu. Allah sarki rayuwa" Maijidda ji ta yi kamar ta make shi, ya ga abin Duniya, jikinsa sai tsuma yake yi. ***** Asal na zaune ta damƙe wayarta iya ƙarfinta, saboda ganin hoton katin gayyatar bikin taron bikin Hammad da matarsa, da kuma naɗe-naɗen sarauta. Hasna ta ce "Asal, ki ajiye wayar nan ki samu ki saka wani abu a cikinki mana" Ta girgiza kai hawaye na gangarowa daga idanunta. Ji suka yi an buɗe ƙofar ɗakin, suka ɗaga baki ɗaya. Hammad ne ya shigo, jikinsa sanye da shiga ta alfarma. Ƙamshin turarensa ya mamaye ɗakin baki ɗaya. Hasna ta risuna cikin girmamawa tana gaishe shi. Asal kuwa ta sunkuyar da kanta, zuciyarta na tsananta bugawa cike da tsoro da fargaba, saboda ba ta taɓa tsammanin ganinsa ba. Kuma ba ta san me yake tafe da shi ba. Da yatsunsa biyu ya yi wa Hasna alamar ta fita ta ba su guri. Ayshercool 08081012143 100 LITTAFIN KUƊI NE, A BIYA KUƊIN KARATU KAN A KARANTA. 0069685771 AISHA ADAM STANBIC 08081012143 Asal ta sunkuyar da kanta ƙasa, ji take yi tamkar ƙasa ta tsage ta shige, saboda matsananciyar kunyarsa da take ji. Ya ƙarasa ya zauna a gefenta, ya ce "Me ya same ki haka?" Ba ta ɗago ba, ta girgiza masa kai. Shiru ya wanzu tsakanin su, babu wanda ya yi magana. Ya ce "Tun da ba za ki yi magana ba shikenan" Har ya yinƙura, ta riƙe rigarsa ta ce "Sakina ka zo ka yi ko?" "A'a, dama ai ni ban kore ki ba, na dai ba ki zaɓin zama da ni ne, amma na ga kamar ke da mahaifinki, kun fi gamsuwa da na sauwwaƙe miki." "Dan Allah Hammad ka yi haƙuri ka yafe mini, na san laifukana ba za su ƙirgu ba, sai a wannan karon Allah ya tona asirina" Yayi murmushi ya ce "Ba zan yi miki dole ki zauna da ni ba, muddin kin san zuciyarki haryanzu tana son Omar" Wata irin ɗagowa Asal ta yi a razane jin abin da ya ce. "Hmm Asal kenan, duk tsawon zaman da na yi da ke, babu abin da ban sani ba, kar ma ki yi zaton ko wani ne ya gaya mini. Saka mini magani da duk wani nau'i na ƙoƙarin illata ni da ki ke yi, duk na sani, kuma ina kallonki. Ba domin babu yadda zan yi da ke ba, sai domin ina jin tausayinki, kuma ke ƙanwata ce" Zamowa ta yi ƙasa cikin kuka ta riƙe rigarsa ta ce "Wallahi na yi nadama Hammad, na san ko ba ka ce mini komai ba, Hakkinka ba zai bar ni ba. Amma ba laifina ba ne ba, ka sani dan Allah ka yi haƙuri ka yafe mini, kar ka sake ni. Wallahi ina sonka" "Dama ai ban ce zan sake ki ba, mahaifinki ne ya nemi hakan, kuma nima na so aikatawa amma na duba idan na yi haka, ba ki da wata kyakykywar makoma, bayan gama lalata rayuwarki da aka yi. Kuma ba na son asirinki ya ci gaba da tonuwa a idon Duniya. Uwa uba Nana tana ta yi mini magiyar kar na rabu da ke. Na so samarwa kaina cikakkiyar nutsuwa da rayuwa da wadda bata harin komai daga gare ni sai alkhairi, amma ban san me Allah zai yi mini a sanadin yafe miki ba. Asal zaki koma ɗakinki bisa sharaɗi, dan ta ni ko yanzu ki ci gaba da duk abin da ki ke yi mini, bai dame ni ba; amma muddin ki ka yi wani na yinƙurin cutar mini da matata ko ɗana, wallahi sai na ɗaure ki, ɗaurin rai da rai ma kuwa. Ba zan taɓa yin wasa da duk wani abu da ya shafe su ba, dan haka zaki amince da babu ruwanki da duk wani abu da ya shafe su, balle a zo ga batun cutarwa" Wani abu raɗaɗi ya tsirga wa Asal,  wai ita ake gindaya wa sharaɗi a kan Nana. Sai dai babu yadda ta iya ta jinjina masa kai ta ce "Na amince" Ya ce "Ki yi tunani da kyau, kar ki saɓa abin da ki ka ce daga baya, na ɗauki mataki ki ji haushina" "Na tabattar da na amince" Ya ce "To shikenan, tashi" Sai dai ƙafafuwanta suka yi mata nauyi, ta kasa tashi, saboda haryanzu tana jin nauyinsa, kenan har soyayyar da suka yi da Omar ya sani, amma ya ƙyale ta a gidansa. Babu tsammani ta ji ya saka hannu ya ɗago ta tsaye. Ya ce "Na saka an ɗan yi mana gyara a gida, zan canza miki komai. Har cikin zuciyata na yafe miki, na san wasu abubuwan ba laifinki ba ne, kuma ko dan kusanto da Nana gare ni da ki ke yi yakamata na yafe miki. Allah ya sanya kin yi tabbataccen tuba" A duk lokacin da ya ambaci Nana, sai ta ji baƙin ciki kamar ya halakka ta. Ya sumbaci goshinta, ya mayar da ita kan gadon ya zaunar da ita, ya ce "Allah ya baki lafiya" Daga haka ya juya ya fita. Wani irin kuka ta saka, gaba ɗaya alamu sun nuna, a yanzu baya ganin mutuncin komai idan ba na matarsa da ɗansa ba. Ƙarara a idonsa da mu'alarsa ake iya karanto tsagwaron son da yake yi wa Nana. Duk da yadda Sultan ya yi watsi da Imam Zahradeen, amma bai yi zuciya ba ya yi uwa ya yi makarɓiya a kan shirin gudanar da bikin ɗan uwansa. Tuni baƙi suka fara hallara, aka ɗauke Nana daga cikin gidan Sultan, zuwa estate ɗin da yake mallakin masarauta, da galibi ake saukar baƙi a can. Estate ɗin da sunan Hammad aka saka masa, wanda a nan ta fara zama tare da Asal da ƙawayenta a ɗaya daga cikin gidajen. Nana ba ta yi zato ba, ba ta yi tsammani ba, kawai ta tarar da mahaifiyarta da ƙannenta su Walida. Gaba ɗaya Nana ta yi wata irin rikicewa, jikinta ya hau tsuma. Maijidda da kanta ta tashi ta nufi Nana cikin farinciki. Nana ta faɗa jikinta ta rirriƙe ta, cikin dashewar murya ta ce "Um.umm.Umma! Umma ki yi haƙuri dan Allah" Maijidda ta ce "Shhh, kar ma ki kawo wannan zancen, ni yanzu lokacin farinciki ne da murna, dan haka kuka ya ƙare. Abin arziki da farinciki ne ya tara mu. Ni dai na gode wa Allah da ya sanya ina da rabon sake ganinku cikin kwanciyar hankali da kuma ƙoshin lafiya" "Umma idan ba ku yafe mini ba, hakkinku ba zai bar ni ba, na yi wauta na yi shirme, na bar ku da fargaba da kuma zullumi." "Duk ya wuce, ya zama tarihi, Alhamdillah tun da Allah ya amsa addu'armu ya haɗa mu cikin aminci da kwanciyar hankali." Tuni idanun Nana suka rine zuwa jawur, ta ƙanƙame Maijidda duk da babu wata shaƙuwar a zo a gani a tsakaninsu, amma wani irin abu ne mara misaltuwa Nana take jin sa a zuciyarta game da Umman nata. Ta ƙwaƙume ta, ta ƙi sakinta ta kwanta lamo a jikinta. Maijidda ta ce "Ai mijin naki ma ya zo mun gaisa, Ubangiji Allah ya sanya alkhairi ya baku zaman lafiya. Na ce a kawo mini jikin nawa na gan shi, aka ce mini yana ƙarƙashin kulawa ta musamman, zan gan shi amma ba yanzu ba" Nana dai babu baki, ba ta iya cewa komai ba. Sai yanzu take ƙara jinjina girman laifin da ta aikata. Ta tuna lokacin da aka raba ta da Muhsin na ɗan kwanaki tashin hankalin da ta shiga, ita kuma ta bar gida kusan shekara uku ba ta waiwaya ba, kuma still ana rarrashinta. Nene ce ta zo, tare da hadimai, da tarin kayan abinci, tare da su Anty Fati 'yan uwan Mai jidda da ta su motar isowarta kenan. Babu abin da Nana take yi sai gode wa Allah, sai murna suke yi da ganinta, tare da taya ta murnar matsayin da Allah ya ɗaukaka ta ya kai ta. Nana ta ce "Nene ga Ummana, Umma ga Mamana ta Niger ni yanzu a iyaye bayan ke, ba ni da wata uwa da ta wuce Nene. A hannunta na haifi Muhsin, ban san ya zan misalta miki riƙon da Nene ta yi mana ba Umma. Ki yi mata godiya." Nene ta ce "Dama idan uwa ta yi wa ɗanta abu, sai an yi mata godiya ai hakkinta ne ta yi" Ta miƙa wa Maijidda hannu suka gaisa, su Anty Fati suka hau yi mata godiya. Nene ta ce "Ni ina ƙaunar Nana saboda Allah, dan haka duk abin da na yi mata ina jin kamar na yi wa ɗan cikina ne" Sam ranar Nana bata rintsa ba, ji take yi tamkar mai Jidda ta mayar da ita cikinta, gani take idan ta yi bacci zai zamana abin da yake faruwa mafarki ne. Aka din ga ɗawainiya da su, Maijidda da ta taho da 'yan kayanta, na ƙara gyara Nana, yadda ta ga Nene na faɗi tashi a kan Nana, sai ta kasa komai. Washegari su Imrana suka iso, mota uku ta 'yan Kano, hatta Suwaiba da ba ta da cikakken hankali, da Jamila da babu cikakkiyar lafiya, haka Mama ta tarkata ta taho da su. Saboda a yi komai a kan idonta. Ana cewa ga motar su Baba can, Nana ta zabura za ta yi waje, Nene ta ce "Nana ya haka? Dole fa ki canza yadda ki ke gudanar da al'amuranki, da da kuma yanzu ba ɗaya ba ne ba. Ki bari za su shigo ai. Ummi ce ta fara shigowa, suka rumgume juna ita da Nana suka fashe da kuka. Su Uwani ma suka shigo gaba ɗaya sai falon ya kaure da koke-koke. Uwani da Ummi kamar su haɗiye Nana, Uwani ta ce "Ummi ke ce haka? Kin ga wani irin kyau da ki ka yi?" Nana ta yi murmushi. Ta riƙo hannun Jamila cike da farinciki, duk ƙasan zuciyarta cike yak da mamakin, yadda ta ga Jamila ta yi wata uwar rama mai ban tsoro. Duk da ba miji ɗaya suke aure ba yanzu sai da Mama ta yi turus ganin Mai Jidda, ba ta taɓa zaton za ta ganta gurin bikin Nana ba. Ta ganta tsaf da ita cikin nutsuwa. Uwani ta zauna kusa da Maijidda da su Anty Fati, suna hirar yaushe gamo. Nana dai kasa hirar ma tayi da su, gaba ɗaya kunyarsu ta hana ta cikakken sukunin haɗa ido da su. Bayan sallar isha'i, barori suka nemi da a yi shiru, Imam Hammad zai shigo. Aikuwa kamar ruwa ya cinye kowa aka yi shiru. Shi ne ya shigo tare da Mahmoudu, da hadaimai biyu, suka tsaya a bakin ƙofa shi kuma ya shiga. Yana ganin Uwani ya saki murmushi, ya tafi gabanta ya durƙusa. Ta ce "Ɗan nan, dama babban mutum ne kai? Ka gane ni?" Ya ce "Ɗa ba zai manta uwa ba ai, kuma ɗan halak baya manta alkhairi. Ba zan manta da ke ba, Allah ya saka da alkhairi" Ta ce "A'a ai ɗa baya yi wa uwa godiya, mun same ku lafiya?" Ya ce "Alhamdillah" Ya kalli Ummi da take ta murmushi ita ma, ya ce "Babbar Yaya, fatan kun sauka lafiya, kuma kun ji daɗin ƙasar tamu" Ummi ta ce "Alhamdillah, mun same ku lafiya?" Ya ce "Lafiya ƙalau, ina sake amfani da wannan damar, gurin sake baku haƙuri, da abin da Asmy ta yi, duk laifin a kaina yake, nine mai laifin amma ina bayar da haƙuri dan Allah a yafe mana. Sannan ina sake yi muku godiya sosai da sosai, Sultan ma ya ce a gaishe ku" Waɗanda ba su san shi ba, suka din ga yaba kyawu da kamalar Hammad. Daga nan ya nemi zai tafi da Nana, za ta je gurin su Baba inda suka sauka su gaisa, sannan a dawo da ita. Su na shiga mota, ya kwanta a jikin Nana yana sauke numfashi ya ce "Da na yi niyyar idan aka gama taron nan, ki yi kwana biyu ki huta, sannan ki tare amma gaskiya yanzu na fasa, ji nake kamar na gudu da ke" Ta marairaice ta ce "Dan Allah ka bari a kwana biyun" "Ba zan iya ba, ana tashi kawai a kai mini ke gida, gidanki ya kammala komai an saka mana, mukaɗai muka rage mu shiga" Yayi maganar yana sumbatar bakinta. "Ya naga jikinki ya yi sanyi ne, kamar wata amarya?" "Wallahi Sayyid tsoro nake ji, ban san da wani idon zan kalli Baba ba, ban kyauta ba abin da na yi ko kaɗan" "A'a ki kwantar da hankalinki, Baba fa tun kafin su zo, na tura an ba shi haƙuri, yau da suka zo an kai shi har gurin Sultan, ya ba shi haƙuri, nima na je na same shi, shi duk damuwarsa ma ya ganki ne. Babu wani abu in sha Allah" Haka suka ƙarasa jikin Nana a sanyaye duk a tsorace take. A wani sashi na gidan Sultan, aka sauki su Baba, tare da Imrana da Gaddafi. Nana ta tsaya cak, ta sanya hannayenta, ta toshe bakinta, wani irin kuka mai ƙarfin gaske yana kufce mata. Gaddafi ne ya taso ya riƙo hannunta, ya ƙarasa gaban Baba da ita. Sai da Sayyid ya ji wani iri, duk da kasancewar Gaddafin yayanta ne. Nana tun da ta buɗe ido, Baba bai taɓa rungume ta ba sai yau, tana kuka yana kuka. Da kyar maganarta take fita ta ce "Baba ka yi haƙuri, ka yi haƙuri dan Allah ka yafe mini. Baba na yi wauta da rashin hankali Baba ka yi haƙuri na san na sanya ku a tashin hankali" Sai da Baba ya yi kuka mai isar sa sannan ya iya furta "Babu komai Nana, ni dai na gode wa Allah tun da kina nan cikin ƙoshin lafiya, Alhamdillah, Alhamdillah na gode wa Allah". Haka ta rungume Nasiru ma tana kukan farinciki, ta ƙara tabattar da duk lalacewar naka naka ne, ta shiga farinciki mara misaltuwa da ganin ahalinta a tare da ita. Har Alhaji Fatuhu ya tafi ranar, Shukura ba ta yi musu bayanin komai ba, sai dai ta kaɗu ta shiga tashin hankali da mutuwar ɗan uwanta. Hajiya Amina ma babu rarrashin da ba ta yi mata ba, amma ba ta yi mata bayanin komai ba. Washegari da rana, sai ga Yusra tare da Sagir da Hajiya Halima da Siyama. Hajiya Amina ta karɓe su hannu bibbiyu. Ta ce "Sagir na zata zan ganka tun a jiya, na kira gidanku na sanar da Shukura ta dawo. Ya ce "Mummy bana gari ne, ina can Abuja fa, Yusra babu lafiya" "Wai Yusra haihuwa ki ka yi ne?" Mummy ta yi maganar tana kallon ta. Shukura ce ta fito, Yusra ta ajiye wa Sagir yaron, ta nufi Shukura ta ce "'yar uwa babu abin da ya same ki ko?" Shukura ta jinjina kai ta riƙe hannun Yusra ta ce "Yusra na gode sosai da sosai, na gode" Yusra ta rungume ta tana rarrashinta. Shukura ta ce "Mummy, ki kira Daddy a yi komai a kan idonsa, na kira Baban Rauda ma a wayarki" Cikin rashin fahimta ta ce "To wai meyafaru?" Shukura ta ce "Shi zan yi bayani" Tana rufe bakinta, Alhaji Zailani ya fito, ya tsaya yana kallon Yusra da kuma Shukura. Yayi murmushi ya ce "Har gangami ki ka yi na tona mini asiri Shukura? Shikenan, mu jira zuwan Fatuhun, ai tun da ki ka dawo na san za a yi hakan." Gaba ɗaya suka tsaya su na kallon Shukura. Hajiya Amina ta ce "Shukura mene wai? Alhaji ka yi mini bayani mana" Su na cikin maganar, Alhaji Fatuhu ya ƙaraso gidan, ya tarar da su a tsaye a falo. Ya ce "Hajiya Amina lafiya kuwa? Shukura ta kira ni a waya ta ce lallai na zo" Hajiya Amina ta ce "Wallahi nima ban san abin da yake faruwa ba, shi ma na ji yana zancen za a tona masa asiri na kasa ganewa" Ya kalli Shukura ya ce "Shukura, mene ne ki yi mana bayani" Shukura ta yi shiru tana kallon Alhaji Zailani, amma ta kasa magana, kawai ta fashe da kuka. Yusra ta ce "Ina gida wayar Baban Haidar ta lalace, ya saka layinsa a wayata, Shukura ta kira ta ce tana wani Asibiti a can wata ƙaramar hukuma a Kano. Wai garkuwa aka da ita ta kuɓuta, wata mata ta tsince ta, ta kaita Asibiti. Na ce ba zan tafi ba sai tare da ita, da magariba wasu suka zo Asibitin su na nemanta za su kashe ta. Shi ne na tafi da jaririn, ni ban ma san yadda aka yi ba na ganni a gidanmu na Abuja daga Asibitin. Amma babanta ne ya saka a sace ta" Gaba ɗaya suka kalli Yusra cike da mamaki. Alhaji Fatuhu ya ce "Kin san me ki ke faɗa kuwa?" Yusra ta ce "Na sani mana, ba fa ƙarya nake yi ba. Ai ita da kunya ta ce ga abin da ya yi, amma ni dai ku yi haƙuri na faɗa" Alhaji Fatuhu ya ce "Amma kamar an ce ai ba ta da cikakkiyar lafiyar ƙwaƙwalwa, wataƙila... Shukura cikin kuka ta ce "Yusra ba ƙarya take yi ba, Daddy ne ya sanya a sace ni, saboda ina bin diddigin yadda aka ce jaririna ya mutu, kuma saboda ya bayar da jaririna a matsayin sadaukarwarsa ta shekara a ƙungiyar asiri. Na so rufa masa asiri na yi shiru, amma ba zan iya ba, mussaman idan ina kallon mutanen da ya zalunta, da yadda yake ganin bayan rayuwarsu. Ni Yusuf ma ina kyautata zaton shi ne ya bayar da shi a kungiyar" Cikin tsawa Alhaji Fatuhu ya ce "Shut up Shukura, mahaifinki ne fa, ki ke yi masa wannan tonon sililin a gaban mutane. Kuma tayaya za ki haɗa kai da abokiyar zaman ki, ku yi masa wannan ƙazafin?" Shukura ta ce "Ko zan yi wa kowa ƙazafi yaya za a yi na yi masa? Bana jin komai ko a gaban waye zan tona masa asiri, iyaka dai a yi mini gori wataran hakan ba zai dame ni ba. Ɗana ya ɗauka ya bayar aka yi tsafi da shi aka yi maka asirin da ka rasa komai ka yi rashin lafiyar nan. Suka haɗa baki da Doctor Sharif aka yi mini tiyata aka ba su jaririna. Tayaya zan iya rufa wa mutumin da ya yi mini wannan zaluncin asiri?. Nan Shukura ta din ga faɗar miyagun ayyukan da Alhaji Zailani ya gaya mata ya yi da bakinsa. Wani irin bugu zuciyar Hajiya Amina ta yi, take ta ji jikinta ya yi wani irin sanyi, tamkar an zare mata lakar jikinta. Wani irin gumi ya fara tsatsafo mata ko ta ina. Alhaji Fatuhu bakinsa na rawa ya ce "Zailani, abin da yarinyar nan ta faɗa haka ne, ko kuma ɗimuwa ta shiga ne?" Yayi shiru bai yi magana ba, sai tsare su da idanu da ya yi. Sagir ya ɗan daddana wayarsa, mutumin nan da suka zo tare da Shukura ne ya shigo, tare da wasu ƙarti majiya ƙarfi su uku. Bayan ya yi musu sallama, ya yi musu bayanin shi jami'in tsaro ne, kuma Likita, shi ne ya haɗu da Shukura a lokacin da nutanen da Alhaji Zailani ya tura, suka gano ta, suka yi yinƙurin kashe ta, ya yi amfani da ƙwarewar aiki, ya kama mutum biyu daga ciki. Kuma sun tabattar da Alhaji Zailani ne ya saka su wannan aiki. Bakin Hajiya Amina na rawa, da kyar ta ce "Me na yi maka haka Zailani?" Daga nan ba ta sake cewa komai ba, ta silale ta faɗi ƙasa. Alhaji Fatuhu shi ma kasa ko ƙwaƙƙwaran motsi ya yi, ji yayi tamkar numfashinsa zai ɗauke. Sai yanzu wasu abubuwan da suka faru suke dawo masa, amma bai taɓa zaton Alhaji Zailani zai iya aikata masa wannan mugun abun ba. Kafin a bar gidan da shi, ya tsaya ya kalli Alhaji Fatuhu ya ce "Kar ka yi mamakin abin da ya faru, domin ban taɓa sonka ba, duba da yadda ka fini ta ko ina, kuma ban yi nadamar abin da na aikata maka ba. Duk abubuwan nan da na yi babu wata cikakkiyar shaida da za a iya kama ni da laifi da ita, balle a hukunta ni. Sai shaidar sace 'yata da na yi, wannan ma na san yadda zan fitar da kaina. Sai dai dole mu yi mutuwar kasko, domin ba ni kaɗai ba ne a ƙungiyar asirin, har da yayarka, da ta sadaukar naka da ɗanka da ya mutu, dan haka ko wani mataki zaka ɗauka a kaina, sai ka haɗa da ni da ita, gara ni abokinka ne kawai, ita kuma 'yar uwakka ce!". ***** Nana ta so sanya kayanta na Nigeria, a gurin bikin nan, Hammad ya ce shigar buzaye za a yi mata. Ta sha gyara ta yi kyau. Agadez ta ɗinke da tarin jama'a. Tun daga kan gashin kanta, lungu da saƙo na jikinta, babu inda bai ga gyara ba. Sai da ta tuna da lokacin bikinsu na farko, yadda aka kawo mata shadda ta alfarma. Yanzun ma haka ne, rigar ta sha aiki ita kanta shaddar ƙamshi take yi na musamman. Babu babban abin da ya razana Nana, irin sarƙar da aka saka mata ta gold da ta sauka har cikinta. Ta kalli mai kwalliyar ta ce "Ni gaskiya a cire mini wannan sarƙar ba zan iya saka wa ba, fariyar ta yi yawa" Matar ta ce "Ba fariya ba ce shugabata, ado ne na mutanen ƙasar nan, dan Allah kar ki ji wani abu, ai ana kammalawa dole za ki cire ne" Sai da aka yi ta fama da Nana sannan ta haƙura, gani take yi kamar ba ta hanyar da ya dace ta yi wa Allah godiya ba kenan, da wannan fariyar. Ta din ga istigfari, da fatan Allah ya sanya kar hakan ya sanya ta ji wani abu na girman kai ko tinƙaho. Ƙaton ɗakin taro ne, ta kowane ɓangare mutane ne, daban daban, 'ya'yan sarakuna da manyan mutane gurinsu daban, ɓangaren danginta daban, abin har ya fara bata tsoro ta ji kanta yana juyawa. Ba iya wannan ba, shi kansa Muhsin da kusan kwana biyar rabon ta da shi, an yi masa ado, kayansa iri ɗaya da na mahaifinsa. Aka buɗe taro da addu'a, da karanto jadawalin abin da za a gudanar a gurin. Aka fara da sake tabattar da rushe majalisar Imam, da zimmar duk wani ɗan sarki Imam ne, amma babu majalisarsu, da kuma cewar lallai su za su gaji sarauta. Aka sanar da sauke wasu daga manyan makusantan Sultan, ba tare da faɗar cikakken dalili ba, sai cewa saboda za a yi gyare-gyare ne a masarautar Agadez. Aka gabatar da roƙo ga gwamnatin tarayya, a kan ta bayar da tallafi su haɗu da masarautar Agadez, a gyara gidan tarihin nan, a faɗaɗa shi a ƙawata shi, ya zamana gurin buɗe idanu sosai ga baƙi. A kuma gina Hotel a ciki ko wajen gidan, saboda samar da masauki ga baƙin da za su din ga zuwa yawon buɗe ido. Daga nan aka sake jaddada dokar, halattawa ƙabilar buzaye auren duk matar da suke so, daga kowace ƙasa. Aka yi ta kaɗe-kaɗe ana shiga ana fita da abinci kala-kala. Daga bisani aka yi wa Imam Hammad naɗi aka ba shi sarautar Sardaunan Agadez, yayin da Imam Zahradeen aka ba shi sarautar Tafawa. Sai kuma abin da ba a taɓa tsammani ba, Sultan ya yi wa Mahmoudu Sarautar Tafeedan Agadez, tare da ba shi auren ɗaya daga cikin 'ya'yansa, wanda za a gudanar a nan take. Gigicewa Mahmoudu ya yi, Nana ma ta waro idanu saboda mamaki. Hammad kuwa ya sani, tare da Sultan suka shirya komai. Kuma ya tabattar ƙanwar tasa ta amince da auren Mahmoudu, ita ma tata mahaifiyar rasuwa ta yi, ita ce 'yar autarsu. Dama ba shi da matsala da Mahmoudu, kuma ya fuskanci su na shiri sosai, shiyasa ya nemi alfarmar Sultan ya yi wannan haɗin. Aka fito da Muhsin, aka gabatar da shi, a matsayin ɗan Hammad, da Duniya ba ta san da shi ba, kuma a ka yi masa naɗin Imam kuma Yariman Agadez mafi ƙarancin shekaru a tarihin Agadez, haka zalika kuma Imam da mahaifiyarsa ta sauya tarihin Agadez baki ɗaya. Nan manyan mutane suka din ga bajinta, da gwangwaje Muhsin da tsadaddun kyaututtuka na ban mamaki. Har sai da Nana ta kalli abin a matsayin Almubazzaranci. Daga bisani aka din ga koɗa Nana ana yi mata kirari, ita ma aka gabatar da ita, a matsayin matar sabon Sardaunan Agadez, kuma mahaifiyar Yarima. Nana gaba ɗaya sai ta rikice, kawai ta fashe da kuka. Aka bata mic a kan ta yi magana, amma ta kasa ƙarshe kawai ta yi sujudu shukur a gurin, jikinta na tsuma tana wani irin kuka. Hammad ne ya din ga rarrashin ta, yana ankarar da ita ranar farin ciki ce a gare su. Ba a bar uwar Yarima haka ba, sai da ta samu sarautar Garkuwar matan ƙasar Agadez. Haka matan manyan mutanen nan, suka din ga guɗa, suna yi mata kyaututtuka. Hammad ya yi godiya ga tarin al'ummar da suka halarci taron, tare da fatan ɗorewar Canjin da aka samu, na halatta auratayya da kuma tabattar da 'yancin kowane kalar fata. Ya yi godiya ga dangin Nana, tare da jinjina mata, da kamba mata a gaban tarin jama'ar nan. Duk bai fito ya bayyana wa mutanen abin da Nanan ta yi yake ta wasa ta ba, amma ya nuna wa Duniya yana ƙaunar Nana, kuma komai zai yi ba zai taɓa biyanta soyayyar da sadaukarwar da ta yi masa ba. "Haƙiƙa yau rana ce mai girima, da ɗumbin tarihi a gare ni, da ma al'ummar ƙasar nan, duk da akwai ranar da ta fi ta da ba zan manta da ita ba, ranar da na mallaki Gimbiya Asma'u a matsayin matata. Ba ni da kalaman da zan yi amfani gurin yi mata godiya, da nuna muku girma da matsayinta a rayuwata ba. Ni dai na san halitta ce mai girma, da ta cancanci na wasa ta, na yabe ta, na so ta na kambama ta ko a ina ne. Asma'u ke rayuwata ce" Ya ƙarasa maganar a raunane. "Allah ya yi miki mafificin tukuici. Haka zalika ba zan manta da ɗan uwana ba, ba sabon Tafawan Agadez ba, dama wannan yayana ne. Ina nufin Tafeedan Agadez. Ba ni da abin da zan iya faɗa, sai dai za ku dauwwama a cikin zuciyata da kuma addu'ata. Sai mai gayya mai aiki uba na gari mai girma Sultan uban ƙasa uban kowa da kowa. Mu na godiya da tarin karamci da dattakunka a gare mu. Iyayena na Nigeria, kafataninku muna ƙara sake miƙa godiya a gare ku" Nana kam kasa jurewa ta yi, ta rasa ma kukan me take yi, na murna ne ko kuma na damuwa. Ba Nana ba hatta iyayenta, sai da suka yi kukan murna, Baba bai taɓa tsammanin a zuriyarsa za a samu irin wannan tagomashin ba. Sai dai shi Allah, mai aikata abin da ya so ne a lokacin da ya so, ya kan ɗaga abu a lokacin da ya ga dama, zuwa ƙololuwar matsayin da zato bai taɓa zata ba. Taro ya watse lafiya, aka tashi cikin farin ciki, duk da zukatan maƙiya ba haka suka so ba. Ai kamar yadda Hammad ya ce, a ranar za ta tare, babu wani abu da ya yi saura da ake jira. Batun sabbin naɗe-naɗen da aka yi, ya sake cika gari, wasu suna ganin Sultan ya nuna son kai, gurin cire manyan mutane masu muƙamai, ya bawa 'ya'yansa. Nana ta so ta huta kafin ta tare, amma Maijidda ta ce a'a, tun da haka mijinta ya ce yana so. Baba duk abin sa, sai ga shi ga babar su Nana, a gurin bikin Nana. Abin mamaki Imrana ne ya sanya su a gaba ya din ga yi musu nasiha, da nuna musu illar gabar da suka din ga ya haifar musu. Nene ta riƙe hannun Nana ta ce "Gimbiyarmu, dan Allah a yi mana godiya, tabbas Hammad ya cika jagora, na ji daɗin abin da ya yi wa Mahmoudu, Ubangiji Allah ya saka da mafificin alkhairi" Gaba ɗaya Nana ta so ta sake sosai a cikin 'yan uwanta. Hammad yana ta shiri a ɗakinsa, Mahmoudu ya shigo, dan bai samu sukunin haɗuwa da Hammad ba, saboda karɓar baƙi. Hammad ya kalle shi ya ce "Ango ka sha ƙamshi" Ya buɗe baki zai yi magana, Hammd ya girgiza masa kai ya ce "Ɗan uwa kai ka ke bi na bashi, dan haka babu buƙatar wani dogon jawabi ko godiya a tsakaninmu, mai girma Tafeeda Allah ya taya riƙo" Ya yi maganar yana fesa masa turaren hannunsa. "Sardaunanmu, godiya ta zama dole a tsakaninmu ai, godiya dole na... Hammad ya tsuke fuska ya ce "To jeka waje ka yi godiyar" Mahmoudu ya yi murmushi ya ce "Wallahi jin abin nake kamar a mafarki, bawa ya zama saraki ikon Allah, amma kana ganin Hanin ta amince da auren nan, tsakaninmu ba soyayya raha ce dai da girmama junanmu" Hammad ya ce "Ka na tsoro ne? Hanin na sonka, da amincewarta aka yi komai". "To kuma tana son baƙar fata" Hammad ya yi tsaki ya ce "Ka na da abin haushi wallahi. Kaf ƙabilar buzaye, ban taɓa ganin baƙi mai kyanka ba, har fararen ma, idan kuma duk baƙar fata gaba ɗaya matata ta fi kowane baƙar fata kyau" A tare suka yi dariya. Hammad ya ce "Kai mutumin kirki ne, mai nagarta na san na yi wa ƙanwata kyakykywan zaɓi ne, dan haka ba ni da fargaba" Suka ci gaba da tattaunawa cikin raha. Nana tamkar wadda za ta yi sabon aure, haka aka zaunar da ita aka din ga yi mata nasiha, Mai jidda ta nanata mata batun riƙe addu'a a duk inda take. Sai da aka kai ta har gurin Sultan nan ma ya yi musu nasiha sosai ita da Hammad. Daga bisani, Hammad ya ɗauke ta daga can gurin Sultan suka tafi, ya ce akwai walimar cin abincin dare tare da ita da danginta kaɗai, washegari kafin su wuce Nigeria. Asal kamar za ta mutu, haka take wani irin kuka tana rirriƙe Hasna. Tafawa ne yake ta bala'i ya ce "Wallahi ko za ki mutu sai ya sake ki, ban ga amfanin ki ci gaba da zama da mutane marasa mutunci ba, babu kunya babu tsoron Allah Jalaludeen ya sauke ni daga kujera ta, ya bawa 'ya'yansa, zai ga matakin da zan ɗauka a kansu." Asal ta girgiza kai ta ce "Dan Allah ka yi haƙuri, amma zan koma gidan Hammad, iya rufin asirin da ya yi mini ya isa, na yi maka biyayya iya yi na, amma ƙarshe na faɗa halaka, kuma buƙatar taka bata biya ba" "Wallahi Asal ki ka koma gidan Hammad babu ni babu ke, na gaya miki sai dai ki canza uba!" 101 Alhaji Sabo ya ce "Ya na ga ka tsaya cak haka?" Da kyar ya harhaɗo maganganun ya ce "Sabo, ce mini kai fa Amina ta mutu?" Ya ce "Eh mana, ranar da ta mutun mutane na ta tambayar ina ka ke, aka ce kana Asibiti, likitoci sun hana a zo gurin ka. Yanzu sai ka maze duk wanda ya yi maka gaisuwa ko ya zo dubiya kawai ka amsa. Ita kuma Shukura lallai ka san yadda za ka yi da ita, ka ɗauki mataki a kanta, ko kuma ka gaggauta bayar da jininta ga ƙungiya kawai" Ya yi shiru bai sake cewa komai ba, har suka isa gidansa, mutane na ganinsa suka din ga zuwa yi masa sannu, suna yi masa gaisuwa. Bai iya amsawa kowa ba, Alhaji Sabo ya ce su yi haƙuri ba ya iya magana, saboda yanayin jikinsa. Har sashensa Alhaji Sabo ya raka shi, suna zuwa ya tarar da hijjabin Hajiya Amina da sallayarta gurin da ta yi sallar walha, kafin ta fita ta bar ɗakin su Sagir su zo. Ya ɗauki hijjabin ya kalli Alhaji Sabo, ya ce "Kana nufin Amina ta mutu? Kalli hijjabinta fa inda ta yi salla" Alhaji Sabo ya ce "To shi ne me, kowa ma na haka ne ai. Kana ganin zaka iya zama a gidan nan kai kaɗai, ko a samo maka wanda zai tayaka zama?" Ya girgiza kai jiki a sanyaye, duk da mutuwar Yusf ta dake shi, amma bai taɓa jin mutuwar da ta daki zuciyarsa kamar mutuwar Hajiya Amina ba. Kan ƙiftawa da Bismillah. Ya ɗauka aljanin da ya bawa mahaifarta shikenan ya tseratar da ita daga ƙungiyar, abin da bai sani ba shi ne, bai isa ya tseratar da ita daga ajalinta ba. Ya nemi guri a gefen gado ya zauna, kawai ya din ga ganinta tana yi masa gizo. Duk izza da ƙafafa ta matan masu kuɗi, da ta'amalli da 'yan aiki, Hajiya Amina ba ta yadda mai aiki ta dafa masa abinci ba. Duk da son da yake yi mata, baya hana shi ya ci mata mutunci wasu lokutan. Amma ko ta yi fushi na lokacin ne ta ware. Ya yi mata wani irin so, mai wahalar mantawa. So yake yi ya samu damar zubar da hawaye, amma abu ya gagara. Vibrating wayarsa ta yi a kan gadon, ita ma yadda ya tafi ya bar ta, haka ya dawo ya tarar da ita. Ya ƙura mata ido daga bisani ya kai hannu ya ɗauka ya duba. Saƙo aka turo masa da lambar Doctor Sharif, ana sanar da shi Allah ya yi wa mai wayar rasuwar, za a yi jana'izarsa da yammacin ranar. Ya fito daga cikin saƙon, ya ga saƙon Yusuf na ƙarshe, da yake ce masa Daddy idan ka ga saƙona ka kira ni dan Allah na kasa samun ka a waya. Ya tuna yadda suka yi waya, Yusuf yana tsara masa yadda zai yi walimarsa na kammala master's da ya yi, suka da daɗe su na waya cikin raha da barkwanci. Ya tuna yanzu duk ba sa Duniya. "Saura kai, nan da anjima kai ne zaka mutu" Ya ji wata zuciyar ta raya masa. A take zuciyarsa ta tsinke ya buɗe idonsa a razane ya miƙe tsaye yana waige-waige. Wata irin fargaba ta shige shi, wani abu da bai san ko mene ne ba, ya tsirga masa tun daga cikin kansa har ƙafafuwansa. Da sauri ya fita daga ɗakin ya koma falonsa yana mayar da numfashi. **** Hammad ya kalli Asal da take ta kuka ya ce "Ko ki yi mini shiru, ko ki fita ki koma tun da ba dole na yi miki ba" Ba shiri ta hau goge hawayenta ta ce "Yi haƙuri, na daina" Ta yi maganar muryarta ƙasa-ƙasa. Gaba ɗaya zuciyarta babu daɗi, har ga Allah ba ta son saɓa wa mahaifinta, amma ta san ba a kan gaskiya suke ba. Kuma idan ya kashe mata auren yaya yake son ta yi?. Ta yi shiru ta rakuɓe a gefen motar, kamar mai tsoron wani abu. Ya saka hannunsa ya janyo nata ya ɗora a kan cinyarsa yana murzawa a hankali hannu ɗaya kuma yana tuƙinsa. Ta ɗaga kanta ta kalle shi, ta ga ya mayar da hankali sosai a kan tuƙinsa. Ji ta yi kamar ta kwanta a jikinsa, amma ta tuna girman laifuffukan da yake kallonta da su yanzu, dan haka ta fasa. Ko da suka je gidan, ta tarar an yi wa gidan gyara sosai, an canza furnitures. Ta kalle shi za ta yi magana, amma sai ta fasa saboda gani take kamar fuskarsa a haɗe take. "Ina fatan canje-canjen da na yi ya yi miki, ban ɓata miki rai ba" Da sauri ta ce "A'a sun yi na gode sosai" "A'a faɗi gaskiya dai, na san ki da iyayi da ƙaƙale, idan bai yi ba a mayar da kayan a canzo wasu, tun da kamfanin wata uku suka bayar idan bai yi ba a mayar" Ta girgiza kai ta ce "Yayi sosai da sosai" Duk barorin gidan ba wani sonta suke yi ba, saboda fi'ilinta da wulaƙanci, amma da suka ga ta dawo sun yi murna, dan duk da wulaƙancinta akwai kyauta. Hannunta a buɗe yake sosai da sosai gurin ungo. Shi ya zo musu da abincin da ya saka aka kawo, daga gidan Abincinsa na Agadez. Ya ci kayansa kamar ya share ta, ganin ta ƙi sakin jiki ta ci, duk da ya ce ya yafe mata, amma wasu lokutan da ya kalle ta wasu abubuwan suke dawo masa. Duk da yafiya aba ce mai wahala wasu lokutan, amma mantawa da laifuka ya fi komai wahala. "Cherié, ba za ki ci abincin ba ne?" Ta ce "Na ci" "Ba ki ci da yawa ba ai, ke da na san ki da son abinci, matso na baki a baki" Haka ya yi ta ƙoƙarin danne komai, kamar yadda ya saba yi a baya. Da suka zo kwanciya ma, kasa sakin jiki ta yi, sai raɓe-raɓe take yi, tana satar kallonsa. Shi kuwa hankalinsa yana kan wayarsa, yana tsokanar Nana da roƙonta dan Allah kar ta kasa bacci, zai zo su haɗe ta mafarki. Emojin dariya ta tura masa, ta ce "Da kenan, ka ke yi mini wannan rufa idon, yanzu ina gane komai, ka yi addu'a ka kwanta sai da safe" Ya yi murmushi ya rufe data. Ya juya ya kalli Asal ya ce "Na canza kamanni ne?" Ta ɗan sunkuyar da kai tana girgiza kai. Ya miƙa mata hannunsa ya ce  "Ƙaraso mana" A hankali ta ƙara, ya rungumo ta jikinsa, ya kwantar da ita sosai a kan gadon. Ya tashi ya je ya kashe fitilar ya dawo ya kwanta a kusa da ita. A ƙasan zuciyarsa ya din ga roƙon Allah ya sanya yafewa Asal da ya yi da sake karɓar ta a matsayin mata, kar ta sake yinƙurin cutar da shi. "Ya Allah da kyakkyawar niyya na yafe wa wannan baiwa taka, saboda ina tausayinta. Ubangiji Allah ka sanya ta gyara rayuwarta mu zauna lafiya" Sosai ya sake da ita, tamkar babu wani abu na rashin daɗi da ya faru. ***** Duk yadda Alhaji Zailani ya so kawar da komai a ransa a kasawa yayi. Ya din ga zagaya gidan yana kallon hanyar ɗakin Shukura, da har a yanzu idan ta zo gidan, a nan take kwana. Ya kalli inda Yusuf yake zama mussaman idan zai kalli ball. Suna kallon ƙwallo tare dukkanin su akwai team ɗin da suke supporting. Ya tuna kai komon Hajiya Amina a tsakaninsu, da ƙoƙarinta na ganin kowa ya samu abin da yake buƙata. Amma yanzu babu Yusuf babu Amina, Shukura kuma babu wani abu da ta tsana a yanzu sama da shi. Gidan ya yi masa wani irin zafi Duniya ta din ga juya masa. Dama salla ba wani damuwa ya yi da ita, domin rashin kiyaye ta na daga cikin dalilan da yake kawo musu rashin jituwa tsakaninsa da Amina. Ya din da ga jin sa tamkar a cikin wata Duniya yake, aka bar shi shikaɗai. Bugun ƙofar da ya yi yawa ne ya tashi ya je ya buɗe ƙofar main falon, ya tarar da mai delivery ya kawo masa abinci, kamar yadda Alhaji Sabo ya yi masa order, ya yi shiru yana tunanin ina mai gadi, da har mai delivery ya shigo haka. Ga harabar gidan babu kowa yan gaisuwa ma duk sun watse ya karɓa ya koma ya ajiye ya nemi guri ya kwanta. Rufe idanunsa ke da wuya, ya ga duhu ya yi, alhalin yamma ce da sauran haske. Ya buɗe idanunsa ya yinƙura zai tashi, amma ya ji tamkar an saka igiyoyi an ɗaɗɗaure shi, ya kasa motsa ko da yatsansa. Yana jin yadda zuciyarsa take bugawa ya sare cewa kan shi ma ya mutu ne, ya din ga rarraba idanu ya ga ta ina zai fara ganin mala'iku sun bayyana. Ya hango cewar shi ma yanzu likkafani za a saka masa a je a binne shi a rami a tafi a bar shi. Ya yi wani yinƙuri domin ya tashi amma abu ya gagara. Wata irin dariya ya ji ana yi mara daɗin ji, cikin sauti mai ƙarfi. "Abin da ka ke gudun sai ya faru, ba za ka tsere wa mutuwa ba, dole ka biya wa dodo buƙatar sa, ko kuma ya yi ajalinka. Ɗif ya daina jin muryar, sai kuma fuskar matarsa ta farko da ɗanta na fari, suka fara fitowa a ɗakin. Ya sake rikicewa sai dai bai iya kowane yinƙuri ba, Shukura ta bayyana jikinta duk jini, kamar ba ta daɗe da haihuwa ba, ta tunkaro shi gadan-gadan da wuƙa ta fara ƙoƙarin caka masa. Kamar wanda aka tasa daga bacci ya gan shi a tsakiyar titi, ƙafafuwansa ko takalmi ko babu. Ya kalli jikinsa babu suturar kirki, gari shiru ko ina duhu alamar dare ya tsala. Sai da ya yi da gaske sannna ya gano cam gaban unguarsu ya tafi. Rashin gurin zuwa ya sanya tilas ya sake koma wa gidan nasa, ya ci uwar tafiya da ƙafa ya koma. Sai dai ƙofar gidan a buɗe, babu masu gadi, abin da bai sani ba tuni zancen ya fara zagayawa, a kan abin da ake zarginsa da shi, kasancewar mai aikin gidan na laɓe ta ji maganganun da aka yi. Suna watsewa da aka tafi da Hajiya Amina Asibiti, aka tafi da Alhaji Zailani ta tattara kayanta ta gaya wa mai gadin abin da yake faruwa ta gudu. Alhaji Fatuhu ya ƙi sanar wa Iyalinsa abin da ya faru, sai dai gaba ɗaya ba shi da nutsuwa, ga kayansa ana ta saya babu ƙaƙƙautawa amma ba ya iya taɓuka komai, sai dai ya ɓuya ya yi kuka. Babu tsammani Fadila ta ritsa shi yana kuka, ya kasa cin abinci. Cikin damuwa ta ce "Daddy, ina gama ka da zatin Allah ka gaya mini abin da yake damunka, da ba haka ka ke yi ba fa. Gaba kamar ma a tsorace ka ke Duniyar, kuka fa ka ke yi dan Allah ka faɗa mini mene ne?" "Wallahi Fadila a tsorace nake da Duniyar, komai tsoro yake bani, ni dama rashin lafiyar da na yi na mutu, ban tashi ba da ban ji wannan abubuwan da damuwa da baƙin cikinsu zai halakka ni ba, bayan warkewr da na yi daga jinya ba" Ba ta san lokacin da ta fara kuka ba ta ce "Dan Allah Daddy mene ne?" "Fadila ba zan iya gaya miki ba, ku yi haƙuri kawai, Allah ya sanya mu dace" Haka ta gaji da rarrashin ta ƙyale shi. Shukura kuwa Sagir da Yusra ba abin da suke yi sai aikin rarrashinta, da bata haƙuri, Yusra ce take kula da Haidar da jaririn da ta haifa aka saka masa Ahmad Annur. Sai dai ta kasa yin lafiya, kusan kullum tana kwance, Alhaji Fatuhu duk kwana biyu sai yaje gidan ya rarrashe ta, ya bata haƙuri tare da kwantar mata da hankali. **** Da sassafe Asal ta nemi Hammad ta rasa, ta tashi ta fita falo, ta hango shi a kwnace a kan kujera yana video call da Nana. Ta tarar da shi yana cewa "Ba fa na ganin komai ma vie, dan Allah ki cire bargon nan" "A'a nifa bacci zan yi ka ke takura mini" "Zan rama ne Asmy, me za ki dafa zan shigo anjima in ganki in sha Allah" "Ba zan dafa komai ba, ai yau kana gurin matarka ta dafa ta baka" Ya marairaice ya ce "Ni ko? Shikenan tun da kin daina so na. Ɗan yi kissing goshina" Yayi maganar yana kara screen ɗin a fuskar sa. Da sauri Asal ta koma ɗaki, wani irin abu yana taso mata kamar za ta fita hayyacinta. Ji ta yi tana neman yin danasanin biyo shi ta dawo gidansa, amma ta tuna damarmakin da ya bata bayan da ya aure ta. Amma ta din ga muzguna masa, saboda hure mata kunne da Imam Omar ya din ga yi. Bai san daɗin aure ba sai da ta fara hankali ta fuskanci ba ya tanka duk rashin mutuncin da za ta yi masa. Idan zai yi magana a dankwafe shi. Sai a gaɓar da ta dawo hayyacinta ta gane shayi ruwa ne, take sonsa a lokacin ta fara karɓar sakamakon abin da ta aikata. Yanzu ba ta da wani abin cewa sai abin da ta gani kawai. Ta sha kukanta ta gode wa Allah. Nana an kai mata hadimai, duk da ba komai ta sakar musu ba. Har gida aka kawo mata dalleliyar motar da aka bata a gurin bikinsu, wanda Imam Zahradeen sabon Tafawan Agadez ne ya ba ta. Banda uban gwala-gwalai da ta samu. Ta fuskanci gold ne kyauta mafi tsada da muhimmanci da suke ba wa mutum mai muhimmanci mussaman ma mace. Lefenta kuwa, sai da ta din ga addu'a, saboda yadda mutane suka camfa duk auren da aka yi ɓarna a gurin yin sa ba ya ƙarko. Sai dai Hammad ya ce mata ai abin da aka yi mata kyautatawa ce, ba wai dukiyar aure ba. Kuma Allah ne ya tsamo ta ya bata rabonta ne. Ya kuma tuna mata a yadda aka yi auren su. Nana abin har kunya yake bata, yadda manyan mata wasu ma sun haife ta suke zuwa gidan, wai sun zo su gaishe ta, kuma in dai za su zo sai sun riƙo abin bata. Ta fara yi wa Nene ƙorafin ita wannan abin da ake yi mata ta gaji. Nene ta ce "Waye ya gaya miki ana shiga dawa dan ƙarya? Ai girma ne ya hau kanki, dan haka dole ki yi haƙuri. Ba kuma a yi wa masu mulki kyauta su mayar su ce a'a, dole ka karɓa. Kuma dole kema ki zama mai yawan kyauta. Sannan ki ƙirƙiro wani abu da zai amfani mata a ƙasar nan, saboda tabattar da za ki iya riƙe muƙamin da aka baki" Nana ta ce "To Allah ya bani iko, abinka da ba a saba ba" "Ke yi wa mutane shiru ke da ba a saba ɗin ba, dole a saba yanzu" Haka Nana ta din ga jin tamkar an ɗaɗɗaure ta saboda takura. Ranar da Hammad zai dawo, ya dawo tare da Muhsin, ta din ga murna dan har ta fara karaya Zahradeen ba zai bata ɗanta ba, ga shi tana jin nauyinsa, amma ta fara matsuwa da son ta yi magana. Nana ta ce "Sayyid amma ya dawo kenan ko?" Sayyid ya ce "To gamu nan dai, babansa sai masifa yake yi, sai da Sultan ya kira shi ya ce ya bamu ɗanmu. 'yan biyu sai kuka suke yi." Nana ta ce "Ina ma zan iya bar masa shi, amma raba ni da ɗayanku kamar raba ni da rayuwata ne" Hammad ya ce "Idan ma bayarwar ne, ba gara ki ba wa Asal ba?" Wani mugun kallo ta yi masa, da ya sanya shi yin shiru, ta saɓa ɗanta ta yi ɗaki. Baba gaba ɗaya ji ya yi kewar Nana ta dawo masa sabuwa fil, kamar a lokacin ta ɓata, daga ita har Imran, amma mussaman ma ita Nanan. Gaba ɗaya ganin da ya yi mata ya ji ɗanɗani haukaci ne. Kusan kullum sai sun yi waya ta what'sapp. Har yake gaya wa Nana an kai wa Gaddafi kuɗin aure. Ta din ga murna sosai. Ta ce "Baba Dan Allah ka yi wa Sarkin baka magana a kansu Suwaiba, dan Allah" "Wallahi Nana a kan yi mini maganar yaran nan, zan daina kira mu yi magana" Gaba ɗaya Nana ba ta jin daɗin hakan da Baba yake yi. Haka take kiran Ummanta ma, su yi waya da su Walida. Sai ga Iliyasu da karɓar waya, su gaisa da Nana yana neman yafiyarta a kan abubuwan da suka faru. Har ga Allah Nana ta tsani mutumin nan, ba zata manta abubuwan da ya yi mata ba, amma ta duba matsayin da Allah ya kaita a yanzu, dan haka ta ga ba girmanta ba ne ma zaman jin haushin wani ba. **** Kwanaki huɗu kenan, Alhaji Zailani kamar wanda aka yi wa asiri, ya kasa barin gidan, ga shi dare da rana tsorata shi kawai ake yi a gidan nan. Banda ihu marasa daɗin ji, a ɗauke shi a yi ta bugawa da ƙasa. Ko ya yi ta maƙabarta waɗanda ya bayar a ƙungiyar asiri, suna ta kokowa da shi za su danna shi a cikin kabari su rufe, yana ihu yana ƙoƙarin fitowa, ko kuma ya ga su na ƙoƙarin kashe shi. Duk yadda ya so sarrafa tunaninsa domin ya je gurin Malam Gambo neman mafita, amma ya kasa jin sa kawai yake yi a wata Duniyar daban. Tsawon kwanakin nan ya galabaita, ba ci ba sha, ba wanka ga kufcewar hankali. Yaje kitchen ya ɗaukko wuƙa ya riƙe yana zazzare ido, da nufin yana ganin sun fito masa ya caka musu. Sai dai Shukura ta bayyana, da wuƙar nan a hannunta, su na ta kokowa da shi, yana ƙoƙarin kar ya caka mata, saboda zuciyarsa na raya masa, itakaɗai ta rage masa yanzu. Kawai ya hango Alhaji Fatuhu na ƙyaƙayata masa dariya yana faɗin "Yanzu wa ya yi nasara? Ka rasa komai Zailani. Ba ka da kowa, ka kashe kowa naka, dukiyar kuma ba zata amfane ka ba. Ni kuma da ka yi niyyar hallakawa, komai nawa ya dawo, ga shi kuma dole mutuwa zaka yi" Ya saki Shukura ya nufi Alhaji Fatuhu yana faɗin "Na tsane ka, ba na ƙaunarka. Ba zan taɓa sonka ba kuma sai ka mutu, sai ka riga ni barin duniyar nan, na yi yadda nake so". Ya yi maganar yana cakawa Alhaji Fatuhu da yake gani wuƙar nan a cikin sa. Jini ne ya fara fitowa ta bakin Alhaji Fatuhu,  ya ce "Zailani wannan shi ne ƙarshen duk wanda ya gaza sarrafa ni. Ka kasa kula da ni a lokacin da na kamu da rashin lafiya. Ciwon ƙyashi ya kama ni, son duniya, hassada, mugunta, ƙeta na bushe na yi baƙi, har ka gaza sarrafa ni kullum burinka biya mini buƙatar duk da na bijiro maka, wanda ina bijiro maka buƙatuna ne, saboda samun sassaucin wannan ciwukan da suka kama ni, ka ƙi kulawa ka bani magani. Ga shi biyan buƙatuna ya sanya ka aikata abu mafi muni, ga ƙarshe mara kyau" Alhaji Fatuhu ya sake caka wa Alhaji Fatuhu da yake gani a gabansa. Wata irin zabura ya yi tare da kurma wani uban ihu, jin wani irin gigitacciyar azaba da raɗaɗi ya ratsa cikinsa. Abin da bai sani ba, da ya ɗauki wuƙar nan kansa y fara cakawa, ya fita waje yana tangaɗi, yana faɗin "Na kashe ku ɗin, na fi son duniya a kanku. A lahira rahamar Allah za ta saka na shiga aljanna a Duniya kuma ƙoƙarina ne zai tara mini abin duniya" Ya din ga surutu yana faɗar miyagun ayyukan da ya din ga aikatawa. Kafin a yi ƙoƙarin ƙwace wuƙar ya sake caka wa kansa a cikinsa, ya sulale ya faɗi ƙasa, jini yana zuba a jikinsa. Yana faɗuwa bakinsa a buɗe, Aljanin da ya mallaka ya bar gangar jikinsa. (Ya hayyu ya ƙayyum ya zuljalalu wal ikram Ubangiji Allah ka sanya mu yi kyakykywan ƙarshe, Allah ka raba mu da mummunan ƙarshe, Allah kar ka sanya mu cuci kowa🙏🙏🙏😭) Abin ka da zamani na amfani da social media, a lokacin da Alhaji Zailani yake wannan tamɓelen, aka samu masu ciro waya suka ɗauki abin da ya din ga yi, suka sanya a shafukan sada zumunta, duk wasu shafukan an sauke videos ɗin, saboda abin da yake ciki na tashin hankali. Tuni aka nemo jami'an tsaro, suka ɗauki gawar Alhaji Zailani. Sagir ne ya fara gani a social media ya tashi hankalinsa a dugunzume, ya tafi gidan Alhaji Fatuhu ya yi sallama da shi. Ya kalli Sagir ya ce "Lafiya kuwa? Ko Shukuran ce babu lafiya, na ganka kamar ba a nutse ba?" Ya ciro wayarsa ya nuna wa Alhaji Fatuhu abin da yake faruwa. Sai da ya jingina da bango sannan ya din ga maimaita Innalillahi wa Innalillahi raji'un. Ya daɗe cikin mawuyacin hali, kafin ya daidaita nutsuwarsa ya dubi Sagir ya ce "Shukura ta gani?" Sagir ya ce "A'a, ai babu waya a hannunta ma" "To ka yi duk yadda za ka yi, kar waya ta shiga hannunta. Tun da Allah ya riga ya yi masa rasuwa, komai ya ƙare. Yanzu muje gurin 'yansanda mu roƙe su a taƙaita lamarin binciken nan, a yi masa sutura a binne shi" Sagir ya sara wa zuciya irin ta Alhaji Fatuhu, a irin abin da Alhaji Zailani ya yi masa, yake cewa su je su karɓi gawarsa a binne shi. Sun sha fama da 'yan sanda, dan hana gawarsa suka yi, sai da aka je gidansa, domin zurfafa bincike. Sai dai da bincike yayi bincike aka din ga gano, abubuwa na tsaface-tsaface da suke ɓoye a cikin gidan. Sannan aka buɗe wayarsa, yanayin tattaunawar sa da wasu daga cikin abokansa, ciki har da Malam Gambo, ya sanya jami'an tsaro kama su. ***** Sayyid a gurin Asal yake, amma yaje yana damunta. Sai da ya fara shirin tafiya, ta ce masa ya jira tana da baƙi su gaisa. "Suwaye baƙin kai a Agadez? Umma ce? (Da yake haka yake kiran Nene, kamar yadda Mahmoudu yake kiran ta)" "Ba ita ba ce" "To suwaye?" "Baƙi masu muhimmancin gaske ne, za ka gani" Ya ce "To bari na je masallaci, kafin su zo" Ya yi alwala ya fita falo, ya ga Nene tare da wata mata da namiji da alamu suka nuna mata da miji ne. Su na ganinsa suka ƙara nutsuwa, domin sukan ji zancensa a bakin Nene. Cikin girmamawa suka risuna su na gaishe shi. Ya amsa yana mamakin dalilin shigo masa da ƙato haka har cikin falo. Ya dake ya ce "Umma dama ke ce baƙuwar, ta dage kar na fita sai kin zo?" Ta yi murmushi ta ce "Ba ma nice baƙuwar ba, ga baƙin nata nan" Ta yi maganar tana nuna masa mata da mijin. Ya yi shiru yana kallonsu, ba su yi kama da 'yan Nigeria ba, sun fi kama da hausawan Niger, mussaman daga yanayin hausar su. Nana ce ta buɗe ƙofa ta fito, da gudu ta nufi Hajara ta rungume ta, Muhsin ya biyo bayanta ya ja ya tsaya a kusa da mahaifinsa. "Hajara, dama zan sake ganinki?" "Gani kuwa shugabata" Hajara ta yi maganar cikin girmamawa. Nana har ƙasa ta durƙusa ta gaida Auwwal, takaici ya kama Hammad, haryanzu Nana ta kasa gane mene ne matsayinta. Banda haka ya za a yi ta durƙusa har ƙasa tana gaida mutumin da shi kansa ya girme shi, da ma dattijo ne da sauƙi. Nene ta ce "Nana ba girmanki ba ne, ai shi yakamata ya gaishe ki" Shi ma a tsorace ya ce "Wallahi kuwa" "Kash, Nene ba ni da wani girma, ni na kasa jin girman nan. Meyasa ba zan girmama mutane mafiya karamci a gare ni ba?" Ta taso tana kallon Sayyid fuskarta sharkaf da hawaye ta ce "Wannan gidan su ne je, lokacin da na baro Agadez na nemi Nene na rasa, a can gidansu aka ɗaukko ni. Sayyid lokacin da na zo Niger na sauka a Maraɗi, ba ni da kowa sai Allah, Allah ya dubi zuciyata ya ji ƙaina ya haɗa ni da mutane masu karamci. Wannan su ne sanadin haɗuwa ta da Nene." Nan ta kwashe komai ta gaya masa. Sannan ta ɗora da cewa "Ina tambayar Nene su, ta ce mini sun tafi ci rani can ƙasar Mali. Sai yau Neme ta kira ni ta ce mini sun zo Niger, su na Agadez za ta kawo su mu gaisa. Ni na so mu je har inda suke amma ta hana" Kukan da Nana take yi kawai ya tabattar masa da ba ƙaramin karamci suka yi mata ba. Ya taka ya ƙarasa gaban Auwall da kansa yake ƙasa, ya miƙa masa hannu su yi musabaha. Da kyar ya iya miƙo masa hannu. Suka gaisa Hammad ya dafa kafaɗarsa ya ce "Na gode sosai da sosai. Mutane a zamanin nan abin tsoro ne, amma ka zama mutum na farko gurin bawa matar da baka sani ba taimako. Na gode sosai da sosai, dama Umma uwata ce, kai ne dai ban sani ba, tabbas tana bani labarinku. In sha Allah ba zaka sake zuwa Mali ci rani ba, da yardar Allah  na gode sosai da sosai Allah ya biya ka" Ya kalli matarsa ita ma ya yi mata godiya sosai. Tare suka je Salla da Auwwal, Hajara ta yi nufin ɗaukar Muhsin, amma ya ƙi saboda ƙyuya. Hadimai suka gabatar da Abinci, da abubuwan sha daban daban. Sayyid a dole yake ɗaga ƙafa a wasu abubuwan duk da azabar kishin Nana da yake yi. Ya yi iya ƙoƙarinsa a kan kar ya yi wani abu da ran su Auwwal zai sosu ko na Nene, ko dan albarkacin ɗawainiyar da suka yi da Nana. Har da kyautar kayan wasan Yara, suka kawowa Yarima Muhsin. A hirar ta su suke gaya wa Nana haryanzu Allah bai ba su haihuwa ba. Ta yi ta musu nasiha da basu misalai masu kwantar da hankali. Sai isha'i suka tashi tafiya, Hammad ya yi musu alkhairi, tare da jaddada musu godiya, ya kuma gaya wa Auwwal lokacin da zai zo Maraɗi, ya ba shi katinsa ya ce idan yaje ya nuna katin za a bari ya gan shi, zai ba shi abin yi. Bangaren Nana ma, kyaututtuka ta ba wa Hajara sosai, da ta ce ba zata karɓa ba, abin da suka yi wa Nana, dan Allah suka yi mata, Nene ta ce mata ba a mayar wa da masu mulki kyauta. Sai da Nana ta karɓi lambar wayar Hajara, ta din ga yi musu godiya kamar ta tsuguna musu. Hammad ya ɗauki Muhsin ya ce da kansa zai mayar da su har gidan da Nene take, kasancewar a gurinta suka sauka a Agadez. Daga can ya so wucewa gurin Asal da Muhsin dan yana kyautata zaton bata taɓa ganinsa ba, amma Nana ba ta sani ba, tsaf za su iya yin faɗa a kan hakan. Kuma da gaskiyar Nana kome nene Asal ce ta janyo, kuma duk abin da Nana za ta yi domin ta ba wa ɗanta kariya. Bugu da ƙari kuma ba ya son duk wani abu da zai kawo musu matsala, saboda wata irin kwanciyar hankali ya tsinci kansa a ciki. Ga taraiya da soyayya da yake samu daga gurinta. Duk da haryanzu Giyaz yana taɓa shi. Amma idan yana tare da ita, da ya gaya mata alamomin da yake ji, take yi masa addu'a ko ma muraran ta ga Giyaz ɗin tare da shi. Ya tattara hankalinsa a kan Nana da ta nufo shi, ta sanya doguwar riga ta cika ta, rigar ta zauna a jikinta. Ta ce "Wannan kallon sai ka saka na faɗi tukuna?" Yayi murmushi ya ce "Sai na riƙo ki kafin ki faɗin. Ta yi murmushi ta zauna a kusa da shi, ta kai kofin hannunta bakinsa ya buɗe baki yana sha. Ta ce "Amma ka yi sauri fa" "Eh, ina kai su na juyo ne, in sha Allah idan muka haɗu a Maraɗi, zan sama masa aikin yi" "Gaskiya ka kyauta, Allah ya saka maka da alkhairi" Ta ci gaba da ba shi labarin irin taimakon da suka yi mata. Ya ƙare mata kallo sannan ya ce "Lokacin mu na Nigeria, ba wuya kin samu rabo, Allah ya sa Niger ma haka ne, Allah ya sanya ƙani ko ƙanwar Muhsin sun samu a cikin nan" Nana ta tura baki ta ce "Sai Yarima ya shekara biyar" "Wace shekara biyar kuma? Kowa so yake sai ya karɓe shi, Zahradeen nata masifa, ga Sultan ya ce gobe na kai masa shi, amma idan Allah ya sa ki ka haihu, ko an ƙwace shi mu na da wani ko?" Kawai ta yi shiru tana murmushi, dan ji take gara ta haifi wasu a ƙwace da a ƙwace mata Muhsin. Su na hira ta ɗauki wayarta, za ta nuna masa abu, sai dai tana buɗe data videon Alhaji Zailani ta fara cin karo da shi a dandalin sada zumunta. Miƙewa ta yi tsaye jikinta na wata irin tsuma, kamar za ta zare. Ya karɓi wayar hannunta ya kalli videon. Ya ajiye wayar ya ce "Shiyasa wasu lokutan shafukan sada zumuntar nan duk ba su da wani amfani" "Sayyid ba ka gane waye ba?" Ya girgiza kai ya ce "Ni ban san shi ba" "Ba ka tuna Alhaji Zailani ba?" Ya yi shiru ya tafi tunanin, kamar ya san sunan, can kuma ya ce "Na tuna, mutumin da muka fara gadi a gidansa da su Mahmoudu. To Allah ya kyauta ke mene ne naki na shiga tashin hankali haka?" "Dan Allah Sayyid ina son zuwa Nigeria" Ta yi maganar cikin tsoro da tashin hankali. "Sati uku da gama hidimar nan ki ce za ki Nigeria, a ƙalla nan da wata biyu nake son mu je tare" Sai ta rikice masa gaba ɗaya a kan ita fa dole Nigeria take son zuwa. Abu kamar wasa ya ɗauka da wasa take yi, sai da ya ga ta yanke jiki ta faɗi, jikinta ya yi sanyi ƙalau. A hankali ya ɗaga kai ya kalli tsuntsun da yake shawagi a saman ɗakin, da hakan ya tabattar masa da Ƙaisar ne ya zo mata. A ransa ya ƙudurce lallai a shirya tafiya Egypt ɗin nan, kafin su zo su ci gaba da samun matsala, su sake hana su zaman aure cikin kwanciyar hankali. Sai dai idan ya ce a yi mata passport a Niger, zai ɗan ɗauki lokaci, dan haka ya yanke shawarar za su je Nigeria a yi mata, sai su tafi. Har wajen ƙarfe goma na dare yana tare da Nana, sai dai ba ta dawo hayyacinta ba. Ya kira Asal ya gaya mata Nana babu lafiya, dan haka ta yi haƙuri ba zai samu damar dawowa a ranar ba. Asal kamar ta haɗiyi zuciya ta mutu, gani take kawai faɗa yayi, dan ya zauna ya kwana a gurin Nana, amma babu yadda ta iya. Shi kansa sai da ya raya za ta yi tunanin hakan, amma babu yadda za a yi ya tafi ya bar Nana a wannan yanayin. Duk yadda su Sagir suke yi wa Shukura ɓoye-ɓoye, sai da ta san Allah ya yi wa mahaifinta rasuwa. Hajiya Suwaiba ce ta fara ganin Videon nan, sai ba ta yi wa Alhaji Fatuhu magana ba, ta je gurin Fadila. Fadila ta ɗan yi mamakin ganin Hajiya Suwaiba a falon ta. Bayan sun gaisa ta ce "Fadila, ko Daddy ya gaya miki abin da yake damun sa?" Fadila ta ce "Wallahi bai gaya mini ba, na yi na yi ya ƙi ya gaya mini" "Kin ga wani video" Fadila ta karɓi videon tana kallo, jikinta ne ya hau karkarwa ta ce "Wannan ai Alhaji Zailani ne? Wai yana nufin Alhajinmu ya yi wa abin da yake faɗar nan?" "Nima abin da ya ɗaure mini kai kenan" Alhaji Fatuhu ne ya yi sallama, ya ga duk sun zubo masa ido, kamar marasa gaskiya. "Lafiya kuwa?" Hajiya Suwaiba ce ta yi kokarin cewa "Daddy wani abu muka gani, shi ne dama abin da ka ke ɓoye mana?" "Me na ɓoye mukun?" Ta miƙa masa wayarta, yana kalla ya ajiya, ya zauna cikin damuwa, ya ce "Koma mene ne ya faru, ya riga ya faru, dan Allah a bar maganar nan ta wuce" Hajiya Suwaiba ta ce "Amma ya batun maganganun da ya din ga faɗa, yana cewa shi ya yi maka sihiri?" "Suwaiba a bar maganar nan dan Allah" "Amma ya zaka ce a bar ta, mutumin da ya tsugunar da mu, ya saka mu a wahala, to wallahi ni dai ban yafe ba." Fadila ta sha mamakin abubuwan da ta ji a videon nan, kuma ta tsorata imani ya ƙara shigarta, sai dai tun da ta ji Alhaji Fatuhu bai musa ba, to tabbas an yi hakan. ***** Nana Bakinta ya ƙi rufuwa, wani irin farinciki take ci, ganin sun kama hanyar Nigeria. Ta din ga tuna lokacin da ta yi balaguro, daga Nigeria zuwa Niger tsawon shekaru, ta tafi zuciya a cunkushe cike da rashin sanin makoma, sai dai kyakykywan yaƙini da dogaro ga Allah. Sai ga shi a wannan karon ta nufi zuwa gidan, cike da farinciki da kwanciyar hankali. Ta so tahowa da Muhsin, amma Hammad fafur ya hana, wai sai zo ɗaukarta zai taho da shi. Sai da suka samu saɓani kafin ta taho, dan cewa ta yi muddin Asal zai kai wa ɗanta gara ta haƙura da tafiyar. Ƙarshe sai da suka kai shi gidan Zahradeen, sannan ta hakura ta taho. A garin Bauchi ta fara yada zango, duk da nan ma abin da ya faru ba zai taɓa gogewa daga cikin ƙwaƙwalwarta ba. Mama tana ta kiranta a waya ta ji ko ta kusa ƙarasowa. Ko da Nana suka isa, Iliyasu ta fara gani a ƙofar gida, ya tsaya yana washe baki, ganin Nana ta fito daga danƙareriyar mota da aka kawo ta a ciki. "Maraba, sannunku da zuwa, sannu da zuwa" Ita Nana ma abun da yake yi matan, kunya ya din ga bata. Ta tarar da su Adda Maryam da Fati da wasu daga dangin Umman, duk sun cika gidan. Sun yi murna sosai da sosai da ganin Nana. Suka din ga yi mata barka da zuwa. Nana ta sha karramawa, mijin umman sai nan nan yake yi da ita, yana washe mata baki har da yi mata raha. Baba ya din ga kiran Nana yana tambayarta sai yaushe zata ƙaraso. Ta ce masa ai ta sauka a Bauchi, sai ta kwana biyu za ta zo. Gaba ɗaya bai ji daɗin hakan ba, saboda yadda yake Alla-Alla ta zo ya sake ganinta. Sai da Nana ta kwana uku a Bauchi, Mama tana a kaita tasha a saka ta a mota, ta ce ai direbanta yana nan a Bauchin bai tafi ba. Suka sake ɗaukar hanyar Kano, jalla babbar Hausa yaro ko da me ka zo an fika. Nana ta yi kewar garinta na haihuwa ba kaɗan ba. Da sallama Nana ta shiga gidansu, Iya suturar jikinta, da yadda ta yi kyau mai ɗaukar ido ya sanya Mama yin saroro da kasa amsa mata sallamar. Nasiru ne ya fito da gudu yana faɗin Oyoyo ga masarautar Agadez da kanta. Masu arzikin zinare, masu kyauta da dama hagu ma ba ta san ana yi ba. Barka da zuwa Garkuwar matan Agadez ke ta Afrika ma gaba ɗaya." Kawai Nana ta tsaya tana murmushi, Jamila ta fito daga ɗakin, ta zo ta rungume Nana, sai Nana ta manta da batun wata Mama, ta hau murnar ganin 'yan uwanta. Nasiru ya je ya ɗaukko mata Akwatinta a mota. Nana ta dake ta ce "Mama ina wuni?" A dole bisa yaƙe Maman ta ce "Lafiya ƙalau Nana, ai kasa gane ki na yi, irin wannan gwala-gwalai haka. Ai na zata ba zaki sake saka su ba, dan kar ki yi almubazzaranci tun da da muka je fama aka yi ta yi da ke, ki ka ce ba kya so" Nana ta yi murmushi, tana tuna karatun da Ƙaisar ya yi mata, amma ta ce "To Mama yana iya, masu abu da abinsu, an ce mini haka suke adonsu, idan ka je gari ka ga 'yan gari da jela, aka ce kai ma ka nema ka maƙala. Gaba ɗaya Mama ba ta san baƙin cikinta ya fito muraran ba. Baba ma da ya dawo ya ga Nana, bakin nan a buɗe ya din ga murna yana yi mata maraba. Babu laifi sun yi nata karɓa mai kyau. Ta yi musu tsaraba mai yawa sosai kamar yadda ta yi wa mutanen Bauchi. Da daddare suna ɗaki suna ta hir da Jamila, take gaya wa Jamila abun da ta gani a waya, Jamila ta ƙara bata cikakken labarin abin da ya faru, da yadda Hajiya Sa'a take bayar da 'ya'yan Alhaji Fatuhu har ma da rashin lafiyar da Alhaji Fatuhun ya yi sai da ta bata labari. Jikin Nana ya din ga tsuma ta shiga tashin hankali, ta ƙudurce a ranta lallai a washegari za ta je gidan Alhaji Fatuhu, za ta je. Suwaiba ma ta dage ta din ga yi wa Nana hira, duk da galibin hirar tata shirme ce, tayi baƙi ƙirin duk ta bushe kamar wadda aka tsotse wa sinadaran jikinta. Gaddafi ma sun sha hira sosai da sosai da Nana. Da Safe da ta ce zata fita sai da Baba ya yi ta mitar daga zuwanta za ta fara yawo. Amma Nana ta nuna masa fitar ta dole ce, gidan Ummi za ta je. Tare da Jamila suka tafi gidan Alhaji Fatuhu. Sashen Fadila suka je, sai dai har suka gaisa ba ta gane su ba, har gara Jamila tana ta ƙoƙarin tuna ta. Yaronta Muhsin ne ya fito ya taso daga bacci, kamarsa ɗaya sak da wancan Muhsin ɗin. Nana na ganinsa ta miƙe tana faɗin "La haula wala ƙuwwata illa billah. Banda na zo gaisuwar Muhsin, da cewa zan yi Muhsin ɗina ne nan". Ta yi maganar tana ɗaukar Muhsin tana shafa kansa. Fadila ta ce "Ya salam, Anty ai sai yanzu na gane ki, malamar Muhsin ko? Ai kin canza kamanni ne gaba ɗaya. Tun da ki ka yi aure bamu sake ganinki ba" Hawaye ya cika idanun Nana, ta ƙanƙame Muhsin, tana tuna wancan. Jamila ma cikin kuka ta ce "Na yi dana sanin Hajiya Sa'a, da tuni wannan ma ta bayar da shi kamar yadda ta bayar da wancan" A razane Fadila ta kalle ta ta ce "Me ki ke nufi?" Nana ta ce "Babu abin da take nufi" Fadila ta ce "A'a ga abu nan tana faɗa, kenan da gaske Hajiya Sa'a ita ta bayar mini da Muhsin ɗina? Ya aka yi ki ka sani" "Fadila na gaya miki wannan zancen ba haka yake ba, meyasa ki ke da gardama ne? Wannan ɗin suwaye su?" Ya kalli Jamila ya ce "Wannan ba ke ce nake gani a gidan Sa'a ba? Ya aka yi ki ka san wannan zancen?" Nana ta katse shi, ta hanyar gaishe shi, ya amsa sai dai tana magana ya gane ta. Ya ce "Nana ke ce?" Nana ta jinjina masa kai tana murmushi. "Baiwar Allah kin san tsawon lokacin da na ɗauka ina neman ki? Na din ga mafarkai daban-daban da ke. Jinya na haɗu da ita bayan kin yi aure" Fadila kasancewar ba wannan maganar take buƙata ba, cikin ɗimuwa ta ce wa Jamila ta gaya mata abin da Hajiya Sa'a ta yi wa ɗanta. Alhaji Fatuhu ya fara ƙoƙarin karewa ya hana, amma Jamila ta ce "Dan Allah ku yi haƙuri, na haddass muku fitina, amma gara na faɗa dan abu ne da yake ta damuna." Nan ta kwashe komai ta faɗa, har abin da Alhaji Fatuhu bai sani ba, da yadda ta shiga ƙungiyar asiri duk sai da ta faɗa, da yadda Abba ya mutu maimakon Muhsin. Cikin kiɗimewa Fadila ta riƙe Alhaji Fatuhu tana faɗin "Amma ka zalunce ni, saboda ka kare 'yar uwakka, ka din ga yi mini wasa da hankali ka ƙi yarda da abubuwan da take faɗa. Ɗana gudan jinina aka ba wa matsafa. Ɗana fa ɗan da na sha wahala na haifa." Nana ce ta sauke Muhsin, ta je ta kamo Fadila ta rungume ta cikin rarrashi ta ce "Yanzu wannan da ki ka haifa kin san Allah zai baki shi? Dan haka ko da ita ko babu ita, Allah ya ƙaddara ba rayayye bane ba. Kuma da na san Jamila zata faɗa ba zan yadda mu zo tare ba. Ki yi haƙuri ba zan ce sai kin yafe ba, amma kar ki ɗaga masa hankali, tashin hankalinki yake gudu ya sanya ya ɓoye miki. Kina kallo ya rasa ɗansa dalilin yar uwassa, abokinsa ya cutar da shi da mugun baƙin sihiri, kar ki ce za ki huce a kansa dan Allah" Ayshercool 08081012143 Littafin kuɗi ne, a biya 1k via 0069685771 Aisha Adam stanbic 103 Fadila ta saki rigar Alhaji Fatuhu, ta koma da baya tana zubar da hawaye cikin matsanancin tashin hankali da damuwa. Nana ta din ga yi mata nasiha mai shiga jiki tare da ba ta misali da kan kanta, irin faɗi tashin da ta din ga yi bayan auren ta. A hankali kuma sai Fadila ta din ga samun nutsuwa, tana jin damuwar ta ta, ta ragu ta kaɗu sosai da sosai da jin irin iftila'i da Nana ta din ga faɗawa ita ma. Alhaji Fatuhu ya ce "Sannu Nana" Nana ta yi murmushi ta ce "Yanzu ga shi komai ya wuce, amma soyayyar da nake yi wa marigayi Muhsin, ta sanya bayan na haihu na sanya wa yarona Muhammad Muhsin, shi ma sunan shi Muhsin, zai yi sa'an wannan Muhsin ɗin" Ta yi maganar tana kallon Muhsin da ya kwanta a jikin Alhaji Fatuhu. Fadila ta ce "Yanzu har sunan Muhsin ki ka saka wa yaronki?" Nana ta ce "Ƙwarai kuwa, Allah shaida ne na so Muhsin yaron nan ya shiga raina nesa ba kusa ba. Bayan shi sai Haidar ɗin Shukura jikan Alhaji Zailani, gaba ɗaya zuciyata ta tsinke ina tsoron a ce shi ma wani abin ya faru da shi" Alhaji Fatuhu ya ce "A'a yana nan cikin ƙoshin lafiya shi" Nana ta sake cewa "Dan Allah Maman Muhsin ina sake baki haƙuri, kar ki ga laifin 'yar uwata tun da har ta nemi yafiyarki ta bayyana duk abin da ya faru ba tare da tsoron abin da zai biyo baya. Yadda aka bi aka saka ta a ƙungiyar asiri ba da saninta ba, kuma a garin ta ceci wannan Muhsin ɗin, ɗan Hajiya Sa'a ya rasa ransa kuma ita ma haryanzu fama take yi da rashin lafiya" Alhaji Fatuhu ya ce "Babu komai, dukkaninmu nan bamu wuce jarrabawa ba. Sai dai mun gode Allah, muna fatan ya zama kaffara a gare mu, domin ni jinya na sha, da sai da na din ga wari da raina, na yanke tsammani da rayuwa na rasa komai. Na ƙi yarda a yi mini maganin addini, ina tunanin ko na Asibiti ne. Wataƙila ma da Muhsin na amince an yi masa na addini da ko zai mutu zai samu afuwa. Ni kaina mafarki na din ga yi da ke kina ce mini sihiri aka yi mini, na nemi magani na yi mafarkin nan ya fi a ƙirga sannan na yarda na fara neman maganin addini. Wallahi rasa ɗana Muhsin bai yi mini zafin yadda nake tausaya wa Shukura da Zailani ya salwantar da rayuwarsa domin wai ya ga bayana ba. Innalillahi wa Innalillahi raji'un" Yayi maganar yana fashewa da kuka, saboda dauriya kawai yake yi, amma abin yana mugun cin sa. Ya kasa sakin jiki ko Allah ya isa ya yi wa Zailani da 'yar uwassa gani yake iya bala'i da masifar da suka jefa kansi ma, ta ishe su a wajen Allah ba sai ya ƙara musu da Allah ya isa ba. Sai azahar su Nana suka bar gidan, sun yi hira sosai da Alhaji Fatuhu jin sa take yi kamar uba. Yake tsokanarta da zai din ga aika mata da kaya Niger tana sayarwa. Daga gidan Alhaji Fatuhu gidan Ummi suka wuce, jikin Nana duk a matuƙar sanyaye, sai abu ya faru ta yi ta tunanin a ina ta san abin, a ina ta taɓa gani, sai ta nutsu sai ta tuna Ƙaisar ne ya nuna mata. Ummi ta din ga yi wa su Nana masifar dan me za su zo da rana haka, bayan tun safe take saka ran ganinsu. Cikin jimami da damuwa, Nana ta kwashe komai ta gaya wa Ummi. Ummi ta kaɗu ta tsure da jin labarin da Nana ta bata, sai dai sam bata bayyana mata, wai Jamila har ƙungiyar asiri ta shiga ba, ita ma Ummin bata nuna mata Baba ya gaya mata ba. Ummi ta ce 'Ina ta saka ran ki zo mu sha hira, amma kin zo mini da abin tashin hankali. Suka watsar da wannan hirar, suka shiga wata. Hira tayi hira har take ba wa Nana labarin Saleh yana gidan yari, saboda sayen kayan sata da suka yi na gwangwan an kulle shi a Lagos. Ta tambaye ta su Barira, ta gaya mata auren Barira ya mutu, Sajida kuma tashi suka yi daga unguwar gaba ɗaya. Ta gaya wa Nana cewar sau biyu Hammad yana aiko mata da kuɗi masu tsoka, ya ce ta ɗauki nata ta tura wa Uwani sauran. Nana ta ce "Ni bai taɓa gaya mini ba ma, ha tsaraba kuma ya sake bani na kawo miki" Ummi ta ce "Allah sarki, Nana kin sha wahala ashe dai Allah ya yi kina da rabon jin daɗi a duniya" Nana ta ce "Ke dai bari, irin wanda ban taɓa tsammani ba. Amma wahalar da na sha sai da na yanke tsammani da samun afuwa. Sai kuma a hankali na lura da wani tsananin da na din ga shiga, shi ya din ga sadani da hanyoyin warwarewar matsalolin nawa. Na koma na din ga istigfari saboda na yi wa Ubangiji halin namu ɗan Adam, raki da kuma gaggawa Allah dai ya ƙara datar da mu" Jamila sai koma wa tayi gefe ta yi shiru, ba ta iya cewa komai. Da suka koma gida bayan magariba, Baba ya yi ta faɗan Nana ga ga da aure, amma taje ta yi dare a waje. Ta idar da sallar isha'i, tana ƙare wa ɗakinsu kallo, ɗakin da ta din ga shan azabar a Ƙaisar a cikin sa. Kawai ta tuna lokacin da ta ga bararoji na shan jinin Suwaiba. Ta kalli inda Suwaiban take, ta koma kamar wata mai shan inna, duk ta bushe ko abincin kirki ba ta ci, ƙwaƙwalwarta ta taɓu sosai da sosai. Ba shiri ta tashi ta aika Nasiru, ya nemo mata tazargade. Da kanta ta ɗauki Alqur'ani ta din ga karantawa tana busa wa a ruwa. Ta idar ta ba wa Suwaiba, ta shashashfa mata ruwan a jikinta, ta rungume ta tana ci gaba da yi mata karatun Alqur'ani ƙasan zuciyarta ta din ga yi mata addu'a da fatan Allah ya yaye mata wannan ciwon. Kullum sai Sayyid sun yi waya da Nana, aka fara processing yi mata passport, da kuma visa a Nigeria. Kwanan Nana uku, sai ga Suwaiba na iya cin abinci, Jamila ma tana cewa yanzu tana iya bacci sosai, ba tare da ana tsorata ta ba. Nana ta yi mata nasiha sosai da sosai a kan kula da ibada da kuma yin addu'a. Yaya Atine da kanta ta wanko ƙafa ta zo gidan, tana bala'in Nana ba ta je ta gidanta ba. Da ta ga Nana ba ta kula ta ba, sai kuma ta hau kame-kame tana faɗin "Haba ta gidana, a ce kin zo takanas bayan tsawon shekaru ba kya nan a ce, kuma ba ki taka kin je inda nake ba? Babu faɗa me ya kawo gaba Nana?" "To Yaya Atine kwata-kwata yaushe na zo garin, sai a hankali ai nake zagayawa amma kin zo kina ta faɗa" Nasiru ya ce "Ke ma dai Yaya Atine da fitina ki ke, ya za a yi ki zo ki rufe basarakiya da faɗa haka, kin ma ci sa'a da ta kula ki. Nanan yanzu fa ba wadda ki ka sani da ba ce" "Aikuwa na ga alama, maganar ma da kyar take yi, aishikenan" Nana duk gidansu ta rasa wanda ya ke da lambar Sarkin baka, kowa sai ya ce mata ba shi da ita. Nana ta kira lambar Sagir, kamar yadda ta karɓa a gurin Alhaji Fatuhu. Bayan sun gaisa ta ce masa kwatancen gidansa take nema, za ta zo gurin Shukura. Ya kwatanta mata ta yi masa godiya ta kashe wayar. Tana katse kiran, kiran Sayyid ya shigo wayarta. Ta yi murmushi ta ɗaga ta ce "Masoyi" Ya yi murmushi ya ce "Bayan kin tafi kin bar ni, kewa duk ta dame ni. Jina nake yi kamar maraya. Tabbas Nana ke rayuwata ce, ina roƙon Allah ya bamu jinkirin rayuwa mai amfani tare da ni da ke masoyiyya" "Amin ya hayyu ya ƙayyum. Ni kaina duk da ina farincikin ganin yan uwana, amma ina kewarka kai da Yarimana" Hammad ya kalli gefensa da larabci ya ce wa Muhsin "Zo ga Ammi, zo ka gaishe ta" Muhsin ya matsa kusa da Hammad ya kalli screen ɗin wayar, ya kwaɓe fuska kamar zai yi kuka ya ce "Ammi ki dawo" Jikinta ya yi sanyi ta ce "Haba yarimana, kar ka yi kuka ka ji, da wuri zan dawo ba zan iya jure ganin ka yi kuka ba" Ya jinjina mata kai. "Wai zuwa ka yi ka ɗaukko shi?" "Eh mana, karɓo shi na yi aro, muka taho gida, tun jiya ma yana gurina" Kamar ta yi magana sai ta fasa. Ya ce "Ki kwantar da hankalinki, ban kai mata ɗanki ba, amma dole zan kai shi ta gan shi, ko da kuwa ba ta ƙaunarsa, amma zan yi hakan ne idan ki na nan. Ki zama cikin shiri daga kowane lokaci wataƙila ta nan Nigeria za ki tafi Egypt mu haɗu a can" "To ai saura kwana uku na taho" "Eh, za a jinkirta tahowar ne, gara ki tafi ta Nigeria." Nana ta ɗan langaɓar da kai ta ce "To ai ni ban san ya ake abubuwan ba, kuma idan na zo ina zan yi?" Yayi dariya ya ce "Idan kin je ba ɓata za ki yi ba, ni zan je na taho da ke" Sun daɗe su na waya, sannan ta ajiye ta shirya. Tun da Nana ta zo gidan nan abinci mai rai da lafiya ake ci sau ukun nan, kuma duk abin da aka girka har maƙwabta ake kaiwa. Mama ga shi tana cin arzikin nata amma baƙin ciki kamar ya yi ajalinta, da ba 'ya'yanta ne a wannan daular ba. Gaddafi ma da yake ta shirin aure, shi ne yake kai komo gurin shirin tafiyar Nana Egypt. Ta gama shirinta, suka fita da Jamila, Baba har mamaki yake yi yadda Nana ta shiga cikin su take rayuwarta, domin shi Jamila tsoro ma take ba shi. Ita kuwa Nana abubuwan tashin hankalin da ta gani a rayuwarta, ba ta ɗauki wata ƙungiyar asiri da Jamila ta shiga da Muhammad ba. Su na ta sallama a falo babu kowa, can ƙasa-ƙasa suka ji an amsa. Nana ta yi shiru tana tunanin kamar ya san muryar. Yusra ce ta fito tana amsa sallamar. Tana ganin Nana ta ruɗe ta tafi ta rungume ta, "Ƙawata kece? Ina ki ka tafi ban sake ganinki ba, kowa na yi wa maganar ki, sai a ga kamar shirme nake faɗa". Cikin mamaki Nana ta ce "Ƙawata me ki ke yi a gidan nan kuma?" Cikin zaƙuwa ta ce "Ai Sagir ya dawo da ni tuntuni" "Ma sha Allah, Alhamdillah ya gida ina Hajiya da Siyama?" "Su na Abuja" "Ƙawata kin canza kamanni, kin yi kyau kin ƙara ƙiba tubarkallah, ina mijinki buzun nan?" "Yana Agadez. Ni gidan wata Shukura aka kwatanta mini kuma na zo na ganki" "To ai ita ma gidanta ne, ba Maman Haidar ba? Mijinmu ɗaya bari na kirawo miki ita, ba ta da lafiya ne ma" Ta juya ta nufi wata ƙofa, Nana ta din ga mamaki. Jamila ta ce "Ita wannan ɗin a ina ki ka santa?" "Gidan da muka yi gadi, a gidan suke" Mintuna kusan goma sha biyar, sannan Yusra ta fito, rungume da jariri a hannunta, ga Haidar ya zama saurayi Sagir kuma ya riƙo Shukura tana takowa a hankali. Nana ta miƙe tsaye, ganin Shukura ta rame sosai ta yi duhu, tana ganin Nana ta fashe da kuka. Cikin sanyin jiki Nana ta nufe ta tana "Faɗin Subhanallah" "Nana kin gani ko? Ki ka ce mini mafarki ba gaskiya ba ne ba, ni ga shi ya zama gaske Daddy ne ya yi amfani da ɗana ya yi tsafi, Mummyna ta mutu, ya kashe Yusuf ya kashe mahaifiyarmu da babban yayanmu. Nana ban yi dacen uba ba" Sagir ya ce "Shukura meye haka wai? Wannan ba sirrinki bane da yakamata ki ɓoye ba?" "Babu abin da zan ɓoye, Nana ta riga ta san komai" Nana ta rungume Shukura tana kuka ta ce "Kina nufin Yusuf da Hajiya Amina sun mutu? Tayaya mafarki ya zama gaske? Waye ya gaya miki da gaske ya bayar da jaririnki, ba gaskiya ba ne" Tamkar za ta shiɗe ta ce "Wallahi gaskiya ne, shi ya gaya mini da bakins, bayan ya saka an sace ni, da niyyar ya sake kashe mini jaririna" Jikin Nana ya yi wani irin sanyi, ta tuna Ƙaisar ya ce mata aljanu na iya nuna wa  mutum abu a mafarki saboda su haɗa faɗa. Sai dai ga shi abin ya tabatta. Ta rasa tausayin wa za ta fi ji ne? Fadila ko Shukura? Haka nan ma ta din ga rarrashinta tana ba ta haƙuri, tana tuna yadda ita ma Alhaji Zailani ya sako ta a gaba. Yanzu duk daɗewarsa a duniya, duk tara kuɗin da burin tara arzikin ya tara ya tafi ya bar shi a banza, ga tonon asiri da mummunan ƙarshe, waɗanda ya bari da za su iya yi masa addu'a duk ya bar musu mummunan tabo a zukatansu, da babu lallai su iya yafe masa balle ya samu addu'a. Ta kalli Haidar ta ce "Ka gane ni Haidar?" Ya yi murmushi ya ce "Eh Anty Nana ce" Sagir ya ce "Amma baka gaishe ta ba?" Ajiyar zuciya da Shukura ta yi, ya sanya Nana mayar da hankalinta kanta, Nana ina ji a jikina nan kusa zan mutu nima, nauyin da ƙirjina yake yi mini da numfashi da nake yi da kyar, na san nima nawa ajalin ya zo. Ki zama shaida idan na mutu kar a ba wa kowa ɗana sai Yusra. Da fari na ɗauki mugun kishi na saka a raina, amma daga bisani abin da Yusra ta yi mini na alkhairi na tabattar da ba kowace kishiya ce kishiya ba, Yusra tana da kyawun zuciya" AREWABOOKS Cikin tashin hankali Yusra ta ce "Ka ga zata ci gaba ko?" Sagir ya ce "Dan Allah Shukura ki daina maganar nan, kina ganin ba ta da cikakkiyar lafiya, tun da ba ta so ki daina dan Allah" Nana ta matsa kusa da Yusra da tuni manyan idanunta suka tara hawaye, ta kalli jaririn hannunta, ta ce "Wannan naki ne?" "Na Maman Haidar ne" "Ma sha Allah" Kawai Yausra ta miƙa wa Nana hannu tana murmushi. Nana ta kama hannun nata. A take ta ji jikinta ya yi sanyi. "Haula" Ta furta a hankali. "Ina yi miki barka da Gimbiyar Agadez, mai ɗauke da abin al'ajabi" Nana ta ce "Haryanzu ba ki rabu da ita ba dama?" "Ke kin sanmu akwai alƙawari, ina yi miki fatan alkhairi" Ta zare hannunta daga na Nana. Nana ta dubi Sagir ta ce "Kana nema mata magani kuwa? Ko kaima ka fi yarda da ciwon Asibiti ne yake damunta?" Ya ce "Haka suka ce mini a gidansu, Asibiti muke zuwa ganin likita" Nana ta ce "Gaskiya yakamata a yi mata na islamic ma" Nan ma Nana ta daɗe tare da su, sosai Shukura ta ji daɗin zuwan Nana, ita kanta Yusra ta ji daɗin zuwan nasu. Nana ta yi wa Shukura alkhairi, suka yi musayar lambar waya, ta tashi suka tafi. Daga gidan su Yusra, kasuwa suka je, Nana ta yi wa su Jamila sayayya sosai da sosai. Su na tafe a hanya Nana ta ce "Jamila, to kuma da gaske kin iya kasuwancin saye da sayarwar da Hajiya Sa'a take yi, ko kuma ba kasuwancin ku ke ba gaba ɗaya?" Jamila ta ce "A'a tana kasuwancin, na iya" "To jari nake son baki, ki je ki fara kema, na yi magana da Nasiru ma, da makaranta nake son ya koma, amma ya ce; shi gara na ba shi jari, zai fara sayar da omo da sabulai da ake yi a kasuwa. Dan Allah Jamila idan kin fara Allah ya sanya albarka, ki kula da iyayenmu. Kuma duk abin da ku ke buƙata muddin bai fi ƙarfina ba, ki yi mini waya tun da Alhamdillah inda nake babu abin da zan ce wa Allah sai godiya. Kuma na san ba wayona ko dabara ta ce, ta sanya Allah ya kai ni inda nake ba. Kuma Allah bai tsame ni ya yi mini wannan ni'imar dan ya fi sona ba. Kuma ina fatan a cikinmu Allah ya ƙara ɗaukaka wani, sama da inda nake ni a yanzu" Jamila har da kuka, tare da bawa Nana haƙurin abubuwan da babarsu da su suka yi mata a baya. "Jamila, idan Allah ya yi wa mutum ni'ima, idan ya yi gaba ba ya waiwayen baya, idan ba alkhairi zai kalla ba, ki manta komai ya wuce kamar ba a yi ba". Jamila ta yi ta nuna wa Mama kayan da Nana ta saya musu, da batun jarin da za ta bata, amma ta kwaɓe baki. Nana ba ta damu ba, ta yi wa Baba ɗinke-ɗinke. Gaddafi ya shigo, ya ce "Nana, mun yi waya da mijinki, ya ce bai same ki ba. Ki shirya jibi in Allah ya kaimu, jirgin ƙarfe goma za ki bi, zuwa can Egypt ɗin" Nana ta ce "Kai da wuri haka, na ɗauka za a kai irin kwanakin nan" Gaddafi ya ce "To ai abin da yake naku ne manya, kuna da alfarma a ko ina, ga shi nan har an yi an gama" Baba ne ya kalli yadda Mama ke yamutsa fuska, a hasale ya ce "Wallahi Rabi idan ba ki yi wasa ba, baƙin ciki ne zai kashe ki. Duk da abubuwan da ki ka din ga yi wa yarinyar nan, ga shi kina ta cin arzikinta da ke da 'ya'yanki, ba ta yi muku baƙin ciki ba, amma da ta motsa, ta yi wani abin alkhairi ko wani abin alkhairi ya same ta, sai ki kwaɓe baki ko ki kushe" "Ni kar ka yi mini sharri, me na yi wa Nanan, Allah na tuba me Nana take da shi, da zan yi mata baƙin ciki?" Baba ya ce "Eh batabda komai, sai abin da yake tukunyarki ki ke ci kika yatsins fuska saboda baƙin ciki" Takaici ya ishi Nana, ta tashi ta bar gurin. **** Nana tamkar idanunta su faɗo, saboda rarraba idon neman Sayyid. Sai kalle-kalle take yi kamar ma dai a tsorace take. Fararen fata da baƙaƙe, sai kai wa suke yi suna komowa. "Kamo ta nan" Yayi maganar yana rungumota, ta zabura a tsorace. Ya yi dariya ya ce "Matsaoraciya kawai, sai rarraba ido ki ke yi" "Shi ne zaka tsorata ni, da na yi ihu fa?" "Sai a yi miki dariya" Yayi maganar yana jan karan hancinta. Ya miƙa mata hannu suka gaisa, ya ce "Ya mutanen Nigeria su na lafiya?" Ya ce "Lafiya ƙalau Alhamdillah, su na gaishe ka" Ya ce "Ma sha Allah, in sha Allah da mun dawo, zamu sake zuwa tare, na gaishe su" Ya riƙe hannunta, suka shiga taxi suka tafi. Katafaren Hotel ne, suka sauka a ciki, gaba ɗaya Nana jin ta take yi, kamar ba ita ba, kamar mafarki take yi. Ya yi order Abinci, aka kawo mata, ta yi wanka tayi salla. Abinci kawai ya iya bari ta ci, ba tare da bata damar hutawa ba, ya ce sai ta biya shi kwanakin da ta yi a Nigeria ba ta nan. Nana dai da ya ishe ta, kawai ta hau kuka, ya lumshe idanu yana ƙare mata kallo. Ya yi murmushi ya ce "Ke yanzu dan Allah ba ki ji kunya ba abin da ki ke yi mini?" "Kai dai za ka ji kunya, haba daga zuwana?" Ta yi maganar tana hawaye. Ya tashi zaune yana leƙa fuskarta, fafur taƙi kallonsa, ƙoƙarin kare fuskarta take yi, amma yaƙi bata damar hakan. Ya ce "Ni fa zuwan nan namu da biyu, honeymoon muka zo" "Wane honeymoon, wanda ka yi a Agadez bai ishe ka ba, sai ka dame ni, daga zuwana ni dama ban zo ba" Hammad ya ce "Gaskiya na Agadez bai ishe ni ba, na fuskanci ƙanin Yarima da rigima ya zo, lokacin Yarima ai ni ake lallaɓawa ina jan aji. Idan kuma ba haka ba, mutum ya musa na tuno wa mutum abin da ya aikata" Murguɗa masa baki ta yi, tana goge hawayen fuskarta. Shi kuwa ya saka ta a gaba, ya din ga yi mata dariya. Sai da suka shafe kwana uku, da zuwa, har sai da Nana ta manta da abin da ya kawo su, sai dai ta ci abinci Hammad ya yi rigimarsa. Kwana na huɗu suka bar garin da suka sauka, suka tafi garin da malamin yake. Kafin su bar garin, sai da ya zagaya da ita ta ga gari sosai da sosai. A can garin ma da suka je, a Hotel suka sauka, sai dai a wannan karon ta tarar da Sultan da Matawalle su ma duk su na Hotel ɗin kowanne ɗakinsa daban amma. Sultan kamar ya ga 'yar cikinsa, ya din ga tambayarta ya ta baro 'yan uwanta da iyayenta. Washegari da safe suka hau mota, suka tafi gidan mutumin. Balarabe ne, sai dai yana jin turanci, tun da suka je gaban Nana ya tsananta faɗuwa. Ya yi musu kyakykyawar tarba, sai dai Nana ko buɗe bakinta ta kasa yi, balle ta gaishe shi. Ya kalli Nana cikin harshen turanci, ya ce "Sannu da zuwa" Ta sunkuyar da kai ta yi shiru, ta ɓangaren Hammad ma, jikinsa sai tsuma yake yi. Da larabci suka din ga tattaunawa, Sultan da mutumin, tana iya fahimtar abin da suke faɗa amma ba duka ba. Ya miƙe tsaye ya kalli Hammad, ya ce ya biyo shi, da shi da Sultan. Nana ta koma gefe ta rakuɓe, ta din ga tunane-tunanen da ita kanta ba ta san daga ina take yin su ba. Gaba ɗaya ba ta cikin nustuwarta, ba ta kuma iya tantance abin da take ji. Wani irin sanyi ya din ga ratsa ta, sannu a hankali ta din ga jin wani irin ihu mara daɗin ji. Ta saka hannu biyu ta toshe kunnuwanta, ta din ga jin tamkar ana ɓarar da kaya, ko ana kokowa da wani irin abu mai nauyi. Har azahar ta yi, Nana ba ta ga fitowar Hammad ba. Aka bata ruwa ta yi alwala ta yi salla, aka kawo mata abinci, amma ta kasa ci, hankalinta a tashe ba ta ga Hammad ba, ga kuma yanayin da take ji a jikinta mara daɗi. Sai wajen la'asar, sannan aka fito da Hammad, Sultan ya riƙo shi idanunsa a lumshe. Hankalin Nana ya tashi, ta miƙe tsaye tana faɗin "Lafiya meya same shi?" Sultan ya ce "Babu abin da ya faru, ki kwantar da hankalinki zai wartsake in sha Allah" Dattijon nan shi ne mai maganin, ya fito ya jagorance su har wani ɗaki. A ciki aka kwantar da Hammad, sai ajiyar zuciya yake yi, jikinsa yayi jawur hatta gashin kansa a hargiste, rawaninsa ma da babbar rigarsa a hannu Matawalle ya fito da ita. Ta din ga mamakin, yaya aka yi haka? Me aka yi masa ya fita daga hayyacinsa haka. Sai warin wasu mayuka yake yi, da ta gaza gane kowane iri ne. Su Sultan suka fita yin salla, Nana ta ƙarasa kusa da Hammad, ta taɓa shi, ta shafa gashin kansa ta ce "Sayyid, Sayyid ka na ji na kuwa?" "Mmm" ya amsa da kyar. "Mene ne, me ya yi maka?" Ya girgiza kai ba tare da ya buɗe idanunsa ba. Da su Sultan suka dawo, suka tarar da ita hankali a tashe. Matawalle ya ce "Ki kwantar da hankalinki, zai wartsake a hankali in sha Allah. Ya ce sai dai mu kwana a nan, mu ga yanayin jikin nasa tukuna, sannan kema ya duba ki" Kasancewar mutumin babban malamin ruƙiyya ne, da magungunan musulunci yana da gurin saukar baƙi, saboda yadda ake zuwa daga garuruwa gurinsa. Sannu a hankali Hammad ya dawo hayyacinsa, har ya yi salla ya ci abinci, amma kana kallonsa zaka gane ba ya jin daɗi. Nana dai ba ta iya tambayarsa komai ba. Sultan ya tambaye ta, za ta iya kwana da shi, ko a bata wani ɗakin, ta ce zata iya zama tare da shi. Ba da wani shiri suka taho ba, kasancewar ba su san za su kwana a gidan ba. Gidan Sarkin baka ne ya faɗo mata, da irin gane-ganen da ta yi a gidan. Ta nemi guri ta kwanta a kusa da Hammad, ta ji ya matso da ita jikinsa, ya ƙanƙame ta. Kamar wadda ta farka daga bacci, haka ta ganta a Libraryn Ƙaisar. Sai dai gurin ya ɗan yi duhu, sheshsheƙa ta din ga jiyowa daga wani guri, ta tafi a hankali tana sanɗa. Tana buɗe ƙofar da take jiyo sautin ta ga wani irin ƙaton guri, Ƙaisar na durƙushe a kan gwiwoyinsa, ya saka wani abu dogo da ba ta san ko menene ba a gabansa, yana wani irin kuka. Da sauri ta ƙarasa gabansa, ta gefen mayafin take hango wani abu baƙi ƙirin kamar an ƙona itace. Sandar Giyaz ta gani kwance a gefen abin da yake gaban Ƙaisar ɗin, a razane Nana ta ce "Giyaz ne ya mutu?" Kawai Ƙaisar ya sake fashewa da kuka, yana yaye mayafin da ya rufe Giyaz. Ya yi wani irin baƙi kamar dutse yayi gobara. Ga wani irin tsawo mara misali da yayi, sai gemunsa da ya ƙara wani irin tsawo. Nana ta ja da baya a razane. Ƙaisar ya kifa a kansa yana wani irin kuka. Ji ta yi an girgiza ta, ta buɗe idonta, ta ga Hammad ya tsare ta da ido ya ce "Lafiya kuwa? Meyafaru?" Kasa magana ta yi, sai ajiyar zuciya da take yi kamar za ta shiɗe. Duk da jikinsa babu ƙwari haka ya din ga rarrashinta, yana tambayarta mene ne, amma taƙi magana. Da kyar ta tashi ta yi sallar asuba. Aka kawo musu abin karyawa, amma ta ƙi ko kallon abincin. Da ta tuno yadda Ƙaisar ya rungume Giyaz yana kuka, sai ta hawaye yana zubo mata. Hammad ya fita daga ɗakin, bayan mintuna kaɗan, ya dawo ya ce ta taso. Jikinta gaba ɗaya babu ƙwari, ta tashi ta bi bayansa. Ko su Sultan kasa gaisar da su ta yi, tana ganin Hammad ya nufi hanyar da aka bi da shi jiya, ta ja ta tsaya. Ya ce "Meya faru ne? Mu ƙarasa mana" Ta girgiza kai ta ce "Kai dai ka je, ni ba zani ba" "Saboda me?" Ta yi shiru ba ta ce komai ba. "Ma viee, ki yi haƙuri babu abin da zai faru in sha Allah, magani za a yi mana mu rabu da wannan larurar, mu samu kwanciyar hankali mu zauna lafiya mu rayu kamar sauran mutane" Ta ce "Ni ba na so" Ta yi maganar tana kuka. Sultan ya ƙaraso ya ce "Meyafaru ne?" "Ni ba zan je ba, a ƙyale ni ba na so" Da gaske Nana ta kafe, ta ce ba za ta shiga ba, Matawalle ya shiga ya yi wa mutumin magana. Mutumin na fitowa ta juya zata arta da gudu. Hammad ya riƙo ta, ya ce "Amsy me yake damunki ne?" "Wallahi ba za a kashe Ƙaisar kamar yadda aka kashe Giyaz ba. Wallahi ba zan je ba. Da ya kashe shi gara ni ya kashe ni" "Asma'u, kin zaɓi aljani a kaina da rayuwar aurenmu kenan? Ki nutsu mana" Hammad ya yi mata magana cikin tsawa. Tana kuka ta ce "Wallahi ba zan tsaya ba, shi ma mai rai ne, kuma yana son rayuwarsa, ba zan tsaya a kashe ƙaisar ina gani ba" Mutumin ya tambayi Hammad, me take faɗa ne. Hammad ya yi masa bayani, cikin harshen turanci, yake gaya wa Nana, ba shi ya kashe Giyaz ba, taurin kai Giyaz yayi shi ya kashe kansa da kansa, amma ba shi ya kashe shi ba" "Ni dai ku ƙyale ni, zamu rabu a hankali, idan na bari aka kashe shi a dalilina ban yi masa adalci ba, ko ya cutar da ni ta wani bangaren bai cutar da ni ba. Ni dai kar a kashe shi dan Allah." Sultan ya sassauta murya ya ce "Kina ji, ba kashe shi za a yi ba, za yi miki tsakani da shi ne ya rabu da ke, amma ba kashe shi za a yi ba. Wancan ɗin ma ba shi ya kashe shi ba, shi ne ya kashe kansa dan kawai an nemi ya musulunta ko a ƙona shi" Nana ta girgiza kai ta ce "Ƙaisar kuka yake yi, an kashe babansa, ni ku bari zan yi magana da shi, yana cikin jimami dan Allah kar ku kashe shi" Ta ƙarasa maganar har da haɗa hannayenta biyu alamar magiya. Hammad ya rungume ta, ganin yadda take neman ta fita daga hayyacinta, ga shi yana kyautata zaton tana ɗauke da juna biyu. Nana tana da matuƙar raunin zuciya, da tausayi banda haka ya za a yi abin da ya wahalar da ita, ta din ga wannan kukan ta ce ba za a raba ta da shi ba. 104 Sosai Nana ta rikice musu, take ta uban kuka, babu irin ban haƙuri da rarrashin da Hammad bai yi mata ba, amma ta ƙi saurararsa tana cewa ita ba za a kashe Ƙaisar ba. Malamin ya ce su rabu da ita, su koma masaukinsu su kwana biyu ta samu nutsuwa, sai su dawo da ita. Har suka koma masauki, Hammad bai kula Nana ba, gani yake yi kawai kamar ta fifita zama da Aljani a kansa, ban da haka ita da kullum cikin taka tsantsan take da imaninta da rayuwarta, me za ta yi da zama da aljani, aljanin da babu abin da ya yi face wahalarwa da muma azabtar da rayuwarta. Ita ma ba ta kula shin ba, ba ta bi ta kansa ba, Sultan ya ja masa kunne sosai a kan kar ya yi mata faɗa, ko kuma ya ce zai takura ta. Kamar wasa Nana abu har da rashin lafiya, zazzaɓi sosai da sosai, ta ƙi cin abinci. Da ta tuna yadda ta ga Ƙaisar yana kuka, sai jikinta ya yi sanyi, shi ma halittar Allah ne, cutar da shi ba zai kawo masalaha ba, wataƙila sai ma ta'azzara wasu abubuwan. Tun bayan tariyarsu, ba su taɓa yin faɗa ba sai a wannan lokacin. Da daddare ma a ƙasa ya kwanta, ba ta ko saurare shi ba, ta haye gado duk da rashin cin abinci da ta yi, ya tsaye masa amma ya dake ya ƙi kula ta. Gefe guda ta hango Ƙaisar, yana zaune ya saka wata hanya a gaba ya takure yana kallon hanyar. Jiki a sanyaye Nana ta ƙarasa gefensa ta zauna ta ce "Ƙaisar" Ya waiwayo a hankali ya kalli Nana ya ce "Na'am" Ta yi ajiyar zuciya ta ce "Ina matuƙar jin nauyinka, da kuma kunyarka, ban ma san me zan ce ba, ina mai baka haƙurin rashin mahaifinka da ka yi". Ya ɗan jinjina kai ya ce "Haƙiƙa mahaifina ya so ni, so mai tsanani, duk mai sonsa to ya so ni. Sai dai bayan mun raba gari babu yadda ban yi ba ya gane gaskiya, amma abu ya gagara. Ban ji baƙin cikin mutuwar mahaifina kamar mutuwar da ya yi a matsayin kafiri babu ta inda zan yi masa addu'a na roƙa masa Allah gafara. Tabbas Giyaz shi ya kashe kansa bayan malamin nan ya takura masa a kan ya musulunta ko ya ƙona kansa." Ya yi maganar cikin matsananciyar damuwa. Nana ta rasa abin yi, a hankali ta ce "Ka yi haƙuri, babu wanda ya isa ya shirya wani, idan ba Allah ba, wannan ita ce taka ƙaddarar" Ya jinjina mata kai, sannan ya ce "Me yasa ba kya son a kashe ni? Ko a raba mu?" Nana ta ja numfashi sannan ta ce "A tarayyata da kai, duk da akwai ƙalubale mai tarin gaske, amma na koyi darrussa daban-daban, kuma na fahimci abubuwa da dama. Tabbas yadda muke da mutanen kirki da kuma ɓata gari, kuma ku na da na kirki da ɓata gari a cikin ku. Kamar yadda nake yawan faɗa, idan ka na son ka zama mafi alkhairin mutane, ka rinjayar da alkhairi a kan sharri. Kuma bayin Allah ne, ku na taku da rayuwar Allah ya sanya mu rayu da mu da ku a Duniya ɗaya, duk da mu na da banbancin halitta, bai kamata ɗayanmu ya zamana yana cutar da ɗaya ba, ko amfani da ɗaya gurin fin ƙarfi da mugunta ba. Ni dai a yanzu zan iya bugun ƙirji na ce a cikin halittar aljanu akwai bayin Allah, sai dai su ma ajizai ne su na aikata laifuka kamar yadda ɗan Adam yake yi" Ƙaisar ya jinjina kai kamar ba zai yi magana ba, sai kuma ya ce "Haƙiƙa nima tarayyata da ke na fuskanci abubuwa da dama game da rayuwa, kuma ina son baki wasu saƙonni da yakamata bil adam ku sani. Na ƙaru da abubuwa da dama ta ɓangarenki. Tabbas ba na cikin baƙaƙen aljanu, kuma ni musulmi ne, sai dai ban tsaya na fahimci addini yadda yakamata ba, gaba ɗaya na fi mayar da hankalina gurin burina, na sanin magunguna. Na ji daɗin samun ahalinki, gurin amfani da su, domin baje kolin baiwar da Allah ya yi mini, sai da kash, Duniya ɗaya muke rayuwa da ku, amma tsarin taku rayuwar ya banbanta da namu da cikin ƙiftawar idanu zamani yake canzawa. A lokacin da ki ka zo, nake farincikin samun cikakkiyar damar ci gaba da ayyukana, ashe lokacin ilimin addini ya daɗe da yawaita, duk da wasu sun rintse idanunsu daga kallon ilimin, su na aikata ɓarna fiye da ta sauran mutanen baya da suka rayu da jahilci. Rayuwa tare da ke, ya ƙara haska mini juriya a cikin ƙaddara, da taka tsantsan da tsananta imani da Allah. Duk tsanani da zafin ƙaddarar da ka ke ciki. Sannan kasancewaka mutumin kirki, ko mai tsoron Allah baya canza ɗabi'ar duniya ta zama mai adalci a gare ka, ko hakan ya hana Allah ya jarrabe ka. Wasu lokutan jarrabawa ta fi tsananta ma a lokacin da ka fi tsananta addu'a. Haka zalika idan Duniya za su taru domin su amfanar da kai wani abu, ba za su amfanar da kai komai ba, face abin da Allah ya rubuta maka, haka zalika idan za su taru domin su tauye ka da wani abu, ba za su tauye ka da komai ba face abin da Allah ya rubuta maka. Ban taɓa tsammanin tsakanin ke da mijinki wani ba zai mutu ba, saboda tasirin mugun tsafin da aka yi masa, ni kuma ga haushinki ina ji, ga burin Giyaz na ɗaukar fansa a kan ki. Haƙiƙa wanda ya dogara da Allah, Allah ya isar masa, ko ba a zo wannan gaɓar ba, ni da kaina zan tafi na bar ki, na yi nesa da ke da zuriyar ki. Zan yi ƙoƙarin shafe duk wani tarihin abin da ya faru a tsakaninmu da zuriyarku, kar a samu wani ya fito daga tsatsona ya nemi sake ɗaukar fansa. Ni kaina zan tafi inda ba a sanni ba, saboda kar wataran na ji na karaya na nemi sake dawowa gare ku, na kasa cika alƙawarin da na ɗauka. Zan ci gaba da neman ilimin addini, zan ci gaba da rubutu, da kuma bincike mai zurfi a kan ilimin sarrafa tsirrai. Sai dai na yi miki alƙawarin zan rubuta labarinki da girmamawa, da alfaharin kasancewarki uwar gijiyata, na fito da kyawawan halaye da kuma ɗabi'unki ababen koyi. Tauhidinki, juriya da kuma gudun Duniya. Zan yi iya yi na na kare wannan rubutu tsawon ƙarnuka, domin ya zama misali mai kyau ga duk wanda zai karanta. Domin zan yi ƙoƙarin nesanta kaina da duk wani abu da zai sanya na shiga harkar bil'adama. A ƙarshe ina fatan ki sanar da mutanenku, darussan da ki ka koya, a tsawon zaman da muka yi, sannan ki fahimtar da su aikata ayyukan jahilici da duk wani abu da kauce hanya, saboda kana iya shukar da ba za ta fito ba wataƙila sai shekaru masu yawa a gaba, a sanya wanda ba su ji ba, ba su gani ba girbe abin da ba su shuka ba, kamar dai yadda ya faru da ke. A ƙarshe ina yi miki kyakykywan fatan alkhairi, da fatan Ubangiji Allah ya sanya jarrabwoyin da ki ka shiga, su zame miki silar shiga aljanna, Allah ya raya miki yaronki da abin da za ki haifa a gaba ya shirya miki su. Ya baki zaman lafiya da kwanciyar hankali na har abada. Ina kuma fatan halittun Allah su gane cewa, jinkirin amsa addu'arsu a gurin Allah, baya nufin Allah ba ya son su, kuma zafin ƙaddara da jarrabawa baya nufin Ubangiji yana ƙin ka, sai ka yi duba ga rayuwar annabawa da salihan bayi. A ƙarshe ina roƙon dan Allah ki yafe mini,  dan na san muddin ba ki yafe mini ba, sai Allah ya saka miki cutar da ke da na yi, ba tare da wata halattacciyar hujja a kan shari'a ba." Nana na kuka ta ce "Ƙaisar na yafe maka duniya da lahira Allah ya yafe mana gaba ɗaya, Ubangiji Allah ya albarkaci rayuwar ka ya sanya ka cikin salihan bayinsa. Ba zan taɓa mantawa da kai ba har abada" "Nima ba zan manta da ke ba Asma'u jikar Lanti. Ina fatan za ki yi ilimi mai zurfi ki karanci fannin ilimin magungunan musulunci da na gargajiya " Nana ta ce "Na yi maka alƙawarin haka. Amma daga nan ina zaka je?" "Can nesa da Duniyarki, zan nemi ilimi sosai " "Dan Allah ka tafi da Haula mana, tana matuƙar sonka da ƙaunar ka" Ya miƙe tsaye yana murmushi, ta ga ya zama wani irin dogo mara misali. Ta ja da baya tana kallonsa. Ta din ga jin muryarsa a sama ya ce "Yi haƙuri, kar na tsorata ki, duk suffar da ki ke ganinmu a cikinta da ni da Giyaz, ba suffofinmu ne na halitta ba, idan muka fito muku a siffofinmu na halitta zaku iya rasa rayukan ku, ko ku zauce. Mu kan suffantu da abubuwa ne da idanunku za su iya kalla. Na gode sosai da sosai uwar gijiyata ina yi miki fatan alkhairi." "Wayyo Allahana, shikenan ko ziyara ba zaka sake kawo mini ba. Tabbas a kan ka na yarda a sauran halittu akwai bayin Allah na ƙwarai, ba zan taɓa bari a raba ka da rayuwarka ba kai ma. Ina yi maka fatan alkhairi uban ɗakina, kuma ɗan uwana. Na san ba haka kurum Allah ya haɗa ni rayuwa da kai ba, duk da mu na da banbancin jinsi" Kuka take yi iya ƙarfinta, Hammad yana riƙe da ita gam a jikinsa, sai mimmiƙewa take yi tana ci gaba da kiran Ƙaisar. "Asmyna, ki yi haƙuri ki daina kukan nan haka" Ta buɗe idanunta a hankali ta kalli Sayyid, ta kalli dattijon malamin nan, ga su Sultan a gefe duk a cikin wani ɗaki. Ta fashe da kuka ta ce "Shi ma an kashe shi ko?" Ya girgiza mata kai ya ce "A'a yarjejeniya kawai aka yi da shi, ya ce kun riga kun gama magana ma, ya yi miki alƙawarin ya tafi ya rabu da ke har abada" "Shikenan ba zan sake ganin Ƙaisar ba? Ya cutar da ni, amma... Sai ta kasa magana ta ci gaba da kuka. "Na sani, na san komai Asmy ki yi haƙuri, mu na da banbancin da ba zai yiwu ki ci gaba da rayuwa da shi" Haka suka din ga rarrashin Nana. Shi kansa malamin ruƙiyyar cewa yayi bai taɓa samun case mai rikitarwa kamar na Nana ba, domin shi kansa Ƙaisar sai da ya yi kuka ba kaɗan ba, kafin ya ƙara tabattar wa malamin ruƙiyyar nan cewar ya bar ta har abada. Kwana biyu suka ƙara a Egypt, Nana sam ba ta walwala kamar wadda aka raba da mahaifinta, gaba ɗaya memories ɗin abubuwan da suka din ga faruwa a rayuwarta a tsakaninta da Ƙaisar suka din ga dawo mata. Tabbas za ta kasance cikin biladama masu ban mamaki da suka yi rayuwa mai kusancin gaske tsakaninsu da Aljanu. Sai da suka ƙara kwana biyun. Haka Hammad ya haƙura ya din ga rarrashinta, saboda yadda duk ta danu, domin yana iya tuna wasu abubuwan da suka din ga faruwa tsakaninsa da Ƙaisar saboda Nana. Suka koma ta Nigeria, har da Sultan da Matawalle, suka gaisa da iyayen Nana, tare da sake jaddada musu godiyarsu, bisa ga abin da Nana ta yi wa yaransu na kulawa, tare da yi musu bangajiya na zuwa biki da suka yi Agadez. Tun da suka koma Agadez, hasashen Hammad ya tabatta, domin kuwa laulayi ne sosai ya kada Nana. Babban abin da yake damun Hammad, bai wuce duk yadda ya so, ya haɗa kan Nana da Asal ba, Nana ta ƙi yarda ta ce masa komai zai yi Asal ta riga ta furta mata ba ta ƙaunarta, kuma duk mutumin da zai nuna baya ƙaunarka ba ta ga abin mu'amala da shi ba. Sai dai ya ci gaba da matsa mata har ya yi fushi. Ta ce "Sayyid, bari na yi maka gwari-gwari tabbas ina jin zafin ƙiyayyar da Asal ta nuna mini, amma muddin za mu din ga haɗuwa, ko ka ce sai mun haɗa kai, ba zata taɓa sakewa ba, zan zame mata takura kasancewar na san sirrinta, za ta din ga ganina da abin. Bana fatan zame wa kowa matsala a rayuwata, ba na fatan Asal ta rayu a takure saboda ni. Dan haka ka yi haƙuri ka ƙyale ni" Ya gaji ya gaya wa Sultan halin da yake ciki da Nana, ya ce duk ya kai masa su can gida. Tun da Asal ta ga Nana, hankalinta ya ƙara tashi, ganin Nana da juna biyu a lokacin ya ɗago sosai, ga kuma Muhsin da tana ganinsa a wallpaper Hammad. Nana ta ƙara cika ta yi kyau sosai da sosai. Sultan ya yi musu nasiha sosai da sosai, tare da roƙonsu a kan komai ya wuce, idan ba haka ba muddin suka tafi a haka, to irin jahilcin da ya din ga faruwa a baya, na faɗan 'ya'yan sarakuna a baya, to kuma zai iya faruwa naku gidan, dan haka ku yi haƙuri ku tura komai baya. Nana sai da ta ɗan sha jinin jikinta, ko a lokacin yanayin yadda ta ga Asal kamar gaba ɗaya a tsorace take, duk ta kame jikinta babu izzar nan da jin kai da take yi a baya. Suka yi masa godiya, Nana ta tabattar masa da in Allah ya yarda komai zai canza. Asal ta lura da yadda shi kansa Sultan ta Nana yake yi, yanzu baya nuna mata kulawar da yake ba ta a baya. Ta lura Hammad ne kawai ya yafe mata yake yin ta. Duk yadda ta so share Muhsin, son da take yi wa Hammad, da kamanin da suke yi da Muhsin ɗin, sai da ya sanya ta tsaya kula shi. Babu inda ya bar Hammad a kamanni. Nana ba ta fasa jin kewar Ƙaisar ba, ita kanta har ƙoƙarin faɗa take yi wa kanta, amma sabo turken wawa, babu yadda ta iya, idan abin ya ishe ta har kuka take yi. Jamila ta riƙe istigfari da addu'a, da magungunan da Nana ta bata, cikin ikon Allah ta din ga samun afuwa, a kan lamarin larura da take fama. Lamarin Suwaiba ne dai ba arziki. A hankali tana juya kuɗin da Nana ta bata, idan jarin ya karye ta kira Nana, ta ƙara bata wani, gefe Nana tana lallaɓa Baba har ya haƙura yake shiga sabgar Jamila. Gaddafi ma ya yi aure, ya sha tagomashi daga gurin Nana. Nana ba iya gidansu ba, hatta maƙwabtansu sai da suka shiga rigar arzikinta. Tana samun kuɗi sosai a Agadez, ga allowance ɗin ta na sarautarta, ga na kasamcewarta matar Sardaunan Agadez. Ga shi Hammad yana sakar mata kuɗi sosai da sosai. Ban da tarin kyaututtuka da take samu. Nana ta ƙyale Hammad yake zuwar wa da Asal Muhsin, sai dai ta tsananta addu'a. Su Tafawa suka zama ba su da wata power ko ƙarfin faɗa a ji, dan hatta dogarai da jami'an tsaron da suke tare da su, sai da aka janye musu, aka yanke albashin da masarauta take biyansu. Hakazalika duk wani kasuwanci da masarauta ke gudanarwa, ake samun riba da Nana da Muhsin a ciki. Watan Nana tara da sati biyu cif ta sake haihuwa namiji. Hammad kamar ya zuba ruwa a ƙasa ya sha, kasancewar kaf Agadez Nana ba ta da uwar da ta wuce Nene, ita ce tsaye a kanta a kan komai. Nana ta yi mamakin ganin Asal ta zo yi mata barka. Ahmad aka sanya wa jaririn, ake kiransa da Hamdan. Har da kyaututtuka Asal ta bayar a ba wa jaririn. Sosai take jin tausayin Asal, a zuwa ukun da ta yi ganin jaririn, duk lokacin da ta zo, daga gaisuwa babu abin da yake haɗa su da Nana, amma idan ta karɓi jaririn tana daɗewa sosai da sosai tana kallon yaron. Iya ƙoƙari Hammad yayi, a kan mantawa da duk wani abu da Asal ta aikata, amma bakin alƙalami ya riga ya bushe, lokuta da dama abubuwan da ta aikata masa su na dawowa zuciyarsa. Ita kanta a dole, take ƙoƙari take rintse idanunta ta kawar da kanta daga wasu abubuwan da yake aikatawa, Nana ke da miji Nana ne da 'ya'ya, kuma take da goyon bayan uban miji, da masaurauta ma baki ɗaya. Gimbiya Bilkisu ta din ga ziga ta, a kan lallai ta haƙura da auren nan, amma Asal ta ce ba za ta haƙura ba. Wataran Mahmoudu ya kawo musu ziyara, tare da matarsa, ana falo suna ta hira, yake bawa Mahmoudu labarin, darun da aka sha da Nana a kan raba ta da Ƙaisar. Mahmoudu ya hau dariya ya ce "Wasa-wasa fa, Gimbiya akwai daru, banda ita wa yake fatan tarayya da Aljani?" Hammad ya yi dariya ya ce "Mahmoudu sabo turken wawa, ita idan ka lura da ita ne, gaba ɗaya rayuwarta ba ta da damuwa, kuma tana da matsanancin tausayi amma Aljanin nan ya azabtar da ita, ni kuma ga mahaifinsa na gana mini azaba, wallahi yarinyar nan Allah ne yake kare ta, da wata ce tsaf zata haukace. Saboda azaba har a zahiri muke ganinsu, na zo da muka koma Buda hannuna na dama ya shanye, bakina ya koma gefe nikaɗai na san azabar da nake sha. Ga laulayi tana yi ga jinyata. Idan na fita daga hankalina na yi yinƙurin kashe ta, sai na dawo hayyacina sai na ga abin kamar a mafarki. Duk yadda zan kwatanta maka azabar da muka sha mutum sai dai ya ji kamar labari. Saboda jarabar Ƙaisar da babansa aka tashe mu daga wani gida da muka zauna aka ce mayya ce. Amma sau ɗaya Asmy ba ta taɓa nuna mini a fuskarta za ta rabu da ni ba, saboda ta yi imanin idan ta rabu da ni wa zai kula da ni. Amma yarinyar nan ina lallaɓata ina tuna mata abubuwan da Ƙaisar ya yi mata na cutarwa sai cewa ta yi ina ruwana, lokacin da na gudu na bar ta na san me ya yi mata? Kuma ai ta yafe masa tun da ya yi mata abin alkhairi. An sha daru kan su rabu. Tana nan tana gaya mini sai ta rubuta littafi guda, a kan Aljanu saboda Ƙaisar. Tun ina kishi da aljanin nan na haƙura da na gane dai duk abu ba jinsinmu ɗaya ba" Suka din ga dariya, Asal dai ta yi shiru, ita zancen ma tsoro ya hau bata. Fadila kuwa ta din ga yi masa tambayoyi, a kan yadda aka yi ya zamana Nana ɗauke da ɗa a jikinta shi kuma Uba. Babban abin da ya bata tsoro da mamaki, cewar da ya yi, har ciwon ɓarin jiki yayi, da irin wahalar jinya da Nana ta yi. Ya din ga misalta musu irin yadda yake ji, idan ciwon nan ya tayar masa yadda yake jin kamar ya kashe kansa saboda azaba. Asal duk sai ta tsargu, ta kalli fuskarsa ta ga hirarsa kawai yake yi, hankali kwance, ba domin da alamar wata manufa a fuskarsa ba. 10YRS LATER Muhsin na da shekaru goma sha huɗu a Duniya, Nana ta kammala karatunta, na ilimin magungunan addinin musulunci. Hammad ya taimaka mata, ta gina katafariyar cibiyar koyar da addinin musulunci, wata a Agadez wata a Nigeria. A lokacin Nana yaranta huɗu duk maza, tana sanye da glass a fuskarta tana rubuce-rubuce, Hammad ya kira ta ya ce mata Asal ce ta kira shi ba ta da lafiya, ko za ta tura mata ko Yarima ne, idan da wani magani da za a bata kuma a bata. Nana ta ce "Ahh me Yarima zai iya yi, bari na je da kaina". Ko da ta je gidan kuwa, tuni Muhsin yana can, Nana ta ce "Amma maimakon ku kira ni ku gaya mini, me Muhsin zai iya yi miki?" Asal dai ta yi shiru, Muhsin yana kusa da ita ya ce "Kawai zuwa na yi nima, na tarar da ita bata da lafiya" Nana ta ce "Ina ganin kawai mu tafi Asibiti" Nana ta taimaka mata ta canza kaya, suka tafi Asibiti. Likitoci suka ce tiyata za a yi mata a cire abin da yake cikinta. Nana ta kira Hammad ta ce masa lallai ya dawo, tiyata za a yi wa Asal ana buƙatar a saka hannu. Ya ce "Ki saka, ba zan iya dawowa a yau ba, sai zuwa gobe in Allah ya kaimu" Nana ta ce "To ai ba zai yiwu ni na saka ba, ko a kira mahaifinta a waya?" Da sauri ya ce "A'a bari na kira Sultan, kuma ki tsaya ki bayar da order, kar wani ya zo a ba shi ɗana, idan ba ke ko Sultan ba, babu yadda zan yi na dawo ne" Haka aka yi, Sultan ya je Asibiti da kansa ba wakilici ba, ya sanya hannu aka ciro wa Asal jaririyarta. Nana aka fara ba wa yarinyar, ta yi wata irin ajiyar zuciya tare da gode wa Allah, sannan ta kai wa Sultan ita. Ya rungume yarinyar yana kallonta cike da ƙauna, ya ce "Kin ga ikon Allah, bayan shekaru kusan ashirin da aure, sai yanzu Allah ya yi ikonsa" Nana ta ce "Tabbas Allah abin godiya, Abin da na yi ta gaya wa Sayyid kenan, ba a cire rai da rahamar Allah. Asal na kwance a post up room, ta buɗe idanunta a hankali, ta kalli Nana da take ta shafa kan jaririyar. Tsawon wannan shekarun, babu wata jituwar arziki a tsakaninsu, sai dai tun kiran da Sultan ya yi musu, ya yi musu nasiha Nana ta daina hana yaranta zuwa inda Asal take. Aka sanar da haihuwar Asal, amma aka hana kowa zuwa Asibitin da take. 'ya'yan Nana haka suka kewaye Asal da jaririyar nan, wannan ya ɗauka wannan ya ɗauka. Da kyar suka tafi gida, saboda makaranta. Ƙarfe sha biyu da rabi Hammad ya iso Asibitin. Ya tarar da Nana tana shirya jaririyar a cikin kaya. Bakinsa ya kasa rufuwa, ya miƙa mata hannu ta bashi, Nana ta ce "Ba tukuici babu komai" "Zan baki idan muka haɗu" Tana murmushi ta miƙa masa jaririyar, ta tashi ta basu guri. Ya ƙarasa kusa da Asal yana murmushi ys rungumota ya sumbaci goshinta. Ya ce "Kin ga ikon Allah ko Cherié?" Ta yi murmushi ta ce "Na gani, kalli kamar ta ɗaya da Yarima, duk kamar ka suke yi" Ya yi dariya ya ce "Ba dole su yi kama da ni ba, ni ɗin na wasa ne. Alhamdillah bayan samari da Allah ya bamu ga 'yar budurwa." Asal ta ce "A saka mata Asma'u" da sauri ya waiwayo ya kalle ta, ya ce "Ba na son wasa" "Da gaske nake, na ga kana sonta da yawa, ko ita ma za ta ci albarkacin son da ka ke yi wa rayuwarta, ka so ta sosai" Hammad ya ce "Kin ga ni ba na son rigima daga haihuwar ki, ke cewa na yi ba na sonki ne?" Ta girgiza kai ta ce "Ai ba ƙarya na yi ba, da na ce ka na sonta sosai, kuma ta cancanci ka so ta, na gane hakan bayan da na saurari yadda aka yi ka aure ta, da irin rayuwar da ku ka yi da kunnen basira. Duk a ajiye wannan a gefe, tsawon wannan lokacin na rayu da ci gaba da sanya ran samun haihuwa da kalamanta da suka bani ƙwarin gwiwa. Lokacin da na dawo gidanka, babu daɗewa, cikin dare na tashi fitsari saƙo ya shigo wayarka ƙarfe uku na dare. Na ɗau wayar na duba sai na ga saƙonta ne, ta ce ; Albishirinka yanzu na tashi daga barci, na yi mafarkin Asal ta haihu, ana ta shagali har na tashi ina jin abin a jikina da zuciyata, ko a kusa ko a nesa mafarkin nan zai zama gaske in sha Allah, ka samu maƙubaci ka bayar da nannauyar sadaka, Allah ya tabattar mana. Kuma idan mace ce sunana za ka saka" Duk da a lokacin da naga saƙon nan, na cire rai da samun haihuwa, amma a duk lokacin da na tuna saƙon nan, sai na ji ina ƙara sanya rai. Tsawon shekara goman nan, wannan saƙon nata yana cikin kaina, ina jin sa ina fatan Allah ya tabattar da shi. Babu wanda na taɓa gayawa sai yanzu da nake gaya maka. Bayan haka sanin sirrina, da abubuwan da na aikata bai taɓa sanyawa ko sau ɗaya ta kalle ni ta yi mini gori, da abubuwan da na aikata ba, banda barazanar da ta yi mini, lokacin da na gano matarka ce ita. Kuma bata taɓa yi mini wani abu, na gadara ko makamancin haka ba, saboda ta haihu da kai ni ban haihu ba. Ko na yi yunkurin sanya wa zuciyata irin wannan tunanin Hasna da Fadila su na ankarar da ni, mussaman da Fadila ta gaya mini Nana tana addu'ar ka da Allah ya sanya mata jin wani abu a ranta, dan ta haihu ni ban haihu ba, balle ta yi wani abu da zai sosa mini rai. A ƙarshe, na san maganin da ka kawo mini, ita ta sarrafa shi a kaina ta yi gwajin maganin haihuwa, kuma Allah ya amsa. Babu riba yin adawa da mutane irinta, rayuwarta take yi kai tsaye, ba tare da ƙyashi ko baƙin ciki ba. Kuma kasancewata tare da su Hasna, suna ƙara saita ni, saɓanin da da nake tare da miyagun ƙawaye. Na san ba zan taɓa kai wa ko rabinta a zuciyarka ba, kuma ba zan yi maka dole ba, iya wannan jihadin na zama da ni ka yi, ya isa a kira ka gwarzo, kuma hakan ne hukuncin da ya dace da ni, kana iya ƙoƙarinka a kaina, amma ni dai ka saka mini sunanta, ba kuma na yi hakan dan na burge ku ba ne, ko a ce tsirfa ba ce, a'a na yi hakan ne saboda jin wani sashin na damuwata da ta yi kamar tata." Gaba ɗaya jikin Hammad ya yi sanyi sosai da sosai. Ya rungumo Asal a jiknsa, yana sumbatar goshinta ya ce "Abubuwan da suka faru sun riga sun wuce, ki daina dawo da su. Kuma tun farko abubuwan ku ne na kishi da yake damunku, amma tabbas Nana tana da halaye da ɗabi'u na kirki, ina fatan Ubangiji Allah ya haɗa mini kanku gaba ɗaya ya shirya mini yarana". Nana ta ƙwanƙwasa ƙofar ta yi sallama, suka amsa, ta shigo da kwanukan Abinci. Hammad ya ce "Wai gida ki ka je?" "Eh na je na ɗaukko Abinci ne, mutane na ta son su zo su ga jaririya fa." "Ki ƙyale su, idan sun koma gida a ganta" Har ranar suna Nana ba ta san sunanta za a saka wa jaririyar ba, aka shirya gagarumin suna a Agadez. Nana ta yi wa jaririyar nan kaya na alfarma. Kawai ta ji Hammad yana gaya wa Zahradeen wai sunan jaririya Asma'u. Nana ta yi turus ta ce "Sayyid, amma da wasa ka ke yi ko?" "Kamar yaya wasa? Da gaske nake" Cikin damuwa ta ce "Dan zatin Allah ka yi haƙuri, wannan ai rigima ce, kawai salon ka ja mini magana a garin nan, shekara da shekaru tana neman abu, ta sha wahala ta haihu kuma a saka sunana?" "To ai ita ta nemi hakan ba ni ba" Nana ta girgiza kai ta ce "A'a ka yi mata fin ƙarfi dai, Asal ba za ta yarda a saka wa yarinyarta sunana ba. Ni dai dan Allah ka canza" Kawai ya hau dariya, ya ce "To ni yaya zan yi muku? Idan kin je gurin sunan, ki tambaye ta" Nana ta ce "A'a ni dai na yafe, dan Allah ka canza mata suna, ya za a yi ka yi mata haka, salon kawai ka saka a ƙara tsana ta" "To ai ni ina sonki dan a tsane ki ba komai tun da ina sonki" Da gaske Nana ta fututtuke ta ce bata yarda ba, sai da ya ɗauke ta suka je gidan. Asal ta ce "Dan na ce a saka wa jaririyar ki sunanki shi ne za ki ce ba kya so? Kina jin haushina kenan tun abubuwan da suka faru tsawon shekaru goma" Nana ta ce "Wallahi ba haka ba ne ba, ba na son a yi miki fin ƙarfi ne, a takura miki abin da ba kya so" Asal ta ce "A'a ni na ce a saka mata, babu wanda ya takura mini" Nana ta yi wa Nana bayani kamar yadda ta yi wa Hammad, sannan ta ɗora da cewa "Nana ni da ke mu na da tabon juna, da ba zai taɓa yiwuwa na ce sai mun yi nu'amala da juna ba. Amma ina son yaranmu su tashi da haɗin kai, kamar yadda ki ka kawar da kai ki ka nuna mini yaranki nawa ne. Ba na fatan a sake samun matsala na rabuwar kawuna saboda mulki ko abin Duniya a tsakanin yaranmu. Ina fatan za ki saka mini takwarar ki a cikin su Yarima, ta samu kyakykywar kulawa. Kuma ina godiya da dukkanin wasu abubuwa na alkhairi da ki ka yi mini, da ɗaukar damuwa ta taki, duk da ba jituwa muke yi ba" Wani irin farinciki ya mamaye ta, ta ce "Tabbas takwarata kin haife ta ne, amma ni ki ka haifawa. Kuma na yi wannan alƙawarin na sanya ta cikin jerin 'ya'yana. Ya hayyu ya ƙayyum Ubangiji Allah ya kawo biyar a bayan ta" Asal ta ce "Biyar sun yi yawa ai, yadda shekaruna su ka ja ɗin nan? Ita ɗin ma na gode Allah" Nana ta ce "Taskar Allah babu abin da babu, ko ba biyar ba Allah ya ƙaro mana wasu, shekara iyanzu a ce an kusa haifo mana wasu. Na gode sosai da sosai da karamcin nan da ki ka yi mini" Jin sunan da aka saka wa jaririya, ya janyo cecekuce sosai da sosai a garin. Da ganin kamar ba a yi wa Asal adalci. Kwanan Husna arba'in, Nana ta buɗe cibiyar magungunan musulunci. Manyan mutane duk sun halarta, har da 'yan uwan Nana na Nigeria. A daidai lokacin ta kammala rubutun littafinta, da ta yi bincike tsawon shekaru, a kan aljanu, da ilimin ruƙiyya da ladduban yin ta. A cikin sunayen mutane masu muhimmanci da ta lissafo a cikin littafin, sai da ta sanya sunan Ƙaisar Giyaz. Ko da aka nemi Asal ta tofa wani abu a gurin taron, Nana ba ta zaci za ta yi magana ba, amma ta karɓa ta taya ta murna, tare da shaidawa duniya, a kanta Nana ta fara gwajin maganin haihuwa kuma Allah ya amsa. Nene ta taimakawa Nana sosai a ɓangaren magungunan, haka Sarkin baka ya halarci taron, Hammad ne da kansa ya gayyace shi. Ya din ga yi wa Nana dariyar ba a guje wa ƙaddara. Nana ta yi murmushi ta ce "Na karɓe ta ta hanyar da ta dace ne" Nana ta yi shiru tana kallon gurin nata. A hankali ta furta "Na cika maka alƙawarinka uban ɗakina" "Nima na cika wanda na yi miki uwar gijiyata, na rubuta tarihinki da alƙalamin zinare a cikin kundi na mussaman da ba zai ɓace ba" Ta ji tamkar muryar Ƙaisar a gurin. Idonta ya sauka a kan award da ta yi da sunansa ta ajiye a gefe guda. Shukura wannan rashin lafiya da ta yi ta fama, da damuwar da take ciki ne yayi ajalinta, Yusra ta shiga damuwa da tashin hankali sosai, sai dai ta rungumi yaran Shukura da waɗanda ta haifa. Jamila ta samu wani jami'in ɗan sanda mai mata biyu ta aura, Allah ya taimake ta, ya ware mata gidanta sai dai tana shan azabar kishiyoyin duk da haka. Ta rungumi sana'arta sosai da sosai. Suwaiba kam ƙwaƙwalwa ta riga ta taɓu haka Mama ta ci gaba da wahala da ita. Allah Al-musawwiru, shekarar Husna ɗaya a duniya, ta sake samun juna biyu, a dole Nana ta ɗauke ta, ta yaye ta. Ta haifi yara biyu mace da namiji. Nana kuma sai a haihuwa ta ƙarshe, ta haifi 'ya mace, duk da ba wani shiri suke yi ba, amma kan yaransu a haɗe yake sosai da sosai. Nana tsaye take a kan tarbiyya da kuma ilimin yaran mussaman na addini. Hatta garin Buda sai da suka amfana da Nana, dan ta sai filin da kukar Lanti take, filin da kukar da aka yi wa Lanti girka, aka buɗe islamiyya. Sannan duk shekara suna samun abin alkhairi na kayan masarufi mussaman da azumi. Ummanta duk ta aurar da ƙannenta mata, Imrana bayan ya kammala karatunsa, ya yi zamansa a faransa, sai da Nana ta matsa masa da batun aure, sannan ya ce ta samo masa duk wadda ta yi mata zai aura. Suka rayu cikin kwanciyar hankali, da son juna. Ta samu kulawa da tsantsar soyayya daga miji, yaransu gaba ɗaya suna matuƙar sonta da ƙaunarta. Husna kuwa tamkar babbar 'yar Nana. Yayin da Yarima yake ɗan gurin Asal. Ta shiga cikin mata da aka sanya sunansu a kundin tarihin Agadez. Ta rayu cikin aminci da nutsuwa, a rayuwar da sai ta so ta yanke tsammani saboda gwagwarmaya. Sai ɗan sauran ƙalubale da faɗi tashin rayuwa da ba a rasa bawa da shi. A hankali ya yi ajiyar zuciya, ya kalli matashin da yake zaune yana saurarensa, ya ce "Ka ji labarin Gimbiya Asma'u, to kai ma shigen abin da ya faru da su ne yake shirin faruwa da kai" Ɗaya matashin ya ce "Allah ya yi mini tsari, idan kuma ni ban taki irin wannan sa'ar da Nana ta taka ba fa? Lallaɓawa zan yi na bi dare na gudu na bar garin nan, sai ta koma bin wani. Haka kurum mahaukaciya ta liƙe mini ta din ga bi na" Ɗayan ya kwashe da dariya, ya ce "Dan Allah kar ka yi haka. Yau wuni ta yi a ƙofar gidan ku, an bata abinci ta ƙi ci, Yaya kawai take faɗa, dan Allah ka je ka bata Abinci kamar ma ba ta da lafiya" "Kai wallahi ba zan koma ba hauka ake yi, idan ta gaji ta ƙara gaba ta nemi wands za ta bi" *Tofa, ko su kuma wannan matasan suwaye? Waye wannan aka ba wa labarin BUZU da Nana, shi kuma wace mahaukaciyar ce take bin sa. Sai mu tara a gaba a cikin jerin littattafan da za su zo muku daga alƙalamina nan kusa ko a gaba* (Waɗanda suka gaza juriya, a farkon littafin da ganin na matsa rayuwar Nana a farko, ina fatan a ƙarshe kun fahimci abin da nake son ku fahimta. Ba kowace Addu'a Allah yake karɓa a take ba, ya kan jinkirtawa bawa, ya amsa masa lokacin da ya fi dacewa. Annabawan Allah misali ne a kanmu. Har kullum ina fatan zamu din ga kamanta wasu darussan da muke karantawa a littafi, da rayuwarmu ta zahiri, hakan ne zai sanya a ɗauki gyararrakin da yakamata.) TAMMAT BI HAMDILLAH. KOMAI NISAN DARE GARI ZAI WAYE. ALLAH YA KAWO MU ƘARSHEN WANNAN LITTAFIN LAFIYA. DUKKAN YABO DA GODIYA DA JINJINA DA KIRARI SU TABATTA GA BUWAYIN SARKI GAGARA MISALI DA YA BANI ARON RAI DA LAFIYA, NA KAWO WANNAN LITTAFIN BAYAN SHAFE TSAWON SHEKARU BIYU INA BINCIKE A KANSA. INA ROƘON ALLAH ABIN DA NA YI NA KUSKURE YA YAFE MINI. GODIYA TA MUSAMMAN GA TEAM ƊIN BRIGHT PENS Aisha Adam Ayshercool Zainab shehu kumurya Na'ima Suleiman Nazeefa sabo Nashe. Ƙungiyar YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION YOTA. Godiya ta mussaman taki kekaɗai Amanar Cool Sai kuma gaisuwa ta mussaman da godiya, bisa taimakawa bincikena da ku ka yi. Maryam Muhammad Mum amnash Dr. Salihu Nura Adam (Salihan nur) Fatima A abdou Nijar Da ma kafatanin marubuta baki ɗaya. Hakazalika ina godiya, ga masu gyara, sharhi da shawara Ubangiji Allah ya saka muku da alkhairi ya fi ni yabawa. Na gode sosai da sosai, da jimirin bibiyata, ina roƙon Allah duk wanda ya karanta littafin nan, ko ya ƙaru da wani abu, ko bai ƙaru ba Ubangiji Allah ya tabattar da zukatanmu ni da ku a kan Imani. Ina miƙa godiya sosai da sosai, ga waɗanda suka kasance tare da ni a tafiyar nan, tun daga telegram har AREWABOOKS. Waɗanda na yi wa kuskure, ina mai baku haƙuri, saboda ɗan Adam ce ni, mai ajizanci. Wanda ku ka sarrafa mini littafi, ta wasu hanyoyi ba da izinina ba, ba a yafiya ranar lahira. Wanda kuka karanta mini baku saya ba, ga account number na zan saka, ku bani hakkin wahalata na wata shida, akasin haka ina muku tuni da duk mai son ci gaba a nasa neman, baya yi wa wani mugunta. Kuma hakkin wani komai ƙanƙantarsa na iya kawo maka naƙasu a naka neman. A saka mini hakkina dan Allah, ko na bar mutum da Ubangijin Musa da Harun, ubangina ubangijinku. 0069685771 Aisha Adam stanbic bank. Sai mun haɗu a littafi na gaba, idan Allah ya bamu aron rai da lafiya. 08081012143 💃💃💃💃