*JADEEDAH* (It's a story of two love birds who are so different from each other ) STORY & WRITTEN BY : (*Cwt~Sumiey*) Marubuciyar littafin MENE NE ABIN YI ? KARAGAR MULKI And now.....*JADEEDAH* https://chat.whatsapp.com/CWkZfMqvD4H0mtd7WW6Xbz https://whatsapp.com/channel/0029VapqU8C002T5Bz8RSQ0a Yabo da Godiya ga Alla Alhamdulillah! Ina miƙa godiya ga Allah (SWT) da Ya bani damar rubuta littafin Jadeeda. Ina roƙonsa da saƙo da ke cikin littafin ya isa inda ake buƙata, ya taɓa zukata, ya zama darasi da amfanin rayuwa. Allah Ka saka da alkhairi. Amin. Sai jinjina ga Yah Abba (Abba Writer),Yah Aliyu (Al'uskun waƙa), Sadeeq Rufa'i(Abu Julaibeeb),Safiyya Muktar Garba da kuma Members na YOTA musamman Excos ɗin su, Allah yai riƙo da hannayensu ya ɗauka su,ya basu nasara a duk cikin abinda suka sa a gaba,ba zan manta da irin gudunmawar da su ke bani ba akan duk abinda na zo masu da shi, Allah ya biya ku da mafificin Alkairi Wannan labarin k`irk`irarren labari ne duk abinda ki ka gani a cikin sa wanda yai dai-dai ko kamanceceniya da wani abu to bisa arashi ne,ban gina wata kalma wadda ta shafi duka `bangarori biyu da zan yi magana akan su ba batare da hujjoji akan haka ba. Wannan page naku ne massoya na Allah ya bar mu tare forever and ever BOOK 1 ♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡ [01/07/2025] PAGE 1 ❤ FREE PAGE Bismillahi Rahamanir Rahim "Ummie Maryama dan Allah kiyi haƙuri ki bar ni in yi zamana anan wallahi tsoro na ke ji ,ji na ke kamar da zaran na fita zan ci karo da Baba Ƙarami na tsaye ya na jiran na fito ya hukunta ni",ta ƙare zance ta na mai share hawayen da su ke ta faman kwaranya a kyakyawar fuskarta. " Haba Hibbah ki kwantar da hankalin ki mana,domin tuni Baba Ƙarami ya tafi Masallaci don gabatar da Sallahr Azuhur kuma kin dan ba zai dawo dan yanzu ba,ke kuma kin ga tun safe ki ke a cikin ɗakinnan ko kayan barci fa ba ki samu kin sauya ba". "Ni dai ki bar ni a haka ban ƙi ba ma in kai tsawon sati a cikin wannan Bedroom ɗin ba muddin hakan zai sa in tsira daga faɗa ko hukuncin Baba Ƙarami ,sosai na ke jin tsoran haɗuwata da shi,ban san me zai faru ba in hakan ta kasance". "Ba wai zan faɗar ma ki da gaba ba ne ko in sagar ma ki da gwuiwa ba ne ba, A'a amma kin sa ni kuma ni ma na sa ni ,dole ce haɗuwar ki da Baba Ƙarami ke ba ma sh ƙadaii ba har da Baba Malam ,da sauran Yayyen ki sai sun neme ki duk iya zille-zillen da za ki yi ma hakan". " Innalillahi wa'ina ilaihirraju'una Ummie Maryama na shiga uku ,Ni yanzu ina zan sa kaina da rayuwata ,ko ɗaya ba na son haka ta kasance domin ban san me zan fuskanta ba a haɗuwata da su". "ki yi haƙuri amma duk tsoranki da hakan sai ta faru domin ta hakan ne kawai za a iya samo hanyar da za a warware wannan rikitaccen al'amari da ya shigo cikin Gidannan ". " Ummie Maryama ba zan iya ba Zuciyata ba zata iya ɗaukar hakan ba ,a yanzu ma haka ji na ke kamar zata tsaga ƙirjina ta fito waje ta tarwatse,saboda tsoro da fargaba". Sai da Ummie Maryama ta sa ki wata gajeriyar dariya kana ta ɗora da cewa,"Kin ga har kin ba ni dariya sai ka ce ba Hibbah da na sani ba duk ina dakakkiyar zuciyar da jarumtar da na san ki da ita ?".duk ta ana yin haka ne don ta ɗan kwantar mata da hankali. Ka sa cewa da ita komi ta yi sai Ummie Maryama ɗin ce ta ɗora da cewa ,"Komi yai farko zai ƙarshe ,yanzu haka wani al'amarin ne babba ya ke tunkaro ki shiyasa Allah ya jarabce ki da wannan ƙaddarar don haka ki daure kuma ki jajurce har zuwa sanda za ki cinye wannan jarabawar kin ji Hibba". " Ta ya ki ke ganin haka za ta kasance tun a yanzu na sare zuciyata ta karye ba na tunanin zan iya cin nasara a cikin wannan lamarin mai cike da rikici,Sarƙaƙiya tare da ruɗarwa ba". "Ban san ki da irin wannan halin ba,duk da nasan cewa kin sa ni cewa saurin sarewa ko miƙa wuya ga lamarin da ba kasan me Gobe zata haifar ba,babban kuskure ne,dan haka ki kwantar da hankalin ki zo mu je yanzu ki yi wanka daganan ki ci abinci". " Ni ba na jin yunwa ko kaɗan, sunan abinci ma ba na son inji an ambata". "Hakanan za ki daure ki ci ko da one cup na tea ne"," Ni dai a'a Ummie Maryama,ba zan iya cin komi ba a halin da na ke a ciki yanzu". "Oh ba ki so wannan lamarin ya zo ƙarshe ba kenan ba,domin ba shakka na san wata cutar ce za ta kama ki kin ga anyi ba ai ba kenan ko,gara ma ki haƙurƙuntar da kan ki da zuciyar ki ki samu ki ci wani abun", da haka dai Ummie Maryama ta samu ta shawo kanta har ta amince su ka fito tare da nufin ta je tai wanka ta ci abinci. Suna isowa Parlour su ka iske Mama Hadiza,Umma Maimuna,Umma jamila,Umma Hafsat da kuma Baba Asabe zazzaune da dukkanin alamu suna tattaunawa akan abinda ya faru ne. Zaraf Umma Maimuna ta miƙe ta nufe su tana mai cewa,Yauwa Ummien Jaheed,sannu da ƙoƙari kin samu kin shawo kanta ta fito kenan ?". Cikin girmamawa ta ta bata amsa da cewa," Eh na samu ta fito wai ko ta samu ta ci wani abun ko ya ya yake,tunda ba yanda za ayi mutum ya zauna da yunwa,daga nan sai ta samu ta yi wanka". "Ai kamata yai ta fara cin abinci in yaso sai tai wankan daga baya kamar zai fi", Cewar Umma Jamila. Hannun Hibba Ummie Maryam ta ja ta nufi Dining area ɗin da ita ta na mai cewa,"To bari ta fara cin abincin sai tai wankan daga baya". Wermars ɗin da ke jere akan dinning ɗin ta fara buɗe mata tare da tambayarta me za ta zuba ma ta. Cikin muryarta wacce ta ke fayyace halin da ta ke a ciki ta bata amsa da cewa," Ki ba ni ruwan Lipton kawai ma ya isa". Sake baki Ummie Maryam tai ta na kallon ta kafin ta ce da ita,"A'a ba za ki sha ruwan Lipton tsuran shi ba,ina laifin ki in baki Tea ko in haɗa maki Black bhazar Coffee ne,Wanda zai ɗan riƙe mi ki ciki",ta kai ƙarshe zancen ta na mai haɗa mata kakkauran Black bhazar Coffeen ta haɗa mata harda Madara ta miƙa mata ba dan Hibba ta so ba ta amsa ta fara kai shi bakinta tamkar ta na shan magani,nan da nan zufa ta fara tsatstsafo mata ,idanuwanta sun yi ja tamkar hawaye za su zubo daga cikin su. "Amma Mama Part ɗin Baba Asabe zata koma da zama ko,kafin wannan lamarin ya ɗan yi sauƙi ko ?",Ummie Maryam ta tambaya. Kasa cewa komi Mama Hadiza tai,sai ma miƙewa da tai ta bar parlour ta nufi hanyar Part ɗin ta ba tare da tace komi ba. Hakan ya sa jikin su Umma Hafsat yai sanyi,sai Umma Maimuna ce ta fara katse shirin da cewa," Kema ai kin san ba zata furta kalma ko guda ɗaya akan wannan zancen ba,sai dai mu zauna mu yanke abinda ya kamata akan hakan". Kwalkwal idanun Hibba su kai nan da nan hawaye su ka fara rige-rigen sauka akan fuskarta,da sauri ta kai hannunta saman fuskarta ta na mai share hawayen sakamakon jin hayaniyar shigowar JAHEED yaro ɗan kimani shekara takwas,turus ya ja ya tsaya a tsakiyar Parlour ya na mai rarraba idanunsa akan mutanen da ke cikin falon Cikin muryar yarinta ya fuskanci Ummie Maryam da tarin tambayoyin da suke a zuciyar shi da kuma ƴar ƙaramar kwakwalwarsa,"Ummie me ya samu Momynah na ga idanunta da hawaye,waye ya bige ta, ko kum ba ta da lafiya ne,ko dai Baba Asabe ce tai ma ta faɗa?".Wacce shigowar Baba Asabe cikin parlour kenan "Kai wannan Yaro dama haka ka ke ban sa ni ba,to ta Allah ba ta ka ba,ahir ɗin ka ka kiyaye ni,ta ya zaka kwaso wannan gingimemen sharrin na ka ka ɗora shi a kaina,ban ji ba ban gani ba,to ni Allah na tuba meye nawa a cikin wannan lamarin ai sai dai gani ko hange daga ne sa". Ko ta kan Baba Asabe bai sa ke bi ba,ya nufi inda Hibba ta ke ya fara share ma ta hawayen da su ke zubo ma ta tare da cewa," Momynah me ya same ki ki faɗa min inji,nima ina jin kamar in yi kuka hawaye sai ƙoƙarin zubo min su ke sakamakon ganin kina kuka,hankalina duk ya tashi ?", Sai da Hibba ta haɗiye sabon kukan da ya taho ma ta kafin ta ce da shi,"My son ba abinda ya same ni,ba ni da lafiya,idona ke ciwo shiyasa ka ga hawaye na zuba daga cikin". Sake baki da idanu yai yana kallon idanunna ta da ta ce suna ciwo har ya,na kai hannunsa ya na ɗan taɓa su a hankali tare da cewa,"To ai Momynah ban ga ciwon ba ko dai wayo ki ke son yi min ?". Buɗe baki tai da niyar ba shi amsa ta kasa sakamakon tsananin firgitar da tai na ganin shigowar wanda ta ke jin tsoro ba ta tsaya ba har sai da ta kai ƙarshen jikin bangon Parlourn ta makure ta na mai jiran tsanmanin abinda zai faru. Baba ƙarami ne ya shigo,bin ta da Ido kawai ya ke,Zuciyarsa cunkushe da tarin bak`in cikin abun kunyar da ta ke k`ok`arin janyo mu su kai tsaye fuskarta shi ke bayyanar da halin da ya ke a ciki,daga ƙarshe kauda kan shi yai akan ta alamun kamar bai son ya cigabada da kallon ta ya ce da ita,"Ki zo babban Parlour Baba Malam na jiran ki,in kin so za ki iya sake tserewa a karo na biyu".yana kaiwa nan ya bar cikin parlourn. Hannu bibbiyu Hibba ta ɗora a saman kata tare da fara sakati da sallallami gami da cewa,"Na shiga ukuna yanzu ya zan yi ina zan sa kai na ",duk ta rud`e sai faman tsalle-tsalle ta ke,ta rasa wani abu guda ɗaya mai muhimmanci da ya kamata ta aikata. Umma Hafsat ce ta riketa gam gami ɗan ɗaga sautin muryarta ta ce da ita,Ke ki natsu mana,wannan ruɗun da tashin hankalin da ki ke ba zai haifar ma ki da ɗa mai Ido ba,gara ki natsu ki tsaya ki fuskanci abinda ke gaban ki,tun da can ba ki san da zuwan wannan ranar ba sai yau ,sai yanzu za ki zo ki tashi hankalinmu ki tashi hankalin ki akan me?". Baba Asabe ce ta anshe zance da cewa," Yauwa ƴar gari kuma ƴar albarka faɗa mata gaskiya man wata ƙila ta manta ita ce sila kuma ummul'aba'isin faruwar duk abinda ya ke faruwa a cikin Gidannan a yanzu".... "Haba Baba Asabe bai kamata ku rinƙa faɗar irin wannan kalmomin a irin wannan lokacin ba,ba ku ga halin da ta ke a ciki ba ne ba?". " Ke ar ja can ba ni wuri,yo Allah na tuba da ke da ita ai duk kanwar ja ce,kwaryar sama ce ke bugun ta ƙasa,ina zargin ma kina da sa hannun cikin faruwar wannan lamarin ".... Umma Jamila ce ta saurin dakatar da batun da cewa," Haba Baba Asabe wannan abinda ki ke bai kamata ba, ku bar mu mu ji da abinda ya ke damun ma na,sai ku tsuro da wani sabon rikicin da zai sa ke dagula ma na lissafi ". Hankakin Hibba ba ƙaramin ƙololuwar tashi ya sa ke yi ba,yau gidan su ne a ke wannan hayaniyar,Wanda a tarihin ba ta taɓa jin labari ko ganin iri hakan ta faru ba,duk da kasancewar Gidan na su babban Gida ne,ko Mahaifinta Baba Malam matan shi huɗu da yara Aishirin da biyar,ba ta taɓa ganin hakan ta faru ba sai yau kuma wai akanta. Muryar Mahaifiyarta Mama Hadiza ta ji ta na mai bata umarnin akan ta wuce ta je ta amsa kiran da ake ma ta tun kafin ta iskota nan inda ta ke, ranta ya sake ɓaci. Jikinta ba kwari ,Zuciyarsa sai faman tsananta bugu ta ke ta nufin hanyar Babban Parlourn ,ji tai daga baya an riƙe ƙafafunta,a sanyaye ta waigo domin son ganin waye ya riƙe ta. Jaheed ne fuskarta shi da hawaye shaɓe-shaɓe ya ce da ita," Momynah zan bi ki,ki tafi da ni,ina so in ba Abbahna haƙuri kar ya yi maki faɗa ko ya bige ki,in ya so ni yai min faɗa,tunda na ga alamun kamar duk sun daina son ki". Sai da ta share wayen saman fuskarta kafin ta ba shi amsa da cewa"Kar ka damu Yarona ba abinda Abbanka zai yi min yanzun nan zan dawo"... Cikin yarinta ya fara tsalle ya na direwa tare da cewa shi bai yarda ba sai ya bita,duk irin lallashin da za tai mai ta yi ma shi amma yaƙi amincewa daga ƙarshe sai Ummie Maryam ce ta zo ta ja shi su ka bar wurin ba don ya so ba,ita kuma ta nufi Parlourn wanda ta na shiga ta ji ƙirjin ta yai wani irin matsanacin bugawa ta sake shiga cikin mafi tsananin ruɗuu da tashin hankalin...... *JADEEDAH* (It's a story of two love birds who are so different from each other ) STORY & WRITTEN BY : (*Cwt~Sumiey*) Marubuciyar littafin MENE NE ABIN YI ? KARAGAR MULKI And now.....*JADEEDAH* https://chat.whatsapp.com/CWkZfMqvD4H0mtd7WW6Xbz https://whatsapp.com/channel/0029VapqU8C002T5Bz8RSQ0a ♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡ PAGE 2 ❤ FREE PAGE Gabad`aya ta diriri ce,ta kasa gaba ta kasa baya, tunaninta ya tsaya cak ta rasa mene ne abinda ya kamata ta yi shin ta shiga cikin parlourn ko ta juya baya ne. Alaranma Sama'ila wanda ya kasance shi ne babban d`a a cikin Gidan ya kira sunanta tare da cewa,"Shigo mana Hibba,me ki ke jin tsoro har haka ko ba ki gane mu bane ba ,duk `yan'uwanki ne a ciki fa ?". A diririce gami da tsanantar rawa da jikinta ke yi, ta shiga cikin parlourn ta samu wuri can nesa da su ta zauna. "Kin ga ki kwantar da hankalin ki ba abinda zai faru da ke, Baba Malam zai shigo ya na waje tare da bak`i ne", Yah Mustapha ya sanar da ita duk dan hankalin ta ya kwanta ta sa ki jikinta. Ɗan muskutawa tai alamun ta gyara zaman takurewar da tai kana ta d`an d`ago da kanta ta na mai saukar da idanunta kan zaratan manyan Yayyen na ta,su wajen sha biyu,Wanda wa su daga cikin su fuskokin su a d`aure su ke,kai tsaye hakan ya sake ta da mata hankali gami da ruguza d`an sauran k`arfin halin da ta ke da shi. Baba K`arami ne ya fara yin magana cikin fushi,Wanda hatta da sautin lafuzan da ke fita daga bakinsa sun bayyanar da hakan," Kin bani mamaki Hibba banyi zato ko tsanmanin haka daga gare ki ba,ban san me ya rud`e ki, ke k`ok`arin lalata gami da tarwatsa asalin wannan Gidan namu ba,shin ko dai Soyayyar da mu ka nuna mi ki,gami da fifita ki cikin sauran `yan'uwanki Mata ce ta rud`ar da ke har ki ka fara k`ok`orin jefa rayuwar ki cikin danasani mara adadi,gabad`aya kin canja wannan ba d`aya daga cikin irin halayen ki ba ne ko dai kin fara biye ma k`awayen banza ne ?",ya kai k`arshe maganarsa ya na mai daka mata wata razananniyar tsawa Wanda hakan ya k`ara tsorata ta matuk`a ainun. Malam Salihi ne ya d`aga ma shi hannu alamun ya na mai dakatar da shi tare da ce ma sa,"Haba K`arami me ya ke damun ka haka taya za ka rik`a yi mata irin wannan tsawar,,shin ko ka manta in rai ya `baci akan wani lamari hankali ake sawa domin a saita lamarin bisa hanyar da ta dace,wannan tsawa da tashin hankalin da kuka jefata a ciki ba zai ta`ba iya saisaita ko gyara abinda ya faru ba,hasalima sai dai ya k`ara jagula lamarin,ku bi komi a hankali ku lallashe ta har mu samu ta fahimci abinda mu ke son ta fahimta ba da tsananin,kyara ko hantara ba". "Haba Yaya Salihi Hibba fa ba k`aramar yarinya ba ce ba balle ka ce mu ririta ta gami da lallashin ta akan wannan batun ba,ni fa har da tsoran ganin irin wannan ranar ya sa ban yarda `yata mace ta wuce makarantar gaba da secondary ba,domin ga irin illarnan ta fara bayyana akanta,tun farko da na ji labarin za ta wuce makaranta na ji ban yarda da hakan ba,dole na ja bakina nai shiru domin nasan ko na fad`a a banza ba amfanin da hakan zai yi". " Maganar gaskiya kai Yaya Musa domin in kai duba da su Yaya Hanne,Badiya,Habiba da dai sauran su da basu yi karatun ba,ai makamanciyar irin wannan bata ta`ba faruwa da su ba amma ita da aka nuna ma so ganin ita ce Auta cikin mu Ashirin da biyar ita ce ta watsa mana k`asa a cikin Ido ta ke neman tarwatsa ma na sunan ko ince tarihin Gida ",cewar M. Auwal . Nan fa kowa cikin su ya fara fad`in albarkacin bakinsa,da kyar Alaranma Sama'ila ya tsawatar ma su su ka yi shiru. Yah Sani Wanda daga shi sai Alaranma Sama'ila ne ya fara magana da cewa," Wannan duk shirmen banza ne ku ke yi,shin ina haramcin abinda ta zo da shi,hasalima abun yabo da jinjina ta zo da shi,don haka in baku yaba mata ba ai bai kamata ku hantare ta ba,kaf a cikin ku ba wanda bai da ilimi ko sani akan abinda ta zo da shi,to dan me za ku tsangwami Yarirnya ku hana ta zaman sakat a cikin Gidan Ubanta?". "Ya Sani ba haka bane ba,ba manufarmu kenan ba,hankalin mu yafi karkata akan abinda ta jawo mana da tereran da ake da mu a cikin Gari,ko baka ji yanda ake ce-ce kuce akan wannan lamarin ba duk inda ka zagaya labarin da ake kenan,mu ne a bakin jama'a sai faman gutsiri tsoma ake,ka fasan nan babban Gida ne da yai shura wajen bayar da ilimi addinin ,tsangayar mu sananna ce kuma babbar tsangaya a fad`in Garin Kano,`bangaren koyi da koyarwa babu kamarta ta zarce sa'a,hakan shine gadon mu,ko kusa ko da alama ba mu da abun fad`a,gori ko jin kunya,meye zai ss ta janyo mana babban lamarin irin wannan da har za a rink`a yawo da mu a baka? "..... " Au zancen mutanen ka ke son fifitawa fiye da k`aruwar da addinin ka zai samu,to wallahi ka ki yayi bakin ka tun kafin Baba Malam (Baban su ne) ya shigo ya ji ka". Rufe bakin sa ke da wuya sai ga Baba Malam ya shigo Alk`asim da Daniel biye a bayan shi,nan cikin su kowa ya samu wurin da zai zauna,gami da aro natsuwa su ka ɗaura akan fuskokin su. Yanayin yanda Daniel ya shigo da kuma suturar da ke jikin sa ya k`ara harzuk`a Zuciyoyin su Baba K`arami ta yi ba,ya tara gashi himili guda an saisaye gefe da gefe ga gashin duk a wani mur-murd`e shi tamkar wanda akayi ma kitso,wandon shi kam duk a yaiyage ya ke wanda matasa ke yayin sa crazy trouser ,sai chain d`in da ke wuyan shi kuwa k`atuwar ce da hoton cross a jiki. Maganar Baba Malam itace ta d`an ja hankalin su da yake cewa,"Ku gafar ce ni,bayan mun fito daga sallahr Asar na tsaya ganawa ta musanman ne shiyasa ku ka ji na d`anyi jikirin kafin na shigo,wasu baƙin da ban tsanmace su ba ne suka kawo min ziyara ". " Ba damuwa ai tunda mu ka ji shiru mun san wani lamarin ne mai girma ya taso",Alaranma Sama'ila ya fad`a cikin girmamawa. "Masha Allah kusan dukkanin mu nan, mun san abinda ya tara mu anan ,k`anwar ku ta zo mana da wani babban lamari ta zo mana da k`aruwa a cikin addinin mu na muslunci,sai dai bayan haka da akwai wani babban lamarin da ke biya da wannan batu,kai tsaye dai zamu ce wannan d`an uwanmu",ya nuna Daniel,tare da cigaba da cewa" Ya yi niyar shiga cikin muslunci tare kuma da rok`on alfamar a bashi Auren Hibba,sai dai kuma tun da dad`ewa mun yi alk`awarin Aurar da ita ga d`an'uwanta Alk`asim,wannan shine abinda ya tara mu anan gaba d`aya",Ya kai k`arshe batun yana mai sauke idanunsa akan Yaran na shi domin fahimtar halin da su ke a ciki. "Allah ya gafarta Malam ai mu wannan abun murna da farin ciki ne a gare mu in a kai duba da irin tarin ladan musulumtar da wani ta ke da shi,kuma bugu da k`ari ya nuna ya na son ahalin mu ai wannan abun alfahari ne a gare mu ba ki d`aya". " Ka yi gaskiya Yaya Sama'ila domin wannan cigaba ne mu ka samu a cikin Zuri'ah mu,Na san mun musulumtar da mutanen da yawa a cikin wannan tsangayar ta mu amma ba mu ta`ba samun wanda mu ka had`a alak`ar Auratayya da su ba, domin ya na da kyau duk Wanda ya musulumta a bashi duk wani abu da aka san zai iya buk`ata ko ya nema ya rasa,a wadata shi da komi don gudun komawa waccan munmunar rayuwar da ya baro,hatta da Sana'a,Gidan zama ko makamancin haka".... "Yayah Kabir ba wai na tari numfashin ka ba ne ba,a'a ina so ka sani ba dole sai an had`a ma shi da Aureb Hibba ba, zai musulumta in har da gaske ya yi niyar musulumta zai musulumta, shin ko kun manta mun dad`e da yin alk`awarin akan ita Hibban,ya zamu yi da girman ko nauyin alk`awarin da mu ka d`auka", Cewar Baba K`arami. Baba Malam bai dakatar da su ba sai da ya saurare kowa daga cikin su ,ɗaya bayan ɗaya da kuma irin dalilin da ya sa ya fad`i ra'ayin da ya ke a cikin Zuciyar sa. Sai da yai gyaran murya ya kuma gyara zaman shi kafin ya ce da su," Duk na saurari duk kanin ra'ayoyin ku da kuma dalilin da ya sa ku ka fad`e su sai dai ina so ku sani gabad`ayan ku ni ke da ahak`k`u akan in yankar da hukunci akan kowanne d`ayan ku ko wanne iri ne,Na ba ku wannan damar ne domin sauke hak`in ku domin in bayan babu ni ku ne za ku cigaba da Jan ragamar wannan Gida na mu da duk abinda ya biyo bayan shi,ina so ku sani mu kan tauye kan mu madamar mu ka ga wani abu da zai amfanar da addinin mu ko ya kawo masa cigaba,to shi zamu d`auka mu kawar da son Zuciyar ko buk`atar mu,Dan haka ku mai do hankalin ku a kaina". Kallon shi ya mai da kan Daniel da ke zaune sai faman rarraba idanu ya ke ,baya gane wata maganar ma da su ke cewa,ya ce da shi,"Yaro da gaske ka shirya musulumta,ka shirya barin addinin Crista,ka yarda cewa Annabi Isa ba d`an Allah ba ne ba kuma ba Allah ba ne ba,Allah bai Haifa ba kuma ba a haife shi,Da Maryam da shi Annabi Isa dukkanin su bayi Allah ne,shin ka amince da hakan ?". Cikin muryasa da ba ta ji Hausa sosai ba ya ce da shi,"Na yarda Annabi Isa bawan Allah ne,haka ma His Mother Maryama itama baiwar Allah ce,babu Allah uku Allah d`aya ne,bai haifa ba ba a haife shi ba,shi ka d`ai yai deserving a bautawa ba tare da an had`a shi da wani ba".. "Masha Allah na ji dad`in jin wannan lafazin da ya fito da ga bakin ka,shin yanzu idan na ce ba zan baka Auren `yata Hibba ba shin za ka yadda ka musulumta ko kuwa za ka fasa ne ?". Sai da Daniel ya runtse idanun sa kam tare da datse bakin sa da hak`oran shi na sama sakamakon jin furucin Baba Malam a kunnensa sanda zai bud`e idanunsa har sun sauya kala kafin ya saita kan shi ya ba shi amsa da cewa," Ba wai don a bani Auren Hibba ba na ce zan musulumta ba a'a kawai dai na fahimci kyawawan halayya da d`abi'u wannan addinin a dalilin ta,shi yasa Zuciyarta ta kwad`aitu da son yin rayuwa da ita,ba zan fasa kar`bar tuba ba wai fan na rasa ta,ina da comrfing Ubangiji zai dube ni da idon rahama ya ba ni wata kamar ta,ya hak`urk`urta da Zuciyata akanta ban ta shi musulumta domin wani dalilin ba,in badan fahimta gaskiya da nai ba". Nan take wurin ya d`auki kabbara,alamun sun ji dad`in abinda ya fad`a. "Tambaya ta gaba,ka tabbata ba wani nai yai maka barazana ko ya tursasa ka akan ka amshi addinin muslunci ba?". " A'a ko d`aya babu wani wanda ya tursasa ni ko yai min barazana,hasalima don rad`in kaina na ji ina son in musulumta domin kyawawan d`abi'u da halayen addinin ne ya ja ra'ayina na amince zan kar`bi tuba". Baba Malam kan shi ya fara gyad`awa alamun ya aminta da zancen da ya ke fitowa daga bakin Daniel kana ya mai da kallon shi kan Hibba ya na mai cewa,"Kin ji abinda ya ce Hibba don haka yanzu kina da damar da za ki za`bi d`aya daga cikin su,Daniel ko Alk`asim da ki kai rayuwa da shi tun k`uruciyarki wanda ya ke da tarin Illimi na addini da na zamani?". Sosai wannan tambayar ta girgiza ta,har ta rasa me ma za ta ce sai faman kame-kame ta ke,har sai da Yah Mustapha ya ce da ita,''Kinga ki natsu ki fad`i abinda ke a cikin Zuciyar ki bawanda zai maki dole za`bi a ka ba ki". Muryarta na rawa ta samu ta saita kan ta kafin ta ce "Abbanmu shima fa ya ce ya na son yai ilimi,ba shi da wani buri da ya wuce ya zama tamkar kai ya gan shi yana koyarwa kamar kai,yai koyi da duk kyawawan d`abi'un ka". Wani murmushi mai cike da kamala Baba Malam ya saki tare da cewa da ita,"Allah yai maki albarka ta shi ki shiga cikin Gida ki turo min Uwar d`akin ta ki". Har ta kusa fita daga cikin d`akin ta waigo ta sauke idanunta akan Daniel idanuwanta sun yi rau-rau kafin ka ce me tuni hawaye sun fara zuba daga idanunta,shi dama tun d`azu ya kasa iya d`auke idanunsa akanta,haka ta na ji tana gani ta sa kanta tai waje ,Zuciyar ta sai k`ara raunana ta ke ,game da tunanin wanne irin mataki ne Baba Malam zai d`auka akan ta da kuma rayuwar ta. Gyaran murya Malam Babba yai kafin ya Kira sunan Alk`asim ya ce da shi,"Alk`asim kasan matsayin ka a gare ni,tamkar d`ana da na haifa ka ke,kusan a hannu na ka girma na san halayenka,Wanda su ne suka kwad`aitar da ni akan had`a Auren ka da Hibba, to sai dai zuwan wannan lamarin ya kawo mana tsaiko,Na yanke hukuncin bada Aurenta a ga wannan bawan Allah,ba wai don wata gazawa ta ka ba, a'a sai dan kwaikwayon kyawawan d`abi'u na magabatan mu,idan mu kai duba da yanda mutanen Madina suka kasance a lokacin da Annabin mu,Annabin da muke koyi da shi Annabi Muhammad (S.A.W) yai hijira tare da muhajiran shi zuwa Madina,a wannan lokacin mutanen Madina matayen su na Aure su ka rik`a saki suna bawa muhajiran su aure,duk dan nuna karamaci,d`abi'u da kuma halayen su ma su kyau a gare su,kun ga kenan ba laifi in mun yi koyi da hakan,ina fatan hakan ba zai zama wani abu na daban a gare ka ba?,idan har haka ta kasance ina mai Neman afuwar ks ,ka yafe ni dan Allah". Sai da Alk`asim ya matsa kusa da Baba Malam ya kama mayafin da ke jikin sa kafin cikin girmamawa ya ce da shi,"Haba Malam kai fa Uba ne a gare ni ka can-canci ka yanke min ko wanne irin hukunci,balle kuma irin wannan lamarin mai girman gaske, ba wai sadaukar da Soyayya Hibba ba ko da fiye da wannan buk`atar za ka zomin da ita zan kasance mai yi maka biyayya akai". "Na gode sosai da jin wannan kalami daga bakin ka,shakka babu Allah zai musanya maka da wacce ta fita". Kallon sa ya maida kan Alaranma Sama'ila ya ce,"Ana son a gaggauta wasu abubuwa ciki harda musulumtar da Wanda ya zo musulumta, don haka zamu lak`anta ma shi kalmar shahada a yanzu,dan haka ka jagoranci lamarin". Nan Alaranma Sama'ila ya fara lak`anta ma shi kalmar shahadar,"*Ashshahadu Allah ilaha illallah,wa Ashshahadu Ana Muhammad rasulullahi,wa Ashshahadu Ana Isa Abdullah wa rasuluhu*",yana fad`a Daniel na maimaitawa harshen shi a rarrabe. Nan fa suka d`auki kabbara baki d`ayansu kowa a cikin su na farin ciki shigar shi muslunci gami da samun k`aruwa da su kai. Alaranma Sama'ila ne ya tambaye shi da cewa,shin kana da wani suna da ka ke sha'awar a maida maka madadin Daniel da ake kiranka?". Shiru na wani d`an lokaci Daniel yai,ya na mai tunanin wanne sunan ne ya dace da shi da ," Am am ina son Abubakar zan so a kira ni da Abubakar saboda na samu labarin irin gudunmuwar da ya baiwa addinin muslunci ". "Tabbas ka yi dacen suna ina fatan kayi koyi da mai sunan,Allah ya albarkaci rayuwar ka ya baka ikon zamowa cikin salihan bayin sa". " Shin yanzu idan Na ce zan baka Auren Hibba, kana da wanda za ka gabatar a matsayin iyayen ka ko da acan asalin Garin ku ne?", Duk`ar da kan shi k`asa Daniel yai kafin ya ce da shi"I don't have any relative in this town, Na zo Garinnan a matsayin bak`o aiki ne ya kawo ne,Ni d`an asalin Garin Jos ne,iyayena sun rasu a wani rikici da akayi su duka biyun,sai dai muna zaune tare da Grandmother d`in mu da kuma Sister na". "Eyyah Allah sarki na jajanta ma ka akan haka,amma ku na da wasu dangi haka bayan su ko?". " Eh to ba na ce babu ba amma na san akwai wani Uncle d`inmu guda d`aya,ya na can Benin da zama ,ya ta`ba zuwa inda mu ke sau biyu bayan rayuwar Parents d`inmu,in fact dai muna rayuwa ne mu biyu da Grandmother d`in mu da ta tsufa sosai,bayan ita kuma bamu da kowa gaskiya ". Shiru duk mutanen wurin su kai kowa na mamakin labarin da ke fitowa daga bakin sa,Sallamar da Ummie Maryam ta yi ce ta ja hankalin su, Baba Malam ne ya bata umarnin shigowa gami da samun guri ta ja ta tsaya tare da cewa cikin mutuntawa da girmamawa matsayin ss na sirikinta," Hibba ta ce in zo ka na son ganina Baba","Eh haka ne ina son ki je ki sanar da mutanen Gidan cewa a yau zan d`aura ma Hibba Aure dan haka da buk`atar ku san da hakan ku shirys mata `yan kayayyakin ta dan da an fito sallahr magariba za ta bi mijin ta". Ba Ummie Maryam ba hatta da su Malam K`arami da ke zazzaune da ya ja bakin sa yai shiru tun fara fahimtar abinda Baba Malam ke shirin aiwatar wa,sai da yai saurin ɗago kansa bakin sa na rawa,saba damar furta komi..... *JADEEDAH* (It's a story of two love birds who are so different from each other ) STORY & WRITTEN BY : (*Cwt~Sumiey*) Marubuciyar littafin MENE NE ABIN YI ? KARAGAR MULKI And now.....*JADEEDAH* https://chat.whatsapp.com/CWkZfMqvD4H0mtd7WW6Xbz https://whatsapp.com/channel/0029VapqU8C002T5Bz8RSQ0a BOOK 1 ♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡ PAGE 3 ❤ Cikin rawar murya Ummie Maryam ta sake mai-maita abinda kunnuwanta su ka jiye mata amma ta sigar tambaya. "Eh abinda ki ka ji shi na fad`a zan d`aura Auren Hibba da d`an'uwanmu Abubakar", ya na mai nuna inda Daniel ya ke zaune ba tare da ya tsaya ba ya cigabada da cewa,"kuma a yau yanzu ma bayan sallahr magariba, kuma zata bi mijin ta a yau d`in ba sai gobe ba, don haka ki je ki aiwatar umarnin da na sa ki", ya kai k`arshe zancen yana mai kaurara muryarsa. Ummie Maryam na tafe na waigen inda Daniel ya ke zaune wanda ya sauya sunan shi daga Daniel zuwa Abubakar . " Amm K`arami shiga da shi sashen bak`i ka nusar da shi duk abinda addinin ya tsara, ya gudanar ya tsarkake jikin shi,sannan ya sauya suturar shi izuwa wacce addinin mu ya koyar da mu musan ya". Jikin Baba K`arami a sanyaye ba tare da ya so ba ya mik`e gami da nuna ma Abubakar hanyar da ta da ce su bi,Alk`asim ne ya dakatar da shi ta hanyar cewa, "Baba K`arami ina so zan bika domin mu aiwatar da wannan aikin ladan a tare". " Ba damuwa mu je",ya bashi amsa a tak`aice,su kuma sauran duk su ka mik`e su ka nufi hanyar da zata sada su da babban masalacin anguwa da suke gudanar da sallah a cikin sa kuma su ke jagorantar duk wani abu da ya ta so a cikin sa. "Ummien Jaheed lafiya na gan ki haka kin shigo jikin ki ba k`awari?", Anty Zulai Matar Yah Mustapha ta tambaye ta . Sai da ta sauke idanunta akan Mama Hadiza,gami da duk`ar da kanta k`asa kafin ta ce da su," Baba Malam ne ya umarce ni da in had`a ma Hibba kayanta domin zai d`aura ma ta Aure yanzu bayan sallahr magariba kuma za ta bi mijinta ". Zumbur Umma Jamila tai ta mik`e bakin ta d`auke da salati ta na cewa," Auren kuma wacce irin magana ce haka mai ya sa Malam zai yanke irin wannan hakunci cikin k`ank`anin lokaci sai ka ce wata mara gata,to wai ma da wa za'a d`aura Auren? ". Sai da Ummie Maryam tai k`asa da muryarta kafin ya ce," Da wanda ta kawo managern da ta ke IT a Company d`in sa". Mama Hadiza runtse idanunta da k`arfi tai alamun maganar da ta ji ta bugi Zuciyarta, Umma Hafsat ce ta amshi zancen muryarta na bayyanar da rashin yarda da hukuncin da Baba Malam ya zarta,gami da cewa"Ba zai yiwu ba,ta ya zai amince da abinda k`aramar Yarinya za ta zo mishi da shi,ba tare da yai duba da zata iya cutuwa ba,bai fa san komi game da shi ba,ta ya zai ɗauki ƴa ya ba shi sai ka ce wacce ya tsinto",d`an tsagaitawa tai gami da maida akalar zancenta akan Mama Hadiza, "Ya kamata ki sa baki a wannan zancen ki dakatar da Malam Babba in kuwa ba haka ba ke ce wacce za tafi kowa zubar da hawaye a cikin Gidannan,ba fa a san asalin wannan Yaron ba ahalin sa gabad`aya duk ba sa Sallahr,a haka za ki bari ya zama Sirikin ki Mihaifin wurin jikokin da za a haifa ma ki anan gaba?". Umma Hafsat ce ta amshi zancen da cewa," Kin fad`i gaskiya Yaya bai kamata mu zuba Ido mu bar wannan lamarin ya tafi a haka ba,an sha yi ma na irin wannan yankan k`aunar a cikin Gidannan a d`auki `ya`yan mu mata a bayar da su ga wanda aka ga dama ba tare da anyi duba da suna son mijin ko a'a ba,ba tare da anyi shawara da wani daga cikin mu ba,amma duk da haka ba a ta`ba kawo mana mutum irin wannan ba,don haka dole zamu had`a k`arfi a tare mu dakatar da wannan k`udirin na su". Kauda kai gefe Mama Hadiza tai gami da saurin d`auke d`igon kwallahr da ta ke k`ok`arin zubowa daga idon ta gami da cewa,"Hmmmm kun manta shima `yar shi ce ya ma fi ni iko da zartar da hukunci akan ta kuma ma dad`in gushi ai ita gata a kai mata,wacce `ya ce a Gidannan ta kawo wanda ta ke so a ka bata shi,sai fa ita,ko kun manta za`bin ta ne,don haka kar ku tada hankalin ku akan d`an wannan k`aramin abun".ta d`an dakata gami da cewa da Ummie Maryam, "Yauwa Matar K`arami(da ya ke ba ta fad`in sunan ta),bari in je in kwaso maki kayanta na cikin d`akina ki had`a da na wajen ki kar lokaci ya k`ure". Ta na kaiwa nan ta wuce ta tafi d`akin ta hannayenta saman fuskarta. Umma Maimuna ce ta niyar dakatar da ita Baba Asabe ta saurin dakatar da ita gami da girgiza mata kai tare da cewa," A'a kar ki je ba za ku iya can za komi ba,domin ba ku Isa ku can ja wannan hakuncin ba,kun san halin Baba Malam ciki ba hatsi ba, ba zai ta`ba can ja maganar sa ba, don haka ku ja bakin ku kuyi shiru kar da kuma ku ta da wata fitinar". Kamar wacce aka hankad`o haka Yaya Zaliha ta shigo cikin Parlourn sai faman haki ta ke ita ce d`iya d`aya da Baba Asabe ke da ita sai kuma Alk`asim shi d`in k`anin ta ne "Inna Hibban ta ke mayaudariya macuciya ki fito inji dalilin da ya sa ki ka fasa Auren k`anina,ki fito gani tsaye ina jiran ki,sai da ki ka bari Yaro yai nisa akan son ki sannan ki zo ki ce kin fasa Auren sa akan me,me ya aikata ma ki", cikin d`aga murya ta ke magana. Saida gaban Hibba ya yanke ya fad`i sakamakon jin wannan kiran da Yaya Zaliha ta ke mata. "Ko da ya ke ai barewa bata yi gudu d`anta ya rarrafe ba daga dukkan alamu d`aki aka sa ki aka hure ma ki kunne akan ki guji d`an'uwanki na jini akan wani banzan bare kafirin banza wanda kaf ahalin sa ba mai yin Sallah,to ki sani za kiyi danasani mai girma wacce ba za ki ta`ba iya gyara kuskuren da ki ka aikata ba,za ki gani a k`ok`on shan ki ki jira lokaci"........ " Kar ki kuskura ki yi mata mugun baki,domin ita ba `yar da ki ka haifa ba ce ba,wannan ina son ki sa ni ko kuma ince ina son ki tuna ita a kaf ahalin ta ba ta ta`ba aikata wani abun kunya ba balle har ki goranta ma ta da shi,bugu da k`ari ita ai alfamar ta yi ma Alk`asim da ta amince za ta Aure shi",Cewar Yayah Hanne da shigowarta kenan itama goye da `yar ta a bayanta, itace babba `ya mace a d`akin su Hibba. Wata tsawa Baba Asabe ta dakawa Hanne gami da cewa,"Ahir d`in ki Hanne anan a tafin hannunna a ka haife ki,don haka ba ki isa ki goranta mata akan abinda ba ta ji ba bata gani ba". "Au ashe babu dad`i Baba Asabe mai yasa ba ki dakatar da ita ba a lokacin da ta ke k`ok`arin cin zarafin Mahaifiyata".... Shigowar Baba K`arami ne ya dakatar da ita ran shi a `bace ya ce da ita,"Au dama abinda Baba Malam ya turo ki ki yi kenan,me ya sa ki ka zo in kinsan tada ma mutanen Gidan hankali za ki yi ?". " Yayah ta ya inaji ina gani zan barsu su ci zarafin Mahaifiyata a gabana kuma in kyale su,wallahi ba ta Isa ba in yanzu ta sake cewa wani abu sai na maida mata da martani "..... " Ba ki da hankali ne Hanne Baba Asabe k`anwar Mahaifin ki ce ta ya za ki tsaya ki na sa'insa da ita". "Na san da haka K`arami,amma me ya sa kaf cikin Gidannan ba su da abokin rikici sai Mahaifiyata, na riga da na dad`e da fahimtar su daga ita har Baba Asabe ba wani son mu su ke ba".... Cikin matsananancin fushi Baba K`arami ya daka mata tsawa" Ki `bace min da gani tun kafin in sauke fushina akan ki,ko dai ki koma Gidan ki in kinsan fitinar za ki tada mana ko kuma kije ki aikata abinda aka Kira ki domin shi,ku kuma lokacin Sallahr magariba yayi kuna iya tashi ",duk yana magabar ne cikin fushi. Kowa tashi yai ya nufi d`akina sa,ba tare da wani ya ce uffan ba,kowa ya san halin Baba K`arami yana da hak`uri da kawaici,amma idan ran shi ya `baci bai iya fad`a ko fushi ba, sanin hakan ne ya sa ba Wanda ya sa ke cewa komi su ka tashi. Shima d`akin da Hibba ta ke a ciki ya nufa ran shi na jin suyar abinda ta aikata. "Haba Hibba mai ya shiga cikin kan ki ta ya za ki zo da irin wannan batun ba ki zauna kin yi tunanin abinda ka iya biyo baya ba,wai me ya sa baki ta`ba zuwa kin sanar dani abinda ya ke faruwa ba har sai da komi ya lalace ?". " Yaya Hanne mutumin kirki ne fa ya na da dad`in zama da kuma kyawawan d`abi'u ".... " Au abinda za ki fara kafa hujja da shi kenan,shin ba ki san kaf ahalin Gidannan ba wanda ke son wannan Auren ba,hatta da Baba Malam ya biye ma ra'ayin ki ne kawai,amma ba wai yana son Auren ba kafin in shigo nan na biya d`akin Mama na iske ta na zubar da hawaye kuma duk akan wannan maganar Auren ne,shin ba ki tunanin wani abun ka iya biyo baya sakamakon rashin amincewar da su ka nuna?". Hankalin Hibba sosai ya tashi da jin batun Yaya Hannenta ,cikin muryar kuka ta ce,"Kuka....Kuka kuma..Mama ke kuka akai na,na shiga uku,ina zan sa kaina inji dad`i,wallahi indai haka ne na fasa Auren ina son Mamata tai alfari da ni ba zan so zubar hawayenta akaina ba ". " Haba Yaya Hanne ya za ki fad`a ma ta haka kin ga fa hankalin ta ya tashi,da kin sa ni ba ki sanar da ita ba",Cewar Ummie Maryam. "A'a Ummien Jaheed gara ta sani tun yanzu ta san irin kuskuren da ta aikata tun kafin lokaci ya kure mata".... " Wallahi indai haka ne na fasa Auren,zan zauna a Gida ko ganinsa ma ba na so,ku sallame shi ya tafi ya bani wuri". "Hmmmmmm kin makaro domin kin fi kowa sanin Baba Malam ba zai ta`ba sauya maganar sa ba,Aure ba fashi kamar anyi an gama". Hannu Hibba ta d`ora aka gami da sakin salati ta na mai cewa," Na shiga uku na bani ni kuma yanzu ya zan yi Allah ba na son sa na daina son sa ina son in zauna da ku ba na son Auren gabad`aya "... Shigowar Baba K`arami ya sa ta dakata,Hawaye sha`be-sha`be a idonta ya iske ta, ta na hango shi ta nufi wajen da ya ke,ta na mai cewa," Yayah dan Allah ka yi hak`uri ka dakatar da wannan Auren,Na hak`ura na fasa Auren ba na Son shi,ka dakatar da Baba Malam Dan Allah, Na fahimci kaf ahalin Gidannan ba wanda ya ke son wannan Auren na rok`e ka kaji Dan Allah".ta kai zance ta na mai had`a hannayenta wuri guda. "Ai kin makaro Hibba domin yanzu haka an d`aura Auren ki da Abubakar,ni da kaina Na ba da Auren ki,shi kuma Baba Malam ya zama waliyinsa,yanzu haka ya na waje ya na jiran ki ki fito ku tafi Gidan ku". " Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un,Yayah wallahi na tuba ka sa shi ya warware Auren ba na son bin shi ni anan zan zauna na fasa Auren ". Wata tsawa ya daka ma ta gami da nuna mata hanyar fita daga d`akin ya ce da ita," Ta shi ki fita ki bani wuri ki tafi can Mijin ki na can na jiran ki,shin da ba ki san da zuwan ranar da za ki bar Gidan ba sai yanzu,don haka tun kafin in sa`ba maki ki `bace min da gani". "Allah na hak`ura na fasa ba inda zani,ba na ma son shi yanzu ka bashi hak`uri Dan Allah,kasa shi ya warware Auren, ka sa ya sake ni".... Ranshi a matuk`ar `bace ya nufi ta,sandar Covebing ya ci karo da ita ya d`auke ta ya nufe ta da ita,ganin yanda ya nufota yasa ta kasa da gudu ta nufi waje hannunta rik`e da mayafinta. Ko da isarta wajen,Jan tunga tai ta tsaya tana mai kai hannayenta saman fuskarta gami da murza idanunta,Anya kuwa idanunta gaskiya suke gane mata kuwa,duk da kasancewar duhun Magariba ya fara amma hakan bai hanata iya gane shi ba Tsaye ya ke jingine jikin motar sa sanye cikin jamfa riga da wando,an dai-daita sumar kansa ya kawo hula jaddara wacce tai dai-dai da kayan da ya sa,hannunsa rik`e da casbaha ya na ja,fuskarta shi sai faman fad`ad`a murmushi ta ke,hasken muslunci ya baibaye shi,da ka yi ma sa kallon guda za ka fahimci ya na cikin,farin cikin natsuwa da kwanciyar hankali. *JADEEDAH* (It's a story of two love birds who are so different from each other ) STORY & WRITTEN BY : (*Cwt~Sumiey*) Marubuciyar littafin MENE NE ABIN YI ? KARAGAR MULKI And now.....*JADEEDAH* https://chat.whatsapp.com/CWkZfMqvD4H0mtd7WW6Xbz https://whatsapp.com/channel/0029VapqU8C002T5Bz8RSQ0a Wannan page naku ne massoya na Allah ya bar mu tare forever and ever BOOK 1 ♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡ PAGE 4 ❤ Duk ta tada ma shi hankali da kukan da ta ke,kwata-kwata hankalin shi baya kan driving d`in da ya ke,ji ya ke kamar ya janyo ta jikin sa ya lallasheta ya tambaye ta abinda ya ke damun ta amma ina hakan ba mai yiwu ba ne ba. "Why are you crying, me ya sa hawaye ke zuba daga cikin idanunki ko na yi ma ki wani laifin ne ban sa ni ba?", ya tambaye ta cikin hausar shi mara fita sosai. `Dago kanta tai tana kallon shi da sauri tai k`asa da idanunta tana mai kasa cigabada da kallon shi tai,muryarta cikin alamun wacce taci kuka ta ce da shi," Ni bana son Auren ka maida ni Gida na fasa bin ka". Sosai Maganar Hibba ta daki k`irjin Abubakar har sai da ya samun wuri yai parking gami da mai da kallon shi kacokan akan ta ba tare da ya iya cewa da ita kumi ba,sai tsura ma ta idanu da yai. "Why....why...Hibba me ya sa za ki ce haka,ko kin manta we are married now,mun yi Aure ni da ke,mu d`in ma'aurata ne,mun zama Mata da Miji,ta ya za ki ce kina son ki koma Gida,yaune fa aka d`aura Auren mu,kuma ki ce za ki koma Gida a yanzu,to ki ce da su me in kin koma ?". Rau-rau tai da idanu,hawaye na sake zubo ma ta daga idaniyarta," To ai duk basa san Auren na mu da kai,fushi su ke da ni,Mamana ma kuka ta ke,hawaye zuba su ke da ga idanunta akaina". Shiru Abbakar yai na wani lokaci,Kafin ya cire baki ya ce da ita,"Ban ji dad`in jin Mama na zubar da hawayenta akan Auren mu ba,amma ki sani na maki alk`awari zan zauna da ke cikin Soyayya da kuma amana,zan kyautata ma ki in baki farin ciki fiye da yanda za ki yi zato da tsanmani,zan zame mi ki Mijin kwatan ce,Mijin nunawa sa'a,ba zan ta`ba bari ki sake kuka ba,zan maye ma ki duk gurbin da ki ka rasa a sanadin Aure na,kuma a sannu in mu ka yi haƙora,wata rana za su yafe mu su amshi Aurenmu da hannu bibbiyu". Kai ta fara girgiza ma shi alamun ba ta amince da duk abinda ya ce a yanzu ba. Marairai ce mata shima ya yi cikin fuskar tausayi ya ce da ita,"Dan Allah kiyi hak`uri kar ki bar ni,ina son in rayu da ke,kar ki bar ni,ban san wacce irin rayuwa zan shiga ba in ki ka bar ni,zan cika mi ki dukkanin alk`awarin da nai ma ki,domin yanzu ba zai yiwu in maida ke Gida a wannan lokacin ba,ran Baba Malam zai `baci sosai fiye da yanda da ki ke tunani,in Mama ce zuwa nan gaba sai mu je mu bata hak`uri, hatta da sauran mutanen Gidan duk za su yafe mana zasu so Auren mu da ke,ki bani wani d`an lokaci kad`an ba zan kunyatar da ke ba, ba zan bari wani abu guda d`aya da ahalin ki su ke tsoran ya faru da ke,ya same ki ba,ba zan ta`ba cin amanar ki ba ko in juya ma ki baya,zan kasan ce da ke a kowanne irin yanayin na dad`i ko akasin haka,ki amince da ni mu tafi tare dan Allah Hibba, you are one and only that I have in my life so please don't live me",ya kai zancen cikin raunanniyar murya. Kalaman sa sun yi tasiri a cikin Zuciyarta har hakan ya sa Zuciyarta ta fara yin sanyi,kukanta ya tsaya amma duk da hakan ba ta iya ta ce da shi komi ba. Cikin muryar shi mai sanyi ya ce mata,"My Wife please shall we go,dare na k`ara yi dan Allah, dan Soyayyar da mu ka nuna ma juna kafin Auren mu ?". Da idanu kawai ta ke binsa,gani ta ke kamar duk abinda ya faru ba gaskiya ba ne ba kamar duk mafarki ne,sai dai ko kusa ko da wasa ba mafarki ta ke ba gaskiya ne,a zahiri komi ya faru cikin d`an k`ank`anin lokaci. "Shall we go,please dan Allah ?", ya sake tambayarta a karo na ba adadi,da kai ta bashi amsa ya ja motar cikin farin ciki da annashuwa. Cikin some minutes ya isa zuwa Gidan shi da ke Jan Bulo,ba wani babban Gida ba ne,two bedroom ne sai kitchen,main parlour da`yar farfajiyar tsakar Gidan daga gefe kuma sai parkin space wurin da ya ke aje motar sa. Tamkar bak`uwa haka take raba idanunta a cikin Gidan duk da kasancewar yau ne zuwan ta na farko cikin Gidan,da kan shi ya shigar da trolleys d`in kayanta da suka taho da su ita kuma sai bin bayan shi take. Har ya Gama shigar da kayan tana biye da shi,kai tsaye ta ke nuna rashin sakewarta,da amincewar a cikin Gidan,sai a sannan ya nuna mata wuri ta zauna,idanu ya zuba mata yana kallon ta kafin ya tambayeta,"Amm nasan kin gaji da yawa kamata yai ki fara yin fresh up kafin nan me ki ke son ki ci in sama maki kafin ki fito?". "Ni ba wani wanka da zan yi,kuma ba na son cin komi". " Seriously ya kamata ki ci wani abu ko da ba zaki yi wankan ba,bazan iya barin ki ki kwana a haka ba,domin ma san ba makawa za ki cutu,ni kuma ba zan ta`ba iya barin wani abu ya cutar da ke ba madamar ina da hanyar da zan iya dakatar da hakan ta faru,don haka ki fad`a min me ki ke son ki ci yanzu in gabatar ma ki da shi ?". "To...to..Just I need a one cup of tea". " Nop ban yarda ba,abincin za ki ci,kin san fa na iya cooking",idanu ta zaro alamun bata yarda da abinda ya ce ba. "Sincerely da gaske na ke,in ma badan kar ki ce na cika baki ba da sai ince I'm the one of the great chief a garin kano", sosai maganarsa ta ba ta dariya,har ya ga alamun ta fara sakewa a cikin Gidan. Gyara zaman shi yai sakamakon nasarar da ya ga ya fara samu,hankalin ta ya fara dawowa kan shi," Ina gaya maki lokacin da ina Jos a time d`in da inada 13 to 14yrs muna tare da Grandma d`ita ni ke mana girgi,a lokacin my Sister Cecelia shi's 5yrs,Grandma na can kasuwa tana kasuwancinta ni ke mana girki,some time's in cika gishiri,Magi ko yaji,wani lokacin har ruwa na ke cikawa,but fa yana yin dad`in in ki ka ci sai kin kusa tsinka yatsan ki kan dad`i ". Dariya sosai Hibba ta ke har ma ta saki jikinta yadda kasan ba abinda ya faru da su . Ya cigabada da cewa,"Ina da kyankyami shiyasa bana cin abincin waje fad`a min me ki ke son ci just mention it yanzunan ki gan shi a gaban ki". Cikin yanayin jin dad`in hirar da suke tace da shi,"Amm to in haka ne ina son zanci tuwo ko d`an wake,waina ko danbu,a cikin su duk wanda na samu zanci". " No...no...no...banda wannan i can't,ban iya girka Hausa food ba,ki choosing wani na daban except wanda ki kai mentioned at the first". "OK kai dai kawai ka ce baka iya girki ba"..... " No I swear na iya girki,kawai ki ba ni dama ki gani,sai kin tsotse yatsun hannun ki". "OK to muje kitchen d`in mu gani amma fa da sharad`i"," Oh sharad`i kuma to inajin ki","Da ni za a tafi kitchen d`in ayi komi a tare","Na yarda mu je",haka su ka tafi a tare zuwa kitchen suka yi komi a tare. Cikin k`ank`anin lokaci suka kammala daga jellof spaghatti da Stew,suka ci cikin farin ciki da annashuwa tamkar komi bai ta`ba faruwa a cikin rayuwar su ba,har dare ya raba, suka nufi d`akin da suka baro. "Ka ga yau ba sai na farka cikin dare ba neman wani abu ba", "Farkawa cikin dare kamarya ?"," Ina farkawa cikin dare a kowanne dare inci wani abun kamar cup of tea ko Coffee something abu mara nauyi ko noodles haka dai haka".ta ba shi amsa "Ikon Allah Babba da ke?", Ya tambaye ta kai tsaye cikin sigar tsokana. " Uhmmmmm zan dai iya cewa halitta ce, don da nima ina tunanin zan daina a lokacin da ina Yarinya amma kuma daga baya na gane halitta ne kawai,Kai dare yayi 20minutes to 12", zaro Ido waje Abbakar yai ya ce da ita ,"Zo ki kwanta kar gobe mu makara wurin tashi", ya kai zancen ya na mai nuna mata bed ta je ta kwanta,shi kuma ya zauna kan bed side drawer yana mai cewa da ita," Zo ki kwanta kin san ma iya tarairayar mutum har yai barci domin a dacan ni ke tarairayar Cecelia har tai barci,kin san itama `yar rigima ce". Murmushi Hibba ta saki tana mai gyara kwanciyar ta ta ce Cecelia na ina yanzu?","Tana can gaban Grandma ta girma fa yanzu, but har yanzu `yar rigima ce",nan fa ya fara bata labarin Cecelia da halayenta na ban dariya da kuma shiririta har barci `barawo yai gaba da ita. Binta yai da irin sanyayyan kallonnan mai cike da shauk`in so da k`auna,ya na mai k`ara gode ma Allah da yasa ya had`u da ita har ta zama sila ko kuma tsanin shigar shi cikin Addinin muslunci, bai yarda ya kwanta ba har sai da ya shirya dukkanin kayanta a cikin wardrobe, kan carpet ya yasar da Philo ya kwanta a k`asa ba tare da ya kula da ita Hibban ba. Sanyin Asuba da ya fara saukowa yasa Hibba farkawa,waige-waige ta farayi taga ina za ta hangoshi kwance a k`asa a hankali ta sauko ta nufi inda ya ke motsin tafiyar ta ne ya farkar da shi ya tashi zaune. "Me ye haka dan Allah,taya za ka zo nan ka kwanta a k`asa, idan sanyi ya kama ka fa?", had`a hannayensa yai guri guda alamun ban hak`uri tare da cewa da ita," Ki gafar ce ni,yau ce ranar ki ta farko a cikin Gidannan ba zan so in takura ki ba,haka kuma ba zan iya tafiya in bar ki ke kad`ai ba,shiyasa Na aikata abinda ki ka gani amma ki gafarce ni kin ji". "OK badamuwa amma dan Allah kar hakan ta sa ke faruwa ka ji,yanda ba ka son wani abu ya same ni haka nima ba na son in gan ka cikin wani yanayi mara kyau". " Tuba na ke my princess hakan ba zata sake faruwa ba i promise ". Clock d`in dake manne jikin bango ta kalla kana ta ce da shi,"Lokacin Sallah Asuba ya kusa da buk`atar ka shirya da wuri", Bathroom ya shiga cikin k`ank`anin lokaci ya d`aura Alwala kamar yanda aka koyar da shi,bayan ya fito ya ke cewa da ita," Da akwai wani Mosque anan kusa zan je in yi sallah a cikin sa". Itama tana k`ok`arin d`aura ta ta Alwalar ta ce da shi,"To sai ka dawo Allah ya tsare amma dan Allah kar ka dad`e",da murmushi d`auke a fuskarshi ya bata amsa. Bayan wajen mintuna Ashirin da biyar sai ga shi ya dawo,jikin shi a sanyaye,da d`an sauri Hibba ta je ta tarbo shi,fuskarta na nuna rashin jin dad`in halin da ta gan shi a cikin. "Lafiya mai ya faru ,na ga ka dawo cikin irin wannan yanayin ko dai wani abun ya faru da kai ne ?". " Hibba ki gode ma Allah da ya hallice ki da ke da ahalin ki a cikin muslunci,a yau na shaida Cewar ba k`aramar rahama Ubangiji ya so ni da ita ba da har na gane gaskiya na bita kuma na amsheta da hannu bibbiyu,ina ma da `yan'uwana da su kai saura za su fahimci irin gaskiya da na fahimta su tuba su dawo kan hanya madaidsiciya ,da sun samu tsira tunda ga nan duniya har lahira,mutanen wannan masalacin sun mutuntani sun karramani a tsakanin jiya da yau na ga asali kuma zahirin Soyayya da ke fitowa daga cikin zukatan muta ne,ina ma da zan iya janyo `yan'uwana su musulumta, ina ma da zan iya fad`a masu gaskiya su yarda ina ma......ina ma".... "Ka ga ya isa haka ba kuka ko tashin hankali ya kamata mu nuna ba,addu'a zamu yi ta yi mu,idan suna da rabon rahama Allah zai kar karo da hankalin su,har suma su musulumta, Dan haka ka kwanta da hankalin ka ji". "In sha Allah zan dage ba dare ba rana har Allah ya karkato min da hankalin su,Gari ya fara wayewa ina son zan je Inga Baba Malam kafin lokacin zuwa office yai". Cikin yanayin murna ta ambaci sunan Baba Malam tare da cewa,"Ka ce in shirya mu tafi tare?". " A'a yanzu zan dawo ya umarce ni ne da in zo da akwai abubuwan da ya ke son ya koyar da ni,daganan zai ba ni littafan addinin da zan rik`a amfanin da su tunda ina da malama ta a cikin Gidana". "Haba dan Allah ta ya za ai ka barni ni kad`ai a cikin Gidannan Allah ina jin tsoro"," I'm so sorry my wify ba abinda zai faru da ke zan rok`i Allah da ya tsare man ke har inje in dawo ba zan jima ba",kallon shi ya maida kan prayer mat d`in da ta gama Sallah akanta take, inda k`ur'aninta ya ke aje akai da alama karatun ta ke,kan prayer mat d`in ya zaunar da ita kafin ya ce da ita. "Cigabada da reciting d`in sa I will be back soon,ina mai tabbata ma ki yanzu zan dawo", "Wayo ko shikenan ma hak`ura tunda abun `yar haka ce",murmushi yai mata gami da nufar hanyar kitchen . Da d`an d`aga murya ta tambaye shi ina za shi nan," Zan duba ne Inga abubuwan da bamu da su eanda zamu buk`ata in na fita sai inbiya in taho da su,daganan sai inje in had`a ruwan wanka ". " Am...to bara na had`a maka ruwan",Hibba ta fad`a ta ma mai nufar hanyar bathroom d`in da wani irin kallon ya bita wanda har sai da ta tsargu ta waigo ta kamashi yana ma ta irin wannan kallon. Shagwa`be fuska tai tare da ce mai,"Wannan kallon fa na me,ko ka manta now I'm house wife ?","I don't say anything, kawai dai ina kallon ki ne kawai",turo baki ta tai gaba gami da nufar hanyar bathroom d`in ba tare da sake ce masa komi ba,shi kuma sai faman binta da murmushi ya ke. *JADEEDAH* (It's a story of two love birds who are so different from each other ) STORY & WRITTEN BY : (*Cwt~Sumiey*) Marubuciyar littafin MENE NE ABIN YI ? KARAGAR MULKI And now.....*JADEEDAH* https://chat.whatsapp.com/CWkZfMqvD4H0mtd7WW6Xbz https://whatsapp.com/channel/0029VapqU8C002T5Bz8RSQ0a BOOK 1 PAGE 5 ❤ Tsawar da ya daka itace ta dakatar da Hibba daga tunkarowa inda yake,hannunta rik`e da robar ruwa mai sanyi da cup,har ruwan dake cikin cup d`in sai da ya zube k`asa alamar ta ji tsoro, dawowar shi kenan daga office yana k`ok`arin shigowa cikin Gidan. "Na gaya maki Cecelia zan zo", ya fad`a cikin d`aga murya," Na gaya maki zan zo,ina da aiyuka dayawa ne anan,nauyi ne ya k`aru a kaina da bazan iya tahowa in barsu ba,that's why ki ka ga na d`au wannan long time d`in ban shigo ba,amma ba hakan na nufin na manta da ku ba". "Oh wani abun mai mahimmanci ka ke da shi shine ne har ya tsare ka,kuma har muhimmancin sa ya kai ka manta da mu,rayuwar ka kawai ka ke kai kad`ai ka manta da mu da dukkanin wani abu da ya shafe mu in ya wuce ka tura ma na da kud`i,ba ruwanka da mu ,har Grandma ta k`araci ciwonta ta warke ba ka zo ka ganta ba,ko an gaya maka kud`i sune kawai matsalar mu,muna buk`atar ganin ka a kusa da mu"... " I said shut up Cecelia are you out of you sense, ba kya cikin hankalin ki ne,ta ya za ki tasa ni gaba kina fad`ar duk abinda ya zo maki a bakin ki,ko ni sa'an wasan ki ne,don haka ki shiga taitayin ki,ki fita a harkata kawai ki zuba min ido in kuma ba haka ba"....... "In kuma ba haka ba fa,uhm me za ka aikata,Na ce me za ka aikata Daniel". " I'm sorry Grandma ba wai wani na ke nufi da hakan ba ne ba,kawai dai jin yanda take magana da ni ne ta `batan mun rai har na fad`i irin wannan munanan kalam a kanta amma dan Allah ki yi hak`uri ". " Ka rik`e hak`urin ka ba na so Daniel,ba na son hak`urin na ka,amma ina son ka sani, I swear to the God idan har ba ka zo Gida mun yi bikin murnar Christmas a tare da kai ba sai na tako k`afata har nan cikin Garin Kanon in ga abinda ka ke `boyewa da har ya zama katanga ko shamaki a tsakanin mu". Cikin rawar murya Abbakar ya ce da ita,"Bbbbb.....ba sai kin zo ba Grandma ni da kaina ma zan zo in sha Allah "," Daniel you said what ?". Cikin yanayin kama kan shi ya ce da ita,"Ina nufin by the grace of God zan zo har Jos ɗin kafin bikin Christmas zan zo". Shiru Grandma tai na wani d`an lokaci kafin ta ce da shi cikin kwantar da murya "Daniel me yake damun ka,dole akwai wani abu da yake damun ka,ba haka na san ka ba,dole akwai wani abu da ke damun ka ko kuma ka ke `boye min shi". " A'a Grandma ni ba abinda ya ke damun kawai pressure d`in office ce yanzu ma haka dawowata daga office kenan ko cikin Gidan ban shiga ba". "Shikenan Yarona Na yarda da abinda ka ce,ka kula da kanka ka ji,kuma kayi k`ok`ari ka zo da Christmas tunda nasan ana bada hutu a lokacin". " Kar ki damu Grandma zan zo","OK shikenan bye take care of yourself I will call letter yanzu ka samu ka huta", A hankali kamar mai yin samd`a haka ta k`araso kusa da shi,hannunta ta kai kan wuyan shi gami da idasa cire masa neck tie din da ya fara cirewa tun shigowar shi, kujerar da ke kusa da shi ta zaunar da shi,ta cire mashi takalmi da sock d`in da ke k`afarsa,sannan ta ba shi ruwa mai sanyin da ta zo da shi. Kan hannun kujerar da yake ta zauna gami da tallafo kan shi ta d`ora a saman k`irjin ta ,tare da cewa da shi,"I'm so sorry kaji my husband, in sha Allah everything will be ok,kar ka manta muna tare da Allah ba zai ta`ba bari wani abu mara dad`i ya same mu ba ",haka dai ta cigaba da fad`a masa dad`ad`an kalmomi har ya saki ranshi ba wai dan ya manta da abinda ya faru ba". "Na gama had`a abincin tun d`azu ,ka zo kafara watsa ruwa sai mu ci abincin"," Mu watsa ruwa dai bak`in ya ke I'm tied bazan iya wanka ni kad`ai ba". "A'a wallahi na fa yi wanka tun d`azu, kuma fa kalli har kwalliya nai maka ko cewa na yi kyau ba kai ba,kuma sai ace in sake wani wankan a'a gaskiya". Ta k`asan ido ya fara kallonta tare da cewa," Ai haba ai ni ban gani ba,kuma ma ai kwalliyar mai sanyi ki kai, Ni kuma kin san nafi son zazzafa,don haka dole a sake min wata sabuwa". Bakinta ta bud`e gami da fiddo da dara-daran idanunta waje ta tana mai cewa,"Allah wannan wayo ne nasan na yi kyau na, kuma kwalliyar ta zazzafa ce,kawai dai kawai",ta na maganar ta na ja da baya daga kusa da shi. Bai fi taku biyu lafiyayyu ya yi ba ya cimmata,tamkar `yar tsana haka ya rabata da k`asa ya nufi bathroom da ita,ba tare da ta yi zato ba ya sakar masu ruwan sanyi akan su,k`ara sosai ta saki tana mai ruk`unk`ume shi,tare da cewa ,"Me ya sa ka aikata haka,kafa san bana son ruwan sanyi",Tai Maganar ta na mai kai mashi duka a k`irjinsa. Zuwa lokacin tuni sun gama jik`ewa sharkaf,kayan su sun man-manne a jikin su sai da,ya raba jikinta da na shi kafin ya bata amsa da cewa,"Ni kuma kin ga ina son ruwan sanyi,kuma da ruwan sanyi ya bige ki sai kwalliyar ki ta zama zazzafa". Dubanta ta kai jikin ta ,matsananciyar kuyan ce ta kamata wanda har hakan sai da ya sa ta shige jikin shi tana mai `boye fuskarta a k`irjinsa. Hannunsa ya kai yana tattare mata gashin kanta da ya barbazu a saman fuskarta tare shafa gurbin tsagarta eleven eleven tsagar rumawa,"Da gaske na ke komi na ki birge ni ya ke,duk wani abu da za ki ko ki ka yi k`arasawa in so ki na ke,ina son ki ina son in k`are rayuwata da ke,ba zan so in rasa ki ba ko da na dak`ik`a ne domin hakan zai zame min babbar illah da kuma silar cutuwa a gare ni"...... Hannunta ta kai saman bakin sa ta rufe,tare da cewa," Ba abinda zai same ka domin na maka alk`awari ba zan ta`ba yin wata rayuwa in har ba da kai ba,zan rayu da kai a kowanne irin yanayi na dad`i ko akasin haka". Sai da ya rankwafo ya had`a kan shi da na ta kafin ya ce da ita,"Thanks, thanks a lot,Thanks yuo for being my wife ina farin ciki da samun ki a rayuwata kuma a matsayin matata". ₹₹₹₹₹₹ A k`agauce ya ke shiryawa yana yi yana na cewa,"Yau na makara sosai na yi late,kuma muna da manyan bak`i da zamu yi meeting da su ban san har Gari ya waye haka ba",ya kai zancen ya na mai maida hankalin sa akanta,matsawa kusa da ita yai ya zauna har ya zauna ba ta san ya zauna ba,sai da ya kai hannu ya cire tagumin da tayi da hannu bibbiyu,Wanda hakan ya sa ta firgita ganin shine ya sa ta saki ajiyar Zuciyar mai k`arfi "Lafiya me ya same ki,ban saba ganin ki a cikin irin wannan yanayin ba,ko dai kina son komawa makarantar ki ne ki gama tare da k`awayen ki?",. Da sauri ta girgiza ma shi kai tare da cewa ," A'a ni bani sha'awar komawa waccan makarantar,hasalima ta fita a raina,photo na na da naka ba inda ba su karad`e ba a cikin makarantar,kuma da labari mara dad`i don haka na hak`ura da ita bana da burin sa ke komawa cikinta". "Ko kin san cewa ba kowanne lokaci ka ke yarda ka bar abinda ka ke so don saboda maganganun wasu muta ne na daban akan ka ba, a lukutta da dama mutanen mu ba su fiye yayata abun alkairin mu ba,sai dai su yayata sharrinmu,kuma ma wai me muka aikata,shin son da muka nuna ma juna mu sa`bo ne ko- ko mun ta`ba aikata wani Zunubi ne?".... Muryarta na rawa ta dakatar da shi da cewa,"A'a aa ni ba haka na ke nufi ba,saboda ata dalilin sa har yau iyayena ke fushi da ni,don haka bana son shi,idan harma zan cigaba da karatun to sai dai in sake wani `bangaren in koma kamar health line haka". "An gama ranki ya dad`e daga yau ki fara kallon kan ki a matsayin malamar lafiya,mafarkin ki zai cika wanne `bangarrn ki ke so ki karanta?". "Ammmm.....Nursing ina son in zama Malamar jinya". "Daga yau ki fara counting d`in kan ki a cikin jerin Malaman jinyar da mu ke da su a cikin Garinnan, I promise za ki karanci Nursing za ki Kira kan ki da wannan sunan da izinin Allah". Cikin yanayin farin ciki ta rungume shi bakinta ya k`i rufuwa,sai faman bin shi da kyawawan Addu'o'i take,"Kar ki damu responsibility na ne naga na wadata ki da duk wani abu da ki ka buk`ata,tunda har na iya rabo ki da iyayen ki,bayan shi kuma da akwai abinda ki ke so". Rau-rau tai da idanun jin ya ambaci iyayenta,", Me kuma ya faru ya Habibaty?",ya tambayeta a k`agauce. " Ban san me zan yi masu su yafe min ba,ina son su ina son in rik`a zuwa inda su ke amma ka na ganin wancan time d`in da mu ka je Baba K`arami ya koroni ko cikin Gidan bai bari na shiga ba,na kasa iya jurewa ko mantawa da wannan rana". "Ki shirya mu tafi zan kai ki da kaina ni da kaina zan kai ki cikin Gidan ki ga duk wanda ki ke son gani", bata san sanda murmushi ya ku`bce ma ta ba alamun taji dad`in abinda ya ce. " A'a ka tafi wurin aikinka kawai ka makara tuntuni,indai ka bar ni sai in tafi ni kad`ai, idan ka dawo sai ka biya ka d`auko ni". "A'a ki dai bari in kai ki da kaina kamar hakan zai fi"," Kar ka damu yau in sha Allah ba abinda zai faru ka taya ni da addu'a kasan fa yau kana da meeting kuma mai muhimmanci ka ga bai kamata in tsaida ka ba"..... "Kema kina da muhimmanci mai tarin yawan gaske a gare ni,kin ga kenan bai kamata in bar ki kiyi tafiya irin wannan ke kad`ai ba". " Kar ka damu in sha Allah ba abinda zai faru da ni zan je in dawo lafiya, ka ga ni zan iya kai kaina can Gidan na mu har ma in dawo amma kuma can Companyn ba abinda zai tafi yanda ku ka tsara in har ba ka,ka ga kenan da buk`atar ka tafi can,kuma ka ga ni ban ma shirya ba balle har mu tafi,kayi tafiyar ka kawai da zaran na Isa Gidan zan Kira ka in sanar ma ka",da haka dai ta samu har ta shawo kan shi ya yarda tya tafi ya barta ita kuma ta shirya a tsana ke kafin ta tafi na su Gidan itama. Cikin shiga ta kamala ta nufi Gidan na su,tun Isar ta k`ofar Gidan fuskarta ta yalwata da mad`aukakin murmushi,a lokacin su Baba Malam suna majalisi Da karad`i a muryarta ta shiga cikin Gidan tana kiran sunayen duk wanda ya zo mata a baki,"Ummie Maryam, Umma Jamila, Umma Hafsat, ku fito ga ni na zo,ina Yarona Jaheed ya ke",Ba iya sunayen wad`anda ta ambata ba har da su Lami Matar Alaranma Sama'ila da ta zo,hatta da sauran matan `ya`yan Gidan sai da su ka fiffito,nan fa kowa ya fara murnar ganinta da yai ta dad`e anan tsakar Gida kafin Ummie Maryam ta ja ta su shiga ciki. "Yanzu ke Hibba idon ki kenan ace sai yanzu za ki waiwayo Gidannan tun tafiyar ku,kar ki so ki ga yanda Baba Asabe ke yada maganganu akan rashin zuwan ki". Rau-rau tai da idanu,hawaye na shirin zubo mata kafin ta ce,", Allah Ummien Jaheed ba laifin na ne ba,har k`ofar Gidannan na zo amma Baba K`arami ya kora ni,badan na so ba ina ji ina gani na hak`ura na koma badan na so ba", Waige-waige Ummie Maryam ta fara yi alamun rashin gaskiya kafin ta fara kwakkwafarta da cewa," To kar ki yarda ki sanar da Mama wannan labarin don ba zai mata dad`i ba kuma hankalin ta zai ta shi". Da to ta amsa mata gami da k`ok`arin mai da hawayen da suke son zubowa daga idanun ta. "Ki yi hak`uri kin ji,kar ki damu da wani abu da ya ke faruwa kin ji wata rana sai labari,ince dai kuna zaune lafiya da mijin na ki,kuma ya na kula da ke yanda ya kamata?". Sai da fuskar Hibba ta fad`ad`a kafin ta bata amsa da gyad`awa mata kai. " Yauwa na ji dad`in jin hakan yanzu maza ki je gurin Mama nasan tana can ta tsumayin ki". "To Ummie Maryam bari inje,amma ina Yarona ya ke ko yana makaranta ne ?". "Yayah yau bai je makaranta ba yana can d`akina kwance ba lafiya". " Ayya bari in je Inga Mama sai inzo in duba shi","To shikenan sai kin biyo". Da sassarfa ta idasa shiga cikin d`akin Mahaifiyarta,a tsaye a bakin window ta hango ta da alama jiranta ta ke kamar yanda Ummie Maryam ta ce. Ambaton sunan ta tai cikin yanayin kewa da kuma rashin ganin ta. "To me ye haka, daga zuwa kuma sai kuka,ko kin manta yanzu kin girma". " Mamana na yi kewanki,ban ta`ba d`aukar irin wannan dogon lokacin ba tare da ke ba,Na yi kewanki ki sosai". "To ba gashi yanzu kin ganni ba,don haka kukan ya Isa haka,ya mai Gidan na ki yana nan lafiya dai ko ?", Sai da Hibba ta duk`ar da kanta k`asa alamun ta ji kunyar tambayar da akai mata kafin ta ba ta amsa da cewa" Yana nan lafiya ya ce in gaishe ki anjima ma zai zo sai ya ku gaisa". Haka Mama Hadiza ta cigaba da yi mata `yan tambayoyin,Wanda za su sa ta fahimci wanne irin zama su ke gudanarwa ita da Mijin na ta,sun d`auki lokaci mai tsawo a tare kafin Hibban ta ce zata je ta gano jikin Jaheed da aka ce ma ta ba shi da lafiya. Sosai hankalin Hibba ya tashi ganin yanda jikin Jaheed yai tsamari,kamar tai ma shi kuka,rungume shi tai sosai a jikinta sai faman lallashin da ban baki ta ke. Shigowar Baba K`arami ne ya sa ta d`an dakata,cikin ladabi da kwantar da murya ta fara gaishe da shi,amma ina ko da wasa bai amsa ba,tun kallon farko da tai ma shi ta sha jinin jikin ta Zuciyarta ta fara kai kawo da tunanin me zai biyo baya. "Ke waye ya baki izinin sake taka k`afar ki a cikin Gidannan ba na hane ki game da hakan ba?". "Baba K`arami kayi hak`uri wallahi Allah ba zan iya rayuwa ba tare da ku ba,na tuba dan Allah ka yafe ni".... "Yi min shiru mara kunyar banza mara kunyar wofi,ki sani kin riga da Kin `bata rawar ki da tsalle a wurina tun ba yanzu ba,abu na k`arshe da zan umarce ki da shi kija `yan k`afafuwanki ki bar Gidannan tun kafin dare yai miki". Har k`asa ta duk`a tana mai had`e hannayenta wuri guda ta na ba shi hak`uri tare da cewa,"Na rantsa maka duk abinda ka ji muta ne na fad`a akan mu sharri ne babu wani abu na `batanci ko na rashin dacewa da ya ta`ba shiga tsakanin mu,sharri ne kawai". " Ba na son jin komi daga gare ki kawai ki tashi ki ba ni wuri",shine abinda ya ce da ita yana mai nuna mata hanyar fita daga na shi `bangaren,ko motsin kirki kasawa Hibba tai,wai yau Yayanta da ya ji da ita acikin kaf ahalin Gidan su yau shine ke kyararta shike korarta ya na fad`in baya san ganin ta,wanne irin Zunubi ne ita kuwa ta aikata da har ta can-canci irin wannan hakuncin. Ganin da gaske ba zata fita ba kamar yanda ya ya ke so yasa da kan shi ya fizge Jaheed dake rungume a jikinta ya ja hannunta a tsiyace bai sake ta ba har sai da ya kai ta tsakar Gida sannan ya jefar da ita har yunk`urin fad`uwa k`asa tai. Tun kafin ya ce komi Baba Asabe dashigiwar ta Gidan kenan ta fara sallallami gami da cewa,"A aha wa idona je gani kamar Hibba, sai yau mu ke ganin ki `yar dad`i Miji ?",Salatin da ta saki ne ya janyo hankalin sauran mutanen Gidan "Ban damu da ki cigabada da zuwa cikin Gidannan ba ko ki daina ba amma da ga rana irin ta yau na haramta maki shigowa cikin nawa sashen,Na yafe ki bani ba ke,ki fita harka ta kiyi taki harka ki aikata duk abinda ki ka so,Na cire hannuna a cikin dukkanin lamuran ki"...... " To sai me idan ka cire hannunka a cikin lamarin ta shin zata mutu ne ko wani abun na daban da babu shi a cikin littafin k`addarar zai same ta?".Cewar Mama Hadiza da fitowar ta kenan "Ki gafarce ni Mama amma wallahi Hibba ta kunyata ni,gabad`aya ta fita a raina taje can ta yi rayuwar da taza`ba ma kanta amma ba shakka wata rana za ta fahimci ta aikata kuskure,a lokacin da ba lailai ne ta iya gyara shi ba"... "Kar ka kuskura ka yima `ya ta baki ,domin ba kai ne ka haifar min ita ba,idan kuma ka sake sai na wanka maka Mari a fuskar ka", Ba shi K`aramin da aka ce za a mara ba ilahirin mutanen Gidan da suke tsaye a wurin sai da suka sha jinin jikin su Cikin sauri,in'ina had`i da sheshshekar kuka Hibba ta shiga tsakanin su ta na mai cewa,"A'a Mama haka ba za ta faru ba,in dai akai na ne bazan yarda ki d`ora hannunki a jikinsa da sunan hukunci ba,zan tafi zan daina zuwa har sai sanda shi da kan shi ya gaiyato ni cikin Gidannan,zan jure zafi,rad`ad`i da kuma kewarku da zan yi har zuwa sanda zai yafe min laifin da yake zargin na aikata,ko kuma ranar da gaskiya za tai halin ta". " A'a Hibba ba inda za ki ,Kema `yace haifaffiya a cikin Gidannan don haka ba inda za ki". "A'a Mama ko da ni ke `ya a cikin Gidannan ban kasance mai yi maku biyayya ba, ko mai sanya ku cikin farin ciki ba,danvhaka tafiya zan yi",ta na kaiwa nan ta juya ta nufi hanyar fita daga cikin Gidan ba tare da ta bi ta kan haka ko wayarta da ke d`akin Mama Hadiza ba. Tana fita kuwa tai sa'a ta ci karo da mai a dai-daita ta shiga,sai da su kai nisa sannan ta tuna da ta baro waya da Jakarta a can,mai a dai-daita d`in ta rok`o ya bata aron wata ta Kira Abbakar. Yana jin muryarta hankalin shi ya tashi , fitowar shi kenan daga meeting d`in nan take yai handling d`in komi a wurin assistant managern sa yayi Gida hankali a tashe. *JADEEDAH* (It's a story of two love birds who are so different from each other ) STORY & WRITTEN BY : (*Cwt~Sumiey*) Marubuciyar littafin MENE NE ABIN YI ? KARAGAR MULKI And now.....*JADEEDAH* https://chat.whatsapp.com/CWkZfMqvD4H0mtd7WW6Xbz https://whatsapp.com/channel/0029VapqU8C002T5Bz8RSQ0a BOOK 1 PAGE 6 ❤ FREE PAGE "Na rok`e ki ki dakatar da wannan kukan,yana tada min hankali,ba zan iya jure ganin ki a cikin irin wannan yanayin ba,kisanar da ni me ya faru?". Cikin sheshshekar kukan da ya ci k`arfinta tace da shi," BBB...bbbb...babu komi babu abinda ya faru kawai na dawo Gida ne". Tsuru yai ma ta da idanu ya na kallonta,fuskarnan ta ta har wani yellow-yellow ta ke saboda kukan da taci. "Ban damu da dole sai kin fad`a min me yake faruwa ba,amma dan Allah ki dakatar da kukannan,Zuciyata ba za ta iya d`auka ba,ina jin zafin da zuciyata ta ke min har a saman gangar jikina", ya kai zance yana mai share mata hawayen da ke zubowa daga cikin idanunta. Kafin ya d`ora da cewa "Ban da damu da duk wani abu da ka iya biyo bayan tarayya ta da ke ba,abu guda,kawai na ke so daga gare ki", tsam ta mai da hankalin ta gare shi gami son jin me zai buk`ata a wurin ta. " Ki yarda da ni, ki bani amanar rayuwar ki,zan zame mi ki bango majingina kuma kafad`ar da zaki d`ora kan ki akan ta,zan baki farin ciki, in maye mi ki gurbin abinda ki ka rasa,burina da kuma fatana ki amince da ni,zan kasance da ke a kowanne irin yanayi ". " Na dad`e da amincewa da kai kuma na yarda da Soyayyar ka a gare ni gaskiya ce,ko da wasa bana da niyar barinka,Na shirya fuskantar fiye da abinda ma fuskanta a yau indai akan ka ne". ''Tu da har haka ne ki daina min asarar hawayennan na ki,domin ni a gare ni suna da matuk`ar tsada,sun fi lu'u-lu'u,Zinari ko tagulla". Yanayin yanda ya kai k`arshen maganar tashi ne yasa ta fara sakin fuskarta har da d`an murmushinta. "Yauwa kin ga yanzu tunda kin saki fuskar ki sai a zo ai girki bari muga yau me za a cika yaji ko gishiri ko kuma dai ruwa za a cika ?". "No...no...wallahi ka bar shi indai haka ne,gara in girka da kaina tunda dama aiki na ne"," A'a ni zan yi ki zauna ki huta abin ki". Haka dai suka dinga jayayya har k`arshe dai su kai girkin a tare ba tare da ya barta ta samu damar da zata tuna abinda ya faru da ita a Gidan su ba. ₹₹₹₹₹₹₹ Cikin natsuwa da kamala Baba Malam ya fito daga motar da ta kawo shi har Gida bayan sun gama taron su na mayan malamai,a koda yaushe cikin shiga ta kamala yake ,hannusa rik`e da casbaha,duk da kasancewar ya manyanta tsufa ya bayyana a gare shi amma ko kusa ba dagazawa ko `yankwanewar tsufa a tare da shi,tun da ya tun karo Gidan na shi ya ji hankalin shi bai kwanta ba har ya sa k`afarsa a cikin farfajiyar Gidan, ganin mutanen Gidan tsaye cirko-cirko ya sa ya k`arasa wajen cikin hanzari tare da tambayar su,"Lafiya me yake faruwa anan?". Cikin sarewa da kuma yanayin da ke bayyanar da d`acin Zuciyar da mai magana yake a ciki Mama Hadiza ta ce,"Gashi nan tambayar shi sai ya fad`a ma ka me ya ke faruwa,ya gaya maka ya kasa d`aukar k`addara da jarabawar da Allah ya saukar akan Hibba, har sai da ya kai ga ya fito gaba da gaba yana fad`ar munanen kalamai da son aibata ta a gaban mutane". "Subbahanallahi K`arami me ya ke damun ka,ina hankali,ilimin da tunanin ka ya tafi,mai yasa kake aikata aiki irin na jahilai ?". "Baba Malam ka gafar ce ni,ba wai ina nuna damuwata akan Auren da Hibba ta yi bane ba,a'a can jawar d`abi'un ta sune abinda ya kasa goguwa a cikin rai da zuciyata". Baba Asabe ce ta d`an matso gaba gami da cewa" Hehehe nanaye yau `yar gwal kuma `yar so ta aikata kuskure,kuskuren da ke neman kawo hatsaniyar da ba a ta`ba yi a cikin Gidannan ba",ta d`an dakata ta na mai fuskanta inda Malam K`arami ya ke da Cewar,"Ni fa ban ga laifin ka ba Yarinyar da idanun ta suka bud`e ai kamata yai a sallamawa duniya ita ta je can taci gashin kanta ",..... "Ki dàkata min na ce Asabe,ki bar ni dan Allah in yanke hukunci a cikin Gidana".Malam Babba ya faɗa a zafafe,duk da ta ji maganar tamkar saukar aradu hakan bai hanata ta turo kallabinta kan goshi ba,sannan ta juya ta na mai `yan maganganu k`asa-k`asa,ba wanda ya sake bi ta kanta. " Ka bani mamaki K`arami da har ka kasa iya jure abinda ka ke ji har sai da ka bayayyanar da shi a ciki kowa ya fahimta,tun bayan yayenta mahaifiyarta ta bar maka ita sakamakon ganin kai ne kad`ai a cikin `ya`yanta Allah bai ba haihuwa da wuri ba, Hibba fa kaine ka raine ta kuma ka tarbiyantar da ita,duk wani abu da take yi koyarwarka ce,ba ta shak`u da uwa Mahaifiyarta ba kamar yanda ta shak`u da kai,ka bani kunya da mamaki tunda yau har sai da ka kai ga k`ureta har ta na k`ok`arin kai hannunta jikin ka,To bari kaji bayan yarda na d`aura Auren Hibba ba sai da nayi cikakakken bincike akanta da ma duk wani abu da ake zarginta,har cikin makarantar ta su sai da na je,kai ba ma iya makarantar su ba har ma'aikatar da ta ke koyan aikin sai da na je,Babu abinda na ji sai yabo da shi albarka game da ita,to ka sani Hibba bata can ja daga Hibban da ka raina ba,har yau har gobe bata aikata wani abu na tir ko ashsha ba,hasalima ni alfari na k`arayi da kasancewar Hibba cikin tsatsona,ya rage ruwanka ka nemi gafarta ko kuma ka cigaba da zarginta,ka sani kaima kana da wasu `ya`ya a haka zaka tarbiyantar da su Zuciyar ka cike da zargi da kuma rashin yarda ?".Baba Malam na kaiwa nan a zancen shi ya bar wurin ba tare da ya bi takan kowa ba,itama Mama Hadiza juyawa tai ta bar gun fuskarta d`auke da farin ciki wanke `yarta da Baba Malama yai a gaban mutane. Haka mutanen wurin da suka taru suka fara barin wurin da d`aya da d`aya,Baba K`arami kuwa jikin sa a sanyaye ya nufi na shi sashen. Hannu bibbiyu ya tallafe kan shi ya rasa wanne irin tunanin ma ya kamata yayi kuma wacce mafita ya kamata ya samu yai amfanin da ita. "Ka gani ko Abban Jaheed so nawa ina baka hak`uri akan ka tsaya kai bincike akan wannan lamarin amma ka k`i yanzu ka ga me Gari ya waya ko?". "Ke dai bari Ummien Jaheed ban san me ya shiga kaina ba,a yanzu na yi danasani har ban san ta ina ya kamata in fara gyaran kuskuren da na tafka ba". "Ka je ka same ta ka lallashe ta ka bata hak`uri,domin ni a gani na kamar hakan zai fi". " Shikenan zan je domin ba lalle ne yau in iya rufe idanuna ba tare da na sata a ciki ba". "Sai dai ko ka kirata ta zo ko kuma ka je Gidan na ta",Sai da yai shiru Na wani d`an lokaci kafin ya ce," Gara dai in je Gidan na ta kamar za ta fi jin dad`in haka kuma tai saurin yafe min mummunan zargin da na yi mata". "Uhmmmmm haka ne kuma sai ka tambaya a raka ka". " A'a ba sai an raka ni ba,Na San Gidan",sai da Ummie Maryam ta fiddo idanunta waje kafin ta tambaye shi da cewa,"Ka san Gidan a taya ?".kau da kan shi gefe yai ba tare da ya bata amsa ba murmushi ta saki a cikin ranta ta na mai cewa,"Ashe dai duk fushin da aka yi da ita Soyayyar ta na nan a cikin ran ka". Ana fitowa Sallahr magariba Malam K`arami ya nufi Gidan Hibba a bakin gate d`in shiga cikin Gidan Abbakar ya iske shi da matuk`ar hanzari ya matsa kusa da shi,har da duk`awar shi kafin ya bashi hannu su gaisa. "Na zo ne ina son ganin Hibba", Baba K`arami ya ce " Haba Malam ai da kasani Kira na kai sai in kawo maka ita har Gida komin dare ba sai ka wahalar da kan ka ka zo ba".Abbakar ya fad`a cikin girmamawa "Kar ka damu babu wani abu kuma na San in na zo da kaina za ta fi jin dad`i shiyasa ma na zo",sosai Maganar ta shigi Abbakar tunda a iya sanin shi Baba K`arami na d`aya daga cikin wad`anda ba sa son Auren sa da Hibba,bai san wanne irin sauyi ne aka samu da sauri daga gare shi ba. " To ka shigo ciki mana kamar zai fi","A'a bar nivanan kawai kai mata magana ta fito sai mu gaisa in koma","A ba ayi haka ba dan Allah ka shigo",da kyar Abbakar ya samu ya yarda zai shiga amma da fir ya rufe idanunsa akan ba zai shiga ba,haka ya jagoranci shi har cikin Parlourn su ,lokacin kuma ita Hibban ta na k`ok`arin tashi daga kan prayer mat d`in da ta idar da Sallah. Duk da razanin da ta shiga na gani sa hakan bai hana ta nufi inda ya ke ba,bakin ta sai k`ok`arin son cewa wani abu take amma ta kasa. " Allah Sarki k`anwata mamaki ki ke na gani na a cikin Gidan ki ko,gami da fargabar abinda ya kawo ni ko ?,to ki kwantar da hankalin ki na zo ne in baki hak`uri akan dukkanin abinda ya faru ,Na gane gaskiyar lamarin ki yafe ni,ban kasance" ...... Sai da ta duk`a har k`asa kafin ta e "A'a dan Allah ka bari ban can-canci haka daga gare ka ba,ni fa k`anwar ce kuma `ya a gare ka bai kamata ka rik`a bani hak`uri ba". " Wa ya gaya maki haka Hibba, ai a addinin mu duk girmanka in har kai ma wani laifi kuma ka gane kuskuren ka,to ka bashi hak`uri ka nemi ya fiyar shi komi k`ank`antar shi ko da kuwa kai ka haife shi ko wani abu makamancin haka,babu girman kai a addinin mu,haramun ne aikata shi dan haka ina rok`ob ki da ki yafe min ki manta komi da ya faru kar ki rik`a shi a cikin ran ki". "Wallahi Allah na yafe maka duniya da lahira kuma ni dama ban rik`e da komi ba kullum addu'a ta Allah yasa ka fahimce ni kar mu cigabada da rayuwa a haka don ba zan iya jurewa ba". " Allah kam ya amsa addu'ar ki ashe ni ne a duhu Baba Malam ya riga da ya dad`e da fahimtar duk sharri akai miku,yanzu haka kowa na Gidan ya san baki da laifin komi ba ki aikata abinda ake zargin ki da shi ba". Sosai fuskokin su suka yalwata da jin wannan labarin,"To ya Mama itama tana farin ciki ?",ta jefo mishi da tambayar. "Eh itama tana farin ciki,ji taje kamar gobe ma ki dawo"," Ai ko in dai haka ne Goben ma zan zo".... "A'a a'a kar ki zo ki bari sai wani lokacin amma zan turo maki da Yaron ki yai miki yini tunda gobe weekend". " To shikenan yanda ka ce,ko a hakan ma zan yi farin ciki,Allah ya kai mu goben ". Duk abinda suke Abbakar na kallon su gwanin burgewa har fata yake ina ma da shi ne da nashi dangi ne a cikin irin wannan yanayin na farin ciki. " Yayah bari in kawo maka wani abu kaci kafin ka tafi". "A'a kar ki wahalar da kan ki domin ba abinda zan ci,tafiya zan yi". " A'a Malam bai kamata ka zo ka tafi ba tare da kaci wani abu a cikin Gidannan ba ko Yaya ya ke". "Kwayi kwa gama ba abinda zan ci,tun da na gama abinda na zo yi kunga ma tafiyata", ya fita abinshi ba tare da sun yi nasarar dakatar da shi ba,ita Hibba san da zata fito daga kitchen har ya riga da ya fita,sai tsaye tai hannunta rik`e da himilin kayan abincin da ta jero ma shi akan tire. " Ya akai ka bar shi ya tafi dan Allah? ",ta tambaye shi cikin shagwa`ba. " To ya zanyi Babe,ya ce a'a kuma kin ga babban mutum ne bazan iya jayayya da shi ba". "To shikenan amma ban ji dad`i ba na so ace yaci wani abu a zuwan shi na farko Gidana". Matsowa kusa da ita yai ya na mai amsar kayaan hannunta ya aje gefasu sannan ya d`ora da cewa," To mene ne na damuwa,ya riga da ya dawo gare ki gabad`aya fa,a koda yaushe fa yanzu za ki iya zuwa ki gan shi,kuma kina da damar da za ki girka duk abinda ki ke so anan cikin Gidan na ki ki kai ma sa har Gida kuma ya ci to me zai dame ki ?". Ba k`aramin jin dad`in lafuzzan da suka fito daga bakin shi tai ba,har sai da fuskar ta ta yalwata da murmushi har kasa rufe bakinta tai sai cewa tai da shi,"Kuma fa haka ne ka yi gaskiya,yanzu zuwa nan da yaushe ka ke ganin ya kamata in sake kai masu ziyara ?". "Yanzu za ki shirya muta fi,k`arshen murna da zumud`i". Turo masa baki tai gami da shagwa`be mi shi fuska,shima yanayin yanda tai da fuska haka yai gami da tsare ta da idanu. Ganin haka ya sa tai rau-rau da idanunta za tai mashi kuka da sauri ya matso kusa da ita yana mai kai hannunsa saman kunne shi ya rik`e ta re da fara bata hak`uri da cewa,"Na rok`e ki kar ki `bata wannan farin cikin dake kwance asaman fuskar ki ,kin ga a yanzu muna da goyan bayan ahali gabad`aya akan maganar Auren mu". " Ni ma tuna hakan nasa ni injini a cikin wani mad`aukakin farincikin in kuma kara sakankancewa da iko,girma d`aukaka da buwaya na Ubangiji na Allah,da ya aikata abinda ya so a sanda ya so akan lamarin mu ". "Haka ne My wife yana da iko fiye da haka ma dan haka yanzu mu gode mi shi akan baiwa da ni'imar da yai mana". " To Habibina yanda ka ce ai haka za ai fad`a taka cikawa tawa",ta kai k`arshe zancen murmushi kwance a saman fuskarta. *JADEEDAH* (It's a story of two love birds who are so different from each other ) STORY & WRITTEN BY : (*Cwt~Sumiey*) Marubuciyar littafin MENE NE ABIN YI ? KARAGAR MULKI And now.....*JADEEDAH* https://chat.whatsapp.com/CWkZfMqvD4H0mtd7WW6Xbz https://whatsapp.com/channel/0029VapqU8C002T5Bz8RSQ0a BOOK 1 PAGE 7 ❤ FREE PAGE "Why are you disturbing me Cecelia, in this early morning, kin kira kin kira na ki d`agawa ba sai ki kyale ni ba haba dan Allah, yau fa Sunday ce,yauce ranar guda kawai da make samun hutu"..... "Deborah ce ba Ceceliar da ka raina ba", Grandma ta katse shi cikin d`aga murya. Cikin in'ina da kuma rud`ewar da yai sakamakon jin muryarta da yayi,"Grandma", ya ambaci sunanta tare da d`orawa da cewa,"Kiyi hak`uri ban san ke bace ba shiyasa ban d`aga da wuri ba". " Oh kayi tunanin marainiyar wayon taka ce ko, to ba ita ba ce nice,Anya Daniel, ba akwai wani abu da kake `boyemin ba wannan sauyin naka ya fara bani tsoro,let me ask you kana ma zuwa Church kuwa?". Wani zazzafan gumi ne ya fara keto mi shi tare da sanyi a lokaci guda,har sai da Grandma ta sake tambayarsa tare da cewa,"Wai ko ba ka jin abinda nake cewa ne?". Shiru Abubakar yai hankalin shi yai matuk`ar tashi hakan ya sa ya kasa iya sarrafa harshen shi. "Na shiga uku ni Deborah, me nake shirin ji haka daga gare ka,Yesu Almasihu ka kawo min d`auki,yanzu Daniel so kake kace min ka daina zuwa Church wanne rud`un duniya ne ya same ka,ko so kake ka ta`bewa ta samu wurin zama a cikin rayuwar ka,me kake so ka zama ?", ta tambaye shi cikin tsananin tashin hankali. "Amm mmm...uhmmm.....Grandma ki yi hak`uri ki saurare ni,you know ranar Sunday ita kad`aice ranar da nake samun hutu,shiyasa nake yawan tashi a makare", muryar shi ta raunana sakamakon k`aryar da zai mata ya ciga da cewa," Amm...ammm...amma fa ina zuwa time to time ". " k`aryar ka ke Daniel, you are a liar ba ka zuwa Church muryarka ta tona maka asiri,Na shiga uku na ni Deborah, Anya ba sauya min kai a kai ba,haka fa nai ta fama da kai ka zo muyi Merry Christmas tare da kai k`iri-k`iri ka k`i zuwa,har happy new year mu kad`ai muka gudanar da shagulgulan bikinta,,wai meke damunka mene ne ya sa kasauya,me kake son kazama da har ya sauya d`abi'un ka har haka,Daniel ka gayamin asalin gaskiyar da ke faruwa anan ?",ta kai k`arshen Maganar da sigar tambaya cikin nuna tashin hankali da kuma fushin da ta ke a ciki. Sai da Abubakar yai da gaske kafin gwarin gwuiwa gami da dakiyar Zuciya ya ce da ita,"I swear ni ba abinda ya canza ni,inayin bauta iyakar iyawata ina zuwa wurin bauta gami da tsarkake ko neman kariyar kaina daga dukkanin wani abun k`i ba lalle sai ranar Sunday ba duk ranar da na samu sassaucin aiki ina kai ziyara zuwa Church ". " Hah Daniel ban yarda da kai ba I'm not believing you,you are a big liar,ka kawo min wata hujja guda ɗaya da za ta iya sawa in amince da kai ". "Grandma i swear ina zuwa Church, mai zai sa in bar asalina,in bar koyarwa da tarbiyar da ki ka bani ba". " To in har haka ne ka tashi a yanzu ka nufi Church d`in da kake attainding ka had`a ni da wani Pastor ko Reberal to fa sannana ne zan gasgata abinda kake cewa". "Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un",shine abinda Abubakar ke ta yawan mai-maitawa,yau ya tabbata sharri ko illah da k`aryar ke dashi,a yau ya k`ara tsanar k`aryar da yake mata tun bayyan musulumtar shi,bai san dalilin da yasa yake tsoro da shakar gaya masu ya musulumta ba,ko dan tsoran kar yarasa su amatsayin su na dangi kuma ahalin da yake da da su akaf fad`in rayuwar sa. Idanuwansa da suka rine sukai jajajur ya sauke akan Hibba da tun farkawar ta a barci taga bashi a cikin bedroom d`in ta biyo sa Parlourn, yanayin da ya gani akan fuskarta yasa shi yai saurin d`auke idanunsa akanta. Ammon muryar Grandma da ya sake karad`e masa kunnensa ya fargar da shi gami da dawowa hankalin shi akanta," I repeat it ka tashi ka je ka had`a ni da Pastor d`in Church d`in da ka ke zuwa ko wani wanda zai gamsar da ni in yarda". "Shikenan Grandma......shikenan zan je yanzu amma ki sani duk abinda ya faru da ni it's your fault, because i'm felling sick, na dad`e kwance bana da lafiya,I spend almost two weeks bana da lafiya,sai jiya aka sallame ni, na dawo Gida". "Jesus Christ amma kuma Daniel shine baka gaya min ba,me yasa kake haka,mai yasa zurfin cikinka yayi yawa,ka ga fad`a min mene ne matakin lafiyar taka a yanzu,ina fatan dai kana samun sauk`i,ka Na dai taking medicine naka akan lokaci ko ?".ta fad`a cikin rud`u " Ina samun lafiya in sha Allah tomorrow zan yi resuming a bakin aikina".... "In sha Allah kuma Daniel, Na ji kamar haka ka ce ko dai kunne na ne ke jiye min ba dai-dai ba ?". A diririce ya ce da ita"I'm sorry ba haka na ke nufi ba,I mean by the grace of God". ."A'a Daniel there are something wrong don haka,....hello.... hello".....ta kasa k`arasawa sakamakon mutuwa da wayarta ta yi a dalilin rashin charge. Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un Abbakar ya fad`a gami da kai hannunsa saman kan shi ya rik`e alamun alamun jin zafi ko ciwon da yake ji,cikin sauri ya sake bin layin nata amma kuma yaji wayar a kashe. " Ya Salam Allah ka sa ba wani abun sabo Grandma ta ke shirin aikatawa ba da har ya sa ta kashe wayar gabad`aya",shine abinda ya fara fad`a bayan gama kirannata. "Me ye zai sa ba zaka fad`a ma su ba,ka sanar ma su da Cewar ka Musulumta a bar wannan `boye- `boyen da kuma shiga cikin irin wannan tashin hankalin".Cewar Hibba bayan ta k`araso kusa da shi game da mik`a mi shi Glass Cup na ruwa mai sanyi. Bayan ya sha ruwan ne ya bata amsa da cewa," Ina jin tsoro Hibba, ina jin tsoran abinda zai biyo baya, idan har suka san gaskiya zan iya rasa su su duka ban san dalilin da yasa na ke jin bugun Zuciya a duk lokacin da nai tunanin ko yunk`urin aikata hakan ba,Cecelia k`aramar Yarinya ce,ita kuma Grandma ta tsufa ga shi ba wata isasshiyar lafiya ce da ita ba,ina jin tsoran halin da za su shiga idan suka samu wannan labarin". "Abu mafi a'ala ka sanar da su sai ka fi samun kwanciyar hankali fiye da ka cigabada da `boye wannan lamarin mai girma a cikin Zuciyarka,ka sani kana tare da Allah, ka Sani dogaro da shi kad`ai ya Isar ma akan komi". " Kar ki damu in sha Allah zan yi k`ok`arin aikata hakan,amma yanzu ya jikin naki,ko dai zamu je hospital ne a sake duba jikin ki da na Babyn gudun faruwar wata matsalar ?". "A'a kar ka damu na samu lafiya,Doctorn da ya duba ni jiya ma ya isa I'm feeling better now". "Anya kuwa na yarda,karda fa unborn d`ina ya samu matsala ",ya kai zancen yana mai d`ora hannunsa a saman cikinta d`an kimanin watannin biyar. Yalwataccen murmushi ta saki gami da cewa," Au ta Unborn d`inka kawai ka ke bayan kuma jiya shine ya hana mu samun wadataccen barci ". "Shikenan tunda na ga abun naka akwai selfish a ciki,tashi mu je in had`a maka ruwan wanka kafin ka fito na gama had`a mana breakfast tunda Garin ya riga da ya waye"," okay to mu je ". Acan `bangaren Grandma hankalin ta a tashe ta kai dubanta kan Cecelia da ke zaune ,ta ca`ba adonta da k`ananan kaya as usual, ta jawo attached d`inta ta d`ora asaman kanta . "Cecelia akwai matsala there is a problem, something happened","Matsala kuma Grandma,which kind of problem, shin ko wani abu ya samu Brox Daniel d`in ne ban sani ba ?". "Ban sani ba Ceceliar, Something wrong ya faru,gabad`aya Daniel ya janca na rasa gane kan shi ko ku ma a abinda ya ke cikin Zuciyarsa".ta kai zancen muryarta na raunana. Kusa da ita Cecelia ta matsa gami da jawota jikinta ta fara lallashin ta da cewa,", It's okay mana,ki bar tashin hankalin ki haka,kin ga ba wata isasshiyar lafiya ce da ke ba kar ciwon ki ya motsa, in Jesus name komi zai dai-daita kin ji". " Ameen Cecelia, ta shi mu je Church d`in nan domin so nake in sa ayimin dogon Addu'o'i akan Daniel lamarin sa ya fara bani tsoro,amma ina mai tabbata maki in har bikin Easter ya zo Daniel bai shigo Garinnan ba ni da kaina zan shirya in je har can Kanon Inga halin da yake a ciki,domin ba na tare da natsuwa ko kwanciyar hankali a game da shi". "Hakan ma yayi dai-dai, da zaran anfara yi mashi addu'a komi zai dawo Normal. Tunda ga wannan lokacin Grandma ba ta sake zama ba kullum cikin yawaita bauta da yin sadaka take akan Jesus Christ ya sa hankalin Daniel ya dawo gare su tayi addu'ar da kanta sannan tasa Pastor ko Reberal yayi,Cecelia ma na iyakar iyawarta. Yau Sunday Cecelia ce zaune a k`ark`ashin wata bishi sun fito cin abinci,ta rafka tagumi da duka hannayenta,,k`arasowar Gloria k`awarta ta sa hannunta ta cire mata tagumin kafin ta fara yi mata fad`a da cewa " Haba Cecelia me yake damun ki,what happen,ko kina son ki cutar da kan ki ne ta ya tun kina `yar Yarinyar za ki rik`a jefa kan ki cikin irin wannan dogon tunanin,kin San how long nake tsaye anan ina maki magana amma ko motsin kirki ba ki ba ?". Sai da Cecelia ta kamo hannunta ta zaunar da ita kusa da ita kafin ta fara ce da ita,"Ki yi hak`uri Besty ina cikin damuwane lamarin Brox Daniel kullum k`ara worth yake,kullum K`ara yin nisa daga gare mu yake,yanda kika san Wanda akai masa asiri haka ya koma,ga Maganar Aurena da Samuel sai matsowa take yanzu haka ya kusa six months bai zo inda muke ba". A firgice Gloria ta mik`e tsaye kafin ta ce,"what kina nufin Brox Daniel Wanda na sani ko kuma wani daban ki ke nufi". "My friend I'm sorry, da `boye miki wannan lamarin da na yi,Na san halin ki ne za ki tashi hankalinmu, saboda tsananin son da ki ke mashi,Na bari komi ya dai-daita sai in sanar da ke".... " It can not be possible, ba zai yiwu ba, I will find him,zan nemo shi a duk inda yake,kawai ki bani address nasa zan je in ga halin da yake a ciki". "Kin gani ko dama abinda na guda kenan shiyasa tun da faru ban sanar da ke abinda ke faruwa ba,but please ina so ki kwantar da hankalin ki domin da akwai shirin da muke shiryawa ni da Grandma,by the grace of God komi zai dawo Normal". " No no Cecelia bazan iya hak`uri ba kawai ki bani address d`in in je in gani halin da yake a ciki"..... K`arasowar Grandma cikin hanzari da kuma fushi shine ya dakatar da Gloria game da san amsar address d`in Daniel a gurin Cecelia da ta ke, hannun Cecelia kawai Grandma ta fara ja tana mai bin hanyar da zata kai su Gida, a firgice Cecelia ke binta sai faman tambayarta me ke faruwa take amma ta kasa sanar mata har sai da su ka isa Gida. "Wai Grandma me yake faruwa haka naga duk kin tashi hankalin ki, nima kuma kin tashi nawa?". Sai da ta fitar da isaka daga bakinta kafin ta sanar da ita abinda ke faruwa da cewa," Yau Pastor ya sanar da ni wani abu game da Daniel wanda ya tashi hankalina,don haka yau ba zan iya rintsawa ba har sai na sa Daniel a cikin idanuna,ba zan runtsaba har sai nayi tozali da shi in my own eyes ". " A'a Grandma ma haka ma ba zai yiwu ba, kin san ko k`arfe nawa kuwa yanzu,zamu yi tafiya dare fa kenan? ". " Yo meye matsalan a cikin ba dai zamu ruski Garin da ya ke a ciki ba komi dare,mu tafi kawai". "A'a ba za ai haka ba gaskiya kin manta k`asarnan yanzu bata da tsaro,taya zamu jajibi tafiya cikin dare alhakin ko inda zamu ba mu sani ba kuma ba mu ta`ba zuwa ba,ga ra dai mu bari sai zuwa gobe early in the morning sai mu tafi". " Ina ni ban aminta da wannan tsarin na ki ba a yau zamu tafi ba sai gobe ba","Haba Grandma taya idon ki zai rufe ga gaskiya ina fad`a maki amma kin k`i amincewa,taya garin gyaran wata `barnar zamu jefa kan mu cikin wani halin na had`ari,Na roƙe ki da suansn Yesu mai cetonmu ki bar tafiyatnan sai gobe,in har ba so ki ke wani abun kuma na daban ya same mu ba",da k`yar Cecelia ta samu tai convincing d`in Grandma ta bar tafiyar sai da safe amma ba ta barta ta huta ba har sai da ta had`a masu duk wani abu da ta san zasu buk`ata kafin ya kyaleta,Ai ko Gari na wayewa ko breakfast bata,bar su sunyi ba su ka d`auki hanya sar Garin Kano don sugano me ya ke faruwa da Daniel d`in su. *JADEEDAH* (It's a story of two love birds who are so different from each other ) STORY & WRITTEN BY : (*Cwt~Sumiey*) Marubuciyar littafin MENE NE ABIN YI ? KARAGAR MULKI And now.....*JADEEDAH* https://chat.whatsapp.com/CWkZfMqvD4H0mtd7WW6Xbz https://whatsapp.com/channel/0029VapqU8C002T5Bz8RSQ0a BOOK 1 PAGE 8 ❤ FREE PAGE "To fa wai wake ta faman kiran wannan wayar ne haka ?,in ka kira d`aya biyu ba a d`aga ba sai ka hak`ura alamun mai wayar ba ya kusa ne ko kuma yana wani abun mai muhimmanci da ya hana shi d`aga kiran", Cewar Hibba wacce sallame Sallahr Isha'in take nan tun tana Sallah ake faman kiran wayar Abubakar da ya barta a charge ya tafi masalaci domin gabatar da tashi Sallahr. Har ta mik`e za ta je taga waye yake ta faman kiran wayar,sai wayar ta katse,sai da Hibba ta ja tsaki kafin ta koma ta zauna. "Grandma ya k`i d`aga kiran ko dai yasan muna cikin Garinnan ne shiyasa ya k`i d`aga kiran wayar ? ". " In ko haka ne da Daniel ya bani kunya,da ya aikata abinda ban ta`ba expecting daga gare shi ba". "To yanzu ya zamu yi Grandma, ko dai komawa Gida zamu yi ?". " God for bid, Cecelia ba inda za ni har sai na sanya Daniel a cikin idanuna ".... Cecelia ta katseta da cewa," Kenan haka Na nufin zamu kwana a saman Street ? "," No my dear ba zamu kwana a saman titi ba,dole wata dabarar zamu sake wata k`ila muyi nasarar samun sa". "To ko dai wata wayar zamu ara sai mu Kira shi da ita in anyi sa'a ya d`aga shikenan","To shikenan Cecelia gwada mu gani",wara idanu Cecelia ta fara yi a cikin tashar da suke,can ta hango wani shop,ta kalli Grandma tace ko can zamu je ga wani shop can sai mu rok`e shi ya ara mana wayar ?"," To mu je mu gani ko zamu da ce". A tare suka isa cikin Shagon,bayan sun gaisa Cecelia tace da shi,"Please ka ara mana wayar ka,muna so zamu yi kira tamu wayar ta mutu ne saboda rashin charge, gashi munyi tafiya mai nisa". Wani irin kallon mai Shagon ya bisu da shi alamun kamar bai yarda da su ba. "Haba Yarona ka taimaka ka ara mana,ba cutar da kai zamu yi ba, idan baka taimake mu ba,ba mu san ina zamu kwana ba,gashi ba mu san kowa a cikin Garinnan ba,please ka tai maka mana". Haka ba dan ya so ba ya basu aron wayar,Cecelia ta sa number,tana fara shiga ta mik`awa Grandma wayar. Sai da Hibba ta ja dogon tsaki kafin ta yunk`ura da k`yar ta nufi inda wayar take,ganin bak`uwar number ne ya sa ta d`aga kiran tare da yin Sallamar tare da cewa," Mai wayar baya kusa a sake Kira zuwa anjima ". Cikin d`aga murya Grandma ta ce, "Who the hell are you, wace ce ke da har zaki d`aga min wayar Yaro ina Daniel d`in yake ?". Ba Hibba kad`ai ba hatta Unborn d`in da ke cikinta sai da ya motsa sakamakon tsawar da kuma murya Grandma da ta ji". " Na ce maki ina Daniel d`in ya tafi a cikin irin wannan daren,kuma ke kuma wace ce da har aka samu wayarsa a hannunki?". Diriricewa Hibba tai Zufa sai faman tsa-tsafo mata take,ta rasa me zata ce da ita,shigowar Abbakar ya d`an saisaita mata tunanin da hanzarinta ta nufi inda yake ta na mai mik`a mashi wayar amma ta kasa iya cewa da shi komi. "Lafiya me yake faruwa ya na ganki a cikin irin wannan yanayin, ko dai jikin ne har yanzu ?"...... " Grandma ce akan line"...shine abinda ta iya cewa kawai "Grandma kuma ina fatan dai baki d`aga ba ko ?","Yanzu haka tana kan layi tana jinka", sosai tsoro da fargaba suka bayyana akan fuskar shi,jikin shi a matuk`ar sanyaye ya kai wayar a kunnensa shi tare da kiran sunanta yanda zai samu tabbacin ita d`ince. " Eh ni d`in ce dai wace kake gudu, kenan saboda mace ka ne aikata mana duk abinda ka ga dama"...muryar shi na rawa ya fara k`ok`arin dakatar da ita,hanashi cewa komi tai sai itace ta cigaba da cewa,"Ka bar komi kake ka zo nan Tasha muna jiranka". "Tasha kuma wacce irin Tasha,to wai ma wacce tashar ki ke nufi".ya faɗa a firgice " Tashar Ubanka na ke nufi,ina nan cikin Garin Kano ka zo ka d`auke mu ,kana da za`bi ko dai ka zo ka d`auke mu ko kuma mu juya mu koma inda muka fito ko kuma mu kwana a Street ya rage ruwanka". "A'a Grandma ba ayi haka ba,ku jirani ganinan zuwa". Haka ya kashe wayar ya nufi inda ya ke aje keys d`in motarsa,rasa ma Ina ya aje su yai sai yai gaba sai kuma ya dawo yai baya,ya ma rasa ne ya kamata yai sai Hibba ce ta d`auko mashi key d`in ya fita,ko da ya fita yawo kawai ya kama yi akan titi,sai daga baya tunanin shi ya fara dawowa jikinsa,sannan ya fiddo wayarsa ya Kira layin da su ka kirashi da shi ya Kira shi ya gayama sa Tashar da suke ya nufi can d`in. "Kin ji tashin hankali Cecelia, wai mace kuma ce ta d`aga wayar Daniel da farko","Mace kuma to wace ce ita,wanne matsayin ne da ita har haka ?"," Ban sani ba,a iya sani na Mace ba ta cikin d`abi'u ko halayyar Daniel ". " Ko dai yana tare da fiance d`in sa ne ?","To in haka ne mai zai sa tun farko ba zai sanar da ni ba,sai ya rik`a gudunmu", "Tom ,ni dai bana ce komi ba ,sai dai mu bari ya zo sai mu ji gaskiya daga bakin sa".haka dai suka cigaba da wannan zancen har zuwa sanda ya iso tashar. Ko da isar shi tashar da hayaniya Grandma ta taso mashi,cikin ladabi da biyayya ya duk`ar da kanshi ya na mai cewa da ita," Na rok`e ki da kiyi hak`uri ki dakatar da duk wani `bacin rai ko fushi da ki ke ji a kaina har sai mun Isa Gida ,in ba haka ba nan mutane zasu taru su san wannan irin hali muke a ciki". Da k`yar Grandma ta iya had`iye abinda take ji a cikin ranta har suka bar cikin Tashar, ita kuwa Cecelia sai faman kallon shi kawai take gani ta ke kamar ba Brox Daniel d`in ta da ta sani ba, kamala da natsuwa duk sun bayyana a tattare da shi. Yanda Abbakar ya fita cikin tashin hankali da damuwa hakama Hibba take a cikin shi,komi na ta ya tsaya ta rasa wanne tunanin ko kuma wani abu da zata aikata ya kawo sauk`in wannan lamarin da ya tun karo su,amma ina kanta a cunkushe yake,tunanin ta ya cure guri guda,babban abinda yafi tsaya mata a rai da kuma sake tada mata hankali muryarta da Grandma ta ji,ya zasu k`arke shin zata kar`beta a matsayin in- law ko kuwa za tai rejecting d`inta. Sanda taji k`arar bud`e gate d`in Gidan da shigowar su sai da numfashinta yai yunk`urin dakatawa da k`yar ta samu ta janyo shi da k`arfinta. Sanda suka shigo cikin Parlourn ba k`aramin sake hargitsewa tai ba,sai ji tai inama da ta sani `boyewa tai bata zauna sun isketa a cikin Parlourn ba. Cecelia ce ta matsa kusa da ita,tana mai binta da kallo tun daga sama har k`asa kafin ta jeho mata da tambaya,"Ke ce ki ka Picking Call ɗin d`azu da akayi ?",a tsorace ta d`aga mata kai alamun eh itace ta d`aga wayar. "Wace ce ke ko dai fiancee d`in sa ce ke ?". Ba tare da Hibba ta iya tsayawa ta tantance ma'anar tambayar da Cecelia ta yi mata ba ,ta sake amsa mata da Eh. Grandma ma ce ta maida kallonta kan Daniel tana mai cewa da shi," Yanzu Daniel for the God sake mene ne haka saboda ka na tare da Mace sai ka manta da mu,ka fidda mu daga cikin rayuwar ka,ka tada hankalin ka ka tada hankalin mu,me ya same ka da har ka aikata hakan?". Abbakar rasa me ce yai ganin yanda suka sauyawa lamarin ma'ana da kuma yanda suka d`auki ke shi da sauk`i,ganin ya kasa iya cewa komi yasa Grandma ta maida hankalin ta kan Hibba, ganin yanda take a firgice yasa ta kamo hannunta suka zauna akan two seater dake kusa da su,cikin kwantar da murya ta ce da ita,"Kin ga My dear ki kwantar da hankalin ki ba abinda za mu yi miki,Na ga duk kin tashi hankalin ki,ko ba ki san cewa ba a san Pregnancy Woman tana shiga cikin tashin hankalin ko damuwa ba, cikin na ki watan shi nawa yanzu?". Cikin rarraba kalami ta bata amsa da,"watan shi bakwai","Oh sannu kin ji ina rok`on Yesu Almasihu da ya kare ki ya sa ki sauka lafiya ke da abinda ke cikin ki". Cecelia ce tamasa cikin murna tare da cewa,"Ina fatan in an tashi a haifi mace sai a sanya mata sunana kin ga ta My first Daughter kuma gata name sake d`ina". Sosai wad`annan maganganun ma su suka tada ma Hibba hankali ba ma ita kad`ai ba hatta da shi Abbakar d`in sai da k`irjin shi ya buga da ya ji abinda su ke cewa. "Ka bani mamaki Daniel,ban ga dalilin da zai sa don ka fara Dating ka k`aurace mana ba, meye nawa don kana tare da wacce ka ke so,iyakacin fa in samu ku albarka tare da fatan alkairi, ba zan hana ka kayi rayuwa da wacce ka ke so ba". Sake baki su duka biyun su kai sosai Abbakar ya Lula duniyar tunanin da San gani dalilin da yasa suke d`auki lamarin ta wannan fuskar, sai a lokacin ya kai dubanta shi kan kayan da ke jikin Hibba k`ananun kaya ne a jikin ta saboda cikin Na sanyata yawan jin zafi,wa da hakan yasa su ke ganin lamarin ta wannan fuskar,su duk a zato da tsanmanin su itama Hibba Crista ce. " Ka tashi hankalina Daniel akan lamarinnan bana samun isasshen barci Na takura ,Na Sanya Pastor yana yi maka addu'a ni duk a tunanin ko wani mugun abun ne ya same ke". Dakatawa tai tana maaida kallonta kan Hibba ta ce da ita,"Kar ki damu da zaran kin haihu zamu had`a da bikin suna da kuma bikin ku musha shagali biyu a lokaci d`aya,fad`a min ya sunan ki"..... "Grandma ba fa abinda ku ke tunanin ba ne ba, ni da ita munyi Aure mu d`in mata da Miji ne". Kamar wad`anda aka d`aukewa wuta haka Grandma da Cecelia suka tsaya cak komi nasu ya dakata na wucin gadi. Cecelia ce tai k`arfinta halin sake tambayar shi abinda kunnuwansu ya jiye masu," Da gaske kake Brox Daniel, wannan ɗin Matar ka ce,kayi Aure,kuma ba tare da mun sani ba, me hakan ke nufi?". Wani yak`e Wanda yafi kuka ciwo Grandma ta saki gami da cewa,"Kinga Cecelia bi komi a hankali ya riga da yayi Auren fa,ba wai zai yi ba ne ba,abu guda da za ki tambaye shi,me muka aikata mashi wanne laifi ne mai girman gaske da mu kai ma shi har da muka can-canci ya fiddamu a cikin lamarin rayuwar sa?",Grandma ta kai k`arshe batun muryarta ta fara rawa alamun batun ya ta`ba mata Zuciyarta. "Ka kunyatar da ni,ako da yaushe in na zauna cikin friends d`ina bani da abun fad`a da ya wuce My son Daniel ya girma,in Aurensa ya zo zan yi kaza,zan sai kaza,zan sa kaza a jikina amma shine za ka yyudare ni ka je can kai Auren ka ba tare da na sani ba?"..... "Ki gafarce ni Grandma ba na aikata hakan don son nuna ba ki isa a cikin rayuwata ba ,ko don kunyatar ki ba, a'a na kasa samun natsuwa , Zuciyata na faɗa min ba lalle ku amshi abinda na zo maku da shi ba,kullum cikin fargaba da tashin hankali na ke"... "A'a Daniel ƙarya ka ke dama can ka ayi biyar kunyata ni,Kai Ni ban ma yarda da abinda ka ke cewa ba". "Ki gafarce ni Grandma da gaske ne nayi Aure,sunanan ta ma Hibba kuma musulma ce,ni ma kuma na dad`e da musulumta". Wani irin tafiya taga-taga Grandma tayi zata fad`i k`asa inba dan yana kusa da ita yai saurin tare ta ba da Allah kad`ai yasan irin fad`uwar da za tai. " A'a Daniel na rok`e ka da ka k`aryata abinda kunnuwana suka jiye min ka ce ba gaskiya ba ne ba,mafarki na ke,mafarkin abinda ba zai ta`ba yiwuwa ba",Grandma ta fad`a hawaye Na rige-rigen sauka akan fuskarta Shima hawayen yake sakamakon ganin ta na hawayen da k`yar ya iya cewa da ita,"Da gaske ne Grandma na yi Aure,kuma sannan Na musulumta ni yanzu ba mabiyin addinin Crista ba ne,ni musulmine ,suna Na Abbakar ba Daniel ba". "A'a Brox Daniel kar kai haka ,kar ka ce ka bar addinin gaskiya, Addinin iyayen da kakannin ka,shin ina wata gaskiya ta ke a cikin Addinin da ba addinin Crista ba,ka tuba ka dawo ya zuwa addinin ka ka ji d`an'uwana Daniel"... Da hannu ya dakatar da ita," Kar ki sake kirana da wannan sunan suna Abbakar ba Daniel ba". "Oh Jesus ka kawo min d`aukin ka, sun asirce min d`a shikenan sun raba ni da shi,ka ga ka biyo ni mu je can Jos in had`a ka da Pastor Yohanna ya ba ka makarin asirin da su ka yi maka". Cecelia ce ta matsa kusa da Hibba idanuwanta na zubda hawaye ta ce da ita,"Me ki ka yi ma d`an'uwana da har ki ka rabashi da tunanin sa ki ka raba shi da addinin shi", ta kai zance ta na mai daka mata tsawa. " A'a wallahi ba abinda nayi masa,hasalima shi da kan shi yai sha'awar shiga muslunci ba tare da an tursasa shi ba ". Hibba ta bata amsa bakinta na rawa "K`aryar ki ke dole da akwai abinda ku ka aikata ma shi ,to ki sani ina mai rantse maki da Allah d`aya sai kin rabu da shi,sai kin bar cikin Gidannan domin nan ba gurin zaman ki ba ne ba"..... Cikin d`aga murya Abbakar ya daka ma Cecelia tsawa tare da fara yi mata warning," Ki shiga hankalin Cecelia Mata ta ce fa,ki fita a harkata domin babu ruwanta a cikin wannan Maganar,don rad`in kaina na ce ina son in musulumta haka kuma ina cikin hankalina na ganta Na ce ina sonta". "A'a Daniel kar ka ce haka,ka zo mu bar wannan Garin zaman ka a ciki ba alkairi ba ne ba,ka rabu da wannan Matar ba son gaskiya ta ke maka ba tunda har ta iya raba ka da Addinin ka,kar ka manta tun kana d`an k`arami ka na raine ka,Na baka kulawa da Soyayya,me ye zai sa yanzu da rana tsaka ka za`bi wata bare kuma ka fifita akaina,don haka ina mai umartaka da ka tashi a yanzu ba sai gobe ba mu bar wannan k`addararen Garin da banga amfanin zaman ka a cikin sa ba,ita kuma kai divorce d`inta ta tafi Gidan Ubanta". Wasu hawayen ne suka sake zubowa daga Idon shi kafin ya duƙar da kan shi ƙasa ya ce da ita "Ki gafarce ni Grandma, nasan kinyi matuk`ar k`ok`ari a wajen rsino da tarbiyar mu,a kan haka nake baki hak`uri domin ba zan iya yi maki biyayya a dai-dai wannan ga`bar ba,Addinin da nake a kai yanzu ya ce babu biyayy ga abokin halitta indai a wajen sa`bawa Ubangiji ne,kuma ni Maganar gaskiya ina son Mata ta da abinda ke cikinta,kuma ban shiga cikin Addinin muslunci don in barshi ba,kuma ina yi maku Addu'ar Allah ya sa ku gane gaskiya ku dawo cikin sa"..... "Dakata min mara kuyar banza mara kuyar wofi, ai ashe bayan nasarar fidda ka daga cikin Addinin ka da su kai har rashin kunya su ka koya ma ka,to bari ka ji madamar ba ka sake ta ka zo mun bar wannan Garin a yanzu,ka bar masu Addinin su anan,tunda dama nan ka same shi,ita kuma ka sake ta da zaran ta haihu sai mu zo mu amshe abinda ta haifa shikenan, in kuma ba haka ba sai dai ka za`ba ko ni ko ita,domin ba zan iya cigabada da ganin ka tare da ita ba". Sai da Abbakar ya duk`ar da kanshi k`asa, hawayen saman fuskarsa na tsananta zuba kafin ya iya cire baki ya ce da ita," Grandma ki gafarce ni amma ba zan iya aikata da`ya daga cikin abubuwan da ki ka lissafo ba,ina son Addini na da kuma Mata ta,haka ke ma ba zan iya rayuwa babu ke ba".... "A'a Broth don't do that, wannan babban kuskure ne ta ya za ka yarda ka rabu da whole family d`in ka akan wata Mace ,Haba Broth think wisely mana,tabbas ka sa na ji Na tsananin wannan Matar har ma da abinda ke cikin ta ban san su ban ko San ganin su,By the grace of God d`an cikin ma ba zai rayu ba,ba za a haife shi da rai ba".....kafin ta rufe bakin ta ya sharara mata mari har biyu da iya kacin k`arfin shi,K`ara mai k`arfi ta saki gami da k`ank`ame Grandma ta na mai ambaton sunan Jesus. "Ba ka da hankali ne a gabana zaka sa hannu ka dake ta kuma akan mace ? "," Grandma ki Na jinta fa,kin ji mugun bakin da kuma aibatawar da ta ke yima iyali na fa". Duka Grandma ta fara kai mashi ta ko ina a jikin sa tana yi tana cewa ya cuce ta tunda har ya yarda ya bar Addinin Crista ya koma musulmine,sai da tai iya yinta ta sanan ta dakata dan kanta kafin ta dakata,"Ka sani daga yau bani ba ka,Na fita daga cikin duk wani sha'ani na ka ko na rayuwar ka,sannan kai ma ina son ka fiddamu a cikin taka rayuwar ba mu ba ka tunda Addini ya raba mu,a yau ba sai gobe ba zamu bar maka Gidan ka ka cigaba da rayuwa da wacce ka za`ba". Tana kaiwa nan ta sa`bi jakar da suka zo da ita gami da kama hannu Cecelia suka nufi hanyar barin Gidan kowa a cikin su fuskar jik`e take da hawaye. "Grandma bai kamata ku fita a cikin wannan daren ba,biside ma ai nan Gidan ku ne,ku yi hak`uri zuwa gobe komi zai dai-daita, please amma kar kuce za ku fita a cikin darennan,gano Jus daga Kano a irin wannan daren ai ba k`aramin abu ba ne ba". Cikin fushi Grandma ta ce da shi,"Ba zan zauna a cikin wannan useless d`in Gidannan ba ko da kuwa ina da tabbacin in Na fita zan gami da accident a saman hayata to na gwammaci in tafi,Na tsanai duk seconds ko minutes da na ke k`arawa a cikin sa kai na gwammaci in kwana saman Street da in kwana a Gidan ka". Sosai jikin Abbakar yai sanyi sakamakon jin abinda ya fito daga bakin Grandma, ita kuwa Cecelia tun d`azu ba abinda take sai kuka gaba ki d`aya ta fita a hayyacinta,sai a lokacin ta d`an d`ago daga jikin Grandma ta na mai cewa da ita," Kin yi kuskure Babba a rayuwar ki ,tunda har ki yarda kuma ki ka amince ki rabani da yayana mutumin da ko tsawa bai ta`ba yi min ba amma yau ki ka sa ya dake ni,ki sani sai kin biya wannan bashin you will regret it ".ta na kaiwa nan a zancenta ta sake boyewa a jikin Grandma don kar ta sake shiga hannunsa. Duk yanda Abbakar ya so su Grandma su zauna a cikin Gidan ko kwana ne suyi kafin Safiya k`in yarda su kai ,haka su ka bar Gidan a lokacin goma da wani abu na dare,kai tsaye Tashar da suka sauka nan suka koma inda Allah ya taimaka su suna zuwa suka samu wata motar kaya anyi Lodi za a tafi suka shiga,dukkanin su ba su cikin natsuwa su,Cecelia kuwa har su ka tashi ba ta daina kuka ba,sai bayan motar tasu ta tashi sannan Abbakar ya koma Gida domin kasa barin su yayi yana biye da su a baya har suka tafi, ranshi a cunkushe ya juya nufi na shi Gidan. *JADEEDAH* (It's a story of two love birds who are so different from each other ) STORY & WRITTEN BY : (*Cwt~Sumiey*) Marubuciyar littafin MENE NE ABIN YI ? KARAGAR MULKI And now.....*JADEEDAH* BOOK 1 PAGE 9 ❤ "Hankalin ka ya kwanta sai ka zuba ruwa a k`asa ka sha don murna,tun jiya da muka dawo Grandma ba ta iya magana,k`arshe mun tashi ko motsin kirki ba ta iyawa,sannan ina mai sanar da kai an dakatar da maganar Aurena sakamakon jin Cewar ka bar Addinin Crista, don haka kayi farinci ,amma ina so ka sani,ban damu da fasa Aurena da akayi ba amma muddin har wani abu ya samu Grandma ba zan yafe maka ba",tana kaiwa nan ta yanke wayar. Sosai jikin Abbakar ya fara rawa,bai san sanda ya kai zaune kan kujerarsa ba,kan shi ya d`ora kan desk sai faman buga kan shi akai yake yana fad`in," It's my fault, ni ne na janyo mata shiga cikin wannan halin". "Ya Salam Manager kana lafiya kuwa,ko wani abun na damun ka ne?".Cewar Abbas Acounter da shigowar shi kenan, kasa iya cewa da shi komi yai,amma tuni idanuwansa sun sauya kala. "Amm...Amm....ba komi amma ina so zan je Gida,kace ma Buhari Isa ya kirani zan bar mashi sallahu", yana kaiwa nan ya zari car key d`in sa ya fita,cikin k`ank`anin lokaci ya isa Gida,yanayin da ta ganshi kad`ai ya tabbatar mata da ba lafiya ba,da k`yar ta yunk`ura ta tashi tsaye. "Lafiya na gan ka yanzu,nasan lokacin tashin ka bai ba,kuma kamar kana cikin damuwa ko dai wani abun ya sake faruwa ne ?". "Grandma ce tun bayan komawar su ba lafiya so shine fa na ke son inje in dubo halin da take a ciki". " Amma ba kai zai driving ba ko?",har ya juya zai tafi Maganar ta ta dakatar da shi. Murmushi yak`e ne kwance akan fuskar shi,kafin ya ce da ita,",Kar ki damu I will be fine,zan je in dawo lafiya lau,ki Kira Ummiey Maryam ta sa a kawo maki Jaheed ya taya ki zama ko da zan iya kaiwa dare". Da to ta amsa mi shi,har bakin gate sai da ta raka shi,tana ji tana gani ya tafi ba dan ranta ya so ba,ta so ko da motar haya ne ya hauwa amma ina bai amince da hakan ba,haka ta ja k`afafunta ta koma cikin Gidan tana mai nemo wayarta ta Kira Ummie Maryam domin ta sa a kawo mata Muhammad Jaheed d`in domin ba zata ji dad`in zama Gidan ita kad`ai ba. Cecelia kuwa hospital takai Grandma, bayan an admitting d`inta an yi mata duk abinda ya kamata ta dawo ta tasa ta sai faman kuka ta ke, tsoranta d`aya kar Grandma ta mutu ko ta samu wata matsalar,domin in hakan ta kasance bata san ina zata sa rayuwar ta ba,duk da kasancewar suna rayuwa tamkar `yan'uwa da `yan unguwarsu da kuma mutanen da suke halartar Church guda d`aya, amma ba ta da kamar Grandma da kuma Broth Daniel,duk da Cewar shi ma ba ya tare da ita,''Broth Daniel ka cuce ni idan har ka zama sanadin faruwar wani abu ga Grandma to ba zan ta`ba yafe maka ma". Motsin shigowa cikin room d`in da ta ji ne ya sa ta saurin d`ago da kanta ,Gloria ta gani hakan ya sa ta ƙara k`arfafa kukanta,da sauri ta k`araso ta na mai lallashin ta,"I'm so sorry my friend na ji abun bak`in cikin da ya same mu ki yi hak`uri ki bar kuka haka kar wani ciwon ya same ki''. "Gloria ki barni dole ne in yi kuka,Samuel ya guje ni,tun bayan dawowar mu a jiya da mutane suka samu labarin abinda ya faru,Mahaifin shi da kan shi ya kira shi ya dakatar da shi,wai tunda d`an'uwana ya bar Addini ni ma wata rana zai iya rinjayata in bar Addini don haka ni ba Matar da ta dace ya aura ba ce,tunda Grandma ta ji wannan labarin bata k`ara cewa uffan ba,zuwa da safe ko motsin kirki ba ta iya yi".ta kai k`arshe zancen ta na mai sake fashewa da kuka. "Na samu labarin komi Cecelia shiyasa ma na zonan,nayi kaico kuma nayi mamakin abinda Broth Daniel ya aikata unfortunately ban ta`ba tsanmanin haka daga gare shi ba,Dan haka ki yi hak`uri,komi da ki ka ga ya faru it's about destiny,kafin in zo nan mun yi magana da Daddy na yace in baki hak`uri zai zauna da Dadyn Samuel sannan ya na son ki had`a shi da Broth Daniel d`in zai yi mashi wa'azi ko da za a samu ya dawo cikin hankalin da natsuwarsa". " Kai..kai ...Gloria I'm so happy Na ji dad`in wannan magana taki ,thank you ban dan da wanne irin baki zan gode maki ba". "Kar ki damu Cecelia wannan ai duk yi ma kai ne,kin san fa irin yanda na ke son Broth Daniel, Na kwallafa raina akan shi,ba na jin zan iya rayuwa ba tare da shi ba,zan yi iya yina na ga mun dawo da shi kan haya madaidaiciya".Nam fa Gloria ta cigaba da lallashin ta har ta samu ta ci wani abu cikin abincin da ta zo da shi. Shi kuwa Abbakar sai wajen Magaribha ya iso Jos sai da ya tsaya ya sauke sallolin da su ke akan shi sannan yai sai duk abinda ya ke ganin zasu buk`ace shi sannan ya Isa hospital d`in da ya ke tunanin ko tabbacin can Cecelia zata kai Grandma, san da ya Isa bai sha wahala ba a ka kai shi d`akin da a ka kwantar da su,Cecelia ya iske ta d`ora kanta kan gadon da Grandma take, barci ya kwashe ta a haka hannunta d`aya na rik`e da da hannu Grandma,kamar mai jin tsoran wani zai kwace mata ita,sosai ta ba shi tausayi ,gefe guda ya samu ya zauna ba tare da ya yi wani motsin da zai tashe su ba,ganin da gaske barcin ta ke ita kuma Grandma an sama mata drift yasa ya shigar da duk abinda ya zo da shi ya nufi office d`in Doctorn Dan yasan me yake damun Grandma d`in da har ta shiga cikin wannan halin. Sosai ya samu kwanciyar hankali bayan ya samu gamsasshen bayani daga bakin Doctor d`in ,"Kar ka damu stress ne ya jefa ta a cikin irin wannan halin amma za ta samu lafiya da izinin Allah,zamu sake dubata zuwa gobe daganan sai mu ba ku sakamakon na k`arshe ",wannan shine batun da Doctor yai masa na ƙarshe. Bai sake komawa Room d`in ba har sai da ya gabatar da Sallahr magariba, lokacin Cecelia ta farka daga nannauyan barcin da ya sace ta,sosai ta rink`a mamaki kayan da ta gani an shigo da su,ganin Abbakar ya shigo cikin d`akina yasa ta d`aure fuskarta gami da kauda kanta gefe alamun bata ma son ganin shi. " Me ya sake dawowa da kai ,ko ka zo ne k`arasata kamar yanda ka d`auko hanya ne ?". "Shut up Cecelia na gaji bana son wad`annan k`ananun zancen , ki bar komi ya wuce,I have my own right to do any religion that I want,don haka ki bar ni,Na zo nan ne domin Grandma ta samu lafiya Dan haka bana buk`atar wani sabon tashin hankalin". Ganin da gaske yake yasa ta ja bakin ta tai shiru,suka cigabada da zaman kurame,shi ya cigaba da yi ma Grandma duk abinda akace ayi mata,duk bayan wani lokaci zasu rik`a motsa mata hannu da k`afafunta don gudun paralysis ya same ta. " Ki tashi ki tafi Gidan su Gloria ki kwana ni zan kwana da ita anan",shine abinda Abbakar ya ce da ita, ta so tayi ma sa musu amma ganin ba fuska ya sa dole ta hak`ura,ta d`ebi kayan abincin da Glorian ta zo da su ta tafi da su. Lokacin da ta Isa Gidan su Gloria ta sanar da ita zuwan Daniel ba k`arami Murnar da mamaki ta yi ba, har Allah Allah take Gari ya waye su je hospital d`in ta gan shi,ta sanya shi a idonta ko ta samu sauk`in daga irin nauyin da Zuciyarta ta ke yi mata akan son shi. Sai dai kash tun kafin su tashi a barci Mahaifiyarta ta yi masu knocking akan su tashi. " Lafiya Mom za ki tashe mu tun yanzu ?", Gloria ta tambaya da alamar barci akan fuskarta,"Surprise Dadyn ki ya shirya maki". Sai da Gloria ta `bata fuska kafin ta ce,"Surprise kuma wanne irin surprise ? ",. My daughter ya Na ga fuskar ki haka kamar ba ki farin ciki da abinda ma fad`a maki ba ?". " Ba haka bane ba Mom kawai da akwai inda na ke son zuwa early in the morning d`innan that's why ". " Ayyah my dear hakan ba zai yiwu ba domin yanzu haka Mota na waje na jiran mu,go back and fack your thing zamu bar Garin Jos yanzu"...."What!....za mu bar gari mu je ina,yaushe aka yanke wannan hukuncin?". "Oh ki kwantar da hankalin ki,domin Mahaifinki ne ta samu matsayin Pastorn a wani Babban Church d`in da suka gama Ginawa yanzu haka yau za a gudanar da bikin bud`e Church d`in shi yasa ya aiko da Mota a d`auke mu a kai mu Airport domin mu samu Isa Lagos d`in don mu samu halarta bikin". "A'a Mom.. No ....hakan ba mai yiwuwa bane ba,ni babu inda zanje,ina da wanda nake son gani a yau ba zan biki ba".... "Kema kin san baki isaba babu inda za ni ba tare da ke ba,koma meye ki bar shi sai wani lokacin ,idan kuma kin musa,min a haka da sleeping dresse d`in zamu tafi da ke". Hankalin Gloria ya yi matuk`ar tashi yai ba, ba shiri ta nufi inda Cecelia take zaune ta rabka uban tagumi ta ce da ita," I'm so sorry, Na so ace tare da ni zamu yi fighting d`in wannan battle d`in da ya tun karo ki sai dai kash hakan ba mai yiwuwa bane ba, ina mai baki hak`uri akan haka,tafiyar gaggawa da ta kamani zuwa Lagos mun koma can da zama gabad`aya da family na,sai dai ki sani a ko ina nake ina tare da ke,zan baki goyon baya hundred percent akan mu dawo da Broth Daniel kan hanyar da ta kamata,zan tafi ba dan na so ba". Haka suka tashi jiki kowa a cikin su a sanyaye ,Cecelia ba ta tafi hospital ba har sai da taga tashin su Gloria kana ta juya ta tafi tana mai share hawayen kewar k`awa ta Gari da tai yi,k`asa hak`uri Gloria tayi har sun fara tafiya ta dakatar da driver d`in da gudunta ta dawo baya tana mai kwalama Cecelia kira,cike da mamaki ta juya tana mai tambayarta. "Lafiya Gloria na ga kin dawo?",Gloria na mai da hakin gudun da ta yi ta bata amsa da cewa," Komi lafiya ina son in baki sak`o wajen Broth Daniel ki fad`a masa har yau har gobe ina son shi,ina jin shi a cikin raina, Zuciyata ba zata samu salama ba har sai na ganni a matsayin Matar shi,ba zan huta ba har sai na ga hakan ta kasance,I promise I will be back soon zan dawo saboda Soyayyar shi,shi shi kad`ai ki gaya mashi hakan".tana kai wa nan a zancenta ta juya da d`an gudun ta ta koma motar su ka tafi Mahaifiyarta ma ta yi mata mitar tsaida sun da tayi amma ita ko a jikinta. Ba k`aramin mutuwa jikin Cecelia yai ba sakamakon jin abinda Gloria tace,wannan wacce irin Soyayya ce,da har za ta bari ta makantar da ita har haka shin ko ta manta yanzu ba addinin su d`aya da Broth Daniel ba ne ba ko me?",abubuwa da dama suka cigaba da kai kawo a cikin rai da Zuciyarta kafin daga bisa ni ta watsar da su ta cigaba da tafiyata zuwa hospital d`in da Grandma take kwance. Sanda ta Isa duk wani abu da ya kamata ayi ma Grandma anyi mata hatta da wanka yasa Nurse d`in asibitin sun yi mata,nan haka suka cigaba da jinyar Grandma har na tsawon kwana biyar tun Cecelia Na jin haushin shi har ta fara ragewa,domin ba abinda ya rage daga kulawar da yake ba su sai ma abinda ya k`aru,kuma zaman shi a tare da su bai sa ya daina ko rage na shi Addinin ba,har mamakin k`arfin halin shi take,tsakanin shi da Hibba kuwa sai dai waya tuni an kawo mata Muhammad Jaheed shi ke taya ta hira. Ranar da suka cika one weak ranar Grandma ta farka,ita kanta ta yi mamakin ganin shi tsaye akan duk lamarin ta ,duk wani abu da ake so ko za a buk`ata shi ake tambaya, ba musu kuwa zai je ya kawo shi,da kallon mamaki kawai ta ke bin shi da shi har daga k`arshe ta ce da shi,"Daniel ina cikin mamaki na sha canja Addini da kai zai sa ka guje mu ka wofintar da dukkan lamarin mu ashe ba haka bane ba, kawai Zuciya da tunanina ne su ke ba ni hakan".Grandma ta fad`a cikin muryarta ta marasa lafiya. "Haba Grandma ta ya za ai in aikata hakan ba fa ni da wasu ahali da ya wuce ku, me zai sa in guje ku,ina son ku ba zan iya barin ku ba ,kamar yarda na ke son Addini na ba zan iya barin sa ba". "Shikenan Daniel indai haka ne na yarda ka cigaba da bin Addinin da,kake so amma Na rok`e ka kar ka barmu,kar ka sauya mu a matsayin ahalin ka. "In Sha Allah ba zan aikata hakan ba,ni ban k`i ba ma ku shirya mu koma can Kanon da ku,mu yi rayuwar mu a tare a can"... Ta katse shi da da cewa," A'a ni babu inda zani nafi son in k`arasa `yar sauran rayuwata a cikin wannan Garin tare da `yan sauran k`awayena da suke Raye,muna daga nan zan dunga yi maka addu'a da ga kai har Matar ta ka". "Dan Allah Grandma ki daina fad`ar mutuwar nan ba yanzu ba ina son har `ya`yana da na Cecelia sai kin gani". " Kayya dai d`annan a haka ma ai mun sha miya,sai dai mu jira mutuwa kawai yanzu,damuwata d`aya a yanzu shine bazan ta`ba iya kama hannun d`anka in tafi Church tare da shi ba,ba za ka ta`ba iya haihuwar `ya`ya kasa sunan mamarka,ni ko babanka ka ba shine kawai damuwata. Cecelia ce tai saurin amshe batun da cewa,"Kar ki damu Grandma ni inna haifi yarana zan sa sunan ki har da ma sunan su Dad". "Kai na ji dad`in haka my dear Allah yasa in ga `ya`yan naku gabad`aya". ''Yauwa Grandma ki K`ara kwantar da hankalin ki hatta da Maganar bikin Cecelia zan yi k`ok`ari in ga na dai-daita ta kafin intafi,kin ga Doctor ya ce ba zai sallame mu ba har sai ya ga kin samu lafiya sosai da sosai". "Kar ka damu Yarona indai don wannan ne komi zai koma normal",haka Abbakar ya cigaba da jinyar Grandma sai da yai kwana goma kafin ya koma Kano, gaba d`aya ya raba hankalin shi Gida biyu yau ba shi Kano gobe ba shi Jos,sosai ya fita cikin hayyacinsa har Rama sai da ya fara ,bayanda za ai ya bar ma Cecelia jinyar Grandma ita kad`ai hakan ya sa dole yake go and come d`in ,ya kan yi aikin shi a system ko da yana can Jos d`in ,Grandma tafi wata kwance a asibitin hakan ya sa ya maida Hibba Gida ganin Month d`in Edd ta ya kusa shi kuma ba mazauni ne ba, sosai jikin Grandma d`in take samun sauk`i hatta fara tafiya amma da taimakon k`arafa hakan ya fara sa hankalin su ya kwanta ita kanta Grandma d`in har tausa Abbakar d`in take gani irin fad`i tashin da yake duk akan su. *JADEEDAH* (It's a story of two love birds who are so different from each other ) STORY & WRITTEN BY : (*Cwt~Sumiey*) Marubuciyar littafin MENE NE ABIN YI ? KARAGAR MULKI And now.....*JADEEDAH* https://chat.whatsapp.com/CWkZfMqvD4H0mtd7WW6Xbz https://whatsapp.com/channel/0029VapqU8C002T5Bz8RSQ0a BOOK 1 PAGE 10 ❤ FREE PAGE "Yauwa Yarona d`an Albarka Na gode sosai, in sha Allah za kai albarka". Sai da ya washe bakin sa alamun yaji dad`in Addu'ar da tai mai kafin ya ce da ita," Momynah na k`agara in ga kin haihu,na ga d`an k`anina da za ki haifi min mai kama da ni".ya kai zancen ya na mai cigaba da matsa mata k`afafunta. Sai da Hibba ta zaro idanunta waje kafin ta ce,"Kai Muhammad Jaheed Namiji kuma ka ke son in haifa,ina laifin ka ce in haifa maka yar Mace,wacce za ka rik`a kama hannunta ku je makaranta, wacce za ka rik`a tayawa Home work, wacce kuma za ka tsaya kai da fata wajen ganin tayi ilimin Addini da na zamani,ka zama bango kuma gatanta,ka cike mata sauran gurbin Ahali da ta rasa",ta kai k`arshen zancen muryarta a raunane. Duk da k`arancin shekaru na Jaheed sai da maganganun Hibba kuma Momynsa suka sa jikinsa yai sanyi,"Shikenan Momynah da ga yau zan rik`a Addu'a Allah ya sa ki haifo mana Baby girl,zan kama hannunta mu tafi ko ina,duk inda zani tare da ita zani,ba zan bari wani Namiji ya shiga cikin rayuwar ta ba balle har yasa ta Kuka,zan kasance mai aikata komi dumin ita,kuma ni zan za`ba mata suna",ya d`an yi shiru kafin ya cigaba da cewa,"Amma fa dole ta rik`a ce min Yayah ko tunda na girme ta ko?".ya kai k`arshen batun cikin sigar yarinta. Sai da Hibba tai dariya kafin ta bashi amsa,"Ba dolenta ba Jaheed, ai dole ta Kira ka da Yayanta,kasan akwai tazara ta wajen shekara Goma a tsakanin ku,ka kenan dole ta girmama ka". "Yehhhhhh Na ji dad`i tunda nima na kusa zama Babba". " Yau to bar k`afar haka naji ta yi min sauk`i yanzu taho mu ci abincin da ka kawo min","A'a ki ci naki ne ni na ci nawa,kuma ni bana jin yuwa"....."Shhhhhh rufa min baki,sai ka ci shi,ki baka ga abincin da yawa bane ba ai nasan irin Cin abincin naka dan haka ha bud`e bakin ka". Sai da Jaheed ya saki murmushi kafin ya bud`e baki ta fara sanya mashi abincin a baki,a cikin Zuciya da Idanunsa kuma ta na k`ara samun k`ima da matsayin mai girma ya rasa wanne irin so,k`auna da kulawa ta ke ba shi,a lokacin da tai Aure ba sa tare ba k`aramin kewa da rashin ta yai ba,ta kan ba shi muhimmanci fiye da dukkan wani abu ko kuma ita kanta,takan `bata lokaci mai tarin yawa don ganin kawai ya yi farin ciki ko nishad`i,ta fi kowa sanin shi da kuma fahimtar halayen shi,ko wannan abincin yasan za ta iya cinye shi har ma ta nemi k`ari amma saboda yana tare da ita ba zata iya cin shi ita kad`ai ba,dole sai sun ci tare,haka ta koma yanzu bunu-bunu ta nemi abinci,ba su wani d`au lokaci wurin cin abincin ba ya mik`e ya ce mata ya k`oshi. "A'a ba ka isaba dawo zauna sai mun cinye shi tare". " A'a ni kam ba zan dawo ba na k`oshi,wannan abinci ai sai dai ke ni yafi k`arfina in ba so kike nan gaba kad`an a kasa banbance ni da ke in zama Orobo kamar ke". Yanayin yanda ya ga ta zaro idanu waje ne yasa ya fara dariya gami da k`ok`arin barin wajen da gudu,"Au guduwa za kai to wallahi Inanan ina jiranka za ka dawo ka same ni ba dai ni kake kira da Orobo ba,zamu had`u ai,inna kama ka za ka basu labari".ta na zancen da fara'a kwance akan saman fuskarta. "Ah aha,su Hibba ne zaune anan Ana hutawa?", Cewar Baba Asabe cikin yanayin izgili da k`arasowarta wurin kenan. Murmushin yak`e Hibba ta saki kafin ta bata amsa da uhm. Bayan ta samu wuri ta zauna ne ta ce da ita," Ananan Ana ta zuba ma ciki lodi ko,ni na rasa wanne irin Aure ne wannan ki ka yi, kin tafi kamar ba ki tafi ba kullum kina cikin Gidannan, wai me ye matsayin da ma'anar wannan Auren,shin mijin na ki gajiya yai da ke ne ya maido ki Gidan ku ko ko sakin ki yayi,ko dai ya kasa d`aukar nauyin d`awainiyar ki ne da ta ke abinda ya ke cikin ki,domin na ga alama shi kan shi da za a bashi dama da cikin Gidannan zai dawo ya tare,shin ahalin su ba su da Zuciya ne komi?"... Kamar an jeho Ummie Maryam haka ta shigo cikin Parlourn tana mai fuskantar ta da cewa,"Haba Baba Asabe wannan wacce irin magana ce,ta ya za ki zo gabanta ki titsitsiye ta da irin wannan zafafan tambayoyin,ai hakan bai dace ba kuma bai kamata ba". "A kamarya bai dace ba,a tunanin ku Dan ku kun Gaza gaya mata gaskiya sai muma mu taru mu zuba mata ido,dole ne mu gaya mata gaskiya, taya mace da Gidan Mijin ta zata dawo zama Gidan iyayenta,gabad`aya ci da shanta har ma dana Wanda ta ke ikirarin Mijin ta ne yana cikin Gidannan,me hakan yake nufi shin ta zama sakakkiya ne ko kuma ya nuna gazawarsa akan ta ne a fili,kullum tana zaune k`ark`ashin bishiya bata aikin fari balle na `baki daga ta ci sai tai kashi,ko da yake duk wanda ya k`i cin biri ya ci dila,haka kuma wanda bai ji bari ba ai ya ji hoho,ayi dai mu gani domin tafi-tafi takardar sakinta za ku ga ta biyo baya ,ko kuma wata rana ku wayi gari ya gudu ya barta".... ''Wa ya gaya ma ki haka zata kasance da ita,ko angaya maki kowa ke da bak`ar k`addara irin ta ki Asabe", Cewar Mama Hadiza da fitowar kenan daga sashen ta hannunta d`auke da jik`on maganin da take baiwa Hibba Dan samun sauk`in nak`uda. A kid`ime Baba Asabe ta waigo jikin ta har yana rawa," Hadiza me kike nufi da wannan kalaman naki a gare ni ?''. "Oh baki gane ba,to bari in yi maki dallah-dallah yanda zaki gane shin kin manta nan Gidan ba Gidan Mijinki ba ne ba Kema Gidan iyayenki ne,Gidan da ki ke zaune tsawon shekaru Ashirin da wani abu tun `yar ki da kuma d`an ki na da `yan shekaru,shin ko kin manta da hakan ne,ke yara biyu ki ka zo da su ,Na rasa me ma tsare mi ki a cikin Gidannan Asabe, shin nayi maki wani abu ne wanda na can-canci wannan cin kashin da ki ke min,ba ki da wani abu sai dai son ki ka ga kin bak`anta min da ni da `ya`yana me na tsare miki dan Allah ?". Hawaye Baba Asabe ta sharce muryarta Na fidda sautin kuka ," Yanzu daga na zo fad`a ma `yarki gaskiya sai ki bi bayana da sharri da kuma gori".... "A'a Asabe k`aryar kike ba gaskiya ki ka zo faɗa mata ba,kin zo ne ki yi abinda kika saba sai kuma reshe ya juye da mujiya". " Mama dan Allah ki k`yaleta ki zo mu tafi,ki bar kula ta ",Cewar Hibba hawaye ma zuba daga idonta. " Babu inda zani don banga dalilin da zai sa in barta ta cigabada da cin kashi a kaina ba,iya Wanda tai a baya ma ya Isa". "Aiko dai maganar ki gaskiya ce Yaya ai Baba Asabe bai kamata ace ita ce ke furta irin wannan laffuzan ba,ita ma Hibba matsayin `ya take a wurinta bai kamata ta fad`i munanan kalamai akanta ba", Cewar Umma Jamila. Umma Hafsat ce ta amshe zancen da cewa" Anya kuwa kun fahimci lamarinnan dai-dai kuwa,ni a tunani na gaskiya Baba Asabe ta fad`a, shin mene ne aibun zancenta anan,ku duba fa ku gani kaf Gidannan ba wata d`iyar da aka haifa a cikin Gidannan da tazo tai irin wannan zaman da take".... Umma Maimuna ce ta matso tana mai gyara d`aurin zanin jikinta tana mai cewa"A'a a'a Kema kin so rashin gaskiya tun farko Yaronnan sai da ya baku uzirinsa,wacce ta ke matsayin mahaifiyarsa ce bata da lafiya,kuma ba a wannan Garin take ba,ita kuma Hibba tana buk`atar kulawa,ta na buk`atar wani a kusa da ita,shi kuma ba shi da kowa anan kuma ba mazauni ne ba,ko kun fi so ya barmu `yar ku ita kad`ai a Gida duk abinda zai same ta ya same ta,shin haka ne manufarmu ku ko wani abu na daban ?". "Bar su kawai su fad`i duk abinda suke so ,amma ina so su kwana da sani Hibba ba inda zata har sai bayan ta haihu, maganarsu kuma ba abinda zata sa ko ta hana", Cewar Mama Hadiza ran ta a `bace. Ummie Maryam ce ta matso kusa da ita tana mai cewa," Dan Allah Mama ku bar wannan maganar haka a barta ta wuce,babu dad`i ace a Gidannan ake wannan hayaniyar, bai kamata ba", Tunda su ka fara wannan hayaniya Hibba ba ta iya cewa komi ba sai faman zubar da hawaye kawai ta ke,ita kanta ta rasa me tayi ma Baba Asabe da har ta tsane ta haka ko dai don rashin Auren d`anta da ba tayi ba ne ba oho. Shigowar Baba Malam ne yasa rikincin ya kwantawa bayan ya ba Baba Asabe rashin gaskiyar abinda ta aikata, kana ya sallami kowa ya bar gun,Ummie Maryam ce ta tafi da Hibba d`akinta tana lallashin,gami da janta da hira ko da wasa ba ta bar ta ita kad`ai ba balle har ta samu damar tuna abinda ya faru ko barin shi a ranta. *Bayan wasu kwanaki* "Gaskiya wannan tafiyar ta ka ta yau tayi sauri ka iso da wuri". "Na ta so da wuri ne,saboda ina son in yi shearing d`in happiness d`in da na samo tare da ke"," Masha Allah na ta ya ka murna tun kafin inji me muka samu". "Grandma ta samu sauk`i an sallameta yanzu haka suna Gida ita da Cecelia ,tana tafiya da k`afafunta ba tare da taimakon k`arafa ba", ya kai zancen fuskarsa na washewa da mad`aukakin farin ciki. " Kai Alhmdllh Masha Allah wannan labarin yayi dad`i,ko ba komi hankalin mu gabad`aya zai kwanta tunda Grandma ta samu sauk`i komi zai koma normal ". " Sosai ma wani k`arin abun farin cikin na yi magana da Mahaifin Samuel wanda zai Auri Cecelia mun sasanta yanzu ya yarda za ai bikin su nan da wani lokaci". "Ikon Allah wannan shi ake kira da dad`i kan dad`i ga Grandma ta warke kuma ga shi za ai Auren Cecelia ba abinda zamu ce da Allah sai Godiya mara adadi domin hakan duk kad`an daga cikin iko,buwaya,k`udira da kuma izininsa". " Haka ne my wife nasani shi kad`ai ke da iko gami da izinin aikata abinda ba kai zato da tsanmani ba,domin a cikin mu babu Wanda yai zaton Grandma zata sake taka k`afafunta, haka kuma babu wanda ya sa ran Mahaifin Samuel zai sauko ya yarda ayi Auren d`ansa da Cecelia kasancewar sa mai tsananin lafiya akan duk abinda ya ce,amma sai gashi Allah ya tankwasar da Zuciyarsa har ya amince da za ai Auren ". " Haka ne gaskiya domin ni kaina yanda kake bani labarin yanayin yanda yake behaving in ka je masa da maganar dai-dai to a tsakanin ku abun har tsoro yake bani". "Wallahi kam,hakan ba k`aramin imani ya k`aramin min ba"," Ai haka ake so,duk abinda ya faru da kai a rayuwa ba hakanan banza ya je zuwa ya tafi ba, dole akwai wani darasi da ake so ka amfana da shi,walau darasi mai kyau ko kuma akasin sa". "Amm na kwaso gajiya ya kamata in zo in tafi, 9pm kar dare yai min sosai"," To shikenan my darling husband Allah ya tsare min kai ". "Amen amma kin san me ?", ya cigaba batare da ya tsaya ba," Ji nake kamar kada in tafi ko dai zaki shirya mu tafi can Gidan mu mu kwana tunda kin ga Gobe Sunday,in ya so sai in dawo da ke ranar Monday early in the morning". Zazzaro Ido waje Hibba tai kafin ta ce da shi,"Ni dai babu ruwana ,ko ka manta Kaine ka kawo ni ka ce sai bayan na haihu zamu koma","To mene ne Dan kin je kin kwana d`aya ko biyu kin dawo Gidan ki ne fa can inda zamu". "Wannan ai rashin kunya ce taya ma zan iya fuskantar Mama da irin wannan Maganar kai ko Ummien Jaheed ba zan iya tunkara da irin wannan zancen ba". `Bata fuska yai alamun bai ji dad`in abinda ta ce ba ya ɗora da cewa," To shikenan na hak`ura tunda haka ki ka ce ya zanyi, I don't have anything to say tunda haka Macen da nake kira da My Woman ta za`ba min". Sai da Hibba ta kama hannunsa ta rik`a kafin ta fara bashi hak`uri, "Bayanda zan yi ne abun na da nauyi ne sosai fiye da yanda za kai tunani,ko ka manta we are Hausa Fulani people an sanmu da kunya fa". Murmushin gefan baki yai kafin ya ce," one day it may kill you,this shame ba hmmmmmmmm it may kill you,in dai zaki cigaba da biye ma wannan k`ananun abubuwan na ku". "Hhhhhh ba abinda zai same mu, ai halayya da d`abi'u ne masu kyawun gaske". " Raba ni da su,ba gasu a ta dalilin su ba ,za ki bar Mijin ki cikin kewa da kad`aice ba,kuma alhalin ko ke nasan kina son Mijin ki tunda gashi na gani a idon ki". "Lah...lah..lah ni dai ban ce ba,yaushe ma na fad`i haka?"," Kin fad`a mana ni naji da kunnuwana","Na fad`a kuma a yaushe ?"," Kin fad`a mana","Ni dai wallahi ban fad`a ba","kin fad`a mana","A'a ban fad`a ba". Rau-rau tayi da idanunta ganin dagaske yake,"Kin ga I'm sorry da wasa nake maki ba ki fad`a ba ni ne na fad`a",Sai da ta kai mashi duka kafin ta ce da shi ni ba ruwana sa kai tunda haka ka koma ",ta kai zancen tana mai mik`ewa tsaye. " Haba Haba ke kaman taya za ai kice baza ki yafe min ba kefa Mace ta Gari ce fa","Hmmmmmm Na gano ka dad`in baki ko, to ba za ai hak`urin ba","Haba ni ne fa kuma ina wani laifi don Miji yayi ma Matarsa dad`in baki ?". "Hhhhhh shikenan naji sarkin wayo Na hak`ura mu je in raka ka kar da kayi dare"," To mu je tunda kora na ki ke. Sai da Hibba ta ja gefe guda kafin ta ce,"Ya Salam wai yaushe ka koma haka ni ban sani ba". "Afuwan kar ki ce kin fasa raka ni,mu je na tuba". Kamar ta ce da shi wani abu kuma sai ta fasa ,amma sai dai me ko da wasa ta kasa iya d`aga k`afarta guda. Yanayin yanda ta fara yamutsa fuskarta ne ya sa ya tambayeta,",lafiya me yake damun ki,ko kina jin wani ciwo ne". Kafin ka ce me tuni Zufa ta rufeta da k`yar ta iya sanar da shi abinda yake damun ta," K`afata,marata Na kasa ita tafiya". "Innalillahi, mai ki ke so,me zan miki, da me zan iya taimaka miki",gaba ki d`aya duk ya rud`e. Ka kira min Ummie Maryam ko Mama kai ni ko wa ma zaka Kira ka kiramin ".. A ruɗe gami da sauri ya fito,Allah ya tai make shi ya na fitowa ya hango Ummie Maryam ta taso k`eyar Jaheed daga wajen Mama Hadiza, tun d`azu take neman shi ya zo ya kwanta ashe yana can ya addabi Mama Hadiza. " Lafiya nagan ka a cikin irin wannan yanayin ","ba lafiya ba Hibba ce....Hibba ce ban dan meke damun ta ba". Kafin ya k`arasa magana tuni Ummie Maryam ta kai cikin d`akin,sanda zau shigo d`akin har ta kamo ta jikinta,"Ka ga maza je ka fiddo motor Haihuwa za tai,dama tun ɗazu na kula da ita,sai faman yamutsa fuska ta ke,amma da na tambaye ta sai ta ce min ba komi". Ko da ya fita daburcewa yai kamar Wanda ya manta hanyar fita Gidan,inda Allah ya taimake su ,tun kafin su je ko ina nak`udar tai tsamari bayan wani lokaci ta haihu a cikin Gida ba tare da sun je asibiti ba,ta haifi `yarta mace,zo ka ga murna bakin mutanen Gidan,karma Muhammad Jaheed da gani yake kamar shi kad`ai akai ma haihuwar. Sai washe gari sannan Abbakar ya samu damar ganin Babynsa sosai da sosai, sosai ya zuba ma ta idanu sosai yake jin sonta na k`aruwa a cikin Zuciyarsa shi har wata ajiyar Zuciya yake. "Lafiya na ji kana ajiyar Zuciya sai ka ce wanda bai ta`ba d`aukar Baby ba "," Na ta`ba d`aukar Baby mana amma irin wannan ce ban ta`ba d`auka ba,idan na tuna wannan `yata ce sai inji kamar ba wani wanda ya kai ni samun kyauta mai girma ,wacce ta can-canci alfari a duniya sama da ni,Na kan k`ara gode ma Allah game da bani wannan kyautar da yai wacce ba kowa ya ke baiwa ba". Hibba kam ba abinda ta ke sai binshi da kallo fuskarta d`auke da murmushi,"Kin ga matso mu gani cikin ni da ke da wa take kama". "Hmmmm wannan d`iyar taka na rasa da wa taje kama ga dai mutum nan amma ban san da wa take kama ba,Na ga dai hancin ta kamar irin naka ne","Uhmmm haka ne idanuwanta ta kuma irin na ki ba". Dariya Hibba tai kafin ta tambaye shi da gaske ya ke," Da gaske na ke, k`ara kallon ta ki gani,kin gani shape d`in sa iri d`aya ne",cikin murna Hibba ta sake zuba mata Ido kafin ta ce,"Lah wallahi haka kuwa,to bakin ta kuma na waye ?",su duka biyun suka sura mata ido don son gano bakinta kuma irin Na waye. Hibba ce tai zaraf ta ce,"Irin Na Cecelia ne",sosai Abbakar ya zaro idanun sa waje tare da ambaton Cecelia kuma? "Eh mana kalla ka gani". " Ta`b indai haka ne kina da aiki tun wuri ki mata nasiha kar ta biyo halin Cecelia because she so disturbant, bata jin magana ga tsiwar tsiya". "Ai Kaine zaka ji da ita in ta tashi tsiwar ta ta"," I'm out babu ruwana a ciki","Hmmmm da ruwanka kai ba ma ruwa ba har ma da tsakinka akwai,kasan me ?". " A'a sai kin fad`a","Jaheed na rok`on alfamar ka bar shi ya za`ba mata suna","Wannan ai ba wani abu ba ne ba,ya za`ba mata in ya so sai ai mata hud`uba da shi ". " Kai amma na ji dad`i Na gode sosai ban San da wanne baki zan iya nuna maka irin yanda na ji dad`in wannan alfamar ba, domin jiya da ya zo ya iske ana mata wanka ya ga tawada a tsakiyar babban yatsanta na k`afarta ta dama murna yai tayi wai da shi take kama tunda shima yana da tawadar". Dariya Abbakar yai yana mai cewa,"Kin can-canci fiye da haka a gare ni shikuma Muhammad Jaheed wannan Babyn tashi ce,in yace ba mai ta`bata sai shi ai ta zauna,tunda na ga kusan tare da shi akai d`awainiyar da cikinta shima ya zama babban Yaya ". Haka dai suka cigaba hirarrakin su Wanda rabi duk akan Babyn ne da kuma shieye-shiryen ranar sunanta . Sosai Hibba da Babynta su ke samun kulawa daga wajen kishiyoyin Mahaifiyarta da kuma Ummie Maryam hatta da matan yayyanta ba a barsu ba,hatta da Yayanta Nasir wanda daga shi sai ita,da ke karatu a Kaduna sai da ya zo ganin baby. Ranar suna Baby ta ci suna *JADEEDA*,lokacin da aka kai Babyn ayi mata askin suna ne Baba Asabe ta bi su ta sa Wazamin yai mata tsagar Gidan ta rumanci wato eleven eleven,sanda aka dawo da ita sai faman canyara kuka take. "Hibba na ga Babynnan kamar anyi mata tsaga ?", Cewar Anty Na'ima Matar Yah Mustapha ta biyu. " Tsaga kuma akan me za ai mata tsaga in ba neman fitina da tashin hankali ba,to wai wama yasa akai mata tsagar,tsagar da tun-tuni Baba Malam ya hana ya ce haramun ce".Cewar Yayah Hanne ta na mai tambayar Jidda da ta shigo da ita. "Ni dai babu ruwana Baba Asabe ce ta sa ayi mata wai ai ba ta da dangin Uba gara a rufa mata asiri a yi mata tsaga hakan zai sa a rik`a zaton ko `yar wannan ahalin ce". "Mene!? aiko yau ba zan kyake Baba Asabe ba,don naga abun nata k`ara cigaba yake,ta ya meye had`in ita wannan Yarinya da wata tsaga,ba fa Mahaifinta aka haifa a cikin Gidannan ba Mahaifiyarta aka haifa fa,yanzu me ki ke tunanin zai faru idan Abbakar d`in ya gani nasan ran shi ba zai so ba". " Kin ga Yayah Hanne dan Allah ki k`yaleta tsaga dai an riga da anyita,ba kuma zata gogu ba,ko kun manta haka ce ta faru a lokacin da Ummie Maryam ta haifi Jaheed duk da Baba Malam ya hana tsaga sai da ta sa akai mashi,wanne irin tashin hankali ne ba ayi ba a ranar,kawai ku barta so take bikin sunan ya watse,kun ga ita ba ruwanta mu ke da asara da bak`in ciki, kuma dama burinta kenan ace ba a tashi lafiya ba,in dai don tsaga ce na samu Zuma mai kyau in rik`a shafa mata har ta `bace". "Kuma da gaskiyar ki Hibba, abinda take so kenan ayi fitina din haka k`yaleta shine mafi a'ala ban manta yanda dangina suka tafi da `bacin rai a ranar sunan Jaheed ba kuma duk saboda ita ba", Cewar Ummie Maryam. " Shikenan tunda haka kuka ce amma wallahi taci bashi kuma sai ta biya shi,in ba dan Mahaifin Yarinyarnan yana da hankali da natsuwa ba ai da bamu san ina wannan abun zai tsaya ba ". Haka dai su ka dunga tausar Yaya Hanne har Allah ya sa aka tashi taron lafiya ba tare da wata hayaniya ba. Sai bayan da su Hibba su kai Arba',in sannan suka koma a lokacin tare da Muhammad Jaheed suka tafi. *JADEEDAH* (It's a story of two love birds who are so different from each other ) STORY & WRITTEN BY : (*Cwt~Sumiey*) Marubuciyar littafin MENE NE ABIN YI ? KARAGAR MULKI And now.....*JADEEDAH* https://chat.whatsapp.com/CWkZfMqvD4H0mtd7WW6Xbz https://whatsapp.com/channel/0029VapqU8C002T5Bz8RSQ0a BOOK 1 PAGE 11 ❤ *After one year (Bayan shekara d`aya)* "Auntynah barka da yamma", " Oh Cecelia ashe kin farka na lak`o d`azu na ga kina barci". "Ke dai bari Aunty gajiya ce duk ta dame ni,tunda na samu na ci abinci nayi wanka sai barci ya kwashe ni". " Ah ai dole akwai gajiya duk da ban ta`ba zuwa Jos ba nasan zai yi nisa daganan Kano "," Akwai nisa kam,wai ina my daughter take ne na ga ban jin motsinta ba ?". "Ah Jadeeda na can na samu tayi barci, kar ki so ki ji dad`in da na ji dana ga za tai barcin da ya ke ba gwanar barcin ba ce ba abinda ta kware da shi sai rikici da `barna'',dariya Cecelia ta saki kafin ta ce," ki ce tana saki aiki da yawa?","Ke dai bari ai Abbanta ya ce ke ta biyo rikici da kukan tsiya duk d`abi'unki ne". "Kai³ sharri zai min,na rantse ba behavior d`ina bane,kawai dai yana son d`ora min laifi don ganin ba idona,inanan zai same ni bari ya dawo ". " Kun fi kusa babu ruwana,yanzu me ki ke son a girka for the dinner ina son in sauri in d`ora kafin Jadeeda ta farka, ko kafin Jaheed ya dawo daga School,kin san yau weekend da yadawo zai aje kayansa ya taho nan wani time d`in ma da uniform d`insa a jikinsa yake tahowa nan, nasan ko barcin me take in yadawo sai ya tada ta,itama da ta ji muryar sa zata farka",Oh that boy da nake jin muryarsa in muna waya ?","Eh shi fa kar ki so kika ga yanda suka shak`u da juna". "Ki bari yau in muku Cooking,ki huta tunda ga k`anwar ki ta zo"," Ina wace ni ai haka ba zai yiwu ba daga zuwan ki sai in bar ki da kitchen, just mention what you need to eat yanzu za ki gan shi a gaban ki","Seriously ki bar ni in mana abinci I'm a good cooker za ki ji dad`in girki na","Na sani mana amma ki bari letter on kin yi mana amma banda yau "," To shikenan I'm give off tunda kin ce haka amma tomorrow ni zanyi,but duk da haka I need to join you,zan bi ki kitchen ɗin"," Ba damuwa Allah ya kai mu goben,amma promise me ba abinda za ki ko da munje kitchen d`in tare". Dariya Cecelia ta saki batare da ta d`auki alk`awarin ba kamar yanda Hibba ta ce, "Au ki ce baki shirya bina kitchen ba,yauwa kin ga Abban Hibba ya ce in tambaye ki ko da akwai wani abun da ki ke son siye anan Garin Kanon sai muje kasuwa mu siya ya bada kud`i yace ai amfanin da su". " No.. No...no I don't need anything, ya riga da ya bani a lot money na yi amfanin da su,kawai dai na zo ne inyi maku ban kwana ". " Mun ji dad`i sosai kuma mun gode da wannan karamcin da ki kai mana,Na jima yana cewa mai yiwa tare da ke za mu wuce can Jos d`in har a gama taron bikin". Ba k`aramin mamaki Cecelia ta yi ba jin wai tare da ita za su tafi,cikin yanayin mamakin ta ce da ita,"Auntynah biki fa sauran sati guda fa kenan ?","Eh mana na sani Cecelia, ko kin manta we are family now,ba ki da wasu ahalin da suka kaimu kamar yanda a gare mu ki ke ta musanman,don haka dole ne mu tsaya tsayain da ka akan duk wani lamari naki da ya taso mu yi iyakar iyawar mu domin mu fidda ki kunya akan shi". "Sai fa bayan Christmas da kwana d`aya sannan za a yi bikin fa"," Na San da haka Cecelia, to wai mene ne abun mamaki a ciki,lafiya lau zamu gudanar da shagalin bikin har a gama a tare da ku". "I'm so surprised sister Hibba ban ta`ba expecting d`in haka daga gare ku ba,ni duk anawa tunanin ba za ku samu halatar bikin ba tunda mun kasance masu mabanbanta Addini,a tunani na addinin ku ba zai bar ku ku halacci bikin ba". " A'a Cecelia si Addinin Muslunci baya raba kan `yan'uwa ko kuma ya `bata zumunta,hasalima shike k`ara k`arfafa su,ina mai tabbatar maki tare da Yayanki za a d`aura Auren ki,ba za ki rasa shi a matsayin dangi ko ahalin da ki ke tak`ama da shi ba, har yau har gobe yana tare da ku". Da gudu Cecelia ta k`arasa kusa da Hibba ta rungume ta ta mai kasa iya cewa da ita komi har sai daga k`arshe ta fara yi mata godiya, "Thanks a lot ina Godiya sosai godiya mai tarin yawa,ita kanta Grandma za ta ji ddad`i gami da farin cikin jin wannan labarin". " Ki ce da na sani ban fad`a maki ba kawai sai dai ki ga mun fara shiri","A'a gara da kika fad`a min yanzu don da ban san wanne irin abu ne zai same ni ba kan murna da farin ciki ". " Kin ga bari in tashi in d`ora girkinan tun kafin `yar rigimata ta farka",da haka su ka canza akalar firar bayan sun shiga kitchen d`in a tare don girka abinda za su ci. ₹₹₹₹₹₹₹₹₹₹₹ "Haba Ummie Maryam wannan fad`an ya yi yawa,Yaro ne fa har yanzu"," Hibba Na ga ji wallahi,wannan bak`in ran har ina,tun jiya ya sa maganar tafiyar ku Jos shikenan ya rasa sukuni,kuma ya sani Abbansa ba zai bar shi ayi tafiyatnan da shi ba saboda School, suna k`arshe term ne kuma gashi in kuka tafi zaku dad`e amma ya k`i hak`ura nayi lallashin na yi ban bakin amma duk a ban za". "Haba Jaheed tun yaushe muka gama wannan maganar da kai ba na ce kar ka damu ba,everything will be OK zamu dawo da wuri,ko dai so kake in fasa tafiyar ne ?", Da kai ya bata amsa ba tare da ya bud`e baki ya ce wani abu ba,"Kin ga ni ko hatta miskilancin nasa yau ya motsa,ina ganin wata k`ila sai dai ki bar mashi Jadeeda anan ke ki tafi ke kad`ai". Cecelia ce ta matso kusa da shi ta na mai dafa kafad`arsa tare da cewa," Haba my friend don me za ka sa kan ka a cikin damuwa,hakan bai kamata ba,I promise da zaran an gama biki za su dawo,they will be back soon". "Kin tabbata dagaske ki ke ?", ya tambayeta yana mai tsareta da idanuwansa,"I'm sure Hundred percent zasu dawo da zaran an gama biki,ba zan barsu su k`ara zama ba,Crying Baby d`in ka kuma ba zan bari wani abu ya same ta ba,ko kuka ba zan bari ta yi ba" Sai a lokacin ya d`an saki fuskarsa,"Ikon Allah ni narasa wacce irin shak`uwa ce tsakanin Jaheed da kuma Jadeeda ko da yake shak`uwar da ke tsakanin ki da shi ne ta koma kanta". ''Yamma na k`ara yi bari mu zo mu tafi,sai kuma Allah yai mana dawowa,My Boy ka kula min da kan ka ka ji,in sha Allah zamu dawo lafiya". "Momynah mu je in raka ku,sai driver ya dawo da ni", Jaheed ya kai maganar ya na mai kama hannun Jadeeda su kai hanyar fita,kasancewar ta Na cika Shekara d`aya ta fara tafiya, saboda k`iriniyarta, sai faman zuba mashi gwaranci da ba a ganewa ta ke,sai da suka koma sashen Mama Hadiza suka zauna gami da sake yi mata ban kwana kafin su fito su tafi. Har farfajiyar Gidan Mama Hadiza ta rako su,gami da yi masu tarin Addu'o'i. "Ikon Allah Hibba, yanzu ke ko kunya ba ki ji ace da wannan arniyar ki ke jerawa kuna tafiya har ma kina bata `yar ki ta d`auka,gaskiya na yarda baki da hankali da ace kina da hankali da ko bangon Gidannan ba zaki bari ta shafa ba balle har ki shigo da ita cikin Gidan ko kuma ta samu hanyar ko damar da zata ta`ba miki d`iya ba", Cewar Zaliha da ita ma ta fito da shirin tafiya Na ta Gidan. " Ahaf ai ke kya fad`a a zauna lafiya da nice na fad`i wannan zancen da yanzu an taso min kamar za a cinye ni d`anya ba gasassa ba,wani dan jin dad`i sai yace k`azafi nai masu ko kuma neman fitina nake". "Omg da wa wannan Matar ta ke,kar dai ace da ni take,kar a ce ni take Kira da Arniya?". " Kin ga Cecelia na rok`e ki ki zo mu tafi,kar ki biye mata ki zo mu tafi". "Gaskiya babu inda za ni har sai ta gaya min dalilin da yasa ta kirani da Arniya kuma a saboda wanne dalilin ne zai sa a hana ni d`aukar d`iyar d`an'uwana ,sai naji dalilin". " A'a dan Allah ki barta ki zo mu tafi,kar ki biye mata".... "A'a Hibba ki barta dan Allah, ai mu yau abun murna ne ace yau an samu wanda zai maida masu da murtani ki barta". "Ke Yarinya kar ki min rashin kunya,dama Na sha jin ance ba kunya ce ta ishe ku ba,balle a kai ga kan tarbiya".... "Haba dan Allah Yayah Zaliha me ki ke aikatawa haka sai kace wata mara hankali ko mara ilimi". Baki bud`e Yayah Zaliha ke bin Alk`asim da Ido gami da rasa abinda zata ce da shi," Alk`asim ni kake kalla ka danganta da kalmar hauka da kuma rashin ilimi, Anya kuwa kai ne ?". "Na fad`a fiye da haka ma zan kira ki da shi,in ba haukan ba mai zai sa ki furta duk abinda ki ka furta ko so ki ke ki zama silar tashin wata sabuwa fitina a cikin Gidannan wacce ba zamu iya kashe ta ba,in kuma rikicin Addini ki ke son tadawa sai ki sanar da mu mu sani tunda wuri". ''Au Alk`asim me nake gani haka,ashe kai ma an shanye ka ban sani ba?"Baba Asabe ta tambaya cike da mamakin abinda ta ga yayi. " Ka ga Alk`asim ka fita a cikin wannan maganar kar abun ya girmama,don wallahi hak`uri na yafa k`arewa".cewar Hibba "A'a Hibba Dan Allah kar kice haka, kiyi hak`uri kin ji", kallon shi ya maida hankalin shi kan Cecelia da ke ta faman `bata rai,da son barinta ta bi kadin laifin kofin zarafin da akai mata. "Kin ga please and please Sis kiyi hak`uri,don't mind her shi's out of her senses,please Dan Allah", sai a lokacin Zuciyar Cecelia ta fara yin sanyi ,kallonta ta maida kan Yayah Zaliha yanda taga tana ta `ba`batu da hayaniya yasa ta yarda da Maganar Alk`asim cewar bata da hankali, bai bar su ba sai da ya tasa k`eyarsu ya fitar da su daga Gidan daga ita har Hibban,daga k`arshe ma har cikin motar shi yasa su ,shi sa kan shi ta maida su Gida,bai bar Cecelia ba har sai da ya ga ta yarda gami da sakankancewa Yaya Zaliha ba ta da isasshiyar lafiya sannan ya tafi,gami da gargad`ar Hibba akan kar ta kuskura ta sake tada batun ta bar shi su tafi a haka,. Ko bayan tafiyar Hibba ta je da niyar ta bata hak`uri, dakatar da ita tayi gami da nuna mata ta riga da ta fahimci daga inda matsalar ta ke,komi ya riga da ya wuce a wurinta. Sosai Hibba ta ji daɗin hakan nan ta barta domin ta je ta sauke Sallahr da ke kanta,ita kuma ta fad`a bathroom don tai wanka,tun kafin ta fito ta fara jiyo wayarta Na faman ringing a gurguje-a gurguje ta fito ta nufi inda wayar ta ke. "Oh my friend Gloria how fa now ya ki ke,I miss you". "Ina lafiya k`awana gobe nake son in taso saboda ina son ayi komi na bikin ki tare da ni"," Yeehhh Na ji dad`in haka sosai shi yasa na ke k`ara sonki". "Hmmmm ai dole ne in yi ina Broth Daniel yake fatan dai yana lafiya, kin san har da son sanya shi a Idona da nake ya sa nake son halartar bikinnan da wuri,bana so a ce ya zo bamu had`u da shi ba,kin san har yanzu ina jin sa a cikin raina na kasa iya mantawa da shi"...." Gloria Anya kuwa...,wai me ya ke damun ki,kin fa san Broth Daniel yayi Aure yanzu ma haka yana d`iyarsa ba za ki kyale shi ki huta ba,ki samawa kan ki lafiya Kema ki fiddo Miji mai sanki ki aura ba,kar fa ki manta ba addinin mu d`aya da shi yanzu ba ". " Cecelia ba zan iya ba,ba zan iya cire son Daniel daga cikin Zuciyata ba kuma ni Addinin shi bai dame ni ba,in har zai Aure ni,kuma wai tsaya ba Mace ce ta yaudare shi har ya bar Addinin sa na gaskiya ba,to ba kya tunanin haka nima zata kasance ta nawa `bangaren ba". "Hehhh Gloria I'm swear ba ruwana ,kin san yanda yake Son Matarsa da `yarsa kuwa,domin yanzu haka ina Gidan su Gobe za mu tafi Jos d`in tare". Zumbur Gloria ta mik`e zaune daga kwancen da ta ke,tace," Seriously da gaske ki ke Cecelia ",sai da Cecelia ta d`an `bata fuskarta kafin ta bata amsa da cewa," Eh mana da gaske nake kin san ai ba zan maki irin wannan wasa ba". "Na sani....na sani Cecelia, but ina neman alfarma a wurin ki na had`a ki da Allah kar ki cemin a'a, ban san mai zai faru ba in baki amince ba".ta kai zancen muryarta na marairaicewa. " Shikenan shikenan faɗamin me ki ke so a garuni,amma ki sani idan har abun akwai cutarwa a cikin sa ba zan yi ba". "No...no there are no any harm in it,kawai dai ina son zan biyo flight gobe ya sauke ni nan Kano, ke kuma sai ki san yarda za ki sa Broth Daniel ya yarda ya amince mu tafi tare da shi zuwa Jos a motar sa".... " Wait.. Wait.. Kina nufin gobe tare da ke zamu yi tafiya tundaga nan Kano har zuwa Jos ?". "That's my friend haka nake nufi",shiru na wani d`an lokaci kafin tace," Anya Gloria ba wani abun a `boye ki ke shiryawa ba da har ki kai saurin yanke wannan hukunci a wannan short time d`in ba". "Oh Jesus na rantse maki ba abinda nake shiryawa kin san ni fa you know me,duk abinda zan iya aikata kin sani,just one thing I know ina son ganin sa,ina son in ganni a kusa da shi kin san mun yi taking d`in long time ban gan shi ba". Shiru Cecelia tai tana,mai son gasgata abinda Gloria tace da ita,horns d`in motar sa da ta ji ne ya sa ta yanke hukunci cewa da ita," let me try but amma ki sani ba zan wani zafafa duk hukuncin da ya yanke ya yanku,zamu d`auke shi a haka kawai ". " Eh I'm agree Na yarda",Gloria tace ta na mai saurin a je wayar tana mai rufe idanunta gami da had`e hannayenta wuri guda ta fara addu'ar samun nasara. "My Broth har ka dawo?",ta tambaye shi tana mai kama kanta alamun tana da abinda take son cewa," Are you OK Cecelia, ko da akwai wani abun da ki ke so ne?". In'ina da kame-kame ta fara Wanda har sai da ya sa gaban Hibba fad`uwa don ita a tunanin ta ko abinda ya faru a Gidan su zata sanar ma sa da shi,kafin ta bud`e baki ta samu damar dakatar da ita har ta riga da da cewa. "You know my friend Gloria wannan neighbor d`in nan ta mu,...wacce na baka labarin sun koma Lagos da zama?"ta,kai zance a d`an d`arare. " Oh Gloria your best friend ?","Yauwa ita mun yi waya da ita ne d`azu take cemin gobe zata bi flight daga can Lagos d`in zuwa Jos don tai attainding my wedding ceremony ,amma yanzu cikin rashin sa'a ta kirani ta ce bata samu ba sai flight d`in zuwa nan Kanon,ta ce min tana son zuwa amma ba ta da wata hanyar,da zaran ba ta samu wannan damar ba shikenan ba za ta attainding ɗin bikin ba, shine na ce in ba damu in tambaye ka ta biyo flight d`in zuwa nan Kanon in yaso sai mu tafi can Jos d`in tare da ita,idan ba damuwa,domin na dakatar da ita na ce sai na tambaye ka". "Oh Cecelia me ye abun damuwa a cikin wannan, bikin ki fa zata zo,AI ko daga Lagos d`in tace inje in d`aukota ai zan je in d`aukota balle kuma daganan zuwa Jos, kar ki wani damu ki ce mata ta shirya ta taho kawai abinta zamu jirata", wani tsalle Cecelia ta daka tana mai fad`awa jikin sa gami da jero nasa godiya kala-kala. " Kin ga sake min Miji kar ki je ki karya min shi",Hibba tace tana mai k`ok`arin rabata da jikin sa,"Kai Sis duka ni d`in nawa na je da zaki ce zan karya shi ?","A'a ba anan take ba,yanzu sai ki ga tsautsai ya gifta ki bar ni da Allah yai abun,bayan ke kuma fa naki Ango na can sabo dal yana jiran ki". Rufe fuska Cecelia tai ta nufi d`akinta tana mai had`awa da gudu ,wayarta ta d`auka gami da kiran Gloria kamar jira taje ta d`aga tare da cewa,"My friend what is the feed back fatan dai anyi nasara ?","Yeeee we succeed mun yi nasara",wata k`ara mai k`arfi Gloria ta saki gami da mik`ewa tsaye ta fara tsalle akan gadonta,Wanda wannan k`arar ce tasa Cecelia saurin kashe wayar ta. *JADEEDAH* (It's a story of two love birds who are so different from each other ) STORY & WRITTEN BY : (*Cwt~Sumiey*) Marubuciyar littafin MENE NE ABIN YI ? KARAGAR MULKI And now.....*JADEEDAH* https://chat.whatsapp.com/CWkZfMqvD4H0mtd7WW6Xbz https://whatsapp.com/channel/0029VapqU8C002T5Bz8RSQ0a BOOK 1 PAGE 12 ❤ "Wawooooo my friend you look so awesome, kin ga yadda skin d`in ki ke shining and glowing wai mene ne sirrin ?". "Yeehh Thanks my dear it's a God luck,bayan haka ba wani abu,amma na gode da yabon ki", ta kai zancen ta na nai jujjuya jikin ta,ta d`an dakata ta na mai cewa," Ina my love yake na ji ban ji motsin kowa a Gidan ba". `Bata fuska Cecelia ta yi kafin ta ce da ita,"Za ki fara ko,kin san na fad`a maki bana son irin haka tunda farko,Na gaya maki Broth Daniel yana san Matar shi,kuma ma Matarsa na son shi,Matanan fa bahaushiya ce kuma kin san halin Hausawa ba sa da kirki ko mutunci in dai akan Mazajensu ne". Yamutsa fuska Gloria tai kafin tace,"I swear bata gabana,haka kuma duk abinda za tai ba zai tsorata ni ba ko da ko kan bala'i da masifa zata rik`a cizon sama ne,muddin Daniel zai nuna yana sona ta nayi alk`awari sai na Aure shi ba tare da duba da ita ba,Matsala d`aya ace bai nuna interest d`in sa a kaina ba".. "God for bid in dai Broth Daniel ne ma ba zai nuna ba domin kin san ni bana son tashin hankali, ba zan so ki zama silar tarwatsa farin cikin da yake samu a Gidan shi ba". Cikin mamakin jin abinda ya fito daga bakin,ta ce" Cecelia me wannan maganar taki take nufi ,kaddai ace kina nufin kin fifita wannan baren kaina,kamar fa haka maganganun ki su ke nunawa,in ko haka ne".....ta dakata sakamakon jin nuryar Hibba na cewa, "Ba dai har bak`uwar tamu ta iso ba,a sannu da zuwa your highly welcome". "Yauwa sannu Aunty ya Gida mun same ku lafiya,ya kuma shirye-shiryen biki ?". " Alhmdllh kumi na tafiya yanda ya kamata, ki samu wuri ki zauna Cecelia ya akai ki ka barta a tsaye ,yauwa gama breakfast can ki had`o mata may be ko tana jin yunwa kinsa ba kowa ke son ya ci abinci a yayin da zai tafiya ba",ta kai zancen tana nai maida kallonta akan Cecelia. "Muna gaisuwar yaushe gamo ne shiyasa, amma bari in had`o mata", tayi hanyar derning d`in har ta fara bud`e wermars d`in abincin ta dakata ta na mai cewa," Amma dai Broth fita yai naga kamar ban ga motorn sa a waje ba?". "Eh fita yai ya samu urgent call ne a office shiyasa ya tafi can ko breakfast bai yi ba". "Eyyah nasan hankalinsa nanan domin ya ce min baya san mu yi dare a tafiyarnan".... Cikin rarraba zance Gloria ta dakatar da ita da cewa," Am...uhmm...ki bar zuba abincin ina so zan yi using resting room,in..Na fito sai ki zuba min". "OK badamuwa muje na raka ki",koda shiga Gloria bathroom kai kawo ta farayi tana mai cewa," Ya zanyi,ta ya zan iya dakatar da Cecelia daga zuba abincin nan I need to eat with Daniel, Na kwashe almost a year ban had`u da shi ba,yau na samu damar da zanci abinci tare da shi ya za ai in wasa da ita,No haka ba zata faru ba I will use this opportunity I can't not lost it ". Shiru-shurun da Cecelia ta ji ne yasa ta fara knocking bathroom d`in ta Na mai kiran sunan Gloria,"Are you ok,Na ji shiru har yanzu ba ki fito ba ?"," I'm coming" ta bata amsa a tak`aice. "Dem it,wai me yake damun Cecelia ne,Anya kuwa zata Goya min baya in samu hanyar da zan mallaki Daniel kuwa I don't think so,bana tunanin haka,amma ko in har ta juya min baya ta biye ma wannan Hausa girl d`in nan ta ci amanar zaman tare,dan haka ba zan barta ba,dole zan bi komi har in gano abinda ke cikin Zuciyarta sannan in yi maganin su gabad`aya", wannan duk maganganun da Gloria ke yi ne a cikin Zuciyarta. K`arar bud`e Gate da shigowar Motar shi cikin farfajiyar Gidan ne yasa Gloria saurin nufar hanyar fita daga bathroom d`in bayan murmushin cin nasara ya bayyana a kan fuskarta. "I'm sorry Beb I keep you wait cikina ne ya d`an `baci that's why", Gloria ta kai zancenta tana mai sosa k`eyar ta. "Hhhhhhhhh my friend kenan k`ya gama `boye-`boyen ki I know you,I kno everything, ke dai kawai ki ce kina son ki yi breakfast da my Broth,ba sai kin shiga bathroom kin rufe kan ki ba".ta kai zance cikin yanayin tsokana. " Au Abar tsokana ma Na zama wurin ki ko,za ki shiga hannuna ne"...."Oh sorry ba haka nake nufi ba,biside ma ai ni banga laifin ki ba you can fight for you love,but I beg you kar ki tada mana wata fitina ki bari mu gama wannan bikin lafiya lafiya daga baya sai musan me zamu yi". "Okay I promise you babu abinda zai faru,har mu gama wannan bikin lafiya, dama babban burina ki bani goyan baya a cikin wannan tafiyar nasan in har hakan ta faru zanyi nasara",sai da Cecelia ta dafa kafad`arta kafin ta ce," Don't worry I'm with you always, I will support you hundred percent, zamu shirya komi yanda ya kamata,sai mun dawo da Broth Daniel kan hayar da ta dace,ko kin manta shi kad`ai ke gare ni da zan iya Kira da sunan family taya zan barshi ya su`buce min,sai dai ki sani a can k`asan Zuciyata ina jin tsoro kar Garin ean in dawo da shi cikin rayuwata ya su`buce min gabad`aya ". "In Jesus name haka ba zata faru ba,komai zai tafi smoothly yanda muka tsara". Shigowar Hibba sa`be da Jadeeda da ta koma barci ta dakatar da su daga zancen da suke yi," Am kuyi hak`uri Na shigo muku without a knocking ba na son in yi knocking k`aryar ta tashi Jadeeda daga barci,domin barcin bai nisa ba,ku fi to muyi breakfast d`in Abban Jadeeda ya dawo yana jiran mu".ta kai zancen Zuciyarta na son hasko mata wani gi`bi da ta hango a cikin zancen na su,A'uxiyya tai gami da watsar da zancen da Zuciyar ta ta take tsamata don son kyautata masu zato,kamar yanda Addini ya koyar. "Am sorry Sis mun tsaya firar yaushe gamo ne,kin San an kwana biyu ba a had`u ba", murmushi Hibba tai tana mai juyawa tayi gaba a tare su ka nufi hanyar zuwa dining d`in,tunda idanun Gloria suka sauka akan fuskar Abbakar k`afafuwanta su kai mata wani irin sanyi,kwarjini,kamala da haibar da ta gani kwance akan fuskar suka sa Zuciyarta ta fara bugawa da sauri da sauri,a d`arare ta iya zama kan d`aya daga cikin kujerun wurin,muryarta hard`ewa ta ce da shi," Brother Daniel Good morning " "Morning Gloria how are you and how about you journey ?". "Bro everything are okoy,kasan flight Na biyo so that's why tafiyan bai wani wahalar da ni ba"," That's good Na ji dad`in hakan,what about Pastor Emeka,Momy Rebecca and your brother Richal ?",'Ahhh they're fine duk suna lafiya,kasan Dad ya samu k`arin girma tun da dad`ewa, Momy ta zama woman leader a Church d`in da Dad ke jagorantar,My Brox kuma ya na Canada karatu". "Masha Allah labarin yayi min dad`i komi na tafiya yanda ya kamata,what about you,wanne mataki ki ke, je a yanzu?". Wannan tambayar ba k`aramin dad`i tai ma Gloria ba har wani blushing tafara yi gami da k`ara gyara zaman rigar jikin ta kafin ta bashi amsa da cewa," Na fara masters anan Herbal institution dake nan Lagos ".... " Haba mana my Brox,ya isa haka mana ,ku dakatar da wannan hirar mana ko kun manta muna da tafiya mai nisa a gaban?","Hehhh Cecelia mene ne haka,shin kina son raba hirar zumunta ne komi ?,mu fa d`au long time ba mu had`u ba". Dariya Abbakar yai kafin ya shiga tsakanin su da cewa,"Bar ta zumud`i take ta na son zata ga groom to be d`inta kin san ta yi spending almost a ten days ba tare da ta gan shi ba". Baki sake Cecelia ta bisau da kallo ita kanta mamakin jin zancen da ya fita daga bakin sa tai,sosai suka zage shi da Gloria suna tsokanar ta,duk abinda ke faruwa Hibba na can tana son barcin Jadeeda yai k`arfi bata san abinda ke faruwa anan Parlour ba. Abbakar ne ya cire baki ya na nai kiranta da cewa,"Madam a zo a bamu abinci we are felling hungry ",sai da Hibba tai k`asa da muryarta kafin ta mai do mashi da amsa da cewa," Please I'm sorry ina so barci Jadeeda yai k`arfi ne,but please Cecelia ki yi sarving d`in ku kafin in zo ". Zaraf Gloria ta mik`e tana mai cewa,"A zauna bari in Sarving d`in ,Na hutashshe ki", Jiki a sanyaye Cecelia ta koma ta zauna ta bar Gloria da sarving d`in su domin ba zata so suyi jayayya a gaban Broth Daniel ba,don gudun kar ya fahimci da akwai wata a k`asa,tunda yasan ba hakan a tsakanin su a can baya. Gab da Hibba za ta isa dinning wayar hannunta ta fara ringing, ganin kiran Mama Hadiza ya sa ta fad`ad`a murmushinta kafin ta d`aga ta fara gaishe ta," Ina lafiya Auta ashe har yanzu baku tafi ba ?","Eh Mama yanzu dai muke shiri zamu tafi ya mutanen Gidan ?","Duk suna lafiya yanzu ma Babanku ne ya ce in sanar da ke ranar bikin Ummien Jaheed, Yayar ku (Yayah Hanne ta ke nufi bata fad`in sunan ta),da kuna Umma Jamila za su zo nan Jos d`in su taya ku murnar gami da Allah sa alkairin ". " Kai Mama na ji dad`in haka sosai Allah ya saka maku da alkairi ya biya buk`ata ya kuma baku aljanar fiddausi","Amen Allah ya kai ku lafiya ya dawo da ku lafiya","Amen Mama,kin ga kuwa da na sani ai da na kawo Jadeeda nan in su Ummie Maryam zasu taho sai su taho min da ita"......"Ahir d`in ki Hibba, ba ki da hankali ne Yarinyar `yar shekara d`ayar za ki aje ki tafi wani waje har na tsawon kwanaki ba tare da ta Isa yaye ba". Cikin rawar murya Hibba ta fara bata hak`uri,"Mama Dan Allah ki yi hak`uri,wallahi haka nan na ji bana son in tafi da ita,kamar wani abun zai iya samunta,gabana sai fad`uwa yake ". "Addu'a za ki yi tayi,in sha Allahu ba abinda zai faru da ke,dole za ki hak`uri ku tafi tare can ma inda za ku ahalinta ne danginta ne,suna da hak`k`i ki kai ma su ita su ganta suma,su Santa su Saba da ita". " To shikenan Mama zan yi ta yin Addu'ar kamar yanda ki ka ce,da zaran mun Isa zan kiraki","Yauwa `yar Albarka ki shafa min kan `yar rigima mai kukan banza,au na manta yau Jaheed da zazza`bi ya tashi shiyasa bai zo maki sallama ba ", "Ayyah Allah ya bashi lafiya zan kira Ummie Maryam sai in yi mashi ya jiki","To hakan yayi kyau amma ki bari sai kun isa don da yaji ba ku tafi ba zai sanya rigima", To Mamma", da haka suka yi sallama ta k`arasa zuwa dinning d`in. Zuwan Hibba dining d`in ne ya rage ma Gloria rawar kan da take,cikin k`ank`anin lokaci suka gama breakfast d`in suka sake had`a `yan sauran kayan da zasu had`a,Hibba ta goya Jadeeda, wacce har yanzu take barcinta kana suka d`au hanyar zuwa Jos daga Kano Sai da su kai tafiya mai nisa kafin Jadeeda ta tashi daga dogon barcin da ta sha,minti kad`an bayan Hibba ta yi feeding d`inta ta fara kai hank`oran zuwa Inda mahaifin ta yake,"A'a Jadeeda yi zaman ki nan wurin Momynki,ba zan iya d`aukar ki ba alhalin ina driving". Duk yanda Abbakar ya so dakatar da Jadeeda k`i tai,babban burinta ta isa gare shi,ganin an hanata ya ta fara kuka gami da ƙara son sai ta isa inda ya ke. " Dama Na sani abinda nai ta gudu kenan ke ko kusa ba ki iya zama wuri guda tsaf",Ai ko kamar ta san fad`a ta K`ara tsandarewa da wani sabon kukan. Cecelia ce ta fara cewa,"Kai³ Momy ce tai miki fad`a to yi hak`uri kyaleta ba zata sa ashoben bikinnan ba,kyauta za mu yi da nata",ta kai zancen ta na mai mik`a mata hannu,ba musu ta tafi wurinta kasancewar ta Yarinya mara k`iwa. "Wawooooo beautiful girl, ai sai yanzu naga fuskarta sosai,kai she's so beautiful,Babyn tamu kyakykyawa ce ta zarcewa sa'a", cewar Gloria,da ita sai yanzu ta gamda dominsanda ta zo ta yi barci. Murmushi kawai Hibba tai ba tare da tace da ita komi ba," Ai tukunna ma sai ma nan da wasu shekaru za ki ga asalin kyau a wurin my daughter "," Maganar ki gaskiya ce Our Father Lord ya bamu Ikon ganin wannan lokacin","Amen...Amen Gloria zan yi farin ciki in na riski wannan ranar kar ma ace in ga ranar bikinta hohoho",Cecelia ta kai zancen ta na mai d`aga Jadeeda sama wacce sai faman wasa da gashin attache da ke kanta ta ke. "Yama sunan ta ?",Gloria ta tambaya ta,na mai amsar ta d`auke ta,Cecelia da take kusa da ita ta bata amsa da cewa" Am sunan ta Jadeeda ",duk yanda Gloria ta so ta mai-maita suna kamar yanda Cecelia ta fad`a amma ta kasa,madadin ta ce Jadeeda sai ta ta ce Jedeeda. Sai a lokacin Hibba ta waigo tace da ita," Ba Jedeeda sunan yake ba Jadeeda ne, J d`in harafin a ne da ita ba e ba". "Oh Jedeeda, Na gane thanks for your correction", Gloria ta ce tana mai sakin fara'a akan fuskarta da tunanin ta faɗa dai-dai. "Ba Jedeeda ba fa Jadeeda", Hibba ta sake gyara mata a karo na biyu. Duk yanda Hibba ta so ta gyara ma Gloria sunan ta fad`a dai-dai amma hakan ya faskara,kuma wani abun Allah ita kuma ta kasa hak`uri ta barta ta kirata da Jedeedan,ita kuna sai faman mai-maitawa take. A karo na ba adadi ta sake bud`baki ta gyara mata. "Please Hibba ki barta ta kira da iya yanda bakin ta ya iya mana, tun d`azu sai faman abu d`aya ake yak`i ci yak`i cinyewa".... " Kamar ya in barta,kana nufin in barta ta cigabada da kiran sunanta da duk sunan da ya zo mata komin munin ma'anarsa".Hibba ta katse shi k`asa Zuciyarta Na yi mata zafi from no way,ba tare da ta san daga inda ya zo ko kuma dalilin zuwansa ba. "No no no I don't mean that, but she try,she can't pronounced it very well, sai ki barta haka". Sororo Hibba tatana kallon sa ba tare da ta iya cewa da shi komi ba,ba wai don ba ta da abin cewa ba ne ba,a'a mamakin furcinsa take. "Kin ga ba wai ina nufin wani abu na daban ba be ba,a'a just bana son abun yai nisa ne,but I'm sorry naga ranki ya `baci I don't mean that, kuma ke ma ai kin san ina son a kirata da sunan ko,son sunan da kuma ma'anarsa yasa na yarda har aka sa mata sunan". " Hmmmmmm si shiyasa ka bada damar da za a rink`a kiranta da kowanne suna ba tare da la'akari da kyawu ko munin sa ba,`yata fa muslmace ta ya zata rik`a kiranta da sunan kafu".....ta kasa k`arasawa sakamakon zazzafan kallon da ya jefe ta da shi. Ita kanta nan take danasani ta rufe ta, gabad`aya ta diriri ce ta rasa me ma zata ce. "Kiyi hak`uri sister it's my mistake I'm regret ba zan k`ara furta sunan ba, har sai na iya,please I'm so sorry". Ko ta,kanta Hibba ba ta bi ba,babban burinta taga ta samu hanyar da zata bashi hak`uri amma ina ko kallon inda ta ke bai sa ke ba,ranshi a `bace ya cigaba da driving d`in. Kamar a mafarki wata babbar mota ta nufi kansu,damuwa,firgice da kuma rud`u duk sune suka rufesa,gashi yana k`ok`arin sauke ko danne damuwar da yake a ciki,ga kuma firgicin abinda take tunkararsa,amma ina duk yanda ya so ya hana hakan faru bai yiwu ba,sai fa gani yai su suna yawo a sararin samaniya. *JADEEDAH* (It's a story of two love birds who are so different from each other ) STORY & WRITTEN BY : (*Cwt~Sumiey*) Marubuciyar littafin MENE NE ABIN YI ? KARAGAR MULKI And now.....*JADEEDAH* *YOTA* https://chat.whatsapp.com/CWkZfMqvD4H0mtd7WW6Xbz https://whatsapp.com/channel/0029VapqU8C002T5Bz8RSQ0a BOOK 1 PAGE 13 ❤ Da k`yar mai motar da ke bayansu ya iya dakatar da tashi motorn,a gaban idon shi komi ya faru,rud`u da tashin hankali duk sun baibaye shi,abun tashin hankalin shi kad`ai ne a cikin tashi motar,iya tashin hankali ya ga tashin hankali, sai da motar ta tsaya dan kanta sannan ya nufi inda take, a yashe a k`asa ya iske Hibba sai Cecelia da Abbakar da ke kwance cikin motar face-face da jini,da k`yar ya iya matsawa kusa da su saboda hayak`in da ke tashi a cikin motar yana haki yana tari ya samu ya fiddo su daga cikin motar,babbar motar da ta haddasa had`arin ya nufa shima da k`yar ya samu ya fiddo Wanda ya ke a cikinta ya bugu sosai shima, ya gigita matuk`a Ainu da ganin yanda cikin k`ank`anin lokaci komi nasu ya sauya karma Cecelia da ko fuskarta ba ka iya ganewa,a gabansa ya zube su sai faman salati da naiman d`auki ya ke,ganin kamar Hibba na motsine ya sa ya garzaya da gudu cikin motar shi ya d`auki ruwa ya watsa mata ,cikin Ikon Allah sai ga shi tana jan numfashinta da sauri da sauri. Lokacin da idanuwanta su ka bud`e ta ga abinda ya faru da su ,kusan k`ara sumewa tai. "Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un Abbakar Abbakar,Na shiga uku baya motsi", saitin inda Cecelia take yashe a k`asa ta nufa,tana mai jan k`afarta da k`yar wacce ta bugu a jikinta, sai dai tana kusantar wurin tai baya a kid`ime,kuma a firgice,ko shakka babu ba rai a jikinta. Kamar anyi ma hanyar baki tunda had`arin ya faru ,sai mutane suka d`auke daga bin hanyar babu wanda ya zo wucewa,sai da aka d`au lokaci mai tsawo sai ga wata motor da mutum biyu ne a cikinta da alama ma mata da Miji ne. "Hubby da alama can accident akayi naga kamar hayak`i ne ke tashi a wurin"," Subbahanallah bari mu matsa mu gani",nan ya Isa wurin da hanzarinsa suka fito suna mai nufar inda Hibba da wannan mutumin suke tamkar mahaukaciya suka ga tana behaving,hankalin su ba k`aramin tashi yai ba sakamakon abinda su ka ci karo da shi. "Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un ",shine kalmar da Hibba tai ta mai-maitawa," Cecelia me zan gani haka ,wannan wacce irin munmunar k`addarar ce ta fito da mu". Munmunar mutuwa Cecelia tai wacce in badan tare da ita suka fito tun daga Gida ba to da bayanda za ai ta iya ganeta,da zaran Hibba ta matsa kusa da inda gawar Cecelia take sai wannan baiwar Allah ta rik`ata ta tana mai son kwantar mata da hankaki gami da bata haƙuri Hannunta na hagu wanda take tabbatar ma kanta ta samu karaya ko tsagewar k`ashi a jikin sa,a ka ta d`ora shi ta na mai cigaba da salati. Mutane ne suka fara taruwa wurin wasu har sun fara rik`eta,ganin yanayin firgicin da kuma rud`u da take ciki. Cak ta tsaya sakamakon tuna wani abu da ya fad`o mata a cikin ranta, "Jadeeda!...... Jadeeda!! .....Jadeeda!!! `yata kina ina ?,ban ganta ba kina ina,ban ga `yata ba,ku tai maka min ku nemo min ko ku sake ni in nemo ,ƴata". Jin wannan Maganar tata ne ya sa mutanen da suke wurin fara rarrabuwa domin su dubo ko dagaske tana tare da d`iyar tata ne kamar yanda ce. Har suka gama bulayin Neman su nan kusa da inda akai accident d`in ba su ga Yarinyar da ta ke kira da `yarta ba,kai har inda babbar motar da ta kad`e su ta gangara sai da suka je nemanta amma bata,basu ganta ba,ganin kamar dai firgicin ne yasa ta ke ikirarin ta taho da d`iyar ta ya sa suka dawo wajen da accident d`in ya faru. " Kun ga mutane bai kamata mu zuba ma bayin Allahnnan Ido a haka muna kallon su ba, kamata yai mu kai su asibiti ko mu Kira motar ujila ta kawo masu d`auki",Cewar wani daga cikin mutanen da suke a wurin. Mijin wannan Matar da suka fara tsayawa wurin ne ya bashi ansa,"Tun zuwan mu nan wurin Na Kira police sun ce suna zuwa,domin kasan ko mun kai su Hospital ba za a amshe su ba sai tare da police ". " Wannan ai Maganar banza ce ta ya za ai ace mutane na cikin irin wannan halin,Na mutuwa da rayuwa ace sai an jira wasu police ai wannan dokar banza ce dokar wofi, rayuwar su fa na cikin hatsari,komi zai iya faruwa da su a wannan d`an tak`in lokacin ". " To ya za muyi wannan dokar k`asa ce,dole zamu bita",...Dokar banza dokar da ake fakewa da ita ana kashemana `yan'uwa ba zamu yarda ba ku d`auke su mu nufi asibiti da su ko zasu San wani taimakon da za su yi ma su,ko da wannan da take Raye ce ,tunda ta ji ciwo sosai tana buk`atar taimakon gaggawa,ga alamanan har a kanta ta bugu ban da sauran ciwukan da suke jikinta"........ K`arar da Hibba ta saki ce gami da kwacewa daga rik`on da wannan Matar tai mata ne ya dakatar da shi tana mai cewa,"Wallahi Na zo da `yata,tare muke da ita,ga zanan goyantanan ga kuma feeder d`inta harma da jakar kayanta kun gansu",ta kai k`arshen zancen ta na mai tarwatsa kayan a k`asa yanda zasu gansu. "Kai Matarnan tana da gaskiya ga alamanan da ke tabbatar da tare take da `yarta don haka bayin Allah muk`ara hak`uri a sake dubata ko Allah zaisa mu dace a ganta ceton rai muke". Duk abinda ke faruwa Gloria na wani k`aton rami da yake nesa kad`an da wurin da accident d`in ya faru,yanayin yanda motar ta jujjuya a sama ne yasa ta watsar da ita can gefe,sautin hayaniyar da mutane ke yi ce ta dawo da ita daga cikin hayyacinta, sai dai bishi-bushi take gani sakamakon buguwar da kanta yai mata sosai. Hannunta ta kai kan idanunta sai faman murzawa don son ta gano a ina take me kuma yake faruwa da ita. Da k`yar ta samu ta fara gani bishi-bishi,idanuwanta ne suka sauka akan Jadeeda da ke fidda numfashinta sama-sama ko kuka bata iya yi,da sauri ta janyo ta jikinta tana mai jijjigata domin son ta dawo dai-dai. Jin motsin kusantowar mutane inda take ya sa ta sake lafewa yanda ba za su ganta ba,ta na mai kasa kunne domin jin abinda suke cewa. A bakin ramin su ka ja suka tsaya Wanda da wani a cikin su zai lek`a zai wuya bai ganta ba, Allah ne kawai ya rufe idanunsu gami da hana su lek`awa cikin ramin, "Kai abokina na ga tashin hankali, gabaki d`ayansu duk sun mutu in banda wannan Matar da ta ke faman neman `yarta ita kad`ai ce bata mutu ba". "Ikon Allah, k`addara ce ta kawo su da kuma kiran ajali kasan shi in yai kira dole aje ko ba a shirya ba"," Haka ne kam to ya za ai sai dai hak`uri haka Allah ya so ba yanda za ai ,nifa gani nake babu wata d`iya da wannan Matar ta ke tare da ita,nan wajen yayi nisa ace anyi had`ari mutum ya zo har nan ,abun da kamar wuya ,ko dai rud`u da firgici ta shiga ne da har ta ke cewa sun taho tare da ita". "Nima haka na fara tunani zai wahala ace mutum zai iya zuwa harnan, abun da kamar wuya gurguwa da auren nesa"," Ka ga mu tafi kawai mu sanar da su ba mu ga kowa ba","Haka za ai mu tafi".suka juya a tare su na nufar inda suka baro. "Jesus Chris kaddai ace mutanen na su na nufi Daniel da Cecelia duk sun mutu,kai a'a No no no hakan ba zai faru ba bari inje in gani". Gloria ta faɗa a firgice Cak ta tsaya tana mai komawa inda take ta zauna, Zuciyarta na yi mata tambaya mai nauyin da bata San amsar ta ba,"To ya kenan in da gaske duk sun mutu,hakan Na nufin duk ta rasa k`awa da kuma Namijin da ta k`wallafa rai akan sa,kuma ba makawa dangin Hibba sune za su amshe Jadeeda daga hannunta,ita kenan za ta tashi a biyu babu,babu k`awa kuma babu Mijin da take burin rayuwa da shi,shiru tai tana mai sake k`ank`ame Jadeeda a jikinta,ta na mai girgiza kanta alamun ba za ta iya d`aukar hakan ba abinda za ta iya ji da shi ba ne,yayi ma Zuciyarta nauyi nauyi mai girman gaske,sake `boyewa tai a inda take don gudun kar wani ya ganta ,rufe idanu tayi tana mai rok`on Allah yasa kar wani ya ganta balle har su samu damar da zasu rabata da Jadeeda wacce a yanzu ta ke ganinta a matsayi mafi girma da ƙolouwa a gareta. " Baiwar Allah gaskiya mun duba iya dubawar mu amma ba muga wata d`iyar ki ba,zai yi wahala ma ace kin taho da ita"....."A'a a'a wallahi Na taho da ita,a bayana Na goyo ta ,a wannan bayan nawa na ke goye da da ita",ta kai zancen tana mai juyo masu bayan Na ta". "Kai ni Na rasa gane wannan lamarin, ta ce ta zo da Yarinya mu kuma mun duba ba ko'ina ba mu ganta,Anya kuwa ba har yanzu tana cikin motar ba", d`aya daga cikin mutanen da suka taru a wurin yace. " Eh to Maganar ka za ta iya yiwuwa,mu je cikin motar mu sake dubata",ya kai zancen suna mai tunkarar inda motar su Hibba take, sai dai ko tsku biyu lafiyayyu ba su yi ba motar ta fara fidda wani bak`in hayak`i daga ƙarshen ta kama da wuta suna ji suna gani ba tare da sun samu damar zuwa su bincika ko Jadeeda Na ciki kamar yanda wani a cikin su ya kawo shawara ba,wata K`ara mai razanarwa Hibba ta saki ta Na mai tafiya k`asa luu za ta fad`i, alamun ta sake suma a kashi na biyu. Cikin Ikon Allah sai ga police sun zo tare da motar asibi a ka nufi asibiti mafi kusa da su,sai da Gloria ta tabbatar babu sauran wata hayaniya a wurin sannan ta fito d`auke da Jadeeda da ke ta faman sauke numfashinta a sama-sama,saman kan hanyar ta tsaya sai faman waige-waige take alamun rashin gaskiya a tattare da ita,ganin in ta tsaya neman ko jiran motor za ta iya samun Matsala ya sa ta tari mai mashin ta hau,ta na mai cewa ya kai ta asibiti mafi kusa. Tunda ta hau suka tafi ya ke ta faman tambayarta lafiya ya ganta kamar a kid`ime ko dai satota akai ko kuma hatsari ta yi". Tsawar gaske Gloria ta daka mashi tana mai cewa,"Dakata Malam, ina ruwanka da ni,why are you asking me, like my father, akan me,ka ja bakin ka kayi min shiru ko kuma ka sauke ni,Haba duk ka bi ka ishe ni da tambaya ka barni inji da abinda ya same ni mana". Shiru wannan mai mashin yai bai ƙara cewa kome ba sai faman tsala gudu akan titi da yake,Garin Jingir nan ne Gari mafi kusa da inda sukai had`arin,Hospital ya kai ta kamar yanda ta buk`ata, sai da suka tsaya sannan gabanta ya yanke ya fad`i, sakamakon tunanin ina za ta samu kud`in da zata biya abun hawan da ta hau. Wani sanyi ne ya ratsa dukkanin gangar jikinta sakamakon ganin side back d`in ta a sagafe,ta yi mata irin sagalawarnan tun daga kan kafard`arta zuwa gefan cikinta na hagu, da sauri ta janyo ta ta fiddo kud`I masu yawa ta bashi,tayi gaba da sauri d`auke da Jadeeda a hannunta. "Sis dan Allah ina ne sashen da ake kula da k`ananun `yara ?"," Ga sashen can ki bi hannunki na dama,can ne sashen kids","Okay thanks na gode". Jiki na rawa Gloria ta nufi sashen,duk abinda ya kamata tayi,tayi domin ta had`u da Doctorn da ke duty a ranar tayi,har ta samu damar shiga don ta ganshi. Ganin halin da ta ke a ciki ne yasa bai wani tsaya tambayarta abinda ya faru ba har sai da ya bata taimakon gaggawa, yai mata duk abinda ya kamata,sai da ya ga ta d`an samu natsuwa sannan ya fuskance ta yana mai cewa. "Me ya same ta wai ?", ya tambayeta bayan ya amshi Jadeeda ya na sake dubata. Shiru tai sai faman raba idanu take da k`yar ta samu ta iya saita kanta ,kana tace,"Ammm.....Uhmmmm....ta fad`o ne daga bane? ",ta samu ta sanar da shi haka ...," Mene baku da hankali ne,ta ya za ku bar wannan `yar k`aramar `yarinyar a bene har ta kai ga fad`owa,me ya sa iyayen zamanin nan baku da kula,ta ya zaku rik`a irin wannan sakacin". "Kayi hak`uri na fita ne na barta ita da `yar aiki shine hakan ta faru".... " Aifa dama haka kuke,duk kun bi kun lalace,yanzu ga shi nan kin ja mata jinya a banza a wofi". A firgice Gloria ta d`ago tana mai cewa,"Doctor me kake nufi ko wani abu munmuna ya samu `yata ne ?". "Eh to ba na ce ba,ina buk`atar in yi mata wasu gwaje-gwaje kafin in tabbatar da asalin abinda ke faruwa da ita, zan kwantar da ku ,domin tana buk`ata ayi cikakakken bincike akanta,she need a bed rest"... "Bed rest kuma a'a hakan ba zai yiwu ba", ta fad`a cikin firgici ba tare da ta sani ba. Baki sake Doctorn ya tsaya ya na kallon Gloria da mamakin abinda ta ce," Me wannan maganar taki ta ke nufi ne,ko da akwai wani abun da ki je `boyewa ko kuma ki ke gudun faruwar sa ne ?",taga-taga ta tafi za ta fad`i a dalilin sarawar da kanta yai mata. "Kina lafiya kuwa na ga kamar ke ma kina buk`atar taimakon"," A'a no I'm okay "," kin tabbata kuwa?",ya sake tsare ta da wata tambayar,kallon zargi ya fara yi mata domin haka nan yaji bai yarda da ita ba,har Zuciyarsa ma na raya masa anya ba akwai wani abu a k`asa ba don ba Uwar da zata iya barin `yarta kamar wannan ta fad`o daga kan bene ,ita kanta sai da ta fahimci yana zarginta akan wani abu,sai da ya sake mai-maita mata tambayar da yayi mata sannan ta bashi amsa a tak`aice ta ba shi amsa da Eh,"okay jirani ina zuwa bari in samo wata allurar da zata sa tai quick recovery". Ya na fita,itama tai saurin d`aukar Jadeeda ta bar cikin Hospital d`in don gudun kar yai k`ok`arin tona ma ta asiri,shatar tacxi ta d`auka tace ya nufi Kaduna da ita kai tsaye,bayan tafiya mai nisa suka Isa Kaduna direct filin jirgi ta nufa, inda Allah ya taimake ta ta na isa ko 30mint jirgin su ya tashi zuwa Lagos, hankalin Gloria ba k`aramin kwanciyar yai ba a lokacin da ta ga ta bar area area da dangin Hibba za su iya ganin ta,babban burinta dama shine taga ta tafi tare da Jadeedan,bayan ganin sun fara tafiya ne ,ta fara sauke tagwayen ajiyar Zuciya, hawaye masu zafi na zubowa daga idanunta ,hannunta ta kai kan goshinta da kuma gefe da gefan kafad`arta gami da rufe idanuwanta ta tai Addu'ar ga Allah da nuna godiyarta game da nasar da ya ba ta a cikin wannan lamarin,k`am-k`am ta rungume Jadeeda wacce ke barcin wahala da likita ya sa ta ,tamkar ta na tsoran wani zai kwace mata ita,sai a yanzu ta fara kukan rashin Cecelia da kuma abun Sonta Daniel. *JADEEDAH* (It's a story of two love birds who are so different from each other ) STORY & WRITTEN BY : (*Cwt~Sumiey*) Marubuciyar littafin MENE NE ABIN YI ? KARAGAR MULKI And now.....*JADEEDAH* BOOK 1 *YOTA* PAGE 14❤ Tamkar za a karye k`ofar room d`in haka ake bugun k`ofar,a zafafe Gloria ta fito tana mai cewa,"Who's there ,waye nan yake damu na tunda farar safiya,ba na ce bana buƙatar ganin kowa ba ?". "It's me your Mom Rebecca open the door".ta kai zancen ta na mai cigaba da bugu k`ofar. Sai da Gloria ta `bata fuska kafin ta nufi hanyar da zata bud`e door d`in da kamar ba zata bud`e ba haka tai,kafin kuma ta je ta bud`e. Kamar wacce a ke shirin hanawa shiga cikin haka Mom ta bankaɗo k`ofar ta shigo,sai faman haki take kamar wacce ta ci gudu,ta maida kallonta akan Gloria," Heeeeeee Gloria why are you take soo long time baki zo kin bud`e min k`ofar ba,ko dai baki so zuwana ba ne ba,why are you not welcoming me,or do you have something else da ki ke hidden d`insa gare ni ?". "No Mom there's nothing,ban ji knocking d`in naki da wuri ba ne ba"....." You're a liar Gloria, You're big liar I'm not truth you, kin sa Gate man d`in ki ya hana ni shigowa I call you several times amma ba kya picking Call ɗin ba,me hakan ke nufi,wanne abun ki ke aikatawa da har ki ke wasan `buya da ni ?". "Mom I'm not doing anything, I don't hide anything to you".... Kukan da Jadeeda ta tsanyara da iya kacin k`arfinta ya sa ta dakata da ga zancen da take ba dan ta so ba,mutuwar tsaye Mom tayi ,bata ƙara shan mamaki ba har sai da taga fitowar Jadeeda sai mutsika idonta take alamun yanzu ta tashi daga barci. Gloria da d`an gudunta ta Isa gareta tana mai cewa," Oh my Baby I'm so sorry na bar ki ke kad`ai ko ?,Tom ai gani yanzu sai mu je ayi wanka sai mu zo in baki breakfast d`in ki ko",ta kai zancen ta na mai d`agata sama da nufin su koma bedroom. Tsawar da Mom Rebecca ta daka mata ce ta sa ta juyo,"Are you out of your sense, baki da hankali ne, taya bayan faruwar wannan a'lamarin mai girma za ki wuce ni ki nufi bedroom who is she,wace ce wannan Yarinya,`yar waye ina ki ka samota me ye had`in ki da ita ?".ta kai zancen a fusace tana mai d`aga sautinta. Sai da Gloria ta k`ank`ame Jadeeda a jikin ta sosai don kar ta tsorata kafin tace,"Haba Mom why are you shouting like that she is a kid,za ta iya tsorata ko kuma ta firgita, idan kuma ta fara kuka ban san taya zan iya lallashin ta ba, Na sha wahala kafin in samu ta bar yin kukan da take". "Na d`aga murya zan kuma cigaba da d`agawa until you tell me who is she,ki faɗa min gaskiya ina ki ka samo Yarinya". Sai da Gloria ta runtse idanunta ,gami da rasa me ma za tai ,kafin daga bisani ta ce" Oh Jesus Christ shikenan shikenan I will told you about everything, but ma rok`e ki da zaran na fad`a miki just go,leave my house I need to be alone,Babyna ba ta son hayaniya".ta kai k`arshen batun tana,mai juya fuskarta alamun bata son su had`a Ido. "She's my daughter",ta bata amsa" Do you adopt her","No ban yi adopting d`in ta ba","A aha to Garin ya ki ka sameta, nasan dai in this few days baki isa ki getting pregnancy har ki haifi zankad`ed`iyar Yarinya kamar wannan ba","Mom ki yarda she is my daughter ", ta bata amsa a tak`aice," At how taya ta zama `yar ki,I swear to the God matuk`ar baki fad`a min asalin gaskiyar da ke cikin samun wannan Yarinyar ba ,I will Call your Dad, rights now Na gaji,Im tied to your childness,kin ce min baki son yin rayuwa da mu a can Main house d`in ,I upper you this house,and then why are you doing anything you want without asking me, whether you told me the thing that you hadden or else I will call you Dad now ". Jikin Gloria rawa ya fara,kafin ta ce," Relax Relax I'm sorry I'm truly sorry zan fad`a maki you know Cecelia ba? "," Yes I know her she is your best friend seen childhood ". Nan Gloria ta kwashe labarin duk abinda ya faru ta sanar da ita kafin ta kai k`arshe tuni hawaye sun wanke mata fuska. "Halaluya do you mean Cecelia da Daniel are all died"," Yer Mom they're all died ",ta faɗi hakan hawaye na sake zubo mata," Jesus Name Na rasata ma wannan Yarinya she is so little and pretty what is her name ?".Mom Rebecca ta tambaya Cikin in'ina da kuma rarraba harshe ta ce da ita ,"Jadeeda","Oh you mean Jedeeda? "," No Mom Jadeeda no be Jedeeda is Jadeeda "," Oh wannan ku ka sani,am ya batun Jos kuma kin san akwai Anty Deborah kin san yanzu ita ke da hak`k`in cigaba da rainon wannan Babyn ",...." No Mom sincerely ba zan ba wani wannan Babyn ba she is mine ni zan rai ne ta da kaina ". " You're a liar Gloria, kin manta,ko ke wace ce ke fa budurwa ce ,wacce bata ta`ba yin Aure ba, taya rainon Yarinya k`arama kamar wannan zai dawo gare ki,biside ma tun yaushe nake lallashin ki akan ki yarda a yi Auren ki ke da Anderson kin k`i amincewa sai yanzu ki zo min da zancen rainon wata Yarinya before marriage, it can't be possible ". " No..no..no Mom don't do that to me,no one diserve to take thin girl like me i love her I will take a good care of her, and I promise to do anything that you want,ba zan ƙara musu ko gaddama da ke ba zan ji Maganar ki a koda yaushe". "Kina nufin har Auren Anderson kin amince da shi ?", Mom ta tambaya a mamakan ce. " Yes up course in har za ku bar ni da My girl mu rayu a tare". Wani k`yatacxen murmushi ne ya bayyana akan fuskar Mom Rebecca ta na mai cewa,"To shikenan tunda haka ki ka za`ba Na amince ki rayu tare da ita matuk`ar dai kin amince da Auren da nake so ki yi","I'm swear to the Jesus na amince". Kan farin ciki harda Jadeeda Mom ta had`a ta rungume ta Na mai sanya masu albarka,"Let me make a call, bari in Kira Anderson in sanar da shi wannan labarin mai matuk`ar farin ciki",ta ce bayan ta sake su tana mai k`ok`arin fiddo wayarta daga cikin hand bag d`inta Kira ne ya fara shigowa tun kafin ta gama fiddo da wayar d`auke da sunan My Sister, d`agawa tai ba tare da murmushin dake kan fuskarta ya gushe ba,"Kin ga kalli Antyn ki ce ke kirana don har ita na kira na ce ta duba min ko kina nan Jos d`in ko can ki ka nufa ",marairai fuska Gloria tai tana mai had`a hannayenta wuri guda tare da cewa," I beg you kar ki fad`a mata komi ,kar ki sanar da ita abinda ya faru",da kai Mom ta amsa ma ta ta na mai d`aukar wayar don kar ta tsinke. ,"Hello my Sis ykk ",ta ce da ita daganan `bangaren sai bayan da suka gama gaisawa sannan ta ce da ita," Do you find you Daughter Gloria ko har yanzu ba ki san inda take ba ?". Sai da Mom ta nisa kafin ta ce,"I found her ashe all this time tana cikin Gidan ta a rufe,sannan ta sa Gate man ya ce bata nan a duk sanda wani ya zo neman ta","Jesus to duk akan me ya sa ta aikata hakan ?",ta tambaya daga can `bangaren. "Kin San ina son in had`a ta Aure da Anderson Yaron k`awata to ita ba ta san haka wannan dalilin ne ya sa ta zartar da wannan hukuncin". " Eeeeyyyeh na wawo my Sis da akwai Matsala duk yanda za ai ki sata ta amince da wannan had`in domin akwai babbar matsala ",Hankalin Mom a tashe ta ke tambayar wacce irin Matsala ce Babba har haka da ya sa ake son ta Aurar da `yarta nan kusa. " Ai nasan kin San Cecelia her best friend to ta `bata ana saura kwana hud`u aurenta da John d`an Gidan Sama'ila na bakin kasuwa". "Kamar ya ta `bata wannan wanne irin labari ne meye dalilin da ya sa za ta gudu ba ita ta ce ta na son shi ba?"," Hmmmmmm baki gane abinda na ke nufi ba,kin san Daniel Yayanta ya bar Addinin gaskiya ya musulumta, ita kuna taje yi masa sallamah an kusa bikinta shiru-shiru bata dawo ba da ,an nemi duka numbers d`in su ba a same su ba,da fari da ana samun su rana d`aya aka daina samun su in an kira ba ta tafiya,nan fa mutane suka fara ce-ce kuce wasu na cewa yanzu haka itama ya sa ta bar Addini ne shiyasa su ka kashe wayar su, ta za`bi ta bi d`an'uwanta ta bar Anty Deborah ita kad`ai bayan wahalar rainon su da ta sha ". " Heeeeeeh wannan labari bai yi dad`i ba Garin ya za su aikata haka?","Hmmmm ke dai bari lokacin da Anty Deborah ta ji yanke jiki tai ta fad`i sai Asibiti a ka kai ta ga ba kowa tare da ita sai mutanen unguwa sai fa washe Gari d`anta Blus na garin Benin ya zo ya tafi da ita, kinga in har Cecelia na nan da ranta wata ranar zata zo taja ra'ayin `yar ki itama ta bar Addinin gaskiya ". " God for bid no my Daughter ba dai `yata ba dole zan zo in yi ma lamarin tufkar hanci kafin hakan ta faru,kin ga bye sai anjima ",tana kaiwa nan ta kashe wayar gami da maida kallonta akan Gloria don son gano asalin gaskiyar da take akan fuskarta". " I swear iyah gaskiya ta,Na fad`a miki kin ga ma wayar Cecelia da ita,ma taho tayi daga-daga hakan yasa ba za su ta`ba samunta ba", ta tashi ta bi bayan ta,kwantar da Jadeeda akan kujera da tuni ta koma barcinta ta d`auko mata wayoyin nasu Wanda Allah ya taimake ta suna cikin bag d`inta tun kafin had`arin ya faru,sai a sannan Mom ta sake yarda da ita. "To amma wani hanzari ba gudu,barin wannan wayoyin a hannunki zai iya janyo wata matsalar zai fi kyau ki salwantar da su", da sauri Gloria ta fita hannunta d`auke da su a hannunta da kanta ta sa k`aton dutse ta yi ma,wayoyin ratsa-ratsa yanda ba za su sake amfanuwa ba bayan ta kakkarya sim's d`in ,kai tsaye dustbin ta watsa wayoyin sannan ta nufi bathroom tai fuloshing d`in sim's d`in. Ita kuma Mom Rebecca tana can suna waya da Anderson"Hello the most lovely Mom in the world ykk"," Ina lafiya,my son fatan dai ba ni na tashe ka a barci ba ?". Murmushi yai ba tare da ya,bata amsar tambayar da tai ba,kasancewar sa matashi mai natsuwa da hankali sai cewa yai,"Mom what is the problem mene ne yasa ki ka kira yanzu ko da akwai abinda ki ke son inyi ma ki ne?". Dariya tayi kafin ta ce da shi,"Ba wata Matsala my Son just it's a surprise but gest what ?". Sai da Anderson ya tashi daga kwancen da yake fuskar shi d`auke da murmushi kafin yace,"Ammmm......Dad will be back",ya fad`a bayan ya d`an d`au lokaci,"Nop baka canka ba",Mom ta fad`a tana dariya. Haka ya cigaba da gesing har wajen sau uku amma bai dace ba sai can ta ce yana mai rarraba zancen,"Gloria..... Accept"......,k`arar ihun da Mom ta saki ne yasa ya gane ya canki abinda yake faruwa,shima k`arar ya saki har yana mik`ewa tsaye saman bed d`in da yake ya na rawa. "Mom I'm coming ganinan zuwa in a no time I will be there", Okay see you soon my son muna Gidan Gloria". Kamar yanda ya ce cikin k`ank`anin lokaci zai Isa hakata kasance,bayan isar ne Mom da kanta tai mashi bayanin komi. Sosai fuskarsa ta bayyanar da tausayin Jadeeda har sai da ya matsa kusa da ita ya na shafa kanta,d`an motsawa tayi gami da turo bakinta gaba alamun cikin rigima take har sauke ajiyar Zuciya ta yi, bai San sanda ya saki murmushi ba gami da cewa,", She is so cute", wannan magana tashi ba K`aramin sanya Gloria farin ciki tai ba don sai da tai dariya har haƙoranta na bayyana, shi kan shi tsayawa yai yana kallonta rabon da ya ga irin wannan yanayin a tare da ita,har ya manta ya sota tunda dad`ewa so mai tsansni da zafi amma sanda ya bayyanar mata da shi sai ta rufe idonta tace masa tana da wanda ta ke so,da kyar ya samu ya hak`ura da ita bayan an sha gwagwarmaya ya fara Dating da wata Yarinya mai suna Juliet bayan tayi getting pregnancy ta ce ba ta son shi ta fasa Auren sa, kuma tace sai tayi abortion ta zubar da cikin jikinta sune rigima har Court, dole ta hak`ura ta haifi cikin ,shima ba da kanta ta haife shi ba,C,s akai mata don tace ba zata yarda ta haihu da kanta ba ,Ana cire Yaron ta basu abinsu ta cigabada da sabuwar rayuwar ta ba tare da ta,k`ara bi ta kansu ba,yanzu haka Yaron mai suna Edwin d`an 5yrs yana hannun iyayensa suke rainon sa. "Mom Na amince zan Aureta kuma,in raini d`iyarta in Kira kaina da sunan Dad d`inta domin Yaro na kowa ne,sai dai wani hanzari ba gudu nima ina da nawa d`an Edwin ina son bayan Aure in dawo da shi gabana in cigabada da rainon sa". " Kar ka wani damu wannan ba wata Matsala bace ba,duka zan haɗa in raine su kaga ko iya su biyu sun ishe mu".Gloria ta bashi ansa cikin zumud`i. "No...no ba su ishe mu ba,ke ma za,ki haifi naki we need to build a big family", ya kai zance yana dariya gami da rungume ta, sosai Mom taji dad`in faruwar wannan lamarin nan da,nan Jadeeda ta samu wani k`arin matsayin a wurinta domin gani take kamar dalikinta ne yasa burin da ta dad`e da shi a cikin ranta zai cika. " Ammmmm....ina son in in rok`i alfarma akan bana son kowa yasan da labarinta har a gama biki, hasalima so nake da zaran an d`aura Auren mu bar k`asarnan, sannan ko da zamu dawo bana son cigaba da zama a Garin Lagos mu sake wani Garin ko da kuwa k`auye ne". "I'll do kamar yanda ki ka ce duk abinda ki ka so shi za a yi,hatta da k`asa ko Garin da zamu zauna ke zaki za`ba wannan shine reward d`ina na farko na jin daɗin amsar Soyayyar da ki kai, but Mom Na manta,ban zo da ring d`in da zan yi proposal d`in ta ba". " Oh to yanzu ya za ai"?",Mom ta tambaye shi like Seriously d`inan. Duk`awa,yai yana mai `boye hannunsa a baya gami da kiran sunanta cikin sanyin murya,"Gloria I know you are the most beautiful woman in the world, Na San kyawawan d`abi'u da kuma halayenki,nasan ke d`in mace ce nagartacciya mai amana please can you married me". Tsalle Gloria take tana mai rufe fuskarta har ya,kai k`arshe zancen yana,kaiwa ta amsa da Yes Yes, da saurin sa ya janyota ya rungume ta,haka yake shi mutum ne mai barkwanci da son ayi dariya,duka Mom ta had`a su ta rungume ta ta mai sake gode ma Allah a cikin ran ta. Cikin d`an lojaci aka d`aura Auren su bayan dawowar Dad d`in Gloria, shi kan shi ya ji dad`in hukunci da ya ga sun yanke ma kan su ko ba komi zasu yi farin ciki tunda su uaka za`bi hakan ,hatta da Visa d`in su ta,kammala bayan gama biki su ka d`auki hanya sai U.K..... *JADEEDAH* (It's a story of two love birds who are so different from each other ) STORY & WRITTEN BY : (*Cwt~Sumiey*) Marubuciyar littafin MENE NE ABIN YI ? KARAGAR MULKI And now.....*JADEEDAH* BOOK 1 *YOTA* PAGE 15 ❤ "Dan Allah ku kyale ni,ku barni ina so in je in ga `yata da kaina,Zuciyata ta kasa hak`uri, ban san a wanne irin hali take a ciki ba,ina buk`atar in ji d`uminta a kusa da ni", Hibba ta kai zancen cikin yanayin jinya da,kuma marairaicewa. " Kin ga Hibba dan Allah ki kwantar da hankalin ki,Jadeeda na can ita ma ana dubata kuma ta na samun kulawa ta musanman,don haka ki natsu ki kwantar da hankalin ki,Yarinyar ki zata dawo hannun ki,da izinin Allah.Cewar Ummie Maryam cikin lallashi da ban baki. Hawaye ne suka fara zubowa daga cikin idanunta, tana mai girgiza kanta alamun bata amince da hakan ba,cikin k`ank`anin lokaci ta birkice musu,"A'a ni ba abinda za ku fad`a min a yanzu in sake yarda da ku,yau kwana nawa wajen kwanana uku da farkawa amma kun hana ni ganin Jadeeda, idan ba za ku bar ni in je inda take ba ku kawota nan in ganta mana, Haba dan Allah",ta kai zancen ta na mai fincike drip d`in dake hannunta har ma da yunk`urin sauke k`afarta da aka d`ageta sama wacce ta samu karaya. "Hibbah!!!! Ki dakata nace ya isah haka,ko baki da hankali ne,ko kin manta cewa ke muslmace,ya ki ke abu kamar wacce kwakwalwarta ta juye ?"...ya d`an dakata ba tare da ya kai k`arshen abinda yake son cewa ba. Jikin duk wanda ke wurin sai da yai sanyi,ganin yanda yake mata tsawar kuma hawaye na zuba daga cikin idanunsa,Lura Mama Hadiza tai ya na shirin cewa wani abu tai saurin shan gaban shi gami da fara girgiza masa kai,runtse idanun sa yai Wanda hakan ke tabbatar ma Mama Hadiza ba zai fasa fad`ar abinda yai niya ba. Tarar numfashin sa tai da cewa," A'a Nasir a kull d`in ka kar ka soma wannan ba shine lokacin da ya dace ba,ka bar komi ya lafa in ba haka ba kuma"......"In ba haka ba kuma me Mama, tsoran me kike ji,me ye ku ke gudun kar ya faru,ita fa Muslmace yarda da k`addara ya zame mata dole, don haka ku gaya mata gaskiya ku fad`a mata cewa Allah ya zartar da hukuncin da yafi dacewa akan ta".... Duk tsansni da tsafin da take ji a k`afartata,haka ta takata,ba tare da ta yi tunani me hakan zai iya haifar mata da wani abu ba,sai ganin ta su kai a tsaye a gaban su tana mai kama hannun Naseer d`an'uwanta ta na mai cewa,"Dan Allah me ke faruwa shin wani abu ya same ta ne, kar ka ce min da gaske abinda na gani a mafarkina shine ya faru da ita,wai tsaya ina Abbanta yake ban yarda da kuka ce min yana can office aiki ya rik`e shi ba". Sai da ya kama kafad`arta ya rik`e har da hannun da ta samu tsagewar k`ashi kana ya ce da ita,"Eh ba gaskiya su ka gaya maki ba, Mijin ki na can kwance rai hannun Allah a sanadin hatsarin da kuka samu har k`anwar Mijin ki Cecelia ta mutu"...bige hannun sa da sauri tana mai fara ja da baya daga kusa da shi tana mai cewa, "A'a Yah Naseer kar ka ce min itama Jadeeda ta mutu,kar ka ce min itama na rasata?". Sai da yak`ara matsawa kusa da ita ,sannan ya bata amsa da cewa,"Ki saurare ni ki kuma natsu Allahn da ya baki ita ya fiki son ta,don haka ya amshi abarsa"....Sai da ta sa hannunta mai lafiya ta hankad`ola shi kafin ta ce "k`arya ka ke Naseer `yata Jadeeda ta na da ranta ba ta mutu ba, domin,ruhina Zuciyata da kuma gangar jikinta suna gaya min ta na raye,kuma bari ka ji yanzu zan fita da kaina in dawo da ita", ta kai zancen ta na mai dosar hanyar da za ta bar room d`in, tangal-tangal ta fara za ta fad`i sakamakon duhun da ya mamaye mata idanunta da sauri su duka Ukun Mama Hadiza, Ummie Maryam da shi kan shi Naseer d`in su kai kanta,jiki na rawa Ummie Maryam ta tafi kiran Doctor bayan sun kwantar da ita . Ta ma fita Baba Malam da kuma Baba K`arami suka shigo cikin d`akin ganin halin da suke ciki ne ya sa ba su sami zarafin tambayar su me ke faruwa ba. "Garin ya akai haka ta faru, wannan wanne irin sakaki ne ?",Doctorn ya fad`a a zafafe bayan ya ji abinda ya faru,sosai Doctorn yai fad`a tana mai nuna nasu muhimmancin kulawar da zasu yi da ita,hak`uri suka ba shi har ya gama yi mata duk abinda ya dace yai mata . A fusace Baba K`arami ya fuskanci shi yana mai cewa," ba ka da hankali ne,ta ya za ka aikata irin wannan d`anyen aikin ko kana hauka ne ?". "Eh Baba K`arami hauka na ke bani da hankali,idan har gajiya da kallonta a cikin irin wannan yanayin shine hauka to ba shakka na hauka ce,da gaske na haukace,shin ba kwa tunani ko jin tsoran kar yawan sanya ta barcin dole da kuma `boye mata asalin gaskiyar da kuke ya jefata cikin wani mawuyacin halin, shin ko so kuke ta koma sai an kwantar an tayar har k`arsheb rayuwarta,ko kuma so kuke ta koma rayuwar kamar irin wacce Mijin ta ya ke yi a yanzu, na rasa gane wannan tausai ne ko kuma wata sabuwar hanyar cutarwa,ya ci a ce ya zuwa yanzu kun gaya mata gaskiya yau wajen kwana biyar kenan da farkawarta da zaran ta tambaye ku game da Mijinta ko `yarta sai ku `boye mata gaskiya a haka ku ke so ta cigaba da rayuwa,don haka ni dai ma gaji ,Na gaji da ganin `yar'uwata a kwance shar`be kamar gawa ina son in ganta kamar yanda na saba ganinta tun muna yara"... Ya kasa kai k`arshen maganarsa sakamakon rungumar da Baba K`arami ya kai masa,sai da ya tabbatar da ya lallashe shi yanda ya kamata kafin ya raba jikin su ya fuskanci Baba Malam da cewa. "Maganar Naseer gaskiya ce,ya kamata mu kawo k`arshe komi,mu bar Garin Jingir d`inan haka mu koma can Kano ,za su fi samu kulawa fiye da wacce suke samu anan". " A'a ni dai ina jin tsoro ta ya zamu bar da su daga cikin Asibiti a irin wannan halin ",Cewar Mama Hadiza. "Mama ki kwantar da hankalin ku ba gani ba,zan iya ba su duka kulawar da ake so,nima fa Doctor ne,a dukaninsu sun fi buk`atar kulawa ta cikin Gida fiye da ta asibiti, domin ya zuwa yanzu sun d`an samu sauk`i da ciwukan da suka samu na external saura na internal " To ba matsala amma ya kike gainin za muyi doguwar tafiya irin wannan da marasa lafiya har guda biyu?","Lafiya lau zamu tafi da su ai referring d`in su zuwa wani Hospital d`in zamuyi don haka za su bamu motar mara lafiya a sanya su a ciki har zuwa can Kanon". "To shikenan sai mu fara Neman Sallamar amma,kafinnan kai K`arami ya ka yi da gawar ita k`anwar Abbakar d`in ?". " Daganan Asibitin suka had`a ni da wani Pastor nai mishi duk bayanin yanda komi ya faru, ya jimanta mana bayan ya saurari duk abinda ya faru sannan ya amshe ta ban bar wurin ba har sai da su kai mata duk abinda suke yiwa `yan'uwansu in sun mutu sannan suka buzne ta,sun bani tabbacin ko nan da shekara nawa zan zo zasu nuna min kabarinta domin har rubutu a takardar sai da muka yi sannan na taho". "Masha Allah hakan yayi domin adalcin da zamu yi mata kenan mu sadata da `yan'uwanta su binneta kamar yanda suke ma `yan'uwansu,kun san zamu iya kiran haka a matsayin hak`k`in ta ne a kan mu ,don haka zamu iya tafiyar mu tunda ba wani nauyin ta akan mu". "Tukunna dai wani hanzari ba gudu ba,shin kun manta a sanda Hibba tai farkawarta ta farko ta ambaci sunan wata ta na mai cewa `yarta na hannunta,to ta ya ke nan idan har hakan ya zama gaskiya, gani na je kamar bai kamata mu bar Garinnan ba har sai mun nemo ta idan mun tabbata ba ta tare da Jadeedan sai my yi tafiyar mu".Cewar Mama Hadiza. Sai da Baba Malam ya fuskance ta kafin ya ce"Ki natsu ki saurare ni,yanzu haka daga police station d`in da suke gudanar da wannan binciken na ke akwai rikitarwa mai tarin yawa a cikin binciken,sun ce min sun yi iya binciken su su basu ga kowa a wurin ba,kai ko wayar mamaciyar ba a gani ba balle ai amfanin da ita a gano shin da gaske da akwai wata Mace wacce suke tare da ita ko babu,to babu wata takardar ko guda d`aya dake nuni da Cewar akwai wata bayan su uku da kuma `yarsu iya ita Hibban Mijinta da kuma k`anwarsa su ka tarar,babu wata shaida da ka iya tabbatar da wanzuwar ita wannan mai sunan da take ambata,saman wani Mutum Wanda a gaban shi hatsarin ya faru,ya tabbatar mana da cewa ya fi zargin buguwar da tayi ne yasa take ambaton wanna sunan ,kai tsaye dai binciken ya fi tabbatar mana da Jadeeda ta rasu ta k`one a cikin wannan motar". "Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un yanzu Malam kana nufin Yarinyarnan ta rasu ta riga mu Gidan gaskiya da wacce fuska zamu itta tarar Hibba da zancen mutuwar `yarta bayan ga munmuna hademarin da ya fad`a ma Mijinta na juyewar kwakwalwa".Ummie Maryam ce ta matsa kusa da ita tana lallashin ta duk da itama tana zubar da nata hawayen ne. " Sai hak`uri k`addarar Allah ce,haka ya tsaro mana ita,don haka dole zamu d`auke ta, domin a yanzu in munce zamu nemo me irin wannan sunan nata,ya ma sunan ya ke ?",ya na mai tambayarta su sunan da Hibban take yawan ambata bayan farkawarta. "Gloria sunan ta",Naseer ya ba shi amsa. " Yauwa Gloria idan mun tashi nemanta a yanzu ina zamu fara,domin mu ba musan daga ina ta zo ba,ya kamanninta su ke bamu san komi daga gare ta ba,iya Abbakar da k`anwar shi su ne suka santa da kuma inda ta fito, ita waccan Allah yai mata rasuwa,shi kuma wannan ya na kan matakin da shi kan shi bai san ko shi waye ba,kai ko ahalinsu bamu sani ba,in kuma munce muje Jos neman ahalin nasu to ta ina zamu fara da wacce hujja zamu yi amfani ,don haka bamu da wata makama wacce ta wuce muyi hak`uri". Naseer ne yace,"Ni da cewa nai ko a d`auki hoton ita Ceceliar a sanya a kafafen television ko Allah zaisa ahalin su su gani kun ga shikenan daganan sai mu fara Neman Gloria "," Hmmmmmm Naseer kenan baka ga yanda Allah ya sauyawa Yarinyar nan kamanninta ba, shiyasa har kake fad`in wannan Maganar,zai wahala ko `yan'uwanta su iya gane ta". "Allah gare ka mu ka zo gare ka muke neman taimako,Allah ka kawo mana mafita a cikin wannan lamarin", Mama Hadiza ta fad`a tana mai share hawayen fuskarta. " Shikenan kin gama magana Mama Addu'ar mu kawai take so,in sha Allahu indai Jadeeda na da rai a doran duniyarnan to zata kawo kanta gare mu har inda muke duk min daren dad`ewa bi izzatillah,zamu duk`ufa wajen gayama Allah kukan mu,ba zamu gajiya ko min daren daɗewa ba".nan fa suka had`a me kansu kowana k`unshe hawaye da kuma bak`in cikin halin da suke a ciki. "Masha Allah, Allah yai maku albarka ya zama gatan ku gabad`aya sai abu guda da zan so daga gare ku,daga yau ko da wasa kar wandaya k`ara tada zancen wata Gloria kai hatta ita Jadeedan mu d`auka a ta rasu bata Raye,ko da ita Hibban ta farka kar wani ya bata goyan bayan akan duk abinda zata zo mashi da shi,karma in na son tada wancan zancene,don haka da zaran mun Isa Gida zamu gabatar da Sallahtul ga'ib (Sallahr da ba gawa),da sunan Jadeeda da fatan Allah ya kai rahama da jink`ai cikin kabarinta". Jikin kowa sai dai ya ƙara sanyi sai dai ba su da yanda zasu yi dole abinda ya kamata suyi kenan su d`au k`addara ta fuskar da ta zo masu,nan Naseer ya fara cuku-cukun sama masu referral zuwa Kano bai huta ba har sai da ya samu a wannan ranar su ka bar Garin Jingir badan sun so ba,Zuciyoyin su d`auke da wani miki ko gyambon da ba zai ta`ba warkewa ba. *JADEEDAH* (It's a story of two love birds who are so different from each other ) STORY & WRITTEN BY : (*Cwt~Sumiey*) Marubuciyar littafin MENE NE ABIN YI ? KARAGAR MULKI And now.....*JADEEDAH* *YOTA* BOOK 1 PAGE 16❤ After some Months Zaune take ta rafka tagumi da hannayenta duka biyu,idanunta na kan bed d`in da Abbakar ke kwance amma a zahiri hankali da tunanin ta ba a nan suke ba,hakan ya sa ko shigowar Mama Hadiza ba ta ji ba,har sai da ta kai ga dafa kafad`unta sannan tai firgigit ta farka tun kafin tace komi hawaye suka fara zubowa a saman idonta. "Hibba me kike yi haka kar dai kice min har yanzu baki d`auki k`addarar da Ubangiji Allah ya saukar miki ba". " Mama ba haka bane ba Zuciyata har yanzu da k`una a cikinta kuma na kasa yarda da Cewar wai Jadeeda ta rasu ta barni,da kaina fa na mik`a ma Cecelia ita ,wannan Gloria ta amsheta,kuma na tuna komi ko da Accident d`in ya faru banga Gloria ko gawarta ba kenan hakan na nufin duk inda Gloria ta ke `yata Jadeeda na tare da ita". Sai da Mama Hadiza ta sauke a jiyar Zuciya sannan ta ce da ita,"Ki yarda da Allah ki d`auki k`addarar da ta same ki,ki sani har jana'izar Jadeeda an gabatar to me yai saura da ya wuce ki yarda da Allahn ki kar`bi abinda ya saukar a kan ki,wanda ya baki `yarnan fa yafi ki sonta shine fa ya amsheta to don me za ki tada hankalin ki,ya kamata ki fara k`ok`arin sake sabuwar rayuwa domin ki samu cigaba a cikin rayuwar ki,ba wai ki nemi sake jefa kan ki cikin wata sabuwar matsalar ki kalli fa halin da Mijin ki yake yana buk`atar taimakon ki,idan ki ka cigaba da tafiya a haka ba iya rayuwar ki kad`ai ba harda ta sa rayuwar za ki lalata". Tsuru Hibba tai tana mai mai-maita maganganun Mama Hadiza a cikin ranta,"Eh da gaske na ke miki ki tashi tsaye ki tallafi rayuwar ki da ta Mijin ki,kuma ki dage da addu'a ina mai tabbatar miki indai Jadeeda na da rai kuma tana taka doran k`asa sai wata rana ta nemeki ta dawo rayuwa da ke",Mama Hadiza na kaiwa nan ta tashi ta mik`e da niyar barin d`akin,shigowar Ummie Maryam ce ta d`an dakatar da ita. "Mama ashe ki na ciki,na shiga sashen ki na iske ba kowa"," Eh inanan na zo na iske ta tana yin sana'ar da ta saba,dan Allah ki rik`a gaya mata gaskiya wala Allah ko ma samu ta dawo cikin hankalin ta ta san abinda ya kamata ta aikata a cikin wannan lamarin "," To Mama amma wallahi inayin iyakar iyawata amma har yanzu ba nasara,hatta da Jaheed ya shiga cikin matsanananciyar damuwa saboda yawan ganinta a cikin irin wannan halin ". Sai da Mama Hadiza ta mai da kallonta kan Hibba kafin ta ce da ita"To ai shikenan tunda haka ki ka za`ba ma kan ki",ta na kaiwa nan ta bar masu d`akin. Wuri Ummie Maryam ta samu ta zauna kusa da ita tana mai d`ora hannunta akan ta ta ce," Kin gani irin wannan abun nake guje maki tun da farko,Na sani kina cikin damuwa da kuma tashin hankali amma ki sani ba iyake abun ya shafa ba,duk wani na kusa da ke ko kuma mai k`aunar ki yana jin zafi rad`ad`i da kuma damuwa kamar yanda ki ke ji,kar ma Mama domin itama d`in uwace ta kan fi kowa jin zafin abu ko murna idan ya samu d`anta,ina mai tabbatar maki ko ke ba lalle ki kaita shiga cikin tashin hankali da damuwa ba,ki kalli yanda ta rame ta fita hayyacinta ko barcin kirki fa ba ta iya samu,ga yawan cuttuka da ke cikin samunta kuma hakan yasamo asaline da sanya damuwar ki a cikin ranta,ya kamata ki ji tsusayinta,ki rage wannan damuwar,wai ma meye zai sa ba za ki saurari Maganar da ta ke fad`a mi ki ko sau d`aya ne ba,ki tsamota daga cikin yanayin da take a kai , ko hakan kad`ai ka iya sawa Allah ya sassauta ko ya yaye maki halin bak`in cikin da ki ke a ciki". Sai da Hibba ta sharce hawayen da ke fitowa daga cikin idanunta kafin tace,"Shikenan Ummie Maryam in sha Allahu daga yau ba za ku sake ganina a cikin irin wannan yanayin ba,zan dan ne duk abinda nake ji in barshi a iya cikin Zuciyata har zuwa sanda Allah zai kar`bi rayuwata in dai har kan ne zai sa ku cikin farin ciki to zan aikata hakan duk da dai"...... Ta kasa iya k`arasa zancen nata, ita kanta Ummie Maryam hawaye ne ke zuba daga cikin nata idanun har ta bud`e baki zata sake cewa da ita wani abu ta fasa sakamakon ganin da take in har zasu cigaba da yin wannan maganar to ba za su ta`ba daina zubar da hawaye ba ko kuma su samu damar kawo k`arshenta ba,don haka sai ta za`bi yin shirin wala Allah zai zama mafi alkairi a gare su. "Ammm Hibba kina da bak`i fa", Ummie Maryam ta fad`a ta na mai kauda idanunta gefe. Cikin sabon yanayin da ya zame ma Hibba jiki ta tambayeta," Bak`i kuma ,a wannan lokacin su waye?","Daga Companyn su Abbakar ne,sun sake zuwa ne don su duba jikin shi ","To ba matsala ki sa a shigo da su mana", da to Ummie Maryam ta amsa mata tana mai juyawa har ta kusa fita ta waigo tace da ita," Ki d`an gyara fuskar ta ki kafin su shigo". Sai da Ummie Maryam ta sanar da Mama Hadiza zuwan na su,domin ta zo su gaisa ta had`a da saka Jaheed ya je ya sarna da su Baba Malam sannan ta sa a ka shigo da su,bayan sun shigo an gama gaggaisawa sun k`ara yi masu ya mai jiki da fatan Allah ya tashi kafad`unsa,sannan Acountern Companyn Abbas ya ce mu su,"Allah sarki Manager mutumin kirki ne dukkanin mu nan mun shaida haka,a d`an zaman da mu ka yi da shi tun yana matsayin Crista ba a ta`ba samun sa da wani yana musayan miyau da shi balle har ta kai su ga yin fad`a ba,ga gaskiya ga kuma rik`on amana gaskiya ba mu da wani abun fad`a akan shi in har ba yabo da jinjina zamu yi gare shi ba,ba kuma wai a gare mu kad`ai ba hatta manya da kuma k`ananun ma'aikata ,suna ta kuka gami da jajantawa akan abinda ya yafaru da shi ne ". " Tabbas Acounter Maganar ka gaskiya ne wanda hakan ne yasa shi asalin mamallakin Companyn ya aiko da wad`annan mutanen wasu likitoci ne guda biyu daga can Abuja suke kawai don su dubasa su bashi kulawar da ta kamata in ta kama a kai ga a fidda shi zuwa k`asar waje ne sai a fidda shi". "Kai Bayin Allah, Allah ya saka maku da alkairi, mun gode mun gode,ku Isar da sak`on godiyar mu ga shi Ogan na ku,ni ban ma San da wanne baki ya kamata in nuna muku jin dad`in wannan abun da kuka zo mana da shi ba,Allah ne kad`ai zai iya biyan ku,ya saka maki da alkairi yai maku tukwuici da Gidan Aljannah", Cewar Baba K`arami Wanda hatta a muryasa zaka gane yana cikin farin cikin game da abinda ya saurara. "Kar ka damu wannan duk can-cantar da shi Abbakar d`in yayi ne,ba sai ka yi wani Godiya ba, suna son a samu wani yayi masu cikakakken bayanin abinda ya ke faruwa da shi,da kuma irin matakin da ya ke akai a yanzu". Nasir ne yai masu cikakakken bayanin asalin da yanda abun ya faru," Ya samu buguwa ne akan shi sakamakon accident d`in da ya gamu da shi Wanda a turance muna kiran wannan cutar da suna Neurological disorder the Conditions affecting the brain, spinal cord, and nervous system (e.g., epilepsy, multiple sclerosis). Also Neuro developmental disorder Conditions affecting brain development (such as ADHD, autism spectrum disorder),a ta haka in ka kalle shi zaka iya cewa barci yake ba dan wannan oxygen d`in da aka sanya mashi ba ,wannan shine matsalar da take damun shi". "Ammmmm but amma in dai condition d`insa a wannan matakin ya ke bai kamata ace kun na jinyarsa a cikin Gida ba,zai fi samun Good treatment da samun ingantattun magungu ba da kuma nagartattun kayan aiki ya akai haka Doctor Nasir ?".d`aya daga cikin Doctors d`in ya tambaya. "Eh haka ne nasan da hakan amma kasan irin wannan problem d`in yana da matuk`ar hatsari da don bin taka tsan-tsan gami da lura dalilin ba d`aya ne da ya sa Na dawo da shi,da zaran wurin da yake,yanzu zai fara shebaring yana shirin fad`owa,yanzu da ace zamu kaure da surutu a cikin wannan d`akin duk da kasancewar sa baya iya ko motsa d`an yatsan shi to da haka ce zata kasance". " Okay na fahimci inda matsalar take yanzu za muyi mashi `yan wasu gwaje-gwaje da zamu je muyi amfanin da su,Amma na so ace zamu iya admitting nasa a Hospital yanda zai samu kulawa da shi 24/7,amma hakan ma ba damuwa zan turo Nurses guda biyu da zasu rik`a taimakawa Madam wajen kula da shi, har zuwa sanda zamu kammala namu binciken". Godiya Sosai Mama Hadiza,Baba K`arami, Nasir da kuna Ummie Maryam suka rink`a yi ba, don ita Hibba ba bakin magana sai faman zubar da hawayen farin ciki ta ke, a tare su duka suka tafi raka su bayan sun gama duk abinda za suyi har sun kusa fita daga Gidan Abbas Acounter ya dakata yana nai cewa da su yana zuwa yayi mantuwa,"Madam zan iya shigowa ?",Yace da Hibba bayan yayi sallama ta amsa. Tsaye take akan Abbakar tana mai motsa mishi wasu daga cikin sashen jikin saboda gudun kar su mutu su daina amfanin,"Am kana neman wani abu ne ko kuwa ka yi mantuwa ne ?",Hibba ta ce da shi. "Madam ba mantuwar da nayi,Na zo ne na Isar da sak`on da aka bayar in baki tun kafin yanzu". " Sak`o kuma wanne irin sak`o ne wannan haka ?",Hibba ta tambaye shi,bai bata amsa ba sai zura hannunsa yai a cikin aljihunsa ya fiddo wani Embolof daga aljihunsa ya mik`a mata yana mai cewa,"Wannan shine sak`on da yalla`bai ya bani akan sai bayan ya dawo bikin k`anwar shi,in ya tafi seminar d`in da yake shirin tafiya sai in kawo maki,to kafin hakan ta faru wannan tsautsayin ya fad`a akan sa,shine na yanke shawarar in kawo maki ko da abun ciki ba zai amfani ba,ni dai na sauke alk`awarin da na d`auka ". Amsa Hibba tai idanuwanta na fara k`ok`arin zubda hawaye, ta amsa tana mai yi mashi Godiya. Jikin Hibba na rawa ta fara bud`e Embolof d`in abinda ta gani ne yasa numfashi da kuma jikinta tsayawa cak,sai da ta d`auki wani dogon lokaci kafin ta dawo cikin hayyacinta,hannunsa guda ta kama ta rik`e kam tana mai d`ora kanta a saman gadon da yake kwance tare da fashewa da kuka cikin mad`aukakiyar murya tana mai cewa "Me idanuwana ke gani,wacce irin cutarwa ce na aikata ma kaina,Na cutar da kai na zama silar salwantar mana da `ya d`aya tilo da muke da ita kai kuma ga ka kwance cikin halin mutuwa da rayuwa,duk don saboda tsananin fushi da son kaina da ban hassala ka ba da idanuwanka basu rufe daga ganin motar da ta tunkarowa mu ba,da yanzu ina tare da kai da kuma ƴata ɗaya tilo da na ke da itanikam wacce irin Mata na zama,wacce irin uwa ce ni mai salwantar ta ran `yarta da kuma ta Mijin ta,bayan kai ka kasance mutum mafi adalci kyautatawa a gare ni,kullum buri da fatan ka ka ga na zama abar kwatance,Na cika buri da duk wani fata da nake da shi,da wacce irin fuska zan kalle ka aduk ranar da ka warke ka tambaye ni ina Jadeeda ta ke, da wanne baki zan iya gode maka irin tarin alkairan da ka yi min a iya d`an zaman da muka yi tare da kai?"...... Da sauri Ummie Maryam ya k`arasa iso kusa da ita tana mai tambayar," Lafiya me kuma ya k`ara faruwa ?".kasa iya cewa komi tai sai nuna mata Peppers guda biyu da ke zube a k`asa ,d`auka tayi ta fara dubawa,d`aya admission na shiga jami'a ne a matsayin d`alibar jinya,sai na biyun kuma dogon bayanin ne akan yanda yake sonta da kuma murnar samun admission da yake taya ta,daga k`arshe ya ke cema ta ta kula da kanta da kuma Jadeeda har zuwa ran da zai dawo. "Mene ne abin tashin hankali a cikin wannan lamarin naga kamar takardar cigaba da karatu a university ce waye ya samo ta?"," Shine ya samo min tun kafin faruwar wannan a'lamarin ya bari ne yai surprised d`ina sai kuma hakan ta faru ". Sai da Ummie Maryam ta samu guri ta zauna tana fuskantar Hibba sosai da sosai kana ta fara cewa da ita,"Hibba ki natsu wannan babban dama ce kika samu, bai kamata ki yi wasa da ita ba,a da idan kin d`auki wannan karatun a matsayin buri ko fatan ki,to a yanzu ki canza ki d`auka Cewar za ki yi karatu dan Mijin ki,za ki rayu dan shi ki yi karatu dan shi,ki manta da komi da ya faru,ki farfad`o da rayuwar ki da tashi a lokaci guda,kar ki wasa da wannan damar". Shiru Hibba tayi na wani lokaci kafin ta bud`e baki tace,"Ummie na yi miki alk`awari zan yi amfani da wannan damar da kuma shawarar da ki ka bani,zan yi karatu ko dan Mijina,zan zama Malamar jinya ko dan shi ya cigaba da rayuwa ya samu kulawa ta, zan yi iya yi na don ganin haka ta faru". Sosai Ummie Maryam ta ji dad`in wannan lafazin na Hibba har sai da ta kai ga ta rungumeta. Wannan kenan After 5yrs A guje ta fito tana mai kwalama Ummie Maryam kira ta na mai d`oki da murna,"Mun samu damar ganin Likitan kwakwalwa a can U.s.a,Ummie muna cikin alkairan Allah ". Cikin zumud`i Ummie Maryam ta ce," Kai Alhmdllh Masha Allah gaskiya muna cikin alkairi yanzu bayan Schoolarship d`in da ki ka samu ,kuma sai ga wannan babban alkairin ya zo ?". "Ke dai bari Ummie ga Mama can ta tafi ta sanar da Baba Malam ,nasan shima zai yi farin ciki, har Baba K`arami da kuma Yayah Nasir na Kira a waya na sanar da su, yanzu haka na san Baba K`arami ya kusa isowa domi mu fara tsara yarda zamu yi tafiyar,kin San fa tare da Yarona zamu tafi", ta kai zancen tana mai fad`ad`a fuskarta da murmushi. " To ai dama nasan da haka Jaheed ai d`anki ne in ki ka tafi ki ka bar ni da shi, ai ba zan iya ji da rigimar shi ba,dan haka addu'a ce tsakani na da ku,yanda kuka sanya mashi rai a wannan tafiyar ai in baku tafi da shi ba ba zaman Lafiya kaf Gidannan don haka Allah ya ba Abbakar lafiya ya sa wannan shine k`arshe wahalarsa,ku kuma Allah ya sa albarka a cikin karatun da za ku yi". Haka dai suka cigaba da murnar su har sanda su,Baba Malam, Baba K`arami da kuma Yayah Nasir su ka zo,suka cigaba da tsara yanda komi zai tafi game da da tafiyar su Hibba, lokacin da mutanen Gidan suka samu labarin wasu sun yi murna wasu kuma a fili suka rik`a bayyanar da hassadar su a fili,amma a cikin su ba wanda ya kula su,sai ma k`ara k`aimi da suka yi game da shirin su. *JADEEDAH* STORY & WRITTEN BY : (*Cwt~Sumiey*) Marubuciyar littafin MENE NE ABIN YI ? KARAGAR MULKI And now.....*JADEEDAH* BOOK 1 *YOTA* PAGE 17❤ Gudu ta ke tsalawa na fitar shari'a akan saman titin Tafawa `Balewa Area 8 ,yanayin yanda take tsala gudun kad`ai ya Isa ya tabbatar maka da ba a cikin natsuwarta take ba,gab da zata hau titin da zai sadata har zuwa babban gate d`in Garki Hospital Abuja ,ta buga ma motar dake gabanta,runtse idanunta kam tai tana ambaton suna Jesus da neman agajin gaggawa a wurinsa. K`arfin bugun ne yasa motar da ta daka kaucewa daga Saman kan titin har sai da ta kai ga bugar wata bishiya dake gefan su,kafin ta tsaya cak kamar an rik`eta cikin gaggawa da hanzari Dr. Imam Muh'd Jaheed shi da Driver d`in da ya d`auko shi suka fito daga cikin Motar da har ta fara fidda hayak`i. Kasa cikakakken motsin kirki Jedeeda ta yi har na wani d`an lokaci,ganin yanda Driver d`in ya nufo ta a fusace ya sa tai hanzarin fitowa daga cikin tata motar tana mai fuskantar shi da jiran me zai fara fitowa daga bakin sa. "Are you out of your sense, ta ya za ki rik`a yin wannan mahaukacin gudun a saman titi,sai ka ce dan ke kad`ai aka yi titin ko kuma na Gidan ku ne titin?".Saurayin Driven ya ce da ita cikin tsawa da d`aga murya. "Hey...hey hold on how dare you are da zaka rik`a yi min magana cikin tsawa,Call the mechanic I will pay the bill".....," Me ne? Maganar kud`I ki ke a irin wannan k`adamin magana fa ake ta tsakanin mutuwa da rayuwa, wace ce ke me ki ke tak`ama da shi da har ki ke wannan kurin ?". "Hmmmmmm bana da Lokacin `batawa da kai ina cikin uziri just name the price or you can call your mechanic I will pay the bill,ka fahimce ni?, ina cikin wani uziri mai muhimmancin gaske".duk wannan abun da ke faruwaDr. Imam Jaheed ya na gefe nad`e da hannayensa a k`irji yana kallon abinda yake faruwa a tsakanin su. "Okay tunda haka ki ka ce let me call the Police ko ba kome za su `bata maki lokacin da ki ke ikirarin baki son `batawa kin ga inya so sai ki biya bill ta hannunsa". " Oh Jesus Christ ",Jedeeda ta fad`a can k`asa tana mai dafe kanta da hannunta na dama," Ka ga zan baka kud`i iya adadin da kake so but don't waste my time, so please accept the money instead of my apology ". Sakin baki Drivern yayi yana kallonta da tunanin ina wannan rashin kunyar ta ta zata kai ta,ji yai ba zai iya kyaleta ba har sai ya kai ga yin reporting d`in ta ko ba komi zai samu sauk`in rashin kunyar da ta yi masa. Ganin da gaske kiran Police d`in zai yi yasa ta saurin dakatar da shi ta hanyar cewa," Ammm......I'm sorry kar ka kira su cause I can not stay,this's my my card you can call me anytime in ya so sai mu kai k`arshen batun ",ta kai zancen ta na mai d`ora masa card d`in nata a saman wayarsa da yake k`ok`arin kiran number Police ta ko ta `baci. " To hell with your card, har ke wace ce,me ki ka d`auki kan ki da har ki ke iya fad`ar duk abinda ya zo maki a bakin ki ba tare da Kin yi duba da irin asarar da ki ka janyo min ba,dubi fa ki ka ga yanda motata ta koma duk a saboda ke ,ita fa ce hanyar da nake ci da ahalina da ita,ke kawai hankalin ki na kan lokacin da za ki `bata,mai yasa ba za ki tsaya ayi ficzing d`in matsalar da ke ki kayi causing d`inta ba, Don haka na rantse mi ki sai Na yi reporting d`in ki ko ke yar wace ce kuma ko da hakan na nufin ba za a biya ni hak`ik`i na ba,ko ba komi zan `bata maki lokacin da ki ka nuna kin fi martaba shi fiye da komi"...... "A'a let her be kyaleta ta tafi,ni zan biya duk abinda ya kamata ayi,ko ba komi kai Namiji ne kuma sama da ita ka ke,ka fita nisan hankali da kuma sani abinda ya kamata,just one thing da na ke so daga gare ka ka samar mani da wata tacxi d`in da zan idasa inda za ni cikin sauri",Cewar Muh'd Jaheed da ya iso inda su ke. Da hanzari Jedeeda ta d`ago kanta ta na mai sauke idanunta akan shi,eh tun d`azu ta san ba iya Driver d`in ne kawai a cikin motar ba, amma hankalin ta bai sake komawa a kan shi ba,rasa me ma za ta ce da shi tai,sai juyawa tai ta nufi inda ta ta motar ta ke domin barin wurin. Cikin d`acin rai da zafin abinda ta aikata Drivern ya bita da kallo ji yake inama wata kyakykyawar isaka zata taso ta yi gaba da ita ,da ya ji dad`in hakan, hakan ya d`ar su a ransa ne sakamakon yanayin k`irar halitta da ta ke da ita,kwata-kwata bata da k`iba shi is slim girl,ta Na da matsakaicin tsawo,wacce ba zaka iya kiranta gajera ko kuma wacce ta cika tsawo ba,irin medium d`in nan haka take,plazon wando ne a jikinta sai kuma wata `yar riga `yar k`arama da iya gabanta kawai ta rufe mata daga baya kamar belt ne ya rik`e ta kawai,ta tara gashin kanta wuri guda sai faman reto yake. "Kaga kira Mechanic d`in da zai iya gyara maka motar ka,domin ina son in bar wurinnan da wuri"..... K`arar da wayarsa ta fara ne ya dakatar da shi, picking call d`in yai muryarsa d`auke da sallama. " Jaheed lafiya dai ko?,ka ce min ka kusa isowa tun d`azu amma har yanzu na ji shiru,Matarnan fa tana cikin critical condition ne fa?". "Uncle Nass mun samu accident ne",....." Subahanallahi kana lafiya dai ko ba abinda ya same ka ko ?". "Ina lafiya ba abinda ya same ni har ma da driver d`in da mu ke tare motarce kawai ta samu Matsala". "OK Masha Allah I will be here right now ka jira ni,tura min location d`in inda ka ke ganinan zuwa", Uncle Nass ya fad`a ya Na mai barin duk abinda ya ke. Kamar wacce aka hankad`o ko kuma wacce aka biyo haka ta shigo cikin room d`in da Mahaifiyarta ta ke kwance ba tare da ta san inda hankalin ta ya ke ba. " Nora ya jikin Momy a wanne mataki ta ke a yanzu ?",shine abinda ya fara fitowa daga bakin ta. Da d`an gudun wacce a ka Kira da Nora ta k`araso kusa da ita idanuwanta na fara zubda ruwa,"Anty she is still in unconscious situation, tun jiya a haka muka kawota",..."What tun jiya a cikin wannan halin take kuma kuka zauna a cikin Hospital d`in,where is Papa ina ya tafi ?","Ammmm Asibitin suna iya bakin k`ok`arin su yanzu haka Ana jiran zuwan wani Special Doctor ne,Wanda yake kula da `ban garen masu lalura irinta Momy,to jin shirun yayi yawa ne ya sa Papa ya tafi ya dubo ko lafiya har yanzu bai iso ba". Jadeeda rasa me ma za tai tayi sai kai da kawo ta cigaba da yi a cikin d`akin Asibitin. Sheshshekar kukan Norah ne ya dakatar da ita tayi kanta da sauri,"Norah lafiya ki ke,me ya same ki,ko kema ba ki da lafiya ne,why are you crying ?",duk ta jero mata wad`anban tarin tambayoyin a hargitse. Cikin muryar kuka ta bata amsa da cewa,"I'm so afraid, ina jin tsoro kar wani abu ya samu Momynah, ina jin tsoran haka,wannan wanne irin ciwon kai ne haka mai tsanani da azaba Wanda har ya ke d`aukewa mutum ji da ganinsa ,Momy fa har fita tai daga cikin hayyacinta tai bata San mun iso wannan Asibitin ba fa". "Kin ga Nora ki kwantar da hankalin ki ba abinda zai faru da ita da sunan Yesu Almasihu, cuta ba mutuwa ba ce,Allah ya na aiko ma bawanda da ita ne don ya jarrabe shi,ya ga zai iya cinye wannan jarabawar ko ba zai iya ba,ko kin manta ISAIAH Chapter 43 Verses 19 yana cewa "Do not lose hope in time of trouble, for God is working in the unseen.His hand is steady, and his timing is perfect in bringing good out of difficulty", haka ma a cikin MATTHEW Chapter 7 Verses 7 yana cewa," Ask and it will be given to you, seek and you will finds,knock and it will be opened", don haka bai kamata ki sa damuwa a ranki ba kin ji ko". Wata sassanyar ajiyar Zuciya Nora ta saki Wanda hakan ke nuni da ta samu sassaucin abinda ta ke jin tsoran game da ciwon Mahaifiyar ta ta,bayanin `yar'uwarta Jedeeda ya kore mata shakku da kuma jin tsoran da ta ke cikinsa a baya,hannu Jeddeda ta sa ta janyo ta kusa da ita tana mai kwantar da murya ta duk dan ta samu ta kwantar mata da hankali,"Let's prayer for her, in Jesus name za ta samu sauk`i kin ji",a tare su ka nufi inda take kwance akan gado,a tare suka kai gwuiwowin su a k`asa gami da runtse idanunsu tare da kama hannun Mahaifiyarsa da ke mafi kusa da su suka rik`e tare da cewa,"Heavenly Father, I seek your healing touch We come before You with hearts full of hope,Our sweet mother lies here, weak and silent.But we know, O Lord, that You are the Great Healer.Please touch her body with Your healing power.Restore her strength, renew her spirit.Let Your peace cover her like a blanket.We still need her, Lord. Please don’t take her from us yet. We trust in You, Lord. Your ways are higher than ours. Even in pain, we will praise You. Heal our mom, dear God, if it be Your will. And help us be strong while we wait. Amen" Bayan sun gama addu'ar ne sai ga shigowar Papa da hanzari Jedeeda ta matsa kusa da shi ta na tambayarsa da cewa,"Ya ake ciki Doctor d`in ya k`araso ko?","Ki kwantar da hankalin ki my Daughter bai iso ba motar shi ta samu matsala amma ga Doctor Nass can ya tafi ya taho tare da shi da zaran ya zo Mahaifiyar ku za ta samu sauk`i". "Oh har hankalina ya kwanta tunda komi zai yi sauk`i da zaran ya zo"," By the grace of God ". A can `bangaren Jaheed hankalin shi kacokan Na kan duba file d`in patient d`in da zai duba tun bayan had`uwar su Dr Nass," Uncle Nass hankalina ya tashi Matarnan she is in critical condition, wannan wanne irin ciwon kai ne mai matuk`ar rikitarwa haka ?","Kai dai bari ni kaina ranar farko da aka fara kawota na ga halin da take ci,shiyasa ma na ce ka zo ko zaka taimaka mata". "To Allah ya taimaka mana,ya kuma bamu ikon aikata alkairi muga abinda za mu iya akan hakan", da haka dai suka cigaba da tafiya har suka isa,ba tare da `bata lokaci ba suka fara shirin zuwa su ga patient ta su. Esther ce ta shigo hannunta rik`e da baskets na abinci Momy Rebecca na biye da ita a bayanta,wan da suma sai yanzu da safe su ka sami labarin rashin lafiyar . Kanta Momy Rebecca tayi tana mai cewa," Oh My Daughter Gloria me ya same ki,wannan wanne irin ciwo ne haka,Yarinya ace ba a wani dogon lokaci da ita sai ace gata can kwance ba ta san inda kanta yake ba"......,"Mom ki yi hak`uri za ta samu lafiya in the name of Jesus Christ, kar ki damu kan ki kin ji". "Haba Revered Anderson ta ya za ka ce kar in damu kana kallon halin da ta ke a ciki kuwa,ko ko..motsi ba ta yi ba ta ma fa san na zo nan ba", " Akwai Doctor yananan zuwa zai dubata,idan har ya dubata naga ba wani improvement sai in fidda ta wata k`asarnan kawai". "Hakan shi ya fi Papa,ni kaina hankalina bai kwanta da wannan Hospital d`in ba", Cewar Nora,shigowar wani Doctor da kuma Nusses guda biyu janye da gadon d`aukar marasa lafiya," Mr Anderson Doctor d`in da zai dubata ya iso yanzu haka an umarce mu da shigar da ita Emergency, Sanan ku kuma a canza maku d`auki kafin a fito da ita"Cewar d`aya daga cikin su. "Okay ba matsala nan ", Nusses d`in su ka wuce da ita Emergency shi kuma ya tafi ya nuna masu sabon d`akin da aka ce ya kai su. After some hours," Congratulations Revered Anderson mun samu mun shawo kan matsalar da ke damunta yanzu haka muna saran farkawarta ta nan da wani d`an lokaci ",shine furcin da Dr Nass ya fara yi bayan fitowar su daga Emergency d`in. " Praise be to Allah,the one who control everything around the world,blessed be to the God Father of our Lord Jesus Christ, wannan shine abinda tun d`azu muke dako da kuma fatan ji daga gare ku",Nan fa kowa dake cikin d`akin su ka fara nuna jin dad`i da kuma godiyar su,don Jedeeda kuwa runtse idanunta tai tana mai had`e hannayenta wuri guda, ita kad`ai ta San me take cewa a cikin Zuciyarta,daga bisa ni ta kai hannunta saman goshi da kuma gefe da gefan kafad`unta. Bayan sun d`an natsa Dr Nass ya ce da shi, "Am Doctorn da ya dubata yana buk`atar ganin ka a office d`in sa","Okay ba damuwa ma iya tafiya yanzu ?"," Yes uppcourse yana can ya na jiranka". Har sun kusa fita Jedeeda ta dakatar da su da cewa,"Papa in biyo ka mu tafi tare ?","A'a ki zauna I will be back soon kin ji my Daughter ".jiki a sanyaye ta koma ta zauna domin Maganar gaskiya ta so ta ji musabbabin wannan ciwon Na Momynta. A mutunce Muh'd Jaheed suka gaisa da Revered Anderson kafin Jaheed ya ce da shi,"Sir ina so ne in san shin Madame ta ta`ba fuskantar wani hatsari ne ko kuma wata buguwa haka akanta ?", Sai da Revered Anderson ya d`an d`auki lokaci kafin ya ce da shi," Yes uppcourse ta ta`ba had`uwa da accident shekaru baya,but amma a lokacine mai tsawo ta ce min ta ta`ba fad`owa daga kan bene,bayan haka ban san komi ba,kuma ba na tunanin an d`auki wani action mai kyau akan wannan lamarin ". " Ayyyah I'm so sorry to say,saboda wannan incident d`in ta samu wani ciwo a cikin kanta Wanda shine ya ke ja za mata yawaitar wannan zazzafan ciwon kan muna kiran wannan ciwon a likitance da Neurogical disorder but amma it minor in sha Allah Na maka alk`awari zamu iya shawo kan matsalar anan". "Jesus Christ Doctor ta ya za ai haka ta faru,it's almost sama da shekaru Ashirin da biyu,ta ya za ai ace sai yanzu illar hakan ta bayyana a yanzu". " Sir ka fahimce ni,ko ba ka ji me Na ce ba tunda farko,it's a minor a baya ba ta kai shekaru haka ba,a yanzu jikin ta ba zai iya jure rad`ad`i da zafin ciwon kan ba kuma ina mai tabbatar maka wannan ciwon kan ba yau ta fara shi ba ,sai dai abinda na ke so da kai ka bincika ka gani za ka tabbatar da abinda na ke fad`a maka". Shiru Revered Anderson ya k`arayi na wani dogon lokaci, kafin ya ce,"Zan yi iya k`ok`arina wajen ganin na binciki abinda ka ce,yanzu wanne mataki ku ka d`auka akan wannan ciwon, sannan me kuke buk`ata daga gare mu ?". "Ta na buk`atar hutu ba ta san hayaniya, don haka mun kai ta d`aki na musanman ,sannan akwai the same case irin wannan wanda ya ke a k`ark`ashi na don haka zamu d`orata kan irin wannan treatments d`in har zuwa sanda za muga k`arshen abun da izinin Allah,Sannan da akwai shawarwari da zan ba ka Wanda su ke da buk`atar a kula da su ,amma yanzu lokacin sallah ya yi zan je in dawo in ya so sai mu sake zama anjima". "To shikenan Doctor Na gode I will wait you", da haka dai suka sallama su ka fito domin zuwa su gabatar da sallah azhur *JADEEDAH* STORY & WRITTEN BY : (*Cwt~Sumiey*) Marubuciyar littafin MENE NE ABIN YI ? KARAGAR MULKI And now.....*JADEEDAH* *YOTA* BOOK 1 PAGE 18❤ "Wallahi Momynah kar ki so ki ga Matar,na yi mamaki matuk`a the same irin case d`in Uncle banbancin d`aya ita it's minor ne". " Ya Salam My son na tausaya ma ta nasan zafi da kuma yanayin jigata ga wanda Allah ya jarabta da irin wannan ciwon na juyewar kwakwalwa, Allah ya bata lafiya ". "Amen Momynah sauk`in ta d`aya Hedeache kawai ciwon ya fara sakar mata a matsayin sing d`insa". " To da d`an sauk`i za ace sai ka natsu ka fara fahimtar a wanne mataki take akai shin Epilepsy,ADHD,Multiple sclerosis ko kuma Autism Spectrum ne daganan sai kusan wanne mataki ya kamata ku d`aura ta akanta". "Eh na duba hakan sai dai na ga ta mataki na Epilepsy mataki Generalized seizures wanda hakan ya ke sa tai loss of consciousness". " Da kyau that's my boy,yanzu a cikin matakai uku da ake d`auka game da wannan cutar wanne matakin za ka fara amfani da shi,Medications to control seizures,Surgery ko Lifestyle changes ?". "Momy I think i chose the number one ,kamar zai fi in hakan bata faru ba sai mu janza da wani options d`in". Sai da Hibba ta nisa kafin tace,"Focus on the person first not their condition. Treat them with dignity and respect ka ji ni?", ta cigaba ba tare da ta tsaya ba,"When referring to someone with a brain-related issue, it's essential to use respectful and person-centered language.By using respectful language, we can promote understanding, empathy, and inclusivity". " In sha Allah Momynah zan kasance kamar yanda ki ka tarbiyantar da ni ina k`arami ba zan ba ki kunya ba zan yi kamar yanda ki ka ce ". " Momynah ko dai za ki zo ki yi takin over akan wannan case d`in".... "A'a ba zan zo ba kai ma ka sani,kuma ni ma nasan you will do better"...." Mom da gaske na ke fa ". " Hmmmmmm Jaheed ta ya zan bar Kano in taho Abuja in duba wata bayan nima ina da nawa patient d`in ai haka ba mai yiwuwa ba ne ba". "Momy please shi's in unconscious condition she need your help" "Ka ga Jaheed abu d`aya ni ke ganin zan iya shima sai in ka ga `bullowar wata Matsala ne wacce ba ka gane ma ta ba, ko dai ta ziyarci ni anan a Hospital d`in da na ke aiki ko kuma in cigaba da treating d`in ta online while kai kuma kana monitoring d`in,shi ne kawai abinda zan iya". " To au ba matsala tunda har za ki iya bata wani d`an lokaci daga cikin lokuttan ki ai hakan ya wadatar mana,mun gode da wannan alfamar",ya kai zancen ya na mai saluting d`inta. Murmushi ta yi kawai ba tare da ta ce da shi komi ba,sai shine ya ce da ita," Ina Uncle yau ba ki bani shi mun gaisa ba". "Jaheed kenan Uncle d`inka yananan yanda ya ke kamar kullum", ta kai zancen ta na mai maida akalar Camerar wayar yanda zai samu damar ganin sa ta Video Call d`in da su ke,an samu canji akan da don yanzu yana iya zama ba kamar da da sai an kwantar an tayar ba,ya kan nuna alamar in yana jin yunwa ko k`ishir ruwa amma daga ba haka ba ba abinda zai iya yi maka ko kalma d`aya daga cikin bakin SA ba ya iya furtawa. " Momy mai yasa ba za mu yi jump to the next level ba akan Uncle, an kwashi tsawon shekaru masu yawa ya kamata ace improvement d`in da aka samu ya fi haka". "Hmmmmmm My son nima na yi irin wannan tunanin amma Dr Liyo ya dakatar da ni ya ce in bari muga zuwa k`arshen wannan year d`in daganan sai asan abinda za ai". "Hakan ya kamata domin ni kaina ma k`osa in ga Uncle d`ina ya dawo kamar yanda na san shi a baya"...... Ya dakata sakamom jin knocking d`in da aka fara yi mishi,ya mutsa fuska ya yi kafin ya ce da ita,"Momy i have a visitor ya katsemin jin dad`i na, Allah har na k`osa lokacin tashi yayi in tafi Gida don ma matsalar ba zan iske daddad`an abincin ki ba mai kamshi da saukar da natsuwa ga wanda ya ke ci". " Au za ka fara tsokanar ta ka ko,yaushe rabon ka ma da cin abincin nawa ?,bayan ga matan ka can `yan zamani wanda su ka fi ni iya girki".....kasa hak`ura yai da cigaba da saurare ta sai d`aga mata hannu yai yana mai cewa,"By Momy I will call you letter da zaran na koma Gida",Ya kai k`arshen Maganar ya,na mai ending call d`in. Sake Knocking d`in akai a wajen karo na uku,"Yes come in",ya fad`a ya na mai gyara fuskar sa ya,koma asalin Iman kuma Dr Muh'd Jaheed,ka sa iya sakin k`ofar tai ta shigo sakamakon yin tozali da fuskar da ba tai zato da tsanmani ba. Ba ita da ta shigo office d`in ba har shi Muh'd Jaheed d`in sai da yai mamakin ganin ta. "May I come in", ta sake tambaya muryarta a rarrabe," Yeah you can come in, have a seat",ya kai zancen ya na mai nuna mata kujerar da za ta zauna. "Da me zan iya taimaka maki",ya tambayeta yana mai tsura mata ido da tattara hankalin shi akanta. Sai da Jedeeda ta tattaro d`an sauran natsuwa da kuma kwarin gwuiwarta kafin ta ce da shi," Suna na Jedeeda Anderson mahaifina ne wanda d`azu ku kayi da shi zai dawo ka bashi shawarwarin hanyoyin da za a bi domin kula da mara lafiyar,ya ce min ka buk`aci wasu papers a wurinsa don haka ya tafi Gida domin ya d`auko daganan yace if possible ka sanar da ni advice d`in".tsura mata ido yai yana son ya gano wani abu mai muhimmanci daga gare ta wanda yake jin yana jan shi zuwa inda ta ke amma kuma ya kasa gano komi ye,dole sai haƙura yayi gami da zuba mata ido yana jin me ta ke cewa. Cikin k`ank`anin lokaci yai mata bayanin irin su kula da shan maganin ta,rashin son hayaniya a inda take,yawan lura da halin da take a ciki a koda yaushe,samun isasshen barci,aikata abubuwan da ta fi so da dai sauran su,ya kai k`arshe zancen da wannan. Jiki a sanyaye Jedeeda ta mik`e ta na mai cewa da shi,"Thanks a lot Doctor na ji dad`in bayanan ka kuma by the will of God za a yi kamar yanda ka ce kuma za a kiyaye abinda ka ce".Hakanan ya ji muryarta har a saman kan shi,har sai da takai shi ga kafeta da idanuwansa masu tasiri ga wanda ya ke kallo. Sai da ƙyar ya iya cewa da ita bayan ya samu ya mallaki kan shi, "Don't Mind in har da zai ku yi amfani da duk abinda na ce in sha Allah a hankali a hankali za ta rik`a samun sauk`i,idan ba wani abu da yai saura za ki iya tafiya". Rasa me zata ce tai ta so ace ko Yaya ne ya bata damar da za ta yi magana akan abinda ya faru da`zu amma ko da wasa bai ba ta fuskar hakan ba kamar ma ba da shi abun ya faru ba,har ta kusa k`ofar fita ta ji ba za ta iya fita ba har sai ta ce da shi wani abu akan abinda ya faru,sai dai tana jiyowa da niyar ko yunk`urin ta ce wani abu,aka banko k`ofar da k`arfi a ka shigo batire da an ba mai shigowar izinin hakan ba. Bakinta na rawa ta fara ambaton sunan shi da cewa," Papa lafiya what wrong with you,ko dai jikin Momyn ne ya motsa ?". Ko d`aya bai saurare ta ba domin gabad`aya hankali da tunaninsa ya na kan kan Dr Jaheed, "Dr kalla ka gani na kasa yarda da abinda na gani a jikin this papers Anya da gaskene Gloria na sane da wannan cutar sama da shekaru Ashirin,kai I can't believe this". Amsa Dr Jaheed yai ya na duba paper's d`in na wani d`an lokaci kafin ya ce da shi," I'm sorry to say Sir domin Maganar gaskiya Madam Gloria ta san da wannan lalurar har ma tana medication d`inta ka ga wannan takardar shaidar ta ziyarci wani babban Asibiti ne U.s a shekarar 2018 wannan kuma photon kwakwalwar kanta ne da aka d`auka a Paris in the year 2007 da kuma sauran test-test da ta gudanar akan hakan". "What Momy ta san da wannan ciwon at how", Jedeeda ta tambaya fuskarta d`auke da mamakin abinda ta ji. " Kun ga bai kamata ku tada hankalin ku ba domin hakan zai iya sake jefa ita patient d`in cikin wani hali in har ta farka ta gan ku a haka,yanzu ba lokacin maganar ba ne ba,ta lafiyarta mu ke,mu gare mu ma bayyanar wannan hujjojin wata sabuwar nasara ce domin zamu yi amfani da ita mu cigaba da d`orata akan medication d`in da ya kamata". "Kai .....hah....why are you doing that for me,how long mu ke a tare amma ba zaki sanar da ni wani abu daya ya ke damun ki ba ,wannan wanne irin betraying ne haka shin dama can ba zaman amana mu ke ba?".... Dakatar da shi Dr yayi ta hanyar zaunar da shi kan d`aya daga cikin Seater's dake kusa da shi nan ya cigaba da bashi baki har ya samu ya shawo kan shi hankalin shi ya d`an kwanta kafin ya maida kallonta akan Jadeeda ya ce da,ita,''Am if possible ki d`auke shi ki mai da shi Gida yai wanka ya d`an huta ya ci abinci sai zuwa anjima sai ki dawo da shi may be zuwa time d`in ma ta farka amma dan Allah na rok`e ku Dan Allah kar wanda ya ta da wannan Maganar for now domin ta na buk`atar hutu". " I promise you ba abinda zai faru ba wanda za sake tada maganar a dai yanzu mun gode da kulawarka a gare mu,thank for your care, kindness and consent ". Da murmushi ya amsa ma ta abinda ta ce d`in nan ta kama hannun Revered Anderson Wanda ya zama kamar sick person su ka fita daga cikin Hospital d`in gabad`aya. ~~~~~~~ "My World da alama dai yau ka yi aiki da yawa domin ga gajiyanan duk ta bayyana akan fuskar ka". Hannunsa ya kai ya na mai shafa kan shi har zuwa saman fuskarsa kafin ya ce," Ke dai bari Gimbiya ta tamkar mutanen jirana su ke,ko kusa ban samu wani lokaci da zan huta ba". "Eyyah I'm so sorry My World na ga hakan kwance akan fuskar ka,ga shi kuma ba kowa a tare da kai sai kai kad`ai". " Ayush kar ki damu I will be okay ,yanzu ba ga ki ba,in sha Allah komi zai koma normal ". " A'a ni ba haka na so ba,iya haka bai wadatar da ni ba". Murmushin gefan baki ya sakar mata wanda yake k`ara k`awata fuskarsa kafin ya ce da ita,"Ko za ki taho yanzu ne kin san zan yi farin ciki da hakan ?". Zaro idanunta waje ta yi tana mai cewa,"Rufa min asiri kar ka sa Ummu Nurain ta zo ta addabe ni da masifar ta babu gaira babu dalilin". "Matsoraciya ki taho mana"....sai da Gimbiya Ayush ta `bata fuska kafin ta ce da shi,"Ni wallahi ba tsoranta na ke ji ba,kawai ba na biye mata ne don kar ajina ya zube,me ye zai sa ma inyi hayaniya ko fad`a da ita sai ka ce ba Gimbiya Ayush ba,in ma ba dan k`addara da ta had`a ni Auren Miji d`aya da ita ba ai da ko hanyar da na bi,ba ta isa ta bita ba". Sosai ta zage sai zuba masifa ta ke,shi kuma ya tsura mata ido tamkar television,ganin kamar ya zuba ma wuri guda Ido ne ya sa ta ta d`an dakata ,sai a lokacin ta fuskanci ita ya ke kallo. " Wai har haka ake kishina kuma ake sona ban sani ba ?"ya tambayeta ba tare da ya tsaya ba ya ce,"Ashe ni Muhammad Jaheed d`an gata ne har haka ban sani ba". Bata iya ta ce mi shi komi ba sai sake tamke fuskarta da ta yi alamun har yanzu ta na kan k`adamin fushi akan Maganar da ya yi. "Ina son ki,ko fushi ki ka yi kyau ya ke k`ara ma ki,komi ki kai burge ni ki ke kuma k`aramin son ki ya ke,kin can-canci a so ki,daga nan ina iya haikato daddad`an k`amshin da ke fita daga jikin ki,ke d`in ta daban ce you are so classic woman". Irin wannan dad`ad`an kalaman ne suka ribaci Gimbiya Ayush wanda tuni ta ma manta da wani batun Ummu Nurain da yai mata har daga k`arshe take cewa da shi," Ya kamata fa ace ka zauna kayi dogo tunani cikin jagorantar Al'umma `bangaren Addini ko kuma kula da lafiyar su wanne za kai ,ka ajiye d`aya,ba na son in rik`a ganin ka cikin irin wannan yanayin, kwata-kwata ba ka samun hutu kullum cikin aiki ka ke". "Hmmmm Gimbiyata kenan ba abinda za a fasa walau jagorantar Al'umma ko kuma kula da lafiyar su domin duka aikin taimako ne ,aikin Allah kuma kin ga bai kamata in janye daga wani `bangaren ba tunda duka suna da buk`ata ta". Bud`e baki Gimbiya Ayush ta yi da niyar za ta sake cewa da shi wani abu ya dakatar da ita da cewa," Addu'ar ki kawai na ke nema da kuma fatan nasara akan komi,sai dai ban sani ba ko hakan ya na sawa in shiga hak`ink`i ba?",ya tambaye ta yana mai tsare ta da idanunsa"A'a ni ko d`aya ,kawai dai ba na son in cigaba da ganin ka a yanayin da na ke ganin ka". "Kar ki damu ba abinda zai faru da ni ,ina tare da Allah, kawai Addu'ar ki na fi so da kuma kulawar da ki ke bani", da haka dai su ka kai k`arshe firar ta su da ita. Gyara zaman laptop d`in da ya ke aiki da ita yai sai dai tun bai yi nisa ba wayar shi da ke gefan shi ta fara rurin nai man a gaji,sai da yanayin fuskar shi ya sauya kafin ya picking d`in call d`in muryarsa d`auke da sallama. " Haba Abu Nurain wannan wane irin rashin adalci ne,me na aikata ma ka har haka da ka za`bi ka wofintar da ni ka nuna ma duniya ni ba kowan kowa ba ce a wajen ka, kar ka manta nifa `yar'uwar ka ce,ko ba so akwai zumta a tsakanin da kai ". " Ya Allah Zeenat mai yai zafi har haka mai ya kawo irin wad`annan k`ananun zancen ?". "Oh k`ananun zancen ma za ka kira maganar da na zo da ita,yau kwanan ka nawa da tafiya ba Kira ba sak`o hasalima ban sa ina ka tafi ba kar ka manta ni ma fa Matar ka ce kuma Uwar d`an ka ina da hak`k`i akan ka". Cire wayar Jaheed yai daga kunnen shi yai kamar zai yanke kiran sai kuma ya fasa ya san hakan ba K`arami K`ara rurar wutar rikici zai ba. Cikin sanyi da kuma gajiyar da ya ke tare da ita ya ce da ita,"Ban san me ki ke so ki mai da ni ba Zeenat,ke fa na zo part d`in ki ki ka rufe min k`ofa kawai dan kin ga na fara shiga Part d`in Gimbiya Ayush bayan dawowata daga office,gabad`aya ki ka tashi hankalina,ki ka hanani natsuwar rai, Randa kuma zan yi tafiya tun da farar safiya na na zo inda ki ke ina maki magana amma ki iya ki bud`e idanun ki ki kalle ni ki ka kasa , balle har in sa ran za ki saurari abinda na zo ma ki da shi,haka na k`araci zamana na gaji a haka ki ke iya bayyana ta ki Soyayyar ta hanyar wani mahaukacin kishi na ki marar amfani ?". " Ni ban wani san ka zo ba,kuma kai ma ai kasan Nurain ba ya wani barina in yi barcin kirki,kullum cikin fitina da k`iriniya da rashin ji ya ke,da safen kawai ne na ke samu in yi barci mai isata,kuma ai nasan waccen Matar son ka sanar da ita kafin ka tafi sai ni da ba a bakin komi na ke ba"...... "Kin ga Zeenat ba na son tashin hankali ,in dai kin kirani don ki tada min hankali ne sai da safe". Tana k`ok`arin sake cewa da shi wani abu ya katse kiran ya barta da wani sabon takaicin a cikin ranta ,ba shi ya tashi daga nan inda ya ke ba har sai da ya kusa raba dare daga k`arshe ya tashi yai sallolin sa kafin barcin wahala ya kwashe shi akan prayer mat d`in *JADEEDAH* (It's a story of two love birds who are so different from each other ) STORY & WRITTEN BY : (*Cwt~Sumiey*) Marubuciyar littafin MENE NE ABIN YI ? KARAGAR MULKI And now.....*JADEEDAH* https://chat.whatsapp.com/CWkZfMqvD4H0mtd7WW6Xbz. https://whatsapp.com/channel/0029VapqU8C002T5Bz8RSQ0a BOOK 1 PAGE 19❤ "Wow Gimbiya Ayush irin wannan Ado haka sai faman k`amshin da walwali ki ke sai ka ce wata sabuwar Amarya,ko dai Doctor na kan hanyar dawowa ne?", Anisa ta tambaye ta na mai sake bin ta da kallo. Sai da Gimbiya Ayush ta rausayar da kanta gami da jujjuyawa kafin ta ce da ita, " Ba d`aya k`anwar biyu,wannan kwalliyar da ki ke gani na yi ta ne domin rad`in kaina ba,babu inda zani Doctor kuma sai nan da zuwa three days zai dawo". "Yauwa Gimbiya Fadeelah ina sak`on da Fulani ta bayar ta ce ki kawo min ?". " Oh ya na motor na baro shi amma in zamu tafi sai in d`auko miki". "Ina ba ki isa ba salan kuma ki manta ki sake komawa da shi Masarauta". " Kai Anty Gimbiya yanzu fa muka zo ko ruwa ba ki bamu ba, ki ke Maganar tafiya sai ka ce wad`anda ki ke kora". "Na fa san halin ki Fadeelah tsaf za ki iya sake komawa da shi,kad`an ne daga cikin aikin da za ki iya,kuma Gidan ai ba bak`on ki ba ne ba ba kin san hanyar da fridge d`in ya ke". " Haba k`awata Fadeelah fa now is a big girl ta ya za ki rik`a mai da ta baya,ita ma fa ta san aikan Fulani ne ba za ta yarda ta manta ba". "Yauwa Anty Aneesa fad`a mata dai,kowa yasan yanzu na girma". " Hmmmm kin girman dai Fulani ta gama sangarta ki ai".....,Anesa ta katseta da cewa,"Wai ke tsaya da za mu wuto na ga k`ofar Part d`in waccan Matar kamar a rufe kar dai ki ce min da ita yai tafiyar ?". Sai da Gimbiya Ayush ta zaro idanun ta waje kafin ta ce"Wai wa ki ke nufi kar dai ki ce min Ummu Nurain, ai ko k`ofar Gida in ba ta zama dole ba ba zai tafi da ita ba balle Gari ya gaarara har Abuja". "Ki ce har yanzu ta na nan da halin ta na k`azanta" ,"Ai in gaya maki sai abinda yai gaba,yanzu da za ki shiga Part d`in ta ba lalle ki iya shak`ar iska ba,sai fitinannen kishin tsiya,kamar wacce ke had`iyar wuta". "Ta`b aiko ta na ruwa,wa ya gaya ma ta yanzu mata na zama da k`azanta ai kai duk ya waye,ba irin wannan duhun kan"," AI ko ban da ita ita da yanzu za ki fara yi mata complain kan bata yin tsabta sai ta ce,maki ai Nurain ne ba ya barin ta zauna sakat,kullum cikin sa ta aiki ya ke, idan ki ka matsa sai ta ce har da laifin Dr. da ya hanata d`aukar me aiki,har ma `yan'uwanta sun kai ga gajiya da yi mata magana sun kyaleta,ke ni wallahi da ni Imam ya fara Aura na rantse zai yi wuya ya k`ara kallon wata mace bare har ya kai ga yin sha'awar Aurenta". "Ikon Allah warnder shall never end wai yau Ayush ke ce ki ke crushing akan d`a Namiji ki ke bayyanar da mayatar son shi a fili abun akwai d`aure kai da ban mamaki".Cewar Anesa k`awarta ce tun yarinta sai kuma Gimbiya Fadeelah da take k`anwarta. " Hmmmm ba za ki gane ba Anesa,dagaske ina son Imam Jaheed so kuma ba irin na wasa ba,Wanda har ya kai na kan iya mantawa da asalina ko ni wace ce idan ina zaune tare da shi rikid`emin ya ke ya koma shine Yariman ni kuma a matsayin hadimar sa, duk wani abinda ya ce shi nake yi ,bana son sa`bawa dokar sa,ki na gani saboda gudun `bata mishi rai ya sa Na sallami duk wata Baiwa da na zo da ita Gidannan ". Sake baki Anesa tai tana mai bin Gimbiya Ayush da kallo," Ki gane Anesa Soyayya da Ustaz akwai dad`i da tsayawa a rai,idan ki ka samu irin wannan dama kar ki yi wasa da ita".....shigowar Hameed ita ce ta dakatar da zancen na ta. `Dan dakatawa yai kafin ya ce,"Anty Gimbiya bak`i ki ka yi ashe ?". "Eh Gimbiya Fadeelah ce da kuma Aneesa,ka shigo ma na ka tsaya daga gefe". " Au ashema ba baki ba ne `yan Gida ne",ya kai zancen ya na mai wara idanunsa a cikin Parlourn daga bisa ni ya samu wuri can gefe ya zauna". "Meet my friend Anesa sai kuma Gimbiya Fadeelah autarmu" cikin mutuntawa su ka gaisa da juna kafin ya ce,"Ai na san Gimbiya Fadeelah amma a IG ina d`an ganin videos d`in ta haka", da d`an sauri Gimbiya Fadeelah ta d`ago tana mai sauke idanunta akan shi. Murmushi ya sakar mata kafin ya ce,"Eh Hameed Abubakar Mai Fata shine suna na har DM na ta`ba yi maki so d`aya amma ba feedback,daganan ban sake ba ".ya kai ƙarshen ya na mai sakin fara'a a saman fuskarsa " Fiye da haka ma za ka gani kai ba a IG ba hatta a Gida cikin Masarauta haka Gimbiya Fadeelah ta ke,sai ka zo ka ka gama abinda ka ke a Gidan ba tare da ka sa ta a cikin Ido ba"Cewar Gimbiya Ayush. "A to Na yi shiru tunda abun haka ya ke", rasa me ma Gimbiya Fadeelah tai sai dai bin sa da kallo da take,shi kuma a lokacin ya maida hankalin sa kacokan wajen Gimbiya Ayush ya na mai cewa da ita," Am ki yi hak`uri tun jiya Yah Imam ya ki rani ya ce in zo in tambaye ki ko da akwai wani abu da ki ke so ko ya k`are a cikin Gidan,sai in je in siyo ma ki". "A'a ha ba yace ya kusa dawo fa?"," Eh haka ya sanar da ni,amma kin sa ko da ya dawo bai fiye zuwa irin wannan wurin ba","Na sani na yi zaton ko ya d`aga Maganar dawowar shi ne","A'a yananan ko d`azu da muka yi waya da shi haka ya gaya min". "Okay akwai kayan abincin wadatattun a store fridge d`ina ne kawai kayan cikin sa su ka fara k`asa sai kuma Vegetables, kai duk abinda ya kamata ka siyo ka siyo kawai". Mik`ewa tsaye tare da cewa,"Okay bari in je yanzu in dawo fatan dai ba inda za ku don sauri na ke da akwai inda za ni in na dawo?". " A'a ba inda zamu,in ma da inda zamu sai in bar maka sak`o wurin gate keeper","To ba damuwa hakan ya yi barin in je part d`in Ummu Nurain in ji na ta sak`on ". "In ka shiga ka gaishe min da ita"..... Da sauri ya katse ta da cewa," Wa!?,Ni a'a ba dai ni ba ai wannan sai ki ja in na shiga in fito da k`afa d`aya". "Yo kai ko me zai ja maka fitowa da k`afa d`aya sai ka ce Wanda ya shiga wani bak`on wuri Gidan yayan ka fa ne". "Hmmmmmm ko ma Gidan waye kin san Maganar da kika fad`a ba za ta haifar da d`a mai Ido ba,kin ma ga tafiya ta ba zan so wannan maganar tai tsawo ba",ya na kaiwa nan ya bar ma su Parlourn, ya nufi Part d`in Zeenat Ummu Nurain. Da shigar shi cikin Parlourn da sallama ya fara cin karo da tarin sharar da akayi ba a kwashe ba da kuma kayan sawa zuzzube a k`asa har ma da,kwaninkan abinci. " Dan Ubanka ba za ka tsaya ba,ka tsaya in cire maka rigar ko kuma in bar ma ka kayan tsiyar ka in ba ka son wanka",shine zancen da ya fara ji a,kunnensa bayan shigarsa Parlourn. A sanyaye ya yi sallama Wanda Nurain Na jin Sallamar ya kwace daga hannun Umansa da gudu ya nufi wurin sa ya Na kiran Oyo yo Uncle Oyo yo ,d`aga shi sama yai yana murnar ganin sa da yai ,"Oyo yo my son ya ka ke ya rashin ji ya `barna"....d`an dakatawa yai yana mai sake kai hancinsa jikin Yaron kafin ya ce da shi,"A'aha Nurain kwata ka fad`a ne da Na ji irin wannan wurin na ta shi a jikin ka?". "A'a ba kwata na fad`a ba,Umma ce ta dai na yimin wanka,sai ta ga dama",idanu kawai Hameed ya zuba mata wanda nan da nan ta sha jinin jikinta ta ce da shi," Ka ga shirmen shi ne kawai fa, ka san yanzu lokacin sanyi ake shi kuma akwai yawan ciwo ga Nemonia da ta ke yawan addabar sa shine fa na koma a sati bai fi in yi nasa wanka sau d`aya ko sau biyu ba duk dan kula da lafiyar sa". Shiru Hameed yai ya na mai k`ok`arin danne abinda ya ke jin ya na taso ma sa a cikin Zuciyarsa,da k`yar ya iya ya ce da ita,"Ya Imam ne ya aiko ni ya ce in tambaye ki ko da akwai wani abu da ki ke so ko kuma ya k`are a Gidan sai in siyo ma ki"..... "Ka koma, ka ce ma sa bama buk`atar komi daga gare shi ya bar mu mutu,in tunani ya,ke don abinda ya ke bamu mu ke Raye har yanzu dan Allah ka ce ya daina bamu komi,ba ma buk`ata". " Subahanallahi Ummu Nurain mai yai zafi haka,ta ya za ki rik`a fad`in irin wad`annan munanan maganganun kan wannan `yar Maganar?,kar ki manta shifa Wanda ya aiko ni a matsayin Mijin ki fa ya ke". "Ka ga ba ruwan ka kai d`an aike ne,ka koma ka sanar da shi abinda na ce da kai,za ka zo ka wani tasa ni da wani k`auli da ba'adi ", ta kai k`arshen zancen ta Na mai figar hannun Nurain,nan ta ke ya fashe da kuka ya na kiran sunan Uncle d`insa. Ko minti d`aya Hameed bai k`ara a Parlourn d`in ba ya fita Zuciyar shi cike da tausayin d`an'uwansa da kuma irin rayuwar da ya ke gudanarwa. "Yauwa Anesa ina sak`ona fatan ke ma baki manta ba kamar yanda Autar Fulani ta man ta min da sak`o", Gimbiya Ayush ta tambaya. " Wa ina ni ina mantawa da sak`on ki Ai ban Isa ba gashi na taho da shi",ta kai zancen ta na mai zuge zif d`in Jakarta ta mik`a mata tare da cewa,"Doctorn ta rubata yanda za ki sha shi sannan ta ce da zaran kin sha zai yi waje ba jira"...... "Anty Gimbiya kar dai ki ce min Maganar Abortion d`innnan har yanzu ta na nan ba,kuma ba Gimbiya Bahijja ta dakargta da hakan ba tunda farko ?".Fadeelah ta katse su gabad`aya da sigar tambaya a cikin lafazinta. "Kin ga Fadeelah wannan rayuwata ce ni ce ahak`k`u da in yanke ko in tsarama kaina yanda na so da ita,ni ba zan bari in yi sakaci har in kai ga aikata kuskure irin wanda ko wacce mace ta ke aikatawa ba,shin ko baki ga misali akan Ummu Nurain ba,tun bayan haihuwar Nurain duk ta bi ta lalace k`azanta kamar ba mace ba,kar ma yanzu da ta ke d`auke da wani cikin,don haka ni ban shirya haihuwa yanzu ba,ina son Mijina ta yanda zan iya aikata komi akan haka,ban shirya tara tarkacen tara yara a yanzu ba". " Ke Fadeelah ki ja bakin ki ki yi mana shiru anan mu sa'annin ki ne, kuma wai ma ina ruwanki da wannan Maganar wa ya kasa da ke,da har ki ke shirin d`auka,shin ko cikin a jikin ki ya ke ?".....Cewar Anesa "Dan Allah ki dakata min Anesa da `yar'uwata na ke magana ba da ke ba dan haka ki d`an saurara min kuma da kike maganar ciki ba a jikina ya ke ba,Na ga kuskuren da ku ke son aikatawa a fili ne,wands son Zuciya da kuma dogon buri ya makantar da ku wannan cikin fa halastaccen ciki ne me ye laifin sa me ye aibu dan kun bari ya zo duniya kamar kowanne d`a,wannan fa ba shi ne karo na farko da ki ka zubar da ciki a cikin Gidannan ba shin ba za ki ji tsoran wani abu ya same ki wajen zubar da cikin ba ko kuma asirin ko ya tonu ?". Da zafi Anesa ta sake ta so mata da niyar ta dakatar da ita,da sauri Gimbiya Ayush ta dakatar da ita da cewa," Kin ga bita a hankali,don gudun samun wata matsalar kin Santa za ta iya yin komi don ganin ta lalata mana shiri gara mu fahimtar da ita ta fuskar da za ta gane ". Kallon ta mai da kan Gimbiya Fadeelah cikin fuskar tausayi sai da ta zauna ku sa da ita ta dafa ta sannan ta ce da ita,"Mun ta so tare ni da ku,duk da kasancewar na girme ku amma ba wata tazara ba ce a tsakanin mu,muna tsaka da karatunmu Me martaba ya katse min karatu ya bada Aure na,duk da bana son Aure a wannan lokacin haka na haƙurƙuntar da kaina na danne dogon burin da ke a cikin rai da zuciyata, Na ji a yanzu ina son Mijina ina son yin rayuwa da shi,shin a matsayin ki na k`anwata kuma `yar'uwata ba za ki taimaka min da hakan ba, Kalle ni fa ki gani duka shekaruna nawa ne da za'ace in fara tara yara yanzu, shikenan fa da zaran na haihu ba ni da sauran lokacin kaina,shikenan duk inda zani zan tafi da yara buuuuuu daga wannan ya ce Momy yunwa na ke ji,Momy toilet za ni,Momy zan sha ruwa,Momy ki dafa min ka za Momy ki siya min ka za,Momy this Momy that,Haba ba zan iya d`auka ba".ta kai zance ta na mai yamutsa fuska. Baki sake Gimbiya Fadeelah tai ta Na kallonta har sai daga k`arshe ta ce mata," A haka ki ka fahimci abun ashe,lalle kin jahilci kan ki,Haba Ayush me ya ke damun ki wai what is on your mind Anya kuwa da gaske ki ke ki Na son Mijin ki kuwa ?,indai har dagaske ki na son shi za ki so tara Zuri'ah da shi in ba shima d`anyen tunani ne da shi kamar na ki ba,ko da ya ke nasan ba shi da masaniya akan wannan lamarin na ki ba,Dan haka ina mai ba ki shawara da ki ji tsoran Allah ko dan gudun kar lafiyar ki ta samu matsala nan gaba". "Kin ga kar ki yi mata baki in sha Allahu lafiya lau zai fita ba abinda zai faru da ita, duka-duka sau nawa aka yi abortion d`in ba sau uku ba ne ba kawai". Mik`ewa tsaye Gimbiya Ayush ta yi tafara juyi a gaban Fadeelah ta nai mai cewa da ita," Kalle ni da kyau tundaga Sama har k`asa kalli irin kyakykyawar hallitar da Allah yai min,ta ya zan bari in fara haihu tun yanzu,structure d`in jikina ta canja, tafi-tafi k`irjina ya kwanta saboda tsabar tsotso ya koma tamkar sleepers, banda hayaniyar yara,bari-barin su da kuma sa aikin tsiya,gara ban haifa ba balle ace ban kula da suba,hakan yafi min sauk`i"..... Mik`ewa tsaye Gimbiya Fadeelah ta yi ,"Ya isa haka dan Allah ki yi duk abinda ki ka so na bar ki da hankalin ki amma kar ki kuskura ko da wasa ki neme ni in ta kwa`be mi ki",ta na kaiwa nan ta sa`ba hand bag d`inta tai hanyar waje. Cikin tarin funshin da Gimbiya Anesa ta ke a ciki ta ce da ita, "Ki gaida na gaba na baya su san da uni", ta na mai maida hankalinta kan Gimbiya Ayush ta na mai mik`a mata maganin ta ce da ita ," Afa shi kafin nan da anjima ayo waje da kayan banza ko kin huta". A yanda Gimbiya Fadeelah ta fita a cikin `bacin rai ko gabanta ba ta gani wanda hakan ya sa ko kad`an ba ta ga Hameed ba da yake k`ok`arin shiga ta shi motar,cikin d`an d`aga murya yai mata magana,"Ya dai kina lafiya kuwa ?",shine Maganar da ta biyo baya daga bakin shi. Cikin inda-inda ta bashi amsa, "Normal lafiya me ka gani?". Cikin siga ya wayance mata da cewa," Kin fito ki yimin rakiya zuwa supermarket d`in ne ko?","A no ba haka ba ne ba,I have something urgently ne shiyasa zan tafi". Sai da Hameed ya gyara tsayuwarsa kafin ya ce da ita,"A'a gaskiya ban yarda ba na ga hakan a cikin idanun ki ne shiyasa Na fad`a dan haka kawai ki biyo ni mu tafi". Yak`e kawai Gimbiya Fadeelah ta ke domin babban burin ta taga ta bar Gidan tun kafin wani abu ya faru a ce da sa hannunta a ciki. "To shikenan in ba zaki yi min rakiyar ba shigo sai in maida ke Gidan", ya katse mata gajeran tunanin da ya ke son ribatarta. " Kar ka damu Na gode this my car ni na zo da ita,don haka in sha Allah zan Isa Gida lafiya ". " Yes I know It's your car but amma Sister d`in ki fa,ita a wacce za ta tafi ba sai ki bar mata wannan ba ni in sauke ki a Gida","Idan na isa Gida zan sa Driver ko d`aya daga cikin fadawa ya zo ya d`auketa". Sai da Hameed ya d`aga hannayensa sama kafin ya ce"Okay okay Na fahimci you did not enjoy my company so I will leave you ". Idanuwa a waje Fadeelah ta zaro ta na mai rasa me kuma za ta ce mi shi,yanayin yanda ta yi ne ya sa ya fara yi mata dariya ya na nunata ,sai da su ka d`an d`auki lokaci mai tsawo kafin kowa ya shiga motar shi yai gaba,bayan ya tabbatar ya rage mata damuwar da ta fito da ita. *JADEEDAH* (It's a story of two love birds who are so different from each other ) STORY & WRITTEN BY : (*Cwt~Sumiey*) Marubuciyar littafin MENE NE ABIN YI ? KARAGAR MULKI And now.....*JADEEDAH* *YOTA* BOOK 1 PAGE 20❤ "Granny I'm serious I hate this country, ke ce kawai ki ka matsa akan sai mun dawo ,but tunda,mu ka dawo ban ga wani abu da dawowarmu ta amfana maki ba,tunda mu ka dawo Momy sai ciwace-ciwace ta ke, kullum ba ta da lafiya"... "Gidan ku Na ce Nora,haka ake yi ma nagaba da ke magana dama,mene ne ya shiga cikin kan ki,ko kina son ki zama disobedient gilr ne?", Revered Anderson ya katse da tsawa. "Ka ga kar kai mata tsawa,she is my granddaughter ,hankali da tunanin ta bai nuna ma ta amfanin jajircewar da na yi akan ku dawo ba". " Eh duk da haka bai kamata ta yi magana da ke a cikin irin wannan lafazin ba dan haka ya zama wajibi ta baki hak`uri don Gobe kar ta kuma ko kuma ta fuskanci hukunci na". Sai da Nora ta matsa har kusa Mom Rebecca sannan ta bata hak`uri, janyo ta jikinta tai ta na mai rungume ta tare da cewa,"Ba ki yi komi ba my love rashin sani ne amma ki sani iya ganin ku kawai da nake a idona abu ne mai matuk`ar muhimmanci a gare ni,ina buk`atar ku a kusa da ni,duk mace da ta kai shekaru kamar irin nawa ba abinda za ta so face ta rik`a yin tozali da `yan jikokinta a kusa da ita". "Na fahimce ki Granny im sorry ba zan k`ara fad`ar irin zancena na baya ba", Nora ta fad`i ta na mai sake shigewa jikin Mom Rebecca. " Yauwa ban tambayeka ya jikin Gloria yake ba,ina zuci-zuci in samu in iso kafin time d`in ganin patient ya wuce amma haka bai samu a gare ni ba sakamakon goslwo da ya rik`e ni". "Mun samu damar ganinta,Jadeeda ce ma farkon shiga kin santa da k`ulafu cin uwa,tunda su ka dubata su ka ce tana cikin yanayin da zamu iya shiga mu ganta ta fara kuka, har twins Nora da Martin sun fi ta dakakkiyar Zuciya da ta shiga ta dad`e ta na yi mata Addu'a bayan ta fito sai su Martin ,Ni kuma lokacin da Na shiga time ya k`ure dole ganin ka kawai na yi na fito,amma jikin da sauk`i sosai domin sun ce yanzu a kowanne lokaci za ta iya farkawa". " Thank God ,Thank you Jesus, thank you for what Haven done for us",ta fad`a ta na mai had`a hannayenta wuri guda idanuwanta Na kallon sama,kafin ta cigaba da cewa,"Na ji dad`in wannan labarin hankali na har ya kwanta",Mom Rebecca ta kai k`arshen zancen. Jadeeda ce ta matso kusa da ita tare da cewa"Ba k`aramin relief na samu ba da na ji Doctorn ya ce Momy should be okay za ta samu lafiya ta warke mu koma gida,don da fari har ma fara jin dama bamu baro UK ba, domin sanda muna can Momy bata fuskantar irin wad`annan ciwace-ciwacen". "Na ga alamun yarannan ba sa san zaman ku cikin k`asar ku ta gado ku ke ba,sai yanzu na K`ara tabbatar da gaskiyar Mom da ta ke cewa kowa ya bar Gida Gida ya barsa,ba Dan barin Nigeria da mukai ba da ba yanda za ai ku sa son wata k`asa fiye da ta ku a cikin ranku har haka ba,har ku ke jin zaman can ya fiye mu ku nan", Cewar Revered Anderson. " Haka ne Revered nima gani nai ba wani relative nawa a kusa da ni na koma rayuwa kamar wacce ba ta da wani gata,shiyasa fa na nace har sai kun dawo,iya ganin ku kawai ma da nayi hankalina ya dawo jikina,Na daina jin kad`aice da kewar Pastor Emeka, duk da har yanzu mutuwarsa ba ta sake ni ba". "Mom I'm sorry domin na gane kuskuren tafiyar da mu ka yi muka barki,Na rasa me ye ya shige min kai da har na biye ma Gloria mu ka kwashe wad`annan shekaru masu tarin yawa, ba tare da mun dawo Gida ba". Shigowar Martin ce ta dakatar da su daga hirar da su ke Wanda a hankali sai ga Easter da kuma Uncle Richal ya biyo ba, sosai shigowarsa ta ba su mamaki, kar ma Momy Rebecca, kanta gadan-gadan yai da sauri ta dakatar da shi ta na mai cewa,Stop! Don't ever touch me,kar ma ka matso kusa da ni,kai mutum ne mai son kan shi da yawa". Bai saurare ta ko kad`an ba har sai da ya dangana da inda ta ke yana mai cewa," Haba Mom ya za ai ki ce haka,ko kin ta`ba ganin inda d`a ya rabu da Mahaifiyarsa ai duk inda ya je zai dawo". Da k`yar ta samu ta cire shi daga jikinta ,sai faman zabga mashi harara ta ke,cikin Girmamawa su ka gaisa da Revered Anderson Mijin yayarsa,sannan daga baya Nora ta gaishe shi,Kafin Jadeeda itama ta gaishe shi ,wacce tun shigowar shi ta fara tsalle murnar ganin shi,bai amsa ba har sai da ya janyo ta jikinsa,"My love fatan dai ki na lafiya ba ki bari firgici da tashinhankali ciwon Momy ya cutar min da ke ba ?". Cikin farin ciki da jin dad`i Jadeeda ta rik`e hannunsa kafin ta bashi amsa da cewa,"Gaskiya Uncle miey hankalina ya tashi,Na ji tsoro sosai,amma yanzu komi ya wuce tunda Doctor Imam ya ce ta na samun sauk`i","Doctor Imam waye kuma haka ?",ya tambaye ta a tak`aice," Doctorn da Asibitin ya d`auko ne Dan ya dubata ya san me ya ke sosai da ba dan shi ba da yanzu ba mu san a wanne hali Momy ta ke a ciki ba". "Oh thanks to the Lord Jesus da ya kawo ma na shi domin ya zama silar samun lafiyarta". " To the best Uncle in the world ka samu wuri ka zauna ka bar wannan parrot d`in d`iyarnan ta ka ka zauna ka huta ga abincinan Easter ta zo da shi a zuba ma ka ka ci",Revered Anderson ya ce . "A'a kai ma kasan inhar ina tare da My daughter ba Na gajiya haka kuma yunwa ba ta da tasiri a kaina,saboda ita d`in ta daban ce komi na ta na daban ne a gare ni".... Nora ta katse shi ta hanyar kiran sunan shi," Uncle ni fa,ba fa ita kad`ai ce Daughter d`in ka ba",ta yi Maganar cikin shagwa`ba. "Wane ni Nora Kema ta daban ce a wurina,in ina kiranta da Princess ke kuma bari mu ga da me zan kira ki", ya kai zance ya na mai tafiya dogon tunani Turo baki Nora ta fara yi ,Wanda hakan ya sa Momy Rebecca janyo ta jikinta tana mai lallashin ta tare da cewa," Rabu da su, can wata rana zamu gan su a rana,shima Richal d`in ai ba wani Garin arzik`i ba ne ba,wai ma ya akai kasan muna wannan Hospital d`in kuma yaushe ka yanke shawarar dawowa k`asarnan bagatatan ba tare da wani ya sani ba,bayan mun kwashe sama da shekaru muna Kira da son ka dawo ka k`i ?".Momy Rebecca ta kai zancen ta tana mai mai da akalar zancen akan Uncle Richal da sigar tambaya. "Momynah kenan Na yi niyar surprise d`in ki ne kawai shiyasa na yo wannan tafiyar ta bazata,na samu labarin rashin lafiyar Sister,hakan ya sa na ji dole ina son in dawo Gida in ga halin da ta ke a ciki,bayan jirginmu yai landing Martin ya fara zuwan min a rai don haka sai na Kira shi a time d`in ya ke sanar da ni ya na Gida yanzu haka ya zo yai Fresh up sai ya koma Hospital d`in kawai sai Na jira shi, har ya gama sannan ya zo ya d`auko ni mu ka taho nan". " Hmmmmmm Richal kenan idon ka kenan sai yanzu sai yanzu ka tuna da Gida sai yanzu ka tuna kana da Mahaifiyar ,sai yanzu ka tuna kana da wasu ahali da su ke buk`atar ganin ka a kusa da su,shekaru har nawa almost five years tun mutuwar Mahaifinku ba ka sa ke d`ora k`afarka a cikin k`asarnan ba, Na dad`e da daina yi maka Maganar Aure na barka da hankalinka ka yi duk abinda ka ke ganin shine dai-dai a gare ka"..... "Haba Momy ya isa haka for God sake, yanzu ba ga shi na dawo ba,I'm begging you ki manta da komi,I promise hakan ba zai sake faruwa ba,kuma ga su Martin duk suna gun". " Da alama ba kasan zafi da rad`ad`in abinda ka aikata min ba, Ni kad`ai fa na koma rayuwa,I live the whole yers lonely tamkar wata mara gata,kuma da ka ke Maganar Yara ai nasan da su,ina maka fad`a ne a gaban su dan su san abinda ka ke aikatawa ba abu ne mai kyau ba,ina iya iyawa akan in ga ka sauya amma hakan ya faskara,ba zan so wani a cikin su ya rik`a aikata irin haka ba,ko kasan sai daga bayanan Gloria ta dawonan da zama ita da Zuri'arta duk dan saboda ni,da ba dan haka ba da bansan ta yarda zan cigaba da gudanar da rayuwata ba",ta kai zancen ta na mai had`iye wani abu mai zafi da d`aci . Zaraf Richal ya baro wurin da ya ke zaune ya iso inda Mom Rebecca ta ke zaune ya na mai duk`awa saman gwuiwowinsa,fuskarsa har ta fara canjawa ya ce,"Momy na rok`e k`i ,for the sake of Father Lord ki bar tada wannan zancen I swear to the Jesus name haka ba za ta sake faruwa ba,I promise zan zama d`a na gari zan yi duk abinda ki ka ce amma dan Allah ki bar bayyana fushin ki a kaina ,tsinuwar Yesu Almasihu za ta iya riska ta in har haka ta kasance,da gaske Na shirya yanzu zan yi Aure zan haifa maki Yaran da za su yi ta wasa a gaban ki ko Sweet Daughter ?",ya kai zancen yana mai maida hankalin kan Jadeeda . Kamar wacce ta ke jira a sata a zancen haka ta iso ta na mai duk`awa kamar yanda Uncle d`inta ya duk`a kafin ta ce,"Da gaske Granny Uncle miey ba zai sake tafiya ya barmu ba kuma zai yi Auren kamar yanda ki ke so,ni da kaina ma zan samo masa macen da ta dace da shi,amma sai kin daina fushi da shi". Allah sarki Zuciyar Uwa nan da nan tai sanyi sai ga shi ba a d`au wani lokaci ba har murmushi ta ke daga k`arshe ta ce da shi ta,"Ban ta`ba ganin irin shak`uwa da Soyayya irin ta ku ba,ina ganin yanda hankalin ta ya tashi saboda ina yi maka fad`a ko ita na ke yi mawa sai haka". Murmushi su duka su kayi daganan Jedeeda ta fara sarving d`in su lunch d`in da Easter ta kawo ma su,suna nan har dare ,sai dai ba su sake samun damar da za su ga Gloria ba ,dole sai su ka hak`ura sai zuwa gobe da safe. *JADEEDAH* (It's a story of two love birds who are so different from each other ) STORY & WRITTEN BY : (*Cwt~Sumiey*) Marubuciyar littafin MENE NE ABIN YI ? KARAGAR MULKI And now.....*JADEEDAH* *YATA* BOOK 1 PAGE 21❤ "Kin ga na fa gaya maki gaskiya ba zan sake dawowa Gidan ki dan yanzu ba,ki aikata duk abinda ki ke ganin shine dai-dai a wajen ki,amma wallahi ba goyan baya na a ciki,kuma kar wani abu ya faru ku sako sunana a ciki". "Eh Na sani Fadeelah,kuma na yarda amma dan Allah ki zo ,akwai maganar da na ke son mu tattaunawa akanta da ke"....."Hmmmmm Na san fa abinda ki ke nufi, kina tsoran kar in sanar da Fulani ko ki kwantar da hankalin ki ba wanda zai ji na yi maki alk`awari".ta Na kaiwa k`arshe zancen ta katse kiran. A fusace Gimbiya Ayush ta ciro wayar daga kunnenta ta na mai cewa,"Kai wai ni wannan Yarinyar za ta katse ma waya saboda tsabar rainin da ya shiga tsakanin na da ita,har yaushe ta kai matsayin haka?". " Hmmmmmm ke ki ka siya da kud`in ki,Dan me za ki rik`a lalla`bata akan me,ba rayuwar ki ba ce ba,ko a jikin ta cikin ya ke,tun jiya Na ke ce miki ki sha pills d`in nan cikinnan ya yo waje kowama ya huta ,amma kin kasa,ko dai kin fasa ne saboda tsoran zugar da za tai maki ? ". "Hmmmmm tsoro kuma Anesa,sai ka ce ba Gimbiya Ayush ba,kin tabbatar ba abinda zai sa in bar cikinnan, kawai dai ina son in bi komi a hankali don gudun afkuwar wani abu mara dad`i tsakanina da Mijina ko kuma Fulani". Wata `yar gajeriyar dariya Anesa ta saki gami da cewa," Ai na sha kin hak`ura domin har na fara gano ki,kina tafe da tirtsetsen ciki sai faman zama da k`yar ta shi da k`yar ki ke"......katseta tai ta hanyar kai mata duka tare da cewa,"God for bid ,Allah ya tsare ni bakin ki ya koma kan ki,ba ki san iya girman tashin hankalin da na ke shiga idan har na tuna cikinnan har yanzu ya na jikina ba, kuma kullum k`ara girma ya ke,kar ki so ki ga irin murna da farincikin da Imam ya nuna a lokacin da ya samu labarin cikinnan ga kulawa ta musanman da ya ke bani,ina hakan a raina duk sai in rasa ina zan sa kaina da kuma tunanin irin halin da zai shiga in ya ji labarin babu cikinnan ". " To ki bar shi mana in kina ganin tashin hankali a fuskar Mijinki sai ki jure duk wani challenge da zai biyo wajen rainon cikin da kuma bayan kin haife sa". "A'a Anesa hakan ba zai yiwu ba domin da akwai shagulgula da manyan taruka da za a gudanar a Masarauta bayan sallah ,a lokacin cikin ya Isa yai girman da zai hanani samun damar lashe kanbun Gimbiya da ta fi kowacce Gimbiya kyawu, Ado da kuma saka kaya masu tsada,bazan ta`ba barin wannan damar da na samu ta kubce daga hannuna ba na sha wuya kuma na d`au lokaci mai tsawo kafin in kawo wannan matakin dan haka ba zan yi wasa da ita ba". " In ko har haka ne ki na da gaskiya bai kamata ki bar cikinnan ba domin ina da yak`inin ko Alkyabba ba za ki sa ta yi maki kyau ba,balle a kai kan sauran kayan Ado,cha`b Ai ko mutum goma ba za ki samu wanda za su ya ba ta ki kwalliyar ba,wata k`ila kuma a samu amma a cikin Bayi amma ba dai `yan cikin Masarauta ko wad`anda ake gayyatowa ba". "Na shiga uku in haka ta kasance da ni ban san ina zan sa kaina ba,ina mai tabbatar mi ki da ba zan sake nuna fuskarta a irin wad`annan taron ba in har haka ta kasance". Wani murmushin gefan baki Anesa ta yi kafin ta ce,"In ko haka ne kar`bi ki sha ya fito waje kowa ma ya huta", ta kai zancen ta na mai d`auko ma ta ruwa a d`an k`aramin fridge da ke ku sa da ita. Amsa Gimbiya Ayush tai ta aje ta na mai kauda kanta can gefe ba tare da ta ce mata komi ba,cikin mamakin attitude d`in da ta yi Anesa ta ce da ita,"Me hakan ke nufi,kin sa ni a rud`u,ko dai so ki ke ce min duk abubuwan da ki ke fad`a ba gaskiya ba ne ba,ko kuma maganganun Gimbiya Fadeelah ne suke son wasa da hankalin ki,Fadeelah ba kowa ba ce face k`anwar ki,har ita wace ce,wanne matsayin ta ke da shi,me ta taka"..... A fusace Gimbiya Ayush ta dakatar da ita,sai dai ba ta iya ta ce mata komi ba har Saida ta saita kanta,ta rage fushin da take ciki gami da sassauta zancen da ke d`auke a bakin ta," Kin ga Anesa na gode da shawarwarin ki da kuma lokacin ki da ki ka ba ni,Na gode da hakan ki zo ki tafi Gida ,zan kira ki daga baya". "Mene! ki na nufin korata ki kai daga Gidan ki,akan me,me na aikata,ko shine sakamakon kasancewar da ke da na yi ?....ni...na ma rasa ne zan ce da ke". Ko motsi Gimbiya Ayush ba ta sake yi ba,har dai Anesa ta gaji da kallonta da ta ke,ta zari Jaka da car keys d`in ta yi hanyar barin bedroom d`in Na ta. "Ki gaishe da Baba Waziri da kuma su Umma Karema", Gimbiya Ayush ta ce da ita,Ko jiyowa ba tai ba balle ta sa ran za ta bata amsa. Kwanciya Gimbiya Ayush ta yi hannunta d`aya a saman cikinta ta na shafa shi,a hankali kamar mai rad`a ta ce," I'm sorry My Unborn Baby,ina son ka so mai yankan shakku dole ce kawai za ta sa in rabu da kai,Zuciyata ba za ta ta`ba bani goyan bayan in barka ba,zan yi fatan nan gaba bayan wasu shekaru ka sake dawowa a matsayin d`ana". ~~~~~~~~ "Momy kin tsorata ni,Na yi kuka na yi Addu'a,har sadaka na yi duk dan son in ga kin warke kar ki tafi ki bar ni". Gloria hannunta ta kai saman kan Jedeeda, cikin muryar majinyaci ta ce mata,"Haba `yata Jedeeda, ina za ni in tafi in barki,zan yi ta rok`on Allah da ya bani tsawon rai inga har `ya`yanki". Wata dariya ce ta kwace ma Jedeeda farinciki fal a cikin ranta," Zan so haka ta kasance ace har jikokina kin ga ni ba ma iya `ya`yana ba". "Momy I beg you kar ki k`ara barin ciwo yaci k`arfin ki har haka,mun shiga tashin hankali da damuwa a saboda haka", Nora ta fad`a ta na mai sake shigewa jikin ta. " I'm sorry kin ji Auta ta,I promise to you daga yau zan rik`a kula da kaina da zaran Na ji wani abu da ban gane shi ba,zan yi saurin yin magana akai ba zan k`ara barin family na su shiga cikin tashin hankali a kai na ba". Shigowar Granny tare da Uncle Rechal ce ta sake dawo da murnar farkawarta ta sabuwa. "Kin ba ni tsoro My Daughter Gloria, wannan wanne irin ciwo ne mai firgita ahali haka?". Cikin muryarta ta majinyata ta ce,"Mom ai yanzu komi ya wuce tunda gashi yanzu na warke,kuma wai kun manta da ake cewa,a woman who gets her strength from God can never ever be broken, don haka ba abinda zai same ni tunda ina tare da albarka Yesu Almasihu da kuma ta ki". Fuska d`auke da annuri Revered Anderson da shi da Martin su ka shigo ,hannun Martin d`auke da sabbin magungunan da aka sake rubuta ma Gloria, da sauri ya aje ledan ya matsa kusa da ita suka sa ta tsakiyar shida Nora. " Papa ya ake ciki ya Doctorn ya ce wanne mataki take a cike yanzu?". "Thanks to the Father Lord, ya ce kiji da sauk`i ,ga sabbin medicine nan ya rubuta mata ya ce ta sha na kwana biyu kafin daganan sai a sake check up d`inta daganan sai ya sa mana ranar sallamah". Fuskar kowa sai da ta nuna farincikin jin wannan batun,Granny ce ta kai dubanta kan su Martin ta ce da su," Kun ga `yan jikokina ku taso ku bata wuri ta d`an huta in ta k`ara samun sauk`i sai ku je ko ciki ne sai ta mai da ku,kun fa girma da wannan halin ak`allafa kun kusa 19 years ai kwa barma yara wannan d`ab'ar ko". Sake shigewa jikinta su duka biyun su kai,Wanda hakan ya sa Gloria ta sake rungume su kafin ta ce,"Mom ki bar su suna kewata ne ,kwana nawa ba su samu irin wannan kulawar daga gare ni ba". Jayayya ce ta `barke tsakanin Rechal da Revered Anderson kowa a cikin su na san ta fad`a mi shi me ta ke sha'awar ci ya je ya siyo mata,ganin da gaske ba Wanda zai hak`ura a cikin su sai kowa ya je ya siya abinda ya ke ganin za ta so shi. ~~~~~~ "A'ah Bibah yau ke ce a Gidan na mu", Ummu Nurain ta tambaya fuskarta d`auke da murmushi. " Wallahi kuwa Aunty Zeenat, ya Gida ya aiki ina Nurain ya ke?". Ta`be baki tayi kafin ta ce yanzu na kora shi ya bani wuri saboda ya dame ni,sai faman bari-bari na ke,ya su Umma Hanne fatan duk suna lafiya ?". "Eh ta na lafiya ta ce ma a gaishe ki,Yah Hameed ne ya je Gidan ya ce baki jin dad`i shiyasa ta ce in zo in da wani abun da zan taimaka mi ki da shi".Bibah ta kai zancen ta na mai wara idanun ta cikin Parlourn, tun kafin ta shigo cikin Parlourn ta tana tsakar Gida ta san yau za ta gaya ma `yan garinsu da aiki. " Shi Hameed d`in ne ya gaya miki ba ni da lafiya?",Ummu Nurain ta tambaya cike da mamaki. "Eh haka ya ce,ya mace daga nan Gidan yake kuma ".... Tun kafin ta kai k`arshen zancen tai zumbur ta mik`e ta na mai nufar bedroom d`inta in da wayarta ta ke,jikinta har rawa yake wajen lalubo Number sa ta fara Kira,Ringing d`aya biyu Ana uku yai picking, muryar sa d`auke da sallama tare da gajiya isowar shi masaukinsa kenan daga Hospital. " Yaushe za ka barni in huta ne,eyeh Abu Nurain, me na maka,shin ba ka jin tausayina ko kad`an, k`aramin cikinka na ke d`auke da shi ga kuma hidimar Nurain da ta taru tai min yawa a kaina, amma duk da hakan ba za ka barni in ji da iya wad`annan ba har sai ka koma kana had`a ni da iyaye da `yan'uwana, so ka ke dole sai sun tsane ni kamar yanda ka tsane ni kaina ,so ka ke sai sun mai da ni saniyar ware kamar yanda ka maida ni a cikin Gidan ka".ta d`an daka ta sakamakon jin wani abu na k`ok`arin tokare mata mak`oshihakan ne ya bashi damar cewa da ita wani abu, "Zeenat me kuma ya faru wad`anne irin maganganu ne su ke fitowa daga bakin ki,me na aikata maki bayan nisa da tazarar da ke tsakaninmu da ke,ina ga fa tunda na zo wannan Garin wannan itace waya ta biyu da mu kai to me nayi maki,ina nan ina ta fad`i tashi duk dan in samu abinda zan rufa mana asiri amma hakan be sa kin ji tausayina ko Addu'a mai kyau ki rik`a biyo ni da ita ba,sai dai tashin hankali da fitina". " Oh iya adalcin ka abinda ya gani ma ka kenan laifina ma ka ke gani,to na gode,amma ina so ka sani daga rana mai irin ta yau kar ka k`ara turo min wani cikin Gidan in har da zummar ka zubar min da mutunci da k`ima ne,ba sai ka k`ara `bata min suna kamar yanda ka yi a baya ba,in kuwa ba haka wallahi zan hauka ce maka a cikin Gidannan ".... " Ki hauka ce mana Zeenat, Dan Allah ki haukace d`in wai ke wacce irin Mace ce, me ye a cikin kwakwalwa da tunanin ki Anya kuwa kin ma san me kalmar Miji da Zaman Aure ta ke nufi,to ki sani Na shirya tarbar duk kalan haukan da za ki zo da shi,dai-dai na ke da ke".yana kaiwa nan ya kashe wayar gami da cillar da ita saman kujerar da ta ke kusa da shi,hanunshi ya kai saman goshi shi yana mai dafe shi tare da furta kalmar Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un a hankali,k`arar knocking d`in da ya ji ne ya sa ya bud`e idanunsa wanda har sun fara sauya kala,haka ya ja k`afarsa ya je ya bud`e ma eanda ya ke son shigowar. "Lafiya dai Imam Na ga yanayin ka duk ya sauya", Doctor Nass ya tambaye shi bayan ya ra`ba ta jikin shi ya shigo Parlourn. " Uncle Nass Zeenat ce,nema ta ke ta tarwatsa min tunanina,so ta ke sai ta samin cutar damuwa ta k`arfi da yaji,Wai Dan Allah haka dama Auren Zumincin ya ke,wannan bala'i har ina?". Sai da Uncle Nass d`in ya kama shi ya zaunar da shi sannan ya ke ce mi shi,"Duka Mata kowa na da irin na ta k`alubalen ba wai sai iya Auren Zuminci ne ake samun tasgaro a cikin sa ba ,ita Zeenat wannan shine na ta k`alubaken,ka yi hak`uri ka dage da addu'a,in sha Allah komi zai wuce wata rana". "Amma Uncle Gimbiya Ayush ba ta min irin abinda ita Zeenat d`in ta ke mani,duk da ita tafita a komi ga dukiya ga Sarauta amma iya abinda na ce mata kawai ta ke yi". Wannan Allah ne ya so ka da rahama ya sauya ma ka da ita don ka samu natsuwa daga gareta,don haka sai kai Godiya kuma ka k`ara da hak`uri", da kai Imam ya amsa ma sa ba tare da ya kuma cewa komi ba. "Na je can Hospital d`in akace min ka taho masaukinka shine fa na zarto nan ga launch d`inka can Madam ta ce a kawo ma ka".ya sanyo wani zancen da zai sa su bar wancan. Murmushi mai tafe da yak`e ya yi tare da cewa," A mik`a min godiya ta wajen Aunty tawa ina ta sa ta d`awainiya tun zuwana". "Oh wannan Ai kun fi kusa,yauwa ya Maganar Mrs Anderson ya jikinta a wanne Condition ta ke yanzu ?". System d`in shi ya janyo ma shi tare da cewa," Ga file d`in ta nan duba ka gani kafinnan bari in d`an watsa ruwa ina fito sai mu tattaunawa yanda ya kamata". *JADEEDAH* (It's a story of two love birds who are so different from each other ) STORY & WRITTEN BY : (*Cwt~Sumiey*) Marubuciyar littafin MENE NE ABIN YI ? KARAGAR MULKI And now.....*JADEEDAH* *YOTA* BOOK 1 PAGE 22❤ "Momy mun yi waya da Papa ya ce ya Isa lafiya ya na saran tomorrow early in the morning zai baro Lagos ya dawo ,domin gabad`aya hankalin shi yana nan ya na son ya ji yanda last result d`in nan zai fita". " Eh nima ya kira ni amma tun bayan isar sa Airport ne daganan ba mu sake yin waya da shi ba,a lokacin ina gab da shiga d`akin Test d`in". Granny ce ta amshi zancen da cewa,"Ya kamata ya zuwa yanzu ma ace result d`in ya fito,tun fa safe gashi 5pm na shirin yi". "Uhm gaskiya kam nima tun d`azu abun na raina", Cewar Martin. "Ko dai zan je in gano ,halin da ake ciki wata k`ila aiki ya yi masu yawa ne shiyasa ba su dawo ta kan mun ba". " Yauwa Aunty Jee ki je ki jiyo mana ko ma samu mu fita daga bakin tunane-tunanen da mu ke a ciki",Cewar Nora da ke haɗa kayan da za su koma da su Gida. "Okay bari in je Allah ya sa mu ji abinda zai kwantar mana da hankali ba ya k`ara tashi ba"," Ameen",Su ka had`a baki su duka. K`arar knocking d`in da ake ne ta sa yad`an d`ago ya kalli Door d`in ba tare da ya bar abinda ya ke ba ya bada izinin shigowa. "Good Evening Doctor", ta fad`a a d`an d`arare ,a hankali ya d`ago da kan shi ," Oh ke ce come in, ina fatan lafiya dai?".ya tambayeta ya na mai cigaba da aikin da ya ke. "Amm.....muna cikin jimami ne,muna ta dakon jin sakamakon test d`in da akayi ko zamu fita daga cikin tunani da damuwa". "Oh Sorry aiki ya d`an rik`e ni,test d`in are yet to be out amma zo zauna have a seat,akwai Maganar da na ke son yi dake", ya kai zancen ya na mai nuna mata wurin zama. Zaunawa yai ya na mai tattara hankalin shi wuri guda ya na kallonta," Ammm Mahaifiyar ki ta na samun sauk`i sosai sai dai da akwai buk`atar taimakon ku a cikin lamarinta in har kuna son lafiyarta ta d`ore,da akwai shawarwarin da na ke son baku ko Allah zai sa a dace". "Doctor ina sauraron ka I'll do everything in har akan samun lafiyar Momynah ne",ta ce da shi a ƙagauce. "Yana da kyau a ce ta rik`a yawaitar yin exercise domin motsawar ga`bo`binta,sannan a rik`a kula da abincinta ta rik`a samun wadataccen barci, a hanata yawaitar tunani ko barinta ta zauna ita kad`ai, banda shan wani abu wanda ya danganci Alcohol da sauran su"....haka dai ya cigaba da jero mata dokokin da ya kamata mai irin wannan ciwon ya kiyaye " Thanks alot Doctor, ban san da wanne irin baki zan iya Gode ma ka akan irin kulawa da kuma sadaukantar da lokacin ka daka yi akan Mahaifiyata ina maka fatan alkairi ". " Don't Mind cause it's my duty kin ga kenan ya zame min dole in aikata abinda ya kamata". "Duk da haka I'm really appreciate ba zan manta da hakan ba", ta kai zancen ta na mai mik`ewa za ta fita,har ta fara tafiya ta dawo,gami da komawa ta zauna ta na mai fuskantar shi da cewa ta ce da shi,"I'm sorry about the last day, I'm swear to the Jesus Name ba halina ba ne,a that day ina cikin tashin hankali da firgicin rashin lafiyar Momynah,ina mai baka hak`uri akan hakan,ba ni da wani za`bi ne I know Abuja Boys ba yaren da suke ji sai na kud`i hakan ya sa nai amfani da wannan policy d`in dan tak`aita zancen amma har cikin raina nasan ban kyauta ba abinda na yi ". " Kar ki damu na fahimce ki ,tun kafin ma ki yi bayani, Allah ya bata lafiya ". Wayar shi ce tai k`ara ya d`aga na wani d`an lokaci kafin ya aje wayar ya na mai cewa," I'm sorry for interruption da akwai wata Doctor ya na da muhimmanci idan zai yiwu ku ganta she is expert about Neurogical disorder zai kyautu a ce kun kai mata ziyara ,idan har kuka aikata hakan za ku fahimci abinda Na ke son sanar da ke". Cikin zumud`i Jedeeda ta ce,"Why not me zai sa ba za mu iya zuwa inda ta ke ba,ai komin nisan inda ta ke za mu je ,mu ke da riba akan hakan fa,mu ke Neman inda Momy za ta samu lafiya ta warke daga lalurar da ta ke damunta,don haka a kowacce k`asa ta ke a shirye mu ke da mu je can,kai ko nawane za mu kashe in har zamu samu damar ganinta".kasaƙe yai yana kallonta ya rasa me yake faruwa da shi,komi nata neman rikita shi yake, murmushinta maganarta,tafiyarta hatta da motsi in tai sai ya riƙa ganin kamar yasan wani ko wata da irin wannan ɗabi'ar, yanayin yanda ta ke juya idanunta tare da yanayin yanda ta ke sarrafa bakinta wajen yin magana,sukan su na ɗaya daga cikin abinda ya ke sake jefa shi cikin kokonto a cikin Zuciyarsa "Ba wani Gari ko wata k`asa ta ke ba anan nan Kano ta ke da zama,sai dai ta na da k`a'ida guda d`aya duk wani patient da za ta duba sai dai ya same ta a Gidanta ,ko kuma mutum ya bi ta Asibitin AKTH Wanda ta ke aiki a cikin sa sau d`aya ko sau biyu a wata".ya ce da ita yana mai son gano wani abu daga gare ta. " Kano kuma ?",ta tambaya fuskarta na nuna rashin jin dad`in abinda kunnuwanta su ka ji mata. "Eh haka na ke nufi ,amma ki bi komi a hankali lamarin it's about a choice sai fa kuna buk`atar ta,idan kun ji ba kwaso ba dole ba ne ba, shi has experience about the case Neurogical disorder, yanzu haka ta na da patient d`in da take kula da shi sama da shekaru Ashirin, kin ga kenan ta san hanyoyin da za a samu sauk`in cutar". " Na fahimce ka amma wani hanzari ba gudu ba,zuwan Momy Garin Kano kai tsaye zan iya ce maka abu ne da ba zai yiwu ba,ba ma ita da kanta ba ko mu ba mu da damar zuwa wannan Garin, baza ta ta`ba yarda da hakan ba,ka sani za mu iya kashe ko nawa ne in dai zata yarda ta zo ta dubata anan". "Warnder shall never end me ye a cikin Garin Kanon da har za ku gitta irin wannan lafazin akan shi,shin wani abu ya faru ne da ita a Garin wanda ba ta son tuna shi ko sake faruwar shi?". " Ba ni da wannan masaniya gaskiya nasan hakan dai a matsayin dokar cikin Gidan mu,...amma ka manta kawai mu koma kan Maganar yanda za mu shawo kan wannan Doctorn ta amince da buk`atar mu". "Hmmmmmm ki yi hak`uri amma dagaske ina mai sanar da ke ba zaki ta`ba iya sanyata ta zo Garinnan ba,idan har kuna buk`atar taimakonta to ku kai mata ziyara ta na da dalilin mai matuk`ar muhimmanci da ba za ta iya bari ta zo nan ba,abu d`aya na sani zan iya had`a ku da ita domin ta rik`a baku shawarwarin da za su amfanar da ku". " Ba wani taimako da zaka iyai mana akan haka,zan so in ga na samu wata hanya da zan taimakawa Mahaifiyata na ga ta warke daga wannan lalurar da ta ke fama da ita,ciwon kan da take fama da shi yai tsanani ba na son in ga ta na yanke jiki ta fad`i ko kuma ta fita a cikin hayyacinta, ba na son haka". "Gaskiya babu", ya bata amsa a tak`aice, shiru Jedeeda ta yi na wani d`an lokaci, kafin ta d`ago ta kalle shi ta ce," I'll do my best, zan yi iya me yiwuwa na ga nayi convince d`inta ta amince mu je ta had`u da Doctor d`in, idan har kana da tabbacin samun sauk`in na ta","Allah shi ke da iko akan komi muna sa ran faruwan haka","Hakan ya yi kyau ga wannan card d`in ta ne,za ki iya yin contacting d`in ta da zaran kun shirya ma hakan,bata da wata matsala zan yi mata bayani",ya kai zancen ya na mai mik`a mata ta amsa,tare da yi mashi godiya "Lokacin tashina ya yi zan wuce,zuwa gobe in na shigo zan duba Test d`in na ta daganan sai in duba yiwuwar discharging na tan".sannan su ka yi sallama ta tafi,shi kuma ya cigaba da had`a abinda zai tafi da shi. Tafe take ta na tunani hanyar da za ta iya shawo kan Momynta,da kuma tunanin dalilin da ya sa ta hana su zuwa garin Kano bayan kuma suna da damar kai ziyara a ko'ina na fad`in k`asarnan kai ba cikin k`asarnan ba har da k`etare suna da damar zuwa,ta kan nuna `bacin ranta matuk`a in taji ko firar Garin Kano su na yi ,kai ko k`awa bata son ta ji sunyi in har `yar Kano ce,to meye ya jawo hakan,tabbas ta d`au aniya binciko ko ma me ye ya ke binne a k`asa, ta yi maganin matsalar in har hakan zai zama sanadin da Momynta zata samu lafiya ,da wannan tunanin ta isa Room d`in da su ke. √√√√√√√√√ "Amm..... Ya ma ki ke da suna,Bibah ki ke ko wa ma ?,ki tattara inaki-inaki ki bar min Gida,tun muna shaida juna ,ki je ki ce wa wanda ya turo ki na kore ki,ba na buk`atar taimakon na ki, shashashar banza, munafuka kawai". " Subahanallahi Aunty Zeenat me ya faru ,mai yai zafi har ka?". "Ban sa ni ba,kawai abinda na ke da buk`ata ki fita ki barmin Gida,ki je ki sanar da munafukai da kuma `yan gulmar da su ka turo ki,lafiyata lau ba abinda ya same ni". " Amma Aunty Zeenat ".....kar ki kuskura ki k`ara cewa da ni komi,salin alin ki d`auki mayafin ki ki fice min a Gida". Ganin kamar ba za ta tafi ba yasa ta daka mata tsawa tare da fara fatali da duk kayan wanke-wanken da ta fara had`awa ta re d`aga sautin muryarta ta na cewa," Za ki fitar min a Gida ta daɗin rai ko ko sai na raunata ki?" Bibah a firgice ta ɗago tana kallon ta gami da rasa me za ta yi, duk ta firgice domin ba ta ta`ba ganinta a cikin irin wannan yanayin ba,sai ta kalli tarin wanke-wanken da ke gabanta wanda ta had`a za tayi da ita Ummu Nurain ta warwatsar da su sai ta kalli Zeenat da ke tsaye a saman kanta sai faman huci da ta ke tamkar wacce tai tsere,ganin cigaba da zamanta ba lalle ya haifar da d`a mai ido ba ya sa ta d`auraye hannunta gami da d`aukar mayafinta ta bar mata Gidanta. "Duk dai-dai na ke da ku munafukan banza da na wofi,ku ne fa kuka zuga shi ya Auro waccen mai kama da karuwan,wacce ta dalilin ta na zama tamkar bola a wajen shi ,Na rantse da Allah ba zan bar ku ba,ku dai jira lokacin da zan sauke abinda ke cikina ku ga irin matakin da zan d`auka ba shi ba hatta da ku sai kun gane asalin wace ce ni".haka dai ta cigaba da maganganun ta har Nurain ya farka da daga barcin wuyar da ta kora shi ya je ya yi,kan ta ya nufa sai faman murza idanun shi ya ke da hannayensa,ya ce da ita," Umma yunwa Na ke ji ki bani abinci in ci".....tun kafin ya kai k`arshen Maganar tasa ta kai masa duka tare da cewa,"Dan Ubanka wuce ka bani wuri ,in yunwar ta tashi ta kashe ka duk ba ta sanadiyar ka ake yimin duk kalar wulak`ancin da ake so ba". Ihu ya sakanmata da iyakacin k`arfin sa ya na kuwwa yana cewa shi yunwa ya ke ji ta bashi abinci,ta tashi ta dafa mai ba zai ci biscuit ba ba zaici Noodels ba,dole ba dan ta so ba ta tashi ta d`ebi wasu daga cikin kayan da za tai amfani da su ta wanke kafin ta d`ora masu girkin. *JADEEDAH* STORY & WRITTEN BY : (*Cwt~Sumiey*) Marubuciyar littafin MENE NE ABIN YI ? KARAGAR MULKI And now.....*JADEEDAH* *YOTA* BOOK 1 PAGE 23❤ "Kar dai kace min nan ka fara sauka ba ka Isa Gidan ka ba,wai sai yaushe za ka girma ne,iyali ne fa da kai ,Anya kuwa Jaheed ?"..... "Momynah Haba dan Allah,welcoming d`ina ya kamata ki yi ba ki tare ni da tarin tambayoyin ki irin haka ba". " Au nufinka in zuba ma ka Ido kawai ka dinga aikata duk abinda ka ke so ka ke ganin dai-dai ne,to hakan ba zai yiwu ba,dole ne in nusar da kai gaskiyar kuskuren da ka ke aikatawa ". Sai da ya maida fuskarsa kalar ban tausayi kafin ya ce," Momynah na yi kewar daddad`an abincin ki ne me sa mutum ya ji ya kusa k`oshi,shiyasa na biyo in d`an d`ana kafin in wuce". "Au tunda k`amshin abincin nawa ya isa mutum ya k`oshi to zo ka tafi ai nasan ka ji k`amshin don haka ga hanyanan ma za zo ka tafi Gidan ka Matanka na can na jiranka". "Momy ki bar ni in k`arasa cin abincin sai in zo in tafi,Allah ban k`oshi ba".zuba mi shi Ido ta cigaba da kallon shi har ya kammala cin abincin. " Ya jikin Uncle, komi na tafiya lafiya lau dai ko?","Jikinsa da sauk`i kamar dai ko yaushe",sai da ya gyara zaman sa kafin ya ce,"To Allah ya k`aro sauk`in ya maganar taron k`arama juna sanin da za'ayi a Canada, shin har yanzu Maganar ta na nan?","Eh tana nan ,ina bibiyar su mai yiwuwa za su iya Kira a kowanne lokaci" "Amma....Momy".....ta katse shi da cewa,"Ya isa haka tashi ka tafi Gidan ka koma meye ma k`arasa shi nan gaba amma banda yanzu,sannan maganar Patient d`in ka da muka fara kabar min sauran aikin,in sha Allah I'll do my best,ka je ka huta idan ka isa ka gaishe mi da `yata Ummu Nurain da kuma Gimbiya Ayush banda wannan d`an mai surutun tsiya", murmushi kawai yai ba tare da ya ce komi ba ya nufi hanyar fita. Tun shigar shi mota ya fara tunani in ya Isa Gidan me zai tadda ,fatan shi d`aya Allah ya sa ya koma me ye zai zo ya zo da sauk`i,Dan bai ta`ba yin tafiya da ta kai sati ba tare da ya iske tashin hankali a cikin Gidan na sa ba,tun shigar shi farfajiyar ya fara ganin sauye-sauye a idanunsa,muryarsa ya bud`e da d`an k`arfi ya kira gate keeper yana mai cewa da shi," Lafiya me yake faruwa na ga Part d`in Gimbiya Ayush a rufe,haka ma na Ummu Nurain,ko wani abun ya faru ne?". "Allah ya gafarta Malam bani da masaniya akan faruwar wani abu gaskiya sai dai d`azu bayan fitowa Sallahr Azahar na ga k`anwar Madam ta Gidan Sarauta ta shigo Gidannan, sun fita tare da Gimbiya a guje ba tare da sun kula kowa ba, da alama dai Gimbiya ba ta da lafiya kamar hakan na fahimta daga gare su,bayan ganin wannan lamarin, Na tafi k`ofar Uwar Gida,Na sanar da ita,amma cikin rashin sa'a ta koro ni ba tare da ma ta saurare ni ba,ta maida ƙofarta ta rufe". " Subahanallahi me ya same ta to, ta na wanne Asibitin yanzu ?",ya jero mashi tambayoyin ba tare da ya yi la'akari ba yanda zai si ya san amsoshin su ba,"Wallahi Allah yalla`bai ban sani ba,kawai dai na ga fitarsu cikin matsananancin tashin hankali bayan haka ban san komi ba".... K`arar Horn da Me gadin ya ji ce ta dakatar da shi yana mai nufar gate d`in da d`an gudun sa,sai da ya fara lek`awa ya ga waye sannan ya bud`e fuskar shi d`auke da hamdala. Motar Na tsayawa Gimbiya Fadeelah ta fito tana mai tallafo Gimbiya Ayush jikinta ,wacce ko tsayiwar kirki ba ta iya yi,da taimakon Gimbiya Fadeelah su ka Isa Cikin Part d`in har bedroom ta kaita ta kwantar da ita,duk wannan abun da yake faruwa Jaheed na biye a bayan su sai faman jera mata sannu ya ke,hannunsa ya kai saman kanta tare da yi mata sannu,hankalin shi ya maida kan Gimbiya Fadeelah tare da tambayar ta,"Me yake faruwa me ya same ta,Allah ya sa koma meye ba mai tsanani ba ne ba ?",ya tambaya a d`an rikice,inda-inda Gimbiya Fadeelah ta fara ta rasa me ma za ta ce da shi,Gimbiya Ayush ta fara kici-kicin tashi zaune Zuciyarta sai faman dukan uku-uku ta ke mata,"A kin ga koma ki kwanta jikin ki ba shi da k`arfin,ki na buk`atar hutu",muryarta cike da rauni irin na marasa lafiya wanda ya ji jiki ta ce da shi, "Zan iya tashi ai,kuma so na ke in yi maka bayanin abinda ya faru,yanda za ka fahimta", gyara mata kwanciyar yai gami da janyo blanket ya sake rufa mata," Ba buk`atar ki wahalar da kan ki ga Gimbiya Fadeelah sai tai min ba yani",ya fad`a a hankali cikin muryarsa mai sanyi. Kam Gimbiya Ayush ta runtse idanunta a cikin ranta sai faman Addu'a da fatan Allah ya sa kar Gimbiya Fadeelah ta kwafsa mata ba k`aramin aikinta ba ne ta kwashe komi da ya faru ta sanar ma sa,da sauri ta bud`e idanun na ta sakamakon jin abinda ke fita daga bakin Gimbiya Fadeelahn take bugun Zuciyarta ya tsananta hankalinta yai mugun tashi sai faman jujjuya kanta ta ke da bin Gimbiya Fadeelah da kallon da zai iya dakatar da ita. "Ina mai baka hak`uri ta sake miscarriage ne ma a wannan karan", Idanuwan shi ya runtse kam ya na mai k`ara k`arfin ruk`on hannunta da yake a cikin nasa,k`arar da ta saki ce ta dawo da shi cikin natsuwarta,tuni idanuwansa sun rine sun sauya kala,duban shi ya maida kan Gimbiya Fadeelah tare da sake jefo mata wata tambayar da cewa,"Shi kuma wannan mene ne silar faruwar shi, me bincike ya nuna, kuma ita ya matakin lafiyar ta ya ke?", tuni idanuwansa Gimbiya Ayush sun fara zubda ruwa,irin haka bata ta`ba faruwa ba,salin alin cikin duk da ta ke zubarwa ya ke fita ba a ta`ba dangana ta da Asibiti ba iya ita kad`ai da shi ne,wani time d`in ma bayanan hakan ya sa ta ke amfani da wannan damar ta tsara masa k`arya da gaskiyar da zai yarda da ita,yau kuma an samu kuskuren da jini ya `balle mata wanda har sai da ta kai ga neman taimakon Gimbiya Fadeelah, Wanda da k`yar ma ta samu ta zo,Addu'ar ta d`aya Allah ya sa kar ta tona mata asiri in hakan ta kasance bata san zai biyo baya ba, hankali da tunanin ba za su iya haikato mata ko mi zai faru ba. "Last two days ta kirani ta ke cemin tana fuskantar Abdominal pain,ta ce min bata son ta sanar da kai kar ka raba hankalin ka Gida biyu ,hakan tasa nai prescribing d`in medication na aiko mata da su, but amma still ciwon bai daina ba,yau da sassafe ta kirani ta sanar min,sai dai kafin in zo har ta fara bleeding, haka na kwashe ta mu ka nufi Hospital, kafin mu kai cikin ma ya fita,a binciken da nayi ne na gano ashe tun farko cikin a bayan mahaifarta yake hakan ne ya haifar mata da Abdominal pain d`in "Ta ida zancen cikin rawar murya da kuma inda-inda. Shiru Jaheed yai na wani lokaci ,ya na mai juya Maganar a cikin rasa,ta ya za ai ace cikinta a bayan Mahaifa yake bayan shi tun bayyanar cikin bai san da hakan ba,motsin da Gimbiya Ayush ta yi ne ya sa ya mai do da ganin sa kanta ya na tambayar lafiya me ta ke so ko akwai wani wurin da ya ke mata ciwo,muryarta a d`arare ta ce ma sa," Yunwa na ke ji ina son in sha ko da tea ne". Gimbiya Fadeelah ta mik`e ta na mai cewa,"Bari in had`o maki","Kin ga zauna ki huta bari in had`o mata ai kin sha aiki,Allah ya bar Zumincin ya kuma biya lada",ya na mai zancen ya nufi hanyar da za ta sada shi da kitchen d`in, da sauri Gimbiya Ayush ta kamo hannun Gimbiya Fadeelah tana mai fara yi mata Godiya,dama da biyu ya sa ta ce zata sha tea d`in, "Na gode sosai `yar'uwata,Na ji dad`in kasancewar da ki ka yi da ni a yau da kuma rifa min asiri da ki ka yi,bazan mata da hakan ba,da badan ke ba da yanzu ban san wanne irin hali na ke a ciki ba,kuma dan taimakon ki gami da rufa min asiri da ki ka yi, da yanzu Aurena ya fara walagigi,ban kuma san ta hanyar da zan iya gyara shi ba". Sa`bule hannunta tayi a cikin nata ta na mai cewa," Kin ga sake ni,hankalin ki ya kwanta kin samu abinda ki ke so sai ki zuba ruwa ak`asa ki sha dan murna,ga wannan magungunan ki ne, sai ki cigaba da sha domin jininki ya yi k`asa ,in so samu ne ma ki bari a k`ara miki wani jinin,sannan ki kula da abinda Doctor Nazer ya sanar da ke"..... "A'a ni bana son a k`ara min wani jini zan sha maganin dai,ba na son wani abun ya biyo bayan hakan"," Okay yanda ki ka so,ni zan tafi ko akwai wani abu da ki ke so in sa a kawo ma ki",Gimbiya Fadeelah ta kai zancen tana mai gyara zaman mayafinta tare da d`aukar Car key na ta,ba ki sake Gimbiya Ayush ta ke kallon ta har ta kai ga k`asa hak`uri ta ce mata,"Wai me ki ke nufi ba dai tafiya za ki yi ba,ta ya ina cikin wannan halin za ki tafi ki bar ni ,kin san ina buk`ata ki a kusa da ni fa","Hmmmmm ta`b wallahi ba zan iya zama ba mijinki ya dawo biside ma ina jin tsoran kar ya gano gaskiya yai tunanin har da ni aka shirya komi dan haka tafiya ta zan yi babu ruwana","Haba Sis kar ki yi min haka dan Allah ki zauna da ni yau ba anan Part d`in ya ke ba yana `bangaren Ummu Nurain kin ga in ki ka tafi,shima tafiya zai yi a bar ni ni kad`ai ". Sunkuyar da kai k`asa Gimbiya Fadeelah ta yi ta nai cewa,"Ni dai ki yi hak`uri amma gaskiya tafiya zan yi,ko ma me kenan na dawo wani lokacin"..... Ta kasa ida cewa komi sakamakon shigowar Jaheed hannunsa d`auke da Tea sai faman tururi ya ke da alama yanzu ya had`a shi. "Ya dai ya na gan ki a tsaye,ba dai tafiya za ki yi ba?", ya tambaye ta bayan ya k`arasa kusa da Gimbiya Ayush ya fara k`ok`arin taimaka ma ta ta shi zaune". " Eh tafiya zan yi Fulani ce ta kira ni ta sanar min Me marta ba ya na kan hanyar dawowa,so shiyasa na ke son in tafi","A ai ya kamata ki tafi in kin Isa ki mik`a min gaisuwata wajen Fulanin". "Yauwa na san kai ai zaka fahimce ni amma tun d`azu na ke ma Aunty Gimbiya bayani amma ta k`i yarda Murmushi ya sakar mata tare da cewa,"Muna Godiya da kulawar ki ,zan cigaba da kulawa da Matana,Allah ya biya lada ya bar zuminci,Doctor Fadeelah ko ince Gimbiya Fadeelah",Ya kai zancen ya na mai sakar mata fuska,murmushin yak`e ta yi tare da cewa,"A'a ka Kira ni da Fadeelah kawai ma ya Isa","Anya kuwa ayi haka kar fa sarautar ki tasa a d`aure ni har igiya tai rara",Ido ta zaro waje ta na mai cewa," Wane ni ai sai Anty Gimbiya ta fasa min kai". Dariya yai ya na mai sake kai mata tea spoon d`in saitin bakinta,"Am ni gani ma nake kamar jininta ya fita da yawa na ga idanunta kamar duk sunyi fari ?". "Eh haka Doctor ya faɗa kuma nima na ga hakan....." Da sauri Gimbiya Ayush ta amshi zancen da cewa,"Ni fa ina da Jini kuma sun ba ni magunguna da zan rik`a sha,in sha Allah zan koma Normal ". " Ni dai kun ga tafiyata ,Allah ya k`aro sauk`i",ta kai k`arshen ta na mai juyawa ta tafi. Kallon shi Gimbiya Ayush ta yi tana mai sakin hawayen da ta ke ta faman rik`o tare da cewa,"I'm sorry na kasa rik`e maka ajiyar da ka bani,Na so ace ma haifo Babynnan ya zo duniya ,ya kira ka da suna Daddynsa ya amsa sunanka a matsayin mahaifinsa".....,"Shhhshhh ya isa haka ai ba yin ki bane ba hakan daga Allah ne k`addarar mu ce ba yanda za ai mu tsallaketa kuma mumini na kwarai ne kawai ke iya d`aukar hakan". "Haka ne na gode da tunasarwarka mutum mai ilimi da hankali ne kawai yasan da haka,ina mai sake Godiya game da saurin fahimtar da ka ke min akan irin wannan abun da ya ke yawan faruwa da ni da wani ne da tuni ya fara zargina akan da sanina hakan ke faruwa".....ya sake katseta a karo na biyu," Ta ya zan iya yin wannan munmunan tunanin a gare ki bayan irin son da nake ganin kina nuna ma Babyn,kuma fa a jikin ki ya ke,kin juri dukkanin wasu wahalhalu da kuma ciwace-ciwace akan kawai ki ga kin haife shi ya zo duniya,ke d`in Mace ta Gari ce kamar yanda na ke fatan wata rana ki zama Uwa ta Gari",Murmushi ta saki har ta `boye fuska a k`irjin sa tare da amsawa da Amen,shima murmushin ya saki tare da cewa,"Kin ga tashi ki shanye tea d`in ki kar yai sanyi ",ta na jikin shi ta ba shi amsa da cewa," Ni na k`oshi,ina son in ji d`umin Mijina ne yanzu".....dakatawa tayi ba tare da ta idasa faɗar abinda ke bakinta ba,gami barin jikin sa bayan,"Bi a hankali mana jikinki akwai ciwo ,me ya furu haka?",ya tambaye ta,sai da tayi kalar ban tausayi da fuskarta kafin ta ce da shi,"Ka tashi ka tafi Part d`in Ummu Nurain nasan zuwa yanzu tasan ka dawo","A'a ba inda zani ina nan,Kina buk`ata ta a kusa da ke",...."A'a kar ka ce haka,wani abu mara dad`i ka iya biyo bayan hakan". "Ba abinda zai faru da izinin Allah, ku duka fa Matana ne kuma a k`ark`ashin ikona ku kenan haka ki jira ni ina dawowa", sake baki ta yi ta na mai bin sa da kallo,shi kuma ya nufi hanyar da za ta sada shi da Part d`in Ummu Nurain, wanda tun dawowar shi bai shige sa ba. *JADEEDAH* STORY & WRITTEN BY : (*Cwt~Sumiey*) Marubuciyar littafin MENE NE ABIN YI ? KARAGAR MULKI And now.....*JADEEDAH* BOOK 1 *YOTA* PAGE 24❤ Da sallama d`auke a bakin shi ya shiga cikin Parlourn, duk wadatar kayan sanyaya muhalli da ke a cikin Parlourn hakan bai hana gur`bacewar iskar shak`a a cikin sa ba,kujerun da suka yi ma Parlourn k`awanya har wani jurwaye suke saboda tsabar daud`a,kan danning table d`in kayan da aka ci abinci ne tsibi guda,idan ka kai dubanka tsakar tyles d`in wandunan,riguna har ma da takalman Nurain a bar batse a wurin,runtse idanunsa yai yana mai had`iye abinda ya tsaya masa a mak`ogwaronsa,murmushin dole Jaheed ya k`irk`iro a saman fuskarsa ya na mai k`arasawa inda Nurain ya ke kwance sai faman bige-bige ya ke alamun sauro ya na d`ibar roma a jikinsa,shafa kan shi yai tare da cewa,"Yarona gajiya da k`iriniya sun sa ka yi barci da wuri kenan,ban ji dad`in haka ba na so ace mun gaisa saboda na yi kewar ka sosai",ya kai zancen yana mai maida kallonta kan Zeenat da ke zaune sai jijjiga jikinta take tana faman cika tana batsewa,kayan jikinta kan su abun tada hankali ne,kanta d`aure da d`an kwalin atanfa,ta d`aura shi kamar kullin magani ya d`auru sosai,jikinta sanye ta ke da rigar material, rigarma a bai-bai ta sanyata,sket ne a jikinta irin Na English weres d`in nan,komi nata a hargitse ya ke. Kusa da ita ya matsa ya na mai zauna wa kusa da ita tare da cewa,"Ummu Nurain sannu da Gida,ya kuke,fatan na same ku lafiya",ko motsi ba tai ba balle ya sa ran za ta ce da shi wani abu,ba tare da ya d`au zafi da abinda ta aikata ba ya kai hannunsa saman fuskarta ya na mai jiyo da ita yanda za ta fuskance shi,ya ce da ita,"Ba ki ce da ni komi ba ,ko ba ki jin abinda na ke cewa ba?",bige hannunsa tayi tare da cewa da shi a zafafe,"Kar ka sake sa hannun ka ka ta`ba ni ". " Ya Salam mai ya faru da yai zafi da har ya kai ki ke furta irin wannan zancen",a sakarce ta d`ago tana mai zuba ma shi idanunta tare da cewa,"Tambaya ta ka ke me ya faru ?,shin kana son ka ce min ba kasan abinda ya faru ba,wallahi ina jin zafi tare da mamaki idan na ji ka yi min irin wannan tambayar, sai in yi tunani kamar ka d`auke ni a matsayin wata banza wacce ba ta ta`ba shiga aji da nufin koyan wani ilimi ba".... "Ammm....dan Allah ki dakata ki bar furta wad`annan maganganun marasa dad`in sauraro,in har akan fara sauka ta Part d`in Gimbiya Ayush ne ina mai baki hak`uri, ba wai nayi hakan intentionally ba,Na dawo ne na iske Gidan ba a yanda na saba riskarsa ba,ina cikin bin ba'asin hakan Motar su ta dawo wai ashe bata da lafiya daga Hospital su ka dawo,hakan ne yasa na fara isa nata Part d`in amma ki yi hak`uri in ranki bai so hakan ba". Ta`be baki ta yi tana mai kauda kanta gefe tare da cewa,"Oh hakan ne yasa aka take namu hak`k`in dan a farantawa Mowar Gida ko,hmmm ai ka kyauta"...ya katseta da cewa" Ta yi miscarriage ne ya kamata ki je ki diba ta",Maganar ta bigeta don ita ba ta ma san ta na da wani ciki ba,don ba wani wanda ya ke shiga harka wani in har ba `yan fitinar ne su ka ta so ba,a dak`ile ta ce,"Allah ya bata lafiya ,amma ni dai kam ba zan je Part d`in ta ba","Saboda me `yar'uwar ki ce fa tana da hak`k`i akan ki kamar yanda ke ma ki ke da shi akanta...",da Katar da shi ta yi ta hanyar d`aga ma shi hannu gami da cewa,"Ka ga dan Allah, ka daina damuna da batun Matar ka,da gaske raina `baci ya ke kana sa in rik`a jin zafi da haushinta akan me dan Allah,ina jin tsanar ta fiye da komi a raina,ka barta tayi rayuwarta nima in yi tawa rayuwar". Subahanallahi, shine abinda ya fara fita daga cikin bakin sa bayan ta kai k`arshen zancenta,ya so ya nusasshe da ita kuskuren abinda ta fad`a amma ina hakan ba zai yiwu ba, domin ya tabbatar k`ara hargitsa lamarin zai yi hakan yasa ya ja bakin sa yai shiru sai da suka d`auki wani lokaci kafin ya d`ago ya ce da ita,"Dama na shigo ne in ga halin da ku ke a ciki daganan sai in yi mu ku sallama domin zan koma can Part d`in wajen ta domin ta na buk`atar wani a kusa da ita,saboda gudun abinda dare zai haifar"...... Wata irin mik`ewa Ummu Nurain ta yi a zabure,jin saukar kalamansa ta yi kamar an watsa mata ruwan zafi,ji tai ina ma da ruwan zafin aka watsa mata zai fi mata sauk`i akan sauraran zafafan lafuzzan da su ka fito daga bakin sa,muryarta na rawa ta kai kunnenta saitin bakin sa tare da cewa,"Me na ji ka ce, fatana Allah ya sa kunne na ne bai jiye min abinda ka ce dai-dai ba ?",kallon mamaki ya bita da shi,shi a nashi ganin bai ga wani aibu ko `batanci a cikin lafuzzan da ya yi ba,shima mik`ewa tsaye ya yi ya na mai fuskantar ta kafin ya mai-maita mata abinda ya ce,"Ce mi ki nai zan koma Part d`in Gimbiya Ayush saboda gudun faruwar wani munmunan abun cikin dare". Wata tak`aitacciyar dariya Ummu Nurain ta saki har tana bugun cinyoyinta kafin ta d`ora da cewa,"Ko da na ji da walakin goro a miya,shin wai kai baka jin kunya babban mutum Malami mai hankali ka rik`a nuna fifiko a Gidan ka Anya kuwa?,to wallahi in dai da amincewata za ka koma wancan Part d`in to ban amince ba ba da yawuna ba ". A tsawace ya ce da ita,"Zeenat wannan wanne irin shashanci ne haka,ta ya za ki saki baki ki rik`a gaya min duk abinda ya zo mi ki a baki,ki sani ba wai na zo nan in tsaya ina musayar yayeu da ke ba ne ba,Na zo ne in sanar da ke hukuncin da na yanke,Dan haka kin ga tafiyata", ya kai zance ya na mai kewayeta ya nufi hanyar fita. Wani tsalle ta daka sai ga ta a gabanshi,hannayenta da k`afafunta ta bud`e ta na mai kare duk wata hanya da zai bi ya fita,tuni hawaye sun fara sintiri a saman fuskarta, amma duk da hakan Zuciyar ta batiyi sanyi ba haka ma bakinta bai mutu ba,"Wallahi rashin adalcin ya Isa haka da ga yau ba zan k`ara bari ka cigaba da cutar da ni ba,ko ka manta kafin ka yi tafiya irin haka ce ta shiga tsakanin na da kai, don haka a wannan Karon na lashi takobi ba zan bar haka ta faru ba,ba zan k`ara bari ka zubar min da k`ima da mutunci a wurin ta ba,ba wani abu da ka ke so kuma ka ke jin dad`in sa wanda ya wuce ka nuna ma mutane gazawata ba,don haka yau ba inda zaka anan za ka kwana,in kuma kana ganin ba haka ba ka ture ni sai ka wuce". "Kin ga bana son tashin hankali da ke don haka salin alin ki bani hanya in wuce"," Na ce an k`i a baka hanyar ka ture ni ka wuce,sannan ne zan gama yarda da ka zama Mijin ta ce,mai danne hak`k`in wata akan wata,in kuma ba ka iyawa kwana ya kama kanan dan dole",a ɗan fusace ya juyo yana mai cewa,"Wai taya ki ke tunani da zaton zan ita kwana a wannan d`akin na ki,kalli tarin bola,k`azanta da tarkacen da ke a cikin sa ke kan ki kalli jikin ki komi na ki a hargitse",.....ta katse shi da cewa"Tooooo tanan ka biyo to ai wannan ba laifina ba ne d`an ka da wannan cikin da ke jikina su ne su ka mai da ni hakan ka ga kenan ba ni za kai ma gori ba,kuma asali ai ba haka ka rabo ni daga gaban iyaye Na ba","Ba wani ba su su ka mai da ke haka ba haukan ki ne kawai ya mai da ke haka ,ko ke ce Mace ta farko a duniya da ta fara zama Uwa,kan ki ne farau haihuwa,don haka tun kina fahimtar me na ke cewa ki bani hanya in wuce",ya kai zance ya na mai son kewayeta ya wuce,sai dai duk inda zai aje k`afarsa sai tai tsalle ta dire gurin ko nauyin jikin ta bata ji gabad`aya masifa da zafin kishi sun rufe mata ido,haka su ka dunga zagaye d`akin,har Allah ya sa ya samu sa'a rik`eta sai da ya,kai ta tsakiyar Parlourn sannan ya sake ta ya juya da sauri ya na mai shirin barin Parlourn har ya kama handle d`in Door d`in zai buɗe,ya ji amon muryarta a cikin kunnensa da cewa,"Wallahi ban yafe maka ba in har ka sake komawa waccan Part d`in, tunda dai hak`ina ne a barmin kaya na,ko da Ko bazan amfana da shi ba,da wani irin sauri ya waigo ya na mai zuba mata idanunsa da suka fara sauya kala,rasa me zai ce da ita yai,ganin hakan da ta yi ta saki kuka mai k`arfi wanda zafinsa ya kan fita har a cikin muryarta daga k`arshe ta bar Parlourn da gudunta ta nufi bedroom kai tsaye. Hannu bibbiyu ya kai yana mai dafe kansa bakinsa ba abinda ya je furtawa sai Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un,daga k`arshe wuri ya samu ya zauna sai da ya kwashi lokaci mai tsawo kafin hankalin shi ya koma kan Nurain da ya ke ta sharar barcinsa sai bige-bigen cizon sauro ya ke,wurin shi ya nufa ya d`auke shi kacokan ya na kara shi a jikin sa ya ji wani irin warin daud`a da zarnin fitsari da ke tashi a Jikinsa kai tsaye Parts d`in shi ya nufa da shi ba tare da ya sake bi takan kowa a cikin matan na shi ba,Zeenat kuwa saboda tsabar bala'i sai da ta lalla`bo taga ina ya yi kana hankalin ta ya kwanta ta tafi ta kwanta badan Zuciyarta ta samu salama ba. Kayan jikin Nurain ya fara cire ma shi, ya samu ya fitar da su daga waje,ya na tafe ya tuna ranar da ya siyo ma Yaron kayan da kuma farashin da ya siyo su duka-duka kayan ba su fi kwanan wata uku ba amma har sun kai ga fita hayyacinsu,tayanda ba zai sake marmarin ya gan su a Jikinsa ba,ruwa mai zafi a bathtub ya haɗa ya dawo ya tashi Nurain d`in a hankali ,"Lah Abbu kaine yaushe ka dawo?",shine abinda ya fara fita daga bakin Nurain, murmushi ya sakar ma shi tare da janyo shi jikin sa ya ce da shi,"Na dawo tun d`azu amma sanda zan shigo sai na iske ka yi barci"cikin muryashi yara `yan shekaru shidda zuwa bakwai ya ce da shi,"Kai amma na ji dad`in dawowarka kasan da baka nan Ummunah tayi ta dukana tana zagina kuma bata bani abinci akan lokaci,ko wanka ba ta yimin sai taga dama,har kuma"......ya dakatar shi da cewa,"Ya isa haka Nurain yanzu ba gashi na dawo ba,ba zata k`ara dukan ka ba kuma ni da kaina zan rik`a yi maka wanka yanzu haka ma ga ruwa can na had`a ta shi mu je in yi maka wanka ka ji Yaron kirki".tun kafin ya rufe baki tuni har ya nufi hanyar bathroom d`in, sai faman kawa yake ba abinda ya dame shi. Sai da ya d`auki lokaci mai tsawo yana musanya ma shi ruwa kafin ya fito da shi,ya shafe masa jiki da lotion mai tsada,ya sanya masa kayan sa masu sauk`in nauyi,da yake dama yana da da kaya a wurin saboda faruwar irin haka,ya kwantar da shi a jikinsa,a hankali ya d`ago ya Na kallon shi ya ce da shi,"Abbu barci na ke ji gashi kuma ina jin yunwa",runtse idanuwan shi yai ya na mai sake jin zafin irin rayuwar da ta ke gudanarwa tsakanin sa da Ummu Nurain, da kan shi ya tashi ya had`a mi shi abinda zai ci d`an simple yana jin ya k`oshi anan take barci ya kwashe shi. Zaman shi ya gyara akan gadon bayan ya d`auko System d`insa da wayoyinsa,kamar jira ake sai ga video call d`in Gimbiya Ayush ya shigo wayarsa,sai da ya ji wata natsuwa ta zo ma shi kafin ya picking call d`in, duk yanda ya so ya kauda damuwar dake kwance a saman fuskarsa kasawa yayi don a kallo d`aya da tai mashi ta fahimci hakan,duk da tun bayan da yafito daga Part d`in yake fad`a da Zuciyarsa akan kar ta sake kawo mashi abinda ya faru a cikin ransa,amma ina hakan ya faskara. "I'm sorry Mijin Gimbiya ban so ta dalili na ranka ya `baci ba ,ban so ace saboda damuwata za ka ga tsawon darennan cikin damuwa da `bacin rai ba",Kauda zancen yai ba tare da ya ce komi akan abinda ta ce ba sai tambayarta yai da cewa,"Ya jikin na ki I hope ba wata damuwa,ba wani sauyin yanayi da ki ke ji a jikin na ki?"," I'm feeling much much better, ba na jin komi","Are you sure?,kin san siled mistake ya ke coursing big problem, ko cikin dare da zaran kin ji sauyin yanayi ki sanar da ni,komin k`ank`antar ciwon da ki ka ji,kin ji". "Okay Mijin Gimbiya I'll inform you", ta amsa mi shi cikin respect gami da d`orawa da cewa,"Da zaran ciwon ya zo zan zaro masa Ido gami da daka ma shi tsawa in sanar da shi koni Matar waye,nasan da zaran ya ji hakan zai ruga ya bani wuri". Murmushin ya saki wanda dama shi ta so ya kafin ya ce da ita,"Ina maki fatan ki kasance cikin amincin Allah har zuwa safiyar gobe daga k`arshe kuma ina mai baki haƙora akan rashin kasancewa da nai tare da ke a lokacin da ki ka fi buk`ata ta", ya na kaiwa nan ya ending d`in Call d`in, gami da gyara kwanciyar yaronsa a Jikinsa da haka barci sarkin ita sata ya sace shi bayan ya gama shan gwagwarmaya da Zuciyarsa kan ta manta da abinda ya faru. *JADEEDAH* STORY & WRITTEN BY : (*Cwt~Sumiey*) Marubuciyar littafin MENE NE ABIN YI ? KARAGAR MULKI And now.....*JADEEDAH* *YOTA* BOOK 1 PAGE 25❤ "Yauwa Momy bari in k`ara maki da wannan so nake ki cinye komi dake soman table d`innan", Jedeeda ta fad`a ta na mai k`arama Momynta Plantains ɗin dake gabanta. " Jedeeda na k`oshi tun d`azu kin san ko lafiya na lau ban cika son cin abincin mai nauyi ba,Na ci omelette,Na sha Oat,kuma yanzu ki ce za ki k`ara min da plantaint,Haba ya isa haka". Turo baki gaba Jadeeda tayi kafin ta ce,"Momy so na ke fa na ga kin maida jikin ki,kalli fa duk kin rame,ba na son ganin ki a haka". "In banda abun ki Jadeeda,Ai sai da muce mun gode ma Allah, Matar da ko Tea bata son sha ,yanzu ta zage ta ci wad`annan,ai lamari yayi kyau", Cewar Granny da ke zaune a gefe. " Mom ai haka Jadeeda ta ke bata da natsuwa ko kwanciyar hankali indai akace maki Momynta ba lafiya,in kin ga ta huta to ta samu lafiya ne,duk wata d`awainiyar da kulawa ita ke yi mata ita". Uncle R ne ya sauke Cup d`in da ke hanunshi shi kafin ya ce,"My Angle ta musanman ce hakan ya sa na ke ji da ita,Ko ba komi tana da kyawawan halaye da za ai koyi da su"Ya ɗan dakata kafin ya cigaba da cewa,"Wai ya Maganar Voice of Convenant, ɗin da ki ke gudanarwa ya yanayin program d`in yake tafiya fatan kuna Succeeding yanda ya kamata?",ya kai zancen da sigar tambaya tare da maida akalar zancensa kacokan kan Jadeeda. Yanayin yanda ta fara raba idanunta ya sa Gloria ta fahimci akwai wani abu da ke faruwa ko ma ya riga da ya faru,a jiye Spoon d`in hannunta ta yi kafin ta ce da ita,"My Daughter ya dai,ko dai kun fara fuskantar wasu matsaloli ne akan program d`in na ku,shin wani abu ya faru ne?". "No Momy ba abinda ya faru,kawai dai bana attainding d`in komi,I'm focus on you ,hankalina baya kan komi ,tun ranar da aka kirani akasanar dani halin da ki ke a ciki ban sake zuwa wani Hall,meeting ko kuma Church ba,in har da sunan gudanar da program d`in da na saba ne".....,"Hah...Jadeeda.... Halalujah..wannan wanne irin hukunci ne ki ka yanke, ai bai kamata ba,aikin da ki ke yana da matuk`ar girma da lada kina fa kiran mutane ne to the word of God, so akan me za ki dakata,shin kin san iya adadin mutanen da suke amfana da abinda ku ke,ina Sister Zarah da kuma Madam Alena suke akan me suka bar ki,ki ka yanke wannan hukuncin?". Fuskar Jadeeda tamkar zata zubar da hawaye kafin ta ce,"Momy ke ce fa baki da lafiya,ta ya Zan iya maida hankalina akan wani lamari bayan ga ki kwance ba ki san inda kan ki ya ke ba"...."Ciwona bai kai yad`a bushara da ki ke yi ba Jadeeda ,haka kuma Ciwona bai kai rera wak`ok`in ban gaskiya da yabo ga Yesu Almasihu ba,ta ya ma za a had`a su ?". " Anty please kiyi hak`uri ban san wannan Maganar tawa za tai coursing d`in wata hayaniya ba,biside ma ta na da gaskiya bata da natsuwa taya za ta iya gudanar da wad`annan muhiman aiyuka za a iya samun Matsala so please ki yi mata hak`uri za ta koma kan aikinta idan komi ya natsa".Cewar Uncle R. "Ko ni ma mun yi wanna Maganar da ita,tunda fari uzirin da ta bani mai girma ne shiyasa na amince ma ta har da sake bata goyan bayan,ta na iya k`ok`ari ta yanzu haka Synagogue, Church of All Nations (SCOAN) da ke Lagos sun za`beta a matsayin wacce zata bud`e masu taro da dad`ad`an wak`ok`inta a ranar Easter". Gaba ki d`ansu murna su ke da jin wannan labarin dan ita kanta Jadeeda bata san da zancen ba,ba ta san san da ta je ta rungume Papa ta na ta zuba masa Godiya ba,"Kai wanna abun farin ciki ne,Anty J za ki tafi Lagos kuma wannan katafariyar Church d`in gaskiya da ni za ki tafi", Cewar Martin,Cikin murna Jadeeda ta ce da shi," Kar ka wani damu gamu can mun tafi tare,Nora Kema za ka biyo mu mu tafi tare ?", sai da ta ya mutsa fuska kafin ta ce,"No Anty J I'll Stay with Mom zan kalli komi a TV or through the Phone". Granny ce tace,"Abun murna ya same mu sai na ke ji kamar in tashi in taka rawa my Granddaughter zata je SCOAN",ta fara girgiza jikinta ta na daga zaune,nan fa suka dunga nuna murnar su a fili,har Uncle R na cewa nan gaba shine zai zamo Bodyguard na ta. "My Daughter matso kusa da ni in rungume ki,Na ji dad`i ban ta`ba tunanin zan wayi Gari in ga irin wannan ranar ba,sai ga shi Allah ya nuna min na rasa ta wacce hanya ma zan bayyanar da farin ciki na,tafiyar ma ta kusa nan da one weeks ne ko ?", "Eh haka ne haka suka sanar da ni so ya kamata ku fara preparing, in ya so sai mu tafi gabad`aya kamar hakan zai fi"..... Cewar Papa,da sauri Granny ta katse shi da cewa," Jikin Gloria har yanzu da sauran shi zai fi kyau ace ta na zaune wuri d`aya ko da na d`an wani lokaci ne,in ya so kai za ku iya zuwa ni sai in zauna tare da ita". "Okay Mom yanda ki ka ce haka za ai,kai lokaci ya ja yau ne fa Edwin zai dawo Na so in shafa'a,har zuwa yanzu ban tura Wanda zai d`auko shi ba". " What!! Yau Broz Edwin zai dawo amma ban sa ni ba ?","Kamarya ba ki sani ba Jiya jiyannan fa muka gama Video Call da shi,ni da na gaji ma nan na barshi shi da Nora, Martin da Granny yana ta faman tsokanar su,kin san shi da barkwanci har ma yana cewa da ya yanke zai Kira ki". Cikin rashin jin dad`i Jadeeda ta ce,"Mom I swear to the God bai kirani ba,ko na kira shi ma baya d`auka mun d`au lokaci mai tsawo a haka,baya picking call d`ina na rasa me na yi masa,kuma a baya ba haka ya ke min ba,muna da fahimta a tsakanin mu". "I'm sorry kin ji ban San haka na faruwa a tsakanin ku ba,da ni da kaina zan kira shi in ji ba'asi amma koma me ye I promise to you ya zo k`arshe tunda ga shi yau zai dawo Gida", Cewar Papa ya kai zancen ya Na mai bubbuga mata baya alamun lallashi. " Papa ka barni in je in picking d`in sha a Airport zan so in fara had`uwa da shi","Ba damuwa sai ku tafi tare da Uncle R da Martin nasan Nora ba lalle ta je ba,ta fi son ta kasance jikin Momyn ta a koda yaushe".Nan ya basu details d`in Flight d`in da kuma lokacin saukarsa,kana ya shirya ya fita dama yana da inda yake son zuwa tare da su Nora ya tafi ya aje su inda suke part time d`in su na koyan Computer kafin fitiwar Jamb d`in su. Haka suka cigaba da hirarrakin su har time d`in ya gabato "Uncle Miey let me take a shower before the flight arive","Take your time I'll Wait you in the car,but please kar ki dad`e ina so mu yi sauri mu dawo,akwai inda na ke son in kai ki I need to surprise you". Sai da tai hugging na sa kafin ta ce," I'll be right back ba zan jima ba,domin kasan ina son surprise d`in ka, dad`i na kusan kashe ni","To ki shirya ma wannan domin kusan ya fi na koyaushe",idanuwanta ta fiddo waje irin da sigar tambaya d`in nan,"Yes I'm sure ke dai don't waste my time ki yi sauri ki fito ",ya kai zancen ya na mai binta da wani kallo mai cike da tarin ma'anoni,ita ko ko a jikin ta sai mik`ewa tayi ta upstairs da saurinta domin ta shirya. Wani dogon tsaki Granny ta saki tare da cewa,"Haka za ka k`are kullum ba ka da aiki sai d`aukar your Niece kana yawo da ita lungu da sak`o amma ba za ka iya fitar da mata kai Aure ba". "Mom Haba mana na ce fa zan yi Aurennan to meye na irin wad`annan k`ananun zancen"," Oh k`ananun zancen ne ma to idan baka son k`ananun zancen ka bari ni in nemo maka Matar Auren ai ni hakan ba abu mai wuya ba ne a gare ni". "Ah no Mom ina da kalar type d`in Macen da na ke so ki bar ni zan nemo da kaina ,in dai Aure ne a bar Ni zan yi,zan za`bi wacce ta yi min", ya kai zancen ya na mai barin wurin gabad`aya. Cikin karyayyiyar murya Granny ta dubi Mom ta na mai cewa," Kalli Gloria ya tashi ya tafi ,ban san har sai yaushe Rechal zai ji ya kuma saurari Maganata ba,har Mahaifinku ya mutu ba shi da wani buri da ya wuce ya ga Aurensa amma Yaronnan ya k`ek`ashe idanunsa ya ce mi shi bai ga Matar da zai Aura ba har ya mutu ya na tuna hakan, yanzuma gashinan sai fama na ke da shi ya k`i ji,wata k`ila nima ba ni da rabon gani Auran na shi ". " God for bid Momy za ki ga Auran shi,by the grace of God, bari ya dawo ni nasan ta inda zan `bullo masa",haka ta ciga da lallashin ta har zuwa wani lokaci. Sanye da gowm wacce bata kai gwuiwarta ba ta fito gashin kannan nata ya sha gyara ta sake shi har gadon bayanta,kafarta kuwa sanye take da high heel shoe, sai k`amshin Oud da ke faman tashi a jikinta,yadda kasan yar bebyn roba haka ta ke taka k`asa,ta yi kyau matuƙa kamar ka sace. "Oh my Goodness Anya kuwa zan yarda mu fita tare da ke a haka,kar fa ki sa in rik`a had`a goslwo ko accident a saman hanya,irin wanna kyau haka,na ga alama da gaske so ki ke, ki samu wanda zai huf ya raba ni da ke". Ah Uncle Miey ba wanda ya Isa ya raba ni da kai,domin duk wanda zan rayu da shi zai so ni bayan son da ka yi mi ni ne,haka kuma zai kuka da ni akan kulawar da ka ba tun ina `yar karamata,har kawo girmaba". " Har yanzu ke Baby ce a gare ni,ban k`i in d`auke ki in goye a bayana in zagaye Gidannan da ke ba,ki sa ni kina da matsayin mai girma da muhimmanci a wuri na duk da kullum a cikin zullumi da fargaba na ke",ya kare zancen ya na mai matsowa kusa da ita. Cikin yanayin Maganar da ya yi ta shiga ranta ta ce da shi,"Uncle miey me ye yake sa ka cikin Zullumi da fargaba a kaina ba tare da na san shi ba?",sai da ya kamo hannunta ya rik`e a cikin nasa kafin ya ce da ita,"Ina tsoran ranar da za ki bar ni ranar da za ki za`bi wani sama da ni ranar da za ki fifita Soyayyar wani akan tawa ban San ya Zuciyata za ta kasance ba ,tabbas zan iya rasa rayuwata akan haka",da sauri ta kai hannunta saman bakin sa ta rufe tare da cewa,"Uncle Miey haka ma ba zata faru ba,kai jini na ne kuma rayuwata babu ta yanda za ai wani ya shigo rayuwata jiya ko yau ya ce zai maye gurbi ko matsayin ka a wurina ka sani ba zan ta`ba barin ka ba a koda yaushe zan rayu da kai ,a duk inda na ke ba abinda na ke tunawa indai har za a ambaci ko me irin sunan ka ne face na tuna,kulawa,Soyayya karamci da halacin da ka ke min". "Da gaske ba za ki barni ba,ko da kuwa nan gaba,ba za ki ce nayi ma ki tsufa ba", ya fad`a ya na mai damtse hannunta dake cikin na sa.Dariya sosai Jadeeda ta saki jin ya ambaci tsufa,`bata fuska ya yi,tare da cewa,"Au dariya ma na baki to shikenan sai ki cigaba tunda na zama abun dariya". " Oh sorry Uncle Miey ba haka na ke nufi ba,just kawai na hasaso fuskarka da furfura ne shiyasa Na ke dariya",shima dariyar ya yi gami da sa hannu ya bud`e mata front seat wurin zaman banza kafin ya shiga ya tada motar su tafi,suna tafe ta na tsokanar shi. *JADEEDAH* STORY & WRITTEN BY : (*Cwt~Sumiey*) Marubuciyar littafin MENE NE ABIN YI ? KARAGAR MULKI And now.....*JADEEDAH* *YOTA* BOOK 1 PAGE 26❤ Saukar Jirgin yai dai-dai da bugawar k`arfe 5pm janye da trolleynsa ya fito sai faman kai hannu ya ke na rik`e kan shi alamar yana sara ma sa ne ko kuma ya na ciwo. "Momy", shine abinda ya furta daga can k`asan bakin shi bayan ya cikaro da abinda ya ke a gaban shi,"Irin wannan ai sai kisa in fita da gudu taya za ki ba Security welcoming card d`auke da suna a jiki ai sai wani ya yi tunanin mai laifi ne ni", shine abinda ya fad`a har ya idasa kusa da shi ya ce mishi," Hii I'am Edwin Anderson "," Hy nice to meet you, how was the trip I hope you enjoy it",ya kai zancen ya na mai mik`a masa wata flowers da ke gefan shi wacce ta ke d`auke da wata Paper,amsa yai gami da yi masa Godiya kafin ya fara warware Paper. Sannu-sannu ya kai kan shi inda su Jadeeda su kai parking, ta hanyar wanna Paper,gabad`aya ya zak`u hankalin shi na kan motar ya k`osa ya isa ya rugumi Momynsa a jikin sa "Momynah sai kin gama wahalar da ni sannan za ki bari in ganki,kin san fa na yi kewar ki,", shine abinda ya ce bayan ya Isa gurin Motar, yanayin yanda aka saukar da glass d`in Motar da fara k`ok`arin fitowar da akai sai da ya sa gaban sa ya fara bugu da sauri da sauri,har sai da ta kai ya fara kai hannunsa ya na dafe kan shi da Ya tsananta ma shi da ciwo. Da gudu Jadeeda ta fito ta yi kansa ,da hannayenta bibiyu ta rik`a kai masa duka a duk inda ta samu a jikin sa,shi kuma kasa dakatar da ita yai har sai da ta yi mai isata kafin kuma ta koma ta rungume shi a jikinta ta Na mai cewa," Me na aikata ma ka, wanne laifi ne na yi maka da har na yi diserving irin wannan punishment d`in,Na zama wararriya a cikin ahalin ka bayan kuma a da,Na fi kusanci da kai akan kowa, me na aikata maka ka sanar da ni?". "Ki yi hak`uri na amshi laifina,kuma a shirye na ke da in amshi wani sabon hukunci fiye da wannan da na amsa a yanzu,amma kafin nan ina so ki sani ba ki aikata min komi ba"....ta katse shi da cewa," What?!,Shut up ka na nufin hakanan ba tare da na yi maka komi ba ka sauya min,no wannan ba abu mai yiwuwa ba ne". "Please and please na rok`e ki da ki bar wannan maganar mu je Gida ,zan ma ki bayanin komi yanda za ki fahimta,ki sa ni nima kaina ina cutuwa da rashin ki a tare da ni". K`arasowar Uncle R wanda ya tafi samoma Jadeeda ruwa sakamakon sark`ewa da ta yi da miyau itace ta sa shi ya d`an dakata ya nufi wurin shi da sassarfa ya na mai murnar ganin sa," My son Edwin kai ne ka zama haka gaskiya ba k`aramin amsar ka Gidan Sojannan yai ba,see you yanda ka kere ni a tsawo",ya kai zancen ya na mai janyo shi Jikinsa ,nan fa suka shiga mota cike da farincikin a fuskokin su,Jadeeda k`in zama front seat d`in tai ta koma can baya wajen Edwin sai faman cika shi da surutu ta ke ba tare da ta fahimci halin da ya ke a ciki ba. Tarba ta musanman ya iske lokacin da su ka Isa , tarbar da bai yi zato da tsanmani ba,kar ma Momy yanda ta zage ta na kula da shi da kuma Jan shi a jiki dama can Momys Son suke kiran shi,shi da Nora ita kuma suna kiranta Momys Daughter kasancewar Momy ta fi nuna kula gami da ji da su,Martin kuwa shine d`an Gidan Papa,ita kuma Jadeeda ita ce `yar Gidan kowa,dukan su suna nuna mata so da iyakar iyawarsu,ta samu gurbi a Zuciyoyin kowa da ke amsa sunan sa a matsayin ahalin Gidan Rev. Anderson. ~~~~~ Washegari tun gabatowar Asuba ya tashi ya shiriya da nufin zuwa Masallacin da yake jagorantar limanci a cikinsa,Bai Kai ga fita ba har sai da ya shiga Apartment d`in Gimbiya Ayush,barcinta ta ke cikin kwanciyar hankali da alama dai babu abinda ya same ta ta samu barci,cikin kwanciyar hankali da natsuwar Zuciya ya nufi Central Mosque kano Wanda ya ke near Emir Place,duk in yana Gari shi ke jagorantar su a limanci,bayan gabatar da Sallahr Asuba ya fara karanta masu littafin Buguyatul Musulimina,inda ya ke karanta masu babin Zina. "Ku sani Zina bala'i ce,Zina masifa ce, Zina alfasha ce Mai girman gaske,Zina tozartar da Kai ta ke,ba wai iya kunyar duniya ta ke sawa ba,takan zubar da k`ima daraja ga duk Wanda ya ke yinta Allah Subahanahu Wata alah ya ce a cikin suratul Israel, ((Wala takrabu zinah inahu kana fahishatan wa sa'a sabilah,haka ma a suratul an'am yace wala takribul fawahisha ma zahara min ha wa bad`ina)),ku sani Zina daud`ar Zuciya ce,kar Kai alfahari ko jin kai don ka kasance me wani nasibi da ka ke salwantar da su ta hanyar aikata alfasha,kar Kai alfahari don yau ka mallaki mota ka na d`aukar `ya`yan mutane a ciki domin ka lalata ma su rayuwar su,kar kai alfahari don ka kasance cikin jerin mutanen da suke da dukiyar da za su ita kama ko wanne d`aki a cikin hotel domin yin lalata da `yar wani,ka sani itama d`iyar wani ce uwar wani,Kuma matar wani,haka kazalika k`anwar wani ce,ya zaka ji in ka wayi gari ka ga wata ta daga cikin jerin sunayen da na lissafo naka a irin wannan matsayin,shin hauka za Kai ko mutuwa za kai?,ke kuma na dawo gare ki `yar'uwa,ba abinda ke kai ku Mata ga halaka irin wannan daga kwad`ayi sai son duniya,son sai kin Kai matsayin da ba ki kai ba,ki zubar da mutunci ahalin da Kuma zuri'ar ku gabad`aya, wai yanzu lamari har yai tsamari ba ga `yan mata ba ba Kuma zawarawa ba,Mafi k`ololuwar tashin hankali wai har da Matan Aure wa iya zubillah ki ji tsoran Allah ki zauna a iya matsayin da ki ke,hakan ne kawai zsi sa ki zauna lafiya har nan gaba ki haifi `ya`yan da za a iya alfahari da su",haka ya cigaba da da wa'azantar cikin d`acin Zuciya game da abinda ya ke magana akan shi,da su har zuwa sanda su ka tashi. Kai tsaye part d`in Gimbiya Ayush ya nufa cikin sa'a ya iske har ta farka tana ma kitchen Kai tsaye can ya nufa cikin murnar ganinsa ta nufo shi da cewa "Good morning my beloved husband fatan ka tashi lafiya?",sai da ya janyota jikin shi kafin ya ce da ita,"Me yasa za ki fito a irin wannan lokacin bayan kin san jikin ki ba kwari ne da shi ba,kina buk`atar hutu da kulawa me zai sa ki takura kan ki",sai da ta shagwa`be fuskarta sannan ta ce da shi,"Ina jin yuwa ne fa,shi yasa na fito,ka ga ma gashinan na d`ora ruwan zafin na rasa me zan dafa,komi ya fita a Raina bana jin son cin komi",ta kai zancen ta na mai raba jikinta da na shi,ta koma ta na mai jawo flak's ta fara had`a shayin Coppe,cikin yanayin girmamawa ta mik`a ma sa. Hannunsa ya d`ora akan Cup d`in ba tare da ya amsa ba sai Mai maida cup d`in yai saitin bakin ta tare da cewa,"A yanzu kin fi ni buk`atar shi don haka maza bud`e bakin ki ki amsa","Ba na son Shan shi fa","Ki daure ko kad`an ne ki sha zai miki amfani",ba dan ta so ba haka ta bud`e baki ta fara kur`bar shayin Coppe,sai da ta kusa shanye shi duka kafin ta ture bakin ta a jikin Cup d`in gami da cewa "Yanzu na Sha nawa saura na ka,bari in had`a maka na ka",ta Kai zancen ta na k`ok`arin had`a masa. "Ki bar k`ok`arin wani girki na sanar da su Ummiey ,sunanan tafe kan hanyar su duba ki,nadan za su zo maki da abun kakaci don haka ba buk`atar ki wahalar da kan ki","Sai da ta zaro idanunta waje kafin ta ce,"Haba Sweathert yanzu ashe sai da ka sanar da su abinda ya faru ?","Ya za ai bazan sanar da su ba,sufa d`in ahalina ne dole zan sanar da su ,su taya ni jimamin rashin gudan jinina da na yi,Kuma ya can- canta su zo su duba halin da ki ke a ciki ai","Na fa ji sauk`i fa Honey",Tukunna dai ni Banga alama ba". Tun dawowar sa Gidan Ummu Nurain ke faman Kai kawo ganin ya nufi apartment d`in Gimbiya Ayush ba k`aramin sake tunzurata yayi ba,tun tana lissafa seconing, minutes har ta kai ta kasa iya rik`e kanta cikin mak`ura Kuma k`ololuwar fushi da Kuma dokin shed`an da ta hau ta nufi apartment d`in. Gab da Gimbiya Ayush za ta Kai Cup d`in saitin bakin sa Ummu Nurain ta shigo kamar wacce aka hankad`ota,har sai da Gimbiya Ayush ta d`an ji tsoro ta ja baya, kafin wani cikin su ya samu damar cewa komi ta riga su da cewa,"To k`anwar karuwa,mara Zuciya,Mai burin son ta raba ni da mijina ,shed`aniya kawai,ni har yanzu ban ga ribar da Auren ki ta kawo ma na a cikin Gidannan ba,wai in tambaye ki Dan Allah har sai yaushe za ki bar ni na zauna lafiya da Mijina?"......"Hold on Zeenat me yake damun ki ta ya za ki shigo har cikin Part d`in ta kina mai binta da munanan kalamai haka Anya ki na cikin hankalin ki kuwa?". Sai da ta rausayar da kanta gefe kafin ta ce"Abu Nurain Kana kashe ni da mamaki,a fili ka ke aikata rashin Adalcin ka Amma da zaran na yi magana sai ka wayance ka nuna kamar ma ba kasan komi game da abinda ka ke aikatawa ko yake faruwa ba,ka sani gab ka ke da ka kai ni k`arshe hak`urina ya k`are".ta Kai zancen ta na mai juyawa ta koma kan Gimbiya Ayush ta na mai tamke fuskarta tare da k`ank`ance idanunta saboda tsabar masifa,"Ki sani na yi alk`awarin tarwatsa Shirin ki ta kowacce irin hanya sai aniyarki ta koma kan ki muguwa Mai bak`ar aniya"...."Wai me ya ke damun ki haka ne ko kin fita daga cikin hayyacin ki ne Zeenat eyeh ?".ya kai zancen ya na mai shan gabanta ya shiga tsakanin su dan ya ga ba abinda Zeenat take so ko yunk`urin yi da ya wuce ta ga ta Kai inda Gimbiya Ayush ta ke. "Kin ga Ummu Nurain ki kwantar da hankali ki domin wallahi ba abinda zuciyar ki ke zargi ne ya faru ba,ya zo duba ni ne ba ni da lafiya ko ba ki samu labarin na samu miscarrage ba?"."Hmmmmmm kar ki wani yi yunk`urin son fahimtat da ni sabon karatu ko darasi game da munafunci ko Kuma kusisina irin taki domin kaf na gama biya alon rayuwar ki tas na shanye,Abu d`aya na ke so da ke ki shiga taitayinki domin kowa ya san karo da kura ba dad`i". A fusace Jaheed ya Muna Mata hanyar fita ya ce ,"Ki `bace min da ganin tun kafin Zuciyata ta sa na aikata ba dai-dai ba a kan ki",..."Idan Kuma na k`i fa sai ka Dake ni na ce maka sai ka dake ni?,haba na gaji wallahi na ga alamun nema ka ke kai da matar ka ku kai ni kushewata tun kafin lokacina ya yi haba dan Allah,ka ji tsoran Allah fifiko da ka ke nunawa ya Isa haka ma na,ni fa `yar'uwar ka ce ko ka manta da hakan ne". "Ke ce dai ki ke manta ko ke wace ce da Kuma matsayin ki a cikin Gidannan,ki sani matsayin ki ya zarce wanda ki ke ba kan ki,Ina biye ma ki gami da d`aga ma ki k`afa ne saboda wasu dalilai Amma ki sani kina gab da Kai ni k`arshe Gimbiya Ayush fa mata ta ce kuma ta sunna me ye aibun Dan na zo inda ta ke". "Eh ai na sani Kuma na gani,hakan ne ma yasa ka ke d`aukar hak`k`ina kana kawowa wurin ta kana cin amanata ko",ta Kai zancen fuskarta na k`ara bayyana d`aci da zafin abinda ta ke ji a Zuciyar ta. Cikin rawar jikin Gimbiya Ayush ta matso kusa da ita tana Mai cewa,"Aa Ummu Nurain na rantse maki ba abinda ki ke tunani ba ne ya faru ba,ya zo duba ni ne ya ga ya na tashi saboda rashin lafiyar da na kwana da ita Amma bayan haka ba wani abu a tsakanin mu". "Kin ga Gimbiya Ayush bar ta ta yi duk tunani da zata yi,ita ya shafa,in ta so ma ta d`auka akan shimfid`a ta zo ta iske mu,duk matsalar ta ce wannan Ina da damar aikata fiye da haka,ita d`in mata ta ce ta sunna,ki sani ko jiya na bar ki da abinda ki ke so ne don son dakatar da fitinar da ki ke son haifar da ita a wannan lokacin,shin hankali ki bai kai kan za ta iya shiga cikin wani Hali ba a wannan Daren,in ta samu wata matsalar da wanne baki zan iya kare kaina,ya ya ki ke ganin idan abun ya zo da k`arar kwana da wacce fuska zan kalli iyaye da ahalinta,shin kina tunanin zan iya yafe ma kaina akan haka,Kuma da wacce fuska zan cigaba da kallon ki da ita,ke kullum hak`k`in ki ki ka sani ba ki duba da hak`k`in Wanda ki ke tare da shi,ta ya za ki zauna lafiya da irin wannan halin,a taya za ki haka za ta faru",Ya Kai zancen a tsawace,tabbas ta fara kai shi bango har ta kai ga fusata shi. Ganin haka da Gimbiya Ayush ta yi yasa tai saurin kama hannunta tare da cewa,"Kinga zo mu je zan maki bayani yanda yanda za ki fahimta kin ga ranshi ya fara ɓaci akan wannan maganar". "Dallah Malama rufa min baki duk ba ke ki ka haddasa komi ba Munafukar banza munafukar wofi",ta kai zancen tana Mai hankad`ata baya cikin tsautsayi ta tafi zata fad`i Bata Kai ga fad`uwar ba Amma ruwan zafin da ta d`ora hannunta ya bugo shi ruwan ya kifo mata a saman k`afarta,a gigice ta saki k`ara gami da sallallami d`auke a bakinta tana mai cewa,"Honey shikenan na k`one ,ta k`ona ni,k`afata zafin,zafin ko ina". A rikice a rude ya nufeta yana Mai kama k`afar domin ganin abinda ya same ta,sakin k`afarta yai ya koma kan Zeenat da jikinta ya fara rawar,kafin ta yi wani yunk`uri ya sauke mata mari hagu da dama,rasa ma me zai ce da ita yai sai daga baya ya koma kan Gimbiya Ayush ya sunkuce ta ya bar kitchen d`in da ita. Wasu zafafan hawaye ne suka fara zubowa daga cikin idanun Ummu Nurain,wannan wacce irin fitinar da bala'i ne ya sauka a cikin Gidanta,idanuwanta a rufe ta nufi part d`in ta ko gabanta ba ta gani. A parlour ya sauke ta ya nufi sashen shi cikin hanzari ya d`auko first aid box ya fara bata taimakon gaggawa. "Kin ga bari in d`auko maki kaya ki sauya mu tafi Asibiti da buk`atar a duba ki da kyau",Cikin yanayin wacce ta ke cikin jin zogi ta dakatar da shi da cewa,"Aa ba sai mun je ko ina ba ban wani k`one sosai ba,zan ma iya taka k`afar bari ma ka gani". Shigowar su Umma Jamila Mama Hadiza,Safina da kuma Biba domin dubiyar jikin Gimbiya Ayush ɗin ce ta ɗan ja hankailinsu. "Aa Jaheed me yake faruwa,na ga Zeenat ta fita daganan a cikin wani yanayin Kuma mun shigo mun ga Gimbiya Ayush a irin wannan yanayin",Mama Hadiza ta tambaye shi. Cikin d`acin Zuciya ya ce da ita,", Zeenat ce to k`onata saboda tsabar rashin hankali da bak`in kishinta","Subahanallahi garinya ya haka ta faru,wannan ai hauka ne,Asibiti ai ya kamata mu tafi ba wai a tsaya a gida ba ", "Haka na ce Amma ta ce wai ba sai anje ba","A'a wannan ba Mai yiwuwa ba ne,tashi maza mu tafi tun kafin abun yai tsamari",cewar Momy Hibba. Hankali a tashe Gimbiya Ayush ta so hana tafiyan Asibitin don gudun kar abinda take k`ok`arin `boyewa ya tuni nu,kar k`ilu ya jawo bau,Amma Ina hakan Bata samu ba domin ba tayi nasara ba,ba dan ta so ba haka suka tafi Asibitin. *JADEEDAH* STORY & WRITTEN BY : (*Cwt~Sumiey*) Marubuciyar littafin MENE NE ABIN YI ? KARAGAR MULKI And now.....*JADEEDAH* *YOTA* BOOK 1 https://whatsapp.com/channel/0029VapqU8C002T5Bz8RSQ0a PAGE 27 ❤ "Anya Gloria ba akwai wani ɓoyayyen sirri da ke wanzu tsakanin Richal da Jadeeda ba ?",Mom Rebecca ta faɗa bayan sun gama yin dinner. Shiru Momy ta yi ta kasa iya cewa komi sai can daga ƙarshe ta sarƙe da miyau, saurin ɗaukar Cup ɗin ruwa ta sha sakamakon ƙwarewar da ta yi,ko ta samu ya lafa. "Mom wannan wacce irin magana ce,me ya kawo ta,kamar ba ta da muhalli a irin wannan wurin ","Hmmmmm Gloria kenanan dama na san irin haka ce zata faru,ba lalle ki yarda da duk abinda zan faɗa ma ki ba a yanzu ba,amma ki sani tuni zuciya ta daɗe da fara kawo zargi kala daban-daban a cikin tarayyar Richal da kuma Jadeeda"...."Mom zargi fa haramun ne,kuma ke fa tamkar Uwaki ke a gare su wannan bai kamata ya fito daga bakin ki ba",Girgiza kai Mom Rebecca tayi kafin ta ce,"To Shikenan tunda haka ki ka ce na bar maganar ba zan sake danganta su da irin wannan magana ba tunda baki yarda ba",tana kaiwa nan a zancenta ta tashi ta bar mata dinning ɗin gaba ɗaya. Tun bayan fitar Granny da ga dinning room ,Momy ta shiga cikin ƙololuwar tashin hankali, Zuciyar ta sai faman saƙa mata munanan tunanin ta ke, kwakwalwar ta cushe,ta kasa samun natsuwa balle har ta samu damar da zata samu makama a cikin zancen,tun tasowar Jadeeda ta san akwai kyakkyawar alaƙa a tsakanin su,ya kan ɗauki dukkanin wani lamarin ta da muhimmanci baya taɓa manta wani abu da ya shafeta,duk da kasancewar ba a ƙasa ɗaya suke zaune ba hakan bai hana shi halartar duk wani abun da zai sa ta farin ciki,shaƙuwar su takai matuƙa har ta kai ya fi kowa sanin sirrikanta da kuma abinda take so,sai dai ko ɗaya bata taɓa kawowa a ranta cewa da akwai manufar hakan ba,sai yanzu zuciyar ta ta fara kawo mata hakan a matsayin zargi. "Kai a'a hakan ma ba zai yiwu ba,Richal ba zai taɓa aikata min irin haka ba,ya na da hankali ya san girman sirrin da ke lulluɓe acikin wannan lamarin ba zai aikata haka ba",Gloria ta faɗi hakan ta na mai cigaba da kaiwa da komowar da ta ke. "Idan kuma hakan ta kasance fa yake nan ?",wani sashe daga cikin zuciyar ta ya sanar da ita haka,sai da bugun zuciyar ta ya ƙaru kafin ta dafe saitin wurin tare da cewa,"Shakka babu kuwa da ya aikata babban kuskuren da bai taɓa aikata shi a rayuwarsa ba,zai yi dana sani mai girma,har sai takai shi ga jin dama bai bari sakarar kuma mayaudariyar zuciyar sa ta rinjaye shi ga aikata abinda ya aikata ba". Tunani ne ya cinkushe mata kai har ta kai ga ta fara iya daina gane komi ji da ganin ta sun fara gushewa ,kanta kuma na tsananta mata wajen sarawa. Amma duk da hakan ta kasa iya dakatar da kanta game da tunanin da take, abubuwa masu yawa sai yanzu suke zuwan mata,misali irin yanda suke ba junan su kulawa da kuma yanda shaƙuwar su take,kafin ka ce me tuni ta fara ganin duhu a cikin idanunta da ƙyar ta samu ta daga bango ta isa bedroom ɗin ta ta zube a kan shi wasu zafafan hawaye na son zubo mata amma zuciyarta ta ƙeƙashe kwata-kwata ba ta son ta yarda da zarge-zargen da suke kai kawo mata a cikin ranta,balle har ta yarda da su. "Anty Jee wai ina za ki ne dare fa ya fara yi na ga sai faman kwalliya ki ke,is there anything special da ki ke expecting ɗin sa ne?","Yeah off course ko kin manta Uncle Miey ya na can yana jirana,zai yi Surprise ɗina da wani abu mai matuƙar muhimmanci,so ya ki ga fitar tawa ta fita ko in sake wata",ta kai zancen tana mai jujjuya jikinta yanda zata ganta sosai,sanye ta ke da mini skect sai wata half ɗin riga mai hannu guda,wacce ko cibiyarta ba ta rufe ba,ƙafarta sanye da high heel shoe,gashin kanta ya sauka har saman shoulder ɗin ta,komi nata shigar red and black, skect da bag ɗin ta black sai rigar jikinta da shoe ɗin ta red. Da yatsun hannunta ta yi mata alamar ta kai maƙura,"Am bari in ƙara fiddo da Anty Jeee ɗina",ta kai zancen tana mai saukowa daga kan bed ɗin da take ta ɗauko eye glass black ta sanya mata,gami da tsara mata simple make up a saman fuskarta,sai da ta ƙara yi mata ɓarin mabanbanta tauraruwa a jikinta kafin ta juyar da ita saitin mirrorn dake ɗakin gami da cewa da ita,"Ya ki ka ganki yanzu nasan in ku ka haɗu da Uncle R ba zai iya noticing ɗin ki da sauri ba". Dariya Jadeeda ta saki gami da kai ma Nora bugu ta goce tare da cewa,"Ba kyau zan yi ba ko da suffa za a sauya min in har Uncle Miey zai iso gare ni da bugun zuciya kaɗai ya isa ya gane ni,balle kuma wata kwalliya da ko matakin Princess ban kai a kira ni da ita ba","Wa ya gaya maki haka ai Auntyna ta wuce da wannan matsayin ,sai dai a kira ki da Queen ba Princess ba","Ma za ki cigaba har wani ya jiki,da anzo zan tsere jikinsa in ce ba ruwana","A haba ai nasan ba za ki aikata hakan ba,ke ɗin ta dabance,za ma ki iya ɗaukar laifin akan ki,saboda tsabar ji da ni da ki ke kin san wani time ɗin ina mamakin yanda wasu abubuwa na mu suka sha ban-ban da na ki,misali yanayin hasken fatar ki,ɗan ƙaramin jiki da ki ke da shi babu wani abu guda ɗaya wanda ku ke kamanceceniya da shi da wani a Gidannan komi na ki so special ke ka ɗai ke da irin sa". Ta buɗe baki za tabata amsa Martin ya shigo a hargitse kamar wanda aka watso shi , Muryar sa na rawa yace da su,"Momy....Momy ....jikinta ya motsa tana can bata iya gane komi da alama ta na cikin mawuyacin hali na yi ta ƙoƙarin in ga ".....ko tsayawa su ji ƙarashen abinda ya ke faɗa ba su yi ba,su ka yi waje gami da budar Room ɗin ta don ganin halin da ta ke a ciki,ba ƙaramin tashin hankali su ka shiga ba lokacin da su ka ga halin da Momy ta ke a ciki,nan su ka fito suna neman agajin gaggawa gurin Driver, Gate Man da kuma sauran masu aikin Gidan. Allah ya tai make su sun isa Hospital ɗin da wuri da ita cikin ƙanƙanin lokaci Doctors su kai ca kanta,sun yi iyakar bakin ƙoƙarin su kanta,duk da kasancewar Doctor Muh'd Jaheed baya nan,sun samu ta dawo cikin hayyacinta amma kuma cikin rashin sa'ah ta kasa iya tan-tance kowa a cikin su,ta kasa iya kama sunan kowa a cikin su, Jadeeda sai ta kira da Momy Rebecca ,Nora Kuma ta kira ta da Martin haka dai ta cigaba da soki burutsu,zance ba kai ba ƙafafu. "Doctor hankali na a tashe ya ke ,ba fa ta iya gane kowa kamar ba ta cikin hayyacinta ?",Rev. Anderson ya faɗa ,da dawowar shi kenan ya iske lamarin. "Am Sir she is out of danger bata cikin wani hatsari,za mu ɗorata akan medicine by the grace of God za ta koma normal", wannan shine abinda Doctor ɗin da ya duba ta ya ce,kasa haƙuri su kai har sai da su ka sake tuntuɓar wasu Doctors ɗin amma maganar ɗaya ce, cewa a hankali za ta koma normal,sai faman kai kawo su ke ,sun kasa kwantar da hankalin su,ga dare har ya fara tsalawa. "Wai ina asalin likitan da ya duba ta ya ke,a kira shi ko ma samu ta fita daga cikin wannan yanayin ?",cewar Granny da hankalin ta yake a matuƙar tashe. "Granny wannan Special Doctor ne ba kowanne lokaci ya ke zuwa ba","Jesus Christ oh father lord ka kawo mana ɗauki. Sai tin bed ɗin Jadeeda ta je ta duƙa gami da dafa ƙafafun Gloria idanuwanta na zubar da hawaye ta fara yi mata addu'a,"Oh Lord Jesus hear me when I call,o God of my righteousness! You have relieved me in my distress have mercy on my Mom and hear my prayer,na sani kai ka faɗa a cikin littafin ka mai tsarki Jeremiah chapter 33 verse 3 kace call to me and I'll answer you show you great and mighty thing wich know not,bari Ubangijin sama da ƙasa ka yaye ma Mahaifiyarta wannan lalurar da ta ke fama da ita,oh Lord father kasa wannan cuta ta zama waraka kuma kaffara gare ta,bari Ubangijin halitta kasa ta miƙeta taka da ƙafafuwan ta,ka warkar da ita ,ka fidda mu daga cikin tashin hankali da ruɗun da muke a ciki ",ta kai zancen tana mai zubar da zafafan hawaye akan fuskarta. "Anty Jeeyy mai zai sa ba zamu nemi alfarmar su kira mana shi ba ya zo ya duba mana ita ko da zuwa gobe da safe ne?",Martin ya ce da ita,"Sai dai mu kwatanta hakan idan zai yiwu,wani lokacin ba a cika yin dacen zuwan su ba","Kin ga Jadeeda ko nawane zan biya in har zai zo ya duba ta,ya ambaci iya amount ɗin da ya ke so zan biya shi matuƙar zai shigo cikin garin Abuja zuwa da safe","Shikenan Papa bari in Yi magana da wani daga cikin Doctors ɗin ko za mu da ce". Haka ta fita sai dai me cikin rashin sa'ah Doctor ɗin da ke unduty a ranar ya shiga treater,sai da su kai jiran sanda ya fito kasa tsayawa ya sauraren su yai ƙarshe ma sai ya sake shiga wata treater ba tare da yaba su wani lokaci mai tsawo ba,wanda hakan ba ƙaramin sake jefa su cikin wani sabon tashin hankali. "Yanzu Papa haka za mu zuba ma Momy idanu ba tare da mun iya taimaka mata da wani abu ba,zuciya ta sai ƙara karyewa ta ke".cewar Nora Sai da ya janyo ta jikinsa kafin ya fara lallashinta gami da son kwantar mata da hankali,ringing ɗin wayar Jadeeda da ta ishe su tun ɗazun ne ta sake ratso kunnuwan su ,sai da ta saki tsaki kana ta jawo wayar da son duba waye ke kira,sunan Uncle Miey ta gani yana yawo akan screen ɗin da sauri ta ɗaga gami da fara ba shi haƙuri gami da sanar da shi abinda ya ke faruwa,bai jira komi ba ya katse kiran gami da nufo Hospital ɗin . "Am ɗan dakata kamar fa ya taɓa bani wani card da zan iya contacting ɗin sa da shi", Jadeeda ta faɗa ta na mai yunƙurin fara laluban jakarta ba ta iya ta samu komi a ciki ba hakan ya sa ta juyawa gami da nufar hanyar fita,nan ta ci karo da Uncle Richal ya na shirin shigowa,a taƙaice ta yi ma shi bayanin abinda ke faruwa ya juya ya bita su ka nufi Gidan tare. Ba su wani ɓata lokaci ba suka isa gidan duk inda ta san ta na aje wani abu mai muhimmanci sai da ta yi watsa-watsa da su ,har sai da ma ta fara cire rai wajen ganinta sanna Allah ya nuna mata ita,tsuru ta zubama card ɗin idanu,Wanda ba wani abu da ke jikinsa daga sunan mallakinsa sai phone number,a Zuciyar ta sai faman mai-maita sunan ta ke Doctor Hibba Ibrahim Neurological Doctor,"Ki kirata mana wata ƙila a dace", Uncle R ya ce da ita sautin maganar da ya yi mata ta sa ta dawo daga dogon tunanin da ta tafi,jikinta har yana rawa ta sanya number gami da fara dialing ɗin ta, har kiran ya gama shiga ba ai picking ba,hankali tashe ta sake dialing ɗin number a karo na biyu,sai dai abinda ya faru da farko shi ya sake faru,amma duk da hakan Jadeeda ba ta sare ba haka ta cigaba da trying ɗin number kira bayan kira. A firgice Hibba ta farka bakin ta ɗauke da salati gami da rarumo wayarta ta duba domin ganin ƙarfe nawa,ganin time ɗin da tayi ne ya sa ta saki wayar cike da tashin hankali ta nufi bed ɗin da Abubakar ke kwance cikin mawuyacin hali,wanda hakan ya hana lura da tararin miscall ɗin da aka tara mata,nannauyan barci ne ya kwashe ta tun bayan sallame sallahar Isha'i wanda hakan ne yasa bata samu damar sanya mashi Drif ɗin da ta ke sama da ba,lokaci bayan lokaci,baƙaramin tashi hankali gani da firgice ta shiga ba , wannan dalilin ne ya sa duk iya kiran da Jadeeda ta yi mata ba ta kula da shi ba.da ƙyar ta samu ta iya control ɗin halin da ta ke a ciki bayan wani dogon lokaci. "My Angel wannan matar ƴar wulaƙanci ce ji bi duk tarin kiran da ki ke mata ta ƙi ɗagawa",....."Uncle Miey mana ka yi mata kyakkyawan zato mana ka sa ni ko ta na da wani uzurin da ya ke gabanta da har ya hana tai picking ɗin kiran","Oh sorry haka ne wannan tunanin bai zomin a rai ba",da haka su ka sake komawa can Hospital ɗin ba tare da sun yi nasara ba,dole sai haƙuri su kai ba tare da sun sami wani taimakon daga wani ɓangare ba,da ga ƙarshe da suka ga halin da ta ke aciki ya tsananta dole su kasa aka yi mata allurar barci. Sai da gari ya waye Doctor Nass ya shigo Hospital sannan ya samu da taimakon Doctor Jaheed daya sanar da shi abinda yake faruwa ta waya ya sanarda shi duk abinda ya kamata ya yi,sannan fa aka samu ta fita daga cikin halin da ta ke a ciki. *Jadeeda* https://whatsapp.com/channel/0029VapqU8C002T5Bz8RSQ0a *YOTA* Page 28 "Mama bari in je Part ɗin Zeenat ɗin in ji haukan da ya sa ta aikata wannan ɗayan aikin sai kace wacce bata da hankali ko kuma wacce wani ke sarrafa tunani da hankalinta"cewar Safina..."A'a ban aike ki ba,barta da halinta, Allah kaɗai ya san iya ina maganar za ta kai da zaran kin furta wata kalma,yanzu uwarta da kakarta sai su maida laifi akai na don haka ta je ta aikata duk abinda ta so","Kai Mama dan Allah ki bar ni in je",.....ta katse ta tare da cewa,"Na ce a'a abinda ya fi ki taimaka ma shi Mamudan ya duba ƙafar ƴar mutane inda yiwuwar sai an dangana da Asibiti a tafi kafin abun yai tsamari". "Yayah Allah da kin bar ta ita Safinan domin ita ce dai-dai da ita,in banda hauka irin na ta taya zata zuba ƴar mutane ruwan zafi saboda tsabar rashin sanin ya kamata irin nata","Ni dai ban sa ku ba,ba na son ace daga zuwa dubiya mun haifar da wani sabon tashin hankalin,duk da Safina ta ke ƙwarta kuma ƴar'uwarta ai bai kamata ta tunkareta da irin wannan maganar ba,ku barta da Mijinta hukuncin da zai yanke mata ma kaɗai ya ishe ta "Ni dai Momy ba sai mun je wani Hospital ba,ban wani ƙone da yawa ba,kin gani ma zan iya taka ƙafar", Gimbiya Ayush ta faɗa ta na mai yunƙurin taka ƙafar,duk dan kar su je Hospital ɗin,babban abinda ta ke tsoro bai wuce gudun kar garin neman magani a gano asalin fitar cikin ta ba ,kar a samu matsalar bayyanar ƙaryar da take lulluɓe ta da fatar gaskiya,"A'a ɗiyata ki yi haƙuri mu tafi Asibitinnan ba zai yiwu a bar ki cikin irin wannan halin ba",Umma Jamila ta ce tana mai son lallashinta da son ta bari su tafi ta daɗin rai. "Umma Jamila ba na son a ɗaga maganar ne,ba na son iyayena su san da faruwar lamarin,idan har su ka ji abun har ya kai mu ga zuwa Hospital za su iya yunƙurin ɗaukar wani mataki ni kuma ba zan so haka ta faru ". "Eh to kuma fa haka ne ƴarnan amma kin sa ba ta yanda za ai ace iyayen ki ba za su samu labarin abinda ya faru ba ko","Na san da haka amma ba za su yi tunanin abin ya na da girma ba har haka, matuƙar ba mu kai ga zuwa Asibitin ba",ta kai zancen tana addu'a Allah ya sa haƙanta ya cimma ruwa. "Uhmmmm tabbas yarinyar nan ki na da gaskiya Allah kaɗai ya san ina maganar nan za ta tsaya in har akace ta yi nisa,don haka yanzu bari in aika can Gida da akwai wani magani da na samo shi da na je can ƙauye,shima maganin ƙuna ne,sai a gwada shi mu gani ko za a dace","Anya wannan shawara mai ɓullewa ce kawai ki bari a kai yarinyar mutane Asibiti kamar zai fi",Mama Hadiza ta e,"A'a Yayah ,ki bar lamarinan a iya nan in ba haka ba fitinar da baki son ta afku ita ce za ta faru,domin ina mai tabbatar ma ki iyayen Gimbiya Ayush ba za su taɓa iya barin wannan lamarin ya tafi a bazan ba" Shigowar Jaheed bayan ya sauyo kayan da ke jikinsa ta dakatar da su daga zancen da su ke daga ganin shigar da yayi ba acikin natsuwa yayi ta ba,shine ma ya ce da su,"Ya ƙafar da zafi har yanzu ko ?", ya tambaye ta yana mai sauke idanunsa kan ƙafar,da sauri kamar wacce wani ke shirin riga ta ce da shi"Da sauƙi ta bar ma zogin",Bai ce da ita komi ba har sai da ya sanya hannunsa ya juyoda ƙafar yanda zai iya ganinta sosai kafin ya ce,"Gaskiya ban yarda da abinda ki ka ce ba,ga ƙafarnan duk ta fara ja",rau- rau ta yi da idanunta kafin ta ce,"Allah da gaske na ke maka,babu wani ciwo da na ke ji,na ma warke"...."Oh har ma kin warke kenan,kodayake laifina ne ma da na tsaya jin ra'ayin ki akan haka bayan nasan baki son duk wani dalili da zai kai ki zuwa hospital,dan haka ki shirya tafiya ba fashi",ya na kai zancen ya maida hankalin shi wajen su Mama Hadiza tare da cewa,"Yauwa na ce Mama ko za ku zauna muje mu dawo,domin in a ka ga mun tafi gabaɗayanmu za su iya tunanin ko wani abun mai girma ne ya faru"......"Dakata Mamuda a bar zuwa Asibitin nan tunda na ga ka ɗan yi mata irin wannan ƴan shafe- shafen na ku ,kuma a gida inada wani magani kasidin ne,in dai magana ake ta ƙunar wuta da zaran an shafa shi Shikenan". "Kai haba Umma Jamila, wannan wanne irin batu ne,ƙonewa fa tai taya kuma za ki kawo batun wani magani da ba asan asali ko ingancin sa ba","Eh fa ina za a san ingancin su bayan duk da irin su aka raine ku,koka manta san da kai ma garin ƙiriniyarka ka zuba ma kanka ruwan zafi,ai na ce da irin wannan maganin mu ka samo kan ka,don haka ba inda zamu yanzu ma zan kira waya imsa a kawo min shi,in shafa mata",...."Amma Umma Jamila hakan kamar bai dace ba,idan wani abun ya faru da ita kuma fa da ga baya?","Ka ga je ka ba abinda za faru,Ni inan ma har sai zuwa an jima mun ga halin da take a ciki,idan naga da wata matsala zan neme ka da gaugawa",ta kai zancen tana mai gyara zama. "Ka ga je ka abun ka in sha Allah ba abinda zai faru,je ka kayi wanka ka shirya kafito ina son gani ka",Mama Hadiza ta ce da shi,ba dan ya so ba. Sai bayan da Mama Hadiza ta tabbata Jaheed ya tafi sannan ta maida kallon kan Umma Jamila ta ce mata,"Yanzu aikata hakan ki ke ganin ya dace?","To ya zamu yi in har ba so ki ke lamarin ya fi haka ba". "To Allah ya kyauta In ya dawo ki ce ma shi,Ni na tafi amma ya same ni a Gida",ta kai zancen ta na mai miƙewa tsaye kafin ta ɗora da cewa ke Bibah,Safina ku ta so mu tafi Gida ,ke kuma A'isha ga kayan dubiyar da mu ka zo Maki da su in kin ji ƴar dama sai ki ɗan ci wani abun, Allah ya ƙaro sauƙiya kuma mai da na aike ya kauda fitina a cikin zamantakewar ku",tana kaiwa nan ta tasa su Safina da har cikin ranta ta ke jin babu daɗi da ba abarta ta juye ma Zeenat ta cikin ta ba. Tun shigarsa Part ɗin sa bai sake fitowa ba har sai da azahar ta gabato,yai wankan shi fes sanye da kaftani sai hularsa ƙube da ya kawo ya sanya,sassayen ƙamshi ne kawai ke tashi daga jikinsa,cikin natsuwa da haiba yake tafiya,ba tare da ya bi takan kowa ba ya nufi Central Mosque inda yake limanci a ciki,bai wani ɓata lokaci ba ya dawo bayan ya idar da Sallar,kai tsaye apartment ɗin Gimbiya Ayush ya nufa don ko kallon Part ɗin Zeenat baya son yi domin har wani zafinta yake jin ya na taso masa in ya tuna da abinda ta aikata,gab da zai shiga Part ɗin ya ga Nurain ya fito a kiɗime sai faman tsalle-tsalle ya ke gami da sakin ihu iyakar ƙarfinsa,sai faman soshe-soshen jikin sa ya ke tamkar wanda akayi ma wanka da wuta,da alama dai zane shi ta yi, da hanzarin sa ya nufesa gami da kama shi ya riƙe kam ,sai da ya tabbatar da ya dawo cikin hayyacinsa kafin ya tambaye shi me ya same shi,cikin sheshshekar kuka ya ce da shi,"Ba Ummu ba ce ba ta yi min duka don na je na ce mata taba ni abinci in ci yunwa na ke ji,shine ta ce na cika hayyata ta zane ni ta koroni waje",sai da Jaheed ya runtse idanunsa gami da haɗiye wani abu mai ɗaci da ya zo ya tsaya ma sa kafin ya ce,"Ya isa haka ka ji Yarona ai dai ka yi break ko ?",sai da yaron ya fara girgiza masa kai kafin ya ce,"Ni ban ci komi ba ruwan Shayi kawai ta bani,da na ce mata ina jin yunwa sai ta koro ni,yanzu kuma da na je sai ta koro ni waje ,ta ce in je wajen ubana ya bani abinci in ci. Jaheed rasa me kuma zai ce yayi duka-duka Nurain nawa ya ke Yaro ne da bai wuce 8yrs ba amma shi Zeenat ke ma irin wannan izayar,ko kayan jikinsa tun wanda ya sa mishi jiya da daddare ne ɗaukar shi yai ya je saitin door ɗin yana bugawa da ƙarfin tsiya,daga can ake tambayar waye,ko kusa kasa buɗe baki yai balle harta samu damar da za ta san amsar waye ke knocking ɗin jin yadda ya cigaba da buga ƙofar ne ya sa ta fahimci waye a tsaye,zuciyarta kasuwa gida biyu tai wani ɓangaren na cewa ta buɗe masa ko kuwa ta kyale shi,wanda hakan ba ƙaramin ƙara tunzura shi tai ba,ganin da gaske ba zai daina knocking ɗin ba ya sa tai shahadar ƙuda ta buɗe ma sa da shirin tarbar duk abinda ya zo da shi,walau na arziƙi ko na tsiya. Wani abun mamaki ko ta kan ta bai bi ba sai kewaye ta da ya yi ya shigo,kai tsaye kitchen ya nufa saɓe da Nurain akan kafaɗar shi ,sai da yai danasanin shigar shi kitchen ɗin domin komi na cikin kitchen ɗin a ƙazance ya ke kuma a wulaƙance ,da ƙyar ya samu ganin wata ƙaramar tukunya ya ɗora takan elactric cikin sauri da azama ya ke komi ko ya samu ya dafa masa ko da Noodels ko kuma ya dama masa Custard ya bar cikin wannan azabbar ƙazantar,domin wasu plates ɗin har sun gaji sun bushe wasu kuma an tsuma ruwa a cikin su. Kamar wacce a ka wurgo haka ta faɗo cikin kitchen ɗin idanuwanta cike da masifa,ko ɗagowa bai yi ba balle ta samu arziƙin ya tanka mata. "Na daɗe ban ji ko ganin wani mutum mai tauye haƙƙin matarsa gami da nuna fifiko akan ɗaya kamar kai ba,wai me nai maka ne,da na can-canci irin abinda ka ke aikata min haka",ko motsin kirki bai yi ba,sai ma cigaba da harhaɗa abinda zai amfani da shi ya ke,"Magana fa na ke maka",ta ce da shi, tana kai zancen ta na mai kwace Cup ɗin da ya ɗauko, ganin da gaske ba zai kulata bayansa ta sauke Pot ɗin dake kan Elactric ɗin tare da cigaba da cewa,"Ga shinan kaima ka watsa min ruwan zafin in hakan zai sa hankalin ka ya kwanta,idan ma hakan bai maka ba,ga wuƙa ka caccaka min in mutu kowa ma ya huta da ga kai har ni ɗin ,na rasa gane wannan tsananin ƙiyayyar da ka ke nuna min ba",yanayin yanda ta ke behaving tamkar sabuwar mahaukaciya shine abinda ya sa ya tsaya yana mai binta da kallo,cike da tunani ko ta zauce ne. "Zeenat ki fita a idona,ki sani ina dan ne zuciyata ne akan duk abinda ki ke aikatawa,bana son ki sani in yanke maki hukuncin da za ki yi dana sani da shi,ki shiga cikin taitayin ki da kan ki,a koda yaushe ina maki fatan shirya a gurin Allah","Na sani ai dama komi ya faru ni ke da laifi,ba za ka taɓa duba da rashin adalcin da ka nuna min ba,kai fa ka ɗauki kwana na ka kai ɗakinta sannan ka dawo da safe, mamadin ka fara isowa sashe na amma sai ka sake nufar na ta ɗakin a karo na biyu, wannan shi ne kake kira da naka salon adalcin ehye ?", "Tunanin ki shine matsalar ki,baƙin kishin ki shine ke jagorantar ki ga aikata duk wani shirmen da ki ke aikatawa,ban taɓa ji ko labarin Mata ko Uwa irin ki ba,idan har ki ka cigaba da tafiya a haka,ina mai tabbatar ma ki da ba wanda zai alfahari da ke cikin makusantan ki,kalli fa wannan yaron ki ne har kawo iyanzu baki bashi kalacin safe ba,bai ci komi ba,a haka kike kiran kan ki a matsayin Uwa,kalli tarkacen ƙazantar da ki ka tara,kwanuka sai ƙudaje ke bi,a cikin ɗakin ki babu wani abu daga warin kayan dauɗa sai tarin datti da ƙazanta,kalli shigar dake ke jikin ki komi na jikin daban ya ke,a haka ki ke kiran kan ki da Matar Aure,abun akwai rikitarwa a ciki,a yanzu da zan tambaye ki a cikin kalma ɗaya ki faɗa min ko ke wacce ya za ki iya ?,ki sani wannan halayyar ta ki kan kashe ni da mamaki,wani lokacin na kan shiga firgici da tunanin wai wa na kawo gidana da sunan Matar Aure,ki sani duk da ina jin ba daɗi amma ki sani kan ki ki ke cuta ba ni ba,domin inada wata mafakar bayan ke, wannan bala'i har ina, Wallahi Allah ya sani na gaji ko dai ki gyara ko kuma in runtse idanuna in kauda duk wata alaƙa in ɗau tsatstaauran mataki akan ki na gaji wannan musiba har ina",ya kai zancen yana mai sa hannu ya ture ta ya sunkuci Nurain ya nufi Room ɗin ta don nemo masa kayan da zai sauya masu da na jikinsa so,sai dai me duk kayan da ya ɗauko sai yai dana sanin duniyan akan siyan su ma da yayi gabaɗaya,yawancin kayan,duk masu dauɗa ne, sai waɗanda akai ma jiƙa-jiƙa ba tare da sun fita ba aka shanya su,ba ruwan ta da la'akari da tsadar kaya ko wanne iri ne in aka sa su sai sun fita daga cikin hayyacinsu,duk abinda yake faruwa ta na biye da shi ,ta na mai faɗin duk abinda ya zo mata a baki,amma ko kusa bai kula ta ba,kalmar da ya faɗa ce ta sa yai tsam gami da zuba mata idanu,"Wallahi kai ba adali ba ne ba,ba ka can- canci jagorantar al'umma ba saboda ka fiye son kan ka da yawa,kuma idan ka ga ka bar wajennan ka faɗa min mene ma'anar duk kalaman da ka faɗa a kitchen a kaina,sai ka faɗa min wanne irin mataki ne ka ke son yankewar a kaina","Ki gode Allah ni ban kasance cikin jerin Mazaje masu bugun Matan su ba,ko ɗazu ma kin aikata abinda ya kamata in nusar da ke kuskurensa ne tunda wuri",shine iya abinda ya iya cewa da ita,"Ai na sani dama Zaka iya aikata fiye da haka in har za a taɓa matar so ,ka sani daga yau babu sauran ragowa tsakani na da ita ,kai ba ma ita ba har da kai ɗin ma muzuba mu gani ɗan halakka ka fasaa".Wani murmushin yaƙe kawai ya sakar mata ya nufi hanya fita ,waje ba tare da ya sake bi ta kanta ba. "Innalillahi wa'ina ilaihir raju'una,na shiga uku tayi nasara akai na,yau Yah Jaheed ne ke irin wannan ikirarin akaina Shikenan ta yi nasara a kaina ta raba Ni da mijina hankalinta ya kwanta,ta lalata soyayyar da aka gina ta tun ƙuruciya,wallahi bazan bar ki ba Gimbiya Ayush,sai dai mu bar Gidannan a tare da ke,domin ba ki isa ki fitar da ni daga cikin Gidan da aka gina shi da suna na ba",takai zancen ta na mai durƙushewa ƙasa gami da sakin kuka da iya ƙarfinta. Kai tsaye Part ɗin shi ya tafi da shi yai mashi wanka ya sake masa kaya kafin ya nufi Part ɗin Gimbiya Ayush ya ga halin da ta ke a ciki , Allah ya taimake shi ƙunar ba ta tashi ba,Umma Jamila tuni ta yi tafiyar ta Gida abinta,sannan ya tafi da Nurain can main house ɗinsu Part 29 Zazzau ne su ke a cikin Parlon ,kowa cikin su fuskarsa a sake ɗauke da haiba da kuma natsuwa,Alaranma Sama'ila,Kawu Salihi,Kawu Musa, Kawu Kabiru dama,Baba ƙarami da sauransu dai, duk nan suke zama idan ya kasance babu karatun da za a gudanar tsakanin sallahr Magriba da kuma Isha'i,"Ya maganar tafiyar ta ka ina fatan ka shirya ma ta ,domin na ga tafiyar kamar ta ƙara so", cewar Baba ƙarami. "Eh Abba na shirya da so nai ma in yi zamana a can Abujan har zuwa lokacin da za ai taron sai kuma na samu saƙon sun maida taron Lagos shiyasa na dawo in ɗanyi ƴan shirye-shiryen da zan yi kafin in wuce","Ya Salam kace tafiyar ta ƙara yin nisa kenan?", Alaranma Sama'ila ya tambaya,"Eh wallahi Kawu haka tafiyar ta koma duk sun canja wasu abubuwan". Kawu Salihi ne ya tambaye su da cewa "A'aha tafiya ce ta kama shi ne zuwa wani wajen"."Eh tafiya ce ta kama shi na manta lokacin da mu ka yanke hukuncin wakilta shi a tafiyar baka nan,amma kamar ai nasa a kira ka ayi maka bayani ko,kan taron Manyan Malamai domin samun haɗin kan mazhabobi da za a gudanar a Abuja to ka ji ashe an maida shi Lagos","Af Af na tuna munyi maganar da kai kuma bayan haka na samu labarin gurin wani Abokin kasuwanci na a can Jigawa","Yauwa to tafiyar ce ta taso,ina tunanin saura kwana biyu ma tafiyar".Nan dai suka cigaba da tsara yanda za su yi tafiyar da kuma ƙarin shawarwarin da zai amfana da su, shigowar Baba Malam tare da Alƙasim nan su ka sake dawowa da zancen farko,daga ƙarshe kuma suka koma tattaunawa akan lamurran cikin Gida da na kasuwancin su. Sai bayan da suka gabatar da da Sallahr Isha'i sannan ya fara shirin tafiya Gidan shi,ya shiga cikin Gidan domin yi ma su Sallama,Momy Hibba ta ce da shi,"Ina Mai Gidan nawa ya ke na ga ka fito ba tare da shi ba,ko nan zai mana kwana",sai ya ɗan haɗe ransa kafin ya ce,"Momy yana wajen Ummiey,kuma ina ga ya dawo nan da zama sai ko zuwa wani lokaci ko da zai koma",itama ba ta kuma ce masa komi ba sai sauke ajiyar Zuciya da ta yi ,kafin kuma ta fara cewa da shi,"Ka yi haƙuri yana daga cikin jarabtar ka, bawa kuma baya tsallakewa ƙaddarar sa,zamu yi maganar ni da Ummiey Maryam kome kenan zan sanar da kai mai yiwuwa za a iya samun maslahar wannan lamarin","To Momy ina godiya,bari in zo in tafi dare na ƙara yi dama zuwa na yi in maki Sallama,Kuma ina son in iske Ummiey kafin tai barci","Okay to Shikenan Allah ya tsare a gaida mutanen Gidan mu ma zuwa goben za mu shigo mu ga mai jikin",da haka yai mata sallama ya nufi wajen Mahaifiyarsa . ~~~~~~~~~~~ "Momy Allah ba na son tafiyar nan jikin ki har yanzu bai koma normal ba,ina tsoran kar wani abu ya same ki bayan ba na nan",sai da Gloria ta tashi zaune da ga kwance da ta ke kafin ta ce,"My Daughter bai kamata ki yi loosing this opportunity ɗin ba,ba kowa ke samun ta ba taron nan yana da matuƙar muhimmanci a gare kin ga ba kowa ke samun wannan babbar damar ba,don haka za ki je wannan taron i promise to you babu abinda zai faru da ni har ki je ko dawo for the sake of father lord". Rau-rau Jadeeda ta yi da idanunta hawaye na son zubowa daga ciki "Kin ga matso kusa da ni,Papa ɗin ku kan shi ba zai ji daɗi ba in ya ji cewar kin fasa attaiding ɗin wannan taron,manyan mutane ne fa suka gaiyace ki,kuma ta hanyarsa ,to me zai sa ki watsa masa ƙasa a ido",haka dai ta cigaba da lallashinta har ta samu ta amince da za ta yi tafiyar,"Wai ina Edwin tun safe da ya shigo ya gaishe ni ban sake jin motsin shi ba ?",Min ta tambaya,"Ba ya wuce Room ɗin shi domin na ga motar shi babu inda ya je","Yana ɗaki kwance?,me yake damun shi wannan ba ɗabi'ar shi ba ce,to ko dai ba shi da lafiya ne ?","Momy ni dai ban sani ba amma Ni kaina na yi noticing sauye-sauye daga Brox Edwin,ya keɓe kan shi,bai cika shiga cikin mu kamar yanda ya saba,ba tsokana ko barkwancin da ya saba jan mu da shi,shi kaɗai kawai ya ke rayuwarsa,ko abinci ba ya ci tare da mu,a Room ɗin sa ya ke komi shi kaɗai". Shiru Madam Gloria ta yi,kafin daga bisani ta ce da ita,"Je ki ki gani in ya na cikin ɗakinsa and call him for me",ba tare da Jadeeda ta ce komi ba ta nufi Room ɗin Edwin,tun kafin ta ƙarasa shiga ta fara jiyo hayaniya daga cikin dakin ana cewa,"Guy kar ka bari wannan maganar ta zama dalilin da zaka sanya rayuwar ka a cikin haɗari say it out,ka fito fili ka sanar da abinda ke damun ka,ka na aikata kuskure ne fa,zurfin cikinnan ba abinda zai haifar maka da shi inda ka sake jefa rayuwar ka cikin wani sabon haɗari"....."Joseph baka da hankali irin wannan maganar ka ke ikirarin in fitar da ita,You Are Mad Ina tunanin ka samu matsala". "Kai ne dai ka ke da matsala amma ba ni ba,kuma za kaga ne hakan nan gaba,ni ba zan iya cigaba da kallon kana cutuwa ba,in har ba za ka fito fili ka sanar da ahalin ka abinda ke damun ka ba ,ni zan sanar da su",a firgice ya ɗago yana kallon sa fuskar shi cike da mamakin abinda kunnuwan shi su ka jiye masa,sai da Edwin ya kwantar da zuciyarsa kafin ya ce da shi,"Ka ga Jesoph ka fahimci ni ,komi na rayuwa family first bai kamata saboda wani buri nawa in sa family na cikin damuwa da tashin hankali ba,zan bi komi a hankali,okay dan haka bar min komi a hannuna". Kasa haƙuri Jadeeda ta yi sai ganin ta su kai a tsakiyar su,a ɗimauce Edwin ya miƙe tsaye,ya na mai nufo inda ta ke gami da kama kafaɗunta tare da cewa,"Jadeeda yaushe ki ka zo,a dai ki daɗe da zuwa ba ko,ina fatan baki ji komi gane da abinda muke tattaunawa ba ?",sai da ta zuba mashi idanunta kafin tace,"Ni ban ji komi ba,kuma yanzu na zo,Momy ce ta aiko ni ta ce ka zo tana san ganni ka","Na ji ganinan zuwa amma kafinnan ki tabbatar min da cewar ba ki ji komi dangane da hirar da muke tattaunawa ni da Abokina ba",saɓule hannun shi daga kafaɗar ta tayi kafin taba shi amsa a taiƙaice da cewa,"Ni banji komi ba",tana kaiwa nan ta bar mi shi Room ɗin gabaɗaya,kasa iya zama yai sai bin bayanta da yai cikin sauri da azama. A tare su ka isa inda Madam Gloria ta ke zaune,suna shiga suka iske Papa da Uncle Richal sun dawo daga sabon shopping Mal da aka buɗe ma Uncle Richal domin san hana shi komawa ƙasar da ya baro. "Lafiya ku ka shigo kamar an biyo ku",Papa ya tambaya yana mai bin su da kallo. Cikin rawar baki Edwin ya tari numfashi sa da cewa,"Papa ba komi Momy ce ta aike ta ta kirani"ya bada amsa a ɗarare. ,"Zo nan Edwin matso ka zauna kusa da ni",jikinsa a sanyaye ya isa kusa da ita ya zauna,da ganinsa kasan ba a dai-dai ya ke ba. "Edwin my son me yake damun ka ,da ganin ka akwai wani abu da ka ke ɓoyewa a cikin zuciyar ka",Madam Gloria ta tambaye shi,inda-inda ya fara kafin ya samu ya natsar da kan shi ya bata amsa,da cewa,"Momy ni ba abinda yake damina,ina tunanin gajiyar tafiya ce","Gajiyar tafiya kuma tun yaushe ka dawo almost a week,har yanzu ba ka huce gajiyar tafiyar ba?,a komi fa ka ware kan ka,ko saukowa ka kaci abinci da Familyn ɗin ka ba ka yi hakan duk gajiya ne",Momy ta sake jefa masa wata tambayar. "Momy i swear gaskiya na faɗa ma ki,yanzu haka ina tare da friend ɗina ne Joseph"....."Momy Allah da abinda ke damun shi,kawai dai ba zai faɗa ba ne ba,ni na riga da na san da haka tun kafin ya dawo ". Papa ne ya maida hankalin shi akan sa tare da cewa,"Fill free my dear son nan duka Familyn kane ka faɗi duk abinda ke damun ka we will sort it together,ba wai kai kaɗai abun ya shafa ba ,duka damuwar mu ne",duk wannan bayanin da Papa yake Edwin baya tare da shi,gabaɗaya hankalin shi,idanun shi da kuma tunaninsa nakan Jadeeda,zuciyarsa na gaya masa tabbacin ta saurari tattaunawarsa da friend ɗin sa. "Edwin kana ji na kuwa",Papa ya faɗa da ɗan ɗaga murya,hakan ne ya yai gigita shi tare da cewa,"Eh Papa zuwa anjima ma zan amso sauƙon",cikin mamaki Papa yace,"Saƙo kuma wa yai maganar saƙo anan?". Har Momy ta buɗe baki za ta ce wani abu Uncle Richal ya dakatar da ita tare da maida hankalin shi kan Edwin yace dashi,''Ka ga tashi ka tafi je ka wajen Friend ɗin naka ba damuwa",....Momyh tari numfashin shi da cewa,"Amma Richal taya za sallame shi alhalin ana irin wannan maganar mai girma da kuma muhimmanci","Sister bai kamata ku turken shi anan kusa lalle dole sai ya faɗa maku damuwarsa ba,mai yiwuwa lamarin bai kai yanda ku ke tunani ba,may be yana jin zai iya dai-daita komi, Edwin fa ba yaro ba ne ya mallaki hankalin sa bai kamata irin haka nashiga tsakanin ku ba,idan lamarin ya kai lamari bani tantama zai sanar da ku",da wannan bayanin Edwin ya samu ya sulale daga cikin su. "Richal ba ka fahince ni ba, dole sabon halin Edwin ya taɓa kowa a cikin Gidannan,kalli fa raha da wasannin da yake duk ba ya yin su kullum jikin sa a sanyaye,haba abun da rikitarwa gami da tsayawa a cikin zuciya da rai","Na sani Sister amma ba ta irin wannan hanyar ya kamata mu bi domin gano damuwarsa ba,hakan ka iya creating wata sabuwar matsalar",shiru su duka su ka yi kafin Papa ya ce,",Kuma fa maganar ka gaskiya ce,to amma yanzu ta wacce hanya zamu yi amfani da ita domin mu gano asalin abinda ya ke faruwa da shi","A bibiyi lamarin shi,ku sake ƙara janyo shi a jikin ku,inda halima a daina barin sa shi kaɗai". Nan dai su ka amince da shawarar da Uncle Richal ya kawo, sannan su ka cigaba da kawo wa su hanyoyin daza su yi amfani da su duk dan su ga sun kai ga gaci akan abinda su ka sa gaba,hatta da maganar tafiyar Jadeeda zuwa Lagos sai da suka yi daga ƙarshe Uncle Richal da kan shi ya ɗauki Jadeeda su ka nufi sabon shopping Mal ɗin sa ya zaɓa mata duk abinda ya tare masa gaba,hatta da kayan da za ta sa in ta isa Lagos shi ya zaɓar mata,komi ya gani in har ya ga zai mata kyau to sai ya ɗaukar mata wasu kayan ma set guda yake samata, choculate ba'a magana,haka su ka dawo da kaya niƙi-niƙi. *Jadeeda* *YOTA* Part 30 "Asiya wai ke ce tunda wannan uwar safiyar",Ummu Nurain ta ce tana mai buɗe mata door ɗin shigowar,"Kai Aunty yanzu ne safiyar yanzu da wajen goma da wani abu","Ke haba har goma ta yi,Ni ban ma san garin har rana ta fito haka ba",",Ai ko dai rana ta yi yanzu haka ma Mamanmu ce ta ce inzo in jiye mata kanun zancen da ake ta yawo da shi a cikin Gida",tsaki Ummu Nurain ta saki kafin ta juyo su ka shigo a tare, Ummu Nurain hamma ta saki gami da yin miƙa tare da cewa "Waɗanne maganganu ne ke ta faman yawo a cikin Gidan?",Ya mutsa fuska Asiya ta yi tare da cewa,"Wai cewa su kai saboda tsabar baƙin kishin ki kin ƙona ƴar Sarki da ruwan zafi". "Munafukan banza a haka za su ƙare ba wani a cikin su da yasan gaskiyar abinda ya faru sai yaɗa gutsiri tsoma","Kenan da gaske kin ƙona ta kamar yanda ake faɗa ?","Mtssssss na ƙona ta mana amma wallahi ba intentionally na ƙona ta ba,kawai tsautsayi ne,kin san ni bana shiga harkarta na je kare martabar Aurena gami da kwatar haƙƙina takawomin wargi nqi kuma na hankaɗar da ita cikin tsautsayi ta ɗora ruwan zafi ya sheƙo mata a ƙafarta". Wata irin dariya Asiya ta kwashe da ita,har ta na tafa hannayenta tare da cewa,"Maganinta kenan uwar kinibibi da iyayi,ai yanzu sai muga da ƙafar da za a nunama mutane isa da gadara,ai ni na so ace ruwan zafin da ya tashi ya saɓule har fatarta muga ta tsiya". "Ba zaki gane ba Asiya amma ina zaman baƙin ciki da takaici a cikin Gidannan kuma duk a saboda wannan munafukar,kan wannan lamarin har marina Yah Jaheed yai wanda irin haka bata taɓa shiga tsakanin mu ba",maganar ba ƙaramin kaɗuwa ta jefa ma Asiya ba,"Mari fa Aunty Zeenat akan wancan shashashar matar tasa ?, wallahi in ni ce da ba iya nan abun zai tsaya ba". "Hmmmmm ai ba ayi komi ba Asiya ,barshi ba dai yau zai dawo nan Part ɗin ba na rantse sai na tada ma shi hankali fiye da yanda ya ke zato da tsammani,kuma ko ɗaya a yanzu bana danasanin ƙonewar da ta yi ko ba komi na zaunar da ita guri ɗaya kuma daga yanzu za ta san ruwa ba tsarar gwando ba ne ba ". "Hehehe ana yi muna jin daɗi,ai babu nadama don kin illata ko raunana kishiyar ki,a ai ba a jira,ba a sanya ki sani in itace ta samu wannan damar ba jira ba sanya za ta aikata miki fiye da haka,gobe ma in ta ƙara kawo maki wargi kome ke kusa dake ki ɗauka ki buga mata a ka in ya so kome ye ya biyo baya",dariya Ummu Nurain ta saki gami dakai mata duka tare da cewa,"Shegiya Asiya ƴar ƙarama dake amma kin iya tuggu,ke wannan in aka yi maki kishiya ai tabani ta lalace"......"a'a a'a bar yi min mugun baki,Ni ko zuwa nai na iske na ci alwashi sai na fidda ta balle kuma a zo a iske ni,Aunty ni fa kwata-kwata na tsani kishi ,Ni fa zan iya aikata abinda za a ƙulle kaf ahalin mu indai akan kishiya ne","A'a Ni kin fi ƙarfina bar ni dai zan aikata abinda shi kan shi mijin ba zai tsira ba,ba shi ba kwanciyar hankali da natsuwa,yanda zan yi rayuwa cikin baƙin ciki haka shima zai rayu cikin rashin kwanciyar hankali". "Ai ko in ki kai haka kin kyauta yauwa wai Nurain da sanin ki aka maida shi,can Gidan na ji ma ance ya koma kenan wai da yiwuwar ma an bar ma Momy Hibba shi",a kiɗime Ummu Nurain ta wai go tare da cewa,"Me ne an bada kyautar ɗana ba tare da na sani ba,duk ikon da ake nuna min a cikin Gidana bai isa ba har sai an raba ni da ɗana da na haifa da cikina,ba fa tsinto shi nai ba ni na haife shi da cikina","To aiko haka muka samu wannan labarin don da Mama da kanta zata zo ta ji ba'asi sai Baba Asabe ta hana ta ce abun magana zai zama gara ni in zo in ji gaskiyar zance ba sai ta zo ba","Wallahi ba zan iya cigaba da irin wannan rayuwar ba na rasa wa yake Aurena cikin Mahaifiyar Uncle Jaheed da kuma Momy Hibba,umarni da hukuncin su ne kawai ke gudana a cikin wannan Gidan ba zan iya ba dole in ma abun tufkar hanci tunkafin a wayi gari in rasa tudun dadafawa a cikin rayuwata". "Da kin kyauta inji kin aikata abinda zai haukata mutanen cikin babban gida, in ki kai haka ba Mama ba hatta da Baba Asabe sai ta ƙara yin alfahari da ke,mudun ki ka aikata abinda ki ka ce","Tabbas ki shaida ma su haka zata faru,zan fara daga waccan sakarar mai ƙaryar Sarauta,sai na nuna mata ita ba bakin komi ta ke ba,daganan in samu hanyar da zan yi waje da ita,babban fata na a yanzu in rabu da wannan cikin da ke jikina duk shine ke hana ni aikata duk abinda ya tare min gaba". "Sai dake ƴar ƙunar baƙin wake ban ce ki raga ma kowa ba,kar ki manta ko ke wace ce ƴa gurin Mama Zaliha kuma jika gurin Baba Asabe,tijara ba sai an koya maki ba,kin gada kuma kin iya,bari in tashi in tafi da wannan". "A'a Asiya ki tsaya ko ruwan shayi ne in haɗa maki bai kamata ki tafi ba ki ci komi a gidana ba","Wa ni a'a na ƙoshi kin san Mama bata wasa indai maganar girki ne,sai da na cika cikina kafin in fito","To Shikenan ba damuwa mu je in raka ki",wani daddauɗan zanin na ta ta ɗauka ta yafa a madadin mayafi suka nufi harabar Gidan,suna tafe Asiya na ƙara famfata,gami da sake tunzurata,wani irin daskarewa wuri guda Ummu Nurain ta yi sakamakon abinda ta gani,tafe su ke cikin nishaɗi da kwanciyar hankali janye da trolys,sai briefcase dinsa sagale akan shoulder ɗin Gimbiya Ayush,ba Zeenat ba hatta da ita kanta Asiyar ta girgiza,sai da tai ƙarfin zuciya kafin ta iya cewa "Kan uba Aunty Zeenat mai na ke shirin gani haka,na ga kamar unguwa za su tare",kasa iya cewa komi Zeenat ta yi sai,zuciyarta ke ta faman bugawa da sauri ta ke,gudun jininta ya ruɓanya da wajen kashi uku,ta kasa iya hassala komi, su ko da alama ba abinda ya dame su,Imam Jaheed sai faman murmushi yake akan labarin da Gimbiya Ayush take ba shi,ko nuna alamun sun gansu ba su yi ba, ganin da gaske tafiyar za su yi Ummu Nurain ta nufi inda suke ta sha gaban su,sai faman huci ta ke kamar wacce ta yi dambe,ko nauyin cikin da ke jikin ta ba ta yi ji,cike da masifa da bala'i ta fara magana da cewa,"Me ye ya ke shirin faruwa anan,na ga kun kwaso trolys kamar kuna shirin barin gari a'a kar ka ce min fita za kai tare da ita,idan ma haka neka sani hakan ba mai yiwuwa ba ne". Waige-waige Jaheed ya fara yana son ya tabbatar da shi ta ke ko-ko da wani daban take,"Wai da wa ta ke,wace ce ita ,nan a wurin dai banga wani ƙaramin yaro da zai dai-dai da ɗan ta ko sa'an ɗan ta ba balle in yi tunani shi take bama wannan umarnin",ya kai zancen yana mai zagaye ta ya buɗe but ya shigar da kayan da suka fito da su,"Kar ka nemi ka raina min hankali Yayah ,Ni ɗin ce ba ka gane ba,ko dai ka fara samun matsala a cikin tunanin ka ne,ka samu juyewar ƙwaƙwalwa ne kome ?". Da fushi ya saki murfin but ya fuskance ta da cewa,"A'a ban samu juyewar tunani ko ta hankali ba,kamar yanda ke ki ka samu,kuma da gaske ban san ki ba,domin ni ban Auro mahaukaciya mara tunani kamar ki ba,ban aje ballagaza kuma mara tunanin irin ki ba,da kuma ki ke tambayar ina zamu ko tafiya za mu yi?, Eh tafiya zamu yi domin ba zan bar maki ita ki kashe ko ki naƙasa min ita ba,ita ɗin mata ta ce,ina samun natsuwar hankali da kwanciyar hankali a tare da ita fiye da ke,ki sani a duk randa ki ka shirya zama mace ta gari ki ka koyi ɗaukar nauye-nauyen da su ke a kan ki ,to daga ranar ni kuma zan cigaba da kallon ki a matsayin Mata ta,amma ba a yanzu da ki ke rayuwar da ko dabbobi ba sa irin ta ba". Cikin rawar baki Ummu Nurain ta tari numfashin sa da cewa,",Me waɗannan munanan kalaman na ka su ke nufi,shin kana nufin na zama sakakkiya,to ka sani wallahi ba ka isa ka maida ni bazawara ba, ina so ka sani ba wata mace da ta isa ta zo har cikin Gidana ta ci ni da yaƙi ta fidda ni daga cikin sa,Aurena da kai mutu ka raba,babu wata da ta isa ta shiga tsakanin mu,ba a haife ta ba,daga kai har ita ku rubuta wannan a cikin ran ku,ba zan yafema cutar da ku ke min ba, sannan ke kuma".ta mai da kallonta kan Gimbiya Ayush,"Kar ki yi farin ciki ko murna domin zato da tsammanin da ki ke karen ki ya kama kura to ba kura ya kama ba damisa ya kama,Ni da kaina zan kawo ƙarshen zaman ki a cikin Gidannan",tun kafin ta gama fadar abinda ta ke cewa Jaheed ya shigar da Gimbiya Ayush cikin Mota ya barta sai ɓaɓatu ta ke,ganin da gaske tada Motar zai yi su tafi ya sa ta shiga gaban Motar ta tsaya ta babbake ko ina gami da ɗaga muryar tare da cewa,"Wallahi in ka ga ka fita da Motarnan to ba na raye,sai dai in gawata za ka taka ka bi ka wuce,amma babu inda za ni inanan",kan shi ya leƙo ta wurin glass yana mai cewa da ita"Au haukan na ki har ya kai haka,to ki tsaya zan nuna mi ki naki lissafin gajere ne,in ya so in ki ka je can lahirar sai ki samu wanda za ki nunama wannan kalar hauka da baƙin kishin na ki", gadan-gadan ya taka mota gami da nufo ta, Gimbiya Ayush runtse idanunta tayi gami da kama shi ta cukwuikuye sai faman salati ta ke gami da ba shi haƙuri akan ya daka ta kar ya bi takanta ,in badan wani tsalle da Asiya tai ta janye ta gefe da yanzu ba wannan labarin ake ba,kai tsaye yai ficewar shi ba tare da ya ko waigo ya ga halin da ta ke a ciki ba. "Aunty Zeenat wannsn wanne irin abu ne haka ta ya za ki sa rayuwar ki da ta abinda ke cikin ki cikin hatsari ko ba ki dubi kan ki ba ai kya yi duba da shi ai ","Asiya ki bar ni.....Asiya me yasa ma ki ka janye ni da kan hanyar da kin bari ya bi ta kaina in ya so sai haddin kisa ya hau kan shi, wallahi Jaheed ka cuce ni kuma Allah ya isa ban yafe maka ba,innan ina jiran ka za ka dawo sai ka yi mamakin bala'in da za ka zo ka iske a cikin Gidannan,ke kin ga wuce mu tafi Gida domin ban ga abinda cigaba da zama cikin Gidansa zai amfanin ba",takai zancen tana mai kama hannun Asiya ta fara ja,su ka nufi hanyar barin Gidan,ko ta kan Gate Man dake ta faman ba su haƙuri ba su bi ba. "Wai lafiya duk kun bi kun ishe mu, wannan sai faman kuka ta ke, wannan kuma sai faman cika ta ke ta na batsewa sai ka ce wacce ake yi ma fanfo",cewar Baba Asabe bayan shigowar su wacce ta ke daga zaune. "Hmmmmm Baba Asabe akwai matsala wai yau Yayah Jaheed ne ke shirin bi takan Aunty Zeenat da Motar don kawai ta ce ba ta yarda ya fita da wancan shashashar matar ta sa ba". "Kamar ya ban gane ba,shi Jaheed ɗin ya fara shaye-shaye ne,ko-ko ya ci kan kare ne ?",Cewar Mama,"Wallahi lafiyar shi lau,babu abinda ya same shi,kawai tsabar balaja'un ɗa Namiji ce",nan fa su ka kwashe ƙarya da gaskiya su ka gaya ma su. "Abun Mamaki wai Jaheed ɗin ne ya aikata duk wannan abun anya kuwa",Mama ta faɗa cike da mamaki,"Yo ban da abunki Zaliha ai fiye da haka ma zai aikata jika ne fa wurin Hadiza,wanne irin baƙin hali ne ba zai gada da ga gare ta ba,saboda tsabar munafunci da iya ƙulla makirci sai da ta raba ni da ɗan'uwana ciki ɗaya,ki bar mutum in ya kasance ya na gadon mugun tsatso,sai da ta ga na baro Gidan sannan hankalin ta ya kwanta"....."Kai Baba Asabe wannan da kamar kin yi ihu ne kin daɓama kan ki wuƙa,ko kin manta nan Gidan ma da ki ke zaune Gidan ɗantane ",Cewar Nabila Yayar Asiya. "A'a meye haɗin fura da kashi,don me ki ke ƙoƙarin danganta koko da giya,ai shi kwata-kwata ba irin halin su ya biyo ba shi wannan sak ɗan'uwana ne Malam Ibrahim Mai sai da fata hafizin Malami,hanya natsuwar sa ce ta a na bashi Auren Uwarku gatanan a zaune,kuma ni dalilin ta na ke zaune anan ba dan wani ba,ato dan ki ji, yo ni Allah na tuba in badan haka ba me zai sa in zo in zauna anan ai da daki". "Ta na kasa ta na dabo,ko kin mata shima Abbanmu shima ita ce ta haife shi,ba fa zai ji daɗi in yaji kuna aibata masa uwa ba".....Asiya ta katse ta da cewa, "Ke dalla ki rufa mana baki waya ce aibata ta ake ba halin ta ba ne ba,ai dole a faɗa ni na rasa wacce irin Zuciya ce da ke Nabilah duk irin cin mutuncin ƴar'uwarki da akayi ba ki gani sai ƙoƙarin kare wasu a banza a wofi da ki ke,mutanen da ba su san ma kina yi ba,in kin ji ba za ki iya goya mata baya ta rama abinda aka yi mata ba ki ja baki ki yi wa mutane shiru "..."Ke Asiya ki yi min shiru domin ba dake na ke ba",....."Ke ce dai za ki yi ma mutane shiru sakaryar banza mara zuciya kawai wacce ba ta san ta taya ƴar'uwarta kare martaba,ƙima da mutuncin ta ba", Ummu Nurain ta katse ta cike da tsiwa muryarta dauke da sheshshekar kuka. Sallallami Baba Asabe ta saka gami da ɗorawa da cewa,"Ni na rasa ina wannan talasurar yarinyar ta samo wannan soloɓiyo ɗin wannan zuciya ta ta ba, kwata-kwata ba ki taya ƴan'uwanki jimamin halin da su ke a ciki","Baba banni da ita da kusa da ni ta ke da tuni na kai ma ta duka a baki wata ƙila daganan sai ta gane ta yi kuskure".Kamar ta ce ta na zaune bakin murhu. Miƙewa tsaye tai gami da cewa da su,"Allah ya ba ku haƙuri amma duk da haka ba zan daina faɗa ba ku bi duniya a hankali, Gimbiya Ayush dai matar shi ce,tafiya kuma ya tafi da ita ba yanda za ku yi sai dai ku ɗauki haƙuri da dangana"......tun kafin ta ƙarasa ta zura da gudu ganin yanda Zeenat ta biyo ta,Baba Asabe ce ta riƙota ta na mai cewa,"A'a kyale ta banni da ita Ni da kaina zan yi maganin,ko kin manta halin da ki ke a ciki ne","Baba dan Allah ki bar ni in je in huce haushina akan wannan yariyar, Allah da sai ta yi dana sanin sani na","Na ce ki kyale ta ki bar ni da ita na wallahi wani lokacin in na kalleta ita da Alƙasim sai in yi tunanin ko musayarsu akayi min ba ni na haife su ba". "Dawo zauna ƴarnan ai yanzu ba ita yakamata ki sa a gaba ba zo mu san yanda za mu yi da wannan babban lamarin da ya tunkaro mu".cewar Baba Asabe. "Yauwa Baba Asabe don wallahi har yanzu ina jin maganganunsa suna min yawo a cikin kai,karma maganganun sa da suke nuni da kamar ya sake ni","Haba shi ɗin banza ya isa ya ce ya ya sake ki,ke ko kuskuren sakin ki yai sai dai ki koma zama ɗakin Mahaifiyarsa,Uban shi fa ƙanin Mahaifin ki ne, sannan da kakanshi Namiji da kakar ki ni ki Mace tsatson su guda,kin ga kuwa kusan ta yi kusan da bai isa ya iya sakin ki ba,shi ɗin banza,waye shi". Wata irin dariya suka saki su duka har Asiya na cewa,"Ina yin ki ƴar tsohuwa,hakan ya sa na ke ƙara ji da ke Allah yakaro nisan kwana mu ƙara yin degree a wurin ki,na tabbatar da ke ce za ki yi mana maganinsu",nan fa ta miƙa mata hannu su ka tafa kafin kuma su cigaba da tsara faruwar duk abinda su je so. Page 31 "Ina mai ƙara baki haƙuri akan dukkanin ƙalubalen da ki ke fuskanta ta dalilin Aurena da ki kai ,na kasa baki farin cikin da kowacce mace ke expecting samu a wurin Mijinta,ki yafe ni",sai da Gimbiya Ayush ta nisa kafin ta ce da shi cikin sanyi,"Na tsorata sosai ban taɓa ganin mace irin Ummu Nurain ba,sosai na tsorata,ina jin kamar Shikenan za mu mutu ne tare da ita,na rasa me nai mata,ko dai Auren ka da na yi shine mafi girman kuskuren dana aikata a rayuwata"......ya dakatar da ita da cewa,"A'a kar ki ce haka, sai in ji kamar na gaza a wani fanni mai girma daga cikin rayuwar ki","Ba ina nufin haka ne ba,sai dai ina jin wani iri idan naga kana biye mata sai inga kamar duka laifin ko nauyin faruwar haka ya na kaina",sai da ya kama duka hannayenta ya riƙe kafin ya ƙara tausasa murya da lafazin shi,"Zeenat ba ta cikin hankalin ta na rasa wa ya canja min ita,ta riga ta zama zuma sai da wuta,idan na cigaba da yi mata sanyi-sanyi lamarin ta zai fi haka,hakan ya sa na fiddo hanyar da zan hukunta ta mafi kyawun hanya wanda da kanta za ta fuskanci kuskuren da ta aikata har ta yi nadama,da izinin Allah wata rana za ta shiryu za ta bar duk abinda ta ke mara kyau,ada na san ba haka halin ta ya ke ba,hakan ya sa na ke da sa ran wata rana za ta gane gaskiya,ta koma asalin Zeenat ɗin da na sani",wani gajeren murmushi ta saki kafin kuma ta ɗora da cewa,",To Ameen Allah ya amince ,yanzu ko dai fasa shiga cikin Masarautarnan zan yi in bika mu tafi Lagos ɗin tare ?","Da na so hakan domin na tabbatar zan kasance ɗan gata kuma ɗan lele,da zaran na dawo na yi ido huɗu da kyawawan idanunan naki zan ji na rabu da duk wata gajiya da na ɗebo,zan samu kulawa da soyayya wadda har za ta iya sawa zuwa gobe da safe in makara zuwa gurin taron",Cikin aji Gimbiya Ayush ta saki wata dariya gami da cewa,"A wayance ka sallame ni gami da nuna min ba zaka je da ni ba","Wane ni ,waye Imam Muh'd Jaheed da har zai ce ba zai yi tafi tare da Gimbiya Ayush ɗin shi ba,ai ban isa ba,domin ina jin tsoran hukuncin da ka iya biyo baya,domin nasan kujerar ta mai adalci ce ba lalle ta yi duba da mi a matsayin Mijinta ba,tuba na ke","zaka fara ko,to bari in zo in tafi tun kafin abun yai nisa",...."Tuba na ke bana kuma ba",ya faɗa yana mai riƙo mayafin ta,"Yaushe za ka dawo?",ta tambaye shi ba tare da ta mai da hankali kan wancan batun ba,"Am inantunanin ba zan wuce four days ba da izinin Allah ","To Shikenan Allah ya tsare,ya kuma bada sa'ah a abinda aka je don shi,ya sanya sauƙin da ake son a isar ya isa ga waɗanda zasu amfana da shi,zan cigaba da yi maka addu'a har ya zuwa san da za ka dawo","Ina alfahari da ke,zan kasance mai yawan tunawa da daɗaɗan kalaman ki har zuwa sanda zan dawo,ki kula min da kan ki,bari in zo in tafi na sanar da Hameed ya same ni a Airport zai dawo maki da motar ko za ki buƙaci yin amfani da ita". "A'a ba sai an dawo da ita ba,ko ka manta akwai wadatar motoci a cikin wannan Masarautar,zan samu Motar da zan yi amfani da ita". "A'a Ni ma ban manta ba,amma a gani na kamar zai fi kyau kiyi amfani da Motar Mijinki,kamar hakan sai ya fi girma ko?","As you said my beloved husband, yanda ka ce haka za ai,zan jira",Nan fa sukai sallama tafito Bayi Mata guda biyu da suke dakon fitowar ta suka ɗauki kayan da ta zo da su,bai bar wurin ba har sai da ya ga tafiyarta, sannan ya isa Airport ɗin kafin terminal ɗin su ya tashi su nufi garin Lagos. "Gimbiya Ayush irin wannan soyayya haka kamar ba za a mutu ba ,tun ɗazu ina hango isowar ku ina daga Upstairs da na yi tunanin ba za ki fito ba har sai anzo an fitar da ku saboda tsabar nunama juna soyayya bakwa ji ba kwa gani",cewar Gimbiya Fadeela da ke tsane gashin kanta alamun ta fito wanka. "Oh ki ce ido ki ka sama na bamu sani ba,yaushe ki ka fara sana'ar sa ido ban sani ba",cewar Gimbiya Ayush,"Ba wani sa ido kawai gaskiya ce na faɗa,na gan ki harda ƙaramin troly ince dai lafiya","Hmmmmm aikin Yah Imam ne,sai da na ce masa ba zan ɗauko komi ba amma ya matsa sai na taho da su,na faɗa masa duk abinda zan amfani da shi akwai a cikin Masarautarnan in babu ma in nazo za a nemo min shi,amma ya ƙi yarda","Ni fa har yanzu ban gane abinda ki ke son faɗa ba,wanne dalili ne yasa ki ka baro Gidan ki ki ka dawo nan ince dai ba wata matsala ko?","Ba wata matsala tafiya ce takama shi zuwa Lagos shine fa na ta sa shi a gaba kan ya bar ni,in zo Gida kafin ya dawo,amma fa da ƙyar na samu ya amince". "Ki ce min kin zo hutu ne, a'a wallahi takawar ki lafiya Gimbiya Ayush amarya a Gidan Imam Jaheed"...."Ke ni duk ba wannan ba,akwai fa matsala ,tun abortion ɗinan da nayi jini sai wasa ya ke min,ga shi kuma time to time sai in riƙa jin motsi a cikin cikin kamar cikin bai faɗi ba","Subahanallahi to garin yaba ki faɗa min tunda wuri ba ko da yake ai laifin ki ne,tun farko sai da na ce ki bari ayi maki ko da wankin ciki ne ki ka ce a'a ai ya fita domin kin ga kin zubar da jini da yawa wanda ya fi wanda ya saba fita in irin haka ta faru". "Ba za ki gane ba Fadeela ina cikin tashin hankali matuƙa ta yanda ba ni da hanyar da zan iya making call irin wannan ba","Tashin hankali kamar ya amma kuma ba ki kira kowa kin sanar da shi a cikin Masarautarnan ba". "Hmmmmm bana son abun yai tsamari ne,domin in har na bar hakan ta faru asirina dana ke ta ƙoƙarin rufe sa zai tuni","Kin bar ni a duhu ki yi min bayani yanda zan fahimta","Ummu Nurain ce ta ƙonani da ruwan zafi idan kuma na bari aka je Hospital asirin zubar da cikin da nai zai iya tonuwa dole sai nai endoring ɗin zafin nayi na riƙa shafa ointment kawai","Taɓ ɗin jam aiko kin yi kuskure ita kuma ta taka sa'a domin da maganarnan ta shigo cikin wannan masarautar da ta kaɗe har buzunta","Hmmmmmai nasan da haka shiyasa ma na dakatar da faruwar hakan tun kafin abun yai nisa,yanzu ya za ai da maganar case ɗin nan da gaske ina takura da yanayin da na ke daurewa kawai na ke","Wannan zan iya cewa kusan ke ki ka jawa kan ki,da kin bar cikin ai duk ba haka ba,amma ruf ki ka rufe idanun ki ,ki ka saƙafa ki ka yi fatali da duk shawarwarin da na ke ba ki,ki ka sa son ranki a gaba".......ta dakatar da ita da cewa,",Kin ga Fadeelah ni bana son wasu tone-tone,kawai ki gayamin yanda za ai solving ɗin matsalar ba wai ki riƙa dawo min da bara bana ba,in kuma ba ki da niyar taimako na sai ki sanar da ni,in samu wani wanda zan biya da kuɗi yai min abinda na ke so". "Abun bai kai har haka ba,ki shirya ko gobe ne sai mu je Hospital ɗin a duba aga me yake cousing ɗin wannan sign ɗin daga nan sai a san matakin da za a ɗauka",ta kai zancen tana mai aje handdrayer da ke hannunta, ,"Yauwa ko ke fa yanzu na ji batu,bari in yi using toilet in na fito sai ki raka ni in gaishe da Fulani da mai martaba in yanan,domin ba inda nashiga nan na fara zartowa","Okay to sai kin fito,amma bana tunanin Mai martaba yananan domin na so in ji zai yi tafiya zuwa".....ta dakata sakamakon ringing da phone ɗin ta ta fara,tsaye Gimbiya Ayush tai tana jiran ta gama wayar ta idasa bata amsar ina Mai Martaba ya tafi,amma har ta gaji ba ta gama wayar ba,la'akari da ta yi da yanda ta ke cike da nishaɗi gami da shauƙi ya sa ta ta yi shigewarta toilet ta barta,ba tare da ta cigaba da kiranta ba,har ta gama watsa ruwa ta fito amma bata gama wayar ba,sai can ta sauke wayar ta na mai cigaba da faɗaɗa murmushin kan fuskarta. "Eyeh Lailah da Majnoon zan kira ku da shi,ko kuwa Remoe and Juliet zan cen na rasa da wanne sunan ma ya kama ta in kira ki da shi,tell me waye shi I'm eager to hear". "Na baki gari ki canka da kan ki","Kin sa I'm not good in guessing tell me mana","Hameed ne yanzu haka ma yace min ya na son ya kawo ma Masarautarnan ziyara amma ya fi son ya shigo ta sanadiyyar ta,don haka yana neman izinin zuwa daga gare ni",. Wani irin tsallen murna Gimbiya Ayush tayi gami da cewa,"Why not ya zo mana,ina fatan kin amince ko,kin bashi damar ya zo ko ?",sai da Fadeela ta rausayar da kanta gefe,kafin ta ce,"Eh na amince na bashi dama,domin zuwa yanzu ina jin ko tabbacin fara son shi a cikin raina,Guy ɗin yayi yana da hankali,kuma ya kasance irin type ɗin Mijin da nake mafarkin Aure yana da hankali natsu,uwa uba kuma ilimi da kamun kan da yake da shi","Heh Masha Allah hakan ya yi min amma ya ya shima da fatan ya faɗa da ke ko?","Uhhmmmm to ina expecting ɗin haka domin duk alamomi sun nuna haka,ina tunani ma zai zo yai proposal ɗin soyayyar sa ne". ''Ki gane Fadeela ban san yarda zan fasaltamaki yanda na ke cikin farin ciki ba,ki gane rayuwa da Ahalin Alaranma Ibrahim Mai Fata abun alfahari ne,mutanen suna da karamci da kuma mutunta juna,suna kasuwancin su,haka suna gudanar da Company ɗin su,ga ilimi da su ke raba shi kyauta ga al'umma abun alfahari ne ka yi rayuwa da irin waɗannan mutanen". "Na fara fahimtar haka daga Hameed domin zai yi wuya muyi wayar minti biyar ba tare da ya amfanar da ni da wani abu ba,yaron yana da hankali gaskiya". "Yanzu duk ba wannan ba,ki sanda duk yanda za ki yi ki jawo Hameed cikin komar soyayyar ki ta yanda zai kasance baya ji baya gani,ya kasance ba wata ɓaraka ko tazara a tsakanin ku,hakan zai sa nan gaba ki tabbatar da duk abinda na ke gaya maki,ina gaya maki Auren mutum mai ilimin addini nasara ce,dace ne babba,kuma ni'imace,ba zaki gane hakan ba har sai wanda Allah ya ba wannan Auren Ustaz shine zai ƙarar da wannan maganar,ina ma kifatan Hameed ya zama na ki ke kaɗai ba tare da an haɗa ki zaman ki shi da irin su Ballagaza Ummu Nurain ba". Dariya Fadeela ta saki gami da cewa,"Wannan ai sai ke,ba wanda zai iya da tijarar wannan matar, in ba ke ba",Hmmmmma ni fa haƙuri kawai na ke amma yanzu ta isa kawo Ni i wuya na kusa fara nuna mata ko ni wace ce,na rantse sai ta fidda kan ta da kan ta daga cikin Gidannan,in har Ina raye Kuma ina numfashi a matsayin Matar Imam Jaheed". "Anya kuwa Gimbiya Ayush aikata hakan dai-dai ne,kar fa ki manta akwai alaƙar jini a tsakaninsu ba kya tsoran reshe ya juye da mijiya",.....ta katse ta da cewa,"Ba abinda zai faru Fadeela sai alkairi ai tuni Ummu Nurain ta watsa ma garin ta ƙasa,banda azababbiyar ƙazantar da take aikatawa yanzu ta ƙaro futsara,rashin kunya da kuma neman fitina ba tare da dalili ba,kin ga kenan ita da kanta zata buɗe min hanyar da zan fidda ta daga cikin Gidan da sauƙin","Kuma fa haka ne da gaskiyar ki duk mace mai irin wannan ɗabi'un ba za ta taɓa zama lafiya da Mijinta ba, Allah ya shirya ta in ta na da niyar hakan",da haka dai suka gama shirin su suka nufi ɓangaren Fulani kafin Mai martaba ya dawo. Part 32 Kai tsaye Jadeeda bayan sun yi landing Eko Hotels and Suites da ke located at Plot 1415 Adetokunbo Ademola Street, PMB 12724, Victoria Island, Lagos, ta nufa hotel ɗin da yake ɗaya daga cikin hotel ɗin da su kai Shura a cikin Garin Lagos ya na ɗauke da kimanin 825 rooms and suites across four multistory buildings,tun kafin su isa ta ke trying ɗin wata number amma cikin rashin sa'ah har yanzu ba ai picking ba,sai faman tsaki ta ke saki time to time ta na ƙara gwada kiran,can kiran na gab da sake katsewa ba tare da an daga ba akai picking,tare da cewa,,"I'm so sorry friendy ,bcos I'm in a noisy environment, that's why I'm not picking your call."shiru Jadeeda ta yi ba tare da ta ce da ita komi ba,hakan ya sa ita kuma ta kasa iya jurewa har sai ta ce da ita,"Ki yi min magana mana kin san tun muna yara bana iya jure shirun ki",cewar Ruth cikin son shawo kan Jadeeda,daga nan Jadeeda na jiyo sautin kiɗan dake tashi a wurin da ta ke,sai a lokacin ta ce da ita,"Ban san sai yaushe za ki sauya ba Ruth yau kina wancan Partyn gobe kina wancan,anya kuwa?"...."No...no..no sis ba haka ba ne ba,na tuba fa na bar duk waɗannan halayen yanzu haka muna Birthday Party Fredrick ne shiyasa ","Oh really?,yanzu fa haka ina cikin Lagos,na so in yi surprise ɗin ki shiyasa ban gaya maki ba har sai da na iso",wata ƙara Ruth ta saki tana mai tsalle kafin ta ce,"Tell me kina ina,gayamin I'm eager to see you,yanzu zan bar duk abinda na ke in taho", murmushi Jadeeda ta saki kafin ta sanar da ita inda suke,"To ai a cikin Hotel ɗin muke gudanar da Birthday Partyn ɗin ganinan maza ƙaraso in yi welcoming ɗin ki,wanne Room ɗin ki ke ne ","Room 263 ",ta Bata amsa a taƙaice,tamkar waɗanda su ka kwashe tsawon wasu shekaru ba su haɗu ba haka suka rinƙa murnar ganin juna,"Na yi murnar ganin ki,ba na jin kin taɓa burge ni irin yau,ban san da wacce murya ko hanya zan iya nuna maki jin daɗi na ba","Kin ga ni kaina I'm so happy,kin san bikin Ester da za ai shine Church ɗin (SCOAN),, Suka gaiyace ni a Matsayin zaɓaɓɓiyar mawaƙiyar su","wata ƙara Ruth ta saki mai ƙarfi kafin ta dakata da cewa,"Kai abun alfari na ji daɗin jin haka,tafi-tafi sai ƙara samun ɗauka ka ki ke yi","Ke dai bari duk hakan ya na faruwa da Encouragin ɗin a da ku ke min tun muna school","Haka ne yanzu abinda ya kamata Sister ta shi ki fresh up mu tafi Partynnan tare da ke,ba ƙaramin murna Fedrick zai yi ba idan ya gan ki a wurin,saƙon isowar ki shine zai zama Birthday gift ɗina a gare sa ","Ah I'm tried I can't go anywhere,na gaji sosai ko kin manta gobe ne z mu fara shagulgulan bikin Ester,don haka ina buƙatar hutu kafinnan","Kema kin san ba zan bar ki ba,kin ji my dear, please just thirty minutes ya isa","Amma dai kin san hakan ba zai yiwu ba ko,oyah mu je tashi ki shirya",da haka ta tursasa ta har sai da ta sa ta shirya suka fita tare. "Ku saura! Kussurara!'',Ruth ta shelanta bayan ta amshi mike a hannun Dj ɗin,"Ko kunsan wannan hall ɗin yana ɗauke da baƙuntar fasihiya kuma sananniya a cikin sa,Look who we have here,the one and the only Lucifer,ita da kanta tana jealous ɗin zaƙin muryar ta,Afrika wake up, waiting to listen her song,the nation rise and shine, her voice is in the anthem of the country,A.k.A Jadeeda Anderson",ta kai zancen ta na mai nuna saitin inda ta ke a tsaye,nan fa gabaɗaya hall ɗin suka fara ihu gami da taɓi da ambaton sunanta,wasu sun santa a fuska wasu kuma muryarta kawai su ka sani. Fedrick ka sa motsin kirki ya yi,bai yi zaton zai sake ji ko ganin ta a sauran rayuwarsa da tai ma shi ragowa ba,yaso ta so mai tsanani,so mai tsayawa a cikin rai da zuciya,so irin mai yankan shakkunnan,ganin da gaske itace ɗin ya sa ya zubar da duk kyaututtukan da su ke a hannunsa ya ƙarasa inda take cike da sassarfa dakuma shauƙin ganinta,yana zuwa bai jira komi ba ya haɗe jikinta da na shi. Sai da ya gaji dan kan shi sannan ya raba jikinsa da nata,"Na yi kewa ki Angelenah,Son ki na ƙoƙarin durƙusar da ni ya hana ni zuwa ko ina ,ya dakatar da ni da ga samun ko wanne cigaba na rayuwa,ina son ki da dukkan raina Jadeeda Anderson",wani ihu gabaɗaya Hall ɗin ya sake ɗauka,"Ki ce da ni wani abu mana ba zan iya samun natsuwa ba in har ban ji wani abu daga gare ki a yanzu ba",ya kai zancen yana mai sake haɗe jikin su a karo na biyu,duka ta kai masa da hannu tana mai sakin murmushin yaƙe a kan fuskarta,sai da ta kai bakinta saitin kunnensa kafin ta fara cewa da shi,"Za ka fara ko,ko kamanta a inda ka ke ne,nan ba University College of London (U.C.L) ba ne ba,don haka ka ɗan riƙe kan ka kaɗan zuwa a tashi",ta kai zance tana mai fuskantar shi gami da jujjuya masa idanunta bai san sanda komi na shi ya daskare ba,wanda ita kuma tai amfani da wannan damar ta sa Dj sakar ma su sautin waƙar Dr Sid and DJ Sose Mai taken Over the Moon,da wannan damar ta samu hankalin mutane ya kauce akan su,sai dai me duk inda za ta sa ƙafarta Fedrick na biye da ita,haka har su ka tashi daga Partyn,a hankali ta ke tafiya ta na yi tana waigen baya duk tana haka ne don ƙoƙarin gujema sake haɗuwa da shi take amma ina haƙan ta bai cima ruwa ba,domin sai ganin shi kawai ta yi ba tare da ta yi zato da tsanmani ba,da alama ya sha ya bugu sosai,bayanda ta iya dole sai kama shi tai ta nufi Room ɗin tada shi,da kyar ta samu ta iya kai shi cikin Parlonta shima sai da taimakon Waiter na hotel ɗin. Kamar wacce tai tsere haka ta ke sakin numfashi da huttai,wayarta ta laluba tana mai fara kiran number Ruth,a ɗan zafafe ta fara yi mata magana da cewa,"Ruth wai ina ki ka shiga ne,tun ɗazu sai neman ki na ke ban gan ki ba,kina ina",cikin rashin gaskiya Ruth ta fara yi mata magana cikin inda- inda,ba tare da ta faɗa mata inda take ba"Koma ina ki ke,ke ki sa ni,amma ki gaggawar zuwa ki fidda min Fedrick daga cikin Room ɗina","....Fedrick Kuma garin ya akai ya san Room number ɗin ki da har zai zo wurin","Ya sha wine ne ya fita daga cikin hankalinsa,Ni kuma ba wani sanin friends ɗin sa na yi ba,balle in samu wani ya tafi da shi,don haka ki ma za ki zo ki san yanda za ki yi ,ki fitar min da shi","Okay okay I'm on my way ganinan tafe". Cikin yanayin wanda ya sha ya bugu Fedrick ya matso kusa da ita tare da cewa,",Ba wai ....sai kin....kin.kin... kira wani ba kawai ki bar ni,mu kwana a tare ko kin manta mu ɗin masoya ne,kuma wata rana Aure za mu yi,don haka kar ki wani damu...",ya kai zance ya na mai yunƙurin faɗowa kan ta da sauri ta janye daga wurin ya faɗa kan three seater da ke kusa da su. "Kar ki bari a tafi da ni don ko an tafi dani sai na dawo,domin zuciyata tana liƙe da ta ki ne,ba zan samu natsuwa a cikin barci na ba har sai na jiki a kusa da ni,sai na ji numfashi da kuma bugun zuciyar ki a saman ƙirjina"......irin wannan maganganun ya rinƙa faɗa har barcin Giyar ya kwashe shi,sanda Ruth ta zo bai ma sani ba,ita da taimakon saurayin da Ruth ɗin ta zo da shi da kuma security guda ɗaya suka sanya shi a motar su ka nufi kai shi gidan sa. Wata kyakkyawar ajiyar Zuciya Jadeeda ta saki ta na mai dafe gefen kanta da yai mata nauyi,wuri ta samu ta zauna gami da rafka tagumi da hannu bibbiyu, abubuwan da suka faru tsakaninta da Fedrick ne suka fara dawo mata a cikin kwakwalwar a lokacin baya ta da sauri ta runtse idanunta gami da miƙewa ta nufi bedroom ɗin ta bakin ta ɗauke da addu'ar Allah ya sa ta gama abinda ta zo yi lafiya ta koma Gida lafiya ba tare da wani abu makamancin na baya ya sake faruwa da ita tsakanin da Fedrick ba,sosai ta dage da addu'ar Allah ya sa su rabu lafiya ba tare da hayaniya ko hargitse ba,ko isasshen barci kasa samu ta yi ,saboda ta sa shi a cikin ranta,har dana sanin kawo shi cikin ɗalinta ta rinƙa yi da ma ta sani a can waje ta yasar da shi ba tare da ta kula dashi ba,balle har ta kawo shi Room ɗin ta. Yau Ester Sunday ta ɗau wankanta cikin expensive dress nata cikin jerin wanda Uncle Miey ɗin ta ya saya mata,ta nufi Synagogue, Church of All Nations (SCOAN),taro yayi taro a wurin haka suka cigaba da gaggaisawa da mutane,sai da manyan Reversed, Pastors da masu faɗa a ji a cikin Church ɗin su ka zo kafin a bata damar zuwa ta buɗe taron da daɗaɗan waƙoƙin ta kamar yadda aka tsara,Revered Anderson na can zaune a high table cikin manyan Reversed fuskar shi ɗauke da farinciki da zallar alfahari game da samun ƴa irin Jadeeda da ya yi. Cikin zazzaƙa kuma maɗaukakiyar muryarta ta fara cewa,"When every knee shall bow and every tongue weather you like it or not it's mandatory that you confese and acknowledge that Jesus Christ is lord,A day is coming when the arrogance people will come to a halt where the pride of people the plignative of men ,the brilliant of people and the intellectual capabilities of people/men will mean nothing and on that day ever knee will bow,and the lamb shall make war revenquish the power of the enemy among us,we mute the voice of the adversery.we discredit the voice of the accuser of your people in the name of Jesus,we command salvation for All",ta ɗan tsagaita kafin ta fara kai kawo a harabar gurin da ta ke. "Now let God arise in the name of he,seated on the right of the father to ever make intercess,our soon coming king, Jesus Christ the son of God ,the lord of the all time and age,you are on the throne, you are the Lord". "We are a chosen generation,we have been called forth to show his excellent, hey all I required for life". Sai da ta kawo nan a zancen ta sannan duk taron mutanen da ke cikin Church ɗin suka zauna kafin daganan ta yi ma gan ɗin ta da suka iso yau alamar da su sakar mata sauti ,cikin tautaysan lafuzanta ta da tsara waƙararta mai taken New soul,"Pass me not O gentle saviour Hear my humble cry. Oh! and while on others. Thou art calling Do not pass me by He he he Pass me not O gentle saviour.... Haka ta cigaba da raira waƙarta hatta kai ƙarshe kafin su cigaba da gudanar da event ɗin su ,kamar yanda su ka saba,sosai ta samu yabo gun manyan mutane da Pastors da ma Revered. A gajiye ta dawo hotel ɗin,bayan ta rabu da su Papa sun tafi na su masauki su.jin knocking ɗin door ɗin ta yasa ta miƙa a ɗan kiɗime tana mai tambayar waye,"Who is on the door",ta tambaya cikin rarrababbiyar murya,"Am ki buɗe ƙofar,Ni ne ba wani abu zai faru ba,i just come to see you","Oh Blood of Jesus Christ Fedrick kai ne wai ,to ka sani I'll not open ba zan buɗe ba,ka koma inda ka fito"...."Ni.no don't say that,Bai kamata ki aikata haka ba,na yi ta bin ki tun a Church Amma ki ka ƙi ssurarana kin ga bai kamata in zo nan ba ki sake watsamin ƙasa a ido ba". "Okay ka cigaba da tsayuwar a wurin in ka gaji ka tafi",ta na kaiwa nan ta kwashi abubuwan da za ta buƙata ta nufi bedroom ɗin ta haka ya cigaba da bugawa ya na magiya har daga ƙarshe ya haƙura ya tafi ,bayan ya tabbatar ba za ta buɗe ba duk da haka a cikin ransa bani wani abu da ya sauya game da ita ba,don haka ma ya ƙudurce a cikin ransa gobe ma zai dawo. Washegari Ester Monday haka suka cigaba da gudanar da event ɗin su kala-kala,kafin daga bisa ni su tashi,taron ya koma gidajensu,irin taron family, friends da sauran su. Ita kanta Jadeeda hankalinta ya yi Gida ta ƙosa ta tafi cikin family ɗin ta su yi Shagali kamar yanda su ka saba,haka ta nufi Room ɗin ta ta fara haɗa luggage ɗin ta domin jirgin safe ta ke son ta bi. "Blood of Jesus!", shine abinda ta faɗa cikin firgici da tashin hankali bayan ta ci karo da Fedrick zaune akan ɗaya daga cikin kujerun da suke a Parlonta..... Part 33 "Wai tsaya kar dai ki ce min tafiyar da na ji Mahaifin ku yana magana akanta ita ce wannan munafukar kishiyar ta ki ta shiga ta fita aka tafi da ita?",Mama ta tambayi Zeenat. "Tafiya kuma Mama dama kin san da maganar tafiyar ne ke","Shakka babu na san da wannan tafiyar amma ban taɓa tunanin zai ce zai tafi da wata a cikin ku ba,domin na ga bai cika tafiya da ku ba in har ba ko aikin Hajji bane ya kama shi","To ai gashinan yanzu ya tafi da matar so ya bar ta ki ƴar da tarin baƙin ciki,da kin sanar da hakan ai da tani ta kasance cikin shirin ko ta kwana". "Taɓ Allah Aunty Zeenat kar ki yarda kar ki kuskura ki bar su ,su ji daɗin zaman garin,ki kira shi ki tada mashi hankali",cewar Asiya. "Ai kuwa haka zan yi barinsa in kira shi","Yauwa Aunty Zeenat kar ki wani yi duba dare ya yi maza kira shi ". Haka ta fara kiran shi amma ana ce mata user busy,shi yana can ya na waya da Baba ƙarami yana ba shi labarin yanda taron ya ke shirin kasancewa. "Abbu komi lafiya,yanzu ma haka dawowata kenan,mun fara tattaunawa akan yarda taron zai kasance zuwa gobe da safe ma in sha Allah za'a fara taron,za'a gudanar da taron live ne ma","Masha Allah a labari ya yi daɗi,ina maku fatan nasara,zuwa da safe zan sake kira,daganan ma sai in haɗa ka da Baba Malam domin ya damu yana son jin muryarka","Allah sarki nima ina kewan rikincin sa,na yi kewan ganin sa",....."Gidan ku Muh'd Jaheed yanzu mahaifin nawa ka ke kira da mai rikici,sai dai ko Hibba ce rikitacciya ba shi ba,shin ko kun haɗu da Alƙasim?","A'a ba mu haɗu da shi ba mun dai yi waya ya ce zai ɓullo mu haɗu da shi","Hakan ya yi in yaso in ka sami dama sai ka leƙa Companyn ka ga yanda ake gudarnar da shi","To in sha Allah zan yi ƙoriri in ga naje",da haka su ka gama hirar ta su,ya nufi Room ɗin sa mai Number 264,kafin ya ƙara sa wayar shi ta sake wani ringing ɗin, dakatawa ya yi,yana mai picking ɗin call ɗin ,"Ka sa a dawo min da Yarona kamar yanda ka ɗauke shi da kan ka",shine lafazin da ya fara ratsa dodon kunnensa,dan ne abinda ya ji yai ta hanyar cewa,"Ummu Nurain ki na lafiya kuwa?,da irin wannan kalamin ya kamata ki tarbe ni,ko kin manta tafiya nai,tafiyar ma mai cike da da hatsari,eh mana hatsari mana tunda na hau flight ne,amma kuma sai ki rasa da me za ki tarbe ni sai da irin waɗannan zafafan kalaman ?". "Zafafan kalamai ai su suka fi dacewa da kai,shin kai ka manta abinda kai min kafin barowar ka Gidan ne ?","Hmmmmmm Zeenatu kenan ,ban san sai yaushe za ki sauya wannan halin na ki ba",...ta katse shi da cewa,"Ka ga ni ba wannan ce ta sa na kira ka ba,kawai ka sa a dawo min da ɗana ko kuma wallahi in je har Gidan inyi tijara iya ta kuɗi Sannan in ɗauko ɗana","Zeenatu dan Allah kar ki fasa ki je Gidan,ki je ki aikata duk abinda ki ka so,ba dai Nurain bane je ki ɗauko shi,Ni kuma ina mai tabbatar maki da sai na raba ki da shi ,ke ko da makarantar almajirai ce sai na kai shi"..... "Ɗan nawa za ka kai makarantar almajirai?",ta tambaye shi cike da mamaki,"Oh kina ganin hakan ba zai yiwu ba ne ba,to ki gwada ki gani,daga nan sai ki ga zan iya aikatawa ko ba zan iya ba". Kuka ta fashe da shi da iya ƙarfinta tare da cewa,"Wallahi Yaya Jaheed baka isa ka raba ni da ɗana ba,ina nan ina jiran ka ba zan bar duk abinda ka ke min ya tafi a banza ba,na rantse sai ka riski tashin hankali,musiba da kuma fitinar da baka taɓa zato ba a cikin Gidan ka ,ina jiran ka ka dawo ka iske ni,abu ɗaya zai hana faruwar duk abinda na lissafi maka ka sa a dawo min da ɗana gabana",tana kaiwa nan ta tsinke wayar gami da ƙara ƙarfin kukanta,tare da cewa,"Mama wai kinji in har na je na ɗauko Nurain sai ya kai shi makarantar allo don ya nuna min ya fini isa da iko akan shi","Makarantar allo kuma akan me ba gatanan ana yi a Gidan su ba mai zai sa ya tafi uwa duniya?". Saboda ya nuna min ni ba a bakin komi na ke a wurin sa ba shiyasa","A'a wannan lamarin ya yi nisa bari Baban ku ya dawo sai na sanar da shi don ayi ma abun tufkar hanci tunda wuri. Sai faman kai kawo Jaheed ya ke,a harabar ƙofar Room ɗin nasa shi bai shiga ba,sai saƙawa da kwance Wa ya ke,shi a nashi tunanin a iya abinda ya aikatawa Zeenat kafin tahowarsa ya isa tai hankali gami da shiga cikin taitayin ta,ya yi tunanin ,za ta zauna ta gano dalilin da yasa ya ke nuna mata irin waɗannan sabbin halayen da kuma ko in kular da ya ke yi mata,amma da alama ya ga hakan ba lalle ne ya yiwu ba,tunanin shi kuma kacokan ya koma wajen samun hanyar da zai nusar da Ummu Nurain kuskuren da ta ke aikatawa,a baya dai yasan ya yi lallashin ya yi mata alkunya,ya fito fili ɓaro-ɓaro ya nuna mata kuskurnta,har ta kai shi ga ƙaro mata abokiyar zama,yanzu kuma ya fara nuna mata halin ko in kula amma duk da hakan ba a samu wani canji daga gare ta ba sai ma ƙoƙarin ƙara fanɗarewa da take,a kullum sake tsiro da sabbin halaye take,a da iya ƙazanta ce kawai ta ke fama da ita,yanzu kuma ta kai har ta iya fuskantar fuskar shi ta gaya masa duk kan kalan maganganun da su ka zo mata a baki,rashin kunya kamar me,ba tare da ta yi la'akari da matsayin shi a wurinta ba,to yanzu ta ina ya kamata ya ɓullo mata ?, shine abinda ya tsaya masa a Zuciya hana shi samun matsaya ko madara akan haka. "Ka ga Fedrick ka fitar min a ɗaki,I said get out of my room,ni na rasa ta wacce hanya ka bi ka shigo min ɗaki","Kin ga Jadeeda babu inda za ni inanan har sai ki faɗa min wanne matsayi na ke a cikin Zuciyar ki,na gaji I'm tried,son ki ya daɗe da yi min illah,yanzu nema ya ke ya haukata ni,ba zan iya ba,akan ki na rabu da iyaye na,na zaɓi in kasance da ke don kawai ina tsananin son ki, na gaji babu inda za ni",ya kai zancen ya na mai gyara zaman shi. Iya ƙololuwar tashin hankali Jadeeda ta shiga ji take ina ma da ta sani ta bi Papa masaukinsa da irin haka bata faru da ita ba. Cikin ƙasa da murya gami ,tausasa ta ya ce,"Haba Jadeeda ki ji tausayi na mana,kin sani iyayena sun daɗe da musulunta na rabu da su na zaɓi da inyi rayuwa da ke,duka Gidan mu Musulmai ne,Ni kaɗai ne mabiyan addinin Cristian,saboda ina jin tsora gami da tabbacin in na rabu da shi kamar na rabu da ki, amma ke a kullum ƙara yin nisa da ni ki ke,babu wata halitta da ki ka tsana ta raɓe ki sama da ni,mai na aikata maki har haka". Can nesa da shi kaɗan ta samu ta zauna tare da cewa da shi,"Ba wai na tsane ka ne ko bana son ka ba ne ba a'a,just ba na son maganar Aure ta na shiga tsakanina da kai,zai fi kyau mu cigaba da yin friendship ɗin mu like yanda mu ka faro tunda farko ",.......ya katse ta da cewa,"Saboda me uhm?, saboda ban kai matsayin fitacciyar mawaƙiya kamar ki ta so ni ba,ko saboda ba na da kyawun da za ki iya nuna ni a matsayin Mijinki ? ". "Oh God Fedrick ka maida hankalin ka jikin ka mana , soyayya fa bata yiwuwa ta ɓangare guda,dole sai kana ra'ayi nima ina ra'ayi,na ce ba na yi ko dole ne,kabar ni dan Allah ka je ka nemi wata". A hargitse ya juyo ya na mai bin ta da shanyanyun idanunsa ,ita kanta sai da ta tsorata ,kasa ce mata komi yai sai da ya janyo bottle ɗin Wane ɗin da ke gefen shi ya ɗaga kai ya sha iya shan shi kafin ya ce da ita,"Ba ki so na fa ki ka ce ?,in tafi in ba ki wuri,anya kuwa ba akwai wani wanda ki ke so ba da ya sa ki ke treating ɗina like that ba?",ya kai ƙarshen tambayar yana mai sake ɗaya bottle ɗin wine ɗin sa sai da ya shanye ta tas sannan ya cire bakin sa a jikinta tare wular da ita a tsakiyar ɗakin gami da miƙewa ya nufe ta yana mai cewa,"ki ba ni amsa ta shin kina da wani wanda ki ke so ne,ko yaya",ya sake tambayar ta cike da tsawa,gami da cigaba da kusantowa inda take". "A'a..... a'a...... Fedrick ka dakata,ka dawo cikin hayyacinta,kar ka aikata abinda za kai da na sani akan sa","Ba wani danasanin da zan yi ,anya kuwa kin don zafi gami da raɗaɗin da nake ji a cikin Zuciyata a saboda san da na ke maki, a'a bana tunanin kin sani,amma ina son in tabbatar ma ki da ina maki mahaukacin so da zan iya aikata komi akan sa,hakan ya sa ba zan taɓa iya jurar ganin ki da wani ba,ba shakka in haka ta kasance mutuwa zan yi baƙin cikin da takaici sune za su zama silar yankewar rayuwata,kin san wacce irin rayuwa na ke gudanarwa tun bayan rabuwa da ke da nayi a U.s na sha wuya ,har jinya na yi kamar zan rasa raina,da ƙyar na samu na farfaɗo da saran zan sake haɗuwa da ke amma ina hakan bai yiwu ba domin kin toshe duk wata kafa da ki ka san zan iya bibiyarta in iso gare ki,wai wacce irin tsana ki kai min for the God sake?". Cikin rawar murya wacce ke bayyanar da asalin tashin hankalin da take a ciki ta ce da shi,"Ba tsanar ka na yi ba,kawai dai ina son".......ya katse ta da cewa,"Ki na son me kar dai ki ce min sunan wani za ki furta min a matsayin wanda ki ke so",ya faɗa cikin sigar wine ɗin da ya sha ta fara aiki a jikin sa. Kafin ta ce wani abu ya ɗora da cewa,"Da in bar hakan ta faru gara in kashe ki , sannan in dawo in kashe kai na na san wata ƙila in muka je can lahira za ki iya so na,in kin ga ba wani wanda y fi ni a kusa da ne ,kin ga kenan zamu rayu a matsayin Mata da Miji a rayuwar barzahu da za mu gudanar",ya kai zancen yana mai rarumo tsagin bottle ɗin da ya sha ya nufe ta da shi sai faman tangaɗi ya ke,alamar ya fara buguwa. Jikin Jadeeda tuni ya daskare ta kasa ko motsin in kacire zuciyarta da kanta da ta ke faman girgizawa dakuma zuciyarta da ta ke faman bugawa da sauri da sauri,in Banda su ba abinda ya rage da ke motsi a jikinta,haka ya nufeta da tsagin kwalbar ,babu kalar addu'ar da ba ta yi ba,duk dan neman agaji da taimako a wurin Yesu Almasihu. Kamar wanda aka sa remote aka dakatar da shi haka ya tsaya ,sai kuma can ya saki tsagin kwalbar da ke hannunsa,yana mai fashewa da wata irin dariya mai cike da ma'anoni kala daban-daban,sai a lokacin hankalin Jadeeda ya fara kaiwa ta nemi taimako ko dai daga Hotel ɗin da ta ke ko kuma ta yi amfani da wayarta,sai dai kash jarkarta na can wajen door ɗin shigowa wacce tai cilli da ita tun da ta yi tozali da shi da farko,tellophone ɗin hotel ɗin kuma suna da tazara a tsakanin su,ƙasa tazame ta maido da ganin ta kan shi sakamakon jin abinda ya ke cewa,"O me ma zai sa in kashe ki,in kashe kaina a banza?,me ye zai sa ba zan yi amfani da wannan damar da na samu ba,ki zama Mata ta tun a duniya ba sai mun kai ga zuwa barzahu ba",ya ce da ida ita yana mai fara ƙoƙarin cire rigar jikinsa. "Ban.....gane ba..... Fedrick......mai ka ke shirin aikatawa wannan babban kuskure ne.....a'a .... a'a ka dakata...ka bar kusanto inda na ke",ta ce da shi tana mai fusgo numfashin ta gami da ƙarfafa zuciyarta,"Na yarda ina son ka amma na roƙe ka da kar ka cutar da ni","A'a Jadeeda kin makaro,domin a yanzu ba zan iya dakatar dakai na ba,zan maida ke tawa,mallakina ni ni kaɗai,daga yau ba za ki ƙara tunanin yin rayuwa da wani ba ni ba,daga yau zuciyar ki zata riƙa bugawa da suna na a kowacce daƙiƙa,Ni ne zan zama jarumi a cikin labarin rayuwar ki,Ni ne zan zama uba kuma jagora a wurin ƴaƴan ki,Ni za su kira da mahaifinsu,bayan ni babu wanda za ki kalla matsayin Mijin ki,Ni ɗin nan daki ka raina ni zan zame me mi ki gata kuma abun alfaharin ki".......duk yana wannan zancen ne yana fidda kayan dake jikinsa,gami da cigaba da kusantar ta duk data na ja da baya daga gare shi. Samun sa'ar damƙar ta da yayi yasa ta saki wata ƙara mai ƙarfin gaske,duka ta cigaba dakai mi shi,gami da kare kanta da duk abinda ya tare ma ta gaba,gami da roƙon shi da duk kalaman da ya zo mata a baki akan ya ƙyaleta kar yake ta mata haddi,dambe ne ya kaure a tsakaninsu,ita ta na ƙoƙarin kwatar kanta shi kuma ya na son cika nufinsa a kanta. Ganin da gaske ya ke haiƙe mata zai yi yasa ta samu wuri Mafi tsoka a cikin fuskar shi ta manna masa cizo da iyakar ƙarfi ta,kafin ya dawo cikin hayyacinsa ta samu Centre table da ke kusa da ita ta kwaɗa masa a ka,sai da ya kai ƙasa saboda kwata-kwata bai shirya tsinkayen haka daga gare ta ba,har cikin kwakwalwar sa zafin ya ratsa shi hakan ya sa ya sake ta batare da ya shirya ma hakan ba,samun wannan sa'ar da Jadeeda ta yi ne yasa ta fara yunƙurin gudawa daga gare shi,sai dai ko taku biyu lafiyyayu ba ta yi ba,ya cimmata,ƙafarsa ya sa ya taɗiyeta nan tai wata irin muguwar faɗuwa har kanta na buguwa da tyle wani Maryan ihu ta saki amma duk da haka ba ya sare ba haka ta cigaba da jan ciki don ta samu ta ga ta tsira daga gare shi,da iya ƙarfin sa ya fara kai mata duka a saitin cikinta daga ƙarshe ya sa ƙafarsa ya take hannun ta gami da murzawa da iya kacin iyakar sa, wannan ne dalilin da yasa ta saki ihu da iyakacin iyawarta tare da fara neman taimako Wannan ihun da kawar neman taimakon da take yi ne,yai dai-dai da kai kawon tashin hankali da Zeenat ta ƙunsama Muhammad Jaheed,a razane ya maida hankalin shi saitin inda ya ke juyo ihun nata, nan zuciyar shi ta rabu gida biyu,wani ɓangaren ya na ya shiga wani kuma ya gargaɗarsa da kar ya je,wata ƙila ma sharholiyar su ta kai sharholiya su ke zabga ihu,jin yawaitar ihun ne ya sa ya kasa iya riƙe kan shi har sai da ya banka ƙofar ya shiga, abinda ya ci karo da shi ba ƙaramin tada mashi hankali ya yiba,a zafafe ya nufi wurin ya na mai yaki ce shi akanta,gami da zabga masa zafafan maruka a kowanne kunci na fuskarsa,zafin marin ne ya fidda shi daga mayen giyar da ya sha,ya dawo cikin hayyacinsa. "Kai ****** waye kai da har za ka shiga tsakanin mu,ka san ko ita wace ce to Mata ta ce,don haka jaye ka bamu wuri",Cikin rawar murya ta ce "....A'a I'm swear ƙarya ya ke,nema ya ke ya keta min haddi,mutuncina ya ke son ya raba ni dashi", Jadeeda ta faɗa cikin karkarwar baki gami da ɓoyewa a bayan Jaheed domin duk ya gama yayyaga mata kayan jikinta,kuma bugu da ƙari a matuƙar tsorace take da shi. "Kai dabban ina ne,idan matar ka ce haka aka ce ka je mata,wanne irin addini ka ke bi da ya koyar da kai wannan haukan?". "Oh ko dai shine wanda ki ke so,wanda a ta dalilin sa ki ka ƙi amsar tayin soyayya ta,to na rantse gara in kashe ki kowa ya rasa a cikin mu",ya na kaiwa nan ya nufe ta,da tsagin kwalbar da ya wurgar ɗazu,hannu Jaheed ya sa da iya ƙarfin shi ya riƙe kwalbar,wanda hakan ne ya hana isartar saitin maƙogwaron Jadeeda,Fedrick da iya ƙarfin sa yake danna kwalbar don ta isa zuwa inda ya ke so,haka shima Jaheed da iya ƙarfin shi ya hana hakan faruwa,tuni Jadeeda ta fara jiyo ƙamshi mutuwa akusa da ita,cikin zafin Nana Jaheed ya hankaɗar da shi can gefe ,gami da bin shi ya fara kai mashi duka da mari a duk inda ya samu a jikinsa, tabbacin da Fedrick ya samu na ba zai iya kwatar kan shi a wurin wannan baƙon mutumin ba ya sa ya fara neman hanyar gudu,bayan ya ɗauki alƙawarin sai ya sake dawowa ya cimma ƙudirin shi akanta. Sosai hakan ya ƙara tada ma Jadeeda hankali amma gani yanda hannun Jaheed ke zubar da jini ya sa ta nufi shi fuskarta ɗauke da damuwa tare da cewa,"Jesus Christ Kalli hannunka ka ji ciwo fa sosai",takai zancen ta na mai ƙoƙarin kama hannun na sada sauri ya janye gami da juyowa don ya ce da ita wani abu,kallo ɗaya yai mata ya kauda idon da a gare ta, hannunsa ya miƙa ya ciro ɗaya daga cikin labulen da su kai ma ɗakin ƙawanya ta rufa mata. "Ki na lafiya koko kina buƙatar a kira maki Doctor ko kuma securityn hotel ɗin ?","Ina lafiya ba abinda ya same ni,sai dai kai ya kamata ka zauna in kira a zo a duba ka",ta kai zancen ta na mai nufar tellophone domin ta sanar dasu,katsewa yai da cewa,"A'a kar kira I'll be okay,ba wata matsala ba ce mai girma, akwai buƙatar ki je kiyi reporting ɗin wancan Mad guy ɗin domin zai iya dawowa,da buƙatar ki kula da kan ki,domin babu wanda ya san me ka iya faruwa anjima",yana kaiwa nan yai hanyar fita ya na mai yarfe jinin da ke faman zuba daga hannunsa. "Gaskiya ba zan iya cigaba da zama a cikin Hotel ɗin nan ba,dole zan bar shi",takai zancen ta na mai lalubo wayarta don tai making call.hannunta rawa ya fara ta ka sa iya aikata komi,ɗago kanta tayi taga ya na gab da fita, sakin wayar ta yi da sauri ta miƙa gami da bin bayansa,amma ina kafin ta cimma sa ya shige cikin Room ɗin sa da ke kusa da na ta,tsaye tai jikin door ɗin hawaye na zubowa daga cikin idanunta. Part 34 Hango ta nufo inda ta ke ne,yasa zuciyarta ƙara karyewa a hargitse taƙaraso inda take,tana mai raɓa ta a jikinta,tare da cewa,"Sis me ya faru da ke,daga ina ki ke,shin kin haɗu da Roberys ne akan hanya",kai kawai ta iya girgiza mata ba tare da ta furta mata komi ba,jikinta ta taɓa ta gami da taimaka mata su ka shiga cikin Room ɗin na ta,"Jesus Christ kar dai ki ce min abinda yasa me ki a cikin Hotel ɗin nan ya same ki,ina securityn hotel ɗin su ke?",Ruth ta faɗa a rikice,zaunar da ita tayi a kan wata seater bayan ta gyara mata ita yanda za ta ji daɗin zaman a kanta ,cikin gaggawa ta fara duba jikinta ,ta na mai tambayar ta ba abinda ya faru da ita,"Hey Jesus wannan wanne irin tashin hankali ne haka,jini fa na ke gani anan ,oh father lord waɗanne mahaukatan ne suka shigo miki har cikin Room su ka aikata maki irin wannan rashin imanin,okay okay kamata yai in natsu,in san me ya kamata in taimaka mi ki da shi, ko dai tashi za ki in kai ki Hospital in ya so in muka dawo sai mu yi reporting ɗin case ɗin,domin lafiyar ki na gaba da komi,wai su ***** su ka aikata maki haka,kuma har su nawa ne ?", Cikin sheshshekar kuka,muryarta ɗauke da zallar tsora,gami da razani ta ce mata,"Fredrick ne ya shigo min","...Mene Fedrick ?",Ruth ta tambaya cikin mamaki,da kanta tai tayi amfanin wurin yi mata comprming ɗin zancen da ta gaya mata "Ko da yake me yasa tun farko ba ki kira Resfetion kin sanar da su ya ake ciki ba, sai ki zauna ya illata ki a banza a wofi","Na rasa mafita Ruth,gabaɗaya a ɗimauce na ke ,ya rufe duk wata hanya da zan nemi taimako, babban abinda ya tsaya min a rai ta yanda ya shiga Room ɗin,na rasa gane ta yanda akai hakan ta faru", Jadeeda ta faɗa ta na mai ƙanƙame jikinta da zazzaɓi ya fara rufe ta," Ah abun a bayyane ya ke ,da sa hannun wani a cikin faruwan haka,dan haka bari in kira Hotel Manager idan mun ga hakan bai yi aiki ba,sai mu yi reporting wurin Police",..."A no kar ki kira su I'll handle it,tunda dai ba abinda ya faru da ni,na gode ma Allah","Kamar ya ki na nufin a bar maganar,kenan Fedrick ya ci banza akan duk abinda ya aikata ma ki,kin kuwa san illar da hakan za ta haifar maki anan gaba ba,idan ba dan Jesus ya aiko wancan mutumin ba da yanzu ba wannan labarin ake ba". Zaune Jadeeda ta tashi,"Bari ina zuwa",ta faɗa muryarta can ƙasa ta na mai nufar hanyar fita,ta na tafiya ta na rangaji,"Jeeey ina zaki a cikin irin wannan halin bai kamata ki fita ba",Ruth ta faɗa ta na mai son tare ta. Sai da Jadeeda ta dafa bango kafin ta ce da Ruth"Zan je wurin sa ina son in yi mashi godiya,daga nan kuma in duba hanunsa ,domin sanda ya tafi yana zubar da jini,kar wani abun ya same shi,da buƙatar in ga halin da ya ke a ciki". "A'a ki yi haƙuri ki bari sai zuwa da safe yanzu dare ya yi kuma kina buƙatar hutu",......kasa tsayawa Jadeeda tai ta saurareta ta cigaba da tafiya ta na rangaji gami da niyar faɗuwa,a haka har ta isa bakin Door ɗin ta fara Knocking,Ruth na biye a bayanta ta na taimaka ma ta a duk sanda taga ta na niyar faɗuwa, kasa iya haƙuri tai ta cigaba da knocking ɗin akai-akai,sai da su ka ɗan ɗauki lokaci kafin ya zo ya buɗe ma su. "Kkk....ki..kkk .ka zo mu je Hospital karda jinin ka ya ƙare wani abun ya same ka,in wani abu ya same ka ba zan taɓa iya .....",ta kasa iya idasawa sakamakon tafiya da tai luuuu za ta daɗi,da sauri ya tarota,yana girgiza ta gami da tambayar me ke faruwa da ita,cikin hanzarin ya shigar da ita ciki domin ya bata taimakon gaggawa, Allah ya taimake su cikin ƙanƙanin lokaci ta dawo cikin hankalin ta,dama sakamakon buguwar da ta yine,a sanda ta faɗi kanta ya bugu da tyle. Idanuwanta ta fara buɗewa ganin ta da ta yi kwance a kan bed ɗin ta kuma a bedroom ɗin ta yasa tai saurin tashi zaune gami da fara waige-waige don son ganin ina saviour ya ke,"Ruth ina ya ke ba dai kin bari ya tafi ba tare da na yi masa godiya ba ?",ta ce ta na mai dafe kanta. "A'a bai tafi ba ya je ya siyo maki maganin da za ki sha,ko kya samu ki samu ƙarfin jikin ki". "Ni fa ina lafiya shi ya kamata ya je a duba shi,domin jinin shi na zuba kar wani abu ya same shi","Kin ga ki kwantar da hankalin ki ba abinda zai faru da shi,tuni jinin ya bar zuba,don haka ki natsu,idan ma baki yarda ba ki jira yanzu zai dawo in ya sosai ki gani da idanun ki". Suna cikin wannan batun sai ga shi ya shigo hannunsa ɗauke da ledar magungunan da ya siyo,"Ya jikin na ki fatan ba kya jin wani ciwo a jikin ki,baya ga ciwon kan ?",ya tambaye ta"Ba na jin komi ya hannun na ka an yi treating ɗin sa ko","Ina lafiya tuni na yi treating ɗin wurin,don haka don't setress you self,ki na buƙatar hutu",da kai ta ba shi amsa ,nan yai mata ƴan allurorin da zai mata ya ba Ruth magungunan ta bata kafin yai masu sai da safe ya ya tafi,bayan ya jaddada masu da sun ji wani motsin da ba su yarda da shi ba su kira Receiption su sanar da su. Tun da ya fita Sallahr Asuba bai dawo ba kai tsaye ya wuce labrary da ke nan kusa da su don yin wani research, Jadeeda kan jikin ta da sauƙi sai ɗan abinda ba za a rasa ba,tun da ta tashi ta ke fama Zarya ƙofar Room ɗin sa,tun a zuwan ta na farko ta tabbatar da baya ciki,amma duk da haka ta kasa iya haƙura da zuwa. "Jeeyyyy ya kamata ki sahale ma kan ki wannan zaryar ,tun ɗazu ki ke faman zuwa bayanan,zai fi ki zauna ki huta"....." Ruth ba za ki gane ba,so na ke in mashi godiya,in masa sallama ba zan so in tafi ba tare da na sake ganin sa ba,ko kin manta Flight ɗina zai tashi around Eleven ,Amma yanzu har past ten ,ta ya hankali na ba zai ta shi ba,rayuwarsa fa ya sa a cikin haɗari saboda ceton tawa rayuwar,don haka kin ga kenan ya na buƙatar girmamawa, sadaukarwa ko ma fiye da hakan". "Na sani mana ya yi deserving duk abinda ki ka faɗa amma ko ba komi ki zauna ki huta har yanzu ba ki gama komawa normal ba","Haka ne Ruth amma ki sani in naga condition ɗin da ya ke a ciki ne Zuciyata da ruhina za su samu salama da hutu amma yanzu cikin raba ɗaya biyu ni ke,ki sani ko da missing ɗin Flight ɗin nan na yi ba zan ji komi ba","Ba za ki missing ɗin Flight ɗin ki ba domin tafiyar ki tafi cigaba da zaman ki alkairi domin ba mu san abinda ka iya faruwa anan gaba ba,don haka ki sama ranki zaki tafi Abuja yau kuma shi ma za ki gan shi har ki isar ma sa da saƙon da ke ɗauke a cikin zuciyar ki,wai Jadeeda ba ki mamakin taimakon da wannan Musulum preacher yai maki ba,duk da kasancewar kuna da mabanbanta addini,da kin gan shi kin ga kamala da natsuwa a tare da shi,amma ba ruwan shi ya shiga cikin lamarin da bai shafe shi ba duk dan ya taimake ki". "Ruth kenan ai dole abinda ya tsaya min a rai kenan,ko kin san ba wannan ne gani na da shi na farko ba","Kamarya dama kin san shi ne?","Yeah na san shi,shine Special Doctorn da ya duba Momy last jinyar da tayi wanda na ke baki labari,he is so kind and humble, maganar shi akwai natsuwa,tafiyar shi akwai natsuwa,shigar shi akwai natsuwa ke impact komi na shi akwai natsuwa a ciki,kar ki so ki ga jajurcewar da yayi akan lamarin Momy shiyasa na ke son in Jaddada masa godiyata kafin in bar Garin Lagos,shi mutumin kirki ne,ba zan ɓoye maki ba zuciyata ta ba shi wani matsayi mai girma a cikinta,ban yi tunanin samun taimakon Jesus daga wurin wani musulmi ba,sai ga shi ya shigo cikin lamarin ya ɗauki lamarin ,ya ɗauke shi tamkar ƴar'uwar sa ya riska a cikin irin wannan halin". "Irin haka na faruwa,akwai mutane masu halin kirki irinsa a mabanbanta wurare a faɗin ƙasarnan,don haka ki ɗauke shi a matsayin ɗan saƙo daga Jesus domin ya ce-ce ki a hannun Fedrick".Haka suka cigaba da tattauna batun har ƙarasowar time ɗin tafiyarta. "Sister Jadeeda da alama dole za ki haƙura ki tafi ba tare da kin samu haɗuwa da shi ba","A'a No ni ba zan iya tafiya ba","A'a Jadeeda kar ki yi jayayya da ni akan wannan maganar domin na fiki gaskiya,ba famu san abinda ka iya faruwa a yau ko gobe ba,dan haka ki tashi mutafi,in yaso ko saƙo ne sai ki bar masa a Receiption ","A'a Ruth ba zan iya tafiya ba",....."Dole ki tafi Jeeyy idan kuma kin nace akan ba zaki tafi ba,zan kira Papa ko Momy in sanar da su abinda ya faru",a ɗan dame Jadeeda ta kalle ta tare da cewa,"Haba Ruth don me za ki faɗi haka"..."To ki yarda ki tafi a yau tun jiya ki ka ɓata zancen da kin yarda an yi Reporting case ɗin da ba haka ta faru ba,yanzu fa a kodayaushe Fedrick zai sake dawowa,idan kuma kin ce za ki dawo apartment ɗina nan ma ba tsaro domin,Fredrick ya fi samun lasisin shiga cikinsa fiye da nan". Haka ba dan Jadeeda ta so ba suka fara shirin tafiya,Ruth na jaye da ɗan ƙaramin trolyn, Jadeeda kam jiki duk yai sanyi komi ta kasa,sai Ruth ke komi da kanta,a Receiption su ka tsaya bayan sun yi Checking Out, Jadeeda duk ranta bai so ba haka ta ke komi. "Ruth please mu ɗan ƙara jira ko na wani gajeren lokaci ne,ina ji a Zuciya ta kamar yana gab da dawowa","Haba Jadeeda mun fa jima mu na jiran shi,kar hakan ya sanya lokaci ya ƙare ki yi missing Flight,hakan ma wani sabon matsalar zai haifar". "Ruth na roƙe ki just give some minutes in har bai dawo a tsakanin wannan time ɗin ba na haƙura zan tafi kawai"."Just give ten minutes ko","Eh haka na buƙata ",gefe su ka samu gami da samun ɗaya daga cikin jerin kujerun da su ke a wurin duk zauna suna mai cigaba da zaman kurame gami da jiran tsanmani. Tun Ruth na duba wrist brace ɗin da ke ɗaure a hannun ta har ta koma kallon Jadeeda kawai,ta fidda rai yau ba makawa sai Jadeeda ta ƙara kwana a cikin Lagos ba tare da ta tafi ba,sai ga shi ya shigo cikin natsuwa da kamala ya nufi wurin Receiptioniss ɗin da ke kula da gun don amsar key ɗin sa,anan ya ke sanar da shi ana jiran shi. Sai a lokacin ya waiga ya gan su a wurin farin ciki kwance akan fuskar Jadeeda,hannunta ta ɗaga ta na mai cewa,"Hy ya ka ke,ya hannun na ka ya keda fatan dai da sauƙin ?". Sai da ya maido hankalinsa gaba ɗaya a gare su,kafin ya ce da ita,"Alhmdllh ina samun sauƙin,kar ki fa wani damu ba wani ciwo ne babba ba, zai warke nan ba da jimawa ba da izinin Allah". "Haka ne Doctor by the grase of God,tun ɗazu na ke ta faman jiran ka na kasa tafiya saboda ina so in yi maka bankwana tare da miƙo ƙarin godiya ta a gare ka,don yanzu haka na kusa yin missing Flight ɗina,Bai fi saura 15mnt Flight ɗin mu ya tashi ba","Ah ba wani abu ki yi tafiya ki,ki manta da duk abinda ya faru,domin abinda ki ka ga na aikata ya zame min dole na ne,domin duk wani aƙili ya ga abinda ke shirin faruwa dake zai aikata fiye da abinda na aikata,sai dai ina son in shawarce ki,akan game da abinda ya so faruwar da ke,domin in kina ganin kin tsira a yau ba ki san me gobe za ta haifar ba, sannan ko ba dan ke karan kan ki ba,za ki iya ceton wasu matan daga faɗa wa cikin irin wannan masifar,ki nemi wani na ki ki sanar da shi ko kuma ki yi Reporting ɗin sa zuwa gurin Police",sosai ya bata shawarwari masu amfani a taƙaice. "Zan yi kamar yanda ka ce ba zan kyale jinin da Fedrick ya zubar maka ya tafi a banza ba,amma ina da tambaya guda ɗaya","Ina jin ki fadi kai tsaye ","Shin nan ma ka zo ne a matsayin Special Doctor kamar yanda ka je can Abuja". Sai da Imam Jaheed ya saki wani gajeren murmushi kafin ya bata amsa da cewa,"A'a ba na zo nan a matsayi na na Doctor ba ne,na zo ne kan taron da zamu gudanar wanda ya shafi Addini,ko da wata tambayar ya ce da ita","A'a babu saura kawai dai zan so in sanar da kai ba zan taɓa mantawa da irin taimakon da ka yi min ba,kusan zan iya cewa ka bani farin ciki a cikin sauran rayuwar da ta yi min ragowa,zan so wata rana nima in saka maka da wani abu mai girma anan gaba in mun sake haɗuwa". "A'a da ba ki ci wani dogon buri akan haka ba domin ni na aikata abinda na ke ganin ya dace ne ,Kinga kenan No need ace za ai reponding ɗina da wani abu ba". "Hakan ba wani aibu ba ne da shi,sai dai kawai zan yi fatan haɗuwata ta uku da Kai ta zama silar mai kyau ba irin wannan da ta faru ba","To Shikenan Allah ya amintar damu akan haka,sai wata rana"...yana kaiwa nan ya juya da nufin barin wurin ita ma ta cire ƙafarta da niyar tafiya taji igiyar takalmin da ke sanye a ƙafarta ya kwance,hakan ya sa ta duƙa domin ta ɗaure,shi kuma a dai-dai lokacin ya amso key ɗin sa shirin nufar Room ɗin sa. Har cikin ran shi ya ji baiji daɗin ganinta a cikin irin wannan halin ba,sanye ta ke da bon short iya cinyarta sai wata riga da ko cibiyarta ba ta rufe mata ba,kasa iya barin wurin yai,ya nufi inda ta ke ya na mai cire coat ɗin da ke a jikin sa ya ɗaura mata a ƙugunta,ba tare da ya ce da ita komi ba ya bar gun,su duk biyun sakin baki su kai suna mai bin sa da idanu har yaɓace ma ganin su..... Page 35 Sosai Hall ɗin ya cika da manyan Malamai,manyan mutane ma su faɗa a ji irin su Sheikh Kabir, Alaranma Musa Kaduna, Sheikh Yahaya,da dai sauran manyan Malamai wanda kasa ke ji da su ,Cikin tsari suka fara gudanar da taron su,dan gane da maudu'in su wanda ya shafi haɗin kai Mazhabobin Addini,har zuwa sanda aka kira Imam Muh'd Jaheed,wanda ya ke wakili daga Kano, domin kora na shi bayani,ya fara da yabo da godiya ga Allah subhanahu wata'ala gami da yin kirari wa fiyayyen halitta Sayyadi sadati Muhammad Rasulullah,aminci da yabo su ƙara ninkuwa gare sa,kafin ya ɗora da cewa,. Addini wani babban ginshiƙi ne da ke taka muhimmiyar rawa wajen gyara zamantakewa, ɗabi'a da fahimtar rayuwa. Duk da cewa akwai bambance-bambancen akidu (imanoni) da tafsirin addinai, duk da haka yawancin addinai suna ƙarfafa wasu manyan abubuwa masu amfani ga rayuwar ɗan’adam. Ga wasu daga cikin abubuwan da addini ke ƙaruwa da su ta hanyoyi mabanbanta bisa akidu: 1. Horo da gyaran ɗabi’a (Kyawawan Halaye) Kusan dukkan addinai suna koyar da: Gaskiya Hankali da ladabi Girmama na gaba da iyaye Haƙuri da gafara Misali, a Musulunci, akwai koyarwar akhlaƙi kamar su Ikhlās (tsarkakakken niyya), taqwa (tsoron Allah) da husn al-khuluq (kyakkyawar hali). 2. Ƙarfafa dangantaka da Ƙalubale (Emotional Strength) Addinai daban-daban suna koyar da yadda za a jimre da ƙalubale ta hanyar: Addu’a Tawakkali Sabar jarrabawa Kyakkyawan zato ga makoma 3. Zaman Lafiya da Jituwa Wasu akidu suna kiran mabiya su zauna lafiya da kowa koda ba mabiyansu ba ne: Kiristanci: “Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar yadda kake ƙaunar kanka.” Musulunci: “Allah ba ya gafarta wa wanda ba ya gafarta wa wani.” 4. Gina Al’umma mai Taimakekeniya (Social Solidarity) Zakka a Musulunci Sadaka a Kiristanci 5. Tsarin Rayuwa (Guidance and Discipline) Addinai suna kawo tsarin rayuwa kamar: Lokutan ibada (sallah, addu’a) Ka’idar abinci da tsafta (Halal, Kosher) Haramtattun abubuwa kamar zina, shaye-shaye, sata, ƙarya Haka yana sa mutum ya rayu da natsuwa da ka’ida. 6. Ƙarfafa Dangantaka da Mahalicci Ko da addinai suna da akidu daban-daban dangane da Mahalicci, sun haɗu wajen: Bada muhimmanci ga bautar Ubangiji Dagewa cikin ibada da kula da ruhaniya Kiran mabiya su zamto masu aminci da tawakkali 7. Ƙarfafa Tunanin Mutuwa da Lahira Musulunci da Kiristanci suna da akida akan lahira, Aljanna da Wuta A ƙarshe: Ko da bambancin akida, addinai suna haifar da amfani mai yawa: Gina zuciya Koyar da zaman lafiya Ƙarfafa al’umma Shiryar da ɗabi’a Duk da irin amfanin da addini ke bayarwa ga ɗaiɗaikun mutane da al’umma baki ɗaya, yana kuma fuskantar matsaloli da ƙalubale iri daban-daban – wasu daga ciki na cikin gida ne, wasu kuma na waje ne da suka shafi zamantakewar duniya. Ga bayani dalla-dalla:️MATSALOLIN DA ADDINI KE FUSKANTA A TA FUSKAR MAZHABOBI (AƘIDU) 1. Rikicewar Fahimtar Akida da Fassarori Mutane da yawa suna fahimtar addini daban-daban, suna ƙirƙirar tafsiri bisa son rai ko ra’ayoyi na wata ƙungiya. Hakan yana iya haifar da: Ƙiyayya tsakanin mazhabobi ko sekto-sekto Rarrabuwar kawuna Tashin hankali da yaɗuwar ƙarya bisa sunan addini 2. Tasirin Tsattsauran Ra’ayi (Extremism & Fanaticism) Wasu suna amfani da addini wajen: Wuce gona da iri (radicalization) Kisa ko tashin hankali bisa sunan jihadi, crusade ko tsarkakewa Wannan yana bata sunan addini, duk da cewa mafi yawan mabiya su masu salama ne. 3. Amfani da Addini don Fa’idar Kai (Manipulation) Wasu shugabannin addini na amfani da matsayinsu wajen: Wawashe dukiyar mabiyansu Yaudarar mutane da annabtar ƙarya Wuce iyaka wajen karɓar sadaka ko kuɗaɗe Wannan yana sa mutane su rasa amana da gaskiya a cikin addini. 4. Raguwa ko Fita Daga Addini (Secularism & Atheism) A wasu ƙasashe, musamman masu tasowa, mutane da yawa: Suna watsi da addini baki ɗaya Suna komawa “Free thinkers” ko “Spiritual but not religious” Saboda: Ƙin amincewa da shugabannin addini Son rayuwa mai 'yanci ba tare da ƙuntatawa ba Wani lokaci rashin iya amsa tambayoyin zamani cikin hikim 5. Sabanin Addini da Kimiyya Akwai tangarda tsakanin addini da kimiyya, musamman a batutuwa kamar: Halittar mutum (evolution vs. creation) Magungunan zamani da tsarin haihuwa Fasahar jikin mutum (organ donation, cloning, IVF) Hakan yana hana yarda da cigaban zamani a wasu addinai ko ke jawo matsaloli tsakanin matasa da dattawa. 6. Matsin Lamba daga Zamani (Modernization & Globalization) Rayuwar zamani tana ƙalubalantar: Tsare-tsaren ibada Shari’ar aure, gado, tafiyar da iyali Kyakkyawan ƙyale-ƙyale da kyawawan ɗabi’u A wasu lokuta, addini yana fuskantar koma baya ko barazana daga kafofin watsa labarai da al’adu na kasashen waje. 7. Hadin Gwiwa da Siyasa (Religious Politics) A wasu kasashe, ana amfani da addini wajen yaɗa siyasa ko mulkin zalunci Idan gwamnati ta yi kuskure cikin addini, to mutane sukan ɗora laifi ga addinin Ko kuma idan wata ƙabila ta ƙwace addini, hakan na iya sa sauran ƙabilu su ƙi bin shi 8. Rigima Tsakanin Addinai (Inter-religious Conflict) Rikice-rikicen da ke tasowa saboda: Tashin hankali tsakanin mabiya addinai daban Ƙiyayya da zargi tsakanin musulmi da kirista, hindu da muslims, da sauransu Rashin zaman lafiya da rashin haɗin kai Taƙaitawa: Addini yana da matuƙar amfani, amma yana fuskantar matsaloli kamar: Rashin fahimta Tsattsauran ra’ayi Kiyayya da siyasa Barazana daga kimiyya da zamani Haka dai taron na su ya cigaba da tafiya cikin natsuwa,. Da ya zo ƙarin fashin baƙi yayi gane da dogon sharhuna Imam Jaheed yai inda ya ɗauki ɓangaren,Siyasa a Addinin Musulunci,inda yai bayani game muhimmanci da hakan yake jawowa da kuma ,rashin fahimtar da ke ciki da kuma tashe-tashen hankalin da hakan kan haifar,sosai taron ya faɗakantar ya wayar ma da mutane da kai game da abinda ya shige masu duhu,daganan bayan a tashi Jaheed luggage ɗin sa yai parking ya taho gida Kano ,inda Allah ya taimake shi by 8pm ya na Gida. √√√√√√√√√√√√√√ Sosai ran Jaheed ya ɓaci sakamakon samun labarin tun tafiyar sa Ummu Nurain ta bar Gida,haka ba dan ya so ba ya nufi Part ɗin shi ya watsa ruwa gami da haɗa ma kan shi shayin Coffee ya sha,ya dan kishingiɗa saboda a matuƙar gajiye ya ke inda ma Allah ya taimake shi ya gama sauke duk wani Nauyi na Sallah a kanshi. Motsin da ya ji ne ya sa ya ɗan waigo don don ganin waye ke tafe,cikin zazzaƙar muryarta mai ɗauke da ladabi da kwantar da kai wacce ke sanya natsuwa ga mai sauraro ta yi masa sallama,bayan ya amsa ne ya ce da ita,"Ba dai girki ki kai min a cikin wannan daren ba ?","To ya zan yi ba dole na na shiga kitchen ba don ka san ba zan iya barin ka kwana ba tare da ka ci wani abun ba,wa ma yasan yaushe rabon ka daka ci wani abinci mai gina jiki",Duk Gimbiya Ayush na wannan zancen ne ta na haɗa masa lafiyayyen girkin da ta haɗo masa. "Allah ya yi maki albarka,na ji daɗin hakan da ki ka aikata,har ban san da wanne baki zan iya bayyanar da hakan gare ki ba". "Kar ka wani wahalar min da kan ka iya wannan farin cikin da kuma albarka daka samun sun wadatar,bari in je Gimbiya Fadeela na jirana kadan tun zan dawo mu ka taho tare,ka santa ƴar daru ce,ganin wai ka dawo shine ta ke son tafiya","A'a kar ki barta dare ya yi zauna har sai zuwa Gobe da safe in Allah yakaimu in ya so sai ta tafin","Ni ma haka na ce mata amma taƙi,wata ƙila yanzu da kai ka sa baki za ta haƙura,bari in je Ina dawowa". "Amma da fatan dai kin fasa tafiyar?","Eh ya zanyi na kira Fulani na sanar da ita amma ta ce in bari sai zuwa Goben". "Hausa na ji daɗin haka to ta zamu yi da maganar zuwa Hospital ɗin,domin wallahi juriya ta ta fara ƙarewa,domin ina jin jiki akan haka","Aunty Gimbiya laifin ki ne tun ranar da ki ka zo Fada na ce maki washegari ki shirya mu tafi ki ka ce a'a,a bari sai lokaci kaza, to gashinan yanzu ya dawo ni kuma ban san ya za ai ba kuma". "Duk yanda zan yi zan yi domin in samu in fito cikin week ɗin nan in ya so da na samu damar haka sai in kira ki,amma kafinnan wanne Hospital ne ki ke ganin ya kamata muje inda ba zamu haɗu da idon sani ba ?",haka suka cigaba da hirarrakin su da yanda zasu tsara fitar ta su. "Anya kuwa Nabila ki na da zuciya a cikin ƙirjin ki,ki tafi ki bar Gida tun kafin faɗuwar rana amma sai yanzu za ki dawo,kina can kina yawan gal-gal ɗin ki,babban abun takaici da baƙin ciki ki rasa wurin wanda za ki sai wurin waɗanda su ke son ganin bayan Ahalin ki, wallahi kin ɓata wayon ki"...."A'a ni wallahi ki dai na danganta mi da mai gantali,ai gara ni ba da auren wani a kaina na ke yawo ba,wata kuwa tana nan zaune Mijinta ya yi doguwar tafiya ya dawo ma ba tare da ta sani ba".......zumbur Ummu Nurain ta miƙa,tare da cewa"Ke Nabila shin da gaske ki ke Abu Nurain ya dawo,ko dai tsokana ta ki ke,zo kiyimin bayani yadda zan fahimta,"A kan me ki je ki bincika", Nabila ta faɗa ta na mai shigewa cikin ɗakin don rage kayan jikinta. Wata tsohuwar Hijabi ta Baba Asabe da ke sagale akan ƙofar ɗakin Ummu Nurain ta janyo ta na mai sanya ta a bai-bai ba tare da ta damu da hakan ba,kai tsaye ta nufi ɗakin Mamasu tana mai cewa da ita,"Mama dan Allah akwai ɗari biyar a hannun ki ki ba mi","Ɗari biyar kuma Zeenatu mai za ki da kuɗi a cikin wannan daren,kuma ina zaki na gan ki sanye da Hijabi?". "Mama Nabila ce ta dawo daga Gidan Baba Malam ta ke ce min Abu Nurain ya dawo shine zan koma Gidana","Au au har kin huce ba zaki bari har ya gane kuren shi ya zo ya baki haƙuri ba?","A'a Mama gaskiya ba zan iya zauna wa a Gida in bar Mijina shi kaɗai ba,da dai ace ba Gimbiya Ayush to da shi ne fa zan iya zaunawa","Hmmmmm ke dai ki ka sani amma kar ki manta duk yanda za ki ki tabbatar da kin rama cin amanar dasu kayi ma ki,amshi maza je ki ki samu ko mai adai-daita sahu ne ya kai ki,amma fa kar ki bi hanyar da ki ka son za ki haɗu da Babanki","To Mama na gode sosai shiyasa na ke ƙara son ki", Ummu Nurain ta faɗa ta na mai amsar kuɗin ta fita, Allah ya taimake ta bata wani ɓata lokaci ba,ta samu abun hawa sanda za ta isa gida wajen tara da kwata,haka ta shiga Gidan sai faman baza sauri ta ke,kai tsaye ya nufi Part ɗin sa ta na mai fatan Allah ya sa yana ciki. "Abu Nurain barka da dawowa ya hanyar fatan ka dawo lafiya",shine abinda Ummu Nurain ta fara cewa bayan ta gama bubbuga ƙafafuwan sa a matsayin hanyar ta da shi daga barcin da ya kwashe shi,gefen kan shi kawai ya iya dafewa da ya ke jin ƙaruwar bugawar shi fiye da asalin yanda ya kwanta . "Zeenat meye haka dan Allah,daga ina ma ki ke daga cikin dare nan",sai da Zeenat ta Turo bakinta gaba kafin ta ce,"Na samu labarin ka dawo ne shiyasa ni ma na dawo". Gyara zama Jaheed yai kafin ya ce da ita,"Yanzu dan Allah baki ji kunya ba ki sa ƙafa ki bar cikin Gidan Auren ki na sunan ba tare da sanin Mijin ki ba,shin mi ye ribar da ki ka samu daki ka aikata hakan,me zaman Gidan ya amfanar da ke?". "Au laifina ma ka ke gani kenan,ba ka ga irin cin fuskar da ka aikata min ba,ka ɗauki Matarka ka tafi da ita ba tare da sani na ba,shiyasa mi ma nai tafiya ta Gidan mu na bari in ka dawo sai in dawo","Oh really tunda dama Auren kin ɗauke shi abun wasa ko,to fita ki bani wuri","Haba Abu Nurain kamar fa korata ka ke,na dawo fa domin ka ne,dan Allah kayi haƙuri,bari in samu wani abu mai ɗan sauƙi in dafa maka na san kana jin yunwa,ko Kanada wani abun daka keson ci dai in girka ma ka".....ya katse ta yanami komawa ya kwantawa,",Kar ma ki wani wahalar da kan ki domin ba na jin yunwa a ƙoshe na ke","Kamar ya a ƙoshe ka ke,me hakan ke nufi?","Wadda tasan daraja da ƙimata ta dafa min na ci,ta hutashshe ki,don haka sai ki tafi ki kwanta ki huta domin na ga alamar ki na buƙatar haka". Wani kuka ne ya kwace mata har sai da ya ba Jaheed mamaki ya tashi zaune ya na kallonta,,"Allah ba inda zani ina nan", "Me ye haka baki san dare ya yi ba ne ba?","Dare kuma ni wannan bai dame ni ba,kawai in ji dalilin da ya sa ka ci abincinta na ke son ji ","Au so kuke in zauna har kawo yanzu ba tare da na ci abincin ba ko in ya so yunwar tai min duk illar da za ta min baki da asara da hakan ko,kin ga dan Allah in har kin san tada min hankali ki ke son yi,ga hanya nan ki fita min a ɗaki ki tafi na ki ɗakin","Allah Abu Nurain ba inda zani sai na ji dalili",ta faɗa muryarta na ta tabbatar da hakan. "Na ce maki in har tashin hankali ki ke nema ki fitar min a ɗaki,na gaji ina buƙatar in huta kusan kwana uku bana samun wadataccan barci,ki bar Ni in huta",ko motsi Ummu Nurain bata yi ba balle ya sa ran ta ji abinda ya ce ba. Ganin da gaske ta ke ne yasa ya sauko da kan shi ya ja hannunta tafiyar da ita da ga cikin yana jan ta tana turjewa,har ya samu ya fitar da ita ya rufe ƙofar haka ta naji ta na gani tai ta faman knocking amma ya shareta,dole ba dan ta so ba ta nufi na ta Part da ya ga yi ƙura,ba tare da ta kakkaɓe ƙurar wurin kwanciyar ta ta ba. Page 36 "Hello Anesa akwai matsala wallahi na kasa jure yanayin da na ke ji ajikina,kullum ni ce cikin kasala,amai ga yawan ganin jiri dole akwai wani abun da ya ke faruwa","Subahanallahi ko dai maganin bai yi aiki ba neba Gimbiya ?",ta faɗa daga can ɓangaren "Ah haba Anesa sai dai wata matsalar amma ba wannan ba,ban fa taɓa bleeding kamar yanda ya faru a wannan abortion ɗin da na yi ba,na gaji da irin pretending ɗin da nake a duk lokacin da na ke tare da shi,ina tsoran kar ya fuskanci hakan". "To zai fi kyau ki koma ki ga Doctor tun kafin ki yi ma kan ki sagegeduwa","Anesa ba za ki gane ba ba lalle ya bar ni in fita a cikin waɗannan kwanakin ba,da zaran na gaya ma shi ina da buƙatar zuwa wani guri ɗayan biyu ce zata kasance ko dai ya kai ni da kan sa ko kuma ya sa cikin jerin ƙannan sa wani ya kai ni kin ga kenan ba a mutuba an karya wuya". "Kar ki bani kunya mana Gimbiya sai ka ce ba Mace ba,wai ko dai an sauya ki ne daga asalin Gimbiya Ayush ɗin dana sani ne, tambayar unguwa ya gagare ki,kin tsaya sai faman rayuwa da ciwo ki ke,to ki tsaya kar ki nemi dabarar da zaki amfani da ita,har kwaɗo yai miki ƙafa,ko ƴar irin ƙaryarnan ta Matan Aure da ɗan planing ɗin da su ke haɗawa ba za ki yi ki samu ki cimma burin ki ba,to ki zauna har abun ya zo ya fi ƙarfin kan ki". "Anesa ni da na kira ki domin ki bani shawara kuma ki jajanta min akan halin da na ke ciki sai kuma ki ɓige da gaggayamin maganganu"....."Allah ya huci zuciyar ki Ran ki ya daɗe ni ba haka na ke nufi ba,kawai dai ina son in nusar da ke kuskuren da ki ke son aikatawa kan ki da kan ki,amma yanzu duk ba wannan ba,yana Gida ko bayanan?","Ba ya nan, Uncle ɗin shi ya kira shi zasu yi wata tattauna akan kasuwanci su","To maza ɗau Car key ɗin ki da mayafin ki ki kama hanya ki tafi sai kin yi nisa sannan ki tura masa text ki ce da shi,wani uzuri mai girma ya ta so maki kin fita inkin dawo za ki yi masa bayani","Ki na ganin in na yi hakan ba abinda zai faru ?","In sha Allah ba abinda zai faru idan ki dawo ki Kirani ina jiran ki",jiki a sanyaye Gimbiya Ayush ta aje wayar hannunta zuciyarta na kai kawo gami da aikata abinda zai fishshe da rayuwar ta. "Kai tafiya zan yi,hankali na ba zai kwanta ba ina son in san halin da na ke a ciki,ko ma me zai faru na ji da shi daga baya, shawarar Anesa ita ce abun ɗauka bari ki gani",ta na kaiwa nan ta zari mayafin ta fita,sai da ta tabbatar da ta yi nesa da Gida kafin ta fidda wayar ta,ta fara kiran Fadeela,",Hello Fadeela kina Hospital ɗin ne ?","Eh Gimbiya ina fatan dai lafiya dai ko","Eh da sauƙin dai gani nan zuwa in na zo zaki ji komi",ta na kaiwa nan ta maida hankalin ta wajen ta tura masa text kamar haka,"Habibi I'm so sorry,na fita ba tare da izinin ka ba,wani lamari ne mai girma ya taso min da zaran na dawo zan yi maka bayani yanda za ka fahince ni, Allah ya tsare min kai sannan ina maka fatan nasara game da abinda aka fita nema" ,tana kaiwa nan ta kashe wayar gami da saita hancin Motar ta zuwa hanyar da za ta kai kanta Hospital ɗin da Fadeela ke aiki". Ko da isarta ba su wani ɓata lokaci ba ta shiga aka fara yi mata a scanning ɗin,gami da sauran tests ɗin da zasu ƙara tabbatar da abinda ke damun ta,wanda su ne suka ɗan ɗau lokaci kafin fitowar su ,Office ɗin Fadeela ta koma ta samu wuri ta kwanta dan kwata-kwata ba ta jin ƙarfin jikinta ko kaɗan,sai da ta huta dan kanta sannan ta tashi,"Wai Fadeela har yanzu sakamakon scanning ɗin bai fito ba ?","A'a Aunty Gimbiya tun ɗazu aka kawo kawai na ga kina buƙatar hutu shiyasa ban barki ki ɗan samu hutu","Okay to mene ne sakamakon result ɗin ?","Ban buɗe ba na bari sai kin farka",Buɗe mana don mi na ƙagara in san me ke damu na,idan cutar da zan iya rabuwa da ita ce,in rabu da ita in huta",ta faɗi hakan ta na mai gyara zaman ta akan kujerar da take zaune a kai. A ɗan firgice Fadeela ta kalleta bakin ta na motsi amma ta kasa iya haɗa harafin da zata yi mata bayani da shi,kasa ce mata komi tai sai faman jujjuya papers ɗin hannunta ta ke,har dai Gimbiya Ayush ɗin ta gaji ta ce da ita,"Lafiya na ga kin tsare ni da idanuwa sai motsa baki ki ke ba tare da kin ce da ni komi ba ?","Gimbiya..... sakamakon ne ya zo ta fuskar da ba muyi zato ba","Kamar ya wata muguwar cutar ce na ke ɗauke da ita ?","A'a ba wata cutar da ki ke da ita,kawai dai You are still pregnant,cikin jikin ki yananan bai faɗi ba"....."What...Amma dai tsokana ta ki ke ko?",a kiɗime Gimbiya Ayush ta miƙe tsaye tare da cigaba da cewa,"Haba Fadeela wannan wanne irin wasa ne,a gaban ki fa komi ya wakana,ke shaida ce akan irin wahalar da na sha sai kuma ki zomin da irin wannan sankaran zancen". "Wallahi Aunty Gimbiya ba tsokanar ki na ke ba, wannan shine gaskiyar scanning da kuma duk wani test da akai maki ,cikin jikin ki bai fita ba,hasalim sai komawa baya da kwanakin da ya yi,"You are pregnant,gaskiya ne hakan kina ɗauke da ciki na tsawon wata biyu da ƴan kwana ki","Innalillahi wa'ina ilaihir raju'una wannan wacce irin masifa ce",shine abinda Gimbiya Ayush ta iya faɗa kenan ta na mai komawa ta zauna akan kujerar da ta tashi. "Kin ga Aunty Gimbiya ki kwantar da hankalin ki, wannan tamkar izina ce aka nuna miki ki natsu ki ki yi ma kan ki faɗa da kan ki,ki ɗau ƙaddara ki, ki haifi abinda ke cikin ki,kamar hakan shine ya fi dacewa da ke,wani na can da dukiya ya ke neman irin wannan kyautar da Allah ya baki amma bai samu ba,sai ke da Allah ya zaɓa ya baki ba tare da kin wahala ba,mai zai sa ki wofintar da wannan kyautar, wallahi hakan kuskure ne,gabaɗaya ba ki da wani dalili da zai sa ki ce ba ki son ki haifi abinda ke cikin ki,in ba tsantsar nuna rashin godiya da kuma rashin tunani mai kyau ba".... "Kin ga Fadeelah ki dakata da wannan dogon bayanin na ki,domin maganar gaskiya ba zan iya barin Cikinnan a jikina ba,ban shirya haihuwa yanzu ba","Hmmmm Aunty Gimbiya ai ba ke ke da wannan ikon ba,tunda har ki kai kuskuren samun cikin ki bari ki haife shi mana,in ya so sai ki ɗauki duk matakin da za ki ɗauka mana a gaba".... " Ki dakatar da wannan batun da ki ke domin ko kusa ko kaɗan ba za su sami muhalli a cikin Zuciyata ba,tambaya ɗaya zan yi maki za ki taimaka min in fidda cikin nan ko a'a,shin kina tare da ni za ki tsaya a bayana ko ya ya?". "Ko kusa ko da wasa babu hannu na a cikin wannan lamarin,sai dai ina so ki sani ba zan daina faɗa maku gaskiya ba kina kan ƙadamin da za ki aikata babban kuskure wanda ba ki san me zai iya haifar mi ki anan gaba ba,kina ikirarin ki na son Mijinki sai dai kalaman ki da duk abinda ki ke aikatawa ba sa tabbatar da hakan,ina jiye maki tsoran randa zai fahimci mummunar fuskar ki dake ɓoye a bayan hijabi,idan hakan ta kasance kar ki yi kuka da kowa ki yi kuka da kan ki"..."Riƙe mugun fatan ki domin ba abinda zai same ni da zaran na ida nufi na zan kira ki ki tayani celebration", Gimbiya Ayush na kaiwa nan ta zari jakarta ta nufi hanyar fita tana tafe tana mai dafe kanta dake faman sara mata,"Ki tsaya in mai da ki Gida", Gimbiya Fadeela ta ce da ita,"Kar ki damu zan iya kai kana Gida",da haka ta bar Office ɗin. Ko da isar Gimbiya Ayush kai kawo ta cigaba da yi, mabanbanta tunanin nika na ta zuwan mata a cikin Zuciyarta,ta na jin ba makawa sai ta fitar da cikin ba za ta iya barinsa ba. A firgice ta juya sakamakon jin an dafata ta baya,"Honey ka tsorata ni kwata-kwata ban ji shigowar ka ba,ban ma tsanmaci dawowar ka yanzu ba",ta faɗa ma shi muryarta a diririce,"Ba dole na in dawo Gida ba kin turo min irin wannan saƙon kuma kina kashe waya,Me yake faruwa,kina lafiya kuwa .". Murmushi ƙarfin hali ta saki game da fara waige-waige,tarasa da wacce kalma za ta yi amfani wurin yi masa bayanin yanda zai fahimta,''Kin ga ki natsu faɗa min ina ki ka je,kin ce in kin dawo za ki sanar da ni komi,yanzu ina sauran ki,Doctor Faisal Abokina ya kira ni ya sanar da ni ya ganki a Hospital ɗin da ya yake, me faruwa wani abun ya na samun ki ne?"....."A'a...a'a ni ba abinda ke damuna ina lafiya","Ban yarda ba gaskiya idanuwanki ba su tabbatar da hakan ba,faɗa min me yake damun ki","Tooooo Na je dubiya ne a Hospital ɗin wata ƙawata Mubaraka to ita a kwantar na je dubawa","Mubaraka kuma wace ce haka ,Ni ban san wannan sunan a cikin ƙasashen ki ba","Ayya ko dai ka manta dai amma Aminiyata ce ta gaba-gaba","Okay na ji ,ina tunanin na manta ta yanzu gaya min ina ki ka je,wacce matsala ce da har tai tsamari ki ka fit ba tare da kin iya jira na dawo ba,ko dai Dubiyar ki ka je ne kawai?",. "Ai jikin Bara'atun ne aka kirani ake sanar tana jin jiki,shine fa hankalina ya tashi har na tafi na ga halin da ta ke ciki kar rabon ganawa ya ƙare","Bara'atu kuma ba Mubaraka ki ka ce ba?"......."Yauwa Eh Mubarakar na ke nufi",tsuru yai mata yana kallonta kafin ya ce da ita wani abu wayar shi tafa ringing hakan ya dakatar da abinda ya ke son cewa da ita,",Ina ka tafi ne ka barmu da aiki mutane sai faman tambayar ka su ke",Kawu Salihi ya faɗa daga can ɓangaren,"Kawai ayi haƙuri ganinan dawowa wani ɗan uzuri ne ya taso na zo Gida amma ganinan zan dawo","To Shikenan ka yi sauri domin so na ke a yau a gama cinikin filayen nan,ko mun samu mu sallame masu su mu huta","Ayi haƙuri ganinan dawowa". "Ki kula zan koma in na dawo ma cigaba daga inda muka tsaya,na fara fahimtar da akwai abinda ki ke ɓoye min tun dawowa ta da ga Abuja",......sororo Gimbiya Ayush ta yi tana mai bin bayan shi da kallo ƙirjinta na tsananta bugu,"Bai dai Habibi ya daɗe da fahimtar Cikinnan na nan bai fita ba in haka ta kasance ina cikin halaka ban san kuma ta ina zan fidda kai na ba",haka dai ta cigaba da tunaninnika a cikin ranta zuciyarta sai aiyana mata abubuwan da za su iya faruwa ta ke masu kyau da kuma akasin haka. ✓✓✓✓✓✓✓✓✓ "Abban Jadeeda ba zan gaji da baka haƙuri ba,domin gazawa ta ta bayyana ƙarara,na kasa iya taimaka maka da wani abu dangane da wannan rashin lafiyar da ka ke fama da ita tsawon shekaru Ashirin da biyar,duk da Alhmdllh akwai nasara a tattare da samun lafiyar ka amma,ina ɗaura laifin faruwar hakan a kaina,ba zan huta ba har sai na ga sanda bakin ka zai buɗe ka yi min magana da kan ka,ka kira suna na da daddaɗar muryar ka,zan so in ga ranar da zaka taka ƙafarka kamar yanda kowa ya ke takawa zan so mu zaga gari a tare ba tare da tunanin wani abu zai iya faruwa da kai ba,in rayu da kai kamar yanda kowacce Mace ke rayuwa da Mijinta,in dafa maka Abincin,in yi maka kwalliya don ka yaba,wata ƙila ma in da rabo in haifa Maka kyawawan yara kamar irin Jadeedar mu da muka rasa a baya".....ta kasa iya cigaba sakamakon kukan da ya ci ƙarfin ta,ba tai nisa a cikin kukan ba ta dakatar da kanta ,da murmushi ta maye gurbin kukan tare da cewa,"Oh baka son ka ga ina kuka ko?,to na daina ka ga ma na share hawayen",ta kai zancen ta na mai goge hawayen da hannayenta tare da cigaba da cewa,","In sha Allah komi ya kusa zuwa ƙarshe da akwai wani program da zamu gudanar da zaran mun halarci shi da izinin mahalicci za ka warke,komi zai wuce,ka cigaba da sani a addu kasan Allah na saurin karɓa Addu'ar Miji ga Matar sa",ta kai zancen ta na mai gyara masa rigar shan iskar da kejikin sa gami da ɗaukar allurar sa ta yi masa",bayan ta sanya masa kaya marasa nauyi a jikinsa,duk ta na waɗannan zantuttukan da kanta ne amma shi ko motsi ba ya yi iya kacin ta kwantar ta tayar in buƙatar hakan ta taso , . Page 37 "Ah aha,ya na ga abincin haka ba dai har ka ƙoshi ba,domin na ga kamar baka ci wani abin kirki ba", Ummu Nurain ta ce ta na mai bubbuɗe Food flask ɗin,ba tare da ya bar abinda ya ke ba ya ce da ita,"Na ƙoshi ne,ki haɗo min shayin Coffee na fi buƙatar shi a yanzu","Haba Abu Nurain duka-duka me kaci a cikin wannan abincin ,kuma tun ɗazu ina kula da kai gaba ɗaya hankalin ka ba ya kan cin abinci kafi karkata akan aikin da tun da ka shigo ka ke yinsa,na rasa wanne irin aiki ne da tunda ka shigo ka rungume system ɗin ka ko san ajewa ba kayi". "Ki yi haƙuri Ummu Nurain aikin ne ya zomin a ƙurarren lokaci,kin san gobe 28 to ina son in sallami duk wani ma'aikaci dake ƙarƙashi na ya ke kuma saran zai sami Albashin sa a Goben,kuma maganar abinci da ki ke,na ɗan ci wani abun ne kafin in shigo nan,zan fi son Shayin Coffeen a yanzu". Turo baki gaba Ummu Nurain ta yi gami da fara tattara kayan wuri guda,"Ka je can ka ci gurin wata ko,Hmmmmmm na rasa har sai yaushe komi na Gidannan zai dawo dai-dai,ita gata matar so ko",...."A'a Ummu kar ki ɗauki alhakin ta domin ba ki san gaskiyar abinda ya faru ba kuma abinda na ci ba daga gare ta ya fito ba","Ko ma daga wurin waye mi ba ruwa na domin kasan zan girka ma ka abinci ai,da wannan tirtsetsen cikin in tashi in ta fangan-fangan wajen ganin na girka maka abinci da za ka ci,sai ka ɗan yi Spoon da bai fi uku ba ka ce wai wani ka ƙoshi,ai ba adalci a ciki ,ai ko ba komi ko dan halin da na ke ciki ka ji tausayi na ka ci abinci ko ba dan in ji daɗi ba". Zazzaro idanu waje Jaheed yai ya na mai binta da kallo mai tarin mamaki,sai ya kalleta sai ya kalli flate ɗin da ya ci abinci ,shi dai a zahirin abinda ya ke gani a cikin plate ɗin ya ci kaso mafi yawa daga cikin abincin amma ga shi tana cewa wanda ya ci bai fi Spoon uku ba,ta na ankare da shi,har a cikin ranta tana cewa,ai baka ga komi ba sai na haɗa plan ɗin da zan dawo da ɗana gaba na ba tare da ka so ba,kana ji kana gani dole ka haƙura, "Allah ya baki haƙuri ba zan kuma aikata hakan ba",ya faɗa yana mai kama kunnensa",Af nasan haka za ka ce dama ai da Matar so ɗin ka ce ai ba za kai kuskuren aikata hakan ba balle" ......"Ya Salam Zeenat wai me yasa ba za mu taɓa zama mu tashi tsakanin ni da ke ba tare da kin ambaci sunan Gimbiya Ayush a cikin zancen ki ba,shin me ye alfanun da ki ke samu a ciki in kin ambaci sunan ta,alhalin ita in har ba ta yi dalili ba hakan ba zata faru daga gare ta ba?". "Ai dama na san in har za ka danganta ni da ita to ni ce zan kasance mai laifi a ciki ,kuma ai abun a bayyane ya ke ni ta shigarma cikin rayuwata ta yi bake-bake,ta hana ni gaba ta hana ni baya,ka ga kenan dole in sata a cikin raina gami da ambaton ta a kowane batu nawa,Ni da ban shiga rayuwar ta ba ai shiyasa ba ta yawon ambatona a zancenta,ita kuwa kullum shiga ta ke cikin rayuwa ta na yi min mulkin kama karya a cikinta". Ɗaga hannun Jaheed sama yai tare da fara addu'a ya na cewa,"Yah Allah ka kawo min ɗauki a cikin Gidana,ka shiryar min da wannan Matar ta wa,ka rage mata zafin kishin nan da ya ke damu ta gami da ɗawainiya da ita",kasa iya cewa komi Ummu Nurain tayi sai faman bin shi da idanu da ta ke,domin lamarin na shi ya kai ta ƙarshe har ta zama speechless akan sa. "Ni fa ba wani abu na ce ba naga kin zuba min ido,kar ki sauya min manufa, Addu'a na yi ,kin san ba ni da wani buri a yanzu da ya wuce ace na ga Gidana ya zauna lafiya, sannan kuma in ga kin sauka lafiya,na tabbata da zaran kin sauka lafiya duk wannan tsiwar da neman fitinar da ke damun ki za ki bar su"...."Au dama kana fatan irin wannan abun alkairin a gare ni,ai na so ace itama ya zuwa yanzu itama na ta cikin yananan ,in yaso itama ta haifu ta ji irin wahalar da ake ji,in ya so itama ka fara fuskantar canji daga gare ta ,zama uwa ba wasan ne ba,raino da kula da yara ba na sangartacciyar mace ba ne ba". "Kin ga dan Allah mu kawo ƙarshen wannan lamarin domin na ga ya fara tsanani,don ban shirya kwana cikin tashin hankali a yau ba so Please mu kawo ƙarshen sa haka,zan iya samun Shayin Coffeen ?",tutturo baki ta fara yi gami da ɗaukar kayan da ta haɗa ta bar Parlon har ta dawo da Shayin Coffeen a hannunta ba ta saki fuskarta ba,yanayin yanda ya ga tana tururi bakin ne ya sa ya saki murmushi gami da ture System ɗin da ya ke amfani da ita gefe tare da cewa,"Allah dai yasa Babyn da za a haifo min ba zai biyo wannan neman rikici da wannan tsiwar ta ki ba". "Ai kai ma kasan duk abinda ka ga ina rikici a kansa to an taɓo ni ne,ko kuma an dainne min haƙƙina shiyasa zan tanka","Wannan Zeenat ɗin da na sani a baya ce ke da irin wannan halin amma ba ta yanzu ba",ya faɗa yana mai karɓar Black bhazar Coffeen da ta kawo mashi. "Me ka ke nufi da wannan maganar da ka yi yanzu,shin kana nufin da akwai ban-banci Zeenat ɗin yanzu da ta baya?",Sai da Muh'd Jaheed ya gyara zaman shi kafin ya bata amsa da cewa,", Banbanci mai yawa ma kuwa, Zeenat ɗin da na sani ƴar gayu ƴar kwalisa ce,mai aji mai natsuwa ga tsabta,komi nata cikin takatsantsan ta ke yin shi, ba ta da hayaniya,bata gardama bare a kai kan jayayya,ga girmama na gaba da ita,uwa uba ta iya tsantsara kwalliya da duk kalan nau'ikan suturu karma in tai shigarnan ta ƙananan ƙaya sai in ji kamar in ɗauke abata in Goya don burgewa",ya kai zancen fuskar shi ɗauke da shauƙin abinda ya faɗa,kafin ya ɗora da cewa,"Ban san ya a kai ba wannan Zeenat ɗin duk ta bar waɗancan kyawawan halayen da na santa da su,tun farkon cikin Nurain komi ta sauya ban san dalili ba,ko ƴar kwalliyar ma bana samu,ya kamata ki koma yin gayun ki,ko in siyo maki wasu sabbin ƙananan kayan domin kina Min kyau a cikin su,don har na tuna wata shiga da kika taɓa yi na wani ƙaramin skirt da kuma wata half ɗin riga,kin kusa tashin kaina da wannan wanka,har yau na kasa mantawa da shi . Da wata irin dariya Ummu Nurain ta kwashe,ta na yi tana kallon fuskar Jaheed,shima sai bin ta da idanunta yai,har sai data yi mai isarta kafin ta ce,"Amma Abu Nurain ka bani dariya taya da wannan ƙaton cikin zan yi Irin wannan shigar,ai yanzu ta fi ƙarfina baka ga muna da ɗa saurayi kamar Nurain ba,ta ya zan iya irin wannan shigar a gaban shi?","A'a Zeenat ba haka na ke nufi ,ina nufin in mun kasance daga ni sai ke,ai ba wai at random za ki riƙa sa su ba". "A'a Ni yanzu irin wannan shigar ba ta wani burge ni,taya zan sa kayan da za su bi duk su yi fitting ɗina ko motsin kirki in kasa ba wannan maganar,mu munci na mu zamanin mun bar ma ƴan baya,taya ina da wannan tirtsetsen cikin zan ƙarawa kaina wata sabuwar,in ma ji da wannan nauyin da na ke tare da shi","Akwai fa wasu na daban irin na ku na masu juna biyu,irin rigunan nan da su ka zarce gwuiwa ko wanda ba su kai su ba",......ta katse shi, da cewa,"Ni fa bana ra'ayin su,sai dai kayi haƙuri Allah Zuciyata ta fara raya min don cikin nan ba a jikin ka ya ke ba shiyasa ka ke faɗin haka da kasan nauyin da mu ke ji da ba za ka ma fara irin wannan zancen ba". Rasa me ma zai ce da ita yai sa bin ta da idanu da ya cigaba,",Hmmmmm Ni ka ga tafiyata na fara jin barci,sai ka taho",da wannan ta yi shigewarta ta bar shi ya na bin ta da idanu √√√√√√√√√√√√ "Hibba kallo ake kenan,na ga na shigo sai sallama na ke shiru ba ki amsa ba hankalin ki nakan television",Ummiey Maryam ta ce ta na mai shigowa ta samu wuri ta zauna a cikin Parlon. "Wallahi Ummiey Maryam idanuwana ne kawai akai amma kwata-kwata ba na gane me su ke cewa","Ah aha wai wannan taronnan meye ne,kusan sau biyu ina zuwa in iske kina kallon shi ?","Taron Ester ne da ya gudana a wata Church dake Lagos,shine fa wannan tashar su ke ta yawan haskaka shi,Ni kuma kin san da kallon ba cika damuna yai ba shine ban damu da in sauya tasha ba". "Ikon Allah yanzu wannan kyakkyawar Yarinyar da ke tsaye Crista ce ba musulma ba?","Sosai ma da alama ta yi zurfi a cikinta irin ƴan na gada ɗinnan ne a cikinta,ina ma zaton kamar zabayar su ce","Kaico Kaico na kusa ince anyi asarar kyau anan dubeta kamar ki taɓa jini ya fito ni gani na ke ma kamar na taɓa ganin wani ko wata mai kama da ita","Ni ma kusan haka na ke ji akanta,tun ɗazu na ke kallon ta dalilin da yasa na kafe tvn da ido kenan amma na kasa gane asalin abinda na ke ji akan ta". "Kin ga watsar da wannan lamarin ga ƴar ki can ta zo sai faman rusa kuka ta ke,nayi nayi da ita ta faɗa min me ke faruwa ta ƙi","Ƴata kuma wacce wa ki ke nufi?", Momy Hibba ta tambaya a mamakance. "Zeenat mana yanda ki kasan wacce aka yi ma mutuwa haka ta shigo cikin Gidannan,inda Allah ya taimake ni ma ba wani wanda ta haɗu da shi daga cikin Mazan Gidan","To fa Allah ya sa lafiya,ko wannan karan me ya faru Allahu a'alamu","Ke dai bari tashi mu je ke ki tambaye ta wata ƙila ke ta sanar da ke abinda ke faruwa". A tare su ka bar Part ɗin da a yanzu Momy Hibba ke rayuwa da ita da Majinyacin Mijinta su ka nufi Part ɗin Ummiey Maryam,har suka isa gursheƙan kukan ta ke,da ƙyar Momy Hibba ta samu ta lalleshe ta kafin ta yi shiru ta fara sanar da su abinda take son sanar da su,kuma dalilin zuwan ta,"Ummiey ku ya fe ni,ban yi niyar zuwa in sanar da ku abinda ya ke faruwa dan in tadar maku da hankali ba, a'a sai dan kar nan gaba wani abun ya ɓullo ace laifi na ne tunda ni ce babba, wallahi Momy Hibba na gaji da irin rayuwar da na ke a cikin Gidan Abu Nurain kwata-kwata baya ganin ƙima balle mutuncina,ba ruwan shi da ni balle kuma haƙƙina da ya rataya akan shi,ko kwana na ne Part ɗin Gimbiya Ayush ya ke kwana,ba ruwan shi da ni,baya cin abinci na balle ai maganar kwana Part ɗina,idan nai magana ya ce na cika ƙorafi ba ni da haƙuri,ba yanda za ai magana mai daɗi ta shiga tsakani na da shi",ta ɗan tsagaita Kafin ta ɗora da cewa,Jiya mun samu saɓani ni da Matar shi,anan take yada min maganganu,ciki har da wacce tai mugun tada min hankali,wai ni sakara ce ba ni da zuciya,na yadda kare ya ɗauka,an nuna ba a sona amma na nace,anmin kora da halin na ƙi ganewa,to in jira har sai an yi min korar kare tunda ita nafi ganewa,kuma wai ko dawo da Nurain nan Gidan ba hakanan ta faru ba, anyi hakan ne da wata manufa,Ni babban tashin hankali na anan ko dai Abu Nurain ya sake ni ban sani ba na ke rayuwa a cikin Gidansa ban tafi namu ba?".ta na kaiwa nan ta sake fashewa da wani sabon kukan da iya ƙarfin ta. "Innalillahi wa'ina ilaihir raju'una wai duk Muhammad Jaheed ɗin ne ke aikata hakan ,ko dai ya samu matsala ne akan shi bai san illar da hakan zai haifar masa babbar gobe alƙiyama",Zaraf Ummu Nurain ta yi ta anshe zan ce da cewa,",Nima Ummiey abinda na ke gudun ma shi kenan, rayuwar gobe inda ba wani mutum da ya isa ya guje ma laifinsa da makomarsa", Cikin fushin Ummiey Maryam ta da ce ita,"Bar ni dashi zai gane kuren shi,tabbas sai na bi maki kadin haƙƙin ki da suka danne barima in kirasa"...."A'a Ummiey Maryam kar ki gaggawar yanke hukuncin,ki bar shi ba sai kin kira shi ba ba dai duk inda yake anjima zai zo ba,kin ga in kina kira shi yanzu ya san da maganar amma anjima sai dai kawai mu rutsa shi kun ga kenan dole ya faɗi gaskiya,to mu jira shi har zuwa sanda zai zo,tabbas sai ya yi dana sanin abinda ya aika","Kuma fa kin kawo shawara bari mu jira shi,ke kuma ta shi ki shiga wajen ƴan'uwanki Mata ki yi wanka ki shirya sai ki zo ki yi kalaci",da ha suka dakatar da case ɗin. Part 38 "Ah aha my dear Jadeeda ba dai har kin sallami baƙon ba,naga yayi wuri ace ya tafi tun yanzu,Ni da na so ace kun ɗauki wani lokaci mai tsawo ko kwa samu ku fahimci juna?","Mom I'm tried,nifa ba ƙaramar yarinya ba ce ,na rasa gane me ki ke nufi da turomin waɗannan guys ɗin". "Ina tunanin mun rigada mun yi gama wannan maganar da ke tuntuni ko,nace maki Aure na ke so ki yi,nan da wani gajeren lokaci". "Haba Mom Aure kuma?, wanne irin zance ne ki ke yi haka,at how comes zaki yanke ma rayuwata irin wannan hukunci,na rasa gane dalilin haka,last week kin kawo Johnson a matsayin baƙo kin ce in sauraren shi,yau kuma kin kawo David shima haka ce ta kasance,shin na yi maki wani laifi ne da ki ke son hukunta ni ta wannan hanyar ". "No my dear ba laifin da ki ka aikata min,kawai dai ina son in ga Auren ki shiyasa hankalina ya karkata akan in ga na samaki Mijin da zai dace da ke,ki yi Aure ki huta ki samu natsuwar hankali "....."Aure kuma da ni,kuma wai da waɗannan mutanen da ki ka kawo, a'a no Momy ban shirya hakan ba,kalli fa ga Uncle Miey da kuma Broth Edwin ba suyi Auren ba ,sai kuma ni, a'a idan ma Auren ne ki bari in kawo kalar type ɗin Mijin da na ke so in Aura mana". Miƙewa tsaye Momy ta yi gami da ɗaukar Car key nata tare da cewa da ita,"Waye ya gaya maki zaɓin ki na ke jira a'a zaɓi na za ki bi,ki sa hakan a cikin ranki,daga Johnson har David ɗin ba nayardawa a cikin su ,dukkanninsu sun fito daga Gidan dattako da kuma girma sannan kuma suna da arziƙin da hatta da jikokin ki ba zasu taɓa yin talauci ba,dan haka ban ga aibun wani a cikin su ba,ya rage na ki ki zaɓi wanda yafi kwanta miki a rai a cikin su ko kuma ni in zaɓa da kaina,yanzu ma haka fitar nanda zan yi tana da alaƙa da wannan maganar da muke,ina son nan da few months in ga na aurar da ke,ko hankalina zai kwanta in kau da mugun tunanin da ke yawo a cikin rayuwata"...."Momy mugun tunani kuma a kaina,shin ko kina zargin ko kina zargina akan wani abu ne,ko na sauya daga kan turbar tarbiyyar da ku ka ɗora ni akan ta ne?", Jadeeda ta tambaya cike da ƙarin mamaki. "Ko kusa ban taɓa kamaki da wani kuskure makamancin wannan ba,kawai dai zuciyata na faɗa min in Aurar da ke ,in sama maki Mijin dana yarda da shi gudun kar ko bayan raina wanda ki ka Aura ya cutar min da ke,ba zan iya lamuntar hakan ba". "Mom..... Haba nahhh ki bar irin wannan ƙananan tunane-tunanen ba su cika zama gaskiya ba fa"....."Ko ma mene Jadeeda ba zan fasa wannan maganar ba,ki sa hakan a cikin ranki,Jiya ma munyi magana da Johnson yace may be tomorrow zai dawo domin ku samu lokaci mai tsawo tare da shi sai ki shirya ma hakan"...Mom na kaiwa nan tai ficewar ta ba tare da sake bi ta kan Jadeeda da kuma abinda take son cewa da ita. Kai tsaye Madam Gloria Gidan ƙawarta da ke Gwarumfa mai suna Sister Tarisa ta nufa,"Ah welcome my friend Madam Gloria da har na fidda ran ba zaki samu shigowa ba kamar yanda ki ka ce", Sister Tarisa ta ce bayan sun zauna ta kawowa Momy abin sha. "Ina tafe My friend Yarinyar ki ta tsaida ni,da alama bore ta ke son yimin akan maganar Aurennan da na zo mata da shi". "Na san za a rina fatana ɗaya ace ba dai da itama Zuciyarta ta faɗa da son Richal ɗin ba"..."God for bid,da na shiga uku in haka ta kasan ce,tonuwar asiri na dai-dai ta ke faruwar wani lamari mai girman gaske,ban ma san ta ina zan fara fuskantar wannan lamarin ba". "Ai dalilin da yasa na ce ki dage ki ga kin haɗa Aurenta da ɗaya daga cikin waɗanda na lissafo miki,shikenan bakin ki alekum,asirin ki a rufe". "Shiyasa ai na zo wurin ki domin naga yiwuwar hakan kamar da wuya","To bari ki ji riƙe mata wuta za ki yi ,kar ki kuskura ki ɗaga mata ƙafa,da zaran kin ji tausayin ta ba iya makomarsa ba har da taki kin ruguza,za ki cigaba da dauwamar da ita a matsayin ƴar ki ta halaliya ne ta hanyar raba alaƙar da ke tsakanin ta da ɗan'uwanki Richal". "Ba na fatan zargi da tunanin da muke mi da Momy ya zama gaske akan shi,domin mudun haka ta kasance sai nasa yayi mugun regret","Kin san me kamata yai ki tare shi ki tuntuɓe shi da maganar idan har kin tabbatar da hakan sai ki dakatar da shi,ki yi mi shi warning na gaske,ki nusar da shi illar da hakan zata haifar ,Ni fa a wannan tafiyar banga abun gari a ciki ba,domin in har ya kasance soyayyar gaskiya ya ke mata bai kamata ya fallasa hakan har mutane ko duniya su sani ba,domin hakan a gare ta tamkar gurgunta asali da rayuwar ta zai yi ba". "Ta yani gani wai makaho ya so gulma,akan wannan lamarin na runtse ido ban ji daɗin makanta ba,ba na tunanin akwai wani amfani da zai samu idan har ya cimma wannan burin na shi". "Kin ga ƙawats Gloria har yanzu akan wannan lamarin zargin Richal mu ke bamu da wata hujja ko makama da zamu ƙarar akan shi game da abinda mu ke zargin nasa,don haka kar mu zafafa mu bi komi a hankali domin gano bakin zaren kar garin gyaran gira a rasa ido kuma". "Anya kuwa Sister Tarisa zan iya riƙe kaina akan wannan lamarin,ina tsoran kar batun nan ta daɗe in kasa iya riƙe kaina","Za ki iya Mu Friend tunda har ki ka iya riƙe asalin sirrin da ke binne a ƙasa har kawo yanzu to wannan ma zaki iya ki bi komi a hankali za ki ga alfanun haka,ya ku ka yi da Mom Rebecca","Hmmmmm kar ki so ki ga yanda hankalin ta ya tashi kusan komi ya hargitse mata","Allah sarki ai nasan dole hakan ta kasance,na ga ma ƙoƙarin ta ","Kin san ita ta fara son fahimtar haka har sanar da ni,in ba dan ita ba da ban san sai zuwa yaushe zan fahimci wannan mummunan lamarin da ke shirun faruwa a cikin Gidana ba","Ki ƙara kwantar mata hankali by the Grace of God ba abinda zai faru",da haka su ka cigaba da hirar su gami da neman hanyar da zata zame masu mafita a gare su. Tun fitar Momy JADEEDA ke faman kai kawo,ta rasa wacce makama ya kamata ta kama ta wacce hanya za ta fahimtar da ita zuciyarta ba ta yarda da wannan ƙudirin da ta zo mata da shi ba, Uncle Miey da ta ke taƙama da shi yayi tafiya, Granny kuma ta je Jos ganin Gida,su ne kawai za ta faɗa nawa suyi ma lamarin tufkar hanci,Papa kam bata maganarsa tunda har Mom ta riga ta yanke wannan hukuncin to da saninsa da kuma yardar sa,dan a yanda ta san su tun yarintar ta komi bisa yarjejeniyar juna su ke tafi da shi,"Ko dai in je in sanar da Brox Edwin da abinda ya ke faruwa ko ba zai min maganin abinda,ai zai iya ba ni shawarar da za ta iya yi min amfani",ta ɗan dakata ta na mai jujjuya maganar a cikin ranta,"Kai bari dai in je mai yiwuwa ma mu haɗu ni da shi mu fahimtar da Mom haɗarin da ke cikin wannan al'amarin da take son sanya rayuwata a ciki",da haka ta tashi ta nufi Part ɗin na sa,ta na tafe ta na saƙawa da kwancewa a cikin ranta. "Broth Edwin!",ta kira sunan shi a hargitse,"Me na ke gani haka aman jini fa ka ke",Jikin shi na rawa ya bar gaban sink ɗin ya nufi inda ta ke,"Kin ga ki saurare ni,ba abinda ki ke tunani ne ba na ci wani abu ne shi ya janyo min faruwar hakan","Kamar ya ka ci wani abu,shine ya sa Jini ya ke fita har ta hancin ka", Jadeeda ta faɗa ta na mai girgiza kanta alamun ba ta yarda da abinda ya ce ba ba, Sosai ya matso kusa da ita har tana jin hucin zafin da jikinsa ke fiddawa,ya kama hannun ta tare da sanyaya muryarsa gami da aro natsuwa yaɗora akan fuskar shi,"Ki fahimce ni jiya mun fita ni da Friend ɗina ya ja ni mun je wani Club so acan na ci wani abinci da na ke da Algy da shi, so shine ne fa nake ta faman aman jini,kuma shima yau da safennan na fara yin sa"..... "A'a no Edwin you're liar,ban taɓa jin cewa kana da Algy da wani abinci na daban ba,biside ma fuskar ka bata gaskata abinda kake cewa ba,ka ga ka faɗa min gaskiyar me ke faruwa da kai,I'm promise ba zan faɗa ma kowa ba,za mu haɗu mu yi maganin duk matsalar da ta ke damun ka,kalle ni ka gani,Ni ce jeeyyyy ɗin ka,ƙanwar da ka fara riƙa a matsayin little sister na ka, wacce ka ke tare ma faɗa idan ta tono,wacce ka ke rago ma duk abinda ka ci a school,wacce ka nuna ma so fiye da kowa ,fiye da kai karan kan ka,na roƙe ka da ka faɗa min abinda ke damun ka,na daɗe da fahimtar kana rayuwa ne cike da wani miki ko tabo a cikin zuciyar ka tun kafin ka dawo,ka sani da damuwa na shigo cikin Room ɗin nan naka,na zo in sanar da kai wani abu da ya ke damuna,amma sai na iske halin da ka ke ciki ya danne damuwar da na ke a tafe da ita,na ɗauke ka a matsayin ɗan kuwa ɗaya da ɗaya da na ke da shi,wanda zai share min kuka na yai min maganin damuwar da na ke da ita,mudun ba zaka sanar da ni ainihi kuma gaskiyar abinda ke damun ka ba,to zan juya da tawa damuwar,na yarda kuma na amince nima tawa damuwar ta illatani ta saka ni cikin irin yanayin halin da ka ke a ciki"..... "No....No...no Jeeyyyy kar ki yi haka kar ki ce ba za ki sanar da ni damuwar ki ba,a shirye na ke in tunkari komi in har akan ki ne,ki sani za ki sake jefa ni cikin wata sabuwar damuwar ne muddin ki ka juya ba tare da kin sanar da ni abinda ki ka zo ki sanar da ni''. "Broz Edwin!....hawaye....hawaye fa ...kuka ka ke yi fa,hawaye ke zubowa daga cikin idanunka",ta ɗan dakata ta na mai kai hannunta ta dangwalo hawayen don son tabbatarwa agaresa,kafin ta ɗora da cewa,"Kenan hakan ya na nufin duk abinda ka faɗa ba gaskiya ba ne ba ko ?", Buɗe baki yai ya na son cewa da ita wani abu,amma ya kasa bakin sa sai rawa ya ke gami da son cewa wani abu ba dama,"Ka ga ni ko,bakin ka ya kasa iya cewa komi domin dama bai saba furta ƙarya ba,don haka ka faɗa ina jin ka kuma ina tare da kai" . "My Jeeyyyy kar ki damu ko ki matsa akan sai kin san me ke damuna domin hakan sirri ne,zai fi kyau ki barshi in cigaba da rayuwa da shi ni kaɗai kuma matsayin sirri,na sani a idanuwan ku kuma ganin kamar ina cutuwa, to a gare ni wannan cutuwar tafi min akan in sanar da ku halin da na ke a ciki,a yanzu ni ke cutuwa amma da zaran wani ya sani Shikenan za mu koma cutuwa a tare,to me zai sa in cutar da wani akan wata ƙaramar matsala tawa?,zai fi kyau mu manta da hakan mu fuskanci abinda ki ke tafe da shi". "Ka juri abubuwa wahalhalu da dama kaina,ka Goya ni a bayan ka ,ka saɓa ni a bayan ka,ka ji da dukkan wasu ƙananin damuwowina,ka sanya ni farinciki a mabanbanta lokuta,sai yanzu zan kasa tsayawa a gefanka ,shin wacce irin ƴar'uwa ce ni mai son kanta,mai fifita son ranta a kan wanda ya saudaukantar da yarintar sa gami da kuruciyar sa a saboda ni ,idan har da gaske har yanzu ina da irin wannan matsayin a wurin ka,kuma kana ji na a cikin ranka kamar yanda na sani a baya,kuma ka na son kada in rayuwa a cike da zargin kaina akan ka to ka sanar da ni abinda ke damun ka a yanzu ba sai wani lokacin ba". Dafe kan shi Edwin yai gami da fara ja da baya,ya rasa makamar da zai tsaya da ita ,shi ya sanarda ita damuwar sa ko dan ya ji tata damuwar ko kuma ya bar ta tafi kowa ya riƙe ta sa damuwar,sai dai wani sashe na zuciyarsa na gargaɗarsa akan kar yai kuskuren sanar da ita domin zai iya yiwuwa,yai biyu babu,ya samu wata hanyar da zai bi da ita ta sanar da shi damuwarta ba tare da shi ya sanar da ita ta shi ba,don kar jifan gafiyar ɓaidu,ya zo tsana, gaba gami da distance ya shiga tsakaninsu madadin kusanci da yake tsakanin su ya ƙara ƙarfi,amma ina ya rasa hanyar ,tunani shi ya cure gami da takurawa guri guda,baya tunani a yanzu kuma a cikin halin da ya ke a ciki brain ɗin sa na iya tan-tance masa tsakanin fari da baƙi..... Part 39 "Ƙarfin zuciya bai zama da sauƙi ba, musamman idan kalmar gaskiya ta tsaya a maƙoshin wanda ya kamata ya faɗe ta",shine abinda ya fi tsayawa a cikin rai da zuciyar Edwin. A tsaye Jadeeda ke kallon Edwin, jikin shi na rawa, idanuwansa sun kumbura da hawaye, bakinsa ya kasa furta komi. Har yanzu bai faɗi komai ba. Sai kawai ya juya ya koma kan kujera, ya dafe kansa kamar wanda ke gudun tunani ya cinye shi. Jadeeda ta taka a hankali ta zauna kusa da shi, ta ɗora hannunta kan kafadarsa,tare da cewa,"Bro Edwin... ka tsorata ni," ta faɗa a hankali, murya cike da laushi. "Ba komai ne zai sa kai kuka ba, sai abinda ya fi ƙarfin zuciyar ka... kuma duk da haka kana ƙoƙarin ɓoye shi. Amma me yasa?" Edwin ya ɗan ɗaga kai, idanuwansa sun cika da wani irin zafin da ba za a iya fassara shi da kalma ba. Sai dai ya faɗa. "Na jima da ɓata hanyar da zan iya komawa asalin yanda ne ke,ki bar ni in cigaba da rayuwa a haka kamar hakan shi yafi dacewa da ni... Na rasa komai Jadeeda, na rasa kai na... kuma bana son ki rasa kan ki ke ma." Zuciyar Jadeeda ta buga da ƙarfi. Wani abu na cikin wannan maganar yana nuna cewa ba lafiyar jiki kadai ke damun Edwin ba... akwai wata annobar sirri da ke cinsa a hankali. "A'a Edwin, ba zan bari ka ɓace ba.ba zan bari ka sake cilla rayuwar ka cikin ƙaƙanikayi ba, Ka dade kana riƙe ni lokacin da duniya ta juya min baya. To yanzu sai na tsaya tare da kai har ka tsira, har ka murmure ka dawo asalin yanda ka ke,na yi alƙawari..." Ya riƙe hannunta sosai, kamar kar ya saki, kamar wannan ƙananan lamarin ne kadai ke hana shi ruɗewa gaba ɗaya,ya so ace ƙaramin dalili ne ke cin sa a ransa ,da ya sanar da ita ko ya samu ya kwanciyar hankali da natsuwa a saman fuskarta,amma ina lamarin ya sha kan shi ya kuma fi ƙarfin zuciyarsa. Sai kuma ya ce da ita a hankali kamar raɗa,"Jadeeda, idan na faɗa miki gaskiya, rayuwarki zata canza... wata kila za ki ƙi ni... wata kila za ki ƙi dukkanmu...ki tsane ni ki tsani kan ki da kan ki" Hawaye suka cika idanun Jadeeda, amma ta daure, ta ce:,"To ka faɗa. Koma me yene, faɗa ɗin kan ka tsaye. Sai dai ni ka sani ba zan juya maka baya ba na yi alƙawari akan hakan." Sai dai kafin ya buɗe baki ya ce wani abu zuciyar shi ta sake bugawa har hakan ya sa ya runtse idanunsa gami da dafa saitin Zuciyarsa, alokacin da Edwin ya dafe hannunta kamar yaro mai jin tsoro, ya rasa ko ya zauna ko ya miƙe tsaye. Kamar wanda za a yanke wa hukunci ne. Sai dai wannan karon… ba zai iya gudu ba,Ya buɗe baki da murya mai sanyi amma mai nauyin gaskiya,"Jadeeda… Ina son ki. Da gaske. Amma ba da irin son da ke da kyau wanda mu ɗauka kamar na ƴan’uwa ba. Ina son ki da zuciyata amma na san wannan so haramun ne…”,Zuciyar Jadeeda ta tsaya. Gaban ta ya fadi. Kamar a mafarki. Kamar ruɗanin da ba shi da fassara,ko motsin kirki ta kasa. “Wannan sirrin na damuna har tun kafin na san ke wacece. Amma tun daga lokacin da na fara jin ki,na saurare kalamanki, jin kukanki, jin karayarki so ya shiga zuciyata. Na ƙi amsa masa, na yi addu’a, na roƙi Allah, na karanta Littafi Mai Tsarki… na karanta inda aka ce “Kada namiji ya auri ‘yar uwarsa.”Na karanta inda aka ce“So da ƙauna su zauna cikin tsarki,amma ina Zuciyarta ta ƙi ji ,na kurumce gami da makancewa akan haka,na yi tur da halina na tsani kaina,na la'anci shaiɗanin da yake tare da ni har ya ke son ya cutar da ni amma ina lamarin ya fi ƙarfina ya girmi hankali da tunani na.” Sai ya runtse idonsa ya ce, “Amma duk da haka… zuciyata ta ƙi ƙyale ki. Kuma yau, na kasa ɓoyewa. Ban san yadda zan fuskance ki ba… amma na fi tsoron ƙarya da boye gaskiya.” Jadeeda ta zare hannunta daga nasa. Ta miƙe tsaye kamar wadda aka zuba wa ruwan sanyi. Hawaye na gangarowa fuskarta, zuciyarta na ɓari. Ta ce da karfi, kamar wadda ke magana da kanta,"Ka haukace Edwin,da gaske ka samu matsala a cikin kan ka,kana buƙatar,a duba lafiyar ka da gaggawa". Edwin ya durƙusa ƙasa, hawaye ya ƙi daina zuba. Sai dai shiru ne a bakinsa. Jadeeda ta fashe da kuka. Ta fuskance shi, ta ce da tsawa mai rauni,"Ka daina sona Edwin. Ka manta da ni! Ka manta da ni gaba ɗaya. Kai ba dan Krista na gari bane idan kana iya soyayya da ƙanwarka!” "Kin ga ki fahimce ni nasan da hakan haramun ne,shiyasa na zaɓi in rayu a cikin ƙunci da kuma ɗacin zuciya......ya ɗan dakata numfashinsa yana barazanar rabuwa da gangar ƙirjinsa,kafin ya cigaba da kokowa da shi. “Ko kuwa....dai .... ka sauya addini ne domin ka samu damar sona?,Domin Ni na san a cikin Bible, kaf babu inda aka halatta ɗan'uwa ya auri yar'uwarsa. Ko kuwa kai na na dab ne, Edwin?”,ba na tunani akwai wani addini a duniya da ya amince da irin wannan kwamacalar da ka zo min da ita". Edwin ya zube ya fashe da kuka mai ƙarfi. Bai iya ce mata komai ba sai dai numfashi ya dinga ja kamar mai shirin mutuwa. “Ina fata Allah ya gafarta maka,” ta ce cikin hawayen da suke ƙona mata fuska. “Ka ƙaryata tsarkin addininmu. Ka ƙaryata martabar ɗan’uwa. Ka ƙaryata ni.” Ta juyo da sauri. Bata waiwaya ba. Bata saurari komai ba. Ta bar Edwin a ƙasa, cikin ruɗani da sirrin da ya shanye zuciyarsa raunana gami da son tarwatsewa a lokacin. √√√√√√√√√√√√√√√ "Safina kin yada ni ba ki da kirki ko kaɗan","Hmmmmm Zeenat kenan to ba dole in ɗaga ma ki ƙafa ba kin san ni kin san hali na,in dai maganar gaskiya ta zo dole in faɗa maki ke kuma abinda ki kai hannun riga da shi kenan". "Na yi tunanin taren mu ta wuce mu bar wani abu ya shiga cikinta yai tasiri har ya kai ga shiga tsakanin mu,ki tuna fa tare mu kai yarinta,mu kai wasan ƙasa a tare mu ka yi karatu atare impact komi namu a tare mu ka yi sa,amma yanzu sai ki kwashe wani tsawon lokaci ba ki ziyarci inda na ke ba,in kuma ni na zo sai ki fara shamin ƙamshi,na kasa jure hakan abun ya na min zafi,ga shi kuma ban san dalilin faruwar haka ba". "Ba na son mu tsawaita zancennan mu bar shi kawai Zeenat","A'a Safina ba zan yi shiru a har sai mun kawo ƙarshen wannan lamarin,ki sanar dani abinda na yi miki ko kuma wani ne ya ke son shiga tsakanin mu ban sani ba ?". "A kan me wani zai shiga tsakanina dake,to idan wannan tunanin ki ke,to ki sauya in ma da akwai wanda ya shiga tsakanin tarayyar mu to ke ce da kan ki,haba dan Allah Zeenat mai ki ke so,mai ki ka nema ki ka rasa,da har ki ka maida rayuwar ki haka,kefa matar Aure ce amma kalli shigar da ke jikin ki,ko kunya ba kya ji ki kazo gidan Surukan ki da irin wannan shigar". "Ai Safina fuska za ki cimin kan na zo wurin ki domin mu sulhunta tsakanin mu,mu gyara ɓarakar da ta shiga tsakani tarayyar da mu ka gina tun yarinta,to wallahi na gargaɗe ki domin kin san tun da can bana ɗaukar raini balle yanzu da girmana har da igiyar Aure a kaina,kin san ko a cikin ƙawayen mu na fi ƙarfin raini wallahi ." "A da kenan ban da yanzu ko?,Ni ƴar'uwar ki ce ta haƙiƙa,bawai ina maki wannan zancen da sigar cin fuskar ba, a'a wallahi har cikin raina ina jin zafin yanda ki ka sauya ki ka mai da kan ki tamkar wata illitrate,haba Zeenat wallahi kin sauya ina mamaki gami da jin takaicin ssuyawar ki,na kan tuna yanda mu ka yi rayuwa dake ,komi na ki gwanin ban sha'awa ,kina ɗaya daga cikin ko in ce mace ta farko mai capacity acikin class mate ɗin mu,amma yanzu du babu,sabo duk kin zubar da shi,shin yaushe rabon da ki ga ɗaya daga cikin ƴan Click ɗin mu takawo ma ki ziyara,duk sun bari,domin duk wacce ta zo ta yanda ki ka banzatar da rayuwar ki sai ta ga ta wuce da ajinki sai ta bar ki,a duk sanda wani abu ya faru mu ka yi taro ko muka haɗu da wasu daga cikin sai an yi hirar ki gami da mamakin sauyawar ki,ina jin zafin haka domin tamkar ni ake suka in aka soke ki,amma ke kullum sake tsiro da sabbin halaye ki ke,ke ce rashin tsafta,haukan kishi kin biye ma Baba Asabe to ki sani son tarwatsa maki rayuwar Aure ta ke." "Safina duk kin san wannan ce-ce ku ce ɗin da ya ke faruwa amma ba ki taɓa zuwa kin sanar da ni ba,kenan gulmata ma kuka koma yi". "Na sha yunƙurin hakan amma duk sanda na zo da na fara yi maki maganar sai ki fusata ,ki nuna ma ba kya buƙatar jin labarin,kuma maganar gaskiya ba gulmar ki ake ba,kin aikata abinda za'a yi magana akan shi ne,Ni kaina ina baƙin ciki in zo gidan ki in ga yanda ki ke tafiyar da rayuwar Gidan ki,kamar ba Auren soyayya ku ka yi tsakanin ki da Yah Imam baamma komi a hauka ce cikin fitina da tashin hankali,duk da na san Auren ku na haɗi ne amma kafin Auren ai kun yi soyayya mai zai sa ba za ki maida wannan soyayyar ta zama linzamin gina rayuwar Gidan ki,ba ki ƙare kullum cikin baƙin ciki da tashin hankali." Ta ɗora da cewa,"Wallahi Zeenat ki gode ma Allah,wasu matan Mijin ma su ke nema amma ba su samu ba,ke kuma Allah ya baki kina wulaƙantawa,ki je ki cigaba watarana in kika zubar da garin ki kya koma cizon yatsa daga baya Shiru Ummu Nurain tai kamar Safina ta san ta taɓa mata inda ya fi sosa ma zuciya ta ciga da cewa,"Da za ki ɗauki shawara da kin gyara kuskuren da ki ka aikata na tsawon shekaru,har yanzu lokaci bai ƙurar ma ki ba,za ki iya mai faɗa soyayyar ki a cikin Zuciyar Yah Imam gama dana ba daina son ki yai ba halayen da ki ka tsiro ne ba ya so,kin ganni ko ba aure ne da Ni ba amma akwai abubuwa da dama da ki ke aikata su wanda ko karan hauka ya biyo ni ba zan iya aikata su ba". "Ba zaki gane ba Safina domin bana tunani haka za ta yiwu, Gimbiya Ayush ta tsare ko ina ,domin Abu Nurain ko kallon arziƙiba ya shiga tsakaninmu saboda ita ta shiga ta raba mu." "Ba wani shiga da tai ta raba ku,in ma ta shiga ke ce ki ka bata fuska,ta hanyar watsar da kan ki da ki ka yi,eh mana watsar da kan ki da ki ka yi mana,domin duk kin watsar da wasu responsibilities na ki na matsayin ki na matar Aure kuma Uwar Gida mai Capacity,ke kin zubar da na ki Capacityn ita kuma ta kwashe,ki farka daga nannauyan barci daki ke kwada ki gani in ba ki kwato Capacity ɗin ki ba,wai wace ce ma Gimbiya Ayush in ba matar cushe ba,don haka ki manta da ita anan ne za ki dawo da asalin ko ke wace ce,zamantakewar ki ba ya nufin ki banzatar da duk wasu buƙatu ko ra'ayi na Mijin ki ba."haka Safina ta cigaba da faɗawa Zeenat gaskiya da kuma hanyoyin da za ta bi don ta magance matsalolin da ta ke fuskanta a Gidanta,har zuwa sanda yamma ta yi. "Au ashe kana tafe na sha yau ba zaka shigo Gidan ba", Ummiey Maryam ta ce da shi tana mai gyara zaman ta,"Ina tafe Ummiey yau tun safe muna Companyn Auduga ne yau zamu fitar da kaya shine fa sai yanzu na shigo,na taho ne a hanya na haɗu da Nurain sun ta so Islamiyya". "Tooh ka Nurain maza je ka sashen Momy ka kira Ummanka ta na can". Da ɗan sauri Jaheed kuma cike da mamaki ya waigo yana son yi tambaya ,shi kuwa Nurain fuskarsa ɗauke da murmushi ya nufi inda aka aike shi,"Ummiey...Ummu Nurain ta zo nan ne,Ni a tunani na na baro ta Gida kuma ba ta sanar da ni zata zo nan ba?","Uhmmmm ta zo tananan",ta ba shi amsa a daƙile. Shigowar Momy Hibba da kuma Ummu Nurain ɗin ya hana shi sake cewa komi sai daman bin ta da ido da yake,a kallo ɗaya da ya yi mata yasan ba alkairi ne ya kawo ta ba da walakin goro a mita. Momy Hibba ce ta umarce ta da ta sake maimata duk abinda ta ce da fari,haka ta jero su,sai da wannan karon muryarta na rawa,ta kuma kasa yarda ta hada ido da wani a cikin su,sai a yanzu take dana sanin zuwan ta gidan gabaɗaya. "Mai ka ke son ka zama ne Muh'd,kana da da ilimi fa,shin baka san haramcin abinda ka ke aikatawa ba,me ye amfanin nuna banbanci ko fifiko tsakanin matan ka",sosai Ummiey Maryam ta ka sa ka shi a gaba ta inda take shiga ba tanan ta ke fita ba,shi ƙarshe ma rasa laifin me ya yi da har aka gurfanar da shi a wannan kotun,ga shi ko kusa ko da wasa Ummiey ta hana shi damar da zai yi magana ko ya kare kan shi, dole ba dan ya so ba ya bar ta ta yi iya yin ta,Duk abinda ake Momy Hibba ba tace komi ba sai bin su da Idanu ta ke a haka ta fahimci duk zancen da Ummu Nurain ta zo da shi ƙarya ne ba abinda ya faru a ciki ,ƙarshe Momy Hibba ta yanke hukuncin su ta fi da Nurain in ya so kullum a riƙa tura Driver ya riƙa ɗauko shi,motsin kirki kasa yi yai,zuciyar shi cike da ƙuna amma ba halin ya bayyanar da hakan ya rasa me ye a cikin kan Zeenat da ta ke aikata irin wannan aiyuka da duk mai hankali da tunani ba zai aikata ba,haka ya kwashe su ya su ka nufi Gida,jikin Zeenat kam a sanya ye ko haɗa ido da shi kasawa ta yi.. PAGE 40. ❤ "Wallahi Nurain ka matsa ka bani wuri ,tun kafin in bud`e idanuna in sa ka a cikin su,a yi Yaro sai fitinanniyar rigama d`an barcin safen ma ba zaka barni in yi ba haba dan Allah....", sautin muryar da ta ji ne ya sa ta tashi a firgice ba tare da ta shirya ma hakan ba,ta sake fad`awa cikin kogin tunani a lokacin da tai Arba' da shi zaune a kusa da ita,sake murza idanuwanta ta yi ,ilai kuwa shine zaune a gabanta ba gizo Zuciyarta ta ke mata ba," Good Morning Ummu,yau Abbunah yai min wanka da wuri kuma ya had`a min breakfast na ci na k`oshi, ke ma ga naki nan mun taho maki da shi",Nurain ya kai k`arshen zancen ya na mai kinkimo farantin da breakfast d`in ya ke akai da sauri Imam Jaheed ya tarbo shi don gudun kar ya zubar,shi ko sai faman washe baki ya ke. Su duka biyun ta bi da kallo ji ta ke kamar ba wa'inda ta sani kuma ta saba rayuwa da su ba ne a gabanta,sanya suke su duka da fararan kaya masu taushi,sai raba idanu take a tsakanin su kar ma Nurain da ta ke ganin fatarsa har wani glowing ta ke,tamkar an musanya ma ta shi,shar da su kamar ba su ba,ko kad`an bata ga alamar fushi ko damuwar abinda ta aikata ma shi a daren jiya a fuskarsa. Hankalin ta ya koma akan k`amshin abincin da ya aje mata nan da nan ta ji cikin ta ya fara kuwwa ba tare da ta jira komi ba ta duma hannu ta fara cin duk abinda ya tare mata gaba,ba ta tsaya ba har sai da tashi komi da ke jikin farantin, sai a lokacin ta mai da kallonta kan Jaheed da ya zaro idanunsa waje ya na binta da kallo. "Kin cinye komi ba tare da Kin tuna Cewar na ci ko ban ci ba, ga shi ko hannu da baki ba wanda ki wanke ". Wata irin kunya ce from no way ta ji ta lullu`beta,kafin ta san me ya kamata ta yi ,saurin muryarsa ya sake ratsa kunnuwanta da kuma gangar jikinta," Yau a Gidannan gasar wanda yafi kowa kyau za ai,ki tashi ga ruwa can na had`a miki a bathroom,ni da Nurain mun shirya ke mu ke jira",jikinta ta bi da kallo sai dai tun kafin aje ko ina tai saurin kauda kanta,zani ne d`aurin k`irjin,gashin kanta kuwa ba a ganin tsagar kitsonta duk ya bi ya susuce. "Tashi mana kar lokaci ya k`ure mana da", ya kai zancen tana mai sauke tiren da ta ci abinci tare da tai maka mata don ta mik`e,jikinta duk ya mutu har wani sanyi ta ke jin ya na ratsata ba tare da ta san daga ina ya ke fitowa ba, bai barta ba har sai da ya tabbatar da ta shiga wankan kafin ya koma wajen Nurain ya bashi kayan wasa yanda za su d`auke masa hankali. Tun shigar ta bayin kasa ta`buka komi tai Zuciyarta sai faman kai kawo ta ke gami da sak`a mata wasi- wasi kala da kala," Duk da kaancewarsa mutum mara rik`o da saurin fushi,Amma abun da ta aikata masa jiya ya yi wuri a ce har ya manta abinda ya faru a tsakanin su jiya da daddare,me hakan ya ke nufi,wannan sabuwar kulawar kuma ta me ye,Allah ya sa ba wani tarkon ba ne ya ke yunk`urin d`ana mata ba", da sauri ta kawar da wannan tunanin tare da cewa,"Aa shi ba haka ya ke ba mutum ne mai saurin yafiya,sannan baya rama cuta da cuta,eh tabbas haka ne yana yi min wannan kyautatawar duk dan in gane kuskurena da na aikata",ta kai zancen ta na mai tabbatar ma kan ta game da abin da Zuciyarta ta ke kitsamata,tun shigarta ba abinda ta aikata ta dai d`auki sponch da soap ta rik`e a hannunta daga nan fa ta tafi duniyar tunanin. Baya taja a d`an tsorace sakamakon d`agowa da tai ta ganshi tsaye a gabanta ya yi folding d`in hannayensa ya zuba mata kaifafan idanunsa ma su sanya mata mutuwar jiki,takowa yai har inda ta ke ya amshi sponch da soap d`in da ke rik`e a hannunta ba tare da ya ce da ita komi ba,hannu ya sa ya sa`bule zanin jikinta, da kan shi ya wanke ta tsab,tun tana kauce-kauce har ta gaji ta daina,har shaving cream sai da yai mata amfani da shi,kitson kanta da bai fi guda shidda ba ya tsefe su ya sa Shampoo mai k`amshi ya wanke kan,ita kanta jin kanta ta rik`a yi tamkar a wata sabuwar duniyar ko kuma wacce aka sabuntawa gangar jikinta. Bayan ya shafe ta da lotion, ya ciro mata wata pich d`in half da da k`adan ta wuce gwuiwarta,kanta kuma ya sanya mata Vanderner wacce ta bayyanar da gashin kanta daga baya,daga nan kuma yai mata `barin Brut perfums mai dad`in k`amshi ,cikin jikinta kuwa ya fito rad`au sai ma ya k`ara fitar da kyawun kwalliyar ta ta, ita kanta sake baki tayi ta na kallon kanta. "Anya kuwa za ai wannan gasar kuwa,tun yanzu na fara karaya", shine furcin da ya fito daga bakin sa tun shigowarsa. Rasa me ma za ta ce da shi tai sai binsa da tarin mamakin da yake bata tun safiyar yau,ba ma a Maganar tarin kunyar da ta kwasa,rabon ta da irinta tun farkon Auren su. " Shikenan an gama mataki na farko na gasa,saura na biyu",Zanin gadon da ke kan gadon ya yaye Wanda yai cud`u-cud`u da daud`a,har ma ba a iya banbance asalin colour d`in sa,sannan ya fara shifid`a wani,ganin hakan da tayi ne ya sa tai saurin kama ma shi suka shifid`a a tare,nan fa suka zage gyaran Gidan kowanne lungu da sak`o na Gidan ,wasu kayan ma in ya fitto da su sai ta ji inama k`asa za ta tsage ta shige cikinta ,hatta da Kitchen, Room d`in Nurain duk sai da suka bi suka gyara shi tsab,duk wani un use da kuma wanda ba zai wanku ko ya gyarubu sai da suka fitar da shi,tamkar sun sabunta komi,kayan wanki kuwa guri guda suka tara su da zumar kiran mai yi masu wanki ta zo ta zo ta wanke, sun gama sun zauna suna maida numfashin tarin aikin da suka sha,Yaron su Nurain sai kara kaina ya ke a tsakanin su wata magana da ya fad`i duk sai da ta sa su kai shock,"Ummu yau kin yi kyau,kin yi kwalliya ta yi maki kyau sosai ban ta`ba ganin kin yi kyau irin haka ba, ko dai unguwa za mu ne ?",ya k`are zancen da sigar tambaya. Da wayo su ka samu su ka kaudar da batun,ringing d`in wayarsa ne ya katse shi, ya d`auka ya na fara gaishe ta cikin girmamawa,kafin ya bata amsar abinda ta ce mi shi,"Eh Momynah yanzu na ke son in shirya na je can babban Gidan,in ga Ummie da kuma su Baba Malam "," Okay daganan sai ka biyo ina son mu tattaunawa akan wani abu mai muhimmanci ",Hibba ta fad`a daga wancan side d`in,da haka suka gama wayar ya mai da kallon shi kanta yanda ya ga tana yamutsa fuska gami da dafe bayanta ya sa ya fara jin tausayina,hanunshi ya kai yana mai tayata har zuwa k`afafunta kafin ya ce," I'm sorry na wahalar da ke da yawa ko,ki yafe ni ba nufina kenan ba"......hannunta ta kai da sauri ta rufe bakinsa tare da cewa,"Ba ka wahalar da ni ba ko kad`an,hasalima sai dai in ce ka taimake ni ne na sauke responsibility na da na kasa saukewa na tsawon wani dogon lokaci,thanks for being by my side,thanks you a lot My Husband, sannan kuma ina mai baka hak`uri akan abinda ya faru a jiya,ba zan kuma ,kuma na janye furucin da na yi mara dad`i,kuma ina tuba akan haka". Murmushi ya sakar mata yace,"Komi ya wuce a gare ni,ko kin manta ke d`in Sarauniyar Imam Jaheed ce,kuma kin san Sarauniya ba ta laifi,dan haka ki manta da komi,yanzu dai zanje Momynah na Kira kafinnan zan he wajen Baba Malam,ki kula da Gidan zan tafi da Nurain ko za ki samu ki huta". "To shikenan Allah ya tsare a dawo lafiya in ka je ka ce duk ina gaishe su". Nan ya tafi ya sake yin wanka shi da Nurain ya shirya su,su ka fito,saitin ta ya tsaya ya duk`a gami da kamo hannayenta ya rik`e ya na mai cewa da ita,"Zan tafi dan Allah kafin in dawo ki yi mana lunch domin na yi kewar abincin ki,zan so in tuna baya,ki sani har gobe har jibi kina nan a raina ina jin son ki a cikin raina ban ta`ba yunk`urin sauya ki da wata ba,ko wacce mace za ta shiga rayuwata sai dai ta biyo bayan ki,ke ce ta fari a gare ni,ina yi maki so mai yankan shakku,zan rayu da ke a cikin kowanne lokaci, dan Allah ki koma kamar Zeenat d`in da na sani bana son cigaba da gudanar da irin wannan rayuwar a tsakaninmu,ina cutuwa da hakan ,Nurain ma na cutuwa,hatta kan ki kina cutar da kan ki ba tare da kin farga da hakan ba,zan so mu cigaba da shinfid`a rayuwar mu kamar yanda muka fara tun farko kafin sauyi ya shigo tsakanin mu". Daskarewa Zeenat ta yi a zaunen da ta ke,ta riga da ta zama speechless,kafin ta samu damar da zata ce da shi wani abu ya kama hannun Nurain su bar mata Gidan cike da k`amshin turaensu. Zuciyar ta ce ta fara gaya mata gaskiya har ta kai ga fara fidda zance zuci a fili, "Wai dama da gaske har yanzu Abu Nurain ya na so Na ,to ya akai na I saka ki da damata ,tabbas Na d`aura d`amara can za duk wani abu mara kyau da na ke aikatawa ko dan dawo da martaba da k`ima ta a idon sa, ke kuma da ki ka shiga ki ka fita ki ka raba ni da Mijina ganinan gare ki ko ni ko ke mu zuba mu gani"... Bai kai ga fita ba sai da ya sake zuwa ya gano jikin Gimbiya Ayush ya ga da sauk`i kafin ya nufi can Babban Gidan. Lokacin da suka isa bai iske su Malam K`arami ba sun tafi wani taro hakan ya sa kai tsaye cikin Gidan ya nufa,bayan yai parking d`in motar sa a parking space Gidan gabad`aya an gyara shi an k`awarta shi da kayan zama ni dai-dai gwargwado,sashen Ummie Maryam ya nufa a zaune ya iske ta cikin ladabi ya zauna a gabanta tare da fara gaishe ta,"Jiya na dawo na biyu tanan aka ce ba kunan ke da Mama",ya ce da ita bayan sun gama gaisawa. "Eh mun d`n fita ne an yi rasuwa nan bayan layi,ya can gurin aikin Na ka komi dai lafiya ko,kuma Na Hibba ta sanar min Na ce wata k`ila gajiya ce ta hanaka ka tsaya ka jira mu?"," Alhmdllh Ummie,ina cikin shirin zuwa in gaishe ku sai ga kiran Momy ta na son gani na","Tooooo Allah ya sa dai lafiya ,ya mutanen Gidan,ina Nurain d`an rikici?",murmushi ya yi kafin ya bata amsa da cewa,"Tare fa da shi Na taho amma tunda mu ka shigo ya saki hannuna yai gaba ban san ina ya shiga ba". "Too Yana can ya shiga wajen yaraka tashi ka tafi wajen nata ,Na San yanzu tana can ta na jiran ka,amma kafin ka tafi ka zo ka amshi wani sallahu da gare ni,ka kai ma mara Lafiyar ",da to ya amsa kafin ya nufi hanyar da za ta kaishi Part d`in Momynta shi.. A tsaye ya iske ta sai faman kai da kawo ta ke, wanda hakan. Yasa ya ya ida sa kusa da ita da d`an saurinsa tare da cewa," Momynah lafiya dai ko ,ya jikin Uncle,, ina fatan ba abinda ya same shi ko ?".duk ya jero mata wad`annan tambayoyin ba tare da ya tsaya ba. Sai da ta dafa shi kafin tace da shi"Ka ga Yarona kwantar da hankalin ka ba abinda ya faru, zo zauna ka ji komi ". " Am ina Maganar taron k`aramar juna sanin da na ke ta ce maka za a yi a Canada to yau sun fidda nan da two days za a fara hakan ne ya sa na nira ka domin ka zo mu tattaunawa yanda komi zai tafi,Na Kira Yayah Nasir ya ce min zai shigo ko da zuwa yamma ne,daga yanzu sai ka kasance cikin shiri ,domin kai ne za ka je taron". Hankalin shi ya maido kanta ya na mai mamakin abinda ta ce ,"Momy ni kuma dama can tun tuni ni ki ke ma wannan shieye-shiryen tafiyar? ". " To AI dama kai ya kamata ka je ba ni ba,kai ne dubbunan al'uma su ke amfana da iliminka amma ba ni da kaina kawai na ke amfanawa ba". "Amma....Momy".....ta katse shi da cewa,"Ya isa haka tashi ka tafi Gidan ka fara shiri,ka sallami iyalan ka ,ni dama tuni Na riga da Na sanar ma da Baba K`arami, don har Na fara k`ok`arin yi maka booking d`in flight, amma dai na ga da yiwuwar sai dai ka bi jirgin yawo domin kamar akwai k`arancin tashin jirage a wannan satin sakamakon sauyin weather da mu ke a ciki". Ba tare da ya yi mata mu su ba ya amin ce da barinta nan ya zauna suka cigaba da tsara yanda komi zai tafi,kusan tare da Ummie Maryam su ka tsara komi ,har su Baba K`arami su ka dawo bai tafi ba ,kowa sai murna da farin cikin samun wannan babbar damar suke gani suke kamar hanyar ko damar samun sauk`in Abubakar ta zo,sai gab da la'asar ya bar Gidan. Page 41 Kiran dare ya ratsa kunne. An riga an gama addu'ar dare, an kashe fitilu. Dukkan gidan ya yi tsit kamar kabari. Sai dai Jadeeda ba ta iya barci ba. Kamar kullum, zuciyarta cike da damuwa da tambayoyin da ba su da amsa. A yau, wani abu daban ya faru,ta kasa iya mantawa da duk abinda ya faru tsakanin ta Bro Edwin,yanayin bugun zuciyar ta har yanzu ya ƙi komawa dai-dai,idan ta runtse idanunta,sai ta ji inama da ace komi zai gushe a cikin su,inama da komi zai gushe kamar bai taɓa wanzuwa ba,taya hankali da tunanin ta zai iya ɗaukar wannan lamarin,tsawon yaushe zata iya mantawa da abinda ya faru,wasu zafafan hawaye ne suka sake kwaranyowa da ga idaniyarta Motsin shigowa ta ji ya sa ta ɗan waiga,Uncle Miey,ya kama hannun ta ya yi, ya zauna da ita a ɗaya daga cikin kujerun da su ka yi ma Parlon ƙawanya. Akwai nutsuwa a fuskarsa kamar koyaushe, sai dai idonsa yau sun bambanta. Yana kallonta tamkar ba mutum ba ne. "Jadeeda," ya fara da murya mai laushi,"wannan yanayin bai kama ce ki ba,ki manta da da duk abinda ya faru ki ɗauka duk zancen da Edwin yai mi ki tamkar sun gudana a mafarki ne,kar ki bar su su zama wani dalili da zai lalata miki rayuwa ko ya jefa ki a cikin,ki manta da shi"......"A'a Uncle Miey wannan lamarin mai girma ne,ya fi ƙarfin in manta da shi haka da sauri, babban lamarine,a ce ɗan'uwana na jini ya bijiro min da batun soyayya ta ya hankali zai iya ɗaukar hakan da sauƙi?". "Shakka babu nasan maganganunsa suna da girma da saka nauyi a cikin zuciya amma bai kai ki bar sa ba,domin hakan zai iya yi miki illah",......."Illah kuma ta nawa Uncle Miey ai sai dai kar a kuma amma Bro Edwin ya dasa miki mai zafi da zurfi a cikin Zuciyata wanda ban san dare ko ranar da zan warke ba". "Zan cutu matuƙa idan har ki ka ce za ki cigaba da rayuwa a haka,cikin tunani da damu,ki sani kwata- kwata hakan bai dace da ke ba,na ji baƙin cikin faruwar wannan lamarin,ina so ki sani,ba zan iya jurar ganin ki a cikin wannan tashin hankalin ba,ki sani ba abinda ke damun Edwin sai hauka da kuma ƙuruciya da ke damunsa,in Banda haka ta ya zai iya fuskantar ki da irin wannan kalamin mai girma,tabbas ya aikata kuskure,ki manta da komi I'll handle everything kin ji". "Ba ni tunanin zan iya fita waje in haɗa ido da ɗaya daga cikin mutanen Gidannan,nauyin su na ke ji ina tsoran jin wani labari da baza iya ɗauka ba,bana son jin wani sabon labari wanda zai sake tada min da hankali,don haka ka bar ni na fi son kaɗaici a yanzu" "A'a a duk sanda na ke cikin damuwa ko tashin hankali ki na tsayawa tare da ni har sai na koma dai-dai don haka ba zan bar ki ba,zai fi kyau mu fita wurin ƴan'uwa, su kan su suna cikin damuwa da tashin hankali akan wannan lamarin". Cikin ƙarin tashin hankali ta fashe da kuka tare dacewa,"Uncle Miey ka bar ni,na fi son zama ni kaɗai,Mommy ta saka ni tsaka me wuya,ta kawo jerin sunayen samari wai dole sai na zaɓi ɗaya daga cikin su ,a matsayin wanda zan aura,ga Bro Edwin ya zo da wata sabuwa a cikin rayuwata,don haka zai fi Min kyau in samu wuri in keɓe ko na samu damar da zan sama ma kaina mafita"..…. A firgice Uncle Miey ya kusanto ta tare da cewa,"No....no..no ...kar ki ce dani Sister Gloria na neman haɗa ki Aure da wani ba tare da na sani ba,don me ya sa zata aikata hakan ?." Ya sake ta gami da fara kai kawo a cikin Parlon,zuciyarsa sai aiyana masa abubuwa kala daban-daban ta ke,tabbas gab ya ke da yin sake,me yasa ya cika zurfin ciki,me yasa ya ke son ɓoye gaskiya gami da son tauye kan shi,don me yasa Sister Gloria za tai yunƙurin kawo wani ko wasu da nufin son zaɓama Jadeeda Mijin Aure bayan dakon sonta da yake ɗawainiya da shi tun shekaru Ashirin da suka wuce. Ganin yanda hankalin shi ya tashi yasa Jadeeda tsura mashi idanunta,ganin tamkar ya na shirin zaucewa ya sa ta nufe shi gami da kamo hannunsa ta ce,"Uncle Miey kana lafiya wannan sauyin na mene ne,na ga duk ka rikice da ga jin wannan zancen nawa duk ka ruɗe har ma kafi ni shiga tashin hankali me yake faruwa?." Kasa ce mata komi yai sai jan hannunta yai ya zaunar da ita akan seater ya tsura mata idanu,zuciyar shi na tsananta bugu wani ɓangaren kuma na ingiza shi akan ya sanar da ita sirrin da ke binne a cikin Zuciyar sa tun da daɗewa kar ya bari ayi mishi Sakiyar Ciki,wani ɓangaren kuma na cewa da shi a'a kar ka aikata hakan domin za ka sake cilla rayuwar ta cikin wata sabuwa kuma ruɗaɗɗiyar ƙaddara,za ka ɓalle wani sirri mai girma na cikin rayuwarta,hakan kuma ba ƙaramin illah zai mata ba,to idan har ka ɓoye ka kasa faɗa mata ya zaka yi a randa ka wayi gari wani daban wani bare ya Aure ta ya bar ka da dakon sonta da ya ginu a cikin rai da rayuwar sa?, wannan lafazin da ya zo mi shi a raine ya ƙara hargitsa shi gami da sake lulawa cikin dogon tunani..... "Uncle Miey say something mana,shirun ka ya fara tsorata ni,ka sanar da Ni abinda ya ke faruwa ka sanar da ni,na roƙe ka"....ta kai zancen muryarta na rawa. "Kar ki yi kuka Jadeeda,ba zan so ganin zubar hawayen ki ba zan faɗa mi ki komi sai dai na roƙe ki kar ki ce zaki guje Ni no meter how,za ki tsaya tare da Ni"......"Ka sanar da ni koma meye domin Zuciyata ta ƙarfi da yasan mene ne dalilin da ya sauya ka kuma ya jefaka cikin irin wannan yanayin". "Za ki iya tuna ranar da na ce ki shirya zamu fita zan yi Surprise ɗin ki sai rashin lafiyar Sister Gloria ya tashi wanda hakan ya sa mu ka fasa fitar ?","Eh na tuna",ta bashi amsa ta na mai ɗaya kanta alamun ta tuna ɗin "Jadeeda ina son ki, I mean I love you,I love you since day one da na fara ganin ki,na ji Muryar ki,na ji kukan ki ya ratsa kunnuwan,tun rana ta farko da na fara ɗaukar ki na danganta ki a jikina,ina son ki da gaskiyata", wannan shine abinda na ke so in sanar dake a ranar". Jadeeda ta yi murmushi mai cike da ladabi, amma jikinta ya fara rawa ba tare da ta san dalili ba. Sai kawai ta ce, "Na gode Uncle Miey." "Ban ce hakan don yabawa ba kawai Jadeeda....." Ya tashi daga kujerarsa, ya matso kusa da ita. "A'a...Jadeeda... ina son ki ne. A zahiri, ni dai ina sonki dakuma dukkan gaskiya ta,ina nufin ina son ki da Aure." Kamar an zuba mata ruwan sanyi haɗe da zafi haka taki sanyi da zafi na keto mata ta rako 'ina . Gaban ta ya fadi. Idonta ya lumshe, zuciyarta ta fara dukan uku-uku,ta fara jin wata hayani da kuma ƙara na zagaye saman kanta, ƙafafuwan ta suka fara raurawa tamkar suna ƙoƙarin kayar da ita. "Uncle Miey… ka ce me?" Ya sa hannunsa kan kafadarta. "Ki fahimce ni, wannan ba laifi bane. Mun riga mun san halayyar juna,na fahince ki kin fahimce ni. Ba na kallonki a matsayin ‘yar ƙanwata. Ina son ki a matsayin matar da nake so in aura." Duhu ya ƙara yin duhu. Sanyi ya fara ratsawa cikin kasan ƙafarta. Tana jin numfashinta ya yi nauyi. Idanun Uncle Miey sun dushe da wani irin ƙiyayya da rudani. Bai kama da mai gaskiya ba. Bai kama da Kirista ba.,"Ni ba zan iya ba!" Ta miƙe da hanzari, tana jin kamar ta fara zufa. "Kai… kai ƙanin mamana ne. Wannan zunubi ne!" Yai dariya da wata murya da ba ta saba jin sa ba. "Zunubi? Menene zunubi, Jadeeda? Ko kina nufin addini zai hana mu soyayya?, to idan kina wannan tunani ki bari don Aure na da ke halattaccen Aure ne kamar ma anyi anga domin har na fara gano ki sanye da wedding gwon sanye a jikin ki an kai Gidana a matsayin Mata ta" Da wani irin gudu ta tafi zuwa cikin bedroom ɗin ta tana kuka. Tana jin ana kiranta da murya, amma ba ta waiga ba. Ranar nan ba ta runtsa ba. Tana jin tamkar duhu ya shige mata rai. Ta fara shakku shin anya ba duka Gidan ne shaiɗan ya shafa ba kuwa ?. Kasa haƙuri Uncle Miey yai ya bi bayanta har cikin Bedroom ɗin na ta yana mai cewa,"Me hakan ke nufi,kar dai ki ce za ki bari ko ki guje Ni,kar ki ce ba zaki amshi tayin soyayya ta domin hakan babban kuskure ne da bazan iya jurar faruwar hakan ba,ki sani My Angel zan iya aikata komi in har akan ki ne ciki har da kisa,ki sa hakan a ranki da gaske na je ina son ki na shirya in rayu ko in mutu duk akan ki",ya kai zance a matuƙar tsawace wanda har sai da Jadeeda ta tsorata gami da dunƙule kanta a jikin gwuiwowinta. Momy ta shigo a hargitse, ruwan zufa na gangarowa daga goshinta, hannunta na rawa, idonta sun yi ja tamkar wacce ta fito daga mafarki mai muni. Ba ta iya furta kalma ko ɗaya ba. Sai dai bakinta yana motsi, zuciyarta na bugawa da ƙarfin da har ana iya jin sa daga waje. Kamar ta faɗi. Sai da ta dafa bango tana neman numfashints,Richal ƙaninta wanda ƴarta Jadeeda ta ke kira da Uncle Miey, yana tsaye a gabanta cikin kwanciyar hankali, kamar wanda ya gama cin nasara akan wani yaƙi. Momy ta ɗaga idonta, ta kalle shi da wani irin yanayi da ya haɗa ƙiyayya, firgici, da bacin rai. "Kana cikin hankalinka kuwa?! Ka san me ka ke faɗa?!”,Tayi ƙoƙari ta doshi gabansa, hannunta na girgiza kamar za ta watsa masa mari. Uncle Miey ya zuba mata ido yayi,sai ya saki murya mai sanyi da kasaita,"Ina cikin hankalina sosai, Gloria. Kuma duk abin da na faɗa, na faɗa ne da zuciyata duka. Ina son Jadeeda. Ina son ta fiye da komi. Kuma babu wani mutum ko wani dalili da zai hanani Aurenta." Momy ta girgiza kai da hawaye a idonta, "Ta yaya za ka faɗi haka? Kai fa ƙanina ne! Kai ka sani da kyau ita ‘yar cikin da ba za ka iya kallon ta da ido mai tsarki ba ce! Kana kallon kanka a mata Krista na gari kuwa?,idan har haka ne ta ya zaka riƙa irin wannan tunani mafi muni fiye da na wulakantaccen mutum?". "Da gaske Ni mabiyan Yesu Almasihu ne,na gaskiya da gaskiya amma hakan ba yana nufin zan bar soyayya ta ta farko ba". Ya ɗan dakata kafin ya ɗora da cewa,"Wai ke duk a tunanin ki kulawar da na ke bama Jadeeda don ta kasance ɗiyar da ki ka haifa ne,na liar wannan ƙarya ne,ki sani son ta na ke Aurenta na ke buri ko da kuwa zai sa ki rasa hankali ki shiga hauka ne wannan bai dame ni ba." Ba Mommy ba hatta da Jadeeda duƙe riƙe tana daman gursheƙen kuka sai da tai saurin ɗagowa gami da dakatar da kukan nata,daga ina Uncle Miey ya samo wannan sabbin halaye,shine tsayar da ta tsaya masu ai su duka biyu,sai daga baya Momy ta iya motsawa gami da cije leɓenta har ya fara zubar da jini. Sai ta juya kamar za ta bar falon, amma sai ta dawo da karfi. "Tabbas ka zo da wani sabon batu Richal wanda ko a cikin jerin mahaukata ban taɓa jin wanda ya aikata irinsa ba,ina so ka sani daga yanzu na shirya ma duk irin haukan da ka zo da shi,ba kai ba ba Edwin ɗin ba dukkan ku a tafin hannuna ku ke,mu zuba mu gani,na yi maka alƙawarin sai na dakatar dakai na kuma ƙaryata duk wasu kalaman ka,zan aikata haka in har na cika kuma ina amsa suna na Gloria" "To Ni kuma ina mai tabbatar mi ki da sai na fallasa ki!,domin a gare ni ba ki da wata daraja tun lokacin da kika boye gaskiya. Ni zan nemi farin cikin rayuwa ta ,a tare da Jadeeda ta kasance,don haka ba makawa Aurena da ita zai kasance!",ya ɗan dakata ,kafin Uncle Miey ya ce da rawar murya, "Na fi kowa sanin wanene ni! Na fi kowa sanin irin wutar da ke ci a zuciyata. Ba zan bari wani ya hana ni son da ya wuce duk wata doka a gare ni ba!" Momy ta tsaya cak. Hannunta na rawa. Idonta ya rine da shudi. Zuciyarta ta fara bugawa da ƙarfi da ƙarfi fiye da da. Sai kawai ta dafe ƙirjinta, ta ce da karamin murya "Ya kamata Richal ka gane kuskure ka ke aikatawa,bai kamata ka ce" .......Kafin ta kammala, ta fadi kasa da wani ƙara mai tsuma zuciya. “Momy!!”,“Gloria!!”,a tare Jadeeda da ta ke cikin mugun halin da ya faskara da ita da Richal suka fara kiran sunanta Suna fadan haka su ka nufe ta domin kai mata agaji. Sai faman jijjigata suke a rikice. Amma ina ba ta iya magana ba,bata motsi. Idonta ya cika da hawaye amma kuma ba kalma ko guda da ke fita daga bakinta ., “Call an ambulance!!”, Richal ya faɗa a kiɗime, wannan ƙarar da ya yi ce ta jawo hankalin mutanen gidan A nan aka fara gaggawa. Aka fito da mota. Gami da nufar asibiti da ita, zuciya cike da firgici da tambayoyi masu ɗaci. Page 42 Jadeeda na tsaya, hawaye na zuba a idonta,Momy na cikin ICU, kwance tamkar gawa mai numfashi. Tana fama da bugun zuciya da matsanancin hawan jini Daga bayan Jadeeda,Nora ce ta iso cikin sanyi da tausayi. Ta rungume Jadeeda da ɗan ƙarfi tana fadin,“Ki kwantar da hankalinki, 'yar uwa… Ki tuna ba laifinki bane.for the sake of the Jesus name za ta samu sauƙi ,komi zai koma Normal",ta kai zancen ta na goge mata hawaye da yatsun ta tana ƙoƙarin yin murmushi duk dan ta kwantar mata hankali ,kafin ta cigaba da cewa,“Rayuwa tana cike da jarrabawa,Aunty Jeeyyyy Wata rana komai zai dawo daidai.” Hannu Jadeeda ta sa ta tureta. Idonta ya cika da ɓacin rai da matsanancin jin ciwo da kuma raɗaɗin da Zuciyata ta ke mata,“Kina tunanin daɗaɗan kalamanki zasu sauya gaskiya?!Noora ba ki san azabar da ke ci min rai ba. Ba ki san irin abin kunyar da na shiga ba!” Kasa iya cewa komi Noora ta yi sai bin Jadeeda da idanu da ta yi “Bro Edwin… shine ya fara. Shine ya rikita komi Shine ya bude wannan ƙofar da sheɗan ya samu damar shigowa da ƙafafuwansa har cikin Gidan mu!”,Jadeeda ta nisa, tana jijjiga kanta da sauri kamar wacce ke shirin tsinke kan nata Nora ta matso a hankali. "Nora wai me su ke nufi ne da Ni ?,anya ba akwai wata manufa ko wani sirri da ban san da shi ba,anya ba sauya min su a kai ba,sai in ji kamar ba Uncle Miey ba ne kamar ba Bro Edwin ɗin da na sani ba ne suka tun kare Ni da irin wancan mummunan kalaman,ma su tsayawa a Zuciya gami da son tarwatsata, ina jin nauyi a zuciyarta tamkar wacce ke shirin ɗaukar nauyin duniya gaba ɗayan ta",Jadeeda ta kai zance ta na mai fashewa da kuka. "Shin kina zargin wani abu wanda ya zama sila ko mafarin wannan cukurkuɗeɗɗen lamarin ", “Wannan ba zargi ba ne ba Nora. Wannan ba tunani ba ne kawai. Wannan gaskiya ce! Wani abu yana faruwa kuma a cikin gidanmu wani sheɗani ya shiga cikin zukatan waɗanda nake kallo a matsayin jagorori.” “Bro Edwin ya ce yana sona a matsayin sa na wanda mu ke Uba ɗaya da shi,hakama Uncle Miey, wanda ya ke matsayin ƙanin Mahaifiyata,wanda na ke ma kallon mutum mafi ƙololuwar girma,kamala da sanin dai-dai da ba dai-dai ba da,Shine wanda na ke kallo a matsayin wanda zai iya maye gurbin Uwa da ubana ko da bayan ran su,shi kaɗai ɗin shi ina mashi kallo a matsayin ahalina amma bai ji kunya ba ya kalle Ni ido cikin ido ya ce ya na so na, wannan wacce irin annoba ce wannan?! Wane irin ciwo ne da ke cin rai da sunan soyayya?” Nora ta yi shiru. Idonta ya cika da hawaye. Ta san gaskiya akwai ciwo,damuwa da tashin hankali ruɗu gami da firgici a cikin wannan lamarin da ya tunkaro su amma ta rasa yanda za ta magance hakan ko kuma ta samu ta kwantar ma ta da hankali. "To Aunty Jeeyyyy, me za mu yi yanzu? Momy na kwance,ba ta san inda tunani da hankalin ta ya ke ba, Granny ba ta nan,Papa ma bayanan ,daga Ni sai ke sai Martin,mun yi kaɗan mu shawo kan wannan lamarin,duba da Momy na kwance,Na rasa gane wane abu ne ya shiga cikin kan mutanen da na dogara da su. Ko sheɗan ne da kansa ya shigo cikin gidan mu don ya tarwatsa mu?” Jadeeda ta juya tana tafiya a hankali, tana fadin, “Idan akwai wata wutar jahannama da ke tafe da sunan ‘kalmar soyayya’, to itace wannan. Kuma wannan ba za ta ƙare ta sauƙin ba. Na rantse, zan zakulo gaskiya, ko da kuwa cikin zaƙulo gaskiyar zan ci karo da raɗaɗin zuciya fiye da wannan da na ke ji.” A can Gida kuwa, Bro Edwin na can sai faman kai kawo ya ke,idanuwansa ne suka sauka kan wani hoto na Jadeeda da aka ɗauka a lokacin church retreat. Akwai wani salo na nadama a fuskarsa, amma a ƙasan idanunsa wani duhu ne da yake ɓoye cike da wasu sirrika,Ya kalli hoton, ya furta a hankali:“Ni na fara... kuma ina jin karshe zai kasance a hannuna Ni zan kori duk wasu matsalolin da suka shigo cikin wannan Family na mu”.....tun bai ƙara sa ba ya ɗauki Car key na shi ya nufi Hospital ɗin da Jadeeda su ka tafi da Mommy. Duk da kalaman ƙarfafa gwiwa da Nora ta ke yi wa Jadeeda da son kwantar mata da hankali,hakan bai sauya komi game da yanda ta ke ji a cikin rai da zuciyarta ba,amma duk da hakan Nora ba ta gajiya ba,ta cigaba ta na yi tana shafa bayanta cikin tausayi da tausa sa wa Jadeeda ta kasa jure girman raɗaɗin da zuciyarta ke sha.,ta ce cikin murya mai ɗauke da rauni,“Anya kuwa......anya zan iya Nora…zan iya…cigaba da ɗauka nauyin wannan lamarin a cikin Zuciyata”........Amma ina kafin kalamanta su gama fita daga cikin bakin ta, ta zube kasa da wani irin rauni mai firgici. Wutar numfashinta na rawa, idonta na hangen sama babu komai duniya ta juye mata kamar ana juyar da zobe a yatsa,amma duk da hakan yunƙurin tashi ta ke, idanuwanta ba su gani komi sai duhu,sai dai zuciyarta ba ta tsaya da aiki ba gami da son gano abinda ya ke ƙoƙarin sauya mata rayuwa gaba ɗaya Cikin kawa Nora ta fara kiran Nass da Doctors dan su kawo mata ɗauki haka su ka shigar da ita ciki Nora sai faman kuka ta ke daga gefe, Jadeeda na kwance cikin gadon ICU,gani take kamar numfashinta na ƙoƙarin barin jikinta. Cikin sarƙewar zuciyarsa Bro Edwin da ya shigo asibitin yanzu,a kiɗime ya nufi inda Nora ke durƙushe ya mikar da ita tsaye tare da jero mata tarin tambayoyi,"Me yake faruwa....Nora....ya jikin Mommy... ina Jadeeda ta ke,me ya same ki ?".... A fusace ta buge masa hannu gami da ture shi daga kusa da ita muryarta cikin kuka ta ce da shi,"Hankalin ka ya kwanta, sai ka je kai da Uncle Richal ɗin ku zuba ruwa a ƙasa ku sha,ku yi murna domin Aunty Jeeyyyy gab ta ke da barin mu ku duniyar ma gaba ɗaya sai ku ji daɗin ku,in ya so sai ku amfana da gurbin da ta tsare ma ku"...."Me wannan zancen na ki ya ke nufi ina Angelenah ta ke ne ,me ya same ta tana inah!?"..... Da hannu ta nuna masa Room ɗin da Jadeeda ta ke,jikin sa na rawa kamar ƙafafunsa ba za su ɗauke shi ba,haka ya nufi Room ɗin,hannunsa na rawa, idonsa kumbure kamar wanda bai taɓa barci ba. Ya buɗe ƙofar dakin da Jadeeda ta ke kwance... Amma kafin ya ƙarasa, ta tashi da karfi tana fuskantar shi da ƙiyayya da tsoro a lokaci guda, "Ka fita!",ta ce da shi "Jadeeda dan Allah..."ya ce da ita a raunane "Ban san ganin ka Edwin! Ka rushe komai! Ka ƙona farin cikin wannan gida saboda girman son ka Ka,ka yaudare ni, ka yaudare momy, ka yaudari kowa na cikin Familyn ɗin mu,dan haka ka fita ba na son ganin ka bana son son ganin ka".....ta kai zancen cikin tsawa gami da sa ke fashewa da wani kukan mai tsuma rai, tana daga murya kamar zuciyarta za ta fashe. "Ban taɓa tsammanin haka daga gare ka ba,kai ne mutumin da zan iya dogaro da shi. Ashe ƙarya na ƙe,ashe Zuciyata yaudara ta ke kai ne rusasshen ginin da na kifa amana ta a akai...!" Kafin Edwin ya iya cewa uffan, aka buɗe ƙofar da karfi,Uncle Richal ya shigo tamkar walkiya. Fuskar sa cike da ƙiyayya, idonsa na ƙuna kamar mai cin wuta. "Me ya kawo wannan shashan nan,shin ka zo ne ka sake rikita lamarin ne?! Edwin! Edwin ya ce,cikin son fahimtar da shi abinda ya ke tafe da shi,"Uncle Richal, dan Allah, ba haka nake nufi ba,ka bar Ni for the God sake babu abinda zai faru......."sai dai kafin ya ƙare magana, Richal ya kai masa wani naushi ya same shi a saitin bakin sa,nan da nan sai ga ruwan jini ya zubo daga bakin Edwin,a fusace shima Edwin ya fuskance shi yana mai cewa,"Kar ka sake dukana domin ba dan kai na zo nan ba,na zo ne domin ita ka bar ni,in Yi magana da ita,don ita na zo",....wani dukan Richal ya sake kai masa wanda har sai da Edwin ya kai ƙasa saboda ƙarfin dukan da ya yi masa. A hargitse Jadeeda ta sako daga gadon da ta ke kwance ,tana mai daka masu tsawa,"Ku fita ,ku bar Ni bana son ganin kowa a cikin ku,na tsane ku ku duka ",ta kai tsancen cikin tsananin ɓacin rai gami da nuna masu hanyar fita. "Amma ban da Ni ko my Sweathert,ai na san Ni dai ba za ki kore Ni ba ko?.......",ta katse shi da cewa,"Har da kai domin kai na fi tsana fiye da kowa ,dan haka fita ku bani wuri". Edwin yana durƙushe ƙasa da jini a leɓensa, ya dube Jadeeda cikin hawaye,"Ni dai na gaza. Amma ina son ki har yanzu,ba wai na faɗi hakan don in tozarta ki ba,kuma na yi danasanin abinda na aikata,na so in rayu Kuma in mutu har a binne ni da wannan mikin amma na kasa iya jurewa,ban san munin lamarin da na zo da shi har ya kai haka ba sai da na g gaba ɗaya gida ya hargitse Momy na kwance ba lafiya kuma kin yanke jiki kin faɗi,da haka na ke cewa na tuba ki yafe ni ." Ko kallonsa Jadeeda ba ta yi ba,sai kallonta ta maida kan Doctorn da ya shigo yanzu ta ce da shi,"Dan Allah ka fidda min su bana buƙatar ganin kowa a cikin su". Haka ba dan sun so ba Doctor yai waje da su sai faman ɓaɓatu Uncle Richal ya ke √√√√√√√√√√√√ "Bari mana Nurain,ko so ka ke ka zuba lemun a cikin Miyar ta ka", Ummu Nurain ta faɗa ta na mai amshe Cup ɗin,ta aje gefe tana mai sanya tissue ta goge masa bakin sa inda ya shafa miya,ɗan dakatawa ta yi tana mai maida ganin ta kan Abu Nurain da ya dakatar da cin abincin shi yana mai zuba masu idanu. "Lafiya Abu Nurain,na ga ka tsaya da cin abincin ko dai bai maka daɗi ba ne?". Zeenat ta tambaye shi cikin kulawa. Sai da ya lumshe idanunsa gami da gyara zaman shi kafin ya bata amsa da cewa,"Fiye ma da daɗi wannan abincin ya zarce duk wata kalma da za ta fito daga baki na in don yabawa ko jinjinawa ne,kawai dai na ga abin kamar a mafarki,ina jin farin ciki mara misaltawa,ina fatan inama da hakan zai ɗore,ina ma da rayuwar mu zata cigaba da gudana kamar kowane Gida,ina ma da zaki koma ma min kamar Zeenat ɗin da na sani na kuma aura tun da farko,ba Ummu Nurain da ke jin duk aikin duniya ya taru akan ta ba,har tana jin bata iya sauke wasu haƙƙoƙina na cikin Gidannan,mu rayu cikin aminci,farin ciki,kulawa da kyautatawa,mu sauke haƙƙin kowanne da ga cikin mu wanda Allah da kuma igiyar Aure ta rataya akan mu,zan so hakan shine mafarki da na jima ina yi gami da fatan wanzuwar shi a zahiri". Cikin tausasa murya ɗauke da tarin nadama Zeenat tace da shi,"Mijina ka ya feni,na aikata babban kuskure wanda zai cigaba da cutamin a cikin rai da rayuwata in har ba ka furta kalmar yafiya a gare ni ba,daga yau na maka alƙawari zan yi maka biyayya,zan bi duk wani umarni na ka,zan aikata duk wani abu da zai saka farin ciki ko ya faranta ranka,zan kasance mai koyi da Matan Annabi(S.A.W) domin bayyanar da kishinsu,ba zan ƙara zame ma ka matsala a cikin Gidan ka ba,dan Allah ka yafemin ka zamo,duk dama nasan kai mai afuwa da tafiya ne a gare ni",ta kai zancen muryarta na fara sauyawa gami da son fara zubar da hawaye. "Ya isa haka komi ya wuce ,na yafe miki, duk da dama ban riƙe ki da komi ba, Allah ya shige mana gaba ya ƙara mana kwanciyar hankali da fahimtar juna a cikin zamantakewarmu".. Page 43 "Amma dai ba za ka jima ba ko,na ga yamma ta fara yi ga shi gobe Early in the morning jirgin ku zai tashi,kana buƙatar hutu da natsuwa". "Mtsss bazan iya ce miki komi ba gaskiya kawai dai sai an ganni domin ina son mu kammala cinikin filin kafin in tafi,kin san Hamed da shiririta wani lokacin,to su kan su masu filin ba su da tsayayyar magana,ina so mu kawo ƙarshen komi a yau,dan haka sai kun ganni". "Okay to sai ka dawo Allah ya tsare,zan shiga Part ɗin na ka sai in haɗa maka duk abinda ya dace wanda za kai tafiyar da su","A'a No ki zauna kawai ki huta in na dawo na haɗa domin na ga jikinnan na ki har yanzu da sauran shi"....ta katse shi a ɗan shagwaɓe,"Kamar ya da saura na ni fa na faɗa maka ba abinda ya ke damuna ina lafiya,lafiya ta ƙalau","A hakan ne ki ke lafiya ƙalau ki na dai ɓoye min abinda ke damun ki,na daɗe da fara fahimtar hakan duk da har yanzu ban wuce one weak da dawowa ba,kawai dai na bar ki ne,da tunanin za ki iya magance komi,ko kuma ki neme ni in buƙatar hakan ta zo,na yi juyin duniya akan ki sanar da ni mene ne damuwar ki kin ƙi, amma duk da haka ban cire rai akan za ki sanar da ni bato sai dai na ga kwata-kwata ba ki da niyar haka,ki sani ganin ki a cikin irin wannan yanayin ya na ƙona min zuciya in aganin kamar na gaza wajen sauke haƙƙi ko nauyin da Allah ya ɗora min",Sai da ta matsa kusa da shi sosai gami da kama hannayensa ta riƙe,cikin sigar natsuwa gami da kwantar da murya ta ce da shi,"Ka yarda da Ni Mijina da gaske na ke ba abinda yake damuna,inma kuwa akwai to bai wuce rashin zaman Cikinnan a jikina ba,kasan na sa rai gami da kwallafa rai akan shi,a tunaninna shine kawai abinda zai iya tsaya min a rai gami da damina kenan","Amma i thought mun riga da mun gama da wannan maganar ko,me zai sa ki barta tai ta zama a cikin rai da zuciyar ki,zata fa iya yi maki illah,kuma kin san wannan lamari ne na Allah ba yin kan ki ba ne,fita dan me za ki nemi ki jefa kan ki a cikin wani hali,dai zai riƙa cutar da ke nuna ya cutar da Ni,gaskiya ban ji daɗin jin wannan zancen daga bakin ki". "Ka yafe ni Mijina na maka alƙawari da ga yau ba za ka sake ganina a cikin irin wannan halin ba,zan yi ƙoƙarin ganin na fidda wannan lamarin a cikin Zuciyata gaba ɗaya ko dan in sake acikin natsuwa farin ciki da walwala,ba zaka sake ganina cikin irin wannan yanayin ba,domin ko kusa ko kaɗan bana don ganin ka cikin damuwa ko wani yanayi mara daɗi,hakan ya na tashin hankali na gami da rasa natsuwata,ka yafe ni dan Allah Mujina","Da gaske za ki cire wannan damuwar da tunanin da ki ka sa a cikin ranki za ki koma Gimbiya Ayush ɗin ki ta asali wacce na sani gami da yin sabo da ita,wacce na ke gudanar da rayuwa da ita cikin farin ciki,natsuwa da kuma tarin ƙaunar juna?",da sauri ta ɗaga mishi kai gami da cewa,"Eh da gaske na ke na yi alƙawari,ka san ba abinda zuciya da gangar jikina su ka fi so fiye da na aikata wani da mafi so ko kuma ka umarce ni da shi". "Na ji daɗin hakan,na gode sosai Allah yai maki albarka sai na dawo",ya na kaiwa nan ya ɗan jawo ta jikin shi kafin ya fita. "Innalillahi wa'ina ilaihir raju'una",shine kalmar da Gimbiya Ayush ta faɗa ta na mai kaiwa zaune kan kujerar da ta ke ba tare da wani ƙarfi a jikinta ba,"Ni wannan wacce irin musiba ce,ta wacce hanya zan bi domin ganin na yi maganin wannan matsalar da kaina,tsoro da firgici ya kama Ni kar asiri na ya toni,ta wacce hanya zan bi ,in dai-daita komi ba tare da na bari wata matsala ta sake faruwa ba?"...Ringing ɗin wayarta da ke kusa da ita ya dakatar da ita,sai da ta ɗan yamutsa fuskanta kafin ta ja tsoki ta ɗauki wayar,ba tare da ta duba waye yiwa kiranta ba,damuwa da kuma tunanin mafita akan lamarin ta ne kawai abinda ya rufe mata idanu,cikin yanayin murya mai ɗauke da damuwa ta amsa wayar,"Hello besty kina lafiya ya na ji Muryar ki cikin irin wannan yanayin ko baki da lafiya ne",da ga can ɓangaren aka ce da ita,"Ohhh Anisa ke ce,ya Gida ya su Umma fatan komi na lafiya"....."Kin ga ki dakata ki faɗa min me ke faruwa da ke,ko dai ba ki da lafiya ne,Muryar ki ba haka na saba jin ta ba akwai matsala gaskiya","Ina cikin tashin hankali da musiba Anisa na rasa mafita ko mi ya na gab da lalace min","Subahanallahime ki ke shirin sanar da ni,kar dai ki ce min asirin da ki ka daɗe ki na binne shi a ƙasa ne aka tono miki?","A'a Anisa amma ina mai tabbatar mi ki da gab hakan ke shirin faruwa,yanzu dai ke kina ina ?","Ina Gida gani nai mun kwana biyu,ba mu haɗu ba kuma ba wanda ya kira juna","Ke dai bari Imam Jaheed ya na gari ya dawo,a dai-dai sanda zan zo inda ki ke ko in kira shi kuma ya dawo hakan ya ƙara dagula min tunani gami da rashin sanin madafa ko makamar da zan yaƙi lamarin da ya tunkaro ni, amma yanzu dan Allah komi ki ke ki zo,ya fita zai yi cinikin filayen da ya ke son siye ya sabunta sabon Gidan shi,zai jima bai dawo ba,kin ga kenan zamu iya tattauna duk wani abu da muke so kafin ya dawo","To Shikenan gani nan zuwa",da haka suka kashe wayar,zuciyoyinsu kowacce cike da tunanin ka. Ba a ɗau wani lokaci ba sai ga Anesa ta iso Gidan a rikice,"Lafiya Gimbiya Ayush sanar da ni me ke faruwa,kin tashi hankalina","Ki zauna ko ruwa in kawo ma ki"...."A'a ki bar shi ki fara sanar da ni abinda yake faruwa ko na samu natsuwa",Sai da fuskar Gimbiya Ayush fuskarta tai kalar damuwa da ɓacin rai kana ta ce da ita,"Anesa....Ciki...Cikin jikina yana nan bai fita ba",ta kai zancen tana mai dafa cikin da hannayenta. "Innalillahi...taya haka za ta faru,anya kin sha maganin da na kawo maku kamar yanda na ce da ke?","Wallahi na sha har over doss sai da nayi","Kai gaskiya ban yarda ba ko dai wani Cikin ki ka samu ne","Ko ɗaya cikin Jikina ba sabo ba ne ba,yanzu haka ya kusa two months,sanadiyar yunƙurin abortion ɗin da na yi ne ya koma baya"."Taɓ ɗi jam wannan shine ake kira da hukumu lahi,yanzu in ba haka ba taya za ai ace duk ƙarfin maganinan da ki ka sha ace Cikin bai fita ba,kin sanar da Fadeelah ko?,me ta ce game da hakan","A Hospital ɗin su aka yi min duk wani gwaji kuma aka tabbatar da cikin yana jikina bai faɗi ba,hakan yasa na rinƙa bleeding ɗin jini tun bayan faruwar lamarin". "To tunda haka ne me yasa tun acan ba ki sa an markaɗe shi ba,a fitar da shi kowa ma ya huta ,ta ya za ki cigaba da zama da shi har kawo wannan lokacin". "Kin san halin Fadeela,ta riga da ta fitar da hannunta a cikin lamarin,duk yanda na so ta fahimci halin da na ke a ciki hakan ya gagara,shi kuma idanunsa a koda yaushe a kaina su ke,ya damu matuƙa akan in sanar da shi asalin abinda ya ke damuna,abu guda ne ya ce-ceni da bai fahimci Cikin yananan bai fita ba,saboda tunda ya dawo bai samu natsuwa da hutu ba,don tabbas da ya zauna da ya fahimci Cikin Jikina na nan har yanzu bai fita ba,a ranar da na je Hospital ɗin sai da wani friend nasa ya kira sa ya ce masa ya ganni,hakan ya sa na kasa iya zuwa wani Hospital ɗin"...."Caɓ akwai babbar matsala bai kamata ki bar Cikinan ba ya kamata mu bi duk hanyar da zamu bi mu zubar da shi kafin wani ya sake farga da shi,shin ko wani ɓoyayyen Chemist za mu je inda ba a sanmu ba,a zubar da shi kawai kowa ma ya huta,na yi matuƙar mamakin rashin aikin wannan maganin ko dan kin saba da shan ire-iren magunguna na zubar da Ciki shiyasa wannan bai yi ma ki aiki ba"..... “Wallahi Anesa da kin gan ni lokacin zubar da cikinnan, da kin tausaya min, Na sha wahala sosai…...na kasa yarda duk wahalar da na sha ta tashi a banza,amma ina cikin firgici da tsoro,ina jin kar garin son kaina da kuma cikar wani buri nawa in gurgunta igiyar Aurena,Ina tsoran kar Imam Jaheed ya fahimci halin da na ke a ciki,ban san kuma ta wacce hanya zan iya fidda kaina a wurin sa ba". “Ke dai kin fi kowa tsoro. Amma wallahi karki fa taɓa barin wannan cikin . Maza ba su da hakuri fa,kuma ba su da kawaici ko kara,in dai a kan mata ne,da zaran ki saki jiki kin fara kwatsa ƴaƴa a Gidansa sai ya fara sauya maki,gami da tsiro da sabbin halaye,ko yana ƙaunar ki sai kin ga wani ɓangaren sa na daban.” Imam Jaheed da shigowar shi kenan ya kasa motsi. Fuskar sa ta sauya launi,bugun zuciyarsa ya tsananta idanunsa suka ciko da hawaye. Ƙirjinsa ya fara bugu da sauri kamar ana dukan ganga. "Gimbiya Ayush? Ita? Zubar da ciki, Abortion kenan fa? Kuma da Aurena akan ta,ba sau ɗaya ba sau biyu ba?..." Ya ɗaga idanunsa masu cike da tambayoyi,kafin ya iya cire ƙafarsa ya tura zuwa cikin Parlon,ba wai iya Gimbiya Ayush ba,hatta da Anesa sai da ta firgita da ganin sa,ita kuwa Gimbiya Ayush sai da numfashin ta ya tsaya na wucin gadi,komi na ta a tsaya,zuciyarta ta fara kai kawo shin ya tsinkayi tattaunawar da su ke,ko kuma bai ji komi ba. Da ɗan saurinta ta yi kan shi don son ta fahimci gaskiyar abinda ta ke zargi,duk da ta kasa karantar komi daga gare shi,"Habibi lafiya na ga ka dawo ko ka yi wata mantuwa ne?". “Kamar dai akwai abubuwa da dama da nake tunanin ban sani ba… Wanda suke faruwa a cikin Gidan ko ?”ya faɗa cike da ɗacin zuciyar da ya ke ta so ma shi. A rikice ta ɗago idanunta ta zuba su akan shi zuciyarta ta buga,kafin ta gama saita natsuwar jikinta ya cigaba da magana, “Idan mace ta ɓoye gaskiya mai girma ga mijinta… me hakan ke nufi? Ƙarya? Kiyaya? Ko kuma tsoro?”, Gimbiya Ayush ta sunkuyar da kanta ƙasa, ta kasa cewa komai. Zuciyarta ta shiga rawar tsoro. Ashe ya ji? Ashe sirrin ya ƙare?,ya bayyana yau ƙaryata ta ƙare,ya riga da yasan ɓoyayyar fuskata da na jima ina ɓoye masa, Cike da mamaki da ciwon zuciya, ya ce da ita, “Kin sani ina kallon ki a matsayin mace mai kamala da amana, Gimbiya Ayush,na ɗau so,ƙauna gami da amana na damƙa ma ki ina kallon ki a matsayin wata babbar kyauta da Allah ya bani,ashe shirmen na ke,ashe ni ki bari ina ta hauka akan son ki,da tunanin na yi dacen Mata ta kwarai,ashe kallon sakarai ki ke min",Yayi shiru.kafin ya ce da karfi, kamar wanda ya kamu da kunya da tsana,"Zubar da ciki bayan kina da yaure? Kuma ba so ɗaya ba? Gimbiya Ayush??!”. Gimbiya Ayush ta fashe da kuka. Ta durƙusa gaban mijinta, tana fadin,“Na ji tsoro ne Habibi… Na ji kamar idan na haihu za ka guje ni,za ka bar ni,na koma ba wani amfani da zan maka illah in zama mai renon Yara a gare ka". Da wani mugun kallo ya bita gami da ja da baya, ya ɗan kalli ƙasa,kafin ya ce “To me kike tunani yanzu da na sani?,Gudan jini na su ki ka zubar,Jini na ɗana shi ki ka zubar a cikin bola da kwatoci Kin san me kika zubar da shi kuwa?",wahalata,Jiɓi na da kuma ƙarfina,kin san kuwa irin wahalar da Uba mahaifi ke sha kafin ya fitar da ɗa daga jikinsa,amma a haka ki ka riƙa zubar mun da su a rariya,tamkar wanda ki ka maida wani ɗan iska,yau ko a waje mu kai wannan cikin ai ya kamata ki shawarce ni kafin ki zubar da shi,kai!..... Abortion a gidana abun da mamaki,gaskiya kin shammace ni,ban san haka ki ka ɗauke ni ba,ashe ni wulaƙantacce kuma abun ƙyama ki ka ɗauke ni ba",ya ɗan tsagaita yana mai cije leɓen shi na ƙasa,zuciyar shi na ƙuna . Gimbiya Ayush ta sunkuyar da kai, hawaye na gudu a fuska,Yayi shiru,kafin ya juya wurin Anesa wacce tuni hantar cikinta ta kaɗa. "Wa ma ki ke da suna,Anesa ki ke ko wa?,ke ce wacce ki ke ba Mata ta shawara akan zubar da Ciki bayan ke ko Auren kin kasa,amma a haka ki ke bata gurguwar shawara,da ya ke ita kuma bata da hankali ta biye miki ba tare da ta san rijiya gaba dubu ki ƙoƙarin jefa ta a ciki ba". "Me na aikata maki da har na can-canci ki bada shawarar da a cutar da ni haka!?",ya kai zancen a tsawace,kafin ta dawo daga razanin da tashiga ta ji saukar mari a duka kuncinta,wanda ba ƙaramin jin marin tai ba,har sai da ta kai ga fasa wata irin razananniyar ƙara gami da yin hanyar fita a guje shi kuma ya rufa mata baya yana cewa sai ta faɗa mi shi gaskiyar dalilin da ya kawo ta har cikin Gidan shi kuma aka haɗa baki ita ana cutar da shi. "A'a.... a'a...kai ya akai me ke faruwa ya na ga kun fito a cikin irin wannan yanayin kamar waɗanda wani abun ya biyo daga ciki ?",Yayah Hanne Mamar Biba,wacce ta ke ƙanwa a wurin Mahaifin shi ta ce wacce shigowarta kenan. Kasa iya magana yai sai faman nuni da hannu ya ke,ya nuna saitin inda Gimbiya Ayush ta ke da kuma Anesa da ke ƙoƙarin wajen ganin ta samu hanyar barin Gidan. "Lafiya me ya ke faruwa ya na gan ka a cikin irin wannan yanayin shin ko akwai wata matsala ne a Gidan na ku?",cikin rawar murya bayan ya samu ya kwato numfashinsa ya ce da ita,"Mama ki ce ta fita...ta tafi ta bani wuri bana son ganinta",ya kai zancen ya na mai nuna inda Gimbiya Ayush take,tun kafin ya kai ƙarshe Gimbiya Ayush ta zube ƙasa tana mai ɗora hannayenta a saman kanta gami da fashewa da kuka tana furta kalamai daban-daban. "Subahanallah me yai zafi haka ta ya zaka yanke irin wannan ɗanyen hukuncin,ai bai kamata ba,idan rai ya ɓaci hankali ake sawa a dawo da shi". "Mama Hanne dan Allah ki fitar min da ita,ta tafi Gidan su,ina jin zuciyata na sake tafarfasa gami da shiga cikin wani ƙunci a duk lokacin da na kalli inda ta ke,dan Allah ki fitar min da ita daka Gidana,ko kuma ni in bar mata Gidan",ya kai zancen hawaye na fara zubowa daga cikin idanunsa. "Kai...kai lamarin nan yai tsamari,ku zo mu shiga daga ciki",fafur Jaheed ya ƙi shiga in har tare da Gimbiya Ayush ne ba inda zai motsa,ganin hakan yasa Yayah Hanne tasa Bibah ta ɗauko Mayafin Gimbiya Ayush su ka bar Gidan shima da ƙyar ta yarda za ta bi su, kafinnan Yayah Hanne ta tafi da shi Part ɗin shi gami da fara lallahinsa. Page 44 "Yau ni Hannatu na gode ma Allah na ga abinda ya fi ƙarfina, wannan wanne irin rikitacen al'amari ne ya kunno kai a cikin Gidannan,ta ya za ai ace nayi-nayi ka sanar da ni me ya ke faruwa amma hakan ya gagara,sai hawaye ne ke faman fita daga idanunka,ka kasa ce min komi". Motsin da ta ji a bayanta ne ya sa tai saurin waigawa,Bibah ce tare Zeenat da ke ta faman raba idanu alamun ba ta san abinda ke faruwa a cikin Gidan ba,sai daga can baya Gimbiya Ayush ce,sai faman rusa kuka ta ke ba ƙaƙautawa,"Umma Hanne me ya ke faruwa na ji Gidan ya cika da hayaniya ?", Ummu Nurain ta tambaya. "Ni ma abinda na ke son in sani kenan,na shigo Gida na ga ƙawar Gimbiya Ayush ta fito a kiɗime in taƙaice maki labari, Muhammad ya wan-wanke Yarinyarnan da mari ta fita Gidannan a gigice,Da bakin shi ya kori Gimbiya Ayush ya ce ta bar mashi Gida,tun daga nan ya shige cikin ɗaki,har yanzu na ya ƙi fitowa kuma nayi-nayi ya sanar da ni abinda ke faruwa wallahi Yaronnan fafur ya ƙi sanar da ni abinda ya faru". Subahanallah yanzu Abu Nurain ɗin yana ciki?", Zeenat tai tambayar a kiɗime ta na mai ƙarasawa wajen Door ɗin ta fara bugu gami da yi masa magiyar ya buɗe. "A'aha Bibah ya na gan ki tsaye a nan wai ko har kin dawo Kaita ki kai ki ka jiyo?","Wallahi Mama ba inda mu ka je,tun fitar mu muna tsaye a waje sai faman kuka ta ke,nayi duk yanda zan yi amma ta ce ita ba inda zata". Sai a lokacin Yayah Hanne ta ga Gimbiya Ayush da ke rakuɓe a can gefe sai faman kuka ta ke da iya ƙarfin ta. Ta backyard Ummu Nurain ta samu ta shiga cikin Part ɗin na shi,da hanzarin ta ta samu ta isa gare shi muryarta na rawa ta ce da shi,"Abu Nurain lafiya me ya ke damun ka,waye yai silar jefa min kai cikin irin wannan damuwar da har yai nasara zubar da hawaye daga cikin idanunka,faɗa min ko shi waye,na rantse ba zan bar hawayen ka su zuba a banza ba",kamar yanda ta zo ta iske shin ,ko motsin kirki bai yi ba balle kuma ta sa ran zai ce da ita wani abu,haka ta cigaba da jero masa tarin tambayoyi ba tare da ta samu amsar ko ɗaya daga cikin su ba,daga ƙarshe cikin fushi ya ɗago yana mai sauke idanunsa da su ka sauya launi ya ce da ita,Cikin kakkausar murya,"Ki bar wurin nan kar ki nemi ki ƙara hassala ni,in kuwa ma ba haka ba kema za ki bita zuwa na ku Gidan". Wannan furuci na shi ba ƙaramin hargitsa ma Ummu Nurain hankali yai ba dan a rikice ta ɗago ta na mai sauke idanuwanta akan shi cike da mamaki. "Eh haka na ke nufi kuma ba da wasa na ke ba fita ki bani wuri domin a yanzu na fi buƙatar kaɗai ci". Hawaye ne suka fara sauka a saman tata fuskar itama,kafin ta ce da shi,"Saboda laifin wani,saboda na yi yunƙurin shawo kan matsala,saboda na yi niyar cire ka a cikin wannan lamarin,saboda na nuna damuwar ka damuwa ta ce,shine za ka furta irin wannan munanan zancen a gare ni?"...ya katse ta da gaggawa,"An gaya maki a irin haka ake raba Miji da damuwar da ya ke a ciki,kin zo kin tasa ni a gaba akan lalle sai na sanar da ke abinda ya faru,kin ga dan Allah ki tashi ki fita I need a privacy",ya Kai zancen ya na mai nuna mata hanyar fita. Jiki a sanyaye ta fito idanuwanta na zubar da kwala,"Ke lafiya ya na ga kin fito a cikin irin wannan yanayin,"Mama nima ya ce in tafi Gidan mu in har zan takura ma shi da tambaya "Kai A'a da sake ni wannan lamarin ya fi ƙarfina,ke Bibah sa waya ki ramin Mahaifiyarsa in sanar da ita abinda ya ke faruwa",da to ta amsa mata kafin ta fara kiran layin cikin Sa'a bugu ɗaya ana biyu ta ɗaga bakinta ɗauke da sallama gami da gaisuwa. "Kin ga ki riƙe gaisuwar ki ganinan Gidan Jaheed na zo na iske su ba a dai-dai ba yanzu haka ma yace duk matan su tafi Gidan su dan haka ki zo kar ai ɓatatta". "Subahanallahi shi Jaheed ɗin ne ya aikata hakan to yayi hauka ne ?","Ba na ce ba na dai san nayi iyakar iyawa ta ganin na shawo kan lamarin amma hakan ya gagareni,ƙarshe ma cewa yai in tafi komi ya wuce amma sai ya koma ya rufe kan shi a cikin ɗaki, nayi-nayi ya fito ya ƙi,don haka ki zo ki gane ma idon ki". "Yayah Hanne ki yi haƙuri amma ba zan iya zuwa wannan Gidan ba,ki kira Momynsa inda hali sai ta zo taga me yake faruwa"...."Amma ke dai kam Allah ya kyauta miki ɗan na ki,in kira in sanar da ke wani abu mara daɗi na faruwa da shi sai ki ce wai a kira wani"."Yayah ai da ni da ita duk ɗaya ne za ta yi fiye da abinda zan yi"...."Ke tafi bani wuri",ta faɗi haka ta na mai katse kiran gami da miƙa ma Biba wayar ta ce ta da ita,"Kira min Auntyn ku Hibba ki ce mata ta zo nan gidan yanzu da gaggawa". Haka kuwa a ka yi cikin ƴan mintinan sai ga Momy Hibba tamkar za ta tashi sama, Allah ya taimake ta tana kan hanyar dawowa daga Hospital wurin aikin ta ta juya alamar Stearing Motar ta nufo Gidan. "Lafiya me yake faruwa wani ne ba shi da lafiya a Gidan,ya na gan ku a haka,ina Jaheed ya ke me ya same ku,na ga Gidan kowa a firgice ya ke?","Ni ma abinda na ke ta faman son in sani kenan,na fi ƙarfin awa ɗaya a Gidan amma har yanzu ba wanda ya iya buɗe baki ya sanar da ni abinda ya ke faruwa,abu guda da na fahimta rikicin tsakanin Gimbiya Ayush ne da kuma ɗan ki Jaheed dan na iske wata ƙawarta da alama ma sai da ya wanwake ta mafi kafin ta bar Gidan". "Mari kuma shi Jaheed ɗin?,to garin ya aika hakan ta faru,Ni a tunanina rikici ko makamancin irin haka ba,in dama da Zeenat ne sai ince sun saba ai",", Wallahi Momy Hibba ba ruwana nima hayaniya su kawai na ji na fito na ke tambayar me ya faru,cikin rashin sa'ah reshe ke niyar juyewar da ni,duk abinda ya faru wannan algungumar ce ta haddasa shi dama shigowarta Gidann ba alkairi ba ce ba abinda ta tsinana mana sai ƙoƙarin rusa kan Gidan da ta ke,munafuka,annamimiya....","Ke!!! yi mana shiru ai ke ce babbar banza a Gidan komi ya faru ke ki ka buɗe ƙofar fara faruwar sa,ki kiyaye kan ki in har na gano da sa hannun ki akan duk abinda ya faru",Momy Hibba na kaiwa nan a zancen ta nufi Door ɗin Jaheed ta fara bugawa cikin tsanaki tana yi tana kiran sunan shi gami da cewa ya buɗe ita ce. Jiki ba kwari ya zo ya buɗe mata ƙofar ya na buɗe mata ya juya nan fa ta bi shi ciki ta na mai dakatar da shi da cewa,"Me ya ke faruwa,garin ya ka ke son aikata wannan shirmen,kana cikin hankalin ka,ina ilimi da hankalin ka su ka tafi,ko ka fara shan wani abu ne?",da wani irin sauri ya ɗago idanunsa cikin rawar baki ya ce da ita,"Momy ke ma har da ke,kin san kuwa me ta aikata min,dan Allah ki ce Gimbiya Ayush ta tafi bana son ganinta,ina tuna ko sunan ta sai in ji Zuciya tana barazanar tashi ƙirjina ya ƙoƙarin fitowa waje",ya kai zancen ya na mai matsowa kusa da ita ya ɗora kansa a kan kafaɗarta,nan da nan hawayen da ya ke son dakatawa su ka fara sauka a jiki ta,ɗimin na ratsa jikinta,ba ƙaramin tashi hankalin ta yai ba,kuka yau Jaheed ne ke zubar da hawaye daga cikin idanunsa akan wani lamari shakka babu wannan lamarin ba ƙaramin ne ba,da kanta ta ja shi zuwa Bathroom ta sashi ya ɗaura Alwala ya fito ta shimfiɗa masa prayer mat,ta ce da shi,"Zauna karanta abinda ya sauwaƙa ko yayah ya ke, zaka samu sauƙin abinda ka ke ji a cikin ranka. Sai da ta ga yafara karatun kafin ta fito gurin da su Yayah Hanne su ke tsaitsaye suna jiran su ga fitowar ta. "Yayah Hanne akwai matsala,koma me ya faru a Gidann ba ƙaramin ba ne,rabon da in ga Jaheed a cikin irin wannan halin har na manta,ina mai tabbatar maki duk yanda za ai ba zai iya fadar abinda ya faru a yanzu ba". "Yau Ni kam na ga abinda ya girme ni,to mu Shikenan yau a nan a tsakar Gida zamu ƙare sai ka ce marasa magayi?",ta mai da kallonta inda Gimbiya Ayush ta ke sai faman rusar kukan ta take,"Ke ƴarnan ki dubi Girman Allah da na Annabi sa ki sanar da mu me ki ka aikata ma wannan yaron da har ki ka jefa shi cikin irin wannan mummunan yanayin,kin ga gaba ɗaya kin tashi hankalin mu,ko iya wannan aka bar ki da shi kin kwashi alhaki mai tarin yawa". Ka sa cewa komi Gimbiya Ayush tai sai ƙara fashewa da kukan da ta yi da iya kacin muryarta,"Ahaf kin gani ko Hibba,da ma abinda na zata kenan ba zata ce komi ba,da ga gani ke ce ba ki da gaskiya tunda na ga irin kukan da ki ke nasan na dana msani ne". Shigowar Motar Hameed ce ta ɗan ɗauki hankalin su,shida Fadeela da suka haɗu a hanya tana ƙoƙarin zuwa Gidan Motar ta talalace shi kuma ya biyu sahun Jaheed,ma su sayar da da filin sun zo shi ake jira,dama ya je ne yana faman jiran su ba su zo ba shine ya gaji ya dawo Gida ashe rabon ya ji ma kan shi abinda zai hana shi zama lafiya ne,ya sauya masa sunan rayuwar farin cikin da ya daɗe ya na yi,wacce ya rada mata suna mafi soyuwa a gare shi. "Momy lafiya ya na gan ku duk a waje Gidan lafiya,ina Yayah Jaheed ɗin ya ke,ko bayanan ne?, shi na zo nema na masu sayar da Filin sun zo". "Yana ciki sai dai amma ba ya cikin yanayin da zai iya haɗuwa da wasu masu sai da fili",Yayah Hanne ta ce da shi. A ɗan rikice ya jero mata tambayoyin da suka zo mashi a cikin rai,"Lafiya me ya same shi,ko bai da lafiya ne,in be lafiya ai Hospital ya kamata a ce an kai shi ba ku bar shi a Gida ba". "Tambayi waccan itace tsunma maƙunshin cutar da ta cutar da shi,saboda tsabar rashin imani da rashin jin tausayin ɗan Adam ta ƙi faɗin me ta yi masa bale a samu a sami bakin zaren",cewar Ummu Nurain da ta kasa iya cigaba da riƙe kanta. A ɗan firgice Fadeela ta iso gurin gami da tunkarar Inda Gimbiya Ayush ta ke,ita da tun da farko bata fahimci abinda ke faruwa ba,ko Gimbiya Ayush ɗin ma ba ta gani ba sai yanzu da aka nuna ta ta ganta,da hanzarin ta ta isa gurin ta na mai haɗa ta da jikinta tana mai lallashinta". Biba ce ta ɗan matso kusa tare da cewa"Mama ko dai za a sa ta tafi Gidan su ne,ko hakan zai sa Yayah Jaheed ya samu sauƙin abinda ya ke ji game da ita,in kuma ba haka ba bamu san ta inda za mu shawo kan matsalar ba". "A'a babu inda za ta har sai ta faɗa mana duk abinda ya faru in kuma ta ƙi sai mu danganta lamarin da iyayenta,domin a yanzu ita kaɗai ce za ta iya sanar da mu asalin gaskiyar abinda ya faru,shi dai a wancan halin da ya ke ba mai iya sauko da shi dan yanzu". Cikin ɗacin zuciyar da ya fara ziyar Gimbiya Fadeelah ta tambaye ta da cewa,"Aunty Gimbiya me ki ka aikata, wanne irin laifi ko zunubi ne ki ka aikata da har ki ka cancanci a yi maki wannan taron gangamin ?","Fadeela dan Allah ki dakatar da su kar ki bari su kira Fulani ko Me martaba su sanar da shi abinda ya ke faruwa,dan wallahi nasan ba za su hukunta ni ta daɗin rai ba". "To in har ba ki son haka ta faru to ki sanar da mu abinda ki ka aikata ma ɗan mu duk yabi ya fita a cikin hankali da tunanin sa".. Sai da Gimbiya Ayush ta runtse idanunta kam jikinta ya ƙara rawa kafin ta fara magana muryarta na rawa,"Asiri na da na daɗe ina binnewa a cikin Gidannan ne ya tuni...","Asiri...asiri kuma wanne irin asiri ?","Ya kamani dumu-dumu muna fira da ƙawata akan yanda zan ...zan zubar da Cikin da ke jikina,bayan na yi niyar zubar da shi tunda farko Allah bai yi ba,duk yawan missacarage da na ke ba na Allah da Annabi ba ne ba ni da kaina na ke shan magani ko allura cikin ya zube,ba yau na fara aikata hakan ba,amma Allah na rantse maku sharrin sheɗan ne,haka ba za ta sa ke faruwa ba,ina son Mijina,Ina son zama da shi dan Allah ku ba shi haƙuri kar ya kore ni". Sallallami sosai Yayah Hanne ta saki kafin ta ɗora da cewa,"Ai lalle dole ne ki ke kuka,ke ko wacce irin Mace ce ke haka,me ki ke nema a duniya da har ya ja ki ki ka aikata wannan ɗanyan aikin,gaskiya kin ba ni kunya,dole ma yake cewa ki tafi Gidan ku baya ma ko son ganin ki balle ya ji Muryar ki,wace ce ke me ki ke taƙama da shi,da har za ki riƙa watsar nasa da jinin sa a rariya,ba sau ɗaya ba sau biyu va sai ka ce ƴaƴan shegu,dan haka tun da wuri ɗau hanya maza a tafi a je a sanar da iyaye abinda aka aikata"..."A'a Yayah Hanne abun bai kai haka ba,ba sai ta kai ga tafiya Gidan su ba maganar za ta yi tsawo da yawa,mu bi komi a hankali,mu tafi da ita zan zuwa gidanmu in yaso ko zuwa gobe ne sai mu zauna mu tattaunawa akan batun kamar hakan sai ya fi",","A'a ko da wasa ban aminta ba,ta tafi Gidansu itama Iyayenta su san irin kuskuren da ta aikata,ai wannan magana ba ta wasa ba ce, Allah kaɗai yasan iya adadin yaran da ta murƙushe ta niƙe su gami da watsar da su a rariya dan haka ta tafi Gidan su,ko ma meye ma biyo sawunta nan",Nan fa hankalin Gimbiya Ayush yai ƙololuar tashi iya tashin hankali ta gani,babban abinda ta fi tsoro Maganar ta koma kunnen Me martaba don ta Fulani mai sauƙi ce,haka dai tai ta ƙoƙarin ganin sun barta a ɗakinta amma fafur Yayah Hanne ta hana,in Momyn Hibba ta bude baki za tai magana sai ta dakatar da ita, ƙarshe Fadeela ce ta tasa ta don dole su ka tafi ba dan ta so ba, Haka su ka ɗunguma su duka su ka tafi can main house ɗin nasu aka bar Ummu Nurain cike da tarin mamaki,a ka barta daga ita sai Jaheed da bai da buƙatar kowa a kusa da shi. Part 45 Jiki a sanyaye Ummu Nurain ta iso kusa da inda ya ke zaune ta aje masa Abincin da ta kawo masa tana yi tana satar kallon shi,har ta miƙe za ta bar wurin ta dawo ta zauna ta fuskance shi da cewa,"Dan Allah ba dan halina ba ko yaya ne ka ci wani abu daga cikin abinda na kawo maka,ba zan iya jure ganin ka a cikin irin wannan yanayin,kuma ga shi tafiya za kai mai nisa ya kamata ka ci wani abun,dan Allah". Shima gyara zaman shi yai tare da cewa da ita,"Ki yi haƙuri,na yi maki tsawa,na horar da ke ba bisa laifin ki ba,ki yafe ni kinji Mata ta". Wata ajiyar Zuciya Ummu Nurain ta saki mai ƙarfi,kafin hawaye su biyo bayan ta,ba ta ce komi ba kan abinda ya ce sai cewa tai,"Me zan zuba ma ka,ko Black bhazar Coffee zan fara haɗa maka",ta kai zancen tana mai ƙoƙarin buɗe plaks ɗin,hannunsa yasa ya riƙe na ta tare da cewa,"Ba abinda zan sha matuƙar ba ki furta kalmar yafiya a gare ni ba,zan zauna da da yunwa har in tafi Bazan ci komi ba". "Ka bari in haɗa maka,domin Ni ban ji zafin ka ba,kawai dai na ji ba daɗi da dana ga laifin wata ya shafe ni,kuma nasan kaima hakan ya faru ba don son ranka ba","Na gode da wannan karamcin na ki,amma ina gani kamar Babban Gida ya kamata ki koma har zuwa san da zan dawo bai kamata kina ɗauke da irin wannan Cikin a ce ,ki zauna ke kaɗai duk faɗin shi","Hmmmmm in ka ce in tafi zan tafi,haka ma in ka ce in zauna zan zauna domin ni gareni wannan Gidan ya fiye min ko'ina,na fi son in zauna a cikin sa kamar Sarauniya","Haka ne amma saboda tsaran lafiyar ki zai fi kyau ki tafi can","To zan tafi Abu Nurain amma dan Allah in ka dawo ka rage wannan yawan tafiye-tafiye mu Ahalin ka muna buƙatar ka,mu na san ganin muna samun lokacin ka ko yaya ya ke",. "Zan duba hakan Ummu Nurain amma ban miki alƙawarin a kan hakan ba,domin duk ɓangarorin guda biyu duk sun zame min kusan dan dole,daga ɓangaren yaɗa Addini sai kuma ɓangaren Ceton rayukan muta ne,to kin ga a cikin su ba wani na bari","Ya kamata ko yaya ne a duba magabana,ko ba yanzu ba","To shikenan zan duba in Sha Allah","Yauwa Abu Nurain bari in je in haɗa maka sauran kayan da za ka tafi da su,domin na fara ɗazu na aje gaba ɗaya hankalina na kan ka saboda ba ka ci komi ba","To bari in zo in taya ki ,in muka gama da nawa sai mu haɗa naki ke da Nurain","A'a zauna ka ci Abinci ka na hutashshe ka yanzu zan gama". √√√√√√√√√√ “Sister Zahara Komi ya kammala ko?", Jadeeda ta tambaye ta a hankali. "Komi ya kammala Jadeeda kamar yanda ki ka so,amma dai...",ta ɗan dakata ta na maida hankalin ta akan Jadeedar. "Kai na gode Allah,na samu natsuwar ruhi da jin haka"."Amma Jadeeda ba ki ganin hakan a matsayin babban kuskure ta ya za ki ce za ki bar gida, Revered Anderson ya dawo ya tsawatar game da lamarinnan,kuma jikin Madan Gloria yayi sauƙi komi fa a hankali ake samun sa" . "Sister Zarah kiyi haƙuri amma ba zan iya janyewa daga wannan tafiyar ba,nasan kin girme ni,mun zauna a tare cike da amana da kuma mutunta juna,ba za ki bani shawara wacce za ta cutar da ni ba,ina baki haƙuri akan ƙin ɗaukar shawarar ki a wannan karon". Sister Zahara ta kalle ta na ɗan lokaci kafin ta ce da ita da cikin taushin murya da son shawo kanta, "Ke kin san, akwai bambanci tsakanin guje wa matsala da kuma fuskantar ta da zuciyar da ba ta jin tsoro,shin dan me zai sa ki yanke wannan hukuncin?,wanda zai iya jefa ki a cikin halaka". Jadeeda ta yi shiru. Idonta ya cika da hawaye, zuciyarta kuma na bugawa.ta dubi Sister Zahara tare da cewa,"Bazan iya ba....ba zan iya janyewa daga wannan tafiyar ba,ina jin acan ne kawai zan samu salama da kwanciyar hankali,komi zai koma Normal idan ya kasance bani nan,domin kumi ya faru a sanadina ne,Ni ce silar komi,domin Ni sheɗan ya samu mafaka a cikin Zuciyoyinsu,za su dawo cikin hankalinsu, natsuwa da kuma tunanin su,idan komi ya lafa zan dawo". Sister Zahara ta bude Jakar da ta zo da ita ta ciro,Biza ta miƙa mata tana yi tana waige-waige don kar wani ya ganta kafin ta ce da ita,"Kafin ki tashi, ki tabbatar kin gama da dukan sirrin zuciyarki. Kasar da za ki je ba za ta share maki hawaye ba sai zuciyar ki ta yarda da ita ce take da ikon yin hakan." Jadeeda ta kalle ta da idanunta a waje da son fahimtar me ta ke son cewa,ganin kamar abun zai ja ta ta da nisa yasa ta amsa kawai gami da yi mata godiya tare da cewa,"Na roƙe ki ki riƙe min wannan a matsayin sirri kar wanda ya sani,ba na son kowa yasan ina zani komi rintsi ko wuya zan dawo da lokacin hakan yayi,na roƙe ki kin ji Sister Zahara"."Indai don ta ni ne kar ki damu,babu wanda zai ji,amma na roƙe ki da ki sake duba wannan lamari Jirgin Ak Peace shi za ki bi zai tashi ƙarfe 4pm amma sai dai ki yi haƙuri domin Jirgin ki Transcit Flight ne za ki iya samun delay na wucin gadi,amma dai by the grace of God za ki isa lafiya , sannan zai fi miki ki sauka a garin Quebec ko kuma Montreal zai fi miki daɗin zama, sannan ki kula da matakin lafiyar ki". "For the sake of father lord ba abinda zai same ni,tamkar zan yi hijira ne, Jesus Christ zai bani kariya,ya sani zan aikata hakan domin guje ma faɗawa daga halaka ko kuma sauka daga kan littafin shi littafin tsira Bible","Amen Jadeeda zan taya ki da addu'a kin ji",ta kai zancen ta na mai dafa kafaɗar ta haka dai su kai bankwana kafin Sister Zahara ta tafi da sauri ta na yi tana waige-waige,sai da Jadeeda ta tabbatar da wucewar Sister Zahara kafin ita tama ta tafi bayan tabbata babu wanda ya gan su. "Aunty Jeeyyyy lafiya me ya faru daga ina ki ke tunda safiyar nan,na shiga Bedroom ɗin ki na iske ba ki nan ?",Nora ta tambaye ta"Ba ko ina na ɗan fita waje ne na shawo iska",ta ba ta amsa ba tare da ta yarda sun haɗa ido ba kuma ta na magana ta na tafiya. Da kallo Nora ta bi bayanta da shi,kafin ta gyaɗa kai ta cigaba da tafiya zuwa inda ta nufa. Jadeeda tunda ta shiga ɗakin ta ke daman kai kawo,"Yanzu ya zan yi, Flight ɗina zai tashi around Four ya kamata ace before time ɗin na bar Gida,kuma in bar Gida ba tare da wani ya farga ba ,domin in hakan ya faru zai iya zama tsaiko ko dalilin da zai hana ni tafiya,to yanzu ya zan yi,gashi yanzu Past Eleven ya zan yi,dole ina buƙatar tafiya da wasu kayan tunda ban san kowa a can ba,to ya zan yi?", shiru ta yi na wani lokaci kafin ta ce," Yes na samo mafita". Wurin Momy ta nufa ta iske ta kishin giɗe tamkar wacce ta lula wata sabuwar duniyar ta tunani,"Mommy kina lafiya kuwa?", Murmushin yaƙe ta yi mata kafin ta gyara zama ta ce da ita ,"Me ki ka gani ne Sweathert?","Mommy duk wanda ya kalle ki yasan You are not in the mood ba haka ki ka saba zama ba ,komi na ki ya sauya kuma duk a saboda ni....","A'a Jadeeda ba laifin ki bane wadancan shashan ne da su ka ja komi sune ke da laifi ba ke ba". Rausayar da kanta gefe tai gami da saurin kawo maganar da ta kawowa kar ta bari damar ta suɓuce mata,"Am Mommy wai Ezekeal ne ya kira wai da buƙatar in zo yana son gani na,wai wani case ya taso a ɗaya daga cikin ƙauyukan da mu ke zuwa Bushara ,to na ce masa ba zan sami damar zuwa ba shine ya matsa na ce bari in zo in sanar da ke". "To mene ne a ciki Dear ki tafi mana ko ba komi za ki ɗan rage abinda ki ke ji in ki ka shiga cikin mutane biside ma aikin lada zaki don haka ba ni da ja ki tafi sai kin dawo ,Yesu Almasihu ya albarkace ki a tafiyar da za ki ki je ki dawo lafiya",sai da fuskar Jadeeda ta faɗa ta rungume ta gami da cewa,"That's My Sweat Mom na Gode da samun ki da nai a ciki rayuwata". "Nima na Gode ma Jesus da ya sanya ki ka kasance ɗaya daga cikin tsatsona,amma dakata ba zaki kai 4pm a waje ba ko". Sai da Jadeeda ta yi jim kafin ta ce"Ehhhhh to ba lalle ba,domin case ɗin na wata ƙaramar yarinya da ke fama da ciwon zuciya to muna son foundation ɗin mu yaɗauki nauyin aikin da za ai mata ne, da zaran mun yi solving ɗin sa zan dawo buy the grace of God". "Okay ki kula ki kira ni ki sanar da ni komi ke faruwa kin ji,in ma da buƙatar mu sa hannu a cikin lamarin sai ki sanar da ni","Wai da na ce ina Martin ya ke ko shine sai mu tafi tare ban san tafiyar ni kaɗai",ta ƙare maganar zuciyar ta na bugawa da ƙarfi da addu'ar Allah ya sa baya Gidan,"Sun fita shi da Papa ɗin ku,ita kuma Nora Unexpected test ce ta taso ma ta tafi school sai dai ko kusa Driver ya kai ki","A indai haka ne Gara in tafi ni kaɗai ,na yi driving ɗin da kaina amma kafinnan in wuce zan shiga Church ɗin Our Lady Queen of Nigeria Pro-Cathedral","Kina ganin ba zaki sanya su ta jiran ki ba","A'a Bazan jima ba zan wuce,ina so in ɗan yi addu'o'in ne kafinnan","okay ba matsala ina maki fatan alkairi sai kin dawo". Da wannan damar ta samu ta haɗa duk abinda zata buƙata tasa a cikin troly ta saɓa ta fitowa ta ci karo da Ester wanda har sai da gabanta ya faɗi,"Aunty ina za ki haka na ga kin fito da sauri irin haka?",sai da Jadeeda ta haɗiye yawun da ya tarar mata a baki kafin ta ce da ita,"Wanki zan bada na","Wanki kuma Aunty ba akwai Machine ba?",Cigaba da tafiya tai kafin ta ce da ita,"Bana da buƙatar shi ",idanu Ester ta zaro waje ta na mai cewa a cikin Zuciyar ta,"Anya kuwa lafiya,Aunty Jadeeda ba haka ta ke ba,ba ta magana da mutun a irin wannan yanayin kuma na ga kamar unguwa za ta ,Uhmmmm ba ruwana",ta ƙare zancen ta na mai tafiyarta abinta. Kai tsaye Church ɗin ta nufa acan ta kwashe tsawon lokaci acan sai da taga gabatowar 4pm sannan ta baro cikin Church ɗin ta samu wani ɗaya daga cikin masu aikin Cleaning a cikin Church ɗin ta kira shi gefe guda ta ce da shi,"Ina son za ka yi min wani aiki zan biya anan take shin kana da interest akan shi?,zan biya ka 50k anan take just delevering ɗin saƙo za kai min zuwa wani address da zan baka",zaro idanu waje yai alamun zuciyar shi na son kuɗin kafin ya ce,"Anya ba akwai wani abu a cikin wannan aikin da ki ke son sanya Ni acikin da ba,ma'ana akwai lauje cikin naɗi akan shi ba","Ba wata manufa a bayan haka,tafiya ce ta gaggawa ta ka mani zan baka keyn Mota ta ka kai min ita,zuwa Gidan mu,da takarda da zaka ba su in ka isa, simple shine kawai,na faɗa maka haka da iya gaskiyata ba zan cutar da kai ba,nan guri mai tsarki mu ke,ba zan faɗa maka akasin gaskiya". "To shikenan na yarda da ke","Amma ina so sai nan da 6pm za ka kai sauƙin",da to kawai ya amsa mata ta je farking space ta nuna masa Motar tafidda trolynta ta ba shi keyn sannan ta tafi ta tari tacxi ta nufi Airport kai tsaye. Bayan awannin biyu da tafiyar Jadeeda a kai sallama a bakin gare ɗin Gare Akan ɗin Gidan ya leƙa ya ga wani Magidanci tsaye da takarda a hannunsa ga kuma Motar Jadeeda tare da shi,"Lafiya Malam na gan ka anan ko wani ka ke nema ne?",Gate Man ɗin ya tambaya. "Eh wani daga cikin Halin Gidan na ke nema domin in isar da saƙon da na zo da shi","Kamarya wani daga cikin Gidan kana da alaƙa da su ne","A'a kawai dai an bani saƙo ne,wanda zan fi son in ba wani ahali na Gidan",Shiru Gate Man ɗin yayi kafin kuma ya ce da shi,"A'a ka dai fara sanar da ni abinda ke tafe da kai sai in ji daɗin sanar da mutanen Gidan abinda ya kawo ka ba hakanan in tunkare su da labarin da ba ni da wata masaniya akan sa ba","Zan dai fi son ka kiramin wani a Gidan sai a yi komi a gaban ja domin Ni ban zo da wata cuta ba".....Isowar Nora wurin ya dakatar da musayar yawun da suke ,ta dakatar da gami da tambayar Gate Man ɗin da cewa,"Baba Joshua lafiya na ga Motar Aunty Jeeyyyy a waje ?","Nima yanzu na fito na iske ta anan da alama dai wannan mutumin ne ya zo da ita",da sauri Nora ta maida hankalin ta akan mutumin da aka nuna da sunan shine ya zo da Motar,"Ina ka sami wannan Motar,Ina mai Motar ta ke,meye haɗin ka da ita", wannan sune jerin tambayoyin da Nora tai mi shi a ƙagauce da son jin amsar su. "Kwantar da hankalin ki me motar da kanta ta bani ita gami da bani address ɗin wannan Gidan ta ce in kawo ,in sanar maku tafiyar gaggawa ce ta risketa,ga wannan takardar da ta bani don ku tabbatar da abinda na ce da gaske na ke",ya kai zancen ya na mai miƙa mata ,tana amsa ya juya yai tafiyarsa ba tare da ya tsaya ba. Ita kuwa Nora a hargitse ta shiga cikin Gidan kamar wacce aka biyo,tun kafin ta shiga ta ke kwalama Momy kira,"Lafiya Nora me yake damun ki za ki shigo Gida a cikin irin wannan yanayin,sai kace makauniya". "Momy ina Aunty Jadeeda,ina ta tafi?","Nima abinda na ke tambaya kenan ki ka shigo",cewar Papa da ke zaune a kan dinning suna cin abinci". "Ohhh,ta tafi duba wata Yarinya mai ciwon zuciya ƙarƙashin Foundation ɗin su, Shikenan ko sai ki samu wuri ki zauna kin shigo kina ƙoƙarin tada ma mutanen Gida hankali".....,"Kin kirata ko kuma ita ta Kirani tun bayan tafiyar ta?",Papa ya tambaya. "A'a na yi ta trying number na ta amma a kashe ba ta tafiya wani lokacin ma sai ace min not reacherble". "To ga Motar can wani ya kawo ya ce,wai a gaya maku tafiyar gaggawa ce ta kamata,da kuma wannan takardar",ta kai zancen ta na mai miƙa masu Papertun kafin wani ya motsa Papa yace,“Ina ita Jadeedar? Me yasa wani ya kawo Mota da wannan takardar?!” Papa ya buge da tambaya, yana ƙoƙarin ɗaukar takardar. Gidan kowa ya firgita, Zuciyoyinsu sai faman kai komo take da son sani ne takardar ta ƙunsa Granny tana zaune dafe da ƙirjinta, Papa har ya fara fitar da ɗigon zufa . Momyn Jadeeda kuwa ba ta iya ɗaga kai ba. Papa ya buɗe takardar cikin sauri, zuciyarsa na dukan bugun tashin hankali. Granny ta daga hannu tana karanto addu’a a cikin ranta, kamar zata faɗi,Papa ya fara karantawa kamar haka “Ina roƙon gafararku… Ba don na tsane ku ba ne na tafi, sai don na rasa inda zan nufa,Zuciyar ta kasa iya ɗaukar abinda ya tunkaro ni. Kowane numfashi a cikinsa akwai ruɗani, tsoro da ɓacin rai. Idan ni ce kuskure, sai na zauna kuma na rayu da shi Ban san inda nake nufa ba, amma ba zan iya komawa inda ku ke ba. Ina mai tabbatar maku da zan dawo amma sai Sheɗanin da ya ƙawata Zukatan Ƴan'uwana kuma makusanta na ya bar gangar jikinsu,to a sannan zan dawo,ina kewan dukkanin kulawa da soyayyar da ku ke nuna min,zan yi rayuwa a inda na ke cike da kewar ku. Uncle Miey har yanzu matsayin ka yanan a cikin raina bai sauya ba,haka kaima Bro Edwin,Nora da Martin zan yi kewar ku,ku kula min da Mommy da kuma Papa har zuwa sanda zan dawo.” Jadeeda Uncle Miey ya dafe bango, yana kallon Edwin,“Mun cuce ta...!” Granny ta faɗi da hawaye. "Kai ne dai ka cuceta,kaine mabuɗi kuma sular faruwar komi,kai ne ka cuceta", Uncle Richal ya faɗa cikin hargowa yana nuna Edwin da ya yatsa Papa ya jefar da takardar, ya nufi inda Madam Gloria ta zube ƙasa tana kuka mai cike da raɗaɗi ba kuka irin na ɓacin rai kawai ba, amma kuka mai tambayar "me ya faru da ƴata Jadee?,ina take a halin yanzu wacce irin rayuwa za ta riska a duk inda ta ke,shin sake jefa kanta cikin wata rayuwar mai cike da hatsari tai ko ko hanyar mafita ta samar kanta a sanadin barin Gida" Amma tabbas barin Jadeeda ya bar ƙura, damuwa, da abin da babu mai iya warwarewa,face sai lokaci domin shine alƙalin da baya ƙaryata,kuma baya cuta ko kaɗan. Ina farin cikin sanar da ku cewa an buɗe Paid Group na Littafin JADEEDA domin masu sha’awar ci gaba da karanta wannan labari mai cike da sirri, ƙauna da ruɗani. Farashi: ₦300 kacal. Za ku samu damar karanta Jadeeda har zuwa ƙarshe cikin sirri da tsari. Account Number: 8102641528 Bank: Opay Sunan Sumayya Usman Kai tsaye za ku iya tuntuɓar ta ta wannan Lambar waya 08102641528 Bayan biyan kuɗi, ku tuntuɓe ni kai tsaye domin a saka ku cikin group ɗin. Mun gode da ƙauna da goyon bayanku kullum. 💕 Cwt~Sumiey ✍️