*FANSAR ƘAUNA!* *HADIZA D. AUTA* MARUBUCIYAR; ABOKIN AIKINA BAƘON YANAYI A'ISHA DIJE ƘARANGIYA AMFANIN FITILA *Na san wasu za su tuno da ɗayan cikin littafanta. To ku karkaɗe kunnuwanku ku sha labari, yanzu ma ta zo muku da sabon salon labari mai cike da abubuwan al'ajabi, ruɗani da tarin rikita-rikita a cikin wannan littafi na fansar ƙauna. Bayan zallar soyayya mai tsuma zuciyar makaranci. Ku biyo mu sannu a hankali kada ku bari a yi wannan sarƙaƙiyar tafiya ba tare da ku ba.* ƊANƊANO! Kano ƙarfe 8:30pm. Motocin ɗaukar amarya jere da juna suna ta gudun tsere a saman babban titin Ahmadu Bello Way. Sun bi layi suna ƙyalli tsabar sabunta, saboda duhun dare ya ƙara ƙawata su a idon masu kallon wucewarsu ɗaya bayan ɗaya. Waɗanda ke cikin motocin kuma, sun yi jugum kowa da abin da yake saƙa wa zuciyarsa, yayin da fuskokin wasun su ke ƙumshe da zallar farinciki da hira a tsakaninsu jefi-jefi. A cikin raha da annushuwa abokan amarya suke ta tsokanar ta ganin yadda ta yi ƙuri da ido tana kallon tsakiyar titi ko ƙiftawa babu. Bayan tagumin da ta rafka da murmushin yaƙe tamkar an yi mata dole yin sa a daidai lokacin, tsabar fargaba da tashin hankali sun yi mata lulluɓi gumi ya hau feso mata a goshi, ta shiga fifita da gefen mayafinta tamkar babu iskan A.c a cikin motar. Shigar jerin motocin a cikin unguwar Nasarawa, da saukar zugar 'yan kawo amarya; ya yi daidai da isowar motar ango da wasu abokansa a ƙofar tamfatsetsen gidan. Wanda ya sha sabon fenti da hasken ƙwayayen lantarkin da ke maƙale a jikin katangar gidan lungu da saƙo, inda hasken ya gauraye ko'ina har cikin gidan da wajensa gabaɗaya. Guɗa ta kaure a lokacin da ango ya isa bakin motar da aka saka amarya, ya fito da ita da kansa, bakinsa har kunne abokansa da wasu danginta suna ta ihun farinciki. Don tarin dandanzon mutanen da ke wurin bai hana shi rungume ta a jikinsa ba, yana maƙale da ita suka fara tattaki a hankali har zuwa cikin gidan cikin takun isa da taƙama. Aka bi su ɗii a baya cike da burgewa ga wasu, yayin da hakan ya bai wa wasu 'yan adawa haushi matuƙa suna guntun tsaki. Duba da yadda ya hana gwaggonnin amarya riƙe ta zuwa cikin gidan da kai ta har ɗakinta, kamar yadda al'ada ta tanadar. Guɗa ta ko'ina sai tashi take yi, hakan ya ƙara raunata zuciyar Nur da ke jefa ƙafafuwanta ido rufe cikin sanyin gwiwa har zuwa ɗakin. Bayan an wuce babban falo aka haye saman bene inda wasu ɗakuna uku suke, sannan da wani ƙaramin falo mai ɗauke da dinning table a gefensa. Da kansa ya zaunar da ita a saman makeken gadonta wanda ya kusa cinye rabin ɗakin, sanan ya shiga leƙa fuskarta da ke cikin mayafi yana wani irin tsadadden murmushi har dimple ɗin sa ɗaya yana lotsawa. Cike da kunya ta shiga sunne kai a lokacin da ta kai bayan hannunta tana goge guntuwar ƙwallar da ta fito idonta tana ƙoƙarin bin fuskarta. Sosai lallen hannunta ya ɗauki hankalin angont,, saboda ya sha jan lalle da baƙi kuma ya fito fes tamkar don ita aka halicci kalar ƙunshin. Dole ta saka shi yin kawaicin sakin hannunta da ke cikin nasa gam-gam, sannan ya dinga kutsawa cikin dandazon matan da suka cika ɗakin ya fice cike da shauƙin ƙaunarta a ransa, yayin da wasu abokan wasansa da nata suka raka shi da guɗa bayan zantukan tsokana iri-iri. Amma iya murmushin kan fuskarsa kawai ke nuna sarai ya ji su, saboda bai iya tankawa kowa ba a dalilin sauyin da jikinsa ya yi a cikin ɗan lokaci. Ficewarsa daga ɗakin, ya bai wa wasu damar tofa albarkacin bakinsu, ta hanyar yi musu addu'ar zaman lafiya da yabon tsarin da aka yi wa gidan da kayan adon zamani masu ban sha'awa. Mintuna a tsakani aka shiga shelar 'yan kawo amarya su zo a mayar da su gida. A hankali mutane suka dinga ficewa zuwa ƙofar gidan bayan sun yi mata sallama da addu'ar zama lafiya. Har aka bar ta da amintattun ƙawayenta guda biyu. Waɗanda suka sha ado tamkar su ma amaren ne. Musamman Minal wadda kusan komai nata iri ɗaya da amarya, kama daga kan lallensu, shigar kayansu da kalar ƙamshin turarensu duka. Saboda Nur da kanta ta feshe Minal da turaren bayan ta gama saka wa jikinta tana cewa, "Ya dace ita ma ƙawar amarya ta yi ƙamshi." Bayan fitar 'yan kawo amaryar; Nur ta miƙe cikin sauri ta nufi ƙofar fita daga ɗakin cikin sassarfa, babu shiri ta waigo saboda hannunta da Minal ta cafko da zummar yin magana. Nur ta riga ta yin maganar jikinta yana rawa muryarta tana sarƙewa ta ce, "Ku..ku ɗan jira ni Amna..., ku..ku..bari zan karɓo saƙona a hannun Aunty Jamila kada ta manta da shi ta wuce gid..." Cikin zafin nama ta fice, ta bar Minal da Amna suna kallon ƙofar kamar masu nazartar samfurinta. Cike da tsumayen dawowarta kusa kafin su sauke ajiyar zuciya a lokaci ɗaya tamkar sun yi shawara da juna. Amna ta miƙe tana ƙara gyara shimfiɗar gadon sannan ta ƙara feshe ɗakin da turarukan ƙamshi tana faɗin, "Yau dai hankalin kowa zai kwanta, mun kawo wa Auncle J matarsa an huta." Minal ta yi shiru na ɗan lokaci, sannan cikin sanyin murya ta ce, "Ni ma yau zan yi bacci har da minshari, babu tunanin za a yi kaza gobe ko wuri kaza za a je tun da sassafe." Suka yi murmushi dukansu kafin kowanensu ya shiga danna waya shiru ya ratsa ɗakin. Tsawon minti goma da fitar Nur amma har lokacin ba ta dawo ba. Minal ta miƙe cike da fara'a saboda tuno halin Jamal da aika-aikarsa a kan Nur ba ya shayin idon kowa. "Kada fa ta shanya mu a nan, dare ya yi mana ango ya raka mu da doguwar sanda. Bari na je na nemo su a kammala komai mu ma mu yi gida mu yada haƙarƙari." Amna ta yi hanzarin faɗin, "Jira! Jira ni na je da kaina, kin san halin Auncl J ba ya jin bari a kan matarsa, wataƙila yana can ya riƙe mana ita su shanya mu a iska." Amna ta fice tana gyara zaman mayafinta a kafaɗa, ta bar Minal a tsaye kafin ta ja ƙafafuwanta zuwa jikin window, laluben tagar ta janye tana kallon farfajiyar gidan da tsirarun abokan angon da ke ta shewarsu kamar sun manta duhun dare ya lula, saboda komai tarwai kasancewar haske ya wadaci ko'ina tamkar rana. Ƙarar shigowar saƙon da ta ji a wayarta ya sa ta bar jikin tagar ta nufi jakarta ta fiddo wayar tana furzar da iska mai zafi a bakinta. Idonta a kan fuskar wayar cike da mamakin ganin Nur ce mai turo saƙon, ta shiga karantawa cikin fargaba tare da zaro ido waje. Kafin tashin hankalin da ya game jikinta ya sa ta ɗora hannu a ka ta shiga kurma ihu iya ƙarfinta babu ƙaƙƙautawa. Sautin ihun nata ya sa ango da abokansa tare da Amna rige-rigen isa cikin ɗakin. Ido tsakar ka suka shiga kallon ta baje ƙasa tana wani irin kalar kuka tamkar wadda aka yi wa saƙon mutuwa. A ruɗe suka shiga tambayar mafari, zancen ya yi mata nauyi faɗi dole da hannu ta yi musu nuni ga wayarta, bayan ta sassauta sautin kukanta tana rafka salati cikin wata kalar murya. Inda ta jefar da wayar ɗaga cikin abokan angon ya ɗauko a lokacin da kira ya sake shiga wayar tana ta ɓurarin. Jikinsa yana rawa ya miƙa mata wayar ta karɓa cikin kyarmar hannu tsabar bugun da zuciyarta ke yi, shiga buɗe lambobin sirrin wayar Amna ta yi hanzarin fisge wayar ta ɗaga kiran ganin sunan Aminiya tarwai a jikin fuskar wayar. "Minal, izuwa yanzu na sani kina cikin tashin hankali saboda ganin saƙona. To ki kwantar da hankalinki Allah ne ya ba ki Jamal." Ƙit wayar ta katse, Amna ta bi kiran cikin sauri amma tamkar almara ta ji layin a switch off. Cikin sauri Adamu abokin Jamal ya karɓe wayar a hannunta ya shiga karanta saƙon Nur da ya gani a rubuce. _'Minal na yafe miki Jamal duniya da lahira, saboda ke ce amaryarsa kuma da ke aka ɗaura auren ba da ni ba. Ki yi masa biyayya sau da ƙafa kuma ki yafe mini laifin da na yi aminiyata.'_ "Ba zai yiwu ba! Sam ba zai yiwu ba!" Furucin angon kenan a lokacin da ya ji saƙon Nur da abokinsa ya gama katantawa a fili. Wayarsa ya fitar daga aljihu jikinsa yana rawa ya shiga kiran ta, sai dai duka layukanta uku babu wadda ta shiga duk wadda ya kira a kashe yake jin ta. Hularsa ya jefar ya shiga yamutsa gashin kansa a haukace kafin ya hau zarya a tsakiyar ɗakin yana cizon haƙoransa, bayan ya cire babbar rigar da ke jikinsa ya wurgar yana tsuma. Cikin hanzarin ya dafe kansa saboda wani mugun bugun da ya ji a tsakiyar ƙwaƙwarsa a kan harbawar da jijiyoyonsa suke yi. Idonsa ya rufe ruf tsawon minti ɗaya sannan ya sake buɗewa babu shiri ya sauke su a kan Minal. Saboda wani tunanin da ya ɗarsu a ransa bai san lokacin da ya isa gabanta ya shaƙo wuyanta ba. Domin riƙon da abokansa suka yi masa da ƙoƙarin ɓanɓare hannunsa a wuyanta bai hana shi zare idonsa da suka rine cikin ƙanƙanin lokaci ba. Magana ya yi cikin kakkausar murya tamkar wanda ba ya cikin hayyacinsa. "Ko ki fito mini da matata ko kuma na zamo ajalinki a cikin wannan dare! Ba ki isa ki raba ni da farincikina ba! Nur rayuwata ce ko mutuwa ba ta isa ta shiga tsakanina da ita ba.... ƙarya ne! Na ce ƙarya ne Nur ba za ta guje ni b...." Kukan da ya sarƙe muryarsa ya sa jikinsa raunin da abokansa suka ci galabar ƙwatar wuyan Minal daga mummunan riƙon da ya yi mata. Tamkar ƙaramin yaro, ya shiga rera kuka wiwi yana faɗar maganganun da babu komai a cikinsu face zallar son Nur da ƙaryata abin da ya faru. Tare da alwashin yi wa Minal mummunan kisa idan ba ta yi gaggawar fito masa da matarsa ba. Da ƙyar abokansa suka fitar da shi daga ɗakin yana nuna ta da hannu, saboda yadda yake ji a ransa idan ya sake furta wata kalma daga bakinsa; zuciyarsa za ta iya fashewa tsabar nauyin baƙinciki ya danne numfashinsa. Oh Allah! Wannan babbar badaƙala ce mai zaman kanta. Ku ci gaba da biyo ni domin jin yadda za ta kaya. Kada ku manta sunan littafin FANSAR ƘAUNA. Ranar 15 ga watan January zan ci gaba daga inda muka tsaya. A taya ni sharing fisabilillahi! D. Auta ✍🏼 *FANSAR ƘAUNA!* *HADIZA D. AUTA* *Albishirunku! Ƙorafi ya karɓu, na janye 15 ga watan January da na faɗa zan ci gaba da yin posting. In sha zan ƙoƙarta ta yadda za ku dinga jin motsina har zuwa lokacin da za mu kammala book 1. Masu jiran sai sun ji ana faɗar labari ya yi daɗi su dinga faɗar daga farko ku taimake ni ku fara bibiya tun yanzu. Fatan alheri gare ku gabaɗaya.* *LAMBA TA ƊAYA.* Fitarsu daga cikin ɗakin ya saka minal fashewa da wani kalar kuka mai ɗauke da majina. Amna da ke tsaye wuri ɗaya tamkar an dasa ta tana zubar da hawaye, kukan Minal ya saka ta matsawa jikinta cike da tausayi ta dafa kafaɗarta tana bubbugawa a hankali, ba tare da tace komai ba. Saboda ita ma kanta ya gama ƙullewa tana buƙatar ƙarin bayani, don ba ta san me zai sa hakan ta faru ba kai-tsaye ba, sanin tana da cikakken tabbaci a kan Minal ba za ta cutar da Nur ba, kamar yadda Jamal ya yi hasashen ita ce ta ta yi sanadin gudunta. Sautin kiran da ya shigo wayar Minal, Amna ta yi saurin isa wurin wayar cikin rawar jiki ta ɗauko mata, saboda ganin an saka sunan Innarmu saɓanin tunanin da ya ɗarsu a ranta ko Nur ce ta sake kira. A cikin dasashiyar murya Amna ta ce, "Karɓi wayarki, Mamarku ce ta kira." Minal ta cakumi wayar cikin hanzari ta kai kunnenta, wani kuka ya sake kubce mata. Saboda lafazin da mahaifiyar ta fara furtawa mai kama da mummunan albishir. "Ki yi haƙuri Amina, ke taki ƙaddarar kenan ki yi ƙoƙarin cinyewa." Cikin hanzari Minal ta shafe hawayen fuskarta cike da mamakin lafuzan mahaifiyarta, saboda ba ta yi tsammanin cewa ita ma ta san wainar da Nur ta toya ba. Cike da ƙarfafa zuciyarta, ta haɗiye kukan da ke cikin bakinta sannan ta yi magana cikin raunanniyar murya ta ce, "Me kike son sanar da ni Innarmu? Ashe ke ma har kin samu labarin abin da Nur ta aikat..." "Ina sane Amina tun kafin yanzu, kuma sanin halin da za ki shiga ya sa na kira ki domin na yi miki kashedi. Amma ki yi haƙuri ki rungumi ƙaddararki da aurenki hannu biyu, kada ki kalli ƙalubalen da za ki fuskanta a wurin mijinki. Don Allah za ki yi kuma sakamakonki zai fito daga hannuns..." Cikin sautin kuka Minal ta katse ta da cewa, "Ban gane ba Innarmu! Ni fa gabaɗaya kaina ya ƙulle! Ta ya ya zan fuskanci abin da nake ji daga bakinki? Jamal angon Nur wanda muka yi taron bikinsu a yau duniya ta shaida; shi kike nufin zan zauna da shi a matsayin mijina na sunnah?" Ta ƙare maganar tana kore hawayen da ke yi mata fareti a kan fuska. Bayan tsumar da jikinta yake yi tamkar mazari tsabar firgicin da take ciki ya ƙara raunata ɗan sauran kuzarin da ya rage a jikinta. Ajiyar zuciya mahaifiyarta ta saki kafin ta yi maganar da ta daskare numfashinta, saboda kalamanta sun ratsa zuciyarta sun saukar mata da wani kalar firgici mai saka mutum zaucewa. "Amina, Jamal ke ya aura ba A'isha ba. Saboda haka ban yafe miki ba matuƙar kika taka ƙafarki wajen gidan da sunan barin sa ba tare da kin bi hanyoyin da za ki sasanta tsakaninki da mijinki ba." Ƙit ta kashe wayar, ta bar Minal riƙe da wayar a kunne tana zarar ido kafin ta fasa ƙara ta buga wayar ƙasa tare da kwarara wani kalar ihun da guntun fitsari ya kufce wa Amna, tsabar fargaba da tsoron Minal sun gama kama ta. Hakan ya sa ta kasa motsi sai idon da ta zuba wa Minal da ke ta birgima a tsakiyar ɗakin tana ƙaraji tamkar mai bugun aljannu. Kasancewar ta ji duk abin da suka tattauna, jikinta yana rawa ta ciro wayarta a aljihun rigarta ta ƙwala wa mahaifiyar Jamal kira, waton Hajiya Mummy. Cikin sa'a tana shiga ta ɗauka, a kiɗime ta yi magana tsabar ita ma ta kusa zaucewa. "Ha..Hajiya Mumm...mummy ki zo gidan Auncle J babu lafiya!" Daga can muryar Hajiyar ta fito raɗam tana cewa, "Ki yi ƙoƙarin kwantar mata da hankali ina kan hanyar zuwa gidan yanzu. Abokansa sun sanar da ni ya fisgi mota ya bar gidan ba mu san me zai faru da shi b..." Ta ƙare maganar cikin muryar kuka sannan ta katse kiran. Jikin Amna ya yi sanyi ƙalau, cike da ƙarfin hali ta isa wurin Minal da ke ta birgima har lokacin ta fara magana. "Ki yi haƙuri, na san dole ne ki shiga irin wanann yanayin a sanadin abin da ya faru. Amma ki sani komai na duniya fararre ne kuma ƙararre. Ki rungumi ƙaddararki kamar yadda Innarmu ta faɗa, wataƙila hakan zai iya kawo sanadin alheri a gab...." "Yanzu har sai na tsaya yi miki bayanin Jamal Nur yake so ba ni ba? Ta ya ya zan iya zama da wanda ba ya so na? Yanzu a gabanki kin ji yana faɗar sai ya kashe ni, mutumin da ke dakon yi wa rayuwata kisan gilla ake so na zauna da shi a matsayin miji da mata? Ba zai yiwu ba...ni ma ba na farincikin rabuwarsa da Nur saboda na sani ita ma tana son sa." Ta ƙare maganar tana zuƙe majinar kuka a cikin zafin zuciyar da take jin hayaƙinta yana ƙoƙarin rufe mata hasken ido. Cikin sanyin murya ta sake magana bayan ta yi durƙuso a gaban Amna gwiwa bibbiyu tana cewa, "Ki taimake ni ki taimaki rayuwar Jamal a matsayinki na 'yar'uwarsa. Don Allah idan Hajiya ta zo ki ce ta roƙi Innarmu ta jaye Allah Ya isarta a kaina. Saboda ko zan bi duniya na yi alwashin sai na bar gidan Jamal, kuma ko da ina fita ƙofar gidansa bakinta zai kama ni na fara ɗaiɗaicew..." "Dakata Minal! Kada ɓacin rai ya sa ki jefa kanka cikin fushin Ubangiji. Ki yi haƙuri ki bari mu ga yadda abin zai kasance, ba tare da kin yanke hukuncin da zai taɓa rayuwarki b.." Minal ta yi hanzarin miƙewa tsaye ta fara taku a tsakiyar ɗakin tana faɗin, "Rayuwa ta ba ta da wani amfani tun da har aka aiwatar da wannan ɗanyen aikin ba tare da sanina ba. Don haka ba zan yi wa kowa Allah Ya isa ba, amma tabbas ba zan taɓa yafewa b..." "Minal!" Amna ta kira sunanta da ƙarfi cikin wani sabon tsoro da ɓacin rai. Saboda jin furutanta kamar tana so ta wuce iyakar hankalinta duk da haƙurin da take ba ta. "Ki bar ni ina da ikon faɗar komai tun da aka yi mini abin da aka ga dama. Saboda ko za a mutu ba zan iya rayuwar aure da Jamal ba, kuma idan aka matsa kafin shi ya kashe ni ni da kaina zan fara aika kaina zuwa lahira." "Innalillahi wa inna ilaihirraji'un! Wannan masifa da me ta yi kama?" Furucin Hajiya Mummy kenan a lokacin da ta faɗo cikin ɗakin har tana cin tuntuɓe saboda kalaman Minal ne suka tarbe ta. "Na sani ba a kyauta miki ba saboda ba a yi shawara da ke ba kafin a aiwatar. Amma ki kwantar da hankalinki babu abin da zai faru sai alheri. Ni ce mahaifiyar Jamal, kuma na faɗa na nanata ban yafe masa ba matuƙar ya sake ki." Wani sabon kuka ya suɓuce wa Minal, hannunta a ka ta shiga kwarara ihu saboda tana ji a ranta gabaɗaya an gama raunata rayuwarta. Daidai lokacin da aka kira wayar Hajiyar, ta dakata daga yunƙurin rarrashin ta da take yi ta ɗauki wayar. Bayan jin abin da aka sanar da ita a wayar ta yi magana cikin haɗe fuska ta ce, "Adamu miƙa masa wayar!" Ɗaya daga cikin abokan angon ne suka kira ta, kuma babu ɓata lokaci suka ba shi wayar muryarsa ta fito a ɗashe cikin wayar yana cewa. "Hajiya Mummy ba zan dawo gida ba sai da tare da matata. Ki ce kowa ya yi tafiyarsa a bar ni zan nemo Nur da kain..." "Ni na ce ka dawo, ga ni a cikin gidan naka kai kawai nake jira." Ta kashe wayar idonta a kan Minal da ta yi tsaye kamar an dasa ice ta kasa motsin kirki. "Ku kwantar da hankalinku in sha Allahu babu abin da zai faru sai alheri. Aure ne an riga an ɗaura, kuma babu yaji ballantana saki sai dai mutuwa ta raba da yardar Allah." Wani kallo Minal ta yi wa Hajiya Mummy kafin ta koma cizon yatsanta tana wassafa yadda za ta bar gidan a cikin daren. Saboda ta ci alwashin haramta wa kanta Jamal har zuwa lokacin da Nur za ta dawo gare shi. Da rarrashi da ban-baki Hajiya ta samu Minal ta yi shiru. Amna tana gefe da tagumi saboda tuno wasu abubuwan da Nur ta yi yayin hidimar bikin, waɗanda sai a lokacin ta gano ma'anarsu da abin da take nufi. Shiru ɗakin ya yi ban da ƙarar Ac babu abin da ke motsi idan aka cire kukan tsuntsayen da ke saman bishiyoyin gidan. Kowa da abin da zuciyarsa take saƙa, duba da yadda suka shiga nutsuwarsu tamkar an saka musu dokar yin shirun. Hajiya Mummy ce ta kawar da shirun, ta hanyar duba agogon wayarta sannan ta sake doka wa Jamal kira. Ranta a mutuƙar ɓace ta sake ba shi umarnin dawowa gida a cikin biyar kacal, saboda ta fahimci idan ba ta yi masa jan idon gaske ba; rashin tawakkalinsa zai iya karya mata zuciya. Kuma faruwar hakan tamkar gayyatar wani sabon tashin hankali ne a cikin ahalinta. Gama wayarsu babu jinawa suka jiyo ƙarar sautin shigowar mota a cikin gidan. Ƙirjin Minal ya shiga bugawa dam-dam saboda sanin arba da Jamal a lokacin tamkar arangama da mutuwarta ne. Musamman da ta tuna irin muguwar shaƙar da ya yi mata yana ƙoƙarin aikata lahira. Zumbur ta miƙe tsaye tana rabon ido a lokacin da takun tafiyar ke ƙarato ɗakin. Buɗe ɗakin da aka yi ya yi daidai da faɗawarta cikin toilet a sukwane, cike da matsanancin tsoron da ya mamaye mata zuciya. Ƙasa ta sulale bayan ta rufe toilet ɗin da makulli, jikinta yana rawa ta shiga wani irin marayan kuka mara sauti. Wanda babu hawaye sai gunjin da yake ƙara yunƙuro mata takaicin ɗaurin talalar da aka yi wa rayuwarta. 'Me ya sa kika yi mini haka aminiyata?' Tambayar da ta jefi kanta da ita kenan a zuciya, saboda ta kasa fahimtar dalilin da ya sa Nur ta zaɓi guduwa ta bar Jamal duk da zazzafar soyayyar da take yi masa. 'Shin Nur ko ta ga wani abu a tattare da ni wanda ke nuna son Jamal nake yi ba tare da na sani ba?' Zargin da ta yi wa kanta kenan wanda babu tabbacin faruwar hakan, idan saɓanin fahimta ne ya jawo Nur ta yi mata irin wannan yankan baya. "Ki dawo ga masoyinki ƙawata, ni ban taɓa ji ina son sa ba." Zancenta kenan a fili tamakr an faɗa mata idan ta yi maganar Nur za ta ji ta, wanda ta yi a cikin sanyin murya da raunin zuciya. Daidai lokacin da ta fara jin sautin Hajiya Mummy a sama tana faɗa. Jikinta ya hau tsuma wata ƙwalla mai zafi ta fara bin fuskarta. Saboda duk abin da take faɗa da amsar da ya ba ta a cikin kunnuwanta. "An ɗaura aurenka da Minal ne a bisa wani uzuri mai girma. Don haka ba zan taɓa yafe nonona da ka sha ba matuƙar ka saki igiyar aurenka da ke kanta. Kuma ka sani A'isha ba matarka ba ce don ba a ɗaura aurenka da ita ba. Idan ka yi biyayya ga zaɓin da Allah Ya yi maka za ka ga amfanin hakan a gaba. Idan kuma ka tayar wa da 'yar mutane hankali za ta bar ka saboda ita ma cushen ka aka yi mata ba tare da ta sani b..." "Hajiya ba zan taɓa son ta ba. Na faɗa miki ne don ki sani saboda ba zan iya yi mata kallon mace ba. Don babu abin da zan so a jikinta duk tsawon zaman da za ta yi cikin gidan nan. Bambancinta da namiji a wurina shigar mata ce kawai..." Kallon da Hajiyar ta wurga masa ya saka shi miƙewa jiri yana ɗibar sa ya sake cewa, "Gaskiya na faɗa miki, saboda Nur na tsara rayuwata kuma zan nemo ta a duk inda ta je a faɗin duniyar nan." D. Auta ce *FANSAR ƘAUNA!* *HADIZA D. AUTA* *Na ji daɗin yadda kuka karɓi littafin nan tun a farkonsa. Kuma in sha Allahu za ku same shi fiye da yadda hasashenku ya bayar. Masu neman littafaina ga su kamar haka; ABOKIN AIKINA, BAƘON YANAYI, JIKI DA JINI (A'ISHA), AMFANIN FITILA, MAKANTAR SO, DIJE ƘARANGIYA, RUWA DA ƘANƘARA, GIDAN AURE. BAKAN GIZO, ZUBAR HAWAYENA, DAKAN ƊAKA.., MUSAYAR ZUCIYA, TARTSATSI, SHAGALALLIYA da sauran su. Ga mai buƙata ya tuntuɓe ni ta wannan lambar; 08022014771.* *LAMBA TA BIYU.* Minal ta jima a bayin ba tare da ta motsa ko ɗan yatsanta ba, saboda duniyar ta gama juya kanta. Ta yadda bakiɗaya ta kasa fahimtar mene ne mafita, kuma me za ta yi, sannan me za ta aikata? Ƙwanƙwasa ƙofar da aka yi ya saka ta dawo cikin duniyar hayyacina, tare da sauke nannauyar ajiyar zuciya. Zumbur ta miƙe tsaye tamkar an tsira mata allura, ta shiga kokawar buɗe ɗakin tare da ƙoƙarin saita nutsuwarta. "Kada ki sake ɗaga hankalinki a kan wannan matsala, saboda in sha Allahu haɗinki da shi alheri ne, kuma matuƙar ina raye ba zan bari Jamal ya yi miki abin da ya ga dama ba." Zancen Hajiya kenan, a lokacin da na buɗe bayin ta riƙo hannuna ta zaunar da ni a kan gado. "Ki yi haƙuri, saboda babu wata kalmar da ta wuce haƙurin nan dai duk da ba daɗi ne da shi ba. Mu za mu je gida, sai da safe idan allah ya kai mu." Ta miƙe tana dafa kanta tare da jera mata wasu albarkatu cike da tausayin ta a ranta. Ta ƙara yi wa auren kyakkyawar addu'ar da ko a cikin zuciyar Minal ba ta ji za ta iya amsa ko ɗaya ba. Tana ƙoƙarin barin wurin Minal ta yi hanzarin riƙo hannunta, sannan ta durƙushe ƙasa gwiwa biyu tana ƙoƙarin danne kukan da ke son kufce mata. A haka ta yi ƙarfin halin yin magana a cikin sanyin murya ta ce, "Don Allah idan kin san dalilin da ya sa Nur ta bar mini aurenta ki sanar da n... saboda ba zan taɓa yafe wa kaina ba matuƙar na shiga tsakiyarta da angonta. Idan kuma har da gaske ta gudu ta bar mini masoyinta a irin wannan rana da ta jima tana dakon zuwanta; zan ci gaba da tuhumar kaina daga yau har ranar da na bar duniya. Ki sanar da ni gaskiya don Allah Hajiya, saboda zuciyata ba za ta taɓa nutsuwa ba matuƙar ban san dalilin da ya sa Nur ta bar mini Jamal ba." "Hmmmmm!" Ajiyar zuciyar da Hajiyar ta sauke kenan tare da miƙar da ita tsaye, sannan ta shiga bubbuga bayanta cikin sigar rarrashi. Saboda a lokacin hawaye sun ba ta haɗin kai ta hanyar zubowa ziii suna layi a kumatunta. "Ko ma me ya sa ta bar miki shi; ki bar shi a matsayin ya wuce daga yau. Don haka ki karɓi mijinki kuma ki kwantar masa da hankali ta hanyar da za ku daidaita kanku ba tare da kowa ya sani ba. Saboda Jamal yana da zafi amma yana da sauƙin kai idan aka biyar da shi ta hanyoyin da yake so." Jim Hajiyar ta yi tana kallon gefe, yayin da kan Minal yake ƙasa tana shesshekar kuka. Cike da son kawar da zancen Hajiyar ta sake cewa, "Dare yana ƙara yi Amina, ki yi haƙuri na manta da abinci a mota Amna za ta kawo miki kafin mu wuce. Kuma ki saki jiki ki ci kada ki yi wa kanki horon yunwa. In sha Allahu komai zai wuce kuma za ki ji daɗin zama da shi idan kuka daidaita." Waɗannan maganganun nata suka sa ta gama sarewa a kan za ta samu amsar tambayar da ta yi mata. Idonta a kan bayansu suka fice daga ɗakin tare da takun saukarsu a ƙasan benen har zuwa lokacin da ta daina jin motsinsu. Ta jima a tsaye inda n'take ba ta motsa ba, kafin ta ja ƙafafuwanta n'ta ɗosana ɗuwawunta a bakin gado. Amna ta dawo da foodflaks a hannunta ta ajiye gabanta cikin sauri ta fice, ba tare da ta ce da ita komai ba. Shiru ya ratsa falon sai sautin agogon bango da ke ta aikinsa yana harbawa ƙit-ƙit. Hakan ya sa ta cira kai tana ƙare masa kallo cike da mamakin ganin adadin lokacin da agogon ya nuna mata. Karfe ɗaya da minti goma na dare 1:10am, amma ba ta gasgata ba har sai da ta duba ƙaramar wayarta da ke cikin jakar hannunta, a nan n'ta ga zahirin abin da agogon ya sanar da ita babu ƙarya. Nan take wani sabon tsoro ya shige ta, saboda ba ta da masaniyar ita kaɗai ce a cikin gidan ko akwai wasu mutanen. Saboda ko kaɗan ba ta yi zaton ƙiyayyar da Jamal ya nuna mata ta bar shi kwana a cikin gidan ba. Sai dai tuno akwai maigadin da ke kula da shiga da ficen gidan ta ɗan rage jin tsoron. Amma tabbas ba ta tunanin zuciyarta za ta samu nutsuwa matuƙar ba ta yi ido biyu da Nur ta amsa mini tambayoyin da ke zuciyarta ba. Hakan ya sa ta shiga ƙwala wa lambobinta kira ɗaya bayan ɗaya amma babu wadda n'ta samu. Ajiyar zuciya ta sauke mai ƙarfi tare da furzar da wani iska mai zafi daga bakina. Gadon ta sauko ta rafka tagumi hannu biyu, don ta gaji da zaman har ƙafafuwanta sun fara kumbura. Saboda ba ta san ta yi zurfi a tunanin da ta lula ba sai da ta sake duba agogon wayarta ta ga 2:30am ƙarfe biyun dare daidai. Kenan ta kwashe awa ɗaya har da wasu ɗorin mintuna a zaunen ba tare da ta sani ba. Guntun tsaki ta ja tare da Allah wadai a kan abin da ya faru, musamman da ta tuno maganganun Nur a lokacin da aka ce ga motocin ɗaurkar amarya sun zo. Da irin diriricewar da ta yi ta faɗa bayin da ke cikin ɗakinsu har ƙawayensu suna tsokanarta. Jimawar da ta yi a bayin ya sa Minal bin ta tana faɗin, "Malama ki fito ke fa ake jira!" Nur ta buɗe bayin tana dariyar yaƙe, domin alamunta duka ya nuna kuka ta yi a cikin bayin, cikin wata kalar murya sassanya ta ce, "Ba sai kin kore ni ba, na sani yau za ki yi kwanan farinciki." "Ke fa wata irin mutum ce wallahi, yanzu rabuwa da ke shi zai sa na yi kwanan farincikin?" Minal ta jefa mata tambayar tana hararar ta cike da jin haushin abin da ta faɗa. "Kwantas Hajiyata, in sha Allah daga yau sai kin jima ba ki saka ni cikin idanuwanki ba." "Ke dai kika sani, kuma komai za ki faɗa ki faɗa, daga yau dai mun sauke nauyinki a kanmu." Zancen Minal kenan wanda ya saka Nur juyawa tana yi mata wani kallo mai ɗauke da ma'anoni da yawa. Kamar ta ce wani abu amma ta yi hanzarin tsuke bakinta gum, fuskarta a cure ta bar wurin tana ƙoƙarin saita kanta a lokacin da mata suka cika ɗakin da guɗa. Wannan nazarin ya ƙara ɗaukar lokaci kafin Minal ta gano kwanan zaune ta yi. Saboda bacci bai ɗauke ta ba sai da asuba ta kawo jiki. Kasancewar ana yanayin zafi hakan ya sa ta ƙara bajewa ƙasan tayis tana nannauyan baccin mai ɗauke da mafarkai kala-kala. Ba ta tashi farkawa ba sai da ƙarfe 9:11am na safiya. ko shi kiran waya ne ya tayar da ita, a firgice ta farka tana dube-duben da ya tabbatar mata ba gidansu ba ne, kuma da gaske abin da ya faru ba almara ne. Cike da ƙuncin zuciya ta nufi bayi, saboda kiran ya katse kuma lokaci ya ƙure mata ba tare da ta yi sallar asuba ba. A gurguje ta nemo hijabi a cikin wardrobe ɗin kayan Nur, ta miƙa raka'a biyu ta tofa addu'ar da ba ta san me ta roƙa ba. Allah Ya taimake ta tun kafin a fito da amarya ta yi sallar Isha. Da ba ta yi sallar ba wataƙila tashin hankalin da ya kunno mata kai ba zai bar ta nutsuwar yin sallar a cikin daren ba. Ta jima saman sallayar da tagumi kafin wani kiran ya sake shigowa cikin ƙaramar wayarta. Muryar Hajiya ta jiyo ta yi hanzarin gaishe ta ba tare da ta amsa ina kwanan da take yi mata ba. Saboda ganin ita ce ya dace ta gaishe ta a matsayinta na babba. "Ki ƙara haƙuri kin ji! Na aiko miki da abinci ki sauka ƙasa ki karɓa. Kuma ki ƙara haƙuri da yardar Allah komai zai daidaita." "Babu komai." Iya abin da Minal ta faɗa kenan saboda bakinta ya yi nauyin da ba za ta iya cewa komai ba. Sannan ta sauke wayar idonta a kan abincin da Amna ta kawo mata cikin dare wanda ko buɗewa ba ta yi ba ballantana ta san mene ne a ciki. Jiki babu kuzari ta miƙe ta ɗauki foodflaks ɗin ta fice, zuciyarta tana jin babu wani abinci da zai burge ta a daidai lokacin. Saboda ko yunwar ma ba ta ji kuma ba ta jin sha'awar cin komai. Amma dole ta isa harabar gidan tana wara ido kafin ta hango maigadin gidan yana nufo ta da wani madaidaicin kwando. Cikin ladabi ya gaishe ta ita ma ta amsa babu yabo babu fallasa kafin ta karɓi kwandon ta miƙa masa foodflaks ɗin ta juya ba tare da ta ce da shi ƙanzil ba. Tana ƙoƙarin shigewa cikin gidan ta ji sautin maigadin yana cewa, "Me za a yi da wannan Hajiya?" "Abinci ne, ka je ka ci." Amsar da ta bayar kenan ba tare da ta juya ba. Ranta yana tafarfasa ta koma saman ta zauna a kan bedside tare da rungume hannuwanta a ƙirji tana cizon leɓenta. Hawaye ta shiga gogewa a kan fuskarta saboda kanta ya yi ƙullewar da ba ta san ta ina za ta fara ba. Saboda tunanin a wane hali saurayinta yake wanda bai zo a ranta ba sai da safiya ta waye ta tabbatar abin da ya faru babu wasa a ciki. Saɓanin kallon da take yi wa abin kamar shirin da zai ƙare Nur ta dawo ɗakinta ita ta koma gida. Zumbur ta miƙe, ta shiga watso kayan Nur da ke cikin wardrobe ɗin ɗakin ta shiga birgima a cikin su. Saboda tuno lokacin da take jera mata kayan da hannunta cike da farincikin burin aminiyarta ya cika ta auri wanda take so. Kayan ta shiga runguma tana shinshina ƙamshin turaren Nur da ta feshe mata kayan da shi yayin jera su. Wani sabon kuka ya zo mata, wanda ta kwashe lokaci tana juya zantuka a ranta babu mai rarrashin ta. Kafin ta ji takun tafiyar mutane yana nufo ɗakin da sautin maganganu sama-sama. Amma ko kaɗan hakan bai saka ta motsawa ba, har aka fara ƙwanƙwasa mata ɗaki ba ta yi magana ba ballantana ta tashi ta buɗe. Muryar Innarmu ce a gaba kafin ta jiyo muryar gwaggonta Salame, waton ƙanwar Babanta. Da ido kawai ta bi su, ganin salatin da suke yi a kan hango halin da suka iske ta cikin sa. "Ahir ɗin ki Amina! Wallahi ki kiyaye ni tun muna shaida jun..." "Dakata Binta, abin fa sai da rarrashi. Kuma abin da kike so ta bi ba zai biyu ta daɗin rai ba. Don haka ki bar mini komai ni zan shawo kan matsalar." Zancen gwaggonta Salame kenan cikin tausasa murya. Sannan ta nufi inda Minal take kwance cikin kayan Nur, ta kama hannunta ta miƙar da ita tsaye tana faɗin, "Kwantar da hankalinki Amina, ai ita rayuwar duniya mai sauƙi ce idan aka bi ta a hankali. Yaushe za ki hana kanki zama lafiya a kan abin da ke ma kina da ikon taimakon kanki da kanki? Don Allah yi shiru share hawayenki lamarin duniya ba a yi masa gaggawa. A sannu ake bin komai har cim ma nasara cikin iyawar Allah." Da waɗannan kalaman Gwaggo Salame ta yi nasarar hana Minal wani kuka, sannan cikin dabara ta zuba mata abinci ta shiga tsakura duk da shesshekan kukan da take yi jefi-jefi. Amma ko kaɗan ba ta son haɗa ido da Innarmu, saboda hararar da take wurga mata kamar ta rufe ta da mugun duka. Bayan ta ɗan ci abincin ta kai ta bayi da kanta ta haɗa mata ruwan wanka ta baro ta, tare da ba ta lokacin da za ta kammala ta fito tana jiran ta. Minal ba ta ɓata lokaci a bayin ba, ta yi wankan a gaggauce ta fito. Gwaggo Salame ta miƙa mata ɗaya daga cikin kayan Nur da ta gama gyara ta mayar wardrobe kamar yadda suke tun farko. Minal kayan ta kalla sannan ta kawar da kai ƙirjinta yana bugawa ta ce, "Ba kayana ba ne." Gwaggon ta matsa kusa da ita cikin ƙarafafa gwiwa ta ce, "Duk abin da kika gani a cikin gidan nan naki kuma haƙƙinki ne. Don A'isha da ta bar miki mijin har da komai nata ta bar miki, tun daga kan kayan ɗakinta har zuwa suturarta." "Gwaggo kayan Nur..." "Kada ki ce komai saka kayan kawai." Ta yi hanzarin katse ta saboda ganin tana so ta kawo mata wasa. Minal ta buɗe doguwar rigar lesin ta saka, wadda ta sha adon aiki mai ɗauke da ɗinki stone work. Sannan gwaggo Salame ta ɗaura mata ɗankwali tana faɗin, "Ko ke fa! Kin ga yadda kika yi kyawu kuwa? Ma sha Allah ki tsaya a haka kada na sake ganin kuka a idonki." Nur ta yi marau-marau da ido ƙwalla ta cika idonta ta saka gefen hannunta ta share. Sannan ta zuƙe majinar kukan tana cewa, "Don Allah Gwaggo ku tausaya mini, wallahi ba zan iya zama a gidan nan ba. Saboda mutane za su zarge ni a kan na ci amanar Nur. Sannan shi kansa angon nata ba zai taɓa karɓa ta a matsayin matarsa b..." Ohh Allah 😔 D. Auta ce🙋 [2/20, 22:02] Hadiza D. Auta: *FANSAR ƘAUNA!* *HADIZA D. AUTA* *Masu neman littafaina ga su kamar haka; ABOKIN AIKINA, BAƘON YANAYI, JIKI DA JINI (A'ISHA), AMFANIN FITILA, MAKANTAR SO, DIJE ƘARANGIYA, RUWA DA ƘANƘARA, GIDAN AURE. BAKAN GIZO, ZUBAR HAWAYENA, DAKAN ƊAKA.., MUSAYAR ZUCIYA, TARTSATSI, SHAGALALLIYA da sauran su. Ga mai buƙata ya tuntuɓe ni ta wannan lambar; 08022014771.* *LAMBA TA UKU.* "A hir ɗin ki amina! Wallahi ki fita idona na rufe. Yaushe arziƙi yana kiran ki tsiya tana korar ki da gudu! To ban son shashancin banza, don ke Allah ya bai wa mijin ba A'isha ba, kuma ita da kanta ta bar miki shi ba matsa mata aka yi dole sai ta aikata ba, yo ɓata lokacinki na me za ki dinga yi a kan abin da kina zaune allah ya ba ki ba tare da kin roƙa ba?" Fusatattun kalmomin Innarmu kenan waɗanda tsabar haushin da Minal ta ba ta ya sa ta miƙe tsaye tana neman hanyar kai mata duka. Ƙur Minal ta kafe ta da ido cike da zargi ta sake cewa, "Yanzu ya zan yi da Aminu? Wanda kowa ya san yadda yake faɗi-tashi a kaina?" "Yi mini shiru sakarya! Shi Aminun idan kika aure shi zai ajiye ki irin gidan nan ne? Ki faɗa mini a kaf cikin danginmu waye ya samu arziƙin zama irin wannan gidan? To ba ki isa ki yi mana baƙinciki ba, dole ne ki zauna ko kina so ko ba kya so! An riga an ɗaura aurenki da shi, kuma babu uban da ya isa ya kunce auren nan! Ke ko mutuwa za ki yi sai dai a fitar da gawarki ehe!" Innarmu ta ƙare maganar tana kumfar baki da zaro wa Minal ido, alamun ƙiris ya rage ta jibge ta don ta gama kaiwa bango a kan lamuranta. Minal ma tsaye take kanta a duƙe tana kallon yatsunta fuskarta a kumbure bayan bakin da ta turo tana gunguni. Tafasar da zuciyarta ke yi ya sa ta yi maganar da take jin dole sai ta amayar da ita ko za a kashe ta. Domin idanuwan da Innarmu ta kafe ta da su ba su hana ta furzar da abin da ke cikin bakinta ba. "Ni fa wallahi ko kaɗan kuɗinsa ba sa gabanta..." "Mu su ne a gabanmu! Na ce miki mu su ne a gabanmu ki je ki faɗa wa duk uban da za ki faɗawa. Kuma za mu ci sai inda karfimu ya ƙare, matuƙar muka samu damar cin sai mun ci...ke Amina wallahi na kusa nakasa ki! Ni za ki gwada wa ƙarfin imani da taƙawa? To idan kin so ki ce da mu kwaɗayayyiya ai ba a kanmu aka fara son abin duniya ba. Wawuyar banza ana nuna miki hanyar arziƙi kina runtse ido. Kuma Aminu da kike zancensa a yanzu babu ke babu shi har abada! Saura kuma na ji labarin kin neme shi ko shi ya neme ki ki ga irin matakin da zan ɗauka a kanku. Sakaryar banza sai na shayar da ke gubar mamaki matuƙar ba ki shiga taitayinki a kan auren nan ba....Salame ni na tafi idan kin gama ki same ni waje ina jiran ki..." Martanin Innarmu ya ƙara lalata nutsuwar Minal, ta kasa shanye zafin maganganun a ranta tun kafin ta dire zantukan, waɗanda ta ji mugun ɗacinsu a zuciya har cikin bakinta. Bayan ta gama kumbura ta fashe da wani kalar kuka cikin ɗaga murya tamkar wadda ake tsula wa bulala. Innarmu tana gama faɗar batutuwanta ta fice daga ɗakin a fusace tana ci gaba da faɗar duk abin da ya zo bakinta cikin faɗan da sautinta yake tashi. Ajiyar zuciya Gwaggo Salame ta saki mai ƙarfi kafin ta riƙo Minal ta zaunar da ita a kan gado. Jarumtar rarrashin ta ta shiga yi har ta samu ta rage sautin kukan da take yi. Sannan ta yi jim na tsawon mintuna kafin ta yi ƙarfin halin faɗin, "Kowace rayuwa da kalar tata jarabawa, ke taki jarabawar ita ce wannan. Don haka ki bar wa Allah lamuranki kada ki yi jayayya da ƙaddararki, saboda ba a sani ba ko ita ce alherinki kina ƙoƙarin turewa." Shiru Minal ta yi ba tare da ta ce uffan ba, saboda maganganun Gwaggo Salame sun shiga jikinta, ta share hawayenta ta koma ajiyar zuciya wata bayan wata. Duk da a ranta ba ta jin ta karɓi cushen da aka yi mata a matsayin ingantaccen auren da ake yi wa kowace mace. Amma kuma ta fi jin daɗin maganganunta a kan na Innarmu masu kama da ana yaƙi. "Abu biyu zuwa uku nake so ki riƙe gam kafin mu ga kamun ludayin tafiyar." Maganar Gwaggo Salame ta farauto hankalinta wuri ɗaya, ta nutsu tana sauraron ta ba tare da ta yi motsin kirki ba "Na farko ki yi haƙuri a kan ba a nemi amincewarki ba, amma ki kalli hakan a matsayin gata ne da wasu iyaye suke yi wa 'ya'yansu. Na biyu ki riƙe Ya Wadadu ɗari huɗu bayan kowace sallar asuba, tana ƙara danƙon soyayya da kwarjini bayan farinjini na yankan shakku. Na uku kuma ki lizimci raya dare da nafilolin biyan buƙatu a wurin Ubangiji. Na san kin sani akwai su kala-kala, amma kafin mu je ɓangaren abin da za ki yi ki jawo hankalin mijinki; zan sanar da ke nafilar da nake yawan yi, wadda ni ma na gwada kuma nake ganin amfaninta, saboda ina so ke ma ki amfana." Shiru ya ziyarci ɗakin tsawon sakonni kafin Gwaggo Salame ta sauke nannauyar ajiyar zuciya ta ce. "Ki tashi misalin ƙarfe ɗaya na dare zuwa biyun daren, ki yi nafila raka'a biyu kacal kuma kowace ki karanta fatiha da Suratul Ahad, waton surar ƙulhuwallahu Ahad. idan kika sallame sai ki yi wata sujuda kada ki ɗago kanki sai kin karanta La'ilaha Illa antassubhanaka inni kuntu minazzalumina sau arba'in. Kada ki bar sujudar har sai kin faɗa wa Allah buƙatunki. Ina mai tabbatar miki za ki ga aikin addu'ar tamkar yankan wuƙa da yardar Allah...." Kiran wayar da aka yi wa Gwaggon ya sa ta yi hanzarin fito da ita daga aljihunta, ganin Innarmu ce mai kiran; hakan ya sa ta tuno ashe ita take jira a waje. Ta miƙe tana gyara zaman lulluɓinta ta ce, "Mu za mu tafi, zuwa anjima za a aiko miki wasu daga cikin kayanki, sauran kuma za a raba wa ƙannenki da wanda Allah ya ciyar. Amma don Allah ki tsayar da hankalinki wuri ɗaya ki nemi zaɓin Allah. Ubangiji Ya ba ku zaman lafiya, kuma ki riƙe sirrin mijink..." Kiran da Innarmu ta sake bugo mata ya sa ta fice da sassarfa ta bar Minal a daskare bakin gadon, don ta kasa motsa laɓɓanta ta yi mata sai anjima ballantana ta raka ta. Bayan idon da ta bi ƙofa da kallo tsawon mintuna da fitarta ba tare da ta ɗauke kanta ba. *** Jamal kuwa, tun da ya fice daga ɗakin bayan ya gama jaddada wa Hajiya ba ya son Minal. Cikin ƙunar rai ya buga motarsa jikinsa yana rawa ya nufi gidansu. Sai dai kuma Allah ne ya kai shi gida lafiya, saboda mahaukacin gudun da yake yi tamkar an koro shi ko kaɗan ba ya cikin nutsuwarsa. Uban horn ɗin da ya dinga bugawa babu ƙaƙƙautawa; ya sa Baba maigadin gidansu ruɗewa jikinsa yana rawa ya buɗe gidan bayan ya tabbatar shi ne ba gizo ya yi masa ba. Amma zuciyarsa cike da mamakin dawowarsa cikin gidan a daidai lokacin, wanda ya dace a ce yana tare da amaryarsa a matsayinsa na sabon ango mai zumuɗi da daren farkonsa. Da ido Baban ya bi shi baki buɗe har Jamal ya shige sashen da ɗaƙinsa yake ba tare da ya bi ta kan motar da ya bari a kunne ba, ballantana ya rufe murfi bayan fitarsa. Saboda idanuwansa ko gani ba sa yi daidai ya faɗa ɗakinsa ya datse ƙofa, a sukwane ya isa bayi ya dinga zuba wa kansa ruwan shawa ba tare da ya cire komai na jikinsa ba. Ya ɗauki tsawon minti talatin idanuwansa rufe ba tare da ya yi dogon motsi ba. Zuciyarsa danƙare da ƙuncin da yake haddasa mata bugawa da ƙarfi tamkar ta ɓalle daga mazauninta ta fito ƙirjinsa. Wata nannauyar ajiyar zuciya ya saki mai ƙarfi, kafin ya fara atishawa wata bayan wata kuma har lokacin ruwan yana sauka kansa zuwa jikinsa. Da lalube ya rufe shawar amma ya kasa ɗagawa daga wurin tsawon mintuna. Saboda zuciyarsa ta ci gaba da hasko masa fuskar Nur tana feshin tsadadden murmushinta har dimple ɗin ta biyu suna lotsawa. Hoton zuciyarsa ya hasko masa ita ne a wani lokacin da suka je yawon shaƙatawa, inda ya ba ta cake a baki tana tauna tana yi masa wani kalar kallon da ya saukar masa da kasala. "Ya Allah!" Furucinsa kenan a lokacin da kansa ya ƙara sarawa tamkar an kwaɗa masa guduma. Dafe da kan ya fito yana layi saboda jirin da ke kwasar sa har ya zube kan gado riƙe da kansa yana faɗar kalmar Innalillahi fili da zuciyarsa. Nan take ya fara rawar sanyi jikinsa ya hau fisga babu ƙaƙƙautawa, cikin mintuna kaɗan numfashinsa ya fara sarƙewa, kafin ya yi luf bayan ya gama tari sama-sama yana dafe da zuciyarsa, saboda idauwansa sun gama kafewa numfashinsa ya tsaya cak. Ya kwashe tsawon lokaci a halin da yake ciki kafin dawowar Hajiya, bayan ta gama neman sa a waya ba ta samu ba. Kuma maigadin gidansa ya tabbatar mata da lalle ya fita. Cikin tashin hankali ta kira maigadinsu sannan ta samu nutsuwar faɗawa mota direban da ya kawo ta ya juya da su zuwa gida. Saboda jin Jamal yana gidan ya rage mata kaso bakwai a cikin goman tashin hankalin da ta afka. Don zuciyarta ta gama tsinkewa cike da tsoron faruwar abubuwa biyu, na farko kada ɓacin rai ya saka shi barin garin ba tare da ta sani ba. Na biyu tsoron kada ya yi tsautsayi ya ja shi ya yi haɗari, don a halin da yake ciki bai dace ya yi tuƙi ba. Makullin motarsa da maigadinsu ya ba ta tare da yi mata bayanin yanayin da ya shigo gidan; jikinta ya yi sanyi ƙalau, amma hakan bai hana ta isa ƙofar ɗakinsa da sassarfa ba. Amna biye da ita a cikin firgicin suka shiga bugun ƙofarsa tare da kiran sunansa a lokaci ɗaya. Ganin babu motsinsa ballantana alamun zai buɗe ƙofar, ga tagoginsa duka a rufe. Hakan ya sa Hajiya ta sa Baba maigadi ya ɓalle ƙofar iya ƙarfinsa. Hajiya Mummy da Amna ihu mai ƙarfi suka fasa yayin da suka yi ido biyu da Jamal a kan gado. Baba maigadi ya hau salati saboda alamunsa ya nuna babu numfashi a tattare da shi. Hajiya Mummy ta faɗi ƙasa tana kuka bakinta ɗauke da kalolin salati saboda idanuwanta sun gama tabbatar mata da Jamal ya jima da barin duniya. Amna kuma jikinsa ta haye tana ihu tare da faman jijjigarsa a kan ya tashi cikin ƙaraji da zaucewa, bayan kururuwar da take yi a kan don Allah a kawo musu agaji. Hmmm!😪 D. AUTA CE✍️ [2/20, 22:02] Hadiza D. Auta: *FANSAR ƘAUNA!* *HADIZA D. AUTA* *Masu neman littafaina akwai free akwai na kuɗi sai wanda kuke so.* *ABOKIN AIKINA, BAƘON YANAYI.* *JIKI DA JINI (A'ISHA), AMFANIN FITILA.* *MAKANTAR SO, DIJE ƘARANGIYA.* *RUWA DA ƘANƘARA, GIDAN AURE.* *BAKAN GIZO, ZUBAR HAWAYENA.* *DAKAN ƊAKA.., MUSAYAR ZUCIYA.* *TARTSATSI, SHAGALALLIYA da sauran su.'Yan kasuwa masu neman a tallata musu hajarsu ƙofa a buɗe take. Ga mai buƙata ya tuntuɓe ni ta wannan lambar; 08022014771.* *LAMBA TA HUƊU.* "Ba..ba..bai mutu ba!" Zancen direban Hajiya kenan a lokacin da ya taɓa gefen idon Jamal, waton tsakanin ƙwayar idonsa da kunnensa, inda ya danne wurin ya ji jijiyarsa tana harbawa ɓal-ɓal. Hakan ya sa gumin tashin hankali karyo masa ya yi maganar a rikice bakinsa yana rawa. Shi ma Baba maigadin yana taɓa wurin ya yi gaggawar nanata zancen cike da jaddadawa ya ce, "Da sauran numfashinsa Hajiya! A gaggauta kai shi asibit..." Kallon da Hajiyar ke yi wa Jamal ya ƙara tabbatar mata da gaske ne. Saboda kallon da take yi musu ya nuna zuciyarta ta gama sarewa a kan sun yi rashin Jamal, rashi na har abada. Amma maganar Baban bayan direban ya gano da sauran ransa sa; sun ƙarfafa mata gwiwa matuƙa, duk a ranta ba ta gasgata abin da suka faɗa ba gaskiya ne ba, duba da abin da idanuwanta suka ganar mata zahiri. Zumbur ta zabura saboda ganin Baban da direban kowa yana bakin ƙoƙarinsa a kan farfaɗo da shi. Cikin sa'a numfashinsa ya dawo, ya yi wani irin ƙugi sannan ya fara tari ɗaya bayan ɗaya a hankali. Jikinsu yana rawa suka yi gaggawar saka shi mota, direba ya fice aguje Baba da sauran baƙin 'yan bikin da suka hankalta da abin da ya faru; suka bi su da addu'ar nasara har suka isa wata asibiti mafi kusa da gidan. Daga Hajiya mummy har direbanta a tsaye suka kwana tamkar haƙori. Sai faman zarya suke yi a baranda, tsakanin ɗakin bayar da agajin gaggawar da aka kwantar da Jamal ɗin, zuwa kujerun da suka zauna suna dakon fitowar likitan da ke ƙoƙarin ceto rayuwarsa. Bacci ko kaɗan bai zo idanuwansu ba tun daga daren har aka yi sallar asuba. Tsabar tashin hankalin da suka shiga baccin da kansa ya kori kansa a cikin idanuwansu. Har gara Amna ta ɗan runtsa a lokacin da hajiya ta matsa mata ta yi baccinta saboda ganin tana zuba hamma wata bayan wata da tangaɗi tamkar 'yar maye. Safayar gadon maralafiya aka kai ta daga gyangyaɗi ta ɗan kishingiɗa sai nannauyan bacci ya yi awon gaba da ita. Bayan an kammala sallar asuba a cikin masallacin da ke asibitin; Likitan da ya tsayu a kan Jamal ya kira Hajiya zuwa ofishinsa. A gurguje ta shafa addu'ar neman lafiya ga Jamal hawaye yana fareti a kan fuskarta ta bi shi cikin sassarfa tamkar ta kifa. Amma idanuwanta a kan ɗakin ceton gaggawar zuciyarta cike da ƙosawa a kan tsaikon zuwa ganin Jamal da likitan ya yi musu. Saboda tun fitowarsa daga ɗakin ta isa gabansa tana jera masa tambayoyi a kan ya faɗa mata a wane hali Jamal ɗin yake ciki, har da magiya tana hawayen ya bar ta shiga ɗakin ta yi masa ganin bankwana. Amma fafur ya ƙi barin ta gan sa, ya ce ta je ta yi sallah idan aka kammala komai za su yi magana. A haka ya bar ta tsaye fuskarsa babu yabo babu fallasa ya wuce ya bar ta da fargaba, saboda ta kasa tantance halin da Jamal yake ciki daga yanayin fuskar likitan. Shiru ya ratsa a cikin ofishin, bayan Hajiya ta samu wuri ta zauna ƙirjinta yana bugawa. Sai da likitan ya gama 'yan rubuce-rubucensa biro a hannunsa yana jujjuya shi sannan ya yi magana. "Hajiya mene ne damuwar yaronki?" Bai tsaya jiran amsarta ba ya ɗora da cewa, "A binciken da na yi masa, na gano yana ɗauke da ciwon kai na damuwa, wanda a likitance muna kiran sa da Tention Headed." "Innalillahi wa inna ilaihirraji'un!" Hajiya ta yi hanzarin yin salati tare da ɗora hannuwanta a ka bayan ta miƙe daga kan kujerar jikinta yana kyarma. Cikin fuskar tausayi likitan ya yi magana cikin sauri ya ce, "Ba wani ciwo ba ne ki kwantar da hankalinki. Saboda a yanzu bai zama matsalar da za ta iya jawo masa manyan cutukan da suka danganci ciwon ba. Sannan abu mai sauƙi ne a shawo kan ciwon matuƙar aka bi shawarar likitoc..." "A ba mu maganin ciwon kawai likita, wanda idan ya sha zai warke nan take." Furucin Hajiyar kenan bayan ta koma zaune kamar yadda ya yi mata nuni da hannunsa, tana haɗa gumi tare da haɗiye wani dunƙulallen yawun da ya tsaya a maƙogwaronta. Murmushin ƙarfafa gwiwa likitan ya yi kafin ya sake cewa, "Magana ta gaskiya babu maganin ciwonsa a hannunmu Hajiya..." "To ai ka faɗa mana inda za mu samo masa maganin..." "Ki nutsu Hajiya a hankali zan warware miki komai. Saboda maganin ciwonsa yana hannunsa idan ya so zai wartsake a cikin kwanaki kaɗan har ma ya rabu da ciwon gabaɗaya." Hajiya ta sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi tare da sake jefa masa wata tambayar, "Ta ya ya zai warkar da kansa a irin mawuyacin halin da yake ciki, bayan ko inda kansa yake a bai sani ba? Kai-tsaye ya ba ta amsa da cewa, "Ta hanyar sanya haƙuri a kan abin da yake damun sa, sannan ya mayar da lamuransa ga Allah. Da cusa wa ransa komai zai wuce idan aka mayar da shi ba komai ba." "Alhamdulillah!" Hajiya ta furta hamdalar tare da ɗaga hannu ta shafa saman fuskarta. Likitan ya yi 'yar dariya sannan ya sake gyara zamansa yana cewa, "Inda matsalar take idan ya ƙi bin abubuwan nan da na lissafo..." "Ba ma za a samu matsala ba." Ta yi hanzarin faɗar maganar tana wara hijabinta tare da ƙara naɗe shi cikin jikinta. Likitan ya ci gaba da bayaninsa, wanda kusan shi ne gundarin abin da yake son faɗa tana shan gabansa da zance. "Ciwon zai iya tashi har ma ya faɗaɗa idan ya kasa saka wa zuciyarsa haƙuri da dangana a kan ko ma mene ne yake damun sa. Kuma idan ya dawo zai iya haddasa masa cutar bugun zuciya, wanda nan take zuciyarsa za ta iya bugawa ya yi mutuwar fuji'a." Hannuwan da ta ɗora a ka tana salati bai hana shi ci gaba da bayaninsa ba tiryan-tiryan ba. "Ko kuma jijiyar ƙwaƙwalwarsa ta tsinke ya samu cutar shanyewar ɓarin jiki da sauran cututtukan da ba a fata. Don haka tun kafin a je fagen da ba a so ya taimaki kansa ya rabu da ciwon tun yana ƙarami kafin ya kai babban mataki." Shiru Hajiya ta yi saboda luguden uku-ukun da ƙirjinta yake yi, idanuwanta a kan likitan ta kasa daina kallon sa kuma ta kasa furta ko kalma ɗaya daga bakinta. "Na san zancen ba zai yi miki daɗi ba, amma ki yi haƙuri, sanar da ku dole ne saboda ku taro kan matsalar tun tana farko kafin ta yi nisan da abin zai damu kowa. Sannan na sanar da ke ne a matsayinki na uwa ko akwai wata gudunmawar da za ki iya bayarwa wurin ceton lafiyarsa da ransa gabaɗaya. Shi ma idan muka samu ya warware za mu zauna da shi mu yi masa irin bayanin da na yi miki saboda fitar haƙƙi. Da ma aikinmu shi ne gano cuta da neman hanyar waraka. Kuma idan an bi ƙa'idojin asibiti sau da ƙafa za a dace da yardar Allah." "Hmmmmm! To Ubangiji ya shiga cikin lamarinsa da namu bakiɗaya. Kuma in sha Allahu zuciyar Jamal ba za ta buga ba, kuma zai rabu da ciwon lafiya ya ci gaba da rayuwarsa kamar kowa." Ta miƙe har za ta fice ranta a jagule ta waigo, tana tambayarsa za ta iya ganin sa a daidai lokacin. Likitan ya nufi hanyar fita ofishin yana cewa ta biyo shi. Jugum Hajiya Mama ta yi a lokacin da ta yi ido biyu da Jamal, saboda likitan ya yi mata jagora har gaban gadonsa, cike da sharaɗin kada ta yi dogon motsin da zai damar da marasa lafiyarsu da ke cikin ɗakin. Hawaye ta shiga sharewa da gefen hijabinta, saboda ganin yadda ya rame a dare ɗaya tamkar wanda ya yi kwanaki yana jinya. A ranta tana tuno kalaman likitan da suka gama tsinke mata jijiyon jiki da na zuciya. Ƙarfen gadon ta riƙe daidai kansa tana tofa masa addu'o'i tana hawaye, kafin likitan ya gama zagayen marasa lafiyar da yake dubawa. Fahimtar ta shiga yanayi mara daɗi ya dawo kanta da kalaman kwantar da hankali a kan Jamal zai farfaɗo cikin lafiyarsa da sabon kuzari. Da ma ƙarin ruruwar wutar ciwon nasa har da zazzafan zazzaɓi. Don haka ta kwantar da hankalinta babu abin da zai sake samun sa. Hakan ya ƙara mata juriya ta fito daga ɗakin zuciyarta cike da gamsuwa da maganganun likitan. Kiciɓis ta yi da Amna a bakin ƙofar shiga a hargitse, raɓa gefenta ta yi ta faɗa tana wara idanuwanta a kan gadajen masu jinyar da ke jere har ta hango shi a kan gadon ƙarshe. Bakin gadon ta ja ta tsaya tana rufe bakinta saboda sabon kukan da ya zo mata babu shiri. Hannunsa ta yi hanzarin kamawa ta ɗora kanta a saman hannun tana kuka mai sauti cike da tausayin sa a ranta. Sanyin hawayenta da ya ji a hannunsa ya ɗan motsa tare da buɗe idanuwansa kaɗan, sannan sake rufewa tare hanzarin dafe kansa yana faɗin, "Nur, ki matso kusa da ni." Amna ta saki hannunsa tana murmushin farinciki hawaye yana zuba a kan fuskarta ta ce, "Auncle J Amna ce.." Juyo kansa ya yi saiti da fuskarta yana kallon ta kamar zai yi magana kuma ya ja bakinsa ya yi shiru bai ce komai ba. Amna ta fice da sassarfa cike da jin daɗi ta sanar da Hajiya ta zo ya tashi. Tare suka dawo har direbanta suna murnar ganin sa a raye kuma ya farfaɗo a cikin hayyacinsa. Da ido kawai yake bin su ɗaya bayan ɗaya kafin ya yi ƙarfin halin furta abin da ke cizon ransa. "Hajiya, har yanzu Nur ba ta dawo ba ko?" Uhum🥲 D. AUTA CE✍️ [2/20, 22:02] Hadiza D. Auta: *FANSAR ƘAUNA!* *HADIZA IBRAHIM D. AUTA* *LAMBA TA BIYAR.* Shiru Hajiya mummy ta yi masa, saboda babu wata amsar da za ta iya ba shi a daidai lokacin. Hakan ya sa ta kawar da kanta gefe kawai tana share hawayen da ke bin fuskarta, zuciyarta cike takaicin abin da ya faru, wanda ya yi silar ciwon da ke barazana ga lafiyarsa. Amna ta matsa jikin gadon tare da dafa hannunsa ta yi magana cikin sigar rarrashi ta ce masa, "Ka yi hakuri Uncle J, ni na sani Nur za ta dawo maka, saboda ita ma tana son ka. Kuma abu ne wanda kowa ya san da hakan ba za ta iya rayuwar da babu kai a cikin ta ba. Don haka don Allah ka taimake mu ka taimaki rayuwarka Uncle J, ka kuma ƙarfafa kanka da zuciyarka ka yi ƙoƙarin cire damuwar komai a ranka Allah yana sane da komai da ya far..." "Laifin me na yi mata za ta guje ni?" Ya wurgo mata tambayar cikin sauri saboda ya kasa shanye takaicin, kuma tambayar da ke ransa kenan tana yawo a ƙwaƙwalwarsa. "Ka bar zancen nan Jamal. Za a yi shi daga baya idan ka samu lafiyarka." Maganar Hajiya kenan cikin kakkausar murya, duk da take ƙoƙarin danne da abin da ke cikin zuciyarta. Saboda ko kaɗan ba ta fatar ta yi asararsa kamar yadda likita ya yi mata mummunan albishir. Daga hakan Jamal bai sake cewa komai ba, sai kawar da kansa da ya yi gefe tare da runtse ido ƙirjinsa yana bugawa da sauri da sauri. Bacci mai nauyi ya ɗauke sa, zuwa lokacin asibitin ta cika da danginsu, 'yan'uwa da abokan arziƙi. Mutanen nesa da suka kwana gidan Hajiya mummy fiye da rabinsu suna asibitin ana jajanta lamarin. Gidansu Minal ma Hajiya ta kira ta sanar da su halin da ake ciki, sannan ta bai wa 'yan aikinta umarnin su yi abin karin safiya su kai wa Minla. Saboda tashin hankalin da take ciki bai hana ta tunawa da amanarta da aka ba ta ba. Wannan dalilin ya sa Innarmu da Gwaggo Salame suka dira asibitin ganin Jamal. Daga can suka zarce wurin Minal bayan sun gama tattaunawa da Hajiya a kan yadda za a shawo kan matsalar cikin sauƙi. Kuma an bar zancen a tsakaninsu ba tare da an sanar da Minal halin da yake ciki ba, gudun ta ƙara tuburewa ta bijire wa auren kuma ta lalata musu sabon shirin da suka tsara. **** Minal kam maganganun Gwaggo Salame sun rage mata kaso huɗu a cikin goman damuwarta. Kuma ta karɓi ƙaddararta, duk da tana jin ba ta gamsu da ingancin auren ba har a cikin zuciyarta ba. Saboda iya sanin ta dakalolin tarihin auren da ta ji ba ta taɓa jin kalar abin da aka yi mata ba. A take zuciyarta ta shiga ziga ta da shawarwari mabambanta, waɗanda ta tsayu a kan wadda zuciyarta ta karɓa, kuma ta riƙe a matsayin makamin kare kanta daga farmakin da ke cikin auren, sannan da riƙon amincin da take yi wa alaƙarta da Nur. Jiki babu kuzari ta ja abincin da Hajiya ta aiko mata ta ƙara ci. Sannan ta fitar da sauran ga maigadi yana ta godiya. Sai dai abin da ya so ƙara saka ta cikin damuwa zamanta shiru a cikin gidan tun bayan zuwan su Innarmu, babu wanda ya sake zuwa gidan har dare. Sannan ta kira Amna ya fi sau goma, amma har wayar ta gama ringing ba ta ɗauka ba. Hakan ya ƙara tunzura ta, ta shiga neman lambobin Nur cike da ƙunar rai, da zaman turaata saƙonni da zummar ko da za ta buɗe wayar ta gan su. Saboda duk kiran da ta yi a sanar da ita layukan duka a rufe suke. Daren ranar ma ta yi kwana rabi da rabi, saboda rashin nutsuwar zuciya da kaloli tambayoyin da take son amsarsu amma babu damar hakan. Abincin daren da Hajiyar ta sake aiko mata ma sai cikin dare ta samu damar ci, a lokacin da yunwa ta hana ta sukuni saboda barcin ya ƙi ba ta haɗin kai. Karfe biyun dare ta duƙufa kai kukanta ga Allah, a kan ya kawo mata sauƙin matsalar da take ciki, sannan ya dawo da Nur ga mijinta ita ma ta auri wanda take so. Saboda katangar kashedin da Innarmu ta yi mata da Aminunta ya hana ta neman sa a waya ta ji halin da yake ciki. Don abu ne da ta sani dole ne hankalinsa ya tashi a lokacin da ya ji an yi wa neman aurensa ƙarfa-ƙarfa. Sannan ita ma Nur za ta dawo ga Jamal komai daɗewar lokaci, hakan ya sa ta dinga amfani da kayanta na gida duk da ba su da yawa. Kayan Nur kuma ta mayar da su akwatunan lefenta da ke ajiye gefen gado. Saboda ta saka wa ranta zaman wuccin-gadi ne za ta yi a gidan ba zaman dindindin ba, don haka babu abin da zai ruɗe ta ta saki jiki a inda babu lasisin zamanta. Ba ta samu bacci mai daɗi ba har sai da ta gama sallar asuba, daga lazumi ta ɓingire a wurin sai barci. Haka ta ci gaba da rayuwar kaɗaici ita kaɗai a gidan Jamal har tsawon sati ɗaya, babu mai zuwa wurin ta idan ba Gwaggo Salame ba. Abin da ya fi ɓata mata rai kenan ganin yadda aka wofintar da 'yancinta bayan an tauye rayuwarta da gingimemen laifi. Hakan ya sa a cikin 'yan kwanakin gabaɗaya ta zuge, saboda ramar ƙarfi da yaji ta dira jikinta har idanuwanta sun zurma tamkar mai ciwo. Saboda wa'azi da nisihar gwaggon Salamen, tare da kulawar da Hajiya ke ba ta kowace safiya; ba su cire ta daga cikin ƙuncin da zuciyarta ke abota da shi ba. Sai ga wani ƙarin tashin hankali, Hajiya ta kira ta a waya tana sanar da ita Jamal zai dawo ranar ta shirya yi wa mijinta girki. Shiru kawai ta yi bayan ta sauke wayar daga kunnenta ƙirjinta yana bugawa ta shiga sharar ƙwalla. Saboda jikinta ya ba ta gara zaman gidan ita kaɗai da rayuwa wuri ɗaya da Jamal. Duba da irin tozarcin da ya yi mata da yunƙurin kisan tun a tashin farko. "Ba zan iya zaman aure da shi ba." Furucinta kenan a lokacin da ta miƙe jikinta yana rawa ta ja dogon hijabi ta zumbula. Da sassarfa ta sauka ƙasa jikinta yana tsuma ta isa bakin gate, maigadi yana tambayar lafiya ganin yadda ta fito gidan kamar an koro ta. Amma ƙanzil ba ta ce da shi ba ta buɗe ƙofar za ta fice. Kiciɓis ta yi da gwaggo Salame tana ƙoƙarin shigowa gidan har kansu ya gwabru da juna. "Subhanallahi!" Furucin gwaggon kenan a lokacin da ta yi ido biyu da Minal, nan take zuciyarta ta hasko mata abin da take ƙoƙarin aikatawa. Fuskarta a cure ta dinga kallon Minal tana nazarin yanayinta, ganin ta ja gefe tana kumbura fuska bakinta ɗauke da gungunin a saman leɓonta. Fuskarta a cure ta yi mata magana cikin kakkausar murya ta ce, "Me ya fito da ke kuma ina za ki je?" Minal ta ɓare baki kamar ƙaramar yarinya ta yi magana cikin kuka ta ce, "Wallahi ni ba zan zauna daga ni sai shi a cikin gidan nan b..." Ta yi maganar tare da rushewa da wani sabon kuka har da buga ƙafafuwa. Baki a sake gwaggon ta bi ta da kallo bayan ta shigo gidan ta rufe ƙaramar ƙofar. Ta fara fa hannnuwa tana salati saboda ta rasa me za ta faɗa. Ganin maigadi yana tsaye yana kallon su ya sa ta ja hannunta tana tirjiya da buga ƙafa har suka koma cikin gidan. A falon sama ta zaunar da ita kan kujera ranta a matuƙar ɓace ta shiga nuna ta da hannu kafin ta samu damar faɗin, "Yanzu Amina sau nawa zan ce ki yi haƙuri? Kenan duk abin da nake faɗa a bayan kunnuwanki yake bi yana wucewa? Saboda Allah duk lokacina da nake ba ki a kwanan nan ashe ba ki gani ba? Ko kin manta ina da tarin abubuwan da nake jinginewa na zo rarrashin ki? Ashe ban sani ba kallon mara aikin yi kike yi mini da nufin na yi a banz.." "Gwaggo ni ba na son zama da shi ne kawai...saboda ya faɗa ba zai mini kallon mace ba kuma ya ce sai ya kashe n..." "Ya kamata zuwa yanzu ki fahimci mijinki ba zai iya cutar da ke ba. Don ko kiyashi ba zai iya kashewa ba ballantana mutum. Saboda duk tsawon kwanakin nan da ba ya kwana gidan yana asibiti ana kula da lafiyarsa. Ya yi ciwo na tsawon kwanaki a yanzu ta kansa yake yi da abin da ke damun sa. Don haka ki kwantar da hankalinki babu abin da zai iya yi miki idan ba alheri ba. Idan ma ya yi miki Allah ma ba zai bar shi ba, kuma hukuma ba za ta ƙyale shi ya ci bulus ba dole ne a ɗauki mataki kans..." "Idan haka ne Gwaggo a sanar wa da 'yansanda tun yanzu, saboda su san halin da ake ciki su hana shi kada ya sake yunƙurin kashe ni...don wallahi ranar ƙiris ya rage ya cire mini maƙogwaro." Dariya Gwaggo Salame ta yi sannan ta zauna kusa da ita tare da janyo ta jikinta, saboda zancenta ya sa ta fahimci firgicin da ya saka ta ne ya sa take jin tsoron zama da shi tun a daren farkon auren. Hakan ya sa ta shiga kwantar mata da hankali har ta saki ranta. A gefe ɗaya kuma tana jinjina ƙarfin son da yake yi wa Nur cikin tausaya wa halin da yake ciki. A ranta kum ta shirya yadda za ta shawo kansa ya daina jin haushin ta su nemo hanyar da za a gano Nur a duk inda ta shiga. Saboda kwanansa uku a asibitin aka sallame shi, a kwana na huɗun ne Hajiya ta ce ya kamata ya koma gidansa da kwana tun da ya ji sauƙi. Amma fafur ya kafe a kan shi da gidan har abada, ta so tirsasa masa kwana gidan a ranar; amma wasu daga cikin dangin Alhajinsa suka ce ta bi komai a hankali. Hakan ya sa ta ci alwashin kora shi gidansa cikin dabara, saboda babu adalci a bar Minal ita kaɗai a gidan shi yana kwana gida. A son ran Hajiyar ma daga sallamar sa a asibitin ya yi wa gidansa tsinke su sasanta da matarsa, amma shawarar da likitan ya ba ta a kan a bi komai a sannu har zuwa lokacin da zai warware ya sa ta ɗaga masa ƙafa. Sai dai kuma a gefe ɗaya ta shiga nata aikin da ta ce idan ya san wata bai san wata ba. Don maganin ƙarfin maza ta dinga ɗirka masa yana sha ba tare da ya san amfaninsa ba. Ko da ya tambaya kuma ce masa ta yi maganin ciwon zuciya ne, duk da bai gamsu ba amma hakan bai sa ya yi kokwanto a kansa ba, saboda cikakken sanin da yake da shi a kan ta fi shi son kansa, kuma ba za ta iya cutar da shi ba. Abokansa ma ta ba su aikin dannar sa tare da rage masa damuwar rashin Nur. Hakan ya sa suka shiga nuna masa alfanun haƙuri da kowace irin jarabawa. Saboda iya binciken da suka yi sun tabbatar Nur ba ta garin, ta yi tafiyar da babu wanda ya san inda ta je. Da taimakon abokan nasa masu ƙarfafa masa gwiwa ya dinga shan maganin Hajiya. Sai dai inda gizon ke saƙar sauyin da ya fara ji a jikinsa, inda ya fara zargin maganin da tayar masa sha'awar mace. Saɓanin yadda ya saƙa wa ransa har abada tsakaninsa da mace, matuƙar Nur ba ta dawo ba babu shi babu kowace irin mace a duniya komai nagartarta. Dole ƙanwar na ƙi Hajiya ta shawo kansa a kan zai koma gidansa da kwana. Daɗin amincewarsa ta aika wa Minal cefane, tare da sanar da ita abincin da ya fi so ta girka masa da kanta. A nan gidan ma Gwaggo Salame ce ta taimaka mata da girkin har suka kammala. Sannan ta saka ta yin wanka da ado a cikin ɗaya daga cikin sabbbin kayan lefen Nur, waɗanda sai da ta sha fama da ita sannan ta saka kayan. Sai dai a a ranta ta ci burin tana fita za ta cire, saboda ta yi wa kanta alƙawarin zama d Jamal har zuwa lokacin da Nur za ta dawo. Kunun aya Hajiya ta haɗa wa Jamal, ta ce ya tafi da shi ya sha tare da Minal, saboda sanin yana mugun son sa, wannan dalilin ta yi masa tarkon da zai kama shi daren ranar. Bayan ta gama yi masa wa'azi da jan kunne a kan zama da Minal bisa amana ko da ba ya son ta. Ganin hawaye a idonta ya saka shi karɓar alƙawarin zama da ita a cikin gidan ba tare da ya yi mata korar karen da ya kitsa wa ransa ba da ya je gidan. Har ya fice da motarsa cikin gidan tana zuba masa addu'ar tsari da abin ƙi tare da neman kwanciyar hankali a cikin rayuwarsa. Cike da jin daɗin addu'o'in nata ya baro gidan cikin karfin zuciya, amma bai fasa hasko hoton murmushin Nur a idanuwansa ba. Hakan ya ƙarfafa masa gwiwar zai ci gaba da neman Nur a duk inda ta je a faɗin duniya. Wasar za ta fara🫠 D. AUTA CE✍️ [2/20, 22:02] Hadiza D. Auta: *FANSAR ƘAUNA!* *HADIZA IBRAHIM D. AUTA* *LAMBA TA SHIDA.* Minal tana zaune falo tana kallon ƙarfin halin da Gwaggo Salame ta saka ta yi. Saboda ita ce ta ba ta umarnin zaman kallon har zuwa lokacin da Jamal zai shigo gidan, kuma ta ce kada ta kuskura ta bar falon ba tare da ya dawo ta gabatar masa da abincinsa ba. Tare da jaddada mata kada ta bari wahalar girkin da suka yi ta tashi a banza. Kuma duk abin da take ji kada ta yi sakacin barin sa ya yi kwana da yunwa. Saboda Hajiya ta sanar da ita ba ta bari ya ci abinci a wurin ta ba, saboda kada ya ƙi cin na gidansa. A haka ta zauna tana kallon MBC2 da tagumi har zuwa lokacin da ta ji buɗe gate da shigowar motarsa. Ƙirjinta ya ƙire ya faɗi a lokaci ɗaya jikinta ya hau rawa ta shiga wara idanuwa tana neman inda za ta ɓoye, kada ganin ta ya sa haukar son Nur ta motsa masa ya nemi illata ta a banza. 'Ko da wasa kada ki sake ki nuna kina jin tsoron sa. Saboda wannan ne damarki ta farko da za ki yi amfani da ita ki nuna masa ke ma kin san kanki.' Tuno kalaman Gwaggo Salamen ya sa ta fara faɗar hasbunallahu wa ni'imal wakil don samun nutsuwar zuciyar da ta bar jikinta tsoro ya mamaye jarumtar da take ƙarfafa kanta. Saboda sautin huɗubar gwaggon da take ji a cikin kunnuwanta tamkar a lokacin take yi mata jan kunnen da gargaɗi. Hakan ya sa ta yi hanzarin gyara zamanta tare da tsuke fuska tana nanata kalmar lahaula wa la ƙuwwata illah billah. Har ta ji motsin buɗe ƙofar falon ƙasa tare da takunsa yana hawa saman cikin sauri. Dam-dam ƙirjinta ya shiga bugawa da sauri da sauri a lokacin da ya kunno kansa cikin falon. Idanuwanta a kan tv ba tare da ta kai kallon ta gare shi ba gudun ya gano halin da take ciki ya nemi cutar da ita babu mai ceton ta. Don a cewar Gwaggon idan ya fahimci tana mugun tsoron sa zai raina ta yawa ta yadda zai dinga yi mata abin da ya ga dama koyaushe. Hakan ya sa shigowarsa bai sa ta kai duban ta gare shi ba duk da hankalinta yana kansa. Sannan bai yi sallama ba ballantana ta amsa, sai jin sa ta yi ya saki ledodin da ke hannunsa suka zube ƙasa, bakinsa yana rawa ya kira sunan Nur cikin ɗaga murya yana cewa, "Nur! Yaushe kika dawo ban sani ba?" Wani kallo ta yi masa kamar ta yi masa babu yabo babu fallasa, amma a zuciyarta sosai ya ba ta tausayin da ya so karya mata zuciya. Sai dai hakan bai hana ta waige gefe da gefe ba cikin basarwa ta ce, "Ina ka ga Nur a nan?" "Ya Allah!" Jamal ya faɗa cikin wata irin murya yayin da ya yi hanzarin dafe kansa da ke sarawa babu shiri. Saboda hango Minal a matsayin Nur ya tayar masa da mikin da yake ƙoƙarin dannewa a ransa. Saboda gizon da ta yi masa sak Nur da ƙamshin turaren Nur da ya ji a cikin falon, wanda tun asali shi ne ya fara yi masa maraba kafin ya isa bakin ƙofar shiga falon. Ƙirjinsa ya hau bugawa babu ƙaƙautawa ya shiga nuna ta da hannu yana faɗin, "Ko da wasa kika sake saka turaren Nur a cikin gidan nan sai na sauya miki kamanni...kuma kin ci sa'a na yi wa Hajiya Mummy alƙawarin zama da ke da a yanzun nan sai kin bar gidan nan wallahi...ahhhh!" Ya ƙare maganar yana dafe kansa ya wuce jiri yana kwasar sa ya faɗa ɗakinsa. Kamar da gayya a ɗakin ma turaren Nur ne ya fara yi masa oyoyo. Gado ya yi hanzarin kwantawa dafe da kansa yana murza goshinsa tare da bubbuga kansa a hankali. Ya bar Minal da ƙamewa wuri ɗaya tamkar an dasa ta, saboda furutansa sun ƙara lalata ƙarfin halin da ke zuciyarta. Zumbur ta miƙe gudu-gudu sauri-sauri jikinta yana rawa ta faɗa ɗakinta, babu ɓata lokaci ta hau cire kayan Nur da ke jikinta. Sannan ta nufi bayi da sassarfa ta shiga darzar jikinta da sabulu tana haɗa kumfa, a ƙoƙarin ta na son raba kanta da ƙamshin Nur saboda gudun ta shiga haƙƙinsa da yawa ciwonsa ya ƙara tashi ta yi sanadin sharri. Don Hajiya ba ta ɓoye mata komai ba ta sanar da ita duk abin da likita ya faɗa a kan ciwon nasa tun kafin ya dawo gidan. Kuma ta nemi alfarmar ta kula da shi tare da juriya a kan halayensa har a shawo kan matsalolin da ke cure su warware. Sai da ta ji fatar jikinta ta fara zafi sannan ta haƙura da wankan ta fito daga bayin. Jikinta a mace ta sake shiri ta fice saboda tuno abincin da take son yi masa ta yi kada ya kwana da yunwa. Ta ɗauki minti biyar a bakin ƙofarsa tana tunanin yadda za ta shiga ɗakin da irin sakamakon da zai biyo bayan shigarta. Kamar wata mara gaskiya haka ta shiga ɗakin nasa tamkar wadda ƙwai ya fashewa a ciki ƙirjinta yana harbawa. Nesa da shi ta tsaya tsawon minti biyu ba tare da ta iya furta masa ko kalma ɗaya ba. Alamun mutum da ya ji a kansa ya yi hanzarin tashi zaune yana ƙare mata kallo cike da mamaki. Kafin ya haɗe girar sama da ta ƙasa ya yi magana cikin kakkausar murya ya ce, "Malama lafiya kika shigo mini ɗaki ko sallama babu!" "Abin..ci...abin...cin...na ce.." Kalmomin da ta yi ƙarfin halin harhaɗawa kenan cikin ininar da ba ta san ta iya ta ba sai a ranar. Saboda ya kafe ta da ido tamkar wadda ya kama da laifin kisa ko ta yi masa babbar sata. "Abinci-abinci kika ce me?" Ya maimaita maganarta cikin sauya murya a sheƙeƙe alamun ya kai maƙura da takaicin ta a ransa. Tana kallon yatsun hannunta ta mayar masa da amsa fuskarta a haɗe kanta a duƙe ta ce, "Abinci ne na dafa, idan za ka ci sai na kawo maka." "Abinci!" Ta yi hanzarin ɗaga kai a tunaninta ta yi masa gwaninta, amma jin tsawar da ya daka mata da maganganun da ya baibaye ta da su; ya sa ta yi hanzarin ficewa sum-sum daga ɗakin cike da tsoro bayan rawar da jikinta ya hau yi. "Ni ne kike zaton zan ci abincinki? Ke mahaukaciyar ina ce da za ki yi tunanin zan iya cin abin hannunki ma ballantana ƙazamin abincinki?" Ganin ta bar masa ɗakin ya fito falon yana ta balbala mata masifa duk da ta shige ɗakinta, amma bai haƙura ba cikin ɗaga sauti tamkar bai san dare ne ba ya zazzaga mata zafafan maganganu tamkar ana yi masa wahayin su. "Idan na sake ganin jemammun ƙafafuwanki a ɗakina sai na saka gitta na sare su gabaɗaya! Daga yau kada ki sake shiga duk sabgar da ta shafe ni...idan kuma ganganci ya ja ki na illata ki a banza na ga wanda zai tsaya miki baƙar wawuya bagidajiya! Kuma ki buɗe kunnuwanki da kyau ki ji ni; matuƙar ba ki sanar da ni inda Nur ta je ba sai na ga bayanki baƙar munafuka mai raba ƙauna!" Minal ta rushe da wani irin kukan da ba ta san lokacin da ya suɓuce mata ba. Saboda kalamansa na ƙarshe sun yi matuƙar gigita mata kwanya. Kuma sun shiga jikinta ta yadda ita kanta ta shiga tunanin laifin me ta yi wa Nur ta yi mata irin wannan sakayyar, ta gudu bayan ta ɗora mata jakar tsaba a ka kaji suna aikin caccaka. Tun tana kukan da hawaye har ta koma yin na zuci tare da ajiyar zuciyar da babu komai a cikin ta sai nadamar zamanta gidan ba tare da ta tsere kamar yadda Nur ta yi ba. 'Matuƙar ba ki sanar da ni inda Nur ta je ba sai na ga bayanki baƙar munafuka mai raba ƙauna.' Maganganunsa sun daki zuciyarta, hakan ya sa suka fara yi mata amsa-kuwwa a cikin kunnuwa babu ƙaƙƙautawa ta shiga jujjuya kanta tana faɗin, "Nur ki dawo tun kafin raina ya zamo fansar guduwarki." Jiki ta ja tana jan ɗuwawu ta isa bakin gado ta jingina bayanta tare da ɗora kanta saman gadon tana haɗiyar zuciya da shesshekar kukanta a hankali. A haka barci ɓarawo ya sace ta daga zaune tana tunani da ajiyar zuciya lokaci bayan lokaci har a cikin barcin. Shi kam sai bayan ya gama sababin da surutan shi kaɗai sannan ya kwanta rigingine yana kallon sili, zuciyarsa cike da tunanin ta wace hanya zai ci gaba da neman Nur. Zuciyarsa ta tsayu a kan zai bayar da cigiyar ta gidan rediyo da kuma posting a social media. Ta yadda abin zai zama viral ya watsu a ko'ina ko za a dace. Da wannan nazarin ya miƙe a lokacin da cikinsa ya fara ƙugin yunwa. Kitchen ya nufa ya yi tsaye bakin ƙofa yana ƙare masa kallo bayan ya kunna ƙwan lantarkin da Minal ta kashe a lokacin da suka gama aiki. Bincike ya dinga yi har ya haɗa kan indomie ya haɗa ta da ƙwai biyu cikin ɗan lokaci ya dafa. Kasancewar ya iya hannunsa tashin hannun Hajiya ɓangaren abinci abubuwa kaɗan ne bai iya ba. Duk da gatan da take yi masa hakan bai hana shi koyon wasu ayukan mata ba. Bayan ya cinye indomin ya tuna da kunun ayar Hajiya, ƙaƙƙarfan tsaki ya ja sannan ya fice daga ɗakin ya nufi bakin ƙofar shigowa babban falon ya kwashe ledodinsa da ya watsar. Kasancewar akwai wadatacciyar nefa kuma akwai ƙanƙara a cikin frizer da ke kitchen. Wadda ya gan ta a ƙanƙare wajen binciken da ya gama yi lungu da saƙo har zuwa store da ke ƙuryar kitchen ɗin. Sai da ya kwankwatsa ƙanƙarar ya jefa a kunun ayar, wanda ya bulbule a cikin dogon jug sannan ya faɗa wanka. Zuciyarsa babu daɗi ya gama wankan ya fito yana tsane jikinsa yana tsaki cike da takaicin Minal ya sake faɗin, "Wawuyar banza mai ƙaton kai! Duk inda Nur ta je ta sani, kuma gobe idan ba ta sanar da ni gaskiya ba sai na ɗauki mummunan mataki a kanta. Ban san me ta yi mata ba don kawai ta gudu ita ta aure n....don ubanta ko za ta mutu ba zan yi zaman aure da ita ba tun da ba na son t...mitsssss!" Ya ƙare maganar da jan dogon tsaki ya ja jug ɗin kunun a tsaye ya kafa masa baki ya fara kwankwaɗa. Garɗi da daɗin kunun, haɗi da sanyin da ya yi bai san lokacin da ya tayar da jug ɗin ba ya ajiye kofin yana gyatsa. Bakinsa ya goge bayan ya koma toilet ya yi brush ya kwanta da towel a jikinsa yana haki kamar wanda ya sha gudu. Da tunanin Nur bacci mai nauyin gaske ya kwashe shi. Kamar almara cikin dare ya fara jin jijiyarsa tana miƙewa, zumbur ya zabura saboda kakkarwar sanyin sha'awa da ya shiga yi. Kansa ya dafe yana salati saboda yanayin da yake ji bai taɓa tsintar kansa a makamancinsa ba. Zarya ya fara yi a cikin falon dafe da kai jijiyarsa a miƙe kamar mai koyon tafiya. Babu shiri ya yi zaman 'yan bori a tsakiyar ɗakin saboda ya kasa juriyar tsayuwa da ƙafafuwansa da ke kakkarwa. "Ya Salam!" Ya yi ta jerawa a bakinsa yana maimaitawa tamkar wanda aka saka yin hadda. Nan take gumi ya hau keto masa yana sharewa da hannu har ta kai ya dafe mararsa yana salati. Tsabar harbawar da jijiyarsa take yi tamkar numfashinsa zai shiɗe yake ji. Halin da yake ciki ya saka shi miƙewa babu shiri ya fara tafiya yana layi ya faɗa ɗakin Minal jikinsa yana tsuma. Ƙafafuwanta ya jawo da ke shimfiɗe a bakin gado, babu shiri ta baje a tsakiyar ɗakin tare da farkawa a haukace cikin wani sabon firgici. Saboda mafarkinsa take yi wai ya zo da wuƙa a kanta yana faɗar ko ta faɗa masa inda Nur ta ɓoye ko kuma ya kashe ta. Ihu ta fasa iya ƙarfinta ta buge shi ya faɗi ƙasa dabas tare da sakin towel ɗin da ke ɗaure a ƙugunsa. Wataƙila halin da yake ciki ya mantar da shi babu komai a jikinsa, a haka ya miƙe jijiya miƙe ya nufe ta gadan-gadan zai kamo ta. Ta sake ƙwalla ƙara tare da zurawa da gudu ta faɗa toilet a sukwane, sai dai kafin ta rufe ƙofar suka shiga kokawa a tsakaninsu. Yana ƙoƙarin shiga ciki yayin da ita kuma take ƙoƙarin tura ƙofar iya ƙarfinta a kan ba zai shiga ba, saboda kuzarinsa ya rage ya kasa shigar kamar yadda ya so. Ganin za ta ɓata masa lokaci ya yi baya da nufin banke ƙofar da jikinsa ko da za ta ɓalle in dai zai samu biyan buƙatarsa. Sai dai yana yin bayan ta datse ƙofar tare da hanzarin saka makulli ta rufe ruf jikinta yana kyarma tamkar mazari. Don a iya tarihin rayuwarta ba ta taɓa shiga tashin hankalin da ya kai wannan ba, don ba ta taɓa yin ido da babban mutum babu tufafi a jikinsa ba, sannan da yunƙurin yi mata fyaɗe ko a mafarki. Hakan ya ƙara ɗaga mata hankali ta shiga zunduma ihun neman agaji. Shirun da ta ji tun daga lokacin da ta rufe ƙofar bai nemi buɗewa ta ƙarfi ba; amma hakan bai sa ta fasa kururuwar da take yi ba. Jamal kam ganin ta yi nasara a kansa ya koma ɗakinsa da sassarfa ya ɗauko ɗaurin kuɗi 'yan dubu-dubu har bandur ɗaya sababbi kar ya tsaya bakin ƙofar toilet ɗin yana magana cikin rawar baki tsabar yadda yake ji a jikinsa. "Idan har ba za ki bari na yi don Allah ba to ga shi zan...bi.. biya ki...tun da...da ma can ke..ba kya... tsoron Allahhhhh...." Cabɗijam!🙆 Na yi kudi🏃 [2/20, 22:02] Hadiza D. Auta: *FANSAR ƘAUNA!* *HADIZA IBRAHIM D. AUTA* *LAMBA TA BAKWAI.* "Wayyo-wayyo Allahna!" Abin da ta faɗa kenan daga cikin bayin dafe da kanta ta ƙwalla ƙara iya ƙarfinta. Ido ta shiga zarewa tana ci gaba ihun da kururuwar faɗin ta shiga uku ta lalace a zo a kawo mata ɗauki. Wannan dalilin ya jawo hankalin maigadin gida ya fito a firgice ya isa bakin ƙofar shiga falonsu yana bubbugawa babu ƙaƙƙautawa yana kiran sunan Jamal. Bayan ya gama zagayen gidan lungu da saƙo da zungureriyar addarsa, yana ta neman inda zai ci karo da wani baƙon fuska ko wata alamar da ke nuna an shiga gidan bai sani ba. Don duk hasken da ke gidan bai hana shi ƙarawa da fitilar hannunsa mai matuƙar haske ba. Sosai bugun ƙofarsu ya saka Jamal diriricewa, saboda zumbur ya miƙe daga ƙasan da ya baje dafe da mararsa yana kakkarwa. Amma dole ya miƙe dafe da ƙugunsa yana tafiya kamar mai tete, a haka ya sauka daga ƙasan benen da towel a ƙugunsa ya buɗe ƙofar. Don bai tsaya wani jinkiri ba ko ɓata lokacin tambayar wane ne ba. Saboda jin muryar maigadi ya saka shi shahadar buɗewa babu shiri. "Baba lafiya?" Tambayar da ya wurga masa kenan a lokacin da ya gan shi tsaye da addarsa a hannu bayan fitilar da yake haskawa gefe da gefensa. "Ranka ya daɗe sautin Hajiya da na jiyo tana ihu tsawon lokaci ya sa na ji tsoron kada a ce wani mummunan abu ne ya faru ban sani b..." "Babu abin da ya faru je ka kwanta." Ya yi maganar ransa a haɗe cike da jin haushin maigadin. Sumui-sumui ya bar wurin yana faɗin, "Allah Ya ƙara tsarewa." Saboda fahimtar inda lamarin ya dosa babu wani abu sai tsabagen rakin amaryar gidan. Duba da yanayin da ya gan shi a birkice sannan da sigar da ya fito a yadda yake ba tare da ya ji kunyarsa ba. Tsaki kawai Jamal ya ja ya rufe ƙofar a maimakon ya amsa masa da amin. Ya koma da sassarfa yana yamutsa gashin kansa da hannun tare da faɗin Ya Salam a cikin bakinsa ta fi a ƙirga. Ɗakinsa ya nufa tare da kulle ƙofa ya nufi bayi cikin ƙuncin rai ya yi ta sheƙa wa kansa ruwan sanyi, sai da ya ji rabin nutsuwarsa ta shiga jikinsa hankalinsa ya dawo, sannan ya fito kansa yana muguwar sarawa ya kife a kan gado. Ajiyar zuciya ya shiga saki ɗaya bayan ɗaya yana nishi dafe da jijiyarsa da ke harbawa har komai ya lafa masa barci ya yi awon gaba da shi. Asubar farin ya farka ya yi wanka da arwala ya fice masallacin da ke kusa da gidansa. Zuciyarsa cike da tunanin irin hukuncin da ya dace ya yanke wa Minal idan safiya ta waye. A gefe ɗaya kuma cike yake da jin haushin kansa, har aka gama sallar ya dawo gida bai daina tunanin dalilin da ya jawo masa shiga halin da ya tsinci kansa ba. Saboda tun a daren farkon auren da Nur ta karya masa zuciya bai sake saka wa kansa zai iya shiga irin wannan yanayin a kurkusa ba. Domin ya ci alwashin har Minal ta gama zaman banzarta ta bar masa gidansa ba zai yi mata kallon mace ba. Amma sai ga shi ya kwafsa tun ba a je ko'ina ba. Minal kam kwanan toilet ta yi idanuwanta sun yi jajir kamar gautan kaji tsabar barcin da ke idon da kukan da ta sha tamkar hawayenta zai tsiyaye. A daddafe ta fito daga bayin a daidai lokacin da ta ji ana kiran sallar asuba. Wayar Gwaggo salame ta shiga kira ana ce mata a kashe take, amma hakan bai hana ta tura mata saƙon taimakon gaggawa ba, da zummar tana buɗe wayar idan ta gani ta kawo mata ɗauki, idan kuma zakara ya ba ta sa'a ta aiwatar da nufinta kuma shi kenan. Saboda ta gama tsorata da lamarin Jamal don ta yi amanna da shaye-shaye yake yi. Shi ya sa da ya bugu a daren jiyan ya so juye mata mayen giyar a saman kanta. Bayan ya gama cewa idan aka cire shigar matan da ke jikinta babu wani bambanci tsakaninta da namiji ɗan'uwansa. 'Gwaggo ki zo da 'yansanda Jamal ya sha giya yana ƙoƙarin kashe ni.' Saƙon da ta tura mata kenan jikinta yana rawa tsabar ta gama tsurewa da lamarinsa gabaɗaya. Kamar ɓarauniya ta fito daga ɗakin cikin sanɗa ta sauka ƙasa da dabara gudun ya jiyo takunta ya sake ya lalata ƙudurin da ta kwana da shi a cikin zuciyarta. Turus Jamal ya yi a lokacin da ya zo shiga gidan ya ji ƙofar a ƙargame. Kiran sunan maigadin ya yi cikin sauri ya buɗe masa yana faɗin, "A yafe ni ranka ya daɗe, Hajiya ce ta so tserewa na hana ta fita." Hango Minal ya yi a tsaye riƙe da ƙugu tana kumbura fuska, bai bi ta kan maigadin ba face kallon sama da ƙasan da ya yi mata ya watsar, sannan ya wuce zuwa cikin gidan ba tare da ya ce da su komai ba. Hakan ya saka maigadin ya sake rufe gidan da kwaɗo ya zare makulli saboda ya gama fahimtar yajin amare ne take shirin dakawa. A ransa ya jinjina lamarin, tare da yin dariyar ashe akwai sauran mutan da masu gudun miji har zamanin da ake ciki a yanzu na buɗewar ido. "Ki yi haƙuri ki koma daga ciki Hajiya, ni ma zan je na yi sallah na ɗan matse barcin idona. Sannan ki bai wa maigidan haƙuri don alamunsa ya nuna bai ji daɗin ganin ki a nan ba." Harara ta wurga masa a ƙufule duk da girmansa ta juya zuwa cikin gidan ranta a matuƙar ɓace, saboda ta so tafiya ya hana ta kuma ta so Jamal ya kula ta ta yi masa tijara. Kamar yadda ta so barin gidan ba tare da kowa ya sani ba. Aka yi rashin dace tun daga lokacin da ta fito cikin gidan a kan idon maigadin. Don yanayin ta kaɗai ya sa ya gano babu lafiya ya dakatar da arwalar da yake yi. Musamman ganin abin da take ƙoƙarin aikatawa, kafin ta ƙarasa jikin ƙofar ya kulle gidan da ƙaton kwaɗo cikin sauri. Duk yadda ta so ya buɗe ta fita cikin magiya; amma kukan da ta yi masa bai saka shi tausaya mata ya buɗen ba. Saboda ya san kan aikinsa kuma ya tuno lokacin da ta so barin gidan a karon farko ta ci karo da gwaggo Salame ta taka mata birki. Idonta a rufe ta fara ƙwanƙwasa masa ƙofa tsabar ta zo wuya tana son a yi komai a ƙare ta kama gabanta. Jamal da ke bayi ya fito ransa a ɓace saboda ya san ba kowa ba ce face ita. Kiciniyar buɗe ƙofar da ta ji yana yi ƙirjinta ya hau bugawa ta yi hanzarin ja da baya riƙe da ƙugu tana girgizar jiki alamun ta shirya a yi komai. Saboda ta yi wa kanta alƙawarin barin gidan ta halin tsiya ko arziƙi, sai dai duk abin da zai faru ya faru amma sai bar gidan ta kowace hanya duk da tsinuwar Innarmu da ke cikin sharuɗan fitar tata. "Ke wace irin daƙiƙiya ce?" Ya yi magana cikin wata kalar murya mai ɗauke da ɓacin rai. Minal ta yi masa wani kallo sheƙeƙe sannan ta kawar da fuskarta a gefe tana cewa, "Ka ce da maigadinka ya buɗe mini ƙofa zan je gidanmu." "Ni na ce da shi kada ya bar ki ki tafi gidan naku ne?" Ya wurgo mata maganar yana zuba mata idanuwansa da suka yi mugun nauyi tsabar barcin da yake ji. "To ai ya hana ni fita, kuma ni gida nake so na je.." Ta ƙare maganar tana wurga masa wani kallo da murguɗa baki, hakan ya sake ƙufular da shi karaf ya rufe ɗakinsa bayan ya buga mata tsaki, saboda ganin tana ɓata masa lokaci a banza. Ɗakin ta sake bugawa tana faɗin, "Ni fa wallahi ba zan zauna a cikin gidan da ake barazana ga rayuwata ba." Banza ya yi mata duk da ya ji abin da ta faɗa, amma yawan bugun ƙofar da take yi tsawon lokaci ya saka shi buɗewa gadan-gadan ya yi kanta. Maimakon ta gudu kamar yadda zuciyarta ke ba ta shawara; sai ta kafe tana aika masa harara har ya ƙaraso ya cakumo kwalar hijabinta. Ya ɗaga hannu da nufin faffalla mata maruka wata zuciyar ta yi gaggawar hana shi, tare da ba shi umarnin ya ladaftar da ita ta hanyar za ta fi jin tsoron sa. "Sai na nuna miki na fi ki zama riƙaƙƙen mara kunya...oya nil dawn!" Ya yi magana cikin ɗaga muryar da tsoro ya saka ta kai gwiwowinta biyu a ƙasa babu shiri. Jikinta yana tsuma ta shiga zubar da hawaye tare da haɗa hannu wuri ɗaya tana faɗin, "Don Allah.. don darajar Manzon Allah..don albarkacin..." "Yi mini shiru!" Ta yi saurin haɗiye maganar bakinta jikinta yana kyarma ƙirjinta yana bugawa ta ƙura wa gefenta ido. "Ɗaga hannunwanki sama ki rufe idanuwanki. Kuma idan kika yi gangancin tashi dukan da zan yi miki a yau sai na cire miki haƙorin gaba. Kada ki ga abin da ya faru jiya ki yi tsammanin ko da son raina na aikata ki nemi raina ni...to ni ma ban san wace kalar ƙwaya na sha jiyan ba har ta fitar da ni cikin hankalina." 'Da ma sai ƙwayar. Ashe da gaske shaye-shayen yake yi.' Zancen zucinta kenan cike da alhini a lokacin da ya yi hanzarin komawa ɗaki saboda kiran wayarsa da ake ta yi, cike da mamaki ya rarumi wayar yana tsaki ya danna kore ganin sunan Gwaggo salame a kan fuskar wayar. "Me ke faruwa ne tsakaninka da Amina?" Jamal ya yi jim kamar ba zai bayar da amsa ba, sai da ta sake maimaita tambayar sannan ya fesar da iska mai zafi daga bakinsa ya ce, "Babu abin da ya faru, gida take son zuwa maigadi ya hana ta." Ajiyar zuciya Gwaggon ta saki sannan ta ce, "Don Allah ka ƙara haƙuri da ita, saboda tana buƙatar a tausaya mata ko don ta rage firgicin da take ciki." "Babu damuwa." Iya abin da ya faɗa kenan ya ajiye wayar, saboda ya gaji da magana kansa ya yi nauyi kuma yana yi masa ciwo sosai. Amin kawai ya faɗa a can ciki a lokacin da ta gama yi musu addu'ar zaman lafiya da haƙuri da juna. Nannauyan barci ya ɗebe shi mai ɗauke da mafarkai barkatai har ƙarfe tara na safiya bai farka ba. Caraf tunaninsa ya kamo masa Minal da ya bari a cikin falo tana karɓar horo, cikin sauri ya faɗa toilet bai jima ba ya fito yana haɗe rai kamar wanda ya yi arba da kashi. Ganin ta a inda ya bar ta baje ƙasa tana barci; cikin zafin rai ya kai mata harbi da ƙafa har sau biyu. Ta zabura tana wara jajayen idanuwanta da ke cike da bacci tamkar wadda ta bugu da maye. "Wa ya ba ki damar yin barci?" Ya jefa mata tambayar a fusace. "Allah ne." Ta ba shi amsa a taƙaice saboda tsoron sa bai hana ta mayar masa da raddi ba. Baki ya buɗe cike da mamakinta ya shiga nuna kansa ya sake cewa, "Ni za ki yi wa rashin kunya?" "Faɗar Allah shi ne rashin kunya kuma?" Ita ma ta amsa cike da jarumta. Ya yi kamar zai kai mata mangari ta yi baya cikin zafin nama ya fisgo gefen hijabinta, babu shiri ta fasa ƙara jikinta yana rawa ta fara ba shi haƙuri tare da rantsuwar ita ma ba ta san barcin ya kwashe ta ba. Tsaki kawai ya buga ya nufi kitchen bai ce da ita komai ba, mintuna a tsakani ƙamshin girkinsa ya fara cikawa Minal hanci. Sai a lokacin ta tuna ashe fa ita ma tana jin yunwa, musamman da ya kammala ya fito da tiren ya ajiye a kan dinning table yana faɗin wash Allah. A gabanta ya yi karin safiya ƙamshi yana dukan ta tana rakuɓe gefen kujerar da yake kai da tagumi, har ya cinye komai tas ya miƙe yana gyatsa zai shige ɗakinsa ta ce, "Zan iya tashi?" Ta yi maganar jiri yana ɗibar ta, tsabar yunwa da baccin da ke cikin idanuwanta. Don ƙarfe goma na safiya har ta haura. Mugun tsaki ya ja sannan ya shige yana miƙa, jim kaɗan ya fito daga ɗakin fuskarsa a haɗe ya kai dubansa ga ƙofar ɗakinta ganin babu kowa a cikin falon ta tafiyarta. Murmushin mugunta ya yi sannan ya nufi ɗakin nata da niyyar ya sake tunzura ta da gangan. "Ke!" Abin da ya faɗa kenan cikin kakkausar murya a lokacin da ya hango ta bakin gado tana bacci. Zabura ta yi tare da tashi zaune tana murtsuka ido saboda dishi-dishi take ganin sa. "Tashi ki wanke mini motata, sauri nake yi fita zan yi yanzun nan! Sannan ki tabbatar kin share mana harabar gidan kaf kafin na dawo." D. AUTA CE ✍️ [2/20, 22:02] Hadiza D. Auta: *FANSAR ƘAUNA!* *HADIZA D. AUTA* *AREWABOOKS: Princessdija.* *Follow the D. AUTA NOVELS channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vb2zCo5JUM2bDSfRzW01* *Na buɗe channel fatar za ku dinga leƙawa akwai wasu littafaina da zan saki ta can.* *LAMBA TA TAKWAS.* Babu shiri ta ƙara ware idanuwanta a kansa sannan cikin wata kalar muryar jin bacci ta ce masa, "Ni ce zan yi maka wankin motar?" "Ke..ke..fa...ga ki nan! Ko kin fi ƙarfin ki yi wankin mota ne?" Ya ba ta amsar a harzuƙe tare da nufo inda take cikin zafin nama, da niyyar ya cakumo wuyan hijabinta ya koya mata hankali. A tsorace ta ƙura masa kallo ƙirjinta yana bugawa, ganin ya nufo ta da gaske fuska babu annuri ta zabura daga kan gadon, jikinta yana rawa ta yi bakin toilet tana faɗin, "Ai ba cewa na yi ba zan yi ba...kuma ban san ma yadda ake yi ba n..." "Mu je zan nuna miki tun da kin saba aikin wahala a gidanku ai wankin mota ƙaramin aiki ne a wurin ki." Ya yi maganar yana bin bayanta don ta riga shi fita daga ɗakin tsabar firgicin da ya saka ta, tana zumɓura baki zuciyarta cike da takaicin rainin da yake yi mata kamar wata sokuwa ta kasa bijirewa. Tare suka fito harabar gidan inda ta ja ta tsaya wuri ɗaya, yayin da shi kuma ya nufi ma'ajiyar kayan wankin motar kai- tsaye. Bokiti ya kawo har inda take tsaye rungume da hannuwa a ƙirji tana harare-hararen gefe da gefenta. Sannan ya gyara tsayuwarsa a gabanta tare da riƙe ƙugu yana faɗin, "Minti uku na ba ki ki yi sauri ki kammala komai kafin na shirya na fito. Kuma ki tabbatar kin gama ba na buƙatar ɓata lokac..." Ganin ta a tsaye babu alamun za ta yi aikin da gaske ya sake harzuƙa cikin ɗaga murya ya ce, "Malama tsayuwar me kike yi a wurin da ba za ki wuce ki fara aikin da na saka ki ba?" Wani mugun kallo ta yi masa ranta a matuƙar ɓace sannan ta ja bokitin ta nufi bakin famfo cikin sauri, tamkar za ta tashi sama tsabar ƙufula da ƙudurin ta yi saurin gamawa ta ƙaddamar da abin da zuciya ta kitsa mata. Bayanta ya bi da kallo fuskarsa a cure har ta isa bakin famfon har ta tara bokitin ruwan ya fara zuba. Sannan ya bar wurin da sassarfa ya koma cikin gida, zuciyarsa cike da alwashin wahalar da ita har sai ta nemi saki da kaifin ƙafafuwanta idan ta gaji da zaman. A gurguje ya faɗa toilet ya yi wanka, cikin minti goma sha biyar ya fito angonsa shar duk da babu cikakken angwancin a zahiri. Domin ya yi kyau a cikin tsadadden farin yadin da ya saka tare da ɗora wa kansa hular da ta ƙara fito da haibarsa a fili, kuma ɗinkin ma ya karɓi jikinsa sosai. Sai tashin ƙamshi yake yi kansa a duƙe yana gyara zaman agogon da ke hannunsa ya iso wurin. Minal kuwa kamar wadda aka kira takunsa ya sa ta yi hanzarin kai kallonta gare shi. Ƙirjinta ya buga dam-dam a bisa tsautsayi ta rusa masa tsari. Domin garin kallon sa ta danna tiyon ruwan ya fantsama a kan fuskarsa zuwa ƙirjinsa har ya bi tafin ƙafarsa ya malala ƙasa. A ƙoƙarinta na son wanke kumfan da ke saman motar ta wanke masa jiki. "Ya Salam!" Abin da ya furta kenan a lokacin da ruwan ya sauka jikinsa, tare da yin wani tsallen da ya saka shi jan gefe babu shiri ya hau buge ruwan da hannunsa. Rigar ya riƙo ransa a ɓace don ta gama yin sharkaf da ruwan, cike da mamakin abin da ta yi masa ya dinga kallon jikinsa yana ƙare mata kallo. A cikin zafin zuciya ya ya danna wata muguwar ashar, saboda ba ƙaramin ɓata masa rai ta yi ba, hakan ya saka shi nuna ta da makullin motar da ke hannunsa yana faɗin, "Na gaji da yawan surutun da kike saka ni...don na fahimci so kike yi ki zamo mini wani sabon ciwon kai bayan wanda ke cikin kain..." "Ka yi haƙuri wallahi ba gangan na yi b..." Ta yi maganar cikin saurin baki jikinta yana rawa saboda ita kanta ta sani tabbas ba ta kyauta masa ba. Katse ta ya yi da faɗin, "Yi mini shiru shashasha! Ke har abada ba za ki taɓa wayewa ba! Komai naki a hargitse babu wani tsari ƙauyanci ya yi miki yawa a zuciya." Zancensa ya datse sauran maganar da ke bakinta, kanta a ƙasa tana sauraron yadda yake magana cikin ɗaga murya tamkar ya rufe ta da mahaukacin duka. "A yi mata haƙuri maigida." Maigadi ya yi magana saboda gudun shaiɗan ya tunzura shi abin ya zamo babban abu. Don duk abin da ke faruwa a gaban idonsa ne, tun fitowarsu har badaƙalar da suke yi bai ɗauke ganinsa ba. Farko ya kalli abin a salon soyayya, amma faɗan da ya ga Jamal yana yi ya saka shi jin tsoro, gudun ɓacin rai ya saka shi aiwatar da abin da bai dace ba. Bai ce wa maigadin komai ba ya juya zuwa cikin gidan, da nufin sauya wasu kayan amma bai fasa tsine wa rashin hankalinta ba. "Allah ma ya sani ni ban yi da niyya ba." Zancen Minal kenan a a lokacin da ta saki tiyon ruwan yana zuba ƙasa tsabar takaici. Ƙugu ta riƙe tana girgizar jiki tare da kallon gefe saboda haushin maganganun da ya faɗa mata a gaban maigadin sun tsaya mata a zuciya. Hakan ya saka Jamal jan birki ya tsaya cak a inda yake, kafin ya waigo cikin fushi ya sake nuna ta da hannu fuskarsa a yamutse ya ce, "Ki shiga taitayinki!" Hararar gefen ido ta yi masa ba tare da ta ce komai ba ta ƙura wa wuri ɗaya kallo, har ya gama tsayuwarsa ya dunƙule hannu ya kai wa iska naushi ba ta sake kallon sa ba. "A yafe mata maigida ba za ta sake b.." "Ka tsaya iya aikika!" Jamal ya ƙare maganar tare da nuna shi da hannu, cikin sauri ya bar wurin amma bakin maigadin bai yi shiru ba sai da ya sake cewa, "Allah dai Ya huci zuciyarka maigida." Ya nufi mazauninsa da ke bakin ɗakinsa yana zancen zucinsa cike da jin haushin kansa a kan shiga harkarsu. 'Ba zan sake shiga tsakaninku ba tun da bayar da haƙurin ma laifi ne. Aure sai ka ce wasar yara daga matar gidan har maigidan kowa da kalar matsalarsa. Um..ku kuka sani dai ni ɗan kallo ne." Daga haka ya kama sabgoginsa. Minal kam bayan Jamal ta bi da kallo har ya shige ba ta ɗauke idanuwanta a kansa ba. Zuciyarta cike da jin haushin kanta a kan me ma ya sa ta kalle shi har ta ɓata masa jiki. Jikinta ya yi sanyi ƙalau duk da ba ta daina jin haushin maganganun da ya yaɓa mata ba. Kamar an dasa ta a wurin tsawon minti biyar zuwa shida ba ta motsa ba. Har Jamal ya fito cikin wata sabuwar shigar yana baza ƙamshi, tare da tsuke fuska tamkar bai taɓa dariya ba. Ta gefen ido ta kai kallonta gare shi ƙirjinta yana bugawa amma hakan bai hana ta magana daga ita sai ranta ba. 'Ka gode mini a yanzu har ka fi kyau m...' A daidai lokacin ya buga wani ƙaƙƙarfan tsakin da ya saka bugun zuciyarta ƙaruwa. Saboda hango ruwa a jikin motar ya nuna ba ta goge masa ba bayan ta gama wankewar. Cikin sauri ya fito da wani towel a boot ya shiga goge motar a ransa yana faɗin, 'Wawuyar banza ita komai sai an ce ta yi sannan take yi.' Ya faɗa motar bayan ya gama gogewa ta ya shiga ba ta wuta, maigadi ya yi hanzarin buɗe masa gate tun kafin ya umarce shi. Saboda ya ci burin tsayuwa iya aikinsa ba zai sake shiga sabgar da ke tsakaninsu ba. Minal kuwa kafewa ta yi a inda take duk ƙugin da motar ke yi ba ta sa ta matsa ba. Ganin ba ta da alamun ba shi hanya ya wuce kamar yadda yake so, yana ƙoƙarin yin kwana ya leƙo kansa cikin fushi ya ce, "Ke wace kalar mahaukaciya ce da ba za ki janye ba sai na yi magana...zan kakkarya shamulallun ƙafafuwanki a banza wawuya kawai...mitsssss..." Ya ƙare maganar da tsaki a lokacin da ta ɗaga masa hanya ya nufi bakin gate yana ci gaba da faɗar duk abin da ya zo bakinsa. Magana ya yi da maigadin ƙasa-ƙasa sannan ya fice gidan. Allah Ya tsare ya shiga yi masa yana ɗaga hannu har ya wuce, amma kafin ya rufe babbar ƙofar Minal ta ƙaraso wurin ita ma. Wuff ta yi da nufin faɗawa waje ta fice ta ƙaramar ƙofar gidan, don ta gama haɗa komatsan tunaninta a wuri ɗaya, a kan yanke iyakar zama da Jamal har abada don ya gama ci mata zarafi a banza. "Ki yi haƙuri Hajiya, maigida ya ce kada na bar kowa ya fita a cikin gidan nan, yau babu shiga babu fita." Wani kallo ta yi masa sannan ta yi magana a ƙufule tana cewa, "Shi maigidan da ya fita me ya sa ba ka hana shi ba sai ni da ka raina?" Yana kulle ƙaramar ƙofar gidan bayan ya sha gabanta ta koma ciki ya ce, "Umarni ne daga shi, kuma aikina nake yi Hajiya. Amma ko yanzu ya kira ni ya ba ni damar barin ki fita an gama zance." Ta jima a wurin tsaye zuciyarta sai ingiza ta take yi a kan ta yi masa rashin kunya ko zai bar ta. Yayin da wata zuciyar ke ba ta shawarar ta zagaya ta bayan gidan ta haura katanga. Kafin ta yi ƙwafa ta bar wurin tana cika tamkar wata kububuwa. A haka ta koma cikin gidan ranta a ɓace ta faɗa ɗakinta tana kuka wiwi. Bayan ta rage ƙuncin zuciyarta ta nemi wayarta kaf ɗakin ta rasa, bayan kuma ta san a kan gadon ta bar ta. Idanuwanta suka kai kan agogon ɗakin babu shiri ta zaro ido, ganin lokacin ya yi gudu da yawa ga kuma ƙugin yunwa da hanjinta suke yi. Don ƙarfe sha biyu na rana har ta wuce, waton ƙarfe ɗaya saura kaɗan ake harare. Kitchen ta nufa faka-faka da niyyar neman abin da za ta ci, jiri yana kwasar ta tsabar yunwa da bacci sun gama ladaftar da ita jikinta. A gurguje ta yi wanka ta yi sallah sai zuba hamma take yi wata bayan wata, sannan ta baje tana wani irin mugun barci mai ɗauke da kalolin minshari. *** Sadam kuwa daga gidansa wurin Hajiya Mummy ya nufa. Saboda nazarinsa ya gama ba shi akwai abin da Hajiyar ta saka masa a cikin kunun ayar da ta ba shi. Kamar yadda ta dinga ɗirka masa maganin ƙarfin maza da sunan na sauƙin zuciya. Bayan sun gaisa fuskarsa babu yabo babu fallasa ya amayar da abin da ke cikin bakinsa kai-tsaye. Inda ya sanar da ita bai ji daɗin abin da ta yi ba. Don bai shirya zaman aure da Amina ba, sannan ya ƙara da cewa, "Yarinyar nan ita kanta damuwa ce mai zaman kanta Hajiya. Kuma idan ina tare da ita ciwon da likita ya faɗa yana gaf da afkuwa komai ya faru a kaina. Saboda zama da ita tamkar barazana ce ga rayuwata Hajiy..." "Ka yi haƙuri, ni da ma farincikinka nake nema. Amma tun da nawa tsarin bai yi maka ba ka je ka yi duk abin da kake so. Sai da ka sani ko da Nur ta dawo ba zan taɓa bari ka yi zaman aure da ita ba, tun da har ta iya tsallakewa ta gudu alamu ya nuna ba ta son ka. Kuma duk wanda ba ya son ka ni ko lahira ba na fatar haɗuwa da shi." Tana ƙare maganar ta ja bakinta ta tsuke bayan ta haɗe rai da fuska alamun babu wani sauran sassaucin da za ta yi masa a kan hakan. "Haba Hajiya, ke fa kika sanar da ni ba da Nur aka ɗaura aurena ba na ɗauki ƙaddarata a yadda ta zo mini, sannan kuma a yanzu ki koma ganin laifinta ki koma a kan guduwar da ta yi don ba ta so na ne? To me zai hana ta guduwa bayan an raba ta da abin da take so? Ina son Nur Hajiya kuma zan nemo ta a duk inda take, ko da a yanzu ita ta daina so n...." "Ni kuma matuƙar ba ka kula da Amina kuka zauna lafiya ba; ban yafe maka ba idan har ka tafi neman wadda ba ta san muhimmancinka ba. Sannan kada ka manta; ko danginta sun gaji da neman ta sun bar wa Allah saboda tsarinta ne aka bi kuma ganin damarta ne...kai a taƙaice aurenka da Amina ma ita ce ta haɗa komai...to a kan me za ka lalata damar da Allah Ya ba ka a kan neman wadda ba ta ra'ayin ka?" Shiru ya yi mata ba tare da ya ce komai ba, saboda maganganun sun shiga jikinsa sun dakar masa zuciya. 'matuƙar ba ka kula da Amina kuka zauna lafiya ba, ban yafe maka ba idan har ka tafi neman wadda ba ta san muhimmancinka ba.' Ya shiga maimaita zancen a ransa nan take damuwa ta ƙara yi masa lulluɓin tashin hankali. "Ta ya zan zauna lafiya da Amina bayan babu so a tsakanina da ita? Me ya sa za ki yanke mini irin wannan hukuncin bayan kin sani Nur ita ce rayuwat..." "Ka mutu a yau ɗin nan Jamal idan har da gaske ita ce rayuwar taka! Saboda wallahi ka ji na rantse da Allah ba zan taɓa yafe maka ba matuƙar ka bar matarka ta sunna ka je yawon neman wadda ba ta san darajarka b...shin har sau nawa zan faɗa maka ita ce ta nemi haɗin aurenka da Amina? Ko so kake yi sai na yi ta shela da lasifika ina bayani sannan za ka fahimce ni? To Nur ba ta son ka, don da tana sonka ba za ta nemi a cusa maka Amina ita kuma ta tsallake ka ta bi duniya ba. Na faɗa na koma faɗa ba zan lamunci ganin cigaban rayuwarka ya tsaya a sanadin wata macen banza ba Jamal!" Tana ƙare maganar ta bar masa falon ta shige ƙuryar ɗakinta tana goge hawaye, hawayen kukan da ta so dannewa tana kokawar kada su fito amma suka kasa ba ta haɗin kai. Wai ya abin yake ne?🤔🥺 Ga link; https://chat.whatsapp.com/ICmrsyihZBzLrpXfmM7DyQ Masarauta group masu tambayar a saka su group da masu buƙata su ma su yi joining. D. AUTA CE ✍️ [2/20, 22:02] Hadiza D. Auta: *FANSAR ƘAUNA!* *HADIZA D. AUTA* *AREWABOOKS: Princessdija.* *Follow the D. AUTA NOVELS channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vb2zCo5JUM2bDSfRzW01* *Na buɗe channel fatar za ku dinga leƙawa akwai wasu littafaina da zan saki ta can.* *LAMBA TA TARA.* Jikinsa ya yi sanyi ƙalau, saboda zubar hawayen Hajiya Mummy ba ƙaramin tashin hankali ba ne a wurin sa. Musamman a ce kuma shi ne ya yi sanadin saka ta kukan da babu farinciki a cikin sa. Ya jima a wurin bai motsa ba, zuciyarsa ta shiga saƙa masa abubuwa da dama. Kafin ya nisa cikin ƙaƙƙarfan sauti ya miƙe cikin sanyin jiki da na gwiwa. A haka ya ja ƙafafuwansa zuwa cikin ɗakin nata fuskarsa a yamutse. Saboda hango ta a bakin gado tana goge ƙwalla da gefen ɗankwalinta. "Kukanki tamkar ɗigar dalma ne a jikina. Me ya sa kike so Allah ya yi fushi da ni Hajiyarmu?" Ya yi maganar cikin sanyin murya a lokacin da ya kai gwiwowinsa ƙasa a gabanta ya dafa cinyoyinta. Sharr hawaye suka shiga malala a kan fuskarsa ba tare da ya damu da sharewa ba. Kansa ta dafa ita ma hawayenta bai daina gangara a kan fuskarta ba, amma hakan bai hana ta yin magana cikin muryar kukan ba. "Duk abin da ka ga na yi ina yin sa ne saboda farincikinka Jamal. Ba burina ba ne saka ka kunci ko damuwa kawai don ina son ka yi mini biyayya. Idan ka riƙe Amina a matsayin mata in sha Allahu za ka yi alfahari da hakan ko a bayan rain...." "Daina ambaton mutuwa Hajiyarmu...ba yanzu ba, kuma ba za ki mutu ki bar mu ba sama da shekaru masu yawa. Sai kin ga 'ya'yana da jikoki kamar yadda kika ga Amna kina shirin ganin aurenta da yardar Allah." Shiru ta yi masa, saboda kukan da ke taso mata a zuciya tana ƙoƙarin dannewa. Idonsa a kan fuskarta ya ce, "Ina son Nur Hajiyarmu, amma tun da ba kya son na je neman ta ba zan je ba, sai zuwa lokacin da kika amince mini." Gefen hannunta ta saka ta goge fuskarta sannan shi ma ta goge masa nasa hawayen tana cewa, "Ubangiji Ya yi maka albarka." Daga haka ya miƙe yana yi mata sallama, bayan faɗar amin a bakinsa ya fice gidan. Zuciyarsa cike da ƙuncin da bai san ina zai saka kansa ya ji sanyi ba. Hakan ya saka shi shawagi a saman tituna idan ya sauka wannan ya koma kan wancan. Ba tare da ya san ina ya nufa ba saboda kansa ya ƙulle ta yadda bai san abin da ya dace ya yi ba a lokacin. A ƙarshe tsayuwa ya yi a gefen titin wani junction, ya ɗora kansa saman sitiyari yana kukan zucin da babu hawaye ko sauti. 'Me ya sa Hajiya za ta yi mini iyaka da Nur?' Tambayar da ya yi wa kansa kenan wadda babu mai ba shi amsa. Ya jima a duƙen yana nazarin yadda zai shawo kan Hajiya ta fahimci abin da yake ji a cikin zuciyarsa. Saboda yana da tabbacin ko mutuwa ya yi ya dawo duniya ƙaunar Nur ba za ta bar zuciyarsa ta huta ba. Ajiyar zuciya ya sauke mai ƙarfi, sannan ya zare wayarsa da ke caji ya shiga danna wa Adamu abokinsa kira. Bayan barkwancin da suka fara ya katse shi da tambayar inda zai same shi, ya yi masa kwatance sannan suka yi sallama. Iska ya furzar mai zafi a jikinsa kafin ya buga motar ya sake hawa kan titin. Tafiya yake yi a hankali har ya isa Jami'ar Bayero University ya yi parking a harabar makarantar. Wuri ɗaya ya ƙura wa kallo, kamar mai nazari a kan mabambanta mutanen da ke ta shawagi. Amma ko kaɗan zuciyarsa ba ta wurin, asali ma ba ya hangen kowa face fuskar Nur da sautin maganganun Hajiya. Kiran da aka yi masa a waya ya saka shi kai kallonsa a kan fuskar wayar. Ganin wanda ya zo nema ne ya saka shi hanzarin ɗauka yana faɗin, "Kai nake jira." Daga haka bai sake cewa komai ba ya katse kiran, tare da bubbuga goshinsa yana hucin iska daga bakinsa. Buɗe motar Adamu ya yi yana 'yar dariya ya ce, "Ango ka sha ƙamshi, na Amina ba da kanka a sare.." Kallon da Jamal ya yi masa ya saka shi barin zancen ya koma murmushin yaƙe saboda fahimtar ba ya cikin yanayin mai daɗi. "Magana nake so mu yi mai muhimmanci, don haka ba na son abin da zai ƙara ɓata mini rai a banza, zancen ango ko wata Amina duka ka jingine shi a gefe mu yi abin da ya kawo ni." "Ok tom, me ke tafe da kai?" Adamu ya yi maganar cikin shiga nutsuwarsa. Nisawa Jamal ya fara yi mai ƙarfi sannan ya rungume hannuwansa a ƙirji ya ce, "Ina so na gama da Hajiya lafiya, amma ba zan iya yin abin da take so na yi ba. Wannan dalilin ya sa na taso ƙafa-ƙafa zuwa neman ka domin ka nemo mini mafita." Kallonsa kawai Adamu ya yi ba tare da ya ce da shi komai ba, hakan ya bai wa Jamal damar sake cewa, "A wannan lokacin da muke ciki ko mace aka yi wa auren dole idan ba ta so za a ga ta'addanci ballantana ni ina namiji a nemi saka ni zama da wadda ba na so. Sannan idan ma aka jingine matsalar gefe raba ni da Nur tamkar saka almakashi ne a datse mini igiyar da nake shanya farincikina. Ba na jin zan iya yi wa Hajiya biyayya a kan rabuwa da son Nur ko da na yi haƙurin zama da Amina. Shin ya zan yi Hajiya ta gano illar abin da take ƙoƙarin yi ba abu ba ne mai sauƙi?" Ya ƙare maganar cikin wata kalar murya mai ɗauke da yanayi mara daɗi tun a kan fuskarsa. "Hmmm!" Ajiyar zuciya Adamu ya yi kafin ya sake cewa, "Babu abin da zan faɗa illa na ce ka yi haƙuri, sannan ka nemi zaɓin Ubangiji maji roƙon bawansa n.." "Kalmar haƙuri ta yi kaɗan ta rarrashi zuciya Adamu. Don haka ban ji wannan ba, idan ba ka da wani abin faɗa sai haƙurin; to kawai mu bar zancen gabaɗaya." Murmushi Adamu ya yi sannan ya yi magana cikin nutsuwar da ya gayyato ya yafa wa jikinsa. Saboda shi kansa ba ya jin daɗin halin damuwar da abokin nasa yake ciki. Hakan ya sa yake roƙon Hajiyar a kan ta sassauta ƙiyayyar da take yi wa Nur duk da ya sani abin da ta aikata dole ne a ji haushin ta. "Lamarin iyaye ba abu ba ne na wasa, na sha sanar da kai Hajiya ba za ta so abin da zai ɓata maka rai da gayya ba. Saboda uwa ce, kuma irin wadda samun irin ta a wannan lokacin abu ne mai wahala. Ta ƙi aure tun tana da ƙurciya ta tsaya kai-da-fata a kanku duk don kada rayuwarku ta lalace. Me ya sa a yanzu ba za ka iya yi mata halacci ba? Ka ba ta dama a kan abin da take so sannan ka bi da addu'a in sha Allah komai zai warware cikin sauƙi. Don haka ka yi haƙuri ko ba ka son Amina ka karɓe ta a matsayin matarka, wataƙila alheri ce gare ka ba tare da ka sani ba." "Idan na karɓi Amina na yi ya ya da Nur?" "Lokaci zai sanar da kai makomarta a gaba. Don haka ka bar wa Allah komai shi zai yi maganin matsalolinka gabaɗaya." Adamu ya yi maganar cikin yanayin da ke tabbatar da yin amanna da duk abin da yake hasashe. Jamal ya yi shiru tsawon mintuna kafin ya ce, "Ni zan wuce, amma ban gama shawara a kan lamarin ba. Sannan zan yi cigiyar Nur ko a cikin gidana ba tare da na tsallake dokar Hajiya ba." "Allah Ya zaɓa abin da ya fi alheri." Adamu ya yi maganar tare da miƙa masa hannu suka yi musabaha kafin ya fice yana ƙara jaddada masa komai zai wuce idan an saka wa zuciya haƙuri. Kai-tsaye ya koma bakin aikinsa, kasancewarsa ɗaya daga cikin malaman Jami'ar kuma masu ruwa da tsaki a cikin makarantar. Jamal ya ja motarsa zuwa wani masallaci ya yi sallar Asr, sannan ya zarce wani gidan abinci, sai da ya yi ƙat sannan ya riƙo abin da yake buƙata ya nufo gida yamma sakaliya. Zuciyarsa a cunkushe saboda ya kasa nutsuwar da zai yarda da tsarin Hajiya. Misalin ƙarfe shida saura ya shiga gidansa, hannu kawai ya ɗaga wa maigadi sannan ya shige da ledodinsa a hannu. Minal ya gani tsaye a falon tana cika tana batsewa alamun jiran shigowarsa take yi. Amma ganin ta bai saka shi bi ta kanta ba ya nufi hanyar shigewa ɗakinsa. "Malam, wayata za ka ba ni." Ta yi maganar a sama saboda ta zo wuya a kan takaicin yadda ya saka ta zaman kaɗaici bayan zaman ƙuncin da take yi a gidansa. Bai nuna ya ji abin da ta faɗa ba, ballantana ya tsaya tankawa. Ɗakinsa ya shige da guntuwar sallama ya ajiye ledodin hannunsa ya faɗa toilet. A gurguje ya yi alwala ya fito babu shiri ya yi turus saboda ganin ta a tsakiyar ɗakin riƙe da ƙugu tana jijjigar jiki. Yi ya yi kamar bai gan ta ba ya zagaye ta yana mayar clips a hannun rigarsa. "Ka ba ni wayar akwai abin da zan yi." Ɗakin ya buɗe yana ƙoƙarin ficewa ba tare da ya bi ta kanta ba, caraf ta riƙe masa riga ta baya hawaye ya fara wanke mata fuska ta shiga rera kukan da ya saka shi daskarewa a wuri ɗaya, ya kasa gaba kuma ya kasa juyowa. "Duk girman ƙiyayyar da kake yi mini ba ta isa ba sai ka ƙara saka ni a damuwa? Mene ne laifina bayan ba ni ce na maƙalaww wa kaina zama da kai ba? Me ya sa ba za ka tausaya mini ba, bayan ka sani ni ma ina da wanda nake so.." Maganarta ta ƙarshe ba ƙaramin duka ta yi wa zuciyarsa ba. Hakan ya saka shi waigowa idonsa a kanta cike da wani irin sabon yanayin da ya shige shi a lokaci ɗaya ya yi magana cikin wata kalar murya. "A cikin gidana kike zancen kina da wanda kike so?" "E, kamar yadda kake son Nur haka ni ma nake son Aminu. Don haka babu adalci idan ka ce za ka hukunta ni a kan laifin da ni ma an yi mini, kuma zaman maneji nake yi da kai ba don ina sonka ba..." A hargitse Jamal ya sake jifar ta da wani kallon mamaki ya yi magana cikin raunin zuciya ya ce, "Ba kya so na?" "Babu ranar da zan iya son ka Jamal. Saboda ba ka cikin kalar mazan da na tsara wa kaina rayuwar aure da su." Murmushin takaici ya yi, kafin ya kalli kansa ya koma ƙare mata kallo sama da ƙasa ya ce, "Mace irin ki ba isa ta faɗar ba ta so na b.... don haka ko da wasa kika sake yi mini zancen wani a cikin gidana; wallahi sai na nuna miki ba iri na ake yi wa iskanci b.." "Gaskiyar kake so na daina faɗa ko son Aminu zan cire a zuciyata a cikin gidan nak..." Karaf ta ji saukar yatsunsa biyar a gefen fuskarta, yana huci ya shiga nuna ta da hannu idonsa a zare ya fara magana a birkice sannan cikin ɗaga muryar da ta ƙara saka ta jin tsoron sa ta fashe da wani sabon kuka. "Ba ki isa ki saka ni gaba kina faɗar abin da kika ga dama ba, kuma ba ki da matsayin da za ki yi mini abin da kike so! Ba Aminu ba ko sunan anta na ji kin sake faɗa a cikin gidana sai na zare harshenki na datsa shi gida biyu!" Yana ƙare maganar ya kai mata harbi da ƙafa kafin ya buɗe ƙofar ya fice daga ɗakin zuciyarsa tana tafasa. Tsabar takaicin rainin da take son kawo masa bayan ɗaurin talalar da Hajiya ta yi wa rayuwarsa a kanta. A hargitse ya yi sallar ya dawo gida bayan sallar Isha. Saboda har lokacin bai daina jin zafin kushen da ta yi masa a kan wani ƙaton banza ba. Kukanta da ya tarbe sa bayan dawowarsa ya ƙara dagula masa lissafi. Hakan ya saka shi zama falo ya yi kwanciyarsa ganin har lokacin tana cikin ɗakin nasa ba ta fito ba. Tv ya kunna aka yi dace MBC Action suna wrestling ya miƙa hankalinsa a kan kallon, amma zuciyarsa ba ta daina jin zogin abin da Minal ta yi masa ba. A gefe ɗaya kuma ba ya jin daɗin sauraron kukan da take yi, don gabaɗaya ta lalata masa kuzarin jiki. Tsawon awa ɗaya tana kukan kafin ta rarrashi kanta ta miƙe a ƙufule ta fito daga ɗakin. Kai-tsaye kitchen ta nufa saboda ta gama kaiwa maƙura a kan halin damuwar da take ciki. Wuƙa ta zaro sabuwa fil ta fito jikinta yana tsuma ta isa kansa ta tsaya. Idonsa a kanta Tv bai ɗauke kansa daga kallon ba, duk da ya ga wuƙar a hannunta amna hakan bai saka shi razana ko ya ji tsoron abin da take ƙoƙarin aikatawa ba. Haushin ko-in-kular da ya yi hakan ya ƙara rura wutar tashin hankalin da take ciki. Hannunsa ta damƙa tare da cusa masa wuƙar a ciki hawaye yana zarya a kan fuskarta ta ce, "Ba don na san hukuncin wanda ya kashe kansa ba, da tuni na kashe kaina na huta da zaman ƙaddarar da nake yi. Don haka ka taimake ni ka kashe ni kawai ka huta da gani na, zan fi farinciki da hakan fiye da abubuwan da kake yi min..." Ta durƙushe a gabansa tana wani irin gunjin kuka tamkar wadda aka lakaɗawa mugun duka. Ido ya bi ta da shi cikin wani yanayi mara misali, saboda jikinsa ya yi sanyi ƙalau kuma kukanta yana taɓa masa zuciya. Zumbur ya miƙe ganin tana ƙoƙarin karya masa zuciya ta ƙarfi, da wuƙar a hannunsa ya nufi kitchen ya kwashe duka sauran wuƙaƙen da ke nan. Zuciyarsa cike da tsoron tsautsayi ya sa ta kashe kanta ta jiƙa masa aiki ya koma masa sabo, don komai ya faɗa ba zai goge kansa daga zargi ba. Saboda ko Hajiya ba za ta yarda a kan ba shi ne ya kashe ta ba. Ɗakinsa ya shige ya datse ƙofa, sannan ya ɓoye wuƙaƙen sannan ya zauna yana furzar da iska daga bakinsa. Ya shiga tunanin yadda zai rabu da Minal cikin sauƙi ba tare da ya cutar da rayuwarta ba. Ya miƙe cikin sanyin jiki ya ɗauko wayarta a inda ya ajiye ta, tun bayan ɗaukar ta saboda binciken da yake so ya fara yi domin ya tabbatar akwai hannunta a cikin guduwar Nur ko babu. Kai-tsaye ya shiga binciken saƙonnin da ke cikin wayar, tun daga kan waɗanda take turawa har waɗanda ake turo mata. Jikinsa ya yi sanyi ƙalau ƙirjinsa ya hau bugawa, saboda cin karo da saƙon da ta tura wa Gwaggo salame a kan ta zo zai kashe ta. Hamdala ya yi ga Ubangiji a kan dabarar kwashe wuƙaƙen da ya yi, amma hakan bai saka shi nutsuwar zuciya ba, sai da ya ajiye wayar ya fito ya same ta a inda ya bar ta har lokacin ba ta daina kukan ba. Tsaye ya yi a kanta hannuwansa zube cikin aljihu ya yi gyaran murya sannan ya ce, "Ki tashi ki zauna za mu yi magana." Ga link; Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/ICmrsyihZBzLrpXfmM7DyQ Masarauta group ne ga masu tambayar a saka su group da masu buƙata su ma su yi joining. D. AUTA CE ✍️ [2/20, 22:02] Hadiza D. Auta: *FANSAR ƘAUNA!* *HADIZA D. AUTA* *AREWABOOKS: Princessdija.* FANSAR ƘAUNA FAN'S GROUP. Idan kun ji joining ku jira zan yi approving. Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/Edh59w1Jcgk799uIkP0CFa *LAMBA GOMA.* Tsawon minti biyu yana tsaye a kanta ba tare da ta motsa ba kuma bata daina kukan ba. Furzar da iska ya yi daga bakinsa ya gyara tsayuwarsa ya sake cewa, "Nace ki tashi zamuyi magana, saboda wannan kukan ba shi ne mafita ba, kuma nemo mafitar da kanmu shi ne abin da ya fi dacewa a wannan lokacin." Minal ta rage sautin kukanta, saboda sautin da ya yi amfani da shi wurin maganar ya yi nasarar shiga jikinta. Hakan ya sa ta tashi daga kifen da take ta zauna tana shassheka tare da ƙoƙarin goge hawayen da suka ɓata mata fuska. Ga idanuwanta sun yi jajir alamun duk wurin ranar da kuka ta yi shi. "Please! Ki daina kukan nan kuma Ki nutsu magana ce za mu yi mai muhimmanci." Sai sai da ya ba ta minti daya zuwa biyu ta saita kanta nutsuwarta ta dawo jikinta ta koma zuƙar majinar kuka. Sannan shi ma ya zauna a kan kujerar da ke fuskantar ta bayan ya rage muryar Tv ya yi gyaran murya ya ce, "Ina so ki faɗa mini gaskiya tsakaninki da Allah. A kan ba za ki ɓoye mini gaskiyar duk abin da zan tambaye ki ba, don ina son mu tattauna da kyau kuma mu shawo kan matsalar ni da ke." Ba ta ce masa komai ba, amma shirun da ta yi tana kallon yatsun hannunta hakan ya nuna tana jin sa, kuma a ranta ta saƙa za ta faɗa masa iya abin da ta sani. Amma saboda bai ji furucin bakinta ba hakan ya sa bai gamsu da shirun da tayi masa ba. Kai-tsaye ya sake jefa mata tambayar kamar yadda ya yi tun a farko. "Kin yi alƙawari za ki faɗa mini gaskiya?" Kai kawai ta ɗaga masa ba tare da ta yi magana ko ta ɗago kai ta kalle shi ba. Hakan ya ƙara masa ƙarfin amayar da abin da ke cikin bakinsa cikin ƙumaji da takaicin da ke cizon ransa. "Ke ce babbar ƙawar Nur idan aka cire Amna, kuma 'yar uwarta wadda na sani mafi kusanci da ita. Don haka kin fi kowa sanin wace ce Nur da yadda matsayina yake a wurin ta. Shin me ya sa ta gudu ta bar ni a daidai lokacin da na fi buƙatar ta? Kuma mene ne dalilin da ya sa ta haɗa aurena da ke bayan ta san ita kaɗai ce macen da na yi wa rayuwata tanadi?" Dam-dam ƙirjin Minal ya buga, ta yadda ba ta san mafarin zuwan wani sabon firgicin da ya farmaki zuciyarta ba. Saboda tambayoyinsa ba ƙaramin taɓa mata zuciya suka yi ba, kuma sun dagula mata duk wani lissafin da ke cikin kanta. Don ta sani komai za ta faɗa ba zai taɓa yarda a kan babu sa hannunta cikin abin da ya faru ba. Amma hakan bai hana ta yin magana cikin ƙarfin hali da jarumta ba. "Allah shi ne shaidata ko da kowa bai yarda da ni ba. Saboda ban san komai a kan abin da ya faru ba, yadda ka ji zancen a sama haka ni ma na ji. Kuma ban san me ta tsara ba sai bayan afkuwar abin da ya faru." Daga haka ta ja bakinta ta tsuke, saboda zuciyarta ta karye wani sabon hawaye mai zafi ya fara bin fuskarta. Hawayen da ya ƙara lalata wa Jamal sauran kuzarin da ke ransa. Saboda har zucinsa ba ya son ganin kukan da take yi. "Yanzu dai a taƙaice kina nufin ba ki san komai a kai ba?" Shiru ta yi masa don maganarsa ba ta buƙatar maimaicin amsa, a kan abin da ta riga ta yi wa rantsuwa. Kallo ya ƙura mata tsawon lokaci yana nazarin ta, don zuciyarsa ta yarda da ita a kan babu hannunta a cikin haɗin auren da guduwar da Nur ta yi. Kuma ya gano hakan tun a kalolin saƙonnnin da ya gani a cikin wayarta. Waɗanda take tura wa Nur ba tare da ta yi shawara da kowa ba, kuma ba ta san zai iya taɓa wayar ba ballantana ya gani ya goge tsatsar da zuciyarsa ta yi a kanta. Tana tura mata saƙonnin ne kawai a duk lokacin da ƙuncin zuciya ya hana ta sukuni. "Hmmm!" Ajiyar zuciyar da ya sauke kenan yana jingina bayansa jikin kujera, tare zamewa ya kwanta tsawon mintuna kansa a sama yana nazari. "Yanzu wane hukunci kika yanke wa zamanmu?" Ya jefo mata tambayar, wadda ta zo mata a ba zata ba tare da ta shirya wa zuwanta ba. Amma hakan bai hana ta dakiya cikin nuna ko in kula ba ta ce, "Komai a hannunka yake." "Kina nufin duk abin da na zartar hakan ya yi miki?" Ya yi maganar ƙirjinsa yana bugawa, saboda ko kaɗan ba ya son fushin Hajiya. Sannan kuma ba zai iya zaman aure da ita ba a bisa ra'ayin kansa. Ita ma ƙirjinta ya buga dam-dam, duk da auren ba ta tabbatar da ingancinsa ba, amma ko kaɗan furucinsa bai yi mata daɗi ba. "Ba zan so na ci gaba da cutar da ke a banza ba. Ki faɗa mini kawai ni duk abin da kike so zan bi shi ko da ba na ra'ayi." A nan ma shiru ta yi masa ƙirjinta yana bugawa, saboda tuno kalaman Innarmu. Waɗanda take yawan yi mata a duk lokacin da ta kira ta a waya. 'Duk kika kuskura kika kashe aurenki ba za ki taɓa samun mijin da ya kai Jamal ba. In don Aminu kike borin yanzu haka an yi masa baiko da wata. Kuma daga ranar da ki bari Jamal ya sake ki ki sauya uwa don ni ban haɗa komai da ke ba.' Furutan Innarmu kenan, waɗanda ke raba mata hankali gida biyu. Tana son yi mata biyayya kuma tana jin takaicin raba ta da Aminu da aka yi ta ƙarfin tsiya. "Ko kina da ra'ayin zama da ni mu ci gaba da zamanmu a yadda muke kai yanzu?" Ya dawo da ita daga duniyar nazarin da ya fahimci ta lula. Amma ban da dukan da ƙirjinta yake yi ba ta iya motsa ko ɗan yatsanta ballantana ta ba shi amsa. Hakan ya sa ta yi masa gum kamar ba ta ji me ya faɗa ba. Har sai da ya sake yin maganar da ta kasa haƙurin shanyewa ɗacin furutan, sai da ta furzar da abin da ke cikin bakinta. "Ga shi ke ba kya so na ballantana ki koya mini son ki na jaraba na gani, ko da zan iya ba ki kaso biyar a cikin goman son da nake yi wa Nur." "Ba na so!" Ta yi maganar a fusace fuskarta a cure, sannan ta miƙe a ƙufule da niyyar barin falon, don ta fahimci lamarinsa akwai kalolin rainin hankali a ciki. Caraf ta ji ya damƙo hannunta ta baya, ta yi hanzarin sandarewa wuri ɗaya ba tare da ta motsa ba. Saboda riƙon da ya yi mata ba ƙaramin jan ranta ya yi ba. Duk da ta so ƙwace hannunta amma ta bi umarnin zuciyarta ta kasa motsawa, sai bugun numfashinta da ya ƙara wa kansa gudu. Ɓil-ɓil zuciyarta ta shiga bugawa jikinta ya hau tsuma, yanayin da take ji ya saka ta ɗora hannu ɗayan a ka ta fashe da kuka iya ƙarfinta tana faɗin, "Wayyo ni kaina!" Zumbur ya tashi zaune bayan ya sake ta idonsa a kanta ya ce, "Me kuma na yi miki kike ƙoƙarin tara mini jama'a? Ko yau ɗin ma za ki jawo maigadi ya bubbuga mana ƙofa ne? To bari ki ji ni babu abin da zan sake nema daga gare ki. Jiyan ma tsustsayi ne da ban san dalilin da ya sa na yi abin da na yi ba. Amma in dai ni ne ki kwantar da hankalinki ko wane irin kallo ba zan sake yi miki ba a cikin gidan nan. Idan kika cire kallon Musulunci shi ma irin wanda shari'a ta tanadar. Ai hakan ya yi miki ko?" Ya ƙare maganar da wata kalar murya kamar wani sakarai. A ƙoƙarinsa na son kwantar mata da hankali take-yanke. Saboda tsoron ta cutar da kanta a banza ko kuma ta yi wa kanta wata illar da za ta jawo masa shiga komar tuhuma. Minal kam ita kaɗai ta san abin da take ji a ranta, hakan ya sa ta kasa daina kukan da take yi kuma ta ƙi barin wurin kamar yadda ta yi niyya a farko. Tsam ya miƙe yana sake roƙon ta yi haƙuri ta daina kukan, tun da ba ta son maganar da safe za su ƙarasa kafin ya fita wurin aiki tun da ta ƙi bari su kai matsayar zancen. Tana kuka ƙasa-ƙasa har ya gama kashe komai na wuta ya shiga ɗakinsa ya ɗauko wayarta ya ajiye gefenta, sannan ya koma ɗakinsa ya datse ƙofa zuciyarsa cike da damuwa. Jikinta yana tsuma ta buɗe wayar ta danna wa Gwaggo Salame kira. Ta yi ƙoƙarin saita kanta wurin magana amma hakan bai hana Gwaggon gano kukan da ta sha ba tun daga sallamarta. Ranta a ɓace ta yi magana tun kafin ta ji dalilin kiran da ta yi mata ta rufe ta da faɗa. Sai da ta tsagaita faɗan Minal ta yi magana cikin sanyin murya ta ce, "Gwaggo ya ba ni zaɓi a kan zamanm..." "Damuwar me za ki dinga yi Amina? Bayan Allah ya ba ki dama ki yi rawar gaban hantsi yadda kike so." "Idan na yi haka na ci amana Gwaggo." "Tun da har A'isha da kanta ta bar miki shi ya dace ki riƙe da kyau ta yadda ke ma zai so ki kamar yadda ya so t..." "Ta ya ya zai so ni Gwaggo? Bayan soyayyarta ta daskare masa zuciya." "Kina mace amma ki zauna namiji yana gasa miki aya a hannu Amina? To ki sauya takunki, kuma ki iya hannunki ta yadda zai yaba wa aya zaƙinta ke ma ya san darajarki." "A'a ba zan iya ba." Daga haka ta katse wayar, cike da zargin ko dai Gwaggon ta gano abin da ke damun zuciyarta. Ta jima a wurin zaune tana saƙawa da kwancewa, tare da zance daga ita sai kanta, inda zuciya ke nuna mata hanya amma tana ƙoƙarin kaucewa. Ta goge busassun hawayenta sannan ta miƙe ta yi nata ɗakin jiri yana ɗibar ta. Kuma cike da tunanin yadda za ta yi ta sanar da shi ba ta son ya sake ta za ta jira har ranar da Nur za ta dawo gare shi. Zuwa lokacin za ta goge duk wani laifinta a gun sa har ta dasa masa tausayin ta a ransa. Sannan kuma Innarmu za ta ji daɗi idan ta ga ta daina bore da ƙoƙarin guje wa zaman auren saboda son koma wa Aminu. Amma fahimtar wane ne Jamal da kalolin rainin hankalinsa ya sa ta ga gara yi masa shiru a kan ta sanar da shi ƙudurinta. Yayin da wata zuciyar ta ba ta shawarar kawai ta sanar da shi don ya san irin zaman da yake yi da ita. Ko don ya sassauta mata zaren wulaƙancin da yake ja ba tare da ya tausaya wa halin da take ciki ba. 'Idan abu ya dame ki, ki hana idonki bacci ki kai kukanki ga Allah. Saboda shi kaɗai ne wanda zai warware damuwarki cikin sauƙi.' Wata nasihar Gwaggo salame ta faɗo a ranta, hakan ya sa ta nufi toilet ta ɗoro arwala cike da kuzari ta shimfiɗa sallaya. Don ta gamsu da babu mai maganin abin da ke ranta da matsalarta face shi. Nafilar da Gwaggon ta koyar da ita ta fara yi kamar yadda ta yi mata bayani, tare da kai kukanta ga Allah a kan shi ya fi sanin abin da ya fi dacewa ga rayuwarta. Don haka ya zaɓa mata mafi alheri zama da Jamal ko barin gidansa. "Idan zama da shi ne alheri Ubangiji ka cusa masa so na ko zai dinga jin tausayi na." Addu'ar da ta dinga yi tana maimatawa kenan, har ta ci rabin dare sannan ta kwanta cike da tsammanin ganin sauyi a tattare da shi kamar yadda ita ma za ta sauya masa kalar nata takun. Duk ta sani za ta sha wuya kafin ta shawo kansa, saboda kafiyarsa da nacinsa a kan Nur da duk abin da ya shafe ta. Da wannan ƙudurin ta kwana cike da ɗokin safiya ta waye. Asubar farin ta tashi duk da ba ta gama biyan bashin barcin da take ci ba. Ta shiga gyaran ɗakinta har zuwa wardrobe ɗin kayanta da akwatunan Nur ta sauya musu mazauni. Sannan ta fito filo ta hau gyara duk da babu wani abin da ta ɗauke, kasancewar komai yana mazauninsa amma sai da ta ƙara wa komai saiti. Sannan ta jawo wayarta ta shiga YouTube binciken kalolin breakfast. Kitchen ta faɗa a gurguje ta shiga fere doya tare da farfasa tarugu tattasai da albasa, a gefe ɗaya kuma ta ɗora tukunyar dafa doyar bayan ta koma fere Irish cikin sauri. Cikin lokaci ƙalilan ta fara haɗa yam ball ta soya faka-faka. Sannan ta koma kan miyar ƙwan da za a ci da zallar farar doyar, wadda ta sha kayan haɗi sai ƙamshi ke tashi. Bayan ta soya wainar ƙwan hatta ruwan zafin tea sai da suka sha haɗin kayan ƙamshi. Sannan ta ɗebo komai ta jera a falo ta koma kitchen gyaran inda ta ɓata da wanke kayan da ta yi aiki da su. Zuciyarta cike da ƙaguwa a kan son ganin sa da irin yanayin da zai tarbi bajintarta. Duk da ta sani abu ne mawuyaci ya ci girkin, amma ta yi don kawai ta auna baiwarta kamar yadda Gwaggo Salame ta zaburar da ita. Harabar gidan ta fita, babu ɓata lokaci ta shiga wanke masa mota maigadi yana kallon ta ta gefen ido. A ransa yana jinjina ƙarfin hali irin Jamal saboda ganin yadda yake ƙoƙarin mayar da aure bauta. Ita kam ko a jikinta ta wanke motar tas ta goge masa, sannan ta koma sharar harabar gidan cike da ƙumaji ta tattara sharar, sai a lokacin maigadin ya ce ta bari shi zai kwashe sharar ya zubar. Tana ƙoƙarin komawa cikin gidan suka yi kiciɓis da juna a bakin falon yana ƙoƙarin fitowa cikin gidan. Don yana hangen ta ta sama a lokacin da take sharar tsakar gidan. Wannan dalilin ya saka shi fitowa daga ɗakinsa, saboda ƙamshin girkin da ya cika masa hanci ko kaɗan bai saka shi sha'awar fitowa ba. Sai dai ganin tana sharar ya ji tausayin ta ya tsirga masa a zuciya. Ya fito da niyyar hana ta amma ganin ta gabansa ya basar, raɓawa kawai ya yi ta gefenta ya wuce ba tare da ya ce da ita komai ba. Ita kuma ƙirjinta da ke bugawa tun a lokacin da suka yi ido biyu da juna bai daina ba har ta isa cikin ɗakinta, dafe da zuciyarta ta jingina bayanta jikin ƙofar ɗakin tare da rufe idanuwanta tana sauke ajiyar zuciya wata bayan wata. 'Me ke shirin faruwa da ni?' Tambayar da ta yi wa kanta kenan, tare da saka yatsun hannu ta yi watsi da ƙwallar da ta cika idonta tana ƙoƙarin gangarowa fuskarta. Wanka ta faɗa cikin kasala bayan zuciyarta da ke ta harbawa tana hasko mata fuskar Jamal da irin kallon da ya yi mata a lokacin da suka yi ido biyu. Uhum D. AUTA CE ✍️ [2/20, 22:02] Hadiza D. Auta: *FANSAR ƘAUNA!* *HADIZA D. AUTA* *AREWABOOKS: Princessdija.* FANSAR ƘAUNA FAN'S GROUP. Idan kun ji joining ku jira zan yi approving. Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/Edh59w1Jcgk799uIkP0CFa *LAMBA SHA ƊAYA.* A gurguje ta kammala wankan ta fito cikin yanayin mutuwar jiki. Tsawon minti biyar tana gaban madubi ba tare da ta yi abin da ya zaunar da ita ba. Jin motsin rufe ɗakinsa ya sa hankalinta ya dawo jikinta. Cikin sauri ta goga mai da turare tare da zumbula doguwar riga ta fito jikinta yana tsuma. Da sassarfa ta sauka ƙasa, gudu-gudu sauri-sauri ta fita harabar gidan cikin bugun zuciya. Saboda hango Jamal yana ƙoƙarin shiga motarsa alamun fita zai yi. Dole ta ja ta tsaya rungume da hannu tana kumbura fuska a ranta tana jin takaicin kanta a kan zaman da ta yi ɗaki ba tare da ta taya masa abin karin ba. Hango ta a tsayen a daidai lokacin yake ƙoƙarin fito da motar a mazauninta; murmushi kawai ya yi don zuciyarsa ta hasko masa sabon sauyin da ya wanzu gare ta, a tsakanin dare zuwa safiya. "Zan je restaurant, daga can na biya shago." Abin da ya faɗa kenan a lokacin da ya nufi bakin gate, ba tare da ya kai kallonsa gare ta ba. Saboda ba don ma ya ɗaga murya ba ba za ta yi tsammanin da ita yake maganar ba. Mamaki da tulin haushi suka dirar mata a ƙoƙon ranta, saboda ganin ta ɓata lokaci wurin haɗa masa abin kari amma ya yi kamar bai san ta yi ba. Bayan motarsa ta bi da kallo kamar ta bi shi ta roƙe shi don Allah ya dawo ya ci nata girkin. Gudun sammakonta ya tashi a iska, amma aikin gama ya gama don ya fice fit har maigadi ya kulle ƙofar gate. Sharr ta ji wani hawaye mai zafi yana bin fuskarta, a fusace ta juya tana danne kukan da yake ƙoƙarin zo mata, a haka ta isa falo ta faɗa kan kujera tana haki tamkar wadda ta sha gudu. Ta jima a wurin da tagumi hawaye yana zarya a kan fuskarta, bayan saƙe-saƙen tunani da kwancewar da take yi. Sannan ta miƙe cike da takaici ta zuba abin karin daidai cikinta, ta fito da sauran ta miƙa wa maigadi, bayan ta sauya kula. Saboda sai da ta tsaya ta darje sannan ta zaɓi kular da ta fi burge ta ta zuba wa Jamal abin karin. Da niyyar burge shi kuma don ya ji daɗi ya yaba wa gwanintarta. Sai ga shi ya lalata mata tsari, tare da ruguza sabon shirin da take ƙoƙarin shiryawa tun a tashin farko. Don sosai ta ci burin faranta masa ya gano amsar tambayarsa ba tare da ta furta ba. Bayan ta gama karin ta nufi ɗakinsa kanta a tsaye, zuciyarta cike da tunani kala-kala. Cikin zafin nama ta gyara masa ɗakin tsaf ta feshe ko'ina da turaren wuta. Misalin ƙarfe sha ɗaya na safe ta koma kitchen ta shiga haɗa masa girki, waton shinkafa da wake. Ɗaya daga cikin kalolin abincin da Hajiya ta sanar da ita yana so. Bayan man ƙuli da yaji har da miyar tarugu a gefe ɗaya ko da zai yi ra'ayin haɗawa. Wayarta ta lalubo ta shiga neman lambarsa, wadda Nur ta yi mata saving lambar da hannunta. A watarana da ta ari wayar Minal ta kira sa saboda tata wayar babu caji. 'Jaan.' Ta maimaita sunan a cikin zuciyarta kafin ta danna masa kira ƙirjinta yana bugawa fat-fat. Sai dai har ta gama ruri ba ta ji an ɗaga ba, babu ɓata lokaci ta sake danna wani sabon kira. Caraf ta ji an ɗaga kiran tare da yin magana a lokaci ɗaya. Nan take hawaya ya shiga bin fuskarta tsabar takaicin da ta ji. "Sorry, idan na dawo za mu ƙarasa maganar." Daga haka ya katse kiran, saboda tsammaninsa a kan maganar da suka fara ne ta neme shi. Ta jima sandare da wayar a hannu kafin tunanin tura masa saƙo ya faɗo ranta. Cikin ɗan lokaci ta rubuta masa ya turo yaro ya karɓi abincin da ta dafa masa. 'Ki jira zan dawo.' Tsaki ta ja tare da wurgar da wayar a gefenta tana faɗin, "Kayan haushi." Ganin amsar da ya mayar mata mai kama da an kwaɗa mata mari. Ɗaki ta nufa ta yi sallar Zuhur saboda a lokacin har biyu ta gota. Ta jima a wurin tana lazumi kafin ta naɗe sallayar ta koma falo zaman jiran sa. Zuciyarta cike da haushi da fargaban hukuncin da zai zartar a kan zamansu idan ya dawo. Jamal kam bai dawo gidan ba har aka yi sallar Isha, kuma da gangan ya ƙi dawowar ya yi zamansa a shagonsu. Hada-hadar saye da sayarwa ya saka shi rage jin kewar Nur da ke cikin zuciyarsa. A gefe ɗaya kuma ba ya son zamansa cikin gidan gudun su sake samun matsala da Minal ta nemi kashe kanta a banza. Sai da ya biya Restaurant ɗin da ya saba zuwa cin abinci, sannan ya je gidan Hajiya suka yi sai da safe ya nufo gidansa. Zuciyarsa a sake saboda tun bayan aurensa bai leƙa shagon ba. Aikinsa kuma yana cikin hutun da ya ɗauka da niyyar cin amarcinsa a kan kari. Minal kam zuwa lokacin ta gama cika tana batsewa, don duk ta wurga ido ta hango abincin da ta yi masa sai ta buga dogon tsaki. Wanka ma bayan na safe sai da ta sake wani saboda, ta kashe ɗaurin ɗankwali da baza turare a jiki amma har ta gaji da jira bai dawo ba. Hakan ya sa lokaci da ta ji shigowar motarsa gidan ba ta motsa daga inda take kwance tana kallo ba. Har ta ji takun hawansa saman ba ta yi niyyar tarbon sa ballantana ta nuna farincikin ganin sa. Illa dukan luguden uku-ukun da ƙirjinta ke yi tun lokacin da ta ji buɗe gate da shigowar motarsa. Da guntuwar sallama ya shigo falon waya a kunnensa yana magana har ya shige ɗakinsa. Jim kaɗan ya fito falon bayan ya gama wayar ya tsaya gabanta fuskarsa babu yabo babu fallasa ya shiga ƙare mata kallo. Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce, "Lafiyarki ƙalau kuwa?" Banza ta yi masa kamar ba ta ji ba, hakan ya sa ya leƙa fuskarta yana faɗin, "Ko barci ne kike y...?" Ganin idonta wuƙi-wuƙi tana muzurai ya yi hanzarin fashewa da dariya sannan ya zauna yana faɗin, "Ke kam wa ya taɓo ki bayan ke kaɗai ce a cikin gidan? Ko maigadi ya bar wani ya shigo gidan nan ban sani ba?" Tashi zaune ta yi, tare da wurga masa wani kallo sannan ta ce, "Babu komai" Ta miƙe da nufin barin falon ya dakatar da ita, ta hanyar faɗin, "Ina abincin da kika ce kin dafa mini? Saboda sai a lokacin ya tuno da saƙon da ta tura masa. Har a ranta ta ji daɗin maganarsa ganin ya fara damuwa da sabgoginta, saboda haka ba ta tsaya ɓata lokaci ba ta nufi kitchen ta jawo kwandon abincin da ta haɗa masa tun ƙarfe ɗaya na rana. Cikin ƙumaji ta shiga baje kayan abincin a gabansa, zuciyarta cike da jin daɗi ta fara buɗe kular shinkafa da waƙen. Bumm warin waken ya daki hancinta, bayan sandarewar da ya yi a cikin kular ya sauya ƙamshinsa daga wake zuwa warin tusa. Babu shiri ya toshe hancinsa bayan ya miƙe yana nuna kular da hannu ya ce, "Wannan shi ne abincin da kike so na ci? Cabɗijam! Allah Ya taimake ni ban da rabon wahala..ahhhh..." Ya fara yunƙurin amai da gudu ya nufi ɗakinsa ya banko ƙofar. Ya jima yana sauke ajiyar zuciya bayan feshe jikinsa da turaruka yana shinshina jikinsa don jin warin ya wuce ko ya maƙale ya biyo shi har cikin ɗakin. oda tana buɗe kular warin waken ya daki hancinta ta yi hanzarin kawar da kai gefe. Wata irin kafurar kunya ce ta dabaibaye Minal, saboda ita kanta ba za ta iya cin abincin ba. Tsabar takaici ta kinkimi kular ta fice harabar gidan jikinta yana rawa ta nufi maigadi tana faɗin, "Baba don Allah almajiri nake nema." Kallon mamaki ya yi mata, saboda sanin wace unguwa suke da irin mutanen da ke cikin ta. Maimakon ya ba ta amsa zura hannu kawai ya yi alamun ta ba shi kular. Girgiza kanta ta yi tana cewa, "Abincin ya lalace ba za ka iya ci b..." "Ke dai ba ni Hajiya, mu kashi ne kawai ya rage mana ci a tsawon zamanmu cikin duniya." Jiki babu kuzari ta miƙa masa kular cike da karsashi ta juya tana faɗin, "Bari na kawo maka miya ka saka." Jikinta yana rawa ta kai masa ta dawo feshe falon da turare ranta a jagule tana Allah wadai da waken da ya tozarta ta gaban Jamal. Bayan ta saita falon ta shiga bubbbga masa ƙofa zuciyarta a tsinke kuma cike tsoron wulaƙancin da zai tarbe ta da shi. Tsawon minti biyar tana buga ƙofar kafin ya buɗe fuskarsa a cure yana ƙoƙarin toshe hanci cike da tsammanin zai sake cin karo da warin waken. Ƙamshin da ya ji yana tashi a falon ya saka shi sakin fuskarsa riƙe da ƙofar ya zuba mata kallon tuhuma ba tare da ya ce komai ba. "Ka yi haƙuri, tun ƙarfe ɗaya na rana na gama abincin shi ya sa waken ya buga." Abin da ta faɗa ya sa ya bar jikin ƙofar ya raɓa ta gefenta ya nufi ɗaya daga cikin kujerun ya zauna yana faɗin, "Zo ki zauna mu kammala maganar da muka fara, saboda ba ba so kina wahalar da kanki a kaina daga yau." Jiki babu kuzari Minal ta nufi kujerar kusa da wadda yake kai ta zauna a ɗarare. Ƙirjinta yana bugawa ta shiga sauraron maganganunsa masu kama da ɗigar dalma a jiki. "Duba da yadda aka yi aurenmu da yadda zaman ya zo mana. Yana da kyau kowa ya san matsayinsa saboda gudun shiga haƙƙin juna. Don haka daga yau kada ki sake saka abinci da ni. Ki dafa iya cikinki ba sai kin ajiye mini ba...ke ko da ina gida ban ce ki dafa da ni ba. Saboda ina da inda nake cin abinci ba na son ɗora miki nauyin cikina." Shiru ya ratsa tsakani a lokacin da ya tsahirta da maganar sannan ya ɗora da cewa, "Kin amince za ki zauna da ni a matsayin abokin zama ba miji ba?" Minal ta wurga masa wani kallo cikin ƙunar zuciya sannan ta yi magana da sanyin murya ta ce, "Zan zauna da kai a bisa umarnin mahaifiyata. Sannan zan ci gaba da riƙon ka kamar yadda Nur ta ba ni ajiyar ka, har zuwa ranar da ta dawo gare ka." Sai da ya yi shiru yana nazarin ta kafin ya sake cewa, "Batu na gaba, tun da kin ji kin gani kina buƙatar mu ci gaba zaman da muke kai; to duk abin da ya biyo baya kada ki tuhume ni. Saboda ni ban shirya zaman aure da kowace mace ba. Kuma ina kan bakana kamar yadda na sha faɗa zan maimaita, da Nur kawai na tsara rayuwa da ita zan yi zaman aure. Amma tun da ƙaddara ta haɗa mu zama ni da ke ba zan bari mu cuci juna ba. Don haka daga yau ba zan sake shiga duk abin da ya shafe ki ba, ki yi rayuwarki ni ma zan yi tawa. Kada ki ga na ɗaga miki ƙafa tausayin ki kawai nake ji, amma idan ke kin zaɓi ci gaba da zaman a haka babu damuwa. Sai dai kafin nan zan ba ki dama ta ƙarshe don kafa shaidu, gobe idan Allah Ya kai mu zan kai ki gidanku a yi komai a gaban iyayenki." Zumbur ta miƙe zuciyarta tana harbawa ta shiga juyi a gabansa cike da jarumta ta ce, "Dube ni da kyau Jamal, daga halittar jikina har halayena babu abin ƙyama. Don haka ban ji haushi don ka nuna ban kai matsayin ka yi zaman aure da ni ba. Saboda haka na zaɓi bin umarnin mahaifiyata da riƙe amanar da Nur ta bar mini duk da zuciyata ba ta farinciki." Sheƙeƙe ya dinga ƙare mata kallo har ta gama tumbuɗin maganganun bakinta. Murmushin takaici ya yi kafin ya ce "Ki daina yaudarar kanki, ko da mazan duniya ke son ki ni ba kya cikin tsarin matan da nake so. Kuma zan dawo da sabgogina da nake yi tun kafin haɗuwa ta da Nur, alƙawarin da na yi mata kuma zan riƙe amma ba zan fasa yin abin da zai rage mini sha'awa ba tun da ta iya tafiyarta ta bar ni. Saboda haka duk abin da kika ga na yi a cikin gidan nan ido ne naki. idan kin gaji da irin zaman kawai ki sanar da Hajiyata, ita ce za ta sa na sauwaƙe miki a duk lokacin da kika buƙaci hakan." Akwai littafina DAKAN ƊAKA...na fara ɗora shi ArewaBooks. Kuma akwai complete book 1-2 1k ga mai buƙatar ya taɓo ni ta nan; 08022014771. D. AUTA CE ✍️ [2/20, 22:02] Hadiza D. Auta: *FANSAR ƘAUNA!* *HADIZA D. AUTA* *AREWABOOKS: Princessdija.* FANSAR ƘAUNA FAN'S GROUP. Idan kun ji joining ku jira zan yi approving. Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/Edh59w1Jcgk799uIkP0CFa *LAMBA SHA BIYU.* Wani ƙololon baƙinciki ya tokare mata a maƙoshi. Saboda maganganunsa ba ƙaramin ƙuna suke yi a zuciyarta ba. Amma da ta tuna ita da nata shirin, hakan ya sa ta yi murmushin takaici ta ce, "Har kullum ina yi wa Allah godiya da babu saka hannuna a cikin ɓatan Nur. Saboda haka idan ma ka ɗauki haƙƙina Ubangiji Yana kallo kuma ba zai bar ka ba." "Duk abin da za ki faɗa kina da damar hakan a yau kuma a yanzu. Amma ki sani daga gobe damarki ta wuce matuƙar kin amince da sharuɗɗaina." "Uhumm!" Iya abin da ta faɗa kenan tare da miƙewa zuwa ɗakinta. Kallo ya bi ta da shi cike da mamakin yadda ta zaɓi zama da shi duk da tarin ƙalubalen da za ta fuskanta. Jiki babu kuzari ya yi ɗakinsa zuciyarsa cike da kewar Nur da irin alƙawurran da ta ɗaukar masa idan sun yi aure. 'Me ya sa kika bar ni bayan kin san saboda ke na shiryu? Me ya sa za ki bar wa wata ni bayan kin sani ba zan so ta ba?' Zancen zucinsa kenan saboda gabaɗaya kewarta ta addabi ransa. Kwana ya yi yana juyi saboda sha'awar da ta yi masa mugun kamu. Duk da maganin da ya lalubo da ƙyar ya gan shi ya kora da ruwa yana rawar sanyi. Amma hakan Bai nutsar da shi ba har daren ya yi nisa, zuciyarsa sai hango masa Minal take yi amma yana ƙoƙarin kawar da kansa a matsayin haramtacciya gare shi. Don ya gama keɓe ta a cikin matan duniya waɗanda zai iya yin mu'amalar aure da su. Ɓangaren Minal kuma kwana ta yi a kan sallaya tana kai wa Allah kukanta. Ita ma ba ta yi wani barcin kirki ba sai Bayan sallar asuba nannauyan barci ya yi awon gaba da ita. Washegarin safiyar dukan su babu wanda ya tashi da wuri. Misalin karfe goma na safiya ta jiyo motsin buɗe ƙofarsa, a lokacin tana tsaka da shiri bayan ta tashi da ƙyar ta yi wanka. Don ranar ba ta yi tunanin yi masa gwaninta ba ballantana ta yi asubancin shiga kitchen. Saboda ita ma ba ta tashi da son cin komai ba, kasanacewar ta dafa indomie bayan Jamal ya shige barci, sai da ta ci ta yi ƙat a lokacin da yunwar dare ta hana ta sukuni, sannan ta runtsa. Motsinsa a falo da sautin Tv da ta ji hakan ya sa ta gano ba zai fita da wuri ba. Cikin sauri ta gama shirinta kamar yadda ta saba kowace safiya, tana tashin ƙamshi ta fito da niyyar yi masa ina kwana. Saboda ta ƙi bin umarnin wani sashen zuciyarta da ke gargaɗinta a kan kada ta je. Kanta tsaye ta nufi inda yake zaune yana kallo, ƙamshin girkin da yake yi yana dukan hancinta. Nan take wata sabuwar yunwa ta taso mata, tsayawa ta yi ɗan nesa da shi tana cewa, "Ina kwana?" Kamar ba zai ce komai ba tsawon sakonni, sannan ya cira kansa yana ƙare mata kallo sama da ƙasa ya watsar yana cewa, "Ke kam har zuwa yaushe za ki waye ne? Mace haka a tsaye babu wata lanƙwasa. Ko ke a naku gidan kalar gaisuwar taku kenan?" "Gaisuwar da ta dace da kai dai!" Ta amsa masa kai-tsaye tana ƙoƙarin barin wurin ba tare da wani jinkiri ba. Kansa ya shiga ɗagawa yana jinjinawa sannan ya sake cewa, "Ehhhh...kuma fa kin yi gaskiya. Da irin wannan gaisuwar na dace a wurin mata irin ki, waɗanda har duniya ta tashi ba za su taɓa wayewa b...kaico!" Sharrr hawaye ya fara bin fuskarta cikin hanzari ta shiga gogewa da bayan hannunta cikin muryar kuka ta ce, "Ban waye ba, kuma ba zan taɓa wayewa ba. A bar ni a yadda nake ai ba jinda na yi aka ba ka sadakata ba. Da rashin wayewar aka gano ni ce wadda na fi dacewa da zama da kai. Kuma a haka za ka zauna da bagidajiya kuna jera kafaɗa a wuri ɗaya." Wata mahaukaciyar dariya ce ta suɓuce masa babu shiri, kafin ya shiga nuna ta da hannu yana ƙumshe bakinsa alamun yi wa dariyar tasa waigi. Haushi ya sa ta bar wurin da gudu tana kuka, tsabar takaicin ganin ya gama raina ta, kuma ba ta san me za ta yi masa ya yaba ba. Jamal kam tsaf ya gama girkin ya cinye kayansa a cikin falon, da remote a hannunsa yana canza channel zuciyarsa wasai kamar ba ya jin tashin kukanta. Saboda ƙoƙarin ƙarfafa kansa da yake yi gudun faɗawa tarkon da aka yi masa a kanta. 'Mu je zuwa, don har yanzu ban gama yarda da ke ba, ba a banza kike son zama da ni ba. Ke ko ma mene ne zan gano abin da kike ɓoyewa kafin wanzuwar ƙudurinki a kaina.' Da wannan nazarín ya datse ƙofar tausayin ta a ransa. A gurguje ya yi wanka cikin shiga ta manyan kaya, har ya nufi hanyar fita ya dawo ya shiga ƙwanƙwasa mata ƙofa. Banza ta yi masa kamar ba ta san yana yi ba, sai da ya gaji don kansa ya murɗa hannun ƙofar ya shiga kansa tsaye yana ce wa, "Hajiya ki fito mu je ke nake jira." Ba ta motsa ba, hakan kuma bai sa ya sake maimaita maganar ba ya fice tare da ja mata ƙofar. Da sassarfa ya sauka ƙasa yana waya, fuskarsa a sake yake cewa, "Ki zama cikin shiri da na sauke wata zan zo na ɗauke ki..ok ..bye." Daga haka ya mayar da wayar aljihunsa cike da farinciki. Fuskarsa a sake suka gaisa da maigadi sannan ya nufi motarsa a ransa yana faɗin, 'Yau kam mota ba ta samu gatan jiya ba.' Ya yi wani kalar murmushi ya faɗa motar cikin karsashi ya shiga ba ta wuta yana horn wani bayan wani. Saboda ya matsu Minal ta yi saurin fitowa ya yi abin da yake hangen shi ne babbar makamarsa. Ita kam jikinta yana rawa ta danna wa Innarmu kira bayan fitarsa. Saboda tsoro da fargaban da take ciki a Kan tafiyar da yake so ta yi, kada Innarmu ta ce don ba ta son zaman ne ta yi abin da zai kawo ƙarshen aurensu da gayya. Bayan har zucinta ta ci burin zama da shi a bisa wasu ƙwararan dalilanta da take ganin su ne makaman da za ta yi yaƙin ƙwato 'yancinta. Aka yi sa'a kira ɗaya tana kusa ta ɗaga, saɓanin wasu lokutan da Innarmu take jefar da wayar ta yi ta sabgoginta, ko idan tana hannun ƙannenta suna buga game su saka ta flight mood don kada ma wani ya kira a kan uzurinsa ya katse musu game. "Innarmu kada ki ga laifina ya ce zai kawo ni gida a yi komai a gabank..." "Me za a yi gabanm...? Ke ki fita idona na rufe Amina! Shin Salame ba ta ce miki ki san dabarun da za ki jawo hankalinsa ba ne?" "Mun yi maganar." Amina ta amsa fuskarta a cure, saboda horn ɗin Jamal da maganganunta sun ƙara dagula mata zuciya. Musamman da Innarmu ta ce, "To ki ce masa kin amince za ki zauna ba sai kun zo gidan b.. " "Na faɗa masa fa wallahi...kin ma ji shi can yana ta horn Innarmu ni kawai yake jira na fito mu z..." "To ku zo ga ni ina jiran ku daga ke har shi ɗin...wallahi muddin auren nan ya mutu kada ki yi tsammanin Zan sake zama da ke a gabana! Mutuncinki ɗaya shi ne ki san yadda za ki yi da shi ki lallaɓa a bar batun nan kawai. Idan ba don ya gaji da halinki ba wane zaɓin zama ko rashinsa zai ba ki...to ki bari auren ya mutu ki dawo gidan ki ga yadda zan yi da ke." Ƙit ta kashe wayar, jiki babu kuzari Minal ta miƙe ranta yana ƙuna ta jawo jaka ta fara loda kayanta cikin fushi. Bayan jarumtar da ta ara ta yafa wa jikinta ta shiga jan jakar iya ƙarfinta har zuwa harabar gidan. A jigace ta isa bakin motarsa ta tsaya tana nishi fuskarta a cure. Ganin ta da jakar kayan ƙirjinsa ya buga dam- dam, saboda tuno kalaman Hajiya kai-tsaye suna shiga cikin kunnuwansa tamkar a lokacin take furta su. 'Ba za ka san darajar Amina ba sai ranar da ka yi gangancin rabuwa da ita. Kuma daga lokacin haukar da ke cikin kanka za ta sake ka ka gano ka cuci kanka.' "Ya Salam! Hajiya me ya sa kike ƙoƙarin Yi mini baƙin baki koyaushe?" Zancen da ya yi kenan dafe da kansa cike da takaici, tsaki ya buga mai ƙarfi sannan ya buɗe murfin motar ya fito ya fisgi jakar da ke gabanta ya wurga bayan boot cikin fushi, sannan ya zagaya yana faɗin, "Malama ki shigo mu je kin ɓata mini lokaci." Minal ta buɗe bayan motar za ta zauna ya yi hanzarin faɗin, "Ba ki isa na zamo direbanki ba! Idan har ba za ki zauna gaban ba ki fita na ba ki kudin adaidaita sahu mu haɗu can. Ƙauyanci kawai ke a komai sai an ci gyaranki..mitsss." Wani kallo ta yi masa na tsawon sakonni ba tare da ta ce komai ba, ta buɗe gaban ta shiga ta zauna cikin tsuke fuska. Sannan ta koma danne kukan da yake ƙoƙarin bayar da ita a gabansa. Don ta ci alwashin daina kuka a gabansa duk tsananin ƙuncin da ke ranta kuwa. A haka suka fice gidan, yayin da suka bar maigadi da tunanin rabuwa auren ne ya yi ko wata tafiya ce za su yi su dawo. Kowanensu fuska a cure har suka ci rabin tafiyar, kasanacewar akwai tazara a tsakanin Nasarawa da Jogana. Amma har suka isa babu wanda ya ce da wani uffan illa wayar da Jamal yake ta karɓawa lokaci bayan lokaci. Dam-dam ƙirjin Minal ya shiga bugawa a lokacin da motar ta tsaya bakin lugun gidansu. Tana ƙoƙarin buɗewa ta fice ya yi hanzarin riƙo hannunta yana cewa, "Ko da wasa kada ki nuna akwai wata matsala a tsakanina da ke, idan ma kin faɗa ni ban san komai ba kuma babu ni a cikin masu shaidu. Yanzu gaishe su muka zo yi zuwa daré zan dawo na ɗauke ki mu koma gida, tun da kin amince za ki iya zama da ni a kowane hali." 'Innalillahi! Wai wannan wane irin mutum ne shi?' 'Ni mutum ne kamar sauran mutane aminiyar matata. Kuma na san darajar mahaifiyata kamar yadda kike ƙoƙarin yi wa taki biyayya." Ya ba ta amsa kai-tsaye tamkar ya shiga zuciyarta ya ji abin da take faɗa. Sai dai kallon da take yi masa ya nuna zahirin ƙullewar kan da maganganunsa suka yi mata. Hannunta da ya riƙe gam ta kalla, inda ta yi maganar ido a kan ya taimaka ya sake ta. "Babu abin da zan ji ko da na kwana da ke a jikina ballantana riƙe hannu. Don haka ki je ki sanar da su zan shigo mu gaisa sauri nake yi akwai abin da zan yi." Sororo Minal ta yi ta kasa motsawa, tsabar ya gama kai ta maƙura ta yadda ba za ta iya fassara manufar abin da yake nufi da ƙoƙarin aikatawa ba. Tana yunƙurin fita ƙannenta da yaran unguwar, suka baibaye da motar. Yayin da wasu suka biyo su tun shigowarsu cikin layin har suka tsaya bakin gidan. Tsalle suka fari yi suna ihu saboda ganin Minal tare da faɗin sunanta suna yi mata oyoyo. Tsaki mai ƙarfi Jamal ya ja a daidai lokacin da ya hango yaran sun yi wa motarsa dafifi, har da masu shafa jikin motar suna leƙen sa. Kasanacewar tintac ya sa ba su gano ita ce cikin motar ba har sai da ta fito suka gan ta. Da murmushin yaƙe ta tarbi yaran tare da kiran sunayensu tana amsa gaisuwar da suke yi mata ɗaya bayan ɗaya. A haka ta shige gidan suka bi bayanta ɗiii har da masu tirereniyar shan gabanta da niyyar su riga ta shigewa. Innarmu riƙe da buta a hannu tun lokacin da ta ji ihun yaran suna oyoyo, tare da kiran sunan Aminar. A gurguje ta fito bayin kuma ta kasa ajiye butar har ta yi ido biyu da Amina. Saboda dukan da ƙirjinta yake yi tsabar fargaba da tashin hankalin da take ciki tun bayan wayarta da Amina. Hakan ya jawo cikinta ya dinga murɗawa tana faɗa bayi cikin gaggawa a duk lokacin da ta tuna suna kan hanyar zuwa gidan. Saboda ba ta san da wace Jamal ɗin ya zo ba. Sai dai kallo ɗaya da ta yi wa Amina ta ji sanyi ya ratsa zuciyarta. Ganin sauyin da ta yi a cikin 'yan kwanaki, fatarta ta sauya saboda zama wuri ɗaya, kuma alamun hutu da jin daɗi ya fara kama jikinta. Amma ko kaɗan ramar da ta ga ta yi ba ta tayar mata da hankali ba, ta ɗora hakan a kan fitinarta ce da rashin danganar da ta ɗora wa kanta. "Innarmu ina Babanmu?" Maganar da Minal ta tare ta da ita kenan, wadda ta dawo da ita daga duniyar nazarín da ta afka. "Ke ma kin sani a daidai wannan lokacin ba za a tarar da shi a gida b..." "To, ki saka hijabinki ya ce a faɗa zai shigo." SANARWAR! INA NEMAN MUTUM 20 MASU SAYEN lLITTAFIN DAKAN ƊAKA.. COMPLETE BOOK 1-2 PRIZE 1K GA MAI BUƘATA YA TAƁA NI TA NAN; 08022014771 ZAN SAKE SHI A RANAR 3 GA WATAN FEBRUARY. D. AUTA CE ✍️ [2/20, 22:02] Hadiza D. Auta: *FANSAR ƘAUNA!* *HADIZA D. AUTA* *AREWABOOKS: Princessdija.* Follow this link to join my WhatsApp community: https://chat.whatsapp.com/I6nbHRDfqd05VKHdFpnfeB *Assalamu alaikum* *Na ce kuna neman inda za ku saya wa yaranku da kuma kanku kaya cikin sauƙi?* *Shin kina neman kayan kitchen da bedsheet masu quality da sauƙi?* *Tom ki shigo ki gane wa idonki idan price ɗin bai yi miki ba ki fece. Shaharariyar 'yar kasuwa; Rukayya Musa Mahmud. Business name; Maman Suhaila. Dealers of all kind of kids clothes. Kitchen Ware's. Necklace. Bedsheet. Shoes and bags.* *Muna Kano Muna tura kaya ko'ina a cikin aminci da kula da amanar kayanku.* *LAMBA SHA UKU.* Wani kallo Innarmu ta yi mata kafin ta juya, jiki babu kuzari ta jawo hijabi ta saka tare da ɗauko tabarma ta shimfiɗa. Sannan ta nemo 'yar tsugunno ta dasa a bakin ɗakinta, waton nesa tabarmar. Minal kam tsaye kawai take rike da igiyar shanya a tsakar gidan nasu, kanta a ƙasa tana zana haruffan sunanta da takalmin ƙafarta. "To hamshakiya mandiya, ga ni na na shirya har na shamfiɗa masa tabarma, kice ya shigo na ji da wace ya zo." Zancen Innarmu kenan tana ɗage kai tare da aika mata hararar gefen ido. Minal ta saki igiyar shanyar ta nufi hanyar fita gidan ƙirjinta yana bugawa. Cike da mamaki ta bi motarsa da kallo, saboda ganin har lokacin bai fito ba. Tsaye ta yi bakin gidan tana aika wa motarsa harara tsawon minti biyu, kafin ta isa jikin motar ranta a ɓace ta fara ƙwanƙwasawa. Duk da ta sani yana sane da ita kuma tana da tabbacin ya gan ta sarai ta gilashi. Zuge gilashin ya yi tare da aika mata wani kalar kallo ya yi guntun tsaki. Sannan ya mayar da gilashin ya ɓalle murfin ya fito yana aika katsa wa wasu yara tsawa tare da aika musu daƙuwa. Saboda dukan bayan motar ɗaya yake yi da bulala, yayin da wani yake dafe da boot yana leƙen ƙasan motar. Kiran sunansu Minal ta yi tare da faɗin su bar wurin, saboda ranta ya yi babu daɗi. Duba da halin Jamal tare da halin yaran ba za a jitu ba. Don tun da suka shigo layin da yaran suka biyo su da gudu yake ta tsaki. Bai yi magana ba amma alamu ya nuna jin haushinsa ƙarara a kan abin da yaran unguwar suke yi masa. Shigewarsa kawai ya yi ya bar ta tana yi wa yaran faɗa. Saboda ya ƙagu ya yi abin da ya kawo shi ya tafi sabgogin gabansa. Tun daga sallamarsa Innarmu ta fara rawar jiki da ganin sa, hakan ya sa ta shiga gaishe shi bayan sannu da zuwan da yi masa baki washe. Ba tare da ta jira shi ya fara gaishe ta ba a matsayinsa na suruki. Minal ta yi kasaƙe a ɗaki ranta a ɓace zuciyarta cike da jin haushin rawar jikin da Innarmu take yi a kansa. Shiru kawai ta yi tana sauraron su har suka gama gaisawa kafin kafin Jamal ya fara magana. "Da ma na zo ne na gaishe su ku, amna na ga kamar Baban ba ya gida." "E, ya fita kasuwa tun da safe. Amma idan ya zo za a sanar da shi zuwanka." Jamal ya sunkuye kai yana faɗin, "Babu damuwa, sai a gaishe shi kafin na dawo a lokacin da zan same shi." Daga haka ya ja bakinsa ya tsuke yayin da yake mutsu-mutsun fito da kuɗi aljihunsa. 'yan dubu sababbi kar ya ajiye mata a gabanta yana faɗin, "Wannan naki ne, a yi haƙuri babu yawa." Sannan ya mayar da hannun yana ƙoƙarin lissafo wasu suka ji sallamar Baban Amina. Dukan su suka amsa a tare, yayin da Amina ta fito daga ɗakin cike da jin daɗin ganin sa tana gaishe shi. Baki har kunne ya amsa mata, sannan ya nufi inda Jamal yake zaune ya miƙa masa hannu suka gaisa cikin mutumta juna. Da murmushi ɗauke a fuskarsa ya ce, "Kun zo ganin mu ashe?" "Mun zo Baba. Fatar mun same ku lafiya" Jamal ya amsa cikin ladabi. "To madalla, dukan mu Alhamdulillah! Ya wajen Hajiyar ita ma?" Jamal ya sake amsawa cikin sakin fuska ya ce, "Tana gaishe ku Baba." "Muna amsawa, Ubangiji Ya yi albarka." Daga haka shiru ya ratsa, yayin da Jamal ya miƙe yana ƙoƙarin saka takalminsa Baban ya ce, "A dai ƙara haƙuri, in sha Allahu alƙawarin da na yi maka yana nan matuƙar A'isha ta dawo gare mu. Don haka kada ka ji komai da sannu Allah zai kawo mana mafitar da za ta warware matsalolin gabaɗaya." "Babu damuwa Baba. Ubangiji Ya bayyana ta cikin gaggawa." 'Ba Amin ba wallahi.' Zancen zucin Innarmu kenan a lokacin da Baba ya dire nasa zancen. Amma daga Minal har Jamal sun karɓa da 'Amin.' Don dukan luguden da ƙirjin Minal yake yi bai hana ta saurin amsawa ba. Kai-tsaye wani sashe na zuciyarta ta ji ina ma Nur ba ta tafin ba, wataƙila da halin da take ciki ba zai riske ta ba, ballantana ta ci karo da abin da zamo mata barazana a gaba. "Ke Amina! Me kike jira da ba za ki bi shi ku koma ba?" Innarmu ta yi maganar tana zare mata idanuwa. Ganin Jamal yana ƙoƙarin fita Amina kuma tana ƙoƙarin komawa cikin ɗakinta. "Ta zauna, sai dare zan dawo na ɗauke ta." Jamal ya yi maganar cikin sauri saboda bai shirya komawa da ita a lokacin ba. Innarmu ta yi saurin washe baki tana faɗin, "To ai shikenan. Tun da ka bar ta yi mana wunin. Amma da ba ka bar ta ba; ƙafa da ƙafa za ka koma da ita." Yana murmushi ya yi gaba, Baba ya raka shi har ƙofar gida yana saka masa albarka. Yayin da suka bar Innarmu dafe da ƙirji saboda ƙaƙƙarfan bugun da yake yi mata babu ƙaƙƙautawa. Sosai hankalinta ya tashi da jin wata sabuwar magana daga bakinsu, wadda ba ta san da ita ba. Tsabar ruɗewa kuɗin da ya ba ta ma a nan ta bar su. Jikinta yana rawa ta isa bayan ƙyauren gidan a sukwane. Sai da ta sha jinin jikinta sannan ta shiga leƙen su ta wata kusufa, tana hangen duk abin da yake faruwa daga inda take. Sai dai ko kaɗan ba ta jin me suke tattaunawa a kau. Har suka gama magana Jamal ya fito da kuɗi daga aljihunsa, kamar yadda ya ba ta shi ma haka ya miƙa masa. Cike da jin nauyi Baban ya ƙi karɓar kuɗin sai da ƙyar Jamal ya ci kansa ya karɓa yana godiya, sannan ya ƙara saka masa wata sabuwar albarka bayan addu'ar gamawa da duniya lafiya. Sai da ya tayar da motarsa ya tafi bayan sun yi sallama, sannan Baban ya koma cikin gidan a daidai lokacin da Innarmu ta isa bakin ƙofar ɗakinta, inda ta fara haɗa kan kuɗin bayan ta bar jikin ƙyauren cikin sauri gudun ya kama ta. Don sun saba, a duk ranar da ya gan ta tana leƙen wa'azin yake zuba mata, sai ta gaji da sauraro ta biye shi sun koma yin faɗa. Yana ƙoƙarin shigewa ɗakinsa, da niyyar ɗaukar abin da ya dawo da shi gidan. Innarmu ta biyo shi baya tana cewa, "Ni kam Malam wai wane irin alƙawari ne ka yi wa mijin Amina ban sani ba?" Juyowa ya yi yana kallon ta kamar ba zai ce komai ba, amma sanin wace ce ita ya yi magana fuskarsa a cure ya ce, "Ina ruwanki." "Uhum, ko ma dai mene ne ai ya kamata na sani Malam. Saboda ko an dafa a ɓoye ai ba za a ci ɓoye ba. Don yana da kyau a ce duk wani abu da ke faruwa ka sanar da ni. Idan dai har abin nan ya shafi Amina." Murmushin takaici ya yi kafin ya ce, "Idan kuma bai shafe ta ba fa? Shi ma dole sai kin sani?" Sum-sum ta bar wurin tana cewa, "Allah Ya ba ka haƙuri, ai da ma can na sani ba ka ɗauke ni a bakin komai ba." "Ke dai kika sani." Ya yi maganar yana ci gaba da abin da yake yi, sai da ya gama sannan ya rufe ɗakinsa yana ƙwala wa Amina kira. Cikin sauri ta fito ta durƙusa gabansa tana faɗin, "Ga ni Baba." Tsayuwarsa ya gyara, sannan ya dafa bango ya yi jim na ɗan lokaci kafin ya ce, "Na so na je har gidanki na yi wasu maganganu da ke. Amma na ƙyale ganin Salame ma ta isa ba sai na je ba. Don haka kafin na ce komai zan ce ki ji tsoron Allah, kuma ki sani aure ba wasar yara ba ne. Kada ki yi duba da yadda auren ya zo ki ce za ki yi wa sunnar Ma'aiki riƙon sakainar kashi. Miji miji ne kuma wajibi ne girmama babba ko da a gidan mashaya ne, ballantana tsakanin mata da mijinta. Saboda haka ki riƙe aurenki tsakani da Allah kuma ki riƙe mijinki za ki ga ribar hakan a gaba. Amma ki sani ban ce ki shiga rayuwarsa da bin diddigi ba kamar yadda kika ga Binta tana yi ba. Saboda kowane namiji da kalar halinsa, idan ita tana yi mini ina ƙyalewa shi ba lalle ne ya ƙyale ki ba idan kika kwashi halinta. Don haka shawara ce na ba ki, amma ban ce dole sai kin bi b..." "Haba Malam! Yanzu shikenan idan ka tashi yi wa 'ya'yanka faɗa ko nasiha ba za ka naɗe tabarmarka salun alun ba har sai ka saka ni zama bis...?" Innarmu ta yi maganar ranta a ɓace kafin ya katse ta. Saboda tun da ya fara maganganun ta saka wa zuciyarta sai sun yi faɗa, don dole sai ya sako laifinta ko kuma ƙarara ya nuna takaicinsa a kan wani halinta a fakaice. "Nononki da ta sha nake tsoron ya yi aiki a gidan aurenta. Don muddin ta biye wasu halayen da kike gwadawa a cikin gidan nan; ba lalle ne halin ya bar ta zama gidan mijinta lafiya ba. Saboda kin fi kowa sanin yadda aka yi auren, kuma an yi sa'a yaron ya san darajar manya. Ya kamata a ce ita ma an zaunar da ita an faɗa mata darajar aure ta wuce sanin da ta yi masa." Ya tsahirta da magana, su ma suka yi shiru babu wanda ya iya cewa uffan. Saboda Innarmu ruwa ya ci kai, duk da ta gaji da abin da faɗan da yake yi mata a gaban 'ya'yanta. Shi ya sa sau da yawa tana son gyara wasu abubuwan amma hakan ba zai hana ta sake kwatawa ba. "Yanzu dai ka yi haƙuri, in dai don na yi tambaya a kan maganar da kuka yi ne; Allah Ya huci zuciyarka. In sha Allah daga yau ba zan sake tayar da zancen ba. Amina kuma ina fatar ta yi zaman aure managarci wanda za ta samu aminci tsakaninta da mijinta, ba irin zamana da kai ba. Tun da har yanzu ban wuce cin fuska da gugar zana a wurin ka ba." Nufar hanyar fita ya yi ba tare da ya ce mata komai ba. Saboda ya jima da sanin daɗin bakinta, kuma in da sabo ya saba da halinta. Ta iya yin laifi kuma ta koma yi masa dabaibayi da maganganun da komai yake son ɗaurkar mataki a kai sai ya sassauta. Illa maganar da ya yi wadda ke nuna da Amina yake yi. Inda ya juyo yana faɗin, "Tashi ki je, Allah Ya yi miki albarka." Daga haka ya fice ya bar su jugum kuma tsaye cirko-cirko a tsakar gidan. Innarmu ce ta kawar da shirun da cewa, "Ni fa wallahi sai dai Malam ya ga laifina, amma ba na fatar A'isha ta dawo garin nan ta zauna da mu kamar baya. Saboda muddin ta dawo ba za ki taɓa samun nutsuwar da za ki samu lada a gidan mijinki ba. Sai inda ƙarfina ya ƙare a kan haka, don ba zan taɓa bari ki zamo bora ba. Wahalar da nake sha a gidan nawa mijin ta isa, ke kam daɗi za ki ji da yardar Allah." Fuska a cure Amina ta ce, "Innarmu..." "Yi mini shiru Amina. Ba fa zan zuba ido a saka mu kunya biyu ba. Kina kallo babu kalar surutun da ba a yi mini ba a kan auren nan naki. Amma duk na shanye zagi da ƙazafin da ake yi mini saboda farincikin kin samu gidan hutawa. To a kan me zan zuba ido A'isha ta dawo rayuwar mijinki ki koma bora? Wallahi ba zai yiwu ba, sai dai a yi duk abin da za a yi amma zama daram ke da shi sai mutuwa. Duk wani ɗan baƙinciki sai dai ya mutu...ke ko ke kika kawo mini gangancin da auren nan ya lalace wallahi sai na ɗauki mataki kanki. Shi ma ina ɗaga masa ƙafa ne saboda a zauna lafiya amma ba wai don ina jin tsoron sa b..." "Don Allah Innarmu ki yi shiru haka nan. Ba na jin daɗin yadda kike sako Babanmu a maganar nan, saboda shi ma yana so na zauna inda hankalina zai kwanta. Ni ma kuma na yi alƙawarin zama da shi komai tsanani sai inda ƙarfina ya ƙare. To me ya rage kuma Innarmu?" Nan take murmushi ya bayyana a kan fuskar Innarmu tana cewa, "Da kin taimaki kanki. Amma muddin kika tsaya kallon ruwa kwaɗo zai yi miki ƙafa. Sannan ko ma wane alƙawarin ne sai na gano shi, don ba zan zuba ido hannun agogo ya dawo mana baya ba..a kan me..ba zai yiwu ba...da sake." Haka Innarmu ta ci gaba da mitar maganar har ƙannen Minal suka dawo makaranta. A nan suka baje ana ta hirar yaushe gamo da bai wa juna labarin abubuwan da suka faru. A nan Minal ta ji labarin an hana kowa zuwa gidanta har ƙannenta. Saboda surutu da gulmar auren da ake ta yi a cikin unguwa da danginsu. Inda aka ɗauki laifin kacokam aka ɗora wa Innarmu, sannan ita ma aka ce ta ci amanar Nur tun da ta ƙwace mata saurayi. Ɓatan Nur ma cewa aka yi Innarmu ce ta yi mata kurciya saboda ta yi nisa da inda aka san ta. Surutai kala-kala kuma duk sun dawo wa Innarmu har shi Babban. Amma kasancewar sun san yadda aka yi auren ko kaɗan hakan bai tayar musu da hankali ba. Hakan ya sa Innarmu ta sha ɗamarar babu wata mace a gidan Jamal sai Amina. Shi ya sa har dare ya yi tana ta maimaita mata zance ɗaya, "Kada ki kuskura ki yi abin da kika ga ina yi a cikin gidan nan. Ni ma wani lokaci ba don ina so ba nake yi. Don haka ki bi Allah ki bi aurenki. Sirrin mijinki ki rufe kuma babu ke babu kai ƙarar sa. Idan ma ya cuce ki ki bar shi da Allah shi ne zai saka miki." Da ire-iren waɗannan nasihohin ta cinye wunin. Don Innarmu ta hana ta zuwa gidan kowa a cikin unguwar har maƙota. Saboda saɓanin da ya faru a kan gutsiri-tsomar da ke shiga suna fita a tsakanin mutanen unguwar tasu. Hakan ya sa ta bushe fitilarta a kan duk uban da ya haɗa auren ya raba idan ya isa. Amma har ƙarfe takwas na dare Jamal bai zo ɗaukar ta ba. Innarmu ta matsa ta kira shi a waya ta ce masa shi take jira. Ba don ta so ba, haka ta ɗaga wayar ta kira shi, amma har ta tsinke bai ɗaga ba. Mintuna a tsakani sai ga saƙonsa ya shigo a kan ta nemi adaidaita sahu ta koma bai gama abin da yake yi ba. Har ta fara surutan ɓacin rai a kan ba za ta koma ba a nan za ta kwana, Innarmu ta tusa ƙeyarta gaba har zuwa bakin titi. Da kanta ta taro mata abin hawa ta shiga, bayan ta biya ta sake yi mata gargaɗi da jan kunne a kan ta riƙe aurenta hannu biyu. Haka suka rabu ƙannenta suna ɗaga mata hannu har suka miƙa titi. Tafiya ɗoɗar suka yi kafin su isa unguwar misalin ƙarfe tara saura minti shida na dare. Da kwatance har adaidatan ya kai ta ƙofar gidan, bayan ta fito jiki babu kuzari ta nufi bakin gate ɗin tana ƙwanƙwasa ƙaramar ƙofar. Maigadi ya buɗe mata bayan ya gama yade fuskarta tas da fitilarsa mai mugun haske. Cike da mamaki ya yi hanzarin faɗin, "Hajiya da ma ba ki dawo gidan ba ashe?" Dariyar yaƙe kawai ta yi masa, a lokacin da ya saki ƙofar ta shiga ta hango motar Jamal a mazauninta. Alamun yana cikin gidan, kuma ya dawo amma ya kasa biyawa ya ɗauko ta. Zuciyarta a cunkushe ta nufi hanyar shiga cikin gidan tana ƙara danne ɓacin ranta saboda tuno nasihohin da ta sha, wuni zungur ana yi mata bitar haƙuri da biyayyar aure. A kan haka ta saki ranta har ta haye sama ta tura ƙofar shiga falon cike da karsashi. Dam-dam! Sautin bugun ƙirjinta kenan a lokacin da ta yi ido biyu da Jamal kwance saman kujera, ya yi matashin kai da cinyar wata mace suna kallo tamkar miji da mata. Hankalinsu a kwance sai dariya suke yi alamun suna jin daɗin yanayin. SANARWAR! INA NEMAN MUTUM MASU SAYEN lLITTAFIN DAKAN ƊAKA.. COMPLETE BOOK 1-2 PRIZE 1K GA MAI BUƘATA YA TAƁA NI TA NAN; 08022014771 ZAN SAKE SHI A RANAR 3 GA WATAN FEBRUARY. LABARI NE MAI ƊAUKE DA RIKICI, HARGITSI, TASHIN HANKALIN DA RIKITA-RIKITA BAYAN ZALLAR TSAGWARON SOYAYYA. D. AUTA CE ✍️ [2/20, 22:02] Hadiza D. Auta: *FANSAR ƘAUNA!* *HADIZA D. AUTA* *AREWABOOKS: Princessdija.* https://chat.whatsapp.com/Dsn5IB2qqtYAG3EDJ04sce *Assalamu alaikum* *Na ce kuna neman inda za ku saya wa yaranku da kuma kanku kaya cikin sauƙi?* *Shin kina neman kayan kitchen da bedsheet masu quality da sauƙi?* *Tom ki shigo ki gane wa idonki idan price ɗin bai yi miki ba ki fece. Shaharariyar 'yar kasuwa; Rukayya Musa Mahmud. Business name; Maman Suhaila. Dealers of all kind of kids clothes. Kitchen Ware's. Necklace. Bedsheet. Shoes and bags.* *Muna Kano Muna tura kaya ko'ina a cikin aminci da kula da amanar kayanku.* *LAMBA SHA HUƊU.* Tsaye ta yi tsawon sakonni tana ƙare musu kallo, zuciyarsa ɗauke da kalmar Innalillahi wa inna ilaihirraji'un. Kafin ta cira ƙafafuwa babu kuzari ta fara taku gumi yana tartsatso mata a jiki. A haka ta isa tsakiyar falon daidai ta gabansu ta ja ta tsaya idonta a kansu, zuciya ta shiga nuna mata ta cakumo macen ta rufe ta da duka kawai. Yayin da wata zuciyar ke yi mata kashedin babu ruwanki gidansa ne kuma shi ya kawo ta. Zumbur macen ta yi ganin Minal tsaye a gabansu cikin tsoro ta kalli Jamal a firgice ta ce, "Babe, da ma kana da mata amma ka ce na zo gidanka na taya ka kwana?" "No, wannan ba matata ba ce. Kada ki wani damu ki tayar da hankalinki a banza. Idan za ki zauna kawai ki zauna gidana ne ina da ikon kawo duk wanda nake so." Daga haka ta faɗa jikinsa ya shiga shafa ta yana shinshinar ta tana faɗin, "Ohhhh... baby ina son...ka." Nan take Minal ta fara ganin dishi-dishi jiri yana kwasar ta ta yi hanzarin barin wurin da sassarfa kafafuwanta suna harɗewa. A haka ta nufi bakin ɗaki jikinta Yana rawa ta murɗa ƙofar cike da jarumta, sannan ta tura a hankali ta shige tare da mayar da ƙofar ta rufe ruf har da makulli. Tsaye ta yi jikin ƙofar bayanta jingine kanta a sama yayin da wani zafafan hawaye ya shiga bin fuskarta wani bayan wani. Saboda jin sautin dariyar da suka bi bayanta da ita babu ƙaƙƙautawa. Tsawon lokaci tana haka kafin ta samu kuzarin furta La haula wala ƙuwwata illah Billah. Hasbunallahu wa ni'imal Wakil. Haka ta yi ta faɗa a fili da cikin zuciyarta, faɗa take yi tana maimaita kalmomin cikin saurin murya. Kamar almara jarumta ta yi mata lulluɓi, don cikin ɗan lokaci ta samu wani ƙarfin zuciya da nutsuwa suka sauka jikinta. Ta bar jikin ƙofar ƙirjinta yana harbawa ɓil-ɓil ta shiga zare kayan jikinta. Ta ɗaura towel kenan da nufin shiga wanka, ta fara jin ana ƙwanƙwasa mata ƙofa. Kamar kada ta kula, don jikinta ya ba ta Jamal ne kuma babu abin da zai faɗa ta saurare shi. Amma a haka wata zuciyar ta ba ta umarnin je ki buɗe ki ji me ya kawo shi. Cikin ƙunar zuciya ta isa bakin ƙofar ta buɗe, abin mamaki babu Jamal sai matar da ta gani tsaye ƙiƙam. Suna haɗa ido ta yi hanzarin juya bayanta tana kallon Jamal ta ce, "Babe ka faɗa mata da kanka." Da ido Minal ta bi Jamal ɗin da kallo tana jiran ta ji me za a faɗa mata. Daga can inda yake zaune ya yi Magana cikin isa ya ce, "Indomie take so ki dafa mata. Kuma kada ta yi yaji kada ki bar ta ta ƙame ruwanta ya tsotse." Mamaki ya so kashe Minal a tsaye, bakinta a sake ta shiga ƙare wa Zee kallon sama da ƙasa riƙe da ƙofa a hannunta. Kafin wani tunani ya faɗo ranta ta yi wani murmushin ba zata a kan fuskarta ta ce, "Ok, yanzu ake so ko za a jira na yi wank...?" "Je ki yi wankan. Ita ma za ta fi jin nutsuwar cin abincinki?" Kafin ma ta kai ƙarshe ya ba ta amsa, tana ƙoƙarin mayar da ƙofar ta rufe Zee ta yi hanzarin daka tsalle tana buga ƙafa cikin shagwaɓa ta ce, "Babe, ni ba zan bari ta yi wankan ba ka ce ta je ta dafa mini a hakan yunwa nake j...." "Ahhhh sorry sorry...je ki dafa mata ɗin kawai." Ya yi maganar da murya biyu, ɗaya ta Zee cikin tattausa harshe. Yayin da ɗayar ta Minal ya sauya ta zuwa kakkausa cikin tsare gida. Minal ta saki ƙofar ta fito tana taku a hankali daga ita sai towel ɗin da ke jikinta iya cinya. Fuskarta babu babu fallasa ta nufi kitchen bom-bom suna juyawa, kasanacewar Allah Ya albarkace ta da lafiyayyen ƙugu da cikar ƙirji daidai jikinta. Hakan ya sa Jamal ya bi bayanta da kallo cike da mamakin ganin halittarta. Abin da ya saka shi kasa ɗauke ido a kanta don bai taɓa hangen surarta a fili ba sai a ranar. Zee ta fasa ihu saboda ita ma ganin halittar Minal ta raina tata halitta. Da rera waƙar kuka ta isa gare shi ta faɗa jikinsa tana faɗin, "Babe ni ba son indomin idan ba ta je ta saka kayanta ba." "Ki bar ta a haka mene ne damuwarki?" Ya Yi maganar cikin sanyin murya, saboda jikinsa ya mutu murus kuma ya shiga yanayin da komai ya Zmzo masa a gaɓa. "Warin hamata Babe, don Allah ka ce ta saka kayanta ni dai...uhum-uhumm Babe zan yi kuk.." Jamal ya miƙe ya nufi kitchen ɗin cikin wani yanayi, don shi ma yana buƙatar sake ido biyu da Minal a yadda take. Zee ta bi shi da kallo tana kumbura fuska cike da mugun jin haushinsa. Don kishin da take yi masa ya sa ba ta so kowa ya raɓe sa sai ita, hakan ya sa ta dunƙule tana faɗin, "Babe kada ka je ka dawo don Allah." Ya juyo idonsa a lumshe ya yi mata wani kallo yana faɗin, "Ba kya so ta saka kayan ne?" Zee ta sake magana cikin shagwaɓa ta ce, "Kawai ba na so ka gan ta ne Babe..plss ka zo ni zan yi mata magana da kaina." "Ok!" Jamal ya yi maganar cikin murya ya dawo ya zauna yana shafa kansa ya rungumo ta jikinsa cikin sabon yanayin da ya fara shiga jikinsa. Zee ta miƙe cikin sauri ta riƙo hannuwansa duka biyu ta jawo shi ya miƙe. Sannan ta kwanta a ƙirjinsa tana faɗin, "Ina son ka." Kanta ya fara shafawa yana leƙen fuskarta ya ce, "Kin faye kishi, na faɗa miki ba matata ba ce, kuma babu komai a tsakanina da ita. Yanzun ma don kin ce na je da ba zan so sake ganin fuskarta b..." "Ba fuskarta ne ba na so ka gani b..." Ta yi maganar cikin sauri tana turo baki, shi ma ya katse ta da cewa, "To mene ne?" Ya yi tambayar yana hango bombom ɗin Minal a cikin idonsa. "Bar Shi kawai tun da ba ka ga komai ba. Zo mu je ɗakinka na ma fasa Cmcin komai." Ta ƙare maganar tana jan shi yana 'yar dariya ya bi ta suka shige ɗakin. Minal kam tsam ta yi da ranta tana kallon indomin da ke tafasa siraci yana fita a cikin tuunyar ƙamshi yana tashi. Rungume da hannuwa a ƙirji take tana cizon leɓenta, saboda duk abin da suka faɗa a kunnenta tana ji. Hakan ya saka ta ƙara samun wani sabon darasin da ba a koya mata a gida ko makaranta ba. Da murmushi a fuskarta ta nemo plate ta juye indomin ta rufe da wani plate tare da cokali mai yatsu a sama, bayan ta soya mata faifai ɗaya na wainar ƙwai ƙwara biyu. Zuciyarta wasai ta fito daga kitchen ɗin ta ajiye musu indomin saman dinning table. Sautinsu da ke tashi daga cikin ɗakinsa ya saka ta jin bugun zuciya, cikin sauri ta koma ɗakinta hawaye yana zarya a kan fuskarta. Ta ci kuka daren ranar kamar hawayenta ba za su kai safiya ba. Sannan ta kwana tana faɗa wa Allah damuwarta da abin da take buƙata a wurin sa. Ruwan addu'o'in da ta zuba ta samu ƙarfin gwiwar ƙarfafa kanta da zuciyarta a kan cewa Allah ya karɓa mata su duka. Baccin da ya ƙi zuwa idanuwanta ma tana tuno ɗaya daga cikin ilmukan da Gwaggo Salame take ba ta tana yi ta samu nannayan barci mai daɗi. 'A duk lokacin da bacci ya ƙaurace wa idonki; ki karanta suratul Falaƙ uku, Nas uku da ƙulhuwallahu Ahad ita ma sau uku. Da yardar Allah ba za ki kammala su ba ki fara jin barci ba. Wannan wani sirri ne da na riƙe ina aiwatarwa a duk lokacin da damuwa ta aure ni. Ke ma ki riƙe duk tsananin damuwa matuƙar kika yi a yadda na sanar da ke za ki yi barci har da minshari.' "Tabbas na ga amfanin hakan gwaggo. Don ba don na yi ba da ba na jin takaicin abin da na gani da wanda nake ji da kunnena yana faruwa su bar ni na runtsa." Furucin Minal kenan a lokacin da ta farka sallar asuba. Domin kamar da gayya tana farkawa zuciyarta ta hango mata Jamal da Zee rungume da juna. Ta jima bakin gadon zaune ɗauke da tagumi tana nazari kafin ta miƙe ta yi sallah. A nan ma ta kai kukanta ga Allah kuma ta yi laziminta tsaf tare Ya wadudu ƙafa arba'in. Sannan ta tashi cikin kuzari ta shiga gyaran ɗakinta har zuwa falo, bayan ta gama ta koma ta kwanta da carbi a hannunta tana ja wani sabon barcin ya kwashe ta. Misalin ƙarfe tara na safiya ƙwanƙwasar ƙofa ya tayar da ita. Cikin sauri ta sauko gadon tana ƙarfafa zuciyarta a kan haƙuri har ta buɗe ɗakin. Ido cikin ido suka kalli juna kafin ya shiga shafa kansa cikin haɗe rai ya ce, "Baƙuwata tana jiran breakfast. Ta ce indomin jiya ta yi mata daɗi yanzu ma abincinki take son ci." Cike da jarumta Minal ta gayyato murmushin ƙarfin hali ta ce, "Ayya! Ka ce ta jira ni kaɗan zan yi wanka na fito." Ta ƙare maganar har da 'yar dariya tamkar babu komai a cikin ranta. Jamal ya yi tsayar da kallonsa a tsakiyar idanuwanta cike da mamaki, yana so ya yi wata magana amma ya kasa. Saboda girar da Minal ta ɗaga masa tare faɗin, "Ummm!" Alamun tabbatarwa ga zancenta. Ya juya yana waigen ta ba tare da ta sake cewa komai ba ta juya ko rufe ɗakin ta kasa yi. Sai da ta sha kukanta a toilet sannan ta yi wankan a gurguje ta fito. 'Za ku ga tsiya.' Abin da ta furta kenan a lokacin da ta shiga buɗe kayan lefen Nur tana zaɓen wasu ƙananun kaya cikin sauri. Can ta hango wani mini siket baƙi iya gwiwa da wata jar riga half vest, wadda ake ɗaure ta gaba a saki jelar a saman ciki. Cikin sauri ta shirya a cikin kayan babu shiri dariya ta ƙwace mata. Musamman a lokacin da ta ga kanta jikin madubi tamkar wata Ingozi, duk da kayan sun hau jikinta ta yi mugun kyau. Saboda tun da take a duniya ba ta taɓa shiga irin wannan ba. Asali ma ƙananun kaya ba su taɓa burge ta ba. Ko kayan lefen da aka kawo wa Nur duk ta ɗaga kayan sai dariya ta zo mata a ranar da aka kawo lefen. Saboda tunanin ta ya ya ita za ta iya saka su a jikinta, don har kullum tana jinjina wa Nur a kan yadda ba ta jin nauyin shiga duk yadda ta ga dama, kuma ko a gaban waye ita babu ruwanta da ɓoye jikinta. Saɓanin ita Minal da ba ta saba da hakan ba, kuma ba ta tashi ta ga ana yi a cikin unguwarsu ma ballantana a gidansu. Har ganin take yi babu ranar da za ta iya shigar 'yan bariki a cewarta koyaushe. "Ashe akwai ranar." Zancen da ta yi kenan tana juya jikinta gaban madubin bayan ta saka wata hula mai kama da pesin cap mahaɗin siket ɗin. Ƙwanƙwasa mata ƙofar da aka sake yi ta yi hanzarin fesa turaren Nur a jikinta har saman hula, sannan ta maƙala passion ɗin ɗan kunne ja da baƙin agogo a tsintsiyar hannunta. Ta nufi ƙofar da sassarfa ta buɗe fuskarta a sake tamkar wadda ke cikin matsanancin farinciki. "Babe!" Zee ta ƙwala wa Jamal kira saboda ganin Minal a yadda take ba ƙaramin firgita ta yi ba. A ruɗe ya iso wurin yana ƙoƙarin tambayar lafiya ta faɗa jikinsa tana dukan ƙirjinsa a haukace tana faɗin, "Zan mutu Babe idan ina ganin matar nan." Haka ta dinga ɓarin sambatun da Jamal bai ma san tana yi ba, saboda hankalinsa da tunaninsa gabaɗaya suna kan Minal. Tsabar mamaki da tashin hankalin da ya Yi masa dirar mikiya a saman ka. Saboda ƙamshin turaren Nur da Minal ta saka zuciyarsa ta shiga birbration. Nan take ya tsinci kansa a cikin wani yanayi mara misali, don Minal ba ta bar shi da iya turaren da shigar ba, sai da ta haɗa masa da kanne ido ɗaya tare da fari da ido tana cizon leɓenta kafin ta koma yi masa wani kallon ƙasan ido tana jingine jikin ƙofar rungume da hannuwanta a ƙirji. Da ma ta ga halin da yake ciki ta ƙara masa da juyi a gabansa tamkar tarwaɗa, tana shafa jikinta da lasar baki cike da ƙwarewa a kan zama gogaggiyar 'yar duniya. Ƙaƙƙarfan dukan da Zee ta kai masa a ƙirji hannuwa biyu ta tura shi, hakan ya saka shi yin baya ya faɗi ƙasa daɓas babu shiri. Amma hakan bai saka shi ɗauke kallon sa a kan Minal ba, tamkar wani sakarai ya saka hannu ya janye Zee da ke gabansa tana masifa, tsabar kishi ya saka ta ƙaramar hauka. Miƙewa ya Yi jikinsa yana rawa ya isa gaban Minal yana muzurai tare da saita kansa cikin ƙarfin hali ya ce, "Je ki sauya kayan jikinki ba na buƙatar sake ganin ki da su." Sai a lokacin Zee ta daina surutai da kukan da ta ja gefe tana yi. Saboda jin daɗin zai rama mata wulaƙanci da cin zarafin da Minal take son yi mata a fakaice. Don surar jikinta ko ita da take mace ta ƙyasa ballantana shi a matsayinsa na namiji mabuƙaci. Minal ko wani kallon 'yan duniya ta yi masa tana 'yar dariya ta ɗaga hannu sama alamun sara masa ta ce, "Ok sir!" Sannan ta juya ta shige ɗaki . Sai a lokacin Zee ta samu kuzarin zuwa inda yake ta faɗa jikinsa tana rera waƙoƙin kuka kala-kala. Ya ja ta jikinta ya rungume tsantsan sannan ya sauke ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya mai sauti. Haƙuri ya shiga ba ta bayan sun isa kan kujera sun zauna, tare da yi mata alƙawarin ba zai taɓa son Minal ba. Mintuna a tsakani bayan Jamal ya shawo kan Zee ta daina kukan tana masa shagwaɓa Minal ta fito cikin wata sabuwar shigar ƙananun kayan. Inda ta saka riga mai hannun best iya cibiya da dogon wandon da ya ƙara fitar da halittar jikinta, don ko bra cirewa ta yi ta bar kan nipples ɗin ta suna maraba da mai kallo. Sannan ta saka wata kwantacciyar hula kamar ta 'yansanda ta saki jelar kitson burazil da ƙanwarta ta yi mata a gida, wanda ya saje da gashin kanta kuma ya sauka gadon bayanta yayin da ta zubo wasu a gaban fuskarta. Da takalmi mai mugun tsini a ƙafarta ta fara taku cikin nutsuwa har ta iso gabansu. Sannan ta shiga fareti tana juyawa tare da buga ƙafa bombom da ƙirjinta suna ta aikinsu na rangaji. Ganin abin da take yi ya ja hankalin Jamal Zee ta fashe da wani sabon kuka tana kai masa duka tare da kiran sunansa. Minal kam ko kaɗan hargowar Zee ba ta saka ta daina abin da take yi ba, sai da ta gama iya juyin da take so sannan ta ƙame ƙam a gabansu ta ƙara sara wa Jamal ta ce, "Me za a dafa mata 'yar laɓai?" Takun ƙaniya🫣 *SANARWAR!* *INA SO KU NUNA MINI KARA RIN WADDA ZAN TABBATAR KUNA JIN DAƊIN BIYA TA A CIKIN LITTAFIN FANSAR ƘAUNA. MUTUM 50 KACAL NAKE SO MASU SAYEN lLITTAFIN DAKAN ƊAKA.. COMPLETE BOOK 1-2 PRIZE 1K GA MAI BUƘATA YA TURO KUƊINSA TA NAN; 9032685442 OPAY. SHAIDAR BIYA TA NAN 08022014771. ZAN SAKE SHI A RANAR 3 GA WATAN FEBRUARY. LABARI NE MAI ƊAUKE DA RIKICI, HARGITSI, TASHIN HANKALIN DA RIKITA-RIKITA BAYAN ZALLAR TSAGWARON SOYAYYA MAI ABIN MAMAKI. NI CE DAI MARUBUCIYAR ABOKIN AIKINA. KUN SAN KALAR ALƘALAMINA BA NA RUBUTA ABIN DA BA ZAI DAMƘO ZUCIYA BA* *SAURA KWANA HUƊU KACAL YA RAGE GA MASU BUƘATAR SHIGA CIKIN WANNAN TSARI. GA WAƊANDA SUKA SAYA SUNA DA KYAUTAR LITTAFAINA BIYU. RUWA DA ƘANƘARA DA BAKAN GIZO.* SAI KUN ZO. D. AUTA CE ✍️ [2/20, 22:02] Hadiza D. Auta: *FANSAR ƘAUNA!* *HADIZA D. AUTA* *AREWABOOKS: Princessdija.* https://chat.whatsapp.com/Edh59w1Jcgk799uIkP0CFa *LAMBA SHA BIYAR.* Ƙaƙƙarfan tsaki Zee ta ja sannan ta zame daga jikin Jamal ta miƙe a fusace ta nufi ɗakinsa, tana goge hawayen da ke malala a kan fuskarta. Kallo Jamal ya bi ta da shi, hakan ya sa Minal da ke tsaye gabansa rungume da hannu ta ce, "Ka tambayo ta mu ji abin da take so na je na dafa mata lokacin breakfast yana ta ƙurewa. Ina so na gama da wuri sai na ɗora mata girkin rana kafin na dare ya zo shi ma." Wani sakaran kallo Jamal ya bi ta da shi cike da mamakin da ta ƙara jefa shi a ciki. A gefe ɗaya kuma kukan Zee yana shiga kunnuwansa, gabaɗaya zuciyarsa ta hautsine. Zumbur ya miƙe ba tare da ya tsaya ba ta amsa ba, cikin sauri ya nufi ƙofar ɗakinsa saboda hango Zee da jakar kayanta tana ƙoƙarin fitowa daga ciki. "Ina za ki je kuma? Ba sati ɗaya za ki yi mini ba?" Ya furta maganar bakinsa yana rawa tsabar ya gama ruɗewa, kuma yana hangen Minal ta lalata masa duk wani tsari. "Ba zan iya zaman b...zuciyata za ta iya fashew.." Ta yi maganar tana murza idanuwanta cikin shesshekan kukan da ta yi har idanuwanta suka sauya. Cikin sanyin jiki ya isa daf da ita ya riƙo jakarta yana faɗin, "Ki yi haƙuri zan ɗauki mataki a kan duk abin da ta aikata miki. Amma ki sani babu inda za ki je har sai kin gama mini kwanakin da muka tsar...." "Tun farko ban san da wata a cikin gidan ba da ban yarda na amince da zuwan ba. Amma tun da idanuwana sun ga komai ba zan yarda a fasa mini zuciyata a banza ba...sakar mini jaka ni ba zan zauna ba.." Ta ƙare maganar tare da fisge jakarta ta yi gaba. Ya bi bayanta yana magiyar ta yi haƙuri ta zauna har suna ƙoƙarin ficewa daga falon, daidai lokacin da suka ji Minal tana faɗin, " Ke! Hajiya kwartuwa, ga shi har za ki tafi ba ki faɗa mini abin da zan girka miki ba." Daga Zee har Jamal kallon mamaki suka bi ta da shi, saboda sunan da ta kira kuma ta bi da zance kamar wadda ta yi abin arziƙi. Babu shiri Zee ta ƙara fashewa da wani sabon kuka tana nuna ta tare da kallon Jamal ta sake cewa, "Babe, kana jin me take faɗa kuma ba ka ɗauki matakin komai b...to na rantse da Allah ni kuma ba zan ƙyale ta b..." Ta yi maganar cikin hargowa tare da sakin jakar ta nufi kitchen da gudu tamkar wata mahaukaciya. Minal da ke tsakiyar falon a tsaye rungume da hannuwa a ƙirji, babu shiri ta fashe da wata mahaukaciyar dariya. Saboda kalar gudun da Zee ta yi ga ta ɗunɗumemiya kamar ta kifa ta faɗa zuwa kitchen. Hakan ya saka Minal dariya sannan da farincikin Zee ta ji haushin sunan da ta kira ta da shi. Ta ƙara sakaws ranta kaɗan ta gani kuma sai ta koya mata hankali. Zee da ke kitchen kamar wata mahaukaciya ta shiga neman wuƙa ta dinga ɓarin kaya, amma duk neman ta ba ta samu ko ɗaya ba. Saboda tun lokacin da Jamal ya kwashe su ya ɓoye a ɗakinsa bai dawo da ko ɗaya ba. Ita ma Minal da dubara take amfani da cokali mai yatsu har ta yanka abin da take so. Ganin babu wuƙar da gaske kuma neman zai ɓata mata lokaci, ta fisgo cakali mai yatsu ta fito a haukace tana ƙoƙarin isa kan Minal idonta rufe. Cikin sauri Jamal ya sha gabanta tare da riƙe ta yana ƙoƙarin hana ta abin da zuciya ke ingiza ta, ita kuma tana ƙoƙarin kufce wa riƙonsa don ta yi kan Minal da nufin ƙaddamar mata, ta huta da takaicin baƙin kishinta da ke cin zuciyarta. Minal dai har lokacin tana tsaye a inda take ba ta fasa dariyar ba, kuma idonta a kansu suna ta kokawa a ƙarshe abin ya koma faɗa a tsakaninsu. Saboda haushin Jamal ya hana ta isa wurin Minal ta yi abin da ta yi niyya; ta ware haƙoranta ta gatsa masa wani mahaukacin cizo a damtsen hannu. Zafin cizon ya saka shi yin tsalle tare da fasa ihu kafin ya sauke mata wani lafiyayyen mari da bayan hannu. Cike da mamaki ta riƙe gefen fuskar tata inda naman kumatunta ke rawa tsabar ƙarfin saukar marin tana kallon sa. Ta jima idonta a kansa bakinta a sake kamar wata gaula, kafin ta ɗora hannu a ka ta fasa wata uwar ƙara ta faɗi ƙasa tana birgima. Saboda takaicin tozarcin da ya yi mata a gaban Minal bayan don shi ta zo gidan, saɓanin tunanin da ta yi a kan ya ci zarafin Minal kuma ya sauke mata ƙananun iskancin da ta hango a tsakiyar kanta. Jamal kam ɗakinsa ya nufa riƙe da hannun da ta gatsa masa cizon ransa a ɓace yana tsaki. Minal ta ƙara fashewa da wata mahaukaciyar dariya tana tafa hannuwa, kafin ta faɗa a kan ɗaya daga cikin kujerun falon tana ta dariyar mugunta har da riƙe ciki. Musamman da ta kalli Zee a dunƙule tana gunjin kuka ta koma kallon jakar kayanta da ke yashe ga banza. Sannan ga Jamal ya shige ɗaki, zogin cizo ya hana shi tsayawa a ƙarasa wasar. Dariyar da Minal ke yi ta ƙara ziga Zee ta fusata, idanuwanta a rufe ta zabura tamkar wata kububuwa tana huci ta yi kanta da duka babu ji babu gani. 'An zo wurin.' Minal ta faɗa a ranta, don da ma can a shiryenta take a kan duk yadda ta faɗi rataya. Saboda ganin Jamal ya bar ta daga ita sai ita jikinta ya ba ta Zee za ta kawo mata wani raini. Babu ɓata lokaci ta saki ƙwanji suka yi ta kai wa juna duka. Kaf! Kif! Kakakaf! Sautin doke-doken da suke yi kenan. Dambe ya kacame suka dinga neman makasar juna, kowace da ƙudurin ta illata 'yar'uwarta. Kasancewar Zee tana da ƙiba, Minal tana samun sa'ar kai ta ƙasa da ƙyar ta haye ruwan cikinta tana kai mata duka ta ko'ina. Duk ƙoƙarin Zee da ƙarfin halinta; bai sa ta ɓanɓare Minal daga maƙalewar da ta yi mata ba tana aikin jibgar ta inda duk hannunta ya je. Dole ta sa Zee fasa ƙara tana jera kiran sunan Jamal babu ƙaƙƙautawa ganin da gaske Minal illata ta take son yi ƙarfi da yaji. Ko da Jamal ya fito baki a sake ya dinga kallon abin da yake faruwa, kafin ya isa wurin a fusace ya fisgo Minal cikin fushi ya wurga ta gefe tana haki. Ransa a matuƙar ɓace ya dinga aika mata kallo cike da takaicin ganin ɓarnar da ta aikata wa Zee. Domin gabaɗaya ta sauya mata fuska, bakinta jini hancinta jini. Hatta idanuwanta ajin jini ne a ciki saboda yakushe mata fatar ido da Minal ta yi. Bayan kumburewar da fuskar ta yi sumtum a cikin ɗan ƙanƙanin lokaci. "Ke wace irin mahaukaciya ce ban sani ba? Kina ganin yadda kika mayar da yarinyar mutane kamar babu imani a zuciyarki! To wallahi duk abin da ya biyo baya babu ruwana duk inda take ta kai ƙarar ki za ta ja haƙƙinta a kan wannan rashin imanin da kika gwada mata... wannan ai rashin hankali ne mai lasisi..kai jama'a!" Ya ƙare maganar a firgice bayan ya ɗago fuskar Zee da ke kife cikin tashin hankali, ganin jinin da ke zuba daga hancinta har ya ɓata gaban rigarta. "Wallahi! Wallahi ko gobe wata kwartuwa ta zo gidan nan, kuma ta nemi ta dake ni sai na yi mata abin da ya fi wannan..." "Ko me ta yi miki ai bai kamata ki yi mata irin wannan aika-aikar ba! Don taƙamar ta zo cikin gidan nan..ni na kawo ta kuma ba gidanki ba ne!" Wani kallon uku kwabo ta yi masa kafin ta mayar masa da amsar cewa, "Kai da ka kawo ta ma ka kwaɗa mata mari saboda ta cije ka. Sai ni zan zuba ido na ƙyale ta dake ni a banza? To duk matakin da za a ɗauka kaina a ɗauka amma wallahi ban yi danasanin sauya mata fuska ba...kai ko mutuwa ta yi a sanadin hakan Allah ba zai kama ni ba don kare kaina ne na yi. Tun da ita ma ta so kashe ni ba don ka karɓe cokalin ba da ba a san me za ta aikata mini da shi ba...to ta yi duk abin da za ta yi ina jira! Tun da ita kaɗai ce mai gata ni ce ba a bakin komai b..." "Yi mini shiru mahaukaciya! Kin yi laifi kina yi wa mutane surutun banza." Ya yi maganar a ƙufule yayin da ya tallafo Zee tana layi tare da ɗaga kanta sama yana bubbuga goshinta cike da zummar jinin ya tsaya idan ma haɓo ne ta yi. Suna ƙoƙarin ficewa daga falon Zee tana gunjin kuka a jikinsa aka turo ƙofar falon. Dam-dam! Ƙirjin Jamal ya buga, saboda firgicin ganin Hajiya a irin wannan lokacin. Ita kanta Minal sai da ƙirjinta ya buga, jikinta yana rawa ta faɗa ɗakinta da sassarfa. Da hanzari ta sauya kayan jikinta da wata doguwar riga ta ɗaura ɗankakwalinta a ka ta fito. Saboda sautin Hajiyar da ke tashi a sama tana faɗa ko'ina ana jin ta. Amma mamakin ganin shu rungume da Zee bai hana ta isa falon ta zauna ba. Fuskarta a yamutse ta dinga bin su da kallo ɗaya bayan ɗaya. don ganin ta ya yi saurin sakin Zee ya rakuɓe gefe yana muzurai. Zee kuma ƙasa ta zube saboda ƙafafuwanta sun yi sanyin da ba za su ɗauki gangar jikinta ba. Don ganin Hajiyar ya sa ta shiga tashin hankalin da ya saukar mata kyarmar jiki, ta shiga haɗiyar yawu tare da ƙara sautin kukanta wiwi. "Macen banza har a cikin gidanka Jamal?" Hajiya ta yi maganar cikin tsurewa, tsabar mamakin ganin abin da idonta ya yi tozali da shi. "Ashe Allah Ya kawo ni ne rabon na ganar wa kaina irin ta'asar da kake aikatawa ba tare da na sani b..." "Wallahi Hajiya sau ɗaya ne...kuma yau ne kawai kin ga jakarta ma gida za ta je yanz..." Jamal ya yi maganar a ruɗe saboda ta gama ganin komai, kuma bai san da wace kalma zai musa mata ba. Kafin ta katse shi da salati tana tafa hannu alamun ya gama kashe ta da wani mamakin. "Ana ganin ta fasa mini baki da hanci amma ba za a yi ta kaina b...to wallahi idan na mutu duk sai kowa ya yi bayani." Zee ta yi maganar tana ƙara bajewa ƙasa tare ƙara sautin kukanta cikin matsanancin hali ta koma birgima. "Ke daƙiƙiyar ina ce da za ki zo gidan matar aure da mijinta ki yi tsammanin za ki fita lafiya lau? To bari ki ji ko kashe ki aka yi ke kika jawo kuma babu wanda zai kai ki asibiti a cikin mu. Ki tashi ki ja jakar kayanki ki fice tun kafin na haɗa ki da 'yan sanda su tafi da ke wallahi!" Hajiya ta ƙare maganar cikin matsanancin fushi alamun ta kai maƙurar ɓacin rai. Zee ta miƙe da ƙyar cikin tashin hankali tana layi ta ja jakarta kamar ta kifa da tangaɗi ta fice ta ƙofar falon. Jamal ya bi bayanta da niyyar rage mata hanya ganin halin da take ciki. "Kai kuma ina za ka je?" Hajiya ta katsa masa tsawa cikin haɗe guyska ta jefo masa tambayar. Muryarsa tana rawa ya ce, "Rufe ƙofar zan yi idan ta fice." "Rufe ka zo." Ta sake magana a taƙaice kafin ta mayar da kallonta a kan Minal da ke rakuɓe jikin kujera tamkar ruwa ya ci ta. "Ke kuma..." Dam ƙirjin Minal ya sake bugawa, saboda ta tsorata matuƙa da ganin yanayin Hajiyar. "Allah ya yi miki albarka." Wani sanyin daɗi ya ziyarci zuciyar Minal, saboda ta yi tsammanin ita ma za ta juye mata fushin a kai ganin yadda ta ɗauki zafi sosai. "Hakan da kika yi ya yi daidai. Gobe ma duk macen da ya sake kawo miki a cikin gidan nan ki yi kaca-kaca da ita ni na ce! Don babu hukumar da za ta kama ki da laifin dukan macen da duk kika kama da mijinki a cikin gidan aurenki. Saboda babu babban raini da wulaƙanci kamar namiji ya kawo wata mace a gidansa ko da matarsa ba ta gidan ballantana tana ciki. Don haka wallah Jamal duk yarinyar da ka sake ɗaukowa ka kawo ta a cikin gidan nan naka sai na nuna maka haihuwar ka aka yi ba kai ka haifo kanka ba!" Shiru ya ratsa falon saboda babu wanda ya iya motsin kirki daga shi har Minal ɗin. A lokacin Hajiyar ta sake cewa, "Amina kuma, tun da ba ka son ta; ka shiga ɗaki ka rubuto mini takardar sakinta ka ba ni yanzun nan! Tun da ka isa da kanka sai ka yi duk abin da kake so! Don ba zan juri ganin kana wulaƙanta 'yar mutane a banza ba. Idan ba ka so akwai dubunka waɗanda ma suka fi ka a komai za su so ta kuma su yi zaman aure na tsakani da Allah da ita. Idan ka sauwaƙe mata sai ka je ga ka ga matan banzan da ka fi so a kant...." "Ni dai don Allah ki yi haƙuri Hajiya. Na san na yi kuskure kuma ba zan sake makamancinsa ba. Da ma na yi ne kawai don na gwada ta." Wani kallo ta yi masa kafin ta yi guntun tsaki ta sake cewa, "Gwaji? Da irin wannan rashin mutuncin kake gwada matarka? Yanzu idan da ita ce ta gwada kawo wani a cikin gidanka za ka kalli hakan a matsayin gwajin? A hir ɗin ka Jamal! Wallahi ina jiye maka tsoron ɓata rawarka da tsalle a kan irin riƙon da kake ƙoƙarin yi wa Amina." "Don Allah Hajiya ki yi haƙur..." "Sai fa ka sake ta yanzun nan ba sai anjima b..." "Wallahi Hajiya ba zan iya tsallake umarninki ba. Amma ki yi haƙuri zan zauna da Amina tun da kina s..." Wani kallo ta wurga masa wanda ya saka shi datse maganarsa. Cikin sauri ta miƙe tare da gyara zaman mayafinta idonta a kan Aminar ta ce, "Tashi ɗauko mayafinki mu je! Duk ranar da shi ya so auren da ke sai ki dawo gidan." "To, Hajiya." Amina ta amsa cikin sanyin jiki da na murya tare da tashi ta nufi ɗakinta. Kafin ta fito Jamal ya isa gaban Hajiya ya durƙusa gwiwa biyu yana cewa, "Ki ba ni dama ta ƙarshe Hajiya. In sha Allahu zan gyara duk abin da na ɓata da hannuna." Banza ta yi da shi, duk da tausayin sa ya sa ta zubar da ƙwalla. Kuma ta so yin jarumtar hana hawaye zuwa cikin idonta. Amma ƙoƙarinta bai hana ƙwallar zuba ba. Hakan ya sa Amina tana fitowa ta ja hannunta suka fice. Ya biyo bayansu yana magiya amma ko waige ba ta yi ba ballantana ta tsaya sauraron sa har suka fita harabar gidan, bakin motar da aka kawo Hajiyar suka isa. Mazaunin baya ta buɗe mata sannan ta ce, "Ina kayanki? Idan mun je ba yanzu za ki dawo ba, ki koma duk abin da kika san kina buƙatarsa ki ɗauko shi mu je, ina jiran ki." DAKAN ƊAKA..Complete document book 1-2. Mai buƙata 9032685442 Opay. Shaidar biya ta nan 08022014771. 10 February zan sake shi da yardar Allah. D. AUTA CE ✍🏼 D. AUTA CE ✍️ [2/20, 22:02] Hadiza D. Auta: *FANSAR ƘAUNA!* *HADIZA D. AUTA* *AREWABOOKS: Princessdija.* https://chat.whatsapp.com/Edh59w1Jcgk799uIkP0CFa *LAMBA SHA SHIDA.* Minal ta yi gaba da sassarfa a bisa umarnin Hajiyar na ɗauko kayanta. Caraf ta tuna jakarta ma tana cikin boot ɗin motar Jamal. Cikin sauri ta dawo ta gefen da Jamal yake tsaye yana muzurai don ya kasa furta ko kalma ɗaya. Hannuwansa a baya yana kallon ƙasa ya ji muryar Minal tana faɗin, "Jakata da ke motarka nake so." Ta yi maganar a hankali saboda ba ta so Hajiya ta ji me take faɗa, gudun ta fahimci abin da ya kai jakar kayan nata cikin motarsa ya ƙara yin wani laifin. Amma sassauta muryar da ta yi bai hana Hajiya yin magana cikin ɗaga sautinta ta ce, "Ke fa muke jira? Tsayuwar me kike yi a wurin?" Inda-inda Minal ta fara yi tana sosa ƙeya, kafin Jamal ya yi hanzarin barin wurin ya isa inda motarsa take ajiye yana faɗin, "Ashe ta saka jakar kayanta a motata ba tare da na sani ba." Wani kallon mamaki Minal ta bi shi da shi kafin wata kalar dariya ta so kufce mata. Saboda ganin ya fuske ƙiri-ƙiri alamun da gaske abin da yake faɗa. Idon Hajiya a kansa har ya buɗe boot ɗin ya ciro jakar ya nufi bakin motar Hajiyar ya ajiye yana sunne kai tare da kumbura fuska. Cike da mamakin abin da ya kai jakar kayan a motarsa ta ce masa, "Kai Jamal! Dube ni mu haɗa ido! Za ka faɗa mini dalilin zuwan jakar a cikin motarka ko sai mun raba 'yan kallo da kai? Saboda jikina ya ba ni akwai abin da kake shiryawa ba tare da na sani ba." Gefe ya ja yana zarar ido tare da shafa bayan kansa yana faɗin, "Ki tambaye ta Hajiya, idan ni na ce ta haɗa kayan ta saka a motar." "Ba zan tambaye ta ba kai na tambaya! Amma ka bar amsarka don na gama gano komai. Kuma hakan da ka aikata ba ƙaramin burge ka yi ba. Don haka na hutar da kai rage mata hanyar zuwa gidansu da ka yi niyya. Da ma can zamana take yi kuma daga yau ta koma hannuna. Kuma ko da wasa kada na ga ka taka ƙafarka zuwa inda nake....wuce mu je ke kuma! Tun da ba za ki iya faɗa mini abubuwan da ke faruwa ba sai da idanuwana suka ganar mini komai." Ta ƙare maganar a daidai lokacin da take shiga motar, bayan ta zuba wa Minal ido har ta shige motar ba ta daina furzar da abin da ke bakinta ba. "Hajiya don Allah ki yi haƙur..." Jamal ya yi maganar a lokacin da ya zuro kansa ta gilas saitin Hajiyar bayan ya marairaice kamar mara lafiya. "Ni matsa ka ba ni wuri! Gida ne an bar maka ka kawo duk wadda kake so. In dai gindi ne kullum safiya sai an kawo sabon samfur a cikin duniya. Kuma duk ƙwarewarka ga iskanci wata macen sai dai ka hango ta daga nesa ka bar ta. Don haka ya rage naka ka zaɓi rayuwar da duk ka fi hangen za ta fisshe k....tafi mu je Malam Habu tun kafin zuciya ta ɗebe ni na yi abin da zai dame ni daga baya." Tana maganar tana zuƙo gilashin motar da ƙarfi ta rufe har tana ƙoƙarin dantse wa Jamal hannu da gangan. Minal dai ta sha jinin jikinta, har suka bar gidan maigadi yana ɗaga musu hannu ba ta daina mamakin Hajiyar ba. Saboda ba ta taɓa tunanin ita ma ta iya masifa kamar Innarmu mu ba. Ganin lokacin auren ba ta tsaurara wa Jamal kamar yadda ta yi masa yanzu ba. Jamal kam ya jima tsaye a inda suka bar shi kansa a ƙasa, hannuwansa zube cikin aljihu yana nazarin abin yi. Saboda ko kaɗan bai ji daɗin abin da Hajiyar ta yi wa Zee ba, hakan ya sa ya ji ba zai iya neman ta ba ballantana ya tafi ganin halin da take ciki. "Maigida akwai wani abun ne?" Zancen maigadin gidan kenan yana 'yan duƙe-duƙen alamun girmamawa. Duk da zuciyarsa cike take da son sanin abin da ke wakana a cikin gidan. Tun lokacin da Jamal ya zo da Zee har zuwa lokacin da Minal ta dawo, kashe yake da kunne yana so ya ji wace irin waina ce ake toyawa a cikin gidan. Ganin zuwan Hajiya da fitar Zee a yanayin da take jikinsa ya ba shi babu lafiya. Ya shiga tsumayin jin wani abu da zai fallasa komai har ya gano kalar wainar da ake toyawa. Duk da zuciyarsa ta gama ba shi satar amsa a kan Jamal ne kawo abin da duk ya haddasa komai. "Aikin bincike na na ɗauko ko aikin tsaron ƙofa da gadin gida?" Jamal ya yi maganar a fusace saboda jin haushin shisshigin da yake son yi masa a cikin gida. "A'a ranka ya daɗe?" Ya yi hanzarin amsawa yana ja baya tare da ranƙwafawa alamun girmamawa gare shi. "To ka tsaya iya aikinka." Jamal ya yi maganar cikin haɗe girar sama da ta ƙasa tare da barin wurin ya koma cikin gidan zuciyarsa a ƙuntace. A kan babbar kujerar falon ya faɗa yana shafa kansa cikin matsananciyar damuwa. Sai dai duk ya rufe idanuwansa Minal yake gani a cikin shigar ƙananun kayan da ta yi wa Zee barazana. Idan ya buɗe idon kuma ta koma yi masa gizo yana hango ta da towel iya cinya tana taku bom-bom ɗin ta suna ta juyawa. "Ya Salam! Wai me ke shirin faruwa da ni ne?" Ya furta maganar a kasalance a lokacin da ya isa inda yake hangen ta da sassarfa da nufin kamo ta ta ƙarfi, ko da zai rage nauyin abin da yake ji a cikin zuciyarsa. Sai dai wayam ya ji ya kamo banza babu komai a wurin sai ginin da ya ci karo da shi ya buge hannunsa da Zee ta gatsa wa cizo. Babu shiri ya bar wurin dafe da hannun ya faɗa ɗakinsa. A gurguje ya yi wanka ya fice gidan zuwa wani babban Chemist. A nan aka yi masa dressing czon, saboda shatin haƙoran Zee ruɗu-ruɗu har fatar ta tashi sosai. Bayan an gama rasa inda zai nufa ya yi, dole ya ƙare rabin wuninsa a wani restaurant. A can ya ci abincin rana har dare ya zo ya sake cin abincin sannan ya nufi gidansa. Daren ranar kwanan takaici ya yi yana tsaki, saboda ganin ya yi uku babu. Zee ta tafi Minal kuma Hajiya ta ɗauke masa ita, Nur kuma ta yi masa nisan da bai san ina zai je ya nemo ta ba. Juyi ya shiga yi saboda ji yake yi kwanciyar ba ko kaɗan ba ta yi masa daɗi. *** Minal kam kwana ta yi mai daɗi har da minshari. Saboda zuwanta gidan cikin wuni ɗaya ta gano tsabagen kirkin Hajiya. Don gaba ta saka ta a kan sai ta cinye abincin da ta zuba mata, dare ma haka aka yi ita ta bai wa zaɓin abin da take so a dafa. Cike da jin nauyin Hajiyar ta yi shiru tana sunne kai ta ce, "Babu abin da ba na ci, kuma komai aka dafa zan ci." "Kada fa ki takura kanki. Sannan duk abin da kike so ki faɗa mini kada ki ji nauyi." Bayan sun gama kallo a falo Hajiya ta kai ta ɗakin Amna inda aka ajiye mata jakar kayanta. Ta ce ta zauna a nan tun da Amnar ta koma makaranta. Kuma ta yi duk abin da take so a cikin gidan babu mai takura ta, sannan ta ɗauka tamkar cikin gidansu take gaban Innarmu. Kuma duk abin da take so idan ta yi ra'ayi kawai ta dafa, idan ma babu kayan haɗi ta sanar da ita za a nemo a kawo mata. Fitaa idan ta yi sha'awa yi ta sanar da ita ba sai ta nemi Jamal ba. Minal ta shiga jin daɗin asirin Jamal da ya tonu da wuri Hajiya ta ga komai da idonta, sannan da gatan da take nuna mata tamkar 'yar da ta haifa da cikin ta. Hakan ya sa ta ci alwashin kafin ta bar gidan sai ta ƙara wa Hajiya ninkin ƙaunar da take yi mata a cikin ranta. Tun da asuba ta fara gyaran ɗakin Amna sannan ta wanke toilet ta koma gyaran babban falon Hajiyar. Sai da ta share ko'ina ta ƙwalƙwale tsaf sannan ta sauya zaman kujerun daidai tsarin da take so. Gari yana fara washewa ta faɗa kitchen cikin zafin nama ta shiga haɗa musu abin kari, saboda ganin komai yana ajiye a mazauninsa, babu abin da za ta tambayi Hajiya. Ko da Hajiyar ta fito riƙe da baki tana mamakin ayukan da Minal ta yi a cikin duhun asuba zuwa ƙarfe takwas na safiya. Ƙamshin da ke dukan hancinta ya sa ta nufi kitchen ɗin zuciyarta cike da jin daɗi, saboda halin kirkin Minal ya burge ta matuƙa. Har ƙasa Minal ta durƙusa cikin ladabi tana yi wa Hajiya ina kwana, fuskarta cike da walwala ta amsa mata tare da saka mata albarka, kafin ta gyara tsayuwarta da carbi a hannunta ta ƙara cewa, "Kin hana idonki barci kina ta wahalar da kanki Amina." "Babu komai Hajiya. Ai kaina na yi wa." "To, Allah ya yi albarka." Hajiya ta juya ranta fes ta koma falo ta zauna tana nazarin gyaran da Amina ta yi wa falon. A ranta ta ce, 'Yarinyar kirki.' "Hmmmmm!" Ta sauke ajiyar zuciya saboda tuno Jamal da irin sagegeduwar da yake ƙoƙarin yi wa kansa. Amina ta haɗa komai a tire ta kawo wa Hajiya, daidai lokacin da 'yar aikin Umma Ade ta shigo gidan suna gaisawa da Hajiya. Amina ma cikin girmamawa ta rusuna ta gaishe da ita, sannan ta koma kitchen ɗin. Umma Ade ta biyo ta tana faɗin, "Amarya, da kin jira na zo wannan duka aikina ne. Yau ma wani jikana ne muka tashi da shi babu lafiya shi ya sa ban yi sammakon da na saba yi ba." Amina tana harhaɗa kayan da ta ɓata da nufin wankewa ta ce, "Ki yi zamanki kawai Umma Ade, tun da na zo gidan ai ni ce mai yin komai.." "Ba za a yi haka ba! Ba ni kwanonin kawai na ƙarasa aikin, ke ki je ki huta ai kin yi mai wuyar." Ganin da gaske Umma Aden ba za ta bari ta yi aikin ba ta ɗebi nata abin karin ta shige ɗakin Amna cike da jin kunyar Hajiya. Saboda ba ta son zamanta falon ya takura Hajiyar, kuma ita ba za ta sake ta yi karin yadda ya dace ba. Bayan ta gama karin ta faɗa wanka, cikin ɗan lokaci ta shirya da ɗaya daga cikin kayanta na gida. Saboda lokacin da ta haɗa kayan gabaɗaya babu kayan Nur ko ɗaya a cikin jakar. Iya nata kawai ta ɗauka, don ta ci alwashin bar mata kayanta kamar yadda suke har zuwa lokacin da za ta waiwayi abin ta. Misalin ƙarfe goma zuwa sha ɗaya na safiya, Jamal ya yi parking motarsa a harabar gidan Hajiya. Zuciyarsa cike da fargaba a kan irin tarbar da za ta yi masa, bayan ta yi masa kashedin kada ya zo mata cikin gida ba ta buƙata. Fuskarsa babu yabo babu fallasa ya shiga babban falon, a inda ya fara yin tozali da Minal ita kaɗai zaune a cikin falon tana kallo, gabaɗaya hankalinta ya tafi a kan wata diramar da ake yi Bollywood. Ƙirjinsa ya buga dam-dam, amma cikin basarwa ya raɓa ta gefenta ya wuce zuwa ɗakin Hajiya fuu tamkar bai gan ta ba. Ita ma sai da ta ji motsin mutum hankalinta ya kai kansa yana ƙoƙarin shigewa ɗakin Hajiyar. Ƙirjinta ya dinga faɗuwa don ta firgita sosai da ganin sa tsidik, saboda sallamarsa ma a ciki ya yi ta ballantana ta ji shi ta amsa. "Ummmm!" Ta yi wani abu da baki sannan ta ci gaba da kallon amma hankalinta ko kaɗan ba ya wurin. Don ta rasa nutsuwar da take da ita kafin zuwansa. Haka kawai ta tsinci kanta da tausaya masa don a kallo ɗayan da ta yi masa ta fahimci babu walwala a tattare da shi kuma ba ya cikin jin daɗi. Mintuna a tsakani ta fara jin sautin Hajiya tana faɗa, kafin ta ji ƙarar buɗe ɗakinta tana ba shi umarnin ya fice mata daga ɗaki ba ta buƙatar ganin shi. Kamar an ingiza Minal ta zabura cikin rawar jiki ta isa gaban Hajiyar ta durƙusa tana faɗin, "Don Allah ki yi haƙuri Hajiyarmu. Kuma ki yafe masa ba don halinsa na san ba zai sake b...." "Yi mana shiru baƙar munafuka bayan duk ke ce kika haɗa komai! Ai ina sane da ke kika kira ta don ta tsine mini ki ji daɗi. To wallahi idan kika sake na riƙa ki sai na kakkarya mini ƙafafuwa baƙar almura mai fuska biyu." Idon Hajiya a kansa amma sai da ya gama amayar da abin da ke cikinsa. Saboda tunaninsa gabaɗaya ya tsaya a kan Minal ce ta kira Hajiyar ba tare da ya sani ba. Minal ta shiga rantsuwar ba ta kira Hajiya ba har da ƙwalla a idonta. Hakan ya sa Hajiyar ta yi hanzarin faɗin, "Daina yi masa rantsuwa! In dai har da gaske ke ce kika kira ni na je kamar yadda ya faɗa; to shi kuma dole sai ya yarda ke ce kika ɗauko masa hayar macen banzar, don kawai na gani ki ɓata masa suna...wallahi Jamal ka fita idona na rufe! Kuma ka fice mini daga gida ka koma wurin waɗanda suka fi mu daraja a idonk..." "Hajiy..." "Yi mini shiru sakaran banza! Allah Ya rufa maka asiri kana ƙoƙarin tona wa kanka....tashi ki tafiyar ki don na fuskanci kwata-kwata ba gaskiya yake so ba." "Ni dai don Allah ki yi mini haƙuri na tuba ba zan sake b...ke! Je ki faɗa wa Umma Ade yunwa nake ji a ba ni abin kari." Ya yi maganar alamun da Minal yake yi, tare da komawa kan ɗaya daga cikin kujerun falon ya zauna yana canza channel daga Bollywood zuwa MBC Action. Wani kallo Hajiya ta yi masa bayan wucewar Minal sum-sum kamar wadda ƙwai ya fashe wa a ciki ta nufi kitchen. Ita ma Hajiyar ta ƙarasa cikin falon ranta a jagule tana faɗin, "Yanzu Jamal matar taka ta sunnah kake kira 'Ke'?" Kansa kawai ya shafa, ba tare da ya ce komai ba. "Kowa dai ya yi mai kyau ya sani, kuma hanyoyin zubar da girma da yawa suke, waɗanda duk mutum ya zaɓi bi a can zai ci karo da gamonsa. Ina tausaya maka duk ranar da ka cika yarinyar nan ta fara boƙare maka za ka yaba wa aya zaƙin ta." A nan ma bai ce uffan, sai da Minal ta dawo ɗauke da abin karin ta ajiye masa tana ƙoƙarin barin wurin ya yi jarumtar faɗin, "Ko kaɗan ba na jin daɗin yadda kike ƙoƙarin yi mini baki koyaushe a kan wannan yarinyar. Hajiya tun da ta shigo rayuwata kika daina tausayi na babu ruwanki ko mutuwa zan yi na je na yi. Wannan dalilin ya sa ko kaɗan ba ta burge ni, saboda a kanta kike yi mini duk abin da kike yi..." "Ci abincin Kawu Bello! In dai wannan ne matsalarka daga yau ta zo ƙarshe. Da ma rashin jin ka ne yake sa muke samun saɓani, amma idan za ka gyara ni me zai sa na yi maka faɗa kawuna? Tun da kai ne uban ni ce ɗiya..." Baki buɗe ya dinga kallon Hajiyar bayan ya guma lomar dankalin turawa a bakinsa. Babu shiri wata kalar dariya ta kufce masa saboda kiran sa da sunan Kawunta. Nan take ya sarƙe ya shiga tari cikin rawar jiki Hajiya ta shiga miƙa masa ruwa a ruɗe tana jera masa sannu. Bayan ya sha ruwan dankalin ya faɗa masa yana murmushi ya sake cewa, "Ashe dai har yanzu ɗiyar Kawu Bello tana so na." Kansa ta dungure tana faɗin, "Kai dai daɗin girkin matarka ne ya ɗebe ka sarƙe." "Wace matar?" Ya yi tambaya cikin sauri, Hajiya ma ta amsa masa kai-tsaye ta ce, "Amina." Babu shiri ya shiga kakarin amai yana cewa, "Dole na sarƙe na ci abincin mayya." Kuma dai 🤣 GARE KU MASU TAMBAYA! Littafin FANSAR ƘAUNA na kuɗi ne. Ku biya ₦500 kacal ga wannan account. 9032685442 Opay. Waɗanda tura kuɗi ta opay yake bai wa wahala ku tura ta Bank Account; 1230094555 Access Bank Hadiza D. Auta Ibrahim. DAKAN ƊAKA..Complete document book 1-2. Mai buƙata 9032685442 Opay. Shaidar biya ta nan 08022014771. 10 February zan sake shi da yardar Allah. D. ✍🏼 AUTA CE [2/20, 22:02] Hadiza D. Auta: *FANSAR ƘAUNA!* *HADIZA D. AUTA* *AREWABOOKS: Princessdija.* https://chat.whatsapp.com/Edh59w1Jcgk799uIkP0CFa *LAMBA SHA BAKWAI.* "Wace irin mayya kuma?" Maimakon ya ba ta amsa, ya shiga kakarin amai tare da nufar hanyar ficewa falon gudu-gudu sauri- sauri. Ya bar Hajiya riƙe da baki tana kallon sa da mamaki ɗauke a fuskarta har ya fice. Yayin da wani zafaffen hawaye ya dinga bin fuskar Minal cike da takaicin tozarcin da yake ƙoƙarin yi mata koyaushe. Bakin famfon da ke tsakiyar gidan ya tsaya yana ta faman wanke bakinsa, don ya gama kakarin aman amma ya ƙi zuwa kamar yadda ya so. Sai da ya ja lokaci a wurin yana mayar da numfashi, sannan ya koma cikin gidan yana ɓata fuska. Sauya mazauni ya yi a cikin falon dafe da cikinsa yana faɗin, "Wash Allah!" Hajiya ta yi banza da shi kamar ba ta san ya dawo ba, hakan ya saka shi tsarguwa ya tashi tsam ya koma kusa da ita ya zauna, tare da riƙo hannunta yana faɗin, "Don Allah a nema mini wani abu na saka wa cikina Hajiyarmu, kin ga cikina babu komai a cikinsa yunwa nake ji sosai." Hajiya ta yi masa kallon uku kwabo sannan ta ƙwace hannunta tana faɗin, "Me za ka yi da abincin mayu?" Da hanzari ya rufe bakinsa saboda dariyar da ta kufce masa, saman kafaɗarta ya kwanta cikin marairaice murya ya ce, "Yarinyar ce ba ta iya komai ba Hajiyarmu. Shi ya sa ba na son cin abincinta. Amma ki yi haƙuri don Allah a sama mini wani abin da zan ci fisabilillahi Hajiyarm...." Hajiya ta ture kansa cikin ƙunar zuciya ta ce, "Wai har yaushe za ka daina halinka Jamal? To daga ni har Ade babu wanda zai sake wahalar da kansa a kanka! Mu ma abincin mayyar muka gama ci yanzun nan, kai kuma da kake tsoron a kama maka kurwa sai ka nemo waɗanda ba mayu ba su ba k..." "Hajiy..." Cikin hanzari ta katse shi da cewa, "Ba fa za a sake dafa komai a cikin gidan nan ba, sai girkin rana idan za ka jira. Idan kuma ka matsu kai da ba mayen ba ka shiga kitchen ɗin da kanka ka nemo abin da za ka ci." Ya miƙe fuskarsa ɗauke da murmushi yana faɗin, "Allah sarki ni Jamal marayan Allah!" Ya bar wurin yana sosa kansa ya nufi kitchen ɗin, zuciyarsa cike da son sake ganin Minal. Amma tsabar bauɗaɗɗen hali irin nasa ko ƙofar ɗakin bai kalla ba ya wuce abin sa. Dam, ƙirjinsa ya buga a lokacin da ya hango Minal cikin kitchen tana aiki. Turus ya yi fuskarsa babu yabo babu fallasa ya gaisa da Umma Ade, sannan ransa a haɗe ya kalle ta ya sake cewa, "Wai ke ko'ina kina nan?" Minal ta yi banza da shi kamar ba ta ji abin da ya faɗa ba. Amma ta gama gano maganarsa sarai da ita yake yi, sai dai ta ci alwashin sassauta wa kanta damuwa a kan halayensa. Hakan ya sa ta ci gaba da markaɗa kayan miyan da take yi a cikin bulanda kamar ba ta san da shi ba a wurin ba. Don duk da maganarsa ta ƙona mata rai har ta shige ɗaki ta yi kuka, amma hakan bai hana ta sakin ranta ta koma kitchen taya Umma Ade aiki ba. Saboda zuwansa gidan ya sa zaman falon ya fi ƙarfinta. "Wai ke ba kya ji ina magana ne?" Jamal ya sake yin magana yana matsawa kusa da ita cikin wata kalar murya, saboda ganin Umma Ade ta fice daga kitchen ɗin ta bar su. A nan ma banza ta yi masa tana ƙoƙarin zube kayan miyan, bayan ta gama markaɗawa a cikin wata roba kamar ba ta san yana wurin ba. Saiti da bayanta ya tsaya zuciyarsa sai zillo take yi masa tsabar sha'awar nan take da ta kawo masa farmakin gaggawa. Saboda ganin tudun bom-bom ɗin ta da shafe ɗin doguwar rigar da ke jikinta ya tona asirin albarkatun ƙugunta. "Wai ke ba ki iya gaisuwa ba ne? Ina ta magana kin yi wa mutane shiru!" Ya Yi maganar a daidai lokacin da ya kasa nutsuwa har sai da ya haɗa jikinsa da nata, yayin da ya rungumota ta baya ya shiga goga mata jijiyarsa da ke miƙe saman bom-bom yana sauke numfashi ɗaya bayan ɗaya. "Innalillahi!" Abin da ta faɗa kenan cikin hanzarin tare da zabura saboda abin da ta ji tamkar almara. Ta ja gefe fuskarta a cure tana nuna shi da hannu ta ce, "Idan maitarka ta tashi ka dinga tsayawa ga iya matan barikin da ka saba bi, saboda ka fi kowa sanin ni ba 'yar iska ba c..." "Amina! Fito ki bar masa kitchen ɗin idan ya gama abin da ya kai shi sai ki ci gaba da naki aikin!" Muryar Hajiya suka jiyo a sama, wadda ta katse mata magana babu shiri. Saboda jikin Hajiyar ya ba ta matuƙar Minal tana cikin kitchen ɗin sai ya samu abin da ya yi mata mara daɗi. Ƙwafa kawai Minal ta yi bayan ta amsa kiran Hajiyar da faɗin 'To' a kan umurnin barin kitchen ɗin. Sannan ta raɓa ta gefensa tana ƙoƙarin ficewa ya damƙo hannunta ta baya fuskarsa a haɗe duk da yanayinsa gabaɗaya ya gama sauyawa. "Ba ki isa ki mini fitsara ba! Idan kuma kika kawo mini tsageranci zan nuna miki na fi ɗanyen kai. Saboda haka ki bi ni a hankali don ba zan juri rashin mutuncinki ba." Kanta ta juya gefe riƙe da ƙugu tana girgizar jiki ba tare da ta ce da shi ƙanzil ba. Ƙirjinta ya shiga bugawa tsabar tsoron sa duk da tana ƙoƙarin nuna jarumtarta a fili. Don maganganunsa sosai suka kama mata zuciya. Amma sai da Hajiyar ta sake ƙwala mata wani kiran sannan ta shiga kiciniyar ƙwatar hannunta daga riƙon da ya yi mata, ta kasa. A ƙarshe ma fisgo ta ya yi gabaɗaya ta faɗa jikinsa ya rungume ta yana sauke ajiyar zuciya ɗaya bayan ɗaya. Ta shiga ture shi zuciyarta cike da fargabar kada Hajiyar ta shigo ta gan su a yadda suke. Babu shiri ta ƙwala wa Hajiyar kira saboda jin hannunsa ɗaya ya cafko mata bom-bom tare da zabura a lokaci ɗaya. Sautin takun Hajiyar da faɗan da take yi tana nufo kitchen ɗin, hakan ya saka fargaba ta shige shi ya yi saurin sakin ta tare da kai wa ƙafarta taki cike da haushin kwarantun kiran Hajiyar da ta yi don ta tona masa asiri. Sannan ya juya bayansa yana ƙoƙarin saita kansa da nutsuwarsa ta ƙarfi gudun Hajiyar ta gano halin da yake ciki. Cikin ruɗewa ya shiga mayar da niƙaƙƙun kayan miyan a cikin bulanda da niyyar sake niƙawa. Minal kuma ta durƙushe ƙasa riƙe da ƙafarta tana yarfa hannu daidai lokacin da Hajiyar ta iso kitchen ɗin a fusace. Idonta a kan Minal tana salati yayin da ta isa wurin kwandon kwanoni ta fisgo ludayin miya ta yi kansa da duka. Da gudu ya fice yana dariyar ƙarfin hali yana gaba tana bayansa har ta kora shi harabar gidan ta rufe ƙofar falon, bayan ta gama yi masa kashe da babbar murya tana faɗin, "Kada ka sake zuwa gidan nan daga yau! Kuma idan na sake ganin ka dawo sai na kakkarya maka ƙafafuwa. Tun da kai ba za ka bar bakin mutum ya huta ba kullum sai ka yi abin magana kake jin daɗi." Motarsa kawai ya faɗa zuciyarsa a ƙuntace ya fice gidan cikin fushi tamkar ya tashi sama. Saboda takaicin Hajiya ta hana shi rage zafi a inda aka tsokano masa sha'awarsa. Da hakan ya shiga tunanin hanyoyin da zai bi ya yi wa Hajiyar wayo ta bar shi ya dawo gidan da zama. Ita kuma Minal ya yi mata dabarar da zai samo kanta cikin sirri ya kwashi ganima ba tare da Hajiyar ta sani ba. Don da ma can amfaninta gare shi kenan tun da har zuwa lokacin bai gama gamsuwa da ingancin aurensu ba. Kuma zuciyarsa ba ta nutsu da karɓar ta a matsayin matarsa ta dindindin ba. A cikin gidan kuma Hajiya ta shiga rarrashin Minal, tare da nuna mata ta daina yi masa kuka, kuma ta bar barin yana cin zalinta a banza ita ma ta dinga ramawa. Umma Ade tana murmushin ta yi magana cikin sigar kwantar da fushin Hajiyar ta ce, "Yaran zamani ne Hajiya. Tasu kalar soyayyar kenan ki bar shiga tsakaninsu." "Babu wata soyayya sai baƙar mugunta Ade. Ana soyayyar zai kasa cin abincinta ya koma ƙoƙarin dafawa da kansa?" Hajiya ta yi maganar cikin ɗaga murya, Umma Ade ma ta sake cewa, "Abincin ne kawai ba ya ra'ayin ci, amma ko a ido ana gano yarona ba ƙaramin so yake yi wa matarsa ba. Don haka a yi masa haƙuri Hajiya zai daina in sha Allah. Saboda shi tasa salon soyayyar kenan sai an dinga yi ana nuna masa hanya." "Ba hanya ba hanyo Ade! Wace irin hanya ce ban nuna wa Jamal ya kasa bi tun tana gidansa ba? Kuma yanzun ma da na kawo ta gabana ya ce ba zai ɗaga mata ƙafa ba? To ƙaryarsa ta sha ƙarya Ade! Matuƙar ya ce zai ɓata mata rai a cikin gidan nan ni kuma wallahi ba za mu taɓa shiryawa da shi ba. Abincin gidan nan ma daga yau ya daina ci, sai dai ya je can inda babu mayu su dinga ba shi yana ci...ai Amina ba baiwa ba ce ballantana ya dinga yi mata abin da duk ya ga dama." Umma Ade ta yi shiru saboda ganin Hajiyar ta hau sama sosai. Minal ma shirun kawai ta yi amma zuciyarta ko kaɗan ba ta jin daɗin ganin yana samun matsala da mahaifiyarsa a kanta. Sai dai dole ta ja bakinta ta yi gum saboda 'yancinta ne take ƙoƙarin ƙwatar mata daga hannunsa. Jiki babu kuzari ta koma kitchen ɗin, don gabaɗaya Jamal ya gama raunata mata zuciya. Musamman abin da ya yi mata duk wani motsi abin take ta gani a cikin idanuwanta kamar almara. Da marece sakaliya Umma Ade tana shirin komawa gida Hajiya ta kira ta har cikin ɗakinta suka zauna. Cike da damuwa ta yi magana saboda abin da yake cizon ranta kuma tana ganin Aden za ta iya taimakon ta tun da ta san komai da abin da ke faruwa. "Ade, ku ne idon duniya, ina za ki samo mini sahihin maganin mata gangariya? Saboda ina so na yi maganin matsalolin Jamal a kan yarinyar nan! Duba da yadda aka yi auren babu wani kyakykyawan shirin da iyayenta suka yi mata. " "Hmmmmm!" Ajiyar zuciya Umma Ade ta sauke mai ƙarfi kafin ta ce, "Tabbas wannan shawara ce mai kyau Hajiya. Don wataƙila har da rashin gyaran ya ƙara rura rashin jituwa a tsakaninsu. Amma idan har wannan ce matsalar, in sha Allahu daga wannan karon an zo ƙarshe. Saboda akwai wata baiwar Allah maƙociyarmu ce, Ubangiji Ya lamunce mata nan ɓangaren. Don alamu ya nuna magungunanta suna aiki sosai duba da yadda matan masu kuɗi suke ta zarya a gidanta koyaushe. Idan kina so zan iya kai ki har gidanta ku tattauna ta yadda za a shawo kan matsalar cikin sauƙi." "Yawwa Ade, na gode miki sosai Ubangiji ya saka ki cikin masu kaso a ladar ke ma. Ki karɓo mini lambarta gobe idan kin zo, sai mu fara yin magana na ji waɗanne iri za mu fara saya mu gwada. Don ina son ta mallake shi gabaɗaya ta yadda kallo ma ba zai ƙara yi wa kowace mace ba da sunan shashanci. Ina so ya tsayar da hankalinsa wuri ɗaya saboda gudun ya kwaso wa kansa ciwon zamani ya bar mu da tashin hankali." "In sha Allahu hakan ba za ta faru ba Hajiya. Allah zai kare shi babu abin da zai faru da shi sai alheri." "Muna fatar haka Ade don ni ma ba na masa fatar hakan, amma mace ko namiji duk wanda bai tsaya inda Allah Ya ajiye shi ba zai haɗu da ɓacin rai watarana, matuƙar ba a kiyaye dokokin Allah aka watsar da ƙyale-ƙyalen zuciya ba." Ade ta muskuta tana faɗin, "Allah Ya ƙara tsarewa Hajiya." Daga haka suka rabu, a kan Ade za ta karɓo lambar mai kayan matan da safe idan ta dawo ta kawo mata. Bayan tafiyar Ade Hajiyar ta kira Amina da ke kallo a falo ta shigo ƙirjinta yana bugawa. Saboda kwarjini sosai Hajiyar take yi mata, ba ta samun nutsuwa idan tana ga wuri har ta ɗaga. Wuri ta samu a ƙasa ɗan nesa da Hajiyar ta zauna a ɗarare bayan ta yi sallama cikin muryar ladabi. Cike da tausayin ta a ran Hajiyar ta ja numfashi ta sauke kafin ta ce, "A cikin kayan da kika zo da su akwai sababbi?" Ta jefo mata tambayar kafin ta ƙarasa furzar da abin da ke ranta. "Babu." Ta amsa cikin fargaba saboda ba ta san dalilin da ya kawo tambayar ba. Hajiya ta sake jefa mata wata tambayar da cewa, "Me ya sa ba ki zo da su ba?" Minal ta yi shiru kawai kanta a duƙe tana wasa da yatsunta. Fahimtar akwai abin da ke ranta wanda ba ta son faɗa Hajiyar ta sake cewa, "Dole ne ki yakice duk wani abu da ke nisanta ki da mijinki. Sannan ki iya ɗaukar wankan da zai dinga jan hankalinsa gare ki. Don ba zai yiwu ki zauna a haka babu wani gyara ko kissa irin ta mata ba. Ki koyi abubuwan da za ki shawo kan mijinki da su a cikin ruwan sanyi ba tare da kowa ya sani ba. Saboda na san wane ne Jamal yana, yana son mace wayayyiya. Wataƙila har da hakan ya taka muhimmiyar rawa wurin nisanta ki da shi. Don haka ki bi matakan gyara kanki ta hanyar da za ki farauto zuciyar mijinki daga matan banzan da ke ƙoƙarin janye miki shi. Saboda ni uwa ce, kuma yadda ba na son abin da zai samu 'ya'yana haka ba na son abin da duk zai same ki mara daɗi." "Na gode Hajiya." Zancen Minal kenan cikin wata murya bayan Hajiya ta tsahirta da bayani. Minal ta shiga share ƙwallar da ta wanke mata fuska cike da tausayin kanta ta ɗan muskuta ta gyara zamanta sannan ta ce, "Jikina yana ba ni koyaushe Nur za ta iya dawowa ga mijinta. Shi ya sa ba na son amfani da komai a cikin kayan lefenta." Kallon mamaki Hajiya ta dinga yi mata tsawon mintuna kafin ta ce, "Daga yau zancen A'isha za ta dawo ga Jamal ya fita daga cikin zuciyarki. Saboda matuƙar ina numfashi ba zan taɓa bari ya yi zaman aure da ita ba. Kaya kuma naki ne halak malak tun daga ranar da aka ɗaura aurenki da Jamal. Don haka komai na lefen naki ne ki yi amfani da duk abin da kike so." "To Hajiya." Minal ta yi maganar tana ƙoƙarin share hawayenta, zuciyarta cike da farincikin jin tabbaci daga bakin Hajiyar, bayan ƙwarin gwiwar da ta cusa wa zuciyarta ya faranta mata rai sosai. A gabanta Hajiyar ta kira Jamal tare da sanar da shi ya haɗa kan lefen duka direbanta zai zo ya karɓa. Sannan tana sauke wayar ta kalli Minal ta ce, "In sha Allah gobe zan sa a kai ki wurin lalle da kitso. idan lokaci ya bayar har wurin masu gyaran jiki duka za ki je a yi miki duk abin da ya dace. Saboda ina so ki yi amfani da wannan damar ta zamanki cikin gidan nan ki ƙwato darajarki wurin mijinki." "Na gode Hajiya. Allah Ya ƙara lafiya da nisan kwana." Daga haka ta ce, "Ta shi ki je, kuma ki tabbatar kin saki jiki kin cire tunanin A'isha a cikin ranki." GARE KU MASU TAMBAYA! Littafin FANSAR ƘAUNA na kuɗi ne. Ku biya ₦500 kacal ga wannan account. 9032685442 Opay. Waɗanda tura kuɗi ta opay yake bai wa wahala ku tura ta Bank Account; 1230094555 Access Bank Hadiza D. Auta Ibrahim. DAKAN ƊAKA..Complete document book 1-2. Mai buƙata 9032685442 Opay. Shaidar biya ta nan 08022014771. 10 February zan sake shi da yardar Allah. D. ✍🏼 AUTA CE [2/20, 22:02] Hadiza D. Auta: *FANSAR ƘAUNA!* *HADIZA D. AUTA* *AREWABOOKS: Princessdija.* https://chat.whatsapp.com/Edh59w1Jcgk799uIkP0CFa *LAMBA SHA TAKWAS.* Minal ta fito daga ɗakin zuciyarta wasai tamkar an sauke mata wani ƙaton dutsen da ke saman kanta. Ta kasa zama falon ta yi ɗakin Amna jikinta yana rawa ta danna wa Innarmu fulashin. Saboda ta gwada kiran ta ji ashe babu ko ficika a cikin wayar. Minti biyu tsakanin fulashin ɗin ta sai ga kiran Innarmu ya biyo baya. Da zumuɗi ta ɗauki wayar tun kafin su gaisa ta ce, "Innarmu Hajiya ta ce ko Nur ta dawo ba za ta bari Jamal ya aure ta ba. Kuma..." "Ke wai ba ki da wani zance a duniya a yanzu sai na Aisha ne? Tsoron me kike ji bayan ke ce da komai yanzu sai yadda kika ga dama za ki yi? To karkaɗe kunnuwanki ki ji; Aisha ko ni na haife da cikina kika samu irin wannan damar ban ce ki yi wasa da ita ba. Ballantana wadda daga ni har ke ba mu san haƙiƙanin danginta ba....ko kin taɓa ganin uwarta ko dangin Babanta sun zo gidanmu?" Minal ta yi hanzarin girgiza kanta tamkar tana gabanta suna kallon juna. Shirun da Innarmu ta ji ta yi ya sa ta sake cewa, "To ki kiyaye ni Amina! Zancen Aisha ya fita daga bakinki, don ba uwar mijinki ba ko ni nan ba zan taɓa bari ki yi kishi da Aisha a gidan aurenki ba. Saboda ita ce ta bar ki shi da kanta babu wanda ya yi mata dole, kuma yanzu ba ta isa ta dawo ta ce za ta hargitsa mana farinciki b..." "Innarmu ina gidan su Jamal tun jiya Hajiya ta ce na dawo gabanta na zauna." "Ki zauna kamar ya ya? Me kika je yi a gidan nasu har da kwana?" Innarmu ta yi hanzarin yi mata tambayar cikin wata kalar murya alamun ranta ya ɓace kuma ƙiris take jira ta dira kanta da masifa. Fahimtar hakan ya sa Minal ta sauya zancen da cewa, "Tafiya ya yi shi ne ta ce na zauna kafin ya dawo." "To..tooo..da sauƙi har na ji sanyi. Amma farko har hankalina ya tashi na ɗauka ko wani laifi kika yi wa mijin ya ce ki bar masa gida kika koma can. Amma don dai tafiya Allah Ya tsare hanya ya dawo lafiya ki koma gidanki ki ci gaba da bautar aure. Kuma wallahi kin ji na rantse ko da wasa kada ki bari ki masa laifin da zai kawo ƙarar ki gidan nan! Kina gani ni ma haƙuri nake yi da Babanku sama da shekaru na kafe sai mutuwa. Don haka ke ma babu fushi babu yaji ballantana kawo ƙarar miji a gida. Duk tsanani ki zauna sai mun ga abin da ya ture wa buzu naɗi har zuwa lokacin da ki ci moriyar haƙurinki. Amma a ce kina cikin wannan kafcecen gida tsawon wata da kwanaki ko katin kira na ba ki mallaka ba, a ce ba ki da sai yi wa mutane fulashi...?" "Innarmu yau kaɗai ne fa!" Ta yi maganar cikin wata murya tare da turo baki alamun ta ji haushin maganar. "Kin dai yi ko? Kuma ko ba ki taɓa ba yau kin fara...ki dai kwantar da hankalinki daga mu har ke a gaba Za mu ji daɗin auren nan. Burina ɗaya ne a yanzu ki samu ciki ki fara ajiye 'ya'ya a cikin gidan." Minal ta yi hanzarin rufe bakinta cike da jin nauyin maganar tana 'yar dariya ta ce, "Cikin lafiya Innarmu?" "A'a cikin ciwo!" Ta amsa mata a fusace sannan ta katse kiran. Minal ta sauke wayar daga kunnenta tare da sauke wata ajiyar zuciya mai ƙarfi ta ce, "Innarmu-Innarmu! Ke komai sai kin mayar da shi faɗa...wai Allah wai ni ce zan yi ciki...ko ya zan yi idan na samu cikin?" Ta ƙare maganar tana shafa cikinta tana dariya saboda hango ta da ƙatoton ciki a gaba taku da ƙyar tana tafiya. Ta jima a ɗakin kwance saman gadon Amna tana juya zancen Innarmu, kuma zuciyarta cike da kewar Jamal da tunanin abin da ya yi mata kitchen. Nan take ta tsinci kanta cikin shauƙi, kuma karo na farko kenan da ta ji a ranta tana sha'awar ya kasance ta. Sai da aka yi sallar magrib sannan ta daina tunane-tunanen da ke ranta ta miƙe ta ɗoro alwala. Tana kan sallaya har aka yi Isha ta gabatar da ita sannan ta fito falo. Daidai lokacin da Hajiya ta fito daga ɗakinta ita ma bayan ta gama sallar da nufin cin abincin dare. Minal isa gabanta cikin sauri ta durƙusa har ƙasa ta gaishe ta. Hajiya ta dafa kanta daga tsayen tana sa mata albarka cike da jin daɗi ita tana faɗin, "Amin Hajiya." kafin Hajiyar ta ɗora tambayar, "Kin ci abinci kuwa?" Minal ta girgiza tare da miƙewa tana faɗin, "Bari na fara kawo miki naki yanzun nan." Ta yi hanzarin juyawa zuwa kitchen, sai da ta haɗo mata komai a kan tire har da ruwa, sannan ta kawo gabanta ta ajiye cike da jin daɗi ta dinga saka mata albarka. Ta koma ita ma ta zubo nata tuwon kaɗan a plate, saboda nauyin Hajiyar da take ji ba zai bari ta saki ciki ta kwashi tuwon yadda take so ba, duk da ya kasance best food ɗin ta waton tuwon shinkafa miyar taushe. Ganin tuwon kaɗan Hajiya ta yi murmushi kawai ammaba ta ce mata komai ba. Suna ta kallon tashar Arewa24 suna cin abincin har Minal ta cinye nata ta miƙe da nufin kai plate kitchen ta wanke. Hajiya ta kalle ta cike da kulawa tana faɗin, "Da ma jira nake yi ki gama cinyewa na ƙara miki wani. Oya kawo plate na zuba miki wannan abincin da kika zubo ko yaron goye ba zai ƙosar ba." Cike da jin kunya Minal ta rufe ido tana faɗin, "Na ƙoshi fa.." "Ba wani ƙoshi da kika yi, kin ga abincin nan sai kin cinye shi duka, loma ɗaya ban ce ki bar mini ba." Minal ta zura hannu tana ƙoƙarin karɓar plate ɗin suka jiyo ƙarar buɗe gate da shigowar mota cikin gidan. Ƙirjin Minal ya buga dam-dam, saboda ko ba a faɗa jikinta ya ba ta Jamal ne ya dawo gidan. Hajiya ta kalli ƙofa bayan ta haɗe rai ta ce, "Waton ya rantse sai ya dawo gidan don ya saka bakina surutu ko! To ai shikenan ya zo ga ni ina jiran sa...ina za ki je ke kuma? Dawo ki zauna ki ci abincinki. Ai wannan karon bai isa ya yi miki komai ba, matuƙar ina wurin nan zaune." Ta yi maganar idonta a kan Amina da ke ƙoƙarin barin falon ta shige ɗaki. Jiki babu kuzari ta dawo falon a ɗarare ta zauna ƙirjinta yana bugawa. Shigowar Jamal da wani mai aikin Hajiya ya sa muka bi su da kallo, saboda ganin suna shigowa da akwatunan lefen Nur ɗaya bayan ɗaya har ƙwara ƙwara bakwai kamar yadda suke a saiti. Fuska babu yabo babu fallasa bayan fitar mai aikin Hajiya ta kalli Jamal tana faɗin, "Shigar mata da su ɗakin Amna!" Kallon ta ya yi cikin sauri baki a sake kamar ya ce wani abu, tuno abin da ke ransa da wayon da yake son yi wa Hajiyar; cikin hanzari ya saita kansa ya miƙe yana gyara zaman wuyan rigarsa. Kamar ya yi dariya amma ya fuske ya fara jan akwatunan da ɗaiɗaya yana kaiwa har ya gama. Fuskarsa a washe ya kalli Hajiya da ke fuske bayan ya kalli Minal ita ma fuskarta a haɗe ya ce, "Ki ce ta gaishe ni Hajiya." Banza Hajiyar ta yi masa tsawon sakonni kafin ta ce, "Dole ne sai ta gaishe ka?" "Yanzu fisabilillahi ban cancanci ta gaishe ni ba Hajiya? Wai don Allah me na yi da kuke sauya mini fuska Kamar na yi wani ƙatoton laifi?" Shi ma ya jefo mata wasu tambayoyin yana 'yar dariya. Saboda ya fahimci sai biyo da siyasa ko zai samu ciyo kan Hajiyar har ta saurare shi. Ganin ta yi masa banza tana ƙoƙarin haɗa kan kayan abincin da ke gabanta, ya sake mayar da kallonsa a kan Minal da idonta suke a kan Tv. Alamun kallon ya tafi da ita, amma a zahiri hankalinta gabaɗaya yana kansa da duk wani motsinsa. Kan kujerar ya sauko ya yi durƙuso gaban Hajiyar gwiwa biyu ya haɗa hannuwansa wuri ɗaya alamun roƙo ya ce, "Na tuba ki yafe ni don Allah Hajiya Mummy. Fushinki gare ni tsaf zai iya jefa ni cikin gararin rayuwa. Idan kuma so ake yi mutum ya bi duniya ai sai ya bi tun da ba a son s..." Ya miƙe da nufin barin wurin fuska a haɗe, yayin da ta yi hanzarin cafko ƙafar wandonsa tare da kai masa duka a ƙafar da murfin kula tana faɗin, "Ka bi duniyar, da ma ka saba bin 'ya'yanta don ka bi ta ai ba wani abu ba ne. Sannan kuma ko na yafe maka ka sake kyarar Amina ko yi mata wani abu mara daɗi za mu ƙara hawa sama da kai." "Ai na tuba yanzu kuma na gane kuskurena Hajiyarmu. A ba ni abinci idan na ƙoshi sai na ƙara neman wata yafiyar." Kallon uku kwabo ta yi masa mai ɗauke da harara sannan ta ce, "Mayya ta dafa fa, na san kuma ba za ka iya ci b.." "Zan ci, a ba ni a hakan tun da kina so na ci ai dole na ci." Babu shiri ta yi 'yar dariya tana faɗin, "Oh! Ni ce ma nake so ka ci ashe? To na fasa son ka bar shi kawai." "Ni nake so a ba ni da kaina Hajiyarm...Ke tashi ki je ki kawo mini kin wani share mutum kamar ba san da shi b..." Irin kallon da Hajiyar ta wurga masa ne ya fara sassauta murya yana sosa kai saboda ko kaɗan ba ya son shirinsa ya lalace. Minti uku a tsakani bayan Hajiya ta gama nazarí sannan ta ce, "Amina kawo masa abincin, kuma kaɗan za ki zuba masa abincin mayu a ci da yawa." Murmushi Aminar ta yi sannan ta bar wurin da plate ɗin da ta ci, cikin rashin sani ta juya juya bom-bom saboda saurin da take yi. Babu shiri ya bi ta da wani kallo har sai da Hajiya ta yi gyaran murya, sannan ya ankara da abin da yake yi ya koma sosa ƙeya yana faɗin, "Ni mamaki yarinyar can take ba ni Hajiya. Shikenan ta raina ni kin ga irin kallon rainin da ta yi mini har da su gwalo?" "Duk abin da ta yi maka kai ka ja." Daga haka kowa ya yi shiru har Aminar ta dawo ɗauke da tuwon ta ajiye gabansa. Babu ɓata lokaci ta shiga kwashe kayan da Hajiya ta ci abinci ta kai kitchen ta wanke, sannan ta nufi ɗakin Amna da nufin yin kallo a wayarta. Saboda tsawon kwanaki babu data a wayarta kuma babu kati, hatta bonus da take mora shi ma ya ƙare. Sannan account ɗin ta babu ko ficika sai kwabo 31 da ke zaman daɓaro mara amfani. Ta shiga neman wayar a cikin ɗaki lungu da saƙo ba ta gan ta ba, tsabar nema har inda Jamal ya ajiye akwati ta duba ba ta gani ba. Kuma iya sanin ta Jamal ne kaɗai ya shiga ɗakin kuma zuciyarta ta ba ta tsaf zai iya ɗaukar ta kamar yadda ya taɓa yi mata. Cikin sauri ta fito falon da nufin ta ce ya ba ta wayar, saboda da ita take rage kaɗaici a wasu lokutan. Sai dai daga shi har Hajiyar ba sa falon, hannu ta ɗora a ka cikin rawar jiki ta fice harabar gidan saboda sautin tashin motarsa da ta jiyo. Bakin motar ta isa a daidai lokacin da yake ƙoƙarin gyara zaman motar da sassarfa ta da leƙa shi tana faɗin, "Wayata za ka ba ni." "Ok, buɗe ki shigo ki karɓa." Ya yi maganar cikin ko-in-kula yana haɗe fuska. Hakan ya sa ba ta kawo komai a ranta ba ta buɗe murfin ta zauna tare da faɗin, "Ba ni na koma sauri nake y..." Jawo ƙofar da ta ga ya yi da sauri tare da kwanto mata a jiki ya mayar da gilasai ruf ya rufe ko'ina jikinta ya ɗauki rawa. Cikin tashin hankali ta shiga magana idonta a zare ta sake cewa, "Ka...ka.. ba ni wayar na ce maka.. sauri nake yi ba na son Hajiya ta neme ni ba ta gan ni ba..ban ma faɗa mata ba da zan fito." Banza ya yi da ita tana ta surutun yana ƙoƙarin cinna kan motar waje kamar bai san tana yi ba. "Malam ina za ka kai ni a cikin daren nan? Ko ba ka ji ina zancen ka ba ni wayata ba?" Ta ƙare maganar a ruɗe tana kallon gefe da gefen titi cikin firgici kamar wadda aka sato. "Idan na ji kuma sai me?" Ya Yi maganar a fusace, ita ma ta amsa masa cikin isa ta ce, "Sai ka ba ni tun da ba kai ka saya mini ba!" Wani kallo ya yi mata kafin ya yi guntun tsaki ya ce, "A Kan wannan jahilar wayar kike mini surutan banza a sama?" "E ɗin, kuma idan ma daƙiƙiya ce mutum bai saya mini ba ballantana ya yi iko da ita." "Ni kike ɗaga wa murya?" Ya yi tambayar yana nuna kansa tare da ƙure ta da kallo alamun ta gama kai shi bango. Kuma sai sharara gudu yake yi a saman titi kamar wanda zai tashi sama. To fa! 😆 GARE KU MASU TAMBAYA! Littafin FANSAR ƘAUNA na kuɗi ne. Ku biya ₦500 kacal ga wannan account. 9032685442 Opay. Waɗanda tura kuɗi ta opay yake bai wa wahala ku tura ta Bank Account; 1230094555 Access Bank Hadiza D. Auta Ibrahim. DAKAN ƊAKA..Complete document book 1-2. Mai buƙata 9032685442 Opay. Shaidar biya ta nan 08022014771. 10 February zan sake shi da yardar Allah. D. ✍🏼 AUTA CE [2/20, 22:02] Hadiza D. Auta: *FANSAR ƘAUNA!* *HADIZA D. AUTA* *AREWABOOKS: Princessdija.* https://chat.whatsapp.com/Edh59w1Jcgk799uIkP0CFa *LAMBA SHA TARA.* Wani masifaffen tsoro ya kama Minal cikin ruɗewa ta shiga haɗu hannu wuri ɗaya hawaye yana fareti a kan fuskarta ta ce, "Don Allah, don girman Ubangiji ka mayar da ni inda ka ɗauko ni, tun kafin Hajiya ta yi nema na ba ta gan ni ba." Banza ya yi mata ba tare da ya ce da ita kanzil ba, ya ci gaba da tuƙinsa fuska a cure tamkar bai taɓa yin dariya ba. Hakan ya sa ita ma ta haɗe rai cike da jin haushin ya ƙi kula ta ballantana ya ji roƙon da take yi masa, ya mayar da ita kada Hajiya ta ga laifinta. A tsure ta shiga kallon titi tana shesshekar kuka zuciyarta cike da tunanin inda zai kai ta. Har ya shiga harabar wani wuri mai ƙaton gate. Ƙirjinta ne ya buga dam-dam, a lokacin da ta ɗaga kai ta kai kallonta gan sunan da ke saman allon bangon ginin. Inda aka rubuta... HOTEL, da hanzari ta dawo da kallonta gare shi a firgice ta yi magana cike da tsoro ta ce, "Me kake nufi da ni da za ka kawo ni hotel? Ko an faɗa maka ni 'yar iska ce za ka kawo ni matattararku ta 'yan bariki?" Wani kallo ya yi mata mai ɗauke da dariya sannan ya gyara parking yana faɗin, "So nake ke ma ki iskance kamar yadda mu ma muke gogaggun 'yan barikin da kika san..." "Wallahi ni kam ba Zan taɓa lalacewa ba, ku dai da kuka ɗauki duniyar wata tsiya ku ci gaba da abin da kuka sa gaba, da ma can kowa da kabarinsa kuma babu wanda za a saka tare da wani, ballantana laifin wani ya shafi wani." "Ke dai kika san..." Kafin ya dire zancensa kiran Hajiya ya shigo wayarsa, da hanzari ya dafe kansa yana faɗin, "Ya Salaam! Ashe na manta ban kashe wayar ba Hajiya ta kira" Wani sanyin daɗi ya ratsa mata a zuciyata, jiki babu kuzari ya ɗauki wayar kamar ba ya so yana haɗe rai, kuma tun kafin ya ji abin da Hajiyar za ta faɗa ya yi hanzarin faɗin, "Ga mu nan zuwa yanzun nan Hajiya, da ma ita ce ta roƙe ni don Allah na kawo ta shopping...na so ta bari sai gobe ta matsa sai da na kawo t...to...ki yi haƙuri yanzu zan kawo t.. ." Ƙit Hajiya ta katse kiran saboda ƙufular da ta yi a kan zancensa. Don ta sani sarai tsarinsa ne Minal ba za ta ce ya fita da ita a cikin daren ba. Tsaki ya ja mai ƙarfi tare da kai kallonsa gare ta cikin harara ya ce, "Idan ma addu'a kika yi mini shi ya sa na manta ban kashe wayar ba har Hajiya ta kira ni, to ba ta ci ba. Don tun da na yi niyyar taɓa ki sai na aiwatar da ƙudurina ko ba yau b..." "Allah ma ba zai ba ka sa'ar cutar da ni ba." Ta ƙare maganar tana murguɗa masa baki, wani kallo ya yi mata alamun zan koya miki hankali. Kafin ya koma motar ya rufe ko'ina ruf ya janyo ta jikinsa tana masifa yana abin da zuciya take ta kwaɗaita masa a kanta, kafin ya yi magana cikin izza da gadara ya ce, "Da ma kin tsaya, don ƙauyancinki ba zai hana ni yin abin da na ga dama ba." Ta shiga kai masa duka tana ture shi saboda ƙirjinta da ya kai wa cafka hannu biyu yana murza tare da wani kalar nishin da bai san yana yi ba. Babu zato ta ji ya cafko bakinta cikin kiɗima ta ƙara zabura tana kai masa duka da hannuwanta amma hakan bai hana shi yi wa bakinta tsotson lollipop ba. Duk da mutsu- mutsun da take yi, sai da ya ga dama don kansa sannan ya sake ta, ya koma dafe jijiyarsa tare da mayar da numfashi cikin sauri tsabar fita daga hayyacin da ya yi cikin ɗan lokaci. Kuka ta fashe tana faman goge bakinta da take jin kamar babu leɓuna a jikinsa. Kafin ta koma tofar da yawu tana faɗin, "Mayen banza kawai." Motar ya tayar fuskarsa a haɗe yana faɗin, "ki gode wa Allah kuma ki gode mini kin samu har na haɗa bakina da naki. Sannan ba na son kayan ƙazanta ki daina yi mini tofe-tofen yawu a cikin mota. Ni ma tsautsayi ne ya aike ni ba don ina so na yi ba. In ban da ƙaddara ma me zan yi da mace irin ki baƙauyiya a komai sai kin nuna halinki na ƙauyanci, ke kullum babu ranar da za ki waye...mtssss!" Ya yi maganar tare da hawa kan titi aguje tamkar an koro shi. Saboda kiran wayarsa da Hajiya ta ke ta yi wani bayan wani babu ƙaƙƙautawa. Sanin dalilin kiran nata ya sa ya ƙi ɗauka sai dai ya ƙara ƙaimin gudun da yake yi. Minal kam wani kallon banza ta yi masa ba tare da ta sake cewa komai ba, amma ta daina tofin yawun kamar yadda ya ba ta umarni, saboda har cikin ranta tsoron sa take ji. Gudun ya ƙara yi mata wani rashin mutuncin don ta fahimci babu ƙiren kunya a cikin idanuwansa. Sai da ya tsaya wani Shopping Mall ya saya mata kayan maƙulashe, sannan suka isa gidan Hajiyar misalin ƙarfe goma da rabi na dare. Bakin ƙofar gidan ya tsaya saboda tsoron ya shiga ta rufe sa da faɗa. "Ga shi na kawo ki, sai ki san yadda za ki ƙarata idan kika shiga ciki don ni babu ruwana." Minal ta buga masa wata jar harara tana ƙoƙarin buɗe ƙofar ta fice ya damƙo hannunta ya sake cewa, "Ko da wasa kika ce mata ni ne na tafi da ke sai na nuna miki ba a mini ƙarya. Don haka ga ledar abin da kika sa na raka ki siye nan, a ci daɗi lafiya." Cike da mamaki ta bi shi da kallo a ranta tana jinjina ƙarfin hali irin nasa da juya zance zuwa yadda yake so, tamkar mai bishiyar aljanu a saman kansa. Idan ban da haka ta ya ya zai sace ta tana masa magiyar ya mayar da ita, amma kuma ya dawo faɗin raka ta ya yi? "Hummmm!" Iya abin da ta faɗa kenan saboda ya gama ɗaure ta da jijiyoyi. Don ta san dole ne sai Hajiya ta yi mata faɗan me ya sa ta bi shi ba tare da ta sanar da ita ba. Bai kashe hasken motar ba har ta kai bakin ƙaramar ƙofar shiga gidan, sannan ya shiga buga mata horn ɗii! Saboda tuno wayarta da ke hannunsa. Kamar ta juya amma sanin rainin hankalinsa ya sa ta shige gidan, ba tare da ta bi umarnin zuciyarta da ke ba ta shawarar komawa ba. Kiciɓis ta yi da maigadi yana ƙoƙarin buɗe gate cike da zaton gidan Jamal zai shiga da motar shi ya sa yake zuba horn. Kai-tsaye ta shige cikin gidan ta bar su suna magana, saboda ganin zai buɗe masa gate ya fito daga motar yana miƙa masa wayar Minal, tare da sanar shi gidansa zai koma ba zai samu damar shiga gidan ba. Suka yi sallama tare da addu'ar Allah Ya tashe su lafiya sannan ya faɗa motarsa ya juya zuwa gidansa. Zuciyarsa cike da tunanin yadda zai kwashe da Hajiya idan safiya ta waye ya shiga yi mata ina kwana. Minal kam jiki babu kuzari ta tsaya bakin falon tana muzurai, tamkar wadda ƙwai ya fashewa a ciki ta murɗa ƙofar, zuciyarta cike da roƙon Allah Ya sa Hajiyar ba ta cikin falon don ta saɗaɗa ta shige ɗakin Amna ba tare da ta gan ta ba. Sai dai tana jefa ƙafarta suka yi ido biyu da juna, gabanta ya ƙire ya faɗi jikinta ya ɗauki rawa. Sum-sum take taku kanta a ƙasa har ta isa inda take zaune ta tsugunna tana miƙa mata ledar ta ce, "Shi ya saya mini." Wani kallo Hajiya ta yi mata fuskarta a haɗe, wanda ya saka hanjin cikin Minal murɗawa babu shiri. Kafin ta baje ƙasa kamar mai neman yafiya ta fara magana cikin rawar murya ta ce, "Wayata ya ɗauka shi ne na je karɓa ya tafi da ni ina ta roƙon ya dawo da ni kada ki yi faɗa, amma sai da ya kai ni shagon da muka je ya yi mini wannan sayayyar..." "Da ma na san zai aikata fiye da hakan. Shi ya sa na dame shi da kira a kan ya dawo da ke. Saboda haka gobe kada ki sake bari yana fita yawo da ke bayan har yanzu bai san darajarki ba." Ta ɗan tsahirta da maganar kafin ta sake cewa, "Dole ne ki iya jan aji idan kina son ki ƙwato martabarki ta mace, wadda yake ƙoƙarin wofintarwa a iska. Don haka ki daina sakar masa fuska har zuwa lokacin da zai gano amfaninki." Kai kawai Minal take ɗaga mata alamun gamsuwa da shawarar da take ba ta, ba tare da ta iya haɗa ido da ita ba tsabar kunya da muzantar da ta yi a gabanta. Sallamar da maigadin ya yi a bakin ƙofar shiga cikin gidan, ya sa Hajiya ta amsa tare da miƙewa ta nufi ƙofar. Minal ta kasa motsin kirki ballantana ta tashi wurin har Hajiya ta dawo da wayarta a hannu ta miƙa mata tana faɗin, "Ga wayarki, ki je ki yi arwala ki kwanta. Ni ma na shige Allah Ya tashe mu lafiya." "Amin." Ta amsa cikin maƙoshi jiki a sanyaye ta yi ɗaki da ledar don Hajiya ta bar ta da ita a hannu ba ta karɓa ba. Ta jima zaune a bakin gadon da tagumi tana nazarin halin Jamal da shawarar Hajiya. Sai da ta fahimci dare ya ƙara yi sannan ta koma buɗe ledar tana kallon chocolate da kalolin biscuits da ke ciki. Murmushi ta yi babu shiri saboda tuna Jamal da birkitaccen halinsa mai wuyar fassara. Sannan ta mayar da ledar gefe ta ajiye bayan ta ƙulle, da nufin sai Hajiya ta ga abin da ke cikin ledar kafin ta taɓa. Daren ranar ma ta yi bacci mai ɗauke da mafarkan Jamal a cikin yanayin da dole sai da ta yi wankan tsarki kafin ta yi sallar asuba. Saboda sabon abu ne da ya zamo mata tamkar almara, wanda take kallon sa tamkar wani babban zunubi, don ta kasa yardar wa zuciyarta aurenta da shi mai inganci ne kamar kowane auren da ake ɗaurawa. Ta yi lattin tashi bayan ta koma barci bayan asuba. Don har Umma Ade ta zo gidan ba ta tashi daga nannauyan barcin da ya kwashe ta ba. Hajiya da Umma Ade a falo bayan sun gama gaisawa ta miƙa mata lambar mai kayan matan tana cewa, "Na sanar da ita za ki kira ta. Ashe ita ma tana rubuce-rubucen littafai a cikin waya. Ni ma a bakin matan su Nura na ji labarin kuma sunanta Surayy, su ma sun yaba sosai da ingancin kayanta. A cewarsu babu asara ga sayen kayanta saboda amfaninsu ya linka ma ƙudin da za a kashe." "Allah Sarki, Ubangiji Ya ci gaba da dafa mana gabaɗaya. Kuma na gode miki sosai Ade, bari na kira ta tun yanzu saboda yaron can ya fara wuce gona da iri a kan yarinyar nan. Ga shi kuma ba na so ya same ta a yadda take, don zai fi raina ta idan bai kamu yadda ake so ba." Umma Ade ta yi murmushi bayan ta ce amin, sannan ta ƙara da cewa, "A dai bi mini yaro a hankali Hajiya kada a yi masa mugun kamun da zai kasa zuwa gaishe mu." "In dai ta riƙe mana shi da kyau to ya sha zamansa mun yafe zuwan, mu za mu dinga zuwa har gidansa ganin shi. Don ya fi alheri a kan ya ɗebo mana wata wutar da za ta gagare mu kashewa." Suka yi dariya gabaɗaya, saboda sigar da Hajiya ta yi maganar tare da kai wa Aden hararar gefen ido. Kafin ta ƙara da cewa, "Ai Ade yaron nan naki babban riƙo kawai ya dace da Shi, saboda kansa rawa yake yi ba ya shayin yin gaban kansa. Wannan dalilin ya sa na jinjina wa budurwarsa Aisha, saboda ba ƙaramin aiki ta yi ba kafin ta raba shi da shashancin da ya mayar ba a bakin komai ba." "Hmmmm! Allah dai Ya ƙara shirya mana su Hajiya. Amma yaran zamani kowa da kalar taɓararsa. Shi ma in sha Allahu daga wannan lokacin ya gama tasa kalar ƙurciya." Hajiya tana 'yar dariya ta ce, "Ke dai ba kya so a ga laifinsa, tafi ki yi aikinki lokaci yana tafiya." Umma Ade ta wuce kitchen, yayin da Hajiya ta nufi ɗakinta da takardar lambar Surayya a hannunta. Wuri ta samu a bakin gadonta ta zauna, bayan ta jawo wayarta ta fara saka lambobin kamar haka 08032773332, zuciyarta cike da ɗokin samun biyan buƙatarta cikin sauƙi. Ɗii! ɗii! Wayar ta shiga ringing a lokacin da Hajiya ta danna kira, aka yi sa'a babu jinkiri ta ɗaga. Bayan sun gaisa Hajiyar ta gabatar da kanta tare da bayanin ita ce wadda ta saka Ade ta nemo mata lambarta. Suka sake gaisawa a mutumce kafin Hajiya ta yi mata bayanin dalilin neman ta. Ajiyar zuciya Surayya ta yi kafin ta ce, "A shawarce, kafin a ba ta kayan matan da ta yi amfani da su, yana da kyau ta fara shan maganin infection kafin su. Saboda wani lokaci ko an sha maganin mata idan akwai infection ba zai bari a ga amfanin kayan yadda ake so ba." "To, babu damuwa. Yanzu a cikin magungunanki bayan na infection wane da wane kike da shi? Kuma nawa ne kuɗin kowanne?" Surayya ta yi murmushi mai sauti kafin ta ce, "Akwai ingantattun kayan gyara na Chad daga Bojuwa Herbals. Sai Sanyi flusher mai wanko dukkan sanyin da yake maƙale a mahaifa da jijiya. Sannan akwai ingantacciyar kazar sababi ta saiwowin Chad mai ciko da mace ta haɗe tamkar sabuwar amary..." "Ita fa wannan amarya ce kuma sabuwar. A ganin ki babu wata matsala idan ta yi amfani da maganin da zai ƙara haɗe ta?" Hajiya ta yi hanzarin tambaya saboda jin ƙara matsewa gudun Jamal ya ji wa yarinyar mutane ta shiga uku. Surayya ta yi murmushi sannan ta sake cewa, "Babu wata matsala Hajiya, ai duka cikin gyara ne irin wanda kowace mace ake so ta yi tun daga kan budurwa har wadda ta taɓa haihuwa. Kada ki damu zan haɗa mata da hakin daka mai kama jiki na mussaman. Tare da tsumin saiwowin da sai isassum mata ke shan su. Don kayanmu duka na Chadi ne masu matukar inganci da rashin illa." Cike da jin daɗi Hajiya ta ce, "To, ma sha Allah, sai ki faɗo mini kuɗin nawa ne gabaɗaya? Sannan sai ki turo account na ba ki kuɗin gobe Ade ta zo mini da kayan, ko kuma na aika direba ya karɓo mini a hannunta. Ubangiji ya ba mu ladar gabaɗaya." "Amin-amin Hajiya. Allah Ya ƙara rufa asiri." Daga haka suka yi sallama, Surayya tana ƙoƙarin ajiye wayar Hajiya ta sake cewa, "Mun gama magana amma ba ki faɗa mini sunanki ba." "Sunana Surayya Dee, marubuciyar littafin HALIN YAU." Sai a lokacin ta tuna ta ji sunanta a bakin Ade. Cike da jin daɗi ta ce, "Madalla Surayya, Allah Ya yi albarka, in sha Allah zan haɗa ki da wata ɗiyata idan ta shigo garin. Ita ma tana son irin kayanku sosai, daga nan har Sokoto ana aika mata kaya har zuwa Yobe. Amma tun da ga ki a cikin garin Kano idan muka ji daɗin kayanki zan ba ta lambarki ku dinga zumunci, don na yaba da kirkinki duk da ban taɓa ganin ki ba." Surayya ta yi murmushi cike da jin daɗi ta ce, "Babu komai Hajiya, in sha Allah za ku yaba da kayan fiye da yadda kuke zato. Saboda bayan abubuwan da na lissafa miki har da haɗin amarya (Bridal package), haɗin maijego da uwargida duka ina yi." "Allah Ya ƙara dafa miki, kuma ya tsare ki da sharrin da ke ciki. Kada ki manta ki turo mini account zan sa a tura miki kuɗin yanzun nan." Daga haka suka yi sallama kowa ya ajiye wayar. Hajiya ta yi jim tana nazarin yadda za ta tsayu a kan Minal ta yi amfani da kayan daki-daki. Ƙir shigowar saƙo a wayar ya sa Hajiyar ta duba, a fili ta furta, "Ma sha Allah, saura kai uban rawar kai, kai ne za ka biya kuɗin ko nawa ne daga aljihunk...." GARE KU MASU TAMBAYA! Littafin FANSAR ƘAUNA na kuɗi ne. Ku biya ₦500 kacal ga wannan account. 9032685442 Opay. Waɗanda tura kuɗi ta opay yake bai wa wahala ku tura ta Bank Account; 1230094555 Access Bank Hadiza D. Auta Ibrahim. DAKAN ƊAKA..Complete document book 1-2. Mai buƙata 9032685442 Opay. Shaidar biya ta nan 08022014771. 10 February zan sake shi da yardar Allah. D. ✍🏼 AUTA CE [2/20, 22:02] Hadiza D. Auta: *FANSAR ƘAUNA!* *HADIZA D. AUTA* *AREWABOOKS: Princessdija.* https://chat.whatsapp.com/Edh59w1Jcgk799uIkP0CFa *LAMBA ASHIRIN.* sallamarsa ta sa ta hanzarin kai kallonta a bakin ƙofar. Ta amsa masa fuskarta a cure tare da amsa gaisuwar da ya yi mata a gajarce tana kawar da kai gefe. Kansa ya shiga sosawa bakinsa ɗauke da 'yar dariya ya ce, "Wurin aiki zan je Hajiyata. Shi ya sa na zo ki saka mini albarka." "Wani kallo ta yi masa kamar ta ce wani abu amma kuma ta fuske, tare da komawa miƙa masa wayarta sannan ta tashi tsaye. Nufar bakin wardrobe ɗin ta yi idonta a ciki kamai mai neman wani abu, daidai lokacin ya yi magana cikin murmushi mai sauti ya ce, "Wayar fa Hajiyarmu?" Ba tare da ta kalle shi ba ta ce, "Kuɗi za ka tura, dubu hamsin da shida a cikin account ɗin da ka gani. Sai arba'in da huɗu a cikin nawa account." Ido ya zaro tare da marairaice fuska yana faɗin, "Hajiy..." "Ba na son wata doguwar magana! Tura kuɗin ka miƙo mini wayata." Ta katse shi cikin sauri tare da kafe shi da ido har ya tura kuɗin sannan ta ɗauke kallonta daga kansa ta koma binciken da take yi. Ya tako a hankali idonsa a ƙasa ya damƙa mata wayar cikin hannunta yana ƙumshe dariya. Ganin yadda ta haɗe fuska alamun babu wasa amma kuma tana so ta yi dariya. "Yanzu fisabilillahi laifin me na yi da aka caje ni waɗannan kuɗin a matsayina na almajiri Hajiyarmu?" Ya yi tambayar a lokacin da ya koma bakin gadonta ya zauna cikin sanyin jiki yana haɗe fuska. "Sa ranka a inuwa, ni ma ba amfani zan yi da su ba, matarka ce take buƙatar kuɗin saboda biyan buƙatarku gabaɗay..." "Amma dai yarinyar nan ta jaza mini aiki! Yanzu Hajiya saboda Allah duk me za ta yi da waɗannan kuɗin? Yarinyar da ko dubu goma wataƙila ba ta taɓa riƙewa a hannunta b..tsakani da Allah Hajiya ki daina sake mata damar da za ta lalace da son kuɗi a samu matsal..." Juyowa ta yi a fusace tana faɗin, "Tafi wurin aikinka ba na son doguwar magana! Kuma daga yau babu kai babu fita da ita yawo ban sani ba, ko da rana ballantana a cikin sulusin dare." Ta yi maganar a fuske, sannan ta juya ta rufe wardrobe ta bi ta gefensa cikin sauri ta bar masa ɗakin. Jim ya yi a tsaye riƙe da ƙugu kafin ya sauke numfashi mai ƙarfi yana faɗin, "Shikenan Hajiya ta fi son ta a kaina." Ya taka a hankali cikin sanyin jiki ya fice daga ɗakin shi ma, a ransa yana faɗin, 'Wayyo kuɗina! Wannan muguwar yarinya ta san hanyoyin haɗa ni da Hajiya kala-kala. Kuma babu damar na gwada ta sai ta ɗauki fansa...ba dai ni ba za ki shigo hannuna ne.' Ya ƙare zancen zucin da ƙwafa, sannan ya fice falon ba tare da ya sake bi ta kan Hajiyar ba. Harabar gidan ya nufa kai-tsaye ya isa wurin motarsa. Saboda irin kallon da Hajiyar ta wurga masa a lokacin da suka yi ido biyu bayan fitowarsa ɗaki, hakan ya saka shi tafiya babu shiri da niyyar ya bar musu gidan tun kafin ya ƙara yin wani laifin. Har ya isa wurin aiki bai daina tunanin hanyar da zai bi ya huce haushin da Minal take ƙoƙarin ƙumsa masa ta hanyar Hajiya. Hajiya kam yana fita ta ƙwala wa Ade kira, daidai lokacin da Minal ta fito daga ɗaki a ɗarare da niyyar yi mata ina kwana. Ga shi lokaci ya ja ba tare da sun ga juna ba, saboda jin motsin Jamal a cikin gidan ya sa ta ƙi fitowa daga ɗaki har sai da ta ji alamun tafiyarsa. Karin safiyar ma a ɗaki Ade ta kai mata, saboda sanin Hajiya ba ta karyawa tun da safe ta bari sai ta nema da kanta. Har ƙasa Minal ta durƙusa gaban Hajiyar ta gaishe ta kanta a sunkuye, cikin sakin fuska Hajiya ta amsa mata tare da faɗin, "Idan kin karya ki shirya direba zai kai ki gidan lalle da kitso. Saboda na sa Amna ta yi wa mai lallenta magana ta ce ki je cikin lokaci saboda a kammala miki da wuri. Zan ba ki kuɗi idan aka gama ko nawa ta faɗa sai ki biya ta. Amma ki tabbatar an yi mai kyau, ba iya irin wanda Amna take yi ba." Minal ta yi dariya saboda tuno zancen Amnar a lokacin da take ba su labarin rikicinta da Hajiyar a kan lalle koyaushe. Don ta fi son a yi mata na gargajiya ita kuma ko kaɗan ba ta son shi, shi ya sa ko ta yi lallen ba ta yabawa sai faman kushen da take yi da harare-harare. Saboda ko zanen fulawar ma kaɗan Amna take so ba ta son a cika mata lalle a jiki. Minal tana ƙoƙarin miƙewa ta ga Umma Ade a gefe tana murmushi, ta raɓa ta gefenta ta wuce ita ma fuskarta ɗauke da murmushin kuma cike da jin nauyin su duka. Don tun da Hajiya ta fara magana Aden ta iso wurin amma ba ta ce komai ba har suka gama gudun ta katse su. Sai da Minal ta bar wurin sannan Aden ta ce, "Ga ni Hajiya." "Yawwa Ade, da ma sanar da ke zan yi mun yi magana da Suraira ɗin..." "Surayya take Hajiya." Ummu Ade ta yi maganar tana 'yar dariya, saboda jin yadda ta sauya sunan alamun ba ta gama riƙewa ba. "To..to haka nan fa Surayya! Na ba ta kuɗin abubuwan da za ta harhaɗa mana, kuma idan direba ya dawo daga kai Aminar zai kai ki ki karɓo mana sauran kayan kafin ta gama dafuwar kazar sababin. Don ina so a yi komai a gaggauce gudun yaronki ya kawo mana matsala ba tare da an gama gyaran ba. "Mutum da matarsa Hajiy..." "A hakan kuma zai bar ta duk nacinsa tun da har ya yi laifin da ta dawo gabana." "Ni dai ina raba ki da yaran zamani. Kin san kuma farinjinin yarona ko bai nema ba mace za ta neme shi da kanta. Kada kina bin bayanta ta zagaye ba tare da kin sani ba ta gane mijinta." Dariya suka saka gabaɗaya, yayin da Ade ta bar wurin tana faɗin, "Bari na kawo miki abin kari. Ga shi an manta yarona ya tafi ba tare da ya karya ba." Hajiya tana dariya ta ce, "Shi ya sani Ade, ya je can ya ƙarata, don zamansa ma saka mutum magana kawai zai yi." *** Ƙarfe goma da rabi na safiya a gidan mai lallen ta buga wa Minal. Aka shiga tsefe mata kai bayan an manna mata lalle. Wanda ta zaɓa da kanta a cikin waya, don tun kafin a shafa jan lallen tsarin jeren salatif ɗin ya fito da ƙafarta fes. Duk da take baƙar mace amma baƙin nata bai hana jan lallen da zanen baƙin lalle mai fulawowi fitowa ya yi kyau a ƙafarta ba. Haka ma fuskarta ta washe, saboda tana da cikar gashi tsawo ne babu, wannan ya ba da damar da aka tsara mata kitso da gashin attach, wanda ta nuna style ɗin da take so. Don da ma can da shi ta fi auki a koyaushe kitsonta ba ya tsallake na ƙari matuƙar za ta yi fitar kunya. Kuna sosai kitson ya yi mata kyau kasancewar ƙwararriya ce ta yi aikin, musamman da aka haɗa mata da na gaba ta ƙara zama 'yar ɗagwas. Zuciyarta cike da jin daɗi ta cashe kuɗin da aka faɗa babu wata gardama, saboda Hajiya ta ba ta wadataccin kuɗi har da saka wa kanta kati a waya, don ita ma an gama burge ta. Ranta fes ta kira Hajiyar ta sanar da ita an gama komai direba ya dawo ya ɗauke ta. Misalin ƙarfe shida na yamma, Jamal ya faka motarsa a ƙofar gidan lallen sannan ya kira ta a waya ya ce ta fito. Ƙirjinta ne ya buga dam tun daga ganin kiransa har zuwa saƙon da ya fesar mata kafin ya datse kiran ba tare da ya jira cewarta ba. Jiki babu kuzari tana haɗe rai ta fito gidan, tare da rakiyar wasu matan da ta ƙulla ƙawance da su a wurin lallen, har da musayar lamba. Bakin motar suka ja suka tsaya suna yi mata Allah Ya tsare, yayin da Minal ta buɗe gaba ta zauna tana dariyar yaƙe suka yi sallama, ganin irin kallon ƙurullar da wata daga cikin su take yi wa Jamal, sosai hakan ya ƙona mata rai. Shi kam bai ma san tana yi ba, don ita kanta Minal bai sake kallon ta ba har ya hau kan babban titin da zai kai su gida, bayan ya bar ƙofar gidan. Ƙirr! Wayarta ta shiga ƙara, cikin sauri ta duba mai kiran, ganin sunan Zulaiha gidan kitso ta ɗauka cike da mamakin dalilin kiran. "Ammm...na ce ba ƙawata.." Zulaiha ta yi magana cikin fargaba. Kafin Minal ta amsa a ƙagauce. "Kika ce me?" Ta yi maganar a taƙaice cike da zaƙuwar son jin abin da za ta faɗa, "Don Allah wannan gayen da ya ɗauke ki yayanki ne ko saurayinki?" "Me ya faru?" Minal ta jefa mata tambayar cikin gatsali tana yamutsa fuska. "Ya burge ni sosai wallahi, kuma idan har ba saurayinki ba ne ni ina ciki. Don Allah ki fara kama mini ƙafa kafin na gabatar da kaina idan kin ba ni lambars...." "Ke wace irin shashasha ce? Sannu Gantalalliya 'yar iska!" Minal jikinta yana tsuma ta yi maganar saboda wani tsinin mashin baƙin kishin Jamal da aka caka mata a tsakiyar zuciya. "Subhanallahi! Ƙawata me ya yi zafi ne daga tambay..." "Ki je ki tambayi ubanki wataƙila shi ya san amsoshin da zan ba ki!" Ƙitt! A zafafe ta datse kiran tare da danna mata block. Sannan jikinta yana rawa ta sake nemo lambar ɗayar ƙawar lallen ta danna mata blocking ita ma. Tana huci fuskarta a cure ta yi magana cikin fitar hayyaci numfashinta yana fisga ta ce, "Da na ba ki lambarsa gara na hango gawarki a kwance ana jana'izark..." Wata mahaukaciyar dariya ce ta suɓuce wa Jamal babu shiri, saboda duk abin da suka tattauna yana ji, kuma tun farkon kiran ya kai kallonsa gare ta cike da son sanin wace ce mai kiran. Fahimtar ƙawance ya koma rigima ya shiga ɓaɓɓaka mata dariya babu ƙaƙƙautawa. Don tun kallon farko da ya yi wa ƙawayen nata ya ɗauke kai, cike da mamakin ina ta san su. Amma da yake bai san komai a kanta ba kafin lokacin, hakan ya sa ya yi tunanin wataƙila da ma can sun san juna. Sai dai fahimtar inda gizon ya yi saƙar ya saka ta gaba da dariya har sai da ta fashe da kuka babu shiri, tsabar haushin Zulaiha da takaicin dariyar da yake yi mata. "Aaa'a fa! Ba za ki cika mini mota da kuka ba, idan kika matsa sai na sauke ki ki nemi abin hawa, don ba na ciki da kayan ihu." Minal ta ƙara sautin kukanta tare da yage baki iya ƙarfinta tamkar wadda aka yi wa mugun duka. Rage gudun motar ya yi, kafin a hankali ya gangara zuwa gefen titi ya tsaya. Tsawon minti biyar yana danna wayarsa tare da sauraron kukan da take yi ba tare da ya ce da ita ƙanzil ba. Fahimtar za ta ɓata masa lokaci Hajiya ta tuhume shi ya kai kallonsa gare ta yana faɗin, "Wai duk zafin kitso da lallen ne kike yi wa kuka haka?" Banza ta yi da shi yayin da ta rage kukanta tana kallon gefe zuciyarta a cunkushe ta dinga jan majinar kuka tana goge hawayen fuskarta da bayan hannunta. "Ko na mayar da ke gidan lallen idan kin kammala da ƙawayen naki na koma na ɗauko ki?" Wani kallo ta yi masa hawaye yana bi fuskarta shaa sannan ta kawar da kanta gefe tana faɗin, "Wallahi duk na sake yin ido biyu da ita sai na nuna mata kuskurent..." "Me za ki yi mata?" Ya yi maganar tare da fashewa da wata sabuwar dariya, a ƙufule ta mayar masa da amsa kai-tsaye da cewa, "Ka rabu da ni Malam! Babu ruwanka da ni." "Haka ne kuma." Ya yi maganar cikin ko-in-kula yana mayar da wayarsa caji fuskarsa a haɗe ya tayar da motar sannan ya sake hawa kan titin. Kallon sa ta yi ta gefen ido kafin ta sake goge ƙwalla tana kallon lallen 'yan yatsunta, zuciyarta cike da jin haushin kanta. Ganin kishi ya sa ta bayar da kanta a gabansa, sai dai dole ta yi wa kanta uzuri don ita kaɗai ta san kalar zafin kishinsa da ke kartar zuciyarta. Har suka isa gidan Hajiya babu wanda ya sake magana, yana parking a harabar gidan ta ɓalle murfin motar ta fice cikin sauri. Kallo ya bi bayanta da shi kafin ya yi hanzarin dafe jijiyarsa da ke harbawa tsabar ta fara tayar masa da jaraba. "Ohh Allah! Wannan yarinya kamar ibilishiya komai ta yi sai ta tsokano ni." Ya jima a cikin motar yana nazarin kishin da ta nuna tare da zaucewar da ta yi a lokaci ɗaya saboda wata ta ce tana son shi. 'Kenan so na take yi ko me?' Ya yi zancen riƙe da haɓa don sosai abin ya ba shi mamaki. Saboda ganin babu wata shaƙuwa ko fahimtar juna ballantana ita kanta soyayyar a tsakaninsu. "Amma me zai sa ta shiga halin da ta shiga don kawai wata ta ce tana so na?" Ya yi wa kansa tambayar a fili kafin ya ɗaga kafaɗa alamun ko a jikinsa ya fice zuciyarsa cike da tunanin Nur da kewar ta a ransa. Saboda babu wani motsin da zai yi ba tare da ya tuno da ita ba, sai dai kawai ya dinga basarwa don shi ma ya gama tsayar da zuciyarsa wuri ɗaya. A kan cewa Nur yaudarar sa kawai ta yi amma babu wani son da ta yi masa shi ne ya ɓata lokacinsa a banza. Bai shiga cikin gidan ba sai da aka yi sallar magrib, sannan ya isa ciki. Faɗan Hajiya ya tarbe shi tun kafin ya ƙarasa, da guntuwar sallamarsa a baki ya samu doguwar kujera ya kwanta tare da dunƙulewa wuri ɗaya tamkar mai jin sanyi. Sosai ya karya wa Hajiya zuciya ta sassauta faɗan da take yi ganin yanayin da ya shigo falon. Saboda fuskar kukan da ta gani ga Minal zuciyarta ta tabbatar mata shi ne ya yi abin da ya saba. Duk da ta tambaye ta dalilin kukan amma ta ce mata babu komai, kuma shi ma bai yi mata komai ba. "Lafiya kake kuwa?" Hajiya ta yi maganar zuciyarta a tsinke tare da isa inda yake tana taɓa wuyansa. "Jikinka dai babu zafi, ko dai ni ce kake yi wa dabara don kana son na daina yi maka faɗa a kan abin da ba za ka daina ba ko na ce ka bari? To ba zan fasa nuna maka ka yi kuskure ba. Amina ko baiwa ce ya kamata a ce ka daina yin abin da zai ɓata mata rai, idan har ka sa girman haƙƙin da ke rataye a wuyank..." "Ni fa Hajiya ban yi mata komai ba! Ita ma idan za ta faɗi tsakaninta da Allah ta san babu abin da na yi mata. Kuma ina zaune kika ce na je na ɗauko ta, sai da na nuna miki a nemi Isah ya ɗauko ta saboda ba na son ki ga laifina. Amma kika ce dole sai na je. Shikenan ni kullum sai kin ga laifina a kanta, salon ta raina ni a banza. Komai na yi laifi ne bayan ita ma har yanzu ba ta san darajar auren ba ballantana ta san darajat..." "Dake ni ubana!" Hajiya ta yi maganar cikin sanyin murya saboda sosai kalamansa sun shiga zuciyarta. Sanin halinsa ya sa ba ta son ya fahimci ta yi laushin da zai ƙara kawo mata wani sabon rashin ji. "Kaina ciwo yake yi Hajiya." Ba ta ce da shi komai ba ta nufi ɗaki ta ɗauko masa paracetamol da ruwa ta zauna bakin kujerar da yake kai ta ɓallo maganin tana faɗin, "Tashi ka sha, kuma idan akwai sauran magungunanka idan ka koma gida ka sha kafin ka yi barci." Ya tashi babu musu ya karɓi kofin ruwan ya sha maganin sannan ya koma ya kwanta idonsa a rufe. Zuciyarsa cike da tunanin abin da Nur ta yi masa, a gefe ɗaya kuma a matse yake da son kusantar Minal. Wannan dalilin ya sa ya yi barcin ƙarya saboda ba ya son Hajiya ta kora shi gidansa. Minal kuma a ɗakin ma kuka ta sha sosai, saboda takaicin Zulaiha da dariyar da Jamal ya yi mata. Ƙarin abin haushi kuma tana buɗe data saƙonni suka fara shigowa ta hango sunan Zulaiha yana yawo a saman notification. Ƙirjinta ya buga dam-dam, saboda ba ta yi ƙasa a gwiwa ba wurin buɗe saƙon ta danna mata ashar. Duba da kalar saƙon da ta turo mata mai cike da rainin hankali da barazana. _"Ko ki so, ko kada ki so, sai na yi soyayya da shi tun da na gan shi na ji ina son sa. Saboda ni babu ɗa namijin da zan yi ido biyu da shi na ji ya kwanta mini ba tare da na farauto shi ta ƙarfin tsiya ba. Ban san ki ba sai a yau, amma zan nemo wace ce ke a cikin kwana uku, sannan ko mijinki ne tun da kika zage ni a kansa sai na nuna miki na fi ki zama kalar 'yan hau. Don haka ki shirya zuwan ranar da za ki gan ni da shi a matsayin mata ko budurwarsa."_ Wata sabuwa 🤔 GARE KU MASU TAMBAYA! Littafin FANSAR ƘAUNA na kuɗi ne. Ku biya ₦500 kacal ga wannan account. 9032685442 Opay. Waɗanda tura kuɗi ta opay yake bai wa wahala ku tura ta Bank Account; 1230094555 Access Bank Hadiza D. Auta Ibrahim. DAKAN ƊAKA..Complete document book 1-2. A turo shaidar biya ta nan; 08022014771. 10 February zan sake shi da yardar Allah. D. ✍🏼 AUTA CE [2/20, 22:17] Hadiza D. Auta: *FANSAR ƘAUNA!* *HADIZA D. AUTA* *AREWABOOKS: Princessdija.* https://chat.whatsapp.com/Edh59w1Jcgk799uIkP0CFa *ASHIRIN DA ƊAYA.* Wurgar da wayar Minal ta yi a kan gado cikin ƙunar zuciya. Kafin ta shiga zarya a tsakiyar ɗakin tana cizon yatsa. "Ba ki isa ba! Wallahi ba ki isa ki mayar mini da hannun agogo baya ba! Ƙarya kike yi, ba Zulaiha kike ba ko ke kika koya wa shaiɗan shaiɗanci sai na nuna miki na fi ki tashanci. Don babu macen da ita ta raɓu jikin Jamal idan ba ni b..." Boyis ɗin da ta yi kenan bayan ta rarumo wayar ta tura mata saƙon, ƙirjinta yana bugawa babu ƙaƙƙautawa. Kafin zuciyarta ta shiga aika mata tambayar da ta saka jikinta yin sanyi laƙwas. 'Ta ya ya za ki yi masa iyaka da mata bayan ke ma har yanzu ba ki gama samun mazaunin dindindin ba?' Hannu ta ɗora a ka tamkar ta fasa ihu, tsabar firgicin da ta shiga ya saka ta ɗimuwa. Da hanzari ta bi umurnin wata zuciyarta mai nuna mata ta sake fesar da abin da ke cikin ranta da gaggawa. Ta sake mayar wa da Zulaiha wanu raddi jikinta yana rawa ta ce. "Idan ke 'yar halas ce ba shegiya ba, ki yi mini kwatancen inda kike a yanzun nan na zo mu yi gaba da gaba da ke, don ina so ki maimaita abin da kika faɗa a gaban idona." Ta saki typing ɗin jikinta yana tsuma idonta a kan rubutun tsabar masifar kishin da ke cin zuciyarta. Ganin shiru minti uku a tsakani Zulaiha ba ta yi mata reply ba ta danna mata kira ta WhatsApp call. A nan ma ta yi banza ba ta ɗaga ba, duk da alamu ya nuna tana online ɗin. Hakan ya sa Minal ba ta haƙura ba ta sake danna mata wani kiran, ringing ɗaya a na biyu Zulaiha ta ɗauka. Kafin ta yi magana Minal ta riga ta da cewa, "Ashe matsoraciya ce ke ban sani ba? Amma kuma kike taƙama da rashin mutunci!" Wata kalar dariya Zulaiha ta yi kafin ta ce, "Allah Sarki, shirun da kika ga na yi miki ba tsoro ba ne matar Jamal. Saboda ja baya ga kowa ya sani shirin faɗa ne. Don haka ki rubuta ki ajiye, in dai da gaske ni Zulaiha ɗiyar sunnah ce cikin uwa da uba, sai na farauto zuciyar Jamal ya bi ni tamkar bawa da uwagijiyars..." "Ƙarya kike yi baƙar 'yar iska! Jamal ya fi ƙarfinki don kakan ubank..." Zulaiha ta sheƙe da wata mahaukaciyar dariya kafin ta sake cewa, "Allah Sarki Minal, ni fa tausayi kike ba ni. Yanzun nan na gama jin labarin ashe ke ma ɗin ba wani sonki yake yi ba...amma me ya sa za ki dinga hauka a kan wanda bai wani damu da ke ba? Shi fa namiji ba a cin alwashi da shi ko da kina da madafun ikonsa a hannunki. Don haka matuƙar ba ki iya allonki ba, to ki daina kishi a kan wanda ba ki da ikon saka shi ko ki hana shi. Na ba ki shawara ne saboda ƙawancenmu na farko, abin da zai haɗa mu na biyu kuma mu zuba ni da ke mu ga wa zai yi nasara Saboda ina kan bakana, ni da ke wanda ya fi iyawa ya ja igiyar faɗan daidai da ƙarfinsa." Ƙitt! Zulaiha ta katse kiran ta bar Minal riƙe da wayar a kunne tamkar wadda aka zare wa lakar jiki. Saboda gwiwowinta sun yi sanyi tun a lokacin da Zulaiha ta ce ta san Jamal ba wani son ta yake yi ba. Wani hawaye mai zafi ya shiga bin fuskarta, saboda takaici da baƙincikin kalaman Zulaiha. 'Ban san me ya sa na biye ta ta faɗa mini abin da ya ɓata raina a banza ba. Amma kuma to wa ya sanar da ita ba ya so na? Ko dai gidan lallen ta ji ana labari bayan tafiyata? Tabbas biri ya yi kama da mutum, daga gidan lallen ne ta ji zancen, idan kuwa haka ne ba zan taɓa yafe wa wadda ta bayar da labarin b...' Ta yi maganar tana goge ƙwallar da ke fareti a saman kumatunta. "Me ya sa tawa ƙaddarar ta zo a haka?" Ta sake jefa wa kanta tambayar da ta ji amsar a bakin Hajiya da ke bakin ƙofar ɗaki tana kallon ta. Wadda ta shigo daidai lokacin da take jefa wa kanta tambayar, cike da tausayin Minal a ranta ta ƙaraso cikin ɗakin ta zauna bakin gado, tare da dafa kafaɗarta tana cewa, "Ita rayuwar duniyar nan da kika gan ta kowa da kalar jarabawarsa. Ki ɗauka taki ita ce wannan, kuma in sha Allah za ta juya duk wani ƙunci da damuwarki zuwa alheri. Yanzu ki yi haƙuri ki goge hawayenki, ki tashi mu je ki ci abinci akwai magungunan da za ki fara sha daga yau ɗin nan zuwa kwana bakwai. Kuma ki sha da kyakkyawar niyya don in sha Allahu su ne warakar duk wata damuwar da kike ciki. In dai Jamal ne ki saka wa ranki tamkar kin mallake shi kin gama. Don Allah ma da ya saukar da cuta sai da ya fara saukar da magani kafin zuwanta. Sannan in dai ina numfashi babu Jamal babu macen da duk za ta gurɓata mana farinciki da kwanciyar hankali. Don haka a kodayaushe ki saka wa ranki ke kaɗai ce a wurin Jamal, kuma ke kaɗai ya mallaka a matsayin babbar kadara rayuwarsa da zuri'arsa gabaɗaya." Kukan daɗi Minal ta fashe da shi babu shiri, saboda Hajiya ta gama wanke duk wata tsatsar fargaban da ke cikin zuciyarta. Sannan kuma ta wanke damuwar da Zulaiha ta cusa mata gabaɗaya. Ranta fes ta sauko daga kan gadon ta duƙa har ƙasa kanta a sunkuye tare da haɗa hannu wuri alamun roƙo tana cewa, "Na gode, na gode miki sosai Hajiyarmu. Ubangiji Ya jiƙan magabata kuma ya ƙara miki lafiya da nisan kwana." Hajiya ta dafa kanta tana murmushi ta ce, "Amin-amin Amina. Ubangiji Ya albarkaci aurenku da zaman lafiya tare da zuri'a ɗayyiba." Cike da jin nauyi ta amsa a ciki kafin Hajiya ta miƙar da ita tsaye tana faɗin, "Mu je ki ci abincin sannan ki sha maganin. Ga shi rigimar Jamal ma ta hana ni sukunin yaba lalle da kitson tun lokacin da kika dawo." Minal ta yi 'yar dariya ba tare da ta ce komai ba suka fice daga ɗakin. Hango shi kwance a saman doguwar kujera ya sa ta yi turus bayan ƙirjinta ya buga dam-dam. Ɗan ja baya ta yi kamar ba za ta shiga falon ba. Nan take Hajiya ta fahimci ba ta son zama falon ne saboda ganin Jamal. "Tsayuwar me kike yi a nan? Ƙaraso mana." Hajiya ta yi maganar cikin haɗe rai tare da nuna mata inda za ta zauna a kusa da ita. Tamkar wadda ƙwai ya fashe wa a ciki ta isa wurin ta zauna idonta a kan Tv ƙirjinta yana bugawa. Plate ɗin tuwon shinkafa miyar yauɗi ta ja zuwa gabanta tana faɗin, "Oya cinye mini shi kafin na fito miki da maganin ki sha." Ta yi maganar tana miƙewa tsaye ta nufi ɗakinta, Minal ta ƙura abincin kallo tsawon sakonni kafin ta wanke hannunta a cikin ruwan wata tasa, sannan ta kai hannun cikin abincin ta shiga juya lomar a cikin miya amma ta kasa kai tuwon a bakinta. Tsabar jin nauyi da kunyar Jamal wanda ya tashi daga kwance bayan shigewar Hajiya yana aika mata kallon ƙasan ido. Wani kalar murmushi ya yi a lokacin da ya miƙe tsaye ya nufo ta. Kanta a sunkuye ta ji takunsa kamar zai fice falon, babu zato ta ji ya cafko ƙirjinta da hannu biyu. Ta zabura babu shiri tana faɗin, "Innalillahi!" Bai bi ta kan buge masa hannuwan da take yi ba ya ranƙwafa daidai fuskarta ya kai sajensa gefen fuskar yana goga mata gashin sajen har zuwa gemunsa. Sannan hannuwansa a ƙirjin yana murza tare da yin wani kalar nishin da ya hautsina ta cikin ɗan lokaci. Motsin Hajiya da buɗe ƙofar ɗakinta ya sa ya yi hanzarin sakin ta ya nufi hanyar fita cikin sassarfa. Da mamaki ta ƙaraso cikin falon tana cewa, "Kai da ba ka da lafiya ina kuma za ka je?" "Masallaci zan tafi na yi Isha na dawo." Iya abin da ya faɗa kenan cikin wata kalar murya, ba tare da ya juyo ba saboda jijiyarsa da ke miƙe, sannan kuma ba ya son ta fahimci halin da yake ciki. Ficewarsa ya sa ta dawo da kallonta a kan Minal tana faɗin, "Ba dai ko loma ɗaya ba ki ci ba tun da na bar ki?" Minal ta yi ƙoƙarin saita nutsuwarta tana sosa kanta da hannu ɗaya ta fara kai lomar abincin a bakinta. Zuciyarta sai zillo take yi tsabar tsantsar jarabar da Jamal ya jefa a ciki ba tare da ta shirya ba. Yamm! Jikinta ya hau tsuma tana haɗiyar loma da ƙyar tamkar mau cin magani. "Ikon Allah! Yanzu cin abincin ne har da gumi Amina?" Cikin sauri Minal ta girgiza kai tana zarar ido tsabar kunya da yanayin da ke son tona mata asiri. "Ni na ga duk kin firgice a lokaci ɗaya, ko ya yi miki wani abin ne bayan tafiyata?" Ta sake girgiza kai tana ƙoƙarin yin magana ta sarƙe, babu shiri ta fara tari babu ƙaƙƙautawa. Hajiya ta ruɗe ta shiga bubbuga mata baya tana faɗin 'Sannu' tare da taimaka mata ta sha ruwa har aka samu tarin ya lafa mata. "Ki ci a hankali kada ki sake sarƙewa." Ta yi maganar cikin kulawa tare da barin wurin ta ɗauko kofi ta dawo ta zauna. Tsawon minti goma babu wanda ya yi magana a tsakaninsu, har Minal ta gama cin tuwon ta kwashe kayan ta kai kitchen, sannan ta dawo bayan ta wanke hannunta. Kofin maganin infection ta miƙa mata, wanda ta cika taf da ruwan maganin sai ƙamshinsa ke tashi. Babu musu ta karɓa ta shanye a lokacin ɗaya, zuciyarta cike da niyyar samun warakar matsalolin da ke tsakaninta da Jamal. Don har ranta ta nutsu da cewa kyakkyawan albishirin Hajiya zai yi tasiri ga rayuwarta cikin ɗan lokaci. Ganin yadda ya fara sauyawa har yana ƙoƙarin haɗa jikinsa da nata cikin nutsuwa ba tare da kyara ko hantara ba. Sallamarsa da ta ji ya sa ta miƙe tana cewa Hajiya za ta shiga ɗaki ta yi wanka ta yi sallah. Ta so hana ta, amma ganin ta fi son tafiyar ya sa ta yi 'yar dariya ta ce, "Jamal ka daina tsorata mini 'ya, ba na son tana ƙin sakewa a duk lokacin da ta gan ka." Bai ce ƙanzil ba sai murmushin da ya yi yana sosa kansa tsawon minti biyu sannan ya ce, "A taƙaice dai na zama dodo." "Kusan haka, don haka ko ka bari ko na ɗauki mataki a kanka." "Ai da ma na san kin fi son ta da ni. Ga shi ma ko lafiya ban da..ina jin kamar a gidan nan zan kwana yau Hajiy..." "Ka je gidanka gaskiya! Ko ba komai za ka sha maganinka a can kafin ka kwanta." Bai ba ta amsa ba sai da ya baje kan kujerar sannan ya ce, "Matsalar jikin ne nawa babu ƙarfin da zan iya yin tuƙi a yanzu. Kuma gidan babu daɗi daga ni sai maigadi." Wani kallo ta yi masa cike da jin daɗin ganin ya fara damuwa da kewar Minal ta ce, "Ji wani sanabe, yanzu duk shekarun kwanakin da ka yi kana kwana a cikin gidan ba ka san babu daɗi ba sai yau da kake son kwana a gidan nan?" "Kawai ki yarda Hajiya, za. Jaraba kwana a nan ɗin, gobe idan na samu ƙarfi sai na koma can." Farinciki fal zuciyarta ta ce, "Ba kwanan ba, ba na son ka takura mini yarinya, saboda haka tashi ka je ɓangarenka ni zan rufe ƙofarmu gudun na manta ta kwana a buɗe ban sani ba." "Idan na tashi zan sanar da ke ki ruf.." "Ba fa zan bar ka a nan ba! Tashi ka je na rufe ba za ka saka ni surutu a cikin dare ba." Ta yi maganar tare da tsare gida alamun babu wasa, haka ya miƙe ba don ya so ba ya koma ɗakinsa da ke harabar gidan. Sannan ta rufe ƙofarta ruf ta bar makulli a jiki tana tofe ko'ina da addu'a. Jamal kam barci ya yi cikin kewar Minal, sai da ya kira Zee a waya suka yi abin da suka saba yi sannan ya rage zafi. Amma a zuciyarsa bai fasa shan alwashin yi wa Minal muguwar mamayar da zai koya mata hankali ba. Da safe bai tsaya kari ba ya fice gidan a gaggauce saboda kiran da aka yi masa wurin aiki. Kasancewar yana da wasu kaya a gidan bai koma gidansa ba daga nan ya zarce ma'aikatarsu. *** Tsawon kwana bakwai Hajiya tana tsaye a kan Minal, sannan da takatsantsan a kan kusancinta da Jamal har ta kammala shan magungunan ta cinye kazar sababi. Don tun daga ranar da ya kwana gidan ya tare a nan bai koma gidansa da kwana ba. Hakan ya sa Minal ta shiga feshin wanka da kalolin shiga cikin sababbin kaya tamkar tarwaɗa. Saboda Hajiya ta sa an yi mata dilka da halawa fatarta ta ƙara murjewa har da haske sai da ta yi. Gyaran da ya ƙara susuce Jamal ya zama bita-zai-zai, Hajiya tana korar sa yana mannewa. Wani lokaci da gangan yake naɗewa a cikin ɗakinsa, saboda kawai ya ce bai da lafiya a kawo masa abincinsa a nan. Don kawai ya yi amfani da damar ya rage zafin da ke ƙona masa jiki tsabar fitinanniyar sha'awar Minal ta yi masa mugun kamu. A farko Hajiya ba ta gano lagonsa ba, sai a wata rana da ta ji Minal shiru ba ta dawo daga kai masa abincin ba, babu jinkiri ta bi bayanta cikin zullumin kada ya samu kanta tun kafin ta gama gyaran. Saboda haka Minal tana shiga ya rufe ɗakin ya shiga luguiguita ta son ransa, don ita ma magungunan da take sha sun fara aiki a jikinta. Ta yadda babu abin da ta fi so a lokacin kamar ya yi mata abin da ya koya mata a cikin 'yan kwanakin. Ko boren da take yi masa da zabura idan ya taɓa ta gabaɗaya ta daina yi, wani lokacin ma har ɗoki take yi da dakon sa a kan cewa a kawo masa abincin don kawai ta je ya ɗora mata sabon darasi. Ranar da Hajiya ta rutsa su a cikin yanayin da ba ya faɗuwa, dole ta tattara mata kayanta ta kai ta gidansa da kanta ta ce Allah Ya ba da zaman lafiya. Da ma Umma Ade ta ba ta shawarar ta miƙa masa matarsa tun da ya kasa haƙuri ya biyo ta gidan ya tare. Amma Hajiya ta kafe a kan babu inda za ta je sai ta gama gyara ta tsaf kuma sai kayan matan sun bi jikinta. Kasancewar bai san Hajiya za ta mayar da ita ba, sai bayan ya dawo gidan bayan magrib cin abinci. Yana zancen abincin, Hajiyar ta ce masa ya je gidansa matarsa ta yi masa girki sai ya ci a can. Sake da baki ya dinga kallon Hajiya sannan ya ce, "Shi ne aka mayar da ita ba tare da na sani ba?" Wani kallo ta yi masa kafin ta ce, "Da na zo da ita izininka na nema?" Sosa kai ya shiga yi yana 'yar dariya saboda har zuciyarsa ya ji daɗin damar da aka ba shi don ya ci karensa babu babbaka. Amma sai ya koma alayen jan Hajiya da hira kamar ba ya son tafiya, har da cewa shi a nan gidan zai kwana bai tashi komawa can ba. Gaba Hajiya ta saka shi da abin bugu ta koro shi har harabar gidan tana yi masa Allah Ya tsare. Cikin wani ƙumaji a ransa ya fice gidan aguje maigadi yana ɗaga masa hannu da addu'ar sauka lafiya. Bai zame ko'ina ba sai Yahuza suya, a nan ya zaɓi ƙosassun kaji biyu da sauran tarkacen ci da sha ya buga motarsa zuwa gida. Zuciyarsa cike da ɗokin zama ango a daren ranar, ranar da ta zamo daidai wata biyu da aurensu. Yanzu wasar za ta fara. GARE KU MASU TAMBAYA! Littafin FANSAR ƘAUNA na kuɗi ne. Ku biya ₦500 kacal ga wannan account. 9032685442 Opay. Waɗanda tura kuɗi ta opay yake bai wa wahala ku tura ta Bank Account; 1230094555 Access Bank Hadiza D. Auta Ibrahim. JERIN LITTAFAINA GA MAI BUƘATA! 1. ABOKIN AIKINA 1K 2. BAƘON YANAYI 1K 3. DAKAN ƊAKA 1K 4. AMFANIN FITILA 1K 5. JIKI DA JINI 1K 6. GIDAN AURE ₦700 7. TARTSATSI 1K 8. MAKANTAR SO 1K 9. ZUBAR HAWAYENA ₦700 10. RUWA DA ƘANƘARA ₦700 11. BAKAN GIZO ₦700 12. MUSAYAR ZUCIYA ₦500 13. DIJE ƘARANGIYA ₦500 14. DACE DA JUNA ₦500 D. ✍🏼 AUTA CE [2/20, 22:17] Hadiza D. Auta: *FANSAR ƘAUNA!* *HADIZA D. AUTA* *AREWABOOKS: Princessdija.* https://chat.whatsapp.com/Edh59w1Jcgk799uIkP0CFa *ASHIRIN DA BIYU.* Minal kuwa, tun bayan gama sallar Isha ta kwaɗa wanka tare da feshe jikinta da fitinannun turaruka, waɗanda Hajiya ta yi mata kyautar su a matsayin tsarabar zaman aure. Ta sha gayunta cikin wani tsadadden lesi fari mai adon golden. Bayan ɗan kunne da sarƙa har da agogo da 'yan hannu ta saka. Ta fito shar da ita ta ko'ina sai juyi take yi zuciyarta cike da jin daɗin yanayin da farincikin zuwan ranar. Saboda jikinta ya ba ta daga ranar farincikin da Hajiya take hasashen zuwansa zai wanzu, matuƙar Jamal ya gano darajarta. Ta zauna falo tana kallon Bollywood tare da dakon dawowarsa. Don ta ci alwashin nuna masa ita daban ce a cikin matan bariki, kuma ta san darajar kanta. Sai dai a gefe ɗaya na zuciyarta yana yi mata gargaɗin kada ta yi abin da zai lalata musu daren, don ta jima tana tsumayin zuwansa. Hakan ya sa tun da ta ji ƙarar buɗe gate da ƙugin motarsa jikinta ya hau tsuma. Saboda tsananin bugun da ƙirjinta yake yi, babu shiri ta zabura ta faɗa ɗaki jikinta yana rawa. Haka kawai ta tsinci kanta cikin wani matsanancin tsoro, ƙirjinta ta dafe tare da rufe ido a daidai lokacin da ta ji motsin buɗe ƙofar falo. Jinin jikinta ta sha saboda jin sautinsa yana faɗin, "Ina matar gidan ne?" Cikin sauri ta kwanta bakin gado tana rufe ido da nufin yin baccin ƙarya. Amma kuma dukan luguden uku-ukun da ƙirjinta yake yi, ya tona asirin lamfon da ta yi a lokacin da ya shigo ɗakin ya yi tsugunno bakin gadon yana ƙare wa fuskarta kallo. Hannunsa ya kai saman leɓunanta yana murmushi ya ce, "Da ma kin tashi don bugun zuciyarki ya tona miki asiri ba wani baccin da kike yi." Dariyar da ta so yi ya sa ta yi hanzarin juya kwanciya ta ba shi baya. Bombom ya ɗin ta ya ƙura wa kallo kafin ya sauke ajiyar zuciya ya miƙe, shi ma ya raɓa ta gefenta ya kwanta tare da rungumo ta jikinsa yana shinshinar ƙamshinta. Ya shiga goga mata gashin sajensa a wuya cikin shauƙi yana faɗin, "Wannan amarya so take yi kawai ta ja mini aji." Ya yi maganar cikin wata kalar murya a lokacin da ya zura hannunsa ɗaya ta ƙarƙashinta, sannan ɗaya a saman jikinta ya rungumo ta gabaɗaya yana sauke ajiyar zuciya. A lokaci ɗaya ya yi nasarar kai hannuwan saman ƙirjinta yana aikin da zuciya take ta kwaɗaita masa. Cikin ɗan lokaci daga shi har ita suka fita cikin hayyacinsu, saboda ya koma samanta yana yi mata wani kalar wasannin da ya jima da sanin su ne makamar kowace mace. Numfashi ta shiga saukewa tana ɗan kukan da ke ƙara hautsina masa lissafi. Hakan ya sa ya nemi haukacewa gabaɗaya yana neman kan hanyar da zai ɓillewa a sukwane. A lokacin nata hankalin ya dawo jikinta cikin tsoro ta shiga ture shi tana ƙoƙarin hana shi abin da yake ƙoƙarin aikatawa. Kasancewar jikinsa ya yi laushin da ba zai iya komai ba, ba ta sha wuya wurin zare jikinta daga nasa tare da tashi zaune tana faɗin, "Malam abincinka yana falo." Ta yi maganar cikin harɗewar numfashi tare da ƙoƙarin saita nutsuwarta. Kifewa kawai ya yi tare da dafe jijiyarsa da ke bugawa tsawon mintuna kafin ya samu daidaitar yanayin da yake ciki. Ido ya bi ta da shi a lokacin da ta sauka gadon ta nufi ƙofar fita tana faɗin, "Ni na tafi ka same ni a can saboda kai na tsaya jira mu ci abincin." Ta fice ƙirjinta yana bugawa zuciyarta cike da kwaɗayin ba shi haɗin kai kamar yadda yake buƙace. Sai dai tuna ba su yi komai na al'adar daren farko da aiwatar da sunnar Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ba, hakan ya sa ta haɗiye ƙwalamar ta bar masa ɗakin. Saboda tana son aurensu ya yi albarka kuma idan ta biye jarabarsa ba zai ɗaga ƙafa ba, ballantana har ya yi abin da ya dace. Tana tsaka da zuba abincin ya iso wurin ya tsaya bayanta, tare da rungumo ta yana shafa mata jijiyarsa da ke tsaye har lokacin. A tsayen ma sai da suka kwashe minti goma suna tsotse-tsotse kafin ta zare jikinta ta zauna babu shiri. Saboda ƙafafuwanta sun yi sanyin da suka gaza ɗaukar gangar jikinta. Shi ma ya ja kujerar kusa da ita yana dafe kansa ya ce, "Ni fa abincin nan ma da an bar shi na fi son babban abincin." Wani kallo ta yi masa tana haɗe rai tare da tura masa plate a gabansa tana faɗin, "Ni dai ka ci tun kafin ya yi sanyi." Abincin ya kai wa kallo kafin ya damƙo hannunta ya fara shafa fuskarsa cikin wata kalar murya ya sake cewa, "Ni dai a ba ni wancan abincin na haƙura da wannan ba sai na ci b..." "Da ma na sani ba ka son cin abincin mayya. Don haka ka bar shi kawai tun da kana tsoron a lashe maka kurwa." Ta ƙare maganar tare da zare hannunta tana jan abincin gabanta ta fara ci, tsawon minti biyu yana kallon ta babu ƙiftawa, kafin ya ja numfashi ya sauke yana faɗin, "Mayya ta gama kama kurwata, abincin ma zan ci tun da kina so. Amma da za a ba ni babban abincin a madadin wannan zan fi farinciki." Wani kallo ta yi masa mai ɗauke da harara, sannan ta ci gaba da cin abincinta kamar ba ta ji me ya faɗa ba. Ya ja cokalin da ke cikin abincin ya fara kai bakinsa yana cewa, "Abincin nan bai isa ya sa a yi fushi da ni ba. Ki bar yi mini kallon uku kwabo gaskiya ce na faɗa na fi son wancan abin da wannan." Ya yi maganar cikin marairaice fuska da muryar shagwaɓa. Yam tsikar jikinta ya tashi, saboda ita kanta ba ƙaramar jarumta ta ara ta yafa wa jikinta ba. Kasancewar ita ɗin ma a matse take da shi saboda magungunan da ta sha sun gama sauya ta koma jarabatu. Don a rana tana sauya pant sau biyu zuwa uku, tsabar taɓon da take ciki koyaushe jikinta cikin danshin jaraba. Musamman da ya tayar da ita tsaye gabaɗaya ya buɗe makunnnin famfonta tun kafin ta fito daga ɗakin. A daddafe suka kammala cin abincin hannunsa ɗaya a cikin nata yana wani irin salon da ke ƙara tayar mata da hankali. Hakan ya sa daga ita har shi ba su ci abincin kirki ba, don ko kajin da ya siyo sai da ya gama lallatsa ta sannan ya ɗauko su daga kan Centre table ya kawo saman dinning, a nan ma suka tsakuri kaɗan suka ture. Da kansa ya kai shi firij ya adana sannan ya fito a daidai lokacin da Minal ta shige ɗaki tana juya mazaunai. Bin ta ya yi dafe da ƙugu kamar mai tsohon ciki, saboda 'ya'yan jijiyarsa gabaɗaya sun haye har sun fara yi masa ciwo. Toilet ta nufa shi ma a can ya bi ta kai-tsaye. Arwala ya ba ta umarnin yi fuskarsa a haɗe saboda zogin da 'ya'yan jijiyar suke yi masa. Babu ɓata lokaci suka fito tare ta shimfiɗa musu sallaya. Cikin minti goma suka kammala komai tun daga kan sallar har zuwa addu'o'in da ake yi. Sosai ya ba ta mamaki ganin yadda yake ɓarin ayoyi da addu'a tamkar wani Balarabe. A ranta ta shiga jinjina girman saninsa ga Addini, da girman kaucewarsa a kan sharholiyar ransa a kan bin mata. Nan take ranta ya ɓaci, saboda tuno Zee da abin da suka aikata a daren da ya kwana da ita cikin gidan. Ta miƙe daga kan sallayar ta fara zare hijabi tana naɗewa fuskarta a cure. Saboda wani hawaye mai zafi ya shiga kwaranyo mata a kumatu. Ganin ta a tsaye tana ƙoƙarin sauya lesin jikinta zuwa rigar bacci, ya yi hanzarin tashi ya isa inda take ya damƙe rigar, tare da fisge ta ya wurgar. Kallo ta ƙura masa daga ita sai pants da bra hawaye yana zarya a cikin idonta. Babu ɓata lokaci ya ja ta jikinsa yana wani kalar nishi idonsa rufe ya shiga sarrafa ta son ransa. Duk da ya ga hawayenta amma zuciyarsa ba ta kawo komai a ransa ba, sai da ta zare jikinta tana nuna shi da hannu cikin muryar kuka ta ce, "Ba zan taɓa amincewa da kai a matsayin mijina ba, matuƙar ban ga shaidar da ke tabbatar mini babu wani ciwo a jikinka ba. Saboda ina son kaina ba na son abin da zai sa iyayena su yi asara ta, a lokacin da ka manna mini wani ciwo a sanadin matan banzan da kake bi." "Ya Salam!" Abin da ya faɗa kenan yana dafe kansa da jijiyarsa da ke ta cika tana batsewa. "A tunaninki zan iya cutar da ke ne?" Ya jefa mata tambayar ransa a ɓace, kafin ya sake magana cikin haɗe rai ya ce, "Babu wani ciwon da ke jikina ballantana na goga miki, dalilin hakan ya sa na shirya wa irin wannan ranar don na san za ta zo. Don haka jira ni minti biyu zan je na ɗauko miki shaidar asibitin da ta tabbatar da ba na ɗauke da kowane irin ciwo. Saboda Hajiya da kanta ta saka ni awon ba tare da kin sani ba, kuma ba don kowa ta yi hakan ba sai don ke da kare haƙƙinki gudun a cutar da ke a banza. Amma tun da ita ma ba ta yi gwaninta ba jira ni na zo ki ga komai da idonk..." Yana ƙoƙarin barin wurin ta riƙo hannunsa hawaye yana fareti a kan fuskarta ta faɗa jikinsa tana kuka. Jim ya yi rungume da ita tsawon minti uku kafin ya sauke ajiyar zuciya ya koma rarrashin ta. Jan ta ya yi har zuwa bakin gadon suka zauna sannan ya sake cewa, "Yadda kika san ba na son wani abu ya same ni, haka ke ma ba zan so na yi silar wargaza miki lafiyar jiki ba. Allah shi ne shaidar ban da wani ciwon da ya wuce ciwon damuwar da ke tare da ni. Shi ma ɗin a hankali ya fara sauka saboda ba na son Hajiya ta rasa ni tun yanzu kafin na ajiye mata jikoki. Wani kallo Minal ta yi masa mai ɗauke da harara ta ce, "Ba sai idan ina haihuwar ba." Ta ƙare maganar tana turo baki, ya yi hanzarin kai bakinsa saman nata ya tsotso leɓunanta kafin ya ce, "A yau zan ba ki cikin 'ya'ya biyu har uku ma idan kina so." Ƙoƙarin zare jikinta ta yi cike da jin kunya tana haɗe rai ta ce, "Ni dai don Allah ina so ka yi mini wata alfarma da alƙawari ɗaya." Duk da ba ta faɗa ba, amma ya fahimci inda ta dosa. Don zuciyarsa ta gama ba shi abin da take so ta faɗa, hakan ya sa ya yi magana tun kafin ta furta abin da ke ranta ya ce, "Tun daga ranar da na yi awon nan, ban sake kusantar wata mace ba. Kuma in sha Allahu ba zan sake ba. Matuƙar za ki dinga ba ni kanki a duk lokacin da na buƙata." "Saura ɗaya tun da ka gano ɗaya. Ina so ka yi mini alƙawarin babu kai babu Nur...." Dam-dam ƙirjinsa ya shiga bugawa, nan take ransa ya ɓace saboda ta tuno masa da abin da yake ƙoƙarin binnewa. "In dai wannan ce matsalarki kuma kike so na yi alƙawari, tuni na yi wa kaina iyaka da Nur, kuma ba zan taɓa koma mata ba har abada. Shikenan damuwar ko?" Ta yi hanzarin faɗawa jikinsa cike da matsanancin farin ciki ta ruƙunƙume shi tana wurga masa kisses kala-kala. Hakan ya ba shi damar ƙanƙame ta cikin ɗan lokaci suka faɗa wata duniyar da ba sa tuna kowa sai kansu. Kafin ka ce me ƙuginsu kawai ke tashi daga shi har ita saboda sun fita hayyacinsu gabaɗaya. Kafin kukan Minal ya fara tashi a hankali har zuwa lokacin da ta fasa ƙara, don Jamal bai yi ƙasa a gwiwa ba wajen fasa tantanin maƙwallaton budurcin ba. Wanda shigarsa ciki ya ƙara rura wutar jarabarsa ta ko'ina ya shiga aiki tsabar jin komai zam-zam a kan mugun kamun da jikin Minal ya yi wa jijiyarsa. Ihu yake yi yana kiran sunan Hajiya tare da godiya ga Allah tsabar daɗin fasa dutsen fintopio da kalar ruwan da ke ɓuɓɓuga tamkar wata ƙorama. Don kukan da take yi bai hana shi sakin jiki ya gurje ta ba son ransa. Sai da ya tabbatar ya gama jigatar da ita ko hannu ba ta iya ɗagawa sannan ya ɗaga ta. Tare da ƙanƙame ta jikinsa yana wani irin nishi tsabar farincikin da ta jefa shi, wanda a tsawon rayuwarsa da girman barikinsa bai taɓa haɗuwa da macen da ta goge masa hadda ba. Hakan ya sa a koyaushe yake yi wa mata kallon abu ɗaya, saboda amfanin mace kawai a wurin sa biyan buƙatarsa ya fece, kafin ya haɗu da Nur ta koya masa zazzafar soyayya. Amma sanin asalin daɗin can wurin sai a wurin Minal ya gano ashe mata ma suna suka tara. Amma baiwarsu kala daban-daban ce don Minal ta zo masa da sabuwar rayuwar da bai san ta a duniyar neme- nemen matansa ba. Hakan ya sa ta samu babban matsayin da ba ya jin za a yi wata ɗiya macen da za ta fi ta a wurin sa ta wannan ɓangaren. Don a take ya saƙa wa ransa ita ce rabin jin daɗin duniyarsa. Kwana ya yi yana rarrashin ta cikin kulawa da wani sabon tausayin ta da ke ransa. Ganin irin juriyar d ta yi, bayan sakin jikin da ta yi masa ta ko'ina ya baje kolinsa, style kala-kala babu togaciya ballantana dogon rakin da zai hana shi sakewa. Sosai ya jinjina wa bajintarta, saboda bai taɓa tunanin za ta yi juriyar da ta aikata ba. Amma ganin ƙafarta ta ƙi taka ƙasa ya fahimci tabbas ya wuce gona d iri, saboda gashin ruwan zafin da ya yi mata ma dole sai ɗaukar ta ya yi zuwa toilet. A can ya ƙara ganin irin dagargazar da ya yi wa matuccinta, sosai jikinsa ya yi sanyi zuciyarsa cike da tsoro. Saboda jinin da ke zuba a jikinta kamar ya wuce jinin al'adar da ake so mace ta zubar a daren farkonta. Dole ya nemo magungunan rage ciwon jiki da paracetamol ya ba ta, don zazzaɓin faraɗ ɗaya ya taso mata bayan ya gama mata gashin. Cikin lallaɓawa tana cije leɓe ya kwantar da ita kan gadon yana jera mata sannu, bayan ya sauya zanin gadon da suka ɓata ya ajiye gefe. Minal ta shiga nishi da rawar ɗari jikinta yana ciccira kafin ta samu barci ya yi awon gaba da ita. Yana kanta cikin ruɗewa yana ta tofa mata addu'o'i bayan ya kama mata kai da ƙula'uzzai don samun sauƙi. Sannu Amarya😩 GARE KU MASU TAMBAYA! Littafin FANSAR ƘAUNA na kuɗi ne. Ku biya ₦500 kacal ga wannan account. 9032685442 Opay. Waɗanda tura kuɗi ta opay yake bai wa wahala ku tura ta Bank Account; 1230094555 Access Bank Hadiza D. Auta Ibrahim. JERIN LITTAFAINA GA MAI BUƘATA! 1. ABOKIN AIKINA 1K 2. BAƘON YANAYI 1K 3. DAKAN ƊAKA 1K 4. AMFANIN FITILA 1K 5. JIKI DA JINI 1K 6. GIDAN AURE ₦700 7. TARTSATSI 1K 8. MAKANTAR SO 1K 9. ZUBAR HAWAYENA ₦700 10. RUWA DA ƘANƘARA ₦700 11. BAKAN GIZO ₦700 12. MUSAYAR ZUCIYA ₦500 13. DIJE ƘARANGIYA ₦500 14. DACE DA JUNA ₦500 D. ✍🏼 AUTA CE [2/20, 22:17] Hadiza D. Auta: *FANSAR ƘAUNA!* *HADIZA D. AUTA* *AREWABOOKS: Princessdija.* https://chat.whatsapp.com/Edh59w1Jcgk799uIkP0CFa *ASHIRIN DA UKU.* Asubar farin ya fita nemo likitan da zai duba ta, saboda jikinta ya yi zafi sosai. Sai dai likitan bayan ya yi mata allurori ya ba shi shawarar ya kai ta asibiti a duba ƙasanta. Don ya fahimci yanayin da take ciki kamar akwai matsala duba da yadda ba ta iya zama da ɗuwawunta, kuma ba ta iya tsayuwa da ƙafafuwanta ita kaɗai. Allurar ma da dabara aka yi ta, sai da Jamal ya miƙar da ita jikinta yana ɓari tana cije leɓe, sannan ya rungumo ta a jikinsa ta lafe tana nishin ciwo. Jim ya yi a falo bayan tafiyar likitan, zuciyarsa cike da tunanin yadda zai yi. Saboda jikinsa ya yi sanyi ƙalau don ko kaɗan ba ya son Hajiya ta sani. Dole babu yadda ya iya, haka ya kira abokinsa Adamu ya sanar da shi abin da yake faruwa. Shaƙiyanci ya fara yi masa kafin ya ɗora da cewa, "Bari na yi wa Dr Jimmai magana, idan akwai dama ta zo nan gidan ta duba maka ita. Tun da ka gama borin kunyar ka aikace yarinyar mutan..." "Kai fa ɗan iska ne, idan ba a son na yi aikin me ya sa aka ajiye mini ta a cikin gidan?" "Taimakonka aka yi, don an san halinka gudun ka je ka buga wata ɓarnar da za a ɗora hannu a ka da salati." "Oho dai, ni dai na yi abin da ya dace, saura ka nemo mai duba ta ko za ka samu ladar kai ma." Yana gama maganar ya katse kiran suna dariya, saboda shi kansa ya fahimci ashe ya wuce gona da iri. Duba da yadda likitan har suka yi sallama yana ta jaddada masa lalle ya kai ta asibiti, kada ya yi sanya gudun wata matsala ta biyo baya. Ɗakin ya koma, ya tarar da ita tana bacci, amma kuma ba ta fasa nishin ciwo ba. Kanta ya dafa ya ji har lokacin zazzaɓin bai sauka ba. Ya gyara mata lulluɓin bargon sannan ya koma kitchen. Cikin ɗan lokaci ya ɗumama kazar da suka ajiye ta yi zafi, sannan ya soya Irish da ƙwai ya haɗa musu ruwan tea da kayan haɗin shayi mai ƙamshi. Bayan ya gama cin nasa ya yi ƙat, ya kwashi nata zuwa ɗakin. Tayar da ita ya yi tana cije-cijen leɓe ya kai ta toilet, ya sake gasa mata jiki da ruwan zafi. Sannan ya yi mata wanka cikin dabara yana ta matse mata ƙirji bayan ya wanke mata baki da brush. Minal kam sai langaɓewa take yi tsabar rashin kuzari, kukan da take yi ma mara sauti ne mai ɗauke da ruwan hawaye. Da kansa ya shirya ta sannan ya ba ta abin karin ta ci, duk da bakinta babu ɗanɗano ko kaɗan. Ya sake taimaka mata ta kwanta shi ma ya bi gadon suna fuskantar juna, ido cikin ido suke kallon juna tsawon minti biyar, kafin hawayen da Minal take ƙoƙarin shanyewa ya fara fita babu ƙaƙƙautawa. Cikin ɓata fuska ya kai hannunsa yana share mata hawayen ya ce, "Daina kukan plss! Na yi waya da Adamu wata likita za ta zo duba ki." Wani kallo ta yi masa cikin zaro ido saboda ganin tonon sililin da yake ƙoƙarin yi mata. "Don Allah kada ta zo na ji sauƙi." Da ƙyar ta harhaɗa kalmomin da ta yi amfani da su yayin maganar. Hancinta ya lakuce kafin ya ce, "Kina wannan langaɓewar kike faɗin kin ji sauƙi?" "Ni dai ba na son kowa ya zo anjima kaɗan zan warware..yanzu ma ai na fara jin sauƙ..." "Kenan zan iya komawa na sake jiƙa alƙalamina ko yanzu?" Harara ta wurga masa kafin ta turo baki tana goge ruwan hawayen da ya sake zubo mata cikin muryar kuka ta ce, "Idan ma kashe ni kake son yi ai ka yi duk abin da kake s..." "Ke fa kika ce kin ji sauƙi to mene ne laifina?" Ya yi maganar yana ƙumshe dariya saboda ganin yadda ta susuce gabaɗaya, don alamu ya nuna sai ya sha wuya kafin ta sake yarda da shi. Ganin ta ƙi daina sharar ƙwallar ya ja ta jikinsa ya shiga shafar ta yana bubbuga bayanta, har wani sabon bacci ya yi awon gaba da ita. Kafin shi ma baccin ya kwashe shi yana nazarin abin da zai yi mata, wanda zai faranta mata kamar yadda ta faranta masa. Ƙarfe sha biyu saura minti uku na rana, waton 11:57am. Wayar Adamu ya tayar da su daga nannauyan barcin da suke yi. Inda yake sanar da shi ga shi a cikin gidan tare da Dr Jimmai. Dole ya wartsake barcin ya fara ƙoƙarin zare ta daga jikinsa, hakan ya sa ita ma ta farka. Bayani ya yi mata sannan ya fice daga ɗakin ya nufi ɗakinsa. Mintuna kaɗan ya fito da shigar baƙar jallabiya ya sauka ƙasa cikin sauri ya nufi harabar gidan. Kai-tsaye ya nufi inda motarsu fuskarsa a sake ya fara gaisawa da Dr Jimmai sannan ya miƙa wa Adamu hannu suka gaisa. "Mu je daga ciki, tun da ka tsaya jiran na fito kamar wani baƙo." Ya yi maganar tare da jan hannun Adamu suka yi gaba Dr Jimmai ta bi su a baya, inda Adamu yake dariya yana cewa, "Rufa mini asiri, ko karen mahaukaciya ya cije ni ai yanzu ba zan shiga gidanka kai-tsaye babu notis ba." "To mene ne a ciki?Ina jin dai ka san amaryar tun ba yau b..." "Na dai taɓa ganin ta amma ban taɓa sanin ta ba ni kam." Dariya suka fashe da ita dukan su har Dr Jimmai, saboda fahimtar inda Adamu ya nufa. A falo suka zauna, Jamal ya koma ɗakin Minal, ganin ta ido biyu har ta gyara kwanciyarta ya gano ba ta koma barcin ba tun bayan fitarsa. "Ki shirya matar za ta shigo ta duba ki tana falo." Narai-narai ta yi da ido hawaye shaa a kan fuskarta. Bai bi ta kanta ba ya fice tare da bai wa Dr Jimmai damar ganin ta, sannan ya koma wurin Adamu bayan ta shiga ɗakin ya rufo musu ƙofa. "Waton mutumina har ka manta babu komai a jikinta na mata, a haka dai yadda take da siffar mazan ka rufe ido ka yi mata kaca-kaca?" Wani kallon ka raina ni Jamal ya yi masa kafin ya fashe da dariya yana nuna shi da hannu a cikin dariyar yana cewa, "Kai kam Allah ya yi maka tayar da zaune tsaye!" "Babu wani tayar da zaune tsaye sai gaskiya mutumina. A gabanmu kuma a falon nan aka yi komai, don da kujerun nan suna magana su ma da za su tuna duk kalmomin da ka faɗa a kan yarinyar nan. Sai ga shi cikin ɗan lokaci ta tashi daga siffar mazan da kake kallon ta ka gano ita mace ce kamar sauran mat.." "Daina faɗar kamar sauran mata. Minal daban ce a cikin duk matan da na sani a tsawon rayuwata." Kallon mamaki Adamu ya yi masa kafin ya ce, "Ehhhh! Lalle wannan yarinya ta zo da babbar sa'a. Amma kuma hakan yana da kyau, kuma na ji daɗin da ta san kan aikin, don Babu mamaki Allah ne ya tashi kama mana kai a sanadin ta. Don ba a yanke hukunci cikin fushi kuma a cin alwashi da izgilanci amma kai duka ka yi. Ma sha Allah, hakan yana da kyau Allah Ya ba ku zaman lafiya." "Amin-amin." Adamu ya yi shiru tsawon minti biyu yana nazari kafin ya furzar da abin da ke ransa ya ce, "Yanzu dai shikenan hankalinka ya dawo ka jefar da zancen Nur ka hut..." "Adamu...plss ka daina don Allah, ba na son jin ko sunanta a bakin kowa. Saboda na gama gano ba so na take yi ba ni ne na so ta, wahalar banza kawai na yi ita tana kallo na a ɗage." Ya yi maganar ransa a ɓace kuma cikin fushi bagan fuskarsa ta sauya daga sakakkiya zuwa tsukakkiya. "Mene ne abin damuwa to tun da Allah Ya musanya maka da alheri?" "Mu bar zancen nan kawai Adamu, saboda ba za ka taɓa gane abin da nake ji bangane da yarinyar nan ba. Amma ko ma mene ne na bar wa Allah kuma ta yi wa kanta." "Fine!" Adamu ya yi maganar cikin wani yanayi mara misaltuwa. Daidai lokacin da Dr Jimmai ta fito tana zare safar hannunta ta ce, "Har an kammala, ɗinki ne na yi mata kamu ɗaya ta ƙasa, sannan za ta dinga shiga cikin ruwan ɗumi sau biyu a rana. Sannan babu aiki mai nauyi har zuwa lokacin da za ta ji sauƙi kuma ɗinkin ya warware da kansa." Jamal ya shiga sosa kai tare faɗin "To..to..to.." saboda tambayar da yake son yi mata amma yana jin nauyi. Fahimtarsa da abin da yake son faɗa Dr Jimmai ta sake cewa, "E, ka bar ta zuwa sati ɗaya in sha Allah za ta warware kafin lokacin. Amma a halin da take ciki yanzu tana buƙatar hutu gaskiya, idan kuma aka yi garaje za ka lalata matarka ne tun kafin a je ko'ina jikinta ya buɗe." "A'ahhh! Babu komai Dr Allah Ya ba ta lafiya." Ya yi maganar cikin sauri saboda ba zai so ya rasa irin daɗin da ya kwasa ba, don ya ƙudurta bajewa a gidansa tare da killace kansa ga Minal ita kaɗai. Don haka duk abin da zai rage masa zaƙin wurin ba ya maraba da shi dole zai haƙura a bi wasu hanyoyin kafin cikar wa'adin kwanakin. Account ɗin ta ya karɓa, bayan ya yi mata godiya ya tura mata kuɗin aikin da ta faɗa har da tukuici a sama. Cikin farinciki ya rako su suna yi wa Minal addu'ar samun sauƙi suka tafi, yayin da ya dawo cikin gidan zuwa ɗakin Minal zuciyarsa cike da zallar tausayin ta a ransa. "Sannu kin ji?" Ya yi maganar cikin kulawa bayan ya kai mata kiss a saman leɓunanta sannan ya zauna bakin gadon. Hannunta ya riƙo hawaye yana zuba a kan fuskarta ya ce, "Me kike so na yi miki ladar shiga gonarki?" Marau-marau ta yi da ido wani sabon hawaye yana bin fuskarta ta ce, "Ba na son komai sai zuciyarka." "Bayan ita fa?" Sai da ta lumshe ido sannan ta ce, "Ita ɗin dai." Murmushi ya yi yana lakuce mata fuska yayin da ya ranƙwafa a saman ƙirjinta, cikin wata kalar murya ya ce, "Dama na ba ki." Shiru ta yi masa tare da rufe ido ta buɗe sannan ta yi maganar da ƙirjinsa ya buga dam-dam. "Ina so ka jaddada mini alƙawarin rabuwa da Nur har abada." Hannunta ya saki, tare da miƙewa tsaye ya yi taku ɗaya zuwa biyu sannan ya tsaya ba tare da ya juyo ba ya ce, "Ban san mai gobe za ta haifar ba, amma ba na jin zan iya sake rayuwa da Nur, ko da daga ni sai ita muk rage a cikin duniya." Tsawon minti biyu babu wanda ya sake magana a cikin su, saboda ƙwallar da ta cika masa ido ya shiga haɗiye gudun Minal ta gano ɗacin da yake ji a kan Nur har lokacin bai bar shi ba. "Ina son ki Minal, kuma na shirya zama da ke har iyakar rayuwata. Kuma zan faranta miki daidai ƙarfina, zan guji duk abin da ba kya so matuƙar bai saɓa dokokin Allah ba." Wani sanyin daɗi ya ziyarci zuciyarta, cike da ƙarfin hali ta yunƙura a hankali ta sauko daga gadon. Cikin taku biyu ta isa bayansa ta rungume shi, tare da ɗora kanta tsakiyar allon bayan ta fashe da wani sabon kuka cikin wani sautin da ya ratsa masa zuciya. Tsawon minti biyu suna haka kafin ya juya ya rungume ta a ƙirjinsa yana sauke ajiyar zuciya bayan rarrashin da yake yi mata. Hannunta ya riƙo a hankali ta fara taku zuwa bakin gadon suka zauna. Hannunsa cikin nasa ta ɗora kanta a kafaɗarsa tana faɗin, "Ina son ka kuma ina tsoron a raba mu. Don Allah kada ka so kowa idan ba ni ba, saboda zan iya yin komai a kan duk wadda ta nemi shiga tsakanina da kai ko ta nemi raba m.." "Babu wadda za ta raba mu, don haka ki daina irin waɗannan maganganun kuma ki bar kawo su a cikin zuciyarki." "Ni kaɗai na san me nake ji." Ta yi maganar tana zubar da wani sabon hawaye. Ya shiga share mata sannan ya kwantar da ita tare da rufa mata bargo yana cewa, "Bari na je na samo mana abin da za mu ci. Time ya tafi an yi sallar Zuhur." Da kallo kawai ta bi shi har ya fice ba ta ce komai ba, saboda wani sabon shauƙin son sa da take ji a cikin ranta. Shi kam wanka ya faɗa a gurguje ya shirya cikin wani yadi fari ya ɗora hula a kai. Sannan ya koma yana yi mata sallamar zai je masallaci daga can zai wuce Restaurant ya siyo musu abinci. Kamar ta hana shi, amma dole tana kallo ya fice yana ɗaga mata hannu cike da kulawa bayan ya sakar mata kisses a goshi. Ajiyar zuciya ta sauke mai nauyi kafin ta juya kwanciyarta tana jin kishin fitar da ya yi gudun wasu mata su kalle mata shi a banza. *** Jamal kam yana gama sallah a masallacin unguwar ya hau motarsa zuwa Restaurant ɗin da ya saba zuwa. Abin mamaki, tun daga shigarsa wurin ya ji ƙirjinsa ya buga, saboda wani ƙamshin turaren da ya ji ya saka jin wani iri, cikin sanyin jiki ya isa kan wata kujera ya zauna. Mintuna biyu a tsakani ya ji muryar wata ma'aikaciyar wurin a saman kansa tana faɗin, "Maigida, me za a kawo maka?" Ba tare da ya ɗaga kansa ba ballantana ya kalli fuskarta ya faɗi abin da yake so, da nufin sai ya ci ya ƙoshi sannan ya riƙa wa Minal nata ya koma gida. Minti biyu a tsakani ma'aikaciyar ta dawo cikin zunuɗi ta ajiye tiren abincin a saman table, zuciyarta cike da tsantsar farinciki ta gama daidai zaman komai sannan ta wuce ranta fes fuskarta a washe tamkar gonar auduga. Ɗan sakonni da tafiyarta ya ajiye wayar tare da jan abincin a gabansa, zuciyarsa wasai ya cire cokali a cikin ledarsa ya jefa cikin shinkafa da miyar da nufin fara ci. Har ya ciko cokalin zai kai bakinsa ya ji caraf an riƙe masa hannu. Kafin ƙamshinta ya daki hancinsa ya yi hanzarin ɗaga kai ya kai kallonsa saman kyakkyawar fuskarta. "Nurrrrrr!" Ya ambaci sunan cikin ƙaraji saboda ganin ta a lokacin da bai yi zato ko tsammani ba. An zo wurin🥲 GARE KU MASU TAMBAYA! Littafin FANSAR ƘAUNA na kuɗi ne. Ku biya ₦500 kacal ga wannan account. 9032685442 Opay. Waɗanda tura kuɗi ta opay yake bai wa wahala ku tura ta Bank Account; 1230094555 Access Bank Hadiza D. Auta Ibrahim. JERIN LITTAFAINA GA MAI BUƘATA! 1. ABOKIN AIKINA 1K 2. BAƘON YANAYI 1K 3. DAKAN ƊAKA 1K 4. AMFANIN FITILA 1K 5. JIKI DA JINI 1K 6. GIDAN AURE ₦700 7. TARTSATSI 1K 8. MAKANTAR SO 1K 9. ZUBAR HAWAYENA ₦700 10. RUWA DA ƘANƘARA ₦700 11. BAKAN GIZO ₦700 12. MUSAYAR ZUCIYA ₦500 13. DIJE ƘARANGIYA ₦500 14. DACE DA JUNA ₦500 D. ✍🏼 AUTA CE [2/20, 22:17] Hadiza D. Auta: *FANSAR ƘAUNA!* *HADIZA D. AUTA* *AREWABOOKS: Princessdija.* https://chat.whatsapp.com/Edh59w1Jcgk799uIkP0CFa *ASHIRIN DA HUƊU.* Da ido ta yi masa magana kamar yadda ta saba a kan cewa tabbss ita ce ba gizo ba. Hanzarin miƙewa tsaye ya yi bakinsa yana rawa tare da nuna ta da hannu ya sake cewa, "Da gaske ke ce nake gani ko a cikin mafarkan da kika saba zo mini ne ko yau ma?" Wani tsadadden murmushi ta yi wanda ya saka kansa sarawa, babu shiri ya runtse ido tare da dafe saitin zuciyarsa saboda ƙaƙƙafan bugun da take yi. Cikin hanzari ta riƙe shi ta baya, tare da yi masa katanga da jikinta. Yayin da ta yi maganar da ke tabbatar masa da tabbas ita ce, kuma wadda ta nan take ya fatattaki kokwanton da zuciya ke yi masa. "Babu wani mafarki Jaan! Ni ni ce dai Nur." Saukar zazzaƙar muryarta kenan a lokacin da ta daki dodon kunnensa, bayan tsadadden murmushin da take jifar sa da shi, wanda hakan ya jawo masa jirin da ya so jefar da shi ƙasa ba tare da ya shirya ba. "Ba na son sanabe! Me ye haɗin ki da shi?" Zulaiha ta yi maganar a fusace tare da buge mata hannun da ta riƙe shi gudun ya faɗi. Saboda haushi da takaicin da suka haɗe mata wuri ɗaya a kuma lokaci ɗaya. Tsabar ganin samu fili amma rashi ya nemi kulle mata ƙofar nasara. Hakan ya sa kallon mamakin da Nur take yi mata ya ƙara ɓata mata rai ta shiga auna mata harara tare da nuna ta tana faɗin, "Tun da kika hana shi cin abincin, kuma kika yi sanadin da wani ya zube ƙasa; wallahi sai kin biya mu kuɗinmu don ba za mu yi asara b..." Wata kalar dariya mai cike da tura haushi Nur ta yi, kafin ta fito daga bayan Jamal bayan ta zaunar da shi a kan kujerar da ya tashi. Taku ta yi a hankali cikin ƙasaita har ta isa gabanta tana faɗin, "Ki saka wa ranki cewa daga yau kin ƙulla ƙawance da asarar da kike gudu. Duk da ban so na fito miki a irin wannan sifar ba, amma sanin halinki da kalar hatsabibancinki; na zaɓi yin ƙwaƙƙwaran shiri tun kafin zuwan wannan ran.." "Me kike nufi? Kina magana cikin isa da gadara tamkar kin jima da sani na, ko kuma na yi miki babban laifin da kika kama ni dumu-dumu." Nur ta sake yin wani guntun murmushi tare da dafa kafaɗarta ta ce, "Kwantar da hankalinki ƙawata, mene ne abin firgita tun yanzu kafin mu shiga fagen buga wasar? Ni fa na ɗauka a yadda kike gwanar jarumta kin shirya taron aradu da ka a kowane lokaci...hummm!" Ta ƙare maganar tana zagayen ta kafin ta koma kan plate ɗin abincin da ta ajiye wa Jamal ta yamutsa shi da cokali tana faɗin, "Abin da kika zuba a cikin abincin nan nake so ki yi bayani da bakink..." "Kin yi kaɗan ki zo har wurin aikina ki nemi cin zarafina! Me na zuba da za ki yi mini ƙazafi bayan ban san ki ba kuma ban taɓa ganin ki sai a yau, yau ɗin ma a yanzu da kike ƙoƙarin manna mini sharr..." "Sharri? Sharri fa kika ce?" Sai da ta yi wata 'yar dariya sannan ta girgiza kai tana faɗin, "Ni A'isha ba na sharri alheri nake sadawa. Hakan ya sa na baro ƙasata takanas na zo Nigeria saboda kare Jaan daga sharrink...." "Innalillahi wa inna ilaihirraji'un! Wai ke mutum ce ko aljan? Ni fa gabaɗaya kin tayar mini da hankali na kasa yarda da mace iri na nake magana ko macen aljana?" Zulaiha ta yi maganar tana nuna Nur da hannu tare da ja baya tana zaro ido, tsabar tsoro da fargaban da ya yi mata mugun lulluɓi, haɗi da gumin tashin hankalin da ya gama fesowa a jikinta tamkar an watsa mata ruwa. "Saurin me kike yi, ke da za ki ga komai a idonk ..?" "Me zan gani? Ni fa wallahi ban san ki ba kuma ban san na yi komai b.." "Yanzu za ki sani?" Nur ta waiga gefenta, tare da nuni ga wani ma'aikacin wurin ya ƙaraso cikin rawar jiki. Umarni ta ba shi da ido ya shiga danna wayar da ke hannunsa, fuskarta a cure ta karɓa ta kai kallonta a kan wayar kafin ta cira kai ta kai kallon ta ga Zulaiha da ke tsaye tana waige-waige. Tsabar ruɗewar da ta yi tare da sabon tashin hankalin da ya yi mata ƙawanya. Gabanta ta isa duk da ja bayan da take yi har ta jingina bango ta tsaya. "Duba da kanki, sai kin tabbatar ke ce ko za a ɗauki matakin da ya dace da ke." Nur ta yi maganar cikin wata kalar murya tana dariya tare da miƙa wa Zulaiha wayar ta ƙi karɓa. Saboda ta gama sarewa da lamarin Nur, kuma ta karɓi laifinta ba tare da wahalar da shari'a ba. Don ƙin karɓar wayar bai hana ta furta kalaman da ke nuna ta aikata abin da Nur ke tuhumar ta ba. Saboda kai-tsaye ta haɗe fuska tana haɗiyar yawu tare da goge gumin da ke feso mata a kan fuska ta ce, "Idan ma ni ce ai ba ki san dalilin da ya sa na aikata ba. Sannan kuma duk ƙoƙarin da kike yi a kan so. tozarta ni ba ki isa ki ce guba ce na zuba ba. Don haka ko ina aka je zan faɗa ba guba na zuba masa a cikin abincin ba, idan kuma kina tantama yanzu zan ci abincin don ki tabbatar ba na kisa, kuma babu niyyar a cikin rain..." "Yi mana shiru!" Shugabar Restaurant ɗin ta buga mata tsawa cikin tsananin ɓacin rai, hakan ya ta shanye sauran maganar da ba ta gama amayowa ba. Ta shiga sosa kai tana muzurai duba da yadda wurin ya cika da mutane kowa yana kallon ta. "Kin ba ni kunya Zulaiha. Yanzu duk halaccin da na yi miki da irin wannan sakayyar za ki yi mini? Ki tuna lokacin da kika zo wurin gwanin ban tausayi kina neman aiki na ɗauke da zummar taimakon ki. Ashe tsintacciyar mage ce ke wadda ba ta mage! To daga yau kin daina aiki a wurin nan, kuma zan koya miki hankali a kan ɓacin sunan da kika jawo wa masana'antata. Wadda na rayu da ita sama da shekara goma cikin gaskiya da rufin asirin Allah. Amma a yau kina neman lalata mana tsari...to ba ki isa ba..ranka ya daɗe a tafi da ita kawai har zuwa lokacin da zan neme ku." Hajiya Inno mai abinci, ta ƙare maganar fuskarta a cure saboda ɓacin ran da Zulaiha ta ƙumsa mata. "Don Allah Hajiya ki yi haƙur..." "Babu wani haƙurin da zan yi da ke, saboda lokacin da kika shirya munaƙisarki ban sani ba. Kuma idan na bar ki ban san iya wanda za ki cutar a sanadin aikin ba. Gara kawai ki tafi hannun jami'ai su sanar da ke bambancin riƙon amana da riƙe gaskiya tsakani da Allah." Ihu Zulaiha ta fasa a daidai lokacin da ta ga 'yansanda sun zagaye ta. "Babu wani shaiɗan! Ai ba yau kika fara ba. Kin jima kina yin abin da kike so kawai asirinki ne yau ya ton.." "Ko aljana ce ke sai na ga bayanki wallah.." Zulaiha tana maganar ta yi kan Nur cikin zafin nama da nufin kai mata bahagon mari, sai dai kafin ta isa ta fara jin ɓarin makauniyar kalolin mari a kan fuskarta. Hakan bai yi masa ba sai da ya yi cikin ta da harbin ƙafa yana ta ƙwallo da ita, yayin da aka samu majiya ƙarfin da ke wurin suka rirriƙe shi, inda ya fara aman magana cikin matsanancin fushi yana nuna ta da hannu yana faɗin, "Duk ranar da hannunki ya sauka a jikinta da sunan duka sai na jijjige shi a mazauninsa na wurgar. Kuma ko da wasa na sake ganin ki a inda duk nake sai na ɗauki mummunan mataki a kank..." "Wallahi ina son k.." Zulaiha ta yi maganar cikin kuka tare da ɗaga murya a lokacin da 'yansanda suka kai mata wawuya tana ƙoƙarin tashi ta yi kansa. "Allah Ya tsine wa irin wannan son naki da babu komai a cikin sa face haɗari. Don abincin da kika zuba masa da ya ci Allah ne kaɗai ya san me zai faru, saboda kin saba cutar mazan mutane don ba yau kika fara haɗa musu tarko ba. A tunaninki kin isa da kanki saboda bokayen da kike biya suna yi miki ƙulunboto kina wasa da rayuwarsu, hakan ya aa kika zaton shi ma za ki yi nasara a kansa? Kin kuskure, don kin yi shuka a idon makwarwa. Saboda duk abin da kika tura wa 'Yan Ajin Tubarakallah Group duka na gani kuma na ji duk zagi da cin zarafin da kika yi kuma kika sa aka yi wa Minal. Sannan na bi diddiginki na gano shirin da kike ƙoƙarin yi a kansa, wannan dalilin ya sa na hana kaina zama har sai da na tabbatar na kama ki da laifin hannu dumu-dumu. Saboda ki gano ba kowane lokaci Allah yake dafa wa mutum a kan zalunci ba. Kuma ina so na karya alkadarinki ko don ki gano ba a fi kare iya kwanciya ba sai dai a nuna masa lulluɓi da bargo. Sannan faɗuwa tana farawa ne daga ba zan iya ba, amma ke taki faɗuwar ta fara ne tun daga lokacin da kika yi iƙirarin tabbatar wa duniya cewa, kin kai kuma kin isa wanzar da duk abin da kike so kuma a lokacin da kika ga dama. Ina miki fatan hakan ya zamo babban darasin da za ki tuba ki dinga bar wa Allah komai tun kafin mutuwa ta ɗauke ki kina zaluntar mutane." Daga haka 'yansanda suka wuce da Zulaiha tana muzurai bayan sun saka mata ankwa, ta yi wa Nur wani kalar kallo mai ɗauke da ma'anoni da yawa tare da ƙwafa tana cije leɓe. Nur ta sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi sannan ta kai kallonta ga Hajiya Inno, minti biyu bayan wucewar 'yansandan da Zulaiha, ta sake cewa, "Na gode sosai Mama, da kika ba ni damar gano gaskiya a kan wannan baiwar Allah. Ubangiji Ya ƙara girma kuma ya ƙara yi wa kasuwa albarka da ma'aikatanki gabaɗaya. Ni zan wuce saboda jirgin ƙarfe biyar zan bi na koma gida." "Babu komai 'yata Allah Ya yi miki albarka, kuma Ubangiji ya kai ki gida lafiya, tun da na karɓi lambarki ai za mu dinga zumunci." Taku ɗaya biyu ta yi da nufin ficewa daga Restaurant ɗin Jamal ya yi hanzarin riƙo hannunta. Kallon kallo suka shiga yi wa juna tsawon sakonni kafin ya yi jarumtar faɗin, "Ina za ki je?" Cike da mamaki ta bi shi da kallo bakinta a sake tana cewa, "Zan koma gida ne, saboda na gama aiwatar da abin da ya kawo n..." "Ba zai yiwu ba! Ke ma kin sani ba zan bar ki ki sake yin nisa da ni ba." Shiru ta yi na ɗan lokaci kafin ta ce, "Kada ka dawo da hannun agogo baya, saboda yanzu da inda aka fito akwai bambanc.." "Na fahimci bambancin da kike nufi tun a ranar da kika gudu kika bar ni. Kuma a yau zan tabbatar miki babu inda za ki je ballantana ki koma gudu na. Na yarda na amince ba kya so na, amma hakan ba zai sa na yi sakacin da za ki sake kufce mini ki ɓace wa idona b..." "Har da idan na sanar da kai ni matar wani ce?" Wayyo😆 GARE KU MASU TAMBAYA! Littafin FANSAR ƘAUNA na kuɗi ne. Ku biya ₦500 kacal ga wannan account. 9032685442 Opay. Waɗanda tura kuɗi ta opay yake bai wa wahala ku tura ta Bank Account; 1230094555 Access Bank Hadiza D. Auta Ibrahim. D. ✍🏼 AUTA CE [2/20, 22:17] Hadiza D. Auta: *FANSAR ƘAUNA!* *HADIZA D. AUTA* *AREWABOOKS: Princessdija.* https://chat.whatsapp.com/Edh59w1Jcgk799uIkP0CFa *ASHIRIN DA BIYAR.* "Wani? Wani fa kika ce!" Shiru ta yi masa maimakon amsar da yake jira. Nan take ransa ya yi ƙoluluwar ɓaci ƙirjinsa ya shiga harbawa cikin sauri. Kafin ya haɗiye wani dunƙulallen yawun da ya tsaya masa maƙwagwaro ya sake cewa, "Yanzu ni kike faɗa wa ke matar wani ce? Yanzu ba ki ji kunya da nauyin idona ki kalle ni ki furta mini irin wannan maganar ba?" Ya yi maganar cikin wani kalar sauti mai cike da laushi bayan ƙwalla ta cika masa idanuwa taf. "Gaskiyar kake so na ɓoye maka?" Hannu ya saka ya bugar da ƙwallar da ke ƙoƙarin gangarowa a saman fuskarsa sannan ya jinjina kai yana cewa, "Tabbas sai yau na ƙara tabbatar da ba kya so na. Don haka ki je ki zauna da wanda kika zaɓa a madadina. Alhamdulillah na samu Minal a yadda ban yi tsammani ba, ko iya haka na sani Allah Ya mini kyakkyawar sakayya a kan abin da kika aika min...ki je..ki je..kawai...matar wani ko? Humm...ya yi kyau." Ya yi maganar tare raɓawa ta gefenta yana tafiya da baya da baya idonsa a kanta yana sara mata. Saboda matuƙar mamakin da ta ba shi, tare da zafin kishin ta da ke caccakar zuciyarsa. Maganganunsa da tafiyarsa sun saka kukan da take jarumtar ɓoyewa ya fallasa ƙuncin da ke cin ranta. Don hawaye ya dinga bin fuskarta shaa tana ƙoƙarin haɗiye amma ya ƙi tsayawa. A haka ta bi bayansa da sassarfa daidai lokacin da ya isa inda ya ajiye motarsa yana ƙoƙarin buɗewa ya shiga. "Jaaan!" Ta kira shi da sunan da ta saba kiran sa. Kiran da ya sa tsikar jikinsa ta tashi yarr kafin ya ɗaga kai ya kai kallonsa a kanta. Tafiya ta ci gaba da yi zuwa inda yake jiri yana ɗibar ta tare da dishi-dishin da take gani. Amma hakan bai hana ta isa gabansa ta durƙusa gwiwa biyu ba, kafin ta haɗa hannuwanta wuri ɗaya alamun roƙo tana cizon leɓenta. Tsawon minti biyu tana haka kanta a sunkuye ba tare da ta ɗago kai ko ta furta abin da take son furtawa ba. Shi ma idonsa a kanta ko ƙiftawa babu zuciyarsa cike da jin haushin ta bayan mahaukacin kishin ta da ke kartar ransa. "Sauri nake yi. Na baro matata a gida babu lafiy..." Ya yi maganar cikin ƙunar rai, tare da nuna mata shi ma ya ɗau zafi a kan furucinta. Sai da ta zuƙe majinar kukan da ke yunƙuro mata, sannan ta yi jarumtar goge hawayen idonta, tare da haɗiye ɓacin ran da ya cusa mata. Zumbur ta miƙe tsaye daidai lokacin da kira ya shigo wayarta. Da hanzari ta fiddo ta a jaka ta ɗaga kiran, saƙon da aka isar mata a cikin wayar ya sa ta magana cikin sauri. "Ka jira ni, in sha Allah yanzu zan ƙaraso kafin lokaci ya cika." Ta katse kiran tare da kai kallon ta a kan agogon hannunta tare da cira kai zuwa kan fuskar Jamal, ido cikin ido suka dinga kallon juna, sai da ta sauke ajiyar zuciya sau biyu kanta a sunkuye kuma rungume da hannuwanta a ƙirji, sannan ta sauya akalar zancen da ta so furtawa a farko, cikin murmushin yaƙe ta ce masa, "Ni zan wuce jirgin da zan bi ya kusa tashi, idan ka je gida ka gaishe da matarka." Tana ƙare faɗar hakan ta juya cikin takunta na taƙama kamar koyaushe ta nufi bakin titi iska yana kaɗa ta. Kallo ya bi bayanta da shi hawaye yana bin fuskarsa saboda wani kalar tashin hankalin da ya dira kansa cikin zaucewa ya ce, "Har abada, ba zan fasa kallon ki a matsayin wadda ta cutar da rayuwata ba, matuƙar ba ki sanar da ni laifin da na yi kika yi kyauta ta ga Minal ba. Sannan ki sani duk taku ɗaya idan kin yi, tamkar tafiya da numfashina ne kike yi. Don muddin kika tsallake ƙasar nan kika sake bari na kamar yadda kika yi a farko, to ina tabbatar miki kafin ki isa inda za ki je za ki ji saƙon mutuwat..." "Jaaann!" Ta kira sunansa tare da juyowa babu shiri, a cikin wani matsanancin firgicin da ya bayyana kan fuskarta. Ta dawo jikinta yana rawa cikin matsanancin fushi ta isa gabansa tamkar kububuwa. Idonta a rufe ta ɗaga hannu ta wanke shi da mari, hawaye yana bin fuskarta ta fara nuna shi tana magana cikin kuka tamkar ta shiɗe. "Da za ka zamo ajalina a yanzu nan zan iya yafe maka Jaan kuma har a gaban Allah. Amma wallahi! Wallahi ba zan taɓa yafe maka ba matuƙar ka kashe kanka a kain...ina son ka Jaaan kai ma ka sani wallahi ina son k..." Ta ƙare maganar tare da fashewa da wani mahaukacin kuka, tare da faɗawa jikinsa ta rungume shi tsantsan tamkar za a ƙwace mata shi. Tsawon minti huɗu tana jikinsa tana ta rera kalolin kukan da ya ƙara raunata ɗan kuzarin da ya rage masa a jiki da zuciya. Saboda ya sandare wuri ɗaya ko motsi ya kasa yi, amma idanuwansa ba su daina ɓarin hawayen da ke malala a kan fuskarsa ba. Duk da tarin jama'ar da suka tara wa kansu ba tare da sun sani ba. Kamar yadda surutan da mutanen suke yi a kansu bai sa sun hankalta sun dawo nutsuwarsu ba. "Woww! An burge ni... Billahillazi an tashi kaina!" Ire-iren waɗannan maganganun aka shiga yi, tare da bidiyo da hotunan da ake ta ɗaukar su. Saboda yanayinsu ya fallasa su a matsayin masoyan da suka samu saɓani, sannan kuma waɗanda ba son rabuwa da juna. "Lafiya 'yata? Me ya faru?" Zancen Hajiya Inno mai abinci kenan, a lokacin da aka sanar da ita cincirindon da aka yi mata a bakin Restaurant. Cikin rawar jiki ta fito gudun a ƙara jaza mata wata fitinar bayan zafin abin da Zulaiha ta yi mata ko hucewa bai yi ba, wanda ya jawo ce-ce-kuce a tsakanin ma'aikatanta da customers har ya so ya koma musu wata sabuwar hatsaniya. Hajiya Inno ta jawo Nur a jikinta fuskarta a yamutse tana ƙara tambayar dalilin kukanta. Musamman da ta hango hawaye a idon Jamal sai abin ya ƙara ɗaga mata hankali. Cikin rawar murya ta sake jefa wa Nur tambaya a ruɗe tana faɗin, "Kin..ga..kin..ga..don Allah ki sanar da ni abin da yake faruwa. Kalli mutane ki gani gabaɗaya ku suke kallo! Me ya haɗa ki da shi ne? Ko duk a kan rikicin da aka gama a kan Zulaiha ne?" Nur ta shiga girgiza mata kai a kan duk tambayoyin da take jera mata. Ranta a ɓace cikin ɗaga murya ta sake cewa, "To mene ne? Ki sanar da ni bakiɗaya an ɗaga mini hankali." Nur ta ja hannunta da nufin su koma cikin Restaurant ɗin, babu musu ta bi ta tare da bai wa Jamal umarnin shi ma ya biyo su. Rufe motarsa ya yi cikin sanyin jiki ya bi su jiri yana ɗibar shi tamkar ya faɗi. Tsabar damuwar da yake ciki, a gefe ɗaya kuma tunanin halin da ya bar Minal a ciki. Wuri na musamman Hajiya Inna ta kai su inda babu zirga-zirga, bayan sun zazzauna ta kalli Jamal cike da zaƙuwar jin abin da yake faruwa ta ce, "Kai ne namiji, da kai zan fara. Duk da na san ka tun ba yau ba, amma ban san tsakaninku ba, sai dai ga dukkan alamu akwai wata keɓantacciyar alaƙa a tsakaninku ba iya yadda ita 'yata ta sanar da ni ba. Don ta faɗa mini kai mijin 'yar'uwarta ne, amma kuma yanayinku ya nuna ba iya wannan alaƙar ce ta haɗa ku ba. Duba da yadda ta ce mini tun daga Niger ta zo nan saboda kawai ta kare ka daga sharrin Zulaiha. Don haka idan kun ɗauke ni uwa kamar yadda nake yi muku kallon 'ya'yan da na haifa, ku sanar da ni gaskiyar abin da ke tsakaninku idan har na cancanci hakan." Ku yi manage, jiki da jini yau an taɓo nawa file ɗin ni ma Minal ta sakar mini ciwon.😪 GARE KU MASU TAMBAYA! Littafin FANSAR ƘAUNA na kuɗi ne. Ku biya ₦500 kacal ga wannan account. 9032685442 Opay. Waɗanda tura kuɗi ta opay yake bai wa wahala ku tura ta Bank Account; 1230094555 Access Bank Hadiza D. Auta Ibrahim. D. ✍🏼 AUTA CE [2/20, 22:17] Hadiza D. Auta: *FANSAR ƘAUNA!* *HADIZA D. AUTA* *AREWABOOKS: Princessdija.* https://chat.whatsapp.com/Edh59w1Jcgk799uIkP0CFa *ASHIRIN DA SHIDA.* Ajiyar zuciya Jamal ya sauke mai ƙarfi kafin ya ɗora kallonsa a kan Nur ya ce, "Ban taɓa tunanin za ki guje ni ba, saboda yarda da amincin da ke tsakanina da ke. Mun gina so da ƙauna a cikin gaskiya da rashin ɓoyewa juna matsaloli. Amma sai dai ashe ni yadda na ɗauke ki ke a wurin ki ba haka nan ba n..." "Kallar ni da kyau ranka ya daɗe, ni za ka yi wa bayanin da na nema, ka ajiye wannan zancen naku kamar zai fi dacewa a tsakaninku." Zancen Hajiya Inno kenan a lokacin da ta ji maganar Jamal ta sauka daga layin abin da take son ji. Murmushin takaici ya yi idonsa a kan Nur ya sake cewa, "Har abada ba zan manta abin da ta yi mini ba Hajiya, saboda haka ba zan iya bayanin komai ba idan ba cin amanar da ta yi wa rayuwata kike son ji ba." "Assha! Ranka ya daɗe komai na duniya fa ɗan haƙuri ne. Kuma idan ka nutsu da kyau za ka fahimci ita ma ba ƙaramin so take yi maka ba, duba da yadda ta baro ƙasarta takanas don tseratar da kai daga matsal...' Nur ta yi hanzarin katse ta cikin fushi tana cewa, "Ki bar shi..ki bar shi kawai Mama, ni duk abin da na yi don Allah na yi da ceton rayuwar 'yar'uwata Minal. Kuma Allah shi ne shaidar ban guje ka don ba na son ka ba. Kuma na yi abin da na yi ne da kyakkyawar niyya ko da kai ba za ka fahimce ni ba. Sannan ban ce dole sai ka yarda da duk abin da na faɗa ba, amma ni dai na sani har abada ba zan bari a cutar da kai ba, haka ma ni da kaina ba zan yi abin da na san zai cutar da kai ba. Saboda haka ka kalle ni a yadda duk kake kallo na, kuma ka ci gaba da kallo na da irin fassarar da kake yi mini babu komai." Tana ƙare maganar ta miƙe tana goge ƙwalla ta bar wurin gudu-gudu sauri-sauri saboda kukan da ke barazanar fallasa ƙuncin zuciyarta. Hakan ya sa duk kiran da Hajiya Innon ke yi mata bai sa ta juyo ko ta tsaya daga ƙudurinta na son tafiyar ba. Daidai lokacin da kira ya sake shigowa wayarta, inda tana ɗauka mai maganar ya sanar da ita jirgin da za ta bi har ya tashi, don ya yi ta kiran ta ba ta ɗauka ba, kuma ya turo mata saƙo ba ta yi masa reply ba. Saboda ya yi ta kiran ta tana danne kiran tun farkon zaman sulhun da Hajiya Innon ta so yi musu, har zuwa lokacin da ta miƙe da nufin barin wurin a gaggauce ana ta kiran ta, don ta san dalilin kiran da abin da ke gabanta idan ta koma Niger. Hannu ta ɗora a ka cikin tashin hankali ta yi magana da wanda ya kira tana cewa, "Ina cikin tashin hankali Adamu, saboda wallahi babu wanda ya san na zo ƙasar nan, kuma kai ka san uzurin da kenan, wanda ko ba na so dole na yi tafiyar nan a yau, gudun na shiga wani sabon bala'i." Shiru Adamun ya yi na ɗan lokaci kafin ya ce, "Idan babu damuwa ki zo na kai ki masaukin da za ki kwana cikin sirri kafin lokacin mu ga yadda za a y..." Cikin rawar murya ta ce, "Gobe ne ɗaurin aurena ka sani, ta ya ya zan iya kwana a nan asirina ya tonu idan aka neme ni aka rasa? Ba zai yiwu ba Adamu, don Allah ka bincika mini idan akwai jirgin da zai tashi ko da cikin dare ne zan bi sh..." "Babu inda za ki je ballantana ki yi auren da kike faɗa!" Ta ji maganar Jamal tsidik a cikin kunnuwanta, cikin hanzari ta juya tana kallonsa, ba ta ankara ba ta ji ya fisge wayar tare da ɗora ta a kan kunnesa, inda yake ƙoƙarin yin magana amma kafin ya ce wani abu ya ji muryar Adamu yana faɗin, "Ki yi haƙuri, zan bincika miki, idan da halin tafiyar a yau sai mu gan..." "Za ka gani kuwa baƙin munafuki! To ko ubanka ne mijin babu inda za ta je sai da igiyar aurena. Kuma ka sani wallahi idona idonka sai na nuna maka ba iri na ake ha'inta ba." Yana ƙare maganar ya ɗora jajayen idanuwansa a kanta, kafin ya fisgo hannunta cikin matsanancin fushi tana tirjiya tare da buge masa hannun, amma hakan bai hana shi cusa ta cikin mota ba. Hajiya Inno da ke kallon abin da ke faruwa ta biyo su tana faɗin, "Ranka ya daɗe ka bi komai a hankali don Allah, ka san tunanin mace ba ɗaya ne da naku maza ba. Kada ka yanke hukuncin da zai jawo danasani daga baya." Uffan bai ce da ita ba, illa hannun da ya ɗaga mata yayin da zai bar wurin yana ƙoƙarin hawa kan titi. Nur da ke zaune gaban motar tsuru-tsuru tana zarar ido, tsabar tashin hankalin da take jin kanta a ciki tamkar ta fi kowa matsala. Ido ta ɗora a kansa tana faɗin, "Ban san ina za ka kai ni ba, amma ka sani rashin komawata gida a yau, da abin da rashin gani na zai haifar ya fi matsalarka girma. Don haka ka tausaya mini kada ka bari rayuwata ta lalace a sanadin biye wa son zuciyarka." Kalamanta ba su sa ya ji tausayin ta ba ballantana ya magantu, illa ƙarin baƙinciki da haushin da suka jefa shi ciki. Gudu ya shiga shararawa a saman titin tamkar wanda zai tashi sama, bai zame ko'ina ba sai a bakin wani Shopping Mall. A gaggauce ya fice bayan ya saka motar a key gudun ta fice bai sani ba. Shigewarsa ke da wuya ta ɗaga waya ta kira Adamu, sai dai har ta yi ringing ta gama bai ɗaga ba, cike da jin haushi ta tura masa saƙo tana faɗin, 'Kada ka tayar da hankalinka a banza, Allah Ya fi kowa sanin gaskiyar abin da ke tsakanina da kai. Don haka duk matakin da zai ɗauka ka yi haƙuri don Allah kada ka biye shi." Bayan ta tura saƙon ta yi shiru tana nazari tare da goge hawayen da ya kasa barin idanuwanta. Mintuna a tsakani ya fito tare da wasu ma'aikatan wurin a bayansa da kayan abinci niƙi-niƙi. Bayan boot ya buɗe aka gama zuba kayan ya rufe tare da buɗe motar ya shiga. Kuma har lokacin fuskarsa a cure ya tayar da motar ya juya aguje ba tare da ya ce da ita ƙanzil ba. Kasancewar ta yi zama garin Kanon tsawon shekara biyu zuwa uku, hakan ya sa ta fahimci inda ya nufa da ita. Kallon sa ta yi cikin wani yanayi mara misaltuwa kafin wani sabon kuka ya zo mata ta yi magana cikin raunin murya da zuciya ta ce, "Me kake nufi da kai ni gidan su Minal?" Bai amsa mata ba, kamar yadda bai kalle ta ba, gudunsa kawai yake yi da motar har zuwa lokacin da ya saki babban titin ya gangara cikin layin su Minal. Sai da ya dira a ƙofar gidan sannan ya yi jim yana kallon gabansa ya ce, "Ki shiga ciki, idan Baba yana nan ki kira mini shi." Ba ta fita kamar yadda ya buƙata ba, sannan ba ta ce da shi ƙanzil ba, illa zuƙar majinar kukan da take yi tare da goge hawayenta jefi-jefi da mayafin doguwar rigar da ke jikinta. "Ki kira shi na ce!" Ya sake yin magana cikin ɗaga murya tare da ɗora kallonsa a kan kumburarriyar fuskarta, wadda tsabar kukan da ta sha ta sauya kala zuwa ja. Ganin ba ta da niyyar fita kuma kukan da take yi ba ƙaramin taɓa masa zuciya yake yi ba, hakan ya sa cikin zafin nama ya ɓalle murfin motar ya fice. Wasu yara ya yafito suka zo da gudu, ya buɗe boot ɗinsa yana fito da kayan tare da ba su umarnin su shiga da su daga ciki, kuma idan Baban yana ciki su yi masa sallama da shi. Sai da aka shigar da kayan duka sannan ya jingina da motar rungume da hannu kansa a ƙasa yana nazarin mafita a kan hukuncin da yake son zartarwa. Duk da ya sani abu ne mai matuƙar wahala, amma duk tsanani gara rayuwa da Nur a wajensa da a ce ya yi rashin ta gabaɗaya. Jim kaɗan bayan shigar yaran suka fito Innarmu a bayansu lulluɓe da zani tana leƙe, don ta gane wa idanuwanta mai mutunci da ya gwangwaje su da kayan abinci irin haka. Caraf ta hango Jamal a bakin motarsa, baki buɗe ta fara rawar jikin gaishe shi tun kafin ya gan ta shi ya fara gaishe ta. "A'ah! Lale-lale marhabin da zuwanka. Allah Sarki ashe kai ne da wannan tagomashin alheri har haka?" Sai a lokacin hankalinsa ya dawo jikinsa ya kai kallonsa gare ta yana murmushin yaƙe. Kafin ya bar jikin motar cikin sanyin jiki ya isa inda take ya rusuna kansa a ƙasa ya shiga gaishe ta, ita kam tuni ta riga shi kai ƙasa tana godiya ba tare da ta amsa gaisuwar da yake yi mata ba. "Amm.. Baban yana ciki kuwa?" Ya yi tambayar kansa a ƙasa bayan ta gama godiyar shi ma ya ce babu komai yi wa kai ne. "Ai ka san Malam ba ya zama a irin wannan lokacin sai dare ake samun sa a gida. Sai dai idan ya dawo a sanar da shi ka zo shi ma ya kira ka ya yi maka godiya. ...ai mun gode mun gode sosai wallahi. Allah dai ya biya ka kawai ya ƙara muku zaman lafiya da Amina." "Amin-amin." Ya amsa kansa a ƙasa kafin ya ɗago idonsa ya kalle ta cikin girmamawa ya ce, "Tare nake da baƙuwa, za ta shiga ta zauna kafin zuwa daren sai na dawo mu yi magan..." "Haba-haba! ai babu komai wallahi an zama ɗaya ta shigo ta zauna gidanku ne kai ma, kuma kana da ikon kawo duk wanda kake so ya zauna a cikin gidan kamar yadda Amina take da iko da shi." Har cikin ransa ya ji daɗin furucin Innarmu, hakan ya ƙara masa ƙarfin gwiwar miƙewa ya isa gefen da Nur take zaune ya buɗe mata ƙofa. Ido cikin ido suka kalli juna tsawon sakon biyu kafin ya nisa, cikin wata kalar murya ya ce, "Fito ki shiga ciki, zuwa dare zan dawo mu yi magana." Sanin Innarmu tana ganin su don ta kasa ɗauke idanuwanta daga kansu cike bin ƙwaƙƙwafin gano wace ce tun kafin ta iso, don har da leƙawa ta gilashin ta yi da zummar hango ta tun a cikin motar. Sai dai kasancewar ba a ganin na ciki ta wajen ya sa dole ta bar zura wuyan ta mayar da kallonta ta saman motar. Dam-dam ƙirjinta ya buga saboda ganin Nur ta fito daga motar, baki buɗe ta ƙura mata kallo har zuwa lokacin da ta ƙaraso gabanta ta durƙusa har ƙasa tana gaishe ta. Cikin kaɗuwa da zaucewa Innarmu ta riƙe ƙugu tana faɗin, "Uban wa ya dawo da ke a cikin gidan nan?" Nur ba ta ɗaga kanta ba, illa sabon hawayen da ya shiga bin fuskarta. Jamal ne ya yi ƙarfin halin isa wurin cike da mamaki ya zuba wa Innarmu kallo kafin ya ce, "Ita ce wadda na kawo ajiya kafin Baba ya dawo mu yi magan..." "Dakata-dakata yaro! Ko dai ka manta nan gidan iyayen Amina ne matarka wadda kake aure?" "Ina sane ba mantawa na yi ba. Kuma kin faɗa ina da iko da gidan kamar yadda Amina take da iko da sh.." "Amina da kai daban! Sannan wannan tsintacciyar magen daban! Saboda haka ba za ta shiga cikin gidan nan ta zauna mana ba ko da sakon ɗaya ne. Don ba mu haɗa komai da ita ba, asali ma babu wanda muka taɓa gani a cikin danginta, shi kansa maigidan da ya ɗebo mana ita daga baya ya gano kuskurensa a kan riƙon wadda bai san komai a kan asalinta ba. Saboda haka ka kwashe ta ku matar da ita inda ta ɓoye tun kafin Malam ya dawo ku jawo mana wata sabuwar fitina." Shiru ya ratsa tsakani bayan maganarta, saboda sabon ɓacin ran da Innarmu ta cusa masa. Bai ce da ita komai ba tsabar ƙimar Amina da ke ransa, sannan da darajar surukantaka da yake kallo a idonsa. "Tashi mu je!" Abin da ya faɗa kenan kafin ya bar wurin ya faɗa matarsa yana ba ta wuta. Nur ta miƙe ba tare da ta ce da Innarmu komai ba ita ma ta bi bayansa. Hakan ya ƙara rura wutar tashin hankalin da Innarmu take ciki, ta shiga tsine wa Nur tare da miyagun lafuzza iri-iri, sai wanda bai zo cikin bakinta ba. Har da iƙirarin duk ta sake ganin ta a ƙofar gidan hukuma ce za ta raba su. "Kin san shagon Baban ne?" Nur ta yi banza da shi har suka hau babban titin Jogana suka miƙi hanyar zuwa kasuwar da Baban Amina yake zama. Saboda ya san kasuwar da yake zuwa tun zamanin yana neman auren Nur, amma bai taɓa sanin wanne shagon da yake aiki ba. Sai da suka je bakin titin kasuwar ya samu wuri ya yi parking, sannan ya ɗaga wayarsa ya kira Baban. Sai dai har wayar ta nemi tsinkewa bai ɗauka ba, cike da jin daɗi Jamal ya amsa sallamar da ya yi masa cikin mutumtawa bayan ya ɗauka. Suka gaisa tare da sa albarka ga Jamal da yi masa addu'ar ƙarin zaman lafiya da Amina, bayan ya gama tambayar Hajiya da saƙon gaisuwa gare ta. "Baba akwai maganar da nake so mu yi da kai." "To..too babu damuwa. Za ka iya zuwa da dare idan na koma gida sai mu tattauna." Sosa kansa Jamal ya yi kafin ya ce, "Yanzu haka ina bakin kasuwarku Baba, idan da halin fitowa ka zo mu tafi gidan tare, saboda magana ce mai matuƙar muhimmanci za mu yi." "To, babu komai ka jira ni yanzu zan fito sai mu tafi." Jamal ya katse kiran yana kallon Nur da ta yi tagumi tana kallon mutanen da ke ta zirga-zirga ta gabansu. Amma zuciyarta ko kaɗan ba ta wurin, don ta tafi duniyar tunanin abin da zai faru idan har aka neme ta ba a san inda ta je ba. Ga shi ta cire layukanta na Niger, ta saka na Nigeria da niyyar idan ta gama abin da take yi ta zare shi ta adana kamar yadda ta yi a ranar da ta bar garin. Akwai kallo🏃 Na gode sosai da addu'o'inku. Allah Ya bar zumunci. GARE KU MASU TAMBAYA! Littafin FANSAR ƘAUNA na kuɗi ne. Ku biya ₦500 kacal ga wannan account. 9032685442 Opay. Waɗanda tura kuɗi ta opay yake bai wa wahala ku tura ta Bank Account; 1230094555 Access Bank Hadiza D. Auta Ibrahim. D. ✍🏼 AUTA CE [2/20, 22:17] Hadiza D. Auta: *FANSAR ƘAUNA!* *HADIZA D. AUTA* *AREWABOOKS: Princessdija.* https://chat.whatsapp.com/Edh59w1Jcgk799uIkP0CFa *ASHIRIN DA BAKWAI.* A ɓangaren Minal kuwa, tsawon miniti goma bayan fitarsa tana nazarin yadda ta samu matsayin da ba ta taɓa tunanin za ta samu a wurin sa ba. 'Ashe ni ma mace ce?' Ta yi zancen daga ita sai zuciyarta, yayin da ta shiga godewa Hajiya a ranta, da Gwaggo Salame da ke dannar ta har zuwa kan Innarmu da ke danna mata ashar a kan wajibi ne sai ta zauna. 'Allah Sarki Babana, ka mini nasiha kuma na ɗauka, in sha Allahu zan bi mijina kamar yadda ka ba ni shawara.' Ta ƙare zancenta na zuci tare da sauke wata nannauyar ajiyar zuciya tana runtse ido. Saboda ta kasa manta rawar ɗuwawun da Jamal ya yi a kanta tsabar ya same ta cikakkiyar mace bayan gyaran Hajiya. "Idan ka ba ni zuciyarka ma ta wadatar da ni. Hakan ya sa ba na buƙatar komai sai kai kawai....Nur kum.." Ta yi saurin toshe bakinta tamkar wani zai ji ta, cikin sauri ta yi niyyar gyara kwanciyarta babu shiri ta ce, "Ashh!" Saboda zogin da ta ji a ƙasanta dole ta lallaɓa a hankali har ta daidaita kwanciyar sannan ta rufe idonta da niyyar yin barci. Sai dai kafin barcin ya yi awon gaba da ita ta jiyo tashin murya a falo ana ta rafka sallama. Ta ƙara lafewa a cikin gadon tare da kasa kunne tana son tantance muryar mai sallamar. Cikin sauri ta zaro ido, saboda jin muryar Inna Ade tana faɗin, "Matar gidan tana kusa kuwa?" "Inna ga ni a ɗaki, ki shigo kawai." Ta yi maganar cikin wata kalar muryar mara lafiya, tare da tsabar jin nauyi da kunyar Inna Aden, gudun ta gano halin da take ciki har ta fahimci abin da ya wakana. Muryar Inna Ade ta so ɗakin tana faɗin, "Ai na ɗauka ke ma ba kya nan ganin yaron nawa ma ba ya gidan. Don na yi mamaki da maigadinku ya ce kina ciki don na yi sallama ta fi goma ban ji motsin kowa ba." Tana maganar har ta tura ƙofar ɗakin ta shiga ɗauke da wani ƙaramin kwando a hannunta. "Ban ji ba ne Inna ai da na amsa miki, saboda barcin da ya fara ɗiba ta sai daga baya na ji sallamar." Ta yi maganar tana runtse ido tare da cije leɓenta saboda yunƙurin tashin da ta yi kafin ta shigo ɗakin amma ta kasa. Bakin bed side Inna Ade ta zauna idonta a kan Minal cike da son tabbatar da abin da take zargi ta ce, "Allah Ya sa dai lafiya lau kike, don na ji muryar taki kamar ta marasa lafiya." Murmushin dole Minal ta janwo a kan fuskarta sannan ta ce, "Ƙalu nake Inna, kawai dai ɗan zazzaɓi ne ya kafce ni cikin dare har sai da aka yi mini allurai." "Allah Sarki matar yarona, ashe Hajiya ta canka daidai. Don takanas ta tayar da ni na zo saboda kawai na kawo miki abin da ta dafa miki. A cewarta ma, jikinta ya ba ta kina can kina kewar ta, ko iya wannan zai sa ki Yi zazzaɓin. Sannu kin ji, Allah Ya ba ki lafiya, amma za ki iya tashi ko na taimaka miki don ki ci abincin. Saboda ta ce na saka ki gaba har sai kin cinye komai na dawo mata da kulolinta." Murmushi Minal ta yi mai sauti, cike da Jin daɗi a ranta ta ce, "Ɗan kama ni dai Inna, jikin ne nawa ko'ina ciwo yake yi. Ga bakina babu daɗi kamar na yi sati ina jinya." Ta ƙare maganar tana cije leɓe Inna ta ɗago ta a hankali cikin dabara ta kai ta jikin gadon ta ɗora mata a bayanta ta jingina. Cike da tausaya wa ga halin da take ciki ta sake ce mata, "Wannan ciwo ya buge da yawa matar yarona, na ji jikin naki da zafi rau har yanzu kamar zazzaɓin bai gama sauka ba." Shiru kawai Minal ta yi cike da jin nauyin ta a ranta, saboda jikinta ya ba ta kamar ta gano abin da ya faru, tana biye ta ne kawai a yadda take so. "Me kike son ki fara ci? Akwai farfesun kaji, akwai na kayan ciki da kuma taliyar Hausa." Minal ta yi murmushi sannan ta ce, "Haɗa mini ruwan tea kawai Inna, saboda bakina babu daɗi ba zan iya cin komai ba." Kitchen Inna Ade ta tafi cikin sauri ta haɗa mata tea mai kauri don ta zabga mata madara. Sannan ta nemo plate guda uku mai faɗi da masu zurfi biyu, tare da cokali ta dawo ɗakin. Cikin kulawa ta miƙa mata kofin shayin tana fara sha ta koma zuba mata taliyar da Hajiya ta dafo mata da hannunta, a gefe ɗaya kuma tana ta jera mata sannu. Sai da shanye shayin tas sannan Inna ta karɓi kofin ta miƙa mata plate ɗin taliyar ta karɓa tana faɗin, "Kaɗan zan ci Inna saboda Hajiya ta ji daɗi, amma ko kaɗan ba na jin son cin abinci bakina babu ɗanɗano." "To ki ci ko ya yake ya fi rashin cin." Kaɗan ta tsakuri taliyar Inna Ade tana matsawa har ta ci rabin plate sannan ta karɓi plate ɗin ta ɗauko wanda ta zuba mata farfesun kajin da suka sha dafuwar ruwa sai ƙamshi ke tashi. Minal ta karɓa yawunta yana tsinkewa ta fara ci tana faɗin, "Wannan daɗin duk ni kaɗai Inna?" Inna Ade tana 'yar dariya ta ce, ni ma umarnin kawowa kawai aka ba ni matar yarona, yadda kika gan shi a haka na gani don Hajiyar ce ta yi komai da kanta. "Ubangiji Ya saka mata da mafificin alherinsa." Ta yi maganar cikin muryar kuka tana goge ƙwalla da bayan hannunta, saboda har zuciyarta mutuncin Hajiya a idonta ya yi girman da dole sai ta zubar da hawaye. "Kuka kuma?" Inna ta yi maganar tana 'yar dariya bayan ta gama faɗin amin. Minal ma ta yi dariyar bakinta a washe ta ce, "Abin da Hajiya take yi mini ko mahaifiyata ban samu wannan darajar a wurin ta ba. Don haka ban san da wane baki zan ce mata na gode b..." "Abu ɗaya za ki yi mata ki faranta ranta, idan kin riƙe mata yaro tsakani da Allah. Da kin yi hakan shikenan kin gama biyan ta, don iya abin da take so kenan a wurin ki kada ki sake barin wasu mata su ɗauke masa hankali. Babban burin Hajiyar kenan, wanda ya sa take sadaukar da komai nata a kan samun wannan biyan buƙatar." Shiru Minal ta yi tsawon mintuna tana nazari kafin ta sauke ajiyar zuciya ta ce, "Da yardar Allah zan riƙe shi irin riƙon da wata mace ba ta isa ta sha gabana a wurin sa ba. Kuma na yi wa kaina alƙawarin zan yi haƙuri da halinsa ta yadda komai zai yi mini zan jur...." 'Nur fa?' Tsam ta yi da ranta a lokacin da Inna Ade take zuba mata ruwan albarka, ita kuma zuciyarta ta tafi tunanin ba za ta iya jurar ganin sa da Nur ba. Za ta iya haƙuri da shi a kan komai amma babu shirgin da ya kwaso Nur a ciki. Don ko sunanta ta tuna ƙirjinta faɗuwa yake yi, ballantana ta tsunduma tunanin rayuwarsu kafin lokacin aure har zuwa shagalgulan bikin da ranar da aka kawo ta cikin gidan. Ajiyar zuciya ta sauke mai ƙarfi tare da kai kallonta ga Inna Ade tana murmushin yaƙe, tare da faɗin, "In sha Allahu Inna." Saboda duk abin da take faɗa ba ta ji komai ba sai ki riƙe mijinki da take ta nanatawa a bakinta. Bayan ta gama jera mata kalolin nasihohi a kan haƙuri da zaman aure da zama jajirtacciya a kan kowace irin matsala. Cikin dabara Inna ta ja hankalinta suna ta hira har ta kusan cinye duka ferfesun da ta zuba mata sannan ta sha romon duka. Cike da jin daɗi Inna Ade ta laƙume sauran taliyar da ta rage, kuma lashe sauran abin da ta rage na ferfesun ta je ta wanke komai da aka ɓata, tare da juye mata da sauran taliyar da ke kula da ferfesun a nata kalolin sannan ta yi sallama da ita da niyyar tafiya. Minal ta roƙi alfarmar ta haɗa mata ruwan ɗumi a bahon wanka, sannan ta taimaka mata ta yunƙura da ƙyar ta kai ta toilet, cikin ƙarfin hali Minal take takawa tare da ƙarfafa zuciyarta a kan jin sauƙin dole kafin Jamal ya dawo, don ta ci burin yi masa sabuwar kwalliyar da idan ya gani zai yaba ita ma ta ji daɗi. Hakan ya sa ta ɗauki tsawon mintuna a toilet ɗin tana gasa kanta har zuwa lokacin da ji ƙarfin jikinta ya dawo. Sannan ta yi wanka tare da ɗoro arwala ta dawo ɗaki, inda ta ga Inna Aden tana share ɗakin bayan ta gyare gadon tas kamar ba a taɓa kwanciya kansa ba. A zaune ta yi sallar Zuhur da Asr ganin Inna ta fice daga ɗakin, kafin ta shafa addu'a ta koma bakin madubi ta shiga tsara kwalliyar tarbon Jamal. Duk da wani gefen zuciyarta yana hango mata rashin kyautawarsa a kan barin ta daga siyo abinci ya dawo har zuwa lokacin bai dawo ba. Amma ta yi masa uzuri saboda yadda ya nuna mata kulawa kafin ya fita tana a ji a ranta bai yi hakan da gangan ba, ta ɗora laifin a kan wataƙila wani babbab uzuri ne ya danne shi wanda ya hana shi dawowa cikin lokaci. Bayan ta gama shirin ta fito fes cikin wata sabuwar shadda golden colour mai ɗinkin doguwar riga ɗauke da aikin baƙin zare da golden ɗin. Sannan ta feshe jikinta da turaruka tana baza ƙamshi ta fito falon ganin Inna a falon kwance. Fitowarta ya sa Inna kai kallonta a kanta tana faɗin, "Ma sha Allahu tubarakallah! Yarona ya yi sa'ar mace mai tsada a gidansa." Murmushi kawai Minal ta yi ta isa inda wayarta take caji tun daren jiya har lokacin. Sai dai ganin ta a zare zuciyarta ta tabbatar mata Jamal ne ya cire bayan cajin ya cika. Zama ta yi da wayar a hannunta bayan ta kunna musu Tv tana 'yar dariya tare da faɗin, "Alamu ya nuna Inna kin fi son yaronki a kaina." "Kamar yadda Hajiya ta fi son ki a kansa Kenan!" Gabaɗaya suka saka dariya, daidai lokacin da ta hau WhatsApp ƙarar saƙonni suka dinga shigowa cikin wayarta. Kacokan hankalinta ya koma a kan wayar, musamman saƙon wata ƙawar Nur da ya ja hankalinta kai-tsaye inda take tambayar ta, "Yaushe Nur ta dawo?" Ƙirjinta ya buga dam-dam, cike da jin haushi ta fita daga saƙonta ta koma bin groups amma hakan bai hana ƙirjinta ci gaba da bugawa ba. Ranta a ɓace ta koma Tiktok tsabar haushin tambayar da Summy ƙawar Nur ta yi mata. Ta shiga Tiktok da niyyar ganin abubuwan da za su rage mata takaicin Summyn, sai dai kamar haɗin baki tana shiga da bidiyon Jamal da Nur ta ci karo inda suke rungume da juna suna kuka. Babu shiri ta zaro ido har da goge su da niyyar gani daidai kada a ce gizo ne suke yi mata. Hannunta a ƙirji ta bi comments inda take jin kalaman yabawa da jinjinawa a kan irin zazzafar soyayya. Cikin sauri ta fita bidiyon ta ja shi sama wanda ya biyo bayansa ma su ne a lokacin da Nur ta kwaɗa masa mari tana kuka tana faɗin, "Da za ka zamo ajalina a yanzu nan zan iya yafe maka Jaaan kuma har gaban Allah. Amma wallahi! Wallahi ba zan taɓa yafe maka ba matuƙar ka kashe kanka a kain...ina son ka Jaaan kai ma ka sani wallahi ina son k..." Faɗawar da ta yi a jikinsa ya yi daidai da zaburar Minal tsaye, dafe da ƙirjinta da ke dakan kuguden tara- tara idonta a kafe kan wayar cikin fitar hayyaci tana faɗin, "Tabbas ba zan iya haƙurin zama da shi ba! Saboda kishin ta zai iya kai ni ƙiyama babu shiri matuƙar abin da na gani ya tabbata!" "Innalillahi mene ne kuma ya faru?" Inna da ke kallo kalaman Minal suka farauto hankalinta da ke kan Tv. Zuwa gare ta. Da sauri ta isa gabanta da niyyar riƙe ta daidai lokacin da Minal ta wurgar da wayar ta daki bango ta tarwatse ɗaiɗaya. Tashin hankali wanda ba a saka masa rana, Minal ta shiga ihu da kururuwar faɗin, "Sai na kashe ta! Wallahi sai na kashe ta!" Ta yi maganar cikin ƙaraji tamkar wadda aljanu suka taka kanta. Ta shiga fisge-fisge da niyyar ficewa falon zuwa barin gidan Inna Ade tana rirriƙar ta cikin tashin hankalin ita ma. Don tsabar hana Minal fita har zaninta ya kwance ta koma daga ita sai buje amma ko kaɗan hakan bai dame ta ba. Da ƙyar da gumin goshi Inna Ade ta samo kan Minal da kalaman Innalillahi wa inna ilaihirraji'un da Hasbunallahu wa ni'imal Wakil. Tana yi tana maimaita a bakinta tare da taro Minal har ta zube ƙasa ta fasa yunƙurin fitar tana wani irin kuka mai tsuma zuciyar wanda ya saurara. "Ba zai yiwu ba! Inna ba zai yiwu na zuba ido Minal ta kassara mini rayuwa ba! Wallahi Wallahi sai na kashe ta! Enough is enough! Abin da ta yi mini ya isa ya isa haka nan Inna! Ba zan lamuci wasa da zuciyar da take son yi mini ba! Na rantse da Allah ni ce nan zan kashe ta da hannuna!" "Subhanallah! Innalillahi wa inna ilaihirraji'un! Waɗannan lafuzan ba su yi daɗi ba, ko kaɗan ba furucin mumini mai imani ba ne." Maganar Inna Ade kenan a lokacin da ta samu ta rufe ƙofar falon da makullin da ke jiki ta zare makullin a cikin kwagirinta ta mayar da zanenta ta ɗaura. Tsabar firgici da tashin hankalin da Minal ta saka ta. Hakan ya sa cikin sauri ta ɗaga waya ta kira Hajiya, babu ɓata lokaci ta sanar da ita ta zo gidan babu lafiya. Sannan ta katse kiran ta zauna kan ɗaya daga cikin kujerun ta yi tagumi. Don har lokacin ba ta san a kan wace ce Minal ta haukace ba. Amma jikinta ya ba ta budurwar Jamal ce wadda ta yi wa dukan kawo wuƙa har Hajiya ta kore ta gidan ita kuma ta dawo da ita hannunta. Tunanin da take yi kenan a ranta saboda Hajiya ta sanar da ita komai kasanacewar ta ɗauke ta 'yar'uwa kuma abokiyar shawara. Tabbas yanzu aka fara🧐 GARE KU MASU TAMBAYA! Littafin FANSAR ƘAUNA na kuɗi ne. Ku biya ₦500 kacal ga wannan account. 9032685442 Opay. Waɗanda tura kuɗi ta opay yake bai wa wahala ku tura ta Bank Account; 1230094555 Access Bank Hadiza D. Auta Ibrahim. D. ✍🏼 AUTA CE [2/20, 22:17] Hadiza D. Auta: *FANSAR ƘAUNA!* *HADIZA D. AUTA* *AREWABOOKS: Princessdija.* https://chat.whatsapp.com/Edh59w1Jcgk799uIkP0CFa *ASHIRIN DA TAKWAS.* Tsawon awa ɗaya Hajiya ta ɗauka kafin ta isa gidan Jamal , amma tsawon lokacin Minal ba ta daina kukan da take yi ba. Saboda kaiwa maƙura har jakar kayanta ta haɗa Inna Ade tana rarrashin ta a kan ta jira sai Hajiyar ta zo a san abin yi, amma hakan bai hana ta harhaɗa duk abin da take so a jakar ba. Duk da ba ta yi wata maganar da ke tona asirin zuciyarta a kan makomar aurenta da Jamal ba. Amma haɗa kayan da ta yi ya bayyana wa Inna Ade manufarta da shirin barin gidan da take yi. Ƙwanƙwasa ƙofar falon da aka yi ya sa Inna Ade fita daga ɗakin cikin sauri ta buɗe ƙofar. Kallon juna suka yi da Hajiya dukan su fuskokinsu ɗauke da damuwa. Don kai-tsaye Hajiyar ta nufi ɗakin Minal zuciyarta a tsinke, saboda tunanin da ta zauna kansa ɗaya ne, a kan cewa Jamal ya ɓarke 'yar mutane saboda ya ji daɗin wuri. Cike da tsoron abin da zai je ya dawo, gudun hakan ya jawo musu surutun jama'a a gari, idan har zancen ya fita. Sai dai abin mamaki, tana tura ƙofar ɗakin ta hango Minal tsaye a tsakiyar ɗakin rungume da hannu tana jijjigar jiki. Wani sanyin daɗi ya ratsa zuciyar Hajiya, duk da hankalinta bai gama kwanciya ba musamman da ta hango jakar kayanta a gabanta. Sannan yanayinta ya nuna babu lafiya duba da kiran gaggawar da Inna Aden ta yi mata. "Amina, me ke faruwa ne?" Nan take ta fashe da wani sabon kuka tare da durƙushews ƙasa ta ƙanƙame jakar kayanta tare da ɗora kanta saman jakar tana ta rero kukan. Shiru Hajiya ta yi na ɗan lokaci kafin ta yi tattaki zuwa wurin ta cikin sanyin jiki da bugawar ƙurji falfal. "Ki faɗa mini abin da ya faru, saboda ni uwa ce gare ki ba suruka ba. Kada ki ji kunyar komai ki sanar da ni ko ma mene ne zan yi maganin abin idan ina da ikon yin hakan." Ta yi maganar tare da tayar da ita zuwa bakin gado suka zauna. Kallon yatsunta Minal ta dinga yi kafin ta gama zuƙe-zuƙen majinar kuka ta ce, "Nur ta dawo, kuma Jamal yana tare da ita yanzu hak..." "Anya dai Amina gaskiya ce kika faɗa?" Hajiya ta yi maganar fuskarta a cure kuma idonta a kanta cike da son tabbatarwa. "Wallahi-wallahi ba ƙarya na yi musu ba! Suna can suna yawo a cikin garin nan har da yin bidiyo kala-kala suna watsawa a social media." "To ke wa ya zo miki da wannan labarin?" "Da idona na gani suna kuka tare da faɗa wa juna kalaman soyayy...." Ta ƙare maganar cikin wani sabon sautin kukan da ya so bai wa Hajiya dariya, amma dole ta fuske tare da ƙarfafa kanta tana faɗin, "Ki kwantar da hankalinki, in dai ni ce na haifi Jamal da cikina ba zai taɓa auren A'isha ba. Ya dai je ya gama bidiyon da kalaman soyayyar ya dawo ya iske ni, don babu inda zan je ina nan har sai ya dawo gidan nan ya same ni." Minal ta yi tsam da ranta tana wasa da yatsunta tare da share hawayen idonta da gefen hannunta jefi- jefi tana ajiyar zuciyar kuka. "Hmmm! Ni dai Hajiya ina da wata shawara, idan da hali ki hana ta yin wani furuci a bakinta. Saboda ni dai kam gaskiya na ji tsoron abin da ta faɗa kafin ki zo, don ta tabbatar mini da lalle sai ta kashe ita A'ishar da ake magana a kanta, kuma ta ce lalle ita ce ajalin ta." "Innalillahi wa inna ilaihirraji'un! Lalle ire-iren waɗannan maganganun suna da hatsarin gaske Amina! Don Allah ki daina yin su ba maganganu ba ne masu daɗi, saboda ko ba ki yi abin da kika faɗa ba, idan wani ya ji zai iya yi miki mummunar fassara, a je garin ɓarin baki ƙaddara ta sa wani abu ya same ta a ce ke ce. Don haka ki kiyaye faɗar kowace irin maganar da ta fito daga bakinki idan har ba ki tauna ta ba. Ita rayuwar nan da kika gani komai mai sauƙi ne idan aka ɗauke shi mai sauƙin. Saboda Jamal namiji ne, ko ba ita ba zai iya ganin wata ya ce yana so, idan kina irin wannan furucin sai ki jefa kanki cikin matsala, idan har tsautsayin illar furucin ya biyo kanki, Allah Ya kare. Don ita magana zarar bunu ce da ta fito ba ta komawa ciki, sannan magana mai daɗi ma babbar sadaka ce, kuma Manzon Allah S.A.W ya ce; a faɗi alheri ko a yi shiru. Idan kin san kina cikin fushi bakinki ba zai iya faɗar magana mai daɗi ba to ki daina yin magana har sai kin huce. Ina roƙon Allah Ya ƙara miki haƙuri, kuma in dai Jamal ne zai zo gidan ya same ni ki ga yadda za mu yi da shi, don ga ni cikin gidan naku ina jiran dawowarsa komai dare. Kuma ko a waya ban ce ki ce masa komai ba, ki bar ni da shi kawai har sai ya zo." Ajiyar zuciya Inna Ade ta saki kafin ta ce, "Ai wayar tata ma ta buga ta a ƙasa ta fashe gabaɗaya. Don ina ganin kamar ba za ta sake moruwa da ita ba, bari na ɗauko miki ita ki ga yadda ta koma." Inna Ade ta fice daga ɗakin cikin sauri, mintuna a tsakani ta dawo da watsattsiyar wayar ta miƙa wa Hajiya. Hajiya ta karɓa zuciyarta cike mamakin mahaukacin kishin Minal, wanda ba ta taɓa tunanin hakan za ta faru a kurkusa ba, duba da yanayin auren nasu da kuma yadda ta sha fama kafin a samo kansa, kuma ta san ita ma ba ta son auren dole aka yi mata." "Shi dai namiji ba a cin alwashi da shi, koyaushe ki saka wa zuciyarki cewa mijin mace huɗu ne. Kuma idan Allah Ya nufa zai tara matan sai dai ki kai zuciyarki nesa ki bar wa Allah komai. Amma idan kika ce za ki yi ta nuna masa irin wannan zafin kishin gaskiya akwai matsala a gaba, don wani a lokacin da kike haukar kishin a lokacin yake ƙara zaburewa. Saboda sun fi son ganin mace tana kishi a kansu idan za su ƙara aure, kuma suna jin haushin mace ta nuna musu ko-in-kula a lokacin da suke neman auren. Don wani a sanadin hakan yake rage rawar kai idan ya fahimci auren ba ya gabanki. Saboda zai yi tunanin anya ma kina son sa kuwa? To da irin waɗannan kissa ake samun kan miji a riƙe babu faɗa babu tashin hankali. Don haka don Allah ki daina abin da na ga kin yi a yau, inda hali ma kada ki sake yi saboda mutuncinki zai zube a gaban duk wanda ya ga abin da kika aikata." Inna Ade kenan da jerin maganganunta da suka ƙara rura wutar takaicin da Hajiya ta cusa wa Minal. Don ba ƙaramin haushi ta ji ba, a lokacin da take jefo mata tambayoyi sannan kuma babu wani tashin hankalin da ta ga ta shiga a sanadin jin abin da Jamal ya aikata. Don ba haka ta so ba, ta so ta dinga masifa ita ma ta ɗauki zafi sosai fiye da yadda ita ta ɗauka. **** Ɓangaren Jamal kuma, minti biyar a tsakanin wayarsu Baban ya fito. Turus ya yi a lokacin da ya yi ido biyu da Nur, don tun kafin ya ƙaraso motar ta fita cike da jin nauyinsa ta durƙusa har ƙasa tana gaishe shi. Mamakin ƙarara a kan fuskarsa, amma hakan bai hana shi gayyato murmushin dole ba ya yaɓa wa fuskarsa. Cikin sakewa ya yi magana tamkar babu abin da ya faru. "A'isha, yaushe a garin namu?" Nur ta yi fiki-fiki da ido cike da jin kunyarsa a idonta ta ce, "Ka yi haƙuri Baba." "Tashi mu je gidan, mutane suna kallon mu." Ya yi maganar tare da yin gaba yana sake gaisawa da Jamal. Gaban motar ya buɗe wa Baban sai da ya shiga sannan ya rufe, ita kam Nur tsaye kawai ta yi zuciya tana yi mata gargaɗin kada ta shiga motar, inda hali ta samu ta zille kawai musu kawai sai dai su shafa su ji babu ta. Amma umarnin da Baban ya ba ta a kan ta shiga motar su tafi, hakan ya sa ta jingine abin da ke ranta ta faɗa motar zuciyarta a cunkushe. Jamal ya ja motar cikin sanyin gwiwa tare da tunanin yadda zai kaya tsakaninsa da Baban. Don ya gama sanin matsayar Innarmu yanzu tasa kawai ta rage, kuma ita ce mai babban muhimmanci a wurin sa. Har suka isa gidan babu wanda ya sake yin magana, sai dai tun kafin su shiga cikin gidan Innarmu ta sha gabansu tana muzurai. Baban ya raɓa ta gefenta ba tare da ya ce komai ba, har ya yi gaba ya juyo yana cewa da su Jamal su ma su shigo. Dole Innarmu ta ba su hanya suka wuce sannan ta bi bayansu da ƙatuwar harara tana faɗin, "Wallahi A'isha daga ni har Amina ba za mu taɓa yafe miki ba! Kin san kina son sa tun farko uban waye ya saka ki dole a kan sai kin bar wa Amina shi? To ku gama duk wani ƙullen-ƙullen da ya kawo ku mu yi ta a ƙare ni da ku." Ta ƙare maganar tana ƙwafa ta nemo kujera ta dasa a tsakar gidan tana muzurai da tsaki jefi-jefi. Baba kam bai bi ta kanta ba, kamar yadda Jamal da Nur ba su nuna ma sun ji me ta faɗa ba. Wuri Baba ya nuna musu suka zauna, sannan shi ma ya raɓa jikin bango ya zauna idonsa a kansu ya ce, "Na gan ku tare, duk da ban yi tunanin hakan ba. Duba da yadda aka sha faman neman A'ishar ba a gan ta ba. Ina ka haɗu da ita?" Jamal ya gyara zama ya ce, "A wani gidan cin abinci muka haɗu. Duk da ta so tafiya ta sake bari na Allah bai ba ta sa'a ba. Inda matsalar take dai na ji tana zancen gobe ne ɗaurin aurenta. Bayan kuma ka mini alƙawarin duk ranar da ta dawo za ka aura mini ita da hannunka." Shiru ɗakin ya ɗauka tsawon minti biyu kafin Baban ya sauke ajiyar zuciya ya ce, "Tabbas mun yi haka da kai, kuma ina kan bakana a kan aura maka ita a duk lokacin da ta dawo. Sai dai zancen auren da ka ce za ta yi, shin su wane ne suka bayar da aurenta ga wanda za ta yi auren da shi?" Kallon Nur Jamal ya yi cike da son ƙarin bayani, amma ba ta ce komai ba. Sai da Baban ya kai kallonsa gare ta yana cewa , "Gare ki A'isha, muna son ƙarin bayani." Hakan ya sa ta cire tagumin da ta yi tana faɗin, "Baba, bayan tafiyar da na yi, abubuwa da yawa sun faru. A cikin su har da haɗin aurena da ɗan'uwana Sulaimane, wanda ya zamo ɗa a wurin yayan Babana, uwa ɗaya uba ɗaya. Shi ne ya ba shi ni, kuma shi saka ranar auren da komai, bayan an sake samun saɓani a kaina, tsakanin dangin Babana da mahaifiyat..." "Idan har haka ne, ba zan iya aurar da ke kai-tsaye kamar yadda na so yi a farko. Duk da mahaifinki da kansa ya damƙa mini ke tare da wasiyyar idan aurenka ya tashi na aurar da ke da hannuna. Amma tun da danginsa suna raye, kuma har hakan ta faru; to ban isa na yi jayayya da su ba. Saboda sun fi ni ƙarfi a kanki, kuma ba zan so na yi abin da zai jawo mini matsala daga baya b..." Cikin matsanancin tashin hankali Jamal ya yi magana tamkar cikin wata kalar muryar kuka ya ce, "Baba, ka dubi girman alƙawarin da ka yi mini, tun da kana da iko da irin taka dama a hannunka; don Allah ka taimake ni ka aura mini Nur a yanzun nan ba sai anjima ba." Wani kalar murmushi Baban ya yi kafin ya ce, "Wallahi, da a ce wannan matsalar ba ta shiga ba; da babu abin da zai hana ni ɗaura maka aure da A'isha. Amma a haka ina jin tsoron abin da zai je ya dawo, ganin ban da ƙarfin jayayya da su a kant..." "Ni zan tsaya a kan komai Baba, ko da wata matsalar ta taso ka bar ni da ita, zan taryi gabanta kuma zan sha kanta da yardar Allah." Kafin Baban ya ba shi amsa suka jiyo muryar Innarmu a kansu tana faɗin, "Na sha ruwan bala'i ba ka isa ka yi wa Amina kishiya tana da wata biyu a gidanka ba. Dole ne ka yi haƙuri har zuwa lokacin da za ta haifa maka 'ya'ya. Sannan auren ma idan da A'isha aka yi ni da Amina ba za mu taɓa yafe muku ba daga kai har ita baƙar munafuka..." Baba ya katse ta a fusace bayan ya miƙe tsaye yana nuna da hannu. "Kin ga...ki yi mini shiru babbar kwabo! Ina ruwanki da shiga maganar da babu ke a cikin ta? Idan ma auren ne an faɗa miki haukarki za ta sa a fasa n..." "Ko ba a fasa ba shi kuma zai sauwaƙe wa Amina. Don babu ta yadda za a yi ta zauna zaman kishi da A'isha. Wallahi dole ɗaya za a yi! Ko ita ko Amina, amma tun da ba macizai ne ba za su taɓa haɗa zama cikin rami ɗaya ba ahe!" Ta ƙare maganar tana riƙe ƙugu tare da jijjigar jiki alamun kaiwa maƙura a kan fushin da take kai. Shi ma a fusace ya ba ta amsa da cewa, "Muddin kika yi sanadin mutuwar auren Amina; to ke ma a bakin naki auren. Don na fahimci sai an fito miki da yaren da kika fahimta za ki hakaltu." Baki a sake cike da mamaki Innarmu ta ce, "Yanzu Malam a kan wannan feƙaƙƙiyar rayinyar kake son saki na? A kanta kake iƙirarin bakin aurena idan na kashe auren Amina? To ita ta je ta yi auren mu gani tun da ta fi kowa a wurin ka. Kuma aura mata shi ɗin ga fili ga mai doki." Wata sabuwa! GARE KU MASU TAMBAYA! Littafin FANSAR ƘAUNA na kuɗi ne. Ku biya ₦500 kacal ga wannan account. 9032685442 Opay. Waɗanda tura kuɗi ta opay yake bai wa wahala ku tura ta Bank Account; 1230094555 Access Bank Hadiza D. Auta Ibrahim. D. ✍🏼 AUTA CE [2/20, 22:17] Hadiza D. Auta: *FANSAR ƘAUNA!* *HADIZA D. AUTA* *AREWABOOKS: Princessdija.* https://chat.whatsapp.com/Edh59w1Jcgk799uIkP0CFa *ASHIRIN DA TARA.* Ta yi maganar tana kumfar baki, bayan ta gama fesar da zantukanta tana huci ta fito daga ɗakin, tsabar tashin hankalin da ta shiga gabaɗaya ta rasa nutsuwarta. Takalmi ma ware daban-daban ta saka, sannan ta ja hijabinta a birkice ta fice daga gidan tana surutai tamkar ta tashi sama. Yayin da ta bar Baban Amina riƙe da baki a kan mamakinta, bayan kunyar da ta bar shi da ita saboda tijarar da ta yi a gaban Jamal. Don Nur ta saba gani, ko kaɗan ba ta yi mamakin jin ire-iren maganganun da ta furzar ba, saboda abin ba sabon abu ba ne a wurin ta ba. "Allah Ya kyauta." Baban Amina ya yi maganar bayan ya sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi. Sannan ya sake kai kallonsa a kan Jamal yana cewa, "Kana dai gani tun kafin a je ko'ina wata matsalar ta kunno kai. Duk da ba a fata, amma matsalolin da za su biyo bayan ƙulla auren sai sun fi haka. Don da a ce zan samu damar ganawa da dangin Baban A'isha; da zan roƙi alfarmar su ba ni izinin aurar da ita. To ina mai tabbatar maka babu abin da zai hana ni ba ka aurenta, kamar yadda na yi yunƙuri yi a watannin baya, Allah bai nufa b..." "Baba ban katsi hanzarinka ba, amma matuƙar ba a ba ni auren A'isha ba; ni kuma ba zan taɓa barin wani ya aure ta ba." Yana gama furta hakan ya miƙe yana sake cewa, "Zan tafi na dawo Baba, kuma don Allah kada ka bari ta je ko'ina." Baban Amina ya bi shi da kallo kawai har ya fice, saboda bai san mai zai ce da shi ba, kansa ya ƙulle ta yadda ya kasa gano wane kalar hukunci ya dace ya zartar a kan matsalar. Duba da jin labarin auren da Nur ta faɗa za a yi mata idan safiya ta waye. Sannan yana jin tsoron dangin Babanta su zarge shi a kan shi ne ya hure mata kunne ta gudo, bayan bai san komai a kanta ba tun bayan barin ta Kano. Hakan ya sa ya sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi sannan ya kira sunanta. "A'isha." "Na'am Baba." Ta amsa kai-tsaye tare da goge hawayen da ke bin fuskarta har a lokacin. "Me ya dawo da ke garin nan, bayan kin tafi ba tare da kin sanar da ni ba?" Zama ta gyara, tare da zuƙe majinar kuka cikin wata raunanniyar murya ta ce, "Ka yi haƙuri Baba, ni kaina na san ban kyauta ba. Amma Allah shi ne shaidar na bar garin nan ne ba don ina so ba, kuma na bar shi ne saboda na samu nutsuwar zuciya. Sai dai da a ce na san abin da zan tarar a can, da ban yi gangancin yin nisa da ku ba. Saboda a sanadin bayyanata, bayan na share shekara uku ba na tare da su, hakan ya jawo mini tashin hankalin da ban yi zato ba. Duk da ba ni ce na kawo kaina a gidan nan ba, kuma ba ni da laifi don na yi wa wasiyyar mahaifina biyayya. Amma an yi mini hukuncin da ya jawo mini danasanin komawata hannunsu. Sannan a sanadin hakan na gano gaskiyar abin da ya haddasa mini tarnaƙin zuciya, wanda ba zai warke ba har zuwa ranar mutuwat..." Ta fashe da wani sabon kukan da ya ƙara ɗaga wa Baban Amina hankali. Ya shiga rarrashin ta cikin kaɗuwa da rawar murya. Tsawon minti biyar kafin ya samu ta sassauta kukan ta sake cewa, "Baba ba zan iya auren Jamal ba, duk da auren da za a yi mini ba son mijin nake yi ba. Amma na zaɓi zama da shi a kan zaman da zan yi kishi da Amina. Saboda ba na son duk abin da zai cutar da ita, haka ma idan ina da iko ba zan taɓa bari Jamal ya auri wata ma ballantana a ce ni na aure shi. Yanzun ma wata ce ta so lalata musu zama, shi ya sa na zo don na kare su daga sharrinta. Saboda ina group ɗaya da ita, kuma tun ranar da hatsaniya ta haɗa ta da Aminar na sani, don duk maganganun da suka yi a tsakaninsu ta kwashe ta tura a group ɗin. Yayin da wasu suke ta zuga ta a kan ta ɗauki mummunan mataki a kan Amina ko don ta huce takaicin abin da ta yi mata. Tun da na ji muryar Amina kuma na gano da ita ake yin rikicin, sai hanalina ya tashi. Musamman da na bi diddigin mai son yi musu sharrin, na gano mugun nufin da take son aikatawa. Don na ƙulla ƙawancen ƙarya da ita, inda na nuna mata ina tare da ita a kan ɗaukar fansar da take son yi, don kawai na gano komai da take son shiryawa. Ita ma ganin lambata ba ta Nigeria ba ce, hakan ya sa ta saki jiki da ni ta kwaye mini cikinta gabaɗaya. Don ba ta ɓoye mini komai ba, ta sanar da ni halayenta da irin tuggun da take shiryawa a kan Amina. Saboda ta sanar da ni a kan Jamal ta nemi aiki gidan abincin da yake zuwa cin abinci. Don ta yi bincike sosai a kansa da Aminar, kuma babban shirin da take yi a kansu na farko shi saka Jamal ya bi ta tamkar raƙumi da akala. Ta hanyar asiri don kawai ta raba shi da Amina, ta yadda zai sake ta saki uku a lokaci ɗaya ba tare da ya yi shawara da kowa ba. Baba, a shirin da ta yi musu ma, ta ce hatta mahaifiyarsa sai ta so ganin shi da idonta ba ta samu damar ganin sa ba. Kuma yanayinta ya tabbatar mini za ta iya duk abin da take faɗa, don ta sanar da ni ba a kansa ta fara ba, kuma ta ba ni labarai a kam mazan da ta afka irin tarkon da take son jefa shi. Sai dai nasa ya fi muni, don raba Amina da shi da ta ƙudurta ba ƙaramin abu ba ne, wanda ta ce ba ta taɓa raba kowa da matarsa ba, sai dai ta juya mazan da ta riƙe gam ta yadda duk samunsu yana hannunta. A sanadin wannan babbar sana'ar da ta riƙa tana tutiya da ita, ta mallaki gidan kanta inda take cin karenta babu babbaka, kuma ta sanar da ni tana da manyan filaye sama da biyar ba tare da kowa ya sani ba." "Cabɗijam!" Baba ya faɗa yana jinjina kai. Nur ta ƙara da cewa, "Tsoron ta raba Amina da Jamal ta sigar da ta so ya sa na baro gida bayan na bugi cikinta na san komai da ta shirya. Sannan kafin na zo na sanar da Adamu abokin Jamal komai, da taimakonsa aka sa mata ido a kan duk wani takunta da na Jamal idan ya zo wurin. Sai dai tabbacin da ta ba ni a kan bai zo ba, amma lalle zai je wurin a cikin kwanakin, saboda kiranyen da ta sa aka yi masa. Hakan ya sa ni ma na kasa haƙuri na biyo hanya babu shiri don a yi komai a gabana, na manta shaf da matsalar da za ta faru biyo bayan hakan. Duk da ƙaryar da na yi a kan cewa wata kakata ce ta kira ni, waton ƙanwar mahaifiyar Babana. Da wannan dalilin na baro Niger cike da zummar komawa cikin lokaci tun kafin asirina ya tonu. Kwanana biyu a nan ba tare da kowa ya sani ba, sannan ina zuwa gidan cin abincin na wuni tare da Hajiya mai abincin amma ita muguwar ba ta san ni ce ba. Saboda hoton wata ɗiyar yayan Babana na tura mata a matsayin ni ce kuma ta yarda...." Daga nan ta kwashe komai da ya faru bayan tonuwar asirin Zulaiha ta faɗa wa Baban Amina. Ya shiga jinjina kai tare da goge wata ƙwallar da ta cika masa ido tsabar mutuwar jikin da maganganunta suka haifar masa. Sai da ya nisa sannan ya yi magana cikin raunin zuciya ya ce, "Tabbas ke 'yar halas ce A'isha kuma mai ƙoƙarin rama halacci. Sannan kin yi gadon mahaifinki tun daga kan kamarsa har zuwa kyawawan halayensa. Saboda kin so wa Amina abin da kike so wa kanki, kuma kin guji abin da zai lalata mana farin ciki duk da abin da uwarta ta yi miki a baya, sannan kuma tana ƙoƙarin ɗora sabo a yau. Allah Ya yi miki albarka A'isha, sai dai abin da na kasa ganewa, shin ya ya aka yi da auren da kika ce za ki yi yanzu, bayan matsalar da kike tare da ita? Ko shi ma.." "An yi bincike Baba, wannan zancen duka ƙage ne ko kuma na ce an yi komai ne a bisa kuskure da ƙaddara. Amma ba ni ce asalin wadda abin ya faru a kanta b..." "Alhamdulillah! Allah mun gode maka!" Baba ya yi maganar tare da kai goshinsa ƙasa yana sujudar godiya ga Ubangiji. Zuciyarsa wasai ya yi maganar da ta saka ta hanzarin kai kallonta gare shi baki buɗe. Bayan bugun da ƙirjinta ya shiga yi babu ƙaƙƙautawa. "Halinki na kirki ba zai taɓe ba A'isha, don haka a yanzu na yanke hukuncin aura miki mijin Amina ko da kowa ba ya so. Da ma can na yi wannan alƙawarin saboda ganin yadda hankalinsa ya tashi a kan rashinki sannan da auren Amina. Don ina da iko a kan aurar da ke, saboda mahaifinki Alhaji Haroun ya ba ni wannan damar da kansa kuma a bisa yardarsa. Saboda haka ba zan bari ki rasa wanda kike so yake son ki tsakani da Allah ba, ko da a garin yin hakan zan rasa raina matuƙar ke za ki samu farinciki." "Baba.." "Yi shiru kawai A'isha, Allah Ya sani ba zan bar rayuwarki ta yi tangal-tamgal ba. Dole ne ke ma a samar miki da farin ciki ko da hakan zai jawo matsalolin da suka fi waɗanda ake hasashen faruwar su." Shiru Nur ta yi masa, saboda ganin ya fiddo wayarsa a aljihu cikin rawar jiki hannunsa yana rawa ya danna wa Jamal kira. Sai dai har ta gama ringing bai ɗaga ba, yana ƙoƙarin sake yi masa wani kiran ta durƙusa gabansa tana magiya, hawaye yana zuba bayan ta haɗa hannuwanta ucealamun roƙo. "Don Allah Baba, don Allah kada ka bari a a jefa Amina cikin tashin hankali. Allah Ya sani na bar mata Jamal har abada, kuma zan yi ƙoƙarin raba zuciyarsa da sona ko don ta ji daɗin zaman aurenta....na yi maka wannan alƙawarin Baba, don Allah ka bar Amina da mijinta su rayu su kaɗai ba tare da na shiga tsakiyarsu ba." Tashi kawai ya yi ya fice daga ɗakin ba tare da ya ce ƙanzil ba. Ya bar ta zugum ta tagumi tana nazari. Har ya dawo ɗauke da kwanon jalof ɗin shinkafa ya ajiye mata gabanta yana faɗin, "Fara ci, bari na je na kawo miki ruwan sha." Nur ta kalli abinci kawai amma ko kaɗan zuciyarta ba ta buƙatar cin komai. Baba ya dawo da kofin ruwa a hannunsa yana waya. Kai ɗaga tana kallonsa cikin wani sabon tashin hankali saboda saƙon da ta ji yana miƙa ga Jamal. "E, ka zo na amince zan aura maka auren A'isha gobe idan Allah Ya kai mu." **** Ɓangaren Jamal kuma, yana barin gidan kai-tsaye wani masallaci ya tsaya ya yi sallar Asr, lokacin ƙarfe biyar har ta gota, sannan ya yi gidan ƙanen Babansa ya tsinke zuciyarsa a ƙagauce da son ƙaddamar cikar burinsa. Cikin sa'a ya tarar da shi gida suka gaisa sama-sama. Don ya fahimci Jamal ba ya cikin nutsuwarsa tun daga kan kallon farko da ya yi masa. "Baba wurin ka na zo!" "To, ga ni Jamal, Allah Ya sa lafiya?" "A kan maganar yarinyar nan ce da na so aure a farko aka musanya mini da 'yar'uwarta...." "To, to na dai gane." Ya gyara zama yana faɗin, "Baba ta dawo yau. Kuma a yadda na ji ta faɗa gobe ne ɗaurin aurenta da wani. Sannan wallahi Baba na sani ba za ta so kowa bayan ni ba...don ina da tabbacin ba ta son ko ma wane ne auren haɗi ne za a yi mata. Baba don Allah..." "Dakata Jamal." Baba Hassan ya katse shi tare da ɗaga masa hannu kafin ya sake cewa, "Ka manta da abin da aka ce ya hana ku auren tun a farkon da aka so yi Allah bai nufa ba?" "Ban san komai ba Baba, babu abin da na sani a kai don ba a sanar da ni ba." "To ka je ka tambayi Hajiyata, ita ta sani don ta san komai tun kafin a aura maka yarinyar da ke gudanka a yanzu. Kuma idan ta amince ka auri yarinyar a yadda taken, ka ce ta kira ni da kanta ni ta sanar da ni zan je na yi wakilcin auren." Baba Hassan ya ƙare maganar yana miƙewa tsaye saboda sanin abin da ya zo da shi ba zai taɓa karɓuwa a wurin su ba. Kuma da gangan ya ce sai Hajiya ta amince don ya san ba za ta amince ya auri Nur a yadda suka san ta ba. Har ya fara yi masa magiya Baban ya katse shi da cewa, ya je kawai ya roƙe ta idan ta amince a cikin daren ma zai nemi a ɗaura auren kafin safiya. Jiki babu kuzari Jamal ya nufi gidan Hajiyar, daidai lokacin kiran Baban Amina ya shiga wayarsa, a nan ne yake sanar da shi batun amincewarsa. Farinciki fal zuciyarsa ya dinga tuƙi wani sanyin daɗi yana ratsa masa zuciya. Bakinsa a washe ya isa ƙofar gidan Hajiyar, sai dai tun kafin ya shiga maigadi ya sanar da shi ba ta nan. Waya ya ɗaga ya kira ta, a lokacin ana ta kiraye-kirayen sallar magrib. Babu ɓata lokaci ta sanar da shi tana gidansa tun da rana. Katse wayar kawai ya yi ya nufi gidan zuciyarsa cike da tunanin abin da ya kai ta gidan duk da zumuɗin da yake yi a kan sanar da ita abin da ke ransa. Sai a lokacin tunanin halin da ya bar Minal ya faɗo ransa, kansa ya dafe tamkar ya kwarara ihu ya ce, "Ya Salam! Minal kin ɓaro mini aiki tun da kika kira Hajiya." Gudun motar ya ƙara tare da buga wani uban tsaki yana faɗin, "Me ya sa ba ta bari har na dawo ba za ta kira Hajiya? Bayan kuma ta sani dole ne sai ta yi mini faɗa.... mitsssss! Wannan tonon asiri har ina? An yi mace babu sirri ita a komai sai ta yi abin da zai sa Hajiya ta ga laifina." Haka ya dinga sambatu masu ɗauke da ganin laifin Minal a kan tunanin da ya tsaya masa a zuciya. Don ya tabbatar wa ransa ita ce ta nemo Hajiyar don jin haushin ya bar ta tsawon lokaci bai dawo ba. Sai da ya tsaya masallacin unguwarsu ya yi sallah sannan ya nufi gidan ƙirjinsa yana bugawa. Gunjin motarsa da Minal ta jiyo ƙirjinta ya buga dam-dam, tsam ta yi da ranta, abincin da Hajiya ta saka ta gaba sai ta cinye ma ta ji ya gundure ta. Fahimtar hakan ya sa Hajiya ta yi magana cikin haɗe fuska tana cewa, "Ki ci abincinki, kada ki ce komai ki bar ni da shi na ce." Minal ta yi marau-marau da ido tana zuƙe majinar kuka, saboda wa'azin da suka saka ta gaba suna yi mata a kan haƙuri da dauriya ya rage mata zafin da ke ranta. Da guntuwar sallamarsa ya shigo falon yana sosa kai, ganin Hajiya da Minal a cikin falon, saboda Inna Ade ta yi gida bayan ta gama girka musu abincin dare. Da muzurai ya isa gaban Hajiyar ya durƙusa cikin wani sabon ladabi yana cewa, "Allah Ya huci zuciyarki Hajiya. Na san na yi laifi amma don Allah don girman Ubangiji a yafe mini." Wani kallo ta yi masa cikin haɗe girar sama da ta ƙasa kafin ta ce, "A yafe maka ka dinga rungumar mata a tsakiyar titi ana yi maka bidiyo?" Baki ya rufe cikin tashin hankali, saboda ba zatar da maganar ta zo masa. Don bai taɓa tunanin abin da ya faru har ya yi watsuwar da Minal z ta sani har Hajiya ta ji labari ba. Ƙoso biyu Hajiya ta yi masa a tsakiyar kai kafin ta nuna shi da hannu tana faɗin, "Wai har yaushe za ka daina bar wa rayuwarka abin faɗi? Yanzu mene ne amfanin yin abin da ka aikata ko daga kai sai ita fanɗararriyar yarinyar ballantana a gaban jama'a?" "Wallahi Hajiya..." "Babu abin da za ka faɗa na yarda da kai, yarinyar nan kuma tun da na sanar da kai babu kai babu ita, muddin aka ce an sake ganin ka da ita sai na tsine maka! Kai ko ƙanwar ubanka ce na raba ka da ita babu kai babu ita! Idan kuma ka ƙi ji sai dai ka zaɓi ɗaya ko ni ko ita." Shiru kawai ya yi yana kallon Hajiyar kafin ya miƙe tsaye yana furzar da iska mai zafi a bakinsa. Hannuwansa duka a cikin aljihunsa bayan kan da ya duƙe yana nazarin abin da zai faɗa, duk ya sani ba daidai zai yi ba, amma kai-tsaye ya ɗago kansa fuskarsa a cure ya kalli Minal yana faɗin, "Na haƙura da aure, kuma na haƙura da rayuwa da kowace macen da za ta amsa sunan matata . Don haka ki haɗa kayanki ki je gidanku na sake ki saki ɗaya." Cabɗijam! Yanzu littafin ya fara. Kuma daga nan na tsaya ƙarshen FANSAR ƘAUNA BOOK 1. Wanda na bayar a free tun daga farko har fejin ƙauna. Sai bayan sallah idan Allah Ya kai mu za mu haɗu a cikin BABI NA BIYUN LABARIN. Wanda nake yi muku albashir abubuwan da ke cikinsa har ya fi wanda ya faru a farko. Don a cikin labarin akwai ban tausayi, ban haushi, sannan da ban al'ajabi bayan kalolin abubuwa masu tsayawa a zuciya. Kada ku manta, har yanzu ba mu san asalin wace ce Nur ba, sannan ba mu ji labarin dalilin da ya sa ta fansar wa Minal Jamal ba. Ga masu buƙata ku biya ₦1k kacal ga wannan account. 9032685442 Opay. Waɗanda tura kuɗi ta opay yake bai wa wahala ku tura ta Bank Account; 1230094555 Access Bank Hadiza D. Auta Ibrahim. D. AUTA CE ✍🏼 *FANSAR ƘAUNA!* *BOOK 2.* *HADIZA D. AUTA* 30. Dirim-dam-dam! Shi ne sautin bugun da ƙirjin Hajiya ya yi, sannan a lokaci ɗaya ta yi suman zaune bayan gumin da ya jiƙa mata goshi. Bakinta a buɗe idonta a kansa har ya shige ɗakinsa ba tare da ta iya furta ko kalma ɗaya ba, don ta kasa matsowa ballantana ta samu cewa wani abu ko don ta rage nauyin da danne mata zuciya. Minal kam hannu ta ɗora a ka cikin tsananin tashin hankalin da ya so zauce ta, wata kalar ƙara ta fasa tare da faɗin, "Innalillahi wa inna ilaihirraji'un!" Salatinta ya farfaɗo Hajiya daga suman zaunen da ya kafce ta, sai da ta sauke nannauyar ajiyar zuciya sannan ta yi magana cikin sanyin murya. "Ki kwantar da hankalinki! Babu inda za ki je sai kin gama idda. Duk abin da kike buƙata ki sanar da ni a waya." Tana ƙare maganar ta miƙe kanta yana sarawa jiri yana kwasar ta ta fice daga falon, da sassarfa ta sauka ƙasa zuwa harabar gidan tana ganin komai dishi-dishi. Da ƙafa ta fara tattaki bayan ta bar gidan ba tare da ta san tana tafiyar ba. Sai daga baya hankalinta ya dawo jikinta ta kira direbanta suka haɗu a hanya ya ɗauke ta. Kasancewar Inna Ade ta yi gida bayan ta gama rarrashin Hajiyar a kan ta bi komai a hankali gudun abin ya ƙara rincaɓewa. *** Minal kam tsabar firgici ya yi mata rumfa bayan fitar Hajiyar ta zabura cikin sassarfa ta bi bayansa zuwa ɗakin nasa gumi yana feso mata a kan fuska da jikinta gabaɗaya. "Ka ƙarasa sauran igiyar biyu! Ina son na san babu wata sauran alaƙa da ta rage tsakanina da kai." Ta ƙare maganar riƙe da ƙugu tana kallon sa ƙur da ido ko ƙiftawa babu, a cikin wani mugun yanayin da take jin zuciyarta tana fitar da hayaƙin wutar da ƙiris ya rage ta kama da wuta. Jamal ƙanzil bai ce mata ba har ta gaji da tsayuwa ta maimaita maganar bai kula ta ba, ballantana ya dakatar da haɗa kayan da yake yi a cikin jakarsa ta matafiya, tsabar sauri cusa kayan kawai ya dinga yi fuskarsa a cure har ya gama zuba duk abin da yake so ya zuge zif. Cikin zafin nama ya fisgi jakar ya yi gaba, ta bi bayansa cikin wani irin yanayi mara misaltuwa ganin abin da yake ƙoƙarin aikatawa, don zuciyarta ta tabbatar ƙwaɓarta ta gama yin ruwa da gaske ba ya buƙatarta a rayuwarsa. Yana ƙoƙarin ficewa ta sha gabansa cikin dakiya duk da kukan da take faman dannewa yana ƙoƙarin kufce mata. "Ba za ka je ko'ina ba sai ka tsinke sauran igiyoyin gabaɗay..." Wata muguwar hankaɗar da ya yi mata ya sa babu shiri ta zube ƙasa tare da fashewa da wani mugun kuka tana faɗin, "Wayyo Allahna!" Babu shiri ya ja birki ya tsaya, tare da hanzarin runtse idanuwansa cikin sauri, saboda ƙarar sautinta ya shiga kunnensa kuma ya ratsa masa zuciya ta dinga bugawa fal-fal. Amma hakan bai saka shi juyawa ba, ko kuma ya fasa abin da ya yi niyya. Gudu-gudu sauri-sauri ya isa harabar gidan ya wurga jakarsa a mota ya ba ta key cikin zafin nama ya fice aguje tamkar zai tashi sama. Tsawon lokaci Minal tana kuka kafin ta haƙura don kanta ta miƙe tana shessheka ta zumbula hijabi ta fice bakin gate. Maigadi bai hana ta ba kamar yadda ya saba, saboda fahimtar akwai abin da yake faruwa a cikin gidan. Tun daga zuwan Hajiya gidan har zuwa fitarta da ficewar maigidan har zuwa tata fitar. Kuma tuna gargaɗin da Jamal ya yi masa a kan haramta masa shiga sabgar gidan; ya sa ya dinga kallon komai da ido ba ya shiga ballantana ya sake yin wani laifin. Don yanayin Minal ya tabbatar masa tana cikin tashin hankali, hakan ya sa bayan fitarta ya jima a ƙofar gidan yana kallon titin da ta miƙe cike da tausayawa har zuwa lokacin da ta ɓace wa ganin sa. *** Jamal gudu yake yi yana dukan sitiyari a lokacin da ya kira wayar Nur sau biyar ba ta ɗaga ɗaya ba. Yana huci tare da goge gumin goshinsa ya isa Jogana ya yi parking a ƙofar gidan su Amina. A daidai lokacin da ake ta kiran sallar magrib a masallatai mutane suna ta arwala yayin da wasu ke ta ƙoƙarin zuwa masallaci. Tun kafin ya fito daga cikin motar Baban Amina ya riga shi fitowa daga cikin gidan yana sauri, wanda alamu ya nuna a zahiri shi ma masallacin zai je. Duba da yadda yake gyara hannun rigarsa da ruwan arwala ya gama jiƙewa. "Ashe ka dawo? Ga ni kuma zan je masallaci." Baban Amina ya yi maganar fuskarsa babu yabo babu fallasa. Jamal cikin wata kalar muryar da damuwa ta gama raunta ta ya ce, "I, na dawo Baba, Nur na zo ɗauka, in sha Allahu gobe zan kai ta gidansu har ƙasar Niger." Ɗan jim Baba ya yi cikin wani yanayi kafin ya kalli ƙofar gidan yana cewa, "Bari na kawo maka ruwa ka yi sallah, saboda ita ma sallar take yi, idan muka dawo akwai abin da nake so mu tattauna kafin ku tafi." "Babu damuwa." Maganar Jamal kenan saboda ba zai iya yin jayayya da shi ba, duk da a ƙasan zuciyarsa bai so yin ko minti biyu a cikin garin na Jogana ba. Saboda ba ya son labarin sakin da ya yi wa Amina ya kawo musu tun kafin ya bar gidan. Don nauyi da kunyar Baban Amina yake ji a ransa, ko babu surukutar Amina akwai ta Nur da yake yi masa kallon mutum mai daraja a idonsa. Ba don ya so ba haka ya yi arwalar jiki a sanyaye ya bi Baban Amina masallacin da ke kusa da gidan. Bayan an gama sallar suka dawo gidan suna tafe kowa shiru sannan da abin da kowa yake saƙa a cikin ransa. Umarni ya ba shi a kan ya shiga cikin gidan, ba don ya so ba haka ya bi shi da guntuwar sallama har zuwa bakin ɗakinsa, inda tambarma take shinfiɗe Nur tana kai da carbi a hannunta bayan ta haɗa tagumi tana share hawaye jefi-jefi. Tsabar fargaba da tashin hankalin da take ciki kala-kala, ji take yi tamkar ta yi tsuntsuwa ta dira Niger ko da za ta rage nauyin damuwar da ke ƙoƙarin dawo mata sabuwa. Kuma ba don Baba ya saka ta yi masa alƙawarin zama har ya je masallaci ya dawo ba; babu abin da zai hana ta tserewa saboda gudun abubuwan da take hangen faruwarsu su wanzu. Ƙirjinta ne ya buga dam-dam tun daga jin sallamar Jamal har zuwa hango shi da ta yi a bayan Baban Amina yana ƙoƙarin isa kan tabarmar da take kai. Cikin hanzari ta ja gefen bango ta makure kanta a ƙasa saboda ba ta son haɗa ido da su gabaɗaya. "Ƙaraso ka zauna." Baba ya bai wa Jamal umarnin zama ganin sa a tsaye yana kallon Nur ya kasa gaba ya kasa baya. Cikin sanyi jiki ya jawo ƙafafuwansa ya zauna nesa da ita kasancewar tabarma ce babba. Shiru ya ratsa tsakani kafin Baba ya sauke ajiyar zuciya ya ce, "Na ji kana zancen mayar da Nur gida, ya aka yi ka sauya wannan ra'ayin?" "Ba zan iya ɓoye maka komai ba Baba, amma wajibi ne gare ni Na mayar da ita gida a aura mata wanda take so, don na gama fahimtar ba ta so na. Rashin son da ya sa Hajiyata ta ji haushi ta hana ni auren ta kai- tsaye, bayan ta ba ni zaɓin ita ko Nur Na zaɓi ɗaya a cikin su. Saboda Amina ta haɗa ni da ita, koyaushe ni take ganin laifi kuma komai na yi sai ta ce ban yi daidai ba, to yanzu na zaɓi rayuwa ni kaɗai ba tare da kowa b..." Sautin kukan Nur ya saka shi yin shiru yana kallon ta, kafin Baban Amina ya nisa cikin wata kalar murya ya ce, "Kada ka shanye tunaninka, yana da kyau a matsayinka na namiji ka dinga aiki da hankali kafin ka aiwatar da komai. Saboda mahaifiya ba abin wasa ba ce, kada zuciya ta ɗebe ka ka aikata abin da Allah zai yi fushi da kai a sanadin bijire mata." Sai da ya ɗan tsahirta bayan shirun sakonnin da ya ratsa bayan dire maganarsa ya sake cewa, "Ban hana ka mayar da A'isha gida ba, amma ka ji tsoron Allah, ka tuna cewa marainiya ce kuma amana ce a hannunmu gabaɗaya. Sannan ka yi imani a kan wani ba ya auren matar da ba tasa ba, duk tsanani idan matarka babu mai hana ka aure ta idan lokacin ya buga. Don haka ka daina garaje, kuma ka nemo hanyar sasanta kanka da Hajiya cikin sauƙi har ta aminc..." Shigowar Innarmu cikin gidan ya sa Baban yin shiru kowa ya mayar da hankalinsa a kanta. Don tun kafin ta ƙaraso ta fara maganganun da ke nuna a shirye take da yin komai aka shiga gonar Amina. Tsam Jamal ya miƙe tare da bai wa Nur umarnin ta tashi su je, Baban ma ya miƙe fuskarsa a cure yana jaddada masa Nur amana ce a wurin su. Jamal bai ce komai ba ya yi gaba ba tare da ya kalli Innarmu ba ballantana ya gaishe ta. Nur ta ƙi motsawa daga inda take saboda ta gama kaiwa maƙura a kan halin da take ciki. Saboda zantukan Jamal sun taɓa ta, sannan yunkurin kai ta gida ya saka ta jin wani faɗuwar gaba, duk da a ranta tana buƙatar hakan ko don wanke kanta daga laifin da za ta aikata idan aka tabbatar ba ta nan. Sai da Baban ya yi magana sannan ta miƙe cikin sanyin jiki ta bi bayan su, yayin da zantukan Innarmu suka raka ta da cewa, "Sum-sum da ita baƙar munafuka wallahi sai na nuna miki ke ƙaramar 'yar duniya ce. Ban da zalunci kin gama ƙulla abu daga baya ki dawo kwancewa saboda mugunta. To dole ne ki bar Amina da mijinta! Don ko za ki mutu ba zai taɓa auren ki ba!" Babu wanda ya bi ta kanta har suka fita ƙofar gidan, Nur ta durƙushe a gaban Baban tana wani irin kuka har muryarta tana sarƙewa. Baban Amina ya dafa kanta yana faɗin, "Ki yi haƙuri A'isha, Allah zai zamo gatanki a duk inda kike." Ya ƙare maganar tare da ɗaga ta sama ya ja hannunta zuwa bakin motar, Jamal ya yi hanzarin buɗe mata gaban motar, amma ta ƙi shiga kamar yadda ya so ta buɗe baya ta faɗa tana ci gaba da rera kukanta. Ƙur da ido Jamal ya yi mata tsawon sakonni kafin ya zagaya ya zauna cikin sauri fuskarsa a cure. Yana ƙoƙarin tayar da motar adaidaita sahu ta kunno kai a cikin layin, sai da ya ja gefe motar Jamal ta wuce sannan ya isa ƙofar gidan ya tsaya. Kan Amina a duƙe tana ajiyar zuciya wata bayan wata kamar an ba ta umarni ta ɗago kanta. Ƙirjinta ya shiga bugawa babu ƙaƙƙautawa ganin motar Jamal tana fita daga cikin layin nasu. Mamaki fal zuciyarta ta fito cikin adaidaita sahun tana ƙoƙarin shigewa gidan cikin sassarfa, saboda zuciyarta cike take fal da son sanin abin da ya kawo shi gidansu, bayan ya gama tozarta rayuwarta. "Malama ba ki sallame ni ba fa!" Mai adaidaita sahun ya yi magana, sai a lokacin Amina ta tuna babu ko ficika a hannunta, asali ma ko jakar hannu ba ta ɗauko ba ballantana jakar kayanta. Gidan ta shige ko waigensa ba ta yi ba, haushi hakan ya sake ɗaga murya yana faɗin, "Malama idan kin shiga ki aiko mini kuɗin sauri nake yi." Ya yi maganar ba tare da ya kashe adaidata sahun ba, tsabar saurin a biya shi ya ƙara gaba. Next page FANSAR ƘAUNA 31. Babu sallama Amina ta faɗa gidan, kai-tsaye ta shige ɗakin Innarmu ganin ba ta tsakiyar gidan. Zumbur Innarmu ta yi cike da kaɗuwa tana ƙoƙarin ɓoye abin da ke hannunta. Fahimtar Amina ce ta shigo ba Babansu da ta yi tsammani ba; hakan ya ta sa ta sauke ajiyar zuciya dafe da ƙirjinta da ke bugawa fal-fal ta ce, "Ke ko me ya kawo ki gidan nan a a wannan lokacin? Kin wani shigo babu sallama haka kawai kin ba ni tsoro!" Zama Amina ta yi a bakin gado duk da tana jin sautin odar da mai adaidaita sahun yake ta zubawa alamun ita yake jira. Ta rushe da wani zakin kuka saboda rage nauyin da take ji a ƙirjinta. "Ke! Dakata! Dakata don Allah! Shin kin zo ne don ki tara mini jama'a ko kin zo don ki ƙara mini wata damuwa a kan wadda nake ciki?" Ba ta jira amsarta ba idonta a zare ta ci gaba da cewa, "Sawunki a likkafa ki tashi ki koma gidan mijinki tun kafin Babanku ya dawo gidan nan ya tarar da ke. Saboda a kan aurenki har barazana ya yi mini da saki muddin na yi sanadin mutuwar aurenki har da faɗin bakin aurena. Uwa-uba ni kaina ba zan so a ce aurenki ya mutu ba har sai kin haifa masa ɗa ko ɗiya a gidansa, ko don na ga ƙarshen iskanci da rashin mutuncin da ake ƙoƙarin yi mana daga ni har k..." "Assalamu alaikum!" Sallamar da suka jiyo a ƙofar gidan ta sa Innarmu yin shiru tare da ficewa daga ɗaƙin cikin sauri ta isa ƙofar gidan tana gyara zaman kallabin da ta ɗaura, wanda ya faɗo ƙasa garin duƙawa saka takalmi tsabar firgici da fargaban da take ciki a lokaci ɗaya. "Kuɗina za a ba ni, sauri nake yi akwai inda zan je tun ɗazu ake jira n.." "Idan ka saka haƙuri tare da ita ma za ku koma, don ita ma ba zama ta zo yi b..." Innarmu ta yi maganar cikin sanyin jiki, tare da juyawa gefe jikinta yana rawa ta cusa hannu cikin aljihun bujenta. Kuɗi ta ciro tana haɗa kansu ba tare da tsayawa tantance nawa ne ba ta miƙa masa, kansa a sama hannunsa a aljihu alamun ya gama yin fushi a cikin fusata ya ce, "Gaskiya ni sauri nake yi a dai biya ni na wuce! Ba zan iya komawa da ita b.." Karaf idanuwansa suka hango masa dubu-dubu da ɗari biyar-biyar bayan ɗari biyu da naira ɗarin da yake hange. Babu shiri ya sauya fuskarsa daga fushi zuwa murmushi ya karɓe kuɗin tare da yin gaba yana cewa, "Ki ce ta fito na sauke ta jira na ake yi." Innarmu ta koma ci shi ya shige cikin adaidatar sahun zuciyarsa cike da jin daɗin haɗuwa da irin Innarmu. Saboda ya gama fahimtar a ruɗe take kuma ba ta tantance adadin abin da ta miƙa masa ba. Shi ma baki- alaikum ya soke kuɗin aljihu, cikin rawar jiki ya dinga faɗin, "Ta fito fa! Kada kada ta ɓata mini lokaci." Hakan ya sa tun kafin Innarmu ta isa bakin ɗakin ta shiga ƙwala wa Amina kira tana faɗin, "Fito! Fito ke kaɗai yake jira don ya ce sauri yake yi." Turus Innarmu ta yi ganin Amina kwance a kan gado ta juya baya tana rera wani kalar kukan da ya sa Innarmu isa bakin gadon cikin sassarfa tana faɗin, "Ko kukan jini kike yi wallahi sai kin koma gidan mijinki ko za ki mutu ƙarewar kuka da ruwan hawaye! Za ki tashi ki je ya sauke ki cikin mutunci ko sai na haɗa miki da duka za ki fahimci da gaske nake y...?" Takaicin Amina ya ƙara yawa, saboda furucin da Innarmu ta yi a kan sharaɗin da Babansu ya gindaya mata a kan mutuwar auren nata; shi ne abin da ya ƙara lalata mata kuzarin bayyana rashin mutuncin da Jamal ya shuka mata. A ranta ta kitsa ba za ta bayyana mata sakin ba, gudun ita ma Babansu ya aiwatar da abin da ya shirya a kanta. Duk da babu hannunta a cikin sakin ballantana dalilin da ya kawo shi. Amma ba za ta so fallasuwar sakin ba gudun abin da ba ta fata ya kasance a tsakanin iyayenta. Hakan ya sa ta sauko daga kan gadon salun-alun da shessheka tana ajiyar zuciya ta ce, "Don Allah ki bar ni na zauna ko iya kwana biyu ne a gidan nan... Innarmu...zu...zu...zuciyata wani irin zafi take y... zan..zann..iya mutuwa idan na koma gidansa a wannan lokacin." Yanayin yadda ta yi maganar muryarta tana sarƙewa dafe da ƙirji; ba ƙaramin karya zuciyar Innarmu ta yi ba, amma hakan bai hana ta riƙo hannunta cikin zallar tausayin ta ta ce ba, "Ki yi haƙuri Amina, komai da kike gani muƙaddari ne daga Allah. Yanzu haka daga wurin Malam Shazaƙi na fito, kuma ya tabbatar mini aure tsakanin mininki da A'isha babu shi har abada. Kuma ke da mijinki mutu ka raba takalmin kaza mutuwa ce za ta raba ku. Yanzu haka kin ga abubuwan da ya ba ni...ya ce idan kika yi komai a yadda yake uwarsa ma sai kin so ya kula ta ballantana A'isha, wadda idan ban da tsoron Allah a dare ɗaya zan sa a kawar da ita kowa ya hut..." "Innarmu..." Amina ta yi maganar cikin wata murya saboda ƙirjinta da ke dakan luguden uku-uku a kan furucinta na ƙarshe. Tana ƙoƙarin sake yin magana Innarmu ta damƙa mata layu da magungunan da ta ɗaure a cikin leda tana faɗin, "Yi sauri ki tafi, gobe idan na samu dama zan zo da kaina na nuna miki duk yadda za ki yi amfani da su kamar yadda malamin ya faɗa mini. Don haka ki kwantar da hankalinki A'isha ba ta isa ta saka mu jin kunya biyu ba." Amina ta fice daga ɗakin jiri yana kwasar ta ta fice gidan Innarmu tana rarrashin ta, da kanta ta shigar da ita adaidaita sahun duk da ƙwallar da take sharewa tare da shessheka. Saboda sun tarar har ya kunna adaidaitasahun da niyyar tafiyarsa, don ya gama kitsa wa ransa cinye kuɗin duka a matsayin ladar zaman jiran da ya yi tsawon lokaci. Har adaidaitasahun ta fice daga layin ta hau kan titi Innarmu ba ta bar kallon su ba, zuciyarta cike da tunanin hanyoyin da za ta bi Amina ta zauna lafiya a gidan Jamal, sannan ta yi mulki irin wanda babu macen da za ta kai ta ballantana a ce ta fi ta wurin sa. Ta yadda ba zai ji maganar kowa ba sai tata, kuma ba zai ga kowace mace a cikin idonsa idan ba ita ba. Amina kam sautin kukanta ya ƙaru a daidai lokacin da ta ga an kama hanyar mayar da ita gidan Jamal, saboda tuna sakin wulaƙancin da ya yi mata bayan kishin Nur da ke cin ranta. Don a duk wani motsin da ta yi sai ta hango su rungume da juna suna faɗa wa juna kalaman soyayya. Idanuwanta a runtse suka isa ƙofar gidan tana ajiyar zuciyar kuka kala-kala. Ƙafafuwanta suna harɗewa ta isa bakin ƙofar gate ta ƙwanƙwasa, sai da ta kwashi minti biyar zuwa shida tana bubbuga gidan kafin Baba maigadi ya buɗe mata, bayan ya leƙa ta ƙaramar ƙofa ya hango ta tsaye tana ajiyar zuciya da zuƙar majinar kuka. "Ranki ya daɗe sannu da dawowa." Ya yi maganar cikin wata murya, saboda har ransa ya ji tausayin ganin yanayinta da halin da take ciki. Hannu kawai ta ɗaga masa ta yi gaba jiri yana ɗibar ta, don ƙafafuwanta sun gama yin sanyi da ƙyar ta ja su zuwa sama kamar ta kifa. Ikon Allah ne kawai ya kai ta lafiya, idanuwanta a rufe ta faɗa kujera tare da fashewa da wani sabon kuka cikin shaƙaƙƙiyar murya, saboda tuno Jamal da sakin da ya yi mata a gaban Hajiyarsa babu shayin komai, sannan da tafiyar da ya yi ba tare da ya tausaya wa halin da za ta shiga ba idan ya guje ta. 'Ko dai Zulaiha ce ta raba ni da shi?' Tambayar da ta yi wa kanta kenan a zuciya bayan ta tsahirta da rera kukan da take yi, duk da hawaye bai bar idanuwanta ba har lokacin. 'Idan ma ita ce ribar me za ta ci idan ta raba ku?' Wani yanki na zuciyarta ya ba ta amsa kai-tsaye, hakan ya sa ta yi tagumi kafin ta cira kai ta hango baƙar ledar da Innarmu ta haɗo ta da ita. Cikin sanyin jiki ta jawo ledar ta buɗe ƙirjinta yana bugawa, saboda ganin layoyin da ke ciki sun tuno mata ɗaya daga cikin nasohohin da Babansu yake yi musu ita da ƙannenta kodayaushe. 'Ko da wasa kada ku bar zuciya ta ingiza ku aikata shirka, wai saboda matsin rayuwa ko wani sauyin yanayi. Don babu abin da yake tabbace face gaskiya da ikon Allah, don haka ku dogara ga Ubangiji yana sane da duk halin da muke ciki ba zai taɓa bari mu wulaƙanta ba.' Maganar Baban ta saka ta jin wani sanyi a gefen zuciyarta, bayan dakiyar da ta zo mata tamkar an yi mata allurar nutsuwa. Saboda tuno lokacin da ya yi maganar da dalilin da ya jawo nasihar. Kasancewar kasuwa ta ja masa baya a wani lokaci, abinci ma da ƙyar suke samun na jefawa a bakin salati. Sai Innarmu ta yi wankau da surfe sannan suke kacancana abin da ya samu. Babansu kuma idan ya samo waje ya ci, idan ma bai samo ba sai dai ya yi kwana da yunwarsa, don ko ya tarar da abin ci a gidan ba ya ci. A cewarsa bai ba su ba kuma ba zai yiwu ya cinye musu ba. Wannan halin matsin da suka shiga ya sa Innarmu ta ba shi shawarar ya tafi wurin malamai su duba masa matsalarsa, kada a ce wani ne ya saka masa hannu bai sani ba, ganin ɗan abin da yake samu ya tsaya gabaɗaya sai wahala suke sha. Kallo ya bi ta da shi tsawon sakonni kamar ba zai yi magana, sai can ya sauke ajiyar zuciya ya ce, "Duk wanda bai dogara a kan Allah ne mai yi kuma shi yake hanawa ba ya ji haushin rayuwarsa. Ai da na je gun wani boka ko Malam; gara na duƙufa faɗa wa Allah damuwata don ba gata suka fi ni gare shi ba. Sannan babu shamakin da ya raba tsakanina da shi, kodayaushe yana tare da ni kuma ya fi kowa sanin halin da nake cik.." Innarmu ta katse shi cikin fusata riƙe da tagumi tana ƙura masa kallo da taɓaryar da take daka a hannunta tana cewa, "Oh Allah! Na jawo wa kaina abin magana daga shawara! Kai kenan kullum idan aka nuna maka hanya sai ka nuna ka fi kowa sanin Allah. To ka zauna ai, ni dai na san manyan malaman da suka shahara a duniya ma ana yi musu asiri ya kama s..." "Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ma an yi masa asiri ya kama shi. Ni ma ban ce ba zai iya kama ni ba, amma dai ba zan je wurin kowa da sunan neman taimako ba don Allah Ya yi mini wannan jarabawa." Baban ya amsa mata cikin faɗan shi ma yana ƙwala wa Amina kira tare da sauran yaransu cikin ɗaga murya, saboda tunaninsa ya tafi tsoron kada Innarmu ta cusa wa yaran nasa irin ra'ayinta. A nan ne ya yi musu nasihohin, waɗanda bai bari suka tashi ba har sai da ya tabbatar suna kan koyarwar da yake yi musu ba irin wadda Innarmu take bi da su ba. "Ya Allah!" Furucin Amina kenan bayan ta gama nazarin shuɗaɗɗun abubuwa da kalolin rikici da diramomin da ake yi a gidansu. 'Tabbas ba zan bari imanina ya lalace a sanadin wannan matsalar ba. Gara kowane irin mataki da wanda Innarmu take so na bi.' Daga haka ta mayar da layoyin ta ƙulle ledar, tare da ƙulle zuciyarta a kan biye wa sabgar Innarmu, amma ta kitsa wa zuciyarta sai ta nuna wa Nur ita ba kowa ba ce a wurin Jamal face abokiya, don ba za ta taɓa zama matar aurensa ba sai dai a yi mutuwar kasko kowa ya rasa. Kai-tsaye ta jawo waya ta kira Gwaggo Salame. Kira ɗaya biyu ta ɗaga suka gaisa babu yabo babu fallasa, kafin Aminar ta sauke ajiyar zuciya ta ce, "Gwaggo kina da labarin ya sake ni?" "Na ji a bakin Hajiyarsa, ta kira ni ta ce don Allah na ba Babanku haƙuri, kuma ta nemi alfarmar ki zauna gidan har ki kammala idda. A bisa hakan ni ma na ga dacewar zamanki gidan da barin maganar a tsakaninmu. Wataƙila kafin ki gama iddar mijinki ya dawo hankalinsa ku sasanta kanku." Shiru Amina ta yi na sakonni kafin ta sauke wata ajiyar zuciya ta ce, "Don Allah ko Babanmu kada ki bari ya sani Gwagg..." "Haba-haba dai...ai ban da niyyar buɗa zancen ga kowa, shi ya sa a inda na ji maganar a nan na bar ta. Ke ma saboda kin nemo ni ya sa na nuna miki na sani. Allah dai ya shiga lamarin ya kawo sasancinku kusa kafin lokacin. Sai kin yi haƙuri, ki kalli komai a matsayin ba komai ba, da sannu za ki ga ribar biyayyar da kike yi. Allah Ya yi miki albarka." "Amin Gwaggo." Daga haka suka kai ƙarshen maganar suka faɗa hirar Innarmu, inda Aminar take roƙon ta yi wa Baban magana su rage zaman doya da manjan da suke yi koyaushe. Saboda tun da ta yi wayo ta fahimci babu jituwa tsakanin Babansu da Innarmu, kuma abin yana damun ta sosai sannan tana jin takaicin 'yar tsamar da suke yi. Sun jima suna tattaunawa kafin su yi sallama a lokacin da katin wayar ya fara sanarwar ya kusa ƙarewa. Next page✍️ FANSAR ƘAUNA 32. *** Jamal tafiya kawai yake yi a kan titi cike da ƙarfin hali da jarumta irin ta maza. Amma a ransa da gaɓɓan jikinsa gabaɗaya ya yi rauni. Don kukan da Nur take yi wiwi ba ƙaramin cusa masa wata sabuwar damuwa ya yi ba. A ransa yana jin kamar ya yi parking har sai ta gama kukan sannan ya ci gaba da tafiyar, don bakinsa ya yi nauyin da ba zai iya rarrashin ta ba ballantana ya ba ta haƙuri. Sannan ya ƙi bin umarnin zuciyarsa da ke nuna masa ya sauka gefen titin saboda abin da yake ji ana yi masa a cikin kansa, har sai da kukan ya kai matakin da ƙwaƙwalwarsa ta fara juyawa, ganin sa ya yi rauni; sannan ya yi magana cikin wata ƙaƙƙarfar murya ya buga mata tsaya, tare da toshe kunnuwa da hannuwansa biyu a lokaci ɗaya yana cewa, "Ki daina! Ba na buƙatar kukan nan...ya isa haka!" Idanuwansa a rufe yana jujjjya kai alamun ba ya cikin nutsuwarsa, hakan ya ƙara dagula mata lissafi, cikin matsanancin tsoro da firgici ta sake yin wani ihun da ya saka shi dawowa cikin hayyacinsa babu shiri. Saboda abin da ta faɗa ta iya ƙarfinta a lokacin da ta fahimci sabon tashin hankalin da yake ƙoƙarin afka su ciki. "Innalillahi Jannnnn! Wayyo Allah za ka yi kisa!" Ta ƙare maganar ido zare saboda motar ta ƙwace masa kuma tana hangen aika-aikar da yake ƙoƙarin aikatawa. Don saura ƙiris ya taushe mutanen da ya ture daga kan mashin, cikin azama ya ja mugun birki, ikon Allah ya tsayar da motar cak tana wani irin ƙugi. Nan take mutane suka janye mashin ɗin cikin sauri, bayan waɗanda ya ture sun yi hanzarin tashi an ja su gefen titin, sannan aka shiga dudduba inda suka gurje a jikinsu, tare da son tabbatar da babu abin da ya same su bayan gurjewar da suka yi. Nan take zage-zage ya fara tashi a bakunan waɗanda Jamal ya tunzura, ganin ya so yin kisa amma kuma ya ƙi fitowa daga cikin motar ballantana ya ce a yi haƙuri. Yayin da wasu ke tunanin ko dai shi ma ya samu matsala shi ya sa bai fito ba. A cikin motar kuwa birkin da ya ja ya saka shi buga goshinsa saman sitiyari, ita ma ta faɗa bayansa babu shiri ta ruƙunƙume kujerar direban da yake kai tana salati idonta a rufe tsabar ya gama kiɗima 'yan hanjinta. Mintuna kaɗan bayan tsayuwar motar, ta ji yana ƙoƙarin ɓanɓare ta daga jikin kujerar, ranta a ɓace ta rufe shi da maganganun da ya kasa ɗauke kallonsa daga kanta, tsabar mamakin da ta ba shi da tunanin ita ce ko wata ce aka sauya masa. Saboda ta yi yunƙurin buɗe motar ta fita da niyyar bai wa mutane haƙuri, sai tunaninsa ya tafi a kan cewa fushi ne ta yi kuma ta tafiyarta za ta yi ta bar shi, saboda ganin yanayin fuskarta. Don haka ya yi hanzarin saka wa ƙofofin lock fuskarsa a haɗe yana aika mata harara tamkar bai taɓa yin dariya ba. Haushin hakan ya sa ta shiga yarfa masa maganganu cike da gayya don kawai shi ma ya ji haushin ya bar ta ta fice, ko kuma zantukan su sa ya shiga taitayinsa gudun ya jawo musu wata matsala kafin su isa inda za su je, garin zafin kansa. "Idan kai ka gaji da zaman duniyar ni ban shirya zuwa lahira a wannan lokacin ba! Don haka ka buɗe mini na kama gabana tun kafin ka yi wa dangina asara." "Danginki ko?" Ya yi maganar cikin wani kalar sautin da ya sa dole ta kalle shi da raunanniyar fuskarta. Hawayen idonta ya sake dawowa shaa yana sauka a kumatunta, tare da kai kallonta a gefenta tana ƙoƙarin share hawayen da gefen hannunta. Saboda fahimtar ba ya cikin yanayi mai daɗi, kuma don ƙarfin hali ba ya iya sauka daga dokin zafin kan da yake kai. Don tana da labarin ciwon da ya same shi a sanadin guduwarta. Kuma jikinta ya ba ta wataƙila ciwon ne ya motsa masa amma tsabar ƙarfin hali ba zai iya rusunawa ba. "Kina so ki koma a aura miki wanda kike so ko? Shi ya sa ba kya son mutuwa a wannan lokacin. Haka n...?" Ya yi maganar cike da ƙarfin hali dafe da kansa da ke sarawa babu ƙaƙƙautawa. Kafin ta ba shi amsa suka fara jin ƙwanƙwasar gilashin motar ta kowace ƙofa, don mutane sun yi wa motar rumfa har an fara shawarar idan ba a buɗe ba a samu abin bugu a buge gilasan domin a ga halin da mai tuƙin motar yake ciki. Da rawar baki Nur ta yi magana cikin dusasshiyar murya tana cewa, "Ka buɗe zan ba su haƙuri ne..." Hannu kawai ya saka ya cire lock ba tare da ya motsa ba. Cikin sauri ta ɓalle murfin tana ƙoƙarin ficewa, waɗanda ke jikin ƙofar suka yi hanzarin janyewa suka ba ta wuri ta fito. Dam-dam ƙirjinta ya shiga bugawa, ganin idanuwan mutanen wurin gabaɗaya suna kanta. Mayafin rigar da ke jikinta ta ja ta goge hawayen fuskarta, kafin ta gyara tsayuwarta ta zuƙe majinar kuka ta ce, "Don Allah ku yi haƙuri, wallahi ba ma cikin yanayi mai daɗi ne, saboda mai tuƙin motar ma bai da isasshiyar lafiya asibiti za mu je da shi yanzu haka. Ƙarfin hali ne ya saka shi yin tuƙin nan, aka yi rashin dace kuma jiri ya ɗebe shi tsautsayi ya saka shi yin wannan aikin..." "Mu ma ba ma cikin yanayin mai daɗi ba ku kaɗai ba ne!" "Wai sai an cuci mutum a dawo cewa ya yi haƙuri." Zancen wasu 'yan bani-na iya kenan tun kafin ta sauke numfashin maganarta. "Babu damuwa tun da uzuri ne, ku je kawai babu komai Allah Ya ba shi lafiya." Ɗaya daga cikin waɗanda aka ture a kan mashin ya yi maganar yana ƙoƙarin yarfe jinin da ke fita daga bayan hannunsa. Wani sanyin daɗi ya ratsa zuciyarta. Cikin rawar jiki ta buɗe motar da nufin komawa su tafi, don ta matsu su bar wurin gudun idon sani su kai wa Hajiyar Jamal rahoton an gan su tare. Amma dole ta dawo jikinta yana ɓari ta buɗe jakar hannunta ta ciro kuɗi ba tare da ta tsaya ƙirgawa ba ta miƙa wa mai raunin tana cewa, "Ga wannan ku yi haƙuri da su, kuma don Allah ku yafe masa har cikin zuciyarku, saboda shi ma ba da gangan ya aikata ba." Ta sake yin maganar a marairaice saboda ganin halin da mutanen suke ciki, don ɗayan da aka ture su tare zaune kawai yake dafe da kansa ba tare da ya ce komai ba. Amma saboda lafazin da wani da ke cikin dandazon jama'ar ya yi mata cikin ɗaga murya, inda ya yi maganarsa kai-tsaye a lokacin da take yunƙurin shigewa motar yana cewa, "Ku dai biya su kuɗi su je a duba lafiyarsu chemist! Don gaskiya ba za a yafe muku kuɗin ba ko da an yafe muku laifin." Ba su kuɗin ya sa ta kulle bakin kowa, cikin rawar jiki ta zagaya ta gaba tare da tsayuwa bakin motar fuskarta a haɗe tana faɗin, "Ka fito zan yi drinving, ba na son a sake samun wata matsalar." Jim ya yi kamar ba zai fito ba, yana yi mata wani kallon tsakiyar ido. Fuska ta ƙara tsukewa tana kallon gefe alamun babu wasa a tattare da ita, tsawon sakonni yana kallonta ƙur da lumsassun idanuwansa, kafin ya sauke nannauyar ajiyar zuciya ya ɓalle murfin ya fice dafe da kansa da ta sarawa. Cikin sauri ta ba shi wuri ya wuce, sannan ta shiga mazaunin direba ta zauna cike da jarumta ta tayar da motar. Sai da ta bari ya daidaita zamansa gaban sannan ta ja tana ɗaga wa masu yi mata Allah Ya tsare hannu suka wuce. Gudu take shararawa a saman titin idanuwansa ƙur a kanta duk da gudumar da yake ji ana kwaɗa masa a cikin kai. Sai da ta yi tafiya mai nisa kafin ya yi magana cikin ƙarfin hali saboda jijiyoyin kansa da yake jin kamar an ɗaure shi da su. "Ina za ki kai mu?" Ba tare da ta kai kallonta gare shi ba ta ce, "Asibiti za mu je a duba ka." Wani kallo ya yi mata kafin ya ce, "Kin maƙala mini ciwo a can kuma yanzu kina son na ga likita. Tafiyar kike so a fasa ko rabuwa da ni ne ba kya so?" Dam ƙirjinta ya buga, hakan ya sa ta basar da shi kamar ba ta ji abin da ya ce ba. Bai sake ce mata komai ba har ta sha wata roundabout tana ƙoƙarin kama wani titin ta miƙe ya sake cewa, "Idan kika samu wuri ki tsaya zan karɓi tuƙin." Ba ta ce masa komai ba har ta samu wurin tsayuwa ta ja gefe tana cewa, "Kana fama da ciwo amma kana ƙoƙarin shiritar da zancen zuwa asibiti. Me ya sa kake wasa da lafiyarka?" "Ina da magani zan sha idan muka je." Daga haka ya ɓalle murfin ya fice, tare da ba ta umarnin ta fito. Babu musu ta fita ta koma mazaunin baya ta zauna. Har ya zauna yana ƙoƙarin tayar da motar, ganin ta a bayan ya saka shi waigawa yana ƙare mata kallo cike da ɓacin rai. A haka ya tayar da motar suka ci gaba da tafiya babu mai cewa komai. Sai dai yanayin yadda yake bugun motar ya sa ta gano ta ƙara ɓata masa rai. Tsam ta yi da ranta saboda ko kaɗan ba ta farinciki da abin da zai taɓa lafiyarsa. Haka kawai ta ji babu daɗi, amma a ranta tana jin ba za ta iya bin ra'ayinsa ba. Sai da ya tsaya ya yi musu sayayya sannan ya wuce inda ya yi niyyar su nufa. Cike da mamaki ta kai kallonta gare shi a lokacin da ta gan su cikin gate ɗin wani babban Hotel. HOTEL Abin da ta karanta kenan a lokacin da ta yi arba da saman allon fuskar ginin Hotel ɗin. "Fito mu je." Ya faɗa yana riƙe da murfin motar idonsa a kanta. Jiki a sanyaye ta fito bayan ta aika masa harara, rufe motar ya yi tare da zagayawa ya fiddo jakar kayansa da ke bayan boot ya rataya, hannuwansa biyu ɗauke da ledodin siyayyar da ya yi musu. Kai-tsaye Reception ya nufa har ya yi nisa ya waigo, saboda bai ji alamun tana biye da shi ba. Kallon da ya aika mata ya sa ta yi fuskar shanu ta biyo shi tana jin wani ɗaci a tsakiyar zuciyarta. Tana tsaye rungume da hannuwa a ƙirji har ya gama karɓar ɗaki aka ba shi kati, ya yi sama cikin sassarfa yake taka matakalan benen, wanda zai sada su da ɗakin da aka ba su. A wannan karon babu ko ɗar ta bi bayansa duk da saƙe-saƙen da zuciya take yi mata. Bakin ɗaki ya ja ya tsaya, bayan ya zube ledodin hannunsa ƙasa, saita katin ya yi jikin na'urar da ke bayar da umarnin buɗe ƙofar. Sai da ta yi wata ƙara ƙirrrr sannan ƙofar ta buɗe ya shiga da sallama, bayan ya ɗauki ledodin ya ajiye a saman bedside durowa. Ƙin shiga ɗakin ta yi, har sai da ya leƙo bayan ya sauke jakar kayansa yana faɗin, "Ko kin ji labarin ina kasuwancin kawunan mutane ne?" Wani kallo ta yi masa kamar ta yi dariya, amma dole ta fuske. "Malama ki shigo ba na son harkar ƙauyanci." Yana maganar ya raɓe gefe ta wuce tana aika masa harara. Rufe ɗakin da ya yi ta ji tamkar an daki saitin zuciyarta, yatsun hannunta ta shiga kallo hawaye yana bin fuskarta ganin yana ƙoƙarin rage kayan jikinsa. Toilet ya faɗa tsawon minti biyar bai fito ba, amma har ya gama kwarara wa kansa ruwa ya yi wanka ya fito, ba ta ɗaga daga inda take tsaye ba. Bayan tsiyayar kukan da take yi ko dogon motsi ba ta yi ba. Mamaki fal ransa, ganin tana inda ya bar ta, sallaya ya fiddo a jakar kayansa ya shimfiɗa idonsa a kanta ya tayar da sallah. Sai da ya gama sannan ya kalle ta ya ce, "Malama ki shiga ki yi wanka ki yi sallah." Baki ta turo bayan ta yi masa wani kallon ido cikin ido hawaye yana zuba a kan fuskarta ta ce, "Ba zan iya zama ɗaki ɗaya da kai ba, saboda ni ba muharramarka ba ce kuma ka fi kowa sanin hakan." Wata guntuwar dariya ce ta suɓuce masa kafin ya ce, "Kina nufin na kawo ki nan ne don na yi wani abu da ke?" Shiru ta yi masa tana kallon gefe tare da ƙoƙarin share hawayenta. "Ni ɗan iska ne kin sani, amma ko wani na ga zai keta miki haddi ba zan taɓa bari ya ƙarasa aniyarsa ba, don dole ne ɗayan biyu ya faru, ko na kashe shi ko kuma na datse masa abar ya rasa ta gabaɗaya....ke ko ni ne na haiƙe miki babu aure ba zan taɓa yafe wa kaina ba. Saboda na san abin da nake yi, kuma na san darajar haƙƙi da girman amanarki da ke hannuna. Ko aurenki na yi ba iya saduwa ce kawai amfaninki gare ni ba, ke ɗin dai nake so kuma komai naki mai daraja ne a wuri na." Har cikin zuciyarta kalamansa sun ƙayatar da ita matuƙa. Kuma sun zare mata tsoro da fargaban da ya lulluɓe ta. Saboda sanin wane ne shi da kalolin jarabarsa, jiki a sanyaye ta nufi toilet ya bi bayanta da kallo har ta shige, sannan ya koma sauke ajiyar zuciya wata bayan wata tsikarsa tana tashi, a ƙoƙarin danne abin da yake ji a ransa ya furzar da iska mai zafi a cikin bakinsa. Wanda ya yi silar jefa shi takaicin iyakar da Hajiya ta yi masa a kanta, saboda tuno zafafan kalamanta. Shiru ya yi dafe da kansa da ke ta sarawa har jijiyoyinsa suna harbawa. Tsam ya miƙe ya fiddo robar takeaway da ke ɗauke da abinci, pepper chicken, ice cream da gwangwanin maltina da ruwa, ya ajiye gefen sallaya sannan ya fiddo rigar baccin da ya siyo mata ita ma ya ajiye a bakin gadon. Ya kwanta gefen gadon jiri yana kwasar shi ya runtse ido cikin wata kalar murya ya ce, "Ya Salam!" Tsam ta yi da ranta a lokacin da ta fito idonta a kansa, saboda ganin yanayinsa ya sa ƙirjinta bugawa, amma hakan bai hana ta isa saman sallayar ta tayar da sallah ba. Cikin minti biyar ta kammala sallar ta ja lokaci tana addu'a, wadda fiye da rabinta a kan nema wa Jamal sauƙi a kan ciwon da ke damunsa ne. "Ki ci abinci." Ya yi maganar idanuwansa a runtse cikin wata kalar murya, ido ta kai a kan kayan da ya jera kafin ta cira kai ta kalle shi ta ce, "Maganinka fa! Ko ka manta ba ka sha ba." Shiru ya yi mata bai ce komai ba, har sai da ta maimaita maganar sannan ya miƙe yana wani irin nishi ya jawo jakarsa ya zuge zif. Wata farar leda ya ciro yana faɗin, "Ki ci abincinki na san kina jin yunwa, don shan maganin ba zai hana ni mutuwa ba." Yarrr! Tsikar jikinta ta miƙe, tsabar shiga jikin da maganar ta yi wa gaɓoɓinta. A diririce ta zabura jikinta yana rawa ta jawo ledar maganin tana faɗin, "Ba yanzu za ka mutu ba. Don haka ka ma daina irin wannan maganar. Allah ba zai taɓa kashe ka ya bar ni b.. dole ma tare za mu mutu a rana ɗaya kuma a lokaci ɗay...." "Shiiiih!" Ya yi hanzarin ɗora hannunsa a saman bakinsa dafe da zuciyarsa yana cewa, "Kina da gata, ba zan so danginki su yi asarar ki b...." Ya ƙare maganar da ƙyar yana ɗauke numfashi, saboda tuno ɗaya daga cikin kalamanta da suka tsaya masa a zuciya. Jikinta yana rawa ta isa gare shi cikin muryar kuka ta riƙe hannunsa tana cewa, "Don Allah...don girman Ubangiji Jaaan ka daina ba na so! Kada ka bari ciwon nan ya cuce mu a banza musamman a irin wannan lokacin! Ka yi haƙuri mu je asibiti yanzu don Allah Jaaannn.." "Babu abin da zai faru, matuƙar za ki daina yin abin da ke dawo da ciwon baya zan samu lafiy.." "Na yi alƙawari ba zan sake yin abin da zai ɓata maka rai ba. Ka sa a ranka idan har ni ce matsalar daga yau lafiyarka za ta dawo in sha Allah." Wani kallo ya yi mata ganin yadda hawaye yake zarya a kan fuskarta. Fuskar da yake gani a mafarki tana yi masa murmushi, fuskar da yake gani a ko'ina tana yi masa gizo. Amma a yau ga ta gabansa tana gani a cikin yanayin da ba ya masa daɗi, don gabaɗaya fuskar ta gama zama ja tsabar kukan, bayan jan ido da kumburin suka yi luhu-luhu tamkar wadda ke ciwon ido. Ƙur ya yi mata da ƙwayar idonsa yana kallon ta tsawon mintuna suna kallon juna, kafin ya yi wata ajiyar zuciya mai ƙarfi, saboda tuno tarnaƙin da ke gabansu, tare da zallar tausayin ta da ke taɓa ransa, duk da yana ƙoƙarin kawar da abin a zuciya saboda tunanin da ke kansa a kan cewa ba ta son sa. "Ke da za ki auri wanda kike so, me kike yi wa kuka?" Ya yi maganar cikin raunanniyar murya yana sauke numfashi a sama. Ba ta ce da shi komai ba ta karɓe ledar maganin ta hau buɗewa ƙirjinta yana bugawa fat-fat. Tsabar tashin hankalin ganin halin da ciwon ya ƙara saka shi. Gaba ta saka shi ya ci abinci kaɗan ba don ya so ba, bayan haka ta ɓallo magungunan kamar yadda ta gani a rubuce jikin kwalayen. Yana nuna ba ya so a haka ta matsa sai da ya sha maganin, da kanta ta gyara masa kwanciya a kan gadon tare da ƙara wa Ac gudu. Kafin ta dawo bakin gadon ta tsaya rungume da hannnuwa a ƙirji idonta a kansa tana zuƙar majinar kuka. Shi ko sai lumshe idanuwa yake yi yana buɗewa zuciyarsa cike da hasashen washegarin ranar a irin wannan lokacin tana tare da wani a matsayin matarsa shi kuma mijinta. Zuciya mai ɗora wa mutum matsala har da hango hotonsu a kan gado suna raya sunnar aure. Salati ta fasa iya ƙarfinta ta yi kansa tana kiran sunansa, saboda nan take wani kalar tari ya turnuƙe shi ya shiga aman jinin da ya sa ta rungume shi jikinta, a firgice ta dinga cakumar sa tana zunduma ihu da kururuwar kiran jama'a su kawo mata ɗauki a cikin zaucewa. Next page. 33. Kwanƙwasar ɗakin da aka yi ya sa ta zabura da nufin buɗewa bayan ta yi ƙoƙarin raba jikinta da nasa. Caraf ya riƙe hannunta da jajayen idanuwansa ya dinga girgiza mata kai saboda ganin abin da take son aikatawa. Tsaye ta yi turus tana kallonsa hawaye yana zarya a kumatunta har ya dafa ta ya miƙe. Hannunta ya ja duk ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin da ake yi, haka ya nufi toilet riƙe da ita cikin ƙarfin hali ya fara wanke bakinsa tare da fuskarsa, kafin ya tara kai a showa tana bugun kansa tsawon mintuna yana ta sauke ajiyar zuciya. Sai da ya kwashi minti huɗu a toilet ɗin kuma har ya gama abin da ya kai shi suka fito bai saki hannun nata ba. Bakin ƙofar ya nufa kai-tsaye bayan ya sake ta, buɗewa ya yi cike da jarumta ya gayyato murmushin dole a kan fuskarsa, sannan ya shiga yi wa securitys bayani a cikin harshen Turanci yana cewa, "Wannan shi ne darenmu na farko, tsoro ya sa amaryata yin raki." Wannan bayanin ya sa suka kalli juna suna murmushi tare da yi masa kalaman ƙarfafa gwiwa cikin raha, suka bar wurin ya rufe ƙofar yana sauke ajiyar zuciya. Bakin gadon ya koma ya zauna, idonsa a kanta ganin tana goge aman jinin da ya yi cikin zafin nama. Sai da ta kammala ya kira sunanta ta kalle shi fuska a kumbure ta ce, "Me ya sa ka hana ni neman mutanen da za su taimaka mana a kai ka asibiti?" "Saboda ba na fatar alhakin ciwon ko mutuwata ya rataya a wuyanki. Domin duk abin da ya faru za ki shiga zargi da tuhumar ke ce sanadi. Mutane za su zargi ke kika aika mini komai duk da babu ruwanki." Wani kallo ta yi masa cike da mamaki a kan fuskarta ta ce, "Yanzu saboda gudun a zarge ni ya sa ka ƙi bari a kula da lafiyarka? Hummm!" Ta ƙare maganar tare da sauke wata gwauruwar ajiyar zuciya sannan ta ɗora da cewa, "Ban san me ya sa kake ƙoƙarin yin wasa da lafiyarka ba. Ka taimake ni ka taimaki waɗanda nauyinka ya rataya a wuyanka ka daina bari lafiyarka tana zama abokiyar wasark...." "Please! Zo ki kwanta dare ya fara yi, gobe da ƙarfe biyar da rabi jirgin da za mu bi zai tashi." Kallon sa ta yi ido tsakar ka ganin ko kaɗan ba ya son zancen ciwon ko zuwa ganin likita. Haushi ya sa ba ta sake cewa komai ba ta nufi kujera ta zauna, kai ta ɗaga sama rungume da hannu bayan ta jingina bayanta ta rufe ido. Numfashi ta shiga saukewa a hankali saboda wani kalar yanayin da take jin kanta a ciki. "Ki dawo kan gadon sai kin fi jin daɗin kwanciyar." Banza ta yi da shi ba ta motsa ba kamar yadda ba ta ce da shi ƙanzil ba. Shi ma ganin ba ta son magana ya sa bai sake cewa komai ba ya koma bakin gadon ya kwanta tare da rufe nasa idon kamar mai bacci. Minti biyar a tsakani nannauyan bacci ya yi awon gaba da Nur a kan kujerar. Ya fahimci hakan ne a lokacin da ya buɗe ido d niyyar satar kallonta kamar yadda yake yi duk bayan minti da sakonni. Saboda wata nannauyar ajiyar zuciyar da ta sauke alamu ya nuna ta yi nisan bacci. Tsam ya miƙe bayan wasu mintunan da ya bayar gudun ya taɓa ta ta firgita. Cancakak ya ɗauke ta sama ta langaɓe masa, a haka ya isa da ita kan gadon ya shimfiɗe ta a hankali kamar wata jaririya. Abin rufa ya lulluɓa mata tare da rage sanyin Ac kafin ya koma kan kujerar ya zauna. Kamar yadda ya ga ta yi haka shi ma ya yi zuciyarsa cike da burin baccin ya sace shi ko zai rage nauyin da yake ji a cikin zuciyarsa. Amma fafur bacci ya ƙi zuwa, har sai da ya saka wayoyinsu a caji sannan ya koma kan kujerar ya ɗora kansa saman wardrobe ɗin kujerar, ya shiga sauke ajiyar zuciya wata bayan wata tamkar wanda ya sha gudu. Ya rufe idonsa cike da ƙoƙarin kawar da kansa daga kan abin da yake hasashen faruwarsa a ransa. Cike da burin ƙarfafa kansa don ya samu damar cika alƙawarin da ya ɗaukar wa kansa da Baban Amina. Kasancewar akwai gajiya tare da shi sannan da jikin ciwo, bayan maganin da ya sha mai saka bacci a cikin magungunansa, cikin ɗan lokaci ya fara sauke numfashin baccin yana nishi a hankali. Bai farka ba sai karfe huɗu da rabi na asuba, inda ya fahimci Nur ba ta farka ba har lokacin; ganin ko kwanciya ba ta juya daga yadda ya ajiye ta tana nan babu dogon motsi. Toilet ya faɗa ya yi wanka, cike da ƙarfin zuciya da jin daɗin sauƙin da ya samu, sannan ya hau kan sallaya yana kai kukansa wurin Allah, bayan ya jera nafilolin da ya ji sun ƙara masa kuzari. Ƙarfe biyar saura Nur ta tashi da salati ɗauke a bakinta, ido ta shiga warawa cike da son tabbatar da abin da ta ga yana ƙoƙarin faruwa a mafarki. Ganin Jamal a zaune idonsa ƙur a kanta ya sa ta runtse ido cikin sauri ta buɗe saboda tuno abin da ke gabansu. Jiki babu kuzari ta miƙe ta yi toilet zuciyarta cike da tunanin Minal da abin ta hango a mafarki. Wanka ta fara yi sannan ta mayar da kayan da ke jikinta ta fito, sai da ya ga tana ƙoƙarin shimfiɗa ɗankwalinta da niyyar yin sallah sannan ya tashi daga kan sallayar yana faɗin ta hau kai ta yi sallar. Babu musu ta ƙarasa sallar tare da guntuwar addu'a ta shafa, ganin yadda yake shiri cikin gaggawa tare da duba agogonsa da ya mayar a tsintsiyar hannunsa. Ina kwana ta yi masa tare da ya jiki amma ko ɗaya bai amsa ba, a gabanta ya shiga sauya kayan jikinsa babu shiri ta kawar da kai cike da jin nauyin sa. Shi kam ko a jikinsa, bayan ya gama ya fara harhaɗa komai da za su buƙata a cikin ledar da ya zo da su, sannan ya bar wanda ba sa so a wurin yana faɗin, "Ga rigar da za ki saka nan... ki yi sauri mu tafi lokaci yana tafiya." Idonta ta kai a kan rigar da ke ajiye bakin gadon. Wadda sai a lokacin ta tuna jakar kayanta da ke wurin Adamu. Amma ko tana son karɓa babu dama gudun ta ƙara saka wa Jamal mugun zargin da yake yi a kansa. Rigar ta ja ta faɗa toilet, cikin sauri, mintuna a tsakani ta fito, ya bi ta da kallo bakinsa a sake tamkar wani wawa. Saboda shigar a jikinta ta ƙara yi wa rigar kyau matuƙa, fiye da yadda ta burge shi kafin ya siyo. Amma dole ya basar ganin ta cure fuska alamun ko kallon sa ba ta son yi. Murmushi kawai ya yi mata ya riga ta fita ɗakin jakarsa saɓe a kafaɗa. Ta biyo shi wayarta a hannu zuciyarta cike da tsoro bayan fargabar komawa gida da ke danƙare a ranta. Kasancewar yana sauri har ya sallama da ma'aikatan wurin ya ba su katin ba ta sauko ƙasan ba. Ko da ta fito cikin girmamawa ta gaisa da ma'aitan sannan ta iske shi bakin mota. Inda ta tarar yana ba ta wuta babu ɓata lokaci ta buɗe baya ta shige. Bai ce da ita komai ba ya ja motar suka fice hotel ɗin, duk da duhun safiya amma hakan bai hana shi saita madubi a kan fuskarta ba. Motsi kaɗan sai ya ɗaga kai ya kalle ta, ita kam dannar wayarta kawai take yi ba ta ma san yana yi ba. Fahimtar hakan ya kasa haƙuri sai da ya furta. "Kin yi kyau fa." Kai ta ɗago ta kalle shi tare da aika masa harara ta ce, "Na gode." Murmushi ya yi saboda garin godiyar har da kallon sama da ƙasa ya samu. Aljihun motarsa ya buɗe, ya ɗauko kwalin turare ya miƙa mata ba tare da ya kalle ta ba ya ce, "Ki shafa." Ido ta ƙura wa turaren nan take wani farinciki ya mamaye zuciyarta, kafin wani hawaye ya biyo cika mata ido bayan ta karɓi turaren ta shiga juya shi kafin ta hau fesawa a jikinta ƙwalla tana sauka a kan fuskarta. Saboda tuno matsayin turaren a wurin ta da girman ƙaunar da take yi masa a ranta. Har suka kai airport babu wanda ya sake cewa uffan. Sun isa saura minti biyar jirgin ya tashi, babu ɓata lokaci aka fara cuku-cukun shiga jirgin kafin tashinsa. ***** Ɓangaren Minal kuma, bacci don yana ɓarawo ya ɗauke ta a ranar. Saboda ƙuncin da take ciki juyi kawai yake yi kan gado idan ta gaji da gefen da take kwanciya ta sauya wani. Zuciyarta cike da kewar Jamal da kalolin soyayyarsa mai tsayawa a maƙoshi, bayan tunanin daren da suka raya a kan gadon tamkar babu mutuwa a cikin duniyarsu ballantana saki a kutso wa rayuwar aurensu. Asubar farin Innarmu ta yi wa gidan tsinke, don rashin baccin dare ya sa wani nannauyan baccin sace ta bayan ta gama sallar asuba. Sallamar da Innarmu ta shiga doka mata wata bayan wata ya sa ta farka firgigit babu shiri. Kamar almara ta hango Innarmu a kanta riƙe da ƙugu tana cewa, "Yanzu duk wannan masifar da muke ciki ashe ke ba ki hango ta babu abin da ya dame ki!" "Na damu Innarm..." Minal ta amsa mata cikin jiri da baccin da ke cikin idonta. Innarmu ta kwaɗa mata wata ƙatuwar harara tana faɗin, "Da ba ki saki baki kina irin wannan baccin mutuwar ba, don alamu ya nuna ba kya cikin wata damuwa ni kika bari da kwanan takaici. To ba ni saƙon da na ba ki jiya na yi abin da ya kawo ni na ƙara gaba." Ta yi maganar a ƙufule tana barin wurin tare da ficewa daga ɗakin ta zauna falo. Ranta a ɓace ta dinga ƙare wa falon kallo tana wassafa wa ranta gidan ya kusa zama nasu, waton daga Minal sai jikokinta. Tsam Minal ta yi a ranta, saboda ta gama tattara hankalinta a kan haƙuri da duk yanayin da za ta tsinci kanta. Ta dogara ga Allah a kan ya yi mata mafita. Amma dole ta bi umarnin Innarmu matuƙar tana so su rabu lafiya. Jiki babu kuzari ta sauko daga kan gadon jiri yana kwasar ta ta ɗauko ƙullin ledar a inda ta yi mata mugun ɓoyo, da niyyar sai ta samu dama ta jefar, sai ga shi Innarmu ta wargaza mata tsari. Ɗaki ta buɗe fuskarta babu yabo babu fallasa ta isa inda Innarmu take zaune tana gaishe ta. Amma ko kaɗan Innarmu ba ta bi ta kan gaisuwar ba ta wafce ledar tana faɗin, "Na fahimci ba ki san wahalar da na sha kafin na samu wannan damar ba. Bayan kuɗina da kika sa na yi asara jiya har dubu goma sha ɗaya da ɗari biyar." "Asara kuma?" Minal ta yi tambaya cike da mamaki, Innarmu tana buɗe ledar ta ba ta amsa da cewa, "Zancen kike so!" Sai da ta miƙe ta fara tafiya sannan ta dakata tana cewa, "Mai adaidaitasahun da ya kawo jiya, shi na tura wa kuɗin gabaɗaya ba tare da na sani ba. Kuma hakan ya faru ne duk a sanadin tashin hankalin ganin ki gidan a wannan lokacin. Don haka ki sani sai kin biya ni, don ba zan lalace a kan hidimarki ke kaɗai ba, waɗannan kayan aikin ma ba ki san nawa na kashe kafin a a ni ba. Saboda haka ficikata ba za ta yi ciwon kai ba, duk lokacin da kika samu kan mijinki ki karɓo mini su a jimillarsu dubu ashirin da huɗu cas har da ɗari biyar." Dariya ta so kufce wa Minal babu shiri ta ƙumshe ta tare da bin bayanta tana cewa, "To yanzu ke Innarmu ina za ki kai kayan a cikin gidan nan?" "Ke dai biyo ni, duk da ban san kan gidan ba zan yi abin da ya dace. Fatana kawai Allah Ya sa haƙarmu ta cimma ruwa buƙata ta biya." Minal ta bi bayanta zungui-zungui har suka sauka ƙasa zuwa farfajiyar gidan. Innarmu ta yi bayan gidan kai-tsaye cike da burin aiwatar da abin da ya kawo ta, yayin da Minal ta kai kallonta a kan Baba maigadi cike da tsoro tana faɗin, "Innarmu kada fa asirinmu ya tonu, saboda Baba mai yana gidan kuma zai iya fahimtar abin da muke ƙoƙarin aikatawa." Minal ta yi maganar a hankali tamkar raɗa, Innarmu kam ko waige ba ta yi ba ta ci gaba da nausa kanta tana faɗin, "Shi ma idan ya samu irin wannan damar a cikin iyalansa so yake yi. Don haka ganin sa ba zai hana ni yin abin da zai kawo mana mafita ba." Cike da jarumta Innarmu ta ɗage interlock ɗaya a can ƙuryar bayan gidan ta saka laya biyu a wuri daban- daban ta danne. Sannan ta ciro ƙullin simintin a jakarta, wanda ta yo guzuri tun daga gida saboda sanin gidan babu ƙasa. Da kanta ta kwaɓa simintin da ruwan fanfon da ke bayan ɗakunan gidan ta liƙe interlock ɗin tsaf ta shafe shi. Sannan ta kalli Minal da ke nesa da ita rungume da hannu ta kasa ta tsare gudun Baban ya yi musu ba zata su ji kunya. Innarmu ta yafito ta da hannu alamun ta je, jiki babu kuzari ta isa wurin ƙirjinta yana bugawa. "Kin ga wannan layar? Ki tabbatar kin saka masa ita a cikin filon da yake bacci da shi. Saboda wannan wata dama ce da zai dinga kwana da ke yana tashi a cikin ransa ko yana so ko ba ya so. Wannan maganin kuma ki saka masa a cikin abinci kuma ki tabbatar da ya ci a gaban idonki. Daga kin yi haka shi kenan kin gama komai sai dai mu jira sakamakon abin da zai biyo baya. Amma da yardar Allah babu shi babu kauce wa umarninki matuƙar kika ƙarasa aiwatar da abin da na ce miki. Don ko uwarsa kika ce ba kya so ya gaishe ta zai daina, ballantana wata koɗaɗɗiyar banza mara asali." Minal ta yi shiru kawai tana nazarin maganganun kafin ta ce, "Ban da damuwa da Hajiyarsa Innarmu, amma tabbas ba na fatar Nur ta sake shiga gabansa kamar yadda ta yi mini a can baya. Don na yi alƙawarin ko da wuta take yawo sai na raba ta da Jamal tun da tun farko ba ni na ce ta bar mini shi ba." Cike da jin daɗi Innarmu ta dafa kafaɗarta tana faɗin, "Ma sha Allah, tun da har kika fara gano abin da nake nusar da ke koyaushe. Ni zan tafi Babanku bai san na fito ba, Allah Ya ba mu sa'arsa a hannu." Suka fito daga bayan suna ci gaba da tattauna zancen har zuwa bakin gate. Minal ta raka ta tana yi mata Allah Ya tsare suka yi sallama, bayan ta fice gidan Minal dawo zuciyarta cike da tunanin anya irin agajin da Innarmu ta kawo wa rayuwar auren nata zai yi alfanu kuwa? Sanin babu wanda zai ba ta amsa ya sa tana shiga ta kira Hajiya, cikin marairaice murya suka gaisa, daga nan ta yi shiru saboda nauyin faɗar abin da ya sa ta yi kiran. Fahimtar hakan ya sa Hajiyar ta ce, "Na faɗa miki idan akwai abin da kike buƙata ki faɗa mini zan sa a kawo miki." Minal ta ji wani daɗi ya rufe ta cikin fara'a ta ce, "Da ma babu kuɗi ne a hannuna, shi ne nake so na riƙe wani abu har zuwa lokacin da zai dawo." "Idan wannan ne kada ki damu, ki turo mini account ɗin ki zan sa a turo miki abin da za ki ɗan lallaɓa kafin wasu su sake zuw..." "Babu damuwa Hajiya na gode ƙwarai Allah Ya ƙara girma. Sannan idan da hali don Allah a haɗa ni da wadda za ta taya ni zama gidan babu daɗi babu motsin kowa." Hajiya ta yi mata alƙawarin kawo mata wata 'yar aikin da za ta taya ta kwana kafin a ga abin da Allah zai yi. Sai bayan sun yi sallama ta kashe wayar sannan ta kira Innarmu cike da jin daɗi. Kira ɗaya ta ɗauka tana faɗin, "Me kuma ya faru yanzu?" Murmushi Minal ta yi kafin ta ce, "Innarmu ki tafi wurin Abba mai p.o.s zan tura masa kuɗi yanzu ki karɓa. Kuma Hajiya ta ce za ta kawo mini 'yark...." "Ki faɗa mata kina da ƙanne su za ki ɗauko su dinga taya ki aikin gidan." Innarmu ta yi maganar cikin rawar jiki da zumuɗi, ganin Allah Ya kashe ya ba su, kuma sabuwar dama ta samu. Minal ta yi 'yar dariya tana faɗin, "A dai bari ta turo 'yar aikin Innarmu ba na son ta gano shirin da muke yi..." "Yi mini shiru sakarya! To don ubanki ko ni aka ce na dinga yi miki aikin zan zo na yi ballantana ƙannenki, to mene a ciki Allah na tuba?" Caiii😅 Next page 34. "Innarm..." Minal ta yi maganar cikin muryar dariya tana rufe baki tare da zaro ido tsabar dariyar da zancen nata ya ba ta. Amma kafin ta faɗi abin da ta yi niyya Innarmu ta katse ta da cewa, "Faɗa mini haramun ne ko zunubi ne zan aikata don na zo gidanki na yi miki aiki? Ai da samu a gidan wasu gara namu gidan, don ke ma kin san aikin da kike sha a gida rabinsa ma ba za ki yi a gidan mijin naki ba. Amma saboda kin samu gidan arziƙi gidan hutu har ana hangen dacewar nema miki 'yar aikin amma ki kasa cewa ga ƙanwaki ta isa. Don haka ki sani ni, a wurina ba abin kunya ba ne don na zo gidanki na hunce tufa ina yi miki aikatau. Sai dai yanzu tun da ba ki yi wannan Hausar ba; ko da 'yar aikin ta zo idan aka kwana biyu sai kin ƙara da Maryama. Saboda ita ma tana son zama gidan naki ta zauna, ko Allah zai ba ta wanda zai ɗauke ta a cikin dangin mijinki ko a cikin unguwar taku ta masu kuɗi, idan ita ma ta samu gidan hutun ai sai mu ƙara hutawa." Sai da ta dire maganarta tsaf sannan Minal ta yi magana cikin dariya ta ce, "Innarmu kin gama yarda da kuɗi wallah..." "To me ake yi da talauci Amina? Ai ko Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama Ya nemi tsari da shi ballantana mu 'yan baya, waɗanda ko sunanmu babu a cikin ahalari ballantana hadisi. Ko so kike yi yadda muka ginu cikin talaucin mu yi sakacin da ginin tsiyar zai rushe da mu a cikin sa?" Dariyar da Minal ta shiga yi babu ƙaƙƙautawa ya sa Innarmu ta sake cewa, "Wallahi laƙada kawas tsakaninmu da talauci izaja'a ƙafa dubu Amina. Don haka komai zan iya yi matuƙar na san za a yi yunƙurin raba ki da wannan gida. Maryama ma irin sa nake yi mata fatar samu tun ranar da na fara zuwa gidan, addu'ata kullum ba ta wuce wannan ba. Don haka ki shirya ko kin samu 'yar aikin Maryama tana nan tafe matuƙar buƙatarmu ta biya dole mu dama." Shigowar alert a wayarta ya sa Minal ta yi hanzarin faɗin, "Allah Ya taimake mu gabaɗaya, sai kin ga kuɗin Innarmu." Minal ta ƙare maganar cikin fara'a. Innarmu ta amsa da Amin suka yi sallama. Baki har kunne ta dinga kallon alert ɗin cike da jin daɗi, ganin 30k lakadan suna kallon juna. Jikinta yana rawa ta tura wa Innarmu rabi ga mai p.o.s ɗin unguwarsu sannan ta biya bashin katin da MTN suke bin ta cikin zumuɗi. Zuciyarta wasai ta raya wa ranta cewa, 'Haka zan yi ta yi ina cin kuɗi har sai na tara kuɗi masu yawa a account ɗi na kafin ya dawo. Ko babu komai na fanshe takaicin zaman da zan yi a cikin gidan ni kaɗai. Nur kuma ko ba ya so dole ya bar ta tun da har suka yi sakacin da na riga ta aurensa.' Ƙwafa ta yi a ƙarshen zancen zucin saboda ƙudurin abubuwa da yawa a cikin ranta. **** Jamal da Minal kam jirginsu ya tashi kamar yadda aka tsara, inda ya bar motarsa ga wani abokinsa a cikin filin jirgin. Mazauni ɗaya suka zauna duk da Minal ta so yin nesa da shi, don ba ta son a gano tafiyarsu guda ballantana wata hira ta haɗa su. Amma dole ta haƙura saboda hannunta da ya riƙe gam ya ƙi saki, ta zauna kusa da shi tana cin magani. Lokacin da jirgin zai tashi ma fuskewa ta yi har ya gama daidaita a sama ba ta bari umarnin zuciyarta ya yi tasiri ba. Don zuciyarta sai wassafa mata ruƙunƙume shi take yi, saboda yadda take jin jirgin yana wani abu kamar zai faɗo da su ƙasa. Murmushi kawai ya yi mata, ganin da gaske ƙoƙarin raba kanta da shi take yi, hannunsa da ke cikin nata ya matse sai da ta yi 'yar ƙara tare da ɗora idanuwanta cikin nasa tsawon mintuna suna kallon juna. Hakan ya jawo musu shiga cikin wani sabon yanayin da dukan su suka dinga aika wa juna saƙon idon ba tare da sun sani ba. "Me ya sa ba kya tausayi na?" Wani kallo ta yi masa kafin ta amsa masa a kan leɓenta tamkar ba ta son maganar ta ce, "Tausayi ko?" Kai ya ɗaga mata yana lumshe ido saboda ƙamshin turarenta sosai ya shiga jikinsa ya saukar masa da kasala. "Akwai yiyuwar ki saki komai da ke ranki, saboda na gama tsara komai kuma ina so mu yi rabuwar da za ki dinga tunawa koyaushe." Ƙirjinta ya buga dam-dam saboda kalmar rabuwar ba ƙaramin dukan zuciyarta ya yi ba. Amma cikin ko-in- kula ta ba shi amsa da cewa, "Da ma can ba ma tare ai." "Ko?" Ya tambaya idonsa a kanta yana haɗe fuska, nan take ta diririce saboda tuno ciwonsa da alƙawarin da ta ɗaukar masa. "Ni..ni..fa ba haka nake nufi b..." Ta yi maganar cikin rawar baki, yayin da ya jefo mata wata tambayar bayan ya sauke ajiyar zuciya. "To, me kike nufi?" "Kawai dai ba na son mutane su zargi akwai wani abu tsakanina da kai a yanzu bayan zumuncin matarka." "Matata ko?" "I, kai ma ka sani don haka ana barin halas don kunya. Yanzun ma idan da hali ina son idan muka sauka ka bar ni na ƙarasa gida, kai ka je sabgoginka." Shiru ya yi kamar ba zai ce komai ba, amma dole ya furzar da iska mai zafi a bakinsa yana cewa, "Alƙawarin da na ɗaukar wa Baban kuma fa?" Harara ta aika masa kafin ta kafe shi da ido ta ce, "Tun da ka kawo ni gida ai shikenan ka sauke." "Ba shikenan ba gaskiya." Ya yi maganar cikin sauri yana murmushi. Ita ma ta kafe shi da ido tana cewa, "To me ya rage?" Ta cillo masa tambayar tana jin wani ɗaci a maƙoshinta. Bai ba ta amsa ba, ganin yanayinta da zuwan ma'aikatan jirgin wurin. Hannu ta zura ta karɓi kofin ruwan bunun da ake miƙo mata cikin fuskewa. Shi ma ya karɓi nasa idonsa a kanta ya shiga juya ruwan da cokali kafin ya fara sha yana kallon gefe. Sai da ya zuƙe ya ajiye kofin ba tare da ta yi wa nata ko kurɓa ɗaya ba. Hakan ya sa ya yi magana cike da basarwa ya ce, "Malama da kin sha tun kafin ki zubar a jikinki." Babu musu ta kai bakinta tana kurɓa kamar ba ta so, wayarsa ya ciro daga aljihunsa yana dubawa, hakan ya ba ta damar shan rabi ta ajiye saura a saman tiren tangaran ɗin da aka ɗora kofin a kai, hankacif ya yi hanzarin miƙa mata a lokacin da take ƙoƙarin goge bakinta da hannu. Kallon sa kawai ta yi sannan ta karɓa tana haɗe rai ta goge bakin tare da gyara zamanta ta lumshe ido. Fuskarta ya ƙura wa kallo yana jin wani yanayin yana tsirga wa cikin ransa da zuciyarsa, gazar-gazar na gashin girarta ya ƙura wa kallo kafin ya dawo kan leɓunanta masu matuƙar burge shi. Ajiyar zuciya kawai ya shiga saukewa wata bayan wata, tare da haɗa cinyoyinsa wuri ɗaya ya matse saboda jijiyarsa da ke harbawa. Nan take jikinsa ya hau rawa, hannunsa da ke cikin nata ya ɗauki gumi da karkarwa. Cikin sauri ta buɗe idanuwanta da ke lumshe ta sauke su a kansa, kafin ta dawo da kallonta a hannun nasa da ke riƙe da nata hannun. A cikin maganar ido ta yi masa tambayar lafiya, amma ya waske kamar bai fahimci komai ba ya shiga goge gumin da ke tsattsafo masa a goshi da wani hankacif yana ƙara matse jiki. Ganin yadda ya takure waje ɗaya hankalinta ya tashi, cikin maraita ta ɗora kanta saman kafaɗarsa tana faɗin, "Idan har ni ce na jawo ciwon don Allah ka yi haƙuri Jaann." Ta ƙare maganar cikin muryar kuka saboda fargaban kada ya sake shiga wani halin da ya fi wanda yake ciki, gudun aman jinin ya biyo baya. Ai kuwa nan take ya fara rawar sanyi, don kalar muryar da ta yi amfani da ita a cikin taushi; hakan ya jawo wa jarabarsa ƙarfi jikinsa ya hau ciccira tamkar mazari yana gumi. "Please! Wai mene ne haka don Allah?" Ta yi maganar a ruɗe cikin sanyin jiki saboda tuno wani lokaci a baya da irin hakan ya faru suna tare. Jikinsa da ya cure wuri ɗaya ya sa ta yi hanzarin riƙe shi tana faɗin, "Ni dai ka sha maganinka don Allah dai..." "Lafiyata ƙalau fa!" Harara ta aika masa tare da rungume shi a jikinta tana faɗin, "Ni dai don Allah ka sha, wallahi ciwon nan naka yana ɗaga mini hankali da yawa. Ba na son ka sake yin amai kamar na jiya zan iya kamuwa da wani ciwon ni ma." Dole ya ƙarfafa kansa tare da gyara zamansa. Kanta ta ɗora a saman hannunsa tana faɗin, "Ba zan sake ba Jaaan, ka yafe mini don Allah." Ta ƙare maganar da hawaye shaa yana sauka a kan hannunsa, zuciyarta cike da tsarguwa a kan cewa ciwon ne ya taso, kuma ita ce sanadin tashinsa. Dole ya shiga saita kansa da nutsuwarsa wuri ɗaya, tare da tabbatar mata babu komai ta kwantar da hankalinta. Don kawai ta gano ba asalin ciwon ba ne ya taso kuma babu wata matsala. Ta bar jikinsa ta zauna daidai tare da makurewa jikin kujerar tana sharar ƙwalla jefi-jefi. Daga haka barci ɓarawo ya yi awon gaba da ita, a ƙarshe da daɗin kwanan ya ɗebe ta jikinsa ta langaɓe har jirginsu ya kai babban Birnin Niamey ba ta san an kai ba. Sai da jirgin ya zo sauka a filin jirgin ne ta farka, daidai lokacin da ƙirjinta ya shiga bugawa fal-fal. Idanuwanta ta kai saitin tagar jirgin a nan ta fahimci sun iso ƙasar. Bayan jirgin ya yi landing aka fara fita ɗaya bayan ɗaya, yayin da Nur take gaba yana bayanta suka sauko daga jirgin jakarsa saɓe a kafaɗarsa. Mutane suka shiga murna da tarbon 'yan'uwansu, Nur da Jamal kuma suka shiga kallon-kallo. Motocin taxi suka dinga shawagi a wurin suna ɗaukar mutane, Jamal ya jefa jakarsa cikin wata taxi da ta iso gabansu yana cewa, "Mu je malama kada ki ɓata mana lokaci." Gaban Nur yana faɗuwa ta isa bakin motar tana magana cikin maraicewa ta ce, "Ina tsoron zuwa gida tare da kai, saboda akwai damuwa idan har aka gano inda na je." Wani kallo ya yi mata kafin ya rungume hannu ya furzar da iskan bakinsa ya ce, "Babu wata hanyar da za ta kare ki idan ba wannan ba, saboda haka mu je kawai ni na san abin da zan faɗa musu wanda ba za a ga laifinki ba." Ba don ta gamsu ba, ta bi umarninsa ne kawai ta shiga motar ƙirjinta yana bugawa. Har motar ta fice daga filin jirgin ba ta yi motsin kirki ba, illa hirar Jamal da direban kawai da take sauraro amma ko kaɗan hankalinta ba ya wurin. Zuciyarta ta tafi hangen taron 'yan biki da jimamin inda ta je. Don ta tabbatar zuwa lokacin an gama gano ba ta garin idan har an duba ko'ina ba a gan ta ba. Ɗoɗar motar ta nufi Zandar, saboda shi ne asalin garin mahaifin Nur, kuma inda ta koma a lokacin ta da gudo daga Nigeria. Next page 35. Tafiya suke yi ɗoɗar a kan hanyarsu ta zuwa Damagaran, hankalin Nur gabaɗaya ba ya jikinta ta shiga zarar ido, musamman da ta ga an kama hanyar zuwa family house ɗin Babanta gadan-gadan. Tsumaniyar da ta shiga yi a bayan da take zaune; hakan ya sa Jamal ya waigo ta bayan, idonsa a kanta ya ce, "Wai ke lafiyarki kuwa?" Ba ta ce da shi komai ba amma ta kasa zama daram da ɗuwawunta, sai leƙen hanya ta gaban motar take yi. Bayan gumin da ta dinga haɗawa ta ko'ina ya shiga karyo mata tana fifita da mayafin rigarta. "Don Allah ki kwantar da hankalinki, babu abin da zai faru sai alheri." Komawa ta yi ta zauna tare da jingina bayanta tana addu'a da fatar leɓunanta bakinta yana muimui, idonta a rufe tamkar wadda ba ta cikin hayyacin ta. Dariya ta bai wa Jamal, amma ganin yanayin firgicin da take ciki ya mazge tare da sake cewa, "Idan kin san akwai damuwa a tsayar ki zauna cikin motar, na ƙarasa gidan ni kaɗai.." Ido ta yi hanzarin buɗewa tana faɗin, "Mu je kawai, amma duk abin da ya faru ka yi haƙuri kuma don Allah kada ka bari ciwonka ya tashi." Murmushi ya yi mai sauti kafin ya ce, "Na shirya ɗaukar komai matuƙar zan wanke ki daga zargi kuma na cika alƙawarin da na ɗauka." Daga haka babu wanda ya sake cewa komai, har suka dinga kutsawa a cikin unguwanni bayan sun shiga tsakiyar garin Damagaran. Da kwatance motar taxi ɗin ta isa bakin wani babban gida mai dogayen katangu, inda tun kafin su isa suka hango dandazon mutane cike a ƙofar gidan. Daga ita har Jamal ƙirjinsu ya hau bugawa, saboda ganin mutanen ya tuna musu tarnaƙin da ke gabansu, wanda ko tantama babu a kan cewa hidimar bikin Nur ne ake yi, duk da ba ta garin kuma ba a san inda ta je ba. Mai taxi da ƙyar ya kutsa cikin mutanen ya samu wurin tsayawa, amma har bayan minti biyar babu wanda ya fito daga cikin su, saboda tsoro da fargaba ya raunata zukatansu. Don takaicin ganin mutanen ya tuna masa da ɗacin auren da Nur za ta yi da wani ta bar shi. Amma sanin ba a bori da sanyin jiki, ya ɓalle murfin motar ya fito cike da jarumta, sannan ya ce ita ma ta fito ta yi masa iso a wurin iyayenta maza. Sai da ta haɗa hannu ta yi addu'ar kariya daga abin da zai taɓa ciwon Jamal ta shafa; sannan ta fito ƙirjinta yana bugawa fal-fal ta nufi cikin gidan ko waige babu. Jikin motar Jamal ya koma ya jingina bayansa tare da rungume hannu ɗaya a ƙirji, yana ta bubbuga goshinsa da ɗayan hannun idonsa a rufe. Saboda shawagin mutanen wurin yana ƙara masa tashin hankali idan ya tuna wai taron auren Nur ne ake yi. Ita kam kutsawa ta dinga yi kanta a ƙasa ta shige cikin gidan, ba tare da ta nemo wani a cikin iyayenta maza ba kamar yadda Jamal ya nema. Sai dai shigarta gidan ta ji gwiwowinta sun yi sanyi ƙalau, sannan jikinta ya yi wa ƙafafuwanta mugun nauyi. Saboda ganin mata cike da gidan ana ta aikin abinci kowa da abin da yake yi, sannan da kallon mamakin da suke bin ta da shi tamkar a ranar suka fara ganin ta. Don kamar yadda yake a al'ada irin tasu, a ranar ɗaurin aure mata suna haɗuwa a yi ta yankan albasa da kayan miyan da za yi girke-girke da su. Sum-sum Nur ta dinga tafiya tamkar wadda ƙwai ya fashe wa a ciki tana ƙoƙarin shigewa wani ɗaki. Sai dai tsawar da wata guntuwar tsohuwa ta buga mata daga gefenta; ya sa ta yi hanzarin tsayawa cak tare da kai kallonta a kan fuskar tsohuwar, bayan ta sha jinin jikinta kafin ta iso inda take. Babu zato ta ji saukar mari ta ɗayan gefenta. Fuska ta dafe tare da ɗaga kai cike da son ganin wane ne mai marin. Caraf idonta ya sauka a kan fuskar Salissou yana huci tare da nuna ta da hannu yana cewa, "Ni za ki tozarta? Ana shagalin bikin aurenmu ki gudu don kina 'yar iska! To wallahi ko za ki mutu sai an yi aurena da gawarki babu fashi kamar yadda aka tsar..." "Dakata Salissou! Ba kai za ka ɗauki mataki ba ka bar ni da ita ni zan yi maganin tsinanniya! Sai ta faɗa mini gidan uban da ta je ana tsaka da hidimar auren nan! Don yadda na tsane ta daga ita har uwar da ta haife ta; ba don kai da nake yi wa kallon jikana na gaske ba, babu abin da zai sa na sake shiga shirgin matsiyaciya. Saboda gaba da ni da ita har abada, matuƙar ba kai ta aura ba; babu ranar da zan ƙaunaci yarinyar nan! Na tsane ta na tsani uwarta da ta kawo mana ita a cikin zuri'armu, Sulaimaney ma da na haifa a kansu nake jin tsanar sa a raina. Har ya mutu yana fushi da ni a sanadin wannan muguwar yariny....yiiiii!" Ta ƙare maganar cikin kuka saboda tuno rabuwarta da ɗanta Suley, waton mahaifin Nur. Don a kullum idan ta tashi kukan rashinsa tana jingina hakan da cewa Nur ce sanadin rabuwarsu ta har abada. Shi ya sa koyaushe tsanar ta ƙaruwa take yi a cikin ranta, don babu ranar da ba ta furta mata kalaman tsinuwa da muzanci matuƙar za su yi ido biyu. A wannan karon ma laifin da ta aikata ya jawo mata tsanar Nenne ta dawo sabuwa fil, bayan jihadin rage ta da shalelen jikinta Salissou yake ƙoƙarin yi kodayaushe, wanda hakan ya jawo buƙatar haɗin aurensa da ita, ko don ta samu sassauci a kan ƙyamar da ake nuna mata, a cikin gidan da ma zuri'arsu ta Zabarmawa gabaɗaya. Nanne ta dinga rusa kuka wiwi tana tsine wa Nur, jama'a suka taru a kanta ana ba ta haƙuri tana ƙara wutar bala'i da faɗanta bakinta yana kumfa. Yayin da wasu ma-ga-isan 'ya'yanta mata suka rufe Nur da duka ido rufe, tare da faɗin idan ta kashe musu uwa da ɓakinciki sai sun ga bayanta ita ma. Nan take gida ya hautsine da hargowa, wadda ta jawo hankalin mutanen waje masu hada-hadar shirin ɗaurin aure. Da ƙyar wani yayan Sulaimanou ya shiga tsakanin Nur da masu dukan ta. Hannunta ya ja suka shiga wani babban falon gidan, yana mai bayar da umarnin a kira duk wani mai matsayin da ya dace a tattauna matsalar da shi. 'Ya'yan Nanne suka rirriƙe ta tana yunƙurin zubewa ƙasa tsabar kuka suna kwaso ta, a haka aka nufi babban falon da ita. Kiran gaggawar da aka yi wa yayu da ƙannen Sulaimanou ya sa aka tsahirta ɗaurin auren da ake ta shirin ɗaurawa, gabaɗaya aka ɗunguma zuwa tattaunawar gaggawa da babban yaya ya haɗa. Yayin da falon ya ɗauki mutane da yawa tsakanin matansu da mazan duka. Tsakiya aka saka Nur kowa da kalar kallon da yake aika mata, ita ko ta dunƙule ƙasa tana shesshekar kukan da babu sauti sai ajiyar zuciya. Don tunaninta gabaɗaya yana kan Jamal da irin tarbon wulaƙancin da za a yi masa idan aka gano tare suka zo. Hakan ya sa ta yi hanzarin zuge jakar da ke maƙale a hamatanta, wadda ta kasa sakin ta duk da kalar dukan da aka yi mata. Saƙo ta shiga tura masa a gaggauce ta yi typing ɗin, gudun a raba ta da wayar tun kafin ta gama. Ai kuwa tana tura masa saƙon wani ƙanen Sulaimanou ya fisge wayar tare da kai mata harbi da ƙafa cikin fushi yana cewa, "Don ubanki har kin samu damar danna waya a gabanmu! Bayan kin gama tozarta mu a idon duniya?" Wuƙi-wuƙi ta yi da ido tana haɗe fuska ba tare da ta ce komai ba. A ranta tana faɗin, 'Idan saƙon ya tafi ai kuma shikenan.' Amma a fili ƙasa ta yi da kanta tana Allah-wadai da baƙar aƙida da al'adar da ta haddasa mata ƙiyayyar ahalinta. Majinar kuka ta ja a lokacin da Babban yaya ya fara magana tare da jefo mata tambaya. "Kamar yadda na ce kowa ya zo, ina son a tattauna abin da ya haɗa mu kafin mu yi abin da ke gabanmu. Amma kafin nan ya dace mu ji wani abu daga bakin ita A'ishar, shin me ya sa ta bar gida ba tare da kowa ya sani ba? Kuma me ya sa ta dawo gidan bayan mun cire rai da faruwar hakan a nan kusa?" Shiru ta yi kamar ba za ta ce komai ba, sai da wata ƙanwar Sulaimanou ta yi mata tsawa da hargowa a cikin faɗa sannan ta yi magana tana zuƙe majinar kuka ta ce, "Ina mai ba ku haƙuri a kan tafiyar da na yi ba ku sani ba. Na bar gida ne saboda ba na jin daɗin zama a cikin ku. Kuma na zaɓi komawa Nigeria a wurin saurayina saboda ba zan iya auren Salissou kuna nuna mini ƙiyayya b..." Salatin da ɗakin ya ɗauka ya sa ta fashe da wani sabon kuka cikin sauti. Ganin wasu masu zuciya kusa har sun fara kawo mata hari da duka, sai da babban yaya ya hana kowa ya taɓa ta. Sannan ɗakin ya nutsu aka daina surutan da ake yi tsawon minti biyar, kafin ya sake jefa mata wata tambaya da cewa, "To mun jin kin bar gida kin tafi Nigeria wurin saurayinki. Ya aka yi kika dawo mana bayan kin san ba ma son ki kuma muna ƙiyayyar ki?" Hawayen idonta ta share, tare da gyara zamanta tana cewa, "Ban dawo don ina so ba, na dawo ne a sanadin saurayin nawa da ya yi tattakin dawo da ni tun daga Nigeria har nan Damagara..." "Ahhhhh! Lalle yarinya ta girma da yawa! Sulaimanou dole ka mutu tun da ka bar mana abin faɗi a cikin dangi." Zancen Nenne kenan tana buga ƙafa ƙasa tare da kai wa cinyoyinta duka tana girgiza kai, tamkar wata zautacciya. Babban yaya ya sake tambayar Nur ina saurayin nata yake. Kai-tsaye ta sanar da shi ya tafi tun a lokacin da taxi ta kawo ta ƙofar gidan suka juya. "Ƙarya take yi! Yanzu haka yana ƙofar gidan nan, na gan shi tsaye jikin motar yana yi wa mutane kallon banza." Salisso ya karɓe zancen a ƙufule saboda ya ga Jamal a lokacin da zai shigo gidan, cike da mamakin abin da ya kawo shi ganin bai san shi ba kuma kalarsa ba ta yi kama da ahalinsu ba, ballantana ahalin mahaifiyar Nur da suke fararen fata kuma buzaye. Wannan zancen nasa ya sa babban yaya bayar da umanin a shigo da shi. Jikin Salisso har rawa yake wajen miƙewa tsaye, har yana cin tuntuɓe yayin ficewa daga falon. Zuciyarsa a wuya ya isa ƙofar gidan, bai tsaya yin komai ba ya ɗaga hannu da nufin kifa wa Jamal mari. Caraf ya riƙe masa hannu cikin zafin nama ya shiga aika masa kashedi da ido. Saboda tun kafin ya iso wurin Jamal ya ga fitowarsa da fahimtar yanayinsa gabaɗaya, kuma saƙon da Nur ta tura masa ya fahimtar da shi babu lafiya, don haka ganin ya nufo shi ya saka wa ransa ba arziƙi ya kawo shi ba. Hakan ya sa ya yi shirin tarɓonsa a kan duk abin da ya zo da shi. Jiki babu kuzari Salissou ya fara yunƙurin ƙwacewa daga mugun riƙon da Jamal ya yi wa hannunsa amma ya kasa, ya shiga muzurai da ido yana kallon mutane cikin basarwa ya ce, "To ka je ciki neman ka ake yi. Don ba ka isa ka yi mana wulaƙanci ka ci bulus ba. A'isha kuma ko za ta mutu sai na aure t...." Wata kalar dariya ta suɓuce wa Jamal babu shiri, saboda zancen Salissou ya bayyana masa shi ne wanda zai aure ta. Dariyar da Jamal ya dinga yi yana nuna shi da hannu har da riƙe ciki ya sa Salissou kallon sa ƙurin cike da alamar tambaya a kan fuskarsa. Don ya kasa gano me yake yi wa dariya, ganin yana nuna shi ya shiga kallon kayan jikinsa cike da son gano abin da yake yi wa dariyar. Shi kuma Jamal yanayinsa kaɗai ya saka shi jin dariyar, ganin wai ashe ma shi ne mijin da ake son aura wa Nur, sai ka ce ta rasa masoya a duniya. Don a kallo ɗaya da ya yi masa ya gama tantance halittarsa duka, baƙi ne wulik kuma siriri kamar sullen kara, sai ƙwala-ƙwalan ido da kunnuwa fiki-fiki tamkar na zomo. Haushin dariyar da Jamal yake yi masa ya saka shi komawa cikin gidan yana faɗin, "Idan ka gama haukar ka shiga daga ciki za mu ji abin da ya kawo ka gidanmu." Daga haka ya shige ya bar Jamal dariya a kan fuskarsa yana magana da mai taxi, don sun gama kaiwa ƙarshe a kan zaman kuɗi yake yi kuma zai kai shi masauki idan ya gama abin da ya kawo shi gidan. Cike da sabon kuzari Jamal ya bi bayan Salissou da ya tsaya jiran sa don su je ƙafa-ƙafa a gano gaskiyarsa ta cewa yana nan ba ƙarya ya yi ba. Kasancewar gidan babban gida ne mai ɗauke da sashe-sashe, haka Jamal ya dinga wucewa yana gaishe da waɗanda ya hango har suka isa bakin falon. Da addu'a a ransa ya shiga bakinsa ɗauke da sallama, kansa a ƙasa ya isa inda babban yaya ya nuna masa ganin mutanen falon shi suke kallo. Cikin ladabi ya rusuna yana gaishe da su amma bayan babban yaya babu wanda ya amsa masa, sai kallon banzan da suke bin shi da shi yayin da wasu ke aika masa harara. "Bawan Allah! Mene ne haɗin ka da A'isha?" Jamal ya faɗaɗa fuskarsa da murmushi kafin ya yi magana kansa tsaye yana cewa, "Soyayya mai ƙarfi ce ta haɗa ni da Nur." Shiru ɗakin ya yi cike da mamakin maganarsa, don baki sake Salissou ya ƙura masa kallo ganin da gaske fassarar da ya yi masa ta mara mutunci haka yake. Nur kam kanta ƙasa kuma ƙirjinta bai daina bugawa ba tun a lokacin da ta yi arba da shi yana ƙoƙarin shigowa falon, don ta yi zaton zai tafiyarsa kamar yadda ta tura masa saƙon ya tafi, duk da ta san shi sarai babu abin da zai hana shi tsayawa matuƙar ya yi ra'ayin hakan. Gabanta ya sake bugawa dam-dam a lokacin da ta ji furucin bakin babban yaya a kan amsar da ya ba shi. "Tabbas na gasgata ƙarfin soyayya taku, ganin yadda ka yi tattaki tun daga ƙasar Nigeria har ƙasar Niger don kawai ka kawo ta gida. Saboda haka na amince kuma na yarda a matsayina na yayan mahaifinta zan aura maka ita tun da ita ma tana son ka." Nan take surutu ya fara tashi a cikin falon, Nenne ta hau rurin kuka da kururuwar matuƙar tana raye ba za ta bari Nur ta auri Bahaushen Nigeria ba. Yayin da wasu ke goyon bayan Salissou da ke ta aika wa Jamal zagi, yana faɗin bai isa ya auri Nur ba sai dai ta tabbata a haka babu mijin aure. Babban yaya ya yi gyaran murya bayan an rarrashi Nenne ta yi shiru ya sake cewa, "Ban amince da wannan auren nasu kai-tsaye don ra'ayina ba, na yi hakan ne saboda gudun A'isha ta sake guduwa ta bi shi ba mu sani ba. Saboda a yadda ta san hanyar barin ƙasar Niger ta tafi Nigeria a kansa; ba a san me zai sake faruwa ba a nan gaba. Don haka masalaha ce ake nema, tun da an musanya wa Salissou zai auri Hadizatou; ita ma a ba ta dama ta auri wanda take s...." "Ranka ya daɗe ina da magana!" Jamal ya katse shi saboda abin da ya kawo shi kenan, kuma dalilin da ya sa ya zaɓi dawo da ita gida da kansa kenan, sannan kuma yake son furta zancen a gaban kowa. Babban yaya ya ba shi umarnin magana duk da kallon wulaƙancin da sauran danginsa suke yi masa. Jamal ya gayyato nutsuwar dole ya yafa wa kansa, saboda abin da zai faɗa yana jin ɗacinsa har cikin tsakiyar zuciyarsa. "Tabbas ina son A'isha, irin son da ban taɓa yi wa kowace mace a duniya ba. Amma a wannan lokacin da nake sanar da ku wannan maganar; ba na jin zan iya aurenta don na gama cire wa raina buƙatar aurenta gabaɗay...." "Da ma ta ya ya za ka aure ta bayan ka gama lalata mata rayuwa! Wa ya san irin tanbaɗewar da kuke yi a can Nigeria ɗin?" "Ai hakan ya yi daidai! Gobe ta sake cira ƙafa ta bi ka Nigeria!" "Tirr da halinki A'isha kin ji haushin duniya Sulaimanou ya bar mana jarfa a cikin dangi. To Salissou ma ba ya son ki yanzu an ba shi Hadizatou a madadinki. Sai ki jiƙa kanki ki sha, da ma a duniya kaf babu mai ƙaunar ki sai Sulaimanou, kuma shi ma ya mutu, munafukar uwarki kuma tun kina ƙarama ta bar wa duniya ke. Daga ita har danginta babu mai son ki ballantana su neme ki, mu ma ƙaddara ta ba mu ke da tuni mun jefar da ke mun huta. Da kin sani ma ɓoyon da Sulaimanou ya yi miki ba ki fito ba, har zuwa lokacin da za ki bi shi zuwa lahira kowa ya huta." Maganar Nenne kenan, ɗaya daga cikin ukun maganganun da suka taɓa mata zuciya, duk a cikin jerin kalolin miyagun maganganun da ake ta jifar ta da su, a sanadin furucin Jamal mai nuna rashin buƙatar auren ta zahiri ƙarara. Tsam ta miƙe ta dinga bin kowa da kallo ɗaya bayan ɗaya hawaye yana bin fuskarta tana nuna kanta ta ce, "Ni...ni...kaina...na yi danasanin zuwana duniya a cikin ku, na tsani kaina kuma na tsine wa mutuwar da ta ƙi kashe ni tare da Baban...." Kukan da ya sarƙe ta ya sa maganar ta tsaya babu shiri, sai da ta haɗiye dunƙulallen yawu ya wuce muƙut a maƙoshinta, sannan ta sake nuna Jamal tana cewa, "Kai kuma...ban san ba ka so na ba sai ka ɗauki wuƙa ka soka a tsakiyar zuciyata zan gan...kamar yadda kalamanka suka bar mini mugun dafin da har na mutu ba zai daina yi mini zafi a cikin zuciya ba." Tana ƙare maganar ta bar wurin idonta a rufe, gudu-gudu sauri-sauri take taku da wani irin mahaukacin kukan da ya turnuƙe mata zuciya. Kamar almara Jamal ya isa inda take ya cafko hannunta. Tana tirjiya tare da kai masa duka cikin jarumta ya kawo ta gaban babban yaya, da hanzari ya rusuna riƙe da hannunta ya sunkuyar da kansa ƙasa yana cewa, "Babu wani aibi ko nakasar da za ta sa na ƙi auren Nur a duniya. Ina son Nur ko da duniya za ta tsane ta, ina son Nur ko da ba ta fito a cikin sunnah ba, ina son Nur ko da ni ba ta so na. Don haka ina neman gafarar ku a kan ƙin karɓar tayin auren ta, na yi hakan ne saboda wani babban dalilin da ba zan iya tsallake shi na yi gaban kaina ba. Don haka tabbas ba zan iya aurenta ba a wannan lokaci..." Ihu da kururuwar da Nur ta fasa ya dawo da hankalin kowa a kan Jamal. Ganin tari ya turnuƙe shi yana aman jini babu ƙaƙƙautawa. Wayyo Jamal😭 Next page😥 Ga mai buƙata ya biya 1k domin ci gaba da jin wannan badaƙala. 1230094555 Access Bank Hadiza D. Aura Ibrahim. Shaidar biya ta wannan layin 08022014771.